Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

AUREN TAGWAYE CHAPTER B KARSHE

AUREN TAGWAYE CHAPTER B KARSHE

- - Post a Comment

 AUREN TAGWAYE CHAPTER B KARSHE
Cike da farinciki suduka suka fad'a kan kujera, Hussaina ta kalli Hassana wlh sister na d'auka bazakizoba harna fara cire rai,


"Injiwaye inanan tafe ai,

"amma naji dad'in zuwanki wlh, dariya Hassana tayi "lallai sister aurennan ya kar6eki kinga kuwa yanda kikayi kyau kikayi wani fresh, kamar kinje wata 'kasar Honey moon, dariya Hussaina tayi tare da kaimata duka cikin wasa "kai sister bakida dama, nidai yanzu bari nafara kawomaki lemu kisha idan kuma kina bu'katar abinci ga kitchen nan zaki iya shiga ki girka dan kema gidankine, bata jira jin abinda zata fad'ba tanufi kitchen tabud'e fridge domin d'aukoma sister dinta lemun.


Bayan shigarta kitchen kuma idon Hassana ya sauka kan jakar dake gefen Hussaina ajiye, hannu tasa ta d'auko jakar tare da zuge zip d'in ganin kayan sawa cikin jakar dakuma yan abubuwan bukata yabata mamaki, bata kai ga rufe jakar ba Hussaina ta dawo d'akin d'auke da lemu da cup d'in glass a hannunta ta ajiye gaban Hassana.


Kallonta Hassana tayi sannan ta tambayeta "sister wannan kayanfa na waye? Matsowa Hussaina tayi ta kar6i jakar ta rufe ta ajiye gefe sannan ta zubo lemun a cup ta mi'kamata "kar6i sister kisha zanyimaki bayanin kona miye....


Ba musu Hassana ta kar6i lemun ta shanye sannan ta kalli Hussaina "uhum ina jinki.


Cikin muryar Neman Alfarma Hussaina tafara magana "dan Allah sis wani taimako nakeso kiyimin wanda duk duniya nasan ba wanda zeyiminshi sai ke.

Cike da mamaki Hassana ke kallonta "ina sauraronki sister wane taimakone wannan?


Matsowa Hussaina ta'karayi kusa da ita "ba wani abu bane me wuya inaso ki zauna a gidannan a matsayina.....


"What? Hassana tafad'a tare da mi'kewa tsaye "me kike cewa sister ban fahimci inda zancenki ya dosaba, kama hannunta Hussaina tayi tare da maidata kan kujera ta zaunar da ita "plz sister ki saurareni mana nasan zaki fahimci inda zancena ya dosa.

"Ina jinki Hassana tafad'a tare da bin yar'uwar tata da kallo.


Hussaina tacigaba da magana "kamar yanda nafad'a inaso ki zauna a gidannan a matsayin nice, ba dad'ewa zakiyiba kwana biyu kawai zakiyi, kuma ni zaki taimaka.


"Kamar ya in taimakeki wannan abinda baze ta6a yiyuwa bane yaushe za'ace wani yayima wani zaman aure, aurefa ba abin wasa bane.


"Hmm sister dan Allah ki taimakamin inshaAllah ba abinda ze faru kuma ba Wanda ze gane, sanin kankine babu Wanda ke bam-banceni dake, ko Momy da daddy suna ban-bancemune ta gurin halayyarmu amma bata kamaninmuba.


"Dakata sister duk ba wannan ba, shin idan na zauna gidannan amatsayinki kekuma ina zaki?

"Yauwa sister tambayar dayakamata kiyimin kenan.

"Wata 'kawatace zatayi aure shine ta gayyaceni to na tambayi jabeer ya Hanani kuma yace idan nasake tunkararsa da maganar ze gayama daddy, to nikuma yanda nike da 'kawar tawa yawuce ace ta gayyaceni bikinta banjeba,


"To shine kuma baki iya zuwa rana d'aya ki dawo?

"Baze yiwu inje rana d'ayaba saboda ba nan garin bane.

"Wane garine? Hasana ta tambaya.

"Yar Kaduna ce, kuma kinsan nisan katsina zuwa Kaduna, kuma daga can Abuja zamu kai amarya kinga dole inkwana biyu.


Tana kaiwa nan a zancenta wayarta tashiga ringing tana dubawa taga sunan Hafiz gabanta yayi mummunan fad'uwa da kamar bazata d'agaba ganin Hassana ta tsareta da ido yasa ta d'aga "Heelow dan Allah kiyi Ha'kuri bani nacemiki zanzoba to yanzu haka wayar damuke ina hanya. Bata jira me Hafiz ze fad'aba ta tsinke wayar.

"Kinganiko sister wallahi tund'azu takemin waya, Amaryar cefa.


Hassana cikin sanyin jiki tace "shikenan na amince zan Zauna amatsayinki "Amma ba nan gizo ke sa'kar ba ya zamuyi da daddy da Momy kinsan  dole zasu nemeni......


Saurin katseta Hussaina tayi tare da dafa kafad'arta "indan wannan kada kidamu, ni zantafi da wayarki zan barmiki tawa koda su daddy sunkira nasan bayanin dazanyimasu.


"To shikenan Hassana tafad'a, kawai dai ta amince da bu'katar 'yar'uwar tata badan komeba sai dan taga yanda ta masifar shiga damuwa, amma can 'kar'kashin zuciyarta cike take da tsoro da fargabar abinda suke shirin aikatawa.


Nan Hussaina ta 'kar6i wayar Hassana ta kwafi Number Hafiz tasaka a wayar Hassana, wacce ke wayarta kuma tasata blacklist tare dayin delete d'in number daga wayarta sannan ta baiwa Hassana wayar.


Nan ta d'auki jakarta sukayi sallama da Hassana tatafi, tana fita takira Hafiz da number Hassana tafad'amashi tana hanya kuma idan ze kirata da wannan number ze kirata dan tabar waccan a gida.


Love u all my Fan's πŸ’ƒπŸ»  shoki 🏊🏻‍♀😏

[1/17, 9:19 AM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­

             πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                    πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                       πŸ•ΈπŸ•Έ

                           πŸ•Έ

*Written & Story by*

*Zee Elkaseem*

*{Mmn khady}*


*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»


Page......................28


Gabanta yashiga dukan tara-tara a zuciyarta tarin'ka tunanin taya zatayi zaman aure da mijin 'yar'uwarta, bayan ba mutuwa tayiba, kuma ba rabuwa sukayba, lallai Hussaina tasakata matsala sai yanzu takejin dama bata amince da 'kudirintaba, amma yanzu aikin gama ya gama dole ta zauna tarufama 'yar'uwarta asiri har lokacin dazata dawo, da wannan tunanin taji ana kiraye-kurayen sallar magrib saboda haka da sauri tanufi bedroom tashiga toilet ta d'auro Al'wala ta kabbara sallah, bayan ta idar da sallar ta dawo falo tsayawa tayi tana tunanin yanda zata fara aiwatar da ayyukan gidan dan da Alama Hussaina duk yau bata gyara gidanba,


Sharar falon tafarayi, tare da yin mopping, sannan tasaka wani 'karamin towel me haske ta goge TV, center table, dakuma dining da sauran guraren da yakamata a goge, bayan ta kammala nan takoma bedroom, ta gayara tashare tare da canjama gadon bedsheet, lokaci guda gidan yayi fes kamar bashiba, freshner ta d'auko me dad'in 'kamshi ta feshe ko'ina hatta da toilet saida tagayara ta fesa freshener abin gwanin sha'awa gidan sai yakoma kamar wani Sabin kaya aka zuba saboda tunda yake Hussaina bata ta6a gyarashiba, kullum saidai ta 6ata.


Bayan ta kammala wannan kitchen tanufa nanma tsayawa tayi tana tunanin me zata dafa, dan tasan duk inda me gidan yake yana gab da dawowa duk da batasan lokacin dawowar tasaba, ta dad'e haka daga 'karshe ta yanke shawarar dafa abu mai sau'ki dan dare yafara gashi anata kiraye-kirayen sallar isha'i.


Jalouf d'in kus-kus ta dafa wanda yaji kayan lambu da kayan 'kamshi, sannan tayi amfani da tsoka nama zallah ta yankata 'kanana aciki yanda ze zamana duk lokacin da wanda zeci ya ebo yakai baki ze had'o da naman, dayake kus-kus ne cikin minti ashirin ta kammala dahuwar ta juye a flask, tare da had'a zo6o had'add'e shima sai 'kamahin flavour yake ta jera kan dining.


Bedroom takoma tafad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito bata wani 6ata lokaci gurin yin kwalliyaba lotion kawai ta murza tare da 'yar hoda sai man le6e, wadrope tanufa ta d'auko wani had'adden less d'inkin Riga da siket ta sanya, wow kayan kuwa sun masifar kar6ar jikinta kamar dama dan ita aka d'inkasu, duk wata sura ta jikinta ta bayyana.


Zama tayi falo tare da jawo wayar da Husaina ta barmata tashiga danne-danne, tana dubawa tashiga inbox bataga komeba, sannan tashiga chat nanma ba kome, dan Hussaina batabar komeba saida tayi delete, dan kada Hassana taga halin datake ciki.


**                 **                **


Daddy ne ke safa da marwa hannunshi ri'ke da waya yanata try number Hassana amma sai acemai switch off, abin na matukar bashi mamaki gashi kuma har 'karfe tara na 'ko'karinyi bata dawo gidaba, Momy kuwa hankalinta yayi 'kololuwar tashi "innalillahi Alhj yanzu ina yarinyar nan tashige, anya kuwa lafiya dan bata ta6a yimana hakaba,


Juyowa daddy yayi ya kalleta shima Hankalinsa a tashe, yace "ni kaina ina mamakin hakan dan Hassana yarinyace me matu'kar tsoro da kiyaye fushinmu amma yau ace tawuce ka'idar dana gindaya mata,


Momy wacce idanunta suka fara kawo kwallah tace bari inkira number Hussaina inji idan Hassana ta taho,  wayarta ta d'auko ta lalubo sunan Hussaina tanata ringing ba'a d'agaba dan ganin sunan Momy a wayar ba 'karamin d'aga hankalin Hassana tayiba, dan tasan duk yanda akayi yanzu itada Daddy sunacan hankalinsu yatashi na rashin dawowarta gida,  bata d'aga wayarba saida kiran Momy na hud'u yashigo sannan ta d'auka ta dannan OK tare da karawa a kunnenta saida ta dai-daita nutsuwarta sannan tace "Assalamu Alaikum.

A d'ayan 6angaren Momy cikin 6acin rai tace Hussaina kina ina inata kiran wayarki har kusan sau hud'u baki d'agaba.


Ba 'karamin fad'uwar gaba Hassana tayiba, tare da daburcewa dan gani take kamar Momy zata iya ganeta.

"Uhn ah am.... Dama bani kusa da wayar ne sai yanzu naji.

"To dama tambayarki zamuyi shin Hassana ta taho gida kuwa.?

"Eh tataho momy ai tun d'azu ta taho tace daddy yace kada ta wuce 'karfe shidda kuma biyar da rabi tabar gidannan.


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Momy tafad'a tare da fashewa da kuka, tama manta ko tsinke kiran batayiba, Hassana kuwa tsayawa tayi ri'ke da waya a kunnenta tana sauraren yanda Momy ke kuka tana gayama daddy cewa "tun 'karfe biyar da rabi Hassana tabaro gidan Hussaina.

"Subhannallah Daddy yafad'a tare da cewa Allah bayyana mamu ita a duk inda take.


Tsinke kiran Hassana tayi tare da sake kiran Momy, ringing d'aya ta d'auka, Nan Hassana ke tambayar "Momy wai meke faruwane, naji kinkira kintambayeni nabaki amsa kuma kinsa salati.

"Hussaina 'yar'uwarki Hassana har yanzu bata dawo gidaba kuma munkira wayarta switch off,


"Innalillahiwa'inna'ilaijirraji'un Hassana tafad'a tare da fashewa da kuka, kafin ta tsinke kiran.

A tunanin momy Hassana tana kukane saboda 6atan 'yar'uwarta.

Itako Hassana kukan nadama da ba'kin cikin halin dasuka jefa iyayensu takeyi, sai yanzu take datasanin yarda da kud'irin 'yar'uwarta.
Love u all my Fan's πŸ’ƒπŸ» shoki 🏊🏻‍♀. πŸ€’

[1/22, 6:47 AM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­

             πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                    πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                       πŸ•ΈπŸ•Έ

                           πŸ•Έ

*Written & Story by*

*Zee Elkaseem*

*{Mmn khady}*


*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»


Page......................29


Zaune take kan d'aya daga cikin kujerun dake zagaye da falon ta buga uban tagumi hannu bibbiyu, ba abinda take tunani sai halin da iyayenta suke ciki,


A zahiri tayi magana "nidai bari inkira Hussaina tadawo gidanta nikuma inkoma gida in fuskanci kowane irin hukunci daddy zeyimin koda kuwa zefi na Hussainar tsanani, dan bazan iya zama cikin tunani da fargaba ba.

Wayarta ta jawo talulobo sunanta ta danna kira amma kuma cikin rashin sa'a sai akacemata wayar akashe, "ya salam tafad'a tare da d'ora hannu bisa kai nashiga ukku, tafad'a tare da mi'kewa tsaye  "kodai inyi tafiyata idan tadawo tamasu bayanin inda taje, "kai bazan iyayima sister hakaba, muddin nasan daddy yaji labarin tayi wannan tafiyar kasheta kad'ai ne bazeyiba....

Wayyo ni Hassana ansakani tsaka me yuwa tafad'a tare da komawa ta zauna kan kujera jiki duk ba lakka.


Horn d'in mota taji gabantane yayi wani mummunan fad'uwa da sauri tanufi window tad'ga labulen tare le'kawa, me gadi ta hango yana 'ko'karin bud'e get, bayan ya bud'e motar jabeer tashigo duk kan idon Hassana yayi parking sannan yafito hannunsa d'auke da jakarsa, da sauri takoma ta zauna sannan tayi 'ko'karin dai-daita nutsuwarta dukda mummunan fad'uwar gaban datakeyi.


Da sallama yashigo falon, Hassana na Zaune jikinta sai kyarma yake tana tunanin wace irin tarba zatayima mijin 'yar'uwar tata, da kyar tasamu ta dai-daita nutsuwarta tare da mi'kewa ta dur'kusa ta kar6i jakar hannunshi tana mashi sannu da Zuwa, jabeer kuwa tsananin mamakine ya lullu6eshi yayi tsaye inda yake yakasa motsawa yayinda itakuma Hassana ta dad'e da shigewa d'akinsa domin ajiyemar jakarsa.


Murmushi yayi a Zuciyarshi kuma yace "ikon Allah, yau kuma ni Hussaina kema wannan tarbar, bin ko'ina na falon yayi da kallo ya ganshi fes-fea ba kamar yanda yasaba ganinshiba kullum kace-kace, sannan tunda yashigo daddad'an 'kamshin girki dana freshner sun had'u sun dakar mai hanci, lumshe idonshi yayi tare dayin wani guntun murmushi sannan yanufi d'akin dai-dai Hassana itakuma zata fito daga d'akin kad'an yarage suyi karo da juna Hassanar tayi saurin ja da baya duk tawani daburce "um ga ruwan wanka can nahad'ama "To, kawai jabeer ya iya amsawa dashi tare da binta da kallon mamaki sannan ya wuce Zuwa toilet d'in, tana ganin shigarsa tayi saurin zuwa wadrope ta fiddo mashi 'kananan kaya marar nauyi tare da ajiyesu gefen gado sannan tafita zuwa falo.


: Yana fitowa daga wankan yayi tozali da kayan da Hassana ta ajiyemai murmushi yayi saida ya murza mai sannan ya d'auki kayan ya sanya tare da feshe jikinsa da daddad'an turarensa, sannan yafito zuwa falo, zaune take kan kujera da waya hannunta tund'azu number Husaaina kawai take try amma switch off, dan tunda jabeer yadawo hankalinta yayi matu'kar tashi jikinta keta kar-karwa tsoronta d'aya kada jabeer yagane ita ba matarshi bace.


Da sauri ta tashi tana mashi sannu da fitowa, tanufi dining ta zauna sannan ta kalleshi "bissmillah mana tafad'a tare da gyaramashi kujerar daze zauna, ba musu yazo ya zauna yana binta da kallon mamaki danshi har yanzu abubuwan dake faruwa ganinsu yake kamar a mafarki wai yau shine Hussaina ke tarairaya haka lallai da walaki amma koma miye ba yanzu yakamata in tambayetaba.


Yana cikin wannan tunanin harta zubamar abincin ta ajiye gabanshi sannan itama ta zuba nata, haka suka faraci dad'in abincin na ratsa jabeer har tsakiyar kanshi, a zuciyarshi yana cewa "yaushe rabon dayaci abinci me dad'in haka kullum yana hanyar zuwa restaurant, 


Da misalin 'karfe tara da rabi na dare suna zaune falo kowanensu yayi ahiru wani Indian film suke kallo a tashar zee cinema, da Alama film d'in yayima Hassana kyau dan ta maida hankalinta kaf kan film din, yayinda jabeer bacci yacikamar ido, sai hamma yake d'aya bayan d'aya tasowa yayi daga kujerer dayake  yazo inda Hussaina take zaune Yakama hannunta "Taso muje mu kwanta, wani mummunan fad'uwar gaba taji tayi saurin kwace hannunta Daga nashi tace kaje ina zuwa saina ida kallon wannan film d'in.


Juyawa yayi ya kalli TV cike da mamaki dan yasan Hussaina bata ta6a yimar musuba idan ya umarceta dasu kwanta, kuma da kallo be dametaba, da wannan tunanin ya wuce d'aki yayi kwanciyarsa kasancewar akwai gajiya jikinsa bacci yayi gaggawar d'aukarsa.Love u all my Fan's πŸ’žπŸ’˜πŸ’žπŸ’•πŸ’–πŸ˜˜

[1/26, 10:09 AM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­

             πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                    πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                       πŸ•ΈπŸ•Έ

                           πŸ•Έ

*Written & Story by*

*Zee Elkaseem*

*{Mmn khady}*


*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»


Page......................30


Husaaina kuwa bayan ta isa gidan Hafiz, cike da murna da jin dad'in zuwanta ya tarbeta, tana isa takira Zuby a waya, ringing d'aya zubyn ta d'auka dama jiran kiran takeyi.


"Hellow 'kawata Zuby tafad'a cike da 'kagara taji abinda Husaainar zata fad'a mata.

"Kawata naji dad'in shawarar da kikabani dan yanzu haka ina tare da mutumin,

Dariya zuby tayi a ranta tace "Zaki gane kurenki zaki gane da zuby kike magana.

Amma a zahiri sai tace "ai dama nagayamaki hakan kawai zakiyi kije inda ranki keso kiyi ko kwana nawa kikeso batare da wata matsala ba.

"Ai shiyasa nake masifar sonki 'kawata Hussaina tafad'a.

Zuby tace "ai nima banida kamarki shiyasa kullum nakeson ki kasance cikin farin ciki, da haka sukayi sallama, kowace ta ajiye wayar


Wata mahaukaciyar dariya zuby tayi tare da tafa hannu " yarinya kinshiga tarkona kad'an yarage in cimma manufata akanki,

Wata sabuwar dariya ta'kara kafin tasha mur kamar bata ta6a dariyaba "Hussaina ina me tabbatar maki yanda kika baro gidan jabeer kin barshi kenan Har abada.


Hussaina kuwa bayan sun gama waya da zuby toilet tashiga ta she'ka wanka, bayan tafito tabi jikinta da lafiyayyen lotion dinta tashafa kayan jikinta ta maida sannan tadawo falo ta zauna tana jiran shigowar Hafiz dan bayan sallar isha'i yafita yo masu take a way.


Be dawo gidanba sai 'karfe tara da rabi lokacin Hussaina nadai zaune kan kujera a falo sai hamma take jerawa d'aya bayan d'aya, ga yunwa na addabarta ga kuma wani irin bacci dake fizgarta


Da sauri Hafiz ya isa gareta tare da ajiye ledar dake hannunsa gabanta, "sorry babyna na dad'e ko? Ya tambaya yana kallonta yanda take lumshe idanu da Alamar jin bacci tattare da ita.


"Uhm, kawai tace tare da 'Kara gyara zamanta kan kujerar datake, "sorry sorry babyna tafad'a tare da nufar kitchen, bayan yan mintoci ya fito hannunsa d'auke da plate da cukulla da cup's, gabanta yazo ya ajiye sannan yazuba masu abincin, da sauri Hussaina ta fara ci saida taji tayi dam sannan ta kora da lemu, toilet tanufa ta wanke bakinta tadawo kan kujerar datake tad'an kishingid'a cikin mintina biyar bacci yayi awon gaba da ita.


Hafiz Kuwa bayan shima ya kammala cin abincin tattara plate d'in yayi da cup's ya mayar kitchen sannan ya wuce bedroom yafad'a toilet yashe'ka wanka yana futowa ya shafa cream wasu tare da feshe jikinsa da turare, jikinsa sanye yake da vest da shortnicar falo yanufa har yanzu Hussaina na kwance inda yabarta kan kujera sai sharar baccinta takeyi,


Tsayawa yayi kanta saida yakaremata kallo, take wata matsananciyar Sha'awarta ta d'arsu a zuciyarsa ahankali yakai hannunsa jikinta yafara shafata yana mata irin salon dayasaba tayar mata da hankali.


Can cikin bacci taji ana ta6ata saurin bud'e ido tayi tare da saukesu kan Hafiz dake aikamata sakon wani shu'umin murmushi, ture hannunshi tayi daga jikinta "miye haka kake shirin aikatawa kasanfa da da yanzu ba d'aya bane, yanda nasaki jiki dakai a da nabaka duk abinda kakeso yanzu baze yuyuba.


Hafiz yad'an 6ata rai "Haba babyna sabodame zaki hanamin kanki?

"Saboda kwakwkwaran dalili, Hussaina tabashi amsa.

"Inaga babu wani dalili dazesa ki hanamin wannan lallausan jikin naki me tarin ni'ima, a da kika amince dani baranrantana kuma yanzu da kome zamuyi baza'a ganeba kawai ki amincemin mu shana, yafad'a tare da jawota jikinsa ya matseta gam.

*sai kunyi ha'kuri da typing saboda 'yar matsalar da wayana ya samu koda aka gyara sai naji duk ta canjamin typing d'inma baya sauri*
Love u all my fan's πŸ’ƒπŸ» shoki πŸ‘„πŸ­

[1/26, 3:05 PM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­

             πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                    πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                       πŸ•ΈπŸ•Έ

                           πŸ•Έ

*Written & Story by*

*Zee Elkaseem*

*{Mmn khady}*


*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»


Page......................31®TALANTED WRITER'S GROUP (T.W.G) πŸ“


Saurin tureshi tayi daga jikinta tare da mi'kewa tsaye cikin 6acin rai take magana "haba Hafiz wannan wace irin rayuwace, kabar ganin nakawo kaina gareka hakan ba yana nufin zan mallaka maka duk abinda kake bu'kataba daga gareni, akwai dalilin dayasa na amince da zuwa gidanka harna baro gidan aurena, duk wannan maganganun Hussaina tanayinsune cikin tsananin fushi da matsananancin 6acin rai.


Ran hafiz ya 6aci da jin maganganun Hussaina  yayi niyyar gayamata magana kamar yanda gayamar amma sai wata zuciyar tace "fushi ba naka bane kabita a hankali har kasamu ha'karka ta cimma ruwa.


Cikin sanyin jiki hafiz ya dur'kusa gabanta shikenan babyna na ha'kura amma kitaso muje mu kwanta yafad'a tare da kama hannunta.


Fizge hannunta tayi daga rikon dayayimata tare da komawa kan kujera ta zauna tace "kaje kawai ni anan zan kwanta, tashi hafiz yayi yanufi bedroom jikinsa a sanyaye a zuciyarsa ba haka yasoba yaso ace ya kwashi gara ta hanyar kusantar Hussaina dan dama ya dad'e rabon dayayi mu'amula da wata mace tunda suka samu sa6ani da zuby kusan sati batazo gidanshiba wanda ada yasaba baya kwana biyu basu had'u suka she'ke ayarsuba.


Da haka ya haye gadonsa zuciyarsa fall da tunani "to miye amfanin zuwan wannan yarinyar guna tunda bazanji dad'i da itaba, amma bari inbarta inga iya gudun ruwanta zuwa gobe kuwa idan ta'ki amincewa zan danneta kota 'karfi, dan nariga na kwad'aitu da ni'imar jikinta da wannan tunanin bacci 6arawo yayi awon gaba dashi, yayinda Hussaina batayi wani baccin kirkiba sakamakon wani mummunan mafarki datayi da Hassana Hakan yasa ta yanke hukuncin komawa gida gobe dan ganin halin da 'yar'uwarta take ciki.


**                **                     **


Kiraye-kirayen sallarY asubah yatashi jabeer daga bacci yakai hannunsa inda yake tunanin jin matarsa amma sai yaji wayam tunaninsa yakai ga tana toilet yadad'e yana jiran firowarta amma har ana niyyar kabbara sallah masallaci batafitoba ahankali ya tura 'kauren toilet d'in ganin bata ciki yabashi mamaki shiga yayi ya d'auro Alwala yafito falo ga mamakinsa ganinta yayi kwance kan kujera ta tada kanta da pilon kujerar tanata sharar bacci.


Cike da mamaki jabeer ya'karema Hassana kallo wacce shi atunaninsa Hussainace a zuciyarsa yace "me hakan ke nufi Hussaina ta canja hali ta ko'ina tana kyautatamin amma kuma yanzu tana 'kauracema shimfid'ata sa6anin da da bata kyautata min amma kuma tana bani Ha'kkina na aure dan koban kirataba zata kawo kanta to kodai tana cikin lalurane, amma kotana lalurar fashin sallah tasan duk hanyar sazatabi ta biyamin bu'kata kuma bata ta6a 'kin kwana tare daniba, amma koma miye zan tambayeta inji dalili.


Da wannan tunanin yatasheta sannan ya umarceta dataje tayi sallah, ba musu tatashi cikinagagin bacci tanufi toilet ta d'auro Alwala ta kabbara sallah, shikuma ya wuce massallaci dan gabatar da tashi sallar.


Bayan an idar da sallah jabeer yadawo gida tundaga falo yake jiyo sautin karatun al'qur'anin da Hassana ke rerawa abin ya matu'kar bashi mamaki dan yasan tunda yake da Hussaina bata ta6a yin karatun Qur'anic irin wannan lokacinba,  cike da mamaki ya wuce bedroom yahaye gado ya kwanta yana sauraren yanda karatun ke ratsa kwalwarsa cikin zazza'kar muryarta.


Saida tayi da yawa sannan ta tsaya tayi addu'a tashafa inda jabeer yake kwance taje  ta zauna nesa dashi cikin ladabi tace "barka da kwana

"Barka dai jabeer yafad'a batare daya d'ago daga kwancen dayakeba.

"Antashi lafiya? Takuma tambayarsa "lafiya lao, ya amsa tare da gyara kwanciyarsa.


Daga nan bata 'kara maganaba tafito tanufi kitchen domin sama masu abin karyawa.


Love u all my fan's πŸ’ƒπŸ» shoki πŸ‘„πŸ¬

[1/28, 8:12 AM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­

             πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                    πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                       πŸ•ΈπŸ•Έ

                           πŸ•Έ

*Written & Story by*

*Zee Elkaseem*

*{Mmn khady}*


*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»


Page...................... 32


®TALENTED WRITER'S GROUP (TWG) πŸ“


Gidansu Hassana kuwa Hankalinsu yayi matu'kar tashi ganin ankwana d'aya ba Hassana ba labarinta, Momy tayi kuka harta godema Allah yayinda dady yarasa sukuni ankai report police station sannan daddy da kanasa yaje duk wani babban asibiti dake garin ko Allah zesa yaga Hassana koda kuwa gawartane hankalinsu ya kwanta anma kome kama da ita be ganiba.


Dole ya hakura ya dawo gida ya zauna hankali a tashe yasaka cigiya gidajen redio da television,


Maganar 6atan Hassana ta bud'e ko'ina 'yan'uwa da abokan arzi'ki sai zuwa suke jaje, Momy Kuwa kuka kawai take idanunta sun kumbura abinci kuwa sai dai tad'an tuttura abinda ya sauwa'ka dan abincinma d'acinsa takeji ga matsanancin ciwon kai dake addabarta.


**                **                  **


Da misalin 'karfe takwas ta kammala had'a masu breakfast ta jera kome a dining Sannan ta hau gyaran d'akin duk da bawani datti yayiba ta 'kara gyarashi ta share sannan ta kunna turaren wuta, a hankali ta tura 'kofar bedroom d'in wani dad'i taji ganin jabeer baya d'akin saboda haka da sauri tashige tare da maida 'kofar ra rufe hada sa key. A gaggauce ta gyara d'akin ta goge ko'ina sannan ta feshe da freshener, kayan jikinta ta cire ta d'aura wani 'karamin towel tafad'a toilet ta she'ka wanka bayan tafito gaban dressing mirror ta tsaya simple makeup' tayi sannan tanufi wadrope wasu riga da siket na less tasaka, kayan sun masifar fito da ainafin kyawunta dukda ba wata kwalliya tayiba.


Lokacin kuma jabeer yafito cikin shirinsa sanye yake cikin 'kananun kaya milk d'in riga da ba'kin wando 'kafarsa sanye da ba'kin takalmi yan kamfanin masaraci, hannunsa ri'ke da jakarsa ta Zuwa office, ajiye jakar yayi kan kujera sannan yanufi d'akin da Hassana take tura 'kyauren d'akin yayi da mamakinsa sai yajishi gar'kame da key, saboda haka nocking yayi sannan yanufi dining ya zauna yana jiran fitowarta dan bayaso ya makara office dan yanzu ayyuka duk sun dawo  hannunsa saboda daddy baya fita office saboda 6atan Hassana


Saida gabanta yayi 'yar'karamar fad'uwa lokacin da jabeer yata6a kyauren d'akin.


Jiki a sanyaye ta bud'e tafito kan dining ta hangeshi saboda haka can tanufa tana takunta cikin nutsuwa, idanuwa jabeer ya 'kuramata ko 'kiftawa beyi wata matsananciyar sha'awarta ke fizgarshi dan jabeer irin mutanannane masu 'karfin sha'awa dan baze iya kwana biyu batare daya kusanci matarshiba kuma itama ta sabamai da hakan dan kobe nemetaba take kai kanta gareshi shikuma bewuce tayi. _lol_


Jitayi dukta tsargu da kallon dayake mata, ba 'karamar dauriya tayiba lokacin data iso taja kujera d'aya ta zauna sannan ta fara zubamar kalacin duk illahirin jikinta kyarma yake.


Haka suka fara breakfast d'in bayan sun kammala ne jabeer ya kalli Hassana yace "waini Hussaina kwana biyu naga kin canjamin kinayimin duk wani Abu dakikasan ze faranta raina sa6anin da davaki damu da damuwataba.


Murmushi tayi "kada ka damu mijina kasan Allah ba yanda baya sauya Al'amarinsa jiya ina zaune ina kallon TV aka sanyo wani malami yana wa'azi, to wa'azin dana tsaya na saurara sainaji kamar hallayatace kaf yake zayyanawa sannan kuma tafad'i irin azabar da Allah yatanada ga mata masu irin halayyarmu shine nikuma abin yad'agamin hankali.


Cike dajin dad'i jabeer yace "kai amma Allah yayima wannan malamin Al'barka

Hassana ta amsa da "Ameen.


Shiru yad'an ratsa nayan mintittika kafin jabeer ya'kara magana karo na biyu "to amma malamin beyi magana kan matar dake "kauracewa shimfid'ar mijintaba dakuma irin azabobin da Allah ya tanadar mata.

Love u all my fan's πŸ’ƒπŸ» shoki πŸ‘„πŸ¦

[1/30, 9:01 AM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­

             πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                    πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                       πŸ•ΈπŸ•Έ

                           πŸ•Έ

*Written & Story by*

*Zee Elkaseem*

*{Mmn khady}*


*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»


Page......................33® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ πŸ“


Shiru Hussaina tayi dan batada cikakkiyar Amsar dazatabashi akan wannan tambayar da yayimata, ganin batada niyyar magana yasashi mi'kewa tare da d'aukar jakarsa "ni zan wuce wurin aiki "Allah kiyaye hanya kawai tacemasa batare data motsa daga inda takeba.


Yana fita ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da sauri tanufi bedroom waya ta d'auko ta shiga laluben sunan Hussaina sannan ta danna kira cikin sa'a kuwa tasamu wayar na ringing amma harta tsinke ba'a d'agaba, batayi 'kasa a gwiwaba ta'kara kira karo na biyu nanma tanata ringing sai gab da zata tsinke sannan aka d'aga

"Hussainace tafara magana Hellow sister ai ganinan ina shiri inshaAllah yau zandawo yanzuma bada dad'ewaba.


Wata ajiyar zuciya Hassana tayi "nidai dan Allah ki dawo kinga muna shiga hakkin mijinki saboda na kula irin mutanennane mabu'kata nikuma kinga ba yanda za'ayi inbiyamasa dan Allah ki dawo saboda gudunmatsala.


Kada ki damu sister inshaAllah yau zandawo "To shikenan tafad'a tare da ajiye wayar kan mirror datake kwalliya gabanshi,

gefe kuma ga jakar kayanta da sauri tagama kwalliya sannan ta jawo jakar taciro wani riga da zani na atamfa ta sanya sannan ta d'aura d'ankwalin kayan wata madaidaiciyar hijab tasaka sannan takoma bakin gado tazauna tana jiran dawowar Hafiz, tund'azu yafita be dawoba shi kawai take jira gashi har 'karfe sha d'aya da mintittika, 'kara duba agogon wayarta tayi lokaci naja wani d'an guntun tsaki tayi tare da ajiye wayar gefenta ta sadda kanta 'kasa tunanin yanda zasuyi Hassana takoma gida batare da wata matsalaba takeyi dan tafi kowa sanin halin daddy.


Wata zuciyar tace ki kira zuby tunda itace tabaki wannan shawara itakad'ai kuma zata baki shawarar yanda za'ayi Hassana takoma gida batare da ansamu wata matsalaba.


Murmushi tayi tare da mi'kewa dan d'auko wayarta, gabantane yayi wani mummunan fad'uwa lokacin dasukayi ido hud'u da ita, sanye take cikin wani matsatstsen wando da wata figigiyar riga wacce da kad'an tawuce 'kugunta  sai wani yabud'ad'd'en gyale datayi rolling dashi fuskarta ba Alamar fara'a ko kad'an.


Cike da mamaki Huasaina ta kalleta tare da fad'uwar gaba, dakewa tayi ta tanufo inda take tsaye ta maida hannuwanta baya tanayima Hussaina wani shu'umin kallo.


"Naji dad'in zuwanki 'kawata kamar kinsan dama yanzu nake 'ko'karin kiranki, Hussaina tafad'a tana fad'ad'a murmushin dake fuskarta.


'Kara d'addaurewa Zuby tayi ba Alamar wasa tattare da ita, duk da haka Hussaina daurewa tayi tacigaba da kusanto inda zuby take, batayi auneba sai jitayi zuby ta hankad'ata iya 'karfinta tayi taga-taga zata fad'i da kyar tasamu ta daddafe ta kalli zuby wacce ke 'kara tinkarota har yanzu dai hannunta d'aya na bayanata, 'kara Hankad'a Hussaina tayi iya 'karfinta wannan karon saida tayi nasarar kayar da ita.


Wata irin fad'uwa Husaainar tayi kanta ya bugu da gefen gado take gurin yafashe yafara zubar jini, Hannu Hussaina tasa ta dafe gurin tana kallon zuby dake tunkarota Hannunta ri'ke da wani 'katon icce.


Cike da tsoro da fargba Hussaina ke 'ko'karin mi'kewa dan samun matsera dan taga Alamar ba wasa ko kad'an a idon zuby kuma ba Alamar d'igon imani tare da ita.


Ganin Hussaina na 'ko'karin mi'kewa yasa Zuby d'aga iccen dake hannunta ta kwantarama Hussaina akai, nan take ta zube jini yagama wankemata fuska, ta kalli Zuby cikin 'karfin hali da kyar ta iya d'aga bakinta tayimata magana.


"Zuby me nayimaki kike neman kasheni, mena tsaremaki a rayuwa?


Wata mahaukaciyar dariya zuby ta gagga6e da ita sannan ta d'addaure kamar bata ta6a dariyaba, sannan ta du'ko dai-dai inda Hussaina take kwance male-male cikin jini tana maida numfashi da kyar tace "Kin taremin kome a duniya Hussaina na dad'e ina ba'kincikin kasancewarki d'iyar masu kud'i nikuma d'iyar talakawa wad'anda talauci yayima kanta.


Sannan na dad'e ina mutuwar son Hafiz beta6a nunamin soyayyaba dai-dai da rana d'aya sai dai yana biyan bu'katarshi dani aduk lokacin daya bu'kaci hakan.

Amma lokaci guda ya nuna ba wacce yakeso sai ke, tafad'a tana nunata da yatsa.


Sannan tami'ke tsaye tayi taku biyu zuwa ukku "ban 'kara shiga tashin hankaliba sai ranar danaje gidanki mijinki yayimin kyautar kudad'e masu yawa tundaga lokacin naji ba wanda nakeso samada mijinki jabeer kuma naci Al'washin sai yazama mallakina.


Na zauna nayi tunani nayi nazari naga ba yanda za'ayi insamu biyan bu'kata saita hanyar kawar dake daga doron duniya.


Hussaina najin haka wani irin kuka da nadama sukazomata lokaci guda.


Zuby kuwa ba tausayi ba imani tacigaba da bugun Hussaina aka da wannan 'katon iccen saida ta tabbatar da babu sauran numfashi tattare da ita sannan tayi saurin barin gidan.


Love u all my Fan's πŸ‘„

[1/31, 9:AYE* πŸ‘­

             πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

                    πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ

     


Da musalin 'karfe biyar na yamma Hassanace Zaune itada jabeer sai janta yake da fira amma ita kwata-kwata hankalinta baya gurinsa itadai fatanta d'aya Hussaina tadawo itakuma ta koma gida dan yau ya kasance weekend jabeer be fita ko'inaba tun safe yake gida sai wani shu'umin kallo dayakebinta dashi.


Wayarta ta jawo tacigaba da try number Hussaina wacce tun misalin sha d'aya  na safe daaukayi waya ta gayamata tana hanya, tundaga lokacin kota kira sai tayi ringing tagama ba'a d'agaba, yanzu kuwa data kira cemata akayi (switch off) kashe take baki d'aya hankalinta ya'kara tashi ga jabeer yatasata gaba da Alama yanada bu'kata.


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ta furta tana 'ko'karin 'kara try number Hussaina lokacin jabeer ya'karaso inda take zaune shima zama yayi kusa da ita har jikinsu na gugar na juna, Hannu yasa ya kar6e wayar tare da jawota yahad'ata da jikinsa "wai tund'azu wa kike faman kira haka kinbarni ni kad'ai sai fira nakemaki amma Sam hankalinki baya gurina yafad'a tare da ajiye wayar kan centre table, itakuwa Hassana yana Had'a jikinta da nashi jikinta yahau 6ari, kyarma take kamar mazari, shikuwa jabeer shiga yayi cikin wani irin yanayi me wuyar fassarawa, wata matsananciyar sha'awa ta'kara saukarmai lokacin yakai 'kololuwa gurin bu'katar mace.


Tureshi tafarayi tana 'ko'karin raba jikinta danashi,

Lokacin ya fahimci halin datake ciki sakinta yayi tare da 'kuramata ido sannan ya kira sunanta cikin wata mabu'kaciyar murya "Hussaina

"Na'am ta amsa batare data d'ago ta kalleshiba.

'Kara kiran sunanta yayi karo na biyu "Hussaina, d'agowa tayi ta kalleshi batare datakuma yin maganaba, gabanta yayi wani mummunan fad'uwa ganin irin cikin halinda jabeer yake ciki idanunsa sun kad'a sunyi ja, magana yafara muryarshi na sar'kewa kamar zeyi kuka "dan Allah ki taimakeni kibani ha'kkina sanin kankine ban iya neman matan banzaba kece halalina bekamata ki gujeniba, banida wanda ze d'aukemin wannan sai ke, kuma tun acan baya kinsabin da bani ha'kkina duk lokacin dana bu'kaci hakan amma cikin kwanaki biyu kingujeni, meyasa ? miye dalili? namaki wani laifine? ya'karashe maganar yana kallonta.


Wani irin tausayinshi yakamata, batasan lokacin da wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanuntaba a zuciyarta tace "Hussaina kin cuci mijinki kinbarshi cikin wani hali wanda ni ban isa in fiddashiba,

Nikuma kinsani tsaka me yuwa, ya Allah ka kawomin d'auki.


Ganin hawaye a fuskarta yasa hankalin jabeer tashi yafara tambayarta "maganar danayimakice ta 6atamaki rai, indan wannanne kiyi ha'kuri nima na ha'kura, yana gama fad'in haka yatashi yanufi bedroom,


Minti sha biyar da shigarsa saigashi yafito sanye da wasu kayan ba Wanda yashiga dasuba ko kallon inda take beyiba yafice daga gidan, tanajin lokacin dame gadi yabud'emasa get yafice da motarsa, fad'awa tayi kan kujera tafashe da wani sabon kuka


Wayarta tajawo tasake kiran number Hussaina amsar dai d'ayace wayar na rufe baki d'aya.


Haka tacigaba da kukanta ita d'aya cikin gida bame rarrashinta,


Da misalin 'karfe takwas na dare jabeer yadawo gidan hannunsa d'auke da leda da sallama yashigo falon, zaune take jikinta sanye da wata 'karamar hijab, sannu da zuwa tayimai tare da kar6ar ledar dake hannunsa fresh milk ce sai gasashshin kaji, zama sukayi tsakiyar kafet d'inda ke malale falon suka fara ci, jabeer ciyake sosai yayinda Hassana take d'an tutturawa dan batada wani sukunin cin abinci.


Duk abinda take yana kula da ita amma be tankamataba, saida yaci ya 'koshi sannan yabi da fresh milk itama madarar ta zuba ta kwankwad'a saitaji tamata dad'i saboda haka duka ta shanye tata, shikuwa jabeer daya gama dama d'aukar sauran nashi milk d'in yayi yanufi bedroom dinshi.

.

Tana gama shan milk d'in taji kanta yamata nauyi duk illahirin jikinta yayi sanyi wani irin bacci ya rin'ka fizgarta duk abinda ke falon takoma ganinsa bibbiyu, da kyar tasamu ta isa bedroom tare dayin nasarar sa key ta kulle 'kofar sannan tafad'a gado ko sauya kayan jikinta batayiba zuwa na bacci.


Kusan minti goma da shigarta d'aki jabeer yafito daga gudan d'akin tura d'akin nata yayi amma sai yajishi gar'kame da key wani irin haushi ya 'kuleshi da sauri yakoma d'akinshi sai gashi yadawo da wani key d'in a hannunsa, sakashi yayi gurin key d'in 'kofar sannan ya murd'a 'Kofa kuwa ta bud'e shiga yayi d'akin haske fayau dan Hassana ko damar kashe fitilar d'akin bata samuba bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.


Tsayawa yayi yakaremata kallo wata irin kwanciya datayi, wani Shu'min murmushi yayi sannan ya rage hasken d'akin ya maida 'kofar yarufe hayewa yayi kan gadon yajawota zuwa jikinsa yafara wasa da jikinta cikin 'kan-'kanin lokaci yabiya bu'katarsa da ita batare datasan inda kanta yakeba.


Saida ya gama abinda yake yafad'a tunani a Zuciyarsa yake cewa "yanaji Hussaina kamar budurwa wacce bata ta6a sanin namijiba abin da mamaki.


Wata zuciyar tacemai ba wani abu yasa kajita hakaba sai dan bada amimcewarta ka kusancetaba.

Nan take yayi na'am da abinda zuciyarsa ta raya masa sannan kuma ya tsinci kansa cikin tsananin farin ciki.


Ahaka bacci yayi awon gaba dashi yana rungume da hassana jiyake wani sabuwar 'kaunarta na'kara shigarsa


Kiran sallar asubar farko Hassana ta farka daga nannauyan baccin datayi, jinta jikin mutum yasata saurin ida bud'e idanunta dan tabbatarma kanta shin abinda taji da gaskene ko mafarki takeyi ganin jabeer kwance yana sharar bacci ga ya had'e jikinshi da nata ya wani rungumeta, ga jikinta ba kaya ko d'aya tana ganin haka tasan aikin gama ya gama, jabeer yagama biyan bu'katarsa da ita, wani 'kululun ba'kin ciki yazo ya tokareta batasan lokacin data fashe da wani irin kukaba.


Kukanta yatashi jabeer daga nannauyan baccin dayakeyi me cike da Farin ciki, tambayarta yashigayi "lafiya Hussaina meyasaki kuka, a zuciyarta tace jabeer tsakanin kaida sister bansan wanda ya cuceniba sanadiyyar haka gashi narasa abinda kowace d'iya mace take ta'kama da tin'kaho dashi.


"Wayyo Allah nashiga ukku tafad'a hawaye nabin kumatunta wasu bayan wasu.

Jabeer kuwa 'kara jawota yayi jikinsa ya 'kara 'kan'kameta yana rarrashinta "please and please tell me, shiru tayimai dan batada amsar dazata bashi.

"Haba Hussaina ki gayamin abinda ke damunki duniya idan baki gayamin damuwarkiba amatsayina na mijinki waye zaki fad'amawa.


Hassana kuwa jitayi kamar tadad'amai tace "bafa matarka bace Hussaina ni 'yar'uwartace, saurin sa Hannu tayi ta toshe bakinta tana cigaba da kuka gani take kamar tunanunta zefito fili har jabeer yaji.


Ahankali ta zame daga jikinshi tana tafiya da kyar tanufi toilet tahad'a ruwan gumi tagasa jikinta sannan tayi wankan tsarki ta d'auro alwala tazo ta tada sallah lokacin shima jabeer yana d'akinsa wankan yayi tare da kabbara sallar a  zuciyarshi yana tunanin dalilin kukan matar tashi danya kusanceta Wanda ba yau suka faraba.


Bayan ta idar da sallah tana zaune kan abin sallar hawaye nacigaba da zuba daga idanunta jabeer yashigo d'akin zama yayi bakin gado yana fuskantarta ya kula da har yanzu kuka take ajiyar zuciya yayi sannan yace "Hussaina yau inaso ki gayamin dalilin 'kauracemin dakikayi kuma dan na kusanceki kike kuka kamar na kasheki.


A zuciyarta tace "kara kisa da abin kunyar dana aikata, nayi matu'kar danasani da amincewa da "kudirin 'yar'uwata.


Maganar jabeer ce tadawo da ita daga tunanin datake "zaki fad'amin kokuwa saina kira daddy 'kila shi ki fad'amasa.


Saurin d'agowa tayi da jajjayen idanunta ta kalli jabeer ba Alamar wasa tattare dashi, gabanta yayi mummunan fad'uwa kawai saita tsinci kanta da gayamashi "dama Hussaina ce...........


"Yanzu kamar ni ina matsayin mijinki ace ban isa ki gayamin damuwarkiba, to shikenan zan fad'ama Daddy 'kila shi kin gayamashi idan ya tambayeki amma kinsan bazan saka maki ido kina matsayin matataba inje waje innemi matan banza.
Bayan Hannu Hassana tasa ta share hawayen dake bin kumatunta sannan ta kalli jabeer cikin dasashshiyar murya take magana "Nifa ba wani abu bane ke damuna kawai ina tunanin 6atan "yar'uwatane yau kwana biyu ko labarinta ba'a samuba.
Tana kaiwa nan tafashe da wani sabon kuka, jabeer har cikin ranshi tabashi tausayi sosai janyota yayi jikinsa yana rarrashinta, da dabara tasamu ta kwace kanta tanufi kitchen domin had'a masu breakfast.
**                  **               **
Daddy zaune daga bakin gado kallo d'aya zakayimai ka tabbatar da tsananin damuwar dake tattare dashi, Momy kuma nakan abin sallah  tana lazimi idanunta fall da hawaye ro'kon Allah kawai take Allah bayyanar mata da d'iyarta aduk halin datake ciki,
Wayar daddy dake jone jikin socket tana chaji tahau ruri alamar shigowar kira, ko motsawa beyiba barantana yad'aga haka ta 'karaci ringing d'inta harta tsinke aka kuma kira karo na biyu nanma beyi niyyar d'agawaba, dan ko kallon wurin beyiba, Momy ce ta kalleshi tasa hannu ta goge hawayen dasuka gangaro kan kumatunta tace "Alhj wayarka fa tana ringing, shiru yayi kamar beji maganar datakeba, magana  ta'karayimashu lokacin da kiran wayar ya'kara shigowa karo na ukku "Alhj yakamata ka d'aga wayarnan dan da alama kowaye yadamu daya gayama kowace mgana ce saboda wanda yakiraka dai-dai wannan lokacin 'karfe shidda na safiya yakira baka d'agaba yanace yanata kira kasan maganar nada matu'kar muhimmanci, tana rufe bakinta wani kiran yakuma shigowa karo na biyar, Momy bata jira daddy ba tanufi inda wayar take ta d'auko ta danna ok sannan ta mi'kamai ba musu ya kar6a yakara akunnensa batare daya kalli sunan wanda ke kiranba.
"Assalamu Alaikum aka fad'a a d'aya 6angaren, me maganar bejira jin abinda Daddy ze fad'aba yacigaba da magana
"Sunana Ahmad turaki comusioner of police, ina fata dai muna magana da Alhj manair company?
"Eh dashi kake magana daddy yabashi amsa a ta'kaice.
Zaku iya zuwa babbar headquarter mu ta police domin tabbatar da wata gawa da muka tsinta kota d'iyarkace.
Saurin mi'kewa tsaye Daddy yayi yana yana salati "to shikenan ganinan zuwa bekobi takan Momy ba ya suri key d'in motarsa jikinsa dagashi sai jallabiya, silifas yazura a 'kafarsa yana shirin fita, momy tabiyoshi tana tambayarshi "Alhj lafiya? Beko sauraretaba yawuce hankali tashe.
Fad'awa Momy tayi kan gado tafashe da wani irin kuka me ban tausayi "ya Allah ka bayyanamin Hassana Allah sa duk inda take tana cikin aminci da kariyarka ya ubangiji, wani sabon kuka ya kubce mata.
Daddy na isa headquarter police bayan sun gaisa da comusioner nan yahad'a daddy da wasu police guda hud'u suka nufi babban asibitin dake garin kai tsaye matuare (d'akin ajiye gawa) suka nufa nan aka jawo dorowar da gawar Hussaina take, Daddy na ganinta yafashe da kuka kamar 'karamin yaro, nan ya tabbatarma 'yansandan d'iyarsace lokacin duk kamanninta sun  canja fuskarta ta kunbura ga jini daya gama wanke mata jiki.
Nan yansandan suka shiga rarrashin Alhj "kayi ha'kuri Alhj inshaAllah zamu tsaurara bincike sai mungano Wanda ya aikata wannan mummunan laifi, dan bincike ya nuna ankashe marigayiyar ne ta hanyar dukan da akayimata aka.
Daddy kasa magana yayi sai kuka kawai dayake, haka aka d'auki gawar Hussaina cikin motar police d'in aka nufi gida da ita.Love u all my Fan's 
[2/2, 9:05 AM] Zee Elkaseem:  *AUREN TAGWAYE* 
             
                
                    
                       
                           
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 

Page......................37
® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 
Momy kuwa tun bayan fitar daddy Daga gidan gabanta keta fad'uwa takasa zaune takasa tsaye.
Jin 'karar bud'e get tayi da sauri tatashi tanufi 'kofar fita daga falon zuwan harabar gidan, ganin motar me gidanta tare data police yasa tayi saurin komawa ciki tare da dafe 'kirjinta saboda jitake kamar zuciyarta zata fad'o saboda bala'in fargaba.
Jin annufo falon yasa fad'uwar gabanta ya yawaita, bata ankareba kawai sai gani tayi anshimfid'ar da gawar Hussaina tsakiyar falon, tana kai dubanta gareta taji duk illahirin wasu jijiyoyin jikinta dake aiki sunyi tsaye cak, kafin ayi wata magana sai ganin Momy akayi 'kasa ba alamar numfashi tattare da ita.
Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un Daddy yari'ka furtawa da sauri ya d'auko ruwa ya yayyafa mata, nan akayi nasarar dawowar numfashinta bakinta d'auke da salati.
Nan Daddy yacigaba da yimata nasiha yana rarrashinta da 'kyar yasamu ta nutsu ba abinda take maimaitawa a zuciyarta sai salatin annabi.
Ranar kafin ad'au wani lokaci labarin mutuwar Hussaina ya bad'e gari dandanan gidan Alhj mansir yacika da 'yan'uwa da abokan arzi'ki wasu na zubar da hawaye wasu kuwa sunyi jugum-jugum. Amma duk a tunananin mutane harma da daddy da Momy Hassanace ta mutu.
**                    **                **
Hassana zaune tana duba wani littafi na addu'oi kad'an-kad'an tayi try number Hussaina wai ko Allah zesa tashiga dan tanaso tagayamata Halin datake ciki, amma kamar kullum dai akashe ake cewa.
Jabeer ne yashigo jikinsa a sanyaye. haka kawai yana shigowa Hassana ta tsinci kanta da wata mummunan fad'uwar gaba.
Kallonta yayi ya matu'kar tausaya mata sannan yace "ki tashi yanzu zamuje gida daddy yana nemanmu, jitayi fad'uwar gabanta ya tsananta lokaci guda hawaye ya wankemata fuska a tunaninta jabeer yakai karartane.
Tasowa tayi jiki a sanyaye ta dur'kusa gaban jabeer "dan Allah kayi ha'kuri indai wannan maganarce nayima Al'kawari wlh zan gyara.
Wani irin tausayinta ya'kara mamaye zuciyarsa "a'a ba wannan maganar bace ban dad'e da isa office ba daddy yakirani yace muzo yanzu nidake nikaina bansan ko miye dalilin kiranba, haba tanajin haka wani sabon tashin hankali ya ziyarceta jikinta yafara kyarma kad'an yarage tasaki fitsari dan bako tantama tasan asirinsune ya tonu kan abinda suka aikata itada 'yar'uwarta nasanya jabeer yin *AUREN TAGWAYE* batare da saninsaba, innalillahi kawai tacigaba da furtawa acikin Zuciyarta, ahaka tanufi bedroom ta bud'e wadrope ta d'auko wata doguwar Riga ta canja kayan jikinta sannan tasaka hijab med'an girma wacce ta tsayamata iya gwiwa, plate shoe tasako sannan tafito falo ta iske jabeer na jiranta, yana ganin fitowarta yayi gaba tana biye dashi har gurin mota yabude gurin driver ya zauna sannan itama yabud'emata gidan gaba ba musu tashiga, amma duk illahirin jikinta kyarma yake dan kallo d'aya zakayimata ka tabbatar da bata cikin nutsuwarta.
Ahaka har suka 'karaso 'kofar gidansu tundaga nesa tahango dandazon Al'umma haka yacanjamata tunanani Zuwa wani daban "to wannan iyayen mutanenfa meke faruwane "innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.
Hankalinta be'kara tashiba saida tashiga harabar gidan nanma cike yake da jama'a maza suna jiran afito da gawa, cigaba tayi da tafiya dai-dai 'kofar dazata sadata da falon gidan taga wasu gun-gun mata zaune sunyi jugum-jugum sai d'aya daga cikinsu ta nuna Hassana tana cema sauran matan "wannan itace Hussainar marigayiyar, d'ayar tace  "oh itace wacce akayima aure kwanakin baya, d'aya tace itacefa Allah sarki mutuwa me yankan 'kauna lalle wannan yarinya tayi rashi Allah bata ha'kuri da dangana.........
Dai-dai wannan lokacin Hassana tanemi numfashinta tarasa sai mutanen dake gurin sukayo kanta anata salati aka kinkimeta akayi ciki da ita.
Dai-dai lokacin kuma aka fito da gawar Hussaina domin kaita makwancinta.

*Anan inso inja hankalin Al'umma akan mutuwa, yanzu abinda aka gane shine da ance wane ya mutu sai mata suje su cika gida wasuma ba dangin iya bare na baba, kuma Alhalin lokacin ana kimtsa gawa irin haka na jawo matsaloli da yawa, da zarar ka mutu 'yan'uwanka da iyayenka sha'kikai ake bu'katar suje ga gawarka bawai mutanen unguwaba, ba'ace kada mutane suje gidan suyi gaisuwaba amma ayi ha'kurin kauda mamacin, mata inajan hankalinku da kunyi gaisuwa ga wad'anda akayima mutuwar kutafi gidajenku shine mafi Alkhairi agareku kada azauna zaman gulma da cin abincin gidan mutuwa. ALLAH SA MUDACE ALLAH KUMA YASA MUCIKA DA IMANI ameen*.
.
Nan fa aka Shiga wani sabon tashin hankali ganin Hassana kwance ba Alamar numfashi tattare da ita, Momy kuka take tama rasa inda zata dosa saboda tsabar rud'ewa.
Sai kusan awa ukku sannan Hassana ta farfad'o lokacin 'Karin ruwane ke shiga jikinta, ahankali tafara bud'e idonta ido biyu sukayi da 'kanwar babanta Haj Uwani tana mata firfita, ganin ta bud'e idonta yasa tafara jeramata sannu.
Bin robar 'karin ruwan dake hannunta tayi da kallo, tunanin 'yar'uwarta tafad'omata arai "yanzu shikenan Hussaina tamutu nashiga ukku, ya zanyi da 'kullallen al'amarin data barni cikinsa, yazanyi in tunkari iyayena da mijin 'yar'uwata da wannan 'kazamin Al'amarin damuka aikata.
Fashewa tayi da wani irin kuka me ban tausayi, tana 'ko'karin tashi daga kan gadon, saurin ri'keta Haj Uwani tayi tare da rarrashinta.
"Kiyi ha'kuri Hussaina dukkan me rai mamacine, addu'a kawai zakibi 'yar'uwarki da ita, dan ita tafi bu'kata akan kome "Allah ji'kan Hassana yakai Haske kabarinta Allah toni asirin wad'anda suka aikata wannan mummunan aiki akanta, Haj Uwani tafad'a tana share hawayen fuskarta.
Hassana kuwa kwance tayi, tayi lamo akan gado tana sauraren yanda Mama Uwani 'Kanwar daddy take kwararo addu'a akanta bayan ita tasan ba itabace ta mutu, amma babu damar tafad'i, hawaye yacigaba da kwarara daga idanunta ba 'kakkautawa. Ahaka Momy tashigo d'akin hannunta d'auke da cup, ganin Hassana na kuka ya 'kara d'aga hankalinta itama kad'an yarage tafashe da kukan da kyar ta rarrashi zuciyarta, ta daure tami'kama Haj Uwani cup d'in hannunta "gashi tunda tatashi 'kara ta daure ko tea tasha kota d'an samu 'karfin jikinta.
Nan Haj Uwani kar6i cup din ta tada Hassana zaune tana 'ko'karin bata tea d'in tana 'kin kar6a da kyar tasamu tasha Rabin cup takoma ta kwanta da tunani barkatai cunkushe a kwalwarta.
        *Bayan sati d'aya*
Hankali yad'an kwanta mutane 'yan'uwa na kusa dana nesa kowa ya koma gida, gidan yarage daga Momy sai Hassana wacce tundaga ranar da'akayi rasuwar tazo bata komaba saboda har yanzu jikinnata ba 'karfi  duk tabi ta rame ta kod'e.
Washe gari ranar kwana takwas da rasuwar Hussaina Momy da Hassana na zaune, Momy na aikin rarrashinta akan taci abinci dan duk yinin yau batasa kome acikintaba, daddyne yashigo gidan da sallama, Momy ta amsa masa sallamar tare dayimashi sannu da zuwa, kallon Hassana yayi yaga yanda tarame ta kod'e cikin sati d'aya duk ta fita hayyacinta, har cikin ranshi ya tausayamata dan yasan ba karamar sha'kuwa tayi da 'yar'uwar tataba, sai dai al'amarin ubangiji ba ruwanshi da sha'kuwar dake tsakaninka da mutum idan yatashi d'aukar rayuwarsa.
"Hussaina, daddy yakira sunanta.
Gabanta yafad'i sannan ta juyo ta kalleshi tare da amsawa, amma kanta sadde 'kasa dan bata yadda su had'a ido dan gani take idan suka had'a ido da daddy ze iya gane cewa ba Hussaina bace.
Daddy yacigaba da magana "inaso kitashi ki shirya dan munyi waya da mijinki yanzu haka yana kan hanya zezo ya d'aukeki sai kitashi ki shirya kikoma d'akin mijinki kicigaba da biyayya, kinga dai abinda yafaru da yar'uwarki saboda haka kicigaba dayimata addu'a Allah kai haske kabarinta, yana gama fad'in haka ya wuce d'akinshi, Hassana kau fashewa tayi da wani irin kuka tafad'a jikin Momy tana maida numfashi sama-sama.
Hankalin Momy ya masifar tashi ganin yanda Hussana ke kuka ga numfashinta na fita sama-sama, amma ba yanda zatayi dan tasan tunda Daddy yariga ya furta takoma tofa ba fashi saita koma yau d'in, saboda haka jiki a sanyaye Momy tatashi ta taimaka mata tayi wanka, tana fitowa tad'an shafa mai sama-sama sannan tacanja kayan jikinta zuwa wata doguwar Riga, bata dad'e da gama shirinba suka jiyo tsayawar motar jabeer a harabar gidan, kafin jabeer yashigo ciki daddy yafito ya umarci Hassana data tashi sutafi kada ta 6atamai lokaci.
Haka ta mi'ke jiki ba laka tanufi harabar gidan tana tafiya tana waige jitake kamar takoma tasanar da daddy gaskiyar Al'amari amma data tuno da irin zuciyar daddy sai tsoro yakamata, dan tasan tsaf itama ze iya aikata inda 'yar'uwarta tatafi.
Ahaka ta isa gurin motar jabeer na ganin tahowarta yashige mazaunin driver tare da budemata gidan gaba tashiga ya tayar da mota me gadi ya bud'emasu get suka d'au hanya.

.
Tun a mota Hassana ke faman kuka har suka iso gida, jabeer nayin parking tafito tanufi cikin gidan dagudu tana 'kara fashewa da kuka, tana shiga falo tawuce bed room tasa key tarufe 'kofa
tarufene dan bata bu'katar jabeer yabiyota yace ze rarrasheta, fad'awa tayi kan gado tacigaba da rizgar kuka Kamar zata cire ranta.
Tunanin Hussaina yafad'omata arai yanda suke kome tare, ba abunda ke rabasu ko bacci basu yadda yarabasu har tayi aure amma gashi mutuwa tarabasu, zaune tatashi ta d'auko wayarta tana kallon Hotunan dasukayi itada Hussaina lokacin suna gida wasu sabbin hawaye suka kwararo a idanunta, tafara surutai kamar wacce ke magana da wani a kusa da ita tana kallon wani hoto na Hussaina "sister mesa kika tafi kika barni da 'kulallen Al'amarin da bansan yanda zanyi in warwareshiba, Hussaina ina kikaje aka rabaki da rayuwarki, me kikayimasu suka kasheki, ya Allah ka toni asirin kosu waye suka aikata maki wannan abin.
Cillar da wayar tayi gefe takoma kan gadon ta kwanta tacigaba da kukanta,
Bata tashiba sai 'karfe bakwai da rabi na dare lokacin wani matsanancin ciwon kai ke addabarta, a daddafe tatashi tashiga toilet ta d'auro Al'wala ta rama sallolin da'ake binta daga magrib har isha'i tadad'e tana lazimi kafin tashafa takoma kan gado ta kwanta, tunani barkatai takeyi a zuciyarta tace "ni yanzu yazanyi in fidda kaina cikin wannan sar'ka'kiyar......


     Bayan kwana goma tunda Hassana tadawo gidan jabeer bayan rasuwar Hussaina bata yadda su had'u da jabeer.
Kalacin safe saitaji fitarshi take fitowa tasamu abinda zata sama cikinta, dukda ba wani abincin kirki takeciba hakanan take tutturwa, da rana zata fito tayi abinci tajera a dining sanan ragyara ko'ina na gidan ta share hadda d'akin jabeer d'in, tana gamawa take ibar wanda tasan ze isheta daga lokacin har dare sannan takoma d'aki bakuma Zata 'kara fitowaba sai gobe idan taji fitar jabeer d'in
Tun jabeer na rarrashinta akan tafito ta daina zaman d'akinnan har yaha'kura ya kyaleta ganin tunda yake magiya ko saurarensa batayi sai dai duk ranar dayayimata magana yajiyo sautin kukanta.
: Bayan sati d'aya tana zaune d'aki kamar yanda tasaba tanajin lokacin da jabeer yafita saboda haka da sauri tafito tahad'a abinda zataci, dankali da kwai tasoya sannan tahad'a tea cikin cup tadawo palo ta zauna tafaraci, bawani dad'insa takejiba dan yau tashi tayi da wata irin kasala ga tashin zuciya dake addabarta, ahaka tasamu ta tuttura dan yunwar jinta takeyi, tana gama cin abincin kuwa yafara tu'karta da gudu tanufi toilet tafara she'ka amai, saida ta amayar da duk abinda taci sannan taji sau'ki-sau'ki
Nan take kuma  wani irin zazza6i yarufeta, tafara   kyarma kan gado tafad'a sannan tajawo wani 'katon bargo ta kudundune dukda uban zafin da akeyi a lokacin.
.
Jabeer be dawo gidan ba sai bayan sallar azahar kamar yanda yasaba dawowa, da sallama yashigo falon kai tsye d'akinshi ya wuce yafad'a toilet yayi wanka danya kwaso gajiya sosai, bayan yafito daga wankan ne ya murzama jikinshi mai sannan ya canja kaya zuwa 'kanana marassa nauyi, falo yadawo kai tsaye dan yakwaso yunwa sosai yasan ze tarar da abinci kamar yanda yasaba.
Falo yadawo kai tsaye ya doshi dining area amma bisa mamakinsa sai yaga wayam bako cokali gurin barantana yasa ran abinci, cike da mamaki yashiga kitchen nanma ganinsa yayi tas ko ina a share a goge ba alamar andafa wani abinci cikinsa, cike da mamaki yadawo falon sannan yanufi d'akin Hussaina nocking yayi ahankali duk da yasan ba bud'ewa zatayiba, hannu yasa yad'an murd'a handle d'in 'kofar da mamaki kawai sai gani yayi kyauren ya bud'e, ahankali yashiga d'akin yari'ka dubawa  inda ze ganta can idanunsa sukayimai tozali da ita tana kwance kan gado ta kudundune a bargo tanata makyarkyata kamar wacce aka she'kama ruwan 'kan'kara, duk zafin da akeyi a garin.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un jabeer yafad'a tare da nufar inda take kwance, zama yayi gefen gadon tare da bud'e bargon yana kallonta sannan yakai hannunsa kan wuyanta, jin wani irin zafi yayi rau ajikin nata, "subhanallah zazza6i Kike amma baki gayaminba sai ki zauna da ciwo ajiki, kitashi mutafi asibi,
: Bejira mezata fad'aba yanufi wadrope ya d'aukomata hijab, da kanshi ya taimaka mata ta sanya hijab d'in sannan suka nufi mota da sauri jabeer yabud'emata gaban mota ba musu ta zauna sannan ya zagaya yashigaazaunin driver suka d'au hanyar asibiti.
Bakin wani private Hospital suka tsaya me suna *Allah Bamu Lafiya* dake cikin garin katsina jabeer da kanshi ya taimakama Hassana tafito daga motar suka nufi cikin asibiti, suna zuwa kai tsaye aka bud'emata file sannan aka turasu gurin likita, bayan yan tambayoyi da likitan yayima Hassana itakuma tayimai bayanin duk abinda takeji, nan take likitan ya danna wata 'yar karaurawa saiga wata nurse tashigo, ta rissina gaban likitan cikin ladabi, ya nunamata Hassana "kije da ita kiyimata wannan gwaje-gwajen yafad'a yana mi'kamata wata takarda, "owk sir tafad'a tare da amsar takardar sannan takama hannun Hasaana suka nufi lab, nan aka ebi jini sannan tanunamata toilet tabata wani d'an konkoni na roba ta umarceta datayo fitsari anan, haka Hassana tayo fitsarin takawo sannan takoma kan wani benci Wanda masu jira ke zama ta kwanta ta kudundune cikin hijab d'inta dan har yanzu wani irin sanyi takeji,
Kusan minti talatin suna jiran result ganin yanda mutane ke 'kara yawa yasa jabeer matsawa kusa da Hassana yace "ko muje inkaiki gidanmu tunda kusane ni sai indawo injira sakamakon dakuma magungunan daza'a rubuta.
'Daga mashi kai kawai tayi, alamar hakan yayimata dan dama ita tamatsu dasubar wannan asibitin ganin yanda mutane suketa zuwa gashi gurin zama ma yana neman gagarar wasu itakuma ga wani irin sanyi datakeji.
Da taimalonshi suka isa gurin mota, bud'emata yayi tafara shiga  sannan shima yashiga yatshi motar suka tafi, kasancewar ba nisa tsakanin asibitin da gidansu jabeer ba'a d'au wani lokaciba suka iso, bakin 'kofar gidan sukayi parking sannan suka fito, suka nufi cikin gidan Ahankali Hassana take tafiya tana biye da jebeer, yanayi yana waigenta har suka isa cikin gidan suka kwad'a sallama Umman jabeer daga d'aki ta amsa, dai-dai lokacin 'kanwarsa nusaiba tafito daga wanka ta kai dubanta garesu cike da fara'a "Lah Yaya jabeer ashe tare kuke da aunty Hussaina, jin an ambaci Hussaina yasa Umma Fitowa daga d'aki tana masu sannu da zuwa, takai dubanta ga jabeer baka cemin tare kuke.
"Eh wlh mama daga asibiti muke shine nace bari inkawota nan tad'an huta kafin agama gwaje-gwajen daza'ayi.
"Subhanallah, Umma tafad'a meyasameta? Ta tambaya tana 'karema Hassana kallo wacce ta saddar da kanta ta'ki bari su had'a ido da Umma, amma hakan behana Umma tagano wani Abu tattare da itaba, murmushi tayi me d'auke da farin ciki, sannan takama Hannun Hassana suka nufi d'aki tanata jera mata sannu.


Jabeer ne zaune gaban likita, saida likitan yayi wasu 'yan rubuce-rubuce sannan yafad'a mashi ainafin abinda ke damun Hassana, sannan yabasu shawarar hanyoyin daza'abi domin kare lafiyarta,
Nan jabeer yayi godiya sannan ya sayi magungunan da'aka rubuta ya wuce gida.
Da sallama yashigo gidan, zaune ya iske Hassana da kwano a gabanta d'an wake ne Mamanshi tayimata shine takeci dan ba 'karamin dad'i yayimataba,  dai-dai lokacin nusaiba tafito daga d'aki cikin kayan islamiyya kalar ruwan 'kasa, cikin ladabi ta isa kusa dashi "yaya harka dawo? "Eh nadawo nusaiba ina mama take ? "Tashiga nan makwabta zata kar6oma Aunty Hussaina kunun aya, tunda kashigo ni bari na wuce islamiyya dama nafara latti baniso inbar aunty ita kad'ai shiyasa nad'an jinkirta.
"To shikenan maza kitafi ga wannan kihau napep dan kiyi saurin zuwa yafad'a yana mi'komata d'ari biyu hannu biyu tasa ta kar6a sannan tayi godiya tawuce.
Kujera jabeer yajawo ya zauna gaban Hassana suna fuskantar juna "sannu ya jikin naki,? "Da sauki, tafad'a tana cire Hannunta daga kwanon d'anwaken, buta ta d'auka tanufi bakin maguji domin wanke hannunta, jabeer yabita da kallo har cikin ranshi yake matu'kar tausayamata ganin yanda tarame sai wani uban fari datakara.
Umma ce tashigo da sallama, dai-dai lokacin Hassana tagama wanke Hannunta zata mi'ke Umma tayi saurin kamata ta mi'ke tana ri'ke da ita har kan tabarma datake ta zaunar da ita, tana jeramata sannu a zuciyarta kuma fall da farin ciki ganin takusa samun jika.
Dai-dai lokacin kuma aka kira sallar la'asar saboda haka jabeer besamu damar yin wata magana da maman tashiba yad'auki buta yayi Al'wala ya wuce masallaci.
**              **                  **
Zaune yake gurin wani sha'katawa, gurin ya 'kawatu da itatuwa da flower's masu kyan gani da dad'in 'kamshi, mutane ne kala-kala a gurin wasu mata da mijine da yayansu, wasu kuma saurayi da budurwa, kowa harkar gabanshi yakeyi babu Wanda yadamu da wani, shikam yakasa zaune yakasa tsaye kad'an-kad'an yaduba agogon hannunsa, dan 'karfe hud'u sukayi da ita zatazo nan suhad'u amma gashi har hud'u da rabi kome kama da ita be ganiba.
Wayarshi ya d'auko yayi 'yan danne-danne sannan yakara a kunne, wani abin takaicin cemasa akayi switch off, wani mugun takaici ya lullu6eshi jiyayi kamar ya kwala wayar da 'kasa dan haushi.
Dai-dai lokacin me napep ya sauketa, sanye take da ba'kin wando pencil da jar riga iyakar cinya, wacce ta d'ameta tafiddo duk wata sura da Allah yayimata, sai wani yala-yalan gyale kalar ba'ki datayi rolling dashi kafarta jan takalmine mai matu'kar tsini, hannunta ri'ke da waya 'kirar iPhone 7 yayinda d'ayan hannun take ri'ke da poss kalar ja, duk illahirin gurin ya buge da 'kamshin tsadadden turarenta, wani 'katon ba'kin glass ne rufe da kwayar idanunta wanda ake kira no respect, cikin takunta na yanga da 'kasaita ta iso inda yake  lokacin yayi zurfi cikin tunanin rashin zuwanta besan ta iso gurinba saida taja kujera ta zauna 'kamshin turarenta ya daki hancinta sannan ya maida dubansa gareta.
"Haba zuby saboda me zaki shanyani anan aka gayaki banida aikin yine tun d'azu nake kiran wayarki gaba d'aya a kashe, cikin tsananin 6acin rai da d'aga murya yake mata magana.
Tashi tayi tsaye tare da d'age bakin glass d'inda ya rufe kwayar idanunta ta d'aga mai hannu "dakata Hafiz karfa kace zaka d'agamin murya, kasani da da yanzu ba d'aya bane, sabodame zakari'kamin shouting a kunne banison hayaniya
Hafiz sakin baki yayi yana kallon zuby yanda take gayamashi magana son ranta, wanda a da koda kud'i aka sakata bazata iya gayamai hakaba.
A zuciyarshi yace lallai dole inyi maganinki zuby, amma a zahiri sai yayi murmushi "sorry abin bekai hakaba yanzu dai zauna muyi magana ta fahimta
Komawa tayi ta zauna ta d'ora 'kafa d'aya kan d'aya tana taunar cingam irinnan gogaggin yan duniya.
"Kingane zuby abinda yasa nakiraki nace muhad'u anan kinga yanzu rabona dake kusan wata biyu kenan kuma kinriga kin sabamin da lallausan jikinki, kin shagwa6ani da shan daddad'ar zumarki 'kauracewarki gareni ba 'karamin cutar dani yakeba yakamata mukoma yanda muke da.

Murmushi zuby tayi me d'auke da rainin wayo, "Hmm Hafiz aini yanzu na wuce ajinka, dan yanzu gaf nake danayi aure, kuma wanda zan aura yafika kyau kud'i wayewa, kai yafika kome wlh.
"Amma waye wannan wanda ze aureki shin besan Halinkiba, ze kwasarma kanshi bala'i "besaniba kuma baze ta6a saniba dan iya sanin da yayimin mutunniyar kirki yasanni kuma ahaka zan bayyanamai soyayyata kuma inada tabbacin ze aureni.
"Kada kaji inata baka labari ban gayama ko wayeba, ba Kowa bane face *JABEER* mijin 'kawata  Hussaina wacce tarigamu gidan gaakiya.
Tana gama fad'amai tasa hannu ta d'auki wayarta da poss d'inta dake ajiye kan table d'in tare da gyara zaman glass dinta a fuska tace kaga tafiyata sai anjima ko...
Tafiya take tana karairaya Hafiz kuwa bin bayanta yayi da kallo yanda take juya mazannai, wani miyau ya had'e 'kutt sannan ya kwalamata kira "Zuby....... A yangance tajuyo ta kalleshi tana wani shu'umin murmushi, hannu yasa Aljihu ya ciro wata agogo ya d'aga mata zaki iya sheda wannan agogon da kuma ranar da kika yaddata.
Wani mummunan fad'uwar gaba taji lokacin data tuno da ranar data kashe Hussaina bayan ta dawo gida tanemi agogon tarasa.
.Dawowa tayi ahankali jikinta yayi sanyi, "Hafiz ina kasamu agogona?
"Murmushi Hafiz yayi me cike da samun nasara "Zuby kenan idan ke sammako kikayi wani a hanya ya kwana, kince zaki auri jabeer ko, saboda kinaso zaki aureshi shine kika raba matarshi da duniya, kina tunanin bansan ke kika kashe Hussainaba.
Kyarma Zuby tafara 'kirjinta na dukan tara-tara ta kalli jabeer, sannan ta dake ta nuna ba Alamar tsoro tattare da ita tace "of course, bazan tsaya jayayya dakaiba Nina kashe Hussaina kuma bazan ta6a danasaniba saboda Hussaina tashiga gonatane ta hanyar rabani dakai, Wanda a lokacin banida wanda nakeso bayanka.
Amma yanzu na canja akalata zuwa ga jabeer kuma nasha Al'washin saina aureshi.
Murmushi Hafiz yayi tare da mi'kewa tsaye yayi taku ahankali yazagayo bayan kujerar datake zaune yadafa bayan kujerar sannan yadu'ko saitin kanta yace
"Karya kike Zuby nasan har yanzu kina sona, kuma inada tabbacin babu wani namiji daze maye gurbina a zuciyarki.
Kawai shawarar dazan baki shine :nasan ke mayyar kud'ice kuma nasan badan kome kikeson jabeer ba sai dan kud'insa.
Idan kinajin shawara me zai hana mu had'a kai inrufa maki asiri idan kin auri jabeer shima ki aikashi inda kika aika matarshi ki kwashe mana dukiyarsa muyi aure mucigaba da jin dad'inmu. Yana gama fad'in haka yadawo kan kujera ya zauna yana fuskantarta.
Wani shu'umin murmushi tayi tacigaba da taunar cingam d'inta sannan tayima Hafiz wani sakaran kallo "baka isaba Hafiz bakuma zeta6a yiyuba kura da shan bugu gardi da kwace kud'i.
Ai dukiyar jabeer tawace ni kad'ai tafad'a tana nuna kanta,
Murmushi Hafiz yayi sannan ya d'auki wayarshi yayi yan danne-danne saiga duk magan-ganun da zuby tayi ashe yayi recording _Of course bazan tsaya ina jayayya dakaiba nina kashe Hussaina kuma bazan ta6a danasaniba, saboda tashiga gonata_ latsa wayar yayi ya kashe sannan ya maida Aljihu, zaki iya fansar kanki da shawarar danabaki idan kuma kinyi gardama zan mi'ka wannan recording d'in ga hukuma.
Take zuby takashi ta duri ruwa ta dad'e da sanin shu'mancin Hafiz tsaf ze kaita a hukuma kuma ya wanke kansa. "Kada ka damu na amince da shawararka amma dan Allah ka goge wannan rocording d'in, tafad'a tana kyarma kamar wacce akayima wanka da ruwan 'kan-'kara.
"Zan goge kada kidamu fatana kawai mucigaba da harka kamar yanda muka saba.
"Indan wannan ne kada kadamu muje koh.
Owk muje kawai yafad'a, mota suka nufa gidan gaba Hafiz yabud'ema zuby tashiga sannan ya zagaya mazaunin driver suka d'au hanya.
Gidan Hafiz suka sauka ranar sun she'ke ayarsu suduka sun nunama juna sunyi missing d'in junansu.
**              **                  **Sai bayan sallar isha'i jabeer yadawo lokacin ya iske Hasaana tagama sallah mama ta zubo mata tuwon masara da miyar ku6ewa ga manshanu, nan Mama ta kalleshi "zakaci tuwon ne azuboma "Eh mama ai kinsan tuwo mutuminane, mama da kanta tashiga kitchen ta zuboma jabeer tuwon
Bayan sun kammala ne sukayi haramar tafiya gida, mama ta kalli jabeer "shin ka kar6o sakamakon kuwa a asibitin naji har zaku tafi bakayiman bayanin komeba
"Eh mama na kar6o wallahi ba wani abu bane ke damunta (Malaria) zazza6in cizon sauro, amma ga magun-guna na siyo likitan yace inshaAllah indai tanasha zata samu sauki.
Fara'ar mama tad'an ragu dan ita a tunanunta cikine da Hassana, amma saitaji sa6anin haka "to Allah sauwa'ke Allah maidaku gida lafiya, nan sukayi bankwana suka d'au hanyar gida.
Suna isa sukayi horn megadi yabud'emasu get jabeer nayin parking Hassana tafito da sauri tanufi d'akinta tarufe da key kamar yanda tasaba tayi kwanciyarta, tunanin Hussaina yafad'o mata a rai batasan lokacin data fashe da kukaba,
Shikenan ni yanzu haka zancigaba da zama, gidan yar'uwata ba gidan mijinaba. Ya Allah ka kawomin mafita ina cikin tsaka me wuya.
.
Washe gari da misalin 'karfe goma na safe jabeer ne zaune office d'insa da wasu fayiloli yanata faman wasu rubuce-rubuce, nocking d'in 'kofar akayi ahankali, d'agowa yayi ya kalli 'kofar sannan ya maida hankalinsa ga aikinsa, kara nocking akayi karo na biyu, aje biron hannunsa yayi sannan yabada izinin shigowa.
Da sallama tashigo office d'in sanye take da riga da siket na less, wad'anda suka kame mata jiki, sai wani madaidaicin gyale data yafa har saman kai dan kan nata bako d'an kwali, 'kafarta sanye cikin plate shoe,
Kallonta jabeer yayi daga sama har 'kasa yace "zuby kece tafe da wannan lokacin,
"Nice tafad'a tana murmushi.
"Bissmillah zauna mana yafad'a yana nunamata kujera.
Ba musu ta zauna tana wani sakar mashi wani shu'umin murmushi, bayan sun gaisa tace "dama zowa nayi inyima gaisuwa dan lokacin da'akayi rasuwar bani gari, gaskiya munyi babban rashi tafad'a tana matsar kwallan munafinci, Hussaina 'kawatace banida tamkarta nayi babban rashi.
A mamakance jabeer yake kallonta, kindai manta Ai Hassanace tamutu ba Hussaina ba.
Wani mummunan fad'uwar gaba zuby tayi lokacin data tuno da shawarar databa Hussaina na cewa Hassana ta zauna maimakinta.
Inkau hakane ba shakka Hassana bata gayama jabeer ba itabace Hussaina idan kuwa hakane akwai aiki babba agabanta.
Jabeer ya kalleta "naji kinyi shiru me kike tunani, firgigi tayi kamar wacce tafarka daga bacci, ah bakome, nizan wuce Allah bada ha'kuri. "Ameen kawai jabeer yace sannan yacigaba da aikinsa.
Jiki ba lakka Tabar office d'in, daga nan gida kawai tawuce zuciyarta cike da tunani barkatai.
Zuby a d'akinta sai safa da marwa takeyi, tana sa'ke-sa'ke a zuciyarta "tabbas Hafiz shine babban matsalata idanko hakane  dole in d'au mataki kanshi.
Wani mugun murmushi tayi lokacin wanda koni zee bansan ma'anar yinsaba.
Wayarta ta d'auko ta danno sunan Hafiz bugu d'aya ya d'auka "hellow zuby na yadai, akwai labari ne?
"Sosaima kuwa akwai labari me dad'in sauraro, inaso muhad'u a park dinda muka saba had'uwa.
"Owk ba damuwa kamar 'karfe nawa?
"Yanzu-yanzu kome kakeyi ka ajiye kataho dan abari ya huce shike kawo rabon wani.
"Owk ganinan zuwa.
Saurin fad'awa wanka zuby tayi ta she'ka wanka, tana fitowa batare da 6ata lokaciba lotion kawai ta murzama jikinta sannan tasaka irin 'kananun kayan data saba sakawa, tana fitowa bakin titi ta tsaida me napep tagayamai inda ze kaita, cikin mintinan dabasu wuce talatinba ta iso gurin ta sallami me napep, wayarta ta fiddo da niyyar takira Hafiz ta tambayeshi ya isone hangoshi tayi jingine jikin motarsa yana sakar mata murmushi, itama murmushin tayi sannan tanufi gurin wasu kujeru kai tsaye ta zauna, shima Hafiz nan yadawo ya zauna kusa da ita a 'kagare dayaji labarin datazo mai dashi.
Kusan minti biyar da zamansu zuby batayi maganaba, a 'kagauce Hafiz ya kalleta inajinki zuby, na bud'e kunne ina sauraron jin daddad'an labari kinyimin shiru.
Kallonshi tayi daga sama har 'kasa "owk kada ka damu nad'an gajine inaso in huta tukun, bari naje can na kar6o mana drink's mud'ansha konaji sanyi-sanyi,
"A'a kibari in anso mana Hafiz yafad'a yana mi'kewa tsaye,
"A'a kabarshi kawai zan amso saurin yin gaba tayi dan kada Hafiz d'in yacemata a'a.
Haka ta isa gurin siyar da drink's kwalbar lacasera biyu ta kar6o duk idanun Hafiz kanta dan tsakanin gurin dasuke da gurin siyan drink's d'in ba nisa.
Gurin dawowa maimakin tabiyo hanya street saita kauce ta inda be ganinta,  tad'an jima sannan tayo zagaye tadawo da lemun guda biyu hannunta.
Zama tayi sannan tabud'e kwalba guda tami'kama Hafiz, itakuma tabud'e guda tanasha suna labari nan takeba Hafiz labarin cewa taje office d'in jabeer kuma ya amince da aurenta, wani dad'i yaratsa zuciyar Hafiz, dai-dai lokacin kuma yagama shan lemun lacasera dake hannunsa ya jefar da robar.
Mi'kewa zuby tayi tsaye tare da kecewa da wata irin dariya tace "anzo gurin kasani Hafiz kwananka ya'kare yau zakayi bankwana da duniya, zuge Jakarta tayi tafito da wata 'yar'karamar kwalba tace "gaga wannan shine ake kira da silent killer, kuma ahine na zubama a lemun dakasha, saboda haka zaka iya zuwa gida karo'ki Umma yafiya kafin ka margaya barzahu, dan baya kisa farat d'aya, ni kaga tafiyata.
Tana gama fad'amashi tami'ke takama hanya tayi tafiyarta.
Hafiz kuwa duk illahirin jikinsa kyarma yake, yasan shu'umancin zuby kome tafad'a zata iya aikatawa, da sauri ya suri makullan motarsa yabar gurin.
'

Cikin tsananin rud'ani da tashin hankali Hafiz ya isa gida, falon mahaifiyarsa ya zube yanata mai-maita istigifari, a zuciyarsa yana cewa "wannan bala'i dame yayi kama, gashi yanzu son zuciya yajamin na jefa kaina ga halaka, 'kanwarsa ce tashigo da sallama ganin yayan nata kwance da alama yayi nisa a tunani ga hawaye kwance a idanunsa dan alamu sun nuna besan da shigowar wani mahalu'ki a d'akinba.
Saida ta matso gaf dashi tadafa kafad'arshi "Yaya lafiya kuwa na ganka haka da Alama kukama kakeyi, saurin tashi yayi ya goge sauran hawayen dasuka ma'kale a idonshi ya 'ka'karo murmushin 'karfin hali yace *Bakome  Zee kada ki damu kaina ne kemin ciwo.
"Kuma shine ka zauna a gida, yakamata kaje asibiti, "to 'kanwata zanje jeki shirya saimu tafi tare dan kan yana matsamin sosai bazan iya driving ba, "owk to ba damuwa bari na sanarma Hajiya kafin mutafi, saurin ri'ko hannunta Hafiz yayi kada kije tana bacci kuma kinsan doctor yahana atasheta idan tana bacci, muje kawai idan mundawo mun gaya mata.
A harabar gidan suka bud'e mota suka shiga Zee ke driving Hafiz kuma na zaune gefenta lokacin yaji cikinsa na juyamasa, ahankali ciwon ke gaba, zee kuwa hankalinta ya matu'kar tashi ganin yanda yayan nata ke magowa gashi har wani kumfa yafara fitowa a bakinsa, wani irin mahaukacin tu'ki tari'kayi dan ikon Allah kawai yakaisu asibitin, suna Isa aka kar6eshi Emergency aka nufa dashi, nan lokitoci suka rufa akanshi, yayinda zee ketai kai komo a bakin 'kofar d'akin da aka shiga dashi tanata sharar hawaye dan ganitake kamar za'a fito acemata Hafiz ya mutu dan yanda aka shiga dashi ba alamar rai tattare dashi.

         *washe Gari*
Da misalin 'karfe goma na safe, Zuby na kwance kan gadonta da waya hannunta tana chat a wani tambad'add'en group data bud'e maza da matane aciki ba abinda ake a group d'in sai maganganun batsa da tura  blue film da sauransu, tana chat din ta Lula duniya tanayi tana matse 'kafafu dan tsabar jaraba, da kuma sauraron voice message d'inda wani tsagera a group d'in yaturo wanda shima Admin ne a group d'in.
ganin wayarta ta tsaya cak tasan kirane ze shigo, tun kafin kiran yashigo tafara buga uban tsaki dan ganin za'a katse mata jin dad'i, amma da mamakinta sai taga number Hafiz a firgice tami'ke tsaye, sai lokacin tatunafa tasaka mashi guba a lemu kuma yasha tasan ba tantama bekwana da raiba, to amma kuma taya aka kirata da number shi.
Tana cikin wannan tunanin har kiran ya tsinke, batare da 6ata lokaciba aka kuma kira karo ba biyu, jiki a sanyaye ta danna ok sannan takara a kunnenta.
"Hello" Zuby tafad'a cikin muryar fargaba.
A d'aya 6angaren Zee tafashe da kuka tare da cewa "Zuby koh?
Zuby ta amsa da "Eh nice amma wacece ke?
Zee ta'kara fashewa da kuka, sannan tace "ni 'Kanwar Hafiz ce naga kece mutum ta 'karshe da kukayi waya dashi jiya, cuma naga call log d'insa duka sunanki yafi yawa da Alama akwai sha'kuwa tsakaninku shine nakiraki in gayamaki jiya da dare Allah yayima Hafiz rasuwa.
"What Zuby tafad'a kamar tana cikin irin firgicinnan, sannan tadoka uban salati "Allah Sarki Allah ji'kan Hafiz,
"Ameen" Zee ta amsa kafin ta tsinke kiran.
Zuby kuwa tana kashe wayar rawa tafara takawa tana rera wa'kar ado gwanja inda yake cewa _Me nemam jini yaje kwata, niko bani zuwa bikin daba mata, mata.....mata....._ ta'karashe wa'kar tana nuna kanta "saini zuby duk wanda yaja dani yajishi kushewa, wata shegiyar dariya tayi sannan tafad'a toilet ta she'ka wanka.
Tana fitowa ta tsaya gaban mirror ta watsa wani matsiyacin make up a fuskarta na marassa mutunci, wasu watsatatsin kaya tasaka dan basuda maraba da shigar arna.
Kai tsaye gidan jabeer tayima tsinke, tana isa me gadi yayimata sannu da zuwa ta wuce dan yasanta kwanaki tana yawan zuwa gidan.
Hassana kuwa ganin tad'anji 'karfin jikinta yasa yau tashiga kitchen tagama girki tana d'aukowa daga kitchen tana jerawa kan dining, tagama jera kome sanan ta tafi da niyyar takoma d'akinta dan tasan jabeer yana gab da dawowa kuma bataso yadawo ya isketa a falo.
Ido hud'u sukayi da zuby wacce ko alama bataji lokacin data shigoba, ba 'karamin fad'uwar gaba Hassana tajiba dan ganin zuby tsaye fuskarta ba fara'a ko kad'an.


*Ido Hud'u sukayi da Zuby wacce ko alama bataji lokacin data shigoba, wani mummunan fad'uwar gaba Hassana taji dan ganinta tsaye bako far'a fuskarta kamar bata ta6a dariyaba*
Dakewa Hassana tayi duk da tsanananin fad'uwar gaban datakeyi, tayima Zuby sannu da zuwa.
Ko kallonta Zuby batayiba ta 'karaso cikin falon da takalminta da kome ta wuce kan kujera ta zauna ta d'ora 'kafa d'aya kan d'aya tana jijjigasu.
Ba 'karamin 'karfin Hali Hassana tayiba gurin d'auko lemu daga cikin pridge tahad'o da cup d'in glass ta ajiye gaban Zuby tana fad'in bismillah ga lemu.
Wani matsiyacin kallo zuby tabita dashi, sannan tayi murmushi "kinga ba wannan yakawoniba zowa nayi inyimaki ta'aziyyar yar'uwarki data mutu.
"Eyyah Hassana wai, Hassana tafad'a jikinta na kyarma.
Zuby tayi dariya, "wacce Hassana kuma? Husaaina dai,
"Innalillahi kawai Hassana ke mai-maitawa cikin zuciyarta ganin da alama zuby tasan kome.
Zuby ta tsiyaya lemu ta kur6a sannan ta ajiye, kafin tacigaba da magana.
"Hassana yau nazo ingayamaki abinda kike zaton ba wanda yasani Hatta da iyayenki,
"Kina Zaune da mijin yar'uwarki amatsayinta, zaman me za'a kira wannan, zaman dadiro ko karuwanci..... Hmm.......
Hassana tunda Zuby tafara magana wani irin gumi ya karyo mata, zufa ta jiketa dukda sanyin a.c daya gauraye d'akin.
Tayi 'karfin halin cewa "Haba Zuby wace irin magana kike fad'i haka kamar baki sanniba, nicefa Hussaina 'kawarki 'yar'uwatace Hassana ta mutu baniba..........
"Dakata Hassana Zuby tafad'a cikin d'aga murya, "kina tunanin bansan komeba, to bari kiji ingayamaki abinda ke kanki baki saniba.
"Nice nan naba Hussaina shawarar ki zauna a matsayinta kafin tadawo daga inda zataje, nasan tayimaki 'karyar zataje biki, Hmm to ba wani bikin dataje nasan kinsan tsohon saurayinta Hafiz, to wurinshi taje, nikuma a duniya banida wanda nakeso sama da Hafiz, nayi matu'kar farinciki lokacin da Hassana ta gayamin anyimata aure   , saboda nasan hankalin Hafiz ze karkato gareni, amma wani abin takaici dukda aurenta bata rabu da Hafiz ba.
Ban 'kara shiga tashin hankaliba sai ranar danazo gidannan Jabeer yayimin kyautar ma'kudan kud'i, kuma sai naji zuciyata ta karkata gareshi.
Hakan yasa nabata shawara akan tanemi ki zauna gidannan amatsayinta dan tasamu damar zuwa gurin tsohon saurayinta Hafiz, kamar yanda tagayamin yanaso su had'u, yayinda nikuma nayi amfani da wannan damar na rabata da duniyar dan insamu in mallaki jabeer,
Cike da tashin hankali Hassana ke nunan Zuby "dama kece kika kashe Hussaina.?
Zuby tayi murmushi "ki dakata mana, me kikeci nabaka na zuba, yanzuma dana gaya maki aiba matsar bakina kikayiba.
Cikin tsananin tashin hankali Hassana tace "Allah ne ya matsi bakinki kuma sai kinyi danasani, zuby batabi ta kantaba tacigaba da kora mata bayani.
"Hmm nayi tunanin mutuwar Hussaina zatasa ki tona kome ki koma gida, nikuma da haka insamu damar auren jabeer.
Tami'ke tsaye tad'anyi taku biyu zuwa ukku sannan tacigaba da magana "Ranar danaje office d'in jabeer da niyyar inbayyana mashi son danakemashi sai ya nunamin aishi ba matarshi ce tamutuba.
Hmm inajin haka nasan baki fad'i gaskiyaba, kuma kincigaba da zama a matsayin matar jabeer, saboda haka ina baki shawara daki gaggauta tonama kanki asiri kuma kibar gidannan, nice yadace nazauna gidannan koda ban auri jabeer ba, tafad'a tana nuna kanta.
Tana gama fad'in haka tatafi da niyyar barin gidan har takai bakin 'kofa ta dawo tace kuma kada ki kuskura ki gayama wani maganganun dumukayi domin yin hakan barazanace ga rayuwarki, idan kuma bahakaba kema zakibi yar'uwarki inda taje.
Zuby natafiya Hassana tafad'a d'aki tasa key tarufe tafara rizgar kuka tana had'a kayanta cikin trolley, dan wani mugun tashin hankali tashiga Wanda tunda take duniya bata ta6a Shiga irinsaba.
.
.Da misalin 'karfe ukku dai-dai jabeer yashigo gidan, kai tsaye d'akinsa ya wuce ya watsa ruwa ya canja kayan jikinsa Zuwa marassa nauyi, sannan yafito zuwa falo dan yaga yau da Alama akwai abinci gidan.
Zama yayi kan dining yazuba macaroni jalouf da Hanta, yanaci abincin nakaimasa karo, saida yaji ba sauran guri a cikinsa sannan yanufi pridge ya d'auko lemu ya tsiyaya a cup yasha , yajima zaune kan dining yana danne-danne a wayarsa kafin yatashi yakoma kan kujera da remote control hannunsa yana 'ko'karin kunna tv yajiyo sheshshekar kuka daga d'akin matarsa, saurin ajiye remote d'in yayi yanufi d'akin dukda yasan idan zeyi juyin duniyan nan da wuya ta bud'e barantana kuma tafad'a mashi matsalarta.
Nocking yafarayi ahankali kafin yakira sunanta, "Hussaina ki bud'e mana bekamata ace ki kulle kanki a d'akiba kuma kina cikin damuwa waye zaki fad'awa kiji dad'i.
Ga kuma jikin naki har yanzu be gama warwarewaba.
Jin maganarsa yasa ta'kara fashewa da kuka, da kamar bazata tanka ba barantana ta bud'e amma sai wata zuciyar tabata shawarar ta bud'e kawai.
Haka tatashi jiki ba laka ta bud'e 'kofar, ganin yanda idanunta suka kad'a sukayi ja, ya tabbatarmashi da ta dad'e tana kukan, wani irin tausayinta ya dira a zuciyarshi, kama hannunta yayi suka koma cikin d'akin ya zaunar da ita gefen gado sannan shima ya zauna dai-dai wannan lokacin kuma idanunsa suka sauka kan trolley data had'a kayanta ciki.
Juyowa yayi ya kalleta da mamaki a fuskarsa, yace "wannan jakar kayanfa lafiya dai.
Shiru tayi dan batasan irin amsar da zata bashiba.
Saida yakuma tambayarta karo na biyu tare da ru'kota yana 'ko'karin had'a jikinshi da nata,
Saurin kwacewa tayi tare da mi'kewa tsaye tafashe da wani sabon kukan, tana ja da baya kamar tana tsoron jabeer d'in.
Da mamaki shima ya mi'ke yana tunkararta "Haba Hussaina danmi kike guduna baki 'kaunar inta6a jikinki ko kad'an amatsayina na mijinki...........
"Kaiba mijina bane jabeer, haka kuma niba matarka bace, matarka ta mutu tsawon wata ukku dasuka wuce,
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un jabeer yafad'a "Hussaina anya kina cikin hayyacinki kuwa, nine yau zakice ba mijinkiba,
ba shakka lallai 'kila kinfara irin shaye-shayennan na zamani.......
"Ko d'aya jabeer ban ta6a shan komeba, kuma dukkan abinda nafad'ama cikin hankalina nake......
Yanzu zanbaka labarin abinda baka saniba, koda kuwa yin hakan nima ze zama 'karshen rayuwata kamar yanda 'yar'uwata tabar duniya.
Wani sabon kuka tafashe dashi, saida tayi me isarta tayi shiru dan kanta batare data samu me rarrashintaba, saboda jabeer yariga ya shiga wani hali, so yake kawai yaji asalin gaskiyar abinda tafad'a wanda zesa ya yarda cewa ita ba matarshi bace kamar yanda tafad'a.
Nan ta kwashe labarin abinsa suka ahirya tsaf da Hussaina lokacin tana raye, na zamanta gidan amatsayin Hussainar wanda daga tafiyarne bata dawoba sai dai aka kawo gawarta, amma bata gaya mashi wacce takashe Hussainarba, sannan kuma bata gayamashi cewa gurin tsohon saurayinta tajeba, tadai gayamashi taje bikine kamar yanda ita Hussainar tagayamata.
Saukar wani wawan mari taji a fuskarta, wanda har saida taga wasu taurari, dafe kuncinta tayi ta zube 'kasa tana kuka,
Shima jabeer d'in hawaye yake, yarasa inda zesa kanshi, innalillahi kawai yake mai-maitawa, yana fad'in *Allahumma ajirni fi masibati wa khalibli khairan minha*
"Hassana kin cuceni, kinsa na aikata abinda banta6a aikatawaba, amma ai Allah yana gani batare da sanina na aikataba, komiye kece sila.
Hassana dai bata 'kara maganaba tun marin dayayimata kuka kawai take tana dana sanin amincewa da 'kudirin 'yar'uwarta.
A fusace jabeer ya d'auki trolley data had'a kayan yakai mota, sannan yadawo ya figeta itama ya bud'e motar yajefata kamar wasu kayan wanki, sannan yatayar da motar yafara dokama megadi horn, da gudu yazo ya bud'e masu get jabeer ya kwashi hanya da gudun tsiya.
.
Wani mummunan fad'uwar gaba Hassana tayi lokacin dataga jabeer yayi parking cikin harabar gidansu, amma a zuciyarta saitaji ta dake akan kome ze faru 'kara ya faru da zaman datake, wanda ita kanta batasan makomarsaba.
A fusace jabeer yafito daga motar sannan ya bud'e but ya d'auko trolley yanufi cikin gidan beko kalli inda takeba.
Da sauri tabi bayanshi tana sharar hawaye har tana had'awa da d'an gudu-gudu.
Momy da daddy suna zaune falo suna kallon labarai a tashar aljazeera, suka jiyo sallamar jabeer, daddy ne ya amsa yana 'ko'karin fita yaga jabeer d'in yashigo janye da trolley, komawa yayi ya zauna yana kallon jabeer cike da mamaki harya 'karaso yasamu guri ya zauna dai-dai saitin 'kafar Daddy yana matsar kwalla.
Cike da alamomin tambaya Daddy ke kallon jabeer, Momy ma da alama hakanne a fuskarta.
Suna shirin tambayarsa saiga Hassana tashigo da kuka share-share a fuskarta, kamar wacce aka jeho tafad'i gaban Momy da Daddy tana cigaba da kukanta.
Daddy ne yayi 'karfin halin tambayarsu "lafiya meke faruwa kukazo haka birkice, wani kuka Hassana ta'kara fasawa dan tasan yau kashetane kad'ai Daddy bazeyiba, amma ta kwammace hakan da zaman datake a gidan jabeer.
Suduka ba wanda yayi magana, shima jabeer d'in hawayene ke zarya a kumatunsa, yama rasa ta inda ze gayama Daddy abinda ke faruwa.
Daga 'karshe dai yayi 'karfin hali ya kalli Hassana yace "ki maimaita masu abinda kika fad'amin.
Daddy ya watsa mata wani kallo wanda yasa saida Hantar cikinta ta juya, sannan tayi saurin saddar da kanta tana hawaye, dan tasan babu wasa ko kad'an tattare da Daddy saboda haka batare da 6ata lokaciba ta fayyace masu kome kamar yanda tafad'ama jabeer kafin suzo nan.
Lokaci d'aya Momy da daddy suka saka salati, kafin Daga bisani d'akin yayi shiru bakajin kome sai sheshshekar kukan Hasaana, wacce jira take kawai taji anrufeta da duka, dan tasan ta caccanci abinda ma yafi haka.
Duk zafin Daddy da d'aukar matakinsa kan abu, yau kasa koda motsi yayi, sai Momy ce tayi magana "Amma Hassana baki kyautaba, itama abinda kawai ta iya fad'i kenan tayi shiru.
Mi'kewa daddy yayi tare da d'aukar makullan motarsa ya kallesu yace "kutaso ku dukanku ku sameni a mota, yana gama fad'i yayi gaba da sauri yabud'e motarshi yashige zuciyarsa cunkushe da ba'kinciki da takaici.
Minti biyar ba'ayiba sai gasu sun fito, gidan gaba Daddy ya umarci Jabeer ya zauna Hassana kuma da momynta baya.
Sannan daddy ya tayar da motar, Malam bala me gadi yabud'e masu get da sauri yana masu Allah kiyaye.
**              **                 **
Zaune suke gaban wani dattijon mutum Wanda kallo d'aya zakayima fuskarsa ka tabbatar da kamala da ilimi tattare dashi, dan ya ajiye sunnah a fuskarsa (gemu) bayan sun gaisa Daddy yayi Mashi bayani dukan abinda ke tafe dasu.
Malam Kasim yayi matu'kar mamakin jin wannan abu daya faru amma dayake shi addini me saukine kuma ya kawo yanda za'a warware kowace matsala saboda haka yafara yimasu bayani bayan yayi addu'a da salatin annabi (s.a.w)
"To kamar yanda kuka Sani tunda ita wannan yarinya dama ba matarsa bace bamu bu'katar ace sai yasaketa, amma tunda har wani abu na mu'amalar auratayya yashiga tsakaninsu, to zatayi istibira'i idan tagama zata iyayin aure.
*(Istibira'i yana nufin zama da wacce tayi zina takeyi a gida na tsawon wasu watanni batare data 'kara kusantar zinaba, dan ta tsarkake kanta kafin tayi wani auren)*
Nan sukayima Malam godiya sannan suka koma gida, Hassana tayi matu'kar mamakin yanda iyayenta suka kar6eta batare da sun nuna matsanancin fushi akantaba.
Tayi mamakin yanda Daddy ya umarci data wuce d'akinta tayi wanka kuma tacigaba da istigifari domin shi Allah gafurun rahimunne.
Haka tawuce d'aki sukuku kamar kazar da kwai ya fashemawa a ciki.
Tana shiga d'akin kuwa tafad'a kan gado tafashe da wani sabon kuka dan tunowa datayi da Hussaina wacce tare sukayi rayuwa a d'akinnan amma yanzu gashi bata raye.
Zuby tafad'o mata arai, a zuciyarta ta rin'ka banka mata Allah ya isa dan duk halin datashiga itace sila, sannan kuma taraba 'yar'uwarta da duniya.

.
             *Bayan Sati Biyu*
Zaune yake yahad'a uban tagumi duk abubuwa sunbi sun dagulemai, ba abinda yake tunani sai tsawon lokacin da suka d'auka suna zaman aure da Hassana wadda duk  a tunaninsa Hussainace wai ashe Hussainar ce ta mutu ba Hassanaba, wasu siraran hawaye suka zubo kan kumatunsa, beyi 'ko'karin gogewaba haka yabarshi yanata zuba wani na bin wani.
Sallamar da ake dokawa daga bakin 'kofar falon ce tasa yayi saurin goge hawayen dake fuskarsa tare dayin 'karfin halin amsa sallamar.
Yauma kamar kullum sanye take cikin irin matsiyatan kayan data saba sanyawa, duk illahirin surar jikinta a bayyyane take.
Da mamaki yabita da idanu yana kallonta ganin wani shu'umin murmushi datake sakarmai, kafin yayi magana ta ida 'karasowa cikin falon ta zauna kan d'aya daga kujerun dake zagaye da falon sannan ta d'ora 'kafa d'aya kan d'aya kafin tafara magana.
"Da farko dai jabeer ina 'kara yima ta'aziyyar matarka Hussaina data rigamu gidan gaskiya, sannan kuma ina jajantama game da cin amana da suka 'kullama tsakaninta da 'yar'uwarta sukasa kayi *AUREN TAGWAYE*  batare da saninkaba.
Ta numfasa sannan taci gaba da magana "kada ka damufa da wannan Allah be ta6a kama bawansa da laifin da besaniba _(niko zee nace kaji su zuby kamar ansan Allah)_
Jabeer kuwa tunda tafara surutunta 'kala be cemataba ita kad'ai keta zuba shikuwa binta kawai yake da ido.
Tasowa tayi daga inda take zaune tana wani girgiza tana rangaji harta 'karaso gabanshi ta dur'kusa.
"Jabeer akwai wata magana danazo da ita amma bansan ya zaka d'auketaba.
Tayi shiru tare da zubamai mayataccin idanunta alamar tanason jin tabakinsa kafin tacigaba.
"Ina jinki kawai jabeer yabata amsa atakaice sannan tacigaba damagana,
"Jabeer na dad'e ina dakon soyayyarka acikin zuciyata tun kafin ka auri Hussaina, ganin tana aminiyata yasa na ha'kura ban ta6a nunamaba, domin masu iya magana sunce ana barin halak kodan kunya, amma yanzu tunda babu ita, kaga zaka iya aurena in mayema gurbinta, kuma..........
Saurin d'aga mata hannu yayi "dakata dan Allah zuby, yafad'a cikin 'kunar rai, dan tunda tafara magan-gamunta jiyake kamar tana watsa mashi garwashin wuta acikin zuciyarsa.
"Kada ki kuma tunkarata da wannan maganar danni yanzu ba abinda ke gabana kenan ba, zuby kisani na tsani rayuwa da wata mace a yanzu saboda haka kada kisa ran zan iya rayuwa dake.......
Murmushi tayi  "Hmm nasan ciwon abinda Hussaina tayimakane yasa ka furta wannan kalamin, amma mata ai mune abokanin rayuwa, babu namijin da baya bu'katar mace kusa dashi matu'kar yanada cikakkiyar lafiya.....
"Fita dan Allah, ki fitarmin daga gida kina 6atamin lokaci, yafad'a yana nuna mata 'Kofa,
Murmushin takaici Zuby tayi a zuciyarta tace "wannan wane irin zuciyane dashi tun bayan wata biyu dasuka wuce naketamai hannunka me sanda dan yagane ina sonshi, gashi har yau na bud'a baki na gayamashi sirrin dake raina amma gashi yana nuna halin ko inkula akaina, tabbass akwai aiki babba agabana.......
"Get out, maganar jabeer ce tadawo da ita daga dogon tunanin datake, wacce har saida tayi 'yar'karamar razana, sannan ta kalleshi ta jefeshi da murmushin takaici kafin tasa kai tafice daga gidan.
Tana fita yabi bayanta, megadi na zaune bakin aikinsa, ganin jabeer yasashi tasowa yana mashi barka da fitowa, fuska ba annuri jabeer yace "daga yau idan ka kuma barin wannan yarinyar shigowa gidannan bakin aikinka...
Me gadi yayi saurin dafe 'kirji tare da fiddo idanu waje, jin an ambaci aikinsa, jiki na kyarma yace "inshaAllah ranka ya dad'e hakanma bazata faruba.
Be tsaya sauraronsaba yakoma cikin gidan, yana Shiga falo yafad'a kan kujera, tinanin rayuwar da yayi da Hassana tafad'o mashi a rai.

.
Tundaga wannan lokacin Zuby ke zarya gidan jabeer amma koda wasa me gadi baya barinta Shiga, idan zatayi juyin duniyar nan be barinta, data gane haka saita koma zuwa office d'insa, nanma Haka ya gargad'i ma'aikatan gurin da kada akuma barinta tana shigowa, haka kuwa akayi dan akwai ranar datazo tundaga bakin get megadi yahanata shigowa, tayi magiyar tayi duk iya dabararta amma yahanata, kawai saita samu guri ta zauna tana kallon masu shiga da masu fita har bayan azahar bataga fitowar jabeer ba sai gurin 'karfe ukku sannan motarshi tafito, hannu rafara d'aga mashi Alamar ya tsaya, shi kuwa bemasan tana gurin ba.
Ganin be gantaba yasa tayi saurin tsaida me napep tanunamashi motar jabeer tace yabi bayanta,
Shikuwa besan tana binsaba, kai tsaye hanyar gidan iyayensa yanufa, dai-dai 'kofar gidansu yayi parking sannan yafito duk kan idanunta ya gaggaisa da mutanen dake gurin sannan yashige gidan nasu.
Bata fito daga napep d'inba wani yaro yazo wucewa takirashi, take tambayarsa ko nanne gidansu jabeer?
Yaron yabata amsa atakaice sannan ya wuce, nan ta umarci me bapep daya kaita gida tagaya mai unguwar suka d'au hanya.
        *Bayan kwana biyu*
Zuby tsaye bakin titi jikinta sanye da riga da zani na atamfa wanda rabon datasaka kaya irin wannan harta manta, sai kuma madai-daiciyar hijab d'inda tasanya wacce ta sakko mata har iya gwiwa.
Me napep ta tsaida, sannan tafad'a mashi inda ze kaita, suna isa ta hango motar jabeer a 'kofar gidan haka ya tabbatar mata da yana cikin gidan, zaure ta tsaya tana fargabar shiga amma haka ta dake tayi ta maza tayi sallama, Maman jabeer dake duke bakin gurin tana alwala ita ta amsa sallamar.
Cikin ladabi zuby tashiga gidan, Maman jabeer tabita da idanu da Alamar tambaya tattare da ita dan bata ta6a ganin zuby ba.
Ganin yanda Zuby ke kakkare fuska da Alamar jin kunya yasa Maman jabeer d'in tayimata iso har d'aki, bayan sun gaisa take tambayarta "yarinya bangekiba,
Murmushi Zuby tayi "dama jabeer ne yace ze kawoni mu gaisa, to shine mukayi waya nake fad'amashi inanan gidan yayata nan 'kasan layinku sai yake sanarmani ai yana nan gidan in'karaso mu gaisa, takare maganar tana saddar da kanta 'kasa alamar kunya, dan tunda tazo bata yarda sun had'a ido da Maman jabeer d'inba.
Aiko Maman jabeer najin haka ta fahimci inda zancen yadosa, wani irin farin ciki ya lullu6eta, dama kullum fatanta be wuce jabeer d'in yayi aureba.
Kusan minti sha biyar Zuby na zaune tana jiran ko jabeer ze shigo amma be shigoba, hakan yasa tayi sallama da mama tace zata tafi.
Mama tace "tun yanzu baki bari jabeer d'in yashigo masallaci yaje, cike dajin kunya  Zuby tace "ba kome mama sauri nake wallahi islamiyya zani nagama har lokacin yafara wucewa.
To ki gaida gida ki gaida mamanki kinji, "to zasuji inshaAllah tafad'a sannan ta fice daga gidan.
Bakin 'Kofa suka had'e da jabeer yana 'ko'karin shigowa gidan, ganin Zuby tafito daga gidan ba 'karamin tayar mashi da Hankali yayiba,
"Zuby meya kawoki gidanmu,? Ya tambayeta yana 'karemata kallo dan ba 'karamin kyau shigar datayi tayimata ba, murmushi tayi tace "meko ze kawoni idan banda tsananin so da 'kaunar danikema.
Dur'kusawa tayi gabanshi idanunta na zubar da Hawaye, "Dan Allah jabeer ka taimakeni ka taimaki rayuwata, wallahi ina sonka ina 'kaunarka tsakani da Allah, nasan kasan zafin so, kasan rad'ad'in so, dan Allah kada kacema ummanka baka sona, dan nasamu kar6uwa a wajenta d'ari bisa d'ari dan Allah kaima ka kar6eni kamar yanda ta kar6eni.
Ganin yanda take kuka tana mashi magiya gashi hartasa hankalin mutanen gurin yafara dawowa kansu yasa wani irin tausayinta ya dirarmai a zuciya besan lokacin daya kama hannuntaba yabud'e mota ya sanyata sannan shima yashiga suka d'au hanya.

Tunda suka tafi ahanya yake aikin rarrashinta, amma ta'kiyin shiru saida ya amsamata daya amince ze aureta, wani irin dad'i ya lullu6eta, tunnan tafara zumud'i tana sanar mashi da bata son asa bikin nesa idan sonsamune ayi kome nanda wata biyu.

Hidima ta kankama sosai dan ahalin yanzu saura kwana goma d'aurin auren jabeer da Zuby, 6angaren jabeer be wani farinciki dan jiyake kamar tilastashi ake auren zuby amma ko kad'an babu dai-dai da kwayar zarra na sonta acikin zuciyarsa,
Ita kuwa Zuby ta dad'e da sanyama ranta zama matar jabeer, tuni tafara tsara yanda za'a gudanar da program d'in bikin itada 'kawayenta, maganar gayya kuma ta dad'e da gama gayyato duka abokaninta maza da mata, program kusan kala bakwai ta tsara za'ayi a cewarta yanzune jabeer zeyi aure na kece raini saboda haka sati guda cif za'ayi ana gabatar da shagulgulan auren.
**                **                  **
Hassana ce kwance d'akinta, duk abin duniya yabi ya dameta ba abinda take tunani sai tsawon lokacin data d'auka gidan jabeer, cikin wannan zaman dasukayi ta la'kanci halayensa da dama ciki kuwa hada tsananin ha'kurin dake gareshi.
Juyi tayi ta gyara kwanciyarta zuwa rigin-gine ta 'kurama silin d'in d'akin ido tsananin so da 'kaunar jabeer na 'kara mamaye zuciyarta.
Wani 'kawataccen murmushi tayi, sannan tatashi zaune ta d'auko wayarta chat ta hau tana dubawa, wanda rabon data hau and'au lokaci me tsawo.
Best group d'inta tafara shiga na *Ciwon 'ya mace* tana duba d'umbun message d'inda ta taras kwatsam idanunta sukayi kaci6is da hotunan wasu amarya da ango da aka turo ana gayyatar duk wanda yasamu damar halatta, ganin yanda aketa maganar bikin da kuma yanda ake fad'in kalaluwan program d'inda za'ayi yasa taji tana sha'awar bud'e hotunan amarya da angon dan taga yayan wani hamshakinne ake gagatawa haka.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un tashiga furtawa lokacin da idanunta sukayimata kaci6us da hoton jabeer da zuby.
Take wani irin gumi ya karyo mata, a hargitse tami'ke ta sanya hijab d'inta sannan ta sanya ni'kaf da safar hannu data 'kafa, sannan ta 'kara d'auko wayarta ta 'kara kallon hoton jabeer da zuby ta 'kara kallo Sannan tafara magana kamar Zuby na jinta "'karya kike Zuby, wallahi 'karyarki tasha 'karya baki isa ki kashemin 'yar'uwaba kuma ki auri mijinta wallahi saina d'au tsatstsauran mataki akanki.
Tana gama fad'in haka tafice daga gidan batare data nemi izinin Momy ko Daddy ba.
**               **                 **
Zuby kuwa kud'i ta amsa masu yawa daga hannun jabeer tasiyo kaya kusan kala goma wad'anda zata sanya gurin bikin, kowane kaya da jakarsa da takalminsa,  yau sukayi da telanta zataje kar6ar d'inkunan saboda haka waya tafarayimashi ta tambayeshi ko ya'karasa, yacemata yagama ita kawai yake jira.
Wata 'katuwar hijab tasaka sannan tafita, dan tunda tasamu tashawo kan jabeer ta daina shigar banza, koma Tayi saita saka 'katuwar hijab.
Minti ashirin ya sadata da shagon *USMAN FASHION*  Wanda ta yarda kuma ta amince da d'inkinsa dan babu wani tela dazemata d'inki taji dai-dai idan bashiba, ya kware a d'inkin mata, danshi baya d'inkin maza, lokacin data shiga shagon saida Hussaina tafad'o mata a rai dan itace ta nuna mata shagon telan sune nan daddy ke kawo masu d'inkinsu duka harda na momy.

.
Bayan angama Had'a mata d'inkunan jabeer tayima waya akan yazo ya d'auketa, 'kofar gidansu ya sauketa sannan yaja motarsa yayi gaba da tsan-tsan kiyayyarta a cikin zuciyarsa,
Washe gari ya rage saura kwana tara d'aurin auren zuby da jabeer,
Zaune yake d'akinsa yahad'a uban tagumi hannu bibbiyu ba abinda yake tunani sai yanda ze zauna da Zuby amatsayin matarshi, ko kad'an bayajin sonta acikin zuciyarsa dai-dai da kwayar zarra, dan dai mamanshi kawai data nuna tsananin son auren shiyasa ya amince, besan me zuby tarika gayamataba kokuma takemata harta yarda da ita d'ari bisa d'ari kuma ta matsamashi akan sai ya aureta.
Wani guntun tsaki yaja gami da gyara zamanshi yajawo remote ya kunna TV lokacin ana labaran 'karfe takwas 
*Da farko ga kanun labaran, ayau ne shugaba muhammadu buhari ya sauka gida Nigeria daga tafiyar da yayi zuwa 'kasar England, Gobene Al'kalin babbar kotun jihar katsina ze gabatar da shari'a tsakanin wata matashiya me suna Hassana  Mansir Company inda take 'karar 'kawar 'yar'uwarta Zubaida wacce akafi kira da Zuby akan tana Zarginta akan kisan  'yar'uwa*.
A firgice jabeer ya mi'ke tsaye, yana mai-maita kalmar "Zuby takashe Hussaina, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, komawa yayi ya zauna hankalinsa a matu'kar tashe,
"Wannan bala'i dame yayi Kama? Anya zuby zata iya aikata kisan kai, meyasa Hassana takai zuby 'kara akan abinda batada kwakwkwarar sheda akansa, amma ita tasani Allah kaimu goben masu iya magana sunce duk wanda yace ze had'iye gatari sai asakar masa 'kota.
Da dare bayan daddy yadawo daga gurin aiki, bayan yasamu labarin shigar da 'karar da Hassana tayi, saboda duk illahirin garin ya d'auka Kowa Allah Allah yake gobe tayi suje kallo.
Momy yasamu zaune a falo ta buga uban tagumi, bayan tayimashi sannu da zuwa yake tambayarta "ina Hassana? "Tana d'akinta, momy tabashi amsa a ta'kaice, "kiramin ita, "to kawai tace ta mi'ke tanufi d'akin Hassana, Zaune ta isketa kan abin sallah da Qur'an a hannunta tana karantawa, domin samun nasara akan shari'ar daza'ayi gobe.
Da sallama Momy tashigo, bayan ta zauna gefen gado ta kalli Hassana "kizo daddynki na kiranki, "to ta amsa sannan tarufe Qur'an lokacin Momy ta dade da baro d'akin, a falo suka zauna itada Daddy suna jiran fitowar Hassana, daddy ya kalli Momy "anya yarinyar nan tana cikin Hayyacinta kuwa? "Saboda me kafad'i haka Alhj, saboda yanda ta shigar da 'kara kotu gashi har ana shirin zama na farko gobe batare data nemi shawarar yin hakan ba,
Murmushi Momy tayi "ai Alhj aikin gama yagama,tunda taji zata iya sai mu barta mugani.
Fitowar Hassanace ta katse masu maganar dasukeyi, cikin ladabi tasamu guri ta zauna, sannan tayima Daddy sannu da zuwa.
Suduka shiru sukayi na tsawon minti biyu kafin daddy yafara magana, "Hassana munji abinda kika aikata, amma amatsayinmu na iyayenki yakamata ki shawarcemu kafin ki yanke shawarar, ita shari'a da kike gani sa6anin hankali ce, kuma idan baka iya kama 6arawoba sai 6arawo yakamaka.
'Dagowa tayi ta kalli iyayen nata da fuskarta wacce Hawaye suka gama wankewa tace "dan Allah daddy da Momy ku gafarceni akan rashin shawartarku danayi, yanzu ba abinda nake bu'kata agareku sai addu'a inashaAllah naji ajikina nice da nasara, "To Allah ya bada sa'a "Ameen, ta amsa sannan ta kalli daddy, kuma dan Allah daddy ina Neman wata Alfarma agareku, "muna jinki daddy yafad'a, "inaso duk zaman daza'ayi a kotu yazama tare zamu tafi daku.
"InahaAllah zamuje Hassana kada ki damu kedai kije kiyita addu'a.
Nagode daddy, sannan ta kalli momynta Momy nagode, kuma inaso kuma ku tayani da addu'a.
Zuby kuwa tana zaune gidansu itada 'kawayenta tana nunamasu d'inkunan data amso daga gurin d'inki, tana gayamasu ranar dazatasa kowane kaya, 'kawayen nata kuwa ba abinda suke sai zuzutata suna yaba duk wani abu data fad'amasu ta tsara...
Ba zato ba tsammani kawai sai ganin yansanda sukayi gabansu, kusan su takwas mata hud'u maza hud'u,
Zumbur zuby tami'ke tsaye dan ba 'karamin razana tayiba kad'an yarage tasaki fitsarin wando.
'Daya daga cikin yansandan tace "zuby ko, munzo mutafi dakeU office d'inmu zaki amsa wasu tambayoyi.
Zuby ido ya raina fata zata fara masu gardama suka hankad'a 'keyarta tanaji tana gani aka sata a mota 'kawayenta kuwa duk sun fito sunyi cirko cirko, hakan yaba sauran yan unguwa damar tsayawa suma suna kallo, haka akaja motar zuby kuwa ba abinda take sai raba idanu.

Jabir zaune yahad'a hannuwansa duka biyu ya tallafi kumatunsa da alama yayi nisa cikin tunani, a zuciyarsa yana ganin gangancin Hassana da wannan mummunan hukuncin data yanke na maka zuby a kotu batare da tanada wata kwakkwarar shedaba.
mama ce tashigo hannunta d'auke da kula da plate ta ajiye gabansa sannan takoma ta bud'e d'an 'karamin pridge d'inta ta d'auko ruwan pure water me sanyi guda biyu ta d'ora a plate takawo gabanshi ta ajiye, zama tayi d'an nesa dashi tare da zuba mashi idanu wani irin tausayinshi ya tsirga mata, tana matu'kar tausayama d'an nata shikuma haka Allah ya jarabeshi da rashin dacen mace tagari wacce duk wata harkallar da'ake ciki yanzu Itace sila, kuma gashi bata duniyar ma baki d'aya.
Wata nannauyan ajiyar zuciya tayi sannan takira sunanshi "jabeer... Firgigi yayi ya kalleta kamar Wanda yafarka daga bacci, sannan ya amsa "na'am mama.
"Tunanin me kakeyi haka? Ajiyar zuciya yayi sannan ya maida dubansa ga mahaifiyar tasa "mama Dole inyi tunani abubuwa da dama sun d'auremin kai nayi tunani nayi nazari amma ban hango wata kwakkwarar hujja da Hassana zata kai zuby 'kara ba.
Shiru yad'an ratsa na kimanin mintuna biyu sannan mama ta sauke ajiyar zuciya "to Jabir yazamuyi da wannan Al'amari tunda sunriga sunyi 'kara ai bakin al'kalami ya bushe mudai fatanmu Allah toni asirin koma waye ya aikata wannan mummunan aiki.
"Ameen jabeer ya amsa yana matukar jin ciwon abinda yafaru dashi arayuwa, sannan yajawo kular abinci yafara zubawa dan rabonsa da cin abincin kirki tun lokacin daya gane Hassana ba ita bace ainafin matarsa Hussaina.
Haka yafara cin abincin kamar yana cin magani badan yanajin dad'insaba Haka mama tatasashi gaba tana rarrashinsa har yad'anci da dama sannan yakora da ruwa me sanyi.
**                **               **
A 6angaren Zuby kuwa tun anar da police suka angiza "keyarta Zuwa office d'insu suka shiga tuhumarta da tambayoyi amma fir ta 'ke'kashe 'kasa tace ita batasan kome game da kisan Hussaina ba. Haka yan sandan sukayi ta fama har suka gaji suka tattara kome suka ajiye suna jiran ranar daza'a fara gudanar da shari'ar a kotu.
*kotu* 
'Katon d'akin gudanar da shari'a yacika ma'kil da jama'a maza da mata yan kallo dakuma  wad'anda shari'ar ta shafa. Zuby kuwa tana tsaye Inda ake ajiye wad'anda ake zargi a kotu, sai raba idanu takeyi, gefe ga d'ansandan dake tsare da ita,
yan kwanakin datayi a kulle har fatar jikinta tayi duhu sai 'kuraje dasuka firfito a jikinta wad'anda suke nuna alamun tasha cizon sauro ga wata irin rama datayi
Guri d'aya kuma momy ce zaune Sai Hassana gefenta wacce tunda tashigo d'akin shari'ar take faman karanto duk wata addu'a datazo bakinta dan neman nasara gurin ubangiji.
Daddy shima suna zaune a kujerar gaba yayinda Jabir yake kujerar dake bayanshi,
Kotu tagama cika mutane an kaure da surutu kowa na fad'in albarkacin bakinsa, shigowar Al'kali yasa mutanen gurin yin shiru tare da mi'kewa, haka Al'kalin ya isa mazauninsa ya zauna sannan sauran jama'a suka zauna, wani littafi dake gaban Al'kalin ya bud'e yayi wasu yan rubuce-rubuce sannan yayi gyara murya yace "afara gabatar da 'kara ta farko.
Me gabatarwa ya mike tare da wata takarda a hannunsa yafara karantawa kamar haka "shari'armu ta farko shine wacce Hassana mansir company take 'karar 'kawar yayarta Zubaida wacce akafi sani da zuby akan tana zarginta da kisan gillar da akayima 'yar uwarta kuma abiyar Haihuwarta wato Hussaina mansir company, bayan yagama karantawa yakoma ya zauna.
Al'kali ya kalli Zuby yace kece Zubaida? Zuby ta gyad'a kai kamar 'kadangarwa tace "Eh nice ya mai girma mai shari'a, Alkali yace kokinada lauya Wanda ze iya kareki tace "inadashi, nanma Al'kali yayi "yan rubuce-rubucensa sannan yace ina lauyan wanda ke 'kara da kuma lauyan wacce ake 'kara.
Lauyan Zuby ne yafara mikewa yafara gabatar da kanshi sannan lauyan Hassana shima yagabatar da kanshi.


.
Al'kali ya gama yan runbuce-rubucensa sannan yafara magana "ko lauyan wacce ake 'kara yanada abin cewa.
Lauyan zuby ya mike "inada magana ya mai girma mai shari'a, da farko inaso in tabbatarma wannan kotu me Adalci zuby ba ita bace ta kashe Hussaina, kodan Idan akayi la'akari da 'kawancen dake tsakaninsu dakuma aminci da yarda da juna, bayan wannan an tabbatar da marigayiya Hussaina batada wata 'kawa bayan zuby, kuma Kowa yasan zuby yasan kyawawan halayenta bazata iya koda kashe 6era ba, barantana mutum, kuma 'kawarta aminiyarta, saboda yarda da ita dakuma kyawawan halayenta yasanyama mijin ita marigayiyar yayi kwad'ayin aurenta Wanda a halin da ake ana saura kwana goma a daura aurenta ita Hassana tayi 'kararta akan  tana zarginta da kisan yar'uwarta wacce batada wasu kwararan shedu,........ Yana kaiwa nan ya russuna yace "nagode ya mai girma me shari'a, sannan yakoma ya zauna.
Bayan Al'kali yayi rubutu, sannan yad'ago yace "ko lauyan wacce ke kara yanada abin cewa, sai lokacin lauyan Hassana yami'ke ya'kara gabatar da kanshi sannan yafara magana.
"Ya mai girma mai shari'a inaso inyima wacce ke 'kara wasu yan tambayoyi, Alkali yace "anbaka dama, "kotu na bu'katar ganin Hassana a gabanta, wani mummunan fad'uwar gaba Hassana taji sannan tami'ke tana karanto addu'oin samun nasara abakinta.
Bayan tatsaya inda aka umarceta lokacin lauya yafara jera mata tambayoyi tana bashi amsa, karshe yace Hassana to ko zaki iya bayyanama kotu dalilin dayasa kike zargin zuby akan kisan 'yar'uwarki? Hassana tagyara tsayuwa tace "itace tasameni har gida tafad'amun lokacin ina zaune gidan jabeer amatsayin matatarsa marigayiya Hussaina, kuma sannan ta gargadeni akan in gaggauta barin gidan da ita yadace da ta zauna amatsayin matar gidan sannan kuma tayimani kashedi da idan na kuskura nafad'ama wani nima zata kasheni.
Lauya ya'kara jefarta da wata tambayar "taya akayi kika zauna gidan jabeer amatsayin matarsa alhalin kuma yana auren 'yar'uwarki?
Wani irin kuka ya kwacemata dan tunowa datayi da abinda yafaru da ita na *AUREN TAGWAYE* dasukayi itada yar'uwarta, ahankali tasa hannu tashare hawayenta sannan takwashe labarin abinda yafaru kaf tsakaninta da marigayiya Hussaina tundaga had'uwarsu da Hafiz har zuwa lokacin da taro'keta akan tanaso ta zauna gidanta amatsayin ita akan cewa zataje bikin 'kawarta Wanda zubyn ce takitsa mata haka kuma tayi sa'a Hussainar ta amince shine tayi amfani da wannan damar takasheta dan tasamu damar aure mijinta, wannan shine iyakar abinda nasani.
Lauyan ya kalli al'kali wanda yake rubutu acikin littafinsa yace "inaso kotu tabani dama inyi wasu 'yan tambayoyi ga mijin marigayiyar, alkali yace "anbaka dama.
Haka kotu ta umarci ganin jabeer, shima bayan yan tambayoyi da'akayimasa yaba kotu labarin iya abinda yasani tundaga aurensa da Hussaina dakuma zaman da Hassana tayi agidansa amatsayin ita marigayiya Hussainar. Daga kan tambayoyin da lauyan yayima Jabeer yajuya gurin Al'kali yace nagode ya mai girma mai shari'a, sannan yakoma ya zauna.
Lauyan Zuby yami'ke yana gyara rigarsa, yace "ya mai girma mai shari'a labarin da wacce ke 'kara ta bayar kwata-kwata beda nasaba da abinda ake 'kara Kanshi, saboda haka ina ro'kon wannan kotu mai Adalci datayi watsi da wannan shari'ar kuma sannan abima zuby hakkinta akan 'kazafin kisa da aka li'kamata wanda batajiba bata ganiba.
Al'kali yace "ko lauyan wacce ke 'kara yanada wasu 'karin bayani? Lauyan Hassana yami'ke yace "babu yamai girma mai shari'a, bayan Al'kali yayi yan rubuce-rubucensa sannan yadago ya kalli Al'ummar dake cike ma'kil cikin wannan kotu yafara jawabi
"Abisa shedu dakuma bayanai da lauyoyi suka gabatar agaban kotu, kotu ta gamsu da bayanan kowane 6angare dakuma shedun dasuka gabatar saboda haka kotu tayi watsi da wannan shari'ar saboda batada makama, sannan kotu taba zuby damar d'auka 'kara akan 'kazafin kisa da aka li'ka mata.
Wani irin kukan takaici Hassana tafashe dashi dan jin abinda al'kali yafad'a, Zuby kuwa wani shu'umin murmushi tayi, take kotu ta kaure da surutun jama'a Kowa na fad'in albarkacin bakinsa.
Al'kali yabuga teburin dake gabansa sannan kotu tayi tsit, yana shirin cigaba da jawabi kawai sai ganin wani matashin saurayi sukayi yashigo kotun yana cewa "nine sheda na 'karshe wanda zan war-warema kotu kome da kome akan wannan case din.
Nanfa kallo yakoma kan wannan matashin sunayin ido hud'u da zuby gabanta yayi wani mummunan fad'uwa, Jikinta yafara kyarma wata irin zufa ta keto mata, Hassana kuwa kallonsa takeyi tanaso ta tuna inda tata6a ganin wannan fuskar amma takasa tunowa.


Baki d'ayan hankalin mutanen dake cikin kotun yakoma kan wannan saurayin daya shigo yana fadin zebada sheda, Hassana kuwa mamakine yakamata azuciyarta tace " toshikuma waye wannan ? meya sani game da mutuwar 'yar'uwata,? anya akwai wata sheda daxe bada wacce zatasa Al'kalinnan ya saurareshi tunda har abinda nafad'a besa ya yarda cewa zuby takashe Hussainaba.
Muryar Al'kalince tadawo da ita daga tunanin datake, jitayi yana fad'in "saurayi daga ina? Kotu tanaso tasan ko kai waye kafin kabada sheda agabanta.
'Kara dai-daita nutsuwarsa yayi sannan yafara magana "sunana *Hafiz* kuma ni saurayin Marigayiya Hussaina ne, wannan kuma friend d'inace yafad'a yana nuna Zuby.
Amma ita sona take kuma batada burin daya wuce in aureta, nikuma a lokacin bata gabana saboda ko d'an iska yanaso ya auri mace tagari ba irin zuby ba wacce tagama watsewa a titi, kwatsam saita fahimci muna soyayya da 'kawarta marigagyiya Hussaina, muna cikin wannan halin mahaifin Hussaina yayimata aure saboda ganin ta 6ullo da wasu Halaye marassa kyau.
Haka dai yacigaba dabada labarin iyakar abinda yasani dangane da mutuwar Husssaina  kuma ya tabbatarma kotu zuby itace takashe Hussaina saboda tanason ta auri mijinta dan ganin cikin irin jin dadin datake dakuma yanda mijinta ke Sonta.
A lokacin nikuma nabukaci da muhad'a kai idan ta auri jabeer ta kasheshi ta kwashe dukiyarsa tadawo muyi aure dan inada tabbacin babu wani namiji datakeso sama dani, jabir najin haka besan sanda yakalli zuby ba yana jin wata muguwar tsanarta cikin zuviyarsa, dama tun can ba sonta yakeba.
Hafiz yacigaba da magana shine tanuna rashin amincewarta, nikuma alokacin na kunna mata recording din danayimata lokacin datake jaddadamin ita takashe Hussaina, nan take ta tsorata dajin wannan recording dan nayimata barazanar muddin bata amince da bu'katataba zan dam'ka wannan recording hannun hukuma, shine tacemin inbata kwana biyu zatayi shawara.
Ranar data nemeni dan gayamin shawarar data yanke ranar tazubamin guba a lemu dan kada natonamata asiri, Allah yasa inada sauran numfashi 'kanwata takaini asibiti da taimakon lokitoci nasamu kaina, shine nasa 'kanwata tabugama Zuby waya tafad'a mata cewa namutu, tunda aka sallameni daga asibiti na tattara kayana nakoma garin Kaduna gurin abokina, ina can nasamu labarin wannan shari'a shine nazo dan inbada sheda yanzu hakama saukata garin kenan nawuto nan.
Yana kaiwa nan yayi shiru, mutane suka fara kallon kallo ana magana 'kasa-'kasa Kowa nafad'in albarkacin bakinsa, Hassana kuwa mamakine yagama rufeta, haka Momy da daddy, Zuby kau raba idanu kawai takeyi  duk illahirin jikinta kyarma yakeyi, zufa tagama rufeta kamar wacce aka she'kama ruwa.
Bayan surutun yad'an lafa Al'kali kuma yayi 'yan rubuce-rubucensa yad'ago ya kalli Hafiz yace "Hafiz kozaka iya gabatarma kotu da wannan recording din dakace ka d'auka lokacinda Zuby take jaddadama itace takashe Hussaina, Hafiz yace Eh ranka shi dad'e yasa Hannu aljihu yaciro wayarsa ya kunno inda recording d'in yake wani mutumi dake zaune gaban Al'kalin ya amshi Al'kali yabashi dama sannan ya kunna mutane sunyi tsit ana saurare bako shakka muryar zuby ce  lokacin datake cewa _of course bazan tsaya ina jayayya dakaiba nina kashe Hussaina saboda tashiga gonata_  mutane najin Haka suka d'au salati wasu suka fara Allah wadai da halin Zuby.
Saida Al'kali yabuga teburin dake gabansa sannan kotun ta saurara,  "Abisa shedun da kotu tasamu tagamsu da cewa Zuby itace takashe 'kawarta Hussaina dan tanaso ta auri mijinta, saboda Haka wannan kotu me Adalci ta yankema Zuby hukuncin kisa ta Hanyar rataya, muna fata wannan zezama Izna gamasu Hali irinna zuby.
Wani irin murmushin farinciki ya subuce daga bakin Hassana tafad'a Jikin momynta tana kukan farin ciki.
Zuby kuwa wata mahaukaciyar 'kara tasaki tana kuka tana tsinema Al'kalin wai beyi hukuncin tsakani da Allah ba
Haka kotu ta watse zuby na hauka tana zage zage da fizge-fizge aka angiza 'keyarta cikin ba'kar mota wacce ake saka masu ba'kin hali irinnata.

      *Bayan Wta Daya*
Jabir ne zaune a office dinsa tunani barkatai acikin zuciyarsa, a wani 6angaren kuma na zuciyarsa soda 'kaunar Hassana ne ke d'awainiya dashi, tunanin irin zaman dasukayi yakeyi, Lallai Hassana macece waccce kowane namiji zeyi fatan tazama mallakinsa, kuma uwar yayansa.
yarasa wace hanya zebi ya bayyana mata irin tsananin sondayake mata, jiyayi zaman office din ba dad'i saboda haka tattara takardun dake gabansa yayi ya ajiyesu tare da rufe office din, kai tsaye inda ya ajiye motarsa yanufa yabud'e yashiga sannan yasa key yatayar da motar yad'au hanyar gida, zuciyarsa cunkushe da tunane-tunane.
'Kofar gida ya ajiye motarsa, sannan yafito, da nusaiba suka had'u cikin fara'a da sakin fuska take gaisheshi, "yaya jabeer sannu da Zuwa, "yauwa ya amsa sannan ya tambayeta ina zaki haka? Cikin ladabi tabashi amsa "nan 'Kasan layinmu zanje gidan kitso, "owk to adawo lafiya, yafad'a tare da wucewa kai tsaye cikin gidannasu, da sallama yashiga, mama ya iske zaune tana sauraren redio, jin sallamarsa yasa tarage sautin redion tare da amsa sallamar "kaine yanzu da rana nan, tafad'a tana kai dubanta gareshi, lokacinne kuma ta fuskanci akwai damuwa tattare dashi, bissmillah zauna tafad'a tana tura mai kujerar dake kusa da ita.
Fridge yanufa yafara d'auko ruwa me sanyi sannan yadawo ya zauna tare da sauke wata ajiyar zuciya, ruwan yafasa yafara sha, ahankali yaji wani sanyi na sauka a zuciyarsa, saida yakarasa shanye ruwan sannan ya kalli mama ya gaisheta cikin girmamawa, bayan ta amsa, shiru yad'an ratsa na kimanin minti biyu, sannan mama ta numfasa tace "da alama akwai damuwa tattare dakai, shin miye damuwarka kafad'amin amatsayina na mahaifiyarka idan inada maganinta zanyima idan kuma babu inbaka shawara, idan itama bazatayiba zan taimakama da addu'a domin babu abinda ya gagari Allah.
Hakane mama, ba wata damuwa bace tafe dani, inasone Hassana ta maye gurbin 'yar'uwarta amma kwata-kwata nakasa tunkarar mahaifinta da maganar.
Murmushi mama tayi me d'auke dajin dad'i tace "ni kaina na jima inayima kwad'ayin auren Hassana yarinya me hankali da ladabi da biyayya, ga girmama nagaba da ita, abinda yasa banyima maganaba Dan ina tsoron kada kabi za6ina kuma a maimaita yar gidan jiya, watakila bakada ra'ayin hakan, amma yanzu tunda ka furta da bakinka kabar kome a hanuna inshaAllah kome zezo da sau'ki.
"Kamar da yaushe Alhj yake gida zanje ni insameshi,
"eh to yana komawa gurin 'karfe biyu na rana sai yakuma fita 'karfe hudu na yamma.
"Kada kadamu inshaAllah gobe zanje gidan dakaina,
Cike dajin dad'i jabeer yayima mamanshi godiya, haka suka d'an ta6a fira, saida yaci abinci sai bayan azahar yabar gidan, zuciyarsa cike dajin dad'i dan abinda mama tafad'a mai gani yake kamar yasamu Hassana yagama.
A 6angaren Hassana kuwa tun ranarda aka yankema Zuby hukunci a kotu take jinta cikin wani farinciki, dan jitake kamar da hannunta tad'au fansar kisan da'akayima 'yar'uwarta.
Wani 6angaren kuma na zuciyarta tsananin son jabeer da 'kaunarsa ke d'awainiya da ita, dan d'an zaman dasukayi da jabeer ta fuskanci halayensa akwaishi da tsananin ha'kuri, ga yawan ibada, wasu hawaye taji sun zubo mata Wanda ita kanta batasan dalilin fitarsuba, tasa hannu tagoge sannan tad'aga hannuwanta sama tafara rokon Allah,
"ya Allah ka mallakamin jabeer amatsayin mijina, yazamo uban yayana, Allah ameen tafad'a tare da saukar wasu sabbin hawaye a kumatunta.
Kusan kullum haka take fama da dawainiya da soyayyar jabeer acikin zuciyarta tarasa Wanda zata fad'amawa kota d'an samu sauki dan ita dama bata cika kwashe-kwashen kawayeba, sai kuma ga abinda yafaru da 'yar'uwarta ta sanadin 'kawa tarasa rayuwarta, itakam ta tsani 'kawa duk yanda take.

Washe Gari Hassana ce keta kai kawo tsakanin falo da kitchen, kallo d'aya zakayimata ka tabbatar tana cikin nishad'i haka kawai yau ta tsinci kanta da jin wani matsanancin farinciki, yanzuma girki tagama shine take jerawa kan dining, bayan tagama takoma tagyara kitchen ta goge sannan tawuce d'akinta kai tsaye toilet tashiga tashe'ka wanka, sannan ta d'auro Al'wala dan ganin lokacin sallar azahar yayi, tana fitowa ta zura wata doguwar riga tare da saka hijab ta shimfid'a abin sallah, saida ta kammala sallar tayi addu'o'inta tashafa sannan ta isa gaban dressing mirror tafara shafa wani cream me dadin 'kamshi sannan ta murza powder a fuskarta tashafa kwalli tashafama lebenta man le6e.
Wadrope tanufa kai tsaye ta d'auko wasu riga da siket na material orange colour d'inkin yayi matu'kar kyau bakamar datasaka ajikinkta, sai jikin nata tare da Hasken fatar jikinta ya'kara fiddo da kyan material d'in.
Kitchen tanufa tazubo abinci tare da d'auko robar ruwa me sanyi, da madarar holandia takoma d'akinta tafaraci zuciyarta wasai kamar wacce akayima albishir da gidan Aljanna, bayan ta kammala cin abincin ta d'auki plate ta maida kitchen tana mamakin kanta yanda yau taci abinci me yawa haka kamar ba itaba, wanda rabon dataci abincin kirki tun ranar data zauna gidan jabeer amatsayin 'yar'uwarta sai kau yau, a zuciyarta tace anya ba wani abu ke shirin faruwa daniba......
Tana cikin wannan tunanin taji tsayuwar motar daddy, tananan hartaji shigowarsa falo sannan tafito tayimashi sannu da zuwa tawuce d'akinta, binta yayi da kallo da alama akwai abinda yake tunani dangane da ita.
Momy kanta ta lura da hakan, itace tadawo dashi daga tunanin dayake ta hanyar 'kar6ar jakar hannunsa tawuce d'akinsa, shikuma yabi bayanta,  ruwan wanka tafara had'a mashi saida yayi wanka ya canja kaya zuwa masu sakai-sakai sannan suka fito zuwa dining, Momy da kanta tazuba masu sannan suka fara ci.
Bayan sun kammala cin abincinne Momy ta kwalama Hassana kira, da sauri tazo tace "gani momy.
Momy ta umarceta data kwashe kayan dasukaci abinci, "to ta amsa sannan tafara kwasa tana kaiwa kitchen saida ta kammala ta gyara gurin tsaf, sannan takoma d'aki wayarta ta jawo ta kunna data best group dinta tashiga na *Ciwon ya mace* ta iske su *Mmn Ummi da Mmn zee da Momyn ramadan da Ameena PA* da dai sauransu anata raha itadai mutanen grouf din na matu'kar burgeta, sallama tayimasu suka amsa, nan fa Ameenoo tafara "oyoyo ga 'kawata, nan Hadiza tace kaji shishshigi 'kawarki ko tawa, murmushi Hassana tayi tace "Hmm kudakata aini banida 'kawa duk grouf dinnan kowama 'kawatace dan gaskiya kuna matu'kar burgeni kun iya zama da mutane.
A falo kuma momy ta kalli daddy Wanda ya maida hankalinsa kan jaridar dake hannunsa, tace "waini Alhj haka zamu zubama yarinyar nan ido tayita zama agida, kuma ita gashi tunda canma bata kula kowa barantana yanzu.
Shiru daddy yayi na kimanin mintuna biyar, itakuma Momy ta zubamai idanu tana jiran taji me zai fad'a.
Numfasawa yayi sannan yace "to me kike tunanin zanyimata kuma,?
Momy tad'an gyara zamanta "nida cewa nayi mezai hana tacigaba da karatunta kafin kuma muga abinda Allah zeyi.
Wani mugun kallo daddy ya watsama Momy wanda saida yasa hantar cikinta ta kad'a sannan yafara magana cikin d'aure fuska
"kada ki kuskura in 'karajin wannan maganar daga bakinki, koda zatakai shekara nawa a gidannan babu maganar cigaba da karatu, munanan tare da ita har lokacin dazataga dama tagfito da miji tayi aure.
Yana gama fad'in haka ya kwashe jaridarsa yawuce d'akinsa yabar Momy zaune sake da baki.
.
Momy kuwa tunda daddy yagama magana yashige d'akinsa yabarta zaune a falo, tunani barkatai takeyi a zuciyarta tana ganin kamar shawarar data kawoma daddy batada makusa amma sai gashi yanda ya nuna kwata-kwata bazebi shawarar tataba.
Tayi zurfi cikin tunani taji kamar ana sallama a bakin 'kofar falon 'kara saurarawa tayi jitayi ankara doka sallamar mi'kewa tayi tare da amsa sallamar ganin maman jabir datayi yasa tasaki murmushi "a'a yau kune a gidannamu lale maraba sannu da zuwa, "yauwa tafad'a itama fuskarta d'auke da murmushi.
Bayan sun gaisa momy tacika gabanta da kayan sanyi, mama tazuba lemun tasha sannan ta ajiye cup ta maida dubanta ga momy "Allah sa dai Alhj yana gida dan maganace me matu'kar muhimmaci take tafe dani.
Numfasawa momy tayi kafin tace "eh yananan bari namaki magana dashi, sannan tanufi d'akin daddy kwance ta iskeshi ya kalli bangon d'akin da alama yayi zurfi cikin tunani, zama tayi bakin gadon sannan tasanar dashi zuwan maman jabeer,
Tare suka fito Alhj na gaba momy na bayanshi, zama sukayi baki d'ayansu a falon bayan daddy sun gaisa da maman jabeer nan take sanar dashi maganar dake tafe da ita na nemawa jabir auren Hassana, da kuma yanda jabeer din yasanar da ita jiya.
Murmushi Daddy yayi wanda ya nuna alamun farin ciki tattare dashi sannan ya numfasa yace "in banda abin jabeer aini matsayin d'a na d'aukeshi koshi da kanshi yafad'amun ai bazan hanashi jininaba inshaAllah babu wata damuwa, yanzu abinda yakamata shine yafara zuwa su fuskanci juna shida yarinyar,
Godiya maman jabeer tashigayi, tana yaba halin kirki da dattako irinna Alhj mansir, mutumne me tarin dukiya, amma Allah be d'oramashi girman kaiba, da raina talaka.
Haka sukayi bankwana momy tayimata rakiya har harabar gidan suna 'kara tattauna al'amarin yaran, da alama ita kanta momy taji dad'in hakan dan kowane iyaye zasuyi burin 'yarsu tasamu nagartaccen namiji kamar jabeer, mutum me ilimi da ri'ko da addini, ga kuma ri'kon amana.
**                **              **
Sanye suke cikin kayan uniform kalar dark blue, matane zallah zaune suke cikin wani 'kazamin d'aki dan ba abinda ke tashi d'akin sai wani irin matsanancin wari, can na hango wata matashiyar yarinya zaune tahad'e kai da gwiwa da alama kuka take, itama sanye take da kalar uniform d'in jikin rigarta ansa number itace number ta sha takwas,  wata 'katuwar mata nagani taje kanta ta tsaya ta ta6ota tana fad'in "yaya dai 'yanmata?
Ahankali wacce akayima maganar tad'ago ta kalli wannan wannan 'katuwar matar, fuskarta sharkaf da hawaye tayi wani ba'kikkirin duk ta rame, jin wannan 'katuwar matar takira sunanta "Zuby yadai yanaganki haka, zuby tasa hannu ta goge hawayen dake idanunta ta 'kara gyara zama batada niyyar yin magana.
Wannan 'katuwar matar dake tsaye ta gagga6e da wata mahaukaciyr dariya cikin muryarta wacce tafi kama data 'kato, saida tayi dariya me isarta sannan tadafa kafad'ar zuby tace "Haba zuby ke kullum kuka kamar ke kad'aice kiduba kiga fad'in wurinana kowa harkar gabansa yake amma ke kinsama ranki tunani kin'ki ci kin'ki sha duk kin lalace.
Kallo zuby tabi mutanen gurin dashi kowace kuwa harkar gabanshi yakeyi kamar ba gidan yari sukeba, sannan tamaida dubanta ga matar tace dole inyi kuka dole ci da sha ya gagareni, rai raifa nakashe, dole tun duniya inga sakayya ko zaman gidannan ma kad'ai bala'i ne.
Wata mahaukaciyar dariya matar tasake bushewa da ita "tace lallai yarinyar nan rayuwarki na 'Kazan ruwa, kowa tuba dan wuya ba lada, ni yanzu jiran lokacin daza'a sallameni kawai nake ind'ora daga inda natsaya.
.
Kallo kawai zuby tabita dashi dan tasan duk abinda tafad'a haka yake *Har a zuciya* na (Fiddausi so Dangi) amma itakam ayanzu tayi nadamar abinda ta aikata, gashi yanzu son abin duniya yakaita ya baro.
Suna cikin wannan maganar wannan katuwar matar taji an d'auketa da wani migun mari, waigawa sukayi bakin d'ayansu wata azzalimar 'yar sanda ce suka gani, dan Duk illahirinsu masifar tsoronta sukeyi har suna suka sakamata inspector zalima, ai da gudun tsiya wannan 'katuwar matar tabar gurin duk kuwa da uwar 'kibar dake jikinta.
Zuby kuwa saboda rashin 'karfin jiki kasa motsawa tayi daga wajen, hakan yaba inspector zalima damar wankamata lafiyayyun mari har guda biyu, dan gani take zuby ta rainata kowa na gudu atafi aiki amma ita ta gagara tashi, zuby kuwa yunwa da kishi, da rashin karfin jiki yahanata mi'kewa ganin haka inspector Zalima tasa bulala tacigaba da zabgama Zuby, saida tayimata rud'u-rud'u duk tafasa mata jiki sannan tabarta. Kuma sannan tatasa keyarta zuwa aikin dazasuyi na kwasar bola da wankin toilet dinsu mai d'auke da 'kazantu kala-kala. _Niko zee kallon zuby kawai nake tsananin tausayinta kwance a fuskata, nace lallai Zuby yau duniya tamata gwatson mage_.
       *Bayan wata 2*
Shirye-shiryen biki ya kankama tsakanin 6angarori guda biyu, Maman jabeer hidima take sosai dan jin bikin take kamar shine tafarayi a rayuwa, kallo d'aya zakamata ka tabbatar da farinciki tattare da ita.
Momy kuwa dama wannan shine bikin dazatayi na farko dan lokacin bikin Hussaina ba'ayi wani shagaliba.
6angaren jabeer ango kuwa kullum cikin hidima yake dan yau saura sati bikin yariga yagama gayyatar duk wanda ze gayyata.
6angaren amarya kuwa wata 'kawar Momy ce ta d'auketa tatafi da ita gidanta can akeyimata gyaran jiki na amare, tsawon sati biyu ana abu guda tundaga kan dilka halawa, da sauran nau'ikan gyaran jiki, sai ingantaccen tsimi me kyau wanda ke gyara mace kullum tajita cikin ni'ima.
Ana saura kwana bakwai d'aurin aure Hassana tadawo gida, da niyyar saura kwana biyu bikin zata koma ayimata gyaran gashi da lalle, wani sihirtaccen 'kamshi ketashi daga Jikinta ga wani haske da santsi da fatarta ta'kara, dole ko mace ta kalleta takuma kallonta dan fuskarta har wani shek'i takeyi. Zaune take d'aki Momy tatasata gaba da wani tsimi da aka had'a na fruits tanaso ta shanye itakuma sai shatake tana 6ata fuska kamar zatayi amai, sotake Momy tabar d'akin ta ajiye.
Lokacin wayarta tayi ringing sunan Hubby tagani akan wayar, kasa d'agawa tayi tana kallon Momy.
Momy tace ki d'aga mana kinbar waya yana ringing, murmushi tayi sannan tace ina tunanin yazone dan munyi waya dashi yacemin gashinan zuwa yanzu.
Daure fuska Momy tayi minti goma nabaki kiyi ki dawo, ince nafad'amaki ya daina zuwa haka, idan kukayi ha'kuri sati d'aya yarage ami'ka mashi ke baki d'aya.
Cike dajin kunya Hassana ta d'auki wani madaidaicin hijab tasaka sannan tafita tsaye ta iskeshi jikin motarsa, batace yashigoba dan taji gargad'in Momy datace minti goma tabata, tana karasawa kusa dashi yaji wani sihirtaccen 'kamshi yadaki hancinsa, ahankali yadago idanunsa yakai dubansa gareta, yasalam yafad'a tare da sauke wata ajiyar zuciya.
Jiyake kamar ya rungumeta yahad'ata da jikinsa yacigaba da sha'kar daddad'an kamshinta
"Sannu da zuwa tafad'a cikin sassanyar muryarta, kanta sadde tana kallon kasa, "yauwa sannu dai amarya, yakike ya kuma hidima?
Murmushi tayi "Hmm hidima ai tana wurinku angwaye, "haka kike gani koh, amma ni a tinanina biki ai na amare ne.
Murmushi kawai tayi dan bataso firar tasu tayi tsayi, shiru yad'an ratsa na yan mintuna sannan jabeer yace "dama zuwa nayi inji dame-dame kk bu'kata na hidima dan naga idan nayi shiru ke bazakice komeba.
Eh ai bana bu'katar kome dan bawani bidi'a za'ayi a bikinnamuba walima kawai zamuyi, tonaji amma baki bu'katar kome na walimar?
"Eh bana bu'katar kome dan momy tagama had'a mana kome.
"Lallai Allah sakama Momy da Alkhairi amma dukda haka ga wannan kirike gurinki koda zaki bu'kata bandir d'in yan d'ari biyar yami'kamata sannan sukayi bankwana yawuce tana d'aga mashi hannu harya 'kule sannan takoma gida.
Yau yakama saura kwana biyu d'aurin auren Hassana da jabeer, yau ne kuma taje akayimata had'add'en gyaran gashi, tare da zana mata flower me kyau a hannunta, wani sihirtaccen kyau tayi dan idan ka kalleta sau d'aya dole ka kara.
Washe gari ana gobe d'aurin aure 'yan'uwa da abokan arziki da yan tsirarun 'kawayen Hassana sun taru a harabar gidan, domin walimar da wa'azi da aka shirya.
Da misalin 'karfe hud'u aka fara gabatar da wa'azin inda wata shahararriyar malama tayi nasiha kan zaman aure, amarya Hassana kuwa tasha kyau dan wata tsadaddiyar atamface Jikinta sai babban hijab data saka.
Da misalin 'karfe shidda aka kammala wa'azi aka rufe taro da addu'a tare dayima amarya da ango fatan zama lafiya da samun zuri'a tagari.
*Rana bata 'karya inji masu iya magana, sai dai uwar d'iya taji kunya*
Dandazon mutane manyan yan kasuwa da 'kusoshin gwamnati ne tan'kam 'kofar gidan Alhj mansir company, wad'anda suka halarci d'aurin auren Jabeer da Amaryarsa Hassana, wanda aka d'aura kan sadaki dubu hamsin.
Ansha shagalin biki taro yatashi lafiya, amarya ta tare gidanta mutane Kowa yanatasa Albarka.
**                 **              **
*Bayan Wata takwas*

Tunda tatashi take faman kuka kamar zata cire ranta, idanunta sun kumbura sunyi suntum sakamakon rashin baccin datake samu, kusan wata da watanni, kullum cikin damuwa take amma da alama damuwar tayau tafi ta kullum.
Wasu yansanda  kusan su hudune suka tsaya kanta, d'aya daga cikinsu ya kwatsa mata tsawa da alama Hausa bata zauna Mashi a bakiba, "oya les go, jiki a sanyaye *Zuby* ta taso tabisu a mota aka sakata, saida akayi tafiya me nisa sannan suka tsaya gaban wani 'katon get megedi yabud'e masu get suka shige, daga nan suka ajiye motar sannan sukayi tafiya me d'an nisa wacce tasadasu da wani d'aki Wanda anan suka iske wasu 'kattin ba'ka'ken mutane tsai-tsaye sunata mazurai wani dogon bencine sai wata igiya ta zuro anyi kullin 'zarge da ita dai-dai yanda kan mutum ze shiga.
Zuby na tsaye ta d'aga kai ta kalli gurin wasu zafafan hawaye suka sauko kan fuskarta, batayi 'ko'karin gogewaba haka suka ri'ka zuba wasu nabin wasu. Wata mace daga cikin yansandan aka mi'koma wata ba'kar hula me zurfi tasaka kan zuby ciki bayan and'orata kan wannan dogon tebur, sannan aka sa'kalo kanta cikin wannan igiyar, wani ba'kin d'ansandan fuskarsa bako annuri yasa 'kafa yature tebur d'in haka yaba igiyar damar tsuke wuyan zuby tayi sama da ita, saiga 'kafafunta suna lilo tanata harbe-harbe kafin daga nan rai yayi halinsa.
*Wannan shine 'karshen muguwa Zuby maci amana, kuma yar ta'adda*
Hafiz kuwa tun bayan da yabada sheda a kotu ya tattara yanashi-yanashi yakoma kaduna da zama, ya canja hali, yazama mutumin kirki kullum zaka sameshi yana istigifari, a haka Allah yahad'ashi da wata yarinya yar mutunci cikin 'kan'kanin lokaci suka sasanta bayan wata biyu aka d'aura masu aure, suna zaune a unguwar dosa Kaduna.
**                **             **
Ahankali take takawa saboda nauyin da cikinta yayimata, cikin wata shidda amma idan ka kalleta yanayin Girman cikin saika d'auka yayi wata tara,ga kumburi tana fama dashi,
kitchen tanufa dan sama masu abinda zasuci na rana.
Lokacin jabeer yayi horn megadi yabude masa get, gurin ajiye motoci yayi parking sannan yashigo gidan da sallama, shiru yaji kuma be ganta a faloba bedroom yanufa nanma bata nan, can yajiyo motsinta kitchen can yanufa isketa yayi tanata ha'kilon had'a musu jalouf din kus-kus harma ta kammala tana shirin d'aukowa takai kan dining, da sauri ya amshi kular hannunta, ya ajiye  sannan ya rungomota jikinsa bayanta had'u da 'kirjinsa sannan ya d'ora hannunsa kan 'katon cikinta yana shafawa ahankali, "haba my sweet nafad'a maki baniso kina wahalar da kanki kina wahalarmin da baby, bari kigani, hannu yasa ya d'auki kular abincin yakai kan dinning table yadawo ta mi'ko mai plate yakai sannan yadawo tami'kamashi cup din fruit salad d'in data had'a yaji 'kan'kara sai ra6a jikin jug din
Bayan sun kammala wannan da kanshi yahad'a mata ruwan wanka sannan yarakata har toilet, yana zaune harta gama wanka da kanshi yashafamata lotion me sanyi sannan ya d'uko mata wata doguwar riga me saukin nauyi ta sanya.
Kama hannunta yayi ya zaunar da ita bakin gado "ina zuwa bani minti goma yafad'a toilet yashiga yashe'ka wanka yafito ya murza lotion sannan yasaka wasu 'kananan kaya riga ash marar hannu sai bakin wando three quarter, sannan yakama hannunta suna takawa ahankali kamar makaho da d'an jagora har kan dining.
Nanma be barta tayi wani aikiba, dan ko zuba abinci hanata yayi shiya zuba sannan  yarika bata da kanshi saida ya tabbatar ta 'koshi sannan yazuba ftuit salad din a cup yatura mata gabanta shikuma yafara cin abinci.

.
Bayan wata d'aya cikin Hassana ya'kara girma idan ka ganta dole ka tausaya mata dan ko tafiya da kyar take iya d'aga 'kafa, hakan yasa Maman jabeer ta yanke shawarar zatayima wata tsohuwa salame a unguwarsu data Zauna gurinta tari'ka taimakamata da wasu abubuwa, Sam Hassana kin yarda tayi da zaman salame a gidanta dan lokacin da salame tafara zuwa gidan kallo d'aya Hassana tayimata taji gabanta yayi mummunan fad'uwa haka kawai taji bata bu'katar zama da ita.
Saboda haka jabeer tasamu yana Zaune d'akinsa da laptop gabansa yana kammala wani aiki na office dinsu Wanda besamu damar kammalawa jiyaba saboda dawowa yayi da wuri yayi girki yayima 'yar'lelensa wanka da gyare-gyaren gida.
Zama tayi bakin gado tare da dafe 'kungunta tana fad'in waih Allah, saurin ture laptop dindake gabansa yayi ya rungumota jikinsa yana fad'in "meya faru baniso inji kina fad'in wash wash d'innan wlh har cikin raina sai inga kamar akwai abinda ke damunki.
Murmushi tayi "ba abinda ke damuna sai nauyin cikinnan dan ba 'karamin nauyi yakeminba, tafiyama da kyar nake iya d'aga kafa, "Eyyah sorry my wife, wlh jinake kamar cikinnan yadawo jikina in'karasa miki rainonsa da haihuwarsa.
Dariya ta kyal-kyale da ita tana fad'in "wai Allah naganka da ciki, wlh bazaka kalluba, hmm barantana kuma ranar haihuwa za'asha raki danna tabbata bazaka iya jurewaba.
'Kara rungomota yayi gabansa, tare da d'ora hannunsa kan 'katon cikinta yace "inji waye yafad'amaki, aini idan da ace maza na kar6ama mata haihuwa toda kuwa bazan bari ki haifi ko d'aya da kankiba zan nunamaki ni gwarzon namiji ne, dan yayannnan goma sha biyar dukni zan haifesu.
Zaro ido tayi tare da dafe 'kirji 'ya'ya goma sha biyar a ina..........
A cikinki mana yafad'a yana 'kara had'eta da Jikinsa.
Amma baka tausayamin kallifa wahalar danakesha amma har kake fatan in'kara irinta sau sha biyar.
Murmushi yayi "ai a ina tausayinki yasa nace sha biyar amma da a yanda nakesone sonike ki haifamin dozin biyu.
Suduka dariya sukasa Hassana na fad'in ashirin da hudu kamar dai haihuwar zomaye.
Shiru yad'an ratsa na wasu 'yan mintittika, Sannan Hassana tace "my hubby akwaifa maganar dake tafe dani gurinka.
"To ina jinki, yafad'a tare da tattaro duk illahirin nutsuwarsa ya maida gareta.
"Umm dama game da maganar salame, sai kuma tayi shiru "ina jinki yafad'a "mezai hana abarta kawai ni hankalina be kwanta da zamantaba, mezai hana Nusaiba tadawo nan ko itama ai zata ri'ka taimakamin da wasu abubuwan.
"To shikenan tunda haka kikeso haka za'ayi, Ammafa kinsan ankusa bikinta saura 3 month idan lokacin yayi tatafi tabarkifa wah kuma kike tunanin za'a samo, "Ah bani fatan inkai wata ukku nan gaba ban haihuba, kaga hakan ya nunamin baka lissafi.
"Ah inji waye nikam nike lissafi nida za'a haifama babies guda hud'u lokaci guda yazan manta da lissafi.
"To shikenan yanzu dai kaba mama hakuri kada taga kamar na raina za6inta, "Kada kidamu indan mama bazataji komeba.
: Bayan wata biyu da zuwan nusaiba gidan da misalin 'karfe hud'u na yamma suna zaune suna kallon shirin *Yan Zamani* a star time tashar dad'in Kowa dan nusaiba na masifar son shirin dan ko lokacin tana gida bata ta6a bari ya wuceta, tunda suka fara kallon shirin Nusaiba ke ba Hassana labarin na baya wanda bata ganiba, amma saita lura kamar Hassanar ba saurarenta takeyiba, dan wani lokacin har d'an cije baki takeyi alamar dai akwai abinda ke damunta, lura da nusaiba tayi da Haka yasa tace "nikam Aunty sai inga kamar yau bakijin dad'in jikinnaki kodai inkira Yaya?
Kallonta Hassana tayi tare da 'ka'karo murmushin 'karfin hali tace "a'a kada ki kirashi ba wani abu inshaAllah, "ah'ah aunty kedai kadafa aje asamu matsala Yaya yaga laifina, "Hmm ba kome Nusaiba kada ki kirashi, "to shikenen tafad'a tare da ajiye wayar kusa da ita, dan da harta d'auko zatayi dialing number jabeer Hassana tahanata
Batafi minti goma da ajiye wayarba wayar tafara ringing Alamar shigowar kira, kallon Hassana tayi batare data d'au wayarba itama Hassana ita take kallo tace "yanzu danace kada ki kira saida kika kira.......
Murmushi nusaiba tayi cike dajin kunya tace "Lah wlh aunty bankirashiba, Hassana ta harareta tace "dabaki kiraba da yaza'ayi yakiraki.
"Hmm aunty kenan aibashibane yakira kallifa kigani tafad'a tana d'ago mata wayar, ganin an rubuta True love yasa Hassana tayi dariya "Hmm Abdul dinne yakira, wannan soyayya taku kamar zaku had'iye juna Allah dai yakaimu lokacin bikin.
"Hmm aunty ai duk soyayyarmu bamu kaiku keda yayaba, "yanzu dai ki d'auki wayar kada takuma tsinkewa.
Tana d'auka yake sheda mata gashinan ya iso gidan yayan nata, nan ta sanar Da Hassana Zuwanshi "Hassna tace saiki shigo dashi ko, nibari nakoma bedroom in huta.
"A'a aunty yi zamanki zamu zauna a lambu bari dai nafita da ruwa me sanyi da lemu. Wlh aunty dan kina haka amma danace yashigo Ku gaisa tafad'a tana dariyar tsokana, Hassana tace "a hakanma sai dai idan ba'ayi niyyar gaisheniba, hmm Nusiba kenan kema duka yaushe zamu ganki hakan kada ki manta yau saura wata d'aya dai-dai.
"Kai aunty kuma dan saura wata d'aya aiba daga zuwa zanzama hakaba, "Hmm Allah dai ya nunamana lokacin Hassana tafad'a "Ameen nusaiba tace tana dariya tayi saurin barin d'akin dan kada Hassanar tace tayi rashin kunya.
.
Tunda Nusaiba tafita kamar an'karomata wani matsanancin ciwon mara da ciwon baya,  tun tana daurewa harta fara nukurkusa, zuwa can taji azabar tayi yawa ta 'ko'karta ta tashi tana ta'kawa da kyar tanufi bedroom.
Tana shiga ta d'auko wayarta ta lalubo sunan jabeer ta danna kira, ringing d'aya ya d'auka dama kullum idan ze fita sai yayimata gargad'i akan dataji ciwo ko yaya takirashi.
Cikin za'kuwa dason jin mezata fad'a yace "Heelow my wife yadai?
Cikin tsananin azabar ciwo tace "wayyo  Hubby na zan mutu ka taimakamin.........
Tana fad'in haka wani irin matsanancin ciwo yatasomata lokaci guda, saboda tsananin ciwo jikinta har kyarma yake, wani irin 'karfi yazomata lokaci guda tayi wani nishi mai 'karfi saigashi ta santalo santalelen d'anta,   kamar kuwa yana jira ya kyanyara kuka,   duk abinnan dake faruwa a kunnen Jabir Dan lokacin data kirashi tsananin ciwo yasa bata kasheba tasaki wayar. 
Shikuma can 6angaren yanata magana kawai said jin kukan jariri yayi, a firgice yatashi yanufi motarshi da sauri,
Tuki yake amma gani yake kamar ba tafiya yakeba, dan gani yayi kamar an'karama gidan nisa,
kasa daurewa yayi, wayarshi yajawo yakuma kiranta tana d'auka takara akunne kamar azabar dataji dafarko ta'karaji nanma wani nishi tayi saiga santaleliyar yarinya, tana fad'owa ta kyanyara kuka, shima namijin datafara haihuwa kukan yake.
Jabir yaji and'au waya yanata hellow hellow yaji shiru sai kukan jarirai yakeji, ai take ya'karama motarsa gudu.
Nusaiba kuwa lokacin sukayi sallama da Abdul d'inta yatafi danta shedamashi tabaro auntynta kamar batajin dad'i.
Aiko tana shiga tundaga falo tafara jiyo kukan jarirai ai dagudu tanufi d'akin dataji kukan tana zuwa tafad'a d'akin batare da tunanin komeba.
Toxali tayi da santala-santalan baby's sunata tsala kuka, Hassana kuma tana dur'kushe kusa dasu lokacin ko cibi ba'a yankemasuba.
Nusaiba cikin tsananin mamaki tace "aunty haihuwa, kuma twowins mashaAllah,
Murmushi Hassana tayi tagayamata inda zata d'auko mata zare da reza tayi karanbani ta yanke cibi tasa zare ta daure, sannan tasakasu cikin zani tashiga kewaye tahad'a ruwan zafi wanka kawai tayi tafito.
Lokacin nusaiba tagama gyara gurin tsaf tasa morning wash tayi morping tafesa freshener lokaci d'aya d'akin yad'au kamshi.
Lokacin da jabeer ya'karaso sai taradda Hassana yayi fess da ita ba 'katon ciki, wani farinciki ya mamayeshi lokacin dayaga baby's d'inshi sunata wutsil-witsil cikin zanensu.
Godiya yayima Allah sannan yabugama mamanshi, bajimawa sai gata tazo ita ta wanke baby's lokacin labarin haihuwar Hassana yagama zaga Dangi,
Daga can gidan su Hassana akasamo wacce ke kula dasu kullum zatayima baby's wanka tayima Hassana, har kwana bakwai.
Ranar suna ansha shagali, yara sun amsa sunansu Hassan da Hussaina.
Hussaina kuwa saida tayi kuka dan tunowa da 'yar'uwarta da yanzu itace zata haifama jabeer wannan baby's d'in.
**             **                **

Bayan wata d'aya da haihuwar Hassana akayi bikin nusaiba, inda aka kaita unguwar g r a gidanta yahadu Bakin iya had'uwa,  Hassana ansha hidimar biki dan sune 'kirjin biki kome za'a itace gaba.
Nusiba kuwa sai nan-nan take da 'yan'biyu hotuna kau sunshasu, dan yaranne dole su burgeka yara yan wata d'aya amma idan ka gansu zakace sunyi wata ukku jikinnan nasu 6ul-bul mashaAllah.
_________________________
*Alhmdlh anan nakawo 'karshen wannan littafi 

Post a Comment for "AUREN TAGWAYE CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...