ZABIN SAMHA CHAPTER 10 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZABIN SAMHA CHAPTER 10

ZABIN SAMHA CHAPTER 10

- - Post a Comment

 ZABIN SAMHA CHAPTER 10


Samha ya mahaifiyarki da fatan dai tana nan lafiya?" Sameer ya tambayeta.


"Ammi tana nan lafiya".


"Insha Allah zan samu lokaci nazo har gida mu gaisa. Amma samha na samu labari cewa Amminki ta kara aure."


"Eh kwanan nan tayi auren, Ta auri VC na makarantan nan. Bakaga yanda yake kulawa da Ammi ba yaya sameer, Abba yanada kirki sosai."


Sameer ya danyi jimm sa'anan yace "kefa is he good to you? Yana kulawa dake?"


Samha tayi sauri ta gyada masa kanta tace "ai Abba ya dauke ni tamkar yar' cikinsa. Yana nuna mana so da kulawa sosai".


Sameer ya jinjina kai yace "Toh masha Allah, haka akeso ai. After all these years, gaskiya ina taya Amminki murna, Allah ya basu zaman lafiya. Kema gashi kin girma kina jammi'a abunki, abu yayi kyau sosai". ya karasa maganar yana murmushi.


Itama Samha murmushi ta sakar masa sa'anan tace "Nagode sosai da kulawar daka dinga bamu shekaru baya da suka wuce. Ai kayi mana kokari sosai yaya Sameer, Allah ya saka".

Sameer still yana murmushi yace "ameen"


Nan suka soma tuna baya wanda ya dangana da tun lokacin Samha tana karama mahaifinta nada rai sameer yana zuwa karban karatu. Yanda kuma Sameer duk sanda zai zo sai ya kawo mata abubuwan makulashe tayi ta murna tana tsale, duk waenan abubuwan sai da suka tuno. Sai faman hira suke cike da anashuwa suna dariya.


Ashe suk wanan hiran da sukeyi oga Sabah yana tsaye ta daga can gefe yana kallonsu.

Samha dinsa ne yake gani tana zance da wani hankali kwance sai faman kyalkyale dariya takeyi babu abunda ya dameta? Wani irin tafarfasa zuciyarsa ke masa nan take yaji kamar yaje ya shake sameer ko zai samu sasauci cikin zuciyarsa.


Shi kansa yasan yanada mugun tsananin kishi akanta duk da dai baya nuna mata hakan. Kwata kwata baya son abunda zai hadata da wani da' namiji da zai kai ga har su tsaya suna zance.


Yana bala'in sonta kuma Baya son taso kowa sai shi kadai, haka zalika baya son yaga ta damu da kowa sai shi...


Don haka jikinsa ne ya dau rawa, kokarin controlling din kansa ya somayi kar yaje ya aikata wani abun da bai kamata ba, don haka ya tsaya yayi shiru yana kallonsu. Har suka gama zancen sukayi sallama, idanunsa na kanta. Gani yayi ta juya ta soma tafiya ita kadai tayi hanyar barin cikin makaranta, shima ya bi bayanta.

Sai da sukayi tafiya na kusan 20 minutes bata ma san yana binta ba.


Gani yayi ta shiga layinsu na'da, bata tsaya ko ina ba sai daidai bakin gate din tsohon gidansu, yaga ta tsaya ta kurawa gidan ido.

Ita kam Samha tunda sukayi hira da Sameer taji gabadaya kewan gidan nasu ya kamata, wani irin nostalgic feeling ta dinga ji, bata ankara ba ta tsinta kanta a kofar gidansu.


Kamar daga sama taji murya a gefenta ana fadin "waye shi?".


Gabanta ne ya tsinke ya fadi ta juyo cikin sauri taga Sabah tsaye yana kallonta fuskansa a daure tamau.


"Lah Sabah wlh ka tsorata ni". Ta fada tana dafe kirji.


A hankali ya karaso har yazo ya tsaya dab da ita, cikin kausashen murya yace "baki ansa tambayata ba. nace waye shi?"


"Ban gane ba? Wa kake nufi?"


"Wanda na ganki dazu a gaban department kuna hira dashi". Ya fada mata kai tsaye.


Gabanta ne ya sake faduwa tace "daman ka gan mu?"


"Who is he Samha?" Ya kara tambayarta.


"Wani family friend dinmu ne, mun jima bamu hadu ba sai yau na ganshi a school".


"Hmmmm" kawai Sabah yace ya kawar da kansa gefe.


Samha kallonsa tayi tace  "Sabah badai kishi kakeyi don ka ganni ina magana da wani ba?"


Tsaki yaja sa'anan yace "kishin me zanyi?"


Harara Samha ta watsa mishi, can kasan ranta tace "hmm kadai ji dashi. Mutum sai shegen fadin ran tsiya".


Shiru sukayi, shi kuwa ya kura mata ido yana kallonta, wani abu ne ya taso masa yana son fadi amma tsabar miskillanci da girman kai bazai barshi ya nuna mata cewa yana kishi ba, duk da dai abun yana cinsa a rai.


Canza topic din yayi yace "Kinyi batan hanya ne? tun daga school nake binki, Ko har yanzu baki saba da dawowa gidan namu bane?"


Shiru tayi bata bashi ansa ba, ta tsaya tana kallonsa da manyan idanunta.


Ajiyar zuciya ya sake sa'anan ya kamo hanunta yace "taho mu tafi".


haka suka soma tafiya, gani tayi still kamar ransa a bace yake sai taji kamar she owe him an explanation don haka ta soma fadin "kayi hakuri Sabah, wanda ka ganni tare dashi dazun he's someone i used to like".  Sai kuma tayi shiru don Ita kanta data fada maganar sai dataji wani iri, nan take ta soma dana sani fada mishi haka.


Sabah tsayawa yayi cak ya juyo yana dubanta yace . "Like seriously?"

Saurin Girgiza masa kanta tayi tace "A da fa nace Sabah, amma yanzu kaima kasan you're the only one i like. Kai kadai nake so kaji. Pls" ta karasa maganar tana riko hanun rigarsa.


Kallon inda ta rike shi yayi yace "meye haka ki cika ni mana".

"Naki sai ka yarda cewa kai kadai nake so".

Duk tabi ta marairaice masa kamar zatayi kuka. Abun ma dariya yaso ya bashi yace "toh shikenan, I believe you. Oya let go off me".


Murmushi ta sake sa'anan ta juyo tana turo dan karamin bakinta ta soma tafiya tace "daman da gangan kakeyi, so kawai kake na baka hakuri. Kuma kai ya kamata ka bani hakuri, kasan ban manta da abunda ya faru da safen nan ba."


Dariya yayi yadan zungure kanta yace "kin cika rigima. Let's go". Haka yajata suka soma tafiya suna hira  yana zolayanta har suka karasa gida. Kowanen su zuciyansa fess.


********************


Bangaren su hajiya bilkisu kuwa, zaune take a makeken parlourn gidanta dake lekki tana karanta newspaper da fararen glasses manna bisa idanunta.


Jikarta Shafa ce ta shigo cikin parlour cike da shagwaba tazo ta zauna kusa da ita tana fadin "mami gaskiya ni yau plantain frittata nake so naci"


Hajiya ta dubeta tace "oh ni ya'su amma wanan  yarinyar da kwadayi kike. Yanzu kuma meye plantain fritate ko meye ma kika kirashi?"


"Mami wallahi tun dana zo nake sha'awan cinsa".


Mami tace "wai ni yaushe hutun nan naku zai kare ne, mahaifunku yazo ya dauke ki. Na gaji da irin wanan damuwan, Nifa nafi jin dadin zuwansu ai'nau akanki. Ke kenan kullum kice kina son wanan kina son wancan, baki gajiya. Nifa bazan iya da wahalan ki ba".


Shafa ta dan kwanto a jikinta, cike da shagwaba tace "Haba mami, kema kinsan fada kawai kikeyi. Kowa yasan i'm your favourite jika."


Mami ta tabe baki bata sake cewa komai ba.

shafa ta kasance first born din Alhaji mubashir wato kanin mahaifin Sabah. Shima yana aure da iyalensa suna nan a lagos da zama. Yaransa uku kuma dukansu mata. Daga shafa wace itace babba shekaranta sha bakawai tana aji daya tana karatu a baze university sai kuma ai'nau wace take ss2 da kuma last born na'ima wace tana jss1. Daman kusan ko wani hutu suna zuwa wajen Mami suyi holiday kafun su koma.


Wanan karan shafa ce ta samu hutu, tana dawowa lagos bata tsaya ko ina ba sai lekki wajen kakar nasu. Don tasan nan ne kadai zata samu ta zuba shagwabanta son ranta.


Mahaifiyarta Hajiya Amina no nonsense woman ce, bata yarda mata da wanan iskancin shagwaban da takeyi don haka tafi gane zuwa can.


Mami ta dubeta tace "toh shikenan, sai kiyiwa driver magana yakaiki ki siyo".


Shafa ta daka tsale tana murna kamar wata karamar yarinya tace "nagode sosai mami, shiyasa nakesonki mamina. duk abunda nakeso baki cemun a'a"


Mami ta tabe baki tace "kinyi na karshe kenan".


Dariya shafa tayi sa'anan tace "Wai mami yaushe zamuje gidansu yayah Sabah ne? Tun dana zo fa ban samu na ganshi ba".


Mami tace "ah laillai yarinyar nan kinada aiki ja' a gabanki. So nawa zan gaya miki ki cire batun Sabah a ranki. Sabah ba tsaranki bane duka duka guda nawa kike da zaki wani sashi a ranki?"


Shafa ta marairaice fuska tace "Mami dan Allah karki mun haka mana. Tunda nazo fa ban ganshi ba, kuma kina fadin Yaya Sabah ba tsara na bane, jinin mu fa daya miyesa zaki ce yafi karfina?"


"Nidai na fada miki, tun wuri ki kama kanki. Banson wanan rawan kan dakikeyi. Kuma Sabah already inada plans akansa don haka ki cire koma meye kika sa a ranki".


Gaban shafa ne ya tsinke ya fadi tace "mami plans fa kikace. Wani irin plans kuma?".


"Ina ruwanki? Kinga bana son yawan surutu ki tashi ki bani wuri".


Shafa mikewa tayi tana kunkuni ta haura sama zuwa daki, tana shiga dakin ta kife akan gado ta zabga wani uban tagumi.


Toh me mami take nufi da hakan, karfa mami tazo ta kwapsa mata plans dinta don ita daman da biyu take zuwa gidan duk don ta samu taga Sabah ne.

Tun tana karama ta taso take dawainiya da sonsa. Ta taso batada wata batu sai nashi. Shi kuwa bai ma san tana yi ba.

So dayawa idan sunje gidansu visiting sai yayi ta faman cin magani ko magana tayi masa baya tanka mata. Akwai ranar daya daka mata tsawa yace ta cika rawan kai, tun daga wanan lokacin take kama kanta idan yana nan. Tana iya kokarinta taga ta birgeshi. Tana mutuwar sonsa kuma jin dadinta da'ya daya kasance dan' uwanta tasan bazata samu matsala ba amma sai gashi kuma Mami tana son ta kwapsa mata.


Wayarta ta rarumo ta bude taje gallery dinta. Hotonsa data samu nasaran screenshotting daga profile picture dinsa na whatsapp ta kurawa ido.


Wani irin sonsa ne taji yana kara fuzgen zuciyarta.


Tasan kota mishi magana ta whatsapp din ba replying dinta zaiyi ba don haka bata ma bata lokacinta tayi texting dinsa.


Haka tasa hoton nan nasa a gaba tayita kallo har ta gaji.


Bayan barin shafa parlourn mami taja tsaki ta girgiza kai. Ita kam ta gaji da shirmen wanan yarinyar. Duk tabi ta kwalaba ranta akan Sabah? A zatonta abun nata ya lapa amma gani takeyi abun nata karuwa yakeyi. Dole ta dau kwakwaran mataki akan wanan lamarin ta zartar da plans dinta kafun lokaci ya kure.


Da wanan tunanin ta mike itama ta haura sama zuwa dakinta.Washe gari tun a school Samha take ta murna tana Allah Allah ta dawo gida don sunyi waya da Anty katibe tace jirgin su ya sauka suna gida.


Ba abunda yake sata murna illa ganin Azirak, don tayi missing yaron sosai.


Ko data dawo gida da murna suka rungume juna, taje ta dauki Azirak kamar zata mayar dashi cikinta don tsabar murna.


Shima dariya ya dinga yi dayaga anata faman tsale tsale dashi.


Bayan sun gaisa da Anty katibe, straight dakinta ta wuce dashi.


Shi kam sai faman mata shirme yakeyi irin nasu na yara, itama biye mishi ta dinga yi sunata wasa.


Sai zuwa la'asar tukuna ta sauko dashi don ya samu yaci abinci.


Bayan Anty katibe ta bashi abinci, Samha ta sake dauko shi suka fito cikin gida.

Nan garden sukaje ta zaunar dashi kan carpet grass sunata wasa.


Bayan kusan 30 minutes motar Sabah tayi

horn, d'aya daga cikin security din yazo ya bude mishi gate ya shigo yayi parking ya fito daga cikin motar, tafiya ya soma yi cikin harabar gidan. Dayake baban gida ne. Daga gate zuwa tsakar gidan ma sai kayi d'an tafiya.


Sai dayazo dai dai wurin garden din ya hango Samha tare da Azirak sunata faman wasa hankalinsu kwance, sai faman guje guje sukeyi tana kokarin kamo shi.


nan take yaji zuciyarsa ta narke abun ya burgeshi sosai, zuciyarsa ta soma hasko masa wani yanayi na daban.

Har ya soma ji tamkar Samha ce da babynsu suke guje guje haka.

Duk tsayuwan nan dayayi yana kallonsu Samha bata san ya dawo ba, gabadaya hankalinta na kan Azirak.


Sabah ya zira hannunsa cikin aljihu ya ciro wayarsa, cameransa ya kuna, yayi saitin daidai inda ta dauki Azirak tana mishi cakulkuli yana dariya ya dauke su hoto.


Dubawa yayi yaga ba karamin kyau sukayi ba. Nan da nan yayi saving ya mayar da wayar cikin aljihunsa ya soma karasowa inda suke.


kamshin turaren signature perfume dinsa taji nan take tasan shine yake tafe.


Cikin sauri ta waiga taganshi tsaye a bayansu, kyakyawar fuskarsa dauke da murmushi.


Itama tsayawa tayi tana kallonsa daga bisani tace "Sabah har ka dawo".


Sabah yace "na dawo kanwata".


Azirak ne ya rarafo yazo ya tsaya dab da inda Sabah yake tsaye ya soma kamo kafar wandonsa.


Sabah ya sunkuya ya dauki yaron yana kare masa kallo yace "kanwata ya naga yaron nan yana kama dake sosai haka?"


Samha ta zaro ido tace "da gaske? Haka mutane suketa fada".


Sabah yayi dariya ya matso dab da ita sa'anan yace "kinga nima haka wata rana zaki haifo mun babies masu kyau irin haka".


Kunya ne ya d'an kama Samha ta sunkuyar da kanta kasa.


Sabah yace "Allah da gaske nake ba wasa ba"

Idanunsa ne suka sauka kan dan karamin waist dinta yakai hannu kamar zai shafa tayi sauri ta kauce tana watsa masa harara.


Dariya ya sake sa'anan yace "kai kanwata kin cika tsoro, me kike tunanin zan miki? Abu fa kawai zan nuna miki".


Azirak ne yasa hannu ya soma wasa da kwalar rigarsa, Sabah ya juyo yana dubansa sa'anan yace mata "ungo nan ga d'an naki ni zan wuce ciki".


Ya karasa maganar yana kokarin mika mata Azirak amma yaron yaqi kememe wai shi zaiyi wasa da Sabah.


Da kyar dai Samha ta samu ta karbe shi ya soma bata fuska kamar zaiyi kuka.


Saida Sabah ya bashi baki yace mishi yana zuwa zai je ya kawo mishi sweet tukuna aka samu ya hakura.


Sabah yana shiga ciki ya tadda Anty fanneh da sistern ta katibe suna zaune a parlour, nan ya gaida su suka ansa mishi gaisuwar.

Anty fanneh tace mishi ga abinci akan dining.


Sabah yace zai haura sama tukuna idan ya sauko zai ci.


Haka ya haura sama zuwa dakinsa, yaje ya watsa ruwa.


Yana fitowa ya tadda miss call guda shida, daya daga Zack ne, biyar kuma yasan me kiran nasa. Dagawa ne kawai bazaiyi ba, don be san me zai ce mata ba.


Goge jikinsa ya soma yi da towel, ya dauko kananan kaya ya sanya. Blue tshirt da black jeans.

Curly hair dinsa daya jike ne ya dauko towel ya soma gogewa, yaje gaban madubi yaga sumar kan nasa ya soma cika don duk tabi ta kwanta bisa kansa da alamun yana bukatan aski.


Daman shi ba ko ina yakeyin aski ba saboda yanayin nature din gashinsa.


Tanada tsantsi da laushi dayawa, irin gashin mahaifiyarsa ya dauko don haka musamman yakeda barber dinsa wanda ya kware a askin irin kalar sumar.


Yana saukowa yaje dining ya debo abinci ya zauna yaci sosai, sa'anan ya mike ya dauki makulin motarsa yacewa Anty fanneh yana zuwa zai d'an fita.


Samha ma already tana kitchen tare da yar aikin gidansu sophie suna kokarin su hada abincin dare.


Sabah yana fita kai tsaye wurin barber dinsa yaje ya rage masa sumar kansa.


Bayan ya gama askin ya fito ya shiga motar sa yaja ya tafi, har yazo daidai kings road ya hango super spar shopping mall yace bari ya shiga ya siyowa Samha da Azirak chocolates da biscuits.


Sai daya jido musu kusan leda uku har dasu ice cream yama rasa mai zai kara musu tukuna ya hakura ya fito rike da ledojin ya zubesu a seat din baya yaja motarsa ya soma tafiya.


Har ya kai daidai inda zai shiga kwanar marine road, from nowhere yaga wata yarinyar yar budurwa rataye da jaka ta bulo ta shigo hanya.


Wani irin mahaukacin birki sabah ya taka yaja ya tsaya. Ita kanta yarinyar sai data firgita tayi tangal tangal ta fadi kasa.


Cikin sauri Sabah yayi parkin ya fito daga cikin motar yazo ya sameta ya tsuguna yana kokarin ya taimaka mata. Fatan shi daya Allah yasa bata ji ciwo ba.


A firgice yarinyar ta damko hannu rigarsa da karfi sai data balle mishi botun riga guda daya tana zaro ido babu abunda take ambatowa sai kalmar innalillahi wa ina illhai raji'un.


Shi kuma sai faman sannu yake mata.

"Ina glasses ina yake?" Ta tambayeshi

Waige waige Sabah ya soma yi ya hango glasses dinta a yashe a kasa, daukowa yayi ya mika mata.


Yace "hope dai baki ji ciwo ba?"


Yarinyar ta girgiza masa kanta tace "i'm okay". Godiya tayi mishi sa'anan ta mike tsaye.


Shima mikewa yayi, har ya juya zai koma cikin motarsa sai kuma yaga taja gefe tana ta fama da eye glass dinta wanda glass daya ya fashe ya fita. Da alamun bata gani sosai in bada taimakon glasses dinba.


Tausayinta ne yaji yaga bazai iya tafiya ya barta haka ba, don haka ya dawo inda take yace " baiwar Allah, glasses din ya balle ne?"


Cike da damuwa ta dago tana dubansa amma gabadaya bata ganinsa don dishi dishi take gani tace "eh wlh".


Sabah yace " tunda baki gani, zo muje muga ko za samu inda za'a gyara miki."


Yarinyar dai bawai ta yarda dashi bane amma babu yanda ta iya haka ya taimaka bata ta shiga cikin motar yaja suka tafi.


Daidai wajen wani eye clinic ya kaita ya samu likitan dayake wajen yayi mishi bayanin akan abunda ya faru.


Likitan yace yaga glasses din, Sabah ya mika mishi ya duba yace gaskiya saidai a sake mata wasu glasses din.


Sabah yace "babu komai, amma wanan karon ayi mata mai kwari wanda bazai iya karyewa da wuri ba".


Likitan yace "babu damuwa. Amma glasses dinmu are a bit expensive don each one goes for 35k"


Sabah yace babu damuwa, haka yaje wurin receptionist din ya biya kudin glasses din.


Har zai tafi yarinyar ta mike daga seat din da take zaune likita na mata gwaji, tace "bawan Allah dan tsaya pls".


Sabah ya juyo yana dubanta, ita kuwa sai kokarin matse ido takeyi tana kokarin taga koda fuskarsa ne, amma hakan ya citura, dishi dishi kawai take ganinsa.


"Daman godiya nakeso na maka, a gaskiya bansan me zance maka ba illa nace Allah ya saka da alkhair, kuma i have something for you".


Hanunta ta zura cikin jakarta ta ciro wata yar karamar box da akayi wrapping dinsa da gold foil paper ta mika masa fuskarta dauke da murmushi tace "ungo wanan".


"Menene wanan?" Sabah ya tambayeta.


"It's tasty, gift to you".


Murmushi kawai Sabah yayi ya karba box din daga hanunta ya juya ya tafi.


Har ta juya zata koma ta zauna, sai taji kamar ta taka abu, tsugunawa tayi ta dauko abun ta tataba da hanunta, taji alamun cewa button din rigarsa ne daya fita dazun.


Mikewa tayi zata kirashi sai taga already ya bar harabar wurin ma gabadaya.


Murmushi ta dan sake sa'anan ta dunkule button din a hanunta ta saka cikin jakarta ta koma ta zauna, zuciyarta cike da tunanin bawan Allahn daya taimaka mata wanda ko fuskarsa bata gani ba ballantana tasan sunansa.Sabah yana barin wajen, straight gida ya wuce, har ya manta ma da abunda ya faru.


Yana shiga cikin parlour ya tadda Samha tana kokarin shirya dining itada sophie.


Ya mika mata ledodin daya ruko yace "ina d'an naki yake?".


Tace mishi "yana can daki tare da mamansa".

Yace "toh gashi nan sai ki kai masa".


Samha ta karba ledan tayi masa godiya, shi kuma ya haura sama zuwa dakinsa.


A kwana a tashi sai dasu Anty katibe sukayi kusan sati biyu tukuna tace zasu koma dubai.

Samha kam harda kuka don za rabata da Azirak. Amma anty katibe tace zasu zake zuwa idan an samu wani hutun insha Allah.

Haka kwanaki suka shude, yanzu suna neman kusan wata daya kenan da aure, zama suke hankali kwance babu wani tashin hankali sai ma peace of mind da anashuwa da ake dadda samu a cikin gidan.


Samha da Sabah still suna soyayyarsu amma koda wasa basu taba barin iyayyensu sun gane hakan ba.


Ita kam bangaren su Mami daman yau ta shirya zata je gidan d'an nata don tunda akayi biki bata samu taje gidan ba. Ta kirasu a waya ta sanar dasu batun zuwan ta. Sukace sai tazo Allah ya kawota lafiya.


Tacewa Shafa ta shirya zata rakata zuwa gidan. Haba murna kuwa a wajen shafa kamar meye.


Yau finally, at long last zata je taga ruhin rayuwarta.


Murna da tsale ta dinga yi sai faman rawar jiki takeyi. Mami ta dubeta tace "idan baki daina wanan rawan jikin da kikeyi ba, babu inda zani dake.".


Cike da shagwaba shafa tazo ta zauna kusa da ita tana fadin "kai Mami, yanzu me nayi kuma? Dan na nuna farin cikina akan zamu je gidansu yaya Sabah shine wani aibu?"


"Nidai na gaya miki, kuma ki cigaba ki gani".


Turo baki shafa ta soma yi, ta mike ta haura sama zuwa dakinta taje ta soma shiri.


Misalin karfe uku na rana suka dau hanya, drivern gidan nasu ne ya jasu a mota suka tafi.


Dayake daga lekki zuwa Apapa akwai d'an nisa gashi kuma ranar an zuba go-slow ba kadan ba. Ba Su da isa Apapa sai karfe shida na yamma.


Anty fanneh ce tazo ta tarbe su tanai musu sannu da zuwa cike da fara'a tace "sannunku da zuwa Mami, kunsha hanya".


Mami tace "wlh unguwan naku ne akwai nisa, ga go-slow da muka tadda a hanya. Abun dai ba cewa komai". Anty faneh ta karba jakan mami daga hannunta suka karaso cikin parlourn tare, suka nema wuri suka zauna.

Shafa ce ta soma gaisheta tace "Anty ina wuni".


Anty faneh tace "ina gajiya. Ya gida?"


"Lafiya kalau". Shafa ta bata ansa. 

Anty fanneh ta dawo da dubanta ga Mami tace "sannu Mami kunsha hanya, bari a kawo muku abu mai sanyi kusha " tana gama fadin haka ta mike ta shiga kitchen taje ta lebo musu lemuka masu sanyi, ta kawo ta jera musu a gabansu, Sai faman yi musu sannu da zuwa takeyi.


Mami taji dadi sosai da yanda Anty fanneh ta tarbe su.


Shafa kuwa sai faman karewa ko'ina na gidan kallo takeyi don bata taba zuwa wanan sabon gidan ba. Sai taga wanan gidan ma ya ninka nada a kyau.


Sai faman baza idanu takeyi ko zata ga sanyin idaniyanta amma bata ganshi ba. Gashi babu daman tambaya.


Bayan sun gaisa Mami ta dubi Anty fanneh fuskarta dauke da murmushi tace "da fatan dai mun sameku lafiya? ya zaman gidan ina fatan babu wata damuwa ko matsala?"


Anty Fanneh ta sunkuyar da kanta kasa tace "babu komai mami wlh. Komai lafiya alhamdulillah".


"Masha Allah, haka akeso ai. Ina Muazzam yake?".


"Har yanzu bai dawo daga aiki ba. Amma munyi waya dashi yace yana hanya".


Mami tace "toh shikenan, Samha fa? ina take ina son ganinta."


Anty fanneh tace Samha tana dakinta, Sabah shima bai jima da shigowa ba, dazun ya haura sama. Bari naje na sanar dasu suzo ku gaisa".

Tana gama fadin haka, ta mike ta haura sama zuwa dakin Samha, sallama tayi ta shiga ciki, Nan ta tadda ta har ta fito daga wanka, tana daure da towel ta zauna a gaban madubi.


"Samha me kikeyi?"


Samha ta ansa sallamar tace "yanzu na fito daga wanka Ammi".


"Toh ki sa kaya ki fito yanzu. Ga mami nan tazo".


"Haba har tazo?" Samha ta tambayeta tana zaro idanu.


"Eh tazo, yanzu take tambayarki kuma naga kamar tana son ganin ku dake da Sabah, don haka karki wani bata lokaci, ki shirya ki sauko yanzun nan. Bari naje na kira Sabah shima".


Samha tace "toh Ammi, bari na shirya yanzun zan sauko".


Ammi mikewa tayi ta fice daga dakin taje ta kira Sabah shima daga bisani ta sauko kasa tazo ta tadda mami tace "mami na kirasu, yanzu nan zasu sauko".


Mami tace "toh"


Ita kam shafa dake zaune a gefen mami, Wani irin damm zuciyarta yayi dataji cewa Sabah da wata Samha zasu sauko. Toh Wacece kuma Samha wace bata sani ba? Ko dai yarinyar matan kawun nata ne? Daman ta samu labarin cewa tanada ya' budurwa.


Sake sake ta soma yi cikin zuciyarta tana warwarewa amma bata samu ansa ba.


Mami ce ta dubeta tace "keh tashi ki koma dayan parlourn ki zauna. Zamuyi magana".


Babu musu shafa ta mike ta shige dayan parlourn, sai ya rage daga mami sai Anty fanneh.


Mami ta dubi Anty Fanneh tace " Alhamdulillah tunda nazo na sameku cikin koshin lafiya. Daman burina bai wuce ace na ganku kuna zaune hankali kwance ba. Kuma naji dadi da yanda naga kike kula da lamarin gidan nan. Dan Allah ki cigaba da kulawa, Allah ya miki albarka kuma yasa ku dore a hakan, Allah yasa albarka cikin wanan auren naku".


Anty fanneh murmushin jin dadi ta sake tace "Ameen mami. Insha Allah zamu dore a hakan, baza'a samu wata matsala ba".


"Yauwa haka akeso".


Mami ta d'an nesa sa'anan ta cigaba da fadin "yanzu kuma abu d'aya ya rage wato Sabah. Shima ina ganin lokaci yayi daya kamata ace yasan me yake ciki, ko ba haka ba?"


"Haka ne Mami".

Bangaren Samha kuwa Ammi na barin dakin ta zauna tayi shiru tana nazari. Toh ganinta na meye mami takeson tayi" ita gabadaya ma a tsorace take, kirjinta ne ya soma bugawa tama rasa meke mata dadi.

Kayanta ta dauko ta sanya, ta ziri doguwar hijab dinta ash colour ta fito ta sauko kasa.


Sabah shima yana kwance, bayan Anty fanneh ta kirashi, ya daura hanunsa a ka, yana jan tsaki cike da takaicin zuwan kakan nasa.


"Yanzu Mami tazo da fitinanta kenan zata sa mutane a gaba".

Tsaki ya kara ja, ya mike ya dauko jalabiyan sa fari ya sanya sa'anan ya fito daga dakin.


Yana saukowa kasa ya tadda su a zaune, ya wani sha mur ya bata fuska, da kyar ya bude baki ya gaida Mami sai wani cin magani yakeyi.

Mami itama kawai ta ansa gaisuwar ne, don inda sabo, ta rigada ta saba da halayen jikan nata, sai a hankali. Kuma ba kowa take blaming ba illa mahaifin nasa don gani take duk shi ya sakar masa ya b'ata shi, yake abunda yaga dama, amma tana ganin lokaci yayi daya kamata ta gyara musu zama.


Kallonsa tayi sa'anan ta dawo da dubanta ga Samha suka hada ido. Nan take Samha taji gabanta ya kara faduwa.


Shafa dake zaune a dayan parlourn tana jin muryansa tayi zumbur ta mike tsaye tazo ta tsaya daidai bakin kofa ta kara kunnenta don taji abunda suke fadi.


Gabadaya ta kosa ta fito ta ganshi ko zata samu nutsuwa cikin zuciyarta.


Sabah k'in zama yayi ya wani tsaya yana dubansu fuskarsa a daure, Anty fanneh ta dubeshi tace yaka tsaya haka Sabah ka nema wuri  ka zauna mana.


Mami tayi saurin katseta tace "a'a ai ba sai ya zauna ba".

Jakarta ta janyo tasa hannu ciki ta ciro wasu kudi ta mika mishi tana fadin "ungo nan, kaje wancan store din dake kan layinku ka siyo mun chocolates."


Kallonta Sabah ya somayi kamar bai gane abunda take nufi ba yace "me kuma zakiyi da chocolates mami".


"Banzo muku da tsaraban komai ba, don haka kaje ka siyo".


Zai sake fadin wata magana mami tayi saurin katse shi tana fadin "kaga nifa bana son dogon surutu kaje kayi abunda na saka. Ina son nayi magana da Samha ita kadai."


Samha najin haka tayi sauri ta zaro ido, Sabah ya sake bata rai yace "so kike na tafi na baku wuri? Toh wani maganan ne za'ayi da ba'aso naji".


"Au tsayawa ma kayi kana tambayata kenan?" Mami ta tambayeshi tana watsa mai harara.


Anty fanneh wace itama gabadaya jikinta yayi sanyi, ta mike tacewa mami tana zuwa zata shiga kitchen. Har tazo daidai inda Sabah yake tsaye, muryarta kasa kasa ta soma yi mishi magana tace "Sabah banson irin wanan musu da gardama haka, kaje kayi abunda kakarka ta saka".


Tana gama fadin haka ta wuce cikin kitchen.


Wani irin kallo Sabah ya watsa musu sa'anan ya juya ya fice daga cikin parlourn Cike da jin haushi, zuciyarsa na tafarfasa. Ya rasa gane meyasa kakar nasa take haka.


Samha tabi bayanshi da kallo kamar zatayi kuka, a ranta tana fadin "na shiga uku, wace magana kuma mami take so tayi dani ni kadai? Kodai ta gano akwai wani abu tsakanina dashi ne? Innalillahi wa ina illaihi raji'un". Bugun kirjin Samha ne ya karu gabadaya ta rikice ta rasa samun nutsuwa.


Mami ce ta kira sunanta tace "Samha..."


Cike da firgici Samha tace "na'am mami".


Mami ta cigaba da fadin " daman maganar da nakeso nayi dake bai wuce akan kusancin ki da Sabah ba, Naga kamar kedashi akwai kyakyawar fahimta tsakaninku".


Kusan mutuwar zaune Samha tayi a wajen jin abunda mami ta fadi "shikenan tamu ta kare yau, mami ta gano mu". ta fada can kasan ranta hankalinta a matukar tashe.


Mami ce ta yanke mata tunanin da take tace " duk da dai nasan keda Sabah ba ciki daya kuka fito ba, kuma babu wata halaka ta jini daya hadaku amma still yanda kuka hada kanku kuna zaune lafiya, ba ko ina bane za iya samun irin haka. Kuma nasan yanda kukeda kusanci haka, bazaku boyewa junanku komai ba, Don haka ina so na tambayeki samha, Sabah yanada budurwa?"


Cikin sauri Samha ta dago tana duban mami don kwata kwata bata fahimceta ba. mami ta cigaba da fadin" ke kanwarsa ce kuma i can see you're close don haka nasan bazaki rasa sani ko yanada budurwa ko baida ita ba".


Jikin Samha ne yayi sanyi ta sauke nanauyar ajiyar zuciya can kasan ranta, don a tunaninta maganar da zasuyi da mami bai wuce akan relationship dinta da Sabah ba.


Dagowa tayi tana duban mami cikin i'ina tace "bb..ban tabbatar ba..mami".


Mami tace "toh shikenan, amma indai ya kasance yanada ita, koma Wacece budurwan nasa sai dai tayi hakuri"


"Ban gane ba mami, wa kike nufi?"


Murmushi mami ta dan sake sa'anan ta zura hanunta cikin jaka ta ciro wani frame dauke da hoton wata yarinya ta mikawa Samha tace " gata nan, itace wace na zabawa Sabah zai aura".


Wani irin dammmm zuciyar samha tayi, nan take taji bugun zuciyarta ta karu, sai faman bugawa take da karfi kamar zata tsage ta fito. Ba karamin tashin hankali Samha ta tsinci kanta ba a wanan lokacin, ji tayi duniyarta ta tsaya mata cak. Anya kunnenta sun jiyo mata da kyau kuwa, ko dai mafarki takeyi?


Daidai wanan lokacin shima Sabah ya shigo cikin parlourn hannunsa rike da ledan chocolates din. idanunsa ne suka sauka kan hoton yarinyar da mami take kokarin nunawa Samha.


Cike da tsananin tashin hankali yake duban mami, muryarsa a d'age yace " Nooo! bazai taba y'uwa ba mami! It's not possible!"


Itama Shafa dake tsaye a bakin parlourn tana jin komai da suke fadi bata san sanda kafafunta suka soma rawa ba, jikinta na bari ta karaso cikin parlourn ta soma fadin "na shiga uku, mami dan Allah karkiyi mana haka".


Sabah da Samha ne suka juyo suna dubanta cike da mamaki dan basuma san tana gidan ba.


Cikin sauri tazo ta tsuguna a gaban mami ta soma magiya akan tana son Sabah, ita ce takesonshi ba wata ba, don haka karta musu haka.Keh, dallah rufewa mutane baki. Wa yayi inviting dinki nan? Ba cewa nayi ki zauna a parlour ba!" Mami ta fada mata a tsawace tana aika mata da harara.


Hawaye ne suka shiga gangaro wa shafa bisa kunci, duk tabi ta rikice tana fadin "Mami wlh bazan iya hakura da yaya Sabah ba. in har ina matukar raye shine *zabina* ki taimaka wa rayuta mami".


Ta fada tana dawo da dubanta ga Sabah dake tsaye yanata faman hucci yana aika mata da harara tace "yayah Sabah dan Allah karka amince da abunda mami take shirin yi. Karka yarda a daura maka aure da wata bani ba. kai nakeso yayana, wlh idan na rasaka zan iya rasa raina nima".


A fusace Sabah ya dakata mata tsawa yace "dallah mallama kiyi wa mutane shiru! Kinsha giya ne? ke dawa zakuyi wanan? Waye sa'anki anan da zaki zo kinawa mutane magiya Kina kirarin zaki kashe kanki, toh ki kashe kanki mana! In kin mutu waye da asara?"


Gabadaya hankalinsa a tashe yake, wani irin haushin Mami da Shafa yakeji a wanan lokacin kamar ya rufesu da duka yakeji. Musaman Mami da take nema ta hargitsa masa rayuwarsa da wani batu na aure da bai ma san dashi ba".


Anty fanneh ce tazo inda Shafa take tsugune tana kuka taja ta tana fadin "yi shiru shafa, ya isa haka taso muje".


Kokarin fusgewa shafa takeyi Mami ta daka mata wani irin tsawa tace ta tashi ta basu wuri da shirmenta, kuji mun shashashar yarinya. Manya na magana kinzo kinai wa mutane kukan munafunci. Sabah dai na rigada nayi masa mata, kuma babu gudu babu ja da baya, don haka ki tashi ki bamu wuri".


Anty fanneh ce ta samu taja ta da kyar ta haura da ita sama zuwa dakin Samha taje ta zaunar da ita tana faman rarashinta. Da kyar dai ta samu ta shawo kanta tukuna ta sauko kasa zuwa parlourn.


Samha kuwa kusan mutuwan zaune tayi a wajen ganin abunda yake faruwa kamar a mafarki, sai faman zaro ido takeyi tana kallonsu daya bayan daya kirjinta na harbawa.


Mami ta da'go hoton yarinyar ta mikawa Anty fanneh tace "gata nan, sunanta Madina, batada matsala kuma tana da kirki sosai ga hankali, itace yarinyar Commissioner ibrahim Salleh. Kuma Kowa yasan wanan family daga babban gida suke Kuma akwai mutunci sosai.


Anty fanneh ta karewa hoton yarinyar kallo tana murmushi tace "Masha Allah kam, yarinyar akwai kyau".


Mami itama tana murmushi tace "ai shiyasa na zabar wa Sabah ita, kinga family din mu dasu kusan 3 generations kenan, tun lokacin kakanin mu ake tare, yanzu mun rigada mun zama tamkar family da'ya dasu shiyasa muka shirya wanan tsarin don a kara dankon zumunci. Kwanan nan Madina ta dawo daga Sudan don acan take karatu, yanzu haka Muazzam yana kokarin ayi mata transfer zuwa Arrayan. Kila ma yanzu an kamala komai"


Anty Fanneh ta d'ago tana dubanta tace "au daman Alhaji yasan da wanan zancen?"


Mami ta gigiza kai tana murmushi tace "a'a bai sani ba, duk wanan tsarina ne. Inaso ita da Sabah su saba sosai don kinga yanzu tana aji uku, shima Sabah gashi yana gab da gamawa don haka yana kammala karatun nasa ko kafun nan ma sai a daura musu auren."


Sabah dake tsaye yana jinsu, zuciyarsa sai faman tafarfasa yakeyi. Samha ce ta d'ago tana dubansa taga ya hade rai sosai daga ganinshi kasan he's ready to burst at any time. Shi ko takan hoton yarinyar ma bai bi ba ballantana yasan ma ya yarinyar take.


Mami ce ta dubeshi tace "Sabah kana jina ko, ka samu ku daidaita kai da wanan yarinyar don mun rigada mun gama magana da iyayyenta, itama yarinyar ta amince".


Hannu tasa ta dauko packet din chocolate din da Sabah yaje ya siyo mata ta mika mishi tace "ungo nan, idan kun hadu sai ka bata, don Madina akwai ta da son irin wanan chocolates din, sai ka dinga siya mata as small gifts".


Dataga Sabah bashida niyan karban chocolates din yasa ta tura mishi a hannu. Babu yanda ya iya yasa hannu ya karba ba dan yaso ba.


Karewa packet din chocolates din kallo yayi sa'an ya dawo da dubansa ga mami ya soma magana cikin kasaushen murya yace "Mami nasha fada miki, ki daina mun irin wanan shishigin cikin rayuwa, bake zaki mun deciding future dina ba kuma bake zaki zaban mun matar da zan aura ba, duk waenan abubuwan da kikeyi are not necessary, i can decide for myself do haka ki kyaleni". Yana gama fadin haka ya dire mata chocolates din a table dake gabanta da karfi wanda saida Anty Fanneh da Samha suka firgita ya juya ya soma haurawa sama zuwa dakinsa zuciyarsa na tafarfasa.


Wani irin kallon takaici mami ta dinga binshi dashi, itama gabadaya ranta a bace yake.


Anty fanneh ce ta soma bata hakuri tana fadin "Mami kiyi hakuri kinsan halin Sabah sarai. A dai bishi a hankali har a samu ya sauko, kinga daga nan sai a lalaba shi ya amince".


Samha juyowa tayi tana kallon Ammin nata cike da takaici da tashin hankali a can kasar zuciyarta tana fadin "Ammi kema kar kiyi mana haka pls. Nida Sabah muna matukar son junan mu. Bazamu iya rayuwa babu juna ba".


Ita kuwa shafa daman tunda Anty fanneh ta haura da ita sama take ta faman rapsa kuka, tayi kuka har ta gaji kamar idanunta zasu fita. Ta rasa gane meyasa mami zata tsalaketa ta fita can waje ta nemo masa mata, bayan gata nan tana matsayin yar'uwarsa. Ta dai san akwai sanda mami ta taba furta cewa ita bata son auren Zumunci gwanda yaran su fita waje su nemo aure. Amma ita still abun yana daure mata kai. Tunanin mafita ta soma yi don ita gabadaya ji take bazata iya hakura dashi ba gwanda ta tashi tsaye, da kanta zata sa a nemo mata yarinyar da mami take shirin hadawa da Sabah.


Bangaren su mami kuwa, suna cikin haka sukaji sallamar Alhaji ya shigo cikin parlourn. Daya daga cikin bodyguards dinshi ne ya biyoshi ya shigo hanunsa rike da jakarsa da kuma wasu ledoji da jakankuna ya ajiye su a parlour ya gaishe dasu mami sa'anan ya juya ya fita.


Anty fanneh ce taje ta tarbeshi suka karaso cikin parlourn tare, Samha ta gaishe shi, ya ansa mata gaisuwar.

Abba yaje ya tsuguna cike da girmamawa suka gaisa da Mami. Mami ta ansa masa gaisuwar cike da fara'a tana tambayarsa ya aiki.


Yace "aiki lafiya lau, alhamdulillah Mami. Kunzo lafiya?"


Mami tace  "lafiya lau".


Anty fanneh ce ta mike taje ta kawo masa ruwa mai sanyi yasha.


Daga bisani Mommy ta soma zayane mishi abunda ya faru. Tace ya ja'wa d'an nasa kunne. Idan yana ganin yafi karfin kowa babu wanda ya isa dashi toh tun wuri zata saita shi. Kuma aure babu gudu babu ja da baya sai an daura.


Abba yayi shiru yana jinta. Shi kansa ya rasa gane meyasa mami take haka. Ta bar yaron nan ya zabi abunda yake so mana. Shifa bai yarda da irin wanan auren hadin bafa.

Amma shima yasan bazai iya musanta mata ba don haka ya soma bata hakuri yace zasu zauna suyi magana dashi.


Mami tace "atoh daya fiye muku daga kai  har shi".


Haka suka tsayar da maganar Anty fanneh ta kai mommy sama zuwa dakinta na musamman da Alhaji ya ware mata anytime tazo visiting. Flat guda ne babu abunda babu a ciki.


Itama Samha cike da sanyin jiki ta mike ta haura sama zuwa dakinta. Nan ta tadda shafa zaune tayi kuka har ta gaji ta zabga uban tagumi sai faman tsake tsake take tana warwarewa.


Cike da sanyin jiki Samha tazo ta zauna kusa da ita a gefen gado itama tayi shiru tana tunani.


Shafa ta dago tana dubanta da jajayen idanunta tace " daman kece Samha? Dan Allah ki taimaka ki fadawa mami cewa ina son Sabah. Kar tayi mun haka, pls" ta fada tana sake rushewa da wani kukan.


Samha ta matso kusa da ita ta soma rarashinta. Ita kanta her heart is in turmoil, ita waye zata je ta tunkara tace tana son Sabah ya share mata nata hawayen? Babu. Don haka, haka tayi kokari ta danne zuciyarta ta cigaba da rarashin Shafa.


Suna cikin haka Anty Fanneh tayi sallama ta shigo dakin ta cewa Shafa Mami na kiranta.


Da kyar shafa ta mike ta bar dakin zuwa side din mami tana share hawaye.


Washe gari da safe, samha ta shirya ta tafi school. Tana haduwa dasu khadie bayan lectures ta soma zaiyane musu cakwakiyar dake shirin faruwa a gidan nasu, koma ace ya rigada ya faru.


Cike da mamaki khadie da Amina suke binta da kallo.


Khadie tace "wai wanan mamin naku meyasa take haka? Auren dole take shirin yi masa awanan zamani? This is the 21st century fa ai an waye an daina irin wanan hadin. Kuma gani nayi Sabah har yanzu yanada lokaci meyasa takeson tayi masa auren gagawa haka?"


Samha ajiyar zuciya ta sake sa'anan tace "wai so take Sabah ya gaji family business din, kuma nan gaba tana son makarantun nan su dawo hannunsa da saurin companies na family. Shiyasa takeson tayi masa auren".


Amina tace "ah lallai kam. Akwai aiki ja a gaba kenan".


Khadie ta dubi Samha tace "yanzu toh ya kuka kare. Shi Sabah din ya amince?"


Samha tace "ina fa zai amince. Kuma kun san halinsa sarai ba amincewa zaiyi ba. Amma yanda naga mami taci serious da gaske take don har Abba ma sai data fada mishi daya ja wa Sabah kunne kar yace zai kawo mata taurin kai. Baku ji yanda gabana ya dinga faduwa jiya ba. Tsoro na daya shine kada Allah yasa mami ta gano cewa akwai wani abu tsakanin mu, da kashin mu ya bushe".


khadie tace "ai kuwa sai ku dinga taka tsantsan kar ku bari ta gano hakan".


Samha shiru tayi tunani kala kala na mata yawo aka. Suna cikin haka lokacin next lectures dinsu yayi suka mike suka shiga cikin class.


Bayan sun gama lectures, Amjad yazo ya same Samha ya mika mata wasu posters na basketball team dinsu yace ta taya shi mannawa a duka notice board din dake department. Shi zaije tare dasu khadie su manna a sauran departments.


Samha ta karba tace mishi toh babu matsala. Ta juya ta soma tafiya, Tana cikin tafiya ita kadai hanunta rike da posters sai ga Sabah nan ya taho.

Yana isowa inda take ya tsaya yana dubanta sa'anan yace "ina kuma zaki da waenan abubuwan a hanunki".


Samha ta bashi ansa da "Amjad ne ya bani yace na taya shi posting a notice boards akan event din da za'ayi na basketball".


Sabah yace "okay, toh let's go then".


Can 6th floor, wurin departmental laboratory's suka nufa Samha ta soma kokarin mana posters din a notice board. Daga ita sai shi babu kowa a floor din.


Shikam Sabah barinta da aikin yayi ya nema seat dake kusa da wurin ya zauna, ya daura kafa daya kan daya.


Samha harara ta watsa masa don a tunaninta zai sa mata hannu suyi su gama, sai taga ma ya share ta ya ciro wayarsa yana buga game. Idanunta ne suka sauka kan thumbtacks wato pin din da ake amfani dashi wurin manna posters tace "Sabah miko mun thumbtacks dinnan"

Sabah bai dago ya dubeta ba yace " a'a ni fa karki wani sani aiki anan, ina matsayin yayanki kuma sai ki dinga aikena kamar wani da'anki?"


A fusace Samha tace " Dan Allah ka taimaka mun mana, ina so na mana abun nan, hanuna ya gaji"

Ajiyar zuciya ya sake sa'anan yace "tunda kince dan Allah a taimaka miki wanan abu mai sauki ne. It's as easy as raising a hand". Ya fada yana mika mata.


Kokarin karban thumbtacks din ta somayi amma hannunta bai kai ba don yayi nesa da ita.


"Ka miko mun mana" ta fada sai faman stretching hanunta takeyi ta karba amma hakan ya citura.


Bata ankara ba from nowhere, taji ya kamo hannun nata, ya fuzgo ta, fadowa tayi bisa fafadan kirjinsa ya zaunar da ita bisa kan cinyarsa.


Samha zaro ido ta soma yi tana kallonsa.  Shi kuwa, murmushi ya sakar mata yana kokarin matsota jikinsa.


Mutsu mutsu ta somayi tana fadin "Sabah meye haka! Ka sake ni, baka san muna cikin school bane? Idan wani yazo ya ganmu a hakan fa?"


Sabah ko ajikinsa yace " toh ni ina ruwana? A gan mu mana".


"Please ka sake ni". Ta fada mishi tana kokarin kwace kanta.


Sabah dariya kawai yayi yace "ahap ai kuma sai kiyi don bazan taba sakin ki ba".


dada matsota jikinsa yayi, ita kuma sai faman fuzge fuzge takeyi tana kokarin kwatar kanta daga rikon dayayi mata amma hakan ya citura.


Sameer ne dake kokarin haurowa sama ya soma jin muryan Samha da kuma na Sabah dayake kwaikwaiyon muryanta yana mata dariya.


Kirjinsa ne ya soma harbawa ya karaso, nan yazo ya tadda su a hakan.


Ba karamin firgita Samha tayi ba data ganshi, sabah ne ya sassauta rukon dayayi mata,cikin sauri ta mike daga kafansa tana zaro ido.


Shi kuwa Sameer sai faman binsu da kallo yake cike da tuhuma da tambaya a fuskansaSabah yana ganin Sameer ya karaso inda suke yayi fuska ya kawar da kansa gefe .


Samha kame kame ta soma yi, Sameer wanda baiji dadin yanayin daya zo ya gansu su bane yace "Samha meke faruwa. What's going on?"


Cike da jin kunyarsa tace "nazo ina posting flyers ne, shine na fadi".


Sameer kallonta yayi fuskarsa cike da tuhuma don bai gamsu da abunda ta fadi ba.

Dawo da dubansa yayi ga Sabah wanda ya cika yayi fum. Sai faman harare harare yakeyi.


Ganin Sameer ya kurawa Sabah ido ne yasa tace " Sameer wanan shine yayana Sabah, wanda na...."


"Na sani. Bashi ne yaron VC ba?"+

Wani irin kallo Sabah ya watsa mishi yace " toh sai me?"


Gaban Samha ne ya tsinke ya fadi jin maganar da Sabah ya fadawa Sameer don haka ta shiga bawa sameer hakuri.


Sameer murmushi kawai yayi yace " karki damu Samha, your brother seems interesting".


Wani irin kallo Sabah ya sake watsa mishi sa'anan ya kawar da kansa gefe, daga nan bai sake cewa komai ba.


Suna cikin haka sai ga miss sophie, daya daga cikin junior lecturers na department din tazo tace "Mr Sameer, dean yana nemanka a office".


Sameer yace "Alright, gani nan zuwa".


Sallama sukayi shi da Samha sa'anan ya juya suka bar wurin shi da miss sophie.


Samha tana tsaye, gabadaya jikinta yayi sanyi kirjinta sai faman bugawa yake, juyowa tayi tana duban Sabah tace " Allah yasa bai gano cewa akwai wani abu tsakanin mu ba"


"Ban gane ba, me kike nufi? His suspicion is correct because definitely akwai wani abu tskanin mu. Gwanda ma tun wuri yasan da hakan". Sabah ya fada mata ransa a bace. Shi daman tun ranar daya fara ganin Sameer yaji gabadaya guy din bai kwanta mishi ba musamman yanda yaga Samha ta sake jiki dashi sunata hira. Wani irin kishi ne yaji yana cinsa cikin kokon zuciyarsa.


Samha data lura da yanayinsa cewa kishi ne karara ke cinsa, yasa taja bakinta tayi shiru. Tasan tana fadin wani abu yanzun nan zasuyi fada.

Sameer kuwa suna cikin tafiya, miss sophie ta dubeshi tace " daman kasan yaron VC ne?"


Sameer yace mata "noo, ban sanshi ba. Yarinyar dake tsaye kusa dashi ne na sani. Itace yarinyar mentor dina"


Miss sophie ta gyada kai tace "okay na gane".


Haka suka karasa wurin office din dean din tare.


*******************


Zack, shinoh, Abbah suna zaune a inda suka saba kebewa bayan lectures wato restroom dinsu.


Zack ne yaketa faman musu da Shinoh akan wani game da suke bugawa.


Suna cikin maganarsu sukaji wani dadaden kamshin turare ya buge hancinsu hade da wata zazakar murya tayi musu sallama ta shigo.


Tare suka dago kai suka ansa sallamar, ai kuwa Sake baki sukayi a tare ganin wata kyakyawar yarinya fara sol tsaye a bakin kofa tana kallonsu da shanyanyun idanunta. Sanye take cikin doguwar riga blue mai ratsin fararen flowers. Sai dan karamin farin gyale data yafa.

Fuskarta babu makeup amma tayi kyau sosai, don kallo daya zaka mata ka gane cewa daga gidan hutu ta fito.


Su Zack ne da Abba suka shagala da kallonta. Shinoh ya bude baki yace "Masha Allah, kunga abunda idanuna suke gane mun kuwa?".


Abbah yace "baba, wlh yarinyar ta hadu babu karya. Kai!"


Duk maganganun da sukeyi yarinyar tana tsaye tana kallonsu.


Gabadaya sai wani dar dar takeyi don ta tsorata da yanayin dasu Shinoh suketa faman binta da kallo.


Zack ne ya taso ya tako har inda take tsaye yace "baiwar Allah, akwai wanda kike nema ne?"


Matsawa da baya tayi, Siririn muryanta na rawa ta soma magana cikin i'ina tace "Ss..Sabah nake nn..nema? yana nn...nan?"


Su Abbah suka kalle junansu sa'anan suka dawo da dubansu gareta suka ce "Sabah baya nan."


Abbah ne dayaga yarinyar sai faman dari dari takeyi a wajen, ga Zack sai faman kokarin matsowa kusa da ita yakeyi tana matsawa baya ne yasashi fadin " Zack meye haka? Ka kyale yarinyar mutane mana. Duk kabi ka tsorata ta, so kake tayi mana kuka a nan?"


Zack dake tsaye dab da ita a bakin kofa ne ya hango Sabah nan tahowa. Samha na biye dashi.


Suna karasowa Zack yace "kai kuma SB haka akeyi? Ace ka samu kyakyawan babe kamar wanan shine bakayi introducing dinmu ba?"


Sabah tsayawa yayi cak, idanunsa kyam akan yarinyar yana kare mata kallo. Kallonta yakeyi yana kokarin ya tuno inda yasan fuskar.


Itama yarinyar binsa take da kallo da shanyanyun idanunta.


Wani irin shock ne ya ziyarce zuciyar Sabah daya tuno inda ya santa.

Ba wata bace illa yarinyar daya kusan kadewa da mota a hanyarsa ta dawowa gida ranan.


Samha dake tsaye kusa dashi itama kurawa yarinyar ido tayi, don ita tun farko ta rigada ta gano ko wacece yarinyar. Ba wata bace illa Yarinyar da Mami ta nuna mata a hoto tana son Sabah ya aura.


Gabanta ne ya tsinke ya fadi, can kasan zuciyarta tace "innalillahi wa ina ilahi raj'un. Meke shirin faruwa ne? Me yarinyar da akeso a hada da Saba tazo nema a school dinmu?"


Yarinyar ce ta soma magana ciki ciki, idanunta cike da tsoro da tashin hankalin ganin Sabah da Samha.


Sabah ya dubeta ya daure fuska sa'anan yace "Me kuma kika zo yi anan?".


Ganin idanun kowa a kanta ne yasa numfashinta ya soma fita sama sama. Bata san sanda ta rufe idanunta gam ta furta "nazo ne na fada maka cewa Bazan iya aurenka ba!"


Shiru ne ya ziyarci wurin, kowa na mamakin abunda ta fadi. Musaman su Zack da basu ma san da zancen ba.


Yarinyar tana tsaye numfashinta sai faman fita yake sama sama, basu ankara ba sukaga ta sulale kasa. Su zack ne sukaje suka tarota gabadaya hankalinsu a tashe.

Samha tana tsaye tana kallon abunda yake faruwa a gabanta kamar film.


Su zack suka taimaka mata suka zaunar da ita kan daya daga cikin sofa's din wajen.


Sai faman sannu suke mata, suna mata fifita.


Zack ya dubi Samha yace "Samha please jeki samo mana ruwa"

Samha ganin yarinyar tana neman fita daga cikin hayacinta ne yasa tayi sauri ta bar wurin.


Abbah ne ya dubi Sabah yace "SB kaga condition din yariyar nan. Ya zamuyi da ita?"


Sabah ya kawar da kansa gefe yace "toh me kuma za'a mata? idan ta gama ta farfado, kuce mata ta wuce gida kawai".


Yana gama fadin haka ya juya ya soma tafiya zai bar wajen.


Shinoh yayi sauri yazo ya tare shi yace "Haba SB, meyasa zaka ce haka?"


"Toh ya kukeso na mata, ai ko wanen ku yaji abunda ta fadi. A gabanku tace bazata aureni ba. Ni hakan ma datayi ba karamin burgeni tayi ba, daman ni banida niyan aurenta".


Zack yace "Toh meyasa tace bazata aureka ba?"


"Oho, ni nasan mata ne?". Sabah ya bashi ansa kai tsaye.


Muryan yarinyar ne sukaji ya katse musu maganar da sukeyi tace "saboda already inada wanda nakeso".


Tare suka juyo suna dubanta cike da mamaki, Yarinyar wace numfashin nata ya soma dawowa dai dai ta mike daga inda take zaune ta karaso inda Sabah yake tsaye tace "kayi hakuri yayana Sabah"


Sabah ya kalle ta yace "Hakurin me kuma kike bani?"


Yarinyar ta dan nesa sa'anan tace "da farko na amince da shirin mami na cewa zan aureka don tun ina sudan Abbana ya kirani ya sanar dani. Ban musanta musu ba na amince amma dawowa na sai na hadu da wani naji ya kwanta mun kuma ina sonshi amma yanzu haka ban ma san inda yake ba".


Sabah kallonta kawai yayi don bai ma gane kan maganarta ba yace "toh ai yayi kyau kuma i think you've made the right decision. Kinga kowa sai ya kama gabansa. Inai muku fatan alkhair dake da masoyin naki".


Cikin sauri Yarinyar ta dubeshi fuskarta dauke da damuwa tace "Amma...."


"Amma me?" Sabah ya katseta.


"Daman inaso na roke ka wata alfarma ne. Ban sani ba, Ko zaka iya amincewa muyi pretending kamar muna soyaya don bana son iyayyen mu su gano. Idan har suka gano cewa nayi rejecting wanan auren Abbana zai iya mayar dani Sudan. Ni kuma na gaji da zaman kasan... ina so na cigaba da karatuna anan baccin haka inada burin na sake ganin wanda nakeso kafun na koma".


Sabah kallonta kawai yakeyi daga bisani ya kawar da kansa gefe yace "No, I won't agree to that. Babu wani pretending da zanyi dake. Yanda kika gani haka, haka nake ban iya pretending ba kuma akanki bazan fara ba, don haka tun wuri gwanda ma ki san me kike ciki. Bana shakkan kowa kuma duk wanda ya tunkare ni zan fada mishi ne kai tsaye."

Yana gama fadin haka ranshi a bace ya juya ya soma tafiya ya barta tsaye a wajen.


Zack ne yayi sauri yazo yasha gabansa yana fadin "Haba SB, ya kakeyin haka. Ka duba fa yarinya ce, ka bita a hankali mana ku samu ku daidaita kanku".


"Daidaita kanmu name zamuyi? Nifa kaga bazan amince da wanan shirmen nata ba. Na rigada na fada mata mind dina, bazai yu bane".


Yarinyar tana jin haka kwala ne suka ciko mata idanu. Cikin sauri tazo ta wuce su ta bar musu restroom din hawaye na gangaro mata bisa fuska.


Ajiyar zuciya shinoh ya sake yace "kai SB ka cika tsauri dayawa, yanzu gashi ka sata kuka".


Sabah ya bashi ansa da "toh ai gwanda ta san me take ciki tun wuri, don ni bazan lalabata ba, wata shagwababiya da ita, tazo tanai wa mutane abubuwa kamar wata baby".


Shinoh dariya kawai yayi yace "still dai SB, ka dinga ragewa. You're too uptight".


Samha da tun dazu taje samo wa yarinyar ruwa, sai faman murna takeyi don taji yarinyar tace bazata auri Sabah ba.


Tana cikin tafiya har tazo daidai wurin department dinsu taga yarinyar ta fito tazo ta wuceta cikin sauri tana goge hawaye daga fuskarta.


Cike da mamaki take bin yarinyar da kallo  tace "toh meke faruwa, ina zata je kuma?"


Babu shiri itama ta mara bata baya, dai dai wurin garden din department dinsu yarinyar ta nema wuri ta zauna ta kifa kanta bisa cinyoyinta tana kuka.


Samha ta karaso inda take tayi mata sallama. Yarinyar dago kanta tayi tana duban Samha fuskarta pal da hawaye tana kokarin sharewa.


Ansa sallamar tayi, samha ta dubeta tace " Madina? Meke faruwa? Ya naganki kina kuka haka?"


Cike da mamaki yarinyar ta soma kallon Samha tace " ya akayi kika san sunana? Wacece ke?"


Samha ta dan sakar mata murmushi tace " sunana Samha, ni ce kanwar Sabah"


Murmushi  madina itama ta sakar mata sa'anan ta cigaba da share hawayenta.


Samha tace "kukan me kikeyi madina?"


Madina ta dan nesa sa'anan tace " babu komai. Sabah ne kawai ya fada mun wasu maganganu da suka bata mun rai, sai nake ganin kamar he dislikes me, baya sona. A tsawon rayuwata, this is the first time da wani yake fada mun maganganu irin wanan"


Samha tayi shiru tana sauraronta sa'anan tace " Sabah da kike gani ba haka yake ba don yanada kirki sosai, don't mind his words".


Madina ta juyo tana dubanta,Sanha tace "yes, atimes zakiga zai gaya miki magana, his words are always harsh, amma he doesn't mean them. Yanayinsa ne kawai. Don in har sai ya tsawata miki ko ya gaya miki magana tukuna zaki fahimta to zai gaya miki. It's just his way of helping others.


Madina tace "yanzu kina nufin duk maganganun daya fada mun so kawai yake na gyara? He doesn't mean them?"


Samha ta gyada mata kai tace "hakane"


Shiru madina tayi tana nazarin maganganun nasa. Nan take Sai taji zuciyarta ta dan sake, murmushi ta soma yi ta dawo da dubanta ga Samha tace "nagode sosai Anty Samha".


Samha ta girgiza mata kai tace "a'a ki kirani da Samha kawai".


Dariya Madina tayi sa'anan ta zira hanunta cikin jaka, wata yar karamar box din chocolate irin wanda ta mikawa Sabah ranan ta bawa Samha tace "gashi nan Anty na, take it as a little gift".


Samha tayi murmushi ta karba chocolate din daga hanunta tace "nagode".


Madina ta dubeta tace "babu komai Anty na. Nagode sosai da wanan bayanin da kika mun don da farko na zata ya tsaneni ne shiyasa ya gaya mun waenan maganganun. Ban san cewa it's just his own way of being kind to others bane".

Post a Comment for "ZABIN SAMHA CHAPTER 10"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...