ABDULMAJEED CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ABDULMAJEED CHAPTER A

ABDULMAJEED CHAPTER A

- - Post a Comment

 ABDULMAJEED CHAPTER A


[6/28, 11:15 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of majesty*✨

Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

       P.M.LπŸ’ͺ🏽'''zanyi amfani da wannan damar nayiwa dukannin masoya da abokai da 'yan uwa musulmi murnan kammala Ramadan lafia, sannan nayi muku barka da sallah fatar Allah ya karb'i ibadunmu ameen'''πŸ‘πŸ½
πŸ“ *Episode* 1⃣⏩5⃣Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…


Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah mad'aukakin sarki, mamallaki sarkin iya halitta, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad(S.A.W)

Tare da sahabbansa da iyalan gidansu da duk wad'anda sukabi tafarkinsa har zuwa ranar ceto

+

_Banyi niyyan rubuta wannan littafin don cin zarafi ko fuska ga wani ba, idan kuma yaci karo da halinka/ki saiki/ka gyara, a guji zargi._


*Ban yadda wani ko wata ya juyamin koda kalma d'aya ne sai tare da izinina*

Tukuici gareku ahalina ina alfahari daku a duk inda naje, Allah yabar kauna ya rayamu a musulunci damu da sauran musulmi baki daya. *ILYSM❣
             *KADUNA STATE*


*kofar mashi*

Garden ne matsakaici mai cike da furanni masu fitar da daddad'an k'amshi da itatuwa ma'abota fruits, gurin yayi kore sharr sai wata sayyayar iska ke kadawa wacce kowane ma'aboci halitta zaiyi sha'awar ya shaka, gurin d'auke yake da resting chairs farare,  ga wata k'orama a gefe tana gudana abin gwanin sha'awa da burgewa.


Na shagala da kallon gurin, inata baza idona abinka da bakauyiya, can gefe cikin daya daga cikin rest chair na hango wani matashi a kwance.


Daf dashi naje domin naji dad'in d'akko maku rahoto dakyau, idanuwansa a lumshe sanye da wani siririn farin glass da alama medical ne, amma hakan bai hanani gane cewa matashin ma'aboci golden eyes bane saboda yadda eyes balls nasa ya fito akan fatar idon, hancinsa ba dogo bane hasalima za'a kirasa da guntu in short, kalar fatarsa abin burgewace wato chocolate.


Kallon nai masa da sama har k'asa na fahimci baida tsayi sosai, baida jiki ko kad'an saidai yana da k'irar k'arfi, gashin kansa irin na hausawa ne amma kan yasha gyara yayi kyau ya kuwa kwanta ba laifi, yana da round face kamar mace wacce ke zageye da man pride, bakinsa mai matukar kyawu d'auke da soft red lip, ina cikin nazari banyi aune ba naga ya mik'e tare da sauko da k'afafunsa kan shoes nasa, mashaa Allah k'afarsa abin sha'awace kamar a rangada mata lalli.


Mik'ewa yayi tare da d'aukar phone masa da iPad nasa dake kan desk yayi, sanye yake da shirt orange da jean baki, idonsa na kalla saida k'irjina ya buga kwayar idon brown ce yayin da farin ya surka da pink, bansan time d'inda nace subhanallah ba, ban tab'a gani irin idonsa ba before.


Inacan duniyar mamaki sai ganin nayi yakai k'ofar fita daga garden d'in, hakan yasa na bisa a 150 saboda ci gaba da samo maku rahoto. Lolz


Wata 'yar k'aramar k'ofa naga yabi sai kawai na gammu '' cikin wani matsakaicin parlour wanda yaji kayan more rayuwa dai2 irin na masu rufin asiri, wata matace zaune wacce i k'iyasce zatayi shekara arba'in da d'ori, a fizge tana kama da matashin, husnul musleem rik'e a hannunta tana dubawa.


Sai wata yarinya dake kwance gefenta tana barci a kalla zatayi ten year, sai yaro a k'asa sai faman zane yake a littafi sa'an wacce ke bacci da alama ma twins saboda kamar da sukeyi.


Zama matashin yayi kan 1seat bayan yayi sallama sannan YACE.


"Maamii sannu da gida."shima yaron yace " welcome ya Abdool. "


"Yawwa big boy me akeyine?"


"Homework ne."


"Ok a bada himma."


Itama Cikin kulawa bayan ta ansa sallamarsa tare da aje husnul musleem tace "yawwa Abdool dama ba fita kayi ba kenan?"


"Eh Maamii nad'an garden ne."


"A toh madalla, toya maganan horsemanship naka?"


"Eh Maamii inshaa Allah 2/3 week dai zasu kiramu."


"Sokoton dai koh" ta fad'a tare da kallonsa.


Shafa kansa yayi yace "itace Maamii."


"Nikam Abdool bansan meyasa ka nace sai Sokoto ba duk hospital d'inda ke Kaduna da zagaye ba wacce tai maka ne ko meye?"


Smiling yayi yace "ba haka bane Maamii inadai son naje gidane nayi wa garina hidima, kuma kinga zan k'ara sabo da 'yan uwana."


Nisawa tayi tasan abinda d'an nata ya gad'a gaskiya km hakan dazaiyi yayi dai2 saidai batason tayi nisa dashi ko kad'an.


Yaron da ke drawing jin yayan nasa na maganan tafiya yasa ya aje book d'in yaje kusa da yayansa yace "yace Ya Abdool da gaske tafia zakayi ka barmu?"


Shafa kansa yayi yace "Ajb ba dad'ewa zanyi ba, kuma zan ringa zuwa ina dubaku kaji my boy."


Girgiza kai yayi yace "nidai zan bika Yaya" ya fad'a yana narkewa jikinsa.


"To karatunfa Ajb?"


"Nayi a can."


Murmushi yayi yace "Ajb rigima, ita Husna tayi nata homework d'in?"dan ya d'auke masa hankali.


"Aa headache takeyi."


Mik'ewa yayi tare da zuga gaban seat ya dafa goshinta yace "Subhanallah tasha magani kuwa?"


"Aa batasha ba tai bacci."


Cikin nuna damuwa ya mik'e zuwa d'akinsa dan d'akko mata magani, Maamii kuwa sai kallonsa take tana k'ara godewa daya had'a mata kan 'yayanta suke tausayawa juna da k'aunar juna, sosai Abdool ke nuna kulawarsa akan kannensa ga saukin kai, yakan wasa dasu sosai sannan ya tsawatar musu idan sukayi ba dai2 ba( _shine gaskiyar rayuwa_).


^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^            *SOKOTO STATE*

*Garin kilgori dake*

"Laure! Laure!! Laure!!!" Firgigit ta juyo tare da baro tagar ajin tazo gun mai kiranta tace "Delu ahe kece ina zakina halan?"


"Kekam Laure bakijin maganar Iya Hari, hi yassa kullum taka bugunki kaman ganga tase bataso kiyi boko, missa kika dagewa sai keyi, wane dadi agga boko?"


Dafa kafad'ar Delu tayi tace "Delu bansan missa Allah ya jarabceni dason boko ba, kullum inaji cikin raina zanyi boko kuma nayi alfahari dahi, amma bansan sai yauhe ba, duk ni gitto ta makaranta ji nikai kamar an damremin kafwa inji hena tsaya naji kara2" ta K'arashe maganar tare da zubar da hawaye.


Cikin tausayawa k'awar tata ta share mata hawaye tare da rungumota jikinta tace "kiyi hank'uri Laure da nuhar Allah zakiyi boko wata rana, yanzu ki d'auko turenki mu wuce gida tun kafin ki husata Iyaa Hari ta jibgeki tunda ba mutunci gareta ba."


Haka taje bakin tagar daga k'asa ta d'akko tiren gyad'arta, suka bar makarntar mai d'auke da 'yan ajijuwa da basu wuce biyar ba, suka doshi cikin gari.......


_Tirkashi to ma'abota karanta novel d'in Meryerm ko biyoni a sannu kuji da wanne salon nazo wannan karon_ love u friendsπŸ’žπŸ“ *Episode* 6⃣⏩πŸ”Ÿ

Da d'an jayawa kafin a isa cikin garin tafe suke k'awar tata naci gaba da bata shawara da k'arfafa mata gwiwa.


Gari wanda za'a kirasa k'auye kuma garin fulani kai tsaye duba da yanayin gine-ginenda ke cikin garin, amma da alama manoma ne kuma makiyaya dan ko'ina ka duba shukace tun daga dajin garin har zuwa cikin garin, kama da gero, Masara, maiwa, albasa, tomatur, ata, tattasai kai har noman taba sunayi, ga kuma dabbobin na ciwo, a takaice dai da alama ba talauci a garin.


Dai-dai k'ofar wani gida Wanda zance duk garin ba irinsa naga sun tsaya, nan k'awarta tace "to Laure ni zan isa gida saike hito anjima Dandali" ta fad'a tare da tafiya.


"Tau Delu ki gaida Gwaggo" cewar Laure tare da sanya kanta a soron gidan, amma kuma fuskar taf tashin hankali k'irjinta sai bugawa yake dan batasan yau kuma wane kalan zagi zata samu ba.


Wata dattijuwace zaune tsakar gidan tana tunka tsawo, bakace mai tsamuraren jiki, ba laifi fuskarta irin ta fulanice saidai ta tamure itama, ga taba ta k'unsa a bakinta redio gefenta tana jin wakar *Barmani toge* cikin sanyin murya tayi sallama.


Dagowa tsohuwar tayi ba tare da ansa sallama ba tace "to gantalalliya sai yanzu kikk'are gantalin naki, keman Laure anyi tambad'add'iyar yarinya yanzu tun abun Hantsi sai yanzu kika dawo mini."+


"Subhanallah, haba Hari wanga bacin k'are dangi da kikai ma diyanga marainiyar Allah dami yayyi kama? Hari wai mi diyanga tayyi miki da baki tab'a nuharta da alheri ba se sheri?" Wani farin dattijo ya fad'a yana aje buta fitowarsa kenan daga bayi.


"Haba Ardo wai missa kullum kurkiiyarga tayyi min laihi baka gani? Saima nawa kaka gani sannan ka bini da ganin laifi, koni kabar yimin irin haka ai sai kasa ta hwandare dama yaya lahiyar kura bale tayi hauka" ta fad'a cikin nuna bacin rai.


Girgiza kai kawai yayi tare da cewa "Allah ya kyauta" inda sabo ya saba da halin Hari Sam batason gaskiya.


"Ramlatuna shiga daga ciki ki aje turen saiki kawomana ruwan alwala garka kejina 'yar Albarka" ya fad'a tare da ficewa daga gidan cike da tausayinta.


Matse hawaye tayi tare da shigewa d'aki ta adon aje tiren, da harara ta rakata tare da banka tsaki tace.


"Munahuka dangin mayyu tai ki dawo ki iskoni saike hwadamin inda kittsaya."...........

_tofa meye sanadin wannan k'yayyar? Nida Ku mubi a sannu harmu gano bakin zaren_πŸ€”πŸ˜”

^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

      *KADUNA STATE*

*3 weeks later....*


Gabadaya sun fito waje domin raka Abdool zai wuce Sokoto saboda an kirasu, sanye yake da jean blue da shirt purple yana sanye da glass nasa as usual, left and right nasa yana rungume da Husna da Ajb, momynsu na bayansa, sai k'anwarsa Nihal data dawo Hutu week before tana rataye da lodge nasa.


Bakin motarsa suka tsaya ana k'ara bankwana, su Husna sun lafe jikinsa Sam basaso ya tafi saidai ba yadda zasuyi saboda tafiya ta zama dole...


"Abdool ka kula sosai ka tsare mutuncinka da kimarka, ka kula da ibadarka ka rike Addu'a sannan ka sada zumunci da 'yan uwanka kada ka nuna musu komai sai Alkhairi, Allah ya kiyaye hanya, ya Baku sa'a da nasara akan abinda kukajeyi."


Ba kad'an yaji dad'in addu'ar Maamii tasa ba, yace "inshaa Allah Maamii zan kiyaye, aci gaba dayi mana Addu'a, Addu'arki itace silar cigabarmu."


"Addu'a ba fashi Abdool Allah ya k'ara shiryaku baki d'aya."


"Ameen Maamii" ya fad'a sannan yace "my guy missing u" yace tare da rungumesu, suma rungumesa sukayi sukace "missing u too bro.


Dak'ar suka rabu yaja car d'insa cike da kewar familyn ya d'auki hanyar birnin Shehu..........

_wasa farin girki muje zuwa friends_ 🏌🏽⛹🏾‍♀'''Manzon Allah (S.A.W) yace:-'''

*Yana daga cikin kyawawan dabi'un musunci mutum yabar abinda bai shafesa ba.*


( _Tirmizih da wadansu suka ruwaitoshi, daga hadisai arba'in_ )

        πŸ“ *Episode* 1⃣1⃣⏩1⃣5⃣


Saida ya biya ta Unguwar Rimi ya d'auki friend d'insa Hakeem Wanda shima a Skk zaiyi horsemanship nashi saidai shi pharmacy ne, t'uki yayi cikin Jean vitae hankali suna tafe suna sauraren wak'ok'in larabawa na *Mishary Raseed Alfasy* dama Abdool ba rigima, tun Hakeem na mitar t'ukin har ya hak'ura dan ba yadda ya iya da mutumin nasa, gashi shi yace bazaiyi driving ba, dole ya bisa a yadda yakeso.


Basu suka isa ba sai after ishaa, direct family house nasu suka wuce, estate ne guda, mai d'auke da compartment 5 mafi girma daga ciki naga sun dosa, direct main parlour suka sauka.


Da sallama suka shiga, wani dattijone zaune kan kujera, ga wasu samari gefensa alaman magana suke dukkansu kusan tsaran Abdool ne, cikin farinciki suka juyo yare da ansa sallamar, tasowa sukayi suka rungume Abdool da Hakeem tare da fad'in.+


"Ur highly welcome home bro" sannan sukayi musabaha, shima cikin murmushi, yace "fatar na sameku lafia?"


"Alhmdllh" suka fad'a tare da k'arasawa gurin dattijon gaba d'aya, fuskarka d'auke da murmushi ko ba'a tambaya ba kasan yana farinciki da zuwan jikan nasa.


Kan hannun kujerarsa Abdool ya zauna tare da rungumesa yace "tsoho mai ran k'arfe  kaga jiya kaga yau."


"Zanga gobe da yardar Allah kuma, likkita bokan turai yau kaina a sakkwato?"


"Sharri kayan kwalba, sai yau ka saba ganina a sokoton?"


"Kai bature kada ka wayance yaushe rabonka da garin?"


Sudai samarin da Hakeem sai kallon drama suke suna dariya babu mai barin ta kwana cikinsu.


Saida suka gama rigimarsu sannan aka gaisa.


"Abdulmajeed ya Maman naku da kannenka duk kuna lahiya dai ko."


"Lafiya qlau Alhaji sunce a gaisheku sosai."


"Kai madallah, haka akason ji, kai sama'ila kuje dasu ciki sud'an huta, kasan halin likitoci basu son wahala" ya fad'a yana kallon Abdool.


Smiling yayi "haba tsoho nida nike sabon jini saidai kai daka kwana biyu jini yayi nisa."

"Ho dan nemanga tahi ka dawo ka taho mu gwada kaga aikin tsohon kashi"


Dariya yayi tare da bin bayan su Hakeem da suka fice suna dariya yace.


"Rufamin asiri dattijo A d'auri kashi ko a bata igiya" ya fad'a tare da ficewa.


Shima dattijon dariya yayi yana maijin dad'in ganin jikan nasa da aka kwana biyu ba'a had'u ba..............^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^Sumui-sumui ta shigo kamar munafuka taje bakin randa da niyyan d'aukar buta tayi alwala, taji muryar Iya Hari tace.


"Tau jikan mayyu, waje Musa ciki Fir'auna kinzo kina wani Abu kamat ta kwarai kewai ga musulma, ki gama gulmarki kizo ki sameni saike bani labarin ubanda kika d'auka a makarantar bokoko da ki k'wuk'wema zuwa dudda na hissheki ciki, ko wani salon karuwancin na a haka eye."


Itadai shiru bata motsa ba bare ta tanka, inda sabo ta sama da irin wad'annan cin fuskar da zagi daga Iya Hari, Sam bata ragamata ko k'adan akan laifin da ba ita ta aikatashi ba, amma kullum a Kanta take saukewa.


"Oho ina magana keyimini tsaye k'ik'am kamar icce niddasa ko, kedai anyi shegiyar yarinya mai bakin hali, maza ki aje butan nan ungu ki kaima Lanti saura ki wuce wurin gantalinki da kissaba."


Cikin sauri hadda hard'ewa ta amshi ledar tare da ficewa da sauri kamar mai jiran cas, da tsaki ta bita tare da cewa.


"Tai ki dawo ki iskoni kici na jaki, bak'ar iri."

Tafe take cikin nutsuwa idan ka ganta ba zakace 'yar kauye bace, saboda tafita daban dasu komai nata a natse kamar wata babbar mace duk kuwa da k'arancin shekarunta.


Daga sama taji ana kiranta, ko bata juyo ba tasan me kiran nata, tsayawa tayi ba tare data ansa ba kuma bata juyo ba.


Wani hargitsatsen matashi ne ya tsaya gabanta, kalar irin ta 'yan daban fulanin nan bakinsa bak'i k'irin irin na 'yan sha, ido jajir kamar gauta.


"Waike Laure minana abbusa kanki, walle keci azzikin ina sonki daba haka ba hmmm khattt...." Yayi kwafa.


Itakam kallo kawai ta bishi dashi ba tare da tace uffan ba.


"Ke halan icce kike ina magana sai kallona kikai ko nayi miki kyauna" ya fad'a yana wani k'wanbewa.


Sanin halinsa idan ba maganan tayi ba ba barinta zaiyi ta tafi ba yasa tace.


"Jauro daga ina haka?"


Wani dad'i yaji ya lullub'esa dan ba k'aramin so yakema Laure ba shiyasa yake daga mata k'afa lokuta da dama ita kadaice weak point nashi, ko Abu ya had'aku da kace don Laure tofa yanzu zai sarara maka, duk kuwa da tsagerancinsa dan duk garin kowa shakkunsa yake saboda dan Sara sukane kowanne lokaci yana tare da makami, ganin badan arziki bane yasa Iya Hari amincewa da soyayyarsu da Laure, saboda kawai ta musguna mata.


Ardo yaji duk abinda ake ciki amma bai nuna ya sani ba, ya barsu yaga iya gudun ruwansu, abinda kawai ya sani bazai taba Aurar da marainiyar Allah.


"Daga daji nike, kehwa INA zakina?"


"Hmm gidan Gwaggo Lanti" ta fad'a a takaice, tare da juyar da fuskarta ganin irin kallon da yake mata na k'urillah.


"To..toh mutai in rakaiki?"


Ganin no way 2 escape yasa ta yadda suna tafe yana mata hira, ita kam sai uh da uhum da to take binsa dashi.


Aiko har suka isa ba'a samu Wanda ya daga ido ya kallesu ba saboda sanin hali, haka yake gadinta kamar kwai, ba kuwa ubanda ya isa ya kalleta balle yace yana sonta duk kuwa da dimbin masoya da takeda shi, amma suna gudun rasa rai dan k'aramin aikinsa ne, kisa.


Saida yaga shigarta sannan ya juya zuwa sabgarsa..........


_Rikici ba gado ba_ 🀣😜My whatpaddio people's are u enjoy d story? Or will u stopping, its already done since 2017, we just copy it right here....ur answers is base on ur vote and comments, thanks allπŸ“ *Episode* 16--20Saida sukayi fresh up suka d'an ci abinci da yake an shirya musu better, amma Abdool kad'an yaci dan idan da abinda ke bashi wahala to cin abinci ne.


Maamii ya kira ya fad'a mata sun sauka lafiya tare da gaisawa da k'anninsa wad'anda ya fara missing tun yau, cikin gida suka shiga suka gaida da kakarsa wato Haj, Saude wacce ta ansa su sama2 ko halinta ne haka oho!.


Daga nan suka shiga sauran gidajen suka gaisa da iyaye, yayyi, da kanni, daga nan suka koma inda tsoho mai ran k'arfe inji Abdool fa.


Hira suka sosai kaman ba wad'anda suka sha hanya ba har 12, Alhaji Sada yace suje su huta zuwa gobe kuma aci gaba.


"Wane gobe Alhaji nida zanyi sammako saidai na barku da Hakeem."


"Au abun 'yar hakane shine ka gudu *Yabo* dan kada ka zauna Sakkwato ?" Alhaji ya fad'a yana hararan Abdool.+


Dariya yayi "Alhaji aiba laifina bane kuma ai anan Sokoto akwai consultant doctors da yawa k'auyukan sunfiku bukatar likita."

"Ho dan nema badai iya fad'a ba, Allah ya taimaka, k'ilama acan ka samo 'yar budurwa, koda yake naga alaman tsoron mata kakeyi, kila sai munyi maka gangami an d'aura maka a k'afa."


"Hhhhhhh kajika da shirmen tsufa, an gayama ni Kaine, aini matata ba'ama haifeta ba" shidai Hakeem sai dariya yake suna burgesa.


"Aa kak'i cewa mamarta ma ba'a haiheta ba, ja'iri zanso naga wacce zata aureka da shirmen nan naka, kaidai ba abinda ka bari na 'yan fari"


Dariya sukayi banda shi murmushi kawai yayi tare lumshe ido.................     _wannan kenan_^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^


Zaune suke a Dandali, wasu na gad'arsu yayin wasu ke samartaka, wasu na siye da siyarwa, "Laure kina zuwa Yabo ran juma'a kai nono?"


"Kai Delu kema kesan dolena intahi inhar inason in tsira da mutuncina, Iya Hari, tun yau tayo tatsarta baki ganai ba mai yawa kuma nid'ai."


"Aa na d'auka ko mutuminki ya hana kinsan shi dole yabi dokarsa koya taka ta."


B'ata fuska tayi tace "wane mutumin nawa?"


"Jauro mana ko kinada wani bayan shina?"


"Ni wallah Delu kibar had'ani da wannan mugun abu" sai hawaye sharrrr..


Tasowa tayi da sauri tare da rungumeta "yi hankuri abukkiyata nifa da wasa nikai miki, amma ai bana fatan ki kasance matarsa koda maza sun k'are ko."


Sauke numfashi tayi tare da share hawaye "wallahi Delu na tsani Jauro bansan ya nikai dashi ba, amma ita Iya Hari ba Wanda takaso saishi, saukina Ardo har yanzu baice komi ba, ina tsoron kar shima ya yadda."


"Ina Ardo bai tab'a aura miki, Jauro kuma inshaa Allah saikin auri d'an arziki kamar kowa, me ake da J......" Kasa isuwa tayi saboda arba ta tayi dashi yana zuwa, da alama a buge yake sai layi yake ya tunkarosu ga muk'arrabansa bayansa suna take masa.


Jin k'awar tata tayi shiru ne yasa ta d'ago dan ganin meke wakana, arba tayi dashi ya kusa kawowa wurin da suke, d'aure fuska tayi tare da d'auke kai.


Cikin muryan 'yan sha yake magana "ya ke Laure baki ganeni ba halan kiyi fuskar shanu tare da d'auke kai" sannan ya kalli Delu da tasha jinin jikinta "ke munahuka tashi wuce gulmammiya."


Aiko da sauri ta d'auki tirenta ta cika bujenta.


"Haba Jauro wai meyasa kakaimin haka, kaga banson haka, hakad'ai ka korar min abokiyata."


STORY CONTINUES BELOW

Tunda ta fara magana kallonta kawai yakeyi cike da sha'awa Sam shi bai gane fad'a take ko hira take masa saboda tsananin so.


Wani daga cikin yaransa ne yace "ke oga kika dagama murya saboda ke rammai?"


Tsawa ya daga masa "kai Shago Laure ce fa, kakewa fwad'a?"


Ya fad'a yana zare ido kaman ya maresa, "tuba nike oga."


"Ka kiyaye gaba" koda ya duba har ta bar gurin, murmushi kawai yayi tare da k'arawa gaba.

_so kenan hana ganin laifi_*Pls friend kuyi hak'uri dani ina fama da matsalan wayatane shiyasa bana typing da yawa.* love u all😘πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„

[7/7, 8:42 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


'''Where r u? Here is ur page, Momyn sultan, Sakwara, Iya Amima, Sadnap, Sadnas, kanwata jannart, Rukie kax and d rest. ur d best among besties. πŸ’•'''

     *In dedicated 2 Abdool all over d world* πŸ’˜


      πŸ“ *Episode* 21--25

Bayan sun dawo da sallar asubah a d'akin kakan nasa ya yada zango, ya iskoshi zaune kan kujera tasbaha a hannunsa yana ja, hannu ya bashi sukayi musabaha tare da yimai barka da asuba sannan ya zauna k'asa dai2 kafarsa yace.


"Ina kwana Alhaji?"


"Lafia lau Abdulmajeed ya gajia?"


"Gajia ta tafi, ya girma ya kuma hak'uri da jama'a?"


"Alhamdullilah, zuwa yaushe zaka tahi yabon?"


"Um zuwa goma nakeso na tafi, shima Hakeem tare zamu fita yaje yayi report a Uduth d'in?"


"Amma anan zai zauna ko?"


"Aa zasu bashi gida to inaga acan zai zauna"


"Ikon Allah tahiya zakuyi gabad'ai?"


"Aa ai Hakeem zai ringa zuwa yana gaida ku, ni kuma zan ringa zuwa end of week inshaa Allah."


"Tau ba damuwa, Allah ya taimaka ya baku nasara a aikinku" sannan ya k'ara da cewa.


"Kaci gaba da hak'uri Abdulmajeed, dama nasan kai mai hak'uri ne, kowane bawa da yadda Allah yake tsara mishi rayuwarsa, idan aka d'auke shi a jarrabawa akayi hak'uri sai kaga ya wuce sai labari, Allah yayi maku Albarka."


"Ameen Alhaji nagode, zan shiga daga ciki nad'an kintsa kafin lokacin yayi."


"Tau yaushe zakaje Argungu can inda kakanninka?"


"Shima idan nayi clearing abubuwa zanje."


"Tau ka shiga ciki kayi sallama da iyayenka da kakarka kaji ko?"


"Inshaa Allah" ya fad'a tare ficewa yana share hawayen da suka zubo masa Wanda ni kaina bansan dalilin zubarsu ba, (tofa kona meye? Mubi a sannu zamu fahimci na meye nan gaba).

Tsaf ya kimtsa shida aminin nasa bayan sunyi sallama da mutan gidan, uduth suka nufa saidai ya tabbatar anyi komai daya kamata ayi sannan ya wuce yabar Hakeem tare cousin nashi su Isma'il, saboda a dalilin sa ya cika garin yaso su samu asibiti d'aya saidai hakan bai samu ba.


Hakeem aminine na kwarai ga Abdool Wanda bayada kamarsa amintarsu ta samo asaline daga secondary har jami'a Wanda har takai ga iyayensu, kullum Hakeem yana lura da akwai wata b'oyayiyar damuwa tattare da Abdool yasha tambayarsa amma kullum amsar d'aya ce ba komai,  ya dad'e da sanin halin Abdool na zurfin ciki Sam baya bari damuwa tayi tasiri akansa yana k'ok'arin boyeta, dole shima ya hak'ura yasan in lokacin ya Sani yayi to tabbas zai gayamasa.


Shima dai ya isa garin Yabo kuma ya samu karb'a mai kyau daga mutanen garin amma kam asibitin na buk'atar ma'aikata da kayan aiki, a dalilin haka yayi alkawarin taimaka musu iya k'arfinsa Dana aljihunsa.


_wannan kenan_^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^


Tana tafe tana tunanin irin k'iyayyar da Iya Hari da Gwaggo Lanti ke nuna mata basu tab'a sonta ba, kullum cikin zaginta suke, k'arshe k'iyayya yakai su zab'a mata jauro a matsayin masoyi.......


"Ramlatuna" ko bata juyo ba tasan duk fad'in duniya bamai kiranta da wannan sunan sai shi kad'ai, juyowa tayi da murmushi akan fuskarka yana zaune bakin gidan yana duba littafi ashmawi Sam bata lura dashi ba ta tafi duniyar tunani.


Dawowa baya tayi tare da duk'awa tace "sannu Baffa, ban kula dakai ba."


Murmushi yai mata "daga ina kike da darenga?"


"Baffa daga Dandali tallen gujjiya."


"Bana hanaki zuwa Dandali da daddare ba?"


Duk'ar da kanta tayi ba tare da tace komai ba.


"Koda yake ba laihinki naba, kiyita hank'uri Ramlah da Hari inada tabbacin wata rana zata gane batai miki adalciba, kuma da yardar Allah inaji a raina sai ke zama abin alfahari a wanga karkara."


Wani k'unshi ya d'auko bayan shi ya mik'a mata "kici wanga nasan da wuya in keci abinci"


Ansa tayi zata shiga ciki tare da cewa "nagode sosai baffa" dakatar da ita yayi tare da nuna tabarma.


"Zauna nan kici" saboda sanin halin Hari idan ta gani ba barinta taci zatayi ba.


Ba musu ta zauna tare da kwance ledar nama ne agashe da zafinsa ci take hannu baka, kallonta Ardo yakeyi cike da tausayi yana mamakin hali irin na Hari, Sam batada zuciyar imani.


Cikin k'ank'anin lokaci ta cinye, ruwa ya bata tasha sannan yace ta shiga ciki, cike ta shiga zuciyarta wasai tana mai jin k'aunar Ardo har cikin ranta.


Shima d'auke kayansa yayi tare da shigewa ciki dama ita yake jira.

*Washe gari*

Kamar yadda ta saba tashinta da ruwan sanyi yauma hakane, dasu ta tasheta tare da binta da zagin k'are dangi kamar yadda ta saba.


Haka ta tashi tayi abinda ya zame mata dole sannan tayi shirin zuwa Yabo.


Zuwa karfe 9 sukaje titi don zuwa Yabo, sun kuwa yi sa'a sun samu mota, tunda suka fara tafia sai murmushi take kallonta Delu tayi "Laure missa meki na farinciki sai murmushi kikai ked'ai."


"Ni kaina bansani ba, nadaiji yau farinciki nikeyi Wanda bansan dalilin inaji a jikina wahalata ta kusa zuwa k'arshe."


"Tau Allah ya tabbatar."


"Ameen abukkiyata."


*A garin Yabo*


Abdool ne zaune kan mota bakin asibiti kasancewar yau ba aiki da yawa patients basuda yawa yaje yayi round shine ya fito waje yana shan iska, yau tunda ya tashi gabansa ke fad'uwa baisam me yasa ba, ya kira Maminsa yaji suna lafia, haka bangarensu Alhaji suma lafia.


Jin bugun zuciyarsa ya tsananta yasa ya rik'e gurin tare da yin Addu'a.


Jin ta sassauta yasa ya d'ago kansa karaf idanunsa suka sauka kan na NATA...........


Lokaci d'aya zuciyarsa ta buga kamar ta fito.....


_wacece wannan_

πŸ€”*Friend kuyi hak'uri da jina shiru da kukayi hakan ya farune a dalilin rashin nepa da mukayi 2days* love u❤[7/10, 1:32 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽*Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa:-*


_baya shiga aljannah wanda mak'wabcinsa bai amincewa ha'incinsa ba._

*'yar uwa koda kafiri kike mak'otaka ya zama dole ki sauke nauyin hakk'in mak'otaka daya rayata akanci, makota abune mai girma saboda fadar manzonmu.*+


"Jibrilu ya kasance yana yimin wasiyya da mak'oci har saida na d'auke idan na mutu zai gajeni".

_Allah yasa mu gyara_ πŸ‘πŸ½         *Point of correction*


_Abdool service sukeyi ba internship ba, fatar kun gane frnds_.      πŸ“ *Episode* 26--30
Sanye take da kaya irin na Fulani, fuskar nan tasha d'ige-d'ge ga k'waryar nono a kanta, kyakkyawace ba laifi farace ga mai tsayi da jiki, tanada kyawun fuska ba can sosai ba, fuskarta d'auke da murmushi amma zaka fahimci tana tare da damuwa, duk cikin sakan da bai wuce 50 ba Abdool ya karance yarinyar wacce ke tare da k'awarta, amma da alama yarinyace sosai saboda fuskarta ta nuna girman jikine kawai, amma abin tambayar meyasa yake ganin kamar ya Santa?, meyasa k'irjinsa ya harba saboda ganinta?


Ganin baida wad'annan ansoshin kuma gashi zasu wuce yana bukatar nonon yasa ya kirasu.


" 'yan fulani masu nono kuzo in siya".


Laure da saukarsu kenan, jin ance 'yan fulani yasa ta kalli, gurin me kiran nasu, k'irjinta ne ya buga ba shiri ta kalli k'awarta.


"Delu kega me kiranmu ko? Diba kigani kamar ba d'an nanniya ba, duba kalar idonsa abun tsoro, jishi d'an gaye, da kayan lifitoci irin na binni, muje ko kar muje"?


Me Delu zatayi inba dariya ba, saida tayi mai isarta ganin mutuniyar an fuske yasa ta sassauta.


" wlh Laure wani lokacin shirme ke dibarki yoni mi'arruwanmu da shi, nono yace zai saye fah, bayan shi mizaiyi muna? Nidai mutahi kar yace ya hwasa".


Tana gama maganar ta Kama hanya, ganin k'awar tata ta tafi yasa tabi bayanta da sauri.


Abdool kuwa dake kallonsu duk da baiji me suke fad'a yasan akansa ne, ganin suna zuwa yasa shi d'an d'aure fuska.


Suna zuwa yace "ke me kike fad'a mata, wato kikace a kalli idona ko"?


Cikin tsoro ta girgiza kai cikin siririyar murya irin ta Fulani " niya bance komi ba akanka".


K'ara d'aure fuska yayi yace "kinsha ba banji me kika fad'a ai naji komai kikace dan haka gun 'yan sanda zan kaiki"


Wayyo zanso kuga Laure kamar ta saki fitsari kunsan bafillace da tsoron d'an sanda, ba ita kad'ai ba har Delu saida ta tsorata jin an kira 'yan sanda, tuni suka fara da sun sani da basuzo inda yake.


Abdool ganin sunyi tuk'u tuk'u dariya suka bashi amma saiya danne yace.


"Nawa ne nonon"?


"Um...em.. Na nawa kakeso"? Suka had'a baki gurin tambayarsa.


D'an yatsina fuska yayi " nawane duka"?


Kallon juna zukayi sannan Delu tace " jikka talatin"


Maimata kalmar jikka yayi "meye jinka"? Ya tambaya yana kallon Laure.


STORY CONTINUES BELOW

Tsuru tai masa da ido dan batasan me zatace ba, suna hakane saiga wani nurse d'an garin ya taho gurin.


" Sir dama kanason nono"?


"Sosai nake shansa Jabir".


" Ayya ai bansani sir na d'auka bakasha da kullum na kawo maka shi, ke kutafi abinku zan kawo masa yanzu".


Ai su Laure dama kamar a k'aya suke tuni suka m'ike suna shirin d'ora nononsu.


"Aa bari nasiya tunda na tsaidasu" ya fad'a tare da mika musu 1k.


Delu CE ta ansa tare da zuba mishi "gashi mun gode, sai anjima" a lokaci d'aya ta fad'a tare da Dora nononsu sukabar gurin ba tare dajin ansa ba.


Jabir ne ya anshi nonon, shikam Abdool da kallon kawai ya bisu har suka bar gurin sannan ya kalli Jabir tare da cewa.


"Bari na shiga gida nad'an huta, idan an samu patient u should let me know".


"yes sir".


Gidanda aka bashi na cikin quarters d'in asibiti ya shige, murmushi kawai yake idan ya tuna yarinyar komai nata abin burgewa a fili yace " beautiful and silly girl" can kuma yace "meke shirin faruwa danine ni *Abdulmajeed*"?


"Kai no impossible".


(Tau kai kad'ai ne dai) lol.

Su Laure kam suna barin gurin sunyi nisa tace " Delu yau Allah ya cecemu da wanga d'an binni mai glass yakaimu inda 'yan sanda aida munci bone".


"Wallahi ko zuwan wannan mutumi ta cecemu".


"Hmmm amma kam dan binni nada kuddi har nonon jikka biyar"?


" Aida gani kilama shina kayinsu diba kigani sabuwa dal".


"Amma kam ban komawa ta hanyagga kar atai ya ganmu ya had'amu da 'yan sanda".


"E walla mubi ta waccen hanya".

Haka dai sukayita tattaunawa har suka isa kasuwa........^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^Wasa-wasa tunanin yarinyar yayi tasiri a zuciyarsa shi yasa kullum daya gama aiki zai fito ya tsaya waje, amma ko mai kamarta bai tab'a bai gani, mamaki yakeyi meyasa ya damu da yaga yarinyar? Meyasa yake son sanin labarin yarinyar?


Ba Wanda zai ansa mishi amma tabbas zuciyarsa ta matsa mishi daya ganta yaji boyayyiyar damuwarta.......


*A garin kilgori...*

Kamar kullum Ardo tare da Amininsa Malam Garba ne zaune daf da magrib yana jiran Ramlah ta kawomusu ruwan Alwala, numfasashinsa ne yaji yana sassarfa kamar zai d'auke sai k'ok'arin janyosa yake.


Malam Garba da suke fira da Amininsa jin yayi shiru, yasa shi d'agowa ya kalleshi, ganin halin da yake ciki yasa ya tashi da sauri tare da kamashi yace.


" subhanallah Ardo ciwon ne ya tashi" duk ya rikice ana haka saiga Laure ta fito ganin halinda Baffanta ya yake, sakin buta tayi cikin kuka ta isa gareshi tana "wayyo Baffa, meya sameka Baffa" kan jikinsa ta kwanta tana kuka.


Jayeta Malam Garba yayi "ba kuka zakiyi ba Laure, jeki kiro Hari muje asibiti".


Da gudu ta shiga gidan "ke tambad'add'ya minana kika shigoma mutane uwa kamun hauka".


" Iya Baffa ....." Ta kasa magana sai nuna mata k'ofar gidan take.


Ganin taki magana taja tsaki "ko minana babu ruwana can ta matsemuku ke dashi" ta bud'e baki zatayi magana.


STORY CONTINUES BELOW

"B'acemin da gani sauna" ta fad'a cikin tsawar da ya firgitata a guje ta fita, koda ta fita har Malam Garba ya kira mashin ana shirin d'ora Ardo.


"Ina Harin"?


" tana zuwa" kawai ta fad'a D'ora shi yayi shima ya hau tare da cewa su samesu a can.


Aiko suna wucewa ta bisu da gudu tana kuka, d'an clinic ne garesu a garin, ba kuma likita sai nurse kawai, ganin yanayinsa yasa sukace a wuce dashi Yabo kawai.

Koda ta iso har an samo mota, an sakashi, ai bata jira jin komai ba ta fad'a ciki driver yaja........_manage pls friends_ πŸ‘πŸ½


πŸ’„ Meryerm Abdool πŸ’„

[7/11, 4:04 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽'''WASIYYAR LUKMATUL HAKEEM GA D'ANSA ITACE :-'''


*Ya kai d'ana kada kayi shirka ga Allah(kada ka had'ashi da wani a gurin bauta) domin shirka itace mafi munin zalunci, ka zamo mai biyayya ga iyaye, domin neman dacewa duniya da lahira.*


*Yakai d'ana ka tsaida sallah, kayi hak'uri da abinda ya sameka, kada ka nemi biyan buk'atarka ga mutane, kada kayi tafiya a cikin k'asa kana mai alfari da tak'ama, domin ubangiji bayason mutane masu alfari da tak'ama.*


*ka zamo mai tafiya cikin nutsuwa, kada ka zamo mai d'aga sautinka a gurin magana domin mafi munin sauti shine sautin jaki.*( _suratul Lukman_)


_Allah sarki, mutum mai mutum mai hikima kenan, ni dah keh dasu wance mun tab'a tunanin yima 'ya'yanmu wasiyya, tofa musani 'ya'ya amanace kuma abin tambayawa ne gaban ubangiji ranar gobe k'iyama._


Allah yasa mudaceπŸ‘πŸ½

       πŸ“ *Episode* 31--36
Suna isa aka k'arbesu I&E aka wuce dashi, haka Laure da Malam Garba suka bi gadon da aka d'orasa, sai hawaye kebin fuskarta ganin yadda numfashin Ardo ke zuwa yana dawowa gani take rasashi zasuyi, idan Ardo ya tafi ya barta shikenan batada sauran gata (Allah ne gatanki Laure).


Suna isa bakin k'ofa aka dakatar da su daga waje, anan reception suka zauna kan bench, sai addu'a take duk Wanda tazo bakinta nah nemama Kakan nata lafeeya, Malam Garba safa da marwa kawai yakeyi yana jiran tsammani tare da tausayawa aminin nasa, dan ciwon bai tab'a taso masa irin hakaba zuwa d'aya, saidai fatan samun lafia yake masa.


Taimakon gaggawa suka fara bashi ta hanyar saka masa oxygen, nurse Zainab ce ta fito, sanye da uniform irin na nurse, domin kiran Dr, Abdool saboda baya nan yaje gida yanzun, gashi ta kira wayarsa yana busy, da sauri ta fita, ganin ta yasa suka taso suna tambayarta jikinsa "da sauki" kawai tace ta fita.


Knocking tayi "yes" aka bata Umurnin shigowa, flat ne gidan mai one sitting room and 2bed room sai kitchen, irin dai na quarters d'innan, kwance yake kan 3seat idon sa lumshe yana waya, kan 1seat ta zauna tana k'arema gidan kallo dan shine first time d'inta shiga, komai neat sai k'amshi ke tashi kamar gidan mace.


"Hmm haba Hakeem duk matan da na gani ABU basu dama min lissafi ba, sai wannan 'yar fillon? Never."


Banji me Hakeem yace ba, murmushi yayi "any way yanzu inada bak'uwa, amma zan shigo end of week inshaa Allah".


STORY CONTINUES BELOW

'Yar dariya yayi tare da cewa "shegen kaya" sannan ya katse wayar.


"Yadai Zainab" ya fad'a ba tare daya bud'e idon ba.


Zainab da tunda taji ya ambaci 'yar fillo, k'irjinta yai mummuman bugawa sai zafi yake Mata.


Zainab itama Attachment takeyi daga Sokoto tazo, tunda taga Dr Majeed haka suke kiransa, taji ba Wanda takeso duk duniya kamarsa, tun daga lokacin take shige masa muddin yana hospital to tana tare dashi tanada kyau sosai itama siririyace mai matsakaicin tsayi kalar fatar tah bak'a CE amma irin mai kyallin nan.


Tayi mamakin yadda ya kira sunanta bah tareda yaga waye ba, kodai shima yana sonta neh? Waye zai ansamata wannan tambayan? Abun ko ba haka bane normally idan Abdool yaji muryanka sau biyu to yana noticing idan ya k'ara jinta.


Jin shiru nad'an mintuna ya sakashi mik'ewa zaune tare da ware manyan idonsa a Kanta.


Karaf ya idonta cikin nasa, cikin rawan murya tace "Sir we have a patient right now, he is in a very critical condition".


" OK am coming " kawai ya fad'a.


Mik'ewa tayi ta fice, binta yai da kallon "ko miye damuwarta oho!" Ya d'aga kafad'ar sah tare da tab'e baki.....Sosai ya tausayawa tsohon dan yana jin jiki sosai, kusan 30mnt yayi a kansa kafin yayi nasarar daidaituwar numfashinsa, allurar jijiya yayi masa sannan yasa aka maidashi d'akin Hutu.


Fitowa yayi yana cire hand glove tare da Handkerchief ya fito dashi yana share zufa, dai2 lokacin Malam Garba ya iso inda yake "dofto ya ake ciki ya mai jikin"?


Murmushi yayi masa " kwantar da hankalinka Baba, ya samu sauki yanzu yana d'akin hutu muje muyi sallah koh"....


Laure data shige duniyar tunani bata masan Malam Garba ya tashi ba sai dubawa tayi bata ganshi ba d'agowa tayi ganin shi da Dr suna magana saidai bayansa kawai take gani, tashi tayi zuwa inda Suke.


Kaman ance ya juyo sukayi four eye cikin mamaki yace "you again"? Itakam tsoracewa tayi ganinsa, ita tama manta dashi.


Sunkuye kai tayi ba tare datace komai ba don batasan meyace ba, ganin idonta jajir alaman tasha kuka " me kikeyi anan."


Malam Garba ne yace "kasantane dofta"?


" eh to na tab'a ganinta anan garin tazo saida nono harma nasiya toh shine nake mamaki."


"Ayyo! Ai kakanta neh  baida lahiya."


K'ara kallonta yayi cikin ransa yace "dalilin kukan kenan"? A fili yace "OK, amma meyasa kuka taho da ita Baba"?


" wallahi d'anga an rud'e ne, ni bammasan ta shigo ba."


Wayarsa ya d'auko yayi kira " Zainab d'anzo reception zakiyimin wani aiki" ya fad'a tare da tsinke wayar.


Minti kad'an sai gata tazo "kije da yarinyar nan gidanku pls" kallonta tayi sannan tace "muje ko" tana mata murmushi.


Binta tayi sannan ta shima Abdool suka fita jin an fara kiran isha'i, bayan sun fito gida yaje ya d'akko bargo da filo ya kawoma Malam Garba sannan yaje yayi round ya wuce gida, har yanzu Ardo bai farka ba, saboda hadda alluran bacci a ciki.


Tana zaune k'asa sai raba ido take, Zainab ce ta fito daga kitchen abinci ta aje mata tare da ruwa da drink, "ya sunanki ta tambayeta"?


" Ramlah " ta fad'a a takaice.


"Wow nice name."


Itakam name kawai ta gane, da yake tadanyi makaranta zuwa primary four Iya Hari ta fidda ita.


Murmushi yake tayi mata, "ciki abinci sai kizo kiyi sallah" Zainab ta fad'a tare da shiga bedroom d'in ta, da yake gidan su 2 ne dashi tare da wata Christan.


STORY CONTINUES BELOW

Aiko tana shigewa Laure ta kama cin abinci hannu baka, sai dadi ke ratsa mata k'wak'walwa tana jinjina ma 'yan birni akan cin dad'i.


Cikin minti biyar ta gama dashi tsaf, cikin kayan gida Zainab ta fito ganin plate kawai tayi, smiling tayi sannan ta d'auke takai kitchen, kunyace ta kama Laure, amma saita share kada ta Renata(hoho su Laure aja girma) lol.


"Muje kiyi sallah" dakin tsaf2 ba wani tarkace gado ne sai wardrobe, toilet ta nuna mata "ruwa nanan a bocket kiyi wanka akwai ruwa a bota na alwala" nagode " ta fad'a tare da shigewa.


Girgiza kai Zainab tayi tare da cewa "kodai itace 'yar fillon"? Tab'e baki tayi tare da fitar mata da kaya, sannan ta shimfida mata dadduma.


^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^*A k'auye...*

Iya Hari jin shiru har bayan isha ba Malam ba Laure yasa hankalinta yad'an d'aga, fita tayi ganin ba kowa yasa ta koma gida rikice ta d'auki mayafi, a waje taga wani yaro ta tambayesa nan yake shaida mata yagansu bakin asibiti an sakashi mota a mace.


K'ara rudewa tayi ta rasa inda zata saka Kanta, 'ya'yanta ta aikawa Lanti da Shatu, suma tuni suka iso a firgice........._love u friends_ ❤.
πŸ’„Meryerm Abdool πŸ’„

[7/13, 10:01 AM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽
'''Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:-'''

_Baya shiga aljannah, maiyin annamimanci._

*Annamimanci yana nufin munafurci, munafurci yana nufin kayi maganan mutum koda abinda ka fada gaske ne abayan idonsa, Wanda ya kasance tozarci ne garesa.*


*a wannan zamanin da muke ciki abin ya zama ruwan dare saidai fatan Allah ya kawo mana sauki, ni dake dasu, muyi k'ok'ari mu duba yadda muke tafiyar da rayuwarmu ta yau da kullum shin mun kiyaye harshenmu ko kuwa Aa.*


Allah yasa mudaceπŸ‘πŸ½_Where r u? Rukie gwando, mlm ubaida, mino, qwlly, Maman Ramlah, Maman Nana, Sarat, Maman xee, sisto shafcy Abdool, oh kuyi hak'uri wadanda ban kira ba, mu had'u wani jik'on. ILYVM FROM D BUTTON OF MY❤_          πŸ“ *Episode* 36--40


Suma rud'ewa sukayi ganin halinda mahaifiyarsu take ciki, barin ma Lanti taji, Shatu CE ta tambayeta cikin nutsuwa, nan ta gayamusu abinda wannan yaron ya fad'a mata, asibitin  garin sukaje suka tambayi inda akaje dashi nan sukai musu bayani, gida suka dawo suka fad'a mata sannan sukai mata sallama da niyyan gobe suyi asubanci.


Iya Hari sai k'ara tsinewa Laure take a nata ganin mugunta tayi Mata tak'i gayamata (oh wannan tsohuwa sai Allah).

B'angaren Abdool kuwa zuwa ten ya k'ara komawa asibiti koda yaje ya samu Ardo ya farka, nurse na cire mishi ruwan da aka saka mishi Malam Garba na gefensa ya d'aga mai filo ya jingina dashi, murmushi yayi tare da cewa.


"Sannu Baba jiki yayi kyau" lokaci d'aya Ardo yaji yaron ya kwanta mishi a ransa, Sam baida alaman wulak'anci ko d'aga kai irin Wanda wasu likitoci keyi (ai ba duka aka zama d'aya ba).

"Alhamdulilah naji sauk'i sosai docta, gashi numfashina ya daidaita, saidai k'arfin jikinne ya rage."


"Ayya shima zuwa gobe zakaji ka dawo normal" ya fad'a yana d'an dubashi, maganinda ya siyomai ya basu tare dayi musu saida safe, sauran ward d'in ya shiga ya dudduba patients.


STORY CONTINUES BELOW

Wani massenger asibitin ne ya kawo mishi wata leader "gashi Sir an samo dak'yar" ansa yayi sannan ya d'aga mishi hannu "well done  zaka iya tafiya" ya fad'a tare da wucewa, gidansu Zainab yaje kiranta a waya yayi.


Tana zaune tana duba wani littafin biology, Laure na gefe a k'asa bacci yayi gaba da ita, ba yadda Zainab batayi da ita ba, akan tahau kan seat tace k'asa ya isa, ita batamasan tayi bacci ba, dan atunaninta kallon da ta saka mata takeyi.


Wayarta ce tashiga Neman agaji "Dr Majeed" tace d'an mamaki a fuskarta, sai kuma tai smiling mai k'ayartarwa kamar tana gabanshi sannan ta d'aga.


"OK" kawai ta fad'a, tare da zura hijab d'in sallarta sai k'asa, dayake kayan bacci ne a jikinta, tana mamakin da Daren nan ya taho gidansu, smiling ta k'ara yi, gefen Laure ta kalla taga bacci yayi gaba da ita "sllly girl" ta fad'a sannan ta fice.


Yana jingine da motarsa ya rungume hannuwansa a k'irji, sanye da blue jean da shirt red ya d'ora lab court a sama, as usual glass dinsa na mak'ale a idonsa, duk kafin ta k'araso ta k'are masa kallo, itadai wannan gayen na tafiya da ita ba kad'an ba.


Sallama tayi masa ya ansa bayan sun gaisa ya Ciro Leda a mota ta bata "gashi ki bama yarinyar nan, dan naga da alama kayan jikinta ne kawai tazo dasu".


Ansa tayi tare da cewa "ai dama baka siyo ba dan nama bata wasu dana d'inka ban riga na saka ba, amma duk cikin k'ari ne an gode."


"Nine da godiya Zainab, thanks once again"


Murmushi tayi "wannan k'anwar taka akwaita da kunya, sam bata magana" (bugun ciki taji ya Suke).


Shima smiling yayi "zan tafi saida safe" ya shiga motarsa...


"Tau gudnyt Sir" ta fad'a tare da wucewa ciki cikin farinciki, tada Laure tayi takaita d'aki "da sannu zanyi nasara ishaa Allah (tunda kikace Allah kin gama komai Zee).


↑←↓→↑←↓→↑←↓→


Laure asuban fari ta tashi saboda sabo, kan gado ta ganta, sauka tayi a gefen gado taga Zainab kan dadduma, murmushi tayi mata " kin tashi cute Ramlah" itama murmushin tayi mata ba tare datayi magana ba.


"Je kiyi alwala kiyi sallah inaga time dinma yayi" girgiza mata kai tayi tare da murd'a k'ofan "am akwai brush a gefe mirror da MacLean sai kiyi" nanma kai ta d'aga mata dan bata fahimci me take nufi ba tadai ansa kawai.


Zuwa 8 Zainab ta shirya cikin uniform bayan sun gama breakfast itama Naomi fitowarta kenan "Sainab kayi bakone" yes Naome she's my sister ".


" wow so beautiful like u" dariya tace "as said always and u are beautiful too".


" ha ah Sainab don't said that again, see me se troubIe, Hmm look like fate-fate"


Dariya sosai Zainab tayi hadda kama ciki, Laure sai kallonsu take tana inama tanajin me suke cewa abin ya birgeta duk da bataji.


"U are too funny Nao, oya let go time is going".


" Hah! na true shaa"

Kallon Laure Zainab tayi "Ramlah zamu tafi asibiti, zan dawo naje dake idan Dr yai magana" narai-narai tayi da ido cikin sanyi tace "zan biku inga baffa".


D'an tunani tayi kada taje da ita kuma Dr baice ba, can dai ta koma d'aki, fitowa tayi tare da kayan Ramlah da wadanda Dr ya kawo mata da NATA wad'anda tazo dasu, da wadanda ta cire jiya " kinga wad'anda yayanki ya kawo maki" tana nuna mata kayan da Abdool ya kawo mata.


"Yayana"? ta fad'a cikin mamaki, " eh doctor da ya had'ani dake koba yayanki bane"?


Kad'a mata kai tayi alaman eh, "well to muje, aranta tace " koma ke meye tasa a sanadinki nad'an samu kusanci da Dr, hmm inasonka Dr Majeed" tai smiling mai tashi tare da lumshe ido....

Suna shiga ward d'in da Ardo yake da gudu ta isa garesa tare da rungumesa, yana zaune wani messenger ya kawo kayan breakfast da Abdool ya aiko ya kawo musu Malam Garba ya had'a mishi shayi yana sha, ajewa yayi tare da Shafa Kanta.


"Ramlatuna Ashe dake akazo, kinga wannan Dr mai karamci da mutunta mutane ko"?


Kai ta girgiza alaman eh " Baffa ya jikinka" na samu sauki Ramlatu ba in kemin ciwo yanzu".


"Allah ya k'ara sauki Baffana" nan malam Garba yayi ta tsokanarta ga Ardo nan bai tafi ya barta ba, haka tai ta cewa jiya tana kuka, fuskarta ta rufe tana murmushi dai2 nan su Zainab suka iso suka duba jikinsa sannan suka wuce suna mishi fatan samun sauki.


Nan Ramlah ta gayamai Alkhairin da tayi mata aiko kiransu yasa tayi yana ta kwararo musu addu'a da sanya Albarka "ba komai Baba yiwa Kaine" ta fad'a tana murmushi don taji dad'in addu'ar.....


Kusan 10 su Iya Hari suka iso Yabo, basu sha wahala ba gurin gane ward d'insu, suna isa Iya Hari sai masifa tahau Laure dashi ba tambayan Ardo jiki ba komai, sai ruwan bala'i hadda fad'in da mijinta ya mutu da sai tayi k'ararta (jimin k'arfin hali).

Ardo kam kwantawa kawai yayi ya rufe ido, yanajin zafi har cikin zuciyarta, wannan wace irin musiba ace ko gaidashi batayi ba ta hau masifa akan rashin dalili, a bak'on  wuri ma ba zata rage ba, kai Allah wadai da hali irin na Hari.


Itama Shatu tunda ta gaida mahaifinta da jiki, ta koma gefe tayi tagumi, ta tsani irin halin mahaifiyarta, musamman yadda take nuna tsana akan 'yar d'an uwanta saboda dalilinta mara tushe, Lanti murna take dan halinsu d'aya da uwar shiyasa tafi k'aunarta.


"Kedai Laure anyi muguwa mai bak'ar aniya jikar mayyu" Kanta sunkuye ranta sai suya yake, malam Garba sai tausar Hari yake amma kamar zugata yake.


Karaf a kunnen Abdool Wanda fitowarsa kenan, maimata maganar yayi "muguwa mai bak'ar Aniya, jikar mayu, wacce ce haka...."?.........

_love u friends_ πŸ˜πŸ’„ Meryerm AbdoolπŸ’„

[7/16, 10:50 AM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽'''Annabi Muhammad (S.A.W) Yana cewa:-'''

_Mafi sharrin mutane mai mummunan masauki a gurin Allah (ranar alk'iyama) shine wanda mutane suka guje masa saboda alfasharsa_ (hakkun mubeen.)+


*nida ke dasu, ya kamata musan me muke furtawa, me muke aikata saboda mu tsira a ranar gobe k'iyama.*


Allah yasa mudace πŸ‘πŸ½      πŸ“ *Episode* 41--45

Kansa ya danna cikin d'akin, da kallon wannan fa yabi Iya Hari dashi, ganin sai masifa take zubawa ita kad'ai, ga Laure kanta duke da alama ita ake mawa.


"To meye had'inta da ita, me tayi mata" ya tambayi Kansa a zuciyarsa.


Malam Garba ne ya kula da tsayuwarsa saboda kowa hankalinsa baya gun "Dr sannu da fitowa" ya fad'a.


Jin hakane yasa Ardo bude idonsa, a dai2 lokacin itama Laure ta d'ago nata idon kan nasa ta sauke dama ita yake kallo, ganin yadda fararen idanunta sukayi ja ranta a dagule.


Gyaran murya yayi sai lokacin Iya Hari tasan da zuwansa, d'an kame-kame ta farayi dan ba k'aramin kwarjini yayi mata ba tare dayin shiru.


"Haba Inna meye, haka a asibiti kike fa? Marar lafiya baya buk'atar damuwa, pls kud'an fita daga waje".


Jiki sanyaye suka fice aka barshi daga shi sai Ardo " kayi hank'uri don Allah docta, kasan mata sai a hankali" murmushi yayi masa.


"Ba komai Baba dama dan lafiyarka ne, ya kakejin yanayin jikinka yanzu"?


"Madallah jiki inajinshi dai2 babu inda kaimin ciyyo yanzu".


D'an duddubashi yayi kujera yaja ya zauna sannan yace "yanzu komai ya dawo normal saidai kana buk'atar rage tunane-tunane saboda bayan asthma har hypertension kanada (baiyi mamaki ba saboda jarabar Hari kad'ai ta isheshi) kuma yawan saka damuwa a zuciya ba naka bane pls ka kiyaye Baba kodan lafiyarka" ledar magani ya bashi.


"Ga wannan kayi amfani dashi" sannan yayi mishi bayanin yadda zaiyi amfani dasu.


"Yanzu zanyi discharge naku, zaku iya tafiya" ya fad'a tare da mik'ewa "Allah ya bida lafeeya.


" d'an nan to nawane kudin maganin"?


"Aa Baba ka barshi Allah dai ya baka lafia" godiya sosai Ardo ke kwarara masa yana jinsa kamar d'ansa "dama akwai sauran irin wad'annan mutanen Ashe" ya fad'a a ransa.


"Ba komai Baba, nima nagode da addu'arka Bari inyi magana dasu, yanaso ya tambayesa game da Laure da alak'arsu saidai yana ganin rashin dacewar haka toya zaiyi?.


Can wani tunani yazo mishi, smiling yayi tare da ficewa.


√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√"To shi kuma wanga wanena? Yaka korarmu iyii"?


Malam Garba yace " dofto na, mai kula da Ardo".


Zata k'ara magana sai gashi ya fito da kallo ya bita Wanda yake na raini, yawu ta had'iye, gefen Laure ya kalla ta rabe Kanta cikin cinyar ta, girgiza kai yayi alaman tausayi.


STORY CONTINUES BELOW

Shatu dariyace ta k'onota saidai ba damar yi ganin yadda uwarta ke raba ido alaman tsoro, dan Hari akwai masifa amma tsoro kamar farar kura, haka take tsoron Jauro kamar ranta.


"Dofto ya ake ciki"?Malam Garba ya tambayesa.


" zaku iya tafiya sai a kiyaye b'ata masa rai, sannan a ringa kula da shan maganin pls Ku kiyaye".


"Inshaa Allahu dakata" Iya Hari ta fad'a don Neman sulhu.


"Madallah dofto za'a kiyaye inshaa Allah, mungode da hidima fa, takardar magani fa? Wanda za'a siya".


" no ku barshi kawai na kai masa maganin, adai kula sosai".


"Kai madallah mun gode sosai Allah yayi Albarka, Bari intai in samo mota, Ku kutai ku kimtsa" yace dasu Shatu.


"Ameen, amma indai wannan Ku had'a kayanku zan kaiku, sai kumin magana idan kun shirya" ya fad'a tare da wucewa.


Da Zainab ya had'u yana daf da shiga office "morning Sir".


" morning Zainab, am kiyima Dr bakori magana yayi replaced d'ina zan fitane".


"OK Sir".


" koda maganan?" ganin ta mishi tsaye ta kashesa da ido.


"No" ta fad'a tare da wucewa, girgiza kai yayi tare da smiling ya Shafa sumarsa "ciwon mu iri d'aya ne, son maso wani" ya fad'a tare da shigewa office d'insa..........


Har k'ofar gida ya kaisu, wannan karon harda su Iya Hari sai godiya ake zubawa (su iya ansha A/c) lol.


Fura zallah Ardo yasa aka damo masa wacce tasha kindirmu damun kyale mod'a(ba'a saka ruwa a ciki) yaji dad'in hakan sosai dan dama Abdool ma'aboci shan furane da nono, nan waje suka zauna da Ardo suna d'an fira, yara kuwa sun zagaye mota sai shafata Suke sunga irin wacce basu saba gani ba, mata kuwa sai lek'e Suke ta Katanga, mutane sai kwararowa suke gaida Ardo da jiki.


Har ya shiga mota zai tafi sai ga Laure ta fito, nono ne da kwan zabi tace Ardo ya bata, tsayawa tayi ta k'asa magana Kanta k'asa, kallo ya k'are mata tsaf komai nata mai kyaune yanzun ma da take yarinya to inaga ta girma Hmmm.


Ganin tak'i magana ga lokaci na tafiya yasa yace "yadai da damuwa ne"?


" Um nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi" still Kanta a k'asa itakam har yanzu tsaronsa takeyi da gaske.


"Hmm damefa"?


Bata ansa ba sai Ledar da ta Mik'a mishi " gashi ka kaima Aunty Zainab ina gaida ita sosai " duk cikin sanyayyiyar murya take maganar.


"Allah ya kiyaye" tana fad'a ta juya ba tare dataji me zaice ba, binta yayi da kallo harta shige, Shafa Kansa yayi tare da smiling harda lumshe ido (tofa me kenan Dr?)...........


Zainab taji dad'in kyautar Laure kuma ta nuna hakan a fuskarta wanda hakan ba k'aramin dad'i yayi ma Abdool ba, amma kuma k'asan ranta tanajin kishi sosai saboda zuwa yanzu ta gane itace dai 'yar fillon da yake magana, to amma meyasa ta damu da yawa batada tabbacin sonta yake ko tausayinta, dan tasan Abdool da tausayi a d'an zaman da sukayi yana d'aya daga cikin hayensa dake k'ara nutsata a k'aunarsa, amma kuma tanaji a jikin ta na Laure ya wuce tausayi to amma meye mafita saboda a gaskiya tana matuk'ar k'aunar sa tare da kishinsa (tofa Zee u say something oo).


"Sir pls idan zakaje Skk dis week zan bika ka ragen hanya"?


Saida yayi Jim sannan yace "OK".....

*End of week....*


Har k'ofar gidansu ya taho d'aukar ta, sanye ta fito cikin Arabian gown black tayi rolling da light blue d'in kashka, light make up tayi, tayi kyau ba k'arya.


STORY CONTINUES BELOW

Tunda ta fito ya bita da ido for d first time daya k'are mata kallo, tayi masa kyau amma kuma bata a zuciyarsa maganan gaskiya, dan ya dad'e da harbo jirginta musamman a d'an lokacin nan da take shige masa yasan sonsa takeyi, kuma har cikin ransa yana tausaya mata saboda yanzu shima yasan dafin so.


Tunda suka gaisa suka d'auki hanya bamai cewa uffan kowa da abinda yake sak'awa a ransa.


K'ira'a ya kunna musu ta *Shaik sudais* cikin suratul bak'ara, cikin kwarewa yake tuk'in yana bin karatun a hankali cikin daddad'ar muryarsa mai killing d'in Zainab, aiko lup tayi a kujera tanajin inama su couple ne, direct gidansu zasu wuce yanzu sai imagining takeyi a ranta tana murmushi( boyar Allah).


Batama san sun iso ba saida taji yana fad'in " ina muka nufa" cikin kasala tace.


"Mabera" gidane mai kyau madaidaici dan Baban ta yana da hali dai2 gwargwado, saboda ma'aikacin gwannati ne kuma ba laifi yanada salary, Zainab CE babba 'yarsa sai k'annenta 4, yana ajeta har zai ja mota tace "pls sir ka shigo Ku gaisa da Momy na".


"Oh! Sowie Zainab I'm urgent now but i promise zanzo when  I'm free".


Godiya tayi masa sannan yaja motarsa zuwa family house nasu.............
*na shiga busy, ga matsalan b3, kuci gaba da hak'uri Dani* one love friends❤πŸ‘πŸ»πŸ’„ Meryerm AbdoolπŸ’„

[7/17, 12:08 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


*Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa:-*


_baya shiga aljannah mai yankewa(yana nufin mai yanke zumunci)_


*to 'yar uwa nidake dasu muyi k'ok'ari muga mun sada zumunci, musamman wanda yayi nisa, ba wai sai zumunci na jini, Aa harna musulunci saboda dukkan musulmi d'an uwan musulmi ne.*


Allah yasa mudace πŸ‘πŸ½'''Double love belong 2 u, ina yinku 😍 momma (Ayshat garkuwa, neighbour(zee Yabour), indon kauye, Fashuna, swerry, Husna, ummyn yusrah,  momyn ihsan, Maman khadija, Seemaluv, Rufy, ummimi, eshat asym, ummu safwan, ummi garkuwa, zarah adami, maskurah, Ayshat hanwa, shukrah, ummihaneefa. Pls wad'anda ban fad'a su tsumayeni next page love u all dearest😍😍'''
        πŸ“ *Episode* 46--50


'Yan dubiya sai zuwa Suke ciki harda jauro anzo kamar mutumin kirki hadda wani duk'awa waishi a dole ladabi yake, Ardo dai kallonsa kawai yayi, yasan dai ba Wanda ya isa ya Aurar da Laure sai shi, ya barsu da shirmensu, 'yar ledar dubiya sai ciki yaje da ita ya bawa Iya Hari, dan ya k'asa ba Ardo.


Ita kuma mai kwadayi baki har kunne ta ansa tana shi masa Albarka, ita da Lanti sai rawar kai Suke, Shatu dai idone kawai nata, Laure ita harta manta dashi d'an kwana daya da basu had'u ba, data ganshi kamar ta hadi zuciya, shiko gogan naka dad'i kasheshi yaga rayuwarsa gata cikin kayan 'yan birni ji yake awa ya d'auke ta ya tafi, ba laifi shima yayi shigar arziki yau anzo dubiyar suruki cikin manyan kaya hadda hula, kamar abin arziki, saidai idonnan kam nanan kamar garwashi (chain! d'an kwaya baiyi ba, Allah ya karemu da zuri'armu Ameen).
Abdool yana isa b'angaren kakansa ya shige, yana zaune kamar kullum yana duba littafan musulunci, gaisawa sukayi cikin fara'a tare da tambayarsa yanayin aiki ya ansa da komai qlau, nan sukayi barkwancinsu da suka saba tare da tab'a hira, sannan ya shiga ciki ya gaidasu kamar kullum kakarsa fuska ba annuri suka gaisa, sannan ya dawo ya gayama Alhaji zai isa inda Hakeem dan zasuje Argungu ne.


STORY CONTINUES BELOW

"Madallah Hakeem yaron kirkine kullum sai yazo dubani ga dawainiya, Allah dai ya sanyama abotarku Albarka kuci gaba har abada ".


" Ameen Alhaji, ai indai Hakeem zaiyi abinda yafi haka" ya fad'a da murmushi dan yasan abokin nasa sarai akwai kirki matuk'a (shi akeso aboki na gari Allah yasa mudace).~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Hakeem ne kwance parlour gidansa sai bacci yake cikin kwanciyar hankali, Ac sai sanyaya sa takeyi, Abdool tsaye kansa ya kama k'ugu kamar mace yana tunanin kalar tasuwar da zai masa.


Saidai ya daddage yakai mishi bugu a baya, aiko sai gashi zaune yana Sosa bayan saboda yaji bugun sai raba ido yake kamar Wanda yayi k'arya.


Abdool kuwa dariya yake masa, dariyarce ta sanar da shi mai aikin, harara ya watsa masa "kaidai anyi mugu wallahi, mutum na baccinsa kazo ka tashesa fisabilillah".


"Kaiko idan ba wauta ba, meyasa ka kwanciya a parlour kuma k'ofa a bud'e salon a saceka ka bani aiki".


Dariya ya basa " imaging a saceni fa? Meye amfanin securitys d'in? A side ma waya kwanciyar bakai ba tun ten na shirya ina jiran ka, amma shiru kaman an aiki bawa garinsu" ya fad'a tare da K'ara da dalla mishi harara.


Siririyar dariya yayi tare kwanciya a seat hadda lumshe ido "hmm ka Bari kawai dude d things are much fa".


" Hmmm ba wani things lover boy, kadai kace love na nuk'urk'usarka period, wai ina labarin 'yar fillo taka"?


"Hmm! Wani bunch of surprise, ina last time da muke waya nace maka ina guest? Kakanta aka kawo emergency....." Nan dai ya bashi labarin duk abinda ya faru.


Hakeem hadda buga k'afa saboda dariyar k'eta "I told oo ur in love, lallai makashin maza, mazane ke kashesha, ina zanga Shukrah da Memzy alhakinsu ya fita.


" kaifa matsala dakai kenan! Ana maganan arziki kanata tsiya, ai kaima kasan ban musu walak'anci ba, an rabo lafiya wata kil ma sunyi aure, whatever dai yanzu meye way out"?


"Hmm kana sonta ka Aureta kawai".


" what! In aureta fa kace, kasan me kake fad'a kuwa?"


"Na sani mana, meye ribar soyayya idan ba aure?"


"Abinda nakeso ka gane, yarinya ce sosai inaga ko sa'ar Nihal batayi ba, sannan gata tsorona takeyi, abar maganar wannan ma ina matuk'ar tausayinta da alama tana cikin damuwa kamar yadda na gayamaka kullum cikin damuwa zaka ganta koda kuwa tana fara'a ne zaka tsinkayo damuwarta".

"Kaji Smart! Well tunda kakanta Nada saukin kai inaga ka fake da zuwa dubashi daganan sai kud'an saba, kaga kamai zaizo da sauk'i".


" wow good idea friend, hakan za'ayi".


"Hhhhhh toya maganan Zee kuma?"


"Kaji wata kuma ai ina gayamaka tare muka taho da ita nayi dropping din ta, hmm taso ta kaimi cikin gida na zille mata".


Dariya sosai yaba Hakeem yanayin yadda yayi maganan " kaji na 'yar fillo da Zainab".


"Fad'i ka k'ara ai gwandani nayi kasuwa kaifa?"


"Hhhh ba komai dai".


" amma kasan me? Ina tausayawa Zainab fa, saboda yanzu nasan rad'ad'in so".

"To ka auresu duka mana".


" caff! God forbid, bazan Iya ba".


"Nidai kaika Jiyo, kaga tashi muje time is going".


" oh zuwa Argungu is no big deal fa, nan da one hour mun isa, kuma ai bayau zamu dawo ba, yawwa ina sak'ona, dan bazan dawo tanan ba".


"Au abin 'yar hakane" Hakeem ya fad'a yana bashi wata k'aramar Leda, dama ya fito da kayansa shi kawai yake jira, ta motar Abdool suka tafi......


STORY CONTINUES BELOW

Tarba mai kyau suka samu daga kakannin nasa na Uwa, da Kawunsa, gaisawa sukayi cikin fara'ar ganin jikan nasu, bayan sun hutane Abdool ya d'auki Hakeem ya zaga dashi gari, dan yasan garin sosai, kamar su gidan Al'adu, matan fada, mala, grand fishing, da dai sauransu basu suka dawo ba sai magrib, bayan sunyi sallah kuwa suka dasa firar yaushe rabo da kakannin NASA.....

Washe gari ma sake fita sukayi dan garin ya burge Hakeem sosai( ai dole ne Hakeem, Argungu garin nabame kowa sarki, gari mai ni'ima da dinbin tarihi, garin sarautar gargajiya data zamani, kabawa ikon Allah Ku adda ruwan nan) lolz.


Basu suka baro Argungu ba sai bayan la'asar tare da tsarabarsu ta kifi.


Anan yabo suka rabu Hakeem ya shiga motar baya zuwa Skk, kamar yadda Abdool yace hakan yayi akayi.


Wanka kawai yayi ya canja kaya, ya d'auki hanya kilgori dan ganin mintin zuciyarsa...........

 _manage pls_ πŸ˜‡πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„

[7/18, 10:05 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


'''#one love # just for u guys,😍 Aunty kausar, Aunty khady, Suhana, Ummu khady, sisin Mama, fateey nashuka, Meryerm mukhtar, Lemancykhan, Salma(momma), samrah, Biebie die, biebie, sumyn bash, Rafe'at, Ayshat Yabour, waleeda wazir, deeja wazir, beebah wadata, Nana fa'ad, miss Hafsy, miss feedy. Heart u guy, ❤Allah yasa ban manta kowa ba😒'''    πŸ“ *Episode* 51--55"Ke bakiga yadda nirrud'e ba jikina sai rawa yake, awa in saki hitsari cikin wando, da nigga nai".


" hhhh hhhhhh dama nasan haka za'ayi ainayi mamaki da nigga ya dawo daku daga asibiti, ahe dama likita na? Hi yassa ni matsu mu had'u in ha labari".


"Yo nima bansan likita na ba, na aza d'an sanda ahe likita na, keni koda munka shiga Yabo hankali na bai tare dani kwata-kwata bangane komai ba saida nigganai nittuna ai nan niya na munka ganehi ranar".


" toya kunka k'are miya hwada ma su Ardo?"

"Ke walle bansani ba danni gidan wata 'yar binni ya kaini nikkwana, Ashe sunada kirki kala biyu ta bani irin na binni, kuma tabbani abincinsu mai dad'i ke shima yanada kirki bakiga hidimadda yayima su Baffa b.........." Nan dai taci gaba da zuba kamar 'ya'yan kanya dan Laure badai surutu ba idan ta had'u da wadda ta saba, dan ma a gida batada abokin yine sai Ardo, ga tambaya amma ai dole fillo akwai tambaya. Lolz


Tun daga nesa ya tsinkayo su da tuluna akai, da alama firar da Suke tayi musu dad'i sai kwasar dariya Laure takeyi, rungume hannuwa yayi a k'irji ya jingina da motarsa sai faman kallonta yakeyi, Ashe tana fira haka? Ashe tana dariya haka? Yake tambayan Kansa.


Dan ba k'aramin kyau tayi mishi ba yadda take dariyar gwanin sha'awa komai tayi burgesa takeyi, komai nata unique ne (oh Dr ka fad'a da yawa fa).


Har sukazo suka wuceshi sam basu kula dashi ba, da yake suna right shikuma yana left.


"Hmmm ki bari Abukkiyata Jauro ya dameni ya hani jin dad'i kamar nid'ai a macce".


" ai bakiga komi ba kwana gudan da kikayi bakyanan baki ga zarya ba wai sai in hwada mishi ina kikaje wai yaje gidan ba kowa, seda niyyi ta yimai rantsuwa sannan ya yadda".


STORY CONTINUES BELOW

Ta bud'e baki zatayi magana kenan.... " 'yan fullo masu tulu aka" ya fad'a cikin daga murya saboda su jiyoshi ai kuwa sunji, k'irjinta ne ya harba, dan ta gane mai muryar tome yazoyi kuma? Ta tambayi Kanta.


Itakam Delu tuni ta jiya ganin mai kiransu tana ganin shine ta tab'o Laure datak'i juyowa "Laure mutumunki ne hwa".

Takowa yayi har inda Suke, cikin girmamawa suka gaidashi, tuni bakin surutu ya d'inke kamar ruwa ya cita " daga ina haka?" Delu ce ta ansa "daga rahi debo ruwa".


" Baba na nan?" Ya fad'a yana kallon Laure, data wani takure saboda bako hijab sai wani siririn mayafi, duk ta jita wani iri dan dama bata saba fita hakan ba, yauma bala'in Hari ne ya fitar da ita ba shiri.


"Um yana nan" ta ansa kai tsaye.


Kowama yayi gurin motarsa yayin da su kuma suka nufi gida, saida yaga sun bace ma ganinsa sannan yaja motarsa.

Yana zaune kamar kullum yana duba littafansa na addini, jin tsayuwar mota yasa ya d'ago, yayi mamakin ganinsa, amma bai nuna a fuska ba, da fara'a ya taresa, bayan sun gaisa, ya shiga ciki yasa. Aka kawo masa fura wacce taji damu da nono fara k'al, yasha sosai dan dama favorite d'insa ce.


Booth yaje ya fito da kayan fruits shake a Leda, sannan ya d'akko wannan ledar sak'on daya ansa gun Hakeem.


"Baba dama maganine na kawo maka wannan in heeler ce da kaji alaman asthma ka shaka ta baki ta saurin saukar da ita, wad'annan kuma magungunan hawan jini ne...." Nan dai yayi mishi bayani yadda zaiyi amfani dasu, godiya Sosai Ardo yayi tare da sanya masa Albarka, shidai yana ganin hankalin yaron sosai har yana raya Wani tunani a ransa game dashi.


Cikin firarsu ne yake cewa yanayin garin na matuk'ar burgeshi, zaiso yad'an zaga garin.


"To ai Bari in kira Ramlatuna ta d'an nuna maka gari, kafin magriba kad'an ga wasu guraren" zanso kuga zuciyar Abdool farincikin bai misaltuwa, dama haka yakeso.••••••••••••••••••••••••••••••••••••


A k'afa suka fito tana gaba yana biye da ita, suna tafe kamar gumaka ba mai cewa uffan, ja yayi ya tsaya yak'i tafiya, saida tayi d'an nisa taji alaman ba'a binda aiko tana juyowa ta gansa tsaye abinsa.


Dawowa tayi inda yake ba tare da tayi magana ba, ganin tsayuwar bamai k'arewa bace ga marece na k'ara yi yasa yace "a haka zaki nunan garin muna tafe kamar kurame? Idan ba zakiyi magana ba mu koma kawai" ya fad'a tare da had'a rai.


Rau-rau tayi da ido tare da turo baki "yo ai Kaina baka dariya, sai had'e huska, ni tsoronka nake".


Dariya sosai ta bashi yanayin yadda take maganar, aiko dariya yayi hadda tafa hannu, itakam tsuru tayi tana kallonsa, saida yayi mai isarsa sannan yace.


"Wama sunanki"?


" Laure" ta fad'a a tak'aice.


"Aa ba shine sunanki ba, ni bazan ringa kiran ki dashi Wanda Ardo ke kiranki dashi nike nufi".


Saida tayi murmushi dan ita Kanta tafison sunan " Ramlatuna " ta fad'a.


Shima murmushi yayi yace "yawwa shi amma Ramlah luv zan ringa kiranki kinaso ko?"


D'aga masa kai tayi dan ita batasan me luv din yake nufi ba "yawwa zamu zama abokai daga yau kin yarda?"


Namma kai ta d'aga mishi "daga yau mun zama friend zakina ringa bani labari?"


"Au wallah zan baka, badai kanaso ba?"


"Inaso sosai".

Haka suka tafi suna hira tana ta bashi labarai barkatai shidai biye mata kawai yakeyi duk inda sukaje tana masa bayanin gurin, aiko yasha labarai sai mamaki yake Ashe haka take da surutu, ada bayason mutum mai surutu shiyasa yake kwaban Nihal saboda itama akwai surutu, amma surutun Laure burgesa yayi duk da kuwa mafi yawa duk shirme ne sa soki burutsu.


Sai ana daf da magarib suka dawo ransa fal farinciki ji yake kamar kada su rabu, shikam Allah ya d'ora masa k'aunar Ramlah, anan yayi magrib tare da Ardo bayan sun dawo ya wuce, yana tafe yana tuk'i tunaninta kawai yakeyi yana murmushi a gaskiya dole ya sanya ranar yau a cikin tarihinsa dan babbace a gurin sa yayi enjoyed nata ba kad'an ba....

Sannu-sannu shak'uwa mai k'arfi ta shiga a tsakaninsu duk da har yanzu Ramlah batasan meye so ba, amma tanijin da Abdool a ranta. Duk k'arshen sati yake zuwa, suje su zaga gari daga nan su dire rafi, inda yake koya mata kara2, dayake tw bashi labarin tayi primary har 4 iya Hari ta fidda ita, zuwa yanzu ba abinda bai Sani ba game da ita da irin musgunawar da Iya Hari take mata, yanajin tausayinta sosai k'aramar yarinya da ita amma tasan wahalar rayuwa, duk abinnan da akeyi Jauro baida labari, saboda irin ranar bai  zama gari suna jeji gurin farauta (kome zai faru idan ya sani? Allah masani).


Iya Hari kuwa cewa tayi dama daga ganin wannan likitan dan iskane yana fama da gilashi awa dan daudu, yazo yaba malam kud'i ya saida mutunci jikarsa, sannan tace "yo dama ai zani ce ta cimma muje dama can tsohuwar sana'arta ce" duk ta yadda ta yadda ta debo musu ciki saidai suk'arasa ita da makwad'aicin kakanta.


Haka taita sakin magana ba dad'in ji, sudai kunnensu kawai suka dad'e, suka barta da Allahu.


B'angaren Zainab kuwa ta d'age da gayawa Allah buk'atarta ba dare, ba rana, shikam Abdool tausayi take nashi, dan yasan dafin so, shiyasa yake d'an sake mata fuska kota samu sassauci (Allah sarki Zee, ba komai kina tare da Allah.)...........

.πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„

[7/20, 9:59 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


😭😭 *kulli nafsin za'ik'atil maut(each and every soul should test d bitter of dead) may ur gentle soul rest in perfect peace, may jannatil firdous be ur final home sisto Hauwa'u (Aunty 'yar gande) may Allah bless ur children's, AmeenπŸ‘πŸ½*
+


       πŸ“ *Episode* 56--60

Kwatsam aka samu wani munafiki ya gayama Jauro, aiko kuzo kuga kunfar baki, kaman yayi hauka wai Laure da wani, gidansu yayi sa'a kuwa Ardo bayanan, nan ya hau Iya Hari da masefa ai duk laifinta ne da take bari tana fita amma zaiyi maganin ko wane shegen ne.


Bud'ar bakinta sai cewa tayi "Yo ai ba laihinshi naba, ita ka biye mai kuma ai da sanin malam shiya d'aure Musu gindi wainan gari taka nuna mai."


Cikin muryan 'yan tasha "wai wane d'an kazar uba ne?"

"Hehehe likitan Malam na, yana kawo musu mai dad'i da mask'i ai dole baki ya mutu(kamar bada ita ake ci ba).


" to nidai ko shi'a asibiti ba likita ba billahillazi ya kiyayi had'uwarmu, bamai kyauta ba aha" sannan ya fita yana huci kamar zaki.


Laure dake gefe tunda ya shigo gidan batace uffan ba, hasalima ko inda yake bata kalla ba saboda tsabar takaici, yanzu idan ba rashin tunani ba taya za'ace gardi kamar Jauro ya ringa shigowa mutane gida kamar gidansu, siririn tsaki taja, Wanda yayi dai-dai da maganar Iya Hari.


"To isasshiya, tsigaggga, sai kitahi ki bashi hak'uri, ke wani lahe kamar d'iyar arziki, shegiya me bak'ar aniya."


Itakam bataga dalilin bashi hak'uri ba, koda kuwa an bada ita gareshi balle ba'a bayar ba...."kin tashi kin tafi kosai nayi mid'imid'i dake anan niya" iya Hari ta katse mata tunani aiko tana shirin d'aukar muciya, aiko a guje tayi soro gidan ba shiri.


Yana tsaye yana jiran fitowarta, dama yasan zata fiton dole, had'e girar sama da k'asa tayi, murmushi yayi yace "haba gimbiyata mi'a na huskar shanu, sakin ran mana".


Harara ta balla mai " haba Jauro missa zaka yimin haka? kasan shi waye gareni?"


"To meye shidin bayan masoyinki".


Dariyar takaici tayi dama hakan ya zamo gaskiya da taji dad'i " haka ar tunanin ka dama? Mizaiyi dani 'yar k'auye? Kabar wanga tunani ma, iyaka dashi mutunci sai kara2 da yake koyamin".


Haka dai ya tafi bawai dan ya yarda ba, sai dai baison ranta ya b'aci, shiyasa ya yadda ya tafi, tare da shan zasu had'u wata rana.


**************************


Zaune Suke kamar kullum bakin rafi ga littafi da Biro gefensu dan yanzu har sun fara koyon, sai kuma k'awa'idi da ka'ida na musulunci, dan har nan Suke tab'awa, bayan ya gama koyamatasu, ta maimaita sannan yace.


"Gud gul, yanzu sai mu koma karatunmu na wancen satin ina fatar kin hadda CE".


"Eh mana, Bari ma kaji" ta fad'a tare da mik'a mishi littafin, tiryen-tiryen ta kawo su ba gyara.


Jinjina yayi mata da hannun tare da tafa mata, yana jinjina saurin ganewa irin nata, da an gayamata abu ta haddace irin su ne gifted by nature, amma anaso a kashe mata dama ga banza.


STORY CONTINUES BELOW

"Aboki my glass?"


Saida yayi dariya saboda sunan da take kiransa dashi "um Ramlah luv, ya akayi".


" kacce love na nuhin soyayya ko?"


Cikin mamaki yace "eh meya faru?"


"To naji kana kemin Ramlah luv, yana nufin Ramlah soyayya kenan, ma'anar sunana soyayya kenan?"


Saida yayi Jim yama rasa me zaice mata gashi ta kifeshi da ido "Aa nadai had'a sunan naki da Kalmar soyayya, kinga kenan ke soyayyar kowa ce saboda kinada ganewa sosai" ya k'arashe tare da yi mata alaman wasa, saboda ta shanshance da zancen.


Aiko dariya tahau nan sukaci gaba da karatunsu cikin nishadi(kara2 yafi jiga idan ana had'awa da wasa)lol.


"Kan ubancen yau za'ayi kazar uban nan niya" sukaji an fad'a daga sama, a tare suka juya dan ganin wane hatsabibin ne.


Kallon wannan fa Abdool ya bishi dashi, Jauro kuwa sandar da ke wuyansa ya d'aga da niyyan kai mishi bugu.


Da hannu d'aya Abdool ya rik'eta tamau yadda ko motsata Jauro bazai iya yi ba, yanzu kam da kallon kama renani yake binsa, Laure ce ta mik'e a fusace cikin fulatanci take magana.


"Haba Jauro Wanga wace irin haukata? Na hidi maka mia tsakanina dashi, wai shin imma masoyina ne, mi zakayi? Hala an baka nina?"


Ba tare daya bata ansa ba, ya dawo da kallon sa ga Abdool.


Cikin muryan 'yan tasha, yana juye baki yake magana "Hai kad'o ina gargad'inka, daga hita hanyar Laure, da duk Ahalin ard'o idan ba haka ba Hmmm".


"Kai kuma waye kai? Kuma meka isa kayimin" Abdool ya fad'a cikin gadara da binsa da kallon renin hankali.


"au bata hwadama ni'a wa ba, toni zan fad'a maka, nina mijinda zata Aura, nina uban d'iyanta, kuma kiyayi had'uwarmu ta gaba" yana gama fad'i yaja sandarsa ya kama gabansa.


Abdool dake tsaye kamar Wanda aka dasa, haka yaji zancen kamar saukar aradu, cikin jarumta da dakewa ya tattaro sauran k'arfin halinsa, ya maida kallonsa ga Laure dake tsaye tana hawaye.


Idan ka kallesa zaka tsinkayo kishi da bacin rai kwance a fuskarsa, amma da yake akwai k'arancin shekaru gareta bata fahimci komai ba.


"Abinda ya fad'a gaske ne?" Tayi ya tambayeta, girgiza kai tayi "ba haka bane hasalima dagashi sai Iya Hari suke zancen, Baffa baice komai ba...." Nan tayi mishi bayani sosai, ya d'an samu nutsuwa amma kuma jin hali irin na Jauro yasa hankalinsa yad'an tashi, dan yana tsaoron yaje yayi mata illah, amma tunda yana sonta yasan kila ba zaiyi mata komai ba.


Shikam ko batason Laure bazaiso a aura mata wannan shashashan ba, balle kuma son nata yake, ganin hankalinta bai kwanta yasa yace suje kawai an k'are kara2.


Sallama yayi Ard'o, bayan sun dan tattauna, sannan ya gaya mishi zaije gida Hutu, fatar Alkhairi yayi mishi "don Allah in kaje ka gaidasu sosai, inji ka gayama mutuniyar taka?"


"Aa Baba".


"Ato bari tazo kuyi sallama, Ramlatuna karatu zai tsaya kenan." Ya fad'a yana murmushi tare da shigewa ciki.


Da zabi da k'wayak'wayi ta fito wai inji Baffa "aboki mai glass hala ina zakana nijji Baffa yace wai ka kai Musu?".


"Gurin Mamana zanje Ramlah luv".


"La ina Maman taka take hala?"


"Can da nisa kinsan Kaduna?"


Girgiza kai tayi cikin mamaki "dama ba Yabo an garinku ba?"


"Eh".


"To nima zan biyoka inda mamar ka".


Smiling yayi " kina son zuwa inda Mamana?"


STORY CONTINUES BELOW

Da sauri ta girgiza mishi kai alaman eh.


"To inshaa Allah, zanje dake, idan zan koma kinji".


" Aa nidai katahi dani yanzu" ta fad'a cikin shagwaba.


"Oh friend yaushe kika iya rigima, kiyi hak'uri kinji zanje dake next time" haka ya lallab'ata har saida ta hak'uri sannan ya tafi, bye ta ringa yi mishi har saida ya bacema ganinta sannan ta share hawayen da suka zubo mata, tabbas zatayi missing d'insa.


Tafe yake yana tuk'i amma yana tuno maganganun Jauro, "Nina mijinta, nima uban d'iyanta".


Da k'arfi ya daki sitiyari  " no it can't happen ever".................
πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„

[7/22, 6:46 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


'''Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:-'''


_Hak'ik'a Allah mad'aukakin sarki baya duba zuwa ga suffofin jikinku ko dukiyoyinku, saidai yana duba zuwa ga zukatanku da ayukanku._

*kyawu da dukiya, ba zasu taba zama guarantee na shiga aljannah, gareni, gareki, garesu ba, tsarkakakkiyar zuciya da kyawun hali, shine kad'ai zai kwacemu a gun Allah ranar gobe k'iyama, nidake dasu mu guji rud'in da sharrin kyawun halitta dana dukiya, mu tsarkake zukatanmu, muyi k'ok'ari mu gyara tsakaninmu da mahaliccinmu domin goben mu, duniya labari ce, komin dad'ewa zamu barta, Allah yasa mudace da rahamarsaπŸ‘πŸ½*
 

    πŸ“ *Episode* 61--65


A yau ne su Zainab suka kammala attachment d'insu, k'warya-k'waryar walima mai gari yasa aka had'a musu tare da taimakon likitocin asibitin, sun yaba musu tare da jinjina musu akan k'ok'arin da sukayi, tare dayi musu fatar Alkhairi.


A tare suka wuce Sokoto da Abdool, dan shima ya d'auki Hutu gobe sai wuce Kaduna, bayan ya sauketa fitowa yayi ya fito mata da kayanta dake booth, ita kuma gida ta shiga ta kira gate man da driver domin su shigo mata da kayan ciki, ta samu har ya shiga motar yana shirin tafiya, gurin k'ofar ta sunkuya cikin marairaicewa.


"Sir pls ka tsaya Ku gaisa da Momyna har nayi mata magana".


" Oh! No Zainab ki bari next time...." Katsesa tayi.


"Pls Sir kai kayi alk'awari fa" ba yanda zaiyi, haka ya fito dole, a parlour Dadynta ta saukeshi, ga kayan motsa baki an shirya kamar hauka,  ciki ta shiga ta kira Mamanta, cikin girmamawa suka gaisa, yau dai taga Dr Abdulmajeed d'inda take shan labarinsa gurin Zainab, itama ta yaba sosai da yaron,  godiya tayi mai da irin kulawar da yake bawa 'yarta, tare dayi musu fatar Alkhairi, shikam kunya yaji kardai Maman tasan Zainab na sonsa.


Bayan fitar haka k'anninta sukayi ta zuwa suna suna gaishesa kudi ya basu shima dak'ar suka ansa sunayi masa godiya ya yaba da tarbiyar yaran "Sir kaci wani Abu mana" ruwa kawai yasa yace zai wuce, ba taso hakan ba amma ba yanda zatayi, dan ita idan son ranta ne, su tabbata haka har abada, har mota ta rakashi.


Wani ring ta Ciro a yatsarta ta bashi "wannan d'in na meye Zainab"?


Murmushi tayi tasan yasan tana sonsa, saidai koda sonsa zaiyi ajalinta ba zata tab'a fad'a masa ba " Sir ka rik'eshi a gunka, idan ka kalla ka tuna dani, pls Sir kada manta dani".


STORY CONTINUES BELOW

Sosai ta bashi tausayi, ansa yayi yasa a k'aramin yatsarsa, tare dayi mata murmushi "bazan tab'a mantaki ba Zainab ki saka wannan a ranki".


Taji dad'i har k'ashinta koda ba har ransa ya fad'i zancen ba, itakam ya faranta mata, shikam yayi hakane kawai dan ya kwantar mata da hankali.


Saida ta daina hango motarsa sannan ta juya gida cikin farinciki harda tsallenta na murna (hohoho! So manya).××××××××××××××××××××××


*Washe gari*


8:00am sukayi sallama da mutan Sokoto suka d'auki hanyar Kaduna garin gwanma, wannan k'aron Hakeem ne yaja motar sai sharara gudu yake, yayin da Abdool ya kebin k'ira'ar da ke tashi a cikin suratul Maryam, idonsa a lumshe.


12:00pm suka isa, gidansu Abdool suka sauka, sun samu Maamii ta tarbesu da tsararran girkinta ko office bata fita ba saboda d'okin dawowar Son d'inta ita Kanta tasan tayi missing d'insa sosai, su Abj ma sai murna dawowar Yaya Abdool Suke, suna nanik'e dashi suna mishi surutu, saida sukayi dam, sukayi fresh up, sannan Hakeem yayi musu sallama, da motar Abdool ya wuce gida, idan yaje ya dawo da ita.....


Hutun one month sukayi sannan sukayi shirin komawa, a wata d'ayan ba k'aramin dad'i hutun yayi ma Abdool ba duk kuwa da tunanin Ramlah na mak'ale a zuciyarsa, sukanyi waya da Zainab time to time, sai yaji inama da Ramlah ne, sai yanzu yakejin haushin rashin barma Ardo waya da baiyi ba, Aida sun rik'a gaisawa da sahibarsa.


Saura kwana uku su koma suna zaune da Maamii suna hira dan a duniya bashida abokiyar hira da shawara kamar ita, har suka gangaro kan hirar Ramlah.


"Yawwa maganar yarinyar nan da muka fara".


"To ai banji daga gareka bane Son, tunda ka dawo bakace komai ba".


Shafa Kansa yayi " Eh wlh Maamii kamar yadda na gayamiki, yarinyar na cikin k'unci, ba K'aramin wahala takesha gun Kakarta ba, gashi shi kakan nata bamai magana bane, wani abin tausayin ma very young inaga iyakarta in tayi Nihal" ya k'ara she cikin pity face.


Itama tausayi kwance a fuskarta tace "toya kake ganin zamu iya taimaka mata ne?"


"Eh ni a tunani na in nemi kakanta ya bani ita na kawo ta nan gurin ki, sai a sakata makaranta in fact dai ta dawo hannun mu sai dai takai musu ziyara amma me kika gani".


"Eh to Zamanta anan d'in ba matsala a ciki amma kana ganin iyayenta zasu baka ita haka nan daga had'uwar asibiti?"


D'an jim yayi shima dan gaskiya maganar abar dubawa ce "hakane Maamii amma zan gwada na gani idan zai yuyu".


"Ina ne garinsu naji kace ba anan Yabon bane?"


"Eh nan kusa dasu ne wani k'auye Kilgori".


"Kilgori" ta maimaita haka taji kamar ta tab'a jin sunan garin saidai ta manta ina taji, sharewa tayi nan dai sukaci gaba da tattaunawa akan lamarin..


Tsaraba sosai yayi mata na suturu dogayen riguna da d'inkuna hijabai hadda takalma da kayan rubuta da kara2 hadda Zainab saida yayi ma tsaraba dasu Ardo su Alhaji, kai har mutanen Argungu anyi ma, Maamii ma ta bada nata.


Ranar da suka dawo bayan ya huta ya bawa su alhaji tsarabarsu, a ranar ya wuce Yabo, zainab ma a tsaitsaye yaje, danko ciki bai shiga ba, mutan Yabo sunyi farincikin dawowar dan ba k'aramin k'ok'ari yake a asibitin ba, mutum zaizo bako asi ya dubasa kuma ya siyamai magani, shiyasa sukejin dad'in sa, suma Suke kawo masa kaya irin nasu na k'auye, nono, kwai, har kaji da zabi.


Da sassafe yaje kilgori, Laure tafi kowa murnar dawowarsa, sai murmushi take, ganin tayi ya kara kyau da gayu, hadda cewa "iyye d'an binni d'an gayu dai" dariya ma ta bashi cikin ranshi yace "Ramlah kuruciya ho".


Sunyi murna da godiya da tsarabar da yayi musu, yaji dad'in yadda suka yaba, bayan ya tafi Iya Hari, kwace kayan tayi ta cirema Lanti da Shatu kala d'aya 2 hadda hijab, wai ai wannan salon munafurci ne menayi mata kaya kaman ya ganta a tsumma, wannan kayan kamar na Aure, imma sonta yake yayi k'arya dan bazata bashi ba( ni kuma nace tunda ke zaki bada ita ba).


Laure kam a ranta tace mi hikai da 'yar k'auye duk matan bunni.


Cikin kala ukun da suka rage ta d'auki d'aya ta kaima aminiyarta Delu, sai murna take da sanya Albarka.


"Nidai Laure anya d'an bunnin nan ba sonki yake ba?"


Murmushi k'arfin hali tayi tace "banda ke da abinki Delu mi yakai Dani, ai wutsiyar Rak'umi, tayima k'asa nisa".


" Hmmm abokiyata ai ba daganan take".


"Kega bar wagga zance, d'auko wata" murmushi kawai tayi sannan suka canja hira.


B'angaren Jauro kuwa ya lashi takobin sai yaga baya ga Abdool muddin yaci gaba da shige  hanci...............


( _tofa gamu gani, wai ansa munafiki bikon aure_😏 )πŸ’„ Meryerm AbdoolπŸ’„

[7/23, 7:02 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


      πŸ“ *Episode* 66--70
*life goes on....*


Zuwa yanzu Laure, ta fahimci abubuwa da dama game da karatun da sukeyi, both Islam and western, har rubuta ta iya, bak'ak'e da wasulla tana banbance su, har hadda izo biyu tayi a gunsa, a tak'aice ba k'aramar rawa Abdool ya taka a gun Ramlah ba, wani sa'in har Delu yake had'awa idan taje gurinsu, dan yanzu anan inuwar gidansu suke zama, da yake Laure ta gayama Ardo abinda Jauro yayi, shiyasa yace su rik'a zama nan, dan yasan kad'an a cikin aikin mahaukacin ya kwaso shegu irinsa suje suyi mashi illah.+


Shikam Abdool baiso hakan ba, yaso su k'ara had'uwa da Jauro danya banbance masa aya da tsakuwa, a bangaren Jauro kuwa zuwanshi biyu bai samesu ba anan ba tare da rundunarsa kamar yadda Ardo ya tsammata, yana ganin basu nan yayi wani ihu irin na 'yan iska.


"Aradun Allah ya tsorata, saini Jauro mai sa maza su sheka da gudu, dan banza yana tsoron uwarshi ta haihi wani ba shiba" haka yayi ta cika baki 'yan korensa naci na k'ara fashe mishi kai.....


Yauma bayan sun gama kara2 zai wuce saiga Laure da leda waiya kaima Aunty Zainab, murmushi yayi tare da rik'e baki "ayya Ramlah luv baki d'oran aikin da yafi k'arfina ba yau kuwa?"


K'walalo ido waje tayi "Aboki mai glass kaima kana kyuya irin ta yara ashe?"


Dariya ta bashi yadda tayi maganar "Waya gayamiki kyuya ce, Zainab d'in ce batanan ai".


" to ina taje?"


"Tana Sokoto gidansu".


"Laa itama ba Yabo take ba kamar kaiya?"


"Um itama Bautar k'asa tazo anan kamar ni, kuma ta k'are nata tun tuni".


"Amma shina baka hwadamin ba, kuma in nicce INA gaisheta saika ke zataji" ta fad'a tana mishi kallon tuhuma.


"Oh my gosh! Mantawa nayi, amma fa ina gayamata gaisuwarki".


"A ina?"


"Ta waya mana, ko in kira maki itane?"


Washe baki tayi "eh inaso kirata".


Wayarsa ya Ciro ya danna mata Kira, ring 2 ta d'auka, bayan sun gaisa ya had'ata da Laure sannan yaje inda Ardo dake zaune yana kallon rigimarsu yana murmushi jin dad'i.


" Docta har zaka tahiya".


"Eh babba amma da magana nazo" gyara zama Ardo yayi dan yaji me yazo dashi "ince dai lahiya ko?"


"Eh lafiya lau dama akan maganar Ramlah ne nazo neman alfarma" nan dai Abdool ya kora mishi jawabinsa nason bashi ita ya tafi da ita idan ya tashi tafiya, dan duka 2week suka rage mishi.


Jim Ardo yayi yana nazari can yace "Bawai nak'i bana yaro, kuma ba ban amince maka naba, saidai hanzari ba gudu ba, kasan yanzu duniya mutum aka ciyyo ba dabba ba, kuma yana zama abin zagi gareni da ita Kanta Ramlah, kasan Abu ga k'aramin K'auye kowa da yadda zai hwassara zancen ga" tunda ya fara bayani Abdool ya k'asa kunne yana saurarensa, sai zufa ke keto mishi, yasan duk abinda ya fad'a gaskiya ne, to amma shi yanzu ya zaiyi da son Ramlah? Kar yaje yana can gida yana jiran ta girma yazo ya aureta yaji labarin an ba wani ita...Ardo ne ya katsesa "kayi shiru d'an ga da hwatar dai ba ranka ne ya b'aci ba".


STORY CONTINUES BELOW

Murmushin yak'e ya k'irk'iro "Aa Baba ko d'aya ai abinda ka fad'a gaskiya ne, amma kana ganin babu mafita?" danshi kanshi gabadaya ya k'ulle.


"Mahitar d'aya CE" bai San lokacin da yayi sanyayyen murmushi ba "Baba meye mafitar" cikin zakuwar son yaji.


"Aure! Idan har kana sonta ni zan baka Aurenta, saboda ka kwanta a raina" Ardo ya fad'i hakanne, saboda ya fahimci yana sonta.


Abdool kuwa k'irjinshi ne yayi mummunan fad'uwa, kamar saukar aradu yaji zancen, cikin rud'u ya kalli Ard'o duk da ba wacce yakeso kamarta, amma bai tab'a tunanin abin zai sama haka, shikam gani yake tayi k'ank'anta da Aure yanzu, bayan haka shi kanshi bai kawo yin Aurensa yanzu ba duk da yasan yana buk'atar auren.....baffa ne ya katsa masa tunani.


"Abdulmajeed kodai baka sonta na" karo na farko daya tab'a kiransa da sunansa.


"Aa Baba wlh ina sonta, Inadai ganin kamar tayi k'ank'anta da Aure ne" murmushi irin na manya Ardo yayi.


"Ina ai takai mataki, indai kana sonta kada kayi tunanin komi, katahi ka shawarci magabatanka, kace 'yan uwanka duk nan Suke ko?"


"Eh"


"To ka tahi kayi shawara dasu ba abin tashin hankali bana, sadaki kawai nika buk'ata ko nan da sati guda kazo a d'aura muku Aure".


"Inshaa Allah Baba, zanyi magana dasu zakaji yadda mukayi dasu" sannan yayi mishi Sallama.


Laure da batasan wace wainar ake toyawa ba, bayan sun gama waya da Zainab, ganin suna magana, yasa taja gefe kan dakali tana duba littafanta, wayarsa kadai ya ansa yayi mata sallama, ganin shi kamar baya cikin yanayin dad'i, yasa yaja jinin jikinta, ba surutu da salo yau, itama haka ta shige gida jiki a sabule....


Bayan gida kwantawa yayi kan kujera yana tunanin to ta inama zai fara? Daga k'arshe kawai yayi deciding d'in ya kira Maaminsa.


Bayan sun gaisa ya kora mata bayanin yadda sukayi da Ardo daga farko har k'arshe.


"Abdulmajeed" jin ta kira sunashi complete yasa k'irjinsa bugawa kaddai Maamii tace bata amince ba....katsesa tayi.


"Ka tabbatar kana sonta?"


"Eh Maamii" ya fad'a cikin sanyi.


"Hakan da wannan dattijon yayi shine dai2, kuma ya nuna yasan meyake yi, dan haka kaje ka samu kakanka kayi masa bayani, sannan ka Baba(cewa da babanta) nima inanan zuwa, kamar  yadda ya fad'a cikin sati d'ayan za'ayi komai inshaa".


"Tau Maamii zanyi kamar yadda kikace.....................
πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„

[7/27, 10:17 AM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*TUKUICI GAREKU SANYIN IDANIYATA*

πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

Abdulmajeed

Ramlah

Rufaida

Baffah

Kausar

Affan

Hanan

Abdallah

Aminah

Amerah

Salma

Salim

Nuseey

Twins

Zee

Amir

Al'ameen

Jidda

Khadija

Khairat

Fatima

Halifa

Mufeeda

Muzammil

Fidoo

Aysha

Muhammad

Ilham

_Hmmm kunada yawa nd rest_

❣may Allah bless be wit u always my kids😘
   πŸ“ *Episode* 71--75

Sauke numfashi yayi bayan sun k'are wayar da Mami, hankalinsa ya kwanta yanzu dan dama ita yakeji kada tak'i aminta, duk da yasan sauk'i irin nata, saidai yaga abin ne, a gaggauce yasan kuwa batason aikin gaggawa, shikam yayi mamakin saurin amintar ta.


STORY CONTINUES BELOW

"Yes! Any way I'm so much happy, zan auri love of my life" ya fad'a cikin farinciki, a ranar kwanan farinciki yayi, da sassafe ya d'auki excuse ya nufi Sokoto.


Alhaji Sada, yayi mamakin ganinsa saboda bai saba zuwa ba sai weekend, sanda ya kora masa bayanin abinda ke tafe dashi, yaji dad'i har cikin ransa, fuskarsa ta k'asa boyewa, kuma ya bashi goyon baya d'ari bisa d'ari, tare da tabbatar masa idan ya tashi komawa yazo ya d'aukesa suje tare a can k'auye.


Daga nan inda Hakeem ya wuce da yake ya gaya mishi zai shigo garin, saidai bai mishi bayanin komai ba.


Dariya sosai Hakeem yayi har saida Abdool ya nuna b'acin ransa sannan ya saurara.


"Aure fa kace dude! Kuma in a week, common kace u r joking, hw come wane irin aure kenan?"


Tab'e baki yayi "koma me zakace, I don't care, nidai nasan Aure zanyi kuma a satin nan, that all I know" ya fad'a tare da daga kafad'a.


"Tau naji Amma dai ba wancen yarinyar ba ko?"


"Ha'ah see u se trouble meye naka a ciki, ina nine me Aure ko, kai naka ido ne kawai, so put ur eyes and shout ur mouth".


Dafasa yayi saboda yaga da gaske ransa ya baci, " cool down! Nifa abin mamaki ne yake bani kawai, kuma naji kace yarinyar is too young" danshi bai tab'a ganinta ba.


"Hmm ai Kaine da abin haushi, na gayamaka dalilin auren nan, ba zuwa zamuyi mu zauna zaman Aure ba, ita Kanta nasan batasan ma me auren ke nufi, Hmmm kuma ai tayi k'ank'anta ba zata iya dani ba" ya fad'a ya shafo sajensa daya kwanta lup.


"Shegen kaya! Wlh bakaji Dr, kai killer ne in silent way, baki kawai na fika".


Smiling din gefen baki yayi "kaga ni ka tashi muje, time is going" tare suka fita gwanin Sha'awa, suka Lula zuwa Argungu.


A can d'imma ba'a samu matsala ba sunyi na'am da da abin da yazo dashi, Innah hadda tsokanarsa wai daga zuwa Har da yi mata kishiya, saboda yanzu ya daina yinta sai ta had'a shi da Ayatul kursiyyu yace ya fasa.


Dariya yayi yace kada ta damu zai bata eating noise, nan dai sukayi ta barkwancinsu sai marece suka koma Sokoto.


Washe gari sukaje Kilgori tare da Alhaji da Hakeem, Ardo ya tarbesu cikin karamci da mutuntawa kuma yaji dad'in ganin Alhajin hakan ya nuna yaron d'an gidan girma ne.


Amininsa Malam Garba kawai ya kira ya tabbatar da ya bawa Abdool, Ramlah ya dawo nan da sati d'aya a d'aura musu Aure, kuma baya buk'atar komai face sadaki.


Godiya sosai Alhaji yayi masa da wannan Karamcin da yayi musu, sannan yace yayi hak'uri amma zasuyi komai da akeyi a al'adance saboda itama a nuna mata 'yace kamar kowa, Ardo yaso su barshi kawai amma Alhaji ya nace shi zaiyi komai, dole ya Hak'ura amma da sharadin komai sai ranar Auren za'ayi, anan take suka bada kud'in nagani inaso dana gaisuwar iyaye, haka dai suka rabu cikin farinciki kowa na ganin karamcin d'an uwansa.


********************


"Ramlatuna!" D'agowa tayi ta kallesa k'irjinta na dukan Tara2 dan tunda Baffa ya kirata taji, gabanta na fad'uwa "na'am Baffa" ta ansa cikin siririyar murya.


"Ke yadda ina k'aunar ki?"

"Baffa ba Wanda yaka k'aunata duk duniya baya gareka".


Murmushin jindad'i yayi " yawwa Ramlatuna tunda harke yadda bani cuta miki, inason sanar dake inshaa Allahu, juma'a mai zuwa za'a d'aura miki Aure".


"Aure baffa!" Kalmar da ta fito bakinta kenan cikin firgici da zaro ido.


"Ko bakison Auren ne Ramlatuna?"


STORY CONTINUES BELOW

Girgiza tayi alaman aa dan ita bamasan maganan ta fito fili ba "Baffa nasan Bazaka cutar dani ba, Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi".


" Ameen Ramlatuna,  inshaa Allahu zakiyi hwarin ciki da wanga Aure, da yadda Allah k'arshe k'arshen wahalarki ya zaka, sannan kiyi shiru kakki hwadama kowa kinji?"


Kai ta daga masa "yawwa 'yar Albarka tashi ki tahi Allah yayi miki Albarka".


" Ameen " ta fad'a tare da fita jiki a darare ba k'wari...

B'angaren Mami ma sai shirin zuwa takeyi, tunda Abdool ya kira ya gayamata an tsaida magana sai shiri take sosai, amma sai ana gobe aure zata zo...


"Mutumina wai sai yaushe za'a buga I.V kaga fa lokaci sai k'urewa yakeyi".


"Kaidai ka cika neman rigima wlh, ai sai  kaje kaita bugawa" ya fad'a tare da juya masa baya.


Dariyar ciki yayi, "Yawwa wai ka gayama Zainab kuwa?"


"Oh! Allah wlh shaf na manta, abubuwa sun sakani a gaba" ya fad'a bayan ya tashi daga kwancen.


"Wo sabon Ango duk rud'un bikin ne".


" kaji dashi, magulmaci" yana gama fad'a ya bar parlour gaba daya, da murmushi ya bisa "wannan yarinyar ta rikita min Aboki da yawa".


Bedroom ya shiga tare da zanyo wayansa ya kira Zainab, yasan zataji ba dad'i amma gara taji a bakinsa da taji wani gun.


Bayan sun gaisa nan yake gayamata maganar Auren nasa, dif taji ta daina ji, wani k'olulun bakin ciki ne ya tokare mata mak'oshi cikin rawar murya tace.


" Allah ya sanya Alkhairi "ta fad'a kawai tare da kashe wayar gaba d'aya, dama yasan za'ayi haka amma toya zaiyi, gara ya gayamata gaskiya taji Haushinsa a lokacin zuwa gaba tasan bai yaudareta ba daya rufe dan tayi farinciki zuwa gaba ta gane yaudaranta yayi(komai zakayi da mutum ka tsaya akan gaskiyarka, dan k'arya fure take bata 'ya'ya, gaskiya kuma dokin k'arfe Allah yasa mudace).


Kuka takesonyi amma yak'i zuwa, lallai ta tabbatar Dr Majeed baya sonta, har iya fad'a mata, zaiyi Aure, shikenan ta yayi mata nisa, nisan da bazata iya cimmasa ba, juyi kawai takeyi duk duniya tayi mata zafi, lallai rashin masoyi bala'i ne.


Tana haka ne ilham k'anwarta ta shigo wai tayi mata assignment, hantararta tayi tare da cewa tafice ta bada guri, kota takata anan, aiko a guje ta fita tana kuka dan bata tab'a mata irin haka ba.


Ganin tana kuka ne yasa Momyn su ta tambayeta meya faru, ta gayamata Zainab ta korota.


"Zainab  kuma Ilham? Me kika mata" dan tasan yadda takeda sauki ga k'anninta.


"Banyi mata komai ba Momy, nadai ganeta kwance ranta a bace" mik'ewa kawai Momyn tayi zuwa d'akin Zainab.


Harta zauna daf da ita batasan tazo gurin ba, saida ta d'ora kanta kan cinyarta tana Shafa mata kai alaman rarrashi sannan tasan da zuwanta, fashewa tayi da kuka kamar ita take Jira "Momy na rasashi, shikenan na rasashi".


" Haba Zainab ki idan hankali ya gushe hankali ake sakawa ya nemosa, d'aure kiyimin bayani yadda zan fahimci abinda ke damunki" duk taji a jikinta bazai wuce Dr Majeed bane.


Saida ta gama kukanta, da sai yanzu yazo, uwar bata hanata ba sannan ta gayamata abinda ya faru.


Sosai ta tausayawa 'yar tata saboda tasan yadda takeson Abdool, sai dai bata nuna mata ba, saboda kada tasa ta k'ara karaya.


Cikin taushi da rarrashi ta shiga bata baki "kiyi hak'uri Zainab dama ita duniya haka take bafa komai da akeso ake samu ba a rayuwa, sannan duk abinda kikaga ya kub'ucewa mutum to dama ba'a k'addara zai samesa ba, kuma duk abinda ya samu mutum, dama ba'a k'addara zai kub'uce masa ba, dan haka ki kwantar da hankalinki idan da rabon Aure a tsakaninku sai kiga yazo har gida ya aureki, kedai ki dage da Addu'a da Neman zabin ubangiji".


Lafewa tayi jikin Momyn nata tana ajiyan Zuciya, sosai jawabin uwar tata ya ratsata tana k'ara godewa Allah daya azurtata da uwa ta gari mai maida ita kan seti idan ta juye(Allah ka k'ara ma iyayenmu baiwa da fasaha, ka k'ara muna k'aunar su da kyautata musu ameen, mungode da ni'imar iyaye na gari).


Saida ta tabbatar ta samu nutsuwa sannan ta fito ta barta.

Ana saura kwana biyu Aure Laure duk abin duniya ya mata yawa ita dai tasan bata murna da wannan aure haka kuma bata bak'in ciki dashi, ga rashin Aboki mai glass, tun ranar bai k'ara dawowa ba, dan ranar da sukaje bata nan.


Kilama Baffa cewa yayi kada ya k'ara dawowa saboda zaiyi mata Aure shiyasa ta ganshi wani iri a ranar, gashi za'ayi Aurenta ba tare dasun k'ara had'uwa ba, wata kila sai lahira ji kawai tayi tana hawaye, da sauri ta share kada wani ya ganta dan Iya Hari da Gwaggo Lanti, tsakar gidan, taci gaba sharan turken dabbobin da take yi.....


Iya Hari kuwa da basusan meke gudana ba sai nanayensu Suke ita 'yarta, Ardo ne ya shigo bayan sunyi mishi sannu da zuwa daga can zaune, k'arasawa yayi inda Suke hannu ya zura aljihu ya zaro kud'i ya bata.


Nan da nan ta Washe jajayen hak'oranta "Malam wanga kudd'i na minana?"


"Auren Ramlatuna, gobe idan Allah ya kaimu" ya fad'a mata kai tsaye.


Cikin zaro ido da masifa "Aure? Wa zata aura?"..................
_pls kuyi hak'uri da juna shiru da kukayi hakan ya farune akan rasuwar da akayi mana_ πŸ˜žπŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„

[7/29, 9:10 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


( We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readers)


❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

'''ina kuke masoyan Abdulmajeed, ga shafinku, ina matukar kaunarku a duk inda kuke Allah yabar kauna.'''

❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣


*Yan uwa masu yimin ta'aziyya, da masu yimin sannu da jiki, nagode sosai da kulawarku, Allah ya barmu tare nagode bunch of love#❣#*

+

  πŸ“ *Episode* 76--80

"Gara ma kace ba'a ta kakai, dan bai tab'a yuyu ayima Laure Aure gobe, ni kuma a hwadamin yau, sai kace ban da had'i da ita, kuma ai Laure da mijinta" shidai Ardo ido kawai ya zuba mata.


"Nasan ko Jauro dani yaka magana bada kai ba, ni nibbashi Laure ba kaiba, to k'ak'a akai mata Aure gobe ace sai yau zan sani, ai wanga maganar banza ta" duk cikin d'aga murya da masifa take magana, ganin ta dasa aya, murmushi yayi.


"Hmm khadijatul kubra kenan" ya kira Iya Hari da anihin sunanta "kamar yadda na fad'a gobe da izinin Allah za'a d'aura wannan Auren ba hwashi, danni adda ikon aurar da Ramlatu, maganar kin tsayar mata da miji ko minana ma, ke kissani kuma ke yashahwa, bakida hurumin tsayarwa da Ramlatu miji, wadda baki k'auna, taya za'ayi ki zabar mata miji na gari? Kina tunanin bansan komi da kukeyi ba, ina sane nadai tsaya naga iyakar gudun ruwanku ne, daga ke har ita lantana nasan baku k'aunar Ramlatu saboda hauka irin taku, kullum tunaninku yaya  zakuyi Ku ganta cikin k'unci shine tunaninku, toshi zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ko ana shawo to sai yayi" cikin kwanciyar hankali ya shiga zare musu magana kai ba kace cin mutunci yake musu ba.


Saida yayi musu tass sannan ya sarara musu, tsabar bak'inciki kamar zuciyar Iya Hari ta fito waye wannan shine ga duka ga tsinka jaka, magana ma kasa yi tayi, Lanti kuwa sai harara take aikawa Laure jira kawai take Ardo ya fita ta jibgeta, kamar ya sani yace.


"Ke Ramlatuna zonan" sannan ya fita aiko har tana had'awa da tuntube bisa da d'an gudunta, da harara su Iya suka rakasu "lallai Malam ni zaiyima cin mutunci akan wannan d'iya".


" Hmmm Inna bari ta dawo yau sai taci na jaki in yaso, gobe akaita gidan miji da kumburaren jiki, shegiya 'yar matsiyata" nan sukaci gaba da zaginta ita Ardo (ni kuma nace Allah ya Baku lafia, dan ciwonku saida Addu'a) lol.

"Ramlatuna naso ace na sadaki da dangin mahaifiyarki kahin in aurar dake, sai dai gashi Allah bai nuhwa ba, ina rokon Allah ya sadaki dasu ko nan gaba kema kiji dad'in dangin uwa Ramlatu" ya fad'a tausayinta cike da ransa, ba kad'an ba yake tausayawa Ramlah Sam batasan wani dad'i na uwa ko danginta ba.


"Ameen Baffa".


"Yawwa ungo wannan" biba bag ya mik'a mata.


"Kitahi gidan Gwaggonki Aisha,  keda abukkanki kinji a can zaku kwana kuyi abin da kukeyi irin naku na Mata" sunne Kanta tayi alaman kunya.


Murmushi yayi, sannan ya wuce yanajin farinciki a ransa, gidansu Delu taje nan Delu ke mata mitan rashin fad'a mata da wuri, hak'uri tare da fad'amata dalilin rashin fad'ar, haka suka biyama sauran k'awayenta sai gidan Shatu, d'aki d'aya ta ware musu da yake tasan da zuwansu.


******************

Bayan fitar Momy sosai nutsuwa ta zoma Zainab tashi tayi ta d'auro alwala tayi nafila tare da karanta Qur'anil Kareem, tuni taji zuciyarta wasai saidai abinda ba'a rasa ba.


STORY CONTINUES BELOW

Gift ta bawa k'annenka suka kaima Abdool, yaji dad'in sosai duk dan hadda na Ramlah a ciki, agogo ne nashi mai kyau na azurfa, Ramlah kuwa sarka ce da abin hannu masu kyau k'irar silver, tare da card na marriage wishes, tukuici ya basu k'annin nata cikin da farinciki.


"Allah sarki Zee" ya fad'a cikin slow voice.


Hakeem kuwa cewa yayi "lallai wannan ko'a mata ita ta daban ce, son gaskiya take maka( bawai nuna zafin kishi ke nuna soyayya ba, so na nufin kyautata da mutuntawa a kowane hali take note girls) lol.


"Hakane" ya fad'a a tak'aice saboda sanin halin Hakeem da jan abu yanzu suyita rigima.


Lumshe ido yayi yau tsawon sati biyu rabonsa da Ramlah yana missing d'inta sosai.........

*Washe gari....*

Tun 12 angwaye suka shirya tsaf cikin farin wanka daga sama har k'asa sak, iri daya komai nasu, su isma'il ma su had'e cikin nasu kalar gayun, Alhaji da kawu Sani(da yake shi kad'ai ne a gidan yanzu) kawai Suke jira su fito dan sunfi son da suyi juma'at a can da an sauko juma'a a d'aura auren kawai.


Alhaji ne ya fito cikin shirinsa tsaf hadda su rawani, haka suka d'auki mota biyu, duk maza ba mace ko d'aya dan koda Alhaji ya gayama Hajia Inna cikin rashin Kulawa tace Allah ya kyauta shikenan maganar, sam baiji dad'i ba, ko kad'an, fatar ganewa kawai yayi mata.


Ganin saukar baki a garin yabawa wadanda basu san me ake ciki ba mamaki ciki hadda Jauro wanda baisan wainar da ake toyawa ba.


B'angaren su Laure kuwa gyara Shatu irin nasu na k'auye dai ba laifi, baffa ma yayi mata nashi k'ok'arin dan tunda satin ya kama yake bata tsumi mai kyau kuwa irin na fulani ko yanzun ma ya aiko hadda kaza, suna cikin d'aki tayi shiru dan k'irjinta ne ya tsananta bugamata ba k'akk'autawa, su kuma su Delu sai tsokanarta suke wai ta gayamusu sunan mijin, shiru tayi dan ba ansa.


Sai Murmushin yake da take yi musu, haka dai sukaci gaba da gadarsu cikin nishadi da raha.


Gidan Ardo, kuwa iya Hari ganin har wayewar gari ba Laure, ga Ardo yaki bada damar ta tambayesa dan shima bata samu ganinsa ba, haka ta zauna zuru cikin rashin jin dad'i, can ga Lanti da kwailarta, nan take tambayarta Laure dan sai mangariba tabar gidan da alwashin dawowa yau ta cika burinta na jibgarta, nan uwar ke gayamata har yanzu bata dawo ba hatta Malam bata saka a ido ba tun jiya.


"Hmm Inna akwai abinda Baffa yaka shiryawa to missa ya boyeta?"


"Nima abinda nika son Sani kenan, gashi bansan yaya nikai da shedanin d'anga ba Jauro, kesan baida mutunci(ato k'aik'ayi koma kan maishi).


"Kyaleshi Inna bai isa yayi komi ba, ai yasan inda yaka haukatai...." Jin k'arar motoci ne ya saka su lekawa.


Ardo ne shima cikin shigar girma tare da Malam Garba suka tarbesu an gyara d'akin gaban gidan tsaf an shimfida tabarmi, komai tsaf, cikin farinciki suka tarbesu, su Isma'il sunyi mamakin k'auyen wai Abdool yaga matar Aure tab! Amma ba laifi sunada karamci.


Abinci na alfarma aka kawo musu daga gidan Malam Garba aka dafa ga fura da abin sha, komai dai mashaa Allah, nan aka gaggaisa ana jiran isowarsu Baba da Abdool yaje d'aukowa kamin lokacin d'aurin auren yayi.


Baba da kawu Mansur ne suka ya d'auko, suna isowa yayi dai2 da fitowar Ardo daga cikin zauran ido hudu sukayi da Baba.


"Malam Umar!" Cewar Baba, cikin tsananin mamaki daya bayyana a fuskarsa.


"Malam Abubakar!" Ardo ya fad'a shima cikin zaro ido........*to masu karatu munga alaman Sanayya amma a INA sukasan juna?*

*ya makata mu warwayi baya, dama hausawa sun ce waiwaye adon tafiya*

*muje zuwa wasa farin girki* ⛹🏾‍♀⛹🏾‍♀STORY CONTINUES BELOW

πŸ’„ Meryerm Abdool ce😘

[7/30, 8:07 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


(We don't just entertain and educate, we touch the heart❤ of the readersπŸ“).


_falyakul khairan auli yasmut_ 🀐

πŸ‘πŸ½ *Allahumma yashfikahπŸ‘πŸ½ wishing d most quickest and fastest jet recovery dear AbdoolπŸ’‹*
     πŸ“ *Episode* 81--85


     *ASALIN LABARI*


Malam Abubakar d'ane ga Malam Mudi Wanda sana'ace ta kawo garin Argungu, d'an asalin wani k'auye na Argungu mai suna, birnin lafiya, ganin ana samu a harkar ga yawon zuwa da dawo yasa ya gina gidansu k'arami ya tare da iyalansa, zuwansu ba dad'ewa ya saka Abubakar da kanwarsa, Hurera makarantar boko da Islamiyya a cewarsa zamanine gara a dama dasu, sannu a hankali sukaci gaba da gungurawa da raywarsu cikin rufin asirin Allah, a haka su Abubakar suka tasa, Abubakar ya tashi yaro Wanda yasan ciwon Kansa kullum burinsa bai wuce ya zaiyi ya tallafawa iyayensa ba, shiyasa kullum ya dawo makaranta to yana kasuwa inda mahaifinsa yana taimaka masa.


Ranar bak'in ciki garesa itace ranar da sak'on rasuwar ahalinsa ta iskosa a sanadin gobara data kama gidansu Wanda komai ba'a samu ya fita ba, da yake cikin dare abin ya faru lokaci yana poly birnin Kebbi, Abubakar yayi kuka yayi bakin ciki amma kuma ba yadda zaiyi dole ya hak'ura, bayan anyi sadaka, dangin mahaifinsa suka da tafi dashi, da yake itama innarsa marainiyace, dangin mahaifi kawai suka rage mishi.


Zaman k'auye ba dad'i koga Wanda ya saba balle wanda bai saba ba, amma ya zama dole haka Abubakar ya dawo d'an gona, kullum suna gona, amma da yake jarumine hakan bai wani damuwarsa ba, lokacin da Hutu ya k'are ya taso da maganar komawa, ina wuta in fad'a haka sukayo caa su basusan wannan zancen ba, saidai yabar karatu, shi kuma ya had'e kai da fata akan yanason karatunsa, ganin ya nace suka yadda ya koma amma da sharad'in sisin su ba zata shiga ciki ba, haka ya koma makaranta bako asi nasu.


Allah ya taimakeshi daf da faruwar wannan abun babanshi ya tura mishi kud'i masu dan dama saboda karatunsa dama kuma yana d'an bige bigensa, da haka ya samu ya biya kud'in makaranta, sannan ya sayi mashin ya fara achab'a, da haka yake biyan kud'in makarantar sa yake d'aukar kan shi haka dai da dad'i ba dad'i har ya kammala diploma, bai wangarta ba ya cika D'E form ya jona HND, yakanje gida ya gansu lokaci zuwa lokaci, su kuma sun zuba mishi ido cewarsu idan ya gaji da kanshi zai dawo.


B'angare gida kuma yana gyaran tsohon gidansu daya k'one, haka ya kammala karatunsa cikin nasara, zuwa lokacin yasan rayuwa dan ya ganta kala-kala saidai ya yadda ba maraya sai raggo, dan haka ya k'ara zage damtse da neman na Kansa, ana hakane Allah ya had'a shi da Habiba anan Argungu, k'anwar wani abokinsa ne, nutsuwarta da hankalinta ne yaja ra'ayinsa gareta, bawani sha wahala ba wajen amincewarta.


Bayan sun sasanta ne yaje gurin danginsa da maganar, bud'ar bakin su cewa sukayi yanada gurin ajeta baiyi mamakin jin haka daga garesu ba, in yayi la'akari da yanda suka danne mishi gadonsa ya lura da mutane su da Kansu kad'ai suka Sani, fatan shiriya yayi musu sannan ya gayamusu ya gyara tsohon gidansu.


Ba'a d'auki lokaci ba akayi aka gama aka dangana da Amarya Habiba gidan angonta, zama sukeyi gwanin sha'awa dan Habiba akwai hak'uri, ko sabani suka samu ko itace mai gaskiyar zata hau bashi hak'uri, shiyasa ba'ajin Kansu duk da Abubakar ya zamo mai zafin zuciya da kafewa akan abu daya.


Haihuwarsu ta farko Mahmud Wanda yaci sunan babansa yana d'an shekara biyu ya rasu daga nan kuma sai Ameena, Asma'u sai auta Mansur.


Suna cikin hakane Allah ya kaddari Abubakar da samun aiki, sunyi farinciki sosai da wannan ci gaban da suka samu, sun wadatu da komai na rayuwa dai2 k'arfi baifi jiki ba, cikin 'yan shekaru ya gina musu gida mai kyau irin dai na mai k'aramin k'arfi, haka yaransu suka tashi cikin tarbiya musulunci.


Amina da Asma'u ba wasu kyakyawa bane na gani kasheshi hasalima ba za'a sakasu cikin ajin farko irin dai bamu cikin 'yan tusa 'yan zawo sun tseremana saidai kam Allah ya azutartasu da diri mai matuk'ar d'aukar hankali Wanda ba namiji ba macce ta gani sai taji kishi. Lolx


Shiyasa kullum suna cikin hijab gudun yad'uwar fitina a al'umma, sannan Allah yayi musu baiwar sauti wato murya kenan, mai matuk'ar sanyi da d'aukar hankalin mai sauraro.


Lokacin su Ameena suna SS3 sun taho ten days d'in nan da ake bayarsa dayake boarding school Suke, Asma'u tana SS2 lokacin, da yammaci taje gidan wata k'awarta Firdausi anso wani Abu data manta a hannunta, bayan ta Amsa sun fito kenan zata wuce gida, a k'ofar gidan sukaga wata mayyar mota ta tsaya k'ofar gidan, wani had'adden guy ne ya fito ciki ba laifi yanada kyau dai2 shi, ga iya wanka, dan kam ya wanku ba k'arya.


Cikin farinciki Firdausi tace "Oyoyo Yaya Auwal kaine a garin yau" glass d'in idonsa ya gyara ma zama yana murmushi yace "Fido 'yar mama kece kika girma haka?".


Murmushi kawai tayi, ita kuma Amina gaidasu tayi tare da jan hannun Firdausi alaman su tafi.


Kallonta yayi Sam bai kula da ita ba wani shock yaji har cikin d'an yatsarsa, dakyar ya ansa da lafia, Firdausi CE tace " Yaya zan rakata na dawo, suka wuce.


Baima ji me take fad'a da kallo ya bisu har suka karya kwana, sannan yayi smiling tare da Shafa Kansa.


Anan Firdausi ta sameshi yanata Murmushi shi kad'ai "Aa Yaya meyasa baka shiga daga ciki bane".


" uhm Fido wannan k'awar taki fa"?


Murmushi tayi "Laa Yaya kaddai kasa..."


Katsaeta yayi "Nidai ina ne gidansu wlh tayimin".


" Aa Yaya daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i? Nidai mu shiga ciki ka huta zan yi maka bayanin komai " ta fad'a cikin zolaya dama taubashinta ne..................
_nayi muku typing mai yawa na taho zan tura ya goge😒 kuyi manage_ 😘

*muje zuwa 🀸🏻‍♀*[8/1, 8:03 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readersπŸ“)
         πŸ“ *Episode* 86--90


"Fido ina wasa dake ne wai? sai yawo da hankali kikemin, jiya dak'ar nayi bacci tunanin yarinyar ya Addabeni, sonta nike da gaske, pls joke a part ki gayamun mana" tunda ya fara magana Firdausi ta kwalalo ido tana kallonsa dan ita ta d'auka wasa yake amma yanzu kan tana gaskiya a cikin idonsa.+


Zama tayi bayan ta d'ora break d'inda ta kawo mishi kan center table "Ya Auwal Allah na d'auka da wasa kakeyi, amma kayi hak'uri, indai akan Ameena ne bakada matsala".


" Ameenah!" Ya maimata sunan cikin lumshe ido.


"Wow what nice name" dariya Firdausi tayi ganin yayan nata na shirin zarewa, "lallai ma Yaya abun naka azimun ne".


"Hmmm ba zaki gane bane, yanzu dai ya za'ayi nifa tayimin sosai ina ne gidansu".


" kwantar da hankali  yaya zanje nayi magana da ita nasan batada matsala, komai zaizo yadda kakeso".


"Yawwa Auntan Mama zaki kuwa samu tukuici mai tsoka" dariya tayi "yanzu dai kayi karinka anjima kad'an zakaji yadda mukayi" sannan ta fice.


Koda taje gidansu Ameena ta sameta tana taya Mamanta aiki, bayan ta gaida Maman, Ameena ta jata zuwa d'akin su.


"K'awata da sassafe haka, fatar dai lafia"?


Nisawa tayi " lafiyarce ta kawo haka...." Nan ta koro mata jawabin abinda ya kawota.


A firgice Ameena ta kalleta tana girgiza kai " Aa Fido bazan iya ba, pls ki bashi hak'uri kawai".


B'ata rai Firdausi tayi "kome yasa ko kinada Wanda kakeso ne daban?"


"Ba haka bane....." Katseta tayi.


"Nagane jini nane bakyaso wato, nina d'auka na wuce haka a gurinki Ameena, har ina bashi tabbacin samunki, ashe nice ke haukana, well thanks" tare da mik'ewa shaye da toka.


Riketa Ameena tayi "wlh ba haka bane Firdausi kuma bawai sonsa ne banayi ina tsoron Baba ne, baya barina tsayuwa da saurayi ban tab'a yi ba, amma kiyi hak'uri".


Komawa tayi ta Zauna "indan wannan ne, Baba ya hanaki kula samari saboda gudun b'ata gari da kuma karatunki, yanzu kuma meya rage mu k'are? Kad'an ne, sannan kada kiyi kwankwanto akan Yaya Auwal mutumin kirki kuma da gaske yazo gareki, amma idan kinji baki sonsa har ranki, to wannan daban ne, dan ba'a dole a soyayya" ta fad'a tana kallonta.


Ita kam tun jiya data ganshi taji ya kwanta mata a rai saidai a gaskiya tanason karatu, kuma muddin Baba ya gane tana soyayya tasan aure ne k'arshe maganar.


Tabota Firdausi tayi "bakice komai ba?"


"Fido in nace banason sa nayi k'arya, amma gaskiya karatu nakeso nayi" dariya Firdausi tayi.


"Lallai ma Meenal to aure na hana karatu ne ko karatu na hana aure?"


Lumshe ido tayi "ya danganta da kalar mijin da ka Aura".


" Hmmm Yaya Auwal baida matsala kamar yadda na fad'a miki, kedai in har kina sonsa ki amince kawai".


Ba yadda ta iya da rigimar Firdausi haka ta amince, tsallen murna kawai Firdausi keyi sunyi nasara, itadai Ameena sai dariya take mata, nan ta wuni gidan tare sukayi aikin rana sai bayan Azzahar ta wuce cike da farinciki dan zatafi kowa murna yayanta zai auri Aminiyarta.


STORY CONTINUES BELOW

Lokacin da taje masa da labarin amincewarta murna kamar ya taka kan jariri, amma ta bashi shawarar yaje gurin Babanta kai tsaye.


Lokacin da ya samu Malam Abubakar da zancen, yaji dad'in hakan domin ya nuna mishi yasan Kansa bai tari 'yarsa kai tsaye ba, yace yaje zaiyi bincike akansa idan ya gama zai nemesa, ansar number sa yayi tare dayi masa godiya.......


******************

*WAYE AUWAL*


Auwal Muhammad Sada shine cikakken sunansa d'ane ga Alhaji Sada canji, tsohon d'an kasuwa Wanda yayi suna a duniyar canji, mutum ne na mutane duk da tarin dukiyarsa hakan bai saka mishi girman kai ko d'agawa ba, kowa nasane, yanada matar aure d'aya Hajiya Kaltume, mace mai nuna isa da tak'ama wacce bata d'aukar raini komai k'ank'antarsa, ta tsani talaka kamar yadda ta tsani mutuwarta, ko a hanya bataso ta had'u dashi, Hajia Kaltume kenan manya masu duniya!.


Suna da 'ya'ya shida Ayuba, Auwal, Sani, Salisu, Rabi'u, sai Iggenta kuma Auta Maryam. Ya'yan sun tashi cikin kulawa, ba abinda suka nema suka rasa, a rayuwarsu sun tashi cikin tsananin gata amma hakan bai saka sun sangarce ba, sun tashi cikin cikakkiyar tarbiya ga girmama na gaba dasu, sunyi karatu a makaranta mai kyau, Ayuba da Auwal tuni sun kammala degree d'insu inda suka fad'a harkar kasuwanci kamar mahaifinsu, Sani da Salisu suna final year inda Rabi'u yake level 3, Maryam kusan sa'an Asma'u ce k'anwar Ameena, itace ta rage secondary a yanzu, Ayuba yayi aure ba da dad'ewa ba, inda ya Auri 'yar k'awar Hajia kaltume, Rafia Hajia taso Auwal ya Auri k'anwar Rafi'a wacce tunda ta ganshi ta mato akansa, amma yace bayaso, su Rafia suma sunada arziki sosai shiyasa Hajia ta yadda aka had'a auren, saidai kam ba tarbiya kota sisi, saidai gyaran Allah kawai.

( *To yanzu ga Awwalu ya d'auko magana wai yanason 'yar talakawa ya kuke gani friend?* ) πŸ€”Too busy🀦🏽‍♀ manage pls😘πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„

[8/2, 6:53 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€

πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬


✨ *Servant of Majesty* ✨


Na

πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„

© *Pure moment of life writers*

P.M.LπŸ’ͺ🏽


(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readersπŸ“)


*# ka zama mai ra'ayin kanka, bamai bin ra'ayin wasu, bazaka iya ma mutane ba, koda kuwa goyasu kake kullum kana zagaye gari dasu, tofa sai sunga laifinsa wataran, kaidai gyara tsakaninka da Allah domin gobenka#* nasiha ceπŸ‘ŒπŸ»

_#one love 😍 Abdulmajeed fans😍 ina yinku guys keep fallowing😘❣❤πŸ’˜#_

       πŸ“ *Episode* 91--95


Bincike sosai Baba yayi game da Auwal, sannan ya kirashi tare sukazo da Jafar yayan Firdausi gaidashi sukayi cikin girmamawa sannan suka zauna k'asa kan carpet,  ya sunkuyar da kanshi k'asa.


"Nayi binkice kamar yadda addini ya tanadar, na kuma gamsu da tarbiyarka, saidai hanzari ba gudu ba, Abu na gaba shine kaje ka nemi soyayyar ta idan ta aminta walillahil hamdu, idan bata amince ba ka hak'uri ba rabonka bace".


Tunda Baba ya fara magana, baice komai ba, saida ya gama, godiya sosai sukayi masa, sannan suka tafi cike da farinciki, Jafar sai zolayarsa yake.


Bai wani sha wahala gurin shawo Kanta ba, duk da ta tsaya jan aji irin namu na Mata, amma komai yazo da sauki tunda dama Firdausi ta share masa hanyar, anan tayi masa maganar son ci gaba da karatu ya tabbatar mata babu matsala zatayi sai Wanda ta zaba.


STORY CONTINUES BELOW

Saida Baba ya kirata ya tabbatar tayi na'am dashi sannan ya K'ara kiransu " to Alhamdulillah ta bani tabbacin ta aminta dakai, saidai ka sani ka fito gidan arziki duk da inada tabbacin bakwa cikin masu raina ma mai k'aramin k'arfi, amma duk da haka banason wulak'anci, ina nufin kada a walak'anrta min 'ya, ina so gami da k'aunar ta amma a hakan zan hak'ura na baka ita saboda ya zama dole tayi aure koba da kai dole zatayi dan shine kimarta, ban kaba ita dan abin hannunka ba aa na bakane saboda ka nuna kana k'aunarta kuma na yarda tarbiyarka, don  haka nake rokonka da kada kai ko danginka su ya walak'antamin 'ya idan naga da walak'anci to zan janye gaskiya" dago ido yayi yace.


"Inshaa Allah Baba hakan bazai faru da yardar Allah, zan kasance cikin masu rike amana".


"To shikenan sai kaje ka turo magabatan naka, Allah yayi muku albarka" da ameen suka ansa sannan suka tafi.


Dama jiran ansar Baba ya tsayar dashi, a ranar ya koma Sokoto dama a can Suke zaune.


A ranar ya Sanar da mahaifinsa yayi murna dad'in labarin dama sun k'agu ya kawo matar, bai tsaya wata ba ya kira mijin k'anwar tasa ( Dadyn su Firdausi) ya tabbatar mishi da yarinyar ta fito gidan tarbiya kuma itama mai tarbiyarce, dama abinda yakeso yaji kenan, anan ya tabbatar masa suna nan zuwa k'arshen sati saboda ayi komai cikin lokaci.


Lokacin da yajema Hajia kaltume da zancen tambaya ta farko datayi masa shine waye mahaifinta?


"Am Momy dama Babanta ba wani bane Headmaster ne a wata primary...."


"What!" Ta katsesa ba tare data barshi ya k'arasa ba.


Mik'ewa tayi tare da nunashi da yatsa "kai Auwalu idan ma barci kake toka farka, dama shiyasa kace bakason Ummita saboda saboda kanason had'ani da dangin tsiya ko? To wlh ahir d'inka badaini Hajia kaltume zaka had'a ma jini da matsiyata ba".


" Momy.... "Katsesa tayi


"Get out, banason jin komai daga bakinka" ta fad'a tana nuna mishi k'ofar fita.


Tashi yayi ya fice jiki b k'wari, dan yasan halin mahaifiyarsa tasa tsaf.


**************************


A satin Alhaji Sada da kannensa sukaje akayi komai na Al'ada aka tsaida rana, wata d'aya bayan sunyi graduation, haka suka watse cikin farinciki da ganin girman juna, dan anyi abinne na mutunci, lokacin su Ameena sun koma tuni.


B'angaren Hajia kaltume jin bata k'ara ji daga Auwal ba ta d'auka yabar maganar taci gaba da sha'aninta, aiko ranar da Alhaji ya gayamata sunje an tsaida rana, tub'ure masa tayi hauka zallah, saida yayi Mata Jan ido tare daci mata mutunci sannan yayi mata kashedi da kada ta yadda tayi abinda auren zai baci muddin tayi to a bakin Aurenta.


"Shima so kikeyi kiyi masa mugun zabin nan da kika yima Ayuba ko? To ban aminta ba tunda ya nuna Wanda yakeso, kuma bata wata matsala to banga dalilin hanashi ba, akan wani bazan dalilin ki Mara asali da tushe"  a babin dole ta hak'ura dan tanason aurenta, amma tace ba ruwanta da auren kuma ko sisinta bazai yi ciwon kai akan tsinannen aure ba.


Ba Wanda ta fad'ama maganar auren, ko 'yan uwanta ko, Rafia da taji batun Auren ba k'aramin tashin hankali shiga dan ita har ga Allah son Auwal take, dan batasan dashi ba sai bayan Aurenta da Ayuba, shiyasa take wani shige masa(wa'iyazu billah kina matar aure wani namiji na burgeki wannan wace irin rayuwa ce, Allah ya gyara).


Ga k'anwar ta Ummita datake mutuwar sonsa taso ya auri Ummita ko an ta d'anji sauk'i tunda ya auri jininta, nan take taji ta tsani wacce zai aura kuma tasha alwashin rabasu, musamman ma da taga Hajia itama batason Aure, Murmushin mugunta tayi(koma take sak'awa a ranta oho! Wai Ameena tun kan ki shiga kin fara samun mak'iya 😞 ).


Alhamdulillah su Ameena sunyi graduation successful, nan aka shiga hada-hadar biki ba'a kama hannun yaro, karma Firdausi taji amara k'irjin biki, itace amarya itace ango, a gefe d'aya kuwa Auwal da Ameena ji Suke kamar sun shekara goma tare saboda tsabar k'auna dake yawo a tsananin su.


Biki akayi mai k'ayatarwa inda kowane b'angare ya taka rawar gani, ba k'aramin k'ok'ari su Baba suka yi ba gurin gyara wa Ameena d'akin ta komai yaji dai2 dai k'arfi baifi jiki, sai fatan zaman lafia, haka aka gama lafia kowa na farinciki, inka d'ebe uwar ango data nuna k'iyayyarta baro-baro, danko dangin ta sai daga baya sukeji, kin gayyatar kowa tayi, duk Wanda ya kawo Kansa kuwa tas takeyi masa, tace munafukai ne.


A sabon gidansu da basu Dad'e da tarewa ba Wanda Alhaji Sada ya Gina, shida 'ya'yansa estate mai d'auke da apartment biyar, anan suka tare, akai amanar gurin surukarta, dutse idan yana magana tota tanka sai k'anwar ta ganin shirun yayi yawa tw ansa musu,haka suka dangana da ita sashinta cike da mamakin uwar mijinta, Allah ya kyauta sukace sannan suka k'ara yi mata nasiha,tare da fatar Alkhairi haka suka barta suka dawowarsu (aure kenan! Shakan yaro)


k'auna mai tsabta ma'auratan Suke gudanarwa, cikin tsantsar so da kulawa kowannesu tattalin d'an uwansa yake.


Duk safiya zataje ta gaida surukanta Alhaji har janta da hira yake dan yarinyar ta shiga ransa jinta yake kamar Maryam d'insa, sabanin Hajia da sai ta gaida ita kusan sau uku kafin ta ansa da lafia, ko inda take bata kallo, bare tayi tunanin tasan da ita haka take karake zaman ta dawo, bai hana gobe ta k'ara zuwa,  haka komai ta dafa zata aika Musu, ko kallon abinci batayi balle tasaran zataci saidai in mai aiki ta taho taci ko taba almajirai.


Sabanin waccen 'yar iskar da bata iya komai ba sai fitsara da kinibibi, ko ruwan zafi bata iya dafawa saidai tazo nan inda Hajia taci ko kuma Ayuba yayi musu take away, gaisuwa ko sai tayi Mata suger takeyi, Alhaji kam saidai in hanya ta had'a su yake samun gaisuwarta.


Auwal duk yana sane da wulak'ancin da Hajia kema matarsa, shima baida bakin hanawa saidai ya sakata d'aki ya bata hak'uri da lallashinta, "lah ba komai wlh ai iyayenmu ne dole mu bisu" kullum maganarta kenan, hakan ba k'aramin dad'i yake mishi ba, yaji sonta ya k'ara nunkuwa ransa.


Kamar yadda yayi mata alkawali har makaranta yaje da kanshi ya anso mata foam, ranar tayi tsallen murna burinta zai ciki, saidai kash!.


Labari na jema Hajia tace batasan zancen ba in Aure, aure in karatu, karatu ..........


_wayyo silly Ameena_ πŸ™†πŸΎπŸ€¦πŸ½‍♀

πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„
[8/3, 2:09 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬
πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€
πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„
© *Pure moment of life writers*
P.M.LπŸ’ͺ🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readersπŸ“)
*wata rana manzon Allah yace da Mu'azu bin jabli "ya Mu'azu shin bana baka labari akan, kan al'amari ba da kuma gimshik'insa da tsororuwar tozonsa?".*

Sai yace *" fad'a mini ya ma'aikin Allah".*

*"kan al'amari shine musulunci, gimshik'insa shine sallah, tsororuwar tozonsa shine jihadi, sannan ya k'ara cewa shin bazan gaya maka abinda ya mallaki dukkansu ba?*+

Sai yace *"sanar dani ya ma'aikin Allah"*

Sai ya kama harshensa sannan yace *"ka kiyaye wannan.*

Sai Mu'azu yace cikin mamaki *"ya ma'aikin Allah, dama ana kamamu da abinda muka fad'a?"*

Sai yace *"kaiconka ya Mu'azu, shin meyasa ake kifarda mutane da a cikin wuta da fuskokinsu ko da tsinin hancinsu sai face akan abin da harshensu yake girbarmusu.*

_Hadisul hasanu_

_to nidake dasu mu guyi fad'ar kowace kalar magana, musan mu muka fad'a, dan wallahi nidake dasu sai munyi bayanin kowace kalma bayan kalma gobe k'iyama ( Allah yasa mudace_ πŸ‘πŸ½

     πŸ“ *Episode* 96--100

Koda Auwal ya gayama Ameena abinda Hajia tace, abin ya Sosa ranta don Allah ya sani tanason karatu, kodon halin rayuwa, amma saboda ta kwantar masa da hankali ganin ya shiga rud'u, bata nuna komai a fuskarta tana murmushi tace "ba komai mijina, bin Umarnin Hajia dole ne, koda kuwa yaci karo da nasu ra'ayin, ina k'aunar ka dole na k'auna ci, abinda Hajia takeso, saboda haka karka damu nina hak'ura da karatun".

Tsabar farinciki rasa bakin magana yayi sai rungume ta yayi yana Sanya mata Albarka, tare dajin k'imarta da darajarta cikin ransa.

Lokacin Alhaji Sada yaji zancen da kanshi ya kira Ameena akan meyasa ta yadda da barin karatunta, kodai dole akayi mata? dan baisan Hajia ta hana ba, Auwal dai yace ta fasa ne,  " Ameena idan iyayenki sukaji ai ba zasuji dad'i ba".

"Baba aina gayamusu nice na fasa yi" duk da cikin ransa ya shakkar haka kawai kuwa, nan dai yayi mata nasiha kamar yadda ya saba tare da bata kud'i masu yawa akan ta fara Sana'a tunda batason karatu, godiya sosai tayi masa sannan ta wuce, girgiza kai yayi tare da cewa "Allah ya kyauta" dan yanaji duk inda aka zagayo aka dawo akwai sa hannun Hajia.

Ameena Nada wata 6 ta samu miscarriage, Wanda basu Masan da cikin ba, tsawon sati biyu tayi a asibiti, ba Wanda baije dubata ba, harda Rafia kusan kullum sai taje dayake ita 'yar duniyace bata nuna k'iyayarta a fili.

Hajia ce kawai bataje ba, saima cewa tayi ai gara da tsinannen cikin ya zube, kuma Allah yasa mahaifar ta lalace gaba d'aya, da dai a haifemata dangin tsiya, maganganu dai ba dad'in ji taita fad'a.

Ko bayan an sallamesu, saida Alhaji ya nuna b'acin ransa sannan taje ta dubata Wanda shine  zuwanta na farko sasan shima daga k'ofar parlour ta tsaya tayi sannu tana wannan cika da batsewa, tayi mamakin ganin yadda aka gyarama Ameena guri, sai tab'e baki tayi tace ai duk dukiyar d'anta ce, dansu basu da komai sai tsiya (oh talaka bawan Allah, komai saidai anyimishi kenan?, kai sharri kayan kwalbaπŸ˜”).

STORY CONTINUES BELOW

*************************

Sani da Salisu sun kammala karatunsu lafia, kuma sun fad'a kasuwanci kamar 'yan uwansu dama karatun anayi ne saboda zamani da k'arin experience akan business d'in, nan maganar Auren su ta tashi to anyi sa'a sun d'auko diyan masu dashi, nan fa Hajia akayi biki na kece raini, sai bak'ak'en maganganu ake yab'awa Ameena, bawar Allah yi takeyi kamar batasan da ita akeyi haka akayi biki aka k'are amare suka tare.

Haka dai akaci gaba da zama yayin da Ameena ke k'ara fuskartar cin fuska da walak'anci ga surukar tata saboda dai ta kasance 'yar talakawa, banbancin launin fata ake nuna mata sosai, sauk'in abin mijinta ta na k'aunar ta kuma suma matan saurin nata ba wacce ke nuna mata raini a gabanta sai dai ko bayan idonta, haka share tace ci gaba da kyautata mata, dai dai da rana d'aya bata taba gayama iyayenta ba.

Haka rayuwa taita shurawa kwanci tashi hasarai rai, duk surukan gidan kowa na d'auke da ciki inka debe Rafia wacce tace haihuwa ba yanzu, sai ta gama shanawa ba zata tsofe a banza ba amma da yake 'yarso CE shiru kakeji, Hajia ko tari (ooh da Ameena ce da anga yakin basasa...hhhhhh) lol
Ameena CE ta fara haihuwa, murna gurin Auwal kamar ya taka kan jariri ya zama Baba, haka ma Alhaji anyi jikan fari, kowa ya nuna farincikinsa nan da asibiti ta cika da 'yan uwa da Abokan arziki, hadda su Rafia anje na munafurci, saida aka tabbatar lafiyar uwar da d'anta sannan aka basu sallama, gida suka wuce dama k'anwar Mamanta tazo Asma'u k'anwar Ameena da yake sunyi Candy, hadda su Firdausi amarya an iso, haka suka dunguma suka wuce gida dan kankanta mata guri dan yau zasu wuce Argungu.

Hajia dak'ar taje shima ko d'an bata ansa ba daganan ta ganshi a hannun Asma'u wacce tunda yaron yazo duniya, taji k'aunar sa ta mamaye mata ilahirin zuciyarta, tanajin jinsa har ranta...

Ranar suna yaro yaci *Abdulmajeed* anyi shagali an kashe nera dan Auwal yayi rawar gani Alhaji ma yayi tashi yace jikan farine, Baba ma yayi nashi k'ok'arin, sai fatan Allah ya raya Abdool, su Firdausi da Asma'u uwar da sune k'irjin biki, Hajia kam ko kallo basu isheta ba dan da alama k'iyayyar uwar ta shafi d'an.

Auwal kuwa duk sati yana Argungu gurin d'ansa mai kama dashi fatar CE kawai baiyi hasken Baban ba, kuma yafi uwar haske yana nan dai tsakiya, Mama kuwa sai aikin gyaran 'yarta ta ciki da waje aiko tuni ta d'auki sheki tun balle bata kusa ga Hajia.

Abdool kuwa kullum yana hannun Asma'u, shan nono kad'ai ke had'ashi da uwarsa, tsabar sonda Asma'u ke mishi ko cikin barci taji kukansa saita farka, Mama tace lallai kuwa ranar da suka koma zai barki da kewa.

Auwal da kanshi ya roki Baba su basu Asma'u, ganin yadda ta shaku da Abdool, kuma tunda tace karatu zatayi, dan tunda taji abinda ya faru da yayarta(ta gayamata abinda ya faru, dan itace abokiyar shawarar ta)tace Aure ba yanzu ba, duk Wanda yazo hak'uri kawai take bashi.

Dak'ar suka shawo kan Baba ya amince, Auwal ya samo musu admission a *Usmanu danfodiyo* ita da Maryam k'anwarsa, Hajia nan habaici ya tashi hadda fad'in saboda an samu banza shine hadda kwaso k'anwa, anga dukiya shine akazo a dangwala, cin fuska dai zalla abinda Ameena ta guda kenan.
[8/6, 8:09 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬
πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€
πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„
© *Pure moment of life writers*
P.M.LπŸ’ͺ🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readersπŸ“)

_πŸ’˜πŸ’˜ where r u my  berries😘 Fatima Bello(momy shatima), Shamsiya Isma'il(fresh daughter) Aisha wanzams (my kanwa) I heart u guys 😘 *#1love#*_

STORY CONTINUES BELOW

 

    πŸ“ *Episode* 101--105Saida tayi mai isarta ta godewa Allah, dak'yar ta mik'e idonta sunyi jajir tare da kumbura, sai Kanta dake matsanancin sarawa tsabar kukan da tasha, Abdool ta d'auka wanda shima sai kuka yakeyi ganin mamarsa nayi, dabin bango ta shiga part d'inta, saboda jirinda ke d'ibarta, a parlour ta zube zuciyarta kamar an d'ora mata dutsi dak'yar ta jawo wayarta ta kira Asma'u akan tazo gida, rud'ewa Asma'u tayi jin murya yayarta wata iri tasan ba lafia, kafin tace komai harta tsinke wayar, aiko kota kan Maryam bata bi ba tayi bakin titi tare da taron taxi.

Auwal kuwa yana shiga part d'insa ji yayi duniyar gaba daya tayi mishi zafi, ga rad'ad'in da zuciyarsa ke masa, ga kukan Ameena da Abdool da yake jiyowa yana tab'a masa zuciya, duk da cewa ita mai laifi ce a gareshi amma zuciyarsa ta k'asa yadda da bak'on al'amarin da ya same shi na rabuwa da Ameena, key kawai ya d'auka yabi ta k'ofar baya, normally kowa nada k'ofar baya wacce zai fita ba tare da sanin wani, motar shi ya d'auka ya fita gidan a tsiyace, tafiya kawai yake shi kanshi baisan inda ya dosa ba.

Ganin yanayin da ta isko yayarta ciki ga Abdool sai ihu yake amma uwar ko kallonsa ta k'asa yi balle tayi tunanin shayar da shi, Abdool ta d'auka, abinci ta had'a mishi saida ta tabbatar ya k'oshi sannan ta goyashi ba dad'ewa bacci yayi gaba dashi sai ajiyar zuciya yace, gurin yayarta ta matsa wanda itama jikinta a sanyaye yake, dafata tayi, nan ta d'ago ta kalleta da rinannun idanunta, "Aunty komai yayi tsanani maganin shi Allah, ki d'aure ki gayamin meke faruwa?"

Kama hannayenta duka biyu tayi, bakinta na rawa, sai a lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo mata, sharewa tayi, nan ta labartawa k'anwarta duk abinda ya faru bayan wucewar ta makaranta.

"Inalillahi wa'inna ilaihirraji'un" shine kalmar da Asma'u tace maimata tawa iya tashin hankali kenan, yanzu ta fita tabar mata da mijinta lafia, amma kuma cikin k'ank'anin lokaci komai ya canja, farinciki ya koma bak'in ciki, batasan lokacin da hawaye suga zubo mata ba, nanta rungume yayarta sukaci gaba da kuka bamai lallashin wani.

Bankad'o k'ofa akayi da k'arfi, a tare suka d'ago dan ganin wanene, da kallon k'ask'anci ta bisu, ba kowa bace face Hajia "to matsiyata 'yan gadon lalata(sadnaf), me kuke jira yanzu kuma?, ina auren ya k'are ko kuma da sauran zance ne iyye" duk cikin masifa tace maganar.

Saida ta saka full stop sannan Asma'u tace "yi hak'uri Hajia yanzu zamu tafi" tsaki tayi tare da cewa "aikin banza sannan ta fice.

B'angaren Rafia kuwa suna isa part d'in Hajia bayan tayi Jim na mintuna tace "Hajia Bari in tafi zanyi wani aiki" part d'inta ta shiga, wannan gardin ne zaune a kureja amma ya maida kayanshi, wata shu'umar dariya tayi sannan ta d'aga mai babban farcenta "weldone Wizzy aikin ka ya tafi yadda akeso" murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba, bedroom ta shiga sai gata ta fito da rafar 'yan duba, bashi tayi tare da bud'emai k'ofar baya ya ware.

Asma'u ce ta d'ibo musu kayan sawarsu trolley biyu, drop suka d'auka sai k'ofar gida.

************************

Lokacin suka isa dak'ar suka shiga ciki, Mama na tsakar gida tana aiki, Mansur kuma na gyara mata alayyahu, ganin da kaya nik'i-nik'i sannan fuskacinsu a jeme duk sun wani yamutse, yasa tasan ba lafia ba, gaisa sukayi sannan suka shiga ciki, itama wanke hannu tayi tabi bayansu, ba wani boye-boye Asma'u ta gayamata abinda ya faru.

Ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, amma saita daure tace "Allah yasan hakan shi yafi zama mafi Alkhairi" dama tunda k'anwarta ta gayamata halin Hajia da irin wulak'anci da tayi musu, yasa ko sha'awa zuwa gidan bata tab'a yi ba, amma wannan sharrin dame yayi Kama, idan so take a saketa basai ta had'a da sharri ba, dan ta yarda da tarbiyar 'yarta ba zata taba aikata hakan ba koda bada Aure ba balle da Aurenta, Allah ya saka Mata, shine kawai ta fad'a a ranta.

Baba ma daya dawo yaji ba ransa ne yayi mummunan b'aci, musamman sharrin da akayi mata, dama Baba akwai zafi, abin ya bala'in k'ona ransa, fad'a yayi tayi da cewa zaije Sokoto gobe, saida Mama ta tausheshi sannan ya hak'ura, dan tasan idan yaje da wuya ayi mai kyau, amma yace gobe su Hafsat da Usman(k'anwar Mama da d'an kanin babansa) suje su kwaso kaya sannan su anso masa
takardar 'yarsa.

Auwal kuwa bayan gari yaje bakin ruwa,  a can yayi zamansa dan gari ya riga yayi mishi zafi, nan yayi ta sak'awa da warwarewa har dare bai samo mafita, ganin duhu ya shigo, yasa shi hak'ura ya koma gida.

Hajia kuma ganin har dare ba Auwal ba labarin sa gashi ta kira wayoyinsa a kashe yasa hankalinta tashi, bakin k'ofar part d'insa ta tsaya zaman jiran dawowar sa.

Dai2 part d'insa yaga Hajia, jiki sukwana ya k'arasa gurinta tare da gaida ita, bata ansa sai fad'a data haushi dashi "wai kai Auwalu wane iri yaro kake, kabi ka tada hankalinka akan yarinyar da ta gama cutar da kai, gara ka fiddata a ranka dan kun rigada kun rabu kenan ehe, to garama tun wuri ka yakiceta a ranka ka rungume Ummita dan har nayi magana da hajiyarta nan ba dad'ewa za'ayi bikinku, sannan ka rubuta takardar waccen matsiyaciyar ka kawo min, zan aika mata har gida" Auwal da zuciyarsa ta gama k'ek'ashewa "tau Momy" kawai yace, sannan ya shiga ciki, itama ficewa tayi tana fad'in "daga Allah ya tona mana 'yar iska" tana shiga part d'inta nan ma Maryam ta isko ta had'a kai da guiwa, dan tunda ta dawo Hajia ta fad'a mata abinda ya faru, ta shiga damuwa hadda kukanta dan ta saba da Aunty da Asma'u ga Abdool Son d'inta, ita sam bata yadda aunty zata aikata abinda akace tayi ba, dan tasan ta farin Sani kullum cikin yi musu nasiha take itada akan su tsare mutuncinsu sannan ace ta aikata wannan barnar.

Tsaki Hajia tayi "kwayi kwa gama" sannan ta shige ciki tana mitar halin irin na 'ya'yanta Sam basu biyota ba(ai sun huta basuyi bak'in gado ba) waya ta kira hajia Umma mamarsu Rafia danso take ayi komai cikin lokaci, saboda ta k'ara cusawa Ameena bak'in ciki.

Auwal na shiga ciki jin ba motsin wata halitta ko'ina shiru, sabanin da, koda zai shigo a parlour zai samesu suna kallon sunnah TV wata ran kuwa su kalli zee TV ko kuma su zauna suna hirarsu gwanin sha'awa, Murmushin takaici yayi tare da shigewa ciki, takardar ya rubuta kamar yadda ta buk'ata yakai mata.

Washe gari kamar yadda Abba ya buk'ata haka su Hafsat da Usman Suka taho da babbar motar kwasar kaya, amma me Hajia tace ba wani kaya da zasu kwasa ai danta ne ya saya, haka aka shiga rigima sun nace sai kwasa itama tace basu isa ba, hayaniyar ce ta kawo hankalin mutanen gidan wad'anda duk abinda ya faru basuma San anyi ba sai lokacin.

Ganin rigimar tak'i k'are wa yasa Sani kiran Auwal ya tambayesa nan ya tabbatar kayanta ne ko tsinke bai siya mata ba, da yake a hand's free ya saka kowa yanaji yasa ta basu suka kwasa, tana biyarsu da habaici da bak'ak'en maganganu, ba Wanda ya kulata har suka k'are tun kafin su tambayi takardar 'yarsu ta kawo musu, tare cin mutunci.

Auwal da tun safe ya fita zuwa yayi ya tattara duk wata k'addara tasa ya sayar, banki yaje ya bud'e kid account ya zuba kudin, iya wad'anda zai rike a hannun sa ya rage, bashi ya dawo ba sai goman dare, d'akin sa ya shiga yayi wanka ya kimtsa sannan ya d'auka diary sabo kal, rubuta sosai yayi sannan ya sake rubuta wasik'u har uku, part d'in Hajia yaje yace Maryam ta d'auko mishi key din part d'in Alhaji dan duk wannan ruguntsumin da ake Alhaji bayanan ya tafi umrah, d'auko mishi tayi bud'ewa yayi sannan ya shiga bedroom, wardrobe d'insa ya bud'e wata leda ya saka daga can sama sannan ya rufe ya fito, Maryam ya kira ya bata keys d'in da wasik'a tare da tabbatar mata da ta bawa Hajia zuwa gobe da tau ta ansa masa sannan ta shige ciki.

Washe gari bayan sun gama breakfast ta d'auko wasik'ar ta bama Hajia.

"Lahaula walah k'uwwati illah billah" shine Kalmar da Hajia ta fad'i tare da zubewa k'asa a sume........

_friends ina barar Addu'arku akan wata buk'ata tawa, ina da tabbacin zan samu. Love u all_ 😍

πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„

πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„
[8/6, 8:15 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬
πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€
πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„
© *Pure moment of life writers*
P.M.LπŸ’ͺ🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readersπŸ“)

'''Wannan page d'in nakune 'yan makarantar madarasatul nurul Islam littahafizil Qur'ani
Kareem,kabino area,Argungu'''πŸ•Œ+

_Irinsu Nafisa muh'd, Fareeda Nana b/mashaya, Mamu Aliyu, Saudat yahya, Meena dikko, Amina Garba, Bilkis, Hajjo, Aina'u Idris and rest kuna raina koda yaushe#❤❤❤#_   πŸ“ *Episode* 106-110


Maryam wacce tana mik'awa Hajia sak'on Auwal ta shige bedroom room d'inta, sai jin k'aran fad'uwar abu tayi aiko da gudu ta fito ganin mahaifiyarta kwance ba numfashi yasa tayi Kanta cikin kid'ima tana jijjigata, amma ko alaman tashi batayi ba, aiko da gudu tayi part d'in Rafia tayi sa'a Ayuba nanan, jin abin ya faru yasa suka biyota cikin tashin hankali, Rafia ce tayi Kanta ta rungume ta yayin Auwal yace a kawo ruwa, da sauri Maryam ta kawo ruwa Shafa mata akayi, nan take ta sauke ajiyar zuciya, bud'e ido tayi a hankali ta sauke a kansu sannan ta maida kallonta ga takardar da ke jinke a hannunta, wani kuka ta rushe dashi "why Auwal, meyasa zakayimin haka".

Ayuba ne yayi k'arfin halin cewa " Momy me kuma Auwal yayi miki?" Takardar ta mik'a masa, ansa yayi tare da karantawa a fili.

_"kiyi hak'uri momynah nasan koda wasik'ata zata sameki ba zakiyi farinciki da ita ba, sai ba yadda zanyi dole ce tasa zan barku, bazan iya ci gaba da zama kusa da inda zanji labarin Ameena ba, alhalin bama tare, dole zan nisanta kaina daku da kowa nawa, kada  ku wahalda kanku nemana danni kaina bansan inda na dosa ba, pls kiyafemin Momy kiyimin fatan Alkhairi, kada ki tsinemin, idan kikayi haka rayuwa zata ga garari, ma'assalam_

D'anki *Auwal Sada*

Koda ya gama karantawa zuface ke keto masa duk da fanka da na'oural sanyi dake aiki, yama kasa magana, Maryam tuni hawaye ya wanke mata fuskarta, Rafia ma tashin hankali taf fuskarta dan batasan haka abin zai zama ba.

Momy kuwa sai sambatu takeyi tana kiran Auwal dan Momy akwai son d'iya, hakan yasa wutar k'iyayyar Ameena da d'anta ta k'ara ruruwa a ranta dan duka ita d'orama laifi, wai ba a banza tabar Auwal ba, wannan son ya wuce hankali, tunda harya kasa ganin girman laifinta ya barsu saboda ita.

Nan dai suka wuni cikin jimami ga tsoro fal ranta na idan Alhaji ya dawo me zatace masa, gashi gobe Suke tsumayen dawowar sa, dak'yar ta kira Maman su Rafia ta gayamata abinda ya faru, Ummita kuwa da raji rud'ewa tayi, dan ita harta fara shirye,-shiryen Amarcewa(tab to ai sai aje a rungumi big sowie Ummita) lol.

****************************

*Washe gari*
*12:00pm.........*

Jirginsu Alhaji Sada ya sauk'a a Sakkwato birnin shehu, Sani, Hajia, Maryam ne sukaje tarbonsa, yayi farincikin ganinsu amma yafi k'osawa yaje yaga 'yan jikokinsa musamman Abdool dan yaron ya shege masa ransa, sonsa yake sosai bada wasa ba, saidai baya nunawa gudun tashin hankali, sanda suka isa kowa saida yazo gaidashi amma ba Auwal da familyn sa, k'asa daurewa yayi ya tambaya ko sunyi tafiya ne.

Ganin yayi kowa yayi shiru, hakan yasa jikinsa yin sanyi dan yafi ba, lafiya a jikinsa, Hajia ce tayi k'arfin halin cewa "Alhaji ka bari kaci abinci ka huta tukunna sai ayi maka bayanin komai" jiki a sanyaye tayi maganar.

STORY CONTINUES BELOW

Ba shida zabi hakan akayi bayan yaci ya huta haka ta kora masa bayanin komai daya faru, har zuwa tafiyar Auwal, shiru yayi nad'an lokaci kafin ya dago idonsa da suka rine sukayi ja ya nuna Hajia da yatsa.

"Ke bani mamaki kaltume duk da babu mamaki in ankai la'akari da rashin son da kike nunama Ameena, tau burinki ya cika Ameena tabar miki gida Auwal ma ya bita yanzu sai kije ki zauna da wad'anda kikeso" ta bud'e baki zatayi magana, ya dakatar da ita "bannson jin komai daga gareki tashi ki tafi" ya fad'a yana nuna mata k'ofa dama daga ita sai shine a d'akin, tashi tayi ta fice jiki ba k'wari, dan tasan hak'uri irin na Alhaji duk yakai gayin fad'a to an kureshi ne, amma ai bai kamata yaga laifinta ba, komai ya faru au Ameena ce sila, itakam wannan shine adakeka a hanaka kuka.

Alhaji sai safa da marwa yakeyi ransa a jagule, tabbas Auwal bai kyauta ba, koma meye ya faru bai kamata yabar gida, duk da iya cuta an Riga an cucesa, dan wannan dagaji sharri ne akayi mata, dan yasan Ameena ba zata tab'a aikata wannan danyen aikin ba, kuma yasan Hajia nada tsananin zafi da ak'ida Mara tushe da asali, amma yasan ba zata aikatawa Ameena wannan aikin ba, to abin tambaya anan waye ya aikata? Babu ansa "Allah ya sawwaka" ya fad'a a fili, dama iya zaman da Allah ya d'ibar musu kenan, koda wannan koba sa wannan ba tabbas sai sun rabu dai2 wannan lokacin

Bud'e wardrobe yayi dan d'aukar Abu kawai sai Leda ta
Fad'o takardune na bud'e account da komai daya k'unsa sai diary da wasik'u guda biyu, bud'e d'ayar yayi yaga ansa *zuwa ga Ameena* rufewa yayi ya bud'e d'ayar Wanda ta kasance tashi ce.

Shima dai ban hak'urin ne da Neman gafara, sai Amanar *Abdulmajeed* daya d'anka masa da kuma bayanin diary da information na Account ya aje hannunsa har sai Abdool ya mallaki hankalinsa ya mallaka masa, sai wasik'a da yake rokon ya bayar a kaiwa Ameena, bayan ya gama karantawa yace "na yafeka Auwal duk da baka kyauta min a matsayina na mahaifi ba, wannan dalilin bai isa yada ka tafi ba, amma ba komai Allah ya tsareka a duk inda kaje ya kuma dawo mana dakai lafia wuri kusa kazo ka kula da d'anka da kanka".......

B'angaren Ameena kuwa kokai waye idan ka ganta dole ka tausaya mata, ta fita hayyacinta gaba d'aya tayi bak'i ta rame sosai kullum cikin kuka take musamman ganin an kwaso kayanta, yanzu shikenan ta zama bazawara, abin tafi tsana a rayuwarta ada sai takega duk matar da ta zama bazawara a dalilin saki to laifinta ne, ita tayi abinda yasa aka saketa, amma a yanzu ta gane ba haka abin yake k'addara wacce bata wuce fata, ta gane Ashe ba matar da ke son a saketa koda kuwa ita tayi laifi, balle irin su da basuji basu gani(to in banda Ameena wake so yayi aure yau gobe ace ya dawo gidansu ai saida k'addara wacce ba'a fata Allah ya kyauta).

Ga Abdool kullum kukan Dadynsa yakeyi Abu duk ya had'e yayi mata yawa, danma ga Asma'u kusa ita ke d'auke masa kewar Dadynsa, Mama da Baba kullum cikin kwantar mata da hankali suke, Mansur kullum yana cikin kawo Abdool kayan wasa da kayan kwalama irin na yara idan yaje School 'yan Kud'insa duk can suke tafiya duk dan su kwantar Mata da hankali, Firdausi ma tazo lokacin da taji, itama Sam abin baiyi Mata dad'i, musamman ma sharrin yafi komai cin rai, inda Allah ya sota duk Wanda yaji kai tsaye yake k'aryatawa, saboda sanin halin kirkinta(tau zama dan kwarai Nada rana dan wata rana ake gujewa mu d'aure mu k'are mutuncinmu).

Alhaji washe gari yazo Argungu, Baba ya tarbesa kamar ba abinda ya faru dan yasan ba laifinsa bane, hak'uri ya k'ara bashi akan abinda ya faru, tare da tabbatar masa Sam koda abin ya faru bashi gari, saida ya dawo yakeji nan yake gayamai tafiyar Auwal, nan Baba ya jajantamai tare da fatar Allah ya bayyana shi, tsaraba  Ameena da Abdool ya fito dasu hadda ma Asma'u yayima dan yasan tana gidan lokacin da ya tafi, tare da kayan buk'atar Ameena da Abdool na yau da kullum, dan yayi Alkawarin kula dasu har sai tayi Aure.

Baba saida Alhaji ya nuna b'acin ransa tukun ya anshi kayan dan yace bazai Ansa ba, saida Alhaji yace bai hak'ura da abin da yw faru ba kenan, ai sun Riga sun zama d'aya tunda har rabo ya shiga tsakani, hakan dai dole ya ansa, har Mama saida ta fito suka gaisa sannan ya bata hak'uri itama.

STORY CONTINUES BELOW

Lokacin da Ameena tazo nasiha sosai yayi mata tare da bata hak'uri sannan ya tabbatar mata har yanzu shi ubane gareta komai ya sameta ta sanar da shi, kud'i ya bata tare da wasik'ar Auwal, saida yayi mata fad'a sannan ta Ansa, haka ya tafi yana tausayawa mata dan bazaiso hakan ra faru akan Maryam ba.

Sosai ya k'ara daraja da girma akan idon Ameena da iyayenta.

Sai dare ta d'auko wasik'ar Auwal da tunda aka bata ta kaita ta ajiye, dan ita yanzu lamarin maza ya fita Kanta kuma duk haushi Suke bata(dama ai duk macen da aka saka tofa duk maza haushi zasu rik'a bata zata d'auka duk Wanda ta aura zai iya sakinta komai soyayyar da yake mata kuwa.

Bud'ewa tayi ta fara karantawa..

_"gareki masoyiyata tahar abada, Ameena nasan zanyi bak'i a gurin ki dan duk wacce aka saka saki uku kai tsaye tabbas zata girgiza kuma zata tsani wannan mijin, harga Allah duk da abinda idanuwana suka ganemin, zuciyata ta k'asa yadda da abinda wani barinta ke gayamata akanki, saidai ki sani dole ne na shiga rud'u dan nina gani ba ji nayi ba, amma inaso ki d'auki wannan a matsayin k'addarar muce, ki tausayawamin ki tausayawa d'ana *Abdulmajeed* ki zame masa uwa da uba agareshi ki bashi dukkanin tarbiya ta gari, dan kuwa ke uwace ta gari a gareshi, pls kada kibar rayuwarsa tayi garari koda kinyi aure ne, ki zama majib'incin lamurransa a dai2 gab'ar da ya rasa dukannin kulawata a matsayina na uba agareshi, na tafi bawai dan bana k'aunar sa ba Aa sai dan samun maslaha a gareni, ina miki fatan Alkhairi, ki saka a ranki zan rayu da sonki a kowanne second na rayuwa"._

*naki Auwal Sada*.
Koda ta gama karantawa hawaye sun wanke mata fuska, zuciyarta sai rad'ad'i take mata da suya, Abdool ta rungume tsam a k'irjinta tana tausayawa rayuwarsa, yaro k'arami ko wace rayuwa zaiyi nan gaba.

"Allahumma ajirni fi musiba"..................


*ina mai Baku hak'uri sa babbar murya, akan jina da kukayi shiru kwana biyu, na shiga busy ne, amma Ku sani kuna raina#1❤#*
πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„
[8/8, 7:45 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬
πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€
πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„
© *Pure moment of life writers*
P.M.LπŸ’ͺ🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readersπŸ“)

πŸ‘ŒπŸ» *d best way 2 love is love for d sake of Allah. And tell d one u love d fact about him, show him d true faith, never tell him lies just 2 make him happy, hmm day he/she find d true u will become his biggest enemy, may Allahu (S.W.T) show us true way of life ameenπŸ‘πŸ½*

Small quoteπŸ‘ŒπŸ»

_Aunty Khaleesat Haiydar ur r so grateful, Aunty Ummi shatu wishing oll d best in ur examsπŸ‘ŒπŸ»_    #heart u aunty's😘#

 

     πŸ“ *Episode* 111--115

Saida aka kai ruwa rana kafin Baba ya yadda da komawar Asma'u makaranta, dan yace ta dawo tayi NCE kawai, dak'yar ya amince amma da sharadin zata kare mutuncin Kanta, ranar da zata tafi da kuka suka rabu da Abdool dan lik'e mata yayi sai taje dashi, Mansur ya fita dashi sannan ta samu ta wuce kice da kewar gida da Son d'inta, dan tasan zatayi missing nashi, Hostel ta koma da zama inda ta dage da karatunta baji ba gani, tayi mamakin rashin ganin Maryam sai daga baya takeji ga k'awayensu an canja Mata school, Hajia ce tasa aka canja mata, a cewarta kada Asma'u ta lalata mata d'iya, tunda tasan muddin suna school d'aya Maryam ba fita hanyar Asma'u zatayi ba, hakanan bataso aka maida ita nursing.

STORY CONTINUES BELOW

B'angare guda kuwa shakuwa ce ta k'ara shiga tsakanin Asma'u da Abdulrahim kullum zaka Kansu tare yana koya mata karatu musamman yanzu data dawo hostel dama shi a hostel yake dan ba dan garin bane, tun basujin komai a ransu game da juna har takai yanzu sunajin zukatansu sunaso su zama d'aya.

( *Tofah wai waye Abdulrahim?*)
Abdulrahim dan asalin kilgori ne wadda ke k'arkashin Yabo local government dake jahar Sokoto, D'ane ga Malam Umar wadda akafi Sani da Ard'o, sarautace irin ta Fulani wato mai gari kenan, Ard'o ya zamo mai garin kilgori ne bayan rasuwar mahaifinsa wato tsohon Ard'o, yana da matar Aure d'aya Hadizatu wacce akafi sani da Iya Hari, auren zumunci ne akayi musu, Ard'o mutum ne na mutane mai sanyin hali, kowa nasane, yayin Iya Hari ta kasance masifaffiyar mace, Mara mutunci kullum cikin masifa take da bala'i, tunda Ard'o ya aureta bai taba k'arda dad'in ta ba, anadai zaune ne zaman hak'uri, bai isa ya sata tayi ba haka bai isa ya hanata ta hanu ba, amma a haka sukaci gaba da zama da yake Allah ya zuba mishi hak'uri, komai tayi kauda kai yake kamar bai gani ba, sunada 'ya'ya uku Abdulrahim ne na d'aya Wanda take kira da Modibbo saboda kasancewarsa d'an fari, sai Lantana wacce ake kira Lanti sai Aisha wacce ake kira Shatu, sam halin Aisha da Abdulrahim ba irin nata bane halin babansu suka d'auko, kai harma kamar dansu farare ne sirara dogeye, kyawawa dasu, yayin da lantana ta biyo kama da halin uwar sak.

Tun Abdulrahim yana k'arami yake sha'awar boko, mahaifinsa kuwa ganin yana sha'awa yasa ya sakashi A yabo dan lokacin ba'ayi anan garinsu ba, haka yake tafiya kullum zuwa yabo don daga k'arshe da mahaifinsa yaga wahalar zatayi yawa sai ya had'ashi da wani malami, yake zama gidansa sai Hutu yake dawowa, Wanda hakan Sam baiyima Iya Hari dad'i ba, rigima ta tada akan ba inda zaiye ya tsaya yayi kiwo in zaiyi, rokonta yayi tayi akan ta barshi, amma tak'i amincewa, dama Abdulrahim baisan dad'in ta ba Sam, dan bata janshi a jiki, wai d'an fari ne, ba wani sabo a tsakaninsu yafi sabawa da Ard'o, haka kuwa ta dage akan ba inda zaije, saida Ard'o ya nuna b'acin ran yaje ya gayama iyayenta, ganin tunda take dashi bai taba nuna Mata bacin ransa haka ba balle har aje ga kai k'ara yasa ta shiga taitayinta ta amince  akan dole.

Hakan Abdulrahim yayi ta karatunsa tun daga primary har secondary duk anan Yabo yayi su, gashi kanshi naja(dama Fulani akwai kai) tunda ya fara harya k'are bai tab'a yin na 3 saidai na 1 ko 2 hakan yasa malamansu bawa Ard'o shawarar kaishi university hakan kuwa ta kasance inda yake karatun medicine, ita dai Iya Hari akan dole yake karatun badon son ranta ba, dan ita gani take lalata yara kawai boko keyi, shiyasa ta hana a saka Lanti Shatu, Abdulrahim kuwa ya goge idan ka ganshi bakace dan k'auyen bane, hakan yasa 'yan matan garin kowa sonsa take, 'yar k'anwar Iya Hari ganin kowa sonsa yasa hankalinta ya tashi, ba kunya taje ta gayama Iya Hari itafa shi takeso, dama itama sunada burin hakan itada k'anwarta na had'a su aure, nanta tabbatar mata da Abdulrahim baida matar aure sai ita, shikam Abdulrahim Sam yarinyar bata mishi ba saboda batada nutsuwa Kanta rawa yake, itakam Saude sai d'aga kai take a garin da tak'ama zata auri d'an boko.
_wannan kenan_

B'angaren Ameena kuwa ganin Asma'u ta koma makaranta, Mansur ma ya koma dake boarding school yake, gidan ba dad'i duk da Asma'u na zuwa duk k'arshen sati, yasa tayima Baba magana tanason itama ta koma makaranta bai musa mata ba, saidai yake ba zataje nursing kamar yadda ta buk'ata ba, dan ko lokacin da Auwal ya kawo mata form abinta ta cike kenan, wannan burinta ne tun suna secondary, amma dole ta hak'ura da ita dan dalilan da Baba ya gayamata na hanata zuwa wani gari kara2, ya gayamata 'yan uwansa zaginsa zasuyi suce a maimakon yayi mata Aure ya turata karuwanci, hakan yasa ta hak'ura zatayi NCE anan *Adamu Augie college of Education Argungu* da kanshi ya anso mata form ta cike inda aka bata Agric/education, nan Baba ya sakata gaba yayi mata nasiha akan taci gaba da tsare mutuncinta tayi abinda ya kaita kawai banda bin k'awaye barkatai, itama Mama tayi tata, nan Ameena ta fara zuwa school cikin nasara, ba abinda takeyi sai kara2 ba ruwanta da kowa haka zatayi shigarta ta kamala taje data gama lec, ba wani tsaye-tsaye direct gida take wucewa dama can daga gida sai makaranta, sai kuma bikin yan uwa ko barka shima akan tilas take zuwa kada ta yanke zumunci, saidai abinda ke kona mata rai data had'u da taubasanta yanzu zasu fara takanarta da kiranta bazawara ina zawarawanta, yake kawai take musu amma Kalmar ba k'aramin k'onata takeyi ba, saidai ba yadda zatayi k'addara ta riga fata, shisa sam bata cika son shiga mutane ba.

STORY CONTINUES BELOW

Zuwa yanzu ta kwantar da hankalinta ta maida kamarta ta kuma rungume k'addarar ta, saidai Aure ya fita ranta gaba d'aya, shiyasa duk Wanda yazo da sunan yana sonta hak'uri kawai take bashi dan bataji zatayi aure yanzu.

Lokaci zuwa lokaci takan tuna Auwal da rayuwarsu ta baya, koyana ina yanzu oho!, Abdool zuwa yanzu ya manta da Dadynsa yayinda ya d'auki Baba a matsayin Babansa, yana 1¼ ta yayesa dan komai ci yake ga kafafu har gudu yake hak'ora ne kawai bai cika ba, bata sha wahala a yayensa ba, dan wani sa'in sauya wuni baisha ba sai dare, tunda ta aka yayesa ya koma hannun Mama can yake baccinsa.

Ta dage sosai da karatunta k'awa d'aya tayi mai suna Sakina mungadi, department d'insu d'aya, tasu ce tazo d'aya shiyasa sukayi k'awance dan itama sakina ba ruwanta da sha'anin kowa abinda ya kaita kawai takeyi(a kowanne lokaci muyi k'ok'ari muyi mu'amala da mutanen kwarai, dan kuwa har lahira kana tare da abinda kakeso, kuma zama da mad'auki kanwa shika haddasa farin kai) a hostel take zaune dan a bk suke zaune da iyayenta, kullum suna tare idan ka gansu gwanin sha'awa cikin shiga ta kamala, Sakina tasan komai gane da Ameena dan har gidansu tana zuwa, tana kuma son Abdool sosai, haka rayuwa taci gaba da tafiya yau dad'i gobe sabanin haka, rayuwar duniya kenan haka ta gada, a gefe d'aya kuma Ameena naci gaba da kasuwancinta kuma duk k'arshe wata har Alhaji Sada na zuwa dubasu da hidima sosai kamar yadda yayi alkawari, su Baba ma na iya k'ok'arin su, so batada matsala a yanzu saidai wacce ba'a rasa ba.....

Suna NCE 2 wani malami na education ya basu Assignment to group discussion ne, kuma each group ten people ne, shiya rabasu da kanshi, from d different faculty, anan aka hadasu da wani Yusuf normally tasanshi saboda suna had'uwa GSE da EDU saidai magana bata tab'a had'asu ba, shine team leader nasu ita kuma assistant, shi d'an ENG/ISS, wannan Had'uwarne ta zama sanadin shakuwa tsakaninta da Yusuf, dan Yusuf social man ne, kokai waye ka zauna dashi sati yayi wuya Baku saba ba, dan akwai barkwanci gareshi burinshi bai wuce yasa mutane cikin farinciki ba, Sam shima ba ruwan sa da shashanci, kara2 kawai ya saka gaba kuma ga kwakwalwarsa tana ja ba dama, dan 3point kawai yake bugu ga G.P, hakan yasa ya saba dasu Ameena ko bayan gama assignment d'insu saiya kasance duk lokacin da basu da lectures sukan zauna suyi discussion a tsakaninsu based on their studies.

Yauma Zaune suke suna tattaunawa sai wayanta tayi k'ara, dauka tayi basuji me aka fad'a a d'ayan b'angaren, sun daiji tace.

"Subhanallah Asma'u meya sameshi?"

Still suka k'ara jin tace "tau ganinan zuwa" mik'ewa tayi a rud'e, tare da musu zataje gida, amma yanzu zata dawo, Sakina CE ta tambayeta meya faru, nan take gayamata Abdool ba lafia.

"Aa to inzo muje kawai".

Murmushi tayi Mata " kada ki damu Besty is not so worst fa, nima I will be back soon inshaa Allah " sannan ta wuce.

Duka sun tausaya mata ganin yadda ta rude har Yusuf ke tambayarta halan k'aninta ne, nan Sakina ta gayamishi a yaronta, ba k'aramin mamikine ya Kama shi ba danshi duk kallon budurwa yake mata ba Wanda zai ganta yace tanada aure hadda d'a, yace

"Amma fa bantaba tunanin matar aure bace, duk da kuwa naga tanada kamun kai".

"Hakane amma yanzu bata tare da mijin" nan dai Sakina ta bashi labarinta, sosai ya tausaya mata, hadda k'wallarsa, tare da sak'awa ransa wani tunani.
*life goes on......*
Kwana d'aya, sati, wata, shekara, haka shekaru keta tafiya a guje kamar ana kora su, zuwa yanzu Abdulrahim ya kammala karatunsa inda yake internship a nan Uduth, Asma'u kuwa tana rubuta final exam nata, soyayya suke gudanarwa cikin tsafta, dan sun dad'e da bayyanawa juna sirrin zuciyarsu, jira kawai suke Asma'u ta kammala karatunta su sanar da magabatansu, ayi taimaka a aurar dasu. Lol

Ayau ne ta kammala jarabawarta cikin nasara, kuma a yaune kowanne su ya shirya tsaf ya doshi familyn sa dan fallasa sirrin da ke ransa,  dan cikar burin zukatansu, lokacin da Abdulrahim yaje da maganar gidansu Ard'o ya goyamasa baya d'ari bisa d'ari, dan yasan d'ansa bazai zabo abinda zai cutar dashi ba, dan haka ya bashi tabbacin a satin zasuje har shi A Argungu domin ganawa da iyayenta.

STORY CONTINUES BELOW

Tashin hankali Wanda ba'a sa mishi rana, ai Iya Hari dukane kawai bata mishi ba, amma ta inda take shiga ba tanan take fita ba, tas tayi masa ta kuma tabbatar masa baida matar aure inba Saude ba, dan bai isa ya banna mata lokaci a banza ba dole ya Aureta(Niko nace kamar shi yace ta zauna).

B'angaren Ameena na kuwa ta kammala karatunta cikin nasara, harta anshi resi d'in ta, Abdool kuwa an girma dan yanzu yakai shekara 5 yana nursery 2 a Emirate dake garin Argungu, gashi da k'ok'ari sosai sai dan Neman wayo da surutu har tsoro yakeba Ameena idan ya fad'i wata magana kamar wani Babba, Niko ya had'u da Asma'u aifa shikenan d'an biyemasa takeyi suyi tayi, itadai Ameena kallo kawai nata tana mamakin wannan shak'uwa dake tsakaninsu.....

Asma'u yayarta ta fara sanar ma soyayyarta da Abdulrahim, Ameena tayi farinciki da jin k'anwar tata ta had'u da *muradin ranta* (maman ussey), amma saida tayi Mata mitar k'in fad'a mata tun farkon soyayyar sai yanzu take gayamata, hak'uri ta bata tare da had'e hannayenta biyu guri d'aya.

Dukan wasa takai mata tare da Kama hannayenta ta maida ita kan bed "ki rage zurfin ciki kanwata kada ya cutar dake wata rana"

Tana dariya tace "yes Aunty ur wish...." Dariya sukayi baki d'aya dai shigowar Abdool shima ya dane gado tare da kamu rungume Asma'u tayi tare da jan guntun hancinsa tace..

"Clever boy kasan me akewa dariya ne hala?"

"Yes tunda Aunty da Mami na dariya nasan suna farinciki ne.." Nan dariyar sukayi gaba d'aya suna mamakin wayo irin na yaron...

Ameena nace taje ta sanar da Babban su game da maganar Asma'u, har da maganan zuwan su Ard'o dan Abdulrahim ya kirata ya gayamata suna zuwa cikin satin.

B'ata rai taga Baban nasu yayi yace ta kira Asma'u, jiki sanyaye ta fita, tare suka dawo.

Asma'u ya kira sunanta cikin kaushin murya, bai jira amsawarta ba yaci gaba da magana.

"Yayarki tazo min da zancen yaron da kike so, yanzu abunda ya faru da 'yar uwarki bai zama izina gareki ba, har kike tunanin Auren 'yan jahar Sakkwato, to bama wannan ba na Riga mun gama magana da Malam Musa zamu had'aku Aure da d'an wajensa Mustapha" tunda ya fara magana Kanta na k'asa haka itama Ameena, harda hawayenta jin anyi mata fami akan ciwon ta.

Sannan yaci gaba "dan haka inaso ki kira wannan yaron ki gayamishi karma yazo da iyayensa dan an Riga anyi miki miji, kinji ko?" Kai ta girgiza masa alaman eh.

"Yawwa kuje Allah yayi muku Albarka" Ameen suka ansa sannan suka wuce, bayan fitarsu inna dake zaune tunda aka fara maganar bata ce komai ba.

"Amma Alhaji kana gani anyiwa yarinyar nan ad......." Katsesa yayi.

"Ya isa Habeeba wannan ba huruminki bane" shiru tayi da bakinta tare da fadin "Allah ya kyauta"...

K'arshen tashin Asma'u ta shiga, rabuwa da masoyi da rana tsaka siddin akwai wahala, sai dai ya zama wajibi gareta tabi umarnin babanta, Ameena da itama d'aure kawai take amma k'anwar tata ta bata tausayi tasan zafin rabuwa, dafata tayi tana tare da k'arfafa mata guiwa(dan uwa rabin jiki, Allah ya barmu da yan uwanmu).

Wayarta ta d'akko ta kirasa amma ina bata zuwa saboda matsalar network, ko ranar da ya kirata saida yaje kan titi dan basuda network cikin gari, haka taita kira tak'i shiga, tsawon kwanaki uku amma ba labari, ana hudun kuma tace bama zata kira ba.

Ard'o kuma duk bala'inda iya Hari yi yayi kamar bai san tanayi ba, Sam bai yarda da tarbiyar Saude ba, kuma bazaiyima danshi auren dole ba, haka suka shirya tsaf  shida Malam Garba  da k'annensa guda biyu sai Abdulrahim suka doshi hanyar Argungu ba tare da sanin Iya Hari ba,  Abdulrahim yaso ya kira Asma'u ya gayamata sai kuma yace kawai bari ya bata surprise.

Basu sha wahala ba gurin gane gidan dan sunbi kwatancen da Asma'u tayi, har k'ofar gida suka isa da motar da yake ta Abdulrahim CE, sunyi sa'a sun samu Baba k'ofar gida tarba ta karamci yayi musu, kamar yasan da zuwansu bayan sun gaisa sukayi mishi bayanin meke tafe dasu, mamaki ya kashe shi wato shi yarinyar zata renawa hankali, tambayan Abdulrahim yayi akan bata kirasa ta gayamai komai ba yace eh bata kirasa ba(kusrensa bai fad'a masa sunada matsalar network ba).

Gyaran murya yayi Sam bai nuna musu b'acin ransa ba "ah naji mi a tahe daku, idan a shirye kuke bani da buk'atar komai daga gareku sadaki kawai zaku bani a d'aure Auren yanzu" cikin mamaki suka shiga kallon juna kamar 'yarda aka gaji da ita.

Kamar yasan me sukewa mamaki yace "ko d'aya ban gajia da ita ba saidai ta zabi abinda takeso dan haka shi za'ayi Mata, kuma in Baku taho da niyyan aure ba to Ku tashi Ku tafi abinku, amma kai kar in sake ji ko ganin kafarka a gidana ko ka kira yata, ka fita hanyar ta gaba d'aya" ya fad'a tare da nuna Abdulrahim.

Duk ya k'ara d'aure musu kai, haka malam Garba ya Zare dubu 20 ya bashi ansa yayi tare da mik'ewa 10 ya d'auka na Sadaki 2 na goro, ya maida musu da saura, cikin k'ank'anin lokaci sai gashi da goro da wasu mutane nan take akayi Addu'a aka d'aura Aure, duk wannan bidirin da ake cikin gida basusan meke faruwa ba sun dai San yayi bak'i amma basusan su waye ba.

Nan yace su jira ya fito musu da Amaryarsu su wuce da ita, sudai kallonsa kawai suke mamakin duniya ya ishesu Abu kamar tatsuniya, ciki ya shiga tare da d'aure fuska tamau ya fara kwalawa Asma'u kira kamar hauka.

A tare suka fito ita Mama Ameena suma cikin mamakin kiran.

"Asma'u ungu wannan" ya mik'a mata kud'in, ansa tayi jiki a sab'ule.

"Sadakinki na inaso ki shiga ciki ki d'auko mayafinki Angonki na waje yana jiranki, saidai inaso ki sani tunda kin zabi Abdulrahim akanmu to daga yau bamu bake, baki sammu ba haka muma bamu sanki, kada ki kuskura kiyi tunanin mu ko tunanin tahowa inda muke, mun yafe masa ke har lahira" ba Asma'u kad'ai ba har Mama da Ameena saida kalamansa suka girgiza su, sai yanzu ta gane kuskuren ta na rashin fad'a mishi, ita kuma taki fad'i gudun matsala, Ashe hakan babbar matsala zai haifar mata.

Cikin sheshshekar kuka ta isa gabansa ta duka da duka gwuiwarta, bakin ta na rawa "Baba don....." Katseta yayi

"Kul kada ki yadda kice komai kiyi kawai yadda nicce miki" rik'e mishi kafafu tayi tana gunshekar kuka, Ameena kukan take haka Mama, Don tafi kowa sanin halin mijinta idan ransa ya b'aci Sam bayaji baya gani, zuciyarsa rufewa take.
Ameena ma ta bud'e baki zatayi magana ya hanata, haka Asma'u ta rarrafa inda Mama ta rungume ta itama Ameena zuwa tayi ta rungume su, suna haka saiga Mansur ya d'auko Abdool daga school, a cikin wanga yanayi suka isko su ga Baba tsaye sai huci yake.

Da gudu Abdool ya yaje ya rungume su shima yana kuka

"Mama kukan mi kukayi, Aunty kema kuka na kikayi, Mami kema" yana tambayan su yana yi shima gwanin tausayi.

Baba ganin zuciyarsa naso ta karaya yasa ya shiga sa kanshi ya d'akko mata hijab d'inta, ya saka mata ya jata, su mama na riketa suna magiya suna komai a banza, Mansur shima tuni hawaye suka wanke mishi fuska, Abdool shima rike ta yayi GAM.

"Baba ina zaka kai Aunty?"

"Abdulmajeed, Aunty bata buk'atar Ku, zan kaita inda wad'anda take buk'ata" ya fad'a tare da banbareshi ya mik'a ma Ameena, sannan yayi waje da Asma'u, Abdool sai kuka yake yana kiran "Aunty" amma Sam bata bai saura ra ba, haka magiyar su Mama suna kika duk bai saurara ba.

Yana fita bai zame ko'ina ba, sai cikin motar ya turata tare da basu Umarnin su wuce, anan su Ard'o  suka fahimci da matsala, suka shiga bashi hak'uri akan ya tsaya a sananta, amma Sam yak'i sauran su, saima kashedi da yaka k'ara yi na karta sake ta tako kafarta gurin su, tare sa gayamusu ya yafe musu ita har lahira, ganin ransa ya gama b'aci yasa suka rubuta no- da garinda Suke idan ya wuce dan Allah ya kirasu, sannan sukaje mota suka tafi...

Asma'u na ganin an tada mota ta k'ara rushewa da wani irin matsanancin kuka................

        🀦🏽‍♀πŸ™†πŸΎπŸ™†πŸΎ

_Masoyan Abdulmajeed INA alfahari daku aduk inda kuke, pls kuci gaba da karfafa mini #ILVMNM❤guys# keep fallowing_

πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„
[8/9, 6:17 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬
πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€
πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„
© *Pure moment of life writers*
P.M.LπŸ’ͺ🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readersπŸ“)

*Yakai d'an Adam meye tak'amarka/ki, meye alfaharin da kake/kike, meye fad'in ran naki/ka, meye d'agawar taki/ki, keda/kaida farkonka/ki ya kasance k'azantaccin ruwa, tsakiyarki/ki fitsari da kashi, k'arshenki/ka abincin tsutsa, mushe to meye abun jinkai da nuna isa.*+

Nasiha ceπŸ‘ŒπŸ»

_bazan gaji da gode muku ba, a zahirin gaskiya kune ni haka nice Ku, sai daku zanyi rubutu wato masoyana masu bani k'arfin gwiwa akan rubutuna, ina alfahari daku, ina rokon Allah yaci gaba da bani damar da zan rubuta abinda zai sakaku nishadi ya kuma amfanar da Ku, #heart u ❤ guys# ina k'aunarku a duk inda kuke #double love😍#_

  πŸ“ *Episode* 116-120

Tunda suka d'auki hanya, take kuka bil hakk'i da gaskiya, kuka take mai tab'a zuciyar mai sauraro, suma mutane cikin motar duk zuciyoyinsu a tsince suke, tausayin yarinyar ya lullub'e musu zuciya, shiru kake ji ba abinda ke tashi sai sautin kukanta, ba Wanda yayi yunk'urin dakatar da ita dan wani lokaci kuka rahama kana jin sauk'i a ranka, sanda tayi mai isarta, sannan ta tsagaita, hakan yasa Ard'o fara bata baki.

"Kiyi hakur'i 'yata duk da bansan ainihin abin da kikayima mahaifinki ba, yayi miki wanga hukunci, a gaskiya hukuncin yayi tsauri, saidai ki Sani su iyaye komai suka yima d'ansu to ya zama dole yayi hak'uri dasu kuma yayi musu biyayya mudin baici karo da Umarnin ubangiji ba,  saboda sun riga sun gama dashi tunda suka haifesa, inaso ki rik'eni a matsayin mahaifi a gareki ni kuma nayi miki alkawarin zan zamo uba a gareki, kuma bawai ina nufin kibar iyayenki ba aa sunanan a iyayenki ba Wanda ya isa ya maye gurbinsu a gareki, kuma inaso ki d'age da Addu'a Allah ya sassauto zuciyar mahaifinki ya yafe miki kuma ya nemeki, muma zamu tayaki da Addu'a inshaa Allah".

Sosai taji dad'in maganar Ard'o, hakan yasa hankalinta yad'an kwanta, ganin tayi sa'ar suruki na gari, cikin nutsuwa ta gayamusu abinda ya faru, sun jinjina abun a ransu tare da  gayamusu kuskurensu daga ita har Abdulrahim d'in, sannan kowa ya bata baki da kalamai masu dad'i, tare da gaya mata ta d'aukeshi a matsayin k'addararta domin rabon ayi auren ne yasa hakan ta faru, tare da sanya ma Auren Albarka, Abdulrahim dake jan motar shima jiki a sanyaye duk sonsa da Asma'u baiso Auren su ya kasance haka ba, amma ba yadda zasuyi dama tun ran gini tun ran zane sai fatar Allah yasan hakan shine mafi Alkhairi a garesu, Ard'o ko tuni yaji yarinyar ta kwanta masa a rai da alama zatayi hak'uri, haka dai suka doshi kilgori kowa da abinda yake sak'awa a ransa, kowa zuciyarsa ba dad'i......

***********************

Baba kuwa yana ganin sunja mota ya buga babbar rigarsa yayi cikin gida, anan ya jefar da takardar da suka bashi nan iska yayi gaba da ita, yanda ya barsu haka ya samesu suna kuka, kallonsu yayi cikin b'acin rai yace.

"Yanzu kunaga banyi muku dai2 ba ko? Baku dubi irin abin yarinyar tayi ba, ta nuna bata buk'atar mu a rayuwarta ta zabi wad'anda takeso amma Ku duk Baku gani ba, to bari kuji duk Wanda ya yadda ya kusanceta koda hanyar bani bashi, kuma ban yafema koda kuwa keda kike uwarta ne" ya fad'a cikin b'acin rai tare da nuna Inna, sannan ya buga rigarsa yayi waje.

Bai zame ko'ina ba sai gidan aminin nasa Malam Musa, dan gayama abin ya faru da Kansa kada yaji a wani gu, yayi sa'a kuwa ya samesa bayan sun gaisa ne yake bashi labarin abinda ya faru tare da bashi hak'uri.

STORY CONTINUES BELOW

"Kai amma Abu baiyi kyau ba, dama ko bakazo ba inada niyyan zuwa akan maganan, dama na samu Mustapha da maganan to shine yace shi gaskiya yana wacce yakeso abar zancen kawai, to shine naso inzo in fad'a maka sai kuma ban samu zuwa ba har ka taho.

Tsananin mamaki da imani ne yayi mishi yawa, yama k'asa magana lallai kowa ya daka ta mutane toya rasa turmin daka nashi, saida sukayi da mutumin nan komai lafia amma yanzu yace ba haka ba, shiya salawantar tashi 'yar akan farinciki wasu, yayin shi kuma ya bawa d'an shi abinda yakeso, nan take nadama ta rufesa lokaci na farko d'aya yi tir da (zuciya irin tasa na Ayusher).

"Alh, Abubakar bakace komi" boye damuwarsa yayi tare dayin murmushi yake Wanda yafi kuka ciwo "ba komai Alhaji Allah ya kyauta, sai anjima" ya tashi ya wuce ba tare dayace komai ba...

Gida kuma bayan fitar baba zaune saukai jugum suna jajanta wannan Abu d'aya samesu, wannan shine ga duka ka kuma tsunka jaka, Abdool Ameena takai d'aki Wanda yayi bacci sai ajiyan heart yake, sannan ta dawo inda Mama suna tattauna wad'annan ibtila'i dake bibiyarsu a d'an tsakanin, lallai Allah shike jarabtar bawansa suna fatar su zamo cikin masu cinye ta, Ameena gani take tafi kowa ganin rayuwa, Asma'un da ta rage mata mai bata shawara sa d'auke mata kewa gashi k'addara tazo ta rabasu, yanzu ma ta ina zasu samu labarin Asma'un bayan ko waya batada ita yanzu, dan daga ita sai kayan jikinta tabar gidan komai bata d'auka, gashi ta manta sunan garin dan tabbas ta fad'a Mata amma bazata iya tunawa ba, ko wacce irin rayuwa zatayi a gidan Aurenta a wannan yanayi sa taje musu zasu karb'eta kosu wulak'anta ta? Nan tayi saurin nema mata sauk'i gurin Allah, haka suka wuni gidan ba dad'i kowa sai jimami yake.

_such is life_
Baba kuwa k'asa komawa gida yayi bayan yazo gaf k'ofar gidan ya dudduba kozai ga wannan takardar amma ina bata ba labarin ta, jin yayi komai baya mishi dad'i, sai gashi hadda k'wallarsa sam baiyima Asma'u adalci ba, yafi kowa sanin biyayya irin ta 'ya'yansa amma ya rufe idonsa, lallai zuciya mugun nama CE, kowa ya biye mata zata kaishi ta baro ne, lallai kowa yahau dokin fushi k'arshen sa nadama ne (yana daga cikin karantarwar manzo S.A.W idan kana cikin fushi kada kayi magana sannan kada ka yanke hukunci cikin fushi dan k'arshen sa dana sani ne) Allah yasa mudace.

Sai dare ya samu sukunin komawa gida, shima jiki ba k'wari ya shiga, kamar yadda Inna ta saba tarbonsa haka ta tarbesa ba tare data nuna mai komai ba, kamar ba abinda ya faru, k'ara jinjina hak'uri irin na Inna yayi sau da yawa yakan tauye mata hakki shikansa ya sani amma bata taba nuna mishi damuwar, lallai mace tagari ni'imace(haka yake duniya d'an jin dad'i ce amma mafi jin dad'in ta Wanda ya dace da mace ta gari).

Haka suma su Ameena sukazo suka gaishe shi kamar yadda suka saba, zasu tashi yace su tsaya yanada magana, ayan da yayi maganan cikin taushin murya, abun har mamaki ya basu, nan dai ya labarta musu yadda sukayi da Abokin nasa, tare da nuna musu nadamarsa.

"Alhaji ka dad'e kana tauyeni sau da yawa kana maida damuwar kowa ba damuwa, damuwarka kad'ai kake dauka damuwa, kama rayuwa da fushi kana yankewa mutane cikin fushi, to yanzu gashi wagari ya waya, ka salwantar mana da yarinyar akan son ran wasu, me kayi kenan" Inna ta gayamai magana cikin nutsuwa.

"Baba shiyasa ake son bawa mutum uziri a rayuwa, lokacin da ka shigo nida Asma'u munaso muyi maka bayani amma haka rufe ido kak'i bamu dama" nan ta basu labarin abinda ya faru a lokacin da Asma'u ta kira Abdulrahim" Amma kayi hak'uri In na fad'i ba dai-dai ba".

"To kaji ma abinda ya faru ko amma saboda rashin bata uzirunka a rayuwa kak'i sauraren kowa".

Shiru baba yayi nadama na k'ara lullub'esa, duk abinda suka fada gaskiya ba karya, sai hango lokacin da Asma'u take rik'e mishi kafa takeyi amma yayi biris yak'i saurarenta, tuni tausayinta ya kamashi lallai baiyi Mata adalci ba.

Hak'uri ya basu tare da tabbacin inshaa Allah zai nemota duk inda take.

Kwana ki sun shura watanni sun wuce kullum Baba yawon Sokoto da garuruwanta saidai kuma ba'a dace ba, ganin abin yayi yawa duk ya dami Kansa yasa Mama cewa.

STORY CONTINUES BELOW

"Ka hak'ura da yawon nan haka idan da rabon mu gaba zaka ganta ta kawo Kanta har gida, idan kuma babu rabo zafin nema bazai kawo samu ba, hakan ya hak'ura dole tare da bibiyarta da Addu'ar fatan Alkhairi aduk inda take.

Ameena kuwa zuwa yanzu zaman gida ya gama isanta gaba d'aya saukinta ma tana teaching da Baba ya samo mata yanzu tsawon shekara biyar kenan da rabuwarsu gashi duk masu zuwa sun d'auke kafarsa, a halin yanzu ba abinda takeso irin tayi aure shine akwai kwanciyar hankalinta (dan Mace komai kamewarta, idan batada aure to mutuncinta ragaggene a idon mutane, balle kuma wad'anda suka d'auki zawarci a lasisin iskanci suka samu tunda yanzu su zawarane ba namijin da zai Aure yace yana Neman budurci, to ai ba anan gizon yake saka ba, walla d more kikayi zina kina bazawara bakida wani hukunci daya wuce a jefeki, ba riba kenan, a tunani zawarci wata damace da mace zata K'ara sanin rayuwa, ta kuma gyara halayenta, kowanne aure yanada sila a rabuwarsa saiki duba meya kashe miki aure dan gyarawa gaba, bawai ki lalace ba, Allah yasa mudace) ayuwar zawarci rayuwace mai cike sa kalubale da tashin hankali, zaman gida ya gama isarta yau idan mace takai munzali tofa da batayi Aure ba, zaman sai kasance gashi nan dai na ganin laifi ne keda iyayenki, shiyasa Ameena ta damu sosai da rashin Auren, sai ba yadda zatayi dan tasan komai lokaci ne.

Yau kamar kullum Mansur ne yaje ya d'auko Abdool daga school, da gudu ya shigo yana murna "Mami kinga Nina yi na d'aya" ya fad'a yana nuna mata result d'in da gift d'inta aka bashi.

"Iyye yaron Inna kaifa akwai rashin ji amma akwai k'ok'ari" Jan tayi zuwa jikinta tana duba idonsa "waini kam idon nan naka Abdool anya lafia ko?"
Inna dake fitowa tace "me idon yayi?"

"Kiga farin yana surkawa da pink," duba idon Inna "tabbas ya kamata kuje asibiti" shikam sai k'ok'arin nunama inna report sheet yake, ba abinda ya damesa....

Likitan ya tabbatar musu ba wata babbar matsala bace, ciwon a jininsa yake so yayi inherited ne saidai ya kamata a nema mishi medical saboda idon yayi lasting, sai yanzu Ameena ta tuna tana ganin idon Auwal suna irin hakanan sometimes, no wonder shiyasa yake amfani da glass always Ashe medical ne.
**************

Har k'ofar gida suka sauke malam Garba da k'annin Ard'o sannan suka isa gida suma.
Da kallon mamaki iya Hari ta bisu sannan tace "malam ina kuka shige tun safe, wagga kuma fa?"

"Ai dai kin kawo tabarma tukun" tabarma tasa Shatu ta kawo tare da shimfida sannan ta kawo musu ruwa.

Zama sukayi sannan Baba yace Asma'u tasha ruwa ba musu tasha, guri ya nunawa Hari da tayi musu tsaye k'erere tana musu kallon dibar arziki, tuni jikin Asma'u yayi sanyi.

Zama tayi sannan Ard'o ya gayamata dukkan abinda ya faru, mik'ewa tayi cike da gatsali.

"Mi wagga uwar mata"................


πŸ’„ Meryerm AbdoolπŸ’„
[8/11, 3:14 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬
πŸ–€           '''ABDULMAJEED'''        πŸ–€
πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„
© *Pure moment of life writers*
P.M.LπŸ’ͺ🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readersπŸ“)

*All thankful and praises be to Almighty Allah, d one who give me chance to live and make Muslim in Muslim ummah without my knowledge,πŸ™πŸ» Patience is a key 2 every success in life,  everything come to he/she who have patient and wait in everything in life, may Allah give us d heart of patientπŸ‘πŸ½*

STORY CONTINUES BELOW

'''Alhamdulillah, mashaa Allah, after long journey and go up and down crossing over many obstacles finally I get it, I mean my NCE result, I wish my self, big success in every stage i go, thank you Allah for every blessing upon to me hidden one and d one that appear''' πŸ‘πŸ½

     πŸ“ *Episode* 121--126

"Mi! Wagga uwar Mata? Hehehe ah dole daga zuwa gaisuwar iyaye da nema, a baku aure baki d'aya, yo dama daga ganin wannan kasan neman kai ake da ita, an tsofe gida ba mashinshini  yo ai  dole, tab wayaga akwala" sannan ta juya ga Abdulrahim tare da nuna shi da yatsa.

"Tir! Amma ka bani kunya, dama akan wannan mai bak'ar huska da bak'ar kamane yassa kak'i 'yar uwarka, yo Allah na tuba wannan ai sa'a tace, to nidai bani cikin wannan kwaba taku ehe" ta k'ara sa tare da hararan Ard'o.

"Ke! Hari ashe dama haukarki da rashin hankalinki yakai har haka, ashe baki da imani bansani ba, yanzu da ace cikin d'iyanki ne hakan ta faru dasu zakiji dad'i?"

"Aa Malam yada kiramin rashin hankali da hauka daga fad'ar gaskiya? Kuma ni d'iyana tuff! Tohe musu mugun yawu, nidai nace bana cikin wannan auren, kuma ban d'auka a sirika ba ehe" tana gama fad'i ta wuce tana gunguni.

Girgiza kai Ard'o yayi "Allah ya shiryeki" sannan ya dubi Asma'u wacce tunda Hari ta fara tu'annatinta kanta ke k'asa tana zubar da hawaye zuciyarta  sai zafi take Mata "inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibatih wa'akhlilni khairun minha, oh ni Asma'u tawa kalar jarabawar kenan, ya Allah ka bani ikon cinyeta...."

"Kiyi hak'uri 'yata Kada kalamanta su dameki, kamar yadda na gayamiki zan rik'e kamar 'ya'yana, kada ki damu ba abinda zai faru sai Alkhairi" sannan ya dubi Shatu wacce duk jikinta yayi sanyi abinda uwar tasu tayi sam baiyi Mata dad'i ba, ita bataga aibun Asma'u ba, dan daga gani tafi Saude nesa, ita dama can Saude bata yi Mata, wannan saidai Lanti da suke k'awance kullum suna tare, tasan Idan taji itama sai tayi tata haukan(dake anyima Lantanar aure).

"Aisha kai matar yayanki wancen d'akin, su fara zama can kafin a Gina mata na, ni zan koma d'akin zaure" (d'akin sa ne da Abdulrahim gina mishi bada dad'ewa ba).

"Muje Aunty" mik'ewa tayi ba musu ta bita, daga Leda sai katifa, kujerar roba sai kwaba da littafan musulunci ke cikin d'akin, zama tayi gefen katifar, ita kuma Shatu ta zauna k'asan Leda "Aunty don Allah kiyi hak'uri da abinda iya tayi miki, haka take komu data haifa yimana take yi".

Murmushi yak'e ta k'irk'iro " ba komai k'anwarta ai nima uwace a gareni kada ki damu" jinjina kai Shatu tayi "lallai yaya yayi dacen mata, duk wannan abun da iya tayi mata" ta fad'a cikin ranta, ita kam Wallahi ta kwanta mata a rai, nan tayi ta mata fira dan ta kwantar mata da hankali.

"Modibbo kaje ka rarrashi matar ka, ni zan fita na samo mata abinda zataci" yace ma Abdulrahim da yayi sugum tsabar kunya da bak'in ciki abinda  uwar sa tayi.

"Baffa Aida ka Bari naje, ka huta kaima" .

Murmushi Ard'o yayi "kaidai kayi yadda nicce kawai" tare da ficewa daga gidan, shima tashi yayi ya shiga d'akin, shigarsa yasa Shatu yi mata sallama ta fita.

Zama yayi daf da ita tare da ciremata hijab jikinsa ya janyota yana d'an bubbuga mata baya Alaman rarrashi, cikin muryan rad'a ya fara mata magana "kada ki damu matata koda duka duniya zata taru ta k'iki nikam ina tare dake, bazan taba barin ki cikin kad'aici ba, zan game miki bango abin jinginawa" haka yayi ta rarrashinta da tsadaddin kalamansa na k'auna, ita kuma tai lahu a jikinsa tana saurarensa yayinda wasu kasu na damuwarta suka tafi ( hmmm k'auna kenan Allah ya had'a kowa da masoyinsa na gaskiya Ameen).

**************

B'angaren Yusuf kuwa tun ranar da Sakina ta bashi labarin Ameenah yaji wani irin tausayi da k'aunarta sun k'ara lullub'esa danshi tun ranar da ya fara ganinta a school d'in, yaji ta kwanta masa komai nata burgeshi yake musamman natsuwarta, saidai bai San ta inda zai fara ba, dan iya sananinsa da ita bai tab'a ganinta da ta kebe da namiji ba, sai shi shima d'in da sunan karatune kuma tare da Sakina, gashi shiba ya tab'a soyayya ba balle yace yasan yadda sai samota barin abin a ransa yayi kawai, saidai daga ranar kullum cikin tambayanta Abdool yake yana lafia, haka zai sayo kayan wasa dana kwalama ya bata ta kai mishi, koya kirata a waya yace ta bawa Abdool suyi hira, yaita yi masa shirme yana biye masa, ita abun har dariya Suke bata wai friends ne, dama ance mai da wawa hakan yasa ta sakance dashi wani lokaci sai sake-sake zuciyarta ke Mata game dashi saidai nan da nan take saurin ka yima Kanta fad'a akan bama zai yuyu ba.

STORY CONTINUES BELOW

Ko bayan kammala karatunsu zumunci bai yanke ba, yakan kira ko ita ta kira lokaci zuwa lokaci, ko lokacin da akayi Auren Sakina yaje Bk dan kawai ya had'u da Ameena danshi asalin d'an Koko-besse(local government ne a Kebbi) ne karatu ya kaishi Argungu.

B'angaren su Hajia kaltume kuwa tun suna saka ran dawowar Auwal shiru shekaru sun tafi ba labari hakan yasa suka fitar da rai, har anyi Auren Maryam da wani Dr, inda suka wuce Germany an turashi course, Ayuba ma ya k'ara Aure, yayi yayi da Rafia suje hospital amma tak'i tana tsoron tonon silili, Hajia kin amince tayi da Auren saboda kar abatama 'yar gaban goshinta, saida ya nace sannan ta yadda dan itama rashin haihuwa na damunta, saidai duk da haka Rafia CE ke mulkinta a gidan sai abinda tace.

_wannan kenan_

***************

Kawunnan Alhaji Abubakar sukazo daga k'auye sukayi masa tas wai ya maida d'iyansa d'iyan yahudawa, ita waccen saboda ta isa da Kanta tabi namiji ta barsu cewa da Asma'u (baki ke yanka wuya shiya kira ya fad'a musu) sannan ita kuma wanga shekararta nawa da rabuwa da mijinta ance karatu to ai tw gama, zaman me take idan ba tana bin maza ba, taya za'ace bata damu ba, cin mutunci dai inda Suke shiga banan Suke fita ba, kalamansu sun mugun b'ata ransa, amma ba yanda zaiyi iyayensa ne.

Bayan tafiyar su ya kira Ameena yace mata tayi k'ok'ari ta fitar da miji cikin masu sonta tayi Aure, amma cikin sanyi yayi Mata maganan dan shima tausayi take bashi, itakam ya zatayi bayan bamai zuwa inda take, da za'a bud'e ranta tafi son tayi Auren nan kota huta da surutun mutane, amma ya zatayi.

Cikin satin Alhaji Sada yazo dubasu shima dai maganar d'aya ce ta daure ta manta baya tayi Aure.

Kwance take kan gado tunanin abin duniya ya isheta, tana matuk'ar son aure dan itama ai rayuwa ce kuma matashiya mai cikakikiyar lafia, saidai tasan komai yanada lokaci da lokaci yayi ba makawa zatayi shi, tana rokon Allah, kuma tana da tabbacin zai ansa mata, ringing din wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunani.

Sunan Yusuf ne ya bayyana kan screen sauke numfashi tayi sannan ta d'auka, bayan sun gaisa ya tambaya Abdool daya dad'e dayin bacci yake CE mata.

"Ameena wai yaushe ne zamuzo Argungu musha biki?"

A bazata taji tambayan shima kenan ya k'osa tayi Aure? Murmushin dole ta k'irk'iro "Umm Yusuf bada dad'ewa ba inshaa Allah"

Jin sukayi gaba d'aya kowa na sak'a Abu a ransa, shikam yau ya shirya fallasa sirrin ransa gareta kota amince ko tak'i, gyaran murya yayi "Ameena" ya kirata cikin wata irin murya "Na'am".

"Inaso kiyima magana ta kyakkyawar fahimta ki d'ora a mizani mai kyau," sannan yaja hanci "maganan gaskiya Ameena I'm deeply in love with u".

" what " shine abinda ta fad'a cikin firgice, tare da katse kiran.

Kanta ta dafe "lahaulah walakuwwati, meke shirin faruwa ne, kai never yaudara kawai zaiyi...." Karan shigowa message taji, bud'ewa tayi.

_"everyone is a someone dream, and ur a my dream, pls don close ur heart to d one that is in need of u, never say goodbye 2 ur lover accept it as destiny, as I said I really love u with one heart, don't let me go astray..!"_

Tana gama karantawa kiran sa na shigowa d'auka tayi ba tare da tayi magana ba "Haba Ameena ki yadda dani da soyayya ta nayi miki alkawarin bazan cutar da ke, zan rikeki Amana da zuciya d'aya pls Ameena ki yadda dani".

" taya Yusuf taya zakace ni, koma manta nifa bazawara ce, bazawarar ma mai d'a, kaifa saurayin da bai tab'a Aure ba, to taya hakan zata kasance?"

"Haba Ameena kada ki canja daga yadda ba sanki mana, nasan ke mai ilimi CE, fiyayyen halitta da wace Mata ya fara? Nina ganki a yadda kike nace ina sonki, saidai idan sonane bakyayi daban ne, amma kima var wancen maganar.

K'aryane ne tace batason Yusuf domin ya had'a komai daya cancanci aso namiji domin shi, to amma ya  fa?.

" Koda zan amince mata saika je kayi magana da iyayenka idan sun amince maka, sannan zan amince ".

"Shikenan Ameena inshaa Allah, zanyi yadda kikeso, ki shafan kan Abdool, saida safe".

Wayar tabi da kallo, ita haka take ganin abun kamar almara, mik'ewa tayi ta d'auro alwala tahau dadduma tayi raka'a 2, sannan ta fara Addu'ar istikhara(Neman zabin Allah) kamar haka:-

_Allahumma inni astahiruka bi ilmika, wa'astagfiruka bik'udratika, wa'as'aluka min fadlikal azim, fa'innaka tak'dir wala ak'dir, wata'alam wala a'alam, wa anta allamul guyuwbu, in kunta ta'alamu anna hazal amru(saika fad'i buk'atar ka) khairun liy fiy deeniy wama'ashi wa'akibatu amri, fak'durhu liy wayassirhu liy summa barak liy fiyhi, wa'in kunta ta'alamu Anna hazal amru sharrun liy fih deeniy wama'ashi wa'ak'ibati amri, fasrifhu anni wasrifni anhu wak'dul liy khairan haisu kana summa raddani bihi._

Fassara

*ya Allah ina Neman zabinka domin iliminka, kuma ina Neman ka bani iko domin ikonka, kuma ina rok'onka daga falalarka mai girma, domin Kaine mai iko ni kuma bani da ikon, kuma kaine masani ni kuma bani da sani, kuma Kaine masanin abubuwan fake, Ya Allah! Idan kasan cewa wannan al'amari (ka ambaci buk'atar) Alkhairi ne a gareni cikin addinina da rayuwata da k'arshen al'amarina (wata rayuwar ) da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa, ka k'addara mini shi, kuma ka sauk'ak'e mini shi, sannan ka Albarka ce ni a cikinsa, kuma idan kasan wannan al'amari sharri ne, gareni a cikin, addinina da rayuwa da k'arshen al'amarina (a wata rayuwar) da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa, ka kawar da shi daga gareni, kuma ka kawar dani daga gareshi, ka k'addara mini Alkhairi a duk inda yake, ka kuma sani in yarda dashi*

(Cikin husnul Muslim take, yana da kyau komai bawa zai gabatar a rayuwa ya nemi zabin Allah a ciki. Allah yasa mudace)
Bayan ta kammala ta nad'e dadduma tare da kwantawa kan bed, tana tunanin wannan al'amarin,sannu a hankali natsuwa ta fara shigarta, a haka bacci mai dad'i yayi gaba da ita.................

_masoyana ina Neman addu'o'inku, I really in need of itπŸ‘πŸ½ ina muku fatar Alkhairi a duk inda kuke_


πŸ’„ Meryerm AbdoolπŸ’„

πŸ’„ Meryerm AbdoolπŸ’„
[8/12, 6:07 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬
πŸ–€ '''ABDULMAJEED''' πŸ–€
πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„
© *Pure moment of life writers*
P.M.LπŸ’ͺ🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readersπŸ“)

πŸ™πŸ» *From he we are, and 2 he we return, oh! Allah forgive our dead one, that find their self in absence of no one to pray 4 them, ya Allah have mercy on them, and make our dead day the day of happiness 2 us, ya Allah don't take our souls until urs happy with our souls ameenπŸ™πŸ»*
+
πŸ“ *Episode* 126--130


Koda Yusuf ya jema iyayensa bai samu matsala da yake yayi dace da iyaye masu hangen nesa, sunce tunda shi yake sonta in har anyi bincike 'yar kirki ce to su basu da matsala, amma 'yan uwansa sunce sudai basu amince ya auri bazawara ba yana saurayi dashi, saida Baban yayi musu fad'a yace "meye naku a ciki tunda a hakan yakeson abarsa, kuma ma in banda abinku, fiyayyen halitta ma da bazawara ya fara, to meye dan yace zaiyi koyi dashi idan har ba zaku bashi k'warin gwuiwa ba bai kamata Ku hanashi dan haka kar in sake jin wani daga cikinku ya soki wannan tafiyar" da haka Baban ya kwabesu dole suka hak'ura badan ransu yaso ba.

Koda ya fad'ama Ameena tayi farinciki sosai a ranta amma bata wani nuna mishi cewa kawai tayi "to yayi" sauke numfashi yayi "Haka kawai zakice Ameena tah, kamar bakya farinciki".

" um inayi mana tome kakeso ince ne".

Smiling yayi kamar tana kallon sa harda lumshe ido " cewa ya kamata kiyi yaushe zaka turo my love".

Dariya zancensa ya bata dama tasan Yusuf da barkwanci kamar me "au dariya KO, ai gara ma ki gayama Baba dan kada ayi mai ba zata, dan bazan tsaya kallon ruwa ba kwado yazo yamin kafa" nan ma murmushi kawai tayi dama Ameena ba yawan surutu...

"Um nidai bana Abdool dan naga yau miskilancin ya motsa" nan ta ba Abdool sukayi ta fira kamar wani babba dama Abdool badai wayau ba, in yayi wata magana ka d'auka fad'a mishi akayi.

Malam Sa'id mahafin Yusuf yayi duk binciken da ya dace ya kuma tabbatar da Tarbiyar Ameena, hakan yasa ya gaya ma 'yan uwansa domin Suje su nema nasa auren.

Lokacin da Ameena taje ma su Baba da labarin sunyi farinciki Sosai dama babban burinsu kenan Ameena tayi aure, shima yayi nashi bincike kamar yadda addini ya tsara, hakan yasa saka shiga cikin maganar har an tsaida rana wata uku masu zuwa.

Suma su Yusuf ba wasu masu arziki bane akwai dai rufin asiri, nan family house d'insu, aka gyara wasu dak'una biyu aka maida mata room and parlour sai toilet, ba laifi zaman dai mutum d'aya a talauce ba sarauce ba.

Alhaji Sada ma da yaji maganan Auren yayi mata murna Sosai, kuma yace ko bayan tayi Aure Abdool zaici gaba da zama gurin su Mama, dan yasha alwashin saidai in Abdool ya girma yakai Kansa Sokoto da kansa tunda dai sun nuna basa ra'ayinsa har gara iyayensa maza suna zuwa dubashi sa'in sai kuma Maryam kafin tayi aure duk da Hajia ta hanata zuwa hakan bai hana in Alhaji zaije ba, ta bishi wani sa'in kuma ta bada Abubuwa akai masa.

Cikin ikon Allah Anyi Aure lafia cikin farinciki ranar Ameena tasha kukan rabuwa da iyayenta uwa uba kuma Abdool shima dai yasha naji kukan dakyar aka banbareshi jikinta, a son Yusuf ma yaso abasu shi amma Baba yace Aa a barshi nan yayi karatunsa lokacin yana 6years yana primary 1, haka dai Ameena ta tare cikin aminci a gidan Angonta Yusuf.

STORY CONTINUES BELOW

Farkon Auren ta had'u da kalubalen dangin miji haka zasuzo suna yad'a mata magana, da yake macece mai matuk'ar hak'uri hakan yasa sam bata nuna tamasan sunayi, Amma kam surukarta suna zaune lafia, yawan kyautata Mata da dawainiya da take Mata, haka zata saka Yusuf ya d'auko kayansu ita da Abbansa su had'u su wanke su goge, komai ta dafa da nasu, suma 'yan uwan nasa da yake yayin nashi Mata ne duka suna gidan mazajensu sai dai in sunzo, shine namiji babba sai k'annin sa, hakan yasa in sukazo tana yawan kyautata musu gada Sam batada rowa ko kyashi tuni suma ta saye zukatansu(dangin miji saida kyautata ake zama lafia note women).

Taci gaba da teaching d'inta dan an samo mata transfer haka tana business d'inta, shima dai Yusuf teaching yake yana kuma zama kasuwa inda mahaifinsa da haka suka rufama junansu asiri Sam bakajin Kansu, zaman k'auna da soyayya suke dan sai yanzu tasan lallai Yusuf son gaskiya yake mata, kullum cikin tattali da nuna mata k'auna yake, Sakina ma anzo bikin tayi murna sosai dama ta dad'e tana hango son Ameena a idon Yusuf.

Tana zuwa Argungu lokaci zuwa lokaci har yanzu dai ba labarin Asma'u abin kullum yana ranta "oh ina zamu ganki Asma'u, Allah ka bayyana mana ita ka tsareta a duk inda take" kullum shine Addu'arta, Abdool na zuwa mata idan anyi Hutu.

Shekararsu 2 da Aure Yusuf ya samu Aiki a NNPC KADUNA, ba k'aramin farinciki sukayi da cigaban da ya samesu ba, haka yaje yayi interview aka bashi upper, watansa uku sannan ya dawo, nan ya gayama iyayensa zai wuce da Ameena dan an bashi gida, nan sukaje Argungu sukayi musu sallama, nan ma Yusuf saida ya tada maganar son abasu Abdool, hak'uri Abba ya basu yace kada su katse mai karatu, hakan suka wuce badan ransu yaso ba, irin kulawarda Yusuf ke bama Abdool shiyasa Ameena k'ara sonsa da ganin girmansa, haka sukayi bankwana da yan uwa da abokan arziki suka lula garin gwamna...
_safe trip_ πŸš—

~~~~~~~~~~~~
Lokacin da labarin Auren Abdulrahim ya bazu a k'auye Kilgore mutane sai tururuwa sukeyi gidan dan ganin amarya da 'yan gulma da 'yan ganin kwam, da masu yabawa da masu tsinewa, su Lanti anzo sai yatsine take dan Uwar ta kitsa mata tana yad'a bak'ak'en maganganu, Abdulrahim ko dayaji tass yayi Mata sannan yace karta k'ara zuwa gidan muddin ba abin kirki zai kawo ba, aiko iya Hari ina wuta in fad'a inda take shiga banan take fita ba, cin mutunci gaske tayi masa, wai karya kuskura ya takurawa 'yarta akan wannan korarriyar wanda iyayenta suka sallama, cin fuska dai sai Wanda ta manta, ranar Asma'u tasha kuka tare da kewar gidansu lallai kowa yabar gida ya barshi, gata ana mata gori ba yadda zatayi, hakan ya k'ara ba Lanti kwarin gwiwar yi Mata iskanci son ranta, saidai batayi in Abdulrahim nanan dan tana shakkarsa, Saude kam haukane kawai batayi ba, da taji Auren Abdulrahim haka tazo har gida tayima iya Hari rashin kunya, wai ai ita tayi mata alk'awari amma tsabar munafurci ta bari ya auri wata ba ita ba, itako Sam bataga laifinta ba saima hak'uri ta bata akan lallai zai aureta ta shigo ta biyo, tace Allah ya kiyaye ta zama ta biyu ta d'auki sauran wata, ta yafe, dama ba sonsa take ba sha'awa ce kawai.

Kamar yadda Ard'o yace haka kuwa akayi an Gina mata ciki da falo hadda bayan gida. Lol

Shanu biyu Ard'o ya Ware yayi Mata kayan d'aki a matsayin sa na uba gareta, an gyara d'aki ba laifi, nan kuma wani gorin ya tashi habaici kam tasha harta gode Allah, zuwa yanzu ta fara sabawa da cin mutuncin Iya Hari da Lanti, amma kullum abin na kona ranta bata dai yadda zatayi ne, ga uban aiki gidan da yanzu ya dawo Kanta, komai ita danma Shatu na kamata inba idon Iya Hari, dan tuni tayi Mata iyaka da Asma'u, in kaga Asma'u saika tausaya mata duk tayi baki ta rame danma ta Saba da aiki a gida da sai tafi wahala, Abdulrahim baida halin magana a balbaleshi da bala'i itama Asma'u tace ya dena magana kada ya had'u da fushin mahaifiyarsa tunda ita ta haifeshi ya zama wajibi yayi mata biyayya, Ard'o ma yayi fad'a harya gajia amma a banza da maganan sa da babu duk d'aya suka ha Hari, saidai in ya samu tanayi yace ta aje inya fita ace tazo tayi dan ubanta (oh Asma'u kina ganin rayuwa).
STORY CONTINUES BELOW

Sauk'inta Mijinta na tausasa mata da nuna mata k'auna, inta zauna sai taita tunani "wato mu haka tamu k'addarar take an jarabcemu da uwar miji, haka aunty Ameena tayi fama, ashe nata nafila ne, gwanda ita ina kusa kuma zata kira gida taji dad'i to nifa ba ko d'aya, yanzu ko sakina akayi INA zan nufa, ya Allah ka sassauto da zuciyar Baba yafemin ya mai domin da family i'm in need of them badly".

Ana hakane akayi posting nasu gurin service ita da Abdulrahim, ba state d'aya aka ajesu ba shi Katsina ita kuma Edo, hakan yasa yaje ya nemi alfarma aka maida ita Katsina, nan ma anyi rigima da Iya Hari wai ba inda zataje, k'aryane meyakai mace bautar k'asa, nan ma saida Ard'o yayi da gaske sannan ta Shafa musu lafia, zaman su Katsina zamane mai dimbin tarihi a cikin rayuwar Auren su dan sai a sannan ne suka samu nutsuwa, dama Dr gida ake bashi, so basuda matsala haka suka gudanar da service d'insu cikin kwanciyar hankali, ko marmarin dawowa basuyi,ranar da suka isa Abdulrahim ya sayomata waya nan ta kira numbobin gidansu amma ba wacce ke nan jikinta ya k'ara sanyi da d'auka kodan karta kirane yasa Baba sasu canja layuka(ba haka bane baraye suka kwase musu wayoyi dare d'aya) lokacin da suka gama zasu dawo kamar karsu dawo sukeji, haka sukayo tsaraba sosai suka dawo amma kam Asma'u ranta fal tsoro za'a koma 'yar gidan jiya.

Hakan ko takasance bayan dawowar su akaci gaba daga inda aka tsaya wannan karon hadda gorin rashin haihuwa ganin suna cikin shekara ta uku da Aure ba haihuwa, Abu dai kullum ba sauk'i sai abinda yayi gaba, gashi anyi Auren Shatu mai tausaya mata.

Cikin ikon Allah Abdulrahim ya samu aiki a uduth Sokoto hakan yasa Ard'o yace ya d'auki matarsa su koma can da zama, Iya Hari cewa tayi bak'in ciki ake mata tunda tana taya ta aiki, banza yayi da ita danya San Neman a tanka ne.

Haka suka tattara suka koma Sokoto, kuma Ard'o yayi Iya kashedin duk ta taka Sokoto bakin Aurenta, dole ta lahe dan tasan rabuwa da Ard'o babbar asarace gareta.

Suna shekara cikin ta 5 da Aure Asma'u ta samo ciki, fad'ar irin farinciki da sukayi ba'a ma magana, haka sukaci gaba da kula da cikinsu cikin so da k'auna har ya isa haihuwa inda Abdulrahim da Kansa ya anshi haihuwar zankad'ed'iyar 'yarsa me kama dashi, baki kamar gonar auduga, su Modibbo anyi 'ya, Ard'o yaje yazo dasu da sunan ayi mata wankan jego tunda haihuwar fari CE batasan makari ba, Amma abin takaici ko kallo basu ishi Iya Hari ba, anyi ba'ayi ba dai kenan dan komai Asma'u ce kema Kanta, da bata iya ba saidai ta rub'e anan, tayi kukan rashin 'yan uwanta harta gode Allah, lallai naka sai naka, da sunanan da bata wulak'anta ba, Abdulrahim ne ke kama Mata aiki sai kuwa Shatu idan tazo shima idon uwarta kamar ya tsiyaye gurin harara, Abdulrahim ko saidai tace shanyayye Mara tayi.

Haka sati ya zagayo ranar suna yarinya taci suna *Ramlah* rago biyu da sa aka yanka, Abdulrahim yayi k'ok'ari dan yayi musu komai na goyo tsadaddi Hari ko sai yad'a magana anyi Aure ba dangi haka suna ma, Abu sai kace mayya, ita Kanta Asma'u abun na matuk'ar damunta, dan Abdulrahim yasha cewa ta bari suje Argungu suba Baba hak'uri, sanin halin mahaifinta na kaifi yasa tace cewa Aa su jira dai(tab aiya canja duniya ta horashi) lol.

Tun kan suyi arba'in ganin wahala tayi ma Asma'u yawa, balle Abdulrahim ya kawo sai k'arshen sati yake zuwa yasa, ga dawainiyar kula da kai da jaririya gana gida yasa Ard'o yace ya d'auketa su wuce kawai, duk k'arshen sati Abdulrahim na zuwa duba iyayensa, idan Asma'u bata zo ya zama abun zagi idan taho ma aci Mata mutunci.

Abdulrahim arziki sai bud'ewa yake tana ganin haske saboda biyayyar iyaye da yake, ga kulawa da iyalinsa da yakeyi, har Saudiya ya biyama Ard'o da Iya Hari, amma Iya cewa tayi ya bata kud'in kawai (hasararriya Mara rabo) Ard'o kam ya k'ara tsorata da lamarin Hari, haka ta kashe su a banza.
~~~~~~~~~~
B'angaren Ameena da Yusuf kuma zaman su lafia lau gwanin sha'awa, kowa na kaffa,-kaffa da d'an uwansa, tare suka kowa makaranta inda take karantar Botany (ilimin tsirrai) sam rashin haihuwar bai tab'a dagama Yusuf hankali ba, shine ma mai kwantar Mata da hankali, idan tana nuna damuwarta, yace "haihuwa ta Allah ce idan sunada rabo zasu samu idan babu Abdool ya ishesu".

STORY CONTINUES BELOW

Suna shekara 4 da aure ta samu ciki, murna sosai sukayi da kyautar da Allah yayi musu, wata tara cip ta sunbulo 'yarta mai kama da Yusuf sak, a Besse suka koma akayi suna inda yarinya taci sunan mamar Yusuf Aisha suna kiranta Nihal, mutane Argungu anzo an kwashi shoki!

Musamman Abdool daya zama dan samari sai murna yaks yayi k'anwa.........

*lol every body a kame kam sabuwar rawa πŸ•΄πŸΎπŸ•΄πŸΎπŸ•΄πŸΎπŸ•΄πŸΎ*

_kuyi hak'uri Dani friends abubuwan ne da yawa #one love# 😍_


πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„
πŸ‘ŒπŸ»πŸ˜‰
[8/16, 8:27 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬
πŸ–€ '''ABDULMAJEED''' πŸ–€
πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
πŸ’„ _Meryerm Abdool_ πŸ’„
© *Pure moment of life writers*
P.M.LπŸ’ͺ🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readersπŸ“)

'''Manzon Allah (S.A.W) yace ma wani yaro:- kayi bismillah(idan zakaci abinci) kaci da hanun damanka, kaci daga abinda ke gabanka.'''

_Ladubba ne nacin abinci mu kiyaye sannan mu koyar da yaranmu_ Allah yasa mudaceπŸ™πŸ»

*Ina mai farinciki da wannan Auren da kikayi Aunty Kausar (kausar M Hasan) Allah ya sanyawa aurenki Albarka tare da zuria dayyiba Ameen #HMLπŸ’*
_Ina mik'a ta'aziyya ga Feedo Deedo (marubuciyar mamata gimbiyata) akan rashin mahaifiyarta da tayi, Allah yayi mata rahama yasa mutuwa hutuce ameen, Ku kuma Allah ya Baku hak'urin rashin da kukayiπŸ‘πŸ½_


πŸ“ *Episode* 131-135


Bayan sunyi Arba'in sukaje Argungu ganin gida da kai musu jaririyar su gani, lokacin da Ameena ta shiga d'akin su, nan taga wasu kayan Asma'u wad'anda ba'a kyautar ba, batasan lokacin da hawaye ya wanke mata fuska cikin jimami take magana "Asma'u kina ina? Tsawon shekara biyar kenan, Asma'u kina lafia kuwa? Kina cikin farinciki ko sab'anin haka, Asma'u kizo gida mu ganki wlh Baba Neman ki yake ruwa a jallo, pls Husnatah sisto na friend dita ever kizo garemu muma buk'atar ki" cikin kuka tace maganar gwanin tausayi, kullum safiyar duniya kira gida maganarta kenan Asma'u tazo, Mama dake tsaye bakin k'ofa rik'e da Nihal dake motsi alaman yunwa dan tunda suka zo take sharar bacci abinta, Abdool na kusa da ita sai kallon ta yake ya tab'a nan ya tab'a can yana matuk'ar son k'anwar tasa, ko yanzun ma Baba ne ya kirashi suka fita.

Itama hawaye take daga nan tsaye, ita ta haifesu gaba d'aya, amma tasan akwai shakuwa mai girma a tsakaninsu sau da yawa idan matsala ta taso a tsakaninsu suke maganceta ba tare da ta sani, saidai idan tafi k'arfin su suka kawo mata, to ya zasuyi k'addara ta riga fata, saidai su bita Addu'a Allah ya k'are ta aduk inda take ya dawo musu da ita lafia, share hawaye tayi kada ta rauna nata.

K'arasawa tayi ciki tare da kamata zuwa bakin gado, cikin muryan rarrashi da tace "Ameena kuka bazai dawo da Asma'u ba, Addu'ar mu kawai take nema, kiyi hak'uri ki daure ki daina kuka kiyi mata Addu'a" haka tayi ta rarrashinta daga k'arshe ta bata 'yarta data fara kuka tare da ficewa cikin sanyi, dan ganin Ameenan kad'ai tuna mata da Asma'unta yake yi.
*****************

Satinsu d'aya a Argungu sun zaga dangi sosai har birnin lafia sunje, gidan Firdausi duk taje, Abdool kuwa kullum yana rik'e da Nihal har goyata yakeyi Mama tayita zolayarsa, da sunan mati sai cewa yake ai k'anwarsa CE, a satin Yusuf yazo nan ya dage da rokon Baba ya basu Abdool su wuce dashi tunda ya k'are primary, ganin sun dage kuma yaga shima yaron yana buk'atar uwarsa a kusa dashi duk da suma ba abinda basa yi masa amma d'a sai uwarsa, kuma ya yaba yadda Yusuf d'in ya nuna kulawarsa akansa, yanada tabbacin zai rik'e sa da Amana, amma duk da haka saida ya kira Alhaji Sada ya shaida masa abin da sukazo dashi.

STORY CONTINUES BELOW

Kai tsaye Alhaji ya amince dan yasan waye Ameena yasan zata bashi tarbiyar da ya dace, shi kanshi yaron zaifi jin dad'i gashi ga uwarsa, nan Baba ya basu Abdool sunyi murna Sosai bakin Yusuf ya kasa rufuwa danshi harga Allah yana son Abdool yana jinshi a ranshi kamar yadda yakejin Nihal.

Ban kwana sukayi ma Argungu garin nabame kowa sarki, sannan suka wuce Besse anan ma sam dangin Yusuf basu nunawa Abdool wata fuska k'ama ko wulak'anci ba, Wanda hakan yayima Ameena dad'i sosai, daganan suka shirya tsaf suka lula Kaduna.....

Zamansu kaduna zamane mai cike da k'auna da kulawa da yaran su sosai Yusuf ke kula da Abdool kaman ma yafi sonsa akan Nihal, dan Ameena cewa take Nihal ce babynta shi kuma yaron Dady, tare suka zuwa masjeed kullum muddin yana gida, haka zai baje a parlour yana mishi lesson don tuni suka sakashi secondary wata private, muddin Yusuf na gida to yana tare da Abdool hakan ba k'aramin dad'i yakewa Ameena ba, hakan ya k'ara wanzar da zaman lafia a familyn.

Sannu a hankali rayuwa taci gaba da shurawa kwanaki na tafiya, Nihal nada four years Ameena ta k'ara haihuwa wannan karon twins ta haifa mace da namiji, nan Ameena ta roki Akan a sakama macen sunan Asma'u hakan kuwa akayi inda ake kiranta da Husna namijin kuwa Abduljabbar, zuwa yanzu Yusuf ya gina musu gidan Kansu a unguwar K/mashi inda Ameena ta k'awata gidan da kalolin furanni masu dad'in k'amshi ga kuma garden had'adde Wanda ya k'unshi kayan more rayuwa, kai da ka taho gidan ba tambaya kasan ka taho gidan miss Botany tun farfajiyar gidan zaka fahimci haka.

Abdool yana SS1 Nihal na nursery, tuni ya saba da saka medical d'insa inda a school d'insu wasu ke ganin jin kai ne da tsabar raini dan yaga yanada Brain yasa yake saka glass dan sauka haka kawai yake sakawa ganin yadda ya zauna mishi tsaf, Abdool ya taso yaro mai kuzari da sanin ciwon kai ga k'auna da yake nunawa kanninsa haka sai saka Nihal gaba yayi mata lesson in Dadynsu bayanan shi kuma inya dawo yayi mishi, shi har mamakin k'ok'arin Abdool yake yaro sai kace dan Jamia komai kana ana bud'e kwakwalwarsa ana zuba masa, ita ma dai Nihal Kanta naja ba laifi sai yake danganta hakan da ilimin Ameena, haka sukaci gaba da gudanar da Rayuwarsu cikin farinciki, sukanje Hutu lokaci zuwa lokaci haka Alhaji Sada na zuwa har Kaduna ya dubasu, yanajin dad'in yadda suke kula da Abdool, tuni Alhaji ya saba da Yusuf haka zasu zauna suyi ta hira in yazo dama ga Yusuf da barkwanci wuni guda kukayi a tare zaku Saba.

*****************

Ranar rabuwa ranar da zukata suka nisanta da juna ranar ruhi da gangar jiki suka shiga maraici ranar da mai rabawa ta raba, ranar da Yusuf yayi accident a hanyarsa ta dawowa Kaduna ya fito daga Besse anan on d sport wuyansa ya kare nan take ya ansa kiran maliccinsa, sai gawa su Ameena suka gani fad'in kalan tashin hankalinda suka shiga anan dan page d'in ga bazai ishemu ba, kowacce ta kwatanta da mijinta ne da babanta ne da d'anta ne da k'annin ta ko yayanta ne ya zataji haka suma Familyn Yusuf sukaji da rashin da ya sameso, a Besse aka wuce da gawar akan kayi komai daya dace da shari'ar sunnar Manzo S.A.W, ba'ayi wani zaman makoki ba, duba da yadda zaman ya koma zaman hira da tsegumi da cin shinkafa, Wanda ya mutu shiya mutu kawai sai kuwa na kusa dashi, da suke cikin jimami rashin sa, duk wannan abun Abdool baida labari dan lokacin yana ABU zariya inda yake matriculation, Wanda Yusuf ne da kanshi ya kaishi ya kuma zaba mishi medicine, ganin yanata kiran Dadyn nashi wayanshi bata zuwa yasa ya kira Maminsa, nan ta sheda mishi suna Besse ba charge a wayansa, sannan tace idan da chance ya samesu Bessen k'arshen sati, nan ya tambayeta lafia dai tace qlau ba komai, amma jikin na bashi ba lafia.

Lokacin da yazo ya samu abinda ya faru, yayi kukan rashin Dady dan sosai ya maye masa gurbin Auwal yanzu gashi ya tafi ya barsu.

(Duniya labari)
Anan ta zauna harta kammala takabanta, akayi rabon gado kamar addini ya tanadar daga an kammala hada komai, tayi sa'a gidansu na Kaduna ya shigo cikin rabonsu hakan yasa tace zata koma Kaduna, sun so tayi zaman ta nan tare dasu dan Ameena mutum ce wacce kowa ke sha'awar zama da ita, saboda iya zamanta da mutane da kyautata,tafi so koda zata cutu ne wani yaji dad'i amma batason wani ya cutu akanta, hak'uri ta basu saboda ta riga ta saba da Kaduna ga kuma karantun yara (weather ma akwai banbanci sosai tsakanin Kebbi da Kaduna) haka taje Argungu tayi musu sallama nasiha sosai Baba da Inna sukayi mata duk da susan Ameena zata tsare mutuncinta aduk inda ta riski Kanta, sannan ta wuce da Mansur d'an yad'an rage mata kewa, da yake Abdool ya koma Zariya saboda karatu, shima Mansur ya kammala NCE inda zaiyi degree a can.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan komarsu ta shiga neman aiki tuk'uru, shine amfanin ayi karatun koba mutuwa akwai sayin yanayi Wanda miji zai nemi agajin matarsa musamman ma inga nauyin iyali, cikin sa'a ta samu aiki ministry of Agriculture inda zata ringa basu shawarwari akan dashen itatuwa da fulawowi da dai duk wani dangin tsirrai, haka kuma gefe d'aya ta bod'e nata gidan koma inda ita kula da abinda sai Mansur da wasu matasa data d'auka take biyansu, in fact dai ita keda mallakinsa nata ne, ga business tana yi da tana bada odar kaya daga Dubai, Alhamdulillah, tafi k'arfin buk'atunta dana yaranta, yayin su kuma ta saya musu shares da gadon su ana jujjuyawa a Ja'iz bank inda suka halattacen kasuwanci da kud'in.

Wata rana in ta zaune sai tayi ta tuna maganganun Yusuf da yake cewa "Ameena ko a yanzu nabar duniya bana shayin Wanda zai kulamin da yara na da tarbiyar su, saboda nasan zaki iya ke namijin duniya ce, wacce kowane namiji ya sameki zaiyi alfahari da ita, ina k'aunarki Ameena har numfashi na, na k'arshe" ita kuma idan yana fad'ar haka saita rufe masa baki tace.

"Ba zaka mutu ba mijina kai kad'ai inshaa Allah saidai mutuwa ta doke mu tare bana fatan ka barni a duniya ni kad'ai, pls ka dena fad'ar haka" murmushi kawai yakeyi ya canja zance, gashi yanzu tana tunawa shikenan ya tafi ya barta, nema masa gafarar ubangiji take dan shine kadai ya rage a tsakaninsu yanzu, ga zawarawa sunyo mata caa abokan Yusuf da abokan aikinta itakam hak'uri kawai take basu, yanzu kam renon marayun yaranta ne a gabanta bata sake jajibo wani Auren ba, ko iyayenta da sukaji sun goyi bayanta dan yanzu tasan meye mai amfaninta da Wanda baya amfaninta...

Ciwo ne ya tasowa Alhaji Sada da gaske har anyi admitting nashi hospital, hakan yasa Abdool zuwa kiran Maminsa akan zaije ya dubasa, sosai ta tausaya masa itama taso taje ta dubasa dan Alhaji kamar ubane gunta ga kirki, har Besse yaje mata gaisuwar Yusuf, amma kuma tana tsoron yadda familyn zasu karb'eta, tsoron abinda zaije ya dawo yasa ta fasa zuwa tace Abdool ya gaishesa sosai.

Alhaji yayi murna sosai da zuwan Abdool Wanda shine na farko tun bayan rabuwar iyayensa haka 'yan uwa da iyayensa maza ga su Isma'il sa'anninsa ga kuma k'anninsu gida ya cika sosai sa zuria, Hajia tunda ta ansa gaisuwarsa a dak'ile bata koda kalli inda yake ba, dan ita har yau haushinsu takeji shida uwarsa, Rafia kowa sai wani son munafurci take nuna masa amma shi Sam bata kwanta masa a rai ba tunda ya ganta(INA kuwa kaga shedan mai raba aure).

A tare dashi akayi jinyar Alhaji har murmure, aka sallamesu a part d'in Alhaji ya tare wadda hakan yasa ta daina shigowa, satin sa 1 yace zai koma saboda makaranta, nan Alhaji ya d'auko wasiyyar mahaifinsa ya danka masa, d'akin da ya zama NASA a part d'in Alhaji ya shiga ya, direct da diary ya fara.

_"zuwa gareka d'ana abin Alfahari sanyin idaniyata, kayi hak'uri d'ana nasan koda wasik'a ta zata sameka, zakace banyi maka adalci ba dana barka tun bakasan waye kai ba, nasan zaka zargeni da tauye maka hakk'inka, saidai ina da tabbacin Ameena zatayi dutyn ta ta kuma had'a da nawa tayi, saboda na yadda da ita"_

Hawayen da suka zubu masa ya share tare da cewa "wannan hakane Abba Mami mace tamkar dubu" sannan yaci gaba, duk wani labari tun daga had'uwarsu da Ameena auren da k'uncin da ta shiga da soyayyar da Asma'u ta nuna masa har zuwa rabuwarsu saida ya rubuta masa, zuwa yanzu kuma yake harda majina yana tausaya iyayen nasa, tare dajin k'ara son aunty Asma'u dayi mata Addu'a akan Allah ya bayyana ta, sannan yace "Abba banga laifinka akan komai ba sai akan tafiyar ka meyasa Abba? Meyasa zaka tafi ka barni, shin kayi tunanin rayuwar da zanyi? Meyasa ka guji mahaifarka kabar iyayenka da begenka, kana ina Abba!? Where r u Abba??" Ya fad'a da k'arfi cikin sheshekar kuka.

Alhaji Sada ne ya shigo jin k'aran sa, yasan za'ayi haka duk baisan mai wasik'ar ta k'unsa ba, dagoshi yayi tare da rungume shi yana dan bubbuga masa baya, alaman rarrashi "yi Hak'uri Abdulmajeed ka d'auke shi a matsayin k'addarar ka, ka yafewa mahaifinka tare da masa fatan Alkhairi kaji" rarrashinsa yayi da kalamai masu kwantar da zuciya....

STORY CONTINUES BELOW

A ranar yaje banking, ya girgiza da ganin tsabar kud'in da mahaifinsa ya aje, masa kud'i bana wasa ba, tun lokacin bare kuma yanzu da komai ya canja, (Allah ya zuba Alkhairi a harkar kasuwanci, don abinda annabawansa sukayi Kenan, muddin bawa zai tsarkake sana'arsa tabbas zaiga akhairai a ciki).

Transfer kud'in yayi zuwa account d'insa, nan ya nemi shawarar Alhaji akan yadda zaiyi da kud'in dan kud'in da yawa kuma shi baya da buk'atar kud'i dan Alhaji ne ke d'auke da karatunsa yanzu tun bayan rasuwar Yusuf, kuma shima yana dan business dan Abdul yarone da yasan ciwon kansa, ko lokacin da yake Argungu shik kula shagon kawu Mansur in ya shiga school kuma tsab zai dawo ya isko kayansa, haka Mami na turo mishi sosai duk da yana cewa ta barshi.

Alhaji shawarar a fara Gina mishi hospital ya bashi tun da medicine yake karantawa, hakan kuwa akayi dan itama Mami hakan tace nan suka sayi fili mai kyau aka fara tsara hospital ta gani a maganta inda kawu Mansur ke kula da ganin da yake yana gari.
*****************
B'angaren Asma'u kuwa yanzu bata da wata matsala dan ba'ayi mata sai in taje Wanda zuwa yanzu ta Saba da jarabar Iya Hari, Abdulrahim kuwa ya rik'e ta da Amana kamar yadda yayi alk'awari suna zaune lafia abinsu bakajin Kansu ko sabani suka samu suke shirya Kansu ba tare da wani yaji ba, Ramlah kuwa sai girma take abinta ga kulawar iyaye tana samu suna matuk'ar kula da ita da bata tarbiyar islama, tuni ta iya haruffa k'ananan surori tana 4 year, er lukuta da ita yanayin jikin irin na Asma'u ne, nan kad'ai suke kama.

A 'yan kwanakin nan mafarkin su Baba da Inna da Aunty Ameena, Abdool ya matsawa Asma'u har yakai ko kwanciyar rana tayi sai tayi, hakan yasa hankalinta ya koma gida baki d'aya, yanzu kam ta shirya runkarar Baba duk da tsawon lokaci bai nemata ba, amma tana fatan idan taje ya yafeta ya maida mata iyalanta, hakan yasa ta tunkari Abdulrahim da maganar son zuwa gida, hakan yayi mishi dad'i sosai dama ya dad'e yana bibiyarta suje tana cewa ba yanzu ba, suka tsara zasuje k'arshen sati.

Da sukaje Ard'o da zancen yayi murna sosai, dama shima ya dad'e ya maganan zuwan, iya Hari ce sai tace taje ita kad'ai da 'yarta amma bada d'anta garin mayu ba, nan ma Ard'o yayi mata fad'an ta daina haka aiko su waye an Riga an zama d'aya tunda ga zuria anyi dan Asma'u na d'auke da wani cikin Wanda harya fara fita.

Koda suka tashi tafiya suka nemi Ramlah suka rasa 'yar gidan Lanti ta shiga gari da ita daga zuwansu hakan yasa sukace zasu wuce, Ard'o yace suje in yaso idan sun shawo Kansa sai su je gaba d'aya hadda su, iya Hari tace bada ita ba gaisuwar uwar kishiya. Lol

Tunda suka d'auki hanya zuciyar Asma'u ta tsinke, tunanin ya zasu k'arke da Baba, tuni ta fara zubar da hawaye, hakan ne ya tada hankalin Abdulrahim ya shiga lallashinta sam hankalinsa ya koma gareta baiji odar da ake masa sai da yayi gab da motar nan ya taki birki da k'arfi Wanda yayi sanadin suka yanke daji, duk sun rud'e ya rasa makama ba abinda ke fita bakinsu sai "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" kiiiiiiii!! Kakeji sun bugi katon icce Wanda yayi dai2 da kamawar motar da wuta....

Koda ja'ama sukazo saidai gawarwaki amma abin mamaki wutar bata kai cikin motar ba so bata k'onasu ba, amma kuma ba rai a tare dasu.

_subhanallah such is life, Allah yasa muyi kyakyawan k'arshe_
Ta hanyar id card jami'an tsaro suka gane garin su, sai gawarwaki aka dawo ma su Ard'o dasu abinda bai wuce 1 hour da rabuwarsu, Allah sarki Ard'o dattijo mai nutsuwa, duk da hankalinsa ya tashi amma sam nutsuwa bata bar jikinsa ba, shida Kansa yayi musu wanka, aka sallacesu dashi aka Sada su da gudansu na gaskiya Wanda kowa sai yaje komai daren dad'ewa.

Iya Hari fa? Sai ihu take zunduma tana fad'ar maganganu na sab'o da rashin hankali, some some ko ba iya sai dai duk a banza dan wannan duk bazai dawo dasu ba, haka aka zauna zaman makoki, mutuwar Abdulrahim ta tab'a gaba d'aya k'auye Kilgori da kewaye dan kowa yasan shi yasan Alkhairinsa da taimakonsa, haka itama Asma'u ga tausayin ta na bata samu ta sadu da iyayenta ba, rayuwa kenan ga Ramlah marainiyar Allah kowa ya kalleta saiya zubar da kwalla, sai Neman Ummi da Abi take tana kuka gwanin tausayi.

Iya Hari tayi sanyi dan mutuwar Abdulrahim ta tab'a sosai d'anta mai biyayya gareta mai kyautata mata, dama sai babu kai ake gane kirkinka ko rashin sa.

Bayan sati d'aya Ard'o da kanshi yaje Sokoto ya tattara duk wani Abu nasu akazo akayi rabon gado, na Ramlah dana dangin mamarta, sokoto jaye ya bud'e account ya zuba su, sannan ya boye duk wani Abu da yake mai Amfani ne gareta, dan yasan Hari ladabin kura ne tayi, hakan kuwace ta kasance dan tunda kafafu suka d'auke ta tada mugun halin ta, har cewa tayi Asma'u takai mata d'a garin 'yan shan jini an shanye(sai kace ita bata mutu ba amma kuma Abu ga jahili ayi mata uziri) tsabar uwar sai tattaro ta dawo kan 'yar bata mata komai na dangin wanka, wanki da duk wani Abu, duk Ard'o ne keyi mata saiko Shatu in tazo kota aiko a ansa, amma iya Hari da Lanti zagi da duka ne kawai ke had'a su, haka ta kashe kayan Ramlah ta bawa yaran Lanti dan tasan Shatu kota bata bata ansa daga k'arshe ta bita da guntuwar nasiharta, tun Ramlah bata fahimtar komai ta gane Iya Hari bata sonta tun batasan meye zagi ba da duka ba harta k'ere dasu, kullum magana Ard'o keyi amma a banza bataji sai abinda ya k'aru, tuni sunanta ya koma Laure abinka da k'auye, Ard'o ne kawai ke kiranta sunanta na asali, tun tana fad'a har saba itama saidai Sam batasan sunan.

Ganin wahala na shirin kashe k'aramar yarinya yasa Ard'o zuwa Argungu kozai gane dangin mahaifiyarta ya hadata dasu amma shiru ba labari haka zaije tun safe har marece ba sa'a haka yake dawowa cike da tausaya mata, duk wani aikin gidan Ramlah ke yinsa ga zagi da duka kamar ganga, talla kuwa tafi kowa a garin safe rana dare aikin kenan, wahala kawai ta sani a rayuwarta, duk Ard'o na iya k'ok'arin amma anfi k'arfin sa ne, dan da maganar da babu duk daya ga Iya Hari.

Haka ya sakata boko, ta fara kamar abin kirki, tana aji hudu Hari ta tada k'ayar baya, ita batasan ta famdare mata kamar yadda ubanta ya famdare akan boko, haka tanaji tana gani ta fidda ta, saida Malaman makarantar suka suka gayama Ard'o dan Ramlah na cikin d'alibban da sukeji dasu saboda hazak'arta, yace suyi hak'uri, amma Iya tayi mirsisi ta hana, karshema sai dukan tsiya yaja mata dole ta gayamai bataso da Kanta, yasan ba yin Kanta bane amma ya kyaleta dan yasan tunda Hari bataso to magana ta k'are, haka Ramlah ta tashi cikin wahalar rayuwa ga Ard'o da Gwaggo Shatu kawai take jin dad'i, haka take rashin iyaye tasan da sunanan da bata tagayyara ba, suma dangin mahaiyarta kullum fatar ta Allah ya bayyana mata su, Ramlah kenan, yarinya k'arama taga rayuwa......
*ASALIN LABARIN KENAN*

MUJE ZUWA YANZU MUKE FA🀸🏻‍♀🀸🏻‍♀⛹🏾‍♀🀾🏻‍♀
_yan uwa wad'anda suka damu da rashin ganina suka bincikani nagode sosai da kulawarku, kuma na samu lafia sosai saidai mura ta rage🀧 #one love#_

Post a Comment for "ABDULMAJEED CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...