Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YANKAR KAUNA CHAPTER A

YANKAR KAUNA CHAPTER A

- - Post a Comment

 YANKAR KAUNA CHAPTER A


Shimfida+


Gwandu babban gari ne a jihar kebbi, masarauta ce guda mai ri'ke da sandar mulki, gari ne da ya Tara manyan 'yan boko da 'yan kasuwa. Gari ne da ya mallaki babban kwallejin 'yan mata na tarayyah wato (FGGC GWANDU) wanda akan sami dalibai daga kowani sassa na kasar nan da Nijar da ke makwabtaka damu.

Gwandu gari ne da yake fama da kwararowan Hamada (desert encrochment) a dalilin haka lokacin sanyi akan samu sanyi mai tsanani a garin haka zalika lokacin zafi yakan yawaita da har mutan garin kan kwana a waje.9


Hausawa suka rinjaye garin amma akan sami tsirarrun fulani a ciki.


Akwai wani abu guda da mutanen gwandu ke dashi wato KARAMCI, suna da dadin zama duk inda ka same su. Sukan maida dan kowa nasu ba tare da nuna bambamci ba.1


Tsayawa fadin karamcin mutanen jihar kebbi ma bata lokaci ne, gari ne mai cike da albarkan zumunci da son juna,1

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”10


{1}


"Keeeeeeeeeet!!" mota k'irar marsandi ce ta bada wannan k'arar a dalilin birki da motar ta taka ba cikin shiri ba, batare da wata-wata ba matuk'in motar wanda zaikai kimanin shekaru hamsin zuwa hamsin da biyar ya fito, bai yi wata wata ba ya share ta da mari ji kake TAAS TATATAAS!!! Hakan ya jawo hankalin mutanen da ke lodi a tashar Malisa, durk'usawa tayi don kunya da azabar marin da ta sha, fadi yake "Wawuya, Sakariya, Talaka!, in banda jahilci da da'ki'kanci da yayi ma d'an talaka yawa bakya gani ne da zaki tsallake titi ko na ubanki ne? Mstwww da ba don Allah ya tsare ba in da na fada (port hole)din can na b'ata motata fa?"17


Ganin ta tsare shi da kallo yasa ya ce " Oh yi hakuri baki taba jin (port hole) ba ko? Rami nake nufi, kinsan dai motata tafi gaba daya danginki daraja."Yana kaiwa nan ya shiga motarsa yayi gaba. Ba tare da ya sake mata kallo na biyu ba.5

"Wanena halan?" Daya daga cikin 'yan union ya tambaya.


"Alhaji Usman na hwa. Baka gani ZUNNURAIN ga jikin lambar mota tai. Ko da yake duk kuna yaka hwadi ma magana ko yak'i da jahilci baku tai ba." Daya daga cikinsu wanda dagani direba ne yake fadi.


"Allah wadaran naka ya lalace, ashe haka mutuminga yake, ko de cikin hushi yake ne, da azumin rabon abinci yakai kuma duk buda baki ga gidanai 'yan shiyarsu ka buda baki, kwano guda fa, kai 'kila ba shina ba'.6


"Shina wulai, Alhaji Usman Gwandu, duk fadin garinga anya da mai arzikin nai, gashi zaune cikin talakawa, shekaran jiya da ya bude gidan mai nai ga zauro ina ga sati biyu kenan ko wolla duk wanda yibba aiki ba dangi nai na ba, haka yake kwansan matasa zuwa Abuja, Kaduna, Zanhwara, Sokwato yana basu aikinyi. Da yake ma yaransa duk mata ne shi yasa"6


"Inji wa? Wolla yana da Da guda, Umair ba kasanga yake ba, ance ko spain ko ina, nima jiya da natai hwadi ma Alhaji mai dakina ta haihu naji suna zantawa ze dawo jibi, wallahi Rago guda da buhun shinkahwa ya aiko min. Allah saka masa da Alkhairi."2


"Ameen shi yassa banga laifinsa ba, da ma ya nakada ma shegiya duka muga qaryanta, ita ba arziki ba daga dai ta dan tai boko shike nan tafi qarfin mazan gari."2


Haka 'yan tashan Malisa suka cigaba da hiransu, ko in ce gulmansu, don duk wanda yazo wucewa se an dauko caftarsa.Tafiya su ke alamun gajiya duk ya bayyana a fuskokinsu, sun fito daga inda ษ—alibai masu karantun zane-zane (architectural students) su ke ayyukan su (Architectural studio)  inda su ka je yin assignment, zane aka sasu suyi mai uban wahala, yau kwanansu 3 kenan kullum cikin studio suke yini kafin su ka kammala. +


Sun dauki  hanyar gate din jamiar kimiyya da fasaha ta jihar kebbi da ke garin Aliero (Kebbi state university of science and technology) . Rufaida Bagudu ce da kawayenta kuma aminanta biyu Naseera  Augie da Firyal Kalgo. Dukkansu dalibai ne a fannin zane-zanen gini (Architecture) y'an mata ne masu kwazo da jajircewa wajen neman ilimi. Dukkansu yaran masu kudi da boko ne in ka debe y'ar bagudo.


Akan ce zaman mutum uku akwai munafunci tsakani amma su kam sun nuna hakan ba gaskiya bane don tun haษ—uwar su a wajen tantancewa (screening) su ka fara kawance, halin gaskiya da rikonta amana ya ษ—aga kawance su zuwa amintaka. Ba sa bambanta junansu saboda wani abin da wani ya mallaka don ko Rufaida da ta kasance daga gidan talakawa ba sa nuna mata komai sai girmamawa. 2


Tafe su ke suna hira abin su, zantuttukansu duk akan abin da zasu siya a kasuwa ne don saboda aikin da aka basu kayan abincin su ya kare ba su wani maida hankali akai ba.  Suna tafiya ba su ankara ba suka ji k'arar cin burkin mota mai razana ruwa, wanda yayi sanadin fallatso musu ruwa a jikinsu. Saboda ruwan da ya kwanta a wajen kasancewar lokacin damina ne.  Cikin fusata suka waiga, tayi matukar kad'uwa ganin  mutumin rannan ne, abin takaici ruwan duk ya bata mata aikinta, (cardboard) din zanenta daga fari ya koma kalan ruwan k'asa, Bak'inciki, fargaba da tsoro duk ya saukan mata. Yana fitowa ya duba motarsa yayi gaba ba tare da ya musu kallon arziki ba.10


Nan take su Naseera da Firyal uwayen tsiwa suka fara masifa, Rufaida bata ce komai ba amma ta sa ma kanta tsanan mutumin nan, tsana ba ko k'ank'ani ba.


"Ku tafi kawai na fasa zuwa" Ta ce tana share hawayen da ya ษ—an gangaro mata a fuska. Ta ina za ta fara? Sai da ta ษ—auki kwanaki ta na yin aikin, cikin mintuna kalilan an ษ“ata ma ta aikin. 


"Ba za'a ayi haka ba, mu je sai mu siyo wani cardboard din, kin ga tun da mu ka gano yanda ake yi sai mu sake" cewan Nasira tana mai kallon Rufaida da ga sama har kasa. 


Doguwa ce, don a matsayin ta na mace dole a kira ta da doguwa, siririya ce mai diri don duk da rashin kibanta zaka hango zubin ta da mazaunan da Allah ya azurta ta da su. 


Wankan tarwaษ—a ce wanda hakan ya ke kara fito da ita kyakkyawar bafillatana gaba da da bai. 


"A'a ni ba ma zan yi assignment din ba in ya so ya bani carry over. Allah ya isa tsakani na da mutumin nan wallahi" tace tana hawaye


"A'a, bai kai ga haka ba, haka Allah ya kaddaro mana kuma babu yanda za mu yi sai hakuri. Ku mu koma hostel Allah barshi sai mu je anjima ko gobe tun da muna da sauran indomie" firyal tace tana share mata hawayen. 


Haka su ka koma ba shiri sai chan da yamma su ka je su ka siyo duk abin da ya kamata, ba su rintsa ba har sai da rufaida ta kammala zanen ta a karo na biyu zuciyar ta na cike da takaicin ZUNNURAIN. 


"An ce kwakwalwa na aiki da sauri lokacin da mutum ke cikin damuwa ko bakin ciki, sai yanzu na yarda" tace yayin da ta kammala. Dariya su ka sa mata sannan su ka yi nafila su ka dan kwanta don samun hutu.


๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’” 


Tun bayan haduwarsu a makaranta bata sake ganinsa ba, har ta manta da wani wai shi ZANNURAIN kasancewa yau shekara 3 kenan. Tun daga ranar da ya fallatsa mata ruwa, karatun su ya cigaba da gudana su na masu jajircewa da addu'ar samun nasara. Allah cikin ikon sa su ka kammala da sakamako mai kyau sannan aka tura su bautan kasa. 


Dawowarta kenan daga jihar Kano inda tayi bautan k'asa (NYSC).  Saukan ta kenan a Malisa zata k'arasa gidansu farinciki fal a zuciyarta. Tafe take kan ta a k'asa, sai ji tayi ta bangaje mutum. Tayi saurin dago fuska, ba kowa bane sai wanda ta tsana a rayuwarta, bata ce komi ba tabi ta gefensa ta wuce. Bin ta yayi da kallo yana tunanin inda ya santa, wani b'ari na zuciyarsa na kimtsa masa abubuwa dangane da ita.Ta isa gida cike da farinciki, nan ta iske mafi soyuwa a gareta wato iyayenta suna jiran isowarta. Mahaifinta ta fara runguma don hakan mahaifiyarta ta koya mata, gaida mahaifi farko don shine shugabansu duka.

"Rufaida 'yar Albarka, dad'a kin kai ga zama (Architect), Allah yasa Albarka ya sa Musulunci ya ci moriyarsa". Fadin mahaifinta bayan ya rungume ta da kyau.

"Aameen Baba na, dafatan na same ku lafiya"? 

"Lafiya lau Alhamdulillah"

 Ta isa ga mahaifiyarta tana mai cike da farinciki. Sun gaisa tana  mai shi mata albarka itama

Bayan tayi wanka, taci  abinci ta zauna da iyayenta suna hira cikin nishadi. Har akai kiran mangariba sannan suka tashi domin gabatar da farali. 

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Sati biyar bayan kammala bautan k'asar Rufaida Bagudo suka fara bikin Naseera Augie, Rufaida da Firyal ne manyan aminanta Wanda amincinsu ba irin na AMINAN ZAMANI bane, suna son junansu kamar rai, sukan hada kai don samun cigaban kowannensu.

Tun ana saura sati daya biki suka tare a gidansu Naseera, an fara shagulgula tun ana saura kwana hudu, yau alhamis za'ayi (mother's day), shiri suke kasancewa ance k'arfe 4 za'a fara kuma basa so ayi (African time).

Karfe 3:30pm sun kammala shirinsu, k'awayen amarya da 'yan uwanta mata sun sa kaya mai kalan (royal blue) da gwagwaro kalan (orange).

Amarya da aminanta sunci kaya mai kalan (lilac) yayin da na amarya an hada  shi da ruwan azurfa (silver) nasu Rufaida iyakanta aka bar musu. 


Angwaye ma baa barsu ba, sun yi kwalilliya daidai tasu. 

Anyi komi an gama cikin  awa biyu, anan wajen abokin tagwaitar ango ya mak'ale ma Firyal shi ala dole yayi mata. Ba b'ata lokaci kuwa suka d'inke.

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Washe gari a wajen dinner, amarya da aminanta sun kara had'ewa sai ka rantse yan gidan sarakai ne, Rufaida ta bada tarihin Amarya yayin da Firyal ta bada tarihin soyayyar amarya da ango. Bayan sun zauna sai (mc) mai bada jawabi yace;

"Tunda munji tarihin soyayyar amarya da ango, yanzu  kuma za'a  kafa tubalin wani soyayyan. Soyayya ne zaa kulla da Umair, shi de ba kowa bane, yayi makarantar sakandare a kwalejin Kanta da ke argungu, ya k'ara da (diploma) a makarantar Waziri Umaru polytechnic. Sana'ar sa  dai aikin DJ ne  kuma shine DJ din wannan biki, za'a kulla soyayyarsa  da Gimbiyar da ta sace zuciyarsa cikin dak'ik'a da bai wuce biyu ba, Gimbiya Rufaida Bagudo".

8

Tafi akai gaba daya  saboda mafi akasarin wa'inda ke wajen sunyi tunanin ya fadi ne don nishadantarwa.

A bangarensu Rufaida kuwa kallonsa tayi ta gilasanta  daga inda take ta gano bai da makusa, fari ne amma ba fau dinnan ba, mai matsakaicin tsawo, kuma ba mai k'iba ba, zata iya kiransa da mai madaidaicin kyau. Duk wannan cikin kallo da baifi na dak'ik'a biyu ba ta gano duk wannan.

3

Firyal ce ta katse mata shirunta da masifanta " Wannan banza ne fa, ya raina mu wallahi, kalle shi fa (common diploma) gare shi amma (he has the guts to say he luv you, you are not just a common graduate but an architect). Mtswww Allah ya isa wallahi, ai kin wuce ajinsa, abokan ango fa tsoron tunkaranki sukai don sun San ke ba matar kowani trash bane...."

12

A fusace ta juyo ga Rufaida ganin tai mata shiru, "mtswwe kefa wata bi can ce, sai murmushi kike (like one Christmas goat, ewu kawai)". 

3

Dariya Rufaida tayi tace "Ni Allah sa ma dagaske yake, ni 'Yar wacece da zance se mai kudi, kin manta gidanmu ne, karatu na bazai taba zama dalili ba, buri na in samu kwanciyar hankali a gidan aure".

4

"Ai sai kiyi, ke da Baki ma kanki fatan cigaba, nai gaba kafin ki bata min rai". Firyal ta fada tana mai qarawa gaba.

Kafin a tashi a dinner de Rufaida da Umair har da musayar lambar waya sukai.Cikin watanni da basu wuce shida ba soyayya mai k'arfi ya k'ullu tsakanin Rufaida da Umair. Soyayya suke mai tsafta ba yamutsi da watsewa irin na zamani (Romantic Courtship). Duk wanda yasan Rufaida toh yana da masaniya akan Umair haka duk wanda ke da kusanci da Umair yasan labarin Rufaida.

+

Zaune yake tare da abokansa da wasu 'yan uwansa suna hira ya daga waya ya ga  k'arfe 5pm ta buga, ya kallesu yace 

"Guys bara na duba madam dina kafin ku gama, yakamata naje ga dare nayi, kunsan bana wasa da abinda ya shafi matata"

2

Dariya duk suka saki, guda daya da suke ce  ma Babs ne yace

"Small Alhaji kace dai zaka je ka rage zafi, wani ya kamata kaje kaga madam, a dai yi a sannu kar a k'one tun  a waje, wannan soyayya da kuke ma juna ai tayi yawa".

Dariya suka sakeyi gaba dayansu, Umair ya dawo ya zauna ba shiri yace 

"Wallahi in zaku yarda ko hannun Rufaida ban taba rik'ewa da sunan soyayya ba, buri na aurenmu yayi albarka, kuma duk auren da sai da aka gama romance ko wani shan minti kafin ayi duk albarkan ake watsarwa a waje, shi yasa mafi akasarin aure a yanzu ba albarka, in an dade wata uku kafin a fara tsanan juna ko samun matsaloli, wasu ma ko satin auren ba'a shigewa ake fara samun matsala kamar basu ne masu soyayyan nan ba , wallahi duk soyayyan zamani ke kawowa".

6

"Ni matan ke ban takaici, in sai kaga mace guda tayi soyayya da maza uku zuwa hud'u lokaci daban daban kafin aurenta, kuma duk sai sun taba shan minti da ta'be ta'be". Nasir ya ca'be

4

"Sosai ma kuwa Naas, ai sau da yawa za Kuga an taru za'a  daura aure se kuma a fasa don ba matarsa bane, in anyi soyayyar zamani kunga ya cuce ta, duk da shima sai an ma nashi" cewar umair 

Su Babs dai baki ya mutu sai hmmmmn hmmmmn suke kamar sabin kurame.

3

Umair ya cigaba "Ni kunganni nan shiyasa bana kallon finafinan batsa (blue film) ko karanta labarai da mujallun batsa (erotic stories and pornograpic magazines) duk su ke bata mana tarbiyya suna maishe mu jarababbu kamar wasu karnuka. Ku barni dai da aboki na Jackie, shima ina rokon Allah ya raba mu. Allah dai ya shiryemu."5


"Aameen" duk suka ce.

"In kun iso Malisa ku jirani, ku ce ma sweet dina zan karbi sak'o ne". Umair ya fada musu ya k'ara gaba.

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Rufaida wacce har ta cire rai da zuwanshi, tana zaune sai ga kiransa, da murnarta ta fita, bayan ya shigo ya gaida iyayenta ta shimfid'a masa darduma ya zauna a zauren gidansu, ita kuma tana kan kujera 'yar tsugune. 

"Kin yi kyau matata, wannan kwaliya haka duk don ni" yace yana kallon ta da ga sama har kasa kamar wanda aka ba aikin tantancewa,. 

"Bayan ma kwalliyan duk ya shige, na ce ko menene ya tsaida miji na, ga shi har ka fi ni kyau, anya zan yarda kuwa" tace tana juya idanun ta. 

"Ai gara na fili kyau tunda kin ga ni kaษ—ai zan mallake ki, yayin da ni kuma mijin mata huษ—u ne" 

"Ai wallahi kai ma ka sani ni 4 in 1 ce, shi ya sa sai da ka nemi agajin mutane na amince da kai" tace tana mai turo baki. 

"Afuwan Habibty, ke kaษ—ai ce wahdaki Laa sharikalaki" Ya ce yana rausaya kai alamun ban hakuri. Duk sai suka sa dariya. 

5

Haka dai su kasha hirarsu har doshin mangariba sannan yayi mata sallama, nan yake fada mata zai danyi tafiya zuwa birnin kebbi don wani kwadago da zeyi. Tai Masa fatan alkhairi tare da raka shi, suna tafe suna hira har kusan titi.

'Daga kan da zatayi sai taga jerin motoci da Mutumin ta a tsaye kamar yana waya. Tsaki ta ja tace " Buddy ni zan koma na fasa isa titin don ga mak'iyi na can yanzu sai ya bata min rai (I hate that man)."

D'agowa yayi a firgice ya kalli wanene wannan data tsana, a rude yace " Buddy mai ya miki kika tsane shi, yana da kirki fa, duk karatu na shine in bacin shi da taimakon Allah da ban kai haka ba, ina da albashi daga aljihunsa kuma iyakata in nai Masa Abu da yawa kai kudi banki, please ki sassauta masa"

"Look!! Umair na tsane shi fa, ba mai chanza shi daga mak'iyi, ina ruwa na da kirkin da yai maka, chan tsakaninku, (all I know is I will live to hate him)".

  "Hmmmn ashe kinsan sunana, kar ki manta manzo SAW ya hore mu da sassauta k'iyayya ko soyayya ga abu don a kowani lokaci yana iya sauyawa. Ina so ki sani  Alh Usman mutum ne mai kirki, Wanda kullum farincikin nakusa dashi ne abin so a gare shi. Amma watakila gaba zaki fahimci haka. Saina dawo" .

2

Yayi gaba abinsa, gefen wani shago ya tsaya, ya ciro wani k'aramin kwalba daga aljihunsa ya d'an kurbi abinda ke ciki kafin ya tafi ya sami abokan tafiyansa sukai na birnin kebbi.

Mamaki ya cika Rufaida, 


"ko me ya bats Masa rai oho,  mstww chan tsakaninku ni de bazan taba son mutumin nan ba, (he s just too arrogant )". Duk aranta take fadin haka. 


Tana isa gida ta sami mamienta na alwala, itama ta daura ta shiga daki, zaune take kan sallayarta tana ambaton Allah har akai kiran sallah.

Bayan ta idar tana nan zaune tayi zikirin maraice tana mai kaskantar da kai ga ubangijinta, har akayi isha' tayi sannan su ka zauna cin abinci da iyayenta, kwano daya  su uku. Wanda hakan ya kasance Al'adan su, kuma hakan ya jawo kauna da tausayi tsakanin su. 

Bayan sun gama suka Dan taba hira kafin ta yi musu sai da safe ta shige daki, iyayenta kuma suka zauna kallon labarin duniya na NTA.

Ta zauna ta dauki wayarta ta lalubo whatsapp dinta group din littafai ko an turo, tana da son karatun littafai amma ba kowanne ba, bata 'bata lokaci wajen karanta marasa ma'ana ba dadin labari ya dame ta kawai ba amma mai zata qaru dashi.

Tana dubawa taga an turo duk Wanda take so, Haka ta fara daya bayan daya tana mai jinjina ma marubutan. Karshe ta kawo kan KAZAMAR GIDA na takwaranta Rufaida Omar, ta jinjina mata a littafin nan, don tasan mata da yawa da suka fi siyama k'azanta, Allah sa masu halin siyama su koyi darasi. 

4

"Kai amma marubutan K'ungiyar FIKRA WRITERS  ASSOCIATION ba daga baya ba, su kan duba  matsalolin  da ke faruwa ne se su kawo gyara cikin sauki, anty Ruffy Allah qara daukaku ki miqa saqon gaisuwata ga sauran". Shi kawai ta tura group din da Rufaida ta turo labarin.

5

Ta shagala wajen karance-karance bata ankara ba se gani tayi karfe 10:39pm, Umair bai kira ba, ta kashe data sannan ta danna Masa kira. Se da ya tsinke, sannan ta sake kira, se a lokacin ya daga

"Assalamu Alaikum gimbiyar Bagudo"

"Waalaikumus salam. Ka kyauta na gode." Kawai ta kashe wayar gaba daya. Don ba ta ga dalilin da zai sa shi yin fushi ba, ko a tunaninsa fushin da ya ke zai sa kiyaya da da ta ke ma mutum ya ragu ko wani abin. 

Yayi kiran duniyar nan yaji wayar a kashe, ba shiri ya aje duk wani fushi da yake yai ta tsara mata  kalamai na ban hakuri da kuma nuna mahimmancinta gareshi. Sannan ya kwanta barci.

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Washe gari bayan ta idar da ibadanta ta kunna waya, sak'onnin da ke shigowa ne take bi daya bayan daya tana karantawa, zuciyarta na qara mata na'am Umair na sonta so bana wasa ba, ba tare da bata lokaci ba suka k'ulle kamar ba'abinda ya shiga tsakaninsu

๐Ÿ’”


          {7}


Satin Umair 2 da tafiya, babu abinda ya sauya a soyayyarsu, shakuwa ya qaru sosai har yana mata maganar da ya dawo ze turo magabatansa.

STORY CONTINUES BELOW

Ita kuma rashin aikin yi yada ba abin da ta ke yi a gida sai zane, da ta zauna tana Mafarkin ido biyu ta hango kanta a matsayin mai kuษ—i ta ke zama ta jawo kwamfutarta, nan za ta fara zana ginin da ya zo mata a mafarki.  

Zaune take, chatting take a group dinsu su uku mai suna TWINKLE SISTERS ita da aminanta, tana basu labarin zanen wani kamfani da tayi, da ace ita mai kudi ce shi zatayi, don tsarin yayi.

"Ina zanawa ina murmushi don wallahi hango ni nake a matsayin MD ษ—in kamfanin" Ta tura tana faษ—in "Allah Aameen" a fili ita kaษ—ai tana tuna kila mala'ikun Rahma na kusa su taya ta faษ—in Aameen. 

"Ki sayar  toh" cewan Firyal

"Wa na sani, kin San inada zanen gidaje sunfi 20 a qasa, da zaa siya ai da nazama hajiya๐Ÿ˜œ".

"Aikuwa akwai wani mutumi da ke Neman Zane, wai ze ma danshi kamfani kera motoci a gwandu, toh ya ki ka yi tsarin? Ki duba inda gyara kiyi se na yi ma mine magana ya amso adireshin. Kamar ofishinsu na Birnin kebbi". Naseera ta turo wannan.

"Wow you are a darling", inji Firyal

"Toh sis se na jiki, gyaran kadan ne bara na tai zuwa Google na qaro idea akan (Automobile workshop)". Rufaida ta fadi.

Haka suka cigaba da hiransu su tabo nan da chan a qarshe Naseera tai musu albishir din samun 'Da ko 'ya nan da wata 7. Sukai sallama suna masu farin ciki. 

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Safiyan litini karfe Tara da minti hamsin (9:50am) ya yi ma Rufaida a bakin offishin UZG Nig LTD  don  ance k'arfe 10am  suke fara ganin baki. Tun da Nasira ta turo mata adrishen da link ษ—in da ake shiga ayi rajista ta aika, sannan ta fada ma Umair, nan ya cika da farin ciki, yana kara mata kwarin gwuiwa. Ranar da ya zo ta fito da zanen da ta je har Kebbi ta wanko su daga kwamfutar ya ce

"in kin ga ba ki samu damar nan ba wallahi Allah ne bai yi su na da rabo ba, ko ni dai da ban san kan gini ba bayanin ki ya sa nayi tunanin ina ma ni mai kuษ—i ne, yanzu a gine ma buddy a matsayin kamfanin ta kawai in koma gefe matata Hajiya ce" Ya ce yana ษ—aga mata gira

"Ai ko yanzu kana iya bugun kirji ka ce matarka Architect ce" Ta ce tana masa gwalo. Haka ta cigaba da tuno masoyinta  wani wajen ta yi murmushi ta karkada kai, zaune take a wajen taron baki na ofishin (reception) ta na jira karfe goma ta yi ta je ta ga wanda aka ce zai duba cancantar aikinta, muryan da taji ne yasa tai saurin dago kai.

"Dady ni wallahi bazan iya sauraran kowa ba, (sweet dad am tired) tunda nazo garinnan hayaniyar mutane sun ishe ni, beside I promise you zanen da zan kawo se yafi na saura, Rufaida is an expert"

Sakin baki tayi tana kallon su.

"Sweet son as u wish,  buri na kar ka ban kunya, kyawawan halayenka, da kiyaye dokokin Allah sannan daraja na k'asa da kai pls ka cigaba. Allah maka Albarka"

"Aameen, samun Mahaifi irinka ai se 1 in a trillion"

"Naughty son" Ya ce yana tallabe masa keya. 

Toh meye hadinsu, wannan de Umair dinta ne, Masoyin da bata hada shi da kowa ba, da kuma Usman da ta tsana, oh UZG wato USMAN ZUNNURAIN GWANDU tab ashe ita ma wawuya ce da bata gane ba. Toh mahaifi fa taji Umair ya ce, ga kayan jikinsa tun daga kai har kafa ya kai ga 200,000 duk da rashin sanin kudin manya kaya da tayi hmmmm. Duk a ranta take maganar nan. Tashi ta yi da sauri don ta bar wajen, ta manta da tsaraban da tayo ma Nasira se da suka zobo,  hakan ya jawo hankalinsu Umair. 

4

Cikin sauri ta tsince kayanta ta juya ta fita, fadin tashin hankalin da Umair ya shiga ma bata lokaci ne, kalamanta da kusan ya haddace su don nuna masa Mahimmancin su da tayi na "I hate lies da I hate that man" su ka yi ta Masa yawo a kai, kawai fadawa yai jikin babansa yana " ka taimake ni na rasata kenan"

2

"Wacece?"

"Rufaidaaaahhhh"

Janshi office yayi ya zaunar dashi yace "me ke faruwa umair?

Nan Ya bashi labarinta da yanda ya mata karyan shi talaka ne, da soyayyansu har inda tace ta tsane shi.

Shiru Alh Usman yayi kafin yace "laifi na ne, mun hadu lokuta da dama ina cikin damuwa se tai min abu cikin kure kuma na wulakantata, bata taba bi na da ko kallon banza ba,kaga kuwa matar aure ce, zan je nema maka aurenta yau ba se gobe ba." Ya karasa yana lallashin ษ—an sa. 

2

"Don Allah dady ka tabbata ta amince, ba sa son kuษ—i ka je musu a mutum mai daraja irin ka ba mai kuษ—i ba" 

"Naughty boy, ranar na faษ—a maka akasi aka samu, ni dai ka kwantar da hankalinka da gaske ana hawan jini fa, so nake ka sa ni a kabari, ka dinga min addu'a ba ni in sa ka ba. Oya ta so yau work free day ne aminina zai yi aure" Ya ce suka tafa kamar wasu abokai. 

2

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Rufaida kuwa tun da bar ofishin ta ke cike da tashin hankali, ikon Allah ne kawai ya kai ta gida don a firgice ta isa Gida, tana shiga  ta fashe da kuka,

"Rufaida wa ya rasu?"

"Mamie bazan auri Umair ba ya ci amanata " 

4

"Da ya miki mene?"

Nan ta bata labari tunda ga haduwarsu ta farko zuwa yau. Tana yi tana kuka, tana girgiza kai cikin jinjina zancen

"Au ashe de baki da hankali, shi Alh Usman din bai isa ya hukuntaki ba kenan, da zaki dau karan tsana ki daura Masa. Mtsww!  zamanin nan ba dama ai maka gyara se kace tsana ne, toh kar ki aure shi man, kiyi ta zaman Gida muna goge kafada".Ko bi takanta Mamie batayi ba, Rufaida kuwa bayan tasha kukanta anan barci ya kwashe ta. Kiran sallah ya tada da ita ta tashi tayi alwala ta bada faralli.

Bayan ta idar taji motsin mahaifinta alamun ya dawo, ta fito ta yi masa sannu da dawowa tare da tambayarsa lafiyarsa da aiki. Cikin murna ya amsa mata sai ya k'ara da tambayarta nasaran abinda ya fita da ita zuwa birnin kebbi. Tayi shiru sai mamie ce ta ce

"Rabu da ita sabbeni, in banda sakarci daga kwanaki Alh Usman Gwandu yayi mata fada, kasan yanda suke tsallaka titi, toh ta tashi shige masa ya fito yayi mata fada shine ta tsane shi".

"Toh shine ya hana mata zuwa birnin kebbin ko mi, haba naga saurin dawowarta"

"Kai dai ina kaika, taje har ofishin nasu fa, shine ta iske shi da wannan yaro mai zuwa wajenta ashe d'anshi ne, shine ta dawo wai bazata aure shi ba" maminta ta k'arasa tana tsaki.

Dariya baban nata yayi yace "Ba zance  komai  ba sai naga Umair din in har yana da ra'ayi  wannan bazai zama dalilin fasa aurenshi ba, amma meye dalilinshi na boye mana asalinsa."

"Shikenan sabbeni Allah ya shige mana gaba, ke kuma tashi ki hado mana abincinmu ".

Bayan sallar laasar akayi sallama ana neman baban Rufaida, yana fita ya iske Umair da Mahaifinshi bayan sun gaisa, Alh Usman ya nemi ganin Rufaida.

"In haka ne duk mu shiga  ciki sai ayi maganar har da mai daki na". Inji baban Rufaida.

Ba musu suka shiga ciki bayan ya shiga ya sanar masu rufaida suka suturce jikinsu.

Kunun aya mai sanyi aka kawo musu sai dublan da mami tayi da safe, sunci sun sha sannan suka zazzauna don magana. Mahaifin Rufaida ya fara magana

"Nayi matukar farin cikin  ganin ka a muhalli na ba tare  da nuna kyama ko kaskanci ba, na k'ara farinciki da naga kunci abincin gidana duk da kun wuce matsayinnan nesa ba kusa ba".

Dariya Alh usman yayi yace "Inji wane yace mun wuce ku? Asalina kenan amma kafin na kai ga cewa komi ina rokon gafaran Rufaida amadadina da d'ana umair ta yafe mana duk laifin da mukayi mata. Rufaida 'yar albarka ce, duk abinda nayi mata bata tab'a ko min kallon banza ba balle ta tanka"

"Haba Alh ai kai uba ne, da ya kamata ka hukuntata ta a duk sanda tai laifi." Cewan Babanta.

"Assalamu Alaikum". Sallamar da akayi ya dakatar da Alh Usman daga magana.

"Lale marhabun da d'an Albarka." Bayan ya zauna, Mamie  ta mike cike da farin ciki, ruwa taje ta dauko ta kawo masa, da kunun aya da dublan. Shima murmushin ya ke yi   cikin tsabar farin cikin ganin iyayensa.

Baban Rufaida ya juya gasu Alhaji Usman da Umair

"Alh Usman ga yayan Rufaida, Ridwan. Yana karatu ne a kasar india, shekaransa goma sha biyu kenan rabonsa da gida saidai sak'o. Ba'a taba wata uku bai turo sak'o ba tun yana d'alibi har yanzu da yake aiki a babban asibitin Bombay."

"Masha Allah, Allah yasa albarka ya raya zuria"

"Alhaji ai yak'i aure kullum cewa yake lokaci ne bai yi ba". 

"Allah ya kaimu lokacin".

 "Aameen"duk suka amsa.

Alhaji Usman ya gyara zama yace " Nazo da k'ok'on baran auren Rufaida ma d'ana Umair amma kafin nan bara na fada maku ko ni waye. In kun amince za ku bani ya in yi murna, in kun hango matsala kuma duk za mu yi na'am da hakan" Ya ce yana gyara zama

"Alhaji in ba wata cuta da ake gado gareku ba ai ban ga wani dalili da zai sa a hana maka ba" Mahaifin rufaida ya faษ—i yana mai gyara zama.

"Ai ba daga nan bane" ASALIN ZUNNURAIN


 Ni sunana Usman amma an fi sani na da ZUNNURAIN, ni d'an asalin garin Gwandu ne kaka da kakanni. Banyi karatun boko ba amma nayi karatun muhammadiyya sosai, don a Kur'ani na taka matsayin gangaran sannan na yi littafan addini Bila adadi. 

Mahaifina malam Muhammadu mai tumatir sananne ne a wancan lokacin don shi kadai ke wannan sana'ar a wannan yankin.

Na taso cike da tarbiyya don mahaifiya ta salamatu mace ce mai hakuri da sanin ya kamata amma hakurin ta bai taba hana mata hukunta ni in dai na kuskure. 

Ina da shekara bakwai na fara bin maihaifina rumfar tumaturinsa, ina tayashi karbo kudi da mik'a ma masu siya kayansu. 

Sannu a hankali har na bude nawa rumfar lokacin inada shekara goma sha uku. Bayan shekara uku na tara riban naira dari hudu da talatin wanda a wancan lokacin ba karamin kudi bane. Sai nayi tunanin k'ara jari na dashi. 

Wata ranar laraba da bazan taba mantawa ba, na fito gida zan je saro kayan miya a jega don ya kasance ranar kasuwan garin a wancan lokacin. Na tako har  nan inda zan sami (lorry) motar kaya da ke kwashe mu zuwa kasuwan se  na hadu da wani tsoho, yana fama da ciwo kwanansa hud'u baiyi fitsari ba, yana neman kudin aiki, nan tausayinsa ya rufe ni, na kwashe dukkan kudi na na bashi dari hudu da naira hamsin, nace ya biya kudin aiki da magani.

Ina komawa gida nayi alwala nayi sallah raka'a biyu na rok'i Allah ya amshi kyautar da nayi a matsayin ibada ya albarkaci rayuwata, kada ya d'and'ana min talauci a nan duniya da lakhira.

Bayan sati biyu sai aka yi  sallama dani, ina fita naga Baban nan ne da nayi ma sadaka, na tarbeshi da murna ta. Bayan mun gaisa yake ce min ; 


"Usman naji dadin taimakon da kayi min, banda abinda zance maka se addua da nake kuma da yardan Allah zakayi arziki na ban mamaki, don Allah kar ka chanza halinka na kyauta da son na k'asa da kai. Ga zoben nan ( ya mik'o min azurfan nan da ke hannu na) duk ka gani kai min addu'an samun rahma ranar da bani, sannan ga jikata, ita kadai ta rage mun duniya ka aureta nasan zaka ji dadin zama da ita"

Ban iya ce masa komi ba sai godiya idona cike da hawaye don buri na a lokacin aure ne kuma na kasa tunkarar kowace mace.

Bayan wata takwas aka daura aurena da Jamila ta tare bayan kwana biyu, nan cikin gidanmu na tada ginin falle daya, anan akai mata jere, sai labule akasa aka raba dakin biyu.

Ba laifi lokacin arziki ya k'aru don Baba na ya daina zuwa rumfa, ni ke sauke duk hidiman gidan kuma har da 'yar kwama (bicycle) na mallaka.

Aurenmu da shekara hud'u,mun haifi yaranmu biyu Maimuna, da Aisha Allah yai ma iyaye na rasuwa, tsakaninsu kwana d'aya. Naji mutuwarsu kamar rai, daga baya na murmure amma duk sallah sai na musu addua.

Watansu uku da rasuwa matata Jamila ta haihu, nan ma mace aka samu na maida mata sunan uwata Salamatu muna ce mata Salma. Ranar sunan Salma se  ga aminin mahaifina da ke ikko, ya zo a motarsa mai kyau da tsada fijo 404. 

Bayan mun gaisa ya ciro kudi dubu d'ari  bakwai da ashirin yace "Zunnurain ( don shi ke kira na hakanan) ga kudinka, kudin mahaifinka ne, banji rasuwansa ba sai shekaranjiya da Ado d'an gidan sarki ya zo ikko kasan chan nake, toh da zan tafi mahaifinka ya kawo kudi rabi na bada rabi naje can ina juya mana. Yanzu dai siminti nake shigowa dasu, wannan kudin da rabin riban da aka samu da rabin uwar kudin kasuwancin ne na hado maka, saika fara juya su. Allah ubangiji ya jikan Muhammad da Salamatu, Yasa Aljanna ce makoma."

2

"Ameen Baba nagode, Allah Ya k'ara girma da d'aukaka. Baba in da hali ka bani auren Safiyyah, hakan zai k'ara karfin zumunci kuma ko Baba na da rai ban tsammaci akwai abinda zaifi wannan faranta masa ba".

Yayi murna kwarai kuma anan take ya ce ya bani, bayan sallar laasar aka daura aure. Jamila ta tayarda hankali sosai akan auren, amma daga baya naga suna shiri har yau bansan dalili ba. 

Shekara biyar da aure na da Safiyyah wacce ita tayi makarantar primary, ta koya min karatu A BA CA DA, ta kara wayar dani don ita tashin ikko (Lagos) ne. Acikin shekarun ta haifa min yara 4, 'yan biyu sau 2. Ni'ima da Na'ima se kuma Saudatu da Sa'adatu. 

Tun daga nan ba'a sake haihuwa a gidan ba sai bayan shekara goma. Arziki ya ninku fiye da tunani, duk sadda nayi sujjada sai nayi ma kakan Jamila da mahaifin Safiyyah addua. 

Har na cire rai da haihuwa sai ga Safiyyah da ciki, bayan wata tara ta haifamin Umair. Nayi hamdala sosai ga buwayi gagara misali. 

3

 Rabin arzikin da na mallaka na fitar aka  ba mutane jari. Alhamdulillah haihuwan Umair ya amfani dumbin al'umma.

2

Umair da sauran yara na sun yi karatu, ni kaina in ina turanci zakayi zaton a k'asar waje nayi karatu. Ranar farko da nayi ma Rufaida wulakanci saida nayi hawaye don gani nayi kaina na zaga. Ranar kuma abinda akayi shekaru fiye da arba'in baayi bane akai, wato fada tsakanin Jamila da Safiyyah. Bak'in ciki yasa nayo gidanmu na gwandu don in huce, sai gata ta shigo titi daga gani a gajiye take ni kuma na gagara mata uzuri. Nayi mata masifa, ba'ayi sati ba muka sake haduwa a makarantarsu ina sauri zanje jana'izan wani malami na shima na watsa mata ruwa, na fito don na basu hakuri, d'aya daga cikin kawayenta tayi tsaki, raina ya baci don ina da jikar da tayi sa'arta, muka sake haduwa malisa na buge ta, bata ce min uffan ba. Amma tun lokacin nake ma Umair sha'awarta, kawo min zancen Rufaida da yayi yasa ban nemeta ba. (Please Rufaida accept my apology by accepting my only son as your life partner)." Ya k'arasa zancensa yana mai tsugunawa a gabanta

13

Bak'inciki  ya cika Ridwan da ke zaune, ji yake kamar ya far ma Zunnurain da naushi."Mayaudara" Ya ce a ransa fiye da adadi 

8

"Haba Alhaji,ai ba sai ka tsuguna mata ba, ajizanci na dan adam ne, nayi ma Ridwan alk'awarin bada auren Rufaida in lokacin yi yayi, ni yanzu na yarje muku neman auren Rufaida wajen yayanta kuma mad'aurin aurenta Ridwan. Allah Ubangiji  Ya tabbatar mana da Alkhairi"

4

Jin hakan su ka kara mika gaisuwa zuwa ga Ridwan yana ta wani basarwa yana shan kamshi kamar wani Saraki. 

9

"Lallai ka iya zuwa don da har can India za mu bi ka neman iri, da fatan za'a aminta da mu" yace yana mai riko hannun sa biyu duk cikin neman alfarma. I

Kiran sallah na magriba da akayi ya tayar dasu, Umair kuwa duk da shan k'amshin da Ridwan ke yi masa bai hana shi janshi da hira ba.

Dasu akayi karatun Kitaabut Tauhid da akeyi tsakanin mangariba da isha'i. Ko da suka dawo sun iske lafiyayyen kwad'on  zogale da ruwa mai  sanyi. Sunci suna masu farinciki. Basu tafi ba saida suka tsaida zasu dawo neman aure ranar asabar. 

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Ranar asabar da karfe hud'u na yamma, maneman auren Rufaida suka iso. Yayyun mahaifiyar Umair dinne maza tare da aminan Alhaji Usman, sun sami tarba na musamman daga waliyyin amarya Ridwan da yan uwan mahaifinta da suka zo daga Bagudo.

An tsaida lokacin biki sati shida masu zuwa wanda zaiyi daidai da ashirin ga watan Rabiu Auwal. Ta kira aminanta ta fad'a musu, daga baya suka d'inke a (Twinkle Sisters) suna mamaki ashe Umair d'an gidan Zunnurain ne. Firyal sai fad'i take "Ashe da na ja miki rashi da kin biye min. (Dis kind kudi wey dem get)."


"Toh lashe money ni bansan gaminki da kudi ba" cewar Naseera.

"Wa yak'i hutu? Yanda nake ma Rufaida fatan hutu ko kaina bana yiwa wallahi."


Sukai dariya suka tashi zuwa sallah ganin an fara kira.

               ๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

A kwana a tashi yau ake fara bikin Rufaida, duk yanda 'yan uwan Umair suka so su dagargaji bidia bai samu ba saboda Ridwan ya hana iyaka wanda shi ya shirya mata a cewarsa kar a raina su.

Kayattacen (event)ya shirya ana gobe d'aurin aure. Wanda ba'ayi k'arya ba, amarya da ango sun sha  kyau abinsu. Dangin Umair sunyi mamaki matuk'a da Firyal ta bada tarihin soyayyarsu bayan Nasira da d'an tsinin cikinta ta fadi tarihin amarya. Nan wasu suka cire zargin auren kudi da suke cewa Rufaida tayi yayin da wasu suka k'ara tsanarta wai Umair na mata so da bai musu ba. Haka aka watse taro kowa da abinda ke ransa.

Bayan sallar isha'i Ridwan ya aika kiranta, yayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki, tayi kuka sosai, amma kalamansa na k'arshe ya tsaya mata a rai inda yace "Saura kuma ki kashe auren in kika hango wanda ya fishi, ban taba zaton zakiyi hali irin haka ba amma kin shayar dani mamaki (in fact the greatest of all surprise)."Kalaman Ridwan ya yi ta ma ta yawo a kwanya, mai hakan yake nufi, ko wajen barci saida ya sace ta, me yasa yayanta mai ji da ita ya mata mummunan fassarar nan. Kodai yaji wani labari ne game da ita, amma ai bai nuna mata komi ba illa murnan aurenta da Umair. Tunanin da tayi tayi kenan.

4

Washe gari an daura aurenta da Umair, daurin auren da ya hada dubban jama'a talaka da mai kudi ba tare da nuna bambanci ba, kowa sai yabonsa yake saboda kyawun halayensa. 

"Kar kayi tunanin na baka auren Rufaida don abin hannunka, na lura da abinda take so ne na cika mata, amma ka sani Ridwan yafi kowa cancantar kasancewa tare da ita don ba yanda za'a yi  na d'and'ana mata bakinciki ko na dak'ik'a guda ne, amma kasani wallahi zan iya kashe rai wajen nemo farincikin Rufaida. Hawayen Rufaida na da matuk'ar tsada (Take note of that)." Abinda Ridwan ya fada ma Umair kenan. In ba kana kusa ba zaka rantse taya shi murna yake suna hira mai dad'i don gaba dayansu murmushi da farinciki ne kwance a fuskokinsu.

15

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Ankai Rufaida d'akinta a gidanshi na Gwandu in da za su fara zama kafin duk su koma Kaduna sabon gidan Zunnurain wanda ya gina musamman don zaman dukkan Ahlinsa. Ridwan ne ya tuk'a motar da ke dauke ta, sannan shi ya damka ta amana ga iyayen Umair, sai sauran yan rakiya da su ka biyo motocin angwaye. An ma 'yan rakiya sha tara na arziki. Kowa ya koma gida cikin farinciki da fatan ma'auratan zasu sami zama lafiya.

4

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Shekara takwas kenan da auren Rufaida da Umair, kyawawan halayenta da son cigaban wanda ke tare da ita ya siya mata SO wajen dangin mijinta musamman mahaifansa, kowa ya tashi MATAR AUTA.

Zaune suke tana shirya masa jakar tafiyansa, zashi (conference) Japan akan harkar k'ere k'eren abin hawa.

"Buddy dafatan iyaka kwana bakwai zakayi, kaga ina so in shirya ma Baba waliman cika shekara saba'in da biyar a duniya. Kuma saura kwana takwas". Rufaida ke fadin haka.

"Kai Buddy kice kawai kin fara kewata, ni iyakata  kwana biyar, in sha Allah dani za'ayi komi"

"Yauwa mijina abin alfahari na d'an Safiyyah,baban Safiyyah". Sukayi dariya.

Can yace "Hajiya yau bamuyi addu'a ba, kira yaran muyi" . Ta tashi ta kira yaranta hudu da suke bitar karatunsu da akai musu.

Bayan sun zauna ya kalli manyan 'ya'yansa tagwaye Safiyyah da Usman yace "Yau addu'ar me ne zamuyi?"

"Dady ka roki Allah yasa mamana da babana su tsufa su fi grand PA tsufa, jiya don nace ban son tsoho shine yace in roki Allah iyayena su kai shi tsufa, kafin in dena  ganinku, dady wai mutuwa ake yi " K'aramarsu kenan, Zainab 'yar shekara uku.

3

Dariya yayi yace "Mami idan na mutu ai sai ki min addu'a  in kasance a aljannah kafin kuzo. Kuma kar wanda yayi min kuka, sai addua, mominku zata kasance tare daku ga grand PA". Cewar Umair

"Mamie na rabu dashi sai yafi grand PA tsufa. Muna nan har ya fara dogara sandar tsufa". Rufaida ta fadi haka   ganin jikin yaran yayi sanyi.

2

Sukayi dariya gaba daya. Ya dad'e yana koro addu'a  kafin duk suka shafa. Duk dare suke adduan Wanda a ganinsu hakan ze sa yaran su saba da yin addu'a ba wai sai bukatar addu'a ta taso ba.

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Da ka shigo gidan zaka san ana jiran dawowar wani mai mahimmaci ne, tayi kwalliya ita da yaranta, an gyara gidan cikin k'amshi, ko wani kusurwan gidan an mak'ala (WELCOME HOME DARLIN) wasu wurin kuma (WELCOM HOME DAD).

STORY CONTINUES BELOW

Kallon agogo tayi awa daya kenan ya kira ta sun sauka a filin jirgin sama da ke mando, awa daya ace bai iso unguwar  sarki ba. Kallon Khadija tayi tace "Dauko min wayata na kira babanku"

Isarta dakin keda wuya ta iske yana tsuwa, alamun kira ya shigo ta dauka tana "Dady kana ina ne? 

"Gani a kawo, hold up ne yayi yawa kai ma mamanku wayar" 

Tana karbar wayar tace "Zamu rufe..." Bata iya kai k'arshe ba  taji k'ara ta cikin wayar, sai"HASBUNALLAHU WA NIIMAL WAKEEL, LAA ILAHA ILLAH ALLAHU MUHAMMADUR RASULULLAH" .

"Hello, Hello, Budy mai ya faru". Shiru take ji, sai ta kashe tunaninta wani hatsarin yagani, don k'arar fad'uwar mota taji.

4

{13}

Shirun yayi yawa, kusan minti talatin kenan da sukayi waya. "Ko ina sarkin taimakon nan ya tsaya ne, yanzu haka sai an kawar da komai zai dawo, mtss, ko meye na kashe waya kuma?"  A zuciyarta take maganar. 

Bud'e kofar da akayi yasa ta mik'e, Alhaji Usman ne da wasu maza, ta gaishe su cikin fara'a sannan ta k'ara da "Grand PA babansu twins fa shiru, tun dazu wai yana kawo shiru har yanzu".

Murmushin karfin hali Alhaji yayi  yace 

"Tare muke dashi, yanzu za'a shigo dashi".

'Shigo dashi fa, me ya same shi?"

"Rufaida nasan kina son mijinki, soyayyar da babu algus a ciki, amma ki sani Ubangijin da Ya halicceshi yafi mu sonshi, dama aronshi ya bamu, toh mu gode masa  ta hanyar tawakkali don Ya amshi abinSa". 

2

Kallonsa take tana jin maganar kamar ana soka mata mashi. Murmushi tayi tace "INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN, Dady ni naji kalamansa na karshe, kalmar  shahada ce, Allah na gode maka  daka bashi ikon cikawa da wannan kalman. Dady a shigo dashi." Tashi tayi ta dauko sabon dardumanta da tasha alwashin yau akai zai ci abinci.

3

Ko da aka shigo dashi ta kira yaranta hud'u tana "Kuzo dadynku ya dawo, Queen (Safiyyah)  kizo da 'yan uwanki"

Lokacin mutane sun fara tsorata da ita don a tunaninsu ta samu tabin hankali.

Shigowar Queen,kai tsaye ta yaye abinda aka rufe Umair dashi tace "DADY kace in ka dawo a kwance in maka addu'ar nan in rufe maka ido ..." Nan ta karanto addu'ar da ake rufe idon mamaci. 5


  

 ุงู„ู„َّู‡ُู…َّ ุงุบْูِุฑْ ู„ِูู„َุงู†ٍ (ุจุงุณู…ู‡) ูˆَุงุฑْูَุนْ ุฏَุฑَุฌَุชَู‡ُ ูِูŠ ุงู„ْู…َู‡ْุฏِูŠِّูŠู†َ، ูˆَุงุฎْู„ُูْู‡ُ ูِูŠ ุนَู‚ِุจِู‡ِ ูِูŠ ุงู„ْุบَุงุจِุฑِูŠู†َ، ูˆَุงุบْูِุฑْ ู„َู†َุง ูˆَู„َู‡ُ ูŠَุงุฑَุจَّ ุงู„ْุนَุงู„َู…ِูŠู†َ، ูˆَุงูْุณَุญْ ู„َู‡ُ ูِูŠ ู‚َุจْุฑِู‡ِ ูˆَู†َูˆِّุฑْ ู„َู‡ُ ูِูŠู‡ِ

Kannenta suka kewayo suka kwanta a jikinshi. Hankalin Rufaida ya tashi, wai Umair dinta ne a kwance. Ranar da aka kaita gidanshi ya fado mata a rai.

Bayan kowa ya watse Umair ya shigo da abokansa, bayan anyi duk wani barkwanci da adduo'i suka tafi suka barsu. Nan ma umartanta yayi da suyi alwala sukai sallah sannan ya kwararo musu adduo'in zaman lafiya da zuria dayyaba. Yayi mata 'yan tambayoyi dangane da addini sannan ya bada daman fadamasa abinda takeso a miji fa Wanda bata so, Daren nan dare ne da bazata taba mantawa ba, dare ne mai tarin maana a gareta. 

"Mumy kin manta dady yace kar muyi kuka". Safiyyah ce me fadin haka sai a lokacin ta lura da hawayen da ke idonta. Nan ta share tana murmushi, 

"Queen ba kuka nake yi ba hawaye ne" 

2

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Ita tayi  masa wanka ta suturce shi tana kwararo masa adduar rahma da gafarar Allah.

An sanya washegari da k'arfe daya na rana za"ayi janaizarsa a masallacin Sultan Bello. 

Anso a hana Rufaida kwana tare da mijinta, amma ta cije, ta tara yaranta suka je, addua suke ta masa har barci b'arawo ya sace yaran. Kiran sallah farko ya k'ara tuna mata rayuwar aurensu domin ba'a tab'a idar da kiran sallar farko batare da ita da yaranta sun tashi ba. Umair ya koya mata K'iyamullail har ta zama ko tana fashin sallah sai ta tashi. Yanzu ma tashi tayi ta sake alwala tayi ta sallah tana mai rok'a ma mijinta gafara.Washegari tun asuba 'yan uwa suka fara isowa daga jihar kebbi, danginshi da na Rufaida sai zuwa suke mota-mota, iyayenta, har aminanta da mazajensu.

+

'Yan uwa sai shiga suke suna masa addua, masu kuka nayi, mahaifiyarsa sumanta uku daga sanda ya rasu. Don ta gagara yarda cewa Umair autanta shine ya rasu ya bar ta da mahaifinshi da sauran yayyinsa a Raye. 

Mutane sun jinjina ma Rufaida da yaranta domin sun nuna tawakkali, sunyi hakurin farko da Allah keso don manzo SAW ya bayyana hakurin farko a cewar  yana sa Allah ya baka fiye da abinda ka rasa sannan ruhin mamacinku na samun daukaka. (Ummu Abdoul nayi muku muku fatan samun tawakkalli da hakurin farko ayayin rashi).

10

Karfe d'aya saura kwata (ambulance) din da za'a sashi a ciki ya iso, suna kallo aka daga shi. Nan hankalin Rufaida ya tashi amma ta cigaba da ambaton Allah, Zunnurain na tafe da wadanda ke rike da gawan mahaifinsa, gefe ya zauna har masallaci, nan ma yana tsaye gefen grand PA a sawun farko.

Su Rufaida ma ba'a barsu a baya ba, dasu aka sallace shi, (sunna ce mata suyi sallar gawa saboda da anyi a zamanin manzon Allah, hadisi daga ummu salama tace " Manzon Allah s.a.w. ya haramta mana raka gawa kabari, amma muna sallatarsu. Sannan a wani hadisin manzo SAW yace " Duk wanda ya sallaci gawa yana da k'eeraat guda daya, sannan idan ya raka shi har aka birne yana da k'eeraat guda biyu, sau sahabbai suka tambaye shi ya rasulullAh menene K'eeraat dinnan sai yace (lada kwatankwacin) manyan dutse (Mountain). Da kuma sauran hadisai, don k'arin bayani ku duba kitaabuj janaaiz a cikin sahihain ko kuma Majmoo' Fataawa wa Maqaalaat Mutanawwi'ah li Samaahat al-Shaykh ibn Baaz , vol. 13, p. 133 ) 


suna kallo aka wuce dashi kushewarsa. Fad'in d'imbin jama'ar da suka sallaci Umair suka raka shi har makwancinsa inda da  mahaifinsa da d'ansa da yayyun mahaifiyarsa biyu aka sakashi a gidansa na gaskiya. Jama'a  sun masa addu'a, anyi hud'uba sannan aka watse, ana mai yaba ma tarbiyyar da sukayi ma zuri'arsu. Fad'i ake "ya za'ayi zuriarsa baza suyi ban shaawa ba bayan Allah Ya bashi macen kwarai, nagari ne ya hadu da nagartacciya, Allah rahamshe ka Umair"

Anyi zaman makoki, anyi sadaka da adduoi ga Marigayi Umair, ranar da 'yan gwandu suka koma nan ma wani sabon makoki a fara, wa'inda basu sami zuwa ba.

"Wai ashe d'an Alhaji Usumanu na yi rasu, walley ban sani ba se jiya, na tai ko zan dace ma gani nai mai daki na ta haihu anka ce an mai rasuwa.

"Allahu Akbar, ka tuna yarinyar nan da yimmawa wulakanci shekaranjiya ga malisa, ni da ado aw wajen, ita na ka auren gudan dansa, wallahi zo kaga yanda Alhaji ka sonta"

"Toh kai ciyaman ai shina ya rasu, ance Gada ta hwad'o  mai a can Kaduna"

"Wacce muku Gada ta, tankar mai ta hwa, inno jiya da ta shiga musu gaisuwa cewa ankayi su na waya ne ma".

4

"Tooh Allah ya jik'a nai, Ya masa rahama, shina ya bani motar da nake anhwani da ita, o'o duniya ba wajen zama na ba".2


A Tebirin mai shayin garin gwandu ake zantuttukan nan.

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

Sati biyu da aurensu, farkon matsalar data samu daga yayyunshi ne kafin su koma gidajen aurensu, su shigo har inda take su zage ta tas, in aka cire Salma da tafisu sanyin hali. Sai da Alhaji Usman ya tara su yayi musu fad'a sannan yasa kowaccensu ta koma dakinta.

STORY CONTINUES BELOW

Umair ya nuna mata so, tun ba zuwansu honey moon ba, sunje (Yankari game reserve) dake jihar Bauchi, satinsu biyu anan.

4

"Rufaida ina sonki, bazan taba ha'intarki ba, (all i want from you is luv and happiness) kar kice zaki guje ni duk runtsi"

Kalaman Umair kenan wataran suna zaune a gefen ruwa da ke cikin yankari. Janta yayi suka fada cikin ruwa. 

Hawaye ne shar  a idonta fadi take " Buddy ka yafemin na gujeka a yayinda aka kaika asalin gidanka, ba yanda na iya ne, Ya Allah ka sada Umair da rahamanka, Ka yalwata masa, Ka sa inda yake yafi nan da ya bari, miji na bawanka ne mai yawan bauta maka a zahiri da badini, ya Allah ka yafe maSa kuskuren da yayi cikin rashin sani ko ajizanci na bil adama". 

2

Kuka take mai tsima ran mai sauraro, hajiya Safiyyah ce tsaye bakin k'ofa, tana mamakin tunanin me Rufaida keyi take murmushi da hawaye, jin kalamanta da kukanta yasa ta karaso.

Rungumarta tayi kamar zata maida ta ciki.

"Haba Rufaida watansa shida da rasuwa duk sannan bakiyi kukan nan ba sai yanzu?  Auta na cikin kyakyawan yanayi inshaAllah, jiya fa kika sa aka hak'a masa rijiya. Me yake buk'ata bayan wannan fisabilillahi?"

"Mummy ina son Umair ya na sona, Mummy mutuwa mai YANKAR KAUNA, ina ma zan mutu in huta"

2

"Kul, kar ki b'ata ibadanki, kinyi tawakalli sanda ake so, shaidan ke neman rusa miki aikin ki saboda haka kar ki bari ya ci nasara akan ki"

"Mummy  ki mun addu'a, ina jin kewarsa sosai, mummy samun miji kamar Umair sai an tona, mummy miji ne mai daraja iyalinsa, mummy zancensa kullum shine Bayan uwata sai ubana banda kowa sai ku Buddy, mummy duk mun kasa biyansa son da yake mana, bamu bishi ba".

"Rufaida ba za ki yi shiru ba wai, toh kiyi ma kanki gata mana ki dawo dashi duniyar." Haj Safiyyah ta fadi a fusace. Sai ta koma lallashinta da yi mata nasiha har barci ya kwashe ta.

"Alhaji yakamata fa asan abinyi, ka sama ma Rufaida aiki (to keep her busy) wannan soyayya ban taba ganin irinsa ba." Haj Safiyyah ce ke fadin haka, da guntun hawaye a idonta.

"Shi yasa lokacin da ake zuga ki kina mata wulakanci na hana ki, kin san cewa Umair ya sha giya?"

"Giya fa kace Alhaji, "

2

"Kwarai kuwa, Allah cikin ikonsa da taimakon Rufaida ya tuba tun aurensu na shekara biyu. Yanda kuwa akai na sani ta hanyar karanta diary dinshi ne, a cikin motar sa aka tsinta, gashi ki karanta"

"Amarya da ango ne yau ake zantawa, ko tsohon (love) d'inne ya motsa". Shigowar Hajiya jamila kenan take fadi.

"Uwargida sarautan mata zancen 'yarku Rufaida muke tasa damuwa a ranta."

"Alhaji me za'a mata ya wuce ta koma gidansu tunda dai ba gadon gidannan gareta ba, abinda ya had'a ya raba. Matar da bata damu da mutuwar mijinta ba, damuwarta kenan gado, yau aka raba zata warke"

Ba Alh Usman kad'ai ba, hatta haj Safiyyah taji haushin zancen. Kallon agogo yayi yaga sha biyu da minti ashirin na safe. Ya daga waya ya kira wani lamba bayan amsa sallama se suka ji yace;

" Yauwa Barrister in baka komi kazo don Allah, da file din Umair....... Toh nagode se kazo."

"Alh yanzu biye mata zakayi, ashe dai dama can ba son Rufaida kake ba, indai  har zancen nan zai tasiri". Tasa kai tayi gaba.

Barister na isowa yaje d'akin bak'i  da kanshi ya kira baban Rufaida kasancewa yazo duba su, yana shirin komawa washe gari.

Alh Usman ya bude taro da addua sannan yace "Na tara mu anan ne domin a sauke ma marigayi Umair nauyin da ya bar mana wato rabon gadonsa, ga barrister nan wanda bayan karatun law yaje jami'atul islamiyya da ke madina yayi karatun rabon gado (Ilmul-Mirath). Yana da dukkan dukiyar Umair a rubuce don haka Barrister bismillah".

Duk suna zaune, Haj Safiyyah kamar ta fashe don haushi yayinda Rufaida kuka kawai take, har barrister ya gama kasafi ya tambayya ko da mai ja.

"Nagode kwarai da rabon nan nawa da Umair ya wasicce a bani, ba abinda zance se Alh ya jikan Umair" haj jamila kenan, ta kammala tana mai rushewa da kuka. Gidan ruwansa da ke anguwan kanawa ya ce a bata tunda bata da gadonsa.

"Ni a matsayina na mahaifiyar Umair kuma uwa ga Rufaida na yafe kasona, na mallaka ma Rufaida halak malak ba don na raina ba sai don tafini sanin yanda za'a sarrafa shi, mungode Barrister, Allah gafarta ma Umair ya yalwata masa". Tana gama fadi ta tashi zata fita, Alh Usman ya hana ta.

"Zanyi magana biyu da nake so duk ku zama sheda,


Ni gado na, na bar ma jikoki na, duk kayan sawan umair za'a aje ma Zunurain, ko da zai kasance baa yayinsa amma nasan zaiyi farin cikin mallakarsu,


na biyu kuma idan na riga Rufaida rasuwa, ko da ace ita tafi kowa kud'i a duniya, a bata kaso daidai kason da za'a ba sauran yara na.4


Allah Ubangiji ya jik'an Umair ya Rahamshe shi". 

Kuka Rufaida ta saki mai tsuma zuciya, fad'i take a ranta wani irin so ne mutanen nan suke mata. Haj Jamila a dayan 'bangaren bak'inciki ya cika ta, mai Alhaji ke nufi.

Duk yanda aka so baban Rufaida yayi magana yak'i, in bacin addua da ya kwarara ma Umair kana yai ma Alh da zuri'arsu bai kara komai a kai ba aka watse taron

Bayan sun tashi, Haj Jamila ta bishi d'aki. Tundaga bakin k'ofa ta fara 


" Injin dai tare da tsohonta zasu tafi, ni a bani 'yan biyu don ban san dad'in d'a namiji ba, Allah barshi safiyyah ta rik'e k'ananun." Idan masu karatu sun tanka ma ta toh ...

Washe gari bayan shatara na arziki da aka hada ma mahaifin Rufaida, Alh Usman yace duk su shirya dasu za'ayi tafiyar. Haj Jamila kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha don murna, bata ko b'oye ba. Ba wanda yasan dalili amma ita Haj Jamila tunaninta Alhaji ya dauki maganarta.
Tafiyar awa takwas ya sada su da garin Gwandu daga Kaduna don ma motar gida ce. Rufaida da mahaifinta da yaran har gida garin Malisa suka isa.
Washe gari da safe Alhaji Usman da matanshi tare da aminansa biyu suka dira gidansu Rufaida. Bayan gaisuwa da yi ma juna ta'aziyya da ban gajiyar hanya, aminin Alh Usman, Alh Bilal Gwandu ya ce,
"Mun zo neman iri karo na biyu, wannan karan ba neman aure muke ba, rok'on arziki muka zo. Tunda kuka bamu auren Rufaida bamu taba d'aukar Rufaida a matsayin suruka ko matar d'a ba, face 'ya, munzo ne neman alfarma ka bamu Rufaida ta kasance k'ark'ashin ikonmu har mu aurar da ita ba don kun gaza ba sai don k'aunarmu gareta".
Shiru ya ratsa wajen, kafin baban Rufaida ya kirata da maminta ya maida musu abinda ya kawo su Alhaji. Sannan yace;
"Jiya na tabbatar da Rufaida tayi dacen iyaye ba don kyautar da kukayi mata ba, sai don ina d'aki Hajiya Safiyyah tazo ta rok'i in bar mata Rufaida, har da kukanta amma nace ta bari nayi tunani akai. Yanzu kuma kun zo  da wani zancen, ko don darajar 'ya'yanta mun bar muku ita, Allah Ya baku ikon riko".
Godiya suka cigaba da yi kamar yayi musu kyautar duniya. Basu bar gidansu Rufaida ba sai bayan azahar, Hajiya Safiyyah ta saki jiki, da ita akai girkin ma.
Washe gari, sukayi harama suka koma kaduna kowa na farinciki in banda Hajiya Jamila da ta dinga fad'in "Kun bari an asirce ku,ni wallahi kurwata kur, nama na d'aci gareshi"
5
Ba wanda ya tanka mata har suka isa Kaduna .
๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”
Bayan sallar isha'i Hajiya Safiyyah ta dauko k'undun sirrin (diary) Umair ta fara karantawa..
Shafin   farko abinda ta fara gani shine "( Am just me, Umair bn Uthman.

Rule 1: I don't Imitate others for no one succeed by imitation.

Rule 2: I don't envy for it leads to failure.

Rule 3: I have no enemies, I luv every one.)
Ni  din nine, Umair bn Uthman.

Doka na d'aya; Bana kwaikwayo,  domin duk mai son cigaba bazai kwaikwayi kowa ba. (Kira ga masu yin abu don wasu sunyi, in wani yayi rawa ya sami kudi wani in yayi jibga zai sha....~Ummu abdoul)
8
Doka ta biyu; Bana hassada domin hassada na kaiwa ga asara.
4
Doka ta uku; Banda mak'iya, ni ina son kowa.
3
Ajiyar zuciya tayi tace
" Umair haka nan kake, baka ma sanya kai mai tsoron Allah da kiyaye dokokinsa ne ba". Ta share hawayen da ya gangaro mata sannan ta  bude shafin gaba.
Ta cigaba da karantawa wanda da harshen turanci duk yayi su.
"Duniya banda amini daga k'undin sirrina sai Jackie. Wanda muka hadu tun zamanin kwaleji.

Ina son Jackie amma yana sani aikata zunubi hawaye.
Ban taba zina ba Alhamdulillah...
Ta tsallake wasu shafika duk zane yayi gashi da yaranshi, ga iyayenshi sun tsufa ya so musu ziyara, abin mamaki sai taga yayi ma Hajiya jamila k'aho irin na zanen shaidanu.
4
Tace "Hmmmn, auta kenan uwar dakinsa ce haka?"
2
Ta cigaba da kallon zanensa kasancewarsa gwani a zane yasa ta iya fahimtarsa.
STORY CONTINUES BELOW

Shafin da ya cigaba da rubutu yace;
"Ni da sweet dina da nafi so a duniya Hehehe za a so sanin sweet, dadyn a ne. Muna tafiya na hango wata kyakyawar budurwa mai kyan sura tafe cikin jallabiya daga gani daga bautar k'asa ta dawo. (Ooshhh!) sunyi karo da sweet dina, Allah Yasa itace matar da nake gani a mafarki ( Umair is in luv) Umair ya fad'a kogin so, (nan ma zane ne daga gani ba tambaya Rufaida ce).
Alhamdulillah, nayi bincike akanta, sunanta Rufaida Nasir  Bagudo. 'Ya d'aya tilo ga iyayenta, Architect ce, bata da son duniya, kuma babbar k'awarta zatayi aure ranar asabar.
Na shirya zuwa bikin a matsayin mc, da kyar aka dauke ni don saida na nuna kyauta zanyi masu (hotel)d'in suka dauke ni don samun b'agas.
2
Hak'ata ta cimma ruwa don Rufaida ta so ni ta karbe ni a matsayin masoyi duk da tsantsan talauci da nake nuna mata ina ciki. Oh ni Umair nafi kowa dace..
Rufaida ta tsani mahaifi na, (nanma yayi zane nemai nuna duk abinda ya faru daga rakiyar da tayo masa zuwa haduwan su a birnin kebbi)..
Shafin gaba zanen hotonsa da na Rufaida sai wani da bata gane ba yasa masa bak'in kala. "Oh ni safiyyah ko waye wannan kuma, Umair kenan Allah Ya maka rahma". Murmushi tayi had'e da d'an hawaye. Ta cigaba...
"Mama Jamie ta tsane ni, tana neman raina kowa nawa mumcy ta kasa ganewa. Guba tasa min a abinci gashi gobe aurena, sai kinyi kuka, don sai nayi yara fiye da naki zan mutu. Nan ya zana k'aton fuskanta tana kuka, k'asa yasa kad'an kenan da fuskansa na dariya.
2
Shiru tayi tana tunani, a iyakar saninta Haj Jamila na son Umair sosai. Bata taba nuna gajiyawa wajen kula dashi.

'Hmmmmn' ta sauke ajiyar zuciya sannan ta bude wani shafin.
"An daura aure na da Rufaida. Allah sa itace uwargida ta har a Aljanna.
Alhamdulillah, Rufaida ta cika 'ya (se da hajiya Safiyyah ta saki murmushi kamin ta cigaba)
A yau ni umair na kasance cikin bak'inciki mahaifiyata ta dauki zugan mama Jamie har sun wulakanta min Rufaida, hakan yasa na sha karamar Jackie kasancewa ban da raguwan wanda nake sha.
4
Na tabbata a buge na dawo, don zan iya tuna na iso falonmu amma bansan mai ya faru ba.
Washegari na farka rungume jikin Rufaida, idanunta ja wur daga gani ba tambaya kuka taci ma'ishi.
"Budy laifin me na maka da zaka sha giya?" Ta karasa tana mai k'ara sa kuka.
Ban iya kallon kwayar idonta ba amma naji kunya sosai don gani nake na gama rasa farinciki na.
Rufaida bata chanza min ba se ma k'ara kula ni da tayi. Akwana a tashi ta fahimci Jackie, ita ta siyo min duk don farinciki na. Har ta sa min timetable din shan Jackie, tun muna sau biyu a sati, muka koma sau daya a sati. Yanzu ma ina sati biyu bansha ba. poorJackie, ya zana  alamun yana hawaye.
5
Ta na karantawa duk sauran soyayyansu ne, nan ta k'ara tausayawa Rufaida ganin duk shan giyan da umair keyi bata fasa kyautata masa ba se ma amfani da dabaru wajen hana shi aikatawa. "Allah ka rahmashe umair, ka sada shi da mala'ikun rahma. Ka biya Rufaida da mafificin sakayya" ta fadi, kafin ta cigaba da karatu
"Shekaranmu biyu da aure, bazance ga aibun Rufaida ba, matar alfahari ce, ga tsafta, ga son 'yan uwana. Ta haifa min yara biyu kyawawa da bana dana sanin kasancewarta uwarsu don zata sa su a turban kwarai (ni kam cewa nayi bata kai takwaranta Rufaida Omar kirki da halin kwarai ba)
4
Text dinta nayi receiving da bazan taba mantawa ba, kuma dalilin barin shan Jackie tare da danasanin fara abota da Jackie. Ga text din kamar haka
" Dadyn twins don Allah k'arin bayani nake nema akan wannan,
( Narrated Umar ibn al-Khattab RA: When the prohibition of wine (was yet to be) declared, Umar said: O Allah, give us a satisfactory explanation about wine. So the following verse of Surat al-Baqarah revealed; "They ask thee concerning wine and gambling. Say: In them is great sin...." Umar was then called and it was recited to him. He said: O Allah, give us a satisfactory explanation about wine.
Then the following verse of Surat an-Nisa' was revealed: "O ye who believe! approach not prayers with a mind befogged...." Thereafter the herald of the Messenger of Allah (peace be upon him) would call when the (congregational) prayer was performed: Beware, one who is drunk should not come to prayer. Umar was again called and it was recited to him).
He said: O Allah, give us a satisfactory explanation about wine. This verse was revealed: "Will ye not then abstain?" Umar said: We abstained. (Dawoud - Book 26, Hadith 3662) ).."
3
Hankali na ya tashi, ban taba fahimtar illar giya ba saida na karanta.
Shiru nayi batare da na bata amsa ba, se can ta sake turo wani cikin yaren hausa "Kad'an daga cikin illar giya shine zai saka ka aikata dukkanin Al'kaba'ir (manyan zunubai) da kake gudunsu. Ga cuta da yake sawa uwa uba zunubi. In baka dena ba zan fara don mu had'u a wuta, kaga mun cuci yaranmu da iyayenmu".
Nayi bakincikin farawa, amma tun daga ranar ban sake ba.
Tayi ta karanta sauran, wasu akan soyayyarsu, haihuwansu da kuma dukiyoyinsa. Har zata rufe sai shafin kusan karshe ya dauki hankalinta.
"Mama Jamie ta kiran yanzu, tana mai tabbatar min mutuwata na kusa, hmmm zangani in rayuwata na hannunta".
"Wannan na iya zama rubutu na k'arshe. Ya Allah ka tsare min zuriata daga sharrin masu sharri. Kasa zunnurain ya zama dodo ga mak'iya na". Yasa hannu, kwanan wata da kuma lokaci, hakan yazo daidai da minti 5 kafin hatsarinsu

Post a Comment for "YANKAR KAUNA CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...