WAYA SAN GOBE? CHAPTER B KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WAYA SAN GOBE? CHAPTER B KARSHE

WAYA SAN GOBE? CHAPTER B KARSHE

- - Post a Comment

 WAYA SAN GOBE? CHAPTER B KARSHE


Fadila tayi murmushi sannan ta tada mota iftihal tace "anty Abba yace munyi kyau wai na zama 'yar gatan anty ni 'yar gatanki ce wai anty?"ta shafa kanta da daya hannun nata tana murmushi tace"iftihal ke 'yar gata na ce mana"


Minti arba'in suka qarasa gidan da yake safiya ce babu yawaitar mutane sai 'yan uwa na jiki sosai,su hajja gana(kakarsu ta gun uba) umma a'i anty hafiza rumaisa da sauran 'yan uwa na nesa da na kusa,Fadila ta fada jikin hajja gana tana cewa bari na more cinyar 'yar tsohuwa" hajja gana ta sa dariya da yake sunfi shiri da Fadila fiye da farida"more abinki kafin kema Allah ya kawo miki masu more taki"murmushi fadilan tayi sannan suka soma gaisawa da yan uwan hajjar na tambayarta mai gidan tace lpy lau yana ma gaisheki


Kafin azahar gidan ya tumbatsa da jama'a,ko ta ina,bayan azahar kuma da kadan sai ga family din aliyyu momi ce kawai banda ita,cikin bedroom din farida sukayi zamansu anata karbar baqi


Rabi'ah ta kalli fadila lokacin da take canza kaya su anty hauwa na sallah tace "ni dai anty idan kuka tafi chinan nan qana nan kaya kawai nike son tsarabata"fadila ta dago ta dubeta bayan ta gama zuge zif din rigarta tace"wace china kuma rabi'ah"dariya rabi'an tayi"kai anty ko baki son asan zaki ne?"cikin rashin fahimta take dubanta tana qoqarin daura dankwalinta"wai wa yace miki zani china rabi'ah?"ta sake qyalqyalewa da dariya tace"tun last week fa yaya aliyyu ya gaya ma momi an gama ginin sabon company dinsa da zai bude zai wuce china cikin satin nan ke da shi,shekaran jiya kuma sai ga shi ma da visa dinku a hannu ta fito jibi zaku tashi da daddare amma anty kice baki sani ba?πŸ˜€"


A badini zancen yayi matuqar kidima fadila ya daketa sosai amma sai ta dake don kada ta bada satar amsa ta qago murmushin yaqe"kinsan halin yayanku akwai lafiyar miskilanci dazun dai yake cemin idan na dawo zai min wani albishir to ina tsammanin shine"sumayya da a lokacin ta sallame sallarta tace "har Allah Allah nake na idar kinga haukan da salima ta dinga yi wai da ita za'a tafi?"su sumayya suka kwashe da dariya rabi'ah tace"qara fa ta kawo gun momi sai gata tayi tsuru tsuru da ya aliyyu yake fadin babu abinda suka iya ba inda zai je da su su zamar masa nauyi"sumayya ta dora "qarshe ma momi da yake zayyano mata matsalarsu kunya ce ta isheta ta bar falon ba shiri tace suje gida su shirya kansu mu dai bamusan ya aka qare ba bata sake tada zancen ba ma"anty hauwa tace"ku kuma gaku sarakan gulma ba,kwaci qaniyarku da ya kamaku kuna labe ai"


Duka wunin ranar bunda ke cin zuciyar fadila kenan zancan tafiyar yayi masifar daga mata hankali,sai ta rasa nutsuwarta gaba daya,lokaci lokaci qwalla kan taru a idonta ta faki idon mutane ta matse ta,gaba daya sai kuzarinta ya ragu,Allah Allah take su kebe da farida,bata tsammani alkhairi aliyyu ke nufi da tafiyarsa da ita,nufinsa ma fa kenan gaba daya tabar aikinta da take masifar so ta kuma fara jin dadinsa yake kuma debe mata kewa?sam ba zata iya wannan tsari nasa ba


Sai bayan sallar isha'i ta samu nasarar tadda farida cikin bedroom dinta zaune gefan gado tana canzawa baby da taci sunan maman mubarak wato(aisha humaira)pampers ta zauna itama a gefan gadon tana duban pampers din da faridan me sawa humairar ,da fara'a farida ta juyo a fuskarta tana duban fadila zata dan tsokaneta sai fara'ar ta janye sakamakon qwalla da ta gani tana bin kumatun fadila tayi hanzarin sauke humaira da ta aza akafadarta tana cewa"lafiya sister?"tamkar ma ta tunzurata sai hawayen suka dadu


Tafin hannunta take sawa tana share su da nufin tsaidasu saidai turereniyar fitowa ma suke abinsu,sai da farida tasa hannayenta ta kamo hannayen fadilan ta sa cikin nata sannan ta sake tambayarta,da qyar kuma cikin muryar kuka fadila ta bude bakinta tace"yanzu tsakani da Allah abinda aliyyu kemin yana kyautawa?"tayi tambayar wasu hawayen sabbi na shirin sake zubowa,farida ta sake fuskantarta a dan kidime tace"meke faruwa sister me ya miki?"ta girgiza kanta cike da damuwa"wai china zai dauke ni mu tafi har kuma na tsawon wata hudu


Sai farida ta sake ta hadi da sakin dariya tana tafa hannu"πŸ€”yanzu sister fadila wannan abun farincikin kikewa kuka kamar wata teddy?"fadila ta katseta"ba zaki fahimta ba farida kwata kwata wata na nawa da soma aikina?"farida ta sake dubanta"😏aikin banza sister fadila,ga inda zaki samu aljannarki kike zancan wani aiki"sake girgiza kai fadila tayi"still farida baki fahimceni ba,zan gaya miki abunda babu wanda yasan yana faruwa sai ke,har yau sister aliyyu bai sona,aliyyu bai qauna ta kalma mai dadi bata taba hada ni da shi ba kallon arziqi bai taba shiga tsakanin mu ba amfani na daya agunsa shara da girke girke tamakar wata 'yar aikinsa tun muna kusa da iyaye kenan tun muna qasarmu kena ina ga nabishi can wata uwa duniya mai kuma kike zaton zai faru a ni?"


Ga mamakin fadila sai taga farida tayi murmushi mai kaa da dariya sai fadila ta saki baki tana binta da kallo tan tsammanin farida bata damu da halin da zata tsinci kanta ba kenan ko yaya?,sai da ta gama dariyarta sannan tace"☺πŸ‘πŸ»bravo! bravo! bravo!,wallahi aliyyu yayi miki gata ba da qarami ba"zaro ido fadilan tayi har ya mamakin bai sake ta ba😳,ganin haka yasa farida ta kama kafadar fadila ta sake juyowa da ita ta fuskanceta sosai,ganin yadda fadilan ta tsure sai ya sake bawa farida dariya daga baya kuma sai ta dawo serious dinta ganin kallon sakarcin da fadila ke mata,ta kuma kama hannunta sannan tace"ni na gano abinda qila ke baki gano ba,kuma ba zaki gano shi ba yanzu,sister duk abin ya aliyyu koya nuna ko kada ya nuna ko ya yarda ko kada ya yarda kina da muhammanci da wani tasiri a rayuwarsa komai qanqantarsa koda kuwa ya qaryata hakan da bakinsa,sister a iya hangena da tunani na na fuskanci cewa don kada ya aliyyu yayi missing girkinki ne baya so yayi nesa da abincinki wanda yasan zaiyi wuya ya samu kamarsa nima shaida ce"ta qarashe maganar cikin sigar tsokana wadda ta zame mata jiki


Ta nuna fadila da yatsa πŸ‘‰�sannan ta dora ke zaki canza wannan manufar ke zaki sauyata da kanki,ke zaki canza wa aliyyu wannan lafazin nasa na bazai soki ba har abada ki qaryata lafazin nasa ta hanyar nuna masa ba wanda *_yasan gobe_* sai Allah,sosai ta gamsu da maganar farida dari bisa dari kaso sittin cikin dari na damuwarta ya tafi,ta jinjina kai hadi da sakin ajiyar zuciya sannan tace"batun aikina fa sister?" "So easy"inji farida ta gada tana murmushi😊"k8na iya daukar excuse a gurinsu ki musu bayani tafiyar gaggawa ce ta sameki zuwa china zaki ajiye aiki amma da manufar zaki je course ne na wata hudu,idan hakan bai samu ba su barki a matsayin wakiliuarsu ta qasar china ta tsawon wata hudu" "great sister!"fadila ta fada cike da farinciki,tabbas dan uwa na gari dadi ne da ahi gashi xikin 'yan mintina qalilan ta warware mata damuwarta,ta rungume faridan tana cewa"thank you sister ya barmu tare ya raya mana humaira"tace "amin Allah yasa kema ki samo mana tsarabar dan china nan da wata tara ko goma mu dauki sabon baby " dariya sosai ta bawa fadila tana jinta ne kawai


Sanda ta dawo gida yana zaune cikin balcony dinsa,tayi maza ta dauke kai gami da qara sauri don ta shige shi


⚜⚜⚜⚜⚜⚜


Washegari qarfe 6:40 pm ta dawo daga aiki sun gama settling komai da managing director na express da freedom sai damuwarta ta sake raguwa qwarai da gaske,tana toilet din falo tana wanka taji moysi kadan kadan a falonta,da sauri ta kammala tana son taga waye don a bude tabar bangaren nata,kacibus sukayi da shi tsaye yake tsakiyar falon yana sanye da kufta dark coffee wadda tasha aikin sarauta sai hukarsa baqa abinka da fari sai yayi matuqar kyau kyansa da jaskensa ya sake fitowa shigar ta amshe shi sosai fadila ta lumshe idonta tana jin wani abu na zagaya jikinta"ki shirya na kaiki gida ki masu sallama,gobe zamu bi jirgin yamma insha allah zamu wuce china"duk maganar nan da yake idonsa na kan wayarsa dake hannun hagunsa damansa kuma cup ne cike da maltina mai sanyi🍺,ta dan langabe kai kamar bata ji mai yace din ba"ina zamu je?""kaiki zanyi na siyar"ya fada yana ci gaba da danne dannensa ta faki idonsa ta manna masa harar ta zagayeshi ta wuce zuwa bedroom


A sanyaye ta kammala shirinta cikin atamfa dinkin riga da zan8 simple style hakanan fadila take bata fiya son abimda ya cika ado da yawa ko daukan hankalin jama'a ba yadda take bata da hayaniua haka dabi'unta suke saidai idan ta so,ta lullube kanta da wadataccen mayafi kalar kayan,ta jawo locker dintabta debo kudaden da suke ciki ire iren kudaden da aliyyun ke basu ne duk qarashen wata da kuma na cefane acewarsa tunda komai suna da shi a ajjiye hatta magi ba zasu buqata ba ta watsa su cikin jakar sannan ta rataya ta ta fito,yana zaune a mazaunin driver tasan bata isa ta shiga baya ba ko ya shiga zai maidoto ne gaba don haka ta bude gaban ta zauna,yadan kalleta hadi da dauke kai ya daga glassan motar gaba daya samΓ  ya rufe su ruf hadi da kunna a.c,wani irin tuqi yake slowly tamkar baza'aje ba tayi tsammani zaiyi irin tuqin nan nasa mai gudun tsiya,a hankali suke ratsa titi nan har suka qaraso cikin anguwarsu fadila


Muje zuwa masu karatu🚢🏻🚢🏻🚢🏻🚢🏻


Mrs muhammad ceπŸ‘‘


πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

[10/16, 1:50 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?...*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


2⃣3⃣&2⃣4⃣


A qofar gidansu yayi parking,bata ce masa komai ba kamar yadda bai tsinka mata ba,ta bude murfin motar ta nufi bakin get din gidan cikin doki ta dan tsaya suka gaisa da malam mai bude masu qofa idan zasu shige da motarsu


Parlour din babu kowa sai qamshin fresher da ya gauraye da na girki ,murmushi fadilan tayi kai tsaye ta nufi kitchen cikin zuciyarta tana cewa"ummi na bakya tsufa kullum gida kamar na budurwa" (haka haj amina take ma'abociyar tsafta ce da gayu,don bata yarda wai don tana da manyan yara harda jikoki ta zauna haka ba,baka raba qafarta da hannunta da jan lalle mai ado irin na yanzun wanda akeyi,hakanan kullum kalolin girkinta daban ne masu dannkaren dadi hakan ne yasa yaranta sukayi gadonta suma,tun aurensu ita da alhj abbas koda wasa bai taba tunanin qaro aure ba donba cewarsa ta isheshi duk dashi qarin aure qaddara ce rubutacciya idan Allah ya qaddaro maka sai kayi


Muhammad ta tarar ciki riqe da babban spoon na qarfe yana ta faman juya fried rice,dariyar da fadila ta tuntsure da ita ita ta saka shi juyowa don bai ankara da shigowarta ba sai lokacin,ya saki murmushi yace"anty fadila yaushe kika zo?" Ta kama baki"πŸ€”ina zaka san na shigo ka taqarqare kana ta jagwal gwalawa ummi abinci,wai yaushe ma ka fara shiga kitchen?"ya saki spoon dinnyana share zufa a goshinsa"😊 ni wallahi ma gwara da Allah ya kawomin dauki ,please anty karbi girkin nan,haka yanzu ummi kemin ko ta daina sona ne ma oho?,amma don Allah anty fadila ina ni ina wani kitchen?,wai gwara na iya tunda ku kun tafi saura ni da ita kawai a gidan"dariya fadila ta sake saki ,ta qaraso kan girkin tana gyara wasu abubuwa sai da ta hada komai ta rufe ta rage mata wuta don ta turara sannan ta tambayeshi ya haye saman freezer yayi zamansa"ina ummi" "tana gun Abba yanzu ya dawo daga kasuwa ne amma tunda an fara kiran sallah yanzu zaki gansu"


Yana rufe baki kuwa saiga dariyarsu cikin falo,da hannu Muhammad yayi mata nuni da falon cikin salin gulma,dariya ma ya bata ta miqe da sauri ta isa falon,ita da abban ne kuwa yana tsaye riqe da abun sallah ummin kuma na dauke da hularsa,da murmushi suke kallonta ta durqusa ta gaida su abban na tambayarta yanzu take tafe?,ta gyada kai yace masha Allah ya mai gidan?,tace abba tare muke yana waje,"ashshsha banda abin fadila shima ai gidansu ne amma don sakarci kika barshi a waje "ummi tayi saurin qwalawa Muhammad kira tace ya zo ya shiga da shi,abba yace barshi naje na sameshi in yaso idan mun idar da salla sai mi shigo tare,a shirya mana abinci kafin mu shigo din


Ummin ta dan rusuna tana miqa masa hularsa tace"insha Allah abban Muhammad a dawo lafiya"ya karba yana dora ta a kansa yace "Allah yasa Allah yayi miki albarka" cikin dariya yaran suka taya ta amsawa da amin


Sai da fadila ta taya ummin suka shirya komai kan dining sannan suka tafi yin sallah ummi ta ahige dakinta fadila ma tsohon nata dakin ta bude ta shiga,bin dakin tayi da kallo komai yana nan kamar yadda yake,dan fridge dinta na boye ice cream 'yar kwanar da take ibadunta,inda take boye kanta idan zatayi kukan Aliyyu,sai komai yake dawo mata"Allah sarki" ta fada a fili tana shafa filonta da take cusa kanta a qasansa ,qwalla ta dan taran mata a ido ta sa yatsanta ta dauketa,toilet ta tura ta shiga ta daura alwala ta dawo inda ta saba yin sallarta tayi,bayan ta idar ta duba kan mirror dinta powder ce kawai akai ita ta dauka ta sake gyara fuskarta sannn ta mutstsika turare ya sauka qasan


Muhammad ne kawai zaune kan table din yana buga game a wayarsa ta zauna kusa da shi hadi sa dan dukan kafadarsa,ya dago ya dubeta yana murmushi, "ka shiga aji nawa ne har ummi ta yarda aka baka waya,cikin dariya yace "haba anty nafa zama senior ina s.s one fa,kuma ma yanzu nine babba a gidan nan"dariya ya bata sosai tana cikin darawar ne ummi ta fito,tuni har ta yi wanka ta canza shiga tayi kyau duk da ba make up take yi ba,fadila na shirin tsokanarta tace tayi kyau sallamar abba da ta aliyyu ta karade falon wadda ta yake hirar da suka so farawa


Abban ne a gaba aliyyu na biye da shi har suka qaraso dining space din abba ya fara cewa da aliyyu bismillah kai tsaye taga yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna sai tayi duru duru har rudewarta taso ta fito,ji tayi ya take mata qafa ta danji zafi ta dago kai suka hada ido yayi mata alama da ido na ta nutsu,sannan ya duqar da kansa ya gaida ummi cikin girmamawa,ita kuma ta amsa masa cikin kulawa tana tambayarsa mutanen gidan


Fadila ita tayi serving kowa banda ummi don tasan ba zata ci ba,tazo kan aliyyu sai ya rasa mai zata zuba masa idonta na kan warmer tace "mai zaka ci?" "Zuba min duk abinda zaki ci" ya fada abunsa tamkar ba shi yayi maganarba,da sauri ta dago kai ta kalleshi saboda wata kunya da ya bata amma sai taga shi ko ajikinsa,ta saci kallonsu ummi sai taga hirar su ma suke da abba kamar basu san da su agun ba,sai kawai ya zuba masa fried rice da farfesun naman kaza mai yawa tana son qureshi taga zai cin?


Sai kuwa ya shayar da ita mamaki don abincinsa yake ci hankli kwance duk da baici da wani yawa ba yafi shan lemo,bayan sun kammala ita ta kwashe kayan ta kaisu kitchen ta hada ta wankesu kamar yadda ta saba tanayiwa ummin tun kafin tayi aure,tana aikin cikin ranta tana gulmar aliyyu bai da kunya


Saman kujera ta tadda su ta parlour ta samu gefan umminta ta rakube,aliyyu ne ya dora kan maganar da sukeyi da abban "sallama mukazo yi muku abba saboda gobe insha Allah zamu wuce china" abban yace "zancan bude kamfanin ne ya taso kenan munyi maganar da abban naku ai wancan watan yake gayamin an dan samu tasgaro ne da tuni cikin wannan watan company n ya fara aiki" aliyyu ya gayada kai yace "eh abba insha Allah wanna karon za'a kammala komai a budeshi daman cike ciken takaddu ne na yarjejeniya tsakani na da gwamnatin qasar ya kawo tsaiko amma yanzun al'a muran saun daidaita


Mrs Muhammad ce πŸ‘‘


πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


1:41 pm 29/8/2016

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?..*


2⃣5⃣&2⃣6⃣


Abban ya jinjina kai yana cewa "kasan qasa ce mai tsari da doka ba irin namu qasaahen ba da sai dai muce inna lillahi wa 'inna ilaihi raji'un,Allahbya taimaka ali ya kuma yi jagora yasa a budeshi a sa'a,Allah yayi ma jagora a dukkanin lamuranka"ummi na amsawa da amin yayin da shima yayi qasa da kansa yana cewa "ameen ameen abba na gode Allah ya qara girma" yana shirin miqewa yasa hannu cikin aljihun kuftanshi na riga ya zaro turare yan ubansu designers ya ajjiue wa abban,albarka yasa masa tare suka qarasa miqewa abban zai masa tattaki kasancewar alhj abbas mutum mai sauqin kai ba ruwansa da wai shi mai shekarune babba ne kowa nasa ne


Sai lokacin fadila ta janye idanunta daga kan aliyyu kallonsa tayi sosai don bata taba ganin sa yayi doguwar magana irin haka ba,yanayin yadda yake maganar cike da girmamawa sai ya sake burgeta ta sake lafewa jikin ummin tana saukar da ajiyar zuciya,ummin ta kalleta sanda suka gama ficewa "au sake ma wani rabewa kike ajikina ke da ake jiranki?" Dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki sai kuwa ta saki kuka,ummin ta saki baki tana kallonta "wai wannan wane irin sakarci ne ko wata matsala kike da ita?" Kai fadilan ta girgiza,ance tsakanin d'a da uwa sai Allah hakanan sai tausayin gadilan ya kama ummin don yasan duk mace kimai jin dadinki baki rasa matsala ta zamantakewar aure,a da rance take mata nasiha hadi da lallashi


Ganin hankalin ummin ya tashi sai tace cikin son kawar da hankalin ummi daga tunanin ko tana da wata matsala tunda tasan halin iyaye yanzu sai ta fita shiga damuwa"ummi bana son na barku ne har wata hudu" ta saku ajiyar zuciya tana godewa Allah "idan banda quruciya irin taki fadila ko kina nan din ma basai ki kusa wata biyu ma baki gan mu ba ummm.....kiyi addu'a kinji Allah ya kaiku lpy ya dawo da ku lafiya kawai" tace amin tana share hawayen cikin dakiya


Ta zuge zif din jakarta ta fito da kudaden nan ta dorasu cinyar ummin,ummin ta kalli kudin sannan ta dubeta "wannan fa na meye?" "Naki ne ke da abba" "ina kika samo su fadila?yaushe kwata kwat kika soma aikin? Ina fatan ba roqonsa kike ba dai ko?", ta girgiza kai "a'ah ummi shi yake bamu kullum idan zai fita" ta dauke kudin ta ajjiye a gefe tana cewa "za'a dai juya miki zan bawa abbanki ko yayanki zasu san inda zasu sa miki su" ta langabar da kai tace "don allah ummi to ko dan wani abu πŸ‘ŒπŸΌ ne ki cira aciki ke da abban ku samin albarka" ta bita da "to naji"


Idonta fal da hawaye zuciyarta a raunane ta fito ,suna tsaye jikin motar aliyun ta qaraso ta tsugunna har qasa idanunta rau rau muryarta na rawa tana yiwa abban sallama "to fadila Allah yayi muku albarka ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya,ki zauna lafiya agidanki bana son fitina kada na ji kada na gani" tuni kukan ya qwace mata "insha Allahu abba"kasa tashi tayi har sai da abban ya daga ta da kansa,aliyyun ya zuba musu ido wani abu yaji ya taba ransa shi ya bude mata motar Abban ya sata ciki da kansa,aliyun ya rufe qofar sukayi sallama da abba ya zagaya ya shiga gun zamansa ya tada motar


Shiru cikin motar sai sautin kukanta danke tashi kadan kadan hadi da sheshsheqa,burki taji yaja bayan ya gangara gefan tati ya kashe motar sannan ya dan kwantar da kujerar da yake kai din ya kwanta rigingine idanunsa alumshe yana sauraran sautin kukan,sai da suka kusan kwashe awa guda ahaka lokacin tuni har kukan nata ya tsagaita,ya miqe a kasalance ya gyara zaman kujerar baice uffan ba ya tada motar suka wuce


Cikin daren bata kwanta ba sai da ta hada duk abinda take da buqata cikin babbar trolly dinta sannan ta kwanta zuciyarta fal da saqe saqe kala kala


⚜⚜⚜⚜⚜⚜


Cike da kasala take janye da akwatin nata har ta iso bakin motar qirar sienna dake fake a harabar gidan,yadine a jikinta mai sulbi blue πŸ”· tayi rolling da red din mayafiπŸ”΄πŸ”΅,sosai rigar ta bude daga qasa takalminta red ne hill sosai πŸ‘ ,motar na bude duk suna ciki nasiru na mazaunin driver aliyu na kusa da shi sai salima dake sit din can baya bisa dukkan alamu ga fuskarta nan ta sha kuka,fuskar samira ba yabo ba fallasa tana sit din tsakiya,yayin da fadila ta zauna a sit din farko nasiru ya karbi troly din nata ya sanya a baya


Cikin hanzari nasiru ke ruqin aliyyu ya sake duba gaogonsa yace "nasiru qara sauri zamu iya missing flight" ya sake qarawa motar gudu don bin umarnin ogansa


Ba dadewa suka isa aminu kano international airport nasiru ya ajjiye motar inda aka tanada don ajiyar motoci,dukkaninsu suka fito daidai lokacin da airport din ta karade da sanarwa neman masu tashi a jirgin ethopian airline,hakan ya tabbatar ma da aliyu sun kusa makarar kam,tuni nasiru ya ciro musu jakankunansu,ya dubi samira da salima da fuska take adinke musamman salima da takejin kamar ta dora hannu aka ta zunduma ihu,"sai na dawo" yace kamar mai jira salima ta fashe da kuka ta taho a guje ta fada jikinsa,ya saki dan qaramin murmushi hadi da sa tafin hannunsa yana dan bubbuga bayanta alamar rarrashi,ya miqawa samira daya hannun alamar ta taho,dauke kai tayi tana turo baki zuciyarta babu wani takaici sosai Idan ta tuna da maqudan kudaden daya barwa kowaccensu tasan zasu sha bushasha don ma yayi misu gqrgadi da jan kunnen akan fita"sai ka dawo"tace kawai,ya dan janye salima daga jikinsa sukayi sallama da nasiru,ya wuve fadila ta rufa masa baya saluma ta bita da harara kamar ta fincikota,batasan itama fama take da fargabar bin aliyyun ba


Reception suka wuce suka qarasa departure ta farko suka shiga layin screening,aka kammala da su aka basu boarding pass suka qara gaba,immigration suka sake duba visa dinsu suka buga musu stamp suka shiga dan dakin jiran jirgi,mintina qalilan jirgi yayi ready suka bi layin shiga jirgi tana gabansa yana tsaye a bayanta


Mrs muhammad ce😘


πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

[10/16, 1:51 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?...*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


2⃣7⃣&2⃣8⃣


25 and 26 ne number din sit din nasu don haka sune maqotan junansu,aliyyu ya daga yar trolly din da aka barsu suka shigo da ita saboda kilo din ba wani mai yawa bane ya sanyata a inda mayafiyan ke ajjiye jakankunan nasu,yan kallo fadila nata kiciniyar sanya tata saboda ta dan yi mata nauyi,sai da ta soma gajiya sannan ya sa hannu ya janyeta ya fada kan kujerarta ya daga trolly din tata ya sanya mata ya koma sit dinsa ya zauna yana gyara zaman suit din jikinsa


Kowa ya zauna a mazauninsu,fadila na bakin window ta zubawa filin airport din ido tana fargabar yadda jirgin zai Lula da su sararin subhana duk da yawansu kasancewar wannan shine shigarta jirgi na farko a arayuwarta


A hankali aka zare matattakalar aka maida qofar jirgin aka rufe bayan sun gama duk wasu yan tsarabe tsarabensu suka bada sanarwar daura belt,fadila ta jawo belt din saidai bata san yadda zata sata ba,tana satar kallon aliyyu ta gefan ido yana daura tasa,ya kammala ya fito sa laptop dinsa ya dora bisa cinyarsa


A hanakali jirgin ya soma qugi hadi da shawagi a doron qasa na kimanin minti goma sha biyar sannan ya yunqura don rabuwa daa doron qasa,fadila ta runtse idonta saboda wani tsoro da ya kamata,ta qanqame belt din dake hannunta wadda ta kasa daurawa jin jirgin na niyyar dawowa qasa ya tarwatse da suπŸ˜‚πŸ˜‚😜😜 lol har naga idon masu karatu aliyyu salim mai tama da fadila zasu mutuπŸ˜‚πŸ˜‚


Ta qanqame belt din dake hannunta jin tana niyyar subucewa daga kan sit din ta,cikin zafin nama aliyyu ya kareta da hannunsa sannan ya amshe belt din ya zagayeta da hannayensa ya daura mata hadi da cewa "silly girl" ya gama ya koma kan danne dannen da yake kan laptop abinsa ba tare da ya sake dubanta ba,a dan sace ta harareshi gami da jan dan siririn tsaki ,ya juyo da sauri don tsakin kunnuwansa sukaji kamar tayin da azama ta dauke kanta ta maida window Allah ya taimaketa basu hada ido ba sai ta waske


Tafiya ce ta awa hudu ta saukesu a *ethopia* don musayar jirgi cikin babban birnin na *ethopia* wato *addis ababa*,ba kwana zasuyi ba amma saida aliyyu ya kama one room apartment cikin hotel din dake kusa da airport din,tamakar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta nemi gefan kujera qwaya daya dake cikin dakin ta zauna a takure,sallar magariba da isha'in da bata yi bane ke damunta amma duk a takure take bare tayi azamar tashi


Tana kallo ya dora jakarsaπŸ’Ό kan gado ya tube takalminsa πŸ‘ž da socks dinsa ya shige toilet,motsin ruwan da ta ji yasa ta raya alwala yakeyi


Kusan minti arba'in ya fito sanye da rigar towel mai budadden qirjiπŸ‘˜,kallo daya ta masa ta dauke kai tsigar jikinta na tashi 😣,gashine kwance luf a qirjinsa baqi sidik tamakar wanda ake sawa relaxer kamar yadda na hannayensa da qafafunsa suka kwanta saboda ruwan da suka sha,ta sake runtse ido gabanta na dan faduwaπŸ’” da alamu ma shi ko ajikinsa don goge sumar kansa yake da dan qaramin towel dake riqe a hannunsa


Ganin ya soma kunce dan zaren da ya taimaka wa rigar ta rufe jikinsa ya sata yin azamar afkawa toilet,ta dade numfashinta na kaiwa da kawowa wani abu na mata yawo a jiki sannan ta iya daura alwalar ta fito,ta cimmasa tuni ya har ya tayar da tasa ta koma gefe ta kalli inda taga ya kalla ta tayar da alama nan ne alqibla har ta kammala tata ta zauna tana lazumi lokaci lokaci tana satar kallonsa har ya sallame


Shirye yake a yanzun cikin jacket masu kalar green da black sabanin dazu da yake sanye da suit baqaqe kullum aliyyu cikin sa kaya yake sabanin wadanda ta sanshi da su,kusan ma zata ce bata taba ganinsa yayi maimaice ba,yana zaune saman qafafunsa ya kammala addu'arsa ya shafa ya miqe tayi saurin yin qasa da kanta don kada su hada ido tana yiwa Allah tasbihi saboda kyawun da taga yayi mata har ya juya ya fice


Fitarsa ba dadewa daya daga cikin ma'aikatan hotel din yayi knocking ya shigo mata da abinci fried spaghetti ce da roosted chicken sai drink da ruwan gora mai sanyi duk da cewa akwai su cikin fridge dake dakin,babu abijda ta iya ci sai lemon da ta sha


Saman kujera ta nade ta janyo wayarta ta kunnata wadda tun shigarsu jirgi ta kashe,babu service da ya hau saboda ya fita daga inda yake da amfani ,ta danna power off ta kashe don bata da wani amfani ta maida kanta ta kwantar a hannun kujerar


A hanzarce ya shigo ya dauki jakarsa πŸ’Ό ya juya yana cewa "let's go"ta miqe ita ma ta dauki tataπŸ‘œ ta bi bayansa


🎊🎊🎊🎊🎊🎊


*_CHINA (SIN)_*


*_guangzhou airport_*


Qarfe hudu ⏰ na yamma da minti ashirin a agogon qasar china qarfe sha daya da minti ashirin agogon Nigeria suka sauka a qasar,iyakar gajiya fadila ta yita,tafiya ce ba kadan ba tamkar ta yada shege zama ne na awanni kimanin goma sha biyar a jirgin wadda bata taba tafiya makamanciyar ta ba


Da qyar take daga qafarta da tayi mata taruwar jini saboda tsabar zama,suka sake bin layin screening immigration suka karbi passport suka kuma duba visa dinsu don tabbatar da cewa sun samu izinin shigowa qasar tasu,bayan sun tabbatar da ingancinta suka buga musu stamp suka wuce


Sauran kadan aliyyun ya bace mata saboda ta lura cike yake da kuzarinsa tafiyarsa yake kamar baiyi wata doguwar tafiya ba bisa dukkan alamu ya saba da irin wannan tafiyar,motar ce mai azqbar kyau da daukan hankali tayi parking gabansu mutum uku ne suka fito dukkaninsu sanye da coart baqaqe baqin space da baqin sau ciki😎,cikin girmamawa suka iso inda aliyyu yake biyu daga ciki suka miqa masa hannu sukayi musabaha,cikin harshen nasara suka fara gaisawa dayan dake gefe ya dauki akwatinansu ya sanya a bayan motar


Bayan ya ruge boot suka dunguna gun motar fadila ta bisu a baya,ita da shi na sit din tsakiya biyun kuma na sit din can bayan driver din kuma ya shiga mazauninsa ya tada motar,hira suke abinsu da aliyyu yayin da hankalin fadila ya kasu biyu,daya ta dora shi ne bisa ga aliyyu yadda yake turanci kai sai ka ranyse

[10/16, 1:52 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?..*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


2⃣9⃣&3⃣0⃣


Yayin da hankalin fadila ya rabu gida,daya ta dorashi ne kan yadda aliyyu ke turanci kai ka rantse da Allah cikakken buture ne gaba da baya,babu tuntuben harshe ko kuskure ko qanqani,daya kuma ya tafine kan kyawu tsari gami da tsaftar garin ,garine mai azabar kyau da tsari,yanayin gine ginensu sun burgeta matuqa da gaske,saidai abu na farko da ya daga mata hankali dan banzan sanyin da suka tarar ana danawa a garin🌫,taji daya daga cikin yan chinan na sanar da aliyyu yanzu ma aka shiga cikinsa wanda irin wannan sanyin a Nigeria shine wucewar jaurarmu


A hankali motar taci gaba da kutsawa cikin cikin kyakkyawan shimfidedan titin har suka shigo cikin wata kyakkyawar unguwa mai tsafta da tsari wanda tafiyar fadila tsakanin airport da inda suke yanzun ta fuskanci haka unguwanninsu suke,basu yi wani nisa a layukan da suke wucewa ba suka sa signal suka gangara wani layi,sun kusa kaiwa qarshen layin driver ya faka qofar wani dan kyakkyawan gida dake yanyame da shukoki daga gaban gidan kuma grass carfet ne to kusan ko wanne gida dake layin haka yake left to right


Driver din ne ya fito ya bude musu qofa sannan ya bude boot din ya fitar da kayansu,Aliyyu ya ciro keys daga aljihun cikin rigar suit dinsa ya miqa masa ya sa hannu ya karba ya nufi gidan ya bude,ya shigar da kayan sannan daga bisani shima ya shiga


Tun fadila na tsaye har ta gaza jure tsaiwar ta maida bayanta ta jingina jikin wata 'yar bishiya dake dashe a gun,shi kam tsaye suke qyam jikin motar shida lukas da andi suna ci gaba da hirar kasuwancinsu cikin harshen nasara,jifa jifa tana tsintar wani abu wani abun kuma ya kuce mata idan tunani ya rinjayeta,tsayuwar awa guda cif sannan ya fito ya qarasa shigar da ragowar kayan da bai dauka ba ya kaisu ciki,ya dawo cikin girmamawa ya ya miqawa aliyyu maqullan ya karba yana tambayarsa "have you finished?" Ya gyada kai gami da cewa "yes sir everything is ready"ya girgiza kai yana cewa "well done"ya juya gunsu andi da lukas ya basu hannu sukayi musabaha gami da sallama ya juya ya nufi cikin gidan su kuma suka shige motar driver ya jasu suka bar gun a kasalance ta rufa masa baya zuwa cikin gidan


Falone wanda ba za'a kirashi qato can ba hakanan ba zaka kirashi da qarami ba,saidai yadda ya tsaru dole ya qayatar da kai ta yadda zaka iya fin sha'awarsa ma fiye da wani qaton,kujeru ne set guda yan madaidaita masu azabar kyau sai labulaye na alfarma da suka kewaye falon ta yadda baka iya bambance ina qofa take center carfet center table da wasu yan qanana dake maqale tsakanin kujera da kujera tafkekiyar plasma TV da home theater dining area mai dauke da dining table mai kujeru hudu komai na falon fari ne tas sai wasu abubuwan masu sirkin baqi kadan,qofofine hudu cikim falon daya kitchen ne sai store sai public toilet sai bedroom,komai tsaf yake kuma qal qal ta tsammaci hakan dama idan tayi la'akari da dan karen son tsafta irin na aliyyu


Fadila ta zabi daya faga cikin kujerun tayi saurin zama saboda yadda take jin gajiya na nuqurqusarta har cikin qashi ji take tamkar ba zata iya daga koda yatsanta ba,tana nan takure kan kujerar tana satar kallonsa,gaba daya sanyin garin ya soma takura ta tun yanzun,ga bashin sallah dake damunta tunaninta daya ta ina zata soma iya taba ruwa da wannan azababben sanyin?


Key yasa ya bude dukkanin qofofin ya tura daya wadda a samanta aka rubuta da wani dan siririn katako mai kyau *bedroom* ya shige,ta miqe itama a gajiye ta shiga public toilet cikin sa'a ta tadda a kwai heater kunna ta tayi ruwan ya dan yi zafi sannan ta kunna famfo na zafin da na sanyin ta saisaita su yadda zai mata dadin alwala,falon ta dawo saidai bata san ina ne gabas ba don haka ta kintaci inda taji hankalinta ya fi karkata ta tada salla


Minti goma ta kammala magrib da isha'i har ma da shafa'i da wutirinta,batabar kan carfet din ba tana duqunqune cikin hijabinta wanda dama yana cikin jakar hannunta haka al'adarta yake ko ba zata sanya hijabi ba to bata rabo da shi cikin jakar ta,a hankali tana duqunqunen idanunta suka soma mata nauyi da radadin bacci tamkar an watsa mata tsakuyoyi a cikinsu gajiya da bacci suka yi mata tarom dangi suka murqusheta bata san sanda ta bingire da bacci ba agun


Cikin sabon shiri yq fito yana sanye da jibgegiyat rigar sanyi mai gashin dabba daga ciki trouser ne da long sleeve shirt duka baqaqe kansa hular sanyi ce ta gashi mai azabar kyau qafafunsa boot ne mai dan tsawo πŸ‘’ya sanyawa hannayensa safofin hannu ya saye idanunsa cikin gilashin nan nasa na ko yausheπŸ‘“ cikin hanzari ya fito da niyyar fita don sama musu abinda zasu ci idanunsa ya sauka kanta tsakiyar centre carfet din dake tsakiyar falon ta cure guri guda


Ya san sanyin garin ne ya soma addabarta shi kansa da ya saba zuwa abroad cikin irin wannan yanayin wannan karon sanyin ya dameshi balle ita da bai tsammanin ta yaba zuwa,ya dawo da baya a hankali ya isa ga makunnin na'urar dumama daki ya kunna ta ya sake juyawa ya zuge gami da rufe duk wasu qofofi windows da labulaye dake abude na gidan sannan yasa kansa ya fice hadi da sa key ya kulle gidan


A hankali ya soma bude idanunta tanajin yanayin dakin ya sauya mata,sanyin da ya takura mata dazu da zata kwanta ya ragu sosai da sosai,ta kasa tashi illa idanunta dake bude tayi zuru tana jin yadda cikinta ke qugin yunwa,idan bata manta ba rabonta da abinci tun a nijeria sai drink da take ta sha har acikin jirgi


Wanka a qa'ida take da buqatar yi da ruwa mai zafi don ta samu ragowar gajiyar ko zata sake ta amma rashin ganinsa afalo yasa take tsammatar yana bedroom din,kasa kunnenta tayi sosai bata jo motsin kowa ba don haka ta miqe akasalance,cikin sanda ta tura qofar bedroom din ,babu kowa ciki daki ne babba yalwatacce ba wani tarkace cikinsa cupboard ce sai dressing mirror hadi da dressing chair sai sofa qwaya daya madaidaicin gado ne mai rumfa wanda aka kafashi daga jikin window sai center carfet da center table daga gaban gadon kenan,komai na dakin shima farine kamar dai falon hatta da kalan furniture din zuwa ga bedsheet


Ta sako kanta ciki bayan ta tabbatar babu kowa akwatunansu na saman gadon a ajjiye nashi akwatin ne ta gani a bude kayan sun dan hargitse kadan da alama ya bude ne ya debi wasu abubuwa,gefe ta zauna ta fiddo da duka kayan nasu ta shirya su cikin cupboard,nashi ne auka cinye fiye da rabinta ta tsaya tana kallon yadfa kayan suka tsaru ita kanta sun burgeta ta karkade hannayenta ta rufe qofofin sannan ta shige toilet din bayan ta ciro kaya kala daya da zata sanya


Ta fito daure da towel wanda ya sauko mata qasan gwiwarta yayin da ta yafa qaramin saman kanta tana goge ruwan da ya dan taba mata shi da wanda ya shigar mata kunne,sam bata yi tsammanin ya shigo dakin ba shi din ma haka yana zaune ne kan bedside hannunsa riqe da lemon kwali yana dan zuqa kadan kadan ,gabanta ya fadi sosai don ta tsorata da ganin nasa,da azama ta juya don komawa toilet din garin haka towel din kata ya zame ya fadi qasa kanta zuwa kafafunta suka fito sarari,gashinta ya kwanta luf bisa dan dogon wuyanta zuwa gadon bayanta wanda ruwan da ya tabashi ya sake sashi kwanciya,da sauri ya dauke qwayar idanunsa ita kam ko ta kan towel din bata bi ba ta koma hadi da tura qofar


Ta hudar dan maqulli take leqensa tana gani ya daga lemon maimakon shan ganin dama irin na dazu dai taga ya daga kwalin bai sauke ba saida ya daddake shi tas sannan yayi cilli da kwalin yayi qas da kanshi yafi Minti guda ahaka sannan ya miqe da sauri ya five a dakin,sai da tabbatar ya fita sannan ta fito da sauri ta sawa qofar key sannan ta shirya cikin doguwar riga mai dogon hannu cotton ce sosai ta yane kanta da mayafi ta duba jakarta don dauko turarenta na shamsul imarat da blue lady


Kaf jakar ta lalube da hannunta ta nemi su sama ko qasa ta rasa,cikin shakku ta zazzage jakar gaba daya babu babu blue lady din babu shamsul imarat din sai wani da ta gani cikin kwalba cikin takaici take kallonsa tasan dai ita ta sayeshi amma ta manta a ina?,ta zumbura baki tana maida kayan da ta zazzage din cikin jakar,ta dauko shi shima zata maida saita shanshana"ba laifi shima qamshinsa"ta fadi haka tana ajjiyeshi a gefanta


Kuyi haquri da aliyyu kudai kuci gaba da bina komai daki daki yake a rayuwaπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Na godeπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»


Mrs muhammad ce πŸ‘‘


πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

[10/16, 1:53 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?...*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


3⃣1⃣&3⃣2⃣


Ta dade a tsaye tana takaicin rashin sako turaren nata da batayi ba don gaba daya tayi tsammanin ta sako su,taja tsaki yafi a qirga ita ba sanin gari tayi ba hasalima yau ta soma shigowa qasar ko da ta sani din ma ai dole sai dai ta yiwa aliyyu magana wadda ita kuma hakanne bata so,to idan kuwa haka ne bata da zabi illa saka wannan turaren tunda sam bata son zama a rayuwarta ba tare da taji jikinta na tashin qamshi ba haka take qamshi a jininta ya ke,ai shima wannan din turarene,sam fadila ta mance aikinsa tama manta a inda ta sayeshi tunda abun bai gabanta tunda ta wulla shi a jaka ta manta da babinsa


Ta kammala shafawa tana lumshe ido gami da cewa "hmmmm" saboda yadda qamshin nasa ya yi mata dadi sosai,qanshi ne mai sanyi ya karade jikinta da ma dakin gaba daya,ta maida shi cikin jakarta ta rataye jakar a abun rataye jakankuna ta jawo qofar dakin ta dawo falo,yana zaune a gaban laptop dinshi πŸ’»(agogo sarkin aiki😏)cewar fadila cikin zuciyarta,aliyyu hardworking person ne komai yasa a gabansa yakan zama serious akai har sai ya kai ga cimma burinsa,yana jin fitowar tata amma bai daga kai daga abinda yake ba bare ya dubi sashenta


Sannu a hankali qamshin ya soma karade falon ya soma kuma fisgar hankalinsa,ya rasa daga inda qamshin ke fitowa,sannu sannu kasala ta soma rufeshi idanunsa suka soma lumshewa,ya daga kansa ahankali ya dubi sashen da take waya ce a hannuntaπŸ“± tana danne dannenta saqonni take dubawa da suka shigo mata,ya maida ido runtse sosai yana qaryata kanshi game da feelings din da yake ji,ya sani tun usul haka halittarsa take yana daga cikin mabuqata,gaba daya ya mance da wannan matter din sanda zai taho aiki ne kawai a gabansa da kuma tsaftar inda zai zauna da abincin da zaici


Cikin lokaci kadan mood dinsa ya canza sosai he needs something really, idanunshi sun jima a rufe aikun da yake ya gagareshi saidai still mood din da yake ciki bai canza ba,ya sake kallonta karo na biyu bata san ma me ake ba har yanzu wayarta na hannunta tana latse latsenta,"take dis bags ki samin nawa a plate ki dauki naki


Juyowa tayi don jin muryar tamkar ba tasa ba,amma sai taga latse latse yake bisa laptop idanunsa na bisa screen din,bata ce komai ba ta ajjiye wayar a gefanta ta debi kayan ta shiga kitchen,shawarma ce da Chinese spaghetti sai roasted chicken ta saka kowanne a aplate din ta hada masa da ruwa da lemo ta jawo dan side table gabansa ta dora masa akai,zuwanta gabansa ya sake sa qamshin ya cika masa hanci,ya sake runtse idonsa hadi da qanqame hannayensa gu guda cikin wani irin lust moode,sam bata lura ba ita dai ta kammala hada masa ta dauki tata ledar ta koma mazauninta,duk yadda ya kai ga son cin abincin haka ya dinga tsakurarsa a kasalance girman kai kuma ya hanashi ya sake koda duban sashen da take


πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…


Ta sake duban agogo karo na uku kenan sha daya da rabi na dareπŸ•¦,tuni bacci ya sake cika mata idanu kamar ma batayi shi dazun ba duk da dama ba wani jimawa tayi ba ta farka,tunaninta daya ko ina makwancinta? Tasan dai ko giyar wake ta sha bata tafiya kai tsaye su hada dakin kwana da aliyyu ba bare ya yarfata


kasa daurewa baccin da take ji tayi saboda haka ta ware mayafinta ta lullube kafadarta zuwa qafafunta ta ja filin kujera qwaya daya ta tada kanta da shi tunda shi kam lura aikinsa yake tuquru hadi da amsa kiran dake ta shigo masa wanda dukka da harshen turanci yake maganar hakan ya tabbatar mata yan qasar ne masu kiran,batasan yayi hakanne bane ko zai samu feeling da yake ji ya sake shi shi uasa ya takura kansa da aiki,ba abunda yake sai faman dirkawa cikinsa coffee flask guda ta hada masa amma ya kusa tafiya abun har yaso bata tsoro


Tsaye yayi a kanta baccinta take sosai,bai taba qarewa fuskarta kallo ba irin yau,gashin gaban goshinta ya sake kwanciya kamar relaxer ta shafa masa komai nata medium mai kyau tamkar ma ba baccin take ba,a hankali abun nan da yake son ya danne ya ci gaba da taso masa,ya tabbatar idan yaci gaba da kallin nata a yanayin da yake ciki din nan zai iya aikata abinda yame ganin ita din ta masa kadan ta iya daukarshi gane yake zai iya nakastata,ya janye ida nunsa daga kan fuskarta yana maida numfashi,yasa hannunsa ya zare filon da take kai kanta ya sauka saman kujerar


Firgigit tayi ta farka don ta dan tsorata ya kalli idanunta wadanda bacci da ta soma da tsoratar da tayi yasa su sukai wani kyau ya dauke kansa gefe guda zuciyarsa na dan bugawa da sauri, ganinsa tsaye bisa kanta yasa ta dan sukuyar da kanta "idan kinga dama ki koma bedroom ki kwanta"ya fada yai gaba hannunsa dauke da cup da flask din tea


Ta dauki a qalla minti talatin a zaune tana doubting din aliyyu ne kuwa ma ya tasheta?idan shi din ne ma ya zata iya kwana daki guda da aliyyu? Aliyyun da yaqi jininta? Bai sonta bai qaunarta?,wani benefit nata kawai yake so tayi masa girki da shara ba wai ainihin ita fadilan ba,ganin babu mafita ga wani sanyi da yake sirarowa falin saboda kashe na'urar falon da yayi ya sanyata miqewa jiki a salube ta njfi bedroom din


Kamar wata munafuka ta tura ta shiga,ga mamakinta yana kwance ne aqasa saman dan qaramun carfet din nan na gaba gado mai dauke da center table ya sauke center din shi kuma ya maye gurbinsa,trouser ne kawai ajikinsa da singlet,yayi ruf da ciki,hannun hagunsa da damansa duka pillow ne ya jajjerasu ya kuma matsesu ajikinsa,faffadan bayansa mai cike da siffar qarfi ya bayyana,ta dauke kanta cikin sanda ta zagayeshi gami da hayewa kan gadon tana mamaki cikin ranta shi kam wannn baijin sanyin garin nan ne?


Ga kuma sofa a dakin doguwa amma bazai hau kai ba?bata da courage din da zata magana don haka ta maida gulmarta ciki ta tattara tafukan hannayenta tayi addu'ar bacci ta shafe ilahirin jikinta da ita ta jawk bargon ta rufa tayi matashin kai da hannunta kasancewar duka filon dake kan gadon aliyu ya kwashesu zasu taya shi kwana😜😜


Idanunta fes a kansa tana gain yadda yake ta mutsu mutsu cikin ranta take munafuncin haka yake wai baccinsa ne shi,tun tana kallonsa har bacci ya rufe idanun nata,taso tayi daddan bacci mai tsawo a a lokacin saidai saidai hakan ya gaza samuwa don ta tashi yakai sau nawa saboda rashin sabo duk kuma tashin da zata yin idanunta na kan aliyyu sau uku tana ganinsa yana canza gurin kwanciya ana hudu ne ta ruskeshi yana qiyamul laili tuni ta miqe don ita din ma lokacin tashi yin tata sallar yayi


Aliyyu na bisa darduma yaga tashinta a zatonsa fitsari zata yi sai yaga bayan ta fito ta tayar da sallah shi da zuciyarsa yaje gulmar isha'i ne bata yi ba kota tsammaci asuba ce tayi?,shi kadai ke kida da rawarsa ita kam ta kafu gaban ubangiji,har ta idar idanunsa na kan fejin qur'anin dake hannunsa yana karantawa yana shafin qarshe ne cikin suratu anbiya'i,kusan yare suka sake miqewa suka tada sallar asuba kowa yayi tasa,yana so ya samu falalar jam'i sai dai girman kansa bazai barshi yayi mata tayi ba,bata jima da soma azkar dinta ba bacci ya sureta ko gamawa bata yi ba


πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…


Sanda ta farka ta duba agogon dake ajjiye kan side drawer tayi mamakin yawan baccin da tayi,ta yunqura da niyyar tashi sai ta ganshi shima kwance kan abun sallarsa yana baccinsa cikin nutsuwa da alama shima surarsa yayi bai shirya ba kamar yadda yayi mata,ta dan zubawa kyakkyawar fuskarsa ido wanda da idonsa biyu bata isa baπŸ™Š,fuskatsa tayi mata kyau tayi wani fresh,ta dan girgiza kai ta miqe tsaye ta soma gyara gadona a nutse cikin taka tsantsan don kada ta sheshi sai da ta kammala tayi mopping ta wanke bandaki duk da baiyi komai ba ta sake kintsa falo,ta koma ta buda jakarta ta fiddo da turaren wuta ta jona abun turaren wuta mai amfani da wutar lantarki ta zuba cikin qanqanin lokaci gidan ya dumame da qamshi har ya leqa moqata ma,cikin sanda ta koma dakin gadon tayi saurin shiga wanka tun kafin aliyyu ya farka ta kasa sakewa


Shigar shadda tayi pink dinkin riga da skert ne sun mata cif sun zuna das ajikinta babu inda yayi kwarara kai ka rantse a jikinta aka dinka su,hida lip glosses sai kwalli kawai ta saka ta taje dogo kuma baqin gashinta ta kameshi da ribbon pink,ta ware dankwalinta tayi daurinta na zamani wanda ake sokeshi(ture kaga tsiya)hakan ya bawa jelar gashin nata damar zubowa ta qasan daurin,rigar sanyi ce wadda ko ciki bata rufe ba mai gashi dogon hannu ne da ita ita ta sanya light blue,ita kanta sai da ta juya ta sake kallin kanta duk da ba wani make up tayi ba amma ta zuba kyau


ta dauko turarenta ta shafe lungu da saqo na jikinta,har ga Allah tana jin dadin qamshin turaren yayi mata ta maida shi sannan ta koma kitchen din shirya break


Mrs muhammad ceπŸ‘‘


πŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻✍🏻

[10/16, 1:56 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?..*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


3⃣3⃣&3⃣4⃣


Tun acikin baccin ya soma jin qamshin na ratsa qofofin hancinsa,duk zuqar numfashi daya da zaiyi yana zuqarsa ne tare da qamshin,qamshin yayi masa,tun yana tsammanin ko amafarki ne har ya soma gasgata cewa a zahiri ne ido biyu ne,sannu a ahankali idanun suka ci gaba da buduwa ya soma zagaye dakin da idanun nasa πŸ‘€,ko ina fes sai qamshin turaren wuta ke tashi da na wannan turaren nata da har yanzu ragowar qamshin bai bar dakin ba


Komai na dakin a kintse neat " I like it" ya fada can qasa,hakan yakeso ko da wani lokaci area din da yake rayuwa ta kasance,ya dan miqa hannunsa ya jawo wayoyinsa da ya dora kan center ya duba agogo,lokaci ya gani ya ja sosai din kuwa qarfe goma sha daya agogon china qarfe shida agogon gida nijeria,ya duba call logs nan ya tadda missed call na mr lin,babban dan kasuwa ne dan qasar china saidai sananne ne a qasashen duniya hakanan yana da companies anan gida nijeria sai missed call din andi biyu sai na salima guda biyar da ya biyo baya,duka baiji ba don a silent wayar take mantawa ma yayi bai kasheta ba don baya kwana da waya a bude saida babban dalili


A hanzarce ya miqe ya watsar da fulallukan da yake kai ya nufi toilet,as usual tun a gida a nan ma haka ya tadda ruwan wanka ready cikin bathtub shigewa yayi kawai abinsa,mintina talatin ya kammala wankan a gurguje ya fito ya shirya kansa cikin baqaqen suit harda baqar safar hannu saboda sanyi sunyi matuqar haska farar fatarsa yayi kyau kamar wani bature tabbas aliyyu badai kyau ba


Da hanzarinsa ya wuce kitchen kai tsaye kamar yadda ya zame masa aladarsa shan ruwa cup guda da safe kafin yaci komai,tun daga falon qamshin girki ya marabceshi,hancinsa ya bude sosai yana sheqar qamshin son ransaπŸ‘ƒπŸ»πŸ˜‹,cikin kuzari ya qarasa kitchen din tana tsaye gabn gas tana kwashe chips don shi kadai ya rage mata dama ta kammala,bayanta yake bi da kallo tayi kyau kamar wata 'yartsana don kayan sun mata cif cif ajiki ya bi gashinta da kallo wanda ke reto a bayanta sai ya tsinci kansa cikin birgeshi da hakan yayi don shi kam ma'abocin son gashi ne tun yana qarami,ya dauke idonsa ya maida kan freezer bayan ya budeta yana jawa kansa kunne


Sam bata san da shigowarsa ba qarar rufe freezer din ita ta ankarar da ita,ta dago ta dubeshi yana shirin ficewa ya dan lumshe idanunsa sanda yake qoqarin barin kitchen din saboda feeling da yake ji sosai irin na jiya da ya hanashi sukuni da bacci mai dadi,bata ce komai ba ta biyo bayansa,har ya samu hannun kujera ya zauna numfashinsa na fita da sauri da sauri,cikin hanzari ya balle hancin gorar ruwan ya kai bakinsa ya soma daddaka


Bai ajjiye ba har sai da ya shanye tas ya wurga robar cikin dust bin dake kusa da shi yana maida numfashi bayan ya rufe idanunsa


"Your breakfast is ready"yaji muryarta kusa da shi tana fada,a hankali ya bude idonsa bai ganta ba don tuni ta wuce sai ragowar bayanta da ya gani sanda take qarasa shigewa kitchen,bai sake komai ba illa wucewa dining da yayi don gwada cin abincin


Ta zuba masa komai hatta tea ta hada masa a cup ya sanya cokali yana motsa shi,mamakin kanshi yake yana kuma tambayar kanshi *meke faruwa?* da shi,ta fito daga kitchen hannunta dauke da dan qaramin cup data hada black tea☕ta zauna cikin falon tana kurba a hankali qamshin ne yaci gana da buwayarsa ta hanyar iska dake kado mishi shi


Ya maida hankalinshi kan tea dinsa yana kurba kadan kadan,comfortably yake jin zamansa kan dining din shi daya,ya debi chips da pork ya kai bakinsa yana ci gaba da monitoring movement dinta da idanunsa,"hey" taji yace ta dago da kanta ya dan dago hannunsa ba tare da ya dubeta ba"come here"ya kirata sai taji ban barakwai,ta ajjiye cup din hannun nata a hankali ta qarasa dining din,ya sake kurbar tea din idanunsa na kan ruwan tea din da yake sha "sit" yace da ita,ta ja kujerar gami da kasa kunne tana sauraran mai zaya ce mata


Bai ce komai ba har ya kammala breakfast dinsa,qamshin da yake ji ne ke rudashi ya rasa wanne irin mayen turare take amfani da shi ya zaro tissue daga cikin tissue dice box yana dan goge hannunsa inda ya bacin "as from today kada ki sake kawomin abinci ki bar gun har sai na kammala understand?"(nikam cewa nayi hmmmmm,fadi gaskiyarka na daure.......) "mutum sai shegen mulkin tsiya ba haka nake masa ba a nijeria wani lokacin bai taba cewa don me ba sai yanzu?wato zai fara fidda sabon salo don yaga ba'a gida muke ba"cewar fadila ita da zuciyarta,a fili kuwa gyada kai tayikata na a qasa "hey" ya sake cewa ta dago ta dubesa ta sake sadda kai "open ur mouth u r not a bruise" to tace masa cikin qosawa da zaman


Har ya ja kujerarsa baya yana niyyar tashi don ya tabbata ya sake qara wasu mintina a gaba bai bar gun ba tabbas bazai iya mallakar kansa ba,abunda yake ji a cikin gangar jikinsa is very strong feeling,yana so yace ta daina amfani da perfume nata amma girman kai ya hana, yana ganin idan ya fadi mata zatayi tsammani ya damu ne da wani abu nata,he feel he can sustain whatever zaici gaba da ji,wayarsa da ta soma kadawa cikin tattausan ringing ita ta dakatar da shi daga tashin da yayi niyya


Mrs muhammad ce πŸ‘‘


πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻

[10/16, 1:57 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?..*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


3⃣5⃣&3⃣6⃣


Ya ciro wayar ya duba mai kiran ya dan saki ajiyar zuciya kadan sannan yayi pressing ok,sunan da taji ya ambata ya sata gane da wadda ya ke wayar,salima ce,hira take yi masa sosai yana dan biye mata,hirar da tasa fadila kasa jure zaman gurin ,satar kallonsa take ta qasan ido gaba daya launin idanunsa sun canza muryarsa ta sake zama so cool


Idanunsa na kan fadila lokacin da ta miqe don basu guri don zuciyarta ta samu salama daga mugun kishin dake taso mata,ya dan daki table din da hannunsa wanda yasa fadila daje shirin sauka juyowa suka hada ido da shi,fararen idanun nan nasa da sukayi returning zuwa ja ya lumshe su sannan yayi mata alama ta koma ta zauna,kamar ta zura da gudu tabar gurin haka taji saidai ba yadda ta iya ta koma din


Minti biyu tsakani yayi sallama hadi da kissing wayar sau uku,lumshe nata idanun tayi tanajin wata dalmar kishi na digar mata cikin zuciyarta,bata bari shaidan ya kitsa mata komai ba ta soma karanta *hasbunallahu wani'imal wakil*,wani gumi ta gani yana tsatstsafo masa ya maida jikinsa ya jingina sosai da makarin kujerar idanunsa a rufe wani weakness yake ji sosai cikin jikinsa


ya dauki aqalla minti goma sha biyar a haka kafin mood dinsa ya dan saisaita ya dinga sakin 'yar qaramar ajiyar zuciya a jajjere,har a lokacin fadila na satar kallonsa tana mamakin meke damunsa haka mood dinshi yayi bala'in canzawa within few minutes,ya sauke doguwar ajiyar zuciya lokacin da yake bude idanun sa,caraf ya kamata tana kallonsa sai yayi wani kicin kicin da rai yana ganin kamar tasan meke damun sa,sunkuyar da kai tayi shi kuma ya zark handkerchief ya share ragowar zufar fuskarsa


Sauka yayi a ahankali daga dining area din ya shige bedroom,tana zaune a gun ya sake fitowa wannan karon yellow and coffe din suit ne ajikinsa da alama kaya ya canza koma wanka yayi ne oho wa yasan masa😜😜😜,hannunsa riqe da brief case yana amsa wayar mr lien a hanzarce yake tafiya ya sanya hannu ya bude pocket din sa ya zaro yuan dari ya ajjiye mata(five thousand kudin naija) kana ya dago suka sake hada ido dukkaninsu sunji jiki ita ta sunkui da kai shi kuma ya fice a hanzarce,ta kalli kudin ta tabe baki "ne me zanyu da kudin qasarsu?tabdijan" ta fada a fili amma qasa qasa kamar mai gunguni


Yana fita lukas da andi na qofar gida cikin motar kamfaninsa da yake shirye shiryen budeshin *maitama group of companies* haka yake kowa yasan da su,da fitowarsa suka sara masa kamar wani soja sukayi handshake kamar yadda yake a al'adar sa don dabbaqa value ba addininsa a ko ina yake,lukas ya bude masa qofar zungureriyar motar ya shiga suka rufa masa baya


Driver din ya bawa umarnin yabi ta lujing road huangtian street zasu fara shiga yueyang hotel yana son ganin ramzan dan india ne wanda yana daya daga cikin wadanda ya bawa contract na ginin factory din nasa,factory ne babba na qashin kan aliyyu wanda ya narkar da maqudan kudade gurin samar da shi,factory ne da zai dinga manufacturing kayan babies blouses na maza da mata


Wunin ranar cikin zirga zirga mai yawa yayi ta ahiga can fita nan,hakan ya taimaka masa sosai gurin rage masa abinda yake ji cikin jikinsa,yayin da a daya bangaren fadila ta wuni kwanciya sai bayan ta idar da sallar la'asar sannan ta shiga kitchen,pepe chicken couse couse da miyar qwai sai mutuminta lemon kwakwa da ya wadatu da madara da flavour wannan shine jadawalin abincinta na dare


Nan da nan ta gama kasancewar gas din nata mai hudu ne,ta turare gidan nata da turaren wutanta bayan ta zuge duk wani glass da window dake gidan,sai gidan yayi wani dumi mai dadi daya gauraye da qamshi,cikin ruwa mai zafi sosai tayi wanka saboda sanyin dake damunta na garin,riga da wando tayi shirya kanta ciki wandon dogone har qas pencil rigar kuma da kadan ta rufe cikinta jacket ta saka mai kauri ta mata wanda ta sauko har qasan gwiwarta tana da dogon hannu sai manyan maballai guda shida masu fadi da aka jera daga gaban rigar kusan sune kadai adonta,rigace da yawanci a turai matansu ke amfani da ita musamman lokacin sanyi


Gashinta ta gyara sosai ta kamashi da band ta saya socks qafa da hannu ko zata samu sauqin sanyin,da turarenta ta shafe jikinta ko ina ciki da waje,ta maida ta tattare abinda ya dan yamutse a dakin ta gyara shi sannan ta ciro jakar laptop dinta da sam ta manta da ita ta cirota tasan saqonnin email na nan na jiranta jingim ta dauki wayarta ta dawo falo


Sai da ta zauna sannan ta duba agogo don ganin ko lakacin sallah yayi don bata tsammanin akwai masallaci anan inda suke tun da tazo bata ji kira ba da agogo kawai take amfani ko dazun ma sauran kadan sallar azahar ta qwace mata,lokaci kadan ya rage lokacin sallar ya shiga don haka sai ta jona chargy na laptop din nata sannan ta zira hijabi ta shimfida dadduma ta tada salla


Bayan ta kammala ne ta ninke hijabin hadi da daddumar ta maida daki sannan ta dawo kan computer din tata,aikam ta tarar da saqonni masu yawa anty hafiza sumayya rabi'ah na sister farida ne akan gaba harda pictures din baby humaira masu yawa har da na ya ahmad ragowar kuma duka na masoya ne na gari dake qaunarta ,na 'yan uwanta ta soma dubawa kowanne na tambayarta ne sun iso lafiya? Da makamantansu,dai sai taji kewarsu ta cikata take ta shiga maida masu amsa lallai duk wanda yabar gida gida ya barshi,sai data gama da su sannan ta soma duba na sauran jama'a wanda ke da muhimmanci ta maida masa amsa mara amfani ta goge shi


A hankali ta daga kai karo na farko ta duba agogo,tara da mintina goma sha biyar,duk da cewa unguwar da haske ta dan soma duhu alamun dare ya soma kenan wasu sun kashe qwayayensu "me ya tsaida shi tun safe har yanzu?" Fadika kewa kanta wannan tambayar da ita kanta bata san amsarta ba,fargaba ta dan soma shigarta da tsoro lokacin da idanunta ke ganin kamar ana gilmawa ta cikin balcony dinsu,ta miqe a dan tsorace ta maida hijabinta bayan ta zare computer din daga jikin socket ta maida daki ta dawo falon ta tayar da isha'i


Har ta idar babu aliyyu ba alamunsa,zama tayi kan daddumar jiki a takure,kewa ce sosai ta kamata,ita ba layin qasar cikin wayarta bare tayi kira,a gogon ta sake kalla ya nuna mata qarfe goma da minti biyu,tsoro ya sake shigarta musamman da taji unguwar ya sake yin shiru ba komai ke tashi sai haushin karnukaπŸ•da keta kai kawo


Dif wutar gidan ta dauke gaba daya,gabanta yayi wani matsanancin bugu yadda duhu ya mamaye gidan ko tafin hannunta bata iya gani,tuni jikinta ya soma rawa ta dunqule guri guda tsoro ya mamayeta haushin karnukan sai take jinsa kamar a qofar gidan


Bata san sanda ta wuntsila tayi bayan kujera ba jin haushin karen a bakin qofar falon hadi da tsaiwar mota wadda aka yiwa full light aka dallare gidan gaba daya daga baya aka kashe,ai bata san sanda ta saki kukan tsoro ba dumin hawayen kawai itama taji,cewa take shikenan na banu,kusan minti biyar sannan ta daina jin motsin karen,zama tayi dabas a qasa hadi da dafe goshinta da tafin hannunta,kuka sosai ta saka,tana bala'in tsoron kare arayuwarta,don duk gidan da zata matuqar suna da kare to komai mutuncin da kuke tafa bar zuwarmuku kenan daman yaya lafiyar kura,yana daya daga cikin abinda yasa bata saba da gidansu aliyyu ba bata zuwa kenan da can suna da karnuka har biyu kafin daga bisani uncle abba yasa aka fita da su


Sam bataji shigowa ba sai takun sawaye ta ji,a guje ta miqe tana neman mafaka a rude ,ji tayi an cafkota cikin duhun,ihu ta bude bakinta da niyyar yi ko da wanda Allah zai sa ya kawo mata dauki sai taji ansa hannu an toshe mata baki dai dai lokacin wutar ta dawo,fuskarsa cikin tata yake kallonta ya zuba mata qwayoyin idanunsa,fuskarta tuni tayi jage jage da hawaye jikinta sai bari yake don sai da wutar ta dawo ta gane ashe tuni har hular kanta ma ta cire saboda tsabar rudewaπŸ˜‚


Ita ta fara janye idanunta hadi da kawar da kanya gefe ganin shi bashi da niyyar janye nasa sexy eyes din da ya zuba mata,qoqarin zame hannunta take har a lokacin kanta na gefe tana kuka mara sauti don iya tsorata ta tsorata,jikinsa a mace yake murus ga gajiyar zirga zirga da ya wuni yana yi tuni rigarshi ma ta saman ya cireta a hannu ya shigo da ita,yaqi sakin hannun nata yayin da yake qara zuba mata wani dafin mai illa ga ruhinta har cikin qwaqwalwarta don baisan me riqe mata hannun ya jawo mata ba,ta kuma rasa me yake yi a tsayen har lokacin don qeya ta juya masa idanunta bai kansa ta kuma qi kallonsa


Gashinta yake kallo dake ta sheqi shigar ta karbeta sosai kamar yasa hannunsa ya shafa gashin saboda sha'awar da ya bashi sai kuma wata zuciyar ta gargadeshi "zaka jawowa kanka raini" a hankali qamshin turarenta ya ci gaba da sakar masa da gabobi da qyar ya Iya dauke idanunsa yana jan tsaki cikin ransa yana jin haushin kansa


Mrs muhammad ce😘


πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻

[10/16, 1:58 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?..*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*PART 2*


3⃣7⃣&3⃣8⃣


Ji tayi an janyota baya an zaunar da ita saman kujera ta dago kai suka hada ido fuskarnan tasa kamar dai koda yaushe,ta sunkui da kai hawaye naci gaba da zuba,tana jin tausayin kanta ne cikin zuciyarta soyayyar aliyu ta gama yi mata illa,yana tsayen dai yayin da ya sauke dukka qwayoyin idanun nasa a kanta yana kallonta ita kuma kukanta take haiqan mara sauti lokaci lokaci tana sa tafin hannunta tan rage ruwan hawayen ta hanyar sharesu hadi da jan majina


Kusan minti biyar sannan taga ya dora mata handkerchief saman cinyarta qamshin turarensa da yake jikin handkerchief din ya daki hancinta,briefcase dinsa ya dauka ya wuce daki,saman gadon ya fada yayi rigingine yayin da qafafunsa ke qasa hadi da cewa *"ya Allah"*


Lokaci sosai ya bata yana maida numfashi tukun kafin ya miqe ya cire kayan jikinsa ya sanya rigar wanka ya wuce bandaki,ko cikin toilet din ma haka ya dade cikin bathtub kafin ya cude jijinsa ya fito,jallabiyya ya gani saka da short nikker gefan gadon a ajjiye bai kawo komai cikin ransa ba bayan ya tsane jikinsa ya shafa lotion dinsa sannan ta taje soft sumarshi ya feshe jikinsa da designers turarukansa ya jawo kayan ya sanya


Har yanzun tana bisa kujerar saidai yanzu har jingina tayi lokaci lokaci ta na dan saki ajiyar zuciya irin na wanda ya sha kuka,kallo daya yayi mata ya dauke idanunsa ita kam dama ko sashin da yake bata kalla ba don haushinsa take ji,sai da ya fara zuwa gun makunnin t.v ya kunna ya dauki remote ya qaro volume gidan talabijin dun qasar ne ke labarai ya maida remote din ya wuce dining,da kansa wannan karon yayi serving din kanshi sannan ya soma cin abincin,yaci abincin sosai ba tare d shi kanshi ya san yaci haka ba


Tuni bacci ya dauke ya dauketa kafin ya kammala,ta takure kan kujerar kamar kwanciyar jariri cikin mamansa,ajiyar zuciya take saki kadan kadan cikin baccin,a hankali ya qaraso gabanta ya tsaya bayan ya kammala duk abunda zaiyi,ya zuba hannayensa cikin aljihun short nikker dinsa ya zuba mata ido "sleeping beauty" yaji zuciyarsa na fada,wata sha'awa matsananciya ta taso masa har wani yarrr yaje ji cikin jikinsa,ya tabbata da da salima yazo kai ko samira ce da tuni an wuce gun


Itama ita gani yake kamar bada kaine ya tunkareta tunda dukkansu sun fita shekaru,ta sake jan wata doguwar ajiyar zuciya cikin baccin nata harda juyawa,ya kalli hannunta handkerchief din da ya bata ne duqunqune tsakiyar dogayen yatsunta,karo na farko wani abu mai kama da tausayinta ya ratsa zuciyarsa,ya tuna yadda ta tsorata dazun ya tabbata rashin dawowarsa ne da baiyi da wuri ba da kuma dauke wuta da akayi wanda qarewar kudin wutar su ne daga can company din ya jawo haka,yasa hannunsa ya danyi mata baya da gashinta da keson shigar mata ido


Da sauri ya janye hannunsa kamar wanda wuta ta ja,ya daga kai ya kalli lokaci sha biyu na dare saura minti shida,yasa hannu a ahankali kamar jiya ya zare filon nata,a tsorace kuwa ta tashi don har sai da yasa hannayensa ya tareta don kada ta fado,sai bayan ta nutsune suka hada ido ya janye hannunsa tayi qasa da kanta,tana jin takunsa sanda ya shige bedroom,sai da ta tsaya ta tattare kwanukan ta mada kitchen dare ya riga yayi ga dan Karen tsoro wanda ya hanata gyare gun kamar yadda ta saba


Tamkar jiya yauma kwance yake saman center saidai yau lullube yake da wani qaton lallausan farin bargo ba irin na kan gadon ba,saidai ya debe gaba daya filallukan kamar jiyan blanket din kawai ya bar mata


Again yauma dai sallar ta tarar da shi yana yi saidai ita bayan sallar asuba bata koma bacci ba breakfast ta hada masa don taji da yana waya kamar yana cewa zai fito da wuri zasu Beijing


⚜⚜⚜⚜⚜⚜


Washegari maqociyar ta ta hannun hagu mr lin ta shigo mata 'yar asalin qasar china dince tana da yara uku,sosai fadila taji dadin kulawar da ta nuna mata sun dan jima suna taba hira har daya mqociyar tata ta shigo,sunanta nadiyya 'yar asalin alqahira ce sai fadila tafi farinciki da nadiyya fiye da mr lin saboda addini da suka hada duk da cewar itama mai kirki ce,saidai ita nadiya yaronta daya mashkur sai mai gidanta abdul-basid karatu ne ya rabosu da qasarsu,sunyi hirarsu da ita sosai cikin harshen larabci don ta nan bangaren ma ba'abar fadilan a baya ba


πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…


Rayuwa aqasar da baka da kowa ba wanda ka sani bata fiya dadi ba ba kamar idan kana qasarka ta gado ba,to hakanne ya kasance ga fadila da zarar aliyyu ya fita ta kammala aikace aikacenta sai ta koma kan waya ko computer ta duba saqonni,idan ta gaji sai ta sanya hijabinta ta dawo balcony ta zauna tana kallon masu shige da fice,duk da cewa unguwa ce da bata da yalwar jama'a amma ba'a rasa masu wucewa jefi-jefi har wasunsu kan tsaya suyi mata magana ganinta baqar fata mutanen qasar mutane ne masu so da girmama baqo hadi da mutunta shi


πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…


A irin wannan ne ranar bayan ta kammla aikinta da wuri ta hau social media dinta ta gaji ta dawo balcony kamar yadda ta saba,saidai yau da gobe sai Allah sai zaman nan din ma ya gundireta,wasu 'yammata su uku ta gani sunzo wucewa dukkaninsu akan kekuna suna tafe ajere suna hirarsu abinsu🚴,sai taji tana da sha'awar zaga koda layin sune zuwa qarshensa


Cikin zumudin tunanin da tayi ta zqro wayarta ta dan yima aliyyu text, _*please zan dan fita qarshen layi*_


Mrs muhammad ceπŸ‘‘


πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?..*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*


*PART 2*


3⃣9⃣&4⃣0⃣


Ta kalmashe wayar a hannunta bayan ta tabbatar saqon ya je,ta miqe ta saya qofar don bata damu da sai ta kulle ba ta san qasa ce mai cike da tsaro


A hankali take ratsa layukan duk da dan banzan sanyin dake bugarta amma yanayin yayi mata dadi sosai,tana tafiya tana cilla hannayenta gaba da baya fuskarta qunshe da murmushi ,unguwar ta burgeta matuqa babu yawan jama'a tunda dama can ita bata son hayaniya,sai yara jefi jefi dake wasa wasu cikin balcony dinsu wasu kuma a qogar gida duk wasannin nasu baya wuce tseran keke da buga qwallo(football)


Abinda ta lura da shi shine su kamar ma sanyin bai damesu ba ba mamki ko don qasarau ce sun saba,har ta fita daga layin da shiga second street bata sani ba,yara ta gani su hudu babbar ciki ba zata wuce shekaru tara ba ma bi mata ba zata wuce takwas ba ta ukun kuma ba ta gaza uku qaramar ce mai alamun biyu amma da yake yanayin qasarsu ya bam banta da namu buka buka da su masha Allah,ball suke bugawa suka bugo mata saidai a qafarta ta sauka basu sameta ba


Babbar cikinsun ce ta fara lura da wadda suka bugawan ta tabo mai bi matan tana mata rada akunne tana kallon fadila duk sai suka juyo suna kallonta,fadika ta sunkuya ta dauki ball din ta nufi inda suke fuskarta dauke da murmushi suma murmushin suke saboda ganin baquwa,ta ajjiye ball din agabanta tabuga ta ta tafi gabansu ai kuwa suka hau ysalle da murna suka dawo mata da ita,duk da bata jin yarensu amma ta gane dadin hakan sukeji


A nan gurin yaran ta bata lokaci sosai ba tare da ta sani ba,yaran sun sake sosai da ita nan ta hada su dukkaninsu ta shige tsakiyar su tayi musu hotuna,suka shige gidajensu suna daga mata hannu,sai alokacin ta duba gari taga ya soma duhu hankalinta a taahe ta juya ta soma laluben hanya garin haka sukayi kacibus da mutumin nata (kare)shaf ta manta kare baya son gudu don a rude take tuni ta takure ta sheqa a guje shi kuwa ganin haka ya rufa mata baya


Motar kamfanin ta ajjiye aliyun a qofar gida yayi sallama da su yana jaddadawa wanda ke gaban motar su tabbatar gobe early in d morning sun kawo engines din nan an qarasa kafasu agurarensu,ya amsa masa cikin girmamawa,suka ja moyar shi kuma ya juya ya shige gidan


Qwan lantarkin na kashe yasa hannu ya kunna haske ya gauraye falon,neat yake kamar ko yauahe cike da qamshi ya jefa rigar samansa da ya cire hade da jakarsa kan kujera shima ya zauna,a gajiye yake tubus ya soma zare takalminsa da safarsa sannan ya kalli inda ta saba ajjiye masa ruwa da lemo wandayake fara sha da zarar ya dawo,wayam babu sai abincinsa dake jere saman dining,yanmiqe ya bude freezer wanda basu kunnata sosai yanzu saboda yanayin sanyin garin ya ciro ruwan roba,ko cup bai nema ba ya balle murfin ya kafa kai sai da yasha kusan fiye da rabi sannn ya maida ya rufe


Bedroom ya nufa don yin wanka hadi da alwala cikin zuciyarsa yana mamakin rashin jin motsi ko yaya cikin gidan,mamakinsa ya dadu ganin babu ita a dakin ya bude toilet babu ruwan wankansa wanda ya riga ya saba ya tadda shi yana jiransa,tunaninsa sai ya tafi ga ko tana kitchen,ya nannade hannun rigarsa ya daura alwala idan yayi sallar daga baya yayi wankan tunda yau bai samu ruwan ba,har ya shimfida abun sallah zai tayar sai kuma ya fasa zuciyars ta kasa samun nutsuwa,sai yakejin wani irin rashin ganinta amma sai ya alaqanta hakan da sabawa da yayi da ganin nataidan ya dawo


Kitchen din ya nufa kai tsaye bata nan,wani dim yaji zuciyarsa ta harbaπŸ’“,ya riga ya sani tunda auke da ita bata taba fita koda qofar gida ne ba tate da izininsa ba,a hanzarce ya koma bedroom inda ya ajjiye wayarsa saman madubi call logs ya shiga da sauri da sauri yana dubawa dinta ko Allah zaisa yaci karo da number dinta,tsaf ya gama bincikensa bai ganta ba,ya saki ajiyar zuciya hankalimsa amatuqar tashe,sai sannan ne ma idonsa ya kai kan 'yar qaramar envelope dake maqale saman wayarsa wanda ke nuni akwai sabon saqo a wayarsa,


Har zai maida wauar aljihu sai ya fasa ya jawo saman wayar ya shiga gun sms,numbers ne guda biyu daya ba suna daya kuma ta mr jake ne,yana gama karanta tex din ya tabbatar ita ta turo masa shi baisan sanda ya juya ba ya zira silifas ya fita a sukwane ,da sauri yake daddanna numbobin jumong daya daga cikin direbobin kamfaninsa wadanda suka fi kusa da unguwar da auke ciki yave ya kawo masa mota yanzu yanzu,bai iya ysayawa jiran mitar ba ya fita da qafafunsa yana ji ajikinsa cewa hanyar dawowa ta rasa


A hanzarce yake tafiya,kasancewarsa giant ma'abicin kuzari sai gashi yayi tafiya mai dama kafin isowar jumong din


Ta waiwayo cikin gudun dai bata fasa ba taqin dake tsakaninta da karen dan kadan ne,ta saddaqar cewa ta gama yawo,tuni tayi surrender ta tsaya cak lokacin da taga ya daka tsalle tana jiran taji ya yago ta,qyam tayi jinin jikinta adaskare,rungumeta taji anyi yayin da qamshin turarensa ya mamaye mata hancinta,tsawq taji ya daka wa karen ta bude idanunta ahankali yayin da dumin jikinsa ke ratsata,sum sum taga karen ya juya cikin sassarfa ya bar gun,sai da ya bace alayin sannan ya juyo ya kalli qwayar idanunta,idanunsa fal da fushi sai huci yake,hannunta ya fincika ya bude bayan motar ya sanyata sannan shima ya shiga jumong ya tada motar


Bai ce mata uffan ba kamar yadda bai sake kallonta ba idanunsa na bisa titi har yanzu kana ganin fuskarsa kasan cikin fushi yake,kuka take kanta na qasa ita kanta ta rasa kukan kuma na mene tunda Allah ya taimaketa,sai da suka qaraso gidan sannan ta tabbatar aahe tafiya tayi mai yawa bata sani ba irin haka?


Ya bude side dinsa ya fito sannan ya bude nata ya damqo hannunta ya fito da ita,jumong nata cewa"gudnyt sir" amma baibi ta kansa ba,saman kujerar ya cillat yana huci,shi kansa bai san me yasa yake jin wani fushi ba don ta bata hakanan yake jin wani tashin hankali da bai ganta ba,cikin jikinsa yake ji kamar *ZATA IYA GUDUWA* wataran tace zata barashi,


Saman kujerar ya dora qafarsa yayin da ya sauke dayar a qasa yana tsayw gabanta,kukanta har yanzu take ci gaba da yi harda dan sautin sheshsheqa,hankalinsa gaba daya ya rabu biyu ,hukunci sosai yake son yayi mata saboda kada ta sake fita har ta bace agaba,yayin da qamshin turarenta keta rarΕ•aba masa hankali,ya kasa komai kukanta na ci gaba da shiga kunnuwansa,hannu ya dunquke ya daki kujerar da suke kai "keep quiet"ya fadu cikin tsawa,hannu tasa ta rufe bakin nata hawaye naci gaba da silalowaπŸ™Š,ya dage girarsΓ  yana fadin"kiwa mutane laifi kuma ki sasu a gaba kina masu kuka?ko don kinga bakinki yafi nawa iya kuka?"ya qarashe maganar da sigar tambaya


Ita dai babu abinda tace,kusan minti biyar shiru ya ratsa falon hawayenta naci gaba da silalowa shi kuma yan ci gaba da kallonta yana jin 2ani abu kamar ya zaqe da yawa why?,a hankali ya juya yana barin gurin hadi da cewa "silly girl"


Abincin da bai iya ciba kenan a ranar ita da kanta kuma sai taji bubu dadi,koma mene tasan batan ta ne ya bata masa rai shi kuma ya jawo mishi,da bacci ya dauketa ma kan kujera da asuba anan ta farka ta ganta bai tashe ta ba kenan


*mrs muhammad ce*πŸ‘‘


πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻


[10/16, 1:59 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?..*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*PART 2*


4⃣1⃣&4⃣2⃣


Kwana uku tsakani tana zaune ya kawo mata foamπŸ—ž,gefan ta ya ajjiye bata san na mene ba sai da ta bude sannan ta duba sosai ta gani ashe na wata instute ce, sabon corse ne kan aikin jarida zasu fara wata uku ne kacal za'a kammala,daga qarfe goma na safe zuwa daya na rana,zaka iya attending classes dinsu kokuma ka dauki lecture din online kana daga gida


Tsalle ta dinga yi cikin murna bata san aliyyu na tsaye ba qofar kitchen ashe ita ya zubama ido,a hankali suka hada ido tayi saurin komawa ta zauna kunya ta kamata shi kuma ya ya dauke kai ya shige kitchen din,a nutse ta dinga cike foam din har ta kammala da maida cikin envelop


πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…


Sosai fadila ta soma jin dadin karatunta duk da online take daukan lecture ko yaushe tana gaban computer din ta,koda ta kammala daukan lecture sai tayi zamanta tayi ta research,tun daga lokacin da abin ya faru itama bata sake gigin fita ba,iyakacinta gidan nadiyya ita din ma ba sosai don gidan mr lin ma sau daya ta taba leqa mata,sai dai su turo mata yaransu suyita taya ta hira don ma bata gane yaren nasu tafi hira da mashkur don ya iya yarensu na larabci sosai


πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…


Zaman garin yanzun bai fiya takurata ba sosai tun lokacin da ta fara daukan lecture dinta,sosai computer din ta sake zama abokiyarta shi kansa uban tafiyar ya lura da yadda gaba daya walwalarta ta koma kan laptop dinta,haka nan sai ya soma jin haushin computer din gani yake kamar ta tsare masa wani abu da ya rasa mene shi gaba daya bata da wani sukuni sai ta zauna a gabanta


Shi yasa wani lokacin da zarar yaga ta dauko da niyyar yin karatu sai ya tsiro wani aikin na babu gaira babu dalili,cikin zuciyarsa yake gulmar "reading like machine"karatu kamar ranta,(hmmm kaji fa gwano baijin warin jikinsa shi da yake wuni zirga zirga da kai kawon bude company dinsa)


πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…


Kamar kullum yauma tara daidai ta kammala dukkanin ayyukanta sabida goma zata zauna lacture,tana sanye cikin kayan sanyi na turawa ta yane kanta da dan qaramin hijabi fari tas iya kafada,shigar orange and white πŸ”Ά⚪tayi sai ta haska chocolate colour skin dinta,tana tsaye a dining area tana zuba masa farfesun kan rago cikin plate ta hada masa tea cikin cup☕ don ya dan sarara kafin ya fito


Taa cikin rufe flask dinne taji takun tahowarsa ,a dabarance ta saci kallonsa ta gefan ido cikin rashin sa'a ya kamata,da sauri ta dauke idonta ya qaraso dining din ya jawo kujera daya ya zauna hadi da dora briefcase dinsa a dayar ya ajjiye wayarsa kusa da cup din teaπŸ“±☕,itama kujerar ta ja ta zauna kamar yadda yakeso kenan idan zaici abinci(πŸ™„πŸ™„πŸ™„ hmmmm)


Ta sake satar kallonsa a karo na biyu suka sake hada ido "hold on ur sight"ya fada yana kai cup din bakinshi,sai ta danji kunya ta kamata duk da shi din ma tasan satar kallon nata yayi har suka hada idon,tsakanin jiya da shekaran jiya zuwa yau gani take mood dinshi ya canza,duk da dama bawai mai fara'a ne ba amma taga sauyi cikin walwalarsa da kuzarinsa,hakanan ayyukan da yake tahowa da su yayi ta lodawa cikin laptop dinsa ya ragu sosai


Haka nan cin abincinsa ya ragu daga kusan kaso saba'in cikin dari,cikin ranta take ganin bata da wani matsayi gurinsa bare tayi gigin binciken meke damunsa,kamar yadda ta zata kuwa tea din kawai ya shanye ya miqe yana rataye jakarsa ya kuma ajjiye mata yuan 100 kamar yadda ya saba,a hankali yake saukowa daga daga step din dining area din kamar mara laka


Tuni qamshinta yayi masa rugu rugu da gangar jiki da kuma zuciyarsa,babu abinda yake buqata a yanzun idan ba mace ba koda samira ya samu ayanzun zai iya maleji da ita,har sai da ya fice sannan ya kauda kanta daga kallonsa ta maida idonta kan table din inda ta hada kayan break,tea kawai itama ta iya hadawa ta sha ta kwashe kayan ta gyara gun takai kitchen ta wanke ta dawo kan computer dinta don yin karatun


Qarfe daya da mintina goma sha biyar ta kammala ta rufe laptop din,ta danyi miqa irin ta gajiya tana yar hamma,ta jawo wayarta ta dan duba saqonninta na watsapp na tsawon minti arba'in sannan ta sauka,sallah ta soma yi don biyu tayi sannan ta kwaba alkubus don shi ta shirya yi yau


Tana tsaka da aikin nadiya ta shigo nan ta zuba ido tana mamakin me fadilan ke hadawa haka?,dariya fadila tayi tace irin abincimmu ne


Sai qarfe uku nadiyan ta tafi fadilan ta rakota bakin qofa tana gaya mata idan ta gama zata ta turo mashkur ya karba mata taci taji,ta saye qofar falon ta koma kitchen din fara aikinta,ta kammala komai da wuri ta gyara gurin ta koma bedroom don daura alwalar sallar la'asar don har tana qoqarin subuce mata


Turus ta ja ta tsaya ta kuma saki baki,jakarsa da rigar suit dinsa na watse saman sofa shi kuma na kwance saman gado ko takalmin qafarsa bai tube ba,cikin mamaki take satar kallonsa tana mamakin yaushe ya shigo gidan don ko alamunsa bata ji ba,kuma ma mainya dawo da shi gida a wannan lokacin


Rabawa tayi ta shige toilet ta dauro alwalar ta fito ta dauki abun sallarta ta koma falo,bayan ta idar ta koma saman kujera ta zauna sai dai hankalinta ya kasu rabi na kan t.v rabi na bakin qofar bedroom din don har yanzu bata ji motsinsa ba


Hankalinta ne ya gaza kwanciya cikin sanda ta miqe ta tura qofar tana leqen saman gadon,har yanzu a kwance yake kamar yadda ta barshi,ta qarasa bude qofar gaba daya a hankali cikin sanda ta qarasa bakin gadon ta duqa ta kama qafarsa a hankali ta zame masa takalman bai motsa ba har ta gama cire masa sai tayi tsammanin bacci yake ta sabule masa socks din ta cusa cikin takalmin ta kwashe su ta maida su muhallinsu


Ta juya zata fice ta sake waiwayowa kalleshi idanunsa na lumshe kan hancinsa yayi wani ja irin na farin mutum kamar an murza gun,ta kauda kai ta fice daga dakin,duk abinda take yana kallonta idanunsa biyu,matsanancin zazzabi da yake ji da ciwon ciki mai azaba wanda ya jima rabonsa da shi shi ya hanashi koda yin motsi,yasan yadda ciwon cikinsa yake idan ya kamashi baya masa ta dadi,sai yaji dadin yadda ta sake dawowa ta dubashin ganin bai fito ba,ya tabbata kasa nutsuwa tayi da rashin ganin bai fito din ba


Sai da ta shigo daura alwalar sallar magariba sannan ta ganshi zaune kan abun sallah a side din gado duk da bata ga fuskarsa ba kansa na aduqe,ta sake wucewa tayi alwalar


Qarfe tara na dare zaman falon ya gundireta ita daya kamar mayya,sabo mugun abune zaman da sukeyi tare duk dare shi ya sanyata kewa ganin yau babu shi duk da ba wani zaman da za'a fadeshi bane kowa harkar gabansa yake duk da da zarar daya yayi wani motsi mai qarfi zaka ga hankalin dayan yayo kansa


Sai da ta hada masa coffee ta hada harda abincin cikin babban tray guda daya don har lokacin bai ko leqo koda falon ba bare yaci abincin nasa,ta dauka bayan ta gama shirin kwanciyar ta cikin night gown riga da wando ne wandon har qasa rigar iya gwiwa cotton ne very soft sai hijabi saboda sanyi


*Mrs muhammad ce*

πŸ‘‘πŸ˜˜


πŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻✍🏻


3:54 pm 5/09/2016

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*WA YASAN GOBE?..*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*


*PART 2*


4⃣3⃣&4⃣4⃣


Ta ajjiye tray din kan bed side tana tunanin ina ne makwancinta yau kuma?,saboda aliyyu na kwancene a kai crossing gadon,bata jin kuma zata iya kwanciyar qasa yadda shi yakeyi domin matsanancin sanyin garin ya girmi qashinta,ta kuma kallinsa karo na biyu yana duqun qune cikin bargo gaba dayan jikinsa kansa ne kawai a waje


Sai ta rasa ta yadda zata tada shi tafi qarfin minti goma ahaka kafin dabara ta zo mata,gyaran murya ta taqarqare ta ja har aai da maqogwaronta yayi mata zafi,a hankali ya bude idonsa ya zubesu fes kan fuskarta tsakiyar qwayar idonta,fadila ce ta soma janye nata qwayar idon tana jin wani magnet na fusgarta,tabbas ba don aliyyu mutum bane zata iya cewa wani mayen qarfene cikin idonunsa da duk sanda ta kalla yake fusgarta,cikin ranta taje mamakin yadda fareren qwayar idanun sa kar suka rine zuwa ja


Cikin jikinta ta soma jin anya lafiyar aliyyun qalau?,ta kawar da wanna tunanin tana ji a jikinta har yanzu ita aliyyu yake kallo, "na zuba maka ne abincin?" Can qasa ta jiyo shi yace " I don't need",ya maida idanunsa ya lumshe,ta kuma kallon nasa tace "but...." "leave me "ya fada can qasan maqoshinsa cikin katseta,ta ga alamun bai da lafiya ne don haka bata yi zuciya ba tace masa "please ko coffee ne kasha mana" shiru yayi kusan minti uku baice komai ba,hakanne yasa ta gane ya yarda


Ta jawo flask din ta tsiyaya masa rabin cup din sannan ta sake matsowa kadan yadda zataji dadin miqa masa "take it pleas",da qyar ya iya miqewa ya jingina da makarin gadon,ta sake miqa masa yasa hannunsa zai amsa ya hade da hannun nata,kamar bashi ya riqe mata hannu ba bai saka ba bai kuma ce komai ba


Wani shocking take ji ga kuma dumin zazzabin jikinsa da yake ratsa ta itama,sai lokacin ta sake tabbatar da ashe bai da lafiyar,a hankali ya zame mata hannun sannan ya riqe cuo din sosai ya sale maida idonsa yaumshe kamar ba zai sha ba,illar da turaren ke masa nada yawa haka yake rayawa cikin zuciyarsa,ya sashi cikin wani yanayi nason kasacewa tare da ita fiye da tsammaninsa,


Bai damu da dan banzan zafin coffee din ba ya daga kai ya kwankwade tayi saurin amshe cup din ta hada kayan ta maida kitchen ta dawo dauke da cup da gorar ruwa ta dora kan bedside,sai ta tsinci kanta cikin damuwa da cutar yasa duk da bai buda baki yace mata komai game da lalurar tasa ba tasan yana jin jiki,tuni ya kwanta a daya side na gadon ya juya wa ragowat sararin dake bayansa baya


A hankali ta haye gadin gami da debe qafafunta ta maida su saman gadon ta rungume gwiwoyinta da hannayenta tana kallon bayansa,tana iya ganin yadda numfashinsa ke sauka a hankali,jikinta ya soma saki bacci ya kamata batasan sadda ta zame ta kwanta ba


_*2:30 pm*_


Can cikin tsakiyar baccinta taji ayi mata wani irin mugun riqo,nishi take ji cikin kunnuwanta sama sama dumin numfashin na dukan wuyanta,a firgice ta farka amma ta kasa tashi sabida namijin riqon da yayi mata gaba daya ya cukuikuyeta,da qyar ta samu ta juya tana fuskantarsa,murqususu sosai yake yana hada gumi numfashinsa ke fita da sauri da sauri,tuni ta gigice ganin yadda yana yinsa ya sauya gaba daya,ta tashi ta zauna dirshan hannunsa na riqe da cikinsa idanunsa adamqe daya hannun kuma ita ya zagaye da shi,sosai ta rikice babu abinda yake fadi sai *"ya Allah"*


Kimanin minti goma ta shude a haka ta rasa ya zatayi,tunaninta suna da first aid kit a gidan?to koda ma akwai din bazai qyaleta ta tashi ta dauko ba don gaba daya a kanainaye yake ajikinta,dabara ta zo mata da sauri ta miqa hannu ta dauko robar ruwanan da cuo din da dazu ta shigo da su,ta tsiyaya ruwan sannan ta sa bakinta ta tofa masa ayatush shifa ta hada masa da _*allahumma rabbin nas,azhibul ba'asi,wash fi antash shafi,la shifa'u illa shifa'uk,shifa'an la yugadiru saqama*_


Ta dan kalli fuskarsa da tayi ja har yanzu idon ke rufe yana hada gumi "pls can you take it?" Ya dan motsa kadan tasa masa cup din abaki yasha kuwa fiye da rabi


Cikin ikon Allah da taimakon ayoyin al qur'ani sai mutsu mutsun da yake ya soma raguwa,riqon tsaurin da yayi mata ya fara sassauta,sai ajiyar zuciya da yakej saki kadan kadan,bata samu sukuni ba sai da taji numfashinsa ya soma daidaita,a hankali jikinsa yayi weak bacci sosai ya daukeshi


Ta saki ajiyar zuciya tana kallin irin yanda ya zagayeta da hannunsa,ta tabbatar da a hayyacinsa yake bazai yi hakan ba,gumin fuskarsa har yanzu da saura,tasa lallausan tafin hannunta tana share masa kadan kadan gami da bin fuskarsa da kallo ganin yadda tayi ja alamun wahala,tayi tayi ta janyeshi daga jikinta cikin dabara saidai abun ya faskara yayi mata nauyi ahaka itama baccin yayi awon gaba da ita


*THIS IS THE BEGINNING OF*............

Yau kam sun makara sosai suka makara don ko sallar daren babu wanda yayi a cikinsu sakamakon bacci da basu samu ba jiya,shi ya fara farkawa ganinta cikin jikinsa ya bashi mamaki,kamar ta san me yake faruwa ta farka itama fuskarsu cikin ta juna,kamar hadin baki da sauri kowa ya janye jikinsa suka miqe a tare,shi ya fara shigewa toilet ita kuma ta shiga na parlour

Ta rigashi idarwa tana zaune tana azkar har ya idar,tana zaune har ya kammala nasa addu'o'insa, tadan waiga kadan tana duben gefansa tace "ina kwana" kamar yadda ta saba ba tare da neman amsa ba tunda ta sani ba masawar zaiyi ba don bai taba amsawa din ba,saidai idan yaga dama ya daga mata hannu kawai,saidai yau ga tarin mamakinta karo na farko sai taji ya amsa da "lafiya",ta sake cewa "ya jiki?" Kai ya daga mata,ta tabe baki ta miqe cikin zuciyarta tana cewa"hmm an ma yi yau abun arziqi" tana kallonsa ya sake komawa gado ya duqunqune

Bai dade da kwanciya ba wayoyinsa dake gefan gadon suka hau ruri,hannu yasa ya debo su bai daga kiran ba hakanan ba tare da ya duba mai kiran ba ya kashesu duka sannan ya maida su kan side drower hadi da jan bargonsa ya sake rufa

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Tana kitchen tana hada breakfast tajiyo muryarshi cikin parlour yana amsa waya,saidai muryan tayi qasa sosai alamun bai cikin jin dadinsa don bata iya jin abinda yake cewa,cikin rarraba hankalinta da takeyi ne ta yanke hannunta da wuqarπŸ”ͺ da take rarraba kazar da take so tayi masa pepper chicken ba tare da ta sani ba,wuqar ta shigeta sosai don yankan ba qarami bane,zafin ya ratsa ta har cikin qwaqwalwarta batasan sanda ta saki razananniyar qara ba,jini ne sosai ke zuba ta runtse idonta tana jin azabar yankan

Ta bude idonta a hankali suka sauka kansa lokacin da yake shigowa kitchen din cikin sauri,hannun nata da yake digar jini yake bi da kallo,da sauri taga ya ajjiye wayar saman freezer,hannun nata dake digar jini ya riqe yana kalla,wani yarrr fadila ke ji har cikin jininta,shi din ma haka,lallausan tafin hannunta yaso haddasa masa wata sabuwar fitinar cikin jikinsa,yayi saurin sakin tafin hannun nata ya kama tsintsiyar hannun

Janta yayi zuwa gaban sink ya kunna famfo ya tara hannun sannan ya barta gaban famfon ya fice da sauri,cikin 'yan sakanni sai gashi dauke da first aid kit,abunda tayi ta tunanin ina yake jiya,spirit ya fito da shi ya janye hannunta daga famfon ya dangwala a auduga ya soma wanke mata kan yankar,zafi sosai take ji yana ci gaba da ratsata ta runtse ido 😣 tana dan yin baya da hannun,cak ya tsaya da wanke matan da yake don spirit din baya samun inda yake so,fuskarta da idanunta ke rufe ya zubama ido har wani abu yaso shagaltar da shi

Jin shiru ya daina sawa ya sanyata bude ido,idonta ya shiga cikin nasa suka hadu,wani magnet ya hadu da qamshin turarenta yaso rikita aliyyu ya manta da abinda yake,amma sai yaso nuna mazantaka ya dake har da qarfin halin kaurara muryarsa "stop it,idan baki buqata zan hada kayana,kau da kai tayi don bazata iya jurar kallon qwayar idanunsa ba,ya duqar da kai yaci gaba da wanke mata daga bisani ya rufe mata da bandage don kada datti ya dinga shiga

Yana maida kayan cikin akwati ta dan motsa labbanta tace "thanks" "for what" ya fadi ba tare da ya dago kai ba bai kuma tsaya da rufe akwatin ba,she became speechless don haka ta zabi yi masa shiru kawai,haka shima bai sake cewa komai ba har ya kammala rufe akwatin ya dauki wayarsa ya fice

Da hannu daya ta qarasa aikin don haka kafin ta kammala duk ta jagwalgwale hannun jinin da ya tsayar mata tuni wani ya soma tsatsatsafowa ta bandejin da ya sa mata,sai da ta gama serving dinsa sannan ya ankara da girkinta ashe ta ci gaba da yi,ya dago ya dubeta tana ta faman hurawa yatsan iskar bakinta,baice mata komai ba ya tashi ya sauka a dining din sai gashi dauke da first aid kit,ta zaro ido cikin tsorata😳 tana tunanin mai kuma zai mata yanzu

Sosai ya riqe hannunta gam tana qoqarin zamewa saboda azabar yadda yake daye bandage din da ya sa mata dazun zai canza mata sabo,sai da ya cire tas ya sake wanke mata ya saka mata sabo sannan ya maida kayansa ya kwashe mai jinin ya sauka da su

Ya dawo ya soma cin abincinsa yana kallonta time to time yadda take ta qwalla "ko da yaushe kina acting kamar baby" hakanan taji ya fada can qasan maqoshinsa,sai da ya kammala cin nasa taga ya ja plate ya zuba mata komai ya tura mata gabanta, "oya" yace hadi da yi mata nuni da plate din da ido fuskarsa a hade,ta dan langabar da kai gefe don bata marmarin cin komai yanzu sai ta tashi a lecture "am ok,na qoshi" kallon nan nasa ya tsareta da shi cikin tsare gida,ta fuskanci hukuntata yake sonyin da ido,tayi saurin janye idanun ta hadi da sake jan plate da cup din gabanta ta soma ci tana yamutsa fuska cikin zuciyarta tana mitar "ya wani tsare mutane sai sunci abinci sai kace wani abbana lokacin da ina gida"

"Good haka abban ke miki saboda baki jin magana kan cin abinci ko?"ya fadi yana fuska a hade yana daga girarsa,da sauri ta dago ta kalleshi batasan sanda tea din da ta kurba a bakinta ya dawo ba,batasan ya akayi yaji abinda take fada ba,anya wannan mutumin ba maye bane?, "am talking to you kin qwalalomin idanunkin nan masu girman tsiya"(lol aliyyu 😜😜😜😜😜) ya fada cikin dan daga murya,kai kawai take girgizawa don babu bakin cewa wani abu,minti biyu tsakani yace "shi yasa kullum store da freezer dinki ke acike kenan basuyin qasa ko?good.....to ni a gidana dole adinga cin abinci.....oya....bismillah ina son naga plate empty"

Daga haka ya maida kansa gun wayarsa dake ruri ya fara amsa wayar mr lien,ci take amma sam bata so,da zarar kuma ta tsaya suke hada ido dole take ci gaba da ci,sai gashi taci abinci mai yawa wanda ita kanta ta jima rabon data ci,ta ture plate din tana dan taba cikinta da taji yayi fam tana yatsina fuska yayi mata wani irin qabe qabe babu dadi, "I think u filled your stomach,let me see" ya fadi yana qarashe kashe wayar"qwalalo 😳 ido tayi tana tunanin anya kan aliyyu daya?ciwon cikinsa na jiya kodai ya taba shi?,she dont know why he behaving like dis?,cikin nata zaya ce ta ta yaye rigarta ta nuna masa?,ta dawo cikin hayyacinta lokacin da ya zare mata ido yace "aha show me" ba shiri cikin sanyin jiki ta dage rigar sanyin hadi da shirt din dake ciki,cikinta ya bayyana, ashafe yake tamkar zai hade da bayanta,ya zuba mishi ido,soft skin tata ta bayyana kanta ko ba'a fada maka,wani irin magnet ke fusgarsa,ya dubeta ta tsira mata ido duk a rude take,muryarsa can qasan maqoshinta yace "up" yana ci gaba da kallon cikin,a zaton ta bai gani bane sosai ta dan sake janye masa rigar "up again" ya sake fada,sai ta tsorata don dukka cikin nata ya fito waje da zarar ta sake janye rigar qirjinta(breast) ne zai bayyana

Ganin bata sake dagewarba yasa ya dauje idanunsa daga kallon cikin ya maida qwayar idanun nasa cikin nata,ya karanci ta tsargu don haka sai ya waske ya bata rai hadi da janyo warmer yana budewa gami da cewa "no ni banga yayi full ba,don banga ya daga ba" ta marairaice tuni qwalla har ta cika mata idanu "I swear idan ka qaramin zanyi amai wlh Allah haka cikina yake" da mamaki can qasan ransa ya tsaya da abinda yake din,dama akwai mata masu irin wadannan halittar cikin?,ya riga da ya saba da matansa masu tumbi

Ya koma ya jingina da kujerar da yake kai yana cewa "ok remove dis items,but be careful with your wound,dama neman mafita taje don haka da rawar jiki ta tashi ta soma gyara gun ,cikin kitchen kitchen tafi minti biyar tana dafe da qirjinta idanunta a lumshe kafin yanayinta ya daidaita "me ya sauya shi haka" can qasar zuciyarta take tambayar kanta

*Mrs muhammad ce*

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻
[10/16, 2:00 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

4⃣7⃣&4⃣8⃣

Ta dade kafin ta baro kitchen din har yanzu yana dining area bisa kujera yana danne dannensa a waya,a falon ta tsaya ta jawl computer din ta ta tafi da gidanka(laptop) ta bude tana shirin kunnawa "hey stop" taji ya fadi cikin wata iriyar murya mai kama da ta mai jin kasala,kasaqe tayi tana jira taji mai zaice "shutdown ur system yau ba daukan lecture,kin mance wound dake fingers dinki ne?" Sai ta rasa mai zata ce tana ganin ai hannunta bazai hanata lecture ba koda guda daya zata iya yi,amma da yake mutum ce ba mai son jayayya ba don haka ta kashe din ta koma ta zauna hadi da zubawa sarautar Allah ido

Tana zaune ya shiga ciki yayi wanka ya shiryo cikin kayan sanyi,kan kujerar dining din dai ya koma ya zauna,babu dadewa kuma door bell ta kada,ya dubeta sannan yace "put your hijab" mayafine yafe a jikinta bayan kayan sanyi masu kauri da tasa,nan ma dai bata tanka komai ba ta koma daki ta dauko hijabin,ko da ta dawo su biyu ta tarar shi da doctor yungpho,ta samj kuje daya ta zauna doctor yungpo mutumin china na gaidata cikin harshen turanci

Suna gefanta doctor ya gama duk hwaje gwaje da tambayoyinsa,ya dago yana duban aliyyu "sir,sanyin garin mu na son taba ka gashi kana kwanciya a inda zai iya affecting health dinka,ya kamata ka kula saboda kada yayi maka yawa ya zamarmaka illa" "ok" aliyyun yace, "sannan ciwon cikinka ciwon marasa aurene me yasa ya taso maka a yanzu bayan kana da aure?...." da sauri aliyyun ya katseshi yana satar kallonta duk da kanta baya fuskantar gun amma hankalinta na gurin haka nan kuma ta dago wani abu duk da ya katse doctor din

Magunguna doctor yungpo ya bashi yana shirin hade kayansa aliyyu yace ya bashi pain killers" ya hada masa duk cikin magungunan,fitarsa babu dadewa aliyyu yasa ta bashi ruwa yasha magungunansa,tamiqa masa ita kuma ta wuce kitchen da zummar dora abincin rana tunda taga alamun da qyar idan yau zaya fita

Sai tsintar aliyyun kawai tayi cikin kitchen din ya damqota yayo waje da ita,saman kujera ya zaunar da ita yana ware mata sexy eyes dinsa kamar wata qaramar yarinya "idan kika sake jangwale ciwonki I will wash it again budewa zanyi in sake wankewa no pity ok?" Tayi qasa da kanta tana kallon yatsan nata mai ciwon,muryarta so cool tace "lunch zan hada mana ne" "we don't need" ya fadi yana juyawa "wo hoho Aliyyu.......Aliyyu...." fadila ke fada cikin zuciyarta,ya sata hutun dole kenan?....... Babu karatu babu girki?.....fine" ta fadi tare da yin kwanciyarta saman three sitter

Wunin ranar tana zaune ita dai sai gani tayi an kada qararrawa da rana an kawo musu lunch hakanan da daddare,coffee kawai ta faki idonsa ta hada,shima tana dire masa ta bar bedroom din don kada yace zai mata fada,sai da ta kintaci kamar yayi bacci sannan ta koma,cikin sanda ta salallaba ta hau daya side din tana jan bargon zata rufa taji ance "good" ta zaro ido tana shirin sake jin mai fada,jin yayi shiru bai sake cewa komai ya sanyata jan bargo ta lulluba tana addu'o'inta cikin zuciyarta tana yiwa kanta dariya,wato ita mai wayo taqi shigowa ta gudu sai yayi barci ashe idanunsa biyu,ta saki ajiyar zuciya wadda ba don kwanciyar kai da qafa sukayi ba da zai iya jiyota

Yafi awa biyu yana yaqi da zuciyarsa,qamshin turarenta ke ban banta masa tunani,ya rasa wace iriyar masifa ce,sosai ya san yana cikin wani hali amma baisan me yasa ta sanadiyyarta yake samun kansa cikin wannan halin ba,sunsha zama haka shi da salima idan ta masa laifi don ya hukuntata,suna daukan tsawon lokaci a haka ba tare da kuma ya damu ba,saidai ita ta gaji ta hanyar gyara laifin da kuma bashi haquri,ya runtse ido,da qarfi yake son tilastawa kansa sai yayi bacci,da qyar wani wahalallen bacci mai cike da mafarkai yayi awon gaba da shi

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Kwana uku tayi babu cas babu as,duk abinda ta dauka zata yi sai yace "stop it,hatta da shara kuwa kawai akan dan yatsanta guda daya,saidai ta faki idonsa ta kimtsa inda taga bai dace ace ana barshi haka ba,da zarar kuwa yazo yaga alamun hakan zai zuba mata ido wanda ta fassara shi da *eyes punishment*,sai ta sunkui da kanta kawai ta wuce sum-sum-sum ta bar gun,kwana biyu yana gida yana jinya babu inda ya fita,sai a rana ta ukun ya koma kan ayyukansa

Sosai itama ta rungumi karatunta tana jin dadinshi matuqa ta bashi mahimmanci mai matuqar tasiri don ta sani zai sake jawo mata qwarewa da kuma daukaka ta fannin aikinta,hakanan tana sake samun goyon baya da qwarin gwiwa daga gidajen rediyoyin da take mu'amala da su,su kansu ko yaushe suna fadi mata yadda sukayi missing aikace aikacenta masu cike da inganci da juriya

πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±
_*SANADI*_
πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±

Cikin nasarori masu tarin yawa dukkan wani shirye shiryen bikin bude kamfanin suka kammala,cikin watansu na uku da sati na uku a qasar ta sin,wanda cikin lissafin da fadika keyi kwanaki goma daka iya zuwa a gaba koma sati guda wato next week zasu iya komowa gida,tun sati uku da suka gabata ta kammala naga coarse din ta kuma fita da sakamako mafi kyau duk cikin daliban

Tuni ya sayi injina masu kyau ya aiko da su gida ta container din max air wanda na wasu kamfanoni ne da yakeson budewa idan ya dawo gida a kano cikin rukunin kamfanoni dake sharada industrial area

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Tsaye take a kitchen sauri sauri take ta kammala girkinta saboda yau tayi late sosai,sanye taje cikin trouser na mata sai rigar sanyi in and top ta saqa ce irin saqar turawa,yar cikin har gwiwa take mai gajeran hannu ta saman ce iya qugu mai dogon hannu,wuyan rigar yankan *V* shape ne,ta taje baqi sidik din gashinta mai sheqi ta sake shi ya sauka gadon bayanta,kanta na saye da hular sanyi na mata mai wadda a jikinta yaje saqale da teddy's qananu,shigar dark pink tayi tayi masifar yin kyau kamar wata black American

Hankalinta sosai yayi gaba,ta bada duk wani attention nata kan girkinta don hatta dan siririn mayafinta da tadan yafa da hular kansu sun zame don haka ko shigowarsa bata ji ba,fresh milk shi din ma ya shigo dauka hade da ruwa don busy din da tayi yau ya sanya ta mance bata ajjiye masa ba yadda ta saba,wani strong abu yaja hankalinsa sosai game da ita,sai ya koma jikin freezer din ya jingina ya harde hannayensa saman qirjinsa kamar yadda ya harde qafafunsa yana bin duk wani moments nata da kallo

Sosai ta tsorata lokacin da ta juyo zata dauki ragowar markadaddun kayan miyan da ta sanya a fridge saboda ganin mutum a tsaye unexpected,tsananin tsoro ya kamata tayi baya zata qwalla qara don rudewa ma bata barta ta kalli fuskarsa ba sai kuma ta taka bawon doya ta zame tana shirin shan qasa saboda santsin tiles da doyar ga kuma ruwa

Gaba daya taji ya rungumeta tsam cikin jikinsa yayi hada bakinsa da nata don hanata yin ihun,zaro ido tayi,cikin yan sakanni ya soma kashe mata jiki saboda yadda yake sarrafa bakinsa cikin nata tamkar ya samu sweet qamshin turarenta na dada ingizashi,cikin lokaci qanqani ya soma burkice mata har ya fara bata tsoro duk da ita din ma tana cikin shauqin abinda yake matan,wannan shine karo na farko da ta soma hada jikinta da wani da namiji a rayuwarta

Caraf tayi qarfin halin riqe hannunsa jin yana qoqarin shiga wani fage,sai lokacin da ta hada hannuntabda nasan sannan ya soma dawowa saitinsa,cak ya tsaya da abinda yake yi din,cikin sauri ta 6ashi daga jikinsa tana maida botiran rigarta hadi da maida gashinta baya wanda tuni ya hautsine,kunyan da tsoro suka hanata tsaiwa ina zata boye?,bedroom nasu ne su biyu duka,kitchen gashi a ciki,gudu gudu sauri sauri ta nufi qofar ventilation da niyyar ficewa

"Hey you" taji aliyyu wanda ke jingine jikin kantar kitchen yana maida numfashi yace "cak ta tsaya ita bata qarasa ficewa ba hakanan bata juyo ba "duba girkinki it burns",sai a lokacin ta tuna doyarta data dora

*mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻
[10/16, 2:02 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺*part 2*

4⃣9⃣&5⃣0⃣

Verry slowly ta juyo kanta a qasa ta kashe gas din ta sulale ta fice ya bita da ido,sirrintacciyar ajiyar zuciya ya saki jikinsa a mace ya juya ya dauki abinda ya kawoshi

Tamkar sirikinta haka ya koma mata gaba daya taqi koda kallonsa a haka ta zuba masa abinci ta miqa masa taja kujera ta zauna tana wasa da nata abincin sai jagwalgwalashi take da spoon baice da ita komai ba har kammala nasa,sai da ta miqe tana shirin hade kwanukan ta maida kitchen taji yace "baki isa ba sit and eat" ya tabo mata abinda taqi jini wato ace taci abinci,ta langabar da kai cike da fargabar ya za'a yi ta iya cin abinci yanzu?,ita hasalima tun abin nan da ya mata dazu taji cikinta ya cike amma taga ma shi ko ajikinsa tamkar bashi yayi ba,tamkar ba aliyyun nan ba kamar kullum canza shi akeyi

Da qyar tayi spoon biyar ta fara yunqurin amai "stop don't vomit,go" hakan dama takeson ji saboda haka da sauri ta kwashe kayan ta maida su,sai ta kasa zama afalon tayi komawarta daki tayi shirin kwanciyarta ta nade abinta a gado duk da a lokacin bata jin wani bacci,a hankali ta dinga tuna yanayin da suka kasance dazu da aliyun moments din yaqi bacewa daga kwanyarta,unforgettable ta fadi hakan a hankali can qasa,sai kuma wani murmushi ya subuce mata ta cusa kanta tsakiyar filo tana jin kunyar kanta da kanta,qaunar aliyun take ji na sake linkuwa cikin ranta,wannan shine karo na farko da suka taba body contact yana cikin saninsa,ta dinga tuna yanayin qamshi da laushin jikinsa,kamar yadda shi dinma yana zaune a falon ya kasa hasala komai ga ayyukansa nan a gabansa amma ya kasa koda sa password ya bude computer din bare akai ga batun yin aiki,tun barci ma fisgarta a hankali har mai nauyin ya saceta

A hankali ta soma ware idanunta saboda jinta da tayi tamkar tana rungume jikin mutum,qamshinsa ne ya bata amsar,a hankali zuciyarta ta tsananta buguπŸ’“ sosai ta gwada yunqurin miqewa saidai ina ya zagayeta ne da hannayensa,ta tsammaci bacci yake ko magagin bacci ne ya sashi yin hakan saidai sanda ta sake yunqurin zare jikinta karo na biyu sai taji shi cikin soft voice can qasan maqoshinsa yace "relax,relax,am not going to do anything with you....just am feeling like am going to froze,I need to warmth my body ar you clear?" Bata ce komai ba ta maida kanta ta kwantar idanunta kan ribbon da hular sanyinta dake watse a gefe da alama shi ya zare mata su don kanshi ya tura cikin gashin yana saukar mata da dumin numfashinsa tsakiyar kanta

Ta lumshe idanunta sanda ya sake janta jikinsa sosai ya nutsa zara zaran yatsunsa tsakiyar gashin nata yana sake sheqar daddadan qamshin turaren gashi data ke fesawa kanta wanda ya cakude da na jikinta yana rarraba masa hankali,turarenda bai taba jinsa kan matansa ba,hucin numfashinsa da ta ji ya dawo sauka bisa dokin wuyanta shi ya sake rikita ta,cikin rawar murya tace "a....a....am" tsayawa yayi cak "is there any trouble?" "N....noo" bata san sanda bakinta ya fadi hakan ba,sake matseta yayi cikin faffadan qirjinsa a hankali dumin jikkunansu ya soma ratsasu,sanyin nan mai ratsa qashi ya ragu matuqa,a hankali takejin wani calmness da bata jin irinsa ba na shigarta,hakanan 2ani daddadan barci mai cike da nutsuwa ya saceta

Ya saki ajiyar xuciya jin saukar numafshinta alamun bacci ya dauketa,ya ciro daya hannunsa yana sake shafa gashin,sam ya kasa daurewa gashinta na burgeshi matuqa kasancewarsa mai son gashi,yaci gaba da shafa shi yana jin dadin santsinsa cikin tafin hannunsa har shima nasa daddadan baccin yayi gaba da shi cike da mafarkai kala kala

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

A hankali ta bude idanunta tadan juya bayanta ba kowa sai qarar saukar ruwa da taji cikin toilet,qarfe biyar na asuba,ta zubawa qofar toilet din ido lokacin da taji an bude ta,aliyyu ne ya fito sanye da rigar towel nan tasa mai budadden qirji,gashin qirjin san nan ya kwanta luf baqi sidik da shi,suka hada ido da shi kansa akwai moisture da alamu wanka yayi na ibada,ta lumshe ido hadi da cusa kanta cikin filo ganin yadda ya kamata dumu dumu tana qare masa kallo,shi kam kau da kansa yayi baiso ta kamashi da yin wanka ba ya dauki jallabiyarsa cumb da perfume nashi ya fice falo,sai da taji ya fice sannan ta zuro qafafunta ta sauko ta shiga toilet din don dauro alwala ta bada nata faralin

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Kamar kowacce safiya tana kitchen tana hada masa break,tayi wankanta ta shirya kamar yadfa ta saba saidai yau ta gaji da sa kayan nasara din haka atamfa ta saka dinkin riga da skert da suka mata cif suka bi shape din jikinta,tana jin shigowarsa lokacin da take juya chips cikin frying pan,addu'a ta dinga yi Allah yasa wani abu yazo dauka yayi ya fice a kitchen din

Saidai addu'arta bata samu karbuwa ba don kai tsaye ya nufi ma'adanin plates ya dauki qwaya daya hadi da jawo plastic chair guda daya daga cikin biyun dake ajjiye a kitchen din ya dawo opposite dinta ya zauna,

Plate din hannun nasa ya hau miqa mata yana yamutsa fuska cikin shirin fita yake "pls help me kada yunwa ta yimin illa" sai yaso bata dariya yadda yake ta faman turo mata plate din idanunaa kamar zasu fada cikin frying pan din,tuni ta gama karantarsa akwai shi da ci ta amshi plate din ta cika masa shi da chips din sannna ta dora masa waina,dayar kujerar ta jawo gabansa tayi masa table da ita ta hada masa tea ta dauko masa ruwa da drink ta dora mishi gaba daya,ta gama hada tea din ta ajjiye masa ta miqe zata gudu don duk a atakure take jin ta don ta kasa hada ido da shi gaba daya ,rashin kunyarsa ma ita take gani kamar baiyi komai ba harkarsa ma yake free

"Thanks" taji ya ambata,cike da shakku da dimbin mamaki ta tsaya cak tana doubting anya su biyu ne kuwa cikin kitchen din nan,don bata gasgata cewa aliyyun ne ya fadi haka ba,don kawai ta hada masa break?,wace irin hidima ce mai tsauri wadda tafi wannan batayi masa ba bai taba yabawa ba ko a ido sai wannan?,sai ta yanke shawarar juyawa don ta tabbatar suka hada ido kuwa lokacin da yake kai chips bakinshi,sai ya tsaya ya fasa kaiwa bakin nasa tare da daga mata gira "yes thank you" da sauri ta juya zata fice don tana tsammanin aliyyu na karantar zuciyar mutum ne "come back,zaki broking rules dina,sai na gama kya fita"kanta a sunkuye ta dawo ta jingina jikin kantar kitchen din tana jira ya kammala

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Yadda wasu lamuran na aliyyi ke sauya salo ke bata mamaki idan yayi wani abun sai ta dinga tambayar kanta anya aliyyu ne?,shi kansa baisan ya canza ba ,sau tari sai ya tsinci kansa cikin sa'ido akan duk wani abu da ya shafeta duk wani movements nata,shi da kansa sai yayi wani abun sai ya koma yana tambayar kansa how comes?,sai kuma ya koma nazarin halaye da dabi'u nata shi kadai idan yana zaune perfect attitude nata,yakan daga kafada yace "perhaps she concern about me I think shine dalili na nima,true?"hakan zaita tambaya da baiwa kansa amsa

Sosai aliyyun yayi wani fresh yayi wata 'yar cika data qara masa kyau da kwarjini,ya gama zirga zirgarsa ya dawo gida ya tarar da lafiyayyen abinci da tsaftataccen muhalli kamar yadda yake so,ita din ma yanayin garin ya amsheta sosai don fatarta ta sake yin kyau da santsi ainihin chocolate clour mai kyau,

Tun daga ranar sai kwanciyarsu ta koma haka,koda tana wani aikin bata shiryawa kwanciya ba dole sai ta taho don yace mata umarnin likita ne ya dinga samun dumi sosai a jikinsa(lol aliyyu 😜😜),ita din ma bata damu sosai ba duk da yana sata a wani yanayi saboda tana samun dumi sosai wanda ke sata tayi bacci nutsatstse kuma mai tsawo ba kamar da da sanyin ke hanata wani baccin arziqi ba

_*ta faru ta qare*_*to be continued*.......

*Mrs muhammad ce*😘


[10/16, 2:00 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*PART 2*

5⃣1⃣&5⃣2⃣

Qarfe bakwai na dare ya shigo gidan bayan kammala sallar magariba da kadan tuni ta kammala komai zaune take kawai tana duba saqonninta na email,kamar kowanne lokaci da sallama ya shigo hannunsa daya riqe da rigar saman kayanshi da briefcase dinsa daya hannun nasa kuma leda ce mai dauke da tambarin wani shago da suke sayar da kayan sawa na mata,ta dago idanunta don amsa sallamar qwayar idanunsu suka hadu,ita ta fara janye idanun nata don tasan idan bata janye din ba bazai fasa kallon nata ba, "wani kallo ya koya" haka fadilan ke fada ko yaushe cikin zuciyarta duk lokacin da yayi mata hakan,har wata rana bata sani ba zancan zuciyarta ya fito fili "see you tell me what you think,me zan kalla a jikinki?" Hakan ya fada still kuma yana ci gaba da kallon nata

Cikin falon ya qaraso ya zube kayan hannayen nasa saman kujera ya zauna hadi da fadin "ya Allah" sannu da zuwa tace hadi da miqewa don zuba masa ruwan sha kamar yadda ta sabar masa,baisan yadda akayi idanunsa suka bita da kallo ba,material ne ajikinta dinkin riga da skirt,sosai dinkin ya fiddo duk wani sharp na jikinta,yau babu rigar sanyin saboda yanayin sanyin da ya fara ja baya a qasar sai kawai ta kunna na'urar dumama gida ta yafa dan qaramin dankwalin a kanta,tana tsugunne gabansa ta cika cup din da lemo ta miqa masa 🍺

Maimakon ya amshi cup din sai ya hade hannayenta duka biyun da nashi hannayen,dumin tafin hannun nasa ya ratsa har ta qwaqwalwar ta,sosai yasa taji wani na yawo cikin dukkan sassan jikinta,ta miqe da alamun tafiya zatayi ko zai sakar maya hannun maimakon haka sai taji ya finciko hannunta ta fado jikinsa gaba daya tayi dirshan kan cinyarsa,suka saki cup din duka su biyun ya tarwatse saman tiles din yayi pieces

Sosai ya matseta tsakiyar faffadan qirjinsa yana cusa hancinsa lungu da saqo na jikinta yana sheqar ni'imtaccen qamshin dake fita ta jikin nata,yamutsa ta yake son ranshi sosai qamshin ke rikita shi,ya dora hancinsa bisa wuyanta hucin numfashin sa ya daketa tsigar jikinta ta tashi,a hankali numfashin nasa ke kaiwa da komowa,tuni ya soma birkita mata lissafi itama kamar yadda shi ya dade da fita daga nasa hayyacin,qirjinta ke bugawa kamar tayi tseren gudu,tuni jikinta ya mutu murus ta kasa wani motsi

Qarar wayarsa ce ta katse masa hanzarinsa,duk da haka bai bata damar tashi ba ba tana jikinsa,yayi qoqarin daidaita nutsuwarsa sannan ya daga wayar "I will call you back" kawai yace ya katse kiran tare da jefata kujerar gefansa,yakalli fadilan da idanuwansa da suka canza launi kanta na sunjuye sai maqyarqyata take,sake matseta yayi a jikinsa yana ci gaba da cusa kansa jikinta kamar zai maidata cikin hancinsa,cikin kasalalliyar murya yace" da wanne perfume kike using?"karo na farko da tambayar ta silmiyo daga bakinsa ba tare da ya shirya ba, "am.....amw.....wan"jin gaba daya a gigice take yasa ya saketa, "shiryomin abinci zanyi wanka" a hankali ta zame daga cinyarsa cikin gudu gudu sauri sauri ta fada kitchen ya bita da kallo

Gaba daya jikinta rawa yake yana zaune shima a gun har ta soma debo kayan abincin yana lure da ita,ruwanshi yake sha yana bin ta da kallo,sai da ya kusa tashi da roba biyu,har barin miya tayi ta kuma taka ta santsin ya kusa dibarta kadan ya rage tasha qasa sai da ya dan riqeta hadi da cewa "take it easy"sai da ta gama jera abincin sannan ya miqe ya shiga wankan

Saman kujerar ta fada tana haki kamar wadda tayi tseren gudu,mirgina kanta kurum take,ta rasa wanne tunani zatayi daga cikin tuna nukan da suka cushe a qwaqwalwarta,me yake son canza aliyyun?ko kuma me ya canza shi din ma? Aliyyun da yace bai sonta?aliyyun da yace bazai taba qaunarta ba koda wani lokacine a anan gaba?me yasa yake son jikinta koda yaushe?bata da amsar kuma babu mai amsa matan

Sai da ya ritsata taci abincinta kamar yadda yake mata ko yaushe,ya jawo ledar da ya shigo da ita ya tura mata" I think jibi ne bikin bude company,ga kayan da zakiyi amfani da su nan" "thank you ta fada cikin sassanyar murya kanta a qasa don kallon da yake mata yana takurata matuqa

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Da qyar yake iya jan numfashinsa saboda azabar da yakeji yana ciki,ji yake idan bai kasance da ita ba kamar zai iya mutuwa,shi kansa yaga matuqar qoqarinsa a yadda yana yin halittarsa yake,wata hudu babu wani abu yana cikin matsananciyar sha'awa?,yana cikin matsanciyar buqata mai tarin yawa,baisan sanda ya sanya hannunsa ba ya janyota a gigice ya matseta gam wanda hakan shi yayi sanadiyyar farkawarta,tayi tsam tana jin yadda yake nishi numfashinsa na kaiwa da kawowa da sauri da sauri tamkar yana shirin kufce masa,bata kawo komai ba cikin ranta illa tunanin ko ciwon cikin sa ne ya tashi?

A gigice ya birkitota sukayi face to face,lullubeta yayi cikin ingarman qirjinsa,saqonni ya soma aika mata masu zafi da tafiyar da hankali wanda shi kansa ya manta da wasu sai a alokacin,tuni saqonninshi suka girmi hankalin fadila,ganin yana neman wuce gona da iri ta soma yunqurin qwatar kanta cikin kasala saidai sam ko motsawa ta gaza yi ya aza mata nauyinsa,loko sa saqo ya dinga bi yana lashewa hadi da rabata da duk wani abu da zai raba tsakaninsa da fatar jikinta

Tamkar a mafarki take gani,sosai taga lamarin na aliyyu da gaske yake gaba daya kamar baya duniyar ya gama fita daga ainihin aliyyun ya burkice mata baya ji hakanan baya gani,tabbas yana so ya mata abinda ta dade tana tsoro da fargabarsa,ganin dan qarfinta bazai amfana mata komai ba sai ta koma magiya da roqonsa yayi haquri,tamakar da dutse take magana ko wani kurman bebe,tuni ya gama rabata da komai na jikinta sai 'yar mitsitsiyar vest da ta rage ajikinta wanda ita kadai dama ta sanya don bata kwanciya da brassiere sai tasa vest mai dame jiki, "pleeeeaaaaseeee aliyyu zaka jimin ciwo,pleeaasee kayi haquri don Allah" hannu tasa tana rufe qirjinta saboda babu wani abu da vest din ta kare na surar qirjinta,dukiyar fulaninta ta cicciko cikin vest din sunyo

Da hannunsa daya yasa ta riqe hannayen nata biyu yasa daya hannun ya tsarge vest din gida biyu ya zareta ya wurgar,tuni dukiyar fulanin ta bayyana,wani iriyar gigicewa yayi laushi da santsin fatarta ya kusa zautar da shi,bai taba karo da qirar da ta taba tafiya da imaninsa ba irin ta fadilan tuni ya sake haukacewa kamar mayunwacin zaki,kamar akuyar da ta shiga garken tumaki,magiya da roqon taga sunqi tasiri gaba daya akan aliyyu sai ga barke da kuka,a hankali ya dinga lashe duk wani hawaye da ya biyo kuncinta bai bari ko guda ya diga a aqasa ba,sannu a hankali ya dinga kashe mata duk wata gaba ta jikinta da wani irin salon soyayya da bai taba gwadashi kan wata diya mace ba,komai nata ya saki ya zare mata duk wata ragowar qarfi da kuzari da ya rage mata

Sai da ya soma aiki tuquru sanan ta soma gane kurenta,ihun kuka ta soma saki a maimakon hawaye zallah,kuka take mai hade da ihun,hawaye da majina kuwa tuni suka hada kogo bisa fuskarta,cizo da yakushi kuwa har sai da ta gaji don kanta,tuni yayi nisa cikin duniyar da bai taba koda giftawa ta kusa da ita ba,ya shiga wata duniya mai wuyar fassarawa a gareshi,tuni sukayi hannun riga da wani abu da ake kira hankali,tun fadila na fahimtar halin da take ciki har ta soma gane komai a hankali idanunta suka rufe duhu ya mamaye mata idanu,dif komai ya dauke mata ba tare da aliyyu ya sani ba

Gefe ya koma ya yashe tare da matseta gam cikin jikinsa ji yake kamar ya tsaga qirjinsa ya maidata ciki,sosai ya rushe da wani irin kuka tamakar qaramin yaro,karo na farko sa hawaye ya zuba a idanun Aliyyu haidar ta silar fadila tun bayan da ya mallaki hankalin kansa,tuni hawaye sukayi male male bisa fuskarsa fadi yake a zuciyarsa har ma a fili "alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus saalihat (godiya ta tabbata ga ubangiji wanda da ni'imarsa ne abubuwa masu kyau suke cika)ashe har yanzu akwai mata masu kai budurcinsu gidan mazajensu?ashe zai samu wannan abun mai daraja?ashe dama babbar kyauta Allah yayi masa?ashe baiwa ce babba a cikin gidansa bai sani ba?ashe gata abbansa yayi masa?ashe soyayya abban nasa ke masa ta gaskiya?....ashe din ta aliyyu a lokacin mai dama ce,nadamarsa mai tarin yawa ce,kuka yake sosai da hawaye masu tarin yawa kwance bisa fuskarsa

Wani abu mai girma yaji yana ratsa shi game da ita wanda tunda yake bai taba jin makamancin hakan ba,ya dago da fuskarta yana kallonta,wani tausayi so da qauna girmamawa da kunyarta suka rufeshi masu tsananin tasiri,ga shatin hawaye nan bisa fuskarta da suka bushe sukayi alama,sai a lokacin yaji baijin sukar numfashinta,yatsunsa ya sanya saman hancinta yaji dif babu alamun fitar numfashi,a gigice ya zareta daga jikinsa ya wuntsulo daga kan gadon da gudu yayi parlour,freezer ya bude ya dauko ruwa,jikinsa na rawa ya balle murfin ruwan ya kwarara mata kan fuskarta,wani dogon numfashi ta ja hadi da saukar da ajiyar zuciya mai nauyin gaske,muryarta can qasa qasa yadda bi jiyota sai da ya zauna tsakiyar gadon ya dagota ya mannata da jikinsa yaji tana fadin "please kayi haquri kada ka qara" qwaqumeta yayi ya dora habarsa tsakiyar kanta "relax am not going to repeat it" jikinsa shi kansa rawa yake har yanzu,ajiyar zuciyar yake saki shima a kai a kai tamkar marayam da ya ci kuka ya qoshi,kana kallonsu a lokacin dukkansu sai sun baka tausayi dukkansu sun koma kalar tausayi

Azabar da fadilan keji ya sanyata sakin wani sabon kukan mai ban tausayi,radadi sosai take ji kamar ana yankarta a gun,sake rufe ta yayi ruf da qijinsa yana cewa cikin rawar murya da ta jiki "am sorry fadila am sorry please"

Duk da tana jin jiki kalaman sun bata mamaki,aliyyu?,aliyyu ne?"a hankali yake dauke hawayen nata da harshensa yana shanayesu gami da shafa kanta zuwa bayanta alamun lallashi yana fadin "am sorry...am sorry"abunda bakinsa kawai ke iya nanatawa kenan kamar karatun sallah,sunfi minti arba'in a haka dukkansu suna sakin ajiyar zuciya,ita bacci ya fara dauka don shi kam ko alamaunsa bai ji,a hankali ya zamar da ita ,ido ya zaro ganin yadda jini yayi face face kan farin bedsheet din,tausayinta ya sake kamashi,shi kansa yasan bai mata kadan ba,ya riga ne ya fita daga hayyacinsa,hannu yasa ya yaye shi gefe ya kwantar da ita a ahankali don kada ya tasheta yaja mata bargo ya lullubeta,yasa hannunsa ya kama mata gashinta da ya yamutse gaba daya ya daure mata shi guri guda,fuskarta da tayi fayau ta bayyana a dan hasken fitilar gefan gadon

Zaman dirshan yayi yana gadinta duk wani motsi nata na kan idonsa,ranar duk qwarewar bacci kan iya sata haka ya haqura yabar aliyyu,har asuba yana zaune dirshan idanunsa na kanta tana wani wahalallen bacci

*mrs muhammad ce*

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻
[10/16, 2:03 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*PART 2*

5⃣3⃣&5⃣4⃣

Jinta kawai ruwan zafi na ratsata,a gigice ta farka saboda azabar zafi,a rude ta qwalla wata gigitacciyar qara duk da muryarta a da she take,ta riqe hannunshi sosai tana sheshsheqar kuka "calm down please,u wil get fine,pain din da kike ji zai ragu" ya fadi cikin taushin murya da kwantar da kai,ba yadda ta iya haka ta maida jikinta tayi laqwas tana jin yadda zafin ruwan ke ratsata har gun ciwonta,a hankali ta dinga jin zafin na dan raguwa sai a lokacinne kuma ta fara lura ashe haka aliyyun ya sunkutota babu komai a jikinta,hannu tasa tana kakkare qirjinta

Shi din ma tun dazun yake qarewa halittarta kallo tana ci gaba da attract nashi ji yake kamar ya maidata ruwa amma raunin da yayi mata shi kansa ya san yayi barna,hankalinsa ya bar jikinsa ne however ma baiyi zaton zai sameta da virginity dinta ba,sai da yayi matuqar kai zuciyarsa nesa kan fadilan saboda yadda surarta ke fusgar hankalinsa,ba halitta ce da zaka iya kalla sau daya ka kau da kanka ba,wanka yayi mata ya nadota a towel kamar wata baby ya maidota daki,kunya babu kalar da fadila bata jita ba yau,shi yasa mata pant har da brassiere tana ta ture hannunsa kan ya qyaleta zata sa saidai yace "am sorry ki barni kawai,ba zaki iya komai ba" ta rasa wacce iriyar rashin kunya ce da aliyyun,doguwar riga ya zira mata harda hijabi ya shimfida mata dadduma sai da yaga ta hau sallayar sannan ya shiga nasa wankan

A kwance ya dawo ya taddata kwance saman abun sallar,komawa taga yayi ya ciro wasu capsule ya zaunar da ita ta sha sannan ya tayar da sallah,tuni bacci ya sake dibarta kafin ya idar nan kan abun sallar ko azkar din ma bata samu tayi ba,cak ya dauketa a hankali don kada ya yada ta kan gadon ya maidata ya zare mata hijabin sannan ya ja lallausan bargon ya rufeta zuwa wuyanta,zaman dirshan yayi kusa da ita yana kallonta tamkar an bashi assignment a kanta,wani abu ke ci gaba da ratsa zuciyarsa,sosai baya ga qauna yake jin qimarta da darajarta na sake linkuwa cikin zuciyarsa,tunaninsa mai zaya mata a duniya tukuici zuwa ga tarin kyautatawarsa gareta?,me zaya mata wanda zai saka mata kan wannan baiwa tata yau da ta masa kyautarta dungurun gum,kyautar da bai taba katari da makamanciyarta ba?,dame zai faranta ranta da shi a fadin duniya?,she deserve anything

Qarfe takwas na safiya a gogon garin har lokacin baccinta take gashi fitar dole ta kamashi saboda yau baqinsa zasu soma isowa,dole shi zai kama masu hotel da zasu zauna andi kuma aikin da ya basu yayi yawa bare ya hada masu da wannan,ga mukhtar (abokinsa ne na kusa)bai qaraso qasar ba bare ya hada shi da aikin,don haka fiya ta kamashi dole,idan banda wannan dalilin kam baijin akwai abinda zai fidda shi daga gidan yau,ya gama shiryawa tsaf cikin suit kamar yadda ya saba sai da ya shiga kitchen ya hada mata tea ya zuba cikin flask ya soya mata chips da qwai ya hada da cups yayi dakin don kada ta tashi babu abinda taci,ya qaraso bakin gadon bayan ya ajjiye tray din kan 'yar locker din nan ta bedside yana sake kallonta,baccin take kawai ko motsawa batayi,shi kansa yasan dole ne kam tayi bacci,ya zira hannunsa a hankali ya sake maida mata gashinta gefe,karon farko cikin nutsuwarsa ya sanya tattausan lebensa ya sumbaci goshinta sannan ya maida leben nasa saman nata leben masu taushi da siranta,ya dan jima yana sheqar hucin numfashinta dake shiga hancinsa yana masa dadi yana jin kamar tana qara masa wata ruyuwar ne ta musamman

Hot kiss ya bata wanda sai da yasa tadan motsa kadan ya miqe yana sake kallonta tare da hade tafin hannunshi da nata,baya son fitar ko kadan,ya sani tana da buqatar kulawa,sai da ya qoshi da kallon nata sannan can qasan maqoshinsa yace"i will back soon" tamkar yana magana da wadda ke idanunta biyu,ya fice a dakin yana waiwayenta hadi da ja mata qofofin gidan

Cikin ayyuka yake da mutane saidai duk wani motsi da zaiyi qwaya daya tana manne cikin zuciyarsa,kaf hankalinsa na gida gangar jikinsa ce kawai a nan,har wasu abubuwan mancewa yake maimakon ya fadi sunansu sai yace "fadilah",sai kuma yace musu "am sorry I mean kaza.....",Allah Allah yake ya kammala abinda zaiyi ya koma gida saidai yana murna ya kammala sai kuma wannan ya bullo dole haka yake sake zama yayi settling

Da kanta taji ta qoshi da baccin ta farka bakinta dauke da addu'ar tashi daga bacci *"Alhamdulillahil lazi aa faani fi jasady waradda alaiyya ruhi wa'a zina li bizikrihi"*,tayi niyyar miqewa kamar yadda ta saba saidai jin yanayin jikinta da ya canza shi ya tuno mata abinda ya faru da ita jiya tsakaninta da aliyyu

Daki daki komai ke dawo mata,tana tuno moment din tar cikin kwayarta *"wanne turare kike amfani da shi?"* tambaya daya da ya maimaita mata ita sau biyu kenan a jiya,sannu a hankali tunaninta game da turaren ya soma dawo mata *"hasbunallahu wa ni'imal wakeel"* ta fadi cikin zaro ido da matsananciyar faduwar gaba,da sauri ta diro a gadon tuni ta mance wani ciwo da take,kai tsaye gun jakarta ta nufa inda taje rataye,tasa hannu ta cirota cikin rawar jiki ta soma laluben turaren ta ciroshi hadi da zuba masa ido tamkar yau ta saba ganinsa

Da sauri ta daga jakar ta zazzage ta kafataninta,dukkayan ciki suka zubo,tarkacen magunguna da suka siya ne gun fa'iza,wannan turaren da nake shafawa shine?shine wannan turaren mahadin magungunan?" Jakar ta saki qasa hadi da komawa baya ta zauna kata ta dafe hadi da sakin wani irin kuka mai cin rai, _*"saboda sha'awa aliyyu ya tara da ita ba don so ba?turare shi ya ja hankalinsa kanta ba qauna ba?me yasa nayi gaggawar baiwa aliyyu kaina ne?me yasa na amince na yaudari kaina? Tabbas aliyyu bai sona kuma ta yarda bazai taba sonta din ba"*_,jikinta ne ya burgeshi ko me? Ta ci gaba da fada cikin zuciyarta,tuni ta gama sarewa,ta gama yankewa kanta qauna da zama tare da shi,babu irin abunda bata gwada ba amma babu nasara to sai yaushe?sai yaushe nasarar zata zo mata ne? Da gaske kenan hasashen anty hafiza na zai soki fadila wataran son da bai taba tsammani anawa wata diya mace irinshi ba,ai babu *wanda yasan gobe sai Allah* ya zama mafarki........?,tana jin wannan karon ya zama dole ta zare aliyyu daga cikin tsarin rayuwarta,ya zama dole ta rabu da shi haka nan ya zama dole ta nisanceshi,ta gama yin duk abinda ya kamata tayi.....ta gama duk abinda zata iya....ta gama bashi kuma duk wani abu da take da shi,kulawa.....tattali....tausayi da soyayya......kai harma da jikinta da zuciyarta gaba daya amma aliyyun ya gaza samuwa,to me yayi saura?,bata da wani ragowar abun bashi banda ta bar masa sararin rayuwarsa itama ko ta samu salama?

Cikin azama tamkar ba mai ciwo a jiki ba ta hada kan kudaden(yuan) da ya jima yana bata su har take ganin basu da wani amfani a gurinta,ta bude locker da ta ajjiye passport dinta ta dauka,har ta juya tana shirin fita sai ta dawo da baya a hankali,ta yagi paper cikin takaddunshi ta dauki biro ta ja dressing chair ta zauna,tafi minti biyar da dora alqalamin kan takaddar saidai hawayen da ya cika mata ido ya soma diga kan takaddar ya hanata ganin komai,ta miqa hannunta ta yago tissue ta tsane hawayen sannan ta samu damar ganin ta,cikin kasala kamar mai ciwon 'yan yatsu hannayenta suka soma rubuta abinda ke qunshe qasan zuciyarta

*amincin Allah a gareka*

*duk da na sani cewa saqona ba wani abu bane da zai dameka ba,domin kuwa ina tsammani irin saqon da ka dade kana tsammani daga gareni*

*aliyyu na soka irin son da ban taba yiwa wani halittar da namiji ba a duniya ba,na soka tun kafin na gama sanin wane ne kai,na soka son da ban yiwa kaina shi ba,na soka a fili na soka a boye*

*saidai kash! Aliyyu ka qini qin da ban taba ganin ka yuwa wata halitta shi ba,ka tsaneni tsanar da na gaza canko mai na maka da zafi haka a rayuwa?,ka qinin ne kamar yadda ka fadamin gaskiyarka tun farko kace baka sona kuma ba zaka taba sona ba hakanan kada nayi tsammanin kuma cewa wata rana ko anan gaba zaka soni*

*A lokacin na dauki zancan tamkar tatsuniya,na dauki zancen tamkar wani labari da wata rana zai iya shafewa ya gushe,ashe na tafka kuskure,nayi kuskure ba dan qarami ba,nayi abinda ni zan gushe ba zancanka ba,ashe ba zaka sonin ba har abada kamar yadda kace din,naji...na gani na kuma gamsu aliyyu...dama hausawa sunce jiki magayi,haka din ne ni ganau ce ba jiyau ba*

*a yau na rabu da kai aliyyu kamar yadda kake bege....na fita a rayuwarka kamar yadda kake muradi.....,wata qila lokacin da kake karanta wannan saqo na dade da fita daga rayuwarka,kuma na yima alqawarin fita fita ta har abada.....koda sonka zai samo sanadiyyar daina numfashina a duniya,I promise I leave yiu forever.........πŸ˜”*

*na sani ko ban roqeka ba abu ne mai sauqi in samu sakina daga gareka,to ina fata zata zamo rubuce jikin takarda don samun shaida ta kuma samu isuwa zuwa ga magabata na,na gode da jurar zama da kayi da halittar da baka so cikin inuwa guda.......na gode da da ci...sha.....suttura da ka dinga bani ba tare da zulunci ko gajiyawa ba thanks for everything,na gode na gode....πŸ™πŸ»*

*fadila Abbas bashir*

Ta ninke wasiqar cikin wani irin kuka mara sauti mai azabar cin zuciya da azabtar da rai,gefan pillow din da ta tashi ta ajjiye ta,cikin azama ta rataya jakarta ta fito hadi da jan qofar gidan,tana son koda sallama ne tayi da maqotan arziqi nadiya da mr lin amma bata son su fahimci wani abu har suyi yunqurin tsaidata,zuciyarta ta riga ta qeqashe duk radadin da ciwonta ke mata hakan bai dameta ba burinta kawai ta baf qasar,burinta ta fice a qasar ta china da take kallonta baqiqqirin

Tana bayan taxi din ta ciro katin tana dubawa ta fada masa address din inda zai kaita branch ne na kamfanin ethopian airline taje ta fara rage bucking tunda tim din fitarta a qasar bai cika ba,cikin lokaci qanqani suka qaraso tace masa ya jirata yanzu zata fito

Tana tsaye a gabansu cike da matsananciyar damuwa tana ta sharar qwalla,tsananta adsu'arta take ya Allah yasa ayau ta samu damar ficewa a qasar,burinta kawai ta nisanci aliyyun,bata son ta ganshi bare sonsa yasa ta karaya ta ci gaba da zama da shi,ma'aikacin dan qasar sin din na sake sauri gun duba mata jirgin da zai tashi yana sake bata baki cikin yaren English kasancewarsu masu girmamawa da tausayi ,cikin sa'a aka samu saidai zai sauka a ehopia kamar yadda aka saba sanann ya qarasa da su nijeria garin *kano*,sit daya ne ya rage suka gaya mata kudin da zasu cajeta suyi mata printing ticket?,cikin sauri ta gyada masa kai tun kan ya kammala printing din ta fito da kudaden ta ajjiye masa a gabansa,yana miqo mata da rawar jiki ta karba tana duba time da jirgin zai tashi awa guda ta rage mata

*mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻
[10/16, 2:04 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*PART 2*

5⃣5⃣&5⃣6⃣

Da sauri ta koma gun mai taxi ta shige gidan gidan baya tana bashi umarnin su wuce airport,koda suka je kasa zaune tayi babu abinda take banda duba agogo hadi da sharar qwalla

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Da qyar aliyyu ya samu ya yage aiki da kuma jama'ar dake dakonsa,ya bawa jumong umarnin ya maidashi gida,cikin motar ya zaro wayoyinsa ya kira lukas yace kada a nemeshi ko menene ya taso shi ko mukhtar yayi handling dinsa,ya wuce gida ne madam ba lafiya,cikin girmamawa ya amsa masa,ya cire wayar daga kunnensa ya hada da wadda ke ajjiye kan cinyarsa ya kashe su gaba daya,ya zuba su cikin 'yar jakar laptop dinsa

Jumong ya tsaida motar aliyyun ya fice,jumong din nata yi masa sallama amma hannu kawai ya iya daga masa ya shige gidan,fuskarta kawai yake da muradin kallo,ita kadai yake son gani,ta bashi wani abu mai tsada muhimmanci da daraja agun 'ya mace,ta bashi abunda ya kasa samu shekaru masu dama,abinda ya debe tsammanin ana samunsa gun matan yanzu,yana jinta sosai cikin jikinsa zuciyarsa ruhinsa...yana kuma jin wani matsayi da daraja mai girma nata cikin idanunsa

Wullar da jakar tasa yayi kai tsaye ya nufi bedroom don yafi tsammanin samunta a can,yanayin yadda dakin ya dan yamutse ya danji mamakin ganin hakan,saboda bai saba gani ba ko tsinke bai taba katarin tsinta cikin kitchen dinta ba ballantana bedroom,to amma bai kawo komai cikin ransa ba sai ya dan ganta hakan da yanayin raahin jin dadin jikinta,saboda haka ya juya ya koma ya duba kitchen,shi yana nan kamar yadda ya barshi da safen babu wani abu da ya canza,sai ya sake komawa bedroom din yana bawa ransa tana toilet to

Gefan gadon ya zauna yana zaman jiranta wanda daidai yake da a kirashi da zaman jiran gawon shanu,har sai da ya dan soma qosawa ya miqe bayansa sama gadon fuskarsa na kallon ceiling,sai yaji qayau qayau kamar ya kwanta kan wani abu,yasa hannun nasa qasan bayansa ya zaro ta yadan jujjuyata sai ya wullata daya gefan gadon,ya mirgina kansa da niyyar duban qofar toilet din sai idanunsa suka sake kaiwa kan takaddar,sai ya tsinci kansa da son budeta yaga mene a ciki don bata barin komai saman gadonsu

Yana daga kwancen ya jawota ya warwareta yakai idanunsa ciki ganinta cike taf da rubutu ya bashi mamaki,paragraph din farko kawai ya karanta sai gashi zaune dirshan tsakiyar gadon ba tare da ya san yaushe ya tashi ba,kafin aliyyu ya kammala karanta saqon tuni ya jiqe da gumi duk da ragowar sanyin dake qasar ta sin,ya kammala karanta layin qarshe na takardar gami da cukuikuyeta cikin tafin hannunsa da qarfi,rawa kawai jikinsa yake tamkar sojan da aka bugawa kugen yaqi,launin idanunsa tuni sun canza daga ainihin fararen nan qal masu haske zuwa jajaye,babu launin na alamun tashin hankali a lokacin da bai bayyana bisa fuskarsa ba,tsananin tashin hankalin da yake ji a lokacin bazai misaltu ba "why?why fadilah?me yasa kika yimin gurguwar fahimta?,me yasa kika fahimceni a abaibai?,ina zaki tafi?ina zaki tafi ki barni?,ba haka bane fadilah....ba haka bane abinda kike zato"shi kadai keta wadannan sumbatun ya dunqule hannayensa cikin junansu takardar na tsakiya

Wurgi yayi da takardar,tamkar an zungureshi ya fice daga dakin cikin matsanancin sauri,"ina zata yanzun?batasan kowa ba cikin qasar? " Tambayar daya takura yake ta faman nanatawa kansa ita bayan yasan shi kansa ba sanin amsad yayi ba,yana gab da fita a gidan wani tunani ya fado masa,cikin zadin nama ya juya ya koma ,kai tsaye inda yaga passport dinta shekaran jiya ya nufa ya hau dubawa wayam baya gurin,cikin zafin nama ya juya ya fice daga gidan,taxi ya tsayar ya shige shaf yama manta da cewar ana gayawa mai abun hawa inda za'a,gani yake ma tamkar taxi driver din yasan inda zai kaishi,saida yayi ta nanata Tambayar inda zai kaishi sannan ya tuna ya gaya masa airport zasu je

Safa da marwa take cikin departure din,hankalinta a tashe yake gani take tamkar aliyyu zai biyota ne ya hanata tafiya,wani bangare na zuciyarta ke tunatar mata babu yadda za'ayi aliyyun ya biyota,abunda kake qauna shi kake nunawa kulawa da damuwa da halin da kake ciki,koda sace ta akayi bata tsammanin aliyyun zai biyo sawunta bare tafiya tayi da qafafunta,duk da haka hankalinta bai kwanta din ba sai da suka hau layin shiga jirgi,ko anan din ma bata fasa sharar hawaye ba,sam bata damu da yadda jama'ar keta kallonta ba har wasu kan gaza shiru suce mata "sorry" kallon da suke mata bai dadata da qasa ba don ji take tamkar ansa mata wani hijabi ne cikin zuciyarta,tuni kowa ya kama sit din sa ya zauna tana sit 34 A,sanarwar daura belt ta biyo baya bayan an rufe qofar jirgin,a lokacin ta tuna tahowarsu da aliyyu qasar ranar da ta kasa daura belt dinta,kuka ne sabo ya sake qwace mata *kukan baqincikin rabuwa da shi ne ko kuma na farincikin rabuwa da shi ne?kukan shaquwa ne ko kuwa na kewa ne?* oho ita kanta bata sani ba,ita dai kawai ta tsincin kanta tana yinsa,a hankali jirgin ya soma qugi yana motsawa sannu sannu har ya ware sosai ya fara shawagi kan kwaltar dake doron qasa

Ko ta kan security dake ta tareshi da tambayoyi bai bi ba har sai fa ya dangane da inda yake son zuwan,duk ma'aikatan gun suka miqe saboda girmamawa don tuni garin na guangzhou ya soma gane wane aliyyu cikin qasar ta sin,sanarwar bikin bude katafaren kamfaninsa ya riga ya karade ko ina cikin qasar,cikin sakanni qalilan ya basu umarnin duba masa list na sunayen mutanen da suka tashi zuwa Nigeria tun daga safe zuwa yanzu,girmansa yasa suka masa haka don kuwa ba kowa ke samun haka ba sai idan jami'in tsaro ne da kyakkyawar shaidar neman wani mai laifi

Tafi yafi har suka zo list din qarashe wanda suka sanar masa jirgin yana daf da cillawa sama,daga qarshe sunan fadila Abbas Bashir ya bayyana,cikin azama ya dakatar da su yana fadin"mai wannan sunan nake nema" "ai tana cikin wadanda jirgi zai daga da su nan da yan sakonni" cikin sauri ya tashi yana fadin yana son a dakatar da tashin jirgin,cikin girmamawa yace "sorry sir bazai yiwu ba mun riga mun gama handling din komai,duk ma'aikatan mu sun san da tashin nasa,haka na qasar da zai sauka" da qarfi ya doki sama table din cikin zafi yace " I said stop the flight now!!!" Ya sake rusunar da kansa yace "sorry sir it can't,but idan kana buqatan tafiya zuwa nijerian ne sai amaka printing ticket"

Ya harde hannayensa a qirji ya lumshe ido yana maida numfashi,shi kadai yasan yadda zuciyarsa ke masa zafi da quna,shiru yayi tamkar baza ya furta komai ba "hasbunallahu wa ni'imal wakeel" yake karantawa cikin zuciyarsa,a hankali ya soma jin temper din na nasa na raguwa,still idanun nasa na alumshen yace"ok ina son jirgin da zai kuma tashi anjima" "sorry sir yau babu jirgin da zai kuma zuwa nijeria" "gobe da safe " "sai da yamma sir" "noooo!!!" Ya fadi sa qarfi hadi da bude idaunsa wadanda suka kuma zama manya ya ware su sosai kan ma'aikacin,ya sake dan rusunar da kansa gami da cewa"sir sai da yamma kayi haquri"shirun ya sake yi yana ci gaba da kallonsa,cikin ransa yake dana sanin rashin mallakar jirgi na kansa da yaqi yi a baya bayan yana da damar hakan,sai da ya gaji don kansa sanan ya sanya hannu cikin aljihunsa ya fito da kudi wanda baisan nawa bane ya ajjiye masa,ya miqa masa ticket sannan cikin sauri ya irgi kudin su ya muqawa aliyyun sauran saboda gudun kada ya karya dokar qasarsa,wani irin wawan kallo aliyyun ya watsa masa wanda ya sashi janye hannunsa shi kuma ya fice abinsa

Tafiya ce mai tsawo tamkar a zuwan ta kawosu airport din addis ababa,hamdala tayi da taji cewar nan da awanni biyu jirgi zai sake kwasarsu ya miqa su nijeria kanon dabo babu batun kwana kenan a ethopia,hakan yayi mata dadi sosai don burinta kawai shine ta bude idanunta ta ganta cikin nijeria zuwa lokacin idanunta sun sake yin luhu luhu saboda kuka wanda ta kasa tsaida shi

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Qarfe takwas na dare agogon nijeria jirginsu fadila ya landing cikin aminu kano international airport,sannu a hankali passengers suka soma saukowa,tun sanda suke kusa da sauka ta soma tunanin ina zata nufa?gata dai a nijeria?,ba zata nufi gidansu ba ko giyar wake ta sha,ta sani idan dai har taje din babu shakka babu ruwan abbanta ko umminta zasu maidata ne gidan aliyyu hankali kwance,ta tabbata ko ta bakinta ba zasu buqaci ji ba,bayan ta riga ta yiwa aliyyu da ita kanta alqawarin yanke zamansu,ta masa alqawarin yin nesa da rayuwarshi,a yanzun bata da muradi ko digo kan ci gaba da zama da shi

*"ta inda aka hau ta nan ake sauka"* haka zuciyarta ta gaya mata,take ta amince da batun zuciyar tata,ta yiwa daya daga cikin direbobin airport din magana kan inda zaya kaita,take ya amince tare da tsula mata kudi,bata damu ba ko a duska din ita ba wannan ne a gabanta ba,ba ta wannan take ba ta kanta kurum take yi

Har a lokacin hawaye bai daina bin fuskarta ba kamar yadda bata fasa gogeshi ba,har ta soma jin babu dadi saboda kukan da take,har qofar get din gidan mai taxi din ya ajjiyeta,ta fidda kudinshi ta bashi,unguwar ba kowa shiru kasancewar haka yanayinta yake koda da rana ma balle dare,ta qarasa ta qwanqwasa get din,mai gadin ya yaso yana tambayar wane? dare ya soma a lokacin don tara ma ta gota,"nice" ta amsa masa bai dai gane wace din ba har sai da ya leqo ta 'yar qaramar qofar dake maqale jikin get din,cikin rawar jiki ya soma ture wagegen get din yana fadin sannu da zuwa hajiya,ga tsammaninsa a mota take,shigewa kurum tayi ta ajjiye masa dari biyar canjin da mai mota ya bata bisa bencinsa tana cewa "rufe get dinka bada mota nazo ba"yawan kyauta da fadila ke dashi yasa yake daukin zuwanta din bata taba ahiga ta fita bata yi musu ihsani ba

Tana shiga anty hauwa na fitowa daga kitchen da yake qofar shigowa falon opposite qofar kitchen din ta ne na qasan,hannunta dauke da food flask guda biyu,baki ta saki galala bayan ta tsaya cak tana kallon fadila,har ta bude baki zata yi magana sai ta lura da yanayinta a hargitse taje ba kamar yadda ta santa ba ba lamaun nutsuwa tare da ita,mamakinta yaushe suka dawo daga china babu labari?,kan tace komai din fadilan ta share wani qwallar "subhanallahi" anty hauwa tace ta qaraso da sauri ta dire flask din saman kujera ta kama hannayen fadilan tana fadin "lafiya fadilah?"a rude,"daga ina haka?" "Daga airport nake anty" ta bata amsa murya a dashe

Bata kuma cewa komai ba don tasan ba lafiya ba ta ja hannunta suka bi ta wani dan madaidaicin corridor dake hannun hagun falon,dakunan bacci ne ciki guda uku,daya na baqi wadanda baza'a kaisu boys quarters ba daya na yaranta wanda du sun kwanta bacci kasancewar da wuri take sasu suna yi saboda makaranta,daya kuma nata ne duk da ba kwana take ciki ba sosai ko yaushe suna sama a tare da mi gidan ta saidai idan yayi tafiya ne,ta tura qofar dakin suka shiga tare,daki ne mai kyau kamar sauran dakunan bakin gado ta zaunar da fadilan hadi da cewa"kiyi wanka kiyi sallolinki,nasan cewa ba lafiya ba lo baki gayamin ba"ta miqe ta fita jim kadan ta dawo dauke da wani cooler madaidaita guda biyu na baincin daya hannun nata kuma sabuwar abaya ce ta ajjiye mata,"ga abinci kici,ga kaya ki sauya don kifi jin dadin jikinki,zani na sallami abbansu kausar right?"ta qarashe da tambayar fadilan,kai kawai ta gyada mata kamar qadangaruwa a sanyaye anty hauwan ta juya ta fice

Cikin abinda anty hauwan tace tayi abu uku ta iya wanka canza kaya sai sallah,tana zaune akan darduma tana share hawayen dai nata,ta yanke hukuncin da taga shine daidai saidai ta rasa me yasa zuciyarta ke son bijere ma umarninta?,anty hauwa ta turo qofar ta shigo ,a sanyaye fadilan ta dago kanta tana masa mata sallamar sai kuma wani dan kukan mai dan qaramin sauti ya kubce mata ta sunkui da kai,dirshan anty hauwan ta zauna gabanta ta riqo hannayenta "cool down fadila mana,ki nutsu ko gayamin me yake faruwa?,ni kuma na miki alqawari tunda kika zabeni kika kawomin matsalarki zanyi qoqarin warware miki ita"cikin sigar lallashi har anty hauwa ta ciyo kanta ta tsagaita kukan duk da hawayen dai basu bar zuba ba

Ta danja majina irin ta mai kuka tace "anty so nake na rabu da aliyyu"zaro ido antyn tayi har da sakin hannun fadilan,daga bisani ta tattro kalaman tambayarta "saboda me fadila?,me ya shiga tsakaninku haka bayan kowa na ma ali murnar morewa aure yanzu?kowa sha'awar zamanku yake?,"murmushin takaici ne ya kama fadila ta girgiza kai "anty zaman mu abun sha'awa ne ga wanda baisan halin da nake ciki ba,ni da nasan me nake ciki banga abun sha'awar ba,banga sha'awa ga tilastawa wanda bai sonka ya zauna tare da kai ba,kin taba ganin inda anty wuta da ruwa suka hadu suka cakuda suka zauna kuma suka rayu suka wanzu gu daya?,banga abin shaawa ga zamantakewar auren da babu soyayya cikinta ba sai zallar qiyayya,anty aliyyu na cutar da ni ta hanyar rashin samun soyayya da kulawarsa,hakana ina matuqar cutar da shi ta hanyar tilasta masa zama da ni baya baya so,baya sona,ina cutatsa ta hanyar sashi kallona a matsayin matarsa,bayan ya gayamin baya sona bakuma zai taba sona ba,don me zan zauna anty allah ya kamani da haqqin cutar da shi?" Ido ta kuma zarowa tace"kamar yaya fadila,kimin gwari gwari ki daina min zancen kurma da bebe"

Ta dago tsaf tana kallkn antin don mafita yanzu take nema,so take ta canza rayuwarta yanzu,so take ta bude sabon babin rayuwa ta manta komai,rayuwartatake so ta maida ta ta mafarki ta fara ta gaske,tana so ne ta manta da aliyyu ta manta ta taba sonsa,baya sonta(a zatonta) itama ya kamata ta qishi(nikam nace hmmm zaiyiwu kuwa????)hmmmmm muje dai zuwa ga *part 3*

🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*alhamdulillahi rabbil alamin,wassalatu wassalamu ala man talaqqal qur'nu mi ladun hakimul khabir*

🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*godiya ga mahaifana*
*sannan godiya ga dukka members din group dina huguma novels readers da dukkan wani masoyi na wa yasan gobe,Allahbya bar qauna ameen summa ameen*

🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*kuci gaba da bina da jin yadda wannan rikita rikita zata kasance,meye ra'ayinku game da jaruman wannan littafi?ina saurarenku ta number wayata*

*na gode*

*mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“šπŸ“šπŸ“πŸ“✍🏻✍🏻✍🏻

[10/16, 2:08 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

WA YASAN GOBE?....**WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HIGUMA*πŸ‘‰

🏼*PART 3*πŸ‘ˆπŸΌ0⃣1⃣

A hankali ta bude bakinta tace "anty *ta inda aka hau ta nan ake sauka* ,kece silar qulluwar igiyar aure na da aliyyu,ranar wanka kuma ba'a boye cibi"............A nutse cikin hikima ta soma labarta mata tun ranarhaduwarsu da aliyyu,ta fara sonshi tun kafin tasan waye ne shi,hakanan tun kafin shima ya san tana yi,ta rufe da cewa "sai ajiya na sake tabbatarwa aliyu ba sona anty yake ba bisa wani qwaqqwaran dalili nawa"(ta rufe ba tare da ta gaya mata ba),tayi shiru hawaye na diga a fuskartaShuru anty hauwa tayi don ta kasa cewa komai,ta jima cikin jimami,ta jima tana gyada kai kafin daga bisani ta saki nanauyan ajiyan zuciya "fadila sannunki da qoqari,ba shakka ke din jarumar mace ce mai son farincikin iyayenta,kin cika 'ya ta gari kuma 'yar halak,dama wannan zaman kike amma bamu taba gani ko a fuska kin nuna alamu ba?,tabbas aliyyu zaici qaniyarsa duk hukuncin da kika daukar masa ya dace da shi,wanne taimako kike da buqata a guna fadila fadeshi,kowanneiri ne zan iya miki shi,nayi da na sanin zamowa silar hada aurenku,na zamo silar xamanki cikin qunci bayan ni ima zaune cikin walwala"anty hauwan ta fadi cikin takaiciGirgiza mata kai fadilan tayi "kada ki soma dana sani anty,domin kuwa qaddarar Allah ce,ya hukunta hakan dole sai ya faru koda babu ke anty......alfarma daya nake so anty....bana son kowa ya san ina gidan nan koda kuwa 'yan gidan mu ne,bana son in sake tozali da aliyyu har sai ya ban sakina,rabuwa nake son nayi da shi saboda na barshi ya sake yayi rayuwarsa ba takura,in barshi ya rayu da masoyansa don rayuwa tare da miqiyi cikin inuwa guda ciwo ne da ita"ta fadi maganar tana jin wani daci har kan harshentaSosai anty hauwa taji wani tausayi nata har cikin ranta ta girgiza kai gami da kama kafadarta"indaiwannan alfarmar kawai kike nema fadila baki da matsala,kin samu dari bisa dari,amma in one condition.....sai kin min alqawarim cire wannan damuwar daga zuciyarki,kin bar wannan dan banzan kukan da kike,ba lokacin ki bane na kuka yanzu lokacin aliyyu ne har taya shi ya kamata ayi saboda asarar mace irinki da yake shirin yi,asarar da bazai taba maye gurbinta ba,dubi fuskarki yadda ta canza saboda tsananin kukaMurmushin yaqe tayi"insha Allahu na bar kukan anty daga yau,bazan sake zub da hawayena ba akan aliyyu,yadda bay sona ni din ma na bar sonsa kenan har abada" "good" anty hauwa tace tana dariya hadi da girgiza hannayen fadilan,sai kuma kunya ta dan kamata yadda ta taqarqare tana gaya mata bata son dan uwanta ita kuma ta kuma tana bata goyon baya ba tare da son kai ko zuciya ba ta sunkui da kai,Murmushi anty hauwan tayi "kada ki ji kunyata fadila gaskiyarki kike fadi,kowanne hukuncikuma da kikayi yayi daidai,don wallahi kinji na rantse miki mace dai dai ce zata iya irin zaman da kikayi ba"πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…Ya sallami mai taxi din da kudin da shi kansa baisanyawansu ba sannan ya shige gidan,bisa kujerar falo ya zube yana maida numfashi,wani azabar ganinta yake son yi ,a hankali ya kai idonsa inda ta saba ajjiye masa ruwa da drinks wayam gun yau ba komai,ba qamshin girkinta babu na freshner dinta,sai yaji gidan tamakar kango garin ya koma masa tamkar maqabarta,burinsa kawai gobe tayi yafice ya bar qasar,wayarsa ta soma karadi ya cirota don takaici bai san sanda ya bugata da qasa ba ta bude komai ya tarwatse a saman centerA sanyaye ya zauna gefan gadon hadi da zubawa farin bedsheet din nasu ido yadda ya baci da jini haryanzu yana bisa gadon,bai son tayar da ita ne a jiya shi yasa ya tureshi gefe ya kwantar da ita,idanunsa suka sake kaiwa kan tray na breakfast da ya hada mata tun safen kafin ya fita,yana nan yadda ya shigo da shi dai dai da cup ba'a juya shi yadda ya saka shi ba da alamun babu abinda taci kenan?Ya daga zanin gadon yana qarewa jinin jiki kallo,shi kansa bedsheet din wata qimarsa yake gani,daga qarshe ya duqunquneshi a qirjinsa da dukka hannayensa biyu idanunsa na a lumshe,wata mahaukaciyar soyayyarta ke ratsa shi,baisan lokacin da ya kwanta saman gadon ba,fuksarta ce kawai ke masa yawo cikin idanunsa,zanen fuskar yake gani sanda suka kasace a lokaci mafi tsada dadaraja a rayuwarsa,lokacin da bazaya taba barin tunaninsa saidai mutuwa ta cire masa shi,lokacin da bazai taba daina ganin darajarsa ba saidi mutuwa ta hana shi,qamshinta ya dinga ji sosai kan pillow din da ta kwata tamkar tana gurin,da sauri ya bude idonsa,vest din ta ce ta jiyan daya yaga saitin hancinsa,da sauri yasa hannunsa ya dauko ta yana sake mannata cikin hancin nasa,tamkar zai shide tamkar zai zuqo fadilan daga jikin vest dinJuyi yake sosai cikin wai irin shauqin qauna da soyayya da bai taba zaton akwai makamanciyarta ba a duniyarmu "why u leave me?why?,I cannot sustain missing you,I can't,me yasa sai da kika mun kyautar abu mai tsada da daraja baki tsaya kin karbikema abu mafi tsada da daraja aguna ba kika barni?,me yasa ba zaki tsaya na saka miki dimbin kyautatawarki gareni ba?,why baki sanar da ni sirrin zuciyarki ba sai lokacin da kika barni why?....." shi kadai qwal cikin gidan harma a dakin yake ta wadannan sumbatuSam ya kasa hassalawa kansa komai,koda suit dinsaya gaza cirewa bare akai ga yin wanka ballantana kuma batun abinci,koda yana da buqatarsa bazai iya ci din ba don harshensa bai gamsuwa da girkin kowa idan ba natan baSai yanzu ya soma tantance son da yame mata ashe yafi wanda yake ma girkin ta?,sai yanzu ya fara ankara da dalilin da yasa yake hasala da yawa idan bata gyara masa part ko bata masa girki ba fiye da yadda yake jin zafi yake hasala fiye da su samira?,sai yanzu ya gane dalilin da yasa yake jin haushi idan ta kammala girki ta bar masa bangarensa kafin ya dawo?,sai yanzu ya fuskanci dalilun da yasa yake qin cin abinci har sai ya tilasta ta ta zauna by his side har sai ya kammala?,ashe sone hakan?,wani irin salon sone wanda bai farga da wane lokaci da kuma yaushe ya shiga zuciyarsa ba sai yanzu?,ba abun mamaki bane don bai taba kamuwa a akaran kansa da *SO* din ba sai a kanta,tamkar ya taso ne ya saba da cusa masa shi ake ta qarfin tuwoKamar ya jawo goben haka yake ji,daren gaba daya ji yayi yayi wani mugun tsawo a gunsa kamar jansa aka dada yi,gani yake kamar gari bazai waye ba,kayanta dake cikin cupboard gana daya ya watsosu ya barbazasu kan gadon ya kwanta akai yana shaqarsu ko zai samu sa'idar zugi da zillo da zuciyarsa ke masa game da ita,saidai inaa....kama da wane bata wane,tamkar wani zautacce haka ya koma idanunsa jazur bashin baccin jiya da yau gabadaya kuma bacci bai ziyarceshi ba sai gab da subaπŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…Kiran wayarsa su mr lun ke tayi amma gaa daya layukan switched off,suna baqatarsa sosai don awanni uku kacal ya rage a soma gudanar da bikin,baqi masu zuwa nata tambayarsa,hakan yasa andi da kansa ya taho gidan takanas ba shiriCikin bacci yaji anataba qararrawa da alamun neman izinin shigowa ake,tsaki yaja ya maida kansasaman filon hadi da maida fuskarsa hannun hagu maimakon dama a yadda take dazu bashi da ko niyyar tashi,saidai mai danna qararrawar yaci gaba da matsata kamar babu gobe har sai da mijin nadiya ya fito abdul basid,hakanne ya sashi miqewaa fusace ya zare rigar saman ya cire tie din ya wurgar ya bar 'yar ciki ya fito cikin haushin kaza huce kan damiSuna hada ido da andin yasan cewa babu lafiya fa,don kalli daya zaka yima aliyyun kasan ya koma wani hargitsatstsen aliyyu,cikin tsawa yace "what doyou want?!" Cikin girmamawa yace "sir d time is passing,u have to prepare........." "leave me alone!" Aliyyun ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu cikin wata tsawar,ya ja qofarsa garam ya kulleta ya koma cikiSaman kujera ya koma ya zauna yana nishi,sai a alokacin idanunsa suka sauka kan wayarsa da ya tarwatsa jiya,yasa hannunsa ya tsince ya maida layukan ya sanya batirin ya kunnata,servicena gama hawa massage suka yita shigowa sun kusa hamsin,ko guda baiyi sha'awar budewa ba bare ya karanta,hasalima hankalinsa bai kanta nashi tunanin daban,cikin haka kira ya shigo,bai ko kalli wayar ba bare akai ga batun dagawa,sai da tayi ta katse har sau biyu,cikin jan tsaki ya sanya hannu ya janyo wayar da niyyar kasheta,number din uncle abba ya gani,bau damar kashewa kenan,luguden bugu kawai zuciyarsa ke masa,ya danna ok,ya gama bada amannar cewa fadila taje musu ne,ba qaramin rudewa yayi ba saboda sanin halin abban nasa sarai bashi da sauqi kan wasu lamuranYa kara a kunne jiki a sanyaye,tambayar da abban nasa ya masa ta sake sashi cikin wani halin ha'ula'in"me kake yi haka ne aliyyu?,lafiyarka kuwa qalau?" Cikin rawar murya yace "abba...wallahikuskure ne....kuskure aka samu kuma....."ya dakatar da shi"ya isa bana son jin komai maza ka tashi ka shirya,mr lin ne ya kirani ya gaya min komai har mutum ya aiko maka ka koreshi,damar da ka ka jima kana jira yanzu don ka sameta shine kakeso kayi wasa da ita?,maza ka ahirya kafin lokacin yayi kamar yadda aka tsara"wata boyayyar ajiyar zuciya ya saki ya maida bayansa jikin kujera "to abba inshaAllahu" suka qare wayar yana masa addu'ar samun nasara tare da sanya masa albarkaYa kashe wayar sannan ya zuba mata ido,yana ji a jikinsa da zuciyarsa bai kyautawa abban nasa ba ma,bai san da qanne ido zai kalleshi ba,cikin kasalartasa ya miqe ya shiga toilet ya hada ruqan wankanshi da kanshi don cika umarnin abban nasa,awanni biyu ya dauka ya kammala shiryawa,komai da yakeyi babu walwala a fuskarsa,dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka? Hakanan babu kuzari ko qanqani tattare da shi,shigarsa ta suit yayi saidia wannan ta musamman ce 'yar ubansu,wadda dama an tanadeta ne domin wannan rana,maqudan kudade aka kashe gun siyan nata,kai da kanka idan ka kalleta ba sai angaya maka ta lashi kudi ba zaka baiwa kanka amsa ash ce mai cakude da yarfin baqi rigar ciki kuma da tie dinsa kuma light pink ne,agogo da ya daura da takalmi na qafarsa ma kawai abun kallo ne,sumarsa tayi kyau sosai kamar yasa mata relaxer,sosai aliyyun yayi kyau tamkar balarabe,yaya dama mai kyau yasa abu mai kya?,saidai cikin zuciyarsa sam babu nutsuwa ko farinciki ko dayaSuna waje suna jiransa cikin dalleliyar sabuwar baqar mota,sabuwar qira ce don a shekarar aka farahawanta,yana daya daga cikin kutane na farko da suka mallaketa ko a qasar chinan,mutum uku ne suka miqe ya watsa musu harara don yana ganin susuka takurashi zuwa gurin tamkar su suka yi laifin,dayan ya bude masa inda zai zauna yayin da ragowar biyun suka bishi da gaisuwa,baiko kallesu ba sun san ba lafiya son haka basu sake cewa komai ba suka shiga mai tuqi ya tafa motarTafkeken dakin taro ne dake cikin ginin kamfanin*maitama factory*,hall ne da yaci sunan hajiya*maimunatu ibrahim muhammad* mahaifiya gareshikenan,cike yake da al'umma mahalarta taron,sosai aka qawata gun,decoration aka masa mai azabar kyau da tsari,kowanne table kujeru hudu ne suka zagayeshi,kusandukka mahalarta taron sunyi shiga ne ta baqaqen coat kamar masu ashobi,maza ne damata jinsin yarw da qabila daban daban,kowanne zaune gurinsa a nutse cikin tsari suna sauraran bayanai daga bakin mai gabatarwa duk cikin dakon isowar aliyyu,babu wata hayaniya kai sai ka rantse babu mai numfashi cikin hall dinShigowar tasa ya sanya duk wani dake dakin taron miqewa tsaye cikin girmamawa,tafi ya cika hall din raf raf raf,tamkar ya zura da gudu ya bar hall din haka yake ji don tafin nasu wani kuda yake masa akunne,sai da ya hau step din da ka tanadar musu don zama gefan hannun hagunsa mr lin kusa da shi miss sisineo ce hannun damansa kuma ramzan ne kusa da ramzan kuma mukhtar ne,sai da auka kmmla zama sanna kowa ya koma.mazauninsaya zaunaDakin taron ya sake yin shiru,mai gabatarwa ya yi wa aliyyi barka da isowa,sannu a hankali aka ci gaba da gabatar da taron yadda aka tsara daki daki,duk anun nan da kae maganar minti biyu aka ritsa aliyyi da bindiga aka ce ya maimaita saidai a harbeshin don baya gurin *gangar jikinsa* ce kawai zaune,hankalinsa na kan fadila da agogo,duk bayanminti guda sai ya duba lokaci,jawabai masu muhimmanci da ka tsara shi zai gabatar babu ko daya da ya iya yi,sai ya bada uzirin baijin dadi sosai,drinks da kayan ciye ciye da ka cika gaban kowa da shi babu qanda ya iya kalla balle ya tantance yana sha'awarsu ko baya yi bare akai ga batun zai ci ko zai shaAwanni biyu aka dauka sannan aka zo gangara,su mukhtar suka tilastashi kan dole ya karba yayi jawabin godiya ga dimbin al'ummar da suka.tako gari ya gari suka zo masa,yana ture lasifiqar yana komai haka mukhtar ya manna masa ,idanu da sukamasa ca yasa ya sa hannu cikin kasala da rashin sanin a halin da yake ciki ya amsa"Fadeelah!" Abinda ya soma mabata kenan cikin bututun maganar,tsit suka yi fiye da wanda sukai dazun tamkar wanda yayi calling attention nasu,ido kowa kr binsa da shi don dai sun san suna.ya ambata "fadeelah ta soni matuqa cikin rayuwarta.....na zauna da ita cikin boyayyen nuni gairin tawa kalar soyayyar gareta",ya danyi jim sannn ya shaqi numfashi ya dora "fadeelah ta barni a lokacin da ya bayyana gareni na dade nima ina sonta ba tare da nawa sanin ba....ta barni a lokacin da nake da buqatar yi mata mafificiyar soyayyar da ba'a taba gwadawa wata 'ya mace irinta ba......ta barni da wani nauyi mai azabar nauyi cikim zuciyata ba tare da na samu na sauke mun raba tare ba......fadeelah ta zama ruhina da gangar jikina"dora hannun sa yayi saman qirjinsa saitin zuciyarsa "fadeelah ta mallaki nan ba tare da saninta ba,ya dade da zama mallakinta ba tare da sanin ku mu duka biyun ba""Na tsinkayi fushi fusata da rashin fahimta masu tarin yawa qunahe cikin kalamanta,qunshe cikin takardar da ta zamo baqa aguna,cikin saqon dake bayyana bankwana da abinda zuciya ke so,cikin shafin takarda qwaya daya tal saidai sun yimin nauyi fiye da littattafai dari masu shafuka dari dari"ya hade tafukan hannayensa guri guda yana yinsa ya sauya soaai da alamun abinda yake fadi din na taba zciyarsa sosai,da alama zancan daga ainihin zuciyarsa yake fita ba daga harshensaa yakeba "ku yimin alfarmar sani a addu'o'inku....ku yimin alfarmar roqa min Allah ya huci zuciyarta,na gode muku baki daya...."ya fadi yana qoqarin komawa ya zauna,gaba daya suka.miqe suna tafi,yanayin salin ne ya burgesu,fuskarsu da zuciyarsu cike da tausayinsa,abunka da mai jajayen kunnuwa akwai girmama soyayya komai tsufanta,miss sisineo ce tabude 'yar jakarta ta fiddo da bangles na gwal guda biyu danqara danqara ta ajjiye gaban aliyyu tace ga kyautar ta a isar da ita ga fadilaSosai abun burgeshi ta yima fadilansa kyauta duk da yana da arziqin da zai siya mata ninkin wanann amma ayi kyauta wa masoyinka ma abun faranta ranka ne,yasa hannu ya dauke yayi masu kyakkyawar ajiya..........*mrs muhammad ce*πŸ‘‘πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜✍🏻✍🏻✍🏻✍?

Bayan ciye ciye da akayi a gun suka soka fita gun ainihin ginin kamfanin wanda aka zagaye shi da wani yadi mai kyau aka daure bakin qofar shigar da shi,aliyyun ne a gaba a tsaye andi ya miqo masa qaramin almakashi ya amsa ya dora saman yadin ya datse,tafi aka saki sannan suka dunguma gaba daya sukayi ciki,guri guri suka dinga shiga daya bayan daya cikin kamfanin,sosai ginin ya tsaru yayi kyau matuqa da gaske,komai cikin fasali gwanin sha'awa

Ba qaramin qaguwa yayi ba,duk bayan minti daya idanunsa na kan agogo,gani yake kamar yanga lokacin yake masa,binsu kawai yake ba tare da fahimtar abinda suke yi ba,sam hankalinsa bai tare da su,cikin dabara ya zame jikinsa ya koma office dinsa wanda aka tanadar masa ko da zai zo wani lokacin,yasa key ya bude ya shiga sannan ya koma ya kulle ya koma saman kujera ya zube,awoyi uku ya rage jirgin nasu ya tashi,baya tsammanin zai iya zaman jira,ya zaro wayarsa cikin hanzari ya kira jumong da mukhtar

Tare sukayi knocking ya tashi ya bude musu,kan kujera mukhtar ya qarasa ya zauna yayin da jumong ya rusuna yana jiran jin umarni,"ka shirya mota zan fito yanzu zaka kaini airport" "ok sir" ya fadi hadi da juyawa cikin hanzari ya fice,yayin da mukhtar ke kallonsa yana son tambayarsa me zaya yi a airport?,bai bashi wannan damar ba ya soma masa bayani da kansa ba tare da ya tambayeshi ba "nijeria zan wuce mukhtar nan da awa uku,ina son na bar komai a hannunka kayi handling dinsa,bazan yi sallama da kowa ba its urgent,ka wakilceni please"cikin rashin fahimta yake dubansa "like how aliyyu baqin naka zaka bari ka wuce nijeria?" "Pls mukhtar if u cannot help just tell me directly" yasan halin kayan sa sarai saboda haka ya gyada kai "is ok,is ok I will" ya miqe tsaye ya sake duba passport nashi da ticket dake cikin jakan sa,yaga komai na nan yadda zai buqace shi,ya dauka gami da zaro master card platinum ya ajjiyewa mukhtar din sukayi hand shake "thanks" aliyyun ya fada a gaggauce sannan ya bude qofar ya fice,mukhtar da mamaki ya cika shi yabi aliyyun da kallo galala,gaba daya aliyyun ya fita daga hayyacinsa sam ya fice daga nutsuwarsa

Ta get din baya ya fice don baison kowa ya tsaidashi,don kuwa baiga abinda zai tsaida shi daga tafiya nijeria ayau din nan ba saidai ikon Allah,ko cikin motar ma gani yake jumong baya sauri laqaqai laqaqai kawai yake,gaza haquri yayi har sai da ya soma masa maaifa kan ya qara gudu "sorry sir ida mukayi gudu ya wuce qa'ida camera na kallon mu za'a iya kama mu" sai a lokacin ya tuna ba'a nijeria yake ba dole ya haqura a haka har suka isa airport din,ko jirgin ma gani yake ba sauri yake ba shirme yake(hhhhhh),da suka sauka ko a ethopia aka basu dakunan kwana kan sai gobe zasu qarasa nijeria jinsa yayi kamar a saka shi a kurkuku,masifa kawai yake yana fadin dole ya sayi private jet nashi,dole yana ji yana gani ya haqura har sai washegarin

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Qarfe goma na safe a garin kano tayi masa,tuni nasiru yazo da mota don daukarshi,gidansu yace ya wuce da shi kundila maiduguri road,yana shirin fitowadaga cikin motar saiga sumayya ta fito cikin shirin tafiya school,da sauri ta sauya akalar tafiyar tata ta nufo gurin motar fuskarta qunshe da fara'a"sannu da zuwa ya aliyyu" ta fadi tana leqa cikin motar cikin neman fadila,"yauwa" yace yana sanyo qafarsa waje,ya dubeta cikin dakiyar nan tasa "ke,me kika bani ajiya kikemin leqe leqe cikin mota" sai ta dawo ta tsaya dai dai cikin fara'a "anty fadila nake leqe ko zan gani yaya,surprising din mu kuka so yi shi yasa ko a waya bata gaya mana ba,kwananta biyu ma bata kira mu ba ashe kuna hanya"da sauri ta juya tana shirin komawa ciki tace "bari na fara yi mawa momi albishir"sosai jikinsa ya mutu basu da labarin ma ta dawo to me yake faruwa ne?"maida qafar tasa yayi cikin motar ya rufe ya bawa nasiru umarnin ya kunnata su wuce sani mai nagge(unguwar su fadila)

Har cikin gidan malam ya bude musu suka shiga,ya fito ya ningina jikin motar bakinshi fal addu'a,yana tunanin yadda zai shiga gidan ne,sai ga muhammad ya fito daga inda suke ajiyar motocinsu hannunsa dauke da qaton almakashi irin na yankan shuka,nasiru ne ya qwala masa kira,da sauri ya juya ganinsu yasa shi nufo gurin yana fara'ar ganin aliyyun,"sannu da zuwa yaya"muhammad ya gaida shi ya amsa masa "kai da anty ne yaushe kuka dawo amma bata gayama ummi zaku dawo ba"ya fadi yana washe baki da son jin amsar inda yayarsa take,innalillahi wa inna ilaihi raji'un"aliyu ke fada cikin wani irin hali,muhammad ya juya yana fadin "bari nakira abba bai fita ba"aliyu na shirin hana shi saiga abban ya fito ummi na riqe da jakarsa

Sosai abban ya nuna jin dadin ganin aliyun,yasa muhammad ya bude sitting room suka shiga,maganar da abban ya qara fadi ita ta sake tabbatarwa da aliyyu fadilan bata zo gidan ba"ina mai kukan tafiya yanzu dai ai kuka ya qare ko tunda gashinan anje lafiya an dawo lpy"aliyun ya sunkuyar da kai wata fargaba na shigarsa "tana lafiya abba" abinda ya iya fada kenan,to shima abban bai takura masa da wata doguwar hira ba ya sallameshi shima ya fice kasuwa

Gidansa kawai yasa nasirun ya kai shi don bai san kuma me ya rage masa ba,tunaninsa ya tsaya cak,a harabar gidan ma'aikata ne kowa na masa barka da dawowa,baijin ma me suke fada hannu kawai yake daga musu,ya sallami nasiru ya fito daga cikin motar yana shirin shigewa ciki aka sake dage gate din gidan,tsayawa yayi hadi da juyowa don hajin wanda aka bude mawar,motar samirah ce wadda ta sake cin ubanta,su hudu ne cikin motar,wata dabance ke driving din samirah na gefanta sai wasu su biyun a baya,dariya suke ta sheqawa sam basu ma kula da wani aliyyu ba har suka yo parking,har ta fito tana sheqa dariyarta kamar wadda aka yiwa albishir din ba zata mutu ba,cak ta tsaya tana kallonsa kamar yadda shima ya zuba mata ido,suma qawayen dariyarce ta tsaya cak,sun san halinsa sarai baya da kyau,sum sum daya bayan daya suka fice daga gidan,kai kawai ya gayada ba tare da yace mata komai ko ya sake kallonta ba ya shiga bangaransa

Yafi mintin talatin a zaune kafin ya miqe yaje yayi wanka,kafin ya kammala shiryawa anyi kiran sallar azahar,duk wani motsi da zaiyi tana manne cikin ransa,duk wani tunaninsa na ina zai sameta?ina zai ganta?ina kuma yanzu zaije nemanta?,cikin yadin tissue fari tas ya shirya,yayi kyau sosai duk da kana kallonsa zaka karanci bai cikin walwala duk da kusan hakan yanayin fuskarsa yake amma wannan karon ya ninka yadda yake da,ficewa yayi kansa tsaye ba tare da ya nemi kowa ba da kansa ya ja motar ya bar gidan

Sai da ya fara tsayawa a masallacin bakin layinsu ya bada faralin sallar azahar dinsa sannan ya wuce,kai tsaye yahaya gusau ya wuce gidan farida,ya dan jima a tsaye a qofar gidan baiga gilmawar kowa ba har yana shirin komawa sai ga dahiru almajirin faridan,da sauri dahirun ya qara so inda aliyyun ke tsaye don ya ganeshi,cikin girmamawa ya gaida aliyyun,ya amsa masa yana tambayarsa matar gidan na ciki?,ya amsa masa da "eh alhaji ko a kira maka ita za'ayi?" "A'ah tambayarka dai nake so nayi"aliyu ya fda yana gyara tsaiwarsa "to..Allah yasa na sani" "tayi wata baquwa tsakanin jiya da shekaran jiya da yau?" "Kai gaskiya a'ah,don suma jiya suka dawo daga lagos ita da mai gidan"ya fada masa cikin bashi tabbaci

Idanunsa ya rufe yana jin wani abu sannan ya bude,ya saki qaramar ajiyr zuciya sannan ya ciro kudi ya bama dahirun ,cikin murna ya amshe yana zuba godiya,bai bi ta kan godiyarsa ba ya shige motar ya tasheta ya bar layin

Har la'asar aliyyu salim na bulayi bisa titunan kano,shiga wancan fita wancan,ko manshi da yake qonawa bai damu ba,ya rasa inda zai zauna bare yayi tunanin mafita,gaba daya feeling kansa yake a matsayin guilty,cikin rudanin inda ta tafi yake,ina ta boye kanta haka?,duk da yana ji daga can cikin wani sashe na zuciyarsa na gaya masa she is safe and she is in safety place

Sai da ya soma ganin gurare daban daban na ta alwalar sallar la'asar sannan ya samu ya kashe motar a bakin wani masallaci ,ya daura alwalar ya bi jam'i,sai bayan da ua idar ne yaji cikinsa na qugi sannan ya tuna rabonsa da abinci har ya mance,ya miqe ya koma cikin motar tasa ba tare da yabi ta kan yunwar dake sakadarshi ba,sai da akayi sallar magariba yana bilayin yawon titina sannan ya gano cewa wannan fa ba mafita bace,tunanin matsalar itace zata samar masa mafita da gano masa inda fadilan ta boye,ya juya akalar motarsa ya nufi gidansu dake kundila. .......

*mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻


[10/16, 2:09 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ‘‰πŸΌ *PART 3* πŸ‘ˆπŸΌ

5⃣&6⃣

Yana shiga ya tadda rabi'ah kan dining area ita da iftihal momy na kitchen,da alamu su din ma zaman na cin abinci ne,da gudu iftihal ta gangaro tana ihu "yeyyyyyy daddyyyy"kamar yadda ta saba ta duqa ta gaidashi,ya amsa mata maimakon ya dauketa ya shilla sama yadda suka saba wannan karon sai taga kawai ya shafa saman kanta yayi hanyar kitchen din,ta tabe baki kamar zata saki kuka

Tana kiciniyar rufe warmer taji an rufe freezer,ta dago kai da sauri aliyyun na tsaye yana daddakar ruwan mai azabar sanyi,sai da ya shanye robar guda momin na kallonsa ta zuba mai ido,ganinsa take a wani birkice duk da jikinsa fes yake kuma ya yi kyau da 'yar cika(sakamakon kulawar da ya dinga samu a china)amma abunka da mahaifiya kallo daya tayi masa t gano akwai damuwa a ransa

Yana qare shanyewar suka hada ido da momin,sai ya kautar da kai ya sanya robar cikin dust bin yana cewa "momi barka da dare ina wuni"bata dai daina kallon nasa ba tace "lafiya lau Ali kun dawo lafiya?" "Lafiya qalau ha fada yana jan kujerar plastic dake kitchen din zai zauna "mun sameku lafiya?" Ya sake tambayar momin yana dauke kai don baya son irin kallon nan na momi,nan da nan take naqaltar mutum,itama sai ta dauke kan tana ci gaba da rufe warmer din tace"lafiya lau,tun safe sumayya tace min gaka,shiru shiru baka shigo ba ko da aka leqo kuma ba kai a gun"ta qarashe maganar idanunta a kansa kamar tana son jin amsa kenan

Ya basar da zancan ta hanyar cewa"rabu da wannan shirmammiyar yarinyar momi,makaramta fa zata tafi amma don gulma ta koma,gida muka qarasa kawai"ta dire warmer din tana cewa"ina 'yata fadila" gabansa sai da ya buga "lafiya"kawai ya iya furtawa tare da miqewa don kada ta sunkuto masa wata tambayar da zai gagara kubutar da kansa,ta waiwayo tana cewa "a'ah ina zuwa kuma?" "Zan wuce gida ne momi" "baku gaisa da abban naka ba,yana gida fa,kuma ma na zaci tare zamuyi dinner ko?" Abinda momi bata sank ba bazai iya jiran abban nasa ba don gani yake kallo daya zai masa ya karanto abinda ke faruwa,karo na farko da aliyyun yayi ma momin qarya a rayuwarsa

"Zani gida ne momi za muyi magana da mukhtar,na baroshi ne da mutane a can wadanda ban sallamesu ba na taho" to da yake ma qaryar bata karbeshi ba sai ya jada harda subul da baka ba tare da ya ankara ba "ya zaka dawo bayan baka sallami baqi ba ali?,wai meke damunka ne haka?,a kunnena fa abbanka ya tursasaka zuwa bikin bude kamfani,yanzu kuma ka taho ka bar jama'a acan,baqonka annabinka fa ali"yayi saurin dosar qofar fita yana cewa"momi ai ba matsala mukhtar zaiyi komai kamar ina nan,sai da safe momi idan abban ya sauko ki gaida shi ina hanya goben"baki sake ta bishi da kallo tana ayyanawa tabbas akwai abinda ke damun yaron nan,gashi da shegen zurfin ciki kamar mace,idan kaji cikinsa to ya ciyoshi ne,ta dan daga murya tana cewa"ka gaida mutan gidan" "zasu ji momi" ya fadi yana barin falon cikin sauri don kada suci karo da iftihal ta tsaida shi

Har ya koma ya bude sashensa ya shiga yayi wanka ba wadda ya gani,shi yama fi son haka din ma,yasa koda sunzo babu abinda.zai samu sai qarin tension,shi kuma yanzu abinda ke damunsa yasha kansa fiye da komai,sai da dibi kusan awa daya da wani abu sai ga salima,fuskarsa ta zubawa ido tana murmushi saboda sosai aliyyu ya canza,ya qara ja sumarsa ta sake baqi sidik,gargasar jikinsa kamar an dada mata baqi laushi da yawa,ya sake kyau,badon fadila da ta hargitsa masa lissafinsa ba da abun yafi haka,hakanan shima ya sakar muta fuska don ya zama dole haqqinsu ne don bazaya yiwu haqqin wani ya danne na wani ba,kuma matsalarsa yasan ba tasu bace indai ta wannan bangaren ne

Da sauri ta qaraso ta zube ajikinsa tana fadin "oyoyo welcome my dear"yadan karata ajikinsa yace "thank you ya muka sameku?" "We are fine but I miss you" yadan saki fara'a "ok,to ai yanzu gani mai zan samu?" Ta tabe baki sannan tace "ba komai tunda ai ba yau kace zaka dawo ba ganinka kawai mukayi tsakar rana,ni ta window ma na hageka ka fice" "ni din ma haka dawowar ta zo min" cikin son bin qwaqwafi tace "ko fadilan ce ta takura sai andawo?" "Eh"kawai yace mata cikin som kashe maganar don tamkar allura ce akan qurji idan aka tada masa da zancan fadila, "but ban gata ba kuma ma bangaren ta akle yake" "eh"ya kuma cewa dai bai buqatar taci gaba da yin maganar

Shiru ya dan ratsa dakin kanta na jingine a kafadarsa,kishin fadilan duk ya cikata gani take kamar wani gun ya kuma kaita don ta huta,samira ta danno kai harda sallamarta kamar gaske kai a sunkuye,duk da haka saboda tsabar neman bala'i sai da ta gasawa salima hara ra,ai kuwa itama bata yi qasa agwiwa ba ta rama don ba qaramin adashen tsiya suka dinga shukawa ba sanda baya nan,kullum sai an raba gari a gidan saidai idan garin Allah bai waye ba,amma kwana suke su wuni suna abu guda kamar karnuka,suna hada ido da aliyyu ya bata tasa hararar tayi saurin sadda kai qasa,gefansa ta zauna cikin tausasa murya tace masa "sannu da zuwa an dawo lafiya?" "Lafiya"yace mata a taqaice,duk sai taji ta muzanta,tafi kowa sanin laifinta,gargadi mai zafi babu irin wanda bai musu ba kafin ya tafi kan fice fice,duk da yau ma tsautsayine amma ta kwan biyu bata saci fita din ba,wannan ne satar fitarta ta hudu salima tayi biyu tana tsammanin tayi na qarshe tunda ya kusa dawowa qasar bata san yau ya dawo ba

Shiru ya gauraye falon kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,aliyyu yafi kowa nisan kiwo cikin duniyar tunani,"dear ya kamata muje ku kwanta ko?"salima ta fada tana kashe masa idanu,da sauri samira ta dago "kamar yaya?"cikin daga murya samira ta tambayeta,itama ta dubeta ta mayar mata "kamar yadda kika kunnuwanki suka ji nace"da sauri ta nunata da yatsa "baki isa ba wallahi kinyi kadan don yadda kike buqatarsa nima hakan take.....ke bari ma nayi miki dalla dalla...yadda kike a matse ni nama fiki matsuwa"ta fada tana wani gayara zama,sai kuwa cece kuce ya barke dama kadan kowacce take jira 'yar uwarta ta tabo ta,sak yayi yana kallonsu,sai ya zama kamar wani mutum mutumi,babu wadda tayi masa wani abu na azo a gani a matsayinsa na matafiyin da yayi wata judu bai cikin iyalinsa yanzu ya dawo musu,shegiya shinkafa fara sol da yaji babu wadda ta turo masa tace gashi,amma aqalla ai ko tsakar dare ya dawo idan da tunani sa tashi su sama masa wani abu ko drink ne,to amma ga drink din ma jibge a freezer dinsa su dauko ma su hada masa da cup suce masa gashi babu wadda ta iya yin hakan,babu wani welcoming na arziqi,amma ko wacce burinta ya kwanta da ita ya biya mata buqata kamar wani inji

Ganin abun nasu ma shirin wuce makadi da rawa don har an fara 'yar lakace lakacen hanci yasa ya dakatar da su ta hanyar daka musu tsawa don idan ba tsawar ya musu ba yadda suka kacame babu wadda zata iya jiyo shi"bana buqatar kowa cikinku,duk ku tashi ku bani waje,tunda ku baku iya kwantarwa da mutum hankali ba saidai ku tayar masa,ko kwana daya banyi ba cikin gidana amma kun fara samin bacin rai?" Tuni samira ta miqe,salima ta rausayar da kai tana cewa "amma aliyu ......." "amma me?Please stay away" ya fada yana nuna mata hanya,samira ta sheqe da dariya tana cewa "ato saiki taso ai mu daye,ki daina naci haka kowa sai ya riqe kwadayinsa tunda yace bai yi" wani banzan kallo alin ya watsawa samiran yana cewa "kin sanni,kada ki bari muyi arangama dake bani da kyau!"tasan hakan kuwa tuni tayi gaba salima ta bita a baya,yan jiyo kici kicin kokawarsu a bakim part din nasa,yayi banza da su

_*12 PM*_

Sha biyu na dare ya dinga gwada maqullan hannunsa a qofar har ya samu na qofar tata,ya tura ya shiga ya haska makunnin fitila ya danna dukka qwayayen suka kama bangaren ya cika da haske,qamshi falon yake tamkar tana nan,kamar bata yi tafiya ba na tsawon watanni hudu ba,hakanan komai akillacensa,kai tsaye ya shige bedroom dinta,shima dai kamar falon cikin qamshi yake da tsafta,gadonta a dame yake komai ajere,pant da brassier dinta ne kawai a gefan pillow,ya qarasa ahankali ya haye gadon hadi da kwanciya pillow din ya janyo hadi da rungumeahi tsam tsam a qirjinsa,qamshi pillow din yake kamar a shafa masa turare ne,ya sake miqa hannu ya dago pant and brassier din farare qal ya zuba musu ido,a hankali ya mannaau a hancinsa yana sheqar qamahin turarenta na shamsul imaraat

A hankali ya shiga sosai cikin zurfin tunani,yanayinta,halayenta,dabi'unta,haquri irin nata kawaici da yakanah,bai taba ganin ta tana fada irin nasu samira ba,bai taba ganinta tana koda sa'insa da daya daga cikinsu ba,duk wata sabga tasu bata ciki,shi da kansa alokutan baya har haushi yake ji idan yaga bata damu da fadan kishi ba,ashe so ne?,ashe haushi yake ji yana ganin kamar bata sonshi ne?

Juyi kawai yake samar gadon,jinsa yake tamkar wani maraya,wani irin kewa yakeji mai zafi da radadi tana kamashi,ya riga da ya saba da kwana jikinsu na gogayya da na juna,ya saba da sheqar qamshinta,sosai ya sake rungume pillow yana sakin numfaahi sama sama,yafi awa biyu kafin wani wahalallen bacci awon gaba da shi ,ko cikin baccin ma bata qyaleshi ya huta ba sai da ta jawo masa yin wanka,ya dawo bakin gadon yq zauna yana tsane jikinsa da towel dinta,idanunsa ya sauka kan wani dan kyakkyawan madaidaicin frame da yake zaune dirshan bisa side bed,yasa hannu a hankali ya dauki hoton ya zuba masa ido yana kallonta,murmushi take yi sosai,fararen haqoranta jerarru reras sun bayyan,yar lobawar dake tsakiyar habarta ta fito sosai,ya sanya bakinshi saitin lips nata yayi kissing,murya qasa qasa yace "I love you"ya dan manna hoton a qirjinshi

Sai da yayi sallar asuba sannanya baro bangaren har ya fito ya manta bai dauko hoton ba ya koma ya dauko abinsa,kan side drower dinshi ya kafa sa,yana shiryawa yana kallon hoton har ya kammala shirinsa tsaf cikin shadda fara tas mai asalin tsadar sai maiqo take da daukan idanu,yayi masifar kyau saidai fuskarnan na kirtibe,qarfe bakwai ga fito ya soma da sashen samira don itace a damansa,yana tura qofar ta bude alamuna bude ta kwana,kai tsaye ya zarce bedroom din ta don yasan tana ciki,yana tafiya yana bin falon da kallo tamkar dakin ajiyar shirgi haka ta maidashi

Dai dai ya sameta saman gado hannu can qafa can,gajeran gashinta maras tsawo wanda bai hadu da mace mai gyara ba duk ya hautsine ya tashi yayi cako cako kamar bishiyar qaya(don ko baki da tsawon gashi matuqar ke mai gyara ce to zai bada sha'awa,amma komai tsawonsa indai ba gyara abin qyamata zai zama),sosai iyyu ya tsani irin wannan kwanciyar tata,don kuwa insha Allahu kuka hada gado daya da samira to ranar fa ka shieya zaka daku da hannu da qafa,haka kullum yake fama da ita,shi yasa ya gwammace ya matseta a jikinsa ayi baccin haka

Ya dan taba qafarta yana kiran sunanta,saidai kamar gawa ko motsi bata yi ba bare yasa ran zata tashi jan minsharinta kawai take,yasan hali dama bata motsa din ba kuwa har sai da ya dage ya daki daki qafar da hannu sannan ta miqe a zabure tana cono baki gami da mutsitstsika ido,sai da ta gama mutstsike idanun sannan ta dubeshi,ganin aliyyu a tsaye ya sata shiga taitayinta,addu'a take cikin ranta Allah yasa maganar laifinta yazo yayi mata,don tasan halinshi shirunsa ba abu mai dadi yake haifarwa ba,fuska a murtuke yace "hala ko sallar asuba bakiyi ba?" Nan ta hau kame kame "zan....zanyi....yanzu ne na tashi ai..." "good" yace da ita cikin takaici yana gayada kai,ya juya zai fita "zan fita sai na dawo" "to" tace kaar wadda aka tilasta ta sai ta fadi hakan,Allah Allah take ya fitan taja bargo ta koma barcinta,bata sani ba shi din ma Allah Allah yake ya bar dakin,don zarnin bandakinta dake cikin bedroom din shi ke busowa har cikin dakin gadon,sai taga kuma ya juyo hadi da cewa "bani key din motarki da wayarki" cikin marairaita tace "don Allah kayi haquri bazan sake ba" a zafafe ya kalleta "will you keep quiet or not? Da baki iya bada haqurin ba kenan sai yanzu?common bani key da phone nace"nuni tayi masa kan hargitsatstsen dressing mirror dinta,ya juya ya kalli kan madubin saboda hargitsewarsa ma shi bai hango wata waya ba ballantana maqulli "ok...ni zanje ma na dauko miki ko?" Dolenta ta sauka daga kan gadon ta dauko ta miqa masa tamakar zata yi ihu,ya amsa ya fice da sauri ba tare da yace mata qala ba don zarnin sake busowa yake,kuma ko yace ta gyara ba zata yi din ba don sau nawa yana fama da ita kan hakan sai tave masa yau fa sati daya kacal da wanke shi ba wani dadewa yayi ba

Salima ma na bisa gadon a nade bacci na dibarta sama sama,ita din ma sai lokacin bakwai da wani abu ta yi tata sallar,saidai yana sallamar ta amsa gami da miqewa zaune kan gadon,murmushi take masa wanda hakan ya sanyashi rage daurin fuskarsa"kar daiace har ka fito" ta soma cewa,ya kalleta yace "eh"yana mamakin yadda basu iya gaisuwa wa mijinsu ba,babu wadda ta fado masa sai fadilan,duk safiya sai ya gaidashi kamar yadda ya zame mata qajibi sannu da zuwa da adawo lafiya duk da sai yaso yake amsawa amma hakan bai dameta ba haqqinta take saukewa, "amma yaci ace yau a gida zaka wuni ko" ta sake shigowa da wani qorafin "a hakan kuna batan ran babu wani caring bare a faranta maka"yayi zancqn cikin zuciyarsa,a fili sai yace "maiduguri zani zuwa anjima zan dawo insha Allah"cikin tuhuma tace "maiduguri?gurin wa?...." "stop your suspicion,sai na dawo" ya katseta, "madalla"tave tana binsa da cike da kishi har ya fice

Cikin motarsa qirar 4matics fara ya zabi yin tafiyar shi kadai,bayan yin addu'o'in matafiyi ya kunna motar ya fice daga gidan cikin tsammani mai yawa da fata na gari akan kanshi

*mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[10/16, 2:10 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ‘‰πŸΌ *PART 3* πŸ‘ˆπŸΌ

7⃣&8⃣

Cikin kwankin kullum cikin kuka take kwana take wuni,a haka ma an samu sauqi saboda takan kaucewa idon anty hauwa don kada ta dinga jin ba dadi,damuwa sosai ta yiwa zuciyarta yawa,tana jimantawa kanta yadda soyayyar aliyu ta gama illata ta,saidai bata barin damuwar ta tsawaita mata da yawa ba ta tsananta yin addu'o'i,da taimakon hakan ta soma samun kyakkyawar nutsuwa cikin ranta,koda yaushe cikin kula da ita anty hauwa take bata barinta ta zauna ita daya bare ta damu sosai,sau da yawa anty hauwan idan tana bata haquri kunya fadilan keji "nifa babu wanda yayimin laifi don Allah anty ki daina bani haquri,kunya hakan yake bani wallahi"

Yara kam murna suke anty fadila ta dawo gidansu sunata tsalle,idan akace babu makaranta to suna liqe da ita wani lokacin har sai anty hauwan ta kore mata su tace su barta ta huta,ita kam dadi take ji idan tana tare da yaran saboda dama can mai son yarance ita,sosai mamansu taja kunnensu da kada su sake su gayawa kowa cewa anty fadilan tana nan gidan saboda yadda taga suna rawar qafa zasu iya subul da baka

Ita kanta tayi mamaki qwarai yadda ta soma ragewa kanta damuwa kan aliyun duk da yake ba abun mamaki bane addu'a ai tafi qarfin wasa,sosai tayi yaqi da zuciyarta,bata bari bacin rai ya rusata ba,da zarar ta soma tunane tunane zata datseshi ta hanyar daukan qur'ani ta karanta,idan ta gama kuma ta shiga shafukanta na sada zumunta,komai anty hauwa ta hanata yi,duk da hakan fadilan taqi yarda don kullum tare suke shiga kitchen yin lunch ko dinner,wani lokaci kuma ta shirya mata yaran da safe

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Gudu sosai ya dinga yi shi daya cikin motar,cikin ikon Allah ya sauka lafiya,saidai tun daga yadda su ya gana ke faman tambayar fadilan ya sare da al'amarin ya tabbatar bata garin ma baki daya bare gidan,sallah kawai yayi ya baro garin,bai damu da yawan tafiyar da yasha ba bare ya nemi hutawa har yaci abinci,juyin duniya ya gana tayi ya tsaya yaci abinci amma qeme me yaqi,ya bata haquri bayan ya ajjiye musu kudade masu dama yace yana da abubuwan yi masu yawa a kano,haka ya kamo hanya ya taho,gudu na ban mamaki ya dinga shararawa ba qaqqautawa,sai da yaji tuqin na neman gagararsa sannan ya samu wani shago kam hanya ya siyi yoghurt yasha,bai fasa gudun nasa ba wanda ikon Allah ne kawai ya kawoshi garin kano lafiya
πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Kwana hudu bai cikin daidanshi,matansa mata ne marasa kulawa,tabbas sunga canji sosai tattare da shi amma babu wadda ta damu da tambayarsa mene damuwarshi,momi kam ganin baice komai ba yasa ta tsuke bakinta ta qyaleshi don ta sani ida dai ya soma zurfin cikin nan nasa bai gayawa kowa komai sai lokacin da yaga dama

*G*idan anty hauwa shine gida na qarshe da hankalinsa ya kai kai,anan ya tattara dukkanin fata da tsammaninsa,duk da wata zuciyar na tantamar mai zaya kaita can bayan ko gidansu bata je ba?,qarfe biyar da shirin na yamma ya gama shirinsa cikin qananun kaya da sukayi matuqar yi masa kyau

Suna kitchen ita da fadilan suna hada abincin dare sunayi suna hirarsu,yara suka jiyo wadanda suka bari a falo suna kallo da yake alhamis ce suna cewa "ina wuni uncle....ina wuni uncle" gaban fadila yayi mummunar faduwa ta saki mirfin hannunta da take shirin rufe miya da shi,"shikenan yau zan amshi takardar rabuwa da shi" abunda zuciyarta ke gaya mata kenan "anty aliyu ne"ta fada tana kallon anty hauwa dake tace shinkafa "aliyu?" Ta fada tana kallon fadilan cikin kasa kunne,"ina zuwa" anty hauwa fada bayan ta ajjiye tukunyar hannunta ta fice da sauri,komawa fadila tayi jikin drawer ta jingina bayan ta hatde hannayenta a qirjinta tana jiyo sweet voice din sa,batasan me yasa take jin qunci a qirjinta dalilin gaya mata da zuciyarta ke yi takardar sakinta aliyun ya biyota da ita

Ruwa aliyun yace ma anty hauwa ta bashi,duk ruwan dake freezer din falonsu ya qare sai lemo,da hanzari anty hauwa ta miqe ta hau sama ta dauko masa a parlour din abban kausar don bata son ya shiga kitchen din,ji yayi bazai iya jiranta ba don haka ya miqe ya shige kitchen din,a hankali fadila ta bude idanunta da a da ke a lumshe,cikin jikinta take jin tahowar tasa,nan da nan tayi wuri wuri da ido tana neman maboya,a asukwane ta shige bayan qofar wadda a kusa da ita freezer din take

Kai tsaye ya qaraso ya dage freezer din ya sunkuya yasa hannunsa ciki,cak ya tsaya da qoqarin ciro ruwan da yake yi,sai yake jin qamshinta cikin hancinsa,irin qamshin da ya ji cikin bargo pillow da undies dinta,sakun murfin yayi ya soma kallen kallen kitchen din yana neman ta inda qamshin ke fitowa,ko ina ya kai idanunsa sai yaga babu kowa,tuni fadila tayi surrender bayan qofa numfashinta kamar zai dauke musamman da taji ua jingina a bayan qofar ya kuma qin barin gurin,yafi minti uku cikim kitchen din yaqi fita din qamshin turarenta na ahlamul arab kawai yake ji,hat sai da anty hauwa ta shigo hankalinta a tashe tana tsammanin ya ga fadilan,sai ta tadda shi a tsaye kawai jingine jikin qofar hannayensa harde a qirjinsa,"ina ka shiga ga euwan can na kaimaka" "ok" kawai yace ya gewayeta ta fice daga kitchen din itama ta rufa masa baya

Ta maida yara dakinsu daga ita sai shi a falon,zuba masa ido tayi sosai tana kallonsa canji qara ta hango tattare da alin,fara'arsa ta sake qaranci sosai,tsiyayar lemon kawai yake yi yana dirkawa cikinsa,yadda bai tanka ba itama bata ce kamzil ba har sai da ya tashi da roba biyu ta ruwa da lemo,ya dago kai ya kalli antin hadi da sakin ajiyar zuciya "ni wai uncle meke damunka?tunda kazo naga kamar a hargitse kake?"wata ajiyar zuciyar ya kuma saki "fadeelah nake nema mummyn kausar" kamar gaske ta nuna alamun rashin fahimta sosai "kamar yaya?fadilan da kuke tare,yaushe dududu sumayya ta ke gayamin kun dawo daga china zaka ce ita kake nema kamar wadda ta bata" "bata tayi....bacemin tayi"ya fadi yana jingina jikinsa da kujera,yayin da fadila dake labe cikin kitchen ta zaro ido jin cewa wai nemanta yake "yayimin me? Me zayayimin ne?"ta tambayi kanta ba tare da tasan amsar tambayar ba

Ya dora cikin wata iriyar murya "tayi tsammanin bana sonta ne bayan nima na dade ina sonta,tayi zatin maqiyinta ne ni alhali duk duniya babu mai sonta kamar ni...ta dauka ina zaune da ita ne bisa dole bayan kan son raina nake zaune da ita.....anty ta yimin gurguwar fahimta,ta gujeni a lokacin da na qara zurfi cikin qaunarta....ta gujeni a lokacin da dukkanmu ni da ita muka fi buqatar kasancewa da juna"ita kanta anty hauwa baki ta saki tana tsammanin ba aliyu bane,aliyyun da tunda take tare da shi zata iya cewa bata taba ji ko ganin yana kwatanta qaunar da yakewa wata diya mace ba aduniya koda uwar 'yarsa,fadila kam dake cikin kitchen duburburcewa tayi,sai jikinta ya fara rawa qafafunta suka gaza daukarta ta lallaba ta ja jikinta ta zauna kan kujerar roba bakinta rufe da tafin hannunta yayin da hawayen da sukayi kwana da kwanaki tana qumshe su yau suka samu qofa.

Lallai ma yaudararta aliyu keson yi?,dama shi din shahararren mayaudari ne,shine a yanzu zai furta cewa yana sonta?wanne irin zama ne basu yi ba baice yana son nata ba sai ayanzu?sai yanzu da ya kwanta da ita?,ya tabbata kenan jikin nata yake so kamar yadda tayi zato tun farko? (Illar zato),sha'awarta yake kenan ba qauna yake mata ta cikin zuciya ba?,kuka ne sosai mara sauti ya kufce mata yayin da shi din ma ke can zaune dirshan gaban anty hauwa yana fayyace mata irin zaman da sukayi da fadilan,kunne sosai ta saka tana jinsa duk da yake tamkar tishi yake mata,duk yadda fadilan ta fada hakanne harda wasu abubuwan da fadilan ta boye ta qi fada

Kafin ya kammala tuni har qwalla ta cika idanunsa duk da bata gai ga zubowa ba amma qiris take jira,soyayyar 'yan uwan taka sai Allah tuni tausayinsa ya kamata don zata iya dafa qur'ani kan aliyyu bai taba shiga makamancin wannan halin ba akan wata mace,ta karanto gaskiyarsa qarara,don dama ko ada bai iya qarya ba tun yana qaraminsa,zai gaya ma gaskiya ne ko za'a tsireshi don haushi,to saidai bata jin kuma zata shiga haqqin fadilan ta karya alqwari da ta daukar mata don aliyyu nata ne,bata jin zata sarayar mata da haqqinta tunda nata din ne,ita ke da iko da abunta,ita kadai tasha haqurinta ita kadai tasan me ta hadiya

Cikin sanyin jiki da qunar rai yace"wai anty roqona take na saketa,tana tsammanin sakin nata abu ne mai sauqi har irin haka a gurina?" Ya kada kai yana cewa"bazan iya ba,bazan iya furta wadan nan kalmomi gareta ba koda duka duniya zata taru a kaina" dole ka sake ni aliyyu dole mu rabu ,bani kake so ba jikina kake sha'awa" ta fadi haka qasa qasa cikin kuka mara sauti,ya miqe "zan tafi tafi tunda kema bata gunki zan ci gaba da nemanta",tuni ya juya ya fice daga gidan,tausayin dan uwan nata ya kamata don tasan wahla kawai qanin nata zaici gaba da sha tunda fadila na tare da ita

Kifa kanta tayi kan cinyarta ta sake sakin wani sabon kukan mai dan qaramin sauti,wani qunci zugi da radadi data rasa na meye take ji cikin ranta,anty hauwa ta kama hannayen fadila tana kallin qwayar idonta "fadila.....fadila,naga abubuwa da dama cikin qwayar idanun aliyu,naga soyayya naga qauna cikin cikin idonsa irin wadda ban taba gani ya yiwa wata 'ya mace ba,kinji komai da kunnuwanki no need na maimaita miki"

Kada kai fadilam keyi,"anty na yarda aliyu na sona a yanzu bazan qaryata ki ba,anty amma ba ni fadilan yake so ba wani abu dake gareni yake so,tun yaushe anty....tun yaushe nake tare da shi nake kyautata masa bai taba cewa yana sona ba sai yanzu?sai yanzu da wani dalili ne ya jawo hakan?...Thank god aliyu na sona yanzu anty,saidai ......is too late anty I already displaced him from my heart,na goge cikin kundin rayuwata zan rayu da shi" kalmar ta fito daga bakinta hade da hawaye

Sai dariya taso kama anty hauwa amma ta gimtse,with confidence fadila ke fadin maganar saidai qwayar idanunta kadai ta ta qaryata ta,bata sani ba ita kanta qaunar aliyyu tayi mata illar wadda take huduwa tun daga zuciyarta har zuwa idanunta da bakinta,bata da abunyi anty hauwa ta sani wani daci ne da fadilan ta dade tana guntsa taje fesarwa idan ta hanata kuma bata yi mata adalci ba,tasan cewa kokwanto ne yasa fadila fadin wadannan maganganun amma ba har cikin zuciyarta bane,ta kuma gama gasgatawa wani irin salon rikicin soyayya ne ya kunno kai kawai tsakaninta da aliyyun,sanoda haka sai kawai tave mata "shikenan fadila kici gaba da addu'o'inki ki yi ta istihara,Allah ya zaba abinda yafi alkhairi"

Har anty hauwan ta kai bakin qofa fadila ta dakatar da ita ta hanyar cewa"am sorry anty idan maganganuna sun bata miki rai" murmushi ta saki "don't mind,banji komai ba araina fadila" murmuahi itama tayi mata tace "na gode" haka Allah yayi fadila bata aon bacin rai ko yashin hakai ko kadan kamar yadda bata son taa ta batawa wani rai ko ta shiga haqqinsa

Kwana biyu yama cikin wannan hali,duk wasu harkokinsa na gida dana waje yaqi maida hankali kan kowanne,daga qarshe dai kasa jurewa yayi gani yake kamar su suka boye masa fadila,yana ganin da wani yashin hankalin gwara wani,da ya rasata gwara a yanke masa duk wani hukunci da za'a yanke masa idan yaso su bashi ita,ya gaza jure kewarta komai nasa ya yi missing dinta,

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Tsakiyat uncle abba da momi ya zauna ya warware masu abinda ke faruwa kamar yadda halayyarsa take fadin gaskiya,momin ce ta saki salati mai nauyi yayin da uncle abba yayi shiru gami da yin tsai da ransa,sai a lokacin ne kuma hankalinsa ya soma tashi momi tayi shiru ne tana jiran jin umarni ko me mijin natazaya fada?,yayin da uncle abba ya rasa me ma zaya ce din?,sama da minti biyar kafin ya dago yace "tashi kaje aliyyu" cikin firgici ya dago kai yana kallon uncle abban,ya sake maimaita masa"ka tashi kaje nace mu zamu nemota" alhaji yaje fa kace?" Momi ta fada cikin fushi,a nutse uncle abba ya kalleta "to maimunatu mai zai zauna yayi min?,yaje kawai tunda ya gama nasa aikin ko,mu kuma ba sai muyi namu ba?"

Tasan sarai halin mijin nata saboda haka ta gamsu da abinda yace "gaskiyane"shi kam aliyyu yadda bai tanka ba sabida rudani haka ya kasa tashi kansa na sunkuye jinsa yake kamar wani mutum mutumi,har sai da uncle abban ya gaji da ce masa ya tashi shi da momin suka taahi suka bar masa falon

Da azahar momi ta dauki wayarta ta kira anty hauwa kamar yadda uncle abba ya ce ta ce mata yana son ganinta ko zuwa najima ne,sai kuwa aka taki sa'a suna cikin gaisawa kausar ta soma qwala kiran "anty fadilah!anty fadila!!na kasa daukowa"nama ne tace ta ciro mata cikin fridge sunce suna son dambun nama to naman ya riga yayi qanqara,tuni momin ta tsaya da amsa gaisuwar "maijidda wace fadilance a gidanki?" Cikin son boye boye tace "am ....fadila ce ta zo mu gaisa,dazun aliyun ya sauketa" "mu kuma dazu aliyyun ya bar nan yana cigiyar ta ba"momi ta katseta "aljanu ke miki wasa da hankali ko gida biyu su aliyun suka rabu?" "A'ah momi ai" "kinga dakata shi aliyun ya riga da ya sanar da babaku komai da kansa,dama maganar da na kira ki kenan akai,saboda haka idan anyi magariba ki dauko ta kuzo"

Hawaye bibbiyu fadilan keyi"anty me yasa kika sanar musu anty,munyi alqwari dake anty,me yasa suka sani?" "Fadila aliyyu da kansa yakai kansa gun abba,momi kuma ta san kina gidan nan dazun da kausar ke qwala miki kira" "me yasa aliyyu zai min haka?,don me yasa zaije ga uncle abba?,me yasa baiyi sakin cikin rufin asiri ba?,so yake kowa sai ya ga laifinshi kenan?"sai lokacin tayi dana sani,tayi data sanin da ta fito tun ranar da yazo gida anty hauwan ya bata takardarta ba tare da kowa yaji ko ya gani ba,suna sake doso unguwar bugun zuciyarta na daduwa,tabbas da kafin su yi nisa naty hauwan ta gaya mata inda zasu babu shakka ba zata ba sauka zatayi,gaba daya jikinta rawa yaje ta kasa nutsuwa sai da anty hauwan ta riqeta sannan ta iya shiga falon.........

*mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[10/16, 2:11 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ‘‰πŸΌ *PART 3* πŸ‘ˆπŸΌ

9⃣&1⃣0⃣

Umminta ta gani da mominta zaune kujera daya,uncle abba da abban nata kuma na kujera daya,sai iftihal dake zaune dare dare kan cinyar abban nata,duk kansu suka amsa sallamar,sosai taji dadi cikin ranta don rabon da tasa iyayen nata a ido har ta manta,sai dai hararar da ummin nata ta watsa mata ita ta sagar mata da gwiwa,anty hauwa ce ta fara gaida su sannan itama ta gaidasun,sama sama ummin ta amsa mata don har gwara abbanta,cikin salubewar jiki ta koma gefan kujera ta rakabe

Aliyyu ne ya shigo cikin sallama yana sanye da shadda dinkin tazarce kansa babu hula,da gudu iftihal tayo gurinsa,hannunta kawai ya iya riqewa bayan da ta gaidashi,gaida su yake saidai abba da umminta ne kawai suka amsa masa,yana shirin samun guri ya zauna uncle abba ya dakatar da shi ta hanyar cewa "kai....dakata ba zama na kiraka kayi ba...ungo nan" ya miqa masa farar takarda da abun rubutu "rubutawa yarinya sakinta tunda Allah yasa mun ganta" da sauri ya daga kai ya soma rarraba ido cikin filin falon yana neman inda fadilan take,can ya hangota a takure a gefan kujera kanta a qas

Gaba daya idanunsa suka rufe,tuni ya manta da cewa akwai wasu wai iyayensa a falon ya durfafeta,idanunsa qir bisa kansa,wani shauqi mai cakude da matsananciyar qaunarta yake fisgarshi,sai da yaje daf da ita uncle abba ya daka masa tsawa wadda ta sashi dawowa cikin hayyacinsa "qaniyarka nace dawo nan" inji uncle abba yana masa nuni da gabansa inda zai zauna din bayan daquwar da ya watsa masa,a salube ya nufi gun yana tafiya yana waiwayen fadilan da kanta ke qasa idonta na digar hawaye,takardar ya sake miqa masa "ungo nan rubuta" sai a lokacin abban fadila yayi magana "haba alhaji bai kamata ba,ya za'ayi yaro da matarsa kuma yana son abarsa a tilasta masa saki,abinda ya faru ai ya riga ya faru,kuskurene kuma babu wanda baya yi,kuma ni idan banda shirmen quruciya irin na fadilan ma banga abun da yayi zafi haka ba,tunda kuma alhamdulillah ya gane sai muyi addu'ar Allah yaci gaba da hada kansu"

"Wa?wannan?"uncle abban ya fada yana nuna aliyu da yatsa, "ai bai isa ba tunda tafiso ya saketa sai ya saketa,ai zaluncin ma alhaji yayi yawa,mun zaba mata miji ba tare da jin ta bakinta ba ko musa mana bata yi ba ta karba harda godiya tayiana biyayya,taje ta zauna da shi zuciya daya amma ya dinga azabtar da ita,babu kuma wanda ya taba sani ko sau daya sama da shekara guda har da kusan rabi,kuma yanzu don bamu da adalci tace bata da buqatar zama sai mu tilasta?don me?,mu zamu yi mata zaman auren?," sai lokacin itama ummi ta tanka "to alhaji tunda ya gane kuskurensa don Allah sai abar maganar,ke fadila wallahi tallahi na kuma jin kin furta mijinki ya sake ki ko mai ya hada ku kuwa sai....." "a'ah hajiya,ya kuke neman daure ma yaro qarqashi ne?" Inji momi" "barsu indai baso suke su nanamin su suka haifi fadila ba"inji uncle abba

Cikin sauri hajiya amina(ummi) tace cikin girgiza kai "Allah ya kiyaye alhaji Allah ya sawwaqe,haba haba da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne"ya dauke kansa ya maida kan aliyyu "saketa nace ko?"ya nuna shi da yatsa "kuma don ubanka" (aliyyu bai yaba jin yayi zagi ba ko da wasa sai ranar "a gidan nan zata ci gaba da zama ni ne dai ubanta "qasa yayi da kansa yaqi furta uffan,babban abunda yasa jikinsu yayi sayi ganin hawaye nabin fuskar aly,mutumin da komai tsanani ba zaka ga koda qwalla bane bisa fuskarsa yau shi ke kuka saboda mace?,anty hauwa kamar ta tayi haka take ji don dai kawai zancan manya ne kuma basj bata damar shiga ba,sauqinta daya ma iftihal tayi bacci kan cinyar ummi

"Abba wallahi ko wuqa zaku sa ku dinga yankan naman jiki na bazan iya sakin ta ba,kuyi min afuwa abba" abban fadila ya dubi uncle abban "don Allah salim a naci albarkacin amintaka ina mai baka haquri kan ka sassauta fushinka kan yarona"falon ya dauki shiru na wasu lokuta kamin abban ya saki ajiyar zuciya "naji...naji,abu na farko da zan fara fada shine alhj abbas kai da hajiya amina ku yimin alqawarin babu wanda acikinku zai tursasawa fadila koda ta bayan fage ne kan sai ta koma gidanta ba tare da ita ta yanke hakan ba?" Ba yadda alh salim ya iya don yana tausayama aliyun yace "nayi" ummi ce tayi shiru har sai da hajiya maimuna tace "baki ce komai ba" "nima nayi"itama ta fadi cike da tausayin aliyu

"Abu na biyu,anan gidan fadila zata zauna har sai taji ta amince don radin kanta zata koma,idan yaso naga mara kunyar da zai koreta don ba gidansa bane haka nan ba da qwandalarsa na hada na gina gidana ba"ya fadi yana muzurai,sarai aliyun ya sani da shi abban yake amma sai ya sunkuyar da kansa,saboda shi kam a yanzu kome zasu fadi yaji ya gani kuma ya yarda suyita fadin,ko bulala dukkansu zasu dauka suyita zabgarsa yaji ya amince zai kuma shanye tunda dak an janye batun saki cikin lamarin,uncle abba ya nuna shi da yatsa "saura kuma naga qafarka inda take bare kace zakayi yunqurin takurawa ko tursasa mata sai na saba maka fiye da tsammaninka,tashi ka bawa mutane guri mutumin banza kawai",bashi da zabi illa barin falom kamar yadda abban ya umarcesu ya miqe ya fita bayan ya duqa yace "na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara girma,Allah kumabya huci zuciyoyinku"yana tafiya yana satar kallonta har yanzu kanta na duqe taqi ma ta dago ya kalli koda fuskarta ne

Sosai uncle abba bayanin dalilin yin wannan hukuncin bayan ya sallami fadilan da anty hauwan,yana sone koda aliyun yayi nadama ya sake sanin darajarta da amfaninta a gunsa kafin ta koma masa,cikin dariya abban ke cewa"haba alhaji ai ba sai kace komai ba,amma dai don Allah a sassautawa yarona haka"dariya duk sukayi,daki aka bawa fadilan kusa da nasu sumayya,amma tace tafiso ta zauna cikin su sumayya,a daren aka kawo mata madaidaicin gado da cupboard irin nasu rabi'ah aka sa mata duka adakin kasancewar dakin qato ne sosai,su suka taya ta shirya kayan suna ta rawar jiki zasu zauna tare,batasan lokacin da su ummunta suka tafi ba sai da anty hauwa ta hauro saman take sanar mata

Cikin daren babu dan qaramin haukan da baiyi ba,kuka ma kasa zuwa masa yayi sai zafi da radadi da zuciyarsa keyi,daurewa kawai yakeyi yana sakar musu jiki don kada ya shiga haqqinsu,wani lokaci idan kewar ta isheshi dakinta yake tafiya yayi bacci cikin bargonta ya kalli hotunanta sannan yake samun relief

(Qalubale a agareku iyayemmu mata har ma da mazan,da kuna ji kuna gani 'ya'ya yenku zasu dinga auri saki,babu kwaba balle hantara,wani lalacewar ma idan anyi sakin wai sai ya kwaso yaran ya kawowa uwar ita ce mai riqe masa kuma tana ziga shi har kina furta gwara da ya saketa,,to ahir din mu domin kuwa kada mu manta mun haifa ko bamu haifa ba an haifa mana,za'a yiwa taki 'yar ko 'yar 'yan uwanki kiji idan da dadi? Ai ko.matar ba ta gari bace akwai matakai da Allah s.w.a yace abi kafin akai ga rabuwar bawai rana tsaka daga an dan saba masa laifin da bai kai ya kawo ba ya karkace ya danqaro saki ba,to wallahi muji tsoron Allah,shi mai sakin dake mahaifiyar me goyon bayansa ina zato a cikin 'ya'yansa ko jikokinki ba za'a rasa mace ba,ya zakuji yayin da aka koro muku ita?,saki yayi yawa musamman acikin al'ummar mu ta hausawa,don Allah mu daure mu gyara ko ma samu gyaruwar al'ummar mu wadda wata tabar barewar tarbiyya daga an saki uwa ne shikenan sai gida ya tarwatse kowane yaro yayi nasa alqibla,babu mao saita siu kan hanya wato uwa ta gari,Allah kasa ku dace mufi qarfin zuciyarmu,ameen)

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Sosai ta koma bakin aikinta don uncle abba yace babu mai hanata,babu yadda aliyyu ya iya haka ya zubawa sarautar Allah ido,ina ma yaga bakin magana koda yana da ta cewar?,don ko yazo gidan iyakacinsa parlour ko kallon upstairs inda dakunan baccinsu yake momi ta shiga balla masa harara kenan,haka zatayi kicin kicin da fuska har sai ya gaji da muzurai ya qara gaba

Ita kuwa uwar tafiyar tun daga lokacin da akayi hukuncin bao sake sanyata cikin idonsa ba,har addu'a yake Allah ya hadasu amma daidai da gilmawarta Allah baisa ya gani ba,tana sane ta sani,matuqar taji muryarsa to babu ita babu fitowa tana qule cikin daki ko kitchen idan a qasa take har sai ya bar cikin gidan

πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…πŸ”…

Da yammacine suna zaune cikin parlour ita da sumayya da rabi'ah,momi bata nan ta tafi dubiyar yayanta da baya jin dadi alh datti ita da iftihal suka wuce,gidan sai su ukun,lokaci lokaci rabi'ah naeqa kitchen ta duba abincin dare da ta daura sumayya kuma na tsefewa fadila calabar din da take kanta,saboda tsawo da santsin gashi da hannu suke tsifar,yayin da fadila ta jawo wasu fuskarta tana tayata,wani film da suke masifar ao suke kallo a m.b.c bollywood,na soyayya ne sosai,jarumin film din na musu kama da aliyyu sosai hatta da halayya,don haka wani lokacin ma ya aliyu suke kiransa duk sanda aka sako film din,suna son film din don haka idan ana kallonsa ko hira ba'ayi,saidai idan anzo wani gun daya burgesu,

A hankali aliyyun ya turo qofar falon with confidence don tun a gate ya tambaya aka sanar masaomin bata nan,basu ga shigowarsa ba sai sumayya kawai don rabi'ah na kitchen duba girkinta,fadila kuwa gashin da ya rufe mata fuska da yadda film din ya yafi da hankalinta sosai yasa sam bata lura ba

Sumayya ta bude baki zata yi masa sannu da zuwa ya dora yatsansa kan labbansa,gum kuwa tayi shiru,ya bata umarni na gaba da ido alamun ta tashi a hankali ta haye samansu,ba musu kuwa cikin sada ta haura saman,gurbin da sumayyan ta tashi nan ya maye,harda dan jawota ya jinginar jikin gwiwoyinsa,fadila uwar 'yan son jiki kuwa ya jingina abunta harda cewa"yauwa sumayya dama baya na ya gaji,calabar ko ashirin bata kai ba amma taqi tsefuwa ta dadin rai?"baice uffan ba ya kama jelar kitson ya soma tsefe mata kamar yadda yaga sumayyan nayi,ita kuma bata damu da rashin amsawar sumayyan ba ta bayar duk film din ne ya dauki hankalinta,rabi'ah ce ta fito da sauri daga kitchen din don kada tayi missing wani gurin,turus tayi ganin aliyyun a gun da sumayya tasan ta bari,itama yatsan ya dora mata kan lips nashi,yayi mata nuni da ido kan ta koma kitchen,nan ne ma fadilan taga giftawar komawan rabi'an kitchen din "rabi'ah za'a wuce gun da kike son kalla fa" "ina zuwa anty ban qarasa hada miyar bane"

Gaba daya ya shagala,wani irin farinciki ke ratsa shi,santsi kyau da qyallin gashin ya hanashi ganin wahalar tsifar,sai gashi sun kusa gamawa saura guda daya,yana ankare da yadda take bawa film din muhimmanci,murmushi kawai take zubawa hadi da sakw gyara zama,sai da aka zo wani gu da yayi masifar qayatar da ita ta saki murmushi tana cewa "hmmmm......soyayya" ta dan waigo tana cewa"don Allah sumayya basu burgeki ba yadda....."kasaqarasa maganar tayi ganin aliyyu zaune dare dare saman kujerar yaa mata tsifa,to sumayya ce ta rikide ta zama shi ko idanunta ke mata gizo?.......

*Mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 2:12 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ‘‰πŸΌ *PART 3* πŸ‘ˆπŸΌ

1⃣1⃣&1⃣2⃣

Sai da yasa bakinsa ya hure mata idon sannan ta dawo hayyacinta,da hanzari ta miqe sannan kuma a guje tayi sama tamkar wadda taga dodo,binta shima yayi a hanzarce yana kiran ta tsaya,ganin da gaske take ba tsayawa zata yi din ba ya sanya shi cafkota a matattakalar qarshe,cak ya dagata yayi dakinsu rabi'an da take son shigewa,cikin sauri sumayya dake zaune saman dressing chair ta fito ta bar musu dakin

Tsakiyar gado ya direta sai haki suke dukkansu saboda gudun da suka kwasa a step din benan bugu da qari yadda zuciyar kowannensu ke bugawa,sun zubawa junansu ido cirko cirko da su kamar zakaru,a hankali yake hawowa gadon yayin da ta soma ja da baya har ya qureta,suka sake zubawa juna ido,shi nashi na tsantsar so da qaunace da suke sake huruwa cikin zuciyarsa take kuma aika saqonni zuwa sassan jikinsa,yayin da nata kuma na jin haushi tsoro da fargaba ne don bata manta wannan dare ba,kasa jurewa yayi sai da ya miqa hannunsa ya janyota ta fado jikinsa ya matseta gam a qirjinsa

Cikin fusata haushi da mamakin aliyyun ta soma tureshi,saidai ko motsi baiyi ba don qarfin ba daya bane,a hankali ya soma sinsinar wuyanta cikin kunnuwanta zuwa gashin kanta,ya dago fuskarta a hankali ya tura harshensa cikin bakinta,tsotsa yake sosai tamkar wanda ya samu sweet yayin da ita kuma take turje turje hadi da yunqurin tureshi daga jikinta saidai sam ma shi baisan tana yi ba,ganin duk iya qoqarinta ta kasa barin jikinsa sai ta fashe da kuka,hawayen da ya gangaro fuskarta ya taba nashi fuskar shi ya ankarar da shi,ya zare bakinsa daga nashi ba tare daya bari ta bar jikin nasa ba,kukanta take sosai yayin da ya zuba mata ido,gaba daya ya marairaice ya koma kalar tausayi " *fadeelahhhhh*"ya kira sunanta cikin wani irin yanayi tamkar mai rada,da sauri ta dago kanta ta kalleshi don wannan shine karo na farko da ta taba jin sunanta a abakinsa, "fadeelah" ya sake kiran nata ta sake itama kallon nasa "please fadeelah forgive me,I know I hurt you I break your heart,babu wanda ya wuce kuskure,fadeelah I love you more than words can say,I can't do without you,na kamu da soyayyarki,pls kada,pls kada kice zaki hukuntani da tarin laifuffuka na,if bazaki iya yafemin ba ma na amince kiyimin kowanne irin hukunci zan dauka,amma bazan iya jure rashin ki ba"

"Haka aliyyu ya shahara da yaudara?,haka aliyu yake?,taya mutumin da ya qika ya kuma sanar maka bazai taba sonka ba yanzun yace yana sonka?,bazai taba yiwuwa ba it can't"ta fadi hakan cikin zuciyarta tana girgiza kai,tayi wani kukan kura ta shammaceshi ta fusge daga jikinsa,jikinsa ya riga da ya mutu shi yasa ta samu nasarar qwacewar,tana yunqurin sauka shi kuma yana yunqurin sake cafkota aka turo qofar dakin,tuni fadila tayi amfani da wannan damar ta shige toilet "qaniyarka,qaniyarka nace" cewar momi dake watsowa aliyyu daquwa,sunkuyar da kansa yayi qasa yana Tsakiyar gadon da tuni ya bedsheet dinsa ya yamutse,ta qaraso cikin dakin tana riqe da murfin qofar dakin da daya hannun ta nunawa aliyyu waje "zo ka fice ka bawa mutane guri mara kunya,ka keta idanun qannenka ka biyota har kan gadonta" "kai momi kamar ba mata ta ba"ya fadi hakan cikin zuciyarsa yana ficewa daga dakin

Momi ta qarasa bakin qofar toilet din ta qwanqwasa tana cewa "fito" fadilan kanta a sunkuye kunya da takaici na sakadarta ta fito,momin ta dafa kafadarta tace "ko wani bak gaya min ba na sani kina son ali,muma kuma bamu taba fatan aurenku ya rabu ba har a qiyama,munyi hakanne don ya sake sanin darajarki da qimarka ta yadda ko nan gana bazai sake wasarere da lamuranki ba,ki samu yi duk mai yiwuwa ki tabbatar da soyayyarki cikin zuciyarsa kin fahimceni?" Cikin gamsuwa ta gyada kai tana yabawa momin ta yadda son kai bai rufe mata ido ba,bata duba cewa aliyyu danta bane bare ta bari tana gani a cutar da ita ba,qaunar momin da qimarta suka dadu cikin zuciyarta

*_1:30 am_*

Qarfe daya da rabi na talatainin dare fadila na kwance rub da ciki tsakiyar gadon ta,gaba daya ta rasa bacci cikin idanun nata,duk juyin da zatayi qamshin turaren aliyyu take ji daga bakinta har kayan jikinta,har kaya ta sauya amma a banza man kare don bata daina ji din ba,tana kallon yadda su sumayya ke baccinsu hankali kwance sai take jin dama ita dince su,basu da wata damuwa,wayarta dake gefan pillow dinta ta soma haske wanda ke nuna alamun kira ne ke shigowa,cikin mamakinta daga wayra tana duban kiran baquwar numbace,ta zubawa kiran ido har ya katse,ba'a fasa kiran nata ba har sai da ta tashi da missed call bakwai ana takwas dinne ta yanke shawarar dagawa ko wani abunne ya faru,ta danna ok ta kara a kunannta tayi shiru ba tare da tace komai ba

"Bakiyi bacci ba fadeelah?" Ya tambaya cikin wata iriyan sassanyar murya wadda har sai data sanya fadila runtse idanun ta,tana jin qaunarsa na yawo cikin jinin jikinta,shiru tayi masa har ya qara cewa "me ya hanaki yun bacci a irin wannan lokacin fadeelah?" Nan ma shirun ta sake yi masa,saidai ita kadai tasan yadda take ni'imtuwa da jin muryarsa mai tsada "nasan kika jina fadeelah,kuma bana tantama abunda ya hanani bacci shi ya hanaki....,sau da qauna ne ke dawainiya damu baki daya,tunaninki shi ya hanani sakat kamar yadda na san cewa tunani na shi ya hana miki yin bacci,da zaki ganni a yanayin da nake ciki zaki tausayamin,da zan iya ciro zuciyata kiga dumbin qaunar ki da ta cikata fadeelah da nayi,na tabbata da sai kin min addu'ar Allah ya rage min,jin shirun yayi yawa yasa yace "hello,are you there?" Ya duba phone dinshi tana nan bata yi hanging up ba,ya sake maida wayar kunnensa yana cewa "please fadeelah say something ko zan samu relief,am sorry fadeelah and I said it really" tsananin mamaki ne ya mamaye fadila,shin da gaske ne ba mafarki take ba aliyyun ne kuwa?aliyyu salim maitama? Aliyyunta?,mafarkinta na kullum,burin zuciyarta,shike gaya mata wadan nan tsadaddun kalamai?....kalaman da ta dauki tsawon shekaru tana dakon jinsu?irin qaunar da ta jima tana lalubenta daga gun aliyyun,shin da gaske ne a yanzu ta samesu?,eh...yes ta samesu but he didn't deserve ya samu amsarta a arha har irin haka,now its her turned,its her field to play her game.....

Muryarsa ta tsinto cikin sanyi yana cewa"fadeelah I know you gave me happiness and I gave you a reason to cray,u gave me your care and I stabbed you from behind,am sorry for having given you nothing in return for you having given me everything am sorry kiyi haquri....." kasa jure ci gaba da jin kalamansa tayi,tasani ko iya wannan ya isheta,ta samu qauna daga gun aliyyun,ta samu soyayyarshi,ya kawo mata kansa yana begging dinta ta bashi soyayyarta.....,tuni ta katse wayar wani dadi na nuqurqusarta,ta sani tabbas zai kuma gwada kiranta saboda haka ta kashe wayar gaba daya,cikin zaqi da gardin kalaman da aliyu ya kasheta da su bacci yayi awon gaba da ita tamkar dama au take jiran ji,bacci ne mai cike da mafarkan aliyyun a yanayi daban daban,shi kam tsai yayi da wayar a hannunsa cike da al'ajabin yaushi mace ke kashe wa waya?,tabbas ya sake yarda fadilan tana da wani matsayi da babu wata 'ya mace da ta kama koda gefanta

⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Tunda ta kashe wayar bata kunnata ba sai washegari sha daya na safe tana shirin tafiya office sha daya na safe,cikin shadda take pinch sai maiqo take dinkin doguwar riga aka mata,cif cif rigar tayi mata kamar a jikinta aka dinkota,ta bude sosai daga qasa rigar,tana cikin yafa orange mayafinta sumayya na koda kyawun da tayi"wallahi anty kyawunki na daban ne Allah kuwa ba don wai nayi ziga ba,ko bakiyi kwalliya ba kyanki fitowa yake,zanso yaya yaga wannan kwalliyar"

Harararta fadilan tayi"ke dai kin shiga tara,tuni rabi'ah ta dade a school ke kin zauna kanzagi kinqi fita,to bazai ga kwalliyar ba,sumayyan ta qyalqyale da dariya hadda kwanciya saman gadon"wallahi anty kiyi a hankali kada amiki qwace don har yau yayin ya aliyyu ake ba'a dena ba,kullum Allah ne da kullum wallahj dai ya fatattaki 'yammata,kada ki dauka qananu,a'a wlh anty hadaddu masu ji da kansu 'ya'yan manya kuma",fadila ta tabe baki kishi na cin ranta duk datasa haka dinne amma sai tace "dawar wani karkarar wani abincin wani kuma gubar wani"ta dauki wayarta dake gefan sumayyan zata fice sumayyan nata sheqa dariya,text ne taji ya shigo hakan ya sanyata dakatawa daga yunqurin fitar da takeyi,number din da aliyyu ya kirata ne jiya

Tun shidan safe saqon ya shigo "if u can't see the tears in my eyes,I beg you feel the pain in my heart....fadeelah na rantse I will do anything and everything just to take away all d hurt that you feel,please na roqeki give me and let me set thing straight,am sorry once again fadeela and I love you I really love you...."gaba daya ya zare mata dukkan kuzarinta,jikinta ya saki,maimakon fita sai ta koma bakin gado ta zauna,sumayya daketa leqen wayar tana qumshe dariya tace "anty lafiya dai ko?" Ta saki ajiyar zuciya gami da dauke idonta daga kan screen din wayar "lafiya lau me kika gani?"sumayya ta kada kai tana cewa "gani nayi kin shirya zaki fita kin dawo kin zauna,jiya kuma fa anty naga cikin dare baki yi bacci ba ko" hararar fadila ta sake aika mata tana kada kai cikin zuciyarta tana cewa "lallai na yarda ba qaramin illa soyayyar aliyyu ta yimin ba,a fili sai kuma tace "naji to sai kuma akayi yaya?" Ta fada tana ci gaba da jifanta da hararar wasa,miqewa summayan tayi tana ci gaba da qunshe dariyarta tace "k'n,uhmmmm,a'ah anty ni bance komai ba daga wannan,amma dai anty kiyi a hankali saboda yayammu gwarzo ne kuma gwani ne,he is hero,zai iya saaaaaace zuciyarki ba tare da kin sani ba"

Pillow dake kan gadon ta jawo ta jefi sumayyan da shi tana cewa "ban guri mara kunya" gocewa tayi ta fice da gudu tana dariya,sake mai da kanta fadila tayi kan saqon taa sake karantawa,ba shakka aliyyu shu'umi ne,so yake ta qarfi da yaji ya wargaza mata duk wasu makaman yaqinta,ya shirya tunkararta da duk wasu makamansa wanda tana tsammanin indai haka ne mawuyacine ta iya kubuta daga kaifinsu,duk ya kashe mata jiki kamar yadda ya saba ta qarfin tuwo ta gayyato dauriya sannan ta samu ta fita,ta tadda momi da sumayyan a falo,ta yiwa momin sallama,sumayya tace "a dawo lafiya anty.....momi dama inason baki labarin abinda na gani dazu,wata soyayya ake mai fada fada aciki"ya fada tana satar kallon fadila dake qoqarin ficewa daga falon fuskarta dauke da murmushi,a sace fadilan ta watsa mata harara mai nufin gargadi a fakaice ta qarasa ficewa,sumayyan nata qyatunta tace "na fasa anty kada ki hanani kudin ankon"..........

*Mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻✍🏻


[10/16, 2:13 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ‘‰πŸΌ *PART 3* πŸ‘ˆπŸΌ

1⃣3⃣&1⃣4⃣

Qarfe hudu dai dai ta kammala sallar la'asar dinta a masallacin mata da nan cikin gidan radiyon,ta goge kyakkyawar fuskarta da hoda,ta murza dan qaramin turarenta na (asaal brush perfume)wanda bata rabo da shi cikin jakarta saboda dadin qamshinsa gashi kuma qaramine baya da cika guri,ta saba jakarta bisa kafada sannan ta dauki wayarta ta nufi office dinsu don ci gaba da aikin takaddun programme dinta na gobe da ta baro ta taho yin salla

Ta tura qofar ta shiga kasancewar babu kowa ciki fauziyya ta tafi yiwo wani aiki a a ministry of education shi yasa bata damu da yin wani sallama ba,

Taja takardun gabanta bayan ta zauna ta dora daga inda ta tsaya,sosai yanayin tsarin programme din na gobe ke burgeta muhawarar da za'a tafka cikin shirin,lokaci lokaci takan saki murmushi gami da gyada kai,hakanan cikin jikinta ta dinga jin tamkar ana kallonta,cak ta tsaida rubutun,kan ta kai ga yin komai an zuro hannu an zare takaddun,tabi hannun da kallo har zuwa fuskar wanda ya gabatar da aikin,aliyyu ne tsaye qyam a agaban teburin nata,sanye yake da shadda ruwan madara(milk colour) dinkin yarbawa,rigar iyakacinta gwiwa hakanan hannun rigar shima gajere ne iya gwiwar hannu,sai manyan aljihu gefe da gefe,wandon dogo ne,kanshi babu hula sai kyakkyawar sumarshi dake cike da gayu da tsafta,idanunsa na saye da gilashin nan nasa fari qal wanda tana iya hango fararen qwayoyin idanunsa dake zube fes a kanta

Kallonta yake sosai ba tare da yace komai ba,da azama ta miqe hadi da ture kujerar da take kai baya,tasa hannu zata dauki jakarta gami da qoqarin ficewa daga tsakanin table din,taku uku yayi ya tsare mata hanyar ficewar,baya tayi da sauri saboda ganin yadda yayi gab da ita kamar mai shirin fadowa jikinta,ganin ta sake yin baya ya sanya shi sake shigowa cikin shima,da haka har ya danganeta da bango,sosai take jin fitan numfashinsa wanda ke cakude da qamshin turarensa

Ya dage sai ya sanya qwayar idanunsa cikin nata,saidai sam taqi yarda hakan ya faru,lumshe idanunsa yayi gami da nufar bakinta kai tsaye yana mai kwadayin tsotsar tattausan lips dinta,tuni ta gano manufarsa ta sunkuya ta qasan table din ta zille,bai san hakan ya faru ba sai da ya jishi ya dangane da bango,da sauri ya bude idanunshi,can ya hangota har ta dora hannunta kan handle,cikin zafin nama irin na cikakken da namiji ya haura ta saman table din don sai yafi masa sauri,taku hudu ya isa gareta,lokacin tuni har ta sanya qafarta waje

Jawota yayi har sai da ta fado jikinsa uasa hannayensa ya rungumeta,da qarfin tuwo take son qwatar kanta saidai hakan ya gagara,batasan wani yazo gilmawa ya gansun a hakan saboda qimar da take da ita agun dukka ma'aikatan gidan ba zata so hakan ya faru ba,ta kuma kasa bude baki balle tace ya saketa sai kawai hawaye ya balle mata,Allah ya taimaketa sai ua dauketa cak ya dawo da ita cikin office din hadi da murza masa maqulli ya kullesu

Kujera ya janyo ya dora ta akai yana maida numfashi,tsaye ya sake yi a kanta ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa yana sake qare mata kallo kai kace ranar ya soma ganinta,ita kuwa tana zaune sai qananun hawaye take,ya sake taku biyu ya matso gabanta cikin wata iriyar cool voice yace da ita "fadeelah pls stop craying,I can't take it anymore,I know shirun wanda aka ma laifi yake nufi...I know,ki hukuntani kawai fadeelah kimin hukuncin da kike jij shi zai sa temper din da kike ji game da ni zai tafi,zan iya dauka,nasan duka girman laifi na ne ya jawomin,amma fadeelah kinja bakinki kinyi shiru,kinqi cewa komai kwata kwata why?,please(ya hade tafukan hannayensa)ko zagina ne kiyi fadeelah indai zakiyi magana indai kuma hakan shi kadai ne hanyar da zai saki ki huce,ko duka na ne ma kike so kiyi indai shine zai saki ki huce am ready fadeelah"

Ko daga kai ta kalleshi bata yi ba balle yasa ran zata ce wani abun,hakan take masa ko wani lokaci,ya tsani shirun nan nata,yana ci masa tuwo a qwarya,ya fuskanci babu ta yadda za'ayi su fuskanci juna babu ta yadda za'ayi ya samu abinda yake buqata matuqar ya barta taci gaba da yin shirun bayan kullum bai cikin nutsuwarshi duk ta sanadiyyarta....duk ta sanadiyyar qaunar da yake mata,bayan kk yaushe bashi da wani muradi sai nata,ta riga da ta gama kashe masa jiki da qwayoyin sonta da bai taba tsammanin akwai kalarsu a duniyarmu ba,banda time to time yana ganinta da yana tsammanin tuni ya dade da zaucewa,yana tare da ragowar matansa amma ita yake gani,zaici abinci amma sai ua bude hotonta cikin wayarsaa fakaice yana kalla ko da su salima na gun sanna zai samu ya iya ci

A yau dai yaci alwashin ba zaya qyaleta ba sai yaji ta bakinta,bazai barta ba sai anyita ta qare,ya jawo daya kujerar ya zauna a gabanta gwiwarsa na manne da tata,yayi mata kane kane ya hanata ta ko motsa duk lokacin da tayi yunquri sai ya maidata ya zaunar,idanunsa sun kada jajur "I promised ko da yau zamu kwana anan indai bakice komai ba na shiryawa hakan,ni ko ke babu inda wani zaya motsa,u stole my happiness any moment in my life am feeling am lonely,ina jin na rasa komai na rayuwata,why me yasa ba zaki yafemin ba?"

"Na sani I let you down,I made you frown,na sani I dont deserve forgiveness,but I want you to see the depth in my apology just listen to mu heart,it has been torn apart broken,but it still beats for you,ina sonki fadeelah ina sonki!!!.....

"Baka sona! stop saying it aliyyu,already ka riga ka gayamin *baka sona baza ka soni ba ko anan gaba kada nayi tsammanin zaka soni*,ka manta aliyu?..ka manta?,duk wanda yace baya sonka da safe ya dawo da yamma yace yana sonka he does not mean what he said,yana nufin wani abu ne na daban ba son ka ba

Sak yayi yana kallonta,bai taba tsammanin tana da baki har haka ba,but....at least yaji dadi...yaji dadi da yau ta bakinta ya gaya masa wani abu da ta qunshe cikin zuciyarta game da shi,don haka yana ganin dama ce ta samu gareshi,hannayenta ya kamo tana qoqarin zamewa,hakan bai dameshi ba ya riqe hannayen qam qam, "duk abinda kike tuhumata da shi na amince na aikata din,annabimmu ya umarcemu muyi soyayya saisa saisa don zata iya juyewa qiyayya,hakanan ya umarcemu da kada mu zafafa qiyayya don wata rana zata iya zama soyayya,na mance da hakan,na tozarta kyautar da iyayena suka min shi yasa yanzu Allah ke mani hukunci,na manta da cewa *babu wanda yasan gobe sai Allah*,but now fadeelah I identified my mistake,I made so many mistaken,sai dai ki zama mai afuwa yafiya rangwami da sassauci" ta sake zame hannayen nata da sauri ya kama su "I love you.....I love you" "nooooo!" Ta fadi hawaye na zirya a kumatunta, "baka sona aliyyu....bani kake so ba jikina kake soo.....don me yasa da can baka kusance ni ba sai da nayi amfani da wani abun?,don me yasa baka soni ba sai da ka kusanceni?,ina buqatar amsoshin wadan nan tambayoyin aliyu!"ta qarasa fada a dan tsawace wadda kanta bata san ta iya ta ba balle aliyyu da ya zuba mata ido hadi da sakin hannayen ta ba tare da ya sani ba

Kafin yace komai akayi knocking qofar ana fadin "yau kuma me muka samu a office din namu anty fadila ta rufe mana qofa?"cewar fauziyya da yarinyarta dake tayata knocking qofar,kasa motsi fadilan tayi koda na yunqurin goge hawayen ta ne,cikin rashin kuzari ya isa ga qofar ya bude,fauziyya ta kalli fadila da aliyyun tana son tuna inda tasan fuskar,sai ta saki murmushi tana komawa baya "oh...sorry na katse ku ko?,ku gafarceni"ta juya zata wuce tana murmushi"anty fadeelah iman tace a rage kukan nan,duk da ta sani na soyayya ne"aliyu baisan sanda yace "baiwar Allah....don Allah sai ya zama laifi don mutum na tsananin aon matarsa?,don kawai.........

Zumbur tayi tace"ni din ma bance laifi bane"fadilan ta katse shi da sauri,dariya fauziyya ta sake yi ta gyada kai bayan ta gama qare musu kallo"wow,salonsoyayyarku abun sha'awa ne,ya burgeni hakan,well.....koma dai mene ne naga zallar son junanku cikin qwayar idanunku,Allah ya bar soyayya"tayi gaba ta kama hannun iman da tuni tayi gabanta tana ta tsalle tsallenta,ta nufi ofishin da zata kai aikin da taje yi

A sanyaye ya koma gabanta ya tsaya ya zubawa qasan office din ido wanda ke shimfide da terrazzo,a hankali ya saki hannayen nasa,ya tsugunna a gabanta tamkar mai kama ruwa ta yadda zai iya gano fuskarta sosai don kuwa kanta na duqe tana sharar qwalla,"fadeelah" shiru tayi ya sake cewa "fadeelah kin daina sona?" Nan ma shiru "fadeelah kin daina qaunata ko?!" Ya fada cikin dan fusata,a zafafe itama ta mayar masa "amsa kake so kaji?"daga girarsa yayi idanunsa na kanta"yes!" "Na daina sonka bana sonka,kai ada din ma ba sonka nake ba,ban fahimta bane sai yanzu!" Ta fada kanta tsaye ba tare da kawaici ba,lumshe idanunsa yayi yana jin radadin saukar kalaman cikin kunnuwansa kamar ana soka masa mashi,kusan wannan itace kalma mafi muni da yaji wadda ya jima baiji irinta ba,mace ta farko da zuciyarsa ta soma so don radin kanta ta kuma yi mata wani irin kyakkyawar masauki can cikinta tunda Allah ya ginata,irin masaukim da bai taba budewa wata mace koda bakin qofarsa...yau ita ke furata bata sonsa,kalmar da tunda yaje babu wata 'ya mace da ta taba furta masa ita sai ita din,wani daci na kalmar qiyayya da aka gaya masa ke ratsa zuciyarsa

Sai yaga bashi da wani mataki da zai dauka saboda haka itama ta dandani makamancin wannan dacin koma wanda ya fishi,saidai yana son tabbatatwa da kansa da gaskene bata sonsa?,ya bude idanunsa ya zubesu fes a kanta har yanzu kanta na qasa tana share qwalla,"fadeelah!" Ya kirata cikin wata iriyar murya,bata amsa ba hakanan bata kalleshi ba,ta sani babu abunda bai so irin shirun nata "fadeeelahhhh!"ya fada cikim qaraji,bata sanda ta dago kai suka hada ido ba,da sauri tayk qoqarin maida kan nata amma sai ya fita hanzari,da sauri ya riqe habarta ya dago kan nata........

*note*:don Allah masu caccanza numbers na novel dina na roqeku ku dainaπŸ™πŸ»,sai nayi typing sai acanza tsarin number a dinga rikitarmin da makaranta na to gaskiya bana so,idan kuma aka ci gaba to ba shakka zanyi Allah ya isa,sannan na samu wata kuma tana samin number din wayarta cikin typing dina,to itama na roqeta ta bari,idan bata ji ba zan kai qararta gurin Allah,don kuwa yana gaggawar amsa addu'ar wanda aka zalunta,ku barmin novel dina yadda na tsara,kuma kuyi naku ba wanda ya hanaku,Allah yasa mu daceπŸ™πŸ»

*Mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 2:13 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ‘‰πŸΌ *PART 3* πŸ‘ˆπŸΌ

1⃣5⃣&1⃣6⃣

Da sauri ya riqe habarta ya dago kanta,"ki kalli qwayar idona ki gaya min baki sona,I promised zan bace daga rayuwarki kamar yadda kikamin alqawari kema!" Ta sani qwarai aliyyun kaifi daya ne,yana aikata duk abinda ya furta komai tsananinsa,tashin hankali da tsantsar rigima da take hangowa yanzun a qwayar idanun aliyyun ba kadan bane,ko bama haka din ba tana jin ko kanta za'a sanya gabas a dora mata wuqa ba zata iya kallon qwayar idanunsa tace bata sonshi ba,ita kanta ma tasan ta yima kanta qarya koda ta fadi hakan,wannan ma wasa ne

Ko motsi kasawa tayi don tasan abinda yake buqata din ba qaramin girma ke da shi ba a gunta, "uhummm.....am waiting,tell me fadeelah.....tell me baki sona kamar yadda kika fada dazun"shirun dai ta kuma yi din bata da abun cewa,yasa yatsunsa ya sake dago fuskarta ta sosai still dai taqi yarda su hada idanun"fadeelah ni na sani kina sona,kina qaunata,amma me yasa ba zaki yafe min ba?me yasa ba zaki manta komai ba?,if u are nt willing to forgive someone,then you don't truly love them,fadeelah silence the mind and hear the heart,ina sonki fadeelah ina sonki har bansan adadi ba"cikin murya dake nuna alamun karaya ta dago kan nata ba tare da ta dubeshi ba ta dawo da tambayarta ta dazu "na gaya ma baka sona aliyu jikina kake so!" Cikin rudu ya sake kamo hannayen nata da ta sabule ya riqe gam "wa ya gaya miki hakane fadeelah?,who told you?" "Ni na gani da idona,baka soni ba aliyyu sai da kwanta da ni?" Bai son wanna kalmar da taje furtawa

bai san sanda ya zauna dirshan ba qasan office din,"wallahi Allah fadeelah idan ba tare muka fara son juja ba to da kadan kika rigani,wani kurman so nake miki fadeelah ki yarda da ni ba tare da ni kaina na sani ba,zuciyata na sonki ba tare da nasan hakan ba,na sani......kuma na zaci haka dama zaki zaci cewa jikinki nake so,saboda ban tashi sanar dake ina sonki ba sai a wannan gabar,bani da kalmar da zan kare kaina da ita,amm abu daya ne zai tabbatar miki da gaskiya ta,abun kuwa shine....ki amince ki dawo gidana fadeelah wannan shi zaisa ki tantance wanne irin so nake miki,zaki gane za kuma ki fahimci ba wani abu daya nake kwadayi tare da ke ba....a'a....kedin gaba dayanki nake qauna nake so fadeelah,na miki alqawarin baza sake taba koda yatsanki ba har sai kin nutsu kin amince da soyayyar da nake miki

"Fadeelah na sani ni da bakina nace miki bana sonki amma wallahi Allah shine shaida ba haqiqanin abinda ke zuciyata ba kenan,ban taba jin qinki a zuciyata ba dai dai da qwayar zarra,wallahi fadeelah da bana sonki bazan aurenki har na iya zama da ke ba,bana iya zama da abunda zuciyata ke qinsa,mata nawa ke sona?mata nawa aka kawo min a take na qisu?,amma fadeelah na amince na aureki na zauna qarqashin inuwa guda dake.....nake ci daga abincin da hannayenki suka sarrafa shi....nake buri da muradin sha daga abunda hannunki ya hada,nake kuma kwanciya bigire daya dake qarqashin rufin kwanon daki guda"

"Fadeelah.....kalli qwayar idanuna na tabbata sun isa amsa a gareki,ban iya qarya ba fadeelah,amma karo na farko da na fara yinta a rayuwata,na bugi qirji nace bana sonki bayan nasan ba haka bane,nace bazan soki ba koda wata rana ne bayan *bansan gobe ba,ba wanda yasan gobe sai Allah*,gashi yau wata ranar tazo ta riskeni ta qaryatani......kuma nima na qaryata kaina da kaina"yayi shiru idanunsa na kanta yana maida numfashi

Gaba daya ya gama da ita,ya lalata mata dukkanin tunaninta,ya tarwatsa duk wani mummunan tunani zato da tsammani da a da take da shi a kansa,maimakon haka ma sai wata sabuwar qauna da soyayya tasa dake ratsata har jinin jikinta,ahankali take fasa qashi tana malala har zuwa bargonta,jinta take kamar ba'a duniyarmu take ba,abinda ta jima ta jima tana bege da yaqin samu gashi yau a gabanta,yau ga aliyyu zaune dirshan a gabanta,yauga aliyyu zaune ya zamo kalar tausayin a qasan qafafunta,bayan babu abinda ya rasa a rayuwarsa soyayyarta kawai yake nema,aliyyun nan dake bata tsoro,aliyun nan dake da girman kai aji da kuma kwarjini yaushi yake roqon soyayyarta?,to itakam idan bata sallama ba tayi haqurin ai ta yiwa Allah butulci,me take nema dama idan ba wannan din ba?,tasan wasu daga halayensa sarai kamar yadda kowa ya shaideshi bai iya qarya ba....shi din kaifi daya ne da ko gaskiyarsa ba zata faranta maka ba hakan bai dameshi ba

Cikin cool voice da wani irin kunya da nauyi kanta a qas tace "na yafe maka,komai ya wuce "lumshe idanunsa yayi wani sanyi na kwara cikin ransa,ji yake kamar an masa gafara da bushara da aljanna,me yafi so dadi?,me yafi qauna faranta rai?,amma duk da haka yana neman qarin bayani,ya bude idanunsa ya sake matsowa jikin gwiwoyinta,"fadeelah kalmomin da zan miki godiya da su na tabbata sunyi kadan,bani da su saidai na kwatanta yin hakan don bani da abunda zan iya saka miki da shi,na gode na gode Allah ya miki sakamako da aljanna,but I need more fadeelah I need more,please tell me kina sona kina qaunata kuma zaki koma gida na"kafin tace komai aka sake knocking,da sauri ta daga kai ta kalleshi "please ka tashi daga qasa ka koma kan kujera,za'a iya shigowa a ganka a haka fa" ya noqe kafada ko matsawa baiyi ba yana ci gaba da kallonta "no,I don't care ko waye ma zai ganni a haka,a gaban fadeelah ta nake kuma ta cancanci komai har ma fiye da hakan,idan tana sone ma na kwanta ta dinga taka gadon baya na tana tafiya am ready if I can make her happy"dariya ce ta subuce mata tasa tafin hannunta tana qunshe bakin,ya kalli qwayar idanunta da suka sake yin kyau da 'yar ragowar qwalla aciki wadda tasa shi ya koma kamar oily eyes ya dage girarsa "oh,kina tantama ne?,let me show you"tuni ya soma qoqarin ruf da ciki a qasan,batasan lokacin da ta kama hannunshu ba tana qoqarin hanashi ba"no haidar,I trusted you"yabi hannayen nasu da kallo yadda ta riqe masa hannu da tattausan hannunta,ganin yana kallon yadda ta riqe shin sai kunya ta kamata tayj saurin janye hannun hadi da yin qasa da kanta tana murmushi,shima murmushin yake sannan ya nufi bakin qofar ya bude,fauziyya ce har ya dawo tace cikin fara'a "ina fatan kun kammala ban sake katse ku ba karo na biyu duk da takaddu kawai na shigo diba zan wuce gida"yasa hannu ya dauki baby iman dake ta miqa masa hannu taba masa dariya tamkar dama can ta sanshi ya soma mata wasa,baice mata komai ba sai hanya da ya bata yace"bismillah"

Yana ji tana tsokanar fadila haddi da yi mata sallama "yau dai ban sani ba ko anan office din zaku kwana ke da ogan" cikin murmushi ta mayar mata "a haba fauziyya,gida za muyi yanzu muma"ya sauke mata iman hadi da zurawa yarinyar five thousand cikin awarwarayenta dake hannunta,yaro ba wayo sai kallon kudin take gami da qoqarin zarosu tana ganinsu kamar abun wasa ne,yana ta murmushi son yara na dada kamashi,fauziyya ta masa godiya,shi ba ma'abocin son ayi masa godiya bane don yayi kyauta don haka baice komai ba ya dauke kansa ya maida kan fadeelah dake qoqarin miqewa don hada kan komatsanta da niyyar tafiya gida,wani jiri ya debeta duhu ya gilma idanunta tayi baya luuuu zata fadi,cikin zafin nama ya qaraso gareta ya mata kyakkyawan masauki cikin faffadan qirjinsa yace "subhanallah",fauziyya dake yunqurin jan qofar ta dakata gami da juyowa "sannu fadila jirin ne dai?" Da mamaki a fuskarsa ya kalli fauziyyan "dama jiri take yi?"
"Wallahi tunda ta dawo aiki take fama da shi,kullum haka take yi,matuqar tayi dogon zama ko zirga zirga,nayi zaton ma ta gaya maka,don nayi nayi da ita taje taga likita sam taqi,don ko jiya sai da na dan riqeta na wasu mintina sannan ta zama normal"
"Thank you" yace ya maida idanunsa kan fadilan wadda ta sake cusa kanta cikin qirjinsa tana shaqar daddadan qamshin da jikinsa keyi,dadi qamshin ke mata sosau kamar su dawwama ahaka haka take ji,maidata yayi ya zaunar saman kujerar ya hada mata dukkan takardun da take buqata din cikin hand bag dinta ya dauka sannan ya zo ya miqar da ita ya rungumeta ta kafadarsa yadda zasu iya tafiya a hakan

*ku yimin afuwa makarata rashin chargy*πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»

Ganin ya nufi qofa alamun ficewa za suyi ya sanya fadila zaro ido "a haka zamu fita?"
Ya dubeta "yes ko yayi miki kadan na daukeki ne?"
Ta kuma zaro ido cikin marairaicewa tace "no,please ka cika ni ka ban jakar,ai na daina jin jirin zan iya tafiya da qafata"
Girgiza kai shima yayi"no,bazan iya barinki ba,bazan bari kisha wahala ba indai ina tare da ke,ko ki bari mu tafi a haka ko na daukeki gana daya na kaiki har cikin motar"
Ta san halin aliyun kadan ne daga aikinsa,zai iya aikatawa ba tare da yaji ko dar ba,tilas tayi shiru suka fita tana sunne kai

Motarsa taga ya nufa da ita,ta dago da kanta tana ce masa "amma da ka bari tunda a motata na zo sai na koma aciki ko?kada momi ko uncle abba su gammu tare"
Ya tabe baki sannan ya saki dan qaramin murmushi dake qayata fuskarsa "kada su gammu tare?,so what?,ai ni dama haka nake so,kinga daga nan sai su tarkata min mata ta mu koma inda muka fi wayo"murmushi ta saki ta maida kanta don dariya aliyun ya bata,ya bude mata gidan gaba kusa da shi sai da ta shiga ya dan kwantar mata da kujerar ya sumbaci goshinta duk tana kallonshi "ki zauna a haka don bani so a ganemin ke a hanya"murmushi kawai tayi cikin jin kunya,cikin zuciyarta tana cewa"idan banda abun sa wa zaya ganni mota duk baqin glass"ya zagaya nasa bangaren ya bude yana shirin shiga

Wasu 'yammata su uku suka fito daga reception,daya daga cikinsu ta finciko hannun dayar tana nuna mata aliyyu,damar da ta jima tana neman kena taga aliyun don haka ta jawo hannunta ta rakota har bakin qofar motar,yana shirin sanya qafarsa yaji ance "ranka ya dade ya kai kyakkyawa" kusan ha saba jin irin wadannan babatun abakin 'yammata saboda haka bai juyo ba sai da ya shiga motar ya rufe qofar sannan yayi qasa da glass din,fuskarsa a yamutse kamar ya ga kashi yake kallonta,yayin da ita kuma ta harde hannaye ta zuba masa ido tamkar mayya tana zabga murmushin neman shiga "kina da matsala da ni ne?",cikin murmushin tace "yes,babba ma kuwa"aliyu ya fasa kunna motar da yake qoqarin yi da dayan hannun nasa ya dogara hannun jikin murfin motar yana shafa sumarshi hadi da tsareta da ido,ya sani sarai qarya take don yaci karo da mata irinta sunfi dari

Sai yayi mata kwarjini domin shi din ba kalar wasa bane,ba tare da ya sake tambayar tata ba ita da kata cikin diriricewa tace "zuciyata ka sace min ne,kuma na jima ina jiran rana irim wannan da zan sanar da kai"fadila dake kashingide cikin motar kalaman suka shiga kunnuwanta,amma sai taga meye nata tunda ba'asa da ita ba,bari taga ya drama din zata kaya,sake kallonta aliyu yqyi cikin raini "ke! Ki shiga hankalinki,ni ba sa'an wasanki bane,bana son shashancin banza" yaja tsaki yana shirin tada motar ya kunnata ya fara dan janta yana duna inda zaiyi ribas,"ko baka sona ni ina sonka wallahi kuma suna na mansurah"ya leqa kansa ta window "sai ki bada himma ko,stupid" "Iove you idan baka soni ba bazaka hanani in soka ba aliyyu salim kuma sai na aureka na shigo gidanka"zuciyar 'yan maza ta motsa ya tsani mata masu naci irinta haka,niyyarsa ya fice yayi maganinta ta kama hannunsa dariya na shirin subuce mata "haba sonka fa tace tana yi ba qinka ba,masoyi ai yafi maqiyi meye laifinta?" Tana gama fada dariyar ta kubce mata

Qyal qyala dariyarta take sosai,cak ya tsaya yana kallonta,kyawunta ne ya fito sosai,tuni ya mance da wasu ya shagala da kallonta,ita kam bata ma lura ba dariyarta take har da toshe baki,a hankali ya kai yatsansa lobawar nan ta tsakiyar habarta da ta dauki hankalinsa sannan ta farga ita yake kallo,ta yi qoqarin gintse dariyar ta janye fuskarta a kunyace,ajiyar zuciya ya saki kana ya tada motar,tuni ya manta da wata halitta wai ita mansura,fadila ce ma idanunta suka kai gun tayi sakato a tsaye tq zuba musu ido ita mansuran sai lokacin ta kula bashi kadai bane cikin motar,tamkar ta fashe da kuka takaici ya cikata,'yar rakiyar tata kam dariya take ta qyalqyala mata"ai na gaya miki mansura,banda abunki ki duba fa kanki ki dube shi ki dubi kuma wadda suke cikin motar tare,wanda yake da kamar wannan ai baki isheshi kallo ba,ke babu lallaima ko a 'yar aiki ya daukeki indai zaki hada kanki da wada suke tare din nan" ashar ta lailayo ta dirka wa qawar,ita kuwa tayi gaba ta fice abunta

Tuqi yake amma gaba daya kaf hankalinsa na kanta,duk second biyar zuwa goma sai ya juyo ya kalleta,sai daga baya ta lura da hakan "please ka maida kanka gun driving,kaga muna kan titi ne"ta fada idonta na kallon kan titi,gani tayi yayi gefan titi a hankali ya gangara gefan kwalta yayi parking din motar sannan ya kashe ta,ta juyo ta dan dubeshi don bin ba'asin abunda suka tsaya yi din,amma sai ta kasa furta komai saboda wani mayen kallo da yaje binta da shi wanda ya haddasa mata jin wata matsananciyar kunya mai kashe jiki,ya sake raunata mata zuciya da gangar jikinta da wani kurman saqon soyayya mai zafi,bata san sanda ta maidq bayanta jikin kujerar ba ta lafe hadi da langabar da kanta gefen kafadarta hagunta

A hankali yasa hannunsa ya juyo da fuskarta zuwa gareshi, "no,kada kimin rowar fuskarki baby na,barni in more abuna" bata ce komai ba sai dan qaramin murmushi da ta saki wanda ya sake shagaltar da aliyyu,sannu a ahankali ta dora qwayar idanunta cikin nasa tana morewa kallon aliyyun,rana ta farko da hakan ta soma kasancewa tsakaninsu,dukkaninsu kallon so qauna aminci da yarda suke wa junansu

A hankali ya soma motsa labbansa da yakejin suna mishi nauyi still idanun nasa na cikin nata yace "please,tell me kina sina baby nah"ta dan lumshe idanun nata tana jin wani shauqi cikin zuciya da gangar jikinta sannan ta sake budesu ta watsa su cikin idon aliyun "bau wasu kalmomi da zasu iya bayyana abinda nake ji cikin zuciyata, I love you more than I did yesterday,and I will love you more tomorrow than I do today,kai na fara so kuma kai zanci gaba da so har qarshen rayuwata,inaji a jikina an halicceni ne kawai saboda kai" jinsa yake tamkar yana yawo a sararin samaniya,yana jin tamakar su dawwama a gun tana ci gaba da bayyana masa irin qaunar da take masa da sweet voice dinta

Karo na farko da fadeelah taga dariya mai cakude da murmushi cike da nishadi kwance bisa fuskar aliyyun,har yanzu idanun nasu na manne dana juna "is what I see in your eyes true or the mirror?"gyada kai tayi tana mai bashi tabbaci "its true,da gaskene miji na" "really?" Ya sake tambayarta "yes its real"ta amsa masa tana sake bashi tabbaci,hannayenta ya kamo ya matse cikin nasa tafin hannun,"please ina neman alfarma guda daya" gyada kai tayi alamun tana saurarensa,ya sake matsowa kusa da itan har suna shaqar numfashin juna yana murza tattausan tafin hannunta "ina roqonki fadeelah if u reprimand me hug me and give me bliss and let it to be a loving touch,please na roqeki kada ki sake yin nisa da ni,kada ki kuma barina,kada ki kuma raba ruhina da naki,kimin alqawari fadeelah na,are you promised to do it?"ta gyada kai tana murmushi "yes I promise you" "good and I promise you too....I will never do it again,all I want is to see you smile forever not just for a while...." ya rungumeta tsam yana fadin"am sorry I will never hurt you again" "ya wuce wallahi ya wuce,Allah ma muna masa laifi ya yafe mana"

Tsawon mintina yana rungume da ita yaqi sakinta,ita din ma dadin hakan take ji sosai,don ba zata yaudari kanta ba sosai tayi missing soft skin nashi,tayi missing scent nashi masu dadi,kai komai nashi ma tayi missing dinsa,sai gashi lokaci guda Allah ya maido mata da shi da kuma abunda bata taba tsammanin ba ma,duk da ta sani addu'a bata faduwa qasa banza dama,kuma lallai wani jinkirin alkhairi ne,sai da taga lokaci na qoqarin qwace musu gashi bai da niyyar sakinta bare ya tada motar su tafi "lokaci na tafiya fa,kada momy taga ban dawo on time ba"ya dagota yana kallonta"sai kice mata kin sha'afa ne kina tare da lovely husband dinki"ta rufe fuskarta da tafin hannunta "momin zan cema haka?"ya dage girarsa "yes kinga sai tace tattara kayanki kibi mijinki,kinga fine komai yayi kyau ko?",sai ta maida jikinta kan kujerarta tana murmushi qasa qasa,qamshin turarensa da ya manne a mayafinta yana sake yi mata dadi tamkar yau ta sanshi

Kusan sai da suka tsaya sau kusan uku kafin sukai gida,kallonta yake ne yaqi maida kanshi yayi tuqin,idan tayi masa qorafin hakan sai ya yace "gaskiya gaskiya bazai iya tuqi baya kallonta ba,saidai a haqura da tuqin idan ya gama kallon nata sa tafi,lokacin da suka isa gida tuni anata tada iqama,tana qoqarin ficewa daga motar ya kamo hannayenta,ta dan fiddo da idanunta tana kallonsa,ta shagwabe fuska kamar zata yi masa kuka " please ka sakemin hannu muna cikim gida ne fa yanzun,it can be possible wani ya fito ya gan mu a....." kanta qarasa tuni ya janyota jikinsa daidai lokacin uncle abba ya fito daga cikin gidan hannunsa dauke da carbi da alamu masallaci zashi

Sarai ya gansu amma sai ya dauke kai tamkar bai kula da su agun ba,farinciki yaji sosai cikin zuciyarsa "alhamdulillah"kawai yaje fadi cikin ransa,bisa dukkan alamu sun sasanta kansu kenan,yanzu yake ji a zuciyarsa zai iya maida fadilan gidan aliyyu,don duka alamu sun nuna na qauna da soyayyar da suke ma juna,fadila ce ta soma ganin abban lokacin har ya basu baya,ta zare jikinta da sauri tana gyara yafen mayafinta zuciyarta na bugawa tace "innalillahi" aliyu ya kalleta"lafiya baby?"
Uncle abba ta nuna masa da yatsa tuni idanunta suka cicciko da qwalla "ya ganmu wallahi,sai da nace ka bari ka bari fa"

Dariya ya saki cikin nishadi "to mene ne?,kinga addu'ata ta karbu kenan,kuma ma baby naga da mijinki ya ganki fa mene na rudewa har irin haka?" Ya jawo hannunta yana goge mata qwallar da ta soma gangaro mata "calm down my unique,don't cry again,kin gama kuka a duniya ai matuqar ina tare da ke,I will never let your tears to fall down again.....muje ma raka ki ciki"sai taga tunda abba ma ya riga ya gansu a dazun don rakata ma cikin gida ba komai bane,abun kunyar dai an riga an gama tafka shi,tayi tayi da shi ya bata jakarta ta riqe yaqi yace sai ya kaita har ciki,sai da yace idan ma ta fiya matsawa zai goyata ne ya kaita har cikin gidan,tasan kadan ne daga aikinsa,tilas ta bar masa tayi gaba yana take mata baya......

*Mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“šπŸ“šπŸ“˜πŸ“˜✍🏻✍🏻
[10/16, 2:15 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ‘‰πŸΌ *PART 3* πŸ‘ˆπŸΌ

1⃣9⃣&2⃣0⃣

Ai kuwa sukayi kyakkyawan gani cikin parlour,momi ce da iftihal dukkansu suna zaune kan kujera sanye da hijabi da alama sallah suka idar,karatun qur'ani iftihal keyi da ka momi na gyara mata kura kurenta,kallo momin ta bisu da shi daga bisani sai kuma ta dauke kanta tamkar bata gansu ba,ya miqawa fadila jakarta da take ta Allah Allah ta bar falon kunya gaba daya ta rufeta,gogan harda hadawa da hannunta lokacin da zai miqa matan,ta zame hannun nata da sauri ta haye sama inda dakinsu yake,ya wani bita da kallo ko kunya baiji ba,sai da ta qare hawa sannan ya janye idonsa ya juya da niyyar gaida momi

Ashe idanunta na kansa take suka hada ido,sai yaji wata kunya ta kamashi,yasa tsinin key din motarsa yana sosa tsakiyar kansa irin najin kunya,yakoma gefe ya tsugunna yana gaidata yayin da tuni iftihal tayo qaura gurinsa,maimakon momin ta amsa sai tace "rasa kunya beran tanka,tashi ka bani guri,kada na kuma ganin kana takura mata daga yau,na gaya maka ka qyaleta tayi hukunci da qashin kanta,idan ba haka ba tamu ce ni da kai"ya miqe yana murmushi lokacin da yake maida iftihal kan kujerar kusa da momin,abinka da wanda bai iya qarya ba sai yace "momi ba takura mata nake ba,ai tama gama yanke hukuncin,mun gama magana da ita momi"baki sake ta bishi da kallo lokacin da ga fara tattaki zai bar falon "iye?,me kace?" 
"A'ah momi bari inje nayi sallah"shima ya fada yana waiwayo wa gami da sakin dariya wa momin har ta fice
"Ja'iri ka maida ni kakar ka ko?"
"Momi ai dama kakarsa ce ke"inji iftihal dake faman wasa da bezar hijabinta,duk sai suka bata dariya 'yar da uban,cikin zuciyarta tqna addu'ar Allah ya daidaita ya sake tsakaninsu

Kowa ya hallara a dining har aliyyu da yaqi tafiya amma qememe fadila taqi saukowa,ita kam ba zata iya ba,bala'in kunyarsu abban take ji don aliyyu ya gama kunya tata,kuma ta sani ko da ta sauko din tunda aliyun na gun ta tabbata sai ya sake kunyatata kafin a tashi,haka abban yace a qyaleta don yasan me take yiwa kunyar,sam sai yaji abincin bai masa dadi don mafi rinjayen zaman cin abincin nasa saboda ita ne,suna tsaka da cin abincin ya soma tari kamar ya qware,sai yaqi daukan ruwan dake kan table din yayi hanyar kitchen su abba na masu sannu,ganin idon kowa bai kanshi sai kawai ya haye matattakalar sadaf sadaf yayi sama,momin ce ta soma ganoshi ta dan tabo uncle abba yadda su sumayya ba zasu gani ba ta nuna masa aliyyun,dariya uncle abban ya saki shida momin duka,

Tana zaune dirshan tsakiyar gadon,gabanta system ce a bude tana faman aiki cikinta,doguwar rigar yellow din material mai santsi ce a jikinta,mai tankakken hannu ne dinkin ,babu abinda ta shafa illa man lebe da ya qarawa lips dinta taushi,sai jikinta dake tashin qamshin turaren asaal,kyakkaywan gashinta baqi sidik mai tsawo da qyalli yasha gayara ta tajeshi ta daure shi da qaramin ribbon yellow ya sauka gadon bayanta yana reto,hundred percent hankalinta na kan system din,alewar mints ce a bakinta tana tsotsa a hankali,sai da ya gama qare mata kallo iya son ranshi "unique lady"ya fada cikin ransa,komai nata mai aji ne,yanayin zaman nata bisa gadon sai ya zamewa aliyyu abun sha'awa,lallabawa yayi ya haye gadon ta bayanta,sai jinta kawai tayi rungume jikin mutum,a dan firgice ta waiwayo ya manna mata kiss a goshinta tare da sakin murmushi"me yasa kika qi saukowa kici abinci bayan kin sani bazan iya tafiya ba tare da na kalli wannan kyakkyawar fuskar taki ba"ya qarashe maganar yana shafa gashinta da ya qayatar da shi

Zumburo baki tayi kamar na shagwababbun yara tana dan kici kicin qwace kanta "haba mana dear dakinsu sumayya ne fa,suna iya shigowa su ganmu"daga hannunwansa yayi yana murmushiπŸ€—"is ok,indai so kike na qyaleki sai idan kin yarda zaki bani hot kisses a matsayin sallamarmu ta yau"sak tayi ta kuma yo kicin kicin da fuska,murmushinsa ya dadu yace "uhm,am waiting dear"nan ma shiru,ya dora kansa saman kafadarta yana leqen fuskarta,saura kadan ya fashe da dariya yadda yaga tana zare idanu,ta gintse dariyar yaba cewa "don't mind dear,if you are not ready kinga sai muyi zaman mu a haka ko?"da sauri ta noqe kafada "no am ready,but.....Please ja rufe idanunka" "ok....ok" ya fadi yana cikata gamida rufe idanun

Shiru yaji hadi da qarar qofa,da sauri ya bude Idanun nasa,ta qarasa sa key din qofar toilet tana qyakqyala masa dariya,sai ya harde hannayensa ya zubawa qofar ido fuskar sa qunshe da murmushi"no baby,kin karya agreement,kisses sun qara nukuwa,sun zama double yanzu,ko ki fito ki bani ko in kunce gidan key din yanzun nan in shigo toilet din"dariyarnan tata mai saurin shagaltar da shi taci gaba da yi

Sai da taji sukur sukur dinshi jikin qofar sannan ya sata nude qofar da sauri,wayo dama ya mata ba wani gidan muqulli da zai kwance,ya cafkota ta fado jikinsa suna dariya,dariyar tasu ta tsaya lokacin da wayarsa ta soma ruri,ya cirota daga aljihunsa yana dubawa,salima ke kira don itace da girki dama yau zata fita,ya kara a kunnensa,da qorafi ta fara masa kafin sallama, "ok gani nan"kawai yace mata ya maida wayar aljihun,fadila tayi lamo jikinsa kishi na sukarta,ya dago fuskarta yana kallo sai yaga alamun ta dan canza,yasan dalilin hakan saboda haka dadi ne ya kamashi don yasan abunda ake so ake kishi, "oya babe,give me"ya fadi yana sake dago fuskarta gareshi,wani hot kisses ta soma bashi wanda ita kanta bata san ta iyasu ba sai yau,sosai ta rudashi har suka gagara tsaiwa suka zube saman carpet,shigowar rabi'ah da komawarta da baya da sauri shi yasa fadila saurin zare jikinta,a kasalance ya maida idanunsa kanta,kanta a qasa tana tattare gashinta da ya yamutse tana maida shi cikin ribbon,ya sake maida idonsa bakin qofa inda rabi'ah ke tsaye a bayan labulan ta yadda yanzun bata iya hangosu "yaya,momi ce ke kiranka" "bace min a gun stupid kawai,baki iya sallama ba zaki shigowa mutane daki kai tsaye?"

Sum sum ta juya tana tabe baki cikin ranta tana cewa "sallamar miliyan nawa kakeso nayi muku ,ka shiga wannan yanayin koda ganga nake sallama taya za'ayi kaji,su yaya aliyyu ashe haka aka iya soyayya?" Sai ta qyalqyale da dariya ita kadai,yasa yatsunsa ya dago da fuskarta yana son kallon qwayar idonta amma taqi yarda "I need more please..."ya fadi muryarshi qasa qasa tamkar mai rada,tuni ta shagwabe fuska tana cewa "please.....Please,na yima fa,kuma momi ke jiranka fa ma"ya yunqura ya miqe yana gyara botiran rigarshi da suka balle yana cewa "ok"sai da ya gama ya miqa mata hannunsa har lokacin tana zaune kanta a qasa "oya get up"a hankali ta dora hannunta saman nashi ya dagata,sai jirin nata ya kwasheta tuni ya riqeta don kada ta sha qasa "fadeela I think you are not well" 
"am well"
"A'ah,ki shirya gobe zan daukeki ta office in kaiki kiga likita" 
"Amma....ai zan...."ya tsansa ya dora kan lips dinsa "shshshsh...kada kice komai"shirun tayi ya leqa fuskarta "zaki rakani gun momi muyi sallama?"girgiza kanta tayi "um um"yayi murmushi "shikenan to kwanta abinki"ya zaunar da ita gefan gadon,system din ya fara kashe mata ya maida mata ita saman madubi,ya dawo inda take yana kallonta ya kama hannunta ya sumbaci sama yana cewa "good night my dear baby na,sweet dreams,I love you"a hankali ya bude bakinta tace "I love you too my dear *haidar*"farinciki ya cikashi kamar ya taka rawa,tuni saboda kunya ta cusa kanta qasan pillow tana murmushi har ya fice

Momin kawai ya tadda a parlour din yanzun ma ita da iftihal dake shimfide kan cinyarta tana baccinta abunta,a yatsine momin ta kalleshi "sannunka kaji?" Murmushi kawai yayi idanunsa na kan 'yar diyarshi,ya shafa kan iftihal din "ayi haquri momi zan tafi sai da safe" "kada naga qafarka da safe a gidan nan" da sauri ya dawo da baya ya taugunna gaban momin "yauwa momi na,Allah indai kika bani fadeelah ta ba zaki kuma gani na da sassafe a gidan nan ba,saima kin aika a nemo miki ni" dariya taso qwace mata amma sai ta kaba habarta yana cewa "o'o'o,sannu mara kunya,to anqi din har sai ta yarda da kanta" ya kama qafar momin yace "wallahi momi fadeelah ta haqura" ta dake dariyar dake cinta "kaga,mu bata gaya mana ba yallabai sai ka jira har sai ta gaya mana da kanta"ya marairaice "momi kunya fa kinsan take ji,ba zata iya gaya muku ba"momin ta tabe baki "ok,sai kai wato rasa kunga shine kazo kayi rashe rashe a gabana kake gaya min ko,don Allah tashi ka tafi gidanka ni na gaji da ganinka anan"

Kai yake gyadawa kamar qadangare "shikenan momi,shikenan sai da safe"ya miqe ya fice cikin zuciyarsa yana fadin "zan shuka tsiya kawai,komai ta fanjama fanjan,su momi basu yanda nake ji bane"uncle abba dake can tsaye yana kallonsu yqna shan dariyarsa ba tare da sun sani ba ya qaraso "haba maimunatu,ayi haquri haka nan a bashi matarsa,tunda sun sasanta kansu,ni kam na fara tausaya masa,kinsan ciwon da namiji ma na da namiji ne"ya qarashe fada cikin zolaya,dariya uncle abban ya bata sosai"shikenan tunda abun wariyar launin fata ce nima ai ciwon 'ya mace na 'ya mace ne,sai na gyara diyata nima,idan yana so jibi ko gata sai a bashi ba don halinsa ba"

Ya sunkuya yana qoqarin dauke mata iftihal daga kan cinyarta "mudai tunda za'a bamun ai shikenan godiya muke,bari in dauke miki amaryar taki,kije ki huta kema"ta saki murmushi tana cewa "godiya nake abba"ta miqe tabi bayansa tana barwa sumayya da rabi'ah dake kitchen auna wanke kwanukan da aka bata don basa barin wanke wanke ya kwana sallahun idan sun gama su kashe duk qwaya qwayai da kayan electronic na parlour da kitchen din

Tunda ya zaunar da ita a gun ta bingire ta kwanta saboda kasala,juyi kawai take tana tariyar abinda ya farun a wunin gau gana daya tsakaninsu,babuabunda take saki sai murmushi,shi din ma koda ya fito daga wanka kasa hasala komai yayi,sai da ya zauna gefan gado ya dauki wayarsa ya kirata,tana tsaka da juyin nata ne kiran ya shigo mata,ta gyara kwanciyarta hadi da rungume pillow sannan ta amsa,sallama ta masa da muryarta mai sanyi wadda ke saka susuta shi "fadeelah bazan iya bacci ba sai naji muryarki"
"But...."sai kuma tayi shiru
"But what?,pls gaya min abu daya wanda zai sani samun nutsuwa idan nazo baccina"
numfashi ta ja sosai sannan tace"i love you for all that you are,all that you have been,and all you're to be my haidar"kalaman sun tsaru sosai cikin kunne da zuciyarsa,ta kashe masa jiki da zaqin kalamansa,idanunsa na a lumshe yace "are you sure babe?" "Yes am sure,duk abinda na fada I mean it"dogon sumba ta bashi a wayar sanna ta kashe tana murmushi qasa qasa,shi kuwa mutuwar zaune yayi gaba daya tsigar jikinsa ta zuba..........

*Mrs muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“šπŸ“šπŸ“˜πŸ“˜✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 2:16 PM] πŸ’πŸ¬πŸ›SalmaπŸ›πŸ¬πŸ’: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ‘‰πŸΌ *PART 3* πŸ‘ˆπŸΌ

2⃣1⃣&2⃣1⃣

Shi kuwa mutuwar zaune yayi gaba daya tsigar jikinsa ta zuba

⚜⚜⚜⚜⚜

Zaune take a nutse cikin office din,sanye take da shadda dinkin riga da zani rapper marun,sosai shigar ta yi mata kyau matuqa ta kuma dace da fatarta,hakanan take kullum ba dai tayi kwalliya a kushe ba,ta iya dressing sosai,hannunta dan madaidaicin cup ne cike da coffee tana dan kurba kadan kadan don babu abinda ta iya ci tunda gari ya waye,gaba daya hankalinta na gun aliyu tunaninsa take,amma idan ka kalleta a zahiri qata news paper dake gefan hannunta ta zubawa ido tamkar mai nazarin wani abu a cikinta

Yafi minti goma a atsaye bakin qofa,sam baya gajiya da kallonta,baiqi su dawwama a haka ba,tsarin shigar tata yayi masifar tafiya da shi tayi wani das tamkar fure,sai kuma aka taki sa'a shi din ma marun din shaddar ce a jikinsa

Har ya iso bata ankara ba,a hankali yasa hannu ya zare cup din coffeen dake tsakiyar tafukan hannayenta "irin wannan zurfi a tunani bai dace da kyakkyawa ba" ya fadi yana maida cup din gefe,yaja kujerar dake opposite dinta ya zauna yana cewa "nasan dai ji kike tunani ko....to gani na iso ai sai abar hasashe a koma zahiri"murmushi ta saki a kunyace tayi qasa da kanta,ya sake binta da mayun idanun nan nasa,gani yake tamkar kullum wayewar garin Allah kyau ake dada mata,ya jawo tattusan hannunta dake zube saman table din yana matsawa,ji tayi kamar wani sinadari yake zubamata cikin jikinta,ta soma qoqarin zame hannunta tun kafin yayi mata illa cikin kunya "no baby,your hand fits in mine like its made just for me,kada ki cire"

Ta dan zame dag kan kujerar ta gaidashi,noqe kafada yayi "naqi,ni ban irin wannn gaisuwar nake so ba,let me show you irin wadda nake so"kafin tace komai ya zagayoda ita zuwa inda yake zaune yayi mata mazauni kan cinyarsa,qam ya matseta,sai da ya yamutsata son ransa sannan yace "irin wannn gaisuwar nake so ko a ina muke right?"gyada ka tayi cikin jin nauyinsa,ta bishi ne da haka amma itakam rashin kunyar aliyyun tafi qarfinta "a'ah dear,ki daina min rowar sweet voice dinki,ki dinga bude baki kina magana sannan ki dinga bude idanunki sosai kina kallona,zuciyarmu ta riga ta zama daya....dubi"ya fadi yana juna mata dressing din da suka yi "baki san me zansa ba nima bansan me zaki sa ba amma saboda zuciyarmu na manne da juna mukayi shiga iri guda"

Murmushi ta saki tana kwantar da kanta a kafadarsa,"ok,I hope kin shirya,don daga nan sai asibiti,gwara muje kiga doctor sa'adah"ya fadi yana sunkutarta kamar wata bebin roba,wutsil wutsil ta soma yi da qafafunta "please my haidar,zan iya tafiya kada ka fita da ni a haka"dariya taga ya saka,ta dan saci kallonsa don bata taba ganin dariyar tasa haka ba,ya maimaita abinda tace cikin kwaikwayar muryarta sannan ya direta "matsoraciya,dama tsokanarki nake"duk da haka bai qyaleta ba sai da ya kamo hannuwanta,a haka suka isa bakin motar,ya bude mata ta shiga sannan shima ya shiga

Ko a office sai da doctor sa'adah tayi masa wayo koreshi waje da qyar don ya hana fadila sakat ,kunyar doctor din fadilan keji shikam ko a jikinshi,da zarar fadilan ta bude baki zatayi magana sai yayi sauri ya rigata cewa "doctor rabu da ita,awo na kawo miki ita,na jefa qwallo a raga" mamaki da kunya suka kama fadila haka aliyyun yake?,tamkar ba wannan aliyyun nata ba,ita kanta doctor sa'adah din tayi mamakin yadda ya sake yana ta raha har irin haka kamar ba aliyu salim maitama ba,mintina talatin doctor sa'adah ta gama duk wani bincike da gwaje gwajenta,madaukakiyar fara'a da farinciki da ta gani kan fuskar doctor din shi ya bata mamaki "congratulations fadila,naji dadi da ya zamo nice ta farko da zan taya ki murna,Allah ya albarkaceki da samun juna biyu"ta fadi tana sanya tafin hannunta cikin na fadilan

Sak fadilan tayi tanajin kunnuwanta kamar basu ji mata dai dai ba,ciki gareta da gaske?,cikin aliyyu a jikinta?,aliyyu masoyinta?, *alhamdulilahil lazi bini'imatihi tatimus salihaat*,wannan baiwa da ni'ima ta Allah da me tayi kama?,Allah kenan mai kyauta da qari,buwayi gagara misali,mai azurta bawa a duk sanda ya so,mai amsa addu'ar bayinsa,yau ga aliyyun Allah ya bata kuma ya bata dan aliyyun cikin cikinta,ya zabeta cikin matansa yace ita zata haifa,batasan lokacin da hawayen farinciki suka balle mata ba,a hankali bakinta ya soma salati ga fiyayyen halitta,sannan ta dora da godiya ga ubangiji, "na godewa Allah gwanin iyawa,doctor pls bana son ki sanar da aliyu batun cikin nan yanzu,nasan bazai iya shiru ba sai kowa ma ya ji,kuma....."

Dai dai nan aliyyu ya turo qofa ya shigo,da sauri ya qaraso a rude ganin hawaye kan fuskar fadilan,dagota yayi ya rungume yana goge mat fuskan"me ya faru ?,doctor me kika yiwa mata ta?"ya fadi cikin hade rai,dariya sa'adah tayi "farinciki ne yayiwa matarka yawa,don ance lafiyarta qalau shine don shagwaba take kuka"ta miqa masa takardar magunguna "wadan nan zata dinga sha,but gaba buqatar hutu da kulawa sosai,idan an gama lallashin ku rufe min qofar office din sir,zani inyi round na marasa lafiya,ta sanya lab coat ta fice tana musu dariya"

Ko cikin motar kanta na langabe ne jikin sit,gaba daya jikinta yayi sanyi,sai ta ruda aliyyun gaba daya ya kasa driving din dole yayi parking din motar yana tambayarta,murmushi ta saki"am fine my haidar" duk da haka sai da ya sanyata cikin jikinsa sannan ya samu ya iya ci gaba da tuqin,ga zatonta zai maidata ne gurin aiki amma sai taga yayi nassarawa da ita,cikin rashin fahimta take dubansa "nayi zaton zaka maida ni ne office ko tunda ban tashi ba"ya girgiza kai "no fadeelah,yau gidammu zamu koma"
da sauri ta dubeshi "gida haidar?,bada izinin su uncle abba ba?"
"Shshshshsh!" Yace "nafi kowa iko da ke fadeelah,na gaji da rashinki,na qosa kiyi haquri kawai idan naje gidan ni zan sanar musu,zan fahimtar da su ba laifinki bane,bare ma ba zasu ce komai ba I know"
Ta zumburo zata sake magana "tuni ya sanya bakinsa cikin nata ya hanata cewa komai,saura kadan sitiyarin ya kubce masa Allah ya taqaita ya kamo shi

Da kanshi ya bude mata part din nata don babu key din a a lokacin a hannunta,sai zumbure zumbure take ita a dole fushi takeyi da shi,shi kam dariyarsa ma yake lokaci lokaci,bai damu ba tunda burinsa ya cika,fridge ya nufa ya ciro ruwa duk da babu sanyi kasancewar wutar bangaren a kashe take,ya jawo gabanta ya durqusa,ya jawo ledar magungunan ya ballo mata,ya bude gorar ruwan sannan ya kalleta "haa" yace da ita,shiru ta masa sai da ya sake cewa "bude bakinki"nan ma tayi shiru,sai ya dire ruwa da maganin kan center ya miqe yana shirin core rigarsa yana cewa "tunda kin zama kurma inada muqullin bude bakinki" a razane ta dubeshi,bata san lokacin da tace "me zaka yimin?"yadda ta razanar da kuma yanayin yadda tayi maganar shi ya bashi dariya,ya tuntsure da dariyarsa yana maida rigarsa da ya soma cirewa har fara qal din vest dinsa ta soma bayyana,ya koma gabanta ya tsugunna yana cewa "ashe dai matsoraciya ce,baki shirya fadan ba amma kika takaloshi,oya bude bakin"bata ko sake musawa ba ta bude ya sanya mata magun gunan sannan yasa maya ruwan a baki har sai da ta hadiye

Ya miqe ya cire mata mayafin da dankwalinta,ya zare mat sarqa da dan kunneta duk tana kallonsa,ya debe qafafunta ya maida saman kujera ya dora mata pillow sanann ya harde hannayensa a qirjinsa yana duba agogon dake manne a bango "oya,maza kwanta kiyi bacci ko na one hour ne don maganin yafi saurin bin jikinki,after one hour sai ki tashi kiyi sallah ok?" Cikin shagwaba wadd ta ruda aliyun tace"amma dai kasan ban kyauta ba ace daga zuwa gun aiki ace na dawo gida na ko?"sauje hannun nasa yayi ya dawo gaban kujer ya tsugunna har yana jingina gwiwoyinsa jikin kujerar,ya koma serious sosai,yasanya tafin hannunta cikin nasa,sosai ya sa qwayar idonsa atata "fadeelah" kallon cikin idonsa tayi,yadda taga ya zama serious hakan yasa ta bawa maganar tasa muhimmanci "duk duniya babu mai haqqi a kanki daya kaini,bana so ki dinga sawa ranki damuwa kan binda yake mai sauqi ne,su momi sun ajjiyeki ne don ku sasanta kanmu da kanmu ba tare da kowa ya shiga ciki ba,sannan ni na sake gane kuskure na,to yadda suke so din duk ya faru,me kuma ya rage?uumm?,sai mu dawo gidan mu fadeelah mu shimfida sabuwar rayuwar auratayya wadda zata kuma farantawa iyayemmu rai,ina kuma fatan zan samu goyon baya daga gareki?"

Sosai take gyada kai "insha Allah mijina,na yi maka wannan alqawarin" ta dam zamo daga saman kujerar ta durqusa itama a gabansa "ka yimin afuwa ranka ya baci,ya saki qayataccen murmushi "ba komai baby na,bakya taba yin laifi a guna"ya sumbaceta sanna ya maidata ya kwantar saman kujerar,"kiyi bacci sosai,banda cewa zaki tashi kiyi aiki,gidanki babu dattin komai,don kullum sai na share miki shi"tana daga kwancen ta qwalalo ido "shara?kuma da kanka?"murmushi ya kuma saki"kina mamaki ne?,kinfi gaban haka,mene ke baki bani ba a rayuwarki fadeelah?"itama murmushin tayi "haqqina ne ai In maka har fiye da hakan" "jiniina kai yayi cikin zuciyarsa yana godewa Allah,babu shakka yayi gamo da katar da mace ta gari,wanda samuntabke matuqar wuya a wagga zamani "ina sonki my baby fadeelah har bansan adadi ba,ina alfahari dake,ina alfahari da kasancewarki cikin rayuwata"ta rufe fuskarta da tafin hannunta "ina sonka haidar dear,nima kuma ina alfahari da kasancewar ka miji a gareni har abada"wani dadi yaji ya kama shi,ya sake sumbatar bayan hannun nata yave "na gidewa Allah fadeelah,sai na dawo,zansa nasiru ya kawo miki motarki ,sannan zan daukar miki excuse gurin aiki su baki hutu na sati"bata ce komai ba don bata son ta kasance mai yawan musu da shi,bare itama zata so hakan,don tana buqatqr lokaci da zatayi wasu 'yan gyare gyare,sabida haka kai kawai ta gyada masa tana satar kallonsa ta tsakanin yatsunta har ya fice,wani annushuwa da farinciki da kwanciyar hankali mara misali taji yana ratsata

Ta janyo wayarta ta nemo number din farida,bugu daya ta dauka tamkar dama tana jiranta ne,cikin ihu take cewa "yeyyyyyy sister yaushe kuka dawo haka babu labari?"cikin murmushi fadeelah ke cewa "wayyo Allah zaki kashemin dodon kunne mana,cikin satin nan ne,kiraki nayi dama nace miki ki turo min mai gyaran jikin nan don Allah"wani ihu faridan ta sake saki cikin dariya "kai mutuniyata,wallahi da labari,tafiya tayi kyau mune winners ko?" "Kai....faridaaaa....sai yaushe zaki girma ne don Allah?" Tayi qasa da murya "kai sister,rowar story zaki mun kenan don Allah?"dariya ta bawa fadilan don tasan farida akwai son jin tsurku "hab abokin kuka ai ba'a boye masa mutuwa,zaki sha labari har sai kin gaji kin toshe kunnuwanki" "a'ah nasan halinki fa sister,zaki dai bani wanda kika ga dama,yanzu zan mata waya na gaya mata"tayi dariya "yauwa ko da yamma ne sai tazo,sau nake ta fara yimin yau don gaskiya nag ta iya" "kai sister sosai ma,ko sau daya fa ta miki sai kinga kin canza gaba daya,akinta da kyau sai tsada,bayan gyaran jiki har kitso da qunshi ma ta iya sosai" 
"to yayi,ina humairata,Allah sarki aishana,nayi missing dinta a lot" 
"Yanzu babanta ya fita da ita sitting room yayi baqi"hamma ta kubcewa fadilan har sai da faridan taji "idan sun shigo kice ina gaidasu ita da abban nata,ni zan kwanta"
Dariya farida ta saka "tabdi lallai sister,kai saidai na zo kawai" 
Katse wayar fadila tayi taba murmushi don tasan halin farida bata qi su kwana suna abu guda ba.........

*Mrs muhammad ce*πŸ‘‘

[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah AbdulmajeedπŸ’ž: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


             *PART 3*


             2⃣1⃣


Doctor sa'adah ta kammala rubuce rubucenta,ta dago ta kalli aliyyu "masu qaramin ciki kamar hakan suna buqatar daga qafa adinga sassauta mata gaskiya"
Zaro ido yayi kamar yaro"what?!,su waye Duke da ciki?"cikin mamaki ta sake dubanshi "oh,baka sani ba.....anyway kaji a bakinta,ga magunguna nan ,ba za'a yi birede a gaba na ba,idan kun tafi nurse zata zo ta kulle qofa"tayi haka ne don tasan za'ayi budurin yadda tasan alin da son yara na masifa

A hankali ya duqa gabanta "da gaskene Fadeelah kina da ciki?"cikin jin kunya ta gyada kai,sai ya hade fuska tsam,ciki tsawa tace"don me yasa zaki boyemin kyautar da Allah yayi min?shin ban can can ci in sani bane?"
A Dan tsorace ta kalleshi,sai Kuma taga ya rungumeta "am sorry dear,banji dadi bane da kika boyemin,kunya Daren jita na cutar da ke,da wa ni Abu ya faru daku keda baby na bazan yafewa kaina ba Fadeelah,bazan gaji da roqamiki rahamar Allah ba,bazan gaji da roqarmiki albarkar ubangiji ba,ke din wa ni alkhairi ce a tartare da ni ,bani d halin da zan miki godiya don tayi kadan,bansan da me zan saka miki da shi ba fadeelah,Abu day dai da na sani kin zama mahadin rayuwata Fadeelah,na tabbatar idan babu ke rayuwata bata da amfani"

Ga mamakinta sai taji ya fashe da kuka sosai,tabbas rabo ajali,rabo ne mai zafi ashe tsakaninsa da fadilan,hawayene sosai ke sauka bisa fuskarsa,hakan ya sake nunawa fadila yadda Aliyyu ke tsananin son yara,ita din ke share masa hawaye tana lallashinsa
"Allah shi ya cancanci ka godewa bani ba,ni da kai duka bayinsa ne yadda yaso haka zamu gani"
Baiyi qasa agwiwa ba Kuwa ya kama"alhamdulillah"ba qaqqautawa
"Allah ka yimin dukkan wata ni'ima a rayuwata,Allah ka bani ikon saka maka ta hanyar yi maka da'a da biyayya da bin dukkan wani umarni naka"

Addu'ar d aliyyun y dinga yi kenan gwiwoyinsa kafe a qasa hannayensa a sama,ba fita daga asibitin ba sai da ya yiwa doctor sa'adah albishir din Kujerar umrah,fadilan ma haΓ±ata tafiya yayi ya kafe sai dai ya dauketa,sai da tasa masa kukan shagwaba sannan ya bari,roqarsa ta dinga yi cikin mota don Allah kada ya fadawa kowa
Girgiza kai yayi"mummunan labari ake boyewa,ban miki alqawari ba ruhina,na dai yarda bazan fada ba amma Duk wanda ya tambayeni zan fada masa"ba yadda ta ita haka ta qyaleshi,motsi kadan yace"sannu,yaya?"
Tun tana amsawa har ya soma bata dariya,

Marairaice masa tayi kan sai ya kaita gida taga umminta,dole ya kaita ganin tanason sa masa kukan nan nata da ba yaso,tayi Sa'a kuwa ta tadda Farida tazo,wayyo dadi gun Fadila ba'a magana,humaira nata rarrafe abunta,yarinyar ta sake kyau kamanninta da fadilan ya sake fitowa,sai ta sake shiga zuciyarta,Fadila na shirin daukarta ummi tace"Allah yasa ta yarda da ke 'yar nema,wai nan qiwa fa take"sai kuwa ta ba su mamaki don luf tayi abunta jikin Fadilan

Can jimawa saiga 'yan biyun Anty hafiza,tunda cikinta ya tsufa ya Ahmad ke tarkatosu gun ummin lokaci bayan lokΓ ci musamman weekend dob mamansu ta huta, ummi ce ta kalleshi"gayamin kwana nawa za suyi,don bazasu zo tafiya amira rigima ba"yayi murmushi"anjima ma zan dau ke su,idan natashi daga kasuwa,naji tana gobe can gidansu za'a kaisu za suyi taro"

Sai kuwa hussaina tace"abba da hassana kawai zaka tafi ko?ni a gun ummi sanya kwana"ta fadi taba fadawa saman cinyar ummin"kiji mai ka irin wayo wato don kin fita baki ko"inji Muhammad daya dungure mata kai din shi hasana ce mutuniyarsa

Ummice ta bige masa hannu"ina ruwanka ,baban kawai"ya qyalqyale d dariya ya dauke hassanar sukayi ficewarsu yana yiwa hussainar gwalo,bata damu ba don ta saba da hakan ta fada cinyar ummin tayi kwanciyarta

*Mrs Muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah AbdulmajeedπŸ’ž: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺            *PART 3*


              2⃣2⃣

Sosai Fadila taji dadin yadda ummin nata keta nan nan d ita cikin kulawa,saidai yadda ummin nata ke binta da ido Duk Indi tayi ke sata jin kunya da rashin sakewa,kiranta ummin tayi lokacin da su ke kitchen su na hada abincin rana ita da farida,gefenta ta nuna mata "zauna a nan bar faridan ta qarasa aikin tunda ita lafiyayyiya ce"kunyar ta sake kamata ,zaman tayi don dama aliyyu ya ja mata kunne da kanta yake tace zataita aiki

Faridan ta fito daga kitchen din tana kallonsu "ya haka sister ina can ina jira?"
"Eh ni nace ta zauna ,jeki qarasa tunda kin fita lafiya"tsalle faridan ta daka kamar yarinya"wallahi ummi sai da nace sister kamar mai ciki ta wani harareni ,ashe na canko gaskiyar lamari"
"Tashi dalla Mara kunya ki bawa mutane guri fitsararriya"inji fadilah dake hararar farida,bata damu ba taci gaba da murnarta

Gab da magariba aliyyu ya iso,ya shigo suka Gaisa da ummi wani kunyarta yakeji sosai,yanata satar Kallon Fadila yana mata alama ta taso su tafi amma tayi qirmisisi kamar bata gane me yake nufi ba,har sai da ya miqe yana yiwa ummin sallama ya fice,ummin ta kalleta "zaman me kikeyi haka,ki tashi mana Ku tafi"
"Haba ummi banga abba ba fa,Kuma ga farida nan ita da ta fini zuwa ma bata tafi ba sai ni"ta fada kamar zata saka kuka
"Nima Motata na gun gyara ne da tuni na wuce,Mubarak ne Zai biyo must tafi"tana qunci tana komai ta fita

Aliyyu sarkin yara,yana jingine jikin motarshi shi da 'yan biyu sunata hirarsu abinsu,shikam dama idan ka ganshi tare da yarda zakayi mamaki,sosai yake sakarmusu hadi da biyewa shirmensu,tahowarta ce ta dauke masa hankali cake daya kan 'yana biyun,tunda ta taho tunda ya lura ranta kamar a bace
"Allah ya taimakeki,wa ya tabamin ke?"y fada yana leqa fuskarta
"Bayan Kaine,ka barni kawai na kwana amma don Allah, yaushe rabona da gida,kunsan five months fa"

Ya harde hannunsa a Qirji ya gyara tsaiwarsa"ba Matsala mana don dai kwana,amma ina fatan kin tanadar mana dakin da zamu kwana diΓ± ko?"
Murnar da take ta koma ciki,ta zare ido"wai ni da kai Zamu kwana a Daki gudan,a gaban ummin da abba?"
Baice komai ba ya bude mata gaban Motar sannan tace"kinga to ashe babu batun kwana my queen, wlh bazΓ Γ± biya ba Fadeelah, daga yau fa sai nayi kwana hudu kafin kwananki ya zagayo,pls ki tausayamin mana Fadeelah baby"

Sai ya kashe mata baki,tabbas aliyyu na qaunarta,bai kamata ta zalunceshi ba,saboda haka babu musu ta shige,cikin jin dadin rashin musu irin nata ya rufe mata qofa,two thousand ya ba wa su hassaΓ±a,da guduvsuka shige parlour suna tsalle su na ce wa"uncle ne ya bamu naira biyarr"don basu San kan kudi ba

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Cikin lkc qalilan Fadila ta fuskanci waye ainihin aliyu,very intelligent simple peace and humble man,mutum ne mai kyakkyawar zuciya mai cike da alkhairi,maye ne Kuma gwanin Soyayya,dau tafi idan ya rudata da salon soyayyarshi sai ta rasa a wacce duniya take?,shin duk duniya ma akwai macen da ta ka ita sa'ar miji?
Soyayya yake gwada mata ba ta wasa ba,wadd ita da kaΓ±ta wani lkc take roqonsa ya rage nuna mata haka

Abinda ke tunzura Zuciya Salima da salima Kenan,sau tari yakanyi wasu abubuwan da gayya wai ko zasu dauki darasi su gyara tsarin rΓ yuwΓ rsu,amma a'a maimakon suyi Koyi da ita sai su sake fandarewa,maganganu kala kala marasa kan gado
"Matsafan chaina dai aka bi,idan baka ga haka ai kafin ku tafi ba haka yake miki ba"dariyarta taci sosai,bata kulasu ba kamar yadda ta saba don aji tΓ yi musu gudΓ  sakasu,Aliyyu ne da yake jinsu yace"Duk wadda zΓ tayi bin mΓ lamai irin nata yaso ni zaΓ± dinga biyaΓ± kudin,indai irin nata ne"

Iya bakin qoqarinsa yanayi don ya saitasu a hanya amma inaaΓ a......kamar sake rubuta su akeyi,ya gama haqaqewa ransa tabas babu Wanda ya isa ya shiryar da batacce sai Allah

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah AbdulmajeedπŸ’ž: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

    
            *PART 3*

              2⃣3⃣

Daga hutun sati sai aliyyu ya birkice Fadila bata komawa aiki,bata iya sa'insa da shi ba sai kunya da ta zauna tana rusa masa babu qaqqautawa,shu kuwa Abu guda dake daga masa hankali kenan,zama yayi dirshan yana clarifying mata dalilansa
"Baby bana so ,duk sanda zaki fita baby na akwai mai kalle min ke,duk sanda na tuna hakan sai naji zuciyata na quna,pls my unique ko don babymmu da kike dau ke da shi ki haqura,ki gayamin nawa kike dauka a Wata nayi alqawarin zan miki multiplying nasa"

Ta share qwallar dake shatata Duk da ba daina zubar tayi ba,"banaso ni aikina nake so,ka ganshi fita ko ina sai tare da kai,matanka su da yake kana sonsu fiye da ni ai gashinan babu inda baka barinsu suje,sai ni da nake fita aiki "ta fadi cikin fushi tana zumburo baki,Dariya ta bashi sosai,don ya lura gaba daya cikin nata yasa mata saurin fishi  hasala da saurin kuka,kan cinyarsa ya dorata yana gorge mata Hawaye
"Gaba maman biyu,kin manta ke din ta musammance?kin manta aliiyunki bashi da kamar yake?ko kuwa kin manta cewa kace mace ta farko da aliyyun ya mallaka mata komai nasa kamàr yadda kika kasançe mace ta farko da ta mallaka wa haidar din komai nata?,hakanan ta farko da ya fara so da kangin kansa?"

"Kiyimin rai ki raini yarona ba tare da yasha wuya ba,dama tun farko aikinki din nan ba Sonshi nake ba,idan ba zaki manta ba ranΓ r farko da zaki fara zuwa irin sharudan da na dinga gindaya miki,wlh a lokΓ ciΓ± zuciyata tΓ fasa kawai take,bans an sink I da na boye ne yasa ni jin haka ba,banda Ahmad ne ya same ni kai tsaye da maganar da ba zakiyi shi ba,na roqeki kiyimin wan an alfarmar ki haqura"ya Jade hannunsa da nata yana Kallon qwayar idanunta,sai taji bazata ita wofantar da alfarmar da aliyyun ya roqeta ba,saboda haka a take ta rubuta letter din barin aikin ta damqa mishi,

Aliyyu ya cancanci komai a gunta,tsananin kulawa da qaunar d yake nuna mata kadai ta isheta,abinda kullum ke dawwamar da ruhinta cikin farinciki da begensa,godiya ya dinga mata har sai da ta rufe masa baki

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Duk cikinsu babu wadda ta ankara da cikin d fadilan ke duke da shi,ba wa ni shiga sabgarsu take ba bare su ganta,don tuni aliyyu yayi mata maganinsu,iskancinsu na da suka so su dawo da shi,su shigo musu ranar girkinta a cinye abiΓ±ci da su,sannan kuma suqi tafiya suyi zamansu,bayan ita ranar nasu girkin da ta shigo ta masa barka d dawowa minti goma ta bar gurin ta koma bangarenta,duk nacinsa bata zama don bazata yi abinda idan ita akaiwa ba zata so ba

To su kam basu sΓ n hakanba,don haka da zarar sun wuce minti goman zai janyota jikinsa ya fara yamutsata,to yanzun nan zaka ga kowΓ cce ta ja qafafunta ta wuce,dariya yakeyi abinsa yace tunda ke kin kasa maganinsu abun ni gashi nayi miki ko?"ita din ma wani lkc dariyar ke ka ma ta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Wata hudu cikin amma idan ka ganshi sai Kayi  tsammani yayi wata shida,sosai abun ke basu mamaki su duka,amma babu abinda fadilan ta fasa,mita da qorafi kam tana shansa,don wa su lokutan ma idan ranar girkinta ne idan zai fita gidan anty hauwa yake kaita tace"ga gajiya nan ya kawo kada a barta tayi koma,idan ya dawo sai ya biyo ya dauketa,da ya ajjiyetan sai fa ta faki idonsa ta masa girki ko da mai sauqine don tace ita kam ladan bai isheta ba

Aliyyu tace"shi kam indai lada ne ya isa haka,don kuwa ko iya cikin jikinta ya isheshi,aljanna kuwa indai shi zai dage mata qafa ta shigΓ  to tuntuni tasa a rage take"dariya taci ranar cikin alfahari da jin dadin kalaman yabonsa a gareta

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Ya kaita gidΓ n Anty hauwa yadda ya saba ita Kuma tace kausar tazo ta rakata gidansu nuratu ayi mata Jan lalle,anty hauwa tace"sannu Fadila da qoqari,ko wuya zaman lallen baya miki?"
Tayi 'yar dariya "wlh Anty bana jin dadin batun hannuna ne haka,Kuma ma ya aliyyu naso"
"A'h tunda ya aliyyu na so sai a bada himma,don na fuskanci kin gama shagwabashi gaba daya,mu nan duka yanzun ganin must yake bamu iya zaman aure ba"ta qarashe maganar cikin tsokana,dariya ta kama Fadila lkcn da take sanya hijabinta "wlh Anty ba haka bane"
"Allah kin gama shagwabashi,idan yaso gidan nan ya dinga min fi'ili kenan"ta sake tuntsirewΓ  da dariya lkcn bilkisu ta shigo tace"Anty kamalu driver yace ya fito da Motar mu fito,tare suka tafi akabar antin a gida

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah AbdulmajeedπŸ’ž: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

             *part 3*

              2⃣4⃣

Har aliyyu yazo daukarta basu dawo ba,nan ya dinga saukewa Anty hauwa kwandon mita ya dinga yi kamar zai ari baki,safe baki kawai Antin tayi tana kallonsa
"To ni meye nawa aliyyu,kwalliya take son yiwa mijinta sai na hana?"
Dariya taso ka nata ganin yadda yaketa safa da marwa kamar Wanda kace an saceta,ga wayarta Kuma na kan Kujerar falo ta manta ta

Minti ashirin Motar su ta shigo,da suri ya  qrasa ya bude mata qofar Gaisa miqa mata hannunsa ta Dora nata a kai,Jan lallen kam yayi dau ya haska idanunsa,Zara zaran yatsunta suka sake yin kyau,diba yasa ido ya sakar mata hararar wasa,ta saki murmushi idanunta cikin nashi tana langabar da kai cike da kissa
"Zaki sani tunda kika ke kikayi zaman lalle kika wahalrmin da baby,punishment dinki na yau babu ke ba tafiya da qafafunki"kafin tace komai har ya sunkuceta ita da cikin jikin nata ba tare da jin nauyinsu ba,yasa kunya ce da ita bata son ya dinga daukarta haka cikin mutaΓ±e

Cikin mitarsa ya sakata bayan ya kwantar mata da Kujerar,cikin shagwaba ta kalkeshi
"Please my haidar,baby I fa sallama da anty ba"
"Shshhhhh"ya dora yatsansa Dan man uni kan lebansa"ta yafe ba sai kin mata ba,mu tafi gida ki huta baby"ya zagayo side dinshi ya tada motar,ai kam kafin su isa gidΓ  har bacci yayi awon gaba d ita,murmushi ya saki ya Shadda fuskarta da daya hannun nasa yanajin wani sonta na shigarshi

Yana tsaida motar ta farka idanunta fes bisa fuskarshi,sukayiwa Kuma murmushi yadda suka saba a duk yayin da suka kalli juna,ya fice ya zagayo ya bude qofar hadi da daukota cak
"Wayyo my haidar ,don Allah ka saukeni"ta fadi tana wutsil wutsil da qafafunta gami da dan dukan qirjinsa kadan kadan
"Kun manta punishment dinki kenan?"

Samira dake manner da earpiece a kunnanta ta fito daga bangareΓ±ta,kamar umarni idanunta suka sauka a Kansu,riqe bakinta tayi a ahankali ta dinga takowa indai su ke idaΓ±unta qyar kan cikin fadilan,ashar din da ta lailayo ne yasa suka ankara da ita  a gun,da hanzari Fadila taci gaba da mutsu mutsu ko zata samu ya sauketa ko don idon Samira
"Kace tuni ka dirka mata mu ka barmu kara zube saboda tsabar iya cin Amana"ta fada sanda ta tsareshi d ido,girgiza kai yayi lokacin da murmushi ya subuce masa,shikam yana mamΓ kiΓ± Samira idan tayi wa ni abuΓ±

baiko kulata ba ya barta nan a tsayen ya nufi bangarensa don baisan  me takeso ya gaya mata ba,qasa qasa Fadila ke cewa"bai kamata ba dear fa,ko nice ba zanji dadi ba"
Baisan lkcn da ya tuntsure da dariya ba"mene bai kamata ba?,cikin naji?,ai bani na baki ba Allah ne ya baki,idan da sun so wataqil da tuni Allah yasa sun Samu tun kafin ke,ko Kuma sahun nata zaki ni?"ya qarashe cikin sigar tsokana

⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Dirshan take zaune saman cinyarsa,ayabarta wadda ita ce abincin yake bare mata,sai zuba shagwabarta wadda take burgeshi take,qaramin wandone a jikinta sai Riga ta vest wadda ta fito d turtsetsen cikinta,Kanta ya sha gyara Wanda Aliyyu ne ya zauna ya gyare abunshi tsaf ya mata parking sonsa

Salima ce ta shi go da sallama ,ragowar sallama ta maqale a maqoshinta,tashin ahankali wanda ba'a sa masa rana shi Salima ta shiga,ciki?ciki a jikin Fadila?yarinyar da ta tsana take adawa da ita fiye da duk Wata halitta dake bayan qasa?,kasa dauke idnunta Sam tayi saga kan cikin,hakanne ya bawa fadila tsoro tuni ta Dora hannun nata saman cikin nata idanunta a lumshe tana ta soma karanto addu'o'in tsari,aliyyu ke Kallon yadda Saliman ke wani numfarfashi kamar maras lafiya,tuni ya soma tambayarta menene ya soma yunqurin Ajjiye Fadila don ya isa gareta

Tuni ta saki handle din ta juya ta five ba tare da tace koma ba,kuka sosai ta rushe da shi,matsananciyar qiyayyar cikin da uwarsa suka lullubeta,wani tsΓ utsayi ne tuntuni ya hanata sakin jiki ta cika gidan aliyyu da 'ya'ya fiye da kowcce mace da da zaya ajjiye?,take ta ciwa kanta alwashin ko ta halin qaqa ba zata taba lamincewa cikin nan ya taka doron qasa ba,domin tana ganin ita tΓ fi kowacce mace cancanta ta sake haifawa aliyyu yara ba Wata cΓ n ba,nan shaidan da Zuciya suka ci gaba da tunzurata gamida shirya mΓ ta sharri kala kala

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah AbdulmajeedπŸ’ž: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

             *part 3*
               2⃣5⃣

Doguwar Riga ce jikinta kamar yadda suka zamo sune shigarta na yau da kullum,sabida cikinta bai bari ta sake cikin ko wani irin kaya idan ba su ba,ita kanta girman cikin na bata mamaki,wayarta ce a hannunta tana tsarawq aliyyu tex na an wuni lpy kamar yadda yake al'adatarta kullum idan ya fita babu fashi koda sunyi Waya koda Kuma ba ranar girkinta bane

Cike da mamaki ta dagi tana masa sallamar Salima wadda ta shi go hannunta dauke da wa ni madaidaicin food flask fuskarta qunshe da murmushi,Fadila ta boye mmakin nata ta Hawa Salima tayi gurin zΓ ma,ta sauna din kuwa idonta na akan fadilan
"Sannu uwar hudu"ta fadi cikin salon son nuna tsokana ,sai itama tayi qoqarin dora murmushin kan fuskarta
"Yauwa sannu an wuni lpy?"
"Lpy qalau"ta fada tana tunda flask din gaba fadilah
"Wannan dama na kawo miki,nasa masu ciki akwaiku da kwadayi,Duk da ba'a gaya mana qaruwr da aka samu ba,ai dan aliyyu namu ne mu duka"ta fada kai ka rantse har zuciyarta,murmushin itama ta sake yi,t janyo flask din tana budewa

Fasten dankali ne Wanda ya sha danyen kifi irin marar qayarnan,a zahiri abincin yayi don qamshin curry kawai yake zubawa,kana Kallon abincin kai kasan ba Salima ce tayishi ba don ba zata iya din ba
Amma maimakon ya burge ta sai ma tashin Zuciya da haifar mata,don ita yanzu a duniya babu abinda yake burgeta take biya ci irin ayaba ,komai dadi ko haduwar abinci,saidai ko lemon zobo,koda ta kwata cin ma amai ne ke biyo baka

Ta rufe da sauri tana mata godiya,maimakon taga salimar ta tafi sai taga tana gyara zama harda qoqarin zuba mata
"Gara kici tun da duminsa,nasan hΓ lin masu ciki yanzu yana kaiwa anjima zai iya fita daga ranki",da sauri fadilan ta dakatar da ita"kada ki zubamin yanzu don banajin yunwa"
Sororo saliman tayi cikin rashin jin dadi har hakan ya bayyana akan fuskarta,tilas ta haqura ta rufe ba don ta so hakan ba,saidai don bata so ta fiya matsantawa har fadilan ta dago wani abu,

Haka ta fice tana jaddadawa mata taci fa,sanda wai sai tana ci tana qoshi,hakanan fadila taji ko bayarwa bata so tayi,saboda haka ta samu baqar leda ta kwafe a ciki ta cilla cikin dustbin

kwana daya biyu salima taji shiru,ba qaramin tashi hankalinta yayi ba,Duk wani shishshigewa da kulawa tayi wa Fadila shi,duk cikin qoqarinta na ganin ta samu yarda gurinta,babu abinda bata dafa ba na kwadayi ta kai mata ba,sai dai kash....abinda bata sani ba babu abinda cikin fadilan ya sani banda ayaba

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Dukkansu sun shirya don zuwa gidaΓ± Momi karbar lefen sumayya da rabi'ah Wanda za'a kawo ranar,mai gidan ne da kanshi zaya kaisu cikin motarshi sabuwa dal da duka dauka shekaran jiya ta iso,yayi haka ne a fakaice don fadila wadda ke sanye cikin doguwar riga ta atamfa exclusive mai adon orange da army green, Duk da turtsetsen cikinta hakan bai hanata yin adonta ba,Kuma tayi kyau abinta,ta fita daban a cikinsu tamkar zahra cikin taurari,hakan ne ya sanya aliyyu ya kasa yiwa idonsa shamaki daga kanta,Duk inda ta motsa idanunsa na biye da ita

Baisan me yake sΓ urin daya fushi ba,kwanakin gaba daya a fusace take,Abu dan qanqani sai ta hau masifa ko tasa kuka,har doctor ya tambaya tace masa kada ya Samu wa su mataΓ± idan su na da ciki hakan na faruwa da su,musamman idan yaw soma tsufa suka fara gajiya da shi,to ko a yanzuΓ± ma ya lura kamar 'yan rigimΓ r na kusa,don ko su Samira da bata kulawa a irin wannan mood din tana jin dai dai take da duk wadda ta tabata a cikinsu

Ya sake kallonta,tayi lullubi har saman kanta da farin mayafi da ya dace da atamfarta,ba kamar lullubin 'yan uwanta ba ita kafada,sai ta sake masa kwarjini,cikin ya mata kyau duk da dan uban girmansa Wanda ke sake sashi jin tausayinta tare da sake mata addu'ar sauka lfy

hannunta harde saman cikinta,tayi kicin kicin da fuska,hada ido sukayi ,ta same qwayar idonta ta wani dauke kanta tamkar bata ganshi ba,dan qaramin murmushin nan nasa ya saki,wani lkçn salon shan qamshinta da miskilancin nan nata na burgeshi,ta iya shariya da dake kai da gangan

Ya dubi salima wadda ita ke dΓ  girki,ba yadda ya iya a zahiri zaifi son ace Fadilar ce kuwa da shi,ya danna madanni ya bude gidan gaban da a dazu yake a rufe yace da  Saliman"shigo nan"

sai ta tsinci kanta da jiΓ± wani bacin rai,suka Kuma hada ido,batasan sanda ta danna masa harara ba gami dΓ  Jan dan qaramin tsaki a ciki,ta shige sit din can baya na qarshe tana kumburi

*Mr s Muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah AbdulmajeedπŸ’ž: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

            *PART 3*

              2⃣6⃣

Jinta take kamar ta fashe,ita kanta tana mamakin yadda yake saurin fusata a yanzu,Duk da ta sani akwai tsananin kishin aliyyu dake dawainiya da ita,tabbas ba kuwa ce maca ce ce zata San Wayne ainihin aliyyun ba ta kada kishinsa,musamman ma ita da kunsan tafi kuwa saninsa zahiri da badininsa

Salima nata rawar kai ta shige gaban,Aliyyu ya tada Motar yana qoqarin gyara madubin motar ta yadda zai samu sukunin gano fuskarta sai dai sam taqi yarda da hakan don tuni ta kautar da fuskarta,dole ya haqura ya soma tuqin hankalinda na rabe gida biyu

Duk yadda salima yaso ta janye hankalinsa suyi hira mai tsawo da dadi ko don ta cusa musu haushi abun ya faskara,dole daga qarshe itama ta haqura ta ja bakinta tayi shiru
Ko da suka shi go harabar gidan tamkar dama Allah Allah take su iso tuni ta rigasu ficewa tamkar bata jin nauyin jikinta,ya biya da ido don ba haka yaso ba

Yaso ne ya datseta a cikin Motar ya mannata da jikinsa ya dan rage mata temper,don a matakin da take ciki tana buqΓ tar wannan,salima dake lure da shi takaici ya cikata,ta sake qullatar Fadila,ta Kuma sake lasar takobin hana abun dake cikinta tayuwa kota halin qaqa

Ya dauke idanunsa lokacin da ta bace wa gΓ ninsa,bai bai ta kan yadda suke kΓ llonsa kamar zasu cinyeshi danye ba ya jaw wayarsa dake gefensa ya latsa number din Anty hauwa ya kira,bugu uku ta daga
"Hello mummyn kausar,ga ajiyata nan as usual, pls abata kulawa ta musamman Anty na"dariya ta saka
"Ho,aliyyyuuuu.......to naji,mene tukuicina?"
"IPhone 7 da kike son siya ki bar kudinki ni Zan Waya miki"ta sake dariya"lallai Ashe abun na yine,to ba Matsala,kada ka damu dan qanina"
"Thanks Anty",ya fadi yana kashe wayar

"Amma fisabilillahi tuni yaushe bace maka ina son iPhone 7 din naΓ± ,kowa cikin qawayena ita suke riqewa ammavkaqi siya mini,sai ganshi rana tsaka kace zata siyawa Waya",Kallon da yayi mata ya sanyata yin daΓ±asaΓ±in yin furucin,tuni kafin yace wani Abu ta balle murfin Motar ta fice tana qunquni cikin ranta Wanda ta bata isa ta yishi a fili ba,don ba qaramin wuya ta ci ba lokaciΓ± da ya amshe mata key din mota da wayarta bakamin ya dawo matΓ  da su

Ya maida idonsa kan salima,tayi qoqarin hadiye bacin ranta don son cimma qudirinta kan fadila cikin ruwan sanyi ba tare da an gano komai ba,ta bude motar itama ta fice ranta na mata wata iriyar suya,tanajin zata iya koda kawar da fadilah ne don ta shigar mata hanci da qudundune da yawa,tasa ta rasa fili da gurbin da ada take jin tana da shi a zuçiyàrsa

Cikin falon ma kowa sannu yake mata,ciki wata bakwai amma sai ka dauka da ka bar gun za'a bika ace ta haihu,haushi,takaici,kishi,qyashi da hassada ta cika zuciyoyinsu,Samira da bata iya shiru ba tace"mu sai a tsine mana albarka ai tunda bamu iya daukan ciki ba"ciki ciki tayi maganar amma wani abun ya dan fito,madina tayi yunqurin magana Momi tayi mata inkiya da tayi shiru kada tabi ta kanta,sama dakinsu sumayya ta haye abinta tayi kwanciyarta Anty hauwa ta cika mata plate da ayaba ta bawa bilkisu ta miqa mata,Momi kuwa tayi ruwa tayi tsaki hawa,hana kuwa hawa,fada ma ta dinga don me yasa bΓ 'a barta ta zauna a gida ba tana fama da kanta haka,batasan ita ta rage lallai sai ta so ba

Baccin kuwa take sonyi,don matuqar ba ranar girkinta bace bata ita wani baccin arziqi,ta riga ta saba bacci jikinsa,yana lΓ llabata kamar qwai harda tausa yake Gara mata,baya runtsawa har sai ta rigashi yin baccin

Kira ya shi go wayàrta tana kwance lamp da tsammanin zuwan bacci,ta duba sai taga sunan *darling blood* sunan da ta sama number dinsa kenan,sosai take da muradin jin muryarsa sai dai tana sane tayi banza da wayarta,sau biyu tana rurinta tana katsewa sai a Kira na uku ta sdaga,ta kara a kunnenta ba tare da tace koma ba,ajiyar zuçiya ya soma saki wadda ta ratsa Fadila har ta tayar mata da tsigar jiki
"Babyyyy..."ya kirata Murya qasa qasa cikin Jan sunan,itama ajiyar zuciyar ta soma saki"I missed you badly"abinda ta iya fadi kenan cikin narkakkiyar murya,ya sani sarai akwai kewarsa dake damunta,kwana hudu ba tare da juΓ±aΓ±su ba abune ba mai sΓ uqi qwarai da gΓ ske,sai tausayintΓ  da sonta ya sake kamashi,iya kawaici tana da shi,gashi nan da kwana biyu zasu wuce umara shi da salima da Samira harda doctor sa'adah wadda ya mata alqawari

"I know baby na,saidai hankalina na tashi idan na ganki cikin rashin walwala,please smile my dearest wife,ko da bana kuwa nasan zΓ nji a jikina"
Bata San lkcn da murmushin ya subuce mata din ba,musayar kalaman soyayya suka dinga yi masu tsuma zukatan ma'aurata,aliyyu yaqi barinta har sai da yaji shiru alamun baccin ya dauketa

*Mrs Muhammad ce πŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah AbdulmajeedπŸ’ž: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

             *part 3*
     
               2⃣7⃣

Kai kawo take a bangaren nata don tuni aliyyu ya sawwaqe mata zuwa nasa bangaren anan bangaren nata yake yada zango har ya kammala yi mata kwanakinta,yayi hakan ne don hanata yin aiki Wanda ta saba da shi Duk ran girkinta sai ta qalqale bangaren nasa da su suke barinshi babu kintsi


Amma Duk da hakan bata fasa Duk wa ni shirye shirye na karbar mai gidan nata duk ranar girkinta,yayi mitar yayi fushin har ya gaji,ta Riga da ta saba bazata iya zaman ba,bata jin nauyin da tayi,uban cikinta bai damunta Kuma bai hanata duk wani abu d ya kamata ba,sosai aliyyu ke yabawa jΓ rumta da juriyarta

kamar yanzun ma ta kammala komai,sanye take cikin wata gown mai azabar kyau,budaddiya ce sosai daga qugu zuwa qasa,hakan yasa bata takurawa turtsetsen cikinta ba sai damar fitowa ma da ta bashi,yayi das a jikinta,qaramin hannu ne da rigar,ta tattara gashinta a tsakiyar kanta ta daureshi da ribbon Kalmar rigar,fuskarta tayi fayau tayi kyau cikin simple makeup, sai qamshin nan nata take zubawa,

Ta jita da niyyar shiga kitchen don dauko banana taji sΓ llamarshi yavshigo parlour din nata hancinsa na sheqar daddadan qamshinta,da sauri suka nufi Kuma kuwa na qoqarin tar bar dan uwansa,shi ya soma nasarar cimmata ya rungumeta ta bata yana sansanar wuyanta cike da farinciki
Fuskarta qunshe da murmushi tace"Baka da dawowa gida mijina"
"Yauwa matata abar alfaharina"ya mayor mata cikin salon qauna da kulawa,sunfi kusan mint I biyar a haka sannan ta juyo da niyyar amsar jakarsa su qarasa daki,zullewa yayi yana noqe kafada"naqi wayo nan naki,a waysnce fa kike Karya min doka daya bayan daya,bayan na hanaki dawainiya da ni"
Murmushi ta saki,ya Dora lebensa a goshinta ya sumbaceta

Qoqarin ta rage masa kayan jikinsa take don ya samu yashiga wanka Sam ya hanata ta gajiyar kama hannuwanta ya zaunar da ita gefen gado,tana kallonsa har ya gama ya daura towel ya shige wankañ,tuni ya tadda ta ta fiddo masa da kayan da zai sa ta feshe masa su da turare,ya gama shiryawa tsaf sannañ ta taka masa ya fice sallah masàllaçi ita Kuma ta koma ta tayar da tata

Sai da ta cika masa ciki da abun ci shi Kuma ya ci ka mata nata da ayaba yana tsokanarta ta zama qanwar monkey, bata kulashi ba sai da ta qarasa cinyewa abarta sannan ta taqarqare ta tureshi ta haye kansa
"Wayo jama'a wayo mummy 'yar lukuta maman baby zΓ ta karyani a kawo agΓ ji"ya fada yana qyalqyala dariyar tsokana,ta turo baki"kyau sai ka gayawa aya zaqinta"
"Wayo 'yar matata ki taimakeni ki dagani kada nayi amai
"To zan daya ka ammΓ  kan sharadi dayΓ "
"Naji fadi indai zaki dagΓ ni nidai"yana riqe da cikinsa yana qoqarin boye dariyarsa hade da yi mata gwΓ lo a fakaice
"Ni ka yima gwalo?"ta na nuΓ±Γ  kanta da danyatsanta gami da shagwabe fuska,dariyar da yake boyewar ta subuce ta fito

"A'ah,ni da baby na da yake ciki fa muke wasa"ta kalli cikin nata sai aliyyun ya bata dΓ riya,sai ta sauka tana ce wa"sharadina kamin doki"tuni kafin ta qarasa ya juyo mata bayΓ n nasa"maza hau,kada ki sauka har sai kin gaji da kaΓ±ki"ta tattare rigarta tana shirin hawa salima tΓ yi knocking,hakan yasa fadila sakin rigΓ rtata ta koma saman kujera ta zauna,da qyar sΓ lima ta samu ta hadiye wa ni dunqulallen Abu mai zafi da ya tokare mata maqoshi,a duniya ta tsani ta bude ido taga fadila dauke da cikin nan a jikinta,ji takeyi da ta dunga ganin Fadila da shi ta gwammace ta bude idoΓ±ta taga baqin kumurcin maciji

Babban Abu na gaba dΓ ke tayar mata da hankali,so qauna kulawa mΓ su nauyi da take gaji guΓ± aliyyu akan Fadila da cikinta,ta sani tayi sake Kuma ta barar da damarta,ta kuma bar kari tuni ran tubani

dumbin kulawa da tarairΓ ya babu wadda bata Samu ba guriΓ± Aliyyu,tuni yΓ  bana mata hanya qwaya daya da zata sake samun damar mallakeshi shine ta hanyar cika masa gida da yara amma sai ta gaza yin hakan,ta watsa masa qasa a ido,a yanzun tana jin shiryawa yin hakan,ta shirya kawΓ r da duk wani Abu da zai zama mata shamaki tsakaninta da Aliyyu,Samira ba matsalarta bace lamarintΓ  mai sauqi ne bata dameta ba kamar yadda Fadila ta tsole mata ido.......

(09063329635 SMS only pls)

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah AbdulmajeedπŸ’ž: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

            *part 3*

             2⃣8⃣

Ta qaraso falcon tana qaqalo murmushin dole
"Uwar biyu"ta sima ce wa da fadilan
"Maman biyu"fadilan ta mayar mata,ta kalli aliyyu dake zaune saman carfet ta zube a gabansa tana masa nacin kallo,qaunarsa na fisgrta tana ara mata qaimi kan qudirinta
"Dear barka da warhaka"fuskarsa sake ya amsa mata,ta turawa Fadila flask kamar koyaushe"ga wainar fulawa nan nasa an miki, itakam Fadila abun na daure mata kai,babu Ragnar Allah da zata fito ta fadi ba tare d Salima ta kawo mata wa ni abun ba,fara'a da kulawa take nuna mata,sai dai dan jarida da lawyer ba wasa bane,can qarqashin murmushinta fara'arta da kulawarta  fadilan na tsakulo wa su yanayi boyayyu kan fuskar saliman,Saidai ita taimakon da Allah yayi mata cikin nata ba mai cite cite bane idan har taci ayabarta ta jiqa zobonta ta share to shikenan

"To na gode"kawai fadilan tace, ta Daki remote ta qaro sautin t.v tare da maida hankalinta kai,saboda jin wani kishi na taso mata yadda aliyyu ke hira da salima cikin sakin jiki ta soma ka ranta "hasbunallahu wa ni'imal wakeel",Samira ce ta shigo gamida ce wa"sllama" kanta tsaye ta nufi kusa da Fadila ta sauna don Neman magana,ta kalli aliyyun yayi da shi din ma ita yake kallo ,cikin ransa yana fadin"can za mutum sai Allah"baar doguwar Riga ce a jikinta kanta babu ko kallabi,d slipper sonta ta shigo har tsakar faloΓ±,hannunta Kuma ga ragowar miya da maiqo nan,ya sake fadin "yanzun haka qila ta taho har nan kenan"

"Gani,ina zaune zan fara cin abinci ka kirani,har na fara ci naga waccar ta taho bace Gwara na haqura da abincin inzo inji kake faruwa kada ayi bΓ bu ni,ko a yimin munafurci a cuceni ganin bani gun"sai Kuma ta maida kanta gun Fadila dake gefanta"ummm,anata mana Kallon banza ko"ta sani sarai da ita yake don ta saba gaya mata haka,wai tana mata Kallon banza tana ganin zata haihu

sau tari dariya Samira ke bata idan ta fadi haka,don ita dai bata ga wa ni Kallon banza da take musu ba,sai bata fiya damuwa da shirmen ta ba,bata da qullaci kanta tsaye take magana,haka idan zata ai kanta kanta tsaye take fadi ba boye boye

Maganar aliyyu ce ta dau ke hankalinta daga kan fadilan
"Jibi insha Allahu zamu wuce umra,za muyi sati biyu da yarda Allah"sai ya bude wa ni file dake Ajjiye kusa da shi ya ciro passport guda biyu ya miqawa salima da Samira,wani uban ihu da tsalle samiran tayi sai gata ta dire a gaba aliyyu,ta ruqunqumeshi,tuni har ta shafe masa ragowar miyar hannunta
"Da gaske don Allah sweet aly,za muje saudiyya,wayo dadi zamu keta hazo"sumbatun murna ta dinga yi,don kafin aurensu ya mata alqawarin fita honeymoon da ita har ta saka rai sosai don bata taba barin nijeria ba,sai Kuma ta barar da damarta

Salima ma murnar take yayin da Fadila tayi kamar Batasan me ake ba,don ta tsammaci zai miqo mata nata passport din tunda yana guriΓ±sa,a hankali ya maida idanunsa kanta bayan fitarsu,ko motsi bata yi ba tana zaune a inda take kamar yadda taqi furta komai
"Babyyyy"ya kira ta ta juyo ta kalleshi,sai Kuma qwalla ta ciko idanunta,ya miqe tsam ya iska Kujerar da take kai
"Baby.......kuka?"kamar jira dama take sai kawai ta rushe da kunya
"Subhanallahi"yace ya kwantar da ita kan cinyarsa,a hankali ya dinga shafa gashin kanta da yasha gyara yana jin sautin kukanta na sauka a kunnensa,bai hanata ba don yasan ba yin kanta bane

sai da ta gama ta qoshi har tana sakin ajiyar zuciya sannan yace mata"baby me ya faru erhmmm?"
"Shine zakayi tafiyarka umra kai da kayan ka wato ni a barni a gida ko?"
Murmushi ya saki mai dan sauti,ai kuwa sai ta sake qufula
"Dariya ma kake mini?ai dole Kayi dariya saboda yanzu bani da mamora kenan"sai ta kuma sakin kuka,masifa ta hau zazzaga masa da bala'i,shi kam ma sakin baki yayi yana kallon dan qaramin bakinta daketa zazzaga masifar yarda qoqarin qwacewa daga jikinsa,sai ya hanata ya matseta a jikin nasa har sai dΓ  ta gaji don kanta tayi shiru,sai Kuma ta dinga sakin ajiyar zuciya alamun ta fara sauka


Yana dagota yaga tuni Ashe bacci ya dauketa,murmushi ya saki ya dagata cak ita da uban cikinta ya kaita bedroom cikin dabara ya suya mata kayan bacci ya gyara mata kwanciyarta sannan ya dawo parlour ya gyara gun dΓ  suka ci abun ci ya hada kwanukan ya wanke mata su tas,don yasan matuqar suka kai safiya saita wanke kafin ta hada breakfast

Lokacin da ya dawo tuni ta Dade da yin nisa cikin barcinta,ya jima zaune yana kallonta,ba qaramin tausayinta yake ji ba haka nan d wannan uban cikin nata da yafi watanninsa girma
"Har yau Baki gama sanin irin matsayin d kike d shi cikin zuciyata ba Fadeelah,sadai na sani lokaci zai ci gaba da nuna miki"ya fada a filing,bayanta ya koma ya kanta bayan ya janyota jikinsa ya sake tofesu da addu'o'in tsari na kwanciya barci,hannunsa daya na saman cikinta yana shafawa a hankali yana jin qaunar abinda ke cikin nata yana sake ratsashi

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Qarfe goma su na falon zaune abinsu,Garin na lullube ne da hadari kadan don haka babu batun rana,sanyin a.c da qamshi mai taushi ne ke ganshi a falon,tun dazun ya tsura mata ido yana dariya qasa qasa,tun safe yake dawainiya da ita,wqnka,shiryata,bata ayabarta amma taqi yarda ko daya su hada ido,kunyar abinda tayi masa jiya ke cin ranta,tana ganin ta zaqe da yawa ta gaya masa maganganu da ya cancanci yayi fushi d a ita amma yaqi maimakon haka ma sai ya buge da yi mata hidima da dawainiya d ita

Zuwa can ya sake tsunkularta ta sa hannunta ta dan bugeshi ba tare da ta kalleshi ba,tasan dai abinda yake so,da dai yaga taqi kallonsa sai ya sure ta gaba daya ya azata bisa cinyarsa yana leqen fuskarta
"Haba baby nah,so kike ne yau na susuce ?,gaba daya yau kin hanamin Kallon sexy eyes dinki"
Sai ta fada qirjinsa tana Hawaye
"Ka yafemin miki na,na maka rashin kyau tsawa jiya,na mance lokacin da ni ka dauke ni mukΓ  tafi Wata qasar tsawon watanni my biyu kacal,kishinka ne yamin yawa har na ai kanta hakan,amma......"

Da sauri ya tura harshansa cikin bakinta ya hanata qarasa maganar tun dazun dama lebunan nata ke bashi sha'awa,daga bisani ya cire yaba share mata qwalla"kada ki sake yamin asΓ rar hawayena masu tsada,bayan already na gayamiki ba zaki sake kuka ba har abada,ni baki yimin komai ba"aliyyu miki ne daya da daya Wanda sΓ munshi a irin wannan zΓ manin sai an tona,wuni sukayi tarairayar juna,ita tana qoqarin faranta masa shi yana qoqarin kyautata mata,ganin bashi da niyyar fita yasa ta tambayeshi
"Kyau babu inda Zani sai la'asar,ina tare da masoyiyata"dariya ma ya bata,aliyyu mayen Soyayya ne wani lokacin idan ya cikata da ita sai ta rasa inda zata tsoma ranta

Duk d cikinta hakan bai hanata sakarwa aliyyu kanta yayi yadda yake so ba Duk da qoqarin boye zalamarsa da yake hakan bai hanata dagoshi ba,shi Kansas mazewa kawai yake amma yasa zaiyi kewarta ita da babynsa ba kewa ba na wasa ba,ya yaba sosai da juriyarta d jarumtarta,sau tari taken danne farincikinta don shi ya samu nasa,hakan yake qara masa qaimi gun kula da duk wani abu da zai kawo naqasu ga walwalarta

Sai da yayi la'asar din sannan yΓ ce zaije shi da nasiru yayi masu handling din koma,ana magariba zai dawo suje ta siyi abubuwan da take da buqata
Ta kashe hand drayer din da take busar da gashinta da ita"my haidar,ni bana guitar koma,kada ka wani kashe kudinka"ya dau ribbon sonta yana tayata faire gashinta "ban son in tafi in bar ruhina tana buqatar wa ni Abu"
Ta saki murmushi "bana tsammanin ko shekara hudu zakayi zan rasa wani abu cikin gidanΓ±aΓ±"ya sani Fadila akwai tattali ,ko kadan bata da almubazzaranci"nasan wace mata ta,amma Duk da haka a taimakeni a yimiΓ± alfarma aje Siyayyar nan"
"Kafi qarfin haka a wajena mijina ,nayi makΓ "

Yana fitΓ  ta shiga kitchen ta Debi fulawa ta kwaba cin cin d cake a mixer,ta Debi zallar tsokar nama ta gyara ta dora kan wuta,abun ka da harkar na'ura nan d nan ta kammala koma da wuri har dambun naman ta nade cikin papers masu kyau,sosai ta gaji don ta jima batayi aiki irin haka ba,don haka ko da ta fito wanka zaune tayi German gado tana daure da towel a haka ya shigo ya taddata
"Kinyi aiki bayan fitΓ ta"tana dariya qasa qasa tace "waye ya gaya maka?"ya qaraso inda take"kin manta zuciyarmu a hade take?,Kuma ina shigowa naji wani qamshi kuma na tabbatar ke kadaice mai irin wannan girkin"cikin son bΓ sar da zancen tace"yanzun dai ka haΓ±zarta Kayi wanka ruwanka na bayi,ya gano wayanta.....

N.b:pls Ku yimin afuwa kwana biyu nayi busy ne wlh,na gode muku da haqurin da kuke da ni,Allah yabar qauna

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/28, 7:58 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

            *part 3*

             3⃣0⃣

ya gano wayonta ya dan kama kumatunta
"Sarkin wayo,zanyi wankan amma bazan bar qorafi ba don Kinyi zirga zirga na San mai yawa"
Dariya itama tayi saboda barotan da yayi,,shi ya shiryata tsaf cikin doguwar riga dark pink ta Shadda,yayi mata rolling da mayafi mai kyau yellow,plate shoes ya bata yellow,cikin tsokano take ce masa"inyee,shikenan idan na samu baby girl,sai na huta abina kawai"
"Hudu nake so ki Haifa min fadilah na"
Zaro ido tayi "hudu?,haba my one,ai bazan iya ba"
"Zaki iya mana Fadeelah babyn aliyyu,abun ai na Allah ne"

Daga parlour suka jiyo tashin muryarta"Ku fito mana haka,anshanya mu fa a tsaye"inji Samira
Da axama ta miqe zata fito,aliyyu dake fesa turare ya riqe hannunta sai da ya gama ya Ajjiye turaren yasa takalminsa sannan suka fito,tayi tayi ta sabule hannunta saboda idonsa ko don su salima amma yayi mirsisi yaqi sakinta har sai da ya sata a sit din gaba ya rude,ina wuta su saka Fadila,habaici suka dinga saki daya da daya amma babu wand ta kula a cikin su,sai ta shirya Yuma aliyyun hira mai dadi wadda ta janye hankalinsa bai fuskantar me su Salima ke fadi,haka take so don dama bata qaunar gaji har ranta ya baci,sai da suka qaraso tazo fita sannan tace musu"idan tukunya na Boris Kant take batawa ba wani ba,idan Kuma na raina ka su wa ko sautu bana yi mata"ta fice abinta

Samira ta kama baki"lallai wuyanki ya nisa yanka,kin riqa fa,dani kike magana"salima kuwa ido ta bita da shi bata ce komai ba zuciyarta na mata saqe saqe kala kala kanta,tana jin ya zama lallai ta Daki mataki,amma dole ta jita su dawo daga umara tukun

Ga zatonta zai zauna ne cikin Motar kamar yadda ya saba,sai dai wannan karon biyota yayi yana tayata zabar duk abinda take so,ya iya Zabe kamar wa ni mace,su na tafe suna hirarsu,yana cikin yi mata Dariya ne taga ya tsaya cake fyskarsa a murtike yana kΓ llon wa ni guru,salima ce tsaye da wani suna hira hardΓ  dariya,sakin kayan hannunsa yayi cikin fusata yana wani irin huci da fishi ya nufesu

Kyakkyawan mari ya saka ma matashin,dago kai yayi cikin fushi "malam me nayi maka!"bai tanka masa ba illa wani naushi da ya kai masa,take bakinsa ya fashe,dafe halin yayi sannan ya duba tafi Hannun"kan bala'i"ya fadi gami da Hawa kan aliyyun da niyyar ramuwa,saidai da hannu daya aliyyun ya kama hannunsa sai ji kake bas!,ya saki wata qara nan ya zube,Kansa aliyyun ya sake yowa da saurin gaske Fadila ta tokΓ reshi da hannunta ganin kamar bai cikin hayyacinsa,sauran kadan ita din ma Takai qasa qasa,tayi taga taga ta dafa Wata kanta ta tsaya

Wayarsa ya zaro sai ji tayi yana magana da d.p.o na areansu yana a turo masa 'yana sanda,da sauri ta sake yunqurawa ta amshe wayar,idanunsa jazur ya dauka wa fadilan tsawa gami da miqa mata hannunsa,salima dake gefe tuni cikinta ya soma jiyaa wa,Dana sani mai tsanani ta rufeta,Fadila ta girgiza masa kai taqi bashi tare da juyawa don tafiya,don Tasan abun ba zaiyi kyau ba,cikin fusata ya fincikota sai gata a qasa,ya amshe wayar yana qarasa wayarsa,wa ni zugi ya ratsa mararta,tada Hannu ta dafe cikin tana runtse da ido

Cikin 'yan mintina sai ga police har biyar ,suka cafkeshi kuwa su Kayi wΓ je d shi aliyyu na fada musu kada su soma Sakinsa ko Waye yazo su ya nasa umarni,wa ni matsiyacin kallo ya juya ya wa tsawa Salima Wanda yasa hantar cikinta kadawa,bala'i ya dinga zubawa Allah yasa area din da su ke ba kowΓ ,idanunsa sun rude ya manta a shoprite suke,tuni tsoro ya cika kowaccensu,sukayi tsuru tsuru gami da sake shirya taitayinsu,ya juye ya koma aliyyunsa sak,kallonsa duka suke,sai da yayi ya gaji don Kansa sannan yayi shiru

Dai dai suke ficewa Fadila na zaune tun dazun da ta fadi tashi ya gagareta,sai ta yunqura sai zugi ya daya ta koma ta zauna, a hankali idonsa ya sauka kanta,wani tausayinta ya lullube shi,ya qarasa a ahankali ya miqa mata hannunsada niyyar bata taimako,tasa hannunta cikin bashi don Tasan dole tana buqatar taimako,ya miqar da ita tsaye ta saki wata 'yar qara,
"Ayyah sorry baby na,Kiyi haquri"ya fadi muryarsa a raunane,shiru tayi masa ta sabule hΓ nΓ±unta kawai tayi gaba ya bita a baya

Tamkar kurame haka suka zauna cikin Motar sai uban gudu da ya dinga tsalawa,yana tsΓ ida Motar yΓ  finciki Hannu salima Zuwa bangarenta,Samira ta dafe ka"oh ni Samira an shiga uku ta jama kanta"ta fita ta debe kayanta ta tafi,ita kam Fadila nata kayan sunfi qarfinta sanda haka sai ta kashe masa Motar da bai kashe ba,ta kukkulle Motar tayi nata bangaren

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/28, 7:59 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

              *Part 3*

               3⃣2⃣

Qarfe tara jirgin su zai sauka sanda haka tuni take as nasiru ya debe su sumayya yarda iftihal wadda itama tasha kit so da qunshinta Zuwa airport din,Fadila ce wa tayi Duke kawai,fitarsu ta shiga wa ka,cikin lokaci qanqani ta shirya kanta tsaf cikin dinkin Shadda buba orange colour mai combination da blue black sai zuba maiqo take da qyalli, ta maqala fashion na sarqa da dan kunne mai duwatsu da abun hannu suka blue black,sani azababben kyau tayi tamkar ka saceta,sai kace ba mai tsohoΓ± ciki ba,ko ina a jikinta qanshi yake zubawa

Zamanta na 'Yan mintina ta jiyo shigowar motar,ta saki ajiyar zuciya tana fadin"alhamdulillah",tsananin farinciki ya hanata miqewa Duk da irin dokin da take nayin tozali da masoyinta,shi kansa tunda suka dauka yaketa taba ido yaga ta inda fadilan tasa zata bullo

Sannu a hankali take takowa har ta iso inda suke tsaye ana fiddo music da kayan su,sallamarta ce ta maido hankalinsu kanta,aliyyu ji yake kamar ya rungumeta sai dai ya dake kawai,qaunart ce ke sake narkewa cikin zuciyarsa,ganin cikin nata yayi ya sake girma fiye da lokacin da suka tafi,Kallon juna suke cike da murmushi ta miqa hannu don amsar qaramar jakarsa bude da fadin"Barka da dawowa"ya noe kamar alamun ba zai bata ba"barks ka dai maman baby"
"Ba magana ne qanwarmu?"cewr Salima da ta zuba mata ido cike da boyΓ yyen kishi,da fara'arta ta waigo ta dubesu
"a'ah.....ina shirin gana wa da oga ne sannan mu gaisa,ya gajiya,kun dawo lafiya?"kusan tare suka amsa sai dai kuwa ce da yanayin da ta masa dan,hankalinsa gaba daya ya raja'a a kanta,Duk motsinta idΓ nunsa na kai,hakan ya sake qulla mugun qulli cikin Zuciyar salima da alwashi kala kala

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Da qyar take iya saga qafafunta,don idan tana tafiya tallafe cikin take,kinsan take kamar zai sauko qasa,gaba daya ta can za kamanninta sun sauya,babu yadda aliyyu baiyi da ita suje Dubai ko India ta haihu a can ba amma ta qiya,tace tafiso ta haihu cikin qasarta da danginta

Fada babu irin Wanda momy batayi ba akan ya dawo mata da fadilan gurinta amma Yaqi,sai dai kullum ya kalallameta da fadin halin zai kawota,batasan shi Baisan Fadila tayi nisa da shi bane,tun bikinsu sumayya da rabi'ah Momi ta so riqeta amma sai ya lallaba ya kai qararta gun uncle abba shi Kuma yace ta bashi matarshi,ta barsu idan sun shirya a nutse ya kawota,tunda ya samu ya dauketa yaqi maidota

tausayin fadilar Momi ke ji,kuwa ya kalleta saidai kaji yace"sannu,Allah ya raba lfy,anya yaro daya ne a cikin nan",to itama momin haka take zato saidai babu wanda ya sani,don ko scanning taqi yarda ayi mata ganin yadda aliyyu keta zumudi,har lallaminta yake taje ayi tace a'ah,kada ayi ma yaa rai kuma hakan bata samu ba,tunda suma hasashe ne sanin gaibu ai sai Allah,ya bari idan ta haihu ai za'a ga ma ko mene ne,tilas momi tasamo mata wadda zata tayata zama tunda taga babu alamu na aliyyu zai dawo mata da ita din,baba talatu cikin dangin Momi take,mace ce mai tsafta da nutsuwa kawaici d juriya,bata da sure t7n rasuwar mijinta,ganshi dama Allah bai bata haihuwa ba har girmanta,kakansu daya da marigayiya mahaifiyar Momi,Fadila na Mutuqar jin dadin zama da ita,tana taimakonta sosai ba a iya harkar gida ba ma kadai

Sai su su Samira sukΓ  tada tsiyar suma sai an nemo musu mai aiki,aliyyu ne ya musu Jan idan nan nasa yace da su shiru dinsu,baaba talatu tamkar kaka take agunsa,kada wadda ta soma kawo masa 'yar aiki gida

Taku hudu biya ta sake juyawa,da qyar ta samu tΓ yi hakan sau biyar don bin umarnin doctor sa'adah,tuni ta hada gumi sharkaf,cikin Dauriya irin tata ta juya ta shiga dakin baba talatu da ta kwanta yin qailula bayan sun gama hira tΓ  tadata ganin lokacin sallar azahar na qoqarin ficewa,ta farka ta dubi Fadila tana Mata sannu,ta amsa a kunya ce saΓ±naΓ± ta daura tata alwalar,a falcon Tatars da baban nayin tata,itama ta zube sannan ta tayar

Baba talatu na saman kujera tana jaΓ± carbi Fadila ta miqe tana fadin"yunwa nake ji baba sosai,kamar ba dazun nan na gama can ayabarba"
Baban ta kalli inda ta Ajjiye ragowar da ta gama ci"ai kuwa dai ga ragowar da Kuma rage can nama manta ban dauketa ba,maza ki cinye a barki ba dadi zama da yunwa,idan baki qoshi ba sai a dado miki"tayi murmushi tana dada qaunar baban,maca ce wayayya Duk d ba tayi karatun boko ba

Ta soma cin abΓ rta kuwa,Sam ta mance ba tayi bismillah ba saboda mahaukΓ ciyar yunwar da takeji,ta bare ta uku tana ci hankalinta kwance,dadi ya kama salima dΓ ke maqale tun dazun jikin window din balcony din ta fΓ dila,wani tsallen dadi tayi ranta da zuciyarta fes,tana qarewa surqumemen sirinjin dake hannuntΓ  kallo cike da farinciki Wanda ya taimaketa ta gabatar da mugun aikinta

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/28, 7:59 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

              *part 3*

               3⃣4⃣

Kimanin awa guda yana tsayen don ko sha'awar zaman baiyi har ruwan ya qare da suri nurse din da ai bari a dakin ta taso ta cire mata ta sanya mata dayan,cikin karaya aliyyu yabi saban ruwan da ta sa mata da kallo zuciyarsa cike da fargaba,sai dai kafin ya dauje idonsa yaji an damqe hannunsa dake cikin nata tsam tsam tmkar zata ballashi,da sauri ya kalleta still idanunta na rufe,a hankali numfashinta ya sima fita da sauri da sauri,wa ni bashi ta soma mai cike da wahala

Tuni nurses din suka danna wa ni Abu,cikin qiftawa da bismillah sai ga doctor sa'adah ta shigo,kanta sukayi suka soma bata taimako,aliyyu na tsaye cike da rudani,tausayinta da qaunarta suka sake Hawa a zuciyarsa,idanunsa ya sake kadawa babu hawaye sai azabar quna da zuciyarsa keyi ganin irin gwagwarmayar d take share,idanunta na rufe amma gunji take da nishi mai ban tausayi,hannunsa dake cikiΓ± nata har yanzu kamar zai balle

"Doctor idan babu dama wuyarnan ta isa haka,Gwara a yimata c.s a cire mata babyn ta hira mana"ta girgiza kai"Daga take da haihuwa,don zata ita haihuwa da kanta"tana rife baki Fadila tayi wani gauron nishi mai qaraji da yasa aliyyu ya sake rudewa sai ga baby ya fado,kukansa ya cike Daki,daya Daga cikin nurse din ta daukeshi,doctor ta taba cikin ganiΓ± fadilan na sakeyin wani nishiΓ±,sai ga kukan wani yaron shima ya taya dan uwaΓ±shi callara kuka
"Alhamdulillah"doctor sa'adah ke fada tana sake dubΓ  fadila

"Mtsweeu,inajin da wa ni yΓ ron a cikin nan"ta soma taya Fadila qoqarin fidda sauran abinda ya rage a cikinta kasancewar qarfinta ya qare,jikinta ya soma saki,da qyar aka zaqulo dayan Maca ce,sai dai ita din wani irin kuka take baya ma fita sosai bisa dukkΓ n alamu taci wahala don har ta fara kashi a ciki,kam wa ni gado doctor ta dorata aqalla mintina girma sannan ta dagota
"Sa'adiyya karbi zaitun ko lotion a goge musu jiki,baza'a yi musu wa ka ba har sai gone"tace da aliyyu Wanda baima San meke gudana a dakin ba ,kacokam hankalinsa na kan matarsa

Ya kalleta"ki nadeshi kawai doctor, bamu zo da komai ba"ya maida hankalinsa kan mΓ tarsa dake ta sakiΓ± ajiyar Zuciya,doctor ta Daga wayarta tayi kira tana bada umarni aje shop din cikin asibitin da yake nata ne a dauko riga unisex mai bude da showel guda uku,cikin qanqanin lokaci aka gogesu fed,doctor ta qaraso kaΓ±su,cikin damuwa ya kalleta
"Doctor taqi motsawa fa har yanzu"murmushi tayi "kada ka damu,mun riga mun kashe Duk wani tasiri na gubar ai zata dawo haΓ±kalinta insha Allah nan da wa ni dan lokaci,yanzu za'a gyara mata jikinta ne don tafi jin fadi,zatayi bacci na minti talatin da zarar ta farka zata koma normal,congratulations *Mr Aliyyu Salim mai tama*,ka Samu yara har uku,biyu maza daya mace"

Jinsa Kayi kamar cikin mafarki ake gayamasa hakan,wa ni sanyi ne mai dadi ke ratsa zuciyarsa,ya zaro idΓ nu"pls doctor bama irin wannan wasan,are you serious?"
"Am serious aliyyu,lokacin da suke isowa Baka ji ba?,gasu can ai"tai masa nuni da su banda macen da aka ware a wani dan gado daban,ya zuba musu ido yanajin kamar ba haka bane
"Kada a fiya daukan baby girl din,don ta bugu sanda mamanta ta fadi,ta fisu shan wuya,zamu riqeku na three days don zamu na bata treatment"

Mai karatu fasalta irin farinciki da wannan family gida biyu suka Shiga wato familyn *Alh Abbas Abdallah* da *Alh salim mai tama* bata baki ne,godewa Allah kawai suke suka qarawa da 'yarsu ta tsallake rijiya da bakya ga kyautar kyawawan yara har uku tare da sake addu'ar samun lafiya ga Fadila dΓ  baby girl dinta,Daki ne qato guda daya mai kyau aka ware musu aka zuba gΓ dajen yaran,aliyyun na zaune dirshaΓ± gaban gadon yana jiran farkawarta ,tuni ya miqa musu yaran bayan ya tofesu da addu'a,ai kuwa dan qaramin biki aka bude a dakin,shikam yana jinsu don ta matarsa yake tukun

Cikin ikon Allah ta farka da qwari a jikinta,da fuskar mijinta ta soma tozali,ya sakar mata murmushi yana fadin "sannu 'yar albarka"ta dan lumshe idonta cike da kunya,shi da Kansa ya taimaka mata ta wanke bakinta ya hadΓ  mata tea mai kauri ta sha,kowa saΓ±nuΓ±sa yake miqa mata

Dukka yaran ya Jere mata a gabanta yana dubanta"Fadeelah na kinga irin kyautar dΓ  Allah yayi mana ko?"kasa magana tayi,cikin zuciyarta godewa Allah take mai hukunta abinda yaso,kunyar su momi take wa sanda ba su San ma suna abinsu ba,da yaga taqi dauka sai ya debesu gaba daya ya dora mata saman cinyarta ya hadasu ya rungumesu gaba daya yana jin duminsu,tuni kowa ya fice a dakin sai juyowa sukayi suka ga Wayam

Fuskarta ta dago Daga kan yaraΓ± tana Kallon aliyyu,gira ya Daga mata yana cewa"kin yarda ni din jarumi ne ko?,Dukkaninsu da ni suke kama,baby girl ce kawai tayo kamar fatarki"sai tayi kicin kicin da fuska"ai zasu dawo kamata ne"ya tuntsire da dariya"inaaa......ai sai dai ki tara a gaba"
Gwalalo ido tayi"haba my haidar,ni kam na gama Daga wannan,wlh sun isheni"ta qarashe maganar kamar zatayi kunya
"No baby,ni Kuma wlh inason kamar haka sau shida,"fashe masa da kuka tayi,Dariya na ciΓ±sa yana lallashinta a haka Momi  ta shigo ta tadda su

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

           *part 3*

             3⃣3⃣

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"ta soma fadi tana riqe tamau d cikinta,cikin azama baba talatu tayi kanta tana tambayarta"lafiya?,me ya faru?"
Sai dai ina!,tuni kafin ta qarasa kanta ta rikito daya kan Kujerar da take zaune ta kifa qasa warwas kan turtsetsen cikinta cikin fitar hayyaci,da gudu baba ta qarasa gami da dagota,jirin ne ke fita ta qasanta da bakinta gami da ragowar ayabar d abata qarasa hadiyewa ba,ko kuwa babu alamun numfashi tare d ita,hakan ne y gigita baba talatu ta saki salati mai Mutuwar qarfi da nuna razana Wanda yasa salima juyΓ wa cikin sauri don barin gurin

Sai dai kafin Takai ga ficewa su Kayi kacibus d samira,tabi Salima da kallo ganin irin saurin da take zubawΓ  tuni har ta wuceta,ita kuwa salatin babarne ya janyo hsnkalinta don wucewa tazo yi,da sauri ta taka tq shige bangaren Fadila don ganin meke faruwa,dai dai lokacin baba jita kokawa da wayarta don Neman mutum daya cikin biyun aliyyu ko momi,abinda Samiran ta gani yaso bata tsoro,da Sauri ta juya ta koma da baya,batayi wata wata ba ta soma qwalawa isyaku kira,sun San halin rashin Kirki irin natΓ  don haka jiki na tmrawa ya iso
"Yi maza ka dauko Mota"

Bai tambayi ba'asi ba ya juya don cika umarninta,sanda ta shigo har baba ta gama Sanar da Momi,Samira tace"rashin maza baba mu kamata ku wuce asibiti kada ta zamar mana gawa my shiga uku gun Ali"(gaboncin magana kenan irin na samira),da ita aka sanya fadilar a Motar sai dai bata bisu ba,ta dawo tana tunanin me ya sameta haka?,dage kafada tayi don bata sani ba ta koma barandarta ta zauna tana nazarta yadda salima ta killed bangarenta tayi lakur a ciki,duk da tana jiyo tarin salatin da ma'aikatan gidan ke ta zubawa

Daga qarshe ta dauke kanta tana tsammanin shegen kishinta ne da yafi nasu ya motsa,Duk da lokaci lokaci tana tambayΓ r kanta me tayi a bakin window din?

Momy,Anty hauwΓ ,farida,Anty hafiza d rabi'ah da tazo gida duk su na cikin asibitin,hankalinsu ya kai qololuwar tashi,tunda aka shige da fadilan wa ni daki har yanzu shiru babu ita babu likitocin,a lokacin aliyyu ya shi go asibitin,wujiga wujiga kamar Wanda akayi wasan kura dashi,idanun nan kyawawa farare tas sun kada sun koma jazur,kai tsaye momi ya tunkara yana tΓ mbayarta ina fadilan ta Samar dashi sun shiga da ita,cikin rudewa ya soma fadin"ya za'ace daga cikin bana na sai irin wannan abu ,kuma ba naquda ba,haba don Allah"

Bana talatu tace"ni kaina abuΓ± ya dauremin kai,muna cikin hira fa sai salatinta naji"
"Baba ko wani ya shigo,ko Kuma kun bar qofa a bude?"aliyyun ya tambayeta
"Eh,tabbas ta dn fiya baraΓ±da ta tattaka yadda likita yace da ita,to kafin ta dawo lokacin ni na shiga ciki na kanta,to ina tsammani ta manta ta bar" qofar a bude,kai tsaye ya nufi dakin da aka shigar da ita din gadan gadan Momi na ta kiransa amma ko daya kunnensa baima ji kiranba har ga Allah

Kafin yakai ga qofar ta bude ,likitoci uku ne suka fito ciki yarda doctor sa'adah,tareta Aliyyu yayi da tambayoyi barkΓ tΓ i har ta rasa wacce zata amsa masa
"Cool down Mr aliyyu,my qarasa guΓ±su Momi",ganin tahowarsu yasa duk suka miqe suna tambayar me ake ciki?,doctor sa'adah tace"da farko dai mun gΓ no ayabarnan da taci tana dauke da gaba mai mΓ tuqar qarfi"
"Gaba!"suka hada baki gurin fada banda aliyyu DA yace"what?!"cikin qaraji"waye ya aikata min haka?,tabbbas ko waye bazan qyaleshi ba"

"Calm down aliyyu,yanzu ba lokacin wannan bane,lokacine na yaya za'ayi a tseratar da ita dΓ  abinda ke cikinta,kada su illata"ya sake tsare doctor din kamar zai dauketa gumi ne kawai ke tsatstsafo masa
"Ok doctor Meye solution?"
"Dole zamu qirqiro mata naquda tunda cikin nata dama ya isa haihuwa har yaso wuce watanninsa,mun sa mata ruwa indai ya qare aka sa mata wani yayi rabi bata haihu ba dole zamuyi mata c.s na gaggawa,sai ayi mata addu'a Allah ya rabasu lafiya"

Tuni kafin ta qarashe bayanintΓ  aliyyu ya shige dakin,tana kwance sambal bisa gadon sai uban ciki a sama tamkar an sake turoshi,idanunta a rufe suke ruf hancinta sanye d oxygen, kayan d asibitin ke sanyawa mai naquda ne sanye a jikinta,fuskarta luf luf tamkar zata yi magana,Zara zaran gashiΓ± idonta sun fito reras,sai dai babu wani Abu dake motsi a jikintΓ ,nurse biyu ne cikin dakin dayar na Gyara zanin da aka rufeta da shi Zuwa saman cikinta,dayar Kuma na tattare kayayyakiΓ± da sukayi magani da su

Zuciyar aliyyu ta karye gumi ya sΓ ke yanko masa,hankalinsa ya sake tashi,ya qaraso bΓ kin gadon ya sanya hannunshi cikin nata yΓ  zuba mata ido"Fadeelah waye ya yamin wannan aikin?me kuka yi masa ?,wanne zuΓ±ubi kuka aikata masa ke DA halittar da bataji ba bata gani ba,pls Fadeelah kada ki tafi ki barΓ±i,Kiyi qoqarin ci gaba da rayuwa da ni don Allah matata,wlh idan babu ke nima babu ni"shi kadai ke zuba sumbatun nurses na kallonshi,sai da ya gaji don Kansa yΓ yi shiru don wadda yΓ keyi don ita ma batasan yana yi ba....

*Mrs Muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

           *part 3*

     
             3⃣5⃣

a haka Momi ta shigo ta tadda su"a'ah,Ali mai Kayi mata ne?"cikin dariya yace",sai Momi don bace ina son kamar yaran nan sai shida"kunya ta lullube Fadila, daquwa momin ta wata masa "ja'iri kawai,amma dai Baka da tausayi ko?,to yanzu zan kora ka kuwa ka tafi gida"ya Daga kafadunshi duka biyun
"Momi na ba sai kun Kore ni ba ma tafiyar zanyi"sai Kuma yanayin fuskarsa ya can za"zanje na binciki yadda akayi poison ya shiga cikin ayabar nan,dolene Duk Wanda ya aikata hakan ya karbi sakamakon sa a hannu"

A hankali ta dago da kanta dake duqen"don Allah yaya kabar maganar nan,ni na riga na yafe tunda Allah ya bani ka fiya da kariyarsa,Wanda ba wayo ko dabararmu bace haka din"
"Shshshsh!,shut up, ni ban yafe ba,kada Kuma na sake jin bakinki a maganar don yanzu hurumina ce"
"Gaskiya Fadila ta fada,idan ka dage da bincike kamar ka yiwa Allah butulcin kubutar amma da iyalinka ne da yayi maka,sai dai Nima ban lamunci a qyale maganar ba saboda gaba,ya zama lallai ka qara matakan tsaro"

Koma wa yayi da baya ya zΓ uΓ±a yana jijjiga kai,ba yadda ya ita tunda Momi ta shigo ciki,wayarsa ya zaro yayi kira,ya soma magana inda yΓ  Daga qarshe suka ji yana bada umarnin a kawo masa c.c.t.v camera guda hudu Daga yau Zuwa gobe(hmmmmm,a juri Zuwa rafi da tulu debo ruwa,wata rana.......)

Kwana uku Fadila tayi ragal da ita har yaran,tamkar babu wani Abu da ya faru da su,tuni haihuwar Fadila ta karade ko ina,dangi da ba dangi ba,'Yan asibiti kam sunsha kallo yawan 'yan barka dake tuttudowa a kullum yasa ta qagu a sallamesu wasu ma fadila bata sansu ba

ga aliyyu dΓ  kulli yaumin yake bata kunya, Duk yawan mutane idan  yazo baijin kunyar rungumeta ko riqeta,sai dai su bude ido suya kuwa ya fashe ya bar musu dakin

Cikin kwana na hudu ne doctor sa'adah ta sallamesu,da yake safiyya ce Daga rabi'ah sai farida dake fama itama da qaramin ciki Duk sauran ba su qaraso ba,cikin motarshi pilot suka shige shi d yaranshi,yayi da rabi'ah d farida kuwacce ta shige tata don su rabi'ah ma sunyi mota suka bisu a baya

Sai da suka kuwa Zuwa titin gidansu taga ya dauke hanya ya sauya titi,ta kalleshi"kai da zaka shiga lamido crescent ya ka canza hanya?"
"Eh ina sani"ya fada mata yana murmushi,sannu a hankali ba tare da wata tafiya mai nisa ba suka qaraso

Baki ta saki cike da al'ajabin abinda take gani,wa ni irin mansion house ne da bata taba tsammanin d irinsa a qasarnan tamu ba,tun daga makekiyar get da zata maka hanya Zuwa ciki ta fara tsinkewa da lamarin gidan,har bakinta ya Gaza yin shiru
"Habiby wai gurin wa maka zo ne?"
"Gidanki ne fadilata"ya fadi yana kashe Motar

Har ya fito ya zagaya baya Inda yaran suke ya dauki babban d mai bai mΓ sΓ  ya rungume a kadarsa tana zaune dirshan cikin Motar sai da ya leqa yace mata
"Mummy 'yan uku fito mana ki dauko baby girl"

Binsa kurum take a baya tana kalle kalle kamar dan qauyen da ya shigo birni,gida ne amma gari guda,duk iya yadda kΓ ke tsmmanin kyau haduwa da tsaruwar gida to ya kai nan,fenti tiles furanni da hadi da roping da Kayi wa gidan duka fari ne,qyalli dΓ  qamshiΓ± sΓ buΓ±tΓ  kawai yake yi

Kai tsaye suka nufi daya Daga cikiΓ± part din dΓ ke kewaye dΓ  harabar gidan,qofa ce mΓ i kyawuΓ± gaske suna zuwa ya Danna wΓ ni maida ni cikin second biyu ta bude suka shige,makekeΓ± parlour ne Wanda ya lanqwame kujeru har set uku,mai karatu sΓ i na kammalΓ  rubutΓ  littΓ fin nan ban gama fasalta muku shi ba,don haka na bΓ r mai kΓ ratu ya fΓ sΓ lta abinsa,

Ya juyo guntΓ  a bayan ya kwΓ ntar da yaran ya karbi macen itama ya kwantΓ r sannan ya kama hannuntΓ  ganin yadda qwayar idΓ nuΓ±tΓ  sukayi raurau,baice mata komaiba ya ja hannunta tana biye d shi,ciki da bai na part din nata yake nuna mata,sama suka fara Hawa,parlour ne shima mai girma gaske sai dakunan bacci gida hudu,daya nasa ne daya nata,daya na yaran,daya Kuma safaya ne kawai,ita dai ido ta zuba,don Duk wa ni Abu na alatu da qawata gida da jin dadi babu Wanda ba'a zuba ba,dakin yaran kawai kansa abun kallo ne,dauke yake da wa su irin hadaddun gadaje na yara musu rumfuna

kowanne da drower dinsa mai zubin cupboard wadda ta kere rabin bango,cike dakin yake da Duk wa ni nau'i na kayan wasan yaran,sai many an frames masu dauke da addu'o'in tsarist maqale saman gadon kowa,idan ka dauke tulin kayan wasan babu surar photo ko daya a dakin,sai wata 'yar qaramar t.v plasma dΓ ke manner a bangon dakin tana fidda sautin karatun alqur'ani,sai c.c.t.v dake manner quryar dakin wadda hatta fadilan bΓ tasan da ita ba,luf luf dakin yake dai dai da buqatar jariri

sake riqota yayi suka sauko suka ratsa ta wani corridor baya ga faluka biyu da suka wuce,dakunan bacci ne guda uku baya ga kitchen store a parlour na biyu,sai kitçhen store public toilet a parlour na farko,daki na uku da suka shiga nan ma dakin yaran ne,gira ya Daga mata bayan ta kalleshi
"Nan dakin 'yan uku zasu dawo da zata kin kuma ajjiyen wasu ukun"
Cikin shagwaba ta soma dukan qirjinsa"Baka tausayi na ko?,ba momy tΓ  hana fΓ dΓ  ba"
"Sorry saΓ±yin idaniyata"ya fΓ dΓ  yana maida hΓ Γ±Γ±uΓ±sa ya rungumetΓ  a qirjinsa

Zaunar da ita yΓ yi gefΓ Γ± gadon,dΓ  Kansa ya dingΓ  dauko dΓ  wadansu irin akwatuna da batΓ  taba ganin irinsu ba,saida ya sauke 12 tana binsa d ido ba tare dΓ  tace komai bΓ 

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

             *part 3*

             3⃣6⃣

"Kayanki ne ke da yarana"ya fadi yana bubbude mata akwatunan gami da yi mata bayani nata uku yaran ma kowa uku uku
Shaqe suke da kayan na alfarma,musamman yasa ma'aikatan company dinsa na india suka fidda taswirar design din kayan ,design ne da sai nan da shejara mai Zuwa ma zasu fidda shi,ita kam ta rasa mai zata ce,da ta bude baki zata yi masa godiya sai yayi kicin kicin,hakanan taja bakinta ta tsuke jiki a sanyaye ta tayashi rufe akwatunan

Yasa hannu ya dauko wa ni qarami dake rude daban ya budeshi,wasu takardu ya fito da su ya dorasu saman cinyΓ rta
"Estate ne guda uku da dake ginawa cikin garin abuja,ga takardunsu nan na mallaka wa 'yan uku,sannan akwai wasu tΓ kardun na company na ne da kikaje rakani budeshi na China,Daga qarshe kika gudo kikΓ  barni"ya qarshe da sigar tsokana da ta bata kunya"na mallaka miki shi fadeelΓ  ke kadai kikΓ  fi cancanta ki mallakeshi,don kinsan sanadiyyar budeshi ce ta jawo kika haifamin wadannan taurarin"

Takardu guda hudu Kuma daya na shaidar mallakar motoci ne guda biyu,daya taki daya ta yaran na,ragowar Kuma ki cike min idan kin samu lokaci na central bank ne kada Kuma ki tambayeni me zanyi da su"

Zamowa tayi Daga kan gΓ don ta durqusa a gabansa
"Na gode mai dear,na gode na gode,bani da abun cewa face Allah ya biya ka da aljanna ya qara budi,ya raya maka zuri'arka"tafin hannunsa yasa ya rufe mata bakinta
"Ya isa Fadeelah,nike da godiya,don naji a jikina har yanzu ban saka miki irin halaccin da haquriΓ± da kika yi da ni ba"
Kanta a qasa tace"alfarma daya nake nema a gunka"
"Uhmm fadeta naji,don kinfi qarfin koma a gurina"

"Wannan kyautar dear tayi yawa,kasa na zama abar zargi ,kada ina cikin zama na ka jawomin wata fitinar ta daban,mun gode da kyautarka amma pls ka barsu"
"Idan mΓ  Momi kike ji ta Dade da samun zamansu,gani ma take sunyi kadan"
Ta girgizΓ  kai"Sam nasan momi sosai,ba ita nΓ ke wa ba,abokan zamana fΓ ?"
"Ina ruwanki da su?,su Haifa mana suga suma idan ban musu ba,wannan kyautatawa ce kina yimin dole Nima nayi miki,sama na yi musu dai dai tasu,na canza musu komai na part dinsu kamar yadda na yi miki,na basu kudade,na canzΓ  musu mota,to me kike buqata?"

Ta karyar da kanta"Duk da haka ina tsoron fitinΓ "sai ransa ya baci ,ya miqe ya kwashe takaddun Daga cinyarta,bai ce uffan ba ya maida cikin akwatin ya fita da su,duk sai taji ba dadi ta bishi da kallo

Kasa tashi tayi har sai da ta jiyo magana sama sama kamar a parlor din farko ta miqe ta fito,umminta ce da Anty hafiza da yaronta khalifa Wanda yaci sunΓ n abba su wato abbas sai farida da rabi'ah da suka Bari a baya,da sauri ta rungume ummin nata tana jin wata qaunar ta na shigarta,tunda tq haihu bata zo ba sai ya,wani hawayen dadi suka soma zuba,ita kanta ummin rungume fadilan tayi,Tasman 'yarta mai alkunya ce da zurfin ciki,tunda har ta ita rungumeta tabbas ba qaramin jin dadin ganinta tayi ba

Farida ta zauna gefan fadilan bayan ta gama zagaye dakunan da gidan
"Sister ki godewa Allah"
"Allah shine abun godiya"
"Gaskiya kam babu abinda za muyi sai godiya ga Allah da ya azurtamu da mazaje na gari"cewar farida
Hira suka dinga yi abun su mai dadi,inda daga qarshe farida Wanda babu ce kawai babu ta Dora musu abun ci,da daya da daya saiga 'yan barka ana rakosu,sai Murna ta zama biyu,ga ta samun qaruwa ga ta canza sabon gida

Qarfe uku Muhammad ya shigo da akwati yana fadin ummi taje inji abba zasu wuce,ai kuwa Fadila taçe ina ai sai ya shigo da kanta ta shigo da shi din,ya dauko yaran ya musu addu'a cike da alfahari da jikokin nasa sannan ya Ajjiye musu check na dubu Dari da hamsin kowa dubu hamsin hamsin,sai akwatin da ummin ta ciko guda biyu na kayan Barka na fadilan da na yaran,kuka kawai fadilan ta saka tana jin qaunar iyayen nata na sake daduwa a ranta,ita da farida suka yi musu rakiya har bakin Motar su

Haka Mubarak shima akwati gud ya musu,farida Kuma dinkakkun shaddodi ne da atamfofi na fitar suna ta yiw 'yaruwarta,haka Anty hafiza da ya ahmad kowa da nashi barkar,yara dai sunzo da wani irin alkhairi mai tarin yawa

_*ina labarin salima?*_

Bangaren salima kuwa tuni ta baza kunnuwa da idanu taga ko taji ta inda labarin Mutuwar Fadila zai fito kwana daya biyu uku shiru,a maimakon haka ma cikin kwana na ukun sai ta jiyo muryar Aliyyu na bawa na shiru umarni yaje company ya amso wa 'yan uku sleeping dress, da gudu ta fito tana fadin"ta haihu?"

A hagunce Aliyyu ke kallonta cike da mamakin yadda ta fito a forgive"eh ta haihu ta samu yara uku kuma duk suna cikin qoshin lfy"da sauri ta saura kanta don ganin irin Kallon da yake mata,ta waske"wlh hankalina a tashe yake tunda aka fita da ita,kai amma naji dadi"
"Eh shi yasa aka rasa Wanda zai bita a cikinku"
"Ba haka bane rudewa mukayi har suka tafi"

Tana shirin komawa ciki ya tsaidata"zan fita ki saΓ±ar da samira an jima na shiru zai zo ya maida sabon gida,ba sa8 kun dauki komai ba sai dai ko kayan sawΓ "ko amsawa bata iya yi bΓ ,shim a bai lura ba don ya rigata barin gun

Tana shiga daki ta Dora Hannu aka ta zunduma ihun baqinciki da takaici
"Wayo Allah na na shiga uku Fadila kin fice ni,kin gama da ni,yara har uku bama daya ba?,wlh bazan qyaleki ba"haka ta dinga Kuka shabe shabe kamar wata qanqanuwar yarinya tare da sake cin alwashi

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

             *part 3*

              3⃣7⃣

Ana saukesu  a harabar gidan Samira ta fito ta qarewa gidan kallo,gida ta saki
"Allah na gode maka,kyau nice a wannan aljannar?"ta kama habarta,sai Kuma ta dubi sashen Fadila da 'yan Baka suke ta kara kaina
"Wai Matar can ta haihu ne?"tayi tambayar ba tare da ta nemi mai bata amsa ba

Ko kula ta salima bata yi ba,don ji take kamar ta shaqeta,a son samunta tana gamawa da fadila Samira ce next target dinta,sai nasiru ne dake rufe Motar yace"ta haihu gajiya 'yan uku Allah ya bayar
"Iyeeee"ta fadi tana kama baki" gaba Samira tayi abinta ta soma gwada muqullanta har ta dace era bangarenta ta bude ta shige

Sai da ta gama zΓ gaye baΓ±garen nata sannan tace bari the bangaren fΓ dilΓ  taga jΓ riran da dai ake fada,haka nan taji t Kasa kushesu yaran sun mata sosai,turare qal da su tamkar diyoyin turawa,qaramar tasu ce kawai mai dan duhu,sai gashi ta dauki kusan minti tΓ lΓ tiΓ± kafin ta baro bangaren

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Tun ranar da aliyyu ya Baro bangaren nata bata Kuma ganinshi ba,Tun tana dan guntΓ  hakan da yawan jama'ar dake wuni zirga zirgar barka a shashen nata hΓ r ta qaryata hakan,don ko kiranshi tayi baya Dagawa,a ranar ne Momi ta kira ta tana mata nasiha me yasa zata maida hannun kyauta baya,ta bata haquri ka ba zata sake bΓ 

Qarfe takwas na dare baba talatu ta gama Gyara yaran tsaf cikin wasu irin hadaddun kayan bacci na jarirai turare qal duk iri daya sai qamshin turaren yaran su ke,itama shirye take cikin kwalliyarta wadda tafi zubi da amarya ba mai jego bΓ ,ta goye qaramar a bayanta,sai ta rasa yadda zata sanar da baban

da qyar ta daure tace"baba Zani in Kai masa su"
"To.....to amma kada ki Dade,don dazun ma ya shigo da kansa ya gansu"yana shigowa kenan ya gansu idΓ Γ± bata kusΓ ,ita dince bai nema yana nufi yayi fushi ne da ita

Sannu a hankali ta qarasa cikin Sa'a kuwa shi kadai ta taras cikin falon yana nutse cikin lausasan kujerunsa,falon lufluf yake sai qmshin freshner yake,sanye yake da jallabiyya blue black da tayi matuqar haska farar fatarsa,idanunsa saye da farin medicated glass dinsa

Ya dΓ go fararen idanunsa yana amsa sallamar tata,sai ya Kasa zama ya miqe ya karbi biyun hannunta ,ta sauna tana niyyar kunto masa ta bayan,tuni itama Yan karbe abarsa ya jerasu reras

Ya cakuli wannan ya taba wancan tamkar mai wasa da mΓ Γ±yan mutane,ido kawai ta zuba musu tana Kallon tsantsar kamar da sukeyi,sai da ta gaji da shariyar tasa don tun gΓ isheshin da tayi ya amsa yayi mata dif
"ranka ya dade ina mΓ gana"
"uhm......me kike fada?"ya tambaya ba tare da yΓ  dubeta ba
"hankali ka nake so pls"
"Ai kunne ke ji ko?"ya sake fada bai dubetan ba,sai zuçiyàrtà ta raunaña,da sauri ta rungumeshi ta baya tasa masa kukan kissa

Sai ya tsaya cak yana ajiyar zuciya,bata sani bane amma yΓ  fita shiga kewa,bai ita daurewa ba sai da ya rungumeta tsam a jikinsa yana lashe hawayen
"I missed you to much "yake fada cikin rudewa,tuni ta lura ya soma fita daga hayyacinsa,tsoro ya kamata tayi qoqarin zame jikinta,sai a lokacin suka ji kukan yarinyar,tare suka kai hannu don daukarta,aliyyu ne yayi nasarar daukartΓ  ya soma lallashinta har tayi shiru

Cikin lokaci qanqani suka shirya Kansu dama ance *fadan masoya hutu*,dama aliyyu mΓ zewa kawai yake
"Baby hassan din nayi nayi masa huduba d Muhammad, usainin Kuma Ahmad, qaramar tasu Kuma khadjΓ "tayi dariya tace"masu manyan suna ne ya kamata a basu nickname"
"As you wish my queen"
"To Muhammad Muslim, Ahmad aslam,khadijah Islam"tafi yasa mata
"Very good, that's my unique, komai naki mai kyau ne kin iya zabe,Muslim aslam Islam,Allah ya raya mana su"
Tayi fari d ido tace"ameen"

Kudi masu yawa ya bata yace ta riqe a hannuñta ,kada Kuma ta wahalar da kowa duk wani Abu naci ko na sha ko na rabo suna nan a shirye za'a kawoshi nasu yin amfàni da shi kawai,bata dà ikon cewa koma sai addu'a cikin zuçiya don godiyar ma ya hana

*Mrs Muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/28, 10:50 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

            *part 3*

             3⃣8⃣

Mai karatu fadar irin shagalin sunan da aka sha bata baki ne,sai dai an ci ansha masu guzuri sun diba har suka suka bari,abunci indai na qasar Hausa ne babu Wanda ba saka samu ba,an rabar gidan kurkuku d na nakasassu d masu rangwamen gata,masu kinsan qwarya a ranar da yawa sun samu rabauta,don aliyyu bai yadda maza sun shiga musu cikin hidima ba,hatta da masu hoto video coverage mata ne

Atamfofi,set na food flask da na jug,jakankuna na mat ra purse masu axabar kyau,agoguna na hannu da na bango,gyalulluka coolers kai kayan dai gasu nan barkatai har yawa sukayi,ka dibi son ranka Kayi gaba,guri na musamman aka warewa *HUGUMA novels reade*,sunyi kyau a gun cikin shiga ta alfarma,kowa sai tambaya yake su waye wadannan?,aka karramasu,sun Kansu sai yau sukΓ  sake kashe qwarqwatar idonsu suka San wace Fadila a gun aliyyu

Cikin ikon Allah taro ya water lafiya,salima na bangΓ ranta zazzabi mai zai na bakin Ciki ya rufeta *huguma novels readers* sun so ganinta nace kada kuje Ku qarasa ta Ku zo mu tafi,

Jaridun washegari kuwa shafin farko hotunan yaran ne an rubuta da manyan baqi *'YAN UKU KYAUTAR ALLAH,DIYOYIN HAMSHAQIN DAN KASUWA ALIYYU SALIM MAI TAMA*

***        ***     ***    ***

_*RANA DUBU TA BARAWO*_…………

Misalin takwas ne na dare bayan ta gama shirin kwanciya,haka ta shirya yaran yadda  ta saba cikin kayan baccinsu,kuwa ne t bashi nono ya qoshi,cikin lokaci anqani bacci yayi a won gaba da su,ta saka kuwa ne cikin gadonshi ta ka musu net din dake saman gadon

Kasancewar ranar ba ita ke da aliyyu ba yasa suka su na samun har baba talatu,ganin sunyi bacçi yasa ta jà musu qofar dakin ta shiga dakin baba talatu don suyi hira kafin lokacin baccinsu yayi

Sadaf Sadaf ta dinga takawa har ta nisa ga jerin dakunan baccin su,ta Kasa kunnenta sosai ba motsin kowa hakane ya tabbatar mata su na sama,cikin dakiya qarfin hΓ li da son cimma buri ta kama step din ta haye,kai tsaye ta nufi dakin yaran,ta tura qofar a hankali farinciki ya cikata ganin ta taki sa'a babu kowa cikin dakiΓ±

Jikinta na rawa ta qarasa bakin gadon ta Ciro muslim ,hannu tasa a wuyanshi ta kwatanta shaqeshi,sai kuma ta tuna zai iya tsala Kuma fa,ta jawo blanket din da aka lullubeshi ta wurgashi bayanta ta Goya shi,ta kifi daya gadon ta zari aslam ta sabashi a kafadar hagu,ta sake gaba ta dauki Islam cikin sassarfa ta fice daga dakin tana waige qirjinta na dukan uku uku har ta samu nasarar zagayawa can bayaΓ± gidan inda tafkeken swimming pool dinsu yake

Dai dai lokacin fadilan ta fito zata komΓ wa dakin yaran ta dauko wayarta da ta mance kan gadon aslam,tayi mamakin gaΓ±in qofar dakin a bude,bata kawo komai a ranta ba sai tayi zaton aliyyu ne ya shiga,don wani lkcn idan ba rΓ Γ±ar girkinta bane kafin ya kwanta sai ya zo ya gansu ya daukesu daya bayan daya ya rungume Yadi da kissing nasu

Ba Aliyyu cikin dakin wayam Kuma babu aslam bisa gadoΓ±shi,cikin sauri ta soma dune dube,wasa-gaske sai ta rasa Islam da Muslim,a gigice ta fito tana qwalawa baban kira,ta fito tana tambayarta lafiya,a rude take gaya mata
"Jeki gun babansu ko shi ya daukesu"
Duk d bata jin hakan don aliyyu baiso a dinga fitowa da su cikin sassarfa qirjinta na wani irin bugawa ta sauko qasan ta nufi sashen aliyu

Samira taga giftawar mace da goyo Zuwa bayan gidan nasu,tayi mamakin wace haka cikin dare,sannu a hankali take binta sai taga Muslim ne Ashe a goye a bayanta,da sauri ta tΓ ko don ta cimmata,saidai kafin ta qaraso din ta daga aslam ta cillashi cikin swimming pool din,yaron ya canyara qara iya qarfinsa yayi qasa,abunda ya razana Samira Batasan lokacin da ta saki razananniyar qara ba cikin firgici

aliyyu dake zaune cikin balcony dinsa yana jiran samiran ta kawo masa file din da ya aiketa tΓ  dauko masa file cikin mota qarar ta ratsa kunnuwansa,da sauri ya miqe ya nufi inda yake jiyo sautin,fadila da taza gurinsa taga wucewarsa ta rufa masa baya gabanta na ci gaba da biyu

Da sauri ta warce Islam da take qoqarin jefawa,cikin razana Salima ta juyo ta kalleta don batayi tsammanin akwai mahaluqin da ya ganta ba
"Ashe ke tsinanniya ce azzaluma,muguntar taki har ta kai da zaki iya kisa"ta fada cikin tsoro da firgici gami da mamakin taurin rai da Zuciya irin nata

Yana qarasowa idoΓ±sa ya kai Kansu,wata iriyar mummunan faduwar gaba ce ta ziyarci Fadila ganin Muslim goye a gun salima,Islam a Hannu samira
"Yauwa don Allah kayi sauri ka shiga cikin ruwaΓ±nan ta jefa aslam ci........"
Kafin ta qarasa fadi tuni ya tsunduma ciki cikin wani irin nau'in tashin hankali,minti biyu kacal ya ciro yaron,

Suna tsaye cirko cirko Fadila na rungume da Muslim Hawaye ne kwance male male bisa kuncinta ,yayin da Islam ke a Hannu Samira,salima kuwa na tsaye tana bari kamar wadda aka sheqawa ruwan qanqara a tsakiyar hunturu,tuni fitsΓ ri ya gama bata ta,Kallon da aliyyu yayi mata yasa a take wata gudawa mai dumi ta balle mata,zuciyarta ta nemi tarwatsewa saboda tsananin tsoro da razani

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 9:51 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

              *part 3*

               3⃣9⃣

Wani lafiyayyen mari ya sakar mata wanda yasa jinta da ganinta ya dauke na wucin gadi sai gata ta zube a qara warwas

Babu numfashi ko alamarsa a tattare da aslam,hankalinsu idan yayi dubu ya tashi,asibitin doctor sa'adah tana masa gyare gyare saboda haka suka wuce kai tsaye d shi *get-well women and children hospital* dake rijiyar zaki,asibiti ne mai kyau saboda haka suna Zuwa aka rufu.kan yaron,sun kasa zaune sun kasa tsaye,Zuciyar Fadila tayi rauni matuqa,qauna da tausayi irin ta da da mahaifi ta dinga taso mata,Hawaye ne kawai ke sintiri kan fuskarta ta kasa controlling din kanta,tana jin wanne irin laifi ta yiwa salima har haka da zata yi mata irin wannan hukuncin?,me ta state mata a duniya?,don kawai sun hada miji daya?,Samira ce mai dan bata baki

Aliyyu kam bai ma tantance a wanne halin yake ba,mintina talatin doctor ya fito,d sauri suka tunkareshi Tun kafin ya kai ga qarasowa
"Doctor ya ake ciki?"
Ya danyi Jim sannan yace"saidai Kuyi haquri,munyi iyΓ  bakin qoqarimmu,amma Allah bai qaddara........"
"Doctor! Doctor!, numfashinsa ya dawo"cewar daya Daga cikin nurse din,da azama likitan ya juya ya koma cikin dakin,Kasa jurewa aliyyun yΓ yi ya riga masa baya

*Zakaran da Allah ya nufa da cara* cikin ikon Allah suka samu ya far fado numfashinsa ya daidaita,nan suka bashi gado dakin mutum daya,kafin lokΓ ciΓ± tuni salima ta jima cikin cell

Duk Wanda ya zo dubiya sai yayi mamakin rashin imani irin na salimar,domin ana zaton wuta ne a maqera sai aka sameta a masaqa,tuni jikin samira yayi sanyi matuqa,Duk iskancinta abunda salimar tayi yayi Mutuwar dau4e mata kai,don a zahirin gaskiya ba zata iya koda kwatanta hakan ba

Lokacin da salima ke musanta abinda ta aikata aliyyu baice komai ba,na'urar c.c.t.v din ya dauko,inda take Adana bayanan ta ya shiga,tiryan tiryan har shigowarta cikin dakin ta bayyana har yunqurin shaqe muslim,wannan ya zama hujja mai qarfi a gurinsa,mataki mai tsauri ya dauka a kanta,inda yasa aka sakaye ta babu Wanda ya isa ma yΓ je ganinta,babu yanda iyayenta ba suyi da shi ba yasa a fito da ita ko kotu ne suje akan ajiyar da yasa aka yi mata amma yace ina bai da lokacinta,koda zaiyi shari a da ita a yanzu ma to sai yaronshi ya warke,don Tun ba yauba take yin yunqurin kisan kai tun Daga kan 'yarta iftihal

ya tabbatar ita tayi poisoning din fadilar a baya,ya sake gasgata hakan fada masa da Samira tayi ganin da ta yi mata a bakin window din fadilΓ ,ya sake hada hujjarsa da irin firgicewar d yaga tayi lokacin da yake Sanar da haihuwar fadilan

Tun suna bashi umarni cikin gadara har suka dawo lallashi amma fir yaqi sauraronsu sai suka dinga biyowa ta gun Momi da suka fuskanci abun na yi ne,
"Babu ruwa na don bani na Haifa musu dan ba,haqqinsu ne ba na wa ba"haka ta sanar da su,suka yita Neman uncle abba da suka ga babu nasara ta bangaren Momi to shi bΓ ya qasar ma ya tafi turkey duba company dinsa na yin carfet dake can

Duk wuni gu Wanda suka San za'asa aliyyu ya fidda salima sunje amma abun yaci tura *sawun giwa ya take na raqumi*,ba su da dukiyar da zasu kara da shi,bai bari an saketa ba sai da yasa tayi attachment na wata uku cikin gidan yariπŸ˜‚,zama ne na azaba da aiki mai tsanani,ta Fige ta palace kai Baka ce Salimar nan bace,nan ma cewa yayi shari'a zasu fara uncle abba yace ya barta hakan ma ko don 'yarsu iftihal,Kuma Allah ai ba azzalumin bawansa bane,zai musu sakΓ yyΓ  walau a duniya ko a lahira

Cikin station din da aka dawo da ita ya barsu,yana shirin bude motarsa ta tareshi,yaja da bΓ ya saboda wani shegen tsami da take bugawa,ta zube a gabansa tana ya yafe mata sharrin shaidaΓ± ne"
"Ta riga ta wuce,idan ba hakan ba ai da baki isa ma ki tsaya haka a gabana ba,Kuma shaidan din dake zugaki kinga ai Abu yayi kyau kenan ko?,abinda zan baki shawara kada ki kuskura ki sake yin gaba da gaba da ni,idan takΓ darki ce kuma already na danqawa d.p.o babu Kare bin damo"

Kafin ta sake ce wa wani Abu tuni ya shige motarsa ya bule mata idanu da qasa ya wuce abinsa,a take a nan ta sulΓ le ta fadi sumammiya ,bata tashi farkawa ba sai a gadonn asibiti,ta farka tana surutΓ i da buge buge
"Ni aliyu zaiwa haka akan Fadila da tsinannun yaranta?,to wlh sai na dau faΓ±sΓ "sai da aka zurkuda mata allurar bacci aka samu sa'ida

***      ***    ***    ***

Rayuwar gidan ta soma sauyawa,wata nutsuwa ce ta zowa samiran, son yaran take sosai,Tun Fadila na Dari Dari har ta sΓ kar mata jiki,cikin lokaci qanqΓ ni tad fuskanci babu abinda ya cuci samirar illa tsantsar jahicin ilimiΓ± addini da shΓ idanun lqawaye dake zugata,amma baya ga haka bata da wata illa

Aliyyu kam ya daukewa Samira wuta matuqa da gaske,don yace itΓ ma bai yarda dΓ  ita ba,Mara baki ma ya aikata ina ga mai baki,kuka ta dinga yi masa tana rantsuwar wlh ko kaza ba zata iya kΓ shewa ba,har tausayi ta bawa fadila,ta dinga masa mita kan ya dainΓ  yi mata haka,ita ta sashi ya siyowa samirar littattΓ fan addini ta samu lokaci tana karanta mata,tun daga kan su ahlari,qawa'idi,iziyya,arba'una hadith,umdatul ahkam,usulus-salasa dadi makamantaΓ±su qananu wadanda za suyi mata sauqin fahimta

*_SHIN MENE MAKOMAR RAYUWAR SALIMA ANAN GABA?_*

*_SHIN YA RAYUWA ZΓ€TA KASANCE TSAKANIN SAMIRA DA ALIYYU?_*

*_RAYUWAR GIDAN ZATA DORE A HAKA_*

*_amsar sai 'yan mutan huguma,kuci gaba da haqurin bibiyarta mun kusa da yardar Allah_*

Cikin ikon Allah ta soma fahimtar rayuwar da take abaya rayuwa ce mai cike da jagwalgwalo da qazanta,tabbas rashin ilimin addini ciwo ne da bashi da magani,makanta ce da ka iya yima mutum jagora Zuwa ga halaka,haka nan duk ilimin zamanin da ba'a hada nemansa da na adidni ba sunansa kwado ko Kuma ince jahilci,sannu sannu kuma zai iya kaika ga ramin da zaka gaza fitowa,ilimin dadi ni gaske ne da kullum yake zamowa dan jagora ga rayuwar bani adam

⚜⚜    ⚜⚜    ⚜⚜

Da aliyyu ya ga Fadila na Matsa masa kan Samira sai ya shirya musu tafiya su d yaran,da tayi magana sai yace honeymoon zasu da ya alqawarta mata kafin ta haihu,qasashe biya suka je,suka fara da saudiyya,Turkey, Egypt, Spain suka qarqare da u.k

Honeymoon kam an shashi babu qarya,jiki da Zuciya duka sun huta,watansu hudu a can alokacin su aslam na da wata biyar suka dawo,ba 'ya'yan ba hatta da iyayen sunyi bul bul fatarsu ganin sha'awa,aliyyu aslam da Muslim da suke farare sun sake haske tamkar ka taba su jini ya fito,Fadila kuwa da Islam fatarsu wuni lumi lumi ta sake yi,da wuni dan haske na hutu da jin dadi

Sosai yaran sukayi wayo,sun San ummin su sunsan abbansu,idan ka ga su sai ka rantse sun ninka watanninsu,bula bula da su,ga wuni she gen kyau da kwarjini da su ke dashi,hakan ya sanya su ke da farinjini,duk inda suka shiga kaga ana sha'awarsu da son daukarsu,maman ni su daya saka su ukun,babu ta inda suka baro aliyyu photo copy dinsa ne illa Islam da ta biyo fatar babarta,sun samu uwa gwanar iya tsΓ fta son qamshi da kwalliya,zanso mai karatu ka ga wannan family mai ban sha'awa

⚜⚜    ⚜⚜    ⚜⚜

Ranar da suka dawo da daddare bayan ta yiwa yaranta wanka itama tayi sun shirya su Kayi kwanciyarsu nan cikin dakinta kan gadonta,baba talatu Tun randa suka tafi tace itama zata gida,babu yadda Aliyyu baiyi ta zauna ba tace LA,LA,LA,

Ya turo qofa dakin ya shigo da sallama yana hararar fadila,ta ams masa tana Daga gira alamar mene ne?
"Kinbi kin kwashe min yara,kun barni ni kadai kamar wani mΓ raya,ko tausayi na baki ji"
Ta danyi dariya cikin lanqwasa murya
"banda abunka gun matarka fa zaka,Meye na Neman yara,me za suyi maka,abinda tun dazun sukàyi baçci"
Harara ya manna Mata mai dauke da salon so,ya soma qoqarin haurowa kan gadon yana ce wa"bari ni na kawo kaina tunda ni baqin jini ne d ni ba'a nemana,bayan nima in buqatar a rungume nin,ba su Islam kadai ke so ba"

Zuba masa ido tayi bayan tayi kicin kicin da ranta,sarai ya lura da ita amma ya share ta don yasan tatsuΓ±iyar tazo bata wuce ta qoqi,ya janye Islam dake kwance saman qirjinta ya ajjiyeta kusa da 'yan uwanta shi Kuma ya maye gurbinta
"Abbu(wani lokaci haka take kiransa,saboda haka tashi yaran sun fara gwarancin kiransa),me yasa kake son yana ka zama haka bayan da ba haka kake ba,yaushe rabon samira d kai,nifa tsawon wata hudu muna tare,me yasa kake son janyomin zargi da zagi n........."
Ya katseta ta haΓ±yΓ r fadiΓ±
"Masu zagin naki suje su yita yi,tunda ba su isa suyi a gabanki ba kinga Kansu suke batawa lokaci"Daga haka ya hana ta furta komai

⚜⚜    ⚜⚜    ⚜⚜

Da safe shi da yaran na zaune a living room Duk sun karade gun kai kace wasu masu shekaru ne,dukkansu tsaf suke sai qamshi suke kamar yadda gidan nata ma baki daya yake kasancewarta wadda bata wasa da tsafta,cikin kitchen take tana hada musu breakfast don sun saba basu karyawa da wuri

Samira ce ta shigo da sallamarta,sanye take da atamfa dinkin riga da zaΓ±i,kanta lullube da mayafi,tsaf da ita duk da babu make up tΓ mkar ba ita ba,ta qaraso ciki aliyyu aliyyu na riqe da hannun aslam suΓ±a ta qyaqyata dariya yayi dama dama da yoghurt har fuskarshi

Kallo su take cike da sha'awarsu,ta karbe Hannu aslam Daga gunsa ganin ya rasa yadda zai da shi yaron akwai hanzari,gashi yana ta qwalawa Fadila kira tayi banza da su ya sani fushi take tun jiya,gyara masa jiki tayi tas,ta dawo tayi zaune cikinsu tana masa wasa yana bangala mata dariya

Ta dire kwanukan abincin bayan ta fito Daga kitchen din tana Kallon yadda suka bararraje su na biyewa yaran,sai taji ma kunyar samiraΓ± ta kamata
"Lallai kam,sannunku kun samu aiki fa"
"Ina ruwa wuni,tunda mudai bamu ce ya zo ya taya mu ba"Tasan tsokana yake sonyi sai taqi Kallon Duk da nacin son ganin qwayar idonta d yake,ta maida kanta gun Samira su na Gaisawa,har ga Allah taji dadin ganin canji sosai gun samiran,don kafin tafiyarsu bata bari karatunta ya yanke ba,da kanta taje *Darul hadith* ta yanko mata foam bangaren kayan aure weekend kawai Tun Daga aji daya

A nan ta sauko musu da break din sukayi tare,samiran ta tayata suka gyara gurin har kitchen ta bita ta tayata suka wanke kayan suka dawo parlour din,tana lura da yadda aliyyu ke ta jifan fadilar da kalloΓ± qauna tana share shi,addu'a take cikin ranta Allah ya bata haihuwΓ  ko ta samu kwatar son da aliyyu ke wa fadila(hmmmm,batasan abun Daga Allah bane)

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 9:52 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

           *part 3*

            4⃣1⃣

Ya miqe bayan ya kwantar da Islam da tayi bacci aslam da Muslim nata wasan su gun Samira
"Madam tazo a shirya ni ko, zan fita"ya fada Kansa tsaye yana wuce wa cikin bedroom sonta,share shi tayi taci gaba da hirarta da Samira don ta fuskanci so yake ya bata kunya,bata Ankara ba sai ji tayi anti sama da ita sai bedroom, zillo ta yi ta dira daga hannunsa

Cikin harara take ce wa"mene haka abban islam?"cikin gintse dariya yace
"Lallai yarinyarnan,ni zan kira ki ki wani jamin aji?,zaki San da Ali haidar kike"yayi guntΓ  gaba daya,ba zata ita hana mishi farincikinsa ba don haka ta qyaleshi ya share budirinsa,bayan sun fito wanka Kuma ya tsareta yace babu inda zata sai ya gama shirya wa sa fito tare
"Amma fa mun bar su Muslim da mummynsu a falo ko?"
"Basa nan"kawai yace da ita yana ci gaba da shirinsa tayi zaune kuwa taqi taya shi sai kumbura take

Tana kallonshi yana kici kicin saka socks da takalmi,dariya ta so qwace mata amma ta maze, ta gama shagwabashi koma ita ke masΓ  a yanzun bai iya koma ba,ya lura da ita d9n haka ya lakuto cream mai yawa ya yaba mata a kumatu,ta juyo tana sake hade rai kamar gaske
"Kin bata ni da yauwa,shirya ka ina ma yanzu gagara ta yake,ke Kuma kin zauna kina min dariya ko?"bata San lokacin da ta fas he kuwa da Dariya ba ganin yadda ya wani mΓ rairaice mata,sai ta hau shirya shi kamar yadda ta saba

Da suka fito falon babu kowa,aliyyu ya leqa dakin yaran sai Islam kawai da ke ci gaba da baccinta nisa gadonta,da a lama su na gun samirar,har Mota ta raka shi kamar yadda ta saba,yace su shirya anjima idan ya dawo zaya kΓ isu su Gaida momi,ta ams masa na siru ya ja Motar suka fice,sai da ta leqa sashen samira ta tabbatar suna can tace"yauwa mommyn su aslam,tunda su na nan bari nake na fidda kayan tsarabar can"
Murmushi tayi "ba Matsala idan kin gama sai Kiyi kirana ,dama ina son ganinki,sirrin tsafta kwalliya da kula da miji nake so a bani"
Murmushin itama tayi mata"to shikenan ba Matsala"ta juya ta fice tausayin Samira na damunta tare da jin rashin dadin yadda aliyyun Yaqui sakewa da ita

Momi ta rasa inda zata sai jikokin  da surukan nata,iftihal 'yammata Duk ta rude anga qanne sai ta dau wan can ta Ajjiye ta dau wannan,Daga momin har uncle abba sunyi mamakin sauyawar Samira,suka sake addu'ar Allah ya kade fitina yaci gaba da hada kansu,tsaraba sosai ta yiwa Momi da iftihal har da uncle abba,sai goma na dare suka tafi

ya ajjiye mata yaran ya fiya da niyyar bada umarnin a kulle gida,tuni kafin ya dawo ta kulle sashenta,Tun yana danna bell har ya dawo bugu tayi masa biris,wayarta dama a kashe take tilas ya haqura ya koma,da safe tana Kallon yarda yake aiko mata da saqon harara,ta share shi kawai tana dariya,don idan bata yi masa haka ba sai a shiga haqin samira,Daga qarshe sai da yasa yadda yayi ya biyota kitchen taci zalinta"gobe ma ki kuma"yace da ita

Wannan karon ziyarce ziyarce sukai har Maiduguri gurbin hajja gaΓ±a,farida ta so Zuwa saidΓ i babu dama sanda tsohoΓ± cikin da take dau ke da shi,sai humairΓ  ta bada aka tafi da ita,tayi Sa'a kuwa ya zo a daidai bikin diyar qanin abba,aka sha biki da ita,kuwa sha'awar Fadilan yΓ ke,Duk inda ta gifta sai ta fita daban cikin mutane,wanda ma ya Dade bai ga Fadila ba yau ya gaΓ±ta har da 'yan uku,don idan Baku manta ba farida dama na mata tsiyΓ r kafin rijiyΓ  ce,ba Zuwa take sosai ba faridan ta fita zuwΓ 

*Mrs Muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 9:54 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?......*
      🌺🌺🌺🌺🌺
*_CONTINUATION_*4⃣1⃣

Da qyar ta cinye kwana biyar aliyyun ya azalzaleta ta dawo shikam ya gaji haka nan,gidan ya zama masa kango,haka suka dawo cike da farinciki don ta faranta wa danginta sosai su Kuma suka cikata da tsaraba

Rayuwa mai kyau da inganci mai cike da tsaftatacciyar Soyayya ce ta kewaye aliyyu d iyalinsa,tana ita bakin qoqarinta na ganin ya saki jiki sosai da samirar sai dai har yau bata kai ga cimma ga ci ba,Duk da ya rage wasu abubuwan

⚜⚜    ⚜⚜    ⚜⚜

Cikar Muslim aslam da Islam shekaru biyu samira ta hada musu gagarumin birthday party,ita kam fadilah nata kallo don tuni suka maida ta 'har Kallon,wannan Abu na daya Daga cikin abinda ya s aliyyun ya sake dan saukowa d samirar,don su Kansu yaran sunyi Matuqar sabo da ita

⚜⚜    ⚜⚜    ⚜⚜

Suna gadon baccin su bayan sun gama komai na shirin kwanciya,duka yaran na gun samira don yawancin lokuta idan ranar Fadila ce to ita ke kwashesu tace zasu tayata kwana

Envelope aliyyu ya miqa mata bayan ya hade girar sama da ta qasa,ga bata ya fadi tabi envelope din da kallo,cikin sarqewar Murya tace"n......na meye.....wannan?"cikin tsawa yace "bude mana ki gani"cikin rawar jiki ta sure ta ta farke,dan qaramin ihu ta saki,ta Daki tsalle ta daneshi,Duk ta rude,shikam dariya yake ta mata har da qwalla wait da har idan guntΓ  sun fito waje sunyi hudun na su Muslim,Sam bata bai ta kan tsiyar da yake mata ba,foam ne na jami'ar Bayero university degree na biyu zata yi kan mass comm

Ya dubeta bayan ta natsu"ki dai na yimin godiya my life,har yau inajin ban saka miki irin tarin alkhairi da haqurinki gareni ba"haka an aliyyu yake mutum ne mai rama alkhairi komai qanqantarsa,cikin nasara karsashi qarfin gwiwa da nishadi ta soma karatunta
,bata da matsalar koma,yaran samira ke kula mata da su,idan lecture ta fado a weekend itama samira na da Darul hadith sai su taba ita ta dau biyu ta bata daya,ganin haka ma sai Aliyyu ya niqi gari da kansa ya tafi gombe ta tattago baba talatu da taqi dawowa,d year ta amince ta biyoshi,don tace bata son zama tsakiyar rayuwar auren yara

Ganin haka yasa cikin gidan Daga can baya aka zuba fasalin irin ganin gidajammu na ga gajiya mai tsakar gida da dakuna aka yi mata nata gidan Duk da ce wa akwai part din da salima ta bari da Kuma wani spare daban amma tace bata sonsu sun mata zamani da yawa,dariya Fadila da samira suka dinga mata tace eh ta ji

⚜⚜    ⚜⚜    ⚜⚜

Cike da nasara Fadila ta kammala karatunta,ta fito da kyakkyawan sakamako cikin makarantar,hutun sati daya kawai tayi aliyyu ya baro musu tafiya China,bata ga passport din samira ba a ciki dama tuni baba tace ba zata ba ita kam indai ba Garin ma'aiki ba,da ta matsa masa da tambayar na samiran ko ba'a buga mata visa bane,sai yace ai ba wuni dadewa za suyi ba,ka ita zaiyi ta diba kamfaninta na can da ya bata,sai wuni daban da zai bude a kwana daya

Tubure masa tayi har ganin samiran,murmushi tayi babu damuwa a tartare da ita"Kuyi tafiyarku abba Islam rabu da ita,ranar da zaki tafin ma Samu fara jarrabawa,kinsan Samu shiga s.s one mun zama seniors ba raini"

Sai ta bawa fadilan dariya,har yanzu fadar magana kai tsaye da calikancin samira na nan tare da ita,sai dai wannan karon yana tafe ne da burbushin ilimi

*_INA SALIMA NE?....._*

Ku biyo ni masu karatu............

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 9:56 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

          *part 3*

           4⃣2⃣

*ina salima?*

Qunci da baqinciki babu Kalar Wanda bata ji ba shi cikin zuciyarta,na farko rabuwa da abinda tafi so Duk duniya wato aliyyu,na biyu Kuma rashin cimma burinta na raba fadila da 'ya'yanta daga sheqar iskar duniya,gash a yanzu babu wata kafa da zata sadata da cikar muradin nata

"Akwai mana"shedaniyar zuciyarta ta gaya mata
"Kiyi auren kinsan wuta kawai sai ki koma gidan ko ta gajiyar asiri ne ya maida ki ko bai cikin hayyacinsa"
Tashin farko ta nemi auwal tsohon saurayinta sukayi yarjejeniyar auren wata guda kacal,da sharadin ba zai kusanceta ba(kaji wata kwamacala)

Ba tare da ta gama idda ba aka daura mata aure,tun daren da aka kaita ta soma gane kurent,kwana auwal yayi yana Abu daya,Duk bakin tsiwa da rashin kunya ya mutu murus,haka nan tana ji tana gaji ya gama budurinsa,dama auwal ya dade yana sha'awarta,taqi bashi hadin kai ne Tun farko saboda tana ganin ta zarta ajinsa,sai kyau ya samu cimma muradinsa

Wata daya na cika ta same shi da zumudinta ta tunasar da shi lokacin rabuwarsu fa ya cika,wata mahaukaciyar dariya ya bushes da ita sannan yace
"Amma bansan ke daqiqiya bace sai yau,in banda ke mahaukaciya ce kina tunanin zan sake ki ne?,to ki sani Kinyi kuskure,auremmu kuwa mutu ka taba takalmin kaza"

Miqewa tayi a fusace tace"tabdi,lallai auwal ka ga dama ta,to wlh bari kaji,ko Baka qaunar Allah sai na bar gidanka,ai Kaine babban mahaukaci,banda haka ai ko makaho ya Shafa ni ya shafaka yasan nafi qarfinka wlh,ni ba'a halicceni don nayi zΓ man aure da kowa ba sai aliyyu jar......."
Gif!,tashi a bakinta,kafin ta qarasa tuni auwal ya dunqule Hannu ya Daki bakin,tuni gurin ya haye ya suntume jini yace salami alaikum,bata gama tantance barnar da yayi mata ya bita ya turmushe ta da duka tamkar wanda ya samu qato dan uwansa

Tun tana qoqarin ramawa har ta dawo sai zagi,qarshe bakin ma ya mutu,sai da ya gaji don kansa sannan ya qyaleta,ya dago yana haki
"Shegiya qaramar 'yar iska,ke har kin isa ki bude kice na sakeki ki koma gidan wancan dan iskan da na sha wuya a hannunsa saboda ke,to gobe ma idan kin cika 'yar iska ki Kuma yimin makamanciyar wannan maganar,ke da fita daga gidan nan sai dai a fidda gawarki"ya tsallaketa ya fice abinsa

Sai da taci kukanta ta qoshi sannan ta ja jikinta sannan ta hada kayanta a trolley tayo waje,sai da tazo har soro saidai abun mamaki tayi tayi ta fita ta Kasa kamar wadda aka daure da Sarqa,a ranar dai tayi yunqurin fita ya kai sau ashirin amma da zata ta zo soro sai tashi kamar an riqeta,qarshe ta fas he da kukan baqinciki ta zube a soron tana hango wajen amma ta kasa fita,

Anan ya dawo ya tarar da ita,dariya ya fashe da ita"yarinya kin makara,ai ba zaki ita fita ko ina ba ba tare da izini na ba,hakanan babu Wanda zaki ita ga yauwa halin da kike ciki,wuce don uwarki ki bani abin ci na,idan Kuma ba Kiyi ba ki dafa min yanzu yanzu ko ki ci ubanki wlh"

Cikin wata biyu ba izayar da salima bata gani ba,gashi ko Karen gidan su Yaqi Zuwa,bata sani ba auwal ne yasa aka kadar da hankalinsu,ko tunaninta basu yi

A hankali cimar gidan ta canza sai qarma qarma kawai,auwal a qarqashin wini alhaji sabo Alfa dake cikin kasuwΓ r kantin kwari yake,ya dade yana cutarsa ta hanyar sace masa manyan kudade yasa an rufe masa ido bai gane ba,auwal bin malaman tsubbu gunsa ko mace ta shafa masa lafiya,da kudadeΓ± yake burga cikin Garin tamkar ubansa wani ne,daga baya da Allah ya yake alh sabo ya gane ya koreshi kudin Kuma da ya sata din da yake ba ta hanyar halal aka samesu ba maimakon ya tattala sai yaci gaba da harkar banza da holewarsa da su har suka soma qarewa

Allah qadiran Ala may yasha'u,cikin hikima ta Allah sai ga cikin auwal jikin salliman,sai Allah ya dora mata son cikin,tana son ganin gudan jiΓ±iΓ±ta a yanzu tunda ta fuskanci rayuwar na dab da juya mata baya,sai dai inaaa.....ba'a yiwa Allah wayo,domin a baya taqi cikin a lokacin da uban dan keson abinsa,to a wannan karoΓ± Kuma  sai ta so cikin a lokacin da uban cikin bai buqatarsa

Har gida auwal ya dauko wani inyamuriΓ± likita har da kayan aikinsa,ya danne masa salima yayi mata allurar kashe baki,tana ji tana gani aka zurmuqa mata qarfe aka zuqe cikin,kai qarshe ma yasa aka gutsire mata mahaifar ma dungurun gun,a cewarsa bai da buqatar wata haihuwa,ta rasa lokacin da zata fara haihuwa sai lokacin da ya fara fama da kansa.......

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 9:56 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*_continuation_*4⃣2⃣

Saura qiris salima ta bar duniya amma da yake akwai sauran shan ruwanta a gaba sai ta warke,tayi kuka tayi nadama da Dana sani maras iyaka,taso kashe Fadila da 'ya'yanta sai gashi ita tana eaten amma tayi Mutuwar tsaye,taqi ta Kuma wulaqanta kyautar da Allah yayi mata lokacin da ya bata cikin iftihal,aliyyu ya biya da lallashi sai ganshi yanzu da uwarta da ubanta aka bai aka zage sannan aka qwaqule cikin ,maimakon ma ya dauki iya ajiyarsa sai da ya hada da ajiyar Allah yasa aka guntile mata mahaifa

"Ashe dama haka rayuwa take?,Ashe Wanda yaqi zaman gidan aurensa ya rains matsayin da yake kai ya butulcewa ni'imar Allah yaqi daukar ixina ta ruwan sanyi duniya zata biyar da shi?

A yanzu take sake qaunar gudan jinin nata qwaya daya tilo iftihal,Ashe ita ka dai ce qwanta a duniya?,ta yima aliyyu  addu'a sosai da ya tsaya tsayin dauka ya hanata yasar da cikin iftihal din,da tuni ta tashi a tutar babu kenan?,qaunar 'yar take sosai sai dai ta sani babu qaunarta ko daya a Zuciyar yarinyar Wanda ita ce sula ita ta haifar da hakan,wannan shi dake kira da Dana sani qeya ce

⚜⚜    ⚜⚜    ⚜⚜

Wannan ce rana ta qarshe Kuma company na qarshe da aliyyun zai qarasa bude wa ,dukkanin yaran nata uku sanye suke  cikin sutura iri daya sai dai su maxan na maza ne Islam Kuma na mata ne haka aliyyu ke sawa ana musu,tuni Muslim da aslam suka saje cikin fararen fata su da abbunsu,Fadila kuwa shigar babarbariyar usuli tayi (kanuri)cikin lafiyayyar laffaya maroon tayi mata kyau matuqa,sosai ta burge mutanen sin har wata Daga cikinsu mr.shengping ta Kasa shiru har sai da ta yaba family din na su

Ahankali bai sake yiwa kanta ba sai da aliyyu ya anshi microphone
"A kyau ina farinciki gabatar muku da mata ta,farincikin rayuwata,zuciya ta jinin jini na,Fadeelah aliyyu Salim"
Tafi suka sa kowa so yake yaga fadilar nan da wancan karon ta ruda Mr aliyyu,dai dai da dai dai take ba wa Matan hannu suna musabaha maza Kuma su na gaisawa ne kawai ta wuce,kallonta aliyyu yake kawai ganin yadda take sarrafa harshenta tamkar haifaffiyar qasashen turawa,bata fiya yiwa yaranta magana da harshen nasara ba don suna yi a maka ranta,tafi yi musu larabci ko barbanci,shi Kuma ya musu fulatanci don su tashi da ainihin yaransu na uwa da uba

An tashi taro lafiya baya ga kyaututtuka da suka samu masu tarin yawa Daga abokan kasuwancin aliyyu,direct gidan mukhtar (abokinsa)suka wuce,a can suka ci gaboncin dare,Fadila na tare da matarsa Aisha suna hirarsu abinsu,Islam tayi bacci ita da Muslim,aslam Kuma na gun abbansa a parlour su na lissafe lissafe kan company din Fadila da irin ribar da aka samu

riba ce mai tarin yawa,da Kansas mukhtar ya shiga ya kirasu fadilan,sun soma mata baya nin irin ribar da aka samu,Tun tana dauka har kanta ya gaza dauka,sai ta sai kuka irin kudaden da dake ambato mata sunfi qarfin kanta,ace kamarta ba 'yar wani ba ta mallaki irin wadannan kudaden a matsayin riba.......

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 9:56 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

            *part 3*

              4⃣4⃣

Ya duba littattafansu na makaranta dayake wuni lkc shike dubawar,ya taimaka musu sukayi assignment, da suka bude na Arabic don son ya tsokaneta sai yace"kai kai 'yan uku wannan yafi qarfina,wannan ai sai balarabiyar mamarku,Ku kai mata maza"
Suka kwashi littattafan sai aslam ya noqe jikin abba nasa don tsoron zuwan yake ji,

Ta kalle su ta dan zare musu idanu
"Yalla Ku tafi gun abbu ya qarasa muku,Nima ban iya ba"suka juya gunsa din kuwa,yadda ta musun sai ya sosa ransa,sai da suka gama ya musu brush ya suya musu kayan bacci ya raka aslam gun samira sannan ya dawo
Tsaye yayi a kanta hannayensa harde saman qirjinsa"me kike nufi da abinda kika yiwa yaran nan?"

Ta dubeshi,sai ta Dakota da shan fruit salad dinta
"Me kuwa nayi musu?"
Sai yaga ta ma raina masa wayo,cikin hasala Zuciya ta tunzura shi yace
"Kinga malama,idan Kema baki sonsu ki fito ki gaya min,ina da inda zan kaisu dama ni na saba ganin hakan,ba kanki farau ba"
Za can ya qona mata rai,cikin gatse tace"shikenan,ka kaisun inda kake so din"taci gaba da shan fruit salad dinta

To Ashe bata sani ba ta tada masa tsohon miki,don haka ransa ya dugunzuma,ya ranqwafo wait in fuskarta"oho......alright, to wa ya sani ma ko ke kika hana kanji sake dauka ciki tsowon wadannan shekarun don wadannan ma baki sonsu ko?"
Wani wal tayi da idanunta ,batasan lokacin da bowl din fruit salad din ya subuce Daga hΓ nnunta ba,mai aliyyu ke nufi?,zarginta yake yi ko me?,a guje tayi bedroom dinta saboda wani kuka da ya qwace mata

Yana tsaye a gun ya bita da kallo,jikinsa yayi sanyi,sai yace jin baiyi furucin da ya dace ba,sautin kukanta da ya soma ji sama sama ya sashi zabura ya nufi dakin,saidai kafin ya kai gareta amai yabqwace mata,ta kuwa dinga kwarashi,Duk sai da tayi aaman fruit salad din da taci,gaba daya ya rude fadi yake"am sorry my queen, sannu kinji"shi ya gyΓ ra gun ya sai Mata ka6an bacci,Duk fuskΓ rshi ta canza kamar zai sai mata kuka,haka shim a ya gama nasa shirin baccin ya jawota ya manna ta da jikinsa,

Kalaman ban haquri yake ta jeranta mata,sai dai taqi ce wa kanzil,kai Daga qarshe ma sai ya juyata yaga ashe tayi bacci,ya sauke gajiyar Zuciya ya sake rungumeta yana jin rashin kyautawarsa har cikin zuciyarsa

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 9:57 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?.....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*CONTINUATION*4⃣4⃣

washe gari asabar ce bai tashi da wuri,hakanan bai fita da wuri sai kusa da wajen azahar,don haka ta lallaba ta gama aikace aikacenta ta fice gun baba talatu wadda ta dawo a Daren jiya,nan suka shiga hirarsu tana bata labarin tafiyar da tayi

Ko da ya farka bai ganta ba yasan tana can,sukuku ya shirya don ya saba ita ke masa komai,wuraren  daya ya daga Waya ya kira nasiru yace yaje ya dauko masa su Islam daga gidan momi wadanda da sassafe suka addabeshi sai da aka kaisu,Fadila na jinsu bata ce musu komai ba a lokacin

Hannunta riqe da kwanon zogalen da da baba ta kwadanta tana ci suna hirarsu cikin nishadi har da dariya, ganin shigowarsu kawai tayi suna rigen rigen fada wa cinyarta banda aslam da ya rakabe,batayi tsammanin dawowarsu haka da wurwuri ba,sai yaron ya bata tausayi amma sai ta dauke kai,don kaxa na take ranta ne ba don bata sonshi ba don ta koya masa darasi ne, duka yaran suka gaidata suka Kuma gaida babar kamar yadda ta saba musu Gaisa babba,shima aliyyu suka Gaisa yayi mata sannu da hanya tare da tambayarta mutan garin

Sai ya kalli baban yace"baba Zuwa mukayi ki taya mu roqo,'yarki muka yiwa laifi Kuma taqi yi mana afuwa"
Baban ta kalli Fadila"a'ah,ni kam na San 'yata bata da riqo,ba shakka laifinku mai girma ne,me kuka yiwa diyata?"
Da sauri Fadila ke girma aliyyu inkiya da ido na yayi shiru don Allah amma Sam sai yaqi kulawa
,"baba,aslam ta daka har jikinsa yayi shatin bulala,Kuma suka shige ciki suka barshi a waje,to nayi fada ne har ya wuce kima,na gane kuskure na na bada haquri amma anqi yafe mana,sai ake mana horo da halin ko in kula"

"Ashsha,ashsha,ya akai haka ta farun?"ta maida tambayar ga fadila,cikin raunin muurya tace"baba yanzu ace fisabililahi kamar aslam idan yayi laifi baza'a hukuntashi ba?,yaron nan sau hudu yana fasamin wayoyi,rashin jinsa duka ya zarta na 'yan uwanshi,ga raini,ya raina Muslim,har fa sai yasa hannu ya dakeshi,haka Islam ma bata tsira ba,dan qanqanin Abu zata masa yasa hannu ya maketa bayanshi babu mai dukanshi wai baya son raini"

"Sannan da ance za'a hukuntashi baban ya hana,to don kawai fa rannan na hukuntashi suka dau fushi ya kwashe kayanshi ya maida gun mominsu,qarshe ma harda cemin wai wa ya sani ko......"sai ta kasa qarasawa hawaye ya subuce mata,ai bai san lokacin da ya isa gareta ba,hannayensa ya sanya yana dauke hawayen,sai baba ta yunqura ta miqe ta fice tsakar gida,don ta lura abun nasu salon maganar nan ce da ake cewa *fadan masoya hutu ne ko sunyi zasu dawo su shirya*

Yayi Kane Kane ya hana hawayen zuba"kada ki yimin haka mana Fadeelah ta,na riga na yima ka ina alqawarin fa ba zaki sake zub da hawayenki ba,kinsa alqawari na ya karye?,jiya Kiyi daya kyau kinyi,ina jin zuciyata cikin qunci duk sa'ilin da naga hawaye a fuskarki,pls ki yafe mana,ni da 'ya'yana bamu saba ganinki haka ba kina hukuntamu"
Sai ya juya gun yaran ya kira su da hannu"Ku zo mu bawa mamee haquri"ai kuwa suka yaso da saurinsu duk suka durqushe a gabanta yadda suka ga abbun na su yayi

Muslim yace"pls mamee kiyi haquri kinji mamin mu"
Islam tana riqe da kunnuwanta tace"sorry mamee,pleaseeeee"
Aslam ya taso ya kama qafarta"mamee na na dai na bazan sake ba,kince annabi nabda haquri Kema Kiyi maker pls,I promise bazan qara ba,Duk abinda kika ce nayi zan dinga yi kanji"
Sai suka suka bata tausayi,ta Miqa musu hannayenta suka taso Muslim a hagu aslam a dama Islam ta dane cinya,ta dinga shafa Kansu tana cewa"na yafe muku,Allah yayi muku albarka"
"Ameen maman mu mana sonki"
Ta saki murmushi"Nima ina sonku yarana"

Aliyyu dake kallo su cike da sha'awa ya Matso yana turo mata kansa"Nina mamee a samun albarkar"cikin hararar Soyayya take kallonshi
Sai ya kwabe fuska shims kamar tarin"kunga maminku taqi shafa min kaina ko?"
Nan suka rude da ce wa mamin mu a shafawa Abbu shima,dariya tayi shima ta shafa masan

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 9:57 AM] My Mom: * 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

               *part 3*

                4⃣5⃣

Sai lokacin baba ta dawo,taji dadin ganin sun sasanta kansu ,nan taja hankalinsu su duka har yaran,cikin gamsuwa sukayi mata godiya
Ya kalli fadilar cikin marairaicewa"to ataimaka azo a yimin Garin pepper chicken din nan mana mai dadi, ni da abokaina duka zamu tayaki aikin"
Ta noqe hancinta tace"a dauri kashi ko a bata igiya,babu abinda kika biya sai qara wa mutum aiki"da sauri Islam ta kalli mamin nata tana nuna kanta da yatsa"banda ni ai ko mamee?"
"Har ke mana"jin haka yasa su Muslim suka qyalqyale mata da dariya,sai ta kwabe fuska ta soma diddira qafafu kan Dariya da su Kayi mata,aliyyu ne ya taba fadan ta hanyar daukarta ya  sabata a kafada aka tafi yin paper chicken din baba talatu ta musu a dawo lafiya bayan sun mata tayi Zuwa tace lazumi zata yi sai sun dawo,islam tace zata kawo mata qashi,Duk suka sa dariya

Haka suka cikata da surutu cikin kitchen din,ba ga yaran ba ba ga babansu ba,aiki dai na surutu kawai suka tayata ta,har ta samu ta gama ta tura musu,ya tasa yaranshi a gaba bayan kowannnensu ya wa ke hannu suka soma ci cikin plate guda

Sai da suka ci kusan Rabi sannan ya dubeta tana zaune gefensu tana lura da yanayin can abincin yaran nata,Duk Wanda ya gutsuro kafin ya ci sai ya miqawa abbunsa, yaran na da matuqar son iyayensu
"Ke baki ci ne mamee?"
Ta zumburo baki "sai da ya rage saura qasusuwa wannan za'a yimin tΓ yi?"
Sai suka soma rige rigen bata a baki,kuwa yana ce wa nashi zata ci

Murmushi ta saki tace musu duka ta gode,Allah ya yi musu albarka ita ta qoshi,taci zogale gun baba,aliyyu yayi qasa qasa da Maurya bayan ya dubeta"anya baby na lafiya qalau kike?,ina lura dake rashin son cin abincinki ya qaru akan na ainihi,fruit salad kawΓ i kike bawa muhimmaΓ±Γ§i,anya ba wani cikin gareki ba?"

Kai tsaye ta Daga masa gira tana murmushi,cikin zumudi har baisan sanda ya daga murya ba yace"are you serious baby?"
"Yes"tace da shi cikin wata iriyar murya mai taushi
Ya lumshe ido a fili yace"alhamdulillah,alhamdulillah"
Sai ya tara yaran yana fada musu sun kusa yin qani,ihun murna da tsalle suka dinga yi abbun na su na biye musu,ta saki murmushi bayan ta dau ke idoΓ±tΓ  daga Kansu
Gaba daya aliyyu ya maida yaran abokanshi"

⚜⚜     ⚜⚜     ⚜⚜

Rayuwa mai cike da jin dadi amunci da qauna suke yi cikin gidan,tuni ganin gidan rediyon Fadila yayi nisa,Wanda bai da nisa da qatuwar islamiyya da dake gana wa samira wadda totally yanzu ta can a idan ka gantΓ  zakayi mamakin yadda ta sauya,ilimin addini sosai ya ratsatΓ 

A nurse aliyyu ya zauΓ±Γ r da Fadila yayi mata ba yamin abinda yasa yake ma Samira haka duk da a yanzu ya soma daidΓ itΓ  lamuran,yana son ya gane turban muzuru tayi ko na gaske,saboda canza mutum haka lkc guda sai Allah,zata iya zama da shi cikin kowaΓ±ne irin halin kamar yadda ita fadilan tayi a baya?,ta Kuma shirya can a tsarin rawarta ta xamo ta dace da ra'ayinshi da tsarinshi?,
"Hakan ya tabbata ai tunda ga zahiri kana gani ko"
Tace da shi

Cikin ikon Allah Fadila ta dauka lafiya,ta samu qatotoΓ± lafiyayyen yaronta Wsuna yaci su na *ABUBAKAR ASSADDIQ*,don su abba ba masu damu wa da wani takwara ne ba

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 10:01 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*CONTINUATION*4⃣5⃣

_*BAYAN SHEKARU GOMA*_

dukkaninsu Fadila,aliyyu,aslam,muslim,islam ,saddiq,umar,usman,iftihal,suna cikin filin wasan da aka tanada cikin gidan domain wasanin motsa jiki,sanye kowannensu yake da kayan sport farare qal,table tennis ake ta bugawa tsakanin Fadila Islam iftihal da Kuma team din aliyyu da ya qunshi aliyyun kanshi muslim aslam,faruq da sadiq ne a gefe su na tilliqa dariya ga duk wanda aka ci,basu da bangare

Ganin dai da gaske su aliyyu na shirin basu kashi yasa ba shiri fadila ta radawa iftihal yake tavtaho da mommy(samira) don itama gwanar table tennis ce,sai kuwa gata tsaf a shirye cikin kayan sport din,su aslam suka sa dariya,aliyyu yace"Duk Ku gama taron danginku,kun sani mune winners ba yau aka fara ba"
"Wlh kuwa abbu"inji aslam

Cikin ikon Allah sai su Fadila suka cinyesu,gufa ya rude iftihal tace"shikenan daddy,mume da ikon zabar qasar da za'aje hutun qarshen shekara"tavfadi tana yiwa su Muslim dariya don ra'ayinsu ya ban bata,haka suka haqura da akaxo dinner suka zaba,wannan karon a Africa za suyi don haka iftihal ta zabi South africa,samira ta zabi Ethiopia tana son taje taga garin da sarki najjashi ya mulka,suka tsara tafiyar kuwa da tafiyarsu saudiyya sauke farali

A Daren aliyyu yasa Fadila ta kira farida tace"gobe driver ya kawo humaira ta tayi da passport dinta za'a buga mata visa din qasashen da zasu,tunda tuni abbanta ya buga mata ta saudiyya,jinin aliyyu ya hadu da na yarinyar sanda kama da takeyi da fadilansa,shi yasa duk hutun da su ke fita da ita ake tafiya,ko unguwa fadilan zata wani lkc ta fita da humairar da Islam sai ayita dauka humairar ta Haifa ba Islam ba,don ita Islam da abbanta tayi kama

Duka family ukun da su aka saukre faralin bana,yarda Anty hauwa da iyalinta,scan ne Fadila ta so lura kamar amai wani Abu tsakanin iftihal da Muhammad(qaninta)sai dai bata tanka ba,ta barwa ranta ne idan lokaci yayi zasu nuna kansu

Daga saudiyya suka wuce hutunsu na qasashe biyun Hutu Kayi mai dadi sosai,Hutu ne da Iyalan suka dinga ji dama kada ya qare,ciki yarda samira domin tuni aka 'yantΓ  ta,sai dai ta riga ta sani ta Kuma saddaqar Fadila ta riga ta yi mata fintikau,tayi mata zarrar da ba zata iya kamota ba ta kuwa ne ganin,saidai ita kanta tana jin dadin yadda tayi wata ta canza,Allah ya nufe ta da gane gaskiya tun lokaci bai qure mata ba irin yadda ya qurewa salima,tana Kuma sake yin addu'a ga Fadila don kaso casa'in na gyaruwar rawarta ita ta bada gudunmawa

To Tun a can Fadila ta soma jin canje canje a jikintq,sai dai tayi shiru da bakinta,suna dawowa gida duka sai suka kwanta ciwo ita da samiran,til as doctor sa'adah ta ziyarci gidan,bayan gwaje gwaje ta shaida musu *duka su biyun suna dauke da ciki*,kuka Samira ta dinga yi haiqan tana gode wa Allah cike da yabo na yadda bai dubi halΓ yenta ba na baya da kurakurenta ba ya azurtata da samun qaruwa

Kasa zama Fadila tayi Duk da jirin dake dibanta sai da ta taho bangaren samiran,ta rungumeta cike da farinciki,jin sumbatun da samirar keta yi ya sanya ta hanata magana tace
"Shi Allah babu ruwansa,Mutuwar Kayi tuba tuba mai kyau to zai gafarta maka zunubinka komai yawansa ko da shirk a ce indai Baka mutu kana aikatawa ba"
Tsananin farinciki ne ya rufe aliyyu,Duk da yaran dake gabansa amma ninkinsu yake buqata,taga kulawa Daga kuwa wadda bata taba katarin gamo da irinta ba

*Mrs Muhammad ce*πŸ‘‘

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 10:01 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

            *part 3*

              4⃣6⃣

Haka suka dinga rainon cikinsu,sai dai Samira lamarin sai a hankali,yau da lfy gobe babu,wata bakwai daidai cikin nasu samira ta soma wani irin ciwo Wanda ya tilasta yi mata c.s aka cire mata yarinya mace aka sanyata a kwalba,saboda yarinyar tayi nauyin da mahaifarta ba zata iya ci gaba da daukan yarinyar ba saboda laushin da tayi

hakan ne ma yasa bayan cire yarinyar aka juya mata mahaifar don doctor tace Duk lokacin da ta sake dauka ciki tayi wata na cikin hadari,za'a ita rasata gaba daya,mahaifarta tayi rauni sakamakon maganin hana daukar ciki da zubar dashi data dinga dirka a baya ba bisa qa'ida ba

Sosai Fadila ta tausaya mata,don kika ta dinga yi mata,irin wuyar da ta ci tamkar ba zata tashi ba,don har ta soma barin wasiyyar abinda ta haifa din a hannun fadila,don ta sani ita ka dai ce zata biya bata irin tarbiyyar da take so kamar yadda ta bawa yΓ ranta

Cikin ikon Allah ta warke sumul taci gaba da shayar da diyarta Fatima(zuhra),ba dadewa aliyyu yasa aka soma gina mata super market qato ne sosai,bayan kammalΓ  ganin aka zuba komai ciki ya soma aiki yΓ na dauke da sunΓ n *zuhra maitama shopping mall*

Wata goma sha daya wannan karon fadila ta santalo 'yan matanta kyawawa guda biyu,wannan karo sai dayar tayi ta sak tamkar humairar farida,dariya aliyyu ya dinga yi mata"babe kinga da daya fa kika tsira cikin yara takwas,to ban sani ba ko a gaba qila ki sake tsira da gudΓ  ko?"
Ta bata fuska"gaba dear,gaskiya ni na gama haihuwa kam daga wannan ai nayi qoqari,idan na ci gΓ ba da yi ai sai na lalΓ ce kaga kaji dadin auro mana wata ko"

Lakuce mata hanci yayi yana qasaitaccen murmushin nan nasa da har ysu bai barin fuskarsa Mutuqar yana tare da fadilan tasa"ban taba ganin Mace iriΓ±ki ba baby na,ko yΓ ushe qara miki kyau ake tamkar ba ke kika haifi wadannan zarataΓ± ba har takwas"
Kallo mai cike da qauna tayi masa "har na kaika?,ni fa har tsoro ma nake kada wata ta qyalla ido ta qwace mana kai"
Dariya ma ta bashi"indai wannan tsoroΓ± kike to ki kwanta kiyi bacci harda minshari,ni aliyyu ba kowacce Mace a gabana zuciyata da ruhina sai ke,Duk kallo su nake tamkar maza 'yan uwana"
Sosai maganar tasa ta fasa mata kai

Take ya yiwa yaran huduba da sunan umminta amina,dayar Kuma yama faridanta takwara kamar yadda mubarak ya yiwa fadilΓ rsa takwara,hakan ya faranta ran fadilan,Islam ta musu laqΓ bi da *afrah da amrah*

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 5:32 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

          *part 3*

            4⃣7⃣

πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰ 🎊🎊🎊 πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰

*_HAZAS SAFHAH,KAS SASAHU LI WALIDAYYA_*

*ALH ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*HAJ SALMA MUHAMMAD LAWAN (SARKIN DOGARAN KANO)*

*my lord,have mercy on them both as they did care for me when I was little, ameen*πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»

 
Bayan ya shigo ta nemi gafararsa,Fadila ta hanata gaya mishi komai,shi dai yace ya yace,godiya ta dinga masa tana zub da ruwan hawaye
Da suka tashi tafiya tamkar ta busy haka ta dinga ji sai dai ina ba hali,ta dinga rings su da kallo cike da sha'aea yadda 'Yan Mayan keta karakainar duba gyaran gashin su jikin mirror

Fadila tace ta sameta a gida bayan kwana uku don gobe da jibi basa nan,ta danqa mata rafa ta 'yan Dari biyar biyar guda daya,godiya ta dinga mata tamkar ta kife

⚜⚜     ⚜⚜     ⚜⚜

Ranar juma'a ce,Duk a parlour din Fadila ake haduwa aci abincin rana bayan sakkowa sallar juma'a matuqar ogan na gari,tana kitchen ita da 'yan matan ta tana ba su warmers plates da cups su na kaiwa kan dining suna shiryawa,ta cake cikin kwalliya tamkar ba Daga jikinta wadannan 'yan mata da samarin suka fito ba

Samira ta shigo ta tadda ta cikin kitchen din,itama tayi kwalliyarta,Kallon fadilan take tayi har suka hada idan,murmushin Fadila tayi don tasan da magana a bakinta
"Mamee fadila na rasa irin wannan sirrin kyau da Γ do naki,har yau na gaza kaiwa inda kike,dole kisa oga ya dinga susucewa gaskiya,I salute you na haqura"ta fadi tana Sara mata irin na sojoji,dariya fadilan tayi ganin yadda ta qame,tuni ta saba da wannan abun na samira,ta sauke mata hannun gamida riqeta
"Muje dining don Allah momyn yara oga na jira idan na biyewa wannan barkwancin naki sai mu kwana nΓ n"

Cikin barkwanci hira mai dadi irin ta familyn da suka fahimçi junà suke cin abincin,kowa tsaf yake cikin kwalliyarshi,sai dai kam aliyyu babu adon Wanda ya burgeshi irin na tauraruwar tasa fadila,sallamar da aka kwada sau biyu cikin falon taja hañkalinsu,tuni aliyyu ya Ajjiye lomar abincin da ya Kai bakinsa,samira kuwa zumbur tayi ta miqe dafe da qirji ido a waje,Fadila ce kadai ta kalleta da sakakkiyar fuska ta kuma sauko daga dining area din tana mata marabà

"Me kika zo yi gida na?"aliyyu ya fada cikin Daga murya take jikin Salima ya hau bari,don har kyau ba5a manta Waye aliyyu salim maitΓ ma ba
"Ko kin biyo su ne a yaΓ±zun ma ki dauka ki kashe?,ina mai baki shawarar ki fice Tun muna shaida juna,don baki da alaqΓ  da kowa a cikin gidannan"
"Wlh kuwa kada ta cuce mu ba,ta cutar mana da yara"inji samira da ta Kasa zama
Fadila ta dan bata fuska tana kallon su"gaba Abby pls mana"
Shima ya sake hade rai"cewa fa nayi ta tashi ta fice,tunda dai ai ba gidan su bane"

Cikin son kau da haΓ±kalin yaran fadilar tace"kuzo Ku gaida mamarku"
Tsawa aliyyu ya daka musu,sum sum suka soma qoqarin fashewa Daga gurin

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 5:32 PM] My Mom: *WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*CONTINUATION 4⃣7⃣*

πŸ‘¬πŸ‘«πŸ‘­πŸ‘¨‍πŸ‘©‍πŸ‘¦‍πŸ‘¦πŸ‘¨‍πŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§πŸ‘©‍πŸ‘©‍πŸ‘¦πŸ‘©‍πŸ‘©‍πŸ‘§πŸ‘©‍πŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘¦πŸ‘ͺ

*_I DEDICATE THIS CONTINUATION TO MY SISTERS AND BROTHERS, SONS AND DAUGHTERS OF ALH ABDULLAHI MUSA HUGUMA*😍😘
*AS'ALUL LAHA TA'ALA AY YUWAH HID SUFUFANA*πŸ‘πŸ»


Ya dakatar da su ta hanyar basu umarnin duka su tafi sashensa su zauna a can,suka fice din kuwa ya rufa musu baya,fadilan tayi ta tsayar da shi yayi banza da ita yace da ita
"Parlor dai naki ne kuma mun bar miki abunki,amma Kiyi a hankali kada Ki manta dai wace ce wannan a gabanki"yasa kai ya fice

Ta dakatar da samira dake qoqarin rufa musu baya,ido dai a waje ta kalleta tana nuna kanta
"Ni?,ai Nima din ai ba tsayuwar zanyi ba wannan ai tauraruwa mai wutsiya ce,banda mana da saura shan ruwa a gaba ai da tuni muna kushewa,zan dai tsaya a waje idan naji kina buqatar taimako na kawomiki"tasa kai ta fice

salima ta rushe da kuka ganin yadda kuwa ya gujetΓ ,Fadila ce ta dinga lallashinta da qyar ta ciyo kanta,tirysn tiryan ta zayyanewa fadilan halin da ta shiga bayan barinta gidan ba tare da ta boye mata wani Abu ba,ta rife da ce wa"abba na da Mimi Allah yayi musu rasuwa sakamakon hatsarin mota,da aka tashi taba gado Kuma Ashe abinda abba ya bari bai taka kara ya Karya ba duk kudin banki ne ashe,sai suka raba yasu yasu,din kowa ya manta da ni,sakamakon asirin da auwal yayi musu,da naje ma da kaina ce wa sukayi ba su sanni ba haka dole na haqura"

Tausayinta ne ya kama Fadila,lallai duniya zancan banza,tab as Wanda baji tsoron Allah ba ya shiga uku,abincin ta sabo mata Wanda yaran da babansu sukayi hijira suka bar mata,yadda take can abincin hannu Baka hannu qwarya kawai ya isheka abun tausayi,to abun ka da an dade ba'a hadu ba,kimanin awarta biyu sannan tace zata tafi,alheri sosai fadilan ta sake yi mata tace zata neme ta

⚜⚜     ⚜⚜     ⚜⚜

Bata sake ce masa komai ba kan abinda ya danganci salimar ba sai ranar dabgirki ya sake zagayowa kanta,sai da suka zo kwanciya sannan ta Sanar masa qudirinta,tana so a kayan da akeyi a company dinta ake kawowa nijeria tana rabawa samira da farida ta saka Salima a ciki,sannan tana so ta Gyara mu'amala da alaqar dake tsakanin salimar da 'yarta iftihal,don mahaifiya ba wasa bace

Bai tanka mata ba sai da ya ware shigar da bayanan harkokin kasuwancinsa cikin computer laptop dinsa ,ya kasheta sannan ya rufe,ya zare farin gilashin nan nasa ya dora a samanta,ya soke yatsunshi cikin na juna yana kallonta
"Fadeelah"yayi kiranta cikin dakakkiyar muryarsa,ta amsa masa a nutse
"Dukiya taki ce,company ma naki ne Kiyi Duk abinda like so da su mallakinki ne ba mallaki na ba,but........akeai Abu daya da nake umartarki ki zare hannunki ciki........za can Gara alaqa tsakanin salima da iftihal,babu ruwanki,na riga nayi magana da yarinyar tace bata buqatarta,Ku kun isheta,so......don Allah kada ki dawo mana da Hannun agogo baya,I hope kin fahimta?"
Ya shige bargo yayi kwanciyarsa abinsa

Duk da maganan bata yi mata dadi ba amma ta shanye,tayi alqawarin sai ta qarshe jihadin nan
Container din kayanta da tazo a satin ta taba kayan harda saliman,kika ta dingabyi tana sake roqarta ta yafe mata,sannan ta rows mata iftihal da aliyyu gafara,tace tuni ita ta yafe mata,suka insha Allahu zata yi qoqari su yafe matan

Ganin Daga aliyyu har iftihal din sunqi su fahimceta,aliyyu ke fiya wa diyarshi bakya sai ta gwada dauka matakin fiya harkarsu gaba daya,ai kuwa ranar dabiftihal tazo gidan yin weekend dinta kamar yadda ta sabΓ ,tana jirin"Mamee,Mamee na"fadila tace ni ba maminki bace,kike ki nemi maminki,tunda ni ban isa na gayamiki ki ji ba

baqaramin gigicewa iftihal din tayi ba,ta dinga kuka bana bawa Mamee haquri,tace indai tana so ta haqura to ta shirya maza yanzu driver ya kaita gun momin ta,ta Kuma gaya mata da bakinta ta yafe mata

Haka kuwa akayi,ranar ma salima sai da ta koka din,ta Gode ma fadilan ba iyaka,ba laid I iftihal din ta saki jiki da ita,don har zancan sure ta da Muhammad din fadilan sukayi,sosai Salima taji dadi

Saidai bayan dawowar Aliyyu Daga office ya tambayi ina iftihal tunda yasa anan take weekends,ya samu labari ta tafi ganin ummanta salima,fada ya dinga zabgawa,ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,ya bata mata rai sosai,amma tunda Allah yaga niyyarta Kuma har murΓ dintΓ  ya cika shikenan,samira ce ta dinga bashi haquri domin itama ta fuskanci fadilan Daga baya,lokacin sunavtare fadilan na biya mata *minhajil Muslim* da Samira ke koyarwa a makΓ antarta,bai ko kula su ba sai da ya gama zazzagarshi ya wuce sashensa

*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*

πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“š✍🏻✍🏻
[1/29, 5:33 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

             *PART 3*
       

               4⃣8⃣

🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊

*WANNAN PAGE SADAUKARWA NE GA DUKKANIN WANI MASOYIN LITTAFIN WA YASAN GOBE*

*_AHABBAKUMUL LAZI AHBABTANI LAHU_*πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜πŸ˜

Kwana daya biyu yaso dauke mata wata kamar yadda tayi masa dif,don irin salon horonta da ba iso kenan Kayi masa a dauke masa wutΓ 
Sai dai inaaaa ya Kasa,ya yarda ya Kuma amince shi sadauki ne Kuma jarumi ta kowanne Fanni na rayuwa,saidai tuni ya dade da sanin cewa shi mugun rago ne indai bangaren abinda ya shafi Fadila ne

Bashi da jarumta kan fushinta,bashi da juriyar haqurin rashinta a kusa dashi,musamman kasancewarta tamkar uwa ga kowa dake cikin gidΓ n,jaruma ce mai juriya da kawaici yakanah da haquri,Duk wa su lΓ lurorin da matsalolin cikin gidan Matuqar baya kusΓ  zata sa kafΓ darta ta dauke su,koda ma wani lokacin yana cikin gidan takan bashi damar hutawa,Bango ce ita a cikin gidΓ n kowa na samun kulawarta

Zakayi mamakin yadda yaran ke qaunarta,kuwa Mamee Kasa,Mamee maza,hatta da Fatima sai Kayi zaton Bataan samira ce mamΓ rta ba,to itama Samira idan ta sabo tarin matsalolinta da shawarwarinta gun Mamee fadilan take saukewa,Tun danginta na ganin tamkar ta shanyetΓ  ne har daga baya suka fuskanta,ganin yadda 'yar uwa tasu ta sauya,Duke Kuma morarta ba kamar a baya ba,Daga qarshe har godiya suka miqa ga fadilΓ 

Qawaye kuwa nata irin na da a yanzu babu burbushinsu ko daya,Tun tuni ta fatattakesu daya da daya,tayi wa tayi kyau ta sauya

πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰

Tana cikin kitchen yau ita daya ce,ita dai Tun safe take jiΓ± kaya kayar yaran suna ta shiri,abbun su na bada direction na inda za'a kai kowa,aslam da Muslim dama na Egypt su na shiru shiryen shiga *jami'atu al azhar* bayan sun kammala secondary dinsu kenan

Zuhra Islam da iftihal yasa aka kaisu gidan ummi,faruq da saddiq Kuma aka kaisu gidan uncle abba,afrah da amrah Kuma sukayi gidan farida,sai gidan yayi tsit,baba talatu na sashenta,samira kuwa tayi gidan su itΓ mΓ  bikin qanwarta,can zata kwana

Ita kam batasan tafiyar tasu duka ta kwana bace don haka har da su take girkin,tanayi tana mita cikin zuciyarta an kwashe mata 'yan aikin,don idan su na gida bata yin komai banda Gyara bedroom dinta da part din abbunsu,nata bada umarni ne da yin gyara inda aka kuskure


*Mrs Muhammad ce*πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸŽŠπŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰
πŸ“•πŸ“•πŸ“—πŸ“—πŸ“˜πŸ“˜✍🏻✍🏻✍🏻
[1/29, 5:39 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

          *part 3*

            4⃣9⃣

πŸ‘¬πŸ‘«πŸ‘­πŸ‘«πŸ‘¬πŸ‘«πŸ‘­πŸ‘­πŸ‘«
🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*wannan page din naku ne HUGUMA NOVELS READERS tare da iyalanku gaba daya*
*Allah ya bar qauna ina godiya*
πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»

Ta juya don dauka abarba cikin freezer zata niqa ta hada zobo,sai riga mutum tsaye a bakin qofa,sqnye yake da long sleeve t.shirt maroon colour wadda tayi masa dai dai jikinsa,sai trouser baqi,idanunshi tsaye da gilashinsa nan,hannayensa duka harde a qirjinsa,gaba daya ya zuba Mata mayatattun  idanunshin nan masu shegen maganadisu,

Tayi masa kyau matuqa da gaske,ba zai iya tuna lokacin da yazo ya sameta ba cikin ado da kwalliya ba,haka itamq din a dan Kallon sakqnnin da tayi masa,aliyyu bai tsufa,ko yaushe kamar ana sabuntashi,idan ka ganshi tare da su aslam sai Kayi tsammanin yayansu ne ba wai mahaifi ba,Duk wani kyau kwarjini da farin jini nashi sunyo shi,ginshira gaji da shan qamshi tamkar shi da su din tagwayene,shine gamboΓ±su

Sai ta kawar da kanta tamkar ba yanzun suke qarewa juna kallo ba,ta duqa don ciro abinda tazo daukan,ya saki lafiyayyen murmushin nan nasa,wato har yanzu fadilan nan tashi ce dai,miskilar nan,mai shan qamshi jan aji da dauke kai,yana jin shima ya kamata ya tuna Mata aliyyun nan nata, *Aliyyu Salim maitΓ ma* mai qarfin hΓ lin nan da yawan qaunarta

Kafin ta kai ga ciro abarbar taji caraf an riqo hannunta,da sauri ta dago gami da juyowa,sai dai tuni yayi mata masauki cikin qirjinsa,yasa hannayensa ya rufeta,kafin ta kai ga furta koma ya hade bakinsa cikin nata

Sai da ya zare mata laka baki daya,tuni tsaiwa ta gagaresu suka zube saman tiles din kitchen,ganin yana qoqarin wuce makΓ di da rawa yasa tayi qarfin halin tureshi
"Abbu so kake muyi abun kunya?,yara fa zasu iya dawowa kowaΓ±ne lokaci"
"Eh shi yasa ai na korasu don kada su hanamin cin amarci da matata,ke da ki gaΓ±su sai after three days"

Harararsa take saidai da ka kalli tsabar qwayar idontΓ  zaka gane cike hararar take da qauna da bege
"Wanne amarci kuma?,mutumin dake shirye shiryen aurar da first born dinshi"
"Haka kika ce,to zamu gani?"yace da ita gami da sungumeta da hannayenshi,bai sauketa a ko ina ba sai a fadarshi,Kallon juna suke suna murmushi cike da shauqi,sake rungume ta yayi cikin faffadan qirjinsa yana rada mata
"Fushinki kashni yakeyi *HASKEN IDΓ€NIYATA*,zuciyata rΓ guwa ce a kanki,zan iya jure koma amma banda lamuran da suka shΓ feki,na tuba *RAYUWA TΓ€*,kace *GATA NA*

itama cikin salon radar take ce masa"idan na dau ke ma wata tamkar ina hukunta kaina ne bisa ga Kasa bin ra'ayinka da nayi,mijina Kaine *DUNIYA TA*gaba daya,na gode wa Allah da ka zamo *uban 'ya'yana*"
Da sauri ya tari numfashinta "ni yafi cancanta na godiya ga Allah da ya rufamin asiri ya hana inyi asararki,da haka ta faru Fadeelah na,........da tuni na dade a kushewa ta"
Sai jin qauri suka cikin kitchen,da sauri suka rige rigen isa kitchen din


*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*
πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠ
πŸ“—πŸ“—πŸ“•πŸ“•πŸ“˜πŸ“˜✍🏻✍🏻✍🏻
[1/29, 5:44 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*YASAN GOBE?........*
πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠ

            *PART 3*

            5⃣0⃣

πŸ’˜πŸ’πŸ’˜πŸ’πŸ’˜πŸ’πŸ’˜πŸ’πŸ’˜

*_I DEDICATE THIS PAGE TO MY LOVELY HUSBAND,MAY ALLAH HELP AND GUIDE YOU,I LOVE YOU_*😍😍😘😘

Shi yayi nasarar kashe gas din,suka kalli tukunyar miyar da tuni ta qone sannan suka kalli  juna,dariya sukayi a tare,ya kama hannunta yasa cikin nashi tafin hannun bayan ya dage girarsa
"Kwanaki ukun nan na amarci ne
Babu girki.......
Babu aiki.......
Babu hayaniya.......
Babu yara.........
Ba surutu........
*just Fadeelah and aliyyu* kawai zasu more duniyarsu"
Itama girar ta daga "wow....I like it, *duniyar Fadeelah da aliyyunta kenan ko?*"ya gyada kai
"Yes!,yes my own"

Riqo hannunta yayi suka jero Tun Daga kitchen din,tafiya Duke very slowly kamar ba zasu isa bedroom din ba,kowanne jikinsa da zuciyarsa ta mutu da qwayar son dan uwanshi

*"na miki alqawarin kasancewa dake har bada"*

*"na maka alqawarin zamowa kusa da kai duk rintsi duk wuya"*

*"na miki alqawarin bata wa zuciyarki da gangar jikinki*"

*"na maka alqawarin zamo wa wata babbar duniya a gareka"*

*"na miki alqawarin dawwamar dake cikin farinciki har qarshen numfashin mu*"

*na miki alqawarin........*
*na miki alqawarin*.........

Haka aliyyu ya dinga hero mata har ta Gaza fadin koma,kukan dadi ya kufce mata,ta samu aliyyu fiye da yadda take zato hasashe ko tsammani,tabbas
*BABU WANDA YASAN GOBE SAI ALLAH*

Tana tsaye tana Hawaye ya zube a gabanta kan gwiwoyinsa,ya lalubo qwayar idonta ya sanya nashi ciki,ya soma girgiza kai
"Um.....um baby, *No more tears* kin manta?, *na miki alqawarin ba zaki sake kuka ba fa har abada*"
Dai dai lokaçin da hawayen idonta suka silmiyo su na qoqàrin dinga a tiles,yayi maza yasa tafin hanñuñshi ya tareshi,tas ya lashe hawayen kan fuskàrta

" *NURY* kukan farinciki samun ka a matsayin miki nake,irin mijin da ke wa mata tsada da wuyar samu a wannan lokaçin"

"Kamar yadda mata irinki ke tsada a wannan lokaci ko
ladabi,biyayyatsafta,dadi ni,haquri juriya da kawaici
Kyau,Zubi diri,kullum kamΓ r ana dada miki yarinta da wani dadi na......."
Da Sauri ta rufe masa baki da tafin hannunta cikin kunya tana boye fuskarta cikin qirjinsa
"Kai dear don Allah"
"Yes,zancena haka yake wlh *qurratu ainy*"

Bakinsu ya subuce a tare suka fadi *ALHAMDULILLAHIL LAZI BINI'IMATIHI TA TIMMUS SALIHAAT*
Sai suka hada ido kowaΓ±Γ±ensu ya sakarwa dan uwansa amintaccen murmushi

       *tammat alhamdulillah*
πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»

*dukkanin wani yabo da godiya sun tabbΓ ta ga Allah madaukakin sarki*

*tsira da aminci su sake tabbata ga dan gatan Allah shugaban dukkan wata halitta baki daya annabi Muhammad s.a.w*

*bakina bazai iya fasalta tarin godiyΓ  ta ga dubban masoya na ba masoyΓ  littafina,Wanda goyon bayΓ nku haquri da juriyΓ rku ya kΓ ini gΓ  bigiren da nake kai yanzu,Allah yayi muku sakamako mafifici,mutane Daga qasashe da garuruwa daban  daban*

*ina Neman afuwa da yafiya ga duk Wanda na bata wa ko littafina ya batawa rai,duk dan Adam ajizi ne,ba lallai Kuma mu sake saduwa bΓ *

*fatan alkhairi ga mahaifana*

*godiya mai qima ga HUGUMA novels readers*

*shin cikin littafina waye gwaninki?*

*wa kika fi so?*

*wa kika fi tsana?*

*me yafi burgeki?*

*me yafi bata miki rai?*

*wanne darasi kika gano cikin littafiΓ±?*

*mene yafi baki dariya?*

*mene ra'ayinki kan wa yasan gobe?*

Post a Comment for "WAYA SAN GOBE? CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...