ZABIN SAMHA CHAPTER 12 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZABIN SAMHA CHAPTER 12

ZABIN SAMHA CHAPTER 12

- - Post a Comment

 ZABIN SAMHA CHAPTER 12


A daren ranar dai Sameer yana ajiye Madina a gida, khaleesat ta kirashi a waya tace tana son ganinsa.

Gidansu ya karasa yana zuwa kofar gida yayi parking ya kirata a waya yace ta fito.


Tana fitowa ta karaso cikin motar suka gaisa. Khaleesat ta kura masa ido na da'an lokaci tana kallonsa taga gabadaya duk yabi yayi wani iri, kuma tasan ba komai bane yake damunsa illa son Samha da yake dawainiya da, cikin zuciyarsa.


Murmushin yake ta da'an sake sa'anan tace "yau ka fita da yar' budurwan taka kenan kun zaga gari, toh ya? Ka samu ka fallasa mata sirin zuciyar naka kuwa?".


Sameer yayi shiru yana jinta daga bisani ya gyada kai yace "eh kusan haka".


Gaban khaleesat ne ya fadi, amma tayi kokari ta dannetace "toh daka gaya mata me tace?"


"Ban sani ba wlh".


"Baka sani ba kuma?"


"ina cikin fada mata aka samu wani da'an accident so babu samu mun karasa maganar da mukeyi ba".


Khaleesat ta da'an nesa sa'anan tace "hmm toh shikenan naji, amma kafun ka samu ansar naka daga gareta, ni bari na fada maka nawa decision din dana yanke".


Sameer ya kura mata ido yana kallonta yana jiran yaji me zata ce.


"nasan laraba mai zuwa shine birthday din Samha, so daga yanzu har zuwa wanan ranar, bazan kara ganinka ba saboda bana so nayi influencing decision dinka. Amma da zarar ranar ta wuce, zan baka tsawon hour ashirin da hudu kaje kayi tunani mai kyau, inason kayi tunani ko akwai future tsakanina dakai".


Sameer shiru yayi yana sauraronta bai ce komai ba tunani kala kala na masa yawo aka.

Ita kanta Khaleesat tasan abu mai kamar wuya ne ta iya canza masa ra'ayi don tasan Yanda ya kwalafa rai akan yarinyar mallamin nasa don haka bata jira taji ansar da zai bata ba, zuciyarta na mata radadi tayi masa sai da safe sa'anan ta fice daga cikin motar tana share kwalar daya samu nasaran gangaro mata.


Washe gari da safe, Samha na zaune cikin aji ana musu lectures, Sameer ne yake gaban ajin yana musu lectures amma gabadaya hankalinta baya wajen.


Babu abunda yake mata yawo aka illa tunanin Sabah, can kasan ranta ta soma fadin "Nasan nida Sabah muna zaune tare a gida daya, makarantar mu daya amma bansan dalilin dayasa nake missing dinshi sosai a duk sanda bamu tare ba".


Sosai tayi zurfi cikin tunanin da takeyi, idanun Sameer ne suka fada kanta yaga gabadaya concentration dinta baya ajin, table din dake gabansa ne ya dan buga ya soma kiran sunanta "Samha?"


Firgigit Samha tayi ta farfado daga duniyar tunanin data afka tace "na'am?"


Cikin harshen turanci ya soma mata magana yace "do you need a break or something?"


Kirjinta na bugawa ta girgiza masa kanta tace a'a. Sameer bai sake ce da ita komai ba ya cigaba da lectures din.


Ana gama lectures Samha ta fito tana tafiya ita kadai, tunani ne suka mata yawa har bata ji sanda Sameer yazo zai wuce ta ba.


Dagowa tayi tagansa tace "ya' Sameer dan Allah kayi hakuri akan abunda ya faru dazu a class".


Sameer ya da'anyi murmushi yace "it's okay. My class is boring ai".


Samha tayi sauri ta girgiza masa kanta tace "a'a fa, ba haka bane. Kaima kasan i enjoy your classes".


Sameer yayi dariya yace "Samha kenan, yanzu ina zaki toh? Ko har kin gama lectures dinki for the day?"


"No ban gama ba yanzu haka inada Stats309".


Sameer yace"toh bari na barki ki karasa karkiyi lati. Sai zuwa anjima".


Haka Samha ta karasa zuwa lectures hall dinsu, Sameer yana tsaye yana binta da kallo abubuwa da dama suna masa yawo aka a game da ita.


Da la'asar misalin karfe uku da rabi, Samha na zaune cikin library tana son ta karasa rubutun assignment da aka basu.


Su shinoh da zack ne makale a wajen book shelf suna tsaye suna kallonta. So suke suje suyi mata magana amma suna shakkan abunda zai biyo baya.


Shinoh ne yayi ta maza ya karasa wajen table din da take zaune ya kira sunanta "Samha?"


Samha ta dago tana dubansa tace "na'am Shinoh yane?".


"Lfy. Wai da gaske ciwon da Madina tajiyo saboda Sabah ne?"


"Inji wa, Accident ne fa kawai aka samu". Samha ta fada mishi kai tsaye sa'anan ta cigaba da rubutun da takeyi.


Abba dake tsaye a can gefe ya karaso yana fadin "Anya kuwa? Saboda nasan SB sarai, da reflexes dinsa da komai ba zaiyu ace Madina ce zata zo ta cece shi ba".


Zack shima ya karaso yace "naji wai saboda ya ganki kuna rungume rungume da Sameer ne yasa yaji haushi".


Sabah ne ya karaso ciki basu ganshi ba, ai kuwa maganar karap a kunnensa.


Shinoh ya cigaba da fadin "Samha kema kinsan yanda SB yake, dan Allah ki dinga kula da abubuwan da kikeyi, bawai Muna blaming dinki bane, amma....."


"Amma meye?!". Sukaji murya daga sama.


Tare suka jiyo cikin sauri sukaga Sabah tsaye hannunsa rungume bisa kirjinsa yana kallonsu fuskarsa a daure. Nan take suka ja jinin jikinsu.


"Tambayar uwar me kuka tsaya kunai mata anan kamar wasu yan jarida? Duk wanda yasan yanada abun fadi yazo ya sameni direct."


Jikinsu ne ya hau bari, don sun san halinsa sarai yanzun nan sai ya hautsina musu tunani don haka tuni suka kama hanya suka soma barin wurin daya bayan daya, yana tsaye yana kallonsu har suka gama fita.


Bayan sun fita ya dawo da dubansa ga Samha wace itama jikinta yayi mugun sanyi. A hankali ta bude baki ta soma fadin "kayi hakuri amma fa kawai tambayata suka zo yi".


"I'm not deaf ai, Na jisu sarai, they were trying to criticize you suna so su daura miki laifi, and kema kinsan I won't take that shit".


Shiru Samha tayi bata sake cewa komai ba.


Sabah yace " taso muje, munada practice yanzu. Amjad yana jiranmu".


Babu musu Ta tattara takardunta tasa cikin jaka sa'anan tabi bayanshi suka fita zuwa Gym.


Suna isa aka fara practice, Sameer ne coach dinsu yana tsaye yana lura da yanayin da suke buga wasan.


Ai kuwa yasha harara ba kadan ba, don suna hada ido da Sabah sai yaga yana aika masa da wani irin kallo wanda shi kansa bai san ma'anarsa ba.


Aliyah dake tsaye kusa da Samha ce ta lura da abunda yake faruwa tayi kasa da muryanta tana fadin "Samha ranan naga ke da Sabah da madina da kuma Sameer kuna tsaye a point road. Meya faru?"


Samha tayi shiru daga bisani tace " Madina ce taji rauni shine muka kaita asibiti. Yanzu haka ma shi ke kaita gida yana daukota".


Sameer ne ya hura whistle ya katse musu maganar da sukeyi yace "practice is over, we're done for today".


Nan take wasa ya tsaya, Amjad ya karaso cikin sauri inda su Samha suke tsaye sai faman ajiyar numfashi yakeyi ga zufa yana karyo masa tako ina yace "Samha kin samu kin kamala rubutun dana baki na meeting dinan? Yanzu fa zamu fara meeting din"


Zaro ido Samha tayi tana fadin "yanzu zamu fara meeting din?! Ina zuwa toh." A guje ta bar wurin tayi hanyar library.


********************


Bangaren su Sabah kuwa, zaune yake cikin library tare da Madinah wace taketa faman rubutunta hankalinta kwance.


Jiran Samha yake ta fito su wuce gida amma shiru shiru baiji duriyarta ba. Ai kuwa ya cika yayi fumm, sai faman hucci yakeyi don shi a rayuwarsa ya tsane jira.

Suna cikin haka sai ga Samha nan ta karaso ciki a guje kamar an jefo ta har tana neman faduwa.


Sabah ya dago yana dubanta fuskarsa a daure yace " meye haka? Kin wani shanya mutane anan, tun dazu fa muke jiranki".


Samha ta marairace fuska kamar zatayi kuka tace "dan Allah kuyi hakuri, wlh yanzu Amjad yake sanar dani cewa munada meeting."


Tana karasa maganar sai ga Sameer nan ya sawo kai ta daga bakin kofar shigowa library din yace "Samha, kiyi sauri kefa ake jira".


"Toh gani nan zuwa". Samha ta fada mishi .


Sabah yana jin haka, ya kara harzuka ya matso inda take suna facing juna yace " tunda haka ne, mu zamu fara wucewa don bazai yu nabar gimbiya tana jira ba". Ya karasa maganar yana murmushin mugunta ya nuna inda Madina take zaune a can gefe. Yayi hakan ne don kawai ya bata haushi, itama taji yanda yakeji a duk sanda ya ganta tare da Sameer.


Ai kuwa burinsa ya cika, don Samha kusan numfashinta ne ya kusan tsayawa jin abunda ya fadi. Ido kawai ta bisa dashi tana ji tana gani ya cewa Madina "Madina taso mu tafi".


Babu musu Madina ta mike ta tattaro takardun ta tayiwa Su Samha sallama Sa'anan tabi bayanshi.


Samha tana tsaye a inda ya barta, ji take tamkar a mafarki wanan abunda Sabah yayi mata.


*****************


Sabah kam suna fita daga library din suka soma tafiya shida Madinah tana biye dashi a baya zuwa inda yayi parking motarsa.


Madina kam da kyar take tafiyan don wani irin matsanancin ciwon ciki ne ya rufeta a wajen.


Tsugunawa tayi ta bude jakarta tana kokarin ciro chocolates dinta na fama, don shine kadai yake iya lafar mata da ciwon mara idan ya tasar mata.


Sabah har ya isa inda yayi parking motarsa, ya jita shiru.


Juyowa yayi ya ganta can gefe a tsugune hanunta rike da mararta tana yarfa hannu.


Cikin sauri ya karaso ya tsuguna a gabanta yana tambayarta abunda ke damunta.


"Chocolates Sabah...chocolates dina ya kare". Ta fada mishi kwalla na ciko mata cikin idanunta.


"Toh sai me idan ya kare? Yanzu kike so kisha ko me?"


Gyada masa kanta kawai tayi tana cigaba da rike cikinta.


Nan take ya gano abunda ke damunta don haka yace "taso muje ki shiga mota sai mu tsaya akan hanya na siyan miki".


Da kyar ta iya tashi suka karasa wajen motar ya bude mata suka shiga.


Gaban kingsway super market yayi parking yace mata yana zuwa, cikin sauri ya karasa cikin supermarket din yaje ya samu cashier din ya soma tambayarta ko tanada irin chocolates din da Madina takeso.


Yarinyar tace "kayi hakuri sir, wlh bamuda shi ya kare. Sai zuwa next week zamu sake restocking".


Sabah yace mata toh shikenan babu matsla. Nan ya fita cikin sauri ya soma duba sauran shagunan da suke jere kan layi amma duk basu dashi.


Haka ya hakura ya dawo cikin motar ya mika mata wani coffee tea mai dumi a cikin gwangwani yace "ungo nan sai ki manna a cikin naki ko zai lafa. Ban samu chocolates dinba".


Madina ta kurawa abunda ya mika mata ido sa'anan ta karba ta manna bisa cikinta.


"Ya akai kasan abunda ke damuna kenan?"


"Oho nidai kawai na siya ne don nasan ku mata kinibibin na dayawa".


Madinah ta da'anyi murmushi tace "ina son chocolates sosai, shi yake lafar mun da wanan ciwon, shiyasa bana rabuwa dashi".


Sabah yace "wanan ai ba so bane, dependency ne kuma babu kyau. Yanzu idan baki samu chocolates din ba ya zakiyi kamar yanda ta kasance miki yau?".


Madina ta sunkuyar da kanta daga bisani tace "meyasa baka bari mun jira big sister ba?"


"Ai ita ba karamar yarinya bace, zata iya zuwa gida dakanta". ya fada mata kai tsaye sa'anan ya tayar da motar suka soma tafiya.


Suna isa kofar gidansu Madina, Sabah yayi parking. Sa'anan Ya fito ya taimaka mata ya bude kofar.


Godiya ta soma yi mishi, suna cikin haka wayar Sabah ta soma ringing, hannu yasa cikin aljihunsa zai ciro, garin ciro wayar wani abu ya fado daga cikin aljihunsa bai sani ba.


Amjad ne ke kiransa don haka yayi saurin kara wayar a kunnesa. Shiru yayi yana sauraronsa daga bisani yace "Samha? Toh shikenan gani nan zuwa".


Ko sai da safe bai yiwa Madina ba, cikin sauri ya karasa cikin motar.


Madina tsugunawa tayi ta dauko abunda ya fadi taga zobe ne. Zata mishi magana tace ya yarda abu kenan taga har yaja motar nasa yayi gaba.Bangaren su Samha kuwa, by the time da suka gama meeting din, dare ya rigada yayi.


Tafiya take ita kadai tunani kala kala na mata yawo a ka, from nowhere taga mota yazo yasha gabanta yayi parking.


Tsayawa tayi gabanta na harbawa don a tsorace take saboda daren daya rigada yayi.


A hankali aka sauke glass din motar taga Sameer ne a ciki.


Kofar gaban ne ya bude mata yace ta shigo, babu musu ta karasa ta shiga motar yaja suka soma tafiya.


Suna cikin tafiya Sameer ya juyo yana dubanta yace "Meyasa baki jirani na kaiki gida ba da aka gama meeting? Baki tsoro Kin gwamace kiyi tafiya ke kadai akan titin nan cikin daren nan? Kema kinsan it's not safe".


Samha shiru tayi tana jinsa daga bisani tace "Sabah nake jira yazo ya daukeni, amma shiru ban ganshi ba".


Sameer kiran sunanta yayi a hankali yace "Samha....?"


"Na'am" ta ansa mishi.


Bai juyo ya kalleta ba ya cigaba da tukin da yakeyi yace "Samha meke damunki? Kuma inaso Ki fada mun meye a tsakaninki da Sabah?"


Cikin sauri ta dago tana dubansa, kirjinta na harbawa amma tasan there's no point in hiding anything don haka tace " Sabah yayana ne, kuma shine wanda zuciyata take so kuma take muradi, amma nasan hakan abu mai kamar wuya ne, don bazai taba yu'wa ba. Iyayen mu bazasu taba yarda ba".


Sameer jin kalamanta yayi tamkar saukan dalma acikin kahon zuciyarsa amma yayi kokari ya dane abunda yaji ya taso masa yace " meyasa kikace abu mai kamar wuyace?".


"Saboda already an rigada an zabar mishi matar dazai aura. Bacin haka taya zamu fara tunkarar iyayenmu da wanan zancen? Musaman Ammi, taya zan fara mata bayanin cewa na kamu da son da'an mijinta?


Sameer ya da'an nesa sa'anan yace "ina so ki dauki wanan soyayyar taku a matsayin kaddara da kuma jarabawa, idan har kedashi kuka samu kuka tsalake, kuka ci wanan jarabawar toh your love will only become stronger, soyayyar dake tsakaninki dashi ba haramun bane kuma aure ya hallata a tsakaninku amma kamar yanda kikace bakisan yanda iyayen naku zasu dauki wanan lamarin ba. Nasan abu mai kamar wuya ne amma ku cigaba da addu'a abunda kawai zan fada miki kenan".


Shiru Samha tayi tana sauraronsa tunani kala kala na mata yawo a ka daga bisani tace "Nagode Ya' Sameer" tana da'an sakar masa murmushi.


Shima murmushin ya sakar mata yace "karki ji komai nima nan zan tayaki da addu'a kuma na dau miki alkawari insha Allah bazan fadawa Amminki wanan zancen da mukayi ba".


Murmushin jin dadi Samha ta sakar masa nan take sai taji damuwar da take tattare dashi ya ragu.


Sabah sai faman sharara gudu yake akan titi yana sauri yaje yayi picking din Samha daga school, har yasha kwana kenan ya hango motar Sameer din ta saho kai, Samha ya gani zaune a gaban mota tare dashi suna yiwa juna murmushi.


Zaro ido yayi yana kallonsu har suka wuceshi zuciyarsa na harbawa da karfi kamar zata huda kirjinsa ta fito.

Zufa ne ya soma karyo masa ta ko ina, babu shiri yayi parking motarsa a gefen hanya yana bugun steering da karfi zuciyarsa na masa wani irin wawan tafarfasa.


Bangaren Samha kuwa, hankalinta yayi nesa bata lura da Motar Sabah datazo ta wuce su ba, har sukayi nisa. Straight kofar gidansu, Sameer yaje ya ajiyeta sa'anan tayi masa godiya sosai hade da sallama ta shiga cikin gida.


Tana isa parlour ta tadda Anty Fanneh ta fito daga kitchen kenan. Nan take ta soma tambayarta "Samha? Ya kukayi dare haka? tun dazu nake trying numberki bata shiga".


"Kiyi hakuri Ammi, wlh yau munyi club meeting ne bamu tashi da wuri ba".


"Toh Ina Yayan naki yake?"


Samha ta da'an zaro ido tace "bai dawo ba?"


"Toh kun samu sa'bani kenan don dazun muka gama waya dashi yace yana hanya zaije ya daukoki".


Cikin sauri Samha ta zira hannunta cikin jaka ta ciro wayarta ta soma kokarin kiransa.


Bugu daya tayi ya shiga amma sai faman ringing wayar takeyi ba'a daga ba.


Bangaren Sabah kuwa, reverse din motar yayi ya kama hanyar komawa gida, har ya sha kwana zai shiga layin estate dinsu yaga motar Sameer ya sawo kai, karawa motar nasa speed yayi yaje yasha gabansa.


Babu shiri Sameer ya taka birki, yana kokarin yaga wani tab'aben ne yazo yasha gabansa haka babu notice.


Ganin Sabah yayi ya fito daga cikin motar  a fusace ya nufo inda yake gadan gadan yana hucci.


Shima bai tsaya wata wata ba ya fito daga cikin motar nasa don ji yakeyi gwanda ayita ta kare yau ya huta da wanan jaraban nasa.


Sabah yana karasowa ya soma watsawa Sameer wani irin kallo yana hucci. Ji yake tamkar ya rufeshi da duka nan take a wajen tsabar haushinsa da yakeji.


Sameer ya dubeshi yace "Sabah naga Alama nida kai jinin mu bai hadu. Pagin mu bai zo daya ba".


"Gwanda ma da Allah yasa ka gano hakan tun wuri don duk abunda ya faru nan gaba i won't be responsible for my actions!"


Sameer ya sake ajiyar zuciya sa'anan yace "Inaso ka gane abu daya, ni nan ina son Samha.... amma a matsayinta na kanwata kuma yar' mallamina."


Kallonsa kawai Sabah yakeyi yana aika masa da wani irin kallo bai ce komai ba.


Sameer bai tsaya nan ba ya cigaba da fadin " a lokacin da marigayi yakeda rai, ya koya mun abubuwa da dama daya dangaci zamantakewar rayuwar, mutuncin dan Adam da kuma darajan dan Adam.......Alhaji ya dauke ni tamkar da'an cikinsa, ban taba ganin mutum mai son jam'a da kuma mara san kai irinsa ba, kowa nasa ne, kuma halinsa Samha ta dauka don Samha yarinya ce mai hakuri ga hankali da kuma sanin yakamata. shiyasa bayan duk tsawon shekarun nan dana sake ganinta nayi matukar farin ciki, saboda na tabbata da marigayi nada rai shima zaiyi alfahari da macen data zama yanzu".


Sabah shiru yayi ya cigaba da sauraronsa bai ce komai ba.


Sameer shima bai tsaya nan ba ya cigaba da fadin "Cikin yan kwanakin nan, na lura da yanayinta kamar bata cikin nutsuwarta kuma nasan tana cikin tsaka mai wuya ne a game da soyayyar da takeyi dakai. Sabah ni nasan Samha tana sonka, kuma duk abunda Samha takeso bazan taba so na zama sanadiyar rugujewar farin cikinta ba, don haka inaso ka kwantar da hankalinka, ni nan na dauki Samha tamkar kanwata da muka fito ciki daya babu wani abun dake tskaninmu kamar yanda kake tunani".


Sai a lokacin Sabah yaji hankalinsa ya da'an kwanta, jikinsa a sanyaye ya juya ya soma tafiya bai cewa Sameer kala ba, har ya isa wurin motarsa ya shige ciki.


Sameer yana tsaye yana kallonsa har yaja ya tafi yana jin zuciyarsa na masa wani irin kuna, don dai kawai yayi abunda yayi ne a matsayin ya kamata amma bawai zuciyarsa naso bane.


Bangaren su Samha kuwa, Gabadaya hankalinta a tashe yake, ta rasa samun sukuni, sai faman kiran layin Sabah takeyi amma ba'a dagawa.


Anty fanneh ce ta dubeta tace "wai har yanzu layin nasa?".


Samha ta marairace fuska tamkar zatayi kuka tace " eh Ammi".


Sake trying tayi taji still bai dauka ba, zumbur tayi ta mike ta janyo hijab dinta tasa zatayi hanyar waje.


Anty fanneh ta dakatar da ita tana fadin "keh, ina kuma kuma zaki haka? Bakisan dare yayi bane?"


Samha hankalinta a tashe tace "Ammi zan je na dubo Sabah ne".


"A'a ki bari dare yayi, Yanzu Abban ku zai dawo, idan ya shigo sai muje mu dubo shi".


Jikin Samha ne ya hau kirma, nan take taga bazata iya juriyan har Abba ya dawo tukuna ba don haka bata sake tsayawa ta saurari abunda Anty Fanneh zata ce ba tayi sauri ta fice daga parlourn.


Anty fanneh shiru tayi cike da mamakin yanda duk Samha tabi ta tayar da hankalinta haka, tabe baki tayi ta dauko waya ta soma neman Abba a layi tana so taji inda yake.


Samha na isa daidai gate, securityn gidan zai soma mata magana ko kallonsa batayi ba ballantana ta tanka masa ta bude gate din ta fita. A kofar gida ta tsaya ta soma waige waige ko zata ganshi, amma ko ina tsit sai dai'dai kun motocin da suke wucewa cikin layin.


Tana tsaye a hakan, sai ga motansa nan ta hango yana tahowa. Nan take taji wani irin relief ya ziyarci gabadaya ilahirin jikinta ta sauke nanauyar ajiyar zuciya.


Daidai kofar gidan Sabah yayi parkinga ya soma horn mai gadi ya bude masa ya shiga, itama Samha tabi bayansa.


Yana parking ya fito, Samha ta soma masa magana "Sabah ina ka shiga ne inata nemanka a layi baka daga ba?".


Fuskarsa a daure ya juyo yana dubanta, yace "toh menene, kinata faman kirana kamar wani biyan bashi?"


Harara Samha ta watsa mishi tace"Idan kasan zaka dinga dawowa gida lati haka ai sai ka kira ka sanar damu, daga ni har Ammi hankalinmu a matukar tashe yake".


"Saboda mun kasance muna gida daya ko meye?"


"Mene?" Samha ta tambayeshi cike da rashin fahimta.


A fusace yace "wai ina ma ruwanki dani ne? Eh! Kin cika sa mun ido! Inada yancin nayi abunda naga dama kuma a duk sanda nakeso, don haka ki rabu dani!".


Tsaki yaja sa'anan ya soma tafiya, kusan mutuwar tsaye Samha tayi a wajen jin tsawar daya mata. Shiru tayi tana dubansa yana tafiya zuciyarta na mata wani irin kuna.


Har ya da'anyi nisa muryarta na rawa ta kira Sunansa "Sabah!"


Tsayawa cak yayi bai juyo ya kalleta ba.


"Sabah yanzu fisabilillah abunda kayi ya dace kenan? hakuri fa nazo na baka, bansan cewa zaka dawo ka daukeni ba, shiyasa na bar Sameer ya kawoni gida".


Sabah still bai juyo ya kalleta ba yace "indai akan wanan ne ba sai kin bani hakuri ba. Ki rike apologies dinki".


Yana gama fadin haka ya gyada kai ya shige ciki ya barta tsaye a wajen.

Kwalla ne suka taru suka ciko cikin idanun Samha tasa hannu ta goge. A hankali itama ta soma tafiya ta karasa ciki. A daren ranar dai da kyar suka runtsa daga ita har shi, kowa da abunda yake masa yawo a kwakwalwarsa.


Washe gari da a safe, Samha ta shirya zata tafi school, jiki a sanyaye ta sauko kasa ta tadda Anty fanneh a parlour tana magana da yar aikinsu sophie.


Bayan sun gaisa Samha tace "Ammi, ina Sabah?"


Anty fanneh tace "ai tun dazun ya wuce makaranta".


Shiru Samha tayi tunani kala kala na mata yawo a ka, tasan saboda ita ne ya baro gida da wuri haka.


Ammi ne ta dubeta taga duk yanayinta ya canza tace "wai meke faruwa ne tsakaninku kedashi? Naga tun jiya sai wani daddake wa juna kukeyi, kunyi fada ne?"


Murmushin karfin hali Samha ta kirkiro ta soma girgiza mata kai tace "babu komai fa Ammi, ni zan wuce school yanzu kar nayi lati. Yauwa Ammi dan Allah ki bar mun dayan motarki mana na dinga tafiya da ita school".


Anty fanneh tace "kema kinsan bana son kina driving akan titin lagos dinan, kinsan yanda hanyoyin suke amma bari Abbanku ya dawo nayi mai magana muji me zai ce".


Samha tace "toh shikenan Ammi, ni na wuce".

A dawo lafiya Ammi tayi mata sa'anan ta fice daga gidan.


********************


A school, Aliyah ce take tafiya daidai corridor din department dinsu ta hango Madina tana tahowa.


Tsaki taja tayi kamar bata ganta ba ta juya zata tafi, ashe Madina ta rigada ta ganta ta soma kwada mata kira.


Tsayawa Aliyah tayi ta juyo tana dubanta har ta karaso.


Murmushi Madina ta da'an sakar mata tace "Aliyah ina kwana".


"Lafiya lau" Aliyah ta bata ansa fuskarta a daure.


Madina bata damu ba ta soma kokarin janta da hira tace "Aliyah kinga Sabah kuwa yau? Inata kiran layinsa baya dagawa".


Harara Aliyah ta watsa mata tace " oho nima ban san inda yake ba".


Tana gama fadin haka ta juya zata tafi, madina ta kira sunanta "Aliyah..."


A fusace Aliyah ta juyo zata gaya mata magana don ta gaji da jarabar yarinyar.


Gani tayi Madina ta zira hannunta cikin jakarta, bata bari ta karasa cirowa ba tace "ke nifa na gaya miki bana son chocolates".


Madinah ta girgiza mata kanta sa'anan ta bude mata tafin hannunta, tana nuna mata wani zoben azurfa mai dan karan kyau sai faman kyalli yakeyi. Zoben da Sabah ne ya yarda jiya da dare daya je sauketa a gida.Bangaren Sabah kuwa shima daidai lokacin ya tuna da zoben da ya yakeso ya bawa Samha nan take ya soma dube dube, jakansa ya bude ya soma dudubawa bai gani ba. Hankalinsa ne ya soma tashi.


Shinoh ne ya karaso inda yake yana fadin " SB wai me kake nema ne?"


Sabah bai tanka masa ba ya cigaba da dube duben da yakeyi.

Aliyah kwace zoben tayi daga hanun Madina ta zira a hannunta tana karewa zoben kallo cike da sha'awa tace "kai, amma zoben nan ya hadu".


Jiki a sanyaye Madina tace "zoben na mata ne ko?"


Juyowa Aliya tayi tana dubanta tace "wani irin tambaya ce wanan, toh da na maza ne?"


Madina ta sunkuyar da kanta kasa muryarta na rawa tace "Aliyah akwai wace Sabah yakeso ne?"


Wani irin freeze Aliyah tayi jin abunda Madina ta fadi.


Madina bata tsaya nan ba ta cigaba da fadin " jiya dayaje sauke ni a gida, ya yarda zoben bai sani ba, kuma ina tunanin ya ajiye zoben ne yanaso ya bawa budurwarsa".+


Aliyah tace "kin gano kenan?"


Madina zaro ido tayi kirjinta na harbawa tace "Dan Allah da gaske Sabah yanada wace yakeso? Na santa?"


Shiru Aliyah tayi bata ce komai ba, can kasan ranta tace " tab ai ba a bakina za'aji mutuwan sarki ba".


"Aliyah? Ki fada mun mana". Madina ta fada muryarta na rawa tamkar zatayi kuka.


Suna cikin haka sai ga zack nan ya taho yana kokarin karasowa inda suke. Cikin sauri Aliyah ta ciro zoben daga hannunta ta bude tafin hannun Madina ta danka mata.


Zack yana isowa inda suke cike da zumudi ya soma fadin "Aliyah, ina kika shiga ne tun dazun naketa nemanki, kin manta yau kinyi mun alkawari zamuje muci abinci tare a cafeteria?"


Harara Aliyah ta watsa mishi tace "dallah can, yanzu ba daman mutum ya danyi lati?"


Zack ya soma sosa geyansa yace "kiyi hakuri gimbiyata, ai ko shekara nawa ne zan iya jiranki. Your wish is my command your highness".


Dariya Aliyah ta dan sake, zack ya dubi madina yace "Madina taho muje muci abinci mana".


Madina ta girgiza masa kanta jikinta a sanyaye tace "a'a nagode, nima dazun naci abincin".


Aliyah ta tabe baki tace "naga Alama ba yunwar kukeji ba, ni kunga tafiyata". ta fada ta soma tafiya ta barsu a wajen.


Zack har ya juya zai bi bayanta Madina ta dakatar dashi tana fadin "zack?"


Juyowa yayi yana dubanta yaga ta zira hannunta cikin jaka ta ciro chocolates har wrap uku ta mika mishi.


Kurawa chocolates din ido yayi, madina ta dan matso tayi Kasa da muryanta tace "ka bawa Aliyah".


Murmushi ya da'an sakar mata yana mata Godiya sa'anan ya kara gaba.


Suna isa Cafeteria suka tadda su Shinoh da Abbah zaune a ciki, nan Aliyah ta soma zayano musu yanda sukayi da madina.


Shiru sukayi suna sauraronta kowanansu cike da jimami da tsananin tausayin Madina.


Zack ne yace "Yanzu wazai fada mata kenan?"


Abbah ya girgiza kai yace "badai ni ba don gaskiya bazan iya ba".


Zack yace "amma idan aka cigaba da boye mata she'll be more hurt. Ni a ganina gwanda kawai a fada mata ta sani tun yanzu".


Aliyah tace "gaskiya kam, gwanda chocolate girl ta sani tun wuri kafun abubuwa suyi nisa".


Shinoh yace "tab ace mutum kamar ki mai daskararen zuciya ta garara fada mata ina ga mu?"


Cikin sauri Aliyah ta juyo tana duban shinoh tana watsa mishi wani irin kallo.


Hannu zack ya buga kan table yana fadin "ya haka mallam?".


Dawo da dubansa yayi ga Aliyah ya soma murmushi yace "kiyi hakuri your highness, yana nufin mace mai hankali da kamala irinkin ta gagara fada mata".


Murmushi ne ya nema kubucewa Aliyah amma tayi sauri ta dane, tayi buruss tayi kamar bata jishi ba.


Abbah tafi yayi sa'anan yace "kai ku matso kuji yanada za'ayi. Inada plan".


Tare suka matso suka hada kai, Abbah ya soma zayano musi yanda zasuyi su shawo kan laamarin.


Bangaren Samha kuwa, har sun gama lectures sun fito tasoma tafiya ita kadai. Tafiya takeyi amma gabadaya tunaninta baya jikinta.

Abu daya ne kawai zuciyarta ke hasko mata shine inda zata ga Sabah, rabonta da ganinsa tun jiya da dare, kuma tana bala'in missing dinsa.


Gym ta karasa don tasan bazata rasa ganinsa a can ba.


Ai kuwa Tana shiga ta hango shi a saman bene shi kadai yana tsaye yayi shiru yai zurfi cikin tunani.


A hankali ta soma haurawa saman matakalan. Kafun ta karasa sai ga Amjad nan yaje ya tsaya kusa dashi yana fadin " Dan Allah Sabah meye haka? Kazo ka tsaya nan kanata faman tunani, nifa ban son ganinka haka. Ban saba ganinka cikin irin wanan yanayin ba".


Shiru Sabah yayi yana jinsa bai ce komai ba.

Amjad ya cigaba da fadin "toh don Sameer ya kasance wanda Samha takeso tun tana karama sai me? Kaima kafi kowa sanin wanda zuciyar Samha takeso yanzu. Toh kishin meye zaka tsaya kanayi?"


Dogon numfashi Sabah yaja sa'anan ya soma fadin "Abu daya ne nakewa kishi Amjad, Shine rashin kasancewar Sameer yayanta.... haushi nakeji cewa nine na zamo yayanta kuma nasan da wuya iyayenmu su amince mana, Amjad bakasan yanda nakeji ba a duk sanda na tuna cewa zan iya rasata ba nan gaba, bazan iya juriyan haka ba don zuciyata zata iya bugawa". Ya karasa maganar yana fuzar da iska mai zafi, zuciyarsa na masa wani irin radadi.


Samha tana tsaye tana sauraron duk maganar da sukeyi. Jikinta ne ya kara sanyi, bata bari sun ganta ba ta juya ta bar wurin.


Library ta nufa ta ciro takardunta ta soma dubawa. Har tayi nisa da karatun nata, from nowhere taji an kipa mata wata katuwar littafi a gabanta.


A razane ta dago taga Aliyah tsaye a gabanta tana fadin "ga journal dinan sai kisan yanda zakiyi kiyi updating dinsa".


"Ni kuma?". Samha ta tambayeta.


"Kwarai kuwa, don Madina ta wuce gida tace yau bazata samu yi ba".


"Harta wuce gida? Meya faru?".


"Oho ban san mata ba, amma kamar ta soma dagowa cewa akwai wanda Sabah yakeso amma bata san cewa ke bace".


Samha ta zaro ido tace "toh yanzu ya za'ayi kenan?".


"Toh ai dole a samu wanda zai fada mata, don ko ba jimawa ko da dadewa dole tasani".


Hankalin Samha ne yayi mugun tashi don tasan idan Madina tasan wanan maganar toh kamar su Mami da Anty fanneh sun gama ji ne.


Da dare misalin karfe bakwai da rabi. Samha zaune take a gefen gado ita kadai a cikin daki tana rubuce rubucenta.


Bata jima da fitowa daga wanka ba, fuskarta fresh babu makeup tana sanye cikin kayan baccinta.


Wayarta ce ta soma ringing a kusa da ita, ta janyo ta soma duba mai kiran nata. Sunan Sabah data gani rubuce a screen din ne yasa kirjinta yayi wani irin harbawa, jikinta na bari ta daga ta kara wayar a kunne.


"Kina ina? Ki fito yanzu ina jiranki". Ya fada mata kai tsaye.


Zatayi wata maganar taji ya katse kiran. Ciro wayar tayi daga kunnenta tana karewa screen din kallo tace "wai wani irin mutum ne wanan, bai ma jira na tambayeshi inda yake ba, ya wani ce na fito".


Turo dan karamin bakinta tayi gaba tana kunkuni tamkar yana gabanta, sa'anan ta mike.


Karar sako taji ya kara shiga wayarta ta dauko ta soma dubawa. Text ya turo mata yana fadin " ki sameni a cikin gida, ina garden".


Tabe baki tayi ta karasa wurin dressing mirror dinta ta dauko turarukanta masu sanyin kamshi ta fesa sa'anan ta dauko hijab dinta ta zira ta fice daga dakin.


Daga harabar gidan ta karasa garden din nan ta sameshi zaune kan daya daga cikin kujerun shakatawa wurin, shi kadai yayi zurfi cikin tunani.


Kamshin turarenta dayaji ne yasa ya dago suka hado ido ya kafeta da kyawawan idanunsa.


Daya daga cikin kujerun ta janyo itama ta samu wuri ta zauna suna fuskantar juna.


Sosai ta Kura masa ido tana kallonsa. Sai taga ya kara haske ga kuma kuma yar'ramar da yayi don kallo daya zaka masa ka gano cewa yana cikin damuwa da tashin hankali.


"Meyasa kazo nan ka zauna kai kadai?"


Shiru ya danyi daga bisani yace "nazo nan ne nayi clearing head dina. Inaso na kauda duk wani unwanted feelings din da nake ji."


"Wani unwanted feelings kakeji?"


"Jiya mun hadu da Sameer kuma munyi magana dashi".


Cike da mamaki Samha take kallonsa tace "Haba dai. Kai da Sameer?"


"Yes. Na hadu dashi a hanyar dawowa".


Huda ta turo baki tana fadin"toh Meyasa baka fada mun jiya ba".


"Saboda haushi nakeji jiyan nan, a tsarge nake".


"Haushin me kakeji?"


"Kinsan yanda na dinga ji dana ganki zaune a gaban motarso ne kuwa?".


Cikin muryan shagwaba ta soma fadin "nidai karka wani daura mun laifi, duk laifinka ne, ina jiyan tafiya kayi ka barni a makaranta".


"Toh ya kikeso nayi? Kinga dai dole naje na sauketa a gida".


Shiru Samha tayi tana kallonsa, tunani kala kala na mata yawo aka. Ba abunda take tunani illa maganganun data jiyo jiya yana fadawa Amjad akan yanda zasu tunkari iyayensu da wanan maganar.


Don haka tace "Sabah yanzu ya zamuyi?"


Shiru yayi daga bisani ya sauke nanauyar ajiyar zuciya don shi kanshi bai san yanda zasuyi ba.


Hannu yasa ya janyota ta fada jikinsa, ya rungumeta tsam a jikinsa yana sake ajiyar zuciya.


Labewa tayi a jikinsa itama tunani kala kala na mata yawo aka, suna tunanin mafita.Madina zaune take a dakinta da zoben a gabanta ta kura masa ido, gabadaya ta gagara samun nutusuwa a cikin ranta sai faman tunani takeyi.


Wayarta ce ta soma ringing a kusa da ita, ta dauko tana dubawa. Bakuwar number ta gani ta daga kiran ta kara a kunne.


"Madina kina gida?"


"Eh ina gida, wake magana?"


"Shinoh ne. Ki fito gamu a kofar gida".


Mamaki ne ya cikata tana tunanin meye zai kawosu shinoh kofar gidansu.


Mikewa tayi ta dauko gyalenta ta sanya sa'anan ta fito.


A kofar gida ta tadda su suna tsaye, murmushi ta sakar musu suka soma gaisawa tace " ya naganku cikin daren nan, wani abun ne ya faru?".


Kame kame suka soma yi suna da'an sosa geya, wanan ya kalli wanan, wanan kuma ya kallo wancen duk sun kasa hada ido da ita.


Madina ta kallesu daya bayan daya cike da tuhuma tace "ku fada mun mana, wani abun ne ya faru?"+


Zack ne ya fara magana cike da i'ina yana fadin "eh toh daman akan Ss..sabah ne".


Madina ta da'an saki ajiyar zuciya tace "indai wanan ne already na rigada nasan cewa yanada wace yakeso".


Shiru dukansu sukayi suna kallonta, Abba ne ya da'an buge zack da kafada yayi mai allamu daya cigaba da mata bayani mana.


Zufa ne ya soma karyo wa Zack don baima san ta inda zai fara ba, don yana bala'in jin tausayin Madinan.


Bai san sanda ya runtsa idanunsa ba ya furta "Madina inaso ki sani cewa Sabah bazai taba yin aure babu soyyaya ba".


Shiru Madina tayi tana kallonsa daga bisani tace "wace Sabah din yakeso.... nasanta?"


Shiru sukayi basu bata ansa ba.


Sai data sake maimaita kanta tukuna shinoh yace "kiyi hakuri, bazamu iya fada miki ba don bamu son muyi hurting dinki".


Abba yace "dukan mu nan muna sonki".


"Kuma koda kin cire Sabah a ranki, nine nan zan fara tambayarki ki zama budurwata". Shinoh ya karasa maganar yana sakar mata murmushi.


Dariya Madina ta soma yi, shima Zack yace "dabadin inada budurwa ba already, babu wanda ya isa yasha gabana wajen kwato soyayyarki".


Murmushi ta sakar musu sa'anan tace musu "ina zuwa."


Bude gate din gidansu tayi ta koma cikin gida bafi 3 minutes ba sai gata ta fito hanunta rike da chocolates ta soma mika musu daya bayan daya.


Godiya suka mata hade da sai da safe, shinoh ne ya dan taba ta yana nuna mata hasken wata hade da zahra sai faman walkiya sukeyi a sararin samaniya, sa'an ya juya suka tafi.


Madina tafi 5 mins tsaye a wajen tana kallon sama tana kokarin ta fahimce abunda Shinoh yake nufi daya nuna mata Zahra da wata.


Cike da sanyin jiki ta juya ta shige cikin gida ba tare da ta samu ansa ba.


****************


Washe gari da safe, Anty fanneh tana kitchen tana faman soye soye tare da sophie a kitchen.


Samha zaune take kan dining tayi shiru tayi zurfi cikin tunani.


Wayar Anty Fanneh ne ya soma ringing, Samha ta mike zata je ta dauko, daidai wurin matakalan taci karo da Sabah shima ya sauko kenan yayi shirin tafiya makaranta.


Kirjinta ne ya harba ta tsaya tana kallonsa, shima kallonta yakeyi, idanunsu ne suka tsarku cikin juna cike da so da tausayin junansu.


Anty Fanneh ce ta karasa cikin sauri taje ta dauki wayar nata ta kara a kunne.


Abbah ma ya shigo cikin parlourn kenan shima yayi shirin zuwa aiki ya soma tambayarta "waye ne yake kira haka da sasafen nan".


Anty Fanneh ta katse kiran tace "Mami ce".


Nan take zukatan Sabah da Samha suka harba jin an ambato sunan Mami.


"Toh me tace?" Abba ya tambayeta.


Shiru tayi daga bisani tace "wai iyayen Madina ne suka kirata suka ce sun fasa bikin".


Zaro ido Sabah sukayi shida Samha, don jin maganar sukayi kamar daga sama.


Abba yace "toh fa? Me yayi zafi haka. Ta fada miki dalilin dayasa suka janye ne?"


Anty Fanneh ta girgiza kai tace "a'a bata fadamun ba".


Abba ya juyo yana duban Sabah  yace "wai kai meke faruwa ne? Nida nake tunani kai da yarinyar nan kunyi zurfi?"


Anty Fanneh tace "a'a Alhaji kasan yaran yanzu, sai kanayi kana binsu a hankali yanzu kilan ita yarinyar ce ta canza ra'ayi tace bata son auren".


Cikin sauri Abba ya karasa inda Sabah yake zaune ya soma fadin "Allah sarki baby boy na, kayi hakuri kaji nasan da ciwo amma inaso kayi kokari ka danne zuciyarka. Karka bari ya dameka".


Hade fuska sabah yayi ya kawar da kansa gefe kamar bada shi Abba yake ba.


Sai da Abba yayi magiyan har ya gaji, a fusace Sabah ya dauki jakansa baiyiwa kowa magana ba ya fice daga parlourn yana hucci.


Abba ya tabe baki yace "oh Allah, wai yaushe yaron nan zai rage zafin zuciya ne haka?".


***************


Samha na isa school, bayan sun gama lectures sun fito tare dasu khadie ta soma zayano musu abunda yake faruwa.


Khadie tace "wato Madina ita da kanta ta janye auren kenan. Toh indai haka ne kinga kakar Sabah din bazata gano akwai wani abu a kasa ba".


Amina tace "amma na tayaki murna Samha, kun samu kun tsaleka wanan obstacle din kedashi".


Shiru Samha tayi tana jinsu bata ce komai ba.


Khadie ta dubeta tace "wai yanaga kinyi shiru, kamar baki so hakan ta faru ba. Ko baki son shida ita su rabu ne?"


Ajiyar zuciya Samha ta sake sa'anan tace "ba haka bane, honestly I don't know how to feel about this. Ya kamata ace nafi kowa farin ciki akan abun nan daya faru amma inaaa... I don't feel happy. Bansan meyasa ba".


Khadie ta tabe baki tace "ai kefa daman haka kike, ba'a gane kanki".


Gani sukayi Samha ta tsaya cak tana kallon wani direction daban, suma tsayawa sukayi.

Madina suka gani tana tahowa idanunta kyam akan Samha. Nan take Samha taja jinin jikinta.


Tana karasowa ta gaishesu sa'anan ta juyo tana facing Samha tace "Big sis, dan Allah inaso nayi wata magana dake idan bazaki damu ba."


Kallon juna su khadie suka soma yi, Jiki a sanyaye Samha tace "toh babu matsala muje cafetaria."


Sallama tayi da su Khadie sa'anan suka karasa cafetaria tare da Madinah.


Suna isa cafetaria suka nemi wuri suka zauna.


Shiru ne ya ziyarce su, Madina tace "Big sis, daman akwai wani abunda nakeso na baki".


Hannu ta zira cikin jakarta ta ciro wata yar' karamar jewelry box ta mika mata tana fadin "Sabah ne ya yar da wanan zoben, ban sani ba ko zaki iya tayani mika masa".


Bude box din Samha tayi ta kurawa zoben dake ta faman walkiya ido.


Madina ta da'an saki murmushin yake tace "ina jin ya siya zoben ne ya baiwa budurwarsa".


Jikin Samha ne ya kara mugun sanyin tayi shiru tana jinta bata ce komai ba.


Madina ta cigaba da fadin " Big sis in har wata rana kin samu kin hadu da yarinyar da zata sanya wanan zoben. Ina so ki tayani koya mata wani abu guda daya".


Cikin harshen larabci Madina ta soma fadin "qalbi yurid sabah wa'yurid  'an 'akun maeah 'iilaa al'abad"


Cike da rashin fahimta Samha take binta da kallo tace "Meye ma'anarsa?"

Murmushi Madina ta sakar mata tace "yana nufin zuciyata tana son Sabah kuma tana son ta kasance tare dashi har abada".


A hankali Samha ta soma kokarin maimaita abunda Madina ta fadi cikin harshen larabci.


Madina ta gyada mata kanta sa'anan tace "haka ne big sis, naga alama kowa ya san da zamanta ni kadai ce ban santa ba. Nasan zuwa na yazo ya ruguza muku lissafi don gaskiyar Aliyah ce data ce na cika son kai".


Samha tayi saurin katseta tace "a'a Madina, bakida wani sonkai. Kinada kirku sosai. Bakiga yanda kowa ke sonki ba, daga ni har Sabah babu wanda yakeso yaga ya ba'ta miki"..


Murmushin jin dadi Madina ta sake sa'anan tace "i feel very lucky. Duk da dai ban samu abunda zuciyata takeso ba, haduwata daku ya zame mun wani shafi na cikin rayuwata da bazan taba mantawa ba. kowa yanason yaga ya kareni, daga Zack, Abba, shinoh, Sabah harta ke big sis, babu abunda zance muku. Kun nuna mun hallaci sosai wanda bazan taba mantawa ba".


Samha tamkar zata yi kuka ta soma fadin "a'a Madina ki daina fadin haka, ba yanda kike tunani bane. Asalima mune masu sonkai da muka dinga boye miki abubuwa da dama, musaman ni ban cancanci wanan yabon daga gareki ba"


"Karki damu big sis, I understand. Kowa nada nasa matslar kuma ni nazo na kara muku da nawa, amma yanzu na hakura na barwa Allah komai addu'a kawai zan cigaba dayi Allah yasa hakan shine yafi zama alkair. Nagode big sis, ni zan wuce yanzu sai anjima".


Tana gama fadin haka ta mike tayi tafiyarta zuciyarta na mata radadi. Wasu hawaye ne masu zafi suka samu nasaran gangaro mata tasa hannu ta goge. Tana ji tana gani ta hakura da Sabah kenan.


Samha tana zaune tana kallonta har ta bace mata daga gani itama zuciyarta na mata wani irin kunna da radadi. Wani irin tausayin Madina ne takeji yana huda kahon zuciyarta. Amma babu yanda ta iya itama.


*********************


Aliyah ne da Amjad zaune cikin class da wasu hotuna zube a gabansu suna dudubawa.


So suke suyi magazine album na basketball club dinsu amma sun gagara zaben hoton da zasu daura a front cover.


Amjad ne ya dubeta yace "wai ke wa kike tunani zamu manna a front cover dinan ya fito mana da magazine din da kyau. Ko musa hoton Zack ne?"


Aliyah ta bata fuska tace "Zack kuma?"


"Toh Shinoh fa?"


Nan ma ta girgiza masa kanta tana yatsine fuska.


"Sabah?"


Girgiza masa kanta tayi sa'anan ta ciro hoton Sameer tana nuna masa tace "wanan cine yafi dacewa muyi amfani da a matsayin cover din magazine dinmu".


Sake baki Amjad yayi yana fadin "masha Allah".


"Masha Allah? Sameer dine baka taba gani ba ko me?"


Dagowa tayi tana dubansa taga bama ita yake kallo ba, gabadaya hankalinsa yana kan wata kyakywar mace dake tsaye a bakin kofar shigowa ajin.


Bakowa bace illa khaleesat wace ta dubesu tace "sannun ku, dan Allah ina neman wani mallami ne mai suna Sameer Yusuf".


Shiru sukayi suna kallonta daga bisani suka ce yana 300level class yana koyarwa.


Shikam Sameer tsaye yake a gaban aji yana addressing class din, idanunsa ne suka sauka kan seat din da Samha ta saba zama yaga bata nan, jikinsa ne yayi sanyi ya soma tunanin inda ta shiga.


Bafi 10 minutes ba ya duba lokaci ya soma fadawa class din cewa wanan shine last class din da zaiyi tare dasu tunda daman yazo ne kawai yayi substituting wa malaminsu nada.


Yana gama fadin haka gabadaya yan'ajin suka mike suka soma tafa masa don ba karamin karuwa sukayi dashi cikin yan' kwanakin daya zo ya koyar dasu ba.


Godiya yayi musu sa'anan ya sallamesu, suka soma barin class din one by one.


Amina ce ta kwaso takardunta ta soma fadawa khadie cewa ita zata wuce don batada wani class bayan wanan.


Khadie tace "toh shikenan, sai zuwa gobe kenan idan Allah ya kaimu."


Sallama sukayi Amina ta fice daga clasa din. Khadie tana kokarin tatara takardunta Sameer ya karaso inda take yana fadin "Khadija wai ina Samha ta shiga ne yau? Ban ganta a class ba".


Kame kame khadie ta soma yi tana fadin "ina jin tana tare da Madina ne don dazun na barsu tare. Kayi hakuri bawai da gangan bane tayi missing class dinka ba. Abubuwa ne suka mata yawa cikin satin nan, tana cikin tsaka mai wuya".


Sameer ya gyada kai yace "babu komai, I understand. Notes din da akayi yau a class ki tayata kwafan su".


Khadie tace "insha Allah zan tayata".


Sallama sukayi harta juya zata bar ajin sai ga Sabah nan shida Amjad sun shigo cikin ajin a guje.


Amjad ne ya soma tambaryasu "ina Samha?"


Sameer ya dubi Sabah yace "yau bata shigo aji ba kuma nasan Samha bata missing lectures. From what I've observed Samha tana cikin damuwa matuka and i think she has reached her emotional limit komai zai iya faruwa idan ba dau mataki ba".


Haba, Sabah yana jin haka a guje ya fice daga cikin ajin zuciyarsa na bugawa da karfi, Addu'a kawai yake faman karantowa cikin zuciyarsa kada Allah yasa wani abun ya sameta. Don idan wani abun ya sameta mutuwa zai yi don bazai iya cigaba da rayuwa babu ita ba.


Bayan barin Sabah ajin, Amjad ya dubi Sameer yace "Teacher Sameer, gaskiya budurwaka ta hadu".Bangaren Samha kuwa gabadaya hankalinta a tashe yake. Gudu takeyi har bata iya ganin gabanta, babu abunda yake mata yawo aka illa tunanin rashin adalcin da take ganin sun yiwa Madina na barinta cikin duhu.+


Bata tsaya ko ina ba sai can saman benen building dinsu. Tana isa saman benen ta rushe da wani irin kuka mai tsuma rai.


Sabah sai faman gudu yakeyi har ya iso wurin building din department dinsu, zack na ganshi ya soma kokarin masa magana, Amma ko tsayawa Sabah baiyi ba ya saurareshi ya hankadeshi gefe.


Su shinoh ya tadda a gaba suma suna tahowa ya hankadesu gefe ya wuce.


Cike da mamaki suka soma binsa da kallo, Zack ne suka gani yazo yabi bayan Sabah cikin sauri. Suma basu tsaya wata wata ba suka mara mai baya.


Can saman benen Sabah ya haura, sai faman hakki yake yana ajiyar numfashi tsabar gudun dayasha.


Waige waige ya soma yi, nan ya hangota zaune ita kadai a can gefe ta kifa kanta cikin gwuiwowinta tanata faman sheshekar kuka.


Wani irin tightness ne yaji har cikin tsokan dake makale cikin zuciyarsa ganin rabin ransa a zaune cikin irin wanan yanayin.


A hankali ya soma takowa har ya karaso inda take zaune yazo ya tsuguna a gabanta yana fadin "Samha kukan me kikeyi anan?"


Samha bata dago ta kalleshi ba ta girgiza masa kai tace babu komai sa'anan ta cigaba da kukan da takeyi.


"Magana fa nake miki kina girgiza mun kai".


Cikin sheshekar kuka muryanta na rawa tace "nna...na rasa yanda zanyi ne Sabah. Ban san inda zansa raina ba na samu saukin radadin da take mun. A dalilin sonka gashi ina hurting mutane da dama. Wai laifi ne don zuciyata ta kasance tana sonka?".


A fusace Sabah yace " I don't care who i hurt indai akan sonki ne, ke kadai nakeso kuma ke kadai zuciyata takeso kuma take  burin ta karasa sauran rayuwa da. Idan bake ba, I don't want anybody else".


Jin kalamansa ne yasa bata san sanda ta mike ta fado kansa ba ta rungumeshi tsam a jikinta har suna faduwa a kasa tare.


Jewelry box din dake dauke da zoben da Madina ta bata ne ya fadi ya tarwatse a kasa.


Idanun Sabah suka sauka kan zoben a gefe, dagota yayi daga jinkinsa ya dauko  zoben yana kare mata kallo yace "wanan zoben fa, a ina kika ganta?"


"Madina ce ta tsinta tace na kawo maka".


Kamo hanunta yayi cikin nasa ya zira zoben a yatsanta na dama yace "no need, daman saboda ke na siya. Na siyo miki ne a matsayin birthday gift dinki. Ki tabbatar kina sata kullum".


Gyada masa kanta Samha tayi tana murmushi cike da tsantsa farin ciki, Sabah ya janyota ya rungumeta tsam a jikinsa yana ajiyar numfashi. Wani irin sanyi ya dinga ji yana ratsa duk ilahirin jikinsa.


Tafin da aka somayi ne yasa Samha tayi saurin kwace jikinta daga nashi tana kokarin mikewa.


Su Zack ne suka karaso suna tafi suna shewa, ita kam Samha kamar kasa ta bude ta shige ciki tsabar kunyar da takeji.


Sabah daure fuska yayi yace "yan sa ido me kuma ya kawo ku nan?"


"A'a mayar da wukan, munzo wucewa ne kawai muka ce bari mu tsaya muga draman dake wakana".


Shinoh ne ya soma kwaiwaiyon muryan Sabah inda yake fadin cewa "ke kadai nakeso kuma ke kadai nakeso na karasa sauran rayuwata da".


Su zack ne suka tuntsure da dariya suna fadin "ashe daman SB haka ka iya soyayya bamu sani ba".


Dariya suka cigaba da masa, a guje ya karaso zaiyi ta kansu, suma suka kwasa a guje suka bar wajen sunai masa dariya.

Guje guje suka somayi kamar wasu kana nan yara.


Itama Samha dariyan take musu tana kallon yanda suketa faman zolayansa suna guje guje.


Wani irin farin cike ne ta tsinta kanta ciki taji gabadaya ta nema damuwar nata ta rasa. Addu'a kawai takeyi Allah ya kawo musu mafita.


Bangaren Su Amjad kuwa, tare suka karasa class dashi da Sameer da kuma khadie.


Anan suka tadda Aliyah zaune ita kadai tayi zugum tana wasa da wasu keys a hannunta.


Amjad ya dubeta yace "Aliyah, ina budurwar Teacher Sameer din take?"


Wani irin kallo ta watsawa Amjad tace "tayi tafiyarta. Kuma yaushe ta fada maka cewa ita budurwa teacher Sameer ce?".


"Ta tafi? To meyasa?" Khadie ta tambayeta.


"Ban sani ba, nima nayi nayi da ita ta tsaya amma taqi, tace sauri takeyi. Kuma ta dau maka alkawarin cewa bazaku hadu da juna ba sai bayan laraba amma akwai saqon da takeso ta baka, gashi nan". Aliyah ta fada tana mikawa Sameer wani package hade da keys din.


"Tace idan na baka, kasan me sakon suke nufi".


Jiki a sanyaye Sameer ya karba package din da makullan daga hannunta tunani kala kala na masa yawo aka.


Khadie ce ta soma tambayarsa "sakon meye wanan teacher Sameer?"


Shiru Sameer yayi daga bisani yace "na jima ina neman abun nan ban samu ba, amma gashi ta samo mun".


"Toh me take nufi data ce bazata iya ganinka ba sai bayan laraba". Amjad ya tamabayeshi.


Kafun Sameer ya bada ansa, Khadie tayi saurin fadin "laraba fa shine birthday din Samha"


Juyowa tayi tana duban Sameer sa'anan tace "Teacher Sameer badai budurwarka kishi takeyi da Samha ba?"


Gyada mata kansa kawai Sameer yayi yace "tasan cewa wanan abun nakeso na siya na bawa Samha a matsayin birthday gift dinta shine ta siyo ta kawo mun".


Kallon mamaki suke binsa dashi, khadie tace "lallai kam tayi kokari da nice bazan iya ba wlh."


Cike da sanyin jiki Sameer yace "duk laifinane kuma ban yiwa Khaleesat adalci ba, duk tsawon shekarun nan ta kwalafa ranta akaina amma har yanzu ta gagara samun ansa kwakwara daga gareni.


Bangaren Khaleesat kuwa, tunda ta bar department din ta samu wani wuri ta zauna tana karewa ko ina na cikin makarantar kallo. Zaune takeyi a wajen amma gabadaya tunaninta baya jikinta.


Tana zaune sai ga Madina nan itama tazo tayi sallama ta nema wuri a gefen kujeran ta zauna.


Ansa sallamar Khaleesat tayi daga bisani sukayi shiru kowane da abunda yake masa yawo aka.


Khaleesat ne ta bude baki ta soma fadin "makarantar ku dinan nada kyau".


Madina ta da'an saki murmushi sa'anan tace "haka ne gashi kuma na kusan barinta"


Juyowa Khaleesat tayi tana dubanta tace "meyasa? Ke ba daliba bace anan?"


"Ni daliba ce amma zan bari saboda tun farko akwai wanda nakeso ne anan shiyasa nazo na fara karatu a nan. Tun farko daman nasan I don't stand a chance with him, yanzu da yayi rejecting dina dole na hakura dashi".


Shiru Khaleesat tayi daga bisani tace "gwanda da kika gano hakan tun wuri baki zurfafa ba. Ni dinan da kike gani kamar ke nake. Saboda wanda nakeso ne yasa nazo wanan makarantar, amma shi har yanzu ya gagara deciding ko yayi accepting din ko kuma yayi rejecting dina. Abun yana mun ciwo, shekaru nawa ina zaune inata faman jiransa amma har yanzu shiru. I don't think i have the courage to wait for him anymore".


Madina tace "indai kana bukatan farin ciki a rayuwarka dole sai kanayi kana karawa da hakuri, mai hakuri yakan dafa dutse har yasha romonsa. Ki cigaba da hakuri da addu'a Anty".


Murmushi Khaleesat ta sakar mata nan take taji yarinyar ta burgeta duk da dai yau ne ta fara ganinta, tace "nagode yar' kanwata. Allah yasa mu samu farin cikin da muke nema kuma Allah ya zabar mana mafi alkair a rayuwarmu".


"Ameen, Ammen". Madina ta fada tana zira hannunta cikin jaka ta ciro chocolates tana mikawa Khaleesat tace "Anty ungo wanan, shine idan nasha nake samu ya kwantar mun da hankali".


Khaleesat tana murmushi ta karbi chocolate din daga hannun Madina tace "nagode kanwata".


Mikewa tayi sukayi sallama da juna kowa ya kama gabansa.


Bayan kwana biyu, yau ta kasance ranar da Madina zata bar makarantar gabadaya ta koma Sudan.


Gabadayansu sukaji babu dadi kamar kar ta tafi, su Zack har da da'an hada mata wata yar' karamar farewell party.


Daidai bakin department dinsu suka tsaya suka dinga daukan hotuna. Sabah ne ma yake tsaye hanunsa rike da camera yanata musu hoto, Samha tana tsaye a gefensa duk jikinta yayi sanyi.


Aliyah kam tana tsaye a gefe taki walwala sai faman hura hanci take wai ita a dole haushin Madina take ji bata son wani abun da zai hadasu.


Bayan sun gama daukan hotunan, driver din Madina yazo zaiyi picking dinta. Tana karasawa wajen motar ta juyo tana dubansu tace "Nagode kwarai da gaske da irin kulawan da kuka dinga bani tun farkon haduwa na daku, bazan taba mantawa daku a rayuwata ba, nasan zanyi missing dinku sosai. Allah ya kaddara saduwa".


Murmushi su zack suka sakar mata suna daga mata hannu, Aliyah kam harara kawai taketa faman aika mata da.


Juyawa Madina tayi ta bude bayan motar ta ciro katuwar roba na chocolates tace "wanan shine gift dina zuwa ga basketball team dinmu... kuma inaso Aliyah tazo tayi accepting dinsa daga hannuna".


Aliyah zaro ido tayi jin Madina ta ambace sunanta. Ganin yanda kowa ya kuro mata ido ne tasa ta tako har inda Madina take ta tsaya a gabanta.


Madina tana murmushi ta mika mata robar chocolates din, karban robar Aliyah tayi tana yatsine fuska.

Har ta bude baki zatayi wata magana Madina tayi sauri ta cusa mata chocolates din a baki.


Wani irin dadi ne Aliyah taji ya ratsa ta, maganar da take kokarin yiya mutu a bakinta.


Shinoh ya soma magana daga inda suke tsaye yana fadin "Dan Allah Madina idan kin tafi karki manta dani. Ina sonki Madina".


Dariya kowa ya soma yi, Madina tace "karka damu insha Allah bazan tana mantawa daku ba".


Tana gama fadin haka ta juya ta shige cikin motar, hannu ta soma daga musu drivern yaja suka tafi.


Suma gabayadayansu daga mata hannu sukeyi cike da tsananin kewarta.


Samha ce Gabadaya zuciyarta ta gagara samun sukuni bata san sanda tabi bayan motar a guje ba tana kiran Madina.


Madina tayi saurin gayawa driver din daya tsaya.


Samha tana hakki ta karaso inda driver din yayi parking ta soma fadin "Madina bazan iya barinki ki tafi haka ba tare da na fada miki gaskiya ba. Zoben da kika bani, kinga nice ke sanye da ita". Ta karasa maganar tana nuna mata zoben a da'an yatsarta".


Shiru Madina tayi tana kallonta bata ce komai ba. Samha ta cigaba da fadin "a garin kare soyayyar dake tsakani na da Sabah shiyasa muka boye miki bamu fada miki ba. Kiyi hakuri ki gafarceni, nasan munyi miki ba daidai ba".


Madina ta girgiza kanta tace "a'a big sis, bake ya kamata ki bani hakuri ba, nice na kamata na baki hakuri danazo na saka ku cikin tsaka mai wuya. Kuma ina farin ciki daya kasance cewa kece Sabah yakeso. Babu abunda zance illa nayi muku fatan alkhair".


"Bakiji Haushina ba?" Samha ta tambayeta


"Ko kadan big sis, banji haushi ba. Kedashi kun dace kuma kada ki manta da abunda na fada miki. Ki dinga furtawa a duk sanda kika tsinci kanki cikin tsaka mai wuya kedashi. Allah zai kawo muku mafita."


A hankali Samha ta soma furta abunda Madina ta koya mata da larabci.


Madina ta sakar mata murmushi sa'ana tace " Nagode big sis, Allah ya barku tare keda Sabah".


"Ameen". Samha ta ansa mata tana jin nauyin dake tatare cikin zuciyarta ya gushe.


Hannu Madina ta soma daga mata sa'an taja glass din motar ta rufe, driver yaja suka soma tafiya Samha na daga mata hannu.


Bayan sunyi nisa hawaye suka soma gangaro wa Madina tana tuno farkon haduwarta da Sabah da kuma taimakon daya mata, da kuma sauran lokutan datayi spending dashi. Tasan ba karamin missing dinshi zatayi ba.


Hannu tasa ta goge hawayen tana kokarin dana zuciyarta don tasan wanan final kenan.

Post a Comment for "ZABIN SAMHA CHAPTER 12"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...