Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

AUREN TAGWAYE CHAPTER A LITTAFIN ZEE ELKASIM MAMAN KHADY

AUREN TAGWAYE CHAPTER A LITTAFIN ZEE ELKASIM MAMAN KHADY

- - Post a Comment

 AUREN TAGWAYE CHAPTER A

.


*Amincin Allah ya tabbata ga wad'anda zasu karanta wannan labari nawa dama Wad'anda basu samu damar karantawaba ina maku fatan Alkhairi akodayaushe*


~Note~

*Wannan labari 'kir'kirarane banyi dan wani ko wataba, ko satar fasahar wani saboda haka duk Wanda/wacce taga yazo dai-dai danata abune yazo d'aya sai ha'kuri*

.

"Hassana waike bazakiyi sauri mutafiba ke kullum idan mutum yahad'a abu dake sai ranshi ya 6aci, yanzu dan Allah so kike daddy yadawo yahanamu fita, kuma sanin kankine muddin idan banje *Dinner* d'innan ba zuby bazataji dad'iba kinsanfa bikinnan na best friend d'inta ne, kuma ta gayyacemu ba dad'i mu'ki attending.


Cikin sanyin murya wacce aka kira Hassana take magana "Haba Hussaina nifa wlh banison wannan abun dakikeyi, ke shikenan koda yaushe da an gayyaceki ferty kin dinga 'kyarma kenan kamar wacce aka gayyata zuwa aikin hajji.


Magan-ganun Hassana suka 'kara harzu'ka Hussaina cikin bala'i da d'aga murya take cewa "dallah malama kada ki gayamin magana, ke dama duk wata harka ta wayewa baki santaba, idan bazakiba basai kin gayamin maganaba kawai ki zauna a gida, haka zaki 'kare, kullum kitchen.


Zama Hassana tayi bakin gado tare da cire mayafin data sanya, "nikam bazaniba kitafi kawai sai kindawo, ni dama wlh hankalina be kwanta da tafiya wannan *dinner* d'inba kiduba agogo yanzufa 'karfe bakwai da rabi na dare.


Jin Hassana tace bazataba yasa Hussaina zuwa kusa da ita ta du'ko dai-dai fuskarta har numfashinsu na gauraya dana juna, sannan tafara magana cikin sanyin murya.


"Haba my sweet sister, plz ayimin ha'kuri kinsan bazan iya tafiya batare dakeba......


Ringing d'in wayarta ya katseta da maganar datake, da sauri tasa hannu ta d'auko sunan Zuby tagani yana yawo kan screen d'in wayar da sauri ta danna OK tare da karawa a kunne.


"Hellow Zuby ya?

A d'aya 6angaren zuby ta amsa

"Haba 'kawata me kike har yanzu baki fitoba, halan wannan sister taki ce take maki kofsi.

Hussaina kallon Hassana tayi sannan tace "a'a yanzu zamu taho, tare da itama zamuzo.

"Dan Allah kuyi Sauri.

"Owk kawai Hussaina tafad'a tare da tsinke kiran.


A Falo suka tarad da momynsu tana kallon tashar sunnah TV, cikin ladabi sukaje gabanta Hassana tace "Momy zamu tafi.

Momy ta kalle yaran nata daga sama har 'kasa babu wata shiga ta aibu tattare dasu, atamface suka sanya d'inkin Riga da zani pieces, sai wadataccen gyalen da suka yafa.


"To amma kada Ku wuce 'karfe tara kunsan dai tara da rabi dadynku yake dawowa gida, Momy tafad'a tana 'karemasu kallo,

Hussaina ce tayi saurin cewa "kada kidamu Momy Tara a gida zatayi mamu.

Hassana tace "insha Allah Momy munyi maki wannan al'kawarin.

"To shikenan kuje Allah maku Albarka

Tare suka amsa da Ameen sannan suka fice daga gidan.

.

Suna fita get sukayi 'yar tafiya kad'an sukasamu napep suka fad'a masa inda ze kaisu.

.

Lokacin dasuka 'karaso had'addiyar Hotel d'in da'ake gudanar da *dinner* d'in kai tsaye suka nufi hall d'inda suka tabbatar da nanne ake farty saboda mutanen dasuka hango ciki.


Suna shiga lokacin Zuby na zaune suna labari itada wani boy friend d'inta wanda tadad'e da afkawa kogin 'kaunarsa tasha nuna masa haka amma ya'ki yagane dan kwata- kwata Zuby bata cikin tsarin kalar yan matan dayakeso kawai dai yabarta a matsayin Friend.

.

Cike da farinciki Zuby ta tarbo 'kawarta Hussaina, ko kallan Hassana batayiba, Hassana ma nunawa tayi batasan da zaman wata halitta wai ita zuby ba, dan ita dama tun can jininta be had'u dana zuby ba.


Guri suka samu suka zazzauna kan kujerun dake Jere a hall d'in.

Zuby ta kalli boy friend d'inta sannan takira sunansa "Hafiz, ga 'kawayena danake gayama 'yan biyu ne, wannan itace Hussaina wannan kuma itace Hassana tafad'a tana nuna Hassana yayinda itakuma ta kauda kanta gefe dan ko kad'an ita batason a had'ata da wani namiji barantana kuma har suyi wata magana, shiyasa kodayaushe Hussaina da Zubby suke kiranta bata wayeba.


Haka suka zauna zuby sai wani shishshigema Hafiz takeyi tanata mashi surutu, shikuma kwata- kwata hankalinsa be kanta, tunda su Hassana suka shigo idanunsa suke kan Hussaina, yariga yagama fad'awa kogin 'kaunarta, wanda zuby bata lura da hakanba, amma ita Hussainar ta dad'e da d'agowa dashi kodan yanda dasun had'a ido yake sakar mata wani tsadadden murmushi, dama gashi kyakkyawa ajin farko, take itama Hussaina taji takamu da sonshi.


Wani irin kid'ane ya tashi lokacin da Mr DJ ya kunna Speaker's d'insa, wayyo jikin zuby har 6ari yake, dama haka take mayyar rawace duk sun dad'e da sanin haka saboda haka basuyi mamakin hangonta tsakiyar fage ita kad'ai tana caskad'ewaba, ba kunya take rawar sai wani kaso shoki takeyi..... _Lol_


Lokacin Hafiz yasamu damar yima Hussina magana, "Ya kike 'yan mata, wayyo wani iri Hussina taji a jikinta lokacin da ta tsinkayi muryar Hafiz a kunnenta, a zuciyarta tace "Wow fantastic, nice voice, Ashe dai yanda yahad'u hakama murayarsa ta had'u gaskiya gayen yagama had'ewa.


Lokacin Hafiz yasake magana karo na biyu batare da Hussaina tabashi amsar ta farkoba, "idan bazaki damuba kisakamin numberki ko bayan kin koma gida sai muyi magana, 

Ba musu ta amsa tasakamai numberta, sannan ta mikamar wayar dayake Hafiz gogaggen d'an duniyane gurin amsar wayar saida yahad'o da hannunta, suduka wani irin shock sukaji lokacin da tattausan hannuwansu suka had'u dana juna, kasa sakin hannunta Hafiz yayi sunkai kimanin minti biyu a haka sai itace tayi 'karfin halin zare hannunta daga nashi, kashe mata ido yayi tare da sakar mata wani 'kawataccen murmushi.


Duk abinda sukeyi Hassna batasaniba duk da guri d'aya suke zaune, hankalinta nakan wayartane tana chat a wani group na Zee Mmn khady me suna *Ciwon Ya mace* tanajin dad'in group d'in sosai yanda ake bada shawara me kyau da kuma yanayin abubuwan amfani da ake turowa, ba kamar kuma Had'in kai da 'yan group d'in suke dashi, duk da yanda takejin dad'in chat da *Mmn Ummi da Ameeno, Mmn Ramadan da rukky abdull* hakan behanta duba lokaciba dan kada suyi dare basu koma gidaba, dan yanzuma data duba 'karfe takwas da rabi, tasama ranta takwas da minti arba'in zasu koma gida.


Muryar Hussaina ta tsinkaya "Hassna dan Allah aromin wayarki zanyi kira, bansan credit d'ina yakareba, ba musu Hassana ta mi'kamata "amma gaskiya dakin gama wayar zamu tafi saboda tara takusa kuma kinsan Al'kawarin da muka d'aukoma momy,

"To kawai Hussaina tace, tawuce tanufi gunrinda akayi parking d'in motoci kamar tana wayar gaske.

Dai-dai motar da Hafiz yafad'amata nan ta tsaya, jingina tayi da motar idanunta akan wayarta.


Tashi Hafiz yayi yabi bayanta, Hassana na kallo amma bata kawo kome a rantaba, iatadai fatanta kawai idan Hussaina tagama wayar datadawo sutafi gida

.

Bud'e motar Hafiz yayi gidan baya suka shiga, kasancewar motar tanada ba'kin glass bazeba wanda ke waje damar ganin nacikiba dukda dama gurin akwai duhun dare,


Ac Hafiz ya kunna musu, take motar tad'au sanyi tare da wani daddad'an 'kamshi

Zaune suke gaf da juna har jikinsu na had'uwa dana junansu, Hafiz ne yafara magana cikin kwarewa da gogewa na yan duniya "Babyna ammafa kin had'u kinganki kuwa kamar matan hurul'ayni, wani 'kawataccen murmushi Hussaina tayi tare dasa hannunta tarufe fuskarta, duba Hafiz yakai kan shantala-shantalan yatsun hannunta wanda yake d'auke da awarwaraye da wani had'adden zobe na azurfa, hannu yasa Yakama hannun nata yamatse a hannunsa, sannan yafara wasa da zoben "kai amma ring d'innan yayimin kyau babyna, amma set ne tare da sarkarki koh?

Yafad'a tare dakai hannunsa kan wuyanta yana wasa da sarkarta, lokacin yagama kashema Hussaina jiki yanda yake shafar wuyanta, ko magana bata iyawa sai maida numfashi datake d'aya d'aya, hakan yabashi damar yin 'kasa da hannunsa zuwa cikin rigarta yafara wasa da breast d'inta, wani irin yarrrr taji ajikinta, saboda ba'kon Al'amarin daya risketa yau, domin Hafiz shine mutum na farko daya fara yimata irin wannan wasan, suna soyayya da Jabeer amma koda wasa beta6a kai hannunsa kan jikintaba, "hakan yana nufin jabeer be iya soyayyabane ko miye....


Tana cikin wannan tunanin taji Hafiz ya rungomota yahad'ata da jikishi, yana rad'amata kalmar "I love you a kunnenta, cikin kasalalliyar murya tace "mee too my Dear,

"Wow nice my Baby, Hafiz yafad'a tare da had'e bakinsa da nata yacigaba da kissing d'inta.


Dare yafara Hankalin Hassana ya masifar tashi dan tanemi Hussaina ko'ina a cikin hall d'in da wajen hall d'in amma bata gantaba, duk tabi tarud'e, gashi Zuby tunda tashiga fagen rawa batako wai-waiyesuba barantana ta tambayeta kotasan inda Hussainar take gashi tatafimata da waya barantana takirata.

Komawa tayi kan kujera ta zauna tayi tagumi hannu bibbiyu,


Can Hankalin Zuby yayo kan inda tabarsu Hussaina amma batagansuba sai Hassana wacce tahad'a hannuwa biyu ta tallabe kumatunta kwalla suncika idanunta, da sauri zuby takaraso inda take "Ke ina 'yar'uwarki?  Hassana batajitaba dan tayi nisa cikin tunanin irin hukuncin da daddy ze yanke masu idan yadawo ya tarar da basunan, batakaran suba ranar momynsuma bazata fitaba dan dady mutumne me zafi tsaye yake kan tarbiyar iyalanshi.


Ta6ota zuby tayi "tambayarki nake ina Hussaina?

Sai lokacin tadawo daga tunanin datake "nima wlh ita nake nema dan Allah ki kiramin ita da wayarki danni tatafi da tawa wayar.

"To ina Hafiz? Zuby ta'kara jeho mata wannan tamabayar

"Kinga ni dukansu bansan inda sukeba, nidai dan Allah ki taimaka ki kiramin Hussaina mutafi gida.


Take zuciyar Zuby tabata akwai wata kulalliya tsakanin Hafiz da Hussaina, idan kau hakane lallai Hussaina tad'auko ruwan dafa kanta.


Wayarta ta fiddo daga cikin poss tafara lalubar number Hussaina, kusan kira takwas zuby tayima Hussaina no answer, hakan ba 'karamin 'kular da ita yayiba, batako kalli Hassanaba tabar gurin tana cika tana batsewa.


Ganin dare na'karyi yasa Hassana tambayar wata budurwa kusa da ita "dan Allah 'karfe nawa?

Duba wayar tayi "karfe tara da Monti takwas tabata amsa a ta'kaice.


Cike da rud'ewa Hassana tatashi tafita harabar hotel d'in Allah ya taimaketa lokacin wani me napep ya sauke wasu, tagayamshi inda ze kaita, saida suka d'au hanya tafara tunanin inda 'yar'uwar tata tashiga "Toni yanzu mezanfad'ama Momy idan aka tambayeni Hussaina, wasu hawaye suka gangaro kan kumatunta.

"Allah sa dai tana lafiya duk inda take.

Tana cikin wannan tunanin har suka iso 'kofar gidansu batamasan sunzoba saida me napep yace "hajiya mun isofa sannan ta sallameshi tafita daga napep d'in.


Jiki a sanyaye tanufi gidansu, ahankali ta kwankwasa megadi yabud'emata bayan yatambayeta tagayamashi itace.


Ahankali tashiga gidan da sallama Momy tagani zaune tayi tagumi koba tambaya tasan jiran dawowarsu takeyi, ganin Hassana yasa Momy sauke wata ajiyar zuciya, "Alhmdlh ina 'yar'uwar taki take?


Hawaye yacigaba da zuba daga idon Hassana batare databa Momy amsar tambayar datayimataba, cikin tashin hankali Momy ta'karaso inda Hassana take takama kafad'unta "ina take nace? Ko wani abu ya sameta? Kifad'amin......


Ganin hankalin Momy yatashi yasa Hassana goge hawayenta "bawani abu yasametaba kawai na nemeta bangantaba, kuma gashi dare yayi...


"Subhannallah Momy tafad'a Allah sa dai lafiya, kin kira wayarta? "Nima wayata tana hannunta.


Hankali tashe Momy tasa wayarta takira Hussaina itama no answer aka gayamata kamar yanda duk wanda yakira ake gayamai, saida tayi kira kusan na goma sannan Hussaina ta d'auka cikin kasalalliyar murya tafara magana dan lokacin tana jikin Hafiz yagama rabata da rigarta yana 'ko'karin ciremata breziya,


Cikin fad'a Momy tace "dan Ubanki kiyi maza ki dawo gidan tun kafin dadynku yadawo, batajira me Hussaina zatafad'aba  Momy takashe wayar


Lokacin sukajiyo horn d'in motar Alamar dawowar me gidan, cikin tsananin tashin hankali Hassana tafara magana "Momy dadyne yadawo nashiga ukku tafad'a tana yarfe hannu.


Da sauri Momy tace "maza ki shige d'akinku kada yazo yaga batanan, Dan batakaran itadayi laifinba mu kanmu sai rayukanmu sun 6aci.


Da sauri Hassana tashige d'aki, zama tayi bakin gado tayi tagumi hannu bibbiyu tana tunanin 'yar'uwarta.


Hassana na daga d'akinsu taji shigowar daddy wani mummunan fad'uwar gaba taji, tanajin lokacin da Momy kemasa sannu da zuwa, yana zama ba abinda yafara tambaya sai "Ina yarannan suke? Cikin inda-inda Momy tabashi amsa "uhm am suna d'akinsu ko Alh....


Kwalamasu kira yashigayi "Hassana....Hussaina....

Hassana naji tayi saurin Amsawa "na'am...

"Kuzo nan ina nemanku "to ta amsa jiki na kyarma tasako d'an karamin hijab d'inta ta fito, durkusawa tayi gaban daddy "gani daddy tafad'a tare da sunkuyar da kanta 'kasa gabanta sai dukan tara-tara yake.


"Ina 'yar'uwar taki? Daddy ya tambaya, "im ahm....uhmmm tafara inda-inda tarasa wace amsa zata bayar domin kare 'yar'uwarta shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta.


Tsawa daddy ya kwatsa mata "ke.... Ba magana nike dakeba ina 'yar'uwarki nace? Jiki na 'kyarma tafara magana tana d'an ja da baya dan taga yanda daddyn nasu ya zuciya a lokacin ze iya mazgeta, "daddy munje walimar bikin wata 'kawarmune shine dazan taho nayita nemanta bangantaba shine nikuma nataho,

"Owk good hakan yayi kyau, shine ita ta zauna dan bata tsoron fushina, aiko ranta inyayi dubu a gidannan yau sai ya 6aci, kallon Momy yayi "kekuma kinsan bata dawoba amma ko ajikinki saboda baki damu da tarbiyar yarankiba ko "haba Alhj ya zakace bandamu da tarbiyarsuba, wlh tun d'azu nake faman kiran wayarta sai tacemun gatanan to ya kakeso inyi? Ko zuwa zanyi intaho da ita,

"A'a ba tahowa zakiyi da itaba, idan bakije kika taho da itaba nizan taho da ita dakaina, yafad'a yana nuni da 'kirjinshi da hannu.


Bejira abinda zatafad'aba ya zari cable d'in jikin tv yafita zuwa harabar gidan,

Me gadi na hangoshi tafe yataso da sauri "Sannu da fitowa Alhj, "yauwa mal bala, abinda kawai ya furta kenan sannan yafita daga wajen get d'in gidan ya tsaya ya maida hannuwanshi duka baya, yafara safa da marwa yana jiran yaga ta ina Hussaina zata 6ullo, tsawon kimanin minti goma sha biyar yana zarya gurin Amma bako Alamarta, mal bala me gadine ya le'ko cikin girmamawa yafara magana "Alhj lafiya kuwa naganka haka kamar hankalinka a tashe?

"Mal bala yarinyarnan ni zata rainama hankali ni zata maida mutumin banza cikin garinnan, da darajata da 'kimata ace wai har kamar 'yanzu 'karfe goma da minti ashirin da takwas yarana suna gantali a gari.

Mal bala yace "amma Alh ai naga kamar sundawo ko? "Gudace tadawo yanzu jiran dawowar d'ayar nake.

"To Alhj Allah maidota lafiya, Allah sa duk inda take tana lafiya.

Komawa mal bala yayi daga ciki ya zauna kan d'an bencinshi, yanda hankalin Alhj yatashi shima duk sai yajishi cikin damuwa, saboda Alhj mutum ne harda rabin mutum.


Da misalin 'karfe sha d'aya saura minti goma, lokacin Alhj yagaji da zarya tsakanin wajen get d'in gidan zuwa cikin gida, yana zaune kan bencin mal bala, tsayuwar mota yaji dai-dai get d'in gidansa da sauri Alhj ya mi'ke le'kawa yayi lokacin Har Hussaina tafito daga motar me motar yayi gaba abinsa,


Momy kuwa da Hassana suna cikin gida hankalinsu a tashe, Hassana banda kuka ba abinda takeyi.


Hussaina kuwa bayan Hafiz ya ajiyeta ya wuce sai lokacin wani mugun tsoro ya dirar mata cikin zuciya, jikinta yafara 'kyarma, hankalinta be 'kara tashiba saida taduba agogo taga 'karfe sha d'aya na dare, ahankali tafara buga get d'in gidan, da sauri mal bala yazo ya bud'e mata tana Shiga,tafara tafiya da sauri tana wai-waye saida tazo gab dashiga falon gidan ta tsaya tacire takalminta dan kada ajiyo 'karar tafiyarta, ri'ke takalmin tayi a hannu sannan tatura 'kyauren falon ahankali.

Jitayi an sha'kota ta baya a firgice ta juyo, ido biyu sukayi da daddy beyi wata-wataba yafara zabga mata cable wayar dake hannunsa nan tafasa 'kara tana ihu, amma daddy be sauraramataba, tsulamata wayar yakeyi iya 'karfinshi, mommy da Hassana suna daga falo sukajiyo ihunta, wani sabon kuka ya kwacema Hassana cewa take "Momy dan Allah ki taimaki Hussaina kiba daddy ha'kuri kada yajimata ciwo, kallonta Momy tayi cikin nuna rashin halin damuwa tace "koma miye ita tajama kanta 'kara yadaketa gobe bazata 'karaba.


Da gudu tashigo falon kamar wacce aka jeho, bayan Momy tanufa tana kuka ta 'kan'kameta "wayyo Momy dan Allah ki taimakeni wlh bazan 'karaba,

6an6areta Momy tayi daga jikinta tare da barin gurin tana cewa "lokacin dakikayi rashin jin naki kinyi shawara dani, dan haka kada ki nemi taimakona can ki 'karata jiki magayi, shigewarta tayi d'aki ta maida 'kofarta tarufe,  wani irin kuka Hassana tafashe dashi ganin momy batada niyyar baiwa dady ha'kuri shikuma beda niyyar hakura, rugowa tayi tari'ke hannun daddy tanamashi magiya "dan Allah daddy kayimata ha'kuri bazata 'karaba, a harzu'ke daddy ya hankad'ar da Hassana gefe guda yacigaba da suburbud'ar Hussaina, suduka suke kuka suna bashi ha'kuri amma beko sauraresuba saida ya tabbatar Hussaina ta daku sannan ya rabu da ita yanufi d'akinshi yana huci yana cewa "gobema ki kara tafiya ki wuce magrib baki dawo gidaba wannan kad'an nayima shashasha kawai.


Kama hannunta Hassana tayi suka nufi d'akinsu, da kyar Husaina take tafiya saboda ba 'karamin duka tasha hannun daddynsu ba,


Zaunar da ita Hassana tayi bakin gado tana sharar kwallah, tace "kinga abinda nake gujemaki koh, ba irin neman dabanyimaki gurin *dinner* d'innan ba amma ban gankiba, wai ina kikajene?


Cikin dasashshiyar murya Hussaina tace "uhm yanzu banida lokacin dazanbaki wannan amsar,

Toilet Hassana tanufa batare data 'karama Hussaina wata maganaba ruwan d'umi tahad'amata tarakata har toilet sannan tajawo mata 'kofar, haka tayi wanka ta gargasa jikinta bayan tafito Hassana tasa Robb ta shafemata jikinta sannan sukabi lafiyar gado, kowace tayi shiru kamar me bacci a zahiri amma kowace da tunanin datake cikin zuciyarta, Hussaina tunanin Hafiz ne fall cukushe a zuciyarta, "lallai Hafiz ya iya soyayya, yanzu nagane jabeer ba kome ya iyaba a fanni soyayya sai dai kullum idan yazo yakamayimani nasiha da sauransu, nikam nafison namiji d'an life Wanda yasan takan love, gaskiya akwai sakal kan maganaraurean da jabeer dan ni yanzu babu namijin danake muradi a rayuwa kamar Hafiz, dan Abinda ya faru tsakaninmu yau yasa naji bana bukatar kowane namiji sai shi.


Hassana kuwa tunani take shin ina 'yar'uwarta tashiga har takai wannan daren bata dawo gidaba, Allah sa dai Hussaina bata biyema samarin shahoba, mayaudara "Hmm tafad'a shiyasa niko Alama bana harkar samari.

Da haka ta gyara kwanciyarta bacci yayi awon gaba da ita.


6angaren dady kuwa bacci gagaran idanunsa yayi tashi yayi ya zauna gefen gado ya zabga uban tagumi, zuwa can kuma yami'ke tsaye yafara safa da marwa cikin d'aki, "lallai dole inyi saurin yima tufkar hanci, saina tashi tsaye kan tarbiyar yaranan, saboda zamaninnan yanzu saika haifi d'a baka haifi halinsaba. Kusan raba dare daddy yayi yana tunani.


**           **           **        **


Washe gari zaune suke kan dining suna breakfast bakajin motsin kome sai 'karar plate da cokulla, kowane ka kallah cikinsu rai a dagule dakuma tunanin abinda yafaru jiya.


Bayan sun kammala daddy yayi gyaran murya "kunajina? Suduka suka jiyo suka kalleshi, "tunda abin naku yazama lalata inaso insanar daku na soke maganar makarntar dazakuje *AMUSLIM COMMUNITY SCIENCE &TECHNOLOGY FUTUA* daga yau kucireta a ranku kuduka aure zanyimaku, ke Hassana inaso kifito da miji nanda wata d'aya, ke Kuma Hussaina ya watsamata wani matsiyacin kallo "kigayama jabeer inason ganinshi, wani irin Fad'uwar gaba Hussaina taji dajin dady yace yana neman jabeer, sadda kai tayi 'kasa "daddy nifa mundad'e da 6atawa da jabeer.


Shiru daddy yayi yana kallonta, toki fiddo miji nanda wata d'aya, idan kika wuce iya adadin kwanakin dana ebar miki zand'au duk matakin danaga ya dace.


Mi'kewa yayi tare da d'aukar jakarsa ta zuwa office sannan ya kalli Momy "maganar fita kuma daga yau nakasheta idan sunbar gidannan a tabbatar islamiyya zasu, yana gama fad'a yasa kai yafice


*Bayan sati d'aya*

Hassana da Hussaina sun daina fita konan da can kullum sai dai idan zasu islamiyya, maganar fitar da miji kuwa kullum sai daddynsu ya tinasar dasu,


Yauma kamar kullum zaune suke kan had'addun kujerun dake zagaye da babban falon gidan, Hassana ta kalli Hussaina, "nikam sister inaso muyi wata magana dake,

"Ina jinki Hussaina tafad'a,

"Wai meyasa kikacema Abba kun 6ata da jebeer Alhalin ba abinda yashiga tsakaninku,

Murmushi Hussaina tayi sannan ta d'au 'kafa d'aya ta d'ora kan d'aya tana girgizawa "ba wani dalili kawai tsuntsun 'kaunarsane ya canja she'ka.


Tana fad'in haka ta maida hankalinta kan wayarta wacce suke chat itada Hafiz suna tattauna yanda za'ayi su had'u dan tun ranar da daddy yahanasu fita tasanar dashi, shikuma kullum sai yakirata yakai sau goma yanamata magiya akan dan Allah tayi dabarar dazasu had'u koda na minti biyar ne.


Sauke ajiyar Zuciya Hussaina tayi, tace "amma Hussaina idan kikayima jabeer haka kinci amana, kinriga kinsan irin so da 'kaunar dayake nunamaki, zeyi wuya kisamu namijin daze soki kamar jabeer.


"Ba wani wuya, Hussaina tafad'a saboda nadad'e dasamun wanda ya mayemin gurbinsa, cike da mamaki Hussaina ta kalleta wannan wanene wanda yayi 'karfin halin raba Zukatan dasuka dad'e suna maradin zama abu guda,


"Murmushi Hussaina tayi tare da mi'kewa tsaye tayi taku biyu zuwa ukku sannan tajuyo ta kalli Hassana wacce kebinta da ido tana jiran jin amsarta "Ba wani bane kinsanshi, Hafiz Wanda muka had'u dashi gurin *dinner* itama Hassana mi'kewa tayi ta isa inda Hussaina take cike da mamaki "indai Wannan Hafiz d'in kike nufi wlh inabaki shawara da kada kiyi sakin na  hannu kamun na guje danni wannan Hafiz d'in da kike gani kwata-kwata be kwantamin araiba da ganinshi yafi kama da yan abi yarima asha kid'a,


Hannunta takai kan kafad'ar Hussaina ta dafata "sister iname baki shawara kada kibari jabeer ya su6uce maki dan samun namiji kamarsa a wannan zamanin sai antona......


"Ke dakata, hussaina tafad'a cikin d'aga murya, kada ki kawomin 'kabli da ba'adi nace banison jabeer idan ke kinasonshi ki aureshi mana wani yahanaki, "Hmm aini tun farko bani yace yansoba, amma in bancin haka banga abin 'ki gareshiba.


"Mtsswww, Hussaina taja wani dogon tsaki sannan tanufi bedroom tabar Hassana nan tsaye cike da mamakin hali irin na 'yar'uwarta.


Hussaina kuwa tana shiga d'aki kiran Hafiz yashigo wayarta, cike da farinciki ta d'auka bayan ta sumbaci wayar dan a kullum 'karajin son Hafiz takeyi cikin zuciyarta.


"hellow babyna,

"uhm my dear ya kake tafad'a cikin shagwa6a.

"Eh to gaskiya ba lafiya...

"subhannallah meyasameka tafad'a tare da gyara zamanta.

"kin'ki muhad'u dan baki d'auki son danikemaki a bakin komeba.

Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke "Haba my dear dan saboda wannan zakace bakada lafiya, indai wannan ne ka kwantar da hankalinka yau idan nafito islamiyya zamu had'u.

"Wow babyna amma naji dad'i, 'karfe nawa kuke fitowa?

'Karfe hud'une mukoma shidda, kaga wannan lokacin ya ishemu mud'an gaisa.

"Eh to hakane amma kinsanfa nayi missing d'inki sosai.

"Hmm sai munhad'un kawai tafad'a

"Owk bye "muaaah yasakar mata wani kiss ta wayar sannan ya tsinke kiran, wani dad'i taji ya ziyarci zuciyarta rungume wayar tayi cike da Farin ciki, harta 'kosa Hud'u na yamma tayi sufita zuwa islamiyya.

.

Da misalin 'karfe hud'u saura minti goma Hussaina tagama shirinta tsaf na islamiyyah cikin uniform kalar ruwan 'kasa,


"Kallon yar'uwarta tayi wacce ke 'ko'karin d'aura farin d'an kwali, tace Hassana kiyi sauri kinga bana bu'katar zuwa a makare, kallo kawai Hassana tabita dashi "Tofah yau kuma kece me cewa bakison makara ince kullum saina gama shiryawa sannan inyi zaman jiranki,

"Naji dan Allah yanzu dai kitaho mutafi kina 'kara tsyar damu, ......

Dai-dai lokacin kuma wayarta tayi ringing dubawa tayi jiki na kyarma takai dubanta ga Hassana wacce tagama shirinta tsaf tana jiran sutafi.


Sunan Hafiz tagani yana yawo kan wayar, dama kuma kobata dubaba tasan shine dan tsakanin 'karfe ukku da Rabi zuwa yanzu 'karfe hud'u yayimata kira yakai tara,

"Hellow yanzu zamu fito daga gidan, tafad'a tana kallon Hassana ta wutsiyar ido,

"To babyna dan Allah kiyi sauri wlh na matsu na ganki dan bakisan yanda nakejibane shiyasa kikai har yanzu baki fitoba.

"Sorry dear ina hanyafa nace ka saurareni mana.

"To shikenan ina gurinda nagayamaki,

To sainazo tafad'a tare da kashe wayar.


Tana juyowa suka had'a ido da Hassana saida gabanta yayi 'yar 'karamar fad'uwa saboda kallon tuhumar dataga tana mata.


Nunawa tayi kamar batasan kome kenanba tace "muje ko kada mu makara naga yau baki bu'katar muyi latti,

"Owk muje to.


Haka suka jero gwanin ban sha'awa kome nasu iri d'aya ga tsananin kamanni dasuke farinsu d'aya tsawonsu d'aya haka zubin jikinsu d'aya, suna matu'kar kamanni wanda hakan kesawa mutane da dama basa gane Hassana basa gane Hussaina, hatta da iyayensu basu cika ganesuba saita gurin halinsu daya bam-bamta.


A falo suka tarar da Momy, cikin ladabi suka isa gabanta "Momy mutafi islamiyyah

"To Allah bada sa'a Yakuma tsareku, Allah yayimaku Albarka, Adawo lafiya.


Amsawa sukayi da Ameen sannan suka fice, suna fita sukasamu me napep suka gayamashi sunan islamiyyar daze kaisu,


Sun fara tafiya Hussaina ta Kalli Hassana tace "sister dan Allah kiyimin taimako d'aya sonike inje gidansu zuby kuma kinsan gida baza'abarni infitaba inaso me napep ya saukeni acan sai awuce dake islamiyya idan antaso kimin waya sai muhad'u mutafi gida.


Da Hassana kamar bazata Aminceba saikuma tace "to shikenan Amma dan Allah kada ki wuce lokacin tashinmu islamiyya, kinsan dai daddy ba sauki.

"InshaAllah kinamin waya zanzo, "to shikenan.


Hassana aka fara saukewa islamiyya sannan aka wuce da Hussaina unguwar Barhim dake wajen Gari, dai-dai inda Hafiz yagayamata yananan nan kuwa tasameshi.


Tana fitowa daga napep ta hangoshi tsaye jikin motarshi ya hard'e duka hannayenshi a 'kirji, sanye yake cikin bakin wando, da yellow riga, sai ba'ka'ken takalmi, sannan ya d'ora wani ba'kin glass Wanda ya'kara fitowa da ainafin kyawunsa.


Yana hangota yafara jefarta da 'kawataccen murmushinsa, itama maida mashi martani tayi harta isa gurinshi suna musayar murmushi.


"Welcome babyna yafad'a tare da rungumata a jikinshi, saurin tureshi tayi tana  waige kada ace mutane suna kallonsu. *{Hmm Hussaina kenan idan mutane basu ganinku ai Allah yana ganinku}*


"kada kidamu babyna ba mutane sosai a unguwar, kodama wani yaganmu ba wanda ze shiga harkarmu, amma tunda naga kamar kina tsoro shigo daga ciki, "dadai yafi, tafad'a

Sannan yabud'emata motar tashiga shima yashiga.


.
Rungumota yayi jikinsa tare da d'ora lips d'insa kan kumatunta yasakar mata kiss,
"Kinsan wani abu babyna? Yafada cikin had'addiyar murayarshi me kashe mata jiki.
"A'a saika fad'a my dear.
"Gaskiya naji dad'i nayi matu'kar farinciki yanda kika amince kikazo inda nake yanzu na'kara yarda da 'kaunar da kikemun hundred percent, wani irin dad'i taji har cikin ranta sannan tafara magana cikin kasalalliyar murya,
"My dear inaso ka yarda dani kamar yanda na yarda dakai,
"Na yarda dake babyna yafad'a tare da saka hannunshi d'aya cikin hijab d'inta yafara wasa  da dukiyar fulaninta, hannunsa d'aya kuma nakan cikinta yanamata wani salo wanda ke 'kara rikitata,
Suduka sun lula duniyar soyayyar shan minti, bakajin komai sai numfashi dasuke maidawa sama-sama, haka sukayita wasanni tsakaninsu tare dajin dad'in kasancewa da juna.
Hassana kuwa tana islamiyyah suna karatu, bayan malamin dake d'aukarsu darasin Qur'an yafita sai me d'aukarsu hadith yashigo, saboda haka tana ganin haka tasan lokacin tashinsu yakusa dan dama hadith shine period d'in 'karshe kuma baya dad'ewa lokacinsa ke 'karewa saboda haka kafin yafara karatu ta d'auko wayarta sunan Hussaina ta lalubo sannan ta dannan kira.
Lokacin Hussaina na jikin Hafiz yariga yagama tayar mata da hankali kwata- kwata bata cikin hayyacinta har wayar takaraci ringing d'inta tagama bata d'agaba, sai a kira na ukku sannan tad'aga
"Hellow sister antashine, "eh kitaho muhad'e yanda zamu koma gida tare.
"Owk ganinan zuwa.
Bayan ta tsinke kiran ta maida dubanta ga Hafiz "yauwa my dear dama inason magana dakai,
"Ina jinki babyna.
"Bawata magana bace dama daddynmune yace yabamu wata d'aya mu fitar da miji, nikuma ba wanda nakeso sai kai shine nace yakamata ka gabatar da kanka gareshi.
Shiru yayi kamar me tunanin wani abu, itakuma ta zubamar ido tana jiran amsar daze bata, ganin beda niyyar yin magana yasata ta6oshi "dear lfy naga kayi shiru kobakaji me nake fad'a bane.
"Murmushi yayi "najiki babyna, kada kidamu aini dama irin wannan ranar nake jira, zanzo inshaAllah kada kiji kome aini me 'kaunarkine.
"Wani irin murmushi tasakar mashi cikin farin ciki sannan taduba wayarta 'karfe shidda saura minti goma a gaggauce sukayi bankwana yabata iyayen kud'i ta'ki amsa saboda tana tsoron gida aganta dasu.
Me napep ta tsaida tashiga zuwa gidansu.
Yana ganin tafiyarta ya kece da wata irin dariya tare dakaima sitiyarin motarshi duka "wow Allah kai damo ga harawa kobeciba yayi birgima, kowa yagayamata zan iya auren macen danagama lugui-guitawa a waje, aini sai kamilar mace wacce tasan darajar kanta ba irinkiba wacce zatabi namiji har inda yake.
A haka yatashi motarsa ya 'kara gaba ranshi fari tass.
Hussaina kuwa napep na ajiye Hassan itama ana ajiyeta, saboda haka tare suka shiga gida babu wata matsala.
   *washe Gari*
Da misalin 'karfe hud'u da rabi na yamma Zaune suke falo suna kallon gidan tv startime tashar farin wata suna shirin addini da Alqibla, kasancewar yau Alhamis ba islamiyyah suduka hada Momy duk sun maida hankalinsu kan shirin amma banda Hussaina wacce hankalinta yana kan waya tana chat da Hafiz Wanda yawanci magan-ganun duk na shan mintine sukeyima junansu.
Tsayuwar mota sukaji a harabar gidan, da sauri Hassana ta le'ka ta window kafin tadawo ta zauna ta dubi Hussaina, tace "jabeer nefa yazo, cigaba da chat d'inta Hussaina tayi bata ko kalli Hassanaba barantana tabata amsar maganar datayimata.
Ganin batada niyyar motsawa yasa Momy cewa "ba magana ake makiba kobakijine jabeer ne yazo,
Turo baki tayi ni wlh momy wannan jabeer d'in yadameni nifa nagayamashi yanzu bani sonshi ko ana dole ne......
Bugemata baki momy tayi "banison sakarcin banza idan kince kin daina son jabeer wa kike dashi wanda yafishi, yaro mutumin kirki me hankali ga nutsuwa, saboda hakama mahaifinku yad'aukeshi tamkar d'an cikinsa.
Tashi tayi tana dira 'kafa cikin shagwa6a ni Momy nafad'amaki inada Wanda nakeso kuma ai yace zezo ya gabatar da kanshi gurin daddy.
"Keni rufemin baki sakaran banza.
Momy ta kalla  Hassana "jeki shigo dashi,
"To tafad'a sannan tanufi 'kofa tana kallon Hussaina
Wacce tadage ita a dole batason jabeer hadda yan guntayen hawayenta.
Bayan shigowar jabeer suka gaisa da Momy sannan tashige d'akinta tabasu guri, Hassana ce tacika gabanshi da kayan ciye-ciye dana sha, sannan tad'an zauna domin su gaisa, lokacin Hussqina tana zaune tabi ta had'e girar sama data 'kasa sai danne-danne take a wayarta,
Shiru ya gifta nayan wasu mintoci, Hassanace ta katse shirun ta hanyar cewa "Yaya jabeer ina wuni,
"lafiya lao ya Amsa yana 'karemata kallo, a zuciyarshi yana cewa wannnan itace hassanar kokuwa Hussainar ce, saida yaji tami'ke tsaye tana cewa "to nikam nashiga daga ciki sannan yagane ashe ga mutunniyar tashi nan gabanshi wacce tunda yashigo ko kallo be ishetaba, taunar cingam kawai take sannan hankalinta duka yana kan wayarta tana ibadar wato chat da Hafiz.
Shiru sukayi suduka anrasa wanda zefara magana dan Hussainama yau ko arzi'kin gaisuwa Jabeer be samuba, illah wani irin haushinsama datakeji dan tadad'e dagayamshi maganar soyayyarsu ya janye ya nemi wata Amma dayake shine d'an anace sarkin naci ya'ki ha'kura.
Jabeer ne ya katse shirun ta hanyar cewa "jiya naga fitarku lokacin zaku islamiyya naso inyimaku magana amma sainaga rashin dacewar hakan kasancewar gurin dazaku yanada muhimmaci bekamata ace na tsaidakuba.
"Hmm aikode, kawai tafad'a tare da yamutsa fuska ta juyar da kanta gefe tana taunar cingam 'kas-'kas
Har cikin ranshi yaji haushin yanda tayi Mashi magana amma sai ya danne kasancewar anason namiji yazama me shariya akan wasu 'kananan abubuwa, magana ya'kara karo na biyu.
"Gaskiya inajin dad'in yanda kuke zuwa islamiyyah fatana akodayaushe kafin Aurenmu ace kunyi safka kunyi hadda koda hizif talatin ga sauran litattafan addini, kinga ko'ina zanyi Alfahari da matata tanada ilimin addini, sannan kuma uwa uba yaranmu zasu koya a gun mamarsu kafin suma asakasu tasu islamiyyar.....
Dakatar dashi tayi ta hanyar d'aga mashi hannu tana magana cikin masifa "dakata malam, wai akan wa kake magana? "Ni, tanuna kanta da hannunta, to indai nice kama daina wannan tunanin kacire soyayyata daga cikin zuciyarka, danni yanzu batakai nakeyi 'karama kanemi me sonka tunda wuri kafin lokaci ya'kurema.
Haba Hussaina donmi kike nema ki gujeni? Menayimaki? Kadafa ki manta mundad'e muna soyayya kullum burinmu be wuce muzama mata da mijiba, amma yanzu Cikin 'kan-'kanin lokaci kina nema ki canja ra'ayi.
"Oh nema manake incanja, tobari kaji in gayama ba nema nakeyiba nama canja gaba d'aya yanzu baka cikin tsarin mazan danike burin aure...
Tuni kuma wani ya maye gurbinka acikin zucyata saboda haka kaje kawai kanemi wata,
Cike da mamaki da takaicin yanda Hussaina ke gayamar magana yabar gidan, dan kosamun damar yin bankwana da Momy beyiba,
Dai-dai harabar gidan suka had'e da Zuby tana shigowa "tana ganin jabeer ta washe baki "a'a'a Manya kenan anzo gun mutuniyar, dariyar ya'ke kawai ya 'ka'karo Wanda hakan baze hana kagane cikin tsananin damuwar dayakeba,
"Eh wlh kuma gashi harna fitoba, to shikenan agaida gida.
Tana tsaye yashige motarsa yatayar da ita Malam bala me gadi yabud'emashi get yanatayimar fadanci dan yasaba duk ranar dayazo yakan bashi nacin goro amma yau sai yaga Alamar ranshi kamar a 6ace yake, haka yabar gidan Malam bala yamaida get yarufe sannan yakoma kan bencinsa yazauna yana cewa "ho yar nema yau ta6atama mutumin rai 'yan aninnan danike samuma yau bansamesuba, sannan yajawo redio ya kunna yana saurare.
Zuby kuwa taso taji wani abu daga bakin jabeer amma ganin ranshi a 6ace kuma bebata fuskar hakanba yasa tayi ciki tana zumud'in ji daga bakin 'kawarta
Da sallama Zuby tashiga falon gidan Har yanzu Hussaina na zaune inda take sai cika takeyi tana batsewa, kallonta Zuby tayi "kawata lafiya naganki haka ko wani abune yafaru.
Kedai bari 'kawata wancen mutumin mana yazo ya dagulamin lissafi,
"Wane mutumi kuma Zuby ta tambaya tare da nuna rashin gane inda abin yadosa.
Haba wane mutumifa banda jabeer, nafa dad'e da gayamashi na daina yayinshi yaha'kura Amma yanacemun,
"haba 'kawata miye aibun jabeer da zaki 'kishi jabeer kau ai namijine na nunama tsara, ga kyau ga wayewa.
"Amma kuma kwata-kwata be iya soyayyayba, Hussaina tafad'a ni kalar soyayyarshi bataminba, kinsan nasha gayamaki nafison namiji d'an life wanda yasan takan love.
"To amma tuni baki gane hakaba kike tare dashi sai yanzu.
"Kwaraiko saboda yanzu nasamu wanda ya iyane shiyasa nagane shi be iya komeba.
'Kara matsowa Zuby tayi tare da d'ora hannunta kan cinyar Hussaina "Amma 'kawata wanene wannan wanda yayi sa'ar saye zuciyarki cikin 'kan'kanin lokaci.
Wani 'kawataccen murmushi Hussaina tayi "Hafiz" wani mummunan fad'uwar gaba Zuby tayi dukda ta dad'e da sanin akwai soyayya tsakanin Hussainar da Hafiz,
"Wane Hafiz ? Ta tambaya danta 'kara tabbatarma kanta abinda Hafiz d'in yagayamata gaskiyane, Hafiz mana Wanda Muka had'u ranar *dinner*  wani busashshen murmushi Zuby ta 'ka'karo "kai amma dole kike susucewa 'kawata ai Hafiz gwanine kan soyayya ga kud'i ga kyau ga kuma harkar wayewa.
"Shiyasa ai nakamu da sonshi cikin 'kan'kanin lokaci saboda iya soyayyarshi amma kin had'a da wancen bagidajen shi kullum yazo beda magana sai wa'azi da sauka da Hadda kamar shine yasakani islamiyyar, kwashewa sukayi da dariya tare da tafawa, "wlh kuwa 'kawata yo ko dady dayasakamu islamiyyar beyimana bin diddigi irin nashi.
Sai gab da magrib sannan zuby tabar gidan, Zuciyarta tana tunanin Hanyar dazatabi ta 'kuntatama Hussaina tunda harta yarda tayi soyayya da Hafiz mutumin datafiso tafi 'kauna akan kome da kowa, 
         *Bayan kwana hud'u*
Zaune Suke a mota itada Hafiz suna soyayyarsu kamar yanda suka saba.
yauma sunfito islamiyyah tayima Hassana 'karyar cewa Zata gano mamar Zuby da aka kwantar da ita asibiti, shinefa tataho inda suka saba had'uwa.
Rungume take jikinsa da kyar tasamu ta kwace daga jikinsa sannan tamaida dubanta gareshi,
"Nikam Hafiz narasa gane kanka koda yaushe idan nace kanasona kace kanasona amma har yanzu ka gagara zuwa gidanmu ka gabatar da kanka ga mahaifina kullum ina sanar dakai lokacin da aka ebar mana yakusa 'karewa ko jiya saida daddy ya'kara mana tuni saura kwana goma idan bamu fito da mijiba ze za6a mana da kanshi, nikuma kasan bazan iya rayuwa da wani namijiba idan bakaiba.
"Kada ki damu babyna nima ina sonki kuma bazan iya had'a soyayyarki data kowace maceba, maganar gabatar da kaina ga iyayenki kuma akwai dalilin dayasa kikaga har yanzu banjeba.
"Haba my dear wannan wane daliline haka?
Kinsan dad d'ina yana 'kasar Cairo hajiyatace ke mana kome to jiya nayimata maganarki shine take cewa inkawoki Ku gaisa kafin manya sushiga maganar, tonikuma ina tsoron gayamaki dan naga had'uwarmuma dayaya mukeyi barantana kuma ace zakije gidanmu.
"Haba my dear indan wannan ne kada kadamu zanzo "haba yaushe to?
"Yaushe kakeso inzo
"Zaki iya fitowa gobe,
"Badamuwa kajirani anan, amma sai antashi islamiyyah zantaho, "to badamuwa.
Da haka sukayi sallama tahau napep tanufi islamiyyarsu suna isa ana taso dalibai saboda haka Hassana suka d'auka sannan suka wuce.
*washe Gari*  bayan sun dawo daga isalmiyyah, Hussaina taje d'akin Momy zaune ta isketa bakin gado tana nazarin wani littafin addu'oi cikin ladabi ta zauna kusa da ita.
"Momy wata Alfarma nazo nema gurinki,
"Tame ina jinki fad'i, momy tace batare data kalletaba,
Nan tashiga inda-inda tana ganin kamar 'karyar dazatayi bazata fishshetaba amma sai wata zuciyar tace "ki kwatanta hausawa sunce a rashin tayi akan bar araha.
"Dama Im...wai asibiti zamuje ganin mamar Zuby shine nakeso dan Allah ki taimakeni kibarni wlh namiki Al'kawarin bazan wuce awa d'ayaba.
"Kinga Hussaina banison abinda zezo yad'agamin hankali ina zamana lafiya, yanzu kije kisamu guri kiyi zamanki kuma mahaifinki yadawo yatarad bakinan wace amsa zanbashi,
"InshaAllah Momy bama zesan najeba,
Haka dai tayita magiya har momy tabarta tare da saharad'in idan daddynsu yadawo bata dawoba zatace batasanma fitartaba, tace ta amince da hakan.
Cikin Zumud'i takoma d'akinsu ta d'auko wani tsadadden swiss less maroon colour tasanya sannan tasanya takalmi milk jaka milk, sai tayi too much kasancewar zaren da akayi kwalliyar less d'in milk ne sannan tabi da milk d'in mayafi, _{mashaAllah koni zee dana kalleta nasan ba 'karamin kyau tayiba}_
Hassana dake zaune tana bitar littafin ibadah wanda akayimasu 'kari yau, ta kalleta "uhm sister wannan gayu haka Kuma sai ina?
"Sorry sister sauri nakeyi idan nadawo zakiji,
"To Allah maidoki lafiya
"ameen kawai tace tafice, A falo ta tarad da momy saida gabanta yayi mummunan fad'uwa dan batayi tunanin ganinta nanba,
Kallo Momy ta'karemata daga sama har 'kasa "keda zaki ganin marar lafiya kuma da wannan gayu haka,
'Ka'karo murmushi tayi "Hmm Momy kuma dan za'a ganin marar lafiya ba'a sa kaya me kyau.
"To shikenan nidai nagayamaki karki dad'e.
"InshaAllah bazan dad'eba.
Tana fita tahau napep sai inda sukayi mahad'a da Hafiz, tana isa kuwa ta iskeshi a mota, bud'emata yayi tashige sannan suka d'au hanya.
Sunyi tafiya me nisa kafin su shiga rukunin wasu gidaje da Alama estate ne, bakin wani gida sukayi parking shine yafara fitowa sannan yabud'emata tafito tare suka jera har zuwa cikin gidan,
Wani 'kawataccen falo yayimata masauki gidan tsit kamar ba mutane amma kuma yanayin kayan gidan zaka kallah kagane akwai mutane, zama sukayi suna fira sama-sama kusan minti sha biyar ba Alamar wani ze fito, nan Hussaina tad'an tsorata ta kalli Hafiz Wai ina mutanen gidanne,
Murmushi yayi haba babyna kamar ba wayayyaba hajiya tana ciki yanzu zata fito, ina zuwa yafad'a tare da mi'kewa yanufi pridge lemun _5ali6e_ ya d'auko tare da cup d'in glass ya ajiyemata,
"Bari ingyama hajiya may be bataji shigowarmu bane, wani d'aki yashiga da Alama bedroom ne bayan minti biyar yafito ya kalli Hussaina wacce kallo d'aya zakayimata kagane a tsorace take "hajiya tana wankane amma tana zuwa, wai bakisha lemunba "Uhm na'koshi nidai sonike intafi gida kada amun fad'a kagafa har bakwai da minti sha tara tafad'a tana duba agogon wayarta.
"Koma miye ai kinsha koda lemunne kinsan idan bakishaba bazanji dad'iba.
Zubowa tayi cikin cup tad'an kur6a kad'an ta ajiye
"Haba me kikasha nan?
Lemun yad'auka yacika cup d'in yafara bata da kanshi da ta'ki kar6a ganin ranshi ya 6aci yasa ta 'kar6a a hannunta ta shanye sannan ta ajiye cup d'in.
Cike da farinciki ya kalleta "kokefa babyna amma da kintsaya wani no'ke-no'ke "Uhm kawai tace dan tunda tasha lemun jikinta yamutu sai wata kasala data rufeta.
Hafiz yana lura da halin datake ciki saboda haka mi'kewa yayi tare dayin hanyar d'akin dayashiga d'azu "ina zuwa nasan yanzu tagama.
Hussaina kuwa hamma tafara jerowa d'aya bayan d'aya tana lumshe idanu cikin minti bakwai bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.
Saida ya dai-daici maganin dayazubamata a lemu ya Isa yin aikinsa sannan yafito ganinta yayi kwance kan kujera tana shara bacci wani shu'umin murmushi yayi tare da 'karasowa inda take.
Daukarta yayi d'af daga kan kujera yanufi bedroom da ita, shimfid'ar da ita yayi kan gado ranshi fari tas wasanni yafara mata yana shafa jikinta ko'ina yakai kimanin minti talatin yana mata haka, lokacin yagama rikicewa yakai 'kololuwa gurin sha'awa, juyar da ita yayi sannan ya zuge zip d'in rigarta kasancewar zip d'in irin me 6allewane yasa besha wahala gurin cire ainafin rigar dake jikintaba, sannan ya kwance mad'aurin zaninta yarage daga ita sai breaziya sai kuma undi 'ko'karin ciremata undi yashigayi, saida yarabata da kome na jikinta bayyanar surar jikinta ya'kara rikirkitashi, yashiga aikamata da sakonni yana wasanni da ita.
Lokacin shima yacire duk wani kaya dake jikinshi shorniker kawai yaragemar, yana 'ko'karin cire shortniker dinne dan yamatsu yacimma burinshi na sanin Hussaina a matsayin mace, lkoacin kuma wayarshi tashiga ringing.
Hannu yasa ya d'auka ganin sunan 'kanwarsa na yawo kan screen d'in wayar yasa yayi saurin d'agawa tare da karawa a kunnensa "Hellow Fatima ya'akayi? Ya tambayeta cikin tsananin jin haushin kiran datayimashi lokacin dayake burin cimma manufarshi.
Cikin muryar kuka Fatima take magana "Yaya kayi sauri kazo gida yanzu jikin hajiyane yatashi ahalin yanzu batasan inda kanta yakeba.
Subhanallah yafad'a tare da saurin mi'kewa ya rarumi kayanshi ya maida bekobi takan Hussainaba wacce taketa sharar bacci tsirara haihuwar uwarata kan gado.
A gidansu Hussaina kuwa Hankalinsu yayi matu'kar tashi ganin 'karfe goma ta gota ba Hussaina ba labarinta, gashi ko ankira wayarta switch up,
Daddy yagama 'kulewa ranshi yayi matukar 6aci.
"Lallai yarinyar nan tana nema ta maidani mutumin banza cikin garinnan, nizata jama abin magana aiko zata dawo ta tarad dani zatamin bayanin inda taje,
Sannan ya maida dubanshi ga momy "kece me babban laifi keda kikabarta tafita bayan kinsan dokar dana kafa a gidannan.
"Haba Alh sau nawa zan gayama bansan fitar yarinyar nanba, ko kana tunanin nizan bata izinin fitane, bayan nasan dokar daka kafa a gidannan.
"Zata sameni nikad'ai nasan hukuncin dazan yankemata, kuma kuduka bance wani yabani ha'kuri akan kowane hukunci zan yanke akantaba yafad'a yana nuna Momy da Hassana wacce ba abinda take sai kuka, tana ro'kon Allah ya maido mata da yar'uwarta lafiya duk inda take.
         *12:30am* ⏱
Da misalin 'karfe sha biyu da rabi na dare Hussaina tafarka daga nannauyan baccin datakeyi ahankali ta bud'e idanunta a tunaninta d'akinsu take, kawai sai ganinta tayi wani d'akin daban wanda bazata iya sheda inda take.
"Subhanallahi tafad'a tare da 'karema jikinta kallo ba kome jikinta, saurin jawo zaninta tayi ta rufe jikinta tana waige-waige taga ta inda mutum zefito daga cikin d'akin amma bataga Alamar hakanba,
Ahankali tunanin abinda yafaru da ita yafara dawomata a kwalwa, sai lokacin ta tuna tazonefa gaida hajiyar Hafiz, to Amma meya kawota nan? Waye yarabata da kayan jikinta? Ganin batada wanda zebata amsar duka jerin wad'annan tambayoyin data jeroma kanta yasata aza hannuwanta duka biyu aka ta kwala wata irin 'kara.
"Shikenan Hafiz ka cuceni kagama da rayuwata ka 6atamin abinda duk wata mace take ta'kama kuma take tin'kaho dashi a duniya, jin damshi-danshi 'kar'kashinta yasa ta'kara tabbatarma kanta da abinda take zargi "shikenan Hafiz yagama dani ya 6atamin budurcina nashiga ukku tafad'a tare da sakin wani wahalallen kuka.
Ahaka ta maida kayanta ta d'auki jakarta koda ta d'auko wayarta kashe taganta baki d'aya bata tsaya kunnawaba sakata kawai tayi a jaka sannan tanufi 'kofar fita daga gidan.
Cikin sa'a taga gidan bud'e batayi wata-wataba tafito tad'au hanya dukda ba'kin duhun dake akwai ga unguwar tsit babu wani mahalu'ki bakajin motsin kome sai haushin karnuka da kukan tsun-tsaye.
Tafiya take batare datasan inda zataba, harta fito titi, nanma wani titi rami'ka batare datasan inda ze 6ulla da itaba.
Tun tana tafiya da sauran 'karfi-'karfinta har tafara gajiya tafara layi kamar wacce tasha tabugu.
Da-dai bakin wani junction taji an haske mata fuska da wata irin fitila me tsananin haske hannu tasa tana karewa muryar wani namiji taji yana cewa "hey your under arrest kune yan'iska masu shaye-shaye da yawon banza ko.
Kafin tayi wata mgana sunsakata mota sai ofishinsu.
Ganinta office d'in yansanda yasa hankalinta yad'an kwanta dan koba kome tasan ta ku6uta.


  
.
Wani d'an sandane ya kalleta Wanda da Alama shine babbansu yace "miye sunanki?
Jiki na kyarma tabashi amsa "Hussaina,
"Ke yar gidan wacece kike yawo da wannan daren?
"Uhm wlh yalla6ai ba yawo nikeyiba, hasalima ni bansan ya'akayi nafito daga gidaba.
"Shut up, yafad'a cikin d'ga murya, ke muzaki rainama wayo, irinki-irinki mungamu yafi a 'kirga, hadama wad'anda sukafiki iskanci.
"waye zefitodake daga gidanku batare da izininkiba, kada kimanta cikin Halin da aka kamaki na maye koshima bakisan ya'akayi kikayi shaye-shayen ba?
"Wlh yalla6ai bansha komeba na rantsema da Allah,
Tassss  saukar wani lafiyayyen mari taji a kumatunta wanda wannan d'an sandan ya d'auketa dashi, marinda saida ya gigitata saboda tsananin azabar tafin hannun d'an sandan ba 'karamin kato bane.
A 'kufule yace zaki fad'amana ke 'yar'waye kokuwa saina sa6amaki.
Cikin tsananin gigicewa take magana "zanfad'a.... Zanfad'a wlh.
"Oya ina saurarenki d'ansandan yafad'a tare da tsareta da manyan idanunsa masu ban tsoro.
"Ni Yar gidan Alhj Mansir company ce.
"What? 'Dan sandan yafad'a tare da mi'kewa tsaye.
"Karya kike yafad'a tare da nunata da yatsa, duk fad'in garinnan waye besan Alhj Mansir kamfaniba, mutumin kirki me halayya ta kwarai ace ke yarsace kina wannan munanan halaye.
Kuma ba wannan ba iya saninmu Alh Mansir bayada wasu 'ya'ya sai yara biyu yan tagwaye.
"Yan la6ai wlh nice ai mune yan tagwayen Nice Hussainar dan Allah Ku taimakeni Ku maidani gidanmu.
"Sajen Habu, dan sandan yakwalama wani daga cikin yansandan kira.
Da sauri d'ansandan ya iso gabanshi ya 'kame tare da saramashi.
"Maza a fiddo mota yanzu zamuje gidan Alh Mansir kamfani "yes sir yafad'a saida ya'kara saramashi kafin yafita zuwa ma'ajiyar motocin.
Dare ya tsala misalin 'karfe biyu na dare motar yan'sandan tayi parking bakin get din gidansu Hussaina, nocking sukayi lokacin mal bala yana kwance cikin d'an karamin d'akinsa yafito da sandarsa a hannu yana tamabayar "waye? Hussainace tayi magana "nice mal bala, "kece wah? Ya tambaya.
"Nice Hussaina.
"Husssaina da wannan daren subhanallah bud'e 'kofar yayi ahankali yana le'kowa yayi ido hud'u da ita da 'yansanda biyu tare da ita.
Da Sauri Hussaina tashiga gidan 'yansandan suka take mata baya, a harabar gidan suka tsaya "kishiga kiyimana magana da mahaifin naki.
Bata ko sauraresuba tayi cikin gidan da gudu,
Lokacin Daddy,Momy da Hussaina suna Zaune a falo, Momy sai Addu'a take Allah maidomata da 'ya lafiya a Zuciyarta tana cewa "danasan haka zata kasance daban amince da fitartaba.
Hassana kuwa kuka kawai takeyi, yayinda dady Zuciyarsa tagama 'konewa jiyake inama yaga Hussaina yanzu Allah kad'ai yasan irin dukan dazeyimata.
Begama wannan tunaninba yaga anturo 'kofar falon, mikewa yayi da sauri dan ganin me shigo masu gida da wannan tsohon daren, ido Hudu sukayi da Hussaina saurin isa yayi Inda take a zuciye ya dun'kule hannu yakaimata wani mugun naushi sannan yasa 'kafa ya hard'ota.
Fad'uwa tayi 'kasa tana maida numfashi sama-sama ko kukanma yakasa zuwamata saboda tsananin azabar datake ciki.
Dukda haka Daddy beyi 'kasa a gwiwaba gurin ciro cherger wata fitila dake jikin soket yarin'ka tsulamata, sai lokacin tasamu damar fasa ihu tare da d'aukewar numfashinta ta sulale 'kasa sumammiya.
Ganin tafad'i yasa Momy 'karasowa gurin tana kuka "innalillahi Alhj miye haka kake shirin kasheta, kabari mana kaji ta bakinta, "Bazanbariba da bata fitaba da hakan be faruba, kuma ko mutuwa tayi bani nadamar kasheta saboda da inyi mugun gani 'kara narasata baki d'aya.
Hassana kuwa ganin 'yar'uwarta kwance ba Alamar rai tattare da ita yasata rud'ewa tafito zuwa harabar gidan dagudu tana kuka, ganinta yasa 'yansanda sukayi saurin tarbarta a tunaninsu Hussainace saida suka kula da kayan jikin wannan basubane jikin wacce suka kawo yanzu "ke lafiya suka shiga tambayarta, a gigice take nunamasu cikin gidan tana cewa "daddy yakasheta, ya kashemin 'yar'uwa.
"What suka fad'a tare da abkawa cikin gidan baki d'ayansu..
.
A gigice Momy tabi Hassana da kallo tare da 'yan'sandan dake tare da ita.
"Hassana Kina Haukane, mahaifin naki kika kirama 'yan sandan.
Cikin muryar kuka Hassana tace "Wlh momy bani nakirasuba ina fita nagansu a harabar gidannan.
Kallonsu daddy yayi a gadarance yace "waya kawoku gidana, kuma da izinin wah kuka shigo har nan? Yafad'a yana nuna inda suke tsai-tsaye.
"Babban cikinsune yayi magana "Sunana inspeter Sabi'u wale, mune wad'anda suka kawo wannan yarinyar gidannan bayan mun tsinceta cikin halin maye, bayan ta dawo hayyacinta mukayimata 'yan tambayoyi shine tasanar damu kaine mahaifinta shine muka kawota, muna tsaye a haraba munajiran tayimana magana dakai shine mukaga wannna tafito tana fad'in a taimaketa ankashemata 'yar'uwa shine dalilin dayasa muka shigo domin gudanar da aikinmu kamar yanda doka ta tanada.
"Owj naji duka bayaninku nagode, inaso kutafi kawai ni zan iya solving kowace matsala tagidana batare da wani yasamin hannuba nagode da taimakon dakukayima 'yata.
"Muma mungode Alhj Amma dan Allah ari'ka kai zuciya nesa, saboda gudun danasani....
Sai a hanzarta a kaita asibiti suka fad'a suna kallon Hussaina dake kwance bako motsi.
Bayan fitar 'yansandan momy ta kalle daddy Wanda yaketa mazurai da Alama har 'yanzu zuciyarsa bata gama hucewaba,
Hussaina kuwa har 'yanzu tana kwance batasan inda kanta yakeba, momyce tamatso inda take ta tallabo kanta ganin ba alamar rai tattare da ita yasata fashewa da kuka, "Dan Allah Ahj mukaita asibiti kada tamutu.....
"Tamutun mana, yafad'a cikin d'aga murya.
Sannan yayi 'kasa da muryarshi yana cewa "ba inda zan kaita na kwammace inrasata baki d'aya da mugun halin datake Neman jefa kanta.
Tajamani abin fad'i a gari, yana gama fad'in haka yashige d'akinshi ya maido 'kofa yarufe.
Cikin kuka Momy ta kalli Hassana tace kawomani ruwa.
Da sauri Hassana ta d'ebo ruwa cikin cup takawo, amsa Momy tayi tashiga kwarama Hussaina a jiki amma ko motsi batayiba saida ta zubamata a fuska sannan tayi firgigi ta tashi ta 'kan'kame Momy tana fad'in dan Allah kibashi ha'kuri wlh bazan 'karaba.
"Ke Hussaina kitsaya mana, ki nutsu nace ba daddynku bane nice Momy
'Kara 'kan'kameta tayi tana fad'in "wayyo Momy wlh bazan 'karaba kigayamashi na tuba.
"Cikin tsawa Momy tace "dallah ni sakeni tare da tureta daga jikinta, kinsan kina tsoro kikaje yawon har kika kai wannan lokacin baki dawoba, itama tana gama fad'in haka tayi tafiyarta d'akinta tabar Hussaina nan tana kuka itada Hassana.
Hassanace tamatso kusada ita takama Hannunta ta mi'kar da ita tsaye suka nufi d'akinsu.
Koda suka shiga d"akin zaune sukayi jugum-jugum suduka suna sharar kwallah.
Ita Hassana tana kukan halinda 'yansandan nan suka fad'i sunkama Hussaina na maye.
Itakuma Hussaina tana kukan yaudara da Hafiz yayimata har yayi nasarar rabata da budurcinta.
Wasu sabbin hawaye suka zubo a kuncinta.
Hassana ta kalleta tare dasa hannunta ta sharemata hawaye
"Dan Allah 'yar'uwata naro'keki ki gayamin gaskiyar inda kikaje har kikakai wannan lokacin baki dawo gidaba, kuma da gaskene abinda 'yansandan nan suka fad'i na kamaki dasukayi cikin halin maye?
Tana gama fad'in haka ta tsareta da idanu tana jiran jin amsar dazatabata "Hmm ko d'aya Hassana wlh bansha komeba, kuma ni ba inda naje nasan dai naje asibiti kamar yanda na tambayi momy zanje kuma ta amincemin, ana gaf da magariba nabaro asibitin ina tsaye inajiran abin hawa wani me mota yatsaya gabana yaro'keni da inshiga yaragemin hanya nikuma ganin ina sauri yasa na Amince nashiga motar to shinefa daganan ban 'kara sanin abinda yafaruba saida na tsinci kaina yashe a titi, wannan shine gaskiyar abinda yafaru.
Hassana najin haka ta 'kara fashewa da kuka tare da rungume 'yar'uwarta tana fad'in "sister Allah yasa da rabon sauran shan ruwanki a duniya, ya Allah na godema daka kwatomin 'yar'uwata daga hannun muyagun mutane.
Hussaina kuwa dad'i taji har cikin ranta dan ganin Hassana ta yarda da 'karyar data tsaramata, a zuciyartama cewa tayi aiko gobe idan daddy da Momy sun tuhumeni abinda zan fad'amasu kenan, da haka suka kwanta bacci yayi awon gaba dasu kowace da tunani barkatai a zuciyarta.
          *Washe Gari.*
Koda suka tashi bayan sunyi duk abinda yadace na gyaran gida, komawa sukayi d'aki sukayi wanka wasu dogayen riguna suka sanya masu kyan gaske tare da 'yan 'kananan hijab.
Lokacin Momy tagama had'a break fast zuna zaune kan dining tana zubama daddy kasancewar tara hartayi yana sauri yafita office saboda yanada ayyuka da dama a can.
Jerawa sukayi gwanin ban sha'awa suka nufi inda iyayen nasu suke sannan suka zazzuna bayan sun gaishe da iyayen nasu.
Hussaina sai sunne kai takeyi alamar rashin gaskiya.
Bayan sunkammala breakfast ne daddy ya kalli Hussaina tare da d'dd'aure fuska kamar beta6a dariyaba yace "inaso kigayamin gidan ubanwa kikaje jiya.
"Uh...im asibiti naje ganin mamar 'kawata.
"Da izinin wah kika fita?
Kallon Momy tayi suna had'a ido Momy ta watsamata wata muguwar harara, ba shiri ta saddar da kanta 'kasa, tayi shiru.
Dadyne yacigaba da magana "koma waye ya d'aure maki gindi a gidannan kike Neman lalacewa tonidai ba agabana ba, kuma yau basai gobeba zan d'auki mataki kanki dan bazan zauna ina kallonki kijamin surutu a gariba, yana gama fad'in haka ya d'auki jakarsa yafice daga gidan ranshi a matu'kar 6ace.
.
Daddy ne Zaune office d'insa yahad'a hannu bibbiyu ya buga tagumi ba abinda yake tunani sai irin rayuwar da Hussaina take neman jefa kanta,
Mi'kewa yayi tsaye ya maida hannuwansa duka biyu baya tare da fara zagaya office d'in  yafara zancen zuci "yanzu wane mataki yakamata in d'auka dan ganin nayima tufakar hanci bata war-wareba, yau kimanin shekara ishirin ina tarbiyantar da yarannan amma lokaci d'aya suna nema su bijiremin, komawa yayi kan kujera ya zauna tare da maida kanshi sama ba abinda yake tunani sai abinda 'yan sandan dasuka kawo Hussaina gida suka fad'i na cewa sun kamata cikin Halin maye, wato rayuwar dazata jefa kanta kenan, wadda daga haka mutum ze iya aikata kome hatta da kisan kai mashayi na iya aikatawa batare da shakka ko shayin irin hukuncin daze biyo bayaba.
"Assalamu Alikum, da sallama jabeer yashigo office d'in hannunsa d'auke da wasu files-files, jin shiru ba'a amsa sallamar ba yasa ya'kara yin wani sallamar karo na biyu, nanma shiru daddy be amsaba dan yayi nisa cikin tunanin dayake, guri jabeer yasamu ya zauna tare da ajiye files-files d'in kan tebur d'indake gabanshi da d'an 'karfi yanda daddy zeji karar ajiyewar. Hakan kuwa ya maidoshi daga dogon tunanin dayake ya d'ago da kanshi ya kalli jabeer "Ah jabeer badai har kagamaba, "eh nagama gashinan saura wad'annan files d'inne sunada 'yar matsala akwai takardun da babu aciki, yafad'a yana ware wasu files guda biyu gefe.
"Owk to ba Matsala idan na duba zanyima magana sai a gyara, "to kawai yafad'a tare da mi'kewa ze fita daga office d'in harya kai bakin 'kofa daddy yayi kiransa "jabeer, cikin girmamawa jabeer ya amsa tare da dawowa ya zauna,
Saida daddy yayi shiru na kimanin minti biyu kafin ya sauke ajiyar zuciya "Jabeer dama inason magana dakai "to Alhj Allah sa dai lafiya,
"Eh to lafiya lao, kan maganar Aurenka da Hussaina kanasonta kuwa har yanzu?
Cike da jin kunyar tambayar da daddy yayimasa ya amsa da "eh.
.
"To bakada matsala inaso da anjima bayan sallar azahar kataho da magabatanka da shedu koda basu wuce mutum gomaba, nima zan sananar da 'yan'uwana za'a d'aura aurenku kaida ita, bani bukatar kome naka sadaki kawai zaka taho dashi naira dubu hamsin,
Kada kayi mamaki kan wannan abin dana aiwatar akwai dalilin yin hakan Wanda nasan koda kaji dalilin na tabbata bazaka'ki jininaba,
Jabeer dai shiru yayi yana sauraron Alhj cike da mamaki a zuciyarshi yana cewa "wannan shine ikon Allah me tsaida wando koba zariya,  kome wannnagaggawar take nufi Allahu wa'alamu.
Haka ya kauda kowane tunani cikin zuciayrshi yayima daddy godiya sannan yakoma office d'inshi.
Koda ya koma tunanin dai yahanashi sukuni saboda haka rufe nashi office d'in yayi Yakama hanyar gida.
         *Waye Jabeer*
.
Jabeer Suleman shine asalin sunanshi Haifaffen garin katsina, Alh sule tankuri shine mahaifinsa sai mahaifiyarsa Hajiya sa'ada sunada rufin asiri Bakin gwargwado amma ba'a kiransu masu arziki, su biyu iyayensu suka haifa dagashi sai 'kanwarsa Nusaiba wacce akwai tazara sosai tsakaninsu dan ahalin yanzu nusaiba bata wuce shekara sha shidda zuwa sha bakwaiba yayinda jabeer yakeda talatin da d'aya.
Tun yana d'an shekara sha bakwai mahaifinsu yarasu lokacin mahaifiyarsu na d'auke da 'karamin cikin nusaiba bayan rasuwar mahaifinsu da wata bakwai ta haifi nusaiba, haka sukacigaba da rayuwa yau da dad'i gobe babu, yayinda mahaifiyarsu ta tsaya tsayin daka dan ganin jabeer yayi karatu, da kyar da sud'in goshi sukasamu ya kammala karatunshi a F.C.Ekatsina kasancewarshi hazi'ki yasa yasamu sakamako me kyau amma dukda haka samun aiki yayi wahala kusan shekara biyu yana neman aiki besamuba, kwatsam rannan yaji ana Neman ma'aikata a Company Alhj mansir badan yasa ran zesamuba yaje yayi interview cikin ikon Allah kuwa  saiga sunanshi cikin wad'anda aka d'auka aiki, sunyi matu'kar farinciki shida mahaifiyarshi da 'kanwarshi, ranar dazefara zuwa aiki mahaifiyarshi tayimashi nasiha me ratsa jiki akan ri'kon amana da gaskiya, sannan tabishi da addu'ar samun s'a.
Bayan wata shidda dafara aikinsa Alhj mansir yalura da Halin gaskiya da ri'kon amana na jabeer hakan yasa yajawoshi jiki tare da 'karamashi matsayi a office d'in Wanda a halin yanzu shine mataimakin manager company.
*Masu yimin magana ta prvt najina dasukayi shiru kwana biyu Dan Allah kuyi hakuri na rashin ganin reply d'ina naga sa'konku saidai be karantuwa kasancewar nasake download whatapp ne nagode da kulawarku.*
.
Saboda haka cike da tunani barkatai jabeer ya isa gidansu, 'kanwarsa Nusaiba yafara gani zaune falo tana kallon wani Indian film me suna salam namaste, da sauri ta tarbeshi tanamashi sannu da zuwa, bayan ya amsa d'akinsa yanufa ya ajiye jakarsa sannan ya dawo falon, har yanzu dai nusaibar ce ita kadai a falo tambayarta yayi "ina mama?
"Tana bedroom,
"Owk kawai yafad'a tare da nufar 'kofar dazata sadashi da d'akin kwanan mahaifiyar tashi, da sallama yashiga d'akin zaune ya isketa gefen gado hannunta ri'ke da waya da Alama waya tagama, kallonshi tayi bayan yasamu guri ya zauna kan bedsite "a'a jabeer yanaganka kadawo tun yanzu ko mantuwa kayine?
"A'a mama ba mantuwa nayiba wani babban Al'amari ya maidoni Wanda ni kaina ya d'auremin kai,
"Wannan wane Al'amarine tafad'a tare da maida duka hankalinta gareshi,
"Watako yanzu danaje office shine Alhj yakirani yake cemin inje insanarda magabatana kuma inbada kud'in sadaki naira dubu hamsin yau ze d'aura aurenmu da Hussaina.
"Alhamdulillahi mama tafad'a tare da d'aga hannuwanta sama tana godema Allah, kai Amma naji dad'i wannan abu ai abun farincikine dama kullum Addu'ata be wuce inga aurenkaba, Allah sanya Alkhairi yabaku zaman lafiya.
"To amma mama kina ganin babu wata matsala, "wace matsala haba jabeer me kanema karasa inaji kadade da kammala gidanka, kuma Hallacin da Alhj mansir kamfani yayimana ai kobakada kome yace ka auri d'iyarsa ka aureta kazubama sarautar Allah ido dan nasan baze barka hakaba,
"To mama Allah dai yasa haka shine mafi alkahiri,
"Ameen haka nikeso naji kana fad'i.
Daga nan yafita zuwa d'akinshi ya canja kaya sannan yakoma yayima mamarsa sallama tare da sanar da ita zeje ya d'auko mutum ukku dangin babanshi sannan mutum ukku a dangingin ita mamar tashi, fatan Alkhairi tayimashi sannan yafita.
         ⏱. *Misalin 'karfe 3:00pm*
Aka taru a masaalacin dake 'kofar gidan Alhj mansir mutane 'kalilan suka sheda d'aurin auren Jabeer Suleiman tankuri da Amaryarsa Hussaina Mansir kamfani, bisa sadaki dubu hamsin.
Bayan ankammala Alhj mansir yasa aka gabatarma duk mutanen dasuka halarci d'aurin auren abun lasawa take away akayima akaiyma kowane suka wuce suna sanya Albarka.
Bayan ankammala wannan daddy yashiga gida da sallama, su duka falo ya taraddasu zaune Momy ce ta amsa sallamar, Hassana tace "daddy sanu da dawowa "yauwa ya amsa,
Hussaina kuwa daddy nashigowa jikinta yafara kyarma dan wani masifaffen tsoronshi takeyi, cikin muryar tsoro tace "d...dad...daddy sannu da zuwa.
Wani matsiaycin kallo ya watsamata sannan yawuce d'akinsa batare daya amsa sannu d'inda tayimashiba.
Can bayan kimanin minti baiyar yafito ya kalli Hussaina "ki shirya yanzu inaso zan fita dake kuma minti talatin nabaki, kinajina "inaji daddy tafad'a tare da mi'kewa tanufi d'akinsu jiki na kyarma.
Daddy kuwa fita yayi harabar gidan, waya yakira jabeer "ya masu aikinnan sun kammala kuwa,? Ya tambaya
cikin ladabi jabeer yake magana "Eh Alh sunyi kusan minti sha biyar ma da gamawa.
"Sun had'a kome dai yanda yakamata ko?
"Eh sun had'a kome 2 bedroom ne da falo 2 sai kitchen ba abinda ba'a zubaba na bu'kata.
"Owk to anjima ka shiryar tarbar Amaryarka,
Kasa magana jabeer yayi saboda kunyar Alhj yakeji sosai.
"Basu dad'e da kammala wayaba wata had'addiyar mota tayi parking 'kofar gidan sannan wasu maza suka ri'ka jido akwatina suna shigowa dasu saida suka shiga da guda goma manya- manya, sannan sukayima jabeer bayani Alhj mansir yace akawo kayan amaryane.
Mamakine yahana jabeer magana danshi harga Allah yayi niyyar had'a wannan kayan Amma Alhj yahashi had'a kome.
.
Da misalin 'karfe biyar na yamma Hussaina tafito cikin shiri sanye take da riga da zani d'inkin simple atamfar brown colour haka takalmin 'kafarta yayi kala da kayan jikinta sai 'katuwar hijab data sanya, ahankali take takowa hartazo gaban dadynsu cikin ladabi tace "na shirya daddy
"Owk muje ko, yafad'a yana nunamata 'Kofa.
Ganin tana tafiya Ahankali kamar kazar da Kwai yafashemawa a ciki yasa daddy yayi gaba ya zauna a mota yana jiran fitowarta.
Fanin fitarsa yaba Hussaina damar yin magana "Momy wai ina zamu?
Momy tace "kin tambayi kaza hanyar rafi.....
Ni kaina da kike gani bansan meke wakanaba nidai kawai abinda nasani naga tunda Alhj yatashi yau yaketa hidima ko zama yaci abinci beyiba.
Hassana dake zaune tace Allah dai yasa Alkhairi ne, ni kaina ina mamakin yanda daddy yace Hussaina ta shirya su fita batare daniba, Alhalin nasan ko'ina tare muke zuwa.
Momy tace "to wannan abu dai Allah kad'ai yasani, kiyi sauri kibishi kada kuma yaga kin 6atamai lokaci.
Juyawa tayi tafita daga falon batare data 'karayin wata maganaba.
A mota ta iske daddy zaune yana jiran fitowarta, gidan gaba tanufa da niyyar tashiga harta kama murfin motar zata bud'e daddy ya watsamata wani matsiyacin kallo "koma baya.
Jiki na 'kyarma takoma ta bud'e bayan motar tashige, sannan daddy yatayar da motar Malam bala yabud'emasu get yana d'aga masu hannu suka d'au hanya sannan yamaida get d'in yarufe Yakoma kan d'an bencinsa ya zauna yana cewa "gaskiya Alhj ya iya maganin d'an iska, wato yarinyar nan wlh da Alhj beyi saurin Aurar da itaba saita d'aukomar abin kunya. Kodayake bansaniba shin itace koba itabace oho nikam bani ganesu, radio shi yajawo ya kunna yacigaba da sauraron abinshi.
Daddy kuwa ba inda ya zarce da Hussaina sai unguwar dutsin safe malali Quarter's inda nan tangamemen gidan jabeer yake, bakin get yayi horn da sauri megadi ya bud'e mashi ciki yashiga ya ajiye motarshi inda aka tanada dan ajiye motocin, fitowa yayi sannan ya umarci Hussaina data fito itama, ba musu tafito tunda suka shigo take yaba kyan gidan, saikuma yanzu ta'kara ganinshi sosai tsarin gidan ya burgeta, a zuciyarta tace "nan kuma ko gidan waye? Amma ko gidan abokanin daddy ne bamu ta6a zuwaba, kuma sabodame daddy yaza6i yazo dani ni kad'ai banda Hassana Alhalin duk inda zamu tare muke tafiya da ita......
Daddyne ya tsinkemata tunanin datake ta hanyar cewa "shigo mana.
Ba musu tabi bayanshi wata 'Kofa yabud'e wacce tasadasu da babban falon gidan me d'auke da maka-makan kujeru irinna zamani a tsakiyar falon gefe kuma kan wani step kujerun dining ne da 'katon table d'insu, daga gaba kuma inda suke facing wata 'katuwar TV ce plasma ma'kale jikin bangon sai manyan speaker's (Home theaters) gefensu kuma wasu kyawawan flower's ne masu d'aukar ido, duka kayan falon sun kasance purple colour hatta da pentin d'akin kalarsa kenan,
Daddy yace "to Hussaina wannan gidan da kike gani bana kowa bane face gidan mijinki......
Dammmm gabanta yayi wani mummunan fad'uwa da sauri tad'ago ta kalli daddy ganin ba wasa tattare dashi yasa tamaida kanta 'kasa gabanta nacigaba da fad'uwa.
Daddy yacigaba da magana "naza6i na aurar dake dakijawomin abin kunya, saboda nan shine gidan aurenki, ki zauna kibi mijinki kiyi mashi biyayya Aljannarki tana 'kar-kashin tafin 'kafarsa idan kinbishi kisamu idan kuma kin baud'e wannan kuma Allah yasan hukuncin daya tanadar maki.
Saboda haka iname umartarki daki zama me biyayya a gareni ni mahaifinki dakuma mijinki ki zauna lafiya.
Nan daddy yayimata nasiha me ratsa jiki kafin yayimata bankwana ya ajiyemata bandir d'in kud'i yan dubu yace "saboda idan kina bu'katar wani abu bance ki matsama mijinkiba,
Bayan tafiyar daddy kasa tashi tayi daga inda yabarta, tunani take "wannan wane irin aurene daddy yayimin kamar auren wasa, to wai yaushema aka d'aura auren? Kuma waye mijin? Ina daddy yasamu mijin daya yarda da aure cikin kwana d'aya tak? Haka tagama jerama kanta tambayoyi amma batada amsarsu kuma batada Wanda ze amsa mata, hakan yasa tafashe da wani irin kuka, tana cewa "shikenan yanzu nasan daddy baya 'kaunata menayi....menayi daza'a yankemin wannan hukuncin.
.
Kuka take iya 'karfinta babu me rarrashinta sai da tayi me isarta sannan ta tashi falo na biyu tashiga wanda shima yaji set d'in kujeru da kayan kallo amma sai dai shi bekai na farkon haduwaba shikuma kome nacikinsa green colour ne, tsayawa tayi ta'karemashi kallo sannan tanufi wani d'akin nan kuma bedroom ne wanda aka zubama kaya yan Dubai ba 'karamin kyau d'akin yayiba, fitowa tayi daga nan tanufi gudan d'akin ahanakali tatura 'kofar tashiga nan ma karo tayi da wani 'kawataccen d'akin kwana shikuma duka kayan yan Nigeria ne aka zuba amma harma sunso Sufi na Dubai d'in kyau.
Bayan tabi ko'ina na gidan ta'karemar kallo dawowa tayi a bedroom ta zauna tsakiyar gadon tare da rufe fuskarta da hijab d'inta, take tunanin Hafiz ya dirar mata a zuciya, wani irin kuka tafashe dashi a zuciyarta tana cewa "yanzu shikenan anrabani da Hafiz mutumin danafi so nafi 'kauna akan kowane namiji, bazan iya zaman aure da kowane namiji ba bayan Hafiz yazanyi da rayuwata, haka tacigaba da kuka tana zancen zuci.
"Yanzu ni waye wanda daddy yaza6amin anya zan iya zama dashi, ita ko kad'an bata kawoma ranta jabeer ne wanda aka d'aura mata auren dashiba.
Zaune take tabuga uban tagumi hannu bibbiyu ba abinda ke mata yawo a kwalwa sai kalar salon soyayyar da Hafiz ke nunamata, yanzu shikenan anrabamu baze 'kara shayar dani zumar 'kaunarsaba.
Mi'kewa tayi tsaye kamar wacce aka tsikara "baze yiyuba tafad'a a zahiri bazan iya rabuwa bada Hafiz ba ko ana ha maza ha mata, Hafiz shi kad'aine namijin dazan aura in kasance cikin farin ciki, ko waye wannan yayi gan-ganci daya yarda da aurena, tabbass zesan abinda ya auro ya kawo gidanshi.
********
Momy da Hassana kuwa tun bayan fitar daddy da Hussaina suketa sa'ke-sa'ke da kwancewa sun rasa ina daddy zashi da Hussaina batare da yar'uwartaba Alhalin shine yasaba masu da duk inda zasu tare suke tafiya.
Da sallama ya shigo falon suduka binshi sukayi da ido ganin yadawo batare da Hussaina ba,
Momy ce tayi 'karfin halin tambayarsa "Alhj ina Hussaina take naga ka dawo kai d'aya kuma bayan tare kuka fita.
"Tana gidan mijinta, yabata amsa a takaice sannan yawuce d'akinsa, binshi tayi daga baya zuciyarta cike da mamaki.
Hassana dake zaune tanajin abinda daddy yafad'a itama tashi tayi tanufi d'akinsu tana cewa "innalillahi wa'innalaihirraji'un "Gidan miji.... tafad'a cike da mamaki, yaushe aka  d'aura auren sister bamu saniba dan gashi alamu sun nuna itama momy batasan da zancen ba,
"Ya salam tafad'a tare da dafe kanta da hannu biyu dataji yana saramata kamar ze rabe biyu, fad'awa tayi kan gado tana zubar da hawaye.
: Cike da 6acin rai momy take magana "haba Alhj ban fahimce inda zancenka yadosaba.
Juyowa daddy yayi ya kalleta tare da yin wani murmushi, sannan yace "baki bu'katar in maimaita maki abunda nafad'a d'azu saboda inada tabbacin kinji kome nafad'a.
"Lalai Alhj yanzu ka tabbatar min da baka 'kaunar Hussaina akan me zakayimata irin wannan hukuncin, aure cikin kwana biyu kamar auren d'iyar kara, haba Alhj kuma amatsayina na mahaifiyarta yaci ace nasan da maganar amma bansaniba kuma banida labari kawai saika tafi da yarinya kace wai wani ka kaita gidan miji, gaskiya ni ban yardaba kawai kafad'amin inda d'iyata take inje in d'aukota idan kai baka sonta ni ina sonta, duk wannan maganganun da momy keyi tanayinsune cikin 6acin rai da d'aga murya.
"Dakata Maryam, daddy yafad'a cikin d'ga murya "wannan auren na d'aurashi kuma yariga ya d'auru ba wanda ya isa ya war-wareshi, ince idan yarinyar nan ta jawo mana abin kunya zagin daza'ayimin baza'ayimaki rabinshiba, saboda haka nariga na yanke hukunci idan kinji hukuncin danayimaki bemakiba zaki iya kama gabanki hanya a bud'e take yara kuma nawane inada iko akansu.
Tunda daddy yafara fad'a momy ke kallonsa cike da mamaki a zuciyarta tace "lallai Alhj da gaske yake kuma ba wasa tattare dashi dole nima inbi ahankali.
Cikin langa6ar da kai momy tamatso kusa da daddy ta dur'kusa gabansa "Haba Alhj meyakai na 6acin rai haka, indai kan wannan maganar ne inshaAllah kome ya wuce Allah sa haka shine mafi Alkhairi a rayuwar Hussaina, itakuma yar'uwarta Allah kawomata miji na gari.
"Ameen daddy ya amsa tare da shigewa toilet ya watsa ruwa sannan ya d'auro Al'walar magrib dan lokacin sallar yayi.
Itama Momy d'akinta tanufa ta d'aura Al'wala ta kabbara sallah bayan tagama ta dad'e kan abin sallar tana kwararo addu'a ga yaranta.
.
Zaune take cikin d'akin tarasa mekemata dad'i a duniya, wayarta ta Dauko sunan zuby ta lalubo sannan ta danna kira, bugu d'aya zuby ta d'auka.
"Hellow 'kawata kin 6oye kwana biyu.
"Hmm kedai bari kawai zuby idan ana sallah ba'a magana.
"Banganeba 'kawata wani abune yafaru dake?
"Abubuwa da dama sun faru dan ahalin yanzu wayar nan damuke dake ina gidana.
Saurin tashi zaune zuby tayi daga kwancen datake "bangane gidankiba 'kawata, gidanki ko gidanku?
"Hmm gidana dai dan daddy yamin aure kuma yau natare.
"Aure kuma Hussaina, to waye angon zuby ta tambaya gabanta na dukan ukku-ukku kada Hussaina tacemata Hafiz ta aura, idan ko haka ta kasance da ba abinda ze hana abkuwar 'karamin ya'ki tsakaninta da Hussainar.
Hussainar ce tadawo da ita daga duniyar tunanin data lula,
"Wlh nima har yanzu bansan ko waye mijin ba, amma inaso kizo gobe,
"To shikenan 'kawata zanzo amma wane unguwane?
Nan Hussaina tabata full address sannan sukayi sallama kowanensu ya tsinke wayar.
Zuby kuwa tashiga tsananin rud'ani, tashi tayi tsaye tafara kai komo cikin d'akin "tabbass idan har tunanina ya tabbata Hussaina Hafiz ta aura tofa sainayi yanda nayi narabasu koda kuwa ta Hanyar salwantar da rayuwartane, inason Hafiz ina 'kaunarsa bazan juri ganinshi tare da wata maceba bayan ni, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta tasa hannu ta goge,sannan tanufi lokar dake jikin gadon d'akin tasa hannu ta fiddo kwalbar kodin ta tuttule a bakinta ta shanye sannan tafad'a gado tana mayarda numfashi kafin bacci yayi awon gaba da ita.
: Hussaina kuwa cigaba tayi da bin d'akin da kallo kad'an-kad'an takai dubanta ga 'Kofa tana jiran ganin shigowar angon nata.
Ringing d'in wayarta tajiyo da sauri tasa Hannu ta d'auka dan tana tunanin zuby ce takirata kozata gayamata wani abu amma sai ganin sunan Hafiz tayi 6aro-6aro yana yawo kan screen d'in Wayar, sai da gabanta yayi mummunan fad'uwa bin wayar tayi da kallo har kiran ya tsinke sake kira akayi karo na biyu nanma batayi gigin d'aukaba dan ganin kiransa kayar mata da gaba yakeyi, duk dahaka beha'kuraba ya'kara kira karo na ukku hannunta na rawa ta daure ta danna OK tare da karawa a kunnenta batayi maganaba sai shi yafara magana.
"Hellow babyna kina lafiya?
Shiru tayi duk illahirin jikinta kyarma yake dan jin muryar Hafiz kad'ai jefata yake cikin wani yanayi me wuyar fassarawa.
Magana ya'karayi karo na biyu "hello babyna ko bakyajinane.
Sannan ta daure murya can 'kasa-'kasa tace "ina jinka.
"Amma kuma kikamin shiru, kinsan kuwa yanda nadamu dake, kinsan halin dana fad'a na rashinki danayi kwana biyu......
Cikin d'aga murya da masifa Hussaina tafara magana "dakata Hafiz bakada wani dad'in baki dazakayimin bayan ka cuceni ka cuci rayuwata karabani da abinda duk wata mace take ta'kama da tin'kaho dashi a duniya.
Amma bakome ba laifinka bane laifinane dana d'auki yardata nami'ka maka d'ari bisa d'ari, gashi yanzu ina gidan mijina banida wata daraja da 'kimar daze kalleni da ita.
Dakata Hussaina nifa bangane inda maganganunki suka dosaba,
"Tunda ka yaudareni ka kaini gidanka da sunan zan gaisheda hajiyarka ashe da wata manufar ka kaini danka ketamin haddi.......
Jitayi ana doka sallama daga falo hakan yasa tayi saurin kashe wayar baki d'aya ta turata 'kar'kashin filo, sannan tayi saurin janyo hijab d'inta tarufe fuskarta dashi.
Jitayi annufo d'akin datake hakan yasa fad'uwar gabanta ya yawaita,
"Assalamu Alaikum warahamatullah, yafad'a tare da 'karasowa cikin d'akin ya zauna bakin gado.
Koda jin muryar kunnenta ya tabbatar mata da tasan me wannan muryar jin 'kamshin turarensa yadaki hancinta ya'kara tabbatarmata datasan kowaye,
Saurin bud'e lullu6in datayima fuskarta tayi dan tabbatarma idanunta abinda take tunani.
Tana bud'ewa kuwa sukayi ido hud'u da jabeer, a firgice ta nunashi da hannunta tana fad'in "Jabeer dama Kaine mutumin dayaimin yankan 'kauna, karabani da Wanda nakeso, kasa daddy yayimin aure irinnan d'iyar wasan yara aure cikin kwana biyu, bayan nadad'e da sanar maka inada wanda nakeso bakaiba, to ina me tabbatarma saikayi danasanin aurena dakayi, idan kayine dan farincikin rayuwarka nikuma ka ba'kantamin rayuwa to wallahi kaima ze zama ba'kin ciki a gareka.
"Haba hussaina banyi haka dan in ba'kantamikiba, kuma da banisonki bazan aurekiba inaso ki d'auki wannan a matsayin 'kaddarace agaremu kuma muyi fatan Allah sa tazamar mana Alkhairi a rayuwarmu.
Wani irin kuka tafashe dashi dan tunawa datayi batadafa wata daraja da 'kimar da sauran mata keda ita barantana tayima jabeer wula'kancin dataga dama abinda yafi kawai tabada kai bori ya hau, sannan tayi biyayya ta zauna lafiya ko Allah zesa yarufamata asiri, goge hawayenta tayi tace "to Allah shigemana gaba kuma Allah tabbatar mana da Alkhairi cikin wannan zama namu.
Jabeer ya Amsa da Ameen har cikin ranshi yaji dad'i da kuma mamakin saukowar Hussaina haka
.
Daga nan ya umarceta dasu gabatar da sallah su godema Allah kamar yanda addini ya tanada, ba musu tanufi toilet ta d'auro Alwala sannan shima ya Shiga ya d'auro tasa Alwalar suka gabatar da sallar nafila, bayan sun kammala ya dad'e yana kwararo masu addu'oi kafin su shafa.
Sannan ya d'auko ledar daya shigo da ita ya ajiye tsakiyar carpet d'in dake malale a bedroom d'in, da kanshi yanufi kitchen ya d'auko masu palate da cup, gasashiyar kazace guda ukku yabaje kan tire tare da fresh milk da lemun 5alive.
Juyowa yayi ya kalli Hussaina wacce take takure duk tabi ta raina gaskiyarta binshi kawai take da kallo, a zuciyarta kuwa tunanin abinda ze biyo baya takeyi bayan Jabeer ya kusanceta yajita ba cikakkiyar budurwaba, wasu guntayen hawaye suka zubo a idonta tayi saurin sa bayan hannunta ta goge batare da jebeer d'in ya luraba.
Jabeer d'inne ya maidota daga dogon tunanin datake ta hanyar matsowa kusa da ita "bismillah gimbiya saurautar mata nasan dai kinajin yunwa yakamata ace kinci wani abu kafin ki kwanta.
Kad'a kai tayi kamar 'kadangaruwa "a'a ni banajin yunwa.
"Ban yardaba gaskiya da ganin wannan cikin ya dad'e rabonsa da abinci, yafad'a tare dakai hannunsa kan cikinta.
Ture hannun nashi tayi "nifa banajin yunwa,
"To naji bakijin yunwa amma ban yarda ki 'ki cin komeba, kawai dai inajin sarautar takice ta motsa, uwar gida sarautar mata, yafad'a cikin tsokana.
Hannu yasa ya yago naman yanufi bakinta dashi da niyyar yabata tayi saurin kauda kanta,
"Haba Hussaina bekamata ace kin'ki kar6ar komeba idan kikayi haka nikam bazanji dad'iba, dan Allah badanniba ki taimakamin ki kar6a.
A hankali ta juyo yafara bata abaki saida ya tabbatar data 'koshi sannan yazubo fresh milk nanma da kyar ta shanye cup d'aya.
Shima sama-sama yaci naman kajin sannan yakora da lemu, d'akinsa yanufa yacire kayan jikinsa yafad'a toilet yashe'ka wanka.
Hussaina kuwa tana ganin fitarshi tanufi wadrope tana bud'ewa taganta ma'kare da kaya, batayi mamakiba dan daddy yafad'amata babu abinda ba'a tanadar mata a gidan ba.
Wata fitinanniyar rigar bacci ta d'auko wacce zamu iya kira akwai ya babu, ta sanya sannan tabi duk illahirin jikinta ta feshi da sassayan turare, sannan tabi lafiyar gado tayi kwanciyarta batare data rage Hasken d'akinba kuma tayi hakane dan tanajin tsoro ganitake kamar idan ta kwanta a duhu-duhu wani abu ze sameta tasaba kullum tanajin motsin Hassana kusa da ita, yau gashi zatayi kwanan kad'aici dan taga Alamar Jabeer banan ze kwanaba tunda gashi yatafi gudan d'akin yabarta, da wannan tunanin bacci 6arowa yayi awon gaba da ita.
Sanye yake da best da short niker, farare 'kal jikinshi sai tashin 'kamshin turarensa yake me suna *story of love* yanufi d'akin.
Ganin d'akin da haske ya tabbatar mai da Hussaina batayi bacciba, da sallama yashiga jin bata amsaba yasashi dubawa kobata d'akinne, can ya hangota kwance kan lafiyayyen gadonta tanata sharar bacci hankalinta kwance, karsa shiga yayi cikin d'akin sannan ya maida 'kofar yarufe, kafin ya isa gareta ya'karemata kallo, yanda rigar baccin jikinta take sharara ba abinda be bayyanaba na surar jikinta, take yaji wata matsananciyar sha'awarta ta kamashi rage Hasken d'akin yayi tare da kunna masu fitila me sau'kin haske, ya haye gadon ya rungumota gaba d'aya jikinsa.A hankali yafara shafa lallausar fatar jikinta, yayinda ya tsinci kanshi cikin wani irin farin ciki marar misaltuwa.
Can cikin bacci Hussaina taji Alamar mutum kusa da ita ahankali ta bud'e idonta, tozali tayi da jabeer Wanda ya lula cikin duniyar 'kaunarta yana aikamata da sa'konni soyayya masu wuyar fassarawa, wani irin dad'i taji cikin ranta wanda ita kanta batasan dalilin hakan ba, 'kara shigewa tayi jikinsa tare da sakar mashi duk wani sashe na jikinta, shikuma yacigaba da sarrafata da kwarewarsa da gogewarsa, Hussaina kuwa mamakin jabeer ne yacikamata zuciya "wai dama haka jabeer ya iya soyayya ya iya salo daban-daban amma lokacin kafin suyi aure yake nunamata shi ustaz ne kullum beda magana sai wa'azi da nasiha.
Da wannan tunanin kawai ta ida mallakamashi kanta, a daren sukasha amarcinsu ranar jabeer yasan Hussaina mace, kuma ba 'karamin farin ciki yayiba na yanda ya sameta cikakkiyar budurwa.

Hussaina kuwa banda kuka babu abinda takeyi saboda zafi da rad'ad'in datakeji, jabeer kuwa rarrashinta yari'kayi, dan wani sabon shau'kin sontane ya'kara kamashi.

Tashi yayi yanufi toilet yayi wanka ya tsarkake jikinsa, sannan yahad'a wani ruwa me d'umi ya dawo ya d'auki Hussaina yanufi toilet d'in da ita, zaunar da ita yayi cikin ruwan dan tad'an gasa jikinta, sannan yafito ya gyara gadon tare da canja masu bedsheets, bayan yagama yakoma toilet d'in lokacin Hussaina tagama wankan zuwa yayi da niyyar ya d'aukota amma saita kauce ta ma'kale kafad'a bataso, be matsamataba tunda ta nuna bataso hannunta yakama suka fito tana taku ahankali, kan gado ya taimaka mata ta kwanta sannan ya 'kuremata a.c d'akin kasancewar lokacin ana zafi.

Komawa yayi toilet ya d'auro wata sabuwar Al'wala sannan yazo ya kabbara sallah, nafila yari'ka jerowa saida yafarajin bacci sannan ya sallame ya dad'e yana kwararo addu'a kafin ya shafa, sannan Yakoma kan gado ya kwanta ya rungome matarshi yanajin wani sabon sonta da 'kaunarta na 'kara kamashi, a zuciyarshi yace "Allah kenan da yanzu bani bane angon dazesha amarci wannan daren yanda Hussaina tanuna tsana da tsangwama agareni batare danayimata wani laifiba, dayake Allah ya nufa nine mijinta yau gata jikina kwance numfashina na gauraya da nata, Allah nagodema....

Da wannan tunanin bacci 6arawo yayi awon gaba dashi.
_{Nikuma Zee danike biye dasu ina kwaso maku labari nace asuba ta gari, *Oya overy body shoki lol*}_

         *Washe Gari*
Da misalin 'karfe tara na safiya me napep ya sauke nusaiba 'kofar gidan Ya Jabeer kamar yanda take kiran sunanshi, Hannunta d'auke da wani babban kwando da kuloli masu kyau a ciki, nocking tayi me gadi yace "waye
Nusaiba tace nice "to ina zuwa da Sauri yanufi get d'in yabud'emata 'karamar 'kofa tashige.

A falo ta zauna tanata doka sallama, jabeer ne yafito jikinsa sanye da jallabiya milk colour me gajeren hannu "A Nusaiba kece da wannan safiyar, "nice yaya ina kwana
"Lafiya lao.
"Gashi Mama tace akawomaku, kai amma mungode.

"Yaya ina auntyn tamu mu gaisa sauri nake zankoma na tsaida me napep, tana ciki bari na gayama, yafad'a tare da nufar d'akin baccin nasu.

Kwance ya isketa idanunta bud'e ba bacci takeba, "kizo ga Nusaiba nan tazo Mama ta aikota zaku gaisa wucewa zatayi,

Wani yamutsa fuska tayi "haba tunda safe kuma, nikam ba yanzu zan fitaba kawai kacemata tabari mun gaisa wani lokacin idan tazo.
"Sabodame bazaku gaisa yanzuba tunda tazo,
"Ni kawai fitarce yanzu banyi niyyaba kozan fitane saboda 'kanwarka.
"A'a amma kinsan ba dad'i mutum yazo har inda kake kuma ya bu'kaci ku gaisa kice a'a.

Cikin fushi tatashi zaune tare da d'agamashi Hannu "dakata Malam nifa banison abinda kakemin 'kanwatace dazakace dole saina fita mungaisa da ita da wannan safiyar, kaida take 'kanwarka kaje kun gaisa to kace nace ta gaida gida, banison yawan magana tana kaiwa nan a zancenta takoma ta kwanta.

,
Duk abinda suke fada kan kunne nusaiba saboda yanda Hussaina take d'aga murya, Haka jabeer yafito jiki a sanyaye cike da fara'a nusaiba ta kalleshi "Halan aunty tamu bata tashiba, idan tatashi a gaishemin da ita nizan wuce,
"Wani busasshen murmushi jabeer yayi dan yasan Nusaibar tajiyosu kawai dai basarwa tayi, "to shikenan Ki gaida Mama ga wannan ki sallami me napep d'in ya mi'kamata d'ari biyar guda tasa Hannu biyu ta kar6a tare dayin godiya sannan tafice a gidan.

Da misalin 'karfe goma jabeer yafito cikin shiri, kafad'arsa rataye da jakar laptop, d'akin Husaina yanufa dan ganin kota tashi, wani babban abin takaici shine yanda yanda ya isketa kwance har yanzu kayan baccine jikinta, batada niyyar tashi.

'Karasawa yayi gab da ita sannan yad'an bubbuga gadon, juyowa tayi ta kalleshi "lafiya Malam,? Ta tambaya cike da rainin wayo.
"Lafiya lao na shirayane zan fita, yakamata ace kintashi ga break fast can Mama ta kawomamu kiyi serving d'ina sauri nake zan fita office muna ayyuka dayawa gashi harnayi latti yafad'a yana kallon had'addiyar agogon dake d'aure jikin hannunsa.

'Kara gyara kwanciyarta tayi tare da juyamai baya, "kaga Malam idan zakaje kayi break d'inka kawai kaje kayi dan naga Alamar yunwa kakeji ni ba yanzu zantashiba dan bansaba kalaci da wuriba.

"Yanzune da wuri kiduba kiga yanda rana ta fito...
"Kaga malam kaje kawai dan Allah banison hayaniya, tafad'a tare da jawo wayarta wacce takashe tun jiya ta kunna.
Message's ne suka ri'ka rige-rigen shigowa, wanda yawancinsu duk jiyan akayoamatasu sakamakon jin wayarta kulle.

Jabeer kuwa falo yakoma ya bud'e kulolin wacce d'aya take d'auke da wainar shinkafa sai miyar alayyahu, sannan gudar kular dake d'auke da farfesun hanta, sai plask shikuma d'auke da kunun gyad'a Wanda yaji tsan-tsar madara yayi fari kal.

Zubawa jabeer yayi a gaggauce yaci sannan yazuba kunun gyad'ar duk da son dayakemashi wanda yasha befi Rabin cup ba saboda saurin dayake.

Jakarsa ya d'auka sannan yafice, Har yanzu Hussaina na d'aki tanajin lokacin dame gadi yabudemar get yafice sannan itakuma tafito.

Kulolin data gani ajiye tashiga bud'ewa, take taji tsohuwar yunwar data tara ta tasomata da sauri takoma d'aki tasheka wanka, tazo gaban mirror ta murza lotion da powder sai man le6e tasama lallausan le6enta sannan tanufi wadrope ta d'auko kaya riga da siket na atamfa tasaka, fitowa tayi tazuba wainar tacika cikinta sannan tabi da lafiyayyaen kunun gyad'a Wanda dad'insa saida ya ratsata har tsakiyar kanta, tana gamawa tami'ke takoma kan three seater ta kishingid'a batare data kauda kayan dataci abincin ba.

Wayarta tajawo tafara karanta text messages farko massage d'in Hafiz tafara karo dashi, inda yake cewa.
_Haba babyna banyi tunanin akwai abinda zesa kirabu daniba, duk irin so da 'kaunar danike nunamaki kin d'aukesu 'karya kinje kin auri wani bayan kinriga kin dasamin bishiyar 'kaunarki a zuciyata, kin yaudareni Kin cuceni kuma kinci amanata, wama yasani ko inmutu saboda 'kaunarki, amma kisani idan har haka ta kasance Allah baze barkiba. Kihuta lafiya *Hafiz*_

Tana gama karantawa wasu zafafan hawaye suka zubo a idanunta, tasa hannu ta goge, tana cewa "ina sonka Hafiz ina 'kaunarka banta6a jin son wani namijiba a duniya bayan kai, ko yanzu ina tare dakai bazan gujekaba komin rintsi.

Sunanshi ta lalubo sannan ta danna kira bugu d'aya ya d'auka nan tashiga bashi ha'kuri "dan Allah kayi ha'kuri Hafiz wallahi ba yaudararka nayiba, har yanzu sonka yana cikin zuciyata ba abinda ya canja, kaine kaja Hafiz da farko na d'auka karabani da budurcina saida naba wani namiji kaina sannan na tabbatar dabahaka bane, kaja na mallamakama wani namiji kaina bakaiba.

"Kada ki damu babyna ni inasonki haka kuma zan iya kasancewa dake akowane hali kike, kedai kawai kicigaba da 'kaunata kamar yanda nike 'kaunarki.

"Kada kadamu babu wani namiji a zuciyata sai kai, tafad'a tana goge hawayen dake fuskarta, to shikenan yimin murmushinnan naki me sanyayamin zuciya, wani 'kawataccen murmushi tasaki kamar Hafiz d'in yana gabanta, wani lafiyayyen kiss yasakarmata ta wayar Wanda yaratsa dukkan sassan jikinta, taji inama kawai taganta tare da Hafiz yanzu ya shayar da ita zumar 'kaunarsa.
.
Da misalin 'karfe hud'u na yamma me napep ya sauke Zuby 'kofar gidan Hussaina, megadi tafara yima magana sannan ya bata izinin shigowa bayan yanemo hakan daga gurin matar gidan, da dallama zuby tashigo 'kawataccen falon, mutuwar tsaye tayi saboda yanda falon yayi amasifar burgeta, batayi tunanin zata tarar da 'kawarta cikin wannan daular ba tunda taga Auren ba cikin shiri akayishiba.

Hussaina ta katsemata tunaninta ta hanyar yimata "welcome my friend, tafad'a tare da kamo hannu Zuby ta xaunar da ita kan d'aya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun dake zagaye da makeken falon.

Bayan sun gaisa Hussaina ta gabatarma da zuby da ruwa da lemu, nan zuby ta zuba lemun tanasha amma duk hankalinta nakan yanda aka kashe dukiya aka 'kawatama Hussaina d'akinta, nan take wani 'kululun ba'kin ciki yazo ya tsayama Zuby a wuya, a zuciyarta tace "tabbas dole inyi yanda nayi na raba Hussaina da gidannan, idan bansamu Hafiz ya aureniba, zan dawoma jabeer, 'karama jabeer d'in ai dan yafi Hafiz kamun kai da kamala, nasan idan har nayi nasarar rabashi da Hussaina nikuma zanyi yanda nayi ya aureni inyi zamana cikin jindad'i da farinciki nima inhuta da l'ikema yayan masu kud'i  danikeyi, muddin idan nasamu nasarar auren jabeer zan mallakeshi kota halin 'ka'ka sannan dukiyarsa sai yanda nayi da ita nima lokacin zan faso gari 'ya'yan talakawa zasu ri'ka likemin kamar yanda a yanzu nake li'kema wasu........
Wani shu'umin murmushi tayi dan lokacin har hangota takeyi zaune a wannan babban falon a matsayin matar gidan tad'ora kafa d'aya kan d'aya ga yan'aiki durkushe gabanta tana bada owk.... _lol_

Zuby ta lula duniyar tunani Hussaina nata faman yimata magana amma ko Alama batajitaba, saida Hussainar ta ta6ota "lafiya 'kawata Tunanin me kikeyi...

Saurin dawowa zuby tayi daga duniyar tunanin data Lula, "a'a ba kome kawai ina tunanin halin rayuwa, yau gidanmu tashi mukayi bamu d'ora tukunyaba ga babanmu bayada lafiya, tana kaiwa nan ta fashe da kuka.

Wani irin tsananin tausayinta Yakama Hussaina dan tasan abinda Zuby tafad'a ba 'karya ko yanayin gidan dasuke zaune kad'ai ya Isa ka gane suna cikin Halin rayuwa.
"Kada kudamu inshaAllah idan jabeer yadawo zansa ya taimaka maku.

Zuby ta'kara fashewa da wani kukan munafunci kamar da gaske "nagode 'kawata Allah saka da Alkhairi, "ba kome 'kawata kada kidamu ai munzama d'aya tafad'a tana bubbuga kafad'ar zuby alamar lallashi.

Suna cikin haka suka jiyo sallamar suduka suka maida hankalinsu ga 'kofar tare da amsa sallamar, Jabeer ne yashigo da sallama, ko kallon inda yake Hussaina batayiba saima kauda kanta datayi gefe tana danne-danne a wayarta.

: Da sauri Zuby ta sauka daga kan kujera ta dur'kusa har 'kasa ta gaida Jabeer da Fara'a ya amsa "Zuby ce yau a gidanmu kice kinzo gun mutuniyar taki kenan, "eh wlh munzo shan manshanun amarya tunda haka akayi Auren ba gayya sai dai kawai mukaji a sama, murmushi jabeer yayi yace "wlh kuwa kinsan Al'amarin ubangiji muma yanda abin yazomaku haka yazo mana, mudai fatanmu atayamu addu'a.
"To Allah sanya Alkhairinsa yakuma bada zamanan lafiya, "Ameen ya amsa sannan ya wuce bedroom.

Saida Zuby ta tabbatar da shigewarsa sannan ta kalli Hussaina "kawata amma yanaga kamar baki murna da dawowar angon naki naga ko irin tarbar nan ta sabbin ango da amarya bakiyimashiba.
Yamutsa fuska Hussaina tayi "ai wannan tarbar sai idan akwai soyayya tsakani akeyinta, nifa yanzu babu soyayyar jabeer ko d'igo a cikin zuciyata, dan wallahi daze sakeni danafi kowa farinciki.

Saida Zuby tad'an razana dajin maganar Hussaina a zuciyarta tace "nifa ta fad'i gasashshiya dan naga Alamar raba Wannan shashar da Jabeer abune mai sau'ki, amma a zahiri sai tadafa kafad'ar Hussaina cikin tsananin nuna damuwa tace "Amma Hussaina sabodame kike son rabuwa da jabeer, yanzu kina tunanin akwai macen dazata samu gwarzon namiji kamar jabeer tayi fatan rabuwa dashi? Amma bansaniba wai hausawa sunce duk wanda ta 'kone rumbunsa yasan inda toka ke tsada..... Bansaniba ko kinada wanda yafishine.

"Yauwa 'kawata anzo wajen, inada Wanda yafi jabeer nesa bakusaba,
"Waye wannan? Zuby ta tambaya.
"hafiz mana, shine namijin da babu wani namijin daze maye gurbinsa a cikin zuciyata.

Wani sanyi Zuby taji ya ziyarci zuciyarta, dan tasan 'kawar tata zatayi ba one ba one, dan kuwa tasan Halin Hafiz sarai baze ta6a Auren Hussainaba, tunda hartayi aure kuma wani namiji ya jusanceta bashiba, dan itama abinda tahanshi aurenta kenan dan tariga tabashi kanta, shikuma tsarinshi baya auren macen da yasani a mace kafin aurensu, yasha fad'ama zubyn haka lokacin datake kwakwar ya aureta, to barantana kuma wacce wani namijin ya kusanta bashiba.

Kallonta zuby tayi, "wow 'kawata nafa manta da wannan guy d'in, gaskiya dole kike rud'ewa ki susuce akansa dan ya matu'kar iya soayayya, ga kuma iya........

Alamar tafiyar dasukaji yasa zuby yin shiru, jabeer ne yafito cikin shigar 'kanan kaya bakin wando da milk d'in riga sai 'kamshin turarensa ke tashi da Alama shigarsa wanka yayi, ganinshi yasa Zuby mi'kewa to 'kawata nizan wuce sai wani lokaci kuma.

Saurin tashi Hussaina tayi "d'an jirani mana, kallon jabeer tayi bako fara'a a fuskarta inason magana dakai, batajira amsarshiba tawuceshi zuwa bedroom, binta yayi daga baya, basufi minti goma da shigaba saiga Hussaina tadawo hannunta d'auke da bandir d'in yan d'ari biyar-biyar Sabbi fill tami'kama Zuby "kawata ga wannan akaima Baba, amsa Zuby tayi hannu na 'kyarma "nagode 'kawata nagode "kada kudamu 'kawata kunzama d'aya.

Nan tayimata sallama ta tafi tana mamakin sakarci irinna Hussaina ace kasamu miji wanda zaka juya haka amma har kana 'ko'karin rabuwa dashi.
Wani shu'umin murmushi tayi tare da cewa "Ni zuby zanyimaki Hankali Hussaina sai kingane ni  *Makira* ce (na Fiddausi sodangi) wataran sai kinzo gidannan namiki korar kare......

.
          *Bayan Sati biyu*
Hassana tana zaune gidan jabeer ne kawai amma babu wata kyautatawa irin ta ma'aurata dake shiga tsakaninta dashi daga 6angarenta.
A nashi 6angaren kuwa be tauyemata komeba, dan ba abinda tanema tarasa, abinci kuwa har jabeer yasaba da cin na restaurant dan ko sau d'aya Hussaina bata ta6ayin girki da sunan faranta ranshiba, kullum sai dai tadafa dai-dai cikinta tazauna taci idan tagama tatashi tabar plate nan, kullum haka zatabar gidan kace-kace hatta da gadon dasuke kwana batasan tagyaraba, duk da wannan abubuwan datakema jabeer amma bata Hanashi kanta idan yabu'kaci hakan, sauran abubuwanma tanayinsune wai kozeji haushi yasaketa amma ko kad'an beta6a nuna alamun ze rabu da itaba sai dai idan abin yademeshi ya zaunar da ita yari'ka mata nasiha,

zata zauna ta saurareshi yana gamawa zatace "Allahu Akbar, kaga Malam idan wa'azi zakayi kaje masallaci akwai masu bu'katar haka dayawa bananba inda bazeyi wani tasiriba, nifa ba dole akayima akan saika zauna daniba idan bazaka iyaba ka sauwa'kemin, ni wallahi da saki a hannuna yake da tuni na sawwa'kema na huta, wannan wane irin nacine kamar ni kad'aice mace a duniya kasakeni ka auro wata mana.

Wani gajeren murmushi jabeer yayi mai cike da takaici, "Hussaina bazan sakekiba, kuma badan ina son kyautata makiba kuma badan bazan iya rabuwar dakeba, bako d'aya kawai bazan iya sakinkiba dan saboda darajar mahaifinki, amma kisani duk abubuwan dakikemin watarana sai kinyi nadama....

Dariya tayi "Hmm nadama badai inyi nadamar rabuwa dakaiba sai dai inyi farinciki, saboda ko yanzu karabu dani inada masoyin daze aureni yari'keni da daraja da 'kima fiye da ri'kon da kakemin...
Saukar wani lagfyayyen mari taji a kumatunta shine yahanata cigaba da magana tare da dafe kuncinta wanda yakemata tsananin rad'ad'i.
"Ka mareni... Wlh bazan yardaba, kuma wlh sai kayi nadamar wannan marin dakayimin azzalumi kawai.
Ganin yayo kanta yasa ta ruga da gudu tashige bedroom tare dasa key ta jingena da 'kofar tana maida numfashi.
Cike da takaici da ba'kinciki jabeer yabar gidan,

**             **               **

Hassanace zaune tare da Momy da Daddy bayan sungama cin abincin rana, daddy yatashi ze fita kenan Momy tayi magana  "Alhj takira sunanshi, dakatawa yayi ya zuba mata idanu yana jiran jin abinda zatace, "nace wai yaushe Hassana zataje tagano gidan 'yar'uwarta yakamata ace kabarta taje yau kimanin sati biyu kenan dayin aurennan amma kahanani kahana yar'uwarta zuwa wannan wane irin abune, ta'karashe maganar cikin ladabi.

"Ba yanzuba, yafad'a tare da d'aure fuska, tun yaushe nake gayamaku lokacin zuwa gidan waccan yarinayar beyiba, idan lokaci yayi da kaina zan umarci da aje, daga yau kada wanda ya'kara tunkarata da wannan maganar idanba so kuke ranku ya6aceba, yana gama fad'a yasa kai yafice.

Yana fita Hassana tafashe da kuka tare da fad'awa jikin Momy "yanzu Momy me hakan ke nufi, daddy yana nufin yarabani da 'yar'uwatane ko miye.

Kiyi ha'kuri hassana ba hakan yana nufin anrabaki da ita bane akwai dalilin dayasa Daddynku yahana muje amma ki 'kara ha'kuri inshaAllah bada dad'ewaba ze barki kije, haka Momy tayita rarrashin Hassana tana kwantar mata da Hankali.

**              **                 **

Da misalin 'karfe Hud'u na yamma Hussainace Zaune tanacin abinci jalouf d'in taliya tadafa da busashshen kifi, gefe kuma ga lemu tanaci tana korawa tana gamawa nan tabar sauran abincin tare da cup d'in datasha lemun, ringing d'in wayarta taji dake ma'kale jikin soket tana charge da sauri tatashi dan ta d'auko wayar tayi kwallo da kwalin lemun data rage Wanda ko rufeshi batayiba, nan yafad'i ya  zube kan carpet amma bata damuba saurin Isa tayi ta d'auko wayar ganin sunan Hafiz yasa tayi saurin danna OK tare da karawa a kunne.
"Hellow dear
"Haba babyna wannan wace irin rayuwace, Hafiz yafad'a cikin zafi-zafi.
Ace kullum muna tare a waya sai inkiraki yakai sau biyar arana amma kwata-kwata kin'ki kiyi dubarar dazamu had'u, gaskiya nalura kinfara son wannan mijin naki nike haukan banza, idan hakane kawai kifad'amin ni inha'kura.
Yayi 'kasa da murya kamar me shirin yin kuka "Amma idan kikamin haka kin yaudareni, tsakanina dake sai.... Be 'karasa maganarsaba ta tsinke wayar sakamakon jin Alamar shigowar mutum datayi,

Nan jikinta yafara kyarma dan ance marar gaskiya ko cikin ruwa yayi ji6i,

Sanye take cikin wani matsiyacin wando pencil, tare da wata d'amammiyar riga wacce ta sakko har gwiwa, kanta tayi rolling da wani shararan gyale Wanda behana ka hango gashin attach d'inda ke kanta, ga wasu muggan takalmi masu tsini dake 'kafarta. *Zuby kenan 'yar duniya Haya'kin taba*

Tsayawa tayi bakin 'kofar shigowa falon tana 'kara 'karema falon kallo, wani shu'umin murmushi tayi a zuciyarta tace "Allah kai damo ga harawa kobeciba yayi birgima, ma'ana idan nayi 'ko'karin raba jabeer da Hussaina koda be aureniba zanja ra'ayinshi ko zaman bariki muyi nikuma lokacin zan samu damar kwashe duk wani Abu daya mallaka
.
"Welcome 'kawata ashe kece, Hussaina ta fafd'a tare da kamo hannunta ta Zaunar da ita kan kujera, Zuby tayi murmushi tace "wlh kuwa hanya ta biyo dani nace bara na le'ko mu gaisa,
"amma kin kyauta kuma naji dad'in zuwanki domin dama ina Neman shawararki dan kobakizoba dama zan kiraki a waya.

To ai gani nazo 'kawata miye matsalarki?
Shiru Hussaina tayi kafin ta numfasa, "Zuby kinsan dai irin son danikema Hafiz kuma nagayamaki muna waya dashi, to halin da'ake yanzu kullum idan mukayi waya sai yanunamin tsananin 6acin ransa akan na'ki yarda muhad'u, nikuma a gaskiya ina tsoron Daddy, kuma nasan jabeer baze barniba, kuma kinga nan gidan mijinane bekamata inkawoshi nan ba.

Murmushi zuby tayi a zuciyarta tace "Anzo wurin, da wannan damar zanyi amafani inraba Hussaina da jabeer,
"haba 'kawata wannan aiba matsala bace zuby tafad'a tana kallon Hussaina.
"Husaaina tace kamar ya ba matsalaba kinsan fa akwai igiyar auren wani akaina kuma nike tarayya da wani namiji ina 'ko'karin had'uwa dashi kuma kice ba matsala bace.

Matsowa zuby tayi gab da Hussaina tare da kanga bakinta dai-dai kunnenta ta rad'amata wani magana. _(wanda koni zee bansan me tafad'a mataba)_

Suduka suka kyal-kyale da dariya tare da tafawa, Hussaina tace "Kai amma wannan shawarar tayi 'kawata shiyasa koda yaushe nake alfahari dake, kinga idan nayi haka zanje gurin masoyina inyi ko kwana nawa nakeso batare da wata matsala ba.

Nan take ta d'auko wayarta takira Hafiz bugu d'aya yad'aga tun kafin yayi magana tarigashi "hellow my dear ka shirya tarbar babbar ba'kuwa gobe-gobe.
"Kai haba da gaske? Hafiz ya tambaya cike da farin ciki.
"Da gaske mana kuma idan nazo kwana biyu zanyima.
"Wow babyna amma naji dad'i kice intashi inyima gidana general cleaning saboda zuwanki,
Nan suka gama wayar zuby kuwa sai kallonta take tana wani shu'umin murmushi.
Kafin ta mi'ke "to 'kawata nizan wuce kome kenan zamuyi waya, "to shikenan sai munyi wayar ko, har kusan get Hussaina tayima zuby rakiya, sannan tadawo.

Hussaina na dawowa ta d'auki wayarta takira Hassana
"Hellow sister kina lafiya?
"Lafiya lao Husaina tafad'a, wai dan Allah sister yaushe zakizo gidana shikenan ace tunda aka kawoni keda Momy ba Wanda yazo.
"Hmm kedai bari sister wlh ko ranar nan saida mukayi maganar zuwana gidanki nida Momy wallahi bakiga fad'an da yayiba wai lokacin zuwa beyiba, idan lokacin yayi ze gayamin da kanshi.
"Hmm sister kema bakiyi niyyar zuwaba, kodayake nasanki da tsoro kamar farar kura, amma in bacin haka me zai hana idan kinfito islamiyya kitaho alabashi idan lokacin tashi yayi saiki koma.

"A'a sister nikam gaskiya bazan iyaba, kinsan halin dady muddin nayi haka yagane kinsan bazemin da sau'kiba,
"To shikenan sis yanzu nagane baki 'kaunata, amma danice ai duk yanda zanyi inzo gurinki zanyi tafad'a tare da fashewa da kuka.....
Hasaana Har cikin ranta taji tausayin 'yar'uwarta yakamata, "shikenan kibari zanyima Momy maganar idan ta amince inanan tafe goben,
"To shikenan nasan ma Momy bazata'ki amincewaba, Allah kaimu goben ina jiranki.

Suna gama wayar jabeer nashigowa, tana ganin shigowarsa tayimashi wani mugun kallo up and down tare da buga wani uban tsaki "mtswww badai Zuciya, tafad'a tare da shigewa bedroom, kallo jabeer ya "karema falon yanda yayi kace-kace can plate nan cup nan robar ruwa, can ledar biscuit can kwalin lemu, ga kuma inda lemu ya zube ba'ayi mopping ba, girgiza kai kawai yayi sannan yanufi d'aki sai gashi yadawo sanye da best da wando threequter, plate da cups yafara kaudawa yakai kitchen sannan yad'auko mopper ya goge lemun daya zube, cikin 'kan'kanin lokaci yagyara falon fess, sannan yashiga kitchen yadafama kansihi indomie dan yadawo da yunwa, cikin minti goma ya gama ya zauna falo yaci.
.
Washe gari tunda 'karfe biyu na rana Hussaina ke faman bugama Hassana waya dan ta tabbatar da zatazo d'in kokuwa bazatazoba,

Hassana na zaune kan kujera tana gyaran farce ta kalli Momy "Hmm kinga Hussaina ta isheni da waya A'kalla yau takirani yakai sau goma, wai dan Allah inzo gidanta kuma na gayamata daddy yahana yace lokaci beyiba amma ta nace da magiya, wai dan Allah in taimaka idan nafito islamiyya inje idan antaso sai indawo ai bazesan najeba shine nikuma nace gaskiya inajin tsoro amma bari in tambayeki idan kin amince sai inje.

Murmushi momy tayi "ba kome kije mana, amma kibari yanzu daddynku ze dawo, idan yadawo yaci abinci yafita, kekuma saiki shirya gurin 'karfe ukku saiki tafi, amma ki tabbatar da lokacin tashinku islamiyya yayi kidawo gida, "inshaAllah Momy aini kinsan banida matsala yanda nake tsoron Daddy inwuce mana ya 6allani cikin gidannan, murmushi Momy tayi "ah to nidai nagayamaki wlh.

Dai-dai lokacin kuwa daddy ya dawo Momy da Hassana sukayimashi sannu da zuwa, Momy ta kar6i jakar hannunshi suka wuce d'akinsa, bayan wani d'an lokqci suka fito tare daddy ya canja kaya da Alama wanka yayi, zama sukayi kan dining Hassana tayi serve d'insu bayan sun kammala cin abinci suka d'an ta6a fira, cikin firar tasune daddy ya kalli Hassana "watako kedai kin'ki fiddo miji kiyi aure ga 'yar'uwarki takusa wata d'aya a gidanta,

Momy ce tace "Alhj to a ina zata samu mijin kullum tana 'kunshe a cikin gida, bata fita ko nan da can, yaushe wani ze ganta yace yanaso, indai ba itama irin na 'yar'uwarta zakamata ba.

"No no Hassana bazan ta6a yimata abinda nayima Hussainaba, saboda nutsuwarsuma ba d'ayaba,
"To Allah dai yaza6a mata miji nagari, Momy tafad'a daddy ya amsa da "Ameen ya rabbi.
Sannan ya kalli Hassana "ki shirya yanzu idan zan fita in saukeki kigano 'yar'uwarki.

Wani irin tsalle tadaka cikin Farin ciki tanufi d'akinsu domin ta shirya.

A gaggauce tafad'a toilet ta she'ka wanka tana fitowa tashafa ainafin cream d'inta coa-coa butter sannan ta murza farar powder, man le6e kawai tashafa sannan tanufi wadrope ta d'au'ko wasu kaya riga da zani d'inkin simple ta Sanya, dan tasan daddynsu baya 'kaunar 6ingilallun kaya da matsatsen siket koda ta sanya zesa taciresu.
Wani madai-daicin hijab ta saka sannan tafito nan sukayima Momy sallama suka wuce, momy har cikin ranta taji dad'in zuwan Hassana gidan Hussaina da Amincewar Alhjn, dan ita dama tun abinda Hussaina tayi take tsoron bada izinin zuwa wani guri batare da saninsaba, duk da tasan Halin Hassana yasha ban-ban dana Hussaina.

Dai-dai 'kofar gidan jabeer daddy ya sauke Hassana sannan ya ciro dubu d'aya yabata "ga wannan kihau napep 'karfe shidda tayimaki gida, "to daddy nagode Allah kiyaye hanya,
Nocking d'in gidan tayi me gadi yataso yana tambayar waye tare da le'kowa ganin Hassana yasa yayi saurin bud'ewa tare da dur'kusawa ya gaisheta "Hajiya sannu da dawowa, wallahi banma kula da lokacin da kika fitaba, murmushi Hassana tayi dan tagane inda maganganun me gadin suka dosa a tunaninsa Hussainace, "Ba me gidan bace 'kanwartace tafad'a tana 'kara fad'ad'a fara'arta.
"To ikon Allah Amma kamarku tayi yawa gashi girmanku d'aya ba wanda ze iya ban-banceku, Allah me iko.....yafad'a yana ri'ke da baki.

Nan Hassana tawuceshi tabarshi cike da mamaki, yana wasi-wasi "Anya ba me gidan bace tafita, wata kila bataso asan tafita shiyasa tace ba itabace, amma in bacin haka ai kamar tayi yawa kome iri d'aya hatta da maganarsu ba ban-banci.
Wannan ai saiku rikita me gidan yakasa gane wacece tashi acikinku.
.

Zaune Hussaina take kan d'aya daga kujerun falon hannunta ri'ke da remote tana kallon wata wa'kar turanci a tashar music plus, wasu had'ad'un Riga da wando na Pakistan ne jikinta tasa gyalen kayan tayi rolling, ga 'kamshin wani had'adden turare dake tashi jikinta, kafarta sanye da takalmi plate me masifar kyau, gefe kuma 'yar'karamar jakartace wacce tazuba kayanta kala biyu a ciki, jiran zuwan Hassana kawai takeyi tatafi gurin Rabin ranta Hafiz dan tun d'azu yake kiranta a waya gani yake kamar bazatazoba.

Agogon wayarta ta duba 'karfe bud'u dai-dai gashi har yanzu Hassna batazoba wani guntun tsaki taja tare da lalubo sunanta ta danna kira sai jiyo ringing d'in wayar tayi a dai-dai kofar shigowa da sauri takai dubanta gurin ido hud'u sukayi da Hassana batasan lokacin data buga wani irin tsalleba cike da farin ciki ta makaleta "oyoyo my sister.

*Tofah Readers me Hussaina ke shirin aikatawane, Me take nufi da son zuwan Hassana gidanta, wace shawarace Zuby tabata duk kubiyo Zee Elkaseem (Mmn khady) yar mutan KATAINAWA domin samun cikakkiyar amsa a cikin littafin AUREN TAGWAYE*

Post a Comment for "AUREN TAGWAYE CHAPTER A LITTAFIN ZEE ELKASIM MAMAN KHADY "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...