Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 2

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 2

- - Post a Comment

 WANNAN RAYUWAR CHAPTER 2


A haka rayuwa ta cigaba da tafiya sakanni na komawa minti na, minti na komawa awa, awanni na komawa kwana, kwanaki na komawa satitika, satittuka na komawa wattanni. Dan har anci wata uku da auren kamar yau akai abin ake gani.+


Muhammad ya samu aikin koyar wa anan wata primary but gwamnati ce ta dauke shi yana daukar albashin sa dubu talatin da wani abu. Watan sa hudu da fara aiki ya samu admission inda zai juya degree din sa anan BUK sai dai ma'aikatar su tace sam ba zata bashi inservice ba saboda bai jima da fara mata aiki ba. Da ya zauna yai tunani sai yaga komai na Allah ne tinda ya samu admission din nan gwara yai fara karatun aiki ai daman bai zama lallai yayi ba ko kasuwancin sa Allah ya bawa sa'a sai ya zama wani abun. wannan yasa ya hakura da aikin kan cewar in ya gama karatun zai koma. Tin kan ya ajiye da yai shawara da Hajiyar sa itama cewa tayi yaje ya karo karatun bai san gaba mai zai zama ba. Wannan yasa ya ajiye da gayya dan shawarar Hajiyarsa.

A wannan lokacin ne kuma Rukayya ta fara laulayin ciki. Dan haka komai shi yake mata sannan ya tafi makaranta. Tinda ya ajiye aiki sai abubuwa suka farai masa yawa dan baya samun zaman shago dan da safe yana dawainiyar gida da rana yana makaranta in ya dawo da yamma ma yana kanta. Da dare shima ya gaji da kyar yake iya bude shagon ya kai goma sannan yakoma gida.


Da yaga abin na yawa ba kudi a gun sa sai yaiwa Hajuyar sa magana ita tace kanin sa yana zamar masa, dan haka sai ya samu rangwami suke gungura rayuwar su a haka.

A lokacin ma Zainab na da ciki karami a lokacin kuma ya samu canjin aiki acan Abuja, Inda suka bashi gida da mota wannan yasa suka fara shirin barin Kano, ganin tana dan laulayi kuma tafiyar nesa ita kadai wannan yasa sukaje har wajen Abba neman alfarmar a basu Ummulkursum tinda ta gama karatu secondary.


Abba yace ya samar mata admission amman Mijin Zainab yace shima zai samar mata acan. Ba dan Abba yaso ba sia dan nauyin sirikin nasa da yake ji ya yadda ya amince. Suka tattara suka tafi da Ummulkursum.

Sailuba kuwa sam bata da ciki sai duniyar ta take ci da tsinke, dan da mijin ya mata maganar komawar ta can gidan iyalan sa sai tai wa Mama magana. Mama tai wa wata kawar ta magana nan suka tafi gun wani malamai har aka samu aka rufe masa baki. Bai kara maganar ba.


Suna komawa Abuja ogan su Suleiman ya samar wa Ummulkursum makaranta ta fara karantar pharmacy. Sam bata da damu dakin ta daban akwai komai haka nan sai abinda take so mijin yayar ta yake mata, itama yayar tata haka. Har yanzu bata canja shiga ba zata saka kaya masu kyau da tsafa amman fa zata dauki hijab da nikaf da safa ta saka. Xaman ta a gari ta kara kyau da wayewa, suna zaune lafiya da yar uwar ta, sai dai suyi waya da can gida ko da Rukayya.

Cikin Rukayya da ya cika wata tara mama tace dole ta koma wankan gida dan ba mai zuwar mata, Muhammad bai so ba amman ba yadda zai yi haka ya barta ta tafi, dan ita kan ta Rukayya bata so komawa gidan ba.


Sai dai tinda taje zaman gida sai Mama ta dinga hure nata kunne, bama da taga yayar ta irin suturar da jin dadin da take ciki ga katon gida da mota, kudi kam sai dai taji ana maganar dubu dari kaza. Tin tana kin biye musu har ta fara jin shawarar yayar tata tana ina ma ita ce.


STORY CONTINUES BELOW

Haka In suna waya da Ummulkursum ko vedio call taga a irin gidan da suke sai duk taji jikin ta yai sanyi. Kullun Mama ce cikin cewa ta fadawa Muhammad ya kawo kaza da kaza, daga baya ma tace ya kawo kudin kayan abincin ta, Rukayya tace

"Haba Mama, a gidan ubana fa nake,"


Mama tace

"A gidan uban naki fa ai a karkashin sa yanzu kike nauyin ki na kan sa."

"Gaskiya Mama bazan iya ba ai sai ya raina mahaifina bayan Abba bai ce ba dan dai cin abinci kawai. In Abba yai magana na masa amman ba ke kike ciyar dani ba."


Kwafa Mama tayi tace

"Wai ke ba dan abinda kike samu a gidan ne?"

"Me zan samu Mama."


"Dan ragowar kudin cefa ne man!"

"Tab Mama ni komai kawon yake har girki yi min yake abinci kadai yake bani a baki shima dan bazai iya cimin bane."


Tsaki mama tayi tace

"shiyasa kike zauna dashi ko yana miki wayo, in kin koma kada ki soma yadda dole yana baki kina cafane kuma dole kina cewa yana miki sutura, mai tsada jibi kayan jikin ki tin na lefe a ciki duk babu dan dubu goma bare ashirin ba dole suna lalacewa ba. Ki kalli yar uwar ki ko Zainab nan da muka raina, ma tafiki ni kam dai ina jin ke ba 'ya ta bace dan ban haifi kalar tsiya da talauci ba sam. Sam baki da irin hali na."


Ita dai bata kula ta ba har ta gama kullum cikin irin wadan nan maganganun take, tin bata dauka har abin ya fara tasiri a zuciyar ta.

A haka ta sauka lafiya, inda ta haifi yar ta mace, anyi murna ba ma Muhammad da Hajiyar sa, da kannen sa, nan ya hado kayan barka dai dai gwargwado karfin sa, aka aika gidan su Rukayya, Mama sai jefan su tayi da dan karamin akwatin da ya ciko da kayan barka na Baby da na Maman Babyn. Sai mita take

"Ita yar ta ba matsiyaciya bace da zata saka atamfar 3500 da leshin 6500, sai wannan matsiya ciyar shaddar, wallahi 'yata tafi karfin wadan nan kayan."


Rukky tace

"Mama ki bari."

Duka ta kai mata abinda yasa tai daki kenan. Yan uwan Muhammad suka tattare kayan suka tafi rai abace.


Ummulkursum da Zainab ana gobe suna suka zo, zo kuga murna gun Umma. Mama kuwa sai hararar su take dan daga kallo zaka san suna cikin jin dadi, shigar dake jikin su kuwa ta haurawa dubu ashirin da wani abu. Dan ko turaren su ma daga kamshin zaka san mai tsafa ne. Suna shiga dakin Mama dakin ya kaure da kamshin su.


Leshi dan twenty five thousand da atampa yar twenty thousand sai wata yar five thousand, sai kayan babies masu kyau da tsada Zainab ta kawo, Sannan mijin ta ya aikowa da Abba buhun shinkafa da katon galan din mai da taliya da dubu ashirin ya aikowa da Mama da Umma dubu goma goma sannan ya basu atamfa super. Amman Mama sam taki amsa, wai itama sirikinta yana kawo mata, basu ji dadi ba. Ummulkursum kuwa ten thousand ta bawa Rukayya, anan jikin Rukayya ya kara sanyi lallai maganar uwar ta gaskiya ne, kalli yan uwan ta, itama tana son komawa kamar su.


Ranar suna Abba ne yayi komai na suna dan Da Muhammad ya kawo Mama cewa tayi sunyi kadan a mayar, sunan Hajiyar sa aka radawa Babyn, Firdausi inda Ummulkursum tace ana kiranta da. jannah Mama ta hau fada wai sunan ta za ana fada, Abba yaji yace magana har da fada yace kuma ana ce mata Jannah. Mama kam kamar ta mutu dan takaici.

Shigar da Zainab da Ummulkursum sukai ka rantae sune masu jegon, dan ma Zainab nada nata tsohon cikin, dan kayan su masu kyau da tsada. Duk sai jikin Rukky yai sanyi. Ana tsaka da walima Muhammad yazo, Rukayya kin zuwa tayi dan sai Ummulkursum ta bawa Baby Jannah ta kai masa, sam su Ummulkursum basu san me ake ciki ba dan Umma bata da wannan surutun da dai Mama ce da kaji labari. Dan haka tana zuwa ta gaishe shi, bayan ya amsa ya kalle ta yace

"Ummu kece kika girma haka lallai Abuja ta amshe ki, me Anty Zainab da Yaya Suleiman ke baki ne?"

Dariya tayi tace

"Yaya Muhammad tsokana dai kawai amman yadda nake da haka nake yanzu ya kake Angon karni? ga Baby Jannah nan tayo kama da kai, ina hajiya dasu Isma'il yanaga ba wanda yazo daga can."


Murmushi yayi kawai yace

"Uhmm ina Rukayya?"

"Tana can cikin jama'a, shiyasa tace na kawo maka Baby Jannah."

Babyn ya kalla wacce akau maga kwalliya cikin daya daga cikin rigunan da Anty Zainab ta kawo mata, ya mika mata yace

"bari naje anjima zan dawo ki fada mata."


"To shikenan sai anjima!!

tayo cikin gida rike da babyn tana tunanin me ya ramar da Yaya Muhammad haka. Daddare ma da yazo kin zuwa tayi sai a washe gari suka kebe da Ummu da Rukayya tace

"Ummu ni fa na gaji da auren nan!"


Dariya Ummu tayi tace

"Kai Anty Rukky me akai da maza! Yaya Muhammad kace jarumi, kema ki daure ki xama jarumar nan da wata shekarar mukara shan sunan."


"Nifa ba haka nake nufi ba, ki kalleni fa kiga duk na lallace ba kamar ina budurwa ba."

Murmushi Ummu tayi tace

"To daman tayaya zaki zauna a yadda kike kar ki manta fa kin sha hannun maza."


Tsaki Rukky tayi tace

"ke Ummu kin fiya wasa, ki kalli Anty Zainab da Anty sailuba, sam basu koma yadda nan koma ba. Gaskiya nima ina so rayuwar jin dadi."


"Me kike so ki fada Anty Rukky, kina son kice min a gidan Yaa Muhammad ba ci ko sha ne? Ko bai miki sutura ko bai kula da ke? Ko bakya cikin kwanciyar hankali?"

"Duk da akwai amman ba kamar yadda Yayye na suke ba."


Kai Ummu ta girgiza tace

"Haba Anty ance ka daina kallon na sama da kai kana kallon na kasa dakai. Kada ki manta ko yatsun hannun mu ba daya bane, ba karatu ya koma ba, ki bashi lokaci ya gama ya samu aiki kiga ke sauyin rayuwar taki, kika san me gaba zata haifar su ba a lokaci daya Allah ke bawa arziki ba dai a hankali bama shi da ba a zaune yake ba, yana da zuciyar nema. Gaskiya Anty Rukky ki canja tunani sam wannan ba tunani me kyau bane. In Allah ya baka abu gode masa kake sai ya kara maka. Ni dai wallahi bana son wani abu ya shiga tsakanin ki da Ya Muhammad dan Allah! Wasu baci ba sha din amman darajar soyayyar dake tsakanin su suke xaune, wasu kuwa matan ke nemowa kuma yaci yana daga kwance. Ki godewa Allah. Da shi zai miki komai."

Nan tai ta mata nasiha da fada anan kam ta dauki shawarar yar uwar tata.

Washe gari Anty Zainab ta tashi a nakuda nan aka tafi asibiti ana zuwa ta haifi dan ta namiji ba matsala dan haka aka sallamo su suka dawo gida.


Zo kuga inda yan uwan Suleiman keyi yawo a gidan kai ka rantse kanwar su ce, dan suna son Zainab akwai ladabi biyayya. Dan kiwa zai zo da kaya niki niki. washe garin da ta haihu kuwa katon sa aka kawo aka yanka mata yace ana mata naman gashi ban da kaji lemuka da madara da kayan abinci dan har fada Abba yayi yace bai ce yayi ba ai shima uban tane.

Nan yace Abba ai nima dan kane ko da Rukayya ko babu ni mai maka abu ne dan haka kayi hakuri ni ba a sirikin ka nake ba a d'an ka nake.


Nan Abba yai ta saka masa albarka. Duk wacce zata zo da kayan barka kuma kaya masu tsada dan ya uwansa dukka masu kudi sule aura haka yayyen sa maza ma suna da kudi shine daman bai dashi yanzu kuma aikin da ya samu ya dago shi dan yafi karfin komai.

Lokacin da aka kawo kayan barka kuwa sai kace lefe dan akwati set guda ya hado na Uwar Baby da Baby dan har da jakuna da takalmi mayafai da dankunne da sarka da su under wears kuna kaya masu tsada dan supers ne da holland manyan leshi+ sannan ya aikowa da Abba shadda Su Mama kuma atamfofi har da Ummulkursum yayi wa kaya akwati guda na fitar suna itama har da jaka da takalmi da under wears. Dan har kudin lalle da kitso ya bayar. Mama da sailuba kamar sa mutu dan bakin ciki. Rukky kuwa sai taya yar uwar ta murna take.

Da safe akai taron suna da yamma kuma walima akai har da abokan ango inda aka raba take away da robobi jakuma da littafai da calendar duk da picture din Baby a jiki. Anyi taron suna lafiya inda yaro yaci sunan Abba ake kiran sa da Jawad.

Suleiman yace suyi sati uku zai zo ya dauke su. Zatai magana Umma ta harare ta nan tai shiru Abba yace sai yazo. Sai da ya tafi Umma ta hau ta da fada akan me zatai magana dan ta gane so take tace sai tai arba'in ai kam hakan take nufi tace

"Umma wa zai je min wanka."


Umma tace

"Kan lokacin kin iya in zaki tafi nayiwa yakumbo magana sai taje in kinyi arba'in ta dawo"

Wannan yasa taji dadi dan tana so tayi tai arbain sannan ta koma.

Satin ta uku da haihuwa ya zo ya dauke su da ita da Ummu da Yakumbo a jirgi ma suka koma. Inda dai har lokacin Rukayya da Muhammad basa jituwa. Ummu dai ta karai mata nasiha kan su tafi. To da ta mata Mama ke hure mata kunne.

A haka har tai arba'in da yace ta dawo Mama tace sai ta zaga dangi dan haka ya zuba musu idk. Da Abba yaga yakumbo ta dawo da kaya niki niki daga gun masu jego b

yace

"Har anyi arba'in?"+


Tace

"Ai yau kwanansu sittin ma."

Wannan yasa Abba ya tuna da Rukayya dake gida bata koma ba. Da yai wa Mama magana sai cewa tayi sai taje ta zaga yan uwa. Haka taje yawon arba'in sai da ta kara sati uku sannan ta dawo nan Abba yace lalli lallai ta koma dakin ta washegari.


Ba yadda zatayi haka ta fara hada kayan ta. Bai ma san da dawowar ba sai da dare ya koma gida ya ganta zo kuga murna gun sa kamar zai hadiye ta. Nan yai ta tarairayar ta har ta dan sauko suka koma kamar da. Duk abinda ya aika Mama taki amsa yana nan ajiye dan haka kayan abincin suke amfani dashi. Kayan harka kuma ya bata abinta.

Sai dai yadda ta fara canjawa tace ita zatai cefane ya bashi mamaki amman haka yake bata amma ta raina wata rana tai shiru kuma in ya bata dari biyar bai fi tai cefane na dari da hamsin ba sauran ta boye. Washe gari tace ba kudin ya kare.


A gidan su uku ne akwai dayar matar da mijin ta ba mazauni bane. Wacce suke a kusa da dakin ta, ta kasance mijin ta ba ma zauni bane sai yai wata shida ma baya gari duk irin kulawar da Muhammad yake bawa Rukayya haushi take ji, dan ita bata samun wannan kulawar. Haka ta shige mata da ta gane matsalar ta sai ta samu abinyi itama ta dinga zuga ta tana fadin

"Me za ai da talaka."


Ita kuma Rukky idon ta ya rufe ta kasa gano a matsalar da makwabciyar tata Asiya take ciki dan sun dinke tana kara daura ta akeken jakai.

Anty Bebi ta dayan bangaren kullum fada da nasiha take Rukky amman sam baji take ba don irin shawarwari da Mama da Anty Sailuba suke bata ga na Asiya.


Tinda ta dawo gida ya kasa gane kan ta komai sai hakuri daga yau tace sai ya siyo mata kaza jibi tace kaza. Haka dai in yai mata dinki ta raina in yayo cefane tace ita yana bata tanayi da dare tace ita ba zata iya cin abinci ba kaza take so ko Furar Rufaida wata rana tace shawarma tsurfa dai kala kala. Kayan shagon sa duk sun yi kasa saboda yadda take cin kayan kamar me? Dan Muhammad nason ta shiyasa komai tace yake mata. Ga Karatu baya ga cin su da shan da kudin haya ga iyayen sa dashi ke daukar nauyin su. Wata rana da kyar yake samun abinda zasuci.


A *Wannan Rayuwar* suka shafe shekara biyu wanda acikin ta sai hakuri yake da halin Rukky, in sunyi waya da ummu tai ta bashi hakuri inda Rukyy sukai tai ta bata rashin gaskiya da nasiha daga baya ma sai ta daina sanar da ita komai. Ita kuwa ummu har kudi take turowa Yaa Muhammad dan Yaa Suleiman duk wata sai ya bata kudi ban da na ckul haka nan Abba ma yake turo mata duk wata ita kuma ba ma'abociyar cin abinci ba, makaranta ma kai ta akeyi. Da tace ya daina bata ya hau ta da fada. Sai tayi shiru. Abba ma yace sam ba zai daina ba kada tana takura Yayan ta da tambayar kudi.

Samari masu kudi da mu'kamai sukai mata rufdugu amman sam duk taki sauraron su, Dan Ummu tafi duk yan gidan su kyau dan ma tana boye kyan nata amman daga sufar ta zaka gane mai kyau ce.


Har yanzu Sailubq bata haihu ba kuma bata damu ba dan ita a ganin ta ma hakan yafi, yanzu da Rukky ta kuna samun ciki zo kuga yadda Anty Sailuba da Mama ke mata sai kace cikin shege ne, duk abin ya dameta da ta fadawa Ummu hankali ta dinga kwantar mata dashi, duk da yar ta shekarar ta uku kuma a lokacin Muhammad ya gama degree din sa inda ya samu scholarship ya zarce masters din sa. A lokacin kuma Ummu na level 400.


STORY CONTINUES BELOW

Rayuwa tai masa zafi duk da dakyar yake samun naci da sha ko makaranta a kafa yake zuwa amman duk da haka baya taba barin Rukky da Jannah da yunwa.

Duk safiya sai yai mata shara wanke wanke da girki yai mata wanki sannan ya fita, amman duk ita bata gani, Anty Aisya tai ta zuga ta amman Anty Babi tace

"Wallahi ni burge ni kuke yi."


Rukayya tace

"A hakan? Ina cikin wahala."


"Ai kam ba wata wahala da kike ciki tinda zakici zaki sha kuma baki da wahalar komai. Wanda yake cikin wahala shi yake fita ya nemo mijin na kwance. Ko ita Asiyan da take zuga ki ai ita ke a wahala dan ba ko da yaushe yake aiko mata da kudi ba kina ganin kullum ita ce a maula ga yan uwan ga ba neman na kai kina gani dai da kyar take samun abun ci amman in mijin ya tashi dawowa wane kalar rawar jiki ne bata yi shin kinga ta na masa abinda take saka kina masa. Ko kinga tana masa tijara ne? Ki zauna ki karatun ta nutsu wallahi ki rike mijin ki wata rana sai labari."


A haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya ar cikin ta yai wata tara da yace ba zata wankan gida ba tai masa rashin kunya ta hada kayan sa ta tafi.


In tana masa wani abu har mamaki yake sai kace ba auren soyayya ba. Da yaje ya samu Abba. Hakuri Abba ya bashi yace

"Muhammad kayi hakuri nasan duk halin da kake ciki amman shawarar da zan baka in ka gaji kawai ka sauwake mata ka huta. Sai su gane kuren su."


Amman sai cewa yayi

"A'ah Abba ba za ai haka ba. Na dai fada maka ne dan a mata nasiha."


"Hmmm Muhammad kenan. Ai uwar ta ita ke daura ta akan komai. Wallahi kaganni nan na saka musu wannan!"

Ya fada yana nuna idon sa. Sannan yace

"Sai addu'a kuma. Kayi hakuri kaji. In ba zaka sake ta ba ka nemo matar aure ni da kaina zan maka komai na auren!"


Rasa karamci irin na Abba yayi tayay zai sakar masa 'yarsa bayan duk abinda yake masa. Dan haka yace

"Ayi hakuri Abba dai."


Da zai tafi Abba har da kudi ya bashi ya tafi yana ta godiya.

Lokacin da ta haihu yan uwan sa suka zo akai musu wulakancin da sai da ransu ya baci. Dan sam Mama ta hana su shigar mata daki wai zasu sa maka warin talauci sai Umma ce ta tarbe su ta kaisu dakin ta har da kawo musu ruwa taje ta amso Babyn wajen Rukayya dan ita ba za ta iya hana Umma Babyn ba.

Mama kuma tace ai yar tasu ce dan haka suje itama su shafa mata jinin talauci. Umma ta kai musu yaron tana mai basu hakuri. Kayan barkan da suka zo dashi haka suka koma dashi. Ransu a bace. Sai yabon Umma suke.


Hajiyar sa kuwa sai hakuri take bawa yan uwa nasu amman wasu kamar ita tai musu fadi suke

"Ai dole yaga wulakanci tinda yaki ya'yan mu yaje gun masu kudi."

Dan duk ciki sun so ya auri yar su.


Sailuba ita tai mata komai na fitar suna. Anty Zainab wannan karon bata zo ba dan laulayi take amma ta aiko da kaya nasu yawa da tsada dan har sunfi na wancan dan yanzu sun san mijin ta bai da aiki sai karatun da yake yi. Ummu ce tazo dan sun samu hutu daga komawa kuma zasuyi second semester suyi exam sun gama sai service kuma.

In kaga Ummu ta zama cikakiyar buduwa inba sanin ta kai ba baza ka gane ta ba dan tayi kyau ta cika tayi haske kamar balarabiya. sai sam bata bada fuska ga samari dan tana da kwarjini.


Lokacin da tazo gun Rukky kallon ta Rukky ta tsaya baki sake tana fadin

"Ummu kece kuwa? Kamar wata matar gwamna, kinga yadda kika koma anya kuwa kina karatun kuwa kamar wata mai jin dadin aure jibeni ko ni bazan kai ki ba. Ah lallai Masha Allah."


"Ke Anty Rukjy kin fiya abin dariya baki min sannu da zuwa ba kin cikani da surutu ni ina Babyn namu? Bani shi daman gun sa nazo ba gunki ba "

Ta dauki Babyn tana kallo.

Rukky tace

"Kuma dai nice taki ba."


Daruya tayi tace

"Kai ki damu ai son ki shi zai shafi dan ki."


"Uhmm!

Kawai Rukky tace. Ummu tace

"Wow masha Allah kamar sa daya da Abban sa. Allah ya raya mana shi."


Jannah ce ta shigo tana kuka wai yunwa takeji Mama ta shigo Ummu ta gaishe ta amman ko kallon ta batai ba ta dauke kai.

"Mami yunwa!"

Jannah ta kara fada.


Mama tace

"Tafi ki ban waje ba abinda zan baki."


Ajiye Babyn Ummu tayi ta dauki Jannah tana dariya tace

"Kyale Granny zo muje dakin Dayar Granny din kisha tea kinji."


Ta fice da ita. Dakin Umma sukaje ta hada mata tea tabata da cake, tana ci ta fito da kayan da Anty Zainab ta bayar a kawo Umma sai albarka take sawa. Ummu tace zan bata 20k ai yayi ko? Yayi Allah yayi albarka ya kara muku zumunci. Ta amsa da Amin.


"Wai ke a ina kike samun kudi ne?"

"Abba ya turon Yaa Suleiman ya bani fa Umma. Shine nake business na kaya nake kaiwa School baki ga yadda ake ciniki ba kuma wannan karon da Yaa Suleiman yaje Egypt ma ya kawon wasu mayafai masu three in one har ke na kawo ma.  Kuma ya dada min jari sai dai in beje wata kasar ba zai kawon kayan siyar wa kuma kyauta fa."


Ta bude akwatin ta ta daukowa Umma takalmi da mayafai da atamfa tana fadin

"Kinga mayafin."


Budewa Umma tayi tace

"ai wannan na yara ne."

"Kai Umma wane yara dan Allah gaskiya sai kin saka wannan shine abun da na farai miki fa ga wadan nan!"

Ta tura mata kayan gaban ta tana fadin naki ne suma.


Umma sai albarka take saka musu da addu'a.


"Umma ya kuwa Anty Rukky, yanzu dai ba matsala tsakanin ta da Yaya Muhammad ko?"

umma tace

"Ina fa? Tin kan ta haihun ta taho gida fa. Baki ga abinda sukaiwa dagin Muhammad ba jiya. Abin tausayi sun kasa ganewa Allah ne mai bayar wa kuma kai hanawa. kuma wa ya fada musu rabon bawa da arziki ai sai mutuwa. Kawai sailuba suke ganin rayuwar ta,"


Ummu tausayin Yaya Muhammad ya kamata, nan ta mike ta nufi wajen Rukky ta farai mata nasiha amman sai Rukky ta rufe ta da fada tana fadin ai ita ba sa'ar ta bace.

Hakuri Ummu ta bata tana mai karai mata nasiha amman tai kunnen uwar shegu da ita.


Daki ta koma taiwa Jannah kitso tai mata wanka. Bayan magariba ta shirya tace

"Umma zanje gidan su Yaa Muhammad!"


"Kiyi musu me?"

Umma ta fada.


"Na jima ban gaishe da hajiyar sa ba kuma zanga Yaa Muhammad na bashi hakuri."

Umma tace

"Ni dai bana son abin magana Ummu"


"Umma bama sanin naje zasuyi ba."

"Shikenan ki gaishe da Hajiyar tashi."


Daki ta shiga ta daukowa hajiyarsa atamfa da mayafi ta dauki dubu goma ta fita yana nunawa Umma. Umma ta saka mata alarka dan Ummu ba dai kyauta ba sam in tana dashi bata ajiyewa sai da ta bayar.


Tana fitowa tsakar gida sai ga Jannah nan ta taho tana fadin

"Anty jan biki."

Daukar ta tayi suka fice.


A tsakar gida suka sumu Hajiya nan ta zauna. Hajiyar tace

"Wa nake gani kamar Ummulkursum ko?"


Kai ta gyada mata tace

"Nice hajiya!"


"Haba ai da na daina ganin ki nake tambayar Muhammad sai yace min kinbar garin."

"Eh wallahi kuma ban cika zuwa ba da yake karatu nake acan!"


"Masha Allah! Allah ya taimaka, ai karatun shine. Shima yanzu sauran shekara daya ya gama masters din insha Allah daga lokacin komai yazo karshe!"

"Haka ne Allah ya taimaka to!"


"Ameen!"

Kallon Jannah Ummu tayi tace

"Baby baki ga Hajiya bane!"


"Ai ba sani na take ba dan ba zuwa take ba, uban ba lokaci ita kuma uwar ba zuwa take ba."

"Hajiya ayi hakuri wata rana sai labari."

Ummu ta fada.


Hajiya tace,

"Haka ne Ummulkursum."


Har akai isha'i sukai sallah sannan ta zubo musu tuwon shinkafa miyar kubewa danya ai kam abincin yai dadi. Nan ta mike ta bawa Hajiya kayan da ta kawo ta daura mata 5k akai sannan sukai sallama tana ta saka mata albarka.

Tana fitowa ta hadu da Yaa Muhammad a soro zai fito.

Tana fita suka hadu da Muhammad zai shigo,
Yaya Muhammad!"
Ta kira sunan sa. Juyowa yayi yana kallonta yace
"A'ah Ummu ce! Yaushe kika zo?"+

"Dazu ya kake ya masu jegon?"
"Lafiya Alhamdulillah! Ya hanya?"

"Alhamdulillah!"
Ta bashi amsa. Sannan tace
"Yaya Muhammad a kara hakuri da Anty Rukky. Insha Allahu zata gyara!"

"Allah yasa toh!"
Ya mika hannu ya amshi jannah yana fadin
"Mama na ya Baby?"
Ummu ce ta amsa da
"Yana lpy!"

Wani envelope ta dauko ta mika masa tace
"Ga wannan bayawa, Allah ya dafa."

"Menene wannan?"
"Kudi ne ba yawa!"

Kai ya girgiza yace
"A'ah ba zan amshi kudin ki ba Ummu. Ke da Abba kuna so na. Abba fa shi ya siyan ragon suna, sannan ya ban kudi masu yawa. yanzu ina da kudi."

"Dan Allah Yaa Muhammad ka amsa, kyauta ce daga kanwar ka."
Sai da tayi da gaske, sannan ya amsa yace
"Nagode kanwata ya ckul din?"

"Ckul tazo gan gara kai fa?"
"Nima haka saura semester daya ai tai mana addu'a."

"Insha Allahu. Allah ya taimaka."
"Ameen!"

"Bari muntafi dare nayi."
"Muje na rakaku."
Har kofar gida ya rakasu sannan ya koma gida.
A gida Hajiya ta nuna masa abunda Ummu ta bata shima ya bude yaga dubu hamsin ta bashi. Nan sukai ta saka mata albarka.
A gida kuwa ranar agunta Jannah ta kwana. Washe gari ta kaiwa Rukky kayan barka. Sai ga Rukky batai wata murna ba duk da kayan sun burgera dan yanzu bakin ciki take yi dan me ita bata samu miji mai kudi ba da zai na siyo mata wadan nan kayan. Danasani take akan me ta auri Muhammad itama dama mai kudi ta aura. Batai godiya ba itama Ummu bata damu da tayi ba dan daya ta dauke su.

Ran suna Baby ya ci suna Abba Ibrahim ana kiran sa da Junaid. lokacin kuma sailuba ta fara kwadayin haihuwa wai ko dan ta samu gado kuma ta nunawa su Ummu itama fa mijin ta mai kudi ne, wanda kudin suke a banza daga ita sai uwar ta dan ko Abba basawa Wani abu. Mijin Zainab kuwa duk wata sai ya ajiyewa Abba kayan abinci da kudi. duk da Abba yana fada amman sai yace
"Yanzu Abba dan na.maka abu sai kana hanani in babu ai ba zanyi ba tinda da akwai kana amsa kana sa min albarka, Abba yanzu in su Abdullahi ne sukai maka suma haka zakai musu. Dan Allah Abba ka dauke ni kamar yadda su Mu'azam suke a gunka."

Abba ya kan ce
"Allah maka albarka. Wallahi Suleiman yadda na dauki ya'yan cikina haka nake daukar ku, domin insone ma nafi son ku. Allah yayi albarka."
Haka suke kusan kullum. Dan Abba sam bai da son abin duniya. Kuna shima haka yake kyautatawa surukan nasa kan jiki kan karfi.

Kan Ummu ta koma ta zaga dagin Umma da Abba kuma duk tai musu alheri iya karfi ta. Sannan ta fara haramar tafiya dan hutun ta ya kare. Tinda tazo bata ga Yaa Muhammad yazo gida ba, A jirgi ta koma da ta koma Anty zainab da Babyn ta sai murnar dawowar ta suke. Sai da ta zauna sannan take fadawa Anty Zainab halin da Rukky ta sauya. Anty Zainab tace
"Allah ya kyauta yanzu itama halin uwar ta zata dauka kenan. Allah ya shirya. Mu da ake ganin matsiya ta ai gashi nan Allah yai mana rufin asiri muna zaune lafiya a gidajen mu. A juri zuwa rafi wata rana tulun zai fashe. Dan indai kace tukunyar wani ba za tai zafi ba taka ko tafasa ba zatai ba. Akace in ka tashi gina ramin mugun ta ka gina dai daikai."

STORY CONTINUES BELOW

"Allah dai ya kyauta!"
Ummu ya fada. Anty Zainab ta amsa da
"Ameen!"

*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-**-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-**-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-**-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-**-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-**-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*
*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-**-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-**-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*Jummai akwai ta da son kudi Dan haka da taga wata a cikin su tana irga yan dubu dubu sai ta matsa kusa da ita tana fadin
"Ke kuwa baiwar Allah a ina kike samo wadan nan kudaden."

Sai da ta jefe ta da kallon banza ta ce
"Ai ke kin tsofa ba iyawa zakiyi ba 'ya ta na dauka na bawa wani Alhaji kinganni nan duk wata sai ya aikin da dubu hamsin Dan kiji sai kace mai aikin gwamnati in kika ga 'ya ta kuwa sai kice yar gwamna ce ko matar gwamna kayan da cimar ta mata Kadai abar kalla ce yau in tana wannan garin gobe tana wacan kasar kwanan nan na dawo daga saudiyya Dan kiji shima kamo ni akai da ba dawowa zan ba kuma kwanan nan zan koma Dan kiji."

Jummai Jin wannan Abu sai hankalin ta ya tashi ta ce
"Yanzu dan Allah baza ki iyai min hanya ba, ina da yan mata har biyu daya shekara ta sha tara dayar kuma sha bakwai amman yar sha taran har tafi yar sha bakwan cika indai za'a Samar min ai nima sai in kawo su."
"Zan yiwa Ameerah magana duk yadda mukai zan fada miki ai kina zuwa nan ko?"

"A'ah yau ne zuwa na na farko abun ne ya ishe ni na fito nema."
"Ai kam Indai kina tare dani kingama samu kar ki damu."

"Nagode sosai."
Suna zaune anan gun zaku ga anzo an bada kudi haka zasu rarraba da yake wajen Babbar hanya ce kuma masu kudi na wucewa sosai. Har yamma suna gun inda da magariba ta gabato Hanne da Yaya Babba suka ce su zasu tafi amman Jummai tace zata taho gata nan.

Haka Yaya Babba ta tafi suna magana da Hanne inda tace
"Kinga gobe ki dauko mana yan kananun yaran nan mu fara bin gidaje muna Neman kayan sawa da abincin ci daga nan sai ki daura manyan yan matan ki akai su cigaba mu kuma mu koma wajen barar can."

"Kar ki damu ai Naga abin alheri ji ba fa ban ajiye kobo ba na tsamo har dubu biyu yau ni ce da dubu biyu Hanne."
"Hmmm ai Dan kince mu taho ne amman ai da dare anfi samu Dan kiji."

"A'ah Allah sanya albarka na baro yara a gida ba abinci ko kadan nasan yanzu ana can ana ta kuka."
Da haka suka karaso gida.

Jummai kuwa suna zaune wasu manyan motoci suka zo yan matan wajen suka kwashe suka tafi. Baki ta bude ta ce
"Ina kuma zasu kai su."

Matar da suke tare suke ta hira tin dazu Hajiya Kaltum ta ce
"Neman kudi gobe in kinga da bugun abujan da zasu zo sai kin rike baki."

"Kai dan Allah kace gobe na taho da Farisa ta ita."
"Taho da ita Jummai."

Suna zaune aka zo aka Kara basu wani kudin kan ta taho gida sai da ta hada dubu biyar da dari da hamsin ai kam tai ta murna inda taga Hajiya Kaltum ko a jikin ta tace
"Wai ke bakya murna ne?"

"Ai yau ba ai kasuwa ba Jummai."
Ido Jummai ta zaro tace
"A hakan?"

Kai ta gyada mata ta mike tace
"Kinga har tara saura minti sha uku bari naje gida na samu nai wanka na kwanta kan gobe kuma."

"Au kema tafiya zakiyi."
"Eh kema gwara ki tafi tinda kince kina da aure kar ya dawo yaga bakya nan."

"Uhmm sai tara da rabi zan tafi Dan Bani ke da girki ba."
"To shikenan sai anjima."

"Aha Dan Allah kar ki manta Dan gobe ma zan taho da yaran kinji."
"Allah ya kaimu."
Ta fada tana tafiya.

Sai Goma saura Jummai ta tafi shima ba dan taso ba dan bayan tafiyar Hajiya Kaltum sai da ta kara samun dubu daya akai haka ta tafi gida tana ta murna.
Yaya Babba kuwa tin a hanya ta tsaya ta sai wata tafiya wacce ake cewa damage ta siyo attaruhu da albasa da gishiri ta isa gida.
Yaran ta sama duk sunyi jugum jugum abin tausayi yan kananun duk sun yi baccin wahala abincin ta daura tayi sallah magariba tana gamawa ta sauke, duk yaran gidan sai da tabi kowa ta zuba masa ko ba a koshi ba an taba dai.

Zo kuga yadda aka Loma da dambe Dan sun mata yaushe rabon da suci taliya ko shinkafa daga gari sai gari kullum haka suke.

Jummai kuwa da ta dawo yaran sunyi bacci sai Farisa da Fauziyya wannan yasa tace
"Kuzo kuga harkar samu yaran kirki."

Suna Zama sukaga ta fito da kudi tana kirgawa ido suka zaro suna fadin
"Umma a ina kika samo kudi haka."

"Kudai ku gani dubu shida da dari biyar fa. Bara kawai."
"Bara?"

Babbar ta tambaya,
"Eh! Bara."
"Haba Umma bara da girman ki."

Dakuwa tayi mata tace
"In banyi barar ba uban ki zan yi shegiya tashi ki ban waje daman ke ai ina Jin ba 'ya ta bace an min canje da na haife ki yarinyar sai wani hali. Ko da yake zo nan dan uban ki ba inda zaki ki zauna kiji kuma gobe da ku zan fita kuje ku samo naku kinga daga nan ba sai ai muku auren ba ko ya kuka ce."
Farisa ita ce karamar kuma kan ta yana rawa tace
"Wallahi Umma ni auren daman nake so."

"To kwantar da hankalin ki cikin karshen shekarar nan zan miki aure kan lokacin mun tara kudin kayan daki kinji."
"Sai Umma ta."

Ita dai Fauziyya tana gefe batace kala ba. Dan ita Sam Bata Jin zata iya Bata kawai sai taje ta zauna bakin titi ana zuwa ana kallon su ana basu kudi.

Sai Yaya Babba bataiwa ya'yan ta kwadayin zuwa yin bara ba gwara yan yaran kamar yadda Hanne ta fada mata to su zasu gwada su gani.

Alhaji Kamis dake ba kula da gidan yake ba Sam bai ga wani sauyi a gidan Ba wani ya fita ko an samu wani canji shi dai ya shige daki yai kwanciyar sa bai damu da sanin halin da matan gidan suke ba.

*Wannan Rayuwar kasha kallo abubuwa kala kala kucigaba da biyayyar labarin a sannu zaku gane komai da komai. Kamar yadda na fada a farkon fara rubutun nan nawa, labari ne da zai tabo mana bangarori da yawa a acikin _Wannan Rayuwar_ da muke ciki, kadan muka fara tabowa wanda in zaku kura chapter One muke a ciki, dan haka muka dauki matsala guda biyu muka fara kuma a sannu zakuga darasin da muke son isarwa ku dai kucigaba da bibiyar wannan labarin namu. Muna godiya da yadda kuke jimirin bibiyar labarin nan namu. Muna godiya madallah da kulawa.*Washe gari haka Jummai ta fice ko tsayawa takan Sa'adatu batayi ba.

Sa'adatu kuwa daga nan gidan Hanne taje wata unguwa suka isa ta masu kudi anan suka fara bin gida suna fadin

"Dan Allah a taimaka mana da sadakar abinci ko kayan sakawa."+


Haka suka dinga bi gida gida cikin hukuncin ubangiji kuma Allah yasa Ba laifi sun samu sadaka dan sai da suka cika wani Katon buhun shinkafa har biyu da kayan sawa hadi da kayan abinci wani gidan kuma a basu dari biyu ko dari uku. Sai da suka dawo gida da dubu hudu Banda shinkafa kwano biyar da taliya guda ashirin ban kayan sakawa daga na yara har na manya.

Tare suka raba da Hanne inda Hanne ta barwa Sa'adatu kayan yan matan tace ta kaiwa yaran ta.

Sai da sukai kwana biyar suna bin manyan unguwanni suna bara sannan suka yanke shawarar yanzu yaran su kananu zata debo Dan sun gane suma ana samun alheri tasu sosai.


Jummai sun kulle ita da Hajiya Kaltum dan har tace mata ta kawo mata yaran nata.

Sa'adatu kuwa yau yaran ta ta deba da Dan shekara biyar da Dan shekara hudu ta fita da su sauran yan matan suna fadin

"Baba ina zaki?"

Tace "yanzu zan dawo."


Tana fita gidan Hanne ta isa tana zuwa suka fita can wata unguwa suka isa a hanya suka koyawa yaran in sunje gida me zasu ce.


Ai kam suna zuwa gidan farko da yake gidan kato ne na dai dai mai rufin asiri ba gate sai kofa Dan haka su Hanne suka tsaya a waje, yaran ne suka shiga cikin da sallama Dan maganar su ko gama kwari ba tai ba.

Matar gidan dake tsakar gida ta amsa tare da fadin

"Daga ina haka."


Dan shekara biyar din ne ya ce

"Hajiya Dan Allah a taimaka mana da abincin da zamuci ko kayan sawa."


Kallon su Hajiya ta tsaya yi duk tausayin su ya kama ta Dan haka ta shiga daki ta debo kayan yaran da zasuyi musu dai dai sannan ta isa gun mai gidan ta fada masa abinda ya faru yace ta basu shinkafa ko kwano ce da dari biyar. Haka tayi ta kai musu da kyar suka fita da kayan Sa'adatu ta karaso ta amsa tana fadin

"kai agode amma."

Nan ta zauna suna bude kayan da aka basu suna murna dayan gidan ma yaran suka tura nan ma akai musu alheri Dan taliya aka basu guda biyu da sabulun wanka. Ranar dai yaran suka dinga aikawa cikin gidajen mutane sun kowa samu musu kayan abinci da dan kudin da baza a rasa ba daga nan gun barar su na jiya suka nufa.


Jummai kuwa daga gida gun bara suka isa acan suka tadda Hajiya Kaltum har tazo tana ganin yan matan Jummai ta yana Dan kyawawa ne sun fi yar tama kyau. Jummai ta bari agun ta dauki yaran ta isa can gidan karuwai dasu ana ganin yan mata masu jini a jiki aka hau rubibin su Fauziyya dai fuska ta hade Farisa kuwa sai rawar kai take yi a haka ta samo musu manyan Alhazawa yadda daga nan suka fice dasu Dan suna da gidan da suke hutawa da yan matan.


Fauziyya dai bin Alhaji da aka hada ta dashi kawai take yi har suka isa gidan sai da suka shiga falon gidan sannan ya janyo ta jikin sa da sauri ta janye jikin ta.


Dariya yayi yace

"zauna ina zuwa."

Zama tayi tana bin dakin da kallo.


Cikin kitchen ya shiga ya dauko wata kwaya a cikin lokar kitchen din sannan ya bude firij wani lemo ya dauko ya saka magungunan da ya dauko guda uku ya cilla ciki, daya na feeling ne dayan kuma saka bacci ne, sai da ya tabbata sun narke sannan ya fita zuwa falon nasa.


STORY CONTINUES BELOW

A zaune ya sameta ajiye lemon yayi  ya dauki cup ya zuba mata. Mika mata yayi yana kallon ta yana lashe bakin sa kamar wani tsohon maye, ya ce

"Bismillah!"


Amsa tayi ta kafa kai dadin lemon yasa ta shanye shi dukka. Suna zaune a haka ya fara mata magana ji tayi jikin ta yayi sanyi tare da Jin wata matsanaciyar Sha'awa wacce Bata taba Jin ta ba. Idon ta taji yana rufewa, hannu ta saka a tsakanin kafafun ta tana cije baki. Hannunta ya kamo amman duk abinda take ji na tana bukatar namiji ture hannun sa tayi tana kokarin mikewa amman kafin ta mike sai ta fada kan kujerar tana mai bingirewa da bacci.


Baki ya lashe yana leka fuskar ta daukar ta yayi ya nufi dakin gadon sa acan ya hau cire mata kayan kallon irin surar ta ya kara hargitsa masa tunanin sa nan ya shiga jagwalgwala ta tana cikin baccin nan har ya shige ta amman duk baccin da take sai da ta sauke wata ajiyar zuciya mai karfi sannan ta cigaba da bacci.


Shi kam ba tausayi duk da ya jita a budurwa haka ya shige ta da karfi sai da ya samu gamsuwa kamar ya samu wata Babbar mace da ta Saba da abin haka ya Jima akan ta. Daga nan ya tashi yai wanka ya fice ya bar ta anan wajen.


Bai dawo dakin ba sai dare a Daren ma sai da ya Kara maimaita abinda ya aikata sannan yayi bacci.


A can bangaren Farisa kuwa daman ita tana da rawar kai ko a samarin ta ta Saba ayi soyayyar Shan minti indai za a Bata yar dari biyar ko dari biyu Dan haka ganin gidan da aka kawo ta da abinda mutumin ya nuna mata yasa ta Saki jikin ta nan suka lulla suna romancing junan su. Wanda Bata fargaba sai da ya fara Neman hanyar da zai shige ta nan ta fara kokarin kare kanta amman ba hali Dan karfin ta da nashi ba daya bane wannan yasa ya shige ta karfi nan ta fashe da kuka na azaba, Sam bai kawo ba budurwa bace Jin ta budurwa ta Kara sa mishi wani dadi inda ya dirjar ta har sai da ya samu nutsuwa tai ta kuka tana Allah ya isa.


Amman ganin yadda yake lallashin ta da mata Alkawarin abubuwan da zai Bata sai duk ta Saki ranta har da yin wanka a tare. Da tace zata tafi hanata yayi da kalaman sa masu dadi yace ta bari zai kai ta har gida Wanda daga nan ya dingai mata tausa har Bata San lokacin da bacci ya kwashe ta ba.

Ba ita ta farka ba sai asuba shima shine ya tashe ta da salon sa yana mai Kara Neman ta. Kuka ta fashe da shi tana fadin

"Wallahi da zafi ciwo wajen yake min."


"Sorry Baby a hankali zan miki bazan fama kiba."

A haka ya fara aika mata da wasannin sa da ya kusan zautar da ita har taji itama tana bukatar Jin sa a jikin ta Dan irin abinda yake aika mata.


Sai da taji ya shige ta taji azaba yasa tayi da na sanin Kara barin sa ya shige ta. Sai da suka wanka sukai sallah sannan ta koma bacci. Karfe 10 na safe yasa aka kawo musu abinci nan ya cikata da kayan dadi inda ta manta da komai ta hau cin abinda wani bata taba ci bama a rayuwar ta. A ranta tana yiwa Mahaifiyar ta addu'ar Allah yasa ka mata da alheri Ashe wannan dadin take gano musu. Sai yamma ya dauke ta ya maida ta gida bayan yai mata syayya mai yawan gaske sannan ya Bata kudi har dubu dari sukai sallama akan gobe zata je.


Fauziyya kuwa sai karfe tara na safe ta farka da wani matsanancin ciwon kai. Kanta ta dafe tana kallon dakin da take tare da tino abinda ya faru da ita jiya. Kuka ta fashe dashi zata dira a kan gadon taji jikin ta yai wani irin tsami kasan ta kuma ya daure ga zafi. Kai ta hade da gwiwa tana kuka dakin aka budo da sauri ta dago ta dago kan ta. Tsaye yake a bakin kofar ba wani Babba bane Dan bai fi shekara talatin da biyar ba ko da takwas kyakyawa ne yana sanye da dogon wando da yar karmar riga armless mai kyau sai tashin kamshi yake fuskar sa a sake alamar yana cikin farin ciki.


Kallon ta ya tsaya yi dan jiya jarabar da yake ciki bai barshi ya gama kallon ta ba. Kyakyawa ce ta karshe dan daga Baban ta har Maman ta bafulanai ne.


In kaga Fauziyya zaka iya zaton balarabiya bace, dan kyakyawa ce sosai ga diri kamar ita tayi kanta. Tausayin ta yaji amman kuma yadda yaji ta baya tunanin zai iya kyale ta dan yasan itama tinda ya fara lalata mata rayuwa da kyar zata iya kula da kanta bata fada harkar neman maza ba dan yawancin yan mata da haka suke farawa daga tautsayi ya fada mata sai ta shiga ruyuwar banza, bata tunanin ta cigaba da rike kanta. Bari muga ko itama fauziyyan ya tata rayuwar zata kasance.


Dakin ya karaso da sauri ya kamo hannun ta da sauri ta kwace hannun ta tana aika masa da wani kallon tsana.

"Yi hakuri tashi na taimaka miki."

ya fada yana shiga bandaki ruwan zafi ya hada mata sannan ya fito yace

"Tashi ki shiga."


Mikewa tayi amman tana daga kafa ta saki wani ihu tana mai yin salati dan irin zafin da taji. Wannan yasa bai tsaya bi ta kanta ba ya dauke ta sai cikin bandakin. A ruwan ya sakata ta saki wani kara tana kamkame shi.

"Yi hakuri zakiji dama dama tsami wajen yayi."

A haka sai da yai mata ruwa uku sannan ya barta tai wanka da kyar ta karaso dakin ta dauki kayan ta tasaka sannan ta mike ta tada sallah. Tana idarwa ya shigo dakin hannun sa dauke da tray.


Tea ya hada mata kin amsa tayi sai da ya hadata da Allah da Annabi sannan ta karba tasha ya bata magani. Daga wannan ba abinda ta karaci tace ya maida ta gida.


"Ki kwanta kiyi bacci in kin tashi kara sitbath kafin nan tafiyar ki zata dawo dai dai sai na kai gida kinji. Sannu."

bata son musu dan haka ta koma wani baccin wanda ta rasa irin baccin da take dan har lokacin maganin bai gama sakin ta ba.


Acan gida kuwa kawar Sakina yar gidan Sa'adatu ce tazo wacce ita ce sa'ar  Fauziyya.

Sakina ta kasance yarinya ce mai yawan sha'awa wannan yasa ta fito da mijin aure amman mahaifin ta yace shi bai da kudin aure. Saboda tasan matsalar ta Bata kula samari Dan tasan komai zai iya faruwa. Dan tasan halin samarin yanzu duk Wanda yazo bama in ba aure ya kawo shi ba zai fara Neman wani Abu a gun ka.

Tana zaune Habiba Kawar ta tazo Zama sukai suna tattauna matsalar rayuwar da irin matsalar da take fuskanta.

"Kinga Saki tinda bakya son yin zina ai akwai hanya mai sauki da zaki na samun yadda kike so ba tare da wata matsala ba, ke wallahi in har kika Zama Babba a harkar kudin da zakiyi sai Allah. Namiji ma sai kinji bakya Neman sa."


"Haba dai Habee da gaske."

"Kalle ni kiga yanzu menene a jikin da za ace ina da aibu, irin matsalar kice dani Saki Abba na yace bazan aure ba sai na gama karatu ni kuwa aure nake so, duk yadda na ke son fahimtar dasu sun kasa ganewa, dole na hakura nafara karantu amman fa matsala ta tana kara gaba. Yadda kike tsoron maza a yanzu a lokacin haka nake tsoron  su dan bana son su batan rayuwa bama inda nake da sha'awar nan. A makaranta na hadu da wata kawata wacce ita ta koyan harkar nan wallahi sau day biyu mukai baki ji ba har yafi sex dadi dan kiji, Ki zo muyi sau daya sai kin ji dadin da baki taba ji ba."


"Dan Allah Baba bazata ganeba."

Dariya Habiba tayi tace

"Shekarata biyu ina yin abun nan amman ba Wanda yasan inayi. Ko kinga wata alama."


Kallon ta Saki tayi sama da kasa tace

"Ba wani canji."


"Hmmm lallai ga kudi kuma dake cikin account dina kamar sayi magana dan yadda nake samun kudi ko Abba na bai Bani ban da matsalar komai."

Duniyar tunanin Saki ta tafi a ranta tace ai gwara ta fada a ciki wannan harkar ta samu nutsuwa sannan tana samun na juyawa.


"Yanzu a ina zamuyi Habee?"

"Akwai gidan kawata ki zo muje."

Ba shiri Saki ta saka hijab suka bar gidan.


Har suka karasa gidan kirjin ta na bugawa Dan tsoro da farga. Sai da sukaje wani bedroom suka shige anan Habee ta cire kayan ta Saki duk sai ta ji wani iri. Ki cire hijab din mana. Ta fada tana nufar firij inda lemuka ne kala kala a ciki kuma an saka kwayar da zata saka Sha'awa. Daukowa tayi ta sha ta zubawa Saki amsa tashi ta sha. Tana zaune Bata San lokacin da ta fara Jin jikin ta na wani iri ba tana wata irin mika take da gwantsarewa.Wannan yasa Habee tayo gunta ta fara shafa ta daga nan suka fada haramtaciyar rayuwa.

Sai da suka samu nutsuwa sannan sukai wanka Sakee sai taji wata nutsuwa tare da Jin ta sakayau suna zaune a gidan har rana Habee ta tafi unguwa, sai ga Kawar Habee nan taga Sakee tai mata nan ta Kara loda mata Abu a lemo ta Bata anan falo sukai masha'ar su da zata tafi har da Bata 10k sukai sallama ta tafi gida cike da murna yau ta samo kudi.+


Da ta koma gida ma Baba Bata dawo ba dan haka ta zauna tana jiran dawowar ta Dan yau ita Bata Jin yunwa taje tace abincin yan gayu da lemo kala kala masu dadi da kudi ga abunda sukai ta Kara Jin dadi sai dai gaban ta yana Dan mata zafi Dan bai Saba ba.


Jummai kuwa data koma gida ba yaran ta ko a jikin ta. Haka tai baccin ta.

Su Baba ma sai magariba ta shigo gida nan ta hau hada hadar daura musu abincin dare. Tuwon semo ta daura wacce suka samo a can yawon barar su tayi miyar kuka sai isha'i ta gama ta mikawa kishiyoyin ta sannan ta bawa yaran ta kowa yaci ya koshi sai bacci Dan tin abincin safe ne da tayi musu kosai da koko.


Washe gari da safe, Jummai ta  tashi tayi wanka takara haramar fita yawon barar ta. bata jima da fita ba sai ga Farisa ta dawo Dan haka ta shiga daki ta kara wanka ta fito ta dauki lemo da biskit tana sha sai ga Samira nan matar baban su ta uku ta shigo.


"A'ah ta gida na kayan dadi aka samo ne, shin wane garan aka samu."

"Anty Samira wannan 'Babban kamu ne,"


"Dan Allah fa Bani in sha."

"Hmmm Anty Samira wani Babban Alhaji ne, kawai in kika bada kai sai abinda kika ce kina so. Ta so mu je ki gani."


Tana mikewa Hafsa sa'ar ta yar dakin Baba Sa'adatu ta shigo tana fadin

"Yar uwa jiya ina kika kwana kika barni da kewar ki ina ta Jin yunwa ina jiran ki dawo nasan Dan tsiren nan zaki shigo mana dashi."


Hannu ta sa ta yafito ta tace

"Zo muje kigani."

Suna shiga dakin su ta fito da kayan da aka siya mata da kudin da ya Bata daga Anty Samira har Hafsa suman tsaye sukai Dan sun manta rabon da suga kudi da irin wannan kaya masu tsada banda kayan ciye ciye masu tsada da dadi."


"Yar uwa a ina kika samo wannan uban kayan?"

"Zo zauna kiji."


Nan ta zauna dasu tana ta basu labari nan da nan Hafsa tace

"Yar uwa nima Dan Allah ki kai ni na samu nima."


Dafata Farisa tayi tace

"Kar ki damu yar uwa."


Ana cikin haka sai ga kiran wayar ta nan nan ta dauka

"Nayi kewar ki Baby!"

Ya fada.

"Nima nayi kewar ka ya kake?"


"Ba yadda nake ina nan ina ta tunanin ki wallahi, dama zan Kara ganin ki a yanzu."

Murmushi tayi tace

"Ka dai bari zuwa gobe."


"Gaskiya bazan iya bari zuwa gobe ba anjima zan zo in dauke ki."

"Uhmm to shikenan."

Sukai sallama. Kallo suka bita dashi. hafsa ce ta amshi wayar tana juyawa tana fadin

"Kai yar uwa kin Faso gari fa."


Ido ta juyawa tace

"Kema kwanan nan zaki shigo gari."

"Dan Allah da gaske?"

Ta rumgume ta tana murna da ihu.

"Nima baza abarni a baya ba."

"Haba Anty da auren ki?"


"Bakusan an fison matan auren ba."

"Ni dai gaskiya ina kishin Baba na."

Hafsa ta fada.


"Ai kam sai na fita wallahi. Ke ai baya kishin mu tinda baya sauke nauyin dake kan mu, ga Yaya Babba da Yaya nan sun zage suma neman kudin suke."


"Kema kiyi irin nasu."

Hafsat ta fada.

"Ina na fison mai aji inda zan nacin mai dadi in sha sanyin raba."


Dariya Farisa da Hafsat sukai suka tafa. Daga nan suka cigaba da daga kayan.

Auwal Dan shekara goma sha daya kuma rake yake siyar wa shine gun duk majalisar da zai ga ana siyar wa, wannan yasa yake yawan zuwa gun wasu yan shaye shaye Wanda suna yawan siyan raken abinda yasa kenan kullum yana gun su.

Bata Kara tashi ba sai la'asar shima ba kowa a dakin ban dakin ta shiga ta Kara shiga ruwa tai alwala ta fito tai  sallah tana idar wa ta kwanta wani baccin ya kuma duk ta, ba ita tashi ba sai magariba shima yunwa ce ta tashe ta Dan haka tana yo alwala tai sallah. Ledar da ta gani a gefen ta shi yasa ta janyo. Abinci ne mai rai da Lafiya da kaji da lemo da ruwa har da magani. Ci tayi ta sha. Tana gamawa anan sallar isha'i sallah tayi ta je Dan fita amman sai taji kofar a rufe wannan yasa ta Kara komawa ta kwanta. Anan bacci ya dauke ta.

Ana magariba Farisa ta sha wanka tana jiran isowar Auwal din ta. Ga Hafsa zaune a gefen ta tana zaune itama tayi gayun ta Dan Farisa ce ta ara mata a cikin kayan da aka siya mata.


Kiran wayar ne ya shigo wannan yasa ta dauka.

"Ina kofar gida."

Ya fada kallon Hafsa tayi tace

"Tashi muje."


Tinda suka fito yake kallon su zai ce bai taba kamun yara kananu kamar Farisa ba ga kyau ga diri ga ni'ima baki ya lashe har suka shiga motar ya tada bayan Hafsa ta gaishe shi.


Suna cikin tafiya ta ce

"Ga kanwar tawa da nai maka maganar ta."


"Eh nayiwa Alhaji Sani maganar ta yace nakai masa ita ma."

"Ok!"


Gidan Alhaji Sani suka isa a gate ya tsaya Alhaji Sani ya fito yace

"Ya akai ina Babyn tawa?"


Glass din motar ya sauke ya ce

"Ga ta nan."


Yana sauke ido a kan ta ya ji duk nutsuwar sa ta gushe. Kofar ya bude ya kamo hannun ta yana wani tattabata.

"Malam kai mata a hankali itama sabon shiga ce fa."


Alhaji Sani bai Sam ma yana yi ba suka shige ciki duk Hafsa sai ta kasa sakewa amman Tina kalaman Farisa da take cewa ki nuna kema yar bariki ce shine za a je dake amman in kina nuna tsoro da gidadanci wallahi zasu zubar dake sun fison wadan da idon suke a bude.


Wannan yasa ta saita kanta. Suna shiga falon sa ma daukar ta yayi yai bedroom da ita. Yana direta ya hau cire kayan jikin sa. Take tsoro da fargaba suka dirar mata wannan yasa ta Dan ja baya.


Kallon ta yayi yace

"Haba Baby kar ki gujeni man. Fada min me kike so zan miki kome kike so kinji?"


Kai ta gyada masa ya janyo ta nan ya fara aika mata da sakonnin da dole jikin ta yai sanyi yai lakwas amman sai da taji zai shige ta taji zafi ta fasa ihu tananeman dauki amman aikin gama ya riga da ya gama Dan haka sai kuka shi kam yana can kwasar gara bai San ma tanayi ba.


Da kyar ya gyale ta Dan abinda yaji yafi karfin tunanin sa. Sai da ya gama yaga aika aikar da yayi da sauri ya shiga bandaki da ita ya hada mata ruwan wanka da yake likitane bayan ya gyara ta ya dubata ya Bata magani ta sha baccin wahala ya dauke ta. Shi kuma baccin farin ciki ya kwashi zunubai.


Su Farisa ma kwana sukai Abu daya duk da tana Jin jiki amman tace kudin da zata samu ba.

*Hattara ga iyaye mata da maza wadan da basa kula da fadi tashin yaran su da wadan da basa sanin halin da yaran suke cike da wanda son abin duniya ya rufe masa ido hakika wannan zamanin bala'in dake cikinsu sunyi yawa dole mu kula da amanar da Allah ya bamu na kula da tarbiyyar ya'yan mu. Shin ina alfahari ace yar ka ta taba yawon karuwan ci wanda na tabbata abun nan sai ya bita tindaga kan iyayen ta ya'yan ta da jikokin ta. Mu dinga hakuri muna godiya da abinda Allah ya hore mana sannan mu kasance masu godiya da amsar kaddarar mu. Nasan ba mu ke da ikon bada tarbiyya dukka ba dan tarbiyya na ga Allah amman Allah yace tashi in taimake ka. In mun tashi mun kai masa kukan mu Allah zai amsa mana ko a lokacin bai amsa ba zai mana canje da wani abu daban. Abuda zance shine mu dake da addu'a sannan mu tsarkake zuciyar mu da niyyar mu akan al amuran rayuwar mu*

Post a Comment for "WANNAN RAYUWAR CHAPTER 2"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...