Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ABDULNASEER ALFAH COMPLETE

ABDULNASEER ALFAH COMPLETE

- - Post a Comment

 ABDULNASEER ALFAH COMPLETE


Wani irin traffic ne aka had'a kan titin central park,wanda ya jawo tsaikon motoci.ko kad'an ma motocin basa tafiya tsaye suke,wasuna fitowa daga cikin motarsu suna hangen abunda ke faruwa,dan dazon mutane ne kan titin yayinda wasu keta fitowa kallon abunda ya faru.nima dai matsawa nai sosai don kashe kwarkwatar idona,mutane nake ta turewa ina kutsawa don isa inda wannan dan dazon mutanen yake..............wow oh may god masha Allah,wani tsalelen guy ne na gani kwance k'asa cikin jini,duk da yadda jini ya wanke fuskarsa da kirjinsa hakan bai hana tsananin kyawunsa fitowa ba,ko makaho ya shafa yasan wajennan akwai kyau na fitar sharia..............araina nace kai mutanen mu sai abarsu yanzu duk nan babu wanda zai iya kawo mashi d'auki......ban idasa tunani naba naga wani guy yashigo wajen a dari da hamsin yana shashsheka,,,,,bai tsaya ko inaba sai gaban wannan guy d'in dake kwance cikin jini.........kuka yake yana jijjigashi yana cewa mutanen dake zagaye dasu. "Don Allah ku tai makeni na kaishi asibiti,bana iya daukarshi....don Allah kuduba halin da yake ciki,ko numfashi fa bayayi."amman saboda rashin mutunci babu wanda ya kulashi saima tsogumi suke akan ya kauda masu shi suna da abunyi,wani babban mutun yakalleshi yace"wai ba d'an gidan ALH MAINAH bane,wannan tsinennen yaron zamu taimaka,ai baida wani anfani,tunda har iyayen dasu haifai ma sun yardashi basu so wa kuwa zai jefa kanshi cikin matsala,gara kabarshi ya mutu domin itace tafi dacewa da mai irin layyarsa la,anennen yaro kawai."
Nanfa kowa yaita fad'an albarkacin bakinsa akan wannan guy dake wance har lokaci baisan wake kanshi ba,kuka guy din dake rike dashi yake yana neman taimako amman babu mai kulashi,daker yajashi gefen hanya yana kuka yana cewa.
"Allah yana tare dakai *Alfah* insha Allah ba yanzu zaka mutuba,kowane mai rai da tashi jarabtar kai kuma haka taka tazo,Allah ya baka ikon cinyewa...........kwantar dashi yayi ya koma bakin titin yana tsayar damai taxi cikin ikon Allah yasamo,da gudu suka zo suka daukeshi shida mai taxin suka sashi cikin motar,basu tsaya ko ina ba sai asibiti.
DOWNLOAD HERE👈

Post a Comment for "ABDULNASEER ALFAH COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...