WA NAKE AURE CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WA NAKE AURE CHAPTER A

WA NAKE AURE CHAPTER A

- - Post a Comment

 WA NAKE AURE CHAPTER A


Tsugunne take idonta sai ruwa yake, saboda Hayak'in dake shigar Mata Ido,dakyal tasamu wutai ta kama, mik'ewa tayi tare da dafe kanta dake mata wani irin ciwo,komawa tayi bisa k'ujera yar tsugunni, ta cigaba da tsintar shinkafar ta Yar hausa dake cike da tsakuwa cikinta, tafi awa biyu tana tsintar shinkafar, ta kusa idawa ne taji shigowar sa,yadda ya saba babu sallama gaban ta ya fad'i Amma ba ta nuna hakan ba, ji tayi an kife tsakuwar cikin shinkafar datake gyarawa cikin sauri ta d'ago idonta ta kalleshi.+


Ko a jikinshi,saima wani kallon banza da yakeyi mata,kanta kawai ta daga tare da cewa"haba Hayatu wane irin abu ne hka?ina aiki ka maida Mani aiki baya?" Zama yayi Bakin barandai data gewaye tsakar gidan,"tun sha biyu akawo maki cefane amma har yanzu baki gama girkiba,k'arfe biyu da rabi yanzu"


"Amma ai tun lokacin da ka shigo da icce nace baka d'anyu ne,basu cin wuta"


Dogon tsaki yaja tare da cewa"lallai yarinya,ai ko nine mijinki baki isa,insawo abu kice in maidaba,ai koshi Usman da yake yayana, bai isa yasani maida Abu ba idan nasawoshi balle...


Bai idaba,wata mata tafito,daga ɗakin tana ɗaga labile,tare da fad'in "kaima kake tsayawa sauraranta,aini ko kallo bata isheni ba"

Juyawa yayi yana kallon mahaifiyar tashi data jawo tabarma ta zauna,shima zuwa yayi yazauna gefenta,tare da bud'e ledar dake hannun shi,wadda kankana ce aciki,aikam Matai tasa hannu tana d'aukar kankanai tare da wurga Saudat harara.


Saudat ta share hawayen fuskarta,ta matsa ta k'ara gyara wutai,ta koma kan shinkafar,taci gaba da tsincewa.

Itace bata gama wannan sanwa ba sai k'arfe hud'u,saukewa tayi daga kan wutai,ta koma bakin ɗakin matai,bata ɗaga labulen ba tace"Mama nagama"


Banza tayi batace mata komiba,sairai Saudat tasan tajita,hakan yasa bata k'ara maimaitawa ba ta juya ta nufi hangar d'akinta.


Shiga tayi,dan tayi shiri tayi wanka,madaidaicin falone dakaganshi kasan ba wani gidan azo agani bane,saidai kuma zakuyi mamakin set d'in kujerun dake falon Wanda k'irar Italian ne,labulan d'akin kanshi abun burgewa ne, babban capet ne a tsakiyar d'akin,ƙofar shiga bedroom Saudat tabi ta shiga,redroom ɗin ma haka yake ɗauke da tsadaddun kaya.


Gadon ta kalla kwance yake yana ta bacci,koma wa tayi ta cire kayan jikinta ta ɗaura towel,ta dawo ta jawo hijab ɗinta ta saka saboda toilet ɗin ba a ɗaki yake ba.


Ƙaramin kwando ta ɗauka soso ne da wasu sabulan wanka masu gyara jiki,sai man wankin kai da kuma shower gel.


Hanyar fitowa ta nufa,ta juya ta kalleshi,har lokacin bacci yakeyi,gannin lokacin salla ne yasa ta juya,ta zauna bakin gadon.


Hannu tasa ta dafa kansh,i tana soka fingers ɗinta cikin sumar kanshi,motsawa yayi tare da buɗe ido,ya na mata murmushi,itama hakanne a fuskarta,wanda murmushin ne ya ƙara baiyanar da dimple ɗin dake fuskarta.


Hannu yasa ya riƙe nata hannun,tare da matsawa kaɗan,ƴar ƙara ta saki,tare da faɗin"lokacin sallah yayi"


Miƙewa yayi ya zagayo kusa da ita,ya ruƙota sosai,kumatunta ya ja tare da manna mata kiss"har kin gama abincin"


Damuwa fal a fuskarta,tace"nagama,amma iccen ɗanye ne nasha wahala"


Janta yayi jikinshi,yana mata alamar rarrashi"sannu tashi kiyi wankan kafin in dawo"


Miƙewa tayi ta ɗauki kwandon,ta nufi hanyar waje,tare suka fito tsakar gidan.


Lokacin Mama tana ta raban abincin,kallonsu tayi ta taɓe baki,Usman ya kalleta yace"Mama sannu da aiki"


"yauwa sannu da tashi"

Usman ya raɓa ya ɗauki sabuwar buta,ya shiga toilet ɗin,Saudat ta koma gefe tana jiran yafito ta shiga.


Hayatu ya fito daga ɗakin yana kallonta,kwandon yake kallo ya nufi inda take tare da faɗin"Muga shi kuma wannan sabulun ƙamshi gare shi?"


Saudat ta kalleshi,ta kauda kai,tayi kamar bata jishiba.

"ko baki jiba"


Miƙa mashi kwandon tayi,ya aje ƙasa yana dubawa ta kauda kai,ya ɗauki shower gel da conditioner ya miƙa mata sauran"waɗan nan zanyi amfani dasu,dan naga wancan dana ansa ɗayan bashida kumfa sosai"


Kwandon ta amsa dai-dai lokacin da Usman yafito daga toilet ɗin,Mama ta kalleta tace"to ai sai ki bani wancan mai jajajajan in...."


Bata idaba Saudat ta miƙa mata,ta bar wajan saboda yadda zuciyarta ke mata ƙuna,duka yaushe ya anshi wasu a wajanta,yanzu kuma shike nan,daga ganin wani yace zai ansa kuma.


Usman kuwa kallon shi yayi,yace"haba Hayatu miye zakayi haka,bata baka wani ba ko sati ba'ayi ba..."


"eyeeeee lallai sannu sarkin Mata,dan an anshi abinta shine zaka kama buɗe mana baki" Tana maganai tana wurga sabulun da ta ansa gabanshi.WA NAKE AURE??


*Whattpad @AuntyHaliloss*

02

Usman yagama Alwala,ya miƙe ya ɗauki sabulun ya je gaban ta ya aje"kiyi haƙuri Mama ni ba dake nake ba,kuma naga shi ɗin gaskiya na faɗi mashi"

Bai jira cewar taba ya fice masallaci,shi kuwa Hayatu ya kalleta yace"ai wallahi abinda Usman keman gidan nan ya isheni"


"ƙyaleshi,ai da baku samun kalar wannan saɓanin sai yanzu,kuma gani nike aurannan ne da yayi"


Wucewa yayi ɗakinshi, ya aje abin yafito ya nufi hanyar waje shima,Lokacin da Saudat ta fito Mama ta tashi daga tsakar gidan,sai kular Abincinsu tagani,ɗakin ta shiga ta aje kayan wankan ta koma ta ɗauko kular abincin,falo ta aje kan caper taje wajan wata loka ta ɗauko spoon da plate ta aje,ta ɗauki jug ta fita ta ɗebo ruwa ta dawo,sannan ta shiga bedroom ta hau shirinta.


Doguwar rigar atamfa ta saka java wax,tanada dark brown a jiki hakan yasa ta haska farar fatar ta ɗan kwalin ta ɗora,tana cikin ɗora ɗan kwalin ya shigo da sallama,bata juyo ba ta amsa tare da faɗin"sannu da dawowa"

"yauwa dear,wannan gayun fa"+


Juyowa tayi tana kallonshi,wani farin yadi ne jikinshi,sai dai bawani tsadane da shima,farine yanada tsawo saidai ba sosai ba,black handsom guy ne,ga sajen daya biyo gefen fuskarshi,Matsawa yayi ya riƙeta"to kallon kuma na miye"

Ta rausayar dakai,tare da ruƙo hannunshi,"your food is ready"


"kinyi kyau sosai"

"tanz dear"

Taja hannunshi suka fice ɗakin,falo ta kaishi kan capet suka zauna,ta jawo kular abincin ta zuba masu a plate ta saka spoon biyu,ta ɗauki nata,ta ɗau abincin ta fara ci.


Ƙinci yayi yana kallonta,ta kalleshi tace"kaci mana kana kallo na"tana maganai cikin shigar wasa,ya riƙo hnnunta,yace"bazan iya ci ba,ina jirane ki bani"


Tayi dariya,tare da matsawa gab dashi,yasa hannu yana shafa kumatunta,ta janye mashi Hannu,tare da miƙa mashi jallop ɗin shinkafai a baki"ai nasan dama haka zaka ce"


Ya buɗe bakin ya ansa abincin,"yanzu da hannu nikeso ki bani,banison spoon ɗin"

Ta marairai ce fuska,ta kalleshi"kaidai kawai so kake ka cige ni"


Yayi dariya,"to bakomi tunda kin ganoni" Haka suka cigaba da cin abincinsu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali,sai dai har zuwa hannan lokacin Saudat tana daure wane taci abincin,saboda gaba ɗaya abincin bawani kayan Haɗi yaji ba,tasan idan taƙici babu abinda zataci,kuma shi ɗin zai ciga damuwa.


Kau da kayan tayi lokacin daya dawo harya kishin giɗa kan kujera,ta zauna kusa dashi,ta kawo wayarta dake kefe,tana dannawa,ta ɗago ta kalleshi"dear wai yaushe zan koma skul ɗin ne kaga har za'a fara lecture hutunmu ya ƙare?"


Sai da yayi jim baice komi ba,sannan ya janye filon daya tada kai dashi,ya tashi zaune ya kamo hannunta,fuskar shi tana nuna alamar damuwa"to Aini Al'amurran ne bansan taya zan ɓullo masu ba,kinga dai ni ba kuɗi ne daniba,sannan ko regestration baki yiba"


Saudat tace"Hakane Amma zanje,inyiwa Pappa magana i know zai bani"


"haba nidai banaso tun yanzu ko wata 4 ba'ayi ba,kin fara zuwa neman abu wajanshi,bayan kuma kinsan irin kashedin da yayi maki"


Saudat tayi saurin ɓoye damuwarta tace"ni dai ka barni inje gobe,zan roƙeshi ne"

"to shikenan"

***

Washe gari ƙarfe takwas na safe suna zaune falo,dan basu ma jima da tashi ba,Hayatu ya ɗaga labulan Falon,da wata leda a hannunshi,ko gaisuwa babu,sai Saudat data ce mashi ina kwana,bai amsa ba,ya wurga mata ledar tare da faɗin"ina ruwanki da kwanana,ai gaisuwar ta gulmace dan kinganshi"


Usman ya ɗauke kai,dan yasan ko yayi magana Mama zata rufeshi da Masifa,dan yasan tana jinsu.


Hayatu kuwa ya juya yafice,Saudat ta kalli Usman tare da miƙewa ganin baice komi ba,ta shigewarta bedroom,Usman ya ɗauki ledar ya bita,kan gado ya tadda ta,kwance tana hawaye.


Saman gadon ya hau"ki tashi ki haɗa tea,madarace da bread"ɗagota yayi sai lokacin yaga kuka take.


"Haba dear kiyi haƙuri,kina gani ko nayi magana babu wani amfani,dan ba fasawa zaiyi ba,kuma kinga Mama goyon bayanshi take"

"Yanzu haka zamu zauna kenan"

"insha Allah komi zai canza"


Miƙewa tayi ta ɗauko kayan dirty data ajiye,kayanshi ne kala Ukku sai kayan baccinta ɗaukowa tayi ta nufo hanyar fita,ya tareta"ina zakije"

"wanki zanyi"

"ki farayin break mana"

"Naƙoshi"


Hannu yasa ya anshe kayan dake hannunta,ya ajiye gefe,ya xaunar da ita"Haba Mylove,my everything idan baki ciba taya hankalina zai kwanta,bayan kuma kinsan yanzu bana iya cin abinci ni ɗaya"


"ai nace maka Naƙo..."


Bata idaba ya jawo tafin ƙafarta,yana yi mata susa,ƙoƙarin zullewa take tare suka saka dariya,gaba ɗaya Usman ya gama sangartar da ita da soyayyarshi har batasan lokacin da sukasha tea ɗinba.


Sai ƙarfe goma tafita da kayan wankin,tana zuwa bakin rijiya,ta ajiye kayan,ta zura guga zataja ruwan Mama ta fito,Saudat tace"Mama sannu da fitowa"

Mama ta kalleta"yau dayake shayi akasha banji motsinku ba"tana naganai ne da gadara.


Saudat dai batace komi ba,saima wani Mamaki daya kamata,wanda shayin hakanan sukashashi ko madarar kirki babu.


Hayatu ya fito daga ɗakinshi da kayan kanikancin shi jikinshi,alamar fita zayayi,ganin Saudatu yasa ya tsaya,sai kuma yakoma ciki.


Fitowa yayi hannunshi da wasu kaya,dai-dai lokacin Usman yafito zai shiga Wanka,Hayatu ya matsa ya aje kayan "ki haɗa da wannan dan kayana sunyi dauɗa"


Usman ya tareshi"kai kwashe kayanka,duk karasa wanda zai maka wanki sai ita"


"Ai naga wanki zatayi"

"to kana nufin ita zata wanke kayan da ka cire"


"Ohhhh yau naga ikon Allah,dan an bata wanki kake tada kafaɗa haka,to shi ina yaga lokacin wanki,yanzu haka gareji zaya neman kuɗiidan ka hanata waye zaiyi"


"Haba Mam..."

"Au habama zaka ce,yaro yana bakin ƙoƙarin shi yana nemo mamu abinda zamuci,kuma ace aiki kaɗan baza tayi ba,saidai taci ta ƙoshi taje kewaye tayi kashi Allah sai tayi wankin nan"


Usman ya matsa"to sai dai ni in wanke"


Mama tana taɓa Hannu tace"Allah dai ya sawake,ai nayi tunanin zuwa yanzu daka Aurota wanki a Enging za'a rinƙa yi maka"


Hayatu yace"nikam Wallahi ita zatayi mani wankin nan.


Usman ya ɗauki kayan ya saka cikin bokiti,ya ɗauki sabulun data aje,Saudat taje gefen kunananshi kamar zata ɗauki abu tace"kabarni in wanke kawai"


Wata harara ya watsa mata,bata ƙara cewa komi ba,Hayatu ya fice,Mama kuma ta koma gefe ta shin fiɗa tabarma tana ta ƴan Maganganunta.


Har suka kusa gama wankin babu wanda yayi magana,saida yaga Mama ta tashi,zai shanya wata riga,ya ɗaga ya sharta da ƙarfi duk ya watsa mata ruwan,tsorata tayi,tana kallonshi yayi mata dariya"sarkin tsoro"


Tana dariya tace "ruwafa ka watsa man".


Suna Gamawa tayi wanka,shima wankan yayi suka shirya,Usman ya kalleta"yaushe zaki tafi gidan?"


"sai nayi girkin rana"

"ok Bari inje ƙofa gida to"


Ƙarfe sha biyu Hayatu yadawo da cefane hannunshi,ya aje ya juya yayi tafiyarshi,Mama ce ta ke har ɗakin ta tadota,dan har bacci ya fara ɗaukarta.


Bata tsaya ɓata lokaci ba,ta cigaba da sanwa,ta kusa gamawa Usman ya shigo gidan,Ɗakin tabishi,"hrka dawo"


"eh zamuje wani wuri ne da Ibrahim Abokina,shine nazo inkawo maki kuɗin adai-daita sahu,koda ban dawo ba sai ki tafi"yana maganai ya miƙa mata 150 tasa hannu ta amsa tare da cewa "Nagode,sai kun dawo"


******

Tana gama sanwa ta barma Mama rabon Abincin,don ita takeshan wahalar girki,amma sai wanda Mama taga damar ɗibar masu,ayi Alwalar salar Azafar ta shige ɗaki tayi salla,ta fito ta ɗauki abincinsu,tana shiga ta zuba taci nata,sabd tasan bayanan.


Ƙarfe Ukku ta fito tsakar gidan,sanye da black din doguwar riga,tayi rolling Ash veil akanta,da plate shoe ɗinta,wayarta da ƴar ƙaramar jaka a hannunta.


Wajan dasu Mama suke zaune ta nufa,taɗan durƙusa tana sakin fuska"Mama zanje Unguwa,yau gida zanje"


Hayatu dake zaune yatasa kwanon din abinci gaban,sai loma yakeyi yace"ai kau ba inda zaki,waye zaiyi girkin tuwan dare,dan yau tuwo za'ayi......

*AUNTY HALILOSS✍🏽*WA NA KE AURE??


          *Whattpad @AuntyHaliloss*


03


Jin Abinda Hayatu yace cikin sauri Saudat ta ɗago ta kalleshi,tare da faɗin"Haba ai na riga na shirya,kuma na tambaye shi,shine yace inje"


Hayatu ya aje spoon ɗin dake hannunshi"ai in gaya maki bazaki sani kamfaraba,kinaji nayi rantsuwa baza kije ba"


Saudat batasan ja'inja,kallon Mama tayi saima taga ta kauda kai,cikin sanyin jiki ta miƙe ta nufi ƙofar ɗakin ta,hawaye na gangaro mata a fuska,wannan wace irin rayuwace Allah ya kawo ta,ko ƙofa bata nufa ba Usman yayi Sallama da rake a hannunshi.


Shigewa tayi ɗakin,ya nufi inda su Mama suke ya zauna,yayi mata sannu da gida,sai wani sharewa take,ya miƙa mata Raken,ta amsa tana ɗaure fuska"ai wannan sai yasani ciwan haƙori"

Shidai Usman baice komi ba,ya miƙe ya shiga ɗakin,kan kujera yasameta,tana kuka,ya zauna yana rarrashinta,da kyal ya shawo kanta,ta faɗi mashi bata tafi ba Hayatu yace bazata fita ba,Aikam ranshi ya ɓaci,hannunta ya kama,ya goge mata hawayen,yace"tashi muje"

Ta miƙe,suka fito tare,yana zuwa yace"Mama zamu fita,sai anjima zamu dawo"


Ai bai isheta kallo ba bare ta bashi ansa,shikuma ya tasata gaba suka fice,sai da sukayi tafiya mai nisa zuwa bakin titi,ta samu Adai-daita sahu,harta shiga,yace"to ki daina turo bakin Hakanan kada kije Pappa yace waya ɓata maki rai?"

Dariya tayi tace"wayace maka turo baki nayi?"+


"gayanan kamar an hura ballon"


Gaba ɗaya sukayi dariya,suka tafi shikuma yakoma gida,dai-dai gate ɗin gidansu Napep ta sauketa,gabanta na faɗuwa ta nufi gate ɗin.


Kwankwasawa tayi,ta ɗan jima kafin Maigadi ya leƙo,ganin itace ya washe baki yana mata sannu da zuwa,tayi dariya tana faɗin "Baba ya aiki"

"lafiya lau"

Ta gefenshi ta raɓa ta shiga,tun a harabar gidan ma aikatan ke mata Oyoyo tana amsa wa,balcony ta nufa ta buɗe ƙofar shiga falon,tayi sallama.


Mariya mai aikice take ɗauke kayan kan dinning,tana maidawa kitchen,tana ganinta ta tace"ga Mamana ga Mamana"


Saudat ta matsa ta rungumeta"sannu Aunty Mariya ina yini"


"Lafiya lau" zauna bari in kawo maki ruwa"

"ina Mami fa?"


"Mami taje gidan Ammi"

"su khairi fah"

"ai su duka suka tafi,Areef ne kawai a gidan shima ciwankai yake"


Dam gabanta yafaɗi jin sunan data ambata,Saudat batace komi ba,Mariya ta tafi kawo mata Abinci,koda ta dawo Saudat cewa tayi"Na ƙoshi ina gama cin abinci nafito"


Mariya ce"A'a Mamana kici"

"Allah na ƙoshi,bari in shiga ɗakin Mami kafin ta dawo"


Har takai ƙofa,hanyar hawa steps ɗin benan sai kuma ta juyo tace"Pappa fa?"


"Pappa yana tare dasu,Amma naji sunce ba jimawa zasuyi ba"


Hayewa  tayi,ta shiga room ɗin farko dake  coridor ɗin falone dake ɗauke da fararen leda chairs sai maroon ɗin cotains madaidaiciyar t.v ce manne a bangon.


Hanyar bedrom ta nufa ta shiga,shima farin set ne,ɗakin yayi kyau sosai,sai dai daka gani kasan,ba a gyare yakeba,Saudat harta zauna ta miƙe ta hau gyara gadon ta gyara ɗakin ta shiga toilet amma a gyare ta tadda shi,ta ɗauko bonner ɗin turaran ƙamshi ta joiner ta saka turaran wuta kafin kacemi ƙamshi ya gauraye ɗakin,hakama falon.


Tana zaune falon,ta kunna t.v tana kallo,tajima har hankalinta yakoma gida,ganin basu dawo ba,tasan zata iya rasa abin hawa a unguwarsu,saidai kuma batason tafiya ba tare da taga ƴan gidan ba.


Har aka fara kiran sallar Magrib,bata tsaya wata-wata ba ta miƙe ta ɗauki mayafinta ta saka,ta na zuwa steps ɗin benan tajiyo sallamarsu, gabanta sai faɗuwa yake.


Mamai ce a gaba sai Khairi da Ilham dake biye da ita,saukowa tayi aikam yaran suna ganinta suka rugo suna murnar ganinta,"Oyoyo ga besty"


Itama rungumesu tayi tana murna"i missed my beaty",sai lokacin Mami taganta,Saudat ta nufi inda take,jiki babu ƙwari tace"Mami sannu da dawowa"


"yauwa" tace tana ɗan satar kallonta,lokaci guda ta gano rama da kuma duhu da Ɗiyar tata tayi,ganin zasu haɗa ido Mami ta kauda kai,tare da faɗin"Lokacin sallah dai yayi kuke nan tsaye"


Tana maganai tana hayewa,Saudat taji babu daɗi cikin ranta,yaran sukace"muje sama Besty"


Haka ta bisu,ɗakin yaran suka nufa,tana ɗan goge hawayen fuskarta,saboda kada suganta,Ɗakin yran kanshi abin kallo ne,yadda aka tsarashi harda side ɗin wasa  daga gefe,alwala sukayi,sukayi salla.


Ta kalli yaran tana tambayarsu karatunsu"Besty ni nafi Khairi maida hankali,rannan har Yaya Areef sai da yayi man gift  saboda ƙoƙari na"


Tayi dariya tana kallon Khairi,Khairi tace"Ilham ba dagaske take ba,shima Ya Areef ɗin sankai yayi"


Nan suka hau hayaniya kamar zasuyi rigima,tace"ya isa kubani labari"


Ilham tafi khairi yawan surutu tace"Besty tunda kika tafi kullun sai nayi kuka ince zanje gidanki Pappa ya hanani"


Khairi tace"ni kuma tunda kika tafi gidannan So boring babu daɗi,kullun kewarki muke"


Duk yaran suka bata tausayi,Ilham tace"tab ai duk Yaya Areef yafi yin kewarki,rashin lafiya yakamayi Akayi Admiting ɗinshi Hospital,har aka sallamoshi bashida lafiya"


Khairi tace"kuma ciwan zuciya ke damunshi,kullun sai Pappa yayi mashi faɗa"


Saudat tace"Nina nayi kewarku,tunda na tafi kullun sai nayi kuka"


Dariya sukayi"kai Besty like a child?"


Dariya tayi tace"yanzu yaushe zakuzo"


"sai Pappa ya bari,dan shi yace babu wanda zaije"


Saudat ta miƙe ta tace"kutashi mufita"


Ɗakin Mami ta shiga,zaune ta ganta kan abin salla,ta zauna gefe tace "Mami ina yini"


"lafiya lau ya ƴan gidan?"

"duk lafiya lau,suna gaidaku"


Mami bata ƙara magana ba,haka itama Saudat tayi shiru,can Saudat ta miƙe ta Sauko daga benen tare da yaran,maganar Pappa ta ringa jiyowa daga Falon ƙasa.


Ɗan taoro taji ta tsaya,Pappa ne zaune da Areef " Wallahi daga yau na ƙarajin bakada lafiya,ranka zaiyi mugun ɓaci,hakanan ka rinƙa wasa da lafiyar k..."


Saukowa sukayi da yaran suna magana,su duka suka juyo suna kallon su,lokaci guda Pappa ya ƙara ɗaure fuska.


Saudat ta shiga tana sallama,ta zauna ɗan nesa dashi,tace"Pappa ina yini?"


"Ya Areef ina yini"

"Lafiya lau"ko gama Amsawa Areef baiyi ba,Pappa ya ɗora"Miki keyi anan"


Da sauri Areef ya miƙe yabar falon,su Ilham suka bishi,Saudat tace"Pappa gaidaku nazoyi sai ban taddakuba"


"da bamunan shine zaki tsaya jiranmu?to tashi maza ki fice"


"Pappa dan Allah kayi haƙur..."

"ki tashi ki tafi nac.."


"Pappa dam da ma,ma ga nar Maka ranta ce da zamu koma" tana maganai cikin inda-inda.


"sai fiya faru,aidai ya barki ki koma ko?"


"eh"

"to Allah ya tsare hanya"


"Pappa maganar kuɗin regestration ne"


Wata ƴar dariya yayi"to miya samu kuɗin regestration ɗin?"


"shi shine nazo zo,Amsa wajanka"

Wani mugun kallo ya watsa mata tare da faɗin"ke kalleni nan,kin manta halina kenan,kin manta sharuɗan dana ƙindaya makine kafin kiyi Auran,kin manta kenan,thank god kinsan bana maimaita magana,maza ki tashi kibarman gidana"


Saudat ta duƙar dakai hawayen dake maƙale idonta suka zubo,zatayi magana ya daka mata tsawa,"Na ce ki tashi ki fice"ba shiri ta miƙe,ta nufi hanyar hawa benan.

"ina zaki,nanne hanyar fita" yana maganai cikin tsawa,yana nuna mata hanya.


Tana kuka ta fito,ƙofar ko Mami batayiwa bankwana ba,duk da itama ba samun sakin fuska tayi a wajanta ba.


Buɗe gate ɗin tayi,sai lokacin taga yadda gari yayi duhu,sabd ko darana Unguwar babu mutane balle kuma dare,hasken fitulun stret ɗin kawai kake gani amma ba alamar mutane.


Kuka takeyi sosai tana tafiya........
*AUNTY HALILOSS✍🏽*WA NAKE AURE??


          *Whattpad @AuntyHaliloss*


04


Sai da tayi nisa kan street ɗinsu,tafiya kawai take dan tasan bazata samu abin hawa ba.


Areef kuwa tunda ya shige dasu Ilham bedroom ɗinshi,dawowa yayi dai-dai corido ɗin dake tsakanin falon da side ɗinshi,tas yake jiyo maganganun Pappa sai dai ita baya jin abinda take cewa,jin Pappa ya koreta yasashi saurin barin wajan,sai da yaga fitarta a ƙafa,ya koma ɗakinshi,harya zauna kuma yayi tunanin ba da abin hawa take ba,take yaji wani tausayinta,miƙewa yayi ya fito harabar gidan.


Driver ya tadda zaune,ya kalleshi yace"Abba yace Saudat tana waje hanyar titi,kaje ka kaita gida."


Driver yana tada mota yafice, Areef yakoma falon.


Saudat tana ta sauri dan tsoron duhu yakamata,hango hasken fitila tayi ta mota,ta kauce daga hanya,sai taga anyi parking gefenta,ga motar gidansu yasata tsayawa,drivern yace"Sauda muje Hajiya"+


Ai bata tsaya wata-wataba ta buɗe ta shige,ko minti 20 ba'ayi ba suka isa unguwar tasu,suna zuwa ƙofa gidan yayi parking ta fito tana faɗin"to Sai anjima"ya amsa mata da "sauka lafiya"


Tana juyawa taga Usman tsaye,sai zuwa yake yana dawowa,nufarshi tayi yana ganinta ya juyo"Allah hankalina yatashi inata tunanin ko riƙeki akayi"


Dan dariya tayi wadda batakai zuciba tace"a'a wallahi naje gidanne na tadda basu gari,nayita jira sai yanzu Mami tayi masu waya akan cewa acan zasu kwana shiyasa sai yanzu na dawo,amma kayi hakuri na tada maka hankali"ita kanta batasan lokacin data ƙirƙiri wannan ƙaryai ba.

"Bakomi mushiga ciki"


Har sunkai zaure,ya ruƙo hannunta yana mata raɗa"idan mun shiga kice ma Mama ni kika tsaya inje mutaho tare sai bance ba,shiyasa kikayi dare"


Koda suka shiga Mama tagama zamanta ta shiga ɗaki,Saudat taje ƙofar ɗakin tare da cewa"Mama nadawo"

Banza tayi batace komi ba,ta juya ta nufi ɗakinta,zaune ta taddashi,taje ta zauna gyefenshi,kamo hannun shi tayi tare da faɗin "nagaji inajin Bacci muje mu kwanta"

"bakici Abinci ba""

Ta kalleshi tace"ni naci a gidan"


Miƙewa yayi suka shiga,Saudat tanajin gajiya ta saka kayan bacci tabi lafiyar gado.


              ****

Washe gari kuwa suna tashi tafito,ɗakin Mama ta shiga ta fara aidata,ta amsa tare da cewa"jiya acan kika kwana?"


"a'a wajan tara da rabi nadawo"


Leda ta tura mata dadankalin haisa tace"gaya nan yanzu Hayatu ya ajeshi,ki soya"


Saudat ta ɗauka tafito tsakar gidan,ta fara aiki,lokacin ƙarfe takwas tayi,Usman ya fito da kwandon wanka zaiyi wanka,ta miƙe tana faɗin "katashi kenan"

"eh aiki kikeyi ne"


"eh bari in sa maka ruwan"

Kusa da ita ya matsa yace"A'a barshi zan ja dakaina,yi aikinki"


Can Mama ta fito daga ɗaki,ita indai taji suna tsakar gida tare to bazata barsu ba,komawa tayi kan dandamlin ɗakinta ta zauna,Saudat ta cigaba da fere dankalin,Usman ya gama jan ruwanshi ya shige toilet.


Mama tace"wai nikau ba wani abinda kika zo dashi daga gidan naku?"

Sai da gaban Saudat yafaɗi,tace"eh"


"tab lallai yanzu duk girman gidanku sai kije ki dawo hannu biyu?"


Shiru Saudat tayi bata ƙara cewa komi ba,Mama taci gaba da maganganunta"Allah ya rabamu da irin wannan abu,ace mutun yaje gidansu ko tsinke bai zo dashiba,kuma zuwan farko,ko dayake bandai saniba ko kuɗi suka baki"


Saudat tagama fere dankalin,har ta ɗora mai a wuta Hayatu ya shigo hannun shi ɗauke da leda,ajewa yayi gefenta,tare da cewa"bafa soya wa zakiyi ba fatan dankalin nikeso"


STORY CONTINUES BELOW

Mama tace"to juye mani mai na kibani in maida cikin kwalbai"


Wani zafi zuciyar Saudat tayi mata,ta ɗauki tsumma kama tukunya,ta juye man ta miƙawa Mama,ta dawo ta gyara tarugu daya aje ta jajjaga ta ɗora,tanayi wasu hawayen baƙin ciki nazo mata sai ƙarfe goma tagama.

             *****


Ƙarfe Ukku ta shiga da kular abincin ɗaki,ta ajiye wani irin ciwo kanta yake mata,kujera ta samu ta zauna,tana dafe kan,tana nan zaune bacci ya ɗauketa,Usman ya shigo ɗakin,hannu yasa yana tadata,ta buɗe idon tana kallonshi,zama yayi tare da cewa"ya dai?"


Saudat taɗan rausayar dakai tace "kaina ne yake man ciwo"hannu yasa ya dafa kan yaji akwai zafi,zaro ido yayi,yana janta jikinshi"hada zafi ma jikin,bari in fita in samo maki magani".


Yana fita ta tashi tayo wanka,ta dawo ta shirya riga da skert ɗin lace ne ta saka,kan gado ta kwanta,tana jiran dawowar shi,nan take ta tuna yadda su Pappa suke mata idan bata da lafiya,wasu hawaye suka zubo mata,hannu tasa ta jawo wayarta Number Mami ta kira har so Ukku bata ɗauka ba,dama tasan hakan ne dan bata ɗaukar wayarta,shikam Pappa dama yayi blocking ɗinta daga kiranshi.


Wani kuka ta fashe dashi,lokacin guda ta tuna da Ammi,contact ta shiga ta fara neman wayarta bugu ɗaya ta ɗauka"Assalamu Alaikm daughter"


Wani irin kuka takeyi tare da faɗin"Ammi ina yini"

"Sauda kina lafiya kuwa"

"kaina ke ciwo"


"subhanallah kunje Asibiti kuwa"


Saudat ta goge hawayenta,bataso tagaya wa Ammi tanada matsala,saurin goge hawayenta tayi tace"eh naje da safe"


"to Allah yasawake,ya mai gidan?"

"lafiya lau yake"

"to ki gaida manshi,badai matsala ko ƴata?"

"a'a"

"to shikenan zanzo gobe in dubaki"

"to Ammi Ngde"


Ban kwana sukayi ta kashe waya Usman ya shigo da pure water a hannunshi,hankalinshi ya tashi ganin tana kuka zama yayi ya jawota jikinshi ya kwantar da ita"kiyi haƙuri ga paracetimol nan sai kisha"


Yana maganai yana saka hannunshi aljihu ya fiddo maganin ya ɓalle ya saka mata baki,ya fasa pure water ɗin yabata, da kyal ta haɗiye yana ɗan bubbuga mata baya,ya ƙara jawo ta ta kwanta jikinshi sosai,bakin shi yakai kan kumatunta,yayi mata pick tare da faɗin"Sorry dear"


Yasa hannu ya cire mata ɗankwalin kanta,yana shafa gashin kanta,ya zage zip ɗin rigarta tayi saurin ɗagowa yayi mata murmushi"ki saka kaya mara nauyi" kai ta daga mashi,ya miƙe ya ɗauko wata doguwar rigar material ya taimaka mata ta saka,ba jimawa bacci ya ɗauketa,sannan  yafita.


Da marece Hayatu ya shigo gidan,lokacin Mama bata nan tashiga maƙota,zama yayi tsakar gidan yanata surutai,shiga yayi ɗakin yana kiran Saudat,cikin bacci takejin shi,ta samu ta fito,ya kalleta"wato bacci ma kikeyi,kina nufin yau baza'ayi tuwo ba komi?"


Saudat tace"kaina kenan ciwo shiyasa"


Hayatu ya aikamata da wata irin harara"to ai tunda kin tashi sai kitai ki ɗora dan bazamu zauna da yunwa ba" yana maganai yana fita da ga falon.


Sunan Allah Saudat take maimaitawa a zuciyarta,jin yadda zuciyarta take buga mata da ƙarfi,ta fita ta ɗauki garin ta kama sanwai duk jikinta babu kwari.


Ana kiran sallar magriba Usman ya shigo,ganinta bakin Murhu ya nufeta"keda lafiya zaki ɗau sanwa"


Hayatu ya aje buta dake hannunshi"to idan batayi sanwa ba mi zamuci?"


Usman yace"yarinya bata lafiya amma bazaka ƙaleta ba,da itace take maka sanwa da zakace sa...."


"to sannu Sarki mai Mata,kana nufin tunda da nikeyi,yanzu ma inyi kenan ko,niga wahalalla,to baka isa ba"


"Amma Mama naga tace bata da lafiya ne"


Cigaba da aikinta tayi Mama tace" Ehh lallai shi yana wahala yana nemo abinci,ni kuma inyi maku sanwa,ita ta kwanta, kai kuma kafita waje ka zauna,idan kagaji kadawo kayi bacci haka kukeso,wallahi baka isaba"

Usman bai ƙara magana,yayi alwala ya fice,ƙin dawowa yayi gidan,dan bayason ganinta tana wahala,lokacin daya,dawo harta kwanta saidai ba bacci takeyi ba.


Zama yayi yana dafa hanta"Dear ya ciwan kan"


"naji sauƙi"

"Allah ya ƙara sauƙi"yana maganai yana janta jikinshi,hawayen idonta suka sauko yace"Haba dear kiyi haƙuri,nasan baki saba irin wannan wahala ba amma babu yadda zanyi,kiyi haƙuri"


Ɗagowa tayi"amma yakamata ace kana sana'a ko yatake,ai duk abinda ke faruwa rashin sana'ar kane,inda kana kawo wani abu a gidan nasan ko Mama tayi mana faɗa to Hayatu bai isa yayi Magana ba"


Ajiyar zuciya kawai yayi baice komi ba,ta miƙe tabar wajan,shikanshi yasan tanada gaskiya.


             ****


Washe gari,Saudat tanata aikinta,shara takeyi lokacin,Hayatu yadawo daga Gareji,kallonta yayi yace"Jaman ruwa inyi wanka"


Saudat ta aje tsintsiyar taje bakin rigiya,ta taja mashi ruwa tabarshi a wajan ta cigaba da aikinta,Mama ta fito daga ɗakin tace"ai gaskiya daga yau waɗancan manyan bokitan za'a rinƙa cikawa basai lokacin da za'ayi amfani da ruwa ba anema"


Hayatu yace"ai idan tagama sharai sai taja"


Saudat ta dago ta kallesu,gaba ɗaya ta tsanesu ko kagana ma bata sonyi dasu,batace komi ba tana gamawa tayi shigewarta daki.


Tab aikam tajawa kanta,domin kuwa har ɗaki Mama ta taddata tasha bala'e,jiki babu kwari ta fito tahau jan ruwa.


Sallamar Ammi abakin ƙofa,Saudat tayi saurin janye guga ta nufo ta tana "oyoƴo ga Ammi"


Ammi tayi dariya"Daughter kin samu lafiya kenan"


"eh da sauƙi,ki shigo"tana maganai suna nufa hanyar shiga ɗakin.


Hayatu dake goge takalmi  ya kalleta"ke ina zaki baki gama jan ruwanba?"

*kubiyo ni*

*Fans comment ɗinku yayi man kaɗan*

*AUNTY HALILOSS✍🏽*

WA NAKE AURE??

          *Whattpad @AuntyHaliloss*

*KUYI MAN AFUWA KWANA BIYU BANYI TYPING BA,MUNYI BIKINE,NAJI DAƊIN YADDA KUKE NEMA NA,DA BOOK ƊINA ALLAH YABAR ZUMUNCI*

05

Ran Saudat ya ɓaci da maganar Hayatu saidai kodan Ammi bataso ta gane wani abu,kallonshi tayi tayi dariya"Allah ya sawake maka da shirme"tana maganai kamar gaske,ta kalli Ammi suka shiga.

Sun jima sosai suna fira,Ammi tace "yaushe zaki zo man wuni?"

"Ammi zanzo insha Allah,ai naje gidan Su Mami suna gidanki saida nayita jiransu"

"Ai sai wajan Magrib suka baro gidan"

Shiru suka ɗanyi,Ammi tace"ya maganar skul naga ankoma,dan su Nihal harta fara lecture itace tace man bata ganki ba ma"

"eh wallahi Ammi wannan satin nakeson komawa danayi regstrtion"tana maganai tana kauda kai daga kallon ta.

Ammi macece mai saurin gane mutun koda bai gaya mata matsala ba,dan ko ganin yadda Saudat tayi duhu da kuma Rama zata gane akwai matsala.

Ammi tasa hannu ta riƙeta"bari in tashi in tafi driver yana jirana"tasa hannu jikka,ta fiddo bandir ɗin ƴan 500 guda biyu ta miƙa mata"to gaya kiyi transport na skul"

Hannu tasa ta ansa tana godiya"Ammi tace komikike buƙata you should inform me,i will asists kinji ɗiyata"+

Haka tayi mata rakiya da kuɗin a hannunta,Hayatu yana zaune bakin ƙofar daki sai kallon hannunta yakeyi,i danma Mama bata gidan nasan da munga abu.
     
        *ASALIN LABARI*

Alhji Mu'azzam Alti,shine mahaifin Saudat,shararran mai kuɗine a cikin garin Kano,shine controler of prison service,ɗan Asalin garin kano ne,su biyune a wajan iyayansu,Alhaji Sa'id Alti shine babba,sai Alhaji Mu'azzam,daga su iyayansu basu ƙara haihuwaba,wata shaƙuwa ce tsakanin ƴan uwan guda biyu,suna son junansu sosai,sunyi ilimin boko dana islama,bayan gama karatunsu,Alhaji Mu'azzam  ya fara aiki a prison shikuma Alhaji Sa'id dama yana aiki yana lecturing,har yayi Aure da Matar shi Zulaihat,bayan wani lokaci Allah yabata haihuwar ɗa namiji aka saka mashi sunan Mahaifinsu Amma ana kiranahi da Areef.

Yaron yataso jikin gata a wajan iyayanshi dakuma kakanninshi,kasancewar basu samu haihuwa sosaiba.Mu'azzam yanason yaron sosai duk inda zashi saiya tafi dashi,yaron yana shekara Ukku ya iya Magana sosai,idan Mu'azzam yayi kwana biyu baije gidanba,da kanshi yake cewa Ammi takaishi wajan Pappa,sunan da yake kiran ƙanin mahaifinshi kenan.

Ba'ajima ba Alhaji Mu'azzam shima yayi Aure,matar shi Asma'u,tunda yayi Auran duk lokacin da ya ɗauko Areef to a gidan yake kwana,Ana haka aka saka Areef makaranta,to lokacin hankalin yaron ya rabu,don yafison zama wajan Pappa saboda yafi samun kulawa,gaya kuma Asma'u batada matsala,gaba ɗaya ta ɗauki yaron kamar ɗanta,wannan dalilin yasa Areef dawowa hannun Pappa da zama.

Asma'u nada wata tara,ta haifa ɗanta namiji,aka saka mashi Muhsin,anyi murna sosai,kaddai Areef yafi labari dan lokacin yayi wayo sosai.

Shekarar Muhsin biyu dadai akayi mashi ƙanwa SAUDAT,murna sosai wan Areef gaba ɗaya hankalinshi yakoma kanta,ki yaushe yana tare da ita,Mami kanta idan Areef yana gida bata ganin ɗiyar tata saidai idan tana kuka.
Bayan wasu shekaru suka taso cikin kulawar Pappa da Mami,itama Ammi ta ƙara haihu,Mami kuwa tunda ta haifi Saudat ta fara planning dan bataso taƙara haihuwa susa kusa.

Alhaji Mu'azzam yana katse kuɗi sosai wajan ilmin yaranshi,lokacin Areef yana ajin ƙarshe a jami'a,Muhsin kumkaratun doctor yake a Sokoto,ita kuma lokacin saudat ta shiga level 1 a  jami'a.

STORY CONTINUES BELOW

Tun gida akwai,shaƙuwa mai ƙarfi a tsakanin Areef da Saudat,komi zasuyi atare sukeyi dan lokacin Saudat tazama kyakkyawar budurwa ga aji,ƙasaita,ga kuɗi,waɗannan abubuwan suka ƙara fiddo da asalin kyanta.

Areef irin samarin nanne da duk inda mace tagansu dole ta ƙara kallonsu,dan yayo kyan iyayanshi fulani,ɗan gayune na ƙarshe,ga tsafta.

Areef kam gaba ɗaya hankalin shi yanakan Saudat,wani kalar so yake mata,wadda bazai musaltuba,itakam batama saniba,duk kulawar da sukewa junansu kawai tana ɗaukane a matsayin Yayanta..........
*Zan ida maku asalin labarin kudai kucigaba da biyoni,donjin yadda akayi haɗuwar Usman da Saudat*

   *CIGABAN LABARI*

Da Marece Usman yashigo gidan,tana bedroom ta fito,a falo suka haɗu,Sannu take mashi tana sakin Murmushi,ɗaure fuska yayi ya kalleta"bazan amsaba"yana maganai yana ware mata hannu,faɗawa tayi jikinshi sosai yayi hugging ɗinta,kiss ya manna mata a wuya"i miss you"tace.

Zama sukayi,ya kalleta,"yau yini guda banmu tare inaji kamar anyi shekara"

Dariya tayi,"an samu aikin ne"
"Fara bani Abinci mana,ko kin manta da cikina bai ɗauka ba"

Su duka sukayi dariya,Saudat ta kawo masu abinci,dan itama bataciba,suna gama ci ya kalleta,"Dear wallahi harna gaji da neman aikin nan"

Ɗan tagumi tayi,dan nasan ba'a samu ba kenan"shikenan Allah ya bamu mafita"
"Amin"

"kaga ni na manta,Ammi tazo bata jima da tafiya ba"

Yaɗan ɗaure fuska kaɗan,dan yasan wacece Ammi a wajanta,Saudat bata damuba tacigaba da bashi labari,zamewa yayi yakoma kan kujera ya kwanta,ganin yayi mata banza,baiyi magana ba,itama ta ɗaure fuska,tana turo baki,dan taji haushi.

Jin tayi shiru ya ɗago ya kalleta,ganin tayi fushi yaɗan saki fuska,dan bayason ganin tana fushi"Naso in taddata dana gaidata"

Sakin fuska tayi"wallah kuwa Ammi tanada kirki"

Hannu ya miƙa mata"zo kiman tausa"

Tamiƙe tana mashi tausa,suna ɗan labari,can tace"namanta bari kaga abinda Ammi tabani"

Bedrom tashiga tadawo da kuɗin hannunta,ta bashi "kagani wai inyi trnsport zuwa skul"

Usman yace"kin gode sosai,sai kije kiyi regestration dan nasan zasu isheki"

Saudat taɗan langwaɓe kai"haba ni ina tinanin droping samester zanyi,kawai ka anshi kuɗin sai kayi business dashi"

Yaro ido yayi yace"haba dai,bazan ansar maki kuɗiba,kiyi amfani da abunki,nikaina bamso ace ta dalilina kin daina zuwa skul"

Haka Saudat tayi-tayi Usman ya anshi kuɗin amma yaƙi,dama ta dage sai ya amsa jawota yayi ya haɗe bakinsu,dole tayi shiru tana ansar saƙon dayake aika mata,daga bisani ta haƙura,can yatashi yafita waje,nan ta tashi tabar kuɗin akan kujera.

Bai jima da fitaba Mama ta dawo gidan,Saudat tayi mata sannu da zuwa ta ɗauki ruwa ta shiga toilet,bayan shigarta toilet Hayatu yashigo gidan ɗakin Mama yaje bai jimaba,ya nufo ɗakin Saudat.

Har lokacin bata fito daga wanka ba,yana ɗaga labulan ɗakin yayi kira baiganta ba,kuɗin daya hanga kan kujera ya nufa,da sauri ya ɗauka ya saka aljihu,cikin sauri yafito daga ɗakin dai-dai lokacin Saudat tafito daga toilet ɗin,tana ganin yadda ya fito gabanta ya faɗi.

Ɗaure fuska yayi yace"ki gama ga surfen masara can ki bakace"

Ko kallonshi bayi ba ta shihewarta ɗaki,ta gama shirinta tsab ta fito,Mama tana zaune gefe,Fauziyya ta zauna tace"Ɗazu Ammi tazo baki nan tana gaidaki"

Tsaki Mama taja tace"to ni ina ruwana,mutann dako sunzo ba abinda zasu iya baka"

Saudat taɗan yi jim,sannan tace"a'a ai tabani kuɗi,bari in ɗauko kigani"

Taɓe baki Mama tayi Sudat ta miƙe ta shiga ɗakin,inda ta aje kuɗin tahau dubawa,wayam batagansu ba,har kujerun ta ɗaga pillos ɗin amma babu,ɗakin ta shiga tana nema,gabanta ya faɗi data tuno lokacin dataga fitar Hayatu daga ɗakin.

Tajima tana nema amma bata ganiba,ta fito tace"Mama bangani ba in tinanin ya fita dasu,ko ya canza masu waje"

Tsaki taja"kudai kuka sani,waya sani ko ƙarya kukeyi"

Saudt takoma ɗakin,ta ɗauki wayarta,number Usman ta kira,don ta tambayeshi,saboda ta fara zargi,ya ɗauka"hello Dear"
"Na'am nace a ina ka ajiyeman kuɗin nan,zan nunawa Mama?"

Usman yace"wane kuɗi,ai anan natashi na barki dasu ko?"

Saudat ta razana,dan tasan shine ya rigata fita"to naga ban gansu ba,amma bari in ƙara dubawa"

Gaba ɗaya Saudat tayiwa ɗakin kacha-kaca tana nema,ranta yagama bata Hayatu ya sace kuɗin.

Batasan lokacin da wasu hawaye suka zo mataba,take ta farajin ƙarfin zuciya,ta goge hawayenta ta tashi tafita tsakar gidan,ta zauna kan kujera,ita kuma Mama tana kan tabarma zaune.

Ta jima a zaune,saiga Hayatu ya shigo,miƙewa tayi tsaye tanayi mashi wani mugun kallo.

In da yake ta nufa ta tsaya,tare da miƙa mashi Hannu"Bani kuɗina dak ɗauka dazu lokacin ina wanaka"

"wane kuɗi?"yana maganai kamar baisani ba.

"Ai wallahi kafi kowa sanin kowane kuɗi,ai naga lokacin daka fito daga ɗakin,ka fiddo man kuɗina kawai"

Zaro ido yayi tare da jawo ashar"Amma yarinyarnan ki maisheni sakarai,ni zaki sakawa sata"

Mama ta miƙe tana sallallami,tare da taɓa hannuwa"kai lallai yau munga ikon Allah,ke yarinyarnan ashe rashin kunyarki takai haka?"

"Wallahi Mama naganshi yafito,kuma mi ba wand..."

Wani mari Mama ta sharara mata,Saudat ta dafe kumci,Hayatu yace"Dan ubanki nine ke maki sata?"

Yana magana yana nufar inda take,cikin zafin zuciya,zai bigeta,cikin tashin hankali,ta durƙushe a wajan, tana ihu....

*KUBIYO NI*

*Ba zaku jiniba gobe,gayanan nayi maku harda na gobe,inayi maku fatan Alkhairi*
*AUNTY HALILOSS✍🏽*WA NAKE AURE??


          *Whattpad @AuntyHaliloss*


*GYARA 👉🏽kuyi mani afuwa,a page  ɗina na jiya page 5,nayi kuskure wani waje xan rubuta Saudat na rubuta Fauziyya,sunan yana raina sbd sunan star ɗin book ɗin dana gamane,Sai yanzu nagane nikaina inason book ɗina mai suna FAUZIYYA😄😄* AFUWAN PLZZ+


06


Hayatu yakai mata bugu dai-dai shigowar Usman,wata fizga Usman yayi mashi,ya bankashi gefe,Usman sai Huci yake,yana tambayar "lafiya?"


Wani mari Mama ta kai mashi"kasan abinda tayi da zakazo kahana ya bigeta,kamar wannan yarinyar zata ja ma Hayatu sheri dan batada mutunci,tace wai ya ɗauke mata kuɗi"


Usman ya dafe kunci"Amma Mama shine zai bigeta,yanzu da Allah bai kawoniba,shikenan yakenan?"

"tam sannu Usman,sannu,kai yanzu bakama kishin ɗan uwanka,lallai"

"nan aiba maganar kishi bace,maganar gaskiya ake,taya ƙarfin namiji da Mace zai haɗu?"


Bai tsaya sauraran amsar ta ba,ya juya ya kalli saudat,wadda har lokacin kuka take,ya maida kallonshi kan Hayatu"wallahi wannan yazama na farko yazama na ƙarshe,duk ranar daka ƙara ɗaga hannunka wallahi sai ranka ya baci"


Yakalli Saudat"tashi ki shiga ɗaki,miƙewa tayi bamusu,ta yi hanyar ɗakinta,itakau Mama wani irin kallo take masu,dan tasan gaskiya take gaskiyar kawai ta ke sabd son zuciya irin nata.


Saudat na shikewa ɗakin Usman ya kalli Mama"dan Allah Mama ku daina irin wannan halin wallahi ba girmanku bane"


Banza tayi dashi ta ƙyaleshi,sai huci da takeyi,Hayatu yace"dan kayi aure kake mani haka,to wallahi nima bazan ƙara wata biyu ba babu mata"


Murmushin takaici Usman yayi,Mama tace"kaima ke tsayawa bashi amsa,kabarshi kawai mana,yatafi wajan matai tashi"


Usman ya juya kawai ya fice daga gidan,yana takaicin hali irin na mahaifiyarsu,da yana ganin abin da sauƙi amma yanzu gaba ɗaya ta ida rikiciwa,tun daya fita bai dawo gidan ba,sai da daddre amma hankalinshi yanakan Saudat.


Sallah ya tadda tagama tana kan abin sallah,ya koma gefen kujera,ya zauna,ko sannu batayi mashiba,ta miƙe ta haye gado,tare da cire hijab da zanan datayi salla,dan dama tayi shirin baccin sabda yadda takejin wani irin ciwan kai.


Bai damuba dan yasan ranta a ɓace yake,kayan baccin yasaka shima,ya haye gadon yana fuskan tarta,juya mashi baya tayi,yasa hannu ya juyo da ita"haba Dear,yanzu miye amfanin kije kice shiya ɗauke maki kuɗi ke kin ganshi ne?"


Wasu hawaye ta goge"abar maganai kawai banso,Allah zai bani wasu,amma wallahi shine ya ɗaukesu,ai naga fitarshi daga ɗakin"


Usman ya lumfasa "shikenan,kiyi haƙuri Allah zai saka maki,ni baƙin cikina registaration zakiyi da kuɗin gaya babu yanzu"

yana maganai yana goge mata hawaye,yana shafa gashin kanta alamar rarrashi.


"Shikenan zan saida wayata sai inyi regestration ɗin"


"a'a kada ki saida"

"to idan ban saidaba dami zanyi"

"inkin saida wayarfa?"

"sai in sayi ƙarama,gobe kafita da ita kawai ka saidaman ita"


           *****

Washe gari Usman ya tafi da wayar,Saudat ta bashi Number wanda zai sayi wayai,yana kaiwa kuwa aka saya ya yadawo mata da kuɗinta da wata ƙaramar waya.


Amsar kuɗin tayi"to ka ɗauki wani abu aciki"


Harararta yayi"kedai ki shirya dawuri goben sai kije"


Washe gari Saudat ta shirya tsab,tasaka doguwar riga,dresing ɗinta na gayu yadda ta daba,tayi kyau sosai,sai dai mayafin akai ta azashi,ta fito tayiwa Mama bankwana Mama tace"ina zuwa?"


STORY CONTINUES BELOW

"zanje makarantane munkoma har sati Ukku yau?"


Mama ta kalleta"wai makarantar boko"


"ashe ke baki gamaba,kace ajinku ɗaya da Usman ɗin"


"a'a Mama shi yana gabana"

Saudat tayi Mamakin ydda yau Mama batayi bala'i ba,ta gyara jikkatta ta fice.


Skul ta nufa,Fatima ƙawarta,takira a waya,tace mata suna lecture, wucewa tayi sukayi lecture,suna gamawa Saudat tace"aini wallahi fushi nike dake"


Fatima tace"Haba fushin mi zakiyi?"

"shikenan sai ki daina zuwa gidan"


Dariya Fatima tayi"haba inkin ganni gidannan to saikin Haihu,ai ina tsoran matar nan"


Itakanta Saudat tasan ko itace baxata komaba,saboda wulaƙancin da Mama tayi mata,wai su sunƙi Aure sai biyo ƙawa akeyi ana cika masu gida,Saudat tayi dariya tace"ke Allah dai yasawake,ai matarnan batada kirki"


Fatima tace"Allah yasawake"


"Amin bani time table ɗinki inyi copying"


Tana gama ɗauka,ta miƙa mata"ashe yau lecture biyu gare mu"


"eh munyi ɗaya kafin kizo,yanzu gida zamu"


"ok aini zanyi payment ne a bank"

"muje in kaiki,idan kikayi sai in ajeki gdan"


Motar Fatima suka nufa,suka shiga,Fatima tasan labarin Auran Saudat,hakan yasa take tausaya mata,Fatima itama babanta yanada kuɗi,tun suna aji ɗaya suke tare da Saudat,sun shaƙu sosai.


Bank sukaje,suna gamawa har gida ta kawota,Usman yana zaune saman dakalin ƙofa gidan Saudat ta buɗe ta fito sai lokacin ya gane tane sune,ya miƙe yana faɗin"yau nakaki sai ana skul zaki zo kenan?"


Dariya Fatima tayi"Wallahi ba haka bane Usman"


Saudat tace"wallahi nima saida nayi mata complain"


Suka gaisa da Fatima,sukayi bankwana,ta wuce sukuma suka shige gidan.


Cikin satin Saudat ba abinda takeyi,data tashi shirin makarantarta kawai take tayi tafiyarta,gaya kuma yanzu kullum Fatima saita biyo ta ɗauketa,haka idan aka tashi saita kawota gida take wucewa,sai tadawo take masu sanwar dare,Hayatu kuwa ya fita harkarta,dama haka takeso,kwana biyu har hamkalinta ya fara kwanciya.


               ****

Bayan Sati Ukku Saudat ta tashi tanata shirin tafiya makaranta,lokacin ƙarfe takwas da rabi,Usman kuwa yana kwance bacci yakeyi lokacin.


Hayatu ya shigo da wasu Matasa a bayanshi,hanyar ɗakin Saudat suka nufa,tana tsaye taji sunata magana.


Hayatu yace"a'a wanan ɗakin za'a rufe ƙofar ciki,sai a fidda wata ƙofa tanan kusa da wannn tagai"


Saudat ta leƙa sai taga maganar ɗakinta sukeyi,Ahankali tasa hannu tana bubbuga Usman"tashi tashi kaji"


Ɗayan yace"ai idan aka maida ƙofar nan to tagaima sai an matsar da ita"


Usman ya miƙe yafito,ya fan jima yana kallonsu ya maida kallonshi kan Hayatu"Ya akayi ne?"


"wanann falon anan xan aje matata,gyara zanyi,daɗe ƙofar ciki za'ayi,sai a fidda maka ƙofa anan"


Usman ya galla mashi Harara"aikai anya kana da hankali kuwa"


"yo Ashe rishin hankali ne maganar aure,kai sadda zakayi Auran kenan bakada hankali"

Usman ya kalli ƙofar Mama datake fitowa tana magana.


"kenan Mama goyan bayanshi kike?"


"inban goyi bayanshiba ya kakeso inyi,aure ne yanzu saura sati Ukku dole ya nemi inda zai aje mata?"

Tsayawa Usman yayi yana Mamakin ace ɗan uwanshi zaiyi Aure Amma ko gaya mashi ba'ayi ba.


Saudat ta fito daga ɗakin,saboda Fatima tace mata tana ƙofa gida tana jiranta,Hayatu ya sha gabanta"ki tsaya ki kwashe komatsanki,kisan inda zaki kaisu dan yau za'a fara aikinnan"


Usman yaji wani mugun takaici bayaso yaga ana wulaƙanta mashi mata,ya kalli Hayatu yace"Bata Hanya"


Hayatu yace"ba inda zata saita kwashe su"


Saudat abin yabata mamaki,tace"ai ga mai kwashe war nan kusa dakai nikam ba ƴar aikin ku bace"


Mama tace"Au jimla ma kikeyi hada ni,to wallahi baki isa ba,yau koni koke a gidanan"


Saudat ta kalli Hayatu"kabani hanya nace"


Tanufa ƙofa zata wuce da ƙarfi,hannu yasa ya bangazata gefe,da ƙarfi,gefensu ta faɗi tana dafe ƙugunta,kafin kace mi jini ya biyo kafafunta,duk ba wanda ya kula ita kanta Saudat bata ganiba.


Usman yayikan hayatu da bugu,Mama tayo kansu tana bala'i.


Wani azaba saudat taji,tasa ɗayan  hannun ta dafe Mararta,jin lema na bin ƙafarta,cikin sauri ta kalla kafar, ganin jinin dake binta, yasata sakin wata razananniyar ƙara,cikin tashin hankali da kaɗuwa,take a wajan ta sulale........
*AUNTY HALILOSS✍🏽*WA NAKE AURE??


          *Whattpad @AuntyHaliloss*


07


A sume ta ida kaiwa ƙasa,ganin haka Usman yasaki hayatu yayo kanta,yana ɗagata,amma ina.


Mama tace"ai gayanan abinda kaja inda kabari anyi anyi sulhu ai ba'a ayi hakaba.


Jin shiru Fatima ta fito daga mota ta nufi cikin gidan,bakin ƙofa taci karo dasu,cikin tashin hankali take tambaya"lafiya Usman?"


"babu lafiya fatima"

Itama kanta Fatima hankalinta yatashi,tace"kamata akaita Asibity"


Bamusu Usman ya sungumeta,mota yasakata,shima ya shiga,saiga Mama tafito da alamar tashin hankali tare da ita,motar ta shiga itama suka nufi Asibity.+


Asibitin ƙasan Unguwar suka nufa,suna zuwa aka ansheta office ɗin doctor aka shiga da ita,taimakon gaggawa suka hau yi mata.


Ta farfaɗo,Sai dai har lokacin jini bai tsayaba,take likitan ya tabbatar masu da ɓarine na ciki wata Ukku,aikam ba ƙaramin tashin hankali Usman ya shigaba,Fatima kam kuka kawai take.


Room aka canza mata,kwance take ga ruwa da aka haɗa mata,hawaye ne kebin idanuwanta,Usman yana gefe wani mugun baƙin ciki yakeji,shikanshi hawayen ke shirin zubo mashi.


Matsawa yayi bakin gadon ya kamo ɗayan hannun,ya riƙe Saudat ta ɗago ido ta kalleshi,sosai tausayinta yakamashi"kiyi hakuri"


Gilgiza kai tayi,wani ciwo takeji"ka kiraman Mami dan Allah"


Fatima ta matsa kusa da ita"kin dan hankalin Mami zai tashi ida...."


Doctor ne ya katse mata magana,ya basu unarnin su ɗan bashi wuri,aune-aune ya hauyi mata ba jinawa yafito,ya sheda masu tana buƙatar jini sannan kuma akwai sauran cikin a jikinta,sbd haka sai anyi nata wankin mahaifa.


Tashin hankali,Usman yaji wasu xafafan hawaye na biyo kumatunshi,Fatima tace"Haba Usman kadaina dan Allah"


"haba Fatima,wannan wane irin abune,yaja mana,yanzu dami zan biya kuɗin aikin nan"


Fatima ta lumfasa,duk ba Matsala bane,bari in ɗauko jikkata a mota,kuma dole za'a kira Mami agaya mata.


Mama dake gefe,tace"bari in koma gida in samo kuɗin sai in kawo maku"


Fatima tagane Mama taji tsorone,shiyasa tayi sanyi,dan kada wani abu yasamu Sauda tasan akwai matsala.


Fatima,takawo mashi kuɗin,yaje  ya biya,wajan Saudat ɗin suka koma,Waya ta fiddo,tace"bari inkira Mami".

Cikin jin jiki Saudat tace"Fatima kice mata faɗuwa nayi a Makaranta"


Usman yace"ƙarya zaki sa tayi?"

Ta goge hawayenta"nidai haka zaki ce mata"

Fatima batayi magana ba,ta nemo layin Mami ba'a jimaba ta ɗauka"hello Fatitti yagda?"


"lafiya lau Mami"

"Ya skul hop lafiya ƙlau?"

"Alhamdllhi Mami dama muna Asibity ne da Saudat batada lafiya"


Sosai hankalin Mami yatashin dan tanaji da yarinyarta,ko gida idan batada lafiya ruɗewa suke babu mai sukuni har saita samu lafiya.


Dakewa tayi tace"to Allah ya bata lafiya"


Fatima najin hakan,taɗanyi shiru itama Mami shiru tayi zuwa can tace"ki gaidata sai anjima"


"A'a uhm Mam mì dama dan Allah kizo,Saudat ɗin ce tace inkiraki,ta faɗi a skul ne,har tayi miscarriege,kuma tanajin jiki,gaya ana buƙatar jinin da za'a saka mata"


Lokacin hankalin Mami yatashi,dan tasan za'asha wahala samun kalar jinin Saudat,gaya kuma tasan ƙara asamu jinin wadda ka sani gudun wata cuta,kuma jinin Muhsin da Areef ne kalar nata.


Da sauri tace"subhanallah wace asibity?"


Take Saudat ta gaya mata,Mami ta miƙe tana saukowa daga Matattaƙalar benan,Muhsin ne yafito daga kitchen hannunshi riƙe da plate ɗin fruit,ya kalleta "Mami ina zaki"


"Saudat ce ba lafiya tana Asibity"


Tsaki Muhsin yayi"to Mami mizakiyi mat..."


Pappa ne ya shigo falon"da zaki fita tambayata kikayi komi? daga bata lafiya shine zaki ɗauko gyale da jikka?to babu inda zaki?"


Pappa irin mutanan nanne masu sauƙin kai,sai dai kuma akwai tsauri da jajircewa,mutunne wadda idan yace baison Abu babu wanda ya isa ya canza mashi ra'ayi,hakan yasa ake shakkar shi,sai dai bako yaushe kake gane hakan ba,sai kayi mu'amala dashi,amma akwai sakin fuska,ga kirki,da taimakon Al'umma.


Mami ta zauna"wallhi Fatima ce ta kirani,Saudat ɗin ta faɗi a makaranta,har tayi ɓari kuma ana buƙatar jini"


Pappa yace"babu abinda zakiyi mata ko kinje,kai kuma Ya Muhsin katashi kaje Asibitin kabada jini,bance ka tsaya ba"


"Pappa cikin satin daya wuce na bada jini a hospital ɗin skul ɗinmu"


Harararshi Pappa yayi"kada ka kawo man shirme"


"Pappa am serious"


Pappa ya miƙe tashi muje,kiraman Yayanku a waya,Muhsin ya ɗauki waya layin Areef ya kira,bajimawa ya ɗauka,Pappa yace "bani shi nan"


Muhsin ya miƙa ma Pappa waya suka fice,Pappa yagaya mashi Asibityn yace ya same shi acan.


            ****

Sun riga Areef isa Asibityn lokacin anyi mata Allurar bacci saboda ciwan dake damunta,Pappa ne yafara shiga ɗakin,Usman yana riƙe da hannun Saudat,shigowa sukayi.


Usman yayi saurin sakin hannunta saboda kunyar Pappa,ya miƙe yana gaidashi cikin Ladabi,Pappa ya ansa tare da faɗin"ya jikinta?"

"Alhamdllh,allurar bacci akayi mata"


Muhsin ya bashi Hannu suka gaisa,Fatima ta gaidasu.


Pappa yace"muke inga doctor ɗin"yana maganai yana kallon Muhsin.


Tare suka fice Usman yabisu baya,bayani likitan yayi masu,akan faɗuwar datayi ne yasata buguwa har takaiga ta samu ɓari,sannan kuma zasuyi mata wankin ciki,gudun matsala gaba.


Pappa ya gamsu yace"yanzu miye abinyi"


"eh jini za'a bada saboda na mijinta ba group ɗinsu ɗayaba"


"Ba damuwa gayanan za'azo abada"


Suka tafi room ɗin da Saudat take,lokacin ta farka,Areef shigo da sallama,Pappa yagaida,ya miƙa masu hannu suka gaisa,saida yayi ƙoƙari sosai ya miƙawa Usman hannu,suka gaisa Areef yace"ya mai jiki?"


"Alhamdllh"


Ya kalli Saudat"Ya jikin ki?"


"naji sauƙi"


Pappa ya kalli doctor"yauwa ga wadda zai bada jinin nan sai muje a ɗiba"


Arazane Usman ya ɗago,yana kallon shi,wai Areef ne zai bada jini asama matar shi,kai bazai yiwuba,lokaci kaɗan idonshi ya canza launi zuwa ja,cikin wata kakkausar murya yace"waye zai bada jinin......."


4

*AUNTY HALILOSS*WA NAKE AURE?


          *whattpad AuntyHaliloss*


*SAƘON TA'AZIYA GAREKU,FATIMA UMAR ALLAH YAJIKAN YAYAH ALIYU,HAƘIƘA MUNYI RASHI,ALLAH YABADA HAKURI.*


*MAIMUNAT ABBA RASHIN MAHAIFIYA WANI BABBAN RASHINE,ALLAH YAJIKAN MAMA ALLAH YA GAFARTA MATA*


*AUNTY MARYAM ADORO,ALLAH YABADA HAKURIN RASHIN UNCLE DA KUKAYI,ALLAH YASA ALJANNA CE MAKOMARSU,MUKUMA ALLAH YASA MUCIKA DA IMANI AMIN*


08


"Waye zai bada jinin,dan an aunani jinin baiyi ba"


"ga Areef nan,shine zai bada Muhsin satin daya wuce yabada jini"cewar Pappa yana ɗaure fuska.


Usman yaja dogon lumfashi,take ya tina shifa Areef ko ba komi ɗan uwanta ne kuma tare ya gansu,wata natsuwa yanemo wa kanshi"


Areef kam wani irin abu yakeji,mutuwar tsaye yayi,ya kalli Pappa,lokacin Pappa bama shi yake kallo ba har ya juya zasu tafi,bai da wani zaɓi daya wuce yabi bayansu,Hakan shima Usman ɗin saidai babu wani sakin fuska a tsakaninshi dasu Pappa.


Ana gama ɗibar jinin suka jira,Areef ya huta,ko wajan Saudat basu koma ba,suka fito,lokacin sukayi karo da Fatima tadawo daga gida da kular Abinci a hannunta.


Muhsin ne ya tsaya sukayi magana,Pappa ya samesu,ya kalli Fatima"zamu tafi"+


Fatima tace"to Pappa Allah ya tsare hanya"


Hannu ya saka Aljihu,ya fiddo kuɗi,ya miƙa mata"gaya ki ajiye a hannunki idan ana buƙatar wani abu sai ki bada"


Ta amsa tayi masu bankwana ta shige,sukuma suka nufi harabar Asibitin,Pappa ƴa kalli Areef"ina fatan lafiyar ka lau"


Areef ya ƙara nemo sakewar fuska yace"lafiya lau Pappa"


"ok Muhsin anshi key ɗin,kayi driving ɗin kuje gida,ni ba gdan zani ba,zan biya wani waje"


Muhsin ya kalli Areef"kawo key ɗin"


"nop brox zan iya"


"a'a kabani zan kaimu"


Areef baiyi gardamaba ya miƙa mashi key suka nufi gida,Mami kam ta jima tana jiransu,suna komawa ta kalli Areef"waye yabada jinin"


Muhsin yace"Yaya Areef ne"


Mami tace"shina da ba kwarin jiki gare shiba shine ya bada jini"


Areef yayi murmushi dan ko lokacin yana ɗanjin juwa,kamar tana ɗibarshi"Mami na warke ba,kuke ganin banda lafiya"yana maganai yana zama kan kujera.


Ya kalli Muhsin"duba kaga idan akwai malt kabani"


Muhsin ya miƙe ya nufi Firij ya ɗauko mashi maltina ya kawo,Mami tace"ɗauko mashi ya haɗa da Nadara"


Shidai Areef baiyi magana ba,haka suka zauna sai lallamin shi suke.


              *****

Tun da suka fita Saudat take ware ido taga dawowar su Pappa,amma bata ganiba,sai da ta tambayi Fatima tace mata,sun tafi,shiru kawai tayi batayi magana ba.


Anyi mata ƙarin jinin,Mama kam tunda ta tafi sai dare ta dawo,Usman kam massallaci kawai ke rabashi da ita.


Washe gari,jikinta yayi ƙarfi,aka sallamesu,Fatima ce ta kwashe su suka nufi gidan.


Hayatu kam abinda yayi niya bai fasaba,domin kuwa duk tsadar kujerun Saudat a tsakar gida suka taddasu.


Abin yaba Fatima haushi,shima Usman ɗin shiru kawai yayi,dan bashida yadda zaiyi idan yayi magana kuma cibi yazama ƙari.


STORY CONTINUES BELOW

Koda suka shiga ɗakin,an daɗe ƙofar falon   an buɗe wata ta bedroom,kuka Saudat ta fashe,dashi,Usman ya riƙe ta yana rarrashinta,Fatima tace"kai Saudat wannan wane irin abune"


Saudat kukanta kawai take ta ƙyaleshi,Usman ya kalli Fatima"dan Allah kibata haƙuri,ita kanta tasan da inada yadda zanyi da baiyi mani haka ba"


Zama Fatima tayi ta cigaba da rarrashinta,shikuma ya fice,saida Fatima ta tabbata ta hakura sannan,ta miƙe tahau gyara mata,ɗakin saboda duk yayi ƙura.


Fatima ta kalli Saudat"yanzu yaza'ayi da kujerun nan"


"abarsu a wajan kawai,tunda ba ɗaki"


"haba ai lallacewa zasuyi,kibari in koma gida sai akaisu can a ajiye


Saidat ta kaɗa kai,tana share hawayenta.


    *CIGABAN LABARI*

Areef da saudat ko wane lokaci suna tare da juna,tunda Saudat ta shiga jami'a Areef yafara canza salon shi zuwa na soyayya a wajanta,ko fita zayayi sai ya jira sun fita tare.


Areef kam yanada ƙoƙari a skul hakan yasa maza da matan Ajinsu,suke tare dashi,sannan kuma baya da wulaƙanci,saidai yanada miskilanci sosai.


Tsaye take a harabar gidan,tana jiran fito warshi,bakin motar shi ta tsaya,gaba ɗaya tana gudun ta makara,fitowa yayi sanye da Maroon ɗin shadda kanshi babu hula,takalmi da agogon hannunshi black ne,sumar kanshi tasha gyara kasancewar shi fari,ga sajen daya biyo gefen fuskarshi.


Juyowa tayi"haba Ya Areef tun jiya nagaya maka inada lecture 8 amma kaga har 8:10"


Harararta yayi"baki iya gaisuwa ba sai complain"


Bata bashi amsaba,ta buɗe mota tashiga,shima ya shiga,har sunyi nisa yaga tana fushi,murmushi yayi kawai,ana cikin tafiya tace"ai dama shiyasa ka cewa Pappa kada yabani mota,dan ka rinƙa sani ina makara"


Gefen titi yaja yayi parkin,ta kalleshi yace"gama faɗanki saimu tafi"


Tasan halinshi sarai zasu iya jimawa a wajan tace"a'a yi haƙuri muje"


Dariya yaɗanyi,suka isa skul ɗin,har zata buɗe mota,ya ruƙo hannunta"tafiya zakiyi kina fushi da Yaya?"


Sai lokacin ta saki fuska,ya saketa,muje in rakaki,nasan dai ba'a shiga lectures ɗinba"


Ta kalleshi"Yaya idan an shiga fa?"


"sai inba lecturer ɗin haƙuri,ince nina tsaidaki"


Zaro ido tayi"kaja ayi mamu dariya a hall kenan,dan cewa zasuyi saurayi nane"


"to mu ina ruwanmu,sai muce eh"


Dariya ya bata,suka fita saidai sunyi sa'a,ba shigaba ya kalleta waɗannan takardun ki saka a bag kada kiyi missing ɗinsu nasanki da sakaki"


"nop baxan yadaba"


Ok yace ya juya yafita.

Darana tana tare da Fatima sun fito daga lectire, restaurant  ɗin makarantar zasu,don suna jin yunwa.


Xaune yake da frnd ɗinshi Salim,sai wasu  cause mate ɗinshi mata guda biyu,dake gefenshi,fira suke suna cin abinci.


Saudat wani mugun haushin yaran takeji,su ko yaushe kuna maƙale da Yaya Areef,duk cikin matan dake yawan zama dashi tafi jin haushin su.


Hannun Fatima taja"muje kinga waɗancan shegun,Allah haushi suke bani"


Fatima tayi dariya"kedai kika sani nace soyayya kuke da Ya Areef kince a'a"


Daidai lokacin suka isa wajan table ɗin Saudat tace"Honey yaushe zamu gida" tana maganai tana marairaicewa.


Ya kalleta"kin gama lectures ɗin ne"


"A'a 4 zan tashi"


"ok lokacin saimu tafi"


"Ah  Areef banace maka,zaka ajiyeni gida ba,drivern mu bayanan saiku ajeni" cewar Hafsa ɗayar da suke zaune.


Harara Saudat takai mata,ta kalli Areef,shima ita yake kallo,yagano ta sarai,ta juya suka tafi.


Ƙarfe huɗu suna tare da Fatima,Areef ya kirata"ina bakin sanate ki zo muje"


Fitowa tayi,ganin Hafsa a gaban motarshi yasata juyawa,wajan Fatima ta koma,ya akayi"tashi muje ke zaki kaini gidan"


"miyasa?"

"Allah bazan hau motar shiba,tunda ya ɗauki yarinyar can"


Dariya Fatima tayi,dai-dai lokacin kiran Areef ya ƙara shigowa ƙin ɗauka tayi,suka fice da Fatima,yajima yana kiranta taƙi ɗauka,yana sake kira ta ɗauka,tace "kasameni gida danni nayi gaba"


Bata jira amsarshiba ta kashe wayar,fizgar mota yayi,yabar skul ɗin,dan yasan ya ɓata ran Saudat,biyawa yayi ya aje  Hafsat ya kama hanyar gida.


Abakin street ɗinsu Fatima ta ajeta,tana gab da isa gate ɗin gidansu Areef ya karyo kwana,kusan a tare suka shiga.


Kafin ya fito daga mota harta shige part ɗinsu,binta yayi,tana shiga ta tadda Mami da Pappa a falon,Pappa yana cin Abinci.


Shiga tayi tana turo baki"Pappa kaga Ya Areef a skul yabarni"


Tana maganai Areef yana shigowa"Allah Pappa laifinta ne"


Mami tayi dariya tace"ai dama su Ilham suna nan dasun maku dariya"


Pappa yace"miyasa kabarman yarinya,halama a ƙafa kika taho?"


ɗaga kai tayi tanason yin dariya,Areef yace"dariya ma zakiyi ko?"yana magana yana cize leɓe"wallahi zan gyara maki zama"


Mami tace"miya haɗaku"


"Mami wai Ya Areef baida wasu ƙawaye sai mata,duk inda ya zauna sai mace tazo wajanshi,shine yau hada ɗauko wata nikuma nace wallahi bazan hau motar ba,na biyo Fatima ta kawoni"


Dariya Pappa yayi"to ina ruwanki dashi"


"to Pappa nima abani key ɗin mota mana"


"Allah Pappa kada ka bata"


Haka suka zauna sunata shiririta,Saudat ta miƙe ta shige kitchen sai gata tadawo da plate ɗin abinci,ta zauna kan capet xata faraci ya sauko daga kan kujera,yasa Hannu tare sukaci abincin,kafin kace mi,har sun kama firarsu kamar ba faɗa suke ba.


Pappa ya Mike"kudai duk wanda ya shiga tsaka ninku zaku bashi kunya"


Mami tace"aini shiyasa babu ruwana da shiga hidimarsu."


             ****

Ranar daddre tana haɗa bag ɗin da zataje skul da ita washe gari,ta saka komi saidai bataga takardun payment da takardar indijin ɗinta,ta duba sosai.


Miƙewa tayi ta sauko daga saman ta dawo babban falonsu.


"Ya Areef Ya Areef Ya Areef" kiranshi kawai take,daga ɗakinshi yake jiyota,fitowa yayi,lokaciɓ su ilham suna falon suna Home work,"haba lafya wanann kira you scare me"


"ina takarduna suke?"


Zama yayikan kujera,"ni kin bani ne,ba saida nace maki ki daka a jikka ba?"


Sai lokacin ta tuno da hakan,ta kalleshi"aikam ina tinanin sun faɗi"


"sakakinki yayi yawa,kina wasa da Abubuwa masu mahimmanci"


Zama tayi kan kujera,"ina tinanin a hall ɗin da mukayi second lecture na bari"


Fira suka cigaba dayi,suna Addu'a Allah yasa tagansu,sai wajan 9:30 kowa ya tashi daga fira,suka nufi ɗakunansu.


Saudat fararan kayan bacci tasaka,riga da wanko,hula ta sakawa kanta, tana kwantawa wayarta ta fara ƙara,Number ba suna tagani abin yabata mamaki sosai,dan ita batada mutane dayawa gaya kuma kiran dare ake mata.


Ƙin ɗauka tayi,jin anƙara kira,ta ɗauka tare da karawa a kunnai"Assalamu Alaikum"


Dan gaban Saudat yafaɗi jin wata girls killer voice,da sauri ta kalli wayar ta ƙara maidawa a kunnanta"ina yini?wake magana....."

"kina magana da Usman Abdurra'um.......
*Aunty Haliloss*

WA NAKE AURE?

          *whattpad AuntyHaliloss*

09

"kina magana da Usman Abdurra'ub,ina fatan ina magana da Saudat Mu'azzam Alti?"

Saudat ta nemo natsuwarta"eh nice"

"kin yada takardunki a skul,so na tsinta a bakin theatre hall,banda chji shiyasa bankira ba tun wuri"

Saudat taji daɗi sosai ta miƙe xaune"kai Amma nagode sosai,insha Allah gobe zan ansa,nagde kwarai"sukayi bankwana ta ajiye wayar.

Washe gari Saudat koda zasu fita ta manta tagayawa Areef ankirata kan maganar takardun,har ya ajiyeta ya koma gida.

Saudat takira Usman domin ansar takardunta,sanye yake da farin yadi saidai ba wani tsadane dashiba,Usman ba baƙi bane hakan bazamu kirashi fariba,yanada kyau iyakar nashi,Usman irin mutanan nan ne idanka gansu lokaci guda bazaka yi saurin cewa suna cikin halin rayuwa a gidan suba.

Inda yake ta nufa"ka daina kira ganinan"

Juyowa yayi,suka gaisa,ya miƙa mata takardun"duba kiga sun cika?"

Dariya taɗanyi"Gaskiƴa ngde sosai,anan skuƙ ɗin kake?"

"eh"
"ngde"

Dai-dai lokacin Areef yayi parkin wajan,yana kallonta,itakam Saudat taɗan sakar ma Usman fuska,sannan sukayi bankwana.+

Sai data juyo sanan taga Areef,murmushi ta mashi tana nufar inda yake,ɗaure fuska yayi tashiga ta zauna,ya tada mota,sun jina suna tafiya ba wanda yayi magana hanyar gidan Ammi ya nufa.

"Laaa shine baka gaya man gdan Ammi zamuje ba?"

Shiru yayi mata,tana kalleshi ta harareshi daidai lokacin ya kalleta"lallai ni kike harara ko?"

"a Ya nifa ba harararka nayiba,Amma sai inta magana kaman banza"

Gate ɗin gidan suka isa,suna shiga ta barshi ta cigewarta,Ammi tana bedroom ɗinta,Saudat ta shiga tana "Ammin mu"

Ammi ta fito,tana dariya"ai danaji kirannan nasan kece,daga ina haka"

"Ammi daga skul"

Areef ya shigo da alamar gajiya a tare dashi,Ammi ta kalleshi"sarkin lakwaikwaita ya akayi?"

"nagaji ne Ammi"
"aikin mikayi"
Saudat ta kalleshi"Ammi shi Yaya Areef haka yake,raggo ne"

"ni abokin kine?"
Yana magana yana zare mata ido,Ammi tace"kai ni bansan haka,miyasa kake raggancin?dan tace shine zaka zare mata ido"

Saudat ta cire afterdreess ɗin dake jikinta,takoma da riga da skert english wears"ni barima in bar maka falon"tana maganai tana shigewa kitchen.

Fruit juice ta haɗa,ta fito da try da cup a hannunta ta ajiye takona ta ɗauko jug ɗin.

Ɗauka yayi zaisha,Saudat ta kalleshi"Ammi kice kada ya shaman kaya"

Ajewa yayi yana kallonta,Ammi ta miƙe"bari kugani,intashi in mutun yana kusa daku baya gajiya da magana"

Ammi tana barin wajan,Areef ya dawo kujerar da take zaune,ya ɗauki cup ɗin yakai baki,itama tasa hannu zata ɗauka,ya riƙe hannun,yana kallonta,idanuwanta yake nemowa da idonshi,sosai suka haɗa ido,kasa ɗauke idonshi yayi"waye kuke tsaye dashi dazu?"

"ji ya Areef kabarni insha lemo na"

"nace waye wanan?"

"ɗan skul ɗinmu ne"

Kallonta yakeyi,yakasa gane gaskiyar maganar ta,ya saki hannun ya canza kujera,sun jima a gidan,sannan suka tafi.

               ***
Ranar dadaddare Areef kasa bacci yayi,dan ya rasa miyake damunshi,wani irin so yakewa Saudat,har yakaiga yana tsananin kishinta kwata-kwata bayason ganin wani a kusa da ita,ya riga yasan batayi mashi ƙarya hakan yasa ya yadda ba saurayinta bane,to amma zuwa yanzu yafara tunanin gaya mata,saidai wata zuciya ta hanashi.

STORY CONTINUES BELOW

Tun ranar Saudat basu ƙara waya da Usman ba,suna haɗuwa dashi a skul so biyu suna gaisawa,kasancewar shina Mass com yake karanta,saidai shi yana final year ne.

Ranar suna zaune,a skul itada Fatima lokacin basuda lecture,sai handout dake hannunsu,cause ɗin yanayi masu wahala,Usman yazo wucewa,ta gabansu,ya gansu,saidai bayaso yana masu magana gidun wulaƙanci,kasancewar daka gansu kasan ƴaƴan masu akwaine,yi yayi kamar bai gansuba,ta kalleshi"Au wucewa za'ayi ba magana"

Juyowa yayi yaɗan kalleta,yana murmushi, fararan haƙoranshi suka baiyana"yi hakuri ban kula dakuba,yakuke"

"su duka suka Amsa da lafiya lau"

"Ya lecture exams nata matsowa"

Saudat tace"eh wallahi,gayanan munata fama wanann cause yana bamu wahala"

Usman ya zaro ido"kai haba wane cause ne?"

Saudat ta gaya mashi,yayi dariya,take Usman yafarayi mata bayani,Fatima tanaji ta matso"gaskiya ka dawo baya dan banjiba"

Waje yasamu ya zauna,ya cigaba da koya nasu,Saudat tasha Mamakin yadda ya iya cause ɗin sosai,sai takoma tana kallonshi.

Daga lokacin sukayi sabo da Usman,da wuya suje skul basu Haɗu sunyi tutorials ba,take suka rinƙa gane causes ɗinsu,daga nan Saudat ko gida take karatu wani abu ya shige mata zata kirashi,shikuma yahau yi mata bayani,wannan dalilin ne yasa sukayi mugun sabo da Usman,cikin ƙanƙanin lokaci,har yakai ga Saudat tana cewa yazo gida idan tanason yakoya mata wani abu,Amma Usman yace mata bazai samu damar zuwa ba,yana gudun yaje gdan sbd aganinshi ba ɗaya suke ba.

             ****
Saudat sun fara Exams,ana gobe zasuyi wani cause sosai suke tsoron lecturer ɗin,dagewa tayi tanata karatu,tashi tayi tayi Salla ta koma ta ɗauki handout ɗin,tana karatun saidai takasa gane wanewa.

handout ɗin ta ɗauko ta sauko ƙasa,Areef yana kwance kan kujera su Ilham suna tsakar falon,"Ya Areef tashi kagani,nakasa gane...."

Tashi yayi zaune,ya kalleta"ina ciwan kaine,kawo in duba maki"

Zama tayi ta dafa kanshi"ayya yi hakuri kuma akwai zafi jikinka"

Baice komiba yacigaba da koya mata,can yaɗanyi shiru,ta kalleshi"ya dai"

"gaskiya wanann sai ƴan Mass com,nakasa gane yadda zan maki bayani"

Yana maganai yana komawa ya kwanta,Saudat ta miƙe"to bari in anso maka Magani wajan Mami"

Koda ta koma,ta kawo mashi maganin yasha sanan ya tafi masallaci domin ƴin sallar la'asar,tana koma ɗakin taga misscall ɗin Usman.

Kiranshi tayi suka gaisa,ta tuna da karatunta"yauwa plzz yaudai zan nemi Alfarma kayiman dan Allah"

"inajinki yakayi?"
"so nike kazo gida wannan cause ɗin zaka ƙara koyaman"

Shiru Usman yayi,dan yasan ba yaune karan farko ba,"inajinka kada kai man musu plzz"

"shikenn zanzo ƙarfe biyar da rabi"

"yauwa nagde sai kazo"

Take Saudat tafara tunanin tarbar da zatayi mashi,ɗakin Mami ta shiga"Mami baƙo gare mu yau,Usman zaizo"

"yaudai zamuga Usman kenan"

"wallahi kuwa" kitchen ta nufa,itada mai Aiki sukayi abinci da drinks,takoma tayi wanka,tashirya cikin doguwar rigar atamfa,rolling tayi akanta,Usman yana zuwa ta shiga dashi falon baƙi,ita da su Ilham suka tafi.

Abinci takai mashi da lemo,shikam kallonta kawai yake sai lokacin yake tantance asalin kyanta,zuciyarshi tana buga mashi,wata kuciyar ta farayi mashi kashedi.

STORY CONTINUES BELOW

Shadda yasa fara babu aiki a jikinta,sai black ɗin takalmi,ruwa kawai yasha yace ya ƙoshi,Mami tazo suka gaisa ta fita,Handout ɗin ta miƙa mashi daidai lokacin suka haɗa ido da sauri ta kauda kanta,zuciyarta na harbawa,Usman yacigaba da koya mata.
Areef ya shigo gdan ganin falon baƙi a buɗe ya nufi wajan,dan a tunaninshi Muhsin ne yazo,dan wani lokaci shida frends ɗinshi yake dawowa abuɗe masu falon baƙin.

Ɗaga cutains ɗin yayi,da sallama,Usman ya amsa,ganinsu yasa shi ɗan yi kamar zaikoma baya,dan baiyi tunaniba,Saudat tace"Sannu ya Areef ya kan"

Wani faɗuwar gaba yakeji,ya kalleta"da sauƙi" da kyal ya matsa ya miƙawa Usman hannu,sukayi musabaha ya shige ciki.
A falo ya tadda Pappa,zama yayi yagaidashi,"Maminku tace bakajin daɗi,ashe sosaine dan naganka ba kwarin jiki?"

"wallahu kuwa Pappa"
"ko Asibity za'a dai?"

"a'a kwantawa kawai zanyi dana huta shikenan"yana maganai yana nufa hanyar da zata kaishi part ɗinsu.

Koda ya shige kan gado ya faɗa,tare da dafe kai,innalillhi ƴake karantowa,dan jiyake kamar zuciyarshi zata buga,sai lokacin ya ƙara tabbatar da son da yakewa Saudat.

Saudat tana gamawa takoma gidan,bata ganshiba tace"Pappa ina Ya Areef"

"yana ɗakinshi maybe bacci yayi"

Cikin damuwa tace"may be ciwan kanne,bari in ganoshi"

Tana zuwa ta sameshi kan gadon,kanshi yana kallon silin,zama tayi kan bed side lokka,tana mashi sannu,baice mata komi ba.

Ta matsa"Ya Areef kodai incewa Pappa aje Asibity"tana maganai cikin damuwa.

Areef ya tashi zaune yana kallonta,"Saudat tun ranar dana ganki da guy ɗin nan i ask about him,kincewai abokin karatun kine...."
Dai-dai lokacin Pappa yazo wajan,yaji maganarshi sosai,tsayawa yayi sai yaji shiru,Pappa yayi mirmushin manya,kasa shiga ɗakin yayi ya juya ya nufi sama wajan Mami.
Sallar magrib tagama itama,ya zauna kan kujera yana dariya"the secind time da nake gaya maki,yaran nan they are in Love with each other kin man gardama"

Ta kalleshi"to ya akayi"

"jinsu nayi yana mata complain akan yaron da yazo wajanta,like yana kishi"

Dariya Mami tayi"to Allah yasa hakana,kaga dai ayi kowa ya huta,muma hankalinmu zai kwanta.

        *****
Tun daga ranai suka fara abubuwa like love tsakanin Usman da Saudat,ba'a 1hr sai sunyi waya,idan ana skul kuma suna tare,lokacin Areef yagama gane soyayya suke.

Dan lokacin dole suka raba tafiya makaranta da Areef,aka bata mota,Areef kam yasan saboda Usman ne yasa ta raba tafiyar,kullun ita take ɗaukarshi a babban titin unguwarsu,har yagama skul.

Usman baya zuwa gidansu Saudat ɗin saidai suyi waya,kuma Saudat ɗince take kiranshi,su daɗe,sai dai Usman bai taɓa yiwa Saudat ƙaryaba,bai ɓoye mata komiba yagaya mata shi ɗan talakawa ne,dan wani lokaci flasing yake mata,sata kirashi.wani lokaci kam a park suke haɗuwa suyi fira.

Aeeef ya gane canjin da Saudat tayi sosai,ba ƙaramin tashi Hankali ya shigaba.

Wata rana Saudat tana sauri,ta gama shiri,gdansu Fatima zataje Yayarta ta haihu,fitowa tayi daga ɗakin ta shigo falon,duk ƴan gidan suna xaune,ta kalli Mami,Mami zan tafi,Pappa ya kalleta"wai yaune sunan"

"eh Pappa"

Hannu yasa Aljihu,ya fiddo kuɗi"gaya ki sayi kayan Baby kikai mata,Yayanku yakaiki"

"A'a Pappa nizanje da kaina"

Murmushi Areef yayi dan yasa,tunda tayi gar dama zasu haɗu da Usman ne,koda ta fita,shima miƙewa yayi yabita.

Ice cream joint tanufa,koda ta isa Usman har yaje,Areef yana ganinsu wani kishi ya shigeshi,lokacin yafara tunanin gayawa Saudat soyayarshi,amma kuma yasan tana tare da Usman.

Hankali tashe ya wuce gidan Ammi,zaune ya tadda ta,zama yayi yana kallonta,itama shitake kallo,idanuwanshi sun canza"ya Akayi ne?"

"Ammi plzz wallhi wani take so,i can't control my self"

Zaro ido tayi,ita kanta batun yazo tagano soyayyar Sauda a tare da ɗan nataba,"tofa ina kasamo ta ita kuma"

Sai lokacin yake tunanin maganar da yayi,dan gaba ɗaya baya cikin hayyacinshi,zai fara kame-kame,Ammi tace"kai naganoka fa,zan samu Mamin taku in gaya mata,but Firtsly  you have to approach her before"

"no Ammi Nafiso aɗauki maganar serious"
Sun jima suna tattauna maganai,sannan yatashi yatafi gida.

Ranar Ammi tanemi Dady tagaya mashi,shikuma ƴaje ya gayawa Pappa,Pappa dariya yayi,ai dama naganosu,kyalesu kawai nayi,gaba ɗaya family ɗin sunji daɗin maganai kowa murna yakeyi,saidai Sauda batasani ba.

Bayan sati biyu Mami ta farayi mata magana,Saudat ta zaro ido"haba Mami nifa ba soyayya nike da Ya Areef ba,taya zaku fara irin wanann magana"

"to aishi Areef ɗin shine yazo da maganar"

Saudat ta turo baki"Nidai Mami kubar maganar nan,dan Usman nikeso"

Wani kallo Mami tayi mata "bakida kunya ashe" nan Mami tahau yi mata faɗa,amma tace itadai abarta,Usman takeso.

Koda Pappa yadawo sukayi Magana da Mami dakanshi yakira Saudat,Amma tace ita batason shi Usman takeso.

Lallashinta Pappa ya hauyi,tare da kwatanta mata yadda rayuwa take,dakuma shi Areef ɗin yana sonta.

Kuka takamayi ita batason Auren dole,aikam tun daga lokacin ran Pappa ya ɓaci,ya koma yi mata faɗa.

Ankai sati biyu ana rarrashinta amma taƙi,sosai ran Mami da Pappa ya ɓaci,shikam Areef dama yasan za'ayi haka.lokacin ne Pappa ya tsananta mata.

Ranar Saudat,taje gidan Ammi tana kuka,Ammi ta tareta da Rarrashi,Saudat ta faɗa jikinta tana kuka"wallahi Ammi Pappa da Mami sun daina sona,ni wallahi bani son Yaya Areef.......
*kubiyo ni*

*Aunty Haliloss✍🏽*WA NAKE AURE?


          *whattpad AuntyHaliloss*


*INA JIN DAƊIN COMMENT ƊIN DA KUKE BANI,HAR BANA IYA RAPLY SADOBA YAWAN MUTANAN,BUT ZAN FARA YI MAKU DEDICATION,KAMAR YADDA NAKE A SAURAN NOVELS ƊINA❤❤❤*


*kuna musamman ne a wajena,BILLY SHANTALY,NAMESY YAR ALBARKA,MRS S WAZIRI,AUNTY JAMILA YAKASAI,MR MUHMUD,MAMAN GIƊADO,FATIMA RAƊƊA, INA YINKU OVER ILYSM❤❤*


10


Hankalin Ammi yatashi jin yadda Saudat take magana,anan Dady ya tadda ta,tana kukan,zama yayi tare da faɗin "lfy mi yake faruwa"


"wlh yanzu ta shigo,tana kuka,ita batason auren Ya Areef"


Dady ya matsa gefenta"shikenan tashi muje gdan"


Tare sukaje gidan tare da Dady Ammi ma saida ta bisu,Pappa ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba,haka Dady yace mashi  lallai saidai Areef yayi haƙuri dan bazai yadda ɗiyarshi ta Aure wanda bataso ba.+


Lokacin Dady ya kira Areef yagaya mashi,tun daga lokacin Areef bai ƙara samun natsuwa ba,lokacin kuma ya sanar da Saudat tacewa Usman ya aiko da magabatanshi.


Koda Usman yaji labarin ba ƙaramar kaɗuwa yayi ba,dan saida yafara zuwa wajan Dady,sosai zikayi magana ta mahimta,Dady ya yaba da hankalin Usman,sannan yace iyayanshi zasuzo ɗin.


Ranar da iyayan Usman sukazo,ranar Pappa ya kira Saudat,falon tashiga ta nemi waje ta zauna jiki babu kwari,ya kalleta"kin zaɓawa kanki wanda bashi mukeso ki aura ba,sbd haka ankawo kuɗi saidai inaso insanar dake zamiyi ƙoƙarin yi maki kowace hidima,amma sharaɗi ɗaya shine,babu ke babu zuwa gidan nan da neman wata buƙata"


Saudat kam,lokacin bata damuba,dan gani take kamar yanzu an daina santa a gidan.


Tunda Areef yaji ankawo kuɗin auran yake cikin tashin hankali,lokaci guda ya canza,itakam Saudat sai ta daina zama tsakar falon,dan tun lokacin idan pappa ya taddata zaice ta tashi tabar mashi falo,takoma sama.


Ƴan Uwan Usman sun kawo kayan saka rana,Pappa yace wata ɗaya yasaka,haka kuwa akayi,Usman kuwa bashida kuɗin yin wasu hidindimu saidai Saudat ce ta bashi cikin kuɗin da suke a Account ɗinta.


Ammi kuwa tsaye take,wajan yiwa Saudat hidima,dan dakanta ta haɗa mata kaya kamar wani lefen,dan wanda aka kawo daga gidansu Usman ba wasu kaya bane.


Mami kam ido tasaka masu,dan tana bayan Pappa,Muhsin ma yayi baƙin cikin abinda ƙanwarshi tayi,Areef kam damuwa bata musaltuwa a wajanshi.


Haka akayi biki,Saudat kam ko ƙawayenta bata gaiyata ba,Fatima ce kawai sukayi hidima a tare,Usman kam yanason  Saudat,kullun cikin bata haƙuri yake,yana rarrashinta.


Ranar da aka ɗaura Aure Areef kasa zuwa massalacin yayi yana ɗaki,haka aka ɗauki Saudat aka kaita gidan Usman,dangi kam sunga ikon Allah dan basuyi tunanin haka zasu taddaba,yarinya tana cikin gata ta zaɓarwa kanta haka.


Tun bayan da aka gama walima,kowa yatafi gida,Saudat tana samun kulawa sosai wajan Usman, don yana nuna mata soyayyarshi.


Bayan satittika,Saudat ta fara fuskantar matsala daga wajan Hayatu ƙanin Usman,dakuma Mama,domin kuwa Mama irin mutananne masu muguwar gulma ga shiga sabgar da ba tata ba,uwa uba,masifar ta,gaba ɗaya Hayatu halinta ya biyo kab babu abinda ya bari,ga zalinci,dan ko yaran Unguwa tsoronshi suke.


Usman kam asalin halin mahaifinshi yayo,babu ruwanshi,dan wasuma cewa suke ba Mamace mahaifiyar shiba,tun lokacin Mahaifin Usman yana da rai yasha fama sosai da Mama,dan tun daga Hayatu bata ƙara haihuwa ba,ƴan uwanshi sukace ya ƙara Aure,aikau su kansu sunjita sosai.

Baba kam dama bashi da abin cewa a gida,Haka yabar Maganar auran har yarasu bata barshi yayi auran ba.


Ɓan garan Areef kuwa,tunda akayi auran Saudat baya yawan zama gidan iyakarshi part ɗinshi,dan duk lokacin daya shiga,yana tuno da Saudat,sbd ba ƙaramin so yake mata ba.


Areef har Asibity ya kwanta,amma yasha faɗa wajan Pappa,dan saboda ciwan zuciya ne ƴake damunshi.


Areef saida yaga ran Pappa ya ɓaci,har shima yafara shiga damuwa wannan dalilin ne Areef yayi ƙoƙarin kauda damuwar da yake tare da ita,sai dai yasan Rashin Saudat wani babban tabo ne a zuciyarshi. *Wannan shine asalin labarin Auran Usman da Saudat*


              *****

Bayan sati biyu da sallamota daga asibiti,Zaune take tasamu sauƙi sosai,dan jikinta yayi mata dama,ta warke sosai,Usman ya shigo ɗakin,da leda a hannunshi,Ayaba ce ya sawo mata da lemo,Amsa tayi tana kallonshi"mi kaci ne yau?"


"ai Mama ta dafa taliya,kina bacci na aje maki sauran"yana maganai ya jawo mata kular dayaci ya rage mata.


Ta amsa,ayaba ta faraci,ta ajiye kular abincin"kaga na ƙoshima wannan ayabar danaci"


Kallonta yayi,ya jawota gefenshi,yana shafa kanta"kinga bikin Hayatu saura sati guda,ga cikon kuɗin dake hannuna kisayi abin da kikeso"


Saudat ta kalleshi"kamar mi?"

"ɗinkin da zakisa"


Usman yana bata tausayi,dan baya ɓoye mata komi"a'a kafidda ka sayi ɗinki,nidai inada kaya da ban saka ba sabobbi"


"ai kuɗinki ne?"


"nikuma nace ka ɗauka ko"


Tunda Hayatu yayi ma Saudat wanann abun,ya fita sabgarta,itama Mama taji tsoro bata ƙara matsa mata ba.


Haka aka shiga hidimar biki,yarinyar ƴar ƙawar Mamace wadda take yawan zuwa gidanta,in kazo Mama batanan to tana gidan Haule.


Ranar biki kam ansha hidima,ita dai Saudat iya karta ido,akayi biki aka kawo amarya,yarinya ce Saudat ma ta girmeta,sai dai tana da girman jiki.


Anagama hidima,Saudat ta koma bakin aikinta a gidan kamar yadda ta saba,Nusaiba kam itama ba daga baya ba,saboda dama talla takeyi,saidai har lokacin iyakarta gaisawa da Saudat.


Ko sati Amarya batayi ba Amma har uwarta ta fara zuwa gidan,suci hirarsu da Mama Nusaiba tana saka masu baki kamar ba surika ba,ita dai Saudat ɗaki take shigewarta,babban jin daɗinta da suka rage ta kurata.


Ankai sati Ukku a gidan Saudat tana aiki,ranar tayi aiki ta gaji,gaya ko tayata Nusaiba batayi,in Hayatu ya shigo gaban Mama zata kama kiran Habibi sannu da zuwa.


tana shiga ɗakin Usman yana kwance,ya murgina yana kallonta,"gaskiya Dear wannan aikin yayi haka,zanyi wa Mama magana sai ku raba aikin keda Nusaiba"


Saudat ta zauna"wallahi kuwa"


Ranar suna Zaune su duka gidan,Saudat tana kan kujera ƴar tsugunni,tana Assgnmnt,Usman kuwa yana ɗaki,Mama da Nusaiba suna kan tabarma guda sai labari sukeyi,dan saudat tagano wani shiri sukeyi kamar saboda ita ne,ko dan taji haushi,dan tafara lura da take-taken raini a wajan Nusaiba.


Hayatu ya shigo gidan,da ledoji a hannunshi,Mama ta kalli Nusaiba,"tashi tashi ki amso mamu"


Nusaiba tana dariya,"to Habibi kawo"


Hayatu ya miƙa mata,"shefanene,Abokaina zasuzo da marece,ayi abincin dayawa"


Nusaiba ta Ansa ta buɗe sanann ta miƙawa Saudat"gashi cefanan ne,kinji abinda yace"


Saudat ta ɗago ta kalleta,yadda yarinyar take magana,kamar zata sakata dole"Ai yau zaki anshi aiki"


Mama tace"Eye lallai kina nufin wannan uban aikin ita zata yishi?"


Saudat tace"Mama naga Abokan shi zasuzo kuma cin girkin Amarya zasuzo"


Hayatu ya anshi ledar daga Hannun Nusaiba,ya miƙa wa Saudat"Anshi keza kiyishi,ita zatayi girkin kamar baiwarki,to ni Matata ba baiwa bace,Abokaina zasuzo fatan doya da shinkafa da Miya zakiyi mas....."


*AUNTY HALILOSS✍🏽*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


_This page dedicated to👇🏼👇🏼_

Abeedah my goggo

Ummu safiyah

Zainab Hassan makawa

Ummu Ahmad

Zakiya

Hafsatt🌹

Ammyn Farhana

Mrs Ayuuu

Ummu Hauwart

Nafsy

Mufeedat Bashir (Arabian girl😜)

Ta birni(yar kauye😜)

Mum hanan

Meenat Abdullahi.

Babybint💞

Zainab Ahmad.

*Really appreciate your commnt🌹🌹🌹🌹*


11


Saudat bata  jira jin abinda Hayatu zai ida cewaba, tace"to ai sai ka bata,saboda nima ba baiwar bace"


"ke ni kike gayawa magana haka, to na rantse sai kinyi abincin nan"


Saudat ta d'auke takardunta ta nufi hanyar d'akinta, anan sukaci karo da Usman, kallinta yayi yace"koma"+


Saudat batayi mashi musu ba, ta bishi baya,Mama kau sai kallon shi takeyi, jiranshi kawai take taji abinda zaice.

Zama yayi can gefen Mama, ya kalli Hayatu"ku zauna ku duka" Hayatu ya kalleshi zaiyi magana Mama tace"ka zauna kaji abinda zaice"


Su duka suka zauna, saudat takoma kan kujerar data tashi, Usman ya kallesu ya maida hankalinshi kan Hayatu"yau sati nawa dayin Auran ku? "


Cikin gadara yace"sati Ukku"


"yau sati Ukku,kaga kenan yakamata ace matarka tafara shiga kitchen, su raba aiki da Sauda, dan aikin yana mata yawa itama, ko dai su raba kwana biyu-biyu ko ukku,amma bai kamata ace ita zata ringa yin duk aikin gidan nan ba"yana ida maganai yana kallon Mama


Hayatu baice komiba, sai shan kunu yakeyi, dan yasan bashi da gaskiya, Nusaiba tace"sai kace wata kishiyata, zan raba girki kwana biyu-biyu ko ukku, to wallahi bazan iyaba"


Mama tace"kibar Babanmu yagama yanke hukunci"


Usman ya kalleta"Mama ba maganar haka bane, dan Allah kubar irin haka, duk sadda za'ayi maganar gaskiya sai ku maida abin babba,kukanku kunsan gaskiya"


Hayatu yace"kace dai ka hanata yin girki, to wallhi... "


"kada kayi rantsuwa, idan ya hana matarshi,aini sai in tashi in girka suci"cewar Mama dake huci.


"a'a niba Hanata nayiba, gaski... "


"Kai da anyi magana, sai kace gaskiya,tomu bamusan gaskiya bane komi, koko yarinya daga zuwanta gida, sai in kama sata aikin wahala"yadda Hayatu yake maganar yaba Saudat Mamaki, itada kwananta biyu ta fara girki,wanda tunda take rayuwarta bata irin wannan wahalar, koda Mami batayi masu horan rashin aikiba, amma basu kad'ai sukeyi ba.


Mama ta tashi ta d'auki ledar da Hayatu yakawo,Nusaiba ta mik'e ta shige d'akinta,Saudat kam tayi Mursisi tak'i amsar girkin, tana ganin zasu had'a ido da Usman ta kauda fuskarta daga kallonshi, ran Usman yayi mugun b'aci.


Hayatu ya juya ya anshi ledai,ya wurga ma Saudat"Allah sai kinyi girkinnan"


Mama tace"kabar soko, yana zaune mahaifiyarshi zatayi aiki, hankalinshi kwance,saboda yana son matarshi"


Saudat batace komiba, ta juya ta shige d'aki, wani k'ululun bak'in ciki ke biyo mata mak'oshi, batasan lokacin da wasu zafafan hawaye suka zubo mata ba.

Tana zama bakin gadon Usman yana shigowa d'akin da ledar a hannunshi, ya zauna kusa da ita"Dan Allah kiyi hak'uri,kiyi girkin nan,bawai su zakiyi mawaba ni nasaki,kuma kinga irin halin da muke shiga duk lokacin da nayi magana akanki, cikin gidannan"


"yanzu kana nufin nizanyi aikin nan"


"kiyi hak'uri nace kinga yadda ran Mama ya b'aci akan hanakiyi da nayi"


Sai lokacin Saudat ta kauda kanta daga kallonshi, wato shi bayason b'ataran mahaifiyarshi, amma ita ta b'ataran nata iyayan ta Aureshi,ita dama iyayanta sunfi nashi kamala da sanin ya kamata, wasu hawayen suka k'ara gangaro mata.1

Usman yasa Hannu ya goge mata, ya janyota jikinshi yana shafa bayanta, alamar rarrashi, mik'ewa tayi ta d'auki ledar ta nufi tsakar gidan ta kama aikinta.

Ankai minti shabiyar saiga Nusaiba ta fito daga d'akinta, ta kalli Saudat,ta saka wata irin dariya, ta kalli Mama dake jan ruwa,taja gefe ta zauna.

Saudat tasan da ita take amma tak'i kulata,saima zama da tayi tana ma Saudat d'in habaici.

Saudat tana gamawa ta mik'e tabar masu abincinsu, tayo wanka ta shige d'akinta,lokacin Usman yafita, koda suka juye abincin,k'in rabawa da su,sukayi,saida abokan sukazo suka tafi aka fiddo sauran da suka rage aka mik'o masu.


           ******

Tunda akayi wannan abun, Nusaiba ta koma kamar kishiyar Saudat,Usman kau ya lallab'ata ita take aikin gidan, tun tanajin wahala har abin yazame mata jiki, data tashi zayi aikinta,taficewarta makaranta,ranar da bata zuwa skul take masu har da girki, idan tana skul, shara takeyi wanke-wanke da janruwa tayi tafiyarta.

Bajimawa Saudat ta k'ara samun wani cikin, saidai bata wani laulayi, ciwankai kad'ai takeyi, hakan yasa kowa na gidan bai saniba, Usman kam har tausayinta yakeyi.

Idan tayi aiki tagaji, dasun shiga d'aki Usman yake mata tausa,Saudat harta gage damuwa, saboda tasan mijinta yana bata kulawa.

               ****

Nusaiba ce zaune sai kwara amai take a bakin maguji,Hayatu ya fito daga d'akin yana mata sannu, mik'ewa tayi tana zama gefe,Saudat tana kallonsu,ta taga, itadai batace komi ba,Usman ne ya tab'ota, yana mata alamar gulma.

"Matar gidannan fa ta kamu"

Saudat tayi dariya"kai ba ruwana"


Ya janyota"matsoraciya,jeki taimaka mata"


"Allah ya tsare ni,nima inji da kaina"


Yayi dariya,Saudat tana zamewa jikinshi.

Ji sukayi Hayatu yana kiran Saudat, Saudat ta kalli Usman tana zaro ido, "wallahi ni tsoron inji yana kirana yake"


Tana maganai, ta fita"Ya akayi"


"ni kikeyiwa wannan maganai? To kije d'akin ta zaki share mata"


Saudat batayi magana ba dan tasan idan tayi tsami maganar zatayi.

Hanyar d'akin ta nufa,tana d'aga labule, duk k'ura d'akin da k'azanta, ga aman da tayi gefe.


Saudat ta gama gyara d'akin taje d'akinta ta d'auko turaran wuta, ta zo tana sawa saboda warin da d'akin yakeyi.

Mama da Haule suka shigo gidan, Mama ta kalli Saudat ta harareta"ke kuma miya kaiki d'akinta?"


"cewa yayi in gyra mata"


Haule tace"a'a ban yadda da hakaba, ki shiga d'akin d'iyata kina wasu Abubuwa"


Mama  tace"wai minene ma cikin kaskon? "


Saudat ta kalli kaskon"turaran tutane na saka mata sabd...?

"Kee Jamila, wannan ba tiraran wuta bane, haba ashe shiyasa baki da ikon yiwa d'anki magana,ta asirce shi, to shima wannan dakika samu yana taimakonki gayanan ana saka masu hayak'i a d'aki"


*much commnt plz*


*AUNTY HALILOSS✍🏽*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


*RUKSAD MAMAN SIYAMA, NAGODE DA ZIYARA,TUN DAGA NIGER HAR NIGERIA,ALHAMDULLAH KO ANAN NASAN INADA MASOYA, DAGA GARURUWA DA DAMA NAGODE SOSAI*


_DEDICATED TO : Esha Mustapha,Sis Bilks U Hamzat❤❤_


12


Hannu Mama tasa,ta bige kaskon garwashin dake hannun Saudat tana kwalawa Usman kira, yana d'aki ya fito,ya kallesu"lafiya Mama?"


"Babu lafiya, yarinyarnan nema take taga bayanmu, yanzu har takaiga tana sakawa Mutane hayak'i a d'aki?"


Usman ya zaro ido yakalli inda aka zudda garwashin, ya kalli Saudat"Miye kikeyi? "


Saudat da lokacin Hawaye sun zubo mata tace"wallhi turaran k'amshi ne ba hayak'i ba"


"k'arya take makira,Allah ya kama ki yau, ashe dama shiyasa kika mallake man d'a bashida aiki, yana nan lik'e dake kullun"


"Wallh.."bata idaba Usman,yace"miye dalilinki na yin hakan? "


Mama tace"Au tambayarta ma kakeyi,bayan ba yau nasaba ganiba, ai duk munafuncin da yarinyarnan takeyi, kallonta kawai nike, saida yau Allah ya tona ta"


Haka Mama taci gaba da d'ora Usman, zuciyarshi tayi mashi zafi, yama rasa miye zaiyiwa Saudat,tunda Mama da Haule sukaga Usman ya d'auki maganarsu, saisuka bar wajan suna Allah wadai da Halinta, wata muguwar Harara Usman yayi mata"Yanzu ke har kina da kud'in bin bokaye? "


"Wallahi dear ba... "


Bai tsaya sauraranta ba, ya fice daga gidan, Saudat tana kuka ta shige d'aki,kukanta tasha sosai, dan tunda suke da Usman bai tab'ayi mata irin hakaba.


Koda Usman yadawo gidan, kafin ya shiga d'aki saida Mama takirashi, sun dad'e suna magana akan Saudat, wanda duka k'arya ce take karanta mashi, koda ya koma d'akin gaba d'aya bai kula taba, Saudat tana kuka tana bashi Hak'uri amma bai d'aukaba, saboda zuciyarshi tagama yadda da Abinda Mahaifiyarshi ta gaya mashi,Haka saudat taci kukanta batasan lokacin da bacci b'arawo ya d'auke taba.

Haka washe gari ko kulawar kirki bata samuba, koda tafito tsakar gidan, lokacin ta k'ara ganin tsana a idanun mutanan gidan, domin sai lokacin taga rashin kuya wajan Nusaiba, sai wulak'anci take tana cika tana batsewa ita a dole mai ciki.


           *****

Tunda wannan abun ya faru Saudat batada inda zata zauna taji sanyi, hakan ya k'ara tabbatar da damuwa a rayuwarta,hakan ya kawo had'in kan y'an gidan,dan Usman yanzu shiri suke da Hayatu,dan har yafara zuwa garejinsu, yana d'an aiki, babbar matsalar koya samo kud'in Mama bata bari, sai ta kama d'auko abubuwa marasa muhimmanci tana d'ora mashi dan sucinye kud'in.

Zaune take lokacin cikin jikinta ya fito sosai,dan ko alokacin yakai wata shidda,gaba d'aya kewar mutanan gidansu take, sai lokacin take tunanin yadda family d'in ta suke sonta, amma takawo kanta anan.

Usman ya shigo d'akin,sannu tayi mashi ya amsa da yauwa, sbd yanzu iyakar gaisuwar kenan, dan harta manta rabanda ya dawo gida suyi huging d'in juna.

Yana cire kayanshi ya canza wasu, ya koma zai fita"ina zakaje kuma"


"Abinci zanci"Batace komi ba, yafita, dan yanzu idan aka gama abinci mashi a d'akin Mama yake zuwa yaci.

Washe gari ta shirya zata makaranta,doguwar rigar atampa tasa, sai mayafin data yafa, ga cikin ta daya turo, saidai ta rame sosai, ta k'arayin duhu, saboda rashin sabun kayan amfani masu kyau.

Usman yana kwance, hannu tasa ta tadashi"Nashirya zan tafi makarantai"


"Saikin dawo"yace tare da canza kwanciyar shi.


STORY CONTINUES BELOW

Tace"inaso in biya gida daga can"


"kije mana, na hanaki ne"


Jikkarta ta d'auka,har ta kawo k'ofa ta tuna da kud'in hannunta duka, d'ari biyu ne, komawa tayi ta zauna, ta d'auki wayarta tayiwa Fatima flshing, takirata, tace idan bata wuce ba ta biyo ta d'auketa,Fatima kam ba jimawa tazo suka tafi.

Lokacin data fito Hayatu yana d'aki, Nusaiba tana tsakar gida Mama kam tafita yawanta,Da sauri Nusaiba ta koma d'akin tacewa Hayatu ga yanan Saudat zata fita.

Cikin sauri Hayatu ya fito lokacin Saudat ta kusa kai k'ofa, tare ta yayi"ina zaki? "


"skul"ta bashi amsa bata kulashiba,ta nufi hanyar fita,tayi tafiyarta, shikuma yayi kwafa yakoma ciki.

Nusaiba tace"lallai ta ma rainaka,jibi yadda take maka magana"


Hayatu yace"ai zata dawo tasameni.

          ****

Saudat tana kuka take gayawa Fatima Halin da take ciki yanzu,Fatima tace"Saudat kiyi hak'uri ki daina kuka, insha Allah komi zai zama tarihi"


"wallahi Fatima, ban tab'a tinanin haka daga wajan Usman ba"


Fatima tace"wannan kad'an ne daga cikin halin maza, ki barwa Allah komi kici gaba da Addu'a"


Abakin gate d'in gidan Ammi,Fatima ta ajiyeta, dan tama fasa juwa gidansu tana gudun zuwa asamu matsala.

Ammi tana zaune Falo,sallama tayi ta shiga k'ofar falon, da gudu yaran suka taso suna "oyoyo ga Besty"


Dariya tayi tana tarbarsu,Ammi tace"kai ku saketa hakanan kada ku kadata"dan ta kula da cikin dake jikinta.

Saudat tazame gaban Ammi tana gaidata,Ammi tace"dawo kan kujera ki zauna"


"a'a nan ma yayi Ammi"


"ya gida ya mutann gidan"


"duk lafiyalau"


Ammi ta k'ara kallonta,tace"kenan da bakizo ba,bazamu san munkusa zama granny ba"


Yar dariya Saudat tayi cikin jin kunya,Saudat ta kalli Ilham da Khairi tace"kufa yaushe kukazo"


Khairi tace"kwanan mu Ukku yau,Pappa da Mami basunan"


Ilham tace"Besty saida mukacewa Pappa yakaimu gidanki muzauna kafinsu dawo Amma yace bamu zuwa"


Ammi tace"Kai Ilham sarkin surutu"


Khairi tace"ai duk laifin wannan Yaya Areef d'in...."


Bata idaba kawai ya shigo falon, baisan da zuwanta ba,shadda ce jikinshi milk colour tayi mashi kyau sosai, agogon hannunshi milk ce, Ya kalli Ilham"zonan k'anwata waye ke gulmata"


Khairat ta dad'e baki, dan tasan yajita, Ammi tayi dariya,tace"kada ka sake ka tab'aman yarinya"


D'agawa yayi yana dariya, yakalli Ammi,"bakiji gulmata take... "sai lokacin yaga Saudat d'in,hakan yasa yakasa ida maganar shi,cikin sauri Saudat tace"Ya Areef ina wuni"


"lafiya lau"ya amsa yana mik'ewa ya fice daga falon.

Ammi tace"Ilham tashi ki d'auko wa Daughter abinci.

Saudat ta jima a gidan, sunsha fira sosai da Ammi, Saudat tace"kuma da gidan Mami zan fara zuwa sai kuma nayo nan"


"aikam da baki taddasu ba, dan yau kwanansu Ukku Umrah sukaje, sati biyu zasuyi itada Pappa"


"Allah yadawo dasu lafiya"saudat tace.

Ammi ta kalleta tace"yaushe ne EDD d'inki dan kada muji kwatsam"


Kame-kame Saudat takamayi, dan bata wanije Asibity ba, lokacin daya dace tafara zuwa bata samun damar magana da Usman d'in hakan yasa ta hak'ura.

Ammi ta ganota,Ammi tace"Amma kinsan muhimmancin zuwa Awon ciki ko? "


Shiru tayi ba Amsa,Ammi ta mik'e tashi muje,Take Ammi ta jata suka wuce wata Private hospital dake k'asan layinsu.

Basusha wahalaba, sukayi mata Aune-Aune da sauran Abubuwan daya dace, anan Doctor d'in yake cewa Ammi, su k'ara kula da ita sosai dan ba'ason BP d'in mai ciki yana hawa dayawa kamar nata, magunguna suka had'o mata,basu koma gidaba, Ammi ta agiyeta a k'ofar gidan ta bata kud'i, farko tak'i Amsa saida ta tuna batada ko sisi hakan yasa ta amsa tayi godiya.

Tsakar gida ta taddasu zaune, Usman yana gyara wata hula,inda suke ta nufa, ta gaida Mama tanayi masu sannu da gida.

Ba wanda ya Amsa, sai Hayatu dayace"wato ke d'azu inayi maki magana, shine kika k'etare kika ficewarki"


Batace komiba, ta kallesu, ba wanda yayi magana,Usman kam ko d'agowa baiyi ba, balle yace wani abu.

Saudat tace"ai nace maka makaranta zani"


"makarantar ce sai yanzu kike dawowa, an kiran sallar magriba, to daga yau bake ba wata makaranta, tunda yawace yawace kike zuwa, shiyasa kike kawo mana abubuwan bokaye a gida"


Mama tace"aiba tun yau nagayawa Usman ta daina makarantar Hakanan ba, Amma yak'i"


Usman ya kalleta yace"daga yau kingama wata makaranta,bazaki k'ara zuwaba"


Hayatu yace"sai ki zauna yanzu kiyi zaman Aure"


Ai Saudat kasa magana tayi danji take kamar an aza mata wani mashi a gaba, batasan lokacin data fara hawaye ba.

Nusaiba dake gefe tayi dariya,harda tab'i tace"ai dama saboda tana ganin tana boko shiyasa take mamu wani gani-gani"


Ganin ko tayi magan batada wani muhimmanci,shigewa tayi d'aki,da daddre Usman ya shigo, yana shirin kwanci ya Saudat ta zauna gefen gadon tace"dan Allah kayi hak'uri kabarni inyi makarantar nan, dukafa baifi wata bakwai ba mugama"


Tsaki yayi yaja bargo ya rufa, tasan bazaice komi ba, ta k'aleshi.

Saudat ta sha bak'in ciki, tayi-tayi Amma yak'i barinta,yanzu tafara sawa ranta hak'uri, ta fara jure matsalolin gidan.

             ****

Bayan sati biyu Usman yana d'akin Mama yakai awa biyu Saudat tana d'an jiyo kamar fira sukeyi.

Girki takeyi, ga hayak'i yana damunta,Usman ya fito daga d'akin, yayi hanyar waje, bai k'ara dawowa ba har dare.

Washe gari wajan k'arfe takwas na safe Usman ya kalleta, "ki shirya kitafi makarantai"


Kamar saukar Aradu taji maganai, murna ta kamayi, tayi mashi godiya, aikam ko minti talatin bata k'araba ta tafiyarta makarantai, dan tanada kud'i hannunta.

Saida tayi k'ok'ari duk abubuwan da suka wuceta taga, k'arfe Ukku ta rabi Fatima ta ajeta, godiya Saudat tayi mata ta shige sauran gidan.

Tana bakin k'ofa take jiyo muryar Mama da Haule, Mama tace"a'a kawai daga nan za'ayi d'aki, sai yasa Amaryar ciki"


Haule tace"ko kuma ita Saudat d'in takoma wannan, ta barwa Amayar nata dan yafi girma........"_ku biyoni_

*AUNTY HALILOSS✍🏽*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*

*Dedicated to My Mentor ZAHRA SURBAJO, rigijigamji, gingima babbar mota,duk lokacin da ake dara to fidda Uwa ake,kina gaba saura na biye,keta dabance,haka matsayinki daban yake a wajena.*


13


Saudat najin maganar da sukeyi, ta zaro ido, dai-dai lokacin Hayatu ya shigo zauren, da sauri ta ke shigewa gidan, Hayatu ya biyota baya"wato ke dan munafunci lab'e kikeyiwa mutane ko"


Mama tace"ai munafuka ce"


Hayatu yace"wallhi a bakin zaure na sameta tana sauraran ku"


Haule tace"Allah dai ya sawke ni nasan idan wannan yaron cikin nata yayo halinta mun shiga tara"


Saudat batayi magana ba ta shigewarta d'aki,cikin zuciyarta tana fad'in Allah yasawke d'ana yayi halinku"+


Tun da ta koma d'akin bata wani sawa kanta damuwaba, dan tasan ko Usman baiyi Aure ba, yanzu ba wani dad'in zaman gidan takejiba.

           ******

Usman zaune cikin majalissar su shida abokanshi,fira kawai sukeyi, Iro abokinsu yazo bai zauna ba ya kalli Usman yace"kazo muje inason magana dakai"


Usman yace"Allah yasa lafiya"yana maganai yana mik'ewa dan duk cikin frnd d'insu babu wanda jininsu ya had'ukamar Iro, dan shine kawai ko kafin auran su da Saudat suka saba, dan har Saudat d'in ma tasanshi.


Gefe suka koma, sun jima suna fira Iro ya farayi mashi fad'a akan maganar da yakeji nason k'ara auranshi,Usman yace"Mama ce takeson yin auran nawa"


Iro yace"haba Usman wallhi tara iyali ba naka bane, bayan bakada wata cikakkiyar sana'a,babban abin bak'in cikin kanada matarka kuna zaune cikin rufin asirinku, kamanta da halaccin datayi maka, amma yanzu zaka saka mata da irin wannan abin"


Sun jima suna fira shikanshi Usman baida wani zab'i,haka sukaita tattaunawa Iro ya shawo kanshi, dan yasan duk abinda yake fad'i mashi gaskiya ne.

Koda Usman ya shigo gidan, bakowa tsakar gidan hakan yasa ya wuce d'akin su, kwance ya taddata, ya zauna kan kujerar dake gefen gadon,kallonta yayi yace"Bacci kikeyi ne,ko baki da lafiya?"


Saudat tad'anyi Mamaki dan tajima raban da ya damu da tambayarta lafiyarta"a'a lafiya ta lau"


Ya jawo wasu takardun shi yana dubawa,sai ya d'auko wata,"duba man nan inga kamar inda photocopy d'inta"


Usman so yake kawai su koma normal shine yake ta yan jaye-jaye, Saudat tayi mamaki, saidai bata dmu ba.

Koda ya fita lokacin Mama ta dawo,Usman yaje ya zauna,anan yake ce mata,shifa babu maganar Aure a tare dashi, Mama tayi fad'a sosai,Usman kam bai damuba, saboda yasan akwai matsala indai yayi auran.

              ****

Fatima ta kalli Saudat, "wallahi cikinki ya tsufa sosai"


Saudat tace"doctor yace nanda 1 week ne zan haihu"

"mi kike shiryawa?"

"babu komi, Ammi tace idan naji ciwo inkirata"


"Yanzu kun sayi kaya kuwa na bebies?"


Saudat taja dogon lumfashi tace"ni dai Usman yace Mama yake ba ta sawo, saidai ni hankalina bai kwanta ba dan nasan halinsu"


"gaskiya babu abinda zata saya hakanan take amsar mashi kud'i"


"ke ni wallahi sana'a nakeson farawa zaman hakanan bayayi"


"hakane, amma kibari saikin haihun"


Fatima tajima suna fira da Saudat sannan ta tashi ta tafi gida,Saudat tanason Fatima kodan halarcin datake mata.

STORY CONTINUES BELOW

             ******

Zaune take dakyal take iya motsawa saboda ciwan da takeji mararta tanayi,Usman ya shigo gidan,kan capet d'in ya taddata tana d'an cige leb'o.

Zama yayi yace"ya dai"yana maganai yana tallabo ta.

"marata take ciwo"


Usman yace"to ko haihuwa ce? "


"nima ban saniba"


Usman ya mik'e"bari inkira Mama to"


Koda Usman ya kira Mama tana zuwa ta kalleta,ko sannu batace mataba, tace"wayace maku Haihuwa ce,ciwan mara ai duk mai tsohon ciki haka take fama, dashi ita dan batada dauriya shine ina zamana zakaje ka tadoni"


Tana maganai tana ficewa,tsakar gida tana k'ara masifarta,Usman ne yakece mata sannu,tanajin Mama tana cewa"baga Nusaiba nan ba, ko ko ita ba cikin ne jikinta ba"tana ta fad'a ta d'auki mayafinta ta fice.

Wasa-wasa ciwo sai k'aruwa yake, Usman yana gefenta, Saudat tace"ni daiko ka kiraman Mamansu Khalifa"wata mak'ociyar suce, babbar mace, tana da kirki sosai.

Usman bai b'ata lokaci ba, yaje sai gasu sun taho tare,Maman Khalifa na zuwa ta kalleshi tace"gaskiya wannan nak'uda ce, wace Asibiti take Awo? "


Usman yace"ai bata awo"


Zaro ido Maman Khalifa tayi, kafin tayi magana Saudat tace"ina zuwa"


Maman Khalifa tace"to kutashi muje can, Saudat jin ance Haihuwa ce, taja waya takira Ammi tagaya mata batada lafiya,tace to su had'u Asibitin.

Maman Khalifa tace"Kai Usman d'auko kayan babies d'in da kuka aje"


Usman yace"ai suna wajan Mama"


Maman Khalifa ta taimaka mata suka fito, shikuma yaje gidan Mama Haule don kiran Mama ta bada kaya.

Mama batasan kiranda yayi mataba, ya kalleta yace"Mama kaya zaki bada Asibity za'a kaita"


Mama ta kalleshi"wane irin kaya?"


Maman Khalifa tayi mata bayani, aikau nan Mama tahau masifa"kayan mi zan baka, kabani ajiyar kayane? Koko ita Nusaiba idan ta tashi haihuwa mizan bata"


Usman kam baahida tacewa, Saudat tanajin ciwan ta tsugunna,Maman Khalifa ta kamata tace muje, suna fita tayi sauri ta shiga gidanta ta samo abin buk'ata lokacin Usman ya samo mai Adai-daita suka tafi asibitin.


Allah sarki, acan suka tadda Ammi tana jiransu, dan ita hankalinta ma tashi yayi,Usman kam ya gaidata da ladabinshi, likitocin na ganinta sukace haihuwace,aka shiga da ita labour room


Nan suka zauna jiran ikon Allah, Maman khalifa, ta bud'e jikkar Saudat ta fiddo kud'i ta mik'awa Usman"gaya tace ka sawo abubuwan da za'a buk'ata"


Ammi tace"aiga kayanan anzo dasu" Sai lokcin Maman khalifa ta kula da katon trolly d'in dake ajiye,Maman Khalifa tayi Mamaki, dan ita a tunaninta Ammi ce maman Saudat.

Tsawan minti talatin, saiga ma'aikaciyar jinya tana buk'atar kaya, Saudat ta haihu,murna wansu ba'a magana, Usman kam kada daurewa yayi,ya fara Addu'oin godiya ga Allah,tare da tambayar abinda aka haifa, tace mashi"na miji".

Ammi kam lokacin tajawo waya tafara kiraye kirayen yan Uwa da abokan arzik'i.

Kafin kace mi Asibitin tacika da yan Uwan Saudat, Mama saude rik'e baki tayi tana Mamaki,ta kalli Usman tace"wai duk yan uwanta ne"


Yagane abinda take nufi, saidai yad'anyi murmushi,Usman kanshi yayi Mamaki dan baiyi tinanin Mami zatazo ba.

Sai ga Mami da Murnarta, Ammi tayi ta dariya, lokacin aka maido Saudat resting room,Ammi ta shiga itada Usman, Ammi ta fiddo Baby,Usman ganin ta fita, yayi hugging d'in Saudat yana kissing d'in wuyanta, ita kanta batasan lokacin data k'ank'ame shiba.


Ya saketa, yace"sannu dear"

Saudat ta kauda kai, tana buro baki"ni bazan k'ara haihuwa ba"


Tabashi dariya"to shikenan sai.. "


Mami ta shigo da Pappa da Dady a baya, Ammi tana rik'e da Jariri, Usman ya sunkuya ya gaishesu suka Amsa, Dady ne ya k'ara da cewa"barka to"


Usman cikin jin kunya,ya sunkuyar dakai dan yakasa amsawa,suka maida kallonsu ga Saudat, itakam murna takeyi yau gata ga iyayanta, Pappa ya d'an matsa ya dafa kanta,"congratltion"


Batace komiba sai hawaye dakebin kumatunta, Usman ya juya yafita, Dady yace"fatan ba inda ke maki ciwo? "


Kai ta d'aga dan bazata iya magana ba,Mami kam batace komi ba,sai tausayin y'ar tata, yakamata, Pappa ya juya ya kalleta"kuyi sauri ku gama zan mu wuce"


Saudat tayi saurin kallonshi, gaba d'aya ya d'aure fuska, Mami tace"ba'anan zaka barni ba"


Baice komiba, yayi mata wani kallo, ya nufi hanyar fita, Dady ya girgiza kai, Mami tace"Ammin yara bari in bishi, kada injawa kaina"


Murmushi kawai Ammi tayi,Dady yace"Allah yaraya,bari in tafi bada mota ta nazoba,tare muke dasu Alhajin"


Ammi tace"to"


Dady yace"idan aka sallame ta, gidan zaku taho da ita ko? "


Ammi tace"to sai iyayanshi sunzo,anyi shawara,mok'ociyarsu ta tafi tagay masu,amma is better takoma gida wanka"


Dady yace"ba damuwa komi kenan let me know? "


Dady yafita,ya tadda Pappa har sun shiga mota jiranshi kawai suke, Dady ya shiga ya zauna saida sukayi nisa Dady ya kalleshi yace"gaskiya baka kyautawa abinda kakeyi, yarinyar nan tayi kuskure,amma ai ba wani laifi bane da zaka d'auki zafi irin haka"


Pappa yace"haka ma kace ko?wannan ne ba laifi ba, to wannan shine babban mistake datayi arayuwarta,ina son yarona ta nuna man cewa ban isa gare taba"


Dady yace"maganar ka d'aya ko yaushe"


Pappa bai k'ara magana ba, har sukaisa gida, Pappa yanason Saudat dan shikanshi baisan irin son da yake mataba, saidai yazama dole ya nuna mata mahimmancin d'an uwanshi awajanshi.

        ******

Ammi tafarayiwa Usman magana tanason tafiya da Saudat, sanin halin Mama yasa yace a jirata, haka suka dawo Mama tanata murnar munafunci wai tayi miji.

Ammi tayi dariya,shikam Hayatu dayake tare sukaje sai cika yake yana batsewa.


Saudat tanakan kujerar dake receiption d'in asibitin saboda an sallamesu,Maman khalifa ce rik'e da jaririn a hannunta,Usman da Hayatu suna gefe, sai k'annan Mami guda biyu.

Ammi tace"to Mama mudai munaso kubamu Saudat ta zauna hannunmu har tagama wanka"


Mama har cikin ranta bata soba, saidai tanajin shakkar Ammi dan tasan tafisu komi, dan in banda Aure ko ance tatsaya kusa da Ammi bazata iyaba.

Mama tace"mukam muma munaso tazauna wajanmu"


Hayatu dake gefe yana jin abinda Mama tace, ya wani matso yana fad'in"wane irin tafiya gida wanka, yaushe rabonda kuji ance maijego takoma gidansu,to gaskiya ba inda zata kom....."


*Ku biyoni masu karatu,nikuma inbi Aunty Hafcy indon kauye,don ita kejan ragamar*

*AUNTY HALILOSS CE✍🏽*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


*DEDICATED TO AUNTY HAFCY INDON KAUYE,AND SAINAH UMMU MEENAL,INA YUNKU SOSAI*


14


Hayatu bai ida magana ba,Usman ya katseshi,"dakai ake magana ko da Mama?"


Dole yaja baki yayi shiri,Ammi ta kauda kanta,saboda tasan da ganinshi ba tarbiya balle sanin girman manya.


Ammi tace"ni dai Mama alfarma zaki man,idan tagama wanka sai tadawo"


Mama bazata iya fitowa tace a'a ba hakan yasa ta amsa badan ranta yaso ba,shikam Usman daɗi yaji,dan koba komi yasan Saudat zata samu kulawa.


Haka suka kama hanyar tafiya gidan Ammi su duka,ko da akaje Mama wangame baki tayi tana Mamakin gidan,ɗaki guda aka saka kayan Saudat,aka shirya tsaf aka gyara maijego da Baby.+


Mama da Maman Khalifa suka tafi gida,Ammi ta kama shirya gida,Saudat kam ba ƙaramin daɗi taji ba data dawo dan tasan zata samu kwanciyar hankali.


Da daddare Usman ya dawo gidan da kayan Saudat,sosai Usman yake girmama Ammi,a falon ya taddasu,Ammi tana fama da ita akan taba Baby Mama,yana shigowa Ammi tace"sannu da zuwa"


"Yauwa Ammi in yini ya hidima?"


"lafiya lau"


Suna gama gaisawa,Ammi ta bar nasu wajan,Usman ya koma kan kujerar dake kusa da Saudat,Saudat ta miƙa mashi Baby,ya Amsa yana kallon Jaririn"kinga yafi kama dani"


Harararshi tayi"ai duk wanda yaga Babyn nan yasan ni yake kama dashi"


Haka suka cigaba da fira,Usman ya ɗauko leda da nama ciki ya miƙa mata,ta amsa tayi godiya,sun ɗan jima suna labari.


Sallamar su Ilham da ihun su ta jiyo dariya ta kamayi,tare suka shigo falon,suna murna suka gaida Usman,ya amsa yana miƙa masu Baby.


Kowa ya ɗauke shi,Ilham tace"wallahi yaron nan da Besty yake kama"


Saudat ta kalleshi"kadai jiko?"


Sallama Areef yayi yana shigowa,ko ida shigowa baiyi ba,khairi tace "Yaya zokaga Baby mai kama da besty"


Shiga yayi yana washe baki,inda Usman yake ya nufa,hannu ya miƙa mashi yana sakin fuska,suka gaisa Areef yace"barka"


Usman yace"barka dai"


"Allah yaraya"


Ya zauna,Saudat tace"Yaya ina yini"


"lafiya ya Baby?"

"lafiya lau"


Areef ya kalli Ilham"ke bani Babyn mana,kin kama kin riƙe,sai in gama kalleshi kin goga mashi muni"


Duka falon akayi dariya,Ilham ta turo baki ta miƙa mashi,Areef yajima yana kallon Babyn,wani mugun son Babyn ya shige shi,Addu'o'e yayi mashi yana tofa mashi.


Ammi ta shigo,Areef ya kalleta"Ammi ga saƙo a mota Mami tace akawo"


Ammi tace"to in kuka tashi tafiya sai a fidda"


Usman ya miƙe yana faɗin"Ammi nizan tafi kada dare yaman a hanya"


"to ba damuwa,sai da safe"


Usman ya miƙe suyi musabaha da Areef,ya fito,Ammi ta kalli Saudat"ki tashi ki mai rakiya"


Saudat ta miƙe ta bi bayanshi,sun jima kafin ya tafi,sannan tadawo.


Areef kuwa har lokacin Babyn yana hannunshi,har yafara son yin kuka,kan kafaɗarshi ya azashi,yana jijjigashi,Ammi tace"ka batashi"


STORY CONTINUES BELOW

Baice komi ba,ya miƙa matashi,ta amsa, ya miƙe tsaye,yana kallon su Khairi,"kutashi mutafi"


Khairi ta turo baki,"wallahi anan zamu kwana"


Ya zaro ido"a ina?"


Ilham tace"ai ni hada kayana,Pappa bai ganiba na saka a mota"


Areef yace"to nidai ba ruwana,kutashi mutafi inba so kuke Pappa yayi faɗa ba"


Ammi tace"kabarsu mana"


"Allah Ammi Pappa ni zaiwa faɗa"


Ita dai Saudat batace komi ba,sai rurruga yaron takeyi,ta kalli Ilham"kutashi indai kunaso gobe abarku kudawo"


Khairi"ni ban gama ganin my bie ba"


Areef yayi dariya"Baki ganin Ammi faɗanshi takeyi"


Duka falon akayi dariya,Areef ya kamo hannunsu,suka fice.


Sai lokacin saudat ta samu damar ba baby nono,Ammi ma ta bishi domin tahowa da kayan da Mami ta bada.


             *****

Tunda Areef ya shiga mota,tunani kala-kala ya dameshi,ganin yadda ƙanwarshi tayi rama,gaya tayi duhu,shi kanshi yasan da anga Saudat ansan tana shan wahala.


Cikin zuciyarshi yake tunanin yanzu da wannan Babyn nashine,wani zafi zuciyarshi tayi mashi,shi kanshi yasan Saudat ta ruguza mashi farin ciki,dan yasan bazai taɓa samun macan da yakeso kamar taba.


Ko Ni'ima data liƙe mashi a yanzu kwata-kwata baya jin sonta aranshi,saidai baya iya wulaƙanta ta,sbd yasan zafin so,hakan yasa yake ɗan kulata wani lokaci,sai dai yanzu yasan tunda Pappa yafara yi mashi naganar Aure baida zaɓin daya wuce Ni'imah.


         *****

Haka akaci gaba da zaman jego a gidan Ammi,duk ƴan uwa sunji daɗin hakan,Saudat kam ta sake,abinda takeso take ci a gidan.


Mami tazo har so biyu,saidai bawata keɓewa tsakaninta da Saudat,ƴan Unguwarsu Usman dayawa sunzo,wasuma ganin kwam yake kawosu dn labari ya baje kan cewa lallai mahaifin Saudat mai kuɗine.


Usman kullun yake zuwa dubasu,Ammi ta fahimci baida wata matsala tsakaninshi da Saudat,kuma ta gane har lokacin sunason junansu.


Duka kwana biyar da haihuwar Amma duk wanda yaga Saudat da jaririnta sai sun shiga ranshi,Dady ba ƙaramin kuɗi yake kashe mataba,ko fita zaiyi sai ya tambayeta in tana buƙatar wani abu,ko tace a'a to saiya aje mata kuɗi masu yawa,idan taba Ammi sai Ammi tace ta riƙe abinta.


Tunda sukazo Mama kaɗai ce ta ƙara zuwa,Hayatu kam ko Nusaiba hanata zuwa yayi,Saudat kam bata damuba tace su ƙarata can.


Maman khalifa ce take ba Saudat labarin halin da Usman yake ciki kan hidimar suna,domin kuwa duk kuɗin da yake ba Mama,Mama tace babu,ai yana ganin hidimar da tayi a gidan.

        

             *****

Ana gobe suna da Marece Usman yazo gidan,a fallon baƙi suka zauna da Saudat,suna fira,Usman ya kalleta,bai masan ta ina zai fara mata baya niba.


Saudat tace"wai mike damunka ne?"


Usman ya dawo kujerar da take zaune,ya riƙe hannunta,"Dear ina baƙin cikin rashin abinda zanyiwa iyalina,ina dana sanin rashin abinyi,na tsani kaina......"


Hannu Saudat tasa ta rufe mashi baki"wannan hukuncine na Allah duk yadda yaso haka zaiyi,ka daina irin wannan maganai"


Usman yace"Yanzu wane haƙi iyayanki zasu shiga,idan sukaga ko abinda za'ayi hidimar suna babu balle ragon da za"


Hawaye suka zubowa Saudat,ta kalleshi,"kada ka damu bari in dawo"


Ɗakin takoma,dubu hamsin ta kawo mashi,Usman kam ya kalleta cikin damuwa"taya zan anshe maki kuɗi duka,ke mi zakiyi amfani da?"


"nidai ka riƙe"


"a'a muraba"


Dariya tayi"ai akwai wasu,amma kada ka sai mani kaya,saboda ina dasu,naba Zainab ta sawo mani,xan gaya mata tabaka saika haɗa cikin kayan da zaka kawo"


"Shikenan ba damuwa"

Saudat ta harareshi"waini baxaka faɗiman sunan dakayiwa Babƴ ba?"


Dariya yayi ya ja hancinta"aidai ke kince bakida zaɓi ko?gobe zakiji"

Sun jima,sukayi bankwana,Usman yafita,a bakin get sukaci karo da Areef ya shigo da mota,horn yayi mashi,Usman ya matsa ya bashi hannu suka gaisa,Ilham ta gaidashi ya amsa yana tambayarta"yasu Mami,sai lokacin ya kula Mami ce a bayan motar"


Cikin girmamawa ya gaisheta,Mami tace"ya hidima?"


Cikin jin kunya ya Amsa,Areef ya fito daga motar ya fiddo kuɗi daga Aljihunshi,ƴan dubu-dubu ya kama hannun Usman yace"ga wannan ayiwa Father hidima"


Usman ya kalleshi yana fara'a ƴaja baya"kai Haba Yaya Areef gaskiya bazan ansaba"


Mami tace"Haba Usman ka ansa mana,ai Baba za'a yiwa Aski"


Usman yakoma waje kuda yaƙi ansar kuɗin,Mami tafito daga mota ta anshi kuɗin daga hannun Areef ta kalli Usman"anshi,ninace saika ansa"


Bai iya yimata musu hakan yasa ya ansa yayi godiya,sukayi bankwana ya suka shiga ciki shikuma ya fita.


Areef kuwa jin daɗin sunan dayasawa yaron ne,wato Mu'azzam sunan Pappa dan yasan ko shine sunan da zai sawa ɗanshi kenan hakan yasa yaji daɗi.


        *****

Washe gari akasha shagalin suna,kaya niki-niki Usman yakawo da kanshi,dan yasan idan yace yaba Mama to lallai za'ayi abin kunya,Saudat kam taga so wajan danginta,dan gidan Ammi cika yayi sosai,haka akasha.


Da daddre duk ƴan hidima sun tafi gidan yayi shiru,masu aiki sun gyara gidan,Ammi tana yiwa Father wanka,sai tsala ihu yake,saida aka fiddashi ruwan sannan yayi shiru.


Saudat tana zaune,Ammi tace"wai bazaki tashi ki watsa ruwanba"


Kafin ta ida Areef ya shigo falon,yana sanye da wata dakakkiyar shadda tasha aiki,sai ƙamshin turare yakeyi,zakayi tunanin shine angon jegon,ya kalli Ammi yace"Ammi asa freshner wallhi yanzu zanje in ɗauko ta"


Ammi ta kalleshi"wai dagaske kake?"


Areef yana sosa kai yace"eh harma ta shirya,dan dole tazo taga  Sultan"


Saudat ta  saki baki tana kallonshi,yadda yake magana,daka gani kasan budurwace,wata mummunar faɗuwar gaba tazo mata,da sauri ta kauda kanta,tana miƙewa,domin zuwayin wankan.


Ammi tace"kaini banison iyayi,shine sai nasa freshner"


Dariya yayi yace"to natafi 10mins mun iso"


Ammi tayi murmushi,tace"Allah ya shiryaka"


Saudat kuwa ƙin shiga wankan tayi,kan gado ta faɗa,wani kuka ta farayi mai tsuma zuciya,ita kanta batasan dalilin hakan ba........


*Muje zuwa*


*AUNTƳHALILOSS✍🏽✍🏽✍🏽*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


*BANA WULAƘANCI BANASO A WULAƘANTANI,BA WAI KINA RUBUTA NOVELS YANA NUFIN KINFI WATA BA, A'A HAKAN YANA NUFIN ZAKI IYA SADAUKAR DA LOKACINKI WAJAN FADAKAR DA MUTANE, DUK WANDA BAYA RUBUTA NOVEL TO ZAKIGA SHIMA YANADA WATA HANYA DA YAKE BA DA GUDUNMUWA ZUWAGA AL'UMMA*


*DUK LOKACIN DA ZAKAYI MA DAN UWANKA MAGANA, KAYI TUNANI KAFIN FITAR MAGANAI,RUBUTA NOVEL BAI NUFIN KA WULAKANTA WANDA KAGA DAMA, IN KINA TAKAMAR GROUP, TO AKWAI GROUP NA NOVEL BASU KILGUWA*


*DUK WADDA TAGA NA FITA GROUP D'INTA,TAYI HAKURI PLZZZ*


*INSHA ALLAH ZAKU SAMU CIGABAN LITTAFINA A WATTPAD @AuntyHaliloss NAGODE*


15


Sai da tayimai isarta, jin k'ara shigowa da Mota yasata mik'ewa ta shige toilet d'in,tajima saidai bama wankan takeba, tunanin ko wace yarinya ce Areef zaizo da ita, tasak'a wannan ta warware.+

Ammi ce ta shigo d'akin tana kiranta, sai lokacin ta fara wankan,cikin sauri ta gama ta fito, kaya kawai tasa, saidai daka ganta kasan akwai alamar damuwa a tare da ita.

Ammi ta kalleta"kije gayacan sunzo"


Saudat tayi murmushin da baikai zuciba, ta daka kaya, suka fito falon.

Kan kujera take, tasa jallabiya black, tayi rolling vail ash,Saudat ta shiga da Sallama,tana sakin fuska.

Areef kallonta yakeyi, gaba d'aya yasan halin Saudat,yadda magana kawai yasan bahar zuciyarta ba,hakan yasashi wani murmushin takaici.

Saudat tace"Yaya Areef sai yanzu kake kawota"


Areef yayi dariya"gatanan tsayawa tayi shiri"


Ni'imah ta d'ago tana kallon Saudat,don dama tanason ganinta, saboda labarinta da taji a wajan Areef.

Ni'imah tace"Ya Baby? "


"lafiya lau Aunty"tana maganai tana mik'ewa, frij taje ta d'auko drinks ta fara aje mata.

Takoma hanyar kitchen ta d'auko cakes da cup ta kawo mata"Aunty ga cakes saidaikiyi hak'uri duk an cinye abincin sunan"


Areef yace" kamar kinsan akwaita akwai cin abinci"


Ni'imah ta d'ago tana harararshi, shikam dariya yakeyi, dai-dai lokacin Ammi ta shigo fallon hakan yasa Ni'imah sunkuyar da kanta.

Saudat kam kallonsu take, Ammi tace"amma dai zaka k'ara kawota ko, dan zuwanan bai manba"Ammi tana magana tana zama


"insha Allah Ammi"cewar Areef.

Saudat ta d'ankauda kai,ta juyo ta kalleshi, "kai Yaya Areef to kabata Babyn mana, ka kama ka rik'e"


Dariya sukayi,Ammi tace"ai shi har mantawa yake idan yana rik'e da Sultan"dariya yayiya ba Ni'imah sultan, Ammi ta sake mik'ewa ta shigewarta d'aki.

Saudat sun d'an jima shiru,Areef ya duk'a yanayiwa Ni'imah rad'a"saura namu Babyn ko? "


Dariya Ni'imah tayi tana janyewa, Saudat tayi Saurin mik'ewa "bari in je insamu ko wani abu adafa mata"


Ni'imah ta zaro ido"haba sister wallhi ki zauna wanan ma ya isah"


Areef yace"bai isa ba"Yana maganar cikin salon wasa.

Saudat tace"to Aunty kisha drinks d'in"


Areef ya d'auko roba guda ya bud'e ya zuba a cup, ya nufi bakinta zai bata,Ni'imah ta kauda kai, Da sauri Saudat ta mik'e tabar wajan ta shige d'aki.

STORY CONTINUES BELOW

Tunda ta shiga d'akin take tinanin, yadda Areef yakewa Ni'imah, wani abu taji har ranta, da sauri tayi tsaki tare da kauda abin a ranta.

Muryar Dady taji,hakan yasa ta fita falon, tsaye ta taddashi,suna gaisawa da ita, Ammi tanayi mashi bayani,Saudat ta gaida Dady,kanta ya dafa"bakiyi  bacci ba, ko baki gajiba"


Saudat tace"Natsaya tarbar Aunty ne" Dady yace"ya taro? "


"lafiya lau Dady"


Juyawa yayi kan Areef yace"Ka kaita gidan Pappan ka? "


"a"a nan muka fara zuwa,kuma lokaci yaja, saidai wani lokacin zan kaita"


Dady yace"ba damuwa,kayi k'ok'ari kakaita d'in" yana magana yana nufa hanyar part d'in shi har yayi nisa ya juyo ya kira Saudat,hannunta ya kama suka shiga d'akin tare kud'i ya bata takawo wa Ni'imah.


Lokacin da Saudat tadawo har sun mik'e suna shirin tafiya, Ammi ta fito da leda ta mik'a masu, Saudat ta bata kud'in tace inji Dady, da kyal ta ansa saida Areef ya amsar mata.

Saudat ta shiga ta d'auko mata turaruka shikin kayanta ta kawo mata.

Ni'imah tayi godiya suka tafi, har mota Saudat takaisu,Areef kallonta yake yadda take nuna kulawarta,saidai yasan ba har zuciya bane.

             *****

Usman kam gaba d'aya gidan ya dameshi, yana kewar Saudat,dan yasaba da ita sosai.


Mama kuma yanzu ita takeyin girki, Nusaiba ko cefane bata gyrawa, saidai ta mik'o kula a zuba masu itada mijinta.

Nusaiba tana zaune Hayatu ya shigo hannunshi rik'e da doya da leda, ya mik'a mata, kallonshi tayi tace"ga Mama can kakai mata, dan bazan iyaba, cikina yaman nauyi"


Ba musu Hayatu yaje yakaiwa Mama, Mama ta kalleshi"to wallahi saika k'aro itace, dan bazan iya da hiyak'in dake damuna ba"


Usman yana, zaune kan tabarma yana kallonsu, baice komiba, saima tunanin Saudat yake,cikin zuciyarshi yace, ashe kinajin hayak'in amma baki damuba idan baiwar Allah tana wahala.


           ******

Saudat ta warware, jikinta yakoma yi kyau, haskenta yafara dawowa,Sultan yayi kyau abinshi,Usman ne yazo ya kalleta,yace"kinga wallahi yaron nan kamar d'an turawa"


Saudat tayi dariya"aini wani lokaci sai inga kamar yana dariya"


Zaro ido Usman yayi"kai banda kuma lie mana,duka 3weeks fa"


Saudat tayi dariya,tace"Yasu Mama dasu Maman Khalifa"


"Mama tana lafiya lau sanwa na barota tanayi"


Saudat tana sane "tace wace irin sanwa kuma?"


"Hmmm ai kinsan duk wanda baya ganin amfanin mai kyautata mishi, to wata rana zai ga amfaninshi"


Saudat batace komiba, dan tasan mahaifiyarshi ce.


"Ammi Ammi  wai ina Sultan d'in yake? "


Ammi tafito daga d'aki"wai zaka dameni da kira, yawon ne zaka fita dashi ko"


Areef yace"ina yake? "


"babanshi ne yazo, suna wajanshi"


Usman suna jiyo Areef, Usman yace"kinajin Yaya Areef? "


Saudat ta yi dariya"ai Yaya Areef baigajiya, jiyafa tunda ya d'aukeshi sai da Ammi ta kirashi waya"


Usman yace"jeki kai mashi shi"


Saudat ta mik'e, taje ta taddashi,waya a kunnanshi"Allah Honey on my way, zan d'auki Sultan ne. Oh sorry ,ok bye muah" yana maganai yana kising d'in wayar.

Saudat kam, yitayi kamar bata ganshi ba, ya ansheshi ita kuma ta koma wajan Usman,suka cigaba da shan soyayarsu.

Areef yanason Sultan sosai,jinshi yake har cikin zuciyarshi, saboda yaron yasa baya gajiya da zuwa gidan,wani lokaci kuma ya d'aukeshi sufice, saboda yaron bashida rigima ko kad'an.


Sai dai, duk lokacin da Areef yake gidan tofa waya tana a kunnanshi, yana zabga soyayarshi da Ni'imah, wani abinma yanayinshine don ganin Saudat, saboda gaba d'aya ba wata soyayya yake iya nunawa Ni'ima ba.

Ita kuwa Saudat zuciyarta har zafi takeyi, sbd ji take kamar ta korashi idan ya shigo.

              ****

Saudat ce da Ammi zaune a falo, Sultan yana hannun Ammi,Areef ya fara shigowa Mami a bayanshi.

Ammi ta mik'e tanayi mata sannu da zuwa,Mami ta zauna tana fad'in"Yauwa Ammi ya gida? "


Saudat ta gaidata"ta amsa tana tambayar ya sultan"


Bata k'ara cewa komiba,Saudat ta gaida Areef ya amsa, yana nufar Ammi"kawo shi nan Ammi"


Ammi tace"ai dama tunda kazo nasan bazaka barshiba"


Mami tace"haka yake jeman dashi inta fad'a"


Yana amsarshi ya zauna wayarshi ta fara ringing,hannu yasa ya d'auka, yana kaiwa a kunnan shi"Honey yane"


Daga ban garenta tace"lafiya lau kadawo daga Office d'in"


"eh gayama, har na kai Mami gida Ammi"


Yana maganai yana tashi,da Sutan a hannunshi, ya koma can nesa dasu ya cigaba da waya.

Ammi tace"Allah ya shiryaka"


Mami tayi dariya"ai indai.... "


Bata idaba Areef ya mik'a mata waya,yana fad'in ga Mamin, Mami ta anshi wayar tasa a kunnai.

Saudat kam Mamaki take,Areef yasaci kallonta, ya zauna gefen Mami,tana gamawa ya anshi wayar ya mik'e.

Mami tace"ai dana koma zan yiwa Pappa magana, a aika gidansu Ni'imai a huta, harna gaji"


Wata mummunar fad'uwar gaba Saudat taji, ta mik'e takoma kan kujera, ta zauna,Ammi tace"lallai kam k'ara haka"


Saudat duk ta canza, ganin kamar zasu ganeta yasa ta mik'e ta shige d'aki.*AUNTY HALILOSS✍🏽✍🏽✍🏽**WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*

DEDICATED TO:I proudly dedicated this page to you guys,members of *QUEENS OF MY HEART GROUP* inajin dad'in yadda kuke son novel d'in  _WA NAKE AURE_ sak'on ku yana samuna ta hannun AMMIN HYDAR,nagode.

*JINJINA GAREKI, _SOPHIE_ kema ina jin dad'in yadda kike sharing book d'in,ILYSM*


16


Har Mami ta tafi Saudat bata fito daga d'akin ba,Areef kuwa da Sultan ya fita,koda Saudat ta fito fira suka cigaba dayi da Ammi.

Shi kam Areef yana ajiye Mami,Ilham ta fito,"Yaya Areef ina zakaje? "


"zanje wajan Ni'ima ne"


Ilham ta wace baki, "dan Allah ya Areef kaje dani"


Areef yana son y'an uwanshi sosai, bayason yaga ya b'ata masu rai, dakanshi ya bud'e mata front sit, "oya shigo muje"+


Ilham tana murna tace"aikam yau khairi sai taji haushi, ba'a je da ita ba"


"tunda bata nan ynz,next time sai muje"


Haka suka isa gidansu Ni'imah, Ilham tana rik'e da Sultan, Ni'ima batasan tare suke da Ilham ba.

Fitowa tayi tana yi mashi sannu da zuwa, kallonta yayi yana ganin yadda take washe bakinta, yasan taji dad'in ganinshi"welcm darling"


"tanz ya gida"


"lafiya lau kawo mu shiga falo mana"


Areef ya juya wajan motar kasancewar tinkt ce,yace"tare nake da Ilham tana mota"


Lokaci guda ta d'aure fuska, yanayinta ya canza,Areef ya kalleta, yanason fahimtar wani abu"yadai"


Murmushi ta k'ak'aro "ba komi"tana maganai ta isa wajan mota,Ilham ta fito, sannu tayi bata, suka shiga ciki,Ilham tace"My Aunty dakyal yayi yazo dani"


Areef ya harareta, yana niyar damk'ota, ta rik'e sultan sosai tana guduwa, "wato sheri zakiman, bayan kina cewa zakizo nace ki taho"


Ilham tasa dariya"daina gudu kada kisa Father wahala, kada yayi kuka"


Take Ni'imah ta d'aure fuska,Ilham tace"Aunty kinga Yaya zai dakan"


Ni'ima bata saki fuskaba ta bud'e k'ofar da zata kaika babban falonsu,suka shiga.

Ilham ta zauna tana kallonta,lokaci guda Ilham tafara tunanin Ni'ima batada fara'a.

Ganin Ilham tana kallonta,yasa Areef jan Ni'imah da surutu dan yasan halin su Ilham akwai gane abu balle yanzu an k'ara wayo,shekarar ta sha bakwai.

Ni'ima takawo masu ruwa da lemu,yan gidan ma sun karrama Ilham.

Areef kam ganin yadda Ni'ima take d'aurewa basu wani jimaba suka dawo gida.

NI'IMA babanta mai kud'ine sosai,iyayanta sunaji da ita,Ni'ima tana da kirki sosai,batada matsala,sun had'u da Areef ne lokacin bikin abokinshi, ita kuma itace k'awar amarya, nan ta nik'e mashi.

Ni'ima tana da k'awaye sosai, yayan manyan masu kud'i,akwai su da gayu,sai dai duk da haka babanta yana k'ok'ari wajan ba yaranshi tarbiya.


Babban gurin Ni'ima bai wuce tasamu miji d'an gayu, mai jida kud'i kyau iya dressing tajima tana gurin samun miji wadda zata iya shiga dashi ko ina, any where Husban acewarta,dan ko k'awayenta sun sani.

Wanann dalilin yasa tunda taga Areef ta kasa samun sukuni, har zuwa wanann lokacin daya hak'ura yafara kulata, Babbar matsalar Ni'ima kishi,gaba d'aya bataso taga wata mace a kusa da Areef,ko labrin Saudat daya bata,ta saurara ne saboda lokacin tanason shawo kan Areef d'in,sai dai Areef bai gane hakan ba.

STORY CONTINUES BELOW

            *****

Mamace zaune tana wanke tsakin tuwo,Nusaiba tana kwance cikin baranda da k'aton cikinta,Usman ya shigo, sannu yayiwa Mama yayi hanayar d'akin, Mama ta juyo ta kalleshi"wai nikau yaushe yarinyar nan zata dawo, ai dai yanzu tagama wanka"


Usman ya tsaya, yayi jima tare da cewa"to nidai ban sani ba"


"saika tambayesu, ai ba haka zaka zauna, kada mata kamar babu ba"


Usman ya kad'a kai anjima zanje, sai in tambayesu"yana maganai ya shiga d'akin.


Mama taci gaba da sanwarta,Hayatu ya shigo, yana tambayar Nusaiba ya jikinta, Mama tace"ai fa ina tinanin nak'uda ce takeyi tsaitsaye"


Nusaiba ta mik'e zaune,Mama tace"ko inje in kira Unguwar zoma agani"


Haka Mama tasaki girkin ta tafi kiran Haule, sukazo tare da unguwar zoma, haka akaita zama a gida ana yanjik'e-jik'e ana bata tanasha, Nusaiba ba k'aramar wahala tasha ba,ranar tasa kuka,ita ce bata haihuba sai da marece,ta haifi mace, daka ganta kasan tasha wuya, ga ba wani abinda zata samu taci mai gina jiki.

          ******

Ranar Saudat ta shirya tanata zaga dangi,saboda ta gama wanka, yau gidan Mami taje zata wuni,sai dai ko da taje bata samu sakin Fuska ba, dan Pappa korota yayi yace, ta tafi bayason siyarai, ranar Saudat tasha kuka kamar ranta zai fita, dakyal Mami ta shawo kanta, tayi shiru.

Suna zaune da Usman a falo yake tambayarta yaushe zata koma, tace sai lokacin da Ammi tace,Usman ya yiwa Ammi magana Ammi tace sati mai zuwa.


Bayan yatafi Saudat ta turo baki"gaskiya Ammi bazan komaba sai sun gama sunansu"


"saboda mi, basai ayi suna dakeba"


Saudat tasan sarai idan takoma, zatasha wahala, dan duk aikin gidan tasan kanta zai k'are.

"nidai Ammi sai nan da kwana goma"


"to shikenan saiki gaya mashi,kafin lokacin kin ida shanye magungunanki"


Saudat ta kaudakai tana dariya, dan tun bayan suna ta cigaba da had'a mata wasu magunguna don gyran jikinta.

           ******

"banason rashin kunya a gidana fa, na lura duk ka koyi rashin ta ido"


"Allah Ammi suna zuwa,Baban ta yace yama saka ranar Auran 3month"


"shine bazaka bari Dadynku yadawo ya gayaman ba sai kai"


Dariya Areef yayi "shikenan Ammi Allah yahuci zuciyarki"

Saudat dake shirin shigowa falon ta juya zata koma, Areef yace"Sister ansar shi yayi bacci"


Saudat ta yi k'okarin kauda damuwar fuskarta, hawayen idonta take maidawa,ganin bata da wani zabi, hawayen har sun zubo, ta duk'ar da kanta tana fad'in "wash idona kamar yaji yafad'aman"


Tana maganar tana murzar idon,duka biyu, Ammi tace"ina aka samu yaji"


Saudat ta dage ta kauda abin, tayi kamar gaske,ta nufi hanyar kitchen,ta wanko fuskar tazo ta d'auki Sultan ta wuce d'aki, kwantar da yaron tayi tahau kuka.

Areef yana fita Ammi tashiga d'akin,kuka ta tadda tanayi"A'a daughter mi yasameki, wani abu akai maki? "


Saudat batada wani zab'i dan tasan Ammi tagane kuka take,Ammi ta zauna tana rarrashinta"ko bakison komawane? "


Saudat ta girgiza kai"Ammi tahau rarrashinta"da kyal ta hak'ura,sai dai koda Ammi ta fita,tambayoyi takeyiwa kanta, miye abin damuwa da lamarin Areef,bayan babu wani abu tsakaninsu face y'an uwantaka.

             *****

Areef kam tunani kawai yake ta yadda yau shine aka sakawa ranar Aure da Wata wadda bai jin ko d'igon sonta a tare dashi,gaba d'aya rayuwarshi baya cikin Natsuwa dole ne yasashi amincewa da Ni'ima, ko dan gudun halin da zata shiga akan sonshi.

Duk wanann abun yasan laifin Saudat ne data gujeshi a lokacin da yake cikin tsananin buk'atarta, yanzu da itace yasan ba k'aramin farin ciki zai shigaba.

Wanann tunani ya zawo mashi massara,da ciwankai,Papa kam yagama ganoshi, saboda sukukun da yayi a gidan.

Pappa ya shigo yasameshi kan kujera kwance,Mami tana zaune kan capet"kakira doctor kuwa"


Areef yatashi zaune"A'a nasamu Sauk'i Pappa"


Tsaki Pappa yaja, yana fiddo waya a yakira doctor.

        

Tunda Areef yaji labarin komawar Saudat gida ya rage zuwa gidan Ammi, don yasan duk ranar da suka tafi zaiyi kewar Sultan.

          *******

Saudat kuka takeyi sosai, Ammi tayi rarrashi amma tak'i hak'ura"Haba Saudat yanzu ya kikeso inyi,kinsan dai ko ba yauba dole zaki koma,kibarni"


K'ara fashewa tayi da kuka ganin ana saka kayansu a boot,Ammi taja hannunta suka shiga Motar,Har suka isa k'ofa gidan Saudat tana kuka.

*nikam Auntyhaliloss nace tana tsoron wahalar da zata cigaba da sha**AUNTY HALILOSS✍🏽✍🏽*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


17


Saudat ta share hawayenta,Ammi tace"mu shiga"


Tare suka shiga gidan,Mama tanata aikin saka ruwan zafin wankan Nusaiba,sukayi Sallama,da fara'arta ta tarbesu.


Sai kallon Saudat take yadda tayi jawur da ita,ga dakaganta kasan tanajin daɗi,Ɗakin Saudat suka shiga,ba laifi Usman ya gyara ɗakin tass an share ko ina.


Mama tace"ashe yau kuke tafe?"


Ammi "yo baigaya maku ba"


Mama tayi tsuru-tsuru"mantawa nayi dayake dai hidindimu sun man yawa.


Saudat dai jinta kawai tace,Ammi ta miƙa mata Sultan,driver ya fara shigo da kayansu Saudat kaya Masu yawa Ammi ta haɗa masu,Dady kam kuɗi ya bata da kayan Abinci.+


Aikam Mama tana ganin kaya hada buhun shinkafa dasu taliya,ta hau nan-nan da su,Saida Ammi ta shirya mata kayan tass sannan tayi shirin tafiya.


Tana fitowa Usman ya shigo gidan,suka gaisa,Usman yayi mata godiya,Ammi tace"yanzu zanbar ganinka tunda na maido ta ko?"


Dariya kawai Usman yayi,Ammi tayi bankwana ta tafi Saudat kasa yi bata rakiya tayi.


Ɗaki Usman ya taddata ta kifa kai tana kuka,yasa hannu ya ɗagota,yana rarrashin ta.


Ranar sosai makwabta suka shigo don ganin Saudat,Saudat turmin Atamfa taba Maman khalifa.


Suna zaune ɗaki Saudat tace"nikau Maman Khalifa wace sana'a kike ganin yagamata inyi?"


Maman Khalifa ta gyara zama,to kinga nan unguwar akwai masu saida koko dasafe,ki saro gero ki rinka saida masu, dan nima da inada jarin shi zan farayi"


Saudat tace"to shkenn zan bashi yasawo man"


Mamn khalifa ta dawo gefenta,ta k'ara kallon Saudat"to saidai abinda zan gaya maki, ke har yanzu baki da wayo yakamata ki daina ragama y'an gidannan dan inba hakaba, ke zaki cigaba da shan wahala"


Saudat tace"ni yazanyi"


"to ai saiki zauna suna baki wahala,haka kawai,idan ita mahaifiyar mijinki ce, ita wannan tsinanniyar fa,da mijinta"


"ni kaina wallahi ko dazan dawo tunani kawai nake halin da zamu shiga, da yarona"


Wani tsaki Maman Khalifa taja"nidai bazan zugakiba amma ingaya maki dole ki koyi zama dasu,kuma bance ki had'a da mijin kiba, kiyi mashi biyayya"


Nanfa Saudat ta zauna Maman khalifa tana koya mata zama dasu, sabd ita Maman khalifa ta girmi Saudat, dan ita yayanta biyar yanzu.

Tunda Maman khalifa ta fita,Saudat ta zauna tana tunanin yadda zaman zai kasance dan ita kanta tafara gajiya da wahalar, kuma dama bata dawo da gurin zama kamar da ba.

Da daddre  suna Zaune da Usman, ya rik'e da Sultan,Saudat tace"dear inaso ka saro man abinda zan fara saidawa kamar gero da masara"


Kallonta yayi yana Mamaki,duk saita bashi tausayi"saboda miki fara saida..."


Bai idaba tace"to haka zamu zauna,ba sana'a dagani har kai,kuma kaima ai dole yanzu ka samu sana'a dan zama hakan bazai mamuba, kana gani yawa muke k'arawa"


Wani dogon lumfashi yaja, dan yasa gaskiya take fad'i, yace"shikenan ba komi gobe sai in saro maki, amma ina zaki fara saidawa? "


"Maman khalifa tace zatayi man tallah"


"badamuwa Allah yakaimu goben"


       ******

Washe gari, Usman yana mak'ale da matarshi da yaronsu, Usman sai wasa yake ma yaron Mama ta lek'o d'akin,tare da d'aga labulan d'akin,da shinkafa a cikin roba,cikin wanda Ammi takawo masune,ta d'ego saboda a d'akin Mama aka ajiye.

Ta kallesu,Saudat ta d'an yi saurin d'agawa daga kan kafad'ar shi, Mama ta watsa masu wani kallo,"gaya Nan ni gidan Haule zan shiga,ki kwalhe mata ruwan wankan kikai mata band'aki, sai ki dafa wanan,anjima Hayatu zai kawo cefanan"


Saudat ta kalli shinkafar,batayi Magana ba Mama ta saki labule ta fice, Saudat ta cije baki,ta cigaba da abinda take.

Sun jima Usman yace"bari in fita, saiki d'aura sanwai"


"to tace mashi"ya aje Sultan dake bacci ya fice.

Saudat kuwa yana fita,ta rasa yadda zatayi dan batason yin wahala kamar da,k'aramin murhu ta jawo ta tak'i tab'a ruwan wankan da Mama tace ta kwashe ma Nusaiba"


Sanwar shinkafar tacigaba da yi, Nusaiba ta fito da jariri a hannnu,tana wani tahowa"ina ruwan suke? "


"wane ruwa? "

Nusaiba tana wani nuna isa"ruwan wankan?"


"gasunan a tukunya"inji Saudat.

"shine tun dazu baki kaimanba, so kike rena tayi banyi wankan ba?"


Saudat ta kalleta"ni ce zan kai kaki ruwan? "


"eh mana,ba inaji Mama ta gaya maki ba"


Banza Saudat tayi da ita, ta cigaba da aikinta, Nusaiba taita tsayuwa,Saudat ta iza wuta ta shige d'akinta.

Itama d'akinta takoma, tayi zamanta,Hayatu ya shigo gidan,lokacin Saudat tagama sanwa, Mama kuma tagamo yawanta tadawo.

Mama bata lura da tukunyarba,Nusaiba najin shigowar Hayatu ta fito daga d'akin,"to Mama wandda kikace takaiman ruwan har yanzu bata kaima"


Mama ta zaro ido"banganeba,kina nufin har yanzu bakiyi wankan ba,ina Saudat d'in take"Mama ta kwala ma Saudat kira,Saudat ta fito tana murtsuka ido kamar mai baccin gaske.

"eh lallai dole insata ki aiki kik'iyi, kikoma ki keanta kega y'ar hutu, to wallahi baki isaba"


Hayatu yace"wanann ai wulak'anci ne, ke dan kinga an cewa ke yar masu kud'i ce, shine zaki fara raina mamu hankali, abin har yawuce yakai kan Mama tasaki aiki kik'iyi? "


Mama zatayi Magana,Usaman ya shigo da masu dako suna shigowa da Buhun Masara dana Gero.

Mama tace"kai wanan abin Arzik'in daga ina?"


Ta juya ta kalli Saudat"ko suma daga gidankune? "


Yadda Mama take maganar daka gani kasan son banzarta ne ya motsa, Usman yace"Na Saudat ne"


"kai Amma mun gode"


"ai Saidawa zan farayi,masu koko zan rink'aba idan sun sayar suna bani kud'in"


Wani zagi Mama ta jawo tana kallon Usman"kai Amma kai anyi sanho,sakarai,kai zakaje sawo mata kayan sana'ai, kai dan bakada wayo Macen zata aike ka? "


"A'a Mama ai it.... "


"kai tafi can Amma ai yanzu aiki nasata,tace batayi"


Usman ya juya yana kallon Saudat.

*Kuyi hak'uri da wanann*
*AUNTY HALILOSS✍🏽*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*

18


Mama taci gaba da fad'a"ni na sata aiki batayi ba, amma kai dayake gakanan, kazama bawan mace ta aikeka kaje"


Sarai Usman yasan Halin Maman shi, bai tsayaba yace"kiyi Hakuri Mama"


Saudat take gefe ta d'au  hanyar komawa d'akin,Hayatu yace"to dawo sai kin kwashe su,tunda so kike ki raina mu"


Mama tace"wai bakiji"


Wani zafi Saudat, taji cikin zuciyarta,ta juya ta d'auki abin kwashe ruwan ta kwashe taje takai mata.

             ****

Ana kwana ana tashi lokaci yana tafiya, babu abinda ya canza a rayuwar gidan Mama, dan Saudat duk yadda tad'au niyar d'aukar wanimataki,bazata iyaba, saboda sanyin hali irin nata, tanaji tana gani take wahala a gidan, ga goyo, dan ma Allah yasa Sultan bashi da rigima.+

B'an garan Sana'a kuwa Alhamdulillah Maman Khalifa tayi mata talla, sosai ake zuwa neman gero, saboda unguwar akwai masu saida kokon dayawa,wannan dalilin ya k'ara kulla zuminci sosai tsakankn Saudat da Maman Khalifa.

Bak'in ciki kuwa wajan su Mama ba'a magana,saboda Bak'in ciki yanzu haushin Maman Khalifa take ji,Nusaiba kuwa angama wanka, sai fama da k'azanta.

Usman baya damuwa da duk abinda Mahaifiyar shi zatace game da Saudat,soyayya sosai yake nunawa matarshi da yaron shi.

Yanzu kam Saudat tayi tsaye ta dage, anraba masu girki da Nusaiba, saidai ba abinda ta iya, duk idan tayi girki saidai suci saboda kada yunwa ta kamasu.

             ****


Yaro ne ya shigo da Sallama, Saudat tana cikin d'aki,Nusaiba tana tsakar gida, yaron yace"wai ance abada gero tiya biyu"


Duk tinanin Nusaiba Saudat bacci take, ta kalli yaron tace"kaje kace ya k'are"


Saudat ta fito da sauri, ta kwalawa yaron kira"kai kawo akwai"


Nusaiba ta juya tana hararar Saudat,Saudat bata damuba, ta anshi kud'in ta bashi ya tafi.

Washe gari suna zaune duka gidan, Saudat ta fito daga wanka, tazo zata wuce Hayatu yace"ke"


Bata juyoba ta tsaya"ke mungaji da wannan aje Hatsin da kike mamu,kina kawo mamu kwari a gida"


Saudat tace"ban gane ba"


"ina nufin da wannan buhun ya k'are kada ki k'ara,dan yanzu nan ina zaune cinnaka ya shigeman riga"


Tsayawa tayi tana sauraranshi, Mama tace"kike kallonshi saikace baki gane abinda yake nufi ba,daga yau kada ki k'ara wanan sana'ar"


Usman ya fito daga d'aki dan yanajin abinda suke cewa,Saudat na ganinshi ta yi tafiyarta hanyar d'akin.

Zuwa yayi ya zauna,ya kalli hayatu yace"kai ina ruwanka da ita, yanzu sana'ar ma tazama laifi yinta"


Mama ta mik'e tana tab'a hannuwa"ina ce nice nayi magana bashiba, aini zakazo kayiwa maganai, bashiba"


"Mama gani nayi.... "


"ai wallahi duk shegen daya k'ara kawo mana kayan kwari nidashi,dan banga wanda zaisa kullun cinnaku suna cizan mutane ba,an fad'i gaskiya shine zakazo ka zauna zaka fara sharhin daka saba ko, to dan Allah in k'ara ganin kashigo da bugu gidanan"


Mama ta ja gyalenta dake rataye kan igiya, taficewarta, Usman ya mik'e jiki babu kwari yakoma d'akin.

Zaune take tana shafa mai,bata kalleshiba, dan tanajin bala'in da Mama take mashi"kiyi hak'uri dan Allah, narasa yadda zanyi..."


STORY CONTINUES BELOW

"yanzu sana'ar dana samu ina rufawa kaina asiri da yarona,shine yazama laifi"


Gefenta ya matsa ya ruk'o hannunta, lokacin hawayen idonta suka zubo, hannu yasa yana goge mata"ni dai ni nace kiyi hak'uri Allah zai kawo maki wata mafitai"yana magana yana janta jikinshi,yana shafa bayanta cikin wani salo,luf ta lafe jikinshi tana kuka.

          *****

B'angaran su Mami da Pappa kuwa shirin bikin Areef kawai suke,dan yanzu saura wata guda, wani makeken gida Pappa ya kera mashi, dagani na fad'a.

Mami kam kayan lefe kawai take had'awa,ba k'ananun kud'i suke kashewa ba.


Areef kam jin abin yake kamar wasa,duk lokacin da ya shigo gidan zai tadda Mami tana duba wasu kaya ko wani abunda tasaya na lefen.


Areef ne ya shigo zaune yatadda Mamai dasu Ilham,atamfar anko suke dubawa,Areef ya zauna yana kallonsu"ku wallahi baku gajiya"


Khairat tace"wallahi Yaya  na k'agara bikin nan"


Harararta yayi ya Mik'e Mami tace"ina zakaje?"


"zanje d'akine"


"A'a ga kayan Anko d'in nan sun iso,sai akaima Ni'ima na frnd d'inta ne"


Gaba d'aya Areef bayason Maganar bikin, shikanshi baisan dalili ba,saidai bayason Mami tagane,"to Mami bari in huta zuwa anjima sai in kai mata"


Areef ko daya shiga d'akin,zama yayi yana dafe kai, danshi gaba d'aya hidimar yanzu ba santa yake ba,bai jiraba ya mik'e ya d'auki kayan har zai tafi Khairat tace"Ya inzo kutafi"


"ba gida zan dawoba gidan Ammi zan wuce"


Khairi tace"ina zuwa"


Ilham ta juyar dakai dan ita basan zuwa take wajan Ni'imah ba dan tafara gano kamar kishin su takeji.

Suna fita Ilham tace"Mami Khairat kwakwa gareta,ita Aunty Na'imar dataga Yaya tare damu saita d'aure fuska"


Mami tace"keni banison tsegumi, maza kibar man falo"

Haka Ilham ta mik'e tabar Mami.

              ****

Areef ya kalleta"ga kayanan amota,Anko d'in frnds d'in kine"


Ni'ima bata wani tsaya yabo ba, tace"to"


Saida suka fito zasu taho,Khairi ta fara shiga Mota,Areef ya tsaya suna magana da Ni'ima sun jin gina da mota, Areef yace"wai miya b'ata ran? "yana maganar cikin sigar zolaya.

Juyawa tayi tace"dan za'a kawo Anko shine saika taho da wata,sai kace wani abu,in inason magana dakai dole sai sunji ni wallhi banson haka"

Areef yace"mi kike nufi"


"abinda kaji"

Sosai taba Areef haushi,dan dama yariga ya fahimta duk lokacin da yazo da k'annanshi take mashi irin haka,Areef kam bai had'a y'an uwanshi da kowaba, take ranshi ya b'aci, dan yadda yakejin yaran bayajin wad'an da suka fito ciki d'aya.

D'aurewa yayi zuciyarshi tana tafasa saboda b'acin rai, har idanshi yayi ja,ya kalleta yace"bana son irin haka,thy are my sisters i really love them with all my heart, banason irin wanann maganai,kada ki k'ara min haka,yana jinsu har cikin raina, ban had'asu da kowaba,zan iya komi akansu"


Tagano b'acin ranshi yana gama maganar ya shige mota, yaja ya fice daga gidan, ya nufi gidan Ammi.

Tunda akayi haka Ni'ima ta fara boye kishinta,ta bashi hak'uri,ganin yadda ta sauko dole shima ya hak'ura, Amma koda Areef ya koma gida saida yayi tunanin yanzu inda Saudat ce bazatayi kishi akan k'annanta ba.

           ******

Yanzu gurin Mama yacika, babban abinda takeso tagansu zaune babu mai katab'us daga ita har matan y'ay'an nata.

Saudat tana zaune da Sultan a hannunta Usman ya shigo gidan,zama yayi kan tabarmar da take,ya rik'o hannun Sultan yana mashi wasa, Saudat ta kalleshi"Yaya inason zuwa bikin Ya Areef"


Ya kalleta"har kin d'inka anko d'in? "


"A'a a d'inke Ammi ta aiko man, saidai wuyan yayi man yawa"


Usman yayi murmushi yasa hannu ya tab'o k'ashin wuya yace"Ammi batasan yanzu kin rameba?"


Itama murmushin kawai tayi, ya kwanto da ita kan kafad'arshi,"kin shigo rayuwata kin rameko, kiyi hakuri haka Allah ya k'addara man"


Hannu tasa ta rufe mashi baki"ni bance hakaba, kadaina fad'in hakan"


Cizonta yayi cikin wasa da sauri ta janye tana dariya.


              ****

Wani trolly bag ta jawo,saboda sunyi da Usman kwana Ukku zatayi wajan bikin,Usman  yana rik'e da Sultan a hannunshi, suka fito tsakar gidan,Usman ya fita waje don yajirata.

Saudat ta lek'a d'akin Mama dan tayi mata bankwana, saidai bata gidan,ta kalli Nusaiba tace"Na tafi bikin idan Amma tadawo ki gaya mata dan Allah"


Nusaiba tace"yo bikin hada kwasar uban akwati? "


"kwana Zanyi"


Dai-dai lokacin Hayatu ya  fito daga band'aki ya ake butar hannunshi yace"Akwatin miye wanan"


Nusaiba tace"ai shine nike tambaya, wai biki zata kwana zatayi"


Hayatu yace"har wane gari ne, kamar zaki bar k'asar? "


Sai lokacin Saudat tace"cikin gari ne"tana maganai tana nufa bakin zauran,Hayatu yayi sauri ya tare k'ofar"ke baki jirama kiji abinda zance zaki fice, nan cikin garin zaki d'auki kaya kije ki kwana daga biki,dan kin maida mutanan gidannan sakarkari, kin manta gobe ke zakiyi girkin gidan nan ne........ "


*AUNTY HALILOSS✍🏽*

WA NAKE AURE?
    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*
*DEDICATED TO MY NAMESAKE HALIMATU,kiyi man afuwa,ina mai bada haƙuri,my namsy,yar Albarka,Ummi,Lady,wannan kirarin kine let me Add with _Fresh leemoo_ ina tayaki Murnar zagayowar ranar Haihuwarki,Happƴ birthday darling🎂🎂🎂and sorry for late wishes dear.*
*Fans nagode da kulawarku,Alhmdllh nasamu lapia na warke*
19

Ai Saudat tsaye tayi tana kallon Hayatu dan tarasa abin cewa,tana tunanin yadda zai hanata zuwa wajan bikin yayan nata.

Mama ta shigo gidan dan dama sallama ba damuwara bace,ta kallesu kafin cikinsu wani yayi magana tace"Jikkar miye nan,ka bata hanya ta tafi in Yaji tayi,saikin dawo Allah ya raka taki gona"

Cikin mamaki Saudat ta kalli Mama,wani ɓacin rai ya ƙara taso mata,wai so takema suyi faɗa da mijinta,Saudat tace"a'a Mama ba yaji zanyi ba,biki Yayanah zani gida,kwana biyu,zanyi shine Hayatu ya tareni wai....."
+
"ina kike ne,marece nayi sai nasu Napep sun maki tsada kinsan...."

Mama ta kalli Usmn daya shigo yana magana,wata harara ta watsa mashi,"wato har kanada kiɗin da zaka biya mata kuɗin mota Amma ka gagara yi mana wani abu,agidan nan"

"a'a Mama wallhî"

"Kai tafican rifeman baki,naga in da zata fita gidannan"

Saudat jikinta yayi sanyi da tasan halin Mama idan tace abu to sai tayi.

Saudat tace"Dan Allah Mama kiyi hakuri kibarni"sosai taba Usman tausayi, yadda takewa Mama magiya akan tabarta.
Usman yace"Mama kinaji ta bada Hakuri"

Wata ajiyar zuciya Mama ta sauke kamar gaske,Usman ya kalli Saudat"ki tafi"

Saudat ta mik'a Hannu ta anshi Sultan, ba wanda tayiwa Magana tabar gidan,Usman ya juya ya shige d'aki dan yasan idan yace yaraka ta yajawowa kanshi wata matsifar.
             ****
Gaba d'aya gidan nasu duk y'an uwa sunzo, na nesa dana,kusa kowa yazo bikin,Saudat ta shiga gidan, da sultan rik'e ga trolly tana ja.
Duk yan bikin kallonta suke yadda ta canza kamar ba Saudat d'in da suka saniba,don ta canza tayi duhu ga rama datayi, dakaganta kasan tana shan wahala, saidai dayawa basajin tausayin ta, saboda suna ganin itace tayiwa kan.

Ilham da d'ai-daikun yan Uwa ne suke mata oyoyo, itadai binsu kawai take da kallo, Ilham ta anshi Sultan daga Hannun Saudat tana fad'in "oyoyo lil sultan"

Saudat tayi dariya "har kunyi shirin k'unshi kenan?"

"wallahi kuwa,muje ciki"

D'akin Mami suka shiga, Mami taji daɗin ganin ƴar tata,sai dai takasa nunawa saboda ƴan Uwan Pappa da suke wajan,su kansu wani kallo suke mata,Saudat ta gaidasu,suka Amsa ba fara'a tare dasu.

Hakan yasa jikin Saudat Yayi sanyi sosai,koda Pappa ya dawo ta gaidashi,shi kam yana tafiya yana amsawa yana  kauda kai.

Haka akaita shirin ƙunshi don a gidansu Amarya za'ayi shi,tunda Khairat ta ɗauki Sultan ita keta yawo da yaron.

Ganin yadda family ɗinta suke kamar nuna rashin kulawa akanta hakan yasa taji duk ba daɗi,take ta farajin ta tsani kanta,dakin su Ilhamta shigewarta kuka tayi mai isarta,dan ƙin zuwa wajan event ɗin tayi.
Khairat kuwa dazasu tafi,Pappa ya anshi Sultan daga hannunta,wasa yayi mashi sosai,yaron ya shiga ranshi,ganin bashida rikici gaya suna kama da Saudat,sai wajan magrib Pappa ya shigo da yaron A hannu,ya kalli Mami yace"ina Mamarshi take?"

STORY CONTINUES BELOW

"a'a ni banganta ba,ai tatafi wajan Evnt ɗinko"

"a'a khairat tace man tana ciki"

Mami ta anshi yaron,Papa ya fice,kira ta kwala,sai lokacin Saudat ta miƙe tafito,jiki babu kwari ta anshi yaron
Sai dare Areef ya shigo gidan,lokacin duk andawo gida,Saudat tana falon gefe zaune,Mami tana zaune da sauran mutane.

Areef ya gaida Mami,duk ƴan falon sukayo kanshi suna zolayarshi,wasuma da biyu suke maganar dan sunga Saudat a wajan,harda cewa wanann zuƙeƙiyar Amarya taka.

Shikam dariya yakeyi,Saudat tace"Ya Areef ina yini ya hidima?"

Areef yanajin muryar yasan itace"lafiya lau" yace yana kauda kanshi,ya kalli Aunty Jamila ƙanwar Mami yana cewa"Auntƴ ina fatan kin ɗauƙo man Matata?"

Aunty jamila tace"sosai kam,amma nasaka wayar chaji yanzu"

"ok zan dawo Anjima in gansu"

Yana maganar ya nufi hanyar fita,saiga Ilham ta shigo,kallon ta yayi yace"ina Sultan yake?"

Ilham tace"yana sama yayi bacci"

Baice komiba,ya fice daga falon,shidai yaron yashiga ranshi.

          ****
Washe gari kamu akeƴi,saidai gaba ɗaya saudat duk batada walwala,bata damun fuska a wajan kowa na gidan sai ƙannanta.,har ta fara tunaninko takoma gidan Ammi dai kuma wata zuciyar tace kiyi zamanki,kin jure wulaƙancin Mama balle na ƴan uwanki,wannan dalilin yasa ta samu sauki a zuciyarta,saidai ita kanta tanason ganin Ammi.

Wajan Karfe ɗaya,ta ɗaki Anko ɗin Kamu tacewa Mami zataje gidan Ammi dagacan zata wuce kamu, tasamu driver yakaita.
Ammi taji daɗin zuwanta,sai lokacin naga sakewar Saudat,ta zama yar gida Abinta.

Marece nayi suka hau shirin tafiya kamu,Saudat kanta saida Ammi tasa akayi mata makeup,tayi kyau sosai,ta yafa mayafinta ta ɗauki sultan a kafaɗa,Ammi ta kalleta tace"a'a kibar manshi,tunda babu ruwanshi da kuka"

Saudat tayi dariya"kai Ammi kibarni in tafi dashi,kinga hidima tayi maki yawa"
Harara Ammi tayi mata hakan yasa Saudat ta miƙa mata yaron,Ammi ta fiddo kuɗi masu yawa ta miƙa mata"ga kuɗin liƙi nan"

Tunda akaje ake jiran,zuwan Amarya da Ango,haradai har lokacin Amarya tafara shigowa Amma babu ango,aka cigaba da gudanar da hidima,Saudat sai ware ido take amma Areef baizoba,ankai 30mint sannan M.C ya sanar da zuwan Ango,ƴan uwan Amarya sai tsegumi ake sabda rashin shigowarsu tare,M.c ne yace Amarya ta je ta shigo da Angon nata.

Sanye yake da white shadda aikin dark blue kalar kayan jikin Amaryarshi,kular kanshi kalar Aikin jikin rigai,kasan cewarshi fari hakan ya ƙara fito da asalin ƴanshi.

Sun zauna,akayi kamu aka gabatar da tsare tsren da aka shirya,anyi rawa sosai,Ƴan uwa sai liƙi ake masu,Saudat ma tayi ƙoƙari ta fara liƙa kuɗin da Ammi ta bata saidai bazata iya ba ta koma ta zauna.haka aka gama aka koma gida.

            ***
Rana bata ƙarya,anɗaura auran Areef da Amaryarshi Ni'ima,saidai har lokacin Areef jin Abin yake kamar wasa,Usman yazo ɗaurin Auran,har yazo ya dubasu Saudat,ƴan uwa har leƙe ake domin ganin mijin Saudat,aka gama hidima,akakai Ango ɗakinshi,washe gari Saudat ta tattara kayanta,tayi bankwana,Mami ta bata kuɗi har dubu ɗari,Saudat kam kasa magana tayi saima ta fashe da kuka.

Mami ta rarrasheta ta tafi,gidan Ammi,Ammi ta matsa mata akan ta kwana Amma tace a a,itama anan kuɗi ta bata,Saudat taƙi ansa,Ammi tahau faɗa,Saudat ta haɗo kuɗi masu yawa tadawo gida.
            ****
"Allah dear ba wani business da zanyi da kuɗin nan,dan ƴan gidannan ba barina zasuyi ba,kaidai kayi yadda nace maka ɗin"

Usman ya rasa mizaicewa Saudat,saida yaja dogon lumfashi yace"yanzu ta ina kike ganin zan fara?"

Saudat tace"ai kace wannan shagon dake rufe na waje babu komi a ciki,kawai a gyarashi,sai ka buɗe provision store a wajan"

Shikanshi Usmaɓ yasan yayi sa'ar Mata,dan samun mace irin Saudat ba ƙaramin nasara bane,sosai ya ɗauki shawararta,ko su Mama bai faɗi mawaba,saidai sukaji ana gyaran shago.

Ta tambayeshi yagaya mata provsn zai fara saidawa,nanfa tahau faɗa,wai wuyanshi yayi kwari har zai fara sana'a bai gaya mataba,ganin yadda take masifa,yaƙi faɗi mata inda yasamu kuɗi,saidai Usman yayi mata ƙarya cewa wani uban gidane yasamu.

Cikin kwana da basu wuce ukkuba aka gyara shago aka zuma kayan iya kuɗin da suke dasu,Saudat kam ranar murna hada kuka,Usman ya kalleta yayi dariya,ya tallabota yace"yanzu kukan miye anan"

Saudat tace"murna ce kawai"

Usman ya ƙara matseta jikinshi"to sai ki cigaba da man addu'a don samun Alkhairin abun"

Abu kamar wasa duk cikin satin duk layin aka gane an buɗe shago a layin,hakan yasa dayawa anan ake sayayya an huta zuwa babban titi.

Mama kam gida-gida duk inda ta shiga,sai ƙara girman kai takeyi wai ɗanta yayi kuɗi,Maman Khalifa ce tazo wajan Saudat tana bata labari,Saudat tayi dariya tace"wai kuɗi,duka ɗan cinikin da akeyi ne take cewa yayi kuɗi"

Itama dariya tayi tace"wallahi ni Usman ɗinne ma yake ban tausayi"

Saudat tace"bakisan abin tausayiba,kwana Ukku da buɗe shagon da bakin ƙofar gida take zama,duk wanda yazo sayayya sai ta ganshi"

Maman Khalifa tace"Allah dai yasa kada ta cinye kuɗin"

Dogon lumfashi Saudat taja tace"ai naga yanzu baya bata,ai yasan cinyewa take ba abin kirki take masu ba"
            ******
Ɓangaran Amare kuwa soyayyarsu sukesha,Areef yana samun kulawa wajan Ni'ima saboda dama tana mugun sanshi,hakan yasa shima yake bata kulawa sosai,basuda wata matsala ko yaushe suna tare da juna.

Babbar matsalar da Areef yake fuskanta,idan ƴan uwan Ni'imah sukazo,to zaiga yadda akeba ƴan uwa kulawa,shikam koda danginshi sukazo ɗaure fuska takeyi,hakan yasa Ilham da Khairi sukayi hannun riga da gidan.

Sai dai Areef yakanga kamar dan tana Amarya ne,duk da dama ya fara fahimtar hakan kafin Auransu.

              ****
Bayan watanni Ukku Usman ba ƙaifi shago yana ta haɓakuwa,ana samun ciniki daidai misali,Usman yana kawo abin da za'a ci a gidan,amma baya kwarar kanshi,Saudat kam sosai yake kyautata mata,ganin canjin da Saudat take samu nanfa Mama tasaka idanu.

Farko Mama tayi tunanin Usman zai rinƙa kwasar kuɗin yana bata ne,da harta fara juya ma Hayatu baya,tana cewa ai kaima da Provsion ɗin kafara saidawa.

Saudat ce tsakar gida tana girki,ga Sultan yana yawo tsakar gida dan yafara koyan tafiya,Mama tana cikin brander tana cin kwaɗo datayi,Nusaiba ta fito daga ɗakinta ta zauna.

Bata jima ba,Hayatu ya fito da yarinyar a hannun shi,"ansarta sai kuka take yiwa mutane"

Nusaiba ta anshi yarinyar,dai-dai lokacin Usman ya shigo,inda Mama take ya nufa,sannu Saudat tayi mashi,ya gaida Mama.

Sai lokacin Hayatu shima ya zauna,ya kalli Usman yana ɗaure fuska,Mama ta kalleshi"yanzu yauma baka sawo mamu bridi ba,ina madarar da kace zaka kawo"

Usman baiyi magana ba Hayatu yace"Ni ba wannan ba,dama shogonka zanje dubu sha biyar nikes kabani bashi"

Usman ya kalleshi yama rasa abinda zaice mashi,da kyal ya iya cewa"nida ba kuɗi naba taya zan ɗauki kuɗin mutane in baka?"

Mama tace"eh lallai kai yanzu baka iya ba ɗan uwanka aron kuɗi?"

Usman yace"Mama ba haka bane,kuɗin nan b nawa bane,dubu sha biyar ai kuɗin cinin kwana biyu ko ukku kenan,kinga ai...."

"ba sauran Abinda zakace man,zance ya kare"tana maganai tana miƙewa tsaye ita a dole Usman ya guje ta.

Dai-dai lokacin Saudat tagama abincin ta tashi ta shigewarta ɗaki,Usman ya miƙe ya bita.

Mama ta kwatsa mashi Harara"binta zakayi ko?itaga Uwarka,sai abinda tace zakayi,ai dama ina lura daku a gidan nan,kazama subtu"
*AUNTY HALILOSS✍🏽*WA NAKE AURE?

    *Vote and follow me on Wattpad @AuntyHaliloss*


20


Usman jiki ba kwari yadawo ya zauna,Saudat kam ko a jikinta dan yanzu ta fara jure maganganun su Mama.


Babban baƙin cikinta rainin da Nusaiba take mata,tun tana habaici har yakaiga tana faɗin suna.


Tana zaune kiran fatima ya shigo wayarta,Saudat ta ɗauka"Frnd kwana biyu"


"wallahi kuwa,ai zanzo gidan gobe zan kawo maki kayan saka rana"


Saudat tace"kai wai dagaske frnd?"


"eh mana" Saudat taji daɗi sosai,tace"Allah yakaimu gobe.


            *****

Tunda wanann abu yafaru tsakanin Hayatu da Usman,Mama ta ƙara ɗauko karan tsana ta ɗora akan Saudat,Hayatu kam idan yashigo gidan zai kama zage-zage Sai dai Saudat tayi banza wani lokaci ta shigewar ta ɗaki.


Hayatu ya kalli Mama yace"Mama ki gane,yarinyarnan ita ke zuga Usman,jifa yanzu daga ɗari biyu baya iya baki komi,amma nasan ita ai yana mata"


Mama ta lumfasa tace"kai nifa abin har yakaini bango,yarinya kamar cingam,ni wallahi so nike ma ya saketa,ta tafi can ta ƙarata"+


Nusaiba ta kece da dariya"waiku baku lura ta mallakeshi ba,taya zai iya rabuwa da ita"


Hayatu yaja lumfashi"ai duk tsiyarta sai tabar gidan nan"Haka sukaita maganganunsu akan Saudat,dayake ko tsakar gidan yanzu tadaina zuwa,daka ganta to akwai abinda zatayi.

Zaune take tagama bakacen masara,Sultan kam yanzu ya iya tafiya,sai neman ɓanna ga ƙiriniya,Mama tana ɗaki,Hayatu ya shigo can ya tadda Sultan wajan tukunyar ruwan Mama dan ita Saudat batasan ma yaje ba.


Hayatu ya daka mashi tsawa,Saudat ta juyo ta kalleshi,Hayatu ya matsa ya kamo hannunshi ya jibga mashi wani wawan bugu a baya"kai dan Uwarka ruwan gidan zaka ɓata"yana maganai yana ƙara murɗe mashi kunne yaro ya fasa ihu,da ƙarfi"Wau daga wanan ɗan bugun shine zaka fashe mamu da kuka,to bari inma nagaske dan Uwarka.


Itadai Saudat kauda kai tayi,Haƴatu ya cire takalmin ƙafarshi,ya shiga bugunshi dashi,yaro sai ihu yake,abin yaba Saudat haushi,har zuciyarta takeji,duka yaro ko shekara ukku bai cikaba Amma yake mashi wanan duka.


Daga shago Usman yake jiyo kukan Sultan cikin Sauri ya shigo gidan,Saudat ya fara tamabaya" lafiya"


Batayi maganaba,yaga Hayatu riƙeda Sultan,ya wurgo shi,"jeka dan Uwarka in ƙara ganin kayi mana ɓanna"


Usman yakalleshi ganin yadda ya wurgo yaron zuciyarshi ta mashi zafi,yakalleshi"Haba Hayatu wannan wane irin bugu ne,yaro fane"


Hayatu yace"Yaro ne yasan yazo ya ɓata wa mutane kaya"


"Wannan bugun ai yayi yawa baka gudun kaji mashi ciwo?"


Mama dakejin duk abinda suke cewa daga ɗaki tafito,"to kai bakaso a hukun tashi ne,ko so kake abarshi yayi duk abinda yaga dama,shiga ɗanso ɗan Matar so ko?to bazai yiwuba"


Saudat najin abinda Mama tace ta miƙe zata bar wajan,Mama tace"ina zaki munafuka,ai nasan ke kika kirashi,munafukar banza,fari kamar lemun Marinda"


Saudat taji haushi saidai batada wani zaɓin daya wuce ta tsaya,Mama tace"to ai saika koma inka gama lallashin shi,wai ɗan fari kuke ma wanann abin?


Mama taja tsaki ta shige ɗaki,Saudat ta tafi ɗakinta,Usman ya ɗauke Sultan suka shige ɗakin.


Usman ya kalleta,"ki daina barinshi yana ɓarna,kinga irin wannan dukan sai aji mashi ciwo"


STORY CONTINUES BELOW

Saudat ta goge hawayenta,don tausayin yaron yakamata,dan dama batun yau take ganin tsanar da suke nunawa yaron ba.

"Amma dai kasan bazan aike shi ba,yanzu shina yaron haka zai taso cikin wahala gaskiya ina jin tausayin rayuwar shi"


Usman ya janye Sultan ya kwantar dashi saboda baccin wahalar daya kamashi,ya kamo hannun Saudat,kiss yakai mata"kiyi haƙuri Allah zai canza mashi rayuwa,insha Allah bazai sha wahala ba"Nan ya farayi mata salon soyayyarshi,har suka manta da abinda ya faru.

          ******

Ganin yanzu Saudat batada abokin fira a gidan,hakan yasa take tambayar Usman zuwa maƙotansu wajan Maman Khalifa suyi fira,data gama abinda take sai ta tafiyarta,ko da daddre kafin ya dawo daga shago.


Aikam wannan abu yana ƙona ran mutanan gidan,yau takwas da rabi na dare ta dawo,dan tasan ƙarfe tara yake rufe shago,ta shigo da Sultan wanda har yayi bacci.


Hayatu yana cikin baranda yana cin tuwon dake,yakalleta yace"waike ina kike zuwa da wannan daran,dankin raina wa mutane wayo,yanzu bakison zama gida"


Saudat bata kula shiba,ta nufi ƙofar ɗakinta,saidai Padluck tagani an rufe ɗakin,ta tsaya tana taɓa kwaɗon,Hayatu dake gefe yace"naga inda zaki shiga"


Abin kwanin Mamaki,Saudat taja ta tsaya,tana tunanin yadda wani banza zai rufe mata ɗaki,sai kace shine mijinta.


Dariya Hayatu ya saka"ki shiga mana"


Ta watsa mashi harara"ai dayake naga ka rufewa matarka"


Hayatu yace"ke ni kikewa irin wanann maganai?ina ruwanki da Matata,ko tsarar kice"


Abin yama ba Saudat dariya,gefe ta zauna,ta aje Sultan kan cinyarta,ba'a daɗe ba saiga Usman ya shigo,touchlight ya haska"yo lafiya?"


Banza tayi mashi ta juya,Hayatu yace"ɗakin na rufe"


Usman kam baice komiba,dan yana gudun wata fitinai,ya kalleahi yace"to bani key ɗin in buɗe"


Hayatu shima baiyi magana ba,ya miƙa mashi makullun,Usman ya buɗe ya maida mashi makullun,Saudat kam abin ya bata haushi,hakan yasa ta ɗauke suna shiga taƴi shirin bacci dan dama taƴi wanka kafin ta fita.


Baya ta juya mashi,ya saka kayan bacci ya hau gadon,ganin suna fuskantar juna yasa ta juya,Hannu yasa ya juyo da ita"to kuma mi akayi maki?"


Saudat ta turo baki"Au ba'a mayi mani komiba"


"nayi tunanin yanzu wanann bai ɓata makirai,idan kika lura da aikin jahilcine yayi,shida ba mijinki ba taya zai kulle maki ƙofa?"


Saudat tace"Amma ai..."

Bata idaba Usman ya haɗe bakinsu,hakan yahanta ida maganar daza tayi.


           *****

"kiyi Sauri ki shirya,Kinga bakin gobe zasu wuce da safe Ammi tace muje yau dan bazasu samu damar zuwa ba".


Ni'ima ta yafa mayafinta"muje" Areef yayi gaba,sai gidan Ammi.


Ƴan uwan Ammi ne da suke zaune a Katsina,dama koda akayi bikin Areef basu samu zuwa ba.


Ni'ima tafara shiga,Ammi tace"oyayo sannu"Ni'ima cikin fara'a take gaida Ammi,Ammi ta amsa tana tambayarta,yagida,dai-dai lokacin Areef ya shigo.


Ammi ta kwalawa yaran kira,"kuzo ga Aunty"


Ƴammatane su Ukku ƙaramar cikinsu zatakau shekara 15 sai namiji,Areef sai washe baki yake"oyoyo sisters"


Namijin yaja baya"wato bandani ko?"


"sorry hadakai"


Ƴan matan suka gaida Ni'ima ta amsa tana tambayarsu ya hanya,kan four sitter da Areef yake suka je suka zauna"haba brox wallahi munyi fushi,ko congrat baka kira kayi mana ba"


Wacce tafi shima tace"a'a niɗai ina amsar result ɗina yaman masage ya kirani"


"tab abin sankaine,kafison Yaya zee kenan" tana maganai tana miƙewa,alamar tayi Fushi,Ammi tace"to baka kyauta ba.


Areef ya riƙo hannunta,"zauna yanzu har gift zan baki"


Ni'ima dake gefe ta ɗaure fuska,tana jan tsaki,Ammi ta kalleta"lafiya"


Ni'ima tabatayi tunanin tsakin yafito ba tace"kaina ke ɗan ciwo"

"Ashsha"


Areef yakalleta,dan yasan halinta,ya ganota sosai,take ya manta da ita,yaci gaba da kula ƴan uwanshi,ya kalli Nur yace"ina Mama?"


"Mama tana gidan Mami su Khairat sun hanata tahowa,sai saidai gobe muje can muɗauketa muwuce"


Ammi yace"to bari mutashi muje can ɗin,mugaidata kada dare yayi sosai naga tara takusa"


Harsun miƙe ƙaramar tace "muje can zan biku wajan Mama ɗin"


Areef yakalli Ni'ima" tashi mutafi"


Ammi tace"ku tsaya chamist kasai mata magani"


To kawai Areef yace dan yasan bawani ciwan kai,suka wuce gidan Ammi.


            *******

Usman ya rufe shagonshi sun tafi wani waje shida Iro abokinshi,Hayatu ya shigo gidan,har lokacin Saudat bata dawoba,dan dama yagaya mata zasuje wani waje da Iro.


Mijin Maman Khalifa ne yashigo,ta gaidashi tayi mashi bankwana,ta ɗauko sultan suka dawo gida.


Tana kwantar da Sultan ta,cire kayanta zane ta ɗaura,ta yafa kallabi,ta ɗauki kwandon wanka,ta shiga toilet.

Hayatu ya kalli mutumin daya samo yace"ta shiga wanka,duk abinda nace maka kayi kada ka ɓata shirin"


Tsaki mutumin yayi yace"wallahi sai ince na fasa,kai ƙaramin ɗan iskane ni zaka koyawa yadda zanyi,duka bubu huɗun daka bani"


Hayatu yasan halinshi,"yauwa to yi haƙuri"


Mutumin ya shiga ɗakin Saudat dagashi sai wando 3qter dama rigar jikinshi Armless ce,gadon ya tumurmuje,ya kwanta gefe,yaɗan rufe ƙafafunshi kaɗan.

Saudat tana fitowa,ta jiyo muryar Usman a bakin ƙofa,sauri tayi ta shiga ɗakin dan taɗan saka turare kafin ya shigo,tsayawa tayi tana labubar touch light.


Mutumin ya fara magana,daidai isowa Usman bakin ƙofar ɗakin"kai gaskiya farincikin rayuwata ban taɓa jin zuma irin ta yauba,tunda nike dake ban taɓa jin daɗi irin wannan ba,gaskiya mijinki yana lasar zaƙi,kai amma yau"


A razane Saudt ta kunna fitilar,Usman ya dafe kai yana shigowa ɗakin,yana salati,Saudat taja baya cikin tsoro tana faɗin innalillhi wainnailaihi raji'un.


Usman yayi kan Saudat cikin tashin hankali,yana huci,Mutumin yabi ta bayanshi ya fice daga ɗakin cikin sauri.


"wanene wannan,wannan wace irin rayuwace kika saka kanki saudat,ƙato a gidana ɗakin Aurena"yana maganai yana hawaye zuciyarshi tana harbawa da ƙarfi da ƙarfi.


Tashin hankalin da saudat tashiga baya misaltuwa,"wallhi na rantse"


Wani wawan mari Usman ya sauke mata,har saida fitilar hannunta ta faɗi,"Allah ya isa tsakanina dake kin cuceni,bazan iya yafe makiba,Saudat kije na Sakeki saki UKKU...

.....


Ai wata ƙara Saudat ta saki,batasan lokacin datakai ƙasaba.
*AUNTƳ HALILOSS✍🏽**

Post a Comment for "WA NAKE AURE CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...