TAURA BIYU CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

TAURA BIYU CHAPTER A

TAURA BIYU CHAPTER A

- - Post a Comment

 TAURA BIYU CHAPTER A


*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒

       _Mi amor-mi vida_....


_viawattpad@mamuhgee_

2

           *1*

_Bismillahir-rahmanirraheem_.

*B* abban gidane sosai daya qunshi 6angarora acikinsa sbd yawa da zuriar gidan sukeda shi,,


Gidane tsohon gini irin na masu arzikin lokacin baya daya gabata,


Mal Zubair shine mamallakin gidan da ahalin gidan gabaki 'daya,


Ya rasu shida Mai 'dakinsa Fatima sunbar 'yaya hudu duka maza,,+


Baba malam hayatu shine babba agidan yanada tsananin zafi da fa'da,

Sam baya kar6ar uzuri ko kuskure duk da kasancewarsu malamai masana addini,2


Baba malam shine Mai zartarda duk wani hukunci acikin gidan Kuma ya zartu Koda baiyiwa kowa dadiba.

yanada mata biyu inna hindatu da iya lami,


Inna hindatu bata ta6a haihuwaba iya lami ce keda 'yaya bakwai, _zayyanu, auwalu, dahiru,Musa,mustapha, abudullahi da sani_.

Baba shehu shine mabiyin baba malam Kuma shima kusan duk halinsu 'daya da baba malam illai shi Yana da'dewa baiyi fadan ba,

Matarsa 'daya shi,mama salamatu Sai 'yaya biyar duk mata,hafsat, Amina, hajaru, zainab da sumayya Kuma duk anyi musu aure.


Sai baba Yusuf Mai sanyin Hali da kawaici dakuma tsananin qaunar 'yanuwansa, shima matarsa 'daya fatima da 'yaya biyu _*AYSHA*_ da nuratu.


Alh Bello shine qaraminsu Kuma fitnannensu Dan masifa da son kansa a fili yake sbd ya 'dan taba yin arziki abaya Amma yanxu Babu shiyasa ko Abu ka'dan akai saiya maidasa babba akan fitina da fa'dansa.

Matansa biyu mama bilki da umma sakina.,

'yayansa bakwai _ahmad, isah, Umar, abbakar Sai saudat Salma da husna_

Dukkaninsu a gida 'daya suke Sai dai kowa da shiyarsa Amma yaransu maza kaf 6angarensu 'daya hakama matan.


Asalinsu buzayen qasar nijar ne malanci yakawo mahaifinsu garin gombe harya gina gida yazama mazauni.


Malamai ne kaf 'dinsu Kuma basuda wani aiki bayan malanta hakama ba wani arzikine  dasuba Sai rufin asiri.


A rayuwar gidan Sam basa auren na waje saidai atsakaninsu sbd yawa dakuma tsananin kyamar wani yare daba nasuba na buzaye.


Qabilanci ne tsantsa acikin jinin kowane 'dan Adam dake rayuwa acikin gidan,

Basa qaunar ha'dawa da ko bahaushe bare wani yare har gwara Fulani.


Wannan aladace dasuka gado tun gurin iyaye da kakanni shiyasa duk kwa'dayi da maita ta kyau da 'yayan gidan sukedashi ba'a tunkararsu da maganarso,


Qiyayyar dasuke fitowa suna nunawa ta rashin son ha'da zuria da wata qabila a qarara yake Dan abin har tsoro da mamaki suke bawa na taredasu.

Yaran gidan kaf dinsu maza da mata ustazai ne kamilallu kullum jikinsu a rufe yake ruf ko qafarsu baka gani fuskarsu ma wani sa'ilin suna rufewa idan zasu fita.,


Mazansu da matansu sun haddace alqur'ani akansu da sauran littafan addini.


Ka'dan ne daga cikinsu sukai karatun Boko sbd bai damesuba sunfi riqe addini shiyasa layin gidan kullum acike yakeda motoci da mashina harda kekuna gurin 'daukar karatu a gidan.

Ayshah,husnah,saudat da Salma kusan sa'anin juna ne 'yan kimanin shekaru goma Sha takwas zuwa Sha Tara.


A al'adar gidan mata basa wuce gaba da secondary aure suke musu Amma wannan karon anbarsu Aysha sun wuce sbd ba'ayi Shirin aurensuba Amma antsayarwa kowaccensu da miji.


A university suke karatu yanxu suna two hundred level.,

Aysha medicine take karatu sukuma sauran gabaki 'daya Islamic sukeyi.

STORY CONTINUES BELOW

Yaya Umar shine Wanda aka ha'da Aysha dashi sbd sonta daya nuna yanayi qarara,


Ya Umar mutum ne Mai zafin Rai kamar iyayensu Dan kamarma ya zarcesu sbd baida hakuri ko ka'dan ga saurin duka dayakedashi bayada kar6ar uzurinta ko ka'dan shiyasa kullum idan sukai fira kwana kuka take sbd da fa'da suke rabuwa,


Sanyin halinta da sanyin jikinta tareda kasancewarta miskila Mara hayaniya shike wahalarda ita ko acikinsu saudat bare gurin ya Umar.


Halin umminta ne ta 'dauko Zak harma ta zartata sanyin halin shiyasa mahaifinta da ummin ke tsananin qaunarta da tausayinta sbd ganin kawaici da hakurinta sa6abin qanwarta nuratu dake da masifa ba'a ta6ata ko ka'dan.


Aysha kyakkyawace Mai kyan jiki Dana fata ko acikin gidan tafisu hasken fata da kyau sbd tafisu rashin son fita duk da dama kulle ake musu basa fita.***********

Yau tun 6 na safe tafara shiri sbd anyi shifting lectures 'dinsu zuwa sabon site 'din university Wanda bakowane course ake maidawa can ba gashi yanxu an rabata dasu husnah dansu yanxu tsohon site suke.


Hakanan batajin dadin rabata dasu da'akai sbd batasan ya can 'din takeba,.


Tsaf tashirya cikin doguwar rigar atampha red Mai adon dark blue saita saka dogon hijab dark blue daya sauka har qasa yanaja danko kalar atampharta ba'a gani bare qafafuwanta,

Jakarta ta 'dauka tareda ficewa taje tagaida iyayensu kowane 6angare kafin tadawo 'dakinsu suka fito taredasu husnah.

A qofa suka hadu da ya Umar da ya Ahmad zasu shigo,


Har qasa suka durqusa su duka suka gaidasu

Ahmed ne ya kar6a Yana shigewa cikin gidan

Ya Umar ne ya amsa tareda kallon ayshah


Qasa tayi da kanta Tana wasa da Jakarta su husna kuwa tuni suka wuce sbd Umar 'din Sam baya wasa yanxune zasuji ruwan bala'i.


Kallonta yakumayi dakyau ahankali yace,


Meyasa baki saka safa ba?


Cikin sanyin murya kanta na qasa tace,


Sunyi dattine na wanke na shanya ruwan da'akayi da dare sun hanasu bushewa.


'daure fuska yayi yace,


Toki tabbatarda kin dawo kan lokaci.


To''''' tace a hankali tareda wucewa cikin sanyinta.

Ajiyar zuciya ya saki ahankali bayan ta wuce Dan hakanan yakejin Sam hankalinsa yakasa kwanciya da karatun Aysha sbd jiyake kamar zai rasata ne duk dayasan bazata kula kowaba.


A bus stop suka rabu dasu husnah ita ta nufi new site Banda faduwa ba abinda gabanta keyi sbd ita mutum ce Mai tsoron shiga jama'a batareda Wanda tasaniba.


Koda ta Isa kai tsaye hall 'din dazasuyi lectures ta nufa kanta a qasa cikin nutsuwarta take takawa Dan duk a takure take sbd yanayin students 'din data gani anan 'din kamarma 'yan iskan makarantar ne aka kwaso aka dawo Nan dasu Dan dukanin alamu sun nuna kusan hakan ne,

Lectures suke Amma Sam takasa samun nutsuwarda zata fahimci lectures 'din Dan wasu samari dake kusada ita suna dariyar shigarta.

Sai kusan six suka fito daqyar taga tafito ta iso gida Dan har wani zuru zuru tayi na fargaba data yini yau aciki.


Tana Isa gida ta tu6e tayi wanka tareda sallah kafin tazauna cin abinci Tana fira da umminta tareda Bata labarin wani fa'da dataga anayi kan hanyarta ta dawowa.

********


Babban gidane dayaji komai najin da'din duniya sbd girma,kyau dakuma haduwarsa..


Babbar mace ce 'yar gayu da hutu tareda ilimin Boko dayagama ratsata yasa manyancinta qin bayyanuwa sosai,


Babbar justice ce a babbar federal high court dake garin hakama Mai tsananin roqoce da addininta na christian Dan har muqami gareta a church sbd riqoda addininta Dan dukda zamanta babbar Mai kudi hakan bai hanata halarta da kula da aikin church ba kullum.. _justice queen aiden Bellamy_ kenan.


'yayanta uku rak a duniya,

*FINN* shine babba mum's boy kenan sbd shine ya 'daukota sawu da sawu Dan shima law ya karanta yanxu lawyer ne kullum tare suke zuwa office sudawo tare suje church tare,

Duk wani Hali nata ya 'dauko Dan harma ya zartata musamman yanda ta tsani kowace qabila da addini idan ba nataba toshima haka.


*_NIK_*,,,,Niklaus kenan, shine nabiyu Wanda shida qanwarsu *DAVINA* kwata kwata halayensu sunyi hannun Riga Dana mahaifiyarsu sbd Sam su Babu ruwansu da wani riqo da addini bare zuwa church,,


Nik 'dan gayune na qarshe daya ha'du iya ha'duwa sbd tun farko a hannun dad 'dinsu yake a qasar Germany danshi Sam bayason takura yanason yayi rayuwarsa a sake shiyasa yaqi biyo mum 'din dazata dawo Sai daga baya ta matsa tareda 'daga hankalinta akan saiya dawo Nigeria.


Gabaki 'dayansu suma farare ne tas bama kamarshi dayafisu son hutawa akoda yaushe kamar mace.


Davina ma kusan kamarsa take 'yar gayu kullum Tana tareda friends ana gurin shopping ko gurin hutawa..


Hutu da gata tareda dukiya sun ratsasu sosai shiyasa kullum cikin qara kyau Nik yake,

Duk wani son life 'dinsa mata basa burgesa tunda yadawo Nigeria sbd Sam bazai iya ko kallonsu ba bare ya iya kulasu yan matansa nacan sunfi burgesa sbd sune sukafi sakasa nisha'di.


Tsaf take cikin kayanta na aiki ta fito ta hawo sama bedroom 'dinsa Dan shika'dai ne 'dakinsa yake sama sbd tsananin so data fili ta nuna qarara tafisonsa fiyeda sauran 'yayan nata.


Tura qofar tayi ahankali sanyin ac da qamshin turarensa na signature hugo ya daki hancin takai kallonta kan lafiyayyan gadon dayake kwance Yana bacci dunqule cikin falin bargo qal.


Takowa tayi ta Isa bakin gadon tareda durqusawa ta rintse ido tafara kwararo masa adduarsu ta church Wanda kullum saitayi Masa kafin tafita office hakama da daddare komai Daren dazaiyi awaje saita jira yadawo tayimasa sbd ba qaramin so takeyiwa 'dan nataba.

Ahankali ya 'daga hannunsa 'daya ya janyo dayan pilonsa batareda ya bu'de idanuba ya toshe kunnensa dashi sbd damun baccinsa da mum din keyi da addua.


Jin ta qara 'daga murya tana fa'din,


Ohhhh Lord I pray for..........Jesu....

Cikin muryar bacci Yana qara tora kansa cikin pillow yace,


Mum pls I hate this...


Miqewa tayi bayan tagama tareda 'duqawa ta shafi fuskarsa bayan ta janye pillon cikeda kulawa tace,


Nik can pls promise me you'll......


Katseta yayi cikin qosawa yace,


Yes I promise I will.


Thank you sweetheart'''' tace tareda miqewa tafice tana murmushi.


'dakin Davina tanufa Kai tsaye daganan.


Kwance take tana bacci itama Amma ki'da ke tashi a hankali cikin 'dakin sbd ita Bata iya bacci Saida kida qaidarta ne.


Tada ita tayi itama kafin tafito ta tsaya Saida masu aiki suka jera komai na breakfast 'dinsu Nik idan sun tashi kafin takalli Finn dake shirye Yana jiranta suka wuce office.

WANNNAN KENAN.


Mamuh💋

_Dont forget to follow,vote and comments_ _@mamuhgee_..*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒

       _Mi amor-mi vida_....


_viawattpad@mamuhgee_

           *2*

Yauma a sanyaye ta iso makarantar sbd duk jinta take a takure badan tana tsananin son karatunba da batajin zata iya cigaba da zuwa sbd wannan new site 'din yafi qarfin abinda qwaqwalwarta zata iya 'dauka.

+

Lectures biyu tayi yau Dan haka da wuri tagama Tana fitowa hall ta fiddo niqaf 'dinta ta rufe kyakkyawar fuskarta sbd kallo dayayi mata yawa Wanda tasan bai wuce na suturartaba sbd har ja hijabinta keyi.

Sauri takeyi ta tafi gida duk da niqaf 'din data saka kanta a qasa yake bazaka ta6a cewa sauri takeyiba sbd cikin nutsuwa take tafiyar kaman yanda addini ya koyar.


Tsayawa tayi cak tareda juyowa ahankali sbd sunanta dataji ankira daga bayanta.


Ajiyar zuciya tasaki sbd ganin wata ayshar ce ake Kira ba itaba.


Juyawa tayi zata wuce batareda sanin isowa mutumba sukai wani irin karon dayasa wayar hannunsa da car keys 'dinsa zubewa qasa.


Ya salam'' tafada ahankali cikin sauri tareda ja da baya jikinta na matuqar rawa sbd jikinsu daya 'dan ha'du Wanda wannan shine karo na farko da jikinta ya ta6a ha'duwa da jikin wani 'da namiji.


Tsayawa kallonta yayi sbd ganin yanda jikinta ke tsananin rawa abin dayafi basa takaici ma kenan,


Samanta zawa qasanta ya kalla cikin qyanqyamin shigarta sannan shibaiji baqin cikin ha'duwar jikinsuba shida yakeda komai na rayuwa musamman kyawunsa dake fuzgar mata Sai itace da fuskarta ke rufe qilama nakasasshiyace shiyasa ta rufe fuskar.


Dafasa abokinsa Murphy yayi bayan ya 'dauko Masa kayansa dasuka zube Yana cewa,


Let's go Nik we're getting more late..


Wucewa yayi tareda qara juyowa ya kalleta yana 6ata fuska.


Hawayen datake dannewa ne suka gangaro mata ta 'dago Kai ahankali takalli inda sukabi dai dai yakuma juyowa manyan idanuwansu suka ha'du da juna.


Atare gabansu ya Fadi yayi saurin 'dauke Kai sbd tsoro da idanuwanta suka bashi danshi mutum ne Mai tsoron mutane sbd bai cikason ko kallon wasu mutanen ba.


Ita ma cikeda tsoro ta juya jikinta na tsananta rawa ta fice tabar makarantar.


Harta Isa gida nutsuwarta bata gama daidaita.


A qofar farko ta ha'du da ya Umar gabanta yakuma yankewa ya Fadi sbd ganin Yana qureta da kallo tai saurin tattaro nutsuwa tareda qaqalo murmushi cikin sanyin murya tace,


Ya Umar ina yini?


Cikin Jin da'di da tsananin qaunarta ya amsa tareda cewa,


Ayshah da gani kin 'debo gajiya ko?


Eh'''tace tana sauke Kai qasa.


Bata hanya yayi ta wuce batareda yakuma wat maganarba.


A 'dakin umminta ta yada zango ta cire hijab 'dinta tareda sakin ajiyar zuciya ahankali.


Washe gari jiki a sanyaye ta shirya ta nufi makarantar duk da yau ya Umar da kansa ya rakota har bus stop tashiga mota.

Tunda suka shiga first lecture 'dinsu taga tamuqar ba tattaro nutsuwa tayiba to bazata fahimci komaiba shiyasa ta 'dan nutsu ta karanto addua tareda maida hankali saigashi tana fahimtar komai.

Sai four suka fito a gajiye take sosai ga yunwa datakeji sbd Sam basa cin abinci a waje komai rintsi shiyasa ko ruwan makarantar Bata ta6a siya tashaba.1


STORY CONTINUES BELOW

Sam bazaka kalleta kace yunwa takejiba sbd acikin nutsuwarta take tafiya.

Saukowa take daga sama Dan hall din dasukai lectures yau a sama yake.


Wasu samari ta hango qasa a tsaye suna sheqa dariya suna nunota

Tasan da ita suke Dan idan da sabo yakamata ace tasaba da tsokanarsu Dan kullum idan zata fita Sai sun tsokaneta suna kiranta da ninja lady Wanda sunan tuni yafara binda acikin makarantar Dan gabaki 'daya yanxu ba Wanda yasan fuskarta sbd kullum rufe fuskarta take cikin niqaf,,

Ba kalar mummunar halittar daba'a kiranta da ita sbd kawai ta cire niqaf 'din aga fuskarta Amma Sam ta danne duk da sau tari idan an mata tana Jin zafi harda hawaye musamman idan matane sukai mata.

1

Ihu suka 'dauka suna Kiran,


Here comes our ninja lady..hahhhhhhh


Sunkuyar da Kai tayi tacigaba da saukowarta sbd Bata ta6a kulasuba.


'daya daga cikinsu mace taci ado ta matse cikin qananun Kaya kamarba musulma ba ta 'daga musu hannu tareda miqewa tsaye cikin 'daga murya tace,


Yau dai Kam dole muga fuskar ninja lady sbd bamusaniba Koda aljana muke tare,,wat do you say guys????


Ihu suka 'dauka cikin shewa suna cewa,,


Yesss ohhhh..


Cak ta tsaya gabanta na tsananta fa'duwa ganin yarinyar ta nufota ana mata kirari gurin na da'da 'daukar ihu sbd kowa dakeson ganin fuskarta ta.


Ayshah mutumce Mai tsananin tsoro da rashin qwarin zuciya sbd Sam batada kuzarin dazata iya qwatar kanta Sai kawai tafara hawaye ahankali tareda rintse idonta tadan ja baya daidai lokacinda yarinyar takai hannu zata bu'de mata niqaf taja baya ka'dan cikin rashin sa'a Ashe takai bakin qarfen stairs 'din ta fa'da.


A tsorace kowa gurin ya 'dau ihu..


Sanye yake cikin wasu tsadaddun designers qananun Kaya blue jins da blue shirt datayiwa farar fatarsa kyau bazaka kallesa kallo 'daya kace christian ne ba sbd yamafi Kama da akirasa bafulatani sbd komai nasa Mai kyawu ne.,


Shigowarsa kenan tareda amininsa nako yaushe Murphy.,Sai Davina dasuka ha'du yanxu cikin school 'din ta maqale Masa wai wani lecturer 'dinsu ya hanata shiga lectures yau shine suka shigo department 'din yayiwa lecturer 'din magana sbd baya tsoron kowane lecturer shi duk da shima student ne Yana final year 'dinsa...Amma ba ruwansa duk Wanda yatakasa takashi yake sbd gata da sakewa daya samu daga uwarsa.

Ba zato yaji saukar mutum akansa saigasu sun zube qasa atare..


Holy Christ...yace da qarfi daidai itama tace,


Ya salam''''..


Da sauri Murphy da Davina sukayo kansa ya miqe Yana yarfa cikin tsananin azaba yace,


Oh God she broke hand..


Wat'''''Davina tafada tana yamutsa fuska.

Zafi yakeji sosai Nan danan student 'yan neman fada suka 'dauko kujera aka zaunar dashi Sambatu yake sbd jiyake baitaba Jin azaba irin wannan ba duk da ba wani ciwo bane.


Mum Davina takira tana 'dauka tace,


Hello my little princess,,,,,


Mum your Nik meet wit an accident his hand and leg got sprained....


Wat,,,, where and how?


One stupid ninja lady fell on him,her face was covered she probably doesn't see where she was going so......


Take him to hospital now  I will be there soon.


Kamasa sukayi zasu fice ya juyo cikin azaba yacewa murphy hand her  to school authorities she did it on purpose.

'dagowa tayi idanuwanta sunyi jajir sbd kuka Dan tunda tafado takasa tashi sbd qafarta da hannunta sun bugu matuqa Amma ba'a ganiba zaa miqata ga hukumar makaranta sbd tafadowa 'dan gata.


Hannu ta zura cikin niqaf dinta ta share hawayenta tareda dafawa ta miqe tabi securities dasukazo tafiya da ita.

Sai gaf da magriba ta iso gida sbd tajima kafin subarta tatafi dukda sun mata  gargadi Mai kyau akan karta Kuma ko lallon hanyarda Nik yabi bare takuma karyasa Dan mum 'dinsa tace next time aka qara bazata yarda ba.

Kodata dawo gida hankalin 'yan gidan tashi yayi dasuka ganta tana 'dingisawa..


Karo na farko data fara qarya arayuwarta kenan Dan cewa tayi 'dan adaidaita ya fa'di da ita.


Zazzafan zazza6i tayi tareda 'yar qaramar jinyar qafarta Dan satinta kusan 'daya rabonta da school Sai yau dazataje.


Sam yanxu tadaina Jin da'din makarantar Kuma takasa fadawa kowa sbd kada ahanata Dan tana matuqar qaunar karatun.

Asanyaye take shiri harsaida husna ta lura tace,


Ayshah lafiyarki kuwa?

Kodai jikin ne?


Safarta ta jawo tana sawa cikin muryar karaya tace,


Lafiya qlau kawaidai inajin kasalar zuwane.


Daria husna tayi tana saka hijab 'dinta tace,


Kodai kin gaji da karatun ne so kike ku zarge keda ya Umar''''ta qarasa zancen cikin tsokana.

Murmushi ayshan tayi tareda tuno fuskan ya Umar,,

Tabbas tana qaunar ya Umar halinsa ne bataso na rashin haquri da zafin zuciya Dan da'ace komai zai rage da tafi sha'awar auren nasu yanxu sbd ta huta da karatun Dan tuni yafara fita ranta sbd jikinta na Bata ba alkhairi  a karatun Nan gaba.


Kwana goma ya share ko cup 'din ruwa  baya iya 'dagawa da hannun duk da Dr ya tabbatarda ba wata karaya 'yar bugewace Amma sun 'dauki ciwon wani irin babba Dan mum har hutu ta 'dauka Dan kula dashi kawai ko dad 'dinsu Saida yazo yadubasa Yakoma Germany and yanda suka 'dau ciwon wani babba.


Koda ya warke Yafara zuwa makaranta Sam hankalinsa bai wani kwantaba sbd ayyanawa ransa da yayi Sam ita ba mutum bace aljana ce shiyasa ko mace Mai hijab ya gani koba niqaf Sai ha'diye yawu

Yanxu ko bakin gate baya iya zuwa Saida Murphy sbd tsoron karya ganta.


Yau suna fitowa lectures din farko ta fito ta nufi ladies toilet 'dinsu sbd period take tanason canza pad Dan ita Sam Bata iya wuce two hours da pad ajiki Bata canzaba.


Restaurant ta nufa danta siyo ruwan dazatayi amfani dashi.


Ku'di ta miqa aka miqo mata ruwan tajuyo kenan yakawo kowannensu cak ya tsaya cikeda tsoron 'dan uwansa yanda jikinta ya'dau rawa haka shima nasa Murphy yayi saurin riqesa tafara takowa ahankali jikinta na tsananta rawa zata bar gun sbd tarigada ta tabbatarda ganinsa ba alherineba.


Ganin ta nufo gurinsu yayi saurin sakin Murphy cikin tsoro da qarfi yace,,


Ghost,,,,

Ghost, ghost...


Aikuwa bashi kadaiba duka sauran mutanen gurin da gudu aka watse Sai ihu ake wasu harsuna fa'duwa.

1

Tsayawa tayi cak tareda duqawa ta fashewa da wani irin siririn kuka jikinta na sakewa.


Murphy dake tsaye shika'dai ne bai guduba Nan take yaji tabasa tausayi ya tako ahankali ya tsaya akanta cikin tausaya mata yace,


Ki daina kuka Kuma karkiji haushinsu sbd basusan Mai suke taredashiba acikin lullu6inki.


Miqewa tsaye tayi tareda ra6ashi ta wuce kukanta na tsananta.

Mamuh💋


_dont forget to vote, follow and comments_*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒

       _Mi amor-mi vida_....


_viawattpad@mamuhgee_

           *3&4*

Toilet tashige da hanzari tareda rufowa tasaki wani sabon kuka ahankali,


Gabaki 'daya rayuwarta a makarantar ta zamar mata masifa Wanda take danganta hakan da qaddararta.


Rarrashin kanta tayi daqyar kafin ta zare niqaf dinta ahankali takalli fuskarta jikin mudubi taga baiwa ta kyau da tsarin halitta da Allah yayi mata rashin sani yasa ana mata 'daukar mummunar halitta.+


Share hawayenta tayi tareda maida niqaf dinta tafito tawucewarta gida gabaki 'daya batareda ta tsaya attending sauran lectures 'dinta ba.

Da daddare bayan sunci abinci itada su husna tareda sauran yaran gidan suka nufi babban palon baba malam gurin 'daukar karatun dare Wanda qaidar gidance kullum da dare saisun 'dau karatu.


Awa 'daya da rabi sukayi sunayi kafin aka gama.


Gyara Zama baba malam  yayi tareda gyaran murya 

Nan kowa ya nutsu sbd sauraron Mai zai fa'da.


Kallon sauran dattijawan qannensa yayi kafin yace,


Mustapha 'dana ne Kuma  ya 'dauko zance Mai girma Don kuwa ya take akidar gidan Nan daya tarar tun kakanni tunma kafin ni mahaifinsa a haifeni..

Ma'ana dai bayan mun tsayarda maganar ha'dashi aure da yar uwarsa jininsa ya tsallake waje yana neman auren wani yaren ma'ana bahaushiya.


Wani yawu iya lami ta ha'diye Dan kuwa tasan mummunan hukunci 'danta zai fuskanta Dan anta6a irin haka can baya abun baiyi kyau ba sbd Saida aka rasa rayuka.

Tsit palon yayi babu Wanda ya motsa sbd jinjina girman laifin da mustaphan yayi.


Cigaba baba Mal yayi da fa'din,

Mustapha kaje kashirya gobe bayan sallar juma'a  za'a 'daura aurenka saudat a goben zaka koma gida nijar tareda matarka Kuma bamu yafe katako qafarka Nigeria ba kokuma Kiran 'daya daga cikinmu Sai bayan shekaru biyar.


Sunkuyar da kansa  yayi hawayen baqin ciki da damuwa suka ciko idanuwansa sbd hukuncin da iyayensa suka yanke Masa bazai iya jadasuba Wanda wannan tarbiyace da'aka ba zuriar gidan kaf tun suna yara.


Saudat kuwa wani irin kukane ya kufce mata ahankali batajiba Bata ganiba laifinsa ya shafeta bayan auren bazata an datse mata karatu gakuma nesa dazatai da gida bako waya har tsawon shekara biyar.


Jikin kowane yasaki Banda iyayensu maxa dake da'da nanata yi musu fadan kowa ya kiyaye aikata irin hakan,


Baba Mal ma fa'da Mai tsanani ya 'dora dashi sbd ran iyayensu ya 6aci matuqa.


Umma sakina kuwa Jan 'yarta tayi cikeda tausayawa suka fice kowama ya fice jiki a sanyaye.


Ayshah kuwa 'dakin ummi tashige ta kwanta jiki asanyaye tana tsiyayar hawayen tausayin saudat da yaya mustapha.


Kallo 'daya umminta tayi Mata ta 'dauke Kai sbd Bata cika kulata kasancewarta 'yar farin..


Cikin sanyi da karyewar murya tace,


Duk lokacinda Abu yasamu 'dan uwanka Mara kyau to kayi qoqarin nesanta kanka da abun Nan sbd gujewa mummunan sakamako irin wannan.


Zuciyata takasa nutsuwa da zuwa makarantar ki Dan haka ki guje afkawa cikin irin wannan mummunan halin.


Tsit tayi tana sauraron nasihar umminta duk datasan Sam ita bazata iya fadawa soyayya da wani yarenba bayan nata Dan itama gwargwado tana qyamatar wani yaren.

STORY CONTINUES BELOW

Washe gari ga murna ga baqin ciki Dan kuwa Banda iyayensu maza da sauran manyan mazajen gidan Babu Mai farin ciki musamman saudat data kwana tana kuka.

Koda zasu tafi bayan 'daurin auren daqyar aka 6an6areta daga jikin  umma sakina.


Ayshah kasa tsayawa tayi takoma 'daki ta lafe tana tsiyayar hawayen tausayin saudat Dan jitake idan itace bazata iya rayuwa ba iyayenta da 'yan uwantaba ko qin ji daga garesu.


Yau Monday kusan kowa nada lectures shiyasa makarantar take cike kowa Sai kaida kawo yake.


Lecture 'daya tayi 8 to 10 Kuma bazatai wataba Sai 2 shiyasa Kai tsaye ta fito ta nufi masallacin Mata na cikin school din ko karatun alqur'ani tayi kafin time 'din.

Tun safe mum 'dinsa ke rigima dashi akan yaje makaranta ya dage akan bazashiba sbd tsoron ninja lady.


Zama tayi bakin lafiyayyan gadonsa dayake dunqule cikin lallausan bargo ta kamo hannunsa

Ya zame hannunsa tareda 6ata fuska yace,


Mum please don't force me,I don't wanna go.


Never Nik,,I will never force you but please Christ sake don't leave your studies for some stupid crazy mask lady,, you're a man Nik so please act like one..


Kwantowa jikinta cikin sanyin murya yace,


I'm scared mum.


Murmushi Murphy dake tsaye tuni yayi yace,


Nik she's a normal human being just like you....


Hararsa mum tayi tareda 'daure fuska tace,


Not like him,

And I'm giving you 7days if she tries even coming closer to him talk to the pc make sure she leaves the school for good,

And you Nik get up and get ready I'm giving you 15 minutes to leave.

1

Tana gama fa'da ta Fice 'dakin Dan itama akwai zafi tana lalla6asa ne sbd tsananin sonda take Masa Amma Bata wasa da harkar karatun 'yayanta hardaishi Nik 'din daba karatun yakesoba sbd son jikinsa da rashin son wahala.


Wurgi yayi da pillow kamar wani qaramin yaro  yanajin kamar yayi kuka sbd har cikin ransa tsoranta yake.

Wanka yayi ya shirya yafito tsaf Sai qamshi yake ga wani shining da fatarsa take.

Saukowa yayi Yana 'daura wani tsadadden Rolex watch 'dins na diamond.


Davina ce kawai zaune a dining tana breakfast taci ado cikin wata tsinananniyar gown iya cinya black saita da'da fiddo hasken fatarta gata dama kyakkyawa kamar Nik din.


Ko kallo dining 'din bai ishesaba ya fice sbd haushin ansashi tafiya makaranta dole

Da hanzari Murphy ya aje tea 'din dayake Sha yabi bayansa.


Tunda suka shiga makarantar yake dube dube gabansa na fa'duwa.


Murmushi Murphy yayi Yana mamakin halayya irinta Nik sbd komai nasa kamar mace yake yinsa Dan qila ko Davina dake mace Kuma qanwarsa tafisa juriya da qarfin zuciya.

Daqyar yaga sun fito first lecture dinsu suka nufi restaurant sbd yunwa yakeji.


Harsun kusa isa ya dakata Yana tuno abinda yafaru last time dasuka zo.


Kallon Murphy yayi tareda nuna restaurant din da ido yace,


Buy everything and Meet me in the car.


Daria Murphy yasaki kafin ya wuce sbd ganin duk Nik din a firgice yake.

Cikin nutsuwarta take tafiya kamar ko yaushe kanta a qasa gurin lectures zata koma Dan Time yayi.


Saurin ja da baya tayi sbd karo datayi da mutum.


Ajiyar zuciya tasaki ahankali sbd ganin macece tayi karo da ita ba namiji ba.


Da sanyin muryarta tace,


Sorry..


'Dif gurin sukayi sbd yau shine karo na farko da wani yaji muryarta a makarantar.,

Zaqi da sanyi tareda laushin muryar yasa kowa qara kwa'daituwa dason ganin fuskarta musamman ma zeey(zeey is back)😜  Wadda tafi kowa takura da tsangwama Mata ko a wancen karon itace sanadin fadowarta stairs harta fadawa 'dan hutu.


Kallonta zeey tayi tareda sakin wani shu'umin murmushi tace,


Yaudai Kam dole muga abinda ke lullu6e cikin niqaf 'din Nan Dan jikina nabani kilama aljana ce muke tareda ita.


Danne niqaf dinta tayi ta ra6ata zata wuce taji ta riqo hannunta tareda dawo da ita baya da qarfi.


Wani qaramin flask taga ta bu'de ba zata ta watso Mata ruwan ciki da qarfi saitin fuskarta tayi saurin juyarda fuskarta gefe daidai da kawowarsa gurin ba zato yaji saukar ruwan zafi a qirjinsa..


Da gudu suka bar gurin shukuma want azababben ihu yasaki tareda sakin wayoyinsa

Da sauri ta juya Dan ganin wanda aka qona shima 'dagowa yayi Dan ganin wanda ya qonasa sunayin four eyes kawai saiya yanke jiki ya Fadi a sume.


Mamuh💋


_dont forget to follow, vote and comments_*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒

       _Mi amor-mi vida_....


_viawattpad@mamuhgee_

           *5&6*


Mummunar fa'duwa gabanta yayi ganin wanda abin ya sama juyawa tayi da sauri tabar gurin sbd Murphy dayayi  mata alamar  ta ta tafi,


Cikin tashin hankali da fargabar masifar mum ya kinkimesa Sai asibiti.

+

Koda su mum suka iso asibiti Banda tashin hankali babu abinda take ciki sbd Murphy cemata yayi coffee mai zafi Nik 'din yaje Sha ya zube Masa.


Koda Dr yafito yayi musu bayanin ba wata qonewa bace dan da alama ruwan basuda wani mugun zafi kawaidai yaji tsorone dakuma qila rashin sabo.


Fita mum tayi Dan Kiran waya hakama Finn bayanta yabi Davina kuwa kujerar 'dakin ta zauna tana chatting tana taunar chewing gum 'dinta.


Kallonta Murphy yayi lokacinda Nik 'din ya farka yaga hankalinta nakan wayarta ya maido kallonsa kan Nik murya qasa qasa yace,


Ninja lady....


Manyan fararen idanuwansa ya ware cikin tsoro,,

Murphy yayi saurin dafesa yace,


Easy Mama's boy,she's not hia but she'll soon be if you tell your mum that she is responsible for this.


Kallon wat do you mean yayi Masa,


Yace,

Yes bcox your mum won't let it go in vain so she's probably coming to take her revange and who knows h....


A tsorace ya katseshi da cewa,

No no no no i won't tell my mum and you too won't tell her anything...


Murmushi Murphy yasaki ganin ya ku6utarda ninja lady cikin sauqi sbd yasan duk mum taji the poor girl will lose everything.

Koda mum takuma tambayarsa akan qonewar yawu ya ha'diye tareda tuno abinda Murphy yafada saiya shagwa6e Mata batareda yabata amsa ba.

Aiki ja yasamesu Dan kuwa jinya ake ba sauki 'dan lele ya qone qiri qiri akasa Dr treatment 'din dole sbd dai shi baiga wata qonuwa ba Amma tunda Mama's boy ya lafe yace yanajin zafi agurin hakanan ake jinyar harkusan sati biyu a asibitin kafin suka dawo gida nanma wata sabuwar kulawar ta tashi masu aikin gidan basuda hutu Sai hidima suke.

Koda yaji sauqi qara lafewa yayi Dan karyaje makaranta mum ta takurasa saiyaje sbd duk son 'yayanta bata wasa da karatunsu.
Shika'dai yau yazo makarantar sbd Murphy na gurin wani program.


Zaune yake kan motarsa bayan ya fito lectures

sanye yakeda black dress da black speck Sai kyau da hasken fatarsa suka qara fitowa sbd duhun kayansa.


Waya yakeda dad 'dinsu saiga wasu friends 'dinsu  dake shige Masa Amma shi Sam bai cika son mu'amala dasuba sbd sun cika neman Mata Dan ko acikin mota suna iya having sex da Mata Sam basuda class ko agurin za6ar matan shikuma mutum ne Mai son Abu Mai kyau tsaftatacce danshi qyamarma wasu matan yake shiyasa bai cika wani shiri dasuba.


Datse Kiran yayi Yana kallon 'daya daga cikinsu Mai suna Josh.


Murmushi Josh 'din yayi tareda Hawa tasa motar ya zauna yace,


Unbelievable Niklaus Aiden...

How could you let yourself get embarrassed by letting people know you're scared of some stupid mask lady afterall you're a man..

Kallonsa yayi da fararen idanuwansa ya lumshesu batareda yace komai ba sbd shima Sam bada son ransaba yake tsoronta gashi yanxu zancen yafara ya'duwa acikin makarantar.


STORY CONTINUES BELOW

Matsowa Josh yayi daf fuskarsa yace,

Let's do one,, let's get rid of this problem..

How?

Yace Yana Danna wayarsa.

Let's scare her....

Meaning?'''''yakuma fa'da Yana kallon fuskar Josh 'din.

Kashe Masa ido 'daya yayi Yana murmushi.

Shiru yayi Yana nazarin shawarar Josh 'din sbd zuciyarsa tayi na'am da zancen.

Murmushi yasaki tareda dirowa motarsa yashige Yana cewa,

I will see you guys tomorrow.


Washe da hadari sosai aka tashi shiyasa jiki ba qwari ta shirya ta wuce makarantar.

Tana Isa makaranta ruwan ya 6arke masu qarfi Nan kowa yafara gudu Dan fakewa.

Fixgota taji anyi tareda jefata cikin mota akabar makarantar a guje da ita batareda kowa ya luraba sbd qarfin ruwan.

Babban filin qwallo ne daya ha'du,

Tsakiyar filin yake zaune kan kujera sauran abokanansu biyu na tsaye riqeda umbrella sun Kare Masa ruwa.

Three quarter jins ne a jikinsa da boot Sai wata jibgegiyar rigar sanyi Mai laushi da hula.

Tsakiyar gurin motarsu ta tsaya suka bu'de tareda jefota inda yake zaune gabansa.

Qanqame jikinta tayi tareda sakin kukan tausayi da fargabar masifar dake gabanta ga ruwan saima tsananta qarfi suke.

Fa'duwa gabansa yayi ya miqe tsaye tareda juya musu baya Dan har lokacin akwai sauran tsoranta a ransa.

Zagayeta su Josh sukayi suna qyakyata dariya.

Rintse idanuwanta tayi tareda qanqame jikinta tana sake sakin Wani sabon kukan.

Niqaf 'dinta Josh ya fixgo tareda wurgi dashi tayi saurin duqar da kanta tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskar.

Hijab 'dinta yakuma fixgowa da qarfi Saida ya 6arke tundaga sama har qasa.

Doguwar rigar wani red shaking material ne ajikinta ruwan dake dukanta yasa tuni ya lafe ya kwanta ko ina a jikinta.

Wani yawu dukkaninsu suka ha'de sbd wata irin kyakkyawar surar fuxgar hankali dasuka gani.

Hannu Josh yakai zai janye hannuwanta don ganin fuskarta sbd shi tuni yagama kwa'daituwa Dan idanuwansa harsun fara wani Jan kwa'dayinta.

Caraf yaji anriqe hannunsa da qarfa.

Dagowa yayi sukai ido hu'du da Murphy.

Murmushi yasaki yace,

What is the rush Murphy?

We're all gonna enjoy so let me go first.

Turesa Murphy yayi da qarfi

Jin sunan Murphy yasa Nik juyowa ahankali idanuwansa Basu sauka ko inaba Sai kanta

Gabansa yayi mummunar fa'duwa...,

Fuskarta soke take tsakinin qafafuwanta babu Wanda yaga fuskarta Sai kyakkyawar farar fatarta da surarta data bayyana.

Kuka take sosai Amma ba'anjin qarar kukan sbd qarar ruwan saman dake sauka Dan dukkaninsu akansu ruwan ke sauka idan kacire shi shida baya shiga ruwan sama Dan yanxun ne zai kwanta ciwo.

Qura Mata ido yayi Yana kallon yanda jikinta ke girgixawa sbd sheshekar kukan datakeyi,,

Duk qarar ruwan saman masu qarfi dasuka hana kowa Jin kukanta shi tsaf yake Jin sautin kukan na shiga kunnuwansa suna amsa amo.

Cak ya qame agurin dukan zuciyarsa na tsananta.

Hijab 'dinta Murphy ya 'dauka ya yafa Mata

'dagowa tayi akaro na farko ta takallesa da manyan idanuwanta dasukai jajir.

Bugawa gabansa yayi da qarfi yaja Baya da qarfi Yana kallon fuskarta.

Dukkaninsu ja da baya sukayi cikin tsoro sbd ganin Murphy ya tsorata da ganin fuskarta sbd dukkaninsu babu Wanda yagani Dan baya ta Basu.

Rintse idanuwanta tayi hawayen ciki suka gangaro takuma kallonsa.

Niqaf 'dinta ya wawuro ya miqa Mata sbd shi kansa bayason yacigaba da kallon wannan kyakkyawar fuskar da baita6a ganin irinta ba Dan zai iya zaucewa.

Kar6a tayi tasaka tareda gyara zaman 6arkaken hijab 'dinta tabar gurin tana tsiyayar hawayen baqin ciki.

A tsorace suke kallon Murphy Dan son yafada musu abinda yagani a fuskarta daya tsoratashi.

Dahar zai fa'da musu saiya fasa ya kalli Nik da ke tsaye kamar andasashi sbd har lokacin kukanta na amsa kuwa a kunnuwansa zuwa zuciyarsa.
1

Mamuh💋
_Dont forget to follow, vote and comments_.*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒

       _Mi amor-mi vida_....


_viawattpad@mamuhgee_

           *7&8*


Harta Isa iga ruwa ake sosai shiya Hana aga 6arkewar hijabinta da jajayen idanuwanta.


Shigewa 'daki tayi ta dunqule da jiqaqun kayan tasaki wani sabon kukan.+


Wasa wasa saigata da zazza6i ciwo kwance rigis sbd kukan datake yawan yi batareda anluraba.

Jinya tayi tsawon kwanaki kotaji alamar sauqi saita lafe sbd Sam batako qaunar taji ankira sunan makaranta bare hartayi sha'awar zuwa

Babu abinda tafi buqata yanxu kamar ace antsaida ranar aurenta da ya Umar anyi ta huta.
*********

Kwance yake cikin lallausan bargon gadonsa idanuwansa a lumshe Yana sauraron Murphy dake Masa fa'da akan abinda ya yarda su Josh suyiwa ninja lady.

Sautin kukan tane yadawo Masa ya cikin kunnuwa ya lumshe idanu tareda qara shigewa cikin bargo.

Kwana biyu mum 'dinsa tarasa gane kansa sbd son jikinsa ya da'du dan kullum daga makaranta Sai gida yazo ya kwanta ya lumshe idanu.

Kwana 'daya kwana biyu har sati batazo makaranta son ganinta yake sbd kullum Murphy bayada zance Sai nata shiyasa yanxu yakeson yaganta yayi Mata kallon mintuna sbd kawai ya cire tsoronsa akanta.


Yau kwana goma rabonta  da makaranta dole tashirya zuwa sbd yawan tambayarta da ya Umar keyi akan rashin son zuwanta makaranta yanxu.

Tsaf tashirya cikin dogon hijab 'dinta maroon da niqaf dinta harma da safarta ta hannu da qafa kamar kullum.


Tunda tafito gida take addua harta Isa makarantar.


Sosai takuma Kama kanta sbd fahimta datayi komai zai iya faruwa matuqar batayiwa kanta babbar katanga da duk wata hanyarda Nik yabi ba.


Cikin ikon Allah hankalinta ya 'dan kwanta sbd kusan sati biyu kenan Basu ha'duba acikin makarantar Nan tasawa ranta Allah ne ya kar6i adduarta yayi Mata tsari dashi.


Sun fara exam shiyasa Bata cika Zama cikin mutane ba saidai taje can baya inda Babu mutane ta zauna tayi karatu kokuma ta zauna tana nazarin rayuwarta a makarantar.

Yau zaune take baya gurin wasu ciyayi dasuka kwanta luf iskar ni'ima na  ka'dowa ahankali tana ratsata.


Ba karatu takeba kawai zaune take tareda lumshe idanu tayi zurfi cikin tunanin rigimar dasukayi jiya da ya Umar akan shima nijar yakeson komawa bayan aurensu itakuma Sam bazata iya rabuwa da iyaye da sauran 'yan uwantab dukda Sam Bata iya ko 'dagowa tayi Masa dogon kallo bare harta iya musa masa saidai tashige 'daki tayita hawayenta.


Zaune yake shima agurin ammashi Saida aka kafa Masa 'yar rumfa sbd iskar tayi Masa  yawa sbd Sam ko ka'dan  jikinsa bayason sanyi sosai Dan Nan take ne zai fara mura ko zazza6i.

Tare sukeda Murphy Amma yaje ya dubo Davina data kirasu yanxu wai gatanan tareda police cikin school 'din sbd glass 'din motarta da'aka fasa aka 'dauke Mata purse da laptop aciki.

Shika'dai ya rage zaune agurin fuskarsa sanye da black goggles daya qara  fiddo haske,kyau,hutu tareda wayewarsa a fili.


Wayarsa yake ta6abawa kamar daga sama yaji Abu na tafiya a kafa'darsa ya zabura da sauri ya Duba...


Zaro idanuwa yayi cikin wani masifaffen tsoro da tashin hankali yayi wurgi da wayoyinsa duka tareda qwalla qara Yana cewa,

Mu..mu..mummmm scorpion,, scorpion,,help help help me,,mummmm

Dummm gabanta yabuga ta bu'de idanuwanta da sauri tareda miqewa sbd itama ba laifi akwaita da shegen tsoro...


Juyowa tayi da sauri zata bar gurin Ashe inda yake ta nufa saigata gabansa turus.


Tsayawa tayi tareda juyawa da sauri cikin tsoro sbd ganin kyakkyawar farar halittar qirjinsa a bayyane Dan tuni ya cire rigarsa yayi wurgi Sai ihu yake Yana qoqarin zare wan.....


Cikinta yayi tareda cukuikuyeta Yana ihu bakin Rai Yana Kiran scorpion..


Tsoro da tashin hankali yasa tafara qoqarin qwacewa Amma ba qaramar cukuikuyewa yayi mataba ba zato Sai gasu a qasa gaba 'daya Kuma har lokacin ihu yake sosai Dan duk ya yage kyakkyawar farar fatarsa sbd tsoro gashi yaqi sakinta.


Turesa tahauyi tana kuka ahankali Dan ita tsoron biyu ya kasar Mata gana scorpion 'din dayake Kira ga nasa.

Idonta ne ya sauka kan wuyansa taga gizo gizo irin Mai kaurin Nan Yana tafiya saman fatarsa...


Hannunta ta 'daga ahankali takai kan wuyansa ta 'dauko gizogizon tareda kai hannunta saitin fuskarsa ahankali cikin sanyin murya  tace,


Look it is not a scorpion,,it's a spider...


Cikin wani irin yanayi ya 'dago sbd mummunan dukan da muryarta tayiwa zuciyarsa da gangar jikinsa taredayin rugu rugu da tsoron dayakeji Nan take.


Fuskarta ya kalla har lokacin a rufe take ya maida kallonsa kan tafin  hannunta data ware tana nuna Masa spidern dake cikin hannun nata.,,


Kyakkyawar farar fatar hannunta fara tas ya qurawa ido gabansa nacigaba da fa'duwa sbd wannan shine karo na farko data cire Safar hannunta acikin makarantar,, Zara zaran fararen yatsun hannun nata dasukaji Jan lalle Mai matuqar tsari ya qurawa ido zuciyoyinsu na bugawa kusan atare....


Ahankali yafara 'daga hannunsa yakai fuskarta zai yaye niqaf dinta batareda ta hanasaba ta rintse ido hawaye suka gangaro tana jiran taji ya yaye niqaf 'din......

Wat da heck Nik''''''sukaji Davina tafa'da da qarfi sbd yanayin dasuka samesu Shiba Riga ajikinsa hakama kwance a qasa Yana maqale da ita.

A zabure ta turesa tareda miqewa tsaye shima miqewa yayi jiki a sake Yana kallon wainda ke tsaye akansu.,,


Davina, Murphy tareda police 'din case 'din motar Davina da wasu friends 'dinsu kusan su shida.


Dukkaninsu kallon Nik 'din suke cikeda mamaki da tuhuma musamman ma Murphy da tuni yaji zuciyarsa tafara quna.

Juyawa tayi jiki a mace kamar munafuka zatabar gurin cikin takaici Davina Tasha gabanta tareda kallonta a wulaqance tace,


Arrest her officers for trying to take advantage of my brother's inno.....


Stop Davina'''''' murphy yafada cikin Jin zafin abinda take fa'da.

Ayshah kuwa cikin tashin hankali takalli Davina da police din Jin tozarci da qazafin daza'ai Mata Dan kawai a lalata Mata suna.


Ido cike taf da hawaye ta juyo gefen Nik takallesa

Ya juyar da Kai tareda juyawa yabasu baya Dan har lokacin bai gama dawowa nutsuwarsaba ta yanayin dasuka kasance tareda ita.

Lumshe idanu tayi wasu zafafan hawaye suka gangaro Mata ganin yanda yajuya baya maimakon ya fa'di gskiar abinda yafaru.

Cikin tsawa Davina takalli officers 'din tace,


I said take her away.

Hannu police 'daya yakai zai kamo hijabinta yaja yaji anriqe hannunsa.


Dukkaninsu kallon mamaki sukabi Nik dashi ganin shine yariqe hannun police din ransa amatuqar 6ace.

Mamuh💋
_dont forget to follow, vote and comments_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒

       _Mi amor-mi vida_....

_viawattpad@mamuhgee_


           *9&10*

Cikin rashin tsiwa ta matso gabansa tace,


Wat do you think you're doing Nik?


Kallon police 'din yayi da alamar kubar gurin da sauri suka bar gurin ya juyo ya kalleta yace,


Yes I mean she's not going anywhere and......


A hasale tace,


Wat?

are you crazy?

You must be out of your mind right?

I mean wat a are you thinkin......


Shut up Davina''''''' yafa'da cikin qosawa da zancenta sbd zuwa time 'din zazza6i da ciwon jiki yakeji sosai na 'yar wahalarda yayi akan spider 'din.


Juyawa yayi zai bar gurin Amma wani irin jiri da azabar ra'dadin da fatarsa ke Masa yasashi yanke jiki ya fa'di a sume.1


A ki'dime sukayo kansa Davina tuni ta 'daga waya takira mum ta sanarda ita Aiko a gigice tabar office tayo asibiti.


Kinkimarsa sukayi sukabar gurin dashi Davina na jifanta da wani mugun qyamataccen kallo Dan tayi alqawarin na'da Mata mugun tarkon dabazata iya fitaba.


Zubewa gurin jiki a mace hawaye na tsiyayo Mata zuciyarta na wani irin nauyi,

Daqyar ta miqe tabar gurin jikinta a sake.


Kodata koma gida saita kasa samun sukuni ta zare hijab 'dinta zata ninke taji wani Abu Mai 'dan nauyi a hijab 'dinta.


'dagawa tayi taduba gabanta yayi mummunar sarawa sbd ganin agogo maqale a hijab 'din

Tabbas koba'a fa'da mataba tasan na Nik ne..


Zarosa tayi jikin hijabin takalla saiga hawaye sun gangaro Mata ta zauna bakin gado tareda rintse idanu tana Jin zafi cikin zuciyarta.

Asibiti kuwa sunga tashin hankali Dan kuwa qaramar haukace kawai mum batayiba ganin jikin Nik duk a yakushe abinka da farin mutum da fatarda Bata Saba da wahala ba tuni yayi jajir har wata fa'dawa yayi cikin qanqanin lokaci.


Cikin sati 'daya ya warke sbd kyakkyawar kulawa da tattalin dayake samu hakama dad 'dinsu tuni yazo sbd yanda suka zuzuta ciwon.

Sauri take ta qarasa gida sbd yamma datayi ga yunwa da gajiyar data kwaso a makaranta.,


Ya salam''  tafa'da ahankali tareda saurin Jada baya sakamakon wata ha'daddiyar jeeb tareda motar police datasha gabanta.


Yawu ta ha'diye da qyar idonta na kawo ruwa ganin Davina ce janye da jeeb din tareda 'yan sanda.


Glass ta sauke takalli officer mace cikin police 'din tace,


Arrest her she's the one.


Girgixa Kai tayi tareda ja baya Amma haka matar tajawota da qarfi ta tura motarsu sukai station da ita.


Suna Isa Kai tsaye aka bu'de file 'din qarar wai ta fasa motar Davina tayi Mata sata hakama tayi amfani da akaifa duk da yayyake jikin Nik.


Ba kunya ba tsoron Allah police suka filen case 'din ahaka

Banda kuka babu abinda takeyi hartana shaqewa.


Address 'din gidansu tabayar sukaje suka sanar dasu cikin qanqanin lokaci saigasu ya Umar da baba alhaji.


Tana ganinsu tasaki wani sabon kuka tana qara tausawa kanta da zuriarta sbd wannan shine zuwansu police station na farko atarihin rayuwar gidan Sai gashi akanta anfara.


Kai tsaye sukace basu yarda da wannan zancenba Dan kuwa sunsan halin ayshah babu yanda zaai su yarda da wannan qazafin.


Money and power Mss queen tayi amfani dasu ta Hana a tsaya a saurari su baba alhaji qarshema turata cell akayi aka rufe

Kuka Babu kalar Wanda batayiba

Gidansu ma gabaki 'daya suna cikin tashin hankali Dan iya zafi sun 'dauka matuqa akan wannan zalinci da toxarci da akai musu.


Kwananta 'daya a cell 'din ciwo ya rufeta ala dole aka saka Umar maimakonta itakuma akai asibiti da ita.


Kwananta biyu taji sauqi suka zo suka Kuma tafiya da ita.


Tunda suka iso police 'din take kuka wannan karon gaba 'daya su harda baba malam da abbanta da baba alhaji sukazo taredasu Yaya abbakar.


Isowar mss queen tareda Finn da Davina yasa dukkaninsu miqewa suna kallonta cikin qyanqyami musamman ma iyayensu dasukafi Jin zafi ganinma Ashe kafiraine wainda suka yiwa ayshah wannan mugun wulaqancin.


Wani kallo tabisu baba Mal dashi kafin tashige office 'din officer incharge tabarsu tsaye kafin shima baba Mal yashiga daga baya.


Alamari dai baiyi kyauba sbd kaca kaca akayi a office 'din hardasu fa'da dansu Yaya abbakar taruwa sukayi sukaiwa Finn duka Suma Nan police suka hau dukansu kan kace me gurin ya ida hargitsewa Saida akaida gaske aka shiga tsakani.

Kwance yake a Palo Yana hutawa Dan har lokacin qarfinsa bai gama dawowaba duk da dai tunanine wannan karon yafi hanasa qarfafa jikinsa.


Three-quarter blue jeans ne a jikinsa da farar designer shirts qal,


Fatarsa tayi kyau hutu ya da'da bayyana ajikinsa sbd tun ranarda aka sallamosa ko gate 'din gidan bai ta6a fitaba Yana lafe kullum ana lilinsa.

Shigowa Murphy yayi cikin yanayi na damuwa ya kalli Nik yafara Koro masa bayanin halinda ake ciki.


Cikin wani irin yanayi zancen ke shiyarsa  ya aje cup 'din milkshake dake hannunsa ya miqe tareda kallon Murphy yace,


Take me to the station...


Gudu Murphy yayi cikin mintuna qalilian suka iso station 'din daidai lokacinda Davina ta 'daga handbag 'dinta Mai qarfe ajiki zata qwalawa ayshah cikin zafin nama ya janyeta ta fa'do jikinsa cikin rashin sa'a niqaf dinta ya zame ya fa'di qasa.


Wani wahallalen numfashi yasaki kunnuwansa da idanuwansa sukai 'dif numfashinta dake fita da sauri kawai yakeji.


Fixgosa ya Umar yayi da qarfi tareda sakar Masa wani wahallalen Marin dayasa hancinsa 6arewa da jini tayi saurin rintse idanuwanta wani nauyi na na sauka zuciyarta.


Ihu mum tasaki tareda shararawa Umar wani gigitaccen Marin itama.


Zaburowa su abbakar sukai aka damqesu tareda turasu cell shikuma mum da Murphy sukaja hannunsa zuwa mota Dan kaisa asibiti Dan hancinsa dake jini

Shikuwa duk baimasan sunayiba idanuwansa na kanta ko qiftawa bayayi

Itakuwa kanta na qasa takasa 'dagowa Dan jikinta yabata idonsa har lokacin na kanta.


A asibiti bayan anyi treating 'dinsa sun dawo gida kwantawa yayi kamar Mai bacci tareda dunqulewa cikin bargo bugun zuciyarsa na tsananta.


Daqyar da biyan ku'din suka samu aka sakosu abbakar suka dawo gida zuciyoyinsu duk a qone da tsananin 6acin Rai da baqin ciki ace wai su rasa abin arxikin dazasuyi fa'da dashi Sai kafirai.


Fa'da da nasiha Kam ayshah tashasu harta gaji.,


Sati 'daya kenan da faruwar alamarin kullum tana 'daki kwance lamo ko doguwar magana batason yi Dan ita tuni tacire Rai da batun komawa makaranta Dan tasan yanada wuya abarta takoma.


Zaune take da safe tana a 'dakinsu tana karanta wani hadisi su husnah nata Shirin tafiya makaranta.


Nuratu ce tashigo cikin uniform 'din makarantarsu takalleta tace,


Anty ayshah ya Umar nakira.


Lumshe idanu tayi tareda rufe hadisin ta miqe tsaye tasaka dogon hijabinta ta nufi 'dakin mama sakina Dan tasan yanacan.


Kallo 'daya yayi Mata ya 'dauke Kai sbd duk ya kalleta yanxu tunowa yakeda fixgowarda wannan shegen Christian  yayi Mata ta fa'da jikinsa saiyaji zuciyarsa na tafasa Dan duk ranar dayakuma ganin wannan gayen ko a hanyane saiya cire Masa hannun daya ta6a Masa aysharsa dashi.


Gaishesa tayi a ladafce taredayin qasa dakai tana sauraron abinda zai fa'da.


Cikin danne baqin cikinsa yace,


Ki shirya kici gabada zuwa makaranta munyi mgn dasu baba sbd bazakibar karatunki kan wasu kafiran banxaba.


Lumshe ido tayi sbd yanda hakanan zancensa ya daki zuciyarta ahankali tace,.  To tareda ficewa tabar 'dakin.Mamuh💋


_dont forget to follow, vote and comments_*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒

       _Mi amor-mi vida_....


_viawattpad@mamuhgee_

           *11&12*

A sanyaye ta shirya tanajin fargaba da tsoron sake ha'duwarta da Nik a makaranta.


Kodata fito nasiha da da'da su baba Mal da babanta suka sake yimata akan kwata kwata ko hanyar da wainnan kafiran sukabi karta kalla bare tayi sha'awar bi.

Tunda suka iso ta fito bus taji hankalinta ya ninka tashi ta rintse idanuwanta ta karanto addua tareda gyara zaman niqaf dinta ta nufi hanyar lecture hall 'dinsu cikin nutsuwa da sanyi.


Cikin ikon Allah har lokacin dawowanta gida Bata ha'du da matsalarta,,,,sunandata saka Masa kenan.


One day,,,two days,,,,three,, four,,, five har one week ko maikama dashi Bata Kuma ganiba shiyasa hankalinta ya 'dan kwanta sbd Sam Bata qaunar sake ganinsa kodan gudun faruwar abinda take gudun ya faru..


+

Yau Kam gabaki 'daya jikinta a sanyaye take jinsa shiyasa

Daqyar tasamu taga sun fito first lecture dinsu tafito Kai tsaye ta nufi hanyar mosque Dan Sai after two hours zasu shiga wata lecture 'din.

Saukowa stairs take cikin nutsuwa kanta a qasa sbd hango su zeey datayi  duk da dai tasaba da tsokanarsu da cin zarafinsu.


Wucesu tazoyi zeey tayi saurin Shan gabanta tana dariya tace,


Ninja lady bazaki fa'da Mana  yaya  zaman police station yake?


Dariya sauran suka sheqe da ita suna cewa,


The officers mst be very scary to see what's behind the niqaf...


Cika idanuwanta sukaida hawaye ta ra6asu zata wuce idonta ya sauka cikin nasa Yana tsare yayi folding hannuwansa Yana kallon duk abinda ke faruwa da alama bai Jima da isowa gudinba.


Cak ta tsaya hawayen datake riqewa suka gangaro Mata Wanda shika'dai ne yaga gangarowarsu daga idonta sbd niqaf 'dinta Amma qurewar kallonsa akanta yasa yaga hawayen.


Lumshe fararen lazy eyes dinsa yayi sbd Jin wani mugun zafi a zuciyarsa yayi saurin dafewa tareda kallon saitin zuciyarsa.


Cikeda tsoro da mamaki ya 'dago saiyaga Bata gurin da sauri Yakoma mota tareda rufewa ya kunna AC Yana sauke numfashi.


Murphy kuwa matsowa yayi gaban guys din yakallesu cikin 'daure fuska yace,


This should be the last ok... because the next time I see you guys making any troubles...hmm it won't be good...so careful guys.

Juyawa yayi yabarsu suna binsa da kallo zuciyoyinsu cikeda haushinsa Dan ganin suke ina ruwansa dasu afterall sune musulmai 'yan uwanta bashi dayake Christan ba.


Ido 'daya mujahid ya kashewa shafii Yana murmushin mugunta.


Dariyar Jin da'din shafii yasaki sbd gano Mai mujahid 'din ke nufi.


Wucewa sukai suna fiton Jin dadi Dan sukadai sukasan abinda suke Shirin qullawa.


Kodata Isa gida yau ta tu6e tayi wanka tareda sallah taci abinci yini tayi

Karatun alqur'ani sbd zuciyarta datakejinta cikin yanayi na damuwa.
Kwance yake bakin pool 'din cikin gidansu cikin rumfar dake gurin Dan hutawa,

dagashi Sai three-quarter farar fatarsa Sai glowing take sbd hutu,

Idanuwansa a rufe suke Banda tunani Babu abinda yake.


Mum 'dinsa dake tsaye bayansa nesa dashi tana kallonsa cikin damuwa ta 'daga waya takira Murphy tace tanason ganinsa now now.

Tana tsaye gurin harya shigo gidan ya iso gurinta tareda gaidata.


STORY CONTINUES BELOW

Bata amsa gaisuwarda yake mataba ta nuna Masa inda Nik ke kwance da ido cikin damuwa tace,


For the past few days he's been acting so weird and it's killing me...


Juyowa tayi ta fuskanceshi tace,


Can you please tell me what is happening,,,...I asked him so many times he said he don't know wat his problem is...


Kallonsa Murphy yayi kafin ya juyo ya kalli mum 'din yace,


I don't know anything mum but......


Katsesa tayi da fa'din,


I want to know wat his problem is by tomorrow so go and make sure you know it all.


Juyawa tayi tabar gurin shikuma ya doshi Nik 'din cikeda tunani kala kala aransa.

Zama yayi kusada Nik din tareda 'daukar cup 'din ruwan dake gabansa yasha kafin ya 'dan juyo ya kalli Nik 'din da still idanuwansa ke lumshe cikin sauke nannauyan numfashi yace,


Wat is it this time Nik?....you seems so serious...


Batareda ya bu'de idanuwansa ba yasaki ajiyar zuciya ahankali cikin cool voice yace,


I want to take her out of my head Murphy but I can't...


I can't sleep,eat..even thinking of anything without her crossing my thoughts....


She's in my thoughts,,,in my dreams,,,,.... she's in me all day..


Bu'de idanuwansa yayi dasukai wani laushi kaman maijin bacci sbd rashin sanin taqamaimai matsalarsa ya tashi zaune tareda facing Murphy murya a karye yace,,


Murphy do you think she's angry...I mean do you think she's taking her revange by making my life miserable by all these thoughts...


Cikin sanyin jiki murya a sanyaye Murphy yace,


No Nik...i think it's all because you are inlove..


Wat....Nik yafada da qarfi zuciyarsa na bugawa da sauri..


Rintse idanuwa Murphy yayi cikin wani yanayin sanyin jiki yace,


Yes Nik..you love her.


No Murphy it can't be true..I mean yes I feel relaxed and happy wen ever I remember her Even in the mask...

Her beauty...her touch and.....


Katseta Murphy yayi da fa'din,


This is called love Nik..love at first sight..


Miqewa yayi tareda kallon sama ya rintse idanuwansa iska na ratsashi ahankali yafara tunano ranar ha'duwarsu ta farko da duk sauran abubuwan dasuka biyo baya..ranar da yafara ganin fuskarta batareda niqaf ba a station yayi tareda tuno yanayin dayaji lokacin da idanuwansu suka ha'du..


Tsit yayi zuciyarsa na kar6ar baqon yanayin dayake shigarsa..


Nitsa'di yaji Yana shigarsa cikin wani irin yanayi ahankali yacewa kansa,,

Could that be really love?


Ba kansa amsa yayi da cewa,

Yes Niklaus Aiden you are really in love..


Mum 'dinsa ya hango tafe ta nufo gurinsu da hanzari ya nufeta ya riqo hannuwanta biyu yace,


Mum am in....


Dont..if you tell your mum she will kill her for this....


Atare mum da Nik suka juyo  cikin  mamaki suka kalli murphy Jin abinda yake fa'da Sai suka ganshi da waya a kunne alamar wayace yake ya qara juya musu baya saiyaci gaba da fa'din,


Yes.. think about it again before splitting it out.


Ajiyar zuciya mum tasaki  cikin mamakin yanda yau Murphy ke waya Yana 'daga murya..


Shikuwa shiru yayi cikin nazari Dan ya fahimci dashi Murphy yake Babu wata waya.,

Tabbas yasan idan mum tasani yanxu she won't hesitate or think twice before harming the poor ayshah and considering wat he is feeling right now about her he can't let anyone harm even one hair of h...


Katsesa mum tayi ta hanyar dafasa tana cewa,


Yes sweetie you're saying something..


Riqo hannuwanta biyu yayi tareda kwantarda kansa saman kafa'darta duk da yafita tsawo kasancewarta bamai tsawo sosaiba for the first time dazai fara 6oye Mata abu yace,


No mum,,I just wanted to thank you for calling Murphy Cox he made me realize something very important.. just relax mum am fine now.


Rungumesa tayi cikin Jin dadi tace,

I love you Nik..


I love you too mum...yafada Yana lumshe fararen idanuwansa sbd fuskar ayshah data fa'do Masa.
Mamuh💋


_dont forget to follow, vote and comments_*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒

       _Mi amor-mi vida_....


_viawattpad@mamuhgee_

           *13&14*


Da daddare kasa bacci yayi sbd wani irin azaba da tiririn son ganinta da zuciyarsa keyi ya sake lafewa cikin lallausan bargonsa tareda lumshe ido ahankali cikin sanyin murya yace,


I love this feeling,,,and I love you my ninja lady...


Daqyar bacci ya'dan fusgesa Amma 7 daidai ya farka tareda saukowa gado yafa'da toilet yayo wanka yazo gaban mirror kaman mace yafara shiri cikin farin ciki Yana waqar _little more (royalty)ta Chris brown_.

Riqeda 'dan qaramin Bible mum 'dinsa tashigo 'dakin don yi Masa addua kaman yanda tasaba every morning saita tsaya turus tana kallonsa cikin mamaki idanuwanta waje sbd arayuwarta bazata iya tuna Rana 'daya dazatace Nik yatashiba da sassafe haka Koda kuwa exams zaiyi.

+

Gabansa ta matso ta tsaya tana kallon yanda yashirya yayi wani masifar kyau cikin wasu classy designer Kaya dark blue dasuka matuqar fidda haskensa da kyawunsa.

Baki tasake tana kallonsa Ya rungumota jikinsa cikin farin ciki yace,


Gud morning my love...


Morning sweetheart''''tace tana Masa kallon tambaya.


Sharewa yayi ya miqa Mata hannunsa tareda nuna Mata agogonsa na white gold dake aje gaban mirror da ido alamar tasaka Masa.


Aje Bible 'din tayi ta dauki agogon tana 'daura Masa  tace,


My boy are you going somewhere im.....


Shihhhh mum,,don't ask am just going to school and pls mum don't ask anything now,,I will tell you everything when I get back... okay?


Ok''''tace ahankali tareda kissing forehead 'dinsa bayan ya 'dan durquso sbd bazata Kai goshinsa ba.

Tareda mum 'din suka sauko hannunsa na riqeda nata.


Finn dake zaune Yana aiki da laptop ga Kuma cup din hot tea ahannunsa Yana kur6awa ya 'dago yayi musu kallo 'daya yaciba gaba da aikinsa Yana cewa,


Gud morning mum..


Amsa Masa tayi tareda juyawa ta kalli Davina data fito bedroom 'dinta cikin kayan bacci ta kalli Nik sama zuwa qasa kafin ta kalli mum 'din tace,


Mum is he alright...I mean are you taking him to hospital..coz I think that is the only thing that will make Nik wake up this early..

Cikin murmushin Jin dadi mum tace,


No my princess,,he is absolutely fine,, my boy is a grown up man now and he's starting to act like one,,, right my boy?


Yes mum''yafada Yana hararar Davina dake Masa dariya Dan tasan da yanxu za'aga Koda kyankyaso a palon to yanxu zai koma kamar qaramin yaro duk ya hargitse gidan...


Grown up man indeed....tafada tana Zama a kujerar dining don yunwa ma ita takeji.

Har mota mum tarakasa tadawo tana murnar 'danta yafara Zama serious kamar kowane 'da.

Yau Kam tundata tashi jikinta ke mace ahakadai tashirya tanufi makarantar.


Very late ta Isa shiyasa kodata Isa lecturer dake cikin hall 'din ya hanata shiga jiki a sanyaye ta dawo ta nemi guri ta zauna tana jiran yagama yafito sushiga next lecture dinsu.

Tunda yasako kan motarsa hanyar department dinsu idonsa akanta yafara sauka sbd wautarsa saiya saki sitarin motar Yana qure kallonsa akanta...


Murphy dayaga da gaske Nik din yake ya manta da driving yake yayi saurin riqe sitarin tareda dukansa a kafada qara yasaki ahankali tareda saurin riqe sitarin yayi parking jiki na rawa zai fita yaje gurinta Murphy ya riqesa tareda ya kallesa cikin sanyin jiki yace,


STORY CONTINUES BELOW

Easy Mama's boy because if you go acting like this she will definitely get scared and run.

Dawo da bayansa yayi ya jingina jikin seat ahankali yace,


Yes You're right.. but how do you think I should...

Apologies...

You'll have to apologise to her first before anything..

Kallonta yakuma yi batareda ya dauke idonsa akanta ba yace,


Murphy do you think she will say yes if I confess my love to her.?

A darare yabashi amsa da cewa,


She won't say yes so easy..


A tsorace yace,


No Murphy she'll have to accept me...help me..


Katsesa yayi da cewa,


No Nik this is your battle that you'll have to fight alone.,,

Be patient,,be strong,,be truthful,, and be a man..

There is a cheos coming so prepare yourself to be strong to fight for your true love..and please don't make me regret this one day.

Yana gama fadar haka ya bu'de motar ya fita ya nufeta Kai tsaye yabar Nik da jiki a sanyaye Dan zancen Murphy 'din tsorasa yayi Amma Kuma yanda yakejin soyayyarta a jininsa zai iya fuskantar koma meyene zaizo.

A Dan tsorace ta 'dago Amma ganin Murphy saitaji tsoranta ya ragu ta sunkuyar dakai batareda tace Masa qalaba.

Zama yayi kusada ita batareda ya kalleta ba yace,


Ayshah.....


Dam gabanta yabuga sbd Bata ta6a tunanin yasan sunantaba.


Cigaba yayi da cewa,


Ayshah inason abokina sosai sbd shine sanadin danake cikin rufin asiri nida mamana da qannena harma nake karatu sbd shine yake biyamana komai.

Cikeda tsoro da mamakin Jin hausa ra'dam a bakinsa ta 'dago ta kallesa batareda tabude baki tayi magana ba.

Murmushi yayi kafin yacigaba da cewa,


Ayshah akwai abinda nakamu da tsananin so tun farkon ganina da abin Amma yau an wayi gari Nik na tsananin son abin fiyeda tunaninsa wandashi bai gama gano hakanba..

Saidai nayiwa kaina alqawarin bar Masa abinnan natafiyata..


Kallonsa tayi cikin mamakin yanda yake fa'da Mata abinda bai shafeta.

Miqewa yayi tareda juyowa ya kalleta yace,


Goodbye ayshah duk da nasan destiny will bring us together again.

Wucewa yayi tabisa da kallo akaro na farko dataji kamar wani alamari nashirin faruwa da ita saidai abinda batasaniba Mai da'dine ko Mara da'di.


Harya 6ace Mata Bata daina kallonsa ba kamar daga sama saitaji antoshe Mata baki da qyalle an 'dauketa tareda turata cikin mota akabar makarantar da ita.

Fitowa yayi mota jiki a sanyaye saiyaga wayam Bata gurin yana 'daga Kai saiga fitar motarsu mujahid makarantar da mugun gudu.

Komawa motarsa yayi yabi bayansu a guje kaman zai tashi sama da motar.

Hanyar wajen gari suka nufa batareda sun lurada Yana biyeda suba suka gangara cikin dajin ka'dan saiga wani qaramin flat Mai kyau sukayi parking suka fito Shahid ne riqeda ita har lokacin bakinta a toshe niqaf dinta ma tuni yacire acikin motar Wanda tuni kyakkyawar fuskarta ta qara rura mugun nufinsu gareta.

Fixgo mujahid yayi tareda 'daga hannu ya sharara Masa Mari yayi baya Yana yarfe hannu tareda sakin qaramar qara sbd xafin da hannunsa yaji alhalin shiyayi Marin Dan baita6a duka ko marin wani ba bare yaji zafi haka.

STORY CONTINUES BELOW

Daria suka sheqe da ita suna kallon yanda yake yarfe hannu Shahid yakallesa a 'dage yace,


You see Mama's boy you can't do anything like a man so stop acting like  child and leave.


Hasala yayi ya qara 'daga hannu zai Mari Shahid mujahid yariqe Masa hannu tareda sharara Masa wani lafiyayyan Marin dayasashi qwalla qara tareda zubewa qasa yana riqe kumatunsa.

Kallonsa tayi tareda rintse idanuwanta hawayenta naci gabada gangarowa sbd tasanda bayada wani qarfinda zai taimaketa.

Ganin hawayenta yasashi miqewa cikin 'yar jarumta ya Sha gabansu yazamto ita tana bayansa yakallesu da idonsa dasukai jajir sbd azaba yace,


If you don't want to end your lives behind bars let us go.


Wata dariyar suka Kuma sheqewa da ita kafin mujahid yafara rufesa da duka Nan take hancinsa da goshinsa yafara jini gashi ko ka'dan baida kuzarin ramawa.

Lilis sukai Masa suka koma yimasa dariya ganin so yake yatashi yakasa.


Ahankali sautin kukanta yafara fita ta juya Masa baya tafara rero kukanta.

Duqowa Shahid yayi yakalli yanda yake Nishi yace,


Stop being stubborn and leave quickly okay lover boy.


Miqewa yayi a daddafe hannunsa riqeda gefen cikinsa dake ciwo sosai ya nufi motarsa.


Saurin juyowa tayi zuciyarta na karyewa ganin tafiya zaiyi ya barta dasu mujahid 'din.


Kallonta yayi yaji duk jikinsa yayi sanyi sbd tun yanxu yafara gane bai cancancetaba tunda har yakasa samun qarfin ku6utarda ita.

Motarsa ya shiga daqyar ya iya Zama ya tada ita yayi ribas ahankali.


Saiti yayi dasu ya taho a guje yayo kansu a gigice sukabar gurin yadaki motarsu yayi saurin fitowa tareda bu'de Mata seat din gaba ganin tatsaya kallonsa ya'daga hannunsa yakamo nata yasakata cikin motar sukabar gurin da gudu.


Tunda yakamo hannunta shi take kallo ko qyaftawa Bata iyayi..


Did he take all this risks to save me from them..


Daf dazasu Isa cikin gari taga ahankali yafara rage gudu saikuma ya gangara ya tsaya tareda zubewa jikin sitirin motar a sume.


A gigice takallesa takalli waje taga hadari ya ha'du sosai har anfara yayyafi alamun saukowar ruwan.

Fitowa motar tayi hankalinta duk atashe saikuma ga ruwan sama sun 6arke masu qarfi sosai.


Bata damu da qarfin ruwanba ta tsaya bakin titi neman taimako Amma Sam Babu alamar mota bare tasaran samun taimako ga ruwan tuni sunyi Mata jagaf.


Dawowa motar tayi taga shima kusan duk ya jiqe sbd glass 'din dake sauke.


Wata muguwar rawar sanyi taga jikinsa nayi sbd ruwan dasuka dakesa Nan take wahala ta canxashi taga yanda ruwan ke dukansa Yana Jan numfashin wahala gashi Sam takasa iya tada glass 'din motar Sai kawai ta fito tazagayo bakin windon dayake ta tsaya ta tare Masa ruwan  na dukanta jikinta na rawar sanyi amma bazata iya bari ruwan yaci gaba da dukansa ba.

Kusan awa 'daya da rabi ana ruwan kafin suka tsagaita zuwa time 'din daqyar take iya bu'de idonta sbd sanyi da mugun zazza6i Mai qarfi.

Bu'de idanuwansa yayi daqyar ya kalleta yaji wata muguwar zazzafar soyayyarta na sake shigarsa ahankali ya tashi zaune jikinsa na rawar sanyi ya fito tareda kamota daidai lokacinda take qoqarin zubewa yasaka cikin mota tareda kwantarda ita ya tayar da glass ya kunna 'dumi.


Ahankali ya 'daga wayarsa yakira wayar Murphy akashe kafin yakira mum 'dinsa yafada Mata inda yake murya na rawa.


Fuskantar juna sukai ya qura Mata ido Yana qoqarin yaqar tsananin ciwo da zazzan zazza6in dayakeji.


Rintse idanuwanta tayi sbd Bata iya cigaba da kallonsa ko jure nasa kallon.

Ahankali ya bu'de baki cikin qaramin sauti yace,


I love you ayeeshah.


Bu'de idanuwanta tayi da sauri hawaye na taruwa acikinsu...


Kafin yakuma yunqurin wata maganar  aka qwanqwasa glass din motar.


Shiyayi qarfin halin 'dagowa yaga wani mutum da wata tsohuwar bus ya juyo ya kalleta yaga idanuwanta a rufe hawaye na tsiyayo da qarfi.


Cikin sanyin murya ya kalli mutumin yace,


Awuce da ita cikin gari.


'dagowa tayi takallesa ya lumshe Mata idanu ta bu'de motar ahankali ta Fice jikinta a sanyaye  zuciyarta na tsananta duka tashiga bus din suka wuce..


Harsun fara tafiya tajuyo takalli motarsa saita rintse idanu wasu sabin hawaye masu zafi suka gangaro mata.
Mamuh💋


_dont forget to follow, vote and comments_*_MAMUH GEEE_*_*TAURA BIYU....*_🍒

          _Mi amor-mi vida...._


_Viawattpad@mamuhgee_


              *15&16*

Kodasu mum suka iso gurin ya Dade da fita haytacinsa Dan dama Yana daurewane gaban ayshah sbd kar abin kunyar yayi Masa yawa anyi Masa duka gabanta Kuma ya ciwo yayi Masa rigis gabanta.


Hankali tashe mum tasa akai asibiti dashi bayan ankira police sun fara bincike agurin Dan ga alamar duka Nan ajikin 'dan nata.

Kodata Isa gida kasa tu6ewa tayi ta shige qarshen gado ta zauna tareda takurewa tana kuka ahankali sbd zazzafan baqon alamarin dataji yana shiga tareda Kama kowace kusurwar jijiyar dake aiki cikin zuciyarta.

Zazza6i ne Mai qarfi itama yakamata Nan take Wanda yasa hankalinsu husna tashi Amma ta hanasu fadawa iyayensu.


+

Kwananta 'daya da yini tana fama da zazza6i da rashin sukunin zuciya.


Gudun zargi da tambaya yasa tashirya tacigaba da zuwa makaranta.

Koda ya farfado kansa ciwo yake sosai Amma haka ya nunawa mum 'dinsa yaji sauqi dole aka sallamesu duk da mura yake sosai sbd dukan da  ruwa sukai Masa.


Lumshe ido yayi Yana tunano ko awane Hali ayshah take ita data fisa Shan dukan ruwan.

A daddafe yayi kwana biyu agidan mum na jinyarsa a kwana na ukun ya shirya yace yaji sauqi makaranta zashi.


Kallon mamaki mum tayi Masa tace,


Sweetheart you're not fully recovered... you're still weak.,,I can see it in your eyes.

Atishawa Mai qarfi yayi tareda saka farin lallausan handkerchief ya tare hancinsa kafin ya 'dago ya kalleta da lazy eyes dinsa yace,


Mum I'm fine.,,I promise.


Cikin kulawa da yar damuwa tace,


Ok my sweet boy,,but please take care..


Yes mum,,,,yace tareda 'daukar wayarsa da key 'din sabuwar motarsa ya sauko ya fice batareda ya tsaya bawa Davina amsar Murphy datake tambayarsa ba Dan shima nemansa yake Amma haryanzu wayarsa Bata zuwa.

Duk inda yake sakaran zai ganta ya Duba bai gantaba Nan take yaji jikinsa yafarayin sanyi..


Tunda yafara nemanta tagansa tayi saurin 6oyewa bayan wata mota tana kallonsa zuciyarta a sanyaye Amma hakanan taji dadin ganinsa yaji sauqi duk da dai tana iya ganin baida wani kuzari.

Tundaga ranar tafara 6oye Masa duk da baqaramin tirsasa zuciyarta takeba gurin aikata hakan.

Tun mum 'dinsa na 'daukar abin wasa saigata hankalinta yayi mugun tashi sbd wata irin damuwa da muguwar Rama data sako Nik 'din agaba sbd rashin ganin ayshar gashi yakasa samun ko wane information akanta.


Sam shida kansa baisan son da yake Mata yakai hakaba Sai yanzu..


Iya bincike da lallashi mum tayi Masa yafa'da Mata damuwarsa Amma yaqi.

Yau tun 6 na safe yatafi makarantar kosu mum basusan da fitarsaba..


Bakin bus stop ya Parker motarsa zuciyarsa sanyaya da damuwar dayake ciki game da ita Dan yau jiyake kozai kwana ya yini agurin saiya ganta zai iya samun sukunin masifar da zuciyarsa take ciki.

Ahankali bacci ya 'daukesa sbd rashin baccin dayake fama dashi na kwanakin.


A kunne yabar motar sbd Ac.

Sai 10 ta iso makarantar ana ajesu busstop ta fito ta nufi hanyarta cikin sanyin jiki sbd rashin kuzarin da itama take fama dashi.

Kamar daga sama ta hangosa kwance Yana bacci cikin motar yayi matuqar ramewa saitaji zuciyarta na neman karyewa tayi saurin juyawa tabar gurin.

Qarfe biyar na yamma ta gama lectures ta fito a galabaice sbd ranar azumi take..


Cak ta tsaya sakamakon ganin har lokacin Yana gurin saidai wannan time 'din yafito jingine yake jikin motarsa yayi wani irin fadawa sbd yunwa da wahala Amma yaqi tafiya.

Kamar ance ya juyo Sai kawai idonsa yashiga cikin nata yayi saurin miqewa tsaye daidai Yana kallonta amarairaice.


Dakewa tayi ta matso tareda ra6asa ta wuce tashige bus tareda sunkuyar da kanta Dan karma su hada ido.


Binta yayi da lazy eyes 'dinsa suna taruwa da ruwa sbd tunanin qila wani laifi yayi Mata.


Matsowa yayi da sauri zai shiga bus 'din cikin  tsautsayi yaron direban motar ya turesa sbd already motan yacika ya fa'di qasa cikin ruwan saman dake taruwa awurin Nan take kayansa da jikinsa ya lalace bai tsaya dubawaba ya miqe da sauri zaikuma matsowa aka tada motar sukabar gurin.

Motarsa yashiga da sauri yabi bayansu saigasu har anguwar su ayshah 'din.


Tana fitowa motar tagansa Yana qoqarin parking ya fito.


Saurin wucewa tayi batareda takuma kallon inda yakeba.


Biyota yayi da gudu batareda ya tsaya kashe motarsa ba..,,


Sauri ta qara gabanta na tsananta fa'duwa daf da zata shiga kwanar layinsu saiga ya Umar...


Wata mummunar fa'duwa gabanta yayi ta saci kallon bayanta taga Sai zubo sauri yake Dan ya iso wurinta ta rintse ido zuciyarta na tsinkewa da tausayinsa.

Kallonta ya Umar 'din yayi Yana son karanto firgicin daya gani tattare da ita.


Kamar ance ya Duba bayanta saiya hangosa Yana zubo sauri tareda tsalle Yana qoqarin fa'duwa sbd agwagi dasuka biyosa Sai tsalle yakeye Yana kallota karta 6ace Masa.


Kallonta Umar 'din yayi cikeda zargi kafin yayi Mata alamar ta wuce da ido.


Sum sum ta wuce Amma saita kasa shigewa konar ta juyo.

Manyan agwagin dasuka fi girma Umar ya 'dauka tareda jefa Masa cikin baqin ciki da takaicin ganinsa.


Baya yayi da sauri cikin tsoron agwagin cikin rashin sa'a Ashe yakai kwata sai gashi zaune cikinta.

Batareda 6ata lokaci ba ya yunquro yataso har lokacin idonsa nakan kwanar datake la6e tana kallonsa.


Qoqarin wucewa yake cikin takaici Umar ya fixgosa tareda wurgar dashi ya nunasa da yatsa cikin xafi yace,,


Zanbarka yau katafi Amma wlh duk nakuma ganin wannan kafirar fuskar taka cikin anguwar Nan saina yanka maka ita da kwalba..2


Juyawa yayi zai wuce tayi saurin barin gurin tayi gida da sauri zuciyarta na wani irin nauyi.

Mamuh💋


_dont forget to follow, vote and comments_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒

          _Mi amor-mi vida...._


_Viawattpad@mamuhgee_


              *17&18*


koda Nik Yakoma gida ya tsaya gaban mirror yakalli kansa saiyaji hawaye sun ciko idanuwansa..

Tubewa yayi ya jefo kayan qasa ta windown dakinsa ya fa'da toilet yayo wanka Banda zazza6in wuya Babu abinda yakeji.


A daddafe ya saka kayan bacci black yashige bargo ya kwanta jikinsa na rawar sanyin zazza6i..


Qarfe Tara mum tashigo dakinsa Finn na biyeda ita tana ganin yanda yake shaking cikin bargo ta qaraso da sauri tana Kiran sunan Jesus..


Tallafosa tayi taji jikinsa da mugun zafi ta kalli Finn cikin tashin hankali tace,


quickly call Dr Finn.+


Fiddo wayarsa yayi daga aljihu ya latsa Kiran Dr cikin gaggawa.


Shigewa yayi jikin mum 'dinsa yana fiddo numfashi ahankali cikin azaba yace,


Mum I'm fine,, it's just a fever,,I will get better soon there's no need to call the Dr....


Cikin karyewar murya kamar zatayi kuka tace,


Quite.. you're not fine my love and it's not a normal fever,, you're hiding something from me,,I  can feel it.


Lumshe idanuwa yayi cikin sanyin murya qasa qasa yace,


Mum,,,,mum..i.i..I'm in love....I love someone.


Wat""""tafa'da da qarfi tareda kallon fuskarsa cikin rashin Jin dadi tareda rashin na'am da zancen cikin damuwa tace,


You can't be in love my boy,, you're too young for that and I ca....


Katseta yayi cikin sanyin murya da cewa,


I love her so very much mum,,,I can't even imagine my life now without her mum...mum..I really want her for myself,i love her mum..I madly love h....


Rungumesa tayi cikin tausayinsa sbd dukkanin alamu sun nuna Mata baqaramin so yakewa kowaceceba..


Share Masa hawaye tayi tana adduar Allah yasa ko wacece kada tayi amfani da wannan zazzafar soyayyar da Nik yake Mata ta cutatar Mata da yaro.


Kwanansa biyu Yana zazza6i Mai zafi ko qasa baya iya saukowa bare ya fita,,

Mum dinsa kuwa hutu ta dauka Dan bawa 'dan lelenta kulawa hakama 'yan uwansa wannan karon dukkaninsu sun matuqar tausaya Masa sbd yayi matuqar sanyi kamar ba Nik ba danko irin muguwar sakuwar dayake acikin gidan ta rage kullum Yana kwance.


Duk iya yanda take danne damuwarta saidata bayyana a jikinta sbd ramar datayi su husna sunyi faman tambayar harsun gaji Amma alamarin bamai kar6uwa bane ko a zuciyarta bare  fa'duwa.


Kwananta biyu kotaje makaranta Bata gane komai sbd dukkanin nutsuwarta ta tarwatse Wanda Sam takasa samun kuzari ko qarfin tattarota.

Ahaka take lalla6awa har tsawon kwana biyu.


Yau Bata samu bus da wuri ba shiyasa tayi yammacin dawowa gida,,


Ahankali take tafiya cikin nutsuwa duk da kwanakin nutsuwarta rawa take,,


Daf dazata shiga kwanar layin gidansu taga su ya Umar taredasu Yaya abbakar kusan su shida kowanne da abun duka jikinsu har rawa yake bama Kamar ya Umar 'din da idanuwansa yafi nakowa rufewa da 6acin Rai.


Mummunar fa'duwa gabanta yayi tai saurin sunkuyar da Kai cikin tsananin fargaba..


Kallonta ya abbakar yayi cikin 'daga murya yace,


STORY CONTINUES BELOW

Meyasa kikai yamma sosai yau?


A sanyaye tace,


Bansamu bus bane yau da wuri.


Shikenan maza wuce gida.


Wucewa tayi a hankali gabanta na tsananta fa'duwa,,

kaman daga sama saitaji ya Umar cikin zafi Yana cewa,,


Duk inda yake Yana guraren Nan sbd da idona nagansa Yana tambayar yara Kuma na tabbatarda akwai abinda yake qullawa.


Cak ta tsaya sbd qafuwanta dasuka 'dau rawa..


Taji ya sani yace,


Wlh Nima yau nayi ido hu'du da shegen kafirin Nan saina karairaya Masa qafafuwa Dan ya koyi tsaya matsayinsa.


Yawu ta ha'diye da qarfi jikinta na rawa sbd fahimtar datayi kenan Nik nacikin layin,,Kuma ta tabbatarda ita yake nema....


Juyowa tayi takalli mugayen gororin dake hannunsu taji hankalinta yayi mummunan tashi Dan tasan duka 'daya za'ayiwa Nik da wannan bazai qara sanin inda kansa yakeba.


'daga kai tayi cikin bugawar zuciya Sai gasa ta hangosa kusada wata qaramar matsatsiyar kwana Yana tahowa..


Wani mumman yawun tashin hankali ta ha'diye tareda juyowa takalli su ya Umar taga ba 6angaren suke kallo ba Amma gaf sukeda juyowa..


Cikin wani irin zafin naman dabatasan tanadashiba tayi saurin Isa gabansa daidai ya Umar ya juyo kawai saita janyosa cikin kwanar da qarfi Saida ya fa'do jikinta.


Wani irin kallo yake Mata cikin Jin da'din ganinta qayataccen murmushi na fita a fuskarsa..


Ahankali takallesa qwayar idanuwansu ta ha'du tai qasa dakanta gabanta na fa'duwa cikin sanyi da laushin muryar tace,


Why are you doing this?


Yana kallon cikin idonta yace,


Because I love you..


Kalmar ta daketa matuqa ta rintse idanuwanta cikin sanyi tace,


It's impossible...so please stop following me...yo don't know wat trouble you're getting your self into..


Cikeda sonta daya rufe Masa ido yace,


I'm ready to face anything for your love..


Girgixa Masa Kai tayi idonta na gangaro da hawaye tace,


We can never be together can't you get it,,,,we are from a different rel....


Shihhhh yafa'da tareda matsota sosai Yana kallon idanuwanta da lazy eyes 'dinsa murya qasa yace,


I'm ready to be like you if that's will b the only way for me to get you..,to be with you...

I love you ayeeshah..


Stop please''''''tafada da 'dan qarfi kuka na qwace Mata..


Kaman zaiyi kuka shima murya na rawa yace,


I love you ayeeshah,,, even if I wanted to get it out of my head I can't...


Muryoyinsu ya abbakar taji suna kusanto gurin tayi saurin 'dagowa ta kallesa cikin kuka tace,


Please go from here,, leave please...


Gyara tsayuwa yayi Yana kallon hawayenta dake ta6a zuciyarsa yace,


I'm not leaving until you tell me why you are so worried like this...

and this tears???'''yafada Yana kallon yanda hawayen ke gangarowa..


Karkace Kai yayi cikin son tabbatarda abinda yake zargi murya na rawa yace,


Ayeeshah,,,do you have any feelings for me too???


Rintse ido tayi cikin qaguwa tace,,


No please go...


Jada baya yayi yace,


No I won't go anywhere...


Matsowa tayi cikin magiya da kuka tace,


They will beat you black and blue... please pls leave.


Kusantota yayi sosai har numfashinsu na ha'duwa Yana kallon cikin idanuwanta da lazy eyes 'dinsa dasuka cikada hawaye yace,


Idan har dukan dazasumin zaisa natabbatarda you love me too then so be it..


Zan jira suzo.


Kuka tasaki ahankali hartana ciccika Nan take jikinsa ya 'dau rawa cikin hawaye yace,


Am sorry my love,,,I know I'm being stubborn but I can't help it because *i love you*......


Kalmar data shiga kunnensu ya Umar kenan daidai lokacinda suka kawo gurin.

2

Mamuh💋


_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*_*TAURA BIYU....*_🍒

          _Mi amor-mi vida...._


_Viawattpad@mamuhgee_


              *19&20*


Zafin zuciya da bugawar zuciya ne suka mugun tasowa ya Umar ya rintse idanuwansa Dan Daman tuni ya fara zargin ayi hakan tun kallonda yaga Nik 'din yayi Mata a station lokacin....

Rufewa idanuwansa sukayi ya qarasa gurin zuciyarsa na tafasa bai tsaya komaiba ya 'daga qaqqarfan hannunsa ya shararawa Nik wani gigitaccen Mari saiga jini ya 6alle ta hancinsa...

Saukar wani mugun zafi  taji a zuciyarta tayi saurin rintse ido ta bu'de hawaye suka gangaro Mata ta 'dago a cikin karaya ta kallesa saitaga ko motsi yaqi yi ita ya qurawa lazy eyes 'dinsa dasukai ja sbd azabar Mari ko qyaftawa bayayi...

Fixgota taji anyi da qarfi ta 'dago jajayen you takalli ya Umar 'din ta bu'de baki zatayi magana  a zuciye ya mare bakin da qarfi...

Durqushewa tayi qasa cikin azaba Amma tabbas azabar da zuciyarta ke ciki taci wannan 'dan Marin..


'dagowa tayi idanuwan Nik suka sauka kan 'dan jinin daya fito gefen bakinta sbd Marin yayi saurin zubewa gabanta jikinsa na rawa hawaye na taruwa idonsa murya na rawa yace,


You're hurt ayeeshah....

Ya 'daga hannu ya nufi inda jinin yake.....


Cikin zafi ya Umar ya riqe hannun tareda mur'dewa su ya abbakar kuwa Nan suka rufesa da duka.

Rintse idanuwa tayi hawaye na tsiyaya akaro na farko dataji wata mummunar qiyayyar ya Umar tana shiga tareda Huda duk wasu jijiyoyin dake aiki acikin jinin ajikinta.

Miqewa tayi batareda tajuyoba takalli irin dukan dasuke Masa ta fara tafiya cikin damuwa tabar gurin.


'dakinsu ta nufa direct batareda ta leqa ko inaba ta gaida iyayensu kaman yanda tasaba.


Kodata shiga su husna basa 'dakin suna 6angaren mama sakina Dan can sukafi Zama a irin wannan time 'din..

Zubewa tayi bayan qofa tareda sakin wani irin  kuka ahankali tana dafe zuciyarta datakejin kaman xata tarwatse...

Hayaniyace ta kaure cikin gidan Nan take tani kowa na fitowa sbd hayaniyarsu ya Umar hardai shi da muryarsa tafi tashi cikin 6acin Rai...


Tanajin an ambaci kafiri ta lumshe idanuwa hawayenta na tsananta zuciyarta na da'da karyewa sbd batasan mummunan halinda suka sako Nik acikiba...

Da daddare bayan tayi sallah Bata tashi kan sallayarba anan ta qudundune sbd damuwa da zazza6in datakeji mai tsanani...


Nuratu ce tashigo 'dakin jiki a sanyaye ta zauna kusada ita takalleta murya asanyaye tace,


Anty ayshah su baba malam na Kira..


'dagowa tayi takalli nuratu da jajayen idanuwanta a sanyaye tace,


Sun kashesa ko nuratu?


Girgixa Kai nuratu tayi cikin tausayin 'yar uwarta tace,


Aa,,,,amma dai abun yayi Muni...


Kuka tasaki ahankali zuciyarta naci gabada tsananin zafi..


Anty ayshah da gaske soyayya kuke?


Batareda ta 'dagoba cikin kukan ta girgixa Kai...

Kafin ta miqe cikin sanyin jiki ta fito 'dakin ta nufi babban palon baba malam Dan tasan yanxu kowa nacan ya halarta..

Kanta a qasa tashiga tareda rakubewa ta zauna qasa..


So 'daya ta 'dago taga yanda kowa ke Mata kallon 6acin rai,qyama da tuhuma..tayi saurin qasa da kanta Tana danne hawayenta.

STORY CONTINUES BELOW

Cikin 'daurwar fuska da zafi baba alhaji yace,


Ayshah meye ha'dinki da wannan arnen.


Cikin sanyi da nutsuwa tace,


Babu komai..


A hasale babanta yace,


To meyasa ya biyoki yau harkuka ke6e?


Lumshe ido tayi ta bu'de sbd akaro na farko kenan dazatayi qarya murya a tausashe tace,


Nazo wucewa ne Sai muka ha'du shine yakeson tambayana nace bazan tsayaba.


Sake zaburowa baba alhaji yayi yace,


To su Umar sunce sun gani sonki shi yaron yakeyi.


Girgixa Kai tayi tace,


Ni banta6a sanin wannan ba hasalima yaza'ayima ta yiyu tsakanin ni dashi ba yare 'daya ba,

Ba addini 'daya ba..

Sai lokacin baba malam yayi gyaran murya sbd anxo gurinda yakeso Kuma yayi na'am da abinda ta fa'dan ya kalleta yace,


Ayshah???


Na'am'''tace a sanyaye batareda ta 'dagoba yace,


Na yarda dake nasan bazaki iya ta6a sa6a Mana ba ko take doka da umarnin mu Dan haka ga garga'di da umarni Mai qarfi,,,,daga yau ko hanyar dayabi karki Kuma kallo bare har wata magana ta hadaku harma afara Kuma irin wannan zargin Dan ni ko maganar wani kafiri banaso acikin zuri'ata bare har irin wannan mummunar zancen ya tabbata..

'dago Kai tayi ta kallesa tareda cewa,


To baba insha allah.

Miqewa tayi ta bar palon ahankali ya Umar yabita da kallon tuhuma danshi yana ganin abubuwa da dama datake 6oyewa Amma saiyasa ta bayyanasu da kanta agaban kowa na gidan.

Koda wasa dama batai gangancin tunanin bacci zaizo Mata ba hakanan ta kwana cikin tunanin wane Hali Nik yake ciki.

Koda gari ya waye taje gaida umminta saitaji duk jikinta ya da'da sanyi sbd ganin ga dukkan alamu ma umminta na cikin tunani da fargabar Kar zancen jiya ya tabbata.


Gaida ummin tayi cikin sanyi tareda kallon nuratu dake Mata kallon tausayi tana gaisheta.


Amsawa tayi tareda kallon ummi tace,


Ummi zan tafi makaranta..


Cikin kulawa da sanyin jiki ummin tace,


Ayshah Dan Allah karki bari zuciya takaiki ga Dana sani da muguwar rayuwa.


Hawaye taji sun taho Mata Dan tasan saidai Kuma wani ceto daga Allah Dan Mai Sha tarigada Tasha.


Zama tayi tareda kar6ar cup 'din kunun tsamiyar da ummin ke miqo Mata ta kar6a badan zata iya sha ba saidan kadata kuma bawa ummin damar wata damuwar.+


Abbanta ne yashigo tareda sallama ta sunkuyar dakai ta gaidasa cikin sanyin murya..


Amsawa yayi kadaran kadahan kafin ya zauna kan tabarmar kusada ummin Yana cewa,


Ki qara kiyayewa sbd gudun jawo fitina da tashin hankali tareda 6acin suna acikin zuriar gidan nan Dan yanxu ina amfanin irin hakan tunda shi yaron sun Masa mummunan duka sun barosa can kangon gidan bayan layi sbd......


Wata mummunar sarqewa tayi tafara tari Mai qarfi sbd gigitar da zancen baban yasata.


Saurin miqa Mata ruwa nuratu tayi tana Mata sannu..,

Baba da ummi kuwa kallo suka bita dashi fa'duwar gabansu na tsanantuwa .

Miqewa tayi ahankali tace,

Na tafi..


Allah tsare ummi tace a gajerance baba kuwa ko amsa Mata baisamu yiba sbd damuwa da fargaba.

STORY CONTINUES BELOW

Bakin titi ta tsaya cikin zurfin tunanin rashin sanin abin yi....


Kusan Rabin Rabin awa tashare bakin titin Dan Sam zuciyarta taqi barinta tafiya...


Juyawa tayi ta canza hanya zuwa bayan layin gidansu.


Bakin wani kangon gida ta tsaya da kusanma anmaidasa bola sbd dadewar da'akayi ba'a cigaba da gininsaba.


Jujjuyawa tayi taga Babu mutane sosai agurin saitayi saurin shigewa gabanta na tsananta fa'duwa Dan jikinta har rawa yake.


Cak ta tsaya tareda zubewa qasa ba shiri...


Kwance yake baisan inda kansa yakeba cikin jini duk gabaki 'daya kamannunsa sun canxa da sbd duka da wahala.


Da rarrafe ta qarasa gurinsa tareda tallafosa jikinta ta fashe da kuka Mai qarfi tana Kiran sunansa.


Kuka take sosai kamar ranta zai fita Dan tabbas batasan sonsa yayiwa zuciyarta mugun kamuba Sai yanxu data gansa cikin wannan mummunan halin....


Jin tayi kamar ya motsa tayi saurin 'dagowa suka ha'da ido sabbin hawaye suka gangaro Mata ta fara girgixa Kai cikin kuka tace,


Why....why...why Nik,,,,why did you choose to make me suffer by seeing you like this????


Duk da a  wahalce yake danko hannunsa bai iya motsawa Amma ganinta yakawo farin ciki sosai acikin ransa barema dayaga halinda tashiga ganinsa haka..


Wani mugun yunqurin amai yayi saiga jini na fitowa ta bakinsa..


Zaro manyan idanuwanta dasukai ja tayi takalli jinin takuma maida kallonta kansa taga Yana numfashi sama sama

Da gudu ta fito tareda mantawa da wani tsoron Kar aganta tasamo taxi itada mai taxi 'din suka sakasa mota..


Baya tazauna taredashi duk da numfashinsa zuwa time 'din yakusa 'daukewa...


Damqe hannunta yayi cikin nasa hawayen wahala na gangaro Masa murya qasan maqoshi yafada Mata sunan asibitin  dazata kaisa.


Shihhhhhhhh don't talk pls""""''''''tace Masa qasa qasa cikin kunnensa  tareda qara damqe hannunsa tanajin zafi da ra'dadin ciwonsa na shiga zuciyarta.

Asibitin daya fa'da can takaisa suna zuwa akai emergency dashi Dr naganinsa yayi saurin zare farin glass 'dinsa cikin tashin hankali da mamaki yace,


Oh my God,,Nik ne wanna ai...


Fitowa yayi tareda kallon nurse 'din data biyosa yace,,,


Waya kawo patient 'din dake ciki?


Ada sauri ta nuna Masa ayshah dake zaune ta sunkuyar dakai sbd kukanta dayaqi tsayawa Dan yanda taga hankalin nurses 'din dasuka kar6esa ya tashi tasan ba qaramin Hali Nik 'din yake ciki ba.


Qarasowa gabanta Dr yayi tareda kallonta dakyau kafin cikin mamaki yace,


Kece Kika kawo Nik?


Kai ta 'daga da sauri cikin tsoron Mai zaice yasamu Nik 'din.


Kallon tuhuma yakuma jifanta dashi kafin yace,


Ina muma 'dinsa da....


Bata Bari ya qarasaba cikin fargaba tace,


Please Dr kafadamin idan zaiji sauqi..


Yes zai zamu sauqi but....


Ok Dr ngd Amma Dan Allah idan kanada number mum 'dinsa kafa'da Mata.


Share hawayenta tayi tajuya batareda tabari yakuma wata magana ba.
Kwance take nurse 'din da'aka 'dauko Mata tun Daren jiya Dan kulada ita tana zare Mata drip 'din dake hannunta har lokacin idanuwanta dasukai mummunar kumbura Basu daina zubar da hawayeba..

Finn ne akusada ita ya kwantarda kanta kan kafa'darsa Yana shafa kanta alamar rarrashi.


STORY CONTINUES BELOW

Mr Aiden ma daya iso da safen zaune yake kusada ita  Davina na zaune kusadashi tashige jikinsa...


Dukkaninsu kallo 'daya zakayi musu kasan mummunan alamarine yasamesu Mai kamada mutuwa.


Waya Mr Aiden ya Kuma 'dagawa akaro na ba adadi yakuma Kiran police yayi Koda akwai wani update Amma still Babu.

Wayar mum ce tafara ringing Amma ko qyafta idanuwanta batayiba bare ta motsa...


Finn ne yayi qarfin halin 'dauka tareda saka loudspeaker...


Gabaki 'dayansu atare suka zabura Jin abinda Dr yafada mum kuwa tuni takai qofa jiri na 'dan 'dibarta Amma batajin zata iya jira.


Da sauri Finn ya riqota suka 'dunguma mota gabaki 'daya Sai asibitin.

Tashin farko da mum taga halinda Nik 'dinta ke ciki Sai ganin sukayi ta yanke jiki Saida dadinsu yayi saurin riqota ta fashe da kuka tana kallon yanda Nik dinta ke numfashi cikin azaba da wahala duk da har lokacin tashiba.


Saidata shaqi kukanta kafin ta miqe Finn ya Kama hannunta suka nufi office 'din Dr suka bar dad da Davina a room 'din.


Dogon bayani Dr yayi musu akan Yana tunanin mummunan dukane akayiwa Nik 'din Wanda harya ja Masa internal bleeding Dan qila andaki kansa.


Share hawayenta tayi ta Kuma kallon Dr tace,


Where did you find him I mean who brought him here?


It was a lady,,, she was all covered by.....I think she's a Muslim.

Tafasa zuciyar mum tafara Nan take 6acin ranta da baqin cikinta suka danne damuwar dayake ciki...


Miqewa tayi tareda kallon Finn dashima yacika yayi fam dajin cewar ninja lady ce tayiwa Nik wannan mummunan aikin.

Kallon Finn tayi bayan sunbar office 'din cikin tuquqin da zuciyarta keyi tace,


I want them to pay double for wat they've done to my poor darling boy...make them cry and regret their lives.


Yes mum""""yafada Yana fiddo wayarsa aljihu Dan making call.


Da daddare ya farka Nan dukkanin familyn suka kewayesa suna basa kulawa cikin so da qauna musamman mum da kamar tayi ihu takeji duk ya motsa taga ya rintse Ido alamar azaba.


Da daddare bayan Finn da Dad 'dinsa sun taimaka Masa yayi wanka ya saka kayan bacci ya kwanta mum ta lullu6esa ya lumshe idanu alamar bacci duk suka fito Dan tafiya gida.


Lumshe idanuwansa yayi tareda sakin murmushin da iyakacinsa zuciya ya tuno baby face da fararen idanuwanta lokacinda take kuka tana Kiran sunansa.


Ahankali cikin maqoshinsa yace'

I love you my sweet ninja lady...
Washe gari ma data fito kasa wucewa makaranta tayi saita samu kanta dabin umarnin zuciyarta ta nufi asibiti gabanta na tsananta fa'duwa Amma ba yanda ta iya Dan batajin zata iya Kai yamma batareda taga halinda yake ciki ba..

Baba alhaji da baba shehu tareda Yaya Ahmad da Yaya abbakar ne suka dawo daga gurin wani taron fatawa...


Daf dazasu Kai anguwarsu wata baqar mota Tasha gaban taxi 'din dasuke ciki kafin suyi want motsi qartin maza majiya qarf suka fito da bindigogi suka tasa qeyoyinsu baba alhaji dayaso gardama aka 'dibesa wani mummunan Marin dayasashi ha'diye maganar dayaso yi sukabar gurin da mugun speed.Kodata isa asibitin Kai tsaye emergency ta nufa cikin sauqi saiga 'daya daga nurses 'din dasuka kar6esa a jiyan ta tareta cikin sanyin murya ta tambayeta room 'din dayake.

Nuna Mata tayi ta nufi 'dakin gabanta na tsananin bugawa.


Nesa ka'dan da 'dakin ta tsaya tareda qurawa qofar 'dakin ido tana qoqarin controlling matsuwarta tason ganinsa.


nurses biyu taga sun fito 'dakin mace da namiji tayi saurin qarasawa ta tare macen cikin sanyi tace,


Please patient 'din dake ciki yaji sauqi kuwa?


Kallon up and down tayi Mata kafin tace,


Eh Amma dai yanxu mun Hana kowa shiga gurinsa har family 'din sbd munason yasamu isashen hutu.


Bin bayan nurse 'din tayi da kallo bayan ta wuce tana tunanin kenan ba kowa a 'dakin.


For the first time taji wani farin ciki bayan tsawon lokaci..


'dakin ta dosa gabanta nacigaba da fa'duwa.


Tsayawa tayi bakin qofa tareda rintse ido tasaki numfashi ahankali tareda tattaro Yar nutsuwa ta tura qofar ahankali.

Cak ta tsaya sbd idanuwanta dasuka sauka cikin nasa Yana kwance ya qurawa qofar Ido kamar Daman yasan itace zata shigo..


Tashi zaune yayi batareda ya 'dauke idanuwansa cikin nataba..


Har ya iso gabanta Bata motsaba sbd garkuwar jikinta da idanuwansa suka kaririya..


Hannunta ya riqo ya jawota ciki ya rufe qofar har time 'din batayi wani qwaqwaran motsiba.


Zaunar da ita yayi bakin gadonsa tareda durqusawa gabanta idonsa cikin nata yace,


Ayeeshah did you came to hia see?


'daga Masa Kai tayi sbd batada kuzarin magana..


Wani qayataccen Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka bayyana ka'dan..


Tasowa yayi ya zauna kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta da wata kasalalliyar murya yace,


Did you love me ayeeshah?


Shiru tayi tareda sunkuyar dakai qasa.


Murmushi yakuma saki yace,


Please talk to me ayeeshah..


Juyarda Kai tayi still batace qalaba.


Murmushi yayi tareda zubewa qasa ya riqe kansa Yana juye juye cikin tsananin azaba.


A ki'dime ta sauko gabansa tana Kiran sunansa cikin tashin hankali da tsoro Amma saitaga Yana qara mimmiqewa saikuma yayi dif ba alamar numfashi ataredashi.


Kansa ta rungumo batareda tasaniba tafara kuka tareda Kiran sunansa...

_*I love you Nik*_,,,pls wake up..

_*I love you so very much*_.....


Miqewa tayi da sauri Dan kirawo Dr taji anriqo hannunta tayi saurin juyowa sukai Ido biyu Yana sakar Mata wani hot smiling...


Kallon mamaki take Masa da sauran guntayen hawayenta Dan tagano da gangan yayi hakan Dan ta fa'di abinda yake son ji..

Wata fitinanniyar kunyace ta rufeta tayi saurin juya Masa baya tana sauke numfashi ahankali...


Zagayowa yayi tareda matsota sosai danshi Sam bai 'dauki hakan komai ba...


Matsota sosai yayi jikin bango tareda duqo da fuskarsa daf da Tata har numfashinsa na mugun ha'duwa ya 'daga hannu ahankali ya cire Mata niqaf tai saurin rintse ido... fuskarta na bayyana wani sahirtaccen murmushin daya Kuma tafiya dashi.


Bakinsa yakai daidai kunnenta cikin wata kasalalliyar murya yace,,


You finally said it my love...


Sake tamke idanuwanta tayi sbd Jin kalar muryar dayayi amfani da ita ba qaramin shigarta tayiba.


Kallon dogayen eye lashes 'dinta yayi yace,


Will you marry me ayeeshah...


'daga Masa Kai tayi ahankali sbd tuni ta manta da wani banbancin yare da addininsu.Su baba alhaji kuwa wani qaton gida aka kaisu suna shiga aka 'daddauresu tareda jiqasu tsaf da ruwan qanqara kafin aka fara jibgarsu baji ba gani.
Mamuh💋

Post a Comment for "TAURA BIYU CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...