YAR KURMA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAR KURMA COMPLETE

 YAR KURMA COMPLETE


Cikin takaici ta nuna Marwanatu da hannu, zuciyarta na  yi mata k'una saboda dariyar da take yi mata. A zafaffe ta kai mata bahagon duka, amma kash! Bata same ta ba ta saki wata giggitaciyar k'ara, ji kake kauuuuuuu! A kunnuwan Marwanatu. Benaziratu  ta k'yalk'yale da dariya ta buga k'afa irin na  Bebaye ta murd'a yatsu, take suka bada sauti d'as! 'Das!! Das!!! Alamun gargad'i tuni Marwa ta ranta ana kare.
      Bata jinkirta ba ta rufa mata baya, ai kuwa suka kasa a guje. In baka yi bani waje, basu samu matsaya ba sai a d'akin Hajja Yakura, bisa tsatsauyi suka zubar mata da biskin geron da ta ajiye. Ai kuwa cikin hargowa ta yo kansu, Marwanatu ta falle caraf ta kama Benaziratu."Wato ke 'yar

kurma bakya jin magana ko?". Benaziratu ta turo baki, bata ji abinda ta furta ba amma bakinta da ta kala ta gane me furucinta yake nufi. Tuni ta hau tirje-tirje Allah ya bata sa'a ta k'wace a guje ta bar sashin. Kafar! Sukai karo da shi, a razane ta d'ago sukai ido hud'u dashi Baana. Cikin razana ta so kaucewa kamunsa amma ina ta makaro. Yana rik'e da ita ya shiga gidan, da salama Yakura ta d'ago tana amsa masa mamakin ganinsa a wannan lokaci yasa ta kasa magana cikin yaransu take kiran mai gidanta tana sanar masa. Bakura ya taso da saurinsa yana nuna farin cikinsa da ganin Baana. Da wannan damar Benaziratu ta kufce ta fyala da gudu, yabi bayanta da kallo yana murmushi karaf suka hada ido da Yakura ya sune kai yana shafa k'eya.
Gimtse fuska tayi ta shimfid'a masa tabarma karauni, ya zauna yana gaishe su tare da tambayar yadda ya same su. Cikin murmushi suke amsawa, shigowar Marwanatu tana kuka ne ya katse su. Cikin masifa Yakura tace"kin tsaya ta dake ki ko?" Marwanahtu tai ajiyar zuciya tana lab'e-lab'e saboda ta san mudin Yakura ta kamata duka zata sha. Saboda kullum gargad'inta ta daina bari Benaziratu na  dukanta ne. Cikin mamaki Baana yace" wace ce ?" Cikin jin haushi ta numfasa.
"Wacce ce kuwa banda Benaziratu?" Ta fad'a da gurb'ataciyyar hausar ta.
Mumushi yayi a ransa yana fad'in "yaushe Hajja zata sauya?". Shiru na  tsayin lokaci, ya yunk'ura zai mik'e " ina zaka"? Cewar Yakura. Kansa a k'asa ya furta "zan je in huta an jima in shiga in gaishe da Abbagana". Murmushi mahaifinsa yayi yace "Allah ya kaimu" k'wafa tayi taja hannun Marwanatu suka bar wajan. Daga shi har mahaifinsa murmushi.
1
Washegari da misalin k'arfe bakwai na  safe Baana yana zaune a dakalin k'ofar gidansu, ya hango tahowar Benaziratu tunda ta taho ya zuba mata ido. Shi dai rayuwarsa yarinyar tana birgeshi, komai nata cikin nutsuwa take yi duk da cewar tana da son barkwanci. Bai ankara ba harta k'araso ta zo giftawa ta d'aga masa hannu tana murmushi gab da zata shiga gidansu ya d'aga murya da k'arfin gaske, ya  k'wala mata kira *"Benah"*. Juyowa tayi ta murgud'a d'an k'aramin bakinta, ta murd'a yatsu suka bada sauti ta shige gidan. Yai murmushi a ransa yana fad'in "hallayar Benah tana nan". Cikin gidan ta shiga da fuskarta d'aure tai salama, duk haushin Baana ya tuk'eta nan duniya ta tsani a kirata da Benah, ganinta kawai iyayine irin na  Baana dan yaje birni karatu.

"Ke! 'Yar kurma" aka fad'a da k'arfi daga gefanta, juyowa tayi tamkar mayunwacin zaki tana huci. Ganin Hajja Yakura sai ta sadda kanta k'asa tana gaisheta cikin gwarancinta irin na Bebaye. Matsowa tayi ta kama kunnanta ta murd'e ai kuwa ta saki k'ara saboda azabar wahala, shar k'wala ta zubo mata. "Dan ubanki me Marwanatu tayi miki jiya, da zaki sata Ku........?" Maganar ta katse sakammakon k'watarta da Bakura yayi yana bambamin fad'a.

"Ke dai Yakura kinji kunya, me yarinyar nan tai miki? Tsabar k'in Allah kin takura mata idan da kara itama 'yar ki ce".

_"Kai! Kai!! Kai!!! Bakura dai na fad'in wannan, Allah suturi buk'wui ina amfanin sai da rai a nemo suna? Wai kai kana tunani zanso wannan abar? Hmmmm! Allah ya kiyayye had'a iri da kishiya". Wata muguwar harara ta makawa Marwanahtu, tuni ta ja hannun Benaziratu wadda take razgar kuka, kasancewar duk da k'arfi Yakura take maganar tana jinta. Kad'a kai Bakura yayi ya shige d'akinsa.

Suna fita sukai kici6us da Baana, hannun Benahziratu ya kamo yana tambayarta. Ta k'wace hannunta dan tuna abinda yai mata d'azu. Bata kula kowa cikin su ba ta warce hannunta tana kuka, kai tsaye gida ta nufa. Cikin raunin murya ya dubi k'anwarsa"Marwah me ya samu Benah"? Murmushi tayi dan taji dad'in yadda ya kira sunan. Tiryan-tiryan tai masa bayanin abinda Yakura tayi, kansa ya ri'ke yana jinjina hallayar mahaifiyarsa a ransa yana fadar" wai shin yaushe Hajja zata sauya?"............
Kai tsaye gida ya shiga, alamu da yawa sun nuna tsantsar damuwarsa. Yana shiga da salama ta amsa  masa babu yabo ba fallasa, ya samu guri ya zauna. Minti biyar babu wanda yace uffan cikin su, ganin babu fuska ya yunk'ura ya bar gidan. Zuciyarsa na  zafi.

STORY CONTINUES BELOW

Kai tsaye gidansu Benahziratu ya nufa, cikin murmushi yai salama. Mamaki ne ya kamashi ganin Benazirahtu normal (lafiya) tana aikin ta. Mahaifin Benazirahtu ne ya fito da murmushi ya ce "a'a Baana barka da zuwa, saukar yaushe?" Ya shafa k'eya d'abi'ar da ta zamo masa jiki da murmushi yace. "Abbagana jiya da yamma nazo hala Benah bata gaya muku ba? Ta gani a jiyan". Cikin murmushi yace "kasan halin kayar ka", zama sukai suka k'ara gaisawa. Can sai ga Hajja Faanah ta fito, suka gaisa da nuni da hannu. Ruwa mai sanyi Benazirahtu ta ajiye masa cikin a kofin kushi, ta sake dawowa d'auke da babban a kushi ta sunkuya ta ajiye. Murmushi ya yi ya bud'e k'amshin manshanu ya yi masa salama, ya lumshe ido ganin biskin gero da miyar kub'ewa ga manshanu. Ai ba jinkirtawa ya sab'a hannun riga ya soma kwasar loma.
           Can ya d'aga murya yace "Abbagana ina ce Hajja ce tayi girkin nan ba wannan ba?". Tsaf ta kalle bakinsa, ta gane furucinsa ai kuwa ta turo baki ta hau buga k'afaffu alamun shagwab'a. Gaba d'aya suka saki dariya, cikun gurbataciyyar maganarta tace "nafi matarka iyawa". Dariya suka sake yi, Hajja Faanah na  tambayar abinda Benazirahtu tace. Mahaifinta yai mata bayani da hannu.

Bayan ya gama ta d'auke kwanukan, ya dubeta "Benah d'auko jakarki ta school (makaranta) in gani kinji", babu musu ta mik'e sai ga ta ta dawo d'auke da'ita, karb'a yayi yana duddubawa a hankali yake mata tambayoyi tana amsawa . Sossai yaji dadin yadda ta maida hankali tana karatu fiye da Marwah.Bai bar gidan ba sai gefun sallahr azahar, a ransa ya k'udiri kyautar da zai mata._
       ************
_Washegari kuwa sai gashi da dogayan riguna, dai-dai ita guda uku bayan sun gaisa da Hajja Faanah ya bata. Godiya sossai sukai masa, Banazirahtu baki yak'i rufuwa ya gonar audiga. Da gudu ta suri kayan ta nufi gidan wan mahaifinta, tun a soro take kwad'awa Marwanahtu kira. Tana fitowa ta hau nuna mata kayan, cikin murna tace "waya baki?" Babu komai ranta tace "Baana"........... Kafin ta k'arasa magana taji an warce kayan kai tsaye cikin murhun girki Hajja Yakura ta watsa su, wata giggitaciyar k'ara Benazirahtu tayi ta shid'e ji ka ke yif! Ta fad'i. Hakan yai dai-dai da shigowar Baana cikin kad'uwa ya furta.
"Benah!"

_Cikin kad'uwa yake girgizata yana kiran sunanta *Banah! Benah!! Benah!!!* amma kash! Shiru Malam yaci shirwa. Hankalinsa ya yi matuk'ar tashi da wani rikitacan kallo yake duban mahaifiyars. Sai dai kawaici irin na  d'a da uwa ya kasa tankawa. Surarta yai bai zame ko'ina ba sai d'akinsa, sossai yake zuba mata ruwa ta k'i motsawa. Ya kasa kunne amma bata motsi, k'irjinsa ya dinga bugawa fat! Fat!! Fat!!. "Kadai ace *Benah* ta rasu"?. Ya fad'i hakan a ransa. Can ya tuno wani bayani da akai musu a wata lecture, yayin da mutum yai dogon suma. Hamdala yayi ga ubangiji, ya toshe hancinta ya bud' e bakinta ya had'a da nasa. Ya soma musayar numfashi kafin minti uku ta soma motsi, cikin sauri ya watsa mata ruwa._

_A hankali ta zuba masa ido, can ta fashe da matsanancin kuka saboda tunawa da kayanta."Baana kayana" , ta fad'a cikin gwaranci. Janta yayi jikinsa yana shafa kanta a hankali tai shiru sai ajiyar zuciya take. Sai da ya tabbatar da ta yi shiru ya d'auko chaculate ya bata, tare da alk'awarin kawo mata wasu sababbun kayan. Da murna tai masa salama ta nufi gida. Tana zuwa ta zauna ta bawa mahaifinta labari, murmushi yayi tare da bata hak'uri ya gargad'eta da kada ta gayawa Hajja Faanah komai, saboda gudun matsala. Koda ta tambayeta cewa tayi "kayan ne sukai yawa canzowa za'ayi"._

_Cikin rashin walwala ya shiga gida, Hajja Yakura ta dubeshi "wai kai dan an k'ona kayan waccan nakasshashiyar *'YAR KURMAR* kake ciwa mutane kunu? Meye abun damuwa da lamarin mutanan da suke da nakasa a rayuwar su? Mtssss!" Ta ja tsaki tana gunguni. Cikin taushin murya ya dubeta._

_"Hajja ki fahimce ni koba komai *Benah* 'yar uwata ce, kuma k'abilarmu d'aya nakasa ba zaisa in nuna mata k'yama ba. Bafa laifi sukaiwa ubangiji ya hallice su haka ba, suma mutane ne kamar kowa kuma ubangiji yana kishin su yana sonsu. Haba Hajja". Ya fad'a da sanyin murya, ai kuwa yana direwa ta hau sababi, kai kace zaginta ya yi jikinsa yai sanyi zuciyarsa na  radad'i yana takaicin hallayar mahaifiyarsa.
_Baana d'a ne ga Alairam Modu kalmar Modu na  nufin  Muhammad kenan, Modu wanda akafi kira da sunan Bakura,saboda kasantuwarsa babba a gidansu. Kalmar Alairam na  d'aukar Alhaji ne a yaran Kanuri ko kuma Aisami wato Alhaji. Hajiya kuma sukan kirata Aisaram, yayin da . Bakura dai haifaffan garin Mai duguri ne, su biyu iyayyansu suka haifa da k'aninsa mai suna Hamza. Sun taso cikin so da k'aunar juna, mahaifinsu fittacan Malamine wanda yake koyar da d'alibai sama da hamsin.Sunansa Aisami Muktar Bunu, wanda da yawan muta ne ke kiransa Malam Bunu. Mahaifiyar su kyakkyawar mace ce mai suna Falmata a salinta shuwa ce.

Sun taso cikin ingantaciyyar tarbiyar da mahaifinsu ya basu, mahaifinsu mutum ne mai neman na  nakansa. Saboda sana'a maganin wulak'anci ce, shi kuma Kanurin mutum nan duniya ya tsani raini da wulak'anci. Haka kuma Kanuri ya tsani  'kazanta baya son rashin gaskiya da girman kai uwa uba d'aukar al'adar da ba tasa ba.
Idan kuwa so kake ka burge Kanuri, to kayi masa kyautar gwal ko hula ko turare mazan su da matansu akwai son k'amshi. Kanuri akwai iya kula da tattalin mace tamkar k'wai, sun tsani rashin iya girki da yawan dariya. Matansu kuwa in kana son burgesu kyautar gwal da mindil. Mindil wani gyala ne na bare-bare, shigar su kuwa mata sunfi yin shigar lafayya, ko riga mai dogon hannu da mindil. Tsofaffun cikin su dama wasu cikin matasa, da yawa suna cin goro.Suna amfani da wani abu mai suna; ingwargo abun yana nan green ne(kore) in suna cin goro suna goge bakin su dashi don hak'orin su ya yi ja.Idan na  tsaya yi muku bayanin Kanur sai mu kwana, saboda suna da al'adu daban-daban ababban sha'awa.

Malam Bunu yana sa'ar d'inkin hula, sai kuma d'an hasafi da yake samu daga masu zuwa ayi musu adu'a. Hakan baisa zuciyarsa ta mutu ba kullum burinsa yaransu sui karatu domin gobansu.

Yaransu na samun kulawa dai-dai gwargwado, sun tsaya kan tarbiyar su. Kaf d'insu sai da suka hadda ce alk'ur ani mai girma sannan suka saka su a makarantar boko. Lokacin Bakura nada shekaru goma cif, Hamza kuwa nada bakwai, sai dai mahaifinsu na yi musu lesson a gida wata rana kuma Falmata tayi musu, wadda suke kira Hajja.Fanin ilmin boko ma babu dama, sun tsaya tsayin daka da karatun su. Bakura na  primary four Hamza na  primary two wani muhimmin al'ammari ya tasowa Alairam wanda hakan ya tilasta masa tashi daga Maiduguri zuwa garin biu d'aya daga k'aramar hukumar jahar Maiduguri.


_Al'amarin ya samo asali ne na wata makaranta
da aka bud'e ta islamiyya a garin biu dan
bunk'asa harkar ilmin addini. Aka d'auki Malam
Bunu zuwa wannan sashi, da farko ya soma
zuwa ya dawowa iyalansa duk mako d'aya wato
kwana bakwai. Daga baya yaga rashin dacewar
hakan, saboda yadda sukai sabo da iyalansa
shawarar Falmata ya nema ya samu k'aramin
gida ya sai musu suka koma can da zama gaba
d'aya. Dama ba wani dangi ne da shi sossai ba
duk sun mutu sai k'anin mahaifinsa guda d'aya
shima ya tsufa sossai. Haka suka tattara suka
koma._
************
GARIN BIU
Garin Biu na d'aya daga cikin k'anannan hukumomin jahar Maiduguri.Shi dai k'auyen Biu
k'auye ne babba, wanda Allah ya a zurta su da noma da kuma karatu.Sun d'auki karatu da
muhimmanci fiye da yadda mai karatu yake zato.Shiya sa suka samu cigaba a cikin
Maiduguri, dama wasu garuruwan a cikin
Maidugurin. Idan kika cire ma'aikaci d'aya na
biyu zaki ga babur ne wato yaransu. Ilahirin
mutanan biu babur ne.Haka kuma ta b'angaran noma, Mata suna yi Maza suna yi. Amma duk da wannan noma, dole yaro sai ya bawa karatu lokacinsa. Suna noman gyad'a masara da
barkono da kuma gauta.
Mutanan garin sun iya zaman duniya da kissa,da kuma wayyo sai dai suna da rowa. Sanan kuma hanyar zuwa biu bata da kyau akwai gargada a hanyar. Allah ya horewa mutanan Biu iya
soyyaya, sun iya soyayya 'yan garin. Matan garin kuwa suna da had'in kai tsakanin su.Mai karatu
kar kayi mamaki in nace maka, zaka ga mace ba abinda take b'oyewa mijinta komai tare
suke.Suna tanadi da tattalin junan su.Idan kuwa ka shiga jami'ar Maiduguri zaka riski,
gungun d'alibai 'yan garin har taron su suke duk k'arshen wata. Sukan yi had'in guiwa wanda ba
shi da kud'i su tara masa.Kishi da jinsin Kanuri akwai wahala, ballantana kishi da matan garin
Biu.Kishi da su yana da wahala saboda suna da bala'in kissa da iya kula da Miji uwa uba
biyayya.Wannan shi ne bayanin garin Biu a tak'ai ce,kuma mudin akai hutun makaranta lokacin
damuna to zaki ga d'alibai mazauna Biu na turruruwar zuwa yin noma garin su.
Komawar su garin Biu bai kawo nak'asu a rayuwar su ba, hasalima cigaba suka samu ta
fannoni da dama. Makaranta mai zaman kanta mahaifinsu ya saka su, sab'anin da da suke zuwa
makarantar gwamnati.Zama suke cike da walwala da jin dad'i, a jikin gidan su akwai
mak'ota guda biyu d'aya 'yan garin Gwaza ce yaranta biyu d'aya sunan sa Alangubro d'ayar
kuma Aysa. Aysa na nufin Aysha, Alangubro kuma ranka ya dad'e.Akwai kyakkyawar alak'a
tsakanin wannan mak'ota. A hanun daman su akwai wata dattijuwa mai suna Hajja Faanah.
Hajja Faanah mace ce mai yakanah da son yara,tun tarewar su jininta ya had'u dana Hamza
sossai. In babu makaranta nan yake yini suna hira tana koya masa yaran su. Hajja Fannah a
salin sunanta Fatima ne, bata da yara d'anta d'aya hamshak'in mai kud'i ne. Ya wadata ta da
komai, yana zaune a garin Gaidahm shi da mai d'akin sa da 'yar su guda d'aya mai sunan
Hajja.Amma kash! Kurma ce haka aka haife ta bata magana sai dai nuni da hannu. Lokaci-
lokaci suna zuwarma Hajja hutu.Kullum Hajja cikin bawa Hamza labarin Faanah take, hakan ya dasa masa zumud'in san ganin ta.

2
_Yawan bawa Hamza labarin Faanah yasa yake yawan yiwa Hajja Faanah maganarta.Tare da tsananin tausayinta a ransa, musamman da ya samu labarin kurma ce. Badan Hajja ce ta gaya masa ba da ba zai yadda ba, saboda yadda yake ganinta a hoto kyakkyawa ce sossai. Ya matsu ya ganta,kullum Hajja cikin bashi baki take saboda basa garin kwata-kwata suna Canada can Faanah take karatunta. Kwanci tashi Bakura ya gama makarantar gaba da primary lokacin Hamza na aji biyar, Malam Bunu ya sama masa admission a jami'ar Maiduguri fanin Islamic. Haka suka cigaba da rayuwarsu abin sha'awa, Hamza na mataki na biyun  k'arshe  mahaifinsu ya rasu, sakammakon annobar amai da gudawa._

       _Mutuwar ta girgiza su sossai, Hamza sai da yayi sati a kwance a asibiti. Cikin k'ank'anin lokaci suka zama abun tausayi, Hajja Faanah ce take taimaka musu da abinci da hidimar yau da kullum.Tilas Bakura ya hak'ura da karatu ya rungumi noma, saboda tallafawa rayuwar su. Kwanci tashi Hamza ya zana jarrabawa, ta fito ranar Hajja har walima ta shirya masa.Bayan watanni biyar sakammakon sa ya fito, sakammako yayi kyau sossai Hajja da kud'inta ta sama masa gurbin karatu, a jami'ar Maiduguri. Lokaci zuwa lokaci yakan ziyarci garin Biu, hakama Maiduguri wajan k'anin Kakansu.Haka ma lokacin noma yakan zuwa sui noma  ya koma .Hamza ya dage karatu yake sossai yana karantar fanin kunne.Kullum Falmata na nunawa Bakura da Hamza su rik'i Faanah da muhimmanci ko bayan ranta. Bayan shekara d'aya  da rasuwar Malam Bunu lokacin Hamza na level one kwatsam, Hamza na zaune a gidan Hajja Faanah suka ji salama. Hajja ta mik'e tana murna cikin yaransu tana raira wak'a abin gwanin sha'awa ta rungume wata kyakkyawar mace tamkar balarabiya. Cikin kulawa tace._
_"Barka da zuwa, barka da zuwa". "Da alamu dai bak'in na musamman ne", Hamza ya fad'a a ransa. Karaf idonsa ya sauka a kan namijin da yarinyar kusa dashi wadda bata gaza shekaru goma sha hud'u  ba. Murmushi ya sub'ucewa Hamza saboda, ganin Faanah yau bayan tsayin lokacin da Hajja tai tana bashi labarin ta._

STORY CONTINUES BELOW

_Zahiri ya santa a hotunan ta wanda suka cika d'akin Kakarta, cikin murmushi ya dubi Hajja yace"yau dai naga takwarar Hajja". Gaba d'aya hankalinsu ya dawo kansa, cikin murmushi mahaifiyar Faanah tace._
_"Hajja wannan waye"?._
_Hajja tai murmushi, "sunansa Hamza mak'ocin mune d'an wajan Malam Bunu da nake baka labari a waya. Cikin murmushi yace"Masha Allah" bayan komai ya lafa suka zauna, ana ta hirar yau sha gamo. Hamza ya mik'e yana murmushi, yaiwa Hajja salama zuwa gida_

_Cikin walwala ya shiga gida yana bawa Hajja Falmata labari, cikin farin ciki tace "yau dai buri ya cika an ga Fauna", murmushi ya yi shigowar Bakura ya katse musu hirar da fara'a yake tambayar abinda ya faru. Hajja ce take bashi labari, da murmushi yasa hannu a aljihu ya fito da kud'i naira dubu biyu."Maza je kayo cefane a sauki bak'i", dan dad'i rungume Bakura yayi yana murna"karka  damu awaana" awaana na nufin d'an uwa.
_Cikin sauri ya nufi kasuwa ya siyo nama, tare da kayan amfani. Nan da nan Hajja ta hau hidimar bak'i, biskin gero da miyar kub'ewa tayi musu yasha manshanu gefe kuma soyyayar kaza ce. Ni kaina sai da nayi sha'awa. Hajja na  gamawa, ta had'a masa ya d'auka sai gidan Hajja._

_Kai tsaye gidan Hajja Faanah ya nufa, cikin nutsuwa ya yi salama. Daskarewa ya yi saboda mamaki, ba komai ya haddasa masa hakan ba face ganin Faanah. Durkushe take gaban d'an magen Hajja tana wasa da shi. Bai tab'a zato haka kyanta yake ba, kwata-kwata a hoto munninta ya hango. Gashinta ya rufe mata ido saboda yawansa da santsi, gyaran murya ya yi yai salama daga ciki Hajja ta amsa. Ya shiga yana murmushi ya sauke farantin hannunsa wanda aka jera kayan. Cikin murmushi Hajja ta dubeshi "sannu da k'ok'ari Hamza, hada hidima"?. Cikin murmushi ya sunkuyar da kai, mahaifin Faanah ya bishi da kallo yaron ya birgeshi sossai cikin ransa yana k'udirta wani lamari._

_Murmushi yayi ya fito zuwa tsakar gida, a hankali ya zauna yana fuskantar Faanah yana murmushi. Cikin barbanci ya ce"ba magana k'anwata?", da hannu ta nuna masa alamun bangane ba. Hamza yai murmushi a fili ya furta "kash! Tsutsa baki cin ragon goro", cikin tausayawa ya dinga kallonta. Fitowar Hajja yasa ya mik'e yana dubanta yace, "Hajja ina so mui magana da takwararki ban iya ba". Murmushi tayi "da sannu zaka iya Hamza rai dai" , murmushi yayi ya kad'a kai yayi wa Hajja salama ya wuce._

_Bakura noma yake sossai, Allah yasa masa albarka. Ubangidansa mutum ne mai saki masha Allah cikin ikon Allah, ya had'a shi da wata budurwa a wani aikin gona da ya fita yi mai suna Yakura. Yakura masifaffiyar yarinya ce ta bugawa a jarida, irin matan nan ne gansama-gansama masu suffar k'irar doki doguwa ce mai tsayi kakkaura. Bak'ace ba can ba tana da tsage guda biy-biyu a kumatunta wanda suka fito da fuskarta sossai hancinta mai tsayi sossai. Tana da yalwar gashi. Asalin mahaifanta 'yan garin Gamborun kukawa ne aiki ne ya kawo su garin Biu. Mahaifinta mutum ne mai mata biyu, da yara guda goma sha biyu. Yakura itace babba mahaifiyarta mafad'aciyyar mace ce. Sunanta Yagana, su biyu ne mata a wajanta ita da k'anwarta Yalfata. Sai maza akwai Alanguburo, Barma Hamza da kuma Muktar. Kishiyarta Yawuri yaranta duk mata ne, hakan ya haifar da k'anannun maganganu tsakanin zaman Babbar 'yarta itace Kundum yarinya mai hak'uri sossai, sai mai binta Bintu da Findu sai kuma Yazeyi da autarsu Yalta.Zaman gidan wani irin zamane na ishasshiyar mace hakan yasa mahaifiyar su Kundum bata da sakewa sossai asalinsu 'yan garin Askira ne .Kundum na aure a Gwaza Bintu a nan Biu Findu ce take Maiduguri Yazeyi Askira take sure sai auta Yalta dake karatu._

_Tunda Allah ya had'a Yakura da Bakura, suke wa juna. Yakura ta shiga ta fita ta hana zuciyarsa sukuni. Daga ita har mahaifiyarta, saboda bata son ya kub'uce mata. Dalili duk wanda yazo neman auranta yaji bata da mutunci guduwa yake, hakan yasa su kaiwa Bakura ruk'on talalla ya kasa koda motsi balle guduwa. Komai ya rarrumo to Yakura ce mutum ta farko, hatta da Hajja da Hamza ya tsaya da hidima da su hakan ya soma kawo nak'asu a karatun Hamza._

_Kwanci tashi kwannan su Faanah uku a garin Biu, zuwa lokacin sun yi wata irin shak'uwa da Hamza sossai, in basu ga juna ba kamar sa yi zazzab'i tun Hamza bai iya maganar kurame ba har ya koya.Faanah gidan su Hamza take yini suna hira abinda ya bashi mamaki har rubutu ta'iya in ya fad'a Hajja ta kanyi murnushi tace "nakasa bata hana bawa zama managarcin mutum"._

STORY CONTINUES BELOW

Kwatsam ranar wata Asabar ana saura kwana hud'u su Faanah su koma Canada, tana gidan su Hamza suna hira suka samu bak'uncin Yakura da Yelta. Lamarin da ya haifar da rud'ani cikin zamantakewa............
_Tunda sukai salama suka shigo Yakura ta kasa d'auke ido akan Fannah, zuciyarta na wani irin suya tsananin kishi ya kasheta. Bakura ya kasa tsaye sai nan da nan yake yi da su. Zama sukai suka gaishe da Hajja ta amsa da fara' a. Hamza kwata-kwata yak'i kallonsu ko d'aya Yakura bata birgeshi, sai da Bakura ya yi masa magana sannan ya juyo ya gaishe su. K' ur! Idanun Yalta a kan Hamza, zuciyarta ta shiga bugawa nan da nan so yai mata dabaibayi. Fuska a d'aure ya juyar da kai ya cigaba da yiwa Faanah hirarsu irin ta ma'abota kurumta sai dariya take wani lokacin tayi murmushi. Yakura ta nisa tace"Bakura dama kana da k'anwa?" Murmushi ya yi  yai mata bayanin Fannah a wajan su.Dai-dai lokacin Hajja ta basu waje, kamar jira take tana barin wajan ai kuwa Yalfata ta kwashe da wata shu'umar dariya"hhh! Nida durum kace bata ji?". A zuciye Hamza yayo kanta bai wata wata ba ya kwasheta da mari, cikin takaici ya nunata da yatsa zuciyarsa na zafi_.

_Bai an karaba yaji saukar mari a kuncinsa, cikin kad'uwa ya juya saboda ganin wanda ya mareshi abin mamaki Bakura ne. Ransa ya yi zafi ya dinga dubansa a wani irin yanayi kawai sai ya girgiza kai ya wuce. Hannun Fannah ya kama suka wuce zuwa gidan Kakarta. Tunda ya fita ya kasa magana, sai ajiyar zuciya yake. Faanah ta kama hannunsa ya zuba mata ido, sai ta girgiza kai shar hawaye ya zubo mata. Rikicewa yayi yana girgiza kansa bai taba ganin kukanta ba sai yau "shin me hakan yake nufi? Kodai Faanah najin abunda nake ji a raina?" Hannu yasa ya share mata hawayan suka nufi gidan Hajja da fara'arsu suka shiga. Hajja da mahaifiyar Faanah da mahaifinta na zaune suna fira, cikin murmushi suka zauna. Faanah nasan yiwa Hajja bayanin abinda ya faru ta kasa. Fahimtar hakan yasa Hamza yai mata bayani gudun zargi. A hargitse mahaifinta ya mike yana masifa" sun san kuwa yadda nakeson 'yata? Kurumta baisa ta zama wofintaciyya ba mutum ce mai cikakken yanci kamar kowa". Hajja ce ta dinga tausarsa haka ma Hamza bayan komai ya lafa Hamza ya dubi Hajja yace "Hajja wai haka aka haifi takwararki ko lallura ce?". Ta bud'e baki zatai magana sai gani nayi ta mik'e zumbur!.
_Cikin murmushi Hajja ta dubeshi "sarkin tsoro naga randa zaka daina tsoron nan naka"dariya ya yi yana soka kai ta cigaba "yau dai zaka ji wacce ce Faanah?"..........._

_*WACCE CE FAANAH*_
_Kamar yadda ka sani ni na haifi mahaifin Faanah, shi kad'ai na haifa a salin mahaifinsa d'an Damaturu ne tsakanin Damaturu da Maiduguri tafiyar 177km ne ya taso cikin taskun 'yan uba su goma ne. Shi kad'aine waraki a cikinsu saboda mahaifiyarsa Bahaushiya ce 'yar Kano. Tsangwama da hantara babu wadda mahaifiyarsa bata gani ba, harta rasu sai tsangwama ta dawo kansa. Saboda Kanuri bayason auran wanda ba k'abilarsa ba sai rantsattsan rabo. Haka ya taso cikin gararin rayuwa, har girmansa Allah ya taimake shi mahaifinsa ya tsaya masa kan karatu. Allah ya had'amu da shi ne a wata ziyara da ya kai garin mu Gaidahm  gidan marayu cikin k'ank'anin lokaci mukai sabo dashi._

_Kasancewata marainiya bani da kowa kawai na taso ne na tsinci kaina a gidan marayu. Bayan dogon bincike aka bawa mahaifinsa aurena, zaman wata biyu mukai a Damaturu akai masa sauyin aiki zuwa Biu. Zamanmu a Damaturu zamane na hantara da hancini, dawowarmu Biu sai muka samu kwanciyar hankali a haka Allah ya bani juna biyu harna haifi d'a namji wanda yaci sunan Muhammad. Dangin mahaifinsa babu wanda yazo mana har ranar suna, kwanci tashi mahaifinsa ya soma sana'ar gwal nan da nan Allah ya bud'a masa ya zama shahararran mai kud'i. Lokaci zuwa lokaci muna zuwa ziyara gidan marayu da kuma Damaturu duk da bama samun wata tarbar kirki.Muhammad nada shekaru uku Kakansa ya rasu, mutuwar ta girgizamu dama shi kad'ai ne wanda ya rage mana. Bayan rasuwarsa sukai raban dukiyarsu kowa akabashi tasa suka watse. Kwanci tashi akasa Muhammad a makaranta kulawa yake samu sossai, harya gama makarantar primary ya shiga secondary. Yana jss two wata masifa ta samemu, barazana da yake samu daga abokan kasuwanci. Saboda ya tara dukiya da yawa duk garin Biu ansanshi, kwatsam wata ranar Lahdi da dare muna bacci aka hauro aka kashe shi. Lamarin daya girgizamu, sunyi bincike basu samu komai ba, saboda duk wata ajiya tasa tana banki wala kud'i wala kaddara._

_Haka muka sha kukanmu muka more, haka na cigaba da rainon d'ana na ingantashi da karatu da tarbiya har ya kammala makarantarsa. Na sama masa gurbi a makarantar kud'i nan yai karatunsa na shekaru shida na gaba da secondary daga nan ya samu admission a jami'ar Maiduguri bayan gama karatun sa na master yai aure, ya auyi Maryam 'yar a salin garin Maiduguri cikakkiyar Kanuri kyakkyawa gaba da baya. Zamansu shekara d'aya ya nemi gurbin k'aro karatu a k'asar Canada. Naso hanashi amma daya gayamun k'udirinsa saina hak'ura suka tafi. Shekarar su daya da tafiya aka haifi Fannah wadda taci sunana. Naji dad'in yimin takwara da akai sossai, daga can ya aiko abokinsa ya tafi dani akai suna na dawo. Sai da suka shekara uku sannan suka zo wajena lokacin Faanah ta girma, abinka da rainon turawa tayi girma sossai kamar 'yar shekara shida gata kyakkyawa. Abinda ya bani mamaki tunda suka zo banga tayi magana ba, tun ina kawaici har na furta. Cikin jimami sukai mun bayanin *KURMA CE* da farko hankalina ya tashi amma daga baya na fawwalawa ubangiji domin shiya hallice ta ya fimu santa._
_*Haka suka gama hutun su suka koma, tun ban iya hira da'ita ba harna koya nayi kewarta sossai. Bayan gama karatun mahaifinta Canada suka d'aukeshi aiki hakan ya tilasta musu zama a can. Zamowar Faanah Kurma baisa ta samu rashin kulawa daga iyayye ba hasalima tsananin sonta suke yi sossai, makaranta mai tsada suka sata abinka da kasasshen ketare sossai Malamai suke bata kulawa. Yanzu Faanah nada shekaru goma sha biyar tana matakin karshe a makarantar gaba da primary, ta iya rubutu sossai saidai bata ji kwata-kwata haka ubangiji ya hallici baiwarsa...........wannan shi ne tarihin Faanah.

Ajiyar zuciya Hamza ya yi yace "kin san me Hajja?" "Saika fad'a Hamza". "Walahi banyi zaton haka aka haifi Faanah ba kin san akwai........


_Kiran wayarsa ne ya katse shi, ya dauko ya daga.Sun jima suna magana sannan ya katse ya soma bayani._

_"K'ananan yara tsakanin wata shida zuwa shekaru uku sukan yi fama da wani irin ciwon kunne da ake kira Otitis media, shi otitis media ciwo ne wanda yake ciwo a tsakiyar kunne._

_Ciwon kunnen yafi faruwa da damina kuma yana zuwa da zazzab'i wani lokaci mai tsanani,sai dai sau da dama bai cika zama abun damuwa ba._

_Akwai kuma wani ciwon kunnen da ake kiransa otitis external, wanda shi kuma yake shafar wajen kunne. Koda yake yara basu cika kamuwa da shi ba  kamar na farkon ba._

_Yawanci k'ananan yara suna fama da ciwon tsakiyar kunne, musamman k'ananan yara daga cikin wannan jerin:-_ _Yaran da aka haifa basu kai lokacin haihuwa ba.Akwai yaran da suke yawan jin sanyi sosai.Sannan akwai yara wad'anda basa son wari, kamar hayak'in taba da sauran su.Ko kuma yaran da ba’a basu nono ba.Da kuma yaran da aka baiwa abincin gwan gwani._

_Wasu k'wayoyin cuta suke kawo ciwon tsakiyar kunne.K'wayoyin cutar na tafiya daga bayan mak'ogoro yayin da Eustachian tube ta lalace,wannan ke kawo ciwon tsakiyar kunne.Shi yasa yara masu yawan jin sanyi ko masu fama da ciwon mak'ogoro ke kamuwa da ciwon kunne.Otitis external shi kuma yawanci yana faruwa saboda rashin tsabtar fatar jiki da k'wayar bacteria._
_Cikin murmushi Mahaifin Faanah ya dubeshi"shin ya alamomin ciwon suke Dr Hamza?". Dariya Hamza ya yi yace"haba Baana ban kai ga zama ba just one level fa". Gaba d'aya sukai dariya, banda Faanah da tai zuru tana kallon su, tausayinta ya cika Hamza ji yake tamkar ya bata kunnuwansa. Kad'a kai ya yi yaci gaba._

_Alamun ciwon:-Ciwon cikin kunne (Otitis media), yawancin manyan yara suna fama da k'aik'ayin kunne da zafi.K'ananan yara basa iya Magana,amma zasu kasance da zazzab'i marar misali._

_Haka nan zasu kasa yin barci, su rik'a sosa kunnen su har yayi jinni, kuma suna kasa iya sauraron k'ara ko amo.Za’a iya samun fitar ruwa mai k'wayoyin cuta daga kunnuwan.Ciwon bayan kunne shima yana da zafi sosai, yana sa k'uraje sossai a bayan kunnuwa._

_Ana iya ba yara 'yan  k'asa da wata shida maganin kashe k'wayoyin cuta (Antibiotics).Shan maganin rage zafin ciwon.Yara suna jin sauk'i yayin da suka fara amfani da maganin kashe k'wayoyin cuta.A nan yana da muhimmanci ga Iyaye su kiayye umurnin likita har k'arshe.Shan Topical antibiotics da man shafawa suna maganin otitis external.Sake ganin likita na da amfani idan yaron yana da ciwon kunne ko yana amai sossai.Idan kuma yana da zazzab'i fiye da sa’a 48, da kumburi bayan kunne, idan yana barci sosai, kuraje a kunne, baya ji sossai ko gaba daya._

_Kunne yana d'aya daga cikin sassa masu muhimmanci sosai a jikin d'an Adam.Wanda ba kasafai ake gane muhimmancinsa ba, sai ya kamu da wata matsala._
_Kuma amfaninsa ba wai kawai a jin magana ya tsaya ba, a’a yakan kuma taimaka wajen sa dai-daito idan mutum ya mik'e tsaye ta yadda ba zai fadi kasa ba._

_Kunne na da b'angarori uku, na waje da tsakiya da kuma can ciki.Fatar kunne da k'ofar kunne ta waje su ne bangare na waje d'in.Amfanin wannan sashe shi ne tare iska da amo ya saita su zuwa cikin kunnen. Wannan b'angare bai cika samun ciwo sosai ba, sai dai akan iya yanke shi a hadari, ko kuma da abubuwa masu kaifi idan wata tarzoma ta tashi misali.Ita kuwa k'ofar kunne ana iya ganin dattin kunne a ciki a fitar ta wannan bangare._

_B'angare na tsakiyar hade yake da mak'ogwaro ta yadda kwayoyin cuta daga makogwaron kan yi saurin shiga kunne, musamman ga yara tunda hanyar da ta had'asu gajeriya ce.Ruwa ma kan iya shiga wannan b'angare na kunne a yayin wanka ya hana mutum sakat._

_Daga can ciki kuma akwai wani b'angaren,inda dodon kunne wato cochlear (da kike tambaya akai) suke, da wasu kasusuwa kanana guda uku.Jijiyar da ke da alhakin sa mutum jin magana a jikin dodon kunnen ta ke.Wato ke nan dodon kunne shi ne ke da alhakin jin magana.Su kuma kasusuwan sukan taimaka wa jiki wajen daidaito._

STORY CONTINUES BELOW

_Abubuwa da dama kan taba lafiyar dodon kunne har a rasashi ta hanyar hujewa;abubuwan su ne kwayoyin cuta (kamar sankarau) ko wasu magunguna, na nasara ne (kamar gentamicin) ko na gargajiya, ko kuma a hud'a shi ta hanyar susa da abu mai tsini, ko kuma ta hanyar fad'awa ruwa da karfi, ko buguwa ta hadai,ko ta yawan shan kara fiye da kima, ko ma abin ya faru tun a ciki, a haifi mutum haka ba ya ji.Akan iya yin dashen wani dodon kunnen idan bukatar hakan ta taso._ _Idan ruwa ya  shiga kunne, misali kamar a lokutan wanka, za a iya sa tsinke mai auduga a goge.Idan bai fita ba a bari bayan kamar kwana biyu zai tsane da kansa.Sai idan ba a ji ya tsane da kansa ba ne ya kamata a je asibiti._ _Masu aiki a kamfanin da suke da injina masu  kara ko filin tashin jirgin sama, dole su rika toshe kunnensu a kullum, domin kiyaye lafiyar dodon kunne.Irin wannan kara ma takan iya fasa dodon kunne.Masu aiki a irin wad'annan wurare yana da kyau su rik'a zuwa wurin likitocin kunne a kalla sau d'aya a shekara don kula da lafiyar kunnensu.Hak'k'insu ne su nemi kamfanin ya samar musu abin rufe kunne da kuma likitoci domin kula da lafiyar kunnensu.A kasashen da suka ci gaba, idan babu irin wannan a kamfanin,ma’aikata za su iya kai kamfani k'ara kotu don a tabbatar an samu yanayin aiki wanda ba zai taba lafiya ba._
_Wad'annan su ne hanyoyin da za su iya sa a kamu da ciwon kunne, dama wasu hanyoyin daban-daban.Ga hanyoyin kariya daga ciwukan kunnen;-A mafi yawan lokuta ba sai an fitar da dattin kunne ba, dattin da kansa yake fita.Wato kunne shi ke wanke dattinsa da kansa.Yakan wanko shi ya turo shi k'ofa kunne.Za a ga dattin launin ruwan kasa a nad'e a jikin wani abu mai dank'o.Idan har ta kama sai an cire wannan abu mai danko, to kada a yi amfani da abu mai tsini.A sa irin abin goge kunnen nan mai auduga a bakin kunnen a fito da shi a hankali._

_*KARIYA*_

_Wanke hannuwanka da na yaro.Shayar da yara da nonon uwa.Dena ba yara abincin kwalba lokacin suna kwance.Daina amfani da kayan susa.Daina shan taba a d'akin da k'ananan yara suke.Yiwa yaro rigakafi da yana rage wannan ciwon.Yin allurar rigakafin mura mai zafi (Fluvaccine) kowacce shekara.A k'arshe, idan yaro ya kamu da ciwon kunne:Kada ayi amfani da auduga a kunnen,domin zata iya k'ara girman k'wayar cutar.Kada a diga maganin kashe k'wayoyin cuta a kunnuwan yara, zai iya kawo fashewar kunne.Kada a share kunne da auduga domin kauda dank'o kunne."_

_Gaba d'aya suka saki ajiyar zuciya, Hajja ta dinga murmushi tana jinjinawa Hamza. Haka ma Mahmmad, a ransa yana ji ina ma Hamza zai yarda ya zama yaron shi saboda yana da burin bud'e shaguna a garin Biu dan hab'aka garin. Kasa hak'ura yayi sai da ya furta sossai Hajja taji dad'in k'udin d'anta. Hamza kuwa murmushi ya yi yace su bashi lokaci ya yi shawara da Bakura da Hajjansu. Sun amince da batunsa saboda yana da na gaba dashi. To nima bari in je in huta kafin in d'ora nagaji da yawa Lol.

_Washegari Hamza bai yi k'asa a guiwa ba, ya sanar da Hajja k'udirinsa. Hajja ta nuna masa rashin amincewarta ta nuna masa karatunsa yafi komai muhimmanci a gareshi. Bai jinkirta ba ya sanarwa da mahaifin Faanah shima baiga laifinsa ba saboda yasan muhimmancin karatun._

_Kwanci tashi kwanaki na shud'ewa, harzuwa lokacin babu jituwa tsakanin Bakura da Hamza. Hamza da Faanah sunyi wata irin shak'uwa sosai. Ranar da mahaifanta suka saka zasu koma Canada, Faanah ta dinga ihu tana kuka kan bazata bisu ba. Hankalinsu ya tashi sossai, a rayuwarsu basasan b'acin ranta saboda yarinya ce mara son hayaniyya duk da kassncewarta Kurma. Tilas suka hak'ura suka barwa Hajja ita da sharad'in zata koma in hutun Hamza ya k'are ya koma makaranta. Haka suka rabu suna ta jimamin rabuwa da juna.

_Ashe tafiyar ajali ce a ranar jirginsu ya samu accident (had'ari), babu wanda ya rasu a cikin su. Lokacin da labari ya samu Hajja fad'uwa tayi sumammiya lamarin daya haifar mata da cutar shanyewar b'arin jiki. Al'ammarin daya d'aga hankalin Hamza da Hajja Falmata Allah sarki Faanah kuka ma gagararta ya yi sai zubar hawaye.

_Kwananta goma a asibiti babu abinda take iya yi, kwata-kwata jikinta baya motsi.Hamza ya shiga faffutukar neman kud'in magani, abun yaci tura. Aikin yi ya gaggara kasancewar damuna tayi nisa, hakan yasa ya shiga mawuyacin hali saboda tausayin Faanah. Cikin ikon Allah ya samu aikin kwaso wani barkono daga wata gona zuwa gidan maigari. Yana kammalawa aka biyashi naira dubu goma, ya juya kud'in ya jinjina a ransa yana tunanin ko zasu isheshi hidimar kulawa da Hajja.Kwana uku yana tunanin lamarin, ya dauki kud'in ya dank'awa likita dan bata kulawar data dace. A haka yaci gaba da neman wani aikin, Hajja Falmata ita take kawo abinci kullum yayin da Faanah da Hamza ke jinya.Ranar kwana na sha hud'u ta amsa kiran mahallicinta. Haka rayuwar take (KULLU NAFSEEN ZA'IKATTUL MAUT),haka aka tattara Hajja zuwa gida akai mata sallah aka sadata da makwancinta na gaskiya. Ubangiji kasa mui kyakkyawan k'arshe amin.

STORY CONTINUES BELOW

Kacokan Hamza ya tattaro kayan Faanah zuwa gidansu, babu uwa babu uba babu kaka. Rayuwa ta yi mata k'unci Hamza da Hakka ne kad'ai take kallo taji dad'i a ranta. Hutu ya k'are Hamza babu kud'in komawa makaranta, duk yadda yaso abun ya gaggara ya tirza ya tirza abu ya gaggara, Hajja ce ta tunkari Bakura da batun, atabau yace bazai bayar ba shi yana so ne ya k'arasa had'a kud'insa ya siyi sissin gwal wanda zai kaiwa dangin Yakura na neman auranta. Sossai Hajja taji haushin abinda Bakura ya yi, amma bata nuna masa ba. Lamarin ya sha kansu sossai, Hamza ya shiga damuwa abokansa duk sun koma makaranta banda shi.
Ranar wata Asabar suna zaune jigum, Hamza yana yiwa Hajja bayanin aikin daya samu na gonar mak'ocinsu mahaifin su Alangubro. Faanah ce ta fito ta ratso tsakar gidan tana murmushi, wani abun hannu mai kauri ta ciro a hannunta guda hud'u ne ta bashi guda biyu, batai magana ba ta tamke fuska ta koma d'akin Hajja yasan ni sarai, koda ya kirata bazata juyoba. Cikin murmushi ya dubi Hajja yace"Hajja 'yarki rigimammiya ce, kwana uku kennan ina fama da'ita wai saina saida abun hannunta na koma makaranta. Hajja bawai siyarwa ne bana son yi ba, asalin abun hannun na mahaifiyarta ne kinga a yanzu Faanah bata da komai data samu daga mahaifanta inba awarwaron nan ba sai gidan Hajja." Ajiyar zuciya ta yi "lallai kayi gaskiya Hamza dad'ina da kai hankali amma tunda ta dage ka karb'a saika siyar da biyun ka ajiyemata biyun. Intaga babu su a hannunta gaba ai banga abunda zata ce a siyar ba".
"To! Shikenan Hajja", da haka suka kashe maganar. Cikin satin aka kai abun hannun kasuwa, abinda ya bashi mamaki dubu d'ari da hamsin aka siyi kowane d'aya, hakan yasa ya saida d'aya ya dawo da d'ayan ya karb'i biyun ya had'a ya ajiyemata. Dubu hamsin ya karb'a ya bawa Hajja dubu hamsin taimusu siyyayar kayan masarufi na dubu ashirin, dubu ashirin yace asiyawa Faanah kayan dangin turare da lafayya da mindil ai kuwa tayi murna sossai. Dubu hamsin ya ajiyeta zai yi noman gyad'a da barkono. A satin ya koma makaranta.

Tun komawarsa makaranta ya kasa sukuni, kwata-kwata tunanin Faanah ya hanashi walwala. Da farko ya d'auka sabo ne, turken wawa daga baya sai salon ya sauya. Lokuta da dama muryarta har gizo take yi masa a kunnuwansa. Lamarin ya d'aga masa hankali ya kan yawar tambayar kansa "ina ni ina soyyaya da kurma?" Amsar da take bashi wuyar samu a koda yaushe. Ba lallurarta yake gudu ba, yadda Hajja zata karb'i lamarin, zahirin gaskiya da farko tausayinta yake ji daga baya ya gama amincewa zuciyarsa san Faanah yake.

Kwanci tashi suka cinye samister d'aya, suna shirin fara jarrabawa kullum adu'arsa ubangiji yasa ya haye matakin karatunsa.
Faanah na samun kulawa dai-dai gwargwado wajan Hajja,tun bayar tafiyar Hamza ta fahimci kad'aici ya yi wa Faanah yawa, ana haka aka bud'e wajan koyon sak'ar hannu kusa da su. Batai wani jinkiri ba ta yankar mata form ta soma zuwa.

Tana jin dad'in zuwa sossai, nan da nan ta maida hankali akai ta soma yin safa da abun goge gumi.
Tun bayan komawar su Yakura gida, Yelfata ta kasa nutsuwa. Kwata-kwata zuciyarta na wajan Hamza ya burgeta matuk'a amma data tuna Faanah sai gabanta ya yanke ya fad'i ta tabbatar akwai wata alak'a irin ta zuciya tsakaninsu. Saboda yadda taga yana nuna mata kulawa a zahiri, da kuma yadda ya taso mata tamkar mayunwacin zakin da ya shekara be ci ba.
Zaune take tayi nisa cikin tunanin, Yakura ta jima a tsaye a kanta bata san tana kanta ba har saida ta d'an tab'ota. A jiyar zuciya ta saki tana dubanta"lafiya Yalfata, meya sameki ?"Hmmm! Babu komai Yakura". "Ke! Dakata ni zaki b'oyewa damuwarki?", tayi jigum tana tunani ta nisa tace "Yakura inason Hamza". Cikin tashin hankali ta zaro ido "awaana Bakura? ('Dan uwan Bakura). Kai ta d'aga mata tana jinjinawa. Yakura ta jinjina, ta sake jinjinawa taja fasali ta dubeta.

Kinsan dai bisa dukkan alamu wannan Kurman budurwar sace, dan haka ki sake dabara sai kace wata mara masoya". "Ni dai shi nake so Yakura wa nake dashi? Bayan duk sun gudu, kema ki hanzarta rik'e Bakuran da kike homa a kansa kafin ya sub'uce miki". Duka ta kai mata tare da cewa"ni zaki yiwa iskanci?". Da gudu tayi ciki, karaf sukai karo da Yalta k'anwar Kundum. A zafaffe ta kwad'awa Yelta marin daya gigitata har ta saki jakar islamiyarta, da sauri ta taro abarta saboda muhimman littatafan da suke ciki.

Bata tanka ba ta sa kai zuwa sashinsu, fuskarta tayi red'u-rud'u abinka da farar fata cikin kunar rai ta ajiye jakarta tana taya Mamansu aiki da take bakacan tsakin biski. Da kulawa ta dubeta"Yalta lafiya?" Share hawayanta tayi, tana yi mata bayanin abinda Yalfata tayi mata. Murmushi tayi ta jinjina kai, "karki sake ki kulata ko me zatai miki na gayamiki, share hawayanki komai lokacine. Fatan dai kinyi karatu sossai?". Tausayin mahaifiyarsu ya cikata, saboda tasan ko kara ta kaiwa mahaifinsu babu matakin d'auka Yagana itace mace mai kwalli a gidan.

Kwanci tashi aka soma gudanar da maganar bikin Yakura da Bakura, rawar jikin da Bakura yake har mamaki yake bawa Hajja. Ta dai tattara ta zuba masa ido,tayi juyin duniya yai al'adun mutan garin Biu a wajan bikin ya kaffe al'adun Kanuri zai yi lamarin daya haifar musu da sab'ani sossai. Gonarsu guda biyu yasa d'aya a kasuwa ya siyar duk sabo da hidimar bikin.
Cikin kwanciyar hankali Bakura ya soma neman auran Yakura.Hajja ta tattara ta zuba ido kan lamarin, kullum cikin yimasa adu'a take.

BIKIN KANURI
Al'adar Kanuri wajan gudanar da auransu, ya bambamta sossai da sauran mutane. Misali. Su dai a bikin bare-bari da farko idan kaga yarinya kana so, idan kuka shak'u kai da ita kuka aminta to zaka fad'awa iyayenka itama ta fad'awa nata iyayen akan cewa za'azo tambaya. To tambayar gidan mazane zasu sayi alewa da goro da minti da cingam, masu yawa da kuma kud'i karshe shi ne dubu ishirin ba'abada k'asa da haka sai sama. Akwai masu bada dubu hamsin, tamanin harma d'ari kawai dai-dai k'arfinka amma kar a gaza ashirin shi ne a talauce. Wannan bayani dana ke muku duk kayan nagani inasone shi ne su ke cewa tambaya.

Daganan kuma sai kayan toshi, shi kayan toshi yadda kukasan kayan aure haka ake had'asu wasu saitin akwati mai biyar wasu mai hud'u wasu mai uku. Harda masu dozin musamman fanin gidan sarauta. Za'azuba kayan duniya ciki k'awaye da 'yan uwa aita zuwa kallo. Idan an gama kallo kamar sati biyu sai a rabawa k'awaye da 'yan uwa rabin kayan kamarsu fant su mayuka su powder (hoda).Hada masu saka gwal da kujerar makka.Abin sai wanda ya gani, hakan al'ada ce wanda bai yi ba da wanda ba ayi wa ba ya zama abun tsegumi.Da wuya ma a kasa yi, tunda suna girma al'adunsu sai dai wata bata kai wata ba.
Fanin danginki uwa da uba kuma, akan basu turame mayafai ke kuma saiki d'inka sauran.Idan aka kwana biyu sai a shirya kayan sa rana.Aje a yanke rana amma basu fiye yanke ranar dayawa ba.Yayin da ya rage saura sati biyu biki zaki amso anko.Miji shi zai wa k'awayenki anko.Ko sun kai ashirin shi kuma zai bada kudin turare da gyaran jiki.Dakuma kudin shiga kasuwa na k'unshi  kuma duk ba kudi kadan ake bayarwa ba.

'Bangaran sadaki kuwa mafi yawa da sisin gwal suke biya, hakan al'adarsu ce.

Sossai Bakura ya yi hidimar auran Yakura, duk wata al'ada da ake yi sai da ya yi ta.Arzik'insa d'aya Yakura bata da k'awaye da yawa saboda masifarta.Haka ya zage ya yi hidima sossai, b'angaran gidan su daga dama ya bige ya yi sabon gini.'Daki biyu da babban fallo da kitchen   da band'aki sai yai doguwar katanga a kai musu tsakani da Hajja.Wajan yasha gyara da siminti, ya dasa fulawowi koraye wanda suka k'awata tsakar gida.
Tunda aka gama ginin kullum sai Fannah ta lek'a musamman in Bakura yana bawa shuka ruwa, a rayuwarta tana son koran ganye.Tun Bakura na korarta har sukai wani irin sabo, har gona take zuwa noman gona.Sossai Bakura ya dawo tausayin Fannah, masu irin lallurarta nasan kusancin 'yan'uwa yau ga Faanah babu uwa babu uba bale Hajja. Ana saura kwana bakwai bikin Bakura Hamza ya dawo, ya yi murna da yadda Bakura ya ware sashin su saboda baya son Yakura ta raina masa Hajjansa. Sai dai ya kad'u sossai da yadda Bakura yai musu, karan    tsaye wajan sai da gonarsu lamarin da har   sai da sukai musayar yawu kan batun.


Cikin ikon Allah aka soma gudanar da bikin Yakura,shagali ake sossai abin sai wanda ya gani.Yagana ta fito da amarya ras,sai k'amshi take tasha gwala-gwalai.+

Anyi biki an kare aka kai amarya d'akinta, masha Allah hada gararta turare kuwa ya yi b'ari kamar kamfani.Tunda aka kawo amarya tsayin kwana biyar, bata tako ta gaishe da Hajja ba.Sabo da zuwa yasa Fannah kullum tana sashin Yakura da wannan damar take galaza mata ta fannonni da dama.

Itace sata wankin kwanuka,girki hada wanki, lamarin na ciwa Hajja tuwo a kwarya,tayi-tayi ta hanata zuwa ta ki dainawa haka ma Hamza.

Kwanan amarya goma yaran gidansu sukai k'ungiya suka kawo mata ziyara.Sun barraraje suna shafta Fannah nata hidimar gida banda Yelfata da ta koma gefe tai tagumi zuciyarta taf damuwa,burinta kawai san ganin Hamza Yakura ce ta kula da yanayinta ta jata suka shiga d'aki.Suna shiga da sauri Yelta tai waje takamawa Faanah aiki,ita dai tana burgeta.

Dubanta Yakura tayi tace.
"Lafiyarki kuwa Yalfata?"ta fada tana dubanta.
"Lafiya ba lau ba Yakura zuciyata na neman fashewa kin sani sarai ina kaunar Hamza amma na lura hankalinsa kaf naga waccan kurmar".Tak'arasa maganar da alamun rauni.

"Mtsss! Kin cika abun haushi walahi Yalfata,du du nawa yaron yake da zai dameki muka bi da Bakura ma bale Hamza?".
"Hmmm!Yakura walahi na buga iya bugawata kafin in tunkareki gazawata yasa na fito miki da maitata fili.Gaskiya zan fito in gaya masa abinda yake raina kawai in huta".
"Shikenan ki gwada ki gani".

Kamar an jeho shi ya shigo sashin ransa a b'ace kwata-kwata ya manta da bata ji"Fannah!Fannah!!Fannah!!!".Hannu yasa ya fincikota daga dakin girkin,ganin yanayinsa yasa tai saurin hada hannuwa alamun ban hak'uri.Harara ya jefa mata da gudu tayi sashin Hajja tana numfarfashi.Da sauri suka fito gaba dayansu, ransa a bacce ya nunata da yatsa"Yakura ya soma isarki ban shiga sabgarki ba karki takuramun. Banda rashin imani me wannan baiwar Allah ta tsaremiki?Kurumta fa ba rashin 'yanci ba ne,kurumta ba rashin gata bane........"bai k'arasa ba ta tareshi a zafaffe.
"Har wani gata ne da mai nakasa irin wannan?" Ta fad'a tana nunata da baki,ta cigaba "Wacce ce ita?Wanne gata ne da'ita?Wadda ba'asan asalin nata ba kake hankoro a kanta?Banda kai din wazai kwasa?Kaima dan kana lallab'awa cikin dare ne kana lalubeta shiyasa meye bamu sani ba?Bonono kawai.......a dai bi sanu shi ramin k'arya k'urarre ne........"bata k'arasa ba ya zabga mata mari kyawawwa guda uku,daga bayansa a ga zabga masa.Cikin zafin rai ya juya ganin wanda sukai masa hukunci yasa jikinsa mugun sanyi. Bakura ne da Hajja,cikin fushi yake dubansa"matar tawa zaka mara?".

"Hamza meyasa kake da zafin zuciya?Hakan ba hallayarka bace".Cewar Hajja.Cike da fitsara Yakura tace"haka zaki ce mana,ai ba karya nayi ba tsohuwar banza ba d'akinki yake turata ba".Cikin zafin rai Hamza ya rarumi muciyar da Yelta take hada biski ya kwadawa Yakura a goshinta.Wani wawan ihu ta saki,Bakura yayi kansa cikin kid'ima. Tsawa Hajja tai masa ya juyo jikinsa na rawa "walahi Hajja sai na d’auki mataki bazan yadda ba".

"Zo ka rama a kaina".
Jin furucinta yasa jikinsa yin sanyi.
Sauke hannu ya yi yana huci,ransa in ya yi  dubu ya b'aci zuciyarsa taf k'unci ya ja Yakura suka shiga sashinsu tana ta kwarma ihu.Hajja ma taja Hamza suka koma nata sashin.Sun jima babu wanda ya tanka daga can Hamza ya dago idanunsa jajjur ya fesar da iska me zafi yace"Hajja ki amince min in auri Fannah".

Tai murmushi irin na manya zuciyarta k'war cike da tausayins"zaka auri Fannah Hamza,amma kaga yanzu akwai tarin abubuwan dake gabanka ka bari mubi komai a hankali".

"Shikenan zanyi yadda kike so",murmushi tayi nan ya dinga jan Fannah da hira rai banza ya had'a hannayansa alamun ban hak'uri ta juya kai.Saukowa ya yi ya sunkuya tare da kama kunansa,murmushi ta yi ta sauke hannuwan suka cigaba da hirarsu.A ransa tausayinta yake,kudin wajan Hajja ya karba ya wuce gona aka dan yin aikin daya dace.
STORY CONTINUES BELOW

'Bangaran Yakura da k'yar Bakura ya lallasheta tayi shiru,yana fita Yelfata ta turo baki "gaskiya Bakura kin cucceni yanzu Hamza zai kara tsanar ahalinmu".Cikin masifa ta tureta gefe"baki da mutunci Yelfata baki dubi iskancin da yai munba wato ke soyayya ko?".Yelta ta k'unshe dariyar da take cinta, banda Allah ya kara babu abinda take musu a ranta.
A ranar Hamza ya siyowa Faanah shukoki ya dasa a gidan Hajja,shikenan ta janyewa zuwa gidan Yakura.

Yelfata tayi gum da bakinta,koda wasa bata gayawa Yagana abinda ya faruba.Fanin sakarta abun ya girmama nan da nan tai suna a garin gata da k'wak'k'alwar fitar da kala-kalan saka.Har abun goyo take da abun rufe televission sossai Hamza ya ji dadi dakin soro da yake sauka in ya dawo ya kashe ya fito mata da kofa.Anayin girbin gauta nan ya zuba mata jari sossai,in ta saka set riga da wando da safa da zanin goyo na yara sai asaka  a leda.Nan da nan makarantun nursery suka soma bata aikin huluna da riguna.

Hankalin Yakura ya tashi bak'in ciki murarran duk lokacin da Hamza ya dawo hutu tare suke aikin.A haka ya gama karatunsa ya zauna jiran sakammako,saidai bai zauna zaman kashe wando ba noma ya dirafafa sossai.

Kwanci tashi result d'in  (sakammako) Hamza ya fito,babu jinkiri ya samu aiki wani asibi mai zaman kansa cikin garin Maiduguri.Hajja tayi murna sossai,haka ma Fannah da Bakura duk da babu jituwa tsakaninsu.Zaman Yakura da su Hajja abin sai wanda ya gani rashin mutunci take shimfidawa san ranta,babu wanda ya isa ya hana ta gama da Bakura sai abinda tace.

BAYAN SHEKARA BIYU.
Abubuwa da dama sun faru,ciki hada auran Yelta kanwar Yakura yar dakin su Kundum.Kwatsam sai ga bayyanar ciki a jikin Yakura babu wanda bai yi murna da hakan ba.Hajja tamkar ta goyata duk iskancin da take mata bata dubashi ba tausayinta take sossai saboda cikin me laulayi ne.
Yakura ta bijiro da san abata Fannah dan taimakawa wajan aiki,atabau Hamza ya nuna rashin amincewarsa a wata ziyara da ya kawo musu ranar hutun k'arshan mako.Har saida sukai hatsaniya da Bakura.Yakura tace ta hakura Yalfata zata d'auko,dama da gaya ta tayar da maganar Hamza yana nan dan tasan bazai amince ba saita bijiro da Yalfata don cimma burin su.
Hamza aiki yake sossai da gaskiya,gidan su na Maiduguri ya gyara ya zauna yana kulawa da Hajja da kanin kakansu sossai uwa uba Fannah.Duk wata yana zuwa dubasu ya kawo musu kayan arziki.Cikin    Yakura nada wata uku aka kawo Yalfata, adaidai lokacin Hamza ya bijiro da batun auran Fannah ya turo kanin kakansa ya nema masa auranta wajan Bakura.
An yi komai cikin mutuntawa,sai bayan an gama komai sannan Bakura ya ke bawa Yakura labari lokacin Yalfata ta kwashe biski tana hada miyarsa tsabar kaduwa batasan lokacin da ta saki tukunyar miyar ba ta kwaro a............. 

Cikin ikon Allah ya zuba a kasa bai taba kafaffunta ba.Bakura ya bita da kallon mamaki,bai tanka ba sai sanu da yayi mata Yakura kuwa takaici ya hanata magantuwa.Bakura ne ya fita saboda kiransa da aka yi a waje,tamkar jira Yalfata take ta dora hannu a ka ta saki kuka mai cin rai.Yakura tana kallonta sai da tayi mai isarta sannan ta tanka.
"Kitashi ki had'amana miyar kizo musamu mafita".
Bata jira cewarta ba ta shige d'aki,kwafa Yelfata tayi a ranta tana ayyana muguntar da zataiwa Fannah.Cikin mintuna shabiyar ta kammala komai,ta nufo wajanta ta dinga binta da kallo tamkar sabuwar makanta harta zauna.

"Hmm! Majanuniyar Hamza har kin gama?".
"Kome zaki kirani bai dameni ba,burina samun mafita ke nake sauraro".Cewar Yelfata.

"Hmmm!Sanin kanki ne baki da gurbi a zuciyar Hamza,saboda yasan wacece ke ta fanin hallaya duk da bai zauna dake ba yana ji ana fada.Dan haka samunsa zai miki wuya sossai.Mafi a'ala mubi kansa da Malamai.Saidai gaskiya zaki sha wuya Hamza yafi Bakura rikon addinni shiyasa kikaga nayi nasara kan Bakura farat daya".

"Nifa Yakura ba gane wannan batun naki nake ba.Mafita kawai nake nema,haka kawai kin tsaya yimun dogon sharhi babu fashin bak'i kawai ki fito kicemun ga mafita".

STORY CONTINUES BELOW

"Yelfata har yanzu ke yarinya ce,nafi ki son ki auri Hamza walahi sai yanzu nake takaicin auran Bakura Hamza namiji har namiji abin tunk'aho.Ki dubi yadda ya zama abin kallo".
"Hahhahaha!". Yelfata ta kwashe da wata shu'umar dariya,ta cigaba."Ke yanzu Yakura ko kunya baki ji ba gotai-gotai dake ki auri Hamza kinfa girmeshi kai alla sitiri buk'ui".

Duka ta kaimata a zafaffe ta kaucewa dukan tana gimtse dariyarta.Gimtse fuska tayi"kinga Yakura kibamu mafita mubar shirme dan Allah zuciyata zata fashe".

Rada tai mata a kunnuwanta suka kyalkkyale da dariya,tare da tafawa."Shawara mai kyau babbar yaya".Cewar Yalfata.

Ana kiran la'asar Yalfata tai wanka ta shirya cikin lafaya.Sky blue abinka da farar mace tayi kyau sossai.Hoda ta shafa ta kawo kwali ta tisa biy-biyunta tar ya fito ta hade gashin kanta ta saka barimar hanci blue dark.Sak Kanuri,wasu turarruka ta dinga bin jikinta dasu masu matukar kamshi kai Kanuri kunyi inji Sanah.Cas ta fito bayan ta yanne jikinta da lafayar.Tana fitowa Yakura tasa shewa "kai gaskiya dole ki rud'a Hamza autar Yagana".Murmushi tayi bata tankaba ta nufi hanyar fita zuciyarta na dukan uku-uku.

Kai tsaye hanyar shagon Fannah ta nufa,duk agama tasan yana can gabanta ya tsananta bugawa lokacin data nufi shagon.Zaune ta hangoshi cikin shigar manyan kaya kansa yasha hula yar Maiduguri gefansa Fannah ce sanye cikin lafaya 'yar ubansu mai tsadar.Zuciyarta tai zafi,bata raba d'ayan biyu Hamza ya yi mata ita.Takai idonta kan hannunta tasha warwarayenta guda uku masu tsada,cikin mutuwar jiki taji kamar ta koma tayi ta maza ta karasa.

Da salama ta shiga,dai-dai lokacin Hamza ya dago kai kallon da yai mata yasa gabanta tsananta bugawa........

*18*
Cikin sanyin jiki ta karasa ciki, muryarta a raunanne tace"Hamza wajanka nazo"ya d'ago yai mata diban karan mahaukaciya ya kauda kai can kuma ya gimtse fuska ya dubeta"lafiya?".
Haushi ya kasheta ta aro juriya "magana nake so muyi"gyara zamansa ya yi saboda yanayinta ya bashi tausayi sossai zatonsa ko wani ne babu lafiya ya numfasa yace"ke nake sauraro".Wani k'ududu ya tokare mata zuciya"a gaban wannan banzar zamui magana?"Ta fad'a a ranta, can ta saki murmushi"koda yake ai kurma ce duk a ranta tayi maganar.Karasawa tayi ta samu guri kusa dashi dab da dab ta zauna, cikin sauri ya muskuta yana duban fuskar Faanah da ta sauya yajayi da alamun damuwa tattare da ita.

"Ina saurarranki"ya furta fuska babu walwala, ta rausayar da kai gefe tai fari da idonta har yai ta maza ya d'auke kansa.
"Dr zakayi mamakin abinda yake tafe dani, amma ba abin mamaki bane in har zakaimun uzuri. Zuciyata ta dad'e tana k'aunarka,ganin babu mafitar da yafi sanar dakai yasa na yanke shawarar aikata hakan, ina fatan zakai maraba dani cikin zuciyarka".Galala yake kallonta,yaro da wayau harta dire batunta,tsabar takaici da mamaki kasa magana ya yi can ya nisa a ransa yana tunanin mai zaice mata. Murmushi ya yi ya dubeta.

"Gaskiya naji dadin kalamanki Yalfata, amma wani hanzari kiyi hakuri zahirin gaskiya kinsan an yi maganar aurena da Fannah. Kuma ko babu batun Fannah bazan iya auranki ba,saboda bakya cikin tsarin matan da nake burin aura ta kowane fanni".

Cikin zafin rai ta dubeshi"duk wani rashin tsarina har nakai wadda take da nakasa tare da'ita? Kurma fa Hamza, Kurma ce ta yaya zaka had'ani da'ita bayan tana da tawaya a rayuwarta? "Ransa yai mummunar b'acci a harzuk'e ya tashi"Yalfata Kurmar da kika raina ta fiyemin ke koran juji".
"Koran kuji? ".
Ta furta da alamun tambaya"Eh koran juji, mace kyakkyawa a gidan da babu tarbiya".Ya bata amsa kai tsaye ya cigaba."Fannah Kurma ce amma ta fiye mun ke sau dubun dubata, na tsaneki na tsani ahalinku masu tarin son zuciya kanku kad'ai kuka sani. Biyan buk'atunku kuke buri in kuka samu kowa ma ya rasa, inaso ki fita harkarta da ahalina as from today (daga yau).Ya fad'a da tsananin b'accin rai, cikin takaici ta dubeshi "walahi Hamza saina d'auki fansar abinda ka shukamun".Da gudu tabar wajan tana kuka, zama yayi yana numfarfashi zuciyarsa na zafi.
        Da kuka ta isa gida tana bawa Yakura labari, hankalinta ya tashi tasan dama za'a rina an saci zanin mahaukaciya zuciyarta tai zafi sossai da kyar ta lallashi Yalfata. Hamza cikin sauri ya hadawa Fannah kayanta yanai mata nuni da su tafi gida. K'yam ta tsaya ta kafeshi da ido tana tambayarsa dalili, bai boyemata abinda ya kawo Yalfataba saboda yana so tayi nisa dasu. Aikuwa ta shak'a hada kukanta nikaina naci dariya Kurma da kishi. Koda suka koma gida saida ya bawa Hajja labari, yana ta dariya abinsa, hankalin Hajja ya tashi dannewa kawai take zahirin gaskiya tana tsoron sharin Yakura da danginta.
STORY CONTINUES BELOW

'Bangaran Bakura abin ya girmama ko zuwa gaishe da Hajja sai ya gadama. Ahaka Hamza ya koma hutunsa, ransa fes cike da kewar Fannah tunda ya koma ya dirfafi aikinsa sossai, hata noman ya dora masu kulawa da fanninsa saboda Bakura gauta yake yi shikuma barkono.Lokaci zuwa lokaci yana aiko da kudin aiki. Tafiyar Hamza da sati biyu suka soma fuskantar wata gaggarumar matsala.Da farko duk sanda Fannah tai aiki ta gama a shago take barin kayanta, sai lamarin ya zamo mata barazana a gareta.

Da zarar tayi aikin ta gama in ta dawo gida, washegari zata iske an b'ale mukulin shagon an lallata kayan, haka in ta kwshe ta gyara wanshekare ma haka zata iske anyi. Tun tana boyewa Hajja harta kai ga furta mata abinda yake damunta, hanlakilta ya tashi, kafin cikar wata guda duk wani abu mai amfani na shagon an lallatashi kaf.Lamarin daya haifar musu da nakasu sossai, saboda kudin dasu suke hidimar gida kafin Hamza ya yo aike tunda Bakura baya ta tasu. Haka suka tattara suka rufe shagon,hakan ya haifarwa da Fannah kad'aici da damuwa Hajja na kokarin kauda hakan abun yaci tura. Wata sabuwa kuma duk lokacin da Fannah ta fita yara saita zame musu abar tsokana, da jifa suna kiranta kurma Yalfata kuwa yar gida take zuwa kamar abin arzik'i tacewa Hajja tazo taya Fannah hira, tun Hajja ja kaucewa hakan harta amince da wannan damar takewa Fannah kisan mimmik'e ta faki idon Hajja taita mintsinin Fannah.

Fannah babu baki sai dai in tagaji da azaba ta bar wajan ta shige daki.Hamza kuwa kulum hankalinsa yana gida,burinsa kawai yanzu auran Fannah kwatsam ranar wata Lahdi aka zo musu da batun zuwa garin Biu dan yin allurar rigafin kunne saboda kusantowar damuna.A ranar yaja abokinsa Alangoburo wanda shi gynean ne suka had'o kayan toshi akwati hud'u washegari suka nufi garin Biu.

Ranar littinin da safe tawagarsu sukaiwa garin tsinke, a masaukin ma'aika aka ajiyesu Hamza yaja Alanguburo suka nufi gidan Hajja. Hajja na zaune taji shigowar yara da kaya, ta mike tana tambayarsu shigowar Hamza yasa ta mik'e tana mamakin ganinsa ranar aiki.
Ranar littinin da safe tawagarsu sukaiwa garin tsinke, a masaukin ma'aika aka ajiyesu Hamza yaja Alanguburo suka nufi gidan Hajja. Hajja na zaune taji shigowar yara da kaya, ta mike tana tambayarsu shigowar Hamza yasa ta mik'e tana mamakin ganinsa ranar aiki.

Da murna ta tareshi aka shigar da kayan ciki,ta kawo musu ruwan sanyi dan saukar bak'i sun jima sossai baiga wucwar Fannah ba tun yana jiriya harya kai ga furtawa.
"Hajja ina Fannah? ".
Alangoburo ya yi dariya yana tsokanarsa.
"To majnunu Fannah"duka ya kai masa suna dariya. Nan da nan Hajja ta hau dube-dube "aikuwa shigowarku tana tsakar gida kodai tana fanin Yakura? ".

"Yakura? "
Ya fad'a fuskarsa a d'aure, bata bashi amsaba tai masa nuni da takalmanta da suke gaban k'ofar d'akinta. Bai tanka ba yaja hannun Alangoburo suka nufi d'akin, da sallama suka shiga das! Gabansa ya fad'i saboda hango yanayin da take ciki.

Cikin hanzari ya k'arasa ta d'ago kai suka ido gabansa ya tsananta fad'uwa.
Kuka take sossai,hada hawaye jikinsa yayi sanyi ya zauna kusa da ita tai saurin janyewa ta matsa ya kali Alanguburo ya kada kai.Cikin nutsuwa yai mata nunu da "menene? " kai ta kada masa alamun babu komai, kansa yai zafi sossai. A zafaffe ya bar dakin idonsa jajjir Alangubro ya rufa masa baya Hajja ya samu murya a tausashe "Hajja miya sami Fannah? ""Meka gani"?.Ta bashi amsa"kuka take"ya fad'a cike da raunin murya.
"Kuka?".
"Eh! Hajjah".
"Taf babban lamari", ta furta jiki a sanyaye take bashi labarin matsalar da suke fuskanta, kansa ya daure ya raunana muryansa"Hajja zanje in dawo ki lallasheta tayi fushi taki saurarona ina tsoron ubangiji ya kamani da alhakinta".
"Kaje Hamza zan ki da komai".
Kai ya kad'a suka nufi masaukinsu a hanya sukai kicibus da Bakura da murna ya taresu,sun jima suna magana nan yai masa batun auransa da Fannah harma da kayan toshin daya had'a yaji dadi sossai karshe ya gayyacesu cin abincin rana zuwa anjima sun ji dadi sossai Hamza ya dinga ayyana ansamu sassauci duk da baiga hakan a tare dasu Hajjah ba.

Da sallama suka wuce, koda isarsu kasa komai yayi, abokinsa ne ke tausarsa har yaji dama-dama.Karfe uku suka nufi gidansu sashin Hajja suka nufa, zuwa lokacin ansamu sasauci Fannah ta fito tana taya Hajja aiki. Da sallama suka shiga,Fannah ce tai musu shimfida ta kawo musu ruwan farau-farau.Hamza na kula da yanayin Fannah tun tana shan kamshi harta sake.
STORY CONTINUES BELOW

Anan Hajja take basu labarin matsalar Faanah, cikin takaici Hamza yace"yanzu Hajja aka rasa wanda zaibi mata kadin lamarin ina Bakura? "Murmushi kawai tayi tace"Yaro yaro ne".Babu wanda ya sake tankawa ciikinsu. Sunci abinci sossai suka zauna tattauna batun auran, Hajja ta dage Fannah nan zata zauna shi kuma Hamza ya dage Maiduguri k'arshe suka ajiye magana zata zauna anan saboda lallurarta Hamza bai soba dandai kawai kowa yaki bin bayansa har abokinsa da yayansa.Bakura abin nasa yayi sauki dama duk tsiyar asiri kwana arba'in ne balle ga jikin musulmi mummuni me bautar ubangiji.Sun ajiye maganar bikin zuwa wata d'aya, lokacin Hamza ya samu gidan dazai ajiyeta bayan sun gama ya zauna dala-dala yai mata bayani,sai da ta gama fahimtarta atabau ta nuna tafison ya gyara gidan Hajjanta su zauna a can, sossai Hajja taji dadin hakan dama hassashanta kenan dan dai kawai abinka da hakin maraya,gudun fadawa hakinta yanzu kuwa tunda ita ta amince Hajja ma ta goya mata baya. Hamza yaso kaucewa amma babu hali, Bakurama yaji dadin hakan.Dole aka kara bikin zuwa wata uku saboda yana son yaiwa gidan gyara sossai.
Tunda Bakura yajewa Yakura da batun zuwan cin abincin su Hamza take d'auki saboda ta samu damar iddar da nufinta.Sarai kan idonta aka wuce da akwatunan daya shigo dasu, zuciyarta ta tsinke sossai ta tabbatar auran Fannah na gab hakan na nufin kuncin kanwarta. Yalfata kuwa zazzabi me zafine ya rufeta, saboda takaici da bakin cikin abinda idanunta suka gani. A hakan ta daure ta shirya cikin lafayya green colour babu laifi tayi kyau tare da Yakura suka shirya abincin gidan sai kamshi yake.Shiru babu su babu dalilin su.
      Lamarin daya fusata su sossai,ana haka sukai baki dangin Babansu.Sun tare su babu yabo ba fallasa, nan Anwar abokin wasan su ne yai zumbur ya dauko jug na lemo ya kwankwad'a Yakura tana kai! Kai!! Kai!!!  Amma ina saida ya shanye tas yana leme baki dai-dai lokacin Yalfata ta fito ganin abinda ya auku yasata sakin giggitaciyar kara ta zube sumammiya.

Ruwan da Yakura ta watsa mata shi ya farfado da ita, kuka take tamkar ranta zai fita tana danasanin biyewa son zuciya yau gashi tayi asarar kud'inta wakan siyo soyyayar Hamza ta bige ga Ammar. Ammar dan kanwar mahaifinsu Yakura ne, suna zaune a can Askira inda danginsu suke matansa uku kuma kowace da yaranta bashi da kirki tsayayyan namijine a gidansa mace bata kawo masa wargi. Hata Yagana shakarsa take sossai, Yalfata ta saki ajiyar ajiyar zuciya bayan gama tuna waye  Ammar a gareta, fuuuu ta bar dakin sun jima suna hira da Yakura duk da rabin hirar umm da eh ne anan Ammar yake tambayarta dalilin suman Yalfata.Ta rasa karyar da zatai masa, can dabara ta fado mata tace masa haka take lokaci zuwa lokaci. Asiri gaskiyar me shi kafin su bar gidan Ammar ya soma nan da nan da Yalfata, Yakura ta tsorata matuka saboda ita ta amso maganin kuma bokan yai mata gargadi kan kaucewa aikata sharudansa dole wanda yaci maganin shi Yalfata zata aura.Tunda Yalfata ta shige daki take gursheken kukan nadama, a haka Yakura ta sameta tana hada kayanta riketa tayi cike da mamaki take dubanta.
"Lafiyarki ke kuwa? ".
Cikin kunar rai ta dago kai tana hawaye"gidanmu zani kinsan aikin bokanki ci yake kamar yankan wuka, kin riga kin cutar dani da zuciyata dole in yi nisa dake"wani giggitacan mari ta wanka mata.
"Ni zakiyi wa iskanci Yalfata daga taimako? Kinsan yadda nake ji a raina game da wannan al'amarin na fiki son ki auri Hamza saboda burina nasan kassara Fannah. Dalilin Fannah nazamo kaskantaciya a idon Hamza harya kai ga marina. Kinsani sarai hana yafiya auranki ba komai bane face fansa ga muradin raina. Kije gida zan san matakin d'auka dole in kauda Ammar a doron kasa mudin zai bani matsala".
"Kisa!?".
Ta furta a tsorace, "tabbas kuwa"cewar Yakura. "Babu ruwana Yakura walahi babu ruwana,son zuciyarki ya yi yawa ina nadamar biyemiki zanje in auri Ammar domin shi ne kaddarata. "Hmmm! Kije zaki dawomun da kafaffunki".
Bata tanka ba ta hada kayanta ta nufi gida, a kofar gidan su tai kicibus da Ammar da hanzari ya amshi kayanta jikinta yai sanyi tabbatar aikin Yakura saboda kwata-kwata Ammar bame sakin fuska bane.
Har ciki ya kaimata kayan, bambarakwai take duban lamarin namiji da suna Hajara. Mahaifiyarta tana tsaka da aiki taga shigowarta tare da Ammar ta dinga dubanta da kallon tuhuma sai dai babu wata k'ofa data bayar dan hango matsalarta kai tsaye sashinsu ta nufa ta rage kayan jikinta ta watsa ruwa taji sa'ida. Koda Yagana ta shigo, tsareta tayi da tambayar dalilin dawowarta amsar dayace babu komai. Kada kai tayi ta fice,tun daga lokacin ta koyi zaman dakai babu ruwanta da kowa. Cikin kwana uku maganin Yakura ya gama yiwa Ammar wani irin kamu, kai tsaye mahaifin Yalfata ya sanarwa kudirinsa sossai yaji dadin batun kasancewar kaf sa'aninta sunyi aure Yalta hada haihuwa ita kuma shiru.Ba jinkirtawa ya bashi auranta, lokacin da yajewa Yagana da batun tsalle tayi ta dire atabau bata aminceba, shi kuma yace yaga me musu da umarninsa saidai ta zaba auranta kona diyarta. Hankalinta ya tashi sossai, Yalfata kuwa ko musu batai ba,saboda tasan shukarsu suke girbewa nadamace cike da zuciyarta suna ji suna gani aka soma shirye shiryan biki watanni biyu masu suwa wanda yai dai-dai dana Faanah.

Kwanci tashi Yakura ta haihu lafiya, ta sami d'anta namiji kyakkyawa dashi ranar suna yaci sunan Muhammad.Hamza yafi kowa murna da wannan suna shi da Faanah saboda sunan mahaifinta ne hakan yasa suke kiransa Baana. Shi kenan sunan ya bishi,yaron ya taso da farin jinin jama'a Faanah duk irin hancin da Yakura take mata kan d'aukarsa bata gajiya Hajja taita yi mata fad'a.Faanah itace wankansa, kashinsa fitsarinsa nan da nan sukai sabo dashi ko'ina ya ganta ya wangale baki gashi da fara'a watansa shida aka tayar da maganar auran Faanah da Hamza haka Yalfata da Ammar gadan-gadan.

Sossai Hamza ya gyara gidan Hajja, babban falo da wajan girki da dakin bacci aka fitar sai bandaki da store sai wajan cin abinci Hamza ya k'awata gidan sossai da shukoki Faanah taji dadi sossai, ya zuba mata kayan d'aki masu kyau da matsakaicin kud'i ga labulaye da carfet masu kyau. Hajja tai hidimar turare sossai Bakurama ya yi rawar gani shiya biya sadaki da sissin gwal.Yalfata ma an yi hidima babu laifi duk da babu walwala tare da'ita aka gama biki aka d'auketa zuwa garin Askira zama cikin kishiyoyi.
   FATAN ALKHAIRI YALAMMAR.................

Faanah an sadata da gidan masoyinta, masha Allah zamansu gwanin ban sha'awa satin Hamza biyu Alngoburo ya yo masa waya yana yi masa tsiya tilas ya hada kayansa ya koma Maiduguri. Da kuka suka rabu da Faanah, Hajja tai ta lallashi.Kafin tafiyarsa ya gyara mata wajan sakarta ta koma aiki sossai, yanzu har Maiduguri ake kai mata. Kullum Faanah tana aikawa daukar Baana Yakura na hanawa, in taci arziki ne Hajja na kusa take yakana ta bata shi gorin haihuwa kuwa iri-iri kota kanta bata bi.
Bari mu waiwayi amarya Yalfata, zamanta babu laifi akwai kulawa saidai matsin kishiyoyi kishi suke na tashin hankali babu wadda ke ragawa wata.Ringid'i-ringid'i suna zaman dadi rana daya Ammar ya sauya mata lamarin da ya jawo kwantsamewarta duk ta yankwane ta fita hayyacinta. Abin babu kyan gani a haka Yakura ta kawo mata ziyara ta dinga masifa kan ta zauna ta koma borar gida........

BAYAN SHEKARA BIYAR.......
Abubuwa da dama sun faru, garin Biu sun samu cigaba an gina musu babban asibiti Hamza yana cikin wanda aka kawo garin. Yaji dadin hakan sossai koba komai ya samu kusanci da danginsa, hidima yake dasu sossai babu k'yashi abun hannunsa bai rufe masa ido ba ga sadaka da tausayin almajirai, duk ranar lahdi ya kan ware lokaci a gida yana duba masu matsalar kunne da basu shawarwari. Hakan yasa mutanan garin ke alfahari dashi suna kyautatta masa.Hakan na ciwa Yakura tuwo a kwarya,Baana ya girma sossai har an sashi makarantar boko da islamiyya yana primary three(aji uku)kullum yana tare da Faanah Abbagana yana yi masa lesson. Tunda ya girma yai wayau Abbagana yake kiran Hamza wato Abbagana na nufin Uncle.Hamza shi yake d'aukar nauyin komai nasa kama daga sutura makaranta da komai.Batun noman Hamza arziki ya habbaka ya bud'e wajan kiwon kifi ya dankawa Bakura.Hajja najin dadin yadda suka had'a kansu sossai yanzu bata da wata matsala.Kwatsam Allah ya bawa Faanah juna biyu, cikin nata ciki ne mai matukar sa laulayi sossai. Komai taci sai ta amayar dashi hakan ya tayar da hankalin Hamza da Hajja,Yakura kuwa ina wuta ta sasu mita take kullum sai kace kanta aka fara laulayi.Tun Bakura na yi mata shiru har ya kai ga tankawa ya yi mata tas  daga nan suka sami sa'ida.
    Cikin Faanah nada wata hud'u cif Yalfata tazo gida da ciki wata bakwai.Babu laifi ta dan ciko, zuwanta Yagana ta riketa tace bazata koma ba saita haihu an sha fama amma kiri kiri ta hanata komawa lamarin daya fusata Ammar ya saketa saki biyu.

Sakin ya girgizata amma lokacin da Yakura ta samu labari,wani dadine ya ziyarceta ko babu komai ta samu hanyar kuntatawa Faanah.

Tsaunuka ne masu tsananin santsi da hadari, ga kayoyi a haka take haurasu duk ta hada gumi. Kashirban hakan bai dameta ba burinta ta isa saman tsaunin,da kyar takai tana hucci tana komai kwatsam sai gata gaban wata karamar buka,zubinta kansa abun tsone zagaye take da kawunan kwarangwal na mutum.Ni kaina sai da suka tsoratani, wata giggitaciyar kara aka saki daga cikin bukar take ta tsorata tai taga-taga k'afarta ta hagu ta gice luuuuuuuu ta tafi k'asan tsaunin................


Caraf aka cafketa,tare da ajiyeta a kan tsaunin Yakura ta saki ajiyar zuciya, jikinta duk ya mutu zubewa tayi tana yi masa kirarin nasa na k'a'ida ta bud'e baki zatai magana ya katseta."Nasan abinda ke tafe dake, burinki kawar da facalarki".Kai kawai ta d'aga masa ya yi wata mahaukaciyar dariya"an gama mudin zaki bi sharad'aina mudin kikai kuskure kamar na farko kar ki tunkari inda nake"."Na amince Bokan Bokaye"ta furta da muryar tsoro, rufe idanunsa ya yi ya soma karanta wasu batuttuwa take wajan ya tirnik'e da wani kakkauran hayak'i Yakura ta soma tarin wahala. Wata gugguwa ta sake had'owa ta murtuke bukkar can hayakin ya soma hucewa haske ya bayyana,idanunta sunyi jajjur sai hawaye take. Wata kwatanniyace ta bayyana a gabansa cike da wani koran ruwa mai tsananin yauk'i da hammami a samanta wata cukuikkuyayyiyar leda ce yasa hannu ya d'aukota aikin sihiri ko danshin ruwan babu ajiki bale yauk'in.

Mik'a mata ya yi cikin sauri tasa hannu ta karb'a, jikinta sai rawa yake ta ciro kud'i kimanin dubu goma ta zube masa."Kije ki zuba mata ta sha ko ta ci, zata mutu babu mai gane abinda kika zuba ciki komai k'wak'war mutum".Cikin murna tace "na gode uban Bokaye","ku sauka da ita" aka fad'a da tsawa luuuu! taji an sauketa k'asan tsaunin da sauri ta zari takalminta ta d'auki hanya.

Kwanci tashi cikin Faanah ya shiga wata shida,a lokacin Hamza ya siyi mota suka kuma hada kudi suka kai Hajja saudiyya.Sai dai kwata-kwata hankalin Hamza da Hajja ya tashi ssboda kunburin da kafafunta suka yi. Kullum suna hanyar asbiti tare da bin shawarwarin likita kan bayanan da yai musu.Wasu lokutan Alangoburo ke zuwa hargida ya dubata a wasu shawarwari da ya basu kan cewar:

_"Ana so mai juna biyu ta guji aikata ayyukan da suke bukatar karfi maiyawa.Idan so samu ne mai juna biyu ta samu wanda zai rika taya ta aiki.Ana so mai juna biyu ta rika motsa jiki, hakan zai kara mata lafiya da kuma kuzari.Ya kamata mai juna biyu ta rika kwanciya da wuri, kuma an fi so ta kwanta a rigingine, yin hakan zai sanya jini ya rika zaga jikin jaririn da mai juna biyu take dauke da shi.Idan mai juna biyu tana son samun natsuwa da jin dadi a lokacin da take kwance,to ta sanya karamin matashi a tsakanin k'afafunta da kuma k'ark'ashin cikinta."_

Cikin ikon Allah kumburin ya yi sauk'i.Baana har kuka yake in yaga yadda take shan wahala, duk da k'aracin shekarunsa yana da tausayi sossai shi yake zuwa ya yiwa Faanah shara duk da dukan da yake sha wajan Yakura sai ya koma.Haka k'ananun ayyuka in yaga Hajja na yi shi yake k'ok'arin karb'a yayi Yakura takaicin duniya ya isheta ita dai a rayuwarta tana adawa da cigaban Faanah.Kwata-kwata yanzu tunaninta ya tafi kan yadda zata zubawa Faanah maganinta.Ta rasa mafita, duk lokacin da tayi yunk'urin hakan jikinta sanyi yake saboda ba sa ga miciji bale ta yaudareta.
BABIN 'KADDARA......
Ranar wata littinin da misalin k'arfe hud'u na yamma ciwo ya turnik'e Faanah, abin tausayi gidan babu kowa sai nishi da murk'ususu take ta juya ta sake juyawa babu mataimaki sai ubangijin bayi.Zaune yake a office haka nan gabansa ya tsananta fad'uwa,cikin sanyin jiki yaiwa Alangoburo sallama ya nufo gida yaso karantar yanayinsa dake ba mutum bane me bin k'wak'wafi sai ya share. Kai tsaye makaranta ya biya ya d'auko *Baana*yana kusantar gida gabansa na tsananta bugawa tukinma neman gaggararsa yake da k'yar yakai kansa gida yana parking Baana ya fito ya nufi shiga gidan.Murmushi ya yi yace.
"Baana ba zaka je ka fara kaiwa Hajja da Mamanka ladan ba?".Turo baki ya yi yace"k'yalesu Abbagana Hajjar nan cewa take wai ni ne mijinta, ko me zanyi da tsohuwa? Abbagana ai Hajja k'arama ce zata haifamun mata ko? ".Ya fad'a yana tsareshi da ido,dariya ya yi yace"hakane Baana".Da haka suka shiga gidan, shiru babu motsinta da sauri ya nufi babban falo bata ciki kai tsaye bed room ya nufa (d'akin baccin su) da hanzari ya shiga sakammakon nishin da yake jiyowa yana shiga das! Gabansa ya fad'i......
Cikin kaduwa ya karasa, gaba daya ta hada gumi
tamkar wadda aka zubawa ruwa a jikinta.Jikinsa
ya yi mugun sanyi, ganin ko ina na jikinta rawa
yake.Hannu yasa ya d'agota ta juyo das! K'irjinsa
ya buga ganin hak'oranta na sark'ewa da sauri
ya nufi kitchen (d'akin girki) ya d'auko cibi wato
cokali ya raba hak'oranta ya saka shi tsakanin
harshanta domin bata taimakon gaggawa saboda
yaga alamun tana gab da fara jijjiga.Ya juya
zashi gidan Hajja, carraf ta rik'o hannunsa ya
kasa motsawa.Murya a raunane yace"Please
Faanah ki sake ni in kira Hajja,asibiti zamu kaiki"
sakinsa tayi tana lumshe ido a guje ya kwasa sai
gidan Hajja.
Mintuna uku suka shude sai gashi tare da Hajja,
da taimakonta suka sata a mota cikin sauri suka
nufi asibiti.Da gudu *Baana* ya nufi gida yana
kuka, yana bawa Yakura labari hankadeshi ta yi
tana fatan Allah yasa Faanah ta mutu. Bakura
daya sawo kai gidan yace"ubangiji ya shiryeki
Yakura" hannun Baana ya kama sukai
waje.Barinta sukai tana ta sakin maganganu,
Bakura ya share masa hawayan suka tari abin
hawa zuwa asibitin.Kafin suje Hamza ya yiwa
Alangubro waye, suna zuwa aka karb'esu da
hanzari aka yi emergancy room (dakin taimakon
gaggawa)da Faanah. Gaba d'aya Hamza ya fita
hayyacinsa, Hajja da Yakura ke tausarsa.Ana
haka aka shigo da Yalfata zuwa dakin haihuwa,
nan Yagana suka hadu da Hajja sai jajjantawa
juna suke.Hamza ya kasa zaune bale tsaye,
shud'ewar rabin awa aka nemi ganin Yagana.
Bakinta har kunne Yalfata ta haihu,an samu
mace nan da nan ta cika da farin ciki.
Hajja adu'a kawai take can Dr Hannafi ya fito sai
gumi yake, ya nemi ganin Dr Hamza.Cikin
damuwa ya dubeshi"Dr i'am sorry to say (kayi
hak'uri da abinda zan ce) dole a yiwa Madam
CS".Jiki a sanyayye yasa hannu, Hajja kuka n
zuci kawai take Hamza kuwa kasa jurewa ya yi
saida ya yi kuka. Alangoburo ne yaja shi office
d'insa ya bashi ruwa ya yi alwala,a hankali ya
dinga yi masa nasiha tare da nuna masa komai
nufin Allah ne. Gab da za'a yi mata aikin ubangiji
ya bata ikon haihuwa da kanta sai dai ta jigatu
matuk'a.Tilas aka nemi jini aka k'ara mata,daga
nan akai d'akin hutu da'ita yarinyar kuwa akai
dakin adana yara da'ita kasancewarta bakwaini
'yar firit da ita a nan suka kuma had'uwa da
Yagana da Hajja kowannensu na yi wa kowa san
barka.
Hamza baki yak'i rufuwa,abokan aikinsa sai
tayashi murna suke yi.Kai tsaye ya yi wa Hajja
bayanin zai je gida ya d'aukowa Faanah kayanta
anan Yagana ta nemi alfarmar ya sanarwa
Yakura haihuwar Yalfata badan ransa ya soba ya
amshi sak'on.
Yana fitowa dakin sukai kici6us da Bakura, gaba
daya sukai dariya Bakura yace"angon k'arni"kai
ya sosa yana sunne shi k'asa Baana ya rik'o
hannunsa "Abbagana ina babynmu?"Dafa kansa
ya yi yace"karka damu zaka ganta".Murmushi ya
yi suka wuce gida baki daya, Bakura ne ya amshi
sakon sanar da Yakura haihuwar Yalfata Hamza
ya wuce kasuwa dan siyo kayan buk'ata.
Da murna Bakura ya sanar da ita haihuwar, babu yabo ba fallasa ta nuna murnarta da haihuwar.Lokacin da Hamza ya dawo nik'i-nik'i da kaya dangin cimar masu jego ya nufo asibitin a bakin k'ofa sauki kici6us da Yakura ta kalleshi ta watsar taja Baana suka nufi shiga b'angaran masu haihuwa.

STORY CONTINUES BELOW

Kar6e hannunsa ya yi ya nufi wajan Hamza"Abbagana muje naga jaririyar Hajja" bai tanka ba yaja hannunsa suka shiga takaici ya kume Yakura tai kwafa a ranta tace "Allah ya kai damo ga harawa"ni kuwa nace"kobai ci ba ya taka Yakura".Ciki suka shiga cikin mutuntawa ya risina ya gaida Yagana ya yi musu barka, tana tsokar Baana "ga matarka" ya turo bako "ni jaririyar Hajja ce matata"kai tsaye wajansu Faanah ya nufa ya iske Hajja na aikin lallashi saboda Faanah taga kowa da jaririyarsa banda ita.Cikin hikima ya dinga lallashinta da k'yar da sid'in goshi ta hak'ura, Yakura tazo taiwa Hajja barka ta koma wajan Yalfata. Cikin takaici tace "kun kira uban yar? "jinkina kai Yalfata tayi ta lumshe ido.
Tsayin kwanaki uku suna asibitin ba'a salami kowaccen su ba, kullum Yakura sai tayowa Yalfata girki sunzo tare da Baana ta kawo mata.Baana na yawan yi mata k'orafi me yasa bata yiwa Hajjansa sai tai masa banza ko ta dake shi. Bakurama ya yi iya yinsa ya zuba ido.

Talatainin dare kowa ya yi bacci, k'ur idonta biyu Yakura ta muskuta ta kali Bakura da yake baccinsa ta sauke ajiyar zuciya.Garin ya yi fayau saboda tasowar hadari,zuciyarta tai wasai ganin ta sami mafitar da ta dad'e tana nema da murmushi ta kwanta Alla-alla take gari ya waye.Washegari da safe da wuri Bakura ya fita saboda gonarsa,Baana yana zaune sai shige da ficenta take hankalinsa na kan karatunsa kasancewar an yi musu hutu yana bita da sun koma sai shiga primary four.K'arar hon d'in Hamza ya jiyo, da gudu ya nufi hanyar waje turus ya tsaya sakammakon kiran da Yakura tai masa cikin daurewa tace"ina zaka? "."Wajan Abbagana zamu ganin baby"ya fada a tsorace tunaninsa fada zatai masa sai yaga akasin hakan saboda lokuta da dama haka take masa.Murmushi tayi ta mika masa kwanon plastic mai kyau"gashi ka kaiwa Auntynka kace ina gaishe da Hajja" cikin hanzari ya karba ya yi gaba har ya kai soro ta gargadeshi in yaci sai ta yanke masa kunne. Yana fita tai shewa"Faanah sunanki matatta",da hanzarinsa ya karasa gurinsa yana shasshekar dariya "Abbagana muje in ga matata yau an budeta? "murmushi ya yi "da saura Baana".Turo baki ya yi yace "ni ni zan koma gida","pls yaron Hajja karka koma, mika rikowa Hajjan?".Dariya ya yi "na Aunty Yalfata ne da Hajjansu in ji Mamana".'Daukarsa ya yi suka tafi, suna zuwa ya kaiwa Yagana ya juyo wajan Faanah rigima yasa musu ina matarsa sai da aka kaishi ya gano ta.

Suna nan zaune Bakura ya shigo ya duba Yalfata da Faanah,daga nan ya wuce gida yana zuwa ya gayawa Bakura Hajjanta na gaisheta cike da mamaki take tambayar ina ya gansu shi ma da mamaki yace"asibiti naje dubasu yanzu Yalfata tace taga aike ta gode".Das! Gabanta ya fad'i cikin inda-inda tace"dama ba'a salamesu jiyan ba?".Cike da ginshira ya bata amsa"ga zahiri kin gani"take jikinta ya dauki rawa ta aro juriya ta yafa ta shige d'aki kawai bata tanka ba. Kafada Bakura ya zunkud'a ya koma gona ko ta kanta bai bi ba.Mintuna biyar da fitarsa ta suri lafaya ta nad'e jikinta cike da sassarfa ta dauki hanyar asibitin.Gudu-gudu sauri-sauri ta karasa tana shiga tai kici6us da Hamza ko kallonsa batai ba ta wuce.Tana shiga d'akin 'yan haihuwar karaf idonta ya gane mata abinda ya razana ta... ....
na bark

Hango Yalfata ta yi tana sid'e hannu alamun ta
gama cin abincin, guiwa a sanyaye ta ja jiki zuwa
cikin d'akin cikin zuciyarta ta furta"ta faru ta
k'are".A sanyaye ta zauna, Yagana ta dubeta"ke
kuma lafiyarki kin taho tamkar wadda aka
gayawa mutuwa? ".
Murmushin yak'e ta yi a ranta tana jin ciwo, ta
d'aga idanu ta kali Faanah sai walwalarta take yi
abinta.Bata jima ba ta mik'e taiwa Yagana
salama zuwa gida.Kamar mahaukaciyya haka ta
kama Baana da duka tai masa lillis, mak'ota ne
suka k'wace shi kowa ya tambayeta me yai mata
sai ta haushi da masifa haka suka tattara suka
k'yaleta a daran kasa runtsawa ta yi.Washegari
da sassafe ta tambayi Bakura zuwa asibiti, bai
hanata ba tana zuwa ta samu an salame su jiki a
mace ta nufi hanyar gidan su.Zuwanta ta samu
Ammar ya zo da kayan jaririya da sauran hidimu
nan ta samu labarin an rad'awa jaririya sunan
mahaifiyarsa wato Marwanahtu.Ta dinga yar
masa da maganganu san ranta, shi dai bai tanka
ba yai musu salama ya wuce. Yagana ta
dubeta"ke nifa bani da kud'i ya zamui da hidimar
suna? Kinsani sarai ba zan so in yi abin fad'a ba
Yakura ta numfasa tana tuna al'adarsu wajan
bikin suna sun bambanta da Babur mutan Biu da
kuma hausawa sossai.Su dai a tsarin su, idan
Mace ta haihu idan haihuwar fari ne a al'adar
bare-bari uwa ita take yin abincin suna wato
uwar 'ya.Idan hausawa ne kuma miji shi yake
yi,sai tallafawa da ba'a rasaba daga
dangi.Baburma haka suke, sai fannin sunan yaro
haihuwar farko mahaifin yaro shi ya ke za6ar
sunan yaro cikin danginsa yasa. na biyuma
haka.Na uku kuma mahaifiya ake bawa
zab'i.Ragon suna ranar suna ake yankawa a soya
a rabawa kowa,aci ana nishad'i da farin ciki.
Haihuwar fari Uwa za tayi kyan goyo,mai yawa
mijima zai yi sanan dangin miji zasuyi nasu
akwati guda kayan sossai abin dai sai wanda ya
gani.Ga abinci mai dad'i da sunasur da miyar
kub'ewa ake ci sai wani abu kamoniya shi kuma
da kayan ciki ake ci. Kamar source haka yake
suna yawan yinsa duk taron suna da shida da
basise.
Shi basise da madara ake yi da shinkafa da
mangyad'a ko man shanu.
*DAHUWAR BASISE*
Shi dai basise da farar shinkafa ake yinsa,
shinkafar tuwo idan kika d'ora ruwa ya tafasa sai
ki wanke kizuba kamar zaki yi tuwo.Idan ya dahu
sossai sai ki dama madara d'an kauri sai kizuba
da suga kituk'a yayi d'an ruwa-ruwa idan ya
sulala sai ki sauke sai kid'ansa mangyad'a ko
manshanu sai ci.
Ajiyar zuciya ta yi ta muskuta tace"Hajja su
Ammar sun fita kunya saura mu".Yagana ta
gyara zama tac"ai shi ne nake sanar miki"Yalfata
tai jigum tana jinsu hannunta kan cikinta ita
kad'ai tasan abinda take ji.Kud'i Yakura ta
zubewa Yagana"Hajja gasu nan dubu hamsin ne
kiyi amfani dasu kafin Bakura ya dawo zan je
unguwa".Ta washe baki ya gonar auduga"sai kin
dawo",har ta kai karshen k'ofa ta juyo sukai
kallon k'uda da Yalfata ta kad'a kai tai waje cike
da ginshira.
(((o(**************************)o)))
Tamkar wadda zata tashi sama haka ta nufi
dajin,cikin sauri-sauri take haye tsaunin har
gocewa take duk hannunta ya k'uk'uje saboda
wahalar data sha tana isa k'arshan tsaunin ta
haye tana muzurai.Cikin rawar murya ta soma
kirari,ga Bokanta.Fit! Yayo fitar burgu daga
saman tsaunin yana dariya sai ta zube ta sa
kuka mai cin rai.
"Na yi kuskure Bokan bokaye, kaimin agaji",dariya
ya yi ya buga k'afa k'ura ta tashi fuu! Yai kukan
kura ya yi kirari yace"dama na gaya miki babu
yadda zan gyara wanda ya ci shi zai mutu".'Bat
ya b'acewa ganinta, jikinta a matuk'ar galabai ce
ta rarrafa zuwa k'asan tsaunin hanya ta nufo
tana sak'e-sak'e a ranta tafiya mai nisa ta fito da
ita bakin titi daga nan ta wuce gida.
Tsayin kwana biyu gaba d'aya Yakura ta kasa
sukuni, har zuwa ranar suna komai a d'ararre
take yin sa sun sha suna an yi abubuwan bajinta
sossai dangin biski, sunasur da sauran su.Har
zuwa yamma Yalfata na walwala cikin jama'a
gab da magarba jikinta ya soma rikicewa.Iya
tashin hankali Yakura ta shiga, tana rik'e da
Yalfata wadda ke murk'ususu ta rik'e cikinta sai
hawayen wahala take gaba d'aya ta
galabaita.Yagana taiwa Yakura tsawa"ki tashi mu
kaita asibiti",jiki a sanyayye ta kamata suka wuce
asibiti da hanzari aka karb'eta tsayin lokaci
likitoci na iya k'ok'arin su a kanta an samu ciwon
ya lafa har ta samu bacci nan Yakura suka shiga
suka ganta.Daganan Yakura ta zauna wajanta,
Yagana ta juya gida d'auke da Marwahnatu a
bayanta dan kwantarwa da jama'a hankali.
Tafiyar Yagana da mintuna goma Yalfata ta farka
cikin matsananci ciwo, a guje Yakura ta fito
neman likita sukai kici6us da Hajja da Hamza
gefansu Faanah da Baana da alamu daga
b'angaran kula da bakwaini suka fito cikin
hanzari Hajja ta rik'o Yakura.
"Lafiya Yakura? "
Cikin kuka tace"Yalfata ce....." sai kuka ya
sik'eta gaba d'aya ta basu tausayi da sauri
Hamza ya kira mata likitan dake kula da Yalfata
suka rufawa d'akin baya a tare gaba d'ayan su.
Da sassarfa suka isa,suna shiga suka tsaya turus
sakammakon abinda idanunsu ya gane
musu.Yakura ta saki wata giggitaciyar k'ara sai
kuma lauu! Tayi k'asa a hanzarce Hajja ta
tarota,rinjayarta take gaban Hajja ya yanke ya
fadi a kidime tace.
"Hamza!".
Firgigit Yakura ta farka ganinta a kan gadon asibiti ya tsinka zuciyarta, jiki na rawa ta diro tana dube-dube cikin sauri ta bud'e k'ofar tai waje dai-dai lokacin aka turo gawar Yalfata Yagana na kuka Hajja na lallashinta.Yakura ta sunkuyar da kai hawaye taf idonta ni kaina taso bani tausayi amma dana tuna k'udirinta sai naji haushin kaina, dama ita mugunta fitsarin fako ce.
Hajja ce ta kamata suka wuce gida, dangi kowa ya yi jigum na alhinin mutuwar Yalfata nan da nan aka hadata zuwa gidanta na gaskiya, ubangiji yasa mui kyakkyawan karshe.Tsayin kwana uku ana karbar gaisuwa,daga nan aka nad'e shimfid'un zaman makoki.Yakura duk ta rame ta fita hayyacinta.Yakura ta so karb'ar Marwanahtu amma Yagana ta hanata kullum ana bata madarar shanu da wannan yarinyar ta samu kulawa.
Su Faanah masha Allah suna samun kulawa sossai,yarinya taci sunan Benazirahtu lokacin da Hajja tai masa k'orafi kan sunnan da ya saka hai jib'anci sunan wani cikin danginsa ba kawai murmushi ya yi yace"Hajja ina son sunan ne kawai"Kwanci tashi gashi har sun share wata d'aya a asibiti kasancewar batai k'wari ba saboda k'a'idar zamansu a kwalba wasu na sati biyu wasu har wata suke in dai basu yi k'wari ba.Sannan idan an dawo da su gida, ba'a fita dasu, suna nad'e cikin d'aki da rigar sanyi da bargo. Sai sun yi wata biyar kafin a fara fita da su,haka kuma ba'asan yawan jagwalggwala su. Abinci kuma abu mai gina jiki ake basu bayan nono daga wata shida.Dangin madara ta yara, frisco cream, custard da sauransu.
Har girman su ma zuwa 3 years(shekara uku) abinci mai gina jiki suke ci.

Bayan sallamarsu asibiti da sati biyu, Baana ya shiga primary five (aji biyar) sossai karatu yake baya wasa.Benazirahtu na samun kulawa sossai,Kwanci tashi zama ya mik'a Marwanahtu da Benazirahtu suka cika watanni takwas tubarkallah yaran b'ul-b'ul dasu baya Benazirahtu kunsan bakwaini inya samu kulawa bai iya girma ba.Shekarsu d'aya da rabi babu inda basa yawo, hakan yasa aka yayye su.Yakura ta d'auko Marwanahtu tun daga yayye tak'i maida ita Yagana ta hak'ura ta bammata.

Shekarunsu biyu Hamza ya samu k'arin matsayi, dai-dai lokacin Baana ya kammala makarantar primary tare da hadda izuf ashirin.Walima sossai aka had'amasa don taya murna,Yakura ta d'auki tsanar duniya ta d'orawa Benahzirahtu har bata iya kiran sunanta kai tsaye sai ta hada da inkiyar *'YAR KURMA* hakan na ciwa Baana tuwo a k'warya sossai tun yana kawaici harya kai ga yin magana,ai kuwa yasha duka ranar harda fasa baki.Suna shekaru uku aka saka su makarantar nursery su da Marwanahtu lokacin Baana yan form two (aji biyun makarantar gaba da primary).
Bakura yaso a saka Baana a bording school(makarantar kwana) amma Hamza ya dage kan bayasan ya samu nakasu a karatunsa na islamiyya gara yayi day school.

Benazirahtu ta taso da farin jini, gata kyakkyawa da ita akwai surutu da saurin dauke abu hatta saka da Faanah take a gabanta k'ok'arin gwadawa take yi fahimtar yawan surutunta yasa Hamza ya sata makaranta da wuri kuma kullum ya dawo aiki sai ya had'asu su duka ukun yai musu lesson.Baana yana sonta sossai, shi dai ransa na son mace mai saurin fahimar abu sai dai inda suka b'atawa akwai ta da tsokana ta inda suka sha bam-bam kenan. Bai cika son dukanta ba hakan yasa duk lokacin da tai masa laifi yake had'a yatsunsa ya murza su bada sauti alamun gargad'i.Benazirahtu kuwa ta d'auki wannan d'abi'a ta rik'e ram sai ma ya zamo abin tsokanarta.Duk inda ta ganshi sai tayi masa wannan inkiya, wani lokacin ya biyota da gudunta zata nufi wajan Hajja yana hucci Hajja zata tare shi tana fad'in"kai da matarka kuma Baana? ".Yakan zub'uri baki yace "Hajjanmu me zan yi da me majina kawai k'azama".Ai kuwa ihu take sawa tana birgima,Marwanatu na gefe tana dariya shi da ya yi laifin har sai ya dawo yana lallashi.Tana mik'ewa kuwa zata huce kan Marwahnatu.Da kuka take korata gida, duk duniya hakan yafi komai batawa Yakura rai sai dai tai ta masifa wani lokacin har rama mata take.Da farko Yakura tana barin Marwanatu taje lesson daga baya saita hanata.Babu yadda Baana bai yi ba kan tabarta amma tak'i,sai ya hak'ura ya tattara ya rabu da ita.Baana ya taso da tsanin son karatu boko da addini hakan yasa Hamza yake alfahari da shi tare da tsaya masa sossai kan hidimar karatu.

Shekarun su Benazirahtu biyar a duniya,Baana yana aji hudu na makaranta yana da shekaru goma sha hud'u zuwa lokacin ya mallaki haddar alk'ur'ani na izzuf arba'in Benazirahtu na da izzuf biyar Marwanahtu ce kwantan baya a shekarar suna aji uku-uku na primary.
Tun Benahzirahtu bata fahimci kalmar *'YAR KURMA* ba harta fahimta, idan Yakura ta gayamata sai tak'i amsawa ko tai gun-guni ta wuce abinta,sunan ya soma tasiri saboda yadda Yakura ta ingiza Marwanahtu take kiran Benahzirahtu da sunan.Bale wata kalma da Benahzirahtu take yiwa kallon iyayi ne kawai wanda Baana ya gadar dashi inda yake kiranta da sunan Benah kanwarsa kuwa Marwa.Ita nan duniya ta tsani sunan Marwah kuwa sossai take son nata sunan shi a fadarsa yai masa tsayi ita kuma tana adawa da Benazirahtu ya fi dad'i.
Sanin tsanar sunan yasa Marwa ta tsaya tsayin daka wajan bin hud'ubar Yakura, saboda ta tsani yadda Mallamai ke nan-nan da Benah ko speech za'ayi sunanta ne a farko.Sossai ta dage da kiranta sunan *Benah 'Yar Kurma*.


Sunan Benah 'yar kurma ya karad'e ko'ina,hakan yasa kullum Baana cikin rabon fad'a yake Hajja kanta abun ya dameta.Data ga babu sarki sai Allah, suna son haukata mata jika zaunar da ita tayi tai mata nasiha.Cikin muryar kuka tace"Hajja duk fa Hajjan su Marwah ce ta samun sunan"jin-jina kai kawai Hajja ta yi tana bata hak'uri.Iyakar kulawar data dace Faanah na bawa Benah,duk da tana matsayin kurma a hakan tare suke komai da 'yarta kama daga girki zuwa hidimar gida uwa uba sak'a Benah akwai fikra wani lokacin har mamakinta iyayanta suke yi saboda da kanta sata zauna ta fitar da (style) na sak'a mai kyau sab'anin irin na Faanah.+

Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji,Benah suka shiga aji hud'u Baana aji biyar.Kwatsam Benah ta kamu da wata irin rashin lafiya mai tsananin zafi, zazzab'i na rana d'aya bayan sun dawo makaranta kafin kafe kwabo ta soma suma.Sai kakkafewa take,hankalinsu ya tashi sossai a kid'ime Baana ya sureta sukai waje cikin ikon Allah ya samu abin hawa suka nufi asibiti.Jikinsa na rawa suka shiga, kai tsaye (office) d'in Dr Hamza ya nufa yana kiran sunanta.Kici6us sukai da Dr.Alanguburo cikin hanzari ya amsheta suka wuce (emergency) wajan taimakon gaggawa.
Likitoci sun duk'ufa a kanta har zuwa lokacin babu wani takaimaiman zance, iya kad'uwa ahalinta sun kad'u Hajja kuwa kuka kawai take Faanah ce ma mai dauriyar cikin su.An samu ta dawo hayyacinta, zuwan Dr,.Hamza likita ya ja shi office yana yi masa bayyanin sank'arau ne ya kamata,hankalinsa ya tashi sossai ya dinga kwantar masa da hankali.Sai da suka shafe sati biyu a asibiti sannan Benah ta samu lafiya.Sai dai me kowar su gida da kwana uku,suka fahimci kwata-kwata Benah bata ji in a kai mata magana sai an yi da k'arfi sossai sannan take ji.

Iya tashin hankali Hajja da Faanah da kuma Baana sun shiga, Bakura yai ta k'ok'arin kwantar musu da hankali Yakuwa kuwa shewa take tana k'arawa hada habaici wai dama ya za'ai kurma ta haifi abin kirki? tayo gadon hallita(genetic).Bakura ya fito ya nunawa Yakura b'acin ransa sossai,har ta kaisu ga sa'insa lamarin da ya jawo yai mata saki d'aya da k'yar Hamza ya je ya dawo da'ita.
Tsayin wata d'aya ana bawa Benah magani, sai dai babu wani canji hakan yasa Dr.Hamza ya yanke shawarar tunkarar Dr.Hannafi kan lamarin ranar yai nasarar samunsa a (office) bayan sun zauna ya mik'a masa hannu suka gaisa yace.

"Dr. Nazo ne kan matsalar Benah, har yanzu babu wani canji sai an yi magana da k'arfi take iya jin abinda aka furta.Ni shawarar dana yanke ko fita za'ayi da ita mugwada ko za'a dace?".

Dr. Hannafi ya numfasa"ban tari hanzarinka ba Dr. Matsayinka na likitan kunne ya kamata kai ho66asa a kai".Murmushi ya yi ya shafi kansa yace"tunanin hakan ya hanani sukuni, amma akwai maganin da zan d'orata akai insha Allahu za'a dace sossai kobata dawo dai-dai(normal) ba za asamu sauk'in rashin jin sossai.Kasan shi Sank'arau matsalarsa yana iya jawo abubuwa da dama".
"Kasan dake ba fannina bane ban san abinda yake haifarwa ba".Cewar Hannafi kenan yana murmushi.
"Eh! To hakane Dr. Amma yana da kyau kasan hakan dan bawa iyali kariyar data dace".
"Ok!  Amma fa ka kawo shawara, in babu damuwa yimin bayani yadda zan fahimta".

Murmushi ya sub'uce masa yace"Dr.Kenan nima saboda yana tab'o kunnene in ya yi tsanani shiya sa ya shigo fannin mu. Kamar yada kaji ana fad'a".

_"Ciwon sank'arau wani nau’in ciwo ne da k'wayoyin cuta ke mamaye mayafin da ke lullu6e k'wak'walwa da lakar wuya da gadon baya wato (meninges) a turance.Akwai nau’o’in ciwon sank'arau daban-daban wanda k'wayoyin cuta iri-iri ke kawowa.K'wayoyin cutar bacteria ne da ake kira (Neisseria meningitidis)ke kawo nau’in sank'arau d'in da muka fi sani.Su wad'annan k'wayoyin cuta suna nan a cikin iskar da muke shak'a mai zafi.Hasali ma kashi daya cikin biyar a cikinmu masu lafiya na dauke da wad'annan k'wayoyin a hancinmu da mak'ogwaronmu bamu sani ba.Ta haka ake yad'asu in anyi kaki an tofar ko kuma ta iska a wuri mai cinkoso.K'wayoyin cutar mutuwa suke da sun ji sanyi.Don haka da wuya ayi sank'arau lokacin sanyi.Idan aka shak'esu ta hanci k'wayoyin na samun shiga jiki har jini ya kwashesu ya kai mayafin kwakwalwa. Nan da nan alamomin cutar suke bayyana"._

STORY CONTINUES BELOW

Cikin murmushi Dr.Hannafi yace"to ya alamomin ciwon suke? ".Shi ma martanin murmushi ya yi ya cigaba.
_"Alamomin ciwon sank'arau yafi kama yara ‘yan shekara 5-10, amma a lokaci na annoba zai iya kama kowa.Alamomin ciwon sank'arau suna da yawa. Da farko dai akan ji ciwon kai mai tsanani.Zazza6i, sai sank'arewar wuya.Wasu lokutan kuma akwa amai rashin son ganin rana ko haske.Wasu kuma sukan suma tare,d'aukewar numfashi akai-akai wanda yakan sa a rasa mutum._
     _A tabbatar dakin barci na da tagogi bud'e a kalla biyu masu kallon juna. Idan taga daya ce abar kofa bude musamman idanmutane fiye da biyu ne a dak'in.A je cibiyoyin alluran riga kafi domin a karb'i allurar riga kafin ciwon sank'arau.Sai face majina inda ya dace ba a cikin mutane ba.Idan wani na kusa a gida ko wurin aiki ya kamu da ciwon to duk mutanen wurin ko da basu yi ciwon ba,su je su karb'i magani a asibiti.A yi saurin kai wanda ya kamu da wannan ciwon asibiti don gudun yad'a cutar ko ya galabaita.Cin abinci mai gina jiki da shan kayan itatuwa na marmari masu tsabta musamman ga yara don kara k'arfin garkuwar jiki masu iya kashe k'wayoyin cutar tun kafin su isa k'wak'walwa. Sank'arau yana haifar da d'aukewar ji na tsayin lokaci, ko kuma daukewar muryar mai ciwon ya zama ta shak'e matuka har ba'a iya jin sautin mai magana.Wannan kad'an kenan daga bayani kan sank'arau."_

Murmushi ya yi yace"sannu Dr.Ubangiji ya ba Benazirahtu lafiya"suka amsa da "amin" gaba d'ayan su. Kwanci tashi haka Benah take rayuwarta, Baana yana takaicin nakasar kunnanta sai dai in ya tuna haka ubangiji ya tsara mata sai dai ya yi mata kyakkyawan fata.Matsalar kunnanta yasa in akai karatu a makaranta bata samun fahimta sossai.Hakan ya ja ta soma fuskantar matsala a karatunta nan da nan ta tashi hankalinta sossai.Da kukanta ta samu Baana tana fad'amasa,sossai ya zauna yana lallashinta daga ranar kullum ya ta dawo makaranta yakan zauna ya duba aikin da akai musu ya k'ara yi mata bayani zuwa dare kuma Dr.Yana k'aramata.Nan da nan ta ware ta dawo (normal) dai-dai.

Kwanci tashi Baana ya kammala makarantarsa, result ya yi kyau lokacin su Benah na aji na shida a makaranta.Zaman wata biyar ya yi a gida a wannan zaman Dr.Ya dage sossai wajan koya masa kiwon kifi da noma,nan da nan ya maida hankali sossai cikin ikon Allah sakammakonsa ya yi kyau Dr. Ya nema masa addimission a b'angare biyu Kano da Maiduguri sai dai kash ba'a samu Maiduri ba sai Kano ya samu jami'ar B. U. K.

Bakura ya ji dad'in yadda d'an'uwansa yake kulawa da d'ansa hakama Hajja.'Bangara Yakura sai addu'a kwata-kwata ta tsani ganin Benah da Faanah har gobe tana da mummunan k'udirinta a kansu.Cikin ikon Allah Baana ya tafi Kano ranar Benah tasha kuka sossai da k'yar suka rabu,farkon zuwansa makaranta kewar 'yan uwansa ta dameshi daga baya ya ware sosai yake rayuwara.Lokaci zuwa lokaci yakan zo hutu in sun samu hutun makaranta, in yazo ya dinga nan nan da Benah wannan na hassala Yakura ta dinga fad'a tun Bakura na zuba ido yana kyaleta har ya soma tsawatar mata.Hajja tsufa yaja sossai,Benah kullum tana tare da'ita suna barkwanci tana koya mata al'ammuran rayuwa tana yiwa Hajja wanki da shara da sauransu.Marwanatu sarkin tsiwa,tayi d'are-d'are kan hud'ubsr Yakura duk inda suka je sai ta yiwa Benah gorin kurumta Benah sarkin rashin hak'uri ta kamata ta loda san ranta.Kullum suna hanyar kawowa Hajja k'ara sai an zauna sulhu amsar dai daya ce "cemin take 'yar kurma" dan haka ita Hajja take bawa rashin gaskiya,Dr.Ya kashe setroom na gidansa ya fitowa da Baana shi waje duk lokacin da yazo hutu nan yske sauka,Benah sarkin son tsafta duk sati saita bud'e ta gyara masa koda bai zo hutu ba, yanzu yana level two Beenah da Marwah na form one a secondary school.
AN DAWO LABARIN ......

Tsayin kwanaki biyu Baana yana jujjuya lamarin
Yakura cikin ransa, sai dai zuwa lokacin ya kasa
samawa kanta mafitar data dace ga Benah
kwata-kwata a kwanakin ta k'auracewa zuwa
gidan ko makarantar ma ta daina biyowa
Marwa.Kamar ko yaushe yana zaune kan dakali
yana duba wani lillafi kan couse d'insa,kamar
ance dubi nan ya daga idanunsa cikin nutsuwa
take tafiya.A hankali ya saki ajiyar zuciya, kwana
biyun da bai ganta ba duk ta rame kad'an cikin
nutsuwa ta gifta shi ko kallonsa batai ba ta shige
gidansu kai tsaye fanin Hajja (kakarsu) ta
nufa.Baana ya yi jim lamarin ya tsinka masa
zuciya, maida kai ya yi ya cigaba da abinda yake
sai dai kash! Zuciyarsa ta kasa karb'ar lamarin
rufe littafin ya yi tsam! Ya mik'e ya shiga gidan.
Turus ya tsaya ganinta tana yi wa Hajja wanki,
hakan yai matuk'ar birgeshi sossai k'arasawa ya
yi ya soma d'auraye wanda ta ajiye ko kallonsa
ba taiba har ta gama sab'awa ya d'auraye.Hajja
ce ta fito daga d'akinta, cikin murmushi tace.
"Sannu Benazirahtu 'yar albarka" cikin murmushi
Baana yace"wannan d'in Hajja?".
'Dagowa ta yi ta jefeshi da wani kallo,ta mugud'a
baki ya guntse dariyarsa yace"kinga zahiri ko
Hajjanmu"sakin tsintsiyar hannunta tayi ta ruga
d'akin Hajja da gudu tana kuka.Hajja ta kafe shi
da ido"Mai sunan manya me ya had'aku? " ya
shafi k'eyarsa yana murmushi ya sadda kai k'asa
yace"Hajja mu shiga ciki ki ji komai".Juyawa ta
yi bata tanka masa ba,a sanyayye ya rufa mata
baya.Suna shiga ya hango Benah tana gyaran
gadon Hajja, ya kad'a kai ya yi murmushi
yace"kayan rigima" bata juyo ba.Ya zauna a
hankali ya warwarewa Hajja komai,ta jin-jina kai
tai murmushi bata tanka ba ta ja fasali
tace"Allah ya kyauta".
Tana fad'in hakan ta bar d'akin, murmushi ya yi
ya kira sunanta ta d'ago ta kalleshi ba tare data
amsa ba.Yanayin kallonta ya tsinka masa
zuciya,ya kanne tare da danne abinda ke cin
zuciyarsa ya cigaba"Benah bakya kyautawa,
saboda abinda ya faru shi ne kike son yanke
zumunci ko?Kin kyauta kenan?".Idonta ya kawo
ruwa k'wal-k'wal ta sunkuyar da kai k'asa ta
share tausayinta ya ziyarci zuciyarsa cikin
bazata,muryarta na rawa tace"Yah Baana ba
yanke zumunci zan yi ba domin ba abune mai
kyau ba amma dole in yi nisa da kusantarku
Hajjan ku bata so ta tsaneni ta tsani Hajja
na.Kullum naje sai tamun gori Hajjana kurma
ce,ta kirani 'yar kurma bani na hallici kaina
ba.Ina duba kusancinmu daku ko dan Abbanku
shi yasa bana tankawa", ta had'iyi miyau ta
d'ago tai masa kallon cikin ido ta cigaba. "Bana
kawaici kan duk wanda ya tab'amun Hajja na
mahaifiyata ce ina sonta a duk yadda take zan
jura komai banda wulak'antata.Ba zan yanke
zumunci daku ba,domin babu kyau cikin addini.
_Daga Jubairu d'an Mud'im, yaji Manzon Allah
(s.a.w) yana cewa: "Mai yanke Zumunci bazai
shiga Aljannah ba._Kaga kuwa bazan so in shiga
cikin wad'anda baza su shiga aljanna ba".Cikin
murmushi Baana ya saki ajiyar zuciya,yana jin-
jina maganganun Benah zahiri yasan gaskiya ta
fad'a ko kad'an bai ji zafin ta ba ya dubeta yace.
" Benah kiyi hak'uri komai nada lokaci".
Murmushi ta yi tace"babu komai Yaya insha Allah
zan dinga kiyayyewa".Kamar an jehota ta fad'o
d'akin babu ko salama tana taunar cingum cikin
gatsali tace"Baana kazo in ji Hajja" a zafaffe ya
d'ago ransa na suya ya dubeta"ke mahaukaciya
ce? Zaki shigowa mutane babu salama yaka aka
koya miki?.Turo baki ta yi tana gunguni ai kuwa
ya shak'a ya kawo mata cafka da gudu ta yi
waje Benah ta kwashe da dariya"kana nuna
k'wanji kan mace?".Harara ya wurga mata ya yi
waje, ta gimtse dariyarta tare da lumshe ido.
Haka Baana ya kammala hutunsa ya koma
makaranta,cike da kewar 'yan uwa da iyaye.Cikin
ikon Allah karatu yake sossai, ya maida hankali
gefe d'aya kuma wani al'amari na mintsinar
zuciyarsa.

STORY CONTINUES BELOW

"Benazirahtu ya kamata ki hak'ura da sak'ar yau, tunda weak end ne mu zauna mui hira."Cewar Dr.Hamza,ta d'ago kai tana murmushi"Abbuna ina so ne in sak'a kayan yara, amma in kana so in zauna zan zauna mui hira".Cikin jin dad'i yace"Beenah wai me yasa kike son sak'a?".Tai jim alamun tunani,ta d'an b'ata fuska"Abbuna bana son Beenah, sarkin iyayi ne yake fad'a fa"."wakenan Benazirahtu? ".
"Yah Baana mana wai wani Benah ko Marwa.Dan kawai yaje Kano ya kama ya aro yaran wasu naga al'adarsu ma ta soma zame masa jiki shiyasa yanzu ba sossai muke shiri ba"."Ke Benazirahtu banda ke ai Beenah ma akwai dad'i, dan bakya so ne".
"Eh!  Abbuna bana so","to an daina yarinyar kirki".
"Yauwa Abbuna na ji dad'i, ina son sak'a ne saboda inason in zamo mai dogaro da kai a duk inda na kasance, saboda Hajja tana gayamun irin yadda dogaro da kai yake da muhimmanci cikin rayuwa musamman matasa. Abbuna akwai hadisan da suke nuna cewa musulmi ya kamata ya zama mai sana’a, babba ko k'arama ba tare da ya raina ba kuma ya guji zaman kashe wando da maula.
_Hadisi na farko a wannan b'angare;An tambayi manzon Allah a cikin arziki, wanne yafi. Sai yace:“Dukkan sana’ar da mutum yayi da hannunsa itace arziki kuma tafi kusa da zama halal (indai ba’a yi ha’inci a ciki ba).” (Imam Hakim ne ya rawaito.)Akwai hadisin Zubairu Ibn Awwam, Manzon Allah yace:“Dayanku ya dibi igiyoyi ya tafi daji ya yiwo itace ya d'oro a gadan bayansa, yazo ya sayar domin ya kare k'imar fuskarsa,wannan shi yafi alheri gare shi fiye da ya roki mutane, ko sun bashi ko basu bashi ba(Bukhari ya rawaito shi.)_
_An karb'o daga Ka’ab Ibn Ujurah yace:“Wata rana manzon Allah na tare da sahabbansa sai wani mutum yazo ya wuce, wanda a jikinsa akwai alamar karsashi da k'uruciya,sai sahabbai suka ce: ‘ina ma wannan yana fagen jihadi fisabilillah (Musulunci ya fa’idanta da kuzarinsa).Sai Annabi yace: “Fitowar nan da yayi daga gida,idan dai har ya fito ne domin neman abinda zai ciyar da kananan yara, to daidai yake da fisabilillahi.Haka kuma, idan ya fito ne domin ya nemo abinda zai ciyar da iyayensa guda biyu tsofaffi da suka gajiya, to daidai yake da yaki fisabiliilah.Haka kuma idan ya fito ne domin zai kare mutuncinsa daga rokon mutane, to dai-dai yake da yak'i fisabilillah."_
_(Dabarani ya rawaito)Saboda haka, dole ne mu dage wajen sana’a babba ko k'arama, tare da dagewa wajen ingantata,da bata muhimmanci,musamman ga mata mazauna cikin gida"._

Tak'arasa furucin tana murmushi, shi ma murmushin ya yi yana dubanta zuciyarsa k'war cike da farin cikin samun yarinya kamarta.
"Aikuwa Benazirahtu zan k'ara bud'add'amiki wajan daga yau, tunda manufarki kyakkyawa ce"."A'a Abbuna yara nake so wanda na girma kad'an in dinga koya musu suma su dogara da kawunansu a nan gaba".
"Amma fa kin kawo shawara d'iyar kirki, ni burina ina so ki karatu mai zurfi Benah"sunkuyar da kai ta yi bata tanka ba.Cikin ranta tana jin-jina k'udirin mahaifinta,mik'ewa ta yi ta d'auko jakar islamiyyarta tana murmushi"Abbu jiye mun haddata tunda yau ba fita".

Cikin zazzak'ar muryarta take rai-rairo karatun,mahaifinta yai tsai da ransa yana saurara harta dire.A hankali ya saki ajiyar zuciya harta k'arasa izzuf d'in suratul ankabut.Cikin jin dad'i tace "Abbuna saurana izzuf ashirin hadda" cikin sanyin murya a hankali yace"Allah yai miki albarka Benazirahtu"bakinsa kawai ta kalla ta gane abinda ya fad'a."Amin Abbuna".

Cikin wata d'aya Dr.Ya gyarawa Faanah da Benah shagonsu sossai, aka zuba kayan aiki tare da zare akaiwa shagon docoration.Gida-gida ya bi da kansa ya nemi yardar iyayyan yara tashin farko aka d'ibi d'alibai ashirin nan da nan aka soma gudanar da koyo ga matasan 'yan mata.Kafin sati sun iya dashin sak'a.
"Hajja nifa gaskiya na tsani ganin yadda Baana yake yiwa Benah, kamar bani ce tilashinsa ba sai yai ta yi mata abu bandani.Kuma kin san halin masifarsa yanzu ina yin magana,zai hauni da bala'i gashi gaba d'aya ya daina mun dariya wai bana son karatu."

"Ke!  Ni tashi ki bani waje sakarya, ai nagaya miki ki dinga yin abinda yake so kink'i ya zan miki?".Turo baki ta yi ta tashi fuu!  Tabar wajan, Yakura tai ajiyar zuciya"oh! Ni Yakura yadda Kurma ta zamemin bala'i haka 'yar kurma take neman zamemin masifa, gaskiya ba zai sab'u ba dole in d'auki mataki".Ta furta hakan a zahiri.
STORY CONTINUES BELOW

Cikin sauri aka d'auketa aka yi clinic da ita ko motsi k'wak'wara bata yi.Allah ya taimaka ta dawo hayyacinta,akai treat d'in goshinta inda ta fashe.Tambayar duniya an mata kan waya ji mata ciwo, babu amsa sai sharar hawaye take tana batasan waye ba haka aka hak'ura aka dawo da ita zuwa aji.Malam na fita ta jawo jakarta da niyyar copyn aikin da akai musu,kwatsam tai karo da abinda ya d'aga mata hankali tama manta da ciwon goshinta ta daddage ta k'wala k'ara ta fitar hankali hakan yai sanadiyar dagawar ciwonta.Ba komai yasata hakan ba face karo da tayi da littafin biology d'inta an yi gutsi-gutsi da shi.Gashi Uncle Tunde ya basu aiki yau zai karb'a hankalinta yai mummunan tashi.

Cikin muryar kuka ta dubi mak'ociyarta,nan da nan yan ajin suka baibayeta suna tambayar dalili.Ta kasa magana sai nuni take musu da hannu, Falmat ce ta finciki jakar ganin littafi gutsi-gutsi a kacaccale yasa tai saurin zazzage jakar tana fad'in "kungani".Gaba d'aya suka had'a baki"la! Garin ya Benah? ".Idonta ya yi k'wal da hawaye tace"nima bansani ba".Jikinsu ya yi sanyi sossai nan da nan sukai tai mata jajje tare da bata hak'uri Falmata ce taja hannuta suka je sukaiwa Uncle Tunde bayani dake akwai shi da fahimta bai ja ba yai mata lamuni. 'Yan ajinsu sunji dad'i sossai, nan da nan akasamu saban littafi wasu suka soma tayata kwafi.

Dole suka koma clinic aka sake gyara ciwonta.Ana tashi ta nufi gida tana tsananin ciwon kai.A k'ofar gida ta had'u da mahaifinta da Bakura gefansu Baanah ta saki ajiyar zuciya,cikin girmamawa ta risina tana gaishesu da kulawa Bakura yace."Benah ciwo kika ji? "Eh Abbu ciwo na ji".Ta fad'a tana sharar k'wala,"garin ya Sis Benah kukan kuma na menene? ".Muryar Baana ta daki dodon kunnanta, cikin amo a hankali ta kaleshi suka had'a ido yarrr!  Tsigar jikinsa ta zuba ya kauda kai yana jadadda tambayarsa"faduwa na  yi".Bata sake magana ba ta shige gida, ya kad'a kai kawai take ya gimtse fuska sakammakon hango Marwa ta jero gefanta namiji tsakiya ita daya gefan namiji ganin su yasa jikinta ya d'auki rawa tai saurin sallamar su ta nufi gida.

"Ke! Marwa zo nan" y fad'a da sautin murya,jiki na rawa ta sunkuya ta gaida su Dr. Tana kame-kame "daga ina kike? Su waye wad'anan da kuka jero tare?"."Yaya da... ga da.... ga makaranta nake, 'yan ajinmu ne" kyakkyawan mari ya wanka mata "baki da kunya baki da mutunci ko Marwa ni kike kallo kice wa 'yan ajinku ne? ".Dr ne ya kamo shi ya dubi Marwa" baki kyauta ba Marwa wannan ba tarbiya bace, haka kika ga 'yar uwarki nayi? Kar in sake gani".Kai ta daga ya sallameta ta wuce gida tana k'un-kuni.Ya juyo kan Baana "na dawo gareka na fahimci kana da zafin zufiya Baana, ka dinga bin komai a hankali mace ce ba'a nuna kwanji a kanta ka ji ko.Sannan ka dinga sanyayya zuciyarka akwai abubbuwan da basu canccanci daukar zafi ba.
_Kamar yadda yazo a hadisi daga Manzon Allah yace.“A cikin jiki akwai wata tsoka idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan tab'aci dukkan jiki yab'aci,wannan itace zuciya.”Wannan hadisi ya nuna mana idan zuciya ta gyaru wato ta tsarkaka,dukkan sauran gururruwa na jiki misali harshe,ido,kunne da dai sauran su suma zasu gyaru wato zasu tsarkaka._

_Zuciya ma’anarta shi ne jujjuyawa, anace mata haka saboda jujjuyawar ta a tunani,amma a isdilahance tana da ma’anoni guda biyu tana da ma’ana ta zahiri wato jis-miy,da kuma ma’ana ta bad'ini wato ma’anawiy.To ma’anar ta ta bad'ini shi ne Malaman Irfan suke bayani akai,shi kuma ma’anar ta zahiri shi ne likitoci suke bayani da kuma kula dashi,tun da ya shafi bangaren gangar jiki ne.Saboda haka idan mutum yaga ambaton zuciya anan,ba ana nufin ma’anar ta ta zahiri ba wato tsoka wanda aka sani tana jikin dan Adam,a bangaren jikin sa na hagu,wato a kirjinsa.A’a ana nufin ma’anarta ta badini,wanda akan wannan asasi ta ma’anarta ta bad'ini zuciya itace mahallin imani,tsoron Allah,son Allah,da dai sauran matakai suluki zuwa ga Allah kuma a irin wannan ma’anar ta badini ake nufin inta gyaru dukkan jiki ya gyaru,inta bacci dukkan jiki ya baci._

Dan haka sai kayi da gaske wajan yakarta,kan aikata alkhairi da sabaninsa".
"Na gode Abbagana" sallama yai musu ya nufi cikin gida dan gaida Hajjansu.Yana shiga ya tsaya cak sakammakon abinda kunnuwansa ya jiye masa.

STORY CONTINUES BELOW

Karaf kunnuwansa suka jiyo masa sautin muryar Marwa"walahi Hajja ta baya na bugata ta doku, shegiya ni so nayi kunnuwan su k'arasa d'aukewa.Sannan na yaga littafin da take matuk'ar so, ai walahi shswararki ce abin bi kisan mummuk'e zan dinga yi mata saina nakasa nakassashiya".Hajja ta saki dariyar jin radad'i, tare da dafa kafad'un Marwa ta cigaba"lallai Marwa kece makami mai linzami dazai zamo abin tunk'ahona a da na d'auka cewa burina na wargaza Faanah bazai cika ba tunda mahaifiyarki ta kasa cika shi sanadin hakan na rasa ki yau na tabbatar ba haka hane.Yanzu ne salon wasan zai soma".Cikin alamun mamaki Marwa ta dubeta, "bangane ba Hajja?"."Zaki gane Marwa yau zan bayyana miki abinda baki sani ba, zaki k'ara rik'e makaminki wajan yak'ar Benah".A hankali ta labarta mata asalin wacce ce ita, tun daga farko har k'arshe.

Kansa ya sara ya dafe kan, duniyar ta soma juya masa ya shirya tsaf ji yake kamar yau za'a tashi duniyar zuciysrsa ta tsinke yaja jiki yana mirgina kai tamkar marayan zaki.Kai tsaye sashin Hajjansu ya nufa, anan ya riski Benah tana taya Hajja had'a biskin gero idonsa jajjur yai salam karaf suka had'a ido k'ur suna kallon juna wani abu ya daki zuk'atansu Baana yau ya kasa d'auke ido a kanta ya lumshe ido gashin idonsa gazar-gazar suka rufe ruf har suna tabo saman idonsa tar ya budesu a kan fuskarta.Tai saurin dauke ido"awaana me ya sameka?" tai furucin da ci da zuci."Benah d'auko mindil d'inki muje asibiti a duba ciwonki" dafe kan ta yi saboda sarawa da ya yi Hajja tai murmushi tace.
"Ai bata ji Benah nan da kake ganinta, tunda ta shigo nake fama taje Abbunta ya kaita asibiti tak'i".Turo baki tayi"kinji ki kakus dake wai Benah,bakinki ya yi sabo da kuka ki bari masu oral English sui iyayin da suka saba".Baana ya kwashe da dariya "yes my unique ga yawa Kakus ta tsufa".Dariya ta yi had'i da cewa"shakiyai ku barmun gidana".Da gudunsu suka fita suna dariya, kai tsaye Baana motar Dr ya karb'a ya d'auki Benah suka nufi *BIU SPECIALIST HOSPITAL*.Dake suna da fayal babu jinkirtawa aka karb'eta, an mata dressing wajan sauranta allura nan take idonta yai k'wal zatai kuka tillas akai kiran Baana.

Cikin tausayawa ya dubeta, "my unique ki tsaya mana" a shagwab'e tace "Yah Baana bana son alura zafi walahi" ya rasa yadda zai mata dabara ta fad'omasa yace "Benah kali can".

Tana juyawa yai saurin kama hannayanta yaiwa Dr inkiya cikin sauri yai mata allurar, ta saki k'ara tare da kwanciya a jikinsa yar!  Tsigar jikinsa ta zuba tare da wani shock a hankali ya sauke wata sasanyar ajiyar zuciya kukanta yadinga taba mashi zuciya. Dagewa ya yi yana lallashinta har tai shiru ya karbi magungunan da alluran yace shi zai dinga yi mata ko Dr haka suka fito asibitin yana ta aikin lallashi.

A mota rafe suke tamkar kurame, babu wanda ke tankawa kowa da abinda yake sakawa cikin ransa, ta nufasa tace.

"Yah Baana kai da ka sauya couse kake cewa zakai mun allura Abbuna dai zai mun".

"Hmmm!  Walahi Beenah bada son raina na sauya ba nafison in zama kamar Abbagana dan dai Abbagana yace karmutare wajan abu d'aya ne, na amshi zama barrister amma kefa?".

Yai tambayar yana tsareta da idanu,kanta a k'asa tana wasa da farcanta tace"Yah Baana nifa nafison kammala hadata saura izzuf biyar, sannan inaso in taimakawa 'yan uwana mata matasa domin su dogara da kansu. Amma inason in karanci gynea ganin kamar Hajja bazata amince ba,shiyasa da Abbu yai min maganar ban bada goyon baya ba amma inaso in yi zurfin karatu kodan 'yan uwana mata.Shi yasa na fara da koyawa matasa kamata sak'ar hannu".

Tunda ta soma magana yake kallon bakinta d'an k'arami kowa ne harafi cike da nutsuwa take furta shi harta dasa aya.Yayi murmushi.

"Beenah zaki karatu insha Allahu, karki damu duk burikanki zasu cika mudin ina raye, fatana ki tsaya wajan kyautatta karatunki babu ruwanki da shasshashun abokai bale samari".

"Insha Allah Yayana" a haka suka karaso gida yana janta da fira gab da zasu shiga gida sukai kici6us da Marwa wani mugun kallo ya watsa mata Beenah ta kallesu  ta murda yatsu murmushi ya yi ya jinjina kai sukai sallama.
Ya dubi Marwa "ki sameni a daki" bai jira cewarta ba ya wuce sitroom dinsa na gidansu Beenah ta kofar ciki ya bata umarnin ta kawo masa abun sha.

STORY CONTINUES BELOW

Kanta a k'asa tana juye-juye ya dubeta zuciyarsa kamar ta fashe, ya hadiyi wani kakkauran miyau tamkar makogwaransa zai yake ya kalleta. "Yanzu Marwa kin kyauta kenan? Cikin mamaki tace"menayi kuma Baana? Ya shak'a sauka kad'an ya kaimata duka.
"Rainamun hankali zakiyi!?" Tuni tayi saranda tana rarrabe tsakanin k'arya da gaskiya zuciyarta ta shiga rud'u ina yaji labarin nan?  Ko dai Beenah ce ta fada'?  Kai ba Beenah bace ita kanta batasan waye ba. To kodai yaji hirarmu d'as!  Gabanta ya fad'i ta numfasa tare da jan ajiyar zuciya."Nifa gaskiya ba Beenah bace, kadai namun iko irin naka walahi ba yadda zan yiba wana munafikin ne yace nice? Ko ita nakassashiyar ce ta tad'a?" Wani kyakkyawan mari ya zabgamata dai-dai lokacin Beenah ta shigo da hanzari ta ajiye ruwan duk da bata ji abinda suke tattaunawa ba jikinta ya bata Marwah ce bata da gaskiya tana rik'e da hannunsa tace"a kullum ina tunasar dakai kadaina nuna k'wanji a kan mace domin ita d'in mai rauni ce karka dinga biyewa zuciya wajan tunzuraka harta kaika ga yanke bahagon hukunci.

Ta sassauta murya tana dubansa tace.
_"Haba Yah Baana Musulunci bai yarda a muzgunawa ‘ya mace ba ta kowane irin hali.Mata wasu halittu ne na dabam, wadanda suka zama dole a girmama su.Addinin musulunci bai yarda a nuna bambanci a sha’anin da ya shafi ‘ya mace ba._
_Annabi Muhammadu (Tsira ya tabbata gareshi) ya fad'a mana cewa: Mata kamar k'asusuwan hak'ark'ari suke, idan har ka yi k'ok'arin lank'wasar da su da yawa, sai su karye, idan kuma ka bar su, su malkwade.Ya zama dole ka dai-daita tsakani wajen kula da mata.Zafaffawarka bashi zaisa fa ta bi umarnin ka ba musamman a wannan tsakanin shekarun tana ganin takai kabi komai a hankali zaifi alfanu._

Sakin hannunsa tayi tana murmushin da ya kara mata kyau, jiki a sanyaye ya zauna yana dubansu su duka Beenah ta zauna ya dubu Marwa "ke bazaki zauna ba ne?" Zama tai tana gun-guni takaicinta zuwan Beenah wajan ta faki idonsa ta zabgamata harara d'auke idonta tayi kamar bata gani ba ya numfasa yana dubansu.

"Naji dad'in tunatarwarki Beenah harga Allah bani da burin wulak'anta dan Adam musulmi balle Mace da nakewa duban kashin bayan al'ummah.Amma Marwa ki sani abinda kikai kwata-kwata baki kyauta ba domin dai kisan cewa.
_'Dan Adam shi ne mafi d'aukakar halittar Allah Ta'ala.Ubangiji subahanahu wataala ya kimsa masa hankali da tunani, ya kuma sanar da wannan zab'ab'b'en halitta tasa kyawawan sunayensa wato asmaul husna.Shima d'an Adam d'in wata babbar aya ce daga cikin ayoyin Allah. Alkur'ani mai girma yana cewa:"Kuma Allah ya sanar d'an Adamu dukkanin sunaye sannan ya kawo su gaban mala'iku yace: 'Ku ba Ni labarin sunayen wad'annan abubuwa in kun kasance masu gaskiya' " Suratul Bakara : aya ta 31Allah ya ba wa mutum daukaka tunda ya halicce shi cikin mafi kyan sura, kana ya hura masa ruhi daga gare shi.Allah subhanahu wa taala yana cewa: "Hak'ik'a mun halicci mutum cikin kyakkyawar halitta."Dad'in dad'awa, Ubangiji ya nad'a mutum a matsayin khalifansa a bayan k'asa.Duk bawan da zaki gani a doron k'asa akwai hikimar ubangiji na hallitarsa ba wai dan baya sansa bane a'a ikonsa ne ya nuna._
_Wad'annan darajoji da Allah ya bawa d'an Adam suna nuna irin matsayi da d"aukaka da Allah ya yi masa.Bisa la'akari da wannan matsayi d'an Adam yana iya kama hanyar aikin k'warai da kamala. Amma idan ya fand'are ya k'i amfani da hankali da daraja da kuma zab'in da Allah ya yi masa, yana iya tab'ewa ya fad'a cikin k'ask'anci.Saboda haka wajibi ne d'an Adam yayi iya k'ok'arinsa domin kaiwa ga k'ololuwar daraja, wacce ta dace da muk'amin Khalifan Allah a doron k'asa, ta yadda duniya zata tsarkaka ta yi kawa.Sai dai cimma wannan zai yiwu ne kawai idan dan Adam d'in ya san hak'k'okinsa da buk'atunsa, sannan ya zage damtse domin kaiwa ga rayuwa ta kamala da sa'ada da kuma kwanciyar hankali.Samun wadannan kuwa yana dogara ne ga yin hob'b'asa da aiki tuk'uru kamar yadda sak'on Ubangiji na k'arshe, wato Alkur'ani mai girma yake cewa: "Ko kuna tsammani cewa Mun halicce ku ne da wasa, kuma ba zaa dawo da ku gare mu ba?".Suratul Mumina, aya ta115.'Daya daga sifofin d'an Adam shi ne yana iya sarrafa mazauninsa wato wannan duniya, ya kawo sauye-sauye cikinta, sab'anin sauran halittu.Wannan sarrafawa ta dogara ne da nau'in tunani da tsare-tsaren da mutum yake sakawa a cikin zuciyarsa.Idan zuciyarsa mai tsarki ce, kuma an zayyana ta da dan Adamtaka da manufofi madaukaka, to duniyar da mutum zai gina zata kasance mai kyau mai armashi.Idan kuwa zuciyar mutum da lamirinsa masu daud'a ne, duniyar da zai gina ma haka zata kasance. Don haka ne matukar sifar dan Adamtaka bata sami kafuwa a zuciyar mutum ba, ba zai iya gina rayuwa mai nagarta kuma abar alfahari ba.Dole ne dan Adam ya fara da tsarkake zuciyarsa,domin zuciyar mutum birninsa da haka har ya sami daman isa ga matsera._
_Dole ne sai tushen dan Adamtaka da take cikin ran mutum, ta tsiro ta yi tofo, kafin sakonnin wahayi masu haskaka zuciya su sami gindin zama su yi masa tasiri.Wannan kuwa ba zai yiwu ba har sai mutum ya san kansa da kuma mahaliccinsa,kuma ya dauki salon rayuwa mai ma'ana.Sakonnin Annabawan Allah masu cike da annuri, suna fadakar da mutane domin su kiyaye mutuncinsu, su tsare hakkokinsu, su kuma more rayuwa ta saada karkashin inuwar dan Adamtaka.Hakkin bil Adama batu ne wanda al'ummomin duniya suke kira gareshi. Tun fil'azal, addinin Musulunci ya bawa mutum hakkoki,kamar yadda na fad'a a baya, a lokaci guda kuma ya dora masa wajibobi, wato akwai hakkokin wasu da ke kansa. Manzon Allah da Imaman Ahlulbaiti sun yi kokari wajen warware matsalolin da al'umma take fuskanta, amma ko wane daya daga cikinsu yana bin salon na musamman wajen shiyarda mutane.Imam Ali ibn Hussaini al-Sajjad (a.s.) ya bayyana koyarwar addinin Musulunci ta hanyar amfani da salon addu'a, wato a cikin addu'o'in da yake koyawa mutane akwai bayanin manufofin addini. Baccin haka Imamus Sajjad ya wallafa littafin da aka fi sani da Risalatul Hukuk, wato Littafin Hakkoki,inda a ciki ya yake koyarda dan Adam hakkokinsa da hakkokin da suka rataya a wuyansa.Wannan littafi, ya kunshi kakkoki hamsin da daya, wadanda hakkokin ne da dan Adam yake da su bisa laakari da dabi'arsa,kuma babu wata doka ko iko da zai iya soke wadannan hakkoki. Idan dan Adam ya kula da wadannan hakkoki ya kiyayesu, zai yi rayuwa mai kyau, mai cike da dan Adamtaka da mutunci.Ga yadda Imamus Sajjad (a.s.) ya fara bayanin hakkokin: "Ka sani cewa Allah Mai Girma da Daukaka yana da hakkoki wadanda suka kewayeka, a duk motsawar da ka ke yi, ko natsuwar da ka yi, ko halin da ka shiga, ko wurin da da ka sauka, ko gabar da ka juyata.." Da haka kuma ya cigaba da bayanin hakkokin Ubangiji kan bawansa, da kuma hakkokin dake tsakanin mutane.Tsara alakokin zamantakewa ta hanyar aiyana hakkoki filla-filla, shi ne tushen farko na tsarin zamantakewar Musulunci"._

Beenah ta girgiza kai tana murmushi, tana jinjinawa Baana Marwa kuwa ta shak'a iya shak'a ji take tamkar ta hadiye Baana in zata iya ta huta.Ta sunkuyar da kai tana gun-guni cikin zafin rai yace"me kika ce?".Ta sake kaskantar da kai "cemaka akai ina neman shiriyar da zaka tasani kanaimun wa'az?".Mamaki ya kashe shi Beenah kuwa kasa tankawa tayi yai murmushi yace "Marwa babu abinda zai tayar da sandarki face nacin daddanawa, ko yanzu baki makaraba hanyoyin shiriya yawa gare su in kinso zaki iya zama mai kirki".Kafin ya dire ta tareshi "yaushe nace inason zama mutuniyar kirki? Mtss mai bunu a gindi dai.....waima yaushe ake kud'in k'asa gari ya tashi? ".Ya yunkura zai yi magana ya maida kayarsa"Marwa banason zamanki da Beenah" "saika kashe ni" ya kad'a kai da sauri "tarbiyarki ce bata gamsheni ba" ya fada cike da son tura haushi. Aikuwa ta shak'a ta mike tana kada jiki "kace in shirya sarkin musulmi zai mak'wabceni".
Fuuu!  Tabar d'akin tana mita, bangare guda kuma tana ganin wautarta saboda sarai tasan halin Baana.Beenah ta saki ajiyar zuciya tana kallon Baana sukai murmushi mai cike da manufofi....


Cikin kwanakin babu jituwa tsakanin Beenah da Marwa, haka ma Marwa da Baana a haka ya kammala hutunsa ya koma makaranta cike da kudirin dake bibbiyar zuciyarsa amma wani nannauyan lamari na neman yi masa katanga da hakan.Kwanci tashi su Beenah suka kammala karatunsu, zuwa lokacin ta yayye d'alibai a kala hamsin kowace ta iya ta k'ware hakan ya rage mata nauyin koyawa saboda samun matai maka.+
Cikin nutsuwa take tafiya, hannunta rungume da alk'ur'ani ji tayi an banganjeta.Cikin sauri ta d'ago kai, batai mamaki ba ganin Marwah ba cikin jin haushi ta dubeta. "Marwa me nai miki banason jan masifa fa,kawai ina tafiyata kawai ina ruwana dake bana son raini kin sani sarai ba kanwar lassa bace bana tsokana amma karya ne kimun ban maida martani ba ki shiga hankalinki". "Da kyau Beenah 'yar kurma, cikar Kanuri kenan kin birgeni amma fa wani b'angaran haushinki naji ina me karancin ji ina rigima? Bakya tsoron a karasa kunnuwan kizamo tamkar waccan kurmar ta gida?Kema wasa kike kinsan nafi k'arfinki zamanmu bazai tab'a zuwa a muhalli guda ba tunda mai iyayine ya tarad da mai kinibibi shawara nazo baki kifita harkar awaana Baana domin Baana na Marwah ne ita kad'ai".Beenah tazo iya wuya, takaici mak'ara a zuciyarta ji take kamar ta shak'eta ta huta ta kanne tana dubanta."Walahi kin bani dariya Marwah me akai akai Baana, da zan tada jijjiyoyin wuya a kansa? Abu daya nasani bazai sauya ba yadda yake awaananki nima awaana nane saidai wata kusan tafi wata.Kin fini kusanci dashi kasancewarsa uwa daya uba daya a gareki, kinga shi ne Bakura a gidanku dan haka kisani Baana awaananki nima haka".Rab'awa tai zata wuceta ta fincikota suka fuskanci juna, suna jin numfashin juna sossai idanun Beenah farare tas manya da kwaya baka sidik suka sauya kala zuwa ja tana dubanta."Kusanci dake tsakanina da Baana haka yake, bai kai nakiba sai dai na fahimci bayan nakasar kunne kina da nakasar kwanya ina nuna miki ne kan Baana shi zan aura dan haka ki fita a rayuwarsa kusancinki gareshi barazanane ga rayuwata!". Cikin jin zafi ta tankada Beenah tai gaba"lallai Marwa kin tabu awaanan naki zaki aura" ta fadi hakan a ranta ta wuce gida saidai wani abu na cin zuciyarta wani bangare nasan gasgata batun Marwa da hakan ta karasa gidan duk ranta a jagule.

Jiki a sanyaye tai salama gida ganin mahaifiyarta a dakin girki da sauri ta ajiye jakarta ta shiga tayata, suna aikin suna hirarsu irin ta diya da mahaifiya can Faanah ta nisa da hannu take mata alamun"meke daminki yanayinki ya sauya?"murmushi tayi ta girgiza kai alamun babu komai.Bata sake magana ba amma tasan ba yadda tai ba, suna gab da gamawa mahaifinta ya dawo aiki nan mahaifiyarta ta barmata aikin ta karbi kayansa zuwa sashinsa.Da murmushi ya nufo kichen din yace"Dr Beenah Baana Biu" ta turo baki"kaga Abbuna kadaina cemun bana so".Cikin murmushi ya shafi gemunsa"ku kasance cikin shiri graduation d'in Yayanku k'arshan wata daku za'a Kano".Tsale tai tana murna"naji dadi Abbu Yaya zai dawo nasamu me lesson din tajweed a gida, dama kai aiki yana yi maka yawa.Noma asibiti ga kiwon kifi, dan ma kana da masu kulawa.Allah Abbu tausayinka nake wasu lokutan"."Beenah diyar Abbunta, kema kike karfafun guiwa kan dogaro da kai Alhamdullilahi kuma gashi an samu,murna zaki yi shima Baana karki manta gwanine kan harkar noma koda ya dawo zai d'orana kan inda ya tsaya.Kedai ki juri yimana addu'a.Batun takardunu gobe ku shirya ku amso keda Marwa result ya fito,sai muga in an dace amema muku gurbin karatu.Har yanzu kina kan bakanki akan likitan mata ko?".Cikin murmushi ta daga kai hadi da furta"eh! Abbuna Baana ne ya zab'amun" "Allah yasa kin ci couse din da zai baki damar hakan" "amin Abbu".
Sashinsa ya wuce ta bishi da ido tana murmushi tare da jin-jinawa mahaifinta.Kafin magarba ta gama ta shirya musu wajan cin abinci, ana kiran magarba mahaifinta yaja su jam'i sukai sallah suka dora da karatun umdatul ahakam, ya biya mata ta maimaita ya jiye mata hadda suka dora da sallahr isha'i da kuma shafa'i da wutri daga nan sukaci abinci.Suna gamawa mahaifinta ya mike yace zaije wajan Dr Hannafi,bai jima da fita ba Hajja Faanah ta umarceta ta kaiwa Hajjansu abinci cikin nutsuwa ta dauka ta tafi.Da sallama ta shiga soron gidan, duhu sossai kasancewar babu nefa gabanta ya fad'i jin motsi ta daure ta shiga tana gab da wuce soron wal! Aka kawo nefa ta dago idonta a sukwane hankalinta yai mummunan tashi ganin Marwa da Muhuyyideen cikin wani irin yanayi.Take ta dafe kanta dake barazanar fashewa ta wuce su a galabaice, kai tsaye sashin Hajja ta nufa ta kai mata abincin nan ta zauna suna taba hira tsoron futowa take kartai mugun gamo.Anan take bawa Hajja labarin graduation din Baana da batun result dinta da zasu amso gobe.Ta jin-jina kai tace "Beenahzirahtu kema karatun yahudancin zaki yi? Bazaki aure ba kinaganin Marwa tana kula samari ke ko mashinshini babu kodai saina samomiki maganin farin jini? Gaki kyakkyawa rubarkallah amma shiru kake ji Malam yaci shirwa, wato kina biyewa hudubar ubanki da Baana ko? ".

STORY CONTINUES BELOW

Beenah ta tamke fuska, cikin zuciyarta tana alawadarai da samari irin na Marwa ta muskuta tace"Kijumun tsohuwar nan, watoma banda farin jinin samari? Toni samarin ne bazan kulaba saboda banda lokacin su karatuna shi ne gatana su kansu mazan basusan auran jahila.Kuma ma kike cewa karatun yahudanci zanyi zuwa fa zanyi in koyo yadda ake amsar haihuwa baki ji dadiba ace jikarki zata koyo hakan? Babu ruwan Baana dama can inason karatu, ke kike cusamun kinsa gara na addini to Hajja kowane nada muhimmanci kin gani neman ilmi yanzu na soma tunda ina dame tsayamun.Kajimun Kakus kawai tsohuwa dake zaki hanani karatu.Ita Marwan aidama bata son karatun run fil'azal".

"La'ilaha illalah walahi yarinyar nan rokiya za'ayimiki auran ne bakya so?" "Hahaha! Kai Kakus rukiya ake cewa bafa rokiya ba".Tai waje da gudunta tana dariya,karaf sukai karo da Marwa cikin sauri ta warce jikinta tana binta da kallon kin bani mamaki.Jikin Marwa yayi sanyi ta sassuta murya"Dan Allah Beenah ki rufamun asiri, walahi bazan sake ba".Ta girgiza kai tana mamaki yau ita Marwa take yiwa magiya lallai duniya juyi-juyi inda ranka kasha kallo. Murmushi tayi tace.
[8/8, 10:33 PM] Sanah S Isma'il Matazu: *'YAR KURMA*
Sanah S Matazu.
*35*
Tace"Me zan miki Marwah?Rayuwa ce fa ke kika zab'awa kanki,kowa da kiwon daya amshesa makocin mai akuya ya sai kura nidai iyakacina nasiha.In kin d'auka kanki, in baki dauka ba kanki wallahi kiji tsoron Allah ki taimaki kanki da rayuwarki kisani in kin b'uya a idon duniya toh fa baza ki b'oyewa mahallicin kiba komai zaki yi yana kallonki.

Kuma wallahi sai kinyi nadama, domin shi Namiji bashi da tabbas ko gobe wata zai sake ya barki da k'uncin zuciya.Waima meye riba a rayuwar da kika d'auka......?".
"Ke dila ya isheni dan kinga nai miki sakwa-sakwa? Ina ruwanki da rayuwata?Kabarinmu d'aya?Aikin banza gayar na ayyaro".
Jikin Beenah ya yi sanyi tai murmushi"kishirya inji Abbu gobe k'arbo result d'in mu"
"Ke ya dama ni nakama dahir".Bata tankaba ta wuce,jiki a sanyaye Beenah ta wuce gida tana mamakin Marwah.

Da sanyin jiki ta shiga gida gudun kar Hajja ta ramfota yasa tai gum.Ta nemi wajen kwanciya ta kwanta,sai dai data rufe ido hotan Marwa ke mata gizo hakan yasa ta mike ta d'auro alwala ta soma jera nafifili har goshin asuba.Washegari da wuri ta gama aikinta, ta sallami d'alibanta ta wuce karbar result d'inta.

Tunda ta nufi office d'in exam officer d'in su gabanta ke fad'uwa, da Uncle Tunde ta soma karo ya washemata baki ya gonar auduga, cikin girmamawa ta gaishe shi ta wuce ciki da sallama.Saida ya gama rubuce-rubucensa sannan ya d'ago yana dubanta fuskarsa d'auke da murmushi."A'a Beenah yar baiwa yau kece?"
"Eh! Malam nice" ta amsa tana sadda kai k'asa"."Hmm! Beenah kirkinki ya yi yawa, tunda kika tafi babu ziyara kodayake Baby tacemun kina fama da d'alibai ko?"
"Eh! Malam". "To! Ubangiji ya taimaka yai jagora ai dogaro da kai abune mai kyau ki dage kinji".
"Na gode Malam".

Wasu fayal ya janyo yai rubutu na tsayin mintuna biyar, ya dubeta yai murmushi ya saka sitamfin a d'ayar,d'ayar kuwa sai da ya girgiza kai ya numfasa ya dubeta."Beenah result ba yau ba sai ranar Monday zamuyi taron sallamar d'alibai, taron harda iyayyen yara ko wakilai,ga takardar gayyata kikaiwa Abbunki dana Marwah".

Jiki a sanyaye ta baro makarantar, kasancewar Juma'a ce bata samu Dr a gida ba sai Bakura, bayani tai masa ya karbi takardun ta wuce gidan Hajja tana mata tsiya.

Tsayin kwanaki biyu, Asabar da Lahdi Beenah cikin damuwa ta yi su saboda tunanin result d'inta,sosai mahaifinta ya lura da yanayinta,nasiha ya zaunar da ita yai mata mai ratsa jiki sosai,nan da nan ta ware ta saki jikinta.

*RANAR LITTININ*
Shiri sukai sosai Hajja Faanah,Dr da kuma Beenah sai Bakura da Marwah,fir Yakura tace babu inda zata je aka kad'a aka raya tak'i,tilas suka tafi babu ita.

Harabar makarantar d'inke take da manyan gwamnati da malamai yan boko, kowace d'aliba sanye take da (uniform) bai d'aya sun zauna cike da nutsuwa,nan da nan aka soma gudanar da taron.Beenah aka kira ta bude taro da addu'a matsayinta na shugabar d'alibai, cikin nutsuwa ta taso ta karbi sifikar nan da nan muryarta ta karad'e ko'ina da daddad'ar sautin muryarta, da yawa daga cikin mahalarta taron fuskarsu d'auke take da murmushi a dalilin nutsuwar da suka samu,wasu kuwa tasbihi suke ga ubangiji (S.W.T) haka ta k'arasa karatun ta dawo ta zauna,wajan ya d'auki kabbara, nan da nan masu bidiyo sukaita d'auka.

STORY CONTINUES BELOW

Shugaban makaranta ya mik'e yai jawabin godiya ga iyayen yara,Malamai da kuma Beenah,ya mik'a sifik'a ga mai gabatarwa,aka cigaba da gudanar da taron cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Rukunin farko na d'aliban da sukai kokari aka soma gabatarwa,sune masu credit tara, bakwai takwas sai mai creadit sha d'aya.Kowace d'aliba burinta ace itace ta farko,a hankali aka soma kiran sunayensu kamar haka;
Falmata Mustapha nada creadit takwas,Kundum Aliyu creadit bakwai,Aysa Bunu creadit tara sai Beenah Dr Hamza creadit goma shad'aya.Take wajen ya d'auki tafi raf-raf ana jin-jinamata.Bayan hayaniyar ta lafa ne aka cigaba da kiran d'alibai suna karb'ar kyautuka daban-daban.
Babu kyautar da Beenah bata karb'a ba,kama daga kan tarbiyya,tsabta da kuma wacce tafi kowa k'okari.Idan ka dubi fuskar mahaifanta babu abinda zaka gani sai murmushin farinciki da suke yi,bayan komai ya lafa akai kiranta don ta tofa albarkacin bakinta.

Cikin nutsuwa ta taso,kanta a k'asa tana d'ago kai sukai ido biyu da Baana ya sakarmata k'ayataccen murmushi,ta sadda kai k'asa zuciyarta cike da tarin tambayoyi. "Yaushe yazo? Waya gaya masa?". Tambayoyin da ta kasa samun amsarsu ta hak'urewa kanta,ta hau step ta amshi abin magana ta d'ago ta saki murmushi saboda ta samu hanyar cusawa Hajja ra'ayinta na son karatu.

"Assalamu alaikum, ina godiya ga ubangijin hallita daya bani ikon ganin wannan rana mai matuk'ar muhimmanci a rayuwata,godiyata ga Malamaina da kuma iyayena tare da.....ta dago ta kalleshi ta juya ta kali kowa sannan ta sake sakin murmushi a karo na biyu wanda hakan ya burge kafin taci gaba da bayaninta.
"Awana Baana Bakura bisa jajjurcewarsu wajan ganin na samu nagartaccen ilmi, Alhamdulillah yau gani a mataki na biyu a fanin karatu,hakan na nuni da cewa mafarkina yana gab da cika. Kirana gareku 'yan uwana d'alibai,iyaye mata iyayena maza shi ne ilmin 'ya'ya mata...D'if wajan ya d'auki shiru saboda gagarumin aikin da kowa ke ganin Beenah ta d'auko mai matuk'ar tsauri.Bata damu da sauyawar jama'ar dake wurin ba ta cigaba.
_Mata!Mata!!Mata!!! Mata sune k'ashin bayan kowace al'ummah,domin idan mace d'aya ta samu wadatacan ilmi tamkar an ilmantar da al'umma ne bakid'aya kasancewarta makaranta ta farko ga yaro,a kwana a tashi._

_Ilmin d'iya mace zai iya kasuwa fanni daban-daban wato boko da addini.Ilmin addini shi ne mafi kyautuwar ilmi awajan kowane mahaluk'i mai neman dacewa ba wai ga d'iya mace kawai ba amma da yake akan d'iya mace nake magana shi yasa zanfi bada muhimmanci akanta._

_Yayin da kika riski kanki a b'igiran da basa b'ukatar karatun d'iya mace mai tsayi, karki zafaffawa kanki wajan cewa sai kinyi, maida hankali wajan neman ilmin addinni wanda zai zamo miki abin alfahari anan duniya da kuma gobe k'iyama.Dashi ne zakisan yadda zaki bautawa ubangijinki cikin tsarkakewa da nutsuwa,dashi ne zakisan kanki da abinda zai amfaneki.Gwar-gwardon ilmin da kika samu koda iya makarantar gaba da primary ne zai amfaneki ya amfani iyalanki muddun kinyi mai inganci.Ilimin boko bai zama koma baya idan mukai duba da yanayin zamani, saboda a yanzu anci gaba sosai komai saida ilimi.Ilmi baya zama b'atanci saidai akwai hanyoyin da suka dace abi wajan nemansa.Wasu lamuran da suka shiga cikinsa ne sukai katutu suka haifar da rud'ani a zukatan al'ummah da iyayyanmu Maza da Mata.Amma banda hakan babban abin alfahari ne ace yau mace ta taka wani matsayi na taimakon al'ummah musamman a harkar lafiya.Abin takaici zaka shiga asibitoci da dama kaga bamu da manyan likitoci mata sai maza, wanda wannan babban abun kaicone a garemu ace Namijine zai duba mace sab'anin mace yar'uwarta,kuma hakan ya samo asaline sakammakon k'arancin mata a wannan fannin,wasu suna so suyi amma babu damar hakan saboda rashin wadata yayin da wasu kuma da wadatar amma iyayensu basu basu goyon baya akan hakan ba._

Haqiqa ilmin 'ya mace nada matuqar muhimmanci,saboda muhimmancinsa nema wasu ke ganin a ilmantar da ita yafi a ilmantar da d'a namiji,hujjarsu ita ce:
"Ita mace Ita ce uwa kuma makarantar farko ga kowanne dan adam,haqqin kula da tarbiyyan yaro yafi yawa ga uwa ko kuma nace gabadaya ma ya ta'allaqa ne akan ita uwa,toh idan bata samu tayi ilmi ya za'ai taba yaronta ingantacciyar tarbiyya?" Wannan shine ra'ayin masu kafa hujjja kan cewa ilimin mace yafi na da namiji.

Annabi(s.a.w) yana cewa"Neman ilimi farilla ne(wajibi) ne akan duk wani musulmi da musulma"
Idan muka duba anan zamuga cewa Annabi bai ware maza zalla kan maganar neman ilimi ba,a'a sai yace" Musulmi da Musulma" Sannan ilimin nan ba wai ana nufin na addini bane kawai a'a harda na zaminin,mu duba hadisin nan na Harijata bn Zaid bn Thabith zamu fahimci hakan,Zaid bn Thabith ya koyi yaren Yahudawa ya kuma yi amfani dashi wajen karanta wasiqa yayinda Yahudawa suka aiko ma Manzon Allah(s.a.w) ko kuma rubuta wasiqa yayin aika musu,shin Idan har akwai wani aibu ko abin tir acikin haka Annabi ya tura shi(Zaid) musamman domin yaje ya koyo wannan ilimi a wajen wadanda suka kasance ba musulmai ne ba?

"Ina tsoron in umarci bayahude ya rubuta min wasiqa yayi qari ko ragi acikina hakanan kuma ina tsoron in wasiqa tazo daga yahudawa ace bayahude ne zai karanta sai yayi qari ko ragi" Inji Ma'aiki(s.a.w)
(Tuhufatul Ahwazee)
Duba da wannan hadisin ya kamata iyaaye su riqa barin 'ya'yansu suna shiga wannan fage na ilimin zamani ana damawa dasu domin ta haka zamu iya ciyar da addininmu gaba, idan kuwa bamu hankalta ba lallai watarana zamu wayi gari muga kafirai sun zamo jagaba akan komai na al'amuran rayuwarmu( Allah ya sawwaqa).

Ya ishi mai ilimi daraja saboda fadinsa madaukakin sarki"Allah ya shaida cewa lallai ne babu abin bautawa da gaskiya face Shi,kuma mala'iku da ma'abota ILIMI sun shiada"
Kuma dai da ilimi ne zaki sauqe abinda ke kankk na bauta ko ibada,da shine zaki zama 'ya mai tsari kuma abar yabo,da ilimi ne zaki kubutar da kanki daga rayuwa ta kaskanci izuwa ga rayuwa mai enci.

Ma'abota Hikima na cewa "Shi ilimi haske ne,shi yake maida bawa d'a sannan ya maida d'an da bashi dashi bawa" Sannan wasu ma'abota hikiman suka kara da cewa"Ilimi yafi dukiya,domin kuwa shi ilimi shi yake tsaron mai shi kuma duk inda yaje tare yake tafiya da abinsa acikin kansa,acikin qwaqwalwarsa yayinda dukiya kuma mai ita ne ke bata tsaro,idan yayi tafiya ba tare da ita ba toh fa bashi da bambanci da wanda bashi da ita"

Sannan idan mukai nazari da kyau zamu ga babu wani mai ilimi daya tab'a mutuwa da aka rabawa magada iliminsa amma mai dukiya kuwa munji mun kuma gani sau ba adadi,Don haka yan'uwa mu tashi mu nemi ilimin addini dana zamani(boko) don gujewa kunci da kuma dana sanin da kan riski marasa su"
Jikin iyaye da dama yayi sanyi,Hajja kuwa tuni taji tana burin karfaffawa Beenah guiwa wajan yin karatu.Baana babu abinda yake sai murmushi tare da yabawa kwazanta gwamnan Maiduguri yai mata kyautar kudi naira dubu dari biyu tasha kyaututtuka sossai da haka taro ya watse.

A gajiye suka koma gida, Hajja sai data kwakkwame Beenah take saboda tsantsar farinciki ji take inama mai gidanta nada yai yau da yayi alfahsri da ahlinsa.


Bayan komawarsu gida mahaifanta sukaita yabawa kokarinta,Baana banda murmushi babu abida yake yi zuciyarsa na raya masa abubuwa da dama.Marwa da Yakura kuwa bakin ciki babu magana musamman da Marwa ta zo da creadit uku pass shida hakan ya konawa Bakura rai.Beenah ce ta silalle zuwa sashin Baana dai dai lokacin ta sameshi yana waya, dam gabanta ya fadi musamman data fahimci da mace yake waya idonsa a kanta harya sauke wayar yana karantar yanayinta.

Yana dire wayar yace "Beenah yadai?" Firgigit!  Ta juyo tana murmushin yake"Yaya waya gayama taron yau? " "Hmm!  Beenah my unique abinda ya shafeki ai ya shafi Yayanki Abbune ya fad'amun" kai kawai ta girgiza "ok" ta furta tai masa sallama ta wuce.Ya rakata da idanu, haka kawai ta tsinci kanta wani abu na mintsinar mata zuciya game dashi das! Gabanta ya fadi saboda tunawa da kalaman Marwa yau ta sawa ranta sai taiwa Hajjansu tambayar dake adabarta.Dan haka tun yamma ta tsiri kwana gidan Hajjan.
Ta gama aikinta tayi komai,shiru Baana bai shigo ba har suka kwanta jin bacci na shirin kawomata farmaki yasa ta mitsuke ta dubi Hajja."Hajja dama mutum na auran awaanansa? dam!  Gaban Hajja ya fadi"ina kika tabajin wannan kwabar Beenah? Ko bokonku da kuke tunkaho da ita basu da wannan tsarin ina kika jiyo kuma?". Ajiyar zuciya ta saki ta kwashe yadda sukai da Marwa ta gaya mata dif!  Tai shiru tana jinjina lamarin a hankali ta warwarewa Beenah alakar Baana da Marwa ta kuma ja kunanta kada tagayawa kowa ta san batun.Jinkinta ya yi sanyi sossai ta dade tana jinjina lamarin a haka bacci barawo ya saceta.

Washegari haka ta yini zungur bataga Baana ba, haka kawai abin ya dunga cimata rai ko wajan aiki bata da wani sukuni.Sai magarba tana shirin tashi daga shago ta sunkuya hada wasu zarurruwa taga inuwar mutum sannu a hankali kamshin turaransa ya gauraye wajan ta dago suka kali juna wani abu ya tsinka zuciyarta mai nauyin gaske.Idanunsa masu zaiba-zaiba suka kafeta.

          Cikin zuciyarta ta dinga wassafa tsarinsa, dogone mai faffadan kirji yana da tsayin fuska mai cikar kasumba baka sidik kwantaciya luf-luf hakama gashin kansa hancinsa ziyat dogo yana da manyan idanu da yalwar gashin gira miskiline da wuya kaga dariyarsa yafi yawaita murmushi...... tai saraf ta kauda tunanin daya ziyarci zuciyarta tana murnushin yake"broth have a sit" ba musu ya zauna yana karewa shagon kallo nan da nan ta sallami dalibanta ta dawo gurinsa.
Cikin murmushin k'asaita ya zubawa hannunta ido wanda yasha kan lalle, karaf suka hada ido ta sunne kai kasa tana wasa da yatsun.
"Beenah nazo ne kan maganar karatunki, tunda naga Hajja ta sassauto kan ra'ayinta zan karbi takardun yanzu in tafi dasu.Zan nema miki gurbin karatu a Maiduguri sai ki koma gidan Kaka(kanin mahaifin su Dr) domin su Abbu sun aminta da karatunki banda zaman hostel.Hajja ce taso bamu matsala itama ta sauko, tunda tace dama tunaninta aure kuma baki da mashinshini bale a kai ga batun aure". Ya karasa furucin yana murmushi, batun ya taba zuciyarta ta kanne tana murmushin tura haushi"share Kakus waya ce mata banda samari?Ina dasu kawai ina son fara karatune sai mu dora daga inda muka tsaya..".Kallon da ya jefa mata ya sanya maganar makalewa a fatar bakinta.

"Wato kina da samari? Ya fad'a da kaushin murya,kai ta gyada masa ya sha mur kome ya tuna ya saki murmushi yace " ok Allah ya taimaka" "amin ta fada da dakakkiyar murya ya wuce be tanka ba.Jiki a sanyaye ta rufe shagon ta wuce gidan Hajja, yinin ranar babu wata maganar kirki data had'asu nan da nan ta hada yanata-yanata ta koma gidansu. Da magarba aka aikata kai masa abinci, lokacin da tai sallama dakinsa ya jima bai amsaba ganin babu alamun amsawar Mansur abokinsa ya amsa mata cike da nutsuwa tai salama bai amsaba bai kalleta ba sai lumshe ido da yayi ya fada bandaki.

Mansur da Muzabil ta gaisar, ta wuce jiki a sanyaye kwata-kwata ya sauya mata.Tana fita ya fito ya sauke ajiyar zuciya, Mansur ya kwashe da dariya"zaka kashe kanka dalilin b'oyayyan so" "hmmm!  K'yaleni Mansur Beenah (is my life) rayuwata ce karaf!  A kunnuwan Marwa da tazo giftawa,ranta ya dugunzuma da gudunta ta bar wajan ta nufi gida tana hawaye.

STORY CONTINUES BELOW

Hankalin Yakura yai matukar tashi ta dinga tambayarta abinda ya faru, sai da ta gama kukanta samnan ta bata lamari ta jinjina kai tare da lallashinta.

Washegari da sassafe cikin shirinsa na kananun kaya,shigar tai masa kyau yai karo da Beenah gab da shiga gida kowa ya daukewa kowa kai.A ranta tana mitar ya dauki al'adar saka kaya kanana,kai tsaye ya shiga yiwa Yakura sallama.Fuskarta babu yabo babu fallasa har ya mike zai bar d'akin ta kada baki ta kira sunansa.

"Muhammad". Kafaffunsa ne sukai sanyi matuk'a bai ta6a jin ta kira sunansa kai tsaye ba.

"Dawo ka zauna zamui magana".

Ba musu ya nemi waje ya zauna ta kalleshi.
"Inaso mui magana da kai umarni nake baka ba shawaraba,ka auri Marwah".

Kansa ya yi nauyi, jim ya d'ago idanunsa jajjur ya sunkuyar da kai "Hajja.." kafin ya dire ta tare"bana buk'atar komai tashi ka tafi Allah ya kiyaye".

Bashi da zabi face bin umarninta, jiki a mace ya fito karaf yai kici6us da Marwa alamun labe tai musu wata muguwar harara ya jefa mata sum-sum ta wuce tana murmushin mugunta.Mak'alk'k'ale Yakura ta yi tana dariyar jin dadi,ta tureta tana fadin ja'ira.

Baana zabar tashin hankali ko sallama baiwa Hajjan Beenah ba daga gidan Hajjansu kai tsaye wucewa ya yi.Hakan yasa basui sallama da Beenah ba Marwa na lekensa ta soro dadi taji sossai ta koma gida.

Bangaran Beenah tunda taga babu shigowar Baana jikinta ya soma sanyi,bayan fitar Faanah shago ta zari mendil d'inta tai gidan Hajjansu cike da murmushi ta shiga gidan.Turus ta tsaya ganin babu Baana ta d'aure ta shiga tana tsokanar Hajjansu.
"Ja'ira burinki dai ya cika dazu Yayanki ya shigo yi mun sallama yake gayamun ya tafi da takardunki ashe gidan Kakanki zaki zauna?". Tuni guiwoyinta sukai sanyi zarginta ya tabbata Baana ya yi fushi ya tafi. Tun tana fuskantar batun Hajjansu, harta gaji tai mata sallama ta koma gida.Yini tayi tana tunani.
A rikice Baana ya nufi gidansu Mansur, yanayin daya ganshi ya bashi mamaki.Baana nnutsatsan mutum ne ba komai yake daga masa hankaliba.Bai b'oyewa Mansur komai ba yai jim yana tunani ya numfasa.
"Baana ka fawalawa ubangiji komai, domin baza kaja da umarinin mahaifiyarka ba uwa uwa ce tafi karfin komai kabita sannu".

"Hmm!  Na gode Mansur, amma kasan inason Beenah nasota tun bata isa abar sha'awa ba yanzu baka ganin auran Marwa zai min shamaki da Beenah"?.

"Tabbas shamakine domin ba kowa keda fahimta ba, amma auran Marwa ko a addinni bazai haramtama auran Beenah ba".

"Na yadda da batunka, amma zan cigaba da boye son Beenah domin bayyana shi fitinane ga ahalina.Inason Beenah fiye da kaina, bazanso shigarta matsala ba zan cigaba da yi mata b'oyyayan so".
"B'oyyayen so?".
"Tabbas Mansur".
"To!  Nikam ina ganin da kamar wuya, domin so duk inda yake baya b'uya".
"Ka zuba ido zakai mamaki".
A ranar suka bar garin Biu, kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji.Baana har yai sati biyu da tafiya zuwa lokacin Beenah ta kai makura wajan dane abinda take ji a ranta har ya soma sata rama.

Tunda aka soma batun zuwan Beenah karatu Dr ya nemi shawarar Bakura kan gyara ainihin gidansu na Maiduguri.Hajja kad'ai suka sanarwa,sossai tayi farin ciki da hakan koba komai zumunci zai k'ara k'arfi.Kudi ya tanada sossai aka bige gidan kanin mahaifinsu da nasu ya dawo garin Biu kafin a gama aikin a d'akin Baana akai masa masauki.
Dake filayene d'iban da sai aka samu wadatar guri sossai, fanni hudu aka fitar kowane d'auke da falo da bedroom biyu a ciki tare da wadatar tsakar gida da band'aki.Duk da hakan akwai ragowar guri wanda zai kai ayi part biyu a ciki kawai sai Bakura ya bada shawarar ayi k'aramin lambu a tsakiya ayi shuke-shuke saboda Faanah.
Hakan kuwa ba k'aramin k'awata gidan ya yi ba.Cikin wata d'aya aka gama ginin gidajan.Aka rufe ana jiran lokacin tarewa,ko Baana bai san da batun ba.

STORY CONTINUES BELOW

Kwanci tashi aka shiga gudanar da shirin saukar su Beenah, an yi shagali sossai hankalin Beenah yai matuk'ar tashi ganin har aka gama bai hallata ba.Kuma taji lokacin da Abbunta ya sanar dashi a waya, haka tai taron sukuku da ita.Falmata ta kula da sauyawarta, tun tana yi mata kawaici harta kai ga tambayarta a hanyarta ta yi mata rakiya bayan gama taron.
Beenah ta kanne kawai tace"babu komai Falmat (just pray for me) ki dai tayani addu'a tunanin rabuwa da gida ne kawai.
"Hmm!  Beenah unique kenan".
"Au! Kema?".
Dariya sukai daga nan sukai sallama.Cikin ikon Allah aka soma shirye-shiryen graduate din Baana, Dr ya dage kan kowa sai ya je saboda akwai abokinsa dake Kano a gidansa zasu sauka.

Beenah taso togewa taga babu dama saboda babu wanda zai zauna.Tun saura kwana hudu tafiya Marwa ke gid'imi itace gyaran jiki kunshi gyaran gashi saboda zasu ganin Baana.
Yakura kuwa sossai take tsumata da tsubace-tsubace turare kwalli da sauransu,tun Beenah na maida hankali wajan sha'anin harta watsar saboda ta lura babu nutsuwa a batun.
          Ranar Littinin taro ya kama su kuma tun Asabar sukaiwa garin Kano tsinke, a unguwar Nassarawa G.R.A gidan aminin Dr wato Barrister Mustapha Muhammad Kurfi.

Mutum mai karamci da kyautattawa, yana da mace biyu da yara takwas.Kawunan matansa a hade yake sossai, babu bambanci tsakanin wance da wance ko 'ya'yan wance.Babban d'ansa na zaune a Abuja da iyakinsa mai suna justice Aliyu.Sai mai bimasa sojane yana Fatakol da iyalansa shi ne Genaral Faisal.Sai Barrister Husnah tana aure a Minna sune yaran uwargida Hajiya Hauwa.Sai Aunty Amarya itace Zainab nada yara biyar Dr Shukura ce babba na aure a Kano sai Juwaira acconter ce tana Dubai da mijinta sai Ammar shi ne yayi aure sai matasan samarin da suka rage wato Samar da Samir duk sun kammala karatunsu.

Samar Bussiness ya karanta hakan yasa shi yake juya ragamar dukiyar mahaifinsu.
Samir kuwa ma'aikacin jarida ne.Akwai yarinyar Justice babbar dake karatu a nan Kano mai suna Asalamiyya matan nada fahimtar juna da kyautattawa tsakanin su.Sun had'u da Dr ne a sanadin karatu tare sukai jami'ar Maiduguri.

Tunda suka sauka ake haba-haba dasu,an musu saukar karamci sossai.Beenah dai bata walwala sosssi,tun zuwansu Aslamiyya take nan nan da Beenah hakan yasa ta saki jiki suketa wasa da dariya juna.
Marwah kuwa sai shisshigewa,Samar take dan ta lura Samir miskiline.Hajiya Hauwa sossai nutsuwar Beenah ta burgeta hartana d'arsa wani abu a ranta.Dadare suka hallara wajan cin abinci,kowa naci banda Beenah datake shan ruwan lipton da meatpie.
Hajiya Hauwa ta kalleta tana murmushi"Benazirahtu kin huta wato bakyacin girkin tsofaffi ko?" ta fad'a da salon tsokana.
Murmushi tayi tana wasa da yatsunta Yakura tai karaf tace"wannan uwar kinibibin na gado".Kowa ya yi sak alamun bai ji dad'in kalamanta ba, maigadi yai salama yana sanarwa akwai bak'o a waje babu tantama Dr yasan Baana ne dan haka yasa Samar ya shigo da shi.
Tunda Beenah taji ance Baana ne,gabanta ya dinga fad'uwa zuciyarta ta shiga rud'u sossai.Sautin muryarsa ya katsemata tunani gaba daya kamshinsa ya cika wajan,ta dago sukai kalon-kalo ya lumshe ido tare tsare gida.Asalamiyya na kula da yanayinsu sai suka burgeta, saurin dauke idonta ta yi ya rissina yana gaishe da mahaifansu cike da ladabi. Bayan an gaggaisa iyayyan suka basu waje sui hirar zumunci, Mazan sukai bangaran maigidan hakama matan.

A hankali Baana yake hira da samarin suna kara fahimtar juna yana sako Asalamiyya itama dake akwai nutsuwa bata cika magana ba Marwa ce dai keta azarb'ab'i Beenah kuwa ko kanzil tanata wasa da wayar Asalamiyya.Lokaci zuwa lokaci suna satar kallon juna, abun yaso bawa Aslam dariya ta kanne.Can Baana ya numfasa yace.
"Beeeeeeenah!".

Cikin nutsuwa ta dago sukaiwa juna wani irin kalo, ta dauke kai tana dubansa.
"Beenah babu magana ko?".

Murmushi tayi amma data tuno abinda ya yi mata, sai ta turo baki ta shagwab'e fuska.
"Bayan ma ka manta dani,kai tahowarka ko sallama".

STORY CONTINUES BELOW

Salonta ya bireshi sossai tare da haifar masa nishad'i, ya langab'ar da kai yana kwaikkwayonta.

"Bakece kikai mun laifi ba".

Aikuwa gaba d'aya wajan suka kwashe da dariya, yaiwa fuskarta tsuru yana kallon jerrarun fararan hak'oranta da suketa haske.Fuuu!Marwa ta bar wajan, ya tabe baki ko minti biyar batai ba saiga fitowar Yakura fuska a gimtse ta dubeshi.
"Baana ka wuce gida sai zuwa gobe".

Jiki a sanyaye ya amsa, bata tankaba ta banko k'ofar ya mike yai musu sallama harya kai bakin k'ofa ya  juyo yaiwa Beenah murmushi.Yana fita Marwa tazo ta wuce tabi bayansa, a tsaye ta sameshi sunkai mintuna shida babu wanda ya tanka ya shiga motarsa ya wuce a zafaffe.Cike da sanyin jiki ta dawo babu kowa a falon sai Aslam nan ta zauna suna hira, jefi-jefi anan take bawa Aslam labarin Baana zata aura.Mamaki ya kasheta, ita dai bataga alamun so a tare dashi ba amma fahimtar da taiwa lamarin yasata gum.Tafi-tafi har dangantarku da Beenah da Baana sai da ta warwarewa Aslam tai jim tace.
"Sis (i'am sorry to say) anya Yayanki ba Beenah yake so ba?". Marwah tai murmushi tace"(iknow) nasani (but) amma walahi mudin ina numfashi saina wargaza tafiyar Baana nawa ne nikad'ai kisa a ranki".

"Amma Marwah hakan da zaki akwai cutarwa.... ".

"Ke!  Dillacan dakatamun, nafa fahimci tun zuwanmu bakya haba-haba dani tamkar Beenah walahi zan nuna miki kalata ta zahiri".

"Hmm!  Marwah kenan".
Mikewa tai ta barmata wajan ta koma wajan, Hajjansu da Beenah suna hira duniya yaran Kanuri suna birge Aslam sossai.

Sai dare sukai mata salama suka nufi makwncinsu, har shadaya Marwah bata dawoba tana sashin su Samar lamarin daya daurewa Aslam kai sossai ta bude bbaki zatai korafi aka turo kofa........
Gaba daya suka maida hankali kan k'ofar, zatonsu Marwah ce sai suka ga akasin hakan.Copy din Aslam ne Hauwa mai aiki ta kawomata ta karba tai mata godiya ta wuce.

Aslam ta dubi Beenah tana murmushi"ashe Marwa matar yayanki ce?" Murmushi kawai tayi ta amsa da "hakane".Marwah ta shigo tana fizge-fizge babu wanda ya damu da shirginta.
Washegari da wuri suka tashi, ta taya Aslam shiga kichen ta dinga mamaki yadda bata da girman kai irin na wayayyun matan da suka d'auki shiga kitchen gidadanci.A hankali ta dinga kalon yadda take komai,girki kala hudu ta shirya.
Kunun gyada ta shirya da k'osan nama wanda yasha had'i da _peak milk_sai funkaso da miyar agushi sai suka soya plantain da dankali.Beenah tace"badan ba zamu dadeba da nayi koyi na girki""kibari zan baki books in dai kinbisu a hankali zaki fahimta nima zaki rubutamun girkin Kanuri kafin ku tafi ki koyamun turarruka". Dariya sukai a tare, kafin takwas da rabi sun shirya wajan cin abincin yadda ya kamata.Kowa ya hallara suka ci abinci da yamma Samar ya zaga dasu shoprite jufatu sahad sune har hills and villy sun zaga gari sossai.A gajiye suka dawo suna parking dai-dai lokacin Baana da Mansur suka shigo gidan.Idonsa a kanta ya tsare gida, cike da nutsuwa suka gaishesu idon Mansur akan Aslam yanayinta ya burgeshi sossai.
Wucewa sukai suka barsu da samarin gidan.

       Suna shiga Aslam ta wuce bandaki, Beenah ta kwanta tare da lumshe ido zuciyarta na zafi.Tunnanin Baana nasan nakasa mata zuciya, kanta ya sara ta dafe idonta yai jajjur.
"Baana ina sonka".
Ta furta hakan, wand labbanta ne kawai suka motsa,tai juyi ta mike Aslam na fitowa ta fada bandaki ta dauro alwala. Ta jima tana addu'a kan darduma daga nan ta dora da sallahr isha'i ta wuce wajan Hajjansu tana zolayarta.

Beenah doguwa ce wankan tarwad'a,mai gashi bak'i sid'ik da shek'i wanda har ya kwanta a kan kafad'unta.Sanye take da lifayar data dace da tsarin fatarta, kalar _pink colour_ ta nade jikinta tas. Fuskarta doguwa mai kyan tsari mai dauke da, idanu dara-dara hancinan siyat da bakinta madaidaici mai dauke da jerrarun hakora fararre tas da hushiryarta tsayayyayiya a tsakiya cas.

Beenah tana da wani irin kyau mai cike da kwarjini, kalo daya in kai mata baka gane hakan sai ka jima.Tana da cikakkiyar hallita kasanta a cike yake dam! Hakama daga sama cikinta ne kawai a shafe tamkar zata karye.Tunda ta fito kamshi yaiwa falon salama Samar kasa dauke idonsa yai a kanta.Aslam kuwa tafi ta shiga yi "yayi Kanurian wannan kamshi haka?" Dariya tayi tana murda yatsu alamun jan kunne.

STORY CONTINUES BELOW

"Karki fasamun kai fa?".
"Ba wani fasa kai Beenah kin had'u sunan ya dace dake, ga mutumin naki kin watso shi".

"Wafa?".
"K'amshi mana walahi shiyasa jinsin Kanuri kuke burgeni.Inason al'adunku".

"Karki damu insha Allah can zaki aure".

Marwah dan takaici kasa zaman falon tayi.
Gaba d'aya suka dunguma zuwa waje, motocine a zube yan ubansu Alhaji Mustapha da Bakura da Dr a mota d'aya.Hajjansu Hajja Faanah da Yakura da Hajiya Hauwa da Aunty Zainab a mota daya wadda Samir keja.Beenah da Aslam da Marwah a mota daya Samar ne ke jansu suka dauki hanyi reras.
        Harabar taron ta cika makil, kowa sai murna yake a haka sukaiwa wajan tsinke.Tunda suka shigo idon Baana na kanta hakan ya sakwarkkwatar da nutsuwata.

Tasowa ya yi ya taresu suka gaisa, a haka aka soma gudanar da taron.Masha Allahu taron ya kayatar sossai kafin biyu aka tashi Baana yasamu point fiye da kowane dalibi hakan yasa akaita daukarsa hotuna.

Dakyar ya faki idon mamansa akai masa hoto daya shida Beenah inda ta dan dora kanta a kafadarsa tai murmushi dimful mata ya lotsa(beauty point) sai hotan yai tsari kasancewar yafita tsayi ya dan rankwafa kansa a saman fuskarta tamkar yana mata rada.A haka taro ya watse suka jiyo zuwa gida, Aslam da Mansur dai bisa alamu sun yi na'am da juna.
Ranar Laraba sukai shirin komawa gida har Baana, ansha kewar juna Alhaji Mustapha yaiwa Baana kyautar mota sabuwa dal.Su Beena kuma sarkokin gwal suda iyayansu mata Samar ne ya siya musu wayoyi su duka ukun ita da Marwa da Aslam kirar iphone mai matsakaicin kud'i. Sossai Dr ya dinga yi masa godiya suka rakasu tasha motarsa ta daga zuwa Maiduguri.
Motar Baana ta rigasu zuwa gida, a Maiduguri suka sauka kowa mamaki yake yadda aka gyara gidan tsarin ya birgesu sai lokacin Dr yai musu bayanin dalilinsa nayin haka.Nan fa Yakura ta dinga bala'i shin Beenah yar gwal ce a saboda ita za'a rabosu da garin Biu.Babu wanda ya tanka mata kwanan su biyu suka wuce Biu cike da walwala.
Tunda suka dawo babu jituwa tsakanin Yakura dasu Beenah musamman yanzu da Baana bashi da wajan zuwa fiye da gidan Faanah.Karfi da yaji sotake ta rabasu lamarin daya fusta Hamza tun yana kawaici harya fito yaiwa Yakura tas.Maimakon a samu sauki sai lamarin ya ta'azara sossai wanda ya haifar da tsana mai tsanani tsakakaninsu.Shi Hamza yana gani bata isaba ita kuma tanai masa kallon a tafin hannuna kake.Beenah an yi registration an gama komai tuni ta tattara kayanta ta koma Maiduguri ita da Hajja,a sashin Hajjan suke ita da Baba Isah sossai tana jin dadin zamanta.Duk weak end Baana na kawomata ziyara tare da siyayya kala-kala lamarin da ya haifar da karin tsananin shakuwa tsakaninsu.
Zumunci tsakanin Beenah da Aslam sai abinda yai gaba, bale yanzu da Mansur ke son d'auko Aslam a matsayin mata lamarin da kowa yaji dadinsa.
Kwatsam Alhaji Mustapha ya nemi shawarar Dr suka soma business kan shiga da barkono kasar Chine nan da nan suka samu hanya.
Kasuwancin daya haifarsu da cigaba sossai, Baana shi ne mai kula da harkar sossai.Kafin watanni Dr ya samu kudi sossai,ya canja mota mai kyau da tsada ya siyawa Bakura mota mai saukin farashi.Cikin ransa ya kudiri kai Baba Isah Hajja da Bakura saudiyya habu wanda ya tuntuba cikinsu saida ya gama komai.Hajjansu atabau tace sai dai yakai Faanah ita ta hakura aka kada aka raya tilas aka kyaleta.
Lokacin da Yakura ta samu labarin tafiyar,rushewa tai da kuka tana Hamza baya kaunarta ya rasa wazai kai Makka sai kurma, me Kurma zata iya a saudiyya?.Baana takaici ya isheshi ya rasa yaushe mahaifiyarsa zatasan Annabi ya faku.Har gida Hamza yazo ya bata hakuri tare da alkawarin kujerar Hajji.

Kwanci tashi su Beenah karatu ya mika har sunci samister daya, a dai-dai lokacin su Hajja suka dawo Saudiyya suka sauka a Maiduguri.Dama an zuba komai a kowanne sashi dangin AC carpet kayan kallo kujeru da kwabar turare da sauran kayan bukatu.Washegari su Bakura da Yakura da Marwa suka nufo garin Maiduguri.Shi kenan sukaiwa garin Biu hijira,makota an rabu cike da muruntawa.Gidan Hajjan Faanah Hamza yasa aka rushe da nasu aka gida makaranta babba hade da masallaci mai suna.
_HAJJA FAANAH ISLAMIC COLLAGE OF QUR'AN_,makarantar ta ginu sossai Dr ya saki kud'i aka k'awata makarantar aka zuba litattafai d'alibai kyauta.

Baana da mahaifinsa su suka cigaba da ziyartar Biu suna kulawa lamarin noma da kiwon kifi.Tafi-tafi ragamar ta koma hannun Bakura kacokan saboda yanayin aikin Baana da kuma Dr shi Dr na kula da shige da ficen kayansu zuwa China.
Dawowarsu Maiduguri ya samawa Beenah walwala, wani sashin kuma takaici saboda yadda kaunar Baana take mata barazana.

Toshima nasa fannin abun sai addu'duk yadda yaso bayyana mata kudirinsa in ya tuna Hajjansa lamarin dagula masa lissafi yake. Akwai ranar da Marwah ta shigo dakinsa ta tarar yana kallon hotansa a guje taje ta kaiwa Yakura gulma ai kuwa sai gata tana bambamin fada zahiri hotan ta gani hannunsa lamarin daya girgizata ta shiga fada babu ji babu gani.

Bai tanka ba sai hakuri daya bata, abin takaici kwatsam yana fitowa ya hangi Beenah da Samar ya hango suna hira da kyalkkyala dariya wani abu ya tokare masa zuciya kallon da yai mata ya sanyayyar mata da jiki tana gaisheshi ko kulata bai ba yana tambayar Samar ysushe yazo yace masa dazu ya shigo sunzo claring din kaya ne a sanyaye ta bar wajan zuwa cikin gida Samar ya wuce sashin baki.
Cikin sauri ya cimmata a corridor ya tsareta da mayan kallonshi, "wato karatu yasa kin soma zama mara kamun kai ko?" Ji tayi tamkar ya dab'a mata wuk'a a makoshi ta kanne kawai ta sunkuyar dakai tsawa ya daka mata ta dago a rikice"wato dariyar takima kowa kike yiwa ko? Uban me yake cemiki?". Ta turo baki kamar zatai kuka "kawaifa cewa yayi ina burgeshi...." bata karsaba ya kaiwa bakinta bugu hada jini aikuwa shar sai hawaye ya murza yatsu.
"In kara ganin dariyar nan wajan kowane gardi saina mazgeki, kauce bani gu".

Da gudu ta wuce tana shasshekar kuka, aikuwa da yamma Samar daya shigo babu kowa sai Baana a falo dai-dai lokacin ta kawowa Baana copy da cake, yana murmushi yace "nima zanci". Tsare gida tayi babu ko digon murmushi Baana yai murmushi yace "kawo masa saida tai jim sannan ta kawo.Shima Baana ta mikawa ya bashi jiki a sanyayye ya amsa nan da nan Baana ya saki jiki dashi suna hira. Bai jimaba yai masa rakiya ya wuce.

Yana shigowa ta sake shan mur, ya gimtse dariyarsa yana dubanta.
"Beenah Hajja na ciki?".
"Bacci take".
Ta bashi amsa a takaice yace.
"Da kyau ta gidana, kin burgeni walahi yanzu ki gayamun wa kike so?".
Murmushin takaici ta yi ta ce, "Babu kowa".Ya ce "ki fad'amun gaskiya bana son karya".Mamaki ya cikata da wannan salon na Baana tace "ka kyale ni nace babu kowa,na lura yanai mun maganar aure ne ni kuma ko'ina sonsa...... "
"Ke!!!".
Ya daka mata tsawa ya murza yatsu "ki kiyayeni" yai waje fuuu!.+

Kanta ta sunkuyar k'asa tana jin-jina lamarin Baana a ranta, ta goge hawaye da kyar ta shige dakinta.Cike da tunani kala-kala a zuciyarta.Wani abu ya lullub'e zuciyarta,ta kasa tantance ko miye.Tana ji bata da wani amfani in babu Baana a rayuwarta, saidai kasancewarsu tare tanajin (impossible) abune mara yiwuwa.
Baana kuwa yana fita ya saki ajiyar zuciya, zuciyarsa cike da tashin hankali.Tabbas yasan ba zai taba boye son nata a zuciyarsa ba idon ko zai cigaba da boyewa to zai illatashi.A filli ya furta.
"Allah ka bani Beenah my unique".

Kwanci tashi aka soma gudanar da lamarin bikin Mansu da Aslam lokacin suna second samister, sun shiryawa bikin sossai fannin ango da amarya kowa murna yake sunyi kamu ranar Juma'a,aka daura aure aka taho da amarya Maiduguri.
Tunda aka daura aure a Kano a ka taho da Aslam Maiduguri,nan aka fara sabon biki.Sossai Faanah ke kulawa da ita da irin kayansu na Maiduguri.
Haka kawayan amarya dakin Beenah sukaiwa tsinke duk cikinsu jinin Beenah da Mufida yafi haduwa sosai komai tare suke yi.

Asabar zasui dinner da dare hakan yasa tun safe Beenah da Mufeedah suka je akai musu kunshi ja da baki, yai musu kyau das! Su ka wuce akai musu gyaran kai da jiki suka fito chas tamkar amare.A hanzarce suka koma gida lokacin an yi la'asar gashi Aslam ta takura musu da kira.A hanzarce suka karaso suka kama aikace-aikace daganan suka amso d'unkunansa.

Shigar doguwar riga sukai su biyun gown, ta materil kalan _golden with yellow_dinkin ya zauna das, daga kasa an masa baza ta bude sossai fuskarsu tasha kwaliya sossai sukai ado da white gold takalminsu hills mai tsanin tsini zaiba da jaka karama sai wani mafici karama shima kalar.Kansu head ne blue ya yi musu kyau sossai sun kammala shirinsu cas.Mufeedah sai bin Beenah take da kallo tana tasbihi kaf wajan bata ga wadda tai kyanta ba.

Huremata ido tai tana murmushi tace.
"Yadai?".
"Kinyi kyau Beenah".
Dariya tayi "kema haka".
Kai tsaye suka fito harabar gidan duhu yayi sai hasken inji,kowa ya hau motar zuwa dinner banda su sabida Munzali ne zai kai Mufeedah ita kuma Beenah duk da bata so hakan ba.Cikin nutsuwa suka ratso harabar gidan yuuu!Idanu suka dawo kansu, cike da salon yanga suke tafiya.Karaf idonta ya sauka a kansa,zaune yake shida abokansa sunata fira shi kuwa yayi gum.Cikin takunta wanda ba kowacce mace ta iya ba, ta taho da nutsuwa gaba daya kamshinta ya cika wajan Mufeedah ce tai baya ta koma gida tilas ta tsaya jiranta.Idonsa a kanta yana tasbihi ga Allah suna hada ido ta lumshe yai saurin daukewa.

"An yi dan kai kuma ka yaba".
Ta fada a ranta, kasa kasa ta zaro wayarta tana amsawa tana satar kallonsa.Ta cigaba da amsa wayar, batai auneba sai jinsa tayi kusa da ita ya wuce.
"Kisameni a ciki".
Dam! gabanta yai mummunar faduwa, ta jima tana,wasikar jaki tai shahada tabi bayansa.

A dakinsu babu kowa yan matan sun wuce, tana shiga ta sameshi zaune kallon daya wurga mata yasa jikinta mutuwa ta zube a kan gado kanta a kasa.
"A hakan zaki fita ko? Wato kema kina biyewa yan iskan kawaye ko? Walahi kikaje dinner din nan saina mummunan bata miki"?

"Awaana..... "
"Enough!".
Ya fada da tsawa yai waje,cikin takaici ta tuge head din ta fashe da kuka,tana man zaune Mufeeda ta shigo ta kada ta raya Beenah ba magana sai kuka saida tayi me isarta ta dubeta.
"kije bazani ba".

Ta kaleta da sharin fahimta"da kin tabbata mara kirki".

"Allah kima tafi bani zuwa".

STORY CONTINUES BELOW

Mikewa tai a fusace tabar dakin, tana nan zaune wayarta nata ring kiran Samar taki dagawa ya shigo ya dauki wayar ya zare sim din ya tauneshi ya watsar ya bude wayarsa ya ciri wani layin special da baya amfani dashi ya saka mata ya zauna.
************************.
Cikin k'unar rai ta d'ago amma ga mamakinta yai mata wani kwarjini ta sadda kanta k'asa zuciyarta na zafi.
"Beenah kina jin zafina ko?"
"A'a awaana".
"Hmm!  Nasani Beenah zafina kike ji, tashi ki gyara fusksrki mu je wajan dinner".
Jin batunsa yas wani farin ciki ya ziyarci zuciyarta, cikin bazata amma gudun b'arar da aji yasata kannewa.
"A'a awaana ka barshi an kusa tashi ma".

"Kitashi nace!".
Ya fada da kakkausar murya, tuni ya koma mata ainihin Baana d'insa nan da nan ta mik'e jiki na rawa ta kafa gwaggwaronta ta mik'e.Dariya ta kamashi ganin yadda ta tsorata,a ransa yace "Allah sarki my unique".
"Gyara fuskarki tukun, ko so kike asan naci zalinki?".

Ba musu ta gyara fuskarta, tsaf ta fito kamar ma tafi farko kyau ji ya yi kamar ya rungumeta saboda yadda zuciyarsa ke harbawa".

Cikin nutsuwa ta dinga bin bayansa, harzuwa bakin motarsa sabuwa dal gidan baya ta shiga yai murmushi.
"Dawo gaba koni drivernki ne wannan sai Samar?".

Ras! Gabanta ya fad'i,"karfa Samar ya jamun sallalar tsiya ina amfanin badi ba rai?".

Lumshe ido tayi lokacin da ta samu mazauni  a gaban motar, saboda sassanyan k'amshin tsadaddan turarransa had'e dana jikinta da kuma sanyin Ac da suka had'e suka zama ababbe masu kwantar da zuciya.Cikin shauk'i ya tada motar, suka soma tafiya cike da nutsuwa ya ware volm wak'ar na tashi a hankali.
_"Love me! Love me!!  Say that you love,Kiss me! Kiss me!!  who you do you miss me"._

Wata kasala ce ta ziyarci gab'an jikinta, duk ta takura sautin wakar na mintsinar zuciyarta gashi data dago saita riski idanunsa cikin nata.Kwata-kwata ya haifar mata da mutuwar jiki can ta aro juriya ta yafa.
"Awaana yaushe zamu je Biu?".

Yabasar kamar bazai amsaba,sai taji haushin kanta dan haka taja bakinta ta tsuke.
"Me zaki yo?".
Bata kalleshi ba ba kuma ta amsaba, yai murmushi kawai ya cigaba da tuk'in wucewar mintuna goma.
"Beenah dake nake".
Ya sake magana karo na biyu, ta muskuta kawai ta motsa bakinta wanda yasha lipstick yai kyau sossai.
"Au! Ban ji ba,kasan  kunnuwan sai a hankali.Ganin Falmaht zani".

Dai-dai lokacin suka k'araso yai murmushi ya lakaci hancinta".

Harabar wajan shake take da mata da maza, kowa yana wane wannan a hankali Baana ya fito daga motar yasha kunu hakan ya kara fito da kyansa tsayyayan dirarran namiji kasumbar nan luf.Beenah ta lumshe ido tana san tsayuwa gefansa tana shaka, fahimtar hakan yasa ya dawo baya ya rankwafa saitin kunnuwanta yai mata rada.
"Madam ki saki jikinki".
Jitai kamar ta suma saboda jin dadi, karaf Mufeeda tai saurin daukarsu hoto batare da sun ankareba jerawa sukai zuwa cikin hall din tun a bakin kofa kallo ya dawo kansu tamkar wasu taurari.Tashin hankali Marwa na shirin kai kofin lemo bakinta tuni ya subuce zuwa jikinta, farin ashobe dinta ya wanke da ruwan lemo.Kwata-kwata rasa matakin dauka tayi har Baana yai mata rakiya zuwa wajan su Mufeedah yai musu sallama.Nan da nan 'yan mata suka hau lankwashe murya suna amsawa, Beenah ta tsare gida murmushi ya yi.
"Muffy ga amanar kanwata nan, zan shiga cikin taro Madam na jiran".

Bai jira cewarta ba ya wuce yana gimtse dariyarsa, ganin yadda ta hade fuska kwata-kwata ya gama fuskantar sirrin zuciyarta.A ransa dadi yake ji da ba shikadai yake kidi ya yi rawarba.
Nan da nan hankalin matan wajan ya dawo kan Beenah"gaskiya kin mori yaya mudai muna kafun kafa" aranta haushin su take tana fadin.
"Na mori yaya kona more miji?".

Bata an kara ba sunanta dana Baana ya fito cikin wanda zasu bada takaitacan tarihin amarya da ango  mintuna biyar suka shude sannan suka fita.Cikin harshan Kanuri Baana yake bayani, cike da nutsuwa da haiba yana ajiye abin magana waje ya dauki tafi.Beenah ta fiti cikin salon jan hankali take tafiya, harta hau step din Baana ya lumshe ido bayanta kawai abin kallo ne duk sai ya ji haushin kansa daya bari tazo wajan.Murya mai cike da dadin sauti ta soma bata labarin amarya harta gangaro in da Aslam ke burin auran kabilarsu ta Kanuri sabanin nata kabilar.Ta jinjina mata tare da cewa"Aslam yau buri ya cika gaki cikin kabilarmu kuma muna sonki, muna maraba dake duk da kasancewarki jiri ba jirinde ba". Aslam tai murmushi tana jinjinawa Beenah.Cikin nutsuwa ta dawo ta zauna, illahirin wajan ta burgesu.Take jerin yara suka soma shigowa shida mata shida maza cikin shigar Kanuri suna rike da wasu kaskwaye masu fida sassanyan kamshi suka zagaye amarya da ango nan fa aka fara kida.
Bayan komai ya lafa aka soma serving din mutane, Baana na gefe hankalinsa na kan Beenah haka ma Samar itama Beenah da Marwa hankalinsu naga Baana gwarzon maza.
Can Marwa tai nasarar zuwa ta zauna wajan Baana, a hankali ta dinga jansa da fira tun yana basarwa harya biyemata yana murmusawa.Sai dai rabin nutsuwarsa naga Beenah saboda yadda ya lura Samar na bibbiyarta da kuma wani a gefanta shima Kanuri ne ya gane hakan ne da tsagensa.Kafin ya ankara ya hangoshi kusa da ita, itama takaicin kula Marwa data hango yana yi ya haifarmata da son kula Marwan, wanda a lokacin yai mata bayanin kansa soka ne dan Maiduguri iyayansa da kowa nasa na garin Askira aikine y kai shi Abuja.Biye masa tayi suna hira, koba komai ta lura besan mu'amalarta da wasu mazan tana jin dadin hakan dan haka ta saki jiki sa Samar dariya take masa sossai fararran hakoranta yar-yar na haskawa amma kasan zuciyarta kamar garwashi.

Marwa sai zuba take ya kanyar da babu dadin sha, ta juyo taga Baana idonsa na kan Beenah sai huci yake idonsa jajjur aikuwa tsabar takaici kasa magantuwa tayi.Cikin sassarfa ya mike, Beenah da rabin nutsuwarta na kansa tana hangoshi tai saurin cewa"Marwan tashi ga Awaana na nan ya hanani kula kowa kar yaima rashin mutunci". Marwan ya hadiye wani abu mukut"aidama kema hankalinsa na kanki ba inda zani ya kashe ni" "Marwan ka tashi!". Ta fada da tsawa dai-dai lokacin ya iso bai wata-wata ba yai mata wata wawar fincika tai lau zata fadi Marwan yakai hannu zai tareta Baana ma haka bisa akasi hannun Marwan ya riga nasa rikota aikuwa bai auneba ya sauke masa kyawawan mari guda uku rigis wani irin figa yai mata ta kasa katabus sai janta yake tamkar rakumi da akala har cikin mota ya jefata yasa mukuli ji kake kum.Cikin masifa ya koma hall din hankalinta ya tashi da ganin yanayinsa.Yana shiga ya damki wuyan Marwan da kyar aka bambareshi ya fito yana hucci.Wani mugun birki yaiwa motar ya jata ya soma sharara gudu.
Tunda ya soma gudu take kuka mai cin rai, Baana kuwa tsabar takaici ya kasa magana kukanta na taba zuciyarsa.Suna gab da shiga gida ya dubeta"yi mun shiru kona babbalaki in kuma in saukeki ki koma wajan dan iskan saurayin naki to ki bude baki kimun magana.Wato kema ina yabanki sallah zaki kasa alwala ko? To walahi bari Abbagana ya dawo seminer cewa zan masa ya cire ki makarantar ya miki aure tunda auren kike so". Gum tayi zuciyarta cike da tashin hankali, suna shiga harabar gidan ya dubeta "ki biyo ni daki" bai jira cewarta ba ya buga murfin motar ya wuce.'YAR KURMA

A hankali ta dinga labarta musu komai, kafin ta gama gumi ya mamaye kowanansu ba kamar Dr Faanah kuwa tayi zuru Hamza ke mata bayanin wasu abubuwan da hannu wani lokacin ta dubi Yakura ta zare ido wani  lokacin ta share hawaye.Tana gamawa ta fashe da kuka ga mamakinta Dr ne yai murmushi tare da Hajja.
"Kaddarar Allah kenan Yakura, ajalinsu ne yazo a hakan kece sila mudai mun yafe miki ubangiji ya kyauta gaba sauranki neman afuwar yan uwanki da ubangijinki.
"Bazan yafe jinin mahaifina ba".

Muryar Baana kenan,kyakkyawan mafi Dr ya zabga masa  cikin fada ya soma magana kamar zai shid'e. "Kana da hankali kuwa?  Mahaifiyarka ce  fa ko kamanta matsayinta a wajanka?. Kana da abin biyanta kuwa a rayuwa? Kamanta cewar.
Ubangiji ya yi gargadi kan mutumin dake daga murya a sama data mahaifansa musamman mahaifiya.Dan kana takama matsayinka na barrister ribar me zaka ci in ka tozarta mahaifiyarka?".

"Yanzu Abbagana sai mu take gaskiya, kan son zuciya?".

Beenah ta dubeshi.

_Awaana kana tare da nutsuwarka kuwa?Hakika iyaye suna da babban matsayi a musulunci domin Allah mad'aukakin sarki ya yi gargad'i da kuma wasiya ga ‘ya’ya maza da mata akan su kyautatawa iyayensu, tare da yi musu duk abin da suke bukata matukar bai sabawa fadar Allah da kuma fadar manzo{ S.A.W } Ba. Allah mai girma da daukaka ya yi gargadi da kuma kwadaitarwa a cikin wurare da dama a cikin Alkur’ani mai girma kuma ya yi bayanin rahama da baiwa tare da samun yardarsa ga duk wanda ya bi iyayensa kuma, ya yi tanadin azaba ga ukuba ga wanda duk ya fandare kuma ya kuntatawa iyayensa, tare da yi masa mumunan sakamako a ranar tonan asiri wato ranar alkiyama._

_Allah mad'aukakin sarki yana cewa a cikin alkur’ani ma girma: mun yi wasiya ga d'an adam game da mahaifansa biyu da kyautata musu, Mahaifiya ta d'auki cikin ka/ki a wahale kuma ta haife ka/ki a wahale, cikinka da yayenka wata talatin ne duk cikin wahala.To acikin wannan aya Allah mad'aukakin sarki yayi mana wasiya wato mu ‘ya’ya akan mu kyautatawa iyayenmu musamman mahaifiya wato uwa, wacce saboda irin tsanance tsanance da ta shiga tun farkon samun ciki har zuwa ranar haihuwa wanda yake ita ce rana mafi shiga tsanani a gareta domin lokacin da mace ta gurfana zata haihu, inda zaka dauko allura ka soki idonta da ita to bazataji komai ba"._
Jikinsa ya yi sanyi ya zube yana kuka yana neman afuwar mahaifiyarsa,Yakura tana share hawaye ta kasa cewa komai.Marwa ta shigo babu sallama babu wanda ta tankawa Dr ya daka mata tsawa take jikinta ya kama rawa ta nemi waje ta zauna nasiha yai musu sossai ya kafa dokar Beenah da Marwah ne zasu ke kula da Yakura daga yau Faanah ta huta Baana yaji dadin hakan nan ya jamata kunne kan saura yaji wani zance.
43
Kwanci tashi Beenah na bawa Yakura kulawa sossai haka Dr cikin wata biyu ta yi bul-bul da ita Marwa dai tattara kayanta tai ta koma wajan Yagana ta kwashe labarin komai ta gaya musu aikuwa mota guda suka yo suka kare mata zagi tare da cewar babu su babu ita.Ranar Yakura tasha kuka wadda ta raina ta ci kashinta ta ci fitsarinta ita ta tona mata asiri sabanin mutanan da taiwa muguwar tsana.
Kwanci tashi asarar mai rai ras Yakura ta warke ranar sun sha murna da farin ciki,saukar alkur'ani Beenah da Baana sukai bayan wata daya Dr ya sata a mota har Biu suka je tare da su Baana ta nemi a fuwarsu suka yafe mata Dr yai musu alkhairi anan suka samu ana shirin aurar da Marwa zata auri dan wan Babanta.Sun ji dadi sossai tare da alkawarin zuwa taron bikin.
Bayan dawowarsu da sati biyu komai ya yi dai-dai Yakura da Faanah in ka gansu sai  ka dauka ya da kanwa ne sossai take taimaka mata wajan ayyukan gida.
Beenah da Baana soyyaya babu kama hannun yaro, dama Hajja Yakura ce matsalarsu kuma ta bada kai bori ya hau nan da nan suka mane Aslam tafi kowa murna lokacin tana laulayin cikinta dan wata hud'u.

Kwanci tashi aka tsaida maganar auran Beenah da Baana, dangi kowa murna yake ya rage saura wata daya bikin akai bikin Marwa aka kaita garin Gwaza mijinta dan sanda ne mai kirki babu laifi.Dai-dai lokacin Yakura ta fita takaba, duk ta yi sanyi yanzu har makarantar islamiyya tasa Dr ya yanko mata form take zuwa.Ganin nutsuwarta yasa Hajja ta yanke Dr ya aureta kota kara samun jikoki,Faanah ta soma tuntuba babu jinkirtawa ta amince hakan yasa ta tunkari Dr.

STORY CONTINUES BELOW

A hankali ta dinga labarta musu komai, kafin ta gama gumi ya mamaye kowanansu ba kamar Dr Faanah kuwa tayi zuru Hamza ke mata bayanin wasu abubuwan da hannu wani lokacin ta dubi Yakura ta zare ido wani  lokacin ta share hawaye.Tana gamawa ta fashe da kuka ga mamakinta Dr ne yai murmushi tare da Hajja.
"Kaddarar Allah kenan Yakura, ajalinsu ne yazo a hakan kece sila mudai mun yafe miki ubangiji ya kyauta gaba sauranki neman afuwar yan uwanki da ubangijinki.
"Bazan yafe jinin mahaifina ba".

Muryar Baana kenan,kyakkyawan mafi Dr ya zabga masa  cikin fada ya soma magana kamar zai shid'e. "Kana da hankali kuwa?  Mahaifiyarka ce  fa ko kamanta matsayinta a wajanka?. Kana da abin biyanta kuwa a rayuwa? Kamanta cewar.
Ubangiji ya yi gargadi kan mutumin dake daga murya a sama data mahaifansa musamman mahaifiya.Dan kana takama matsayinka na barrister ribar me zaka ci in ka tozarta mahaifiyarka?".

"Yanzu Abbagana sai mu take gaskiya, kan son zuciya?".

Beenah ta dubeshi.

_Awaana kana tare da nutsuwarka kuwa?Hakika iyaye suna da babban matsayi a musulunci domin Allah mad'aukakin sarki ya yi gargad'i da kuma wasiya ga ‘ya’ya maza da mata akan su kyautatawa iyayensu, tare da yi musu duk abin da suke bukata matukar bai sabawa fadar Allah da kuma fadar manzo{ S.A.W } Ba. Allah mai girma da daukaka ya yi gargadi da kuma kwadaitarwa a cikin wurare da dama a cikin Alkur’ani mai girma kuma ya yi bayanin rahama da baiwa tare da samun yardarsa ga duk wanda ya bi iyayensa kuma, ya yi tanadin azaba ga ukuba ga wanda duk ya fandare kuma ya kuntatawa iyayensa, tare da yi masa mumunan sakamako a ranar tonan asiri wato ranar alkiyama._

_Allah mad'aukakin sarki yana cewa a cikin alkur’ani ma girma: mun yi wasiya ga d'an adam game da mahaifansa biyu da kyautata musu, Mahaifiya ta d'auki cikin ka/ki a wahale kuma ta haife ka/ki a wahale, cikinka da yayenka wata talatin ne duk cikin wahala.To acikin wannan aya Allah mad'aukakin sarki yayi mana wasiya wato mu ‘ya’ya akan mu kyautatawa iyayenmu musamman mahaifiya wato uwa, wacce saboda irin tsanance tsanance da ta shiga tun farkon samun ciki har zuwa ranar haihuwa wanda yake ita ce rana mafi shiga tsanani a gareta domin lokacin da mace ta gurfana zata haihu, inda zaka dauko allura ka soki idonta da ita to bazataji komai ba"._
Jikinsa ya yi sanyi ya zube yana kuka yana neman afuwar mahaifiyarsa,Yakura tana share hawaye ta kasa cewa komai.Marwa ta shigo babu sallama babu wanda ta tankawa Dr ya daka mata tsawa take jikinta ya kama rawa ta nemi waje ta zauna nasiha yai musu sossai ya kafa dokar Beenah da Marwah ne zasu ke kula da Yakura daga yau Faanah ta huta Baana yaji dadin hakan nan ya jamata kunne kan saura yaji wani zance.
43
Kwanci tashi Beenah na bawa Yakura kulawa sossai haka Dr cikin wata biyu ta yi bul-bul da ita Marwa dai tattara kayanta tai ta koma wajan Yagana ta kwashe labarin komai ta gaya musu aikuwa mota guda suka yo suka kare mata zagi tare da cewar babu su babu ita.Ranar Yakura tasha kuka wadda ta raina ta ci kashinta ta ci fitsarinta ita ta tona mata asiri sabanin mutanan da taiwa muguwar tsana.
Kwanci tashi asarar mai rai ras Yakura ta warke ranar sun sha murna da farin ciki,saukar alkur'ani Beenah da Baana sukai bayan wata daya Dr ya sata a mota har Biu suka je tare da su Baana ta nemi a fuwarsu suka yafe mata Dr yai musu alkhairi anan suka samu ana shirin aurar da Marwa zata auri dan wan Babanta.Sun ji dadi sossai tare da alkawarin zuwa taron bikin.
Bayan dawowarsu da sati biyu komai ya yi dai-dai Yakura da Faanah in ka gansu sai  ka dauka ya da kanwa ne sossai take taimaka mata wajan ayyukan gida.
Beenah da Baana soyyaya babu kama hannun yaro, dama Hajja Yakura ce matsalarsu kuma ta bada kai bori ya hau nan da nan suka mane Aslam tafi kowa murna lokacin tana laulayin cikinta dan wata hud'u.

Kwanci tashi aka tsaida maganar auran Beenah da Baana, dangi kowa murna yake ya rage saura wata daya bikin akai bikin Marwa aka kaita garin Gwaza mijinta dan sanda ne mai kirki babu laifi.Dai-dai lokacin Yakura ta fita takaba, duk ta yi sanyi yanzu har makarantar islamiyya tasa Dr ya yanko mata form take zuwa.Ganin nutsuwarta yasa Hajja ta yanke Dr ya aureta kota kara samun jikoki,Faanah ta soma tuntuba babu jinkirtawa ta amince hakan yasa ta tunkari Dr.

STORY CONTINUES BELOW

Sun sha fama kafin ya yarda,su Beenah basu san abinda ke faruwa ba kawai sai wayar gari sukai an daura aure aikuwa sunyi murna sossai babu kamar Baana dan bayasan yai nisa da Yakuransa yanzu wani ji yake da ita yo dama yaji da ita balle yanzu data sauya hali.
Beenah na shiga level two aka soma hidimar biki, dangi daga Gwaza Damaturu Askira Biu Kano ko'ina gidan nan babu masaka tsinke Beenah ji take kamar almara yau zata auri burin ranta.

Ranar Larabar sukai kamu, tare da Kanuri day salo mai nishadantarwa shigar Kanuri akai zala an yi barin turare sossai an ci biskin gero da miyar kuka ko kubewa ko taushe ko agushi da man shanu da kakide sai wanda ka zaba. Daga nan sai dinner ita kuma ranar Alhamis. Juma'a daurin aure da yamma aka kai amarya.

Gidanta ya kayatu masha Allah ta lumshe ido tana tsananin farin ciki na auran abin sonta.
*BAYAN SHEKARA SHIDA*

Cikin ikon Allah Beenah ta gama karatunta harta soma aiki matsayinta na cikakkiyar likitan mata.

Cikin nutsuwa take saukowa daga kan matattakar benan sai kamshi take, takar wadda tai barin turare cikinta dan kimanin watanni shida zuwa bakwai yai kif a jikinta. Sanye take cikin lafaya kalar sararin samaniya fuskarta wasai sai murmushi take hanunta daya rike da rigar likitoci ta karaso cikin salon jan hankali ta kwantar da kanta kan kafadarsa tasa hannuta tana wasa da kasumbarsa.
"Beeeenah!  Zan aske fa kina damuna da yawa".
Ta shagwabe fuska ta turo baki,"dan kaga ina so shi ne zaka ce zaka aske? Nima kuwa zanwa babies dinka horan yunwa kaga an fanshe".

Cikin hanzari ya juyo da ita zuwa cinyarsa"a'a Beenah my uniqie inason babies kar ki soma,in dai kasumnace zanta gyara miki ita tana kyau ni dai ki kulamun da babies dina.Walahi banda kina son aikinki da babu abinda zaisa in barki fita tunda akace biyu ne nake zumudin zuwansu duniya, ina so mu tarawa Hajja babies da yawa kinga mu kadai ne jikokinta ko ba kya so?".

Ya fada yana hada fuskarsa da tata, tai murmushi tare da lakace masa hanci.
"Ka bani Awaana".

"Waye Awaanan jaki?".

"Au!  Na tuba".

"Yauwa mu je in kai ki tawan" ba musu suka rankaya zuwa motarsa ya sauketa asibitin da take aiki ya wuce ya gaishe dasu Hajja daga nan ya wuce aiki.

Bayan wata biyu Beenah ta haifi yaranta kyawawa gud biyu, kowa na dangi murna yake da samunsu ranar suna suka ci sunan mahaifin Baana dana Beenah suna kiransu Bakura da Abbagana.Suna ya kayatar sossai an ci an sha an wadata.Masha Allah Baana arziki ya wadata aikinsa yake cikin gaskiya da rikon amana.Fanin gona ma ubangiji ya habaka musu.

Tammat bihamdullah.
Nan na kawo karshan wannan gajeran labari mai suna yar kurma, ubangiji yasa abinda muka ji muka saurara mu fakada a kansa.


Post a Comment for "YAR KURMA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...