WA NAKE AURE CHAPTER B - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WA NAKE AURE CHAPTER B

WA NAKE AURE CHAPTER B

- - Post a Comment

 WA NAKE AURE CHAPTER B


WA NAKE AURE?
    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*

*FANS KUYI HAKURI USMAN KISHINE YA KAMASHI,DUK MAKIRCIN HAYATU NE, MASU CEWA MAFARKINE ,HHH TO BA MAFARKI BANE USMAN YASAKI SAUDAT,DUK GROUP DIN DA NAKE COMMENT YAYI YAWA, MASU MAN MAGANA P.C KUYI HAKURI MASSAGE YAMAN YAWA, MASU KIRANA NAGODE,NAGODE DA FATAN ALKHAIRINKU*2

21

Usman kam kaba ɗaya rayuwarshi ta canza,Hayatu ne yayi saurin shigowa yana faɗin "miya faru?"

"taci Amanata bazan yafe mataba,ta cuceni ta cuci rayuwata"

Mama ta shigo Gidan"hayaniyar minikeji"

Saudat tayi Saurin miƙewa "wallahi wallahi Mama ni bansan mutuminba,asalima daga gidan..."

"ƙarya kike munafuka,aidai yau dubu ta cika,asirinki ya tonu,anzo ƙarshe tunda ya sakeki har Ukku,sai atattara akoma can aji da baƙin hali"+

Innalillhi Saudat take maimaitawa,Usman ya matsa kan Loka ɗin gado yana kuka Mama tace"rubuta matashi a rubuce"

Usman ya ɗauko biro da takarda ya rubuta mata sakinta,kamar yadda ya faɗi,Mama ta anshe ta miƙa mata,Sai lokacin wani kukan baƙin ciki ya ziyarci ta.

Mama tace"afita ayican"tana maganai tana neman turota waje,Saudat matsa kan wadrop ta jawo doguwar hijab ɗinta da kaya,Abayar ta zura,ta kama hannun Sultan wanda yatashi jin hayaniya.

Mama tace"ina zaki da shi"
Hayatu yace"barta ta tafi dashi,wama yasani koba ɗanmu bane"

Usman dake gefe yace"kada ka sheganta min yaro"

Saudat bata saurareshi ba,ta fice daga gidan lokacin goma na dare yayi,ta rasa yadda zatayi,tunawa tayi da Maman Khalifa,saidai tasan sun rufe gida,hanyar gidan ta nufa tana kwankwasawa tana kuka,Mijin ne ya fito yana tambayar waye"Ni ce Saudat"

Yana buɗe gidan yana tambayarta lafiya,Saiga Maman khalifa,"saudat ya akayi?"

Kuka Saudat ta ƙara fashewa dashi mai tsanani,ta miƙawa Maman khalifa takarda,Maman Khalifa ta buɗe,tana karantawa ta dafe kai tana salati,mijinta yace"miye?"

"saki Ukku Baban khalifa"tana kuka tana miƙa mashi takardai,Yana karantawa ya girgiza kai,ya ce"shiga ciki"

Ba musu Saudat ta shiga,tsakar gidan kan tabarma suka zauna,yana tambayarta abinda ya faru,Saudat tana kuka ta basu labari,su duka sunji zafin Abin,Maman khalifa tana masifa ta miƙe "wallahi bari inje masu,ƴan iska tsinannu wallahi sai Allah yasaka maki"

Baban khalifa yace"kada kisake kije,zuwanki baida amfani saidai wata fitinai,saboda dai saki Ukku ba wani gyara"

Nan suka zauna sunata ba Saudat Haƙuri,taji sanyi cikin ranta sosai,sai dai zuciyarta yanzu ta fara hasko mata babban kuskuran da tayi,tasan da tabi Umarnin Pappa da hakan bai faruba,sun jima suna mata nasiha,taji sanyi sosai,Baban khalifa yace"kuje ku kwanta da safe sai ki ɗauko kayanki kitafi gida".

Haka suka mike suka shiga ciki,Saidai Saudat yadda taga rana haka taga dare,dan ko ɓarawon bacci bai ɗauke taba,Ana gama sallar Asuba Saudat tace zataje ta ɗauko kayan ta wuce kafin gari yayi haske.

Itada Maman Khalifa suka je gidan,a buɗe yake sabda Usman yana fita sallar Asuba,shiga sukayi suka nufi ɗakinta,Su Mama najin Motsi suka fito,Nusaiba saidai ta kwashe da dariya tana faɗin"andai yi Abun kunya"

Saudat tana kuka ta haɗa kayan da tasan zasu buƙata ita da Sultan,Maman Khalifa ta haɗa mata kayan da ta bari a waje guda.

Suka fito tsakar gida,Nusaiba tace"anyi na farko anyi na ƙarshe,sai a nemi wani sarkin Amma ba nan ba"

Maganar tayiwa Maman khalifa zafi,ta juya Saudat tayi saurin ruƙo hannunta,Nusaiba ta bangaje Saudat"barta muga abinda zataiman,wama yasani ko tare kuke iskancin ku"

Aikam Saudat najin Haka,tayi kukan kura ta maƙuro wuyan Nusaiba,tafara bugunta kamar an aikota,bugunta kawai take,Nusaiba taji wuya tafara ihu,lokacin Saudat da kadata ta haye ruwan cikin ta,Mama ta rugo zata kwaceta,Maman khalifa ta tare ta,saiga Hayatu ya shigo gidan,dagudu ya fincikar da Saudat daga kan Nusaiba.

Aifa nan aka kama hayaniya,faɗan mata,wanann ya maida wannan ya maida,saiga Usman ya shigo daka ganshi kasan ba ƙaramin tashin hankali yake cikiba.

Itakam Nusaiba,baki harya kumbura hanci duk yakawo jini,Saudat ta kalleta"yarinya wanann shizaisa ki gane inayi maki ragine,saboda darajar tsohon mijina,bawai dan bazan iya dukanki bane"

Ta juya ta kalli Mama"ke kuma Allah ne kadai zai saka mani abinda kukai mani,keda zuri'arki,na zaman Aure da ɗanki amma gaba ɗaya bansan *WA NIKE AURE BA* karshe kun haɗa makirci,yayi sanadin rabuwarmu Allah bazai barku ba"

Ta juya ta kalli Usman"wanann shine sakaiyar Abida nayi maka,ka nuna man kai ɗan halak ne,tunda nike ban taɓa aikata zina ba,ko kafin Aure na balle da Aure na,Allah shine shaidata,shizai mana hisabi"

Tana maganai tana kuka,Usman kam bashi da bakin magana,jikinshi yayi sanyi,sai wasu hawaye dake zubo mashi.haka suka fito daga gidan,suka shiga gidan Maman Khalifa ta ɗauko Sultan,Maman Khalifa harda mijinta sukazo rakota bakin titi,Maman khalifa sai kuka takeyi,yau zasu rabu da Saudat.

Haka ta samu Adai-daita tahau,suka tafi,Nan fa Saudat ta ƙara fashewa da wani kukan baƙin ciki,ganin tana kuka shima Sultan saiya fashe da kuka,jawo yaron tayi ta ƙara rungumeshi tana kuka.

Bakin gate ɗin gidansu,aka ajiyeta,ta fito ta ɗauki kayanta ta nufi gidan,Mai gadi ya buɗe yana ganin itace ya anshi trolly ɗin kayansu,duka biyun yana mata sannu da zuwa,"Allah yasa dai lafiya"

Itadai Saudat ko magana bataiba,illa kanta data saka cikin gidan tana kuka,kan dinning ta tadda yaran da Mami,saidai Pappa baya wajan.
Mami ta tareta,tana tambayarta,Su Ilham sukayo kanta,kuka ta saka Mamai ta taso ta tare ta,Saudat ta miƙa ma Mami takarda,Mami ta anasa ta buɗe tana karantawa ta xaro ido"saki Ukku? Innalllhi wa innna ilaihi raji'un"

Nan Saudat ta durƙushe tana kuka,Muhsin ya fito daga ɗakin shi yana cewa"Mami miya faru?"

"Saudat ce,wai yasaketa daki Ukku"

Ido yazaro yana faɗin"subhanallah"

Da sauri Pappa ya ƙaraso falon,yana tambayarsu abinda ya faru,Mami ta gaya mashi ta miƙa mashi takarda.

Pappa ya zauna yace"ni mizanyi da takarda,ki miƙa mata abinta,idan ta ansa ta tashi ta koma inda ta fito"

Saudat ta ɗago ta kalleshi,tasan da gaske yake,wani kuka ta fashe dashi,Pappa ya kalli Mami ya daka mata tsawa"ba kijin Abinda nace ne?"

Take Mami ta miƙa mata takardai,Pappa yace"maza kibar man gidana kada kin ƙara ganin ƙafarki"

Saudat tahau bashi haƙuri,tana kuka mai tsuma zuciya,Pappa yace"idan kika bari na miƙe tsaye wallahi sai kinji jiki,kin mance lokacin da nake rarrashinki? Kada in ƙilga Ukku baki fice ba"

Ai take yaran suka fara kuka"Dan Allah Pappa kayi Haƙuri,ka yafe mata,Allah bazata ƙaraba"

Pappa ya daka masu tsawa"kubar falon nan"yana maganai yana miƙewa tsaye yayo kan Saudat,cikin Sauri Saudat ta miƙe ta kama hannun Sultan.

Muhsin ya kalleta,shi kanshi yana tausayin ƙanwar tashi,ko da shima ya juya mata baya amma yanzu bazai iyaba,ya juya ya kalli Mami"Mami kiba Pappa haƙuri"

Mami ta kaɗa mashi kai,dan bazata iya tunkarar mijinta ba idan yana cikin wanann halin.

Muhsin ya matsa wajan Pappa,tun kafin yayi magana,Pappa ya fara nunashi da yatsa,Muhsin ya durkusa yakamo ƙafar Pappa yana neman yafiya,Pappa ya janye ƙafarshi,yayo kan Saudat"fice man daga gida"

Cikin kuka Saudat ta fito ta nufi hanyar titi,ita kanta hankalinta baya tare da ita,ga yaro tana ɗauke ga akwatin kayanta,kuka kawai take zuciyarta tana harbawa...........
*ku biyoni*

*AUNTY HALILOSS✍🏽*

WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


*WANDA SUKAYI MAN MAGANA SONA SON SU SAYI KAYAN ƘAMSHI,TURARAN KAYA NA JIKI DANA ZUGUNNI,DUKA AKWAI,KUYI MAN MAGANA CHART ƊINA YA GOGE NE*

*DEDICATAD TO ALL WA NAKE AURE FANS,IDAN NACE IN FAƊI SUNA ZAKUGA KAMAR NAYI SANKAI*


*AUNTY NAPPY AM WAITING FOR KAXAR MANSHO🍗🍗😋😋*


22


Mai Napep ta samu,ya ɗauke su,gidan Ammi suka nufa,Ammi tana ganinta tafara salati "lafiya daga ina kuke?"


Jikin Ammi ta faɗa tana kuka,Ammi ta ɗagota"miya faru"


"Ammi wallahi sheri sukaman,Allah ban aikata ba"


Ammi ta riƙeta tana tambayarta,ta miƙawa Ammi takarda tana faɗin"Ammi ya sakeni"


Salati Ammi taɗauka,ta jata suka zauna,Ammi ta karanta"hasbunallh kai wannn wane irin sakin wulaƙanci ne?miya haɗaku Saudat".


Saudat tana sharar hawaye tafara ba Ammi labari,harda wahalar da tasha a gidan,har zuwa yau,Ammi ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba,nan tahau lallashin Saudat tare da faɗi mata wannan kɗan daga halin mazan wannan zamanin ne.


Saudat tace"Ammi wallhi nayi nadama,dan Allah kiba Pappa hakuri,bazan ƙaraba"


Ammi taji tausayin Saudat,"shikenan tashi kishiga ɗaki,kiyi wanka ki gyarawa Sultan jikinshi"


Ba musu Saudat ta miƙe,taje ta ajiƴe kayansu,ta yiwa Sultan wanka ta  saka mashi kaya,sannan itama tayi wanka,Ammi ta shigo ɗakin"taso kuje kuyi breakfst"


Saudat ta gohe hawayenta,Ammi ta zauna"kada ki ƙara kuka,duk abinda ya faru take it as kaddararki,kuma kidaina damuwa kada ki sakawa kanki ciwo"


Saudat ta ɗaga kai tare da miƙewa,suka nufi falon,anan ta tadda Dady,zuwa tayi ta gaidashi tana kuka,Dady yasa hannu ya dafa kanta alamar rarrashi"shikenan ya isa haka"


"Dady kaba Pappa haƙuri"

"kada kidamu zai sauko,am always here for you"


Haka tayi kukanta,Dadƴ ya kamo hannunta"oya ci abinci"


Saudat ta zauna,ta itada Sultan sukaci abincin su sosai,hankalinta ya ɗan kwanta ganin yadda Dady ya maida hankalinshi kansu yana rarrashinta.


Saudat batajin zafin sakin da Usman yayi mata,babban baƙin cikinta rashin samun karɓuwa a wajan iyayanta,sai kuma yaronta da take tausayi zai taso ba tare da soyayyar ubanshi a kusa dashiba.


          ******

Gidan Pappa kuwa koda Mami tayi mashi magana faɗa ya hauta dashi,dole ta haƙura,Muhsin kanshi yaji haushin abinda Pappa yayi saboda gudun Saudat ta shiga matsala.


Pappa kam fita yayi gidan ya nufi Office,yakasa mance abinda Saudat ɗin tayi mashi,duk soyayyar da yake mata yazama dole tagane kuranta,haka yayi aikinshi yana tunanin irin hukuncin da zaiyanke mata.


Koda ya tashi daga Office ƙarfe biyar gidan Yayanshi ya Nufa wato Dady babansu Areef dan yasan lallai can ta nufa.


Yanayi Parking ya fito a harabar gidan yaci karo da Sultan yana ta wasanshi,Pappa ya matsa ya kamo hannunshi,"wasa kakeyi ne?"


Yaron yafara yimashi gwaranci,Pappa yayi dariya,ya ɗaukoshi"ashe ka iya magana"


Dady ne ya fito daga Ƙofar part ɗinshi,Pappa yana ganinshi ya ɗaure fuska,ya nufi hanyar shoga main palo ɗin gidan,sarai Dady yasan abinda yakawoshi.


Hakan yasa ya bishi baya,yana shiga yatadda su zaune ita da Ammi Aje  Sultan yayi,ya kalleta"wato dana koroki nan kika taho,ai nanma gida nane tunda gidan Yaya nane,baki isa ki zaunaba,tunda kikaƙi ɗan uwanki toni ina son nawa ɗan Uwan maza ki tashi ki koma wakan wanda yafiye maki mu?".


Ammi ta miƙe tsaye ta ce"Haba Pappa miyake damunka ina kakeso taje?"


"ki barshi ba inda zata,tunda kai ba'a rarrashinka,taya zaka yanke irin wanann hukuncin akan mace,duniya kakeso tabi komi"


Pappa ya kalleshi,"Kabar min haka,duk laifin datayi bakwa gani,har wani gata za'a bata,bayan tayi wurgi da damarta"


Nanfa Dady yahau faɗa,Pappa kam ko ajikinshi,sai ma yi yake kamar Ana ƙara tunzurashi,ya nufota,ya korota waje,Pappa da Ammi suka biyo su harabar gidan.


Pappa ya riƙeshi"waikai ni ban isa in saka kayi abuba?"


"ina kakeso take?"


Dai-dai lokacin Areef ya shigo da hancin motarshi,tun kafin ya buɗe ya fito yagansu,yakuma fahimci akwai matsala ganin riƙon da Dady yayi ma Pappa,da Sauri Areef ya fito daga mota.


Sanye yake da black shadda babu hula a kanshi,takalmi da agogon hannunshi black ne,abinka ga farin mutun hakan ya ƙara fito da Asalin kyanshi.


Saudat kam kuka take kamar ranta zai fita,Pappa ya kalli Dady yace"ka sakar man riga,wanann yarinyar harta isa ta haɗani da ɗan Uwana,wallahi baki isaba"


Yana magana yana yunƙurin yowa kanta,Dady yaja ya tsaya"shikenan kayi duk abinda kaga dama,tunda ka nuna man ni ban isa gare kaba,kuma banida iko da iyalinka"


Pappa yace"Allah duk wadda za'ayi saidai ayi lokacin da ta bijirewa maganarmu,tamanta da irin wannan ranar,yanzu ina soyayyar ina son da take mashi,wannan shine son,ya nuna mata soyayya Saki Ukku lokaci guda duka aure ko shekara huɗu ba'ayi ba,to sai dai tasan inda zata ko takoma ashi tunda yafita akanmu"


Areef ya shiga kaɗuwa jin maganganun Pappa,sai kallonsu yake,Ammi Kanta kuka takeyi,dan tunda take da mijinta bata taɓa ganin sunyi sa'insa da ɗan uwanshiba balle faɗa irin haka.


Areef ya matsa ya kama hannun Sultan dake ihu saboda ganin hayaniya da kukan da Mahaifiyarshi keyi,ya riƙe yaron ya nufi inda Pappa yake,ya kalli Dady,su dukansu ransu aɓace yake,badai kamar Pappa da yake huci.

Areef dakyal ya iya buɗe baki,yace"Dan Allah Pappa kayi hakuri ka...."


Ai Pappa bai jira cewarshi ba,yace"kada inji bakinka,ka tambayi ɗan Uwanka abinda nayimashi a gida"


Ya juya yakalli Ammi yace"ki ɗauko mata akwatin kayanta,maza tabar gidan nan,dan ni inason ɗan uwana,bazan taɓa gudun shiba"


Ammi kam tasan duk wannan abinda yake soyayyar da Pappa yakeyiwa ɗan uwan shice ta shafi Areef,to ita taya zataƙi Saudat,bayan tunda suke da mahaifiyar Saudat hansu a haɗe yake.


"ki ɗauko mata kayanta nace"


Dady yace"ai nidai bazaka ƙarajin bakina ba,tunda kafi ƙarfina"


Saudat ta tsugunne a wajan tana wani mugun kuka,wanda koda Usman ya saketa batayi irin shiba.


Areef ya kamo hannun Pappa,Pappa ya fizge,shikanshi Areef bai taɓa ganin family ɗinshi a irin wanann yanayin ba.

Areef ya juya ya kalli Ammi yace"Ammi ɗauko kayan nata"Ammi ta kalleshi,Areef ya ɗaga mata kai,danshi kanshi idanuwanshi sun canza.


Ammi taje ta ɗauko kayan,Pappa ya koma kan resting chair ɗin harabar gidan ya zauna yana huci.


Ammi ta jawo trolly ɗin,Areef yazo ya ansa ya saka a motashi,ya buɗewa Sultan ya shiga,ya dawo ya kalli Saudat cikin murya mai kaushi yace"zo muje"


Take Pappa ya miƙe"ina zaka kaita?"yana maganai cikin faɗa.


Areef ya matsa kusa dashi"kayi Hakuri Pappa,zan ɗauki ƴar uwatane zuwa gidana,tunda ka hanata zama hidan ɗan Uwanka"


Nan Pappa yajawo wani faɗan akan Areef bazai ɗauke taba,Dady ya matso yace"to kuma ina ruwanka anan"


Areef yace"4give me my Luvly Pappa kasan banayi maka musu,amma yau kayafeman,nima yar uwa tace ai"


Pappa yayo kanshi,yana masifa.......


*follow me*

*AUNTY HALILOSS CE✍🏽*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


*FANS COMMENTS ƊINKU YANA RIKITANI,KADA KUSA INTA TYPING BA TSAYAWA,INA GODIYA MY PEOPLE*+


23


Areef bai jira cewar Pappa ba yaja Hannun Saudat mota ya sakata,ya gewaya ya zauna ma zaunin driver,revass yaƴi tare da sakin wani horn da ƙarfi har saida maigadin ya rikice garin buɗewa.


Dady,Pappa,Ammi babu wanda ya iya motsi,Ammi ce tayi wani murmushi ta juya ta shige part ɗinsu,Dadƴ kam kallon Pappa yake yana mamakin irin wanann tsauri nashi.


Pappa ya juya ya kalleshi,baiyi magana ba ya nufi motarshi,ya shige yabar wajan.


Saudat kuka kawai take rusawa,Areef kan wuta yake ƙara ba mota,ga Sultan a gefenta yayi bacci saboda kukan da yayi,Saudat ganin sunyi tafiya mai nisa yasata tsaida kukanta tana shashshekar kuka"Ya Areef ka ajiƴeni anan,ni bazanje gidan kaba"


Areef baiko tsaya jin taba tuƙi kawai yake,sai zuciyarshi da take harba mashi,Saudat ta ƙara maida hankalinta kanshi "Nidai ka akiyeni anan,bazanje gidan kaba"


Speed ɗin gudun ya rage ya ɗan karkato yana kallonta"dama kinada inda zaki ake korarki kikaƙi tafiya?"


Da sauri Saudat ta kalleshi,batada wata amsa da zata bashi,hakan yasa ya cigaba da tafiyar shi,sun shiga street ɗin gidan Areef yaja ya tsaya.


Fitowa yayi daga mazaunin driver ya dawo baya,kusa da Sultan ya zauna ya kalleta"ya zama  dole kije gidana,saboda bazai yiwu kije wani wajeba,sai dai abinda zan gaya maki shine,kinsan inada Mata ina mugun santa,then banason Abinda zai ɓata mata rai,to yazama dole ki kiyayi wanan,saboda itama matsayin Yayarki take"yana gama maganai ya juya zai fita,Saudat tace"Ya Areef shiyasa nace bazanje gidanka ba,banaso na ɓatawa matarka"


Areef ya koma yana kallonta,jin batayi magana ba yace"duk wanann damuwar inaso ki cireta before entering the  house"yana Kaiwa nan ya buɗe ya koma mazaunin driver tafiya kaɗan suka isa gate ɗin gidan.


Saudat kam yanzu batada wani zaɓi tasan tariga ta shigo,saidai tana tunanin ƙalubalan da zata fuskanta.


Areef ya fito ya buɗe mata,ya gewaya inda Sultan yake,ɗauko shi yayi,ya saɓa a kafaɗa,yazo ya kalleta,baiyi magana ba tagane abinda yake nufi,bata tsayaba ta miƙe ta rufe mota suka shiga babban falon gidan.


Ni'ima tana zaune tana kallo Areef yafara shiga,ta kalleshi"a'a daga ina,naganka da yaro?"


Bai tsaya bata amsa ba,saiga Saudat tashigo,Ni'ima basaita tambayaba koda ganinta ɗaya da Saudat,to kuwa ai akwai pics ɗinsu itada Areef a gidan,Ni'ima ta kalleta cikin faɗuwar gaba tana amsa mata Sallama.


Areef ya aje Sultan kan kujera,ya koma kusa da Ni'ima ya zauna,Ni'ima ta daure ta kalli Saudat tace"ki zauna mana sister"

Saudat jiki ba kwari ta zauna kujerar da ke kusa da ita,tace"ina wuni"


"lafiya lau ta amsa"


Areef bai kalleta ba,ya juya yana ƙarewa falonkallo,sai dai idonshi kan pics ɗinsu dake tsakiyar falon shida Saudat,sai nasu da Ni'ima a Sauran bangayen ɗakin,sai pics ɗaya na family ɗinshine hada Mami da Pappa.


Areef  ya maido hankalinshi yana kallon Ni'ima,ya ɗan riƙo hannunta"ya gidan?"


Ɗan langwaɓe kai tayi,tace"lafiya ƙlau"ta janye hannunta ta miƙe ta kawo mashi ruwa,ta ɗauko lemo da ruwa ta ajiyewa Saudat.


Har zata wuce Areef ya riƙe hannunta"zo rakata ɗakin can takai Sultan dake bacci"


Gaban Ni'ima ya faɗi,ta kalli Saudat saidai batada abinda zatace dan tasan Halin Areef bayasan raini.


STORY CONTINUES BELOW

Ta kalli Saudat "taso muje"Saudat ta ɗauki Sultan suka shiga corridor,Ni'ima ta tura ɗakin ta shiga Saudat ta bita,ta ajiye yaron Ni'ima tace"zo muje idan kin ajiyeshi"


Saudat ta bita ba musu,koda suka dawo Areef baya falon,zama sukayi,saidai ba wanda yayi magana,sai Ni'ima data kasa haƙuri tace"sister daga ina kuke"


Gaban Saudat ya faɗi,dakyal ta iya cewa "gidan Dady". Ni'ima ta kaɗa kai,ta miƙe ta bi wata hanya,wadda dagani ita zata kaika ɓangaran maigidan.


Wasu hawaye suka gangarowa Saudat,tayi saurin gogewa,tana tunanin yadda wannan zaman zaiyi itada Ni'ima,haka tayita zama tana ƙarewa falon kallo,gabanta yafaɗi lokacin da idonta yakai kan pic ɗinsu,Saudat ta zaro ido tana Mamaki, pic ɗinta itada Areef a falon,kasa ɗauke idonta tayi tana tunanin yadda akayi Ni'ima tabar pic ɗin  bayan taji su Ilham suna faɗin Ni'ima kishinsu take.

Kwance yake gefen gadon idonshi arufe kamar mai bacci,Ni'ima tasan bai isayin bacci ba,ta zauna bakin gadon"in kawo maka Abinci ananne"


Ido ya buɗe yakalleta,yace"kin ba baƙuwarki abincin ne?"


Ni'ima ta ɗaure fuska ta harareshi,Areef ya tashi zaune,yana kallonta,yaɗan ɗaure fuska,yace"Ni'ima"


Cikin Sauri ta kalleshi,tana mamakin kiran,yagane hakan ya ƙara maida hankalinshi kanta"sarai nasan halinki akan yadda kikewa ƴan uwana,ba tun yauba nagaya maki yadda nakeji da ƙannena,duk Family ɗinmu nine babba,sannan kuma inada halin riƙe duka ƴan uwana,abinda nakeso dake shine kiji-ki ƙiji,ki gani kiƙi gani,kema dole girma yakamaki,Saudat sun rabu da mijinta,and anan zata zauna"


Tunda Areef yafara magana Ni'ima take sauraranshi,sai dayayi wanann maganai ta ida kaɗuwa,tana kallonshi,shikam Areef seriously yake magana,Ni'ima ta kalleshi"wane irin anan zata zauna,haba Areef mi kake nufi anan?"


Areef ya kalleta"ina nufin tadawo nan gidan da zama"


Ni'ima tace"haba dai ai abinda bazai yiwu bane,duk gidanjan da ke akwai sai nan zata zauna,taje gidan Pappa mana,ko gidan Dady,amma sai nan"


Areef ya kara kallonta,dama yasan zasuyi haka"anan dai zata zauna"yace dan yasan idan yayi mata sanya zata kawo mashi matsalane.


Ni'ima ta miƙe"to gaskiya bazai yiyuba,ina zamana wata tazo man gida,dan sun rabu da mijin ba inda zata zaunane,akwai dai yadda akai"


Aref yace"kamar mi kenan?"

"kamar ƴadda nace"


Areef yaji zafin maganai,saidai kuma yasan duk macan da akaiwa haka dole ranta ya ɓaci hakan yasa yafara rarrashinta.


Ganin yana rarrashinta,sai ta ƙara narkewa tana matsifa yayi-yayi ta haƙura amma taki,hakan ya ɓata ran Areef yace"to nan dai gida nane ni nakeda ikon yin abinda naga dama,anan zata zauna,haka nikeso"


Yana maganai yana shirin ficewa,Na'ima ta biyoshi tana kuka"Allah baka isaba,dama ka kawotane dan kaciman mutunci,inba hakaba,nizaka cewa haka,amma dai kasan innan gidanka ne nima inada ikon cewa bazan zauna da itaba."tana magane tana biyoshi.


Areef kam gani yayi kamar bai mata Adalciba,take ya juya yakama hannunta suka koma ɗakin,kan gado ya zaunar da ita"calm down dear,duk ke kika ja,amma ai kinsan Saudat kanwa tace,mizaisa ki damu"


kaɗa kai tayi,ta juya Areef ya jawota jikinshi"Nasan nan gidan kine,amma kibar kanwata ta zauna,kema ta zama ƙanwar"


Ni'ima tasan halin Areef baiso yana rarashinta, tayi kamar yana zugata"to shikenan na yarda"


Areef ya miƙe"bari in fita cikin gari,mi kikeso inkawo maki?"


"bakomi"

"fushi kike kenan"


Ɗan sakin fuska tayi,ta ce"a'a"tana maganai ya miƙe,koda ya fito Saudat bata falon,ta shiga ɗaki Sultan yatashi daga baccin.


Stool ya ɗauka,pics ɗinshi da ita ya ciro daga bangon,yana saukowa kan stool ɗin Ni'ima tace"ya kacire?"

"ai dama nace maki dakaina zan cire ko?"yana maganai yana jan hancinta.


Ni'ima taji haushi sosai,ta juya ta shige ɗaki,Areef kuma ya fita,zama tayi tana tunani miye dalilinshi na fidda pic ɗin bayan har faɗa sukayi akan pic ɗin yace bazai fidda ba,wannan dalilin yasa Ni'ima zafin zuciya dakuma ƙarin jin haushi.


Saudat tana zaune ɗakin itada Sultan,ɗakine mai ɗauke da family bed sai resting chair dake gefe,cutains ɗin ɗakin kansu abin kallo ne,sai wadrop ɗin bango da ƙofar shiga  toilet,ɗakin ba wani kwalliya gareshu ba Amma yayi kyau sosai,sanyi A.c ke ratsata,tana zaune gefe tana tunani,tafi awa ukku a haka.


Ni'ima ta kwankwasa ɗakin ta shigo,Saudat tace"Sannu Aunty"Saudat tana ce mata Aunty ne saboda darajar yayanta,dan ko bata girmi Ni'ima ba to zasuzo sa'anni dan itama tayi digree ɗinta.


Ni'ima ta zauna gefenta ba yabo ba fallasa tace"ku taso muje kuci abinci mana,kun zauna ɗaki dagake sai yaro"


Saudat ta ɗan saki fuska,tace"to"ta kama hannun Sultan.


Falo sukazo suka zauna,Ni'ima ta fara kawo masu abincin,Saudat tace"bari in tayaki ɗaukowa"


Saida suka kawo Abincin suka fara ci,Sultan daban suka zuba mashi,sun ci abincin,amma Saudat ba sosai taciba saboda rashin sabo.


Sun gamaci sun kwashe kayan Areef ya shigo,hannunshi riƙe da ledoji,Ni'ima tayi mashi Sannu ya zauna,Saudat ta gaidashi,tana miƙewa,Areef ya kira sunanta yace"zauna ina zaki"


Saudat batayi musuba tadawo ta zauna Areef ya kalli Ni'ima,ya maida hankalinshi kan Saudat,su duka ya kira sunansu,anan fa ya kamayi masu nasiha akan su zauna lafiya,yace Ni'ima ta riƙe girmanta Saudat Kuwa ta rinƙa girmama Ni'ima sbd matar yayantace.


Saudat bataji komiba,dan tana ganin zama da Ni'ima bazai mata wahala ba tunda har ta zauna da su Mama.


Areef ya miƙe ya kama hannun Sultan,kan dinning suka zauna,Areef ya kalli yaron"zakaci abinci?"


Sultan cikin kwarancin shi yace"kwaci abirci"yana nufin naci abinci,Areef yayi dariya yace"eh ye yaron Baba ashe ka iya magana"


Ni'ima ta tashi ta kai mashi ruwa Saudat ta miƙe ta cige ɗakin da tasan shine aka basu.


Areef ya kalli Ni'ima ga tsarabar ki can,ɗayar ledar kayan Sultan ne,Ni'ima tace to,ta ɗauka take takai ma Saudat ta dawo.


              ******

Haka akayi har sati kowa yana ɗakii,duk basuda sakewa Saudat batasan fitowa,sabda Areef dan bataso Matarshi ta zargi wani abu,da safe Saudat tana fita ta tayata aiki,sukan ɗan yi fira,kadan jefi-jefi.


Areef kuwa idan ya shigo gidan baya jimawa a falon zai wuce ɗakinshi,iyaka Saudat ta gaidashi,Sultan kuwa harya saba da Areef sosai,daya shigo zai fara murna oyoyo Uncle,itakam Saudat yaron tausayi yake bata,dan tasan inda babbane kwana biyu bai isa ya manta da Baban shiba.


Areef kam duk cikin kwanakin saidai kajishi da Sultan suna labarinsu,sosai yake kula yaron.


Areef da Ni'ima suka fito zasuje Unguwa,Ni'ima ta leƙa ɗakin Saudat,ta dameta kwance"badai bacci zakiyi ba?"


"a'a kwance kawai nike"


Ni'ima tace"zamuje shopping sai zuwa dare zan dawo"


Saudat tace"to Aunty adawo lafiya,ina Sultan ɗin kada abarshi falo yayi ɓanna muje in taho dashi"


Tare suka shigo falon da Ni'ima shima lokacin yafoto,yadine jikinshi sky blue hular kanshi dark blue haka takalmin shi,Sultan a hannunshi,Saudat tace"to taho"


Sultan ya maƙe hannu bayason suwa wajanta,Areef bai saki hannunshiba suka ci gaba da tafi,har sukakai ƙofa"wai baka tahowa,Yaya kawo shi"


Sultan yace"ban zuwa" Areef baiyi magana ba,dan ba saka baki a magana yake mataba,idan tana ma Sultan,duk da yaron yabashi dariya.


Duƙawa Areef yayi ya ɗauke yaron ya saɓa a kafaɗa,suka fice,hakan yabata Amsar tare zasuje.


Ni'ima wani baƙin ciki yakamata,take tacanxa,dan batayi tunanin tare da yaron zasuba,dan dama kwana biyu Areef hankalinshi duk ya karkata kan yaron.1

*Just manage till tomorrow*


*AUNTƳ HALILOSS✍🏽*WA NAKE AURE?

*Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


24


Jiki ba kwari Saudat ta koma cikin gida,sukam mota suka shige suka bar gidan.+


Wani ƙaton Mall sukaje,kaya sosai Ni'ima ta kwaso,Areef ya kama ɗaukarwa Sultan kaya masu kyau da kuma tsada,takalmomi ba'a magana,kayan wasa masu yawa.


Ni'ima ta kwashi kayan ta,Sai ana sallar magrib suka dawo gidan,Areef ya kwashi kayan Sultan,Ni'ima ta ɗauko nata suka taho,Afalo suka aje,Areef yace"ki kai mata kayan Sultan ɗin,ni zan wuce massallaci"


"to "Ni'ma ta amsa,ta ɗauka ta shiga ɗakin,dai-dai lokacin ta zauna,Saudat tace"sannu da dawowa Aunty"


"yauwa ga kayan Sultan nan"tana maganai tana barin ɗakin,Saudat ta matsa ta buɗe kayan,ita kanta tasan yaron yazama ɗan gata,irin kayan da Areef yasawo zakace shine ya haifi yaron dakanshi.


Saudat ta kauda kayan ta fito falo, ta tadda Ni'ima,itama ta zauna"Aunty na dafa Abinci idan zakici"


"sanwa kikayi kenan,dama na fara tunanin girkin,dan duk nagaji,ga cikina yana man ciwo"


"Ayya Allah yasawake,bari in zubo maki to"


"a'a yi zamanki bazan iya ciba,sai naɗan huta"wani lokaci Ni'ima tana sakin fuskarta,dan tasan babu yadda zatayi da saudat.


Zaune suke falon,saiga Areef ya shigo,yana gyara hannun rigarshi,kan kujera ya zauna,ko inda Saudat take bai kallaba,ganin Ni'ima tana ɗan yamutsa fuska,ƴace"yadai?"


Ɗan ƙara yamutsa fuska tayi,ya miƙe yadawo kusa da ita"Baki da lafiƴa ko?have you take your drugs?"


Girgiza tayi,Areef ya miƙe yana ɗan faɗa"kin dawo kinajin baki lafiya and you have medicine bazaki ɗauko kisha ba"hanyar ɗakinta yayi ba jimawa ya dawo hannunshi da magunguna yana ɓallewa daga jiki.


Saudat tayi saurin miƙewa,ta ɗauko ruwa da cup ta miƙa mata,tanayi mata sannu,Areef ya Anshi cup ɗin,abaki ya bata.


Yakoma ya zauna,Ni'ima ta jingina da jikin kujera,Saudat tace"Aunty ko in haɗa maki tea"


Ta girkiza kai"a'a banason cin komi,saidai zuwa anjima"


Saudat tace"Allah yasawake"zaman yaɗan yi mata wani kala,ta miƙe,tana faɗin"bari inyi salla"


Ta shiga ɗakinta,Areef kam nan yayi zamanshi wajan matarshi,bacci yaɗan ɗauketa,Saudat saida tayi kusan 1hr ta fito,lokacin Ni'ima ta tashi.


Saudat ta zauna tace"ya jikin?"


"Naji Sauƙi,dayake bacci na ɗanyi,nasamu relief"


Saudat ta shiga kitchen ta ɗauko kayan Abincin ta aje tsakiyar falon,ta sami plate da spoon ta zuba ma Ni'ima ta miƙa mata"kici Abincin mana"


Zatayi magana Areef ya Anshi Abincin,ya aje wayarshi da yake dannawa ya koma kujerar da Ni'ima take.


Saudat kam tanason tambayarshi zuwa gidan Ammi,saidai taga Ni'ima ba lafiya Sultan ta ɗauka dake bacci takaishi ɗaki,ta jima kafin ta fito,ta tadda Areef bayanan,Ni'ima tana wajan t.v tana haɗawa.


Saudat ta ce"Aunty kinji sauƙi ko"


"eh ya lafa man,haka yake man walahi,inashan wahala sosai"


"Allah yasawake,kin gama da abincin in kwashe kayan"


"A'a Uncle bai ciba" sunan da suke ce mashi kenan agidan sboda Sultan.


Saudat ta zauna bajimawa sai gashi yadawo,da leda hannunshi,ya xauna,ya ba Ni'ima,robobin ice cream ne a ciki.


STORY CONTINUES BELOW

Ni'ima ta buɗe ta ɗauko wani,Areef ya kalleta"bakiga akwai free sugar acikiba,kinson shan zaƙi bayan kinsan baki lafiya"


Ni'ima ta canza ta miƙawa Saudat Sauran ledar Saudat taje ta buɗe frij ta ajiye.


Areef ya kalleta ba wani sakin fuska"ki tada Father yasha,baici komi ba kika barshi yayi bacci"


"kona tadashi bazai shaba"Areef bai ƙara magana ba,Saudat tayi ƙoƙari tace"Ya zanje gidan Ammi gobe"


Spoon ɗin Abinci yakai baki,bai kalleta ba yace"Allah yakaimu"


Yana cewa haka,Saudat ta miƙe tace"Aunty Saida safe Allah yasawake"


"Amin bazakiyi firaba"


"a'a bacci nikeji" Saudat ta shige ɗaki,Areef kam idonshi kan t.v yana kallo,Saudat koda ta koma ɗakin ba wani bacci tayi ba,sai tunanin yadda Yayanta baya sake mata fuska take,bayan da ba haka yake mata ba.


******

Saudat tana yin Sallar Asuba,ta ɗan koma bacci,batajima ba Sultan ya tadata,wanka tayi mashi tayi mashi brush,ta shirya shi,doguwar Abayar jikinta,ta fito falon,kitchen ta shiga don ɗaura masu break fast,cikin 1hr ta gama haɗa kalacin ta saka a wormers takai kan dinning lokacin har 8 tawuce.


Sultan ya kama kuka dole saita zuba mashi,Saudat tace"kabari sai anjima mana"


Ihu ya saka mata,takama rarrashin shi,amma yaƙiyin shiru,ta jawo hannunshi ta zaunar dashi kan kujera"zauna nan in ƙarajin bakinka kaman kuka,Allah saina sa maka bulala".


Ni'ima tafito tasa wata doguwar riga,ta material,tace"wai kuntashi kenan?"


Saudat tace"eh ina kwana,ya jikin"


"ina jin har yanzu,Amma yanzu Uncle zai fita ya samoman wani magani"


"Allah yasawke"

Areef ne yayi saurin fitowa daga ɗakin Ni'ima,saboda tun yana shiri yake jiyo kukan yaron,lens ɗin hannun riga yake sakawa,Camtan ne jikinshi maroon colour ɗinkin yayi mashi kyau.


Saudat batasan yazoba har yagama saka lens ɗin a hannun riga Saudat tana duƙe kan Sultan"kajini da yaro,shine zaka kaman man kuka,to wallahi zaneka zanyi"


Areef yace"ke wani ya zaneki ne,zaki saka yaro gaba kina mashi faɗa"


Saudat batada abin cewa ta tashi tsaye tace"ina kwana"


Hannu ya miƙa ma Sultan,yaron ya tafi wurinshi,tare suka fice yana kuka,Saudat tace"Aunty ga break fast nan bari inyi wanka in shirya.


"to"Ni'ima tace,Saudat ta shihe ɗakin tayi wanka ta shirya cikin jar Atamfa,riga da skert,batayi kwalliya ba,sai turare kawai datasa,amma duk da haka tayi kyau saboda jikinta yafara canzawa,daga wahala dan cikin kwanakin har haskenta ya dawo saboda fresh soap da take amfani dasu.


Saida ta shirya ɗakin ta gyara,itace bata fitoba sai ƙarfe goma.


A kan dinning ta tadda Areef shida Ni'ima,Sultan ya nufota yana bata sweets da chocolates ɗin da Areef ya sawo mashi,Saudat ta Amsa,"iya bari insha"


Ni'ima tace"kizo kiyi break mana"


Saudat batason zama tare dasu,ta kalleta tace"ina bazanci ba"tana maganai tana ɗan sakin fara'a hakn ya fiddo da dimple din fuskarta.


Dai-dai lokacin Areef ya kalleta,da Sauri ya ɗan kauda kai,saboda ya daɗe baiga fara'arta irin haka ba,take yafara tuno rayuwarsu ta baya,dan indai yana gida to ko yaushe v

Cikin fara'a suke,ganin zai shiga wani tunanin yayi saurin kaudawa,ya ci gaba da cin fried Potatoes ɗin da yakeci.


Ni'ima tace"saboda mi"


Saudat ta zauna kan kujera tace"yau kalacin Ammi zanci"


"da wuri zaki kenan"

"eh harma na shirya"


Areef ya aje spoon ɗin hannunshi yace"are you still using your old bank Accnt,daga can kiyo shpping"


Yi tayi kamar bata jiba,Saida Ni'ima tace dake yake,Saudat kam tunaninta tamanta rabanda ta saka kuɗi ko tafidda ta Accnt ɗin,saidai tasan Accnt ɗin yana nan sbd suna ɗan yi mata remainder lokaci zuwa lokaci,tace"a a eh dashi nake Amfani"tana maganai tana inda inda.


Tun nan take,Areef ya fiddo wayarshi,ko 5mint ba'ayi ba akayi mata Alert 150k a Accnt ɗin,ya tura mata,ta miƙe tace"nagode"tana maganai ta miƙe tana shiga ɗakin.


Tayi mamakin ganin Areef har yanzu bai manta Acvnt details ɗinta ba.


Tajima sannan tafito,ta saka mayafi fari, saidai Areef bayanan harya fice,Saudat tace"Aunty natafi saina dawo"


Ni'ima tace"ga key can ya aje maki,motar tana rufe da red cloth"


Saudat ta ɗauka,ta fice,Sultan ta aje ɗayan site ita kuma ta zauna, mazaunnin driver.

****

"Ammi Ammi" tun kafin ta shiga take kwala kira,Ammi tayi saurin fitowa"lafiya"Saudat tayi dariya"Haba Ammi na ƙagara in ganki"


Ammi tayidariya,tace"ina Sultan fin waya kawoku"


Saudat tayidariya Ammi "zauna ma,inbaki labari,nayi ƙoƙari,shekara kusan 4 banyi driving ba"


Ammi ta zaro ido"kai Allah yasawke shi saiya baki turi Allah dai yakawo ku lafiya"


Saudat tayi dariya"Amma lafiya lau nazo"


Ammi ta zauna,Saudat ta wuce kan dinning"Ammi mi kakayi mana?"


"duba kigani


Saudat taje tayi break ɗin saiga Sultan ya shigo,Saudat tace"kai duk wanda kagani saika liƙe mashi"


Haka Saudat ta daɗe,sunata fira da Ammi,Saudat tace"Ammi yaushe zanje in kwaso kayana"


"eh dama gobe nike shirin cewa aje a kwaso wanda kikeso,kamar nasawa Sauran kuma Abar mashi ya ringa kwana"


Saudat tace"ai wallhi ban bar mashi,ai da in bar kayana wannan gidan ƙara inba Maman Khalifa,dan bazan manta halarcin datayi manba"


Mama tace"gskiya yarinyar tanada kirki"


"kuma tsakani ga Allah take zaune dani"


Ammi tace"ai samun maƙota na gari babbar rahma ce"


Saudat tace"kujerun suna gidansu Fatima,sunkai shekara 3"


Ammi tace sai a ɗauko a haɗa mata,Saudat tace"yaiwa nagde Ammi"


Haka sukaita fira,har suka gaji,Saudat tace"barima inje gidansu Fatima dan batasan mafa na dawo gida ba"


Ammi tace"to shikenan"

Saudat ta ɗau mayafinta"daga can zanje shopping,Yaya yabani kuɗi"


"to kada ki daɗe dai"


Saudat ta tafi,anan tabar sultan,gidansu Fatima kuwa Fatima tasha mamakin ganin Saudat,Nan Saudat ta ba Fatima labari A-z.


Fatima tace"kai wanann ƙaddara"


"keni wallahi banji komiba,asalima ko tina tsinannu banyi"


Fatima tayi dariya"wallahi in naji sakin Aure hankalina tashu yake Amma wanan banji kimi ba"


Saudat dariya tayi tace"kedai Allah yasawake"


Sunjima suna fira suka tashi sukaje gdan wasu frnd ɗinsu,itace bata tuna dawowa ba sai wajan magrib,Suna mota da Saudat ta zaro ido namanta banyi shoping ɗinba.


Take suka nufi hanyar *LEMARH--COLLECTION CENTRE* suka shiga,sun daɗe suna Sayayya kayan sawa ta kwasa sosai da dogayan riguna,takalma,jikkuna masu kyau,nikaina kayan sun gurgeni.


Sai goma saura sukafito,Saudat tace"nashiga tara,wai haka dare yayi"


Fatima tace"ki fara ajeni saiki wuce,saboda kaya dake mota"


"a'a ki ajeni saiki wuce gobe kin kawo motai"


Fatima tace"a'a ki dai akeni,saiki wuce"


Dole saudat ta haƙura,ta ake Fatima,sanann ta wuce gidan,da speed sosai ta isa gidan Ammi.


Tana shiga tayi parking tafito ta shiga,Areef ne tsaƴe bakin ƙofa ya juya baya yana kallon cikin falon,yana duba agogon hannunshi,ƙananun kayane jikinshi,yana ɗauke da Sultan a kafaɗa,sbd kukan da yaron yasha.


Ammi tana Zaune gefe, jin shigowarta,Ammi tace"sannu da zuwa kinyi dai-dai"


Areef ya juyo da sauri yana kallonta.........

*AUNTY HALILOSS CE✍🏽*

WA NAKE AURE?
*Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*

*ALHAMDULILLAH KO YANZU NASAN SAƘONA YANA KARƁUWA,KUMA YANA ISA GA MUTANE,GANIN YADDA AKE COMMENT NA FAHIMTA AKAN NOVEL ƊIN _WA NAKE AURE?_*.

*DEDICATED TO MY WATTPAD FANS,KU MA INA TARE DAKU,KUMA INA GANIN SHARHINKU,NAGD ILYSM*

25

Saudat ta kalli Ammi tace"Dan Allah Ammi kiyi haƙuri nasan nayi laifi,wllh gdan ƙawayenmu mukaje can muka cinye lokaci"+

Areef ya kauda kanshi daga kallonta,ya juya yana fafin "ina takalmin shi?"
Ammi tace"gayacan wajan kujera"Areef ya matsa ya ɗauko takalman,yace"Ammi saida safe"

Areef ya juya yafice,baima jira cewar Ammi ba,Ammi tace"to kuje saida safen goben sai ki shiryoda wuri dan aje can ɗin"

Saudat ta fito lokacin Areef yasaka Sultan abayan mota,Saudat tayi sauri ta shiga ganin shima Saurin yakeyi,ta buɗe gidan gaba ta zauna,Areef yaja mota.

Suna isa gida basu tadda kowaba a Falon,Ni'ima ta tana ɗakinta,Saudat dama tunda tazo bata taɓa shiga ɗakin Ni'ima ba,hakan yasa itama ta shige nata ɗakin ita da yaronta,sukayi shirin baccinsu.

******
Ni'ima ce da Saudat a kitchen suna break fast,Ni'ima yanzu tasake ma Saudat sosai suke fira,ganin Areef baya kulata.

Saudat doguwar rigace jikinta,ta yafa mayafi babba,sbd rigar batada nauyi,"na jima ina jiran kidawo jiya,harna gaji na shige ɗaki"

Saudat tace"ai jiya yawo mukasha"

"ai Ammi tayo ma,Uncle waya,yazo Sultan na kuka sabda ya daɗe bai ganki ba"

Saudat tace"ai yauma zanje,saboda zamuje kwashe kaya,amma ina tsoron tambayarshi"

Ni'ima tace"tab ai shifa haka yake,akwai ......"

Ji taƴi ankamo kunnanta an murɗe ta baya,Areef yace"gulmata kike ko"saidai yana magani ba dariya tare dashi.

Gaba ɗaya basusan da zuwan shiba,Ni'ima tariƙe hannunshi,tana dariya,janta kawai yayi suka fito falo suka zauna,Saudat tacigaba da aikin,ba'a daɗeba tafara jiyo dariyarshi da Ni'imah

Ta daɗe tana haɗa kalacin,ta fito ta ɗora kan dinng table ɗin,Areef yana gefen matarshi,Saudat ta gama ta shige ɗakinta donyin wanka.

Suna break fast,kasan cewar weekend ne,Areef baya zuwa aiki,yadawo ya zauna falo,shida Sultan suna game,da wani chocolate suna sha,Saudat ta fito da wata doguwar rigar lace,saman yayi shape ɗinta,sai buɗewa datayi sosai,lace ɗin yana da ratsin lemon green hakan yasa mayafin data saka lemon green ne.

Tazo falon ta ɗan tsaya,Areef kallo ɗaya yayi mata ya kauda kai,itakam Saudat hakan yana bata haushi,ta yadda yanzu baya sakar bata fuska,tsayawa tayi tace"Yaya zanje gidan Ammi"

"mizakiyo"

"unguwa zamuje da ita"

Areef Ammi tagaya mashi cewar zasuje kwashe kayan Saudat,amma yayi kamar baisani ba.

Ɗagowa yayi"ai kinje jiya,babu inda zaki yau"yana maganai ya ɗauke Sultan suna shirin shigewa part ɗinshi.

Saudat ta kalli Ni'ima,Ni'ima tayi mata dariya,Saudat ta ɗaure fuska,Ni'ima tace"ai wallahi dama nasan bazai barki ba"

Dariya Saudat tayi tace"wallhi dama bansawa raina ba,sa'a ce nike nema"su duka sukayi dariya,Saudat takira Ammi ta gaya mata,Ammi tace bakomi zasuje suyi komi.

*****
Haka lokaci yake tafiya,ranaku suna wucewa,tsawan watan Saudat biyu a gidan,Ni'ima yanzu gaba ɗaya yanzu ta sauko akan Saudat,sosai suke fira,har yawo suke ɗan fita tare,Saudat batada wata matsala,hankalinta kwance,Areef kam sabonda sukayi da Saudat farko yanajin babu daɗi akan horon da yake mata,amma yanzu har ya saba,itama Saudat tuntana damuwa harta bari,duk abinda take buƙata saita tambayeshi,baya hanata,wani lokaci ma Ni'ima yake ba ta bata.

STORY CONTINUES BELOW

Zaune suke kan kujera,suna ɗan fira da Ni'ima,Ni'ima tace"Idan kika fara aiki zan yu kewa"

Saudat tace"ai Ammi tace in bari sai na ida Idda,Amma wallhi da yanzu na fara zuwa kinga ko jiya saida suka nemeni,nace subari nanda 1month"

Sultan ne ya fara shigowa,da Uniform,sai lunch box a hannunshi,yana hayaniya yadawo gida,Saudat tace"to manya sun dawo yanzu zasu damemu"

Areef ya shigo da bottle ɗinruwan Sultan daya bari a mota,Ni'ima tayi mashi Sannu,Saudat ma haka,bai amsaba ya shige part ɗinshi Ni'ima ta bishi,Saudat taja Hannun Sultan suka shige ɗakin ta cire mashi Uniform.

Saudat tana kitchen Areef ya shigo gidan yana kwalawa Sultan kira,Ni'ima tana zaune Falo,ta kalleshi"Sultan fa yana gidan Pappa"

Zama yayi ya kalleta,yace"yau da sauƙin ciwan ko?

"eh naji sauki"

Saudat ta fito da tea a hannunta,cup biyu ta miƙawa Ni'ima huda,ta koma kan dinning,ta zauna ta jawo bread ta haɗa,Ni'ima tace"kai hada bread da rana tsaka"tana maganai tana ɗan dariƴa.

Saudat tace"Aunty jinayii nason haɗawa ne shiyasa"

Areef sai lokacin ya kalleta,take ya tuno lokacin da suke haka a gida,wani lokaci idan bread yakusa ƙarewa sai Mami ta rabasu,dan kowa zaice saiya ɗiba,wani lokaci ya kwashe ko ita ta kwashe.

Nan yaji yason shan tea ɗin,miƙewa yayi yayi hanyar cikin ɗin Ni'ima tace"mika keso?"

"zan haɗa tea ne"
"to ka ɗauka wanann mana"
"a'a keda bakida lafiya kisha bari inhaɗa"

"bama zan iya shanye shiba,kasha"

Areef yadawo yazauna ya ɗauki tea ɗin yana sha a hankankali-ahankali pink lip ɗinshi suna juyawa.

Saudat ta gangaro daga steps ɗin dinning ɗin,ta shiga kitchen ɗin,bata jimaba ta dawo hannunta ɗauke da wani cup ɗin ta miƙawa Ni'ima,harga Allah Saudat tana burge Ni'ima saboda yadda take kyautatta mata,badai kamar idan ciwan cikin nan nata ya taso,don duk idan zatayi period haka take fama,tun kafin tayi Aure,Ni'ima tace"Nagode"

Areef ya Sauke cup ɗin dake bakinshi,ya murja lip ɗinshi,ya kalleta ya kauda kai,ya miƙe"bari inje in ɗauko Sultan ɗin"

Ni'ima tace"muje tare,sis taso muje"

Areef baiyiwa Ni'ima gardamaba,sai ya juyoyayi murmushi"kin warke shiyasa kike neman yawo"

Haka suka fito suka nufi gidan Mami,Saudat dama tanason zuwa dan tunda ta dawo so ɗaya taje gidan shima bata jimaba,dan tana gudun kada Pappa ya taddata,ita kam Mami dama tsakanin Uwa da ɗiya sai Allah tuni ta sauko.

Tun a parking space taga motar Pappa,gabanta sai faɗuwa yake,tare Ni'ima ta fito da Areef,Saudat kam kasa fitowa tayi.

Saida sukayi nisa Areef ya juyo,yaga bata fitoba,dawowa yayi ya buɗe motar,Areef yakalleta,Saudat idonta sun kawo hawaye"Pappa na nan"

Ganin hawayenta,yaji babu daɗi har a zuciyarshi baiji daɗiba,ya ɗan ƙara kallonta,"oya lets go,bazaice komi ba"

Saudat ta fito jiki ba kwari ta bisu,suka shiga,aikam Pappa yana cikin falon zaune,gidan shiru babu kowa dayake su Ilham suna Katsina,acan aka nema masu Admtion.

Shiga sukayi lokacin Ni'ima tagama gaida su ta zauna,Saudat cikin sanyin jiki ta gaida Pappa,ganin Ni'ima Pappa ya amsa.

Ya maida hankalinshi kan Areef,Saudat koba komi yau taji daɗi Papa ya amsa gaisuwarta,ta koma wajan Mami suka cigaba da fira su ukku.

Areef sun daɗe suna magana da Pappa,Pappa ya miƙe yace"Ni'ima in xaku tafi kiman bankwana"kullun haka Pappa yake ba ranar da zasuzo baiyi mata kyautar kuɗiba.

STORY CONTINUES BELOW

Yana tafiya tace" Pappa nasan bankwanai ai,shikenan ni bangajiya da amsar kuɗi"

Mami tayi dariya,Areef yace"Mami gida shiru ke ɗaya yanzu"

"wallahi Son yanzu sai in wuni banyi doguwar magana ba"

Yayi dariya yace"kai ai Ilham hukumace ana candai ansamu new frnds"

Mami tayi dariya,yace"ina Sultan ɗin"

"Ai dama tunda naganka,nasan shi kazo ɗauka,wajan Azahar Ammi tazo suka tafi"

Areef kam yasaba da yaron,bayason yayi mashi nisa,"kai Mami"yana magana kamar zaiyi shagwaɓa,Mami tace"to yi aiga Ni'ima nan tana kallonka"

Su duka sukayi dariya banda Saudat dake chart ɗinta,duk da tanajinsu,Areef yace"ai ita daɗi taji dan tasan wani yawon za'a wuce,to ba inda zamu,gida zamu koma Ammi taje ta kaishi"

Ni'ima tace "kaidai akeji baniba"

Basu ƙara jimawa ba suka miƙe,Mami tace"Kije kiyowa Pappa bankwana"

"a'a Mami wallahi danaje kuɗi yake bani,mutafi kawai muyi kamar mantawa mukayi"

Suka fice,suna fita,Pappa ya fito ta harabar gidan,ya kallesu"wucewa zakuyiba bankwana ko?"

Pappa ya sa hannu Aljihu,ya fiddo kuɗi yaba Ni'ima,ta amsa dan tasan faɗa yake idan tace bata ansa.

Ya maida hannu Aljihu ya fiddo yaba Saudat,Saudt har sauri take ta anshi kyauta da Pappa,don tun kafin Auranta raban da yabata,godiya tayi.

Pappa ya kalli Areef yace"to ko hada kai ne?"yana zolayar Areef,sosa ƙeya yayi,yana dariya ya shiga mota suka bar gidan.

*****
Yanzu ba Masu karatu idan kukaga Saudat,zakuyi mamakin ganin soft and smothy skin ɗinta,with a Natural beauty and look,asalin gyanta ya gama dawowa,bata kwalliya sosai,dan gani take tana jawara miye abin kwalliya *nikuma Auntƴ haliloss nace,baki kama da zawarawa* dan sai angaya maku zaku san cewa ta taɓa aure.

Gayu,shafta,da kuma iya dreesing ɗinta yadawo,ga tsaddun kaya da take sawa,wani lokaci idan tana tunani ita kanta sai taga Sultantake tuna tayi Aure,wani lokaci tayi dariya idan ta tuna zaman wahalar datayi,tana ganin rashin hankalinta,sai yanzu ta gane ashe son Yaya Areef ne take,shiyasa tun kafin Auransu bata iya ganinshi da mace tabbas sai tayi mashi masifa,take ta tuno lokacin da Mami ta rabasu faɗa akan yayiwa frnd ɗinshi lift.

Yanzu Saudat abinda Areef yake mata nashan ƙamshi,burgeta ma yakeyi,dan idan ta shiga ɗaki har kallon madubi take tana kwaikwayonshi.

Ta fara aiki a wani gidan F.M redio saboda kunsan M.com ta karanta,Saudat tasan aikinta sosai,gaya ta iya jarida,yanzu gidan redion ji suke da ita,sbd duk program ɗin da zasu bata she will make it success.

Farko Areef zuciyar shi kamar ta buga,tunda ta fara aikin,in yana mota tofa gidan redion da take aiki yake kamawa,more expecially idan yasan tana Office.

Areef kam kanshi yana daurewa ne saboda abinda tayi mashi na ƙinshi,amma har a zuciyarshi so ɗayane Saudat yake mawa,saidai ya ɗau alƙawarin ko so zai kasheshi bazai atempting ƙara nemanta ba.

Ni'ima kam yanzu ganin Saudat ta ƙara canzawa,hankalinta yafara tashi,saidai kuma bata gano wani abu awajan mijinta ba game da Saudat shiyasa ta ba zuciyarta ruwan sanyi.

Saudat ta dawo gidan hannunta ɗauke da wasu takardu,saidai ta tadda ƙawar Ni''ima tazo,ta tsaya suka gaisa,taje kan dinning ta ɗauki plate ta saka abinci ta zauna tana ci kaɗan kaɗan.

Areef ya shigo riƙe da wata leda a hannunshi,yayi Sallama,Saudat bata ɗagoba taci gaba da cin abincinta.

Tsayawa yayi ya gaisa da ƙawar Ni'ima ya tambayeta yaushe ta dawo,tace"wllahi shekaran jiya,yace in gidaka kafin mutaho tare"

"Ina amsawa,kuma muzamuzo mu anshi tsarabar India"

Saudat ta ɗan kalleshi,yadda har ya sakewa wata suna magana,tayi saurin kauda kai,Sultan ya dawo daga skul yana shigowa yayi wajanta yana haya niya.

Saudat tace"kai kazo man nan,da Allah kai baka gajiya,waye ace kaje da ball ɗin"

Sultan ya kama kuka"ai bansan ina na aje ba kuma baya cikin jikkata"ya zo yana tuttureta,Hankalin Areef yana kansu,saidai yasan Sultan bai ganshiba da wajanshi zai taho.

Saudat tace"i will slap your face Idan ka ƙara tureni"Sultanbai bariba,yacigaba Saudat ta biyeshi"nace katai kaban waje"tana maganar tana ƙara bugunshi.

Areef yayi Sauri ya tashi yaje wajan yana mata tsawa"miyasa zaki bigeshi,danyazo yagaya maki,har yai abun bugu anan?"

Yaron yakoma wajan Areef ya na kuka"sorry go an remove your uniform,kanason in sawo maka new Ball?"

Ya kama hannunshi suka tafi part ɗinshi.

Saudat ta tashi,ta ɗauke takardunta ta shige ɗakinta.

Ummi ta kalli Ni'ima tace"ke wannan waceve kuma,ko Aure Areef yayi ban sani ba?"

Gaban Ni'ima ya faɗi tace"ke wannan ƙanwar tashice Saudat wadda yake bamu labari kafin Auranmu"

"ohhooo ashema matar Aure ce,ai wallahu nayi tunanin wani abu"

Ni'ima tace"ke ai yanzu sun rabu da mijin kusan 5month kenan"take Ni'ima taba ƙawarta labari yadda akayi,har da dawowar Saudat gidan.

Ummi tace"kai amma ke yanzu nagane bakida hankali,ke baki lura,ashe duk kishin da kike kanshi na banza ne,to wallahi ki tsaya kigani,tundafa yazauna nan hankalin shi yana kanta har yaron nan ya shigo"

Hankalin Ni'ima yaƴi mugun tashi,take ta fara tunanin yadda zasuyi da Saudat dan Ƙawarta ta fahimtar da ita.
*zakuga akwai typing err dayawa,banyi editing ba,nagaji*

1
*ku biyo ni*

*Aunty Haliloss ceWA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*

26


Ni'ima ta daɗe suna fira da Ummi,take tunaninta ya ƙara canzawa,Saudat kam batasan wainar da suke toyawa ba,tana ɗakin tana haɗa wani labari da zata fitar washe gari.


Sultan ya shigo yasameta,buks ɗinshi ya ake mata,har sunyi home work ɗin shida Areef,littafin ta saka cikin jikka,ta tafi dashi toilet wanka tayi mashi ta saka mashi manyan kaya,tare suka fito lokacin Ummi ta miƙe tanayiwa Saudat bankwana.


Saudat tayi mata bankwana ta ɗauki wani biro dake falon takoma ɗaki.


Da daddare Saudat ta zo falon,Ni'ima tana zaune ta ɗaure fuska,Saudat taxo ta zauna"Auntƴ gobe ƙarfe nawa zamu fita bikin,dan ina da program ƙarfe ukku na rana"+


Ni'ima bata kula taba sai ma ƙara ɗauke fuska da tayi"na fasa zuwa ai"


"kai Aunty sabodami?"

"wannan ra'ayi nane ba ruwan wani"


Saudat tayi Saurin kallonta,dan Ni'ima bata taɓayi mata irin hakaba,ko farkonzuwanta gidan bata taɓayi mata magana haka ba,take Saudat tayi tunanin ko wani abu yafaru.


Saudat ta miƙe tabar mata wajan har safe bata ƙara fitowa ba dan dama taci abinci,tana jiyo ɓuruntu kitchen ta miƙe saboda tasaba taya Ni'ima aiki,duk aikin da za'ayi a gidan tare sukeyi.


Abaya ta ɗora kan doguwar rigar baccin ta fito,tsakiyar falon suka haɗu da Areef zaifita,saidai ga alama ba shirin fita yayi ba,"ya ina kwana"


"lafiya"kawai yace ya fice,ita kuma ta shiga kitchen ɗin,"Aunty ina kwana"


Banza tayi da ita,Saudat tace"Aunty idan laifi nayi Allah yabaki hakuri"


Plaintain Ni'ima ta jawo zata yanaka,Saudat ta je zata ansa,Ni'ima ta kauda hannunta"an fera da kaina"


"a'a Aunty kodai laifi nayi maki bansani ba?"


Ni'ima ta juya tace"ba wani laifi haka ra'ayin gidana"


Wannan maganai da Ni'ima tayi Saudat ta fahimceta,hakan yasa ta fita kawai,ta fara gyara falon,tana kan dinning table Ni'ima ta fito da kulolin ta ɗora ta kalli Saudat"bani towel ɗin"


Ba musu Saudat ta miƙa mata,tabar mata wajan,ta koma ɗaki,tana shiga Sultan yatashi tayi mashi wanka,tayi mashi shirin zuwa School


Saudat taje kan dinng ɗin zata zuba ma Sultan abincin Ni'ima tafito"to nan dai abincin miji nane balle ki ɗiba"


Maganar tayi wa Saudat zafi,bata tsayaba ta shigewarta ɗaki dan tasan lallai Ni'ima akwai wani abu,Nan saudat tafara tunanin abinda tayi mata amma tarasa.


Tayi wanka ta shirya,tayi zamanta ɗaki,abinda Ni'ima tayi mata saima taji bata ra'ayin cin abincin,tanajin Areef yadawo daga kai Sultan makaranta,bajimawa kuma ya fita tasan Office ya tafi.


Tashi tayi ta tattara kayan tafiya aiki,ta saka jikka ta saka I.D cart ɗinta,ta ɗauko jikka ta sa mayafi ta fito,bata tadda ta falonba,hakan yasa tayi ficewarta,driving take tama rasa ina zata nufa,dan sai 3 zataje Office,gidansu Fatima ta wuce,a gidan tayi zamanta sai 2 ta fito ta tafi wajan aiki.


            *****

Areef yana zaune Office,redion yake saurare English program ne tana interview da wani ɗan siyasa,sosai ya maida hankalin shi kan program ɗin.


Wani yashigo da Files a hannunshi,ya kalli Areef "kamar kasan shirin da nakeji kenan"


Areef ya kalleshi"ok bani files ɗin mugani"


"Ai Saudat ta iya program,Any time zatayi program sai kaji yayi daɗi"


Areef ya kalli Shi"dan Allah ka daina man surutu"


STORY CONTINUES BELOW

Zaks yace"nasan miyasa"yana maganai yana dariya,Areef yace"matsala ta dakai kenan any time,bakasan lokacin firaba"


"duk abinda zakace dai na riga na ganoka,idan zakaba kai bori yahau to,in kuma sai wani ciwan yakamaka ai kaika sani"


Areef yace"waikai ni na gaya maka?"


"a'a nina gane,tunda ta dawo gida duk ka canza,gama amsa nan,tunda nike dakai ni ban taɓa ganin kana jin F.M ba zai yanzu da kakejin voice ɗinta.


Tabbas abinda Zaks yafaɗi hakane,dan haka bashi da amsar dazai bashi.


Saudat kam tana tashi daga Office taƴohanyar gida,saidai tanakan hanya motarta ta kama jacking tana ciccijewa,da kyal tasamu tayi parkin gefen ti-ti,Atamface jikinta ɗinkin riga da skert bai matsetaba sosai,sai wani mayafi puple da jakka,fitowa tayi,batasan miyasami motarba dan lafiya lau ta taho.


Tsayawa tayi tana tunanin yadda zatayi tasan dai,ba wani mai gyaran mota tasaniba,komawa tayi ta jingina da mota tana neman mafita,Waya ta jawo number Yaya Areef take nema.


Tajima tana ringing kafin ya ɗauka"hello"


"yaya dan Allah motana ta tsaya need help"


Areef ya ɗan tada hankalinshi,dan yasan tsayawar mota ba daɗi balle ita macece,"ba sai ki nemi mai gyara ba?"


Abin ya bata haushi,in tanada wanda zai taimaka mata zata kirashine,wannan wane irin abune Yaya Areef yake mata,sai kace baisan darajarta ba,jitayi wasu hawayen haushi sun zubo mata,ta latse wayar ta riƙe.


Jin ta kashe ya ƙara kira ta ɗauka,tayi shiru"inane motar ta tsaya?"


Gaya mashi tayi saidai yaji muryarta kuka takeyi,miƙewa yayi cikin sauri ya kira layin mai gyara yagaya mashi,ko minti 15 ba'ayiba Sai gashi ya iso.


Ta kauda kanta,ya shiga ya tada motar,ya fito,saiga mai gyaran  yazo,ya kalleta"bashi key ɗin mutafi"


Saudat tayi yadda yace taje ta buɗe gidan gaba ta zauna,shikuma ya tsaya yana magana da mai gyaran sannan yazo yaja suka tafi.


Gidan suka nufa straight,suna shiga da mota Ni'ima ta fito tayi shirin ta fiya unguwa,da jaka a hannunta,Areef yayi parking saidai bata  lura da Saudat a wajan ba,sai da ta matsa zatayi magana ta ganta,take ranta ya ɓaci ta ɗaure fuska.


Areef yafito,Saudat ma haka,Saudat ce tace"Aunty tafiya zakiyi?"


Ko kallanta batayi ba ta juya kan Areef da yake matsowa wajanta,"ya dai"yatambayeta dan yaga yadda ta canza"dama ai dole ka tambaƴeni,tunda yanzu bani gabanka,how manƴ call i give you baka ɗauka ba,sai yanzu kun dawo kace man wai miye,ai dakaƙi ɗaukar wayar ƙara ka gayaman cewar kuna tare"


Areef yayi saurin kallonta danjin abinda tace,yasan kishine ya motsa,ya ɗan ƙara matsawa kusa da ita,"muje in kaiki"


"zanje da kaina,kaje kawai,tunda tafini muhimmanci ka..."


Shitttt Areef ya ce mata yana ɗora hannu kan lips ɗinshi,Saudat tayi gaba ta shigewarta part ɗin,don tagama gano Ni'ima, kan gado ta faɗa tana kuka tunani takeyi miyasa Ni'ima zatayi haka,bayan tasan ba wadda Areef yakeso sai ita,duk bata tashi hakanba saida ta bari zuciyrta taƴi nisa wajan san yayan data.


Tajima tana tunani,dan ita kanta kishin Ni'imar takeji saboda gani take itace dalilin dayasa Yayan nata bai damu da ita ba wannan lokacin,tabbas zaman su bazai yiwuba indai Ni'ima zata cigaba da haka.


Kuka sosai Saudat tasha,Sultan ya shigo ya hau gadon yana faɗin"Momy zo kiga abinda Uncle ya sawo man"


Saudat ta goge hawayenta,Sultan ya zaro ido"Momy miya saki kuka"


STORY CONTINUES BELOW

"bakomi ba kuka bane,abu ya faɗa man a ido"


Miƙewa tayi ta jawo manyan bags ɗin dake gefe,ta buɗe wadrop ɗin kayanta,kayan ta ta kwashe tass cikin lokaci,ta kwashe na Sultan ta saka a bags ɗin,ta jawo ta fiddo waje,drivern gidan Ammi takira tace yazo yaɗauketa da Sauri,bajimawa yazo.


Kayan ta saka ya ɗora a mota,yaja suka nufi gidan Ammi,tana shiga ita da Sultan Ammi tace"daga ina ana shirin magrib"


"daga gida"tana zama driver ya fara shigo da manyan jikkunan kayan,Ammi tace"lafiya daiko kayan miye"


"kayan mune Ammi"


Nan Hankalin Ammi yatashi,ta fara tanbayarta ko Areef ya koreta,tace a a,ko bakijin daɗi zama gidan"Allah a'a Ammi lafiya lau kawai wajanki nikeson zama"


Ammi tace"shikenan,kitashi kije ki shirya kayan a ɗaki" Saudat ta miƙe taje ta jera kayan,cikin wadrop bata gamaba sai wajan 9,sannan ta fito tadawo wajan Ammi suka cigaba da fira.


Areef kuwa dayakai Ni'ima acan yabarta,sai bayan isha'i yakoma ɗaukarta,suka nufi gida,su duka ba mai magana saboda faɗan da sukaƴi kafin su fita.


Suna shiga gidan,ya shiga falon,yasan lokacin Sultan yayi bacci Amma duk da haka saida ya ɗan kwala kira,jin shiru ranshi yabashi su duka sunyi bacci.


Ni'ima ta wuce ɗakinta,ta barshi,part ɗinshi ya nufa yayi shirin bacci,tunda ya kwanta bacci ya ƙauracewa idonshi,shidai tunda yake bai taɓajin irin son da yakewa Saudat ba,ita kaɗai yakewa irinshi,Amma yasan bazai samu ko rabinshi awajanta ba,shi kanshi yasan bazai iya tunkararta da maganar so ba.


Haka yayi ta tunani har bacci ɓarawo ya ɗauketa,Saudat ba ma ɓangaranta hakane,don Soyayyar da takewa Areef bazata misaltuba,tana tunani tana kuka,ga wata azabar soyayyarshi dake damunta.


           ****

Yau Areef da wuri ya shirya,wajan 7:30 ya fito,Ni'ima tana kitchen tana girkinta Atunaninta dan jiya bata bari sunyi aiki tare da Saudat ba,shiyasa yau taƙi fitowa.


Baiga Sultan a falonba,dan dasafe idan zai kaishi skul zai tadda ta shiryashi yana jiranshi,Kitchen ɗin ya shiga Ni'ima tace"ina kwana"


"lafiya lau"ya Amsa ya fito yana kiran Sultan yaji shiru,ya koma kitchen ɗin"jeki ce yafito yau Sauri nike inada meeting 8"


"break fast ɗinfa"

"zanyi a Office" Ni'ima ta fito ta shiga ɗakin Saudat,saidai bataga kowaba,ta tura toilet ɗin ta fito tace"baya nan"


Ɗakin ya shiga Ni'ima ta bishi,sai lokacin ta kula da babu alamar kaya a ɗakin,ta buɗe wadrp ɗin Areef yana gani gabanshi yayi muguwar faɗuwa.


Ni'ima ta juyo suka haɗa ido,tagano tsantsar ɓacinrai a wajnshi saidai baice komi ba ya fita,mota ya shiga,ya tada ya fice daga gidan,Ni'ima ta taɓe baki ta komawarta kitchen,cikin zuciyarta tace,inda banyi hakaba da batabar gidanba,Abinda bata saniba,hakan kamar wata ƙoface tabasu.

Gidan Ammi yayiwa tsinke dan yasa babu inda zata nufa sai can,Yana shiga falon ya tadda sun fito Sultan da Uniform ita kuma ta saka material red ɗinkin riga da skert kanta babu ɗankwali sai gashinta da yasha gyara ya biyo wuyanta.


Sultan ya Sauko daga kan kujera,yana "oyoyo Uncle"Sai lokacin Ammi da Dady suka juyi suna kallonshi,Saudat kam dakewa tayi batayi magana ba.


Zuwa yayi ya gaidasu Ammi,dady yace"ya naganka da safe".


"eh nazo ɗaukarsu Sultan ne,dan bansan tahowarsuba"


Duka suka kalli Saudat,Saudat ta cigaba da cin Abincinta"ban ganeba"inji Ammi dake kallonshi"nazo kai Sultan ne yanzu naga basu gidan.


Dady ya kalli Saudat"ke ya akayi kika bar gida bai saniba,wanann gangancine"


"babu komi dady"


Ammi tace"Akwai dai abinda ya faru,kuma saikin faɗi mani"


STORY CONTINUES BELOW

Areef yaja kujera ya zauna ya zuba Omelet a plate yanaci,Dady yace"kai mikayi mata ta taho ba tare da sanin kaba"


"ka tambayeta ni bansaniba"


Dady ya tambayeta tace babu komi,su duka suka ɓata ran Dady,driver ya zo yatafi da Sultan Saudat tace"kajira katafi dani inka ajeshi saika wuce dashi"


Dady yace ma driver yayi tafiyarshi,Saudat tayi shiru,Ammi tace"ai inba wani Abu bazata bar gidanba,kai Areef nasan laifinka ne dan"


Wayar Areef tayu ƙara,ya ɗauka"ina zuwa 15mints plzz"


Dady yace"ku duka ba inda zaku,sai kun faɗi yadda akayi tabar gidan"yana maganai yakoma cikin falon ya zauna kan kujera Ammi ta taso itama ta dawo falon.


Daga Saudat sai Areef dake cin wainar egg ɗin a hankali,Areef ya ɗagokai yana kallonta,ta aje plate ɗin tana miƙewa,takai idonta kanshi,4eyes sukayi da sauri tajanye idonta,tayi hanyar Room ɗin tadawo hannunta riƙe da jikka tana rolling gyale akanta.


Falon tazo jiki babu kwari tayi kamar zata fita Dady yace zauna,batada zaɓin daya wuce zaman ta zauna tayi shiru.


Areef kuwa ganin an zaunar da ita yaƙi tashi,ya cigaba da latsa wayarshi ga time yana ƙure mashi,ya tashi yace"Ammi inada miteeng 8 gaya harta wuc..."


Dady yace "nima nan meeting ɗinnikeyi,dan haka ka zauna"stool ya zauna Dady yace"ina jinku"


Areef shidai bazai faɗi yadda akayiba,Saudat kam yasanta da kafewa,Wayar shi ya ɗauka kiran Zaks yayi bajimawa yaɗauka"hello place Annouce the imformation,inada aiki yanzu bazan samu zuwa meeting ɗinba,Na ɗagashi zuwa 11"


Kasan cewar Areef babba hakan yasa Zaks bai tsaya tambayarshi miyasaba,saboda koda yake frnd ɗinshi idan suna maganar aiki Zaks yana bashi girmanshi.


Dady yace"kama maidashi gobe,dan ko zakukai 11 anan ba wanda zai fita"


Saudat ta latsa wayarta,ƙarfe takwas da minti goma itada zatayi program 8:30 yakamata ace yanzu tana hanya.


Rufe idonta tayi tana ta miƙe ta shiga ɗaki ta ake bag ɗinta da mayafinta,ta ɗauki waya G.M ɗin Office ɗinsu ta kira,tagaya maahi tanada matsala,bazata iya zuwa program ɗinba.


Dr Moh'd yana mugun tsanani ga ma'aikatanshi,amma indai Saudat ce batada matsala,duk abinda takeso shi yakeyi,"hop lafiyarki lau daiko"


"Eh to lafiyata lau Amma wata matsala ce shiyasa bazan samu zuwaba"


"wace matsala kenan"

"oga kayi haƙuri basai na faɗi makaba"


"nidai ki faɗiman"shi baima damƴ da batasan zuwaba,sai son janta da surutu yake,Saudat kam so take ta yanke firai tace"ok zan faɗi maka anjima"tana magani ta kashe waya ta koma falon.


Zaman falon abin dariya don babu wanda yake Magana,saima Dady da Ammi lokaci zuwa lokaci,Areef ya tashi yakoma kan kujera ya xauna Dady yace"better don zakafi jin daɗin zama a wajan"


Saudat abin yama bata dariya saidai ta kasa yin dariyai,don batasonma yaga tana dariya,zuna zaune har tara tayi,tara da rabi,goma,Dady da Ammi kawai suke fira.


Saudat kam chart kawai take,ta miƙe ta je kitchen ta haɗa lipton yaji citta da kayan ƙamshi,tasa sugar kaɗan, ta jawo babban tire,ta zuzzuba tea ɗin a cups guda huɗu,ta ɗora kowane a sosa,ta ɗora kan try ɗin.


ɗaukowa tayi ta fito lokacin goma da rabi,Dady ta fara miƙawa try ɗin ya ɗauka,ta ba Ammi sannan ta wuce kan kujerar da yake,ya ɗauka yana kallonta ita ma shi take kallo,wata harara ya sakar mata,batasan lokacin dataƴi dariyaba.


Both Dady da Ammi suka juyo suna kallonsu,kwafa yayi ya juya,Saudat ta ɗago da sauri ta ɗaire ganin su Dady na kallonsu.


Ammi tace"kaga raina mana hankali zasuyi ko"


Areef yace"Amma Ammi ni miye laifina anan,banfasan ta tahoba"


Dady ya kalli Saudat "miyasa kika taho?"


"nafison zama  nan"


Dady ya gyara zama"wallahi ƙarya kuke bakuda gaskiya ku duka"


Areef ya kalli Dady "nifa Meeting gareni tun 8 namaidashi 11 kuma gaya har takusa,idan na dawo sai in ɗaukesu mutafi"cikin damuwa yake maganai,Saudat sai taji yabata tausayi.


Ammi tace"naga inda zaka fita,ai tunda tarasa shirinta na safe dole kaima bazakayi shiba,indai baku faɗi yadda akayi ba"


Areef ya kalli Saudat,tayi saurin kauda kai,ya ɗauko wayarshi yana niyar tura massge.


Saudat tace"nifa Ammi ba wani abu akayiba,zaune muke lafiya kuma ni bamu taɓa samun saɓani da Ni'ima ba tunda nike,kawai kwana ukku Nawayi gari bata ansa gaisuwata,na tambayeta laifin mi nayi bata,tace haka take ra'ayin zama gidanta,duk aikin da za'ayi tare mukeyi ina tayata,tun lokacin tace bataso,jiya mota ta ta lallace..."


Tunda take bayani Areef yake kallonta,jiyake kamar tana labaru,Dady ma kallonta yake,Ammi kuwa Areef ɗin take kallo tana murmushi,ganin yadda yayi mata zuru.


"ina hanyar dawowa daga Office,shine nakira shi yazo akaɓmba mai gyara motar nikuma ya ɗaukeni mukaje gida,Ni'ima zata unguwa ashe ta kirashi bai ɗaukaba,tana ganimu takama faɗa,wai nafita muhimmanci shiyasa yayi lokacina ya ƙaleta"


Saudat na zuwa nan ta lumfasa,tana ƙoƙarin maida hawayen dake shirin zubo mata tacigaba"Dady nikuma gaskiya baniso nazama silar matsla tsakanin Yaya da Matar shi,don na lura kishine shiyasa"


Dady ya kalleshi"wai haka akayi?"


"to nidai bansan hakan ta faru tsakanin suba,Amma nasan naɗaukotan ita kuma tayiji haushi tace Saudat tafita muhimmanci"


Ammi tace"saudat tayi dai-dai kuma tayi hankali,dan idan ta zauna faɗa zasuyi da matarshi,kaga kuma za'aga laifinta hakan datayi shine dai-dai"


Areef yakalli Ammi"Ammi Amma ai nariga na fahimtar da ita komi,nagaya nata Saudat ƙanwatace ba sonta nikeyi ba,nagaya mata idan natashi ƙara Aure bazata hananiba kuma xanne mi watane,kuma yanzu ta fahimta"Areef yana magai yana cijewa kamar murarshi zata ɗauke dan yasan ƙarya yake faɗi


Saudat kam ba ƙaramar kaɗuwa tayiba,har batasan lokacin da zufa tazo mataba.


Ammi da dady maganar tayi nasu wata iri,wai Areef yake cewa basan Saudat yake ba,Ammi kam ta ƙaryatashi cikin zuciyarta.


Dady yace"shikenan anjima sai kazoku tafi Amm...."


Saudat ta fashe da kuka"Allah Dady babu inda zani,dan bazan koma gidan ba, taya zan koma gidan shi bayan kunajin abinda yace"*AUNTY HALILOSS*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


27


Areef ya yakallonta,yasan maganar tayi mata zafi kuma dama haka yakeso,ya miƙe yana ficewa dan ko bankwana baiyi masu ba.


Saudat kam itama miƙewa tayi ta shige ɗaki,ta kwanta tana kuka,Dady ma fita yayi Ammi ta shigo ɗakin tana lallashinta"to miye abin kuka tunda kince bazaki komaba,ai shikenan ko"


Saudat kam ita kaɗai tasan yadda zuciyarta ke bugawa,ga wani zafi da take mata kamar zata fashe,maganar Areef keyi mata yawo a kunnai.1


Miƙewa tayi ta shiga toilet ta wanko fuskarta,tare suka fito da Ammi,kitchen ta shiga domin yi masu girkin rana,wunin ranar cikin ƙunci Saudat tayishi.


Angama sallar magrib Dr Mohd yayo mata waya,suka gaisa kiman kwatancen kidan ku gani nan zuwa"


Saudat tace"oga muyi waya dai basai kazo ba"


"inson jin abinda ya samekine"


Saudat ta lumfasa tasan Dr Mohd yana mata mutunci,tace"ba wata damuwa bace dan har nayi solving case ɗin dont worry your self plz"


Haka sukayi waya,sannan sukayi bankwana,dama Dr Mihd haka yakeso ya samu yaga yana mu'amula da ita dan yanasonta sosai.


Fitowa tayi falon,doguwar rigace jikinta bara nauyi saidai free shape ce,hula ce kanta,sai waya a hannunta,tana kiran Sultan.


Areef yace"tashi kaje Momy na kiranka"


"no Uncle Momy jiya a gida kuka take,yauma dana dawo sckul kuka takeyi,banason Momy tana kuka bazan keba"


Areef ya kalli yaron yadda yake magana,Saudat batasan yazo gidan ba,ta ida isowa falon,takallesu,da sauri ta kauda kanta ganin zai kalleta.


Farin yadine jikinshi,yadin yanada silk farin takalmine ƙafarshi,yayi kyau sosai,Saudat ta zauna "ina wuni"


Bai kalleta ba,bai kuma amsa ba,Ammi ta fito daga part ɗin Dady Saudat tace"Ammi mizamuci yanzu,yunwa nikeji"


Ammi ta taɓe baki"dole kiji yunwa bakicin Abinci"


Areef ya ɗago ya kalleta,ba makeup fuskarta amma tayi yau sosai,dogon hancinta ya kalla,ya kalli red lips ɗinta,lokacin tana ma Ammi magana,gani yake kamar tana masu wani salo.


Ammi ta kalleshi tace"kaifa yaushe kazo"

"yanzu na shigo"


"daga ina?"

"daga gidan Mami nike,Sadiq yaman waya ɗazu wai nextweek zai dawo"wato junior brother ɗinshi,Ammi tace"Allah yadawo dashi lafiya.


Areef yace amin,ya miƙe zai nufi ɓangaran Dady,ya juyo yace"kinga na manta ingaya maki,Mami tace iyayan yarinyar Muhsin sunce a aika,shine tace inzo ingayawa Dady danshi Pappa har ya yanke hukuncin gobe ne zasu"


Ammi tayi dariya"lallai kam Muhsin Allah yakaimu goben,ya shige ɗakin Dady bajimawa suka fito tare lokacin Saudat tana kan dinning tana haɗa tea dan yunwa takeji sosai.


Dady ya kalleta,"mi kikeyi?"


"Dady tea zansha yunwa nikeji"


"babu abinci ne a gidan?"

Ammi tace"tace batason cin abincin"+


Dady ya zauna kujerar dake kallon Areef,ya kalli Ammi yace"Areef ya faɗi maki maganar tafiyar matarshi ne?"


Areef yayi sauri yace"a'a ai kaina fara gaya mawa"


Ammi tace"ina zataje ne"


Areef yace"ɗazu babanta yakirani yace yashirya fita da ita India don likitoci suduba ko akwai matsalar mahaifa,saboda duk asibityn da mukaje sunacewa itace da matsala"


STORY CONTINUES BELOW

Ammi tace"to Allah ya taimaka ya bada sa'a,yaushe zasu tafi?"

"eh yace sati mai zuwa saidai basu fidda rana ba"


Dady yace"tare zakuje ne"


"a'a gaskiya saidai in bisu daga baya idan tafiyar tayi tsawo"


Ammi tace"to shikenan Allah yasa ayi sa'a"


Saudat tanajinsu,sai lokacin ta tuna duk lokacin da Ni'ima zatayi period sai tasha wahala,shikuma Areef yayi ƙokari sosai wajan nema mata magani,sannan kuma koda sukaje Asibity duk inda sukaje sai ace masu ciwan marar da takeyine yake hanata ɗaukar ciki,Amma gaba ɗaya Areef bai taɓa damuwaba balle ya nunawa Ni'ima,saidai su iyayanta sun damu saboda dama sunsan tanada rashin lafiyar tun kafin Auransu.


Haka sukayita fira,wayar Saudat tayi ƙara,ta miƙe tana ɗauki cup ɗin takai kitchen ta dawo zata shiga ɗaki Sultan yace"momy zo"


Ammi tayi dariya "Momyn kake cewa tazo?"


Saudat ta matsa wajanshi ta murɗe kunnanshi"ni zanzo ko"


Ya riƙe hannunta yana shirinyin kuka,Areef ya zura mata ido,taƙi sakin kunnan Sultan ya fashe da kuka yana"kunne na"


Tace "waye zaizo tsakanin nidakai"


Dady yace"sakar mashi kunne"

"barta ai ƙila cire shi zatayi"


"Dady kanajifa yaron nan,wai inzo,ta daki kunnan ta duƙar da bayanshi tayi mashi dundu"ai an sakwaɓaka ko,to wallahi ni jibgarka zanyi"


Areef yasan da biyu take maganai,dan tasan shi yake sagwaɓa yaron,ya kalleta yadda take Acting ɗin ya mashi kyau,ta ɗaga hannu zata ƙara bugunshi Areef ya janye yaron.


Wayarta ta ƙarayin kuka Dr Mohd ne,Saudat ta duba wayar taɗanyi tsaki dan ta lura matsa mata zaiyi,ta zauna gefe,Areef kam idonshi yana kanta.


Bai ƙara jimawa ba ya miƙe yayi bankwana,Sultan yace zai bishi,ya koma ya zauna"aiba yanzu zaniba"


Ammi tace"aikam yau rabaku zaiyi wahala"


Saudat kam ko kallansu batayi ba,saima daɗi da taji,dan koba komi tanajin muryarshi suna fira.


Areef kallonta yayi yaga kamar batasan yanason tafiya ba,Dady yace"taso muje ɗakina kaga wani Abu"


Sultan yace"wallhi Dady dana tafi Uncle zai barni"


Areef yayi dariya"yaron nan wayo yamashi yawa"saudat kam cije dariya takeyi,tana latsa waya.


Can anjima ta miƙe zata shige ɗaki,tana tafiya tana latsa waya"Ammi saida zafe"


Tana can ɗaki tana chart,tana sauraransu har lokacin bai tafiba,shikuna Sultan yaƙiyin bacci Agogon wayarta ta duba,ƙarfe goma na dare.


Mayafi ta ɗauka ta axa saman rigar baccin jikinta,ta shiga falon ta zauna,Dady bayanan sai Ammi dake tayasu fira.


Saudat tace"Sultan kayi home work yau"


"no bari in ɗauko Uncle yayi man,yana maganai yana miƙewa yana shirin rugawa,Saudat ta miƙe tabi bayanshi,yanaji ta maido ƙofar ta rufe da ƙarfi.


Areef yayi dariya ya tashi yayiwa Ammi bankwana,ta window Saudat take kallonshi yadda yake tafiya,harya tada mota tana wajan tana kallonshi yafice.


Sati yana zagayowa Ni'ima suka tafi india,gaba ɗaya Areef yanzu ko Office ya dawo gidan yake sauka yaci abinci.


Itakam Saudat wani lokaci tana Office saidai Dr Mohd ya matsa mata sosai,don tuni ya baiyana tsantsar soyayyar da yake mata,Saudat kam tasan ya makaro dan babu wanda yake cikin zuciyarta a yanzu sai Yayanta.


Satin bikin Fatima yazo,hakan yasa batada zama hidima kawai suke sosai,Sabida dama saida aka ɗaga bikin,kullun Saudat bata zama gida,Haka Areef yake zuwa yayi zamanshi wani lokaci yana zuwa zata fita.

         ****

Zaune yake ɗakin Ammi,Ammi tana kan gado shi kuma yana kan stool da plate yanacin Abinci.


Saudat tazo wajan corridor ɗin ɗakin Ammi,atamface jikinta anko ɗin kamune,straight gown ce ɗinkin yakamata sosai,tayi makeup sosai saidai light ne bata cika fuska ba,gashinkanta ta riƙo da hannunta,ga waya a kunnanta.


"Nop yau kamu ne zamuyi hop zakaje"


Daga ɗayan ɓangaran aka ansa,saidat tace"kasan banason hayaniya gida na dawo yanzu zan samesu a hall ɗinne"


Dai-dai lokacin ta shiga ɗakin Ammi,"ok am waiting take care"tana maganai ta kashe waya.


Areef ya na Saurarranta sai gabanshi ke dukan Uku-ukku,dan baisan dawa take wayaba,daji kuma namiji ne.


Ta sauke wayar kan kunnnta,sai lokacin ta kula dashi"yaya ina wuni"


"lafiya klau"

"Ammi Sultan bai kawoman cumb anan ba kaina nakeson tajewa"


Ammi tace"saidai ki duba,ko ki nemi nawa"


Saudat ta tafi wajan bedsite locca ahankali take tafiya rigar fito da shape ɗinta sosai,cumb ɗinta ɗauka takima kan mirrow ta xauna tana sharce gashin.


"wai nikau Ammi Sadiq ya baki key ɗina?"


Ammi tace"ai kinsan halinshi nave yabar ɗaukar maki mota yaƙi,tunda idan yatafi baya dawowa"


Waya ta jawo"hello brox ka maidoman motana fitafa zanyi "


Jim kaɗan ta kashe waya,Areef yana jinta,lokaci zuwa lokaci yana satar kallonta.


Wayarta ta ƙarayin ringing"sorry frnd ganinan zuwa"


TAshi tayi takoma ɗakinta,ta ɗauro ɗan kwalinta ta riƙo siririn mayafinta,da handbag ta fito A falon ta tadda shi,ta zauna"Ammi wallhi idan na hana Brox fita da motana kada kice komi"


"baruwana tsakaninku ne,duk wanda ya shiga zaiji kunya tunda yadawo,haka kuke jiya dana sa maku baki a nikuka bari arana"


Wayarta ta ɗako,ta dnnna kira"ƴes but ba mota hannuna,kazo saika ɗaukeni mutafi"


Areef baisan lokacin daya kalletaba,tunaninyake kenan harta fara soyayya,waye zai ɗauketa,taya wani zai ɗauketa sutafi.


Wayarshi ya jawo,ya danna kira,Sadiq yakira"Hello"bai jira cewar shiba yafara faɗa yana masifa"miyasa zaka ɗaukar mata mota,kai ina taka,duk motar dake gidan nan saika ɗauki tata,tun yaushe ta maka waya ka kawo,wallahi i one give you 10mint kadawo ko ranka ya ɓaci"


Saudat ta kalleshi tace"Yaya daka barshi ma yanzu zantafi maybe yana wani Uziri ne" Saudat tana magani cikin wani salo dan Ammi ta tashi daga falon,dama tayi hakanne dan shiɗin,dan takasa gane gaskiyar lamari daga wajanshi,some time sai taga kamar yana sonta idan yayi mata wani abun kuma kamar ta mutu.


Ammi tadawo falon,Areef ya miƙe "tashi muje inkaiki"


Saudat ta kalleshi"za'azo a ɗauke ni ne"


Areef ya ɗauke fuska ya miƙe tsaye"Anshi key ɗina kije da motana"


"nifa nace maka ɗaukata za'ay...."


"bazai yiwubawaye zaizo ɗaukarki?"


Ammi tace"wai ya akayi"


Areef ya faɗi mata yaɗora dacewa"yanzu ammi aiba girmanmu bane aga wani yazo yaɗauke ta sun tafi event da daddre,sai mutane su..."


"nidai Ammi..."bata idaba yace"Allah ba wanda zai ɗauke ki it either to go with my car kokuma kifasa zuwa"


Ammi ta zauna "ya isa haka,keki anshi key ɗin kitafi,kinga abinda yafaɗa gaskiya ne"


Areef ya miƙa mata key ɗin,ta ansa tana turo baki ta fice binta yayi da kallo,ta fita kuma hankalinshi bai kwanta ba,harya zauna ya miƙe ya shiga room ɗin Dady wani makullin mota ya ɗauko yazo yafice.

Ahankali take tuƙi,kamshin motar yana ratsata,gaba ɗaya jitake kamar Areef yana kusa da ita,musics ɗin motar ta kunna,tana kunnawa taji kamar F.M ta kalla saikuma taga ba redio bane,Muryarta taji tana gabatar da wani shiri.


Kallo tayi sai lokacin ta kula da revording ne akayi,gabanta ya faɗi,ta cigaba da saurare,tana murmushi kenan recoding ɗinta yake idan tana program.


Ahankali da take tafiya yasa Areef ya taddota har suka isa Hall ɗin,saidai bai bari taganshiba,fitowa tayi tayi da waya a kunannta,kamar tana waige-waige Areef yana mota yake kallonta.


Can ta nufi wani dake jingine da mota,Areef yana kallonsu,Saudat ta tsaya suna gaisawa,wata mota ta haska motar dake nesa dasu,ganin motar Dady tayi ta kalla domin tantance gaskiyar.


Motar ta haska sosai,sai lokacin ta kula da Areef ne a cikin motar......*AUNTY HALILOSS*

WA NAKE AURE?
    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*

28

Ita kanta Saudat bataso Dr Mohd yazo wajanba,saidai babu yadda zatayi,Areef yana gani sukayi bankwana,lokacin ne wasu frnds ɗinta mata sukazo suna magana suna shirin shiga Hall ɗin,saidai gaba ɗaya hankalin Saudat yana kan motar da Areef yake ciki.+

Gani tayi ya buɗe marfin mota yafito yana nufosu,Ahankali taɗan rage tafiyar sukayi gaba,ita kuma tayi kamar tana latsa waya,Areef ya iso inda take,wayar Hannunta ya anshe.

Ta juyo ta kalleshi kamar batasan yana wajanba,"laaa Yaya plzzz bani wayana ashe kazo?"tana maganar cikin salon jan hankali.

Areef yakasa magana dakyal ya fara magana cikin faɗa "wato har so kike ki fito ki ringa fira da maza,to wanann ba mutuncinki bane,zaki zudda mituncin Family ɗinmu.

Ita kam kallonshi kawai take,ya kalleta,"muje gida"

"Kayi hakuri yanzu fa nazo ko shiga banyu ba"

Areef ya ƙara ɗaure fuska,Saudat taɗan tsorata,motar da tazo da ita ya nuna mata,ta shiga shima ya juya ya shiga motar Dady,Saudat taja motar tana fita main road tafara wani azababban gudu wanda koshi namiji sai yaji tsoran yinshi.

Itakam Saudat kuka take a motar tana gudu,tarasa mike damunta kenan ya Areef ba kishinta yake ba kawai darajar gidansune yake karewa,wannan abu yasa zuciyarta ke tsananin bugawa,haka ta isa get ɗin gidan,Horn take dannawa wani na dukan wani ba tsayawa da gudu mai gadi ya buɗe.

Ta shiga ko fitowa daga motar batayi ba Areef ya shigo da hancin tashi motar cikin gidan,Dady ne ya leƙo ta falonshi dan ganin wanda yashigo sabida yadda yaji Horn dakuma speed ɗin da ake a harabar gidan.

Hanyar Main falon ta nufa,Areef ya bita,Dady yana kallonsu shi dariyama suka bashi girgizakai yayi ya koma ciki har ya zauna Falonshi ya fara jiyo hayaniƴar Areef shiga yayi falon yana kallonshi.

Ammi kanta kallon Areef take yadda lokaci guda ya canza"taƴa za'a sa maki ido kiyi yadda kikaga dama,shi idan tsakani ga Allah yake sanki the door is open ba sai ya ringa binki a wajan event ba,yanzu duk wanda yaganki a wajan akace ke diyar Dady ce ko Aka faɗi sunan Pappa am very sure mutane ƙalilan ne zasuce basusan iyayan muba,last warning inhar kika ƙara ko waye zai aiko ayi maganar auranku dan bazaki ɓata mana suna ba"

Dady ya shiga ya zauna,Saudat Kuka kawai take rusawa,Ammi kam ta rasa ta cewa ganin yadda ɗan nata ya haukace lokaci guda.

Babban bakin cikin Saudat wai Yaya Areef kecewa ta Auri wani,wani bakin ciki ya ƙara kamata,kenan bayasanta,kawai baiso ta ringa mu'amula da mutane ne.

Dady yace"ya isa haka,shikenan Saudat kinga abinda ya faɗa gaskiya ne,duk wadda zakiyi fira dashi yazo gida gudun zagi kinji ƴata?"

Ammi tace"kubar man ƴata,taso muje"

Dady yace"ai dama haka kuke Mata,ana faɗin gaskiya kuna goyan bayan yaranku mata"

Saudat da Ammi suka shiga ɗaki,Dady ya kalli Areef ya kirashi,Areef maida lumfashi yake sosai,Dady ya riƙo hannun shi yafara magana ƙasa-ƙasa "Areef kanason ƴata ne?"

Tambayar tazo mashi a hautsine,dan bai taɓa tunanin hakan ba a wannan lokacin"haba Dady nifa kawai ina son kare mutuncintane"dakyal yake magana,Dady yace tashi kaje,Aeeef jiki babu kwari yabar gidan.

Ammi kam lallashi Saudat tayi,da kyal tasamu tayi. Shiru sannan tabaro ɗakin,ta nufi ɗakin Dady,ta zauna tana kallonshi"kaga yaran nan ko"

"wallahi ina ganinsu,har na kasa haƙuri saida na tambayeshi sonta yakeyi ko,Amma yace wai mutuncinta yake karewa"

STORY CONTINUES BELOW

Ammi tayi dariya "ƙarya yake dan Ubanshi,ai wannan haukane ma abin ya wuce kishi"

Dady shima dariya yake,suka cigaba da tattaunawa kan maganai.
Saudat kam Ammi tana fita tacigaba da sabon kuka,wai yau itace Areef yake wulaƙantawa irin haka,wayarta ta ɗauko ta nemo number ƙawarta dake Office ɗinsu,sun shaƙu da ita sosai,suna yawan hirar samari,saidai ita budurwace.

Saudat ta kara wayar akunne,tanaji ta ɗauka"Hello BILY SHANTALI dan Allah kitaimaka man wallahi yaya Areef ba sona yake ba zan iya mutuwa idan na rasashi"ta ida maganai tana kuka,Bily hankalinta yatashi, tafara tambayarta yadda akayi,saudat ta bata labari"Ke wallhi kishi ne kawai"

"Allah Shantali bakiga yadda yakeyiba,wallahi zuciyata zata iya fashewa"

Billy shantali tayi dariya,tana ƙara ba Saudat haƙuri,dan koda bataga yadda Aréf yayi ba tasan kishine.
       ****
Haka Saudat ta mutu wajan soyyar Aeeef har takaiga ko abincin kirki bata iyaci kwana biyu lokaci guda Ammi ta fahimceta kuma tagama ganota.

Shikam Aeeef tunda yaga Dady yayi mashi wannan tambayar sai ya sake salo,ya dage wajan kare son da yake mata gudun kada ta gane,dan gani yake kada amai-maita yar gidan jiya,saidai duk zafin da zuciyarshi keyi mashi to yana iya ɗauka.

Canjin da Areef yayi shiya ƙara haukatar da Saudat dan gaba ɗaya ta gama amincewa zciyarta,babu soyayyarta a wajan Areef duk sadda taje office firar neman samun mafita takeyi ita da ƙawarta Billy shantali.

             *****
Saudat tana zaune tayi tagumu,Sultan yakan capert yana aikin da aka basu Islamiya,Ammi tana zaune tana fira da Sadiq.

Areef ya shigo gidan hannunshi riƙe da wata leda,Sultan ya fara murna ga uncle,Areef gaida Ammi ya zauna Sadiq yace"Yaya tun jiya nake nemanka banganka ba"

Saudat ta ɗago ta kalleshi shaddace jikinshi Ash colour with black shoe,sai car key dake hannunshi,Babu hula kanshi sumarshi tasha gyra,yayi kyau sosai.

Areef a ɗago ya kalleta,da sauri ta kauda kai"Yaya ina Kwana"

"lafiya ƙlau"ya amsa, Saudat ta ɗora ƙafarta kan center table ɗin dake gabanta,tana tunani,Ammi tace"tashiki samo mashi wani abu"

Saudat bataji ba sabda hanklinsu baya wajansu,Sadiq yace"Sister ana magana"

Saudat ta kalleshi,da wasu jiraran hawaye dake zubo mata,tayi saurin gogewa,Sultan ya matsa"Momy kibar kuka har yanzu aikin ya matsa maki"

Areef ya kalleta wani abu yaji ya daki zuciyarshi,mi takewa kuka,ya kalli Ammi"batada lafiya ne"

"gaka gata ka tambayeta nina gaji,wallahi jiya danaji haushi har Mami nakira waya nagaya mata"

Saudat ta dawo da cake da drinks,ta aje mashi,Areef ya riƙo hannunta ya zaunar da ita gefenshi"Miya samu ƴar ƙanwa,Ammi ce ko?

Saudat da tunda ya riƙe hannunta gabanta ke faɗuwa,shikanshi dakyal ya iya daurewa sabd wani shock dayaji.

Saudat ta girgiza kai,Areef ya ƙara tambayarta"To broz ne ko?"
Sadiq yace"nima ba ruwana,dan gidanma yazama so borring saboda batada walwala"

"faɗiman to,miye problem ɗinki" Saudat kam kamar tace kaine,saidai babu dama.

Areef yace"shikenan,kinga Ammi tadamu batason ganinki a damuwa ki daina"

Ɗaga kai kawai Saudat tayi,ta miƙe ta shihe ɗaki,taji daɗi koba komi dai yau Areef yayi mata magana softly and ya nuna kulawarshi akanta.

            ****
Tunda kayi haka Saudat tadaina zama gida idan ta fita Office batasan dawowa,saboda idan tana gida damuwa take shiga,saidai sosai ta dage da Addu'a neman samun mafita.shi kuwa Areef matarshi ta dawo yanzu,kuma an bata magunguna,yanz bai wuce yaje gidan so ɗayaba kuma baya taddata kullun Ammi zatace tana Office.

STORY CONTINUES BELOW

Wannan abu ya ƙara tada hankalin Areef shima ya shiga damuwa.

          ****
"Yes Billy zan gaya mashi koda zaifito yace baya sona,ƙara insan hakan da ciwan da nike fama dashi,nasan yanzu idan na mutu banida dalilin mutuwa Amma idan na faɗi mashi yace bayasona,idan na mutu to tabbas ƙiyayyar da Yayana ya nuna man ce,kuma nasan banyi Asarar faɗi mashiba,saboda ba kaina aka fara ba"tana maganai tana goge hawayenta,Billy tace"shikenan Saudat insha Allah zai Amince"

*GIDAN MAMA KUWA*

Tunda Areef ya saki Saudat hankalin ƴan gidan ya kwanta gaba ɗaya bakajin kansu,Usman kam bai damuba sabd yana baƙin cikin abinda Saudat tayi mashi.

Ko wata batayi da tafiyaba,Usman yaba mama shawar zaije ya dubo ɗanshi,Mama ta kona gefe ta hana ƙarshe tace indai yaje batare da yardar taba bata yafe mashiba,wannan shine dalilinshi daƙin zuwa.

Mama taji ta Amince yanzu duk aikin gidan ita takeyi,tayi shara,wanke-wanke girki Nusaiba tana gani tace batayibata iyawa,Hayatu kam ko a jikinshi.

Saidai Usman duk sadda ya tadda mama tana wanan aikin tabbas zuciyarshi tana sosuwa,yanajin baƙincikin rabuwa da Saudat.

Usman yana samun kasuwa sosai,Hakan yasa Mama ta matsa mashi dole sai yayi Aure,shidai gaba ɗaya baya ra'ayin aure,Amma ta takurashi,ta samo mashi wata mata Zubaida itamadai yarinyar gidansuba wani mutuncine da suba babban abin tashin hankalin tsananin bin bokaye da sukeyi.

Usman ba laifi yana kautatawa Mama,bakin ƙarfinshi,Saidai tunda ya Auri zubaida labari ya canza yanzu Mama tana kwasar azabarta da baƙin ciki,dan zubaida ta mallake Usman sai abinda tace yakeyi,yanzu haka ta hanashi kawo abincin kirki,saidai kullun  yakawo mata drinks da wani abu suci.

Mamace zaune cikin baranda tana hura wuta,Nusaiba tana gefe da wani cikin Zubaida ta kirata"ke Nusaiba zonan"

Nusaiba ta taƙarƙara ta tashi tace"gani" saboda mugun tsoronta takeji,dan farko taso tayi mata abinda takema Saudat,tasameta ta laƙafa mata mugun duka saida akayi mata ɗaurin ƙugu.

"ke dan Uwarki haka ake shara,to wallahi saikin canzata"

Usman ya shigo gidan,da leda a hannunshi ya kalli Zubaida ya miƙa mata,sannan yaje ya gaida Mama,Mama bata da wata magana yanzu,dan zubaida ta sa Usman baya yi ma Mama biyayya datayi magana zai gaya mata ba haka bane.

Buɗe ledar tayi ta naman kazane da kwalbar lemo pepsi,buɗewa tayi ta faracin naman kaɗan taci taji ta ƙoshi,su Mama suna kallonta sai haɗiyar yawu suke,Zubaida ta miƙe ta ɗauko waya ta kira ƙanwarta,tace tazo ta anshi sauran Naman dan ita ta ƙoshi.

Haka take masu taci gabansu ta hanasu,saura ta ɗauka ta ba ƙannan ta sukai gida.

              ****
"Ammi natafi Office saidai daga can inson wucewa gdan Mami"

Ammi ta kalleta haryau takasa gane kan Saudat,kaɗa kai tayi tace"shikenan ki gaida man ita Amma kidawo da wuri"

Saudat ta fice tabar gidan,tunda taje aiki gaba ɗaya takasa gane kanta kaɗan-kaɗan sai gabanta ya faɗi,haka ta samu tagama aikin ta nufi gidan Mami.

Acan suka haɗe da Areef batayi tunanin ganinshiba,gabanta yana faɗuwa ta zauna tagaida Mami,Mami ta amsa tare da faɗin"wai ke bakida lafiya ne?"

Saudat bata bata amsaba,ta juya ta gaida Areef Ya amsa yana nazarinta tabbas yasan tarame,Mami tace"bakijin abinda nake cewa ne?"

"Mami nifa lafiyata lau"

Areef yace"Mami kibarta tun yaushe ake fama da ita"

Saudat ta kalleshi ta miƙe ta ɗauki plate,a can kitchen tasamu damar typing ɗin massge _zuciyata tana tare dakai ko yaushe,duk lokacin dana ganka farin ciki yakan ƙara baiyana a rayuwata_ ta sabon layin da tasaya tana zama ta tura saƙin.

STORY CONTINUES BELOW

Ta sa abinci a plate"wai Mami yaushe zamuje duba su Ilham ne?"

Daidai lokacin wayarshi tayi ƙara,saƙo ya shigo,Mami tace "to ni zan fidda maku ranai ne"

Saudat ta jawo wayarta tasakata airplane mode,ta faracin Abincin,Areef yayiwa   wayarshi zuru yana karanta saƙon,bai damuba dan yayi tunanin wrong ne aka samu wajan turawa.

Ya kalli Mami "kawai ashirya nextweek aje katsina"

Saudat ta ture plate ɗin gabanta,"zakaje ne Yaya?"

Ya kalleta yana ɗan yamutsa fuska"inason hakan"

Komawa tayi ta maida plate kitchen daidai zata zauna saƙon ya ƙara shigo mashi  _idan rayuwa zata tafi a haka,baƙin ciki zai cigaba a tawa rayuwar,sabda rashinka a kusa dani_

Areef ya karanta ya fara neman Number saidai baya samu,ya ƙara shiga massge yana karanta saƙon,ya ƙara kiran Number amma still bata shiga.

Saudat tana kallonshi ta kauda kai,ya juyo ya kalleta,saidai babu waya hannunta Mamaki yake wacece wanan.

Saudat ta mike"Mami zan tafi gida Ammi tace kada in daɗe?"

Mami tace "ki gaidata ai nima zan shigo gobe"

Areef yana kallonta,ta juyo ta kalleshi,taɗan saki fuska "Yaya natafi"

"ok agaida Father zanzo da daddre in ganshi"

Tunda Saudt ta koma gida,take tunanin ta wace hanya kuma zata ƙara bullo mashi ta ɗauki wayarta ta tura mashi _ko da baka kusa dani to zuciyata tana kusa dakai dafatan zakayi marece lafiya_

Areef kam take yafara tunanin,dakunason sanin mai turo mashi wannan saƙonnin,kwance yake yana tunanin inama ace Saudatce take mashi irin wannan saƙonnin,zumbur yayi ya miƙe saboda tunawa dayayi yace mata zaije gidan.

Wanka yayi yasa shadda dark brown sai sheƙi take,falon ya fito yasamu Ni'ima tana kallo.

"ina zakaje"
"zanje gidan Ammi ne"Ni'ima ta kalleshi,gidan Ammi ne sai anyi gayu haka,sai lokacin ya kalli kanshi yayi dariya"to yanzu wanan shine gayun"

Ni'ima ta turo baki"ai gani nayi kamar zaka zance"

"Nidai natafi"cikin zuciyarshi kuma yace ai zancenma zani.
Yafito ya shiga mota,ya na tafiya ahankali,wayarshi tayi ƙara massge ya shigo,hakann yakeson sanin miye saƙon ya ƙunsa ya buɗe _zuciyata tana ƙara jin kusancinta da taka,idanuna suna mararin ganinka,hankalina ya ɓata garin son ganinka_

Baisan lokacin da yayi murmushiba,ya ƙara karantawa ya jefa wayar gefe,saida yaje gidan ya ɗauka.

Zaune take tasa lace light purple ɗinkin doguwar riga tayi kyau sosai,Sallama yayi Ammi ta amsa Sultan ya ruga yana mashi Oyoƴo.

Ɗagashi yayi sama yana jijjigashi,suna dariya,Sultan yace"Uncle in baka labari"

Saudat tayi saurin ɗagowa tace "Allah idan kayi maganata saina zaneka,sarkin surutu kawai"

Su duka sukayi dariya,Areef yayi dariya"kaizo bani labarin ai kanason gobe muje park ko"

Ya ɗaga kai,yasa hannu ya toshe baki"labarin Momy nefa"

Saudat ta tashi zaune,tana kallonsu,kanta babu ɗan kwali,cikin zuciyarshi yace,itadai batason kitso.

Ammi tace"aimu yanzu bamuda ikon yin abu a gidan nan"

Saudat tace"haka jiya saida yagaya ma Dady na shigar mashi ɗaki,Allah sainayi maganinka"

Zaiyi magana saƙo yashigo wayarshi  _kaine hasken rayuwata,duk lokacin dana ganka idanuna sukan makance bana ganin komi saikai,ka kasance dani akoda yaushe_

Tana gani ya tillar da wayar kan kujera ya kama hannun Sultan yaje dashi mota ya ɗauko mashi ledar sweet suka dawo.
Saudat tace"zoka bani insha kaji yaro na" Sultan yaƙi bata ta ce"mun ɓata daga yau"

Areef yayi mashi wayo ya ɗauki guda ya kalleta,"oya takam"ya wurga mata da kyal ta caɓe,ta ɗauka tana sha "kai Amma chocolate ɗin very sweet,a karaman"

Areef yayi dariya"so kike yatada mamu yaƙi kenan"

Tayi dariya,Ammi tace"to ni abani"
Ya juya yana wa sultan wayo, wayarshi tayi ƙara,yasa hannu ya ɗauka  _any thing from you is sweet_

Yaɗan zaro ido,ya kalli Ammi,Ammi tace lafiya,yamaida hankalinshi kan Saudat,dojewa tayi kamar bata saniba,ya dai-dai ta nutsuwarshi,suka cigaba da fira.

Saudat tace"Yaya zakaci Abinci?"
"nop daga gida nake" Ammi tace "ya jikin Ni'imar" "taji Sauƙi sosai"

Saudat tace"Allah sarki Ni'ima,kwana biyu"

Ammi tace tazo last week bakinan,Saudat tace "Ayya"

Areef yace"Yayi bacci bari in tashi in tafi"

Wayarshi tayi ƙara,yakasa dubawa,saidai ya Kalli Saudat,yaƴi masu Ammi bankwana ya fita.

Ko mota bai shigaba,ya tsaya duba massge ɗin  _i will miss you untill next time we meet_
*AUNTY HALILOSS*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


*DEDICATION:self love nima na sadaukar da page ma kaina,saboda yabon da kukeman nima na yabi kaina❤❤❤*


29


Saudat ta miƙe,ta ɗauki Sultan suka shige ɗaki,tayi shirin bacci,saƙonnin ta ƙara tura mashi masu zafi sweet dreams and gud night massges.


Areef ya kwanta yana buɗawa,sai zuciyarshi tabashi Saudatce ɗayan ɓangaran zuciyarshi kuwa tayi mashi gardama sabida duk lokacin da saƙon zai shigo wayar to yana ganin babu waya a tare da ita.


Nan ya kwanta da shirin gobe zai je abincika mashi mai Number a Office ɗin 9mobile, Ni'ima ta shigo ɗakin tasa kayan bacci,Kallonshi tayi tace"Dear bakayi bacci ba" gaba ɗaya hankalin Areef yanakan wayarshi,baiji shigowarta ba.


ta  zauna tana kallonshi,wayar ta ƙarayin ƙara,ya jawo ya duba  _hop we will be together at this time some day,sleep well My Habibi_


Murmushi Areef yayi ya gyara kwanciyarshi,sai lokacin yaga Ni'ima tan kallonshi,abinka ga Namiji dole saika gane rashin gaskiyarshi,aje wayar yayi ya miƙa mata hannu,alamar tazo,Ni'ima ta fashe da kuka"yanzu kaje zancanka kadawo,shine kuma kazauna kana chart,har na shigo ɗakin baka sani ba"+


Lallashinta ya kamayi"nifa bazance naje ba"


"Allah bazan taɓa yadda ba,taya zakayi wanka kafita,wallahi kwana biyu ka canza man da ba haka kake ba" Areef ya kwantar da ita kan jikinshi yana lallashinta saidai yadda take sonshi bata iya ignoring saƙonnin da yake bata ba


          *****

Areef kuwa yana tashi da safe yayi shirin fita Office,saidai ba can ya nufa ba,9mobile office yatafi,yana shiga ya miƙa masu Number yace aduba mashi details akan Number.


Lokaci kaɗan Matar ta kalleshi "Oga this Number,is an female owner,civil savan,with male nex of Kin"


Areef ya  matsa ya kalli matar"plzz Open the details for me"


"ok sir"


" Name:Saudat Mu'azzam,Occption :Civil S,nex of kin Sultan Usman"


Areef yaji wata faɗƴwar gaba,ga wani farin ciki dake zuciyarshi,wai Saudat take mashi irin waɗan nan massges ɗin,Kallan matar yayi"ok thank you have a nice day"ya fito yaja motar ya nufi Office.


Yana shiga Office ya tadda Zaks har ya zauna,ya kalleshi"kai yaro yaufa game is Over finally nagano tana sona"


Zaks ya kalleshi"ai nagaya maka,duk abinda takeyi sonkane cikin zuciyarta"


"amma Zaks inason sanin asalin son da takeman"


Bai ida magana ba saƙo ya shigo wayarshi tayi ring,ya ɗauka ya duba  _ mornng Habibi,Kullum soyayyarka tana ƙara zama a zuciyata,idanuwa na zuna kewar ganinka,ina maka fatan Alkhairi_


Areef yayi dariya ya shiga raply _gaba ɗaya rayuwata tana cikin mararin ganin masoyiya irinki,inason damun daman kasan cewa dake,plzz kibani damar sanin ki mana_


Wani ihu Saudat ta saki ganin saƙon,cikin Sauri takira Billy shantaly taga ya mata,Billy tace"kimai raply kibarshi ku haɗu Amma koda zaku haɗu a park zakice mashi"


Haka Saudat ta zauna tana tura mashi massge shima ya maida mata,tofa wunin ranai Areef da Saudat abinda suka wuniyi kenan.


Yana tashi gada Office gidan Ammi ya wuce saidai yayi rashin Sa'a tana Wajan Aiki,ko zama baiyiba ya cewa Ammi zai dawo anjima.


Marece nayi sai gashi yadawo,lokacin tana toilet tana watsa ruwa sbd dawowarta kenan duk ta gaji,ta shirya ta fito falon,tana ma Ammi sannuda gida.


Ta kalli Areef "Yaya yaushe kazo?"

Yaɗan kaɗa kai"na ɗan jima sai dai banga Sultan ɗinba"


"ai yayi bacci"tana zama saƙo ya shigo wayarshi, _ina farin ciki duk lokacin danaga fara'a a fuskar_


Areef ya kalleta yana mamaki shidai baiga waya hannuntaba to ya akaƴi kodai ba ita bace?hankalinshi ya dan tashi Ammi ta kalleshi"yaushe zakuje katsina?"


"ranar Asabar sbd ranar sukansu basuda lectures"


Saudat tace"aikam inda inter view ranar,saidai bari inga idan zan ɗaga tunda ba ranar za'a fidda program ɗinba"


Areef ya kafeta da ido,ganin zata kalleshi yasashi kaudakai,ya miƙe zai tafi wayarshi ta ƙara ruru,take ya juyo ya kalleta,ta kaudakai,ya koma ya zauna  yana typing masage a wayarshi _A ranar nikaina zan kasance cikin farin ciki, plzz kiceman gobe mana_


Ya miƙe yafice daga gidan Saudat takoma ɗaki takira Billy shantali,ta bata labari sukayi dariya,Billy tace"wallhi ya ƙagaya yaga ko wacece,kawai bari ince mashi mu haɗu gobe sai kije wajan"


"a'a saidai muje tare"

"shikenan ba damuwa"


Abinda Areef baisani ba shine,sim biyune akayi mata activating,ɗaya yana hannun Billy ɗaya yana wajanta,Saudat akwai wata ƙaramar na'ura dake jikinta,a Office ɗinsu ta ɗaukota,sun Amfani da itane wajan ɗauko labarun sirri,idan yana tare da ita to Billy tanajin abinda akeyi,ita take turo mashi saƙo shiyasa baya ganin Saudat tana latsa waya.

Ita kuwa Saudat batada labarin ya binciko itace mamallakiyar Number.


             *****

Washe gari  Areef sun shirya haɗuwar su a Unique park,ƙarfe biyar  na marece.


Areef gayu yayi mata sosai,hakan ta faru a ɓangaran Saudat,wani voil lace ne ta saka ɗinkin riga da sket,Bilƙy ta kalleta "plzzz dan Allah kidaina rawar jikin nan"


Saudat ta dafe ƙirji,"wallahi dan bakiji yadda nakejiba"


Ƙarfe huɗu da rabi suka isa wajan,zama suka gaba ɗaya hankalinta baya tare da ita,dake wa kawai take,basu jima ba sukaga shigowarshi.


Saudat ta zaro ido"wallhi gaya nan"


Bily tace"dan Allah kada ki ɓata mana plan,kada yagane akwai fargaba a tare dake kiyi kamar yadda muka shirya"


Yana tsaye jingine da mota,ya fiddo waya yana tura saƙo Saudat ta miƙe ta samu waje ta tsaya,Yayi mata massge yana wajan,taya mashi inda take.


Ta gaban Bily ya wuce,tsaye yasameta tana juya baya tana zare ido saboda ƙamshin turaran shi.


Gabanta yaje ya tsaya yana kallonta,jiyake kamar yayi hugging ɗinta,kallonta yayi,tayi saurin nemo natsuwa tasawa kanta.


Takardar hannunshi ya miƙa mata,ta ansa ta duba,details ɗin layinta ne datake mashi massge tagani.


Ta ɗago ta kalleshi,hawaye suka zubo mata,yaji ba daɗi"to ya akayi kike ku?"


"Allah Yaya inasonka,wallahi nayi nadamar abinda nayi,Wallhi kaine kawai a zuciyata,dan Allah kada kace baka sona,zan iya rasa rayuwata,gaba ɗaya zuciyata kai take muradi"tana maganai tana kuka.


Areef wani,daɗi ne cikin ranshi,yama rasa miye zaiyi,yau jiyake duk wani baƙin cikin rayuwarshi babu shi,yau gashi ga Saudat tana faɗin tanasonshi.


Cikin sauri ya kalleta yana zaro ido"haba wannan wace irin magana ce,kina tunanin yanzu zan ƙara kallan wata mace batan Mata ta,so ɗayane nayi maki shi,na rasashi a wajanki,bayan lokacin kuma nayi kyautar shi ga wata babu wani gurbin daya rage dan zaman wata a zuciya ta"


Yana maganai Saudat tana ja da baya,tasa hannu tana rufe kunnuwanta"dan Allah kadaina faɗi,wallhi bansan jin haka" ja take da baya kamar tanajin tsoron wani abu,Areef kam kallonta yake yadda ta fita haiyacinta.


Saudat ta sauke ɗayan hannunta daga saman kunnanta tana dafe ƙirjinta dan yadda takeji zuciyarta kamar zata tsaye,da kyal take faɗin "bansan jiiiiii""


Tayi maganar da karfi,tana sulalewa ƙasa,Ai Areef baisan lokacin daya matsa dan tarota ba,sai dai kafin ya isa harta faɗi.


Maganr da Billy ta jiyo tayi saurin nufosu,Areef yana jijjigata,Bily ta ce"Saudattt"gaba ɗayansu hankalinsu yatashi,badai kamar Areef,shina ɗin sunanta yake kira da ƙarfi"Saudatttt"


Amma gaba ɗaya ba lumfashi tare da ita,da Sauri Areef ya sungumeta,yayi hanyar mota da ita........
*AUNTY HALILOSS*

WA NAKE AURE?
                NA
     *Aunty Haliloss*

*👑ROYAL WRITERS ASSOCIATION👑*

Wattpad @AuntyHaliloss

*DEDICATION:INAJIN DAƊIN COMMNTS ƊINKU*
_Ummu Aness_
_mamansadiq💗💗_
_Mamn bilal_
_Aunty faty_
_Halima musa_
_Oum Elham_  ILY WUJIGA-WUJIGA.

30

Haka Bily tabishi a baya cikin tashin hankali,a gidan baya yasakata Bily ta shiga,Areef ya gewaya ya zauna yaja mota,gudu kawai yake sheƙawa,yana tuƙi yana waiwayota,dan ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba.

Wata Asibity mai zaman kanta dake kusa ya shiga yayi parking,ma'aikata suka fito domin taimaka masu saidai gaba ɗaya Areef bai Saurare suba,ya ɗauketa yayi cikin receiption ɗin da ita,basu tsaya buɗe file ba akayi Office ɗin Dr da Saudat,Billy ce ta tsaya ta buɗe mata file.+

Take aka fara dubata,ɗaki aka canza mata,cikin lokaci likitan yafara dubata,Bily hankalinta ya tashi,gaƴa an hanata shiga,Areef kam yace dole sai ya shiga.

Dr. da ma'aikatan jiya suka cigaba da dubata tare da nemo lumfashinta,ya cire abin dake Kunnanshi ya kalli Areef "zuciyarta ce take bugawa da karfi hakan yayi sana diyar lumfashinta yayi ƙasa"

Areef yace"plzz Dr. Kataimaka man,ka ceto rayuwarta"
Dr ya je Office ɗinshi yadawo dawasu Allurai,ya zubasu a cikin ƙarun ruwan da suke mata.

Ya kalli Areef yace"insha Allah zata dawo haiyacinta within a shot period of time"

Areef yayi mashi godiya,yafita,yana fita Bily ta shigo,Areef yana gefen gadon yana kallonta,hannu yasa ya riƙo hannunta sosai ya riƙeshi,yanajin tashi zuciyar tana bugawa.

Billy tace"plzz ka kira Amminta ka gaya mata"

Sai lokacin ya kalleta,yanason sanin wacece ita,saidai babu lokacin hakan,Areef ya saka hannu Aljihu,sai lokacin ya tuna yabar wayar a mota.

Bily tace"kayi Amfani da tawa"

Ya ansa ya saka Number Ammi,bajimawa ta ɗauka,Areef yace"Ammi gamu a Asibity Saudat ba lafiya,batasan ina kanta yakeba"

Hankalin Ammi yatashi,take ta tambayeshi wace Asibity,yagaya mata.

Ya miƙa mata wayarta,ya jingina da bango yana dafe kai,Bily ta kalleshi"ka kwantar da hankalinka zata farfaɗo"

"taya zan kwantar da hankalina,bayan kina ganin rayuwata zata tafi ta barni,wallahi ina santa,nakasa gane gaskiyar Saudat akan san da take man"

Bily ta ja kujera ta zauna,ta kalli Areef tayi murmushi,take tafara bashi labari tun daga sunanta dakuma mu'amularsu da Saudat,Areef wasu hawaye suka gangaro mashi"yanzu Saudat ce takeman irin wannan son?"
"tabbas hakane,nasan a yanzu Saudat tafika..."

Hannu ya ɗaga mata ya matsa bakin gadon da take"plzzz ki tashi Allah ina sonki,ke kaɗai ce a cikin zuciyata,wasa nake maki"yana maganai,ya riƙo hannunta guda wadda babu drip ɗin,yakai bakinshi tight and lov pick yayi mata ya ɗago yana kallonta,ya ƙara kissing ɗin hannun"i really love you,an i mean it,i cant live without you, plzz weak up"

Areef ya ɗago ya kalli Bily "dan Allah idan Ammi tazo kice bakisan miya sameta ba kawai tace tanajin gabanta na faɗuwa,saidai kikaga ta faɗi"

Billy taɗaga mashikai,tana kallon yadda shikanshi ya rikice,yake kalamai akan wadda batasanma yanayi ba.

Sunan saiga Ammi da Dady sun shigo,bakin gadon suka nufa suna tambayar halin da take ciki,Dady ya kalli Areef"ina Dr. yake"

"yanzu ya fita yace zata farfaɗo bada jimawa ba" Dady ya fita yaje Office ɗin Dr. sai gashi sun dawo tare.

STORY CONTINUES BELOW

Suna shigowane Saudat ta fara motsa ƙafafunta,tana son ɗaga hannuwanta,Ammi,Dady,Bily,Dr. gaba ɗaya suka gewayeta,Areef kam riƙo hannunta yayi.

Saudat ta fara motsa bakinta tana buɗe idonta,ta fisge hannunta tana rufe kunnan ta,ta na faɗin"bansan jiiii"da ƙarfi tayi maganai.

Dady ya kalli Dr. ,Dr yafara kiran sunanta,Saudat ta ɗago tana kallonsu,wasu hawaye suna zubo mata,Saudat ta samu ta bufe bakinta tana faɗin"Ammi"

Ammi ta matsa ta riƙe ɗayan hannunta,tana mata sannu,Ƙoƙarin miƙewa take,Dr. Yace ta kwanta,take ya kira ma'aikata suka kawo mashi kayan aiki,ya cigaba da dubata,allura ya ƙarayi mata ya buƙaci ruwa,aka buɗe ƙaramin firij ɗin dake kefe,Ammi ta bata maganin daya basu.

Su duka suna gefe,wata Nurse ta shiho da wata na'ura,take Dr ƴace su fita,Areef ne kawai yaja gefe,ya tsaya,Dr ya aza wani abu a ƙirjinta,ya kunna cumputer ɗin,nan yake ganin yanayin bugun zuciyarta.

Areef ya kalli Dr.sabda yana ganin Abinda ke faruwa,ya zaro ido,likitan yace"ya rage bugawa amma har yanzu bai dai-dai taba.

Lokacin bacci ya ɗauke Saudat,sabd Allurar baccin daya haɗa mata,Su duka suka fita,Dr.ya kira Areef da Dady Office ɗinsu,nan yafarayi masu bayani.

"yarinyarku tanada damuwa and har abun ya taɓa zuciyarta,amma wannan lokacin zai iya yiwuwa an faɗi mata magana mai zafi idan kukayi lura da kalaman data farko dasu"

Dady yace"Allah yasawake,Amma minene abinyi?"

"zata samu lafiya,insha Allah,nasan idan ta tashi daga baccin zata koma normal"

Godiya sukayi mashi suka fito,tunda suka fito Dady da Ammi suke tattaunawa Ammi tace"ba tun yau nake tambayar damuwar yarinyarnan ba,amma taƙi gayaman,yanzu ga inda ta kaita,zata halaka rayuwarta"

Areef kam ɗakin yakoma,lokacin Bily ta tafi ta ɗauko motar da sukaje da ita park ɗin,Areef yazauna kujerara gefen gadon,sai kallonta yake,ƴafarajin tausayinta sabd shina kanshi yasan zafin daya shiga lokacin data ƙishi.

Sunanan saiga Muhsin shida Mami sunzo,Mami ma hankalinta ya tashi tana tunanin to wane irin ciwone yakama ɗiyar tata,Muhsin ya kalli Areef yace"Brox amma ta farka ko?"

"Eh yanzu Allurar bacci ce akayi mata" Haka suka zauna sunata jimamin Abin Areef kam shidai bakajin bakinshi saboda yasan takan abin.

Tsawan awa ɗaya da rabi sanann ta tashi daga baccin,duk sukayi mata sannu,Ammi ta ɗauko farfesun da takoma tayo mata a gida,a plate ta zuba ta miƙa mata.

Tashi tayi jiki babu kwari"Ammi bari inyi sallah"
Ammi zata taimaka mata tace tabari zata iya,Taje tayo Alwala tadawo taƴi sallah,sosai tayi Addu'a tana neman samun dakewa dakuma juriya,take taji tasamu natsuwa a zuciyarta, *Allahu galibun Alakulli amrin* take ta karantawa a zuciyarta,Ammi tace"ki koma kan gadon."

"Ammi naji Sauƙi,zan iya zama,ina Dady"

"sunje masallaci yanzu zasu dawo"

Ammi ta miƙa mata plate ɗin,plastic chair ɗin dake wajan ta zauna,taɗan faracin farfesun,har lokacin Addu'a take karantowa,wata nutsuwa ke ƙara shigarta.

Tana cin farfesun suka shigo ɗakin,Duk kanta sukayo suna tambayarta yajiki,Saudat ta yamutsa fuska taɗanyi murnushi"na warke"

Sadiq yace"dama farfesu kikazo sha"

Saudat ta kalli Dadi tace"Dady kaga dai abinda yace,yana nufin ciwan ƙarya nike"

Duk sukayi dariya,shidai Areef bayada abin cewa,saidai hankalinshi ya kwanta ganin ta samu lafiya.

Mami tace"Muhsin muje gida ko"

Ammi tace"tun yanzu zaku tafi?"

"eh Pappa baya gari,kuma yana hanyar dawowa"
"to shikenan ace muna mashi sannu da hanya"

STORY CONTINUES BELOW

Wayar Areef dake aljihunshi tayi ƙara,yasa hannu ya ɗauko Ni'ima yagaji ɗauka yayi ya kara a kunnai"hello"

"Alhamdllh lafiya lau, a'a banga kiranbane,Nop muna Asibity ne Saudat ce ba lafiya,Amma da sauƙi"

Daga fayan ɓangaran aka fara masifa,saboda dama taga shirin da yayi kafin ya fita,Areef yajima baice komiba,sanann yace"ki jirani inzo gidan"yadda yake maganai kasan ranshi a ɓace yake.

Saudat kam ko a jikinta,dan ko inda yake bata kalla ba,shikam so yake yaga sun haɗa ido,Saudat ta miƙe ta koma kan gadon.

"Ammi ku kira Dr. dan bazan kwana ananba"

Sai lokacin Areef yayi magana"dole zaki kwana baki ganin jikinki ba kwari"

Shiru tayi mashi,Dady ya shigo,sabd yafita tare dasu Mami,saidai yajima waje,Ammi tace"to gatanan wai saita tafi gida yau"

Dady baice komiba ya nemi kujera ya zauna,zamnshi ba wuya Pappa yakirashi waya,"Hello"

"wane Room ne ina cikin Asibitin?"

"bari infito" Dady ya fita bajimawa suka shigo tare da Pappa,duka suka gaidashi,Pappa ya tsaya wajan Areef,ya miƙa mashi Hannu,yana hararar shi,Areef ya maida hannu baya"minayi Pappa?"

"kamanta ko?"

Areef yafara sosa ƙeya,Pappa ya juya ya kalli Dady yace"yau kwana na biyu da tafiya Abuja amma yaron nan ko flashing balle kira"

Ammi tayi dariya,Areef yace"yi haƙuri Pappa nah,Allah aiki ne"

"aiba yanzu ka fara aikinba"

Dady yace"kaidai yaran yanxu ka kallesu kawai" Pappa yasaba indai yayi tafiya to Areef arana saiya kirani yakai so ukku,shikam Areef gaba ɗaya ya manta ma sabda Massges ɗin da suke exchangin da Saudat.

"Pappa bakace kayi haƙuri ba"
"shikenan nayi haƙuri"yana magana yana zuwa bakin gadon da Saudat take,hannu yasa ya dafa kanta,ya taɓa wuyanta,ya kalli Ammi yace"lafiƴarta lau ai"

Ammi tace"dan bakaga yadda muka sameta ba"

Pappa ya kalli "Dady nizan tafi"

Ammi cikin zuciyarta tace har yanzu Pappa yanada matsala,ace har yanzu yaƙi hakura daga zuwanshi yace zai tafi,har yana cewa wai lafiyarta lau.

Pappa kam koda yaga Saudat yasan batada lafiya,yayi hakanne kawai don kada taga kamar ya kulata,Dady yace"Ai nima yanzu zan tafi,ta matsane ita bazata keana anan ba"

Pappa ya juyo ya kalleta"Kwana biyu zatayi,muje Office ɗin Dr. ɗin" pappa yasan batada lafiya,kuma dole tasamu kulawa sosai shiyasa ya hana a sallameta.

Areef baibar Asibityn ba sai ƙarfe goma saura,yana isa gidan ranshi a ɓace dan maganganun da Ni'ima tagaya mashi sun mashi zafi,direct ɗakinshi ya nufa,yayi kwanka yabi lafiyar gado,take yacigaba da tunani.

Saudat kuwa bacci ya gagari idonta,tashi tayi tayo Alwala tazo ta yi nafila,ta ɗaga hannu tana roƙon Allah sauƙi akan lamarin da take ciki.

              *****
Washe gari ƙarfe tara Areef yazo Asbitƴn da ledoji a hannunshu, tins abubuwa yasawo masu a super market,Ammi ta amsa tace"ai Dr ɗinma ya sallamemu amma yace mujira,wanann ruwan ya ƙare sannan.

Haka Areef yakoma kan kukera yazauna,suna ɗan fira da Ammi,Saudat kam dama tin shigowarshi ta rufe idonta.

Sallama akayi aka shigo,Billy ce agaba sai maza biyu da wata mace,Billy ta shigo dasu,suka gaisa tare da tambayar yamai jiki.

"Ammi tace da Sauki Bily ya aikin?"

"Alhamdllh,yanzuma ƴan Office ɗinmune sukazo dubata"

Ammi taji daɗi sosai tayi masu godiya,suka Matsa bakin gadon Saudat ta buɗe idonta,sukayi mata ya jiki ta amsa Dr.Moh'd yace"ashe bakiji daɗiba,sai yanzu Billy tace wajanki takeson zuwa tanason permition"

STORY CONTINUES BELOW

Daudat tace"wallahi kuwa Amma naji sauki ai"

Daudat ta tashi xaune takalli Ammi tace"Ammi wannan shine General manager ɗinmu,ta nuna sauran ta faɗi sunayansu,sukuma Abokan aiki ne"

Ammi tace "Allah sarki mungde sosai"

Areef yana gefe yana kallon yadda Dr.Moh'd yake kallon Saudat zuciyarshi kamar ta tsage dan Haushi,Sunɗan jima Dr.Moh'd yace"muke ko"
Yana magana,yasa hannu Aljihu ya aje ma Sauda kuɗi gefen gadon,tana a'a amma ya aje.

Sukayi bankwana,ya miƙawa Areef hannu sukaƴi musabaha,ya juyo ya kalli Bily yace"anan zamu barki kiyi jiyar abokiyar gulmarki"

Duka sukayi dariya Ammi tace"ashe gulma sukeyi"

Dr.yace"haka suke Mama basuda aiki sai gulma dasun zauna,shiyasa na raba masu Office amma duk da haka ɗaya saita tadda ɗaya"

Duka akayi dariya,ɗayan yace"badai kamar idan sukaga bani wajan"

Bilƙy tace"aikai ɗansa ido ne"

Haka sukayi dariya,suka tafi Ammi  ta kalli Biƙƙy tace"kunyi sa'ar GM akwai barkonci"

"eh amma idan ya ɗaure duka bamuji da daɗi"

Areef ya matsa baikin gadon da Saudat take,tana ganinshi tayi saurin rufe ido,shi abinma dariya yabata,ya kalli Ammi yace"bari inkira dr. Yacire mata,don yaƙare ruwan.

Areef yafita yakira Dr.aka cire mata,take ya ƙara nusar dasu kan arage gayamata hurters words.

Gida sukayo strainght,Areef yana ajesu yace za leƙa Office,ya tafi,Ammi kam kitchen ta shiga domin girka masu wani Abu,ya rage daga Bily sai Saudat a ɗakin.

Saudat tace"nagaya maki,Yaya baya sona,wannan shine karo na biyu daya faɗiman"tana maganai tana goge hawayenta.

Bily takoma kusa da ita"wallahi inada tabbacin soyayar da Areef yake maki,komi lokacine"

Saudat tace"kitayani Addu'a Allah ya fiddaman bala'in danakeji"

Ita kanta Bily ta tausayama ƙawarta,saidai kuma tasan Areef yana sonta yadda mai tunani baya iya misaltawa.

         *****
Tunda wannan Abu yafaru Saudat ta rage mashi magana,iyakarta dashi gaisuwa,ta fara nuna Almun kamar ta haƙura dashi,Amma ita kaɗa tasan zafin da takeji,badai kamar idan yazo gidan.

Yau Saudat bata da aiki,amma saboda suyi fira taje Office ɗin duk da yanzu Office ɗin bayayi mata daɗi saboda Dr.Moh'd dake matsa mata,har abokan Aikinsu sun gane,wani lokaci ita kanta Oga suke ce mata,sabd GM yanasonta,saidai kawai tayi dariya.

Suna zaune Dr.Mohd yazo,ya zauna kan kujerar dake gefenta,zaiyi magana Billy tace"kodai intashine"

"a'a yi zamnki,zabata wani aikine"

Ya fiddo ya miƙa mata wasu takardu,"zakiyi fira da Ministan tsaro ne"

Saudat tace"kai Oga aikin nan zaiman nauyi dayawa"

Billy tace"haba wane nauyi,kinyi magana da Governor balle"

Saudat ta ɗauki takardun"karfe nawane?"

"gobe ƙarfe goma nasafe"

Ta miƙe tayi masu bankwana,yasan haka takeyi dan batason diguwar magana tana haɗasu.

Koda ta kima gida,a falo ta tadda Areef,yana shan coffe ya ɗago ya kalleta,suka haɗa ido,tace"yaya ina yini?"

"ya aikin"

"lafiya lau tace ta shige ɗaki,Ammi ta kirata"wai Areef yace gobe zakuje katsina wajan su Khairat ɗin?"

Saudat ta kalleshi,taɗan haɗe rai,"Ammi gaskiya bandani,banida damar zuwa"

Ammi tace"to shikenan,amma su gobe zasuje"

Areef ya aje cup ɗin dake hannunshi yana kallonta,yadda take magana,cikin zuciyarshi yayi darya.

Saudat ta juya tana faɗin "Allah ya tsare hanya"ta shigewarta ɗaki.

        ****
Washe gari saudat ta shirya tayi ficewarta Office,tana zuwa ƙofar falon shikuma yazo ɗaukar Ammi dasbd su duka zasuje.

a bakin ƙofar falon ya tsaya,ya kalleta,tace"ina kwana"

"yanzu su Ilham ɗinne bazakije ki duba ba"

"zanje amma yau inada program ne kuma life ne ba recording ba"

Tana maganai tana nufar ƙofar dole ya bata hanya tafita,wanann abu da Saudat ta farayi mashui yanzu yafara damunshi.
Saudat tayi fira da Comissioner with success and shikanshi ya bata lambar yabo,sabda yadda take aikinta,baibar Gidan redion ba saida ya ansa Number Saudat.

tana dawowa gidakam yafara damunta da waya,tun ranar yakasa haƙuri Saida ya nuna buƙatar soyayarshi,Saudat kam kasa bashi amsa tayi tadaice sai tayi tunani,sun jima suna waya yayi mata kwarjini sosai,hakan yasa bata iya wulaƙantashi.

Su Ammi kwansu guda suka dawo,ita kanta tayi missng zuwa ganin ƙannan nata.

Saudat ta zauna,tana ba Ammi labari,Ammi tace"ai mun fara sauraran shirin munayin nisa da gari shikenan"

Saudat ta miƙe"Ammi bari inje in samo abin motsa baki,anjima zanyi baƙi,ta faɗi maganar tana miƙewa.
*AUNTY HALILOSS CE*

WA NAKE AURE?
            NA
     *Aunty Haliloss*

*👑ROYAL WRITERS ASSOCIATION👑*

Wattpad
@AuntyHaliloss

31

Lokacin data dawo,bata tadda Areef ba harya fice,Donut,cakepizza da snacks masu yawa ta sawo,sai dai bata sawo drinks ba dan tasan akwai drinks a gidan.

Ana gama sallar magrib Saudat tayi wanka ta shirya cikin wani tsadadden lace,ɗinkin riga da skert saidai skert ɗin straight ne,batayi wata kwalliya ba.

Ta fito falon Ammi ta kalleta,Saudat ta kauda kai ta buɗe firij ta barshi a buɗe,Ammi tace"ya akayi?"

"so nike lemun su huce,sunyi ƙanƙara"

Ammi dai mamaki take tana tunanin baƙin da Saudat zatayi.

Ɗakin Dady Ammi ta nufa,take ta fara gaya mashi,dariyr manya yayi yace"kibarsu muga iya gudun ruwansu"

Dady ina gudun yar gidn jiya ta sake faruwa,wllhi nasan Areef yanason Saudat"

Sudat kam lokacin ya commisioner ya kirta,yace yana bakin gate ɗin,yayi horn aka buɗe maki y shigo da motar shi.

Saudat ta fito hrabr gidan,wajan motr t nif tan mshi sannu da zuwa,Commisioner ya kalleta yana amsawa,tare d faɗin"any wannan Saudat ɗin dana gani ce jiya"

Saudat taɗan zaro ido,tace"miyasa ka tambya?"

"saboda naga ta ƙaramn kyau"

Saudat tayi dariya tana ɗan kare fuskar ta da hannunta,shima ɗin dariya yake.

Dai-dai lokacin Areef ya sulala motarshi gefensu kaɗan,yana kallonsu,ya buɗe mota ya fito,wani yadine jikinshi dark green,yayi mashi kyau,ga sajan nan nashi kamar baƙo daga india,yayi kyau iyaka,zaka iya cewa shine ma yazo zancan,zuciyarshi tana bugawa da ƙarfi,yayi saurin kauda kai,Sai lokacin Commisioner ya lura da Areef,sallama yayi mashi yaɗan matsa ya miƙa mashi hannu.

Areef kam kamar kada ya amsa,Saudat kam batasan lokacin da yazo wajanba,tave"yaya Sannu da zuwa"

"yauwa" yace yana shirin shiga main part ɗin,Dady ya leƙo,hakan ya hana mashi shiga,ya tsaya bakin ƙofar,ya kalƙi Saudat.

"ya zakibar baƙo A tsaye ki shiga dashi ciki mana"

Saudat ta kalli Dady tace"to Dadƴ"tana maganai cikin jin kunya,Commission ya kalleshi cikin girmamawa,ya gaidashi,Dady ya sakar mashi fuska"a ka shiga zanzo mugaisa"

Areef wata mummunar faɗuwar gaba ta ziyarce shi,Dady kenan yasan da zuwan mutumin,Dady ya saci kllon Areef yace mashi"muje ciki"suka shiga suka tadda Ammi,saidai Areef hanklinshi baya tare dashi lokaci gida ya fita haiyacinshi,idanuwanshi sun kaɗa dag fari zuwa jaaa,Dady kam janshi da fira yake,shida Ammi Amma sun karantar hƙin da yaron nasu yake ciki.

Wajansu Saudat kuwa sun zauna,ta ɗauko snacks da drinks takawo msshi, commisioner yaɗansha drinks ɗin ya kalleta yaja lumfashi,Comnisioner shima ɗan gayu ne,saidai Babbane yana da yara shiddane amma matarshi ɗaya.yace"nasan dai basaina faɗa maki wani abu dangane daniba,saboda kin riga kinji"

"Hmmm taya zakace naji"

"au kin manta lokacin da kika tsareni da tambayoyi?

Saudat tayi dariya"ai lokacin bani kake gaya mawaba,masu saurare kakewa bayani"

Shima murmushi yayi"sunana Abubakar Imam,ni ɗan asalin garin kanone,Inada yara shidda da mata guda,da fatan zaki amince dani,Gaskiya Saudat inasonki,sannan kuma ba wasa yakawo niba inason jin wani abu daga wajanki"

Saudat ta lumfasa,ta farayi mashi bayaninta dakuma sanar dashi ta taɓayin Aure hada yaro guda,Commsioner yace"ai wannan byanin duk nasanshi,dan tun jiya na nemi sanin ki kuma anbani kyakykyawar sheda akanki"

Saudat tayi mamaki,wai har yayi bincike akanta,take sukaci gaba da magana,Saudat ta amince Mashi saboda tasan tarasa Areef abinda yafi mata tayi haƙuri tayi Auranta.

Haka sukayi fira saidai Dady baizo sun gaisaba,har yatafi,Saudat ta Zauna falon takira Billy tagaya mata yadda sukayi,Billy tace"miyasa kika amince mashi?"

"haba Bily koke mai bani shawarace,amma taya zan zauna zuciyata ta mutu kan mutumin da bai damudani ba"sukai mgana da Billy ta kwaso sauran kayan snaks ɗin ta taho part ɗinsu.

Har lokacin yananan,Ammi ta kalleta tace"yatafine,baƙon da ake ɓoyewa?"

Kunya Saudat taji,ta ɗan saci kallon Areef dake latsa waya,tace ta aje kayan,Dady ya kalleta"ina kikasan commsner?"

Saudat taɗan sosa ƙeya"a'a Dady i"

Dady yace"i mi?"

"jiyane da nayi program dashi shine yazo yau"

Ammi tayi dariya "Allah ya tabbatar mana da Alkahirin abun"

Dady yace"ba matsala i mutumin kirki ne,idan kunyi waya kice inason ganinshi"

Areef yayi saurin kallon Dady,yana ɗaɗɗaga ido,waishi a dole mai gaskiya"haba dady daga tayi fira dashi,shikenan sai yace yana sonta,haba dai,mi zakace mashi ko yazo,ita kuma daga haɗuwa jiya har ta Amince mashi yazo gida"

Saudat ta kalleshi,zuciyarta na bugawa,baya sonta amma yana shirin hanata  aure,wanda tana ganin ƙara tayi auran ko zata rabu da azabar sonshi dake damunta.

"Yaya kaifa kace,idan Mutun yana so yazo gida,saboda kada a zubda mutuncin family ɗinmu"

Dady yace "hakane"yana maganai yana miƙewa,Ammi ma tabishi.

Saudat ta miƙe"Yaya bari in kawo maka cake kaci"wani mugun kallo Areef yayi mata,wato ma wauran wani zata bashi,taje ta dawo da try ta aje,"nace maki in son cine"

Ta ɗauka ta buɗe,ta miƙa mashi yasa hannu ya riƙe hannunta,ya saka idanshi cikinnata,ya ɗan matsa hannun"kai yaya dafa zafi"

"to ai nace maki na ƙoshi"yana maganai idonshi yana kawo hawaye dakyal yasamu yana maidasu,Saudat ta juyar da kanta gefe,Sultan ya shigo da gudu yadawo daga tahfiz.

Areef yasaki hannun yana kallnshi,ya faɗa jininshi,ya kalli Saudat yace"Momy sabon Uncle ɗin da kikace yazo?"

Areef ya kalleta da sauri,dagabshi na faɗuwa,ya aje yaron ya miƙe ya samu ya fice,wajan motarshi ya nufa,tare da Sultan,ta ɗauko sweet ya bashi.

Ya shiga motar yaja,ikon Allahne yakai Areef gida Amma baya cikin haiyacinshi,gaba ɗaya hankalinshi a tashe yake.

Kan gado yafaɗa yana juyi,tare da tunani,miƙewa yayi yana faɗin" impossible i will never lose you again"dafe Kai yayi saboda juya mashi do Takei, sa Sauri yakoma  bakin gadon Ya zauna yajawo wayarshi Yana danna kira.
*Muje zuwa*

*MY MARYAMCY KIN MATSAMAN SAIDA NAYI TYPING YANZU😏😏*

*Aunty haliloss ce*

WA NAKE AURE?
             NA
     *Aunty Haliloss*

*👑ROYAL WRITERS ASSOCIATION👑*

Wattpad
@AuntyHaliloss

*KAI GASKIYA AREEF AKWAI FARIN JINI,SAUDAT KAM DUK TAUSAYINTA KUKEJI,KUDAINA SAURI LOKACI NA ZUWA,KUDAI KUCIGABA DA BANI GOYAN BAYANKU*

32

Yama rasa waye zai kira yaji sauƙin abinda yakeji,komawa yayi ya kwanta yana son samun natsuwa a zuciyarshi,Ni'ima ta shigo ɗakin,ta zauna tana mashi magana,sai takula da halin da yake ciki,ta kalleshi"lafiya kuwa?"hannunta ya kamo,yana faɗin"banida Lafiya ne,amma inajin sauƙi".

Sannu tayi mashi,amsa mata kawai yake,yana ɗan samun sauƙi a xuciyarshi take yafara tunanin idan yagayama Saudat soyayarshi,taƙi amincewa wane hali zan shiga,wannn dalilin yasa yafara yanke shawarar bazai gaya mataba,miƙewa yayi ya shiga toilet ya sakarwa kanshi shower.
Tun Saudat takoma ɗaki kuka kawai tasha abinta,dan tasan idan har ta auri wani to tabbas da soyayyar Yayanta zata tafi,tajima tana kuka sannn ta miƙe tayo Alwala tana gabatar da nafila,lokaci kaɗan tasamu nutsuwa har tasamu bacci ɓarawo ya kwasheta.+

Washe gari dataje Office Dr.Moh'd yatareta da maganar baƙon da tayi jiya,bata ɓoye mashi komi ba ta gaya mashi,yanson Saudat hakan yasa yayi mata fatan Alkhairi,dan yasan bazai iya haɗa son Abu guda da Commsioner ba kodan amintar dake tsakaninsu.

Yau tadawo gida duk tagaji,ta aje jikkar ta,ta zauna gefe Ammi tace"an gajine ƴata?"

"eh wallahi"

Ammi tace"yaushe raban da kije gidan Mami?"

"Ammi na kwana biyu"
"yakamata kije ki gaidota"
"yaushe Ammi?"

"yau mana" Saudat tace "kai ai nagaji,gobe naje kawai,tunda bana zuwa Office"

Ammi tace to,Haka suka wuni a gidan,duk wunin ranai Areef bai leƙa gidanba,gaba ɗaya tunda yadawo daga aiki,yana gida,Ni'ima kau gani take kamar rashin lafiyar gaskece sai tausayinshi takeji,ko dacan Areef babu ruwanshi da yawo wajan frnds,haka da yayi Aure,saida Saudat ta koma gidan shine yake ɗan fita,bayan ta koma gidan Ammi shima yakoma yawan zuwa gidan Ammi.

Da daddre Saudat waya tasha da Dear,sunan da take cemashi kenan,sun tattauna sosai kan maganar auransu,Commisoner yace"wallhi harna ƙagara inzo wajan Dady,saboda ayi magana,in maidoki gdana"

Saudat ta ɗanyi dariya,ita abinma jinshi take kamar wasa,sun jima suna waya sukayi bankwana ya kashe waya.

        ****
Da safe ƙarfe goma ta isa gidan Mami,Mami taji daɗin zuwanta,sun zauna sunata fira tana breakfst dan batayi ba ta taho,Mami tace"waini baki kawon baƙon yagaidani ba"

Saudat tayi dariya"kai Mami wai har Ammi ta gaya maki"

"eh mana"

Saudat taɗanja lumfashi tace"zaizo Mami" Mami ta kalleta yadda take maganai,tace"wallahi namayi tunanin kuna soyayya da Areef ne,sai kuma naji wani yazogida"

Kwata-kwata Saudat batayi,tunanin wannan maganai daga bakin Mami ba,daurewa tayi taɗan dai-daita nutsuwarta tace"ni dai Mami kiyi man Addu'a kawai"

Mami tace"a'a gayaman yadda akayi,kinsan fani mahaifiyarki ce,babu wanda zaki gayama matsalarki sama dani"

Saudat ta share hawaƴenta ta kalli Mami,ta bata labari duk yadda sukayi,ta ɗora dacewa"Mami abaya nayi kuskure,kuma nagane kurena,nayi nadama,yanzu kuma ga haƙin da nake ciki,Amma dan Allah Mami mubar maganar tsakanina dake,Allah na yadda zan iya zama da Commsner"tana magani ta goge hawayenta,Mami ta tausayawa yarinyarta,tama rasa abin cewa Saudat tace"Mami inhar kika faɗi maganarnan,to tabbass Dady zaice sai Areef ya aureni,kinga kuma auran tilass akayi mashi,wanda gudunshi yasa na faɗa wahalar danasha abaya,idan Pappa yaji shima zai kafe akan Areef bazai Aureni ba,kinga kenan rigima zata taso tsakaninsu"

STORY CONTINUES BELOW

Mami ta lumfasa duk maganar da Saudat ta faɗi gaskiyane,hakan yasa ta ɗauki Alkawarin bazata faɗima kowa ba.

Ranar sunyi fira tsakaninsu,wadda harsun manta raban da su samu lokaci kamar wannan

Ƙarfe biyar ta fito zata tafi,harta je wajanmota ta tuna tamanta saƙonda Mami tabada akaiwa Ammi,takoma ciki ta ɗauko ta dawo,ta shiga mota tanayin reverse ta saita gate ɗin gidan tanayin horn.

Mai gadi ya buɗe mata,daidai lokacin Areef ya sako hancin tashi motar,duka cikinsu sunyi blockin babu mai iya wucewa.

Areef ya kalleta ta glass,ita ma ɗin shi take kallo,kusan atare suka danna Horn da ƙarfi,alamar kowa yana buƙatar wucewa.

Saudat ta ƙarayi mashi horn,shima haka,sai kawai ta tsaya tana kallonshi,dan shine baida gaskiya,tunda ita ta rigashi kusa da gate ɗin.

Areef ya fito ya kalleta"kin man blocking hanya fa"Brown voile ne jikinshi,anyi mashi aiki sosai a jiki,voile ɗin sai sheƙi yake ga wani ƙamshin turare dake tashi.

Saudata tayi ƙoƙarin cewa"Amma ai kaika kareman hanya ko" Sanin baida gaskiya,yasashi kallonta yace"to shikenan,yana maganai yayi hayar main part ɗin gidan yabarta anan.

Wani ƙululun baƙin ciki ya isheta,ta ɗan tsaya tana tinanin abinyi,fitowa tayi,ta nufi cikin gidan itama tabar tata motar anan.

Ta tadda har sun gaisa da Mami,ya zauna,Mami tace"waike baki tafiba"

"Mami na fasa tafiya"tana magani ta nufi hanyar step ɗin ta nufi ɗakin Mami tayi kwaciyarta,shima Areef yayi zamanshi suka cigaba da Firarsu.

Gab Magrib Pappa yadawo saidai ya tadda motar Areef a tsakiyar gate ɗin,yayi horn harso Ukku,maigadi ya leƙo yagaya mashi,Pappa ya fito yana kallon motocin cikin Mamaki,ya koma ya gyara parkin ɗinshi ya nufo cikin gidan.

Tun a ƙofa yake kiran sunan Saudat,Mami tace lafiya yace"tana ina?"

Mami ta kwala mata kira ta fito,tana zowa taga Pappa,zata gaidashi yafara magana"wato dankin rainawa mutane wayo,anan zakiyi man parking a gida,nanne wajan parking"yana maganar cikin zafi"to nan ba gidanki bane balle kiyi iko,ko gate ɗinkine dazaki hana ashigo,"Areef kam tsuru-tsuru yayi yadda yaga Pappa yana faɗan,shi kanshi yasan shine baida gaskiya gaya yaja mata faɗa.

"maza ki janye motar nan daga wajan,ko in saɓa maki,nida gidana kiman yadda kikaga dama,ko akwai sisinki lokacin da nayi building gate ɗin"Saudat kuka kawai take,ta yi hanyar saman domin ɗauko jikkarta,wata tsawa ya kuma daka mata"ina zaki kuma"yana maganai ya nuna mata hanya,Saudat ta fice ba shiri,tana kuka ta isa wajan motai,Sauƙin tama tabar key ɗin ajiki.

Ta zauna tana kuka,ta matsar da motar baya,tanajin zafin abinda Pappa yayi mata,wulaƙancin yayi yawa kamar bashi ya haifetaba.

Ta ƙagara tabar gidan,saidai ba hanya,Areef yana ciki,ya jingina da kujera ya lumshe ido,yanajin ciwan abinda Pappa yayi,da sauri ya miƙe,dan ya tuna bazata iya fitaba saiya janye tashi motar.

Pappa yace"ina zaka bamu gaisaba"

"zan dawo,zan janƴe motana ne"

Areef bai jira cewar Pappa ba,ya fito,ya ga yadda ta haɗakai da sitiyari,yasan tabbas kuka take,take zuciyarshi ta ƙarayi mashi sanyi jiyake kamar yaje ya lallasheta saidai ba dama,motarshi,ya shigo da ita,jin ƙarar mota yasata ɗagowa.

Cikin sauri taja tata motar da ƙarfi ta fice gidan,saidai kafin ta koma,harta samu ta janye damuwarta,dan tasan Ammi zata matsa mata da tambayar abinda akayi mata.

             ****
Abu kamar wasa,tunda Areef yaga wani yazo wajan Saudat raban da yazo gidan dan yau kusan kwana goma kenan,ranar kuma Commisoner yazo yaga Dady sunyi magana sosai,Dady yabashi izinin aiko da magabatanshi,bayan nan yasamu Pappa da maganai,Pappa yace ai duk hukuncin daya yanke yarinyarshi ce.

STORY CONTINUES BELOW

Pappa kam koda Dady yatafi saida yayiwa Mami maganai Mami tace"ai tunda kaga basu ce sunason junaba,to basu soyayya,tunda inda Areef yanasonta bazai bati akai maganar zuwa yanzu ba"

Pappa yace"Allah ya shige mana gaba,amma har yanzu inayiwa Saudat kwaɗayin auran ɗan Uwanta"

Ammi da kanta takira Areef ta tambayeshi ko lafiya taga baya zuwa,yace mata aikine yayi mashi yawa,amma zaizo yau.

Saudat kam bawata soyayace tsakaninta da commisoner ba,saidai suyi fira idan yayi mata labarin soyayya saidai tace"Uhm"

Yauma yazo gidan,fira suke a falon baƙi,Commsioner yace"kinga dakin zama Matata na huta yawan zuwa wajanki kullun muna tare da juna,gamu ba yaraba balle su matsa mana"

Saudat ta ɗanyi murmushi"idan mukayi yaran fa?"

"ai ba yanzuba,sai mun huta da yawa kamar mun ɗauki shekaru"

Cikin Mamaki Saudat ta kalleshi,da alama bai cika san yaraba kenan,tace"to ai ko Sultan sai ya matsa mana"
Murmushi yayi yace"sai mu barwa Ammi shi"

Gaban Saudat yafaɗi Amma dai wannan ɗan rainin wayone,baisan yadda takeji da yaron taba shiyasa yake faɗin su rabu,tabarshi wajan Ammi.

Saudat tayi saurin janye maganai gudun kada yaganota.

Bayan kwana Biyu iyayan commisioner sukazo,sun kawo kuɗin Aure da kayan sa rana,take Dady yace zai haɗa auran dana Yayanta Muhsin sati shidda masu zuwa.

Ita kanta Saudat batayi tunanin hakaba,aikam ranar tasha kuka,ta ɗauki waya ta kira Fatima,tana ɗauka ta fara magana cikin kuka"karo na biyu ansa ranar Aurena saidai ba da Muradin rainaba" Fatima hankalinta yatashi,tayi ta lallashin ƙawarta.

Tana gama waya da Fatima ta kira Billy shantali,dan sune kawai ƙawaye biyu data amince dasu arayuwarta.

          *****
Tashin Hakankalin da Aref yashiga bazai misaltuba,wai sati shidda masu zuwa Saudat zata zama Amarya kuma ba tashi ba,ya shiga wani hali wanda dakaganshi kasan yana cikin matsala.

Ana cikin haka Ni'ima ta kama rashin lafiya,sai hankalinshi yakoma kanta,Amai,ciwan ciki,masssra da yawan ciwankai.

Gaba ɗaya Areef tausayin Ni'ima yakeji,Suka shirya sukaje Asibity,likitoci sukayi ƴan aune-aunan su,suka basu tabbacin cikine gareta sati Ukku.

Aikam murna tsosai sukeyi,Ni'ima kanta kamar tayi Hauka dan Daɗi,saidai ciwan dake damunta yahanata nuna farin cikinta.

Areef ne yake tambayar Dr,maganin yawan ciwan da takeyi,likitan yace"duk laulayine,matsalar ɗayace ciwan marar da takeyi Amma zamu ɗaurata kan Magunguna nasu kyau.

Haka suka dawo gida,bayan sati guda taɗan samu sauƙi,saidai duk ta rame,lokaci kaɗan duka Family akasan Ni'ima tanada ciki,an taya Areef murna sosai.

Ammi kam ta tareshi akan miye matsalarshi,yake rama irin haka,Areef kam cemata yayi babu komi rashin lafiyar Ni'ima ce kawai.

Saudat kuwa batasan lokacin da taji kishin Ni'ima ba,saidai tayiwa  zuciyarta faɗa akan ita ina ruwanta,koshi zata aura miye nata aciki.

           *****
Duka ɓangare biyu,gidan Pappa da gidan Ammi shiri kawai sukeyi,dan gaba ɗaya duka bikin baifi Saura sati biyu ba,Su Ilham yan makaranta sun samu hutu sun dawo gida,hakan yasa duk shirin da akeyi sune kan gaba.

Commsner yazo mata dasonyin event,tace ita batada ra'ayi tunda daiita ba budurwa bace,duk yadda yayi da ita taƙi,haka yasa ya haƙura.
Saura Sati ɗaya biki aka kawo lefenta,ranar kam Ammi kasa gane kan Saudat tayi,kuka ta kwayi a gida,Ammi tayi lallashi amma taƙiyin shiru.

Areef kam yazo yaga kaya hankali tashe yabar gidan,gidan Ammi ya nufa a hargitse saidaibabu kowa Khairat ce kawai,Ammi taje sayayya itada Ilham.

Khairi ta kalli Areef"Ya besty lafiya kuwa"

Zama yayi kan kujera yana dafekai,ya kalleta,zuwa wannan lokacin ji yake idan bai faɗi maganar zuciyarshi ba,to tabbas xai iya rasa rayuwarshi.

Khairat ta zauna kan kujerar da yake,"baka da lafiya Yaya?"

Areef ya ɗago yakalleta,wasu zafafan hawaye suka zubo mashi,hankalin Khairat yatashi sosai,take Areef yafara bata labari,tun daga farko.

"haba Yaya wannan wane irin abune kukayi,wallhiwannan duk laifinka ne,yanzu ta ina kakeso mufara"

Ya kalleta,"Ƙanwata kwantar da hankalinki,ba abinda zamuyi,sabd lokaci ya ƙure mamu"

"a'a Yaya"

Areef yakalleta yacigaba da fahimtar da ita,sosai ta fahimta,ya nuna mata matsalar da za'a samu idan suka furta maganai,Ammashi ya haƙura.

           ******
Saura kwana Ukku biki,ɓangaran su Muhsin harsun fara event ɗinsu,Saudat kam kallon mutane kawai take,tana zaune ɗaki ita ɗaya,saboda Ammi tatafi wa'axin auran.

Commsioner yakirata,suka hau fira,take gaya mashi duk ƴan gidan sun tafi wajan event ɗin.

Yace"ke miyasa baki tafiba?"

"inason shiryawane,zanje inyiwa Sultan sayayya dan shima bai kamata yatafi ba sababbin kayaba"

Commsner ya lumfasa,danshi bayason aje mashi da wani yaro gida"a'a bazaki barshi sai daga bayaba,idan zamuzo ɗaukarshi sai asayo mashi"

"a'a yanzu zani"

Ranshi yayi mugun ɓashu,yafara nuna mata bayason taje da Sultan,hankalin Saudat ya ɓaci tace"haba dai ni kakeso kenan bakason Abinda zaizo daga wajena,to mi kake nufi?"

Nan yakama kame-kame,Saudat tace towallahi bazai yiyuba,ita da yaronta zata,tana kuka ta kashe waya,har dare kuka takeyi.

Tunlokacin ta ƙaleshi tabar ɗaukar wayarshi.

       ****
Ranar daran ɗaurin Aure dasafe suna tare da Billy Saudat tana kuka,Billy haƙuri kawai take bata,Saudat tace"Billy idan kince inyi haƙuri inbar Sultan a gida,to wallahi dakanshu yagayaman so yake muyi shekaru bamu haihuba,wannn abin ke tada man hankali.

Daƙal Billy tasamu suka cigaba da hidimarsu,da marece suna ɗaki su Ukku hada Fatima,tazo itama hada cikinta.

Wayar Saudat tayi ƙara harso Ukku,fatima tace"kiyi haƙuri ki ɗauka"

Billy tajawo wayar,ta ɗauka ta kara mata a kunnai,yaji daɗin ɗaukar da tayi yace"da Massge zan maki Amma tunda kin ɗauka zan gaya maki"

"inaji"

"yanzu ke tun yanzu kin nuna banida ikon saki Abu kiyi,to wannan ba matsala bane nasan kona aureki bazakibi dokar dana aza makiba,to banyi Mamakiba"

Saudat ta ce"saboda mi"
"tunda naji labarin Auranki na farko,bawanda mahaifinki yakeso kika Auraba,kinga kau shima baisaki abuba balle ni"

Kasancewar wayar A speekr take,duk su Fatima sunajin maganarsu,hankalinsu ya tashi,Saudat ta fashe da Kuka,"ki daina kuka,kuka banaki bane,nina haƙura dake,Na fasa Auran nan,waɗannan sune dalilin dana kawo maki, sai anjima"
Innallhi suke maimaitawa,take Saudat hankalinta yabar jikinta ta miƙe tace"shikenan ai"

Tana magani tana fita falon,hankali,tashe Fatima da Billy suka bita.

Falon ta shiga,Dady da Ammi ne zaune,Ammi tana mashi list ɗin abubuwan da suke buƙata.

Saudat ta je tsakiyar falon,daka ganta kasan bata cikin hankalinta"Dady ku tashi kudaina lissafi,yace yafasa,bazai Aureni ba,dama ba sona yake b......."

Bata ida maganarba,lumfashinta ya ɗauke,ta sulale,da Sauri su Billy suka riƙota.

Dady Ammi hankali tashe suka taso suna tambayar lafiya.

*AUNTY HALILOSS*

WA NAKE AURE?
             NA
     *Aunty Haliloss*

*👑ROYAL WRITERS ASSOCIATION👑*

Wattpad
@AuntyHaliloss.

33

Ammi tayi hanyar firij ta jawo ruwa,cikin Sauri ta  ɓalle marfin,fara yayyafa mata,saidai babu alamar motsi jikinta,Dady ya anshi ruwan ya zuba mata har cikin kanta,sai lokacin tafara motsawa,Dady hankalinshi yatashi.+

Saudat ta buɗe idonta,wasu hawayen baƙin ciki suna zubo mata,ta riƙe hannun Dady tana faɗin"Dady wannan kuskuren danayi farko yasa wani bazai iya Aure naba,ashe haka rashin bin unarnin iyaye yake,Ammi wallahi nayi nadama"

Dady ya kalli Bily yana tambayarsu yadda akayi,su kanshi kuka suke,Fatima ce ta daure ta gaya masu abinda ya faru.

Ammi da Dady sunyi baƙin ciki,Dady ya zaunar da Saudat kan kujera"shikenan kiyi haƙuri,Allah zai baki wanda yafishi,Allah yasa hakan Alkhairine a rayuwarki"

Yana zama,ya kalli Ammi zaiyi magana wayarshi tayi ringing,baƙuwar Number yagani,ya ɗauka suka gaisa da mutumin daji babban mutun ne,anan yayi mashi bayanin kanshi,ɗaya daga cikin waɗanda sukazo nema ma Cmmisioner Aure ne,Dady yace"eh nagane"

"to dama Alhaji munkirane akan yaron mu ya zanje maganar Auran nan"

Dady yaji zafi A zuciyarshi,yace"to Allah yasadamu da Alkhairi"yana faɗan haka ya kashe waya.

Fiddo waya yayi take ya fara typing massge ya turama,Muhsin Pappa,Sadiq,Khairat da kuma Areef akan yanason ganinsu a gidan Pappa inthe next 30mints saidai bai gaya masu abinda ke faruwa ba.

Haka Dady ya miƙe ya dafa kafaɗar Saudat"shikenan wannn ya wuce a rayuwarki,kada ki saka damuwa aranki ƴata"yana gama maganai ya fice daga gidan.

Ammi kuwa jingina tayi da kujera tama rasa abinyi sabda baƙincikin da takeji,haka akayi ta zaman shiru da tsakaninsu.

Har Saudat ta miƙe ta koma ɗaki ta nemi kan gado ta kwanta tana kuka.

             ****
A gidan Pappa kuwa Dady ne ya fara isa,saidai Pappa bayanan Amma yakirashi ya tambayeshi ko lafiya,yace mashi lafiya lau Amma yadawo gida ɗin.

Duka yaran family ɗin sun haɗu kamar yadda Dady ya buƙata,Areef Muhsin,Sadiq,Khairat,Dady da kuma Pappa,a falon Pappa suka haɗu.

Pappa ne ya fara magana,"munajinka wannan zama haka cikin gaggawa"

Dukansu sunso suji miya faru,Areef ya miƙe ya koma kan kujera ya zauna dan zaman ƙasan bai mashi daɗi ba.

Take Dady yafara basu bayanin abinda ya faru,hankalin kowa ya tashi,Pappa yace"to ai shikenan,mudai bazamu fasa Auran Muhsin ba dan an fasa na wata"

Khairat kam Areef take kallo,dan ita wani farin ciki taji saboda fasa Auran dan tasan tabbas Yaya Areef bazaiyi sake ba a karo na biyu,Areef kuwa zuciyarshi harbawa kawai take da ƙarfi gabanshi yana faɗuwa.

Muhsin yace"shikenan Dady Allah yasa hakan ya zama Alkhairi"

Areef ya kalli khairat lokacin itama shi take kallo,gira ta ɗaga mashi alamar kwarin guiwa.

Areef yayi ƙokari wajan gyara muryarshi,amma duk da haka rawa takeyi,"Dady tunda haka ta faru,bai kamata a fasa Auranba,Ni a ɗaura Auran dani"

Wata kyakyawar ajiyar zuciya Dady yayi ya kalli Areef yana murmushi" Nagde yarona,Allah yayi maka Albarka"

Pappa kam wani farin ciki ya ziyarci zuciyarshi,Areef ne kujerar dake gefenshi,yasa hannu ya dafa Kanshi,hawaye suka zo mashi"Ina Alfahari dakai ɗana,Allah yayi maka Albarka"da kyal yamaida hawayen gudun kada sugani.

STORY CONTINUES BELOW

Pappa ya ɗora da cewa"saidai ina tsoron halin da zakuyi zama,saboda nasan babu soyayya a tsakanink..."

Muhsin yace"ba wata matsala Pappa dan Allah kada wannan tunanin yazo mamu"yana maganai yakamo hannun Areef saboda halarcin da yayiwa ƙanwarshi.

Dady yace"shikenan sai kaje kayi shiri"

Pappa yace"kanada ƙalu bale gabanka,sabda dole saikayi haƙuri wajan rarrashin matarka"

Areef yaji daɗi sosai,yau Pappa bai kawo matsala ba,ya kalleshi yace"insha Allah Pappa nagde"

Haka suka cigaba da tattaunawa,nan Areef yace kada agaya ma Saudat cewa dashi za'ayi auran.Suna gama maganarsu duk suka tashi.

Su Pappa suka fice,Muhsin ya tafi shida Sadiq sabda dama yayi shin kamu ɗinshi.

Areef ya juya ya kalli khairat,Khairat ta matso tayi hugging ɗinshi,Areef ya riƙeta shima"Nagde sosai ƙanwata nagode"Khairat ta sakeshi ta kalleshi"shikenan ki Yaya?"

Dariya yayi daka ganshi kasan yana cikin Farin ciki saiga Mami ta shigo falon,ganin suna murna Mami tace"lafiyarku dai?"

"Mami yau gurin Yaya Areef ya cika,zai Auri Besty"

Mami ta zaro ido,nan Saudat tahau bata labari,harda labarin halinda Areef ya shiga,Areef ya kalleta"ke gabana kike wannan maganai"

Khairat tace"au ashe ka iya zare ido"

Sukayi dariya Mami tace"Allah yasa Albarka,sannan dan Allah kayi ƙoƙarin yin adalci kaga kana da Mata"

"Insha Allahu Mami".ya taso ya bar gidan,sabda fara shire shiren shi.

Areef duk wanda yasanshi da Saudat saida yakirashi yagaya mashi,daya kira Billy tayi murna sannn yace kada ta gayawa Saudat ɗin.

Gida ya nufa,anan fa akayita tsakanin shida Ni'ima dan ko tsyawa gaya maku yadda suka ƙare ɓata lokacine,saidai ita tana ganin dama yasan da bikin dan ya cucetane,yayi namijin ƙokari wajan lallashinta,saidai harya gaji yabar gidan kuka take tana alawadai da hali irin na maza.

             *****
Rana bata ƙarya,ayau ne za'a ɗaura auran Saudat da Areef,Muhsin da Hasana,gaba ɗaya family ɗin murna ake.

Saudat dama tariga tayi duk wani abu daya tsafi gyaran jiki kunshi dakuma wankin kai.

Ammi ma kanta murna takeyi,danyau tasan gurinsu zai cika.

Saudat ta shirya ƙarfe 12 zasuje gidan Mami domin bikin yayanta,Ammi ta fiddo wasu kaya ta miƙawa Fatima,idan kunje sai tasa,wani tsaddaden lecine pink colour,zanen jikinshi Purple da kayan haɗinshi takalmi jikka da kuma gyale,

Haka suka nufi gidan Pappa bikin Ya Muhsin Acewar Saudat,tunda sukaje duka mutan gidan murnar ganinta suke,family ɗinsu kowa yazo,sai "oyoyo Amarya"suke ce mata,ita duk a tunaninta basusan anfasa Auranta bane,saidai kawai binsu take da murmushi.

Suna shiga Khairat tace"muje sama,dama saboda ku na rufe ɗakinmu"

Billy tace"kai Amma kin kyauta,Mai makeup ɗin tazo?"

"eh tanacan tanayiwa matar Yaya amma daga can nan zata taho"

Sama suka hau,sukayi wanka,Saudat ma ƙarayin wankan tayi,basu jimaba saiga Mai makeup sun iso,Saudat tace"waiku wace kwalliya zanyi dan Allah ku ƙaleni"

Fatima tace"just a light one"

Saudat ta zauanta miƙa fuskarta,Mai Makeup taci gaba da zuba fasaharta a fuskar saudat,ba wani abubuwa tasa mata masu colour ba,Nude makeup tayi mata.

Billy ta miƙa mata kaya,Saudat ta tsaya tana kallon kayan Fatima tace"Abeg wear mana"

Saudat ta saka kayan,doguwar rigace,strainght ɗinkin ya anshi jikinta saboda shape ɗinta da yayi fitting out,ɗan kwalin aka ɗaura mata,yankunne,darƙa,agogo,zobe duk silver ne tasaka,ta ɗauki takalmin tasa.

Masu karatu Saudat tayi kyau iya kyau,nasan ko wani daga cikinku yaganta tabbas dole ya yaba.

Saudat ta duba madubi tace"haba kun cuceni wallahi so kuke aga kamar amarya,Allah wankewa zanyi"

"wallhi kinyi kyau,kuma ai bata amare bace makeup ɗin"

Tsaki taja ta zauna,suma suka hau shiryawa,Ana nan saigaya anraki wata ance Saudat tayi baƙuwa,suna shigowa taga Maman Khalifa,Saudat taji daɗi sosai,ta miƙe "bari in kawo maki drinks,gaskiya naji daɗin ganinki"

Billy tace"nop zauna bari in ɗauko mata"

Bajimawa gida ya ɗauki hayaniya da guɗa,a harabar gidan kuwa sai kaɗe-kaɗe ake da busa alamar andawo daga ɗaurin Aure,hakanan kawai taji gabanta na faɗuwa.

Fatima tace"Alhamdllhi andawo"

Billy Shantali ta fiddo purple ɗin gyalen dayasha stones sosai a jiki,ta miƙawa Saudat,kutashi muje mutaya Yaya murna.

Saudat ta miƙe tana faɗin"kuzo muje inga Ya muhsin Ango"

A wajan harabar gidan suka fito,duk ƴan uwansune maza sai gaisawa suke,can suka hango Muhsin wajan falon Pappa,Saudat tace kunga Yayan acan.

Areef kuwa yana gefen Muhsin ya juya baya suna magana da Pappa ga Dady a ɗayan site ɗin.

Saudat taje inda Muhsin yake,Fatima da Bily suna binta sai gumtse dariya suke,ta ruƙo hannun Muhsin da ke magana da Khairat daga nesa tace"congrat brox"

Haɗa kafaɗar ta yayi da tashi yaɗan yi huging ɗinta,simple"Congrat to Sister"

Dady ya kalleta ya matso inda suke,Saudat tana gaidashi,Areef yanajin muryarta gabanshi sai dukan tara-tara yake.

Dady ya riƙo hannunta,yana mata dariya,har lokacin Areef magana yake da Pappa,Dady ya riƙo hannunshi ya juyo dashi.

Sai lokacin Saudat taga Areef ne a wajan,dan batayi tunanin hakaba,white shaddace yar ciki da babbar riga sai gold ɗin aiki,hular kanshi ma gold.

Lokaci guda suka haɗa ido,Dady ya ƙara matse Hannuwansu"HML"ana maganar yana haɗe hannuwansu waje guda.

Wani faɗuwar gaba tazowa saudat ta ɗaga tana kallon Dady,Dady ya sa hannun Areef saman nata yayi holding ɗin hannunta cikin na Areef.

Billy da Fatima,Muhsin sadiq da khairat da suka iso wajan suka ɗauka "HML" Suna maganai suna tafi....
Saudat kam sai tafara tunanin kamarta manta abinda Happy marriage life ke nufi,ta fara waiwaye waiwaye......

Muhsin yace"yes kinzama matarshi"

Sai lokacin tagane,take zuciyarta ta yadda da maganar da taji,Zaro ido Saudat tayi,ta saka wata muguwar ƙara tare da Maƙalƙale Yaya Areef tighty tayi huging ɗinshi tana ihu....

*AUNTY HALILOSS*WA NAKE AURE?

             NA

     *Aunty Haliloss*


*👑ROYAL WRITERS ASSOCIATION👑*


Wattpad

@AuntyHaliloss


*DADICATED TO MY FANS,AUNTY HALILOSS FANS GROUP ALLAH YA TSAREMAN KU ILYSM GUYS,INA TARE❤❤*


34


Areef shi kanshi baisan yadda zai misalta wannan ranaba,saidai yakasa maida mata Hugging ɗin saboda su Pappa da ke wajan.


Saudat ta janye jikinta,ta ɗago ta kalleshi,shima ɗin ita yaƙe kallo,ta juya ta kalli Dady da Pappa dake wajan zuwa tayi gaban Pappa sai lokacin na kula da hawayen dake fuskarta.


Hannun Pappa ta riƙe"Pappa tabbas nasan na aikata maka laifi,dan Allah kayafe man"


Pappa kam yau shi kanshi baya iya misalta farin cikin da yake ciki,ya dafa ƙafaɗar Areef tare da ta Saudat,sai lokacin nakula da camera da aketa ɗaukarsu pics.


Pappa yace"na yafe maki ƴata,Allah yasawa Auranku Albarka,kiyiwa mijinki biyayya kinji"


Hannun Areef ta riƙe sosai tana hawaye"Pappa insha Allah bazaka sameni da laifi akan hakan ba"


Shikam Areef murmushi kawai yake,shima ɗin ya riƙo hannunta,Dady yace"Allah yayi maku Albarka"


Yana maganai sukabar wajan shida Pappa,Saudat ta ɗago ta kalli Areef dake riƙe da Hannunta,shima ɗin ita yake kallo,su kaɗai sukasan abinda sukeji a zuciyoyinsu,Saudat ta janye hannunta.


Ta kalli su Billy dake masu pics tana harararsu,saidai har lokacin basu fasa ɗaukarsu ba.


Haka suka tsaya saidai babu wanda yake magana,Saudat ta koma wajan ƙawayenta"kumu tafi tunda kun kawoni nan naji kunya"


"mun kawoki kiyi huging ɗin mijinki dai zaki ce"


Gaba ɗaya sukasa dariya

Cikin gida suka koma,aka cigaba da gudanar da hidindimun biki.


Saudat kam ɗakin ta wuce,ta faɗa toilet tayo Alwala,sallah tayi tana ɗaga hannu tana ƙara godya ga Allah daya mallaka mata muradin ranta.


Har marece ƙawaƴenta sai zuwa suke,Saudat taji daɗi sosai,lokacin kam taga kulawa wajan danginta,kowa janta yakeyi hamdala kawai takeyi ga Allah.


Khairat ce tazo suna zaune lokacin ankusa magrib,fira kawai suke da frnds, tace"Besty ance kizo,yanzu za'a kaiki"


Lokaci kuda hankalinta yatashi,ta kalleta,idanuwanta suka kawo hawaye,Khairat tace"Haba Aunty nidai aikoni akayi,kike hararata"


Hawayen idonta zuka zubo,Khairat ta zaro ido"laaa yi haƙuri Aunty,wallhi Dady ma cewa yayi sai gobe za'a kaiki,dan ba'a ida haɗa part din ki ba"


Sai lokacin Saudat taji sanyi"nidai Am not your frnd balle ki jani"


Khairat tayi dariya"Sorry ki taso shirin Dinner za'ayi"


"wace irin dinner,nifa nace bazanyi wani event ba"


Nan Khairat ta gaya mata Areef ne ya shirya,Saudat tace"nikam bazan keba"


Har Frnds ɗinta,suka sa baki,amma taƙi"wai ni sokuke azageni,dan kawai banda jikin girma,yarona shekara 4 aganni ina hightable"


Fatima tayi dariya tace"to duka ke kanki shekarunki 24 ne"


"ai ko 4 ne bazanje dinner ɗinnan ba"


Khairat ta miƙe,tabar mata ɗaki taje tagaya masu Saudat tace bazata jeba,ana gama sallar magriba wayar Saudat tayi ƙara layin Yaya Areef tagani,gabanta yayi muguwar faɗuwa,karo na farko daya kirata waya a matsayin jikinta,wani sanyi taji a zuciyarta.


STORY CONTINUES BELOW

Tajima tana kallon wayar bata ɗauka ba,saida Billy tayi mata magana,ta ɗauka ta kara a kunnai,su dukansu shiru sukayi,ba wanda ya iya magana,gaba ɗaya kowa ya rasa ta ina zai fara,Areef yayiƙarfin halin faɗin"the dinner will start at 9:00,am coming to pick you by 8:30,get ready before the time" daga haka baice komiba,yayi shiru,jin batayi magana ba yace"kin jini?"


"eh "


"ok"yace tare da kashe waya,Fatima tace"dama mu kikewa gardama"


Saudat ta harareta tayi dariya,ta miƙe ta shiga toilet tayi wanka,tafito Fatima tace"an maki misscall"


Saudat ta ɗauki wayar ta duba,sai taga Ammi ce,murmushi tayi kawai lokacin taji kunyar Ammi take ji,har zata kira saiga wayar tayi ƙara,Saudat ta ɗauka"Hello Ammi ina yini,ya hidima"


Ita kanta Ammi taga canji ko a muryar Saudat,tace"lafiya lau ƴata,Ance bakisan zuwa dinner,kiyi haƙuri kije kinji,tunda ya riga yayi invating frnds ɗinshi"


"to Ammi ai gaya harma na fito daga wanka"


"Yauwa Allah yayi maki albarka" Saudat ta amsa sukayi bankwana,ta aje wayar.


Saiga Khairat ta rako mai Makeup,Khairat ta aje troly ɗin hannunta"ga kayan da zakisa nan"


Harararta tayi,ta kalli su Fatima tace"Aunty Fatima kutaso muje,wadda zatayi maku makeup tana ƙasa,kuma wasu frnd ɗinku sunzo,na ajesu falon Pappa dan gidan a cike ake"


"ok muje"


Tsawan 1hr ana ma amarya kwalliya,ana gamawa ta buɗe troly ɗin  ta ɗauko kayan,White weeding gown ce,Saudat ta ɗaga tana ƙarewa rigar kallo,taɗan ja tsaki ta saka.


Rigar,tabi jikinta daga sama,sai wajan ƙugunta tabuɗe sosai,kamar babyn roba,kasan cewar Saudat bata da ƙiba,hakan yasa rigar tayi mata kyau.


Mai makeup ɗin ta jawo net ɗin ta aza mata akai,gaya gashinta yasha gyara,kana ganinshi saboda net ne kana ganin gashinta.


Yankunne,sarka,zobe da ƴan hannunta duk stones ne farare,ga makeup ɗin ta anshi fuskarta,Nan mai Makeup ta cigaba da ɗaukarta pics Sosai Saudat tafito,saikace ba itace tayi tsaman ƙunci a gidan Usman ba.


Billy ta kira a waya,tace suzo sun barta ita ɗaya,Billy tayi dariya tace"aimu muntafi,amma Khairat tana kan hanyar dawowa"

Saudat tayi tsaki"ku wallhi kunada Matsala"


Tanann zaune saiga Khairat ta shigo"Besty tazo muje"


Suka Sauko,Saudat a hankali take tafiya saboda takalmin dake ƙafarta,sunada tsini da yawa,hakan yasa tafiyarta ta ƙara canzawa ,Saudat taga ƙasan bakowa"wai ina ƴan gidan"


"kowa yatafi Mami kuma tana gidan Ammi tare zasu tafi"


Saudat cikin zuciyarta tace"wannan uwayan amare da abin kallo suke"


            ***

Zaune yake a wata zuƙeƙiyar mota,fara,tink ce sosai,baka ganin wanda ke ciki,Khairat ta buɗe mata ɗayan site ɗin,wani ƙamshi ya ziyarshi hancinshi,Saudat  tayi ƙoƙarin zama kafin Khairat ta rufe mata.


Areef ya juyo ya kalleta,lokacin itama ta juya ɗin shi take kallo"ina yini"


"lafiya lau"


Khairat ta koma gidan gaba ta zauna,Zaks yaja mota suka wuce wajan Dinner ɗin,tunda aka fara tafiya babu wanda yayi magana,sai Khairat da tace"Aunty su waye zasu shiga dake"


Saudat tayi mata banza ta juya ta kalli glass,Areef ya kalleta yadda ta turo baki,abiɓ dariyama ya bashi"to waye kikeso ya shiga da ita?"


"eh ai naga Fatima cikinta yayi jirma"


"Nizan ɗauketa in shiga da ita"


Tayi saurin juyowa ta kalleshi,shima sai ya juya  ya kalli glass ɗin dake site ɗinshi,batace komi ba dai-dai lokacin suka isa bakin gate ɗin.


STORY CONTINUES BELOW

Fitowa sukayi,Khairat tana riƙe mata rigarta saboda jan ƙasa da takeyi daga baya,ahankali take tafiya,dai-dai zasu shiga ƙofar gate ɗin,Areef ya kalleta,ya buɗe hannunshi ta site ɗin da take alamar ta saka hannunta.


Yi tayi kamar bataganshi ba,Khairat ta riƙe hannun Saudat ta saka cikin na Areef,Saudat gabanta sai faɗuwa yakeyi.


Haka suka shiga ciki ga wani cool music dake tashi,Hall ɗin cike yake da ƴan Uwa da abokan arziƙi,sosai Al'umma suka ziyarci event ɗin.


Mazauninsu suka zauna,nasu pics da vedio sai aikinsu sukeyi,Nan frnds suka fara zuwa wajansu,sai lokacin Saudat ta fara dariya sosai tayi kyau.


Areef ya duƙa wajan kunnan ta"wannan washe bakin yayi haka"


Dariya tayi,tace"frnds ɗina nagani"


Yasa hannuya riƙo hannunta,"ni zaki kalla kiyi dariya ba suba"


Saudat ta kalleshi,ganin yadda yake mata smile,duk sai ya kashe mata jiki,ta ƙara holding ɗin hannunshi tana dariya,Nan fa aka cigaba dayi masu pics.


M.c ya kira domin su yanka cake ɗinsu,tare da Iyayansu,Sai lokacin Naga Ammi da Mami,Pappa da Dady sunyi kyau sosai.


Saudat ta zaro ido a hankali tace"kaji su Ammi wai hadasu"


Areef yayi dariya ya kamo hannunta"murna take yarinyarta zatayi Aure" Saudat ta ɗanyi dariya.


Amarya da ango ne a tsakiya,Dady da ammi suna kusa da Amarya,Pappa da Mami kuma a kusa da Areef,agaskiya sun burge kowa na wajan,sosai mutane sukaji daɗin ganin ƴadda family ɗin suke da halinkai,duk da ba yawane dasuba.


Ana gamawa aka ƙara chashewa,saidai duka Amaryar da angon ba rawa sukayi ba.


Haka aka nufo hanyar gida,tun a mota Saudat ta duƙa tana cire takalmin ƙafarta dan tagaji.


Ƙafar ta ɗago ta ɗora kan ɗayar dan takasa cire belt ɗin,Areef ya kalleta yaga yadda take ƙiƙiniyar cirewa,hannu yasa ya riƙe hannunta,ya riƙe belt ɗin yana cire mata,tsayawa tayi tana kallonashi.


Ya cire ya aje ƙafar,ya janyo ɗayar,kan cinyarshi ya ɗora ƙafar saidai wannan lokacin ba cirewa yake ba ƙafar yake kallo,jin shiru,Saudat ta kalleshi,tana shirin janye ƙafarta.


Areef ya riƙe ƙafar,yasa hannu ya cire belt ɗin,ya maida mata ƙafarta"Nagode"tace ƙasaƙasa saidai yana jiyota.


Suna isa gidan ba kowa duk basu dawoba,Saudat ta ɗauki takalminta a hannu zata fita daga motar,Areef ya miƙe hannunta,"ki saka takalman"


"Allah nagaji bazan iya saka waba"


Zaks ya kalla yace"plzz ka gyara parkin ɗin zuwa ƙofar part ɗin saita Sauka"


Zaks yace"ba inda zan matsa,kabata takalminka mana"


Areef yace"ɗan iska hakama kace ko"


Xaks yayi dariya,Areef ya kalli Khairat yace"ke rufe idonki"


Khairat ta kalleshi"kai Yaya"


Hararrarta Areef yayi,tasa hannu ta rufe idonta,Areef ya buɗe marfin mota,ya gewaya ɓangaran da Saudat take,ta zuro ƙafarta hannunta ya riƙo,ya saka hannuwan shi jikinta.


Saudat ta kalleshi,kafin tayi magana ya sungumeta kan kafaɗarshi,Zaro ido tayi ta ce"Yaya plzzz"


Bai saurareta ba yayi cikin gidan da ita,kan kujera ya ajeta zama yayi shima yana faɗin washh"yarinya sai nauyi"yana maganai yana ɗaure fuska.


Saudat ta miƙe ta nufi hanyar sama,Areef kam kallomta kawai yake,wani daɗi yakeji,yau Saudatce a kusa dashi a matsayin mata.


Shima bai jimaba yafice daga gidan,Saiga ƴan gidan sun fara dawowa,Lokacin Saudat tayi wanka tasaka kaya marasa Nauyi,don lokacin bacci takeji sabd sha biyu na dare ta wuce.


STORY CONTINUES BELOW

Washe garikam,tun wajan Ƙarfe tara Saudat tayi wanka ta shirya,atamface tasaka riga da zani,ɗinkin yayi mata kyau,falo ta tadda Mami da wasu daga cikin ƴan uwanta.


Saudat ta yafa gyalen dake hannunta,Mami tace"ina zakije ne?"


Saudat ta zauna saman hannun kujera,ta turo baki,Mami tace"ko Areef ɗin ke kiranki?"


Saudat tace"A'a ni gida zani"


Duka falon aka kama yi mata dariya,Saudat kam gaba ɗaya gidan ya isheta tafison ta tafi wajan Ammi,Mami tace"ke yanzu tafiya zakiyi"


"wai Mami miye dan na Tafi zasu kamayi man dariya"tana maganar ta miƙe tana turo baki dan sun bata Haushi,tafito harabar gidan,tana ma driver magana.


Areef ne ya shigo da Kan motarshi gidan kasancewar gate ɗin a buɗe yake saboda yawan shige da ficen da ake yi gidan.


Parking yayi ya juyo yana kallonta,mamaki yake inda zata,da Sauri yafito daga motar ganin tana shirin shiga motar,ya ɗan haɗe rai sosai"Ina zakike?"


Saudat ta kalleshi,Onion colour shaddace jikinshi yaƴi kyau sosai ga hular daya aza akanshi tayi mashi kyau"na ce ina zakije"


Ƙara turo bakin tayi"gidan Ammi zanje,ni can nakeson tafiya"


Mamakinta yake sosai,ya ƙara dai-daita tsayuwarshi"mizakiyi acan"


"wajan Ammi zan koma"


Dariya ta bashi sosai,saidai baiyi dariyarba"koma muke ciki"


Yana maganai yana nufa hanyar part ɗinsu,jitayi kawai tafiyarta zatayi,har takai bakin mota ta tuna mijinta nefa yanzu,kallon bayanshi tayi har ya kusa shigewa,itama binshi tayi ciki.


Gaban Mami ta taddashi,tashigo ta wucesu,tayi hanyar step ɗin benen,Wata abokiyar wasansu tace"ɗiyar Ammi anfasa zuwa wajan Ammi ne"


"Ban sani ba"tace,duka sukayi dariya,Nan suka zauna suna ɗan fira,Mami tace"wai muna zaune tafito zata tafi,nace Allah ya tsare hanya"


Areef yayi dariya"Ai nayi tunanin da ƴan walima zasu tafi gaba ɗaya"


"ai batama jira akayi mata bayaniba ta fice"


Areef yayi murmushi,ya miƙe,saman benan ya nufa,ɗakinsu khairat ta shiga dan yasan tana can.


Zaune take kan kujerar,tana ɗan sharar hawayenta,Areef ya tura ƙofar,ya tsaya yana kallonta"dan ance ki dawo kike kuka"


Ɗagowa tayi ta kalleshi,ta juyar da kanta gefe"ki bari su shirya saiku tafi tare tunda sunce walimar 11 ce"


Shiru tayi mashi ya shiga yazauna gefenta,jiyake kamar yajawota jikinshi"Kinji?"


"to"


"yauwa"yace yana miƙewa,ya baro ɗakin dan bazai iya zama a kusa da itaba ƴadda yakejin ƙamshin turaranta.


Ƙarfe goma da rabi,suka shirya suka Nufi gidan Ammi,wani tsadadden Material ne ta saka,ɗinkin doguwar riga yasha stones work a jikin patern ɗin,red ne sai ratsin lemon gren hakan yasa mayafinta da takalmi da jikkarta duk lemon green ne.


Mami sosai tayi mata Nasiha akan tayi zaman haƙuri,kuma tayiwa mijinta biyayya,tunda dai wannan bashine auranta na farko ba.


Lokacin da suka isa gidan Ammi duk mutane an haɗu,harabar gidan anyi decoration ansa kujeru,ga wajan da aka tanada domin zaman Amarya kaikace kamu ne za'ayi.


Haka aka fara walima,sai ƙarfe biyu aka gama mutane duk aka watse,ƴan uwan Mami suka miƙawa Ammi Amanar ɗiyarta.


Tunda Saudat take gaban Ammi ta rufe fuskarta,saikace ranar ta fara ganinta,Ammi tace"Billy ku tafi ɗakinta,kinga yau ɗiyata kunyata takeji"


Billy tai dariya suka shiga ɗakin,suna shiga Saudat ta rufe ɗakinta saka key,Billy tace"lafiya?"


"tayani haɗa kayan nan plzz"


Billy tayi dariya"mara kunya"


Haka Billy ta kama mata,duk suka haɗa kayayyakinta cikin manyan jukkuna,tace"kinga ɗauka kawai za'ayi baza'a tsaya haɗawa ba"


"Hakane kuma"Nan suka zauna wasu ƴan skul ɗinsuma sunzo sunsha fira sosai,sai ana sallar Magrib duk suka tafi,yarage daga Saudat sai Khairat,saboda tayi-tayi Billy ta zauna taƙi.


Ammi ta shigo ɗakin da leda a hannunta,ta miƙawa Saudat gayanan kiyi wanka ki saka,saidat tayi wanka tasaka swiss voil ne,orange colour,yayi mata kyau sosai.


Ƙarfe takwass na dare Ammi takira Areef a waya akan yazo,Areef ya shigo gidan ya tadda Ammi da Masu aiki sai gyran gida sukeyi.


Ammi ta kwalawa Khairat kira,tana zuwa tace takira mata Saudat zasu tafi gida,Khairat ta koma tasan idan tace mata tafiya zasuyi awai problm"Aunty kizo ga Yayan nan yazo Ammi ke kiranki"


Saudat ta miƙe ta ɗaura mayafinta akai,plate shoe ne a ƙafarta,falon ta samesu tana zuwa Ammi tace "muje palon Dady,Dady keson magana daku"


Areef ya miƙe yana kallonta,Saudat kam lokacin jikinta duk yayi sanyi,Dady yana zaune kankujera,Ammi ta zauna kujerar dake kusa dashi.


Areef ya zauna gefen su saman capet,Saudat kam kanta a ƙasa,Dady yace"zoman ƴata"


Gefen shi ta Zauna saman Capet,Dady yayi gyaran murya,shima ɗin nasiha yayi masu sosai yakalli Areef yace"yanzu aiki ya ƙaru akanka,sai ka zama jajirtacce wajan Adalci a tsakanin matanka,kuma dole zaka ƙara hakuri akan wanda kake dashi,kada ka cutar da yarinyar mutane,saboda wannan ƙanwarka ce,haka kuma kada ka kuskura ka cutarman Yarinya"


Saudat kam lokacin kuka takeyi,Dady ya juya kanta Nasiha yayi mata sosai,Ammi ma sosai tayi mata Nasiha.


Dady yace"Allah yayi maku Albarka ka ɗauki matarka kutafi"


Areef ya miƙe tsaye,hakama Dady dayayi hanyar ficewa,Saudat ta duƙe tana kuka,Ammi ta kamo hannunta"haba haba,miye Abin kuka"


"Ammi dan Allah kice mashi yabarninan"*AUNTƳ HALILOSS*WA NAKE AURE?

             NA

     *Aunty Haliloss*


*👑ROYAL WRITERS ASSOCIATION👑*


Wattpad

@AuntyHaliloss


35

Areef yayi gaba yana cije dariyar da tazo mashi,Ammi ta shiga Lallashin Saudat,Har mota suka rakata da Khairat,ita kanta khairat ɗin sai da taji babu daɗi.


Areef yana Zaune yana jiranta,Khairat ta buɗe mata mazaunin mai zamn banza,Saudat ta zauna,Khairat ta rufe motar.


Areef yayiwa mota key,Saudat ta duƙe tana kuka,shiru yayi mata yana tuƙin shi a hankali,wata waƙa ya kunna yana ɗan bin waƙar ƙasa-ƙasa.


Tashi tayi ta jin gina da kujerar motai,tana goge hawayenta,Areef ya kalleta,har idonta sunyi jaa"ki daina kukan"


Saudat kallon titi take dan yama bata haushi,saida yaga ta haƙura yake cewa ta daina kuka.


Wani joint ya tsaya yaɗanyi masu sayayy sannan ya dawo suka ida isa gidan.


Part ɗin dake gefen na Ni'ima anan aka haɗawa Saudat,Areef ya kalleta"muje ko"


Yana maganai yana fitowa daga mota,ya gewaya ya buɗe mata,Saudat ta fito gabanta na faɗuwa Addu'oi kawai take karantowa cikin zuciyarta domin samun tabbatuwar zamn su lafiya a gidan.


Wani sanyi takeji yana ratsata,shikanshi Areef baisan farin cikin da yake jiba ayau gashi Saudat tashigo gidanshi a matsayin matarshi.


Falo suka shiga,Saudat taɗan tsaya tana kallon gidan Areef yace"hop gidan yayi maki?"


Saudat ta sauke idonta,ta zauna kan kujera,Areef ya kalleta"kitashi muke in  nuna maki yadda tsarin gidan yake"


Saudat tazama kamar kurma dan kasa magana,binshi kawai take,Areef ya nuna mata ko ina,3bed room ne ɗaya nashi sai nata dana baƙi kowane da toilet a ciki,dai Dining area daga gefe kuma ƙoface da zata sadaki da ƙaton kitchen ɗin da aka ƙawatashi da kayan aiki kala-kala.+


Bed room ya shiga da ita,babbane sosai akwai set ɗin kujeru a ciki,ga gado a gefe,shine nashi.


Suka shiga wani saidai shi babu kujerun,saidai resting chair gida ɗaya.


Bazan iya tsayawa kwatanta maku haɗuwar kayan da aka dakama gidanba,saidai kukanku zakuyi laka'ari da tsadddun kayan da aka kai mata a gidan Usman,kunsan anan ba'a magana.


"Nan shine bedroom ɗinki"


Saudat batayi magana ba tayi zamanta bakin gadon,Areef ya juya ya ficewarshi.


Saudat ta miƙe tana kallon ɗakin ta buɗe wadrop ɗin Nan taga kayanta da Khairat tace sun fara kawowa.


Toilet ta shiga tayo wanka,ta fito ta shafa mayuka masu kyau,ta fiddo wata rigar bacci fara,tana da ratsin pink a wuya dakuma hannunta,rigar tayi mata kyau sosai,ta fiddo soft shoe ɗin rigai ta aje.


Komawa tayi har zata kwanta,ta jiyo ana taɓa ƙofar Areef ne ya shigo ɗakin,shima ɗin kayan baccine jikinshi riga da wando Farare ne sosai jikinsu,cotting ne,sun anshi jikinshi.


Tsayawa yayi yana kallonta yadda kayan sukayi mata kyau,ta juyo ta kalleshi,gabanta na faɗuwa,Areef ya aje ledar dake hannunshi kan bedside locca.


Ya kalleta"bacci zakiyi ne?"saudat ta ɗan yamutsa fuska,"eh"


Areef ya harɗe hannuwan shi a ƙirjinshi,sosai tayi mashi kyau,ta ɗauko hula tana sakawa akanta,saidai hular taƙi shiga kan.


Zama tayi bakin gadon,ta tattara gashin kanta,ta ɗaure sannan ta kawo hular ta saka,ta juƴo ta ƙara kallonshi,ganin ita yake kallo tayi Saurin kauda kai.


"Ga Abincinan kici kada ki kwanta da yunwa"


Yana maganai yana nufa hanyar fita,har yakai ƙofa ya juyo,sosai zuciyarshi ke bugawa,ya fice daga ɗakin.


Yana fita Saudat ta kalli ledar da ya aje,sotake taga miye,buɗewa tayi,wasu kajine guda biyu manya,Saudat ta kalli naman ta ɗan taɓe baki,maida ledar tayi kamar yadda ya aje,ta kwanta tare da jan bargo

*AUNTY HALILOSS*

WA NAKE AURE?
             NA
     *Aunty Haliloss*

*👑ROYAL WRITERS ASSOCIATION👑*

Wattpad
@AuntyHaliloss

*ALHAMDULILLAH NASAMU SAUƘI SOSAI,NAGODE DA ADDU'O'IN KU,ALLAH YABARMU TARE*

36

Areef kam koda ya koma,tunani kawai yakeyi,yau Saudat ta zama mallakin shi ya daɗe bacci bai ɗaukeshi ba.

Da Asuba Areef yana tashi yayi wanka,ya saka wasu kaya,ɗakinta ya nufa domin tadata,saidai yana zuwa bai ganta kan gadon ba saijin motsi da yayi a toilet,hakan yasa ya ficewar shi yaje part ɗin Ni'ima yatada ta,san nan ya wuce masallaci.

Tunda Saudat tagama Sallah tayi lazimi,tana gamawa ta hau gadon ta kwanat itace bata tashi ba sai takwas da ƴan mintoci.+

Ɗakinta ta gyara,ta shiga tayi wanka,ta wanke toilet ɗin,ta fito ta fara shiri,turaruka da cream masu kyau tayi amfani dasu,ta shafa powder kaɗan ta kawo lipgloss white ta shafa,saidai yaɗanyi pink saboda lip ɗinta dake da pink,wata Gizner shadda ce ta ɗauko ta saka,ɗinkin doguwar riga,shadar taji aiki sosai,fan kwalin take ƙoƙarin ɗaurawa saidai tama kasa,Ajeshi tayi gefe,ta ɗauko cumb ta gyara gashinta gida biyu,ta kitseshi biyu kowane ya biyo kafaɗarta.

Turare ta saka ta fito falon,saidai babu wani dirty hakann dai ta ɗan gyara,ta koma ta zauna kan kujerar Areef kam shima lokacin yagama shirinshi,Maroon captan ne jikinshi yasha aikin baƙin zare saidai babu hula akan shi.

Sosai ta maida hankalinta kan t.v ɗin,Areef ya shigo falon kallonta yayi,yadda duk hankalinta yake kan t.v ɗin tayi mashi kyau sosai,zama yayi kujerar dake gefen ta,yaɗan ja stool ɗin dake wajan,sai lokacin hankalinta ya dawo.

Kallonshi tayi taɗan kawai dakai"ina kwana"

"kin tashi lafiya"

"lafiya lau"

Wayar hannunshi tayi ƙara,ya ɗauka yana dubawa"Hello Ilham ya ne?"

"ok May be mai gadin yaɗan tashine,ok to"

Jin Areef ya anbaci Ilham tagane Ilham ce tazo gidan,wani daɗi taji,Areef ya tashi yana nufa ƙofa,itama ta ƙagara taga ƙanwar tata,tare suka isa ƙofar kowa yanason wucewa.

Areef yaja ya tsaya yana kallonta,itama shi take kallo,hannu yasa ya ja jelar gashin dake binta"ina zaki bako kallabi"

Sai lokacin ta tuna da babu ɗankwali akanta,ɗan langwabe kai tayi ta koma ta bashi hanya ya fita,yana zuwa maigadin yana buɗewa,Areef yadawo.

Ilham ce driver ya kawota,Ta fito daga mota tana gaida Yaya Areef,ya amsa"ya Mami"

"Mami lafiya lau tana gaidaku"

Tare suka shiga falon Ilham tayo kan Saudat"oyoyo Aunty"

Saudat ta kalleta"daga ina"

"daga gida break ne Mami tace inkawo maku"

Daidai lokacin,Areef ya zauna saman kujerar da take,yakalli Ilham yace"kamar kinsan yanzu ta matsaman ita yunwa takeji"yana maganar yana alamar wasa.

Saudat ta kalleshi"ni nacema yunwa nakeki,kaidai kejin yunwa"

Duka sukayi dariya,Areef ya ruƙo hannunta"nidake aga wanda zai fara cin abincin"

Ilham ta miƙe"eh bari ma in kwaso abincin Aga wanda kejin yunwa"tana maganai ta fice,Saudat taɗanja jikinta daga kusa dashi,yana jinta saidai baiyi magana ba.

Ilham ta dawo,Saudat ta miƙe ta ansheta,"muje kan dinning"

Ilham ta aje ta ɗauko wata kular ta kawo,Saudat ta zauna ta kalleshi"wallahi kataso kaci,nasan daurewa kawai zakayi dan ace maka Oga"tana maganai tana mashi dariya,Areef ya miƙe,kujerar dake kallon tata,ya zauna Saudat ta ɗauko plates ta zuba abincin.

STORY CONTINUES BELOW

Plate biyu ta zuba ta ja kujerarta kusa dashi ta saka spoon da fork ko wane biyu a ciki,lokacin yagane tana nufin tare zasuci.

Saudat ta kalli Ilham"Oya ki zauna kici"

Ilham ta ɗauki handbag finta data aje kan table ɗin"a'a ni tafiya zanyi "

Areef yasaka fried potato a baki"ina zakije"

Lokacin hartakai tsakiyar falon"gida mana"

Saudat taji ba daɗi ta miƙe ta biyota,"waike tafiya zakiyi"
"Mami tace kada in dafe aiki zamuyi,kuma Khairat tana gidan Ammi"dole Saudat ta haƙura,Ilham ta tafi.

Tana dawowa,ta zauna kujerar da tatashi,Areef yana kallinta shidai wani kyau take mashi,abincin data zubawa Ilham ta jawo,Areef ya kalleta"wannan zakici"

Itama shi take kallo saidai batayi magana ba,ta ɗauki spoon ɗin sukaci gaba da ci atare,saidai ahankali take cin abincin duk ta kasa sakin jikinta.

Lokaci guda tafara tuno gidan Usman,ko yaushe tare suke cin abinci,dama cikin kula ɗayane ko isarsu bayayi dole saidai suci tare susha ruwa,wani lokaci kuma daya ɗanci zai haƙura yace ita ta cinye.

Kallonta Areef yake,riƙe take da spoon amma takai 5mint batayi motsiba,ya ɗebo abincin ya nufi bakinta,sai lokacin ta ɗago,ta kalleshi,hawayen idonta suka zubo,hankalin Areef yatashi sosai.

Ya miƙe yaja kujerar shi kusa da tata,"miye kuma?"
Saudat ta sa hannu ta share fuskarta"Babu komi"

Yaɗan ƙara kallonta yana nazarinta"don Ilham ta tafi,ko in mata waya tadawo"yadda yake maganai kamar ƙaramar yarinya yake mawa,Saudat ta kaɗa kai"to banason kuka ni,dan idan naga Matata na kuka nima kuka nikeyi"

Abinma dariya yabata,sai kawai tayi dariya,shikam ko a jikinshi,ya tura mata plate ɗin ki cinye,ta miƙe ta buɗe Macrowave ta fiddo naman data saka ta ajiye mashi.

Kallonta yayi,yadda yakai mata naman haka yake,ya janye abincin,ya tura mata namn "maxa kici bari in dawo"

Saudat tana kallonshi ya fice,taɗanci naman kaɗan ta ɗora da drinks ɗin ta maida mashi ta ajiye ta tattara kayan takai kitchen ta wanke.
Ta koma ta zauna,ta kunna redion wayarta tana sauran gidan redion su,Areef ya dawo daga bakin ƙofar ya tsaya"ɗauko mayafinki"

Saudat ta kalleshi,ta miƙe ta ɗauko wani farin mayafi ta aza,binta yayi da kallo sosai tayi mashi kyau ji yake kamar yayi hugging ɗinta.

Juyawa yayi ta bishi baya,Falon dake tsakiyar part ɗinta dana Ni'ima suka shiga,ya zauna kan kujera,Ya nuna mata kujera,itama zama tayi.

Sunɗan jima,Saudat ta fara latsa wayarta dan shirun yayi mata yawa,Areef ya kishingiɗa kan kujerar ya kara waya a kunnai"ki fito ke nike kira"

Sai lokacin Saudat tagane Ni'ima ake jira,gabanta ya faɗi,Ni'ima ta shigo falon da doguwar riga mara nauyi ga ɗan cikinta daya fara fitowa dan yanzu yayi wata huɗu.

Zama tayi fuskarta babu fara'a,Saudat tace"ina kwana"

Banza tayi batace komiba Areef ya tashi daga kishinhiɗar da yayi Addu'a yafarayi,Sannan ya vigaba da koro bayananshi akan tsarinshi dakuma neman haɗin kansu.

Ni'ima sai cika take tana batsewa,yana kallonta,saidai yayi kamar bai ganiba,dan dama yasan hakan,saboda saida sukayi tsiya kafin ya tursasata ta fito.

Ya maida hankalinshi kan Ni'ima"kece babba,sabda haka banson rigima a gidana,kuma bawai sabda kowace tana da sashenta hakan yana nufin babu alaƙa a tsaknin kuba dole saikun haɗe kanku"

"ke kuma kinsan Ni'ima Matata ce kuma anan kika sameta,dole zaki bata girmant banason maganar raini anan"

Ni'ima tace"Ato gaya mata dan ni bazan lamunshi rainain hankaliba"

STORY CONTINUES BELOW

Areef yace"dake nake ne,ko nayi magana dake"

Saudat dai btace komi ba"yanzu ya kuke ganin zaku tsara aikinku"

"aiki kamar yadda yake haka za'ayi kwana biyu,kaga gobe sashena zaka koma kenan"

Areef yace"ke fa ya kika gani"

Saudat ta daure tace"duk hukuncin daka yanke yamani"

Areef yaji daɗin maganarta sosai,wani sanyi yaji,koda dama yasan Saudat bamai rigima bace"Shikenan,Zanƴi sati guda a ɓangaran Saudat,sannan inkoma kwana biyu-biyu"

Ni'ima tace"kam ai wallhi bazai yiwuba,tana jawara zakayi mata sati guda,aik addini kwana huɗu yace ayi"

Saudat wani ƙululu ya bigi zuciyarta,take fuskarta ta canza,Areef yace"ashe kinsan haka kikace gobe zan koma wajanki,saboda haka zanyi kwana Hudu,sannan akoma 2-2days hop hakna yayi maku"

Ni'ima tace"koma bai mataba yayi,dan dole tayi haƙuri,tunda ta auri mijin matar so"

Areef kam shima ɗin ba iya wata rigima yayiba,kawaidai yana jajircewane,ya kalli Saudat"Hakan yamaki?"

"eh yayi Allah ya tabbatar mana da Alkhairin shi"tana maganai tana miƙewa,ta bar falon,Areef ya bita da kallo,N'ima taja tsaki,Areef yace"wallahi nagaya maki,muddin kinason zaman lafiyarmu a gidannan dole ki gyara,dan bazaki ɓataman gida ba"

"ai wallhi gdanka lafiya lau yake,wannan dai datazo zata ɓatashi,wai kai ko kunya bakaji karasa wacce zaka Aura sai zawara ko..."

Areef bai tsay sauraranta ba ya miƙe yabar falon,lokacin da ya koma Saudat tana ɗakinta,shiga yayi ya sameta taɗan kwanta saman gadon,kallonta yayi,ta juyo itama"hop bakida matsla?"

Zama tayi ta kalleshi"a'a baki da matsala"

Ya zauna bakin gadon shima,"kiman list ɗin abinda kike buƙata na lefenki"

Yi tayi kamar bata ganeba"lefe kuma"

"ƴes anjima zan fita inyo maki,ko zakijene"

Far tayi da ido"a'a kabarshi,ni inada kayan amfani"

Miƙewa yaƴi yace"nidai bansan abinda kike soba,zan sawo kawai tunda bazaki faɗi ba"yana maganai yana ficewa,Saudat ta miƙe ta fito falon
Fitowa yayi da key ɗin mota hannunshi,ta zauna kan kukera"Na fita"

"saika dawo Allah ya tsare"

Baisan sadda ya juyo yana kallon taba,ko yaushe ta iya addu'a ga miji,sai lokacin ya tuna tafa taɓayin Aure,"Amin yace ya fice"

Saudat ta miƙe ta shiga kitchen ɗin,so take tayi girki amma babu wani abun cefane a gidan,hakan yasa ta koma falon ta cigaba da kallonta.

Wajan Azahar ta miƙe taje tayi sallah harta kwanta ta tuna yace mata kasuwa zai shiga,wayarta ta jawo daga kan kado,layinshi ta fara kira.

Driving yake lokacin harya gama haɗa mata abubuwanta an saka mashi a boot,ya kalli wayar ganin Best sis yasashi ɗagawa,ya kara wayar a kunnai"Hello yakike,hop ba matsala?"

"A'a lafiya lau,dama ince maka,babu abin amfani a kitchen kuma girki xanyi"

"girki kuma?"

Saudat ta gyara kwanciyata"Uhmmm"

"ok to"

Take ya juya,ya shiga super makert ɗin kaya ya kwaso sosai irinsu abubuwan  amfani,yana fitowa yaje kasuwa,Cefane yayo sosai ya dawo gidan.

Yagaji sosai hakan yasa,ana shigar mashi da kayan na Ni'ima ya kwasa yakai mata,yakoma ɓangaran Saudat,ya shiga ɗakinshi,wanka yayi ya kwanta,sai bacci ya ɗauke shi.

STORY CONTINUES BELOW

Saudat kam dama taji shigowarshi,shirya wa tayi cikin wata exculusive super holland dark blur ce atamfar riga da skert ce,ta ɗan ɗora ɗan kwalin yayi mata kyau sosai.

Fitowa tayi falon ganin kaya a zube ga akwatuna ajiye,Saudat ta nufi kayan,na ledar ta duba taga kayan kitchen ɗinne.

Kwasa tayi taje kowane ta ajiyeshi mazaunin shi,na firij ma ta saka,haka naman da kifin.ta gyara wajan,saidai anan tabar Akwatunan wanda sunyi mata kyau sosai.

Ta koma kitchen ɗin nan tafara tunanin abinda zata girka,Coconut Dolman ta fara tunaninyi,da stew,ta ɗauko Namn ta gyara ta haɗa stew ɗin lokaci kaɗan gidan yafara ƙamshi,tana gamawa ta kai kan dinning ta ake ta kawo abubuwan buƙata ta ajiye.

Ta koma ta maida kayanta,saboda dma cirewa tayi da zata shiga kitchen ɗin.

Ƙarfe biyar har lokaciɓ Areef bai tashiba,Saudat kam kwata-kwata batama san yana gidan ba,wayarshi tayi ƙara Mamice ta kirashi yadauka,nan tace mashi yazo ya ɗaukar masu Abinci babu kowa a gidan.

Areef yatashi ya kalli agogo,da sauri yayi wanka,yayi Alwala yai sallah,ya saka kaya ya fito.
Tana Zaune falo ya fito,kallonta yayi,tayi Saurin kauda kai dan itama ɗin shi take kallo"ina yini?"

"kina sane,ina bacci har lokacin Sallah ya wuce haka"

"Nop ni bansan ma kana gidan ba"

Zama yayi ya kalleta"Ammi ta kawo abinci ne?"

"ya akaƴi"

"inajin ƙamshin girkinta"

"nacewa Ammi kada ta bawa kanta wahala"

"eh Wato Sai Mami zatayi wahalar kawo abinci ko"

Dariya ta ɗanyi,ya kalli kayan gefenta"wanann fa mi sukayi maki da bazaki ɗauke ba"

Saudat ta kalli kayan,akwatunane guda shidda,Pich colour,ta kauda kai,ya miƙe yana shirin fita"Bari inje gidan Mami tace babu wanda zai kawo abincin"
Saudat tace"ai nagama abincin ma tun dazu"

Juyawa yayi yana kallon dinning ɗin,yakoma ya zauna"kinyi ƙoƙari"

Saudat ta miƙe"in kawo maka nan ne ko zakaje can"

Ganin yadda take tafiya kwanin burgewa,ji yayi baigajiya da kallonta"Nop kawo man nan"

Haka ta shiga kitchen ta ɗauko table mat babba tazo ta shinfiɗa kan capert ta kona ta cigaba da kwaso abincin.

Areef ya miƙe,ya fara kwashe mata akwatunan ta nufi hanyar ɗakinta,itama sauran ta ɗauka ta bishi kuka ajiye kayan.

Yana dawowa kan capet ɗin ya zauna,Saudat tazo ta durƙusa tana zuba mashi abinvvin,sosai abinvin ya burgeshi,ta aje mashi gabanshi.

Spoon ɗaya ta saka,Areef ya ɗauko ɗaya ya ƙara a ciki"Muci"

Saudat ta kalleshi,ya kalli Abincin ya faraci,hakan yasa takasa cewa komi,itama ta faracin abincin,bai ciba sosai,balle ita,ya aje spoon ɗin,Saudat ta kalleshi,sai taga kamar ko baiyi mashi daɗi bane,ta kauda kanta ta aje spon ɗin itama.

Glass cup ɗin ta zuba mashi coke ta miƙa mashi yakoma kan kukera yanasha,tas ta kwashe kayan ta gyara wajan duk yana zaune yana kallonta.
Aka fara kiraye kiran Sallar Magrib,ya miƙe ya tafi massallaci,bai dawoba sai bayan sallar isha'i.

A falon ya sameta,ya kalleta bai ida shigowa ba,"plzz ɗaukoman car key a ɗakin"

Saudat ta miƙe taje ɗakin ba dirty saidai,gadon a hargitse yake,ga ledar wasu chocolate da yasha,ta ɗauko mashi key ɗin ta miƙa mashi,baiyi nata magana ba tace"daika dawo"

"Allah yasa"yace ya ficewar shi.

Saudat kam harta koma ɗakinta ta tuna da yadda taga bedroom ɗinshi,miƙewa tayi,taje ta gyra gadon sosai,ta share falon,airfresh na ta fesa,ta kunna A.c,haka ta shiga toilet ɗin,komi na toilet ɗin blue ne,saɓanin nata da yake red,toilet ɗin yayi mata kyau,ta gyra tasa abin ƙamshi ta fito.

Tana shiga ɗakinta,ta watsa ruwa ta fesa turare ta ɗauko pink ɗin rigar bacci da wandonta iya guiwa,tayi parking ɗin gashinta baya,rigar batada hannu sai ɗan zaren da ake ɗaurewa.

Dakinshi ya nufa,yana buɗewa ƙamshi ya ziyarce shi,tsayawa yayi yana bin ɗakin da kallo,toilet ya shiga canma a gyare hakan yasa yagane ta shigo ɗakin,murmushi yayi ya yi wanka,ya saka kayan bacvin shi kalar na jiyane saidai na yai ba farare bane brown ne light,takalma yaska masu taushi ya nufo ɗakinta.

Tana zaune ta buɗe kayan tana dubawa,kayan sunyi kyau sosai taita mamakin yadda har yanzu Yaya Areef bai banta colour ɗin da tafi soba,wani set ɗin kayan Makeup ne ta ɗauko tana dubawa.

Ya shigo ya tsaya yana ƙare mata kallo,ta aje set ɗin saman cinyarta,ta na jawo wani,ya ce"wannan bai maki bane?"

Tsoro taji ta saki kayan tana miƙewa,dariya tabashi,yana dariya yana shigowa bakin gadon ya zauna,ya riƙo hannunta ya zaunar da ita,kusa dashi.

yasa hannu ya ɗauki set ɗin"basu da kyau ko?"

"a'a sunyi kyau,najima ina nemansu bansamuba"

Taɗanja jikinta,tanajin ƙamshinshi na shigarta,"ok" ta rufe akwatunanan ta kaudasu daga inda suke,kallonta yake kamar yaran india,ta ɗauko wani takalmi ta saka,ya kalleta ina zakike"ba ko ina"

"na aje jeda a firij ɗauko ta"

Tafiya tayi ta ɗauko ta dawo robobin icecreem ne ya amsa ya buɗe,ta haye kan gadon tace"Yaya ɗagaman bargo bacci zanyi"

Ya kalleta"inkinsha Ice cream ɗin zakiyi baccin ko"Yana maganai yana miƙa mata hannu alamar tazo.

*AUNTY HALILOSS**👑ROYAL WRITERS ASSOCIATION👑*

WA NAKE AURE?

             NA

     *Aunty Haliloss*

Wattpad

@AuntyHaliloss.


37


Matsowa tayi tasa Hannu ta anshi Ice cream ɗin,ta fara sha Areef kuwa ya kuya mata baya,Saudat ta sha ta ajiye,taja bargonta,Areef kam kasa shan nashi yayi,wani irin yanayi yakeji,robar ya ɗauka ya miƙe tanajinshi yakai ƙofa,ɗaga bargon tayi tana kallonshi,dai-dai lokacin shima ya juyo yana kallonta"baki da Matsala dai ko?"


Ya tambayeta cikin rashin sanin abinda zaice mata,Saudat ta kaɗa mashi kai alamar babu,Areef ya shige ɗakinshi,saidai yau kam bacci yayi mashi nisa,yau yanason kasanvewa tare da Abin ƙaunarshi,saidai wata zuciyar tana raya mashi yabarta ba yanzuba,don gani yake kamar bata gane kurantaba.

Saudat kam mamaki take,wai Yaya Areef babu ruwanshi da ita,har gaya zatayi kwana Biyu a gidan,wannan dalilin yasa ta fara rayawa zuciyarta,babu soyayarta a zuciyarshi,wata zuciyar kuwa tace kodan yana ganin zawara ce,kamar yadda matarshi tace,tabbas wannan magana ta Ni'ima ta ɗagawa Saudat hankali,Sai dai hartayi bacci batada wata mafita acikin lamarinta.


Da Asuba kuwa Areef baizo tadata ba ganin jiya ta tashi da kanta,Saudat kam koda tayi Salla bata koma bacciba,zuciyarta sai saƙa da warwara take mata,tagaji da juyi ta miƙe ta fito ta fara gyara gidan tsab tasa turaran ƙamshi,ta koma kitchen ta ɗora break fast,wajan 8 tagama komi,ta gera kan table,ta koma ta gyara ɗakinta,ta shiga tayi wanka.+


Zama tayi tana shafa mai,ga mirrow dake gabanta,kallon kanta kawai take,tama kasa ida  shafa man,candai taga hakan bazai fishsheta ba,ta cigaba da abinda take tana gamawa ta ɗauki atamfa,riga da sket,ɗinkin ya anshi jikinta sosai,ta ɗora ɗankwalin ta kawo turaruka ta sakawa jikinta,komawa tayi tana kallon mirow ita kanta tasan tayi kyau.


Tana saka takalmi zata fita Areef ya turo ƙofar ɗakin tare da Sallama,ta amsa tana faɗin,voil ne jikinshi fari,kana ganin farar singlet ɗin dake ciki,Agogon Hold dake hannunshi silver ce kanshi babu hula,yayi kyau matuƙa "Yaya ina kwana"


"How was your night"

"fyn"

"zanje Office"yace yana ɗan juyawa zai fita,Saudat ta ɗanbi bayanshi dan batasan miye zatace ba,Har sunkai Falo tai ƙoƙarin faɗin"Ga break akan table fa"


Ya juyo yana ƙara kalonta,danshi kanshi ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,saidai kawai yana daurewa ne"Idan nake Office zanyi"


Ran Saudat ya ɓaci wato kwana biyu da tarewarta zai tafi Office ba wani hutu,take ranta yaɗan sosu wani kishi yazo mata,ganin taɗan ɓata fuska yace"ya akayi"


Saudat tayi Saurin dai-daita Nutsuwarta,"a'a to ko katafi dashi sai kaci acan?"


"ina Sauri na makara"Yana maganai yana kaiwa ƙofa"

"Allah yabada Sa'a"


"amin" ya faɗa,yana fita ɓangaren Ni'ima ya shiga,zaune ya sameta kan capet,suka gaisa Areef yace"zanje Office baki buƙatar wani abu"


Ni'ima ta kaɗa kai,tana dariyar Mugunta a zuciyarta,tace"A'a saika dawo ya Amarya"


Yana kaiwa ƙofa yake faɗin"lafiya lau".


Tunda Areef ya fita Saudat ta kasayin komi,ɗakin ta koma kan gado ta faɗa tana kuka,Sosai zuciyarta ke mata zafi,saida tayi mai isarta,sannan ta miƙe taje ta zuba Omelet a plate.


Falon ta dawo ta zauna da lemo a cup,tana cin wainar kwan Ni'ima ta shigo part ɗin,tana Sallama,Saudat ta amsa,tana gyara zamanta"sannu da gida"


"yauwa ina kwana?"


"Break kikeyi,ashe kingama naga Kuma yaje part ɗina Yayi kalaci,Nayu tunanin baki idaba"


Wata mutuwar zaune Saudat tayi"eh lokacin bangama ba kuma yana Sauri,ki zauna mana"


STORY CONTINUES BELOW

"a'a ba zama nazo yiba,kashe din hakan nakawo maki,bazai yiwukina aiki,ni in dama abinci inbashi yaci ba,kodai ki ringayi da wuri kokuma ki gaya mashi kada ya ƙara jeman part yana cin abinci ranar girkinki"


Saudat ta kalleta,itafa bata iya irin wannan abunba,sabd tagane kishine,dan koda tayi zama dasu Mama ba haka suke mata ba sai munafunci,Saudat tace"to ai wannan koke zaki iya gaya mashi"


"au haka kikace nakawo maki magana zakice haka,to wallahi ki shiga hankalink...."


Saudat ta miƙe ta shige ɗakinta,cikin zuciyarta tace nayi zama da Mama balleke ƙaramar ƴar rainin hankali,Ni'ima ta juya ta fice,haushi takeji dan so tayi Saudat ta ɗauki maganai.

Sai wajan 11 ta fito,kitchen ta shiga tama rasa miye zata dafa mashi fried spagetti with liver Sop tayi ,tana gamawa tayi ganishing slad ta saka a frij,ta jera Sauran kulolin kan dinning sau lokacin ta fiddawa masu gadi Sauran break ɗin dan itama ba wani ci tayi ba sosai.


Ƙarfe ɗaya tagama komi,ta gyara kitchen ɗin ta goge,ta ƙara gyara falon ta saka abin ƙamshi,ba ɓata lokaci gidan ya ɗauki ƙamshi.


Hanyar ɗakinta ta nufa domin yin wanka,har ta shiga ta tuna da ɗakinshi,zata fito kuma ta koma,sauri taƴi tayi wanka,ta saka doguwar riga jallabiyace bata kama jikinta ba,ta ɗauko ɗan kwalin rigar ta yafa,ta kalli kanta a madubi,sosai tayi kyau saidai bata shafa kwalliba,ɗauka tayi ta shafa,tasa turare ta fito ta nufi ɗakinshi.


Kamar kiya yauma babu dirty,gadon ta gyara,ta shiga toilet ɗin,wajan coridor ɗin toilet ɗin ta tsaya ta buɗe laundry basket,singlet ɗinshine 2 set a ciki da boxers harta rufe kuma ta kwasa ta nufi toilet ɗin dasu,wankewa tayi,harda towels ɗinshi,ta shanya kan dryer ta gyara toilet ɗin,tasa freshner ta fito.


Magic coal tasa a kasko,ta aza kan bedside locca,ta zauna bakin gadon hannu tasa ta buɗe locca ɗin,chocolate tagani ta jawo tana ɗauka,ta ɗora kan cinyart taja ƙafafunta ta maida kan gadon,ta miƙesu,ɗauka tayi ta buɗe tana sha,sosai yayi mata daɗi.


fulo tajawo ta jingina dashi,gaba ɗaya tama manta ɗakin Areef take,ta ƙara buɗe ledar wata chocolate ɗin Areef ya shigo ɗakin da wani file a hannunshi.


Kwata-kwata bataji buɗe ƙofarba,ta saka a bakinta,Areef ya tsaya yana kallonta,tayi mashi kyau sosai,yau kuma shigar larabawa tayi,Sallama yaƴi gudun kada taji tsoro ko tayi tunanin kallonta yakeyi.


Da sauri ta ɗago,ta ajiye container ɗin ta sauke ƙafarta,"sannu da dawowa"


"yauwa ya gidan"


"lafiya lau tace,ta buɗe tana gyara pilon data jingina,ta ɗauki Kaskon abin wutai,lokacinma harya cinye"ina zakije?"


"zan maida kitchen ne"

Bayaso ta fita,hakan yasa yace"barshi anan"


Batayi musuba ta ajiye,ya  aje takardun hannunshi,ya zauna yana cire takalmin ƙafarshi saboda rufaffine,tasan sarai wanka zaishiga,hakan yasa tayi hanyar tafiya"ina zakije"ya ƙara tambaya,Saudat tace"ɗaki zani"


"ok dawo ɗauki chocolate ɗin"

Kunya taɗanji,dan ta taɓa mashi abu,kuma har cikin locca ya aje ba samaba,ta koma ta ɗauka,ya kalleta yace"akwai sweets acan ki ɗauka"


Saudat tace"a'a Wannan ya isheni"ta fice,Areef yarasa gane kalar ƙamshin da yakeji a ɗakin gadai ƙamshin jikinta ga kuma turaran data saka,jikinshi ya mutu sosai,dakyal ya iya miƙewa ya shiga toilet ɗi,Saida zai ɗauki toilet yaga bai gansu ba yaɗan juya sai lokacin ya kula dasu akan dryer,baisan lokacin da yayi murmushiba.


Jingina yayi jikin bango,yana kallon kayan,yau Saudat ce ta mishi wanki,ya daɗe fuskarshi ɗauke da smile,ya juya ya ɗauko wasu towels ɗin.

Saudat kam koda ta koma,ta ajiye chocolate ɗin,falo tadawo ta zauna,dan tafara tunanin yadda za'ayi idan ya fito,kada yaƙicin abincin,kallo ta kunna tanayi.


STORY CONTINUES BELOW

Tsawan 30mints sannan yafito,ƙananun kayane yasaka,blue jeans with sky blue polo shirt,yayi Kyau matuk'a,kuma kyan sun anshi jikinshi.

Bai zaunaba,yayi parking kan dinning ɗin,Saudat wani sanyi taji,ta miƙe ta nufi wajan,lokacin ya ɗaga plate,zai zuba abincin.


"let me help"baice komiba ya miƙa mata,ta zuba mashi abincin,ƙamshi ke bugun hancinshi,ta saka spon ta miƙe ta buɗe firij ta ɗauko ganished salad ɗin ta aje mashi gefe.


Spoon ya ƙara ya kalleta,itama shi take kallo"kici Dan ɗan Abincin da kikaci ɗazu bazai ishekiba,tunda ba kalacin kirki kikayi ba"


Saudat taɗan zaro ido,shi  ya akai yasan bataji abinciba sosai,to kodai Ni'ima tagaya mashi,ta ƙara kafeshi da ido,shikam Areef yasan yadda yaga tayi kafin yafita zaiyi wahala taci abinci.


Sosai Areef yaci abincin saboda yayi mashi daɗi,Saudat ta cire Spoon ɗinta,saboda ta ƙoshi,ta kawo kulai tasa seving spon ta ƙara ɗibar abincin ta zuba mashi.

Ya kalleta"kada ki ƙara na koshi"


Miya ta zuba tasa salad ɗin,ta miƙe ta koma falon,Areef ya ƙaracin abincin,sannan ya miƙe,baiyi mata magana ba ya fice,tasan dai bazai wuce wajan Ni'ima ba tunda bai ɗauki key ba.


Yaɗan jima sannan yadawo,ya zauna falon,yana zama wayarshi tana ringing,ya ɗauko"ello Amminah"


Saudat tayi mashi wani mugunkallo,ta miƙe taje inda yake,tsab yake kallon ta,zama tayi kusa dashi,tasa hannu ta anshi wayai"Amminah,kinjishi wai Amminshi"tana maganai cikin sagwaɓa.


"barshi ai jinshi kawai nake,daɗin baki zaiman"


Saudat ta langwaɓar dakai side ɗinshi,kan kafaɗarshi yadda takewa Ammi"Ammi ina kewarki"


"nima haka ƴata,nasan idan Khairi takoma skul zanji ba daɗi"


Tanajin Sultan yana hayaniya,Ammi tace"zoga Momy"


"Hello Momy"

"Sul yakake"

"Momy inata nemanki,bangankiba,Ammk tace kina wajan Uncle,jiya nace yazo dani Ammi ta hana"


"Ayya ai nakusa dawowa"


"yee Momy Ball ɗina ya fashe kizoman da sabo"


"kai ni barni,nice zan kawo maka Ball ɗin,nice nake saya maka dama"


Tunda Saudat ta aza kanta kan kafaɗarshi,yakasayin magana dan yana gdun kada ta tashi,saidai jin tayiwa Sultan haka ya anshi wayar"Father live her,i will buy another one for you"


"thanks Uncle i love you"


Areef yayi dariya,Saudat ta janye jikinta,ta kalleshi,basarwa taƴi tace"ban gama magana da Ammi ba"


"ina wayarki?"

Kafin tayi magana Ni'ima ta shigo ɗakin,Saudat ta kalleta,ta maida kanta kan kafaɗarshi tasa hannu tana kiciniyar amsar wayai"Nawa ba chaji kabani naka plzzz"


Tana maganai tana hayeshi,shikuma ya janye  wayar ɗayan hannun,dan kwata kwata baiga Ni'ima ba,Saudat ta samanshi ta miƙa hannu tanason ansar wayar,saidai hannunta bai kaiwa,Dariya ya farayi mata,ta turo baki"nifa da naka zanyi,so kake katina ya ƙare"tana maganai tana wurgi da ɗan kwalin data yafawa kanta,gashinta ya baje,Areef yasa hannu yana janye mata daga gefen idonta.

Ni'ima wani ƙululu ya tsaya mata,tace"Ashe kadawo tun dazu baka shigaba"sai lokacin yaganta,Saudat ta zame jikinta tana dariya a zuciyarta,tace"Sannu da zuwa"


Areef yace"eh Nadawo shigo ki zauna"


Saudat tace"bari in kawo maki abinci"

"A'a barshi,yadda ya baki nima yabani,basai naci naki ba"


Areef ya gyara zamanshi ya miƙa ma Saudat wayai yace"Nashiga ina tunanin lokacin kina wanka"Yayi hakanne danya kauda maganai data ɗauko zata fara,itadai haka take,rayuwar Areef ya tsani ƙananun maganganu,shiyasa ko part ɗinta baya son zuwa yanzu.


STORY CONTINUES BELOW

Saudat ta miƙe ta ɗauko mata lemon pepsi,da cup ta ajiye mata,Ni'ima tace"Nagoshi ai yanzu Baby baya barin shan pepsi saidai milk drinks"tana maganai tana wani kisisina


Saudat tace"Ayya to"ta ɗauke lemonta ta maida firij,Areef kam yasan ko cikin week ɗinnan saida ta matsa mashi akan ya ƙaro mata minerals dayawa.


Saudat ta koma ta zauna tana ɗaukar selpi da wayarshi,ƙarar wayar kawai kakeji camera na bugawa,kat-kat-kat,gaba ɗaya ta fita harkarsu,sai gyara styles ɗin pic ɗinta take.


Ni'ima taji haushi sosai,wani kishi ya ziyarceta,ta miƙe"ni zan tafi ai dama kai kace murinƙa zumincin,to yanzu gayanan,nazo ta wulaƙantani,tacigaba da wani ɗaukar pic,ai dama haka rayuwa take saika gama Rainon mutun daga baya yazoya nuna zai wulaƙantaka,badai kamar idan ya aure maka miji.


Saudat ta sauke wayar,tayi niyar bata haƙuri saidai kuma ta ɓata maganarta,fan zaman da sukayi shine take cewa tayi renonta,Areef ya kalli Saudat,lokacin Saudat ta maida dubanta kanshi,Ni'ima kuma taƙi tafiya jira kawai take taji mizaice.

Saudat tayi saurin cewa"wallhi ba haka bane kawai dai naga kamar fira zakuyi shiyasa,Amma kiyi haƙuri"


Tana faɗar haka tayi shiru,Ni'ima tace"ai dama hakane,matsalar auran zawarawan da idonsu ya buɗe kenan,a mai....."


"wai ba inaji ta baki haƙuriba,haba kinsan yawan maimaita zance ke kawo rigima,duk wanda ya baka haƙuri to kamar ya rufe bakin kane...."


"kaidai wallhi yanzu bakasan gaskiya,dandai kawai tana ƴar uwarka,Amma"


Saudat ta miƙe tabar wajan ta shige ɗakinta batasan yadda suka ƙareba,wayar Bilƙy ta kira tana bata labari Billy tace"kam aikam akwai matsala dun kishiyar dake maka irin haka batada daɗin zama,kuma wata rana dole tayi maka maƙirci"


Saudat tace"ni wallhi baniso tana shigoman part"


"aikuma idan kikace zaiga laifinki,zaice kin karya mashi doka,kedai kawai kada kije sashenta"


"Amma wallhi maganganun da takeyi sun fara isata"


Sun jima suna tattaunawa,kafin sukayi bankwana,ta ɗauki wayarshi tana duba pics ɗin da tayi,ita kanta sunyi mata kyau.

    *GIDAN MAMA*


"Ke wallahi Mama bar ganin nasamaki ido kinaman yadda kiga dama,ko Hayatu daya ajiyeni a gidan nan bayamin wannan abin in ƙyaleshi"

Zubaida tayi shewa tace"Nusaiba barta,tayi mai isarta ɗanta yadawo tasan yadda zatace mashi"


Mama dake zaune mie da ƙafa tace"nidai bazan iyayin girkin nan ba,ni kaɗai nasan yadda ƙafata keman ciwo"tana magana duk fuskarta ta ƙoje ta ƙara duhu.


Hayatu ya shigo gidan,Nusaiba ta gaya mashi"to basai ki zauna kaman kukera kiyi girkinba,duka cikinsu waye zai maki sanwa"


Usman ya shigo hannunshi riƙe da leda,Zubaida ta miƙa mashi hannu yace"wannan na Mama ne"


"ashema Mama to wannan ƴar ledar bazata isheniba balle in bata har leda ɗaya,indai na ƙoshi na bata sauran"tana magana ta shige ɗaki,Usman ya zauna branda yana dafe kai,dan gaba ɗaya wannan halin da suke gidansu ya isheshi,shiba haka yayi zama da Saudat ba,ko lokacin da bashida halin sayan wani abj bata damuwa,amma ita wannan eanda zataba mahaifiyarshi abu ya gagara,gaya bashida ikon yin magana,yanzu wani dana sani yake zo bashi,saidai har lokacin yana ganin laifin saudat na kawo mashi wani a ɗaki,hawaye yaji sun zo mashi.


Mama ta tashi tana ɗangisa ƙafa,data goce garin yawanta,dan zaman gidanma gagarata yake sabda bala'in da su Nusaiba ke haɗa mata,gaya dama tuni sun ɓata da Haule.


Zubaida ta fito da mayafin ta akai,ta kalli Usman tace"na tafi gida sai dare zan dawo"


Batakira cewar shiba tafice,Hayatu kam yanzu baki ya mutu,Zubaida ta gyara mashi zama,bashida abin cewa a gidan,dan yanzu tasan mijinta ne ke cidasu.


STORY CONTINUES BELOW

Shikan duk sana'ar daya fara,sai abin yatsaya,yanzu shine ɗan zaman banza,gaya mutane sun daina ganin mutuncinshi.


Haka Mama ta kama aiki,ga ƙafarta na mata ciwo,ga hayaƙi,ga bala'in da Nusaiba take mata kada tayi masu ƙazanta,saikace ita ɗin mai tsab tace.

           *****


Har Ni'ima ta anshi girki,Areef babu abinda ya dameshi da Saudat kuƙawa yana nuna mata,wani lokaci kam har suɗanyi fira idan dare yayi ya shige ɗakinshi.


Duk wani adalci Aréef yanayi a tsakaninsu,baya bati ɗaya taga yafi san ɗaya,saidai kawai Ni'ima da take rikita mashi gida,tabbas yasan zatayi hakan,sabda kafin auransu tayi balle yanzu.

Ƙarfe tara na safe ya shigo gidan,yayi shirin tafiya Office,saidai kuma Ni'ima tana bayanshi,Areef yakalleta lokacin tana goge center table ɗin dake falon.


Sosai tayi mashi kyau saboda rigar dake jikinta ba nauyi gareta ba"Ya Ina  kwana"


"kin tashi lafiya?"


"lafiya lau,Ina kwna"ta gaida Ni'ima dake wani shan ƙamshi.


Saudat ta kaudakai,yace"bakida Problem"


Jim taɗanyi,tama rasa abinda zatace"a chocolate ya kare"


Dariya yaɗanyi"shikenan saina dawo"


Saudat itama taɗanyi dariya,ta ƙara matsowa inda yake"Allah kalar wancan nakeso"


"zan sawo maki,saina dawo"


"Watoma har chocolate ma zaka sawo mata,Hajiya ai saiki bari sai ranar girkinki sannan ki nuna mana isa,bawai yau yana kwana na ace za'a kawo maki wan...."


Saudat ta ɗanyi murmushi"nidai kada ka manta plzz"


"ok"yace yana juyawa,Ni'ima ta tareshi"ai wallahi bazaka sawoshi ba,cuta ƙiriƙiri,na rantse da Allah kinyi kaɗan a sawo maki..."tana maganai tana nufar inda Saudat take,Areef yayi saurin ruƙota,baida abin cewa hannunta kawai ya riƙe ya juya suka fice.


Wajan Mota ya tsaya da ita"ki daina Ni'ima banason wanann halin,banaso,plzzzzz"yana maganai daka gani kinsan takaishi end.


"taya zatace ka sawo mata chocolate ranar girkina,ai dama wallahi tun kafin auran nan,nasan ba ƙaramar cin amana zakuyi man ba,ai dama nasan tana sanka"


"Ni'ima babu laifi dan kina girki na sawo mata abu,ke nawa na kawo maki,baki taɓa cewa yau bakece da girkiba,kuma"


Bata tsaya sauraron shiba,ta wuce part ɗinta cikin fushi,ya tsaya yana kallonta kafin ya shige mota yayi tafiyarshi.

Saudat kam ta cigaba da aikin gabanta,ita kanta ita tasan abinda takeji a zuciyarta,ina riwanta dan zaizo wajanta sai kishiƴa ta biyoshi.


Tana zama Ni'ima tana dawowa part ɗin,"wallahi kishiga hankalinki bazan lamunta ba,mayaudariya,da kince baki sanshi,kinje kinga wahala kin kaso auran kin dawo wajanshi"


Saudat ta miƙe tsaye ɗan Ni'ima takaita ƙarshe"ke dakata,waike bakida labarin irin soyayyar da Areef yayi mani,ko bai faɗa maki irin rashin lafiya da ciwan zuciyar da ƴasha ba saboda rasani da yayi,kina maganar ni zawarace a hakan kuma yanada matar kamarki,yakoma yana durƙuso akan in aureshi,to ingaya maki,tausayinshi naji na aureshi,saboda idan har ban aureshi ba,to tabass zaki rasa miji"


Saudat nagama faɗin haka ta wucewarta,ta ja ƙofar ɗakinta,waɗannan maganganu sun ƙona ran Ni'ima,gaya bata tsaya itama ta maida mata amsa ba,Ni'ima ta fito tana huci.


           ****

Daran ranar Saudat zata anshi girki,duk ta tsaftace gidanta,sai ƙamshi ke tashi ita kanta tayi gayu da lace finta black mai ratsin ja.


Tana zaune ya shigo da ledoji a hannunshi,ta miƙe ta amsa,"Nop barshi"aje ya saka a kitchen yadawo ya zauna kan capet yana miƙe ƙafar.


Ta kalleshi"Sannu"tace dan taga akwai alamar gajiya a tare dashi,"Yauwa,su Ilham da Khairat basu zo ba?"


Ta ce"a'a zasuzo ne"


"i thnk so,dan jibi zasu koma skul,may be sai gobe"


Saudat ta miƙe plate ta ɗauka ta zub mashi abinci a dinning ta saka spoon ta kawo mashi,gyara zama yayi "ƙaro cokali"


Saudat ta zauna"ni bazan ciba" Aréef yaci abincin shi,yabarta,ta ɗauko mashi ruwa da lemo ya anshi ruwan yace ta maida lemun.


"Namanta na haɗa da wata leda,ɗauko ta a kitchen"Saudat ta miƙe ta tafi kitchen ɗin,saidai tana shiga aka ɗauke,Nepar gidan,dubu yayi sosai.

Saudat ta zare ido ga babu waya hannunta,da Sauri ta kwala mashi kira"Yaya hasko wayarka duhu"


Baice mata komiba ya mike ya nufi kitchen ɗin"Yaya" motsi ta jiyo ana tahowa,da Sauri ta zabura ta baro kitchen ɗin dai-dai ƙofa sukayi karo dashi ta fasa ihu zata ruga,Areef ya ruƙota yayi haugging ɗinta"kada kije kiji ciwo fa"


Jin shine,yasata sauke ajiyar zuciya danta tsorata,shikam ya kasa sakinta,sosai ya riƙeta gam,wajan kunnanta yake mata lumfashi sama-sama,take ta fara rikicewa tana janye jikinta,dai-dai lokacin haske ya gauraye falon.

Areef yace"zakije kijiwa kanki ciwo"


Yana magani ya saketa,yana riƙe hannunta,dan baigaji da jinta a jikinshi ba,Saudat ta janye hannunta takoma kitchen ɗin ta ɗauko ledar ta kawo mashi.

Areef ya anshi ledar ya nufi hanyar ɗakinshi yana faɗin"gud night"


Mutuwar tsaye taƴi,ta juya ta ɗan zauna falon,can kuma ta miƙe ta shigewarta nata ɗakin.


Washe gari su Ilham sukazo,sunsha wuni,saidai suna maƙale da juna,hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Arewf ba,dan ji yayi kamar yaran su zauna a gidan.


Sunyu bankwana,Areef zai kaisu,Saudat tace"zanje"


Ya zaro ido"ba ruwana,Dady faɗa zaiyi idan mukaje"


"ai sai in boye"


"a'a ki zauna,zan kaiki"

Saudat ta fara turo baki,Areef ya ruƙota,ba ƙaramin Kyau tayi mashiba,Ilham tayi dariya"kai Aunty wallahi sai ki..."


Bata idaba Areef ya kamo wuyanta yaɗan kifa jikinshi,saboda tsawo daya ɗan fita,wuyanta da kuma kunta yayiwa pick"ki jirani bazan jima ba"


Kasa motsi Saudat tayi harya fice saboda ganin abinda zai mata su Ilham suka fice suna dariya,hannu tasa tana shafa wuyanta da kumatunta,da Sauri ta shige ɗaki tana kallon madubi,sai duba wajan take tana smiling,yau Yaya Areef yayi kishin ɗin ta.


            *****

Sunkai Sati Huɗu babu wani labari tsakanin Areef da Saudat,nanfa hankalin Saudat ya ƙara tashi,baidai kamar idan ta tuna yana tafiya wajan matarshi,ta zauna tayi kukanta mai isarta,nanta kama neman mafita saidai har lokacin bata samuba.


Waya takira Billy akan tazo,ranar kau sai gata tazo,sunsha fira sosai,Saudat ta kokanta mata abinda ke danunta,Ita kanta tayi mamakin Areef ace duk san da yakewa Saudat amma hakan ta faru"kinsan Allah kawata Yaya Areef yana sonki,And wallhi baxai iya rabuwa dakeba,kawaidai yana hakanne shi adole hukunci yake yi"


Saudat tayi ajiyar zuciya"keni nagaji,kuma fa yaje wajan matarshi nikam.."


Raɗa suka komayi,banajin abinda suke cewa Saudat tace"bari in baki transper sai kiyi Amfani da kuɗin,gaskiya ina sonki ƙawata"


Nan hankalin Saudat ya kwanta,Billy ta tafi gida.
*kubiyoni muga shawarar Bily shantali*


*Aunty haliloss**👑ROYAL WRITERS ASSOCIATION👑*

WA NAKE AURE?

             NA

     *Aunty Haliloss*

Wattpad

@AuntyHaliloss


38


Zaune take saman capet Areef ya shigo gidan,Saudat ta ɗago ta kalleshi,manyan kayane yasa,ɗinkin bashida tsawo sosai,shadda ce ruwan kwai,tayi mashi kyau sosai.+


Saudat ta kalleshi"ya dare"


"Lafiya ƙlau,baki kwanta ba?"

"eh" tana maganai ta miƙe domin kawo mashi ruwa,ya zauna saman hannun kujera,Saudat taje ta kawo mashi ruwa a glass cup,Hannu yasa ya amsa ta zauna saman kujera,yasha ya aje cup ɗin saman ƙaramin side table ɗin kujerai.


Ya ƙara maida kallonshi kanta,itadai kullun kyau take ƙarawa,yau Ni'ima ce da girki,hakan yasa ya miƙe"zan tafi,ina fatan ba Matsala"


Saudat ta tashi itama"a'a babu,said....."


Bata ida ba Ni'ima ta turo ƙofar,tana masifa"to Wallahi a gidannan sai an canza zama,taya zan zauna jiranka kazo nan kayi zaune,bayan kasan nice da girki,Ni wannan abu bansan irin shiba,ka zauna kanawa zawara irin wannan zaɓolaka,zawaraima wadda ta taɓa haihuwa,amm...."


Areef kam kallon Ni'ima yake sai lokacin ya aza mata hannu saman baki,Saudat ta ƙara matsowa ta kalleta,Allah yasani Ni'ima ta kaita ƙarshe,ta kalleta"kinsan duk inda akace maki matar so,to tabbass saidai ayi haƙurin zama da ita,tun yaushe nake cemashi ya tashi yazo wajanki amma yakasa,ina tunanin shifa baisan ni Zawara bace,saboda baiji alama ba,kinsan da yawan zawarawa sunfi matan gidan,nasan wanann dalilin yasa yake liƙe dani  ko"


"kambuuu to wallahi ke baki isa kice kin fini ba,keɗin banza"Ni'ima tana maganai tana nufar Saudat,Areef yasa hannu ya riƙeta"kada ki fara"


Ya maida hankalinshi kan Saudat"je ɗaki"


"wallhi babu inda zani ka saketa,na Rantse da Allah saita gane batada wayo"


Ni'ima ta matsa,tana shirin isa inda Saudat take saidai Areef ya riƙeta,sai ƙoƙarin anshewa take Areef ya daka mata tsawa"ke wai miye haka,ke yanzu idan na sakeki ,zaki iyayin wani abune,baki ganin yadda kike,ko baki jin nauyin jikin ki"


"shikenan dan inajin Nauyin jikina,zan zauna kamar wannan yarinyar tana raina man hankali"


Saudat ta samu kujera ta zauna,harta zauna haushi ya ƙara kamata,ta miƙe taje wajan ta riƙo hannunshi"dan Allah ka saketa"

Harararta yayi dan yaga yadda ranta ya ɓaci,"bar nan"cikin tsawa yayi mata magana,ta juya ta zauna,ya kalli Ni'ima yace mata"wuce muje"


Saudat tana kallo yajata suka fice,Tunda suka shiga part ɗin Areef ke zuba ruwan bala'e akan Ni'ima ta rainashi,faɗa yake mata sosai amma ko a jikinta,ƙarshema cewa tayi tunda ya goyi bayan ƴar uwarshi,to yanzu ta fara.


Saudat kam wani mugunhaushi takeji,itakan wannan Zawara da Ni'ima take faɗin ankawomata yana mata ciwo,dogon tsaki taja ta miƙe ta shige ɗakinta.


Washe gari Billy tazo giɗan,ledoji ne niƙi-niƙi tazo dasu,Saudat ta kalleta,suka fara buɗe kayan,"kewai duk ina zankai kayan nan"


Bily tayi dariya"ai kinsan idan kikasa banaso ki maimaita"

"Amma ƙawata ƙara kuɗi kikayi"tana maganai tayi dariya ta ɗaga wata ƴar riga,wadda iyakarta cibiya,"haba wannan saikace ta jaririya" harararta Billy tayi"Allah english wears ɗin ni kaina sunman kyau"


Saudat ta miƙe"bari inkai cikin wadrop,"saida Billy ta kama mata sanann.


Suka dawo falon suka zauna,suna ƙara fira Areef ya shigo"a'a yau kuma baƙi garemu"


Billy tace "wallhi kuwa" Nan suka gaisa sosai ya sakar mata fuska,kujerar da Saudat take sama ya zauna yana mintsilinta,tayi saurin janye jikinta"kai Yaya da zafi"


STORY CONTINUES BELOW

"Nasani ai,babu sannu ko" Saudat tace"sannu da zuwa"


Billy tace"baka cin miƙe,tunda saida ka tambaya" dariya yayi yace"yes"


Saudat ta miƙe,ta ɗauko mashi lemo,yasha,tace"Abinci a dinning"

"ba yanzu ba"

Ta zauna,yasa hannu ya taɓa cikinta,dagani bakici  Abincin ba,Billy tace"aikam ni ɗaya naci"


Ya juya ya kalleta,ta kauda kai,yaɗan jawo hannunta,ya matse"ban hana zama da yunwa ba?" Saudt ta marairai ce,ko yaushe ma yahana zama da yunwai,tasan duk abin nan da yake wai dan kada Billy ta gane wani abu,itakam Billy kallonshi kawai take,dan kamar tayi dariya,wai ita zaiwa duniyanci.


Billy tace"bari in tashi in tafi"


Areef ya miƙe"A'a kiyi zamanki,ni xan fita ne"


Yana maganai yana tafiya,har yayi hanyar waje ya dawo ya shiga ɗakinshi bai jimaba ya fito,kuɗi ya miƙawa Saudat"ki bata tasa Mai a mota"


Billy tace "a'a" Saudat ta ansa,Areef ya tafi,Billy tayi mashi godiya.


Yana fita Billy tace"kai yayan nan naki akwai abin dariya,waini zaiwa basaja"


Saudat tayi dariya"ai wallahi harna ƙagara jibi tayi in koma Office"


Haka sukaita fira Billy ta tafi gida,Saudat kam kodata shiga ɗakin kayan tacigaba da dubawa,wasu mahaukatan ƙalanan kayane Billy ta kwaso mata,Saudat ta ɗaga,tace kai wannan dukda mijinka zaka sawa akwai kunya,wata zuciyar tace to zauna jin kunyar,ke zakisha wahala.


           ****

Washe gari Saudat tun wuri ta tashi tayi masu kalaci ta koma ɗaki tayi shirinta dama ga gidan sai ƙamshi ke tashi.


Boneshot ne jikinta sai wata vest bata rufe cibiyarta ba,dukansu red colour ne,tsayawa tayi bakin madubi tana kallon kanta,kwata-kwata wandon iya karshi rabin cinyarta,rigar takama jikinta sosai shape ɗinta ya fito.


Dariya tayi ta zauna dan itakam kunyarma fita takeyi,wadrop ta bude ta ɗauko wata boyfriend jacket black ce saidai sharara take kana ganin jikin mutun,ɗorata tayi saman kayan,saiɗai batasaka hug ɗin gaban ba,a buɗe ta bari.


Turare ta saka ta saki gashinta a baya,ta kalmi ta saka,ta nufo hanyar falon,saidai ta rasa abinyi,harta zauna ta miƙe ta shiga kitchen ɗin.


Tea ta haɗa tazokan dinning tana saka sugar,Areef ya fito daga ɗakinshi,tana jin rufe ƙofar gabanta faɗuwa kawai yake.


Baya ta juya,Areef ya kalleta,yaɗan tsaya kafiɓ ya ƙare mata kallƙ har ƙasa,Saudat ta ɗako cup ɗin ta juyo,Areef yayi Saurin tahowa,saida yaga ta kauda kanta,kafin ya kallita dreesing din ya anshi jikinta sosai,kasan cewar ba wani jikin kirkine da ita ba.


Saudat taja mashi kujera,tana faɗin"Ina kwana"


Areef kam lokacin yagama ruɗewa da kyan datayi mashi dakyal ya iya faɗin"How are you?"


"fyn"tace,ta aje cup ɗin hannunta,gaba ɗaya ba abinda ta kawo kan dinng ɗin,sai lokacin ta shiga kitchen ɗin ta fara kwaso kulolin.


Areef kam kallonta kawai yake badai kamar idan ta juya tatafi,yadda Hip ɗinta ke juyawa,gaba ɗaya yarasa abinda zaiyi,gudun kada taga kamar kallonta yake,ya jawo cup ɗin tea ɗin data aje ya fara sha.


Kodata gama,ta gabanshi tadaw tana fuskantarshi ta zuba mashi fried yam with egg and kidney soup,ya kalleta,lokacin ta ɗago tana kallonshi"Yaushe kikace xaki koma aiki?"


Saudat taja kujera ta zauna,ta miƙa mashi spoon ɗin"monday ne"


"Allah yakaimu"ya ɗauki spoon ɗin yafaracin abincin,gaba ɗaya yarasa sukuni,itakam Saudat k a jikinta,taci abincin sosai,Areef yace"yau zan taho da Sultan"


STORY CONTINUES BELOW

Saudat ta kaɗa kanta"a'a Yaya kabarshi wajan Ammi can yafi kusa da Skul ɗinsu,sannan ita kanta Ammi yanzu gidan shiru zai mata"


Tana maganai tana miƙewa,takawo ruwa ta ake mashi,ya ɗauka yasha ya miƙe"Ai dama Ammi tasaba zama babu kowa a gida"


Saudat ta miƙe itama,ya ƙara kallonta"Nidai nace kabarshi can"


Bai jira cewarta ba yafita,tace"saika dawo"


Tana konawa ɗaki,tasan tabbas saiya ɗauko Sultan,itakam batason yaronta yazo ga kuma Halin da suke da Ni'ima ƙarshe ta ringa yiwa yaran gori.


Waya ta ɗauko ta kira Mami ta gaya mata,sannan ta fahimtar da ita yadda suke da Ni'ima yanzu,Mami ta fahimta hakan yasa yana Office ta kirashi,sosai sukayi magana,saidai bata nuna mashi dalilin da yasa bataso sultan yakoma gidanba,hakanna Areef ya haƙura.


Ƙarfe Ukku yau yadawo,green Coloured rice da miya sai coslow,ta aje kan table da duk abin buƙata,ta kona ɗaki taƴi zamanta.


Baby Pink half gown ce jikinta,roba ce sosai,ta kamata,donut tayi da gashin kanta,rigai tanada wani buɗewa a gabanta,circle wajan breast ɗin,tayi kyau sosai.

Tunda Areef ya dawo yake ware ido bai ganta ba,ya shiga yayi wanka,yasaka ƙananun kaya,red chak shirt ce jikinshi,yadsaka white jeans,yayi kyau sosai shima.


Ya daɗe kafin ya fito,massalci yaje yayi sallar la'asar yadawo gidan,ya shiga wajan Ni'ima,lokacin daya koma part ɗinta tana jinshi,itama ta gama sallah ta cire jallabiyar data ɗora kan kayan,ta koma  ta ɗan kwanta.

Areef kam tsab ya tadda gidan,saidai yawanci yasan dataji shigowarshi take fitowa,harya zauna flon ya miƙe ya nufi ɗakinta.


Tana jiyo takonshi ta gyara kwanciya,kamar mai bacci,gaya rigar kanta iyakarta guiwa,shape ɗinta ya fito sosai,ta juyama ƙofar baya.


Areef ya shigo tanajin turo ƙofar,tsayawa yayi yana ƙare mata kallo,hip ɗinta ya fito sosai,kasa sakin ƙofar yayi,itakam sai sauki lumfashi take kamar baccin gaske.


Areef yafara tunin ko batada lafiya ne,shiga yayi ya tsaya bakin gadon,ya jima hakan,ya duƙa yasan hannu yana dafa goshinta,baiji komiba,yasa hannu kan wuyanta.


Saudat ta mirgina ta juyo ɓangaranshi,inda rigar ta buɗe yake kallo duk rabin na filaninta a waje,zama yayi bakin gadon,ya ƙara dafa wuyanta sosai,baiji alamar zazzaɓiba.


Saudat tasa hannu tana janye inda taji yana taɓata,kamar baccin gaske ya riƙe hannun,ta fara buɗe idota tana murtsukasu,ganin haka Areef ya ɗan jata jikinshi yana tadata Zaune.


"bakida lafiya ne?"


Saudat taɗan gyara zamanta"lafiyata lau,bansan bacci ya ɗauke niba"


Areef ya kalleta"kinyu salla?"

"eh" tana maganai tana miƙewa"muje kaci abinci"

Binta yayi da kallo,taje wajan shoe rag tasaka takalmi ta nufi hanyar,ba musu yataso ya bita,har suka isa kan Table ɗin bai daina kallon yadda take tafiya ba,ta xauna tayi serving ɗinsu,suna gamawa ta dawo falon ta zauna tana kallo.

Areef ya tashi ya koma kan kujera ya xauna,ita kawai yake kallo,gaba ɗaya tazama kamar yaran india ga yadda ta naɗe gashin kanta,gaba ɗaya itadai batason kitso.


Saudat ta juyo ta kalleshi,suna haɗa ido yace"wato shine kika gayawa Mami zan ɗauko Sultan ko"

Tashi tayi daga kishingiɗan da take ta harɗe ƙafarta"Ai nace maka can yafi kusa da Skul ƙara ya zauna can,gobema daga Office gidan Ammin zan wuce"


Harararta yayi ta kauda kai"to wayace ki wuce gidan Ammin?"


Bata kalleshi ba tace"Bakowa"


Ta miƙe ta shiga kitchen,ta jima kafin ta dawo,koda ta taho da plate ɗin fruit a hannunta,gabnta kawai yake kallo,gankn zata kalleshi ya kauda kai,ta zauna Ƙamshinta ya bigi hancinshi,ta bashi plate ɗin.


STORY CONTINUES BELOW

Sun jina a haka sannan akayi kiran Salla,Areef ya miƙe ya tafi massallaci,ita kuma ta shiga ɗaki domin gabatar da tata sallai.


Saudat tasan indai harya fita sallar magrib sai angama isha'i yake dawowa,hakan itama tayi zamanta,tana gama sallolinta,ta watsa ruwa ta saka kayan baccinta.


Areef kam yana dawowa,ya shiga part ɗin  Ni'ima,saidai ya taddata batajin daɗi,mararta tana ciwo,Asibity sukaje,taga likita,magunguna ya bata,shikanshi likitan yana tausayawa Ni'ima ganin cewa duka cikinta wata Huɗu da kwanaki,amma wani lokaci ciwan mara saiya matsa mata.


Koda suka dawo gida,Areef saida yaga bacci ya ɗauketa kafin yatafi ɓangaran saudat,saidai lokacin yasan tayi bacci,room ɗinshi ya shiga,sai ji yake kamar yake ko ganinta yayi amma bazai iyaba gudun kada tayi tunanin yanzu yana yawan shiga ɗakinta.


          ****

Tunda Saudat tagama haɗa abin kari,Areef ya fito da shirin Office,Saudat tagaidashi tana jan wuyan rigar jikinta kasancewar taɗan Sauka,kayan ya kalla,ya zauna yana faɗin"yakika tashi?"


"lafiya ƙalau" ba wanda ya ƙara magana cikinsu,suka gama break ɗinsu,Arewf ya miƙe har yakai falon tace"Yaya waye zai kaini Office ɗin"


Sai lokacin ya tuna da aiki zataje yau,ya juyo wandon likinta yake kallo skin tight ne sosai,ga rigai bata sauko ƙugunta ba"ƙarfe nawa zaki tafi?"


"mornng gareni,it's 8:30"


"Amma baki shiryaba?"Na shirya"


Areef ya kalleta"mi kikace?"yana maganai yana kalonta wato tama shirya,ya cike leɓo.

Saudat kam wata dariya takeji tace"eh nashirya kaya kawai zan saka"


Areef ya zauna kan kujera"10mint"


Tagane mi yake nufi itama tadawo ta zauna,ya kalleta"idan na tafi bazakije ba yau"


Saudat ta zaro ido ta tafi tana sauri hip ɗinta na juyawa,Areef ya jingina da bango yana ɗan dafe kai,ba jimawa ta fito tasaka doguwar rigar Atamfa ta yafa mayafinta har kai,tana saka wayarta a jikkarta.


Areef ya miƙe suka fito Hanyar part ɗin Ni'ima ya nufa,ja tayi ta ɗan tsay wajan motar,har ya tafi ya juyo"muje ki dubata batada lafiya"


Saudat ta bishi rabanda tashiga part ɗin,tun ranar da tabar gidan,aiki suka tadda tanayi,Areef yace"Sannu kinji sauƙi kenan?"


"eh"  Saudat tace"Sannu ya ƙarfin jiki"


"Lafiya lau" ta juya ta cigaba da ɗauke plate ɗin ta nufi kitchen,tana dawowa Areef yace"Zan tafi Office"


Ni'ima tace"aida watace ba lafiya daka zauna amma dayake nice ka..."


Saudat bata jira cewarta ba,ta juya tayi ficewarta dan batason a ɓata mata rai a banza,tajina tana jiranshi a wajan motar sannan ya fito suka tafi.


Office ɗinsu ya nufa ta kalleshi"ka fara ajeni mana,koka manta dani"

"ban manta ba"


Suna isa Areef ya fito,ya gewaya ya buɗe mata,itama ɗin fitowa tayi,key ɗin ya miƙa mata,"kije da motan"


Saudat ta amsa key ɗin"zan dawo in ɗaukeka ne"


Areef ya juya yana faɗin"muyi waya dai"


Saudat taja mota tanufi wajan aiki,gab take da makara hakan yasa tana zuwa studio ta shiga ta fara gabatar da shirinta,bayan tagama suka hau fira da Billy tana bata labarin yadda sukayi da Areef Bily tayi dariya"muje zuwa dai,ahankali"


Sai 1:30 ta fito tana yin signing ta kira wayarshi,ya ɗauka ta tambayeshi"na tashi zan biyo ne mutafi"


Areef yace"Ban gama ba,but muhaɗu gida kawai"


STORY CONTINUES BELOW

"Babu mota hannunka fa"


Areef ya lumfasa"eh a ƙafa zanzo"


Ta ɗanyi dariya,tace"sai anjima"


Areef kuwa tun 12 yabar Office ɗinsu,cikin gari suka shiga,copuning motoci suka gewaya sun jima kafin yasamu wata tsaddar mota,fara ya sai mata.


Areef dakanshi ya tuƙa motar zuwa gida,yana fitowa yaje ya duba Ni'ima sannan ya shiga part ɗinta.


Tana jinshi ta ɓoye toilet da wayarta,leƙaw yayi ko ina baiganta ba,ya yana ta kiranta,tayi shiru,tanajin ya shigo ɗakin ya fita,yakoma falo ya zauna,wayarta ya kira ta ɗauka"Hello"


"yakk"


Bai bata amsa ba yace"Kina ina"


"ina gidan Ammi"


Areef ya ɗaure fuska "au gidan Ammin kikaje ko?"


saudat taɗanyi shiru,yace"to maza ki taho gida fita zanyi da motata.


Saudat ta kashe wayar tana dariya,ta kalli mirrow ta gyara zaman rigar jikinta dan batada hannu kamar vest take saidai tana da kwari,dogon wandon jeans ne jikinta ya kamata sosai,dan da kyal ta sakashi,tasha wahala sosai wajan sakashi,amma bata fasa sawa ba,taja rigar ta rufe ƙugunta,ta ɗauko wasu takalmi sunada tudu ta saka.


Wani glass dake cikin lefen da yayi mata ta ɗauko ta azawa face ɗinta,tayi kyau sosai.


Wayarta ta ɗauko da car key ɗinshi ta fito,remote ne hannunshi yana kunna t.v,Saudat ta fara magana"Yaya ga Key ɗin"


Gaba ɗaya baiyi tinanin tana gidanba,saurin juyowa yayi yana kallonta,wani shock ya shiga don ganinta yayi kamar a fashion t.v,ya kasa kauda idonshi.


Gewayowa tayi ta zauna tana jan rigai baya,tana rufe mazaunanta,Areef ya kalleta ji yake kamar ya ruƙota,baisan yanayin da zuviyarshi take mashi ba,yasa hannu ya anshi key ɗin,yana haɗawa da hannunta"kika ce kina gidan Ammi"


"a'a kawai dai Nafaɗi ne,saboda inason zuwa"


Kallon ta yayi kamar yasa hannu ya riƙe booms ɗinta,dakyal ya iya sakin hannunta yana faɗin"gobe sai kije"


"Yeeee" tace tana jijjiga jikinta alamar murna,tana komawa ta zauna kan kujera,kafin ta tashi ta tafi ta saka mashi abinci a plate takawo mashi,gayadda take tafiya daka gani kasan wandon jeans ɗin ya takurata.


Areef ya fiddo wayarshi,silent yasaka fa ya shiga cemera,taje ɗauko mashi ruwa,ya farayi mata vedio,saida yaga ta dawo ya kauda wayar yayi saving.


Yaci abincin sosai,yana gamawa ya fiddo key ɗin sabuwar motar"ga wanann key ɗin motar tana waje,ki hauta kwana biyu kiga idan tayi maki"


Wani daɗi Saudat taji,saidai bataso ta nuna gudun kada yaga kamar dama  tanason hugging ɗinshine,shikam Areef ya bata key ɗinne dan yayi san He deserve a good hug,Saudat tace "lot of thanks,Allah ya ƙara ɗauka ka,ya tsare mana kai"


Yaji daɗin Addu'ar sosai,ta miƙe ta ɗauko dogon hijab ɗinta tasaka"ina zakije?"


Zanga Car ɗin mana,tana maganai tana dariya,shima ɗin dariya yayi the firts time da suka fara exchanging smile truly.


Shima ya fito sosai Saudat taji daɗin ganin motai,ta juya ta kalleshi"tayi kyau gaskiya"


Ta buɗe zata shiga Areef yace"Basmala"


Saudat tayi smile tace"Bismillahi tawakkaltu alalla"


Ta zauna Zata rufe Ni'ima ta fito daga Part ɗinta,Saudat na ganinta tace"gaskiya motar nan taman"


Tana maganai tana fitowa daga motai tayi wajan Areef,tight hug tayi mashi kafin ta sakeshi,ta kama hannunshi tayi mashi pick"Thanks alot really appreciated Allah ya ƙara ɗaukaka"


Areef baiga Ni'ima  ba,shikanshi yaji hug ɗin ya kalleta"Nagode da Addu'a"


Ni'ima ta tsaya tana kallonsu,Saudat ta kalleta"Sannu ya jiki?"


Ni'ima ta juya ta kalli Areef wanda shima lokacin ya maida hankalinshi dan ganinta,Hannu ta miƙa mashi tana riƙe ƙugu,ya riƙe hannun,yana matsawa,Ni'ima tace"bani nawa"


Areef ya kalleta"mikenan"


"inace motace ka bata?"


Areef tace"eh ai...."


"Bani tawa wallhi,dan Allah baka isa ba"


Saudat ta juya tana nufar part ɗinsu batasan yadda suka ƙareba,Areef har part ɗinta yayi lallashinta,akan cewa ai itama ya sai mata,tunda motar da take hawa shiya sai mata,Amma taƙi yadda,ƙarshe dai dayaga taƙi ji yace bazai sayaba.


Massallci ya tafi,lokacin daya dawo 9 takusa,Saudat tana ɗaki tanason cire wandon saidai ko ƙugunta yaƙi wucewa.


Zama tayi tana ja amma yaƙi,ta miƙe duk yadda tayi takasa cire jeans ɗin,ita kanta dariya takewa kanta cikin zuciyarta tace gayu da wuya.


Dakyal tasamu ta fiddashi zuwa cinyarta,nan ta zauna bakin gadon tana hutawa,ƙaramin boneshot ne jikinta,sai ƙokari fidda jeans ɗin take.

Areef ya shigo ɗakin,Saudat ta kauda kanta,tana jan wandon ƙasa ƙarfinta tasa sosai,saidai wandon baya matsawa.


Areef ya kalleta ya zaro ido"ya akayi ne?"


"babu komi"


Tacigaba da aikinta,dariya ta bashi sosai,ya daure ya riƙe dariyar,ya daɗe yana kallonta,tabar ta wandon ta ɗaga rigai ta cire daga ita sai brexia Areef kam gabanshi sai dukan tara-tara ƴake.


Ta koma tana son cire jeans ɗin abin ya gagara,Lokacin Areef ya harfe hannuwa a ƙirji yana kallonta.


Ta miƙe tsaye tanason zuwa wajan mirro taji zata faɗi,takoma ta zauna,Areef ya juya zai fita,Saudat tace"dan Allah ka miƙon rezo a cikin locca ɗin mirrow nan"tana maganai ta kauda kanta


Gumtse dariya Areef yake ya matsa inda take,ya tsugunna ya kama ƙafai,Saudat ta saki tana kallonshi,ya fara jan wandon,ƴa ɗago ya kalleta yana dariya dan yakasa riƙewa"waye ya saka maki"


Banza tayi ashi,ya juya yace"shikenan saiki fidda ina tambayarki zaki man banza"


Saudat tace"nina saka"


Dakyal Areef ya fidda ƙafa guda yana kallonta,ya koma ya zauna gefe,Saudat ta kalleshi"Dan Allah ka cire man Allah fitsari nikeji"


Areef ya kalleta,dariya kawai yakeso yayi,ya matso wajanta,ya kama ƙafar yana cire wa,dakyal yaja da ƙarfi,jeans ɗin ya cire zaiyi baya Saudat tasa hannu tayi Saurin ruƙoshi.*AUNTƳ HALILOSS*

*👑ROYAL WRITERS ASSOCIATION👑*

WA NAKE AURE?
             NA
     *Aunty Haliloss*

Wattpad
@AuntyHaliloss

*DEDICATED TO*
*Khairat Din mommy*
*UMMU Muhsin*
*UMMU HAIDAR*
*Maman Abeedah*
*Ummu irfaan*
*Zainab Ahmad*
*Lainat*
*ILYSM GUYS❤❤❤*

39

Areef ya ɗago ya kalleta yadda ta riƙeshi,da support ɗinta ya miƙe tsaye"kinyi dinner?"

Bata bashi amsaba ta shige toilet,yasan dariyar dayayi mata tabata haushi,ya fice ɗakin yana dariya.

Saudat kam wanka tayi ta shirya,kayan bacci ta saka,Ash colour silk,tasaka turare ta fito falon saidai bata ganshi ba,ɗakinshi ta nufa tayi Knowking,Areef yana kwance yayi shirin bacci,Saudat ta kalleshi,kayan sunyi mashi kyau sosai,cikin zuciyarta tace shidai yanason white pygamers.+

Ya ɗago ya kalleta,Saudat ta riƙe ƙofar"kazo kaci Abinci"

"Nasha freesh Yo,akwai a firij idanzaki sha"

Saudat batayi magana ba,ta saki door ɗin ta juya Areef kam lokacin ya fara tunaninta,Miƙewa yayi ya fito,kan Dinnng ya taddata saidai zaune kawai take,firij ɗin ya buɗe ya ɗauko mata freesh yoo ɗin ya aje mata,ta kalleshi,ta ɗauka,yaja kujera ya xauna.

Saudat ta buɗe ta farasha,ta kalleshi"kaje ka kwanta mana"

"banjin bacci"

Saudat ta tura mashi robai,"ka ƙara nina ƙoshi"

Areef ya amsa ya miƙe ya maida a firij ɗin,saidai bai dawo ya zauna ba,falon ya koma ya kunna t.v,Saudat ta kona ta zauna kan kujera,itama ɗin ba baccin take jiba,sun kai 1hr wani lokaci yaɗan jawo magana,ta bashi amsa,duk yawan maganai akan aikinta ne,can Saudat ta fara gyangyaɗi,Areef ya kalleta"tashi mu kwanta,kin fara gyangyaɗi"

Murza idonta tayi,ta miƙe,shima ɗin kashe t.v ɗin yayi suka wuce,tana gani ya shige room ɗinshi,tana shiga ɗakin tafara kiran wayar Billy,sun jina suna fira Billy tace"haba saurin mi kike,kibarshi zai gane kuranshi"

Saudat taja lumfashi ta juya,kafin sukayi bankwana,tana kashe wayar kiran Fatima yana shigo mata,nan ta gaya mata ta haihu,ai Saudat murna tahauyi.

         ****
Dawowarta kenan daga Office,a gidan ta samu Areef dan yau ya rigata dawowa,xama tayi tana mashi Sannu,"yauwa ya kika dawo"

"lafiya lau"tana maganai ta xauna tana dafe kanta dake ɗan sara mata,Areef ya kalleta"kinje gidan barka ɗin?"

"eh ai dayake gidansu takoma"

"ok munje muga Baby"

Saudat ta miƙe,ta shiga ɗakinta wanka tayi tasaka duguwar riga enhlish wears dark green tanada wasu tutoci a jikinta,Falon ta dawo,zata shiga kitchen Areef yace"ki zauna kawai tunda akwai cake kada ki girka komi"

Saudat ta dawo ta zauna shikam dama abinda yafi so kenan,sun jima a zaune,Saudat kam kallonshi kawai take,nan tafara tunanin Usman inda shine da yanzu sunyi magana tafi a ƙilga.

Areef ya juyo zai kalleta,tayi saurin ɗauke kai Yace"yadai?"

"babu komi"

Ta miƙe takawo masu cake da drinƙs ɗin,suka ci Suka cigaba da zama.

Daran ranar Areef yakoma ɓangaran Ni'ima,hakan yasa washe gari tana tashi tayi shirinta ta tafi Office,saidai yau da wuri ta dawo,tagama duk abunda ta saba na aikin gida ta koma tana ɗan hutawa,Areef ya shigo ɓangarenta sanye yake da dark brown ɗin shadda.

Saudat tayi mashi sannu,kayan jikinta ya kalla,red t.shit sai wani mini skert shima red ne,"kindawo kenan banji dawowar kiba"

Saudat ta kaɗa kai"i thnk na rigaka dawowa ma"

STORY CONTINUES BELOW

Zama yayi yace"ki tashi muje inga Babyn Fatima kinga har gobe suna"

Saudat ta miƙe takawo mashi abin motsa baki kafin ta shiga ɗakin,material ta saya ɗinkin yayi mata kyau sosai,shikanshi Areef ɗin yasan tayi kyau.

Juyawa yayi kamar bai ganta tace"na shirya"tana maganai tana saka mayafinta"

Ya ɗago ya kalleta"Nop ki saka atamfa mana"tsayawa tayi tanason gane mi yake nufi,jin batace komi ba,ta kalli ƙasan kayan,Areef yace"Purple ɗin kaya basu maki kyau"

Batace komi ba ta juya,ta canza kaya,ta fito suka tafi,a harabar gidan ya kalleta"bani key ɗinki"

Miƙa mashi tayi,hakan yasa ta gane da motarta zasu fita,yana buɗe mota zai shiga,Ni'ima ta shigo da motarta gidan,ganinsu yasata saurin ƴin Parking ta fito,Areef ya shiga mota,haka ma Saudat,Ni'ima ta nufo wajan,sai lokacin Areef ya ganta.

Wani kallo take watsa masu,Areef ya Sauke glass ɗin motar zai mata magana ta fara zazzaga bala'e,Areef ya buɗe motar ya fito,Saudat kam tsayawa tayi tana kallonsu,yadda Ni'ima ke masifa wai zaifita da wata bayan itace da girki.

Areef ya kalleta"unguwa zan kaita ba jimawa zanba,ki jirani"

"Na rantse da Allah abinda kakeman ya isheni,taya ina kallo ko da yaushe saidai inyi haƙuri,yanzu kuma abinda za'azo man dashi kenan,ranar aikinta ku shige part ɗinta,saini ranar nawa aikin,afita abarni niga sakarai,anbarni gida"

Tsayawa yayi yana mata magana akan,kowacece keda girki zai iya fita da wadda takama,bawai dan wata tana girki bazai fita da wata ba,Ni'ima ta koma gefe tace batasan hakanba.

Ita dai Saudat tanajinsu batace komiba kuma bata fito daga mota ba.

Areef kam haushi yaji ya nufi marfin motar zai buɗe,Ni'ima taja hannunshi,"wallahi babu inda zaka"

"wai ke yanzu idan nace zan fita zaki hanani ne,Haba Ni'ima wai miyasa ki..."

"ai wallahi saidai dukabinda za'ayi ayi"

Areef ya fizge hannun rigarshi,ya buɗe mota"to wallahi indai ka tada motai saina fasa glass ɗin motar nan"tana magana ta zaro takalminƙafarta.

Bai jira cewarta ba yayiwa mota key,Ni'ima ta sa takalmin wajan tsinin ta buga glass ɗin gaban motai,take ya fashe ta kuma bugawa,ƙarar glass kawai kakeji.

Areef yayi saurin jawo Saudat yana rufeta da ƙirjinshi gudun kada glass ɗin ya taɓasu,sosai ya ƙanƙameta,gabanshi sai dukan Ukku-Ukku,hakan take ga Saudat.

Jin sunbarjin ƙarar suka ɗago,ya kalleta"bakiji ciwo ba?"

Kaita kaɗa mashi,alamar a'a,Areef ya buɗe marfin mota yafito,yana kallon yadda Ni'ima ta sauke rabin glass ɗin gaban mota,ya juya yana kallonta,tace"Ai wallhi dama na gaya maka,indai ka tada motar  to sainakashe motai"

Gaba ɗaya Areef shi bai saba irin wannan abinba,hakan yasa yarasa abin ce mata,saima tsayawa da yayi yana kallonta.

Saudat kam dama duk jikinsu akwai glass,ta dafa sit ɗin motar zata fito,akau bata ganiba ta danna hannunta cikin glass ɗin,da sauri ta janye tana dubawa glss ɗin ya shige tafin hannunta,tasa hannu ta cire,tana cirewa Jini ya biyo sosai.

Saidai gaba ɗaya batajin zafin ciwan,ta bufe marfin ta fito,kallonsu kawai take,wani takaici yakamata,ta kalli motar sai lokacin wani haushi ya kamata.

Ta juya ta kalli Ni'ima"kika fasa man mota ko,to nima bazan yadda?"tana maganai tana nufar inda take,Ni'ima itama tayo kanta"naje na fasa kiyi yadda zakiyi,ninace ku ce zaku fita"

Wani kukan kura Saudat tayi tana yin kanta,damƙota tayi tana shirin wujijjigata,da Sauri Areef ya riƙeta Ni'ima ma lokacin ta riƙe Saudat,ganin Areef ya riƙe Saudat Ni'ima tasamu damar ɗaga hannu ta kwasawa Saudat mari,Saudat tayi ƙoƙarin Anshe riƙon da Areef yayi mata,amma takasa"Ka cikani,wallahi ka cikani Nace"

STORY CONTINUES BELOW

Areef kam gaba ɗaya yagama ruɗewa yadda yaga marin da Ni'ima tayiwa Saudat,Ni'ima tace"ka cikata ɗin"

Saudat ta kalli Areef"kana gani ko,kana gani ta mareni,nace ka cikani"

Zuciya takawowa Saudat,Areef kam daka ganshi kasan ya shiga tashin hankali"idan na cikaki baza'ayi kai kyauba,kinga ita ba ita ɗaya bace"

"wato kenan ta Mari banza ko,tana maganai ta na kallon Ni'ima dake cika tana batsewa,tana cije leɓo.

Ta ƙara kallon Areef,gaba ɗaya hankalinta bai tare da ita"Yaya mari nafa tayi"

Hannunta ya riƙe,"nasani kiyi haƙuri"

Ni'ima tace"ai kekanki kinsan dama auran mijin wata ba daɗi bane,mutun yana zaune da mijinshi lafiya azo a takura mashi"

Saudat ta kama hannun Areef lokacin zuciyarta ta fara sauko mata,tace"ciki zan shiga kabarni"

Areef kam sai lokacin ya kula da jinin dake zuba a hannunta"Ai saidai ki shiga ciki danko kinzo nan,saidai kici na jaki"

Saidat ta kalli Areef"kace ta biyani motata"

Kai ya kaɗa mata,shikanshi ba ƙaramin tashun hankali ya shigaba,Saudat tayi hanyar part ɗinta,sai lokacin Areef ya saketa,ya juya yana kallo Ni'ima"Amma wallahi arziƙinki ɗaya cikin dake jikinki,amma tabbas kisani kin ɓataman rai yau,ke ban isa ince ki bar abuba"

Tsaki taja ta juya ta shiga part ɗinta,Areef ya duƙa ya auki mayafin Saudat dake ƙasa,Falo ya taddata,ga jini yana bin hannunta.

Ganin zai shigo ta juyarda kanta gefe,wasu hawaye suna zubo mata,Areef ya matsa kusa da ita,ya kama Hannunta"muje ki canza kaya inkaiki Asbity"

"ni baxanje ba"

Aifa nan Areef hankalinshi yatashi,ganin ga jini kuma gaya ta kafe akan bazataje ba,ta goge hawayen fuskarta,ta miƙe tsaye ta shige ɗakin kayan ta janza,tana fitowa baya falon,saidai abubuwan daya aje ya shiga ɗakinshi.

Kallon kujerar falon tayi,hada car key ɗinshi ya aje,Saudat ta ɗauka,ta ja mayafinta ta fice,Areef kuwa room ɗinshi ya shiga domin canxa kayanshi,sabda jinin daya ɓata rigarshi.

Saudat kam motarshi ta fija sai gidan Ammi,Sadik tafara cin karo dashi a bakin falon,nan yafara tambayarta lafiya,Ammi ta fito daga ɗakinta Saudat ta fashe da kuka.

Tararta tayi tana faɗin "lafiya?"
Saudat kasa bata amsa tayi sai zuciyarata dake tafasa ga kuka tanayi,Hannun Ammi ta riƙe"miƴe yaji maki ciwo?"

Sadik yafawo yana tambayarta,frts aid box ya jawo yana shirin duba mata hannun,Ammi tace "wai miye ya yankeki"

Sadik yace"barta Ammi,bariin gyara mata wajan" Nan Sadik yasa Akayan aikin ya gyara mata wajan,ciwan ba sosai bane saidai wajan ya yanku sosai.

Yana gamawa yasa bandeji da pilasta,saudat ta kwanta kan kujerar tana maida numfashi,Ammi takawo mata ruwa,saudat sai lokacin take maimaita innalillhi a cikin zuciyarta.

Jitayi taji sauƙin abinda takeji,sai lokacin tafara tunanin abindama yasa tazo gidan Ammi,Xaune ta tashi ta kalli Ammi tace"kai naji zafin ciwannan fa"

"Glass ne ko mi?" "eh wallhi"

Ammi kam nazarinta kawai take,yadda Gaba ɗaya ta canza"Wallahi nafito ashe glass ya mutu,bansaniba nasa hannu na"

"Assha ina Areef ɗin"
"Yana cikin gida,amma baisan naji ciwon bama"

Itakam Saudat jitayi bata iya gayawa Ammi abinda yafaru,dan gani take wanann ai kaɗanne akan zaman gidan Mama.

Areef yana fitowa ya shiga ɗakinta bata nan,ya duba ko ina baiganta ba,yasa waya yana kiran wayarta,ji yayi wayar tana ringing,wayar ya ɗauka,harya fita ya dawo ɗaukar key ɗin motar shi,saidai bai gani ba,ya fita yaga babu motai.

Komawa yayi ciki,ya boɗe locca ya ɗauko wani key,ya fito,cire cloth ɗin wata mota yayi,harya shiga kuma yarasa ina zaije.

Wayarshi ya zaro,ya fara kiran wayar Ammi,Saudat tana gefenta,Ammi ta ɗauka"hello  Ammi"

"ya akayi"
"lafiya lau Ammi Saudat tazo nan gidanne?"

Ammi taji yadda yake maganai,ta kalli Saudat,Saudat ta ɗanyi murmushi,Ammi tace"gata nan xaune"

Areef ya kashe wayar ya nufo gidan,Saudat kam jiranshi kawai take yazo,dan gaba ɗaya hankalinta yatashi.

Juyawa tayi tana ɗan zaro ido,jin ƙarar mota Saudat tayi Saurin fitowa gabanta yana bugawa,da Sauri tayo harabar gidan, tayo kanshi.

Ammi kuwa tana ganin hakan ta miƙe tana leƙawa ta taga.
*Aunty Haliloss*

Post a Comment for "WA NAKE AURE CHAPTER B"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...