BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 3 by sumayyah Abdulkadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 3  by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 3 by sumayyah Abdulkadir

- - Post a Comment

 BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 3

by sumayyah Abdulkadir


Su bada feeder da sauya pampas, goyo, tsarkin kashi da goge tumbidi duk ya kware a kansu. Nurse mai raino sai ta zama mai Zaman banza tana cin aljihun Ubansu a bagas. Hutunsu ya kare za su koma makaranta, kuka yake sosai shi ba zai tafi ya bar matarshi ba. 


Da lallashi da ban-baki da tausasawa Alh. Aliko ya taho da shi Najeriya suka koma 


makaranta. 2K ok ok ok atan ‘yan biyu uku da _ haihuwa_ su Almustapha suka sake samun hutu, satinsu daya a Kaduna ya uzzirawa Daddy suka taho wajensu a Bournmouth. 


Girman ‘yan biyu ya bashi mamaki kwarai, sun zama kamar ‘baloons’ din da ake hurawa, ga kuzari da karfi, ga gashi yala-yala a kan Safah, yayin da Marwa da take fara sol bata da yawan gashin. Suna 

zama daram, kamar ‘yan watanni bakwai. Ya dauki Safah dinshi ya goya da zani, yana juyi da ita a tsakar dakin yana cewa, “T missed you SAFAH!” 


Suna da watanni shidda sun iya rarrafe sosai, da kama kujera su mike, sun fara sanin mutane. Sun san su yiwa wanda ba dan gidansu ba kiwa. Kamar yadda ya bayyana ga kowa, Imam (Almustapha) ya fi son Safah, duk da tsawatarwar da Mami ke mishi. Sai dai yayi na ganin idonta. Hajiya Mama rannan ta ce, “Don Allah ku kyale yaron nan ya yi yadda yake so da kannensa, ai ba su biyu zai hada ya aura ba, soyayya hadin Allah ce, ba yin mutum ba. Tunda dai ba dukan ta yake ba, ba zaginta yake ba”. 


Alh. Aliko ya ce, “Amma in suka girma a haka, zumuncinsu zai samu rauni, ita Marwa ba za ta dinga jin dadi ba, alhalin tana ganin yana banbanta tsakanin ta da ‘yar uwarta”’. 


To Hajiya Maama ta yarda da hujjarsu, 

don haka cikin hikima da barazana itama take nunawa Imam itama Marwah ya dinga daukar ta. Ko ya daina daukar su gabadaya. Don haka ya tsorata, yaya za’ayi ya iya daina daukan Safah ya daina rainonta? Wannan wani abu ne da bazai lya jurewa ba. 


Sai ya dawo yana daukar ta itama jefi-jefi, amma ba kamar yadda yake daukar Safah ba, da yanayin sakewar da yake yi yana yi mata hira da kulawa ta har kololuwar zuciya. 


Sai da ‘yan biyu suka cika watanni goma, a lokacin suna gudunsu ko’ina, sunyi bulbul kamar kajin Agric, suka tattaro suka dawo gida Najeriya. 


Kowa ya dora ido a kan ‘ya’yan Aliko Dan Kasa, su hudun nan, sai sun bashi sha’ awa, domin kamar su daya. Marwa ce kadai zakka a cikinsu, da take kama da Hajiya Zainab. 


Bakake ne sirara masu tsayi sambal, da dogon hanci da rashin cika ido, irinna mutanen Chikun, domin itama Safahn data 

kara girma sai kibar abincin turawan ta zaizaye ta koma kamar Shahida wajen rashin kaurin jiki kamar ka huresu su fadi. Marwan ma haka, saidai ita duk ta fisu dan kauri. Tun suna kanana Hajiya Mama ba ta wasa da nema musu kowanne irin dafa’i na tsarin jiki, da maganin baki (rubutun Lahaula), da su _ kaikayi koma _ kan 


mashekiya. 2K 2k ok 


Shekara kwana ga mai yawan ral. A yau 


ake bikin yaye su Almustapha daga sakandire, bayan sun kammala zana WAEC da NECO. Yayin da Shahida ta kammala karamar sakandire, idan an koma hutu za ta shiga SS1. Almustapha ya kwaso kyaututtuka na ban mamaki, shine wanda ya fi kowa tsafta a shekararsu, shine wanda ya fi kowa iya technology (as a subject) a makarantar baki dayanta. Sannan kyautar wanda ya fi sauran dalibai iya sarrafa na’ura mai kwakwalwa. 

Idan ya karbo kyautar sai ya mikawa Daddynshi, shi kuma ya mikawa Hajiya Zainab, suna ta murmushi, cike da alfahari da dan nasu. A karshe dai Daddy rungume shi ya yi a bainar taron, yana sanya masa albarka. 


2K OK OK K uka jama’ar gidan ne a kan tebir suna kalaci, 


in ka dauke Hajiya Mama wadda ke sassanta tana sallar walha. 


Safah ta cika bakinta da ‘plantain’ ta kuma budeshi za ta yi magana, nan da nan ta kware. Imam dake gefenta yayi saurin mika mata ruwa a tambulan mai garai

garai, ta amsa ta soma kwankwada. 


Ya harareta, sannan ya ce 


‘Na hana ku kuna cin abinci kuna yin magana, is a bad manner”. (Ba tarbiyyah bace). 


Da saurinta ta ce 


“Na daina Ya Imam’. Don bata son hararar Ya Imam ko kadan, manyan idonsa masu sheki da maikon silber, kokarin fadowa suke yi (a ganinta). 


Da wani lallausan murmushi makale a siririyar fatar bakin sa irin nata ya dubeta, don ya wanke mata razanarta dashi, kan hararar da yayi mata wadda ya san bata so, ya ce, 


“To ko ke fa?” ya fada da karyayyen sauti nai nuna lallashi. Ya russunar da kwayar idanun nasa a kanta. Suka hadu suka lumshe ahankali don kansu, sakamakon azababbiyar soyayyar da Allah Ya sanya a zuciyarsa, tun bai san me hakan ke nufi ba, tun bai san kansa ba. 


Bayan sun kammala, Daddy ya mike Imam ya rufa masa baya zuwa balcony, suka 

zauna bisa irin sakakkun kujerun nan na gargajiya da ake sakawa da zaren roba, wadanda sautari anfi samunsu a gidajen manyan masu ido da_ kwalli, da madaidaicin tebir din kaba a tsakiyarsu. Imam ya zuba ruwan ‘coca-cola’ mai sanyi yana kumfar ‘gass’ a zungureren tambulan ya mikawa Daddy, wannan ne kadai lemon da Alh Aliko yake so, domin yana kara masa kuzari, ya karba ya soma sha yana kallon Imam din, yana masa murmushin kauna. Saida ya bari ya shanye ya aje kofin, sannan cikin ladabi ya ce 


“Daddy admission dina ya fito, daga jami’ar da na nema a Loughborough”. Yace, “Wane kwas suka baka?” 


Ya ce, “kere-keren motoci (AutomotibeEngineering), ka ga ba da jimawa ba zan kera maka mota wadda babu irinta a duniya da hannun nan nawa”. Ya fadi yana nunawa Daddy damatsan hannun nasa. Daddy ya yi murmushi yana kallon shi cikin ido, cike da kauna ta Uba ga Dan sa, ya ce, 

“akwai motar da babu irinta a duniya Imam? Ai tunda anyi jirgin sama, babu motar da baza’a iya yi ba. Har da mota mai fukafukai in ana so. Na so a ce Marketing ka dauka, ko don ka karbi ragamar harkokina in kwanta a gida in huta hakannan”’. 


Ya yi murmushi ya ce a ransa karatun ragwaye, a fili kuma yace “Daddy bana sha’awar business ko siyasa. Tunda Alhamdulillahi kana da hazikan daraktoci irin su. ZAHRADDEEN MAITAMA, Ahmad Kutama, Peter Kissinger da sauransu. Wadanda suke tare da kai cikin amana tsayin shekaru masu dama. 


Don haka ne bana haufin kin shiga cikin harkokin ka, don na san ko babu ni harkokinka ba za su durkushe ba, ko don Zahraddeen”’. 


Da wannan suka kawo karshen hirar tasu. Daddy bai ji ko dar na narkarwa Imam miliyoyinsa ba, don ya yi karatun koyon kera motoci a babbar Jami’ar Loughborough (Loughborough 

Unibersity), dake Leicestershire a UK. Karatun da zai debeshi tsayin shekaru takwas. 


Cikin watanni biyu komai ya kankama, cikin rakiyar iyaye da ‘yan’uwa, Almustapha Zubair Dan Kasa , ya tashi zuwa Loughborough, inda ya soma karatu a kan kere-keren motoci babu wasa, babu kama hannun yaro. Ko don ya fita kunyar Daddy da ya narkar da (pounds) dinshi don ya faranta masa, ba tareda ya taba komai ba cikin gadonsa dake dankare cikin asusun gida da waje ba. Ya san Daddy yayi hakanne don ya inganta rayuwar sa. Amma baya son ko na yini daya yayi nisa dashi, daurewa kawai yayi don ya cika masa burinsa, don ya lura baya son kasuwancin da gaske. To shi kuwa in haka ne, me ya rage masa banda ya jajirce ya faranta masa shima da _ kyakkyawan sakamako??? wanaki ke shudewa a hankali su koma watanni, watanni su rikide su koma 

shekaru, cikin hikimomi da_ iyawar Ubangiji, har ya kasance a yau ‘yan biyu sun kammala karatun firamare sun fada kwalejin ‘yanmata ta gwamnatin tarayya dake Kazaure. 


Cikin shekarun nan Almustapha bai zo gida ba ko sau daya. Sai dai su sun ziyarce shi sau uku cikin shekaru biyar da ya yi baya gida. 


Abinda kowa ya sani ne wato Safah Imam ke riko, wadda ke cikin shekaru sha hudu a lokacin. Sai dai ita Safah din babu wani tunanin hakan ko wani abu can soyayya a gabanta, face karatunta. Ita bata sani ba bata san wannan ba. Ita abinda ta rike a ranta kawai Ya Imam Yayan ta ne, da suke ciki daya. Bayan wannan ba wani abu duk da tana ji kowa ce mata yake matar Imam. Wata irin miskilar yarinya ce da dawuya ka fahimci inda tasa gaba, domin fuskarta bata nuna abinda ke zuciyarta. 


Ta iya danne abu cikin zuciyarta komin girmansa da muhimmancinsa, koda dannewar zata cutar da ita. Ta dage da son 

cimma burinta na son zama cikakkiyar likitar hakori (Dentist). Ko don ta gyarawa Marwah cinyayyun hakoranta da chocolate ta cinye, ta kuma likawa Hajiya hakoran roba biyu da suka fice daga bakinta na kasa. Yayin da Marwa ke da burin zama cikakkiyar mai harhada magunguna (pharmacist), ko don ta harhadowa Hajiya magunguna masu inganci ta daina shan jike-jiken data ke sha duk sanda wata lalura ta sameta don ita bata yarda da maganin asibiti ba. 


Suna son Kakarsu sosai yadda take son su, domin rabin rayuwarsu tareda ita suke yi, su sata a tsakiya su kwana tare sai in sun koma makarantar kwana ne Hajiya zata kwana ita kadai, sun damu da ita har fiye da Uwarsu don yadda take kula dasu, kuma rikon da take yi musu ba rikon Kaka bane, riko ne na gangariyar tarbiyyah da cusa musu kyawawan dabi’u a zukatansu tun suna kanana. 


Mami kowa ya san Imam ta fi so kuma a gaban kowa bayyanawa take, Shahida ce 

dai gata nan halinta sai Allah domin tanada son girma, bata wasa dasu kada su rainata. Suma kuma tsoronta suke fiye da Mami don haka ne Hajiya bata shiri da Shahidah tace tana takurawa kannenta, don bata san yaya sukayi ta addua kafin Allah Ya basu su ba. 


Suna da bambancin ra’ayi a abubuwa da dama, basu taba hada ra’ayi a kan son abu guda ba, kamar ba ‘yan biyu ba. 


Kamar yadda suke da bambancin ra’ayi a al’amuran rayuwa, haka suke da bambanci a akida da halayya. 


Safah shiru-shiru ce bata son hayaniya, bata son shiga jama’a, bata da wani buri da ya wuce karatunnan nata. Takarda da biro sune manya-manyan abokan hirarta. Kowa nata ya san hakan, don haka ba’a fiya shiga shirginta a gidan ba, in zata kwana uku ba’a ganta a falo ba ba wanda ya damu, ta zabi rayuwar kadaici da goal attainment (cimma buri) fiye da komai. 


Duk wasu abubuwa na debe kewa da zamani ya kawo Safah bata da sha’awa a 

kansu, kamar yanar gizo da abubuwan da ta kawo, waya da sauransu. 


A ganin Safah, duk da karancin shekarunta a lokacin, wadannan duk ababene na asarar lokaci irin na bature, a kokarinsa na nakasa kwakwalwar matasan mu su ki karatu, don yadda mu muka mallaka rayuwar mu a Kansu (social networks), shi ba haka yake amfani dasu ba, yana amfani dasu ne kawai a lokacin da bukatar hakan ta taso ba kamar mu ba da muke kwana mu wuni muna amfani da ita, kuma ba za su amfane ta ko su kareta da komai ba, illa su karar mata da abu mafi daraja a rayuwar dan adam wato LOKACI. 


Babu yadda Imam bai yi da ita ba ta rike waya ko don su dinga gaisawa amma ta ki, don haka yake yi mata e-mail, wanda bai san sau dubu ya aiko da sakon ko gani bata yi ba. Shikansa email ID din Marwah ce ta bude shi da combination na sunansu, itace kuma ke karantawa ta bashi amsa, cikin yi masa dariyar mai son alhuda-huda bata san yana yi ba, da dadadan kalamai masu 

taushi da tausasa zuciya da take koyowa a karance-karancenta na zamani, ita kanta bata san dalilinta na damuwa da Ya Imam ba yadda ba’a zato. 


Yayin da abokiyar tagwaitakarta ta kasance akasin ta. Marwah Aliko Dan Kasa, fara ce sol mai siririn hanci irin na Hajiya Zainab, ba ta da yalwar suma, sai dai ba ta rasa na kullewa cikin ‘ribbon’ ba. 


Yarinya ce mai son hulda da jama’a, tana da wayewar kai fiye da ‘yar’uwarta, sakamakon huldar ta da mutane dabandaban tana da kawaye sosai a makaranta, don haka tafi Safah sanin zamani da halin da yake ciki. 


Tana da son sarrafa ‘yanar gizo’ da shiga duk wani sabon abu da zamani ya kawo; su facebook, bbm, whatsapp, android, twitter da sauransu. 


Marwah ta san tun tana karama Yaya Imam bai damu da ita ba, ita kuma nan duniya babu wanda ta damu da shi irin sa. Ba ta iya kwana bakwai ba ta tura mishi sakon gaisuwa ba, amma da sunan Safah. 

Marwah ta sha zama ta yi tunani a kankanta, me yasa Yaya Imam bai damu da ita ba? Duk da kowa ya san Safah yake so da aure, wannan ba hujja ba ce da ita Zai watsar da ita a matsayinta na jininsa, ‘yar’ uwarshi ta jini. 


Safahn da yake so ba ta damu da shi ba, karatunta kawai take. Shin idan ya san ko sau daya Safah ba ta taba yi mishi e-mail ba tun tafiyarshi yaya zai ji a ransa? 


Zai ji irin ciwon da itama take ji na yin biris da al’amarinta da yake yi. Tunda cikin sakonninsa gaba daya da _ yake aikowa Safah, bai ko taba cewa a gaishe ta ba. 


Duk da ba kalaman soyayya yake cika Safah din dasu ba. Galiban, gaisuwa ce da karfafawa a kan karatun ta. Sai dai in ka nutsu sosai cikin karatun sakonninsa, za ka fahimci kwantacciyar kauna mai sanyi da motsa zuciya cikin kalaman nasa. 


Har take cewa a ranta, ina ma ita ce Safah? Safahn ba ta san bikin da suke yi ba. Akwai ranar da ta tari aradu da ka, ta yiwa 

‘yar’ uwarta nasihar ta dinga duba sakonnin Yaya Imam. A kalla ko bazata bashi amsa ba. Safah ta rufe ido ta yi amfani da mintocin da ta girmi Marwah din dasu ta balbale ta da fada, fadan da bata taba zaton cewa ta iya ba, idan akayi la’akari da shiru-shirun ta. A fusace take fadin “Miyid’a kongatta, miwatta tegal joni, midalimo yauti’amo” Ni na ce miki ina da lokacin shirme?” (Ta fada cikin fulatancin Mami, wanda Mamin ta fi yi musu magana dashi). Amma Safah bata yi sai ranta ya baci. Marwah kuma bata iya mayarwa amma tana ji. “Wannan tsagwaron shirme ne (soyayyah). Ni kuma duk wani shirme, to bana cikinsa. 


Ke dai tunda baki da aikin yi ki je ki yi tayi, ko an ce da shi aure zan yi yanzu? Ina amfanin soyayyar tunda ba aurenka zan yarda nayi ba? Ni da aure ma ina jin nan da shekaru goma nan gaba albarka! Mijin auren ma ba’a haifeshi ba. Don haka kada ki kara damu na da zancen Ya Imam. Shirmammiya kawai!” 

Marwa ba ta yi fushi ba, sai ta langabar da kai, tayi murmushi ta kwantar da murya cikin lallashi, 


“Ki yi dai tunani Safah, Yaya Imam Yayanki ne kuma mai sonki, tun kina cikin mahaifa, har aka haifo ki, har zuwa girmanki bai daina hidima dake da son ki ba. 


Idan kika ce bakya sonsa baki yi adalci ba. Kuma na rantse da Allah kika yi saken da ya kubuce miki, zakiyi nadamar da bazata yi miki amfani ba. Gara ka auri wanda ke son ka, akan ka auri wanda kake so! 


Ban ce bazaki samu mai son ki bayan sa ba, amma ba kamar sa ba. Ratar da ingancin da yawa. 


Na ji ni bani da aikin yi, zan ci gaba da amsa mishi sakon gaisuwa da kaunarsa gareki, tunda dan uwana ne, bazan iya ganin irin wulakancin da kike mishi ba, balle in taya ki, ba kuma zan taba bari ya gane ba ke kike amsa mishi ba, sai in ke da bakin ki kika gaya mishi tunda na lura baki da hankali, a bit lunatic....!!!". Ta fada 

cikin dan daga sauti saidai ba yadda Mami zata jiyo ba, har ido ta zazzaro mata sabida takaici da bacin ranta karara (Fadansu na farko kenan a rayuwa). 


“Ni ce bani da hankali Marwah, lunatic? Ni???” Ta fada tana nuna kirjin ta, tareda kallon kanwar tata cikin ido. Fuskarta dauke da tsananin jin mamakin kalmar. Gyada kai ta yi, cikin tabbatar da kalamanta. 


“Babbar mara hankali kuwa, kuma mara kirki, sannan marar tunani da kara. Ai in da alkawari ruwa bazai dafa kifi ba. ALHERI na binki kina gudu. Domin auren Ya Imam alheri ne a gareki. Muhimmi shine iyayenki zasu dawwama cikin farinciki dake har karshen rayuwarki, amma kina so ki janyowa kanki bacin ran iyaye da asara..... Dube ki da Allah (ta nuna ta sama da kasa tana mere baki) “...... Me kika fi Ya Imam? Baka-kirin dake, sirigalau kamar karan raken-takanda, ban da so gamon jini ai baki ko ishi Ya Imam kallo ba, banza mai kama da ‘yan kauyen 

Chikun. 


Kina tunanin ranar da Daddy ya san abinda kike ciki zaki kai labari?” Safah ta jinjina kai, takaicinta ya kai intaha, sannan ta harare ta, ta ce, 


“baki burge ni ba, sai kin gayawa Ya Imam din haka. In ya so sai ya gaya miki dalilin sa na son karan-raken takanda. Ki kuma yi aniyar zuwa gayawa Daddyn, tunda kin zama munafuka, ko baki fadaba rana na zuwa da zan fada da kaina; mihed’aki hitkimo, awattayan dole miyid’amo, tunda na’an ha’b’bata tegal, yitki god’d’o wala ye so’an (ban taba son sa ba, kuma bazaki tursasani ba, tunda ba ke zaki daura min auren ba, ke kije ki aure shi mana?) ta kara da cewa “ I don’t habe time for stupidity, mara aikin yi kawai”. Ta tattara takardun dake gabanta ta mike ta bar mata dakin tana cigaba da cewa 


“Ki yi da wani kuma, ba dai da ni ba”. 


Kwanan su biyu basa Magana da juna, ko hanyar da daya ya bi, daya baya bi. A 

rana ta uku dukkansu sun jigata, kasa jurewa suka yi, sabida abu ne da basu taba yl a rayuwarsu ba. 


Suka yi ta kuka a daki su kadai, dole suka nemi afuwar juna da alkawarin daya ba zai kara yiwa daya abinda baya so ba. 


Tun daga ranar Marwah bata kara yi mata zancen Yaya Imam ba. Email dinma rufeshi tayi, don fita daga abinda ba nata 


ba. Da gudun bacin ran ‘yar uwarta. 2K OK AK ok 


Sun shiga hutun kirsimeti, wanda in sun koma za su shiga ajin karshe a sakandire. Taron yaye su Imam ya zo. 


A satin gaba daya Alh. Aliko, Haj. Zainab da Hajiya Maama basu zauna ba, ana ta shirye-shiryen dawowar sa. Kama daga muhallin da zai zauna cikin gidan da kayan da zai yi amfani dasu. 


Hatta sittirun da zai sanya Daddy ya dinka masa namu na hausa, kasancewar Imam da son shaddah haka Daddy ya bayar aka yi ta dinka su, dakakkun shaddodi kala-kala 


Post a Comment for "BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 3 by sumayyah Abdulkadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...