ZABIN SAMHA CHAPTER 11 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZABIN SAMHA CHAPTER 11

ZABIN SAMHA CHAPTER 11

- - Post a Comment

 ZABIN SAMHA CHAPTER 11


Bangaren Sameer kuwa, bayan sun koma school kowa ya watse ya kama gabansa.


Sameer ya biya wajen wata friend dinsa mai suna Khaleesat.


Khaleesat ta kasance tanada babban wuri na cin abincin kusa da makarantar su.

Sun jima suna abota tare kuma ta jima tana mutuwan son Sameer shine dai bai bata fuska akan suyi wata soyayya ba.


Khaleesat tasa aka kawo masu lemu masu sanyi sa'anan ta nema wuri ta zauna kusa dashi tana tambayarsa ya trip din nasu.


Sameer yace mata lafiya lau.


Khaleesat ta da'an nesa tana dubansa sa'anan tace "ya ka samu kaga yarinyar malamin naka kuwa?"


Sameer ya gyada mata kansa yace "eh"


Tace "toh how was the reunion?"


Sameer yayi shiru yana dubanta yace "meyasa kikeso ki sani?"


Khaleesat tace "haka nan. Kawai i just want to know. Baccin haka baka ce nan da yan kwanaki bane birthday dinta ba? Ai nasan saboda hakan ka dawo don ka taba fadamun cewa a da tun tana karama baka taba missing birthday dinta".


Sameer yace "Khaleesat kenan, you think too much".


Khaleesat ta danyi murmushi tace "haka ne mana. Shekara da shekaru nawa i've been watching you. Kana nan kana ta faman jiran yarinyar ta girma".


"Khaleesat dan Allah ki bar wanan maganar. Nidai nasan kaina kuma nasan bada wata manifa nazo ganinta ba".


"Khaleesat tace "Ka cigaba da denying sameer".


Sameer yace "Khaleesat ban gane waenan tambayoyin da kike mun ba. It doesn't sound like you at all".


Khaleesat ta sake ajiyar zuciya tace "toh shikenan, na bari. Mikomun wallet dinka".


Sameer ya dubeta yace "me kuma zakiyi da wallet dina?"


"Kai dai ka miko mun".


Sameer yasa hannu ya ciro wallet dinsa daga cikin aljihu ya mika mata ta karba ta bude, hotonsa ne da Samha wanda sukayi tun tana karama a bayane a jikin wallet din ta nuna masa hoton tace " in har ka tabbatar da gaske kakeyi ba jiran yarinyar nan kakeyi ba toh ka cira wanan hoton kasa nawa".


"Ban gane ba, meye a cikin hoto Khaleesat? Picture doesn't mean anything". Ya fada mata yana kurba lemunsa.


Khaleesat ta tabe baki tace "i think wanan hoto yana nufin jira. A lokacin dana fara haduwa dakai, nasan akwai wata yarinyar mai suna Samha data samu gurbi na musamman cikin zuciyarka, kana jiranta ta girma.. that why bance komai ba all these while I've been very patient with you."


"Ba haka bane Khaleesat, it's not what you think"


Khaleesat ta girgiza kai tace "you don't have to convince me, ka fara convincing kanka tukuna. Sameer bari na fada maka wani abu kaga yarinyar nan daka kwalafa ranka akanta, ba lallai bane ta kasance kamar yanda kake expecting ba, Ni yanzu i'm the one who's with you, and understands you the most. Ni ya kamata kasa a ranka ba wata ba".


Jikin Sameer ne yayi sanyi tunani kala kala suka soma masa yawo a ka.


Suna cikin haka yaji an kira sunansa. Dagowa yayi yaga Anty fanneh tsaye kusa da motarta tayi parking ta fito.


Kallonsa takeyi cike da mamakin ganinsa.


Khaleesat ta dubeshi tace "kasan wancen matar da take kiranka ne?"


Sameer ya mike cikin sauri yace " eh nasanta, itace mahaifiyar Samha bari naje mu gaisa".


Cikin sauri ya karasa inda Anty fanneh take yaje suka soma gaisawa.

********************


Bangaren su Samha kuwa, tunda suka dawo daga ita sai Sabah babu kowa a gidan, haurawa sama tayi zuwa dakinta ta da'an watsa ruwa a jikinta sa'anan ta sauko kasa zuwa parlour ta nema wuri ta zauna ta zabga uban tagumi.


Tayi zurfi cikin tunani, Sabah ya sauko kasa ya karaso cikin parlourn ya tadda ta a hakan.


Sanye yake cikin comfy wears daga gani shima bai jima da fitowa daga wanka ba.


Kamshin turaren jikinsa mai dadin kamshi ne ya mamaye Gabadaya parlourn .


Ya nema wuri ya zauna kan daya daga cikin two seaters  sa'anan ya dauko newspaper dake kan table ya soma dubawa yace "yadai big sister naga kin zabga wanan uban tagumin?"


Samha ta watsa mishi harara tace "babu komai".


Sabah ya dago yana dubanta sa'anan yayi mata alamu da hanunsa yace mata "zo nan".


"Baza'a zo din ba". Ta fada mishi tana murguda masa baki.


Sabah ya tabe baki yace "toh ai shikenan. Kisha zamanki". sa'anan ya cigaba da duba newspaper dake hanunsa.


Shiru ne ya ziyarce su, Samha ta kura masa ido taga harkan gabansa kawai yakeyi. Ga tambayar da takeso tayi masa yana nan yana cinta a rai.


Kasa daurewa tayi tace " Sabah yanzu ya zakayi da batun Madina?"


"Batun mene? Ban gane ba". Ya tambayeta kamar bai san abunda take nufi ba.


Samha tace "a gabana fa ta fada maka cewa tana sonka".


Sabah ya ajiye newspaper din a gefe ya mike yazo ya zauna kusa da ita yace "toh sai me don tace tana sona?"


Samha ta juyo tana dubansa cike da takaici tace "sai me fa kace?"


Ajiyar zuciya ya sake sa'anan yace "karki damu kanwata. Mata da dama suna kawo kansu gareni suce suna sona don haka ba sabon abu bane, da sannu kema zaki saba"


Haushi ne ya cikata bata san sanda ta mike tsaye tace "wlh Sabah ka cika ji da kanka, toh ni Ina ruwana da yan'matan da suke sonka? Ce maka akayi na damu ne?"


Sabah shima ya mike tsaye yace "Oho sai kije ki tamabayi wanan tsohon saurayin naki ya baki ansa".

Samha ta dubeshi taga duk yabi ya hada rai kamar hadari ya taso bata san sanda  ta fashe dariya ba tana fadin "daman na sani ai, kishi kakeyi da Sameer, shine zaka zo ka wani juye a kaina".


"Oho dai. Ke kika san wanan".


"By the way, akan meye zaka kirashi tsoho? Sameer is very matured kuma yanada hakali sosai".


From nowhere taji sabah ya mike ya turota kan kujeran ya soma mata cakulkuli yana fadin "wato nine childish ban san me nakeyi ba ko?" Ya fada yana cigaba da mata cakulkuli.


Ita kam sai faman kyalkyalewa da dariya takeyi tana kokarin kwatar kanta tana rokonsa da ya kyaleta ba dashi takeyi ba.


Amma ko sauraronta baiyi ba ya cigaba da wasa da ita yana jan dan karamin hancinta yana mata cakulkulin.


Basu ankara ba sukaji an turo kofar parlourn , Anty fanneh ce ta shigo hade da sallama ai kuwa sallama da bata karasa ba kenan taci karo dasu a hakan.

Gabanta ya yanke ya fadi ta tsaya curuss ta sake baki tana kallonsu.Sabah yana ganin Anty fanneh yayi zumbur ya mike.


Itama Samha mikewa tayi kirjinta na wani irin mahaukacin bugu.


"Innalillahi wa ina illahi raji'un! Shikenan yau kashinmu ya bushe. Ammi ta gano mu" samha ta fada can kasan ranta, zufa na karyo mata ta ko ina.


Ammi ta tsaya tayi shiru tana kallonsu, Kirjinta ne yake bugawa da karfi tana kokarin ta fahimce abunda ke faruwa.


Sabah ya Kirkiro murmushin karfin hali yana da'an sosa kai yace " Ammi kin dawo?".


Anty fanneh ta dubesu cike da tuhuma tace "Sabah, samha... meke faruwa anan?"+


Kame kame Samha ta somayi jikinta na bari tace "bb..komai Ammi kawai tsokanata yakeyi".


"Anty kijawa Samha kunne, rashin kunya take mun, ni kuma a matsayina na yayanta bazan bari tanai mun rashin kunya haka in kyaleta ba".


Anty Fanneh tayi shiru tana kallonsu don tama rasa mai zata ce. Tunaninta ne yake kokarin zuwa wani direction na daban amma tayi saurin kaudawa, don tasan akwai shakuwa sosai tsakaninsu kuma tasan yar'nata bazata taba aikata abunda zuciyarta take hasko mata ba. Amma still yanayin data zo ta gansu bai mata ba don haka ta dau alwashin zata zaunar dasu tayi musu fada akan irin wasan da sukeyi, bai dace ba.


A hankali ta karasa shigowa parlourn, hannunta rike da ledan cefanen datayi.


Samha ta karaso zata karba ledan daga hannunta, Ammi ta dakatar da ita.


Haka ta ja gefe ta tsaya jiki a sanyaye.


Ammi bata sake ce dasu komai ba ta wuce cikin kitchen.


Samha da Sabah suka kalli junansu cike da fargaba, barin ma Samha wace gabadaya hankalinta a tashe yake.

Suna tsaye a hakan Samha taji an kwada mata kira daga kitchen.


Jiki na bari ta karasa kitchen din, Anty fanneh tace "kizo ki tayani yanka vegetables dinan, inason na hada mana miyan nan kafin Abbanku ya dawo".


Samha tace "toh Ammi". Taje ta dauko wuka ta fito da vegetables din ta soma yankawa.


Bayan shigan Samha kitchen, Sabah ya juya ya haura sama zuwa dakinsa. Zuciyarsa fal da tunani. Babu abunda yake masa yawo a ka illa yanayin da Anty fanneh tazo ta riske su, da kuma reaction dinta. Dukda dai baya shakkan kowa kuma baiki kowa ma ya sani ba amma yana tunanin yanda iyayyen nasu zasu dauki abun don shidai a gaskiya yana  bala'in son Samha, baijin zai iya rayuwa da wata ya' mace idan ba ita ba, don kullum sonta dadda karuwa yake cikin zuciyarsa har baya iya controlling kansa idan ya ganta.


Yana cikin wanan tunanin wayarsa ta soma ringing yasa hannu ya dauko. Number daya gani a rubuce jikin screen dinne yasa shi jan tsaki ya wular da wayar gefe. Ba kowa bane illa Shafa, kwana biyun nan ta dauko wani saran kiransa ne da bai gane ba. Akalla a rana daya sai tayi mishi miss calls kusan sau hamsin ko sama da haka.


Sai da wayar tayi ringing kusan sau tara tukana ya daga ransa a bace. Zata soma yi masa magana, ya dakatar da ita yace " wai ke shafah, wace irin mayyar yarinya ce ke? Ana so dole ne? Ki rabu dani mana! Nace bana sonki. Wallahi idan na sake ganin kiranki a wayata sai nazo har gida nayi miki dukan fitan hankali. Shasha kawai mara kunya! Wai har ni zaki duba tsabar idona kice kina sona. Yaushe aka haifeki kika girma da har kika san wani abu wai shi so?"


Cikin muryan kuka Shafa ta soma fadin "wlh yaya Sabah ka yarda dani ina sonka. Banjin akwai wata macen da zata soka kamar yanda nake sonka. Wai meye aibuna da bazaka soni ba? Me na rasa?"


"Tambayata ma kikeyi? Toh idan soyayya ce nace bana yi! Kuma daga yau sai yau kinji nayi miki last warning kenan. Karki sake yunkurin kirana kice zaki fada mun wanan shirmen. Shashasha mara hankali kawai".


Yana gama fadin haka ya katse kiran, ya kashe wayar ma gabadaya.


Wani irin haushi yakeji, gabadaya shafah tazo ta sake dagula masa lissafi.


Mikewa yayi ya fada bayi ya watsa ruwa a jikinsa sa'anan ya dauro alwala ya fito ya tada sallar magrib.


Yana idarwa ya mike, yaje wardrobe dinsa ya fito da comfy wears dinsa, white tshirt da black trousers ya sanya.


Sumar kansa wace bata gama bushewa ba ya dauko towel karami ya soma gogewa. Yana gama gogewa ya dauko fav turarensa "storm for men" ya feshe duk ilahirin jikinsa dashi, sa'anan yabi lafiyan gado Ya kwanta yayi shiru yana tunani. Tunanin yanda zasu bullo wa almarin su tunkari iyayensu shida Samha yakeyi, yasan abu ne mai kamar wuya su amince musu.


Yana cikin wanan tunanin yaji an soma kwankwasa kofar. Mikewa yayi yaje ta bude kofar, Samha ce ya gani tsaya a bakin kofar, manyan idanunta masu rikitar masa da lissafi ta zubesu kyam akansa.


Shiru yayi yana kallonta bai ce komai ba.


Samha tace "Sabah ya ka kashe wayarka? Ammi ta kammala girki tace nazo na kiraka. Abba ma ya dawo".


Tana gama fadin haka ta juya zata tafi, Sabah yayi sauri ya kamo hannunta ya janyota cikin dakin.


A firgice take dubansa tace "a'a Sabah, kaga abunda ya faru dazun bana so ya sake faruwa don haka ka sakeni kawai na wuce".


Sabah bai sake mata hannu ba, yayi shiru ya tsura mata ido yana kare mata kallo na da'an wani lokaci, hannu yasa ya soma shafo kyakyawar fuskarta, Samha ta lumshe idanunta a hankali tana jin wani irin feelings na taso mata, jikinta na kara moving akan matsanancin soyayyar da Sabah yake nuna mata.


Saukar numfashin dataji bisa fuskarta ne yasa ta bude idanunta cikin sauri taga fuskarsa dab da nata yana kokarin ya hada bakinsu wuri daya tayi saurin kau da kanta gefe tana fadin "Sabah kayi hakuri, amma bazai yu mu ci gaba da hakan ba. Ina matukar jin tsoro wlh. Kaga dai reaction din Ammi yanda tazo ta riske mu dazun. Bana son hakan ta sake faruwa".


Sabah yayi shiru bai ce komai ba, ajiyar zuciya ya sake sa'anan yasa hannunsa duka biyu ya tallafo gefen fuskarta ya manna mata kiss a goshi sa'anan ya saketa yace "toh shikenan jeki, nima gani nan zuwa".


Jiki a sanyaye ta juya ta fita daga dakin. Sabah yabi bayanta da kallo yana jin wani irin shauki da sonta yana kara fuzgar zuciyarsa.


Komawa yayi ya dauko wayarsa daga kan gado sa'anan ya sauko kasa.


A dining ya tadda suna zaune suna hira. Sabah ya gaishe da Abba sa'anan ya nema wuri ya zauna a gefe.


Anty fanneh ta dauko plate ta soma serving kowa abinci. Already ta rigada ta da'an saki ranta don tun a kitchen suna girki tasa Samha a gaba tanai mata fada. Samha harda da'an hawayenta ta dinga mata magiya tace mata wasa kawai sukeyi itada Sabah amma daga yau bazata sake ba. Fada sosai Anty fanneh tayi mata tace shima Sabah din zata kirashi tayi masa fada.


Suna cikin cin abincin Anty Fanneh ta dubi Samha tace " Samha meyasa baki fada mun ba?"


Gaban Samha ne ya fadi ta dago cikin sauri tana duban Anty Fanneh.


' me kenan Ammi?" Ta tambayeta.


"Batun Sameer, daman yana gari har ma yana koyarwa a makarantar ku shine baki sanar dani ba?"


Sabah da Samha suka kalli junansu.

Abba yace "waye Sameer kuma?


Anty fanneh tana murmushi tace " daya daga cikin daluban marigayi ne. Dazun zanje kasuwa na ganshi. Ai Alhaji yaron nan yanada kirki kuma yanada hankali sosai, tun Samha tana karama take kirarin cewa shi zata aura don sun shakku sosai". Anty fanneh ta karasa maganar tana dariya.


Shima Abba dariya yayi sa'anan yace " toh ai bata bace ba, idan yana so ba sai a hadasu gabadaya har dana su Sabah ba?"


Abba ya juyo yana duban Sabah yace "yauwa Sabah, dazun mukayi magana da mami akan batun aurenka da yarinyar nan, tace tana so a tsayarda magana tunda kai da ita kun samu kun gana, kuma yarinyar ta amince tace tana sonka. Don haka, Inaso cikin weekend dinan ka shirya zamuje gidansu ku gaisa da mahaifinta".

Wani irin haushi ne ya turnike zuciyar Sabah barin ma Samha wace taji kamar ta kurma ihu nan take a wajen.


Anty fanneh ce ta lura da yanayin Sabah taga ya hada rai tamkar hadari, har ya bude baki ransa a bace zaiyi magana Anty fanneh tayi sauri ta girgiza masa kanta allamun karya ce komai yayi abunda mahaifinsa yace.Sabah yayi shiru bai sake cewa komai ba, har Abba ya gama maganar da zaiyi ya dasa aya.


Haka suka karasa dinner dinan, parlourn tsit, babu wanda ya sake cewa komai. kowa da abunda yake masa yawo a ka.


Bayan sun gama cin abinci, Sabah ya mike zai haura sama, Anty fanneh ta dakatar dashi tace ya tsaya tana son magana dashi.


Sabah ya dawo ya zauna, bayan su Abba sun haura sama, Anty fanneh ta juyo tana dubansa tace "Sabah, inaso ka saurareni da kyau. Wanana maganar da mahaifinka ya gama yi inaso ka dauki maganar da muhimanci. Gobe ka shirya kaje gidansu yarinyar nan ku gaisa ku soma sabawa da juna. Bana son naji wani musu".


Jiki a sanyaye Sabah yace "toh Ammi". Badan yaso ba don dai kawai yana jin nauyin Anty fanneh bazai iya mata musu ba.+


Mikewa yayi ya mata sai da safe sa'anan ya haura sama zuwa dakinsa zuciyarsa na masa tafarfasa.


Ita kam samha tunda ta haura sama zuwa dakinta ta nema nutsuwarta ta rasa. Sai faman zarya takeyi a dakin tana kaiwa da kawowa. Yanzu Daddy da gaske yake zai daurawa Sabah aure da Madinah? Ya zatayi kenan? Ina suke tunanin zata jefa kanta, don tasan bazata taba iya rabuwa da Sabah ba. Wani irin dishi dishi ta soma gani, ta nema wuri a gefen gado ta zauna.


Wayarta ta janyo ta soma nemansa a layi taji a kashe don haka ta mike ta dauko hijab dinta ta zira sa'anan ta fito daga dakin ta nufa bangarensa.

Tana isa kofar dakinsa ta tsaya ta soma bugawa a hankali, sai datayi knocking kusan sau goma bazo an bude ba sai ta soma tunanin ko yayi bacci ne? Wata zuciyar tace mata inaa, Sabah ai baya bacci da wuri, wani sa'in ma yana fitowa yaje fridge din kasa ya nema dan abun motsa baki Don haka wuri ta nema a kusa da step ta zauna ta zabga uban tagumi.


Sabah a tunaninsa duk mai buga masa kofa ya rigada ya tafi yasa yazo ya bude kofar a fusace.


Juyawan da zaiyi ya ganta a zaune ta zabga uban tagumi.


Kallonta yayi na yan sekoni sa'anan yace "ke zaman me kikeyi anan? Dare bai miki bane?".


Samha ta dago tana dubansa ta da'an turo baki tace "jiranka nakeyi ka fito".


Ajiyar zuciya Sabah ya sake sa'anan yazo ya nema wuri kusa da ita ya zauna.


Daddaden kamshin turarensa ne taji duk ya bibiyeta, ta lumshe idanunta a hankali don ji tayi tamkar ta daura kanta bisa kafardarsa su dore a hakan.


A hankali ta bude baki ta soma fadin "Sabah bana son ganinka cikin damuwa. A duk sanda na ganka haka hankalina baya kwanciya".


Sabah ya dubeta yace "ce miki nayi ina cikin damuwa?".


"Basai ka fada mun ba. Zuciyata da naka tamkar daya suke yanzu, idan kana cikin farin ciki ina sani haka zalika idan kana cikin bakin ciki duk ina ji a jikina".


Murmushi Sabah ya da'an sakar mata sa'anan yace "toh shi Sameer fa? Baki sanin farin cikinsa ko walwalansa?"


Samha ta girgiza masa kanta tace "koh daya kai kadai ne a zuciyar Samha. Kai kadai zuciyar Samha take so".


Sabah ya da'an wasa mata hararan wasa yace "toh ni kuma i saw something different a diary dinki. Inda kike kwararo masa zuciyarki akan yanda kike sonsa. Wai tun yaushe kika soma rubutu a diary dinan? Tun kina jss1?"


Zaro ido Samha tayi tace "Sabah ina kaga diary dina ka karanta?"


"Oho tsinta nayi".


Mikewa tayi tsaye hankalinta a matukar tashe kamar zatayi masa kuka don tasan irin kwabe da yarantar data dinga zubawa a cikin diary dinan.


Sabah ya mike tsaye shima, Samha ta kamo jelar rigarsa tana fadin "ka bani diary dina Sabah, akan me zaka dauko mun diary ka karanta. Ka bani kayana ko na sa maka ihu yanzu kowa ya fito".


"Baza bada ba, kiyi ihun mana".


Dayaga tana niyan ta shige dakinsa taje ta dauko, yasa yayi sauri kwacewa daga rikon datayi masa ya shige cikin dakin a guje tana binsa a baya.


Kafun ta isa ya rigada ya garke ya sawa kofar key.


Samha ta soma bubuga kofan tana masa magiyan daya bude ya bata diary dinta.


Bude kofan Sabah yayi ya watsa mata gwallo yana fadin "sai na gama karantawa tass tukuna zanyi deciding kona yaga ko kuma na konata" yana gama fadin haka ya sake garke kofar.


Bugun duniyan nan tayi yaqi budewa haka ta hakura ta koma dakinta zuciyarta na tafarfasa.


Shikam Sabah yana komawa cikin daki, ya dauko diary din ya soma karantawa, ai kuwa zuciyarsa ce ta kusan bugawa don abunda ke rubuce ciki ba karamin tayar masa da hankali yayi ba.


A hankali yake bin pages daya bayan daya yana karantawa, duk page din daya karanta yaga tana faman zazzaga soyayarta akan sameer sai yabi ya yaga. Dayaga ma abun ya isheshi yasa ya yaga diary din gabadaya ya watsar, ya kwanta akan gado yana hucci.

Wayarsa ce ya dauko ya kunna ta, ya shiga snapchat.


Sakkonin Samha ne ya soma cin karo da. Cikin sauri ya shiga snap dinsu ya bude. Wasu hotuna yaga ta turo masa.


Ai kuwa yana downloading bai san sanda dariya ta kubuce masa ba, yanda yaga ta hada rai ta cunkushe da'an karamin hancinta tana turo masa full bottom lip dinta alamun wai ita tana fushi dashi kenan.


Sauran hotuna kuma wasu funny faces takeyi da bai gane kansu ba. Dariya kawai yayi yana girgiza kansa. Komai na Samha burgesa yakeyi, gashi bata fushi. Kotayi kokarin yin fushin ma bata iyayi da kyau. Komai nata, her childish behavior, cute face dinta, everything about her kara dilmiyar dashi yake cikin kogin sonta.


Chatting suka farayi ya soma zolayenta tana masa shagwaba da magiya akan kar ya karanta mata diary shi kuwa yace ya rigada ya gama karantawa. Haka suka cigaba da rigima a chat, har bacci ya samu nasaran daukan su.


********************

Washe gari ta kasance ranar friday, don haka yau shigan manyar kaya yayi. Wata hadadiyar kaftan ya saka Ash colour, kayan sun masa kyau sosai sukayi contrasting da farar fatar jikinsa. Bai saka hula ba don shi ba gwanan son saka hula bane idan ya saka kaftan.


Curly black hair dinsa ta kwanta luuu bisa kansa sai faman fidda shekki takeyi.


Yana saukowa kasa yaci karo da Anty fanneh, bayan sun gaisa ta sake jaddada masa akan ya tabbatar yaje gidansu Madinah yau dinan.

Sabah yace insha Allah zaije.


Bayan sun gama lectures a school, misalin karfe hudu na yamma. Sabah ya fito daga department dinsu kenan yana tafiya shi kadai ya hango Madina tana tafe ita kadai.


Sanye take cikin doguwar abaya baka, tayi wrap round da mayafin. Yau kam sanye take da glasses manne bisa kyakyawar fuskarta.


Madina tana ganinshi ta barke da murmushi, ta soma karasowa inda yake zuciyarta cike da matsanancin farin cikin ganinsa.


Tsayawa tayi a gabansa tana aika masa da tsadadden murmushinta.

Sabah yayi shiru yana kallonta na ya'an sekoni bai ce komai ba.


Tsura mata ido yayi yana kallonta, abubuwa da dama na masa yawo a ka. Shikam yasan Madinah batada wata makusa ko muni a tare da ita da zai kita. Sai dai shi sam kwata kwata baya jin sonta a zuciyarsa. Don matukar Samha tana raye a doron kasa, bazai iya rabar wata mace da sunan soyayya ba ballanta aure. Sunfi tsawon minti goma a hakan suna kallon juna.


Madinah tace "Sabah ka bani number wayarka. Banida ita".


Da zaiqi, sai kuma ya tuna da kashedin da Anty fanneh tayi masa don haka yace "ina zaki?"


"Gida zani, yanzu muka gama lectures". Ta bashi ansa kai tsaye.


Sabah yace "toh muje na kaiki gidan". bai jira yaji ansarta ba ya juya ya soma tafiya.


Jin maganar tayi kamar daga sama don bata taba kawowa a rai cewa zai saurareta ba ballanta yace zai kaita gida. Don haka cikin zumudi tabi bayansa har suka karasa inda yayi parking motarsa.Suna shiga cikin motar ya tayar, wani irin sanyin kamshi ne taji ya bugi hancinta.


Sabah ya dubeta yace "kisa seat belt dinki."


Babu musu ta janyo seat belt din ta makala sa'anan yaja suka soma tafiya.


Kwatancen gidansu ta soma yi masa sai yaga ma basuda nisa da juna don avenue daya ce ta rabasu. Bai sake ce da ita komai ba kawai gani tayi yabi dasu hanyar awolowo road. Can island suka nufa ya kaisu wata babbar creamery inda ake siyar da kayan makulashe don ya lura da ita tana son kayan zaqi sosai.


Kokarin jansa da hira takeyi, tun baya bata ansa har yazo ya soma da'an sakin jiki da ita suna hira harda dariya.+


Gabadaya Sabah yaji company dinta is not boring kamar yanda yake tunani. Yaga she's a very free person batada matsala sai dai yaranta dayake da'an damunta.


Don tana ganin wani wuri da ake siyar da Ice cream tasa tsalle tana tafi kamar wata yar karamar yarinya tana fadin"wow Sabah kaga wancen ice cream din? Ban taba ganin ice cream mai tsawo irin wanan ba. Ko a sudan ban taba gani irinta ba".


Dariya kawai Sabah yayi sa'anan suka karasa inda ake siyar da ice cream din yayi musu order suka samu wuri suka zauna suka soma sha suna hira.


Suna gama shan ice cream din, Sabah ya dubeta yace "kin taba zuwa bakin ruwa?"


Madina ta girgiza masa kanta tace "rabona da bakin ruwa tun ina karama".


Sabah ya mike yace "toh taso muje."


Mikewa tayi tabi bayansa suka shiga mota ya kaisu zuwa bakin ruwan.


Madina tana saukowa daga motar a guje ta soma karasawa wurin ruwan, iskan wurin na ratsa ko ina na jikinta.


Har tayi nisa sai kuma ta sake dawowa ta kamo hannun Sabah ta soma janshi suna gudu tanai masa dariya don Allah Allah takeyi taje bakin ruwan.


Dab da bakin ruwan suka tsaya, ita kam sai faman bin ko ina takeyi da kallo tana murmushi.


Shikam Sabah shiru yayi yaje ya nema wuri a gefe ya zauna ya kura mata ido yana kallonta.


Takai kusan 10mins a hakan tana kallon ruwan da kuma jiragen da suke yawo akai. Juyowa tayi ta gansa zaune a gefe, cikin sauri ta karaso inda yake ta soma fadin "Sabah, larabci na ya soma kwari yanzu bari kaji. Lumshe idanunta tayi a hankali sa'anan ta soma fadin "qalbi yurid sabah wa'yurid 'an 'akun maeah 'iilaa al'abad"


Sabah shiru yayi ya tsura mata ido yana kallonta, don ya gane sarai abunda take nufi don tun suna kanana mahaifiyarsu take musu larabci amma yayi fuska yace "me kenan kike nufi? Ban gane ba. Nifa bahaushe ne, gwanda kimun da hausa yanda zanfi ganewa".


Madina tayi murmushi tace "ina nufin zuciyata tana son Sabah kuma tana son ta kasance tare dashi har Abada".


Murmushi kawai Sabah yayi yana Girgiza kansa.


Madinah tace "kaga na iya kunshi, wanan ma ni nayi da kaina". Ta fada tana nuna masa kunshin hanunta.


Sabah ya tabe baki yace "na gani, kin da'anyi kokari".


Madina ta turo baki tace "toh girki fa? Kaga na iya abinci kala kala. I know how to cook coconut fried rice with seasoned beef. Kai wane ka iya?" Ta tambayeshi tana dariya.


Sabah yace "oho nidai ci nakeyi. Ina ruwana da wani girki".


"Toh ko kanaso na girka maka? Me kake son ci?"


"Kin iya dafa fasolia baida?"


Madina tayi shiru tana nazari daga bisani tace "ai ban ma taba jin sunan ba".


Sabah yace "toh ai shikenan".


Madina tayi shiru sa'anan tace "i can walk very fast idan na saka high heels".


Sabah ya juyo yana dubanta yace "toh kiyi tafiyanki mana, waya hanaki?".


Madinah tayi shiru tana tunani don tama rasa abunda zata ce don ta burgeshi.


Cike da sanyin jiki tace "duk weaenan abubuwan dana lissafo maka, they're all the things I'm proud off. Na fadesune kawai don na burge ka, but naga kamar baka damu ba".


Sabah shiru yayi yana sauraronta bai sake cewa komai ba.


Cike da sanyin jiki ta mike suka soma tafiya. Sunzo wucewa ta wani shago Sabah ya hango wasu zobuna masu kyau na azurfa.

Zobe daya wace takeda design na star ne ta dauke masa ido don haka ya karaso cikin shagon Madina na biye dashi a baya.


Ciro zoben yayi yana kare mata kallo, Madinah ta tsaya daga can gefe tana kallonsa. Dagowan da zatayi taga wani abu daya dauke mata hankali don haka ta fita daga cikin shagon.


Mai shagon ya dubi Sabah yace "indai wancen yarinyar zaka siyar wa, karka dauki wanan kallan".


Sabah ya dago yana duban mai shagon yace "ban taba haduwa da mutum irinka ba, da wani ne ko baiyi ba zai ce mun yayi don kawai yan son ya sayar da kasuwansa".


Mutumin yace "kasan mun dade a wanan harkan kuma munsan irin kallan daya dace da mutum. Kuma wanan zoben da kake rike da ita tana dauke da tambarin zara wato matar wata".


Sabah ya da'an saki murmushi yace "haka ne, ina son na siya na bawa taurariyar da take haskaka zuciyata. Itama sunanta Fatima Zahra".


Ya tambayi mutumin nawa kudin zoben, mutumin ya fada mishi. Babu musu sabah ya ciro kudi daga aljihunsa ko kirgawa baiyi ba ya bawa mutumin sa'anan ya juya zai tafi, zuciyarsa fal da farin ciki yana tunanin Samha dinsa.


Mutumin ne ya kirashi yace ai kudin daya bashi sun wuce. Sabah yace mishi babu komai ya rike sauran.


Godiya sosai mutumin ya dinga yiwa Sabah yana sa masa albarka yana mamakin halin yaron.


Sabah yana fitowa daga shagon baiga Madina ba. Waigawa yayi ya ganta tsaye a gaban wata yar karamar yarinya yar talla da tray a kanta tana siyar da gyada. Yarinyar bazata wuce shekara shida zuwa bakwai ba.


Madina bata lura da Sabah dake tsaye a can gefe yana kallonta ba, ta da'an durkusa gaban yarinyar tana murmushi tace "yan' mata inaso ki siyar mun da duka gyadanki sai ki samu ki koma gida da wuri ko?"


Yarinyar ta dubeta tace "toh Anty, nagode. daman kanena suna jirana na dawo gida da wuri nayi musu homework".


Madina tace "toh yayi kyau. Ga kudin gyadar ki". Ta fada ta ciro wasu yan kudade ta mikawa yarinyar.


Yarinyar ta karba kudin ta tsuguna ta soma auna mata gyadar ta juye mata a leda sa'anan tace "gashi Anty".


Madina ta karba tace "yauwa,tunda yanzu inada gyada dayawa, bazan iya cin chocolates ba kuma".


Hannunta ta sake zira cikin jakarta ta ciro packet din chocolates ta mikawa yarinyar tace "ungo wanan ku tayani ci keda kananki a gida".


Yarinyar bata karba ba ta tsaya tana kallonta.


Madina ta bude hannun yarinyar tace "c'omon ki karba mana. Kinga idan baki karba ba zai zama waste a zubar".


Yarinyar bata ce komai ba ta karba chocolates din tayi mata godia sa'anan ta juya ta soma tafiya.


Madina ta tsaya ta tsurawa yarinyar ido tana tafiya har tayi nisa.


Muryar Sabah dataji kusa da ita ne yasata juyowa cikin saurin inda yake fadin "daman ance women a unpredictable, bakuda tabbas. Yanzu har kin gaji da chocolates din kike neman kai dasu?"


Gydar ya lebo daga ledar zai bare, Madinah ta girgiza masa kanta tace "ni ban damu da gyada ba".


"Sai kayan zaqi koh. Toh ungo nan". Ya bare gyadar yana mika mata.


Kallonshi tayi sa'anan ta kalli gyadar daya miko mata, Sabah yace "karbi mana".


Jiki a sanyaye tasa hannu ta karba, Sabah ya da'an sakar mata lalausar murmushi wanda sai dayasa zuciyarta ta da'an buga da karfi.


"Toh mu wuce gida koh? Ko akwai wani wurin da kikeso kije?"


Madinah ta girgiza masa kanta tace "a'a"


Yace "toh bisimillah, muje".


Tare suka karasa inda yayi parking mota, suka shiga yaja suka tafi.

Bangaren su Samha kuwa, tafiya takeyi cikin school ita da Sameer, wanda tun a class yaketa kokarin janta da hira.


"Gida zaki wuce yanzu?" Ya tambayeta.


"Eh na gama sauran lecturers dina so zan wuce gida".


"Toh muje mana na rage miki hanya".


Samha tayi dariya tace "a'a Sameer, karka wani wahalar da kanka".


"Wani wahala kuma Samha? Ya kikeyin haka ne?"


Samha tace "toh shikenan muje". Gabadaya hankalinta baya tare da ita don tun jiya rabonta data ga Sabah. Koh a school ma bata ganshi ba. Toh ina ya shiga? Ta tambayi kanta amma bata samu ansa ba.


Tare suka karasa inda Sameer yayi parking motarsa yaja suka fara tafiya.


Hira suka soma tabawa, Sameer yace "akwai wani littafi da Daddynki, Allah ya jikan rai ya taba bani lokacin ina zuwa karban karatu wajensa? Littafin nan ba karamin taimakamun yayi ba lokacin danaje school".


Samha tayi murmushi tace "na tuna lokacin da zaku zauna kai dashi kuyita karatu, nima sai na dauko yan' littatafai na nace nima sai nayi karatun har bacci ya tafi dani".


Dariya Sameer yayi yace "kinsan me daddynki ya taba fa mun?"


Samha ta girgiza masa kanta tace a'a.


Sameer ya da'an nesa sa'anan yace "tun kafun a haifeki a lokacin Anty fanneh tana dauke da cikinki yace mun idan macece yana son a sa mata suna Fatima Zahra'u. Ana haifenki kuwa kikaci suna Fatima amma kasancewa sunan kakarki aka sa miki, yasa Anty fanneh take kiranki da Samha har sunan ya biki".


Samha cike da mamaki take dubansa. Sameer ya da'anyi murmushi ya cigaba da fadin "lokacin daya fara daukanki a hannunsa yaga sai murmushi kikeyi abun yabawa kowa mamaki don jinjiraye ai basu san wani abu wai murmushi ko dariya ba. tun daga lokacin yace insha Allah zaki zamo mai kawo farin ciki da walwala a cikin zukatan mutane, kuma bazaki taba kasancewa cikin bakin ciki ba, kullum addu'a da fatan dayake miki kenan".


Haka suka karasa tafiyar Sameer yana ta bata labarin abubuwan da suka faru tun tana karama.


Suna zuwa kofar gida yayi parking motar, Samha tayi masa godiya hade da sallama sa'anan ta fito daga cikin motar, hannunta rataye ta jakar makarantar ta.


Sameer kallonta yakeyi yana jin wani irin feelings daya jima yana dannewa yana kokarin taso masa a game da ita. Wata zuciyar ce ta bashi shawara akan kar ya bari ta kubuce masa wanan karan, yaje kawai ya fallasa mata sirrin zuciyarsa ko zai samu sukuni.


Cikin sauri ya fito daga cikin motar yana kiran sunanta. Samha ta tsaya cak sa'anan ta juyo tana dubansa.


Sameer ya karaso yazo ya tsaya a gabanta yana kallon cikin kwayar idanunta.


Daidai lokacin da shima Sabah ya sawo kan motarsa kenan zai kai Madinah gida ya hango Samha tsaye a kofar gida tare da Sameer.Babu shiri Sabah yayi parking motarsa a gefen hanya zuciyarsa na masa wani irin tafarfasa.


Madinah ce ta juyo tana dubansa cike da mamaki don yanda ya taka birki yayi parkin a gigice ba karamin tsoratata yayi ba.


Gani tayi ya hada rai murtuk, ya kurawa wani direction ido, ko kyaftawa bayayi.


Kallon inda ya kurawa ido tayi taga Samha tsaye tare da Sameer.


Sameer wanda yazo ya tsaya a gaban Samha, zuciyarsa na bugawa da karfi ya soma fadin "Samha....."


Samha itama kallonsa takeyi da manyan idanunta tace "na'am".


"Samha akwai abunda ya jima yana damuna a cikin zuciya, na jima ina dawainiya da wanan abun kuma i think lokaci yayi daya kamata na bayanata ko zuciyata zata samu sukuni".


Shiru yayi yana kallonta daga bisani ya cigaba da fadin "Samha na jima ina nadamar abu guda daya, ina nadamar rashin kasancewa tare daku alokacin da Allah ya dauki ran mahaifinki. Kamata yayi ace ina tare dake, ina share miki hawayenki, na yaye miki duk wani kadaici da zaki tsinci kanki ciki a sanadiyar rashin mahaifinki. Samha tun lokacin dana tafi banida wani tunani sai naki, a koda yaushe kina nan cikin raina."

Ya karasa maganar yana kokarin kamo hanunta ya rike.+


Haba Sabah yana ganin Sameer ya kamo hannun Samha ya rike, jininsa ne ya kusan hawa, nan take jikinsa ya hau tsuma ya soma rawa, Bai san sanda ya bude murfin motar ba da karfi, ya fitto yana hucci kamar wani mayunwacin zaki. Madina na ganin ya fita itama cikin sauri tabi bayansa ta fito daga cikin motar hankalinta a tashe.


Inda Samha da Sameer suke tsaye Sabah ya soma nufa gadan gadan. Kan titin ya hau ko dubawa baiyi ba ballanta yaga motar dake tahowa tana sharara gudu akan titi.


Ai kuwa Madina na ganin motar ta sake wani irin razananen kara tana kwalawa Sabah kira daya kauce a hanya.


Amma inaaa, it's too late.


Karar da Samha taji ne yasa ta juyo a firgice taga Sabah yana tahowa ga kuma mota ta taho zata bugeshi. A razane ta kwada mishi kira "Sabah!!!..."

Sabah juyowa yayi yaga motar data nufoshi gadan gadan, nan take ya zaro ido yayi freeze ya tsaya kirjinsa na bugawa da karfi don already ya rigada ya sadakar.

Madina ce ta biyo bayanshi a guje ta hankadeshi daga kan hanyar, driver din daya taho a guje, kokarin tsayar da motar yake, yaja wani irin dogon birki, cikin ikon Allah motar ta tsaya dab da Madinah dake kwance yashe a kasa saura kiris motar ta hau kanta.


A rikice Sabah ya karaso inda Madina take kwance a kasa yana fadin "Subhanallah Madinah? Meya sameki? Are you alright".


Samha da Sameer suma suka karaso a guje, suma hankalinsu a matukar tashe, ganin jinin dake kwarara daga kafar Madinah ne yasa Sabah bai tsaya wata wata ba ya dauketa cak ya karasa yaje ya sakata cikin mota sai asibiti.


Samha da Sameer suma suna binsu a baya. Tare suka isa asibitin nan Sabah ya fito da ita suka shiga ciki ya soma kiran attention nurses din.


Nan da nan aka karbi Madinah aka shiga da ita ciki.


Tunda aka shiga da Madinah, Sabah yaketa faman zarya yana kaiwa da kawowa hankalinsa a matukara tashe. Tunani kala kala ne yake masa yawo aka yana addu'a Allah yasa ba wani serious ciwo taji ba.

Bayan kusan minti talatin suna tsaye a hakan Samha tace bari ta shiga ta dubasu.


Bayan shigan Samha ciki, Sameer yazo ya tsaya dab da Sabah yana fadin "ka kwantar da hankalinka insha Allah babu abunda ya sameta, mu cigaba da mata addu'a kawai".


Wani irin kallo Sabah ya watsa mishi yana hararansa sa'anan ya kauda kansa gefe bai ce komai ba.


Ganin haka ne yasa Sameer yaja bakinsa yayi shiru ya koma gefe ya cigaba da tsayuwa. Suna cikin haka, can sai ga Samha ta fito hanunta rike da Madinah wace take tafiya tana dingishi, ga katuwar plaster an manna mata a kafan.


Cikin sauri Sabah da Sameer suka karaso. Sameer ne ya soma yiwa Madinah sannu yana tambayar Samha abunda likita yace.


Samha tace "sunce ba wani serious ciwo taji ba, kawai kujewa tayi".


"Toh Alhamdulillah, Allah yasa abun yazo da sauki".


Madinah ta juyo tana duban Sabah tace "Sabah are you okay? Hope dai bakaji wani ciwo ba?"


Wani irin kallo Sabah ya watsa mata cike da jin haushinta yace "mallama cut the crap! Yanzu Meye amfanin abunda kikayi?!"


Madina zata bude baki tayi magana yace "yanzu da wani abun ya sameki ina kikeso na saka kaina. Me kikeso na fada musu a gida?! Eh? Please daga yau, sai yau don't ever try this kind of thing again with me, bana so".


Madinah shiru tayi ta sunkuyar da kanta kasa cike da tausayin kanta don tama rasa me zata ce mishi.


Samha ta kurawa Sabah ido taga yanda yake hucci ransa a bace tamkar zai rufesu da duka a wajen. Amma tasan duk masifan nan dayake yi, still yana cike da matsanancin damuwa ne akan abunda ya faru da Madina.


By the time dasuka baro asibitin dare ya rigada yayi. Sameer ne ya dubesu yace " dare yayi why not muje na sauke ku a gida."


Wani irin kallo Sabah ya watsa musu gabadayansu da suke tsaye a wajen sa'anan yaja tsaki ya tafi ya barsu.


Samha data san halin kayanta, ta dubi Sameer tace "kasan me Sameer, ka kai Madina gida kawai ni bari na wuce da Sabah".


Sameer baiji dadin abunda ta fadi ba amma babu yanda ya iya, kai kawai ya gyada mata yana kallon Sabah wanda har ya kusan karasawa inda yayi parking motarsa.


Samha ta juyo tana duban Madina tace "Madina dan Allah ki kula da kanki, idan kafan naki ya soma miki ciwo kisha magungunan da likita ya rubuta miki, kinji? Allah ya kara sauki".


"Ameen" Madina ta ansa tana murmushi sa'anan tace "ai Big sis, yau kam banjin zan iya bacci saboda tsabar farin ciki".


"Farin ciki me kenan?" Samha ta tambayeta cike da rashin fahimta".


Madina tana murmushi tace "yau nida Sabah mun fita, ya kaini wurare da dama mun zage gari. Har wani wuri musamman inda ake siyar da ice cream mai dan karen dadi mukaje. Ban taba shan ice cream mai dadi irin wanan ba. Daga nan mukaje bakin ruwa mukaga manyan jirage na yawo ta ko ina." Madina sai faman zuba takeyi babu iyaka.


Gaban Samha ne ya yanke ya fadi, nan take taji jikinta ya mata wani irin sanyi hade da wani irin zafin kishi taji ya taso mata.


Sameer dake tsaye a gefe yana jinsu, ya katse musu maganar da sukeyi yace "Madina yanzu idan kinje gida me zaki ce musu game da wanan raunin da kikaji a  kafarki?"


Samha cike da sanyin jiki tace "haka ne kam, kinga ya kamata asan me za'a fada musu a gida don karsu daura laifin akan Sabah".


Sameer yace "karku damu, muje kawai nasan bayanin dazan musu".


Sabah wanda yake zaune cikin mota yana faman jiran Samha ta karaso, a fusace ya bude murfin motar ya fito ya soma kwala mata kira.


Cikin sauri Samha ta yiwa su Sameer sallama sa'anan ta karasa inda yake.


Tana karasowa ya kamo hannunta yaje ya zagaya da ita ya bude motar ya turata ciki sa'anan ya rufe motar da karfi, shima yaje ya zagaya ya shiga ciki ya zauna yana hucci.


Harara Samha ta soma aika masa dashi ta soma turo baki tana magana kasa kasa.


A fusace Sabah ya juyo yana dubanta yace "wai ke bana hanaki shiga sabgar da babu ruwanki ba? Surutun uban me kika tsaya kikeyi dasu kika barni anan inata faman jira?".


Samha ta dago tana dubansa da manyan idanunta tace "wai ya kakeso nayi ne Sabah? Kana ganin yarinya taji ciwo a sanadiyar ka kace babu ruwana? Sabah duk abunda ya shafeka nima ya shafeni, i can't help but to worry. Kai kuma naga alama ko ajikinka. Yanzu haka ma, i'm more worried, more confused than ever. Ka dinga tausayawa zuciyata mana". Ta karasa maganar kamar zatayi kuka.


Sabah shiru yayi bai ce komai ba ya tsura mata ido yana kallonta.


Samha bata tsaya nan ba ta cigaba da fadin "dazun bakasan irin tashin hankalin dana shiga ba a sanadiyar abunda Madina tayi ba. Gani nakeyi tamkar zuciyarka zata karkata zuwa gareta ka soma sonta saboda abunda tayi maka".


Sabah cigaba yayi da kallonta yana jin wani irin feelings da emotions yana taso masa yanai masa yawo a kwakwalwa.

Damuwanta kenan? Shi da zuciyarsa fal take da tsoron kar Sameer yazo ya kwace masa ita tunda yaga alama it dashi sunada connection tsakaninsu right from time, tun tana karama akwai history a tsakaninsu?


Wani irin kishi ne yaji ya sake taso masa, bai san sanda ya janyota ta fado bisa fafaden kirjinsa ba ya rungumeta gam a jikinsa tamkar za'a kwace masa ita.


Sunfi 10 mins a hakan daga bisani  ya sasauta rikon dayayi mata ya dago yana kallon cikin kwayar idanunta.

Tsura mata ido yayi yana kallonta na kusan 5 mins yana jin sha'awarta da zazaffen kaunarta na kara mamaye zuciyarsa.


A hankali yakai Soft lips dinsa bisa goshinta ya manna mata soft kiss a wajen daga bisani ya saketa.


Juyawa yayi yasa key ya tayar da motar yaja suka soma tafiya.


Shiru ne ya ziyarce su, babu wanda yace ma wani kala kowa da abunda yake masa yawo a ka.


A hakan suka karasa gida. Suna shiga suka tadda Anty fanneh zaune a parlour.


Anty fanneh tana ganinsu ta mike tana fadin "ya kukayi dare haka?"


Samha ta soma mata bayani tace "Ammi mun da'an samu traffic a hanya ne shiyasa".


Anty Fanneh tace "toh" sa'anan ta dawo da dubanta ga Sabah ta soma fadin "Sabah mami ta kira tace tana son yin magana dakai. So karka manta, ka kirata".


Gaban Samha ne ya fadi can kasan ranta ta soma tunanin kodai Mami har taji abunda ya faru ne an kirata an fada mata Madina taji ciwo?


Suna cikin haka wayar Anty fanneh ta soma ringing tace "gashi nan ma ta sake kira. Ungo nan". Ta fada tana mika masa wayar sa'anan ta karasa kitchen.


Sabah kara wayar yayi a kunne yace "hello Mami, Sabah ne". Shiru yayi ya soma sauraron masifar da takeyi daga bisani yace "toh yanzu me suke so na mata kuma? Kin kirani kinata wani fada, idan basu gamsu ba su kaita asibiti mana a dubata".


Mami ranta a bace ta soma rufeshi da ruwan bala'i da masifa ta inda take shiga ba tanan take fita ba tace taga yau ya tabbatar shi zai dinga zuwa gida yana kaita makaranata haka zalika idan an tashi shi zai dinga daukota daga makaranta yana mayar da ita gida, tunda a sanadiyar shi taji wanan ciwon".


Sabah zaiyi magana yaji ta katse kiran. Ajiyar zuciya ya sake sa'anan ya nema wuri ya zauna akan kujera yana dafe kai.


Samha ce ta zo ta zauna a gefensa ta soma tambayarsa abunda mami tace.


Shiru yayi yana nazari daga bisani ya fada mata abunda mami yace .


Anty fanneh ta karaso ciki itama ta nema wuri ta zauna tace "kaga Sabah, tunda abun nan ya rigada ya faru ka rungumi kaddara kawai, kuma kaga dole iyayenta su shiga cikin damuwa, Mami tanada gaskiyarta kawai kayi abunda tace kana zuwa daukota, I'm sure Samha bazata damu ba".


Anty fanneh ta dawo da dubanta ga Samha tace "kinga you're more independent so ki bari yayanki yana zuwa daukan yarinyar nan har ta samu lafiya".


Samha shiru tayi batace komai ba. Anty fanneh ta cigaba da fadin "yauwa ban ma tambayeki ba. Kin samu ganin Sameer kuwa yau a school?"


Dagowa Samha tayi suka hada ido da Sabah taga ya hada rai, kawar da kansa gefe yayi, yayi kamar bai jisu ba.

Post a Comment for "ZABIN SAMHA CHAPTER 11"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...