YANCIN MATA CHAPTER B KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YANCIN MATA CHAPTER B KARSHE

YANCIN MATA CHAPTER B KARSHE

- - Post a Comment

 YANCIN MATA CHAPTER B KARSHE


* Da kallo Ummee ta bishi tana tausaya masa.

+

Hafiz kuwa yana fita yayi murmushi yace "Wasa farin Girki."


Alwala yayi ya huce masallaci.

Har suka dawo Hafiza bata farka ba , cikin sanyin jiki yayi musu sallama ya tafi gida.


Abbie ne ya kalli Ummee yace "ya kike ganin zamu b'ullowa Wannan lamarin?".

Ajiyar zuciya tayi tace " ni abun ya fara bani tsoro wallahi kalli yadda Hafiza ta koma lokaci d'aya anya kuwa ba asiri akayi mata ba?".

Abbie yace "Allah ne masani mu bari ta farka muga yanayin jikin nata, ni mijin tane yake bani tausayi ji yarda ya koma shima kai Hafiza tayi dacen miji mai sonta."

Ummee tace "nima addu'ar Dana kewa Hanifa kenan Allah ya bata miji kamar Hafiz."

Har dare yayi amma Hafiza bata farka ba .

Hafiz kuwa yana can gida amma ya kasa komai gani yake gidan yayi masa girma , jinsa yake kamar wani sabon maraya .

A lokacin ya kuma tabbatar da irin son da yake yiwa Hafiza , a fili yace "kiyi Hak'uri Hafiza banyi niyar fad'a miki yanzu ba amma ganin yadda kika shiga damuwa yasa na sanar dake , banyi hakan da cutar dake ba , komai zai tafi yarda kike so farin cikin ki shine nawa" haka ya dinga magana shi kad'ai har bacci ya d'auke shi.

Hafiza kuwa bata farka ba sai cikin dare , mik'ewa tayi ta kyar sabida yadda kanta ke ciwo sosai , alwala tayi ta gabatar da sallah .

Bayan ta idar tunani ta fara a ranta tace "Lallai ma Hafiz ya cika d'an wasan kwaikwayo yayi wasa da hankali na yanzu kuma yana wasa sana iyaye na , ya zanyi nayi abinda nake sonyi? ".

Ajiyar zuciya tayi a fili tace " in har inason samu shaida a kansa dole na cigaba da zama dashi amma badan zaman aure ko wani Abu ba zan zauna dashi ne akan ina bincike a kansa , tabbas haka za'a yi tunda gobe nake son shigar da k'ara kotu inason samun tsaida kafin a fara sauraren k'arar ."

Murmushi itama tayi ta cigaba da fad'in "Dole gobe naje na tattaro duk wacce nasan yayiwa fyad'e , k'arshe ka yazo Hafiz" ta fad'a idon ta na cikowa da hawaye Dan tabbas tana mutuk'ar k'aunar Hafiz amma babu yadda zata yi Dole ta cika alk'awari .


STORY CONTINUES BELOW

Washe gari Hafiza ta tashi fes da ita kamar ba ita ba , ganin haka sai hankalin su Ummee ya kwanta .

K'arfe takwas motar Hafiz ta tsaya a k'ofar gidan su Hafiza , cikin nutsuwa ya fito daga motar ya aika yaro aka sanar da zuwan sa.

Izini aka yi masa da ya shigo , cike da tak'ama ya k'arasa gidan bakin sa d'auke da sallama.

Bayan sun gaisa da su Ummee aka shigar dashi parlour ya zauna.

Babu jimawa Hafiza ta fito ba tare da ta kalle shi ba tace "Me kazo yi gidan mu a Wannan safiyar?."

Murmushi yayi yace "Haba Hafizty ko gaisuwa babu ? To wajan Matata nazo ko nayi laifi?".

Tsaki tayi tace " kaje ka samu matar ka danni ba matar ka bace , na amince zan zauna dakai amma fa ba zaman miji da mata nake nufi ba zan zauna da kai a matsayi na na wacce take bincike akan ka , yau zan shigar da k'ara kotu nasan zuwa sati mai zuwa za'a fara sauraran k'ara , zaka iya d'aukar lauya idan kana so domin ya kare Mara gaskiya , sai nayi nasara a kanka insha Allah. "

Murmushi yayi mai sauti yace "Ok to Yanzu muje a shigar da k'arar ko ?".

Tab'e baki tayi tace " Oho maka dai nidai na fad'a maka, Ku......" Maganar ta katse sabida shigowar Hanifa d'auke da tiri na kayan tea.

Ajiyewa tayi ta fita .

Kallon Hafiza yayi yace "Hafizty zuba min abincin mana."


Wani banzan kallo tayi masa tace "indai ni zan zuba maka wallahi baza ka ci ba".


Yace " ok ni kuma bazan ci d'in ba , yanzu ya maganar k'arar da zaki kai?."

Ganin yana nema ya mayar da ita mahaukaciya sai ta tab'e baki ta kauda kai bata ce komai ba.

Murmushi yayi danshi wallahi burgershi take Ashe in tana fushi kyau take k'ara yi .

Yace "Yauwa jiya kince ki tsane ni right?."

Ba tare da ta juyo ba tace "Kwarai kuwa domin bazan tab'a son fasiki ba."

Tashi tsaye yayi tsam ya matso kusa da ita sosai ya rik'e hannun ta gam yadda zata iya kwacewa ba yace "ki kalli ciki idona ki maimaita abinda kika fad'a."

D'ago wa tayi ta kalli idon sa amma ta kasa furta komai sai k'ok'arin kwace kanta take .

Yace "Ashe dai har yanzu kina sona tunda gashi kin kasa fad'a min" ya fad'a yana jawo ta jikin sa.

Rungume ta yayi tsam a jikin sa yana sauke ajiyar zuciya , cikin wata irin murya yace " Nayi missing dinki sosai my Dear."

K'ok'arin kwace kanta take amma ta kasa sai mutsu-mutsu take .

Cikin tsiwa tace "kaga Malam ni ka cika ni bafa y'an matan da kake sawa ake d'auko maka bace."

Banza yayi mata bai kula taba kuma bai sake ta ba, ganin haka yasa tace "Aikin banza daman an saba yiwa y'ay'an mutane f......." Had'e bakin su yayi waje d'aya yana aika mata hot kiss.

Nan take jikin ta yayi sanyi ko ko motsin kirki ta kasa yi , bak'in ciki ya cika ta gashi a cikin gidan su salan wani ya shigo.

Bai sake ta sai da ya gaji Dan kansa sannan ya cika ta ya zauna a kan kujera yana lumshe ido.

Hararar sa tayi tace "Tsabar iya fasikanci a cikin gidan mu a kake Neman yi min fyad'e."

Yana jinta amma baice komai ba .

Ba tayi aune ba taji ya jawo ta ta fad'o jikin sa , bai tsaya wani tunani ba ya d'aga rigar ta yana shafa cikin ta.


Yace "oh my unborn nayi missing dinka sosai fa" ya fad'a yana yi mata kiss a ciki.


STORY CONTINUES BELOW

Fincike jikin ta tayi ta mik'e tana fad'in "wai meye haka ne ? Ka saba tab'a y'ay'an mutane a cikin gidan su shiyasa nima kake min to ni baka isa ba wallahi."

Zuba mata ido yayi yace "Hafizty na kenan kema fa kin zama y'ar iskan yanzu tunda gashi har cikin d'an iska ne dake, Any way d'auko mayafin ki mu tafi" ya fad'a yana mik'ewa.


Ciki! Hafiza ta maimaita a ranta , "Kai wasa yake bani da wani ciki" da Wannan tunanin ta sakar masa harara ta shigewar ta d'aki.

Mayafi ta d'auko tana masifa ita kad'ai tana cewa "wallahi ba daman akwai abinda nake nema ba da babu dalilin da zai saka na koma gidan sa " yafa mayafin tayi ta fito daga d'akin.


Sallama suka yiwa su suka fito daga gidan.


Tunda suka shiga motar babu Wanda yayi magana a cikin su kowa da abinda yake sak'awa a ransa .

Hafiza tana tunanin gata ga mai laifi kuma wai a matsayin mijin ta , wannan abun yana b'ata mata rai fiye da tunanin mai karatu , musamman  idan  ta tuno irin yawan mata da yayi mu'amala dasu sai taji ranta ya kuma b'aci .

Hafiz kuwa tunanin yadda shari'ar nan zata kaya yake Dan yasan Hafiza baza ta tab'a samun nasara akan sa ba sai in shi yaso ,amma zai bada akan a ko dan ya sauk'ak'a mata amma fa kafin ya bada kansa sai ya walahar da ita sosai sai ta rasa yadda zatayi wallahi , murmushi ya saki ya juyo ya kalle ta ya cigaba da tuk'in sa.


Basu wuce ko ina ba sai babbar kotun garin Kaduna.


Suna tsaya ta bud'e motar ta fita , wajan wasu mata ta nufa a cikin su har da Iman y'ar mak'otan su da alama duk Wanda suka shiga hannun Bad man ne.

Tare suka shiga suka shigar da k'ara akan case d'in , da yake daman abinda ake jira kenan nan da nan aka bata sammaci ta bawa Bad man.

Nan da nan mutane suka fara kallon Hafiza ana mamakin inda ta samo Wannan mutumin har kuma ta shigar da k'ara a kansa.

Kafin kace me y'an jarida sun cika wajan kowa yana son yaji ta bakin Hafiza.

Wani d'an jarida ne yazo inda Hafiza take yace "Barr ko zaki iya fad'a mana yadda kika yi kika gano waye Bad man duba da irin lauyoyin da suka neme shi amma basu same shi ba?."

Tsayawa Hafiza tayi tare da kallon motar Hafiz sakar mata murmushi yayi yana shafa sajen fuskar sa , kallon d'an jaridan tayi tace "Zuwa jibi za'a fara sauraren shari'a kowa zai ji komai" tana gama fad'ar hakan ta koma wajan y'an matan.


Kallon su tayi tace "To yau mun shigar da k'ara akan sa idan akazo kotu ko wacce ta fad'i gaskiya abinda ya faru da ita , kar kuji tsoro rashin maganar Ku shine zai ja sunyi nasara akan mu , amma idan kuka bud'e baki kuka yi bayani ina kyautata zaton zamuyi nasara."


Ko wacce ta amince da alk'awarin zasu yi , sallama tayi musu ta koma mota.


Tana shiga ta mik'a masa takardar tace "ga sammaci daga kotu saura kuma yau ka gudu."

Y'ar dariya yayi yace "Keda kike matar Wanda ake k'ara ki rik'e kawai idan ranar tazo kya fad'a min."

Yace "uhum wai wancan matan Dana ganku dasu fa suna lauyoyin ne?".

Cikin fad'a tace " Wad'anda ka b'ata wa rayuwa ne."

Zaro ido yayi yace " tab daman a cikin harda waccan mummunar ?".

Haushi maganar sa ta bata , juya tayi ta kalli yaran tace "Yanzu duka wad'an can yaran babu wacce baka Santa y'a mace ba" ta fad'a tana fashewa da kuka.Jingina kansa yayi a kujera ya lumshe ido shi kansa yana mamakin hakan amma sai yace , "Allah sarki kishi ke damun ki ko?".


Tsaki tayi bata ce komai ba , amma a ranta wani bak'in ciki take ji , zuciyar ta na zafi.


Yace " Duk ba wannan ba nifa yunwa nake ji" ya fad'a tsare ta da idon da suke kashe mata jiki.

D'auke kai tayi tace "Sai ka samu mai dafa maka ai".


Matsowa yayi dai-dai satin kunne ta rad'a mata wani abu , da sauri ta d'ago tana kallon sa.

Kashe mata ido d'aya yayi yace " ko bazan samu bane?".

Bata ce komai ba yaja motar suka bar wajan.

__________πŸ“–* Mamaki Hafiza take tana tunanin abinda ya kawo Dr gidan ta , kallan tagar tayi taga babu kowa a wajan da alama an rasa ta inda za'a shigo d'akin.

+

Cikin sauri Hafiz ya d'auki waya ya kara a kunne ya fara cewa "Yahya ina so yanzu ka turo min y'an sanda Wanda zasu kwana a nan yanzun nan aka shigo min gida."

Daga d'aya b'angaren banji me akace ba sai naji Hafiz yace "yauwa na Gode sosai sai sun iso".

Ajiyar zuciya yayi ya kalli Hafiz da tayi nisa cikin tunani ya dafa kafad'ar ta yace " Kar ki damu Hafizty babu abinda zai same mu kinji."

Hafiza ta sauke numfashi tace "Nifa gani nake kamar nasan Wanda ya shigo yanzu."


Hafiz ya k'ura mata ido yace "Ta Yaya kiga sanshi keda baki ga fuskar sa ba?".

Hafiza tace" da zoben hannun sa na gane shi kuma zanyi binkice indai har shine to tabbas zargina ya tabbata".


Hafiz yace "ki daiyi a hankali kada kije ki jefa min akan ki a cikin matsala".

Ya kalle ta yace " bara naje waje yanzu y'an sanda zasu k'araso ". Ya fad'a yana fita daga d'akin.Bai jima ba suka iso ya bud'e musu gate d'in suka a ransa yana tunanin yadda akayi b'arayi suka shigo gidan sa bayan da mai gadi, budawa yayi yaga mai gadi na kwasar bacci , cikin damuwa ya kalli security d'in yace,


" Dan Allah Ku tsaya Ku kula Dan yanzu nan aka fita daga gidan , ni ina zargin ma har yanzu yana cikin gidan nan".


D'aya daga cikin su ukun yace "kar ka damu insha Allah zamu kiyaye komai".

Godiya yayi musu sannan ya bar wajan.


Har yayi hanyar parlourn sai kuma ya dawo yayi baya yaje dai-dai tagar da Wannan mutumin ya tsaya yana kalla ko zai ga tsaidar da zata nuna masa waye , babu komai a wajan da alama mutumin ya k'ware wajan iya shiga gidan mutane , har ya juya zai tafi yaji yaji ya taka wani Abu .

Sunkuya yayi ya d'auki abun , handchief ya gani ya kalle shi sosai sannan ya ninke ya saka a aljihu ya koma d'aki.


Lokacin da ya koma har Hafiza ta kwanta amma bata yi bacci ba sabida tsoro ta cure waje d'aya tana kallon k'ofa, yana shiga ya kulle k'ofar ya k'arasa bakin gadon yana murmushi ya cire Jallabiyar sa sannan ya kwanta yana fad'in "Oh ni Hafiz an kawo min matsoraciyar mata , Hafizty meye na Wannan curewar nan kamar za'a d'auke ki?" Ya fad'a yana dariya k'asa-k'asa ya d'aura hannun sa dai-dai satin zuciyar ta .


STORY CONTINUES BELOW

Tana jinsa tayi masa shiru tana murmushi , ganin yana tsorata ba sai Hafiz ya canja murya yace "Gani na dawo".


Ai bai rufe baki ba Hafiza tayi sani ihu ta juya ta k'ank'ame shi tana runtse ido .

Dariya yayi sosai har yana rik'e ciki , yace " kwantar da hankalin ki babu kowa nine na tsokanar ki kawai nayi".

Cike da shagwab'a ya janye jikin ta tana turo baki , dariya yake mata sosai har sai da ya bata haushi ta fashe da kukan tab'ara.

Ganin da gaske kukan taka sai ya daina dariyar yana cewa "shikenan na daina yi Hak'uri kinji my Soul".

Tana jin sa tayi shiru tana kuka k'asa-k'asa , ganin tak'i shiru sai ya hannu ya juyo ta yana murmushi yace " haba Hafizty kiyi Hak'uri kinji , kiyiwa mijin ki afuwa kinga har na kama kunne na" ya fad'a a shagwab'e.

Yadda yayi maganar ya bata dariya ta d'an yi murmushi tace "to na Hak'ura amma idan ka ...." Bata k'arasa ba ya sakamakon had'e bakin au waje d'aya da yayi.


Ganin da gaske Hafiz yake sai na juyo na fito dan big Mom ta Gaskiya ta hana ni lab'e.


*******


Zagaye yake a parlourn yana tunanin yadda zaiyi ya raba tsakanin Hafiz da Hafiza , zama yayi a kan kujera yana jin k'aunar Hafiza na yawo a jinin jikin sa .

Waya ya d'auko aljihun sa ya d'auko waya ya shiga gallery yana k'arewa fuskar Hafiza kallon cike da So , baki ya kai goshin ta yayi mata kiss yana sauke numfashi zuciyar sa tana harbawa da sauri .

Mik'ewa yayi yace "Sai nasan yadda nayi na raba tsakanin su , Hafiza tawa ce ni kad'ai , aikin banza yanzu yana can yana yiwa matar mutane fyad'e, zan kama kane Hafiz ka kuka da lokacin da zaka shigo hannuna daga kai har matar ka" yana gama fad'ar hakan ya juya ya fita daga parlourn.
********

Kwance take tana Fitar da numfashi dak'yar ana ganin ta anga wacce tasha wuya sosai , Hafiz ne ya fito daga toilet yana kallon ta cike da Tausayi Dan yasan tasha wuya sosai , kusa da ita ya tsuguna ya dafa goshin ta yaji zafi sosai , dafe kai yayi ya furta "ya salam" .

D'aukar ta yayi ya shigada ita toilet ya saka ta a ruwan zafin da ya had'a , jinta cikin ruwan zafi yasa ta dawo cikin hankalin ta , nan take ta fara kuka mai sauti ga bak'in cikin abinda yayi mata tsabar bashi da tausayi ga kuma bak'in cikin yazo ya saka ta gaba a band'aki ko k'yalle babu a jikin ta.


K'ara sautin kukan tayi tana bubbuga k'afa, shima baisan lokacin da hawayen tausayin ta suka sakko daga idon sa ba.

A hankali ya fara mata magana cikin dashewar murya yace "Am sorry sweet mata nasan nayi miki laifi amma ayi min afuwa" ya fad'a yana shirin aka hannun sa cikin ruwan wankan.


Bige hannun sa tayi tace "ni ka fita ka bani waje zanyi da kaina."

Mik'ewa yayi yace "zaki iya yi da kanki?".

Haushi maganar ta bata cikin haushi tace " Nidai ka fita kawai."

Juyawa yayi ya fita cikin sanyi jiki , bedsheet d'in ya cire ya shiga d'aya d'akin ya Wanke ya shanya , wanka yayi shima sannan ya koma d'akin.

Har lokacin bata fito ba , a hankali ya k'ara wajan yace "Hafizty lafiya baki gama ba har yanzu?".

Jin sautin kukan ta yasa ya shiga ciki da sauri , a zaune ya ganta a gefe jakuzzi tana kuka da alama ta kasa tafiya ne , cak ya d'auko ta ya fito da ita , a bakin gado ya zauna da ita ya d'auko doguwar Riga ya saka mata , paracetamol ya d'auko ya bata tasha sannan ya kwantar da ita yana fad'a mata magana mai dad'i yana shafa kanta har bacci ya d'auke ta.

Ganin tayi bacci sai ya mik'e cike da farin ciki yayi alwala ya tayar da sallah yana godiya ga Allah.

Koda asuba bai tashe taba Dan yasan taci wuya , ko masallaci bai fita ba sabida gani yake yana fita za'a d'auke masa ita .

Bata farka ba sa k'arfe takwas na safe , tana bud'e ido abinda ya faru ya fad'o mata , tunowa tayi bata yi sallah ba cikin sauri ta mik'e tana takawa a hankali har ya shiga cikin band'akin , wanka tayi ta k'ara gasa jikin ta sannan tayi alwala ta fito ta saka kaya ta tayar da sallah.


Tana zaune akan sallaya ya shiga yana fad'in , barka da tashi uwar gidan Hafiz kuma Amaryar Hafiz , barka da tashi farin cikin Hafiz , barka da tashi nutsuwar Hafiz, barka da tashi sirrin Hafiz, barka da tashi bugun zuciyar Hafiz, barka da tashi ruhin Hafiz, barka da tashi y'ar Aljanna , hak'ik'a Hafizty kin sani farin ciki jiya kinsa ni nutsuwar da ban tab'a shiga ba a rayuwa ta , bani da bakin yi miki godiya sai dai nace Allah yasa ki gama da duniya lafiya."

Wani irin dad'i Hafiza take ji take kamar tayi rawa , sunkuyar da kai tayi tana jin kunyar sa sosai.

Tsugunawa yayi a gaban ta yace "d'ago ki fad'a min abinda kike so ni kuma nayi miki alk'awarin baki shi koda jirgin sama ne".

Murmushi tayi ta k'asa sunne kai k'asa tana kallan sa ta gefen ido , zama yayi a gabanta ya takwashe k'afa yace " am waiting for u ki fad'a mana kina wani sunkuyar da kai waike a Dole kunya kike ji bayan jiya kin gama cewa Miss xerks kizo Hafiz zai shek'e ni"πŸ˜‚ ya fad'a sana kwaikwayon murya ta.

K'ara rife fuskar ta tayi tace "ni kai kad'ai nake so indai ka mallakamin kanka ka gama yi min komai a duniya , fatana ka rik'e ni amana".


Murmushi jin dad'i yayi yace " ai ni kin Riga kin gama samu har na zama ke kin zama ni , kawai ki fad'a min abinda kike so".

Hafiza tace "shikenan abinda nake so ai".

Yace " tunda bazaki zab'a ba ni zan zab'ar miki kyautar da ta dace dake , yanzu dai ga break fast dinki can na had'a. "

Zaro ido tayi tace "kai kayi da kanka ? Maimakon ta tashe ni nayi" ta fad'a kamar zata yi kuka.

Kwaikwayon muryar ta yayi yace "haba dai kamar ba MATAR SO ba, kar ki manta kece jinin jikin Hafiz".


Tashi yayi ya fita ya kawo mata Abincin , hannu tasa zata had'a tea ya rik'e hannun yace " kul kar ki sake indai ina kusa ni zan dinga ciyar dake."

Babu yadda ta iya haka ta Hak'ura ya dinga ciyar da ita.


Bayan sun gama cin Abincin Hafiz ya zubawa Hafiza ido yana kallon ta , ganin yadda yake kallon ta idon sa har wani ruwa yake a ciki sai ta d'auke kai ta Kalli kan mudubi , zaro ido tayi tace "Sweet H me ya kawo Wannan hankicin gidan nan?".

Kallan wajan yayi yace " au jiya ne bayan Wannan abin  ya faru na fita sai na ga Wannan a inda mutumin ya tsaya na tawo dashi ne Dan na sami tsaida".


Hafiza tace "tabbas abinda nake zargi ya kusa zama gaskiya domin Wannan kyallen na Wanda nake zargi ne".

Hafiz yace " Hafizty kenan to duk duniya Wanda kike zargi shine kad'ai yake da irin Wannan hand chief d'in? Ki daina yawan zargi fa sabi...... ".

K'arar wayar ta yasa bai k'arasa abinda zaice ba , d'aukar wayar tayi tana kallon fuskar Hafiz , cikin sanyin jiki ta ajjiye wayar .

Hafiz ya b'ata rai yace " waye ya kira ki? Kuma me akace miki?".

Hafiza tace "Dr Amin ne ya kira ni wai an kuma samun case d'in Bad man."

Tsaki Hafiz yayi yace "to sai me kuma, kina nufin fita zakiyi kome?".

Hafiza tace ...........

__________πŸ“–* Ko da suka isa gidan babu Wanda yayiwa wani magana Dan ba k'aramin haushin sa take ji ba.


+

D'aki ta shiga ta zauna tana tunanin yadda shari'a zata kasance.

Hafiz ne ya shigo d'akin ya zauna a bakin gado yace "Hafizty ki bani abinda nace mana."

Tsaki tayi tace "ka tafi wajan y'an matan ka mana."

Had'e rai yayi yace "kar fa kiga ina lallab'a ki ki dinga neman raina min hankali , ko meye hali na har yanzu a matsayin mijin ki nake kuma dole kiyi min biyayya in ba haka ba ki shiga fushin ubangiji , kuma kina tunanin wannan abinda kike yi min shi zai saka kiyi nasara akan wannan shari'ar? Hafizty in banyi niya ba baki isa kiyi nasara ba wallahi , nasan Allah zai taimake ki amma komai yana da sanadi take note" yana gama fad'ar hakan ya fita daga d'akin.


Shiru tayi tana nazarin maganar sa , ita kanta tasan tana aikata zunubi kwana biyu , ta rasa yadda zata yi amma Dole ta Hak'ura ta daure ta cigaba da yiwa mijin ta biyayya domin samun aljannar ta. ( Anan nake so naja hankalin Mata y'an Uwana , mijin ki zaiyi miki laifi sai ki fara yi masa rashin mutunci da zagi da tsaki , ki sani duk abinda yayi miki yana nn dai a matsayin mijin ki dole kiyi masa biyayya indai kina son lahirar ki tayi kyau, an San wani abun babu dad'i amma babu yadda zaki ai daman bautar aure kika zo yi ba tashin hankali ba , Allah ne ya d'aura miki nauyi kuma dole ki d'auka, Dan Allah mu kula mu gyara rayuwar kodan mu had'u da ma haliccin lafiya.)

Dak'yar ta mik'e ta fito daga d'akin ta shiga kitchen zuciyar ta a cunkushe.

Bata San lokacin da hawaye ya fara zuba daga idon ta ba , wai ace ga mai laifi tana tare dashi a matsayin mijin ta wannan abun yafi komai b'ata mata rai.

K'arar wayar ta yasa ta fito daga kitchen ta d'auka tace "Ummee ya gida?".

Ummee tace " wai Hafiza me yake damun kine ? Labari ya cika gari kinje kotu kin shigar da k'ara , ina kika sami mutumin ? Hafiza anya aikin nan bai tab'a miki kwakwalwa ba?".


Shiru tayi ba tayi magana ba har ta gama sannan tace "Kar ki damu Ummee nasan abinda nake yi kudai Gobe ku kotun cikin gari domin ganewa idon Ku."

Ajiyar zuciya Ummee tayi tace "Allah ya kaimu " ta fad'a tana kashewa wayar.*****"Uncle kaji abinda ake ta sanarwa a radio ? Wai an shigar da k'arar wannan mutumin da yake yiwa y'an mata fyad'e a Kaduna."


Janan ta fad'a tana kallon Uncle.

Uncle yace "Naji labarin wallahi, kuma wai Hafiza ce zata yi case d'in."

Murmushi jin dad'i Janan tayi tace "Shiyasa nake so muje ayi a gaban mu wallahi."

Uncle yace "babu damuwa ai bara muji shari'ar zata kaya gobe in yaso ranar a aka bada a dawo sai muje , kinga badan aikin da ya tsare ni ba da tuni muna can."

STORY CONTINUES BELOW

Janan tace "Allah ya kaimu".

******


Tunda Hafiz ya fita daga d'akin bai K'ara bi ta kan Hafiza ba , ko kallan ta ma bayayi in ya fito.


Hafiza kuwa duk da bak'in cikin da yake damun ta haka ta d'aure ta dafa abinci amma ko kallan abincin baiyi ba bare ta saran zai ci.

Ganin yaki ci yasa ta d'auka gabad'aya ta kaiwa mai gadi tace ayi sadaka Dan baza taje ta rarrashe tace yaci ba ai ta fita hak'k'in sa.


A daddare tana zaune Hafiz ya shigo ya zauna yana danna waya.

Gyara zama Hafiza tayi tace " Idan baza ka damu ba ko zan iya tambayar ka?".

Ko d'ago wa baiyi ba balle ta sa ran amsa mata , ganin bai amsa ba ta cigaba da fad'in "Meyasa kake lalata y'ay'an mutane?."

D'ago wa yayi ya kalle ta ya tab'e baki ya cigaba da abinda yake yi.

Haushi ya taba amma ta jure tace "magana fa nake maka."

Yace "au wai dani kike ? Sorry na d'auka waya kike , maimaita banji abinda kika ce ba."


Iya k'uluwa Hafiza ta k'ulu amma sanin abinda ta shirya sai ta daure tace "meyasa kake lalata y'ay'an mutane?."


Zuba mata ido yayi yace "nima ban sani ba."


Cikin takaici ta kalle shi tace "Da gaske fa nake ka fad'a min mana".

Zare ido waje yayi yace" nace miki ban sani ba ana dole? Tunda dai nine Wanda kike nema ai shikenan babu abinda ya shafe ki da dalilin da yasa."

Shiru tayi ba tace komai ba .

Cigaba yayi da fad'in "meyasa nake rapping yara shine tambayar ki right? To ra'ayi nayi ba Dan wani Abu ba , ba kin kira ni d'an iska , fasiki , mazinaci ba , to duk ki d'auka hakan ne" ya fad'a yana mik'ewa tsaye.

Kallan ta yayi yace "shikenan idan kin gama ni kam sai da safe" ya fad'a yana shiga d'aki da yana jin haushin yadda take fad'a masa magana kawai dai kyale ta yake Dan yasan yayi mata laifi.

Tsaki tayi tace "kaji dashi wai ciwon ajali a d'an yatsa, nidai tunda na samu abinda nake so ai shikenan" ta fad'a tana d'auko wayar bayan ta da alama recoding tayi.

Murmushi tayi tace "na samu hujja ta farko tunda gashi ka amsa da bakin ka kowa yaji muryar yasan taka ce."

Cikin farin ciki ta jona wayar a charji ta shiga d'aki ta kwanta.


B'angaren Hafiz kuwa yana shiga d'aki ya kwanata yana juyi, tabbas yasab abinda Hafiza ta fad'a gaskiya ne shi fasik'i ne mazinaci , amma shi kansa yana mamakin hakan.

Tsaki yayi yace "ko ma dai meye ai mijin tane ni bai kamata ta dinga yi min rashin mutunci ba" ya fad'a ya mik'ewa tsaye.

Parlour ya fito ya zauna Dan ba bacci yake ji ba , kallon yake yi a haka har bacci ya fara d'aukar sa.


Mik'ewa yayi da niyar kashe socket sai kuwa ya taka wayar Hafiza ta jogane daga charji , tsaki yayi ya tsuguna da niyar gyara sai ya ga abinda yake kan wayar da alama Hafiza bata fita daga wajan recoding d'in ba.


Har zai kashe sai kuma ya shiga recoding d'in , jin maganar da suka yi Yanzu yasa yayi murmushi ya goge shi sannan ya mayar ya koma d'aki.Tunda ya kwanta yake juyi Dan tunda suka yi aure jiya da yau ne kawai basu kwana waje d'aya ba , tun yana juyi har bacci ya d'auke shi.Washe gari.


Da wuri Hafiza ta tashi dan raran za'a fara sauraren k'ara , abinci ta had'a tayi wanka ta shirya komai nata ta zauna tana jiran fitowar Hafiz.

Babu jimawa ya sakko cikin manyan kaya da suka amshi jikin sa , hanyar fita yayi cikin sauri tace "gafa abincin ka".

Yace " No need barshi kawai, ki fito mu tafi kinsan dai lokaci ya kusa " ya fad'a yana fita daga parlourn.


D'aga kafad'a tayi alamun ko a jikin ta ta bi bayan sa suka fita.

Sai da motar ta fara tafiya sannan tace "ina kwana."

Juyowa yayi ya kalle ta yace "Sai yanzu kika damar gaishe ni ? Hafiza kina wasa da aljannar ki wallahi bani da damuwa domin ni uwata ta mutu cikin saka min albarka, kece cikin hatsari domin aljannar ki tana k'ark'ashin tafin k'afa ta , amma naga kin fifita aikin ki akan lahirar ki , ko da yake bai daman ba ki cigaba Allah ya bada sa'a naga ko wannan sabon halin da kika d'auko shi zai saka kiyi nasara a kaina."


Shiru tayi idon ta ya ciko da kwalla ita ta rasa abinda zata yi , tana jin zafi a duk lokacin da ta tuna Hafiz yasan mata da yawa kafin ita , sannan tana bak'in cikin zama da mai laifi kuma ita take bincike a kanta , ita abinda yake d'aure mata kai meyasa ya aure ta?.

Share hawayen tayi zata yi magana ya katse ta ta hanyar d'aga mata hannu yace "kar kice komai nasan abinda ke ranki , kar ki damu indai rabuwa tsakani na dake zai saki farin ciki na amince ana gama shari'ar nan zan sake ki kije ki auri Wanda kike so , farin cikin ki shine nawa a ko da yaushe."

Dai-dai lokacin taga ya karya k'wana ya shiga wani k'aton restaurant.


Bata yi magana ba sai kuka da yaci k'arfin ta Wanda bata San dalilin zuwan sa ba.


Fita yayi daga motar , ganin ya fita itama ta fito suka shiga cikin gidan abincin.

Order abinci yayi , babu jimawa aka kawo masa ya fara ci ba tare daya kalle ta ba.

Shiru tayi Dan ita bana jin yunwa taci abinci a gida.

Yana cikin cin Abinci wata budurwa y'ar kimanin shekara 24 tazo ta zauna a wajan tace "hiii handsome."

Banza yayi mata da farko amma ganin Hafiza ta kalle shi yace yayi murmushi ya kalli yarinyar yace "Hello yakike?."

Cike da farin ciki yarinyar tace "Normal , am Rufaida kaifa?".

Murmushi yayi ya kalli Hafiza da ta b'ata rai yace " nice name , am Hafiz. "

Tace "Wow naji dad'in had'uwa da kai".

Y'ar dariya yayi ya kalli Hafiza sannan ya juyo ya kalli Rufaida yace " Ku gaisa mana" ya fad'a yana nuna mata Hafiza.

Cikin tsine fuska Rufaida tacewa Hafiza "Sannu ko".

Hafiza kuwa tsabar bak'in ciki kasa kallon ta tayi balle ta amsa mata .

Kallan Rufaida yayi yace " she is my ex wife."

Zaro ido Rufaida tayi tace "tsohuwar matar ka fa."

D'aga gira yayi yace " Ashe kinji abinda nace."

Sai kuwa Rufaida aka fara yiwa Hafiza kallon banza , tana iyayi tana gyara Riga.


Mik'ewa Hafiza tayi cikin fushi ta koma mota tana kuka kamar ranta zai fita , babu abinda yafi b'ata mata rai sai yadda ya kira ta da tsohuwar matar sa .

Bata San yadda suka k'are ba sai ganin sa tayi ya shigo motar ya bar wajan.


Bai kula ta ba har suka k'arasa kotun , tun daga bakin gate zaka tabbatar da babban case za'a yi yau sabida irin mutanen da suke wajan.

Parking Hafiz yayi Hafiza ta bud'e ta fita ba tare da ta kula shi ba .


Cikin sauri ta saka kayan ta na lauya ta fito Dan har an shiga kotu.


Kotu tayi mak'il ko ina ya cika da d'an Adam , Hafiz yana baya a zaune yana danna waya abinsa.


Farskiton ne ya Mik'e yace "A yau 5 ga wata 1 shekara da dubu biyu da ashirin wannan yayi dai-dai da 10 ga watan jimada ula kotu zata saurarin shari'ar y'an Matan da aka lalata musu rayuwa na'ana aka yi musu fyad'e " yana gama fad'ar hakan ya mik'awa alk'ali file d'in ya koma ya zauna.

__________πŸ“–* gyaran murya Alk'ali yayi yace "Lauyoyi bismillah."

+

Mik'ewa Hafiza tayi tace "ya mai girma mai shari'a sunana Barr Hafiza Kabir nice lauyan Wanda suke k'ara" tana fad'ar hakan ta koma ta zauna.


Mik'ewa wani yayi yace "Ya mai girma mai shari'a Sunana Barr Nazir Usman nine lauyan Wanda ake k'ara" yana gama fad'ar hakan shima ya zauna.

Alk'ali ya gyara zaman glass dinsa yace "Ko lauyan mai k'ara tana da abin cewa?".

Mik'ewa Hafiza tayi tace " ina dashi ya mai shari'a , inaso kotu ta kira min Hafiz inason in yi masa wasu y'an tambayoyi."


Alk'ali yace "kotu tana Neman Hafiz idan yana kusa ana buk'atar ya fito."

Murmushi Hafiza tayi tace "Nagode ."


Cikin tak'ama Hafiz ya taso ya isa inda aka tanada ya tsaya .

Matsowa Hafiza tayi tace "Bawan Allah ko zaka iya fad'a mana cikakken sunan ka?".

Jim Hafiz yayi kamar bazai magana ba sai kuma yace " Sunana Hafiza Aliyu."

Hafiza tace "Malam Hafiz ko zaka iya fad'a mana a wanne gari kake?".

Kallon ta yayi ya saki murmushi yace " ni d'an Kano ne amma ina aiki anan garin Kaduna. "

Hafiza tace "ko zaka iya fad'a mana dalilin da yasa kake lalata y'ay'an mutane."


Zaro ido Hafiz yayi yace "ban gane abinda kike nufi ba fa".

Murmushi Hafiza tayi tace " Ina nufin meyasa kake yiwa y'ay'an mutane fyad'e? Ka kuma canja suna ka koma Bad man?."


"Inada ja ya mai shari'a , bai kamata ace Barr tayiwa Hafiz wannan tambayoyi ba hakan yana nuni da tana so ta d'aura masa laifin da baiji ba bai gani ba." Barr Nazir ya fad'a.

Alk'ali yayi gyaran murya yace "Barr ki kiyaye."


Tace "Nagode ya mai shari'a".

Ya juya ta kalli Hafiz tace " Meye yaja ra'ayin ka ka fara aiki a Kaduna? ".

Hafiz yace " ra'ayi nane wannan. "


Hafiza tace "da  haka ka fake kana canja kama kana lalata y'ay'an mutane ko?".


" ina da ja ya mai shari'a , wannan tambayoyin da Barr take yi sunyi tsauri da yawa bayan kuma bata da hujjar da zata tabbatar wa sa kotun abinda take fad'a " Barr Nazir ya fad'a yana wuci.


Hafiza tace "ina da shaida ya mai girma mai shari'a inaso kotu ta bani dama na kunna recoding d'in da Malam Hafiz ya amsa sa bakin sa shine Bad man."


Alk'ali ya daba umarnin a d'aukar waya.


Kunna wayar tayi tana duba recoding d'in , sai dai babu shi babu alamar sa , gaban ta ya fad'i cikin sanyi jiki tace "Banga recoding d'in ba."

STORY CONTINUES BELOW

Alk'ali yace "zaki iya komawa ki zauna."

Cikin sanyi jiki ta koma ta zauna tana tunanin inda recoding d'in nn ya shiga.

Alk'ali ya kalli Barr Nazir yace "ko lauyan Wanda ake k'ara yana da tambayoyi da zan yiwa Malam Hafiz?."

Mik'ewa Barr yayi ya nufi inda Hafiz yake yace "Malam Hafiz ko zaka iya fad'a mana meye sana'ar ka?."

Hafiz yace " Inda company da bake sarrafa kayan abinci a garin nan."

Barr yace " A ina kafi zama tsakanin Kano da Kaduna?."


Hafiz yace "A da nafi zama a Kano amma tunda nayi aure zama na ya dawo Kaduna."

Murmushi Yaya ya kalli alk'ali yace "ina rok'on wannan kotu da ta duba zubin Hafiz kana gani kasan baiyi kama da Wanda zai aikata aiki irin wannan ba, sannan inaso kotu ta buda irin k'azafin da Barr Hafiza take son yiwa Hafiz ta hanyar cewa tayi recoding amma da aka buda ba'a ga komai ba , da wannan hujjar nake rok'on kotu da tayi watsi da wannan shari'a sabida babu k'wak'warar hujjar da zata tabbatar Hafiz shine Bad man, Nagode ya mai shari'a" ya fad'a yana komawa wajan sa.

Alk'ali ya kalli Hafiza yace "ko Barr Hafiza tana da abin cewa?."

Hafiza ta mik'e tace "Ya mai girma mai Shari'a inaso wannan kotu mai adalci da ta bani lokaci domin k'ara bincike akan wannan Abu."

Alk'ali ya kalli Hafiz yace "Malam Hafiz zaka iya komawa ka zauna."


Hafiz ya juyo ya kalli Hafiza ya kashe mata ido d'aya ya koma wajan sa.Alk'ali yace "sakamakon rashin k'wak'wk'warar hujja kotu ta d'aga wannan Shari'a zuwa nan da sati mai zuwa, sannan kotu tayi Umarnin da kada a tsare Hafiz domin har Yanzu ba'a tabbatar da zargin da ake masa ba."

Aka buga guduma dummm dummm , aka had'a baki akace "kooootu" .

Alk'ali ya fita kowa ma ya kama gaban sa.

Fita Hafiz yayi ya shiga mota ya zauna ya murmushi.

Cikin fushi Abbie ya kalli Hafiza yace "Ku same ni a gida Yanzu" yana gama fad'ar hakan suka bar wajan.


Tunda Hafiza ta fito ake mata ruwan hotuna , ko wanne d'an jarida murin sa ta tsayi yayi hira da ita.

Tsabar bak'in ciki ko kallon su bata yi ba , kallon motar Hafiz tayi tayi tsaki ta yi hanyar bakin titi.

Keke napep tahau ta nufi gidan Ummee.


Shi kuwa Hafiz tab'e baki yayi yaja motar sa yayi gida.

A kan hanya ya tsaya ya kira wayar Abbie , yana d'aga wa Abbie ya fara fad'in "Dan Allah Hafiz kayi Hak'uri ni bansan abinda yake damun yarinyar nan ba wallahi , ace yanzu kai take zargi akan wannan case d'in? Kayi Hak'uri dole nasa ta zanje wannan k'arar."

Hafiz yace "babu komai ai Abbie farin cikin Hafiza shine nawa , Kar ka sata ta canje ka kyale ta ta cigaba ta haka za'a gano Wanda yake aikata laifin , gata nan ma naga tayo gidan Dan Allah kar kuyi mata fad'a Dan Allah."

Abbie yace "Shikenan Hafiz Allah yayi maka albarka."

Murmushi jin dad'i yayi yace "Ameen" ya kashe wayar yana y'ar dariya.


Hafiza kuwa tana shiga gida Ummee ta fara ruwan bala'i ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba.


Ita dai Hafiza shiru tayi har ta gama sannan tace "Kuyi Hak'uri shari'ar gaba insha Allah komai zaizo k'arshe kudai Ku cigaba da yi min addu'a , nasan abinda nake yi kuma ina cikin hankali na wallahi , tabbas Baku San waye Hafiz bane shiyasa amma zaku sani kar Ku damu."

STORY CONTINUES BELOW

Tsaki Ummee tayi tace "kyaji dashi dai Dan kinga Allah ya baki miji mai sonki shine kike k'ok'arin d'aura masa wannan mummunan laifin."

Murmushi tayi ta kalli Hanifa tace "Hanifa zo muje d'aki."

Suna shiga d'aki Hafiza tace "sister Shari'ar gaba zana gayyato ki gaban kotu domin ki bada shaidar abinda kika gani a hannun Bad man , Kar kiji tsoro ki saki jikin ki kiyi bayani , Yanzu tashi ki raka ni wani waje."

Hanifa tace "to Aunty, amma sai nake ganin kamar baki yiwa Hafiz adalci ba wallahi."


Hafiza tace "kar ki damu kedai tashi muje."


Shiryawa suka yi suka fito , basu wuce ko ina ba sai asibitin cikin gari.

Suna zuwa taje ta samu nurse d'in da take duba yaran da Bad man yayiwa fyad'e , magana sukayi akan zata je ta bada shaida , cikin rashin tsoro ta amince Hafiza tayi mata godiya suka bar asibitin.


Hanifa ta koma gida ita kuma Hafiza tayi nata gidan.


A parlour taga Hafiz yana waya ko kallan sa bata yi ba ta shiga d'aki tayi wanka ta shirya ta dawo parlourn.

Abincin da ta dafa da safe ta d'auka taci , bayan ta gama ta kalli Hafiz ta tab'e baki tace " Ashe ma abin tsoro ne tunda gashi mutum bai amsa laifin sa ba."

Murmushi yayi yace "daman na fad'a ai ba'a isa ayi shari'a dani , in kinga kinyi nasara akaina to wallahi ni naso."

Hafiza tace "Daman nasan kai ka goge min recoding d'in nan."

Yace " Baki da wayo shiyasa wallahi dama nice ke."

Hafiza tace "Allah ya kaimu zama na gaba zaka wayo na ganin idon ka."

Murmushi Hafiz yayi yace "Ameen".


Cikin kwanakin Hafiza ta Tara iya hujjojin da take ganin zata yi nasara akan wannan lamari.


Har zuwa lokacin babu wani Abu da yake shiga tsakanin Hafiza da Hafiz gaisuwa ce itama kuma ba kullum ba.

******

"Wai uncle yaushe zamu Kaduna ne?".

Uncle yace " Sorry y'ar uncle wallahi aiki ne yayi min yawa shiyasa wallahi , amma ranar da za'a yanke hukunci ranar sai muje muga waye wannan mugun."

Mama tace "Ai ni nayi bak'in cikin saurari shari'ar nan a radio ba kasan ranar muna gidan biki."

Janan tace "Eh wallahi Mama nima naso naji."


Uncle yace "sai Ku saurari ta gaba."

Hira suka cigaba dayi cikin nishadi.

*****


*KOTU*


Wannan karar har anfi zaman farko cika sabida kowa yana so yaji yadda shari'a zata kaya.


Kotu tayi shiru kowa da abinda yake sak'awa.

Alk'ali yace " Ko Barr Hafiza tana abin cewa?. "

Hafiza ta mik'e tace "ina dashi ya mai shari'a, inaso wannan kotu ta bani dama na gayyaci Hanifa d'aya daga cikin Wanda Bad man ya sace domin inyi mata tambayoyi."

Alk'ali ya bata dama.

Fitowa Hanifa tayi ta tsaya Hafiza take kusa da ita tace "ko zaki iya fad'a mana sunan ki?."

Hanifa tace "Sunana Hanifa Kabir."

Hafiza tace "Malama Hanifa ko zaki iya bamu labarin yadda akayi kika je hannun Bad man?".

Hanifa tayi bayanin yadda aka sace ta.

Hafiza tace " To tunda kince kina gani kad'an-kad'an ko kinga wani Abu a gidan Bad man?."

Hanifa tace "Banga komai ba sai da naga hannun sa irin rubutun da yake yiwa matan haka shima akwai irin sa hannun sa, kuma fari ne sosai."

Murmushi Hafiza tayi tace "mun gode Malama Hanifa " ta fad'a tana komawa ta zauna.


Mik'ewa Barr Nazir yayi ya nufi wajan Hanifa yace "Malama Hanifa bayan rubutu da fatar jiki baki ga komai ba ko fuskar sa ko dai wani abun?".

Hanifa tace " bayan wannan banga komai ba."

Murmushi yayi yace "Zaki iya komawa ki zauna."

Hanifa ta koma ta zauna.

Barr Nazir yace "ya mai girma mai shari'a Hanifa bata ga wata alama da zata nuna mana cewa Hafiz shine Hafiz ba domin bata fuskar sa ko wani Abu ba , da wannan shaida nake rok'on kotu da tayi watsi da wannan k'arar" yana fad'a yana komawa ya zauna.


Rubuce-rubuce alk'ali yayi yace "ko lauyan mai k'ara tana da abinda cewa ?."

Mik'ewa Hafiza tayi tace "ina dashi ya mai Shari'a , inaso kotu ta kira min Hafiz da kuma Sa'adatu."

Alk'ali yace "Ana Neman Hafiz da Sa'adatu."

Fitowa suka yi kowa ya tsaya a waje d'aya.


Wajan nurse d'in ta nufa tace "malama Sa'adatu ko zaki iya fad'a mana menene aikin ki?".

Nurse tace " Ni nurse ce a asibitin cikin gari kuma nice mai kula da y'an matan da Bad man yayiwa fyad'e tunda indai akayi fyad'en asibitin mu ake kawo su."

Hafiza tace " ko zaki iya fad'a mana abinda kike gani a hannun yaran?".

Nurse tace "Ana yi musu wani singing a hannu da manyan bak'i an rubuta Bad man , ciki kuma idan ka kula sosai akwai Kalmar H a ciki ."

Murmushi Hafiza tayi tace "Ya mai girma mai Shari'a da wannan hujja nake so kotu tayi lakari da Kalmar H d'in da take ciki tunda farkon sunan Hafiz kenan , Nagode ya mai Shari'a."

Wajan Hafiz ta koma tace "Ya mai girma mai Shari'a inaso kotu ta bada umarnin da Hafiz ya bud'e hannun sa na haggu ."

Alk'ali yace "kotu ta bada dama."


Babu tsoro Hafiz ya cire lins dinsa ya bud'e hannun sa , babu komai a wajan tas take sai gashi da yake Kwance.

Gaban Hafiza ya fad'i ta d'ago ta kalli Hafiz tana mamakin hakan sabida haka fa bata fad'a masa hujjar da zata gabatar ba sabida kar ya goge.

Barr Nazir yace "ya mai Shari'a idan Barr bata da abin cewa inaso nayiwa Nurse wasu tambayoyi."


Cikin sanyin jiki Hafiza ta koma ta zauna.


Barr ya kalli nurse yace "Kince a cikin rubutun akwai Kalmar H ko?".


Tace " eh tabbas akwai na d'auki hoton wajan ma sabida rana irin ta yau."

Umarni aka bata da ta nuna , alk'ali aka bawa ya gani tabbas akwai wannan Kalma a ciki amma sai ka k'ura ido zaka gani.

Nazir yace " ya mai girma mai Shari'a wannan kalma ta H ba tana nufi Hafiz bane , zata iya yuwa Halifa ake nufi , ko Huzaifa , Hassan , gasu nan dai da yawa , kuma idan akayi alakari da abinda Barr ta fad'a na cewa akwai a hannun Bad man sai kuma aka duba hannun Wanda ake zargi babu komai , wannan tarin hujjoji nake rok'on kotu da tayi nazari zata gane Barr bata da wata shaida da zata nuna cewa Hafiz shine Bad man ,da haka nake rok'on kotu da ta kori wannan k'arar".


Alk'ali yace "ko lauyan mai k'ara tana da abin cewa?."

Girgiza kai tayi alamun A'a.

Rubuce-rubuce yayi yace "Sakamakon shaidu da aka gabatar har yanzu kotu bata samu hujjar da zata nuna cewa Hafiz shine Bad man ba , dan haka kotu tana Jan hankalin lauyan mai k'ara da idan bata samo shaida a zama na gaba ba kotu zata kori wannan shari'ar sabida kotu ba wajan wasan yara bace , kotu ta d'aga rauraren wannan k'ara zuwa nan da kwana goma , zama na k'arshe insha Allahu."


Kooootuuuu.

__________πŸ“–* Ko ya fita daga cikin kotun banda  Hafiza dasu Ummee.

Cikin b'acin rai Ummee ta kalle ta tace "Meye ribar ki a nan? Kina k'ok'arin yiwa mijin ki k'arya idan so kike ya sake ki ai basai kinyi mai k'azafi ba kawai kice ki gashi da zama dashi , kin bani mamaki wallahi mijin ki guda " tana gama fad'ar hakan tayi tsaki ta bar wajan.

Hanifa ta dafa ta tace "Aunty Hafiza na yarda dake nasan baza kiyiwa Yaya Hafiz k'arya ba , amma kuma ya kamata kiyi bincike sosai domin ki gano gaskiya , haba Yaya ta Hafiz fa mijin kine har yanzu yau in kika so samun shaida wallahi sai kin samu ke macece kin san yadda zaki yi kisa shi ya fad'a koda baya cikin hankalin sa , kiyi tunani" tana gama fad'a ta bar wajan.

Shiru Hafiza tayi tana tunanin maganar Hanifa , dukan table tayi tace "oh my God meyasa banyi Wannan tunanin ba ? Tabbas rashin kula Hafiz da nake yi bashi ne zai saka nayi nasara ba , tabbas yau zata canja zani" mik'ewa tayi da sauri ta fita .

Hafiz kuwa yana gida a Zaune yana tunanin yadda Shari'a take wahalar da Hafiza , murmushi yayi a fili yace "kar ki damu Matata zanyi komai da kaina".

Sallama Hafiza tayi ta shigo parlourn fuskar ta d'auke da murmushi.

Amsawa yayi yana d'auke daga kanta , shagwab'e fuska tayi taje ta zauna kusa dashi ta kwantar da kanta a kafad'ar sa tace,


" Na gaji". Ko juyowa baiyi ba balle ta sa ran amsawa .

Hannu tasa ta bayan ta zagayo da hannun ta har saman cikin sa tace "Ina magana kayi min shiru kuma nasan ka jini."


Shiru yayi bai amsa mata ba sai lumshe ido da yayi , Haushi ya fara data amma sai ta daure tace "Kana ji ina yi maka magana kayi min banza haba ka yafe min laifi na mana."

Sai a sannan yace "Hafizty kenan kina maida ni k'aramin yaro wallahi."

Tace "nidai kawai kaiyi Hak'uri ka yafe min mu cigaba da zama kamar da , b'angaren Shari'a daban nan daban".


Murmushi yayi yace "Zama tare ai ya k'are Hafiza kin manta nan da wasu kwanaki kin zama ba tawa ba , nidai burina ki kular min da baby na a duk inda kike bana so wani Abu ya same shi."

Shiru tayi tana jin wani iri a ranta , ya cigaba da fad'in "Hafiza na kuma tabbatar wa so kike na sake ki shiyasa kika daina kula ni , baki damu da yarda na kwana ina buk'atar ki ko bana yi wannan duk bai dame ki ba , kin San halin Dana shiga cikin kwanakin nan? Baki sani ba sabida abinda nake buk'ata kin ajjiyewa sabon mijin ki , Hafiza inason ki ina k'aunar ki a kullum sonki k'aruwa yake a cikin zuciya ta , amma babu yadda zanyi farin cikin ki shine nawa dole na sake ki tunda naga baki da burin da ya wuce wannan, "

Ajiyar zuciya yayi ya cigaba da cewa " Nasan ni mai laifi ne a wajan ki amma kin tab'a zuwa cikin lallami kin tambaye ni meye ya jefa nu cikin nan hali? Baki tab'a ba sai da kizo cikin gadara kice min meyesa nake lalata y'ay'an mutane bakin San wannan Kalmar nayi min zafi ba , koda yake ba damuwa kika yi akan ki sani ba" yana gama fad'ar hakan bai jira mai zata ce ba ya zare hannun ta daga jikin ta ya bar wajan.

Yana barin wajan ta fashe da wani irin kuka Wanda bata San dalilin zuwan sa ba.

STORY CONTINUES BELOW

D'aki ta koma tayi wanka ta canja kaya sannan ta fito ta shiga kitchen ta had'a abinci , bayan ta gama jerawa a kan dining ta nufi d'akin Hafiz.

K'wank'wasa tayi taji shiru ba'a amsa ba , tura k'ofar tayi ta shiga gaban ta na fad'uwa.

K'arar ruwa taji da alama wanka yake .

Kallon d'akin tayi ta ganshi to ba'ace yayi daud'a sosai kuma ba'ace baiyi daud'a ba , tunowa tayi rabon ta da ta shigo d'akin sa tun ranar da ya fad'a mata gaskiya.

Cikin sauri ta fara gyara d'akin , kafin ya fito daga wanka ta gyara d'akin tana tana goge Mudubi ya fito d'aure da towel a k'ugu.

Kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai ya zauna a kujerar mudubin yana shafa mai, itadai kawai kallon sa take ganin yadda ya rame kamar bashi ba.

Mik'ewa yayi ya saka kaya sannan ya dawo wajan yana taje sajen fuskar sa.

Karb'ar cumb d'in tayi tana taje masa tana shafa fuskar sa a hankali.

Lumshe ido yake yana jin wane Abu na yawo a jikin sa , ta b'angaren Hafizan ma haka wani iri take kawai daurewa take.

A hankali ta yo k'asa da hannun ta tana shafa wuyan sa a hankali , jin tana Neman sashi wani yanayi sai ya rik'e hannun ta yace "please ki bari".

Kallon sa tayi tace " Meyasa?".

Yace "Bana so na shiga yanayin da babu mai fitar dani a halin Yanzu."

Tace "nifa meye amfanina?."

Zuba mata ido yayi sosai yace "kona nema ba bani zaki yi ba , na nemi Abinci ma baki bani ba balle kanki".


Shiru tayi tana jin wani iri a ranta tace " A'a ban hana ka Abinci ba Kaine ka k'i ci , kuma kana mijina ya za'a yi na hana ka kaina."

Yace " Hafiza kenan nasan fa duk kina yi min wannan abun sabida ki samu abinda zaki bawa kotu , badan Allah kike yi ba na gane ki kema kuma kin sani ."

Shiru tayi bata ce komai ba sai sunkuyar da kanta tayi .

Murmushi yayi yace "Ya kika yi shiru haka ne ko? Nasan ai ni kin tsane ni kamar yadda kika fad'a nasan zaman jiran sakin ki kawai kike yi kar ki damu komai yazo k'arshe".

Hafiza tace " Ni ba haka nake nufi ba kawai inajin zafi ne idan na tuno da cewa bani kad'ai ce macen da ka sani ba a rayuwa."

Murmushi takaici yayi yace "Kin tab'a tambaya ta dalilin hakan? Baki tab'a ba sabida baki damu ki sani ba."

Tace "Na damu mana yanzu fad'a min to".

Girgiza kai yayi yace " A'a wallahi tunda baki nema da kanki ba shikenan, yanzu me kika samu da zaki bayar a zaman gaba?".


Murmushi tayi ta matso da fuskar ta ta had'e ta da tasa tace "Kaga abinda na samu nan" tana fad'a ta had'e bakin sa Data.


Sosai suka fita daga yaiyacin su suna faran tawa juna rai .


Basu suka dawo dai-dai ba sai da suka kwashe kusan hour d'aya , jayo ta yayi jikin sa yana sauke numfashi yana shafa kanta.


Ba tayi magana ba ta mik'e ran ta a b'ace ta fita daga d'akin.

Shima tashi yayi ya shiga wanka .

Kota ta fita d'aki ta koma tana jin haushin kanta , meyasa ma ta kula shi har ta bashi kanta? Ta sani ma ko yana da wata cutar , mutumin da yake lalata y'ay'an mutane haka kawai babu wani dalili ai ba abokin zama bane.

Wanka tayi ta shirya ta fito , tana cikin cin Abinci ya fito daga d'aki.

Zama yayi kusa da ita yace "Hafizty shine ko ki jira ni" ya fad'a fuskar sa d'auke da murmushi.

STORY CONTINUES BELOW

Tab'e baki tayi tace "Gashi nan ai basai ka ci ba".

Murmushi yayi yace " Har yanzu tsanar tawa na nan ko?".

Shiru tayi bata yi magana ba , yace "Hausawa sun ce shiru alamu ne na amsawa kenan har yanzu kin tsane ni d'in , kar ki damu na fad'a miki komai yazo k'arshe" yana gama fad'a mata haka ya mik'e ya fita.


Itama mik'ewa tayi ta fita bakin gate ta bawa mai gadi kud'i tace yaje chemist yace a bashi PT .

Babu jimawa ya dawo ya bata ta koma ciki.

Band'aki ta shiga tayi shiru ta saka Pt d'in a ciki , 5mint ta bashi sannan ta cire.

Tana dubawa taga positive alamun tabbas tana d'auke da ciki.

Gabanta ya fad'i ta shafa cikin ta tace "Yanzu kenan da gaske inada ciki? zan haihu da fasik'in mutum kenan , A'a bazai yu ba dole na zubar da cikin nan."

Da k'arfi taji ance "wallahi tallahi kika zubar min da ciki sai nayi mummunan sab'a miki" Hafiz ya fad'a yana shigowa toilet.

Jayo ta yayi ya fito da ita daga toilet d'in jikin sa na rawa yace "Zan iya jure komai idan kika yi min amma bazan jure ki zubar min da ciki ba , Hafiza kar kiyi wannan Kuskuren zan iya yin komai a kan wannan cikin na fad'a miki kuma" yana gama fad'ar hakan ya bar d'akin.


Tsaki tayi ta koma cikin band'akin tana mita.


Bayan Kwana Takwas.


Duk cikin kwanakin nan Hafiz baya shiga harkar Hafiza Dan yaga alama in ya shiga harkar ta shine take Neman ta dinga yi masa rashin kunya , yasan tabbas bai kyauta mata ba amma ai bai kamata ta dinga yi masa haka ba.


B'angaren Hafiza kuwa ko a jikin ta Dan ita haushin sa ma take ji .


Suna zaune a parlour babu Wanda yake wa wani magana wayar Hafiz tayi k'ara.

D'auka yayi bayan sun gaisa Uncle yake sanar masa da zuwan su , Hafiz yayi murna sosai sannan ya kashe suka yi sallama.


Hafiza tana zaune a wajan amma bata yi magana ba sabida kanta da yake mata ciwo sosai.

Hafiz ya kula da yadda take cije baki tana dafe kai , cikin tashin hankali yace "Baki da lafiya ne?."

D'aga masa kai tayi alamun eh , da sauri yace "bara muje asibiti."

Hijjabi ya saka mata ya rik'e ta suka tafi asibitin kusa dasu.

Koda suka je likita ya duba ta yace "Ba abun damuwa bane kasan mace mai juna biyu Dole a dinga samun irin wannan , sai dai bata cin Abinci sosai ya kamata ka saka ta ta dinga cin Abinci kodan samun kwarin jikin ta."

Hafiz yace "insha Allah, Dr ko zamu iya sanin kwanakin cikin?".

Dr yace " eh mun duba cikin satin hud'u dai-dai."

Hafiz yayi masa godiya suka dawo gida.

Kitchen ya shiga da kansa ya dafa Mata jellop ta taliya ta kawo mata.

Zama yayi kusa da ita ya kwantar da kanta jikin  sa yace "Daure ki bud'e bakin ki kici kinji."

A baki ya fara bata tana ci , kad'an taci tace "na k'oshi ni amai ne ma yake taso min".

Cike da tausayi yace " sannu kinji Allah ya baki lafiy...." Bai rufe baki ba ta fara shara amai kamar zata amayar da kayan cikin ta.


Rik'e ta yayi har ta gama sannan ya mik'e ya d'auko tissue ya goge mata baki ya cire mata hijjabi Dan duk ta b'ata shi da amai.

STORY CONTINUES BELOW

Ruwa ya bata ta kuskure bakin ta , mik'ewa yayi ya d'auko moper ya goge wajan , sannan yace "Me zaki ci yanzu?".

Yatsine fuska tayi tace " Bana son cin komai".

Yace "A'a baki ji ance ki daina zama da yunwa ba , pls ki fad'i abinda zaki ci."

Tace "D'anwake da manja da yaji da cucumber da dafaffen kwai da lemon tsami."

Yace "An gama bani nan da minti biyar."


Kitchen ya shiga babu jimawa ya gama had'a mata d'anwake kamar yadda tace.

Babu laifi taci sosai kuma bata yi aman sa ba.

Bayan ta gama Hafiz ya d'auke ta cak ya shiga da ita d'aki ya cire nata kayan jikin ta ya saka mata na bacci ya kwantar da ita yayi mata addu'a ya kashe mata hutar d'akin.


Washe gari da huri ya tashi ya had'a mata break fast yana gama fad'awa ya fita , koda ta tashi wanka tayi ta fito parlour Dan tana jin

kwarin jikin ta .

Kallon Abincin tayi nan take taji tausayin Hafiz ganin yadda yake ta d'awainiya da ita , shaid'an ne ya zuga ta sai kuma tayi tsaki tace "ai Dole ma ya kula dani tunda shi ya kunsa min cikin."

Zama tayi taci Abincin ta ba tare da ta neme shi ba.


Hafiz kuwa yana can yasa a gyara gidan uncle Dan yace masa gobe da safe zasu sauka.

Yana can amma gabad'aya hankalin sa na kan Hafiza , ko lafiya take oho.

Bar musu aikin yayi ya tawo gida.

A zaune ya same ta tana kallo.

Ajiyar zuciya yayi yace "Sannu Hafizty ya jikin?."

Tace " Da sauki".


Yace "kinci Abinci dai ko?".

Tace " Naci sosai ma".

Yace "Haka ake so, goben kuwa zaki iya zuwa kotun?."

Tace "Sosai ma ai banga abun da zai hanani zuwa ba duk da nasan bani da wani muhimmin Abu a hannu na amma dai ina fatan narasa da Burina na karb'i Y'ANCIN MATA."

Murmushi yayi baice komai ba ya bar wajan.Har dare Hafiza bata samu wata kwakwkwarar hujja akan Hafiz ba amma da Allah ta dogara kuma shine zai taimaka mata.

Hafiz kuwa duk ya kula da yanayin ta tana so ta tambaye shi Abu amma sai ta kasa ta share, shima kuma bai ce mata komai ba Dan yasab in bai yi niya ba wallahi dole gobe ya kori k'arar.

Da safe da huri Hafiza ta shirya ko Hafiz bata jira ba ta tafi kotu.


shima shiryawa yayi ya tafi Dan ya ga Fitar ta.

Kotu ta cika mak'il babu masaka tsinke sabida kowa burin sa yaji ya Shari'a zata kasance.

Bayan kowa ya gabatar da kansa alk'ali ya nemi a fara gabatar da shaida.

Duk wata shaida tana ga Barr Nazir Dan Hafiza bata da komai .

Barr Nazir ya cigaba da gabatar da shaida inda ya bukaci Asp Yahya da ya fito.


Barr ya kalli Asp yace " Yahya ko zaka iya fad'a mana alak'ar ka da Hafiz? ".

Asp yace " Abokina ne tunda yazo Kaduna muke tare."

Nazir yace "shin kasan Hafiz da wani hali na daban?".

Asp yace " Gaskiya ban sani ba Dan indai kasan Hafiz to zaka San halaiyar da , ba mutum ne mi yananiya ba Hafiz akwai rik'on amana ga tausayi , kuma duk inda yaji mutum yana Neman taimako zai je wajan da kansa ya bashi."

Nazir yace "Mun gode Malam Yahya, ya mai girma ma Sharia da wannan hujjoji nake so wannan kotu tayi adalci sa ta saba tayi laka'ari da cewa Hafiz bashi da laifin komai tunda gashi ko hujja mai k'arfi ba'a samu ba wacce zata nuna cewa Hafiz shine Bad man , da wannan nake Neman kotu tayi watsi da k'arar Dan babu komai a cikin ta sai k'azafi da kuma shirme."

Alk'ali yace "Ko lauyan mai k'ara tana da abin cewa.?"

Hafiza ta mik'e tace "bani dashi ya mai Shari'a" ta fad'a jikin ta yayi sanyi sosai.


Ganin haka yasa Hafiz yace "ya mai Shari'a ko zan iya magana?."

Alk'ali yace "Babu damuwa fad'i."

Hafiz ya kalli jama'ar wajan yace "Duk abinda Barr Hafiza ta fad'a a kaina Gaskiya ne nine Bad man nine nake yiwa y'ay'an mutane fyad'e ba tare da sun sani ba , ina jiran hukunci."


Da sauri Hafiza ta d'ago kai tana kallon sa , nan da nan kotu ta hargitse ana hayaniya kowa da abinda yake fad'a.

Alk'ali yayi gyaran murya yace " Hafiz ko meye dalilin ka na cewa Kaine?."

Hafiz yace "Sabida nasan ni d'in ne " hannu yasa ya tattare rigar hannun sa nan take singing ya fito , baiyi magana ba ya Ciro spray a aljihun sa ya fesa a wajan rubutun ya baje kamar babu shi.


Ya kalli Alk'ali yace "Ina ganin yanzu zaka fi yarda akan abinda nace ."

Alk'ali ya girgiza kai cike da mamakin yawo da basira irin ta Hafiz yace "to ko meye dalilin ka na lalata y'ay'an mutane?."

Hafiz yace "bana so ayi min Wannan tambayar Dan ni kaina bani da amsar ta."

Alk'ali yayi rubuce-rubuce yace "sakamakon amsa laifin sa da yayi duk da wahalar da ya bawa kotu , kotu ta yanke masa hukuncin........"


A Dakata A Dakata!!!


Wani mutumi ya fad'a yana shigowa kotun.

Kallon sa kowa yake ciki harda Hafiz , alk'ali yace "Malam lafiya daga ina ? Meye dalilin ka nacewa a Dakata?."

Mutumin yace "Ni daga k'aune kacako nake dake garin Kano , dalili na nace a cewa d a dakata kuma sabida Sam Hafiz bashi da laifi akan abinda ake zargin sa dashi Dan baisan San yana aikatawa ba shiyasa yace maka bai sani ba."

Kotu tayi shiru baka jin komai sai k'arar fanka , alk'ali yace "ko meye dalilin ka na fad'ar hakan".


Mutumin yace " Sabida asiri ke yawo a jikin sa kuma ba wani ne yayi aikin ba nine nayi shi ni ma kuma wasu mutane ne suka sani tun Hafiz bai kai haka ba.!!!"

__________πŸ“–* Alk'ali ya gyara mazan glass dinsa yace "Ko zaka yi mana bayani sosai?."

+

Mutumin ya gyara tsayuwa yace "Sunana boka cika aiki kamar yadda na fad'a ina zaune a k'auyen kacako dake garin Kano , ni hatsabibin mutum ne hakan yasa mata suke tururuwar zuwa waje na Dan Neman biyan buk'atar su,"

"ina zaune wata rana wata mata tazo ta same ni a zaune tace tana so a sa Hafiz Aliyu ya haukace gabad'aya kowa ya tsane shi ya daina sonsa , duba k'asa nayi ni kuma nace mata Sam bazai yu ba sabida Hafiz mutum ne mai addu'a sai dai a canja wani Abu,"

"Nan take tace to asa ya dinga Neman y'ay'an mutane kuma ciki a saka ya neme k'anwar wato Janan, Banyi k'asa a gwiwa ba na duba naga dai hakan bazai yu ba sai dai zamu saka shi ya dinga Neman mata amma ba tare da mutane sun gane shi ko wani abun , murmushi matar tayi tace babu komai ai tasan duk daran dad'ewa maganar zata fito,"

"Nayi aiki akan sa ta inda daga lokacin da asirin ya motsa zai fita a hankalin sa bazai kuma sanin inda kansa yake ba sai bayan lafawar komai , amma fa yasan yayi hakan akwai lokacin da yake yi d'in bazai gane ba, kunji abun ya faru."

Kotu tayi shiru kowa yana mamakin wannan mugunta .

Alk'ali yace "Boka cika aiki ko zaka iya fad'a mana dalilin ka na zuwa ka fad'i gaskiya?".

Boka yace " hak'ik'a Allah ya shirye ni yanzu bana aikin komai kuma duk inda nasan Na yiwa mutum wani aiki Babba nake zuwa na neme shi duk inda yake ya rok'e shi akan ya yafe min , to tunda naji ana Shari'ar nan na tabbatar da cewa Hafiz ne sabida sunan da yazo iri d'aya. "


Alk'ali yayi rubuce-rubuce ya d'ago yace "ko zaka iya fad'a mana sunan wacce tasa ka aikin?."

Boka yace "Bana tambayar mace sunan ta idan tazo wajena , Amma dai fara ce tana da d'an jiki kad'an kuma tana da d'a namiji."

Alk'ali yace "Sakamakon gaskiya da ta baiyana duk da dai ba'a haiyacin sa yake wa yara fyad'e ba amma duk da hakan zamu yanke masa hukunci biyan diya ga duk yarinyar da yayi fyad'e, kotu ta yanke......"

"A Wannan b'angaren ma bashi da laifi domin Hafiz bai tab'a yiwa wata yarinya fyad'e ba!" Aka fad'a daga wajan zaman y'an kallo.


Kowa kallan wajan yayi yana mamaki .

Mutumin ya fito yace "nasan zakuyi mamakin jin hakan dole na fad'i gaskiya sabida mugayen mafarkan da nake yi a duk lokacin Dana kwanta bacci."

Alk'ali yace "muna jinka".

Mutumin yace " sunana Jibson guy ni d'aya ne daga cikin yaran Bad man wato Hafiz , a duk lokacin da Hafiz ya samu d'auko yarinya idan muka kai masa ita yakan kasa yi mata komai , da farko zai fara shafa yaran kamar gaske amma daga baya sai ya rik'e kai yana cize baki , rubutu zai yiwa yarinya a hannu ba tare da yayi mata komai ba sai ya fito yace muzo mu d'auke ta , mu kuma idan muka fito ba dawo da yaran muke ba suka tsaya a hanya nida Usy muji dad'in mu da yaran daga nan sai muje mu yarda da ita , Dan Allah Dan Annabi Hafiz ka yafe min wallahi sharrin shaid'an ne" ya fad'a hawaye na zuba daga idon sa.


Runtse ido Hafiz yayi yana maimaita salati a ransa , zuciyar sa nayi masa zafi.


Alk'ali yace " yanzu ina d'an uwan naka Usy d'in? ".

Jibson guy yace " Gashi can a zaune " ya fad'a yana nuna inda yake.

Fitowa yayi yana kuka yace "Dan Allah Ku yafe mana mun San munyi laifi, " ya kalli Hafiza yace "Ki yafe mana a matsayin ki na matar sa."

Matar sa!! Kowa yake maimaitawa , Nan da nan kotu ta d'au hayaniya kowa da irin abinda yake fad'a akan Hafiza.


Alk'ali yace "Sakamakon Gaskiya da ta k'ara baiyana kotu ta Wanke Hafiz daga ko wanne zargi da ake masa, kotu ta yankewa Jibson guy da Usy hukuncin shekaru biyar biyar a gidan yari da tarar naira million 10 ga ko wanne d'ayan , kotu tana mik'a jinjina da ban girma ga Barr Hafiza sakamakon jajircewar ta a wajan aiki da kuma son taimakawa Mata sabida ta karb'ar wa mata Y'ANCIN su ta Shari'a da mijin ta , da ace a duniyar nan da muke ciki za'a samu mutane lauyoyi kamar Hafiza da munji dad'i da kuma masu laifi sunyi k'aranci a wannan zamani " yana gama fad'ar hakan ya buga gudama akace kotuuuuuuuu.Kowa ya mik'e ya zuwa wajan Hafiz ana taya shi murna .

Shi kuwa Hafiz gabad'aya kansa ya kulle wace tayi masa Wannan asirin? Shine abinda ya damun sa sosai.

Da guda Janan tazo ta rungume shi tana kuka  , d'ago ta yayi ya goge mata hawaye yace "A'a Janan yaushe kuka zo?".

Uncle ne ya k'araso ya rungume Hafiz yace " tun iso tun safiya sai kawai muka yo nan , kai Alhamdulilah naji dad'i da gaskiya tayi halin ta Allah ya baiyana wacce tayi maka Wannan abun."

Hafiz yace "Ameen ".


Wajan su Ummee yaje ya tsuguna yace " Abbie Ku yanke duk hukunci da kuka ya dace dani , nayi wasa da hankalin Ku sosai Ku yafe min."

D'ago shi Abbie yayi yace "kar ka damu komai ya wuce Allah ya dad'a kiyayewa."

Ummee da Hanifa gabad'aya tausayin Hafiz suke ji suna gefe suna goge hawaye.

Hafiza tazo wajan tana kallon Hafiz , suna had'a ido ya d'auke kai kamar bai ganta ba ya cigaba da abinda yake yi.

Fitowa suka yo gabad'aya nan Y'an jarida suka yiwa Hafiz ca aka kowa yana so yaji ta bakin sa.

B'angaren Hafiza ma haka kowa so yake yaji ta bakin ta ya akayi ta iya kai mijin ta kotu.

Hafiz bai kula su ba suka shiga mota shida su uncle suka bar wajan zuciyar sa cike da son sanin Wannan mata.

gidan Hafiz suka wuce gabad'ayan su , a parlour suka zauna uncle ya kalli Hafiz yace "Hafiz daman wannan abun yana faruwa shine baka tab'a fad'a min ba?".+


Sauke numfashi yayi yace " naso na sanar dakai amma duk lokacin da nayi niyar hakan sai na kasa sabida ina jin kunyar hakan."

Uncle yace "Wannan ai ba dalili bane daga yau ka dinga sanar dani komai".

Hafiz yace " insha Allah, babu abinda yake damuna yanzu kamar nasan wannan muguwar matar data cutar dani."


Uncle yayi ajiyar zuciya yace "Nima abinda nake tunani kenan wallahi."

Sai a sannan Mama tayi magana tace "Ni kuwa sai nake gani kamar Maimuna ce."

Uncle ya d'ago yace "komai zai iya faruwa amma gaskiya ni bana zargin ta duka da tsabar tsanar da take nunawa Hafiz bana tunanin zata yi haka."

Shidai Hafiz yayi shiru yana jinsu baice komai ba.

Janan tace "D'azu Humaira ta kira ni tace wai gobe zata zo ."


Murmushi Uncle yayi yace "Allah ya kaimu goben."


Da sallama Hafiza ta shigo parlourn , amsawa sukayi fuskar su d'auke da murmushi .

Kusa da Janan ta zauna tana sunkuyar da kai Dan ba k'aramar kunyar su take ji ba.

Uncle yace "y'ata ki daina jin kunyar mu kema kamar y'a kike a wajen mu kinji?".

Murmushi tayi ta d'aga kai.

Mik'ewa uncle yayi yace " To mu bara mu wuce".

Da sauri Hafiza ta Mik'e tace "A'a Abba bara na dafa kuma abinci Dan Allah kar Ku tafi" bata tsaya sauraran sa ba tayi cikin kitchen da sauri.

STORY CONTINUES BELOW

Babu jimawa ta kamalla ta kawo musu , ci suka yi sosai bayan su gama suka mik'e Dan tafiya.

Janan ta kalli uncle tace "Dan Allah Ku barni a nan na kwana Ku ku tafi."

Mama tace "A'a Janan ki tawo mu tafi in yaso gobe da safe sai kizo."

Hafiza tace "A'a Mama tunda tana so ku tafi ita ta zauna a nan d'in."

Uncle yace "to shikenan mu mun tafi , naga alama yau Hafiz y'an miskilancin ne a kansa."

Sai a sannan Hafiz yace " A'a ba haka bane uncle , muje na raka Ku" ya fad'a yana mik'ewa.

Raka su yayi har bakin mota suka shiga suka tafi.


A parlour ya tarar da Janan tana danna waya , kallan ta yayi yayi murmushi baice komai ba ya shiga d'aki.

Ita Janan murmushi tayi masa tana jin kaunar Yaya nata sosai , tana zaune Hafiza ta fito tace "Janan ana zaune".

Janan tace " Eh wallahi ni bacci ma nake ji".

Hafiza tace "To kije ki kwanta mana daman ai kun kwaso gajiya."

Mik'ewa Janan tayi ta shiga d'akin baki ta kwanata bacci yayi gaba da ita.


Mik'ewa Hafiza tayi ta nufi d'akin Hafiz , da sallama ta tura k'ofar ta shiga.

Amsawa yayi yana cigaba da danna laptop din'sa.

Zama tayi kusa dashi tace "Hafiz Dan Allah duk abinda nayi maka a baya kayi Hak'uri ka yafe min rashi sani yasa nayi hakan."

Cigaba da abinda yake yayi ba tare da ya kula ta ba , ganin yayi shiru yasa ta kuma cewa "Baka ce komai ba."

D'ago kai yayi ya kalle ta yace "komai ya wuce kar ki damu , amma kiyi Hak'uri nasan ban cika miki alk'awarin Dana nayi bako ? Ina sane zan sallame ki soon."

Runtse ido tayi tace "ni ba abinda ya kawo ba kenan , Hafiz Ashe baka yafe min ba tunda har kake tunanin rabuwa dani."

Murmushi yayi yace "Hafizty farin cikin ki shine nawa ke kika cemin kin tsane ni bakya sona kuma saina sake ki , kinga dole nayi abinda kike so kiyi Hak'uri gaskiya ta baiyana na gane Wannan matar ranar Dana San wace ranar zan sake ki."


Hawayen takaici ne suka sakkowa Hafiza ta rik'e hannun sa tace "Dan Allah ka daina Irin wannan maganar na rantse da Allah inason ka ina kaunar ka bani da burin da ya wuce zama da kai , a baya ma abinda yasa na furta hakan b'acin rai ne kuma kai kayi tunani da ace nice kai a da wanne mataki zaka d'auka? , Sweet H kishin ka yasa nayi hakan badan wani Abu ba" ta fad'a tana fashewa da kuka sosai.


Shiru yayi yana kallon ta can yace "Ranar Dana fara ganin ki ranar na fara sonki Hafiza har yanzu ina sonki sosai nima amma bana so na saki azumi kin manta har rantsuwa kinyi akan sai na sake ki?."

Hafiza tayi sauri kauda zancen tace "Da farko meyasa kazo gidan mu Neman aure na?."


Hafiza ya rungumota jikin sa yace "Da farko na shirya hakan ne Dan nayi wasa da hankalin ki na kuma bak'an tawa ranki , amma tunda naje gidan Ku na ganki naji duk duniya babu wacce take so sai ke da farko naso na baiyana miki koni waye amma yarda kike furta kin tsane Bad man yasa nak'i fad'a miki muka cigaba da zama a haka , lokacin da kika ce kina zargi na tabbas naji tsoro ko kin gane nine amma yadda na tsara ki nan da nan  kika sakko yasa hankali na ya kwanta , Hafiza nine da kaina na d'auke ki nakai ki gidana daman banyi niyar yi miki komai ba dan na tsorata ki yasa nayi miki wannan hoton , lokacin Dana ajjiye ki kafin ki k'arasa gidan Ku na Riga ki isa muka cigaba da Neman ki nida Abbie , da dare kuma Dana zo wajan ki daman na riga na turo pic d'in cikin d'aya wayar tawa muna zaune a lokacin na kunna network d'in wayar sai sai kuwa sak'on ya shigo , ganin hankalin ki tashi yasa ni kuma na cigaba da kwantar miki da hankali",

STORY CONTINUES BELOW

Ajiyar zuciya yayi ya cigaba da cewa "Duk wani messages da ake miki nine nake yi ba wani ba zan turo miki message a private number daman na kashe network d'in wayar ina kunnawa zai shigo , number ki na same ta a wajan wannan nurse d'in ta asibiti ba tare da tasan wa ta bawa ba , Hafiza tunda kika fara bincike a kaina nasa miki tsaro duk inda kike akwai yaro na a wajan har a bayan office d'in Dr Amin hakan yasa kike mamakin Fitar sirrin ki , dalilin fad'a miki gaskiya ganin yarda kika tayar da hankalin ki sai kin kama ni yasa na fad'a miki Dan bana son b'acin ranki".


Ajiyar zuciya tayi tace " Lallai ka iya tsara film".

Murmushi yayi ya jawo ta ta fad'o jikin sa had'e fuskar su waje d'aya yace "Da gaske?".

Tace " Uhum" Dan yadda yake yawo da hannun sa a jikin ta ba k'aramin kashe mata jiki yayi ba.

Hannun sa yasa yana shafo cikin ta tana jin dad'i wai yanzu da d'an sa a nan.

Ita kuwa Hafiza gabad'aya ta fara fita haiyacin ta , a hankali ta lalubo bakin sa ta had'a da nata tana kissing d'insa .

Yana k'ok'arin cire mata riga suka ji kiran sallar la'asar , a hankali ya zare bakin sa ya mik'e yana fad'in "da yake kinsan an kusa kira yasa kika tsokanoni to ki sani bashi kika d'auka" yana gama fad'ar hakan ya shiga toilet.

Itama mik'ewa tayi ta fita daga d'akin tana sauke numfashi.


Da daddare suna zaune suna hira Janan tana kusa da Hafiz a zaune suna kallo.

Hafiz yace "Sweet k'anwa".


Janan tace " Na'am sweet Yaya na. "

Yace "Saura wata nawa ki gama diploma d'inki?."

Janan tace "Saura wata uku lokacin da zan gama lokacin Yaya Fadil zai dawo ."

Hafiz yace "In kinga kuma sai aure?".


Rufe ido tayi cikin shagwab'a tace " Kaji Yayan ka sani jin kunya".

Dariya Hafiza tayi tace "Gaskiya kam hakan ya kamata kinga sai mu fara shiri , waye sirinkin namu?."

Janan ta mik'e da gudu tana fad'in "Ni sai da safen Ku".

Sosai ta bashi dariya yace " Allah ya shirye ki , yanzu haka fa son auren take zata wani fake da jin kunya mtwss."

Kallon Hafiza yayi yace "Meye kike murmushi?".

Tace " Kuji mutum ina ruwan ka dani ."

Zaro ido yayi yace "dani kike?".

Ta murgud'a baki tace " Eh d'in a d'au mataki".


Mik'ewa yayi yana girgiza kai yana nufo inda take.

Mik'ewa tayi tana ja da baya tana dariya shi kuma yana biyo ta.

Caraf ya rik'o hannun ta ya juyar da ita ya rungume ta baya ya kwantar da kansa a kafad'ar ta yana shafa cikin ta , a hankali yace "Gashi na kama ki kuma kar ki manta d'azu kin d'au bashi."

Ita kuwa Hafiza tsigar jikin ta tashi tayi jikin ta yayi sanyi tana lumshe ido.


Harshen sa ya zura cikin kunnen ta yana jujjuyawa shi .

Numfashi Hafiza take fitarwa tana lumshe ido , ganin abin zaiyi nisa cikin wata irin murya tace "a parlour fa muke muka Janan tana nan."

Bai ce komai ba ya d'auke ta cak sai bedroom dinsa.


Janan kuwa da ta fito da niyar d'aukar wayar ta da sauri ta koma tana dariya tana mamakin daman haka Yayan nata yake .Washe gari kafin su tashi Janan ta had'a komai na break fast ta gyara ko ina au kawai take jira.


Koda suka fito Hafiza kallo parlourn tayi tace "Janan duka wannan aikin ke kika yi?".

Janan tayi dariya tace " Haba Aunty wannan har wani aiki ne , kedai ki cigaba da shan love dinki keda Yaya. "

Zaro ido Hafiz yayi yace "Janan haushe kika zama haka."

Dariya tayi sosai sannan tace "Tun jiya da daddare bayan na shiga d'aki" ta fad'a tana shiga d'aki da gudu.

Dariya suka yi Hafiza tace "Ai duk kai kaja komai gashi nan Ashe tana kallon mu."

Tab'e baki yayi yace "To sau me".

Haka suka dinga hira har suka gama cin Abincin.K'arar mota suka ji a harabar gidan duk a tunanin su Uncle ne , Cikin sallama Aunty ta shigo itada Humaira da Mu'azzam.


Da fara'a Hafiza ta mik'e tana fad'in " Sannun Ku da zuwa".

Humaira kuwa tuni sun shige d'aki ita da Janan suna hira.


Hafiz kuwa ya had'e rai kamar bai tab'a dariya ba.

Aunty tace "Hafiz nasan zaka yi mamakin ganina a gidan ka ba wani abu ne ya kawo ni illa Neman gafarar Ku."


Da mamaki Hafiz yake kallon ta , ya akayi ta sakko har zata neme gafarar su? Me tayi musu ?.

πŸ“–* Aunty ta cigaba da cewa "Hafiz hak'ik'a ta cutar da kai na nuna maka tsana fiye da yadda baka tunani , ba komai yaja wannan ba sai zallan kishin da nake da mahaifiyar ka , Hafiz gani yau ina Neman gafarar ka ka yafe min duk abinda nayi maka."

+

Da mamaki Hafiz yace "Amma meyasa kika zo Neman afuwa ta?."

Aunty tace "Humaira ta samu mijin aure har sun gama magana sai daga baya iyayen sa suka ji labarin hali na da kuma abinda nake yi maka kaida Janan sai suka ce sun fasa baza su had'a zuri'a dani ba Dan k'ila halin mu d'aya da Humaira , da farko abin bai dame ni sai da daga baya na zauna tayi tunani na gane hakan da nake yi ba dai-dai bane shiyasa na kawo Mu'azzam da Humaira wajan ku ."

Ajiyar zuciya Hafiz yayi yace "Shikenan Aunty komai ya wuce , ni daman ina son y'an Uwana kuma ina burin zama dasu ."

Aunty tayi murmushi tace "Nagode sosai Hafiz ina Janan?."

Dai-dai lokacin sun fito daga d'aki ita da Humaira Janan tace "Gani Aunty ."

Aunty tace "Janan Dan Allah ki...." Janan ta katse ta da fad'in "Haba Aunty basai kin nemi yafiya ta ba nida man ban rik'e ba wallahi."

Uncle da Mama ne suka yi sallama suna shigowa parlour .

Juyawa Aunty tayi tace "Kuma nasan nayi muku laifi Dan Allah Ku yafe min."


Uncle ya saki murmushi yace "Kar ki da Maimuna komai ya wuce."

Mama kuwa kauda kai tayi tana tab'e baki.

Cikin farin ciki a ka zauna a parlourn ana hira , suna cikin hira Hanifa tayi sallama aka zauna har ita ana wasa da dariya.


Tunda Hanifa ta shigo Mu'azzam ya kasa d'auke ido daga kanta , tana d'ago wa zata kama shi yana kallon ta , tsaki tayi ta d'auke kai ta cigaba da hirar ta.


Da daddare Aunty da Mu'azzam suka tafi Dan Humaira tace baza ta tafi ba.

Bayan kwana biyu.

Cikin kwanakin kullum sai Mu'azzam yazo wajan Hafiz sunyi mutuk'ar sabo sosai , Hafiza kuwa farin ciki take tana godewa Allah da ya had'a kan su.

Sauri Hafiz yake dan so yake yaje ya gaida su Mama daga nan ya wuce office.

Hafiza tace "Kayi a hankali mana sai sauri kake."

Yace "baza ki gane bane Hafizty inso naje na gaida su Mama daga nan na wuce office sai waya ake min tun d'azu ko gidan Aunty ma b zani ba sai na tashi daga office."

Hafiza tace "to break fast d'in fa?".

Yace " Samin shi a mota baci a office" ya fad'a yana fita daga d'akin.

A basket ta had'a abincin ta saka masa a mota ya tafi.

Humaira da Janan suna zaune Hafiza ta dawo ta kalle su tace "Y'an biyu kuna zaune Ashe."

Dariya Janan tayi tace "Ai nasan baki kula da mu ba sabida love ya rufe muku ido keda Yaya ko kunyar mu bakwa ji."


Murmushi Hafiza tayi tace "Allah ya shirya min ke Janan " ta fad'a tana shiga d'aki.

Humaira ta kalli Janan tace "ke nifa wallahi ba k'ara min burge ni Soyayya Yaya da Aunty Hafiza take ba , baki ga yarda suke tattalin juna nan su kamar a India."

Janan tace "Nima haka wallahi ina buri nima in nayi aure mijina ya dinga kula dani kamar Yaya na."


Humaira ta rik'e baki tace "Aure kike so kenan?" Ta fad'a tana dariya.

Janan ta zaro ido tace "Ni bance ba kar yi min sharri , ni gobe ma zan koma gidan uncle sabida zama a gidan nan sai ka shirya Yaya Hafiz babu ruwan sa a gaban mu yake shan soyayyar sa Aunty Hafiza."

Humaira ta saki dariya tace "Wato kinga abinda yafi k'arfin ki, ai gwara mu koma kar mu takura musu."


Hafiz kuwa yana fita gidan uncle ya wuce , bayan sun gaisa da uncle ya shiga parlourn Mama.

Ganin bata parlour yasa ya nufi bedroom d'inta.

Tana zaune a kan kujera ta juyawa k'ofa baya tana waya.

Cak ya tsaya sakamakon jin abinda Mama take cewa.

Mama tayi tsaki tace "Nifa banso kishiyar uwar sa tazo suka shirya ba naso na d'aura mata laifin yiwa Hafiz asiri wallahi."

Shiru tayi alamun daga d'aya b'angaren ana magana , ta cigaba da cewa "Hmm kedai bari ni kaina ina jin tsoron ranar da asirina zai tonu in har Abban Fadil yasan nice nayiwa Hafiz wannan asirin ai na shiga uku Dan nasan dak'yar in bai sake ni ba ,"

Dariya tayi tace "ke koni Wallahi na tsani Hafiz d'in nan kawai daurewa nake ina sakar masa fuska amma na tsane shi sabi....." Maganar ta katse sakamakon juyo da tayi suka yi ido hud'u da Hafiz a tsaye a bayan ta yana wuci.

Gabanta ya fad'i amma sai ta basar tace "A'a son yaushe ka shigo?" Ta fad'a tana murmushi.

Hafiz da idon sa ya koma ja tsabar Bak'in ciki ya kasa furta komai sai kallon ta yake .

A hankali yake takowa yazo kusa da ita ya duk'usa yana hawaye masu zafi gabad'aya ya kasa magana.


Ganin haka Mama tasan yaji komai , jin alamar motsi a jikin k'ofa yasa Mama cakumar rigar Hafiz ta k'arfin tsiya ta yaga ta , cire d'an kwalin ta tayi ta yar ta hank'ada Hafiz ya fad'i ta saki ihu mai k'arfin tsiya tana fad'in "Wayyon Allah Abban Fadil kazo ka taimake ni Hafiz zai yi min fyad'e" ta fad'a tana kuka sosai.


Dai-dai lokacin Uncle ya shigo d'akin da sauri.

__________πŸ“–* Cikin b'acin rai Uncle yake kallon Hafiz da ya kasa magana , cikin tsawa Uncle yace "Bana son ganin ka Fitar min daga gida kar na k'ara ganin k'afar a cikin gidan nan , na tsane ka tsana mai muni ma kuwa fita ka bani waje."
+
Duk yadda Hafiz yaso ya furta magana kasawa yayi sai hawaye da yake fita a idon sa , fita yayi daga d'akin jiki a sanyaye .
Ganin ya fita yasa Mama tayi murmushi ta taso da gudu tana hawaye ta fad'a jikin uncle tana kuka , rungume ta Uncle yayi yana bubbuga bayan ta alamun rarrashi .
D'ago ta Uncle yayi ya kalli cikin idon ta yace "daman ya saba yunk'urin hakan?."

Cikin kukan munafurci tace "ya tab'a yi sau biyu ina kyale shi ban fad'a maka ba sabida kar na fad'a maka kaga kamar k'arya nayi masa , shine yanzu ina zaune naji ana shafa ni ni na zata ma kaine ina d'ago wa nagan shi shine muka fara kokawa har na yaga masa riga , yaci amanar ka ban tab'a tunanin makamancin haka daga wajan Hafiz ba ka rik'e shi tun yana k'arami Amma wai yau da abinda zai saka maka kenan" ta fad'a tana kuka sosai.
Sosai ran Uncle ya b'aci jin har sau biyu yana Neman matar sa ga yau yayi na uku , zaunar da ita yayi akan kujera yace "kiyi Hak'uri kinji Nagode da kika rik'e min mutuncin ki shi kuma Hafiz zaiga abinda zan sama" ya fad'a yana fita daga d'akin.
Yana fita ta k'yalkyale da dariya tace "ai tunda na tabbatar kaji cewa ni nayi maka asiri to bazan tab'a bari Abban Fadil ya yarda da hakan ba dani kake zancen."

Hafiz kuwa ikon Allah ne ya kai shi gida koda ya shiga parlourn babu kowa hakan yasa ya wuce d'akin sa da k'yar Dan yadda jiri yake d'aukar sa .
Hafiza tana d'akin tana gyarawa taji an bud'e k'ofa an shigo , duk zaton ta Janan ce tana juyowa taga Hafiz yana tangad'i .
Da gudu tazo ta rik'e shi tana tamabayar lafiya? Amma ko iya bud'e ido baya yi sai cize baki da yake .
Taimaka masa tayi ya kwanta a bakin gado , sunkuya tayi ta cire masa takalmin k'afar sa sannan ta masa hula , ganin yadda yake gumi yasa ta k'ara k'arfin As tana kallon sa yana lumshe ido kamar mai bacci.

Kallon rigar sa tayi ta ganta a yage , gaban ta ya fad'i a ranta tace "Allah yasa ba wani Abu ne ya faru dashi ba."
Zama tayi kusa dashi ta d'ago kansa ta d'aura akana cinyar ta tana shafa kansa a hankali , tace "Dan Allah ka sanar dani abinda ya faru".

Sai a sannan ya fashe da kuka mai sauti har da shashshak'a kamar k'aramin yaro, jin yadda yake kuka itama bata San lokacin da hawaye ya fara fita daga idon ta ba , hankalin ta ya k'ara tashi duk tunanin ta kasa gane abinda ya faru dashi.

STORY CONTINUES BELOW
Sai da yayi kuka mai isar sa sannan ya fara sauke ajiyar zuciya , mik'ewa tayi ta sauka daga kan gadon ta bud'e fridge ta d'auko ruwa mai sanyi tazo ta d'ago shi ta bud'e robar ruwan taba fara bashi , sai da yasha fin Rabin robar sannan ya cire bakin sa ya jingina da gado ya runtse ido.

Cikin sanyin murya Hafiza tace "Ka fad'a min abinda yake damun ka Dan Allah."
Shiru yayi baice komai zuciyar sa tana masa zafi kamar ana tafasa ta , Hafiza ta rik'e hannun sa tace "Shikenan tunda baza ka fad'a min ba kayi Hak'uri komai na duniya mai wucewa ne ko wanne mutum da irin tasa k'addarar kuma bai isa ya tsallake ta ba , ka cire damuwa a ranka insha Allah komai zai yayi dai-dai" tana gama fad'ar hakan ya mik'e zata fita daga d'akin .

Rik'e hannun ta yayi a hankali ta dawo ta zauna kusa dashi babu wanda yayi magana a cikin su .
Cikin dashashshiyar murya yace "Hafizty Ashe Wanda ka yarda dashi zai iya cutar da kai? Wanda kuma kake ganin zai cutar da kai sai kaga masoyin Kane Mama ta bani mamaki ban tab'a tunanin ko a mafarki zata yi min haka ba".
Hafiza tace " Meya faru mai Maman tayi?."
Bai b'oye mata komai ba tunda daga wayar da yaji tana yi har kan sharrin da ta had'a masa har shigowar uncle.
Kafin ya gama Hafiza hawaye ya Wanke mata fuska cikin kuka tace "Nima banyi tunanin haka daga wajan ta ba".
Hafiz yace " Ni ba wai asirin da tayi min ke damu na ba abinda yake damuna shine sharrin da tayi min da wane ido zan kalli uncle? Ko a mafarki bazai tab'a yarda dani ba , kuma meye dalilin ta na yi min asiri ? Shine kawai abinda yake damuna".
Hafiza ta share masa hawaye tace "Kar ka damu Allah yana tare da kai duk daran dad'ewa Gaskiya zata yi halin ta ka cigaba da Hak'uri."
Girgiza kai Hafiz yayi yace "baza ki gane bane Hafiza , a hannun uncle na taso nayi karatuna komai uncle ka kya ganin yadda zai d'auki abun a ran sa ."
Hafiza tace "Na fahimce ka kuma idan nace maka uncle bazai zarge ka ba nayi maka k'arya domin ko yau ace uncle ne ya haife ka yazo ya ganka a yadda ka bani labari wallahi dole ya zarge ka kuma dole ya yarda da abinda ta fad'a masa , amma ai Allah na tare da mai gaskiya a duk inda yake nasan abun nayi maka ciwo a rai sosai haka zaka daure kayi Hak'uri komai zai dai-dai."

Ajiyar zuciya yake Dan sosai ya gamsu da maganar ta baice mata komai ba sai hannu da yasa a cikin rigar ta yana shafa cikin ta .
A hankali take shafa gashin kansa yana lumshe ido har bacci ya d'auke shi.

Ganin yayi bacci yasa ta rife shi da blanket ta rufo masa d'akin ta dawo parlour.

Janan da Humaira suna zaune suna hira Hafiza ta fito , kallon su tayi tace "y'an mata ana zaune ana hirar samarin" ta fad'a fuskar cikin fara'a sosai.
Janan tayi dariya tace "Kamar kin sani kuwa matar Yaya ."
Hafiza ta rik'e baki tace "lallai Janan Zan fad'awa Sweet H ayi a aurar dake."

Dariya tayi sosai tace "To ni Janan Yaya Hafiz d'in ne kuma Sweet H ? Na d'au style nima haka zan dinga cewa nawa miji."
Humaira kam murmushi tayi tace "Ke kuwa Allah ya shirye ki Janan ko kunyar matar Yaya bakya ji?".
Hafiza tace " Kyale ni da ita zanyi maganin ta."
Janan tace "ko kusa bana jin kunyar Matar Yaya sabida yadda na d'au Aunty Salima haka na d'auke ta wallahi."
Hafiza tace "Shiyasa Mina ai bana jin kunyar Ku ko kad'an , yaushe Aunty Salima zata dawo ne?."
Janan tace "Munyi waya da ita d'azu tace min wai k'ila sai wani satin".
Hafiza tace " Allah ya kaimu , bara mu shirya lunch ko?".

Janan tayi dariya tace "lunch ai sai na gobe tun yaushe mun gama nida sister , ai tun daga motar Yaya Hafiz nacewa Sister to mu San nayi Dan Matar Yaya mijin ta ya dawo" ta fad'a tana k'ushe dariya.

Dariya Hafiza tayi tace "Allah ya shirya min ke , sannun Ku da aiki."
Humaira tace "Babu komai wallahi matar Yaya ."
Hafiza d'aki ta shiga ta barsu a zaune.

Gab da la'asar Hafiz ya tashi jikinsa duk babu dad'i , wanka yayi ya shirya zama yayi a d'akin yana tunani.
Hafiza ce ta shigo tace "Au har ka tashi kenan ".
D'aga mata kai kawai yayi baice komai ba, hannu ya mik'o mata alamun tazo , k'arasa wajan tayi ta zauna a kusa dashi.
Hannu yasa a rigar ta yana shafa cikin ta ji yake kamar d'an ya fito sabida yadda yake farin ciki idan ya tuna ya kusa ajjiye d'a.
Hafiza tace " Bai kamata ka zauna a d'aki ba sabida bana so su Janan su fahimci halin da kake ciki gwara ka dawo parlour ko baza kayi magana ba ."
Hafiz yace "Hafizty ni Mama tace zanyi mata fyad'e nifa, kome zanji a jikin ta oho?."
Hafiza tace "Hak'uri zaka yi komai zai wuce , ba komai yasa tayi hakan ba sai Dan kada ka fadawa Uncle abinda kaji tana fad'a yanzu kaga ko zaka rantse da alkur'ani uncle bazai yarda da maganar ka ba cewa zaiyi sharri zaka yi mata shiyasa tayi hakan , yanzu dai ba wannan ba tashi kaje gashi can ana kiran sallah a masallaci."
Bai musa ba ya mik'e ya nufi masallaci.

Koda ya dawo a parlour ya zauna kana ganin sa kasan yana tare da damuwa .
Janan ce ta fito ta zauna kusa dashi amma baisan tazo wajan ba , tab'a shi tayi yayi firgigit ya juyo yana kallon ta.
Cikin damuwa Janan tace "Yaya na meye yake damu ka?" Ta fad'a muryar ta na rawa .
Ganin zata yi kuka yasa yace "Babu abinda yake damuna ".
Janan tace " Bayan ga damuwa nan a fuskar ka kuma tunda ka zauna kake tunani Dan Allah ka fad'a min."
Rik'e hannun ta yayi yace "Kaina ke min ciwo kuma nasha magani."
Kwantar da kanta tayi a kafad'ar sa tace "ina son ka Yaya na bana son naga wani Abu ya sane ka."
Humaira ce ta fito tana kallon su cikin burgewa , hannu ya mik'a Humaira itama ya zaunar da ita a gefen sa yana murmushi.

Banko k'ofar parlourn da akayi ne yasa yayi suka yi saurin d'ago wa suna kallon mai shigowa.
Uncle ne ya shigo fuskar a d'aure kamar ba tab'a dariya ba , kallan Hafiz yayi yace "Duk abinda kasan mallakina ne a hannun ka kayi maza-maza ka kawo min yanzu nan da bana son ko k'ara kallon fuskar ka."
Janan ce ta k'araso tace "Uncle Yaya Hafiz nefa ko baka gane mu bane?".
Wani banzan kallo yayi mata yace " daga ke har shi bana son ganin ku tunda Yayan ki maci amana ne mayaudari ni kuma bana zama da wad'annan mutanen."
Fashewa Janan tayi da kuka tana girgiza kai cike da tashin hankali.

* Kallon Janan uncle yayi ya d'auke kai ya mai da hankalin sa kan wayar sa, kashe wayar yayi sannan ya kalli Hafiz yayi murmushi ya matso kusa da Hafiz ya dafa shi yace ,

"D'ana Kar ka damu lokacin da abin ya faru naji komai ina kallon Duk abinda ya faru , hak'ik'a Huwaila ta bani mamaki ban tab'a tunanin haka daga wajan ta ba abinda yasa kaga nayi maka haka a gaban ta shine idan na nuna na amince da kai zata yi yuk'urin yi maka wani asirin shiyasa kaga na biye mata , yanzu ma Dana shigo ina sane nayi muku haka sabida taji komai a waya , Hafiz ka kwantar da hankalin ka nasan ta yarda zan b'ullo mata."

Wata sassanyar ajiyar zuciya Hafiz yayi yana godiya ga Allah ya da kawo masa sauki .


Yace "Uncle yanzu da gaske ka gane bani da laifi ?".


Rik'e hannun sa Uncle yayi suka zauna yace " Nasan baka da laifi kuma naji Duk abinda ta fad'a kar ka damu ."

Hafiz yace "Alhamdulilah."

Janan ta kalli Hafiz tace "Yaya wai me yake faruwa ne?".

Uncle yayi murmushi yace " zaki ji komai gobe in Allah ya kaimu, Gobe zamu zo a gaban kowa zan sata ta fad'i dalilin da yasa ta aikata haka ".

Uncle ya Mik'e yace " ni zan koma sai Allah ya kaimu Goben ko kuma kai Hafiz kuzo namu gidan ayi maganar a can" ya fad'a yana fita daga gidan.

Zama Hafiz yayi ya lumshe ido yana yana farin ciki na ratsa shi , Janan ta k'araso ta zauna kusa da Hafiz tace "Yaya dan Allah ka fad'a min abinda ya faru."

Ganin yadda ta damu Hafiz bai b'oye mata ba ya sanar da ita komai ya d'aura da cewa "Amma kar kisa damuwa a ranki komai yazo k'arshe insha Allah."

Kuka Janan take sosai yana mamakin halin Mama tabbas Mama fuska biyu ce , rarrashin ta ya dinga yi har tayi shiru .

Har dare Janan bata da walwala dan gabad'aya haushin Maman ma take ji , Hafiza ta kula da ko abincin karki bata ci ba zama tayi kusa da ita tace " Haba Janan yanzu baza ki kwantar da hankalin ki ba? Gobe iwar haka an warware komai dan Allah ki cire damuwa a ranki."

Janan ta share hawaye tace "Matar Yaya Mama tayi tuk'ar bani mamaki banyi tunanin haka daga wajan taba ."

Hafiza tace "Haka d'an Adam yake Wanda kike ganin kin yarda dashi bazai cuce ki ba sai kiga shine makashin ki, dan Allah ki kwantar da hankalin ki."

STORY CONTINUES BELOW

Janan tace "To, bara naje na kwanta" ta fad'a tana shiga d'aki.


Washe gari karfe sha d'aya na safe gabad'ayan su suka nufi gidan uncle.

Bayan sunje suka yada zango a parlour suna jiran fitowar Uncle d'in, Mama ce ta fito cikin tak'ama ta kalli Hafiz tace " kai ba ance kar ka k'ara shigowa cikin gidan nan ba ? Me ya kawo ka maza tashi ka fita."

Ko kallon ta baiyi ba balle ta sa ran zai amsa mata , muryar Uncle taji yana cewa "ni nace suzo" ya fad'a yana k'araso wa parlourn.

Tab'e baki tayi tace "Amma dai Abban Fadil baka da kishi wallahi mutumin da yayi yin k'urin yiwa matar ka fyad'e amma shi ka kuma kawowa gidan ka?".

Murmushi Uncle yayi yace " kedai zauna kiji dalilin da yasa na kira su."

Zama tayi tana shan k'amshi kamar wata gimbiya , Uncle yayi gyaran murya yace "Ba wani dalili yasa na Tara ku nan ba illa akan abinda ya faru jiya."

Tsaki Mama tayi tana hararar Janan , Uncle ya juyo ya kalle ta yace "Huwaila meye dalilin ki Na yiwa Hafiz asiri? Kuma meye dalilin ki na yi masa k'azafi."!

Kamar saukar aradu taji maganar gaban ta ya fad'i amma sai ta daure tace " Ban gane ba me kake nufi? ".

Uncle yayi murmushi yace " Nasan kin gane abinda nake nufi kawai ki bani amsa ta" ya fad'a yana had'e rai.

Cikin rawar murya Mama ta fara cewa "Ka bani mamaki Abban Fadil ban tab'a tunanin zaka amince da abinda Hafiz zai fad'a maka ba bayan ga abinda kazo ka gani a zahiri ,hakan ya nuna kafi son sa akaina kenan shikenan nagode , kai kuma Hafiz aniyar ka ta bika" ta fad'a tana mik'ewa.

Cikin tsawa Uncle yace "Na rantse da Allah in baki yi min bayani ba wallahi tallahi sai na sake ki saki uku , an fad'a miki banji komai ba lokaci da kike waya da kuma lokacin da kika had'a masa sharrin? Kyale ki kawai nayi dan naga iya gudun ruwan ki sha-sha-sha kawai , mai Hafiz yayi miki da zaki aikata masa Wannan d'anyen aiki? Me ya tare miki ? Kinyi masa asiri dan ya dinga bin mata sannan kuma kinzo kiyi masa sharri da wanne kike so yaji? Kin bani mamaki Huwaila ban tab'a tunanin haka daga gare ki ba ko wani ne yace zaki aikata hakan bazan tab'a amincewa ba sai gashi da kunne da naji hakan kinji kunya wallahi."

Cikin sanyin jiki Mama ta d'ago kai tana hawaye tace " duk abinda na aikata Kaine kaja ba wani ba , ka d'auki son duniya ka d'aura wa Hafiz ka fifita Hafiz fiye da d'an da ka Haifa , ni uwa ce inaso naga d'ana cikin farin ciki duk da Fadil bai tab'a nuna min rashin jin dad'i sa akan abinda kake yi ba , yadda Hafiz yasan abubuwa da suka shafe ka koni matar ka ban sani ba ta Yaya bazan tsani Hafiz ba ? Ko Kaine ya zaka ji a ranka? Wannan dalili yasa na yiwa Hafiz asiri dan idana kaji ka tsane shi" ta fad'a tana fashewa da kuka.


Shiru Uncle yayi yana sauraran ta cike da takaici dan shi baiga abinda yayi ba anan.

Tsaki yayi yace "Baki da k'wakwk'waran dalilin da yasa kika aikata hakan, Hafiz kamar Fadil yake a waje na shima d'ana ne domin amanar d'an Uwana ne , kawai dai kinyi abu cikin rashin hankali da kuma tunani, kin bani mamaki mutuk'a dan haka bazan iya zama dake ba duk Wanda baya son Hafiz nine baya so domin Hafiz d'an Yaya nane shi nake gani kamar Yayan nawa , son zuciyar ki yasa zaki yaja zubewar mutuncin ki a idon kowa na nan dan haka kije na......"

"Abba dan Allah kayi Hak'uri indai akan abinda tayi min zaka sake ta wallahi tallahi na yafe mata " Hafiz ya fad'a tana rik'e k'afar Abba.


Cikin kuka Mama tace "Dan darajar Annabi kayi Hak'uri ka yafe min wallahi sharrin shaid'an ne da kuma sharrin k'awaye su suka dinga zuga ni har na aikata hakan , dan girman Allah kayi Hak'uri nayi nadama wallahi" ta fad'a cikin kuka sosai.

Cikin kuka Janan da Humaira suka durk'usa gaban uncle suna rok'on sa amma Uncle ko kallan su yak'i yayi.

Mik'ewa Hafiza tayi a hankali ta k'araso inda Uncle yake ta durk'usa tace "Uncle Dan Allah ka yafe mata tunda dai tayi nadamar abinda ta aikata , Uncle Allah da ya hallice mu muna yi masa laifi kuma ya yafe mana da ace Allah baya yafiya da babu Wanda zai shiga Aljanna , Uncle Allah yana son me yafiya da girman Allah ka yafe mata ."

Sosai maganganu Hafiza suka ratsa Uncle amma sai ya daure yace "Bazan iya zama da mace mai bin bokaye ba mace mai shirka mai had'a Allah da wani , ta nuna kenan Allah boka ne zai biya mata buk'ata ba Allah ba , wai meyasa mata idon Ku yake rufewa ne musamman akan kishiya? Sai kaga mace taje wajan boka wai ya taimaka mata mijin ta zaiyi mata kishiya , shi kuma da yake baya tsoron Allah sai yace buk'atar ta baza ta biya ba har sai ta bashi akan , tsabar rufewar ido da son duniya sai ta amince a lokacin yayi zina da ita , ina zata kai tarin laififfukan nan? Gana shirka Wanda Allah yana yafe komai amma banda shirka tun daga lokacin da kike je wajan boka har kwana Arba'in Allah bazai karb'i sallar ki ba, gana kuma zina Wanda tana d'aya daga cikin manyan laifuka , ku kula mata Ku gane babu Wanda zai biya maka buk'ata kaf duniya in ba Allah ba , kar kuga kun rok'a amma Allah bai Baku abinda kuke so ba kuyi Hak'uri d'an jin kiri ne kuma wani jin kirin alkairi ne , Annabi Yak'ub sai da ya shekara arba'in ko k'asa da haka yana rok'on Allah da ya nuna masa d'ansa Annabi Yusuf , Allah ya amsa amma bai nuna masa ba sai da ya tsufa , to Annbawa mafa kenan balle mu da kullum cikin sab'o muke , har yanzu mamakin ki nake Huwaila kuma bazan daina ba har abada , na yafe miki kamar yadda y'ay'a na suka rik'a."


Bai jira mai zata ce ba ya Mik'e ya bar parlourn gabad'aya.

Ko wanne a cikin su jikin sa yayi sanyi , Mama kuwa kuka take sosai tana Dana sani.

Cikin kuka tace "Dan Allah Hafiz Ku yafe min sharrin zuciya ne."

Hafiz yace "babu komai Mama mun yafe miki duniya da lahira kije ki ta istigifari kina Neman yafiyar ubangiji Allah yana son Wanda yayi laifi kuma ya nemi yafiyar sa , Allah maji k'an bayin sane zai yafe miki amma kar kai kara maimaita hakan Mama."

Mama tace "insha Allah bazan kuma wannan d'inma nayi nadama wallahi."


Basu wani jima suka dawo gida duk da Hafiz yana so yayiwa Uncle magana amma ganin ran sa a b'ace yasa ya kyale shi.Ko da suka dawo kowa d'aki yayi sabida yadda jikin su yayi sanyi sosai.


Hafiz kuwa d'aki ya shiga yana tunanin rayuwa , da sallama Hafiza ta turo k'ofar ta shigo d'akin.


Tace "Hafiz kaga ikon Allah ko gashi yau gaskiya tayi halin ta."

Hafiz yayi murmushi yace "haka ne , ni yanzu ma wallahi Mama tausayi take bani."


Hafiza tace "da tausayi nima yanzu tausaya mata nake mugayen k'awaye ne suka kaita suka baro."


Mik'ewa Hafiz yayi yazo dafa da Hafiza ya rik'e kafad'ar ta yace "Yau gaskiya tayi halin ta yau zan sauke nauyin da yake kaina."

Hafiza tace "wanne nauyi kuma?".

Hafiz ya saka hannu aljihu ya d'auko wata takarda a nannad'e ya mik'awa Hafiza , gaban ta ya fad'i cikin tsoro tace " Meye wannan?".

Hafiz yace "Amsoshin ki suna cikin wannan takardar , Hafiza inaso ki kuma ina k'aunar zama dake amma ke Sam bakya son hakan tunda kince kin tsane ni , wannan dalilin yasa na baki wannan idan ki bud'e zaki ga abinda yake ciki."


+

Hafiza tsabar bak'in ciki tasan lokacin da ta fashe da kuka ba tace "me nayi maka Hafiz zaka sake ni? Wancen lokacin ma Kuskure nayi muka nace ka yafe min , kishi ne yasa na furta hakan ba tare Dana sani ba Amma wallahi inaso ka har yanzu ka fahimta mana."


K'ara had'e rai yayi yace "wannan bai dame ni ba na fad'a miki amsar ki tana cikin takardar."


Cikin kuka Hafixa ta fita daga d'akin a guje.


Murmushi yayi yace......


Murmushi yayi yace "Hafizty tawa " zama yayi ya cigaba da aikin sa yana yi yana murmushi.

+

Hafiza kuwa d'aki ta koma tana kuka sosai ta damk'e takardar a hannun ta amma ta kasa Bud'ewa, share hawayen ta tayi ta mik'e ta d'auki hijjabin ta ta fito daga d'akin.

A hankali ta take tafiya dan bata so su Humaira su fito parlourn , tayi sa'a kuwa har ta fita daga gidan babu wanda ya sani.

Bata yuce ko ina ba sai gidan Aunty dan ita gani take baza ta iya zuwa gida tace Hafiz ya sake ta ba tana jin kunyar hakan dan Ummee cewa zata yi daman ita ta nemi sakin.


A parlour ta tarar da Aunty a zaune tana cin abinci , Hafiza ta zauna a kan carpet ta suka gaisa da Aunty.

Cikin kulawa Aunty ta ajjiye abincin hannun ta tace "Y'ar ta lafiya kuwa ?".

Fashewa da kuka Hafiza tayi tace " Aunty Hafiz ya sake ni". Cikin tashin hankali tayi salati tana tafa hannu tace "me kika yi masa ya sake ki? Anya yana cikin hankalin sa? Bara na kira uncle d'in nasu yazo ayi magana".

Waya ta d'auka ta kira Uncle tayi masa bayani yace mata gashi nan zuwa gidan .

Bayan ta kashe wayar ta kalli Hafiza tace " Ki kwantar da hankalin ki Yanzu Hamisun zaizo wannan ai shirme ni me kikayi masa da zai sake ki?."

Taba b'oye wa Aunty ba ta fad'a mata duk abinda akayi a baya ta d'aura da cewa "Wallahi Aunty shikenan abinda ya faru kuma na bashi Hak'uri yak'i Hak'ura."


Tsaki Aunty tayi tace "bara yazo zai same ni ai."


Babu jimawa Uncle ya iso gidan , Aunty ta saka hijjabi ta fito suka zauna , Uncle ya kalli Hafiza yace "Me ya faru?".

Kamar yadda tayiwa Aunty bayani haka tayiwa Uncle tana yi tana kuka.

Waya uncle ya d'auka ya kira Hafiz yana d'aga wa yace " Duk abinda kake yi kazo ka same ni yanzu a gidan Auntyn ku" yana gama fad'ar hakan ya kashe wayar.


Shi kuwa Hafiz ko kusa bai kawo Hafiza bace Dan shi baiyi tunanin zata je gidan Uncle ba .


Mik'ewa yayi ya shirya ya fito daga d'akin, kallon k'ofar Hafiza yayi ya ganta a kulle k'arasawa wajan yayi ya tab'a k'ofar yaji ta gam alamun an kulle k'ofar.

Gaban sa ya fad'i a ransa yace "me nake shirin aikatawa ne? Me nayi kenan? Ina ta tafi ?" Duk bashi da amsa , Janan ya k'wallawa kira tana fitowa yace "zan fita Yanzu kuma Hafizty ma bata nan ku kula da gidan" ya fad'a yana fita daga gidan da sauri.


Da sauri ya k'arasa gidan Aunty bayan yayi parking ya fito ya shiga ciki , da sallama ya shiga parlourn Aunty ta amsa tana hararar sa.

Waje ya samu ya zauna Dan shi bai kula da Hafiza ba Sam a wajan.

Uncle yace "Hafiz ka bani mamaki banyi tunanin zaka aikata haka ba , me kayi kenan? ".

Cikin tsoro Hafiz ya d'ago yace " Uncle me ya faru?".

STORY CONTINUES BELOW

Cikin fad'a Aunty tace " Ba'a sani ba kaji zaka raina mana hankali. "


Uncle yace "me yasa ka saki matar ka ? Me had'a ku gaka gata nan."


Sai a lokacin ya kalle can k'arshe kujera ya hango ta a zaune ta had'a kai da guiwa tana kuka sosai.

Bai San lokacin da yayi murmushi ba har hak'oran sa suka baiyana ya juyo ya kalli Aunty yace " Aunty ita tace miki na sake ta?".

Cikin takaici Aunty tace "Ban sani ba , Hafiz ka fita daga ido na wallahi ya zaka dinga raina mana hankali na yi maka magana kana dariya ka maida mu sha-sha-she ko?".

Murmushi ya kuma yi yace " Nifa ban sake ba wallahi. "

Uncle ya kalli Hafiza yace "y'ata kika ce ya sake ki".


Takardar ta mik'awa Uncle tace " Ga takardar da ya bani."

Karb'a Uncle yayi ya bud'e takardar ya fara karantawa , murmushi Uncle yayi ya mik'awa Aunty takardar , karb'a tayi itama ta karanta .

Tana gama karantawa tayi tsaki tace "amma dai Hafiz ko kad'an baka da kunya wallahi" tana fad'a tana shigewa d'aki.

Uncle ma mik'ewa yayi yana murmushi ya fita.

A hankali Hafiza ta k'arasa ta d'au takardar ta bud'e ta fara karantawa,

_Assalamu Alaiki masoyi ta Hafiza , an fad'a miki zan iya sakin ki ne? Ko a mafarki bazan iya hakan ba , nayi missing d'in kwanciya a fatar jikin ki my soul , ina sonki Hafiza bazan kuma iya sakin ki ba , ki shafa min kan baby na._


Sunkuyar da kai Hafiza tayi tana murmushi cike da jin kunyar sa .

Dariya Hafiz yayi sosai yace "Wai ke da gaske ki d'auka sakin naki nayi? Lallai kina ruwa."

Mik'ewa tayi cike da shagwab'a ta fara kukan tab'ara tana dire k'afa.


Ta baya ya rungume ta ya kwantar da kansa a kafad'ar ta yace "ya kika ga tsanarin nawa?".


Kwace kanta tayi tace " Bai yi ba kuma nima saina rama ."

Murmushi yayi yace "zamu had'u ne zaki gane kuranki ".

Aunty ta fito ta harari Hafiz tace " in ka kamo ka cewa Janan su tawo nan zaman can d'in ya isa haka ".

Hafiza ta bud'e baki zata yi magana Aunty ta d'aga mata hannu tace " bafa zasu zauna ba kar ma ki rok'e ni su dawo nan."

Shiru tayi bata ce komai ba , Hafiz yace "dan Allah Aunty ki bar mana su zuwa wani lokaci."

Hararar sa tayi tace "bafa zasu zauna ba kana zuwa yanzu ka turo min su minyi waya da Salima ma tace tana kan hanya gobe."

Hafiz yace "to zasu tawo insha Allah, mu bara mu tafi" .

Aunty tace "to Allah ya kikaye hanya".


Suka amsa da Ameen suka bar gidan.


A parlour suka tarar da Humaira a zaune tana charting , Tana ganin su ta mik'e tana fad'in " Yaya kun dawo?".

Yace "Eh mun dawo ina Janan?".

Tace " tana d'aki bacci take".

Yace "ok shikenan Ku shirya anjima zan kaiku gidan Aunty tace lallai yau Ku koma gida."

Humaira tace "to shikenan Allah ya kaimu."

D'aki Hafiza ta wuce ta shiga wanka.

Babu jimawa Hafiz ya fito ya kai su Janan gidan Aunty bayan sun samu abin arzuk'i daga wajan Hafiza da Hafiz.

Da daddare bayan Hafiz ya dawo daga masallaci a parlour ya tarar da Hafiza a zaune , Zama yayi kusa da ita ya jayo ta jikin sa yana shak'ar k'amshin wuyan ta yana shafa cikin ta .

Kwace kanta tayi ta kauda kai tana had'e rai tana turo baki , Murmushi yayi yace "haba dai my soul har yanzu baki gama fushi dani d'in ba? Am sorry nasan nayi laifi ki yafe min kinji?" Ya fad'a yana k'ara matsowa kuda ita sosai.


Cikin sauri ta mik'e tana fad'in "Ni babu ruwa na dai kuma sai na rama nima."


Kallan ta yayi aka yi sa'a kuwa suka had'a ido sai kuwa ya k'yalk'yale da dariya yana rik'e ciki .

Cikin dariya yace "ni kinsan wallahi dariya kika bani d'azu oho su my soul an jiyo kamshin zawarci" ya fad'a yana cigaba da dariya.

Iya k'uluwa Hafiza ta k'ulu sai kawai ta fashe da kuka tace "eh dai naji koda ka sake ni ai bazan rasa mai sona ba gasu nan da yawa Dan ma da wannan cik...." Bata k'arasa ba ya bige mata baki ya had'e rai yace "kar na k'ara jin kin furta wannan maganar ".

K'ara k'arfin kukan ta tayi sosai tana turo masa baki , had'e bakin su yayi waje d'aya yana kissing d'inta.

Bayan kwana biyu .

Fadil ya dawo daga England ya zama cikakken likita , babu Wanda ya kai Janan murnar ganin Fadil .

Da yamma gabad'aya suna a parlourn Uncle suna jiran sa , babu jimawa Uncle ya fito ya zauna yace " Abinda yasa na taro Ku anan shine kai Fadil tunda ka gama karatun ka sai ka fito da matar aure , Mu'azzam kaima haka, Janan keda Humaira Kuma ku fito da mijin aure in kuma da Wanda kuka daidaita Ku sanar dani."

Fadil ya sosa k'eya yace "daman ni Abba akwai wacce nake so ".

Uncle yace " alhamdulilah wacece to a ina take?".


Kallon Janan yayi yayi murmushi yace "Abba ba wata bace sai Janan."

Murmushi uncle yayi mai baiyanar da farin ciki yace "kai alhamdulilah to ita Janan d'in tana son ka?".

Da gudu Janan ta mik'e ta bar wajan tana dariya .

Abba yace " To alhamdulilah kai an gama da kai , Mu'azzam kaifa?".

Sosa kai yayi yace "Abba ni Hanifa k'anwar matar Yaya nake so itama mun gama magana da ita."

Uncle yace "A'a kaima dai Ashe ta gida ce to Masha Allah gaskiya naji dad'i sosai."

"To ke Humaira fa?".

Sunkuyar da kai tayi tace " Uncle mun gama magana da Asp abokin Yaya " tana gama fad'ar hakan itama fita da gudu.

Dariya Hafiz yayi yace "Lallai kace daman jira kawai suke kayi magana lallai ma Asp haka zamuyi dashi."

Uncle yace "To Alhamdulilah haka nake so ai Yanzu Sai a tsayar da lokacin biki ."

Hafiz yace "Uncle in bazaka damu ba ina Neman wata alfarma a wajan ka Dan Allah".

Gyara zama Uncle yayi yace " ina jinka".

Hafiz yace "Uncle ina Neman alfarmar ka auri Aunty Dan Allah."


Uncle ya kalli Hafiz yayi murmushi yace "to sai nayi shawara akan hakan".

Fadil yayi murmushi yace " Dan Allah Abba ka amince".

Mu'azzam dai banda murmushi babu abinda yake yi.


Cikin satin aka tsayar da lokacin biki wata goma basu zuwa.*BAYAN WASU WATANNI.*

+

Cikin Hafiza ya shiga watan haihuwa hakan yasa Hafiz ko office ya daina zuwa kullum yana gida yana kula da Hafiza.

Biki yana ta matsowa yanzu ya rage saura wata biyu kacal zuwa lokacin har an d'aura na Uncle da Aunty .

Da yamma Hafiza suna zaune da Hafiz a d'aki Hafiz yace "nifa na k'agu baby na fito " ya fad'a yana shafa cikin ta.


Shiru tayi Dan ita kad'ai tasan abinda take ji cize baki tayi tace "Wash baya na ya rik'e."

Cikin rud'ewa Hafiz yace "kodai mu tafi asibiti ne?".

Cikin sauri ta girgiza kai tace " Lafiya k'alau fa babu abinda nake ji kawai dai ji nayi baya na ya rik'e ".


" A'a Hafizty muje asibiti bana son wani Abu ya sane ki fa."

Tace "Nace maka babu komai ka kwantar da hankalin ka , yanzu fa saura wata biyu mu sha biki wallahi ji nake kamar na jawo lokacin."

Hannun sa yasa a gashin ta sannan yace "Nidai fatana Allah ya raba ki da wannan Cikin lafiya".

Tace " Ameen , yunwa fa nake ji" ta fad'a tana ya mutse fuska.

Da sauri ya mik'e ta tafi kitchen babu jimawa kowa mata Jellop d'in shinkafa, bata ya dinga har ta d'an ci da yawa sannan ta daina ci.


Cikin dare Hafiza ta kasa bacci sabida yadda marar ta take juyawa , mik'ewa tayi zaune tana nishi k'asa-k'asa .

Mik'ewa tsaye tayi tana zagaya d'akin tana rik'e baya , wata irin murd'awa marar ta tayi bata San lokacin da ta zube a wajan ta saki k'ara mai k'arfi.

Da sauri Hafiz ya mik'e ya nufo wajan ta yana fad'in "tun d'azu naga alamar baki da lafiya amma kin ki yarda da hakan" ya fad'a yana d'aukar ta da sauri sai mota .


Gudu yake sosai Dan kafin su k'arasa asibitin Hafiza ta gama galabaita sosai , cikin gaggawa aka karb'e ta direct d'akin haihuwa aka shiga da ita .

Hafiz kuwa yana waje yana faman zuba mata addu'a , can wajan minti ashirin sai ga Nurse d'in ta fito da gudu Hafiz ya k'arasa wajan ta yana tambayar ya mai jikin?.

Nurse d'in tace "har yanzu dai labour take gaskiya ta wahala da yawa zuwa nan da minti goma in bata haihu ba za'a yi mata operation."

Dafe kai Hafiza yayi ya kasa furta komai sai gaban sa da yake fad'uwa .

A can labour room kuwa Hafiza tana can tana fama gabad'aya ta fita daga hankalin ta , wani nishi tayi mai k'arfi Cikin ikon Allah sai ga baby ya fad'o , nurse d'ince take cewa "kai da wani fa naga twice ne a Ashe" bata rufe baki ba santaleliyar yarinya ta fad'o.

STORY CONTINUES BELOW

Babu b'ata lokaci aka gyara ta aka gyara babyn suka yi tsaf , da sauri suka fita aka sanar da Hafiz haihuwar Hafiza.

Fad'uwa yayi a wajan yana mik'a godiya ga Allah da ya bashi wannan kyauta .

Sai a time d'in ya kira su Aunty dasu Ummee ya sanar dasu , aikam babu jimawa suka cika asibitin kowa yana burin yaga abinda aka samu.

Shi kuwa Hafiz ko d'aukar yaran yak'i yi wai indai bai fara ganin Hafiza ba to ba zai ga baby's d'in ba.

D'akin suka shiga ana tayiwa Hafiza sannu shi kuwa Hafiza zuba mata ido yayi ganin ta rame kamar ba ita , had'a ido suka yi sai kuwa tayi masa murmushi , shima murmushin yayi ya d'auki baby's d'in yana kallon su cike da so.

Da safe aka basu sallama suka dawo gida.


A zaune a parlour kowa yana baya kyaun yaran , Janan tace "Amma dai Aunty Hafiza ba gida zaki tafi ba ko?".

Ummee ce tace " wane irin gida ai yanzu wannan lokacin ya wuce an daina zuwa gida tayi zaman ta a nan sai a kawo mata mai kula da ita."

Aunty tayi murmushi tace "Gaskiya kin burge ni dan ni banga amfanin zuwa gidan nan ba haka kawai a bar miji da aiki, sai a zo a d'auke masa mata har zuwa kwana arba'in aka sani ko bazai iya jure yawan kwanakin ba? Shiyasa fa wasu suke k'ara aure wallahi amma ai tsohuwar alada ce ni Sam bana ra'ayin ta sabida za'a shiga hakk'in mijin wallahi."


Haka dai suka dinga hira har rana tayi.

Ranar suna da yake mace da namiji ne yarinyar aka saka mata sunan mahaifiyar Hafiz wato Amina ana kiran ta Ra'isa namijin kuma sunan mahaifin Hafiz ana kiran sa Ra'is.

Anyi hidima sosai a sunan anci ansha an goge baki da nama, babu kamar y'an Gaskiya writer's sunfi kowa ci.


Bayan wasu kwanaki.


Shirye-shiryen biki ake Sosai Dan saura kwana biyu a fara , su Hafiza sune a gaba a lokacin su Ra'is suna da wata biyu a duniya .

Yau ta kama Ranar kamu amarya Janan da Humaira sunci ado cikin kaya iri d'aya sai fa suka burge kowa na wajan , aka fara gudanar da event , bayan an gama nasu da daddare aka tafi ta Hanifa da Mu'azzam , a can naga My Zeey an bud'e ciki ana kwasar kaji sai da masu raba abincin suka Kore ta sabida ta karb'a yafi sau gomaπŸ˜›.


Washe gari aka yi lunchig mai kyaun gaske , da safe aka d'aura aure.


An kai amare lafiya bayan sun sha nasiha mai ratsa jiki.


*BAYAN SHEKARA BIYAR.*Su Hafiza an zama Mama Dan bayan haihuwar su Ra'isa ta haifi mace aka saka mata sunan Ummee .


Su Hanifa kuwa ko wacce ta diri d'a a duniya dan Humaira da Janan cikin na biyu ne dasu Janan ce take hutawa.


Hafiz ne zaune a parlour yana aiki a laptop Hafiza tazo ta zauna kusa dashi tace "Bad man aikin me kuma ake yi?".

Dariya yayi jin sunan da ta kira shi dashi yace " In ma aikin nake tunda matar Bad man tazo wajan ai dole na ajjiye."

Murmushi tayi tace "Har na tuno lokacin da kake raina min wayo ni kuma da yake sokuwa ce Sai na kasa ganewa."

Dariya yayi sosai yace "ai har yanzun ma sokuwar ce indai kince ke ba sokuwa bace kiyi kissing d'ina yanzu."

Jin abinda yace tayi murmushi tace "sarkin wayo to baza dai ayi min wayon ba eye".


Zata gudu ta jawo ta fad'o jikin sa yace "yanzu sai ki fad'a min meye sirrin naga kin k'ara wani fari kodai?" Ya fad'a yana kashe mata ido d'aya.

Hafiza tace "kodai me? Bani da komai bara kaji na fad'a maka."


Yace "Really".


Tace " yesss am sure."

Yace "ok let me check" ya fad'a yana k'ok'arin cire mata Riga.

Shigowar Ra'isa da gudu ne ya hana shi abinda yayi niya , duk da haka dai bai sake ta yace "Mama na lafiya kike gudu".

Cikin shagwab'a tace " ba malamin islamiyyar mune yace wai Yaya Ra'is yafi ni k'ok'ari ba".

Hafiz ya d'auke ta yace "To ai ba Abu damuwa bane kema Ku dage ki fishi kinga sai na dinga siya miki sweet ko?".

Dariya tayi tace " Haka ne kuma Dady na bara naje nayi karatu " ta fad'a tana shiga d'aki a guje.

Murmushi Hafiza tayi tace "Ra'isa rigama na rasa rigimar wa tayo kila dai kana yaro kayi rigima ko da yake ai har yanzu kana da ita".


Kwafa yayi yace " zaki shigo hannu ne yarinya."


Bayan sallar i'sha suna zaune gabad'ayan su suna karatun alkur'ani a tare .

Bayan sun idar Ra'isa ta kalli Hafiz tace "Dady wai Momy baza ta k'ara siyo mana wani k'anin bane?".

Dariya Hafiz yayi ganin yadda Hafiza ta had'e rai yace " Ta kusa siyo muku ranar da zata shiga kasuwar ya kusa " ya fad'a yana kallon ta.


Ra'is yace "Nima so nake a siyo namiji tunda an siyowa Ra'isa k'anwa Nima sai a siyo min k'ani."

Hafiz yace "kar ka damu an kusa , to mu d'aga hannu muyi mata addu'a".

D'aga hannun suka yi suna addu'a cikin farin ciki da soyayya.
*ALHAMDULILAH*πŸ’ƒπŸ»_ANAN NA KAWO K'ARSHE WANNAN LITTAFI MAI SUNA Y'ANCIN MATA , KUSKUREN DANA YI A CIKI ALLAH YA YAFE MIN ALLAH YASA MUTANE SUN ANFANA FA SAK'ON DA NAKE SON ISARWA A CIKIN SA._

Post a Comment for "YANCIN MATA CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...