ABINDA KE BOYE COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ABINDA KE BOYE COMPLETE

ABINDA KE BOYE COMPLETE

- - Post a Comment

 ABINDA KE BOYE COMPLETE


Ayyiriri yiriri!Buwale!Asibi!Baraka!Lanto!Kande!kai dukkan Jama'an garin ga ku fito ku gane mani sabon lamari a gidan MALAN LADO………"Cewar wata yar tsamurmurae tsohuwa da ta fito kofae gidan da daurin kirji a jikinta……

  Kamar ana angazo mata da kananan yara daga gidanjen su !haka sukayi dandazo gabanta ko wace sae wurga ido take tana jiran taji me zata fadi Wasu da daurin kirji wasu ma ko dankwali bassu dashi…… "Kundum lahiya kika tara mutane haka?ko dae tsohun Haukanne ya motsa……"Cewar wata yamutsatstsar tsohuwa da ta iso lokacin dauke da bahon Tafasa a kanta……

  Kundum ta sake rafka guda tana fadin "Yau de Hafsatu ta haihu!Mai tafasa an samu dad'in jika Sae dae mu bamu san waye Uban yaron ba……"ta karashe maganar tare da kecewa da dariyar mugunta har da rike cike……

  Sauran matan dake tsaye suka dauki wani bahaggon salati tare da taba hannunawa suna kiran "Hafsatu kam an cuci Malan lado……"

 Maitafasa kam aje bahon tafasar tayi tana fadin "Watsatstsan Zance kundum!Dama wagga rana nake jira ranar da hafsatu zata haihu wallahi sae ta bar gidan Lado……"Shiga tayi gidan tana fadin "Ke Hafsatu fito nan munafuka dama yau nake jira sae kin fada man cikin uban waye kika haife a gidan d'ana……"

 Matan garin suka mara mata baya har cikin gidan tare da yaransu ……wasu har bisa katanga ……

  Hafsatu dake duke tsakar dakinta ……ta janyo wuka ta langa langa ta yanke cibiya da kyar sannan ta janyo wani yamutstsan tsumma ta goge jaririyar tare da nadeta cika sannan ta janyo wani tsumma ta shinfida saman lomatsatstsar katifar dake tsakar dakin ta kwantar da jaririyar……

  Jin Mai tafasa na kiranta yasa ta gabanta ya fadi ta mike idonta cike da kwallah ta fita ta tsaya bakin kofar dakin tana sadda kai kasa……

  Gabanta maitafasa tayi birki tana watsa hannu baya "Da kwarankwatsa kinci amana Hafsatu!kin ci amanar lado da aurenki kije kiyi cikin shege sannan ki haife a gidan mijinki……Ke Hafsatu kwarankwatsa da kudi gareni da kotu na makaki a birni a kasheki kowa ya huta da wannan abun kunyar……Fadan Cikin uban waye kika haifa ……?

  Cikin kuka Hafsatu tace "Wallahi inna Cikin lado ne kuma d'iyar lado ce na haifa……!

  "Lado!badae ladon mai tafasa ba……"Matan garin suka dauka tare surutai kasa kasa……

  Maitafasa kam watsa bakaken hannunta tayi saman fuskar Hafsatu tana fadin "Ubanki!Uban lado!nace Uban ladon!D'ana zaki wa sharrin Hafsatu?Ladon dake kwance tsawon Shekaru takwas kamar gawa sae yarda akayi dashi shine zaki haihu ki lik'a mashi ruwan sharri don kinga baya iya magana ……to Uwarsa Maitafasa nanan kuma ban karba ba……"

  Yar matashiyar yarinya ta shigo rike da kwaryar nono ganin gidan a cike ga maitafasa tana ta bala'i yasa ta bata fuska ta matsa tana fadin "Maitafasa lafiya aka cika mana gida haka……?

  "Ina fa lafiya Uwarki ta janyo mana abun kunya……"cewar mai tafasar tare da matsawa kusa da wata bukka tana fadin "Lado!kana ina……?

  Yarinyar ta sake bata fuska tana fadin "Shine dan rashin mutunci zaa cika mana gida haka ……inace uwar tawa tana da miji ……"

  Kundum tace "Da mijinta amma munsan ba cikinshi bane……"

  A Fusace tace "Zanci mutunciki kumdum!ku kuma ku jira har in shiga daki na fito wallahi sae,na fasawa duk shegen da na gani kai……"

  "Wa yace tayi abun kunyar……"Cewar wata mata dake tsaye bakin katanga

 Bata ce masu komae ba ta shige dakin ……ganin jaririyar tana kuka yasa ta dauketa tana jijjigawa ……

Maitafasa kam tana shiga bukkar lado ta rushe da kuka tana fadin "Lado Hafsatu ta cucemu !An cucemu lado anci amanarmu ……wallahi yai Sai na saki Hafsatu lado……"

  Kuka yake mara sauti yana kokarin daga mata hannu amma ya kasa……ido yake rufewa yana budewa da karfi hawaye na fita kamar an bude famfo ……
  "Nace kayi hakuri lado ……Dan cuta an cuceka kamarka a garinnan ace matarka taci amanarka ,to wallahi sae ta bar mana gida yau dinnan ……"

  Zata fita ya zabura ya kife tare da sakin kukan da muryar bata fita ……
Juyowa tayi tana fadin "Ka bar kukan lado nasan yarda kake ji amma,in dae ina raye lado baran,bari a ci mutuncinka ba ……"

  Fita tayi ta iske Har lokacin Hafsatun na tsaye inda ta barta tana kuka……
Kundum tace "Dan cuta an cuceku Maitafasa kamar lado a garinnan don anga baya lafiya sae a ci mutuncinsa……?

  A Fusace maitafasar ta juyo tana fadin "Ke Kundum bansan munafunci……"ta karashe maganar tana watsa hannu gaba

  Matan gidan suka dauki dariya tare da sowa ……Maitafasa kam ture Hafsatu gefe tayi ta fada dakin tana fadin "Yau zaki,bar gidannan,wallahi ……ni maitafasa uwar lado na saki Hafsatu saki uku!ke kwarankwatsa da ana saki Hamsin da yau shi na maki Hafsatu……"ta karashe maganar tana wullo jikkunan,bakon dake tsakar dakin ……

 Yarinyar dake rike da jaririyar ta mike tana fadin "Wane irin wulakancine haka wae……Wannan,rashin adalcine Ummana tana da mijinta amma dan ta haihu shine zaa mana haka?

  Rike haba maitafasa tayi tana fadin "Owo Lauratu rashin kunya zaki man ,To kema wallahi sae kin bar gidan !Uban wa ya sani ko kema ba diyar tashi,bace……"

  Ta karashe maganar tare da turota waje ……Zatayi magana Hafsatun ta rufe mata baki sannan,taja hannunta suka fita daga gidan ba tare da sun dauki komae ba ……

  Mai tafasa ta bisu tana fadin "Shegu gayyar tsiya……"

  Yayin da matan garin da kananan yara suka bisu da ihu da jefa har suka bar garin ……# *FEEDOHM��*
[12:03, 24/11/2017] hm: ���� *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   ����
                      ��

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHM��_*
          *_&_*
 *_PRECIOUS HAJJA CE��_*


*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu**3 & 4*


  K'ira'ar Shiekh Ahmed sulaiman ke tashi cikin katon falon dake dauke da mayan kujeru……Gefe daya Wani kyakykyawan matashin yarone ke bin karatun cikin natsuwa idonshi a lumshe ……
Kujeran dake kallon tashi wata yar dattijuwar mata ce itama kyakykyawa zubin larabawa ……Kallo daya zaka mata ka gano tsantsar kamar da take da saurayin ……Sannan cikin second biyu zaka gane hutu da jin dadi sun ratsa mutanen dake zaune a falon ……

  Wayarshi kirar Iphone 8 ta dauki addu'ar Shiekh sudais a hankali ta yarda bara ta dami wanda ke kusa da ita ba ……
Lumsassun idanunshi ya bude ya kalli wayar sannan ya mayar dasu ya rufe……

      "Ma'aruf ba wayarka bace ke ringing……"Kamilallar matar dake zaune ta fada tare da kurawa wayar ido……

  Bude idonshi yayi  tare da bata fuska yana fadin "Message ne ya shigo Madre……"

  Mika hannu tayi tana fadin ……"Bani wayar na gani……"

  Kamar karamin yaro yace "Madre office ne fa ake kirana……!

  Harara ta sakar mashi tana fadin "Sae ka dauka kaji me zasu fada !kuma wallahi ta tsinke sae ka kira sh……Wae me yasa kake hakane Ma'aruf? idan bara kayi aikin ba ka aje mana  ka huta ko an maka dole……?

  Kallonta yayi da lumsassun idanuwanshi yana fadin "Madre shikenan mutun bara ya huta ba kullun aiki kamar engine……"

 Banza ta mashi ta juyar da kai gefe guda……
Wayar ya bi da harara sannan yasa hannu ya dauka yayi shiru ……
 
   Daga dayan bangaren akace "Sir akwae wani case na AFP da akayi reporting a jihar katsina ……So yanzu aka turo kai zakayi verifying dinshi daga England……"

 Kallon Madre din yayi yaga shi take kallo "Hello……"ya fada kamar zaiyi kuka tare da yanke wayar ……
  "Madre bana jin abunda suke fada ……"ya fada kamar ya fasa ihu

  Wayarta kirar IPhone7 ta mika mashi tana fadin "Ka kirasu anan !wallahi Ma'aruf duk abunka sae ka dauki wayarsu……"

  "Madre ……!ya fada kamar yayi kuka sannan ya dauki wayar tashi ya sake kira ……
  Bai amsa sallamar da akayi ba yace "Ka turo man Number State consultant dinsu……"daga haka ya mike ya bar falon ……

  Kyakykyawar matashiyar yarinya ta shigo sanye da atampha mai ruwan goro sae zanen ganye da akawa ado da ruwan toka kayan sun dace da jikinta……
Da fara'a ta isa gurin tana fadin "Madre Barka da safiya……"

 "Yauwa Sumayya!shiga dakina saman mirrow ki dauko trcts ki kaima Ma'aruf idan ya fita ya mikawa Abbansa office ni zan fita……"

  "To……" ta amsa tare da mikewa ta shiga dakin ta dauko sannan ta fita daga falon……
Sai da ta wuce balcony sannan tayi tafiya mai tsawo ta isa wani katon part dake zagaye da glasses……Wani red abu tayi clicking a jikin kofar sannan ta bude ta shiga ……
Katon falone kamae wanda ta baro sae dae wannan ya banbanta da wacen saboda complete kayan dake falon red ne harta plasma dake ciki ……

  "Yaya Ma'aruf ……"ta fada tana bin falon da kallo……
  Banza ya mata yana zaune bisa kujeran dake bayanta ……ganin zata shige bedroom dinshi ya sashi fadin "Sumayya……"Kasan makoshi ……

 Juyowa tayi tana turo baki tare da fadin "Shine ka shareni……?
 Ba tare da ya kalleta ba yace "Menene?

Kujeran dake kusa dashi ta zauna tana fadin "Madre tace na kawo maka ka kaiwa Abba idan ka fita……"

  "Aje ki tafi……"ya fada ahankali ba tare da ya kalleta ba ……

 Ta san hanlinshi sarai ta mike a sanyaye ta bar dakin ……

《》《》《》《》

  Tafiya sukayi mai tsanin nisa sannan Hafsatun ta zube bakin wani iccen kanya tana haki ……

  "Sannu Umma……"Lauratu ta fada tana dafa bayanta ……
 A Wahale ta gyada mata kai sannan ta sa hannu ta karbi jaririyar dake ta mutsu mutsu a hannu Lauratu ……

 Mama ta bata yarinyar ta karba da sauri tana wuntsila kafafuwa ……Murmushi Lauratu tayi ta kama kafar yarinyar tana fadin "Ummana da gaske wannan diyar Baffa ce……?

 Da Sauri Hafsatun ta kalleta da idanunta da suka cika da kwalla sannan ta sadda kai tana goge hawayen ba tare da tace komae ba ……
  Jikin Lauratun yayi sanyi tare da nadamar tambayar da tawa Umman tata duk da itama tana mamakin ta yarda zaa ce umman ta haihu ……Bayan tana sane da Baffanta da yayi shekara takwas a kwance ko hannu baya iya dagawa ,a inda yake nan yake kashi yayi fitsari sae dae Umman tata ke wanke mashi ……amma rana tsaka ace Umman ta haihu dole kanka ya daure……

  "Kiyi Hakuri Umma dan Allah bansan tambayar zata maki ciwo ba ……"Lauratu ta fada tare da dafa Umma……

 Bata ce mata komae ba sae bin kafafuwanta da kallo da tayi ,wanda suke wanke da jini ……rumtse ido tayi jin wani abu na tsira a kasanta sannan ta mikawa Lauratun Yarinyar ta mike da kyar tana fadin "Mu tafi Lauratu……"

  Cire zaninta tayi ta goya diya dashi sannan ta kama hannun Umman tata suka yanki daji ……

  Wannan karan tafiya kadan sukayi suka fara hango rukuni rukunim gidajen fulani dake cikin dajin ……

  Wani Gidan gandu suka nufa ……
Yara dake wasa kusa da gidan suka dauki ihu "Ga Hasfuwalle ga hafsuwalle……"

  Matan gidan da tsofaffi suka fiffito bakin kofar gidan suna fadin "Aradun Allah da gaske Hafsuwalle ce ……Sannu Hafsuwalle ansha hanya……Harda Lauratu yasin……"

  "Ato Meye haka nake gani bayanki lauratu……?Cewar wata tsohuwa dake kama da Hafsatu kamar an tsaga kara……

  Kallon Ummanta tayi da sauri sannan ta kalli tsohuwar tana fadin "Jaririyace Inno……"

  "Ina kuka sameta……?cewar matan dake gurin kamar hadin baki ……

  Wannan karan ma sae da ta kalli Umman tata wadda ta sadda kai kasa tana hawaye sannan tace "Ta Umma na ce……"
*#HAJJA CE��*
*#FEEDOHM��*
[12:03, 24/11/2017] hm: ���� *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   ����
                      ��

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHM��_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*��


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*       Page *5-6*

    *M*uryar inno ce ta kuma dukan dodan kunnan Hafsatuwalle "wai hafsatu sai kuka kike mana daga tambaya. Shin a ina kika samu jaririya d'anya sharaf?"

Kasa d'agowa tayi ta kallesu ganin gaba d'aya idanuwan su na kanta yara da manya karaf idanuwan jummai ya sauka akan kafar Hafsatuwa da jini ke bin ta tace.

"Shiiii kenan wallahi 'yar tace ga alamar jinin haihuwa nan mun shiga uku." Gaba ki d'aya mutanan wajan suka saki salati suna tafa hannaye, hakan ya k'ara tayarwa da Hafsatu hankali cikin sauri lauratu ta ja hannun Umman nata suka doshi cikin gidan da matan suka fito.

Cikin d'akin Inno suka shiga, itama da sauri ta bisu ciki "bafa zaku zauna min a d'aki ba alhalin bansan a ina kuka samo wannan jaririyar ba."

Inno ta fad'a tana nuna jaririyar dake rungume a jikin lauratu wadda ke ta faman bacci hankalinta kwance.

A hankali muryarta na rawa hawaye sun kasa tsayawa a fuskar ta Umma tace, "jaririyata ce inno ni na haifeta yau d'innan..."

Salati Inno ta kuma saki tana kama ha6ar ta "Hafsatu tayaya kika samu cikin har kika haifi yarinya duk bamu sani ba, kuma ai munsan malam lado ba lafiya gare shi baya iya komai sai anyi mai taya kika samu ciki kuma 'yar waye..?"


*{{   }}*

   "Bari ni kundum wallahi yarinyar nan ta bani mamaki ta rasa cikin wa za tace sai lado, ladon da kowa ya sani ba lahiya ce dashi ba amma tace cikin shine..."

Mai-tafasa tayi maganar tana sosa wuyanta alamar taji kaikayi a gurin. Kundum ta sake rafka gud'a ayyirrrr-yirrrrr, "koma dai menene *Abunda ke b'oye* ya fito fili sauran bayani dai yana wajan Hafsatuwalle."

"Tallahi kinji na rantse ko kundum? Yau da ace lado lajiyar shi lau hukuncin da zai yi kan Hafsatuwalle sai ya ninka wanda na mata..."

Lado dake kwance a d'aki sai faman k'ok'arin son yin magana yake amma ya kasa, hawaye ne suka fara zubo mai masu zafin gaske. Mai-tafasa ce ta lek'a d'akin ta ganshi sai kuka yake tayi saurin k'arasawa kusa dashi cikin takaici tace...,

"Yi shiru lado nasan Hafsatu ta cuceka, ganin baka iya komai yasa ta danganta cikin nan da cewar naka ne. Kayi hakuri lado wallahi da raina da lahiya ta bazan bari a cuce ka ba.."

Lado kam banda girgiza mata kai da yake yi babu wani abunda yake, hakan shine kawai sign d'in da yake iya yi hakan yasa ko fitsari yaji baya iya fad'a sai dai ya sake shi a wando. "Kayi shiru lado dan babu wanda ya yadda da zance Hafsat..."

Mai-tafasa ta fad'a tana fita daga d'akin ta karasa gurin kundum dake tayawta surfan masara suka ci gaba da tattaunawa akan maganar....,


*{{  }}*

     Bayan fitar Sumayya da kyar Mu'aruf ya mik'e, bathroom ya shiga wanda ya had'u yaji komai ya k'arasa ya shiga jarkuse wanda aka cika da ruwa mai k'amshi. Ya dad'e a ciki kafin ya fito da bathrobe a jikin shi. Dressing room ya wuce wanda shima ya gaji da tsaruwa sosai, direct underwears drawer ya wuce ya bud'e gasu nan ajere kamar a company ya zari vest da trunks yasa saka sannan ya k'arasa dressing mirror ya zauna kan stool yana shafa lotion mai kamshi tamkar bayasan shafar.

Drawern kayan shi ya k'arasa ya bud'e wadda baki d'ayan gurin suit's ne kamar na siyarwa kala-kala ya d'auki black color d'in ya sanya bayan yasa ta cikin white color...,

Gashin kanshi ya gyara sannan ya bi duk ilahirin jijin shi da turaruka kusan kala 6 masu kamshi ya sanya socks da sandal ya fito daga room d'in, be koma side d'in Madre ba kawai ya wuce parking lot ya bud'e motan shi white paradox dake ta kyalli ya bud'e yashi ga, office d'in abban shi ya fara zuwa...[13:32, 26/11/2017] hm: ���� *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   ����
                      ��

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHM��_*
     *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CE��_*


*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


     Page *7-8*


*Y*ana shiga office din ya iske Abban nashi baya ciki Messenger Office din ya tambaya ina Abban ?yace mashi sun shiga meeting ne ……Sakon ya bashi ya juya ya fita tare da gaisawa da wadanda ke mashi magana ……

WHO Office dinsu ya nufa ,Tunda ga waje zaka fahimci wayeshi ta yarda dukka mutanen gurin suke bashi girma Cikin mutunci yake amsa masu  gaisuwarsu saboda babu wanda bai girmeshi ba a gurin kawae Sa'ar Rayuwa Allah ya bashi……
Hadadden office dinshi ya nufa wanda ke dauke da kayan alatu na rayuwa
Coat dinshi ya cire sannan ya ja kujera ya zauna Bude laptop din dake saman table din yayi tare da saka siririn glass din dake aje kusa da wasu tarin files……Cikin natsuwa ya fara bincike yanayi yana lumshe idonsa wanda ya rigaya ya zame masa d'abi'a……
Duk wani abunda ya shafi case din da garin da abun ya faru an rigaya an turo mashi ta email dinshi har ta hotel da room number da zai sauka an turo mashi da number State Consultant da LGA facilitator dinsu ……

Dogon tsaki ya sake lokacin da ya rufe laptop yana fadin "Gwadabniya" tare da tabe baki……Bai bata jin sunan garin ba a rayuwarshi bare ya saka ran zaije wata rana ……Kara sakin karamin tsoki yayi ya dafe kanshi kamar ya sake ihu tare da cire glass din……

Komawa yayi bisa tarin takardun da ke aje ya fara bincikawa cikin natsuwa har ya fitar da da wani file。 sannan ya mike ya fita ya baiwa Messenger dinshi yace ya kaiwa Doctor Habib…………Gida ya nufa don ya shiryawa tafiyar saboda yarda ya tsara bara yayi kwana biyu ba a garin……


《》《》《》


 *M*alam Sani Mahaifin Hafsatu yayi sallama gidan…… tun kafin ya karaso cikin gidan Jummai ta tare shi a zaure tana rike da tabarya "Malan Hafsuwalle ta zo……" ta fada murya kasa kasa ……

  "Ahhaba ki ce baki mukayi yau, Marhaban da mutanen Keteriya!amma ita haka ake zuwa babu sanarwa ……?ya karashe maganar yana kokarin zagayeta ya shiga cikin gidan

 Cikin sauri tace "Har da jaririyar ta danya shar Malan……"

Yar dariya yayi irin ta manya sannan yace "Ai kunga abunda yafi haka indae Hafsatuta ce ,akwae janye janye yanzu haka ta makwabtace ta dauko!Hafsatu a akwae son mutane……"

  Murya kasa kasa tace "Kai Malan Hafsatun ka ta haifeta da cikinta…"ta karashe maganar tana nuna cikinta da hannu

  Wani kallo ya jefa mata yana fadin "Bana son zancen banza jummai,Malan lado ya warkene?

  Watsa hannu baya tayi tana fadin "Ina fa ya warke malan?abun kunyane ta janyo maka da mutuncinka a garin nan……"

  Bai ce mata komae ba ya wuce ya shiga gidan yana kwalawa hafsatun kira,Daga jin yarda yake kiran kasan bana kwanciyar hankali ba ne ,Dukka mutanen dake cikin d'akunansu suka fito sukayi cirko cirko suna maganganu kasa kasa wanda daga ji kasan gulma suke……Daga Hafsatun har Inno da lauratu suka fito waje……Hannu Hafsatun ya kurawa ido sannan ya kalli fuskarta ……

  Jikinshi yayi sanyi lokaci guda ya kalleta yana fadin "Hafsatu ina kika samo jaririya haka…?

  Kasa magana tayi sae kukan da ta saki a hankali tana kallon kasa ……
  "Dake nake Hafsatu!ina kika samo jaririya danya haka……"

  "Jaririya ta ce Ard'o…" ta fada cikin kuka…

 "Mijinki ya warkene Hafsatu……?ya tambaya cikin sanyin jiki

 Girgiza kai tayi tana share hawayenta ……
  "To Ina kika samota Hafsatu? d'iyar wacece haka?
  "Ard'o d'iyar Lado ce……!ta fada har lokacin tana kuka

  "Watsatstsan Zance Hafsatu ……Wanga zancen naki ko Shanun gidannan bara su karb'a " Cewar mutanen gidan kamar hadin baki……

   Da Sauri ya karbi jaririyar daga hannunta ya nufi wata katuwar bukka yana kwalawa Sallau kira …Sallau ya fito daga bayan gida rike da katuwar sanda a hannunshi yana fadin "Shanun ne suka balle Ard'o"
 
  "Fiton da Turmin kurtumi Sallau……"Cewar Ard'o yana nuna bukkar da hannu……

  Matan gidan suka dauki magana kasa kasa tare da kallon juna suna taba hannuwa……

   "Malan karka yi kisan kai ,ka dae san wannan jaririyar bata halak ba ce tunda tsawon shekaru takwas mijinta baya da maraba da gawa……"Cewar Jummai tana kokarin karbar yarinya

  Cikin matan wata tayi zagal tace "A Kara ya kasheta da wannan mugun abun kunyar da ake niyyar dauko mana"

 Hafsatu banda kuka babu abunda takeyi ,ita kam lauratu shiru tayi tana kallon ikon Allah ,haka Inno bata iya cewa komae ba don ta yarda da Hafsatu bara ta aikata abu mai muni irin haka ba ……

 Gangaro da katon bak'in Turmin ne yasa gidan ya kara kaurewa da maganganu kasa kasa……

Ard'o bai ce komae ba ya jefa yarinyar cikin Turmin ya ma sallau alamar da ya miko mashi tabarya……

  Babu musu Sallau ya mika mashi katuwar tabaryar tare da ja baya……*HAJJA CE��*
*FEEDOHM��*
[13:32, 26/11/2017] hm: ���� *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   ����
                      ��

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHM��_*
&
*_K.A.S Precious HAJJA CE*��


*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu*        Page *9-10*


    *G*aba ki d'ayan mutanen gurin jikin su yayi sanyi dan sunsan yau kwanan jaririyar ya kare. 6angaran Hafsatuwalle kuwa ko d'ar bata jiba sai dai hankalinta a tashe yake dan tasan ko anyi wannan abun babu wanda zai yadda da ita cewar yarinyar lado ce, ba tare da ta ankara ba sai jin daka tayi tumm... *!!!* nan ta bi Ard'o da idanu yadda ya zage yana daka jaririyar tamkar yana daka gumba.

   "Kur'anin Allah 'yar nan ta halak ce, gashi nan da ranta garau..."

Cewar Sallau yana k'okarin fito da jaririyar da Ard'o ya gama kir6awa tamkar ma babu abinda aka yi mata dan yadda aka sata haka aka fito da ita subul...

Duk jama'ar gidan suka waro ido da tsananin mamaki kafin kowa ya maida hankalinshi ga Hafsatu dake kallon k'asa tana wasa da jelar gashin ganta. Inno ta dafe k'irji tana kallon Hafsatu cikin nuna sonjin k'arin bayani.

   "Hafsatu gamu ki gaya mana ya akai kika samu wannan cikin harkika haife shi bayan munsan lado bashi da mamora tsawan shekaru..."

Fad'in yabint tana daga nesa amma tana son jin tsegumi da jin kwakwaf...

     "Yabint *!* ai na gaya muku cewar jaririyar nan ta lado ce tunda gashi turmin kurtum ma ya shaida gaskiya..."

Hafsatu ta kuma fad'a nan da nan magan ganu suka ci gaba daga baku nan mutanan gidan k'asa-k'asa, Ard'o ya zabura tamkar zai tashi sama yana kallon Hafsatuwalle yace...,

    "Aradun Allah wannan maganar tak'i Hafsat akwai d'aure kai, muna son mu shaida zancenki tunda ga turmin kurtumi ya shaida amma ai lado bashi da lahiya bayya iya yin komai taya wanga lamari ya faru? Zamu je can shi gwadabniya dan mu shida."

Turmin kurtumi dad'add'an turmine tun zamanin iyaye da kakannin, al'adar garin ce in dai mace ta haihu dole ne aje a sashi ciki a kir6a dan tabbatar da cewar yaron ko yarinyar ta halak ce.  Tsafataccen turmi ne sannan kuma yarda da imanin da alummar garin suka yi da hakan shine yasa indai suka daka mutum a ciki be mutu ba to hakan ya tabbatar musu da cewar d'an halak ne duk kuwa da cewar tsakanin ma'auranat akwai sadaki amma duk sanda suka haihu sai an saka yaro a cikin turmin kurtumi ko kuma cikin wuta da take ci ganga-ganga tamkar za'a kuna karamin daji..."
    (Wannan ke nan)

Kus-kus aka farayi kafin inno ta furzar da huci mai zafi tace.

     "Ni dai kam Hafsatu zaman ki ba dai a d'aki naba. Ard'o sai dai ka sama masu inda zasu tsafa rayuwar su ni dai kam bada niba..."

Guri ya kaure da hayaniya kowa ya nuna badashi Hafsatu zata zauna ba, sallau yasa suka yi shiru Hafsatu na hawaye ganin kowa yak'i ta lauratu ta k'arasa tare da kama hannunta itama cikin kukan take mata magana k'asa-k'asa.

     "Umma ta kiyi shiru ki dena kuka, idan kowa ya guje ki ni ina tare daku kiyi hakuri Umma na..."

Kafin Hafsatu tayi magana sukaji muryar Ard'o na cewa.

     "Mukam dai Hafsatu sai dai ki zauna a rumfar Yafindo, amma damu da yaran mu babu ruwan mu daku karku shafa mana *Abunda ke 6oye* har sai randa munkaji gaskiya."

Nan da nan hayaniya ta kaure a cikin gidan Kafin kace me, tuni an watse daga gurin kowa ta kama harkar gaban shi ana ta yada magana lauratu taja hannun mahaifiyar ta suka shiga cikin d'akin Yafindo da aka basu shi. Babu koma cikin sai k'asan ma duk k'asa ce haka suka shiga lauratu ta cire mayafinta ta nunkashi tasa a k'asa sannan ta kwantar da yarinyar akai.

    "Umma ya kinka sa sunan jaririyar...?"

Tana hawaye jikinta na rawa ga jini sai zuba yake ta k'arasa gurin jaririyar tana shafa kanta tace "lauratu na sanya mata suna *Hafsat* Allah shi raya mana ita."

Lauratu tace "amin Umma....."


* *      * *

     *G*wadabniya *!*.... Sunan dake yi mishi yawo a cikin brain d'inshi kenan, mtww ya saki tsaki yafi sau ashirin ko sunan ya tuna ranshi 6aci yake baran tana idan ya tunu cewar shine zashi can d'in....,

    "Ma'aruf ya dai lafiya ko?" Madre ta tambaya bayan ta shigo cikin parlorn daga gani itama daga wajan aiki ta dawo.

    "Madre gobe zanyi tafiya zuwa katsina kan wani case da zanje nayi solving d'in shi..."

"Shine Ma'aruf ka zauna kanata faman 6acin rai kai d'aya?" Madre ke fad'in haka tana kokarin zama cikin d'aya daga kujerun da suka k'awata d'akin.

Shiru Ma'aruf yayi yana turo baki ya k'i kuma had'a Ido da ita Madre ta girgiza kai da mamakin shi cikin zuciyar ta tace.

     "To ka tashi kaje ka shirya mana ka zauna sai tunani kawai kake yi. Flight d'in nawa zaka bi..?"

A harzuk'e ya tashi tsaye fuskar shi a d'aure ya ce mata "Madre 8:00am." Yana fad'a be jiraci cewar ta ba yabar parlorn kamar zai tashi sama wajan fita suka yi karo da Sumayya amma ko ta kanta be biba ya wuce part d'inshi.

Bedroom ya wuce ya fa fad'a kan bed tare da rik'e kanshi me barazanar tsagewa sabida tsabar sara mishi da yake yi. Ya kusa 2hours a kwance kafin ya tashi ya koma dressing room ya fara shirya kayan shi. Har aka kira magrib sannan yayi alwala ya wuce masallaci dan gabatar da sallah, ana idarwa ya koma side d'inshi ya ci gaba da shiryawa har ya kammala ya koma parlorn shi ya zauna yana jin tsanar zuwa kauyan.

    "Yaya Ma'aruf Madre na kiranka." Sumayya ta fad'a cikin d'ar-d'ar tana kallon shi. "A'm coming."

Yace da ita ba tare da ya kalleta ba, kura mishi idanuwa tayi cike da tambayoyi uwa uba kaunar shi da soyayyar shi dake addabar rayuwarta ya d'ago tare da sauke mata uwar harara ta juya da gudu tabar d'akin.

Ko 2minit bata yiba sai gashi, zama yayi Madre ta dube shi tace, "kazo kayi denner Ma'aruf." Lokacin abban shi ya shigo duk suka yi welcoming nashi kafin suka wuce dining gaba d'aya.

Tsakurar abincin kawai yake kafin yace "Abba gobe zan wuce katsina akan mai Apf d'in nan by 8:00am jirgin zai tashi."

"Good my son, Allah ya bada sa'a I know my son is a nice musamman akan aikin shi, Allah ya baka sa'a my son."

Madre da Ma'aruf suka had'a baki wajan cewa "amin..." Sumayya ta saci kallon shi suka had'a ido ta sakar mai kayataccen murmushi ya harareta tare da mikewa yace ya koshi sannan yabar side d'in zuwa nashi.

Washe gari yana gama shiryawa wajan 7:00am ya fito dan tafiya airport cikin shigar shi ta suit milk color abinka da beauty sai yayi bala'in kyau. Room din Abba ya shiga tare suka fito suka had'o da Madre a kitchen ta fito hannunta rik'e da wata kyakyawar leda ta mika mai suka rakoshi har inda drive ke jiranshi suna ta mai fatan alkairi da samun nasara, jiyayi tamkar karya tafi ya barsu amma Abba ya karfafa mai gwaiwa suna d'aga mai hannu har suka bar compound d'in.

Sumayya kam bata san ya tafi ba sabida tsabar baccin da take yi, sai da ta farka wajan 11:15am sannan take tambaya Madre tace "ya tafi kilama sun sauka yanzu....."
*FEEDOHM*��
&
*HAJJA CE*������ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   ����
                      ��

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHM��_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CE��_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


   page *11-12*Tunda asuba Lauratu ta tashi fita tsakar gida ta iske Jummai na surfen geron da za'ayi karin kumallo dashi yau "Gwaggo jumma Ina kwana?ta fada tare da dukawa har kasa

  Yatsina fuska tayi tare da tabe wargajejen bakinta sannan tace "Lahiya"
Mikewa Lauratun tayi ta nufi murhu ta debo kakare ta hada wuta sannan ta dauki tukunya ta nufi randa zata debi ruwa……

  Da Sauri jummai ta matso tana fadin "Ke ke tsaya ruwan me zaki diba kuma?

  "Ummana zan daurawa ruwan wanka……"

 Wani kallo ta watsa mata sannan tace "To bada ruwan gidan nan ba wallahi don babu shegen da yace ta haihu acikin mu……"

  "Haba Gwaggo Jumma tunda fa ta haihu batayi wanka ba ,dan Allah ki sammani na diba ko ya yane ta samu taji karfin jikinta "ta karashe maganar tana kallon kasa idanunta cike da kwallah……

  "Kar ta ji karfin jikinta lauratu!idan abun ya dameki kije ki debo mata a rafi mana ina jin kinsan inda zaki debo mata!Muma mazajenmu suka debo mana don muyi amfani dasu ba dan ayiwa Shegiya wanka ba……!ta karashe maganar tana tada jijiyoyin wuya

  Juyawa tayi ta dauki tulu ta fita ba tare da tace komae ba sae dae zuciyarta dake tafasa kamar ta kone……Da tsaki Jummai ta raka tana fadin "Shegu masu abun kunya"

  Cikin Sauri ta debo ruwan ta dawo ta sake hada wata wutar har sae da sukayi zafi sannan ta leka bangaren Inno ta aro katuwar ruba ta juye rabi……
Sauran kuma ta zuba a bokiti ta kai ban daki……

Jaririyar ta amsa daga hannu Umman tace "Umma ki tashi kije kiyi wankan na kai maki ruwa a bandaki……"
 A Hankali tace "Nagode ……"sannan ta mike ta fita tayo nata wankan……Jaririyar ta saka cikin ruwan ta gasata sossa……

  Tana gama mata wankan ta ladeta cikin kallabinta tana kallonta ,Tausayin yarinya ya kamata sosae ganin ko Dan kamfai bata dashi,Daukarta tayi ta goya sannan ta fita daga gidan……

Gidan mai unguwa ta shiga ta tambaya ko akwae Surfe,Cikin sa'a suka bata masara tiya goma suka ce a surfa zasuyi tuwon sadaka da ita ……

  Haka ta ja masaran ta koma gida lokacin mutanen gidan sae karin kumallo suke ,Bukkarsu ta nufa ta iske Umman a zaune ba'a kawo mata komae ba ,hawaye taji suna niyyar zubo mata ta fita da sauri tana tambayar Jummai ina abun karin kumallon su……
Matan gidan suka dauki sowa suna fadin "Ashe har abinci gareku bayan abun kunyar da kuka dauko mana "
Wata ta amshe da fadin "Shi kwarton uwar taki bai kawo maku komae ba?ko bai san ta haihe mashi diya ba ?

  Jummai ta amshe da fadin "Ke nifa ban yarda da yadda Ard'o ya k'irba yarinyar nan ba! don wallahi kadan yake saka tabaryar a ciki ko diyar bata tabawa"
  "Nima wallahi abunda nake son fada kenan,kawae raina mana wayau yayi don ya fahimci shegiya ce……"

Inno dake tsaye tana jinsu ta kira lauratu ta mika mata nata abun karin kumallon ta juya a sanyaye ta koma dakinta ……
Lauratu kam Umma ta kaiwa abun karin kumallon ta juya zata fita ta kira ta tace tazo ta zauna taci ……
Duk da irin yunwar da take ji murmushi tayi tace "Nasha nawa Umma"

 Ta dade tana kallonta sannan ta gyada mata kai tana share hawayen da suka zubo mata ,Da sauri lauratun ta fita ta fara surfan masarar ……
Kafin rana ta take ta gama surfewa har an bata kudinta naira d'ari ……Jaririyar ta kwanto tana fadin "Umma ki bata abinci yanzu zan fita da ita……"

  Cikin sanyin jiki tace "Ina zaku je Lauratu?
  "Umma dan kamfai zan sawo mata da riga a Gwadabniya nan garin ba'a siyarwa……"

  "Ina kika samu kudi?
  "Umma surfe nayi yanzu"ta fada tana rike kafar Jaririyar……
Shiru tayi tana kallonta har sae da jaririyar ta dauke kai daga MaMan sanna lauratun ta dauketa suka tafi……

【】

 *M*a'aruf yana isowa aka bashi Guard mace sannan suka nufi Ward din cikin HLuxur……,Focal person suka dauka sannan suka nufi Gwadabniya……Ganin yarda suke keta daji ya sashi sakin tsaki lokaci lokaci ,Bai taba tunanin akwae mutanen da ke rayuwa ba a wannan dajin ……
Saukin suma Hluxury ce ba'a cika gane wahalar tafiya da ita ba don bata raina tudu da gangare ……
Gidan Mai unguwa suka sauka Ma'aruf na cikin motar bai fito ba .Mai unguwar ya leko yana washe jajjayen hakoranshi ,daga mashi hannu kawae yayi sannan ya bude motar ya fito Guard dinshi na a bayanshi……

  Gidn Malan Lado suka nufa tare da dandazon yaron da suka zagayesu……Har cikin bukkar ya Shiga ya dubashi sannan ya fito yana karewa ilahirin mutanen dake gidan kallo ……
Uban wari ke fita ta ko'ina ga ruwan da ya kwanta tsakar gida ……Dan karamin tsaki ya sake ja lokacin da Maitafasa ta iso gabanshi tana fadin "Yaro yaya kaga jikin nashi?dan Allah ku taimaka ya warke ko ya dauki Fansa a kan cin amanar da matarshi ta mashi ……"

 Banza ya mata ya juyar da kai gefe guda tare da fita daga gidan suka tsaya jikin motar yanawa Focal person magana ……

Lokacin Lauratu ta iso garin tana hango dandazon yaran da matan aure da itama ta kutsa kai cikinsu ta tsaya gaban Ma'aruf din tana sauraren abunda yake fada duk da dai ba ganewa take ba saboda mafi maganarshi turanci yafi yawa ……

Uban Ihu Jaririyar ta saki tana kuka …
Kallonta yayi ya dauke kai saboda baya kaunar kuka yana fadin "Bar nan gurin……"Fuska a daure

  "Ina Saurarenka ne Bature……"ta fada tana jijjiga yarinyar,Cigaba da kukan jaririyar tayi tana mutsu mutsu a bayanta ……Kukan ya fara isarshi cikin tsawa yace "Shut up ki bar nan gurin……"

  Dariya tayi tace "Ba sunana Shutu ba Sunana lauratu!yar kanwata kuma Hafsatu……"

  "Hafsah……"ya fada yana kallonta "Kawota mu gani……"ya karashe maganar tare da mika mata hannu

Da mai unguwa ake kokarin kwanto yariyar tare da mika mashi"Me yasa ba'a saka mata kaya ba?ya fada idonshi na kan yarinyar……

"Bata dasu Bature shegiya ce ita ce warda Uwarta taci amanar mijinta da ka dubo yanzu……"Cewar mai tafasa sannan ta kalli lauratu tace "Karbeta ki bar nan tun kafin na fasa maki kai……"

  Fitinannen kallo ya watsawa Mai tafasar sannan ya fito da kudi akalla sunkai 50k ya mikawa Focal person din yace "Ka sayar mata duk abunda ya dace……"Mikawa lauratun ita yayi ya bude mota ya shiga Sannan Focal person din ya karbo sample Urine din da akace a kawo suka shiga motar suka tafi ……

  Mai tafasa da sauran mutanen garin Mamaki ya hana su magana har sae da suka bar ganin kurar motar su sannan Mai tafasar ta juyo da niyar Zazzagawa Lauratun ruwan masifa amma ta nemeta ta rasa……

Lauratu kam bayan gida ta zagayo ta shigo ta karare ta shige bukkar Malan Lado ……Kwance ta iskeshi kamar kullun idonshi a rufe sae dae hawayen dake zubowa……kwanto jaririyar tayi ta daura mashi saman kirji ,ya dube ido da sauri yana kallonsu ,lokaci guda ya fara gyada kai yana murmushi dake dauke da hawaye yana kallon yarinyar ……
Jikin lauratun yayi sanyi tace "Baffa yarinyar ka ce ko?

Gyada kai yake da sauri yana murmushi ,Itama murmushi tayi ta janyo kwanon furan da ta gani gefe tana fadin "Baffa ka sha?

  Girgiza mata kai yayi yayin da murmushin fuskarshi ya bace ,Shiru tayi sannan ta dauke diyar daga jikinshi ta dago kanshi tana bashi furar……
Sae da yasha sossae Sannan Jaririyar ta tsangare da kukan da yasa Mai tafasa da kumdum suka nufo bukkar suna fadin "Wane Shegene anan ciki?

Kwantar dashi tayi da sauri ta dauki jaririyar ta fice ta yar kofar dake bayan bukkar ta bi ta karare ta fita ,Suna shigowa suka ga babu kowa……

Kundum tace "Lado hala wannan Shegiyar yarinyar ce ta shigo……"
  ���� *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   ����
                      ��

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHM��_*
&
*_K.A.S Precious HAJJA CE*��


*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu*


        Page *13-14*

    *S*hiru yayi ba tare da yayi magana sai faman binsu da kallo yake har suka fita suna wa lauratu masifa ga bak'in cikin ganin uban kud'in da aka bayar wai a siyama jaririya kaya.

"Kur'anin Allah ko Mai-tafasa? Ina tausayin Hafsatuwalle duk ranar da lado ya samu sauk'i. Cewar kundum tana kokarin fita daga gidan gashi daga ita sai karigirji da zanin tsohowar atamfa wanda yaji dunyi ta d'ora akanta ko yaya ta d'aga hannu gashin hammata ne cacim tamkar zakayi kitso.

"Humm *!* kaji ki Kundum da wani zance, yo ce miki aka yi yadda zai yi? Jira kawai nake aradun Allah yaji sauki har gida zamu je ya tona mata asiri, dan taga ba magana yake yiba shine zata mai sharri muguwa kawai."

"Mudai muna jiran ganin irin hukuncin lado, dan a lokacin ne *Abunda ke b'oye* zai hito hili..."
    Kundum Tana fad'a tabar gidan da ragowar guntun gulman ta, lado kam yana ciki kwance yana jiyo su ji yake tamkar ya tashi amma ba dama hawaye suka zubo mai kafin kuma yayi murmushi yana kallon kirjinshi dai-dai inda laurtu ta d'ora mai jaririyar.

*{{ }}       {{ }}*

    Lauratu na shiga kauyan su da farin ciki dan har tama manta da zance wani 6acin rai sai da tashiga gidan su taji fad'uwar gaba ta k'arasa cikin rumfar su.

A zaune ta ga Umman ta tayi ta gumi wanda daga gani tayi nisa cikin tunani, duk sallamar da lauratu keyi Umma bata jita ba sai da ta k'arasa kusa da ita tare da janye hannun ta wanda ta tallafi habarta dashi tace "Umma na lahiya ko?" Kallon lauratu tayi tare da k'ak'alo murmushi wanda be kai cikin zuciyar taba, "me zata cewa lauratu bayan duk tunanin ta yana kan yadda taga tun yanzu ana muzguna musu *!* ana kyarara su tamkar tumaki, koda yake yanzu tumakin su sun fisu daraja da kima a idanun mutanan gidan." Umma Hafsatu ta fad'a cikin zuciyar ta, ganin irin kallon tuhumar da lauratu ke yi mata ne yasa ta kara wani murmushi cikin sanyin murya tana kallon Hafsat dake hannunta tace.

"Ba komai lauratu ina nan ina tunanin ku karkuje wasu suyi muku wani abun. Har kin samo mata kamfai d'in?

Umma ta fad'a cikin yana yi na bagarar da tunanin lauratu da ta kafeta da manyan idanuwanta. Zama lauratu tayi akan langa-langan data kwana akai jiya sai faman k'ara yake k'arass-k'arass ta bud'e guntun d'ankwalin da ta nad'e Hafsat dashi tana nunawa Umma kanfan (pant) da ta sai mata tare da cewa.

"Eh Umma na samo kuma munje gidan Mai-tafasa har muka tarar wani bature mai kyau yazo yana duba Baffa. Sannan Umma ya bada kud'i yace a siyawa Hafsat kaya amma banga mutumin ba sabida na zaga gurin Baffa har yaga Hafsat yayi murna."

Hirarsu suka yi ba tare da kowa ya lek'osu ba. Ganin rana tayi ne yasa su fitowa tsakar gida dan su kamawa mutanan gidan aiki. Da sauri Bultuwa ta janye kwanan garin dake gaban ta ganin Umma na kokarin kar6a dan ta tayi tankad'an cikin nuna kyama Bultuwa na sosa cikin hancinta tace.

"Kaunan Hafsatuwalle ki bani guri da wannan kazamin jikin naki. A kul *!* na sake ganin kinzo wai da nufin ki kamamin aiki na bana so." Cak... *!* Umma ta tsaya tana mata kallan mamaki lauratu ta sunkuyar da kai cikin takaicin ganin yadda ake musu wulakanci Mai-aya dake rik'e da tukunya tace.

"Aikuwa dai gara kiyi kayanki kar a goga miki cikin kato kema wataran kiyi." Wata mata itama dake gefe guda tana yiwa yarinyarta tsifa gashin yarinyar jawur kamar anrina shi ga uban kasa akai amma jira ake a tsefe ayi kitso ba tare da an wanke ba tace, "Bultuwa kinyi dai-dai tallahin Allah k'ara da kika d'auke kayanki."

Jin maganganu sunyi yawa ne yasa Umma da lauratu komawa cikin rumfar su, zama suka yi akan mayafin lauratu da ya zamar musu kamar da6en kasa Umma na kuka k'asa-k'asa ta kalli lauratu da itama hawayan take yi "lauratu kiyi hakuri kuma ki yadda dani cewar Hafsat ta lado ce k'anwarki ce karki biyewa bakin mutanan nan...."

Lauratu ta gir-giza kai sannan tace, "Umma rik'eta naje na dawo yanzu." Kar6arta Umma tayi tana kallon lauratu "ina zaki kuma da rana haka Laure???"

"Umma gidan mai-unguwa zani ana bada tuwon sadaka nima bari naje na kar6o mana." Tana fad'ar haka ta fita bata jira cewar Umman ba.....

*{{ }}*

Yana komawa cikin hotel d'in da aka kama mai ya cire kayan jikin shi tare da shigewa toilet, wanka ya dingayi sabida shi a tunanin shi ya kwaso wannan warin da yaji a gidan da suka je, sai da ya tabbatar ya cud'a ko'ina sannan yayi alwala yafito jikin shi d'aure da towel hannunshi da small one ya k'arasa jikin dressing mirrow yana goge jikin shi mai d'auke da kwantaccen gashi mai yawa a k'irjin shi da hannayen shi da kafafuwa.

Tsaki yayi ta faman saki yana tuno yadda yaga suna shiga kauyen daga manya har yara dukun-dukun dasu hanci duk majina sunyi fututu kamar suna birgima a jar kasa, suna hango mota kowa ya fara gudun shiga gida, yaji haushi sosai sai kace wasu 6arayi.

Zama yayi akan stool ya fara shafa k'amsassun lotions a jikin shi, murmushi yayi wanda yasa fararan hak'oran shi bayyana masu kama da kankara lokacin da ya tuno sanda ya ce "shut up *!*, tace "ba sunana Shatu ba sunana lauratu kanwata kuma Hafsatu.."

A hankali cikin sauti k'asa-k'asa ya furta "village girl.." Lokacin ya kammala shafa duk wani abu da yake bukata sannan ya doshi drower ya janyo boxer short da vest ya sanya tare da d'aukar phone d'inshi yayi dailing numbern Madre.

Tana shiga yaji muryar Sumayya cikin d'oki, kafin tayi magana yayi saurin katseta da cewa "where is my Madre? Please ban son wani magana ki ba ta ina son yin magana da ita." Ranta ya 6aci tayi kamar zata yi kuka tace.

"Amma Yaya Ma'aruf me yasa baza ka bari mu gaisa ba? Sai kace ba kanwanka ba kayi ta min haka?"

Tsaki yayi tare da lumshe idanuwa a hankali yace "to naji mu gaisa amma bana son k'orafi." Bata yi fushi ba duk da taso tayi mai korafin me yasa ya tafi basu yi sallama ba amma ya hana hakan yasa ta cewa.

"Ina yini ya aiki? Normal." Kawai yace mata yayi shiru jin haka yasa tace mai "Yaya ga Madre d'in." Tare da mik'a mata ita kuma ta koma gefe tana jin Madre nayi mai fad'a akan yadda yake nuna cewar baya son zuwa kauyan wai basa wanka shi kanshi marar lafiyar yana bukatar gyara, nan tayi ta nuna mai cewar duk d'aya suke sai wanda yafi wani tsoran Allah.


*FEEDOHM*��
&
*HAJJA CE*��


*HAJJA CE��*
  &
*FEEDOHM��**_HAJJA CE_*��
&
*_FEEDOHM_*��
Copied By
YAYA HAYAT
        (admin
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
                   AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)


      WHATSAPP NO:
   +2349030159301
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


    Page *15-16**M*aganganun Madre su shigesu sosae ……Sun dade suna waya sannan ta yanke , Lokacin sumayya na zaune kusa da ita ta kalleta tace "Madre wae Yaya Ma'aruf bara yayi aure bane……?

 Dariya Madre tayi sannan tace "Wane irin Aure Sumayya?Duka Ma'aruf din nawa yake?He's 24yrs idan wannan month din ya mutu,Kawae Allah ne ya bashi sa'ar rayuwa……"

 Bata Fuska tayi tana fadin "Amma Madre ai yana da abunda zai rike mata yanzu!kuma wallahi baki ga yarda yan mata ke sonshi ba a waje,don babu wanda zaice bai kai 30years ba gaskia a nema masa yarinya cikin family dinmu yayi aure kawae……!

  Dariya kawae Madre din tayi ba tare da tace mata komae ba……Ita kam bara ta kashe danta ba tun yana yaronshi tafi son shekarun shi su kai 32 sannan yayi auren don lokacin ta tabbata ya san yarda zai zauna da Mace ……

  Sumayya kam haushi taji da Madre bata yarda da zancenta ba Ita idan san samu ne tafi son da ta gama secondary School a mata aure dashi tunda yanzu SS3 Take domin a tsarin rayuwarta babu batun cigaba da karatu……

*Ma'aruf*

Ma'aruf Muhammed Ma'aruf shine cikakken sunanshi !D'and'a ne Ga Alh M Ma'aruf da Hajiya Hafsat Madre!Suna Zaune a garin Kaduna Unguwar Sarki Mahaifinshi Babban Dan kasuwane yana da company a Ibadan da suke fitar da sweet ta Splash sannan yana da wani a kaduna da suke buga robobi……Yaransu biyu Maryam ce babba sae Ma'aruf !amma ita tayi aure har da yaranta biyu……Ya tashi cikin gata da kulawa tare da tsantsar addini daga gurin iyayenshi da yar'uwarshi ,Yana da shekara Sha bakwae ya gama secondary school dinshi cikin shekara daya ya samu admission kasar Egypt cikin Cairo anan yayi karatunshi tsawon shekara 4 bangaren Laboratory sannan ya dawo Nigeria! Allah ya bashi sa'ar rayuwa ya samu aiki a World health organization a matsayin WHO Consultant……!
 
  Sumayya yarinyar k'anin Madre ce tun bayan rasuwar Babanta ta dawo hannun Madre da zama, tun lokacin da ta dawo ta dauki Son duniya ta daurawa Ma'aruf  bata da wani tunani sae tunanin ta aureshi……Shi kanshi Ma'aruf din ya sani saboda tasha fada mashi amma ko kallonta bayya yi……!

【】
 
  Ma'aruf Bayan Madre ta yanke wayar Ya dauki siririn farin glass dinshi ya saka sannan ya janyo laptop ya duk'ufa yana yan bincike ……

Focal person din kuwa suna rabuwa da Ma'aruf LGA meeting suka shiga sae da suka gama sannan ya shiga central market ,yan kayan jarirai ya sawo mata da basu wuce na 10k ba sannan ya dawo ya kawo ma mai ungua yace ya kai masu ……

Mai ungua ma sae da ya tsintarwa yarinyarshi sannan ya taka da kanshi ya kaimasu ,Lauratu ta amsa tare da godiya sannan ta kaima Umman nata……

《》《》《》

Rayuwa su Hafsuwalle suke cikin k'yara da tsangwama Dukkan gidan babu mai zuwa kusa dasu hatta yara k'anana an hanasu zuwa inda suke zaune ……Sae dae kullun Lauratu zata dauki kanwarta suje Gurin Baffa a sace ba tare da kowa ya sani ba……

Haka Hafsuwalle ma takan Saci jiki taje ta gano mijinta ba tare da kowa ya sani ba wani sa'in sae taje take bashi abinci sannan ta gyara mashi inda yake kwanciya……

  Abinci da zasu ci ya fara gagaran su don Sau daya ake basu abinci a rana shima sae da daddare kuma ko Lauratun bara ya isa ba bare su biyu……don haka Hafsuwallen da Lauratu suka dage suna surfen kudi……da kudin suke samu su sayi gero da yar masara suyi abinci duk ranar da basu da abunda zasu ci haka zasu wuni da yunwa ko da za'a zubar da abinci gabansu……K'ara ma Inno wani sa'in tana kula dasu ……Abunka ga Uwa sae ta fara tausayinsu ta je ta samu Ard'o tace ya masa kamata suje gidansu Malan Lado suji me ake ciki……

  Bai musa mata ba ya shirya shi da Hafsuwallen da jaririyarta suka tafi ……Suna shiga garin yara suka taresu da "Ga Gayyar Tsiya……"

  Ard'o Ya kalli Hafsuwallen a sanyaye jin abunda yaran garin suke fada ,Duk'ar da kai tayi k'asa tare da gyara goyonta ,Cikin k'ank'ani lokaci mutane suka fara fitowa daga gidanjensu don ganin su waye Gayyar tsiyar ……

  "Lallae Gayyar Tsiya ……"Cewar Kundum tare da komawa cikin gida ta samu Mai tafasa Da ke zaune tana tsige tafasarta tace "Abun kunya baya karewa su Hafsuwalle "

A Zafafe Mai tafasa tace "Ke kundum ni bana son munafunci!dan kinga bana son ko jin sunan Hafsuwalle shine da gulmarki ta motsa sae ki dinga k'ira man ita ……"

  Watsa hannu tayi tana fadin "A Hayye ……Maida wukar Mai tafasa!Hafsuwalle da tsohunta na gani sun nufo gidan ga Shi yasa na zo na fada maki don ki tanadi kalamun ci masu mutunci……"

  Zumbur ta mike tare da hankad'e kwaryar tafasar ta zube kasa tayi waje tana fadin "Da kwarankwatsa yau garinnan sae nayi kisan kai !Banda dibar Albarka bayan cin amanarmu da akayi shine za'a kwaso kafufuwa ace za'a shigo mana gida!Uban me ya kawoku kai kuma tsohon banza ka kwaso lauyayyen wuyanka kamar rakumi ka taso yarinya gaba me zaku fada mana!

  Tsaye sukayi kamar an dasa kara suna kallonta har ta karaso gaban Ard'o ta tsaya tana watsa hannuwa baya"Na ce me ya kawoku kuma? ……Lallae Ard'o ka cika babban banza tunda har baka ji kunyar shigowa garinmu ba ……Da kwarankwasa kunji kunya maciya amana kawae……"

Danne Fushin shi yayi yana fadin "Kiyi hakuri Tsohuwa mu shiga ciki sae muyi magana……"

Hannunta ta watsa saman fuskarshi"Anki a shiga d'in Tsohon kawae marasa mutunci watsatstsu masu gadon abun kunya!Mu shiga ciki kayi mani me yan iska?wallahi Ard'o ni da ku sae rashin mutunci a tsakani "

 Juyawa yayi a fusace yana kallon Hafsuwalle "Kinji Kunya Hafsatu kin saka an wulakantani a inda ba'a isa ba, tur dake!

Kuka ta saki da karfi tana girgiza mashi kai "Ka Gafarceni Ard'o Wallahi ban aikata abunda suke zargi ba"

 "Tur Dake Hafsatu!Me yasa lokacin da Ladon ya nemeki baki nuna mashi aibun da abun zai haifar ba kin biye mashi kin saka an wulakanta mu !kin haifar mana da abun kunya a zuri'armu wa zai yarda d'iyar Lado ce ……!

  Kundum tace "Can ta matse maku munafukai Sae a k'ara gaba Don Mai tafasa ba sakarai bace da zata karbi Shege!

  "Bana son fa munafunci Kundum idan ina tsiyata ki daina saka man wagegen bakinki……!Mai tafasa ta fada tana watsa hannu gaba sannan ta shige gidan tana fadin "Wani kukan ma Sai ranar da Ladona ya warke……"

*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
   *&*
*FEEDOHMπŸ’ž*

πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


_Assalamu alaikum masoya masu bibiyar *ABINDA KE B'OYE..!* fatan alkairi gare ku tare da d'inbin godiya, hakika muna jin dad'in yadda kuke bibiyar labarin tare da ganin d'inbin comment d'inku mungode Hajjafeedohm suna sonku baki d'aya_πŸ’―

    _Ina kike *AMAL BAII..?* wannan shafin nakine danjin dad'inki ke kad'ai, mun gode da soyayya we love you muma sosai-sosai_πŸ‘ˆπŸ’žπŸ˜˜    Page *17-18*


    Juyawa suka yi Hafsatun na kuka suka tafi ……Sauran mutanen garin suka bisu da ihu tare da zagi har suka bar garin ……

  Koda suka koma Gida Ard'o duka mutanen gidan ya tara tsakar gida a fusace yace "Ni kam dae na yafe Hafsatu cikin yarana don haifi yarinyar da zata saka a wulakanta ni ba……"

 Kuka Hafsatun take kamar ranta zai fita yayin da ta duk'a saman guiwarta tana bashi hakuri amma sam yak'i kulata ya juya zai tafi ……Inno ta kasa jurewa ta tareshi a sanyaye tana fadin "Ard'o ka saurareta dan girman Allah!ka gwada wanga jaririya ka gane ta halak ce mai yasa zamu k'ita?

  "Saboda iyayenta yarinyar basu karbeta kuma nima na kasa gasgata Hafsatu akan Hafsatu yau aka wulakanta ni a ci man zarafi taya zan karbi Hafsatu?Ban hana Hafsatu rayuwa a gidana ba amma ko k'wayar hatsi ban yarje a bata ba……" Yana gama fadar haka ya juya ya bar gidan

【】

  Bayan Sati biyu Ma'aruf ya bayar da Magunguna aka kawo ma Malan Ladon kafin su gama bincikensu a kanshi sannan ya koma gida ……

Tarba ya samu sosae gurin Madre da Abba……Sumayya kam sai iyayi take amma ya nuna bai san tanayi ba ……
Sae da ya huta sannan ya kalli Madre yana bata fuska yace "Madre karatu zan koma wallahi wannan aikin duk karyace an rigaya anyi eradicating cutar a nigeria hakanan muke wa mutane karya……"

Hararanshi tayi tace "Bana son haka Ma'aruf aikin naka kake karyata?

 Langwabe kai yayi yace "Madre gaskia na fada ni karatu zan koma"
 "Kace karatu zaka koma Ma'aruf Simple!
 Lumshe ido yayi yace "Eh Madre
Murmushi tayi tana girgiza kai sannan ta janyo wani littafi ta mika mashi tana fadin "Ka duba wannan littafin akwae addu'o'i da yawa a ciki sannan yau kayi istihara ka nemi zabin Allah akan karatun ko barinshi Kafin na Fada Abbanka ……"

  "Thank you Madre……"ya fada yana murmushi
Daga haka suka cigaba da firansu……

  Bayan yayi istihara ya fadawa Madre din cewa yana tunanin Karatun nashi alkhairine Ita da kanta ta fadawa Abbanshi……Abunka da masu kudi cikin kankanin lokaci aka shirya tafiyarshi kasar India ……Kuka kam Sumayya tasha shi kamar zata mutu……

【】

Su Hafsuwalle rayu suka fara yau da dad'i gobe ba dad'i Har Hafsat K'arama ta fara wayau dukan gidan daga Lauratu Sae Umma ke daukarta tun tana ganin mutanen gidan tana mika masu hannu alamun su dauketa har ta daina sae dae idan Lauratu na aiki ta rarrafa kusa da katuwar bishiyar kukar dake gaban gidansu ta zauna anan zatayi wasanta ita kadae har sae lokacin da Lauratun ko Umman suka gama aikinsu sannan su dauketa su shigar da ita gida ……Wani Sa'in har a gama Magrib tana zaune gurin sannan ko zatayi kukan duniya babu wanda zai kulata daga iyalen gida bare ya dauketa ……Gashi Allah ya zuba mata wani irin kyau kamar ita tayi kanta da farin jini ga mutanen waje amma na gidansu basu kaunarta……

Lokaci na kara ja Har Hafsa karama tayi shekara hudu da haihuwa lokacin ta fara magana sossae sae dae bata cika surutu ba idan kaji tana magana to da Lauratu takeyi……bata kula ko wane yaro kamar yarda babu mai kulata,Duk wani hidimarta ta ya koma hannun Lauratu abunda ke hadata da Ummanta idan sunzo bacci!amma zata wuni tana wasanta a bakin bishiyar kukar ita kadae saboda duk sun hana yara tsaranta wasa da ita……

Cikin lokacin kankani ta gane wani irin kuka na masifa duk in lokacin Magrib yayi haka zatayi ta ihu tana zambarwa tare da mike mike kamar zata shid'e ……Tun abun baya damu Umman har ya fara damunta yarinya zata wuni tana wasanta amma da Magrib tayi ta gama walwala har sae dare ya take !wani sa'in ma haka za'a wuni ba'a ganta ba Sae gab da mangrib sannan Lauratun Zata ganta zaune kusa da katuwar kukar dake gefen gidan……

Cikin Dan lokacin Sallau yaron kanwar Ard'o ya nuna yana son Lauratu da aure ……Dukkan mutanen gidan kin amincewa sukayi wai kada a goga masu abun kunya……Amma da yake Tsaye yake ya nuna babu wanda ya isa ya hanashi auren Lauratun tunda ba ita ce tayi abun kunyar ba……
Ba dan anso ba aka saka baikon Lauratu da Sallau……Da yake gidan gandu ne anan ya yanki fili ya yi karamin dakinshi ……

  Lauratu na Zaune tana wanke kwanunkan da sukayi amfani dasu, Ummansu kuma tana surfa masara……Mutanen gidan kowa na aikin gabanshi masu yada masu magana nayi masu habaici ma nayi amma babu wanda ya kulasu  ……

Hafsa karama na zaune bakin bishiya tayi bud'u bud'u da jikinta ko riga babu a jikinta d'iyar kara ta hada tana saka mata kayan leda hankalinta kwance sae murumushi take zubawa kamar tana wasa da mutane……

Jummai ta gifta ta gabanta tare da kwallo da kayan wasanta tana hararanta tace "Shegiyar yarinya ita ba gidan ubanta ba amma ta cika mana gida da tarkacen hauka…… "

Dagowa tayi tana hararanta cikin maganar da bata biye mata baki ba tace "An Dummai Allah ya isa ……"

  Finciko ta tayi ta wanka mata mari sannan tace "Shegiya mara kunya ni zaki ma Allah ya isa to k'ara man Allah ya isan ki ga yarda zanyi dake a gidanki"

Dukar da kai tayi tana surutai kasa kasa tare da hararan jummai ta kasan ido, lauratu tayi saurin zuwa gurin ta kamata tana fadin "Me yasa kika mata Allah ya isa K'arama?

 Shiru tayi tana kallon katon cikin Jummai sannan tace"Ba abincin amarya bane ta zubar!Kuma sae na fadawa Ayd'o Mijinki ya satar mashi kaza kun dafa a daki kun cinye"

  "Eyeh Ni zaki jawa Sharri k'arama"Jummai ta fada tare da fiddo idanu waje sannan ta bar gurin buguzum buguzum tana waigensu kai da gani kasan bata da gaskia……

 Da Kallo Lauratu ta bita sannan ta ja hannun Hafsah din suka nufi inda suke aje ruwa tana fadin "Kar na sake jin wannan maganar kinji ko ?sannan waya fada maki Sun Saci Kazar Ard'o K'arama?

  Kallon lauratun tayi da idanuwanta da suka rine suka koma jawur dasu wanda har lauratun sae da ta tsorata ta saketa tare da ja baya sannan tace tace "Ni na gani kuma idan karya nayi ki duba cikinta akwae sauran naman da bai narke ba……"

 Dafe kirji tayi tare da ja baya tana kallon Hafsa tace "Na Shiga uku ni Lauratu ya za'ayi naga cikin mutun K'arama ?

  Shiru ta mata ta debi ruwa tana sha lokaci guda idanuwan suka washe suka koma fararensu tas sannan ta nufi bukkarsu ta bar Lauratun tsaye tana kallonta……
Da Sauri ta nufi gurin Ummansu tana fadin "Umma kin ga Idon K'arama kuwa?

 A Sanyaye tace "Me ya sameta?
Zatayi magana ta hango Hafsa din tana niyar Fita daga gidan bayanta ta bi tana kwala mata kira amma ko ta juyo…… har sae da ta kai bakin bishiyar  da take zama sannan ta zauna ta dauki wani katon Dutse ta daura a cinya tana girgiza kafa tare da murmushi……

  Tsaye tayi tana kallonta sannan ta koma gida ta cigaba da aikinta sai dae duk jikinta yayi sanyi ……Sae da suka gama abinci sannan ta je da kanta ta janyota suka shiga bukkar su suka zauna……
Daga kai tayi ta kalli Ummansu Tace "Yaya Lauratu Baffa nake son gani……"*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
      *&*
*FEEDOHMπŸ’ž*
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S Precious Hajja ce*πŸ‘ˆ


*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu*


        Page *19-20*


    *D*asauri lauratu ta kalli k'arama tana zaro idanuwa cikin tsananin mamaki ganin dare ne amma take cewa gurin baffa zata, cikin tsoro wanda ya bayyana karara a fuskar lauratu tace cikin sanyi, "K'arama ya zamu je can gwadabniya cikin daran nan tsakani da Allah?"

Baki ta turo cikin shagwa6a, kafin kace me tuni fuskar hafsat k'arama ta sauya tayi saurin kwantawa akan zanin dake shimfid'e a k'asa inda suke kwana tayi shiru tamkar me bacci Umma da lauratu suna ta tashinta amma tayi kamar tana bacci hakan yasa lauratu dubawa taga lallai baccin take sannan ta kalli Umma tace "Umma 'yar rigimar Mu tayi bacci muma Mu kwanta yadda zamu tashi da wuri muyi sissikar nan."
   Daga kwancen da suke suka yi 'yar hira kad'an abinka da gajiyayyu tuni bacci ya d'auke su gaba d'aya. Jin saukar numfashin sune yasa Hafsat saurin mikewa sai faman zazzare idanuwa take gashi yadda take yi d'in tamkar wata babba, sim-sim-sim ta fito daga d'akin ba tare da kowa ya ganta tayi kauyan gwadabniya harda 'yar wakar ta.

Sai da ta fara lekawa d'akin mai-tafasa, ganinta tayi tayi bajebaje akan garu tana bacci baki sake hanci a sama sannan ta juya ta shiga inda lado ke kwance da fitilar kwai a kunne wadda take shirin mutuwa sabida k'arancin kananzir. Kallon fitilar kawai k'arama tayi sai ga haske ya k'aro lado kwance yayi fitsari gurin sai zarni yake babu me gyarawa suka had'a idanu tayi mai murmushi tare da k'arasawa gurinshi tana janyo tuwan da tagani wanda ko alamar ta6awa ba'a yi ba tace.

"Baffa bata baka abinci ba ko?" Ta fad'a tana shirin gutsurowa tare da kaiwa bakin shi yayi saurin bud'ewa sabida dama yinwa yake ji amma babu me bashi, yana ci yana jin kaunar ta na k'ara shigar shi, sai dai yana mamakin yadda yaga duk k'ankantar ta amma shigen surutu da iya sannan yadda zata yi komai, ta dad'e a gidan kafin ta koma gida, sai da ta dad'e a gurin bisjiyar kukan nan kafin ta shi ga ciki har lokacin babu wanda ya farka ta lalla6a tsakiyar su ta kwanta.....,

*{{ }}*

*INDIAN NEW DELHI*... All cikin university d'in cike take da al'umma kowa ka gani da abunda yake yi sannan babu ruwan wani da shiga harkar wani a cikin masu fitowa daga cikin wani katafaran hall harda Ma'aruf yafito hannunshi rik'e da brief case kai da ka ganshi kasan yana d'aya daga cikin wad'anda suka kwaso gajiya, tafiya yake a hankali amma shi a hakan mugun sauri yake, sai dai kai da kagan shi zaka ce ko baya san taka k'asa ne. Da d'an gudu budurwar ta k'arasa inda yake tare da sakar mata murmushi, kallonta yayi cikin takaici dayan baya buqatar komai yanzu banda ya kwanta gashi ita kuma zata uzzara mai, cikin tsuke fuska yace.

"Please n please Aisha kinga yanzun na fito daga lecture so ki barni naje na huta karki sa raina ya 6aci." Ma'aruf ya fad'a yana kallon cikin idanunta, kasa musa mai tayi sabida wani irin kwarjinin shi take ji hakan yasa yan zuma matsawa tayi ya wuce tabi bayan shi da kallo cikin tsananin so da begenshi har ya tari texi ya shiga tana tsaye.

Aisha budurwace kyakyawa gata da kamun kai, ba 'yar kowa bace hasalima da shocolaship tazo university d'in. Tunda idanuwanta suka dira akan na Ma'aruf taji duk duniya babu wanda take so bayan shi, da ta ganshi zata je inda yake wai ko zai kulata amma ina tayi hakan yafi sau d'ari hakan yasa duk tsananin kunyarta sai da ta tunkare shi akan suyi friendship amma kullum da uzurin da zai kawo mata duk da irin nacin da take mai.

Ma'aruf na komawa hotel d'in da yake brief case nashi ya ajiye kafin ya cire kaya ya shiga bathroom, wanka yayi sannan yayi alwala ya fito, pray mat ya shimfid'a yasan ya jallabiya coffee color ya hau yayi sallan asar, sai da ya idar sannan yayi shafe-shafen shi lokacin aka yi nooking door d'in ya bud'e ya kar6i odern abincin da yayi, dawowa yayi ya zauna a kan pray mat d'in yafara cin abincin tare da kunna t.v yana kallo. Sai da ya kammala komai sannan ya koma kan bed, laptop ya kunna ya fara laluban focal person  d'inshi dan yana son yaji karin bayani akan gwajin da suka yiwa lado.....

*{{ }}*

Yanzu kam baki d'aya al'ammuran hafsat k'arama ya fara bamawa kowa tsoro kasan cewar duk wanda yayi wani abun a gidan sai ta tona mai asiri, har wannan lokacin iyalan gidan nan babu wanda ko da wasa ya ta6a d'aukarta yara sa'aninta da wad'anda aka haifa bayanta duk basa kulata, jin dad'in ta kawai taje jikin bishiyan kuka ta zauna anan zaka ga farin ciki da nisha d'inta.

Zaune take yan zuma jikin kukar hannunta rik'e da wani kara karami sai kallonshi take tana dariya gashi daga ita sai pant yayi dukun-dukun da jirwayen fitsari hancinta duk majina ta bushe, Ard'o ne yazo wucewa da yaron shi a kafad'ar shi sai mika mata hannu yake Ard'o na bigiwa wai baxa shiba. "Ayd'o yana wasa ka bashi ni muyi taye."

Hafsat k'arama ta fad'a tana kallon Ard'o ya wurga mata harara "ke ki raba kanki da iyalina idan ba haka ba kaniyar ki zanci." Cewar Ard'o yana gyara wa Tanimu d'anshi rikon da yayi mai ta kuma kallon shi idanunta jawur kamar taruwar jini tace.

"Iya julai (zulai) matar Ard'o tana shama hira (fura) daka iteye (ajiye) a taki (d'aki)..." Numafar gidan Ard'o yayi yana shiga rumfar shi ya hangi zulai akan nono da furar daya ajiye yace sai dare zasu sha.

"Zulai *!* ya fad'a yana zaro idanuwa tare da ajiye Tanimu a kasa ya k'asa ciki yana kare mata kallo jikin ta sai rawa yake yau asirinta ya tuno tana goge baki Ard'o yace "daman kekike shanye duk abinda na kawo gidan ga amma kike cemin awaki ne ke shigowa ciki? Yau dai k'arama ta tona miki asiri kuma zan d'auki mataki akanki kinsan halina..."

Yana fita tayi kwafa tare da yin alwashin cin kaniyar hafsatu karama tunda ta tonata bayan shekara da shekaru babu wanda ya sani. Ita kuwa Umma Hafsatu har ta dena damuwa da halin da Hafsat k'arama ke yi dan idan ta hanata tonan sililin ma kamar k'ara zuga ta ake yi......*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S Precious HAJJA CE*πŸ‘ˆ


*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu*        Page *21-22*

Hutun da yazo ne kwana biyu wanda sati biyu kawai zai yi ya koma shiyasa shi shiryawa dan komawa katsina, cikin shirin shi ya fito na blue jeans da white d'in t.shit hannun shi d'aure da whech mai ratsin color blue a jiki sai cover shoe white da siririn glass a fuskar shi yayi hanyar side d'in Madre.

"Ahh Ma'aruf yau kuma sai ina? Cewar Abba dake kokarin fita suka had'u a k'ofar parlorn. Kallon shi Ma'aruf yayi tare da yin k'asa da idanu yana sosa cikin dumbujejan lallausan gashin kanshi yace "Abba zan shiga katsina ne ina son zan nayi solving problems na wannan men d'in, so yau zan shiga gobe ko jiba zan dawo."

Abba yayi murmushin jin dad'i tare da cewa "To my son Allah yayi jagora ya kuma baka nasara." Ma'aruf yace "amin abba na gode sai na dawo." Daga haka suka yi sallama abba ya fita shi kuma ya k'arasa gurin Madre ta bashi breakfast yaci sannan suka yi sallama tayi masa fatan alheri ya shiga mota drive yaja. wannan karan ma ba su yi sallama da Sumayya ba tana bacci ya tafi.

Yana sauka aka kuma had'ashi da wata sabuwar guider d'in, ta wannan karan tantiriya ce idanunta a soye suke sai dai kuma suna had'a idanu taji tana wani mugun tsoran shi ba shiri ta koma normal na matsayin ta na guard. Focal parson d'insa ne ya karaso sannan suka shiga mota suka wuce kauyan gwadabniya.


*{{ }}*    *{{ }}*

Yauma kamar wancan karan mutanan kyauyan suka dinga gudu tamkar zunga zakuna, suna karasawa kofar gidan malan lado kundum ta fito da sauri tare da yank'are baki tana kiran Mai-tafasa...

"Wallahi ke dai kam kundum kin shiga uku sauran ki kirss ki lalace, aikin banza ke ba dai ajiki da bakin alheri ba sai akan su Hafsatuwalle, *!* aikin banza ai na san dama yaune ake d'amrawa lauratu aure amma dan tsohon muna hirci kinzo zaki min gulma da....." Bakinta ya mutu lokacin da taga shigowar su Ma'aruf cikin gidan.

Direct cikin d'akin da lado yake kwance suka shiga Ma'aruf sai faman toshe hanci yake sabida tsananin d'oyi, wari da hamami dake tashi a gidan, da kyar ya iya tsayawa a gurin lado yana mai gwaje-gwaje duk da anyi dama amma anga cutar AFP d'in sai dai rashin yin rigakafinta ya sanya yayi haka sannan kuma ba ita kad'ai ce tasa mai wannan larurar ba domin da itace zai iya moruwa da wani sashe na jikin shi amma wannan duk jikin shi babu mamora. "Mai kyau Allah yasa dai lado na zai warke?"

Cewar mai-tafasa tana dashare mai wawulan bakinta wanda yayi jawur gashi gaban ba hakura, banza yayi mata tare da bada wani magani focal person d'in ya d'ago lado ya bashi yasha sannan suka fito dan zuwa gidan mai unguwa sumai karin bayani.....


*{{ }}*

Tararwa suka yi an gama d'aurin auren lauratu da sallau akan sadakin akuyar da sallau ya bada, karasawa suka yi gidan mai unguwa mutane suka biyo su mata da maza yara da manya ciki harda mutanan gidan su Hafsatuwalle, ita kad'ai ce bata fita ba kasan cewar ko taje da zagi da cin mutunci zata dawo. Carpet focal person ya fito dashi daga cikin mota ya shimfid'awa Ma'aruf sannan mai unguwa ya zauna a shimfid'ar shi yana dasharewa Ma'aruf wangalelan bakin shi...

Banza yayi mai zai fara bayani sai ga lauratu ta karasa kusa dashi cikin farin cikin ta tace, "bature ashe zaka dawo garin mu? Ai munga  kaya sunyi kyau kuma ankasawa Hafsat tayi kyau itama Allah ya biya." Ajiyar zuciya ya sauke yana mamakin kafatanin 'yan garin da irin halin su "bature nima yau aka d'amra aure na kaga mijina can sallau." Muryar lauratu ta dakar mai cikin kunne, bin point d'in da tayi mai yayi da kallo har ya kai ga fuskar sallau yayi saurin rintsa idanuwan shi ya zura hannu ya Ciro 10k ya bata yace tayi hidima idanun mai unguwa akan kud'in yana son yasan yadda zai samu wani abun aciki kud'in.

*AFP* (Acute Flaccid Paralysis) ita ce ake cewa cutar shan'inna, sannan Likitoci sun ce a yankin kudu da Hamadar Sahara, mutum miliyan 12 zuwa 15 ne ke fama da cutar amosanin jini kuma kashi sittin cikin 100 suna Najeriya.

   Ba a san haΖ™iΖ™anin yawan masu cutar amosanin jini ba, amma dai Ζ™wararru na cewa mutum miliyan ashirin zuwa miliyan ashirin da biyar ne ke fama da ita a duniya. Haka kuma duk shekara ana haifar mutum kimanin 2,400 masu wannan cutar.

Mafi akasarin inda ake samun yawan wannan cutar ta shan'inna shine a *kauye*, cutar AFP na samuwa ne ta hanyar kazanta, rashin tsafta sune suke kawota, kuma tana samuwa ta kananan yara daga shekara 1 zuwa shekara 5. Malan lado yana d'aya daga cikin wad'anda ke da cutar sai dai rashin kulawa da rashin yadda da rigakafi da kauyan suka yi shine ya janyo mishi samun matsala a cikin jikin shi, wani lokacin idan ciwon ya motsa jikin shi babu inda yake mai aiki ko kuma yayi ta cewa a matsamai jiki sabida yadda yake ji a haka har..." Ma'aruf ya zaro idanuwa kirjinshi na dukan uku-uku ganin wata hallita tazo ta zauna akan cinyar shi sai wangale mai hakora take yi tamkar wata aljana. "Allahumma ajirni filmusibati fakalufli min khairu minha."

Ita kawai Ma'aruf ke fad'a a fili, ganin haka ne yasa guard d'inshi saurin zuwa dan ta d'auke ta sai taga idanuwan yarinyar sun koma wani irin abu tayi saurin matsawa baya tamkar wadda aka kafe ta tsaya. Masifa 'yan garin suka fara masifa ita kuwa Hafsat k'arama ta juya tana kallon Ma'aruf wanda ke zaune cikin tashin hankali da tsananin tsoro, sauran kiris ya saki fitsari ya jiyo muryar mai unguwa na cewa.

"Ke shegiya yarinya k'arama kin tashi daka kan bakona ko sai na ham6are ki ja'irar yarinya fitinanniya...?" Ya fad'a yana kokarin tashi yaji ya kasa, shi kam Ma'aruf daya tambatar da cewar mutum ce sai ya dawo cikin mode d'inshi amma duk da haka kirjinshi be dena bugawa ba ya kalleta yana kokarin  mikar da ita yaji tana shafa mai sajen da ya kewaye fuskar shi da hannuwanta masu bududu da jar kasa, ya lumshe idanuwa zuciyar shi na shirin fitowa waje.... "K'arama zo mutai gida gurin Umma mun barta ita d'ai." Lauratu ta fad'a tana karasawa gurin tare da kallon Ma'aruf tace "bature Hafsat ce wadda ka siyawa kaya shekarun baya..." Tayi saurin jan hannuta shi kuma jin sunan yasa shi saurin bud'e ido........

*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*     Page *23-24**D*a sauri ya mika mata hannu yana kiran "Common ……"

  K'arama tayi saurin fincike hannunta daga Lauratun ta dawo tare da zama saman cinyarshi ta zuba mashi manyan Idanunta !Kallonta kawae yake, yarinya mai kyau amma tayi duk'u duk'u da ita ……Idan baka kai zuciya nesa ba sae ka rantse ruwa bai tab'a hawa jikinta ba……

  "Yaro Ummana tace idan yaya Lauratu tayi aure dakinta zan koma……"Maganar da ta doki kunnenshi kenan yayi saurin maido natsuwarshi ……

 A Sanyaye yace "Ko……"

  Mai'unguwa yace "K'arama da k'warank'watsa na mike sae na ci Ubanki idan baki d'aga man bak'o ba……"


 Hararanshi tayi k'asa k'asa tana turo baki tace "Balan Sauka in ba! b'arawon masara……"

 
   "Uban Waye b'arawon "Ya fada a harzuke sannan yace "Kai bawale je kace Uwar wanga diya ta sameni gida idan rana ta take……"

  Ma'aruf ya kalli guard dinshi a raunane don har ga Allah ya gaji da zaman K'arama a jikinshi yace "Dauk'e ta zan tashi……" kafin ya rufe baki ta sakar mashi fitsari a jiki da sauri ya runtse ido zuciyarshi kamar ta fito dan takaici

  Zaro Ido tayi tana fadin "Sir wallahi baran iya taba ta ba ji kamar wata Vampire……"
 
  Lauratu ta matso a sanyaye ta kama ta da kyar suka shiga gidan tana turje turje ……

   A hankali ya mike ba tare da yace komae ba ya bude mota ya fito da robar swan ya fara tsiyayawa inda ta mashi fitsarin !Gashi duk inda ta taba a jikinshi kamar an debi bakin tukunya a shafa a gurin !tsaki ya saki lokaci guda ya shige motar yana kakkab'e jikinshi……Mai'unguwa ya rakashi ya rufe mashi motar sannan guard dinshi ta shiga suka tafi ……Suna tafiya mai unguwa ya fada gidansu yana kiran "Ke Lauratu fito"

  Cikin sauri ta fito ta tsaya gabanshi ta sadda kai a kasa don ta tabbata ba abun kirki ya kawoshi ba……Gulmammun matan gidansu da ba'a kira ba suma suka fito sukayi cirko cirko tsarkar gida suna jiran su ji ta inda zai fara ci mata mutunci'
 
  Bata fuska yayi yana hura hanci yace "Ina kudin da bak'ona ya baki……?

  Kanta na K'asa tace "Suna a daki na aje! idan Umma ta gama Sallah zan gwada mata "

Hura hanci ya kuma yana fadin "Rabasu Uku ki bani kashi biyu……!

  Da Sauri ta kalleshi take idanunta suka ciko da kwallah tace "Dan Allah mai ungua ka rufa man asiri ka bar kud'in dan Allah! wallahi ko langa Ummana bata sayar man ba da za'a ba uwar mijina!Yan kudin da muka tara kwanaki an sacesu tun dazu ummana ke kuka bata da abunda zata kai man a daki !Dan Allah ka rufa mana asiri tunda Allah yaji k'anmu mun samu !Wallahi idan bamu sayi komae ba Gori zamu sha da cin mutunci har ya'ya' da jikoki……"

  Banzan kallo ya watsa mata yana fadin "Bansan Shashanci banza !idan da bai baki kudin ba ya zakuyi!Ni mai unguwa nace kije ki raba kudi uku ki kawon kaso biyu idan kuma kika kara magana da k'warank'wasa duka zan karbe "

  Jummai ta tabe baki cike da bakinciki tace "Wallahi kama yi masu arziki da baka amshe duka ba Yo aikin me ta mashi da zai bata kud'i……!
 
  Laminde ta dauka da fadin "Yo Banda ma kana adalin Mai unguwa taya zaka bata kaso daya ka dauki biyu bayan gurinka yazo! aikin uban me ta mashi……?

 Washe baki yayi yana fadin "Kin kuma yi Gaskia Laminde ……"

   Lauratu ta fito rike da kudin a hannunta ta mika mashi Dubu Shidda ta dauki Hudu  tana hawaye …… kirgawa yayi yana fadin "Dubu Shidda kenan !ke nawa ne a hannunki?

  A Hankali tace "Dubu Hudu ne"

Bahaggun salati suka dauka suna fadin "Amma dae Lauratu anyi munafuka!Ina laifin ki dauki dubu uku tunda uku yace ki raba !wato mai unguwa zaki munafunta ko ?

  Girgiza kai tayi tana kokarin danne kukanta tana fadin "Wallahi a'a canji zan samo na cika mashi jikka uku da murtala……"

   Jummai tace "Uwar canji zaki samo bayan kin lahe kudi a hannunki !an dae ji kunya har mai unguwa ba'a raga mawa ba……"

  Warce kudin yayi daga hannunta yana fadin "Kin rasa duka wallahi munafuka kawae !ni wallahi na gaji da zamanku a wannan kauyen kun dauko zunubi kun hana mana bunkasar arziki……"

  "A Hayye……"Matan gidan suka dauko tare da kashewa suna dariya !Wata ta dauka "Mun ga abunda uwar taki zata hada maki zuwa gobe tunda an karbe wadannan masu bakin hali anyo abun kunya an dawo an tile mana anan …"

  K'arama dake tsaye bakin kofar bukka tana murda hannunta ta kallesu tare da kwashewa da dariya tana tabe baki "Wae abun kunya an tilele……"ta fada tana saukowa daga tudunkar ta nufo Lauratu dake kuka tace "Sae kiyi Hakuri Tunda shima ku'in (Kudin)nashi zubewa zasu har da na aljihunshi……"

  "To Mai bakin baki ……"Cewar Zulai matar Ardo tare da matsowa tana kallonta
 
  "Anya K'arama ba Mayya bace?Jummai ta amshe tana rike Hab'a
 
  "Idan itace ma yanzu zanyi maganinta wallahi!Jummai samman barkono da Tsakin kuka tare da kakkabin daudawa……"Zulai ta fada tare da fincikarta ta wulla wata tsohuwar Bukka dake kusa dasu……

  Da Sauri Lauratu ta rike Zulai tana fadin "Wallahi Inna Zulai ba Mayya bace dan Allah karki mata hayaki yarinya ce……"

 "Idan ba mayya bace ki bari a mata hayakin mana Tsohuwar munafuka" Jummai ta fada tare da mikawa Zulai Barkonon da tsakin kuka da Daudawa har da uban garwashin da ta debo a katuwar tukunya……

  Da Gudu Laure ta nufi Bukkarsu tana fadin "Umma dan Allah ki fito wallahi zasu kashe K'arama wae mayya ce"Turus tayi ganin Umman nasu tsaye tana lekensu ta wata yar kofar dake cikin bukkar tana kuka……

  Cikin kuka tace "Umma ki fito dan Girman Allah……"

  Girgiza mata kai tayi tare da rufe bakinta ta sulale gurin ta fashe da kuka mara sauti ……Sanin ko zata kwana a gurin Umman nasu bazata fita ba ya sata fita daga dakin da gudu ta nufi tsakar gida ……
 
  Tari ta fara da karfi tana dafe kirjinta jin azabar barkonon dake fitowa cikin Bukkar da suka rufe K'arama ……Bukkar ta nufa jin Tarin da K'arama keyi tana kokarin budewa amma Jummai ta kwalfa mata mari tare da hankadata gefe tana fadin " Yau *ADUNDA KE B'OYE* Ga wagga yarinya sae ya fito dan ubanki ……Kuma da k'warank'wasa ya tabbata mayyace sae mun hada wuta mun jefa Shegiya"

  Har Sae da Hayakin ya bar fitowa daga Bukkar sannan Zulai ta bude, lokaci guda ta waro ido tare da ja da baya tana fadin "Na ga Shegiyar yarinya !Wato dan ubanki carafke kike ko ……"ta fada hade da karasawa cikin dakin ta janyota tare da watsa mata mari tana fadin "Idan ke ba mayya bace to ke Shegiya ce kuwa!

  Kwace hannunta tayi tana wurga mata Harara ta K'asan ido tace "Kece Mayyan Julai……"

  Sannan tayi gaba ta barsu tana tsallenta har ta shige Bukkarsu ta fada saman cinyar Umman tana fadin "Na ci dad'i yau Ummanmu……"

   Kasa ce mata komae tayi sae rungumota da tayi tana kuka ……Ita kam K'arama bata ga abun kuka ba don ta haka ta ware idanu tana kallon Umman tata ko kyaftawa batayi……

  Lauratu kam bayan Zulai ta mareta bayan gida ta zagaya ta zauna tare da hade kai da guiwa tana kuka ……Dafata da akayi ne ya sata dagowa da sauri tana kallon Matashiyar yar fillon dake tsugunne gabanta ……
 
   Cikin Fara'a yar fillon ta janye hannunta daga jikin lauratun sannan ta janyo wata karamar jikka ta mika mata ……K'in karba tayi tana kallon Yar fillon cikin rashin sani don bata taba ganin mai ko kama da ita ba a yankinsu……
 
  "Ungo Lauratu……"Yar fillon ta fada tare da kamo hannunta ta daura mata jikkar ……Kafin ta bata amsa ta mike da sauri ta bar gurin……

  Kallon Jikkar Lauratu tayi a sanyaye sannan ta mike ta koma cikin gida har lokacin tana kuka mara sauti ……Ganin matan gidan ko wace ta kama harkar gabanta yasa ta shige bukkarsu da sauri……Ganin Umma kuka ya sata sulalewa a k'asa tare da yarda jikkar ta hau nata kuka ……Ita kam K'arama raba ido take ta kallansu……


《》《》《》《》

  Ma'aruf kam tunda suka shiga motar ya rufe idonshi gam ya kasa budewa K'arama yake hangowa lokacin da ta saka k'azamin hannunta ta shafi sajenshi !K'ara runtse idonshi yayi yana girgiza kai ……

  Driver ya kalleshi yace "Sir da matsala ne……?
 
  Girgiza mashi kai yayi a hankali yana ware hannunshi daga jikinshi……Guard din ta saki dariya cikin sigar jan hankali tace "Sir ya hadu da aljana ne……"

  "Haba dae……"Driver ya fada yana dariya a hankali……

  Dariya ta kuma yi tare da leko kanta tana kallon Ma'aruf din tace "Serious!Sir ka bude idonka mun bar garin sossae fa……"ta karashe maganar tana kashe murya……

  Duk abunda suke fada yana jinsu amma tsabar Aji irin nashi ya hanashi bude ido bara ya kula su ……

  Office dinsu suka yi parking lokacin Yan'mata ke ta dawowa daga aikin da suka fita ……

  Katuwar tabarma ce cikin barandar office din Focal Persons na wards tare da team volunteer da CCO da Facilitator ke zaune suna cin abinci hankalinsu kwance……

  Rab'a su yayi ya wuce ya zauna bisa kujeran dake gefe guda tare da rufe ido kamar yana ganin wani abun cuta……
 
  Gaidashi sukayi ya amsa masu ta hanyar daga masu hannu ba tare da ya bude idonshi ba ……

  Facilitator ya matsa yana fadin "You're welcome sir!Tun dazu Director ke jiranka
a ciki……!
*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
  *&*
*FEEDOHMπŸ’ž*
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*       Page *25-26*


Ba tare da ya bude ido ba yace "Ta fito nan……!
  Cikin kulawa facilitator din ya kalleshi yace "Da matsala ne Sir……?
 
  Kafin ya bada amsa Guard din tace "Oga da Matsala wallahi !wata aljanar yarinyace ta haye jikin Sir duk ta birkita mana shi……"

  A Fusace yace "A ina?

   Tabe baki tayi tana fadin "A Wannan karamin kauyen da ake samu mai AFP case dinnan fa……"

 "Ina Mai unguwar garin?Meye amfaninshi da za'abar yara suna zuwa kusa dashi?kema meye amfanin ki? sannan meye amfanin driver'n da aka hadaku dashi?Kin san waye shi……?ya karashe maganar cikin tsawa

  Jiki a sanyaye tace "Sorry oga wallahi yarinyar ce kamar Vampires ……"

 "Keep quite!wallahi wani abu ya sameshi ba katsina state ba dukka nigeria sae munyi Sharing tears !WHO Consultant ne shi……Kiraman driver yanzu ……"

  Bude ido yayi yana kallonsu sannan ya bude baki da kyar yana fadin "Am Ok……!

  Da Sauri Facilitator yace "Sorry Sir wallahi ban san wannan shashancin zai faru ba da dani aka je kauyen!

  Maida idonshi yayi ya rufe yana fadin "Is ok……

  Bala'i Facilitator din ya cigaba da yi shi kadae ita kanta Guard din tayi nadamar fada da tayi ……Sae da yayi mai isarshi sannan ya shiga ya kira Director din ……Sama sama suka cigaba da maganar sannan aka kawo mashi abinci amma yarda suka aje haka ya barshi har sae da lokacin meeting yayi sannan ya mike suka tafi ……

A Gurin meeting din ma sae da Facilitator ya fadawa Hakimi abunda ya faru ……Shi kanshi hakimin cewa yayi zai saka a kira mashi Mai unguwa Audun yaji dalilinshi na barin yara suna zuwa gurin bak'onsu har su tabashi……

Shi kam wanda akeyi donshi banza ya masu don bai ga abun tada jijiyoyin wuya ba!aciki bakin cikinshi d'aya kayanshi da ta b'ata tare da fitsarin da ta mashi a kaya, ga wani irin wari da yake ji yana yi duk idan ya rufe idonshi ……

【】

 Mai unguwa kam tunda ya karbi kudin ya soke aljihu ya kama dan kekenshi ya haye ya yanki daji yana y'ar wak'arshi a hankali ……Yayi nisa da tafiya ya hangi wata yar K'aramar yarinya tsaye gefen hanya tana kuka ……

  Sae da yaje gabanta sannan ya tsayar da keken da kyar yana kallonta yace "Na ci Gidanku !Banda iskanci sae yara su zo su tsaya tsakiyar hanya suna wa mutane kuka !Ina iyayenki……"

 Da Hannu yarinyar ta nuna mashi cikin daji har lokacin tana kuka !Tsaki yaja yana fadin "Ni k'warank'watsa ma ban taba ganin mai kalarku ba a cikin yankina ……dan biri "ya karashe maganar yana dariya sannan yace "Ke yarinya yaushe kuka dawo nan yankin?

 Da katuwar Murya tace "K'wanan mu biyar……"

Dariya ya saki yana fadin "Kam bala'i ka ji man yarinyar da Muryar k'arti !Ba mamaki wannan K'wababbar fuskar taki ita ta dace da wannan Hegiyar muryartaki……"Ya karashe maganar yana dariya……
 
  Kafe kekenshi yayi jikin hanyar Sannan yayi hanyar da ta nuna mashi yana nade katuwar rigarshi yace "Mu je ki gwada man iyayen naki naji shegen da ya basu damar zama a yankina ba tare da izini na ba……"
 
  Bata ce mashi komae ba tayi gaba ya bi bayanta sae surutai yake shi kadae……Tafiya sukayi mai nisan gaske amma da yake ya shirya rashin kirki bai lura da nisan ba!Wasu yan bukkoki suka iske a tsakiyar daji sannan ta shige bukkar da sauri ta barshi tsaye ……

 Wage baki yayi yana fadin "Owoo ni za'awa Shegantaka a barni tsaye? to yayi dai dai yarinya ba da ke zanyi ba yanzu da iyayenki zanyi !
 
  Daga Murya yayi yana fadin "Bai zama dole na maku sallama ba tunda ban san da zamanku a yanki na ba!Ina mai gidan fiton ka fada man wane Shege ya baka izinin zama k'asata ba tare da yarda ta ba……"

  Wani dattijo ya fito sanye da rawani irin na buzaye yana fadin "Marhaban wa ke kirana haka ……?

  "Mai ungua Audu ne……!ya fada yana mazurai
 
  "Maraba mai unguwa……"Tsohun ya fada yana matsowa

   "Ba wani maraba dattijo zuwa nayi naji wane she……"Maganar ta katse ganin bindi a bayan dattijon

    Girgiza kai tsohun yayi yana fadin "Ka ce mene Mai unguwa Audu?

  Mazari ya fara yana fadin "Na…ce rigim rigigim !na kuma cewa Bindi……"Kwasawa yayi da gudu yana nade babbar riga !gudun ya tsaya lokacin da wasu karnuka suka tare mashi gaba……Ihu ya saki yana sakin fitsari kafin ya canza hanya ya kara kwasa da gudu……

   Gudu ta dinga yi cikin dajin yana haki yayin da karnukan suka mara mashi baya suna wani irin Haushi ……Da kyar ya fito hanya! bai tsaya daukar kekenshi ba ya yanki hanyar Garinshi ……Sae da suka kusa shiga garin sannan karnukan suka daina binshi suka juya suka shige daji ……
 
  Kusa da gidanshi sukayi Karo da Mai tafasa ya ja numfashi ya tsaya yana fadin "Na Shiga Uku ni Audu wane irin mutane ne yau na gani……"

 Watsa mashi harara tayi tana fadin "Amma dae Mai unguwa Audu an tab'e !Me ya biyo maza da suke tafiya suna sakin fitsari a wando?

  "Ke Mai tafasa bana son ruwan tabbata nine na Tabe……"ya fada har lokacin yana haki

 Watsa hannu tayi tana fadin "Idan akwae wani Audu mai jikakken wando anan gurin to dashi nake !Bana son munafunci bani kudin Tafasa ta da ka ci jiya!……ta karashe maganar tare da wurga mashi hannu kusa da fuska

  Tsaki ya saki yana fadin "Don kina bina Muttala zaki shine zaki man tabbata……!ga dubu ki bani canjina kuma da k'warank'watsa ko motsi ba zakiyi ba sae kin bani canjina……"ya karashe maganar tare da lalubo aljihunshi ……

   Ido ya wurgu waje jin babu komai a aljihun sae kullin wani abu a leda ……Fiddon shi yayi da sauri yana jujjuyawa ganin Nono ne kindirmo a cikin ledar "Wa kuma ya bani nono……"Ya fada tare da maida hannunshi aljihu yana lalubar kudin amma wayam babu su ……

  A rude yake fadin "To ina na yarda kudinnan……"

  Juya mashi baya tayi tana d'age kallabinta ta fiddo keya tace "Koma ina ka yardasu Mai tafasa dai kudinta take bukata……"

  "Kinga wallahi Mai tafasa da kudin aljihuna……"Ya fada kamar yayi kuka……

  "Wallahi banda mutunci Audu ka fiddo man kudina yanzu !

  Da kyar ya lallabeta ta hakura ta tafi gida tana mita……sannan ya shiga gida kamar ya fasa ihu yana tunanin kila gurin gudu ya yarda kud'in kuma babu damar komawa ya duba ……Bai samu ya samu sauki ba sae da ya fitar da kwallah saboda bak'in cikin kud'in !Ranar duk wanda ya mashi magana a gidan zai sha zagine har na fitar hankali……ji yayi dama ya barwa Lauratun kudin bai karba ba……

*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
  *&*
*FEEDOHMπŸ’ž*
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*       Page *25-26*


Ba tare da ya bude ido ba yace "Ta fito nan……!
  Cikin kulawa facilitator din ya kalleshi yace "Da matsala ne Sir……?
 
  Kafin ya bada amsa Guard din tace "Oga da Matsala wallahi !wata aljanar yarinyace ta haye jikin Sir duk ta birkita mana shi……"

  A Fusace yace "A ina?

   Tabe baki tayi tana fadin "A Wannan karamin kauyen da ake samu mai AFP case dinnan fa……"

 "Ina Mai unguwar garin?Meye amfaninshi da za'abar yara suna zuwa kusa dashi?kema meye amfanin ki? sannan meye amfanin driver'n da aka hadaku dashi?Kin san waye shi……?ya karashe maganar cikin tsawa

  Jiki a sanyaye tace "Sorry oga wallahi yarinyar ce kamar Vampires ……"

 "Keep quite!wallahi wani abu ya sameshi ba katsina state ba dukka nigeria sae munyi Sharing tears !WHO Consultant ne shi……Kiraman driver yanzu ……"

  Bude ido yayi yana kallonsu sannan ya bude baki da kyar yana fadin "Am Ok……!

  Da Sauri Facilitator yace "Sorry Sir wallahi ban san wannan shashancin zai faru ba da dani aka je kauyen!

  Maida idonshi yayi ya rufe yana fadin "Is ok……

  Bala'i Facilitator din ya cigaba da yi shi kadae ita kanta Guard din tayi nadamar fada da tayi ……Sae da yayi mai isarshi sannan ya shiga ya kira Director din ……Sama sama suka cigaba da maganar sannan aka kawo mashi abinci amma yarda suka aje haka ya barshi har sae da lokacin meeting yayi sannan ya mike suka tafi ……

A Gurin meeting din ma sae da Facilitator ya fadawa Hakimi abunda ya faru ……Shi kanshi hakimin cewa yayi zai saka a kira mashi Mai unguwa Audun yaji dalilinshi na barin yara suna zuwa gurin bak'onsu har su tabashi……

Shi kam wanda akeyi donshi banza ya masu don bai ga abun tada jijiyoyin wuya ba!aciki bakin cikinshi d'aya kayanshi da ta b'ata tare da fitsarin da ta mashi a kaya, ga wani irin wari da yake ji yana yi duk idan ya rufe idonshi ……

【】

 Mai unguwa kam tunda ya karbi kudin ya soke aljihu ya kama dan kekenshi ya haye ya yanki daji yana y'ar wak'arshi a hankali ……Yayi nisa da tafiya ya hangi wata yar K'aramar yarinya tsaye gefen hanya tana kuka ……

  Sae da yaje gabanta sannan ya tsayar da keken da kyar yana kallonta yace "Na ci Gidanku !Banda iskanci sae yara su zo su tsaya tsakiyar hanya suna wa mutane kuka !Ina iyayenki……"

 Da Hannu yarinyar ta nuna mashi cikin daji har lokacin tana kuka !Tsaki yaja yana fadin "Ni k'warank'watsa ma ban taba ganin mai kalarku ba a cikin yankina ……dan biri "ya karashe maganar yana dariya sannan yace "Ke yarinya yaushe kuka dawo nan yankin?

 Da katuwar Murya tace "K'wanan mu biyar……"

Dariya ya saki yana fadin "Kam bala'i ka ji man yarinyar da Muryar k'arti !Ba mamaki wannan K'wababbar fuskar taki ita ta dace da wannan Hegiyar muryartaki……"Ya karashe maganar yana dariya……
 
  Kafe kekenshi yayi jikin hanyar Sannan yayi hanyar da ta nuna mashi yana nade katuwar rigarshi yace "Mu je ki gwada man iyayen naki naji shegen da ya basu damar zama a yankina ba tare da izini na ba……"
 
  Bata ce mashi komae ba tayi gaba ya bi bayanta sae surutai yake shi kadae……Tafiya sukayi mai nisan gaske amma da yake ya shirya rashin kirki bai lura da nisan ba!Wasu yan bukkoki suka iske a tsakiyar daji sannan ta shige bukkar da sauri ta barshi tsaye ……

 Wage baki yayi yana fadin "Owoo ni za'awa Shegantaka a barni tsaye? to yayi dai dai yarinya ba da ke zanyi ba yanzu da iyayenki zanyi !
 
  Daga Murya yayi yana fadin "Bai zama dole na maku sallama ba tunda ban san da zamanku a yanki na ba!Ina mai gidan fiton ka fada man wane Shege ya baka izinin zama k'asata ba tare da yarda ta ba……"

  Wani dattijo ya fito sanye da rawani irin na buzaye yana fadin "Marhaban wa ke kirana haka ……?

  "Mai ungua Audu ne……!ya fada yana mazurai
 
  "Maraba mai unguwa……"Tsohun ya fada yana matsowa

   "Ba wani maraba dattijo zuwa nayi naji wane she……"Maganar ta katse ganin bindi a bayan dattijon

    Girgiza kai tsohun yayi yana fadin "Ka ce mene Mai unguwa Audu?

  Mazari ya fara yana fadin "Na…ce rigim rigigim !na kuma cewa Bindi……"Kwasawa yayi da gudu yana nade babbar riga !gudun ya tsaya lokacin da wasu karnuka suka tare mashi gaba……Ihu ya saki yana sakin fitsari kafin ya canza hanya ya kara kwasa da gudu……

   Gudu ta dinga yi cikin dajin yana haki yayin da karnukan suka mara mashi baya suna wani irin Haushi ……Da kyar ya fito hanya! bai tsaya daukar kekenshi ba ya yanki hanyar Garinshi ……Sae da suka kusa shiga garin sannan karnukan suka daina binshi suka juya suka shige daji ……
 
  Kusa da gidanshi sukayi Karo da Mai tafasa ya ja numfashi ya tsaya yana fadin "Na Shiga Uku ni Audu wane irin mutane ne yau na gani……"

 Watsa mashi harara tayi tana fadin "Amma dae Mai unguwa Audu an tab'e !Me ya biyo maza da suke tafiya suna sakin fitsari a wando?

  "Ke Mai tafasa bana son ruwan tabbata nine na Tabe……"ya fada har lokacin yana haki

 Watsa hannu tayi tana fadin "Idan akwae wani Audu mai jikakken wando anan gurin to dashi nake !Bana son munafunci bani kudin Tafasa ta da ka ci jiya!……ta karashe maganar tare da wurga mashi hannu kusa da fuska

  Tsaki ya saki yana fadin "Don kina bina Muttala zaki shine zaki man tabbata……!ga dubu ki bani canjina kuma da k'warank'watsa ko motsi ba zakiyi ba sae kin bani canjina……"ya karashe maganar tare da lalubo aljihunshi ……

   Ido ya wurgu waje jin babu komai a aljihun sae kullin wani abu a leda ……Fiddon shi yayi da sauri yana jujjuyawa ganin Nono ne kindirmo a cikin ledar "Wa kuma ya bani nono……"Ya fada tare da maida hannunshi aljihu yana lalubar kudin amma wayam babu su ……

  A rude yake fadin "To ina na yarda kudinnan……"

  Juya mashi baya tayi tana d'age kallabinta ta fiddo keya tace "Koma ina ka yardasu Mai tafasa dai kudinta take bukata……"

  "Kinga wallahi Mai tafasa da kudin aljihuna……"Ya fada kamar yayi kuka……

  "Wallahi banda mutunci Audu ka fiddo man kudina yanzu !

  Da kyar ya lallabeta ta hakura ta tafi gida tana mita……sannan ya shiga gida kamar ya fasa ihu yana tunanin kila gurin gudu ya yarda kud'in kuma babu damar komawa ya duba ……Bai samu ya samu sauki ba sae da ya fitar da kwallah saboda bak'in cikin kud'in !Ranar duk wanda ya mashi magana a gidan zai sha zagine har na fitar hankali……ji yayi dama ya barwa Lauratun kudin bai karba ba……

*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
  *&*
*FEEDOHMπŸ’ž*

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S Precious HAJJA CE*πŸ‘ˆ


*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu*


        Page *27-28*


   *M*ikewa k'arama tayi tabar musu d'akin ganin sai faman uban kuka suke yi, gurin mai unguwa ta koma ta tarar baya rumfar shi sannan ta koma gindin bishiyar kuka ta zauna sai dariya take tana faman surutu, duk wanda ya ganta sai ya tabbatar da cewar ta samu ta6in hankali ta yadda take kwasar dariya ba kakautawa....,

"Ard'o wallahi k'arama ba mutum bace dan mun tabbatar da hakan yau d'innan." Cewar laminde da taga shigowar Ard'o yayi saurin kallonta da mamaki yana kokarin ajiye sandar korar awakin shi yace.

"Laminde ban shaida zancen kiba, hito kiyi min hila-hila." Cewar Ard'o yana kallon rumfar su Umma hafsatu, laminde tace, "kur'anin Allah bari jummai tazo kaji karin bayani."

K'arama ce ta biyo Tanimu yana rarrafe yana dariya har ya karasa kusa da Ard'o cikin 6acin rai ya kalli k'arama tare da gallara mata harara yace, "dan kaniyar ki ban ce kar in kuma ganin ki da yarana ba? Ja'ira kawai fitinanniya marar tushe."

K'arama ta tura mai baki tana mai kunkuni har jummai ta fito daga makewayi (toilet) duk ruwa jikinta daga gani tana nufin wanka tayi amma duk wani gurin bema san an hallici ruwa ba ta karasa inda suke dama tun a ciki take jiyosu gulma na cinta ta fito tana cewa "Ard'o babu shakka yau mun tabbatar da cewar k'arama mayya ce dan munyi mata hayak'i karshe ma caraffke mukaga tanayi a ciki.."

Zaro idanu yayi cikin tsananin mamaki da tsoro yace "ta6 d'i jam *!* abinda ba zai yiwu ba kenan shine take son ta fara takan yaro na kenan...?"

"Ke Hafsatuwalle... *!* zo nan." Ard'o ya fad'a cikin d'aga murya, Umma ta fito bayan ta goge hawanta. "Ke kam wallahi hafsatu kin janyo mana bala'i, ko waye uban k'arama ya had'a jinsi da mayyu dan haka Mu bazamu yadda ba mun baki nan da sati biyu idan baki binciko mana uban k'arama ba wallahin Allah zaki gane kuran ki."

Kuka ta sanyi a gurin zuciyar ta na zafi k'iris ya rage ta kone kurmus a yadda take yi mata zafi da rad'ad'i. "Umma tashi Mu koma d'aki dan Allah.." Cewar lauratu da itama take sharar hawaye tamkar ba amarya ba haka suka koma cikin rumfar su.

Kusan awar su biyu sannan suka share hawayen su Umma ta kalli kud'in hannun lauratu tace "Laure wannan kuma daga ina?" Ta fad'a tana tsinkar zogalen da zata dafa tabawa lauratu a matsayinta na amarya me jiran tarewa anjima a d'akin ta.

"Umma wata fillo ce ta bani, ban santa ba kuma har tambayar ta nayi amma ta wuce bata ce min komai ba." Kar6ar kullin Umma tayi tana bud'ewa taga kud'i masu yawa wajan 22k duk an cure su guri guda. "Lauratu kud'ine... *!*" Umma ta fad'a hannuta na rawa idanunta a waje tana kallon lauratu, "ke nan kyauta ta bani? Amma ban santa ba hasalima ban ta6a ganin gilminta a yankin Mu ba."

K'arama ta shigo tana rik'e da d'ankwalinta a hannu ta kallesu duk sunyi zugum abin tausayi, karasawa tayi ta zauna ta kalli Umma tare da wangale bakin ta tace "Umma fillo ce ta bayar a siyawa ya laulatu (lauratu) kwanika shabida (sabida) su jummai kalltuyi (karsuyi) mata gori..."

"Naji k'arama amma waya gaya miki...?" Umma ta tambayeta k'arama tace "fillo ce Umma." Nan da nan suka yi murna tamkar su zuba ruwa su sha. Nan da nan kuwa Umma ta mik'e ba wanda ya sani rabar gidan harta je ta dawo babu wanda ya lura.

"Inno a fito da amarya Sallau ya gama komai." Cewar matan gidan wad'anda suka fito kwansu da kwarkwatar su suna jiran a fito da lauratu aga kwa-kwaf.

Inno dake cikin rumfarta tana ji tayi shiru dan ita kanta kunya take ji, ya zata fita guri ace anyiwa jikarta aure ba ko cukali, gara tayi zaman ta dan baxata fita ba suje can suyi tayi babu abin da ya shalleta. Mutanan gidan kuwa sai munafirci suke suna kus-kus, cikin d'aki kuwa Umma ce ke yiwa lauratu nasiha sannan kwanikan da ta kar6o gidan jauro guda biyar ta ajiye su guri guda sai guru daya siyar mata 5k shima duk yaci duniyar shi sabida kayan matar shine da ta rasu kuma dama ba a kauyan take ba irin filanin nan ne masu tafiye-tafiye shi yasa shi kuma yake siyar da kayan d'akin nata.

"Ahayyeeee ayyrrrrrrrri.... *!*" matan gidan suka d'auki shewa gaba d'ayan su harda mazajen su ganin Umma ta fito da lauratu cikin lullu6inta, a haka ita da k'arama suka shiga d'akin da yake a matsayin na lauratu Umma ta zaunar da ita a wajan da taga an ajiye tabarma sannan ta koma rumfarta ta d'akko garun da langunan ta kuma komawa inda lauratu take, ganin ta shigar da kaya yasa mutanen gidan bin ta suna mamaki har ta shimfid'a mata garun tare da ajiye mata sauran kwanukan ta ra6a mutanan ta wuce tana sharar hawaye.

"Ahayye nanayeee Tambai ku ganemin a ina suka samu wanga kaya..?" Jummai ta fad'a tana rik'e da ha6a cikin tsananin mamaki, maganganun sune yasa inno fitowa itama ta leka nan taga lauratu zauna gefe kuma langunan tane inno tayi d'akin Umma da sauri cikin tashin hankali.

Karo na farko kenan da inno ta ta6a shiga cikin d'akin Umma, karasawa tayi tana tambayar ta "Hafsatuwalle ince dai na sahun 6arawo kuka fara ba..? Ina kunka samu wanan kaya haka nayan baku ajeba bare ku bayar da ajiya." Umma ta kalli inno tana mamakin yadda mahaifiyar ta tak'i ta cikin sanyin jiki tace "inno daga Allah ne, Allah ne ya bamu."

"Karya kike Hafsatu ai komai akwai sila ki sanar min kamin ranki ya kuma 6aci." Ta fad'a cikin d'aga murya, shigowar k'arama ne yasa inno juyawa tana kallonta k'arama tace "Inno gashiya (gaskiya) Umma na ta gaya miki domin fillo ce ta bawa ya laulatu tashi Umma na ta shiyo mata kayan..."

Tunda k'arama tayi magana inno taji ta kasa musawa gashi ranta na son furta abu amma bakinta ya gaza fad'a a haka tabar d'akin tana mamakin alamarin. "Ard'o da laminde sune suka 6oye tukunyan baba shallau.." Suka jiyo muryar k'arama na fad'a a tsakar gida, da gudu laminde ta bita tana zagi wai tayi mata sharri kumma haka ne sun 6oye dan azo ana cigiya ace Umma ce ta d'auke.

Ba jimawa bayan kowa ya gama gulmar shi sallau ya shiga ciki murna tamkar an bashi sarautar garin, koda ya shiga d'akin dashare baki yayi yana murna, shi duk be damu da komai ba illah kawai ya yanshi da lauratu dan ba karamin sonta yake yi ba daga nan kuma......


*{{ }}      {{ }}*

     *"M*ai-tafasa wallahi idan baki rabu dani ba zan bar  miki gidan, haba mata sai jarabar tsiya shi yasa bana son zuwa gidan nan sabida masifarki." Cewar mai unguwa cikin 6acin rai, ga bak'in cikin zubewar  kud'in shi gashi ita kuma ta sashi a gaba tana sakar mai magana.

"Yoo ni ina ruwana cewa nayi ka dinga fita da kud'i ko ina? Sabida baka yadda da kowa ba toh kur'anin Allah sai ka biyani kud'ina ahe..." Mai-tafasa ta fad'a tana kokarin shiga d'akin da lado yake ciki a kwance gwanin ban tausayi duk yayi kashi d'akin sai d'oyi yake yi tamkar bayin da ba'a wankewa.

Ko takan kashin bata yi ba nan ta ajiye mai farau-farau d'in data yi tasa kai ta fita, tana fita k'arama ta shiga ta d'ayar kofar ita ce ta gyara mai jikin shi sannan ta bashi farau-farau din tare da bashi labarin auran lauratu har hawaye yayi yana ta faman jin-jina kanshi abin tausayi.

Ta dad'e a gurin shi sannan tafi gida lokacin lauratu na d'akinta har lokacin bata fito ba sabida tsananin kunya da take ki, sallau ne keyin komai hakan ya Kara tabbatarwa da mutanan gidan komai ya wakana....

πΉ° πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


 
         Page *29-30*


   K'arama kam Tana ganin Sallau ya fito ta fad'a dakin da gudunta ta Samu lauratu rakub'e jikin bango sae sunne sunnen kai take ……Kusa da ita ta rab'a ta zauna tana leken fuskarta tare da dashire dan k'aramin bakinta tana fadin "Yaya Laulatu yau ba'a d'akin Ummanmu kika kwana ba ko?
 
 K'ara sunne kai tayi kamar tana magana da wata babbar mace ba tare da tace komae ba

 "Yaya Laularatu bakin ki ke ciwo ne?K'arama ta tambaya ganin tak'i mata magana……

  Cike da kunya ta girgiza wa K'arama kai ita ala dole kunyarta take ji……
 Tabe Baki K'aramar tayi tana kallon Sallau da ya shigo dak'in rike da katuwar langa a hannunshi tace "Su Malan Sallau angon Yaya Laularatu!Uhm ango da amarya manya !Bara dai na tashi Nasan Ummana na can tana jirana……"

 Sallau d'in ma sunne kai yayi k'asa yana satar kallon Lauratu da murmushi kwance a fuskarshi!Sannan ya aje langar hannunshi ya juya da sauri kafin K'aramar ta fita ya bar dakin ……

 K'arama na ganin ya aje langa gaban Lauratu ta kuma k'yalla ido ta ga naman zabbine a ciki an dafa su da barkono ta dawo ta zauna tare da janyo langar sossae gabanta tana fad'in "Yaya Laulatu ki sako hannu ki ci idan kuma baki ci ni na cinye maki bs ruwana ……"

  Shirun da K'arama ta ji ne ya sata saka hannu ta fara cin abunta hankali kwance tana lashe hannu har sae da ta ci kusan rabi sannan ta debi wani a hannu ta mike tana fadin "Idan bara ki ci ba ki aje man anjima zan dawo na karasa cinye abuna ………" Har ta fita Lauratun bata dago kai ba wae kunyar K'aramar take ji ……Ita kam wadda akeyi dominta bama tasan me take nufi ba !ta dai fita dakin da namanta a hannu ……

  Munafukan gidan suka dauki salati tare da taba hannu suna kallonta rike da nama a hannu !Kukan kura Zulai tayi ta warce naman daga hannunta tana fadin "Amma K'arama anyi shegiyar yarinya yanzu naman da ko ni da na dafa ban ci shi ba shine kika shiga dak'i ki cinye shi dan kina karamar mayya ko ……"

 Turo baki tayi tana murguda baki kasa kasa kafin ta zagayesu ta wuce ba tare da tace komae ba !Har sae da ta kusa fita bakin kofar gidan sannan ta juyo tana kallon su tace "Allah ya wa'e (watse)maki albarka Julai……"Ta fice gidan da gudun tsiya ……

  Zulai ta d'aga kafa zata bita jummai ta riketa tana fadin "Barta inna Zulai! ki kyaleta ai anan zata kwana ko?da k'warank'watsa tunda har ta zageki yau bara tayi bacci lafiya ba……" Gantsarewa tayi jin an kamar an soka mata allura a baya takai hannu ta sosa ,tana gama sosawa taji wani gurin ya dauki k'aik'ayi sosawa ta kuma yi tare da daukar tabaryarta zata wuce !Cak ta tsaya tare da cire rigarta tana fadin "Laminde taimakan dan sosan bayana kinga ya karad'e da k'aik'ayi ……"

  Tabe baki Laminde tayi tana fad'in "Ke ni bana iya tab'a wannan hegen bayan naki da kike wata baki sa mashi ruwa ba ……"

  Ta bude baki zatayi bala'i taji kamar ana kara mata azaba a bayanta ……jikin bango ta matsa ta ci gaba da goga bayanta da karfi amma kamar ana karasa !Abu kamar wasa sae ga Jummai na birgima tsakar gida tana ihun k'aik'ai ……Ganin da gaske take yasa matan gidan fara taimaka mata ana sosa mata da cokulla tare da yan jik'e jik'e da aka yi ta d'ura mata ……Kusan awa biyu sannan azabar ta fara ragewa suka kamata suka shigar da ita daki ……

  Umma kam tana di'bar icce bata san wainar da ake toyawa ba sae da ta dawo sannan ta iske K'arama ta haye ruwan cikin wani yaro dan gidan Fulani tana jibga tare da ihu kamar ita yake duka ……Yara kuwa sun zagayesu sae dariya suke !Da kyar ta samu ta janye K'aramar daga jikinshi tana ihu ta shigar da ita cikin Bukkar su sannan ta ce "Me ya had'a ki dashi K'arama ?

  Dago kai tayi tana kallon Umman da rinannun idanunta tace "Ce man yayi Shegiya, meye Shegiya Umma?

  Shiru ta mata tana kallon idanunta sannan ta mike a sanyaye ta janyo wata kwaryar fura ta bude ta fara bata ……Bata damu ba ta fara sha tana lashe baki kafin ta bude baki tace "Ummana wa ya baki kanya da kika fita?

  Da sauri ta kalleta tana fadin "Ba wanda ya bani kanya K'arama"

  Tabe baki tayi tana kallon cikinta sannan tace "Kuma na ganta a cikinki yanzu ……?

  Da sauri ta buge mata baki tare da sakin kuka a hankali tana fadin "Ban hanaki Fadar haka ba K'arama? so kike mutane su tsane mu bayan azabar da muke ciki yanzu?Na shiga uku ni Hafsatu wace irin d'iyace haka Allah ya bani ?Ya Allah na roke ka bayyana *ABUNDA KE B'OYE* a tare da wannan d'iyar ko ma huta da azabar rayuwa……"

  Dafe Bak'inta tayi tana hararanta kasa kasa tare da fad'in "Ni kika daka Umma?

 Bata kalleta ba ta cigaba da kukanta a hankali tare da daga hannunta sama tana addu'a sannan ta juyo tana kallon K'arama da har lokacin ita take kallo ……

  Tsaki K'aramar ta saki a hankali tana hararan Uwar tata sannan tace "Dallah ni Bari kallona!Ina Ruwana dake ni ……"Ta karashe maganar tana watsa mata harara tare da jujjuya baki……
 
  Wani Sabon kuka ya k'wacewa Hafsuwalle najin abunda K'aramar take fada ta saka hannu tare da kifa mata mari tana fad'in "Ni kikewa Tsawa K'arama?

  Fashewa tayi da kuka ta mik'e tana tana kallon Umman tata lokaci guda ta saka hannu tare da duma mata K'ulli ta bar bukkar da gudun tsiya tana fad'in "Ai dai na rama "

  "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un "Hafsuwalle ke fada tare da dafe inda K'aramar ta daketa tana fitar da kuka gwanin ban tausayi ……


【】

 *M*a'aruf ko da ya koma gida ya fadawa Madre abunda ya faru " Wae wata aljanar yarinya ta mashi fitsari a jiki har yanzu gurin bai bar wari ba ji yake dama ana cire k'afa da yau yaje an cire tashi……"

 Dariya ta fara mashi don sam bata ji Haushin Yarinyar ba !Tana sane da yarda Ma'aruf ko daukar yara bayayi don kar su mashi fitsari……

  Kallonta yake kamar ya fasa mata kuka sannan ya kalli sumayya da ta shigo daga ita sae Three quater da blouse tana tambayar Madre abunda take wa dariya ……
 
  Aiko Madre din na fada mata ta hau dariya tare da rashewa saman rug din tana nunashi ……

   Kallon Madre yayi sannan ya kalli Sumayyar yana fadin "Bansan yaushe raini ya shiga tsakaninmu ba Sumayya"

  Nunoshi tayi da hannu tana kokarin danne dariyarta tare da fadin "Yaya Ma'aruf ana plastic surgery fa!
 
  Cikin tsawa yace "Wallahi ko ki bar nan gurin ko na maki shegen duka "

 Sanin zaya iya ne ya sata mikewa tana fadin "Allah ya baka hakuri" ta koma daki da gudu tana dariyarta ……

 Kallon Madre yayi yana fadin "Kin gani ko Madre wallahi sae na duki waccan yarinyar yau "

  Gintsewa tayi tana fadin "Allah ya baka hakuri Auta nima na daina"
 
  Shiru yayi ba tare da yace komae ba !Itama Madre din shiru tayi tana kallon Autan nata ganin ya lumshe idanu sannan ta shafo kanshi tana fadin "Sorry kaji ko Autana kaine da abun dariya wae aljana ta maka fitsari a jiki ……"

  Shiru ya mata tare da kwantar da kanshi saman kafadarta ya lumshe ido ……

  Sallamar yayarshi Maryam da yaranta biyu Afra da Ihsan ya sashi bude ido tare da sakin karamin tsaki ya na shirin mikewa ……

  Ihsan ta kwace hannunta daga na mamanta rugu ta hayeshi tana fadin "Oyoyo Uncle "

  Bata fuska yayi yana kallonta yace "Headache" a takaice

  Maryam kam gurin Madre ta nufa ta zauna yayin da Afrah ta rabe jikin kujera tare da sakin kuka da karfi ……

  Su duka suka kalleta kafin Madre tace "Zonan Afrah ya akai?

 Ma'aruf ta kalla sannan tace "Ba Uncle ke harara ta ba tunda muka shigo……"

  Hararan ya sake mata yana fadin "Zan bata maki rai Afrah yaushe na harareki……"

  Da gudu ta karasa jikinshi tana fadin "Uncle Baka Sona kullun nazo gidan nan sae ka harare ni dan Allah ka daina ina sonka kaji Uncle ……"

  Jikinshi yayi sanyi don ya tabbata da ya harareta !janyo ta jikinshi yayi yana fadin "Is okey kinji ko Afrah ……Ihsan ya dai?
 
  Madre kam dariya tayi tana kallon Maryam da ke ta faman korafin wae Auta ya bar Madre da Kumba a jiki ……
*HAJJA[truncated by WhatsApp]
?πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


_ASSALAMU ALAIKUM, masoya masu bibiyar *ABUNDA KE B'OYE...!* hak'ika muna ganin sakwannin ku ta yadda baki bazai iya lissafoku ba, sai dai muce kusani Hajjafeedohm na ganin saqwan kuma suna jin dad'i, fatan Allah ya bar kauna da soyayya, Mu samman 'yan grps na *HASKE WRITER'S FANS 1-2* hak'ik'a kud'in masoya na mun gode_ *#Hajjafeedohm* LYSM😘


     Page *31-32*


     *F*uska a d'aure ya kalleta yana fad'in "Tunda gaki sae ki yanke mata……"
  Harara ta sakar mashi tana fad'in "Ni kake fad'awa magana Auta?Yaushe na fara wasa da kai ban sani ba……?"

  Murmushi yayi mai sauti sannan yace " Allah ya baki hakuri Sister ……"
  Itama murmushin tayi tace "Madre yaushe mara kunyar Autanki ya sauka……?
  Shiru Madre d'in tayi tana kallonsu cike da kauna sannan tace " Bai je gidanki ba ranar friday?

  Da Sauri ya kalli Maryam d'in yana langwabe kai tare da kanne mata ido d'aya ,Yar dariya ta saki ta juyar da kai tana kallon Madre sannan tace "Ihsan Uncle yazo ranar Friday……?

  Waro Ido yarinyar tayi tana girgiza kai alamu a'a tare da bud'e baki ……
  "Ma'aruf……"Madre ta fad'a tana mashi kallon tuhuma

  "Madre ba na fad'a maki motar ne ya samu matsala kafin na karasa gidanta……"ya fad"a yana kokarin guduwa daga falon ……

 Jefa mashi pillow tayi tana girgiza kai cike da takaicin halinshi sannan ta juyo tana fad'in "Sae da nace yaje gidanki ranar Friday ashe baije ba?"

  "Ban san wane iri hali Gare shi ba Madre!Ina Sumayya take ne……?"

   "Tana ciki yanzu Ma'aruf ya koreta……" Madre ta fada tana kallon dakin Sumayya……

  Dariya Maryam ta saki tana fadin "Madre anya ba yar gida za'ayi ba?don d'iyarki na son Autanki"

  Dariya Madre d'in tayi don ita kanta ta lura da take taken Sumayyar sannan suka shiga ba da firansu har Abbansu ya dawo suka gaisa……su Afrah da Ihsan kam kamar suna jira suka bishi part dinshi suka cika shi da shegen surutu don ma yana da son yara sossae……

  《》《》《》

  Har Dare ya take Hafsuwalle bata ga K'arama ta dawo ba sossae hankalinta ya tashi ta mike ta nufi inda take zama amma ko alamunta bata ji ba……
  Bayan gida ta leka amma wayam babu K'arama babu dalilinta a sanyaye ta dawo tana tunanin ko tana d'akin Lauratu ne !Ta dad'e tsaye tsakar gida tana sauraren ko zata ji motsinta amma shiru, Zulai ta fito rike da buta a hannu ta kalleta a wulakance ta watsar tana fad'in "Wane munafunci ake shiryawa anan kuma Hafsuwalle?ko jarabar ce ta tashi ake neman namiji!

  Shiru Hafsuwalle tayi sannan ta rab'e ta koma cikin Bukkarsu yayin da hankalinta ya k'ark'ata K'arama na dak'in Lauratu acan zata k'wana !Gabanta ya fad'i da ta tuna indae Mutanen gidan suka tabbatar da K'arama ta k'wana d'akin Lauratu to zasu sha wulakanci !Tunda a k'a'idar garin Amarya bata fitowa sae tayi sati d'aya haka babu wanda ke shigar mata dak'i har sae ta fara harkokin tsakar gida……

  Kwanciya tayi tana addu'ar Allah yasa K'aramar ta fito ba tare da ta k'wana ba !A haka bacci b'arawo ya kwasheta ……

  *K'*arama kuwa tunda ta ma Ummanta k'ulli a baya ta fice daga gidan !K'auyensu Malan Lado ta nufa da yake yanzu ta san hanya sarai bata buk'atar rakiyar wani ……
Ita Kad'ae ta yanki daji har ta isa garin sannan ta zagaye ta bayan gida ta shiga Bukkar Baffanta ……

  Kamar Kullum a kwance ta iskeshi idonshi na kallon sama d'akin sai doyi yake !Bata damu da warin d'akin ba tunda ba sani tayi ba ta rab'a ta tsallakeshi ta bude furar da Maitafasa ta kawo mashi ta fara sha !Tsaf ta shanyeta saboda yunwar da ta k'waso sannan ta kalli Lado tana fadin "Bara na karo wata sae na baka ko Baffa……?

 Ta mike da sauri ta bar d'akin !Lumshe ido yayi a ranshi yana fad'in " Karki Fita kin ji d'iyata!bana son wani abu ya sameki saboda ke kad'ae nake gani na samu sauki a rayuwata"Hawaye suka gangaro mashi ganin babu mai jin maganarshi ga K'aramar ta fice da gudu kuma yana jiyo Maganar Maitafasa da Kundum……

  Tana Fita ta iske Kundum na ma Maitafasa kitson Zanen Hannu Mai tafasar ta zage sae bala'i take wae Kundum ta matse ta a cinya ta sakar mata tusa ……
 Bahaggon salatin da Kundum ta saki shi yasa Maitafasa zabura ta mike tana fad'in " Amma Kundum anyi lalatarta!ina Macijin da kikewa wannan salatin na rafke shege tunda ke mata kika rako duniya"

 Juyawar da zatayi suka hada ido da K'arama dake tsaye tana dage gira tare da miko kwaryar fura……
  "Allah ka yafe man na kashe shegiyar nan kowa ya huta"Ta yayi tabaryar dake kusa da ita ta nufi K'arama zata doke……

  Ji kake Tim Maitafasa cikin makeken ruwan k'watar dake baje tsakar gidansu……
  Wata Dariya K'arama ta saki tare da tab'a hannu har da tsalle tana nuna Maitafasar dake kokarin tashi……
  "Amma wanga diya anyi hegeyi yanzu Maitafasar kikewa dariya don ta fad'a kwata?cewar Kundum tana kokarin gimtse tata dariyar muguntar

  "To bakar munafuka bud'e baki kiyi taki dariyar mana !Da kwarankwatsa na dade da sanin ke kundum algunguma ce……"Maitafasa ta fada tana kokarin mikewa amma kamar wasa taji cinyarta ta rike yayin da azaba ta fara mamaye cinyar……

  Jehowa K'aramar Tabarya tayi tana fad'in "Wallahi kika bari na tashi yau sae anyi sallar gawarki a garin nan……Sae na maki karyawar rashin mutunci "

  Dariya Kundum ta saki tana watsa hannu baya tace "A hayye su Maitafasa a cikin fitsarin shanu ……Yo ba k'ara inyi dariyata ba tunda abun naki ba mutunci "

  Ihu Maitafasa ta saki tare da rike cinyarta tana fad'in "Kundum taimaka kamar cinyar zata cire nake ji……"
   "Yo ta cire mana !Mai ya shafi Kundum bakar Munafuka……!Cewar kundum tare da tsallake Maitafasa ta shige makewayi babu ko buta……

  K'arama kuwa d'akin Maitafasa ta fad'a tana tsalle harda tab'a hannu ta dauko katuwar kwaryar da ta gani cike da fura ta koma d'akin da Lado yake ta fara bashi ……
Shi kanshi Ladon Yana mamakin yarinyar yarda take iya mashi komae ba tare da ta tambaya ba wani sa'in har tsoro take bashi saboda ko kad'an babu wanda zaice K'arama na iya bawa wani ko da abinci bare yarda take janye shinfidarshi ta canza mashi wata ta kuma gangaroshi sannan ta wurga kayan da ya bata tsakar gida ……Sae dae Maitafasa ta dauka ta wanke tana bala'in duk lokacin da ta kama mai canza mashi shinfida birni za'a rabasu……

  Wasa wasa maitafasa ta kasa tashi har Sae da Kundum ta tausaya mata ta kira makwabta aka kamata aka kaita d'akinta sannan ta lek'a ta kira mata wata tsohuwa dake d'auri tazo ta murji kafar ba tare da tasan menene ciwon ba ta tafi ……Ana gama murzar kafar wahalallan bacci ya kwasheta……

  K'arama kam batayi tunanin komawa k'auyensu ba ta rab'a gefenshi ta kwanta itama anan bacci ya d'auketa yayin da Malan Lado ya kura mata ido yana jin soyayyarta tare da tausayinta na ratsashi ji yake ina ma zaya iya daya fadawa duniya su bar sheganta mashi diya domin halalinshi ce……

【】

Ma'aruf kam Kafin Ya koma Madre tawa Abbanshi maganar tana son a hadashi Aure da Sumayya !Da fatan alkhairi Abban ya bisu don ya tabbata barata tab'a zab'awa Autansu mace ta banza ba !kuma yana da yak'inin Sumayya ta samo tarbiyya mai kyau tunda Hannunsu ta tashi ……

  Shi da kanshi yawa Ma'aruf din maganar ya bashi Sumayya !Wata irin faduwar gaba ya samu a ranar don ko kad'an bai tab'a tunanin zai auri Sumayyar ba beside ma bata cikin matan da yake tunanin aure !Sai dae ko kad'an baya iya gardama da iyayenshi ……Don haka kai tsaye ya amsa a baki sae dae a zuciyarshi kamar ta kone yake ji !Bai nuna ma kowa bai ji dad'in zab'in da iyayen nashi suka mashi ba sae dae ya barwa kanshi!
  Ko kwana biyu bai karayi ba ya tattara kayanshi ya koma india tun da lokacin saura 3 month ya dawo baki d'aya……kuma a yarda iyayen nashi suka fada da ya dawo za'ayi bikin nasu ……!
*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
  *&*
*FEEDOHMπŸ’ž*

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


    _πŸŽ‚πŸ”₯πŸŽ‚You are the best gift our parents could ever give us. You are the one who made our childhood unforgettable. Wish you a very sweet and warm birthday. Our aunty, our support, we love you  so much sister *UMMI AISHA*πŸ‘Œ.πŸΎπŸŽ‚_
   

*Assalamu alaikum sisters, kuyi hakuri yau kunji shiru, sistern FEEDOHM ce Allah yayi mata rasuwa, Allah yaji kanta da rahama yasa karshen wahalar kenan, idan tamu tazo yasa Mu cika da imani Amin*πŸ˜­πŸ‘


    Page *33-34**S*umayya kam Sai da ya tafi da kwana biyu sannan Madre ta fad'a mata !kamar zata mata sujjada dan murna babu kunya ta dinga wangale baki harda su rawa ta zama Mrs Ma'aruf……Madre kam da kallon mamaki ta bita dashi tana jin-jina rashin kunya irin na sumayya !!

  A ranar ta fad'awa duk wasu friends nata har wad'and'a ta manta dasu cewa ta zama Mrs Ma'aruf yayin da ta canza suna a dukkan account d'inta na social media zuwa Mrs Ma'aruf……

  Saboda bala'in zakewa ranar tama wata friend d'inta Beeba waya wai ta kawo mata mai magungunan mata zata saya ta fara amfani dasu tun yanzu ……

    "Ikon Allah tun yanzu Sumayya?abunda Beeba ta fad'a kenan tana rike baki kamar tana gaban ta

  "Kinga laifina ma kenan Beeba ko?Kawae ki samo mun masu kyau ki kawo mun yanzu, bana son nakai gobe ban fara amfani dasu ba……"

  "Allah ya kyauta." Abunda Beeba ta fad'a kenan ta yanke wayarta kit!……
Tsaki Sumayya ta saki ta matsa gaban madubi ta fesa turare sannan ta d'auki wayar ta kira Ma'aruf, amma har ta kare ringing bai d'auka ba!ba kuma don bai ga kiran nata ba a'a hasalima wayar na bisa kirjin shi yayin da yake kwance rigingine yana kallon sama……

  Kusan sau uku tana kiran shi bai d'auka ba sannan ta zauna ta rubuta gutun message ta tura mashi _"Please pick my call i wanna hear you rancid voice despites the fact you're the light that brighter my heart……It's me Mrs Ma'aruf."_

  Yana jin shigowar text d'in amma bai duba ba har sae da ta sake kiranshi sau biyu sannan ya d'auka ba tare da yayi magana ba……

  Cikin Zumud'i tace "Hello……"
      "Yaya Ma'aruf……"
     "Kana jina……?"

 "Sumayya... *!*" ya fad'a a takaice……
  Cikin shagwab'a tace "Shine kuma kayi shiru ka kyale ni……"

  "Bana son surutu me kike son fad'a……?ya fad'a a hankali idonshi a rufe.

  "Allah ya baka hakuri Yaya Ma'aruf dama ina so ne na tambayeka zan d'an fita idan beeba tazo na rakata inda take aje motarta tunda naga yanzu na zama matarka komae kai ya kamata na nemi izini gurinka……"

  Dariya da takaicinta suka dirar mashi lokaci guda har bai san lokacin da yace "Uban wa yace kin zama matata ki kirani ki tambayeni idan zaki fita Sumayya?ya karashe cikin sanyin muryarshi amma a nashi tunanin fad'a yake ……

  "Madre tace an baka ni……kuma laifine don na tambayi mijina zan fita?ta fad'a a shagwabe……

  Yanke wayar yayi tare da bin ta da harara !Shi kam an hadashi da bala'i wallahi !abunda ya fad'a kenan a fili tare da jan karamin tsaki……
  Ita kam Sumayya bata ji komae ba illa tsallen da tayi ta fad'a saman gado tana juyi ita kadae……

 【】

  "Uban wa na kama yanzu ……"Cewar Matar Fulani tare da cakumo wuyan K'arama da ke zaune gurin kuka tayi bud'u bud'u da ita kamar ba gobe……

  Ido ta k'walalo mata tana kokarin aje k'aton dutsen dake goye a bayanta tana fadin "Ni kika kama!
  Duka ta sakar mata akai tana fad'in "Uban me ya hadaki da Jabiru……?

  Turo baki tayi tana dafe inda ta bugeta tace "Ba shi bane ya ce man shegiya……"

  Kara dukanta tayi tana fadin "Karya ya maki dan ubanki ba shegiyar bace !uban waye bai san amanar Malan lado aka ci ba aka haifeki" ta karashe maganar tare da hankad'ata ta fad'a ta zauna kasa tana harba kafafuwa ……

  Juyawa Matar Fulani tayi tana zage zagenta !K'arama kam dutsen dake bayanta ta dauka yayin da ta saita duwawun Matar fulani ta jefa mata ta watsa da gudunta ta bar gurin……

  Dafe gurin tayi ta juyo amma babu K'arama babu dalilinta wani uban zafi ta ji ya soketa kamar lokacin aka jefa mata shi ,ta d'aga kai ta kalli kukar da ke kusa da ita tana luliya gurin ……
  Mace ta hango sama tana washe mata baki hakora a waje kamar na shanu……
  Kwaryar nononta ta saki tare da dafe kai ta baza da gudu ta koma gida tana dafe da inda K'arama ta jefeta……

  Ranar da Lauratu ta fara fitowa ranar matan gidan a waje suka shinfida buhu suka zauna duk da azabar ranar da ake ……Jira kawae suke Lauratun ta nufi Bukkar da Hafsuwalle take su fadawa Ard'o ya mata rashin mutunci Tunda yanzu ta zama karkashin Garka ta fita daga hannun Hafsuwallen……

  Tana lura dasu don haka ko bukkar bata kalla ba har Sae da K'arama tazo ta raba kusa da ita ta zauna tana washe mata tace "Yaya Laulatu har an gama dafa ki a d'akin?

  Kallon mutanen gidan tayi taga kowa ya zuba ido yaji ko zata mata magana !hawaye suka taru a idonta ita dai bata jin zata iya k'yale K'arama ko da za'a fidda mata rai ne ……
  Goge hawayen tayi ba tare da tace komae ba ta janyo K'arama jikinta ta rungumi ita kanta ta san tayi rashin kanwarta……

  "Shikenan Lauratu yanzu Ard'o bai isa ya saka doka ki bita ba?cewar matan gidan kamar hadin baki ……

  Kuka ya kwace mata tace "Wallahi bazan iya rayuwa babu K'arama ba a kusa dani dan Allah ku barni da ita"

  "Idan Ard'on yazo sae ki fada mashi haka……"Cewar Laminde tare da nade buhunta don dama abunda take jira kenan……

  Hafsuwalle ta leko tare da kiran K'arama don duk abunda suke tana saurarensu ……Cikin Sa'a K'arama taje ta sakata Bukka da wayau da dubara ta zaunar da ita tana mata tatsuniya ……

  Inno kam girgiza kai tayi a hankali don har ga Allah abunda akewa su Hafsuwalle ya fara isarta kawae tana daurewa ne don babu uwar da zata ce bata son d'iyarta a duniyar nan ……Ko da Ard'o ya dawo suka fada mashi banza ya masu saboda yana jin Kunyar Lauratun yanzu tuda ta rigaya ta zama surukarshi !

  Tun daga lokacin Hafsuwalle ta daina barin K'arama na yawan shishshigewa Lauratun saboda matsalar cikin gidan ……Tun tana mata kuka idan ta sakata bukka har ta daina saboda ko'ina Umman zataje sae ta ja hannunta su tafi ……

  K'arama kam ganin Umman tata na lallabata yasa ta itama take jin maganarta sossae amma hakan baya hana idan ta daketa ta mike ta rama ta gudu ga rashi kunya duk lokacin da abun ya kad'o mata ……
  Mutanen gidan ma bata ragawa duk wanda ya daketa sae ta rama idan kuma bata samu ramawa ba to kai kuma ranar baka bacci ……zaka kwana kana ihu ana baka tsoro! hakan bai saka sun daina takura masu ba don basuyi tunanin saboda ita ake basu tsoro ba ……

  Maganar Idan kaci abu ka fito ta kalli cikinka tace ga abunda kaci har lokacin bata daina ba sae dae ta kanci dan banzan duka gurin tsofaffin garin wata rana……

   *Two month later……*

  Tana bayan umman ta sun debo ruwa sae uban surutu take kamar an bude fanfo ……Aje tulun tayi ta juya baya da gudu tare da leka Zauren wani gida da aka saki buhun kofar Sannan ta matso kusa da Ummanta tana tab'a hannu had'i da tab'e baki ……
  "Umma jiya Habi Surukar Fulani tace man wae yar iska……"ta a fad'a idonta na kan zauren

  A Sanyaye Umman ta kalleta tana girgiza kai saboda ta san wani abun take shirin aikatawa……
   Hade hannu tayi sannan ta dauki tulun ruwanta tayi gaba abunta tana murmushi……Tana ajewa kafin Umma ta shiga d'aki ta aje Zanin lullubinta ta fito ta shige kewaye ta dire ta katanga ta bar gidan……

  Gidan Fulani ta isa ta tarad da Habi da Matar Fulani suna sussukar masara ……
  Da yar ficiciyar muryata tayi sallama ta mak'ale zauren gidan ba tare da ta shiga ba ……

  "Wacece nan ta labe…?cewar Habi
 "K'arama yar iska ce ……"ta fada tare da yin tsalle daya ta fado cikin gidan ……

  A Harzuke matar fulani ta matso tana fadin "Ke ce dama ?Uban me ya kawoki gidannan ?Wae Habi bance kar wannan shegiyar yarinyar ta kuma shigowa gidan nan ba?

  Kyafta idanu ta farayi tana fadin "Babban d'an iska na gani a zauren malan bashe shine nazo na fad'awa matar d'an iska da surukar d'an iska……"ta karashe maganar tare da rike kugu tana girgiza kamar wata budurwa……

  Kamar ta saka masu gas haka suka hayyako mata ta kwasa da gudu ta bar lungun……


*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
*&*
*FEEDOHMπŸ’ž*
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S Precious HAJJA CE*πŸ‘ˆ


*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu*


        Page *35-36*

     *B*ayan Ma'aruf ya kammala karatun shi ya dawo Nigeria Aisha budurwar shi dake tsananin son shi da kyar ya samu ta rabu da shi lokacin har kuka tayi da yace mata anyi mishi baiko da wata tayi kuka sosai dan ba karamin so take mai ba shima lokacin yaji tsananin tausayin ta amma ba yadda zai yi dole yasa ya gaya mata gaskiyar lamari.

Zaune yake a parlorn Madre yana karanta wata jarida Sumayya ta fito, tana ganin shi ta koma room d'inta tare da kara turare a jikinta kasan cewar tasan yana son kamshi. Parlorn ta koma ta zauna bayan ta gaidashi ya amsa tamkar baya so, kafin ya d'ago ya kalleta suka had'a idanu guri d'aya yace.

"What are you looking for?" Ya fad'a bayan ya d'aure fuskarshi
   Sumayya tayi murmushi tare da gyara zama ganin yana son magana tace "Yaya Ma'aruf naji ka shiru baka min zancen yadda bikin Mu zai kasan ce ba kayi shiru..."

Jaridar hannun shi ya ajiye tare da kallonta, "Zo nan me kike so na gaya miki..." Da sauri ta mik'e ta k'arasa kusa da shi tana mamakin jin cewar yace ta dawo kusa dashi, shi kuwa tun sanda ta shigo parlorn kamshin turaran ta ya bugar mai hanci ya ji yana son kamshin turaren da ta shafa ……

"Kin gane ko Sumy *!*, bana bukatar yin wasu bidi'a just kawai a yi lalle ranar d'aurin aure sai ayi walima kawai, albarkar auren muke so ba wani abu ba...."

Turo baki tayi cikin shagwa6a, hannunta na cikin nashi ji yake tamkar ya rungometa amma bazai iya ba gudun kar ya janwowa kanshi fitina, abinku da lafiyayye giredin namiji mai ishashishiyar lafiya. "Haba Yaya Ma'aruf ko dinner ma baza muyi ba, please dan Allah mana sai kace ni da kai ba wayayyu ba...?"

   "Mteww... *!*, yaja tsaki cikin jin haushi a hankali ya zame hannun shi dake cikin nata ya d'auki jaridar shi daya ajiye yace "Ok fine, kije kuyi but ni dai baza ku ganni a wajan ba that's all..."

"Yaya Ma'aruf Me yasa zaka yi mana haka..?" Sumayya ta fad'a kamar zata yi kuka, Madre ce ta fito hannunta d'auke da memo da biro ta k'arasa parlorn ganin su tare yasa ta saki murmushi tace,

"Yauwa gara da na ganku tare Ma'aruf ina so naji wane color kake so na punitures d'in ka?" Madre ta fad'a bayan ta zauna cikin d'aya daga kujerun.

Cikin rashin son maganar shi ya kalli Madre tare da miskilalliyar fuskar shi yace "Madre bana da wani zabi so choose me any colorful..." Murmushi tayi dan tasan color d'inshi ta koma kan Sumayya dake ta faman cono baki daga gani tana cikin fitina Madre tace...,

"Ya haka kuma Sumayya..? Waya ta6a minke haka da safen nan? Sumayya ta juya tana nuna mata Yaya Ma'aruf da hannu fuskarta a shagwa6e. "Sorry baby kinji rabu dashi zo ki gaya min abinda yayi miki...."

Zama tayi kusa da Madre tace "kinji shi wai baza muyi kowanne event ba, ko zamu yi shi bazai je gurin ba kawae Madre so yake ya zubar man da mutunci gurin friends dina...." Madre ta zaro ido tana kallon Ma'aruf cikin mamakin shi tace "Me ke damunka ne Ma'aruf?Wane irin mutum ne kai ..? To Ba abunda za'a fasa kuma sai kaje komai kaji na gaya maka..."

"Shikenan Madre amma a tunanina albarkar auran ake so, amma tunda kince haka zanje..." Yana fad'a ya bar parlorn kamar ya sake ihu side d'in shi ya wuce ya d'auki laptop d'inshi yana wani research......


*{{ }}       {{ }}      {{ }}*

      Karasawa suka yi cikin gwadabniya har cikin d'akin da lado ke kwance, Ma'aruf ya kalli side d'in da wani babban malami yaje wanda suka zo tare yace "bismilah malan kalla..." Malan Kalla ya matsa kusa da lado dake kwance yana binsu da ido, wata jaka ya bud'e gaba d'aya d'akin ya kaure da kamshin almuski da wani farin ruwa mai dukan kai sossae nan da nan Lado ya fara zaro idanuwa yana kokarin yin motsi da 6arin jikin shi d'aya.

Kura mashi Idanu Ma'aruf yayi yana nazartar wani abu daga jikin shi, malan kalla ya fito da garin ganyen magarya da jikakiyar kanwa ya fara watsa wa a gurin da lado ke kwance. Ayatulkursiyu yace su karanta baki d'ayan su mutanan gurin su focal parson, guard, Ma'aruf, mai unguwa da makocin su malan sahabi kowa sai mamul-mamul yake da baki idan ka d'auke malan kalla da Ma'aruf da focal parson sune kawai suke yinta dai-dai, nan da nan ana watsa mai ruwan kanwa da ganyen magarya lado ya fara wani irin kuka kirjin shi na d'agawa, Ma'aruf ya gazgata zargin shi na cewar asiri aka yiwa Lado.

Wata irin murya suka ji gaba d'aya ta kaure cikin d'akin tamkar zata tsaga bango, kallon Lado malan kalla yayi tare da cewa "Wace ce ke..? Me kike yi ajikin bawan Allah kike wahalar dashi tsawon shekaru..?

    "Siiiiiiiiii..... *!*, suka ji yana fitowa daga bakin Lado ……Malan kalla ya shafa mai ruwan kanwa sai aljanar ta fara magana a fusace.

"Ku-ku-kun takura mana fa... *!* kai.., ta nuna Ma'aruf da yatsan lado tace "ka takurawa rayuwar mu, ka hanamu sukunin da muka dad'e muna yi, ina ruwanka damu da zaka tahu mana da kalla...... *!*?" Ma'aruf yayi murmushi cikin nuna rashin tsoro duk da bugun da zuciyar shi ke mishi yace.

   "Ko" Ya fad'a tare da mai da kallon shi gurin Malan yace "continue Malan daga inda ka tsaya..." Ayoyi malan kalla ya dinga kwararowa aljanar tana ta magana kafin ogan yayi shima cikin zunduma uban zagi dama bamagujene malan kalla yace.

"Ina jin ku me ya faru..?" Ifiritu yayi magana a kausashe yace "turo mu aka yi kuma mun samu gurin zama dan munyi katon gini a jikin shi..." "Waya turoku jikin shi..." Hhhhhhhh.... *!* ifiritu yayi wata mahaukaciyar dariya tare da cewa "Babu ruwanka."

Karatu malan kalla ya cigaba dayi su kuma suna ihu suna cewa yayi hakuri zasu fita kuma zasu fad'a amma yak'i denawa lokacin duk mutanan gurin sun shiga cikin rud'ani sai da ya kusa konasu da ayar Allah sannan ya watsa musu ruwan kanwa yace "toh muna ji waya turo ku?" Ifiritu a wahale tamkar d'an giya yace "Hansai ce matar mai-unguwa ta biyu, ta turo mu saboda yafi kowa amfanin gona har da d'anta badaru hakan yasa ta turo mu muka shige shi karku kona mu muna da yawa muda iyalanmu...."

"Kanbala'i! Aradun Allah bazan yadda wato daman Hansai ce ke son lahanta min lado...?" Cewar Mai-tafasa dake bakin kafa, "tallahi banga me rabani da Hansai ba a garin nan daman tuntuni naga take takenta!daga murya tayi tana fadin " kundum, buwale, Asibi, baraka, lanto kai duk mutanan garin nan kuzo kuji min Hansai ta cuce ni ita ce ta kwantar da lado..."

Kafin kace me sun cika gidan yaran su da manya, nan mai-tafasa ta kara narka wani bala'in su lanto suna zugata haushi da takaici yasa Ma'aruf ya fito yana kallon su tamkar yayi amai sabida tsamin da ke tashi a jikin su yace, "shut up *!*, duk da basu gane me yake cewa ba amma sunga yayi tsawa sannan fuskar shi a murtuke yasa suka yi shiru yace su fita daga gidan su basu guri, sim-sim suka fita harda Mai-tafasa sannan yayi tsaki ya koma cikin d'akin malan kalla nata karatun alkur'ani su kuma sun zuba musu idanu, karasawa yayi suka ci gaba tare har kusan tsawan awanni biyar kafin sukayi nasarar kona su baki d'aya.

Waige-waige lado ya fara yi yana kiran Hafsatu, ganin bata fito ba yasa ya kalli mutanan yaga Mai-unguwa yace "Baffa malan ina Hafsatu na..?" Sai ga mai-unguwa na hawayen murna yau yaji muryar lado daya dad'e beji ba. "Tashi mugani.." Ma'aruf ya fad'a yana kallon lado cikin ido, "ba zan iya ba rankashi dad'e..." Lado ya fad'a yana zubar da hawaye Ma'aruf yasa focal parson ya tatta6a shi sai yaga 6arin jikin shi na hago baya aiki nan yayi musu bayani daman hakan zata faru kasan cewar yana da matsalar AFP sannan kwanciyar da ya dad'e guri guda yasa hakan yayi tasiri yanzu haka lado sai dai a samo mai weal chair da keke ya dinga amfani dasu, sun d'an jima kafin suka bar gurin su Ma'aruf suka koma state dan sanar dasu abunda ke akwai.......,*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


*ASSALAMU ALAIKUM FAN'S!, Nagode da sakwannin ta'aziyarku gareni, masu k'ira, PC, text message da masu yi min a grps, Allah ya bar kauna ita kuma Allah yaji k'anta da rahama yasa karshen wahalar ta kenan.*πŸ‘


   _Masu neman Novel d'in daga farko dan Allah a dinga tambaya a grps wallahi babu abinda yafi tura novel daga farko haushi gashi ba mutum d'aya ke soba, gashi idan ka hana aji haushi, idan baka yi typing bama aji, please dan Allah ku dinga mana afuwa ko masu su suje shafin *Wattpad* @Hajjac zai samu kafin Feedohm ma na bud'e, ko su bari ayi document sai abasu, thanks._😘😘     Page *37-38*


     *S*ai da ya kammala komai sannan focal person d'in shi ya kai shi can airport ya hau jirgin zuwa kano, tun a hanya yayi waya aka turo mai da drive. Suna dira ya hango parado d'in shi da ya siya a ita aka zo d'aukar shi ya k'arasa yashiga driver yaja, har suka je gida amsa wayoyi yake yi direct ya wuce side d'in Madre kai da ka ganshi kasan a gajiye yake ya zauna kan sofa tare da killar da phone d'in shi a gefe ya rintsa ido.

"Ma'aruf ka dawo ke nan?" Madre ta fad'a tana k'okarin fitowa daga kitchen. Amsawa yayi a wahale har ta k'araso kusa dashi tana kallon shi cike da tausa yawa dan ta hango gajiya sosai a fuskar shi.

"Toh kaje kayi wanka sai na turo Sumayya ta kawo ma abinci, da kaci sai ka kwanta ka huta..." Da sauri ya hau gir-giza kai alamar a'a cikin turo baki tamkar karamin yaro yace, "no Madre please karki turo min ita wallahi ciwon kai zata samin, ko ta tambaye ki na dawo kice mata a'ah kawai."

Yana kaiwa nan ya mike yayi hanyar fita, yana jiyo Madre na cewa, "a'ah yaro ni kam ban iya karar  ku ba, idan ta tambaye ni Zan gaya mata gaskiya."

Yana shiga ya fad'a kan rog yana sauke numfashi, gaba d'aya abinda ya faru da lado ne yake mai yawo yana mamaki ace wai kishiyar uwar ka ita ce zata illataka sabida wani sakar ci, sai yanzu yake jin haushi da be tsaya yasa an hukunta Hansai ba amma ya bar shi har zuwa lokacin da zai koma garin.

Mtww... *!* yaja tsaki tare dayin juyi bayan ya tuno cewar kwanakin bikin shi sun kusa zuwa shi bama wanda ya sanarwa, mtww... *!* ya kuma jan wani tsakin tare da mik'ewa tsaye ya shiga bathroom bayan ya rage kayan jikin shi.

Daga shi sai small towel a kugunshi ya fito, tunda ya bud'e bathroom d'in ko'ina na cikin d'akin ya fara fitar da wani daddad'an kamshi me azabtar da zuciya, dressing mirrow ya k'arasa ya d'auki wani k'aramin towel d'in wanda yafi na jikin shi kan-kanta ya fara goge jikin shi dashi, yana gamawa ya fara shafa mayuka masu  tsada da kamshi sannan ya wuce dressing room ya fito da sweetshit green color da jeans white color ya sanya yasa takalmi trainer's kalar green ya feshesu da kala-kalan turaruka masu masifar kamshi ya sanya ear muffs a kunnan shi yana jin suratul tauba a haka ya shiga side d'in Madre.

Zaune ya same ta tana danna laptop gefenta duk takadda ya k'arasa ya zauna a 2seater tare da kallon ta yana turo baki like small boy. "Kaje dining kaci abinci." Kurum Madre ta ce mai ba tare da tad'ago ta kalle shi ba dan tasan idan ta d'ago me zata gani.

K'in tashi yayi sabida beji abinda take cewa ba sakamakwan ear muffs d'in dake kunnan shi, a hankali ta kalleshi tayi mai alamar ya cire da hannu sannan yayi yadda tace d'in but still bakin shi a zumbure ta ta6e baki tare da cewa,

"Kaje kaci abinci nace ka dawo daga tafiya kak'i bawa ciki hakk'in shi, ko a koshe kake?" Ta tambaye shi tana ture laptop d'in gabanta, Ma'aruf ya gir-giza kai tare da cewa.

"Please Madre muje ki bani..." Kallon shi tayi da mamaki sannan ta mik'e tayi hanyar dining d'in tana cewa, "ni gara ma kayi auran Ma'aruf na ga alamar yanzu tabarar taka neman yin yawa take yi...."

A baya ya bita yaja kujera ya zauna, sakwara da miya ta zuba mai wadda taji nama da stock fish ga uban ogu leave sai kamshi ke faman tashi ta zuba mai lemon kwakwa da ya sha peak milk ya wanke hannu a cikin boul d'in dake gurin ya fara ci kenan sai ga Sumayya ta dawo.

"Oyo-yo Yaya Ma'aruf dama yau zaka dawo?" Cewar Sumayya tana k'arasowa wajan shi da sauri cikin farin ciki da murnar ganin shi da tayi... Banza da ita yayi yana ci gaba da cin abincin shi tamkar be jita ba har ta k'arasa kusa dashi taja kujera a kusa dashi ta zauna.

"Welcome Yaya Ma'aruf..." Ta sake fad'a ya sa 'yar k'aramar sakwarar da ya gutsuro a cikin bakin shi kafin ya tauna ya had'iye yace "thanks..." Cikin ranta tace "thanks kuma kai da zaka ce min OK ko yauwa sai kace wani thanks sai kace nayi ma kiss..." A fili kuma tayi murmushi tare da kura mai ido, ba k'aramin kyau yayi mata ba, ji take inama zai tsaya da ta rungume shi taji shi a jikinta wannan pink red d'in lips d'in nashi ba abunda zai hanata d'ora nata akai ta lumshe idanu ta bud'e su tar akan nashi....

"Yaya Ma'aruf ina ta maka zancen different event d'in da za'ayi kayi shiru baka ce min komai ba, dan Allah yau karka tashi bamu gama magana ba." Duk abinda suke yi Madre na jinsu, har mamakin Sumayya take yi irin yadda taji tana zuba surutu kuma duk akan yadda bikin su zai kasan ce ne, shi kuwa gogwan yayi shiru sai faman cin sakwarar shi yake tamkar jariri ake bamawa. Da yaji surutun nata yayi yawa ne yasa shi kallonta da manyan sexy eye d'in shi yace.

"Sumy... *!*, wai ba kya gajiya da surutu ne...? And ina cin abinci kike son muyi magana da yake haka aka yi teaching d'inki...? Bana son hayaniya kije ku shirya kome zaku yi I don't have a time to talk akan wannan abun abi..?"

Bata wani ji haushi ba ta d'aga mai kai tare da m'ik'ewa tabar gurin hannunta rik'e da wata leda mai d'auke da magungunan mata da taje Beeba ta rakata suka siyo gidan wata hajiya mai komai da ruwanki. Da kallo ya bita har ta shiga room d'inta ya gir-giza kai tare da wanke hannun shi dan appertained d'in shi nacin ya gishe.

Sumayya na shiga d'aki ta zube kayan akan gado sun fi kala ashirin ko wanne da amfanin shi ta d'auki wata katuwar jarka ta fara kwankwad'ar abunda ke ciki ko rashin dad'in ba taji ba har tasha rabi sannan ta d'auki wasu ta fara cusawa a ppt d'inta da Cotton wood.... Lol amarya.

*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


     Page *39-40*


*FEW MONTH LITTER*

    *G*idan cike yake da 'yan uwa da abokan arziki na both amarya da ango, Madre bak'i yaki rufuwa ana aurar da auta duk inda ka ganta bakin ta da murmushi ta k'awayanta na gurin aikin su sai zolayarta suke sai dai tayi dariya kawai ta wuce dan murnar da take ciki tafi komai yawa a zuciyar ta.

Tana fitowa compound ta hango Ma'aruf yaji uwar kwalliya kai da ka ganshi kasan cewar shine ango, abokan shi guda uku suna biye dashi suma duk sunsha ado Madre ta sakar mai murmushi tare da komawa cikin d'aki dan kar mutane suga zak'ewarta a tafi ana yi da ita abaki. Waje suka fita inda maza suke manyan mutane da kananun ma'aikata kai da gaka tarun kasan ba k'aramin people ya tara ba, Ma'aruf yayi mamaki dan shi yasan ba wani invitation card ya raba ba amma kakaf abokanshi na k'asashen waje dana gida Nigeria d'ai-d'ai kune babu "Toh waya sanar musu..? Ya tambayi zuciyar shi amma ba amsa "ko Naseer ne yayi mai wannan aika-aikar...?" Ya juya yana kallon Naseer dake ta faman gaisawa da mutane "amma kuwa idan shine sai ya yi mai rashin M." Ya fad'a a cikin zuciyar shi sannan ya fara smiling yana gaisawa da mutane.

Kunnuwan shine suka jiyo mishi ana cewa an d'aura auran Muhammadu Ma'aruf da Sumayya akan sadaki dubu d'ari biyu da mukullin mota.... Daram-Dam... *!* k'irjin shi ya buga cikin ranshi yace "Dubu d'ari biyu sadaki...? Waye yace musu zai bada har wannan kud'in shi da yake son albarka aure, uwa uba harda car key shi da beyi niyar siyawa Sumayya mota yanzu ba sai yaga irin takunta.."

Saleem ne ya ta6o kafad'ar shi ganin tamkar be san an shafa fatiha ba yayi figigit yana kallon shi kafin shima yakai tafin hannunshi masu tsananin taushi ya shafa fuskar shi "kai Ma'aruf ka saki jiki mutane sai kallonka suke yi sai suyi tunanin baka son auran please dan Allah."

Fitar da komai yayi daga ranshi aka fara gudanar da taro cikin kwanciyar hankali, sai da abokan shi suka fara tafiya sannan ya samu damar shiga cikin side d'in shi su da su Naseer sai tsiya suke mai yak'i kula su. Yana zuwa ya cire babbar rigar dama duk ta isheshi jiyake tamkar an d'aura mai katon dotse yayi saurin shiga bathroom ya fad'a cikin jarcuxe yana sauke ajiyar zuciya "ikon Allah..." Ya furta cikin ranshi "wai yau shi ake d'aurawa aure..? Ikon Allah shi be ta6a kawowa zai yi aure kusa haka ba sai gashi lallai kar mutum yaja da ikon Allah, shine mai komai sannan mai yin komai. Ya dad'e a cikin ruwan kafin ya fito ya sanya bathrobe ya wuce dressing room, nan d'in ma sai da ya dad'e sannan ya fito cikin shirin shi. Shadda ce yasa ash color tazarce tayi mai bala'in kyau ya fita parlor su Yaseer, Naseer da Sameer sai tsiya suke mai yana musu murmushi. Yana zama su Hidaya suka shigo da warmers na abinci suka dire musu suna kallon su, "uncle Ma'ar gashi nan inji Madre tace za'a kawo sinasir yanzu..."

Wani mugun kallo ya bisu dashi jin sunan da suke kiranshi a gaban friends d'in shi "Tasleema bana ce kar wanda ya sake kirana da wannan stupid name d'in ba..?" Ya fad'a ranshi a had'a suka fara kalon juna Hidaya tace "sorry uncle Ma'ar... Sai tayi saurin rufe baki jin ta sake fad'a ya kallesu tare da nuna musu kofar da suka shigo yace "get out... *!* marasa kunya kawai." Fita suka yi suna dariya Inteesar tace "ah su uncle angon Yaya Sumy gaskiya sun yi perfect wallahi, matsalar d'aya da Yaya Sumy zata sha fama miskilanci..." Suka kuma sakin dariya sannan suka shiga cikin d'aki gurin amarya.

Zaune suka same ta ana mata makeup duk kawayan ta suma suna tayin nasu, kallonta suka yi inteesar tace "gaskiya Yaya Sumayya kin yi dace da miji, uncle Ma'aruf ya had'u ta ko ina kinga kyawun da yayi kuwa yanzu...? Hidaya ta kar6e zancen "wallahi uncle handsome guy ne ya had'a komai a rayuwa." Tasleema tace "kyau, ilimi, nasaba, kud'i, daraja, biyayya, tausayi, in fact shi have everything what I mean komai da komai..."

Wani kayataccen murmushi ta saki tare da sauke ajiyar zuciya lokacin an gama makeup ta mike tasa wata doguwar riga bridal tace "intee yana ina yanzun...?" Inteesar tace "yana side d'inshi tare da friends nasha.." Sumayya ta kalli Beeba "please Beeba d'akko min wannan turaran." Beeba ta kalleta da mamaki tace "kin san dai ba yanzu zaki amfani dashi ba sai an kaiki gidan miji uwar zumud'i kawai.."

Ganin Beeba ta hanata yasa tayi tsaki, ita yanzu so take kawai ta ganta a gurin shi sabida ta tsuma ga wanda Madre tayi mata ga wad'an da tasha a 6oye hakan yasa duk take jinta wani iri tana jin tamkar takai kanta sai dai yawan mutane yasa ta kasa zuwa. 8:00pm aka fara tafiya dinner wanda daga an gama an dawo za'akai amarya.

"Ma'aruf kaje ka shiga mota ana jiran ka kaji ko....?" Madre da ta shigo d'akin shi ta fad'a dan gaba d'aya event din da aka yi sai tazo ta sashi yake fita. Yanzu ma be so zuwa ba shi yasa tazo ta mai magana, yana jin haushi haka ya shirya cikin wani shegen yadi milk color da ratsin blue ajiki, hula yasa zanna blue da shoe cover yayi kyau sannan su Sameer suka kai shi motar da aka tanadar musu shi da anarya.

A ciki ya sameta gaba d'aya kamshin turare dana khumra sun turare motar, Ma'aruf kenan, yana matukar son kanshi hakan yasa yayi tasiri a zuciyar shi ya zauna kusa da ita tare da matsawa jikinta ya riko hannunta, jikin ta ya fara rawa nan da nan taso rud'ewa kamar ya gane ya janyo ta jikin shi yana kara shakar kamshinta a haka aka ja mota......
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*       Page *41-42*


        *D*inner akayi ta kece raini kowa ya ci ya sha daga abunda aka tanadar yayin da Madre tayi barin kudi kamar ita ke bugasu……Sae kusan 10 Na dare sannan aka tashi gidan Madre din aka koma kafin zuwa Safe ayi walima Ango ya tafi da amaryarshi don ba'a bukatar yan kai amarya ……

  Tunda Asuba aka fara shirya shiryen walimar AA Event & Design dake kabo crescent off Ahmadu bello way Garki 900242 Abuja ……Madre ta dauko sukayi decorating harabar gidan ……
     Sun kawata gurim sossae ta yarda ko makiyi bara ya kushe ba ……Karfe 4:10pm aka fito da Amarya Sumayya sanye da Arfo Lace white da ratsin Baki a jiki……tayi masifar kyau sai sheki take tana sargale da hannu Ma'aruf shima kanshi abun kallone Sae dae kallo daya zaka mashi ka tabbatar da murmushin Yaken dake kwance a saman kyakykyawar fuskarshi sab'anin Sumayya dake murmushin farinciki ……

  Sae da suka fara zuwa suka gayyar da dagin Abbah sannan suka koma ga dangin Madre suka saka masu albarka sannan suka koma inda aka tanadar masu kujerunsu suka zauna ……Yayin da sauti mai taushi ya karad'e gurin……

  Wajen magrib sannan jama'a suka fara watsewa yayin da Madre taki yarda tawa Ma'aruf nasiha ta koma part din Ma'aruf tayi kwanciyarta sae dae Abba da Maryam kadae suka masu Sannan suka ce ya dauki matarshi su tafi……

  Ko irin kukan da ake Sumayya bata yi illa murmushin da take tana yake hakora duk da irin sharrin da abokan wasa ke mata……Bangaren Ma'aruf kam yarda kasan shine Amaryar haka ya koma kallon mutanen gurin yake kamar ya fasa kuka yana neman Madre amma sam bai ganta ba !kasa hakura yayi ya kira Maryam ya tambayeta "Ina Madre?

  Ita Kanta tasan Madre boyewa tayi saboda son Autan nata sae dae ta kalleshi cikin kwarin guiwa tace "Auta Hidima tawa Madre yawa tana can gurin Family din su Abba suna kara gaisawa"
  Daga haka ta ja hannunshi k'annan Madre suka rufa masu baya har kusa da sabowar motarshi da Abbah ya bashi yau suka shiga suka tafi ……

  Haka suka isa gidanshi dake GRA wanda tun daga waje zaka gane tsaruwar da gidan yayi ……
  Baban falon gidan dake dauke da Royal chairs suka samu masauki yayin da ya zube saman three siter ya dafe kanshi dake masifar sara mashi ……Ita kam Sumayya tsaye tayi ta ware hannaye tana juyi a hankali tare da karewa falon kallo har tsawon minti goma sannan ta dawo ta zauna saman hannun kujeran tare da dafa bayanshi tayi kasa da kanta ta kira sunanshi ……
  Dagowa yayi ya kalleta sannan ya da kamo hannunta ya dawo da ita gefenshi ya zaunar da ita ya mayar da kanshi ya tallabe tare da lumshe ido ……

   " Yaya Ma'aruf yunwa fa nake ji ……"ta fada lokacin da ta kai hannunta ta shafa sajenshi ……

  Shiru ya mata ya sauko wayarshi ya typer message ya tura sannan ya kalleta yace "Ki jira ga Ahmed nan zuwa "

  Turo baki tayi tace "Aa ba sae ya zo ba gaskia na daina jin yunwar……!

  A Hankali ya kalleta yace "Why?

  Kai tsaye tace "Wannan lokacin bai kamata kowa ya shigo mana gida ba !

  Ya bude baki da niyar mata magana yaji karar doorbell ya mike ya nufi kofar ……Ahmed ya gani rike da leda ya mika mashi tare da mashi bankwana ya juya ……

  Ko da yazo gabanta ya aje ledar ya juya ya shige part din dake kallon tsakiyar falon abunshi ……

 ,Ita kam Sumayya gyara zama tayi ta fara cin naman kajin dake ciki sannan ta kwankwadi Fresh milk tare da lumshe ido sannan ta mike ta nufi handbag din ta ta fito da wani ruwan magani ta shanye tas ta aje robar ta kara janyo wani dunk'ulen bak'in abu kamar curin dawo ta fara ci tana yatsina fuska saboda masifar d'acin da abun ke da shi ……Wasa wasa sae da ta fiddo kalaluwar magani kusan Biyar ta cinye sannan ta mike tana mika ta tsallake ledar kajin ta nufi Part din ta taga Ma'aruf ya nufa ……

  Tsaye ta iskeshi gaban mirrow daure da towel yana combing din sumarshi !Ta cikin mirrow din ya hangota ya dauke kai kamar bai ganta ba ……

  Murmushi tayi sannan ta fada toilet rike da handbag dinta a hannu!shi kam tab'e baki yayi ya d'auko jallabiya fara k'al ya sanya tare da shinfida prayer mat ya kabbara sallah ……

  Koda Sumayya ta shiga toilet inserting magunguna ta fara yi kamar hauka sannan tayi wanka ta fito daure da towel a k'irji lokacin har ya sallame sallarshi har ya koma ya kwanta saman gado abunshi ……

  Daga bakin toilet din ta saki Towel dinta ta hawo gadon ta kwanta bayanshi saboda masifar feelings din da take ji saboda kayan matan da ta kwankwada ……
    Gabanshi yayi masifar faduwa take ya fara tunanin anya Sumayya bata bin maza kuwa?Wani bangaren na zuciyarshi ya bashi amsa da ina zata gansu bayan kullun Madre na tsare da ita a gida ……

  Kiran sunanshi da tayi ya katse mashi tunaninshi yayin da ta fara fad'in "Sorry Bana iya kwana da kaya a jikina bayana ke rashes"

  Gyada mata kai yayi ba tare da ya juyo ba !Ita kam hakan bai hanata yawo da hannunta saman kirjinshi ba tare da daura kanta a bisa wuyanshi ……

  Duk irin yarda yaso ya daure kasawa yayi dole ya juya ya fara mayar mata da martani yayin da ta fara fita hayyacinta tana kiran sunanshi cikin Zakuwa ……


  《》《》《》《》

  Hankalinta ta mayar Kan Sallau dake tambayar Lauratu ina zata je ……

  Cikin ladabi Lauratun tace "Zan je na duba Baffa ne da jiki "

  Daure fuska Sallau yayi yana kallon Fuskar Lauratu da tayi wa ado da kwalli tare da uban jan baki har saman goshi sannan ya kalli K'arama dake rike da hannun Lauratun tana lilo yace "Haba Lauratu Ahaka zaki fita mazan waje su kalle man ke fisabilillahi?

  Shiru Lauratun tayi tana kallon K'asa yayin da K'arama ta sheke da dariya tace "Amma ko an cuci maza !Yaya Lauratu me zasu kalla da fuskanki duk bak'in kwalli?ni dai mu tafi "

  Da yake ya san halin K'aramar bai ce mata komae ba ya kalli Lauratun cikin sanyin murya yace "Ki Taimakeni Lauratu karki fita da wannan kwalliyar ko wa ya kallah sannan dan girman Allahi ki saka katon Zani ki kulle duk jikinki ki zo muje na rakaku ku ganoshi mu dawo "

  Gyada kai Lauratun tayi sannan ta koma daki ta goge kwalliyarta tare da dauko katon Zani ta lulluba ta sake fitowa ta iskeshi shi kadae ……Cikin sanyin murya tace "K'arama fa?

  Kafin ya bata amsa suka hango K'arama ta fito daga dakin Zulai rike da katuwar kwarya ta nufi bukkarsu ta aje sannan ta ja ta tsaya bakin kofar gidan tare da juya masu baya ……

  Zulai kam fitowa tayi daka bandaki ko buta babu ta wurgawa K'aramar harara kamar wata kishiyarta sannan ta shige daki tana waka a hankali ……
  *HAJJA CE*πŸ‘ˆ
&
*FEEDOHMπŸ’ž*

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*     Page *43-44*


Da Sauri Lauratu ta nufi gurin K'aramar taja hannunta suka fita yayin da sallau ya mara masu baya kamar wani mai gadinsu yanayi yana kare Lauratun gudun kar yan garin Su kalle mashi mata sannan duk wani motsinta saman idonshi takeyi !Ita kam hankalinta naga K'arama dake ta faman fitar da numfashi kamar namijin zaki……

  Suna shiga gidan suka iske gidan cike da jama'a an zagaye Lado dake kwance a tsakar gida yayin da maitafasa ke tsaye tana ta zuba ruwan tijara ita kadae ……
  Sallamarsu ce ta saka matan garin fad'in "Gasu nan ma Maitafasa"

  Ta watsa hannuwa baya ta nufosu ta cakumi wuyan K'aramar ta dire kusa da Malan Lado tana fadin "Kalli Fuskar wanga d'iya Lado ta gidan Ubanka tayi kama da zuri'armu da zaka fada man cewa d'iyarka ce "

  A Sanyaye yana Zubar da hawaye yace "Wallahi Inna wannan d'iyar jinina ce "

  "Lado banda mutunci fa !da kwarankwatsa ka k'ara maimaita wannan zancen sae na zabga maka mari a kumatunka duk da kake haka "ta karashe maganar tare da dungure mashi keya ……

  Tab'e Baki Kundum tayi tana fadin "Ba'a banza ba Lado ya amshi wannan d'iyar ba Maitafasa……"

  Juyowa tayi tana karkad'a yatsu tace " Fad'a man  a me ya amsheta algunguma? Yatsina hanci Kundum tayi ta juya k'eya ba tare da tace komae ba sae uban tsokin da ta ja……

  Wata mata dake tsaye cikin garke tace "Taya bara ya amsa ba bayan ita kanta yarinyar Mayya ce "

  Da Sauri Maitafasa ta saki wuyan K'arama tare da dafe kirji tana fadin "Raba ni da aikin mayu !Ke Lauratu "

  Daga kai Lauratun tayi ta kalleta sannan ta kalli K'arama dake ta raba ido tana kallon mutanen gurin !ta d'aga k'afa zata isa gurin Sallau ya kamo hannunta yace "Zan Dauki komae a duniyar nan amma banda cin zarafinki Lauratu "

  Kallonshi tayi da idanunta da suka ciko da kwallah ta gyad'a kai a hankali sannan ta zame hannunta daga rik'on da ya mata ta nufi inda su Maitafasar ke tsaye ta kama hannun K'arama ta rike ……

  Ihu Kundum ta saki tare da zubewa k'asa tana fadin "Dan Allah kiyi Hakuri karki cinyeni yar nan "

  Mutanen gidan suka dauki bahaggun salati mara karshe suna fadin "Shi kenan ta kama Kundum" yayin da suka yo kan K'aramar suka danketa kamar wata katuwar Mace suna fad'in "Wallahi Sae kin tsallaka ta munafukar yarinya daga zuwa zaki kama ta" wata ta kai mata rankwashi a tsakiyar kai ……

  Dafe gurin tayi tana turo baki tace "Wace?

  Uban rankwashi Maitafasa ta kuma kai mata tana fadin "Hafsuwalle ce dan ubanki "tare da watsa bak'in hannunta saman fuskarta sannan ta kashe ta da mari lokaci guda ta ta cakumi kwalar rigarta ta d'aga ta sama ta tsallake Kundum da ita sannan ta direta k'asa cikin mugunta da zulunci ……

  A Jiyar Zuciya Kundum ta saki ta mike zumbur ta nufi bukkarta tana d'angyasa kafa rike da kirjinta tana hucin wahala tare da zare idanu ……

  K'arama kam kuka ta saki da karfi saboda yarda Maitafasa ta direta k'asa har sai da dutsi ya fasa mata tafin kafarta !Yayin da Lauratu ta rungumeta da sauri tana kuka ta nufi Hanyar barin gidan da ita !amma mugayen matan dake zagaye da gidan suka fara dukansu suna fadin " munafuka……"

  Sallau dake tsaye bakin Zaure ya karaso cikin gidan ya zame masu kamar Mahaukaci ya kwaci Matarshi ya rungume suka bar kauyen yayin da ita kuma tana rungume da K'arama dake ta faman tsuka tana goge hawayenta!

  Kundum kuwa na shiga daki ta fara karkada jimammen kugunta tana gwatso tare da gwalo !Ji tayi kamar ana dukan fatar jima a kasa !bata damu ba ta janyo wani kodadden zani zata daura lokaci guda dakin ya kauraye da duhu yayin da ta gwalalo ido waje tana lalubar kofa amma ta rasa ta……

   Cikin dauriya ta fara karanto addu'ar su ta jahilai mutanen da "Yar kyalwa baiwaye dakin Kunduma tantar tantar yar kyalwa kunna hitila ……"
 
  K'arama ta gani duke gurin kafarta yayin da ta kama agararta ta ja cikin mugunta ……

  Cikin jin haushi Kundum tace "Awo kece munafuka to da kwarankwatsa sae dae a fitar da gawarki dakin nan " Ta Duka da niyar cakumo K'arama amma ta nemeta ta rasa…… Ihu ta k'wala yayin da fitsari ya samu damar sulaluwa ……

  K'arama ta gani tana yawo saman dak'in dauke da katuwar wuka jawur da ita tana cakama iska !Duk lokacin da ta caka wukar Azabar a cikin Kundum take karewa ……Ihu ta farayi tare da zawo tana neman taimako amma babu mai jinta duk mutanen dake cikin gidan ……Yawan K'arama ya linko sau shiddah yayin da manyan hakora suka fito ta karkashin habarta ta fara zagaye Kundum dake fitar da nishi sama sama ……Azabar tsoro ta saka Kundum sandarewa a gurin yayin da ta sulale ta gaba ta fadi saman tarin kasar dake zube a tsakiyar dakinta ……

  Malan Lado kam tunda ya rufe idonshi yana hawaye bai sake budewa ba har sae da tarin matan dake tsakar gidan suka watse sannan Maitafasa ta matso ta zauna kusa dashi tana Fad'in "Ladona Ladona ashe bayan kana kwance Hafsuwalle Bokaye ta fara nema don ka amsa Wannan Mayyar diyarka ce"

  Girgiza kai yayi cike da takaici yana da tabbacin Sharri ne irin na Maitafasa ……

  "Ladona shi yasa naga wannan yarinyar tana zuwa baka abinci ashe magani suke barbada maka a ciki" Ta karashe maganar cikin sigar kwantar da murya……

  Har lokacin bai bude idonshi ba sae dae hawayen dake zuba ……Dariya tayi tace"Yanzu da bakinka Ladona babu sauran kuka yanzu ma jira nake Hansai ta dawo garin don jiya Mai unguwa yace man yau da mairaice zata dawo shi yasa kaga yau ko tafasa banje debowa ba na tanadi gororina da sanduna na dukan Hansai !kai Lado har dae likafanin Hansae na tanada don wallahi karamin yaki zaayi a wannan kauyen yau……Ina Sonka Ladona duk wanda yace zaya tabaka a garimnan to wallahi baya da riba a rayuwa……"

  Shiru yayi ba tare da ya bude idonshi ba haka ta kare zamanta tare da surutun ta bai tanka mata ba ……
    Wani Yaro ya shigo da gudun tsiya yana fadin "Hansai ta dawo Maitafasa……"

 《》《》《》《》

   INA AMARYA SUMAYYA?

    Dakyar Ma'aruf ya shigeta lokacin ba ita kadae ba shi kanshi ya wahala……Azaba da rad'ad'i suka dirar mata lokaci guda yayin da numfashinta ya janye gaba daya ……Ma'aruf kam bai san wainar da ake toya wa ba kawae aiki yake ba tare da ya lura da bata numfashi ba !Tun yanayi abun yana gamsar dashi har ya koma yanayi don dole saboda ya k'asa hakura ya barta !Sae wajen asubah sannan yayi kokarin tilasta kanshi ta hanyar sulalewa kasan rug din dakin ya zube ba tare da yasan inda kanshi yake ba ……

  Sanyin asubah ya hura Sumayya ta ja numfashi da kyar ta kwalla Kara saboda axabar rad'ad'in dake ratsata……Uban gayyar kam Uban tsoki ya saki wanda shi kanshi ya rasa na menene lokaci guda ya dafe cikinshi yana juyi a hankali ……

  Kusan Awa daya tana kuka da karfi tare da kwala mashi kira ta kasa koda motsi !Da kyar ya mike yana kallonta da idanunshi da sukayi jawur lokaci guda ya dauke kai tare da mikewa yana dafa bango ya nufi toilet……

   Ya dade cikin bathtub din sannan ya fito har lokacin yana jin Kukan da Sumayyar take !Tausayinta yaji lokacin da ya fito yaga yarda bedsheet din yayi kaca kaca da jini ……Sae da ya zura kayanshi yayi sallah sannan ya kalleta tayi lamo jikin pillow kukan ya daina fitowa ! Shi kam duk da baya neman mata amma yana zargin akwae abunda Sumayya tayi amfani dashi da ya kusa halaka su haka ……Kit din da Maryam ta saka mashi a mota ya fita ya dauko ya bude ya fito mata da jallabiya baka da hijab ya aje saman gado ya kalleta cikin kulawa yace ta saka ya kaita asibiti……

  Kuka ta saki cikin shagwaba tace "Ka Saka man Ya Ma'aruf wallahi bana iya koda d'aga hannuna……"

  Gyad'a mata kai yayi ya janyota ya cire blanket din da ta rufe jikinta dashi ya fara canza mata kaya !Bala'in da take ji bai hanata tuna Matarnan mai kayan mata tace mata bayan komae ya kammala ta sake saka wani magani dake cikin karamar roba cikin ruwan zafi ta zauna zata sake komawa kamar budurwa……

  Girgiza kai tayi da ta tuno azabar da tasha jiya yayin da wani bangare na zuciyarta ke bata shawarar ta sake gwada may be don farkone shi yasa ta wahala haka ……Kallonshi tayi a sanyaye tace "Ya Ma'aruf ina son zan shiga toilet nayi wanka tukun ……"

*HAJJA CE πŸ‘ˆ*
&
*FEEDOHMπŸ’ž*

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


      Page *45-46*


Ba tare da ya kalleta ba yace "Zamu je asibiti Sumayya……"

  "Wankan na da amfani……" ta fada tana kallon erection dinshi
    Kallonta yayi sannan ya kalli inda hankalinta yake ya saki Dan karamin tsaki ya mike yana zabga mata wani uban kallo ya nufi Bakin gadon ya dauki wayarshi ya kunna sannan ya zo ya sabeta ya fita da ita ……

  Sae da suka je asibitin sannan ta gane kuranta don ba karamin aiki ya mata ba !Sae da aka mata Propofol injection sannan aka mata dinkin ……Doctor din kam bai samu fuskar wa Ma'aruf din dogon sharhi ba ……

  Sae kusan 12 sannan suka dawo gida ya iske Madre ta aiko masu da breakfast mai rai da lafiya !Sae da ya bata taci sae shagwaba take mashi sannan ya bata magungunan da suka basu tayi bacci !tsayawa yayi yana kallonta ba laifi itama ta had'u kuma yana mata son da yakewa yan uwanshi sae dae sam baiyi tunanin zai iya rayuwar aure da ita ba saboda masifar rawan kanta!

  《》《》《》《》《》


  Su K'arama na isa gida suka iske mutanen gidan cirko cirko tsakar gida ummansu kuwa na tsakiya durkushe daga mai dunguri sae mai zagi ……Kallo Da K'arama ta mata ta dauke kai ta koma bakin Bukkarsu ta zauna ta zauna tana duba kafarta inda Maitafasa taji mata ciwo……

  Zulai ta juyo tana kallon Lauratu da tayi mutuwar tsaye tana kuka ganin kaskancin da akewa Ummansu tace "Kuka yanzu kuka fara Lauratu indae har Uwarku bata daina halin bera ba……"

  A Razane take kallon Zulai sannan ta kalli Inno dake tsaye bakin bukkarta tare da kallon Sallau ta sake kuka tana fad'in "Wallahi Ummana bata halin Bera sallau……"

  Gyada mata kai yayi shima kamar yayi kukan yace "Na gasgata Lauratu!Inna Zulai dan girman Allah ku daina abunda kuke yi ku tausayawa wannan baiwar Allah ku bar zuciyarta ta huta!

  Gaba daya suka rafka salati wanda dama sarar mutanen gidan ce yayin da jummai tace "Sallau kaima an jike ka kenan……"

    "Wallahi baa jikeni ba !Shin me ta maku da zaku sakata tsakiya kuna wulakantata haka Inna Zulai?Shin ita ba diyar nan gidan bace ?koko ance maku Inno bata kaunar yarta take zuba maku ido tana kallonku shin ku baku san Kawaici bane inna Zulai……"

  Matar Bedo tace "Yanzu dae Sallau kana kare surukarka !Hafsuwallw daga ido ki kalli Sallau ki ce bake kika Saci Kwanon Man Shanun Inna Zulai ba……?

  Saurin Kallon K'arama sukayi shi da Lauratu sannan ya mayar da kallonshi ga Hafsuwalle dake duke tana hawaye amma ta kasa dagowa ta kallesu ! Tana da tabbacin dakinta aka ga kwanon man shanun amma tayi imani sae dae idan K'arama ta dauko shi……

  K'arama tayi tsallen kura ta dira gaban Umman tata tana dangyasa kafa tare da yarfe hannu baya tace "Abun Sata na Sata ne Zulai……"
  Hafsuwalle ta janyota ta zaunar da ita kasa tana kallonta da rinannun idanunta alamar tayi shiru ……
  Makale Kafada tayi tace "Ba zanyi shirun ba Umma bayan itama man Shanun na sata ne gidan Fulani ta shiga ta iske sun gama kad'i Habee ta shiga daki ta dauko kwarya ta satoshi……"

  Uban Mari Zulai ta zabga mata tana fadin "Dan Ubanki ni zakiwa Sharri K'arama ?In je in sawo man shanun hayin dan malan ki ce sato shi nayi !To da kwarankwasa bara Ardo ya shigo yau sae dae ni ko ku a gidannan ……"

  Mikewa tayi tana Murd'a hannu ta fita yayin da zulai ta cigaba da zabga ruwan tijara yan gidan na tayata !Hafsuwalle da Lauratu kam sun yarda da abunda K'arama ta fad'a sae dae babu wanda ya motsa daga inda yake ……

  K'arama kam gidan Fulani ta nufa ta iskeshi Zaune yana gyara lalataccen kekenshi ……Da yake tasan basu zama inuwa daya dashi don haka ta tsaya daga nesa ra d'aga murya tace "Fulani an kama barauniyar Man shanunku……!
  Da Sauri ya mike ya dauki katuwar sandarshi yana fadin "Ke K'arama ban san shegantaka yasin na iso nan sae na k'wadeki……"

  Tab'e baki tayi tana d'age kafa guda tace "Yasin da gaske nake Fulani Zulai Matar Ardo ce ta sace maku man shanu kuma kazo gidan yanzu na,nuna maku……"

  Kamar sakarai ya biyota har cikin gidan yana fadin "Yasin idan karya kike sae na k'wad'eki……"

  Murgud'a baki tayi tace "Idan da gaske nake fa?
 
  Washe baki yayi yace "Zan baki naira Goma……"
Dariya tayi sannan suka karasa cikin gidan kallo ya koma kan fulani da K'arama ta shige bukkarsu ta fito da Kwaryar Man shanun da ta kai ta mike mashi tana fadin "Zulai ta Sata shine nima na dauke na kai Bukkar Ummanmu mu dinga sha !Sae suka gani suka ce Ummana ta sata ……"Ta kalli Lauratu tace "Dan Allah yaya Lauratu ba kowa ya rasa ba kenan ?
 
  Ita kanta Lauratun bata san sadda murmushi ya subuce mata ba ta kama hannun Ummanta ta dagata ta kaita har bakin bukkarsu sannan tace "Allah zaya warware komae Ummanmu……"Daga haka ta juya ganin K'arama ta rike kwarya tana fadin "Bani kudina Fulani sannan kaje ka turo matarka tawa Zulai yarda tawa Ummanmu……" Kudinta ya bata ya juya yana kwafa ……

  Matan gidan kam surutai suka fara yi Kasa kasa sannan suka watse suka bar Zulai da ta fara Borin karya!!!!!

  【】

  Maitafasa kam jin cewa Hansai ta dawo ya sata kwasawa bukkarta da gudu ta dauko wata katuwar gora tare da farin yadi ta fita gidan ! Kirjin Malan Lado ya fara dagawa da karfi saboda masifar bakin cikin dake cike da zuciyarshi ……Lokaci guda numfashinshi ya fara sarkewa hakoranshi suka fara,haduwa da juna !A Hankali ya fara maimaita kalmatusshahada sannan idonshi ya rufe ruf da guntun hawayen da ya gangaro……

   Inda ake aje Mankara Mai tafasa ta leka tare da cilla farin yadin tana fadin "Likafaninki da mankararki Hansai sun shirya "Sannan ta fada gidan Mai unguwar !Cikin Sa'a ta iske Hansai tayi goho tana damawa Shanu dussar ai kowa ta daddage ta maka mata sandar a baya……Kara ta kwalla tare da gantsarewa ta kife cikin dussar don ba karamin duka Maitafasa ta mata ba……
 
   Matan gidan suka nufo su dakyar suka rirrike Maitafasa da ta cigaba da kwadawa Hansai Sandar bayan ta kaita kasa ……Dakyar suka kwaci Sandar lokacin Hansai an jigatu jini ya wanke mata fuska hannunwanta kuma da take kare dukan sunyi sumtum dasu……
  "Ku barni na Kashe kafura tun kafin ta kashe man Ladona……"Mai tafasa ta fada tare da rarumar katun dutsi ta jefawa Hansai dake jan Kafa ta fada,bukkar Mai unguwa tana kwala mashi kira……

  Da yake matan gidan sun san abunda ke tsakanin Hansae da Maitafasa masu bata hakuri nayi masu turata nayi……
   Hawa take kamar fulawa ta cigaba da fadin "Wallahi ni da ke Hansai Allah kadae ya isa ya shiga tsakani don ko mijinki bai isa ba wallahi !Duniyar nan duk mai shirin kashe man Lado ta wallahi ni zan fara kashe shedani !Ni Uwar Mai tafasa Uwar Lado da ka taba Ladona kara ka kona mai unguwa da ranshi wallahi!

  Da Kyar suka samu ta bar gidan ta fita tana fadin "Wallahi sae na dawo kuma daga yau duk abunda ya samu Ladona sae na dawo na juyeshi a kanki banza bakar munafuka !Yo dake Hansai ba kara Kundum ba faran munafuka akanki baka…Banda jaraba har yanzu baki bar kishi ba dani bayan mijin yayi shekara sha biyar da rasuwa Hansai !Kiyi kishi da Buwale da Kande mana tunda yanzu mijinsu kike aure………"
   Da Haka har ta bar gidan ta shiga gidansu Lanto ta karbo Curin hura uku da nonon Goma ta nufo gida zata damawa Lado……

    Tana shiga gidan ta wuceshi ta dauko kwarya da koshiya ta fito ta zauna tana fadin "Su Ladona bacci aka samu ?
    Shirun da taji ne ya sata cigaba da damun furarta tana yar waka tare da daga murya tace "Wae Kundum lahiya kike shiru?Kundum dake zube tsakar daki bata san me ake ba ……

  Sae da ta gama damun Furar sannan ta matsa tana bubbuga shi tace "Ladona tashi ka kurbi fura sae ka cigaba da baccinka ko?

  Zaro idanu tayi ta wuntsilo ta dawo gefen da yake kallo ganin babu numfashi a tare dashi ta kanga kunnenta a hancinshi tana kiran sunanshi a rude tare da jijjigashi ……

  Kururuwa ta saki tare da dafe Kai tana kiran "Ladona" sannan tayi hanyar dakin Kundum tana kururuwar daya dawo da Kumdum daga duniyar doguwar sumarta……
    A Tare suka fito dakin ko wace ta kama hanyar gabanta ……

  Cikin lokaci Kadan gari ya gauraye da Rasuwar Malan lado yayin da Maitafasa ke kuka kamar zatayi hauka ! Duk wanda yaji rasuwar sae ya tausayawa Maitafasa saboda an san irin son da takewa Lado ……

  Likafanin da ta tanada don Hansai dashi aka nannade Ladonta !Maitafasa bata rage kukan da take ba sae da aka dawo rufo lado Limamin ya kirata yana fada mata cewa a kabarin Lado sun iske ruwa mai sanyi a kwance tare da goro fari kyal guda biyu a ciki ! Sannan ta sassauta kukan da take ……Gida ya cika da mutane har da wasu yan garuruwan amma Kauyen su Hafsuwalle basu san wainar da ake toyawa ba ……*HAJJA CE πŸ‘ˆ*
&
*FEEDOHMπŸ’ž*

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


       Page *47-48*


K'arama na bisa iccen mangoro Ard'o yazo wucewa Kallonta yayi ya kuma kallonta ganin ta kwantar da kanta jikin wani reshe tana kuka !har zai wuceta yaji ta bashi tausayi karo na farko tun tasowarta don yana da tabbacin bai tab'a gani K'arama a haka ba ……
   Sae da yayi Jim sannan yace "Hafsatu……"
  Kallonshi tayi ta rufe idonta kwallar dake ciki ya gangaro saman kuncinta ……

  Tausayinta yaji sossae ya saka hannu ya daukota ya dire ta k'asa yana tambayarta abunda aka mata ……

  Kasa magana tayi sae dae Hannunta da ta watsa alamum oho……
   Cikin kulawa yace "Wani ya dakeki ne Hafsatu?
  A Hankali tace "Kai ni Bansani ba Ard'o……"

 Gyada kai kawae yayi ya wuceta ya shiga gida !har zaya wuce ta gaban Bukkar Hafsuwallen sae ya kasa !wani bangaren na zuciyarshi na kwad'aita mashi ganin Hafsuwallenshi yayin da Tausayi da Kaunar da yake mata ya tsaya mashi a zuciya !A Sanyaye ya tsaya daga bakin Kofar ya kira sunanta "Hafsatu……"
 
,,Da Sauri ta fito don tabbatar da ko Ard'on ne ke kiranta kowa gizo muryashi take mata ……Ganinshi ya sata zubewa gabanshi tana goge hawayen farin cikin da suka zubo mata ……

  Kau da Kai yayi yace "Hafsatu ya na ga Hafsatu K'arama cikin damuwa shin ko wani abu ke faruwa ne ?
 
  Girgiza kai tayi tace "Babu Abunda ke faruwa Ard'o" muryarta na rawa……

   Kallonta yake cike da tausayi tayi bak'i ta jeme kamar ba diyarshi ba !anya ya mata adalci a matsayinshi na Uba?Cikin tausayi yace "Ki je ki daukota Hafsatu Idan yunwa take ji ki shiga cikin bukkata ki dauko fura ki bata na yarje maki Hafsatu……"
   
   Kallonshi take ya dawo mata Ard'onta mai kaunarta……Ta Girgiza kai tana share hawaye tare da murmushi lokaci guda tana kallonshi har ya nufi Bukkar Zulai……Sanan ta mike ta dauko mayafinta ta fita neman K'arama……

     Bakin iccen ta ganta jingine tana dafe da kanta kiranta tayi amma bata amsa ba haka bata dago ta kalleta ba ……Har sae da ta zo kusa da ita ta dafa bayanta sannan ta kalleta tare da fashewa da wani irin kuka !

  "Me aka maki K'arama?Ta fada a hankali tana kallon jikinta da ke kyarma ……
 
    "Baffa Ummana !ance baran sake ganinshi ba "ta fada tare da rungumeta……
 
  Cikin sauri tace "Waya fada maki K'arama?
 
   Kai tsaye tace "Yar Kudundub'a ce !
Girgiza kai tayi duk da gabanta dake fad'uwa tace "Wacece Yar kudundub'a? Karya take maki Ko jiya ba kinga Baffan naki ba?
 
  Shiru K'arama tayi tana kallon Umman kafin ta jata da karfin kamar ba ita ba ta nufi Hanyar garinsu Lado!Duk Yarda Umnan taso ta ki zuwa amma ta kasa !har sae da suka isa bakin garin sannan gabanta ya tsananta fad'uwa!Hango mutane a kofar gidan ya tabbatar mata da zancen K'arama……Yayin da taja ta turje bakin wani katon icce tana kuka mara sauti ……

   K'arama na ganin ta tsaya ta saki hannunta ta nufi cikin gidan har lokacin hawaye ke kwance a fuskarta !Kusa da Maitafasa ta rab'a ta zauna tana kallonta Kamar yarda maitafasar ta tsareta da ido tana jan majina ……

  Hannun K'arama Maitafasa ta kamo sannan ta mike ta tsaye ta fashe da kuka tana fadin "Indae ba Hansae ba to Wannan yarinyar ta Kama Ladona"
 
   Maganganu mutanen dake cikin gidan suka fara k'asa k'asa kafin Kundum dake ta cije lebe tana son tayi magana amma tana tsoron Abunda ya faru ya sake faruwa!daurewa tayi tace "K'arama ko shegiy……"Maganar ta makale yayin da ta hadiye miyan tsoro tana murje idanu……

  Kukan Maitafasa ya tsananta tace "Dan Allah Hafsatu K'arama indae har kinsan ke kika cinye man Lado ki taimaka ki fad'a man a tonoshi ki tsallakeshi ya tashi !wallahi ina son Ladona kamar raina ki taimaka man yar nan na tuba ki yafe man ……" jan majina tayi sannan ta kara da cewa "Ni Maitafasa ban tab'a ganin munafuka mai son raba uwa da d'a ba irin……"ta kuma yin shiru tana kallon K'aramar sannan tace "Na Tuba Hafsatu……"

  Girgiza kai K'arama tayi ta rungume Maitafasa da sauri yayin da Maitafasar ta fara kokarin tureta amma taki Sakita sae Uban kukan da takeyi……


《》 《》《》《》

  Ma'aruf kam yana kokarin bawa Sumayya hakkinta soyayya yake nuna mata dae dae gwargado dan ma wani lokacin rawar kanta na bata mashi rai !Ga Uwa uba rashin sirri duk wanda ya shigo gidan sae ta bashi labarin rayuwar da suke ……Yau ma kamar kullun ya shigo gidan ya iske Beebah kawarta zaune suna fira a falo ……

  Shigowarshi bata sanya Sumayya daina fadin "Ke wallahi Beeba Aure dadi gareshi !ke ni fa yanzu bana kwana bisa pillow sae dae bisa kirjin mijina ……Kin san me yafi birgeni a jikin Ya Ma'aruf?

   Beeba ta girgiza kai yayin da kirjinta ke dukan uku uku don tunda take bata tab'a ganin Ma'aruf ba sae a hoto sae kuma yau !don ko da akayi bikin Sumayya bata kasar sae dae friends dinsu dake ba da labarin kyawunshi……

  Yar Dariya Sumayyar tayi sanna ta mike ta nufi Ma'aruf din tana fadin "Wallahi kawata gashin da ke kwance a kirjinshi shi yafi birgeni sae sajenshi ……Ke bari dae in dawo akwae chapter……" Amsar jikkar dake hannunshi tayi ya mika mata fuska a daure ba tare da ya kalli Kawarta ba

  Kissi ta kai mashi a check dinshi sannan ta rugumeshi tana fad'in "I've Missed your warmety "Sake daure fuska yayi ya wuceta ……Itakam Beeba binshi tayi da kallo har suka rufo kofa sannan ta saki ajiyar zuciya tare da waro yan mitsi mitsin idanunta waje kafin ta dauki wayar Sumayya dake aje bisa hannun kujera tana dubawa ……

   Suna Shiga daki ya watsa mata harara yana cire Coat dinshi !Murmushi tayi sannan ta bude fridge din dake cikin d'akin ta dauko hollandia ta zuba mashi a cup tana fad'in "Welcome Oga……"

  Karba yayi ya kurba tare da zama saman kujera yana fadin "Me ke damunki ne Sumayya?
 
Bisa cinyarshi ta zauna tana fadin "Me nayi kuma Ya Ma'aruf"

Sae da lumshe ido sannan yace "Kin cika surutu Sumayya mara amfani sannan baki da sirrin mijinki Sumayya!menene na fad'awa K'awa irin wad'an nan maganganun?

  Zunburo baki tayi tace "Laifine don na yaba k'yawun mijina a gaban kawata?

  Girgiza kai yayi hadi da tabe baki yace "A'a ki cigaba"
Shiru tayi tana kissing wuyanshi !ya tureta a hankali yace "am Hungry……!

  Nan da nan ta b'ata Fuska tana fad'in "Ai Laifin Madre ne sae da nace ta samo mana mai aiki amma shiru har yanzu bata samo ba kuma yau ko Lunch ba aiko mana dashi ba……Sae dae mu ci Cake da coke"

  Wani wawan kallo ya watsa mata yace "Ke meye amfaninki "
 
  Tayi Fari da idanu tace "Na Kula da Kai na tarairayeka kadae !idan an gama abinci nayi feeding dinka da hannuna……"
 
 Tab'e Baki yayi yace "Amma ke bara ki iya dafawa ba?

  Shiru tayi tana turo baki sannan tace "Amma Ya Ma'aruf na maka kama da matan dake girki dan Allah?

   Girgiza mata kai yayi ya mike ya dauki Keys dinshi ya fita har lokacin Beeba na zaune inda suka barta tana ganinshi ta mike tana gyara siket dinta tace "Barka da fitowa Sir"

  Kallo daya ya mata ya kauda kai ya fita tare da daga mata hannu dai dai lokacin Sumayya ta fito tana fadin "Sorry Beeba na barki ke kad'ae wallahi rikeni yayi wae dole sae yaji dumin jikina !Kinsan Ya Ma'aruf da soyayya kawae sae ya fara kissing dina…… yanzu ma da kyar na samu ya barni don sae da nace Ina Son ice cream sannan ya fita ya sawo man wallahi Beeba ya iya tattalin mace……"

  Watsa mata harara Beeba tayi tana fad'in "Ke kau kinji dadinki kawata !Bara nazo na wuce gida !

  Cikin Sauri Sumayya tace "A'a dan Allah ki bari ya dawo ki dauki course yarda ake bawa Amarya abinci ……"ta karashe maganar tana dariya kasa kasa
 
  Uwar Harara Beeba ta sake mata ta k'asan ido tana yatsina fuska sannan ta fizgi handbag d'inta tayi gaba tana fad'in "Ina da aikin yi Baby ……"*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
&
*FEEDOHMπŸ’ž*

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


_Sakwan gaisuwa da godiya gareku masoya *ABINDA KE B'OYE* hak'ika bazamu iya lissafuku ba domin kunada yawa sosai sai dai muce Allah yabar kauna da soyayya_😘


     Page *49-50*


   *K*afin ya dawo Sumayya ta kuma gyara jikinta na instating dana shafawa duk tayi tana zaune zaman jiranshi, yana shigowa hannun shi rik'e da ledoji guda uku yashigo yaganta daga ita sai pant da bra irin bikini d'in nan pink color suna had'a idanuwa yayi saurin d'auke kanshi ya shiga kitchen direct ya wuce coffee machine ya tsiyaya sannan yayi toasting bread ya d'ora saman plat, yana kokarin juye farfesun naman ragon da ya siya sai gata ta shigo k'irjin shi har bugawa yayi sabida yasan indai tayi wannan iskancin shigar toh tana buk'atar shi, shi kuma wahalar da yake shane yasa har tsoran ganinta yake a haka....,

"Welcome Oga my." Sumayya ta fad'a bayan ta shigo cikin kitchen d'in tana lasar lips d'inta na sama tare da cizan na k'asan tana kashe mai ido d'aya.

Ta bayan shi ta ringume shi yayi saurin janye jikin shi daga nata yana yatsina fusa cikin sanyin muryar shi yace "please Sumy leave me along, na gaya miki am feeling hungry, kin kasa neman mun abinda zanci nazo ina had'awa ke kuma kina kokarin takura min please easy to me..."

Bata wani ji haushin maganar shi ba sai ma kokarin karb'an boul d'in hannunshi da take tana faman kashe mai ido,dole ba yadda zai yi ya bata suka k'arasa zuwa dining area ta ajiye mai. Zama yayi sai faman had'e rai yake amma tak'i yin zuciya sai ma zama tayi akan jinyar shi tana kwantowa jikin shi, cikin b'acin rai dama ga yinwa ya daka mata tsawa.

"Can you get up me Sumayya or easel..? *!* baki ta turo mai bayan ta d'aga shi sannan taja one chear ta zauna tana shagwab'e mai fuska tamkar wata k'aramar baby.

Ganin ya fara ci ba tare da yayi mata tayi ba yasa itama ta koma kitchen ta d'akko spoon,dawowa tayi tasa suka ci tare still yak'i sakar bama fuska, "Oga my muje ka huta I know kaji a office sosai." Sumayya ta fad'a tana karkad'a kafanta idanunta na kallon na Ma'aruf.

"No *!* nagode ina da aikin da zanyi yanzu na office cos ina son komawa gwadabniya duba peitents d'in nan." Yana gama fad'a yabar gurin tare da komawa bedroom. Kayan jikin shi ya cire ya zamana daga shi sai boxer da best Sumayya ta k'araso cikin salon jan hankali ya kauda kai tamkar be ganta ba harta k'arasa gurin shi tare da mak'alo shi ta baya.

"Dan Allah Sumayya ki...." Bata bari ya k'arasa magana ba tayi saurin zura bakinta cikin nashi domin feeling's d'in jikinta yayi over sabida magungunan data narka daga fitarshi. Ma'aruf kam ba yadda zai yi dole ya biye mata sai dai yana mamakin yadda ita kwata-kwata bata gajiya da harkar ta zama tamkar wata zakanya irin wanda suka fito farautar nan.

Da kyar ya kwaci kanshi a gurinta bayan tun yanayi yana jin dad'i har abun ya fita a ranshi yayi shigewar shi bathroom, tsananin mamaki yasa shi kasa tunanin komai haka yaji brain d'in shi tayi d'if sabida yadda Sumy take.yana gamawa ya fito jikin shi d'aure da towel itakam tana kwance cikin blanket tana hangoshi taji tamkar basu yi komai ba, k'arasawa tayi gurin shi tare da rarumar shi cikin hanzari yayi saurin shiyawa yabar gidan sabida ya kasa gane inda jarabar Sumayya zata kaishi tamkar wani inji. A haka rayuwar su ta cigaba da tafiya Ma'aruf na kokarin ganin ya sauke duk wani hakkin sumayya dake kanshi......,

Bayan sati d'aya yana kwance yayi ruf da ciki,gaban shi kuma laptop ce yana aiki a ciki ya bada duk wani nutsuwar shi akai. Sumayya kwance a gefen shi duk ta kanainaye shi cikin rud'ani ta mik'e a rud'e tana toshe bakinta da gudu tayi hanyar toilet,be mik'e ba yabita da kallo tare da gir-gixa ya mai da hamkali wajan aikin shi. A hankali kunuwan shi suka dinga jiyo mai tana yinkurin amai baki d'aya ta gama gala b'aita yayi sarin zuwa tareda tallabo ta zuwa jikin shi,sosai ya tausaya mata hakan kuma ya tabbatar mai da cewar ciki ne da ita.

Jikinta ya gyara mata sannan ya sanya mata doguwar riga sai faman narke mai take a haka ya tafi da ita asibiti.suna zuwa gwajin farko ya tabbatar da cikin ta 4 month's, sosai Ma'aruf yayi farin ciki sai dai ya kasa nuna mata sabida karta kuma narke mai. Tunda ya tsaida motan tayi saurin fita zuwa sashen Madre cikin karad'i ta dinga kiran sunan ta Madre! Madre!! Madre!!!... Tayi upstairs da gudu cikin zumud'i tana zuwa ta fad'a jikin ta tare da kankameta ba kunya Madre tace,

"Lafiya Sumayya kike irin wannan murnar? Madre ta fad'a tana rik'e da kafad'ar Sumayya wacce bakinta yaki rifuwa, idanta kyar cikin na Madre take fad'in.

"Madre am pregnant!,wallahi yau four months kenan Madre." Ta kuma kankame ta, Madre ta zaro ido cikin mamaki, Ma'aruf dake kokarin shigowa yayi cak!,yana jin kalmar da Sumayya ta fad'a a hankali ya juya cikin takaici ya koma downstairs yana jin wani bak'in ciki a zuciyar shi.

"Why Matar shi bata da sirri ne a rayuwar ta? Me yasa take son fallasa duk wani sirrin su, bata jin kunya ciki har da mahaifiyar shi? Demit....!


*《》 《》《》《》*

K'ara k'ank'ame Maitafasa k'arama tayi tamkar zata shige cikin ta, tsoro da bak'in ciki suka had'u suka yiwa Maitafasa tayi saurin ture k'arama daga jikinta tana fece majina idanuwanta sunyi jawar tayi hanyar da girken dabbobinta ke gurin, wani dogon ice ta d'auka tayi kan k'arama dashi karaf ta sauke dukan jikin Hafsatuwalle wadda ta k'araso gurin da saurinta.

"Wallahi tallahin Allah sai taci na jaki, yau yarinyar nan baxata kwana ba sai tabi ladona inda takai shi.." Maitafasa ta fad'a tana k'ara dokawa Hafsatuwalle icen hannunta.

Da sauri mutane suka rufar musu Umma na kuka ta kare k'arama da hannunta wadda ke faman ture Umman tata amma tak'i sakinta, isowar mutane yasa Umma mik'ewa da sauri taja hannun k'arama suka sa gudu amma duk da haka mutanen kyauyan basu dena binsu da duka ba k'arama na cizon Umma dan ta sake ta amma taki gurin har fashewa yayi amma tak'i sakinta sai da suka dangana da kauyan su.

Da guru tashiga cikin bukar su tana kankame k'arama take mata wani razananan kallo tamkar wata kura, da kakkausar murya tace "Umma ki sakeni nace... *!*."

Muryar su jummai ce ta k'atse Umma dake shirin yiwa k'arama magana. "Wallahi yau sai kun fito daga cikin d'akin nan, sabida kar asirinku ya tonu shine an samu lado ya warke zai fad'i gaskiya shine 'yar kaniyar maiyyar 'yarki taje ta cinye kurwarshi, toh wallahi k'aryar ku ta kare cikin gidanga...." Baki d'aya mutanen gidan dana kyauyan su lado suka amsa da kwarai kuwa wallahi....

Ard'o ne ya shigo a rud'e ganin gugun mutane yasa shi k'arasawa gurin yana tambaya. "Yo meye kuwa Ard'o, banda shegiyar yarinyar nan da aka kafe cikin gidan nan tana ta iskancin da take so... *!* toh yau maitar tata tafara aiki dan taje ta cinye kurwar lado sabida ya warke zai fad'i gaskiya...."

Zulai ta fad'a tana cillara hannu sama tare da dukan cinyar ta idanuwanta har kankancewa suke sabida jaraba tamkar ita akayiwa rasuwar. Su Maitafasa ne suka k'araso harda katuwar addar ta wadda ada lado yake zuwa farauta da ita, suna zuwa gida ya kuma kacamewa da tashin hankali a cikin gidan.

Lauratu na jikin bangon d'akinta sai rusar kuka take yi gashi sallau baya gidan ya tafi kasuwa. Inno ma tana tsaye bakin bukkarta tama rasa abin yi sai ido kawai da ta zuba musu.......

*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


_Wannan shafin nakune kyauta domin jin dad'in ku, hak'ika *hajjafeedohm* na alfahari daku grps d'in *Feedohm Novell'sπŸ’ž & Hajja ce πŸ‘ˆnovels grp* we so much love you people d'in dake ciki...._πŸ˜˜πŸ˜…


     Page *51-52*

*T*sawa Ard'o ya daka musu baki d'aya suka yi shiru,inno ma ta k'araso jikinta duk a sanyaye,lauratu kuwa kasa fitowa tayi sai faman kuka take cikin masifa Maitafasa ta kali Ard'o tana mai masifa.

"Kaji dallah can gafara kasa anyi shiru kayiwa mutane tsaye, inzaka yi magana Ard'o kayi kuma kasa mutanan nan su fito komu mushiga ta k'arfi ardun Allah." Mai-tafasa ta fad'i tana yi kamar zata makewa Ard'o fuska, nan da nan mutanen wajan suka suma hayani guru ya kuma kaurewa da maganganu da habaice-habaice.

Cikin bukar kuwa danbe ake sha tsakanin Umma da k'arama, cikin wani mugun kallo da k'arama kewa Ummanta ta kalleta tana huci numfashin ta tamkar ta tattaro ma al'umar garin ta had'a tace wa Umman ta "baza ki kyaleni bane?... *!* tallahin Allah aradu zan makeki na fita wallahi sai na rama dukan da akai miki, Umma ki rabu dani ki kyaleni ki kyaleni." Kalaman da k'arama keta gayawa Umman ta amma ta matseta sai faman naushin cikin ta take yi Umma na kuka sabida azabar zafin da takeji a cikin.

"Ya isa haka kowa yazo ya fita, kubar min yarinya ta ni yanzu na yadda cewar k'arama 'yar lado ce dan...." Ai basu bari ya k'arasa ba suka fara mai tufin Allah tsine inno sai sharar kwallah take domin cin zarafin yayi yawa Mai-tafasa tace, "Aradun Allah Ard'o yau ko kaine Mai-unguwa kace ka yadda k'arama jikar kace sai inda Allah ya barmu bare k'arama mayya ce tacinye min lado lokacin da nake murnar ladona ya warke, yau kama sai k'arama ta bakunci lahira..."

Nufar d'akin suka yi baki d'aya mutanan gurin, kafin kace me sun fito da Umma dake makure da k'arama a jikinta idanun Hafsatuwalle sunyi luhu-luhu sunyi jawur sabida azabar kuka da tashi amma na k'arama a suye sai wani kallon jummai take tana zaro manyan idanuwanta kafin ta tuntsire da dariya tamkar mahaukaciya sabuwar kamu tace "Ard'o kaga inna jummai yau da farau-farau d'in Tanimu tayi karin kumallo ana bashi ta karbe mai idan nayi karya ta bari a bud'e cikin agani..."

'Lahh kaji min shegiyar yarinya nima cinyeni take son yi dama tun data farka yau take kawo min hari Ashe dana fita karfi ne taje tacinye lado shine bata koshi ba take son had'awa dani yanzu na Shiga uku ni jummai Maman Gaddafi..." Mutane suka yi kan k'arama Ard'o da inno suka yi saurin karewa yayin da Umma ke durkushe a gurin ta rik'e cikinta da hannuta lokacin lauratu ta fito bayan ta gano shigowar sallau.....,


*《》 《》《》《》*

"Madre wallahi ni yanzu ban iya yin komai babyn nan yana wahalar dani amma Yaya Ma'ar yayi ta cewa bana kaza bana kaza, kuma nace ki samo min me aiki Madre kinki ni yanzu ya zanyi.. *!* gashi kasala ta kuma yi min yawa." Sumayya ta fad'a tana daga jikin Madre dake rik'e da mediceted glass d'in ta, cikin kulawa da nuna tattali Madre tace.

"Sorry Sumayya na fara bin cika miki, wadda aka samu d'in tana son yi amma 'yata na kwance ba lafiya amma nasa a kuma binciko miki wata me aikin nima ai at this stage zanso ki samu mai temaka miki da wasu abubuwan." Cikin sauri Sumayya ta kalli Madre tare da cewa.

"Yauwa Madre na! Toh yaushe za'a samo? Dan Summay yanzu bata aikin uban komai hatta wanke pant vest, da bra duk ta dena. Madre tayj murmushi tare da fad'in.

"Sai randa aka samu amma nace karya wuce cikin week d'in nan." Lokacin Ma'aruf ya shigo cikin gayun shi, wankan suit yayi white color yayi bala'in yin kyau ya k'arasa ciki tare da gaishe da Madre dake kallon shi cikin mamaki.

"Ma'aruf ina zuwa kuma haka...?!"

Sai daya sauke numfashi sannan ba tare da ya kalli inda suke ba yace "zan je na gano mutumin nan, ina son na tabbatar da ya samu komai hatta sana'ar da zai iya yana daga zaune so flate d'in 2:00pm zan bi." Ya fad'a tare da juyawa zai fita Madre na mishi addu'ar dawowa ita kuma Summaya tayi saurin bin bayanshi. A k'afar fita suka had'a ta matseshi ta baya tare da kissing d'in wuyan shi cikin shauk'i dan ba k'aramin kyau yayi mata ba har wani masifaffan kishi da sha'awar shi suka dirar mata at once.

"Sweetheart please kaje dani." Ta fad'a tana shafar wuyan shi, kallon mamaki yayi mata tare da kallon cikin jikin ta, a zuciyar shi addu'a yake Allah yasa kar babyn shi ya kwaso d'abi'un ta a fili kuma ya janyeta a jikin shi tare da shafar gefen fuskarta yace.

"Bye take care."

Da sauri ya shiga mota driver yaja suka fita yana jimamin halayyan sumayya da be san haka take ba sai bayan sunyi aure.

Yana sauka garin katsina aka had'a shi da guide sai focal person d'in shi suka nufi gwadabniya kauyan su malan lado, tun da suka fara dosar kauyan basu ga mutun ko d'aya ba hakan ya bawa Ma'aruf mamaki sai yaji duk babu dad'i yau ba'a biyo suba har suka je k'ofar gidan. Focal person d'in ya shiga cikin gidan amma tsit hakan yasa shi nufar d'akin da yasan lado na kwance amma shima ba kowa hakan ta dawo ya sanarwa da Ma'aruf,  "what did you said? Toh ina suka tafi baki d'ayan garin? Oh my God... *!*." Ma'aruf ya furta cikin mamaki.

"Mu k'arasa fadar Mai-unguwa wata kila mu asamu bayani." Cewar focal person d'in yana kallon Ma'aruf dake ta faman shafar kyakyawan quarter million d'in fuskar shi "ok." Ya fad'a tare da shiga cikin motar suka wuce kauyan su Hafsatuwalle mamaki fal zuciyar shi.

*《》 《》《》《》*

Da sauri ya k'arasa gurin ta yana tambayar "lauratuna lafiya kuwa? Kama hannuta yayi suka k'arasa gurin mutanan ko wanne da makami a hannunshi can ya hangi Mai-tafasa ga inno da Ard'o suna kare k'arama da Ummanta shima ya k'arasa gurin yana bada hakuri duk da cewar besan meke faruwa ba.

"Wallahi yau sai k'arama ta bi lado ba zasu sake kwana cikin gidan nan ba." Mai-tafasa ta fad'a tana kuka tamkar an mareta yayin da su jummai ma ke ta fad'a cikin karayar muyar inno tace.

"Kuyi hakuri indai k'arama ce da Hafsatuwalle zasu bar muku garin amma karku d'auki mataki akan kashe k'arama...."

"Su tashi subar gidan toh kafin mu kaddamar musu." Ard'o ya kalli inno yaga sai kuka take lallai yau yazama dole su Hafsatuwallen shi su bar garin idan ba haka ba aiyi musu aika aika ya juya yaga Umma sunkuye lauratu ta rik'o ta sai kuka suke yayin da k'arama ke zaune tana kwakular kasar gurin. A gaba suka tasa su mutane jingim Umma ta rik'e da k'arama sai tirjewa take yi akan sai ta saketa taje ta rama dukan da Mai-tafasa tayiwa Umma lauratu sai kuka take ganin ana  korar su da jifa da zage-zage har suka baro gidan suka nufi hanyar barin garin.

Jibgegiyar motar data doso ce ta sa suka tsaya tare da bin motar da kallo, gaban su ta karaso focal person yayi saurin mod'ewa Ma'aruf kofar ya fito cikin nutsuwa tare da karewa mutanan gurin kallo ciki harda Mai-unguwa da shima ya k'araso gurin ba jimawa, wani banzan kallo yake aikawa da Mai-ungawa wadda yasa shi muzurai da idanuwa...........,


*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


       Page *53-54*Kusa da Hafsuwalle ya k'arasa ganin jini a fuskarta a hankali ya tambayeta "Me ke faruwa anan?……Saboda ya lura ita kadae ke da sauran hankali a gurin ……

  Sunkuyar da kai tayi ba tare da tace komae ba sae kukan dake fita a hankali mai cin rai!Mai ungua ya k'araso kusa dashi yana fad'in "Ranka ya dade wallahi yanzu na k'araso na tarad da wannan hargitsin……"

  Kallo d'aya ya mashi ya watsar ya kuma tambayar Hafsuwalle me ke faruwa……K'arama ta ba shi amsa da "Wasan jifa suke da mutuwa shine Maitafasa ta jefe Ummana……"tare da saka hannu a aljihunshi ta fito da katuwar wayarshi da ta lek'o……

  Maitafasa tace "Bani guri buwalle na karashe shegen wasan jifan da tace anayi akan shedaniyar yarinyar can……!

  Wani sakaran kallo ya watsa! kafin yayi magana Mai'ungua ya ce "Yallabai rigima suke akan wannan yarinyar da kake gani!Da farkon fari yarinyar Shegiyace!Sannan Mayya ce!A Kakkabe a kare d'azu ta lashe kurwar Ubanta mutumin nan Malan Lado da ku ka san da zamanshi a fad'in kauyennan……"

  Dafe kanshi yayi yana maimata Inna lillahi wa inna ilahir raju'un!Idan ya fahimci maganar Mai ungua Malan lado ya rasu kenan!Mai tafasa ta katse mashi hanzari ta hanyar watsa mashi tafin hannunta a saman fuskarshi tana fad'in " Bani guri Bature !Ni maitafasa bana daukar iskanci aradun Allah!Kai din wofi baka isa ka hanani daukar mataki ba!Da k'warank'watsa Tunda har ta lashe man Lado to kai din banza baka isa ka hanani kasheta ……"

  Wawan Marin da ya zuba mata ya katse sauran Maganarta !Yayin da tayi baya ta hantsila ta fad'a jikin Kundum……Ji kake Tumm Kundum ta janye jikinta cikin mugunta tana cije baki……

  A fusace ya kalli Mai ungua yace "Ku iskeni gidan Hakimi yanzu!Sannan ya karbi wayarshi dake hannu K'arama ya kalli Hafsuwalle yace "Shiga mu je……"

  Babu Musu ta ja hannu K'arama guard ta bud'e mata motar suka shiga da kyar aka tada motar……
 
Inno kam Juyawa tayi gurin Ard'o cikin kuka tace "Ka gaza a matsayinka na maihafin Hafsatu Ard'o!ka gaza gurin kula da hakkin da ya rataya a wuyanka,shin kana da wani abu da zaka fad'awa ubangijin da ya baka Hafsatu na banzatar da rayuwarta da kayi? ko kana tunanin Allah bara ya tambayeka akan digon hawayen Hafsuwalle bane!Baka yarda da tarbiyyar diyarka bace ?ko ko Hafsatu ba jininka bace da ka wofintar da ita a idon duniya!Duk abunda ya samu Hafsuwalle ka raba biyu ka dauki kaso daya Ard'o kaine sila da ka kasa warware komae……!A  Hankali ta juya ta kama hannun Lauratu suka shige gida……Ard'o kam tsaye yayi ya kasa koda motsi……

  Kallo d'aya zaka ma Mai'ungua ka gane yana cikin rud'u a sukwane ya kalli Mai tafasa yace "Shi kenan kun janyo mana bala'i Maitafasa!Aradun Allah kafin kice komae a gaban Hakimi sae kinsha tsumagiyar dukan da kikayi masu…"
 
Cikin sauri tace "Ni kam na yafe Ladona!Mai ungua kaje kace masu suyi hakuri wallahi na tuba!Ni shegiya inje gaban hakimi inci ubana……"

  Kundum ta taba hannu tana fad'in"A A Maitafasa ke da kike neman kudin zuwa birni k'arar Hafsuwalle! Yau kuma kin samu dama ki ce bara ki je ba……"

  Kukan kura tayi ta cakumi Kundum tana fad'in"Na Dade da sanin ke bakar munafuka ce dama Kundum!Gidan Uban wa nace maki ina son kai hafsuwalle birni k'ara?
 
 Kundum ma cakumar Maitafasa tayi suka kaure da nusar cikin juna yayin da yan garin ke fad'in"Gaskia Kundum ke ce baki da gaskia Yarda Maitafasa ta shiga wannan bala'in kuma ki kawo mata wata maganar……"

  Sakin Kundum din tayi ta watsawa mai maganar harara tace "Dalla gafara munafukai!Ba har daku aka dakesu ba……"

  "Da k'warank'watsa babu ruwana……"Cewar Bulawale yayin da ta tafi buguzum buguzum ta nufi hanyar komawa kauyensu ……Kafin kyaftawar ido matan garin duk sun sab'e an bar Maitafasa da Ard'o sae Mai unguwa dake tsaye kamar sakarae……

   Sae da Mai'ungua yawa Maitafasa jan Ido sannan ta yarda suka hawo mashin d'aya suka nufi birni yayin da Ard'o ya samu mai mashin shima ya bisu……

  Gidan Hakimi suka nufa acan suka iske Hafsuwalle da K'arama zaune cikin fada ……
 
  Guri suka samu suka rakub'e kafin Hakimi ya shigo!Maitafasa ta rarrafa kusa da hafsuwalle tace "Hafsuwalle baki ji kunyar zama shari'a da ni Maitafasa ba?Haba Hafsuwalle tuno lokacin da kike Amaryar Ladona!Ni ce Zabbi!Ni ce Fura!Ni ce manshanu!Haba Hafsuwalle mu sasanta tun kafin naji tsumagiya a gadon bayana……"

  Karaf K'arama tace"Idan ta tuna lokacin da kika kwala mata k'ota fa……"

  Kafin tayi Magana Hakimi ya shigo tare da Ma'aruf suka zauna dae dae lokacin da Ard'o shima ya shigo ya zube ya kwashi gaisuwa sannan ya kuma ya rakub'e a bango!Maitafasa kam banda mazurai da soshe soshen karya babu abunda take !

 Mai ungua aka nema yayi bayani !Da kyar ya bayar da labarin tun daga farkon rikicin har karshe sae kame kame yake shima yanayi Maifasa na fad'in "Wutarka daban dake Mai unguwa" "Yaushe nace K'arama ta cinye Lado……?ko kuma tace" Allah ya had'a Munafuki da warin kabari……"

  Sae da dogari ya kwatsa mata tsawa sannan ta kama bakinta……
 
   Hakimi ya tambayi "Wanene Uban Marigayin?
 Mai unguwa yace "Mahaifinshi ya rasu sae dae nine matsayin Ubanshi ranka ya dad'e……"
 
  Hakimi ya kallesu d'aya bayan d'aya yace"Wacece Uwar marigayin?

   Zumbur Maitafasa ta mike tana fad'in "Gani anan Ranka ya dade!Matsowa zanyi ne koko kai zaka matso yarda zaka ganeni……"Mai ungua ya janyota ta zauna ……

 Hakimi yace "Ina Mahaifin Hafsatu?

Ard'o ya kalli Hakimin sae dae bakinshi ya masa nauyin amsa sunan Mahaifinta!Shi Hafsuwallen ta kalla hawaye na zuba a idonta ta nunashi da hannu……
 
A Hankali yace "Nine Mahaifinta kafin na zubar da k'imata saboda zancen mutane……"

  Tambayar Maitafasa akayi ko gaskia Mai ungua ya fad'a amma ta karyata rabi da kwatar zancenshi !illa iyaka ta yarda da cewa K'arama ba jikarta ba ce !

 Hafsuwalle kam iyakar gaskiyarta ta fad'a cewa K'arama diyar Ladoce !Shi kanshi Hakimin baya da hujjar da zai karbi zancen Hafsuwallen ko na Maitafasa……

   Ma'aruf kam shiru yayi yana jin dramarsu yayin da yake Kallan K'arama dake harkan gabanta har da su dariya!Sae da taji Maitafasa na fad'in "Da kwarankwatsa ta fad'o mata yanzu bata ce K'arama ta cinye lado ba……"

  Sannan ta kwasa da gudu ta fad'a gidan Hakimin tana fad'in "Aiko zata fad'o maki yanzu……"

  A Cikin gidan ne ta kalli cikin matar Hakimi ta kece da dariya tana fad'in "Yan birni harda ganyen ciyawa suke ci……"
 
 Daga farkon Matar Hakimin banza ta mata Sae da K'aramar ya janyo hannunta tana fad'in"Baku da tuwo ne kika ci ganye da wake?

  Harara ta watsa mata don ta saba ganin y'an kauye irin haka……Ita kam K'arama binta tayi har kitchen tana fad'in"Jiya kinci Nama da Ankaha yau kuma kinci Ganye da wake shin baku da tuwone ku?Ga yan cikinki duk sun harde guri guda……!

  Matar Hakimi ta kwala ihu yayin da dogari ya shigo da sauri ta fad'a mashi abunda ya faru ya kuwa kama K'arama da kyar ya maidata fada ya fad'awa Hakimi abunda tace ……

  Nanne Maitafasa ta rafka gud'a tace "Ahayye yanzu kam na amsa Nace Mayya ce tunda har tayi ma Matarka……"ta karashe maganar tare da watsa Hannu……

  Hakimi cewa yayi shirman yara ne a kyaleta amma Maitafasa tayi karab tace "K'arama meye a Cikin Hakimi……"

  Cikin rashin Damuwa ta kalli tukeken cikinshi tace " Ni dae wake na gani da wani abu kamar tuwo amma ba tuwo bane……!Aikam Hakimi ya fara mazurai tare da kare cikinshi da hannu ……

  K'arama ta kalli Maitafasa ta kwashe dariya harda tab'a hannu tace"Ke kam Maitafasa banda Tafasa da Zawo a gefe babu abunda nagani……!

  Dariya Ma'aruf ya sake mai sauti ganin abun yake kamar shirme sae da juyo tace mashi "Kaine kad'ae kasha Madarar shanu!

   Kafe ta da ido yayi !Hakimi kam cewa yayi a kira sarkin Mayu yanzu !Cikin mintina kadan Sarkin Mayu ya iso akace ya dubata ko Mayya ce……Duk binciken da yayi ya tabbatar masu da babu Maita illa iyaka Aljanu suka bude mata ido!

Cikin Hikima Hakimi ya neme ya masu sasanci su koma gida sanna yayi wa Ard'o magana akan banzatar da ita da yayi ya nuna masu koda ace K'arama ba diya Lado bace bai kamata su mata haka ba balle Hafsuwalle da auren sannan tsakanin Miji da mata sae Allah!Kuma yanzu babu wanda ya isa ya warware wannan matsalar sae Ubangiji su tafi Allah zai fito da *ABUNDA KE B'OYE* Sannan Maganar K'arama Mayyace bata taso ba tunda ance Aljanune shi yayi alkawari zai sama mata magani har ta warke ……Maganar sakin da Maitafasa tayi wa Hafsuwalle bata taso ba tunda ba Lado ya saketa ba !ta koma gida tayi wa mijinta ta kaba……

  Maitafasa kam datsewa tayi ta fara yayyafa ruwan tijara wae karyane kawae ana so arufe maganar ne ita kam ta rigaya ta saki Hafsuwalle kuma bata da gadon Ladonta!K'arama mayya ce kuma yanzu ta ce ita ta cinye mata Lado babu wasu aljanu don haka dole a bi mata Hakkinta!Sam ta manta gaban Hakimi take yayin da take watsa hannu tana mayarwa tare da girgiza kai……

  Sae da Hakimi yace a mata bulala Goma sannan tayi shiru tana zare ido !Tana ganin za'a daketa ta tuno da lokacin da akayi k'arar Dan gidan Mati a kauyensu gurin mai unguwa……Yaron ya dage yawa Mai unguwa dukan tsiya akace aljanune……Don haka ta saki duwawu ta fara banka Tusa da harba kafafu tana d'aga hannu sama……*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
&
*FEEDOHMπŸ’ž*


πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*         Page *57-58*    Maitafasa Kam da yake machine daya suka hawo da Mai'ungua tunda suka taho take ta ruwan bala'i kamar shi ya daketa……Munafuki kam da yana tsiru da ya fito a goshinshi!sae da suka shigo daji sossae sannan tayi wani uban juyi ta tik'oshi kasa!Mai machine ya yi niyyar tsaya tace "Bar shege hannun nashi a bujena yana lalubata kuma ba miji na bane!
 
 Mai machine ya gyad'a kai yace "Allah ya kyauta ai wasu mazan yan iska ne"

  Banza ta mashi tare da gantsare baya tana cije baki!Yayin da ta kullafi dukkan mutanen kauyen!kuma tasha ALWASHIN duk shegen da take bi bashi sae ya biyata yau ko da kuwa uwarsa zai saida……!Sannan gaba da Hafsuwalle kam yanzu ta fara tunda sanadinta ne aka kai birni aka daketa……

  A Haka har Mai machine ya shigo kauyen ya tambayeta inda zaya ajeta ta nuna mashi kofar gidan mai ungua da hannu!Tana sauka ta kama hanya zata shiga gida……

  "Inna kud'in fa?mai machine ya tambaya……

Hannu ta watsa tana fad'in "Kai yaro ba wani Inna!sunana Hansai……Idan na shiga zan turo yaro ya kawo maka!idan na manta kuma ka turo yaro kace Hansai ta baka kudin babur d'inka……"

  Gyad'a kai mai machine yayi !Yayin da tashige abunta tana watsa hannu !ta wani sird'ad'e dake gefen zauren gidan ta fita daga gidan ba tare da ta shiga ciki ba!ta sulale ta nufi gidanta……

  Tsakar gida ta iske kundum na surfe !kallo daya ta mata ta watsar ta rafka gud'a tana fad'in "Ayyiriri!Bakaken munafukai masu hakuran shanu ga Mai tafasa ta dawo da ranta!

   Dariya Kundum ta saki itama ta rafka shewa tana fad'in" Ahayye!Maraba da Maitafasa ga ruwan zafi can a gasa duwawu……"

  Tab'a hannu tayi da niyar watsawa a fuskar Kundum!tayi saurin janyewa da ta tuna marin da watsa hannun ya ja mata!lokaci guda ta saki tsaki tana fad'in "Yo Ruwan zafi haihuwa nayi algunguma?

  "Ko baki haihu ba jamammun idanunki sun nuna kinsha dan banzan duka Mai tafasa……"Cewar Kundum tare da tilla tabarya sama ta cabke tana dariya……

  "Sakarai ake duka a zauna lahiya Kundum!Mai tafasa kam tafi karfin bugu a birni!sae dae buga in buga!Yo banda lalataccen mai mashin da ya turbude ni k'asa ai wallahi da baki ga walle na ba har ki ce duka na akayi……" Mai tafasar ta fad'a tayi gurin Bukkarta……Kundum kam shewa ta dauka kamar babu gobe! Don ta san shegiyar karyar Mai tafasa……

 Mai machine kam yayi tsayuwar kusan rabin awa sannan ya taka da kanshi ya leka ya kwad'a sallama!Wani yaro ya leko yana tambayar wanene……Yace "Je kace Hansai ta bayar da kudin mana"

  Yaro ya koma ya fad'awa Hansai dake cikin garka tana shara!Ta rafka uwar ashar ta fito daure da daurin kirji ta tsaya gaban mai machine ta gantsaro kirji tana fad'in"Kace Hansai ta maka me?

  "Kud'in machine" ya fada a taikaice……
"Gidan uban wa na hawo maka babur……? ta tambaya had'e da turo kallabi gaban goshi……

  Da yake yana da sauran hankali yace "Kiyi hakuri bake ba Inna !wadda ta shigo d'azu nake nufi……"

  Yayyafa ruwan tijara ta fara tana watsa hannu !ganin zata tara mashi mutane ya sashi jan machine dinshi ya fita tare da Allah wadaran da halin mutanen garin……

  A Hanya ya gamu da Mai ungua yana tsayar dashi amma ya watsar ya zagayeshi ya tafi abunshi!Shi kam baya tunanin zai kuma zuwa wannan sakaran kauyen har abada……

  Hafsuwalle Kam mashi na suka hawo kowa da nashi ita da Ard'o har kofar gidansu sannan Ard'on ya biya kudin suka shiga ciki!Sababbun suna tsaitsaye tsakar gida suna jiran bayani……
  "An kasheta……" Cewar Zulai tare da tab'a hannu sama……

Banza Ard'o yayi mata sannan ya aiki Jummai ta kira Inno dake dakin Lauratu tana bata baki!A tare suka fito da lauratun yayin da tayi gurin Hafsuwalle tana tambayarta ina K'arama……

  Kamar daga sama taji Ard'o na fad'in "Tana birni Lauratu"

   A Rude take tambayar me yasa aka barota……Ard'on ya tsaya ya masu bayani sossae akan abunda ya faru !sannan ya fada masu K'arama ba mayya bace aljanu suka shafeta sannan ya fada masu tana can za'a nema mata magani!Wasu matan sun yarda da zancenshi yayin da tsirarru daga gidan suka karkade kunnuwa alamun karya ne!

  Daga karshe ya masu gargadi da kakkausan murya akan Hafsuwalle tare da tatabbatar da rayuwa mai iganci a gidan ubanta……
  Zulai kasa hakuri tayi tace "Shin Ard'o ya batun yake waye uban K'arama ko har yanzu Hafsuwallen bata fad'a ba"

 "Ni ne Uban K'arama daga rana irin ta yau……"Cewar Sallau da ya shigo lokacin……

  Duka yan gidan suka juya suna kallonshi yayin da Ard'o ya gyada kai ya wucesu ya nufi gurin Hafsuwalle dake tsaye ta sadda kai ……Hannunta ya kama ya kaita har bakin Bukkar Inno yana fad'in "Kiyi rayuwa mai inganci diyata !Ni Ard'o na kaunaceki Hafsatu……!

  Zulai kam kusa da Jummai ta matsa tana fad'in "Ko dae Sallau ne Uban K'arama na gaskia!

  Murya k'asa k'asa Jummai tace "Wa ya sanar masu!

   Baraka ta amshe "Haba ki duba yatsun kafafunsu kusan iri daya dana sallau fa!
  Ba haggun salati suka rafka baki daya tare da rufe bakunansu ganin hankalin su Sallau ya dawo gurinsu ……
Sannan suka rankaya suka nufi bukkar Zulai baki d'ayansu……

 
《》《》《》

 Beebah na fita Sumayya ta dauki maganin ta nufi Toilet tana juyi!Na goran ta zuba kadan a buta tana fad'in "Bara nayi tsarkin sae nayi inserting wancen anjima na k'ara tsakin idan na zo zan cire……"

 Hanci ta kai ta sunsuna ta yatsina fuska jin warin daddawa "Dan bauchi……"ta fad'a tare da juyi tana ware hannaye……

  Duk'awa tayi tana tsarki hankali kwance sannan ta gutsuri curin kad'an ta saka ta mike!Rufe ido tayi gam jin kamar tayi tsarki da ruwan barkono……
 Karamin tsaki ta saki ta fita daga toilet din ta zauna baki gado har lokacin tana jin zafin na karuwa!Tun tana daurewa daga zaune har ta kai ga mikewa tsaye ta fara tsalle……Itakam bata jin zata iya cirewa don so take Ma'aruf ya jita kamar sabuwar Amarya……
  Cikin kankanin lokaci idonta yayi jawur ta mike ta kunna AC da fanka ta cire zaninta ta bude kafafu iska na shiga wae ko ta rage zafin……
   Kasa daurewa tayi ta fashe da kuka hadi da kiran number Beebah!ringing din farko beebah ta dauka tana fad'in"Yadae Sumy?

 Cikin kuka tace "Wallahi Beeba nayi inserting wannan abun sai shegen zafi!zan iya fidda wa yanzu tunda ya dade……"

  Murmushin mugunta ta saki tace "Haba Sumy!dama magani mai kyau a dole yayi zafi!ki daure ki bari sae anjima sannan……"

  K'ara fashewa da kuka tayi tace "Wallahi kamar na saka pepper aciki Beebah……"

  Tabe baki tayi tana wani sakaran murmushi tace "Da Farincikn ki k'ara na mijinka Sumy ki daure !dama kin san duk magani mai amfani dole yayi zafi……"

  Shiru tayi ta katse wayar!a hankali take kuka tana mirgina saman rug d'in tare da tura hannunta cikin pant!ganin abun bana wasa bane ta mike da gudu ta nufi toilet tana kuka har da majina zata cire taga duk ya nake a ciki!kad'an kad'an ta fara fitar wa sannan fad'a cikin ruwan sanyi ta zauna sauran ya cigaba da biyo ruwan yana fitowa……

  Tafi awa daya cikin ruwan sannan ta fito ta daura towel ta rashe tsakar dakin ta ware kafafu iska na shigarta……

   Wajen karfe 7:46pm taji  Mai gadi na bude gate ta mike  tana share hawaye!kamar mara lafiya take taka kafafunta saboda azabar zafi……riga ta saka doguwa ta fita falon tana jiranshi……

   Da Sallama ya shigo d'auke da K'arama a kafad'a ta tayi bacci!Waro ido tayi tana fad'in "Ya Ma'aruf me yasa ka dauko Ihsan dan Allah……"

  Shiru ya mata ya kwantar da K'arama bisa kujera sannan ya kalleta ya kalli K'arama dake minshari yace "Ba Ihsan bace……"

  Ware ido tayi sossae tana kallon K'arama sannan ta kece da dariya tace "Ina ka samo wannan abun haka?Lallae Ya Ma'aruf rufe maka ido akayi ka dauko wannan dattin a kafadarka……"

  "Huh……" ya fada sannan ya zauna yana fito da wayarshi……

  "Ka man magana man ina ka samota?

  "Kauyensu……" ya fada lokacin da yayi dialing number Madre

   "Wannan ai barata iya wani aiki ba Ya Ma'aruf gaskia a canzo wata……"ta fad'a cikin salon shagwab'a

"Na Sani" ya fad'a a takaice……
 
 Zata sake magana taji yana gayar da Madre cikin waya!tare da fad'a mata ya dawo kuma dauko wata yarinya amma gobe zai zo ya mata bayani……

  Bata san me Madre d tace ba sae dae taga yayi murmushi tare da yanke wayar……
  Harara ta watsa mashi tana fad'in "Kaman bayani mana inda ka samo wannan yarinya tunda kace ba yar aiki bace ……"

  Cikin sanyin Murya yace "Wae Sumayya baki iya tarbar miji bane?Na dawo ba tambayar ya hanya!ba ruwa amma kin sani gaba sae maganganu kike?

   Zunbura baki tayi ta nufi kitchen ta hado mashi tea ta d'auko bread ta zo ta aje gabanshi……Ware Ido yayi yana kallon Tea da bread din sanasn ya daga ido ya kalleta ya mayar da idonshi ga K'arama dake ta jan minshira ya mike "Ko ni Maye ne Baran ci wannan abun ba Sumayya……"

   Kamar yayi kuka ya sake fita ya bawa maigadi kudi yace yaje gidan Madre ya karbo mashi abinci……sannan ya dawo ya hade kai da guiwa kamar k'aramin yaro!

  Ita kanta ta san batayi dae dae ba ta matsa tare da dafa bayanshi tace "Dan Allah kayi hakuri wallahi babynka ya hanani shiga kitchen da na mike sae naji kamar zai fad'o……"

  Bai ce mata komae ba haka bai d'ago ba!kwantar da kanta tayi jikinshi tace "Am sorry dear!Amma dan Allah ka fad'a man inda ka samo wannan yarinyar……"

   Yasan tana da hakk'in ya fad'a mata don haka ya dago a hankali yace "Mahaifinta ya rasu bata da lafiya shine na taho da ita na nema mata magani……"

  A Hankali tace "Amma duk kauyensu aka rasa mai daukarta sae kai……!me ke damunta……?

     Ya san surutu irin na Sumayya dan haka yace "Tana da kidney problem……"

   Harara ta watsa mashi tace "Dole ta dinga man aiki kam don yanzu ba'a zaman banza kafin ta tafi……"

  "Huh……" kawae ya fada sannan ya mike jin sallamar maigadin!ya fita ya karb'o sakon ya dawo……
   Mikewa tayi ta dauko plate Alkubus ne da miyar k'oda …… ta zauna ta zuba mashi suka fara ci a tare sae da ya koshi sannan ya matsa kusa da K'arama ya kira sunanta a hankali……
  Shiru yaji sae uban minsharin da take sha ……
   "Hafsah……" ya kira yafi sau goma amma ko juyi batayi ba !Sumayya ta kwashe da dariya tana fad'in "Waya fada maka haka ake tada mutun bacci a kauye!bara ka gani……"
  Kafin ya bata amsa ji kake tassss a kumatun K'arama……
*ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*

   _This Chappy is for you FATIMA OMAR FAROUK……ILYSM_


       Page *59-60*


    A Zabure ta wulkita ta fad'o kasa tana zare idanu kafin ta turo baki tana fadin "Waya mareni?

  "Babu……" Ma'aruf ya fada a takaice……

 Sulalowa tayi tana k'arewa Falon kallon sannan ta mami Sumayya ta kwalfa mata mari ta nufi bayan kujera tana fad'in "Na Rama……"

  Zafin ya shigeta sosaae ta dafe check dinta tana kallon Ma'aruf din da yayi mutuwar zaune !ganin baya da niyar magana ya sata zabura zata mike tana fad'in "Wallahi sae naci uwarki kuma kin daki zamanki a gidan nan……" yayi saurin janyota jikinshi ya rungume yana kokarin danne dariyarshi……

  Fashewa tayi da kuka tana fad'in "Ni ka kyaleni!a gabanka fa ta mareni idan kai baraka rama man ba ka barni na rama……"

Murmushi yayi mai sauti yace "A gabana kika mareta itama……"

  Ta sake fashewa da kuka tana kokarin kwace jikinta" Haka ka ce ko?ka fi sonta a kaina ko?to wallahi sae na daketa……"

  "Aljanu gareta……" ya fada cikin whisper
 Waro ido tayi tare da lafewa jikinshi ta kasa motsi……
  "Kina dukanta zasu rama mata tsakar dare!ya fad'a cikin dakewa……
  A Hankali tace " Amma wallahi bata zama yau zaka mayar da ita……"

  A Hankali yace " Duk inda ta shiga bata fita Sumayya"

   "Saboda me……"
Dago kanta yayi yace "Aljanunta ke mak'alewa gidan basu tafiya su dinga bawa yan gidan tsoro karshe ma su kashe auren mutanen gidan……Ki bari zata baki hakuri kuma zan fad'a mata matata ce karta kuma tab'aki!Amma kema ba ruwanki da ita……"

  Shiru tayi tana raba ido ……
 Murmushi yayi ya kira " Hafsah……"
Amma shiru kake ji !Janyeta yayi ya leka a hankali bayan kujeran !ya tarad da sakaran sheme bacci ya kwasheta……dama bata gama baccin ba sumayyan ta tada ita……

  Komawa yayi ya lallab'a Sumayya ta yarda ya kai K'arama dakinta ya kwantar sannan suka koma dakinshi……

  Wanka ya shiga ya fito ya kabbara sallah sannan itama ta dauki goran ruwan da ta rage ta shiga toilet!ta dade tana tuna azabar da taji yayin da wani bangaren na zuciyarta fad'a mata "Curin ke da zafi……"
  Haka ta shahada ta tsiyaya tayi tsarki dashi……
  Tun kafin ta mike ta fara jin zafi !ta taka a hankali ta fita d'aure da towel ta haye gado ta kwanta tana cije baki……

  Sae da gama sallah sannan ya mike ya fita ya leka d'akin da K'arama ke ciki ya mata addu'a ya rufeta da bargo sannan ya dawo gurin gimbiyar……

  Kamar kullun ita ta koma kamar mijin ta janyoshi tana kissing dinshi tare da shafa shi!Cikin kankanin lokaci zafin barkonon dake cikin abunda tayi amfani dashi ya fara shafarshi!kamar yarda yake damunta!maimakon suyi enjoying sae ya koma tana kukan azaba yayin da ya janye ya kwanta gefenta idanunshi sun kad'a sunyi jawur……

  A Hankali yace "Me kikayi amfani dashi?

   Cikin kuka tace "Babu komae……"

  Mikewa yayi ya fincikota zaune yana kallonta!A Tsawance yace "Uban me kika saka a jikinki……"

  "Wallahi babu komae yau kuma ni'imar ce tazo da zafi……! bata rufe baki ba ya tsinka mata mari ……

  "Ki fada man uban me kikayi amfani dashi da kike son cutar damu……"ya fad'a a tsawance……

  Kuka ta saki da karfi tare da dafe inda ya mareta!Kukan ya janyo hankalin K'arama dake ta shawagi cikin falon ta nufo kofar da taji kukan na fitowa ta daddage ta tura da karfin bala'in !da yake ba rufe take ba ta fad'a tsakar d'akin timmm……
  Da sauri Ma'aruf ya janyo bargo ya rufe jikinshi tare da kunna lamp yana kallonta……

  Tsawa ya daka mata hade da tambayarta "Menene……?

  Kallon d'aki take baki bud'e sannan tace "Kuka naji shine ya shigo na ji menene?

  "Menene……?ya maimaita a hankali yana kallonta had'i da girgiza kai……

  Kai tsaye tace "Eh……Idan fad'a kuke na rabaku mana……!

   Takaici ya kashe Sumayya tace "A Hakan dan Ubanki zaki shigo ki ji Menene?to Ubanki ne……"

  Kallon Sumayya tayi na yan mintina sannan tace "Uhmm Fad'an daddawa kuke ko?Kayi hakuri kaga ita bata san me ke cikin jarkar ba kawae ta kama ta wanke kashinta……Hala warin daddawar ka ji ?
 
  Zabura tayi zata mike ta koma ta kwanta saboda har lokacin azabar bata saketa ba!

  "Get out……" ya fada a hankali yana kallon K'arama……

   Ita kam K'arama tunaninta da Sumayya yake sae ta kalleta tace "Yace ki d'auko ya gani……"

   Nunata yayi yace "Da ke nake Get out……!

  Ware hannuwa tayi tana fad'in "Ohon maka……"

  Tsaki yayi yace "Fita anan!

 Ta turo baki tace "Yunwa nake ji!a kauyenmu sau Uku yaya lauratu da Umma ke bani abinci……"

  A Hankali yace "Fita ki jira bakin kofa ina zuwa……" A Hankali ta fita ta tsaya jikin bango tana tab'a hannuwa……

  Sumayya ya kalla fuska a daure yace " Ki fiddo man abunda kika yi amfani dashi kafin na fito……"Ya mike ya saka jallabiya ya fita !ba tare da ya mata magana ba kunna filitan falon ya shiga kitchen ya debo mata abinci a plate ya dawo ya tura mata a gabanta……

  Ta ture spoon din ta fara cin alkubus d miyar koda tana yatsina fuska !loma daya tayi zuwa biyu ta ture plate din tana fad'in "Bana cin wannan tuwon nafi son irin na garinmu……"

  Banza mata ta kura mashi ido tana jiran yayi magana!ganin ba kulata zayayi ba ya sata mikewa ta matsa kusa dashi……

  "Kai……"ta fad'a tana tabashi……
"Uncle……"Ya fad'a,kai tsaye……
   "K'arama dae ba Bunkul ba……"ta bashi amsa……
  Dafe kanshi yayi yana kallon agogon falon !Karfe biyu har da rabi na dare……mikewa yayi ya jata har d'akin Sumayya ya kwantar da ita yana fad'in "Kiyi bacci dan Allah……"

  Zatayi magana ya kashe haske ya rufe dakin ta yarda barata iya bud'ewa ba ya koma gurin Sumayya……

   Makure ya tarad da ita rungume da goran Maganin da roba!Harara ya watsa mata ya karb'a tare da sunsunawa……
  "Wa ya kawo maki wannan?
 "Dan Bauchine?ta fada kanta na kasa
    "Waya kawo maki?ya daka mata tsawa……
  "Beebah"……

【】

  "Sallama……"
Bulawe dake d'aki ta fito tana tab'a hannu "Maitafasa yaushe aka dawo birnin……?

  Harara ta watsa mata tana fadin " Ke Buwale ba wannan ya kawoni ba……"

  Tabe baki Buwale tayi tana kallon kafad'Aar Maitafasa dake dauke da sahun bulala tace " Amma birni ba imani ashe sae da kika sha tsumagiya……"

  Harara ta banka mata tace " Bansan munafunci!Ina binki Murtala ta tafasa!sannan kinci bashin daddawa ta goma!kika amshi hura ta talatin!ga surfen da na maki na ashirin!tattaro ki bani kudina……"

   Kwantar da Murya Buwale tayi tana watsa hannu "Yanzu Maitafasa ina zan zamo wad'annan kud'in na biyaki……"

  Maitafasa ta watsa hannu baya tana fad'in "Da kwarankwasa duk inda zaki samo ki samo kafin na sake zagayowa……"

  Tana fita ta shigd gidan dake gaba !Suma can lissafin tsofaffin bashin da takd bi tayi!Sannan ta fita tana watsa hannu……Duk wanda tasan tana bi tsohon bashi garin sae ta mashi sallama ……

  Sannan ta dawo tun daga farko tana bin gidajen……

  Duk wanda bai bata kudinta ba sae ta kama akuyarshi ko kaza ta tafi……

【】

  Cikin farinciki Lauratu ta kalli Umma tace "Umma Baturen zaya nemawa K'arama magani ta warke……"

   Gyada kai tayi a hankali tana kallon Lauratun !Rabon da ta zauna sunyi fira da Lauratun har ta manta……
  Kamo Hannunta tayi tace "Umma sae ta warke zaya maidota……?

  Sallamar Sallau ta hana Hafsuwalld fad'in abunda tayi niyya……ta Dukar da kai cikin jin kunya!Shima Sallau din a kunyace yace"Inna Hafsatu Barka da dare……"

 A kunyace ta masa da "Yauwa "Idonta na k'asa……

  Lauratu ya kalla cikin so yace "Lauratu ga rake can ki dauko a dak'i ki d'ebarwa su Inno……"

  A Hankali ta mike ta fita d'aga dakin ya bita a baya!Sae da ta shiga d'akin sannan ya tare bakin kofa yana aika mata da kallo na musamman……

  Juyar da kai tayi cike da kunya ta sunne kai……ya kamo hannunta ya rike cikin kwantar da murya yace" Wa yace ki fita d'azu……?

  A Hankali tace "Hura na sawo gidan fulani……"

  K'ura mata ido yayi yace "Ban yarda Lauratuta ta dinga fita mutane na kalle man mata ba……"

  D'aga kai tayi tana kallonshi tare da gyad'a kai a hankali……
  Sakin hannunta yayi ya bata hanya ta dauki raken ta fita……
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


_Wannan shafin na kune dan jin dad'inku, Mai-tafasa na fushi daku sabida kuna mata dariyar tayi....., *Aunty Maijidda Musa, aunty bilki,aunty Zuwaira, aunty haiba, Ummy fingers, Meenet, Mmn ihsan, Mmn Khalid, arfat lawan, precious Hindu,Meenar parrot, Rasheeda tabaco, Hayat A Idris* kai gaskiya kuna da yawa masu yiwa Mai-tafasa dariya wannan kad'an kenan domin kunfi ku nawa..!!!_✋


     Page *61-62*

Ranar k'arama kasa komawa bacci tayi sabida kamshin da room d'in keta faman yi, zuwa tayi wajan k'ofar cikin duhu ta dinga bugawa amma tak'i bud'u ta kwanta k'asa still bataji dad'i ba tayi wajan wata k'ofa tana bud'e toilet ne shima sai kamshi yake yi nan da nan tasa kuka daga baya ta hango window sai ta fara murmushi tare da mik'ewa ta bud'e tabar d'akin.

Cikin filawas d'in gidan ta shiga tayi kwanciyar ta duk da nan d'in ma a tsaftace yake amma yawan su yasa taji d'an dama-dama sai faman surutai take yi tana tunrserewa da dariya cikin dare.

Acan d'aki kuwa Ma'aruf ne ya tsare Sumayya da bala'in shi yana cewa,

"Wallahi Sumayya baki da wayyo,ke sakarai ce shasha-sha, baki da sirri gashi nan garin haukanki kinsa ana neman kashe mu ko a illatamu. Toh bari kiji na gaya miki *!*, daga yau daga rana irin ta yau idan kika sake shan wani abun da cewa na ni'imane wallahi zakiga abinda zan miki sakarai kawai."

Bakinta ta turo mai ganin sai balbala mata masifa yake yi cikin jin haushin kalaman shi tace,

"Amma Yaya duk ina yin wannan abun ne dan kaji dad'i shine kuma yanzu zaka tayi min fad'a? Wannan ma matsala aka samu amma na baya duk da nayi ai.... *!*"

Bakin nata ya buge da bayan hannun shi hakan ya hanata k'arasa maganar da take yi, "wa wuya kawai garin hakan zaki je ki illata d'an cikin ki? An gaya miki masu ciki suna irin wannan ciye-ciyen? Ku da yake matan hausawa bakuda yadda a haka duk sai kuyi ta illata kanku wai dan a janyo hankalin miji haka ake yi dama? Why baza ki min biyayya ba? Kiyi min girki kamar yadda Madre keyiwa Abba ba? Duk inda naje na dawo duk abinda kikeyi ki ajiyeshi kizo ki temaka min da abunda zan bukata amma duk sai na saki a hakan ma kina yi kina cewa  kin gaji ko vazaki iya ba, to hakan ya isa bana so na fisonki a yadda kike natural idan kinji to idan baki jiba wallahi Sumayya you will see...."

Yana kaiwa nan ya kwanta tare da juya mata baya zuciyar shi na kona. Sumayya tana ta ture turen baki ta kwanta it am a tare da matsawa jikin shi ta ringume ta baya yana jinta tana shafar jikinshi yayi mata banza dan har lokacin be huce ba.

Tun sallar farko ya farka sannan ya shiga bathroom yayi wanka tare alwala yayi sallar nafila duk Sumayya na kwance.yana idarwa yafita dan gano k'arama amma me *!* yana shiga wayam babu ita ya lek'a toilet ba kowa hankalin shi ya tashi yana mamakin ina ta shiga? Gashi kofar yadda ya rufeta haka yazo ya bud'e ya shiga uku...."

K'iran sunanta ya shiga yi da k'arfi cikin tashin hankali "Hafsa! Hafsat!! Hafsatu!!! Kina ina? Where are you?" Ya fito zuwa parlor yana dudubawa babu k'arama hankalinshi ya kuma tashi da sauri ya fita zuwa parking lot yana dubawa nan ma babu ya k'arasa wajan me gadi....,

"Am bakaga wata 'yar yarinya ba ta fito?!"

Me gadi ya kalli Ma'aruf daya tashi hankalin shi cikin rashin fahimtar maganar tashi yace.

"Ranka ya dad'e ai na d'auka su hajiya Maryam basu zo gidan ba! Ni kam banga 'ya'yanta ba ko d'aya a nan gidan."

A rud'e Ma'aruf ya kalleshi tare da dafe goshin shi yace,

"No ba 'ya'yanta nake nufi ba, yarinyar dana shigo da ita jiya da....." Beh!, k'arasa ba suka ji tana cewa.

"Kai ina zakaje?!" Hhhhhhh "duk kunji tsolona nice fa k'alama anwan Yaya laulatu." Tayi magana irin ta yara tana b'abb'aka musu dariya,hannunta Ma'aruf ya kama yana janta zuwa cikin parlor ya rage tsawo dai-dai nata sannan ya kama kunnanta d'aya fuskarshi a d'aure ya zare mata idanuwa yana cewa.

"Idan na sake ganin kin fita baki sanar min ba saina cire miki kunne d'aya...!"

K'arama ta kuramai danuwa tare da dashare masa baki hak'oran nan nata yalaye tamkar tasha d'orawa sannan takai hannunta d'an k'arami saman hancinshi tana shafawa tace.

"K'alya kace yi bazaka cire min kunnena ba dan naji tsolo kace akan..."

K'irjin Ma'aruf ya buga jin abinda ta fad'a, nan da nan ya fara tunanin yadda zai yi da ita sabida ba karya tayi ba ta gano abinda ke zuciyar shi ne. Cikin dakewa shima ya zare mata idanuwa tare da jan hannunta ya kai ta d'akin yace ta kwanta tayi bacci kafin ya dawo.fita yayi zuwa d'akin shi nan yaga Sumayya a tsaye tana kallon shi ya rab'ata ya wuce bathroom yayi alwala lokacin an idar da asuba hakan yasa yashimfid'a pray mate yayi sallahn.

Sumayya na tsaye yana yin sallama tace mai, "Yaya Ma'ar yarinyar nan baza ta k'ara kwanan gidan nan ba,bata da kunya inajin sanda take ce maka karya kake."

Lazimi ya fara ba tare da yayi mata magana ba dan har lokacin be huce ba.matsawa tayi bakin gado ta zauna tana turumai baki ganin yayi mata banza yasa ta rik'e bayan tana yarfe hannu tare da cizon lips....

"Wayyo Allah na *!*
"Wayyo na shiga uku Yaya cikina... *!*

Ta fad'a tana rintsa ido tare da dafe cikin da hannu.da Yaya mata banza amma daya san ciki zai iya yin komai sai ya k'arasa wajanta yana tambayarta.

"menene Sumayya.?!"

K'arama ce ta shigo cikin d'akin sai faman kale-kale take kafin ta juya tana kallonsu ta saki dariya tamkar wata babbar mata. Matsawa tayi kusa dasu tana kallon Sumayya dake jikin Ma'aruf tana rik'e da ciki k'arama tace....

"Kai.. *!* wallahi k'ayya take yi babu ciwo a cicinta."

Wata uwar harara Sumayya ta rafkawa K'arama tare da zare mata idanuwa yadda Ma'aruf ba zai ganta ba.itama K'arama kwalalo mata ido tayi tana kallon cikin Sumyyar,dariya tayi tana zama kusa da Ma'aruf tana cewa,

"Kai... *!* akwai yaro an kallallami a cikinta she motsi yake yi, lah yana tayi wallashi zo kagani kaima....!"

Tayi magana tana k'ok'arin kamo hannun shi cikin sauri Sumayya ta bige mata shi da kafa,cikin masifa take magana.

"Waike dan ubanki baki san dai-dai bane? Tashi ki fita dalla can sai uban zarni kike yi salon kisa min tashin zuciya... *!*"

Ma'aruf ya bita da kallo yadda yaga ta zage sai masifa takewa K'arama,ga mamakin Sumayya sai taji tana cewa...,

"Wallashi bazan tahi ba, bayan d'a zuma sai da kika sha na cikin jarka har kika yi amai irin wanda amaryar ilu takeyi....."

Zaro idanuwa Sumayya tayi tare da shigewa jikin Ma'arufa ta fashe da kuka tana cewa,

"Yaya wannan yarinyar mayya ce,nidai gaskiya bazaka barmin ita a cikin gidan nan,Yaya Ma'ar wannan yarinyar wata rana d'an cikina zata cinye dan Allah ka fitar min da ita ni wallahi bana sonta bana son zama da ita shegiya mumafuka kawai....!"

"Ke aradun Allah ba inda zani,idan kinga nabar gidan ga kwananane ya k'are,kuma kwarankwatsa dubu kika sake cewa ya fita dani zaki sani.... *!*"

Cewar k'arama tana faman yiwa Sumayya wani irin bahagwan kallo wanda yasa silalowar tusa jikaki buttt...!!daga jikin Sumayya dake faman zaro ido tana kallon na k'arama tamkar rik'e mata su aka yi bata san ma ta fito ba.

Wata dariya ce ta kwacewa Ma'aruf wadda be shirya yinta ba,kallon shi Sumayya tayi cikin jin haushi ga k'ara da cikinta keyi tamkar wata me baseer da d'an kanoma ta mik'e a fusace tayi toilet tana kuka mai cike da takaicin su. Tana shiga shi kuma ya samu dariyar ta tsaya sannan ya had'e rai yana hararar K'arama dake ta faman kallon kamar tana nazarin shi ya d'an daka mata tsawa amma ko gezau ba tayi ba hakan yasa shi tab'e baki yana kallonta yace...,

"Ke little daga yau karna sake jin kince ga abinda ke cikin mutum kina jina...? *!*

Kawar da kai k'arama tayi tare da sauke numfashi tamkar katon namiji sannan ta kalleshi tana share majina sabida sanyin daya bugeta yasanya mata mura tace mai.

"Kai..! Nifa wunya nakeji (yinwa) aradun Allah da a kyauyen mune tuni Umma ko Yaya lauratu sun bani naci...."

Shafa sumar kanshi yayi tare da mik'ewa tsaye yana kallonta itama shi ta kurawa ido kaika rantse cewar mayyar ce sabida har lasar lebenta take tana kwakular tasono idan ra samu ta goge a jikinta....

"Oya jiki ki jirani sai na zo muje kici abincin... *!*"

Ya fad'a dan so yake tabar d'akin ya sauya kayan jikinshi,tashi tayi tsaye tana ka gyara yagaggiyar rigar jijinta ta fita. Da sauri ya zura wando da riga dan karta shigo sabida yasan ba hankali gareta ba,yana kokarin fita Sumayya ta fito sai faman uban nishi take tana kokarin yin magana ya d'auke car key yafita.....


*{{ }}*

Suna shiga gun Madre suka tarar da ita a kitchen tana had'awa Abba breakfast, Ma'aruf ya zaunar da k'arama a parlor tare da cewa yana zuwa. Kitchen ya nufa yana yiwa Madre magana...

Daga bakin k'ofar ya tsaya yana kallonta,

"Morning madre..!"

"Yauwa Ma'aruf yau da sassafe haka kuma ko wanka banajin kayi a haka..?!"
Ma'aruf ya sauk'e ajiyar zuciya ya k'arasa cikin kitchen d'in ya fara yiwa Madre bayani akan k'arama. Acan parlor kuwa k'arama ce ta kurawa plasma TV idanuwa tana kallon mutane tamkar zasu fito,k'arasawa tayi gurin tana magana tamkar me magana da mutanen gaske tana cewa.....,

"Lalalah toh ku hirhito mana kawai he ku kama ku b'uya? Taga kamar basu jita ba sai ta fara masifa......

"Idan zaku hito ku hito bana son kayya,wayahi kuhito...... *!*"

Karad'in ta yasa suka fito da gudu kafin su tsaya suna k'are mata kallo ita ta juya tana kallon cup d'in hannun Madre da gudu ta karasa tana cewa.

"Zan sha! Zan sha kunu...!!!"

Cup d'in hannun Madre K'arama ta fizgi kofin tare da karawa a damilallan bakinta, sai da ta shanye tatass sannan ta sauk'e kufin tana kallon Madre tare da dashare yalayen hakoranta tace,

"Umma zan k'ara ban kohi ba a gida Yaya lauratu a kwanan shan ruwa take bani farau-farau inha in kohi sannan taha itama...!"

"Allah buwayi... *!*" Madre ta fad'a tana k'ok'arin komawa cikin kitchen. "Kai baza ka shaba?!"

K'arama ta tambayi Ma'aruf, girgiza kai yayi sannan yace "zan sha ba yanzu ba kema kuma baza ki k'araba sai anyi miki brush da wanka sannan zaki k'aracin wani abun..."

Sumayya tana ganin ya fita taja tsaki mai tsawo,phone d'inta ta janyo tana kiran beeba, ta kusa 6miss call kafin beeba ta d'auka wadda tana zaune bakin gado tana kallon sarkar gold d'in da Sumayyar ta bata. Da kyar ta d'aga tana yatsina fuska kai da ka gani kasan bata son d'agawa.

"Hello beeba...!Na shiga uku wannan maganin a memakwan ya kankaro min mutunci da soyayyar Yaya Ma'aruf sai ma neman rabamu yake beeba wannan maganin zasu lalata soyayyata da mijina d'an uwana... *!*"

Sumayya ta fad'a cikin hasala, beeba tayi murmushi tana kuma damk'ar sark'ar hamnunta,cewa tayi mata.

"Toh Sumy yanzu me kike nufi?!"

"Ki sake kawo min wasu irin na da sunfi kyau dayin aiki,beeba ina son mijina inason kullum ya dinga jina tamkar sabuwa please yaushe zaki kawon sababbi..?"

Sumayya ta fad'a yana jiran taji amsar beeba,cikin dauriya beeba d'in tace mata.

"Toh shikenan naji zan samo miki but! Yanzu wadda take yin na da d'in bata nan tana sokoto amma idan ta dawo zan kar 6omiki...."

"Yauwa beeba thanks kinsan yanzu ina da ciki kuma karki ga yadda Yaya Ma'aruf yake son shi yanzu na k'ara zama abar kaunar shi sosai,inason kishiga ki fita wajan samar min ingantattun magunguna."

Tunda Sumayya ta furtawa beeba cewar tana da ciki zuciyar beeba ke bugawa ta dinga furta kalmar ciki a cikin ranta. Da kyar ta ce mata "karki damu za'a kawo miki."

Tana kaiwa nan ta yanke kiran tare da mik'ewa tsaye,yanzu kam maganin da zai 6arar da cikin shi zata nemo cikin *ALWASHI* ta furta.

"Sumayya sorry wallahi, baki dace da Ma'aruf ba domin ni yafi cancanta daya aura ba ke ba.zan fitar dake na dasa k'iyayyarki a zuciyar shi zaki gane baki da wayyo ke shasha shace wawuya kawai.... *!*"

Kiran Kausar beeba ta hauyi tana d'agawa tace,

 "kina ina?
 "Ina skull wani abun ne?"

Kausar ta tambaya beeba tayi kwafa tare da cewa "all right idan kin dawo kina free let me know."

"Ok bye..!"


*{{ }}  {{ }}*

   *M*adre ce tafito ta jere kayan karin kumallon akan dining table tana jin tausayin K'arama dan aljanu basu da dad'i akwai 'yar kanwarta da suka ta6a shafarta har ta koma ga Allah bata ta6a yin aure ba sabida sun aure ta.

"Madre bari naje na samo mata kayan da za'a saka mata wad'annan sun yake sai uban wari suke yi....!"

Ma'aruf ya fad'a yana k'okarin fita Madre tace mai toh,yana fita ta kalli K'arama dake faman muzurai upstairs tayi dan sanarwa da mai gidan nata cewar breakfast is ready. Tare suka fito da tsananin mamaki suka kalli K'arama dake faman tura soyayyar doya a cikin bakinta Madre ta saki salati  tana tafa hannaye tare da cewa,

"Hafsat....... *!!!*"*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


     Page *63-64*


"Hafsat... *!!!*"

Madre ta dakawa K'arama tsawa lokacin kuma sun k'arasa wajan,bata ko kulata ba sai faman dannawa bak'inta doyar take. Da sauri Madre ta buge hannun K'arama tama manta da cewar basu ihsan bane sai da Abba yayi mata magana "Hafsat rabu da ita." sannan tunaninta ya dawo.

"Ka aleta bayan nace mihe inajin yinwa hinefa yace mutaho nan kuma munzo ga abuncin amma wai he anyi min wanka kuma ni banaso.....!"

A hankali Mandre ta k'arasa wajan K'arama wadda ke ta faman zarar idanuwa yatsunta cikin bakinta tana lashewa yau taci abinci mai dad'i da karkad'a kunne.

"Hafsatu ai da kinjira nazo sai na zuba miki amma yanzu gashi kin cinye ta sauran guda uku."

"Na dena toh shikenan?!"

K'arama ta fad'a tana kallon juck d'in kunu, Madre ta kalli Abba tare da cewa,

"Kayi hakuri alhaji bari na soya maka kwai tunda ta cinye wannan..."

"No kibarshi kawai nayi latti yanzu, yau idan naje nasamu wani abun naci acan, ita kuma a gyarata idan na dawo sai ku sanar dani wacece..."

Yana kawai nan yiyi hanyar fita dama yafito da brief case d'inshi,Madre taje ta raka shi sai da ya tafi sannan ta dawo ciki. Bata ga K'arama ba a dining area d'in hakan yasa ta shiga kiran sunanta tare da dube-duben inda zata ganta.

"Hafsatu! Hafsatu!! Oh ni Hafsat yau naga ta kaina wannan wace irin yarinya ce...? Kizo muje a tsaftace ki amma kunk'i...!!!"

Madre nata sababi abinda bata saba yiba koda Sumayya na nan amma yau K'arama tasa sai zagaye take tana bud'e murya. A haka Ma'aruf ya shigo hannun shi rik'e da ledoji yaji Madre sai kwalawa K'arama kira take yi, ya kalleta cikin mamaki tare da tambayarta lafiya,

"Ma'aruf wannan yarinyar anya zan iya da ita kuwa? Yanzu breakfast d'in dana had'awa abban ka kafin naje nasanar mai ta cinye doyar tatass! Sai hakura yayi ya tafi aiki a haka yanzu na,dawo na nemeta na rasa kuma bamu fitaba tare bare nace kin shigowa tayi..."

Kayan ya ajiye shi kanshi yasan ya d'ebo ruwan dafa kanshi,amma so yake ya ceceta kodan albarkacin jinyar da Mahaifinta yayi gashi ita yarinya ce da take buk'atar a temaka mata.

Tare suka shiga nemanta amma ba ita ba labarinta, ita kam K'arama gurin Sumayya ta koma zaune ta tarar da ita tana kallon curin maganin nan da beeba ta kawo mata, tunani take yi akan Tasha ko ta hakura duk da cewar hatta warin maganin sai ya dad'e bebar cikin bak'inta ba gashi babu wani dad'i haka dai taji zuciyar ta na so kawai ta gutsira tana shinshinawa zata kai cikin bakinta taji muryar K'arama na cewa.

"Lalalah idan kikaci daddawa da fulawa sai na gaya mai ince sheda kika kala ci....!"

Sai da k'irjin Sumayya ya buga ganin K'arama yasa ta mik'ewa a fusace tana nunata da yatsanta tace,

"Ke ni ubanki zanci wallahi,shegiyar yarinya mayya kawai toh kurwata d'aci gareta tafi karfinki kuma sai kin bar gidan nan yau aljana kawai..."

K'arama ta kurawa cikin Sumayya idanuwa tana murmushi tare da karkata kanta sai kuma ta fara matsawa gurin Sumayya tana k'ok'arin kai hannunta saman cikin wanda hakan yasa Sumayya yin baya tana zaro idanuwa tana fad'in.

"Idan kika kuskura kika ta6amin ciki ya zube ba aljanu ba yau ko shuri ne a kanki sai na sauke miki shi..."

"Toh ba wasa zan mihi ba."
"Ba'a so shegiyar yarinya kawai."

K'arama tace "sheh anyi d'in."

Tana fad'a sai ga Sumayya a gefen gado a zaune idanuwan ta sun firfito gumi ya fara wanke mata riga,ganin idanuwan K'arama tamkar na zaki yasa cikin ta ya kuma juyawa a haka K'arama ta k'arasa tana shafa cikin da d'an k'aramin hannunta sai b'ab'aka dariya take tamkar mahaukaciya tana cewa.

"Yalo idan ka fito tare za muyi wasa amma hmmm!"

Tayi shiru bata k'arasa abinda zata ceba, sai da ta gama wasan ta a cikin Sumayya sannan tace,

"Na tafi suna can suna jira na."

A tunanin Sumayya aljanun ne suke jiranta hakan yasa zuciyar ta k'ara hargitsewa tabi K'arama da kallo har tabar d'akin sannan ta kurma ihun a kawo mata d'auki (k'ila ta manta ba kowa a gidan).

*{{ }}*

A zaune suka ganta wajan step da kufin kunu a hannunta tana sha ta mik'ar da kafarta samb'al tana kad'asu, Ma'aruf ne ya fara ganinta cikin had'e fuska dajin haushin tanajin su tayi shiru ya kalleta yace,

"Bakiji ana kiranki ba shine kika yiwa mutane shiru stupid kawai?!"

"Toh bana zata wanka za'a min ba, ni bana son wanka kuma baza amin ba d'in."

Tayi maganar tana turo baki tare da rarraba idanuwa,Madre taje ta kamo hannunta amma ta fizge ita a dole baza je ayi mata wanka ba. Cikin azama Ma'aruf yaje ya zata suka je bathroom ya kalli Madre tare da cewa,

"Madre idan bata tsaya ba ki Zane ta marajin magana kawai."

Yana fad'a yayi parlor ya zauna kan kujera yana jiran fitowar su, Madre ta kalli K'arama baki d'aya idan bata kawo zuciyar imani ba bazata iya tab'ata ba sabida tayi dik'il-dikil da ita ga uban zarni da take yi cikin murmushi Madre tace,

"Idan banda ke mai sunana ai ba'a zama da dauda ki bari ayi wanka kema zakiji dad'i."

Karamin hijjab d'inta ta cire mata sannan ta fara k'ok'arin cire mata kaya amma K'arama taki yadda,rigima suke inda Madre ke mamakin k'arfi irin na yarinyar kafin ta fito daga bathroom tayi hanyar parlor tana cewa.

"Yo ina dalili haka kawai yarinya ta dinga  hankad'e ni,kai Ma'aruf yarinyar nan bata son wanka kaga yadda ta dinga ture ni tamkar wata babba,toh bazan iya ba ni kam."

"A'a Madre yarinyar nan dole ayi mata wanka, har wani wari-wari take yi ga zarni tamkar bayin da yake shekaru ba'a wanke ba please Mamana."

Kallon shi kawai tayi sannan tace, "a'a tashi muje kila idan tana ganinka zata tsaya amma yarinyar akwai iya fad'a."

Tare suka k'arasa bathroom d'in nan suka tarar da ita ta tatse makilin kaf ta had'a shi da shampoo,conditioner tana kad'asu cikin bukiti.

"K'arama menene hakan? Oh ni Hafsatu..."

Tana ganin Ma'aruf ta fara dariya tana washe mai hak'ora yayi d'an tsaki sannan ya cewa Madre "ku fara idan bata tsaya ba kuma sai na mareta." K'arama tayi saurin kallon ganin da gaske yakeyi yasa ta bari Madre ta cire mata kaya pant d'in jikinta yayi dikil-dikil duk jurwaye gashi an kulleshi daga gefe Madre tasa hannu ta cire shi da kyar tamkar tayi amai,kanta a cukurkud'e da kyar Madre ta warware shi duk Ma'aruf na tsaye yana kallon su yana jin tausayin ta.

Da kyar aka wanke kan sannan aka yi wanka harda yi mata brush ana yi bakin na jini tamkar an naushe mata shi, cikin towel Madre ta nad'ota tace Ma'aruf ya d'auketa ya kaita d'akinta,sai da ta kwashe kayan takai bula sannan ta bisu d'akin.

Kayan da ya siyo mata aka sa mata amma fur tak'i bari ayi kwalliya,sai a lokacin ne Ma'aruf ya Kara tabbatar da cewar lallai mutum ya d'akko ba aljanaba aljanun kawai ajikinta suke. Tayi kyau cikin doguwar riga 'yar kanti red da white ne colorn gashin ma tak'i yadda a gyara duk kuwa iya kokarin da Ma'aruf yayi wajan ganin an gyrata amma fur da haka yayi musu sallama yace anjima zai zo idan yaje ya sanarwa da ya sayyadi dan jin yadda za'a farowa lamarin.


*{{ }}    {{ }}*

GWADABNIYA

   *M*ai-tafasa ce a tsakar gida tana ta tsinkar tafasa tana sawa cikin buhu dan yanzu ta gano cewar duk sanda taje ta d'ebo to idanuwan Kundum na kanta tana zargin cewa tana d'ibar mata dan mafi akasari Kundum tafiyin tuwo da miyar tafasa kuma ba siya take yiba hakan yasa take sawa cikin buhu yanzu.

Gefe guda kuma wasu garken tumaki ne da kaji da agwagi da taje ta kwasowa duk wanda be biya ta bashin da take binshi. Asibi ne da Buwale suka shiryo munafunci suka taho gurin Mai-tafasa ta kallesu ta watsar tana gunguni Buwale tace,

"Yoh ke Mai-tafasa ai jama'ar gari aradun Allah suna nan suna hirya miki yadda zaki bi lado d'azu muka jiyo ana shirya yadda za'a yi miki ta bayan gida..."

"Jakar uban nan! Aradun Allah Buwale bana son muna hurci,ni nan da kuke gani ko a cikin birni Hakimi hakuri yake bani bare mutanan kauyan nan,aradun Allah kuma ku fita idona ahe...*!*"

Kundum tayi saurin fitowa daga d'aki tana gyara zani ta kalli Mai-tafasa tana dukan gefen cinyarta tace,

"Aradu acan binni Hakimi zane ta yayi, nan tazo tana cire kaya mukaga shatin tsumungiya amma tana cewa wai Hakuri ya bata mtw...!"

Maitafasa tayo kan kundum su Buwale suka koma gefe suna kallon su kafin kace me tuni ancika gurin 'yan team d'in Kundum sunfi yawa sai cewa suke "yauwa kundum yauwa kundum." Maitafasa na surfa musu zagi baki d'aya tun mutuwar ladonta komai ya kara rud'ata.da kyar kande da lantana ne suka raba dakyar duk sun jigata.

*
Hafsatuwalle kam rayuwa.......


hh

*FEEDOHM*πŸ’ž
&

*HAJJA CE*πŸ‘ˆ


[22:06, 12/27/2017] ‪+234 806 677 6651‬: πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


_Wannan shafin naku ne kuma dan jin dad'in ku *Ayush, Maman sultan, Mira fodio, Mmn zainab, Aysha b fullbe, haleema Mahmoud, Jidda Adam, Olo* asha karatu lafiya_     Page *67-68*


   Wajan la'asar Sumayya na parlor sai ga beeba ta zo, da murnarta ta tare ta tare da komawa cikin bedroom bayan taja hannun beeba, kallonta beeba tayi a yatsine tana bin d'akin da kallo Sumayya tace,

     "Kawata kinsan kuwa wancen magungunan bama su kyau bane? Wallahi nasha wahala yanzu ma na gama shanye na cikin jarkar duk da Yaya Ma'aruf ya hanani shi dan shima ba k'aramar wahala yasha ba."

Sumayya ta fad'a tana yatsina fuska tamkar yanzu ne take shan maganin, beeba ta tab'e baki sannan tace,

    "Ni kinga ba wannan zancen ba yanzu ina shi Ma'aruf d'in yake...?!"

Mtww Sumayya taja tsaki tare da turo shi tana cewa,

    "Baya nan wallahi beeba ya tashi ya kawo min wata yarinya mayya har d'an cikina take gani,d'azu da tazo kuwa beeba na rantse miki da Allah kusan kashe ni tayi sai da na barta tayi wasa da cikin yan jiran honey nake yi dan wallahi bazai bar min yarinyar nan a gurina ba yar k'aramace salon a barni da raino...."

Beeba dai ta tab'a baki cikin rashin damuwa da maganar ta zuge Jakarta ta ciro wani garin magani a roba k'arama mai garai-garai tana mik'awa sumayya.

    "Ga shinan wannan na k'ara ni'ima ne zaki sha shi da ruwan d'umi idan zaki kwanta yana da kyau sosai wallahi."

Cikin murna da d'oki Sumayya ta karb'a tana godiya tare da kankame beeba tamkar zata had'iyeta, bedside drower ta bud'e ta bata wani turare me kyau da tsada beeba ta karb'e ta danna cikin jakarta aranta tana fad'in,

     "Zaki gane baki da wayyo Sumayya, cikin ki na b'arewa zan mallaki Ma'aruf cikin ruwan sanyi ke kina nan kina hauka."

Hira suka d'an tab'a tun beeba na saka ran ganin Ma'aruf har aka kusa magrib taka bashi ba alamar sa kawai ta mik'e tayi shirin tafiya.

    "Toh uwar biyu ni na tafi sai gani na biyu."

Beeba ra fad'a tana sab'a Jakarta a kafad'a, Sumayya ta biyo bayanta tana fad'in.

    "Allah na d'auka sai bayan sallar isha zaki tafi, any way nima na samu nasha magani na nasan kafin ya dawo na kusa jik'ewa daya zo kinga kafin yayi wanka sai ai....."

Beeba tayi saurin katseta ta hanyar cewa,

    "Naji nidai kinga tafiya ta." Tana fad'a tayi waje da sauri tun kafin maganar Sumayya ta illatata."

Tana tafiya Sumayya ta koma cikin bedroom d'in, da kyar ta tsaya tayi sallar magrib sannan ta fara kokarin fara amfani da maganin da beeba ta kawo mai, sai da ta fara shiga kitchen ta d'akko kufi ta tsiyayi warm water a cikin Despenser sannan ta koma d'aki. Neman maganin tayi amma sama ko k'asa ta rasa, to ina yake! Ta duba ko'ina babu har hawaye tayi dan bak'in ciki sai kuma tayi saurin kiran wayar beeba tana d'agawa ta fara magana.

     "Beeba wallahi banga maganin ba."

     "Eh mana duk na duba ban ganshi ba beeba ya zanyin yanzu please do something to me kinji kawata."

    "Kai ya ilahi yanzu kenan sai wani satin? To bari dai na sake duba dan wallahi ina son yau muyi har...."

Kafin ta k'arasa abinda take shirin fad'a beeba ta yanke kiran, Sumayya ta kuma mik'ewa tahau neman maganinta.


*{{ }}   {{ }}*

   *K'*arama kuwa tun sanda ta haniniyi tuwanta ta d'anyi wasa sai ta sheme akan center carpet tana sharar bacci wanda minsharinta ya hana Madre sakat a cikin parlorn sai tashi tayi tabar gurin ta koma d'aki. Bayan sallar isha Abba da Ma'aruf suka dawo a tare suka shiga ciki K'arama ta fellah da gudu tare da rungume Ma'aruf hannunta duk miya tana shan rumon naman da Madre ta zuba mata gaba d'aya duk ta b'ata mai wandon jikin shi.

    "Oh my God small Mom duk murnar gani nace, toh oya muje ciki k'i k'arasa cin abincin ki."

Ma'aruf ya fad'a yana tura keyarta suka koma cikin parlon, abban Ma'aruf yayi murmushi tare da kad'a kai tunawa da yayi shi yaushe rabon da idan ya dawo gida ayi mai Oyo yo har ya manta.

    "Sannu da zuwa abban Ma'aruf.!"

Madre ta fad'a tana k'arb'an brief case d'in hannunshi, yana kallonta cikin kulawa yayi murmushi tare da cewa,

    "Yau kin samu 'yar hira ko kirana baki gani ba ko?!"

Madre tayi dariya jin abinda yace tana kokarin d'aukar wayar ta tace,

    "Kaina bisa wuya ban ga kiranka ba course yarinyar nan hmm Allah dai ya bata lafiya kawai."

    "Madre yau ta saki surutu ko?!"

Ma'aruf ya fad'a yana zama cikin d'aya daga cikin kujerun parlorn, K'arama kam komawa tayi ta d'auki boul d'in da ruman ta ke ciki ta dawo kusa da Ma'aruf tana mik'a mai tare da fad'in.

     "Kaima muha a tare kaji?!"

Ma'aruf yayi saurin kauda kanshi yana fad'i "no no no, bana sha na koshi...!"

Ta tab'e baki tare da cewa "kai fa ni bani da nono irin na Yaya laulatu kani."

Tayi maganar tana k'ok'arin d'aga mai rigar ta yayi saurin da kar ta ita yana kallonta suma su Madre na kallonsu suna jinsu tare da yin dariya yace mata,

     "Cewa nayi a'a bana sha na k'oshi."

K'arama tace "au to ni bara na shanye." Ta fad'a tare da kafa kanta yana mata magana amma inaa sai data shanye ruman tas sannan ta kalleshi tana dariya tana sauke numfashi da kyar. Nan Ma'aruf ya sanar da abban shi labarin K'arama tare da d'orawa yana cewa,

    "Gobe zamu zo da ya sayyadi zai dubata insha Allah za'a fara yi mata addu'o'i da ruk'iya."

Abba da Madre suka taya shi da addu'ar samun nasara kafin yayi musu sallama ya tafi dan anan zai bar K'arama sabida baya son rigima bare Sumayya ta takurai mai. Yana shiga parlon su sai yaga K'arama zaune kan kujera tana mai wani irin kallo, kalle-kalle ya farayi yana tambayar kanshi da cewa "ta ina ta shigo?! Ganin ba amsa yasa shi nufarta yana addu'a a cikin zuciyar shi.

    "Kaga maganin da aka kala kawo mata wai tasha, bata gani ba kuma na d'auke kaga fa na zubar da yaron cikinta ne kuma ni ina son ya fito mu dinga wasa."

Tun Ma'aruf na tsora harya dake ya k'arasa tare da k'arb'ar robar maganin yana dubawa, cikin zuciyar shi tambayoyi ne fal ya kalli K'arama sannan ya wuce bedroom d'in Sumayya a hargitsan shi tamkar iska yana kwala mata k'ira, yana shiga ya ganta kan bedside tayi jigum duk ta lalata d'akin, tana d'agowa taga rubar maganin a hanin shi hankalinta ya tashi ta fara inda-inda ganin yadda ya had'e rai wanda bata tab'a gani a fuskar shi cikin masifar da ba saba yinta yayi ba yace.

     "To he'll with you Sumayya..."

Sannan ya buga rubar a kasa maganin ya bud'e gabaki d'aya ya zube yayi kaca-kaca da d'akin sannan ya nunata da yatsa idanshi yayi jawur yace,

     "Idan kika kuskura kikayi abinda yasa cikin nan ya zub'e wallahi Sumayya kin zubar da auranki...."

Yana kaiwa nan yabar mata d'aki tare da bugo mata kofa, K'arama dake tsaye ta lekata tare da fad'in,

    "Wullo..."

Sumayya ta jeho mata pillow sai dai be sameta ba K'arama ta dinga mata dariya wadda kesa Sumayya k'ara hasala. Yau kam duk kulaficin ta akan shi bata samu ba dan fata-fata yayi mata yayi kwanciyar shi a nashi d'akin itama haka amma tasha kuka ta tsinewa K'arama yafi cikin d'akinta.

Cikin dare yana bacci yaji mutum a jikinshi yana dubawa yaga K'arama, be wani ji tsoroba yayi mata addu'a sannan ya juya ya kwanta shima......


*{{ }}   {{ }}*

  Washe gari tun asuba ya duva yaga bata d'akin yayi addu'a ya fito ya leka d'akin Sumayya yaga tana bacci sannan ya koma ya shiga toilet yayi alwala yayi sallah.

Kamar yadda suka yi sa ya sayyadi ana idar da sallar juma'a suka tafi gidan Madre lokacin itama Sumayya na can takai karar shi, kota kanta be biba ya sanarwa Madre ga liman yazo ina K'arama.

     "Tana nan d'akin bak'i na rasa abinda take yi a cikin shi kuma dana leka zan ganta a zaune."

Can ya tafi yana kiranta amma tsit bata amsawa, har ya shiga be ganta ba ya duba bayi bata ciki nan da nan aka hau neman K'arama ba ita ba labarinta har wajan la'asar liman ne ya gano cewar guduwa tayi.

     "Ma'aruf sun gudu da ita babu mamaki sunji labarin abinda za'ayi mata shi yasa, amma ka bari zamu san wata hanyar."

Ya sayyadi ya fad'a mamaki ya kusa kashe su a haka yasa aka maida liman suka koma cikin gida nan suka ganta zaune a wajan stairs tana wasa da wata 'yar tsana tana musu dariya.......

*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
[15:42, 12/30/2017] ‪+234 806 677 6651‬: πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*πŸ‘ˆ


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


          Page *69-70*


            K'arasawa yayi kusa da ita tare da tsugunnawa ya kura mata ido cikin sanyin murya yace "Hafsa……"
  Dariya ta sake tare da wurga yar tsannar sannan ta mike tana daga doguwar rigarta tace " Baka ganni ba ko……?
  "Ina kika shiga?

Kai tsaye tace "Yo bayan kujelu……"

  Cikin sanyin murya yace "Me yasa kika boye?Bakya son ki warke ki kuma gurin Ummanki Hafsa……"

Waro ido tayi tare da rike baki tana kallonshi kafin ta girgiza kai tace "Yo wa zaya koma gurin Umman……?

 Da hannu ya nuna ta yana kallon yarda ta kafe shi da ido……

  "Tallahi ba inda za'ani!kawae in koma na cigaba da cin tuwo kullun ina kwana a buhu? ka raina ni!da k'warank'wasa komin bala'inka bazan bar nan gidan ba sae dae ayi yadda za'ayi……"ta fad'a tana kyafta idanu tare da murgud'a baki……

  Dariya ya saki mara sauti sannan yace "Ba yarda za'ayi Hafsa!Indae gida ne kiyi zamanki amma dan Allah idan kinga Malan ki daina guduwa kinji ko……"

 Murgud'a baki tana kyafta idanu tare da gunguni ta juya baya……
  Shiru yayi yana kallonta kafin ya mike tsaye yaja hannunta……

【】

Dukar da kai yayi yace "Malan ya kake tunanin zamu bullowa wannan matsalar tunda yarinyar bata bari ku hadu kuma ni ban tab'a ganin wannan kalar aljanun ba ko a labari……"

  A Hankali ya sayyadi yace  " JINNUL ATFAL sune aljanun dake shiga kananan yara Ma'aruf su irin wadannan aljanun suna da wuyar sha'ani saboda sun riga sun saba da yaran tun suna k'anana!kuma sakakin iyaye ke janyowa yaran aljanu!kaga yawan barin yaro shi kadae yana bawa aljanun kwarin guiwar shafar yaranmu!sannan yawan barin yaro gabancin magrib ya zauna shi kadae ko yana wasa shima yana sa aljanun shigar yaron da sakaki da addu'a ga uwar yaron ko barin yara ba kaya ajikinsu……"

  Shiru yayi yana sauraren shi kafin yace " To Malan yanzu menene Mafita……?

 Murmushi yayi a hankali yace "Zan fad'a maka wasu magunguna da zaka sawo yanzu idan ka fita ka had'a mata Inshaa Allah ko da ban ganta ba zata samu sauki ...
• GARIN KUSDUL HINDI (SANYA) .
• MAN ZAITUN
• MAN HABBATUSSAUDA,
A hada waje daya sannan a sa shi a wuta yayi zafi sosai sannan a sauke idan ya huce sai a samu kwalba ko wani abu a zuba a Rink'a shafa mata amma in son samu ne a karata……
• AYATUL KURSIYU
• KULYA
•FALAKI DA NASI
• TABBATI YADA
• KULHUWA
• SURATUL FATIHA.
TO IN SHA ALLAHU WANNAN YANA MAGANCE ISKA DA SAURI DA YARDAR ALLAH.……Haka kuma idan zata kwanta a shak'a mata tare da shafe jikinta dashi insha Allahu zata samu sauki zuwa sati daya sae ka dawo ka fad'a man yanayinta……"

  Godiya yayi sossae sannan ya fiddo da kudi masu yawa ya aje mashi!amma sam yace ya kwashe abunshi bai masa dan ya biyashi ba……Haka ya dauk'a ya tafi daga nan islamic chemist ya wuce ya sawo abunda malan ya fada mashi sannan ya wuce gidan Madre ya kai mata !Ita da kanta ta hada tare da karanta surorin da yace sannan ta bashi tace idan yaje ya fara mata amfani dashi……

 【】

  "Allah ya tsinewa mai abunda aka hanashi……!

  Da sauri Sumayya ta kalleta tare da wurga mata harara ta gefen ido sannan tayi kitchen tana boye garin maganin da beeba ta kawo mata wae tayi hayakin HQ dashi……

  Itama hararan ta jefa mata tana rufe baki da hannu sannan tace "K'ala jikawa zaki yi ko?Yarinya kin mutu ba ruwana……"

  Kamar ta fasa ihu ta juyo tana fad'in "Wae dan ubanki meye hadina dake……!

  Washe baki tayi tace "Bunkul(Uncle)Shi ya had'amu……!

  "Ubankine Bunkul din……"ta fad'a tare da jeho mata cup din dake hannunta……Sallamar Ma'aruf ta katsewa K'arama abunda tayi niyyar fad'a……Tayi gurinshi da gudu ta kankameshi tana washe baki……

Kayan dake jikinta ya kalla sunyi diki diki kamar bai mata wanka ba yau!……

Dariya ta saki da karfi tana kallon Sumayya data tako a hankali ta rungume Ma'aruf tace "Lahhhhh amma ke babbar yar iska ce aradu……"

  Kuka Sumayyan ta saki tana fadin "Wallahi Ya Ma'aruf na gaji da wannan mayyar!dan Allah ka mayar da ita garinsu……"

  "Aradun Allah ba inda zanje……"K'arama ta fad'a tare da watsa hannu baya kamar yarda ta ga Maitafasa nayi……

  Kamo hannnunta yayi yana rungume da Sumayya ya zauna saman kujera ya dubi K'arama yace "Hafsa me kika wa Auntynki……?

  Waro ido tayi tana dashire hakuranta tace "Ba abunda na mata kwarankwatsa……"

A Hankali yace "Ban hanaki wannan rantsuwar ba?Shiru tayi tare da rufe bakinta da hannu tana kallonshi……

 Lumshe ido yayi yace "Ce tayi hakuri……"

  Ba musu tace "Kiyi hakuri……"
Sumayya kam kara kankame hannunshi tayi tana fad'in "Dan Allah ka mayar da ita gurin Madre……"

 Cikin sanyin murya yace "Sumayya ke bara ki iya zama da ita ba amma kike so akai ta gurin Madre……?

  Turo baki tayi tace "Madre tsohuwa ce nikam amarya ce !Tun zuwan wannan yarinyar ta hanani jin dadin aurena……"

  Tabe baki yayi yace "Dan tana fad'ar Gaskia?

  Shiru ta masa ta mike ta dauko shinkafa da wake da mai da ta masu ta zuba mashi!Da yake yana son Shinkafa da mai haka ya sauka yaci ya koshi yasha juice ya mike ya shige daki !K'arama kam komawa tayi ta kwanta rigingine saman carpet taci gaba da kallonta har sae da taga ya shige d'aki sannan ta mike ta koma inda ya tashi ta zauna tare da cinye sauran abincin da ya rage……

 K'aramin tsaki Sumayya ta saki lokacin da ta fito tace "Shegiya a cici……"

  "Bunkul yace wanda yayi shiru shi ke da hankali!Na fiki hankali……"Cewar K'arama tana lashe hannunta……

  Tsaki ta saki ta nufi dakinta a can ta iskeshi yana kokarin bude windows din jin dakin na fitar da wani karni karni ……

  "Warin me ye haka Sumayya……?
Yatsina fuska tayi tace " Oh na manta d'azu Ahmad ya kawo man kifi shine da naci na manta ban yar da ledan ba!ka ganshi can under bed……"

  A Hankali ya girgiza kai!za yayi magana wayarshi ta hau ringing!ganin new number ne yasa har ta katse bai dauka ba……Wanka ya fad'a!A Ka kuma kiran wayar Sumayya ta kai hannu ta dauka!dafe gabanta tayi ganin number Beeba ke kiranshi……Jikinta na kyarma ta dauka tayi shiru……

  Beeba kam langwashe murya tayi tace "Good Afternoon Sir ……!

 Ware baki tayi tace "Beebah!Uban wa ya had'aki da number Ya Ma'aruf……?

  K'aramin tsaki Beeba taja tana fad'in "Dadina dake Sumayya ke banza ce!Idan ba dalili ba me zanyi da number mijinki?kinga ni kin hutar dani dama yanzu zance ya baki zanyi magana dake !

  Cikin d'aga murya tace "To ni me ya sami wayana da baraki kira ba?

  Tsaki ta kuma ja tana hararan wayar tace "Kinga karki man ihu akai!Na kira wayanki Not reachable,ki zo ki karbi magani yanzu aka kawo man idan kuma bakya bukata nace ta tafi……"

  Kwantar da murya tayi tana fad'in "Hoo My Beeba wallahi kin kayar man da gaba!amm……"Kife wayar tayi tana kallon Ma'aruf da ke tsaye bakin kofa yana kallonta……

  A Hankali ya tako ya mika mata hannu "Da wa kike waya?
  A Hankali ta mika mashi wayan tana fad'in "Beeba ce……"

  "A wayana kuma?。

。Gyada mashi kai tayi a hankali……

  "Ke kika kiranta?ya fad'a yana fiddo idanu
 "Ita ta kira……"
"Ok……"Wayar ya fara dubawa!A Hankali ya dago yana kallonta tare da nunota da wayar yana lumshe mata da ido……Ganin Number beeba ce ya sata gyada mashi kai ……
 "Karta kuma kirana……!ya fad'a kai tsaye
Shiru ta masa tana fad'in "Sae kace ba kai take gyara mawa ba……"Cikin gunguni……
 Harara ya sakar mata ya fita dakin ya iske K'arama ta sata TV gaba kamar zata mayar da ita ciki!
  "Muje ki dauko kayanki masu dauda……"Ya fada tare da nufar kofar dakinta……
 
  Gabanshi ta sha tana waro ido tace "Ayi me dasu?

  Kai tsaye yace "A Wanke maki!

   "Tallahi babu mai wanke man kaya……"Ta fad'a tare da yin dakin da gudu ta hau tattara kayan ta tura karkashin gado!Tsaye yayi bakin kofar har ta gama turawa sannan ya karasa shiga ya dauko kayan yana hararanta!Kuka ta saki iya karfinta ta fadi kasa tana birgima!
  Girgiza kai yayi ya fita da kayan ya bawa Mai wanki zannan ya dawo har lokacin tana kwance kasa tana birgima……

Kusa da ita ya tsugunna yace ……
  "Wae anya kina Sallah ma……?
Kamar an mintsineta ta mike tsaye sannan tayi shige toilet ta fancalo alwalarta ta fito babu ko hijab ta kabbara sallah!Yana tsugunne amma tayi sallah yafi raka'a Sha biyu……
  Tsayar da ita yayi yana fad'in "Wae Sallan ba zata k'are bane……"

  A Cikin ruku'u tace "Har da ta gobe nake!
Shiru yayi yana kallonta har ta gama sannan tace "Na gama sallah Bunkul!Na cigaba da kukan?
 Girgiza kai yayi yana fad'in "Ki bari sae anjima tukun……"
  "To…amma Bunkul Waccen matar bata sallah fa…"ta fad'a a hankali tana kallon kofa
 Banza ya mata ya mike ya shiga toilet ya hada mata ruwan wanka sannan ya kwala mata kira!bata dauka wanka zai mata ba ta shiga toilet din……
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*πŸ‘ˆ


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


          Page *71-72*


   Tana shiga ya riketa ya cire mata kaya!Fizge fizge ta fara tana fad'in "Bana so!dazu fa ka man ……"
  Daure fuska yayi yace "Ko ki tsaya ko na kifa maki mari!
 Murguda baki tayi tace "Sae in rama……"
Bata rufe baki ba ya maretan yace "Oya rama……"
 Dafe gurin tayi tana kallonshi sannan tace "Na yafe ma……"
  "Allah ya shirya ki……"
Bata amsa ba har ya gama mata wankan ya kama hannunta ya je ya shafa mata mai ya canza mata kaya tare da kashedin karta b'ata kayan jikinta……


【】

  "Munahurci dodo mai shi yakan hadiye!Cewar Maitafasa tare da wurgawa Kundum harara……

  "Mai jaraba……Yi hoho!Kundum ta fad'a tare da yin taga taga ta fad'a cikin fitsarin shanun dake malale tsakar gidan……

  Shewa Maitafasa tayi tare da gwatso tana murgud'a kugu tace "Kowa yasan ke munahuka ce Kundum shi yasa ma k'asa ta kadaki yanzu……!

 Kundum kam rike kugu tayi tana cije baki tace "Taimaka man Maitafasa da k'warank'watsa kamar bayana ya kare……"

  Yatsina fuska tayi taja majina ta matso tana fad'in "Duk da bana sonki kundum kuma bana son ku mutu ki barni……"

  Kama hannun kundum tayi ta d'agata ta mike da kyar tana dafa kugu har suka isa inda suka shinfida buhu suka zauna sannan kundum tace "Nagoda Maitafasa……"

  Tsaki ta ja da karfi tace "Komae sae kinyi Munahurci Kundum!meye na tausasa murya kuma?

  Banza kundum ta mata tana so ta rike gulmar dake cinta amma ta kasa a hankali ta tab'o Maitafasa tace "Wae Maitafasa……"

  A Harzuke ta juyo tace "To Uban me ye kuma kike tab'a man buje?

  "Ba Bujenki na tab'a ba!Wae ni kam ina labarin su Hafsuwalle?ta fad'a ahankali tana tsoron amsar da maitafasa zata bata……

  Banza ta mata tare da jan dogon tsaki ta kai kwanon fura a bakinta !

 "Maitafasa kinji labarin Mijin Buwale kuwa……? ta sake fad'a cike da gulma……

 "He ni Maitafasa na shiga uku!Shin ke Kundum idan bakiyi gulma ba baki jin dadi ne?

  Tab'a hannu tayi tana fad'in "AA Maitafasa kawae naji ana fad'in wae amre zai k'ara ba tare da sanin buwale ba……"

  Tsaki ta kuma ja ta tattara bujenta ta mike ta leka ta katanga ta d'aga murya tana kiran "Buwale……"

  Da sauri Kundum tace "Mai tafasa me zaki fad'a mata……"

  Banza ta mata ta cigaba da k'walawa Buwale kira har ta leko da daurin gabanta tana fad'in "Lahiya ……?

  "Mijinki na nan?Ta tambayeta tana watsa hannu baya……

  Buwale tace "Eh Maitafasa lahiya?

Kallon Kundum tayi da tayi mutuwar zaune sae raba idanu take sannan tace "Ku zagayo tare turke za'ayi!

  Bata jira komae ba ta koma tayi zamanta tana watsa hannu!Tab'ota Kundum tayi tace "Dan Allah mai tafasa karki fad'a masu!Da k'warank'watsa karya nake babu wanda yace man mijin buwale zaiyi amre!tallahi jiya naga ya sayi hurar yar gambo shine na dauka ko sonta yake……"

  Yatsina fuska tayi tace "Ke dae ake ji……!

   Sallamar buwale da mijinta yasa cikin kundum sake duran ruwa tayi cikiciki da idanu tana kallonsu……
  "Lahiya Maitafasa……?
Watsa hannu tayi tace "Kundum tace mijinki zai kara amre baki sani ba!shine na kiraki ta fad'a maki ubanda ya fada mata!idan kuma mijinki ya fad'a mata to ta fad'a maki meke hadinta dashi……"

  Cakuma Buwale ta kaiwa mijinta tace "Aka ce me zakayi?

  Da yake tsayyaye ne ya tsinka mata mari tare da fincike rigarshi ya nufi fita yana fad'in "Da nasan wannan shashancin ne tallahi da banzo ba……"

  Buwale kam ba zafin marin ya dameta ba !kan kundum ta koma tana dunguri tare da tambayarta wanda ya fad'a mata!shiru kundum tayi tana raba idanu……Tas ta mata sannan ta na hargagi!dunguri kam da mauza Kundum ta shasu !sae da Buwale ta fita sannan maitafasa ta kalleta ta kwashe da dariya……

【】

  Tun tsakar dare Sumayya ke labour yayin da kugunta ya matse gam yaki bud'ewa!Asibiti ya kaita amma duk yarda aka so ta haihu da kanta taki yiyuwa saboda maganin da take yawan sha ya matse mata kugu ta yarda bara ya iya budewa ba bare ta haihu da kanta!CS aka shiga da ita cikin sa'a aka fito da Yarinyar ta kyakykyawa sak Ma'aruf sae da duhun da wasu bangarorin na jikinta da yayi kuma duk sanadin maganin matan da take sha……

  Sae da komae ya natsa sannan aka kira Madre da Maryam da sauran family din aka fad'a masu !asibitin kam cika yayi kamar anyi shela……

  Ma'aruf ya fad'a wa Madre cewa maganin matan da take sha ya hanata haihuwa sosaae Madre tayi mamaki don ita ko da Sumayyan zatayi aure bata dirka mata irin wadannan magungunan ba ……Ce mashi tayi zata wa sumayya fad'a ta daina sha idan ta warke……

  kwanansu Uku aka sallamesu!Gidan Madre aka koma da ita ……Kwata kwata Ma'aruf ya fita harkan Sumayya saboda so yake ya hukunta ta aka laifin da take,sossae ta shiga damuwa ta rasa inda zata saka ranta!ranar daren suna ta sami Madre a d'aki tana tambayarta wae ina yaya Ma'aruf duk yau bata ganshi ba ?

  Kallonta Madre tayi ta juyar da kai tace "Ki kira wayarshi mana idan ganinshi kike sonyi"

  Kamar tayi kuka tace "Ai baya dauka!

Duk da Madre ta san dalilin rashi daukar sai cewa tayi "Kin mashi laifi ne?

 Girgiza kai tayi tace "Ban masa komae ba…"
  A hankali Madre tace "Bata yiyuwa!

Hannun Madre ta kamo tace "Allah kuwa……"

  K'arama ta fad'o tana fad'in "Ba wani karya kike kin masa man!

  Kuka Sumayya ta saki tana fad'in "Kin gani ko Madre wae karya nakewa wannan shegiyar yarinyar……"

 Daure fuska tayi tana kallon K'arama sannan tace "Zo nan Hafsah ba na hanaki karyata mutun ba!

  "Ai sae tayi hakuri……"K'arama ta fad'a tare da ware hannu……

 Lokacin Madre ta samu ta ma sumayya magana akan magungunan da take sha!daga farko cewa tayi babu abunda take sha amma daga baya da taga ran Madre ya b'aci dole ta sauko tace tana sha……Sossae Madre ta mata fad'a tare da nuna mata illolin da abun zai janyo mata gaba……

 Daga Farko ta dauki fad'an sannan ta tsorata ganin cewa maganin yasa aka mata CS Amma daga baya sae ta fara tunanin idan babu maganin kamar barata yi daraja ba gurin Ma'aruf din!Don haka ta kira Beeba tace ta hado mata wasu……

  Ranar suna hidima sossae akayi yayin da yarinya ta ci sunan Madre wato HAFSAH……Suna kiranta da Udutti……Su ihsan sae murna ake an samu Sister……

  Watansu Biyu gidan harda K'arama!cikin dan lokacin ne Madre ta farawa K'arama amfanin da magungunan da aka bata!Cikin ikon Allah ta fara rage wasu abubuwan kamar fad'ar abunda mutun yaci sam ta daina!Ga wata natsuwa da ta shigeta.Ga kunya da Allah ya daura mata don ko had'a ido da mutane ba ta yarda tayi saboda kunya!Wani lokacin ma idan Ma'aruf ya shigo gidan kafin ya mata magana zata sulale ta bar gurin!Cikin wata biyu ta warke ras kamar ba ita ba!yayin da jin dad'i da kwanciyar hankali ya tabbata akan fatar jikinta……

   Ita kanta Sumayya yanzu tana jin d'ad'in K'aramar saboda kullun tana zaune gurin Udutti tana mata wasa!Idan kaga K'arama na dariya to tana gurin Udutti ne!

 Ko da zasu koma gidan Ma'aruf din Sumayya ta kafa naci sae sun tafi da ita saboda Madre cewa tayi a barmata ita ta samu abokin fira……

 Kwanciyar Hankali ta sake fito mata da usulinsu na Fulani !Tsaf ta juye kamar ba ita ba Sannan ko kadan bata kama da Hafsuwalle kallo d'aya zaka mata ka gane tsantsar kamar da tayi da MALAN LADO hatta Muryarta da yatsun hannunta duk nashi ne……

   Bayan wata hudu ne Ma'aruf ya k'ara tabbatar da warkewarta yace wa Madre zaya maidata gida!Ita kanta Madre din ba haka taso ba ta so K'arama ta zauna da su iya tsawon rayuwarsu saboda yanzu duk wanda zai zauna da K'arama bara ya so ya rabu da ita ba……

 Tana goye da Udutti Ya shigo da sallamarshi!kanta na k'asa ta amsa ta cigaba da jijjiga yarinyar!Bisa kujera ya zauna ta juya zata shige d'aki kamar munafuka……

  A Hankali yace "Bunkul……"

  Da sauri ta juyo ta saki dariya tare da rufe bakinta da hannu !kanta na kasa tace "Uncle dae ba Bunkul ba……"

  Dage gira yayi yace "Ashe yanzu kin iya……!
Hannu ta saka ta rufe fuskarta zata tafi …… *HAJJA CEπŸ‘ˆ*
&
*FEEDOHMπŸ’ž*
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*πŸ‘ˆ


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


          Page *73-74*


      "Zo nan Ina Auntyn ki……?

  Ba tare da ta juyo ba tace "Tana kitchen……"

  Tabe baki yayi yace  "Zo ki zauna anan ……"

A Hankali ta dawo ta zauna a kasa tare da tallabe yarinyar ta sunne kai k'asa……
  Cike da zolaya yace " Baki fad'a man me na ci ba a waje……"

  Still rufe fuskarta tayi da hannu ……
"Kunya ko Hafsah!Good……Gobe zan mayar dake gida kin ji ko!ko a bari sae wani month din bakya son komawa?

 Da sauri ta girgiza kai tana fad'in "Ina so mana……"

 Dariya yayi mai sauti yace "Kenan kin yarda ki koma ki ci gaba da cin tuwo kullun……"
 
Murmushi tayi kanta na k'asa !Sumayya ta shigo ta zauna gefenshi tana fad'in "Yaushe ka dawo ban ji ba……"

  Kallonta yayi a hankali yace " Kina can kitchen dama ya zaayi kisan na dawo!Me kike had'a mana naji kamshi ya cika mana gida……"

 Far tayi da ido tare da kama hannunshi sannan tace "Daddawa nake soya mana zamuyi kwad'on wainar da Madre ta aiko mana d'azu……"

  Mamaki ya hanashi magana na tsawon yan mintina sannan yace "Kwad'on Waina a gidannan Sumayya a matsayin Lunch dina?

  Fari ta kuma tace "Ai yaji albasa……"

  Tsaki ya saki da karfi yana fad'in "Ba zanci ba gaskia!Zan kai K'arama tawa Madre bankwana ki samar man abunda zanci kafin na dawo……"

  Turo baki tayi tana gunguni!banza ya mata yana fad'in "Bata ita ki dauko Hijab Hafsah…"

 A Hankali ta juya ma Sumayyan baya ta cire yarinyar amma sae cewa tayi "Ki je da ita mana……"

  Kallonta yayi ya tabe baki had'e da girgiza kai yace "Idan ta maki yau gobe bara ki ganta ba……"

  Da sauri ta kalleshi tace "Ina zata……?

  Kai tsaye yace "Gidansu……"tare da mikewa tsaye……shiru tayi tare da binta da ido kamar mai nazarin wani abu yayin da jikinta yayi sanyi sossae……

  Bata ce komae ba ta shiga daki ta dauko Hijab suka tafi!

  Bankwana sukayi da Madre sossae ta hada mata yan kayan sawa tare da chocolate masu yawa tace ta bawa yan garinsu tsaraba sannan ta tsinto tsufaffin kayanta tace ta bawa yan garinsu suma!Ita kanta Madre din daurewa kawae take amma har ga Allah bata son K'arama ta tafi!lokacin da ta rakosu harabar gidan ta bawa Ma'aruf 100K din da Abban ya bawa K'arama tace ya biya da ita super market ya mata sayayya!Ma'aruf din yana lura da Madre da ta juya ta goge hawayen da suka zubo mata!A sanyaye ya amshi Udutti dake ta tsala kuka ya shiga motar yayin da K'arama ta shiga itama tare da hade kai da guiwa ta saki kuka mai sauti……

  Driving kawae yake amma sam kukan ya hanashi natsuwa!Cikin lallashi yace "Bakya so ki tafiya ne Hafsa……"

  Girgiza kai tayi har lokacin tana duke tace "Ina son ganin Ummata da yaya Lauratu!kuma bana so na bar Madre na kuka……"

  Shiru yayi yana kallonta sannan yace "Bara ki barta ba kinji ko Hafsa!Zan je wata rana na daukoki ki mana hutu kinji ko……"

 Gyada kai tayi a hankali……

 "To bar kukan mana Small mom!kina son Makaranta?

  Still gyad'a kai tayi tare da dagowa tana kallonshi…

  Baiyi tunanin kaita super market ba ya wuce da ita gida sannan ya fita yayo mata tsarabar……

【】

  Sae da ya fara kaita gidan Hakimi sannan!Shi kanshi Hakimin bai ganeta ba sae da Ma'aruf ya mashi bayani sannan ya ganeta!mamaki yayi sossae ganin yarda ta koma kamar ba ita ba!ko da Hakimi ya tok'aleta da magana shiru tayi tana sinne kai!hadashi da guard akayi sannan suka nufi kauyensu……

  Kundum ce ta fara ganin motarsu ta katanga!Da gudu ta iske maitafasa a bukkarta tace " Mai tafasa bature ya dawo!

 Bingil ta fito tana fad'in "Yana ina na buge hege!!

  A Tare suka fita sae dae kafin su fita waje har motarsu ta wuce kauyen su Hafsuwalle!Da daurin kirji suka nufi kauyen kamar zasu tashi sama……

  Dae dae gidan Ardo motar ta tsaya yayin da Ma'aruf da guard din suka fara fitowa!Mutane suka yi cirko cirko suna zuba ido!Zulai dake wanka ta fito da gudun tsiya jin cewa Baturen da ya dauki K'arama ya dawo……

  Fitowar K'arama daga mota yasa numfashin mutanen dake gurin ya sark'e kamar had'in baki suka kira sunanta tare da dafe baki K'a.. K'a.. K'arama…!!!

  "Ta shiga engini tayi bilihin (engin bleaching)……"cewar Zulai tana dafe bak. Hafsuwalle kam kusan mutuwar tsaye tayi na ganin K'arama ta canza kamar ba ita ba yayin da Lauratu ta k'araso gurin ta tsaya sae kyarma take son k'arasawa gurinta take tana gudun ta kama K'arama guard d'in dake gurin ya daketa……

 Murya a sarke tace "K'arama..!ke ce kuwa?" Murmushi tayi ta juya tana kallon Ma'aruf sannan ta rufe fuskarta da tafin hannunta k'arasawa tayi wajan ta tare da kwantar da kanta bisa kafad'ar Lauratun……

  "Ta kwarankwatsa ita ce!K'arama ke ce kika koma haka?!Aradun Allah sak Ladon Maitafasa badaban da bature kika zo ba babu abinda zai hana muce fatalwar ladoce tayi suffar mace……" Cewar Jummai tana tafa hannuwa!
 
K'arasowar Maotafasa wajan tana fad'in "Kai ku bani guri!Ta k'warank'watsa yadda yasa aka ci mutuncina a birni yau sae na ci……!Shiru tayi tare da kafe K'arama da idanuwa baki sake kirjinta ya tsananta bugawa cikin sarkewar murya Maitafasa tace!

    "Ladona……!" ta sulale a wajan ta sume sabida tsabar ganin suffar d'anta lado ajikin k'aramar yarinya. Da kyar aka samu ta dawo hayyacin ta idanunta akan K'arama baki na kyarma tace,

     "Lado na..." Ta fad'a tare da fashewa da kuka ta cigaba da fad'in "Dama shege na biyo Wani a kamani bayan shi sanda akayi iskancin yana kwance ba lahiya?"

 Mutanen gurin kam kaurewa suka yi da surutu kasa-kasa, zuwan Ard'o ne yasa Lauratu kama hannun K'arama suka shige ciki yayin da Ard'on ya ja hannun Ma'aruf suka shiga bukkar shi yasa Inno ta kawo mashi fura……
 
Mutanen gurin kam tsaye suka yi suna maganganu K'asa k'asa……

Godiya sosae Ard'o ya masa sannan ya k'ara da cewa "Ranka ya dad'e duk wanda yaga yanayin Hafsatu ko ba'a fad'a bs ya san ta warke!Mun gode sosae Allah ya kaimu lokacin da zan biyaka alherinka nima."

Cikin natsuwa Ma'aruf yace "Ameen Baba!Amma nayi wannan abun ba dan a biyani ba……"

Dariya Ard'o yayi yace "Ai ko dole mu biya ka Da Hafsatu……"

Cikin rashin fahimta yake kallon Ard'on sannan yace " Na gode sosae amma ta ya za'a biyani da ita?ita kanta tana son zama gurin Mamanta bare ace a bani na tafi da ita gaba d'aya ……?"

  Cikin natsuwa Ard'o yace "Shin Hafsuwalle zata amri Hafsatu ne?

A Hankali ya girgiza mashi kai alamar a'a!

"To ka gani!ka ga kenan dole mu baka sadakar auren Hafsatu……" Ard'o ya fad'a a hankali.

Da sauri Ma'aruf ya kalleshi bakin shi na kyarma yace "Wace Hafsatu?

Kafeshi Ard'o yayi da ido yana fad'in "Hafsatu K'arama da kamaido mana da ita yanzu!shine kadae zamu iya biyan ka dashi akan taimakon da ka mana akanta……"

Da sauri Ma'aruf yace "Waccen yarinyar?yana nuna cikin gidan da hannu……

  Dariya Ardo yayi yana girgiza kai sannan yace "Idan na iya lissafi Hafsatu K'arama na da shekara bakwae!Kenan saura shekaru biyu ta cike Tara!wanda dama a ka'ida shekara tara muke aurar da 'ya'yan mu!kaga kenan idan na amrar da K'arama yau banyi garaje ba sae ta ida cike shekaru biyun a d'akin mijin ta…!"

Zumbur Ma'aruf ya mike yana kallon Ard'on kafin ya fita daga d'akin da sauri ya shige mota ……Biyo shi Ard'o yayi yana fad'in "Ka taimaka mana wallahi babu masoyin Hafsatu duk wannan yankin……Sun ce shegiya ce babu wanda zai bari d'anshi ya aureta……"

Da sauri Ma'aruf ya fito ya tsaya gaban Ardo yace "Karya ne ba shefgiya bace !"

Wuf Maitafasa dake jingine tana jiran fitowarsu tace "Idan karya ne kaine Ubanta?

  "Idan ina magana kika kuma saman baki wallahi sae na saka an rufe man ke……!" ya fad'a a fusa ce ……

Hayaniyar su ta kuma janyo hankalin Su Lauratu da sauran mutanen gidan suka fito waje……

  Watsa hannu tayi baya tana fad'in "Idan baka sa aka kulleni ba ka raina Uwaka!" ta karashe maganar tare da yi mashi dakuwa……

  Guard d'in shi ya taho zai kamata amma Ma'aruf ya dakatar dashi "Barta tayi abunda take so zuwa gobe bazata samu damar yi ba……"

  Watsa hannu tayi tana tafi "A Barni d'in ta Allah ba taka ba!Kulya Dubu saba'in a kurwar Maitafasa!Nan gani nan bari Maitafasa aniyarka ta bika!ta kwarankwatsa na dad'e da sanin ku duka munahukai ne!An d'auki yarinya ankai birni!an lalata ta !tayo bilihin ta goge (bleaching) ……to me ya hana ka barta acan ka amreta.......?


 

*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
&
*FEEDOHMπŸ’ž*
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*πŸ‘ˆ


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


          Page *75-76*


       Ard'o da ya kai iya wuya dajin abinda Maitafasa ke fad'a  bai san lokacin da ya kifeta da Mari ba sae gata zaune a k'asa tana bori a Fusace yace "Na gaji da rashin Mutuncin……" Bai rufe baki ba tayi zumbur ta mik'e tare da kwarfa mashi mari shima……

Hafsuwalle kam kuka ta saki a gurin ganin duk bala'in da ake yi akanta ne da d'iyarta yayin da mutanen gidan jikinsu yayi sanyi……

  Hannu Ma'aruf ya d'aga zai mareta amma K'arama ta rugo tare da rik'e hannun tana kuka tace "Dan Alla Uncle karka daketa..!"

  A Hankali ya mayar da hannun shi k'asa yana kallon Maitafasa……Maitafasa kam ihu ta saki tana fad'in "To Bakar munahuka ki barsa ya dake ni mana!kai kuma asararre yarinya ta hanaka d'aukar mataki!Yi huhuhu!Dangin 'yan iska, Idan kai kacika d'an Halak ne ka dauke su ka amre Uwar da d'iyar……!"

Kanshi ne yaji yana juyawa don tunda yake bai tab'a ganin kalar masifar wannan matar ba, anya tana da cikakkiyar hankali kuwa?Wani b'angare na zuciyar shi ya tabbatar mashi da hankalinta kawae tsabar jahilci ne kawai..!Ard'o kam hawaye  ne suka cika mashi ido A Hankali ya ja hannun Ma'aruf tare da kai shi bakin motar shi ya had'e hannayen shi biyu yace "Ka gafarce mu dan girman Allah."

Muryar Maitafasa suka ji tana fad'in "Yo ya tsine maka mana me ya shille ni ni Maitafasa?tsohun batau kawae!an dawo mana da bala'i cikin gari, ta k'warank'watsa kai ba d'an halak bane tunda har ka k'asa barinta gurinka ka amreta!wae ni Maitafasa za'a jonawa haushi shine har da tafiya da ita!ashe abun na wohine (wofi) sakarai kawai……"

 A Hankali ya juyo yana kallon K'arama dake zaune k'asa tana kuka cikin sanyi murya yace "Hafsah kin san menene aure?zaki iya aurena?na maki alkwarin rayuwa mai inganci!ban damu da kankantarki ba!bazan cutarki da ke ba da yardar Allah.!"

Kamar an d'auke ruwan sama haka gurin yayi tsit!yayin da Maitafasa tayi baya jikake timm ta darshe k'asa baki a bud'e tana kallon Ma'aruf!K'arama kam a razane ta d'ago tana kallonshi yayin da hawayen idonta suka kafe da sauri tace "Uncle Aure irin na yaya lauratu?

Gyad'a mata kai yayi idonshi cike da hawaye tsabar takaici da bak'in ciki……,

Cikin kyarma Ard'o yace "Zaki aureshi Hafsatu ki samu rayuwa mai inganci babu wani kwaciyar hankali a kauyen nan sae wuya da bakin jahilci ……!"

Hafsuwalle ta kalla wadda bata san lokacin da ta gyad'a mata kai ba tana rufe bakinta da hannu alamar ta yadda!Mayar da kanta tayi ta had'e da guiwa taci gaba da kukanta……

A Hankali Ma'aruf yace "Ku shiga muje gidan Hakimi……"

Sannan ya nufi K'arama ya sa hannu ya d'agata ya bud'e mata motar ya shigar da ita!Ard'o kam shiga yayi ya zauna shi da Sallau!

  Mai unguwa Ma'aruf ya hango yana k'ok'arin k'arasowa gurinsu wanda da alama yanzu ya zo gurin……

  Cikin Kyarma Mai unguwa yace "Ka gafarceni Tallahin Allah shanuna ne suka……

Bai K'arasa ba Ma'aruf ya cewa Driver su tafi……Suka tada mota suka wuce da gudu tare da bad'e mutanen gurin da k'urar taya……

  Suna tafiya Mai unguwa ya fashe da kuka yana kallon Maitafasa da ta daskare a zaune a gurin don har ga Allah bata tab'a tunanin Ma'aruf zai yadda da gatsan da tayi mai ba kawae tayi ne don ta ci mishi mutunci amma sae gashi shi ya ci mata nata mutuncin ya bad'a mata kasa a ido a bainar mutane……

  "Kin cuceni Maitafasa……" Mai unguwa ya fad'a cikin kuka……

Kundum da jikinta yayi sanyi tace  "Yau dai kam *ABINDA KE B'OYE* ya fito hili (fili) Tallahin Allah baki kyauta ba Maitafasa!Idan kin duba da kyau ta k'warank'watsa dubu K'arama jininki ce saboda ga tanan Sak Ladonki!kuma tallahi harta yatsun kafafunta nashi ne!Kuma tallahi ke ni kaina nasan K'arama d'iyar Lado ce domin zan iya rantsewa akan idona aka samu cikin ta, tun lokacin da Hafsawalle na gidan Lado nasha lek'ensu idan suna Rayuwar amre (aure)!Ni kaina ina mamakin su kamar jarababbu!sannan kuma tallahi wani lokacin Ladonki ne ke bukatar Hafsuwalle sae ta taimaka mashi har ya samu gamsuwa tana yi tana kuka tare da kale-kale dan karki isketa.... *!*

Duk abunda suke haka zan zagaya ta 'yar kofar dake bayan bukka ina lek'en su ina zagin su sabida ina ganin ai sa bari a samu waraka!Dan Allah Hafsuwalle ki yaheman (yafemin)……"

Ta K'arashe maganar tare da fashewa da kuka mai cike da nadama

Kuka Maitafasa ta saki tana harba k'afafuwa a k'asa tace "Amma kin cuceni Kundum kin ha'ince ni ta k'warank'watsa!me na maki haka a rayuwarki Kundum?"

 Mutanen gurin ne suka fara tofa albarkacin bakin su akan lamarin!Wad'anda suka ga K'arama suka fara zuzuta irin kamar da take da Lado yayin da wasu na fad'in har muryasu iri d'aya!Hafsuwalle kam kuka ta saki mai tsuma rai yayin da Inno ta ja hannunta da Lauratu suka shige cikin Bukkar ta……

  Maitafasa kam kuka ta cigaba da yi tana harba k'afafu kamar wata k'aramar yarinyar tare da jan majina yayin da Kundum ita ma ke kukan!sauran mutanen kauyen kam suka fara zarewa tare da tofin Allah tsine ga Maitafasa da Kundum……

Ma'aruf Kam suna zuwa gidan Hakimi ya kira Madre ya fad'a mata abunda ke faruwa!Ce mashi tayi a jirasu yanzu zasu biyo private jet ita da Abban shi su zo!sam bata k'yamaci abun ba sae dae addu'ar ta Allah yasa hakan ya zama mafi alkairi Alkhairi……

Hakimi ya tura motar Police a ta fi a d'auko Maitafasa yanzu nan kafin su k'araso!Cikin awa biyu Su Madre suka zo tare da Abbahn Ma'aruf!

  Suna isowa suka shiga fadar bayan sun gaisa Ma'aruf ya sake fad'awa su Madre abinda ya faru!Abban shi kam murmushi yayi irin nasu na manya yace "Ma'aruf kam Dan halak ne i sha Allahu zai nuna musu hallacci!ina Uban wannan yarinyar? ina nemawa d'ana Ma'aruf auren Hafsatu……"

Thumb Madre ta masa ya dukar da kai yayin da kirjin shi ke dukan Uku uku!K'arama kam rakub'ewa tayi jikin bango ta had'e kai da guiwa tana hawayen domin duk rikicin nan tasan akanta ake yi gashi har Ma'aruf na zubar da hawaye……

  Cikin kankanin lokaci aka d'aura auran Auren shi da K'arama wanda Sallau ya zama waliyinta tare da sadaki dubu dari……

  Kallo d'aya zaka ma Ard'o ka tabbatar da yana cikin farin ciki!Sadakin aka bawa Ard'o sannan aka yi duk abunda ya dace tare da sa hannun Hakimi sannan Ard'o da Sallau suka koma kauyen su!Yayin da K'arama da Madre da Abba suka juya katsina suka bi private jet suka koma aka bar Ma'aruf anan gidan Hakimi saboda akwae aikin da zayayi!

【】

  "Bala……!!"

Da gudu ya taho ya zube a kasa yana fad:in "Gani ranki ya dad'e……"

Yatsina fuska tayi tace "Kasan sassaken Bedi……?
  Da Sauri yace "Eh na sani ranki ya dad'e……"

   "Yauwa shi zaka jeka d'ebo min yanzu!"

 Mikewa yayi yana fad'in "To Ranki ya dad'e……"
  Banza ta masa ta koma cikin gida!mintina kad'an ya dawo rike da bakar leda ya mika mata Udutti ta basa wai ya jijjigata kafin ta gama girki!K'arbar yarinyar yayi ya koma dakin shi da ita tare jib'eta saman tabarmar shi ya ciga ba da bankar tabarshi……

Yarinyar tayi ta juye juye daga k'arshe ta fashe da kuka!banza ya mata amma jin kukan na damun shi ne yasa shi janyo kafafunta ya dawo da ita gaban shi yana mazurai!Ganin ba shiru zata yi ba yasa ya tafka mata duka a kirji yana fad'in "Dan ubanki ki min shiru!banda son banza irin na wannan matar meye na bani wani raino……!"

  Yarinyar ta cigaba da kukanta da k'arfi!babu tausayi ya d'auketa tare da tsinkulinta a cinya ya fita d'akin ya yiwa Sumayya sallama daga parlor……

  Fitowa tayi da NAN a cup ta mika mashi tana fad'in "Karbi ka bata may be yunwa take ji……"
  Idonta ya faka ya kuma tsunkuli yarinyar a cinya ta fashe da kuka yace "Ranki ya dad'e dan Allah ki karb'eta kinga kuka take yi……"

  Harara ta watsa mashi tana fad'in "Yarinyar ma baza ka iya rikewa ba!? to je ka yarda da ita kani ko……"
  Zai yi magana ta saki tsaki ta juya ta shige abunta!Shima juyawa yayi yana surutai ya koma d'akin ya kwantar da yarinyar a kasa yana fad'in "Baki yi Sa'ar Uwa ba Alqur'an……"

NAN d'in ya d'iba a spoon ya kai a bakin shi yaji da dad'i ai kuwa bai yi wata wata ba ya d'aga cup d'in ya shanye ta tas!bako tausayi......
_ALLAH ya nuna mana sabuwar shekara lafiya bada wayun muba ba dabarar mu ba Allah ya nuna mana k'arshenta da rai da lafiya da imani Amin_πŸ‘

*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
&

*FEEDOHMπŸ’ž*
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


     Page *77-78*

*H*akimi ne ya kalli Maitafasa wadda keta faman soshe-soshe tana wuwulk'ita idanuwa yace mata "ke wai ya sunanki ne ma?!"

Mai-tafasa ta sharce majina tana jan wata zuwa cikinta ba tare da tayi magana ba, tunawa da tayi da shegen dukan da taci kwanaki shi ya k'ara rud'ar da ita cikin tsawa bafadan hakimi yace "baza ki fad'a bane sai jikijnki ya gaya miki?!"

Da sauri sukaji tace "Suwaiba....!"

"Toh me yasa baki da hankali ne?!"

Hakimi ya tambaya yana tsareta da idanuwa, ta kalleshi da sauri tana rik'e da habarta cikin tsananin mamaki tace,

"Inji wane shege yace banida hankali? Aradu wuta bal-bal ban yaheba gaduk wanda yace maka wai banida hankali aheeee...."

Bafadan ne ya kuma daka mata tsawa ta hanyar cewa, "ke! Hakimi na tambayar ki kina rashin ladabi? Ana tambayar kine idan kina dashi ki fad'a idanma babu ki fad'a dan asan hukuncin da za'ayi miki."

Muzurai ta fara yi da idanuwa tana tunanin wanda zata zab'a hankalin ko rashin sa wanda ba zai sa a jibgeta ba, baki na rawa tana kallon Ma'aruf ko zai yi magana taji yayi shiru ranshi a had'e sai zabga mata harara yake bafadan ya kuma daka mata tsawa a rud'e Mai-tafasa ba tare da ta saniba tace,

"Da sauk'i dai aradun Allah Hakimi wani sa'in bana sanin nayi abu sai daga baya, dan Allah kada kasa a dokeni tsofai-tsofai dani...."

Tayi maganar tana matsar kwalla kamar gaske, tsaki Ma'aruf yayi dan yasan karya take kawai ta fad'a ne dan kar a k'ara dukanta, Hakimi ne yayi magana yana kuma kare mata kallo ganin ta kasa zama waje d'aya sai canzawa take.

Hakimi ne ya kuma kallonta da tsantsar mamaki ganin k'irik'iri ta nuna mai cewar  tana da matsala a kwakwalwarta, gyaran murya yayi tare da cewa,

"Toh koma dai menene kisa a ranki cewar kece dangin Hafsatu K'arama,an d'aura mata aure yanzu itada Ma'aruf kisawa ranki Hafsatu jikarki ce shi kuma sirikinki ne."

Dukan cinyarta tayi tana cewa "tallahi Hakimi na yadda da cewar K'arama 'yar lado nace domin *ABIN DAKE B'OYE* ya fito hili kamanin shine sak dan dai ita macace amma bazan fasa tsine mata ba domin itace ta cinye min kurwar ladona ba,tsakanina da K'arama sai Allah ya isahh...."

Rintsa ido Ma'aruf yayi yana jin tamkar ya shak'i wuyan Mai-tafasa, girgiza kai kawai Hakimi yayi tare da cewa,

"Tashi ki tafi..."

Cinyarta ta buga da hannu kafin ta mik'e tana gyara zani, Hakimi ta kalla tana gatsine cikin kuluwa tace mai,

"Rankashi dad'e abani na mahin mana kur'anin Allah sisin kwabo bana magani gahe mai-unguwa ba zuwa d'aukata zaiyi ba."

Ma'aruf ne ya zaro 1k yabata dan yasan kakar K'arama ce hakan yasa ya bata amma badan halinta ba,ganin wanda ya bata ne yasa ko na gode bata ce maiba ta kalli Hakimi tare da washe mai jajayan hakuranta wad'an da wasu suka fara cirewa tace,

"Ranka shi dad'e toh yanzu kuma heyauhe za'a nemeni?!"

Ko kulata Hakimi beyi ba ganinta akwai surutu sai bafaden shi ne ya rakata har bakin kofa tana fad'in.

"Aradun Allah Hafsatuwalle munahika ce, tazo kuma ta haifi mayya gashi nan ta cinye kurwar mahaifinta ta rasa tsuntsu ta rasa tarko ta kare a zaman gidan arna da karuwai oh ni Mai-tafasa Allah gata na nima dan nafi karfinta ne da tuni k'ila ta lasheni....."

Har aka fitar da ita bakinta be mutuba Ma'aruf yayi tsaki tare da mik'ewa yayiwa Hakimi sallama akan washegari zai dawo,hotel yaje ya kama baki d'aya ya gaji kanshi tamkar zai fad'i dan tsananin ciwo da karad'in Maitafasa.

Wanka ya fara yi sannan yayi sallolin da ake binshi azahar da la'asar, gado ya hau tare da d'aukar phone d'inshi nan ya tarar da miss call wanda kusan duk na Sumayya ne, Madre ya k'ira yaci sa'a ta d'auka, ajiyar zuciya ya sauke tare da kiran sunanta,

"Madre...!"

"Na'am Ma'aruf ya akayi?!"

Kwanciya ya gyara tare da lumshe idamuwa, k'irjinshi banda bugawa ba abinda yake yi da kyar ya samu yace,

"Kun k'arasa ne?!"

Madre tace "A'a muna cikin motar Ma'aruf mun kusa dai,kabi komai a hankali idan ka dawo maya magana kaji ko?!"

"Eh Madre amma bana son Sumayya taji yanzu har sai na dawo."

Ma'aruf ya fad'a cikin sanyin murya, dariya Madre tayi cikin sanyaya rai tana shafa kan K'arama da tayi bacci tace mai.

"Toh ai ba komai sai ka dawo Allah yayi maka albarka." Yace amin daga nan ta bama Abba shima yayi mai fatan alkaire tare da addu'ar dawowa lafiya.

Sumayya ya kira bayan sun gama waya dasu Madre, cikin kashe murya tace mai "Yaya tun d'azu nake kiranka kun k'arasa ne ka juyo?!"

"Sumayya... *!*" ya kira sunan ta cikin janshi, sake kashe murya tayi tana daga kwance akan doguwar kujera tace "uhmm Yaya nah." Ma'aruf yace "ina Udatti naji ban jiyo motsinta ba ko tayi bacci ne?!"

"A'a wallahi Yaya tana wajan bala tun d'azu,wallahi ta isheni da kuk....." Bata k'arasa ba taji ya rufeta da fad'a wanda bata tab'a jin yayi ba a rayuwarta.

"Ur not serious Sumayya,jaririyar zaki bawa me gadi ajiya? Wallahi wallahi baki da hankali 'yarki mace wadda bata son komai ba amma baza ki iya killaceta ba sai dai ki bawa getman? Sumayya kin kasa killace 'yarki da kanki wanene zai kular miki da ita? Idan bakije kin karb'ota ba yanzu wallahi sai ranki ya b'aci mtwwww... *!*"

Ma'aruf yaja wani katan tsaki kai da kaji shi kasan ankai mutum mak'ura,yatsina fuska Sumayya tayi tare da gyara kwanciyarta. Bata dad'e ba sai ga Bala yayi mata sallama mik'ewa tayi tana hararar sa yayi kasa da kai tare da cewa,

"Wai gata inji oga."

Sumayya ta fizgi yarinyar tare da fad'in "dallah can bani ita dama ba son rainanta kake ba mtww aikin banza kawai."

Shi kam Bala da ya samu ta k'arb'eta sai ya sulale shima yana cewa "kut aikin banza nayi gadinku sannan a wani bani raino dan tsabar son banza da rainin wayo." Yayi bakin get inda yake zama ya zauna yana sharce gumi.

Kwantar da yarinyar tayi ta koma d'aki ta kuma had'a mata NAN sannan ta dawo zama tayi ta dinga tura mata duk cikin haushi dan Sumayya ta tsani raino (wa iya zubillahi ace ka haifi d'a/'ya a cikin ka amma kana hantarar shi baka son hidimta mai kuma kasa ran jin kanshi a gareka gadai Udutti bata yi sa'ar uwa ba Allah ya rabamu da irin wad'annan iyayan).

Tana bata tana sha ham-ham sabida tsananin yinwar da takeji kafin wani lokaci ta shanye tayi bacci,kayan jikinta dukun-dukun kasan cewar bala kawanta da ita yayi akan tabarmar shi gata duk k'asa baya karkad'ewa amma Sumayya ko ta cire mata haka ta barta tana jin haushi wai duk akan tane bata bari sunyi waya da Yaya Ma'aruf cikin nutsuwa ba.....


*{{ }}*

Maitafasa na komawa gwadabniya ta fara yiwa kundum tijara wadda ita kam shiru tayi dan tasan tabbas dole sai Maitafasa tayi hakan akan b'oye mata duk wasu abubuwa dake *b'oye* cikin takaicin bakak'en maganar da Maitafasa ke gayawa kundum tace,

  "Wuta balbal Maitafasa idan ki kuma ce min munahika, na sanki sarai a lokacin idan na sanar dake abinda ke faruwa zaki hanasu kusantar juna bayan hi ladon hine yake bid'ar Hafsatuwalle, yo banda toshewar kwakwalwa ai kinhi kowa sannin halayyar Hafsatuwalle amma kika yi mata wannan herrin sabida kinhi kowa son d'a, yo dama ni bani da d'a bare jika hiyasa na biye miki yadda kike so....!"

Kukan kura Maitafasa tayi kan Kundum nan da nan suka kaure da kukawa tamkar yara da gudu su Asibi suka shigo gidan aka b'anb'are Maitafasa daga jikin Kundum sai uban haki suke tsabar ko wacce taji jiki.

"Ta kwarankwatse Kundum kin cuceni hegiya munahuka Allah ya isa tsakanina dake algunguma aradun Allah bazan yahe miki ba...."

"Oho dai ko kina so ko bakki so K'arama jikarki ce, yo ma ai ko maitace toh ajikinki ta gada kwarankwatsa dubu ma kuwa..."

Askwane Maitafasa ta kuma yowa kan Kundum aka tare ta nan da nan ta fara surfawa Kundum zagi taba kwashe mata albarka da kyar aka samu tayi shiru amma cikin ranta ba wai hakura tayi ba sai ta yiwa Kundum abinda sai sa ta kasa bacci ranar.


*{{ }}*

Washe gari tunda safe Ma'aruf yaje suka yi sallama da Hakimi, kauyan su Hafsatuwalle ya biya yana zuwa suka had'u da Sallau zai fito daga gidan, gaisawa suka yi a mutunce kafin Ma'aruf yace.

   "Yauwa Sallau dan Allah ko zan samu ganawa da Umman K'arama?!"

Kallonshi Sallau yayi na 'yan lokuta yana dariya sannan yace "kwarai ma kuwa me zai hana, bari naje na shaida mata he ka higo.."

Ma'aruf ya girgiza kai alamar toh sannan Sallau ya juya dan sanarwa da Hafsatuwalle zuwan Ma'aruf, zaune ya tarar dasu ita da lauratu da inno suna karin kumallo ya gaidasu sannan ya sanar da Hafsatuwalle sakon Ma'aruf.sai da kirjinta ya buga dan ta d'auka da K'arama ya dawo cikin rawar murya Hafsatuwallen tace,

    "Sallau da..da..da K'arama ya dawo?!"

Sallau ya kalli Hafsatuwalle yaji wani mugun tausayin ta na ratsa shi, tsaye ya mik'e yana cewa,

   "A'a Umma shi d'aya ne yazo ai yacce min ita tayi gaba zuwa birnin su..."

Ajiyar zuciya ta sauke tare da ajiye farau-farau d'inta, wani kod'add'an hujjabin ta shi ta sanya duk yasha d'inkin zare da allura tayi kofar gida, Ma'aruf na hangota ya k'arasa wajanta suka shiga rumfar Ard'o Hafsatuwalle ta tsugunna tana niyar gaidashi. Duk da cewar a shekaru ya girmeta kawai dai auran kauye ga rayuwar wahala sai tayi kamar wata tsohowa me shekaru, da sauri Ma'aruf ya tsugunna shima suka hau gaida junansu.

   "Umma dama tafiya zanyi shine na biyo muyi sallama, insha Allah zan rik'e miki Hafsat da gaskiya da amana, kuma wata rana zaki yi alfahari da ita a matsayin 'yarki, Umma muna bukatar addu'arki, sannan ina da wata matar harda yarinta guda d'aya......"
*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


     Page *79*

Sunkuyar da kai Umma ta sake yi tana matsar hawaye, ya zata yi dole ta yadda domin zaman K'arama a gurin su shine mafi jin dad'inta da kwanciyar hankalinta, cikin rawar murya tace mai,

  "Mun gode Ma'arufu Allah ya saka da alheri ya baku zaman lafiya da duka matan naka, nasan baka son auran K'arama dole aka yimaka kayi hakur...."

Saurin katse ta yayi ta hanyar cewa, "a'a Umma ki dena cewa haka, dama can Allah yayi Hafsat mata tace so babu yadda zanyi ki dena damun kanki."

Mik'ewa yayi tare da zaro 10k ya ajiye mata kusa da kafarta dan yasan idan ya ce sai tasa hannu toh zasu d'auki lokaci shi kuma sauri yake dan jirgin karfe tara da rabi zai bi, da sauri yabar rumfar jin zata fara mai magiya akan kud'in daya bata,mota ya shiga drive yaja shi zuwa airport be dad'e ba jirgin su ya lula.....

*******

Gidan Madre ya fara zuwa, yana shiga yaji tsit ba kowa a parlor sai ya nufi kitchen dan ya san ba'a raba Madre da shiga kitchen yana zuwa nan ma bata nan. Kanshi ya girgiza sannan ya nufi upstairs nan ya fara jiyo muryar Madre na waya, a hankali ya murd'a handle d'in ya bud'e ya shiga, zaune ya tarar da Madre a bakin gado waya take da Yaya Maryam tana bata labarin auran Ma'aruf da K'arama.

   "Bari kawai Maryam ni kaina mamaki nake sai dai ba'a mamaki da ikon Allah,

   "Oho ni kaina ban san ta inda za'a fara sanar mata ba kinsan inajin tana bawa kawayanta labari akan duk ranar da Yaya Ma'aruf yayi mata kishiya haka tace ko ita, ko shi ko amaryar sai sun bakunci lahira, bari kawai Maryam ni kaina bansan yadda zanyi da Sumayya ba bari anjima mayi wayar kin ganshi nan ya dawo..."

Katse wayar tayi tana kallonshi duk yayi wuri-wuri kamar marar gaskiya, shagwab'e fuska yayi kamar yadda yake mata idan yaga suna waya da Maryam kamar zasu cinye juna cikin halin gajiya yake fad'in,

   "Madre nayi tafiya na dawo amma kinyi min banza sai biyewa ya Maryam kike ina shan wahala."

Dariya tayi tana k'okarin bashi amsa sai ga K'arama ta shigo d'akin jikinta d'aure da towel tayo wanka kunnanta duk kumfa,kallon ta suka yi daga shi har Madre baki bud'e yayin da ita kuma tana ganin Ma'aruf ta b'oye fuska alamar kunya ta k'arasa wajan Madre tana cewa,

    "Nayi wanka."

    "Kinga kunnanki kuwa Hafsat? Duk kumfa sai da nace ki bari nazo nayi miki amma waike kin girma bakyaso harda ce min yanzu Udutti za'a dinga yiwa wanka gashi nan ai duk baki fita ba."

Madre ta fad'a tana janyo ta jikinta tare da d'akko cotton bud tana goge mata kumfar, K'arama kuwa bata juyo ba ta fara k'ok'arin gaida shi.

    "Uncle ina kwana ina Udutti zanje wajanta."

Yana kallonta ya tab'e baki tare da cewa "ke yanzu duka-duka guda nawa kike da zaki ce an dena yi miki wanka? Lallai ma toh gashi nan duk wankan beyi kauba...."

Ba tare da ta damu ba ta kuma kallon Madre "Ina kayan da zan saka uncle ya kaini wajan Udutti...?!"

    "Gasu nan akan gado."

    "Wai Madre baza ki sake mata wani wankan ba..?!"

K'arama ta turo baki bata iya kallon shi ba tace, "toh ba sanda ina gidan su Udutti da kaina nake yi ba, kuma shine yanzu za'a dinga yimin,nidai bana so."

Shareta yayi ganin ita adole a kyaleta ya kalli Madre yace "inajin yinw fa and inason zuwa gida kinsan basu san kwana zanyi ba."

Mik'ewa Madre tayi bayan ta mik'awa K'arama wasu riga da siket na les dark blue da zanan fari-fari ajiki sannan ta fita tana cewa "gasu nan kisa kai kuma kafito dining gashi nan zan had'a maka." Ma'aruf yace toh tare da kallon K'arama wadda ta juya tamkar wata babba tana sa kaya bayan ta rufe jikinta da towel d'in, kamar yayi shiru ya fita sai kuma yace,

    "Toh me kike b'oyewa haka?!"

Bata juwo ba tace mai "Toh ai kaya nake sakawa."

   "Uhmm! Shine kike wannan sunkuye-sumkuyan? Idan banda abinki nima me iya saka miki ne, any way idan kin shirya kizo sai muje gurin Udutti d'in tare...."

Yana kaiwa nan ta bar bedroom d'in yana dariya,ita kuwa K'arama tana gamawa ta fito kayan ba karamin amsarta suka yi ba nan ta nemi guri ta zauna tana jiran ya gama su tafi duk ta k'agara taga Udutti ji take kamar ta shekara basu had'uba.

Ma'aruf na kammalawa suka yiwa Madre sallama suka fito, K'arama tace "uncle toh da ka tambaye ni zan iya auranka ka aureni d'in?!" Yayi saurin kamo hannunta cikin nashi ya tsuguna sitin fuskar ta yace "lil Mom kiyi shiru kidena fad'a kar aunty Sumayya taji ta duke ki kinji ko?!" K'arama tayi kasa da kai tare da ware idanuwa tace "Toh uncle, kaga kuma danaga Yaya lauratu naga cikinta kato itama haihuwa zata yi?!" Ma'aruf ya mik'e tsaye suna tafiya yace mata "eh mana."

Da sallama suka shiga cikin parlorn amma ba kuwa, K'arama ya kalla dake faman lek'e-lek'e yace mata "ina..." Ma'aruf be k'arasa ba ya hango Sumayya ta fito sanye cikin wasu 'yan iskan kaya tana wani irin tafiya tamkar baza ta yi tafiya a k'asa ba.

"Oyo-yo honey."

Sumayya ta k'arasa gurin shi tare da ware hannuwa ta tayi hugging d'inshi tana ta faman murmushi, kukan Udutti ne yasa K'arama yin cikin d'akin da gudu tana tsalle, kallan Sumayya yayi tare da cireta a jikin shi yana binta da kallo a hankali yace,

"Kinyi kyau but matsalarki d'aya baki da kunya. Sumayya be dace ace da kika fito kika ganni da yarinyar nan ki k'araso a haka ba, jifa sauran kad'an ya rage a hango pant d'in jikinki idan ma akwai..."

Ma'aruf ya fad'a yana nuna tsagar jikin dugowar rigar jikin Sumayya,tsagar da aka yiwa rigar tundaga k'asa har sama wajan kugunta kad'an ya rage ta rab'e biyu,kirjinta kuwa rabin shi a waje yake ko bra bata saka ba. Jikinta tabi da kallo tana son gano illarta, cikin shagwab'e fuska tana shafar fuskar shi tace,

   "Honey ai ni bamu yi da kai zaku dawo da Hafsa ba so yanzu ma bansan da ita kuka shigo ba kuma ni ina son na burgeka ne shi yasa na k'araso."

Ma'aruf ya kuma jan numfashe tare da kama hannuwanta suka wuce bedroom d'in shi Sumayya sai murna take yi, dama ta riga ta banki abubuwa tayi cushe-cushenta a HQ duk dan farin cikin shi, aikuwa sai da ya biye mata duk kanainaye shi tayi har sai da suka raya ranar.

Sauri yayi ya shiga wanka dan har yau gani yake kamar K'arama na ganin abubuwa idan anyi, cikin shirinshi ya fito na k'ananan kaya jar riga ce me gajiran hannu gabanta anyi rubutu ansa *_stay with me_* ya sanya blue d'in Jean's yayi kayau sosai.

A parlor ya gansu K'arama sai wasa take wa Udutti yarinyar sai b'angula dariya take tana cilla kafafuwa, murmushi yayi ya k'arasa wajan yarinya d'aukar ta yayi a kan cinyar shi ya d'aura ta ita kuma K'arama tayi saurin komawa kusa dashi ta zauna tana wasa da yatsun hannuta,

    "Lil Mom yanzu dai kinga Udutti sai ki tashi na maidake wajan Madre..."

Had'e rai tayi tana turo baki batayi magana ba, mik'ewa yayi tsayi tare da cewa,

   "Oya tashi kisa hijjab mu tafi sauri nake yi zani wani guri."

   "Uncle ni kabar ni anan nafi son nan gidan wajan Udutti.."

K'arama tayi maganar kamar zata yi kuka dan bata son rabuwa da yarinyar,ganin haka yasa shi mik'ewa tsaye yarinyar ya bata ya juwa ya tafi yana cewa,

    "Sha zaman ki lil Mom nan da can duk d'aya ne..."

Wasan ta cigaba dayi mata sai dariya take yi, Sumayya kuwa bata fito ba bacci taci gaba dayi ko wankan ma bata yi ba har Ma'aruf ya dawo wajan karfe 2:30pm, a kwance ya tarar da K'arama k'asan center carpet tayi shiru daga gani gajiya tayi da wasan gefenta Udutti ce keyin bacci hankali kwance, k'arasawa yayi gurinta tana ganin shi tayi saurin mik'ewa zaune tayi k'as da kanta tare da kamo kafar Udutti tana wasa dashi.

    "Lil Mom ina auntyn taki take?!"

Shiru K'arama tayi bata yi magana ba ya sake cewa,

   "kunci abinci kuwa?!"

K'arama ta girgiza mai kai alamar a'a,mamaki ne ya kamashi direct ya wuce bedroom d'in Sumayya bata ciki ya wuce nashi kwance ya hangeta yadda ya barta haka ya dawo ya tarar da ita wani kolulun takaici ya tsaya mai a makoshi ya k'arasa cikin takaici ya daka mata wata uwar tsawa wadda tasa Sumayya tashi da sauri cikin razani.

  "Sumayya wai me kika d'auki aure ne hmm? Kin d'auki aure a matsayin kawai mu kwanta tare duk sanda muke so, baki son cinaba bare shana, Sumayya kinfa haihu yanzu kin zama uwa Udutti tana bukatar kulawarki da tattalinki tarbiyarki ta yadda nan gaba zata ji kanki tayi alfahari dake amma itama baki damu da itaba bayan ke kika haifeta da cikinki a haka kike son nuna min so? You don't know how to take good care to my child, yanzu kinsan lil Hafsat na gidan nan tana miki raino amma daga ita har 'yar taki baki san halin da suke ciki ba, toh ki fita kiji ki samar mata wani abun taci..."

Parlor ya koma yana zuwa ya tarar itama K'arama tayi bacci ta manne jikin Udutti, kitchen ya wuce ya dudduba yaga a kwai komai na kayan abinci amma kullum sai dai tayi musu indomei da rana kuma wake da shinkafa, parlor ya koma yana aikin shi cikin laptop cikin shigar English wears ta fito har lokacin haushin fad'an da yayi mata take hakan yasa ta wuce bata kula shiba shima ya shareta.

Kamar ya sani indomie ta dafa ta zubo cikin plate biyu ta kawo parlor, kai da kaga indomie d'in kasan zata yi yaji sabida attaruhun dake cikinta, k'asa ya sauka yana tashin K'arama dan yasan yinwa ce ta sanyata bacci, tashi tayi taje ta wanke baki sannan ta dawo tana cin abincin.

Sumayya ta kawo musu nasu spoon d'aya yaci yature sabida tsabar yaji shi kuma baya son shi, ko ta tambaye shi dalilin da yasa shi kinci kawai ta gyara zaman plate d'in gabanta ta ci gaba da ci, jifi-jifi yana kallon K'arama tana ci tana sharar majina ga ido fal hawaye sabida yaji.

    "Lil Mom zaki iya ci kuwa?!

Ya fad'a yana kallon K'arama, tana ci tana bashi amasa, "Eh uncle zan iya." Kai ya kad'a ya koma yaci gaba da aikin shi duk kuwa da cewar shima yanajin yinwar....

Ana kiran sallar la'asar yabar gidan be dawo ba sai dayayi sallan isha'i, a parlor ya tarar da K'arama goye da Udutti sai faman jijjigata take yi kallon ta yayi tare da bin parlorn da kallo be ga Sumayya ba yace,

   "Lil Mom ina auntyn ki take?!"

Kanta a kasa tace mai "suna bedroom d'inta." Ya kad'ai kai sannan yace "kinyi sallah ko?!"

    "A'a."

Ta fad'a sai faman jijiga yarinyar take ita kuma tana waka irinta yara idan ana jijigasu zasu yi bacci,

    "Subhanallahi garin yayi aka yi haka baki yi ba?!"

K'arama kamar zata yi kuka sabida yawan tambayar shi tace "ai aunty Sumayyan ce bata fito ba kuna Udutti idan na tafi kuka zata yi fa."

Zama yayi yana mik'a mata hannunshi yace, "oya kawo ta nan kije kiyi sallah kafin Allah ya konaki da wuta."

Da sauri taje ta mik'a mishi ita kuma tayi hanyar bedroom d'in da yake a matsayin nata sai da ta kusa shiga ta juyo tana kallon shi tace mai,

   "Sallah biyu zanyi ko?!"

Ma'aruf ya kalleta yace "Eh magriba da isha'i sannan kiyi addu'a."

Shigewa tayi bata jima ba sai gata ta dawo wai ta idar, suna zaune yana tambayar ta yadda tayi sallar su Sumayya suka fita ya kallesu ya watsar  yana ci gaba da nunawa K'arama yadda ake yin sallah.

    "Ina yini Yaya Ma'aruf?!"

Cewar beeba tana murmushi k'asa k'asa tanajin wani abu na fisgarta game dashi, ko kulasu be yiba suka wuce beeba ranta a b'ace suna zuwa compound tace,

    "Kawata wannan mijin naki miskilancin shi yayi yawa, any way ni kinga tafiya ta."

Sumayya tayi saurin riko hannun beeba cikin sanyin murya tace "sorry kinsan shi besan hud'a da mata sai ni kawai kuma kema dan dai besan godun mawar da kike bayar wa bane amma zan sanar mai kiyi hakuri dai."

Beeba ta fizgi hannunta tayi gaba abunta itama Sumayya ta koma ciki tana ta b'acin rai wai yayi wa kawarta wulakanci.......


*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


     Page *81*

*W*ayar shi ya ciro daga aljihun gaban rigar shi gallery ya shiga ya zubawa wani hotanta ido tamkar yana photocopy d'in shi,shafar screen d'in yayi yana sauk'e ajiyar zuciya a hankali, yafi minta talatin zaune cikin motar yana kallon hotan kafin daga bisani ya rufe wayan ya ajiye tare da fizgar motar yayi hanyar komawa gidan Madre.

Yana shiga wani wrong parking yayi ya nufi cikin parlorn zaune ya gansu a kan kujera mai cin mutum uku gefe da gefe Bassam ne da BarraQ tsakiya kuma K'arama ce tayi shiru tana kallon face d'in phone d'in hannunta, a k'asa kuma a gaban su ikram ce da inteesar suna ta hira dasu zuciyar Ma'aruf ta sake sark'ewa a fusace yama manta dasu Madre a zaune a parlor cikin tsawa yace,

   "Your very stupid! Kin tashi anan ko sai na 6allaki, sannan ki d'auki mayafinki ki wuce muje ga aunty d'inki can ashe test zata miki shine baki fad'a ba kika biyo mu...!"

K'arama jiki na karkarwa ta kasa gane inda maganar Yaya Ma'aruf d'in ta nufa ciki rawar murya zata yi magana ya sake had'e rai tare da nuna mata hanyar fita yace,

   "Get out or else...!"

Da sauri kamar zata kifa tabar wajan tana matse idanuwa Madre ta kalleshi da mamaki itama a fuskarta tace,

     "Ma'aruf ya haka ne! Kwanan nan fa naga ka fara d'aukar zafi abu kad'an ka maidashi babba musamman idan laifin Hafsat ne, shin wani abun tayi maka da zaka dinga yiwa yarinyar mutane tsawa da fad'a?!"

Shiru Ma'aruf yayi tare da rintsa idanuwa ji yake tamkar azo ayi mai dukan tsiya dan yadda zuciyar shi ke turiri, ko samun damar magana beyi ba kawai ya juya yabi bayan K'arama, kafin ya fito har taje gidan sabida gudu tayi dan karma ya tarar da ita wani abun ya biyo baya. A tsaye ya ganta tana dube-duben inda zata hango aunty d'in amma bata ganta ba sai shi daya nufota k'irjinta ya sake bugawa tayi saurin yin baya yazo ya bud'e tashiga.

Suna shiga ciki da sauri Ma'aruf ya janyo K'arama, a cikin k'irjin shi ya sata tare da matseta tamkar zai tsaga kirjin shi ya zura ta, ganin haka ne yasa K'arama sakin kuka yadda bazai jita ba yayin da jikinta ya hau rawa kafafuwan ta suka fara yin sanyi tana neman fad'uwa. Shi kam Ma'aruf ajiyar zuciya kawai yake sauke wa yana shafar kanta a hankali, ya dad'e a haka lafin ya d'ago fuskarta yana kallonta, nan yaga tayi shab'e-shab'e da hawaye jikin shi yayi sanyi ya tallafo hab'ar ta idonta a lumshe cikin sanyin murya yace,

  "Lil Mommah why bakya jin magana ta ah? Ko ban isa da keba ne?!"

Bata bud'e idanta ba a haka ta girgiza mai kanta alamar a'a sannan ya kuma kura mata idanuwa musamman lips d'inta wanda take ta faman tsukewa tana tsotsar su yayi saurin tureta daga jikin shi. Tafiya ya fara yi ita kuma tana tsaye a inda ya barta dan har lokacin tsoro ne fal a zuciyarta uncle Ma'aruf ya sauya sosai gashi ta kasa gane inda ya dosa.

Zama yayi akan d'aya daga cikin kujerun parlon jin bata taho ba yasa shi jiyawa yana kallonta,kanta a k'asa tana wasa da k'asan rigarta cikin kasalalliyar murya yace mata,

  "Come here Momma...!"

K'arama taji ya fad'a ya kuma juyar da kanshi yana facing t.v, k'arasawa tayi tare da rakub'ewa jikin kujera sai faman sauk'e ajiyar zuciya take, kusa dashi ya muna mata yace,

   "Dawo nan tambayar ki zanyi."

A d'add'are ta tashi kusa dashi ta zauna tamkar za'a ce mata kulle tace cass, hannunta ya kamo yana matsawa a hankali jikin K'arama ya hau rawa sai faman raba idanuwa take yi murya a slow yace.

    "Lil Mommah so kike yi na mutu ne."

Da sauri K'arama ta zaro ido tana faman girgiza mai kai cikin tashin hankali, d'ayan hannunta wanda be rik'e ba tasa tana goge kwallar data zubo mata shi kuwa kallonta kawai yake yi soyayyar ta na k'ara azabtar dashi share hawayen tayi sannan tace,

   "Uncle menayi?!"

Kamar ya sanar mata gaskiyar *ABIN DAKE B'OYE* sai kuma ya kad'a kai tare da sakin hannunta, a hankali ta d'ago tana kallon shi suka had'a ido tayi saurin mayar da nata k'asa tana saukar da ajiyar zuciya alamun tayi kuka,

   "Uncle ina aunty chegozie d'in, kuma ni wallahi ban san zamu yi test ba bata gaya minba uncle.kuma k'ila mantawa tayi ai yau Sunday kaga bata zuwa sabida tana zuwa church...."

Kwantaccen gashin bakin shi Ma'aruf ya shafa cikin basarwa ba tare da ya kalleta ba yace,

  "Eh bata zoba ban san me zance ba shi yasa na fad'i hakan kin wani zauna cikin tsakiyar garadan maza kun manne da juna, toh ni ba irin tarbiyar da nayi alk'awari zan baki ba,

   Lil Mommah nasha sanar dake bana son in dinga ganin kina mu'amula da ko wanne namiji, ke ko malaman ku tsakaninki dasu shine su koya miki ko tsawaita yin questions bana son kina musu ko kuma yawan basu amsa idan sunyi muku questions..."

Waro idanuwa K'arama tayi cikin tsananin mamakin Ma'aruf, baki ta toshe  da tafin hannunta domin bata ma san abinda zata gaya mai ba, haka suka zauna yana ta janta da hira har dare lokacin da su Sumayya suka dawo, tare suka zo dasu ikram dan anan zasu kwana wajan K'arama koda suka dawo Sumayya bata tambaya ba ko K'arama tayi test d'in sabida ita 'yar I don't care ce....

*{{ }}*

   "Iyyyirrrrrrrr! Ahayyyyye!! Nanayeeee!!! Aradun Allah ko duk jikina kunne ne bani yadda da maganar ki Maitafasa, yo kin manta wacece Kundum ne kika zauna kina shirga min wannan uwar karyar?!"

Kundum ta fad'a tana gantsaro bayanta yayin da Maitafasa ta d'auki buta tayi makewayi ba tare da tace komai ba, tana fitowa taga su Asibi da lanto dasu buwale can sai ga baraka itama ta shigo Maitafasa ta fice majina da gefen zani ta k'arasa inda suke zaune da izgilanci tace musu,

   "Ku kuma fa haka waya sanar daku cewar na mutu da zaku zo kuna zaman makoki...?!"

Bawale ce tace "haba Maitafasa wane irin makoki kuma muda muka zo miki sannu da dawowa." Lanto ta d'ora da cewa "ke kam dai kin samu sa'a ana ta nemanki a birni kakarki ta yanke..."

Maitafasa ta kuma fece majina da gefen zaninta, goro ta b'alla taci sannan ta kalle su tace,

   "Kunjini da munahika Kundum, aradun Allah nasan irin zaman da zan ringa yi da ita wai daga fad'i mata cewar Hakimi na sona shine ta fara ruwan masifa har da cewa k'arya nake yi! Yo tallahin Allah banda na taka mai birki da sai dai kuji zance a gidajen radio.... *!*"

Gabaki d'ayan su babu wacce bata razana ba jin furucin Maitafasa, ita kam ta fad'a ta maze tamkar da gaske takeyi nan ta fito da dubu uku tana k'irgawa da wadda Ma'aruf ya bata da kuma wadda ta samu a bakin tasha sai wadda ta tsinta a kofar gidan Hakimi ta dawo a kafa batare da tahawo mashin ba, kallon da taga suna yi mata ne yasa ta cewa.

   "Aradu kunga kud'in nan! Toh hine ya bani su wai naci goro kuma ni kwarankwatsa dubu bani auran shi tsofai-tsofai dani... *!*"

Jikin kundum ne yayi sanyi lokacin da taga kud'in tasan lallai da gaske Maitafasa takeyi dan idan ba haka ba babu inda zata iya samun wad'an nan kud'ad'an masu yawa.

   "Aradu da kin sani kin yadda."

Asibi ta fad'a tana rik'e hab'a Kundum kam bata k'arayin magana ba Maitafasa tace,

  "A'a bani yin amre a hekaruna gara kam nayi zamana ni d'aya tunda dai babu lado na uban kowa ma ya mutu aradu."

 "Ni kam dama zai kira ni tallahi ba abinda zai hanani amran Hakimi... *!*"

  "Hehehe wi! Yo an gaya muku hakan nan nake he yasan abin da ya gani jikkina yace iya sona kundai son ba irin mu d'aya ba ahh toh..."

Sake-sake Kundum keyi ta yadda zata gano asalin gaskiya duk da cewar zuciyar ta neman yadda take da zancen Maitafasa. Haka suka ci gaba da zama kullum burin Maitafasa ta kuntatawa Kundum ita kuma tayi tayi takasa gano al'amarin dake tsakanin Hakimi da Maitafasa kasan cewar bata da hanyar da zata ji wani labari daga cikin gidan hakimi.......

****

   "Sannu kinji lauratu Allah ya saukeki lahiya wannan abu yana baki wahala aradu.."

Murmushi kawai lauratu tayi ba tare da tace komai ba bare ta amsa addu'ar da inno kiyi mata sabida tsananin kunya da kawaici. Hafsatuwalle ce ta shigo cikin rumfar zama tayi a can gefe tare da d'aukar gyad'a me b'awo tana b'arewa, inno ce ta kalleta tana fad'in.

  "Kunyi magana ne da Ard'o?!"

Hafsatuwalle ta kad'a kai alamar a'a sannan ta kalli inno tace "inno lahiya dai ko inci ba wani laihin nayi ba...??!"

   "Baki komai ba, dama batun kud'in sadakin K'arama ne kiga suna da yawa hene yace ko shanu za'a siya mata he a kiwata mata anan.."

Shiru Hafsatuwalle ta kuma yi dama inno tasan ba magana zata yi ba dan haka ta d'ora da cewa,

   "Nace mihi a siya dan haka he kiyi tasa musu alheri har Allah yasa itama tazo taga abubuwanta..."

Bata sake cewa komai ba suka ci gaba da hira har lokacin d'ora sanwa yayi kowa ya mik'e dan gabatar da nashi uzurin, haka rayuwar su ta ci gaba da tafiya yau da dad'i gobe babu har tsawan shekar masu d'an yawa.....

*{{ }}*

Yana zaune a cikin office aiki ne sosai a gaban shi kasan cewar kwana biyu baya nan yayi tafiya zuwa k'asar Cairo, files ne da yawa yana ta faman dubawa wayar shi ce tayi ringing sai da ya mulu sannan ya d'auki wayan, sunan Sumayya ya gani ya d'aga ba tare da yayi magana ba. Muryar K'arama ce ta doki cikin kunnan shi hankali a tashe, da sauri ya fara tambayar ta shima cikin tashin hankali.

   "Uncle! Uncle aunty ce gata nan tana kuka watak'il haihuwa zata yi, uncle ka taho dan Allah karta mutu... *!*"

   "Okk wait gani nan zuwa ki zauna a wajanta kinji ko.?!"

   "Toh."

Da sauri ya fito daga office d'in parking lot ya nufa mutane sai magana suke mai amma yak'i tsayawa da gudu yaja motar sai gida, yana zuwa upstairs ya nufa da gudu nan ya ga Sumayya a duk'e sai faman yarfa hannuwa take yayin da K'arama ke zaune a gabanta kamar me neman gafara sai kuka take yi itama, k'arasawa yayi tare da rungumo Sumayyan ya mik'ar da ita, kallon K'arama yayi tare da cewa,

   "Oya ki ciro kayan baby da nata ku biyo mu hospital yanzun nan keda drive."

Fita suka yi yayin da K'arama ta nufi inda kayan baby suke ta fara d'ebowa tana sawa cikin wata jaka shi kuwa direct asibiti suka wuce, suna zuwa aka shiga da Sumayya labour room. Ta jigata sosai gashi haihuwa tazo amma ta kasa yi da kanta sabida wajan a tsuke yake dole wannan karan ma aka sanar da Ma'aruf sai ya sa hannu anyi mata aiki dan ceto rayuwar su ita da babyn.

Dole Ma'aruf yayi sign aka shiga da ita, successfully aka yi aikin tare da ciro mata kyakyawan baby boy d'inta sai dai idonshi guda d'aya ya samu matsala dan wani abune ya tattare gurin yayi kamar shuri, Abba ne da Madre dashi Ma'aruf d'in suka shiga ciki nan suka ga yaron wanda shima sai anyi mai aiki an yanke abun.

   "Toh likita ina ita mahaifiyar yaron take?!"

Abba ya tambaya yana kallon doctor Al'ameen, furzar da iska yayi tare da fad'in,

  "Sorry Alhaji itama tana bukatar yin wani operation d'in co's akwai problem a gefen mararta wanda hakan yana faruwa ne ta sanadiyar shan magunguna da yawa musamman idan mace nada ciki shima babyn abinda yayi affecting d'inshi kenan... *!*"

   "Kinji ko Madre na gaya miki yarinyar nan bata jin magana, yanzu jibi ta lahanta min yaro na ta kuma janyowa kanta larura biyu a jikinta mtwww..!"

Ma'aruf yaja wani dogwan tsaki tare da fita a cikin room d'in, a reception yaga K'arama da Udutti zaune sunyi kalar tausayi, ko magana beyi musu ba ya wuce gurin mota tare da bud'ewa ya shiga ya zauna bayan ya kifa kanshi jikin steering.

    "Udut ina zuwa bari naje wajan uncle na dawo."

Jakar kayan ta tura kusa da kafar Udutti sannan ita kuma ta wuce wajan motar da Ma'aruf ke ciki, saidata kwankwasa kafin ta bud'e ta shiga. Ma'aruf kam be d'ago ba bare yasan ko waye sai muryar ta yaji tana kiran sunan shi, kasa amsa mata yayi illa kawai yana sauraronta ganin haka yasa K'arama cewa.

   "Bunkul me aka yi maka?!"


Da sauri ya d'ago yana kallonta cike da mamakin jin sunan shi da ta kira wanda ada shine sunan da take ce mai, k'asa tayi da kanta tana wasa da yatsunta.......


#Ana tare masoya
#hajjafeedohm lvs u*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


*INA kike ya hajja Fatee?! Here is your page, kiyi hakuri munyi iya yin mu wajan ganin anyi da yawa abun ya cutura but we promise you next page sai kin gaji da read more...*πŸ˜‚πŸ‘ˆπŸ’ž


     Page *82*


     "Mommah said it again please...."

Shiru tayi tana ci gaba da wasan da take yi da hijjab d'in jikinta, komawa yayi yajingina jikin kujera da bayan shi tunani yake yi kala-kala ganin haka yasa K'arama sake maida kanta tana kallon shi cikin sanyin maganarta ta kuma cewa,

  "Bunkul me aka yi maka, ko bata haihuba ne?!"

Wani sakaran murmushi yayi na gefen baki tare da numfasawa, ba karamin dad'in jin sunan yayi ba a bakinta. Tada motar yayi tare da figarta suka fita daga cikin hospital d'in, kallon shi tayi cike da mamaki cikin rawar murya take cewa.

   "Uncle ban sauka bafa dani ka taho."

K'in kulata yayi har suka k'arasa gida yayi horn me gadi ya bud'e shiga yayi ciki yana yin parking ya fito tare cikin kallonta yace,

   "Biyo ni."

Kamar jela haka ta bishi suka shiga cikin parlor, kamar rakumi da akala haka ta dinga binshi jikinta a d'ari-d'ari tana tsoran ko yauma wani laifin tayi mai ba tare da saninta ba, hannunta ya kama yana zanta zuwa ciki a mugun tashin hankali K'arama ta fara magana.

   "Dan Allah uncle kayi hakuri wallahi yau babu wanda na kula dan..."

Bata k'arasa ba taji ya matseta a jikin shi tare da d'ago fuskarta bakin shi ya zura a cikin nata ya fara tsotsa tamkar mejin yinwar shi(toh waya sani tunda ya dad'e yana b'oye son yin hakan)Lol.

Ya kusa one hour yana abu d'aya wanda har ya kaisu ga zubewa a k'asan tail's d'in parlorn, K'arama kuwa kuka ta dinga yi mai bayan ya sake ta komawa gefe tayi tana kuka harda birgima tamkar k'aramar yarinyar shi kuwa kasa motsi yayi shi yasa be hanata kukan ba can yaji cikin kukan ta wanda ke k'ara bugar mai da zuciya yaji tana cewa,

   "Uncle me yasa kake son lalata min rayuwa ta bayan kasan cewar rayuwar tawa tana hannun Allah tana gurinka? Uncle dama wannan dalilin ne yasa ka hanamin kula ko wane d'a namiji sai kai? Uncle dama irin tarbiyar da ka zab'a min kenan shi yasa ka haramta duk wani mutum indai namiji ne...?!"

Shiru yayi mata yanajin kukanta tamkar saukar ruwan dalma a cikin zuciyar shi, afusace ta mik'e tsaye tana hawaye tare da goge majina da bayan hannunta cikin tsananin kuka wanda yasa maganar tata fitowa a hankali take cewa,

   "Uncle why?!"

Cikin sanyin jiki ga wata masifaffiyar kaunarta na k'ara wulakantar da zuciyar shi Ma'aruf yace,

   "Enough Hafsat enough please! Ya kike neman haramta halal kike neman dilmiyar da zuciyata cikin kunci da damu bayan wanda nake ciki yanzu? Idan baki saniba yau ki sani Hafsat you are belong to me yes I mean ni d'aya nine naki kuma *ZAN RAYU DAKE* koda kuwa bakya so, sannan ke mallaki nace nini kad'ai domin kuwa ni mijinki ne...!"

   "Uncle wait! Wait! me yasa kake neman halattawa kanka abunda ya haramta a gareka? Kai nake gani a madadin mahaifina, Allah gatana kaine jigona uncle me nayi maka da na cancanci wannan hukunci? Dan Allah idan mafarki kake uncle ka temakamin ka farka ko zuciyata zata wanke min zargin da nake yi akan ka ayanzu dan Allah....!"

Tayi maganar cikin rushewa da kuka, daga bakin k'ofa suka jiyo muryar Yaya Maryam tana cewa,

   "Wacce irin magana nake ji haka K'arama! Uncle d'in naki kike gayawa wannan maganar?!"

Daga can bayan K'arama Ma'aruf ne yake ta faman girgizawa Yaya Maryam kai alamar karta tona mai *ABIN DAKE B'OYE* banza tayi mai ta ci gaba da maganarta tana nufowa wajan da K'arama ke a tsaye tare da kamo kafad'unta duka biyun tace.

   "Ki dena zargin uncle d'inki akan duk abinda zai yi miki domin bazai tab'a wulakantaki ko tuzarta ki, kiyi mai biyayya akan duk abinda ya umarceki akai domin bazai cuceki ba kinji?!"

Shiru K'arama tayi domin ta kasa amsawa taya dan yana marik'in ta za'a ce ta tsaya yayi mata duk abinda yaga dama bayan tasan ilar hakan da kuma harramcin shi cikin addininta ba zai yiwu ba hakan yasa ta fara girgiza kai tana k'ok'arin zame jikinta daga rik'on da Yaya Maryam tayi mata.

Ma'aruf kuwa guri ya samu ya zauna tare da kama kanshi ya rik'e yasan yau asirin shi wajan K'arama ya gama tonuwa tunda Yaya Maryam tazo. Ganin yadda duk ta rud'e ne yasa Maryam saurin yin murmushi tana kallon K'arama tace,

    "Kiyi hakuri wannan abun daya faru tsakaninku shirine, mumuka shirya yin hakan nida uncle d'inki akan ya gwadaki ko zaki iya biyewa samarin zamanin nan kinsan uncle d'inki da rashin yadda da maza."

Ajiyar zuciya Ma'aruf ya sauk'e jin abinda Yaya Maryam ta fad'a samun kanshi yayi dajin dad'i ganin bata fad'i gsskiya ba, K'arama kam kunya ce ta rufe ta sunkuyar da kanta tayi tanajin kunyar uncle Ma'aruf d'in Yaya Maryam taja hannunta suka nufi inda yake a kunyace tace,

       "Uncle sorry."

Satar kallon yaya Maryam yayi ta girgiza mai kai alamar yaja aji, aikuwa yayi shiru tare da mik'ewa tsaye yana gyara hannun rigar shi, kallon Yaya Maryam ya kuma yi tare da cewa,

   "Sister mu koma hospital d'in nan ko?!"

 Yaya Maryam ta kad'a kai alamar toh sannan tayi waje tana jiran su, a hankali ya k'arasa wajan da take a tsugunne d'ago ta yayi ji yake tamkar ya sake rungumeta amma gudun karta fassarashi yasa ya kama hannunta suka fita kanta a kasa ita kam bata ga abinda suka zo yi gidan ba sai ma tashin hankali.

Mota suka shiga suka koma asibitin sanda sukaje an shiga da babyn cikin teater room, ita kuma Sumayya an barta sai ta d'an huta za'ayi mata, gabaki d'aya ta shiga damuwa kuka kawai take yi tana nadamar shan magungunan da tayi ta yi kamar ba'a nuna mata illar hakan.

Satin su d'aya a asibitin inda ya kama ranar suna yaro yaci suna Al'amin suna kiran shi da Amir gashi kyakyawa sai dai idon nashi duk da aikin da akayi an cire abun amma be koma normal ba sai yayi kamar harara garke, Sumayya kam jinya biyu take yi hakan yasa duk ta koma kamar ba ita ba ko tashi bata yi sai dai a temaka mata hakan yasa rainan yaron duk ya koma kan K'arama ko school taje hankalin ta na gida data dawo zata d'auke shi ta goya domin tana masifar son taga tayi goyo tana aiki.

Da yake gidan Madre suka koma hakan yasa ana kula da Sumayya sosai da beeba taje ta ganta dariyar zuci ta dinga yi mata tana fatan Allah yasa ma ta mutu ita kuma sai ta auri Ma'aruf uban girman kai yadda beeba ta samai sunan kenan dan kwata-kwata yak'i sauraronta bare yaji da abinda taje.

Kamar kullum yauma K'arama na zaune a wani corridor kayan Amir take wankewa dan ta hana a bawa kowa ita keyi mishi ta goge mai, gefen ta Udutti ce ke home work tana tambayar ta idan ta bata amsa saita rubuta a haka Ma'aruf ya shigo ya same su. Udutti ya kalla tare da fad'in.

   "Udut come here... *!*"

Da sauri ta mik'e tak'arasa wajan shi tare da cewa "papa good afternoon how is you're work?!" Murmushi yayi yana shafa kanta sannan yace,

     "Jeki canza kaya kizo muje park ke da aunty me kyau...."

Kasan cewar haka Udutti ke kiran K'arama tun tana k'arama taji wasu yara na fad'a shi kenan itama ta ci gaba shi har yanzu ta kasa denawa Sumayya tayi fad'an harta gaji itama watarana haka take kiran K'arama dashi. Udutti na tafiya shi kuma ya matsa wajan K'arama ba karamin kyau tayi ba cikin riga da zani kalar atamfar peance green light yayi mata kyau d'inki kirjin nan dai-dai da yanayin jikinta beyi yawa ba sannan beyi kad'anba.

Gabaki d'aya kunya ta rufe K'arama dan tun ranar da abun ya faru bata bari su had'u, ko makaranta da sun shirya zasu gudu drive ya kaisu da taji shigowar shi kuwa zata b'oye dan bata son suna had'uwa kunyar shi take ji sosai.

    "Jiki d'akko mayafi muje mu dawo sai ki k'arasa wankin sa kai... *!*"

Da kyar K'arama ta iya magana cikin sanyin muryarta tace,

     "Uncle sai dai kuje kai da Udut ni dana gama karatu zanyi kaga gobe zamu fara zana waec..."

    "I said kije ki d'akko hijjab ku ba kya ji."

Tsam K'arama ta mik'e tare da tsame hannunta daga cikin ruwan wankin, kusa da kufar shiga parlorn ya tsaya tana zuwa tad'an tsaya ba tare da tace mai ya matsa ba a tunaninta ko shiga zaiyi sai taga ya d'an matsa alamar ta wuce, hanyar tabi da kallo tasan inda zata wuce toh dole saita gogi jikin shi ita kuma bata so.

    "Zoki wuce mana ku nake jira fa."

Ma'aruf ya fad'a cikin basarwa yana latse-latsen waya, a hankali taje ta rab'a amma duk da haka saida ta goge shi tana shiga ya cafko hannunta ya rik'e yana bin ta da wani fitinannan kallo wanda shi kad'ai ne yasan ko na meye.

Bata juwa ba ta fara kokarin kwace hannunta basu zata ba kawai sukaji muryar Sumayya daga nesa.

    "Yaya Ma'ar what d he'll is this?!"

Da sauri ya saki hannun K'arama sai wani cika yake yana batsewa had'e gira yayi K'arama ta ruga d'aki zuciyar ta na harbawa dan tasan yau sai taci masifa wajan Sumayya,

      "Yaya wai meke faruwa ne?!"

Ya kuma had'e fuska dan karta kawo mai raini yace,

     "Ko kema fitsarar zaki min kamar yadda itama take son yi min?!"

Ya fad'a kamar da gake, jin abinda yace gashi sai faman kumbura yake yi yasa Sumayya tab'e baki ta nufushi, jikinshi ta fad'a ya d'agota yana kallonta ganin ba damuwa yasa shi cewa,

     "Unguwa zamu rakiya zasu yi min."

Lokacin sun fito Sumayya ta kalli Ma'aruf "zuwa ina kuma?!" Yace "park zamu zan karbo wani sako." "A can park d'in zaku karb'o sakwan?!"

Juyawa yayi ya fara tafiya yana cewa "Ehh shi yasa ma nace su rakani idan munje su suyi wasa kafin na gama abinda ya kaini, ku kuwuce mota."

Duk iya kokarin ta na ganin ta gano wani abun bata gane ba hakan yasa tayi musu bye-bye tanajin tamkar aje da ita dan haka kawai bata yadda dasu ba dukkan su.

#hafsma'ar
#love you all
#hajjafeedohm

*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*πŸ‘ˆ


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


          Page *83*


Yawo suka yi sosai ya kaisu gurin shak'atawa da daya duk inda suka je barin su yake yi ya zauna a gefe yana yi musu video cikin jin dad'i.

Hotona kuwa yayi musu shida K'arama yafi ashirin shida ba son yin su yayi amma yau sai da yayi son ranshi, sai wajan karfe 9:00pm suka koma gida da kayan kwalan da makulashen da ya siya musu.


* *

  Cikin d'an lokacin ne ya kasa danne son da yake mata sam ko kad'an baya so ya d'auke idon shi a kanta idan tana guri ga wani irin feelings da yake ji a kanta kamar zai kashe shi !Da yake har lokacin Suna gidan su Madre ya samu ya fad'a mata zasu je garin su K'arama saboda shima zai je aiki a can don haka zai tafi da ita har ya gama aikin sai su dawo tare, bai samu matsala ba gurinta sai ta masu fatan dawowa lafiya, ita ta had'a masu komai na tsarabar da zasu kai masu…

Ranar da zasu tafi Tun da asuba Sumayya ta saka rigimar wae sae an tafi da Udutii tunda hutu suke Ma'aruf yace bazasu tafi da ita ba amma K'arama sai tace "Uncle Tafiyar da Udutti zai k'ara maka wani nauyi ne?please dan Allah mu tafi da ita…!"

Gyad'a kai kawai yayi sannan aka shirya Udutti cikin irin na K'arama sai kayanta  pakistan kalar jah kamar yadda K'arama ta shirya aka zuba mata 'yan kayanta a cikin jakar K'aramar, har parking lot su Madre da sumayya suka rako su hannun Madre d'auke da Amir, A Gaban mota suka zauna su duka biyun sannan suka d'auki hanyar zuwa Katsina…

Udutti ke ta zuba surutu ita kadai yayin da K'arama ta mayar da kanta jikin window ta lumshe ido kamar mai yin bacci.
  Ma'aruf kam daga "Huh" "Uhum" Eh! A'a" yake amsa mata yayin da yake satar kallon K'arama duk bayan second…

Da yake gudu yake yi sosai karfe 2:45pm suka isa Crc ko gidan hakimi baije ba ya d'auki hanyar kauyen su K'arama.

Da sauri ta kalleshi yayin da gabanta ke fad'uwa wanda ta rasa dalilin a hankali tace "Uncle.!"

Cikin kulawa Ma'aruf yace "Na'am Hafsah…"

Shiru tayi tare da sadda kai k'asa Udutti ta saki hamma ganin sun yanka cikin daji tace "papa bush zamu shiga mu kamo lion?"

Kallon juna suka yi shi da K'arama ya sakar mata wani lallausasan murmushi sannan yace ma Udutti "Zaki dai iya kamo lion din ko?

Tabe baki tayi tana kallon K'arama sannan tace "papa kasan film d'in joda?"

Gyad'a mata kai yayi yana kallon hanya tace.

   "Yauwa toh Irin Murmushin kake yiwa Small Mom inka!"

Waro ido yayi yana kallonta lokaci guda ya kalli K'arama da ta waro ido itama tana kallonta cike da mamaki sannan ta sunne kai tana dariya k'asa k'asa…

Hararanta yayi cike da sonta sannan ya kalli Udutti dake ta murza point d'in phone d'in shi yace "baki ga tana kama da joda in ba itama…?!"

Kallon K'arama tayi kamar yau ta tab'a ganinta sannan ta saki dariya tana gumtse bakinta dan karta fito sosai…

Suna zuwa garin su Maitafasa K'arama ta runtse idonta tare da kwantar da kanta saman cinyarta Ganin yanayinta ya sashi yin parking a dae-dae kofar gidan Maitafasa kafin su fito mutane har sun kewaye motar…

Udutti ta kalli Ma'aruf tace "papa basu tab'a ganin motor bane?"

Tab'e baki yayi ya juyar da kai ya hango Maitafasa tana kokarin fitowa daga gidan d'aure da d'aurin gaba tana watsa hannun ta a baya duk da baya jin me take fad'a amma ya tabbatar da cewar bala'i take…

  A hankali ya kalli K'arama yace "Mu fita ki gyadar da kakarki…"

Saurin d'agowa tayi tana kallon shi da mamaki lokaci guda ta kalli Maitafasa gaban ta yayi mummunar faduwa bata san lokacin da ta rungumeshi ba tana fad'in "A'a Uncle dan Allah mu tafi mu dai karta yi min fad'a…"

Bayan ta ya shafa ya d'aga kai a hankali yana kallon mutanen dake lekowa ta glass suna kallonsu yayi k'asa da kai yace "Ina tare dake Hafsah Bazan bari wani ya cutar dake ba Hafsa!Ki fita ki gyadar da ita ko baki yarda dake Jikarta bace kema?

Shiru tayi tare da d'aga kai tana kallon shi saurin janye jikinta tayi ta matsa jikin door d'in tana kallo waje Udutti da ta matse ta saka hannu ta b'angarenta ta bud'e kofar kafin tayi magana ta fice yayin da Ma'aruf ya bi bayanta shima…

Idonta ya ciko da kwalla ta bud'e kofar a sanyaye ta fito… Gurin yayi d'im suna kallonsu yayin da Maitafasa ta kafeta da ido kamar an tsikareta kuma ta matso kusa da ita ta saka bakin hannunta ta d'ago Fuskar K'arama tana kallo jikinta na rawa…

Sakinta tayi ta koma baya tayi zaman 'yan bori ta saki wani irin ihu tana fad'in,

   "Ta kwarankwatsa wannan yarinyar d'iyar ladona ce!Yau na shiga uku ni Maitafasa…"

 Jiki a sanyaye K'arama ta matsa tare da tsugunnawa kusa da Maitafasa ta dafa cinyarta tana kallonta da idanunta da suka ciko da kwalla tace "Kiyi hakuri dan Allah ki tash…"

Wata zabura Maitafasa tayi wadda tasa K'arama firgitar da sae da tayi baya ta zauna a kasa tana kallon Udutti da tayi gurin mutanen tana tambayarsu "Wae me suke kallo a jikinsu?

Wata wawar runguma Maitafasa ta kaiwa K'arama tare da sakin kukan 'yan bori tana fad'in.

    "Ta kwarankwatsa jikata ce 'yan nan Sak ladona!Na tuba Hafsatu ki yahe man tallahi na yarda ke jikata ce,babu yarda za'ai ki d'auko kamannin Ladona in dae ke ba jinin,shi bace Na yarda aradun Allah duk wani munahurci toh bakar munafukarcan ta had'ashi…"


Cikin gida ta ja hannunta suka shiga nan da nan mutane suka bisu kai kace wani mai mulkinne yaje kauyan.

Abun Allah sae gashi har da Maitafasa aka je kauyen su Hafsuwalle ta saki jiki sosai sai labarin Kundum takewa K'arama wanda tsabar mamaki ya hana K'arama cewa Uffan Ko da suka isa kauyen Ard'o baya nan sae Sallau da suka iske rik'e da d'an yaron da Lauratu ta haifa na biyu da sauri K'arama ta k'arb'eshi tana kallon Ma'aruf da ya kafeta da ido ganin bakin yak'i rufuwa ya sashi murmusa, Udutti kam gurin sauran yaron Lauratu ta nufa suka cigaba da wasansu kamar ta dad'e da sanin su Yayin da Hafsuwalle da sauran mutanen gidan suka k'arbi K'arama hannu biyu biyu saboda sak ta canza tamkar ba danginsu ba ga wani kwarjini da tayi wanda karyar mutum ya iya had'a ido da ita ya fad'a mata ba dad'i…

Ma'aruf kam bukkar Ard'o sallau ya kai shi sannan ya zagaya can bayan gida ya kira Ardo!cikin sauri ya zagayo yana cewa,

  "Maraba lale da mutan binni."

Karo yayi da Maitafasa ta tsayar dashi tana bashi hakuri da yake bai kullace ba sae yayi dariya yana fad'in "Wallahi Allah ba komae." Yayi gaba ya shige bukkar sa gurin Ma'aruf cikin mutunci suka gaisa ya saka aka kawo mashi dambu da madarar shanu tare da ruwan randa mai sanyi…

Hafsuwalle kam baki yaki rufuwa bama kamar lokacin da yara suka fara shigo da tsarabar da su K'arama suka zo da ita taga mutanen gidan sae washe baki suke suna sakawa K'arama albarka wanda bata tab'a tunanin zasu samu hakan ba a gurin mutanen gidan… Ita kanta K'arama ta saki jiki don har wanke wanke ta taya Zulai yaran gidan kam bata kyamaci kuwa ba acikin su duk da yarda suke duku duku haka take rungumarsu cikin tsantsar mutunci!

Sae kusan Magrib sannan Ard'o ya shigo gidan ya kirata suka koma bukkar sa a tare dashi kafin ya shiga ya hango Udutti tana dambe da jikan zulai akan goriba ya matsa yana rabasu…

Ganin Ma'aruf zaune ya sata komawa gefen shi ta zauna tana kallon shi tace "Uncle Ka ci abincin mu kuwa?

A Hankali ya girgiza mata kai yana waro ido waje…

Cikin kulawa tace "Me yasa?ko baza ka iya cin abincin mu bane?

Gyad'a mata kai yayi yana kallon yarda ta kwantar da kai tana kallon shi…Ga mamakin,shi kuma sae ganin hawaye yayi kwance a idonta yayi saurin ware ido yana fad'in "Kuka Hafsa?Kinga wasa nake duk abunda zaki iya ci zan ci shi kin ji ko?na ci sosae kuma ya man dad'i…ki koya kafin mu koma gida kinga sae ki dinga min ko?ya karashe maganar tare da kanne mata ido d'aya.

 Zaman Ard'o ne ya sashi yin shiru tare da barin kallonta…Cikin natsuwa Ard'o ya fahimtar da ita Matsayin Ma'aruf gurinta tunda ya fara maganar kanta na k'asa ta kasa dagowa har sae da ya kai aya sannan ya d'auko sadakin ta da tunda aka bashi gidan hakimi ya zo ya boye ko kud'in bai canza ba ya dan da zai yi mata kiwo ya fasa dan yasan sacesu za'ayi. Ya matso ya mika mata kin karb'a tayi har sae da yace "Hafsatu sadakin mace hakkinta ne ki karb'a dan girman Allah ki rabani da azabar Allah domin cin kud'in Sadaki ba karamin bala'i bane."

Hannunta na kyarma ta karb'a ta aje k'asa mikewa yayi ya fita ya bar su kadae a hankali ta runtse idonta tana tuno duk abunda ya faru a baya har lokacin da Ma'aruf d'in ya tambayeta a bainar jama'a ko zata aure shi, zuciyarta na harbawa jikinta na rawa ta fara tunani (kenan abunda ya fad'a kwabaki gaskiya ne, amma me yasa aka rufeta, me tasa lokacin da yaya Maryam ta gansu bata gaya mata gaskiya ba sai ma kwana-kwana da tayi mata? Allah kad'ai masani sai kuma su)…

Wani lallausan murmushi ya sub'uce mata sam bata yi nadamar hakan ba ita kanta tasan Uncle wani haskene a cikin rayuwarta to me yasa yake wani b'oye b'oye?Lumshe ido tayi sama ta rigaya ta manta da Ma'aruf dake zaune kusa da ita hannun shi taji saman fuskarta ko bata bud'e ba tasan kallonta yake yi…

Dukkan hannuwan shi ya saka ya tallabo fuskarta yayin da ya aika mata da wani yalwataccen murmushi kamar mai rad'a yace "Kin amince dani a matsayin mijinki?ya karashe maganar tare da had'e fuskarsu guri d'aya,

Kafin ya sake magana suka jiyo Muryar Udutti ta shigo tana fad'in "Lah lah papa Me kake yi mata?

Bai d'ago ba haka bai janye fuskarshi ba kusa da tata sae ma kissing da ya bata a saman eyelashes inta yana fad'in "No Wani abu ya fad'a mata nake cire mata."

Kusa da su ta matso K'arama na kokarin janye fuskarta amma ya riketa sosae a hankali tace "Please Uncle ka daina mana…"

 Udutti tace "Abba kamar Muahh! naga ka mata a Idonta!

Still kiss ya kuma mata a idon sannan yace "A Idon ya fad"a ai Udutti."

Tab'e baki tayi ta juya tana yarfa hannu ta fita da sauri K'arama ta tureshi ta tashi da gudu ta fita daga cikin bukkar… Cak ta tsaya a bakin bukkar tare da dafe kirji tace "Na shiga uku Aunty Sumayya… *!*"


Karaf Udutti ta amshe da fad'in "Me Mami na  tayi Aunty Mai kyau?

Kallonta tayi da sauri ashe tana bakin bukkar tana kwalkwalar k'asa tana wasa bata ce mata komae ba ta d'agata suka shige bukkar Inno inda su Ummanta suke…

Ma'aruf kam kud'in da ta aje ya d'auka yana murmushi ya fita a bakin icce ya iske su Ard'o tsaye yana magana da Maitafasa duk da ba fad'a take ba amma tana yi tana watsa mashi hannu a fuska wae kuma hakuri take kuma bashi…

  "Allah ya kyauta…"

Ya fad'a tare da girgiza kai ya matsa kusa da Ard'o Kanshi Maitafasa ta koma tana bashi hakuri gyad'a mata kai yake don har ga Allah ta ishe shi da kwaratsi tare da watsa hannu a saman jikin shi…

Kud'i ya ciro ya bata sannan ta tafi tare da rafka masu albarka tana musu faran alkairee ya juya yana fad'awa Ard'o zai tafi zuwa sati d'aya zai dawo ya tafi dasu tun da shima akwae abunda zai yi a katsina wanda yake tunanin zai kai shi sati d'ayan…

Fatan alkhairi Ard'on ya mashi  suka rakashi har bakin mota shi da sallau ya shiga har zai tafi Ard'o yace Sallau ya kira su K'arama suyi bankwana kafin ya tafi!shi kanshi Ma'aruf d'in yaji dad'i sae dae bak'in cikin shi d'aya yana iya ganin duka mutanen gidan sun fito suna kallonsu…Haka kam akayi kusan duka mutanen gidan ne a bayan K'arama kamar su aka kira.

Girgiza kai yayi cike da takaici yana kallon K'arama da ta toge tak'i k'ara sowa gurin da yake, A Hankali ya tab'e baki ya mikawa Udutti hannu amma ta makale kafad'a tare da rike hannu inno tana kyafta mai idanu…

Kallon K'arama ya kuma yi suka had'a ido ya kashe mata ido d'aya tare da d'aga masu hannu ya tayar da motar shi, Duk abunda yayi mutanen garin idonsu na kanshi don haka yana tayar da mota suka d'auki gud'a "Ayyyiriri……!!"


【】

Cije baki tayi tare da dafe gefen cikin ta dake ta murd'awa ta kalli Madre tace,

   "Madre ina so na tambayeki ne…"

Shiru tayi tana jinjina maganar a bakinta lokaci guda kunyar madre ta dirar mata dan tambayar ta kunya ce…

Cikin kulawa Madre tace "Menene Sumayya?

K'asa tayi da kanta sannan tace "Madre wani yellown ruwa ne ke fitowa ta kasana kuma ya fara wari-wari."

Da sauri ta kalleta tana fad'in "Yellown ruwa Sumayya a Vagina inki ko ina?

Shiru tayi tana kallon k'asa cikin tsawa Madre tace "Bakya jina ne tun yaushe yake fitowar?

A Hankali tace "Yafi Ten month gaskia Madre kuma a tunani na ni'ima ne wallahi to kuma ya fara wari shine nake so na tambayeki dama idan ni'ima tawa mace yawa tana irin wannan warin…?!"

Uban Mari Madre ta bata tana aika mata da wani mummuna kallo kafin tace "Ashe baki da hankali Sumayya?

Dafe inda ta mareta tayi ta saki kuka tana fad'in "Me nayi Madre?

Shigowar yaya Maryam ta hana Madre bata amsa ta mike ta bar masu d'akin Maryam d'in ta tambayi Sumayyan me ke faruwa bata b'oye mata komae ba tace "Wani ruwa ne fa ke fitawa a vagina ina wallahi yellow haka da bayya da wari amma yanzu wari yake sosai shine nake fad'awa Madre ta mareni."

Girgiza kai Yaya Maryam tayi tace "Amma tun yaushe yake fita Sumayya?

   "Kusan wata goma kenan." ta fad'a kai tsaye tana turo baki

A Hankali tace "Shine baki fad'awa Madre ba kuma ko?Ko shi Brother ya sani?

 A Hankali tace "Ban fad'a masa ba don na d'auka ma ni'ima ne…"

Tsaki ta saki ta mike tace "sai ki ta tashi muje je asibiti." kafin ta shirya ta shiga gurin Madre ta fad'a mata ita dae Madre takaici yasa tace "A Dawo lafiya." tayi banza da Maryam d'in……

Ko da sukaje asibitin laboratory aka ce taje ayi mata test…wata sister a kace ta d'auki sample d'in dake fitowa sheath d'inta wari-wari gurin keyi da kyar sister in ta d'auka akace su jira kafin result ya fito.

Kusan one hour sannan sister d'in ta fito rike da result d'in ta nufi office d'in wata doctor Safiyya suka bi bayan ta suma…

Ita kanta Doctor Safiyya rasa wace irin cuta ne a Vagina d'in tayi don result ya bada ba infection.. Tambayarta tayi abunda ta ke ji a tare da ita…

Ba tare da damuwa ba tace "Discharged ne kawae sae bleeding da nake kad'an-kad'an wanda is not related to menstrual (Fitar ruwa ko jini wanda baya da alaka da al'ada)……

#hajjafeedohm love

*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
&
*FEEDOHM*❤
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*πŸ‘ˆ


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


          Page *84*


    Ba tare da damuwa ba tace "Discharge ne kawae sae bleeding da nake kad'an-kad'an wanda is not related to menstrual (Fitar ruwa ko jini wanda baya da alaka da al'ada)……

A Hankali doctor d'in tace "Kina jin Pain during sexual intercourse?!" (kina jin Zafi yayin saduwa da miji?!")

Gyad'a kai tayi tace "Eh amma ba kullun ba."

Kallonta ta kuma yi tace "Pain when urinating?" (Zafi yayin fitsari)!Still Sumayya gyad'a kai tayi doctor d'in tace "Akwae pain in pelvic area?Still gyad'a kai tayi.

Yaya Maryam tace "Menene Matsalar? Natsuwarta ta dai-dai ta sannan tace "It seens kamar Adenocarcinoma (Vaginal Cancer)."

A Tare suka mike suna fad'in "Menene?!" Itama mikewa tayi tace "Please ku zauna Calm down Having these symptoms does'nt always means that you have Vaginal cancer infact these symptoms are more likely to be caused by something, beside cancer like an infection the only way to know for sure what causing these problem is to test you Sister kawae na fad'a ne amma banda tabbaci saboda inda infection ne a first result d'inki zamu gani…!" (Ki kwantar da hankalinki Wad'an nan alamomin basa nufin kina d'auke da cutar daji ta farji, kawae wad'an nan almomin sunfi kama da na wadda ke d'auke da cutar sanyi ne, hanya d'aya ce da zamu tabbatar da abunda ke damunki shine mu yi maki gwaji, kawae na fad'a ne saboda da ciwon sanyi ne da tun a sakamakonki na farko zamu gani).

Su dukan su jikin su yayi sanyi bama kamar Sumayya da ta shiga cikin tashin hankali kawai ta saki kuka tana girgiza kai cike da tashin hankali da damuwa mai yawa. Doctor d'in ta kwantar masu da hankali sosai…

Laboratory ta kuma turata tace a mata Pelvic Exam ,PAP test & Calposcopy a gani… da yake suna da kayan aiki a take nurse d'in ta kwantar da Sumayya aka mata Pelvic exam d'in tare da Pap test suka d'auki sample na cell d'in dake a jikinta.

Har kusan La'asar sannan result d'in ya fito wanda ya tabbatar da tana d'auke da Vaginal cancer saukinta ma d'aya bata yi Spreading to other areas ba iyakar ta a Vagina d'in kuma bata da wani karfi a jikin sosai, gaba ta sakata tana tambayarta ko tana shiga toilet d'in dake da mutane masu yawan amfani dashi?!" Nan ma tace "a'a."

Tambayarta ta kuma "Toh ko kina wanke Vagina d'inki da sabulu kamar give ko olive ko honey haka?

Cewa Sumayya tayi "Tana wank'ewa amma bada sabulun give ko olive ko honey ba a'a da irin wanda ake had'awa na mata…!"

Jingina kai tayi ta kuma tambayarta "ko kina cushe-cushen kayan mata a jikinta Sumayya?

 Babu kunya tace "Eh amma 'yan bauchi ne suna da kyau sosai."

Ita kanta doctor Safiyya sae da ta jinjina amsar Sumayya sannan tayi mata fad'a sosae tare da ganar da ita illar duk abunda za'a baka ace kayi matsi dashi.

Magunguna sosae doctor in ta rubuta masu don cewa tayi inda tayi k'arfi da sae an mata Radiation therapy sannan tace ta dinga yawan shan kankana (water melon) don ita ce zata koro mata sauran cutar dake makale a cikinta sannan ta daina tsarki da ruwan sanyi kwata-kwata ta dinga shiga ruwan dumi da aka zuba gishiri a ciki…

Suna komawa gida takaici yasa Madre tace maza-maza Yaya Maryam ta tattara Sumayya ta mayar da ita gidanta tun da bata isa ta sumayya fad'a mata matsalarta ba bare ta ji maganarta, Duk yadda yaya Maryam ta so Madre tayi hakuri ta bar Sumayyan ta k'ara samun sauk'i amma ta k'iya karshe ma ita da kanta ta tattaro kayan Amir dake part d'inta ta kawo masu tace kafin dare har Maryam d'in ta tabbatar ta bar mata gida!Ganin abun bana wasa bane yasa suka fara shirin kowama muhallin su…

Wajen Magrib Yaya Maryam ta d'auki Sumayya dake ta faman turo baki tana kuka ta mayar da ita gidanta. Ta mata fad'a sosae ta k'ara jaddada mata  illar abunda take sha tare da wanda take cusawa da mata misali da Amir dake da matsalar ido tare da Udutti da jikinta yake dabbare-dabbare wanda duk sanadiyar maganin matan da take amfani dashi ga kuma CS d'in da take sha sannan Uwa uba cutar da take d'auke da ita yanzu…!

Sosae jikinta yayi sanyi tana kuka tace wa yaya Maryam "Sister insha Allahu bazan sake ba!amma kuma to zan iya saka white miski saboda warin ya rage…?!"

Cikin natsuwa Yaya Maryam tace "No Sumy Duk abunda zaki yi inserting a steath d'inki Sumayya to akwae matsala ko menene hatta miski da hulba da lalle da muke d'auka mu saka don kwae muna ganin maganin natural ne to wallahi duk suna da side effect d'insu ke dae ki rike ruwan zafin da doctor ta ce maki da kankana da tab's d'in da muka saya, Idan kina ganin ma zaki jaraba da na hausa to zan kawo maki ZAITUN ORIGINAL, GARIN SHAMAR DA KUMA GARIN FUREN LALLE sae ki kwab'a da ZUMA Ki dinga sha yana magani cancer sosae ko wace iri ce…"

Sumayya tace "toh." Ita dai kawai idan za'a mata abun da zai sa mijinta yaji dad'i to zata sha ko menene. Da haka Yaya Maryam tabar gidan tana mamakin Sumayya kowa ya gaya mata haka ake mallake miji oho...


《》《》

*KATSINA*

   Zamansu cikin jin dad'i da kwanciyar hankali suke yi a jauyan, tsaraba kam ba gidan da ba'a kai ba yayin da mutanen kauyen baki d'aya suke haba-haba dasu bare ma Udutti da ta ware tana shiga gidajen mutane kowa ya santa su Maitafasa kam kullum sae an kawo masu tafasa da curin fura!Kundum ma ba'a barta a baya ba da yake shiri take nema da Maitafasa ta ciwo bashin gero rabin tiya ta daka masu fura ranan da akace Ma'aruf zai zo d'aukar su zata kai masu.

Kafin ta kai masu ne Maitafasa ta lura da ita ta kuwa watsa hannu tace, "Kundum wa zaki kaiwa hurar nan ne?

 A Hankali tace "Hafsatu K'arama zan bawa tayi tsaraba."
  Tsaki ta saki tana watsa hannu tace "Bana san munahurci Kundum…! aka ce maki bani da kud'in daka masu ne?

   "Ta k'warank'watsa Maitafasa ba haka nake nuhi ba kiyi hakuri ki yahe min komae ya wuce."

Kundum ta fad'a tana matse hawayen karya.

Sosae Maitafasa ta matsa tana leken fuskarta sannan ta kwashe da dariya tace "Kundum idan munahurci ya ganki har wata runguma yake maki aradun Allah!banda kina bakar munahuka meye na matse hawayen karya a huskarki?ko kiyi kuka ko kar kiyi kin sani Maitafasa na kamnarki Kundum matsalar bana son munahurcinki amma komae ya wuce, sai dai amma aradun Allah kika kuma shiga harkata sae na balli dawon battar ubaki…!

Shiru tayi ba tace komae ba a haka suka jera suka fita a bakin k'ofa suka ga mai unguwa Kundum ce ta tsaya ta gaidashi sab'anin maitafasa da ta hura hanci tayi gaba tana wakar habaici "Da Mai-uguwar kauyen mu k'ara bak'ar jaka a hayyeee…!"

Girgiza kai yayi yana kallon Kundum cike da gulma amma tak'i kallon shi tayi gaba tana kallon k'asa… Suna tafiya tana jan Maitafasa da labari amma tak'i kulata sae da tace "Ke ni ruhe min baki, ko kuma Allah tsine uban munahuki." amma sam kundum tak'i zuciya sae dae lallab'a Maitafasa take har suka isa kauyen… a d'akin Inno suka yada zango suka mimmike kafafu ko wace ta ja baki gefe…
 
Lauratu ta shigo d'auke da Udutti tayo mata wanka sabida karta b'ata jikinta da k'asar gidan suka tsallakesu ta aje ta, Kusa dasu Udutti ta koma ta kurawa jajjayen hakoran Kundum ido tare da kwashewa da dariya tace "Bakya brush ko? yarinya ki dinga yi gashinan hakoranki sunyi daty."

Maitafasa ta amshe da fad'in "Ina fa ta keyi yarinya!matar da bata aje komae ba sae munahurci itace za tayi brum (brush)? ta samu tayi assalatu ma kadae…"

Yarinyar ta girgiza kai ta fita da gudu K'arama ta maidota… ta duk'a har k'asa ta gaidar da Su, Kundum ta kad'a baki zata amsa amma Maitafasa ta make bakin da bayan hannunta tana fad'in." Ruhen baki ke ta gaida da shegen shishshigi zaki amasa?, Lahiya lau Hafsatu K'arama ya d'ari d'ari da kauyan namu?

Dariya K'arama ta danne ta mik'e ta tabbata Maitafasa baza ta tab'a canza hali ba sae dae ta rage to meye laifin kundum don ta amsa gaisuwarta?

Yaran da suka fad'o d'akin suna fad'in  "Ga mota ga mota.!" Shi yasa gaban K'arama mummunar fad'uwa yayin da Maitafasa ta mike ta fita kamar ita aka kira!Ma'aruf kam yana zuwa suka shige bukkar Ard'o suka gaisa sannan Ard'on ya kira mashi Hafsuwalle itama suka gaisa ya aje masu kud'i masu yawa yace sauri yake su K'arama su fito zasu wuce…

Sosai Umma tayi wa K'arama gargad'i akan k'inbin Umarnin mijinta haka ma Lauratu ji take kamar karta tafi sati d'ayan ji take kamar yanzu suka zo zasu koma harda hawaye tayi.

Har bakin mota mutanen gidan suka rakosu suka shiga sannan Ma'aruf d'in ya bawa sallau kud'i yace ya raba masu bayan ya bawa Maitafasa ya ja mota suka d'auki hanya komawa gida…

Har suka kusa fita kauyen K'arama bata kalleshi ba sae Udutti dake ta faman zuba kamar b'arkakken fanfo…

Murya k'asa k'asa yace "Ba magana ko lil Mommah?

A Hankali ta kalleshi sae taga ya mata kyau na musamman!ji take dama ya tsaya a haka tayi ta kallonshi ba tare da ta d'auke ido ba, da yake hanya yake kallo sae ta saki jiki tana kallon shi har da su murmushi kafin Udutti tace,

   "Papa tana kallonka…" Udutti ta fad'a tana kallon K'arama. Da sauri ta mayar da kanta k'asa cike da kunya ta sa tafin hannunta tana rufe fuskarta.
 
Murmushi yayi yana jefawa K'arama harara sannan ya kalli Udutti yace "Ko?

Kai tsaye tace "Ta k'warank'watah…!

Da sauri suka kalleta ta kwashe da dariya tace "papa wannan Maitafasan take fad'in haka fa."

Da yake yasan da sun bar gurin zata manta sae yace "Huh…" kawae ya cigaba da driving d'in shi…

Har suka hau titi sannan K'arama tace "Uncle ina Aunty Sumayya?

Hararanta yayi ta gefen ido sannan yace "Gata nan a bayan mu."

Dafe kirji tayi had'i da waro ido ta juya baya da sauri don har ga Allah ta d'auka da gaske yake, ganin ba kowa ya sata sakin ajiyar zuciya tare da hararan shi…Kallonta yayi ya tab'e baki had'i da jujjuyar da kai…

Cikin shagwab'a tace "Bunkul ko?Toh Sorry Good Morning…"

Banza ya mata yana hararanta ta gefen ido wadda ta kasa fassara ta ko mai cece… Babu wanda ya kuma magana a ciki har suka yi tafiya mai nisa da yake a kauyen ba wani bacci suke samu ba don haka daga Udutti har K'arama suka ciga ba da bacci a cikin motar…

Madre ce ta kirashi suka gaskisa tare da tambayar shi hanya a lokacin sun kusa isowa gari sae ya fad'a mata sun kusa, cewa tayi mai ya wuce gidan shi domin Sumayya ta koma bai tambayi dalilin komawar Sumayyan ba don yasan Madre baza ta yi son zuciya ba koma menene toh da dalili.
  Sae ana gab da Magrib sannan ya shigo cikin gari direct gidan shi ya nufa har lokacin Bacci suke sae da maigadi ya bud'e masu gate sannan K'arama ta farka gabanta yayi mummunar fad'uwa a wahale ta kalleshi tare da dafe kanta da hannu d'aya Sumayya kadae ke fad'o mata!Ya lura da canjinta don haka bai kalleta ba sae da ya gama parking sannan ya dube ta ya sake mata murmushi yace "Sleeping belle…"
 
Mayar mashi da murmushin tayi tare da bud'e kofar ta sab'i Udutti da kyar sabida tayi mata nauyi yanzu suka yi gaba. karar bud'e gate ya fito da Sumayya daga wanka d'aure da towel a jikinta duk kumfa tazo ta tsaya bakin kofa tana tsalle Su K'arama suka fara shigowa ta basu hanyan suka shige falon ta kwantar da Udutti tana fad'in "Aunty Sumayya mun dawo."

Ma'aruf na shigowa ta daka tsalle tare da bashi hot hug kamar zata koma jikin shi shima hugging nata yayi yana fad'in "Oyoyo Mamin boy…"

Rashin dace ya saka K'arama d'agowa tana kallonsu wani abu ya soki zuciyarta kamar taci mad'aci, karo na farko kenan a rayuwarta da ta tab'ajin hakan, saurin zub'ewa tayi k'asan rug idanunta suka kawo ruwa a hankali tace "Na shiga uku me kenan?Kishi nake da Aunty Sumayya ne?kai no yunwa nake ji shi yasa…"

Da sauri ta mike ta shige kitchen ba tare da ta kallesu ba ta fara bud'e warmers ta samu jallop rice da taji koda da kwae sae kamshi take ko ba'a fad'a ba tasan daga gidan Madre aka zo dashi cikin sauri ta cika plate ta zauna cikin kitchen in tana turawa hawaye na bin kumatunta wanda ta rasa dalilin zubuwarsu…

Ma'aruf kam yana ganin K'arama ta shiga kitchen ya janye Sumayya daga jikin shi yana fad'in "Ina boy?

Fari tayi tace "Yayi bacci dear!ya hanya?

   "Alhamdulillah." ya fad'a ta k'ara hugging nashi tare da mashi peck a kumatu ta ja hannunshi ta zaunar dashi saman kujera tana fad'in "K'arama kawo mashi juice da abinci na nan a kitchen bara naje na shirya ni kuma…"

Hannunta ya janyo yace "Ke baza ki iya kawo man ba?
 
Fari ta kuma yi tace "Dear ban fa k'arashe wankan ba naji ka shigo kasan bazan iya hakura ba banganka ba…"

Kafin yayi magana ta shige ciki tana maimatawa K'arama abunda ta sata… K'arama kam na jinta amma a zabar dake yawo a zuciyarta ta hanata mikewa bare ta kawo mashi abunda ta sata…

Shirun da yaji ne ya sashi mikewa ya nufi kitchen d'in, ya dad'e tsaye a bakin kofa ya hard'e hannayen shi a kirji yana kallonta kamar an mata dole take tura abincin tana kuka motsin da yayi ya sata mikewa da sauri ta juya mashi baya tayi saurin goge hawayenta… a hankali ya matso kusa da ita jikinshi na gogar nata hannunta ya kamo cikin nashi ya d'aura kanshi saman wuyanta kwantar da murya yayi yace "Me nene Hafsah?

Kokarin janye jikinta tayi amma ya zagaye hannunshi a shafaffen cikinta cikin rad'a yace "Me aka maki kike kuka?
 
 A Hankali tace "Ka sakeni please…"

K'ara matseta yayi yana kissing wuyanta yace "Fad'a min kukan me kike?wani abu aka maki daga shigowarki zaki dawo kitchen ki zauna kina kuka kina cin abinci… ?

 A Hankali ta tsayar da wuyanta tare da lumshe ido tace "Yunwa nake ji kawai."

Gira d'aya ya d'age yace "Kawai?

 Juye-juye ta fara da k'arfi ta janye jikinta ta juyo suna kallon juna lokaci guda ta sadda kai k'asa tace "Ai harda Headache."

Ido ya waro yace "Yaushe ya fara maki ban sani ba?

Banza ta mashi ya saka hannu ya janyota jikin shi ya matse yace "Karya bata maki kyau Hafsat… Fad'a min me kikewa kuka?

Muryar Sumayya suka ji a tsaye bakin kitchen tana fad'in "Kut! Na shiga Uku !Ya Ma'aruf me nake gani haka?K'arama a jikinka....???!"


   *Ku taimakawa K'arama a hannun SumayyaπŸ€₯……HajjaFeedohm kam mun sab'e ta k'warankwatsa ba damu za'a jibgi K'arama ba!Team Maitafasa ku kawo wa jikarku d'aukiπŸ™…πŸ»‍♀*
*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
&
*FEEDOHMπŸ’ž*
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*πŸ‘ˆ


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


          Page *85*


     *ZIB Gaisuwa da babbar murya Wannan page din nakune kuyi yarda kuke so dashi  #Much loveπŸ’ž*    Muryar Sumayya suka ji tsaye bakin kitchen tana fad'in "Na shiga Uku !Ya Ma'aruf me nake gani haka?K'arama a jikinka?

   K'ara ta saki tare da tureshi daga jikinta…a rud'e take kallon Sumayya tare da Ma'aruf da ya nuna halin ko in kula yana kallonta kuka K'arama ta saki ta nufi gurin Sumayya tana fad'in "Wallahi Aunty…

 Wani gigitaccen Mari ta sakar mata tare da angazata da karfi tana fitar da numfashi kamar zaki!a jikin Ma'aruf ta fad'a ya saka hannunshi duka biyun ya zagayeta yana kallon Sumayya…Da sauri K'arama ta tureshi tana girgiza kai tana kuka

  Kukan kura Sumayya tayi tana fad'in "Wallahi sae na kasheki sae na rabaki da numfashi yau, ni zaki cuta?Ashe dama cutata kake Ya Ma'aruf sonta kake shi yasa tun tana mayyarta ka daukota ka nema mata magana ashe Kaunace?Plate din dake kusa da ita ta janyo ta jefa mata tana kuka…kaucewa yayi plate din ya fad'a kasa ya saki K'arama ya matsa tare da rungume Sumayyan a jikinshi kwace kanta ta fara kokarin yi tana d'urawa K'arama ashar ya dauketa cak ya nufi d'aki da ita ya kwantar da ita saman bed tare da rungumeta jikinshi…

  Dukanshi take tana fad'in "Ka cuceni kaci amanata Allah ya isa!Wallahi ban yafe maka ba mugu, azzulumi, dan iska kawae…Ka aureta mana daka tsaya kitchen kana rungumeta…"

  A Hankali yace "Dan Allah kiyi hakuri ki tsaya muyi magana sossae Sumayya…"

  Duka ta kuma kai mashi kamar Mahaukaciya tace "Nak'i na tsaya d'in…Uban me zaka fad'a man bayan da idona naga kana rungume da waccen shegiyar mayyar munafukar yar kauyen wallahi sae na kasheta ka sakeni banza azzalumi macuci,uban me yaja hankalinka a jikinta Ma'aruf yarinyar da kama wanka?wannan banzar k'azamar yar kauyen fa ce Ma'aruf?Diyar cikinka amma ita kake runguma a kitchen?

  Kwalarshi ta shaka tana fad'in "Ka fad'a man uban me ta mallaka da ya ja hankalinka Ma'aruf?

 Runtse Ido yayi yace "Dan girman Allah ki natsu!

 "Wallahi baran natsu ba!Da idona na ganka Ma'aruf rungume da yarinyar da ba matarka ba!ka fad'a man yaushe ka lalace har ka fara Zina…?

  Sam maganganunta basu b'ata mashi rai ba saboda yasan duk macen da taga mijinta a haka dole ta ji ba dadi a hankali ya rungumota yace "Matata ce Sumayya…

 A Razane ta dankara mashi cizo tare da tureshi da iya karfin da Allah ya bata!wani kallo take jefa mashi cikin kyarma tace "Gidan ubanwa ta zama Matarka?

 Lumshe ido yayi bayya so ya nuna fushinshi akanta murmushin takaici ya saki ya k'ara rungumota yana fad'in "Ki natsu na maki bayani Sumayya…

  "Wallahi bazan Natsu ba Ma'aruf…!Ta fad'a kai tsaye tana turo duk abunda ke saman gadon ganin zata fita yasa shi saurin maidota d'akin ya rufeta ta waje ya kira Madre a waya ya fad'a mata abunda ke faruwa ce mashi tayi ya jira gasu nan zuwa har da Abban yanzu…

  Kitchen ya lek'a ganin ba K'arama ya sashi lek'awa d'akinta amma babu ita a hankali ya kira sunanta tare da lekawa toilet a mak'ure ya tarad da rungume da Amir da bai san inda ta daukoshi ba, k'arasawa yayi cikin toilet ya d'agota a hankali ya had'eta da jikinshi yana bubbuga bayanta a tare suka furtawa juna "Sorry…"Sannan sukayi shiru kamar ruwa ya cinyesu sae da yaji tsayuwar motar Abba sannan ya janyota ya zaunar da ita kan gado ya fita!yana fita ta rungume Amir ta saki kuka mai cin rai da tasan shigarta kitchen zai janyo wannan bala'in da ta tsaya ko da zuciyarta zata daina aiki……

 Su duka aka tarasu a falo a take Abba ya warware mata komae kuka ta fara da yake tana masifar tsoron Abban tana fad'in "An cuceta…

  "Waya cuceki A cikinmu Sumayya?Abba ya fad'a tare da kafeta da ido

  Cikin kuka ta nuna K'arama tace "An dae cuceni Abba…

 Gyad'a kai yayi tare da masu nasiha sosae su duka ya bata hakuri sosae har ta natsu a gabansu…

 Madre tace "Ya kamata ka rabasu komae kafin mu tafi ta yarda za'a bawa ita Hafsa din hakkinta a matsayin matarshi bawae a matsayin YAR RIKO ba…"

  Harara Sumayya ta watsa mata tare da sakin kuka
Abba yace "Kamar me kenan Hafsat?

 "Ina Nufin ka raba masu zaman gidan…!ta fad'a kai tsaye

 A Hankali yace "Wannan ai hakkin mijinsu ne…"

 Girgiza kai Tayi tana kallon K'arama Ma'aruf yace "Abba ka raba masu komae zata fi dauka da mutunci…"

  Mikewa yayi yana fad'in "Kwana biyu biyu kamar yarda shari'ar islama ta raba……

 Kukan kura Sumayya tayi tace "Wallahi ban yarda ba…

 A Natse Abba ya juyo yace "To ya kike so ayi?

Ba kunya tace "K'wana bakwae bakwae…

  Madre zatayi magana Abba ya tsayar da ita yace "Maganar ta ce da mijinta Hafsat mu je kar na kuma jin wata magana ta taso…"

 Suna tafiya sabon bala'i ya sake tashi sae dae iyakarta fad'a a baki tare da zagi amma ta dauki maganar Madre bata tab'a K'arama ba,sae dae ta dage akan sae dae ayi kwana bakwae bakwae!Ma'aruf yace "Bata yiyuwa Sumayya kwana biyu biyu na tsara maku…"

 Tsaki ta saki tare da wurgawa K'arama harara tace "Wallahi indae ba kwana bakwae ba sae dae ka dinga kwana gidan Madre…

 Dariya ta bashi amma yayi k'ok'arin danneta zaiyi magana K'arama tace "Dan Allah Uncle ka barshi a yarda tace …

 Duka ta kaiwa bakin tace "Wane shege ya tsoma bakin ki a ciki banza munafuka…Ko ku yarda ko karku yarda abunda na tsara kenan!

 "A matsayinki nawa? Ma'aruf ya tambaya kai tsaye

"Na bala'in gidanka… " ta fad'a kai tsaye

 Ranshi ya fara b'aci ya nunata da hannu yace "Mind your laguage and even extra cure of your tongue Sumayya karki ga kamar a kyaleki ne ki kawo man raini wallahi zan sab'a maki sannan ki bar man gidana kuma ki sani babu wanda ya isa ya man dole a cikin zama dake…"

 Harara ta balla mashi tana girgiza jiki K'arama kam mikewa tayi ta dauki Amir zata shige d'aki Amma Sumayya tayi kukan kura ta cafko yaron tana fad'in "Aje shi dan ubanki tunda bake kika haifa man shi ba…"

 Tana hawaye tace "Aunty dan Allah kiyi hakuri…

 A Fusace tace "Na rantse maki da Allah kika kuma kirana da Aunty sae na maki shegen duka a gidannan…

A Hankali Ma'aruf ya tako ya ja hannun K'arama ya turata daki sannan ya kama hannun Sumayya ya shigar da ita daki!Cikin lallashi da dadin baki ya lalaba Sumayya har ta sauko…Sam kin barinshi tayi a fita daga dakin sannan ta kafe dole sae dae ayi kwana bakwae bakwae kuma gurinta zai fara kwana "To" kawae yace mata yana bata hot kiss amma sae tureshi take…

 Shi kansh mamaki yake kamar ba Sumayya ba ganin rikicinta ba mai karewa bane ya sashi gyara kwanciya ya juya mata baya tashi tayi zata sauka daga gadon ya maidota da hannu yana fad'in "Kika fita daga d'akin nan sae na bata maki rai wallahi...

 Tsaki ta ja tace "Udutti zan dauko ko sae na barta a falo"

Zaune ya mike yana kallonta sannan yace "Dama a gurinki take kwana Sumayya?

 Hararanshi tayi tace "Yau nake so ta kwana gurina..."

  "To bara ki daukota ba..."Ya fad'a kai tsaye

Cikin daga murya tace "Wallahi sae na daukota"

 "Bismillah..."Ya fad'a fuska a daure


Hararanshi tayi tana kokarin sauka daga kan gado ya sa hannu ya fizgota tare da kifa mata mari sannan ya turata saman gadon yana fad'in "Ki sake jaraba sauka sai na baki wanda ya fi wannan wallahi...!

 Kuka ta saki tana fad'in "Wallahi ka daki aurenka mugu kawae...!

Dariya yayi mai ciwo yana yace "Bara na sake dukan auren nawa ta yarda bara ya sake gigin dawowa gurina ba..."

 Da sauri ta mirgina karshen gadon tana hararanshi ...shi kam juya mata baya yayi ya kwanta ...da yake muguwar matsoracoya ce kasa fita tayi ta sulale ta kwanta gefe tana kuka...

 Da asuba kafin ya tadata sae da ya leka dakin K'arama ya isketa rungume da Udutii suna bacci !leka fuskarta yayi yana kallon,busassun hawayenta sannan ya shafi kanta tare da kiran sunanta...

 A Hankali ta bud'e idonta ta mike zumbur tana kalle kalle kafin ta saki kuka tace "Uncle Aunty Sumayya fushi take dani !dan Allah ka bata hakuri matsayin uwa na dauketa bana son fushinta "

  Rungumota yayi tayi saurin tureshi tana girgiza kai……*_Mutane wallahi ba kuyi ba, Kamar jiran mutum kuke yayi wani abu ku tasan masa da kanannan maganganu OH!🀦🏻‍♀ MUN CE ALMISKI na da side effect kuma baza mu canza ba..!Yeah munsan NANA AISHA (R.D)tana amfani da Almiski duk bayan d'aukewar al'adarta, ke duk bayan al'ada kike amfani dashi koko duk lokacin da kika bushi iska zaki zuba a gabanki…? Sannan irin,Almiskin da Nana Aisha tayi amfani dashi kike amfani dashi kema?karyane Almiskin da ake sayar muku dashi 200 500 karshe 2k shine pure miski a gurinku?Idan haka kuke tunani to tabbas karamar kwalwa gareku.😏Saboda masifar iskanci saei a biyoka pc a dinga maka maganganun da mutum bashi da ilimi akansu,kafin kuyi magana ku tabbatar kuna da ilmin abunda zaku fad'a...KAUYAWA KAWAI😊*

*HAJJA CEπŸ‘ˆ*
&
*FEEDOHMπŸ’ž*
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


     Page *86*

*U*ncle please dan Allah ka dena janyo min fitina ka fita kaje wajanta kafin yanzuma tazo har ta hanamu yin sallah."

K'arama ta fad'a tana kokarin kwatar kanta a wajan Ma'aruf, ganin duk ta rud'ene yasa ya saketa tare da mikewa tsaye dai-dai kunnanta ya rad'a mata yace,

 "Matsoraci kawai."

Kasa tayi da kanta zuciyar ta cike da tsoro, juyawa yayi ya fita yana murmushi cikin sa'a kuwa haryaje cikin bathroom Sumayya bata farka ba. K'arama ma tana ganin ya fita ta shiga bayi alwala tayi tazo tayi sallah sannan ta tashi Udutti itama tayi sannan suka kuma komawa suka kwanta sai dai K'arama ta gagara yin bacci tunani kawai take yi na yadda zata samu su dai-daita zaman su ita da Sumayya dan bata so ace sunyi zaman kishi.

Yana idar da sallar Sumayya ta farka, gadon Amir ta fara dubawa taga yana nan sannan ta harari Yaya Ma'aruf dake zaune kan sallaya yana lazimi be kulata ba dan yasan dole idan ta farka sai ta ci gaba da tijararta, mamakin shi d'aya yadda yaga ta iya bacci suna tare amma bata rungume shi ko kuma duk cikin kishin ne oho ya tab'e baki.

Sumayya na fitowa ta zari hijjb ta kuma d'aukar extra sallaya sannan tayi hanyar parlor, anan tayi sallah kasan cewar tasan idan a d'aki zata yi toh Ma'aruf zai iya fitowa yaje d'akin K'arama. Shima kamar yasan target d'inta dan haka yana kammalawa yayi bathroom ya kunna heater sannan ya koma kan gado, laptop d'in shi ya bud'e ya fara aiki sai dai duk kusan rabin hankalin shi yana ga K'arama, ko tayi bacci, ko kukan ta cigaba dayi duk babu wanda ya sani dan haka zuciyar shi ta fad'a cikin zullumi.

Ihun daya jiyo shiya sashi fita da gudu, a d'akin K'arama ya jiyo dan haka ya karasa ciki me zai gani! Sumayya ce zaune a ruwan cikin K'arama sai jibgarta takeyi sannan ta shak'i wuyanta, shima iya karfinsa yasa tare da yin ball da ita nan tayi gefe har kanta ya bugu da katakwan gadon d'akin.

Da sauri ya d'aga K'arama wadda ke ta faman rik'e wuya tana tarin wahala, Ma'aruf na niyar yin fad'a ya hango Udutti makure a karshen gado sai kuka take yi, saurin sakin K'arama yayi ya k'arasa wajanta tare da d'aukarta duk da tana da girma jan hannun K'arama yayi suka fito, ganin haka da Sumayya tayi yasa ta kuma yo kukan kura tasa hannu biyu tare da tura K'arama tayi gaba tare da buguwa da k'ofar d'akin kafin kace me goshinta da hannun hagonta sun bugu.

Wani wawan juyi yayi tare da kai idanunshi k'asa inda K'arama ke zube goshinta na fitar da jini, da sauri ya kalli Sumayya lokaci guda idamuwan shi sunyi jawur kamar taruwar jini ita kuma ta rik'e kugu sai girgiza take jira kawai take ya kawo mata duka itama ta zage ta rama amma sai taga sab'anin haka, d'ago da K'arama yayi tana mik'ewa tsaye ta saki wani uban ihu tare da komawa k'asa ta sulale sabida ji tayi tamkar zai cire mata kafad'a.

  "Uncle hannuna ya cire."

K'arama ta fad'a tana kuka, cicib'ar ta yayi suka fita ganin ya d'auke ta yasa zuciyar Sumayya tunzura da gudu tayi hanyar kitchen ta d'akko muciya, Udutti na zaune sai kuka takeyi a haka Sumayya ta tsallaketa, sai da ya shigar da K'arama cikin mota sannan yayi saurin komawa drive seat yana zama kawai yaji taratsatsa! Kallon gurin yayi a tsora ce nan yaga Sumayya r'ike da muciya ta fasa mai glass na setin da K'arama ke kwance.

  "Wallahi yau sai naga karshen cin amana, sai naga karshen wulakanci a gi.."

Bata k'arasa taji wani gigitaccen mari a duk gefen fuskarta wanda yayi sanadiyar sa hakorinta yin girgid'i, damkar ta yayi yana janta zuwa waje mai gadi da maiyi musu wanki da goga suka fito suna bashi hakuri, ko sauraran su beyi ba ya bud'e karamar kofar gidan tare da tunkud'a Sumayya waje, ihu ta dinga kurmawa shi kuma ya koma ciki tare da figar motar afusace yayi hanyar get har yana neman latsewa me gadi yatsun kafar shi.

Wani pravite hospital ya nufa zuciyar shi a jagole, yana zuwa nurses suka d'auki K'arama aka shiga emergency room da ita sai faman kuka take tana jin ta tamkar ba ita ba, yana tsaye yaji ringing d'in wayar shi zarowa yayi nan yaga sunan my everything wato Madre, wani zazzafan yawu ya had'iya kafin yayi peaking tare da karawa a kunne yayi shiru ba tare dayayi magana ba dan zuciyar shi wani zafi take yi mai.

Cikin kakkausar murya yaji Madre na tambayar shi,

"Ma'aruf kana ina?!"

"Hospital."

Ya fad'a a hankali yana kallon kofar room d'in da yake jiyo ihun K'arama, cike da mamaki Madre ta kuma cewa,

"For doing what?!"

K'irjin shi ya dafe tare da rufe idanuwan shi sannan yace,

"Madre na kawo Lil Hafsat ne za'ayi treatment d'inta."

"Treatment kuma Ma'aruf me yasa meta sannan kuma meya had'aka da Sumayya harka fasa mata baki tare da yi mata d'ankaran duka kuma ka koreta?!"

Shiru yayi dan yasan yanzu idan yace zai yi magana toh zuciyar shi na gab da kumbura dan haka sai daya dad'e kafin yace,

"Madre ki taho *Haske pravite hospital* zaki ga komai sannan zaki ji komai da idanki a kuma zahira ba labari ba."

"Ok I am coming soon..!"

Ko miniti 10 ba'ayi ba sai gata, number d'in room d'in ya gaya mata taje. Madre na shiga taga K'arama a kwance an nad'e goshinta da bandege hannan kuma nannad'e an sargafe mata shi da wani zare ya biyo ta wuyanta, salati Madre ta saki tana tafa hannuwa har takai kusa dasu tana kallon K'arama wadda Ma'aruf ke zaune akan kujera yana kallonta.

"Hafsatu meya faru haka yau na shiga uku ni Hafsat me zanji mezan gani."

Zama Madre tayi bayan Ma'aruf ya tashi yabar mata kujerar, cikin alhini ta kuma tambayar abunda ya faru nan ya sanar da ita iya abinda ya sani sannan ya d'ora da cewa,

"Wallahi Madre bansan yadda zanyi da Sumayya ba, duk iya yadda zanyi daga jiya zuwa yau na ganin ba'ayi abinda zai tada rigimaba sai da nayi Madre, amma yarinyar nan sai da ta yi tasan abinda zai janyo tashin hankali a tsakanin mu na kasa gane meke damunta dan wannan ba kishi bane..."

"Hmmm Sumayyatu kenan, ai ni dataje babu ko d'an kwali tana kuka tace min kana tashi daga bacci gurin Hafsat katafi dama da dare saidaka ci mata mutunci bayan mun tafi, toh shine bayan ta fito ta ganka da Hafsat kana shan bakinta oh ni Nana hafsatu, toh shine dan tayi maka magana ka rufeta da duka sannan ka korata gida kaji abinda ta ce min."

Ma'aruf kuwa yana jin Madre tace Sumayya tace wai yana shan bakin K'arama yayi saurin rintsa idanuwa, shin wannan yarinyar wace irin mata ce da batada kunyar furta ko wace irin kalma a gaban ko waye ciki kuwa harda mahaifan shi. Allah ya shiryeta ya ganar da ita yasa ta gane illar furucin ta a bainar jama'a da kuma karyar data koya. Ya fad'a a cikin ranshi, yana rik'e da goshin shi yaji muryar K'arama cikin kuka tana yiwa Madre magana,

"Madre wallahi Allah ba haka bane, ita aunty Sumayyan ce ina kwance nida baby Udut kawai ta shigo d'akin ta na duka na wai..wai...wai karna lalata mata 'y..."

Ta kasa k'arasawa sai kuka take zabga, a kid'ime Ma'aruf da Madre suka zaro idanuwa jin furucin K'arama na karshe dan ko bata k'arasa ba sun fahimci abinda take nufi.

Hakuri Madre tayi ta bawa K'arama suna nan harta fara bacci, gado aka basu har na tsawan kwanani uku kasan cewar gocewar k'ashi K'arama ta samu a hannunta, Madre ce ta kalli Ma'aruf yayi shiru harya d'an fad'a sabida shiga tashin hankalin da beyi tunanin zai shiga ba.

"Ma'aruf tashi kaje gida inyaso sai ka d'ebo yaran dan duk a gida kuka barsu itama bata d'akko kowa ba."

Zambir Ma'aruf ya mik'e dan sam ya manta da Udutti da Amir a gida, car key d'inshi ya d'auka da azama yayi saurin barin d'akin yana cewa,

"Ok ina zuwa Madre."

"Toh sai ka dawo Ma'aruf."

*******

 Ma'aruf na shiga gidan tun daga compound yake jin kukan Aminr yayi saurin fita a cikin motar ko kasheta beyi ba ya nufi cikin parlor, mamaki ne ya kusa kasheshi dan ganin Sumayya da yayi a zaune kan kujera tana kad'a kafa yayinda Udutti ke makure jikin kujera ta matse Amir a jikinta suna faman kuka.

Kutakan Sumayyar bebiba yayi saurin zama tare da d'ora su akan cinyar shi gabaki d'ayan su, lallashin su ya fara yi cikin sa'a ya samu Udutti tayi shiru sai ajiyar zuciya da take yi jefi-jefi ya zamana Amir ne kad'ai keta faman kuka yana janyo gaban rigar Ma'aruf alamar yana neman abincin shi, ganin haka yasa Ma'aruf tausasa murya ba tare da ya kalli Sumayyar ba yace,

"Kizo kibashi ya sha dan shi bashida laifi nine kuma ni zaki wulakanta amma shi yanada hakk'i akan ki..."

Wani shegen kallo ta watsa mai na irin zoka kwata d'in nan amma da yake ba kallonta yake yi ba sai taji be tanka mata, tsaye ta mik'e tana gyara su a cikin riga lokacin ya d'ago yana kallonta jin batayi magana amma ta mik'e, yatsina fuska tayi sannan tayi taku d'aya biyu tana ce mai,

"Oho ashedai nima ina da rana a gurinka Ma'aruf? Toh bazan bayar ba dan Allah kaje ka kawai waccan shegiyar yarinyar ta bata ai daman amfanin ta kenan, amma ni wallahi bazan bayar ba yadda ka fasa min bakin nan.. *!*"

Sumayya tayi maganar tana jan tsaki tare da rik'e kugu kamar yadda tayi d'azu,

"Tab lallai da ace ba uwa d'aya bace ta bamu tar biya ba da zan iya cewa ke d'in Sumayya tsinanniya ce, dan baki da mutunci ki haifi d'an da kanki sannan kizo kibashi abu yashi shine zaki ce min naje gurin wadda bata son meye haihuwa ba ta bashi...?!"

"Ashe kaji ni, ai wallahi Yaya au Ma'aruf ka d'ebowa kanka masifa dan sanin kanka ne bana kaunar kishiya amma kaje kayi min da yarinyar da ta tashi a gaban idona dan ka raina min hanka...."

Bata kai karshe ba taje an buge bakin nata, cike da masifa ta waigo tana zagi wa zata gani, kawai sai taga..... Shima Ma'aruf ganin haka yasa shi saurin mik'ewa yana kallon su baki bud'e.....

#readers
#Hajjafeedohm


_Wannan shafin na duk wani makarancin *ABIN DAKE B'OYE* ne, mungode muku da soyayya tare da binmu sau da kafa, harda *real mai dambun 'yan gayu na kabeje bana zogale ba* mun gode muku all_πŸ’ž

*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ

πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CEπŸ‘ˆ_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


     Page *87*

*A* tsaye taga Mama Hindu kanwar Mamanta fuskar nan a d'aure cikin b'acin rai take kallonta bayan duk taji abinda take fad'awa Ma'aruf d'in dan haka ranta ya b'aci sosai tace.

"How dare you da zaki zauna kina fad'awa mijinki uban 'ya'yanki wannan maganar Sumayya? Bari kiji in gaya miki mu d'ukan mu ann aikin banza ne a yanzu a wajanki domin sai kin nemi aljannar ki a gurin shi sannan zaki shiga aljanna, sannan nonon mahaifiyar shine kawai baki shaba amma Hafsat itace taci kashinki taci fitsarinki amanki wawuya sakarai kawai,

Sannan da kike cewa ba zai yi aure ba ke yanzu me zaki iyayi mai Sumayya? Bayan kin rigada kin wulakantar da rayuwar ki wannan abun da aka gaya min shine daliliin da yasa kika ganni a cikin gidan nan, domin koda Ma'aruf be auri Hafsatu ba toh sai nasashi ya dad'a yin wani auran."

Baki Sumayya ta turo tana yatsina fuska tare da bubbuga kafafuwa tamkar k'aramar yarinya, Maman hindu d'in ta kalla tare da cewa,

"Gaskiya ni dai Mamah kiyi shiru ya kike min fatan kishiya bayan kefa Mamah baki da ita kuma itama Madre bata da kishiyar nan sannan har Ummata tabar duniya batada kishiya, Yaya Najib da Yaya Suhaima dama Yaya Maryam duk babu me kisha ko mata biyu a cikin su sai ni za'a sawa ido ni wallahi bazan yadda."

Tayi maganar tana kuma sakin kuka, kallon banza Mamah tayi mata shi kuma Ma'aruf gabaki d'aya an sashi a duhu ya kasa gano inda maganar Mamah ta nufa dan haka beyi k'asa a gwaiwa ba ya tambayi Maman hindu,

"Mamah meke damun Sumayya wanda har yasa kika taso tun daga Adamawa zuwa nan har ma da kwararamin gwaiwar yin wani auran..?!"

K'arasawa tayi wajan shi ta k'arbi Amir, Sumayya ta kalla tare da cewa,

"Zo ki karb'e shi maza-maza ki bashi yashi sakaran wufi kawai, Sumayya waya gaya miki ana fushi da 'ya'ya amma dan sakarci ke jariri ma kike horawa da yinwa.."

Amir ta k'arb'a sai hararar shi take yi kafin ta fito dashi tasa mai a baki, ganin tana bashi yasa Mamah ta koma kan Ma'aruf dake faman kallon Sumayya dan karta kashe mai yaro tunda yaga alamar yau hauka takeji, muryar Maman hindu yaji tana cewa.

"Ma'aruf ka koma can asibitin muma yanzu drive zai maida mu can gidan Madre, idan komai ya lafa lokacin sai muyi magana akan matsalar Sumayya d'in...."

Yace "toh Mamah amma ku bari na kaiku da kaina mana."

Mamah ta kad'a kai alamar a'a sannan ta d'ora da cewa,

"Zo ka tafi ai tare nake da drive kai dai kawuce kawai."

Mik'ewa yayi ganin haka yasa Udutti saurin tashi itama tare da rik'e mai k'asan riga, kuka take yi tana cewa,

"Papa please take me out, bazan zauna a nan ba Mami dukana zata yi please.... *!*"

Kallon Sumayya Mamah tayi cikin takaici bata yi magana ba ta kalli Ma'aruf dake niyar lallab'e Udutti tace.

"Tafi da ita Ma'aruf ba kowa yaja wannan abun ba face uwarta, dan haka tafi da ita inda hankalinta zai kwanta."

Yace "Toh Mamah."

Daga haka ya mik'e tare da kama hannun Udutti suka nufi k'ofa, nan da nan Sumayya ta fara bala'i tama manta da cewar Maman Hindu na nan.

"Wallahi Allah ya isa, ai ni Matar shi ce amma me yasa ba za'a dinga kula dani ba sai wata can banza wawuya sakarai 'yar kauye za'a wani....."

Tassss! Sumayya taji wani gigitaccen mari, aikuwa ganin wanda yayi mata yasa ta kuma rushewa da kuka tare da ture Amir daga shan nonon da yake yi ta ruga da gudu cikin bedroom d'inta tare da kullowa. Kokarin dawowa ciki Ma'aruf yayi dan ganin yadda Mamah ta mareta da hanzari Mamahn ta nuna mai hanya ba tare da tace komai ba, jikin shi duk a sanyaye ya juya suka tafi ita kuma ta fito tasa drive ya maida ita gidan Madre bayan ta tsaya a super market ta siyi madarar da zata dinga bawa Amir.

Sai da K'arama ta kwana uku a hospital sannan aka sallamesu kasan cewar ciwon dake goshinta ya warke befi sauran k'arashe ba, sai gocewar kashin dake hannunta shi kuma sai a hankali, a tsakanin ranakun abubuwa da yawa sun faru, ana sallamar su gidan Madre suka wuce acan suka tarar Mamah tayi musu lafiyayyan girki mai rai da motsi, sai da Mamah tayi wa K'arama wanka kasan cewar bazata iya ba sannan suka koma parlo akaci aka sha, wajan karfe 7:08pm sai ga Sumayya babu abinda aka nuna mata hakan yasa ta shiga ciki ta zauna sai faman hararar K'arama take yi.

A d'add'are K'arama tace,

"Aunty Sumayya sannu da zuwa ina wuni..?!"

Mtwwwwwww! Sumayya taja wani shegen tsaki mik'ewa tayi ta nufeta zata d'auke Amir dake kan cinyar K'arama Maman hindu tayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa,

"Kul Sumayya! Kika sake naga kin tab'a yaron nan wallahi sai na lahira ya fiki jin dad'i marar kunyar yarinya."

"Toh wallahi ni dai a d'aga min yaro daga kan wannan wawuyar yarinyar mayya da iyayenta suka kasa kula da ita sai aka bawa wani..."

Babu wanda ya kulata ganin haka yasa ta saki kuka nan ma still akayi mata banza sai ma hirarsu da suka ci gaba dayi, K'arama kuwa tunda tayi kasa da kai bata sake d'agowa ba har sai da taji shigowar su Abba da Ma'aruf, tana d'agowa suka yi ido hudu ya sakar mata wani kayataccen murmushi tayi saurin maida kanta k'asa kirjin ta na bugawa kartaje ko aunty Sumayya ta gani.

Duka guri suka samu zama suka yi yayin da Abba yabi Sumayya da kallo wadda ganin shi yasa ta fara kukan kasa-kasa sab'anin da datakeyi kamar an doketa ya kalleta yace,

"A'ah Sumayya ya da kuka kuma a gaban yaranki?!"

"Abba Maman jindu ce."

Ta fad'a tare da yin shiru tana turo baki kai kawai ya kad'a Ma'aruf ya kalleta suka had'a idanuwa, baki ta murgud'a mai tare da hararshi. Muryar Abba suka ji yana cewa.

"Ya isah toh yanzu dai komai ya riga ya wuce sannan kuma kai Ma'aruf ya kamata yau kasan matsalar dake damun matar ka wanda ba kowa ya jawoba sai ita kanta dan haka Hafsa (Madre) sai ki fad'a mai yaji..."
 
Da sauri Sumayya ta turo baki tare da cewa,

"Gaskiya abba a fara cewa waccan yarinyar ta tashi wannan zancen sirrina ne be kamata ace wannan gajar taji ba gaskiya.."

Dukan su aka kalleta da sauri, K'arama tayi saurin janye Amir daga kan cinyar ta kwantar dashi tayi  akan carpet tana kokarin tashi tabar wajan jikinta har rawa yake yi abba yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa.

"Zauna kema Hafsat domin kema yanzu kin zama ta cikin gidan kuma kema yana da kyau kiji abinda ya faru da ita dan kema ki guji abinda ya jazamata shiga cikin matsalar... *!*"

Komawa K'arama tayi ta zauna yayin da Sumayya keta cika tana batsewa anan Madre ta sanarwa da Ma'aruf cewar Sumayya na fama da vaginal cancer da sauri Ma'aruf ya tashi yana kallonsu cikin wani irin yanayi tare da furta Kalmar "innalillahi wa'innailaihir raji'un how...?!" Madre ta d'ora da cewa,

"Sanadin shan magunguna barkatai nayi fad'an nayi nasihar babu abinda banyiwa Sumayya ba akan shan maganin matan da takeyi amma yarinyar na tayi kunnan shegu bata yadda ba tafi yadda dasu Beeba da shawarwarin su gashinan ga inda suka jefata yau ina yanzu ina Beeba da Kausar suke? Amsar itace basa nan ke kuma gaki an barki cikin matsala da shiga cikin ha'u'ila'in rayuwa.."

Sai a time d'in Sumayya taji kukan gaske yazo mata hakan yasa ta dinga yinshi baji ba gani, kusa da ita Ma'aruf ya matsa yana kallonta amma ita ta kasa had'a idanuwa dashi shi kanshi yasan yana sonta d'abu'unta da halayanta ne bayaso tun a baya gashi yanzu taje tajawa kanta matsala cikin tsananin tausayi ya bud'i baki yace.

"I am so sorry Sumayya, nasan duk abinda kika yi dan nine kike yi but ban tab'a cewa bana sonki ba sannan nasha gaya miki cewar bana son kina shan wad'annan abubuwan amma kin kasa ganewa gashi yanzu ya ja miki muguwar matsala Sumayya yanzu meye mafita ah?!"

Rintsa ido tayi hawayen na sirarowa akan hanuwan Ma'aruf, a hankali ya fara shafar kanta yana jin tausayinta har cikin jinin shi. K'arama kuwa kauda kai tayi tanajin wani abu na yawo a cikin jikinta uwa uba zuciyarta, kallon Abba Ma'aruf yayi tare da cewa,

"Abba zan kaita asibiti zan nemi asibiti acan chaina insha Allahu zata warke ta samu lafiya."

Kuma rik'eta yayi gaba d'aya tausayin ta ya kamashi dan yasan tana sonshi sosai,  Maman hindu ce ta kalleshi cikin jimami tace,

"Hmm Ma'aruf kenan wannan ciwon fa na Sumayya sai dai Allah kawai amma cuta kam tariga ta cuci kanta dan tayiwa rayuwarta illah karma kasha wani wahala kabarta ai tare zamu tafi tunda komeye ita tajawa kanta... *!*"

Cewa yayi "A'a Mamah Sumayya har yanzu matatace kuma hakk'ina ne na samar mata lafiya dan haka yanzu addu'ar ku kawai muke buk'ata.."

Duka suka amsa da amin tare da sanya misha albarka Sumy kuwa ji tayi kaunar shi ta kuma narke mata a cikin zuciya ta kuma makalewa a jikin a hankali ba tare da kowa ya gani ba K'arama ta sulale ta gudu d'aki sai bayan yaga Sumayya ta dena kuka sannan ya b'anb'areta a jikin shi ya zauna ganin bega K'arama ba yasa shi sakin sassanyan murmushi cikin ranshi ya furta cewar "Mata kenan." Amma a fili gyara zama yayi suka fara tattaunawar yadda tafiyar zata kasance duk da rabin hankalin Ma'aruf yana wajan new sahibar shi.

Mik'ewa Abba yayi ya wuce bedroom d'inshi nan itama Madre tabi bayanshi, kallon Sumayya Mamah tayi sannan ta mik'e tare da cewa,

"Biyo ni Sumayya ina son magana dake."

Ba musu ta mik'e dan yanzu kam jikinta yayi sanyi sai yanzu take nadama suna shiga Ma'aruf ya mik'e ya nufi hanyar d'akin su K'arama dan yana kyautata zaton nan ta shiga, aikuwa zaune ya hangota a gefen gado tana wasa da zaran da aka sargafe mata hannu dashi tana ganin shi tayi saurin mik'ewa tsaye tare da zaro idanuwa tana kuma kallon kofar da yake shigowa, cikin rawar murya tace.

"Un.. Un.. Uncle...!"

Yana karasawa wajanta tana yin baya dan bata son ya tab'ata Sumayya ta shigo a kuma ji mata rauni, sai da ta dangana da jikin wardrobe tana kwalalo mai idon yayi murmushi tare da sakata a tsakiya bayan yasa hannuwan shi ajikin wardrobe d'in, kasan cewar ba hijjab a jikinta ya sanya shi ganin yadda zuciyarta ke bugawa har na shanunta ke harbawa suma yayi murmushi tare da kafe ta da nashi idon, tsawan lokaci suna a haka can K'arama ta fara kokarin zamewa k'asa shima yayi saurin tarota tare da k'ara jinginata a jikin wardrobe d'in sannu a hankali ya zura harshensa cikin bakinta, da hannu d'aya me lafiyar K'arama ta dinga dukan shi amma ko gezau har sai da yayi son ranshi sannan ya cire gani yayi idanuwanta a runtse.

Hannunta yaja suka zauna a bakin gado still idanunta a rufe tak'i bud'ewa, ji tayi yana matsa mata yatsu tare da fad'in.

"Hafsat do you love me?!"

K'ara rufe ido tayi nan da nan jikinta ya hau rawa, sake maimaita mata kalmar yayi baki na rawa K'arama tace.

"Nidai Uncle ba ruwa na tsoro nake ji dan Allah kayi hakuri wallahi aun...."

Bata k'arasa ba taji hannunshi a cikin rigar ta, saurin ware idanuwa tayi tare da zaro su tana kallon Ma'aruf Wanda yake kashe ta da wani fitinannan kallo wanda yasa dole tayi shiru ta kasa cewa komai kafin wani lokacin ta fita a hayyacin ta sai wani irin nishi da take yi mai..."

Muryar Udutti ce da suka jiyo alamun zata shigo tana cewa,

"Aunty me kyau! Aunty me kyau Lil Mommahn papa bari ki gani."

Shine dalilin da yasa Ma'aruf saurin mik'ewa tsaye yana faman sosa gemu ya kalli kofar nan Udutti ta shigo yayin da K'arama ta juya baya idanuwanta a lumshe, kugu Udutti ta rik'e tana kallon Ma'aruf tace,

"Papa kaga kayan da Mamah ta kawo min masu kyau.."

Karb'a yayi yana d'agawa tare da furta mata,

"Woww! Looking so good, yayi kyau toh ina na aunty me kyau ko babu ita a rabon?!"

"Kai lalala papa bari naje na karb'o mata nata akwai kaya da yawa a gurin Mamah."

Tana fad'a ta juya da guda shi kuma dama jira yake yayi saurin komawa wajan gadon, d'agota ya kuma yi ya kara manna bakinsu guri d'aya tsawan lokaci kafin ya barta yayi saurin ficewa daga d'akin domin jin shi yayi ya fad'a cikin wani yanayi marar musaltuwa, yayin da itama K'arama ya barta cikin wani irin bad moment...

Cikin 'yan kwanaki Ma'aruf ya kammala yi musu boking na tafiya asibiti dashi da Madre da Sumayya sai Bassam, bayan sun kammala shirin tafiya ne ana gobe zasu tafi da daddare Ma'aruf ya samu K'arama a d'aki suna game ita da Udutti dan lokacin an cire mata zaran tana iya d'aga hannun yayi motsi,

"Udutti oya jeki wajan Madre ki zauna zanyi magana da auntyn ki."

Ba musu ta mik'e ta fita tana waigensu, tana fita yayi saurin rufe kofar tare da komawa wajan da K'arama take tana mai kallon mamaki.

"Yah? Ko baki ganeni bane kike kallona?!"

Kai ta girgiza cos ta kasa magana babban tashin hankalinta rufe kofar da yayi ko me zai mata oho. Janyota yayi tana faman nok'ewa sai da ya kaita gado sannan ya kalleta cikin wani mugun yanayi taji muryar shi k'asa-k'asa yace,

"Please Hafsat help me...help me kinji?!"

Tashin hankali iya tashin hankali K'arama ta kalleshi cikin tsoro tace,

"Uncle for..for..for what....?!"

A hankali cikin hikima yana zame mata rigar jikinta yace,

"Hafsat for your......"

Tayi saurin rufe mai baki da gashin kanta wanda yake a tsefe tayi parking d'inshi.....


*FEEDOHM*πŸ’ž
&
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*πŸ‘ˆ


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


          Page *88*

 Lumshe Ido tayi tana k'arbar sak'on ninshi sam bata yi k'ok'arin hanashi abunda yake niyyar aikatawa ba tunda tasan illar abun sae da jikinta dake k'yarma sosae…Mintina kad'an ya dauka yana tsotsar bakinta yayin da ya kasa tsayar da hannunshi guri d'aya a hankali  ya janye daga jikinta ya koma gefe guda ya kwanta yana mayar da lumfashi!kamar an tsikareshi ya mike ya fad"a toilet ya fito da alwalarshi sannan ya dubeta ido a lumshe yace "Shiga kiyo alwala Hafsatu"

 Ba tare da ta kalleshi ba ta mike ta shige tayo alwalar kamar yarda ya bukata sannan ta fito ta iske har ya shinfid'a masu abun sallah binsa tayi sukayi raka'a biyu sannan ya sallame tare da mata addu'a kafin ya mike ya kama hannunta ya zaunar da ita gefen gado fita yayi ya dawo dauke da cup din ruwan zafi a hannunshi da plate dake dauke da naman kaza da kwae dafaffe ko'ina ya samosu oho…Har lokacin idonta na k'asa ta kasa d'agowa bare ta kalleshi wata irin masifar kunyarshi ta hanata sukuni…

 Zama yayi bisa sofa yana kallonta a hankali yace "Ga abinci kinji Hafsatu…!

 Murya k'asa k'asa tace "Uncle munyi dinner "

Hannunta ya kamo yana murzawa yace "Na sani Hafsatu ina so ki ci wannan ne "

 Sam bata son ta mashi gardama don haka ta dauki cup din ruwan zafin tasha kadan tare da kwae ta aje wanda ta rage ya dauka ya sha ya mike ya mayar da sauran kitchen sannan ya dawo ya shiga toilet yayo wanka ya dade tsaye gaban mirrow yana shafe shafe kamar mace ba tare da ya kalleta ba sannan ya saka kayan bacci ya kullo kofa ya dawo ya zauna gefenta…

 Hannunta ya kama ya had'e da nashi murya k'asa k'asa ya mata nasiha sosai mai ratsa jiki tare da fad'a mata hakkokin miji akan matarshi tare da tambayarta wasu abubuwa akan addininta duk da yana da tabbacin tasan wasu !bai samu matsala ba tunda dai dai gwargwado ta bashi amsa gamsashshiya!cikin wayau ya jata jikinshi sannan ya kwanta bisa gadon tare da murginata k'asanshi…

 Wasu bak'onnin lamurra ya fara gabatar mata cikin natsuwa da hankali…Lumshe ido tayi tana k'arbar sak'on ninshi ba tare da ta furta ko da kalma d'aya ba!A Hankali ya tafiyar da ita har ya samu abunda yake bukata ba tare da ya cutar da ita ba !duk da ta ji zafi hakan bai saka ta masa ihu ba sosae. Ta nuna jarumta had ya mayar da ita cikakkiyar mace kamar kowa, addu'a kam ta shata tare da albarka…

  Da Asuba ya d'ad'e yana kallonta yana murmushi shi kad'ai kafin yayi kissing lips dinta ya mike ya shiga toilet ruwan zafi ya sakarwa kanshi yana jin wani farin ciki da natsuwa na ratsashi tabbas tun da yake bai taba samun gamsuwa irin wadda ya samu gurin Hafsatu ba ko dan ita bata tab'a shan wani magani da niyar ya k'ara mata ni'ima akan wadda Allah ya bata ba?tabbas Natural beauty ce babu had'i bare algusur a tare da ita…Ya dade sannan ya fito ya zira jallabiya ya k'ara lullubeta da bargo ya bud'e kofar da sauri ya fita zuwa masallaci…

  A Hankali ta bud'e idonta tare da janye bargon ta sauko da kafafunta kamar mai koyon tafiya ta shige toilet!cikin ruwan pure ruwan zafi ta shiga ta zauna ta runtse idonta ruwan na ratsata sosae…Ma'aruf kam ana gama sallar ko addu'a ba'a gama ba ya taso sauri kawae yake kar ta tashi bai koma ba, yana shiga dakin ya ga wayam babu ita karar ruwan da yaji a toilet ya tabbatar mashi da tana ciki murmushi ya saki a hankali ya k'arasa bakin toilet d'in yana knocking…

 Duk da tana jinshi ta masa banza don bata ga abunda zai mata ba …A Hankali yace "Lemme help you Hafsatu"

 Banza ta masa ta cigaba da wankanta ganin ba bud'ewa zatayi ba ya sashi fita ya shiga d'akin Sumayya bisa gado ya isketa tana baccinta hankali kwance yayin da Udutti ke kasan bed din ko ba'a fad'a mashi ba yasan fadowa tayi, ya duk'a ya dauketa ya mayar da ita bisa gadon sannan ya matsa a hankali yaja yatsan kafar Sumayya…Da sauri ta dube ido tana hamma ba tare da ta rufe da hannunta ba kallonshi tayi sama da kasa tare da bud'e hanci tana shakar kamshin sabulun da yayi wanka dashi, harara ta sakar mashi tace  " Wankan me kayi da asuba?

Kamar saukar aradu yaji tambayarta to me ya shafeta da wankanshi a hankali yace "Don nayi wanka da asuba sae na fad'a maki dalili Sumayya?ko da bana wanka a duniya bai kamata ki man wannan tambayar ba bare kin san kullun idan na tashi sae nayi wanka "

 Turo baki tayi ta mike ta fad'a toilet ta barshi tsaye, a sanyaye ya lullube su Udutti sannan ya fita ya koma d'akin K'arama bisa pray mat ya isketa ta d'aga hannu tana addu'a ya k'arasa kusa da ita ya tsugunna har sae da ta karashe addu'ar sannan suka shafa tare…

 Murmushi ya sakar mata ta mayar masa da martani sannan ta mike ta linke praymat din ta cire hijab din tare da duk'awa har k'asa tace "Good morning Uncle…!

 Hannunshi biyu ya daura saman shoulder inta ya d'agota ya had'eta da jikinshi cikin rad'a yace "How're you?

 Bata amsa ba sae dae janye jikinta da tayi ta taka a hankali ta yaye bedsheet din gadon ta nufi toilet dashi saurin bin bayanta yayi ya k'arbe yana jefa mata hararar wasa ya dauketa cak ya mayar da ita saman gadon ya saka duka hannayenshi ya danneta kamar k'aramar yarinya yana fad'in "Sleep…"

 Murmshi tayi idonta a lumshe ba tare da tace komae ba wani irin farinciki take ji wanda tunda take bata tab'a tunanin samun irinshi ba …rabin jikinta ya danne yana leken fuskarta tare da kissing wuyanta…Hannu ta saka ta tureshi ta gyara kwanciyarta shi kam mikewa yayi ya shiga toilet ya wanke bedsheet din sannan ya koma kitchen yana k'ok'arin had'a masu break don ya tabbata ko sama da k'asa zata had'u Sumayya bara ta tab'a had'a masu ba bare ma ta fahimci abunda ke faruwa…

 Irish ya soya masu da kwai sai ruwan zafi da ya had'a sannan ya leka d'akin Sumayya don ya tadata ta shirya saboda karfe 9 zasu tafi amma gaban mirrow ya isketa tana kwance kanta da mamaki ya kalleta yace "Meye haka Sumayya?Ya baki shirya ba kin tsaya tsifar kai bayan kinsan tafiya zamuyi?

 B'ata Fuska tayi tace " Ba wanka zanyi ba ai ..

 "Bangane ba?ya tambaya a hankali


   Sama da kasa ta kalleshi wani irin kishi na fizgarta tace "Kaya kawae zan sake nace"

 Bai ce mata komae ba ya girgiza kai tare da matsawa kusa da Udutti ya kama hannunta ba tare da ya mata magana ba ya nufi d'akin K'arama da ita yana shiga ya wuce toilet ya had'a mata ruwan wanka zai mata da sauri K'arama ta mike ta bi bayanshi tana fad'in "Uncle barshi na mata..."

 Kallonta yayi dauke da murmushi yace "Barta kin ji Hafsatu kiji da jikinki.."

  Udutti tace "Papa ka bar Aunty ta man !yauwa jiya na dawo inata knocking amma kak'i bud'e man ko papa?me kukayi?

 Kallon juna sukayi sannan K'arama ta fita toilet din da sauri binta da kallo yayi tare da girgiza kai yana bala'in son mace mai kunya a rayuwarshi…Sae da ya mata wankan sannan ya d'aukota ya maidata d'akin Sumayya ya dawo ya shiga kitchen ya dauko break din da ya had'a ya dawo d'akin K'arama dashi!Kwance ya isketa tana kallon sama ya k'arasa ya aje plate din a sofa sannan ya zauna bakin gadon yana kallonta a hankali ya kira sunanta "Hafsatu…!

 Bata kalleshi ba ta amsa "Na'am…!

Hannu ya saka ya tadota zaune yana kallonta cike da so tare da janyota jikinshi sosae yace "Ki tashi kiyi breakfast sae ki koma ki kwanta kin ji ko…"


 Kanta ta sunne k'asa tana jin wata irin kunyarshi na ratsa ta sam ta kasa had'a ido da shi sae sunne sunne take cup din tea ya kafa mata a baki duk da yasan da zafi …

  Ta kusa furzar da sauri tana kallonshi a shagwabe tace "Uncle da zafi ka bani…"

 Kashe mata ido yayi yace "Ko?

Ta turo baki tare da janye jikinta daga nashi ta juyar da kai …Dariya ta bashi ya kara janyota tare da kafa mata cup din a baki wannan karon turewa tayi tana hararanshi k'asa k'asa tace "Uncle da zafi fa nace maka kuma ka k'onani…"

 Kamar gaske ya dafe kai yana fad'in "Oh to yi hakuri muga inda kika k'one?ya k'arashe maganar tare da tura hannunshi a bakinta yana lalubar saman tongue dinta…sannan ya kai bakinshi dai dae nata ya hade su tare da tsotsar tongue dinta na yan mintina sannan ya zare yana kallon yarda ta lumshe ido ……

 A Hankali yace "Ya warke ko?Shiru ta masa idonta har lokacin a lumshe…

 Murmushi yayi mai sauti yana fad'in "Sorry bara na hura maki ya huce…!

  A Hankali ya ciyar da ita har sae da ya tabbatar da ta k'oshi sannan ya mike ya mayar da plate din kitchen ya dawo d'akin

Kamar tayi kuka tace "Uncle ina son zan gayar da Aunty "

 Hannu ya mika mata ta kama ta mike suka fita, d'akin sumayya suka shiga suka iske tana sakawa Amir kaya daga bakin kofa K'arama ta toge ta tsugunna tace "Aunty Ina Kwana?

 Banza ta mata ta cigaba da abubda take Ma'aruf ya matsa kusa da ita tare zama bisa cinyarta yace "Tana gaidaki"

 Tureshi tayi tace "Na dauka da Amir take"

Waro ido yayi yana murmushi don yasan tana sane da ita take ya janyota jikinshi yana fad'in "Da ke take Sumayya"

 "Ok…"ta fad'a tana hararanshi

  K'arama kam a sanyaye ta mike ta bar d'akin yayin da Sumayya ta bita da kallon sannan ta mayar da kallonta ga Ma'aruf cike da tuhuma kamar zatayi magana kuma ta share ta cigaba da shirinta shima wanka ya shiga ya shirya sannan ya kira Su Madre suka ce su suke jira, gurin K'arama ya koma yace ta shirya su tafi!sae da ta kuma wanka sannan ta saka wani atampha sky blue da ratsin orange a jiki ta dauko after dress ta daura sama tare da rolling da gyalenta powder kawae ta shafa tare da lipstick ta fesa turare……das ta fito da ita kamar ba ita ta dauki plate shoes orange ta saka tayi k'ok'arin dae daeta tafiyarta ta fita!a falo ta iskesu yayin da Sumayya ta bita da wani shegen kallo tare da kwafa ita kam hannun Udutti ta rike kanta a k'asa tayi gaba Sumayya ta mara mata baya sannan suka tafi…A Gaban mota Sumayya ta shiga yayin da Su K'arama suke a baya……
 Ta glass din motar ya kalleta ya sakar mata lallausan murmushi tare da kashe mata ido ya dauko wayarshi yana latsawa sannan ya tashi motar …

 Dan guntun text ya shigo a wayarta ganin sunan Uncle yasa ta kalleshi da sauri sae taga sam hankalinshi naga Sumayya ko mai yake fad'a mata oho ta ga dae tayi dan guntun murmushi tana harararshi……

 Text din ta bud'e "Let's stay this way forever. I love you" Abunda ya rubata kenan…Kallonshi ta kuma yi cikin sa'a suka had'a ido ya sakar mata mayun idonshi ta mirrow tayi saurin sadda kai k'asa cikin kunya…Taso ta tsayar da idonta cikin nasa amma ya mata kwarjinin da bara ta iya ba tana da tabbacin Uncle dinta na da kaso mafi tsoka a cikin zuciyarta idan tace bata jinshi a ranta ta yi karya mafi muni a rayuwarta tabbas shine jigonta domin ta d'ad'e da sanin haka…Lumshe ido tayi tana k'ara jin wata kaunarshi na zagaye mata duk wani tunaninshi sam bata ganin girmanshi ko shekarun da ya bata kaunarshi kawae take gani a zuciyarta ……

 Sae da suka d'auko Madre da Abba sae Mamah hindu sannan suka tafi airport sam Sumayya ta hanashi keb'ewa da K'arama tana makale dashi duk da yana bukatar hakan, har Abba yace su taho su koma… A Hanya ya tsaya ya sayar masu fruit da yan tarkace sannan ya aje su gidansu Udutti ya wuce shima……

【】

 Hafsuwalle kam zaune suke cikin jin dadi da kwanciyar hankali ga wata soyayya da mutane gidan da kauyen ke nuna mata ko da yaushe Ma'aruf cikin aiko masu da kudi da kayan abinci yake duk da K'arama bata sani ba, sam bata da matsala a rayuwarta sae dae aure da aketa maganar tayi amma tace ba yanzu ba …

 Lauratu ma duk da tana kauye tayi bul abunta domin Sallau bai rageta da komae ba!Ma'aruf ya aiko aka saka yaranta tare da wasu yaran na cikin gidansu makaranta a cikin gari sannan idan suka tafi tun karfe 8 sae 6 na marece zasu dawo saboda boko ce da islamiyya sannan kullun motar aikinsu zata zo ta dauki yaran ta kaisu Makaranta ta dawo dasu sam basu da matsala a rayuwarsu sannan duk abunda yake sam K'arama bata sani ba……

 Kafin Ma'aruf ya bar k'asar sae da ya masu hanya Unicef ta dauki nauyin yima kauyen titi tare da gina masu karamar makarantar boko da karamin Asibiti !sosae Hafsuwalle take samun girma daga gurin ilahirin kauyen da makwabtansu ganin duk sanadinta suka samu cigaba ……
 Maitafasa ma an ware mutunci bad'a bad'a da su Hafsuwalle soyayya take nuna mata kamar itace marigayi Ladon don bata kwana biyu bata zo ta ganta ba kuma bata zuwa hannu d'aya sae ta taho mata da tafasa da hura …Kundum ma ba laifi ta rage duk wani munahurci tana bin maitafasa so da kafa zamansu gwanin ban sha'awa sannan suma duk lokacin da Ma'aruf yayi masu aike akan debi wani abu akai masu…

  Yauwa kamar kullun maitafasa tana tsige tafasa Kundum ta fito daga ban daki tana tsefe kanta tsaki Maitafasa taja tana watsa hannu tace "Wae Kundum anya gurin gyatumarki kikayi wayau kowa?
 *HAJJA CE*πŸ‘ˆ
&
*FEEDOHM*πŸ’ž
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*πŸ‘ˆ


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


 *Missing Some one Likely to call her back 【Aunty SisπŸ’ž】*


       Page *89*


     *D*ariyar yak'e Kundum tayi tace "Oh ni Kundum me kuma nayi haka maitafsa?

Ta kuma watsa hannu tace "Banda rashin sanin ciwon kai da rashin fad'an gyatuma meye na tuge kai a makewayi?

Tab'e baki Kundum taya ta watsa hannu gaba ta fad'a bukkar ta tana fad'in "In ko rashin fad'an gyatuma ne Maitafasa to kema bana tunanin kin iske gyatuma a raye tunda kema kina toge kan a makewayi."

"Ki kace me! ban iske gyatuma a raye ba?" Maitafasa ta fad'a cikin d'aga murya.

Banza kundum tayi mata ta mike tana watsa hannu tace "Ta kwarankwatsa Allahu ya kaimu lokacin da bature zai yi mani aike Aradun Allah ko kwayar hinkaha bakici…"

B'urum! Kundum ta fad'o tsakar gida tana fad'in "Me yayi zahi Maitafasa?ta kwarankwatsa ba haka nake nuhi ba…"

Banza Maitafasa ta mata kusa da ita ta motso tace "Haba Suwaibatu kakarsu Hafsatu da lauratu dan kin hanani kayan arziki me kika yi kenan?duk duniyar ga kowa ya sani sanadin jikarki kauyen ga ke ta bunk'asa, kowa yasan jininki jinin daraja da arziki ne Suwaiba!Idan kinga dama yanzu zakice a kwashe kwaltar titin kyauyan nan ko kuma ki hana kowa bi ta saman shi tunda mijin jikarki ne yasa a kayi shi, ko kuma ki rushe boko da arabi babu wanda ya isa ya tanka Suwaiba Mai abun Alkhairi kakarsu Hafsatu matar Bature. Aradun Allah yanzu baki da kamata a kauyen ga!aradun Allah haka nima banda kamarki yanzu ki ya heni nima na dangwali arzikin jikarki Suwaiba…!

K'irarin ya sata washe jajjayen hakoranta tare da kaiwa Kundum duka a kirji har zaninta yana kwancewa tana fad'in "Dad'i na dake Kundum kin san lagwan Maitafasa, ta k'warank'watsa ni dake mutu ka raba!tahi ki hirya muje gano jinin alheri (Hafsuwalle) hinkafa kam har sae kin ture ta aradun Allah."

****

Ard'o ya shigo yana kwalawa Inno k'ira kamar had'in baki mutanen gidan suka fito cirko-cirko ya bisu da kallon takaici yace "Wai wane irin iskanci kuke haka ne?me yasa idan an kira mutun d'aya sai ku fito kamar ku aka kira gulma ko me?!"

A Hankali suka fara watsewa ko wace ta kama gabanta inno ta fito yace "Biyo ni akwae zance inno…!

Bukkar shi ta bishi sai da suka zauna sannan yace "Yanzu Hakimi ya turo aka d'aukeni, Inno yazo min da wani gatsaren labari mai shegen firgitarwa …!

Dafe k'irji tayi had'e da fiddo da idanu tace "Me kuma ya faru Ard'o?Hala dai daga Hafsatu K'arama da mijinta ne?

"Ina fa wai Hafsuwalleta yake neman ya amra…" ya fad'a kai tsaye yana k'walalo idanuwa waje.

A Zabure tace "Kace me?Hakimi ke bid'ar amren Hafsuwalleta?Allah da gaske ko da wasa Ard'o?

"Aradun Allah da gaske yake Inno...!" Ya fad'a kai tsaye,

Kunya ce ta hanata rafka gud'a sai dai ta maida kanta k'asa tana fad'in "Allahu mai yarda yaso!kasan farkon rayuwarka amma baka san tsakiyarta da karshen ta ba…Allah ya sanya alkhairin shi lallai Hafsatu K'arama Haske ce garemu baki d'aya sanadinta komai ya canza."

Ard'o ya samu Hafsuwalle da maganar tare da bata shawarwarin ta k'arbi zancen da kyakykyawar addu'a kada rashin Lado ya hanata auren wani, sosai ta karb'i shawararshi tare da amincewa da neman zabin Allah……

Ba'a d'auki lokaci ba aka saka ranar d'aurin aure da tarewa sam K'arama bata san da zancen ba saboda lokacin Ma'aruf yana k'asar waje sae dae shi ya sani a waya aka sanar mai……


【】

K'arama kam tun da suka tafi Madre ta d'auko wata 'yar tsohuwa ta zauna tana taimaka mata, sosae take kula da Udutti don da Amir aka tafi… Hankalinta ya kwanta fatar jikinta ta nuna tsantsar hutun da take samu ga wani kyau na musamman da ta k'ara mai sanyaya rai…

Cikar kyau ta wanzu sosai a tare da ita ta juye izuwa fulanin usul sak mahaifinta Lado hatta gashin idonta gazar-gazar irin na Lado ne tare da girarta bakinta…Banbancinta da Lado bai wuce biyu ba ta fishi karan hanci da kuma sharp d'in idanun su wanda nata yake sexy eyes kamar na mage yayin dashi yake da rowbll…,

Kullum Ma'aruf zai kirata sau uku a rana da safe da rana sae da daddare sosai yake nuna mata soyayya duk da basa kusa amma shakuwa ta k'ara wanzuwa a tsakanin su duk wata kunya K'arama ta ajeta gefe soyayya suke murzawa kamar ba gobe babu wata kalma da zai fad'a mata ba tare da ta samo amsarta ba ta bashi ko dan bata ganin kwayar idonshi oho…! Dan Sai su fi awa biyu suna waya sai sun gama sannan zata bawa udutti su gaisa itama…

Sumayya kam akan magunguna suka d'aurata saboda cancer bata yi karfin da za'a mata Radiation therapy ko Chemotherapy treatment ba, sannan sun fad'a mata da kyar idan zata kuma haihuwa sosau ta shiga tashin hankali yayin da ta saka shi a gaba tana kuka tausayinta ya kamashi ya lallashe ta tare da bata baki har ya samu tayi shiru, k'yak'yk'yawan kashedi suka mata akan ta kiyayi abubuwan da take amfani dasu don da tayi k'arfi wallahi wahalar magani gareta don duk treatment d'in da za'a bata warkewa don zata yi spreading a pelvic d'inta sannan ta cigaba da spreading to other part na jikinta wanda ko an anyi treatment ta warke bayan wani lokaci kad'an za'a sake ganin ta b'ullo wani b'angare kuma a haka za'ayi ta wahala karshe sai dai a hakura har Allah yayi nashi hukuncin akai……

   _Babban abunda dake janyo mana vaginal cancer wanke farji da sabulu ko wane irine kowa hatta virgin soap da muke ganin danshi akayishi to duk cuta ce, sannan yawan cushe cushe a al'aurar mu ko hayaki na itacen da bamusan daga inda suke ba wani ma ganye kawae zai samu ya debo yayi had'e had'enshi ya kawo maki ke kuma ki saya kina washe baki ke zaki burge miji!Je ki burge mijin yar 'uwa zuwa lokaci mijij zai burke ki……!A Yanzu mata mun dauki Almiski mun bashi wani matsayi na babba a rayuwarmu muna ganin yana matsemu ko?tabbas zai matseki amma bayan ya dauke damshi da ni'imar da Allah ya baki!ki k'watanta zuba ruwa a cikin auduga zatayi taushi da dad'in tab'awa ki tsira tsinke a ciki zai wuce cikin dadin da kwanciyar hankalu sannan ki zuk'e ruwan ki matsewa zata matse ta dunkule guri daya sam bata zatayi dadin tabawa ba bare ma tsinki ya shiga …haka al'aurarki take da zaran kin zuba miski zaya zuk'e damshinki sannan ki matse kamar yarda kike so amma babu sauran ni'ima da ta rage maki ……Almiski da muke amfani dashi wallahi tallahi yana da mugun illa garemu mata yakan daukewa mace danshinta gaba daya ya rabata da ni'imarta mun ga matan da hakan ta faru dasu sosae !bawae an hanaki amfani dashi bane aa ana amfani dashi duk bayan daukewar al'adarki don ya kawar maki da karnin jini kamar yarda NANA AISHA RD tayi amfani dashi kuma itama ba can cikin al'aurarta ta saka ba a'a waje waje take sakawa!Sannan ku lura da kyau kun gane Almiskin da muke amfani dashi yanzu wallahi ba pure bane an riga an mashi hadi anyi ha'inci a cikinshi wani salon ma da aka zo mana dashi wai har da sabulun Miski ake sayar mana mu dinga tsarki dashi anan zaki lura kamar yarda syka hada sabulun haka suka hada miskin da suka sayar maki !Akwae matan da duk lokacin da miji zai rabesu sae sun saka miski a jikinsu me kenan?…Yar 'uwa kada gurin neman gira ki rasa ido wallahi duk yarda namiji ya kai ga sonki da kin rasa wannan gurin kin tashi aiki!Karki je gurin faranta mashi ki kwari kanki ki nakasa kanki ki zalunci kanki Karshe kina gani ki zama wulakantatta ya auro wata ya barki da raino idan ma ya maki adalci bai turaki gida ba…_

  _Me zai hana ki saki kayan mata ki mata ya'yan itatuwa?Me zai hana ki bar wanke farjinki da sabulan mata ki zauna a ruwan dumi?Me zai hana ki kiyayi cushe cushe domin inganta lafiyarki ?Me zai hana ki rike Allah da biyayya domin dorewa zaman lafiya?Me yasa su maza basa shan kayan da zasu kara ni'ima?ko basa so su burge matayensu?koko sanin ciwon kansu sukayi?sae ke yar'uwa ?duba da kyau kiyiwa kanki karatun ta natsu!komai da lafiya a ke komai in babu lafiya shagarle……_

Cikin d'an lokaci Sumayya ta samu sauki ta warke ras!sosai Ma'aruf yake kula da ita sannan ya kan bata lokacinta dai-dai gwargwado yakan guji yin waya da K'arama a gabanta duk lokacin da zai kira K'arama sai ya fita harabar Hotel d'in da suke ya samu k'eb'ab'b'en guri sannan ya kirata… Ana gobe zasu dawo Nigeria bayan sun dawo daga sayayyar kayan tsaraba mai taxi ya taya su shigar da kayan su ciki sannan yayi hanyar fita yana latsa wayar shi kallo Sumayya ta bishi dashi tare da tab'e baki tana hararan shi, juyowa yayi suka had'a ido ya sakar mata murmushi yana fad'in "Wannan hararar na meye my dear?

Tab'e baki tayi still tana hararanshi sannan tace "Ka je kayi abunda ke gabanka, bana son burin kunya ni."

Dariya ya saki mai sauti yace "Me ye na borin kunya Sumayya!matata fa zan kira shine borin kunyar?!"

Tsaki ta saki taci gaba da jera kayan su a jaka dawowa d'akin yayi yana dariya ya zauna yana fad'in "Toh Na ma fasa."

Banza tayi mishi ya cigaba da janta da hira ganin ba kulashi zata yi ba ya sashi mikewa yana fad'in "Tunda kin min banza bara nayi abunda zai fi min."

Kai tsaye tace "Kai dai ka sani…!

Fita yayi yana kiran K'arama ringing d'aya ta d'auka tare da shagwab'e murya tace "kaiii Bunkul sai yanzu ka tuna dani ko?

Murmushi yayi kamar tana ganin shi yace "Waya fad'a maki Hafsatu?kina a cikin raina…"

Dariya tayi mai sauti tace "Da gaske Uncle ?Ina Aunty Sumayya da Amir?

Windown su ya kalla sannan yace "Tana d'aki tana shirya mana kaya…"

K'arama ta shagwab'e murya tace "Gaskia kaje ka taya ta na yafe maka wayar yau tunda gobe zaku dawo…!

Cikin salon shi shima yace "Me kika tanadarwa dawowa ta Hafsatu?

Cike da kunya tace "Komai ma Uncle Ni dai kaje ka taya Aunty had'a kayan." ta k'arashe maganar cikin sigar jan hankali.

Ido ya waro yace "Ba fa wani aiki bane Hafsatu……"

A Hankali tace "Duk da haka Uncle kaje…"

Lumshe ido yayi tare da kissing d'in wayar a hankali yace "Okk Bye-bye." Shiru suka yi babu wanda ya katse wayar sai itama da ta rungumeta a kirjinta tsawon mintina sannan ta kashe ya koma dakin su a zaune ya iske Sumayya ta rafka uban tagumi ya zauna tare da janyota jikin shi yana rad'a mata kalamaj masu kwantar da zuciya ga mai jinsu…,

Murmushi ta masa yace "Sumayya kin San Allah Hafsatu bata d'aukeki a matsayin da ke kika dauketa ba, wallahi tana sonki da zuciya d'aya ki bar ganin laifinta ki tsaya kiyi tunani da kyau ita kanta lokacin da na aureta bata san menene duniyar ba kuma nima ban aureta da wata manufa ba na aureta ne saboda yanayin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki." Sosae ya mata nasiha cikin kwantar da murya har taji ta kuna fahimce shi……

Lumshe ido tayi tana lalubar bakin shi yayin da ta fara tsotsa cike da yinwarsu tabbas tayi missing komai nashi cikin k'ankanin lokaci suka lula wata duniya mai wuyar fassara…

Sae da ya tabbatar da ya wanke laifin shi sannan a hankali ya janyo wayashi cikin dabara ya turawa K'arama goodnight text yana murmushi tare da makaleta cikin jikinshi.


【】

Tunda ta tashi da Asuba ta shirya Udutti ta tafi makaranta ta shiga kitchen ta fito da kaza daga fridge ta aje ta huce sannan ta fito da hanta da kayan miyan da tasa Bala ya siyo mata masu kyau jawur dasu jiya duk da suna da markad'add'u a cikin frigde, wankesu tayi ta yanka slice sannan tayi grinding attarugu da albasa da garlic ta aje gefe guda, Man gyad'a ta d'aura saman fryingpan da wuta k'asa k'asa ta wanke kazar ta yankata ta bad'eta da curry da thyme da spices kala kala kafin ta juyeta cikin man ta zuba albasa da attarugun da garlic da tayi grinding a sama ta rufe frying fan din ta rage wutar sosai…

Tukunya ta kuma d'aurawa ta juye kayan miyan da ta yanka tare da ruwa kad'an ta rufe Sannan ta fera doya ta d'aura a saman wata tukunyar da sugar kad'an a ciki…

Kwakwata ta samu ta gurje bayan duk bakin ya fita sannan ta gurzata kanana kanana ta aje a fridge, Ganin kayan miyan sun dahu ya saka tasa abun kad'a kwai ta murje kayan miyar har sai da suka burgu sannan ta cire zare zaren kayan miyar tare da zuba mangyad'a da spices ta rufe, Cabbage ta yanka da carrot da hanta ta zuba a cikin kayan miyan har sae da ruwansu ya shanye sannan ta bude ta cigaba da motsawa a hankali sannan ta koma ta sauke doyar ta aje gefe……

Kazar ta bud'e ta iske ta dahu sosai cikin man har ta fara soyuwa yayin da tayi kore shar tayi kyau kayan miyan duk sun like a jikinta cigaba tayi da soyata sama sama sannan ta kwashe ta juye a warmer ta kai dinning…

Gurin miyar ta koma ta iske ta d'an soyu ta fasa kwae ta zuba akai taciga da juyawa a hankali har kwan ya murje yayi fari-fari sannan miyar ta washe tayi kyau, curry ta kuma zubawa ta k'ara spices sanna ta rufeta tayi k'asa da wutar sosai yadda ba zai kama ba…

Maimakon ta saka ponded engine sai ta d'auko turmi ta wanke sannan ta saka doyar ta cigaba da dakawa har ta daku tayi laushi da santsi sannan ta dauko madara peak ta zuba akai ta cigaba da dakawa!sae da ta tabbatar da sakwararta tayi lafiya lau sannan ta kwashe ta mulmula a leda ta saka a warmer ta rufe sannan ta d'aura k'wak'warta(Coconut)bisa wuta ta zuba ruwa kad'an Sae da ta dahu tana kumfa fara sannan ta sauke ta zuba peak biyu da sugary kad'an ta juye a jug ba tare da ta tace dussar ba ta saka a fridge, Zuwa lokacin miyar ta soyu don haka ta kwasheta ta kai ta ajiye…

Tsohuwar dake zaune da ita ta tayata gyara falon ta goge sannan ta gyara mata kitchen…

'Dakin Ma'aruf ta koma ta gyarashi sosai ta saka turaren kamshi da freshner sannan ta koma d'akin Sumayya itama ta gyara mata kafin ta shiga d"akinta ta fad'a wanka ganin har karfe 12:30pm Kuma yace mata biyu zasu iso…Simple Make up tayi cikin lace sky blue da ya mata masifar kyau d'inkin riga da siket ya fito mata da sharp d'inta sosau. Tana sallah taji tsayuwar motarsu wani dad'i da fad'uwar gaba ya ziyarce ta lokaci guda, A hankali ta matsa jikin window ta d'age labule tana lekensu…

Ma'aruf ta hango Yana d'auke da Amir cikin kayan Pakistan na maza sosae kayan suka mashi kyau bata san lokacin da murmushi ya sub'uce mata ba ta saki labulen ta jingina tare da dafe kirjinta. Shigowar su falo ya sata fita da hijab d'in a jikinta Sumayya ta fara shigowa da gudu ta rungumeta tana murna, Ita kanta Sumayya sai ta samu kanta da zagaye K'arama da hannunta tana murmushi!Turus Ma'aruf yayi ganinsu a haka kuma ba karamin burgeshi suka yi ba kusa dasu ya matsa ya rungumo sumayya ta baya tare da K'aramar baki d'aya K'arama ta fara janye jikinta sannan ta dukar da kai tace "Aunty Sannu da zuwa…"!
 
*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
&
*FEEDOHM*πŸ’ž
πŸ’§πŸ’§ *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      πŸ’§

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_


        *_NA_*
  *_FEEDOHMπŸ’ž_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*πŸ‘ˆ


       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
 *Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*


          Page *90*
            *【End】*

 
    'Dan murmushi Sumayyar tayi tana k'ok'arin danne wani bak'in abu da takeji yana taso mata tun daga k'asan zuciyarta tace,

"Yauwa." sannan tayi cikin Falo ta fad'a saman kujera tare da dafe kai tana rintsa isanuwa, K'arama kuwa Sam bata kalli inda  Ma'aruf yake ba ta d'auki Amir ta koma kusa da Sumayyan ta zauna tana murmushi sannan tace,

"Aunty Ina wuni, Ya hanya?Ya kuma jikin?!"

A Hankali tace "Alhamdulillah…"

Shiru Suka yi yayin da Ma'aruf ya shige part d'inshi yana harararsu cike da jin dad'i yace,

"Ni baza ai min sannu da zuwa ba ko?"

Tab'e baki Sumayya tayi don tasan ba da ita yake ba sannan ta mike ta shige dakinta, K'arama kam mikewa tayi ta nufi part d'in Ma'aruf ko zata taimaka mashi da wani abu… Ganin shi jingine jikin window ya sa jikinta yayi sanyi sai take ganin kamar rashin maganarta ya sashi jin ba dad'i ita kuma har ga Allah saboda ganin Aunty Sumayya yasa bata nuna mishii jin dad'in dawowar shi muraran ba kuma tana ganin *MIJINKA SIRRINKA* ne ba gaban kowa ya kamata ka masa wasu abubuwa ba.

A Hankali ta tako ta tsaya a bayan shi tare da k'iran sunan shi a hankali cikin muryar da bata san tana da ita ba tace "Uncle…"

Har cikin magudanar rashin yaji maganarta saboda komai nata daban ne amma yayi mata banza don yana bukatar ta sake k'iran sunan shi cikin sigar da tayi a yanzu…

Cikin sanyin Murya ta kuma cewa "Uncle good afternoon, Ya hanya?" Ganin yak'i juyowa yasa ta shagwab'e murya kamar zata yi kuka tace "Uncle nayi laifine daga dawowar kuwa wayyo ni hafsat?

Kamar me rad'a ya juyo yace "Haka akewa miji idan ya dawo daga tafiya Hafsatu?

Ware hannu tayi ta rufe fuskarta ganin irin kallon da yake watsa mata tana murmushi… Sosai ya matso kusa da ita ya tallabo kanta yana kallonta har numfashin su na had'uwa a hankali ya kai lips d'inshi kan wuyanta yana fad'in,

"Kin manta kin ce kin tanadarmin abubuwa na musamman?!"

Ya saketa tare da yin baya ya ware hannayenshi yana jefa mata wani kallo na musamman alamar tazo gareshi… Cikin natsuwa ta shige jikin shi ya mayar da hannuwan ya rufe yana mayar da Numfashi itama zagaye waist d'inshi tayi da hannunta ta d'aga kai ido a lumshe…

Bisa lips d'inta ya d"aura hancinshi yana kallon eyelashes d'inta da suka yi gazar-gazar… A Hankali ya matsa ya zauna bakin gado dasu yayin da ta ware ta mashi oyoyo mai shiga rai sannan ta mike ta had'a mashi ruwan wanka da suka ji kayan kamshi ta dawo ta cire mishi takalma tare da d'aga hannunshi ta cire mashi rigarshi ya zama daga shi sai vest ta juya da sauri zata fita.

Janyota yayi ya zaunar da ita bisa cinyar shi yace "Ina zaki gudu baki k'arasa aikin ba ai…!

Rufe fuskarta tayi da hannu tace "Na gama mana…"

Lakuce mata hanci yayi tare da kama hannunta ya d'aura saman trouser d'inshi yace "Kin tabbatar kin gama hafsatu?

Murmushi tayi tana sake rufe fuskarta da hannu a hannun ya sakar mata kiss yace "Hafsatu Kunya!karki damu ki bani zuwa nan da gobe zan cire maki wadda ta rage maki…"

Mikewa tayi da gudu ta fita daga d'akin ta shige d'akin ta, ta dad'e zaune gefen gado tana murmushi sannan ta mike ta shiga d'akin Sumayya tama Amir wanka dake ta ihu zafi ya dameshi sannan suka fito da Sumayya suka zauna a dinning…

A Hankali Sumayya tace "Ki shiga ki kira Ya Ma'aruf K'arama." Duk da taji ta sai tayi shiru kamar bata ji ba sai da ta k'ara maimaita mata sannan ta mike a sanyaye ta shiga d'akin shi shima daga bakin kofa ta tsaya tace "Uncle ka fito kaci abinci.."

Yana combing kanshi ya kalleta ta mirrow ya d'age mata gira ta juya da sauri ta koma tana fad'in "Aunty Gashi nan zuwa…!

"Huh." kawai tace tana kokarin bud'e warmers amma K'arama tayi saurin karb'a ta bud'e mata cike da ladabi…

Waro ido Sumayyan tayi cike da farin ciki don favourable food d'inta ce Sakwara ta kalli K'arama d"auke da murmushi tace "Thank you Hafsat kin san ina son sakwara kenan?!"

Ma'aruf ya zauna yana fad'in "Shi yasa ta maki ai." ya juyar da kai yana hararan K'arama yace "Banbanci ko?ni ina nawa Favourable food d'in…?!"

Rufe fuskarta tayi tana murmushi mai tsayawa a rai Sumayya ta janyo hannun K'arama tana hararan shi tace "Kayi hakuri ka ci nawa idan kuma bai maka ba Hafsat shiga ki had'o masa tea da bread…!

B'ata fuska yayi yana harararta yace "Son kai ko..?

Murmushi suka yi baki d'aya sannan tayi serving nasu kowa da plate d'inshi Sumayya ta tura masu nata a tsakiya tana fad'in "We are one family bai kamata muna raba plate ba yanzu."

Su duka suka kalleta cike da farin ciki barama Ma'aruf da ya janyo hannunta yayi kissing cike da jin dad'i… A Tare suka yi lunch d'in cike da jin dad'i sai da ta janyo coconut drink sannan Ma'aruf ya ma Sumayya gwalo yana fad'in "She made me complete tunda tamun abunda nafi so a drink."

Dariya suka d'auka baki d'aya sannan suka koma falo suka cigaba da firansu cike da jin dad'i!Shigowar Udutti yasa firan ya sake rud'ewa ta ishesu da tambaya da ihu har da tambayar K'arama "Aunty naga kina wa Mommah dariya ta baki fuskarta ne ki rama mari da dukan da ta maki ko kin yafe mata...?!"

Murmushin yake Sumayya tayi cike da nadamar abunda tayi zata yi magana K'arama tace "Waya fad'a maki duka na tayi?wasa muke yi fa ranar…!

Tab'e baki Udutti tayi tana kallon Ma'aruf tace "Papa ni za'a maida sakarai ko?bayan har da jini a fuskar Aunty mai kyau ranan Momma kice mata tayi hakuri…"

K'arama ta jata ta shige da ita d'aki don ta gaji da surutunta itama Sumayya bayan su tabi ta zauna a sanyaye tana bata hakuri akan abinda ya faru a baya…

Waro Ido K'arama tayi tace "Dan Allah Aunty ki daina bani Hakuri wallahi ban d'auki komai ba kuma na yafe maki da zuciya d'aya…!

****

Daddare bayan sun gama dinner Sumayya ta ja Ma'aruf har d'akin K'arama suka zauna anan ta nemi su yafe mata su duka sannan ta k'ara da fad'in ta basu sati biyu domin K'arama ta mori mijinta itama, sosai Ma'aruf d'in yaji dad'i ya rungume su baki, d'aya tare da k'warara masu albarka baki d'ayan su sannan Sumayya ta mike ta barsu su kad'ai tana kokarin danne kukan dake niyar kwace mata…… Tana fita shi kuwa janyo K'arama yayi jikin shi yana rad'a mata kalamai masu dad'i da sanya natsuwa sam kasa bari yayi suyi wanka saboda yayi missing d'inta fiye da yadda bata tunani sannan ya kashe lamp tare da rufesu da bargo…

Duniyar Ma'aurata suka lula mai cike da kwanciyar hankali, wannan karan ma cikin natsuwa ya tafiyar da ita har suka samu gamsuwa su duka biyun kafin bacci yayi awon gaba dasu manne da juna cike da kwanciyar hankali.

Zama suke cikin jin dad'i tare da kwanciyar hankali Sosai suka had'e kansu yayin da Sumayya taja K'arama jikinta itama kanta K'arama tana k'okarin kyautatawa Sumayya sannan takan guji duk abunda zai bata mata rai a zaman su… Wani abun burgewa ma dasu idan suna zaune baka gane wacce ke da girki a cikin su suna respecting junansu ko kad'an basa shishshigewa miji a gaban juna duk wani abunda zaki wa miji sai kun shiga d'aki daga ke sai shi sannan ki nuna masa soyayya…

Sam Sumayya ta gyaru ta daina shan komai sai dai idan sun tashi su markad'a ganyen zogale su zuba peak su sha a tare ko kuma su markad'a kankana da peak su sha a tare don gani suke duk abunda za suyi mijinsu za suyi mawa sannan idan har suka yi sake baya samun gamsuwa gurin d'aya daga cikinsu to wata na iya shigo masu. Sam ta rage son jiki takan zage ranar girkinta suyi abinci mai rai da lafiya tunda dama ba rashin iyawa bane tsabar lalaci ne komai a tare suke sannan yaran Sister Maryam suka zo masu yawo haka suma akan kai su Udutti gidan… Har numbern beeba Sumayyq ta goge daga wayarta don bata bukatar sake had'uwa da ita…

Cikin lokacin ne ya d"aukesu su duka ya kaisu katsina Gidan hakimi acan K'arama tayi mutuwar zaune ganin Ummanta zaune a matsayin matar hakimi bakin ta yaki rufuwa murna sosai tayi bama kamar yadda taga hankalin Umman nata ya kwanta ita kanta Umma taji dad'in ganin su yayin da tayi ta nan nan da Sumayya da Udutti da Amir don baza ma ka tab'a tunanin K'arama ce d'iyar ta ba……,

Kwanansu biyu a gidan sannan ya d'auke su ya kaisu kauyen su Lauratu nan ma tayi mamakin canzawar kauyen sai da lauratu ta fad'a mata cewa Ma'aruf ya saka hannu aka canza masu komai, sosai ta jinjina mashi tare da bashi matsayi na musamman azuciyar ta kwannansu d'aya suka je suka gaido da Maitafasa itama ta nuna masu gata sosai kaya sosai suka jide masu sannan suka juya zuwa gida Maitafasa ta kalli Kundum tace…

"Tun randa kika tona *ABIN DAKE B'OYE* nike ta ganin alheri, haushi na d'aya da baki fad'a ba har ladona ya rasu da yanzu dashi za'a ci wanga arziki amma ba komai rayuwa ce."

Duk jikin Kundum yayi sanyi hakan yasa ta kasa cewa komai sai sharar kwalla da takeyi da bayan zani.

***

Idan ka gansu bazaka tab'a tunanin kishiyoyi bane zaman su gwanin ban sha'awa sukan fitar da lokaci suyi wasa kamar volleyball da lido, table tennis da golf idan su Udutti sun tafi school Ya Ma'aruf kuma ya fita aiki sai suyi tayi.

***
*After one year*

Bayan shekara d'aya K'arama ta haihu 'ya'yanta 'yan biyu sak mahaifin su, mace da namiji ne sam haihuwar bata bata matsala ba saboda a gida ta haihu tare da taimakon Sumayya shagali sosai aka yi don har su Maitafasa da kundum da 'yan gidan Ard'o sai da Ma'aruf ya saka aka d'auko su ranar suna yara suka ci sunan macen aka saka mata AMINATU yayin da Namijin kuma AMMAR wanda Sumayya ce ta zab'i sunan da kanta…

Rainon yaran ya koma hannun Sumayya baki d'aya tana masifar nuna masu gata kamar yarda K'arama ta nunawa su Udutti. Da farko Sumayya ta d'an fara nuna alamun damuwa akan rashin haihuwar ta ganin K'arama ta haifi nata kuma sun mugun bata sha'awa amma da taimakon K'arama Sumayya ta washe ta fauwalawa Allah ta cigaba da addu'o'i… A lokacin Ma'aruf ya mayar da K'arama makaranta inda taci gaba da karatunta hankali kwance…

Ba tare da sanin K'arama ba Ma'aruf  ya samarwa Sallau Mijin Lauratu aiki a wani company dake buga robobi shi da kanshi ya sayar masu d'an matsakaicin gida ya zuba masu kaya dai-dai gwargwado sannan ya samu mota ake je a d'auko su suka dawo cikin gari…Ranar da ya kai K'arama gidan ta ga Lauratu har kuka tayi saboda murna yayin da ta rasa bakin da zata gode mishi dan yayi mata komai a rayuwar ta. Ganin taki barin kukan har lokacin da suka baro gidan yasa yayi parking gefen titi ya kashe motar tare da b'ata rai yace "Zan fita idan kin gama kukan ki kirani sai mu wuce."

Wata irin runguma ta mishi tana girgiza kai yayin da bakinta ya rasa kalmar da zai furta. A Hankali ya d'ago kanta yana kallonta sannan ya saka babban d'an yatsan shi ya goge mata hawayen tare da sakar mata lallau san murmushi yace "Na san me kike son Fad'a bara na fad'ar maki kiji." Gyara murya yayi yana kwaikwayon Muryarta ta yarinta yace "Bunkul ta k'warank'wata aradun Allah nagode maka na kuma gode maka gobe zaka k'ara man k'ankayar nonon shanu mai zak'i (Ice cream)."

Dariya ta saki tare da kai mashi dukan wasa tana hararan shi tace "Ni ba haka zance ba fa." Ta kwantar da murya tace "Uncle wallahi ban…"

Hannun ya d'aura saman lips d'inta yana jefa mata harara yace "Indai kin san ba abunda na fad'a zaki ce ba to kiyi man shiru zaki fi birgeni idan kika kuma haihuwa man wasu twins d'in nan da wata Bakwai…" Ya k'arashe maganar tare da ja mata hanci…

Jikin shi ta shige tana sunne kai tare da dariya k'asa-k'asa daga haka kukan ya kare yaja motar shi suka koma gida cike da farin ciki…


 *TWO YEARS*


Shagwab'e Fuska tayi tana kallon Sumayya tare da d'aura mata Ammar a cinya tana fad'in "Kinga ko Aunty wallahi yaron nan ya fiye rigima."

Harara ta sakar mata tana murmushi tace "Ai dama bance ki d'aukar man yaro ba bare ki zo kina bani labarin rigimarsa."

Udutti ta shigo hannunta d'auke da Aminatu ta fad'a saman kujera tana turo baki K'arama ta matsa tana tambayarta "Menene my Udut?

B'ata Fuska tayi tace "Aunty fitsari ta man a jiki kuma fa yanzu nasa kayan…!"

Harara Sumayya ta watsa mata tana fad'in "Kuji kinbabbiya ke bakya fitsarin ne an gaya miki?common bani d'iya ta nan…!

Ma'aruf dake tsaye bakin kofa ya saki murmushi mai sauti wanda ya janyo hankalin su… rige-rige ake tare da shigewa jikin shi K'arama da Udutii suka fara fad'awa yayin da yayi masu kyakyawan masauk'i kafin Sumayya ta k'araso da su Aminatu a hannunta tana dariya  tana fad'in "Yau mun yadda an rigamu amma Allah ya kaimu gobe." sannan itama ta fad'a jikin su suka d'auki "Oyoyo gaki d'aya!

Kissing yama ko wace a forehead harda su Aminatu sannan K'arama ta k'arbi briefcast d'in hannun shi da yake ita ce da girki ta shige part d'in shi…

Suna shiga ta sake masa oyoyo d'in shi na musamma mai shiga rai tana zagaye da waist d'in shi ya d'ago kanta ya had'e goshin su yana kallon cikin idonta a hankali yace "Kin kawo min haske a rayuwar gidana Hafsatu Allah ya maki albarka…"

A Hankali tace "Kaine silar komai Uncle ban…" Cakulkuli ya mata tayi shiru tana dariya yayin da yayi sama da ita ya direta saman gado sannan ya zauna saman cinyarta yana shinshina wuyanta cikin sanyin murya tace…

"Uncle please..., yayi saurin zura harshanshi cikin bakinta wanda lips d'in yasha red d'in janbaki, a hankali ya zare bayan ya d'ora hannunshi d'aya saman na shanunta yace cikin muryar rad'a,

"Nace bana son wannan Uncle d'in da kike cemin, please karki ja ki haramta min kanki ki canza min suna now."

Kamar zata shid'e sabida abunda yake mata, da kyar tana wani irin nishi tace,

"You you're my everything my first and last love, you're the father of my children you're the angel from about who takes my pain my love for you is so strong it always just the same, I love you my sweetie pie and I need you right now..."

Tana gama fad'a ya zura bakin shi cikin nata ya fara tsotsa Yaya hajja baki bud'e sai da Feedohm ta tunrsire da dariya sanna tasa hannuta ta rufe idanuwanta sannan ne ta ankara ashe sun gama Feedohm ta ja hannunta suka fito suna dariya....


  *_Alhamdulillah_*
*Muna godiya da Allah da ya nuna mana karshen wannan littafin lafiya ABIN DAKE B'OYE. Kuskuren dake ciki Allah Ubangiji ya yafe mana baki d'aya*

Post a Comment for "ABINDA KE BOYE COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...