Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZABIN SAMHA CHAPTER 15 KARSHE

ZABIN SAMHA CHAPTER 15 KARSHE

- - Post a Comment

 ZABIN SAMHA CHAPTER 15 KARSHE


Samha muryanta na rawa tace " nan fa kitchen ne ya kakeso tayi? Knocking zatayi kafun ta shigo ko meye? ".


Tsaki Sabah ya buga cike da jin haushi ya juya ya fice daga cikin kitchen din.

Ajiyar zuciya Samha ta sake nan take ta nema yunwar ta rasa ta ajiye the plate din abincin a gefe ta fito. Ko data fito bata ga kowa a parlourn ba ta soma kwadawa sophie kira, taji shiru ba'a ansa ba. Haurawa sama tayi tunani kala kala na mata yawo aka don tasan yarinyar ba fada zatayi ba. Amma toh da Ammi ce tazo ta tadda su a hakan fa? Ya zasuyi? Nan take ta tsinci kanta cike da tsananin fargaba.


Da dare misalin karfe bakwai da rabi suna zaune kan dining suna cin abincin dare gabada'yansu sun halara. Anty Fanneh da Abbah suketa faman hiransu banda Sabah da Samha da sukayi shiru suna sauransu. Sabah sai faman latse latsen waya yake Samha tanata satan kallonsa ta kasan idanunta. Suna cikin haka taji wayarta tayi vibrating kusa da ita allamun sako ya shigo. Daukowa tayi ta soma dubawa.


Sako ne daga Sabah kamar haka "ki sameni a daki idan mun gama"


Tana gama karantawa ta da'go ta dubeshi, taga still idanunsa na kan waya, ta tura mishi da reply din toh.


Abbah ne ya soma fadawa Anty Fanneh cewa ya kamata babynan aje America a haifesa ya samu full citizenship. Dariya kawai Anty Fanneh tayi tace ita dai abarta anan babu wani kasan wajen da zataje ta haihu. Sosai suka zurfafa Abba nata tsokanarta kamar wasu sabbin aure ko kula dasu sabah basuyi ba. Sabah ne ya fara mikewa yayi musu sai da safe sa'anan ya haura sama zuwa dakinsa.+


Sophie tazo ta soma tatara dining, Samha itama ta mike tayi musu sai da safe sa'anan ta haura sama zuwa dakinta. Bayi ta fada taje tayi tayi wanka ta dauro alwala sa'ananta fito tayi Sallan ishah hade da shafi da wutr. Bayan ta idar ta mike ta shafa mai da humran ta mai dadin kamshi sa'anan tasa kayan baccinta ta zira hijab sa'anan ta fito tayi hanyar dakin Sabah.


Yana zaune a gefen gado daga shi sai bakin wando a jikinsa yana aiki akan system, yaji tayi sallama ta shigo. Dagowa yayi ya zube mata manyan idanunsa yana kallonta ya ansa sallamar. Ganin ta tsaya bakin kofa taki karasowa ciki ne yasa ya da'ga mata gira daya hade da fa'din "mallama lafiya kika tsayawa mutane a bakin kofa haka?"


Still bata tanka shi ba tana tsaye tana jinsa. Ajiye system din yayi a gefe a ransa yace "yan rigimar na kusa kenan". Yana tare da Samha tun bai san yanda ake rarashin mace ba har yazo ya koya tsabar iya shagwabanta, akanta ne kadai ya tsinci kanshi da iya tolerating shagwabar mace, shi ada da ko kallo mace bata isheshi ba idan tana abunta amma sai gashi yanzu ya tsinci kanshi da mikewa yasoma takowa har yazo ya tsaya inda take.


"Menene?" Taji ya tambayeta ha'de dasa hannu ya da'ago habarta yana kallon cikin kwayar idanunta.


"Ba komai" ta fada mishi tana kawar da fuskarta gefe.


Hannunta ya riko cikin nasa sa'anan ya karasa bakin gadon da ita ya zaunar da ita kan laps dinshi hade da kwantar da fuskarta bisa kafadarsa har tana iya shakar daddaden kamshin jikinsa. A hankali ya soma tambayarta. "what's wrong baby? Wani abu kikeso ne?"


Girgiza mishi kanta kawai tayi.


"Toh menene?"


A hankali ta soma motsa lips dinta tace "dazun da muka fita dasu Khadie na hadu da Jabbar a mall. Meyasa baka sanar dani cewa zai koma can kasar mahaifiyarku da zama ba".


Ajiyar zuciya taji ya sake, ya lumshe idanunsa a hankali sa'anan ya budesu can taji ya soma fa'din " na hadu dashi last week, naje can gidan doctor Sageer inda yake da zama. Abba yace mun naje na dubashi".


"Toh meyasa baka fada mun ba? Sabah meyasa bakasan discussing anything family related dani, aside from being your wife nima fa yar'uwarka ce yanzu. Bana jin dadin yanda kake boye mun wasu abubuwan. Kuma inaso ka dinga jan yan'uwanka a jiki, zumunci nada matukar muhimanci, ga mahaifiyarka ma ban taba jin ka dauko mun batunta ba. Ban san meyasa ba. Dan Allah ka dinga kokari kana zumunci da ita".


Shiru Sabah yayi yana sauraronta tana expecting taga yayi fushi ko ya mike amma sai taga akasin haka. Mamaki ne ya cikata data ji yace "toh baby, i'll try Insha Allah".

Nan take kuma taji dadi a ranta jin yace zai kokarta, at least it's a step.


Shiru ne ya ziyarce su daga bisani tace

"Me kakeyi ne?"

"Ina aiki akan System ne, akwai wasu documents da Abbah ya bani inyi musu creating a websites kinga tun dazun naketa fama." Ya fada yana kara janyota jikinsa, shiru tayi daga bisani tace "Sabah haka zamu cigaba da irin wanan zaman? Muna cigaba da boyewa iyayenmu. Wlh kullum cikin fargaba nake, kwata kwata hankalina ba'a kwance yake ba musamman idan na tuno da cewa at anytime asirinmu zai iya tonuwa".


Ajiyar zuciya ya sake yasa hannu yana shafo smooth face dinsa don shima abun yana ransa. "Baby, ni kaina i've been thinking about this don na gaji da boye boyen nan, amma Amminki nake dubawa. A halin yanzu bata bukatan wani abu tazai tayar mata da hankali, why not mu bari idan Allah ya sauketa lafiya koma meye sai a sanar dasu?"


Shiru Samha tayi tana sauraronsa tana jin yanda kirjinta ke tsananta bugu. Bayanta ya shiga shafawa a hankali yana mata rada a kunne akan ta kwantar da hankalinta ta daina haddasawa zuciyarta tunani babu abunda zai faru insha Allah iyayensu zasu yiwa auren sirrin nasu kyakyawar fahimta. Sai daya tabbatar da tayi relax sosai ta saki jiki tukuna ya soma yawo da hanyensa bisa sansar jikinta don a bukace yake da ita, idan bai sameta ba bazai taba samun nutsuwa ba. Hannu yasa ya cire hijab din data saka ta saura daga ita sai kayan baccin data saka mai bala'in tsantsi daya tsaya mata iya gwuiwa very transparent kana iya hango every part of her sexy body. Idanunsa ne suka shiga yawo bisa sansar jikinta yana kare mata kallo tun daga sama har zuwa kasa da idanunsa suka sauka kan dukiyar fulaninta wanda ko bra bata sanya ba, nan take jikinsa ya hau tsuma yanayinsa ya soma canzawa yaji babu abunda yake bukata a lokacin sai ita. Gyara zamanta yayi akan cinyarsa ya juyo da ita suna fuskantar juna ya shiga kissing wuyanta zuwa saman boobs dinta dayan hannunsa yana yawo dashi kan slim waist dinta har ya gangaro zuwa ass dinta ya shiga mamatsawa a hankali. Wani irin dadi ne taji ya ziyarce duk gabadaya illahirin jikinta ta kara kankameshi a jikinta tana nishi, don har ta soma fita hayacinta tun basuyi nisa ba. Kallonta kawai yakeyi idanunta a lumshe yana mamakin yanda take saurin responding ga touches dinsa a duk sanda ya tabata koda basuyi zurfi ba. Ji yayi itama ta soma mayar masa da martani tana yawo da hanayenta bisa lalausar fatar jikinsa ta sunkuyar da kanta tana kissing duk inda taci karo dashi a jikinsa har ta gangaro zuwa face dinsa ta bude idanunta a hankali suna kallon cikin kwayar idanun juna dake cike da zallan sha'awa da mugun bukatuwa da juna.

A hankali ta kai lips dinta ta soma kissing gefen fuskarsa sa'anan tazo ta  hade bakinsu wuri da'ya suka soma tsotsan lips din juna, sosai suka zurfafa yana kissing dinta itama tana mayar masa da martani, tasa hannunta cikin lalausar sumar kansa tana cakudawa a hankali whilst kissing him. Kasa jurewa Sabh yayi ya juyar da ita suka fada kan gadon tare ya soma rabata da kayan jikinta yana cilli dasu ita kam sai kara shigewa jikinsa takeyi tana shafa chest dinsa. A hakan suka cigaba da aikawa juna zafafan wasani masu rikittar da kwakwalwa sai faman nishi sukeyi suna sumbatu, sai da suka gama gamsar da junansu komai ya lafa a tsakaninsu ya mike hade da ruko hannunta suka fada bayi sukayi wanka sa'anan suka fito tare makale da juna.

Ko da suka dawo suka kwanta can cikin dare Sabah ya sake tashinta suka sake fadawa don shi indai tana tare dashi baya gajiya da ita. Sai wuraren karfe uku na dare ya hakura ya barta lokacin ta gaji sosai kuma bacci ya soma cin karfinta ya dauketa cak ya kaita dakinta ya kwantar da ita kan gado yana gyara mata kwanciya ya manna mata kiss bisa goshinta sa'anan ya fito daga dakin ya rufo kofar shima ya koma dakinsa.


Haka suka cigaba da rayuwansu, idan bataje dakinsa ba shi zaizo nata su raba dare ba tare da sanin iyayensu ba.


******************


Yau ranar Alhamis misalin karfe bakwai da rabi na safe Sabah ya fito daga dakinsa ya sauko kasa sanye cikin kananan kaya black trouser da black tshirt da yayi contrasting da farar fatar jikinsa ya kara fito da ainin siffarsa ta cikkaken namiji. Lalausar Sumar kansa ta ciko ta kwanta bisa kansa kana ganinsa kaga cikakken Arab. In ba an fada maka ba, bazaka taba cewa he's mixed ba. Sai faman baza kamshin turaren Calvin klein yake. Babu kowa a parlourn already Abbah ya rigada ya bar gida tun da sassafe saboda important meeting da yake dashi yabi jirgin asuba zuwa Abuja. Anty Fanneh tana can sama dakinta don tunda cikinta ya fara tsufa bata cika saukowa parlourn kasa ba. Rai da rai tana sama. Samha kuwa tana dakinta tana shirin zuwa school saboda yau lectures din safe ne da ita kuma by 9 za'a fara class.


Wuri Sabah ya samu akan daya daga cikin three seaters din makeken parlourn Ya ciro wayarsa daga cikin aljihu ya shiga lalatsawa yana jiran saukowar Samha tazo ta hada musu breakfast sa'anan su tafi school ya sauketa. Yana cikin haka, daga kasan lashes dinsa yaji giftawar mutum, da'gowa yayi idanunsa suka sauka kan Sophie wace ta shigo ta bayan kofar kitchen zatayo dining ta ganshi zaune akan kujera ta soma kokarin barin wajen a guje.


"Keh!!" Ya daka mata tsawa.


Cak ta tsaya jikinta na bari, ta kasa juyowa  kirjinta na harbawa da karfin gaske.


"Dan ubanki bada ke nake ba? Ki zo nan!" Ya fada mata a tsawace.


A hankali ta juyo ta soma takowa tazo ta tsaya d'an nesa dashi. Kafeta yayi da mayatattun idanunsa yana kare mata kallo sa'anan yace "gujegujen uban meye kikeyi idan kinga mutane?"


Muryanta na rawa ta soma fadin cikin hausanta da bai gama kwarewa ba tace "i'm so sorry oga.. kayi hakuri bazan sake ba"


" ai ba cewa nayi kiban hakuri ba.. tambayarki nake meyasa kike wanan guje gujen. Nayi miki kama da aljani ne ko me?"


Saurin girgiza mishi kanta tayi.


"Bakida baki?"


"A'a oga. Bakayi mun kama da komai ba"


"Toh uban meye yake saki wanan gudun" taji ya sake tambayarta amma wanan karan ba tare da da'gin murya ba.


"Wlh oga nima tsakanina da Allah ban sani ba"


"Kina so ki cigaba da aiki a gidan nan?"


Cikin sauri ta da'go masa kai hade da zaro ido tace "yesss...yess oga".


"Toh ki kiyayeni. Idan kika sake ganina kikayi irin wanan gudun dana kamaki kinayi yanzu kamar wata munafuka zakiga abunda zan miki a gidan nan. Now get out of my sight".


Cikin sauri Sophie ta juya ta bar wurin hade da sake bashi hakuri. Daidai lokacin Samha ta sauko kenan sanye da blue less dinkin riga da skirt dayayi balain ansar jikinta tayi kyau sosai, ta karayin fresh kamar ba ita, hanunta rike da farar jaka tasa farin takalmi to match sai light blue gyale data yafa. Tana tsaye Sophien tazo ta gaisheta hade da wuceta cikin sauri. Cike da mamaki Samha ta bita da kallo sa'anan ta dawo da dubanta ga Sabah daya sha mur, yana kallon gefe.


"My love lafiya? Meya hada ka da Sophie kuma?" Ta karaso tana tambayarsa.


Da'gowa yayi yana kallonta da fararen idanunsa ya soma binta da kallo yaga tayi mishi kyau sosai nan take ya nema baccin ran nasa ya rasa. Amma still fuskarsa a daure yace "shashashar yarinyar ce duk tabi ta raina mutane, bansan waye sa'anta a gidan nan ba".


Murmushi Samha ta da'an sake hade da fadin "Haba yayana, a da'an dinga rage zafin rai mana. Sophie yarinya ce karama kuma babu ruwanta bata shiga sabgan mutane ba. She's just doing her thing".


"Wanan katuwar ballagagiyar kike kira yarinya karama? Toh shikenan ta cigaba ta gani."


Dariya kawai Samha tayi ta manna masa kiss a gefen fuskarsa tace "Sorry my lovely husband. Allah ya hucci ran maza. Yanzu me kakeso a hada maka na breakfast?"


"Ke nakeso a matsayin breakfast dina" ya fada yana kara janyota jikinsa ya manna mata hot kiss a wuyanta. Saurin mikewa tayi tana fadin "tabdi da sanyin safiyan nan?"


"Yess" ya bata ansa.


Tabe baki tayi tace "kai baka gajiya wlh".


"What do you expect? I'm a healthy man with a healthy appetite. Dole na bukaci naki dumin jikin matata kusa dani all the time".


Ganin maganganun nasa ya soma fin karfinta kuma idan tace zata biye masa zatayi latin class dinta ne yasa ta shige kitchen taje ta hada musu shayi ta soya kwai tazo ta jera kan dining, sa'anan ta dibawa Ammi nata ta haura dashi sama ta kai mata daki ta sauko. Suna gama breakfast din ta kira Sophie tazo ta tattara wurin sa'anan suka fice yaje ya sauketa a school.


*2 weeks later*


Da safe misalin karfe goma da rabi Samha na zaune cikin class tare dasu khadie ana musu lectures, bayani lecturern ke musu amma gabadaya mind dinta baya kan abunda ake koyarwa. Wani irin nanauyen bacci ta soma ji hade da kasala yana bin duk ilahirin jikinta. Nan take ta soma blaming abunda takeji akan rashin baccin da bata samu ba jiya da dare saboda jarabar Sabah.


Wasa wasa sai faman hamma takeyi, Khadie ce ta dubeta tace "Samha lafiya kiketa wanan uban hamma?"


Cike da kasala Samha tace "wlh khadie na gaji bacci nakeji. Mr Bolaji yayi ya gama surutun nan nasa yayi gaba, tun dazun sai faman maimaita abu da'ya yake, haba ni na gaji gida zani wlh. I can't continue".


Amina ce ta dubeta ta tabe baki tace "ai sai ki da'an kara hakuri, saura 20 mins ya gama class din".


A hakan dai suka cigaba, da kyar Samha ta samu aka gama class din da ita ta kwashi jakarta sai gida. Tun data kwanta bacci bata farka ba sai bayan la'asar. Duk jikinta ya mutu ta tashi da kyar tayi sallah. Tana idarwa ta dawo tabi lafiyan gado ko hijab dinta bata cire ba ta cigaba da baccin.Cikin dare zafin jikin Samha ne ya farkar da Sabah, a hankali ya soma jin zafin jikin na ratsa jikinsa. Ya bude tsumammun idanunsa ya da'go yana dubanta yaga sai faman kwasar baccinta take.


"Subhanallah" ya fada can kasan ransa hade da shafo fuskarta. "Da alamun kamar zazabi kesan ya lulubeta kamar na daren farkonsu. To meya sameta kuma?" Ya tambayi kanshi.


Shiru yayi ya kura mata idanu yana tunanin abun yi. Da kamar ya tashe ta sai kuma ya fasa aikata hakan ya sake janyota jikinsa ya matse gam, har suna iya shakar numfashin juna. Within minutes zafin jikin nata ya soma rabar jikinsa. A hankali ta bude idanunta wanda ke cike da giyar bacci ta soma kallonsa.


Jin ta farka ne ya da'go yana dubanta yace "Baby what's wrong? bakida lafiya ne, ya naji jikinki da zafi haka?"


Da'an bata fuska tayi sa'anan tace "lfy na kalau, please kishi nakeji ka kawo mun ruwa nasha"


Mikewa Sabah yayi yaje ya dauko mata bottle water dake wajen dressing mirror dinta sa'anan ya kawo mata ta karba ta soma sha. Tana gama sha ta mika masa robar ya ajiye. Kafun ya juyo har ta koma baccin. Kura mata ido yayi yana kallonta sa'anan ya duba lokaci yaga hudu da rabi na asuba ya soma tunanin ko zai iya tafiya ya barta cikin wanan halin amma sai yaga ta cigaba da baccin nata ko a jikinta. Yafi 10 mins yana wanan tunanin ya sake kai hannunsa ya tabata yaji zafin ya da'an sauka sosai.+


Ajiyar zuciya ya sake sa'anan ya mike ya fice daga dakin ya koma dakinsa, bai koma bacci ba yaje ya dauro alwala yazo yayi rakatainul fajr Sai da gari ya kusan wayewa tukuna ya mike ya fada bayi yaje ya watsa ruwa a jikinsa ya fito. Yana kokarin sa kaya ya soma jin sautin muryan Anty fanneh. Cikin sauri ya iddasa sa kayan nasa ya fito yabi inda yakejin sautin muryanta na fitowa. Daga direction din dakin Samha ne yasa ya karasa cikin sauri ya shiga dakin ganin Anty Fanneh yayi tanata faman ririke Samha daketa faman kwara amai tamkar zata amayo da kayan cikinta. A firgice yake binsu da kallo don yanda taketa faman yunkurin aman yayi mugun tadda masa hankali. Bai san sanda ya karaso shima ya riketa ba yana mata sannu, gabadaya ta fita hayacinta. Sai da asuban nan Zazzabin ya ciyota da karfi hade da azababen ciwon kai. Da kyar dai aman ya samu ya lafa mata, Anty Fanne da Sabah suka taimaka mata tazo ta zauna a gefen gado nan take ta fashe kuka "wayyo Allah Ammi, kaina, jikina duk ciwo".


Hankalin Anty fanneh a tashe ta taba wuyanta taji zafi radau ta da'go ta soma fadin "oh Allah nidai na gaji da kananan zazzabi zazzabin nan da kikeyi Samha. Anya ba malaria bane ke damunki? Sabah ko zaka kira mana doctor fahad ne yazo ya dubata ayi treating abun nan once and for all?"


Babu musu Sabah ya fice daga dakin hankalinsa a matukar tashe yaje kiran doctor Fahad. Bugu daya Dr Fahad ya da'ga Sabah yayi mishi bayani yace toh gashi nan zuwa dayake family doctor ne kuma ya taba duba Samha tun kafun Anty Fanneh ta auri Abba.


Within 20 minutes sai gashi nan yazo da kayan aikinsa, suka gaisa da Sabah sa'anan ya haura dashi sama zuwa dakinta. Tana kwance Anty fanneh na gefenta suna faman mata sannu. Nan take likitan ya soma tambayarsu abunda ke damunta Anty Fanneh ta soma mishi bayani likitan yace zai debi jininta yaje yayi mata test tukuna a gano meke damunta. Haka dr Fahad ya deba jinin nata yace zaije ya dawo. Bayan barin likita gidan Anty Fanneh ta kira Abba a waya tana sanar da shi cewa zazzabi na damun Samha. Hankalinshi ne ya da'aga yace a kaita asibiti mana. Anty fanneh tace ai likita yazo ya dubata har ya deba jininta za'ayi mata test. Abba yace toh shikenan Allah ya bata lafiya shima gashinan kusa da gida. Ba'a jima ba sai ga Abba nan ya shigo shima ya soma mata sannu, yana karasowa inda take kamshin turarensa ya bugi hancinta nan take ta kuma yunkura cikin sauri ta mike ta fada bayi sai amai, sallati Abba ya soma yi yana mata sannu Anty fanneh taje ta riketa, tun tana yunkurin amman har tazo ta kasa saboda babu komai a cikinta. Duk jikinta yayi weak. Kasa juriyar ganinta a hakan Sabah ya juya ya bar musu dakin ya koma dakinsa hankalinsa a matukar tashe.


Sai bayan kusan hour da'ya Dr Fahad ya da'wo da test results, wanan karan bai ma haura sama ya tsaya daga parlorn kasa ya don ya tadda Abbah yana zaune. Bayan sun gaisa, Abba ya soma tambayarsa abunda ke damun diyar tasa. Shiru doctor Fahad yayi yana tunanin yanda zai soma fadawa Abba wanan maganar.


"Dr ina sauraronka mana, kayi mun bayani. What's wrong with my daughter?"


"Eh toh Alhaji gaskiya bazan boye maka ba, test results ya nuna cewa ciki ne da ita. She's pregnant har na kusan 3 weeks"


Saurin cire glasses dinsa Abba yayi daga idanunsa yana kallon dr Fahad kamar wani zarare. "What?" Wani irin magana ce wanan Fahad? Ni zaka duba tsabar idona kace mun ya'ta nada ciki? Anya hankalinka da'ya kuwa?"


"I'm sorry Alhaji wanan aiki nane, i see no point in hiding the truth from you. kuma bazan iya maka karya ba Alhaji. Abunda results ya nuna kenan".


Ran Abba ya bace sosai don gani yake Dr Fahad yama rena masa hankali ya shiga masa masifa. Suna cikin haka sai ga Anty Fanneh nan ta sauko tana turo ciki gaba ta soma tambaya "ya Alhaji lafiya? Me likitan yace ke damunta?"


"Gashinan he's just saying nonsense, wai har ni zai dubi tsabar idona yace mun Samha nada ciki?"


A firgice Anty Fanneh ta juyo ta soma duban likitan ta maimaita "ciki?! Wacece keda ciki?"


Shiru dr Fahad yayi bai ce komai ba. A tsawace Anty Fanneh ta sake fadin " magana nake maka likita! Wacece kace keda ciki?!"


"Hajiya please inaso ku gane cewa ni abunda results ya nuna mun kenan, amma in har baku yarda ba, kuna iya duba wani asibitin".

Ganin yanda Anty Fanneh tayi mugun tada hankalinta ne yasa Abba yazo ya soma rarashinta yana bata baki yace ta rabu dashi zasu je wani asibitin a dubata. Symptoms din malarian ne zai wani juya yace ciki?


Kirjin Anty Fanneh ne yake wani irin mahaukacin bugu ta mike cikin sauri ta haura sama zuwa dakin Samha. Tana kwance idanunta a lumshe tana fidda numfashi a hankali. "Ammi me likitan yace ke damuna?" Samha ta soma tambayeta muryanta kasa kasa.


"Sorry baby, karki damu yanzu zamu Shirya akaiki asibiti a dubaki da kyau. Wancan likitan bai san aikinsa ba".


"Ammi ki fada mun mana".


Shiru Anty Fanneh tayi bata tanka mata ba tazo ta soma shiryata har ta gaji da tambayar tayi shiru. Bayan sun gama shiri suka sauko kasa tare, Abbah na jiransu. Sabah shima ya sauko aka nufa asibitin tare, daman shi tun a waya dr Fahad ya sanar dashi ga abunda ke damun Samha. Maimakon ya tsinci kanshi cikin tashin hankali sai yaji kwata kwata he's not bothered don yasan cikin nasa ne, matsalar dai iyayensu ne yanda zai bulo musu da al'amarin. Yaso ace sai Ammi ta sauka tukuna a fada musu amma yanzu dai babu wata boye boyen. Aje asibitin dai ayi confirming.


Lagoon hospital suka nufa inda Anty Fanneh take zuwa awo. Abbah ya biya aka bawa Samha special room, nan likitoci suka zo suka soma gwaje gwajensu. A office dai likita ya kira su Anty Fanneh ya soma musu bayanin abunda test results ya nuna, the same thing dai da Dr fahad ya fada.

Kusan mutuwan zaune Anty Fanneh tayi zuciyarta ta tsaya cak na huccin gadi sa'anan ta dawo ta cigaba da bugawa, kallon kallo suka shiga yi ita da Abba cike da tsananin tashin hankali.

"Alhaji kana jin abunda likitan nan shima yake fadi? Wai Samha na ke dauke da ciki?" Anty Fanneh ta tambaya muryanta na rawa zuciyarta na mata wani irin kunna don ji take kamar ana zarar ranta. Ita har yanzu she can't believe this. Kuka sosai ta shiga yi da karfin gaske Abba shima a rikice cike da tsananin tashin hankali yazo ya soma kokarin riketa suka fito daga office din doctor din suka nufa dakin da aka kwantar da Samha. Ga Sabah yana zaune kusa da ita a gefe, shima kirjinsa yana masa matsanancin bugu don besan yanda za'a kaya ba. Shi bama takan iyayen nasu yake ba, gabadaya tausayin Samha yakeji.


Anty Fanneh banda kuka babu abunda takeyi har suka karaso cikin dakin, tana ganin Samha tazo zatayo kanta gadan gadan Abbah yayi saurin rukota.

"Ka sakeni Alhaji! Yau sai na kashe yarinyar nan da hannuna! Ciki a gidana? Na aifi ya' ta kawo mun cikin shege har cikin gidana?! Ba dani za'ayi wanan abun kunyar ba..Gwanda na kasheta na kashe banza... Samha kin cuceni kuma kin cuci kanki don nasan ba irin tarbiyan dana baki kenan ba. Abunda zaki saka mun dashi kenan?" Anty Fanneh Ta tambaya tana kara rushewa da wani irin kuka mai mugun tsuma rai.


Sosai Sabah yaji zafi dayaji ta danganta cikin da cikin shege amma yayi kokari ya danne. Samha dake kwance akan gado a firgice ta mike jin Amminta ta ambato ciki, maganarta ba a iya kunnenta ya tsaya ba harta gangan jikinta taji sautin muryan Ammi tamkar saukan aradu. kirjinta na bugawa da matsanancin karfin gaske tace "ciki Ammi?"


"Dan ubanki waye yayi miki cikin jikinki?"


Kuka ne ya kwacewa Samha ta dora hannu aka "wlh Ammi ba...."


"Abba Anty, ku daina wani tada hankalinku da wanan hayaniyar. Cikin dake jikinta nawane".

Maganar Sabah ne ya tsayar da maganar da take kokarin yi ta tsaya cak, zuciyarta dama gangan jikinta gabadaya ya tsaya na huccin gadi daga bisani yazo ya cigaba da bugawa. Ba Samha kadai ba harta su Anty Fanneh sai da suka firgita da furucin Sabah.


Cikin tsanani tashin hankali Samha ta soma furta kalmar "innalillahi wa innalillahi raji'un"

Wanan kalmar ce ta farfado dasu Anty Fanneh suka dawo cikin hayacinsu suka soma binta da kallo cike da mamaki da tsananin tashin hankali. Sabah kam ko a jikinsa yana tsaye yana kallonsu.Kallo cike da tsantsar mamaki da al'ajabi hade da tashin hankali Abba da Anty Fanneh suka shiga bin Samha dashi suna jiran suji ta karyata abunda Sabah ya fadi.

"Da gaske ne abunda kunnuwansu sukaji ya jiyo musu ko kuwa karya ne?"


Abba ne ya dubi Sabah yayi kokari ya hadiye abunda yaji ya tasar masa yace "Sabah.... what are you saying? Da gaske kai kayi cikin dake jikin kanwarka ko kuwa kunnuwa na ne suka jiyo mana ba daidai ba?"


A hankali Sabah ya da'go kansa ya zube fararen idanunsa kan mahaifin nasa yana jin yanda kirjinsa ke tsananta bugu, numfashi da kyar ya janyo sa'anan yayi releasing a hankali yace " eh Abba, cikin jikin Samha nawane kuma inason abuna"


Kalmar innalillahi wa innalillahi raji'un daga Anty Fanneh ne ya dakatar da sauran magana daga bakin Sabah.


"Samha kina jin abunda Sabah yake fadi? Wai cikin jikinki nashi ne kuma yana son abunsa? Innalillahi yau wace irin bakar rana ce gareni? Me zancewa duniya? Da wani ido duniya zata kalleni? Ya Allah karakasa wanan abun ya kasance gaskiya.." numfashin Anty Fanneh ne ya soma fita sama sama sai faman sumbatu takeyi.


Abbah kuwa yana tsaye ya kurawa Sabah ido yana kallonsa cike da matsanancin mamaki. Kwakwalwarsa ne ya shiga carji da tunanin yanda akayi suna zaune gida da'aya wanan abun ya faru? Ya akayi cikin? Garin ya? Su kuma suna ina? Tambayar da Abba ya shiga yiwa kansa kenan bai samu ansa ba.+


Samha ce ta mike cikin sauri taje ta durkusa gwuiwowinta duka biyu a gaban Ammi tana fadin "Dan Allah Ammi kiyi hakuri ki gafarceni wlh bada...."


Wasu irin gigittatun maruka har guda biyu Anty Fanneh ta dauke Samha dasu tana fadin "Tashi ki bani wuri yar iskar yarinya maciyar amana kawai! Abunda zaki saka mun dashi kenan bayan duk wahalar dana sha dake?! Me zancewa dangin mahaifinki? Me duniya zasu fada akaina?"


"Abba dan Allah kayiwa Anty magana ta bar dukanata haka, ina matsanancin son Samha Abba, kuma na rigada na fada muku cikin nan nawa..."


Shima marin da Abba ya daukeshi dashi ne yasa ya tsayar da maganar da yake kokarin yi. "Dan ubanka kana sonta shiyasa kayi mata ciki? Kasa abunda ka aikatawa kuwa? Nasan Samha bazata taba aikata hakan ba in ba dole ba, tursasta mata kayi". Wanan shine karo na farko da Abbah ya ta'ba daga hannu ya taba lafiyar jikin da'an nasa don ya ciyo shi sosai.


Sabah cike da tashin hankali yake duban mahaifin nasa yace "Abba wlh ba tursasa mata nayi ba... Abbah Samha matata ce"


"Matar ka....?"


Abba bai iddasa maganar da zaiyi ba sukaga Anty Fanneh ta yanke jiki zata fadi, Abbah yayo kanto a gigice ya rukota ya soma jijigata. Nan take Samha da Sabah suma suka yo kanta suna kiran sunanta, samha na kuka kamar ranta zai fita ta kamo hannun Anty Fanneh cikin nata hawaye na bin kuncinta.


"Ammi...! Ammi..!! Dan girman Allah ki tashi Ammi na tuba karki mutu ki barni. Idan wani abun ya sameki bazan ta'ba yafewa kaina ba!" Sosai Samha take kuka tana jijigata.


Cikin sauri Sabah ya mike ya fice daga dakin, within 5minutes sai gashi nan ya dawo da likita da wata nurse suna biye dashi a baya. Likitan na ganin yanayin da Anty Fanneh take ciki ne yasa suka shiga bata taimakon gagawa, da kyar aka samu numfashinta ya dawo.

Gabadayansu a wajen sun gigice sun di'mauce, kallo da'ya zaka musu kasan suna cikin matsanancin tashin hankali, barin Samha da takeji gabadaya duniyarta ta tsaya cak.


Numfashi Anty Fanneh ta shiga saukewa tana ajiyar zuciya jikinta na wani irin kirma tare suka shiga jera mata sannu.

Anty Fanneh tana ha'da ido da Abba ta sake fashewa da matsanancin kuka numfashinta har kagewa yake, sai da Abba ya yiwa likitan magana aka zo aka bata alluran bacci tukuna kuka nata ya lafa. Har lokacin Samha bata daina kuka ba, Abbah ya juyo yana duban Sabah dake tsaye a gefe jiki a sanyaye.


"Sabah ka biyo ni". Yana gama fadin haka ya juya ya fice daga dakin. Jiki a matukar sanyaye Sabah yabi bayanshi suka fito suka nemi wuri suka zauna Abba ya juyo yana dubansa zuciyarsa na masa wani irin zafi yace "Sabah meyasa ka aikiata haka? Kayi hakan ne don ka tozarta ni a idon duniya ko meye. Kanwarka fa kuna zaune gida da'ya? Yanzu me kakeso nacewa Mami?"Abba ya shiga tambayarsa cikin raunanar murya.


Shiru Sabah yayi yana sauraronsa daga bisani yace "kayi hakuri Abba, ka gafarceni amma banyi haka don na tozartaka ba, nayi hakan ne don kawai ina matsanancin son Samha. Na jima ina dawainiya da sonta Abba. Kuma mami, Abba har gida zanje dakaina nayi mata bayanin komai. Don a halin da ake ciki yanzu babu abunda za iyayi don Samha ta rigada ta zama matata, mun jima da yin aure ba tare da sanunku ba".


Sabon mamaki ne ya cika Abba, ya tsaya yana binsa da kallo. "Samha matarka ce? Toh yaushe ta zama matarka?"


"Abba zaka iya kiran uncle na Abuja ka tambayeshi. Shi ya daura mana auren".


Wani irin zufa ne ya shiga karyowa Abba ya soma furta kalmar innalillahi wa innalillahi ilahi raji'un can kasan ransa. Gabadaya kansa a daure yake. Wai Sabah dinsa ne yake fada mishi yayi aure ba tare da saninsa ba? Yau wace irin rana ce garesa komai yana neman dagule masa.


Suna cikin haka, wayar Abba ya soma ringing. Ya dauko yaga uncle ne ke kiransa nan hankalinsa ya kuma da'gawa. Don Sabah yana fita ya kirashi a waya ya soma sanar dashi abunda ke faruwa yace ya kwantar da hankalinshi zai zo har Lagos din yayi musu bayani ayita ta kare.


Abba yana da'ga kiran suka soma gaisawa da uncle, bayan sun gaisa Uncle ya shiga mishi nasiya sosai ta waya yace duk abunda ke faruwa da sananshi ne kuma zai kira kanwar nasa wato mami ya sanar da ita yana nan zuwa gobe goben nan insha Allah. Abba yace toh shikenan Allah ya kawo shi lafiya. Jikin Abba ya mutu sosai ya rasa abunyi, ga condition da matarsa take ciki ga kuma wanan bala'in daya sawo kai. Amma abunda yafi daure masa kai shine meyasa tun farko Sabah bai zo ya tunkareshi da wanan batun ba? Meyasa zai bi ta baya? Don daya fada mishi tun farko da abubuwan basu kai ga haka ba. Katuwar ajiyar zuciya ya sake sa'anan ya mike Sabah yabi bayansa suka koma dakin da aka kwantar da Anty Fanneh. Har lokacin bata farka ba, ga Samha durkushe a gefenta sai faman kukan take. Abba da Sabah ne suka shiga rarashinta suna bata hakuri akan tabar kukan haka, ya isa insha Allah zata samu lafiya.


Sai da yamma tukuna aka samu Anty Fanneh ta farfado, tana tuno da abunda ya faru hawaye suka soma zubo mata da kyar take iya motsa labbenta. Abba ya dubi Sabah da Samha yace su fita su da'an basu wuri. Jiki a sanyaye haka suka mike suka fice.


Bayan fitan su Sabah, Abba ya dubeta ya soma fadin "Fanneh dan Allah ki bar zubar da hawayenan hakan, da wanan condition din naki bai kamata kina sakawa kanki damuwa haka ba".


"Haba Alhaji? Ya za'ayi kace karna damu? Cikin shege fa a gidana kuma nida kai muna nan? A gaban mu? Me zamu cewa ubangiji? Ba abunda yake mugun tayar mun da hankali kamar Mami idan taji wanan maganar, me zamu ce mata? Don Sai data gargadeni akan barin yaran nan su kadai a gida na nunar mata cewa ba haka suke ba, nasan irin tarbiyan dana yiwa ya'ta. Sai gashi yau ta kunyata ni... wayyo Allah na" Ta karasa tana kara rushewa da wani irin kuka mai cin rai.


Rarashinta Alhaji ya shiga yi yana bata baki akan tayi hakuri "kadarar ce tazo a hakan, amma abun yazo da sauki tunda akwai aure tsakaninsu. Sabah yayi mun bayanin komai. Cike da mamaki ta soma binshi da kallo. Nan ya kwashi komai da Sabah ya fada masa ya gaya mata. Shiru tayi bata ce komai ba har ya da'sa aya tana jin yanda zuciyarta ke mata matsanancin bugu.


A ranar dai kwanan bakin ciki akayi, babu wanda ya runtsa tsakaninsu. Washe gari da safe aka sallamo su suka dawo gida, uncle ya kira a waye yace gashi nan zuwa shida kanin Abba wato kawu Mubashir, sunbi jirgin safe har sun iso suna Lagos, gasu nan tahowa. Kai tsaye gidan Mami suka nufa suka daukota tukuna suka dauki hanyar zuwa gidansu Sabah. Tambayar duniyar nan Mami ta shiga yiwa uncle don tayi mamaki sosai zuwansu kai tsaye babu notice, tayi tayi da uncle amma yaki fada mata yace suje gidan baban da'an nata koma meye zata ji. Hankalin Mami yayi mugun mugun tashi don a tunaninta wani abun ne ya samesa.


Ko da suka isa, dukansu suna zaune a parlour kowa yayi jugum ana jiran isowarsu. Anty Fanneh da Samha suna jin sallamar Mami sun shigo gabadaya zukatansu suka shiga harbin tara tara, sosai suka firgita don basu san wani irin tarba zata yiwa maganar ba. A lokacin ne hankalin Mami ya da'an kwanta ganin ko wanan su yana cikin koshin lafiya. Bayan sun zauna an gagaisa ko ina ya dau shiru ana jiran Uncle yayi magana. Gyaran murya yayi sa'anan ya soma musu bayanin yanda abubuwa suka kasance, tun lokacin da Sabah ya fara zuwa ya tunkareshi da son auren Samha cikin sirri, kuma da dalilin dayake son ya aikata hakan, da kuma zuwansu na biyu shida Samha aka daura musu aure, komai dala dala daki daki haka ya dinga musu bayanin har kawo situation din da ake ciki yanzu.


Kusan numfashin Mami daukewa yayi jin bayanin da uncle yakeyi, kallonsa kawai takeyi tamkar bata taba ganinsa ba don tayi mugun firgita sosai. A hankali ta juyo tana duban Abba wanda yake zaune yana sauraronsu fuskarsa babu yabo babu fallasa. Kallonsa ta cigaba dayi domin samun karin bayani yanda hakan ta kasance. Sabah yana zaune a can gefe yana sararonsu ko ajikinsa, jira kawai yake ayita ta kare su shafa masa lafiya shida matansa.


Uncle ne ya cigaba da fadin "aure tsakanin yaron nan da wanan yarinyar ba haramun bane tunda ba ciki da'ya suka fito ba. Kuma kuskure ce babba da aka so aikatawa sai Allah ya kiyaye. Yanzu dabadin yaron nan Sabah yazo mun da wanan batun ba ya kuke tunanin abubuwa zasu kasance? kamar yasan abunda zai faru kenan yazo mun da bukatarsa don haka Mugodewa Allah dayasa da aure ne wanan abun ya...."


A lokacin ne Mami ta dawo cikin hayacinta ta katseshi cikin sauri " Dakata Hashim! Wanan wace irin magana ce sai kace wani wasan yara?! A ina aka taba irin wanan auren daba tare da iyaye sun sani ba Kuma da ransu da lafiyarsu? waya bada izinin daurin wanan auren?! Toh wlh ban yarda ba, yarinya taje ta roro cikinta a waje za'a zo a likawa jikana? Daman tun farko nake ganin take takenta batada kamun kai, sai dana fadawa uwarta amma taqi kememe tace ita yarta kaza ce, yarta kaza ce! Toh ai gashi nan. Yanzu kun rasa yanda za'ayi ne kuka zo za'a likawa jikana a fake da auren karya?! Toh wlh baku isa ba! Kaima Hashim ka bani mamaki daka biye musu, dakai da muazzam duk kun kyauta. nidai ban yarda da wanan shirin ba!"


Shiru ne ya ziyarci parlourn, Abbah dake zaune akan two seater ya rafka uban tagumi, gabadaya ji yake abun duniya ya cunkushe mishi wuri daya . Anty Fanneh inbanda hawaye babu abunda take zubdawa jin furucin Mami game da yar'ta.  Samha kam ba'a cewa komai don itama sosai take kuka a gefe. Uncle Mubashir kuwa, gabadaya abun ya daure masa kai ya kasa fahimtar abunda ke faruwa. Sabah ne kadai yake Kallon Mami cike da tsananin jin haushi don kalamanta ba iya kunnuwansa ba har zuwa gangan jikinsa yake jinsu.


Ran uncle ne ya bacci sosai yace "Haba Bilkisu, ya kike magana irin wanan ne? In kwaso jiki tun daga abuja nazo in muku bayani kice karya nake? Wai meke damun kwakwalwarki ne?"


"Nidai Hashim bazan yarda bane kawai, yaron nan Sabah na rigada na mishi mata, don haka cikin dake jikinta taje can ta nema wanda yayi mata amma ba jikana ba.... haka kawai za'a kawo mana cikin shege cikin zuri'a.


Cikin zafin rai Sabah ya furta "Mami karki kuma danganta mun da' da cikin shege. Cikin dake jikin matata na sunnah ne, kuma babu wanda ya isa ya canza hakan".


Cike da mamaki kowa ya soma bin Sabah da kallo, barin ma Mami a fusace tace "Sabah ni kake gayawa haka? Toh sai ka saketa dan ubanka! Matarka tana can tana jiranka. Mara kunyar banza mara kunyar wofi!"


"Babu wani sakinta da zanyi Mami don banida wata mata sai ita, ina nan tare da ita mutu ka raba." Ya fada mata ko shakka babu.


"Muazzam kana zaune kana jin abunda da'anka yake fadamun? Ina fada, yana fada?" Mami ta fada hade da dagin murya.


Ajiyar zuciyar Abba ya sake gabadaya kansa a daure yace " Toh mami ni kaina bansan me zance ba, ga uncle nan dai ya gama bayani. Yace yaron nan yazo ya sameshi kuma shi ya daura musu aure, abu ya rigada ya faru toh me kuma zance?"


"Hmm tabdi! Kuna wasa dani kenan. Wlh auren nan sai an warwareta".


"Toh ke yanzu meye dalilinki na san warware auren nan? Meye yaran nan suka tare miki?"


"Saboda already na rigada na zabar masa wace zai aura. Daurin aure ne kawai ya rage".


"Wai Bilkisu yaushe zaki fahimta ki gane cewa an daina wanan yayin? Ba'a yiwa yaran yanzu auren dole, ki bar yaro ya numfasa. Kinyi na farko abu bai yu' ba toh ki kyaleshi mana!" Sosai Uncle ya shiga yiwa Mami fa'da hade da wa'azantar da ita. Daga karshe dai kuka ta fashe musu da tana fadin cewa sun cuceta, sun gama da ita masu mayar da ita bakin komai ba, sosai ta shiga surutai ta inda take shiga ba tanan take fita ba.

Abu kamar wasa fa Mami taki fur tace sam bata yarda ba. Sabah ya mike a fusace yace zai dauki matarsa ya bar musu gidan gabadaya, sai da Abba ya daka mishi tsa'wa tukuna ya koma ya zauna. Aka shiga rarashi kowa sai bawa Mami hakuri akeyi. Da kyar dai aka samu ta da'an sauko tace zata amince amma bisa sharadi da'ya sai dai idan Sabah zai kara da Shafa, yar wurin Uncle Mubashir.

Sabah yana jin haka can kasan ransa yace "wlh babu wanda zai tilasta masa karo wata macen. Samha kadai ta isheshi"

"Haba Mami, ki duba kiga duka duka yaron nan guda nawa yake? Ina zai kai mata biyu fisabilillah?" Uncle Mubashir ya tambayi Mami cike da takaici.

"Wani kuruciya ne a tare dashi yanzu? Mutumin da har ya iya dirkawa mace ciki zaka dangantashi da yaro? Ai ya wuce tunaninka yanzu.Don haka tsab zai iya zama da mata biyu. Yarinyar nan dai Shafa ta jima tana mun magiya akan tana sonshi, kuma yar'uwarshi ce don haka yar'gida za'ayi."

"Mami, shafah ya'ta ce. Kuma ni gaskiya ban shirya mata aure ba yanzu. Karatu nake so tayi". Uncle Mubashir ya fa'da cike da takaicin mami.

Kowa dai ya lura batason had'in Sabah da Samha ne kawai. Tafi son ya auri zabinta. Abba zaiyi wata magana uncle ya dakatar dashi yace su barshi da ita, Sai da Uncle yayi da gaske tukuna ya samu ta da'an sauko Amma tace ko ba yanzu ba ko nan gaba Sabah ya shirya sai ya kara da shafah. Sabah zai musanta Abbah yace dashi yayi hakuri abi komai a hankali. Uncle yace zasu je gida da Mamin su sake tattaunawa har ya samu ya shawo kanta. Abbah yace toh, haka suka bar gidan Mami sai faman zuba ruwan bala'i take tana fadin ba'a dauketa da daraja ba.+

Bayan tafiyan su Mami, Anty Fanneh ta mike ta haura sama, Abba na kokarin mata magana ko tankashi batayi ba ta shige dakinta cike da tsananin da'cin rai da bakin ciki. Itama Samha wasu zafaffen hawaye ne suka cigaba da zubo mata, ta mike jiki babu kwari ta nufa da'kinta. Sai bayan la'ssar tukuna Sabah yaje da'kin Samha don ganin ya take. A kwance ya sameta akan gado idanunta a lumshe, tunanin duniya duk ya isheta, da'ga jiya zuwa yau ta kara yin wani irin rama ta fita hayacinta.

Hankalinsa yayi matukar da'gawa ganin yanayin da take ciki tana faman zubda hawaye. Wani irin tausayinta ne ya kara ji yana fuzgarsa . A hankali ya soma takowa har yazo ya tsaya bakin gadon yana kare mata kallo da fararen idanunsa. Kallo da'ya tayi mishi ta kau da kanta tana tunanin yanda za'ayi ta fada mishi ya sauwake mata kawai, yabi umarnin Mami. "Toh cikin jikinki ya za'ayi dashi zuciyarta ta tambayeta? wani irin zafi Samha taji kirjinta na mata don tasan tabbas dabadin matsanancin son da take yiwa Sabah ba, babu abunda zai sa ta tafka irin wanan babban kuskure game da mahaifiyarta.
Tsugunawa yayi a gefenta yasa hannu da'ya ya juyo da fuskarta tana fuskantarsa, kura mata ido yayi yana cigaba da kallonta damuwarsa da'ya a yanzu shine wanan hawayen da take faman zubda. A hankali yakai hannunsa ya soma share mata hawayenta sa'anan ya kira sunanta muryansa kasa kasa "Samha..."

Wani irin yanayine taji ya ziyarceta dataji ya kira sunanta. Tana jinsa amma taki ansawa sai da'ya kira sunanta a karo na biyu ta dago manyan idanunta masu cike da ruwan hawaye ta zubesu akansa. "Yanzu meye damuwarki.. i thought this secret marriage shine damuwarki toh yanzu komai ya fito filli sun sani. Uncle yayi musu bayani komai ya daidaita. Yanzu meye kike asaran hawayenki haka?"

Wani irin takaici ne taji ya lulubeta tace " babu abunda ya daidaita Sabah.. duba halin dana jefa Ammina saboda son zuciyata. Ga Mami tace ita sam bata yarda da wanan auren ba, cikin jikina bana halal bane. Ya kakeso nayi da rayuwata Sabah.,Ina dana sanin aika...."

Cike da zafin rai Sabah ya katseta da " don't even say it... karki kuskura kice kinyi nadaman abunda ya faru, because ni I don't. I'll never regret meeting you in my life, tun lokacin dana fara dora idanuna akanki, naji a jikina cewa you're the one for me. Kece kika kawo mun haske cikin rayuwata, ban'taba tunanin zanso wata ya'mace kamar yanda nake sonki ba. Nasha gaya miki indai akanki ne a shirye nake dana ba'ta da kowa, and I don't mind who i hurt in the process. Abba da Anty basu da wata damuwa indai akan auren mu ne, just give them some time zasu sauko. Mami kuma borinta na da'an lokacine don daidai nake da ita, she can't dictate my life for me, ba ita zatayi mun zaman aure ba."

Duk maganganun nan dayake Samha tayi shiru tana sauraronsa. Hannuwanta ya kamo cikin nasa ya cigaba da fad'i muryansa kasa kasa "yanzu abu da'ya nakeso dake Samha, ki taimakawa rayuwata ki daina wanan tunanin in ba so kike ki i'llata mun baby ba"

Tana jin abunda ya fad'i ta turo baki ha'de da janye hanunta daga cikin nashi ta juya mishi baya tana runtse idanunta. Hakan datayi ne yasa ya mike daga inda yake tsugune yana murmushi yazo ya kwanto bisa bayanta ya janyota jikinsa ya cigaba da rarashinta yana kokarin kwantar mata da hankali. Shima bangaren Abba da Anty Fanneh, kwana yayi yana aikin rarashi ita kam sai faman kuka take don kalaman Mami akan yar'ta sun mugun tsaya mata a rai don taji zafi sosai. Da kyar dai Abba ya samu kukan nata ya lafa ya cigaba da bata hakuri yace karta dauki maganganun Mami tasa a rai, itama baccin raine yasata furta waenan kalaman amma she doesn't mean them.

Kwanan uncle hudu a Lagos, sai daya tabbatar ya sassanta komai tukuna ya koma Abuja. Kafun ya koma ya yiwa Abba magana akan kayan lefen da Sabah ya yiwa Samha suna nan gidanshi a Abuja, Mamaki ne ya kara cika Abba dayaji har da kayan lefe da'an nasa ya hada. A ransa yace "yayan zamani kenan". Yacewa Uncle tou bari komai ya lafa insha Allah za'azo a kwaso.
Bangaren Anty Fanneh kuwa, da farko ta dauki dogon fushi da Samha don da kyar take ansa gaisuwarta. Daga baya ne ta dawo ta soma jin tausayin yar' nata ganin duk tabi ta fifige ta fita hayacinta ga shigan ciki dake damunta. Da kanta ta dawo ta rungumi yar'ta a jiki don tasan ba laifinta bane, kaddarariyar soyayya ce ta jawo musu haka, kuma suna gudun toye musu farin cikinsu ne yasa sukayi a boye, Anty Fanneh ta shiga godewa Allah daya sa da aurensu wanan abun ya faru don sunyi tunani mai kyau da suka aikata akan. Sabah dai tun a ranar har yanzu bai samu damar kebewa da Samha ba, shi kanshi yasan ta galabaita dayawa don haka ya bata space, sosai ya nesanta kanshi gareta don ta samu lokacin recovery.

Bayan sati uku da faruwan abun, abubuwa ya soma dawowa normal a gidan, har lokacin Abba bai dauke kafa wurin zuwa bawa Mami hakuri ba, musamman ya tursasa Sabah agaba suke zuwa. Wani sa'in ya aika Sabah shi kadai. Wanan abun ba karamin bakantawa Sabah rai yake ba, shi ya rasa gane meyasa Mami zata dau abun da zafi haka ba, tunda ba ita zatayi masa zaman auren ba. Amma sai yayi tunani idan ba lalabanta akayi ba, bazata bari su numfasa ba, kuma yasan yanda take ba'lain sonsa har cikin ranta don haka dole shima ya sauko ya soma binta a hankali. Cikin ikon Allah sai yaga plan di'insa yayi working don wanan last zuwan dayayi wajenta sai yaga ta sauko sosai har tana tambayarsa Samha d'in sabanin da dako sunanta bataso taji an ambato a gabanta. Sai kuma yaji dadi ya cigaba da lalabata har ta sauko gabadaya. Maganar aurensa da shafah dinma bata daukowa, ta shafa masa lafiya.
Bangaren Anty Fanneh babu yanda ta iya haka ta kira dangin mahaifin Samha dake Yola ta sanar dasu. Babu wanda bai fada albarkacin bakinsa ba don daman ba wani shiru dasu takeyi ba. saukinta da'ya kawu Moddibo daya halarci daurin auren shine dai yayi musu bayanin komai suka ce toh Allah ya kyauta, ai daman tun farko ta rigada ta nuna musu itace me ya' don haka wanan abunda ya faru ba abun mamaki bane a wajensu.

Bayan wata biyu da yan sati, A lokacin cikin Samha ya shiga wata na uku,idan baka kura mata ido sosai ba, bazaka ce akwai ciki a jikinta ba. kullum zaka ganta sanye cikin doguwar riga shar shar bazaka taba hango komai ba. A cikin satin Abbah yasa aka gyarawa Sabah gidansa na island akayi furnishing sosai. Yace zai iya tarewa amma banda Samha ya barta ta huta a gida tukuna. A lokacin itama Anty Fanneh cikinta ya tsufa sosai don ta kusan shiga watan haihuwarta, da kyar take iya takawa saboda nauyin cikin. Tana jin Abbah ya gyarawa Sabah gidansa tace ya hade ya tattara da matarsa su koma don bazai yu tana jan ciki itama yar'nata na ja suna jerawa cikin gida ba, su tattara su bar mata gida. Abba yayi dariya yace, yanzu idan Samha ta tafi wa zai dinga taimaka mata? Tace tayi magana da Anty Katibe sisternta dake aure a Dubai zata zo ta zauna da ita har ta haihu, don tunda Anty Katibe taji labarin Anty Fanneh nada ciki tace zata dau hutu tazo ta zauna da ita. Abbah yace toh ta bari idan Katiben tazo sai Samha ta tare gidan mijin nata amma for now let her remain with her in the house.

Ko da Abbah ya sanar da Sabah bai musanta ba haka ya tare a gidan shi kadai. By then ya rigada ya rubuta final exams dinsa har sun kammala project. Kamfaninsu na family business guda biyu aka damka mishi a hannu ya dinga kula da, saboda Abba ya kusan retire. Ga kula da makarantu abun zai masa yawa. Jira kawai yake Jabbar ya gama karatun nasa shima yazo yayi takeover. Samha kam har lokacin batayi resuming school ba, shiru shiru su khadie basu ganta a school bane yasa suka kawo mata ziyara har gida. Wani irin mamaki ne ya cika su da sukaga da canza faral da'ya kamar ba ita ba. Tayi wani irin haske na fitan hankali, ga ciki ya soma fitowa.Khadie ce ta soma tambayarta "Samha ya haka? Meya sameki?"

Itama Amina binta kawai take da kallon mamaki. Samha tayi ajiyar zuciya sa'anan ta soma kwararo musu labari tun daga farko har zuwa karshe bata boye musu komai ba.
Wani irin mugun mamaki ne ya cika su. Suka sake Baki suna binta da kallo har ta dasa a'ya. "Yanzu Samha daman da aure akanki all this while shine baki fadamana ba?" Amina ta tambayeta. "Why did you hide all these from us?"

"Wallahi khadie bazaku gane bane, it's complicated amma kuyi hakuri. Alhamdulillah dai komai yazo karshe".

"Yanzu ina shi Sabah di'in?" Khadie ta tambayeta.

"Yana can gidansa".

"Toh kefa? Me kikeyi anan".

"Hutu mana".

"Ban gane hutu ba, kin bar mijinki can yana zaune shi kadai?".

"Toh ya kukeso inyi... bayan abubuwan da suka faru, i need peace and rest please".

"Peace and rest ko? Zakiga peace and rest ki zauna nan. Kinsan mijin naki hot cake ne kina zaune kikayi wasa wata zata zo tayi wuf dashi. Ga Aliyah can na jira"

Harara Samha ta watsawa khadie hade da fa'din "kin jiki.. ai babu yanda za'ayi Sabah ya kalla wata macen bayan ina nan. Kuma shaida ne"

"Hmm ki Bar cika baki dai. Namiji ne fa". Khadie ta fada.

Amina ce ta katse musu magana da "Nidai ba wanan ba...Samha ki fadawa Sabah babyn nan sunana za'a saka mata. Nayi booking". Ta karasa maganar tana murmushi tana kallon cikin Samha cike da sha'awa.

"Ke dallah.. baza'a samata sunan tsoffi ba. Na rigada na bata suna Javeria, shi za'a saka mata."

"Ke da wanan sunayen yahudawan naki... wani suna ne kuma javeria?" Amina ta fa'da mata tana ta'be baki.

Sosai kawayen nata suka ba Samha dariya tace "Juwairiyya dai kuke nufi kuce ko? Ai sunan matan Annabi ne"

"Ai na sani, shegen iyayi ne yasa ta lankwasa sunan, wai wani javeria". Amina ta fada tana watsawa Khadie harara cikin wasa.

"Ku in banda abunku, kun dage akan mace ce. Kuka sani ko namiji ne?"

"Kutt kice kinaso ki haifi Sabah na biyu kenan zaki ha'da guguwa cikin gidanki" Khadie ta fada tana rike baki. Dariya dukansu sukayi suka cigaba da hira suna zolayan junansu. Anty Fanneh tazo ta lekasu a daki, cike da fara'a tace bari a kawo musu abinci suci. Bayan 10 mins sai ga Sophie tayi sallama ta shigo hannunta rike da tray na kulolin abinci tazo ta jera a gabansu suka sauko suka soma ci suna hira. Samha dai bata ci ba, cerelac ta dauko ta dama ta soma sha don tunda cikin nan ya shigeta anything madara tana so, karnin madaran ba karamin kwantar mata da zuciya yake ba, tana zaune haka nan zata ka'da madara abunta tasha. Sai wuraren magrib tukuna su khadie suka wuce gida.
Sabah kwance yake cikin bathtub na wanka ya lumshe tsumamun idanunsa yana jin yanda zafin ruwan yake kara ratsa jikinsa. A hankali yake fidda numfashi yana jin yanda kirjinsa ke kara bugawa. Shi kadai yasan yanda yakeji a wanan lokacin, Babu abunda yake masa yawo a kwakwalwa illa kyakyawar fuskar matarsa da kuma yanda yayi matsanancin kewanta. Yayi missing dinta sosai har bai san yanda zai kwatanta ba. yau kusan sati biyu kenan bai sanyata a idanunsa ba don rabonshi da can gida ya da'an kwana biyu sai dai shi da ita suyi magana ta waya.

A hankali ya bude fararen idanunsa yana ajiyar numfashi. Mikewa yayi ya fito daga cikin bathtub din ya daura towel sa'anan ya fito zuwa da'ki ya karasa wajen wardrobe dinsa yasa kaya, ya dauko turare ya fessa jikinsa sa'anan ya koma kan gado ya kwanta.

Tun dazun yaketa so ya huta amma bai samu dama ba, kasancewar yau weekend su zack sunzo sunata faman kallon ball tare. Tunda sukaji labarin abunda ya faru suka shiga masa tsiya har da kiransa babban baby. Kusan every weekend tare suke spending. Shinoh ne kadai baya tare dasu don suna rubuta final exams dinsa yayi tafiya zuwa kano ganin iyayensa.
Wayarsa ya dauko ya soma lalatsawa ya shiga what'sapp ya turawa gimbiyar nasa message yana so suyi video call amma kamar bata online. Layinta ya shiga nema bugu da'ya ta dauka.

Zaune take a gefen gadonta ta fito wanka kenan tana kokarin taje silky hair dinta, data shafawa mai tasha gyara tana fidda shekki na musaman. Tana cikin hakan ne taji kiran nasa ya shigo cikin sauri ta da'ga wayar ta kara a kunne tana jin yanda kirjinta ke kara mata bugu don tayi kewansa sosai, yau gabadaya basuyi waya ba yasa gabadaya hankalinta ya da'ga. Sanyayar muryarsa ne taji ya doki kunnenta "Hello kanwata".

Ajiyar zuciya ta sake dataji sautin muryansa ta lumshe idanunta a hankali tana jin yanda jikinta ke kara moving da matsanancin soyayyarsa. "Ina ka shiga ne yau tun safe?" Yaji ta tambayeshi.

"Meya faru kinyi missing muryan mijin naki ne?"
Muryanta kasa kasa tace mishi "eh"

Lalausar murmushi ya sake wanda yake karawa halittar fuskarsa kyau yace "banji ba. me kikace?"

Tasan cewa yaji sarai so yake kawai ta sake maimaitawa don haka tace "yess nayi missing dinka sosai sosai".

"I've missed you too baby...me kikeyi yanzu, kizo online i want to see you"

Tace mishi toh, ba tareda ta bata lokaci ba ta kunna datanta sa'anan ta shiga contact dinsa ta bude, tana budewa sai ga call dinshi ya shigo ta da'ga. Ganin kyakyawar fuskarsa ya bayana ne yasa ta kara jin wani irin abu na mata yawo a duk sansar jikinta. "Ya baby na? Hope kina bata abinci sosai tana ci?" Taji ya tambayeta. Idan akwai abunda Sabah yafi kauna a duniyan nan bai wuce cikin jikin Samha ba. so tari idan sunyi video call sai yace ta yi kasa da camera di'in yaga cikinta, ita kuma sai ta biye mishi suyita ta faman shirmensu tana zuba masa shagwaba.

"Sosai ma kuwa, yau babynka da kwadayin dan'wake ta tashi sai dana kwaba naci tukuna hankalinta ya kwanta".

Dariya ya shiga yi sa'anan yace "Allah baby ana shigar mun hakki dayawa wlh na gaji da zama ni kadai. Gaskiya zanyiwa Abba magana cikin satin nan ki tare. Nayi kokari".

"Haba babyn baby, yanzu idan na tare wa za bari da Ammi? Kadan kara hakuri mana".

"Yaushe Anty naki zata zo ne?"

"Ammi tace sunyi waya, karshen satin nan zata taso".

Sabah badan ransa yaso ba yace "toh shikenan. ya na'iya"

Muryanta a shagwabe tace "toh kaifa... bazaka zo gida ba?"

"Zanzo... monday insha Allah ina tashi daga aiki zan biyo ta gida naga babies dina sa'anan na wuce. Me dai me sukeso na kawo musu?"

"Madara" ta bashi ansa kai tsaye.

Dariya yayi sa'anan yace "toh shikenan, nima idan nazo za'a ban madaran nasha ko?" Kunya ne taji ya lulubeta don ta gane sarai abunda yake nufi. Haka suka cigaba da hiransu cike daso da kauna, kamar kar su daina wayan.Ranar monday da yamma Samha tana zaune a parlour ta kunna tashar discovery world tana kallo don tashan yana birgeta sosai. Ko ina shiru in banda karar makeken tv dake parlorn da kuma sanyin Ac dake tashi ba abunda akeji. Ammi tana sama a dakinta tana kwance.


Sosai Samha tayi zurfi cikin kallon from nowhere taji saukan hannun na yawo bisa wuyanta. A firgice ta da'go zata sake yar' kara idanunta sukayi ido hu'du da Sabah wanda ke tsaye a bayan kujeranta ya kura mata ido yana kallonta. Kallonsa take tamkar a mafarki tana jin yanda kirjinta ke tsananta bugu saboda firgitan datayi. Bai ma kirata a waya ya sanar da ita zuwansa ba.


Wani irin farin ciki ne taji ya lulubeta Cikin sauri ta mike ta zagayo tazo ta rungume shi tsam a jikinta tana ajiyar numfashi. Shima kara matsota jikinsa yayi sosai yana jin dumin jikinta da daddaden kamshin jikinta na ratsa jikinsa. Sunfi 5 mins a hakan suna jin yanda bugun kirjinsu ke karuwa cike da matsanancin son junansu.


A hankali ya da'ago yana karewa kyakyawar fuskarta kallo, tun daga manyan idanunta zuwaga dan madaidaicin hancinta sa'anan ya gangaro zuwa ga karamin bakinta yana kare mata kallo. Zatayi magana taji ya hade bakinsu wuri da'ya ya shiga kissing lips dinta, ya kamo lips dinta na kasa yana tsotsa. Sunfi 5 mins suna tsotsan lips din junansu har tsayuwa ya soma neman gagarasu, A hankali Sabah ya ware lips dinsa daga nata ya bude idanunsa ya zubesu cikin nata sa'anan ya hade goshinsu wuri da'ya  suna ajiyar numfashi a tare. Muryansa kasa kasa yace "you don't know how i've missed you.. missed kissing you". Ya karasa maganar yana kai mata kiss a wuya.+


"I've missed you too" ta fada mishi hade da lumshe idanunta.


A hankali taga ya shafo cikinta yana murmushi yace "and how's my princess doing... da fatan dai kina kulan mun da ita ana bata abunda takeso?"


Dariya Samha tayi tace "eh mana...yau kuwa coldstone takeson sha".


"Toh an gama.. bari aje a karbo mata".


Suna dariya suka karasa three seatern tare  suka zauna. Sabah ya soma tambayarta Anty Fanneh. Tace tana can sama dakinta tana bacci yace toh idan ta tashi zaije su gaisa.

"Bari na kawo maka ruwa kasha". Ta fada hade da mikewa tayi hanyar kitchen. Shi kuwa ya bita da kallo, yanda take karya kugunta kamar ba mai ciki ba yasa ya shagala da kallonta har taje ta kawo masa ruwan ya karba yana binta da wani irin mayattacen kallo cike da zallar sha'awarta.


A hankali ta shiga janshi da hira, ya soma zolayarta kamar yanda ya saba ita kuwa sai faman zuba mishi shagwaba take. Suna zaune, ya ciro wayarsa ya shiga musu ordern icecream din datace tana kwadayin sha. Within 30 mins delivery guy din yazo ya tsaya a gate, Sabah ya aika da'ya daga cikin securities din suka karbo.


Katuwar roba manya manya guda uku ya diresu a gabanta. Samha miyau har tsinke mata yake cike da murna ta mike ta shige kitchen ta debo madaran garri a cikin plate. Sabah yana zaune yana kallon ikon Allah yaga ta debo icecream din ta kwaba da madaran ta soma sha tana wani irin lumshe ido cike da tsansar jin dadi.


Matsowa tayi kusa dashi ta debo kwaben nata tana kokarin kai masa baki yaja da  baya hade da girgiza mata kansa yace bazai sha ba.


Tabe baki tayi tace "tab..ka bar dadi yasin".


Haka ta cigaba da shan icecream dinta tana lumshe ido tana sumbatu cikin kankanin lokaci har ta tashi da roba da'ya.


A haka Anty Fanneh ta sauko ta samesu tana ganin Sabah tace "a'a Sabah yaushe ka shigo?"


"Ban jima da shigowa ba Anty. Ina wuni Ya karfin jiki?"


" lfy kalau Sabah Jiki alhamdulillah". ta fada hade da samun wuri ta zauna. A lokacin ne idanunta suka sauka kan Samha dake zaune a gefe da robobin ice cream jere a gabanta. Sallati Anty fanneh ta shiga yi tana fadin "na shiga uku..yanzu Samha abunda kikeyi kin kyautawa kanki kenan? Kiyita dirkawa cikinki Kayan zaki da sanyi? Kai kuma Sabah kake biye mata ko?"


Hannu Sabah yasa yana sosa keyarsa yace "kiyi hakuri Anty, ita ta damu wai tana so".


"Hmm.. ita ta damu tana so ko? Toh shikenan Idan ta haifar maka da' da ciwon sanyi kwa jidashi".


Haka tayita fa'da har Abba ya dawo sai data kai kara wajensa. Abba yace ta da'ga musu kafa. Sharrin ciki ne amma nan gaba zata daina. Sai wuraren karfe tara na dare tukuna Sabah ya koma can gidansa, kamar karsu rabu shida matar nasa.

Weekend Anty katibe ta duro kasan, Anty fanneh tayi murna sosai da zuwan yar'uwartata. Samha kuwa tafi kowa murna don da Azirak akazo, wanan karan ya kara wayo sosai yana gudunshi kota ina.


The following week aka soma shirye shiryen tarewan Samha gidan Sabah. Aka kwaso kayan lefe daga Abuja, su Anty Fanneh bude baki kawai sukayi suna bin kayan da kallon mamaki don ba karamin kudi Sabah ya kashe wurin mata siyayaen ba. Abbah kam girgiza kai kawai yayi. Yan uwan Anty Fanneh dake Bagada Anty Fanneh ta kira suka zo har gida sukaga kaya itama Anty Fanneh da Abba suka karawa Samah akwati har guda uku. Gado kayan daki da sauran kayan kitchen musaman Abbah ya bada order daga kasan waje aka kawo aka jerawa Samha a gidanta. Abun dai ba'a cewa komai don Abba ya taka rawar ganin wurin kayace gidan Ya'yan nasa.


Ranar da zata tare, Samha tayi kuka sosai kamar ranta zai fita rabuwa da Amminta. Anty Fanneh tun tana daurewa itama kuka ya kwace mata da kyar dai aka samu kukan nasu ya tsaya. Nasiha sosai suka shiga yiwa Sabah da Samha, Sabah yace insha Allah zai rike kanwarsa amana kuma zai kula da ita. Sai da yamma tukuna Sabah ya tafi da matar nasa. Gidan baban gida ne duplex harda penthouse a saman. Mamaki ya cika Samha tana karewa ko ina kallo. Tasan family dinsu Sabah nada kudi na fitan hankali amma wanan kam is beyond her expectations, don gidan ya hadu sosai.


Sati biyu da tarewar Samha a gidanta, suna zaune da Sabah a makeken parlournsu suna hira, ta daura kanta bisa cinyarsa tana wasa da hanunta bisa fafadden kirjinsa, kiran wayar Sabah ne ya katsesu. Ganin Abba ne ke kiransa yasa ya da'ga cikin sauri, nan Abba ya soma sanar dasu cewa suna asibiti da Anty Fanneh tana nakuda".


Cikin sauri Sabah ya mike, Samha itama tabi bayansa tana zaro ido. "Menene?" Ta jeho mishi tambayar.


"Ammi na asibiti.. yi sauri ki shirya muje".


A rude Samha ta haura sama ta dauko hijab ta sanya kirjinta na bugawa da karfin gaske ta sauko suka nufa asibitin.

Koda suka isa, har lokacin Anty Fanneh na labour room. Abba da Anty katibe hankalinsu a matukar tashe don likitan ya fito ya sanar dasu cewa bazata iya haihuwa da kanta ba dole sai an mata CS. Abba yasa hannu yace ayi indai matarsa will be alright. Sai faman karanto addu'oi yake Allah ya fito dasu lafiya. Samha ma gabadaya duk tabi ta rikice har kuka take tana adduan fitowan Amminta lafiya.


Sai can anjima tukuna likitan ya fito fuskarsa cike da damuwa. Abbah yaje ya sameshi hankali a dage ya soma tambayarsa lafiyan matarsa. Likitan yace ya biyoshi office, suna shiga ya nemi wuri ya zauna ya soma sanar dashi cewa ya kwantar da hankalinsa both mother and child are in good condition, an samu bouncing baby girl. Wani irin hamdallah Abbah ya soma yi cike da tsantsar farin ciki yana godewa Allah. Ji yayi tamkar doctor yayi mishi albishir da gidan aljanah. Baby girl... ya jima yana matukar son ya samu di'ya mace a rayuwarsa, ya samu Samha gashi kuma Allah yazo ya kara masa da wanan. Farin ciki a wajen Abbah kamar meye. Yana fitowa ya sanar dasu Sabah suma suka shiga murna, barin ma Samha ta takeji tamkar a mafarki wai yau tayi kanwa,ita da take ganin wasu da kanne abun yana bata sha'awa sai gashi yau itama she can claim one.


A tare dukansu suka shiga dakin da aka kwanatar da Anty Fanneh, da ita da babyn duk an tsaftace su. Anty katibe ta karasa wajen yayarta tana mata sanu, suma Sannu suka shiga mata don kana ganinta kasan ta galabaita dayawa. Samha ce ta fara zuwa inda aka kwantar da babyn ta daukota ta kura mata ido tana kallonta cike da tsantsar so da kauna bata san sanda hawaye suka fara zubo mata ba tsabar farin ciki. Yarinyar kamarsu da'ya da Abba tamkar an tsaga kara haka zalika babu inda ta baro Sabah shima. Hancin da bakin iri daya, a hankali Sabah shima ya matso yana karewa kanwar nasu kallo, nan take yaji matsanancin son yarinyar ya kamashi yana jin farin ciki na ratsa jikinsa. Juyawa Samha tayi ta kaiwa Abbah dake tsaye a gefen gado babyn tana fadin "Abbah gata".


Abba yayi bismillah yasa hannu ya karba babyn yana kare mata kallo yana jin kansa a lokacin as if he's the most happiest man in the world. "Fanneh kinga kyautar da Allah yayi mana cikin dan' kankani lokaci ko. Nagode my Queen." Godiya sosai Abbah ya shiga yiwa anty fanneh ha'de dasa mata albarka. Nan take ya kira Mami ya soma sanar da ita daga bisani ya kira yan'uwa duk aka sanar dasu, cikin kankanin lokaci asibiti ya cika yan uwa da abokan arziki aka zo aka soma tayasu murna.


Bayan kwana uku aka sallami su anty fanneh daga asibiti suka koma gida, Anty katibe ita take tayata da komai. Mami ma tazo da ita ake komai, sai a lokacin take nadamar abunda ta aikata, wani irin kunyar Anty fanneh taji ya lulubeta. Musamman tajata gefe ta bata hakuri akan maganganun data fada mata a baya baccin rai ne kawai ya janyo haka amma tayi hakuri. Anty fanneh taji dadi sosai tace komai ya wuce. Itama Samha tana gida har akayi sunna yarinya taci sunan Mami aka rada mata suna Bilkisu amma sai suke kiranta da Nehal. Sai da akayi arba'in tukuna Anty katibe ta koma can Dubai.


Gidan ya rage daga Anty Fanneh sai Abba da diyarsu Nehal sai kuma sophie dake taya Anty Fanneh da sauran aikacan gida. Nihal tana watanta na uku a lokacin ta da'an kara wayo kamaninta da mahafinta na kara fitowa. Jabbar ya dawo Nigeria hutu don tunda Abbah ya sanar dashi Anty Fanneh ta haihu duk yabi ya tada hankali yana so yazo yaga kanwarsa. Yana dira a Nigeria yaje gida yaga Nehal, tunda ya daura idanunsa akanta yaji babu abunda yakeso a duniyar nan sama da ita, rai da rai a hannusa take sai zata sha nono tukuna take raban jikin Anty Fanneh amma babu mai karbanta a hannunsa. A lokacin ya samu zuwa gidan yayan nasa, yaje suka gaisa Samha tayi murna sosai na ganinsa. Har hutunsa ya kare ya koma can kasan nasu.


**************


Yau talata, Samha tana kwance a bakin gado a dakinta ta fito daga wanka kenan daga ita sai towel, tana jin jikinta na mata wani irin nauyi hade da kasala a gabadaya gabobin jikinta. Ga cikin nan nata ya fito sosai don yanzu tana watanta na bakwai kenan. Tana kwance a hakan taji anyi sallama an shigo. Sabah ne kuma da allamun yanzu ya dawo daga aiki.


A hankali ya karaso ciki yazo ya tsaya inda take kwance yana kare mata kallo yaga yanayinta wani iri. Hannu yasa ya da'gota yana fadin "baby what's wrong?"


"Nothing. Babu komai" tafada mishi.


"Talk to me please. Idan kinada damuwa ko wani wurin ke miki ciwo ki sanar dani".


"Wlh babu abunda ke damuna. I'm just feeling tired ne kawai". Ta fada hade da mikewa tana mishi sannu da zuwa sa'anan ta soma kokarin cire masa kayan jikinsa. Bai hannata ba don daman sabonta ne idan ya dawo daga aiki ita ke tayashi rage kayan jikinsa. Shirt da tie dinshi kawai ta tayashi cirewa ya rage daga farar singlet sai bakin wando a jikinsa. mikewa yayi ya janyo hannunta sukayi bayi, daidai wajen mirror dake saman hadaden wash hand basin suka tsaya suna karewa kansu kallo ya janyota jikinsa sosai yana shakar daddaden kamshin sumar kanta..

hannunsa yasa yana shafo cikinta zuwa kasan mararta yana lumshe idanu. Muryarsa kasa kasa ya rada mata a kunne "I can't wait to see abunda zaki haifar mun kanwata.

Juyo da ita yayi suna fuskantar juna a lokacin jikinta ya rigada ya gama mutuwa sai yanda yayi da ita. A hankali ya hada bakinsu wuri da'ya ya shiga kissing dinta ha'de da aika mata da zafafan wasaninsa itama tana mayar masa ta samu ta rabashi da kayan jikinsa gabadaya itama yayi flinging da towel din nata. Gabadaya sun gama fita cikin hayacinsu. A hakan ne har ya samu ya ratsa cikin jiinta nan take taji wani iri sanyin dadi yana ratsa gabadaya jikinta har cikin kwakwalwarta.


A hankali dai ya dinga binta saboda cikin dake jikinta har suka samu hankalinsu ya dawo jikinsu suna ajiyar numfashi. Sai da komai ya lafa tsakaninsu tukuna suka karasa wajan shower ya kunna musu suka soma wanka, suna gamawa suka fito tare manne da jikin juna suka sa kaya sa'anan suka sauko kasa sukayi dinner suna hira abunsu gwanin ban sha'awa.


A kwana a tashi Samha har ta shiga watan haihuwarta, cikin dare nakuda ya tasar mata, ta dinga jin kasar mararta hade da bayanta na mata wani irin juyi tamkar zasu balle mata. wani irin zufa ne ya shiga karyo mata babu shiri ta tayar da Sabah dake kwance gefenta. Ganin yanayin da take ciki ne yasa ya tashi a rude ya shiga mata sannu. "Sabah cikina... bayana, marata... wayyo Allahna"


Nan take ya gano cewa nakuda ne yazo mata gadan gadan don tun jiya ya lura da yanayinta sai a hankali. Cikin sauri ya duro daga kan gadon ya dauko t shirt dinsa ya sanya yazo sa'anan ya dauketa cak yayi parlourn kasa da ita ya zaunar da ita yana mata sannu har lokacin sai faman sallati take tana yarfe hannu hade da runtse idanunta.


A ki'dime ya fice daga parlourn yaje waje ya tada motarsa ya yiwa mai gadi magana daya bude masa gate. Cikin sauri ya dawo ya dauki Samha wanda a lokacin har ta sauko daga kan kujeran saboda tsananin azaba. A bayan seat ya ajiyeta yana mata sannu sa'anan ya dawo driver seat ya tada motar mai gadi ya bude musu gate sai Lagoon hospital da'yan branch din dake bourdillon road cikin ikoyi don babu nesa dasu.


Suna isa cikin gagawa likitoci da nurses aka karba Samha, a lokacin har ta soma fita hayacinta. Sabaha yana kallo hankalinsa a matukar tashe aka shiga da ita, nan take ya ciro wayarsa ya soma neman Abba dasu Anty Fanneh a layi, cikin idon bacci Abba ya daga kiran yana jin abunda Sabah ya fada mishi nan take baccin ya washe daga idanunsa ya mike hade da tashin Anty Fanneh yace zai je asibiti anyi admitting Samha tana nakuda. Zumbur itama Anty Fanneh ta mike tace zata biyoshi yace tayi zamanta dare yayi wazai zauna da Nehal.

"Tabdijan Alhaji ya'ta ce fa take asibiti rai a hannun Allah tana nakuda kace nayi zamana? Bari kaga".


Dauko Negal tayi dake kwance cikin gadonta ta sabala ta a baya ta dauko zani ta koya sa'anan tace "muje Alhaji.." bata jira taji me zai ce ba cikin sauri ta sauka kasa kirjinta na matsanancin bugawa.


Suna isa asibitin ba'afi 20 minutes ba likitan ya fito yace dasu ta sauka lafiya don bata wani dauki lokaci wajen nakuda ba, abun yazo mata da sauki. Hamdallah su Abbah suka shiga yi suna mikawa Allah godiya. Sabah kusan yafi kowanansu murna don ji yake kamar ya zuba ruwa a kasa yasha jin Allah ya sauki Samha lafiya. Ya shiga godewa Allah.


"Likita me aka samu ne?" Abba ya tambayi likitan.


"An samu baby girl. Bissimillah kuna iya shigowa ku gansu".

Farin ciki a wajensu Sabah kamar meye, cikin sauri suka bi bayan likitan suka shiga da'kin da aka kwantar da Samha. Tana kwance ga babynta kwance cikin cot a gefe an kimtsa ta, sai faman mata sannu suke.


A hankali Sabah ya karasa inda take ya kamo hannunta cikin nashi yana mata sannu, yana kallonta cike da tsananin jin tausayi. Anty Fanneh ce ta karasa wajen cot din ta dauko babyn tana kare mata kallo hade da fadin "masha Allah... Alahji kaga baby tamkar baturiya, jibeta fa dan' Allah".


Abba ya matso kusa ya karba babyn yana karewa jikarsa kallo. Kyakywa da ita tamkar yar baturiya ga gashi daya kwanta kota ina duk yabi ya lulube mata kai. Ko nurse din data shigo sai datayi magana akan babyn don tayi mugun tafiya da imaninta. Sai faman yaba babyn take tana fadan albarkacin bakinta.


"Sabah bazaka zo ka ganta bane?" Abba ya tambayesa. A hankali Sabah ya baro inda Samha take ya karaso Abbah ya mika masa babynsa ya karba ya kura mata ido yana kare mata kallo. Zuciyarsa ne ya shiga harbawa da karfi ganin tsananin kama da yarinyar takeyi dashi babu inda ta baro shi. Wani irin sanyin dadi ne yaji yana ratsa zuciyarsa dama gabobin jikinsa gabadaya yana jin yanda son kyakyawar yarinyar ke kara ratsa jikinsa. Matsowa kusa da Samha yayi yana nuna mata kyautar da Allah ya basu. Samha ta kurawa yarinyar ido tana binta da kallo cike da mamaki tana tambayar kanta anya kuwa ita ce ta haifi wanan babyn?


Washe gari da Safe, sai gasu Mami nan suna iso itada Uncle Mubashir wanda shi daman yana Lagos tun satin nan daya wuce. Kowa yaga baby sai ya fada albarkacin bakinsa yana tubarkallah. Mami har da fadin cewa idan aka yayeta gaskiya ita zata dauketa ta dawo hannunta . Sabah yana jin abunda ta fa'di can kasan ransa yace "tab'dijan ai baki isa ba. ga dayar jikar ki nan kije kiji da ita amma babu mai daukar mun ya".


Kwanan su Samha biyu  asibiti aka sallamosu suka dawo gida amma can ainin gidansu suka nuda saboda ta samu kulawa na musaman daga wajen Amminta.

Ranar suna, diyar Samha da Sabah taci suna Juwairiyya don tunda Khadie ta kwalafa rai akan sunan har Sabah ta yiwa magana shima yaji sunan ya kwanta masa yace babu matsala idan macece za'a saka mata.
Khadie na jin an sakawa yarinyar suna Juwairiyya tafi kowa murna, taji dadi sosai. Aka sha suna lafiya. A lokacin Nehal tayi wayo sosai har ta soma takawa, kyakyawa da ita itama don tana shan gyara daga wajen Anty Fanneh kamar yanda takewa Samha lokacin tana karama. Nehal bata yarda da mutane sai yan gidansu. Ko Samha ma bata yarda ta dauketa amman tana barin Sabah ya dauketa ko don yana bata sweet tana sha. Anytime ta ganshi sai taje ta kwanta a jikinsa wani sa'in har tayi bacci a kafansa. Sosai Sabah yake ji da kanwar nasa.

Sai da Samha tayi kusan wata biyu tukuna ta koma gidanta da ita da kyakyawar di'yarta suka cigaba da rayuwarsu cike da tsantsar so da kaunar juna. Juwairiyya rai da rai tana hannun Sabah, bacci ne kawai yake rabasu, yana dawowa daga aiki zai dauketa suyita wasa, har tayi bacci a hannunsa. Ji yake Samha ta gama masa komai data bashi wanan fine baby girl din. Juwairiyya a lokacin tana wata bakwai har ta fara zama abunta tana gane mutane. Duk inda suka shiga idanun mutane na kanta abun har yazo ya fara ba Samha tsoro, Anty fanneh tace ta di'nga mata toffin adduo'i. Yauma kamar every weekend sun fita shakatawa. Jara mall dake sabon ikeja terminal suk nufa suna da'an grocery shopping, Sabah yana rike da Juwairiyya a hanunsa na dama, da'yan kuma na tura trolley. Samha tana biye dashi picking abubuwan da suke bukata a gida.+

Kiran sunanta da akeyi ne yasa Samha ta da'go hade da juyowa.wani irin shock tayi da idanunta suka sauka kan mai kiran nata. Madina ta gani tana kokarin karasowa inda suke cikin sauri. "Heartbeat kalla Madina ce fa ke kokarin karasowa inda muke".

Juyowa shima Sabah yayi idanunsa suka sauka kan Madina. Wani irin farin ciki ne ya lulube Madina tana karasowa ta rungume Samha tsam a jikinta tana fa'din "wayyo Antyna ashe inada rabon sake ganinki! Kwana dayawa!"

Itama Samha rungumeta tayi cike da farin ciki tana fa'din "Madina yaushe a gari. Yaushe kika shigo kasar namu" ta tambayeta tana kare mata kallo taga ta kara yin kyau tayi fresh sosai abunta".

"Wlh cikin satin nan. Sabah ina yini". Ta juyo tana gaishe da Sabah. Sabah cike da walwala ya ansa mata gaisuwar nata shima yayi farin cikin ganinta. Sai a lokacin idanunta suka sauka kan Kyakyawar yarinyar dake hannun Sabah. Wani irin shock ne taji ya ziyarce ta mika hannu ta karbi juwairiya tana fad'in masha Allah. Instantly taji yarinyar ta shiga ranta. "Samha babynku ce wanan? Na samu labari ai kunyi aure. Shinoh ke fa'damun last time da mukayi waya dashi" ta fada tana karewa Juwairiyya kallo cike da sha'wa, a ranta tana fa'din da itace yanzu da mallakin wanan kyakyawar babyn.sosai suka zurfafa da hiran yaushe gamo. Madina take sanar dasu harta gama masters di'nta gashi ta dawo gida. Yanzu aure ne kawai ya rage mata. Samha tace mata karta damu komai lokacine da sannu itama Allah zai fito mata da nata. Anan sukayi Sallama, Madina ta karba number wayar Samha tace insha Allah zata kawo musu ziyara har gida.

Juwariyya na cika shekara da'ya da yan' watani Sabah ya soma yiwa Samha magana akan ya kamata suje lebanon suje suga mahaifiyarsa don tunda taji yayi aure har matarsa ta haihu ta matsu kwarai akan tana son ganinsu. Ko jiya da sukayi waya da Sabah sai data dauko masa batun.

Sabah dayaje gida ya sanar da Abba batun son tafiyarsa Lebanon, Abbah ya goya bayan haka don tun ba yau ba yake ta son Sabah yaje ya ganta. Cikin da'an kankanin lokaci Sabah yasa akayi musu processing visa na zuwa kasar. Samha na cike da fargaba don bata san me zata je ta tarar ba acan.
A ranar da zasu bar kasar, su Anty Fanneh har airport suka raka su, Nehal harda kukanta wai sai ta bisu, da kyar Sabah ya samu ya lalabata tayi shiru hade da mata alkawarin sweets da biscuits iri iri, tukuna ta hakura. Jirginsu na landing a kasar Lebanon, Sabah ya kira mahaifiyarsu ya sanar da ita sun iso. Musamman ta tura driver yazo yayi picking dinsu daga airport. Samha ta shiga bin ko ina da kallo tana jin wani irin sensation na daban don kasar ba karamin burgeta yayi ba. Everything is so different there harta mutanen kasan duk larabawa ne, tun da sukayi landing a airport bata kuma ganin wani bakin fata ba.

Wani hadadden gida driver din ya kaisu yayi parking sa'anan suka fito cikin harabar gidan. Tun da'ga bakin kofar shiga parlourn gidan suka hango wata kyakyawar mace balarabiya fara sol da ita ta tunkarasu tana murmushi, idanunta kyam akan Sabah tazo ta rungumeshi tsam a jikinta tana jin wani irin farin ciki na ratsata duk illahirin jikinta. Yaushe rabon dataga dan'nata tun yana karami ta baro Nigeria sai yau. A hankali ta da'go tana kallon kyakyawar fuskarsa idanunta suka ciko da kwala tsabar farin cikin ganinsa ta soma mishi magana cikin harshen larabci. Shima Sabah wani irin yanayi ya tsinci kanshi ganin mahaifiyarshi after all these years.A hankali ya soma tuno da abubuwa da dama da suka faru a baya da kuma rashin kusancin shi da ita. Yayi kewanta har bai san yanda zai misalta ba.

A hankali matar ta dawo da dubanta ga Samha dake tsaye da Juwairiya a hanunta tana kallonsu cike da tausayi. Cikin harshen larabci ta juyo tana tambayar Sabah ko matarshi ce da yar'shi yace mata eh. Cikin sauri tazo ta rungume Samha da Juwariya tana musu barka da zuwa cikin hausanta daya saje da accent din Arabic. Da kyar Samha take fahintar abunda take fadi. Sabah yace ma mahaifiyarshi tayi mata turanci kawai tana ji. Dariya tayi sa'anan ta karbi juwairiyya daga hannun Samha tana kare mata kallo tana ji tamkar ita ta haifeta.
Hannunta rike dana Samha tayi musu bissimillah suka shiga ta daga ciki, ko ina fess sai yan aikin da suketa faman zarya cikin gidan. Suka zo suka soma jera musu abubuwa a gaba. Bafi 20 mins ba wani mutum shima balarabe ya sauko kasa yazo suka soma gaisawa. Tayi introducing inshi a matsayin mijinta, suna da da'guda da'ya amma baya nan yana boarding school sai anyi hutu zai dawo. Mutumin bashida matsala yayi musu tarba mai kyau. Dukda dai Samha bata jin abunda suke fa'di taji dadin yanda suka karbeta hannu bibiyu. Da yamma ne Jabbar ya samu ya shigo gida saboda tun safe yana school yana fama da lectures, tunda yaji labarin zuwansu yaketa Allah Allah ya dawo gida yazo ya gansu.

Murna a cikinsa kamar meye, suma sosai sukayi murnan ganinsa. Satin su Sabah uku a lebanon sa'anan suka dawo Nigeria saboda aikinsa. Mahaifiyarsa ji tayi kamar karsu tafi don cikin dan kankanin lokaci suna saba sosai har ta soma koyawa Juwairiya larabci itama tana da'an mayar mata da baby talks dinta. Sabah yayi mata alkawari cewa insha Allah idan an samu hutu zasu kuma zuwa.

A kwana a tashi juwairiya har ta kai shekara biyu, Nehal kuma na neman shekararta na uku, aka sasu a school suna zuwa. Juwairiyya ta kasance shiru shiru batada hayaniya da wuya ka ganta tana kuka ko wani abu sabanin Nehal uwar rigima abu kadan ke sata kuka. Juwairiyya na shekara kusan uku akayi mata kani, Samha ta sake haifo da' namiji yaci sunan Abba Mu'azzam amma sai ake kiranshi da Ayman shima kyakyawa dashi babu inda ya baro iyayensa a fanin kyau.

Bangaren Khadie da Amjad kuwa anata faman shirye shiryen biki amma a kano zasu zauna saboda can akayi posting Amjad wajen aikin custom daya samu. Amina ce kadai Allah bai fito mata ba har yanzu. Zack da Aliyah ma suma ana gab da shirye shiryen nasu. Lokaci nayi aka sha biki kuwa don babu wanda su Samha basuyi attending ba don ansha gwagwamayar rayuwa tare.
Musamman suka ha'da get together babu wanda bai halarta ba a cikinsu. Daga, Sabah, Samha, Zack, Abba, shinoh, Madina, Aliyah, khadie, Amjad, Amina. Duk sun halarta. A get together di'ine khadie ta soma tuna baya tana bada labarin how each and everyone of them met.. Tun daga crushing akan Amjad da Samha ta somayi, da fitinan Sabah ya rikitata har tazo tayi switching feelings zuwa gareshi da competition da suka dingayi da Aliyah akansa, aka dinga dariya. It was fun those days. Rayuwa kenan, you meet new people and before you know it they become such an important aspect in your life. A haka taron ya watse suka koma gida. Aka cigaba da tafiyar da rayuwa, Samha da mijinta suna zaune lafiya babu mai jin kansu, ga kyawawan ya'yan da Allah ya basu kullum kara gode masa sukeyi suna zaune lafiya cike da matsanancin son junansu.

The end.

ALHAMDULILAH, da wanan masu karatu na kawo muku karshen ZABIN SAMHA, my first completed hausa novel. kuma ina kara godewa Allah daya bani ikon kammalawa lafiya. To all ZABIN SAMHA FANS, su Anty Nabila, Maryam, sha'wa, zainab thanks for all the comments❤️ We've come such a long way Allah barmu tare. you guys are great.

Post a Comment for "ZABIN SAMHA CHAPTER 15 KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...