SAUDALA CHAPTER B KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SAUDALA CHAPTER B KARSHE
SAUDALA CHAPTER B KARSHE
Kallan ta yayi har zai yi magana sai kuma ya fasa ya kalli Mama yace , "Mama ki bawa Saudat wan'nan sak'on ta kawo min ". Yana gama fad'ar hakan ya juya ya fita . Mama ta mike ta dauko abu a leda ta mikawa Saudala tace , " Maza tashi ki kai masa". Jiki babu k'wari Saudala ta mike ta nufi part dinsa. Tunda ta kai bakin k'ofar gaban ta yake fad'uwa , dak'yar ta tura k'ofar ta shiga da sallama. Tana shiga ta ganshi a zaune ya d'aura k'afa d'aya kan daya yana kad'awa A hankali ta k'arasa inda yake tace , "Yaya Abdul gashi in ji Mama." Ta fad'a tana miko mai ledar . Banxa yayi mata kamar bai jita ba , ta kuma maimaita Amma ko kallan ta baiyi ba . Tashi yayi yaje ya kulle k'ofar parlourn san'nan ya dawo ya dauki belt ya zauna. Saudala ganin ya kule k'ofar ga kuma belt a hannun sa sai hankalin ta ya tashi . Tayi aune ba taji ya zuba mata a baya . Aikam ta kwa'la k'ara tana susar bayan ta . Ya kuma zabga mata a baya, san'nan ya kalle ta yace , "Wato ke indai ba dukan ki akayi ba baza ki dawo hankali ba ko? Tunda dukan kike so kin had'u dashi." Ya fara duka ta ko ta ina zabga mata yake . Ihu take tana fad'in, "Dan Allah yaya Abdul kayi hakuri yasin bazan k'ara ba ." Ko kula ta bai yi ba balle ya daina dukan ta . Sai da yayi Mata duka san'nan ya kya'leta yace, "Daga yau indai kika muka yi min kunya sai nayi miki dukan da yafi haka, nonsense ." Saudala kuwa muryar ta ko fita bata yi sosai sbd kukan da tayi . Cikin tsawa yace "zaki tashi ki barmin d'aki ko sai na k'arya ki ." Dak'yar Saudala ta mike ta fara tafiya tana kuka .😭 Har ta fita daga d'akin bata ce komai ba. (lallai Saudala taji jiki πŸ˜‚) Fadila tana zaune a parlour taga shigowar Saudala tana tafiya tana dafe kai. Cikin tashin hankali Fadila ta nufe ta tana fadi'n, STORY CONTINUES BELOW "Sister lfy mai ke damun ki?" shatin belt Fadila ta gani a jikin ta , abinka da farar fata jikin ta duk yayi ja. Fadila tace "Sis wa yayi miki wan'nan d'ukan?" Ita dai Saudala ta k'asa magana ji take in tayi magana kanta zai fashe sbd ciwon da yake mata. Cikin d'aga murya Fadila take fad'in, "Mama ! Mama!! Kizo kiga Saudat bata da lafiya." Cikin sauri Mama ta fito daga d'aki tana fad'in, "Lafiya Fadila meya faru?" Fadila tace " Mama Saudat bata da lafiya." Sai a san'nan ta lura da Saudat a kwance a kan kujera. K'arasawa wajan ta tayi tana fad'in, "Lafiya me yasa same ta?" Fadila tace " ban sani ba naga dai jikin ta yayi alamar dukan ta akayi." waya Mama ta d'auko ta kira family Dr din su tace yazo yanzu tana neman sa. Jikin Saudala kuwa yayi zafi sosai , jijiyoyin Kanta har'bawa kawai suke. Abba ne ya sauko yana tmbayr lafiya. Ganin halin da Saudala take ciki hankali sa ya tashi , dan baya son abinda zai tab'a d'ayar k'anin nasa. Koda Dr ya iso bayan ya budu ta yayi mata al'lura bata dad'e ba bacci ya d'auke ta . Magani ya rbt yace a siyo ta dinga sha. Abba yace " Dr me yake damun tane ?" Dr yace " D'ukan da aka yi mata yafi k'arfin jikinta shine abinda ya haifar mata da zazzab'i da ciwon kai , Alhaji in tasa kasance tayi laifin da za'a daki ta to gaskiya a daina yi mata irin wan'nan dukan dan wata rana sai ayi mata illah ." Yana gama fadar hakan ya tattara kayan sa ya tafi. Abba ya kalli Mama yace, " Wanene yayi mata wan'nan dukan? " Mama tace " Ni kaina ban sani ba , ni dai nasan na tura ta d'akin Abdul ta kai masa magani amma bayan nan basan ida taje ba." Iya ce ta shigo d'akin tana matsar k'wallah tana fad'in, "Waye zai dake ta kuwa inba wancan mai k'atan kai ba , tunda ya dawo gidan nan ya takura mata yanzu ji dukan da yayi mata ." Tana gama fad'ar hakan ta koma kusa Saudala ta zauna .(Iya ta SaudalaπŸ€£πŸ˜†) 1 Abdul kuwa bayan ya Saudala ta fita sai yake jin bai kyauta ba , dan yasan ta daku sosai . Amma in ya tuno rashin kunyar da tayi masa sai yayi tsaki yaji gwara da ya Zane ta. Wayar Sace ta ka'tse masa tunani ,nmbr Abba ya gani, yana d'agawa tun kafin yayi magana Abba yace, "Kazo yanzu ina son ganin ka," yana gama fad'ar hakan ya kashe wayar. Mikewa Abdul yayi ya nufi main parlour. Koda ya shiga bai gansu ba , muryar Mama ya jiyo a d'akin su Fadila sai ya karasa d'akin. Yana shiga tun kafin yayi magana Iya ta fara fad'in, "Ka dake ta kaji dadi da kasani baka bar ta da rai ba tunda baka kaunar ta". Abba yace " kuzo muje parlour muyi magana sbd kar maganar mu ta tashe ta daga bacci. " Suka koma parlour suka zauna , Abba ya kalli Abdul yace, STORY CONTINUES BELOW "Abdul kai kayiwa Saudat wan'nan dukan?" Abdul yayi kasa da kansa bai ce komai ba. Abba yace "shirun da kayi ya nuna min kai kayi mata wan'nan dukan, Amma banyi tunanin zaka iya yi mata haka ba , Ashe baka dauke a matsayin k'anwa ba , nayi tunanin ko wani ka gani yana dukan ta zaka tsaya ka rama mata, Ashe tunani na ba haka bane tunda gashi kai da kan ka kayi mata wan'nan dukan kamar zaka kashe ta ,meyasa kayi hakan?" Shiru Abdul yayi bai ce komai ba. Abba yace "Nasan halin Saudat akwai ta da tsokana amma ai kai ba yaro bane bai kamata ka dinga biye mata ba , yanzu gashi biye matan daka yi ga abinda ya jawo." "Dan haka ki da wasa kar ka k'ara maimaita abinda kayi , bance in tayi laifi kar a hukunta taba amma ayi mata dai-dai da shekarun ta ,kaji na fad'a maka". Sai a san'nan Abdul yace , " Kayi hakuri Abba insha Allah hakan ba zai kara faruwa ba." Abba yace " yayi kyauta". Suka amsa da Ameen. Abdul yace "Abba mganr tafiya ta Cross river dazu aka yo min waya ake sanar dani an fasa tafiya jibi gobe da asuba zamu wuce ." Abba yace "to Allah ya kai ku lafiya ." Suka amsa da Ameen. Da Asuba ana fitowa daga Abdul ya tafi Cross river. (Bye AbdulπŸ‘‹πŸ»πŸ€¨) Saudala kuwa bata farka ba sai karfe takwas na safe . Tana tashi ta mike zaune nan abinda ya faru ya dawo mata cikin brain . Ajiyar xuciya tayi tace, "Nima sai na sami hanyar da zan rama dukan da kayi min , dole nema in rama ." Fadila ta shigo tana fad'in, "Sister kin tashi Ashe, ya jikin naki?" Murmushi Saudala tayi tace , "Da sauki." Fadila tace " kina bacci d'azu yaya Abdul ya tafi Cross river kuma zai Dad'e a can ." Kallan ta Saudala tayi tana maimaita yayi tafiya bata rama dukan da yayi mata ba . Sai kuma tayi murmushi a ranta tace , "Gwara ma da yayi tafi k'afin ya dawo na gama tsara abinda zan yi masa ." Mama ce ta shigo tana fadin....................... Comment & Share Neat Lady✍🏼 [9/3, 20:26] Sady Beb: 🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ πŸ‡³πŸ‡¬® _*ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION(YAN ASALI)*_πŸ“š✍🏼 [❄Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.] _*DON'T 4GET TO VOTE,COMMENT & ALSO FOLLOW US ON WATTPAD*_ _*@AboriginalWrtersAsso.*_ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏼 *Bismillahir rahmanir rahim* 33&34 A haka Fadila ta shigo d'akin ta ganta a zaune tana faman kuka . Fadila ta zauna a kusa sa da ita tace , STORY CONTINUES BELOW "My sister lafiya kike kuka?" Saudala ta share hawayen ta tace , "Babu komai." Sanin halinta yasa bata k'ara tambayar ba taje ta kwanta. Washe gari Saudala ta tafi makaranta, sosai ta mai da hankalin ta wajan karatu . bayan an fito" break" Saudala tana zaune a Aji sai ga wata" student" tazo wucewa ta taka Saudala kuma ko juyowa bata yi ba balle ta bata hakuri. Mikewa Saudala tayi taje wajan da'libar tace, "Ba kya gani ne kin taka ni kuma kinyi wucewar ki?" Cikin tsiwa ta dago kai tace , "An taka ki d'in kiyi duk abinda zaki yi ba..........." Ai k'afin ta 'karasa Saudala ta tsinka mata mari har gudu biyu (Daman baka shiga har'kar Saudala bama ya ka cika balle ka tsokane taπŸ˜‚). Cikin sauri Yarinyar ta d'aga hannu zata rama Saudala ta naushe ta a baki. Ai kam suka fara kokawa . Cikin sauri aka je aka fadawa principal ana fad'a Kafin principal ya 'karaso tuni Saudala ta kai Yarinyar 'kasa . Office principal ya tafi dasu aka saka su "kneel down" san'nan yace , "Me ya had'a ku?" Kafin Waccan tayi magana tuni Saudala ta fara zuba, tayiwa principal bayanin komai san'nan d'aura da cewa, "Ta isa ta raina min hankali ban gyara mata zama ba , kuma aradu ba k'yaleki nayi ba zamu had'u ne." Tsawa principal yayi mata san'nan tayi shiru. Principal yace " in aka kuma kama ku kuna fad'a a Aji sai nasa anyi muku duka." Tab'e b'aki Saudala tayi tace, "Wuyar ta ta kuma tsokana ta aradu abinda yafi fad'a ma sai nayi."🀭 Sarai yaji ta Amma bai tanka ba dan kar ta yar'fa shi . Yace " ku tashi ku bani waje ." Saudala ta Mike ta kalli Yarinyar tace , "Zamu had'u ne." Ta b'ude k'ofa ta fice . Gab da za'a tashi Saudala taje ta siyo wani Abu ta b'oye ta shigo ta zauna. Yarinyar da suka yi f'ada da Saudala akayi k'iran ta ta Mike ta fita. Tashi Saudala tayi ta karasa wajan sit din waccan cikin sauri ta dauko abinda ta b'oye ta zuba a wajan . Yarinyar tana dawowa bata kalli wajan ba kawai ta zauna , tana zama aka kad'a tashi. Tana zama taji abu ya jika ta mikewa tayi dan taga meye , ai tana Mikewa Saudala ta fara f'adin. "Yanzu ke da girman ki ki kayi fitsarin zaune ?, amma kinji kunya ."πŸ˜‚ Ai kam sai kowa ya juyo yana kallan ta ana yi mata dariya. Yarinyar da taga dariyar tayi yawa sai ta dau school bag dinta ta fita daga Ajin tana kuka. Biyo ta Saudala tayi tana w'aka tana f'adin. " Me fitsari a Aji wan'nan ce ." Ai kuwa kowa ya fara kallan ta yana dariya . Sai kuwa Yarinyar ta fashe da kuka tana dana sanin abinda tayi wa Saudala. STORY CONTINUES BELOW Ganin ta kur''kusa tana kuka ga yara suna yi mata dariya , Sai Saudala taje ta tsu'guna a kusa da ita tace, "An f'ada miki ana raina min hankali a zauna lafiya ne ? , to bara kiji daga yau kin fara ganin wulakanci kala-kala." Cikin kuka Yarinyar tace , "Dan Allah Saudat kiyi hakuri, wallahi bazan k'ara yi miki haka ba." Murmushi Saudala tayi tace, "Kin hutawa kan ki". Tana ga f'adar hakan ta mike tayi tafiyar ta. Bayan ta koma gida tana zaune a parlour taji k'arar horn din motar Abdul. Cikin sauri ta mike ta dau wata siririyar igiya ta d'aura a b'akin k'ofar parlourn. In baka kula sosai ba baza ka gane an d'aura wani abu a wajan ba. Abdul kuwa part dinsa ya wuce yayi wanka ya shirya ya tawo part Mama. Bai kula da wani Abu a jikin k'ofar ba kawai ya shiga. Ai yana zuwa yaji abu ya har'de shi ji kike timmmmmm ya f'adi . K'afar sa ta rike da d'akyar ya Mike yana d'ingishi . Daga baya kujera Saudala ta fito tana dariya ta f'adin,πŸ˜‚ " Ka ganka kuwa lkcn da ka f'adi tab nida kabewa , Ashe baka da 'kwari rago kawai. "πŸ˜‚ Shikam Abdul ya Sara mai zaiyi , gaba'daya ya kasa mgn kallan ta kawai yake . Wajan k'ofar taje ta ciro igiyar ta ta kalle shi tace, " Ramuwar Marin da kayi min kenan mai hancin karas." Tana gama f'adar hakan ta shiga d'aki. Da yake babu kowa a parlourn babu Wanda yasan abinda ya faru. D'akyar Abdul ya Mike dan k'afar sa ta bugu ya tafi d'akin sa. Koda ya koma d'aki tunani yake anya Saudala bata da t'abin hankali ko Al'janu?. Wata xuciyar Tace masa babu wasu Al'janu tsabar raina ka da tayi ne . Haka ya dinga tunane-tunane amma ya kasa samo amsa . K'arar wayar sace ta k'atse masa tunani , number Abba ya gani yayi picking ya Kara a kunne. Abba yace "Abdul kazo main parlour ina son ganin ka ." Ya amsa da "to Abba gani nan". Ko da ya isa parlourn Abba da Mama da Iya ne kawai a zaune. Abba ya kalle shi yace, " Abdul lafiya naga kana d'in'gishi ?" Abdul yace " dazu ne nadan bige ". Mama tace " To Allah ya k'ara lafiya." Abba yace " Abdul dalilin da yasa na k'ira ka akan maganar auren ka ce , d'azu uncle din ka ya k'ira ni ya f'ada min yadda suka yi da mahaifin Yarinyar , mahaifin Yarinyar wato Alhaji Abubakar sun tsaida ranar nan da shekara mai zuwa." Abba ya cigaba da f'adin , "A yadda uncle din ku yaso a sa ranar nan da wata goma masu zuwa, Amma su d'angin Amaryar sun fison a bar shi nan da shekara D'aya tunda tsakanin wata goma da shekara D'aya babu wani yawa sosai, yanzu dai an tsaida shekara d'aya in Allah ya kaimu." Abdul yace "Hakan yayi Abba daman akwai wani course da nake son naje nayi a cross river kuma daman course din shekara D'aya ne ." Abba yace "to hakan yayi Allah ya nuna mana, amma nan da yaushe zaka tafi Cross river din?" STORY CONTINUES BELOW Yace "Zuwa jibi in Allah ya kaimu." Abba yace "Allah ya kaimu." Yace "Ameen." Lah'ila'ha'illallahu Muhammadur rasulil'lahi (S A W). Iya ce ta r'afka wan'nan salatin tana tafa hannu. Tace " yanzu kai Umumaru sai ka bar yaron nan ya k'ara shekara d'aya babu aure?" Abba yace "to ai Iya ba kiji yace daman akwai wani course da zaije yayi ba na shekara D'aya kinga koda an sa auren nan kusa dole a d'aga sai ya dawo." Iya tace "Daman ai nasan goyon bayan sa zaka yi , Amma wan'nan k'aton ace sai nan da shekara d'aya zai yi aure , ku ga yan' boko ko , to kuje kuyi abinda kuka ga dama , amma in dai na isa da mai k'atan Kai bazai kai shekara d'aya babu aure ba." Tana gama f'adar hakan ta mike ta bar wajan. Murmushi Abba yayi yace, "Hajiya Iya kenan ". Suka watse daga wajan kowa ya kama gaban sa. Saudala kuwa tunda ta shiga d'aki take dariya yadda hawaye , dan ko banza tasan shima yaji a jikin sa. Da dare suna zaune Abdul ya shigo. Tun k'afin ya 'karaso Saudala ta fara dariya tana f'adin, "Gurgu mai bashi da k'afa ." Tana f'ada tana kuma yin dariya. Kallan Abdul yayi yace.............. Team din Saudala gamuπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Comment & Share Neat Lady✍🏼 [9/3, 20:26] Sady Beb: 🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ πŸ‡³πŸ‡¬® _*ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION(YAN ASALI)*_πŸ“š✍🏼 [❄Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.] _*DON'T 4GET TO VOTE, COMMENT & ALSO FOLLOW US ON WATTPAD*_ _*@AboriginalWrtersAsso.*_ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏼 _*Ni haleema ashe haka nake da masoya daman, kwana hud'u da nayi banyi typing ba anan naga ruwan masoya na , nasu k'ira na a waya da masu yi min mgn ta prvt, babu abinda zance muku sai dai nace Allah ya bar kauna , hak'ik'a naji dad'in kulawar gare ni kuma nagode sosai.*_🀝🀝🀝😻πŸ₯°πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ₯° *naji dad'in Addu'ar ku Allah ya bar mu tare*😘😘😘😘😘 _*Kai dan dad'in sai da nayi kamar na kunna gas na zauna akai*_πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *_daga yau posting d'in zai koma ranar Friday da Saturday , hakan ya faru ne sabida wani dalili , amma insha Allah duk rana daya zan dinga yi muku two page._* 🀦🏻‍♀ *Bismillahir rahmanir rahim* 37&38 Mama ce ta shigo tana fad'in , "A'a Saudat kin tashi kenan ya jikin ?" Saudala tace " Mama da sauk'i ." Mama tace " to Allah ya k'ara sauk'i ." STORY CONTINUES BELOW Fadila ta amsa da Ameen . Iya ce ta shigo tana fad'in , "Yanzu Haleema sai da kuka bar wan'nan mai k'atan kan ya tafi , yanzu da gaske sai nan da shekara Ι—ayan zai yi auren ko ?" Mama tayi shiru bata ce komai ba dan bata da abinda zata ce mata. Iya tace " to shikenan bara Ummarun yazo ". Wajan Saudala ta tafi tana cewa , " Sannu Ζ΄ar nan ". Saudala tace " Yauwa Iya". Babu Wanda ya kuma magana a cikin su kowa yayi shiru. Bayan dawowar Abba Iya tasa shi a gaba akan maganar auren Abdul . DaΖ™yar ya shawo kan ta ta haΖ™ura . Washe gari Jikin Saudala ya warke sosai saidai har yanzu akwai ragowar tabo a jikin ta . **** Abdul kuwa suna Lafiya ya kira gida ya sanar dasu san'nan ya shiga yin abinda ya kai shi. *** Saudala ana zuwa makaranta dan sosai take fahimtar komai dan yanzu a cikin masu k'ok'arin ajin dole Saudala ta shiga cikin su. *BAYAN WATA GOMA* Kwanci tashi babu wuya a wajan Allah. Su Saudala an shiga jss 3 an kusa fita jenior . Saudala ta k'ara girma sosai dan yanzu ta d'anyi k'iba da tsa'wo amma ba sosai ba , alamun girma sun bai yana a jikin ta amma har yanzu halin yana nan. A yau ne Saudala ta cika shekaru goma sha hud'u a duniya . Shirye-Shiryen birthday d'in da Fadila ta had'a mata ake . Mai make up Fadila ta kira har gida aka zo taka yi musu . A harabar kuwa anyi decoration na flowers pink color masu k'yau . A jikin wani k'aton frame an rbt _HAPPY BIRTHDAY SAUDAT_. Khadija k'awar Saudala kuwa sune a gaba dan gaba d'aya da ita ake shirye_shiryen . Sosai Fadila tayi gayya kamar biki k'awayen ta sun zo sosai. Tunda aka gama yiwa Saudala make up Fadila take kallan ta dan gabad'aya ta canja kamar ba ita . Tana sanye cikin doguwar riga Ζ΄ar kanti mai fad'i daga ka'sa, anyi mata d'auri baya an fito da gashin ta . Mama ce ta shigo tana fad'in , "Wai har yanzu Baku gama ba kun bar mutane su......... Maganar ta mak'ale sak'wamakon Saudala da ta gani kamar ba ita ba. Mama tace " Masha Allah Saudat kinyi kyau sosai. " Fadila rik'e hannun Saudala tayi suka fito . Sai kuwa kallo ya dawo kansu dan ba k'ara min k'yau suka yi ba. Sai kuwa aka fara ruwan hoton na . Wajan da aka tanada na zaman Saudala nan Fadila ta raka ta ta zaunar da ita . Wani k'aton cake aka d'auko aka ajjiye a gaban Saudala , a jikin cake d'in an rubuta *Happy birthday Saudat*. Wuk'a aka kawo mata Fadila ta rik'e hannun ta suka yanka cake d'in tare. Sai kuwa wajan ya rud'e da tafi . STORY CONTINUES BELOW Yankowa Saudala tayi ta bawa Fadila a baki ita kuma ta bata. A haka aka gama taro bayan an raba memo da jaka da ke d'auke da hoton Saudala. Da Daddare Abba ya bawa Saudala k'yauta yana taya ta murnar birthday d'inta . Mama ma ba'a barta a baya ba dan duk wani Abu da akaci aka raba a wajan taron ita tayi shi. Fadila tana zaune a d'aki Saudala ta shigo tana fad'in , "Wlh na gaji ". Fadila tace " kema ki kwanta ki huta mana." Wanka Saudala tayi san'nan tayi sallah tabi lafiyar gado. Fadila kuwa charting take ita da k'awayen ta tana yi musu ban gajiya . Hotunan da suka d'auka su biyu ita da Saudala ta turawa Abdul. San'nan ita ma ta kwanta. Abdul kuwa lkcn suna zaune shida abokin sa Mustapha suna tsara yadda bikin Abdul zai kasance. Wayar sa ya d'auka yana kun'na data sak'on da Fadila ta turo mai ya shigo . Bud'ewa yaga hotunan da turo mai . A k'asan hoto ta rbt birthdayn d'in Saudat. Bud'e hoton yayi yana kallah , lkcn da ya bud'e na Saudat sai da gabansa ya fad'i . tunani yake a ransa anya kuwa wan'nan Saudat ce ? Cigaba yayi da kallan hoton baisan dalilin da yasa yake jin fad'uwar gaba ba. Ya shagala da kallan hoton , Mustapha ne ya tab'a shi. Firgigit ya juyo yana kallan sa . Mustapha yace "Lafiya tunanin me kake?. Kafin ya bashi amsa ya karb'i wayar yana muga abinda kake gani. Yana k'arb'a idon sa ya sauka akan hoton Saudala da tayi murmushi dimples d'in ta suka lob'a. Mustapha tace " Tabara'kallah Masha Allah , Allah yayi halitta anan wajan ." Sosai shima ya shagala da kallan k'yakyk'yawar fuskar ta. Kafin Abdul yayi magana ya riga shi da fad'in , "Abdul wan'nan fa?" Ya fad'a yana nuna masa Saudat. Bai San meye dalili ba yaji gaba d'aya haushin Mustapha yake. Cikin jin haushi yace " k'anwa ta ce." Mustapha yace " to ya akayi ban santa ba , nidai nasan Fadila ce kawai k'anwar ka." Cikin gajiya da zancen Abdul yace , "Y'ar uncle ce ". Murmushi Mustapha yayi yace , " Tabbas yau na sami matar aure , hak'ik'a ban tab'a jin k'aunar wata mace ba a raina sai wan'nan. " Tsaki Abdul yayi yace " wan'nan y'ar Yarinyar kake so ? Gabad'aya fa shekarun ta 14 ." Murmushi Mustapha yayi yace, "Haka nake so daman ni nafin San na auri yarinya , kaga kafin nayi aure k'ila ta kai sha biyar , nidai ina rik'o ." Wani irin b'acin rai Abdul ya keji, cikin fusata yace , "Kaje ka same ta mana ina ruwa na." Mustapha yace " to meye naji haushi Mr man , nifa ba Hadixa nace ina so ba." STORY CONTINUES BELOW Abdul yace " baza ayi mata aure yanzu ba tayi k'ank'an ta ." Mustapha yace " ko nan da shekara goma ne na yadda zan jira Wallahi. " Mik'ewa Abdul yayi yana fad'in , "Oho maka dai , sai da safe ." Ya fad'a yana shigewa d'aki. Mustapha kuwa wani irin k'aunar Saudala yake ji tana yi masa yawo jiki. Cikin sanyin jiki ya Mik'e shima ya shiga d'aki sa. Abdul kuwa tunda ya shiga d'aki yake tunanin me yasa yake jin haushi Mustapha dan yace yana son Saudat? A fili yace " to meyasa nake jin wani iri akan wan'nan Mara kunyar?" Tsaki yayi ya kawar da tunanin a zuciyar sa. Amma cikin ransa kawai tunanin ta yake. Sai ya sami kansa da son k'ara kallan hoton ta , wayar ya d'auko yana k'arewa Fuskar ta kallo. Sai ya sami kansa da yin murmushi. A haka bacci ya d'auke shi. Bayan kwana biyu Sosai Mustapha ya takurawa Abdul da zancen Saudala, indai suka zauna bashi da zance sai na Saudat. Shikam Abdul wani haushin sa yake ji a duk lkcn da zaiyi masa zancen ta , shiyasa da ya d'auko zancen sai Abdul ya sako wani zancen . Shi kansa ya rasa dalilin da yasa baya son Mustapha yayi masa zancen yana son Saudat. ***** A yau Saudala ta tashi da wani irin ciwon ciki kamar zata mutu. Family Dr d'insu aka k'ira ko da ya duba kallan Abba yayi yace, "Ba wata matsala bace kawai girma ne yazo mata ,sai an kula da ita sosai Alhaji domin duk Yarinyar data t'sinci kanta a wan'nan hali tana jin kanta dai-dai da kowa , dan haka a kula da ita sosai." Yana gama fad'ar hakan ya tafi. Tagumi Iya tayi tace, "Oh zamani wai yanzu y'ar shekara sha hud'u ce ta fara al'ada." Murmushi Mama tayi tace , "Iya kenan ai yanzu zamani ya canja y'ar sha uku sai kiga ta fara , sai dai muce Allah ya tsare su." Iya ta amsa da ameen. Bayan Saudala ta farka Fadila ta shigo ta zauna kusa ita tace, "My sister Ashe kin tashi ya jikin.?" Saudala tace "da sauk'i." Fadila tayiwa Saudala bayanin abinda ya same ta. Fadila tace "ai anyi muku a islamiyya ko?" Cikin kunya Saudala tace, "Eh". Fadila tace " yauwa yanzu tashi kije ki gyara jikin ki". Tashi Saudala tayi ta shiga toilet. bayan ta gama shirya wa ta kasa fitowa parlour dan kunyar Mama take ji. Dak'yar ta fito ta zauna nasiha Mama ta kuma yi mata daga nan kowa ya cigaba da abinda yake gaban sa. Bayan wata d'aya. Shirye-shiryen Bikin Abdul kawai ake a gidan . Kayan lefe ake shirin kai wa Kano . An had'a lefe ak'wati ashirin komai na cikin kayan mai tsada ne. STORY CONTINUES BELOW Su Baba ake jira su k'araso Dan maza ne zasu kai ba mata ba. Sosai Saudala take murnar zuwan su Baba. An gyara wa su Baba part d'in su wanda komai iri d'aya ne da part d'in Abba. Saudala tana tsaye a bakin gate tana jiran isowar su. Tana tsaye sai ga motar su ta shigo cikin gidan. Comment & Share Neat Lady✍🏼 [9/3, 20:26] Sady Beb: 🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ πŸ‡³πŸ‡¬® _*ZUMUNCI WRITER'S ASSOCIATION*_πŸ“š✍🏼 [ *Zumunci mai d'orewa*🀝🏻] *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏼 *Dedicated to all my fan's*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ˜»πŸ˜» *Bismillahir rahmanir rahim* 39&40 Tun kan su k'araso Saudala ta nufe su a guje . Tun kan su k'arasa bud'e motar take k'ok'arin bud'ewa . Rungume Umma tayi tana farin cikin ganin Umman nata. Sakin ta tayi ta nufi wajan Baba ta ruk'unk'ume shi tana murna. Kallan ta Baba yayi yace , "Kece kika girma haka Saude"? Dariya tayi suka shiga parlourn gabad'ayan su. Bayan sun zauna Fadila ta kawo musu ruwa ta ajjiye. Abba yace " ai kamata yayi ku huce part d'inku in kun huta sai kuzo a gaisa ." Baba yace "ai gwara a fara gaisawa in yaso sai muje mu huta d'in". Gaisawa suka yi cikin mutunci da girma'mawa. Iya ce ta fito tana fad'in, " A'a Ahmadu Ashe kun iso ." Ta fad'a tana zama akan kujera. Har k'asa Baba ya durk'usa yace, "Iya barka da yamma, da fatan mun same ku Lafiya". Iya ta washe baki tace , " Lafiya lau Ahmadu ya mutan k'auyen ?" Yace " duk sun ce a gaida ke." Iya tace "Masha Allah". Umma ta gaida Iya ta amsa cikin mutunci. Iya ta kalli Baba tace " Ahmadu Amma dai kunzo kenan ko?" Baba kallan Abba yayi yaga shima shi yake kallo yace , "Da bayan Bikin Abdul zamu koma in yaso daga ba........... Kafin ya k'arasa Abba yace, " A'a babu inda zaku kunzo kenan ." Iya tace "Hakan yafi dan in har suka koma nasan hali ba lallai ya kuma dawowa ba." Shikam Baba murmushi kawai yake . Ita kuwa Saudala tana mak'ale da Umma dan gani take kamar zata gudu ta barta. Mik'ewa suka yi suka nufi part d'insu. STORY CONTINUES BELOW Saudala tana rik'e da hannun Umma har suka k'arasa. Bayan sallar i'sha su Abba da Mama da Fadila suka tafi part d'insu Baba dan yau a can za'a ci abinci. Aka ci abinci cikin farin ciki daga nan kowa ya koma part d'in sa. Saudala kam yau gata ga Umman ta . ***** Sosai Mustapha ya ta kurawa Abdul da maganar Saudat. Shi kuwa Abdul da Mustapha ya fara yi masa maganar Saudat sai yasan yadda akayi aka bar zancen. Yau dai Mustapha ya tsare Abdul yana tambayar , Mustapha yace, "Abdul ina da wani hali ne da zaka iya bani k'anwar ka ba?" Abdul yace "ni bance kana da wani hali ba." Yace " to meyasa duk lkcn da zan yi maka maganar ta sai ka dinga basarwa .?" Abdul yace " baka ganin yarinya ce har yanzu bata gama jenior school bama balle har tayi candy." Mustapha yace " na yarda zan iya jiran ta koda shekara goma ne." Ajiyar xuciya Abdul yayi yana jin wani iri a ransa. Kallan Mustapha yayi yace , "To naji ka bari mu koma gida tukunna." Mustapha yace " Allah ya kaimu." *Wanene Mustapha?* Mustapha Aminu shine cikakken sunan sa haifafen gari Abuja ne . A primary school suka had'u da Abdul . Tun daga nan jinin su ya had'u dan Abdul mutum ne mai k'ok'ari shima kuma Mustaphan haka wan'nan ne dalilin da yasa suka zama abokai. Tare suka yi secondary school daga , burin Abdul a duniya shine ya zama sojo haka shima Mustapha. Tare suka tafi England suka yi karatu har lkcn da suka tafi soja., Allah ya basu sa'a babu Wanda ya fad'i. Mustapha shine aminin Abdul dan Abdul bashi da wani aboki kamar Mustapha. Mustapha mutum ne mai mutunci da sanin ya kamata , bashi da wani hali Mara k'yau. Wannan kenan. Abdul da Mustapha shirye-shiryen dawowa gida suke dan sun gama abinda ya kaisu . Washe gari da asuba suka d'auki hanyar Abuja . *** Saudala kuwa ko makaranta bata je ba sabida murnar ganin iyayen ta . Suna zaune a main parlour gabad'ayan su Abbaya shigo yana fad'in, "Su Abdul fa sun taso tun Asuba ." Baba yace "To Allah ya kawo su lafiya." Saudala da take a zaune kamar bata San me ake cewa ba a ranta tace , "Ranar ramuwa tazo kenan ". (Wai daman Saudala bata manta ba🀭) Mama ce tace " Saudat maza ki shiga d'aki na ki dauko key d'in d'akin Abdul kije ki gyara masa." Babu musu Saudala ta Mik'e ta dauko ta tafi. Koda ta shiga kallan parlourn take tana tuna inda yayi mata duka. K'wafa tayi san'nan ta Gyara d'akin . Koda ta fito daga d'akin kullewa tayi ta koma dakin su. STORY CONTINUES BELOW Su Abdul basu iso ba sai dare , koda ya shigo gidan babu kowa a parlourn alamun kowa yayi bacci kenan. Part d'in sa ya nufa yana shiga d'akin bai tsaya wani Abu ba ya fad'a toilet dan yayi wanka ya rama sallolin dake kansa. Horn d'in motar su ne ya tashi Saudala daga bacci , daman kuma ba wani bacci tayi sosai ba dan dare bai yi sosai ba. Mik'ewa tayi cikin sand'a kar Fadila ta farka, fita tayi daga d'akin. Kitchen Saudala ta shiga ta d'auki k'wano ta zuba kuka ta had'a da ruwa ta juya . Fita tayi daga kitchen d'in cikin sauri ta nufi part d'in Abdul Dan tasan yanzu wanka yake. Ta shiga direct bedroom d'insa ta wuce , k'arar ruwa taji a band'aki alamun wanka ake . Murmushi tayi san'nan ta zuba wan'nan kukar a bakin toilet d'in, jin shiru alamun an gama yasa tayi saurin barin d'akin. Abdul kuwa ya fitowa bai kula da komai ba ya taka da k'arfin . Suuuuuuuuuuuuuuuuu timmmmmmmmmmm Abdul a k'asa ya kasa mik'ewa . Cikin dauriya ya mik'e amma Sam k'afar sa tak'i takuwa dak'ar ya mik'e ya zauna a bakin gado. Kallan bakin toilet d'in yayi yaga abu a wajan , kallan wajan ya kuma yi yana tunanin me ya kawo wan'nan baki toilet kuma. Saudala kuwa tana fita daga d'akin ta dinga dariya kamar zata shid'i .πŸ˜‚ Tana fad'in " kad'an ma ka gani mai hancin karas." Dak'ar bacci ya dauk'e Abdul da zugin da kafar sa take masa. Da Asuba k'afar Abdul tak'i dakuwa dak'ar yayi sallah ya koma ya zauna. Har gari ya waye Abdul bai shigo ba . Mama tace "wai jiya Abdul bai dawo bane."? Abba yace " ya dawo mana ." Tace "to lafiya har yanzu bai shigo ba." Abba yace "nima nayi tunanin hakan , amma bara naje na duba." Abba ya tafi d'akin Abdul, koda ya shiga a zaune ya tadda Abdul . Abba ya k'arasa wajan Abdul yana cewa, "Abdul lafiya har yanzu baka fito ba?" Abdul yace "Abba ina kwana." Abba yace "lafiya lau , lafiya baka fito ba?" Abdul yace "wlh jiya bayan na dawo na fito daga toilet kenan na zame na fad'i." Abba yace "Subahanallah sannu". Baba ne ya shigo yana tambayar meke damun Abdul d'in. Abba yayi masa bayani Baba yace, " To a kira me gyara mana." Abba yace "ai ni bansan ma a ina zan samu mai gyara ba a garin nan ." Baba yace "to ina Saude tazo ta duba masa." Abba ya kalli Baba yace , "Daman Saudat ta iya gyaran targad'e ne?" Baba yace "sosai ma dan a k'auye har zuwa ake yi to sbd halin ta yasa na hanata , dan in anzo gyaran indai tana jin haushin ka to Wallahi baza ta gyara ba sai dai ta dad'a fama maka." Murmushi Abba yayi yace, "Ai halin Saudat sai ita." Waya Abba yayiwa Mama yace ta tro Saudat. STORY CONTINUES BELOW Saudala kuwa daman tasan za'a yi hakan. Shiga d'akin tayi da sallama , tace , "Abba gani". Baba yace " yayan ki zaki yiwa gyara, saura kuma kiyi halin naki." Murmushi tayi ta k'arasa wajan Abdul tana dariya mugunta. Jama'a ga Saudala zata yiwa Abdul gyaraπŸ€­πŸ˜‚ Nasan akwai drama 🀣 Ina team din Abdul πŸ™„ Comment & share Neat Lady✍🏼 [9/3, 20:27] Sady Beb: 🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ πŸ‡³πŸ‡¬® _*ZUMUNCI WRITER'S ASSOCIATION*_πŸ“š✍🏻 [ *Zumunci mai d'orewa*🀝🏻] *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my daughter Fatima*😘😘 *Bismillahir rahmanir rahim* 41&42 Inda yake kwance Saudala ta k'arasa tana dariya k'asa-k'asa. Zama tayi san'nan ta kalle shi tace , "Ina ne yake ciwon ?" Shikam Abdul gaba d'aya ya zuba mata ido gani yake anya kuwa itace? . Abba ne ya katse masa tunani da fad'in , "Abdul ana tambayar ka." Kallan ta yayi yace "me kika ce? ." Dan k'aramin tsaki taja san'nan tace , "Ina ne yake maka ciwo?" Kallan ta yayi san'nan ya nuna ma wajan idon sawun sa. Da k'arfin gaske Saudala ta rik'e wajan ta fara murzawa cikin mugunta. Abdul bai san lkcn da yace, "Washhhhh". Kallan sa tayi san'nan ta juya tace , " Abba kaji da girman sa yana cewa wani washh kamar ba soldier ba." Baba ne yace "Kin san meya yake ji ne?." Tab'e baki Saudala tayi ta kuma danna wajan da k'arfi. Abdul ya cije baki dan yana jin zafi kawai daurewa yake. Abba yace "to nidai bara na koma ciki Allah ya k'ara sauk'i." Abba ya Mik'e ya fita Baba ma ya bi bayan sa. Saudala tana ganin sun fita ta kalle shi tace , "Nasan zaka yi mamakin ya akayi ka fad'i ko , to nice nan na zuba maka kuka a wajan ramuwar dukan da kayi min kenan." Kasa magana Abdul yayi ya zuba mata ido dan shi gaba d'aya ma ya manta da wani duka da yayi mata. Mik'ewa tayi tana fad'in, " to nidai na gama aiki na sai anjima ". Har kusa fita ta dawo baya tace , " Har yanzu ina nan akan baka ta indai kayi min sai na rama." STORY CONTINUES BELOW Sallama akayi aka shigo d'akin. Amsawa Abdul yayi yana fad'in , "Mubarak shigo mana." Shi kuwa Mustapha gaba d'aya hankalin sa nakan Saudala da take jira ya bata hanya ta wuce. Ganin irin kallon da yake mata sai taja tsaki tace , "Zan wuce ". K'ara lumshe ido Mustapha yana jin yadda muryar ta ke ratsa jikin sa. Cikin d'aga murya Saudala tace , " zan wuce kaban hanya!!." Firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi ya bata hanya ta wuce, "Sorry beauty wuce." Tsaki tayi ta fice daga d'akin. Bayan ta yabi da kallo yana k'ara jin sonta a ransa. Abdul kuwa ya cika yayi fam , sai wani b'ata rai yake. Cikin sanyin jiki Mustapha ya k'araso cikin d'akin yana fad'in, "Wallahi tafi k'yau a fili ." Banza Abdul yayi masa kamar bai ji shi ba. Ajiyar xuciya Mustapha yayi yace, "Wai Lafiya kake wani b'ata rai?" Abdul yace "bani da Lafiya kazo ka ishe ni da maganar Saudat." Mustapha yace "sorry ban sani ba , mai ya same ka?" Abdul yace "barshi bana buk'ata ." Murmushi Mustapha yayi yace , "To nace ai kayi hak'uri ko?." Abdul yace "to naji". Hira suka cigaba dayi. Saudala kuwa tunda ta bar d'akin take mita Mustapha ya cika kallo. Washe gari Abdul yaji dad'in k'afar sa sosai dan har main parlour ya fito ya zauna ana hira dashi. Suna zaune ana hirar yadda bikin Abdul zai kasance. Mustapha yayi sallama ya shigo parlourn. Mama tace " A'a Mustapha sannu da zuwa." Murmushi yayi yace " yauwa Mama, ina wuni.?" Cikin sakin fuska tace , "Lafiya lau , ya wajan Momyn take.?" Yace "Lafiya lau tace a gaida ke." Mama tace "ina amsawa." Hira aka cigaba dayi har Mustaphan . Sallama Saudala tayi ta shigo parlourn tana fad'in, "Mama wlh yau na gaji." Mama ta kalle ta tace " sorry my daughter ". Sam bata kula dasu Abdul da suke zaune a parlourn ba . Mama tace " Saudat baki ga Mustapha ba ku gaisa." Sai a lkcn Saudala ta lura da su a zaune , kallon su tayi tace , "Ina wuni?." Tana gama fad'ar hakan ta shige d'aki . Da kallo Mustapha ya bita yana yaba yadda uniform d'in yayi mata kyau. Shi kuwa Abdul wani irin abu yake ji a ransa yadda yaga wani d'an siket d'in da kad'an ya wuce guiwa. STORY CONTINUES BELOW A ransa yake fad'in , "Kuma yanzu haka maza suke kallan ta ko?." Wani abu yaji ya tokare masa k'irji . Sam babu wanda ya lura da halin da ya shiga . Tashi Mustapha yayi yai musu sallama ya fice. Abdul tashi yayi ya koma part d'in sa. Ko da ya koma tunani yake wai mai yasa ya damu da Yarinyar nan? Mai yasa yake jin wani abu akanta Wanda ko akan Hadiza baya jin sa. Zuciyar sa ta bashi amsa da cewa , "ka manta ita k'anwar kace." Da wan'nan tunanin ya kawar da wancan. Bayan kwana biyu. Yau ta kama saura sati hud'u bikin Abdul kuma yau ake shirin kai lefe. Bayan su Baba sun je Kano sun kai lefe anan mahaifin Hadiza wato Alhaji Abubakar yake fad'in , "Wato Alhaji Ahmad ina Neman wata alfarma a wajan ka." Baba ya muskuta yace , "Fad'i mana ina jinka." Yace "daman so nake nace maka mun d'aga bikin mun kai shi wan'nan da wata wata shida sbd na fison Hadiza ta kammala degree d'in ta kafin nayi mata aure, to da a cikin wan'nan shekarar zata gama amma yanzu ta sami matsala sai nan da wata shida zata kammala ." Tunda ya fara magana Baba yake kallan sa har sai da yakai aya san'nan Yace, "To banda abinka ba sai ayi auren ba in yaso sai ta k'arasa a gidan ta." Alhaji Abubakar yace "gaskiya nafi son ta kammala a gida hakan shiyasa na d'aga bikin." Ajiyar xuciya Baba yayi san'nan yace, "To zanje muyi shawara abinda muka yanke sai muyi waya." Yace "to shikenan ina jira". Suka yi sallama suka tawo Abuja. Ko da Baba ya koma bayani yayi ma Abba da Abdul abinda suka ce. Abba ya kalli Baba yace , "To ya kake ganin za'a yi yanzu?" Baba yace " abinda za'a yi tunda dai yana son Yarinyar kawai ya d'aga d'in. " Abba yace "ai Iya ce baza ta tab'a yarda ba." Kafin Baba yayi magana Iya ta shigo tana fad'in, "Menene naji ana bazan yarda ba.?" Abba yayi Mata bayanin komai bai b'oye ba. Iya tace "ai kam wan'nan abin bazai tab'a yuwa ba , bazan zuba ido ina kallan yaron nan har wata shida babu aure, wancan lkcn kun rok'e ni kuma na hak'ura wan'nan kuwa bazai yiwa ba." Baba Yace "to so kike a fasa auren ." Tace A'a-A'a na yarda su k'ara Bikin amma ni sai dai tazo a ta biyu dan bazan yarda ya kai wata shida babu aure ba , k'ila ma daga wata shidan su ce wata shekarar , to baza ta sab'u ba nan da sati biyu zai tare da matar sa." Baba ne ya saki baki yana kallan ta dan mamaki maganar ta yake tana nufin aure zata yiwa Abdul. Baba yace "Iya da ki bari lkcn yayi ai kamar yau zakiga wata shida tayi, amma kama.................." Kafin ya k'arasa ta katse shi da fad'in , "Ahmadu indai kun d'auke ni a matayin uwa to kar wadda ya kuma yi min wata magana, Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Kunji uku ko auren nan kamar anyi an gama." Tana gama fad'ar hakan ta bar wajan . Abba ya kalli Abdul da yake a zaune ya kasa ko motsi yace, "To Abdul ka dai ji abinda Iya tace sai dai kayi hak'uri ka karb'i k'addara dan tunda tace sai kayi auren nan to fa sai anyi , daman waccan lkcn dak'ar na shawo kanta ta yarda wan'nan lkcn kuwa baza ta yarda ba." Shiru Abdul yayi yana jin duk abinda suke cewa . Baba yace "Abdul sai dai kayi Addu'a in wan'nan auren da Iya zata had'a alkairi ne Allah ya tabbatar, in kuma sab'anin haka ne to Allah ya gag'gauta kawar dashi." Ajiyar xuciya Abdul yayi yace , "To Baba Allah yasa haka shi yafi alkairi." Baba yace "Ameen Allah yayi maka albarka ." Abdul ya mik'e jiki a sanyaye ya fita daga parlourn. Baba ya kalli Abba yace, "Da inda yadda zanyi da Iya ta hak'ura da wan'nan auren da nayi." Abba yace " kaja bakin ka kayi shiru indai baso kake ranta ya b'aci ba." Baba yace "Allah yasa haka shi yafi alkairi." Abba ya amsa da Ameen. ****** "Dady nifa Wallahi bazan iya bari har sai nan da wata shida zanyi aure ba , ina son Abdul Dady na yarda zan cigaba da karatun a gidan sa." Hadiza ce take wan'nan ihun. Dadyn ya kalle ta yace "haba daughter ki bari ki k'arasa karatun ki in yaso sai kiyi aure." Hadiza tace "A'a Dady ni nafi so na k'arasa a can in ma ya hanani na yarda zan zauna ." Dady yace "haba daughter ki bari ki k'arasa mana." Cikin d'aga murya Hadiza take cewa, "Indai ba bar Bikinnan a yadda yake ba aka ce sai nan da wata shida wallahi sai na shiga duniya." Tana gama fad'ar ta bar parlourn. Momy ta kalli Dady tace , "Nifa Allah Alhaji gwara abar Yarinyar nan tayi auren ta kar muje ta aikata abinda tace ". Dady yace " yanzu so kuke nace a mayar da bikin yadda yake .?" Momy tace "gaskiya haka shiya kamata." Ajiyar xuciya Dady yayi yace, "To k'ira min ita". Momy ta mik'e taje ta k'ira Hadiza. Zama tayi tace " Dady gani". Dady yace "na yarda za'a rage biki amma ki bari ya zama nan da wata biyu kinga lkcn na dawo daga London ." Hadiza tace "to na yarda ". Dady yace " yauwa my daughter Tashi tayi tabar parlourn. *WACECE HADIZA ?* 🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ πŸ‡³πŸ‡¬® _*ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION(YAN ASALI)*_πŸ“š✍🏼 [❄Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.] *_DON'T 4GET TO VOTE,COMMENT &ALSO FOLLOW US ON WATTPAD_* _*@AboriginalWrtersAsso.*_ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏼 *Dedicated to Saudala fan's*❤πŸ’ƒπŸ»❤ _*In kin san ke ba team din SAUDALA bace gwara ki fece*_πŸƒπŸΌ‍♀πŸƒπŸΌ‍♀πŸƒπŸΌ‍♀ *Bismillahir rahmanir rahim* 35&36 Kallan ta yayi har zai yi magana sai kuma ya fasa ya kalli Mama yace , "Mama ki bawa Saudat wan'nan sak'on ta kawo min ". Yana gama fad'ar hakan ya juya ya fita . Mama ta mike ta dauko abu a leda ta mikawa Saudala tace , " Maza tashi ki kai masa". Jiki babu k'wari Saudala ta mike ta nufi part dinsa. Tunda ta kai bakin k'ofar gaban ta yake fad'uwa , dak'yar ta tura k'ofar ta shiga da sallama. Tana shiga ta ganshi a zaune ya d'aura k'afa d'aya kan daya yana kad'awa A hankali ta k'arasa inda yake tace , "Yaya Abdul gashi in ji Mama." Ta fad'a tana miko mai ledar . Banxa yayi mata kamar bai jita ba , ta kuma maimaita Amma ko kallan ta baiyi ba . Tashi yayi yaje ya kulle k'ofar parlourn san'nan ya dawo ya dauki belt ya zauna. Saudala ganin ya kule k'ofar ga kuma belt a hannun sa sai hankalin ta ya tashi . Tayi aune ba taji ya zuba mata a baya . Aikam ta kwa'la k'ara tana susar bayan ta . Ya kuma zabga mata a baya, san'nan ya kalle ta yace , "Wato ke indai ba dukan ki akayi ba baza ki dawo hankali ba ko? Tunda dukan kike so kin had'u dashi." Ya fara duka ta ko ta ina zabga mata yake . Ihu take tana fad'in, "Dan Allah yaya Abdul kayi hakuri yasin bazan k'ara ba ." Ko kula ta bai yi ba balle ya daina dukan ta . Sai da yayi Mata duka san'nan ya kya'leta yace, "Daga yau indai kika muka yi min kunya sai nayi miki dukan da yafi haka, nonsense ." Saudala kuwa muryar ta ko fita bata yi sosai sbd kukan da tayi . Cikin tsawa yace "zaki tashi ki barmin d'aki ko sai na k'arya ki ." Dak'yar Saudala ta mike ta fara tafiya tana kuka .😭 Har ta fita daga d'akin bata ce komai ba. (lallai Saudala taji jiki πŸ˜‚) Fadila tana zaune a parlour taga shigowar Saudala tana tafiya tana dafe kai. Cikin tashin hankali Fadila ta nufe ta tana fadi'n, STORY CONTINUES BELOW "Sister lfy mai ke damun ki?" shatin belt Fadila ta gani a jikin ta , abinka da farar fata jikin ta duk yayi ja. Fadila tace "Sis wa yayi miki wan'nan d'ukan?" Ita dai Saudala ta k'asa magana ji take in tayi magana kanta zai fashe sbd ciwon da yake mata. Cikin d'aga murya Fadila take fad'in, "Mama ! Mama!! Kizo kiga Saudat bata da lafiya." Cikin sauri Mama ta fito daga d'aki tana fad'in, "Lafiya Fadila meya faru?" Fadila tace " Mama Saudat bata da lafiya." Sai a san'nan ta lura da Saudat a kwance a kan kujera. K'arasawa wajan ta tayi tana fad'in, "Lafiya me yasa same ta?" Fadila tace " ban sani ba naga dai jikin ta yayi alamar dukan ta akayi." waya Mama ta d'auko ta kira family Dr din su tace yazo yanzu tana neman sa. Jikin Saudala kuwa yayi zafi sosai , jijiyoyin Kanta har'bawa kawai suke. Abba ne ya sauko yana tmbayr lafiya. Ganin halin da Saudala take ciki hankali sa ya tashi , dan baya son abinda zai tab'a d'ayar k'anin nasa. Koda Dr ya iso bayan ya budu ta yayi mata al'lura bata dad'e ba bacci ya d'auke ta . Magani ya rbt yace a siyo ta dinga sha. Abba yace " Dr me yake damun tane ?" Dr yace " D'ukan da aka yi mata yafi k'arfin jikinta shine abinda ya haifar mata da zazzab'i da ciwon kai , Alhaji in tasa kasance tayi laifin da za'a daki ta to gaskiya a daina yi mata irin wan'nan dukan dan wata rana sai ayi mata illah ." Yana gama fadar hakan ya tattara kayan sa ya tafi. Abba ya kalli Mama yace, " Wanene yayi mata wan'nan dukan? " Mama tace " Ni kaina ban sani ba , ni dai nasan na tura ta d'akin Abdul ta kai masa magani amma bayan nan basan ida taje ba." Iya ce ta shigo d'akin tana matsar k'wallah tana fad'in, "Waye zai dake ta kuwa inba wancan mai k'atan kai ba , tunda ya dawo gidan nan ya takura mata yanzu ji dukan da yayi mata ." Tana gama fad'ar hakan ta koma kusa Saudala ta zauna .(Iya ta SaudalaπŸ€£πŸ˜†) Abdul kuwa bayan ya Saudala ta fita sai yake jin bai kyauta ba , dan yasan ta daku sosai . Amma in ya tuno rashin kunyar da tayi masa sai yayi tsaki yaji gwara da ya Zane ta. Wayar Sace ta ka'tse masa tunani ,nmbr Abba ya gani, yana d'agawa tun kafin yayi magana Abba yace, "Kazo yanzu ina son ganin ka," yana gama fad'ar hakan ya kashe wayar. Mikewa Abdul yayi ya nufi main parlour. Koda ya shiga bai gansu ba , muryar Mama ya jiyo a d'akin su Fadila sai ya karasa d'akin. Yana shiga tun kafin yayi magana Iya ta fara fad'in, "Ka dake ta kaji dadi da kasani baka bar ta da rai ba tunda baka kaunar ta". Abba yace " kuzo muje parlour muyi magana sbd kar maganar mu ta tashe ta daga bacci. " Suka koma parlour suka zauna , Abba ya kalli Abdul yace, STORY CONTINUES BELOW "Abdul kai kayiwa Saudat wan'nan dukan?" Abdul yayi kasa da kansa bai ce komai ba. Abba yace "shirun da kayi ya nuna min kai kayi mata wan'nan dukan, Amma banyi tunanin zaka iya yi mata haka ba , Ashe baka dauke a matsayin k'anwa ba , nayi tunanin ko wani ka gani yana dukan ta zaka tsaya ka rama mata, Ashe tunani na ba haka bane tunda gashi kai da kan ka kayi mata wan'nan dukan kamar zaka kashe ta ,meyasa kayi hakan?" Shiru Abdul yayi bai ce komai ba. Abba yace "Nasan halin Saudat akwai ta da tsokana amma ai kai ba yaro bane bai kamata ka dinga biye mata ba , yanzu gashi biye matan daka yi ga abinda ya jawo." "Dan haka ki da wasa kar ka k'ara maimaita abinda kayi , bance in tayi laifi kar a hukunta taba amma ayi mata dai-dai da shekarun ta ,kaji na fad'a maka". Sai a san'nan Abdul yace , " Kayi hakuri Abba insha Allah hakan ba zai kara faruwa ba." Abba yace " yayi kyauta". Suka amsa da Ameen. Abdul yace "Abba mganr tafiya ta Cross river dazu aka yo min waya ake sanar dani an fasa tafiya jibi gobe da asuba zamu wuce ." Abba yace "to Allah ya kai ku lafiya ." Suka amsa da Ameen. Da Asuba ana fitowa daga Abdul ya tafi Cross river. (Bye AbdulπŸ‘‹πŸ»πŸ€¨) Saudala kuwa bata farka ba sai karfe takwas na safe . Tana tashi ta mike zaune nan abinda ya faru ya dawo mata cikin brain . Ajiyar xuciya tayi tace, "Nima sai na sami hanyar da zan rama dukan da kayi min , dole nema in rama ." Fadila ta shigo tana fad'in, "Sister kin tashi Ashe, ya jikin naki?" Murmushi Saudala tayi tace , "Da sauki." Fadila tace " kina bacci d'azu yaya Abdul ya tafi Cross river kuma zai Dad'e a can ." Kallan ta Saudala tayi tana maimaita yayi tafiya bata rama dukan da yayi mata ba . Sai kuma tayi murmushi a ranta tace , "Gwara ma da yayi tafi k'afin ya dawo na gama tsara abinda zan yi masa ." Mama ce ta shigo tana fadin....................... Comment & Share Neat Lady✍🏼🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ πŸ‡³πŸ‡¬® _*ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION(YAN ASALI)*_πŸ“š✍🏼 [❄Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.] _*DON'T 4GET TO VOTE, COMMENT & ALSO FOLLOW US ON WATTPAD*_ _*@AboriginalWrtersAsso.*_ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏼 _*Ni haleema ashe haka nake da masoya daman, kwana hud'u da nayi banyi typing ba anan naga ruwan masoya na , nasu k'ira na a waya da masu yi min mgn ta prvt, babu abinda zance muku sai dai nace Allah ya bar kauna , hak'ik'a naji dad'in kulawar gare ni kuma nagode sosai.*_🀝🀝🀝😻πŸ₯°πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ₯° STORY CONTINUES BELOW *naji dad'in Addu'ar ku Allah ya bar mu tare*😘😘😘😘😘 _*Kai dan dad'in sai da nayi kamar na kunna gas na zauna akai*_πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *_daga yau posting d'in zai koma ranar Friday da Saturday , hakan ya faru ne sabida wani dalili , amma insha Allah duk rana daya zan dinga yi muku two page._* 🀦🏻‍♀ *Bismillahir rahmanir rahim* 37&38 Mama ce ta shigo tana fad'in , "A'a Saudat kin tashi kenan ya jikin ?" Saudala tace " Mama da sauk'i ." Mama tace " to Allah ya k'ara sauk'i ." Fadila ta amsa da Ameen . Iya ce ta shigo tana fad'in , "Yanzu Haleema sai da kuka bar wan'nan mai k'atan kan ya tafi , yanzu da gaske sai nan da shekara Ι—ayan zai yi auren ko ?" Mama tayi shiru bata ce komai ba dan bata da abinda zata ce mata. Iya tace " to shikenan bara Ummarun yazo ". Wajan Saudala ta tafi tana cewa , " Sannu Ζ΄ar nan ". Saudala tace " Yauwa Iya". Babu Wanda ya kuma magana a cikin su kowa yayi shiru. Bayan dawowar Abba Iya tasa shi a gaba akan maganar auren Abdul . DaΖ™yar ya shawo kan ta ta haΖ™ura . Washe gari Jikin Saudala ya warke sosai saidai har yanzu akwai ragowar tabo a jikin ta . **** Abdul kuwa suna Lafiya ya kira gida ya sanar dasu san'nan ya shiga yin abinda ya kai shi. *** Saudala ana zuwa makaranta dan sosai take fahimtar komai dan yanzu a cikin masu k'ok'arin ajin dole Saudala ta shiga cikin su. *BAYAN WATA GOMA* Kwanci tashi babu wuya a wajan Allah. Su Saudala an shiga jss 3 an kusa fita jenior . Saudala ta k'ara girma sosai dan yanzu ta d'anyi k'iba da tsa'wo amma ba sosai ba , alamun girma sun bai yana a jikin ta amma har yanzu halin yana nan. A yau ne Saudala ta cika shekaru goma sha hud'u a duniya . Shirye-Shiryen birthday d'in da Fadila ta had'a mata ake . Mai make up Fadila ta kira har gida aka zo taka yi musu . A harabar kuwa anyi decoration na flowers pink color masu k'yau . A jikin wani k'aton frame an rbt _HAPPY BIRTHDAY SAUDAT_. Khadija k'awar Saudala kuwa sune a gaba dan gaba d'aya da ita ake shirye_shiryen . Sosai Fadila tayi gayya kamar biki k'awayen ta sun zo sosai. Tunda aka gama yiwa Saudala make up Fadila take kallan ta dan gabad'aya ta canja kamar ba ita . Tana sanye cikin doguwar riga Ζ΄ar kanti mai fad'i daga ka'sa, anyi mata d'auri baya an fito da gashin ta . Mama ce ta shigo tana fad'in , STORY CONTINUES BELOW "Wai har yanzu Baku gama ba kun bar mutane su......... Maganar ta mak'ale sak'wamakon Saudala da ta gani kamar ba ita ba. Mama tace " Masha Allah Saudat kinyi kyau sosai. " Fadila rik'e hannun Saudala tayi suka fito . Sai kuwa kallo ya dawo kansu dan ba k'ara min k'yau suka yi ba. Sai kuwa aka fara ruwan hoton na . Wajan da aka tanada na zaman Saudala nan Fadila ta raka ta ta zaunar da ita . Wani k'aton cake aka d'auko aka ajjiye a gaban Saudala , a jikin cake d'in an rubuta *Happy birthday Saudat*. Wuk'a aka kawo mata Fadila ta rik'e hannun ta suka yanka cake d'in tare. Sai kuwa wajan ya rud'e da tafi . Yankowa Saudala tayi ta bawa Fadila a baki ita kuma ta bata. A haka aka gama taro bayan an raba memo da jaka da ke d'auke da hoton Saudala. Da Daddare Abba ya bawa Saudala k'yauta yana taya ta murnar birthday d'inta . Mama ma ba'a barta a baya ba dan duk wani Abu da akaci aka raba a wajan taron ita tayi shi. Fadila tana zaune a d'aki Saudala ta shigo tana fad'in , "Wlh na gaji ". Fadila tace " kema ki kwanta ki huta mana." Wanka Saudala tayi san'nan tayi sallah tabi lafiyar gado. Fadila kuwa charting take ita da k'awayen ta tana yi musu ban gajiya . Hotunan da suka d'auka su biyu ita da Saudala ta turawa Abdul. San'nan ita ma ta kwanta. Abdul kuwa lkcn suna zaune shida abokin sa Mustapha suna tsara yadda bikin Abdul zai kasance. Wayar sa ya d'auka yana kun'na data sak'on da Fadila ta turo mai ya shigo . Bud'ewa yaga hotunan da turo mai . A k'asan hoto ta rbt birthdayn d'in Saudat. Bud'e hoton yayi yana kallah , lkcn da ya bud'e na Saudat sai da gabansa ya fad'i . tunani yake a ransa anya kuwa wan'nan Saudat ce ? Cigaba yayi da kallan hoton baisan dalilin da yasa yake jin fad'uwar gaba ba. Ya shagala da kallan hoton , Mustapha ne ya tab'a shi. Firgigit ya juyo yana kallan sa . Mustapha yace "Lafiya tunanin me kake?. Kafin ya bashi amsa ya karb'i wayar yana muga abinda kake gani. Yana k'arb'a idon sa ya sauka akan hoton Saudala da tayi murmushi dimples d'in ta suka lob'a. Mustapha tace " Tabara'kallah Masha Allah , Allah yayi halitta anan wajan ." Sosai shima ya shagala da kallan k'yakyk'yawar fuskar ta. Kafin Abdul yayi magana ya riga shi da fad'in , "Abdul wan'nan fa?" Ya fad'a yana nuna masa Saudat. Bai San meye dalili ba yaji gaba d'aya haushin Mustapha yake. Cikin jin haushi yace " k'anwa ta ce." Mustapha yace " to ya akayi ban santa ba , nidai nasan Fadila ce kawai k'anwar ka." Cikin gajiya da zancen Abdul yace , STORY CONTINUES BELOW "Y'ar uncle ce ". Murmushi Mustapha yayi yace , " Tabbas yau na sami matar aure , hak'ik'a ban tab'a jin k'aunar wata mace ba a raina sai wan'nan. " Tsaki Abdul yayi yace " wan'nan y'ar Yarinyar kake so ? Gabad'aya fa shekarun ta 14 ." Murmushi Mustapha yayi yace, "Haka nake so daman ni nafin San na auri yarinya , kaga kafin nayi aure k'ila ta kai sha biyar , nidai ina rik'o ." Wani irin b'acin rai Abdul ya keji, cikin fusata yace , "Kaje ka same ta mana ina ruwa na." Mustapha yace " to meye naji haushi Mr man , nifa ba Hadixa nace ina so ba." Abdul yace " baza ayi mata aure yanzu ba tayi k'ank'an ta ." Mustapha yace " ko nan da shekara goma ne na yadda zan jira Wallahi. " Mik'ewa Abdul yayi yana fad'in , "Oho maka dai , sai da safe ." Ya fad'a yana shigewa d'aki. Mustapha kuwa wani irin k'aunar Saudala yake ji tana yi masa yawo jiki. Cikin sanyin jiki ya Mik'e shima ya shiga d'aki sa. Abdul kuwa tunda ya shiga d'aki yake tunanin me yasa yake jin haushi Mustapha dan yace yana son Saudat? A fili yace " to meyasa nake jin wani iri akan wan'nan Mara kunyar?" Tsaki yayi ya kawar da tunanin a zuciyar sa. Amma cikin ransa kawai tunanin ta yake. Sai ya sami kansa da son k'ara kallan hoton ta , wayar ya d'auko yana k'arewa Fuskar ta kallo. Sai ya sami kansa da yin murmushi. A haka bacci ya d'auke shi. Bayan kwana biyu Sosai Mustapha ya takurawa Abdul da zancen Saudala, indai suka zauna bashi da zance sai na Saudat. Shikam Abdul wani haushin sa yake ji a duk lkcn da zaiyi masa zancen ta , shiyasa da ya d'auko zancen sai Abdul ya sako wani zancen . Shi kansa ya rasa dalilin da yasa baya son Mustapha yayi masa zancen yana son Saudat. ***** A yau Saudala ta tashi da wani irin ciwon ciki kamar zata mutu. Family Dr d'insu aka k'ira ko da ya duba kallan Abba yayi yace, "Ba wata matsala bace kawai girma ne yazo mata ,sai an kula da ita sosai Alhaji domin duk Yarinyar data t'sinci kanta a wan'nan hali tana jin kanta dai-dai da kowa , dan haka a kula da ita sosai." Yana gama fad'ar hakan ya tafi. Tagumi Iya tayi tace, "Oh zamani wai yanzu y'ar shekara sha hud'u ce ta fara al'ada." Murmushi Mama tayi tace , "Iya kenan ai yanzu zamani ya canja y'ar sha uku sai kiga ta fara , sai dai muce Allah ya tsare su." Iya ta amsa da ameen. Bayan Saudala ta farka Fadila ta shigo ta zauna kusa ita tace, "My sister Ashe kin tashi ya jikin.?" Saudala tace "da sauk'i." Fadila tayiwa Saudala bayanin abinda ya same ta. Fadila tace "ai anyi muku a islamiyya ko?" STORY CONTINUES BELOW Cikin kunya Saudala tace, "Eh". Fadila tace " yauwa yanzu tashi kije ki gyara jikin ki". Tashi Saudala tayi ta shiga toilet. bayan ta gama shirya wa ta kasa fitowa parlour dan kunyar Mama take ji. Dak'yar ta fito ta zauna nasiha Mama ta kuma yi mata daga nan kowa ya cigaba da abinda yake gaban sa. Bayan wata d'aya. Shirye-shiryen Bikin Abdul kawai ake a gidan . Kayan lefe ake shirin kai wa Kano . An had'a lefe ak'wati ashirin komai na cikin kayan mai tsada ne. Su Baba ake jira su k'araso Dan maza ne zasu kai ba mata ba. Sosai Saudala take murnar zuwan su Baba. An gyara wa su Baba part d'in su wanda komai iri d'aya ne da part d'in Abba. Saudala tana tsaye a bakin gate tana jiran isowar su. Tana tsaye sai ga motar su ta shigo cikin gidan. Comment & Share Neat Lady✍🏼🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ πŸ‡³πŸ‡¬® _*ZUMUNCI WRITER'S ASSOCIATION*_πŸ“š✍🏼 [ *Zumunci mai d'orewa*🀝🏻] *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏼 *Dedicated to all my fan's*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ˜»πŸ˜» *Bismillahir rahmanir rahim* 39&40 Tun kan su k'araso Saudala ta nufe su a guje . Tun kan su k'arasa bud'e motar take k'ok'arin bud'ewa . Rungume Umma tayi tana farin cikin ganin Umman nata. Sakin ta tayi ta nufi wajan Baba ta ruk'unk'ume shi tana murna. Kallan ta Baba yayi yace , "Kece kika girma haka Saude"? Dariya tayi suka shiga parlourn gabad'ayan su. Bayan sun zauna Fadila ta kawo musu ruwa ta ajjiye. Abba yace " ai kamata yayi ku huce part d'inku in kun huta sai kuzo a gaisa ." Baba yace "ai gwara a fara gaisawa in yaso sai muje mu huta d'in". Gaisawa suka yi cikin mutunci da girma'mawa. Iya ce ta fito tana fad'in, " A'a Ahmadu Ashe kun iso ." Ta fad'a tana zama akan kujera. Har k'asa Baba ya durk'usa yace, "Iya barka da yamma, da fatan mun same ku Lafiya". Iya ta washe baki tace , " Lafiya lau Ahmadu ya mutan k'auyen ?" Yace " duk sun ce a gaida ke." Iya tace "Masha Allah". STORY CONTINUES BELOW Umma ta gaida Iya ta amsa cikin mutunci. Iya ta kalli Baba tace " Ahmadu Amma dai kunzo kenan ko?" Baba kallan Abba yayi yaga shima shi yake kallo yace , "Da bayan Bikin Abdul zamu koma in yaso daga ba........... Kafin ya k'arasa Abba yace, " A'a babu inda zaku kunzo kenan ." Iya tace "Hakan yafi dan in har suka koma nasan hali ba lallai ya kuma dawowa ba." Shikam Baba murmushi kawai yake . Ita kuwa Saudala tana mak'ale da Umma dan gani take kamar zata gudu ta barta. Mik'ewa suka yi suka nufi part d'insu. Saudala tana rik'e da hannun Umma har suka k'arasa. Bayan sallar i'sha su Abba da Mama da Fadila suka tafi part d'insu Baba dan yau a can za'a ci abinci. Aka ci abinci cikin farin ciki daga nan kowa ya koma part d'in sa. Saudala kam yau gata ga Umman ta . ***** Sosai Mustapha ya ta kurawa Abdul da maganar Saudat. Shi kuwa Abdul da Mustapha ya fara yi masa maganar Saudat sai yasan yadda akayi aka bar zancen. Yau dai Mustapha ya tsare Abdul yana tambayar , Mustapha yace, "Abdul ina da wani hali ne da zaka iya bani k'anwar ka ba?" Abdul yace "ni bance kana da wani hali ba." Yace " to meyasa duk lkcn da zan yi maka maganar ta sai ka dinga basarwa .?" Abdul yace " baka ganin yarinya ce har yanzu bata gama jenior school bama balle har tayi candy." Mustapha yace " na yarda zan iya jiran ta koda shekara goma ne." Ajiyar xuciya Abdul yayi yana jin wani iri a ransa. Kallan Mustapha yayi yace , "To naji ka bari mu koma gida tukunna." Mustapha yace " Allah ya kaimu." *Wanene Mustapha?* Mustapha Aminu shine cikakken sunan sa haifafen gari Abuja ne . A primary school suka had'u da Abdul . Tun daga nan jinin su ya had'u dan Abdul mutum ne mai k'ok'ari shima kuma Mustaphan haka wan'nan ne dalilin da yasa suka zama abokai. Tare suka yi secondary school daga , burin Abdul a duniya shine ya zama sojo haka shima Mustapha. Tare suka tafi England suka yi karatu har lkcn da suka tafi soja., Allah ya basu sa'a babu Wanda ya fad'i. Mustapha shine aminin Abdul dan Abdul bashi da wani aboki kamar Mustapha. Mustapha mutum ne mai mutunci da sanin ya kamata , bashi da wani hali Mara k'yau. Wannan kenan. Abdul da Mustapha shirye-shiryen dawowa gida suke dan sun gama abinda ya kaisu . Washe gari da asuba suka d'auki hanyar Abuja . *** Saudala kuwa ko makaranta bata je ba sabida murnar ganin iyayen ta . Suna zaune a main parlour gabad'ayan su Abbaya shigo yana fad'in, "Su Abdul fa sun taso tun Asuba ." STORY CONTINUES BELOW Baba yace "To Allah ya kawo su lafiya." Saudala da take a zaune kamar bata San me ake cewa ba a ranta tace , "Ranar ramuwa tazo kenan ". (Wai daman Saudala bata manta ba🀭) Mama ce tace " Saudat maza ki shiga d'aki na ki dauko key d'in d'akin Abdul kije ki gyara masa." Babu musu Saudala ta Mik'e ta dauko ta tafi. Koda ta shiga kallan parlourn take tana tuna inda yayi mata duka. K'wafa tayi san'nan ta Gyara d'akin . Koda ta fito daga d'akin kullewa tayi ta koma dakin su. Su Abdul basu iso ba sai dare , koda ya shigo gidan babu kowa a parlourn alamun kowa yayi bacci kenan. Part d'in sa ya nufa yana shiga d'akin bai tsaya wani Abu ba ya fad'a toilet dan yayi wanka ya rama sallolin dake kansa. Horn d'in motar su ne ya tashi Saudala daga bacci , daman kuma ba wani bacci tayi sosai ba dan dare bai yi sosai ba. Mik'ewa tayi cikin sand'a kar Fadila ta farka, fita tayi daga d'akin. Kitchen Saudala ta shiga ta d'auki k'wano ta zuba kuka ta had'a da ruwa ta juya . Fita tayi daga kitchen d'in cikin sauri ta nufi part d'in Abdul Dan tasan yanzu wanka yake. Ta shiga direct bedroom d'insa ta wuce , k'arar ruwa taji a band'aki alamun wanka ake . Murmushi tayi san'nan ta zuba wan'nan kukar a bakin toilet d'in, jin shiru alamun an gama yasa tayi saurin barin d'akin. Abdul kuwa ya fitowa bai kula da komai ba ya taka da k'arfin . Suuuuuuuuuuuuuuuuu timmmmmmmmmmm Abdul a k'asa ya kasa mik'ewa . Cikin dauriya ya mik'e amma Sam k'afar sa tak'i takuwa dak'ar ya mik'e ya zauna a bakin gado. Kallan bakin toilet d'in yayi yaga abu a wajan , kallan wajan ya kuma yi yana tunanin me ya kawo wan'nan baki toilet kuma. Saudala kuwa tana fita daga d'akin ta dinga dariya kamar zata shid'i .πŸ˜‚ Tana fad'in " kad'an ma ka gani mai hancin karas." Dak'ar bacci ya dauk'e Abdul da zugin da kafar sa take masa. Da Asuba k'afar Abdul tak'i dakuwa dak'ar yayi sallah ya koma ya zauna. Har gari ya waye Abdul bai shigo ba . Mama tace "wai jiya Abdul bai dawo bane."? Abba yace " ya dawo mana ." Tace "to lafiya har yanzu bai shigo ba." Abba yace "nima nayi tunanin hakan , amma bara naje na duba." Abba ya tafi d'akin Abdul, koda ya shiga a zaune ya tadda Abdul . Abba ya k'arasa wajan Abdul yana cewa, "Abdul lafiya har yanzu baka fito ba?" Abdul yace "Abba ina kwana." Abba yace "lafiya lau , lafiya baka fito ba?" Abdul yace "wlh jiya bayan na dawo na fito daga toilet kenan na zame na fad'i." Abba yace "Subahanallah sannu". Baba ne ya shigo yana tambayar meke damun Abdul d'in. Abba yayi masa bayani Baba yace, " To a kira me gyara mana." Abba yace "ai ni bansan ma a ina zan samu mai gyara ba a garin nan ." Baba yace "to ina Saude tazo ta duba masa." Abba ya kalli Baba yace , "Daman Saudat ta iya gyaran targad'e ne?" Baba yace "sosai ma dan a k'auye har zuwa ake yi to sbd halin ta yasa na hanata , dan in anzo gyaran indai tana jin haushin ka to Wallahi baza ta gyara ba sai dai ta dad'a fama maka." Murmushi Abba yayi yace, "Ai halin Saudat sai ita." Waya Abba yayiwa Mama yace ta tro Saudat. Saudala kuwa daman tasan za'a yi hakan. Shiga d'akin tayi da sallama , tace , "Abba gani". Baba yace " yayan ki zaki yiwa gyara, saura kuma kiyi halin naki." Murmushi tayi ta k'arasa wajan Abdul tana dariya mugunta. Jama'a ga Saudala zata yiwa Abdul gyaraπŸ€­πŸ˜‚ Nasan akwai drama 🀣 Ina team din Abdul πŸ™„ Comment & share Neat Lady✍🏼🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ πŸ‡³πŸ‡¬® _*ZUMUNCI WRITER'S ASSOCIATION*_πŸ“š✍🏻 [ *Zumunci mai d'orewa*🀝🏻] *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my daughter Fatima*😘😘 *Bismillahir rahmanir rahim* 41&42 Inda yake kwance Saudala ta k'arasa tana dariya k'asa-k'asa.+ Zama tayi san'nan ta kalle shi tace , "Ina ne yake ciwon ?" Shikam Abdul gaba d'aya ya zuba mata ido gani yake anya kuwa itace? . Abba ne ya katse masa tunani da fad'in , "Abdul ana tambayar ka." Kallan ta yayi yace "me kika ce? ." Dan k'aramin tsaki taja san'nan tace , "Ina ne yake maka ciwo?" Kallan ta yayi san'nan ya nuna ma wajan idon sawun sa. Da k'arfin gaske Saudala ta rik'e wajan ta fara murzawa cikin mugunta. Abdul bai san lkcn da yace, "Washhhhh". Kallan sa tayi san'nan ta juya tace , " Abba kaji da girman sa yana cewa wani washh kamar ba soldier ba." Baba ne yace "Kin san meya yake ji ne?." Tab'e baki Saudala tayi ta kuma danna wajan da k'arfi. Abdul ya cije baki dan yana jin zafi kawai daurewa yake. Abba yace "to nidai bara na koma ciki Allah ya k'ara sauk'i." Abba ya Mik'e ya fita Baba ma ya bi bayan sa. Saudala tana ganin sun fita ta kalle shi tace , "Nasan zaka yi mamakin ya akayi ka fad'i ko , to nice nan na zuba maka kuka a wajan ramuwar dukan da kayi min kenan." Kasa magana Abdul yayi ya zuba mata ido dan shi gaba d'aya ma ya manta da wani duka da yayi mata. Mik'ewa tayi tana fad'in, " to nidai na gama aiki na sai anjima ". Har kusa fita ta dawo baya tace , " Har yanzu ina nan akan baka ta indai kayi min sai na rama." Sallama akayi aka shigo d'akin. Amsawa Abdul yayi yana fad'in , "Mubarak shigo mana." Shi kuwa Mustapha gaba d'aya hankalin sa nakan Saudala da take jira ya bata hanya ta wuce. Ganin irin kallon da yake mata sai taja tsaki tace , "Zan wuce ". K'ara lumshe ido Mustapha yana jin yadda muryar ta ke ratsa jikin sa. Cikin d'aga murya Saudala tace , " zan wuce kaban hanya!!." Firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi ya bata hanya ta wuce, "Sorry beauty wuce." STORY CONTINUES BELOW Tsaki tayi ta fice daga d'akin. Bayan ta yabi da kallo yana k'ara jin sonta a ransa. Abdul kuwa ya cika yayi fam , sai wani b'ata rai yake. Cikin sanyin jiki Mustapha ya k'araso cikin d'akin yana fad'in, "Wallahi tafi k'yau a fili ." Banza Abdul yayi masa kamar bai ji shi ba. Ajiyar xuciya Mustapha yayi yace, "Wai Lafiya kake wani b'ata rai?" Abdul yace "bani da Lafiya kazo ka ishe ni da maganar Saudat." Mustapha yace "sorry ban sani ba , mai ya same ka?" Abdul yace "barshi bana buk'ata ." Murmushi Mustapha yayi yace , "To nace ai kayi hak'uri ko?." Abdul yace "to naji". Hira suka cigaba dayi. Saudala kuwa tunda ta bar d'akin take mita Mustapha ya cika kallo. Washe gari Abdul yaji dad'in k'afar sa sosai dan har main parlour ya fito ya zauna ana hira dashi. Suna zaune ana hirar yadda bikin Abdul zai kasance. Mustapha yayi sallama ya shigo parlourn. Mama tace " A'a Mustapha sannu da zuwa." Murmushi yayi yace " yauwa Mama, ina wuni.?" Cikin sakin fuska tace , "Lafiya lau , ya wajan Momyn take.?" Yace "Lafiya lau tace a gaida ke." Mama tace "ina amsawa." Hira aka cigaba dayi har Mustaphan . Sallama Saudala tayi ta shigo parlourn tana fad'in, "Mama wlh yau na gaji." Mama ta kalle ta tace " sorry my daughter ". Sam bata kula dasu Abdul da suke zaune a parlourn ba . Mama tace " Saudat baki ga Mustapha ba ku gaisa." Sai a lkcn Saudala ta lura da su a zaune , kallon su tayi tace , "Ina wuni?." Tana gama fad'ar hakan ta shige d'aki . Da kallo Mustapha ya bita yana yaba yadda uniform d'in yayi mata kyau. Shi kuwa Abdul wani irin abu yake ji a ransa yadda yaga wani d'an siket d'in da kad'an ya wuce guiwa. A ransa yake fad'in , "Kuma yanzu haka maza suke kallan ta ko?." Wani abu yaji ya tokare masa k'irji . Sam babu wanda ya lura da halin da ya shiga . Tashi Mustapha yayi yai musu sallama ya fice. Abdul tashi yayi ya koma part d'in sa. Ko da ya koma tunani yake wai mai yasa ya damu da Yarinyar nan? Mai yasa yake jin wani abu akanta Wanda ko akan Hadiza baya jin sa. Zuciyar sa ta bashi amsa da cewa , "ka manta ita k'anwar kace." Da wan'nan tunanin ya kawar da wancan. Bayan kwana biyu. Yau ta kama saura sati hud'u bikin Abdul kuma yau ake shirin kai lefe. Bayan su Baba sun je Kano sun kai lefe anan mahaifin Hadiza wato Alhaji Abubakar yake fad'in , STORY CONTINUES BELOW "Wato Alhaji Ahmad ina Neman wata alfarma a wajan ka." Baba ya muskuta yace , "Fad'i mana ina jinka." Yace "daman so nake nace maka mun d'aga bikin mun kai shi wan'nan da wata wata shida sbd na fison Hadiza ta kammala degree d'in ta kafin nayi mata aure, to da a cikin wan'nan shekarar zata gama amma yanzu ta sami matsala sai nan da wata shida zata kammala ." Tunda ya fara magana Baba yake kallan sa har sai da yakai aya san'nan Yace, "To banda abinka ba sai ayi auren ba in yaso sai ta k'arasa a gidan ta." Alhaji Abubakar yace "gaskiya nafi son ta kammala a gida hakan shiyasa na d'aga bikin." Ajiyar xuciya Baba yayi san'nan yace, "To zanje muyi shawara abinda muka yanke sai muyi waya." Yace "to shikenan ina jira". Suka yi sallama suka tawo Abuja. Ko da Baba ya koma bayani yayi ma Abba da Abdul abinda suka ce. Abba ya kalli Baba yace , "To ya kake ganin za'a yi yanzu?" Baba yace " abinda za'a yi tunda dai yana son Yarinyar kawai ya d'aga d'in. " Abba yace "ai Iya ce baza ta tab'a yarda ba." Kafin Baba yayi magana Iya ta shigo tana fad'in, "Menene naji ana bazan yarda ba.?" Abba yayi Mata bayanin komai bai b'oye ba. Iya tace "ai kam wan'nan abin bazai tab'a yuwa ba , bazan zuba ido ina kallan yaron nan har wata shida babu aure, wancan lkcn kun rok'e ni kuma na hak'ura wan'nan kuwa bazai yiwa ba." Baba Yace "to so kike a fasa auren ." Tace A'a-A'a na yarda su k'ara Bikin amma ni sai dai tazo a ta biyu dan bazan yarda ya kai wata shida babu aure ba , k'ila ma daga wata shidan su ce wata shekarar , to baza ta sab'u ba nan da sati biyu zai tare da matar sa." Baba ne ya saki baki yana kallan ta dan mamaki maganar ta yake tana nufin aure zata yiwa Abdul. Baba yace "Iya da ki bari lkcn yayi ai kamar yau zakiga wata shida tayi, amma kama.................." Kafin ya k'arasa ta katse shi da fad'in , "Ahmadu indai kun d'auke ni a matayin uwa to kar wadda ya kuma yi min wata magana, Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Kunji uku ko auren nan kamar anyi an gama." Tana gama fad'ar hakan ta bar wajan . Abba ya kalli Abdul da yake a zaune ya kasa ko motsi yace, "To Abdul ka dai ji abinda Iya tace sai dai kayi hak'uri ka karb'i k'addara dan tunda tace sai kayi auren nan to fa sai anyi , daman waccan lkcn dak'ar na shawo kanta ta yarda wan'nan lkcn kuwa baza ta yarda ba." Shiru Abdul yayi yana jin duk abinda suke cewa . Baba yace "Abdul sai dai kayi Addu'a in wan'nan auren da Iya zata had'a alkairi ne Allah ya tabbatar, in kuma sab'anin haka ne to Allah ya gag'gauta kawar dashi." Ajiyar xuciya Abdul yayi yace , "To Baba Allah yasa haka shi yafi alkairi." Baba yace "Ameen Allah yayi maka albarka ." Abdul ya mik'e jiki a sanyaye ya fita daga parlourn. Baba ya kalli Abba yace, "Da inda yadda zanyi da Iya ta hak'ura da wan'nan auren da nayi." STORY CONTINUES BELOW Abba yace " kaja bakin ka kayi shiru indai baso kake ranta ya b'aci ba." Baba yace "Allah yasa haka shi yafi alkairi." Abba ya amsa da Ameen. ****** "Dady nifa Wallahi bazan iya bari har sai nan da wata shida zanyi aure ba , ina son Abdul Dady na yarda zan cigaba da karatun a gidan sa." Hadiza ce take wan'nan ihun. Dadyn ya kalle ta yace "haba daughter ki bari ki k'arasa karatun ki in yaso sai kiyi aure." Hadiza tace "A'a Dady ni nafi so na k'arasa a can in ma ya hanani na yarda zan zauna ." Dady yace "haba daughter ki bari ki k'arasa mana." Cikin d'aga murya Hadiza take cewa, "Indai ba bar Bikinnan a yadda yake ba aka ce sai nan da wata shida wallahi sai na shiga duniya." Tana gama fad'ar ta bar parlourn. Momy ta kalli Dady tace , "Nifa Allah Alhaji gwara abar Yarinyar nan tayi auren ta kar muje ta aikata abinda tace ". Dady yace " yanzu so kuke nace a mayar da bikin yadda yake .?" Momy tace "gaskiya haka shiya kamata." Ajiyar xuciya Dady yayi yace, "To k'ira min ita". Momy ta mik'e taje ta k'ira Hadiza. Zama tayi tace " Dady gani". Dady yace "na yarda za'a rage biki amma ki bari ya zama nan da wata biyu kinga lkcn na dawo daga London ." Hadiza tace "to na yarda ". Dady yace " yauwa my daughter Tashi tayi tabar parlourn. *WACECE HADIZA ?* Comment & Share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ πŸ‡³πŸ‡¬® *_GASKIYA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“š✍🏽_* [Gaskiya d'aya ce,daga k'inta sai b'ata,burinmu mu fad'akar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.] *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to Sisters* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ *Bismillahir rahmanir rahim* 43&44 Hadiza Abubakar Musa shine cikakken sunan ta , haifaffiyar garin Kano ce . Ita kad'ai ce mace a wajan iyayen ta sai yayyan ta maza gudu uku . Iyayen ta sun d'auki son duniya suka d'aura mata duk abinda take so shi ake yi a gidan. Su had'u da Abdul a lokacin da tazo bikin wani abokinsa a Kano . Tunda Hadiza taga Abdul ta kamu da son sa . Hadiza wayayyiyar mace , shi kuwa Abdul daman yana son macen da ta waye tayi karatu . Tun daga lokacin suka fara Soyayya da Abdul. Hadiza fara ce amma ba sosai ba bata da k'iba ko kad'an yadda kika number one yaka take. Wannan kenan. STORY CONTINUES BELOW **** Har zuwa kwana biyu mahaifin Hadiza bai yo waya ba ya sanar dasu yadda suka yi ba. B'angaren Mustapha kuwa ya takurawa Abdul kan maganar Saudat , a kullum bashi da magana inba tata ba . Shikam Abdul ya rasa abinda yake damun sa , a duk lokacin da Mustapha zai yi masa maganar Saudat sai ya dinga jin wani iri a ransa. Saudala kuwa karatun ta take hankalin ta k'wance bata da wata damuwa . Ranar Asabar da yamma Iya ta k'ira su gaba d'aya aka zauna a parlour. Iya ta kalli Baba tace. "Ahmadu har yanzu iyayen Yarinyar basu janye akan maganar k'arin auren ba?" Baba ya gyara zama yace "Har yanzu dai basu ce wani abu ba." Iya tace "Ashe maganar auren da zaiyi yana nan kenan." Baba yace "Iya da a bari abar maganar auren nan kamar yau zaki ga wata shida tayi ." Iya tace "Dakata Ahmadu wannan auren ba za'a fasa shi ba ." Baba yace. "To Iya wai wa zaki aura masa ne?" Kafin Iya tayi magana Saudala ta shigo cikin dogon hijjabi da alama daga islamiyya take. Ta gaida su ta wuce d'aki. Iya tace "Na yanke shawarar zan had'a Abdul da ........ Kafin ta k'arasa Abdul yace. "Iya ki bar maganar auren nan bazan tab'a son wacce zaki aura min ba gwara ki bar zancen." Cikin masifa Iya tace , "Kar ka amince nidai na Riga na yanke hukunci zan had'a ka da k'anwar ka Saude."! Cikin tashin hankali Abdul yace.......... Am sorry bani da charji ne .🀦🏻‍♀🀦🏻‍♀🀦🏻‍♀ Comment & Share 🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya Ι—aya ce,daga Ζ™inta sai barinta,burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_ *STORY & WRiTTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my sisters*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *Bismillahir rahmanir rahim* 45&46 Cikin tashin hankali Abdul yace , "Amma dai wasa kike ko.?" Iya tace "Abinda yafi wasa nake ba wasa ba , wallahi tallahi kaji na rantse ko auren nan babu fashi." Abba ya kalli Iya yace, "Iya har nawa Saudat d'in take da zaki ce zaki Mata aure yanzu k'watak'wata shekarun ta nawa da za'a fara zancen auren ta." Iya ta galla masa harara tace , "Toh mai y'a ai gwara ka nuna min cewa y'ar kace , toh bara kaji wan'nan aure kamar anyi shi angama." Shikam Baba tunda aka fara maganar ko uppan bai ce ba. Mama ce tayi k'arfin halin cewa, "Iya kidai duba bai kamata a katse mata karatu ba san'nan............, STORY CONTINUES BELOW Iya ta katse ta da fad'in , " ni bance zan katse mata karatu ba ta cigaba da karatun ta Amma maganar wai tayi yarinta ke shekarun ki nawa aka kawo ki cikin gidan nan ? Ina baki fi shekara goma sha uku ba , dan haka bana son wata magana akan wan'nan auren , indai ba fatan alkairi zaki yi to kaja bakin ka kayi shiru. " Baba ne yace "Toh Iya Allah ya sanya alkairi ." Iya ta washe baki tace , "Yauwa da haka daman kuka ce tun farko ". Shikam Abdul ya rasa abinda yake masa dad'i , farin ciki yake ko kuma bak'in oho. Iya ta k'walawa Saudala kira , cikin sauri Saudala ta fito tana cewa gani. Iya tace " to kizo ki zauna mana". Zama Saudala tayi tana fad'in , "Gani ". Iya ta kalle ta tace "Saude na yanke hukunci zan had'a aure tsakanin ki da Abdul." Wata dariya Saudala ta fara tana nuna Iya tana fad'in, "Haba Iya yau kuma rikicin tsufan naki ne ya tashi ko, yo in ba rikicin tsufa ba ina ni ina wan'nan k'aton gardin, k'wata-k'wata nawa nake da zaki ce zakiyi min wani aure." Sakin baki Iya tayi tana kallan ta . Abba kuwa dariya Saudat ta bashi hakan yasa yy murmushi. Baba kuwa har cikin ransa yana son wan'nan had'in indai hakan ya kasance zai fi kowa murna. Cikin masifa Iya tace , "Jakar uban ki , mahaukaciya ni da zaka dinga yi min dariya , kuma maganar auren nan kamar anyi an gama." Wata dariya Saudala ta kuma saki tana fad'in, "Aure manya ". Ta k'ara k'yalk'yalewa da dariya harda k'wanciya. Cikin k'uluwa Iya tace"Aure kuwa kamar anyi an gama dan nan da sati biyu zuwa uku za'a yi auren." Tashi Saudala tayi tana fad'in, "Hajiya Iya tawa ". Ta juya zata shiga d'aki Baba yace, "Dawo ki zauna ." Zama tayi tana kallan Iya. Abba ya kalli Saudala yace , "Saudat Iya ta yanke hukuncin had'a aure tsakanin ki yayan ki Abdul, ba rikicin tsufa bane gaskiya ne ba wasa ake miki ba , ina fatan zakiyi mana biyayya a matsayin mu na iyayen ki." D'agowa Saudala tayi tana kallan Abba , ita dai tasan Abba baya yi mata irin wan'nan wasan , to da gaske auren za'a yi mata kuma ita da mai hancin karas . Ido ta zubawa Abba ta kasa magana gabad'aya. Abba ya katse mata tunani da fad'in, "Nasan kina tunanin makarantar ki to ki k'wantar da hankalin ki zaki cigaba da zuwa makaranta kinji." Ganin kowa yayi shiru amsar ta kawai ake jira sai kuwa ta fashe da kuka tana birgima a k'asa. Mama tace "Saudat Lafiya kike kuka .?" Cikin kuka tace "Aradu ba zan auri mai hancin karas ba, haka kawai ya dinga duka na kamar ya sami ball , gashi masifaffe , gashi k'ato kamar brown stroman na cikin wan'nan kokawar da aunty Fadila take gani , nidai bazan yarda ba ." Haba mai Mama zatayi inba dariya ba , cikin dariya Mama tace , " Au Saudat Abdul d'in ne brown stroman ". STORY CONTINUES BELOW Baki Saudala ta turo tace , " Ai yafi hakan ma." Baba ne ya daka mata tsawa yace , "Ki shiga hankalin ki ko yanzu nayi miki duka !." Shiru Saudala tayi tana share hawaye. Iya tace "Ai ko ki amince ko karki amince wan'nan aure kamar anyi an gama." Abdul kuwa yana zaune ya kasa magana Dan bai San mai zai ce ba. Shi kansa Abba yana farin ciki da wannan fad'i na Iya , Mama ma har cikin ranta tana son hakan ta kasance. Umma kuwa da tunda aka fara maganar ta bar parlourn bata sake dawowa ba. Saudala kuwa ido ta zubawa Abdul tana kallan sa tana tuno irin marikan da tasha a wajan sa. Ko mai ta tuna sai tayi murmushi ta kalli Iya tace...................... Ita kuma wan'nan mai ta tuna πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ *Ashe haka masoyan Saudala suke da yawa , ban san masoyan book d'in nan sunkai haka ba yasin , har wad'an da bana tunanin suna karantawa Ashe suma y'an lab'e ne, bani da bakin godiya a gare ku sai dai nace Allah ya bar kauna , Allah ya had'a mu tare a Aljannatul fiddausi Ameen.*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜ Much kauna my fan's😘😘 *kuyi hak'uri da wan'nan Aradu yau bana gida ina can ina k'waso shoki*😁😁😁😁😁😁😁😁 Comment & Share Neat Lady✍🏻 Neat Lady ✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya Ι—aya ce,daga Ζ™inta sai barinta,burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to Kululu and Saudala fan's groups.*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° *Bismillahir rahmanir rahim* 47&48 Kallan Iya Saudala tayi tace , "Iya na yarda ". Tana gama fad'ar hakan ta mik'e ta bar wajan da gudu. Washe baki Iya tayi tana fad'in, " Allah yayi miki albarka , kai naji dad'in wan'nan abu sosai ." Shikam Abdul mamakin Saudala yake ganin lkcn d'aya ta amince kamar ba ita ta gama kuka ba anya ba wani abu ta shirya ba . (nima dai haka nace yasin πŸ˜‚) Abba yace "to Alhamdulilah tunda dai itama dai ta amince ai shikenan ." Baba dai banda murmushi babu abinda yake . Abdul ya kalli Abba yace , "Abba na manta ban sanar daku ba tun muna cross river Mustapha ya dame ni akan maganar yana son Saudat kuma yanzu ga m............, Katse shi Iya tayi da fad'in , "kai kasan wani Mustapha ni dai na gama magana nan da sati biyu masu zuwa za'a d'aura maka aure da Saudat." Abba ya kalli Abdul yace , "To ai maganar Saudat kuma ta wuce sai dai ka k'ira min shi na fad'a masa da kaina , san'nan za'a kira can gidan su matar taka a sanar dasu abinda yake faruwa ." Abdul yace "to shikenan Abba zan kira shi insha Allah." Da haka kowa ya mik'e yabar wajan. Saudala kuwa tunda ta shiga d'aki take k'yalk'yala dariya harda tsalle , Cikin dariya tace "Zaka gane kuran ka mai hancin karas yasin duk abinda kayi min sai na rama ."( tab wata ramuwar zata yi kenan 🀣) STORY CONTINUES BELOW Zama tayi tana tuno muguntar da zata had'awa Abdul . Abdul kuwa tunda ya shiga d'aki yake ta tunani wai mai yasa Saudat ta amince da wan'nan auren ? , yanzu ya Hadiza zata ji idan taji zai auri wata kafin ita , yasan Hadiza da d'an banzar kishi yasan za'a yi bala'i. Bayan sun tashi daga meeting d'in Baba ya d'au waya ya kira mahaifin Hadiza ya sanar dashi abinda suka yanke . Alh Abubakar yace "babu matsala ai daman namiji mijin mace had'u ne , amma daman muma mun rage lkcn Bikin ya dawo nan da wata biyu in Allah ya kaimu." Baba yace "babu komai Allah ya kaimu ." **** Bayan Dady ya kashe wayar nan ya kira Momy ya sanar da ita abinda ya faru . Cikin masifa Momy ta fara fad'in, "lallai ma ai fad'a musu bama son y'ar ne da zamu aurar da ita gidan kishiya , to wallahi bazata sab'u ba wai bindiga a ruwa sam babu yadda za'a yi Hadiza ta shiga gidan kishiya , ita kad'ai fa muka Haifa mace , haba sam bazai yuba ." Dady yace "A'a to naga namiji mijin mace hud'u ne dan iyayensa zasu aura masa wata ai banga aibun hakan ba." Momy tace "ai gwara a fasa auren da ta shiga gidan kishiya , ni kad'ai ce matar ka a duniya dan haka ita ma baza ta zauna da kishiya ba ." Tana gama fad'ar hakan mik'e ta shige d'aki. Tsaki Dady yayi ya d'auki waya ya kira Hadiza yace tazo yana Neman ta a parlour. Shigowa tayi ta zauna tace "Dady gani ". Yace " Hadiza yanzu dangin mijinki suka yi min waya suke sanar dani mahaifiyar su wato kakar Abdulrahman ta had'a aure tsakanin da y'ar kanin mahaifinsa kinga ke a matsayin ta biyu dan nan da sati biyu masu zuwa za'a d'aura masa aure da ita." Wani irin ihu Hadiza tayi Wanda yasa Momy fito daga d'aki da sauri , ihu take tana fad'in , "Wallahi bazan zauna da kishiya ba sai dai ya zab'a koni ko ita ." Tana gama fad'ar haka ta fice daga parlourn tana ihu kamar sabuwar kamu. Momy ta kalli Dady tace, "kaga abinda nake fad'a maka ko , haba taya za'ace yarinya y'ar shekara ashirin da hud'u zata zauna da kishiya , haba ai da sake wlh." Fuuuuu ta fice daga parlourn tana sababi. Dady kuwa hankalinsa ya tashi ganin yadda hankalin y'ar lelan Ζ΄arsa ya tashi. **** Abdul kuwa yana zaune yana tunani wayar sa ta fara ringing yana dubawa yaga an rubuta _Habibty_ cikin sauri ya d'aga , tun kafin yayi magana fara magana cikin kuka tana fad'in, "Ashe baka sona Daman ,Ashe zaka iya auren wata kafin ni , to gaskiya sai dai ka zab'a koni ko ita ". Bai katse taba har saida ta gama san'nan yace , " haba my Hady yanzu idan akace miki bana sonki zaki yarda? bayan kin San kece mace ta farko dana fara so a dunyar nan , haba my Hady ki kwantar da hankalin ki dan wacce aka had'a mu auren da itama ni sam ba sonta nake ba , kwata-kwata bata cikin tsarin mata da nake so , ke k'adai ce a raina my Hady kinji." Ajiyar xuciya Hadiza cikin shagwab'a tace, "Amma pls kayi min alk'awari ." Yace "ki fad'i duk abinda kike so insha Allah ni kuma zan yi miki." Hadiza tace "bana son wani Abu ya shiga tsakanin ka da ita , kayi min alk'awari nice mace ta farko da zaka fara sani , kwata-kwata ma bana son ka Santa Ζ΄a Mace in sabida kar ta rainani." Murmushi yayi a ransa yace , "banda abinki mai zaisa na kula wan'nan Mara kunyar Yarinyar." A fili yace , "nayi miki alk'a........... Wayar sace ta mutu babu charji ba tare da yayi mata Alk'awarin ba. STORY CONTINUES BELOW Amma shima har cikin ransa baya jin zai iya had'a jikin shi da Saudat , baka yi mata komai bama ya ka cika da rashin kunya bare kuma ......🀭 (nidai nace Abdul kenan). Duk abinda yake fad'a Saudala tana bakin k'ofa tana jinsa , sai da ya gama wayar san'nan ya shigo tana fad'in, " Mai hancin karas an fad'a maka nima ina sonka ne ? , Hmmmmm na amince da auran ka ne sabida wata manufa tawa amma da ko a k'afa aka d'aura min kai Aradu sai na kwance na gudu ." gwalo tayi masa ta juya ta fice a guje .😜 Am sorry kwana biyu ina busy ne 🀦🏻‍♀ I need more comment yasinπŸ˜‰ Comment & Share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya Ι—aya ce,daga Ζ™inta sai barinta,burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to HAYATUL MAHAYAT fan's group*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° *Ina jin dadin comment dinku sosai, musamman ma UMAIMA ALIYU, bani da bakin da zan gode miki sai dai nace Allah yabar zumunci.*😘😘 *_Congratulation sis khadija to completed ur comedian novel KULULU, kuskuren da kika yi a ciki Allah ya yafe miki,Allah ya baki ikon fara sabon book, don't forget ur sis Neat Lady she always supporting u._*πŸ₯°πŸ₯° *Bismillahir rahmanir rahim* 49&50 Tunda ta fita Abdul ya bita kallo yana mamakin wayon da Saudala take dashi. ****** Hadiza ce zaune a d'aki ta zuba uban tagumi , har Momy ta shigo d'akin bata San ta shigo ba , tab'a Momy tayi tana fad'in, "Daughter Lafiya me kike tunani har na shigo baki sani ba?". Kallan ta Hadiza tayi ta fashe da kuka tana fad'in, " yanzu Momy kema kin yarda na zauna da kishiya kenan , kina ji kina gani za'a kaini gidan kishiya,wlh Momy ina mutukar kishin Abdul ji nake zan iya kisa a kansa." Momy tace "yi shiru my daughter ki kwantar da hankalin dabai zaki shiga gidan ba , ita wacce za'a had'a sun ai nasan ba sonta yake ba ke ko yana sonta sai nasan yadda nayi aka fitar da ita daga cikin gidan , shikuma ki mallake shi bb abinda ya isa yace , dan haka bana son kisa damuwa a ranki ." Ajiyar xuciya ta sauke san'nan tace , "shiyasa nake sonki Momy na , Amma Momy kiyiwa Dady magana a k'ara rage bikin kinji." Ta fad'a cikin shagwab'a . Momy tace "ai daman nima so nake ya dawo nan da kamar sati hud'u kinga tsiran ku da wacce za'a aura masa sati biyu kenan, zan yi masa mgn karki damu." Murmushi Hadiza tayi tace , "Allah ya bar min ke my Momy." Momy tace "yanzu dai ki kwanta ki huta bara naje na same shi." Ta fad'a tana ficewa daga d'akin. ***** Saudala ce zaune a parlour tana kallo ita da Fadila, kasancewar sun sami hutun makaranta shiyasa kullum tana gida. Abdul yayi sallama ya shigo parlourn , Fadila ce kawai ta amsa masa dan Saudala ko juyo bata yiba. Zama yayi yana fad'in, "my k'anwa ina Mama ?" , Fadila tace "tana d'aki bacci take yi." Yace " Umma fa?" Fadila tace "itama haka". Bai k'ara cewa komai yayi shiru yana satar kallon Saudala da take kallon ta . STORY CONTINUES BELOW Restyling suke kalla a MBC Action , ana haka kuwa aka hasko brown stroman ya fito yana huci , kallan TV Saudala tayi san'nan ta juyo ta kalli Abdul da shima ita yake kalla , sai kuwa ta fara dariya tana cewa,πŸ˜‚ " Mai hancin karas kaga mai kama da kai , Aradu komai naku iri D'aya ne har muguntar , ka daure kaza k'ato kamar sa ."🀣 Haba sai Fadila ta fara dariya kamar zata shid'e , shikuwa Abdul maimakon yaji haushin ta sai kawai yaji ta birgeshi yadda take dariya ba k'aramin kyau tayi ba . Ita kuwa Saudala ganin bai ji haushi bs ya zuba mata ido kuma sai tace , "Wanda yake kallona Allah yasa ya zamu mai k'aton tumbi kamar Nuhu kansila na dad'in kowa ." maganar ta bashi dariya sosae hakan yasa yayi d'an yi dariya kad'an πŸ˜„ kuma ya had'e rai kamar bashi ba.😠 Ganin yadda ya had'e rai Sai Saudala ta rike baki tace , "Tab wayaga Ladi kod'au." tana gama fad'ar hakan ta mik'e ta shiga d'aki. Shikam Abdul Sam baiso ta tashi daga parlourn ba , yaso ta zauna ya cigaba da kallan ta. Fadila kuwa dariya take hadda hawaye tana maimaita maganar Saudat. Mik'ewa Abdul yayi ya fice daga parlourn yana murmushi . Da dare Mustapha ya amsa kiran Abba , Abba yayiwa Mustapha bayanin komai yana kuma bashi hak'uri duk da daman bai zo ya sanar yana sonta ba. Sosai Mustapha ya danne B'acin ransa ya kuma karb'i k'addara. Bayan ya fito daga wajan Abba d'akin Abdul ya wuce , a zaune ya same shi yana danna waya , da sallama Mustapha ya shiga parlourn yana fad'in, "kaga angon two weeks ." Murmushi Abdul yayi yace , "Mustapha yaushe ka shigo?" Mustapha yace ,"Dady ne yayi kirana ya sanar dani abinda yake faruwa. " Dafa shi Mustapha yayi yace , "kar ka damu komai ya wuce a wajena , yanzu kawai mu fara shirin biki." Abdul yace, hmm shirin me"?. Mustapha ya harare shi yace , "ban sani ba ." Murmushi Abdul yayi yace , "na bar maka komai a hannun ka duk abinda ya dace ayi." Mustapha yace "yauwa kokai fa da anaso ana kaiwa market." Shidai Abdul bai kula shi ba. Mustapha yace "Kai mutumina da zafin ka ka taso mata biyu a lkcn D'aya." Ya fad'a yana dariya . Tab'e baki Abdul yayi yace , "ka daina saka wan'nan kwailar a magana malam." Rik'e baki Mustapha yayi yana fad'in, "wace Kwaila a cikin su to ."? Ya fad'a yana dariya. Hararar sa Abdul yayi yace , " wace kuwa in ba wan'nan Mara kunyar Saudat ba, badan Iya ta matsa ba ni mai zai kaini auren yarinya , Yarinyar ma kuma wai Saudat mtwsss." 🀭 Dariya Mustapha ya fara yana fad'in , "kai dai ka fad'i gsky dan na dad'e da fahimtar son Saudat d'in kake , sbd yadda idan inayi maka maganar ta sai ka dinga wani b'ata rai." Tsaki Abdul yayi yace , "Na rasa wacce zan so sai waccan kwailar , mai zan so a jikin ta,Allah ya ki yaye." Mustapha yayi murmushi yace , "kada nan gaba kace mana in ba ita ba sai rigiya." Hararar sa Abdul yayi yace, Aikam ranar baza tazo ba." Sallama akayi a tare da shigowa parlourn, Saudat ce ta shigo tana wani yamitse fuska. Ganin Mustapha a parlourn yasa tace , "ina wuni." Amsawa yayi yana murmushi . Kallan Abdul tayi tace , "brown stroman kazo inji Abba ." tana gama fad'ar hakan ta juya ta fice daga parlourn. Mustapha kallan Abdul yayi yace , "A'a yaushe kuma ka koma brown stroman.?" Ya fad'a yana b'oye dariyar sa. Banza Abdul yayi masa ya mik'e ya fice daga parlourn. Koda ya shiga parlourn Abba shida Baba da su Iya ne a zaune , zama yayi yace, "Abba gani." Baba yace "gidan iyayen matar ka ne suka yo wai sun maida Bikin ku nan da sati hud'u ." Tun kafin Abdul yayi Iya tace , "kai Amma wad'an nan mutane suna raina mana hankalin , to baza mu amince ba su bar shi yadda suka saka da farko." Baba yace "to yanzu mai kuke ganin za'a ce musu , dan kunga gsky bazai yu ace an d'aura auren sa nan da sati biyu san'nan kuma sati biyu masu zuwa a kuma gaiyatar mutane ba sai dai in a had'e d'aurin auren." Abba yace "gsky ne mgnar ka sai dai in had'ewa za'a yi dana Saudat d'in." Iya tace , "Sam baza'a had'e ba domin Saude nake so ta zama uwar gida ba ita ba , sai kuyi gayya Ana farko na biyu kuma sai ku danyi saffa-saffa." Baba yace, "yanzu kenan an barshi nan da sati had'un ko.?" Iya tace, "eh an bar shi Dan mu ba k'ananan mutane irin su ba." Shi kuwa Abdul wani haushi yake ji a ransa wai nan da sati hud'u yana da mata biyu kamar wani tsoho. Abba ya katse masa tunani da fad'in, "Abdul ya gidan naka an gama komai ko.?" Abdul yace "eh Abba an gama komai ansa ." Abba yace " to Alhamdulilah , zaka iya tafiya." Mik'ewa Abdul yayi ya fice daga parlourn. *BAYAN SATI D'AYA* I need more comment 🀺 Comment & Share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya Ι—aya ce,daga Ζ™inta sai barinta,burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to My Fan's*πŸ₯° *_Bazan manta da k'aunar da kuke nuna min , ina yinku nima irin totally d'in nan πŸ’ƒπŸ»._* *Bismillahir rahmanir rahim* 51&52 *Bayan sati d'aya*. Shirye-shiryen biki ake sosai , ta b'angaren Abdul kuwa har yanzu ya kasa tantance abinda yake rainsa, farin ciki yake ko akasin haka oho . + B'angaren Saudala kuwa gyara take d'auka wajan Mama , Dan yanzu in ku kaga Saudala ba lallai ku gane ta , ta k'ara fari sosai har wani yellow take ,ta k'ara ciki kamar ba y'ar sha hud'u zuwa sha biyar ba . Sam Saudala bata damu da wani aure ba dan in ba tuna mata akayi ba mantawa take. Saudala ce a zaune tana tunanin wai ita za'a yiwa aure , a ranta tace , "Wai yanzu iskancin da 😲 malamin islamiyya ya fad'a mana anayi in anyi aure nima sai nayi". A fili tace , " Tab ni ba y'ar iska bace Aradu bazan yarda ba , in ba haka ba sai na had'a shi da Abba da Baba🀭 Da wan'nan shawara ta kawar da zancen daga zuciyar ta. An had'awa Saudala lefe kamar yadda aka yiwa Hadiza itama haka aka yi mata . Bayan kwana biyu Yau ta kasance saura kwana uku d'aurin aure , B'angaren Fadila shirin biki kawai take . Abdul kuwa baya wani shiri Mustapha ne kawai yake shirin biki. Da daddare ana zaune a parlour ana hirar yadda biki zai kasance. Saudala kuwa tana d'aki tana game , yunwa ta fara ji hakan yasa ta mik'e ta fito parlour, bata tsaya kula mutanen parlourn ba direct kitchen ta shiga . Abinci ta zuba san'nan ta fito parlour ta zauna tana ci . Mutanen parlourn kuwa banda maganar biki bb abinda suke yi, duk tana jinsu tayi musu banza kamar bata san me suke cewa ba. Haka suka gama hirar su suka tashi kowa ya wuce part d'insa . *Rana bata k'arya* Yau juma'a bayan an sakko daga masallaci aka d'aura Auren *_Abdulrahman Umar Abdulrahman_* da *_Saudat Ahmad Abdulrahman_* akan sadaki dubu D'ari. Bayan gama d'arin auren Abdul ya shigo gidan shida MMustapha, main parlour suka shiga suka tadda Hajiya Iya akan kujera an d'au kyau , tana ganin sa ta washe baki tana fad'in, "kaga ango wan'nan babbar riga haka ." Murmushi yayi baice komai ba ya juya zai fita , muryar Fadila yaji tana cewa , "ina kuma zaka je bayan ba'ayi hotuna ba." Juyowa yayi yace "To gani ai na tsaya." Fadila tace "kokai fa , bara a kira Saudat d'in." Juyawa tayi ta shiga d'akin , babu jimawa ta fito tana rik'e da hannun Saudala. Fadila tace "yauwa bro ga Saudat d'in ta fito." Yana juyowa suka had'a ido da Saudala , aikam ta sakar masa wata harara tare da murgud'a baki. STORY CONTINUES BELOW Shikam Abdul gabansa ne ya fad'i ganin yadda Saudat tayi bala'in k'yau. Ganin kallan da yake mata yayi yawa sai kuwa tayi tsaki tace , "wai kai Lafiya kake kallona, da wani idonka kamar na mage ." ta fad'a tana murgud'a bakiπŸ˜— Cikin sauri ya d'auke kai ganin tana niyar yarfa shi.πŸ˜‚ Iya tace, "Amma Saude anyi y'ar jakar uba , mijin naki kike fad'awa haka." Ta fad'a tana rik'e baki. Cikin tsiwa Saudala tace , "su miji manya."🀣 Tafa hannu Iya take tana fad'in, " lallai kin rik'a , to bara Iyayen naki suzo sai ki maimaita abinda kika fad'a. " Tsaki Saudala tayi tace, "Wai me zanyi ne kika saka na fito." Ta fad'a tana kallan Fadila. Fadila da take kallan dramar Abdul da Saudala tace , "hotuna fa za'a yi." Zare ido Saudala tayi tace, "nayi hoto dawa."? Fadila tace " gabad'ayan mu." Saudala tace "yauwa yanzu naji mgna." Fadila ta rik'e hannun Saudala tayi suka k'arasa wajan dasu Abdul suke , kallan mai hoton tayi tace "Bismillah zo ka fara." K'araso photograph yayi yace ,"ku shirya zan fara d'auka." Kusa da Abdul Fadila ta kai Saudala san'nan tace , "yauwa d'auki." Cikin sauri Saudala tace, "kuturu yasin bazan tsaya kusa da brown stroman ba sai dai a fasa hoton." Ta fad'a tana shirin barin wjn. Abdul ganin tana shirin ba dashi a gaban mutane cikin zafin nama ya jayo Saudala ta fad'o jikin sa . Bud'e baki Saudala tayi tace, "wayyo Allah na shikenan na zama y'ar iska."πŸ˜‚ *TSOKACI* _*wannan azumi na tasu'a da Ashura yana fa mutuk'ar falala , duk Wanda ya azumci wan'nan azumi Allah zai yafe masa zunuban sa na shekarar da ya wuce da kuma wacce zata zo , Dan haka y'an uwa musulmai mu daure mu azumici wan'nan ranaku ko da bamu samu na yauba mu daure mu kauda shed'an muyi na gobe , na gobe wato ashura shine wadda Annabi yayi har yace wata shekarar zaiyi gabad'aya, to Allah baisa ya kai wata shekarar ba yayi wafati , Allah yasa muna daga cikin wad'an da Allah zai yiwa rahma a cikin wan'nan rana Ameen.*_πŸ™πŸ» _*masu bina prvt suna cewa na turo Saudala dg farko pls su tmbya a cikin group , message suna yi min yawa aradu.*_πŸ˜‰ _kwana biyu ina busy ne ku diga hak'uri πŸ˜₯_ Comment & Share Neat LadyπŸ˜€✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to this guys Mai gwaza , Jikanyar mai Auduga , Ummu nabil, Ummu Hanash , Inna horo ,Zeey, Aunty Baby , Aysha Aliyu, Mrs basakwace, Kausar luv, Fauziyya, Aisha, Mmn adnan, Mummy and my special sis miss xerks.* _love u all my sisters, πŸ₯° don't 4get ur k'anwa neat Lady she always love u._ _*happy happy happy happy happy happy🎸 birthday to me*_πŸ’ƒπŸ»πŸŽ‚ STORY CONTINUES BELOW *TODAY IS MY BIRTHDAYπŸŽ‚πŸŽ‚ AM + 1*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *Bismillahir rahmanir rahim* 53&54 "Wayyo Mama kizo kar wan'nan mutumin................🀭 Saudala ce take wan'nan ihun harda wata munafukar k'wallah .πŸ˜‚ Hannu yasa ya toshe Mata baki yana hararar ta , amma a jikin sa jiya ke kamar su dauwama a haka . Hakan da sukayi yayi bala'in k'yau , hakan yasa camera man ya fara zuba musu pic. Wani abokin Abdul ne yayi tafi yana fad'in, " Wow gsky fa kunyi bala'in dacewa da juna , wan'nan irin style kamar a India, Allah ya bar k'auna mutumina ."πŸ˜‰ Cikin sauri ya cika Saudala ta bar jikin sa. Dariya Fadila take tana fad'in, "kai Amma hotunan sunyi k'yau sosai." Abdul kallan Mustapha yayi da yake k'unshe dariya , hararar sa Abdul yayi yaja hannun sa suka bar parlourn. Ganin ya fita abokansa da suka shigo suma suka bi bayan sa. Iya ta bishi da kallo tana fad'in, "Munafiki yana so yana kaiwa kasuwa , dan rashin kunya yanzu a gabana ji yadda ya wani dadimi Saude , kai yaran zamani sai da a barsu."😏 Ihun Saudala ne yasa suka juyo , a kwance suka ganta tana faman birgima a k'asa tana fad'in, " shikenan ya tab'a ni ya mayar dani y'ar isa , wayyo Umma kizo yayi min ciki. "πŸ˜‚ Sakin baki Iya tayi tana kallon ta dan ita kanta Saudala ta bata dariya , Iya ta kalle ta tace , " kuji min yarinya dan ya rik'eki shine zaki ce yayi miki ciki , tab lallai da sauran ki." Cikin kuka Saudala tace , "ai Umma ce ta fad'amin tace indai namiji ya rik'e min hannu shikenan yayi min ciki." Fadila kuwa dariya take hadda rik'e ciki .πŸ˜‚ Jin ihun Saudala yasa Mama fitowa da sauri tana tambayar abinda ya faru. Iya tace "Wai Dan mai k'aton kai ya rik'e ta shine take ihun yayi mata ciki , ki jimin yarinya to yanzu in yayi mai gabad'aya fa shikuma tace me." Ba Fadila har Mama sai da maganar Iya ta bata kunya . Durk'usa Mama tayi ta d'ago Saudala da ta b'ata k'walliyar da kuka , d'aki suka shiga ta zaunar da ita san'nan ta kalle ta tace , "haba Saudat yanzu dan Abdul ya rik'e miki hannu kike wan'nan ihun."? Kallan ta Saudala tayi san'nan Tace , " bafa hannuna ya rik'e ba a jikin sa ya sani sai kace wata karuwa."🀣 Dariya Mama ta k'unshe san'nan tace , "to ai yayanki ne , Amma tunda bakya so zan masa magana kar ya k'ara yi miki hakan." Hawaye Saudala ta share san'nan tace , "to Mama cikin da yayi min fa.?" Sakin baki Mama tayi tana kallan ta , zallar k'uruciya Mama take gani a tare da ita , a ranta tace , "daman banda abin Iya mai zaisa a yiwa Saudat aure yanzu." "Mama kinyi shiru". Saudala ta katse mata tunani. Mama tace " ai dan Abdul ya rik'e ki babu abinda zai faru ai yayanki ne , da dai wanine daban to shine zance yayi miki cikin Amma banda d'an uwan ki." Shiru Saudala tayi alamun ta yarda da abinda Mama tace , cikin sanyin murya tace, "Mama Amma ki fad'a masa karya kuma." Mama tayi murmushi tace , "zan fad'a masa, yanzu tashi ki gyara fuskar ki ." STORY CONTINUES BELOW Tashi Saudala tayi ta shiga band'aki Mama kuma ta fita daga d'akin. Fadila ta shigo d'akin ta zauna tana dariya a ranta tana fad'in, "Tab Ashe ak'wai aiki a wajan Bro , daga rik'eta Tace yayi mata ciki ina balle yayi Mata wani abun, gsky zanyi missing d'in wan'nan dramar ." Abdul kuwa part d'insa ya wuce shida Mustapha , yana shiga ya cire malun-malun ya ajiye , zama yayi akan kujera yana ajiyar xuciya. Ido ya lumshe yana tuno abinda yaji lkcn da Saudat ke kwance a jikin sa, mamakin halin da ya shiga yake shi dai yasan Saudat bata isa yaji wani Abu a jikin ta ba, to meyasa yake jin wani iri a jikin sa ? , babu mai bashi wan'nan amsar . (yan Saudala fan's suna da amsa πŸ˜‰) Mustapha ne ya katse masa tunani da fad'in, "yadai Mr man har yanzu baka dawo normal ba .?" Tsaki Abdul yayi yace , "to me kake nufi." Dariya Mustapha yayi sosai san'nan yace , "naga yadda lkc d'aya ka canja tunda ka rik'e Saudat."πŸ˜‚ Tsaki Abdulrahman yayi yace , " To mai zanji a jikin wan'nan kwailar , kai nifa na k'agu my Hady ta shigo gidan nn." Dariya Mustapha yake sosai har sai da ya k'ular Abdul . Tsagaita dariyar yayi yace , "kwana nawa ne Hadizan zata zama taka , saura sati biyu fa , Kai Amma fa Saudat ta bani dariya wai shikenan ta zama y'ar iska." Murmushi Abdul yayi baice komai ba. Mustapha yace, "Abdul maganar booking d'in wajan dinner d'in d'azu naje mun gama komai nace musu Friday ba mai zuwa ba ta sama." Abdul yace "yauwa daman abinda nake so na tambaye ka kenan , yanzu sai maganar bugo gate pass ko.?" Mustapha yace "shima karka damu angama komai." Murmushi Abdul yayi yace , "kai amma nagode sosai Mustapha, bani d..........." Katse shi Mustapha yayi yace , "ka wuce haka a wajena bana buk'atar godiyar ka." Murmushi Abdul yayi yace "taso muje ka raka ni wani waje." Mustapha yace "tab babu inda zami gaskiya Sai ka dawo." Ya fad'a yana kwanciya a kan kujera. Mik'ewa yayi ya fito, mota ya shigo ya fita daga gidan . ****** Kuka take sosai kamar wadda aka yiwa mutuwa , Momy ce ta dafa ta tace , "haba Hadiza yanzu baza ki daina wan'nan kukan ba , kema fa kamar yau ne zaki zama matar sa." Cikin kuka tace , "Momy Ina mutuk'ar kishin Abdul , yanzu Momy yana can zai tare da wata bani ." ta k'ara fashewa da kuka. Rarrashin ta Momy keyi har ta samu tayi shiru bacci ya d'auke ta. ***** Saudala kuwa tana zaune ta zuba tagumi gabanta na fad'uwa , Sam bata San dalilin hakan ba. Fadila ta dafa ta tace , "Saudat Lafiya.?" D'agowa tayi tace , "wlh bansan abinda yake damuna ba , haka kawai nake jin fad'uwar gaba." Fadila tace "ayya Addu'a zakiyi ba tagumi ba kinji." Kai kawai Saudala ta d'aga . Fadila tace "yauwa maza ki tashi ki fito ga k'awaye na zaku gaisa." Mik'ewa Saudala tayi suka fito tare. Tafiya Abdul yake yana tunanin abinda yake ji a jikinsa akan Saudat. Horn ake masa Amma Sam hankalin sa baya Kansu, mutane magana suke masa sabida k'atuwar motar da take nufi shi. Cikin tsautsayi motar ta ture motar da Abdul yake cikin , aikam ta hantsila jefen titi. STORY CONTINUES BELOW Cikin sauri mutanen wajan suka nufi motar Abdul suka fito dashi ko numfashi ba yayi. 😭😭 _Note_ _gaskiya yanzu bakwa son yin comment yadda ya kamata 🀨 idan book d'in ya ishe ku ku fad'a min na daina wahalar da kaina, Nasan akwai wad'an da basa missing d'in yin comment to basu nake ba da y'an lab'en grp nake , sai aukin turo min sticker 😏_. *ina godiya gare ku , pretty (Queen of comment 1) πŸ₯°, Momyn Khaleed (Queen of comment 2)😘, Hadiza , cwty sister, Mr's Abdul, khadija, hak'ika bazan gaji da yi muku godiya ba , Allah ya bar zumunci .* Comment & share Neat LadyπŸ’ƒπŸ»πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ² 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Bismillahir rahmanir rahim* 55&56 Cikin tashin hankali mutane suke k'ok'arin d'aga shi dan a kaishi Asibiti , daya daga cikin su ne yace , "Bara na kira mahaifinsa na sanar dashi ." Waya ya d'auka ya kira Abba , lkcn Abba suna tare da Baba suna tattaunawa akan maganar tarewar Saudat , wayar Abba tayi k'ara yana budawa yaga bak'uwar number , d'aga yayi ya kara a kunnen sa . Tun kafin Abba yace wani abu mutumin ya fara cewa, "Alhaji kuzo Asibiti bayan ku yanzu d'an wajan ka yayi hatsari a mota yana emergency ." Cikin tashin hankali Abba yake fad'in , "gani nan zuwa ." Bayan ya kashe wayar ganin yadda hankalin sa ya tashi sai Baba yace , "Lafiya kuwa.?" Abba yace , "Abdul ne yayi hatsari yanzu yana Asibitin bayan mu." Cikin kid'ema Baba ya mik'e yana fad'in, "mu tafi ." Cikin sauri suka d'auki mota suka fita. A mota Abba yayiwa Mama waya ya sanar da ita yace su tawo asibitin yanzu. Ko da suka k'arasa Asibitin emergency suka nufa , anan suka tarar mutanen da suka kawo shi , ganin su Abba sun iso sai suka yi musu sallama bayan Abba yayi musu godiya suka tafi. Wajan minti ashirin da zuwan su Abba amma har yanzu babu likita d'aya da ya fito daga d'akin , hankalin su Abba ya k'ara tashi , sunan zaune babu Wanda yake wa wani magana har isowar su Mama. Ganin yadda su Baba sukayi jugum-jugum sai kuwa Fadila ta fashe da kuka mai ban tausayi. Umma ta rik'o ta tana rarrashin ta , Mama kuwa kukan zuci take dan ita kad'ai tasan tashin hankali da take ciki. Su Iya kuwa an zabga uban tagumi ana matsar k'wallah. Sunan zaune likita ya fito daga d'akin , da sauri Baba ya k'arasa yana tambayar sa jikin Abdul. Kallan sa yayi yace "ku biyo ni office." Abba da Baba suka bi bayan sa . Bayan sun shiga office d'in likitan ya kalli Abba yace , "Alhamdulilah baiji wani ciwo sosai ba sai d'an buguwar da kansa yayi sai kuma kukkujewa , Amma gasky ya kamata ya kuyi masa fad'a ya rage damuwa da yawan tunani , kuma yana buk'atar kulawa sosai dan ba'aso ya dinga zama a waje mai hayaniya , san'nan kar ya cika yin aiki, sabida buguwar da kansa yayi in ya ciki aiki ko zama a waje mai hayaniya zai iya haifar masa da ciwon kai , zuwa gobe insha Allah za'a sallame shi." STORY CONTINUES BELOW Baba yace "mun gode likita kuma insha Allah zamu kiyaye , ko zamu iya ganin sa yanzu." Likita yace "Sosai kuwa Bismillah ." Tashi suka yi suka fito daga office d'in , a bakin k'ofar d'akin suka tadda su Mama suka shiga gabad'aya. Zama sukayi suna kallan sa , an d'aure masa kansa da bandeji sai kuma ciwuka a hannu da k'afa, idonsa a rufe alamun bacci yake. Kowa yayi shiru babu Wanda yake magana a cikin su . Abba ya kalli Fadila da take tsare hawaye yace, "Ina Saudat ."? Fadila tace " lkcn da zamu fito bacci take shiyasa ba'a tashe ta ba." Shiru ya kuma ratsa d'akin kowa da abinda yake tunani, har kusan one hour suna zaune Abdul bai farka ba. Ido Abdul ya fara bud'ewa tun yana gani dishi-dishi har idon ya Bud'e yana kallan d'akin. Cikin muryar marasa Lafiya Abdul yace , "Ruwa". Cikin sauri suka kallo inda yake suna yi masa sannu, Fadila ta d'auko ruwa ta mik'ewa Baba , dak'yar ya mik'e zaune yana dafe kai , mik'a masa ruwa akayi ya karb'a ya sha. Fadila ta fita ta sanar da Dr ya farka, tare duka dawo d'akin da likitan . Duba shi ya kuma yi san'nan yace , " sannu ya kake jin ciwan kan yanzu.? " Abdul yace "har yanzu dai yana ciwon sosai." Likitan yace "babu komai zuwa anjima shima zaka ji sauk'in sa, Allah ya k'ara sauki." Ya fad'a yana fita d'akin. Iya ta kalli Abdul tace , "Oho yanzu fa saura k'iris ya Saudat ta zama k'aramar bazawara ko."πŸ˜† Gaban Abdul ya fad'i Wanda shima bai San dalilin hakan ba. Dariya su Mama suka yi , Fadila tace " Iya abinda kika hango kenan. " Shikam Abdul yayi shiru a ransa yana tunanin mai ya hana Saudat zuwa duba shi? Mustapha ne ya shigo d'akin a firgice , ganin Abdul d'in a zaune sai hankalinsa kwanta , sannu yayo masa shima ya shiga jerin masu tsokanar sa. Zuwa dare jikin Abdul yayi sauk'i sosai , ko da likitan ya shigo Abdul ya nemi alfarma a sallame shi Dan baya son zaman asibiti. Likitan ganin ya samu sauk'i sai ya basu sallama suka dawo gida. A harabar gidan kuwa sojoji sa aukin k'amewa suke muna kwasar gaisuwa. A main parlour suka zauna , Iya ta kalli Abba tace , "amma dai Ummaru baza ku bar yaron nan ya kwana shi kad'ai bako ?, sabida lalurar dare , ga kuma ciwon kan da yake fama dashi dole a sami mai kwana a part d'insa." Abba ya gyara zama yace , "eh maganar ki gaskiya ce sai dai to waye zai zauna a wajan sa?" Baba yace "Ga Saudat nan ta koma can har ya sami Lafiya." Iya tace "kamar ka shiga zuciyata wlh , abinda nake niyar fad'a kenan ." Abba yace "Haba Ahmad ta yaya sa Saudat zata iya jinyar Abdul.?" Iya tace "To ba matar sa bace , da ban wan'nan hatsarin ba da yanzu tana gidan sa , dan haka halima kije ki fad'awa Saudat d'in." Mik'ewa Mama tayi ta shiga d'akin su Saudat. Shikam Abdul yana jinsu baice komai ba. Mama ta shiga d'akin lkcn Saudala ta fito daga wanka tana shafa mai. STORY CONTINUES BELOW Mama ta kalle ta da murmushi tace , "A'a Saudat anshi daga bacci kenan." Saudala tace "Mama wai ina kuka shiga tun d'azu ina Neman ku." Ta fad'a Kamar zata yi kuka. Mama tace "baki San yayanki Abdul ne yayi accident ba, tun d'azu muna asibiti." Saudala tace "ayya Allah ya k'ara sauk'i." Mama tace "Ameen, amma bashi da Lafiya dan yanzu likitan yace kar ba barshi ya kwana shi kad'ai sabida ciwon kai." Saudala tace "tab Amma duk Wanda zai kwana dashi ya shiga uku da masifa." Mama tayi murmushi tace "akwai wadda zai kwana dashi in ba keba." Saudala ta zaro ido tace , "ni kuma , Amma dai wasa kike ko Mama.?" Mama tace "da gaske mana ai naga kece matar sa ke ya kamata ki kula dashi." Hannu Saudala ta d'aura a kai ta fasa ihu .πŸ™†πŸ» *toh ga Saudala zatayi jinyar Abdul* πŸ˜‚πŸ˜‚ Comment & Share . Neat Lady ✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Bismillahir rahmanir rahim* 57&58 "Wayyo Mama kiyi hak'uri kar ki tura ni wajan mugun can." Rife mata baki Mama tayi tana girgiza mata kai , "Haba Saudat sau nawa zan fad'a miki Abdul yayan kine ke kuma k'anwarsa ce , kin tab'a jin labarin da yaya ya cutar da k'anwar sa.?" Girgiza kai Saudala tayi alamun A'a, Mama ta cigaba da fad'in, "to kin gani , kuma yanzu bashi da Lafiya yana buk'atar kulawa , pls maza ki shirya Fadila ta raka ki part d'insa." Saudala tace "Amma fa Mama darajar ki yaci wallahi da bb inda zani , san'nan kiyi masa mgn kar yace zai dinga tab'ani." Mama tayi murmushi tace , "yauwa y'ar albarka na yarda yaci darajar tawa , kuma zan masa mgn babu ruwan sa dake." Saudala tace "Mama Amma ba can zan dinga kwana bako.?" Mama tace "A can zaki kwana mana kin manta nace miki bashi da Lafiya ,kuma idan ciwon ya tashi cikin dare kinga tunda kina nan sai kiyi mana waya." Shiru tayi tana tunanin maganar Mama. Mama tace "maza ki shirya kizo ki wuce ." Juyawa Mama tayi ta fita daga d'akin . Saudala kuwa kaya tasa san'nan ta tsaya tunani a ranta tace , "tab wai yanzu a d'aki d'aya zamu kwana da brown strowman sai kace wata y'ar iska , wlh bazan yarda ba saidai asan yadda za'a yi." Mama ta shigo tana fad'in , "baki shirya bane .?" Ganin ta sanye cikin kayan bacci Riga da wando , Mama tace "Ashe ma kin shirya , to maza d'auko hijjabin ki ki fito." STORY CONTINUES BELOW Hijjabi Saudala ta d'auka ta saka san'nan ta fito parlour. Iya tace "yauwa Saude maza ki d'auki abinci ki tafar muku dashi , dan shi har ya wuce part d'in nasa ma." A xuciya Saudat tace "tab Dan samun matsayi abincin ma ni zan kai masa hmmm." Kitchen ta shiga ta d'auko abinci suka fita ita da Fadila. A bud'e k'ofar parlourn hakan yasa suka shiga da sallama. Amsawa yayi cikin sanyin murya. Kallan sa Saudala tayi taga kansa a d'aure alamun yaji ciwo kenan , tausayisa taji ganin yadda yake dafe Kai alamun ciwo. Fadila tace "sannu Bro Allah ya k'ara sauk'i, ni zan wuce sai sa safe." Ta fad'a tana fita daga parlourn tare da kullo k'ofar. Kunsan minti uku babu Wanda yayi magana a cikin su , Saudala kuwa tana tsaye inda Fadila ta bar ta. Cikin dashewar murya yace "in baza ki zauna ba ki koma inda kika fito kinzo kin tsaya min aka." Tab'e baki Saudala tayi tace "kaga mutum dan an tilastani nazo kuma zaka fara yi min masifa." Ta fad'a tana murgud'a bakiπŸ˜™ Kallan ta kawai Abdul yayi yana tunanin da ace Lafiyar k'alau da babu abinda zai hana ya mare ta. A kan kujera ta zauna tace "ga abinci ance na tawo maka dashi." "Bana ci". Ya fad'a a tak'aice. Kwantar da murya Saudala tayi tace " ba'a son Mara Lafiya ya dinga zama da yunwa fa." Tsaki yayi yace "nace bana ci ana dole , kin zo kin cika min kunne da surutu." Hararar sa Saudala tayi tace "Ka huta ciki ka ba mawa ba." Banza yayi mata bai kuma kallan taba Dan karma tayi masa rashin kunya. "Brown strowman bacci fa nake ji." Ya fad'a cikin shagwab'a. Ko kallan ta baiyi ba bare ya bata amsa. Mik'ewa yayi ya shiga d'aki Dan ya gaji da surutun ta. Zama yayi a baki gado ya dafe kai sabida ciwon da yake masa. Ganin ya shiga d'aki Saudala tayi tsaki tace "kanka ake ji." Zama tayi tana kallo , ta cire hijjabi ta kwanta akan kujera , tun tana kallon har bacci ya d'auke ta. Jin shiru babu motsin ta Abdul ya fito daga d'akin , gano ta yayi akan kujera tana kwasar bacci. Ganin wuyan ta ya lank'washe sai ya k'araso Dan ya gyara mata kar yayi mata ciwo. Kare mata kallo yake ganin yadda Allah ya bata baiwar hips kamar ba k'aramar yarinya. Hannu yasa ya tallafo kanta ya dauki pillow ya sa mata. Firgigit Saudala ta bud'e idon tana kallan sa , ganin yana rik'e da hannun ta sai kuwa ta kwalla k'ara tace " na shiga uku da gaske d'an iska ne."🀣 *Bani da charji kuyi hak'uri da wan'nan.* Comment & share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ STORY CONTINUES BELOW ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *JUMA'A MUBARAK* πŸ•Œ *Bismillahir rahmanir rahim* 59&60 Sakin hannun ta yayi ya dafe kai Dan ihun da tayi kansa har sarawa yake. Ganin ya sake ta sai ta mik'e tayi hanyar fita tana fad'in, "wlh banza zauna da d'an iska ba , kuma sai na fad'awa Mama kayi min fyad'e ."🀭 Ganin tana niyar fita yayi saurin k'arasawa ya kulle k'ofar ya cire key d'in. D'aki ya koma ya kwanta , maganar tace take masa yawo a k'wak'walwa, wai yayi mata fyad'e , murmushi yayi a ransa yace " kwaila kawai."☹ Saudala kuwa zama tayi ta takure waje D'aya , jira kawai take gobe tayi ta fad'awa Mama mai hancin karas yayi mata fyad'e . Anan zaune bacci ya d'auke ta . Da Asuba Saudat ta farka , ta rasa a ina zatayi alwala kuma gsky tsoro take ji baza ta Iya fita waje ba . Mik'ewa tayi ta shiga bedroom d'in Abdul , cikin sand'a take tafiya dan bata so ya farka ya ganta a d'akin sa yayi tunanin itama ta zama y'ar iska .πŸ˜‚ A hankali ta Bud'e k'ofar toilet d'in ta shiga , cikin sauri tayi alwala ta fito , tsayawa tayi tana kallan sa a kwance a kan gado, tab'e baki tayi tace, "jibe shi ana sallah yana bacci." Ganin alamun kamar zai farka sai ta fita parlour da sauri. Shi kuwa Abdul ciwon kan ne ya matsa masa ko tashi ya kasa yi, duk abinda take yana kallan ta . Har Saudala ta idar da sallah shiru mai hancin karas bai fito ba, ranta tace "ko dai bashi da Lafiya ne .?" Cikin sauri ta mik'e ta shiga d'akin, yana zaune akan gado ya dafe kai da hannun sa duka biyun. Tausayin sa taji ya kamata sosai , Dan Saudala daman akwai tausayi.🀫 Cikin sanyin jiki ta k'arasa wajan sa tace , "sannu baka da Lafiya ."? D'agowa yayi yana kallan jin yadda tayi masa magana cikin sanyin murya. Shiru yayi mata baice komai ba. Tace " tun d'azu an idar da sallah fa." Nan ma shiru bai amsa mata ba. Iya k'uluwa Saudala ta k'ulu , cikin rashin kunya tace , "kaga mutum Dan ma kasamu nazo ina yi maka magana zaka dinga wulak'antani , kar kayi sallar mana ina ruwa na ai ba kabarin mu D'aya ba." 😏 tana gama fad'ar haka mik'e zata bar d'akin. Murya can k'asa yace "zo ki d'ebo min ruwa a roba nayi alwala bazan iya mik'ewa ba." Jin muryar sa wani iri yasa Saudala ta k'ara jin tausayin sa , cikin sauri ta shiga toilet ya d'ebo ruwan tazo ta ajjiye a gaban sa. Sunkuyowa yayi da niyar fara alwala sai kuwa kansa ya Sara yayi saurin d'agowa yana cije baki. Tana tsaye tana kallan sa ta rasa abinda zatayi , wata dabara ce ta fad'o mata , juyawa ta ta jayo center table d'in d'akin har ya takawo shi gabansa kamar zai ci abinci , ruwan ta d'auka ta d'ora shi kan table d'in . STORY CONTINUES BELOW Kallan sa tayi tace "ka gwada a haka zaka fi jin sauk'in sunkuyawa." D'agowa yayi suka had'a ido ta sakar masa murmushi tayi masa alama da ya fara alwalar. Yana gama alwalar ta d'auke abin ruwan ta mayar toilet san'nan ta dawo ta janye table ta shinfid'a masa sallayya . Ido kawai yake binta yana mamaki , dan shi bai tab'a tunanin zata taimaka masa ba. Ganin ya zuba mata ido sai ta murgud'a baki tace "Lafiya kake kallona kamar nayi maka sata."πŸ˜’ Murmushi yayi a ransa yace " mai hali baya fasa halin sa." Saukowa yayi ya tayar da sallah ita kuma ta koma parlour. Gyara parlourn tayi ta kuma turaren wuta ta goge tv , parlourn yayi kyau sosai sai kamshi yake . Zama tayi tana jiran ya tashi daga bacci ta gyara bedroom d'in. Har gari yayi haske sosai Abdul bai tashi daga bacci ba , gajiya tayi da jira ta mik'e ta nufi part d'in Umma. ******* "Momy ! Momy !! Wai har yanzu baki tashi daga bacci bane." Momy ta mik'e zaune tace "haba Hadiza wan'nan kira haka kamar nayi miki laifi." Tab'e baki tayi tace "Momy kin san fa yau zani Abuja dubiya ." Momy tace "waye kuma bashi da Lafiya?" Idon ta ya kawo ruwa tace "bana ce miki in na kara Abdul ya waya baya d'auka ko , wai Ashe jiya bayan d'aurin auren sa accident yayi ." Momy tace "Allah ya kiyaye gaba , yanzu in anjima zaki tafi.?" Tace "uhum zuwa anjima zan tafi dan har na siyi ticket ." Momy tace "Allah ya kiyaye , kiyi masa sannu in kinje ." Tace "zuwa anjima ko kina bacci ni zan tafi basai na tashe kiba." Momy tace "to shikenan, ki Bud'e bed side ki d'auki dubu hamsin ." B'ata rai tayi tace "haba Momy gaskiya ni dubu Hamsin tayi min k'adan , ni d'ari nake so ." Momy tace "yanzu Hadiza dubu Hamsin d'in ce tayi miki kad'an , kifa tuna aure zakiyi kina tunanin ko wanne miji ne zai dinga baki kud'i masu waya ,? Ki nutsu ki shiga hankalin ki." "Ni kawai in baza ki bani ba ki fad'a min." Momy tace "A'a mai zai hana na baki , ki bud'e ki d'auka, Allah ya kiyaye." Tashi tayi ta fita daga d'akin . ****** Saudala kuwa bayan taje part d'in Umma wanka tayi ta shirya ta fito parlourn Umma ta zauna. Umma tace "Saudat ya jikin Abdul d'in.?" Saudala tace "da sauk'i, Umma bara naje na gaida su Mama." Ta fad'a tana fita daga d'akin. Part d'in Mama ta shiga a kitchen ta ganta tana had'a break fast . Kallan ta Mama tayi tace "A'a Saudala har kin shirya.?" Tace "Mama ina kwana.?" Tace "Lafiya lau , ya mai jikin .?" Saudala tace "da sauk'i, Amma har yanzu kansa yana ciwo, kuma wlh Mama jiya ma daddare sai da y........." Saukowar Abba ya katse mana abinda zata ce, ta gaida amsa ya amsa cikin sakin fuska. Mama ta kalle tace "maza ki d'auki abincin ku ki tafi dashi." D'auka tayi ta fita tana k'unk'uni. Shi kuwa Abdul tunda ya tashi yajisauk'in ciwon kan sosai, wanka yayi ya shirya ya zauna yana dan'na waya. Da sallama ta shiga parlourn , amsawa yayi yana kallan ta. Zama tayi kan kujera tace "sannu y jikin.?" Ya amsa da cewa "da sauk'i.". Tab'e baki tayi tace " ga abinci. " D'auke kai yayi yace "sai zuwa anjima." Shiru tayi bata k'ara cewa komai ba shima kuma haka. Waya ta d'auka ta kira Fadila tana fad'in "Fadila gani na k'araso kizo ki tawo dani. Fadila ta amsa da " gani nan zuwa." Fitowa daga d'akin tace "Mama ga aunty Hadiza tazo tana airport zan je na tawo da ita." Mama tace "to Allah ya kiyaye , in kunzo ku fara zuwa part d'in Abdul Dan zan d'an fita nida Umman ku zamu je gaisuwa Amma ba dad'ewa zamuyi ba." Fadila ta amsa tana fita daga parlourn. Kusan minti ashirin Saudala tana zaune bata k'ara magana ba shima kuma haka. Mik'ewa Saudala tayi zata zuba tea tasha , shima Abdul ys mik'e zai koma d'aki. Wani irin sarawa kansa yayi aikuwa yayi baya zai fad'i , cikin sauri Saudala ta mik'a hannu ta taro shi sai kuwa ya fad'o kanta suka fad'a kan kujera.🀭(in Saudat ina brown strowman balle tace zata tare shiπŸ˜‚) Dai-dai lkcn aka bud'e k'ofar parlourn. Comment & share Neat Lady ✍🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 _*kai gaskiya jiya nayi mutuk'ar jin dad'in comment d'inku my fan's, Allah ya bar mu tare.*_😁😁😁 *Bismillahir rahmanir rahim* + 61&62 "Kutumelecy ni Hadiza mai zan gani , yanzu Abdul daman cin amatana kake.?" Hadiza ta fad'a cikin b'acin rai. Jin muryar mutum yasa Saudala saurin mik'ewa daga jikin Abdul tana hararar sa. Dak'yar Abdul ya mik'e yana kallan cike da mamaki. Cikin dashewar murya yace "My hady yaushe kika zo?". Cikin d'aga murya tace " ban sani ba!, Ashe daman duk abinda ka fad'a min yaudara ta kake , wai a tak'aice ma wace wan'nan .?" Ta fad'a tana nuna Saudala. Juyawa yayi ya kalli Saudala da take auki hararar sa yace , "K'anwata ce ." "Daman kana da wata k'anwa ne bayan Fadila, kada kace min wan'nan ce Saudat d'in ." Saudala tace "nice Saudat a ina kika sanni ? , Dan nidai nasan kaf dangin mu babu mace kamar skeleton." Cikin hargagi Hadiza tace "ni kike kira skeleton ?". Murgud'a baki tayi tace " ai da hakan kika dace , aba kamar muciya." Da sauri ta k'araso da niyar Marin Saudala Abdul ya rik'eta yana fad'in , "wai meye haka my life , wan'nan fa ba girman ki bane." A fusace ta juyo tace "ina so ka fad'a min da bakin ka wan'nan itace matar ka Saudat.?" Gyad'a Kai Abdul yayi alamun eh. Sai kuwa ta fashe da kuka tace "Ashe baza iya cika alk'awarin da ka d'auka ba , kace min wani Abu bazai tab'a shiga tsakanin ku ba , Ashe duka dad'in baki kake mun." Ta k'arasa maganar tana kuka. Rik'e hannun ta yayi suka zauna akan kujera yace "haba my life yanzu idan akace wani Abu ya shiga tsakanina da wan'nan yarinya zaki yarda?, me take dashi har da ja hankalina na kula ta nida ba sonta nake ba, ki k'wantar da hankalin ki yanzun ma ba wani abu bane kinji." Hadiza ta share hawayen ta tace "shikenan na yarda , Amma ina jin tsoro kar wata rana a kula Yarinyar nan dan ina da kishi sosai zan iya kashe ta." Abdul yace "ki kwantar da hankalin ki babu komai." Saudala kuwa tana tsaye tana kallansa, har cikin ranta taji wani iri da yace baya sonta amma sai ta dake tace , "ai sai yanzu na gane wan'nan ce Hadiza taka , tab Amma gaskiya mai hancin karas Sam baka iya zab'e ba , ka rasa wacce zaka zab'a sai wan'nan abar , Aradu da shigo na zata namiji ne wai ashe macece , tab wan'nan ko a cikin mazan ai irin su ne masu k'wantai ." ta fad'a tana dariya. Juyawa tayi ta kalli Abdul da yake kallan ta dan shi gabad'aya ya manta tana d'akin ya zata ta fita, tace "Maza guda biyu a zaune ." tana gama fad'ar hakan ta fice daga parlourn. STORY CONTINUES BELOW Tafiya take tana tunanin abinda Abdul yace , wai baya sonta , tsaki tayi tace "zaka gane kuran ka Mai hancin karas." Rarrashin Hadiza yayi sosai Dan yaga taji haushin abinda Saudala ta fad'a mata. Sai wajan awa d'aya suka fito daga part d'insa shida ita, main parlour suka shiga Dan su gaisa da mutan gidan. Da sallama suka shiga parlourn , Iya dasu Umma duk suna zaune da alama sun dawo daga Unguwar. Amsawa su Umma sukayi cikin sakin fuska sana yiwa Hadiza sanin da zuwa. Kan kujera Hadiza ta zauna tana kallan Mama, cikin wata irin murya tace "good evening Mama." D'an turus Mama tayi tana.kallan ta san'nan tace "Lafiya lau , ya kuke." Ta yatsine fuska tace "Lafiya lau duk sunce a gaida ku." Mama tayi murmushi tace "muna amsawa." Juyawa tayi ta kalli Iya tace "sannu kakus." Tafa hannu Iya ta fara tana fad'in , "Ashe da gaske macece yasin da ta shigo na zata namijine yasa kayan mata , Aradu wan'nan tasa babbar Riga da hula cewa za'a yi namiji ce , sannu kinzu gidan sirikai kin wani zauna akan kujera kina taunar cingam ,Amma dai kin gaida yayar ki ko.?" Hadiza kuwa ranta ya b'aci da irin maganganun da Iya ta fad'a Mata , kallan Iya tayi san'nan tace "wace yayata kuma.?" Iya tace "uwar gidan mijinki mana , gata nan a zaune." Ta fad'a tana nuna Saudat. Cikin sauri Saudala tace "haba Iya wan'nan gwaggon zaki cewa k'anwata , haba ai wan'nan tayi jika dani." Tana gama fad'ar haka ta shige d'aki , tana cewa "hmm bake kika yi niyar Marina ba , kin shiga uku wlh." Murmushi dole Hadiza tayi tace "mun gaisa tun d'azu, nidai zan tafi sai anjiman ku." Tana gama fad'ar haka ta fice daga parlourn da sauri. Abdul kuwa shi kansa baiji dad'in yadda Hadiza ta gaida Mama ba , kuma baiji dad'in yadda Iya da Saudala suka ci mata mutunci ba , gashi bashi da Lafiya balle ya bita. Tsaki Iya tayi tace "banda rashin kunya ina sirika ina zuwa gidan iyayen mijinta , harda wani zama akan kujera tana kallan mutane ." Babu Wanda yayi magana dan kowa yaga rashin kunyar Hadiza . Hadiza kuwa tafiya take ranta a b'ace , Dan ba k'aramin jin haushin maganganun su tayi ba. Mota ta samu ta isa airport ta koma kano. Da yamma Saudala tana zaune Mama ta bata abinci tace ta kaiwa Abdul. Karb'a tayi ta fita daga parlourn. A parlourn ta ganshi yana waya da Hadiza da alama rarrashin ta yake , zama Saudala tayi tana Tab'e baki. Kashe wayar yayi yana kallan yace , "Lafiya.?" Tace "Abinci akace na kawo maka , san'nan abinda kayi min d'azu ina sane sai na fad'awa Mama." Yace "wai yake komai kice anyi miki iskanci sai kin fad'awa Mama .?" Murgud'a baki tayi tace "eh ai iskanci kayi." Murmushi yace "zan nuna miki ni cikakken d'an iska ne , badai a d'akin nan kike ba hmmm." Saudala tace " Aradu duk abinda kayi min sai na fad'awa Abba." Banza yayi mata baice komai ba. Da daddare Saudala tayi wanka ta shirya cikin doguwar ta bacci , hijjabi tasa ta nufi part d'in Abdul Dan Umma har tayi magana. STORY CONTINUES BELOW *_Yace zai nuna mata shi Dan iska neπŸ˜‚ kome zai yi mataπŸ€­πŸ€”_* Comment & Share Neat Lady ✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *ihuuuuuuuuuuu 🀸🏻‍♀🀸🏻‍♀ kai gsky comment d'inku na sani wani irin farin ciki 😁, kai tsabar murna jiya saura k'iris na fad'a kogiπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ€«.* *Bismillahir rahmanir rahim* 63&64 Da sallama ta shiga parlourn tana b'ata rai, amsa sallamar yayi ba tare da ya d'ago ba. Zama tayi tare da fad'in "Haka kawai a takura wa mutum bayan an san bana son zuwa wan'nan d'akin." Ta fad'a tana turo baki. Ko kallan ta baiyi ba balle ya tanka mata . Had'e rai yayi ya kalle ta yace "yauwa ke d'azu shine kika yiwa my hady rashin kunya ko, to ki shiga hankalin ki karki k'ara yink'urin aikata haka , in ba haka ba hmmm." Saudala cikin mamaki tace "waye kuma hadi ?, nidai nasan ban san wani hadi ba ." Tsaki yayi yace "ba hadi nace miki ba my hady da tazo d'azu ." Kallan sa Saudala tayi ta k'yalk'yale da dariya tace , "yo ni inba skeleton kace ba bazan tab'a ganewa ba , Ashe kaima kasan suffar Maza ne da ita tunda gashi kana ce mata wai hady , ba wani hady wayo kake mata kana fad'a mata sunan maza." Kallan yake yana mamakin yadda lokaci d'aya ta canja masa magana . Dariyar tace ta katse masa tunani , dariya take sosai tace , "kawai so nake bikin ku yazo Inga mutane zasu bambance waye angon wace Amaryar tunda suffar ku d'aya." Murmushi tayi tace "ka zuba ido zaka ga saurayina da zan aura kai kanka sai ya burgeka." Cikin fushi ya mik'e ya nufi inda take ya mik'ar da ita yace , "idan kika k'ara zancen wani saurayi wallahi saina b'alla ki ,, banza Mara kunya, ni zaki kalla kice wai Wanda zaki aura.?" Cikin mamaki da tsora Saudala take kallan sa , tsoronsa ne ya kamata ganin yadda lokaci d'aya ya wani birkice kamar bashi ba. Dakewa tayi tace "to ba gaskiya na fad'a ba ." Wuyan ta ya rik'e ta baya Yace "har yanzu baza ki daina fad'a bako , wato ke dai baza ki daina yimin rashin kunya baki ? , yau zanyi maganin baki da yake rashin kunyar." Yana ga fad'ar hakan ya had'e bakinsu waje d'aya . Mutsu-mutsu Saudala take tana k'ok'arin k'wace kanta. Shikuwa Abdul ya kasa sakinta sabida wani sabon yanayi da ya tsinci kansa a ciki. Saudala kam gabad'aya lips d'inta zafi yake , banda hawaye babu abinda takeyi. Ganin yana k'ok'arin cire mata hijjabi yasa ta ture shi da k'arfi tayi d'aki da gudu. STORY CONTINUES BELOW Kan kujera ya zauna yana maida numfashi , idon a lumshe yana tunanin shida yake k'ok'arin koya mata hankali sai gashi yana k'ok'arin matsala. Fitowa tayi daga d'aki tana goge bakinta , kallan sa tayi tace, "Allah isa , mugu kawai , kuma sai na fad'awa Mama." Bud'e ido yayi ya kalle ta yace , "oh har yanzu bakin ki bai mutu ba , bara ki gani ." (kuji mutum da k'arfin haliπŸ˜‚) ya fad'a yana jayowa ta jiknasa , hijjabin jikinta ya fara k'ok'arin cirewa , aikam suka fara kokawa, mird'e mata hannu yayi ya cire hijjabin . Hannunsa ya fara yawo dashi a jikin ta , ita kuwa Saudala banda kuka babu abinda take . Rigar ta ya d'aga sama yana k'ok'arin cire ta gabad'aya. Rik'e masa hannu tayi tana girgiza masa kai tana hawaye. Abdul kuwa gabad'aya ya fita daga cikin hankalin sa, romancing d'inta yake sosai . Wani k'arfi ne yazo mata ta ture shi ta mik'e a guje tayi d'aki tana maida numfashi. Shikuwa Abdul rik'e ciki yayi jin yadda marar sa take murd'awa . Kwanciya yayi murk'ususu , fitowa Saudala tayi da niyar barin part d'in gabad'aya, ganin sa tayi a kwance yana rik'e ciki yana cije baki. Kamar ta share shi sai kuma taga kamar da gaske yake . K'arasawa wajan tayi a hankali tana gudub karya kuma rik'e ta , a hankali tace, "Yay Abdul Lafiya ?". Ganin da gaske ciwon yake sai tace," bara naje na fad'awa Mama." Ta fad'a tana niyar barin wajan . Hannun ta ya rik'e yace .......... *Hmmm komai zai faru , mu had'u a next page*🀸🏻‍♀🀸🏻‍♀🀸🏻‍♀🀸🏻‍♀ Kuyi hakuri da wan'nan ina wani aikine shiyasa.😁😞 Comment & share Neat Lady ce ✍πŸ»πŸ˜‚πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ² 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to All my fan's*😍😍😍😍 *ina yinku masoyana irin over d'in nanπŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜˜* *_Masu bina prvt suna na turo musu Saudala daga farko ko daga page kaza kuyi hak'uri ku dinga tambaya a group , sbd ni kaina daga page 1 to 42 nake dashi , bance bani sauran ba inda su sai dai bansan inda zan gansu ba , Amma indai na duba na gansu duk group d'in da suka tambaye ni zan turo musu insha Allah , ko kuma kai tsaye ku ziyarce mu a Wattapad @ GaskiyaWritersAsso don karantawa daga farko ba tare da wata whl ba ._* *LOVE U ALL MY FAN'S*❤❤❤❤ *Bismillahir rahmanir rahim* 65&66 Hannun ta ya rik'e yace "ki shiga d'aki ki duba cikin durowa ki d'auko min magani ." ya fad'a cikin dashewar murya. STORY CONTINUES BELOW Cikin sauri Saudala ta shiga d'akin ta duba ta d'auko ta kawo masa had'e da ruwa. Karb'a yayi ya sha yana ajiyar zuciya, kujerar da yake a zaune Saudala ta zauna tana yi masa sannu. A hankali yace "had'o min black tea Amma karki saka sugar ki matse min lemon tsami a ciki ki kawo min." Mik'ewa Saudala tayi ta had'o masa ta kawo masa, karb'a yayi ya sha yana rintse ido har ya sheye rabin kofin san'nan ya ajiye , jingina kansa yayi da yaban kujera har ciwon ya lafa. Saudala kuwa kallan sa Kawai take , har cikin ranta tausayi yake bata , inda ta tashi ta koma ta zauna tana fad'in, "sannu ya ciwon cikin.?" Sai a san'nan ya bud'e ido da suka koma ja yace , "da sauk'i ." ya fad'a yana kwantar da kansa akan cinyar ta. Yunkurin mik'ewa take cikin sanyin murya yace , "pls ki barni nafi jin dad'in hakan." Hak'ura tayi ta zauna tana kallan sa. Shikuwa Abdul tunani yake a ransa, wai yanzu wan'nan y'ar k'aramar Yarinyar ce ta jawo masa ciwon mara ? Wan'nan y'ar ficikar , Da wan'nan tunanin bacci yayi gaba dashi. Itama tun tana tunanin abinda yayi mata har bacci ya d'auke ta a zaune. Cikin dare Abdul ya farka , zaune ya tashi yana k'arewa Saudala kallo da take bacci a zaune . Mik'ewa yayi ya d'auke ta ya shiga d'aki ya k'wantar da ita a kan gado, toilet ya fad'a yayi wankan da ya hau kansa yayi alwala yazo ta tayar da k'iyamal'laili. Bayan ya idar ya shiga tunanin halin da shiga a d'azu , juyawa yayi ya kalle ta bai San lkcn da murmushi ya sub'uce masa ba a fili yace , "Sleeping beauty." Mik'ewa yayi ya dawo kusa da ita ya k'wanta, rungumota jikin sa yayi ya cire mata hijjabi yana jin wani irin nishad'i yana ratsa shi , a haka bacci yayi gaba dashi. Da Asuba Saudala ta tashi tana salati , kallan d'akin take tana tunanin mai kuma ya kawo ta nan ? , kallan Abdul tayi ya idar da sallah yana lazimi. Da mamaki ta kalle shi tace , "ya akayi nazo wan'nan d'akin.?" Abdul ya kalle ta yace "ki tashi kiyi sallah ba tambaya ba." Mik'ewa tayi ta shiga toilet ta d'auro alwala ta fito. Buba jikinta tayi taga babu hijjabi , idonta takai bakin gadon, hijjabin ta gani a ajiye, mamaki ya k'ara kamata Amma sata danne ta d'auki hijjabin ta tayar da sallah. Bayan ta idar da sallah tayi addu'a san'nan tace , "ni ka bani amsa meya kawo ni d'akin nan ?, bayan ni nasan a parlour nayi bacci." Kallan ta tayi ganin yadda take magana ko had'iyar yawu batayi, murmushi yayi yace, "baki iya gaisuwa ba.?" Bud'e baki tayi tana kallan , cikin tsiyawa tace "kaji wani sabon salo wai yin brush da t'sint'siya da in na gaishe ka amsawa kake .?" Murmushi yayi ganin yadda take motsa baki , yace "to yau ina so a gaishe ni." Tab'e baki tayi tace "wan'nan kuma kai ta shafa ba niba, nidai ya akayi nazo d'akin nan shi kawai nake son ji." Abdul yace "kinsan dai bani da Lafiya Amma kike surutu , ko so kike ciwon kaina ya tashi.?" Cikin sanyin murya tace "A'a, Amma gaskiya ina so........" Katse ta yayi da fad'in "ni bacci nake ji pls kiyi shiru." Ya fad'a ya k'wanciya akan gado. Shi kansa mamakin kansa yake, daga jiya zuwa yau duk abinda Saudala zatayi bata bashi haushi sai dai ta burgeshi. Shiru tayi a ranta tana cewa "kaji dashi , kuma sai ka fad'a min ya akayi nazo nan." STORY CONTINUES BELOW Mik'ewa tayi ta fara gyara d'akin. Wajan k'arfe goma ta fito daga part d'in ta shiga part d'in Mama. Anan ta gansu gabad'ayan su suna break fast, gaishe su tayi san'nan ta shiga d'aki tayi wanka itama. Bayan ta shirya ta fito tayi break fast ta zauna suna hira. Umma ta mik'e ta koma part d'inta Dan tana da aiki a can. Abdul yayi sallama ya shigo parlourn , amsawa Iya tayi tana fad'in , "lallai mai k'atan kai jikin yayi k'yau." Murmushi yayi san'nan ya gaishe su , amsawa sukayi suna k'ara yi masa sannu. Iya tace "yanzu dai babu abinda yake damun ka ko.?" Kafin Abdul yayi magana Saudala ta riga shi da fad'in, "kai jiya ma sai da yayi ciwon ciki , nace zan zo na fad'a muku ya hana ni." Iya tace "ayya Allah ya k'ara Lafiya." Suka amsa da "Ameen". Saudala ta kalli Mama tace " Mama wallahi jiya da daddare sai da yayi .........." Kafin ta k'arasa Abdul yace "Saudat bani abinci." Mik'ewa tayi ta kawo masa abincin , zama tayi ta kuma cewa , "Mama kina ji daman nace saina fad'a , jiya kafin ya fara ciwon cikin sai da yayi ......" Katse ta Abdul ya kuma yi da fad'in, "wai ke bakin ki baya shiru ne?". Kallan sa tayi tace " Mama kin gani ko yasan bashi da gaskiya shiyasa yak'i bari na fad'a. " Iya tace "to kai in kasan kana da gaskiya ka bari ta fad'a mana." Saudala tace "yasan bashi da gaskiya ne shiyasa , kuma Mama kin San wai abinda yayi, jiya fa harda............" Tarin k'arya Abdul ya fara yana bubbuga k'irji. Cikin sauri Fadila ta d'auko ruwa ta kawo masa tana yi masa sannu. Mama kuwa sarai ta gane abinda Saudala take son fad'a , kuma itama taji dad'in fara tarin Abdul duk da tasan k'arya yake. Shikuwa Abdul ganin tana niyar kunya tashi shiyasa ya fara tarin k'arya. D'aki Saudala ta koma da niyar in anjima sai ta fad'awa Mama. ******** Hadiza kuwa tunda ta koma gida babu Wanda ta sanarwa abinda ya faru a gidan su Abdul. Ta kawar da komai ta cigaba da shirin biki. ******** Tunda Abdul ya koma part d'insa yake ajiyar zuciya, a ransa yace "yanzu badan nayi haka ba da tuni ta fad'a, wai da na shiga uku a wajan Iya ." Yana cikin tunani Mustapha ya shigo suka fara hira. _A gurguje_😎πŸ€ͺ Bayan sati d'aya Shirye-shiryen biki ake Dan ance tunda Abdul d'in ya samu sauk'i baza'a d'aga ba. Cikin satin Abdul ya shak'u da Saudala Sosai duk da ba wani shiri suke ba . Tun daga ranar da yayi kissing d'inta bai k'ara k'ok'arin maimaitawa ba Dan yasan shi zai shiga matsala. Kullum sai Saudala tayi bacci sai ya d'auko ta ya shigo da ita d'akin, idan ta tambaya sai yace kansa ciwo yake. STORY CONTINUES BELOW Ranar litinin ya rage saura kwana hud'u d'aurin auren Abdul da Hadiza. Da daddare Abdul ya shigo parlour ya tadda Saudala tana kallo ita kad'ai a parlourn. Zama yayi a kan kujera Yace "tun d'azu nake jiran ki Amma baki zoba, bayan kin San bani da Lafiya." Kallan up and down Saudala tayi masa san'nan tace ........... *ku tayi ni da Addu'a yau bana jin dad'i*🀦🏻‍♀ Comment & Share Neat LadyπŸ₯°πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ² 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my family*πŸ₯° *Bismillahir rahmanir rahim* 67&68 Kallan sa tayi tace "Ni babu inda zani ,daman ai dan baka da lafiya ne aka sani naje , yanzu kuwa ai kaji sauΖ™i." Ƙura mata ido yayi yana kallonta , shiru yayi bai Ζ™ara cewa komai ba. Mama ce ta fito parloun tana faΙ—in, "A'a Abdul yaushe ka shigo.?" Yace " ban daΙ—e da shigowa ba." Ya fad'a yana kallon Saudala. Mik'ewa Saudala tayi tace , "Mama sai da safe ." ta fad'a tana shiga d'akin su. Mama kallan Abdul tayi da ya zubawa Saudala ido tace , "to ai ta shiga d'aki sai ka tashi ka tafi." Sosa kai da Abdul yayi Dan yasan da ganshi, Mik'ewa yayi jiki ba k'wari ya fita daga parlourn. Murmushi Mama tayi tace , "yaran zamani sai dai a bar su." Tunda Abdul ya shiga parlourn sa yake ganin d'akin yayi masa fad'i , zama yayi yana tunanin zaman su da Saudala. Tuno taimakon da tayi masa lokacin da ya da yake fama da ciwon kai , murmushi yayi yana jin wani Abu na masa yawo a cikin jikin sa . Mik'ewa yayi ya shiga d'akin ya kwanta. Ɓangaren Saudala ita kanta jinta take wani iri , juyi kawai take a kan gado , a haka bacci ya Ι—auke ta. Ranar alhamis da daddare Abdul yana zaune a garden Ι—in gidan yana hutawa , dan cikin kwanakin nan kullum a busy yake . yana zaune yans danna waya Saudala tazo wucewa , sam bata lura akwai mutum a wajan ba . Tafiya take kanta a k'asa , jitayi tayi karo da mutum , cikin sauri ta d'ago kai dan taga Wanda ta buge . Tana d'agowa suka had'a ido da Abdul yana tsaye ya zuba mata ido . Tab'e baki tayi ta rab'a ta gefen sa zata wuce , hannun ta ya rik'e ya dawo ita ya rik'e kafad'un ta yace , "ina kika shiga kwana biyu bana ganin ki.?" Turo baki Saudala tayi tace, "ai mun koma makaranta." Ta fad'a ta k'ok'arin barin wajan. K'ara damk'e hannun ta yayi yace , "Ai bance ki tafi ba , yanzu ina zaki .?" STORY CONTINUES BELOW Saudala tace "Umma ce ta aike ni." B'ata fuska yayi yace "shine kike fitowa harabar gidan nan babu hijjabi bayan kin San ke matar aure ce ." D'auke kai tayi bace komai ba , Dan ta gaji da magana. Yace "sai wani b'ata rai kike ko duk cikin kishi ne ? , nasan kina tunanin gobe zaki zama mai kishiya ko.?" Ya fad'a yana kashe mata ido d'aya. Girgiza kai Saudala tayi san'nan tayi murmushi tace , "Ai Wanda ake so shi ake kishi ba Wanda ba'a so ba , kamar yadda kake fad'ar baka sona nima ai ba sonka nake ba , kaga kuwa babu abin wani kishi a nan." Ta gama fad'ar haka ta fizge hannun ta ta bar wajan. Abdul kuwa yana tsaye kamar an dasa shi a wajan , Sam baiyi tunanin zata iya furta masa bata son sa ba. Komawa yayi ya zauna ya dafe Kai da hannu biyu , wani iri zafi yake ji a ransa , tunani yake wai yaushe ma Yace baya sonta a gabanta?, nan take ya tuno lokacin da Hadiza tazo tabbas ya furta haka Amma lokacin baiyi tunanin zata ji wani Abu ba idan ya furta haka ba , to wai meyasa ma nace bana sonta?, bayan nasan tun tana Yarinya nake dakon sonta , ajiyar xuciya ya sauke yana tuno kalmar _NIMA AI BA SONKA NAKE BA_, rintse ido yayi yana jin zafi a zuciyar sa. Saudala kuwa tunda ta bar wajan take tunanin yanzu gobe skeleton zata shigo gidan nan a matsayin matar Abdul , tsaki tayi tace, "Wai ni meyasa na damu , ina ruwana da auren sa." Kawar da tunanin tayi a ranta ta cigaba da harkokin ta. Washe gari aka tashi da shirin tafiya Kano d'aurin aure . Bayan sun tafi Saudala ta shirya ta tafi makaranta dan zasuyi test . ****** A can Kano kuwa amarya Hadiza jira kawai take taji ance an d'aura , tana zaune taci gayu cikin wani less lemon green yayi mata k'yau sosai , k'awayen ta zagaye da ita ana shan hira. Da misalin karfe sha d'aya na safe mutane suka shaida d'aurin auren *_Abdulrahman Umar Abdulrahman da Hadiza Abubakar Musa_* akan sadaki naira dubu D'ari . Hadiza tunda taji an d'aura take murna tana rawa , k'awayen ta suna dad'a zuga ta. B'angaren ango kuwa babu laifi yana cikin farin ciki , Amma a xuciyar sa banda tunanin abinda Saudala ta fad'a masa a daren jiya babu abinda yake. Babu dad'ewa masu d'aukar amarya suka baiyana Dan a can Abujan za'ayi shagali. Tak'aitatcen lunching aka had'a a meena event center , an sha shagali Amarya sai rawa take tana juyi, shi dai Abdul kallan ta kawai yake yana murmushi. Bayan an tashi aka shirya Amarya aka yi mata nasiha sosai , ita dai Hadiza so take Kawai ta ganta a gidan ta. Gab da la'asar aka d'auko Amarya a jirgi aka tafi garin Abuja. Angwayen sun riga su sauka Dan sun riga su tawowa , Abdul yana zaune a parlour shida abokansa ana ta tsokanar sa ana dariya. Koda su Hadiza suka iso gidan su Abdul suka shigo , da yake iyayen Hadiza y'an boko ne cewa sukayi Hadiza ta zauna a gidan su Abdul a k'arasa biki sabida su london zasu wuce. part aka basu a gidan ita da y'an uwata da k'awayen ta . Har aka idar da sallar la'asar Saudala bata dawo gida ba , babu Wanda ya lura bata gidan sabida hidimar biki. Waje su Abdul suka koma shida abokansa suka zauna suna hira . Mota ce tayi parking dai-dai inda su Abdul suke , bud'e gaban motar Saudala tayi ta fito , tsayawa tayi tana yiwa Wanda ya kawo ta bye . Kallan inda su Abdul suke tayi , gabanta ya fad'i ganin wadda Abdul yake wuci , idon sa yayi ja , cikin sauri ta shiga gida tana waiwaye. Kafin ta k'arasa main parlour taji an rik'e hannun ta ana janta, bai tsaya a ko ina ba sai a cikin parlour sa , hankad'a ta parlourn yayi yana wuci ,kafin tayi wata magana ya d'auke ta da mari , kafin ta gama jin zafin sa ya kuma kifa mats wani, nunata yake da yatsa yana fad'in, "Uban waye wa sauke ki a mota Yanzu?, daga Ina kike?, wa kika tambaya kafin ki fita?". Ja da baya Saudala take tana girgiza kai tana yarfe hannu, Tara wace amsa zata fara bashi . Cikin tsawa yace " bada ke nake magana ba.!" Culinary kuka tace "wallahi Yaya Abdul daga makaranta nake , in kuma baka yarda ba muje ka tambaya." "Me kika tsaya yi har wan'nan lokacin bayan kuma yau Friday." Tace "wallahi lesson muka tsaya yi , kasan mun kusa fara junior waec." Ajiyar xuciya yayi san'nan yace "Waye ya sauke ki a mota ?" Share hawaye tayi tace " Yayan y'ar ajinmu ne yazo d'aukan ta yaga ina tsaye har lokacin ba'azo d'auka taba sai yace bara ya kawo ni , Amma wallahi ban tab'ama yi masa magana ba, kuma ko ita khadijan ta sani." Zama yayi ya jingina da kujera yana ajiyar xuciya. Cikin sanyin murya yace "karki k'ara tsayawa lesson ba tare da kin sanar dani ba, san'nan kar ki k'ara shiga motar wani kowaye shi in ba haka ba daga ranar ki daina zuwa makarantar ." D'aga kai Saudala tayi alamun ta amince . Murmushi yayi yace "good beauty , san'nan daga yau babu ke babu saka wan'nan siket d'in , kuma wan'nan hijjabin ma yayi kad'an shima zaki ajjiye shi, zanje makarantar da kaina zanyi musu bayani ." Saudala tace "Amma Yaya Abdul kowa fa haka yake sawa ." ta fad'a cikin shagwab'a. Y'ar dariya yayi Dan tayi bala'in birge shi , san'nan Yace "bak'ya ganin ke matar aure ce , ai dake dasu ba d'aya bane ." Turo baki tayi tana k'unk'uni k'asa-k'asa . Kallan ta yayi yace "ke kika ce?". Cikin sauri tace " zan koma part d'in Mama." Yace "tashi ki tafi." Mik'ewa tayi ta fara tafiya har ta rik'e handle d'in k'ofar ya dakatar da ita da fad'in, "Dawo ki zauna baa ki fita da wan'nan siket d'in ba , bara naje wajan Fadila ta bani kayan ki." Ya fad'a yana Mik'ewa ya fita . Yana fita ta kalle shi tace "wan'nan brown strowman d'in ya takura min , kuma sai na fanshe Marin da yayi min." Shikuwa Abdul.......... *Am sorry yau kun ganni late, daky'ar nayi wan'nan din ma*🀦🏻‍♀ Comment & share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sisters*❤ *Bismillahir rahmanir rahim* 69&70 Shikuwa Abdul part d'in Mama shiga babu ko kuna mutanen da suka parlourn yayi shigewar sa d'akin Mama.+ Ita da Fadila ne a d'akin da ya shiga da sallama. Amsawa Mama tayi tare da fad'in , "Abdul kuna tare da Saudat ne.?" Abdul yace "eh Mama bata dad'e da dawowa ba , wai lesson suka tsaya yi a makarantar." Ajiyar xuciya Mama tayi tace "maza kira min ita ga mutane tun d'azu suke son ganin ta." Yace "to bara na kira ta, Fadila zo in aike ki." Ya fad'a yana fita daga d'akin. Bin yaban sa Fadila tayi tace "gani ". Had'e rai yayi san'nan yace , " ki shiga d'aki ki d'auko min kayan da Saudat zata saka yanzu ina jiran ki a part d'in na." Yana gama fad'ar hakan ya juya ya bar wajan. Da kallo Fadila ta bishi tana tunanin yaushe suka fara shiri da Saudat har haka , d'aki ta shiga ta d'auko kayan ta fito. Da Iya suka had'u tazo zata shiga d'akin Fadilan , tana ganin ta tace , "yauwa Fadila maza ga bak'i can kije ki kai musu abinci." Fadila tace "to Iya, Amma bara na kai wan'nan sak'on ko." Kallan abin hannun ta Iya tayi san'nan tace "ina kuma zakije da kaya a hannun ki.?" Fadila tace "kayan Saudat ne Yaya Abdul ne yace na ka masa part d'in sa." Ta k'arasa maganar tana barin wajan . Rik'e baki Iya tayi tace "toh lallai mai k'atan kai ya cika Mara kunya." Bayan Abdul ya fita daga part d'in Mama nasa ya koma , a inda ya barta anan ya dawo ya same ta . Zama yayi baice komai ba itama kuma haka. Fadila ce ta shigo d'akin da sallama , kallan inda Saudala take tayi san'nan tace , "Yaya Abdul gashi." Ta fad'a tana mik'a masa kayan . Karb'a yayi ya ajiye a kusa dashi ya kalli Fadila Yace, "zaki iya tafiya." Fadila tace "Amma bro zafa ayi mata make up , sai dai na kira mai make up d'in nan in yaso tayi mata anan d'in." Yace "naji ki kira Dan bazata fita da wan'nan munafukin siket d'in ba kamar wata wacce zata tsallake wuta." Murmushi Fadila tayi tace "idan ta gama shirya a sai kayi min waya muzo da mai make up d'in." Ta fad'a tana barin parlourn. Kallan Saudala yayi yace "tashi kije ki saka kayan ." ya ce yana mik'o mata . Karb'a tayi san'nan tace "zan shiga wanka kar ka shigo d'akin har sai na gama." Ta fad'a tana murgud'a baki. Sakin baki yayi yana kallan ta yayi murmushi yace, "d'aki nane inda ikon da zan shigo lokacin da naga dama." Ba tace komai ba ta shiga d'akin ta saka key . STORY CONTINUES BELOW Yana zaune a parlour har ta shirya ta fito cikin dark blue d'in material yayi mata k'yau sosai. Zama tayi a kan kujera tana wasa da hannun ta. Tunda ta fito ya zuba mata ido yana kallan ta , gani yake kamar ba ita ba dan kayan sun haska ta . Fadila ya kira yace suzo ta gama. Babu jimawa suka k'araso, Abdul ya fita ya koma wajan Abokansa da sukayi masa waya Dan shi harga Allah ya manta dasu. Bayan gama make up d'in suka fito daga part d'in Abdul suka nufi na Mama . Anan Saudala taga mutanen Adamawa sun k'araso ciki hadda aminenta Talatu da Dije , murna Saudala take kamar me , suma kuma haka. Da daddare aka fara shirin tafiya dinner mutane har sun fara tafiya. B'angaren Amarya Hadiza an shirya cikin light blue d'in gown , tayi mata k'yau kamar y'ar tsana.🀭 Tana zaune kiran Abdul ya shigo wayar ta , d'auka tayi tana wani kashe murya tace , "Hello my husband na gama shirya wa." Abdul yace "zaki iya fitowa mu tafi ." Fitowa sukayi harabar gidan , babu kowa da alama kowa ya tafi kenan . Cikin takun k'asaita Hadiza take tafiya har ta k'arasa motar da Abdul yake ciki. Bud'e gaban motar tayi ta shiga tana wani fari da ido. Kallan Abdul tayi nan taji ta raina kanta dan ko kusa bata kama k'afar k'yau da Abdul yayi ba. Yana sanye cikin Golding d'in sadda ya d'aura hula gold , ga agogo gold , kai ko mai gwaza taga Abdul sata yaba balle Hadiza .😜 Yace "ya dai my hady wan'nan kallan fa.?" Ya fad'a yana kashe mata ido. Murmushi tayi tace "kayi k'yau sosai." Hancin ta yaja yace "kema haka" ya fad'a yana kunna motar suka d'auki hanya. Saudala kuwa suna tare da Fadila suna shiryawa , Mama ce ta shigo d'akin tana fad'in, "Haba Fadila yanzu kowa ya tafi ke kuna nan har yanzu Baku shirya ba.?" Fadila tace "mun gama Mama yanzu zamu tafi." Mama tace "ai gwara ku tafi , Saudat juyo naga k'walliyar ." Mik'ewa Saudala tayi ta juyo tana kallan Mama . Mama tace "masha Allah gaskiya fa kinyi k'yau Sosai." Murmushi Saudala tayi bata ce komai ba. Khadija k'awar Saudala ta shigo tana fad'in , "gaskiya Saudat kinyi k'yau , kuma sai kukayi anko da angon ." Fadila tace "da gaske shima Golding color yasa .?" Khadija tace "wallahi shima Golding d'in sadda yasa , Amarya kuma blue." Murmushi Fadila tayi tace "haka ake so." Fitowa sukayi suka shiga motar Mama suka d'au hanya. Lokacin da suka je har angon ya shiga , hall d'in sukayi su uku, suna shiga kallo ya dawo ya kansu , babu kamar Saudala da wasu ke cewa anya tana jin Hausa. A hankalin suke takawa har suka isa table d'in da aka tanadar musu suka zauna. Saudala ta juya ts kalli wajan da ango yake zaune , aikuwa suka had'a ido ya zabga mata harara tare yin k'wafa. Mayar masa da hararar sa tayi tare da murgud'a baki. D'auke kai tayi bata kuma kallon inda yake ba. STORY CONTINUES BELOW Fadila tace "Saudat bara naje ba yiwa bro liki tunda kince ke sai anjima." Saudat tace "to sai kin dawo." Aka fara rabon abinci da na sha , Saudala dai tana zaune ko motsawa bata yi ba . Abinci aka Kai table d'in y'an Gaskiya writer's , haba su mai gwaza da Ummu Hanash har da safayar wani a Leda, miss xerks kuwa ai ba'a magana kawai ci ake kamar me , sauran dai sun zuba ido suna kallon ikon Allah.πŸ˜‚ Abinci aka kai table d'in da Saudala take , bata d'ago kai bana balle ta kalli abinci wayar Fadila take dan'nawa. Wani saurayi ne ya zauna a kusa da ita yace , "barka da hutawa y'an mata." D'agowa tayi ta kalle shi ta cigaba da abinda take bata amsa masa ba. Saurayin yace "y'an mata ina magana kinyi shiru , ko sai na baki abincin a baki ne .?" Ya fad'a ya d'ibar abincin yakai bakin ta. Tasssss kike ji an d'auke saurayin da mari , ita kanta Saudala sai da ta tsoro ta tayi saurin d'ago kanta taga waye wan'nan. Four eyes sukayi da Abdul da ya baro Amaryar sa yana wuci . Cikin rawar murya tace "Yaya ......Ab...dul .....wal..." Kafin ta k'arasa ya ja hannun ta suka bar hall d'in . Hadiza kuwa ranta yayi bala'in b'aci , cikin fushi ta mik'e ta bar Hall d'in. Nan da nan taro ya watse kowa ya kama gabansa , Ummu nabil dai bata so haka ba Dan bata gama k'wasar gara ba . Gudu Abdul yake a mota kamar zai tashi sama sabida fushi . Ita dai Saudala kuka Kawai take Dan tasan yau ta shiga uku. Yana isa gidan da k'arfi yake danna horn , cikin azama aka bud'e masa ya shiga a guje. Cikin sauri sojojin sa suka k'araso Amma ganin fuskar ogan nasu yasa kuja baya. Janta yake har cikin parlourn sa , suna shiga ya sawa k'ofar key san'nan ta juyo ya fara cewa, "Mai yasa kike son b'ata min rai ? , so kike zuciyata ta buga ?, meyasa Saudat, kin san yadda nake sonki kuwa , kinsan yadda nake kishin ki kuwa , baki sani ba shiyasa kike k'ok'arin ganin kin samin ciwon zuciya, INA SONKI SAUDAT ! INA SONKI. Da k'arfi aka danno k'ofar parlourn. Comment & Share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sisters❤* *JUMA'A MUBARAK*πŸ•Œ *Bismillahir rahmanir rahim* 71&72 Juyawa yayi yaga wani mara hankalin ne wan'nan , ido hud'u sukayi da Hadiza tana faman zare ido. Cikin hargagi Hadiza ta fara fad'in, "Amma gaskiya ka cika munafiki , yanzu duk abinda kake fad'a min akan wan'nan Yarinyar daman k'arya kake, kace min baka sonta kuma baza ka tab'a sonta ba , to wallahi bazan zauna da wan'nan Yarinyar ba sai dai ka zab'a koni ko Ita." Tana gama fad'ar hakan ta fita da gudu. STORY CONTINUES BELOW Juyawa Abdul yayi ya kalli Saudala da take tsaye , ta rasa maganar wa zata d'auka a cikin su. Rik'e hannun ta yayi ya zaunar da ita a kan kujera yace , "ki yarda dani Saudat wallahi ina sonki , kece mace ta farko Dana fara so a rayuwa ta , tunda aka haife ki Allah yasa min k'aunar ki a cikin raina , dai-dai da second d'aya ban tab'a jin sonki ya ragu a cikin zuciyata ba, pls Saudatu kada kice baki yarda da abinda nake fad'a miki ba." Ya k'are maganar yana kallon cikin idon ta. Shiru Saudala tayi ba tace komai ba . Jijjiga hannun ta yayi yace "say something mana " Mik'ewa Saudala tayi tace "zanje na kwanta , sai da safe. " bata jira mai zaice ba ta fice daga parlourn. Jingina yayi da kujera ya lumshe ido yana k'ara jin sabuwar k'aunar ta tana yawo a jikin sa , B'angaren d'aya na zuciyar sa banda haushin Hadiza babu abinda yake ji. Saudala kuwa part d'in Umma ta shiga jiki a sanyaye , zama tayi kusa da Umma ta kwantar da kanta akan kafad'ar Umma. Umma tace "mai yake damun ki na ganki wani iri.?" Saudala tace "babu komai Umma kawai bacci nake ji." Umma tace "kafin kiyi baccin daman ina son magana dake " Saudala ta mik'e zaune tace "ina jinki Umma." Umma tayi k'ok'arin kawar da kunya idon ta tace, "Saudat ki bud'e kunnen ki dak'yau kiji abinda Zan fad'a miki, duk abinda kike yi a cikin gidan nan ina sane dake na zuba miki ido ne naga iya gudun ruwan ki , to naga abin naki kullum gaba yake ki bud'e kunnen kiji abinda zan fad'a miki, Abdulrahman mijinki ne duk abinda ya shhiga tsakanin ki dashi kar na k'ara ji kin fad'awa wani a cikin gidan nan balle har ki dinga kiran sa da d'an iska, nasan an koya miki mai aure yake nufi a islamiyya kuma nasan wani abun kina sane kikeyi , Abdul yana da ikon yin duk abinda yaga dama dake , domin Allah ya halatta masa ke tunda ke matar sa ce , Dan haka ki shiga hankalin ki , ko me Abdul zai miki kar ki sake ki fad'awa kowa ko nice kar ki fad'a min , ki barshi tsakanin ke dashi , ina fad'a miki tunda nasan gobe i warhaka kina gidan ki , Saudat kiyiwa mijinki biyayya , babu zancen ramuwa a tsakanin ku duk abinda yayi miki bakiji dad'in saba ki barshi a ranki kiyi hak'uri kar kice sai kin rama , shi aure da kike ganinsa hak'uri shi yake rik'e dashi , duk son da mijinki yake miki in baki da hak'uri baza ku tab'a zama Lafiya ba , domin dole wata rana ku sami sab'ani a tsakanin ku, zaman tare ya gaji haka dole wata rana sai an sami sab'ani indai za'a zauna waje d'aya, Allah ya Baku zaman Lafiya , tashi kije ki kwanta dare yayi." Mik'ewa Saudala tayi jikinta yayi sanyi sosai , maganganun Umma sun yi bala'in tasiri a cikin zuciyarta . Tunda ta kwanta take juyi akan gado , gabad'aya maganganun Umma da Abdul ne suke mata yawo a cikin k'wak'walwarta , a haka har bacci ya d'auke ta. B'angaren Hadiza kuwa tunda tabar part d'in Abdul take kuka . Waya ta d'auka ta kira Momyn ta a cikin Daren, Momy na d'agawa Hadiza ta fashe da kuka ta zaiyane mata abinda ya faru. Sosai hankalin Momy ya tashi , Amma sai tace ," kiyi hak'uri daughter ki kwantar da hankalin ki , ko barmin komai a hannu na , san'nan kar ki sake ki nuna masa bak'ya son ita kishiyar taki , kije ki bashi hak'uri ta haka zamu samu damar aiwatar da aikin mu." Hadiza tayi na'am da shawarar Momy hakan yasa ta cire komai a ranta tayi baccin ta. Washe gari Tun safe Abdul yake baza ido ko zaiga Saudat Amma shiru har kusan azahar bai ganta ba . Ya shiga damuwa sosai kawai daurewa yake. Saudala kuwa tana part Umma gabad'aya tak'i fitowa daga part d'in , acewar ta kunyar Mama take ji.(oh ni y'asu Saudala najin kunyar MamaπŸ˜‚) STORY CONTINUES BELOW Mama tayi aiken duniya Amma Saudala tak'i fitowa, hakan yasa tazo part d'in da kanta Dan a fara shirin kaita. Da yamma bayan an tashi daga walima wacce aka gaiyato malamai mata suka yiwa amare nasiha mai ratsa jiki, tun anan Saudala ta fara kuka har akazo za'a tafi kaita. Abba da Baba sun yiwa Saudala nasiha sosai , daga nan aka tafi kai Saudala gidan mai hancin karas. Da dayake gidan babu nisa yasa nan da nan aka k'arasa, tun daga bakin gate nake kallon gidan nida Aunty Baby, tsayawa fad'ar had'awar sa b'ata lokacine , part uku ne a gidan na farko shine na Saudat na tsakiya shine na Abdul na gefe kuma na Hadiza. Aka shiga da Saudala d'akin ta aka zaunar da ita , a hankalin mutane suka fara watsewa ya rage daga Fadila sai Khadija a wajan Saudala . Suna zaune aka shigo da Amarya Hadiza itama aka wuce da ita part d'inta . Sai wajan k'arfe Tara na dare san'nan ango Abdul ya k'araso , babu wasu abokai daga shi sai Mustapha. Part d'in Saudala suka shiga , a parlour suka gansu a zaune ita da Fadila Dan Khadija ta tafi tun d'azu. Babu dad'ewa Mustapha ma ya fito shida masoyiyar sa Fadila suka bar gidan. Abdul kallon Saudala yake wacce take kuka kamar ranta zai fita, tashi yayi ya dawo kusa ita ya zauna , san'nan ya rungumota yana shafa bayanta alamun rarrashi. Babu Wanda yayi magana a cikin su , ganin ta rage kuka sai ya mik'e ya nufi part d'in Hadiza. A zaune ya ganta a parlour taci k'walliyya cikin rigar bacci y'ar k'arama wacce ko guiwa bata k'arasa ba. Ta ganin sa ta mik'e cikin yanga tace , "wel come my dear." Ido ya zuba mata yana mamakin wan'nan wace irin Amarya ce . Zama yayi a kan kujera yace , "ki tashi ki saka hijjabi ki same ni a part d'in Saudat." Yana gama fad'ar haka ya mik'e ya fita daga parlourn. Ran Hadiza ya b'aci sosai , da kamar bazata je Amma da ta tuna abinda Momy tace mata sai ta saka hijjabin ta fito. A zaune ta ganshi kusa da Saudala ya zuba mata ido kamar ya lashe ta. Zama tayi san'nan tace "gani." Gyara zama Abdul yayi Addu'a san'nan yayi musu nasiha akan zaman Lafiya , san'nan ya d'aura da cewa, "maganar kwana kuma kamar yadda al'ada ta tanadar za'ayi kwana bakwai a d'akin Amarya to ku tunda ku biyu ne za'a raba shi kwana biyu-biyu, san......" Kafin ya k'arasa Hadiza tace "wani irin kwana biyu bayan ita ba jiya aka d'aura maka auren da ita ba, ai kwanan ta ya wuce yanzu nawa ne." Ganin tayi shiru sai Abdul yace "kin gama, to bara kiji yadda aka kawo ki yau itama yau aka kawota , Dan haka yau kwanan tane ba naki ba." Sai kuwa Hadiza ta mik'e tace "wallahi baka isa ba , sai dai yau a raba Daren biyu, Dan bazan yarda ka fara sanin wata Mace ba kafin ni." Cikin b'acin rai Abdul yace, "wai ke wace irin Amarya ce Mara kamun Kai, to bara kiji sai dai kiyi haukan ki ki gama Amma yau da gobe ba naki nabe, rubbish kawai." Da gudu Hadiza ta fita daga parlourn tana kuka. Tsaki yayi yace "ban tab'a ganin Amarya irinta ba , wai amarya ce take Neman miji." Itadai Saudala duk tana jinsu babu abinda tace . Kallan Saudala yayi yaga ko d'ago kanta batayi ba , wani sonta yaji yana k'ara bin jikin sa , nan da nan ya nemi b'acin rai ya rasa . STORY CONTINUES BELOW Cikin sanyin murya yace "Saudat tashi muje d'aki." Shiru tayi bace komai ba, ko motsawa batayi ba, ganin haka Abdul ya d'auke ta cak sai d'akin sa.πŸ˜‰ Comment & Share 🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 '''Dedication to my blood sisters❤''' *Bismillahir rahmanir rahim* 73&74 D'akinsa ya shiga da ita , har suka shiga d'akin bai sauke taba. Cikin dashewar murya tace , "Ni ka sauke ni ka wani d'auko ni kamar Mara Lafiya." Murmushi yayi yace "wato kedai bakin ki baya mutuwa ko,? Ai na zata kurma kika zama tunda bakiyi magana ba sai yanzu, to yi alwala muyi sallah." Ya fad'a yana sauke ta k'asa. Turo baki tayi tace "banga abinda zai sa bakina ya mutu ba , Allah ya yaga min baki ace bazan yi magana ba, ai d'azu ina bud'e baki na to wallahi dariya zanyi ,Dan tsinken matar taka dariya take bani ." Y'ar dariya yayi yace "kodai kishi ki ke ?." Kallonsa tayi ta tab'e baki tace "kishi wa zanyi , kishin Wanda bayata k'aunata kome ?." Ta fad'a tana shiga toilet. Shiru yayi ya zauna a gefen gado ya dafe kai , wani irin zafi yake ji a cikin ransa , numfashi kawai yake fitarwa. Har ta fito daga toilet d'in yana zaune , kallan sa tayi taga ya dafe kai sai taji ya bata tausayi , nan da nan ta shiga dana sanin abinda ta fad'a masa. Cikin sanyin murya tace "nayi alwalar." D'agowa yayi ya kalle ta saurin d'auke Kai tayi ganin yadda idon sa ya koma red colour , bai ce komai ba ya mik'e ya shimfid'a sallaya suka tayar da sallah. Bayan sun idar yayi mata tambayoyi akan addini yana tambayar ta tana bashi amsa, Sosai ta k'ara birge shi Dan har ga Allah yana son mace mai addini kodan sabida tarbiyyar yaran sa. Tashi yayi ya fita , bai dad'e ba ya dawo d'auke da plates da juices , ajiyewa yayi a gabanta yace , "Bismillah." Duk abinda yake fuskar sa a had'e take. Girgiza kai Saudala tayi alamun ta k'oshi. Wata harara ya watsa mata ai bata san lokacin da tasa hannu ta fara ci ba . Bata ci da yawa ba ta mik'e tace , "na k'oshi, bacci nake ji." Mik'ewa shima yayi ya k'araso daf da ita har suna jin numfashin juna Hannun ta rik'e yace "Saudat.....", wani iri taji a jikinta , tace " Na'am. " Yace "meyasa har yanzu kin kasa yarda da abinda nake fad'a miki ba , meyasa har yanzu baki yarda da son da nake miki ba , wallahi! Wallahi !! Kice mace ta farko da na fara so a rayuwa ta , tun ranar da kika fad'o cikin duniya Allah ya d'aura min sonki, duk abinda kika ga nayi miki a da nayi shine ba'a son raina ba , Saudat ki amince da abinda nake fad'a miki koda baza ki soni ba ki yarda da son da nake miki, ina sonki , bazan iya rabuwa dake ba ." ya k'arasa maganar yana hugging d'inta. STORY CONTINUES BELOW Bugun zuciyar sa take ji har brain d'inta . A hankali ta zare jikin ta daga jikinsa ta koma ta zauna , ganin haka yasa ya juya ya fita daga d'akin . Ganin ya fita yasa ta cire kayanta ya gare daga ita sai vest sai under , ko fitilar d'akin bata kashe ba ta kwanta zuciyar ta a cukushe. Shi kuwa Abdul parlour ya koma ya zauna , tunani ya shiga yi , tuno lokacin da Saudat take Yarinya da yadda bata yarda da kowa in bashi ba , lumshe ido yayi yana tuna lokacin da take kula dashi da bashi da Lafiya. Bai san dare yayi ba sai kallon agogo yayi yaga sha biyu har tayi . Mik'ewa yayi ya shiga d'akin Dan ya kashe mata fitilar d'akin, yanayin da ya ganta a ciki ne yasa ya zuba mata ido yana kallon ta , siket d'in ya d'age sama cinyoyin ta gabad'aya a waje , vest d'inta ta zame ana ganin rabin breast d'inta. Lokaci d'aya ya fara fita daga haiyacin sa yana jin wani Abu nayi masa yawo a jikin sa, kashe wutar d'akin yayi ya koma bayan ta ya kwanta ya jayota jikin sa , cikin bacci Saudat taji ana shafa ta , tana bud'e ido suka had'a ido da Abdul, bud'e baki tayi zatayi ihu yayi saurin had'e bakin su waje d'aya. Mutsu-mutsu Saudala takeyi tana san k'wace kanta amma ta kasa , ganin Abdul da gaske yake yasa na fito da sauri na kulle musu k'ofar , Dan miss xerks ta hana ni leken ma'aurata. Jin ihun Saudala da sheshshek'ar kuka yasa na fita na tafi part d'in Hady. Hady kuwa tunda ta bar part d'in take kuka kamar ranta zai fita , wani irin kishi take ji a ranta ji take kamar ta k'ona gidan gabad'ayansu su mutu. K'arar wayar tane ya katse mata tunani , ganin sunan Momy yasa tayi saurin d'agawa tare da fashewa da kuka. Momy tace "daughter Lafiya kike kuka haka meya faru?." Cikin kuka Hadiza ta kwashe komai ta bawa Momy labari , ta d'aura da cewa "wallahi Momy ji nake kamar na kashe Yarinyar , akanta ya wulak'antani , yanzu haka yana can tare da wata bani ba ." ta k'arasa tana fashewa da kuka. Momy tace "kash kinyi wauta daughter , bai kamata ki nuna masa kinji haushin abinda yayi ba , na fad'a miki ki dinga nuna masa ke a matsayin k'anwa kika d'auki Yarinyar , yanzu da gobe da safe kisa a had'a musu break fast ki kai musu da kanki , ki bashi hak'uri akan abinda kikayi masa , ki dinga nuna masa kina son matar tasa har ya gama yarda dake , to anan aikin mu zai fara , zan fad'a miki duk abinda zakiyi , sai munsa Yarinyar ta fita daga ransa gabad'aya , kedai ki kwantar da hankalin ki duk abinda na fad'a miki kiyi ." Ajiyar xuciya Hady tayi tace "to Momy insha Allah zanyi duk abinda kika ce , Allah ya bar min ke Momy na." Momy tace "Kar ki damu daughter ki kwantar da hankalin , ki kwanta kiyi bacci ." ta fad'a tana kashe wayar. Kwanciya Hady tayi tana murmushi mugunta. B'angaren Saudala kuwa tun tana kuka har ta daina numfashi gabad'aya, A kwance gabad'ayansu babu Wanda yake numfashi alamun dukkan su a sume suke , (oh kwaila ta sumar da AbdulπŸ˜‚) Abdul ne ya fara farkawa , kallan inda Saudala take Abdul yayi ganin har yanzu bata motsi yasa ya Mik'e da sauri ya nufi wajan ta. Towel ya d'aura a jikin sa ya d'auko ruwa ya shafa mata a fuska, duk abinda yake a rud'e Yake yinsa . Ganin bata farfad'o ba yasa ya d'auke ta ya shiga toilet yasa ta a ruwa zafi, ajiyar xuciya Saudala tayi tare da sakin k'ara mai sauti. Had'a ido sukayi da Abdul sai kuwa ta fashe da kuka kamar wacce aka yiwa mutuwa , shima Abdul d'in hawaye yake Dan gabad'aya tausayin ta yake ji. Cikin dashewar murya ta fara fad'in , "ni ka fita ka k'yale ni tunda baka sona , kuma bazan k'ara kwana a gidan nan ba tunda kashe ni kake sonyi." STORY CONTINUES BELOW Hawaye ya share mata Yace "am sorry habibty ni kaina basan lokacin da haka ta faru ba , am sorry pls ." Cikin masifa Saudala tace "nace ka fita zanyi da kaina." Mik'ewa yayi ya fita daga toilet d'in , bedsheet d'in ya cire yaje ya wanke ya shanya san'nan ya shima ya shiga wanka. Har ya dawo d'akin bata fito daga toilet d'in ba , kukan ta ya jiyo yayi saurin shiga yana tambayar Lafiya. A zaune ya ganta a toilet d'in , tsugunawa yayi a gabanta yace , "Lafiya me ya faru?." Cike da jin haushi Saudala tace "na kasa tafiya , shikenan na zama gurguwa na daina tafiya ." ta k'ara fashewa da kuka. Dariya ta bashi Amma sai ya danne gudun karya k'ara jugwalo wata rigima yace , "Ayyah bara na taimaka miki." Ya fad'a yana d'aukan ta, Fitowa yayi da ita ya kwantar da ita akan gado , zama yayi kusa da ita yana shafa kanta. Abdul ne ya fara cewa "Allah yayi miki albarka habibty , hak'ik'a kin sani farin cikin da ban tab'a mafarkin shiga ba a rayuwa ta , ina sonki Saudat , baza tab'a daina furta miki wan'nan kalma ba har k'arshe rayuwata ," wani Abu naga ya fito dashi daga aljihun jallabiyar sa , rik'e hannun ta yayi ya saka mata a finger d'inta , kwalin waya ya d'auko k'irar iPhone 11pro ya mik'e mata yace , "Wan'nan kyauta ce ta vigin d'inki da kika kawo min har cikin d'akina , nasan ko duniyar zan baki bazan tab'a biyan kiba , na baki wannan ne dan kema kisan kina da matsayi babba a wajena, kin k'ara k'ima a cikin idona , kin k'ara martaba a idon , ina rok'on Dan Allah ki rik'e min mutuncin ki , inada kishi akan abinda nake so , bawai ina zargin ki da wani Abu ba A'a ina fad'a miki ne har cikin zuciyata , Saudat ina yi miki son da ko kaina bana yiwa , ina kishin ki kishin da ko magana bana so ta had'a ki da wani namiji , ki soni Saudat ni kuma nayi miki alk'awari zan dinga saki farin ciki har k'arshen rayuwa ta." Saudala kuwa wani farin ciki take ji yana ratsa ta , sosai taji dad'in gifts d'in daya bata , duk maganar da yake bata d'ago kanta ba dan baza ta iya had'a ido dashi ba ,a hankali tace , "Nagode sosai , kuma nayi maka alk'awari zaka same ni mai bin duk abinda kake so , nag......." Katse ta yayi ta hanyar rife Mata baki yana girgiza mata kai yace , "Nine ya kamata na gode miki ba ke ba , bara na d'auko miki paracetamol naji jikin ki da zafi sosai." Ya fad'a yana Mik'ewa ya fita . Sai a san'nan Saudala ta d'ago kai , Dan ko kad'an bata son had'a ido dashi Dan kunyar sa take ji kamar k'asa ta tsage ta shiga ciki. Jim kad'an ya dawo kusa da ita ya zauna yace , "tashi kisha magani." Girgiza kai tayi cikin shagwab'a tace , "ni ba saina tashi ba kawai ka bani ko ka fita daman inaso zan saka kaya." Murmushi yayi yace "wai kunya ta kike ji , tab lallai to me kike b'oyewa bayan na gama ganin komai , har tab'a wa nayi ." ya fad'a yana kallonta. Rife kanta tayi da blanket tare da fashewa da kukan shagwab'a, Mik'ewa yayi yace "naji na fita." Ya fad'a yana fita daga d'akin. Dak'yar ta mik'e ta saka kaya ta sha magani ta koma ta kwanta sai bacci. Dawowa yayi d'akin ganin har tayi bacci shima ya kwanta a bayan ta . Washe gari da wuri Abdul ya tashi yayi wanka ya fito main parlour d'in gidan. Kamar yaje part d'in Hady sai kuma ya fasa ya Zauna yana tunanin abinda zai samawa Saudat na break fast kafin ta farka . Knocking yaji anayi , Mik'ewa yayi ya bud'e k'ofar drivern Mama ya gani ga kula na abinci , bayan sun gaisa ya bashi abincin ya juya ya koma. STORY CONTINUES BELOW Yana zaune yaji an bud'e k'ofar parlourn , yana juyawa suka had'a ido da Hady taci k'walliyya cikin atampa red colour tayi Mata k'yau sosai. Da murmushi ta k'araso cikin parlourn tana fad'in , "morning my life." Kallan ta yayi Dan har yanzu haushin ta yake ji , dak'yar Yace , "morning , kin tashi Lafiya." Far tayi da ido san'nan tace , "Lafiya lau , my life Dan Allah kayi hak'uri da abinda ya faru Daren jiya , nasan nayi kuskure insha Allah hakan bazai k'ara faruwa ba , ka yafe min pls , wallahi kishin kane yasa na aikata hakan ." ta fad'a tana hawaye. Sosai yaji ta bashi tausayi , alama yayi mata na tazo , rungumeta yayi yana bubbuga bayan ta , yace , "Shikenan ki daina kuka komai ya wuce ." Jin k'arar taku yasa ta k'ara kwanciya a jikin sa tana kukan munafunci . Saudala ta k'araso parlourn ganin yadda suke ba k'aramin b'ata mata rai yayi ba , Amma sai ta danne tace , "sannun ku." Cikin sauri Abdul ya saki Hady Dan shima baiji dad'in yadda ta same su ba. Mik'ewa Hady tayi yana fad'in , "barka da fitowa yayata." Kallon mamaki Saudat take yi mata , katse mata tunani Hady tayi da fad'in , "Sis kiyi hak'uri ki yafe min duk abinda ya faru kinji." Tab'e baki tayi tace "ni bakiyi min komai ba balle ki nemi yafiya ta." Ta fad'a tana shirin komawa part d'inta. Cikin sauri Hady tace "Sis ga break fast fa na had'a miki." Juyowa tayi tace "Nagode , ta fad'a tana fita daga parlourn. Cikin kissa Hady ta kalli Abdul tace , " My life kaje ka taya ni bata hak'uri naga har yanzu fushi take dani , kuma ni yanzu a matsayin yaya na d'auke ta." Mik'ewa Abdul yayi ya rik'e hannunta yace , "kar ki damu bata jin dad'i ne shiyasa , Amma bara naje na same ta ." ya fad'a yana barin parlourn Dan shima baiji dad'in abinda tayiwa Hady ba. Suna barin parlourn ta fashe da dariyar mugunta tace , "zaki sani ne Yarinya, yanzu aka fara wasan." Fita tayi daga parlourn tana jin dad'in shawarar Momy. Abdul kuwa...... *Tab wan'nan Hady d'in fa ......*πŸ€” Comment & share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sisters*❤ _Dan Allah a daina turo novel group d'in SAUDALA 1&2 indai ansan novel d'in na kudi , bai kamata ku dinga turo abinda aka ce Allah ya isa ba, duk wacce ta kuma turowa zan cire ta._🀷🏻‍♀ *Bismillahir rahmanir rahim* 75&76 Shikuwa Abdul part d'in Saudat ya shiga , zaune ya ganta tana danna wayar daya bata . STORY CONTINUES BELOW Kusa da ita ya zauna yana fad'in , "Amarya ba gaisuwa." Murmushi tayi ta sunkuyar da kai cikin kunya tace , "ina kwana." Tab'e baki yayi yace "sai da na rok'a , yauwa Saudat meyasa Hady tana yi miki magana kika k'i kula ta,? Kuma naga har hak'uri ta baki." Kawar da kai tayi san'nan tace , "to me tayi min da zata bani hak'uri tsabar gulma , an fad'a Mata tafini wayo Dan tafini shekaru ai bata fini wayo ba , da wani bakin ta kamar na agwagwa." K'ura mata ido yayi ganin yadda take magana babu ko tsayawa , sai da ta gama san'nan yace , "A'a Saudat tunda dai yazo ta bada hak'uri kuma tace baza ta sake ba ya kamata kema ki hak'ura ku zauna Lafiya , kinga a shekaru ta girme ki Amma ta ajiye girma tazo ta baki hak'uri ai kema sai hak'ura ko." Turo baki Saudala tayi tace "ai ko baka ce ta girme ni ba ai nasan ta girme ni , to ai ni ganina ke ko kai ta girme ka bani ba , a k'alla wan'nan skeleton d'in zatayi shekara talatin da biyar."🀣 Tab'a rai yayi yace " ni bashi na tambaye ki ba, nidai burina ku zauna Lafiya bana son tashin hankali. " Saudala tace "kaga mai hancin karas kasan halina indai ta amince da zaman Lafiya nima na amince , Amma kasan ni bazan d'auki rainin hankali back eheee." Ta fad'a tana murgud'a baki. Rik'e baki yayi yace "wai har yanzu baza ki daina rashin kunya ba , to shikenan bara nayi maganin bakin rashin kunyar , " ya fad'a yana shirin kamo ta. Da sauri ta mik'e tana dariya tana fad'in, "lallai ma brown strowman an fad'a maka zaka yi min yawo ne , to tun kafin a haife ka nake da wayo." Ta fad'a tana yi masa gwalo ta shiga d'akin. Murmushi yayi yana jin farin ciki na ratsa shi. Hady kuwa koda ta koma part d'inta rawa take tana juyawa ta had'a su fad'a , waya ta d'auka ta kira Momy ta sanar da ita abinda ya faru. Farin ciki Momy tayi sosai san'nan ta kuma bata wata shawarar . Fadila da Khadija suka zo suka sha hira da Saudat , ko kad'an bata gaya musu wani Abu da ya shiga tsakanin su da Abdul ba , sai dai yanayin tafiyar ta yasa suka gane komai. Da yamma sukayi mata sallama suka tafi , Da daddare bayan sallar i'sha Abdul da Saudala suna zaune a main parlour Saudat tana zabga masa shagwab'a , shikuma yana ta aikin lallab'a ta. Hady ta shigo parlour ganin yadda suke yasa taji ranta ya b'aci , Sam ba haka taso ta same su ba , taso tazo yaga kowa yana hararar d'an uwansa , Tana tsaye bata k'arasa cikin parlourn ba , Abdul ne ya ganta yace , "my Hady ki k'araso mana ." Cikin sauri ta saki ranta tare da murmushi yak'e tace , "Sannu ku da hutawa." Ta fad'a tana zama akan kujera. Abdul yayi murmushi yace "yauwa sannun ki , maza ga abinci can kije ki zuba kici." Kallan Saudala tayi da ta d'auke kai tace , "Aunty sannu da hutawa." "Oh my god , dan Allah ki daina cemin aunty , duk ranar da akace na girme ki ai na daina fita , su Iya sune Wanda suka girme ki sune suka dace da aunty bani ba." Saudala ta fad'a tana kawar da Kai. Sosai Hady taji haushin abinda Saudala tayi mata Amma sai ta basar tace , "eh nasan na girme ki a shekaru Amma a gidan nan ai kece babba , to my life sai da safen ku na tafi." Ta fad'a tana shirin barin parlourn. Mik'ewa Abdul yayi yace "bara na raka ki , ki d'ibi abincin ko ?." Murmushi tayi tace "am ok naci abinci d'azu." Ta fad'a tana barin parlourn. STORY CONTINUES BELOW Juyowa yayi ya gallawa Saudala harara san'nan yabi bayan Hady. Tsaki Saudala tayi ta mik'e ta shige Part d'in ta. Hady kuwa part d'inta ya wuce da sauri Dan Saudala ta b'ata mata rai , a parlour Abdul ya ganta ta zabga tagumi . Zama yayi a kusa da ita ya cire hannun ta akan fuskar ta yace , "ki daina irin wan'nan tagumin." K'wallah ta share tace "na rasa abinda nayiwa Saudat gabad'aya bata sakar min fuska , ni kuma harga Allah so nake mu zauna Lafiya." Ta fad'a tana share k'wallah. Tausayi ta bashi sosai ya jayota jikin sa yana shafa bayan ta san'nan yace , "ki k'wantar da hankalin ki, Saudat Yarinya ce shiyasa , Amma insha Allah zanyi mata magana , yanzu ki tashi kije ki kwanta dare yayi." Mik'ewa tayi tace "toh sai da safe my life , ka gaida sis na ," Pick yayi mata a goshi san'nan ya juya ya fita daga part d'in. Yana fita ta k'yalk'yale da dariya tace "zaku sani ne wallahi saina had'a ku fad'an da sai kun tsani junan ku , mu zuba mu gani." Ta fad'a tana shigewa bedroom. Part d'in Saudala Abdul ya shiga , a tsaye ya ganta a bedroom tana shirin kwanciya. Shigowa d'akin yayi ciki fad'a-fad'a yace "Saudat meyasa bak'ya jin magana ne ?, wai baza ki kwantar da hankalin ki ku zauna Lafiya ba , bana son irin abinda kike fad'awa Hady wan'nan ai cin fuska ne , Dan haka bana son irin wan'nan maganganun." Kallansa tayi tace "ka gama , to ni bacci nake ji, ka kashen fitilar in zaka fita, ta fad'a tana kwanciya . Kallan mamaki yake mata , wato ta mayar dashi mahaukaci yana ta magana shi kad'ai. Sanin halin ta da d'an bazan taurin Kai yasa ya k'wantar da murya yace , " Haba Saudat ina yi miki magana kika kwanta kika barni.?" Mik'ewa tayi tace "to ya kake so nayi , kazo kana ta fad'a akan abinda bai kai ya kawo ba , nace maka ni bata yi min komai ba , zaman Lafiya kuma tunda ta nemi hakan Bismillah Allah ya bamu ikon zama tare ." K'arasawa yayi ya zauna kusa da ita yace "why kike fad'a mata maganganun marasa dad'i,?" Tab'e baki tayi tace "duk abinda na fad'a ai gaskiya ne ." Murmushi yayi yace "to ki daina bana son irin wan'nan , wai to ma dame kika fita k'iba , naga kema dai ba wani jiki ne dake ba." Girgiza kai tayi tace "duk lalacewar k'wad'o yafi gaya albarka , ai idan na kaita a siranta yasin na daina fita." D'an tsaki yayi yace "stop, ki daina nace bana so kina fad'a mata irin haka , ko kece naji tana fad'a miki haka zan hana ta , pls ki daina." Tace "to na daina." Yace "yauwa habbity na , yanzu tashi mu tafi part d'ina." Zaro ido tayi tace "part d'inka ? , rufa min asiri maza su kaini ba mata ba , tab nida zuwa part d'inka ai saidai tsautsayi , " ta fad'a tana kwanciya akan gado. Murmushi yayi shidai mamakin wayo da surutu irin nata yake kamar ba y'ar sha biyar ba , lumshe ido yayi yana tuno k'yawun suru da Allah ya bata kamar babbar mace , tuno first night d'insu yayi , nan da nan ya fara fita hayyacin sa , cikin tashewar murya yace , "To naji bara na kwanta anan nima ," Saurin mik'ewa tayi tana fad'in , "Dan Allah kayi hak'uri ka koma part d'inka." Ta fad'a cikin shagwab'a. Shagwab'ar da tayi ta dad'a sashi cikin wani yanayi , yace " tab aikam anan zan kwana." Ja da baya take tana harfe hannu , sai ga hawaye na bin fuskar ta . STORY CONTINUES BELOW Cikin tashin hankali yace "Me nayi miki kike kuka,? Ya matso ya rungumeta yace " ki kwantar da hankalin ki babu abinda zanyi miki kinji." D'aga kai kawai tayi , k'wantar da ita yayi san'nan ya shiga wanka , bayan ya fito ya saka sleeping dress yayi musu Addu'a ya kwanta ya jayota jikin sa. Washe gari da wuri Saudala ta tashi ta gyara ko ina na part d'inta da part d'in Abdul ko ina sai kamshi yake. Kamshi turaren wuta ya tashi Abdul daga bacci , bud'e ido yayi yana bin ko ina da kallo , wani sabon farin ciki ne da k'aunar Saudat ke ratsa ko ina na jikin sa , yana son mace mai tsafta sosai . Shirya yayi ya fito , a parlour ya same ta tana jera abinci a dining. Tana ganin sa tace "barka da fitowa , an tashi Lafiya.?" Murmushi yayi yace "Lafiya lau , badai ke kiyi abinci ba.?" Saudala tace "Bani nayi ba yanzu aka kawo daga gida." Ta fad'a idon ta cike da k'wallah. Abdul yace "oh Saudat me kuma ya faru.?" Ta fashe da kuka tana fad'in, "yau kwana biyu fa banga su Baba ba ," Yace "shikenan share hawayen ki , zuwa gobe insha Allah zaki je ." Gyad'a kai tayi san'nan suka fara cin abincin cikin Soyayya . Bayan sun gama Abdul ya tafi gidan Mama Dan ya gaishe su. Bayan ya bar gidan ya wuce wajan Mustapha. Da daddare ya kama Hadiza ce da miji , da wuri ta shirya ta fito main parlour ana jiran miji. Saudala kuwa tana part d'inta tana waya da Khadija , bayan ta gama wayar ta fito main parlour , tunda ta shigo parlourn Hady take aikin hararar ta , sarai Saudala ta ganta sai ta d'auke kai kamar bata ganta ba. Abdul ne ya shigo parlourn da sallama , cikin sauri Hady ta Mik'e taje tayi hugging d'insa tare da bashi wel come kiss a kumatu. Tab'e baki Saudala tayi ta juya ta bar parlourn. Part d'in Abdul suka wuce shida ita , Hady sai wani kashe masa ido take , wanka yayi ya ci abinci san'nan yace , "To bara naje nayiwa Saudat sai da safe ." Cikin kissa Hady tace "hakan yayi k'yau, kace ina gaida ta." Murmushi yayi Dan shi har ga Allah ya gama yarda Hady tana son a zauna Lafiya , yace "toh zata ji." Ya fad'a yana fita daga d'akin. D'akin Saudat ya shiga tana zaune tana karatun alkur'ani , tsayawa yayi yana sauraron muryar ta mai dad'i , har ta idar ta shafa san'nan yace , "Daman haka kika iya k'ira'a ban sani ba." Murmushi tayi tace "muna koya dai." K'arasa yayi ya bata kiss a goshi yace " babu abinda kike bukata ,?" Tace "babu komai , Allah ya tashe mu Lafiya." Ta fad'a tana kwanciya. Addu'a yayi mata ya Tofa mata san'nan ya kashe mata fitilar d'akin ya fita. Runtse ido tayi tana jin wani irin zafi a cikin zuciyar ta , sunan Allah ta fara kira nan da nan taji komai ya wuce bacci ya d'auke ta. Abdul kuwa koda ya koma part d'in Hady umartatta yayi tayi alwala , sallah sukayi raka'a biyu , Bayan sun idar ya fara yi mata tambayoyin addini , nan fa Hady ta fara zare ido ban gaskiya karatun islamiyyan ta ba wani nisa yayi ba . Abdul yace " gaskiya kina da gyara akan addinin ki , wai meyasa yanzu aka fi bawa boko mahimmaci akan karatun islamiyya , wai sai kaga uba mahaifi babu ruwan sa Dan baka je islamiyya ba , Amma idan boko ce baka je ba kila ma sai da Zane ka , wato an fifita duniya akan lahira kenan , gaba abinda zai amfane ka duniya da lahira Amma sai ka dau duniyar lahirar ko oho , ace wan'nan k'ananun tambayoyin kika kasa amsawa , yanzu kin kusa kammala degree akan boko Amma a B'angaren addini ko certificate na secondary baki dashi , dole ki koma islamiyya domin ina so yarana su tashi cikin tarbiyyar addini , k'wanan nan zaki fara zuwa islamiyya kinji ni ko."2 STORY CONTINUES BELOW D'aga kai tayi alamun eh , Gabatar mata da kaza yayi , babu laifi ta d'anci sosai , daga nan suka kwanta. Shafa ta ya fara yi tare da kissing d'inta, nidai fitowa nayi na bar musu d'akin. Bayan wasu awan ni na koma d'akin , a zaune naga Abdul da alama har yayi wanka , Hady tana kwance akan gado tana faman shagwab'a . Shikuwa Abdul tunani yake lallai Saudat tayi gaskiya da take kiran ta skeleton , kamar ba babbar mace mai shekaru ba , gabad'aya Saudat ta fita sura nesa ba kusa ba , breast sai kace wacce ta fara irgar dangi . Kwanciya yayi ya jayo ta jikinsa , ko babu komai ta kawo budurcin ta cikin gidan ta , Amma tunanin surar ta yak'i fita daga ransa , Allah ya sani yana son mace wacce take komai yaji ,da wannan tunanin bacci ya d'auke su. Da safe ya Riga ta farkawa , mik'ewa yayi ya shiga wanka ya shirya , bud'e bed side yayi ya d'auko wata sark'a mai k'yau ya ajiye a kusa da ita , san'nan ya fita Dan sauri yake anyi masa waya ana Neman sa. Part d'in Saudat ya shiga , ta gama gyara ko ina yayi tas kamar karki fita. Cikin sauri suka gaisa ya fita daga gidan. Hady kuwa sai murna ake an sami kyauta , waya ta d'auka ta sanar da Momy , Momy ta taya ta murna sosai , san'nan suka cigaba da shirya plan. Bayan kwana d'aya Da yamma Saudala tana zaune a main parlour Hady ta shigo , Sam Saudat bata ji shihowar ta ba , tana can tana karanta littafin *KULLU NAFSIN* na miss xerks , sosai littafin ya d'auki hankali har bata ji shigowar ta ba sai ji tayi an kifa mata mari. Da sauri ta d'ago tana dafe kunci , Hady ta fara fad'in , "duk abinda kika yi min ina sane dake kar kiga kina kyale ki , ina yine sabida Abdul ya zata sonki nake , to bara kiji bazan tab'a sonki ba wallahi, kuma ki rubuta ki ajiye sai na raba ki da Abdul wallahi." Cikin zafin nama Saudala ta kifa mata mari har guda biyu , dai-dai lokacin Abdul ya shigo. Sam Saudala bata lura dashi ba ta fara fad'in , "ni zaki dinga fad'awa wan'nan maganar , ina ruwana dake , na shiga har karki ne kome , to bara kiji bazan tab'a d'aukar wan'nan rainin hankalin ba , banza shashasha." Tasssss Saudala taji an d'auke ta mari . Da sauri ta juyo , had'a ido suka yi da Abdul yana faman wuci , Hady na ganin sa ta fashe da kuka ta fara fad'in, "Na rasa abinda nayiwa Yarinyar nan my life, daga nazo wai muyi hira shine take fad'a min wan'nan maganganun , kuma kasan da ina da k'anne wajan k'anwata tace ta uku Amma ni ta d'aga hannu ta Mara , " ta k'ara fashewa da kuka. Rungumeta Abdul yayi sannan ya kalli Saudala da har yanzu hannun ta na kan kuncin ta yace .......... Comment & share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sisters*❤ 🎸🎸🎸🎸🎸 _*BUBA RANA 🌝 DA WATA πŸŒ™ SUNA DA HASKE☄ FAN'S D'INA SAIKU SOYAYYAR KU HAR ABADA 😁, I LIKE MY FANS , LOVE U MY FANS , SOYAYYAR MU HAR ABADA .πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»*_ STORY CONTINUES BELOW '''Kai Ashe haka Saudat take da fan's ban sani baπŸ€”, Har fan's d'in Abdul duk ta had'a ta kwashe πŸ˜™, Allah sarki Hady banga Wacce tace tana yin tabaπŸ˜•, to nidai na koma HadyπŸ€ͺ.''' *Ina godiya masoyana da kaunar da kuke nuna*🀝🏻🀝🏻🀝🏻😻 *Bismillahir rahmanir rahim* 77&78 Cikin b'acin rai Abdul ya kalli Saudat yace , "wai meyasa bak'ya son zaman Lafiya ne a rayuwar ki , yanzu rashin kunyar taki har ta Kai ki d'auki hannu ki marar min mata , kenan nima wata rana marina zakiyi kenan , to bara kiji rashin mutuncin naki ya isa haka haka , haba Hady nason ku zauna Lafiya amma ke bak'ya son haka ko, ta bazan d'auki wan'nan rashin mutuncin naki ba , ace ko sati d'aya ba kuyi ba a cikin gidan nan har kin fara fad'a, kuma fad'an har ya Kai ki fitar da hannu ki mare ta Dan kinga tana baki girman ki , ki shiga hankalin ki duk ranar da kika kuma aikata irin wan'nan kiyi kuka da hukuncin da zan miki." Ita dai Saudat ta zuba masa ido tana kallan yadda yake zuba masifa ba tare da ya tambayi ba'asi ba, mai k'wallar ta tayi Dan bata so tayi kuka a gaban Hady san'nan tace , "Yayi dai-dai , ka yanke hukunci ba tare da ka tambayi abinda ya faru ba , Amma ka sani zakayi Dana sanin abinda ka aikata Yanzu." Tana gama fad'ar haka ta d'au wayar ta ta bar parlourn cikin k'unar rai. Hady kuwa dad'a kankame shi tayi tana dariya k'asa-k'asa, d'ago ta yayi ya goge mata hawaye , yana bata hak'uri, cikin makirci tace , "Gaskiya my life banji dad'in fad'an da kayiwa Saudat ba , duk da nasan tayi laifi Amma kaga ai Yarinya ce bai kamata kayi mata haka ba, Yanzu dai kaje ka bata hak'uri ni har cikin zuciyata ha yafe mata ." Wani irin tausayin Hady Abdul yaji , Dan ba k'aramin burge shi tayi ba , kallan ta yayi yace , "Share ta ai ita ya kamata ta bada hak'uri , Yanzu muje na raka ki part d'inki kinga magariba ta gabato , " Hady tace "to , Amma Dan Allah kaje ka rarrasheta nasan Yanzu tana can tana kuka." Tsaki yayi yace "nace ki manta da ita Kawai." Cikin jin dad'i Hady tace "to ". Part d'in Hady suka shiga ya zaunar da ita san'nan ya fita ya nufi part d'insa zuciyar sa a cunkushe. Ai yana fita Hady ta d'auki waya ta kira Momy ta sanar da ita abinda ya faru , dariya Momy tayi tace " Amma wan'nan mijin naki baya ganewa wallahi ,baza mu k'ara yin wani Abu ba sai nan da kamar kwana goma ko sati biyu sai musan wane plan d'in zamu kuma had'awa , Amma ki dinga samo mana information akan su ta yarda komai namu zai tafi dai-dai. " Ihu Hady tayi tace "Allah ya barmin Momy na , Amma fa naji zafin Marin da tayi min ." Momy tace "dalla can share Yanzu baga shi an ninka miki shi ba ." Dariya Hady tayi tace "kuma fa haka ne my Momy , " Sallama sukayi suka kashe wayar. Saudala kuwa tunda ta shiga part d'inta take kuka , cikin kuka tace , "Bai tsaya yaji abinda ya faru ba Kawai ya yanke hukunci sabida ya fi sonta dani , bazan tab'a bari suci bulus ba daga ita har shi sai sun gane basu da wayo , dani suke zancen ." ta fad'a tana murmushi kamar ba ita take kuka ba. Tashi tayi ta shiga wanka ta shirya cikin wando three quarter ta saka riga gabad'aya cikinta a waje yake , ta gyara gashinta ya sauka gadon baya , tsayawa tayi a gaban mirror tana k'arewa kanta kallo , ita kanta tasan tayi k'yau , tunani take yanzu kuma a haka Abdul zai ganta , ajiyar xuciya ta sauke tace , "Gaskiya ina jin kunya Sosai." Fitowa tayi parlour ta zauna tana danna waya. STORY CONTINUES BELOW Shikuwa Abdul tunda ya koma d'akin sa yake tunanin kamar abinda yayi bai k'yauta ba , Saudat masoyiyar sace bai kamata yayi saurin yanke hukunci ba , ko ba komai ma ai y'ar uwarsa ce kuma Yarinya ce k'arama , ajiyar xuciya yayi a fili yace , "ya kamata naje na rarrasheta ," ya fad'a yana mik'ewa ya nufi part d'in ta. Yana shiga parlourn kamshi ya daki hancin sa , lumshe ido yayi yana jin wani irin yanayi yana ratsa shi . Turusss yayi ya tsaya yana kallon ta , gabad'aya ta tafi da imanin sa , kasa d'auke ido yayi daga kanta yana had'iyar wayu. Jin motsi a bayan ta yasa ta juya duk da tasan shine , d'auke kai tayi kamar bata ganshi ba ta cigaba da abinda take yi, mik'ewa tayi tana wata irin tafiya , saura k'iris Abdul ya fad'i sabida salon Saudala yayi bala'in rud'a shi . Dawowa tayi ta zauna ta cigaba da abinda take yi. Abdul ganin tsayuwar baza tayi masa sai ya jawo k'afar sa dak'yar ya k'arasa ya zauna akan kujera yana kallon ta. Gyaran murya yayi ya fara cewa "am sorry Saudat d'azu nasan ban kyauta miki ba , duk dadai laifin kine bai kamata ki dinga fad'a mata irin wan'nan maganar ba , bayan maganganun kuma harda mari ai ko babu komai Hady yayar kice bai kamata ki d'aga hannu ki mare ta ba , Yanzu dai kiyi hak'uri nasan ban kyauta ba." Kallan sa tayi tace "ita kasan abinda tayi min ne , baka sani ba kana zuwa ka mare ni kamar wata jaka bayan nata Marin da tayi min , Dan baka sona sai ka dinga wulak'an tani kamar wacce bata da gata , naji ka bani hak'uri amma ka sani bazan hak'ura sai dai muje ka bani hak'uri a gabanta to a san'nan zan yafe maka maganganun da ka fad'a min , mari kuma da kaina zan fanshe daga ita har kai." Yace "naji zan baki hak'uri a gabanta , Amma maganar zaki fanshe mari bai taso ba yanzu kizo ki rama kawai." Ya fad'a yana dawowa kusa da ita. Saudala tace "no ni bazan iya Marin ka ba , Amma zan fanshe ." Rik'e hannun ta yayi yace "dame zaki fanshe .?" Tace "wan'nan kuma bai dame kaba ," ta fad'a tana mik'ewa. D'aki ta shige tana fad'in "ana kiran sallah ." Dak'yar Abdul ya mik'e ya tafi masallaci . Bayan sallar i'sha ya dawo direct main parlour ya shiga , a zaune yaga Hady tana kallo , zama yayi yana fad'in, "Ke kad'ai ce a zaune kenan." Tace "eh wallahi tun d'azu nake jiran Sis Saudat d'in Amma bata fito ba ." Yace "ai nasan y........" Maganar ta makale sakwamakon gano da saudat da yayi an chanja k'walliyya , da sallama ta k'araso parlour ta zauna . Sakin baki Hady tayi tana kallan ta , nan da nan kishi da hassada suka tararwa Hady . Shikuwa Abdul kamar wani wawa ya saki baki yana kallon ta , ji yake kamar ya jayota ya rungumeta Amma ganin yadda ta had'e rai yasan babu mutunci. Hady tace " Sis kiyi hak'uri da abinda my life yayi miki d'azu , ni nace na yafe miki abinda kikayi min." Murmushi mugunta Saudat tayi tace "kar ki damu komai ya wuce." D'an gyara zama Abdul yayi yace , "Saudat nima nasan ban kyauta miki ba , am sorry." Saudala kallon Hady tayi da take kallon Abdul Cikin mamakin abinda yake cewa . Y'ar dariya Saudala tayi tace "kar ka damu mine komai ya wuce." Lumshe ido Abdul yayi yana dad'a maimaita sunan da ta kira shi dashi , MINE shine abinda yake maimaitawa , da gaske ni nata ne , Hady kuwa kamar ta shak'e Saudat haka take ji , STORY CONTINUES BELOW Mik'ewa Saudat tayi tana fad'in "sai da safen ku, har tayi gaban sai kuma ta dawo tace , " Mine nabarwa Amarya kuma k'anwata kwanan yau , asha amarci Lafiya. " ta fad'a tana barin wajan. Shikuwa Abdul kamar wani soko ya bita da kallo , Hady ce ta katse masa tunani da fad'in, "My life sai ka taso mu tafi , kamar Sis tasan zanyi missing d'inka yau ." Abdul kuwa ransa ne ya b'aci, wai yanzu sadaka tayi dashi kenan, mik'ewa yayi Yace "bara naje na dawo." Bai tsaya jin abinda zata ce ba ya bar mata wajan , part d'in Saudala ya shiga ransa a b'ace, a kwance ya ganta akan gado , Cikin fushi ya fara fad'in, "wato wan'nan shine fanshewar da kika ce zakiyi ?, shine wani harda k'yautar kwana , to bara kiji Allah yasa ba ke kad'ai ce dani ba , kuma abinda kike min rowa ki jik'a ki sanye ." ya gama fad'ar haka ya juya ya fita. Saudat kan ko a jikinta a fili tace , "wa ya fad'a maka wan'nan ne fansar da zan d'auka , hmmm." Haka Abdul ya kwana ransa a b'ace. Washe gari kamar yadda Saudala ta Saba yauma haka tayi , bayan ta gama ta saka hijjabi ta fito parking space d'in gidan , direct wajan mai gadi ta nufa , cikin girmamawa ta gaishe shi san'nan tace, "Baba Dan Allah chemist zaka je kace a baka maganin zai sha idan ya dad'e baiyi bayan gida ba , Dan Allah kace su baka mai k'yau." Cikin sakin fuska Baba mai gadi ya karb'e kud'in ya tafi Aiken Saudat. Babu jimawa ya dawo d'auke da Leda a hannun sa , mik'e mata ledar tayi yace , "gashi , sunce idan za'a sha asha murfi d'aya in kasha da yawa zai zame maka gudawa." Karb'a Saudala tayi tayi masa godiya ta koma ciki. Abincin da aka kawo daga gidan Mama ta jera akan dining, san'nan ta bud'e fridge ta d'auko lemuka ta jera akan dining d'in. Bud'e lemukan ta fara yi one by one tana zuba maganin a ciki , sannan ta bud'e flusk d'in tea ta kuma zuba maganin san'nan ta rufe. Tana tsaye tana gyara wajan su Abdul suka shigo sun wani k'ank'ame juna suna zuba love. Murmushi Saudala tayi tace "mine barka da fitowa." D'auke kai Abdul yayi Dan har yanzu haushin ta yake ji , Dak'yar Yace, "Yauwa, kin tashi Lafiya." Ta kalli Hady tace "Amarya an tashi Lafiya." Murmushi yak'e Hady tayi tace " Lafiya lau." Saudala tace "ga abinci an kawo , u can eat if u like." Tana gama fad'ar haka ta juya . Cikin rangwad'a Hady ta mik'e ta zubo masa tea kamar yadda yake so, ajjiye masa tayi san'nan itama ta had'a nata. D'auka Abdul yayi ya kafa baki ya fara sha, Hady kuwa sai da aka fara shan lemo san'nan aka d'oura da tea. Suka shanye tea d'in tas suka ajiye cup d'in , Babu jimawa cikin Hady ya bada wani sauti ji kike kululullulu , ai da gudu ta mik'e zata shiga toilet d'in parlourn , ai kafin ta k'arasa Abdul ya tunkud'e ta ya shiga ko rife k'ofar baiba ya fara zuba aiki , ji kuke farrrrrrrrrrr πŸ˜‚ Hady kuwa da sauri tayi hanyar part d'inta ai kafin ta kara sa cikin toilet d'in ta saki wata tusa mai had'e da kashi.🀣 *wai ina team din Abdul ne kuzo kuyi wanki 😷*πŸ˜‚ Comment & Share Neat Lady✍🏻πŸ€ͺ🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ STORY CONTINUES BELOW 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sisters*❤ *Bismillahir rahmanir rahim* 79&80 Duk abinda suke Saudala tana lab'e tana kallon su , banda dariya babu abinda take yi , inda yafi bata dariya shine lokacin da suke rige-rigen shiga toilet . cikin sauri ta dawo parlourn , banda k'arar gudawar Abdul babu abinda ake ji a parlour, cikin sauri ta kwashe lemukan ta ajiye wasu ta zubar da ruwan tea d'in ta ajiye sannan ta tafi part d'in Hady. a parlour ta ga Hady a zaune da alama a wajan tayi kashin dan ga k'uda nan ya binta . wata mahaukaciyar dariya Saudat ta fara tana fad'in, "Amarya ya naga duk jikin ki kashi, kodai a samo pampers ne a saka miki dan naga abin naki ba mai k'arewa b.........." kafin Saudala ta k'arasa maganar Hady ta saki wata gudawar ji kuke fessssssssssss πŸ˜‚, ai da sauri Saudala ta juya tana fad'in , "tab gaskiya parlourn nan ya zama kogin kashi." ta fad'a tana fita daga parlourn. Abdul kuwa yana bakin toilet a zaune yana faman ajiyar zuciya, lokaci d'aya har ya rame ya fita daga haiyacin sa, Saudala ta shigo parlourn ganin yadda yake yasa ta basar kamar bata san abinda ya faru ta k'arasa wajan sa tace, "lafiya na ganka anan mai ya same ka?" kallan kawai yake ya kasa magana , dan jan numfashi tayi tace , "haba Yay Abdul yanzu da girman ka kayi kashin wando? , kalli yadda k'uda suke binka da Allah , gaskiya wa........" tusar da Abdul ya saki ya hanata k'arasa maganar, kafin tayi wata magana har ya koma cikin toilet d'in. jikin Saudala yayi sanyi ganin yadda yake ta fama wayon band'aki , gashi lokaci d'aya ya rame kamar bashi ba . nan da nan nadama ta shiga cikin zuciyar ta , zama tayi shiru ta rasa abinda zatayi . tana zaune ya kuma fitowa yana haki , zama yayi yana kallonta , cikin dashewar murya yace , " ki d'auki waya ta ki kiramin Dr Ahmad kice yazo ina neman sa." ya fad'a yana lumshe ido. cikin sauri ta d'au wayar ta kira likitan , kafin likitan yazo ya koma toilet sau biyar , waya likitan yayi yace gashi a bakin gate sojoji sun hana shi shigowa, Saudala da kanta ta fita ta shigo da likitan , a parlour likitan ya kwantar dashi ya bashi magani sannan ya sa masa drip dan jikinsa yayi weak sosai. Saudala ta kira wata soja mace tace ta raka shi part d'in Hady itama a duba ta . koda suka je jikin Hady yafi na Abdul weak , allura yayi mata sannan ya sa mata drip ya bar wannan sojan ta kula da ita , komawa main parlour yayi ya tarar Abdul har ya sami bacci ,anan yake yiwa Saudala bayanin wani magani suka sha yayi musu yawa shine ya haifar musu da gudawa amma insha Allahu ta tsaya baza su kuma yi ba. godiya tayiwa likitan ya tafi , waya ta d'auka ta kira su Mama ta sanar dasu sannan ta cigaba da kula da Abdul. gab da Azahar ruwan ya k'are , da kansa ya cire sannan ya mik'e dak'yar ya zauna yana dafe kai. STORY CONTINUES BELOW a hankali Saudala tace "sannu ya jikin.?" kai kawai ya d'aga mata alamun da sauk'i , hannu ya mik'o mata alamun ta taimaka masa ya tashi , dak'yar ya mik'e ya ta taimaka masa ya shiga part d'insa yayi wanka yayi sallah sannan ya kwanta.(su brown strowman an sha aikiπŸ˜‚) Hady kuwa bayan ruwan ya k'are itama wanka tayi ta d'an burbura sallar ta sannan tabi lafiyar gado. Saudala tana zaune a parlour bayan ta gama gyara toilet d'in su Iya suka shigo , da murna Saudala ta tare tana farin cikin zuwan su . bayan sun gaisa Umma tace "to ina mara lafiyar yake.?" Saudala tace "sunyi bacci ." iya tace "au itama mai kamar mazan bata da lafiya ?, to wai mai ya same su.? Saudala tace "likitan yace wani magani suka sha shine ya haifar musu da gudawa." iya tace "haba shiyasa tunda na shigo d'akin nan naga k'uda na yawo ashe yau masan gidan ya cika , wai wa yaga kashin mai k'antan kai nida samandagari." had'e rai Saudala tayi tace " kuji min iyan nan wai k'uda na yawo kiga parlour a sai kamshi yake kice wai k'uda yana wayo." sakin baki iya tayi tana kallan ta tace, "to zoki dake ni, da wani bakin ki kamar shantu." Fadila tace "ai gwara ku tab'a fad'an kun dad'e baku yi ba." ta fada tana dariya. Umma tace "to kafin Abdul d'in ya tashi muje mu duba ita Hadizan ko." Mama tace "haka ne kam mun tsaya suna jin dramar su Iya." ta fad'a tana mik'ewa . part d'in Hady suka a zaune suka same ta har ta tashi daga baccin, zama sukayi suna yi mata sannu. Hady ta gaishe su suka amsa cikin fara'a banda iya da ta zuba mata ido kafin Hadiza tace wani abu Iya tace "oh matsalar mutum bara k'iba kenan yana yin cuta zai dad'a ramewa , kinga yadda kika koma kuwa nida tsinken kwa-kwa." kauda kai Mama tayi tana mamakin Iya . ganin Iya tana neman basu kunya a gaban sirika sai Umma ta mik'e tace "to mudai zamu tafi Allah ya k'ara sauki." Hady tayi murmushin yak'e tace "to ku gaida gida an gode." part d'in Saudat suka koma suka zauna , nan da nan da Saudala ta kawo musu mutsa baki , basu jima ba Abdul ya fito yana murmushi , har k'asa ya durk'usa ya gaishe su , sannan ya koma ya zauna. Iya tace "ashe kuma cutar kashi ce ta kama ka , to Allah yasa kar kayi musu na kwance yau." hararar Iya yayi yace "oho miki dai." haka suka gama hira suka yi musu sallama suka tafi. bayan fitar su Mama Abdul ya kalli Saudata yace "mai likita yace da yazo.?" Saudala tace "yace wai wani abu kuka ci ya b'ata kuma ciki shiyasa." ta fad'a tana kallan sa taji ko zai gane karya take. Abdul yayi jim yace "ai kuwa bamu ci komai ba jiya , sai dai ko break fast d'in da mukayi d'azu ." cikin sauri Saudala tace " to ni meyasa bai min komai ba , kaga kawai tunda Allah ya baka lafiya ai shikenan." abinka da ma'aikaci tsaro nan da nan yaji bai yarda ba sai yayi binkice, shiru yayi baice komai ba. Saudala tace "wai yaushe zan koma makaranta ne?" ta fad'a a shagwab'e . kallan ta yayi yace " zuwa jibi insha Allah zaki koma , inaso na canja miki uniform kafin ki koma." shiru Saudala tayi ba tace komai ba. mik'ewa yayi yace "bara na duba jikin my Hady." ya fad'a yana fita daga parlourn. yana fita Saudala tace "ina sane ban fad'a maka ni na zuba muku ba sabida nan gaba in kuka kuma yi min rashin mutunci na kuma hukutaku." Bayan sati d'aya Saudala tana zaune a parlour da yamma bayan ta dawo daga makaranta tana karatu , Abdul ya shigo parlourn yana fad'in "kaga y'ar makaranta ana karatun ne." ya fad'a yana murmushi. y'ar dariya Saudala tace "kasan mun kusa fara exams shiyasa." murmushi yayi yace "to ni ba wannan ba tashi ki kawo min abinci in kin dafa." da mamaki take kallon sa tara dalilin da yasa tunda aka daina kawo abinci daga gidan Mama indai ranar girkin Hady ne a wajanta yake cin abinci. katse mata tunani yayi da cewa, "ki tashi mana." mik'ewa tayi ta kawo masa sannan ta cigaba da abinda take, amma tayi alk'warin yi masa magana. Hady kuwa tana can sun gama had'a plan da Momy , cikin murna ta nufi main parlour. turuss tayi tana kallan Abdul yana cin abincin Saudala ranar girkin ta, yak'e tayi ta danne b'acin ranta tace, "A'a kuna zaune ashe." Abdul yace "uhum muna zaune." Hady ta kalli Saudat tace "yauwa sis d'azu bayan kin dawo daga makaranta wani yazo a mota yace wai kin manta wannan a motar sa shine , ni kuma lokacin na fita zanyi aike sai ya bani yace dan Allah na baki kuma wai nace miki yana jiran ki gobe." ta fad'a tana mik'o mata wata takarda. gaban Saudala ya fad'i da jin maganar da bata san da ita ba. kafin Saudala ta karb'i takardar Abdul yayi saurin fizgewa cikin b'acin rai. *KUYI HAKURI DA WANNAN INA WANI AIKI NE*🀦🏻‍♀🀦🏻‍♀🀦🏻‍♀ comment and share neat lady❤😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sisters*❤ *Bismillahir rahmanir rahim* 81&82 Cikin b'acin rai yake bud'e takardar , tsayawa yayi yana karantawa yana huci , wular da takardar yayi ya juyo yana kallan ta cikin b'acin rai. Saudala kuwa ja da baya take tana fad'in, "ka tsaya kayi binkice wallahi babu Wanda ya kawo ni , " Cikin tsawa yace "ki rife min baki !, in ba shi ya kawo kiba waye ya dawo dake ?," Girgiza kai Saudala take tana hawaye tana fad'in, "na rantse da Allah babu Wanda ya kawo ni , nasan dai drop na hau tunda ina ta jiran drivern bai zo ba shine kawai na hau drop na dawo, kuma kaje makarantar ka tambaya nasan za'a fad'a maka wallahi babu Wanda ya kawo ni ," ta fad'a tana fashewa da kuka. Juyawa yayi ya kalli Hady da take ta murna, cikin tsawa yace, "Kinga Wanda ya kawo tan da idon ki ?" , nan da nan jikin Hady ya fara rawa kamar mazari , tana tunanin Allah yasa kar ya gane k'arya take. Katse mata tunani yayi da fad'in , "zaki fad'a min ko saina ci uban ki," Cikin rawar murya Hady tace "na......g....an....sh......, " Kafin ta k'arasa ya d'auke ta da mari yana fad'in , "karya kike kenan , " Ihu Hady tayi Dan Marin ya shige ta tace , "sai dai indai mutumin kuskure yayi yazo gidan nan." Ta fad'a jikin ta na rawa. Yace "kuskuren uban ki , daman k'arya kike kenan , daman sharri zaki had'a mata kenan?" Girgiza kai tayi alamun A'a, Yace "to meye , wallahi in baki fad'a min ba saina lahira yafi ki jin dad'i." Ja da baya Hady take tana girgiza mai kai , ganin ya juya yasa ta fice a 360 , Saudala kuwa tuni ya gudu d'aki ta kulle kanta tana haki , a fili tace, "tayi min sharri tana so a dake ni gashi nan dukan ya koma kanta , daman hausawa sun ce *IN ZAKA GINA RAMIN MUGUNTA* ka gina shi dai-dai kai da wata rana zaka iya fad'awa, yanzu da tuni nI yake ta jibja ." Ajiyar zuciya tayi tace "Allah ya cece ni", Abdul kuwa safa da marwa yake a parlourn , yana son sanin wace mai gaskiya a cikin su , in kuma da gaske ne fa?, cikin sauri ya juya ya kuma d'aukar takardar yana karantawa, _Gaskiya naji dad'in kasancewar mu tare yau , ina fata gobe ma mu kuma mu kasance tare, really miss u my dear_. Sake maimaitawa ta karantawa yake yana jin zafi a cikin zuciyar sa. Tunani yake a ransa to ai wan'nan a waya ya dace a turo ba a rubuta a paper ba , to idan kuma salon Soyayyar tasu ce haka fa, da k'arfi ya buga table yana fad'in , " bazai yu ba , zanyi binkice duk mai Mara gaskiya a cikin su ya shiga uku". Ya fad'a yana fitowa harabar gidan. STORY CONTINUES BELOW Hady kuwa tana can tana faman Dana sani , tunani take Yanzu idan Abdul ya gane k'arya nake me zata ce masa , a fili tace , "Na shiga uku wallahi kashe ni zaiyi ," cikin sauri ta d'au waya ta k'ira Momy tana ta ringing Amma bata d'auka ba , Hady ta kuma rud'ewa ta rasa abinda zatayi. D'aki ta shige ta kulle kanta da tana fad'in, "sai da ya b'alla k'ofar amma bazan bud'e ba." Abdul kuwa wajan masu gadin gidan ya nufa , suna ganin isowarsa suka fara k'amewa , su Kansu ganin fuskar ogan nasu sai da suka tsorata suna tunanin Allah yasa Lafiya. K'ara had'a rai yayi yace "D'azu waye yazo gidan nan a lokacin da small madam ta fito har ya bata sak'o,?" Kallan kallo suke Dan sudai sun san babu Wanda yazo , hasali ma yau gabad'aya small madam bata ta fito ba , tsoron fad'a masa suke sabida kar yace sun k'aryata masa mata. Tsawar da yayi musu ce ta dawo dasu daga tunani , cikin b'acin rai Yace , "ba magana nake muku ba ." Cikin tsoro d'aya daga cikin su yace "wallahi oga mudai bamu ga kowa ba , kuma yau kwata-kwata bamu ga small madam ba , big madam d'in ma tunda ta dawo daga makaranta bata k'ara fitowa ba." Yana gama fad'ar hakan ya sunkuyar da kai. Abdul yaja numfashi yace "wace mota kuka ga ta sauke big madam lokacin da ta dawo daga makaranta.?" Shiru suka yi suna tunani, cikin sauri d'aya daga cikin su yace "oga drop ya sauke ta , " Ajiyar zuciya yayi yace "ok shikenan ku koma bakin aikin ku." Yana gama fad'ar haka ya juya ya nufi part d'in sa. Zama yayi yana tunanin yanzu kenan abinda Hady ta fad'a k'arya ne kenan, to meyasa take son yiwa Saudat sharri , mik'ewa yayi yana fad'in, "itace zata bani amsar wan'nan tambayar." Koda ya shiga part d'in Hady k'ofar a kulle ya ganta , cikin d'aga murya yace "kizo ki bud'e in ba haka ba kika sake na b'alla k'ofar nan kin shiga uku wallahi ,"! Jin haka yasa Hady k'ara tsorota , jikin ta banda rawa babu abinda yake , Abdul yace " idan kika sake na irga uku baki bud'e ba babu abinda zai hana na b'alla ki a cikin gidan nan." Cikin sauri Hady ta bud'e k'ofar tana kuka , Shiga d'akin yayi yana kallon ta , belt ya zare yana nannad'e ta a hannu , Ja da baya Hady take tana hawaye har ta kai bango , Hannu yasa ya matse mata fuska yana fad'in , "wato ke da k'arya kika so kiyi mata ko, to Allah ya toni asirinki na gane k'arya kike babu Wanda yazo k'ofar gidan balle har ya baki sako, wato ke ga makira ko , " Hady kuwa iya matsa ta matsu cikin dashewar murya tace, "kayi Hak'uri Dan Allah wallahi k'awata tace ta zuga ni tace nayi hakan , amma nima ba ason raina ba ." Hannu yasa ya d'auke ta da mari yana fad'in, "ok Ashe ke mahaukaciya ce tunda bak'ya bambance Abu mai k'yau da Mara k'yau ko , to bara kiji duk ranar da kika k'ara aikata makamancin abinda kikayi sai na sumar dake a gidan nan." Cikin rawar jiki tace "wallahi bazan k'ara ba wan'nan d'in ka sharin k'awata ne ." Belt d'in hannun ya fara zabga mata mata yana fad'in , "gaki nan babbar masharranciya , shegiya makira , ki kuma yin abinda kikayi kiga abinda zan yi miki." Hady kuwa banda ihu babu abinda take tana Neman taimako, sai da yayi mata duka san'nan ya kyaleta ya fita ya barta a d'akin. Part d'in Saudat ya k'arasa cikin sanyi jiki ya shiga , a zaune ya ganta ta zabga uban tagumi tana tunani. STORY CONTINUES BELOW Tausayin ta yaji yana mai yawo a jiki , a hankali ya k'arasa ya zauna a kusa da ita , hannu yasa ya cire mata tagumin da tayi . Saudala tana ganin sa ta fara cewa "Yaya Abdul ka yarda dani wallahi babu Wanda ya kawo ni , " Rungumeta yayi yana shafa bayan ta , a hankali yace, "shikenan nasan ai baza ki aikata hakan ba, ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce kinji." K'ara kwanciya tayi a jikin sa tana share hawaye, d'ago da fuskar ta yayi yana lashe hawayen fuskar ta daga nan ya gangaro zuwa kan lips d'inta yana lashewa a hankali, kiran Sallah ne ya dakatar dashi da barin abinda yayi biya , mik'ewa yayi ya fita daga d'akin. Hady kuwa tana kwance tana fama kuka , wayar ta taji tana ringing tana budawa taga sunan Momy , cikin hanzari ta d'auka ta fashe da kuka , Cikin tashin hankali Momy take tambayar abinda ya faru , Hady ta kwashe komai ta sanar da Momy , san'nan tace "nidai Momy bazan k'ara yarda da wan'nan shawarar taki ba, gwara mu canja wani abun." Rarrashin ta Momy tayi Sosai san'nan tace "ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai kuma faru dake , zamu basu lokaci baza mu kuma yin wani plan din ba , zuwa lokacin ya manta da abinda kikayi , daga nan kuma zansan abinda zanyi." Hady ta yarda da shawarar Momy suka yi sallama ta kashe wayar. Wajan k'arfe goma na dare Saudala tana d'aki tana shirin bacci Abdul ya shigo d'akin , da kallo take binsa tana mamakin abinda ya kawo shi d'akin ta yau bayan ba itace dashi ba. Ji tayi ya rungumota ta baya ya kwantar da kansa a wuyan ta yana shafa cikin ta , Kwace kanta tayi tana fad'in , "ya haka bayan kasan yau ba gir........" Bata k'arasa ba ya fara kissing d'inta, tun tana basarwa har itama ta fara mayar masa da martani , cikin lokaci k'ank'ani suka fita daga haiyacin su , nidai na fito na rufe musu k'ofar. _A gurguje_😞 Bayan kwana biyu Abdul ya fita harkar Hady gabad'aya, ko magana bata had'a su da ita Dan haushin ta yake ji. Hady kuwa kullum cikin kuka taki tana Neman afuwa a wajan sa , ganin alamun tayi nadama yasa Abdul ya yafe mata suka cigaba da zama kamar da. Ranar Monday bayan Saudala ta dawo daga makaranta tana zaune a parlourn ta tana tunanin shawarar da malamar su ta bata, har Abdul ya shigo ya zauna bata sani ba , Iska ya hura mata a fuska , firgigit ta dawo daga tunanin da take , kallansa tayi tace , "yaushe ka shigo.?" Had'e fuskarsa yayi da tata yana fad'in, "kina can kina tunani ta yaya zaki san na shigo tunanin me kike yi?". Ajiyar zuciya Saudala tayi tace " wallahi d'azu a makaranta wata malamar mu ta k'ira tace min nice akace inda aure ko nace mata eh shine tace tunda saura shekara uku na gama makaranta gashi kuma mun kusa fara exmas wai mai zai hana nayi family planing sabida exams da ciki zata bani sosai , shine tace na nemi amincewar ka nayi pl........." Maganar ta katse sakamakon bige Mata baki da yayi , cikin b'acin rai ya fara cewa, "Ban yarda ba , Sam baza kiyi planing ba exams kuma ai Allah ne yake bada saa ba wani ba , bara kiji daga yau kika k'ara yi min wan'nan maganar sai ranki yayi mummunan b'aci , Dan baki da hankali ke in ance kiyi planing d'in sai kiyi , baki tab'a haihuwa ba kije kisha magani ya lalata miki mahaifa gabad'aya , ba'a planing ba'a tab'a haihuwa ba sai bayan an haihu ke kanki kinsan kina da Lafiyar mahaifa , amma in kikayi planing baki haihu ba zai iya samar miki da matsala , Dan haka Kar na K'ara jin wan'nan magana a bakin ki , Sam ni bani da tsarin yin family planing a rayuwa ta , in ba so kike ranki ya b'aci ba kar ki k'ara fad'in hakan." Ya fad'a yana shirin mik'ewa daga wajan. STORY CONTINUES BELOW Cikin sauri ta rik'e shi ta kwanta a jikinsa ta fashe da kuka tana fad'in, "Dan Allah kayi hak'uri wallahi bazan k'ara fad'a ba , ka yafe min." Kallan yayi Dan yasan yarinta tace tasa ta fad'i hakan, shima rik'e ta yayi yana fad'in, "shikenan komai ya wuce , in malamar taku ta tambaye ki kice ance babu ruwan ta a cikin wan'nan maganar, kai dole ma gobe naje makarantar nasa ajawa malamar kunne , meye ya shafe ta akan maganar auren student d'inta , gobe zamuje tare dake ," Saudala ta ce " to" , ta mayar da kanta jikin sa. Duk abinda suka fad'a a kunne Hady dan tun farko fara maganar tasu tana lab'e a jikin k'ofa tana jinsu , a hankali ta bar wajan ta koma part d'inta ta k'ira Momy ta sanar da ita abinda taji , Cikin farin cikin jin wan'nan information d'in Momy ta k'ara bata wani plan d'in da zasu had'a , murna Hady take da daga jin wan'nan plan d'in kasan zaiyi Sosai. Bayan sati uku Abubuwa da dama sun faru ciki harda fara exams d'in su Saudala da kuma saka ranar auren Fadila da Mustapha, Hady ma taje Kano anan suka kuma tsara abinda zasuyi ita da Momy. Ranar Talala da safe Saudala ta tashi da wani irin ciwon kai mai tsanani , gashi kuma tana da exams , dole ta tashi ta fara shirya Dak'yar tana yi tana dafa bango. Da yake ranar girkin Hady ne shiyasa Abdul bai san halin da take ciki ba , tana fito daga wanka kenan Abdul ya shigo d'akin, Ganin yadda take dafa bango yasa ya k'arasa wajan ta da sauri yana tambayar Lafiya, ai Saudala tana jin kamshin turaren sa ta fara amai , hankalin Abdul ya k'ara tashi cikin tashin hankali ya kira family Dr d'insu a waya yana shaida masa halin da ake ciki, likitan yace gashi nan zuwa, D'aga ta yayi ya sa mata kaya san'nan ya fito da ita parlour ya kwantar ya zauna yana jiran isowar Dr , babu jimawa ya k'araso , bayan ya buda ta ya bawa Abdul wata roba yace tayi fitsari a ciki ta kawo masa , Abdul ya taimaka mata ya kaita toilet tayi fitsarin san'nan suka dawo ya bawa likitan robar , Dr Yace "bara naje na duba zuwa anjima zai dawo da result d'in, " Godiya Abdul yayi masa ya juya ya fita daga parlourn. Wajan mitina talatin Dr ya dawo fuskar sa d'auke da murmushi , Hannu ya mik'awa Abdul yana fad'in, "Congratulation my friend madam tana d'auke da ciki na tsahon sati biyu." Kasa magana Abdul yayi , kawai sai ya juya ya kalli gabas yayi sujjada yana godewa Allah da wan'nan baiwar da ya bashi. Mik'ewa yayi ya kallo Dr d'in yace "Nagode Dr da wan'nan albishir d'in ," Dr yayi murmushi yace "babu komai , Allah ya raba Lafiya." Juyawa Abdul yayi ya d'auko key ya mik'ewa Dr , karb'a Dr yayi yana jiran k'arin bayani , Murmushi Abdul yayi yace "idan ka fita parking space d'an gidan nan ka duba zakaga mota k'irar Benz E 350 ta d'auka na baka , gift d'in wan'nan albishir d'in da kayi min." Kasa magana Dr yayi , yara da wane baki zai yi masa godiya, Dr ya dinga godiya harda kuka , san'nan y tafi cikin farin ciki. Abdul kuwa waya ya d'auka yana fama kiran y'an uwa da abokan arzik'i yana shaida musu, Saudala kuwa tuni bacci yayi gaba da ita, B'angaren su Mama kuwa tunda suka ji suka farin ciki , nan da nan Mama tace a dawo da Saudala gida , Abba Yace A'a basai ta dawo ba , tunda dai basu da nisa ai shikenan. STORY CONTINUES BELOW Kulawa sosai Saudala take samu daga wajan Abdul , babu abinda yake barin ta tayi komai shi yake yi , Hutu ya d'auka a office musamman dan kula da Saudat , Saudala kuwa da yake cikin baya wahalar da ita idan ka ganta baza kace tana da ciki ba , don cikin jikinta ya bi ,sai breat d'inta ya ciko sosai , Kudi Abdul ya biya aka cigaba da zama mata exams a makaranta. Hady kuwa babu laifi ta d'an ji haushi, Amma da yake ita babu tsarin haihuwa a tare da ita ko a jikin ta dan Saudala ta samu ciki , a cewar ta bazata tsufa da wuri ba. Cikin Saudala ya shiga wata biyu , da yake tunda ta samu ciki babu abinda take so kamar fanta , Yau ma ta fito main parlour tana zuwa ta bud'e fridge ta dau fanta mai sanyi , babu tunanin komai ta bud'e ta kafa kai ta shanye fantar tas, Tana gama sha ta dawo ta zauna ta ajiyar xuciya, Kusan minti biyar da shan fantar marar ta ta daure kamar zata cire , mik'ewa tayi Dan ta koma d'aki ta kwanta , Ai tana mik'ewa jiri ya kwashe ta ta fad'i a wajan jini yana zuba daga jikin ta. Shigowar Abdul kenan ya gano ta , cikin tashib hankali ya d'auke sai asibiti , Emergency aka kaita , cikin sauri likitoci suka rufu akanta suna k'ok'arin ceto rayuwar ta . Abdul kuwa banda safa da marwa babu abinda yake yi a wajan , gabad'aya ya kasa zama , Wata nurse ce ta fito tace da Abdul ana bukatar jini yanzu , Abdul yace "muje ki d'ibi nawa indai zaiyi." Tare sukuje lab akayi saa jinin sa o+ ne nan da nan aka d'ibi laida d'aya aka je aka sawa Saudat. Babu dad'ewa nurse d'in ta kuma fitowa , Abdul ya kalle ta yace , "Ya jikin nata.?" Nurse d'in tace "anyi saa jinin ya tsaya , sai dai cikin ya zube sakamakon maganin zubar da cikin da tasha ." Cikin rawar murya Abdul yace "mag...an..in.... zubar... Da ciki fa kika ce." Nurse din tace "eh tabbatas matar ka tasha maganin zubar da cikin kuma tayi nasarar zubar dashi, zaka iya shiga ka ganta," tana gama fad'ar hakan ta bar wajan. Kamar zaki haka Abdul ya shiga d'akin da Saudala take, Lokacin Saudala ta farka daga baccin , Kallon ta yayi yace "munafuka , wawiya , mahaukaciya, kin zubar da cikin kinji dad'i , wato wan'nan malamar takuce ta zuga ki kika zubar min da ciki ko , Ashe bak'ya sona , Ashe bak'ya kaunata tunda bak'ya son ki had'a jini da ni , na tsane ki Saudat , bazan iya zama da wacce bata kauna ta balle jini na ba, Saudat kije ki tattara kayan ki na....................😭😒😀 *Ayi min afuwa yau kun ganni sai yanzu ko , ina can ina yi muku long page , Amma fa kila harda na gobeπŸ€ͺ.* Comment and share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } STORY CONTINUES BELOW 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sister MISS XERKS*❤ *Bismillahir rahmanir rahim* 83&84 Saudat kije ki tattara kayan ki na ...... "Kana sakin ta kaje ka nemi wani uban amma bani ba", Abba ya fad'a yana shigowa d'akin cikin b'acin rai. Mama ta kalli Abdul d'in tace " ban tab'a sanin baka da hankali ba sai yau, kai yanzu in ance ka saki Saudat sai ka sake ta , Yarinyar da aka aura maka ita badan ta zab'e ka a matsayin miji ba , ta hak'ura ta zauna da kai duk da k'ananun shekarun ta , Amma yau kaine kake shirin sakin ta ," Abdul ya girgiza kai Yace "Mama kin fi kowa sanin yadda nake son Saudat , amma bazan iya zama da ita ba , tunda itama ba k'aunata take ba , inda tana k'aunata bazata d'auki maganin zubar da ciki ta sha ba , sa........" Marin da ya sauka a fuskar sa ya hana shi k'arasa fad'ar abin yayi niya , juyawa yayi yana kallan Abba da mamaki , wai yau Abba shi ya Mara abinda bai tab'a yi masa ba tun yana yaro ,akan wacce Mara hankalin Yarinyar Abba ya mari shi , Abba ya katse masa tunani da fad'in, "lallai Abdul baka da hankali baka da mutunci , kai kake bud'e baki kana fad'in ka tsani Saudat, gaban idona , gaban idon mahaifiyar ka , a gaban idon mahaifin Saudat , agaban idon mahaifiyar ta , kai ko kunyar furta hakan baka yi ba , ta zubar da cikin sai mai , wallahi kaji tsoron ranar da zaka yi Dana sani , a lokacin da bazai amfana maka da komai ba , Dan duk ranar da kayi nadamar abinda ka aikata ni kuma a ranar zan sa ka sake ta ko kana so ko baka so, shashasha kawai Wanda baisan darajar d'an uwansa ba , fita ka bawa mutane waje ko na sab'a maka." Juyawa Abdul yayi ya bar Asibitin ma gabad'aya. Saudala kuwa ban da kuka babu abinda take , ita dai tasan bata sha wani abu na zubar da ciki ba , hasali yau fanta kawai ta sha , Kawai dai yana so ya sake ta ne shiyasa ya fake da ta zubar da ciki, Mama ce ta katse Mata tunani da fad'in, "sannu Saudat ya jiki ?" Ai kamar jira take ta fashe da kuka tana fad'in , "wallahi Mama ban sha komai ba , hasali ma yau banda fanta babu abinda na sha , ina gama shan fantar ne ban kuma sanin inda kaina yake ba sai yanzu , wallahi Mama ban sha komai ba." Abba ya k'araso ya rik'e hannun ta yace "ki kwantar da hankalin ki nasan daman baza ki aikata hakan ba , zan sa ayi bincike a gano min gaskiya ," Umma dai tana gefe gabad'aya tausayin y'ar ta take ji Baba kuwa yana gefe yayi shiru , amma shima tausayin Saudat d'in yake yi. Likita ne ya shigo d'akin , bayan sun gaisa dasu Baba sai ya fara buda Saudat, Bayan yayi y'an rubuce-rubuce can sa ya kalli su Abba yace , " ina mijinta ?" Abba yace " ya fita amma kayi mana bayani kawai" . Dr yace " kuyi hak'uri akan abinda nurse tayi d'azu, basa tsayawa suyi aiki yadda yadda kamata d'azu tace muku cikin ya zube alhalin cikin yana nan bai fita ba, sai dai tana bukatar kulawa sosai , sabida maganin ya tab'a Lafiyar abinda yake cikin ta , Allah ya taimaka bata sha maganin da yawa ba Dan da tasha da yawa d'azu cikin ya fita , kar a barta ta dinga aiki sosai in da dama ma kar a barta tayi komai ta haka ne abinda yake cikinta zai zauna Lafiya , ko yaya tayi wani aikin mai yawa zai haifar mata da bleeding Sosai , indan mijin nata ya dawo a turo shi office d'ina akwai abinda nake son fad'a masa ," yana gama fad'ar hakan ya juya ya fita. STORY CONTINUES BELOW Mama tayi murmushi tace "Alhamdulilah Ashe ma cikin yana nan bai fita ba " . Abba yace " an godewa Allah , Amma bana so ko da wasa Abdul yasan cikin nan bai fita ba kar Wanda yayi ganganci fad'a masa , aci gaba da zama a matsayin cikin ya zube bara na sami likitan ma na nemi alfarmar karya sanar dashi ." Abba ya mik'e ya nufi office d'in Dr. Saudala dai tana jin duk abinda ake ba tace komai ba. Abdul kuwa gudu yake a mota kamar zai tashi sama, ikon Allah ne ya kai shi gida Lafiya. Main parlour ya shiga yana kallon inda Saudala ta suma , an goge jinin wajan amma har Yanzu robar fantar tana nan inda aka barta , Tsaki yayi yana jin wani irin b'acin rai da tsanar Saudat na yawo a jikinsa. Hady ce ta shigo parlourn tana fad'in " yanzu ashe Saudat bata da Lafiya shine baka sanar dani ba, gaskiya baka kyauta min ba ," tana fad'a cikin damuwa. Kallan ta yayi baice ya d'auke Kai baice komai ba. Tace "Yanzu ya jikin nata,?" Mik'ewa yayi ya bar ba tare da ya bata amsa ba . Yana barin wajan tayi murmushi tace "Allah yasa dai ya sake ta, " Shi kuwa Abdul d'aki ya koma ya zauna yayi tagumi , Tsaki yayi yace "meyasa ma na damu ne duk abinda tayi taje dan kanta, duk son dana ke mata Amma ta rasa da abinda zata saka min sai wan'nan abun, " Hady ce ta shigo d'akin tana goge hawaye, Tace "meyasa kake min haka ne my life?, idan ka gaji dani ai gwara ka sallame na koma gidan mu, Dan kaga ina sonka sai ka dinga wulak'antani, d'azu ina yi maka magana kayi min banza kuma nasan kaji ni," ta fad'a tana fashewa da kuka. Wani irin tausayin taji ya kama shi, ko ba komai bai Hady tana k'aunar sa sosai Dan yasan Hady bazata tab'a yin abinda Saudat tayi masa ba , yana nunawa Saudat so amma sam Ashe k'aunar sa take ba ,gwara ya bar rik'e wacce yake hannu biyu , mik'ewa yayi ya rik'e hannun ta yana sakar mata murmushi yace "am sorry my Hady raina nane a b'ace shiyasa ," ya fad'a yana rumgumeta yayi yana bubbuga bayan ta . Shiru tayi tana jin farin ciki a ranta , ko banza tasan ko bai saki Saudat ba zuwa yanzu haushin ta yake ji. Saudala kuwa likita ya basu sallama yanzu Dan jikin nata yayi sauk'i sosai. Likita ya dad'a jaddada musu akan a kula da Saudat sosai , daga nan suka shiga mota suka tafi gida. Iya tana zaune a parlour tana jiran dawowar su , tana zaune suka shigo Mama tana rik'e da hannun Saudat. Mik'ewa Iya tayi tana fad'in "ya jikin Saudat d'i?", ta fad'a tana rik'e Saudat d'in. Zama sukayi san'nan Abba yayiwa Iya bayanin komai har k'ok'arin saki da Abdul yayi. Sai kuwa Iya ta fara fad'in " Amma dai mai k'atan kai bashi da mutunci, yo ko cikin ta zubar sai ya sake ta , bayan ya gama lugwigwitata ya mayar da Ita babbar mace ta k'arfi san'nan yace zai sake ta , gwara da kuka tawo da ita nan dan wan'nan shegiyar matar tasa babu abinda baza tayi ba , Dan ni ita nake zargi akan wan'nan abun." Baba yace "shikenan ai yanzu komai ya wuce , Allah ya bata Lafiya." Suka amsa da Ameen. Saudala ta mik'e tace "Mama zan shiga na kwanta." Mama tace "to shikenan , ai gwara ki huta ," STORY CONTINUES BELOW Tunda ta shiga d'akin ta zauna tayi tagumi tana tunanin abinda ya faru, bak'ar maganar da Abdul ya fad'a mata take tunawa , _wawiya, mahaukaciya_, wani irin tsanar sa taji tana wayo a jikin ta. A fili tace "nima na tsane ka kamar yadda ka tsane ni." Ta fad'a tana kwanciya a kan gado. Hady kuwa bayan ta bar part d'in Abdul nata ta nufa , cikin farin ciki ta dau waya ta sanar da Momy komai yayi dai-dai, Sosai Momy tayi farin ciki suka yi sallama suka kashe wayar. Washe gari Abdul bai fita ko ina ba sabida har lokacin ransa a b'ace yake. Shiryawa yake yana son zuwa gidan Mama su gaisa , fitowa yayi ya nufi part d'in Hady. Hady kuwa tana zaune tana waya da kawarta suna shewa suna dariya , Hady tace "ai na baki labari wallahi baza tab'a yarda na dau ciki ba , haka kawai da yarin tata na zama tsohuwa , shiyasa kwanakin baya lokacin da naje Kano naji alamun Kamar inada ciki sauri nayi na siyo tsinke PT ina gwadawa naga ina da ciki , babu b'ata na sha magani na zubar dashi , da tuni yanzu ina nan ina ja da kyar," Ta k'yalk'yale da dariya tace "ke dai Bari kawata da tuni kun ku........." Maganar ta makale sakamakon Abdul da ta gani tsaye yana kallan ta. *Kuyi hak'uri da wan'nan ina busy ne wallahi*🀦🏻‍♀ Comment and share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sisters*❤ *Bismillahir rahmanir rahim* 85&86 Kallan ta yayi yace "Lafiyar ki naga kin wani tsorata sai kace Mara gaskiya," ya fad'a yana zama akan kujera. Ajiyar zuciya Hady tayi tana godewa Allah da baiji abinda suke cewa ba . Shagwab'e fuska tayi tace "ba kaine ka tsorata ni ba," Y'ar dariya yayi yace "sai dai in baki da gaskiya. " Mik'ewa tayi taje ta zauna akan cinyar sa tana shafa fuskar sa tana murmushi makirci. Abdul yace "ni d'aga ni ki taje ki d'auko min break fast yunwa nake ji." D'an b'ata fuska tayi tace "my life wai ina sis Saudat ne gabad'aya jiya da yau banji motsin ta ba?", Jin ta ambaci Saudat gaban Abdul ya fad'i , runtse ido yayi yana jin iri a jikin sa , shi kansa yasan yayi kewar Saudat , Dan Saudat ko baka sonta indai zaka zauna da ita dole ta shiga ranka , Ganin yanayin da Abdul ya shiga yasa tayi murmushi tace " kayi shiru ," Abdul yace "nace ki tashi ki kawo min abinci ko." STORY CONTINUES BELOW Mik'ewa ta shiga kitchen ta d'auko abinci ta ajjiye a kan center table tana fad'in , "Gashi to na Kawo," Bud'e abincin yayi ya d'iba ya kai bakin sa, da sauri ya zubo da na bakin sa yana kallan ta. Cikin b'acin rai yace "wai yaushe zaki iya koyi yadda ake abinci ne ?, dake har y'ar aikin naki babu abinda kuka iya , to wallahi baza d'auki wan'nan abun ba , da mutunci na bazan dinga yawon restaurant ba ," ya fad'a yana Mik'ewa ya fita daga parlourn . Turo baki tayi tace "to ni ban iya ba , a gidan mu ko dafa noodles ban tab'a yi ba ," Abdul kuwa part d'in Saudat ya wuce , yana shiga parlourn ya ja ya tsaya yana kallon parlourn. Sam ya manta Saudat bata cikin gidan, Babu abinda ya canja a parlourn , komai yana nan tsaf kamar tana ciki banda kamshi babu abinda yake yi. Zama yayi yana tunanin da tuni yanzu tana zaune a kan kujera, A fili yace "why Saudat zaki aikata hakan bayan kin san ina bukatar ki a rayuwa ta, why ! ," ya fad'a yana dukan kujera. Sai kuma yace "meyasa na damu da wacce bata sona , yadda bata sona nima na tsane ta, " a fusace ya fita daga parlourn ya shiga mota ya bar gidan. Saudat kuwa tana zaune a d'aki tana game a wayar ta , gabad'aya ta cire damuwa a ranta tace tunda yace baya sonta itama bata son sa . Su Mama suna parlour gabad'aya suna hira , da sallama Abdul ya shigo parlourn , Suka amsa suna had'e fuska, cikin fara'a Umma tace "A'a Abdul Kaine tafe da safe ." Ya durk'usa har k'asa ya gaishe su, fuska a had'e Mama da Iya suka amsa , sab'anin Umma da ta saki murmushi ta amsa. Abdul yace "Mama Abba ya nan?". Mama ta galla masa harara tace " baka san inda yake ba kaje ka duba mana." Sunkuyar da Kai yayi yana jin wani irin haushin Saudat , duk akanta Mama take masa haka. Mik'ewa yayi ya shiga parlourn Abba, a zaune ya gansu shida Baba suna shan fruit, Abba yana ganin sa ya had'e girar sama da k'asa yace "kazo ka kawo mata takardar sakin har cikin gidan su kenan ko?", Abdul yace " Dan Allah Abba kayi hak'uri ka yafe min ," Baba yace "haba ya daga zuwan yaro ko gaisawa ba'ayi ba ka fara yi masa fad'a, " Abba yace "ka rabu dashi ba ya nuna mana bamu isa dashi ba , yaje yayi duk abinda yake so." Shiru Abdul yayi bai ce komai ba, Baba yace "to ai sai ka bari a gaisa ko , kuma tunda ya bada hak'uri ai komai ya wuce ," Abdul yace "Abba daman zuwa nayi na sanar da ku zan tafi garin Abia gobe akwai wani aiki da ya taso , kuma zamu iya kai wata biyu zuwa uku." Baba yace "Allah ya tsare , Allah ya bada sa'a , Allah ya dawo daku Lafiya," Sosai yaji dad'in Addu'ar da Baba yayi masa , ya amsa da Ameen ya mik'e ya fita daga parlourn. Baba ya kalli Abba yace "ya kamata ka daina fushi da yaron nan haka ," Abba yace " ba yanzu ba ", ya fad'a yana Mik'ewa . Baba yayi murmushi baice komai ba. STORY CONTINUES BELOW Abdul kuwa part d'in Mama ya koma ya sanar dasu zance tafiyar sa , Addu'a suka yi masa suka cigaba da hirar su. Fadila ce ta fito tace " A'a bro yaushe ka shigo?," Murmushi yayi yace "ban jima da shigowa ba." Fadila tace "Mama wai inji Saudat ki bata paracetamol kanta ciwo yake ." Mama tace "ayya gashi can maza ki d'auka ki kai mata." D'auka Fadila tayi ta shiga d'aki. Abdul dai yana zaune jin ance kanta na ciwo sai yaji wani iri , amma da ya tuno abinda tayi masa sai yaji wata irin tsanar ta a cikin zuciyar sa. Mik'ewa yayi ya yi musu sallama ya fita. Saudala kuwa tana jin shigowar sa banda haushin sa babu abinda take ji. Washe gari da safe Abdul ya dau hanyar Abia state , Bayan tafiyar Abdul Hady taje Kano tayi kwana biyu ta dawo. Saudala kuwa ta sake babu abinda yake damunta yanzu , kullum cikin walwala taje da farin ciki. Abdul kuwa tunda ya tafi kullum sai yayiwa su Mama waya , duk da ba ko wanne lokaci suke d'auka ba. _A gurguje_😎 Bayan wata biyu Cikin Saudala ya fito sosai tunda yanzu ya shiga wata biyar , kowa mamakin girman cikin ta yake , kamar ba haihuwar fari ba ba. Hady kuwa tun tana sa ran dawowar Abdul har ta daina ta cigaba da abinda yake gaban ta. Yau su Abdul ran dawowa gida , babu Wanda ya sanar wa har ya isa gidan sa , Part d'insa ya shiga yayi wanka ya shirya san'nan ya fito ya nufi part d'in Hady. Har ya rik'e handle k'ofar zai bud'e sai kuma ya tsaya sakamakon jin abinda Hady take cewa, Hady kuwa suna tare ita da k'awatar tana bata labarin duk abinda ta had'awa Saudala. Hady tayi shewa tace "kedai Bari ai ina sane na kyale su na wani lokaci, ina jin labarin ciki gare ta na dau alk'awarin zubar dashi balle kuma naji duk abinda take fad'a masa akan malamar su tace tayi family planing, da wan'nan damar nayi amfani na zuba mata magani a ciki fanta , Dan nasan Abdul da shegen son yara indai cikin ya zube nasan sai ya sake ta ," K'awarta ta k'yalk'yale da dariya tace "Amma ke kam anyi muguwa wallahi ," Hady tace " to ai da banyi hakan ba da yanzu na zama tamkar y'ar aiki a cikin gidan nan." K'awarta tace "ai kinyi min dai-dai wallahi , da........" Bugo k'ofar fa akayi ne ya hana ta k'arasa wa , Cikin sauri Hady ta juya Dan ganin waye wan'nan , had'a ido suka yi da Abdul yana wuci kamar zaki , idon sa yayi ja Sosai, Ganin sa yasa gaban Hady ya fad'i tana Addu'ar Allah yasa baiji abinda suke cewa ba. Kafin ta gama tunanin ya d'auke ta da mari, yasa k'afa ya daki k'afar ta ta fad'i a wajan , ball yayi da ita kanta ya daki center table d'in parlourn, Cikin b'acin rai yace "kin cuce ni Hady kin gama dani a rayuwa ta , amma nima baza saurara miki ba , yanzu Ashe ke kika zubawa Saudat maganin zubar da ciki a lemo , kice kika kashe min d'ana tun kafin yazo duniya , kece kika na zargi Saudat akan abinda bata sani ba , to wallahi kema baza kyale ki ba , sai na ci uban ki s cikin gidan nan, " ya fad'a yana zare belt , STORY CONTINUES BELOW Dukan ta ya fara yi kamar hauka , tun Hady tana ihu har muryar ta ta dashe, d'ago ta yayi yace "wallahi ko ki fad'a min da bakin ki ko yanzu ns b'alla ki." Cikin muryar wahala Hady tace "nice nake had'u kumu komai a cikin gidan nan , kuma nice na zubar da cikin Saudat , Amma Dan Allah kayi hak'uri." Hannu yasa ya d'auke ta da Mari yana fad'in, "Kin cuce ni , bazan tab'a yafe miki abinda kika yi min ba , " Cigaba yayi da duka ta kamar ya sami jaki, Kallan yayi yace "kafin na dawo ki tabbatar kin barmin gida , ki koma gidan ku na sake ki saki biyu." Har ya juya zai fita ya hango k'awar ta a rakub'e a jikin kujera. Nuna ta yayi da yatsa Yace " ki d'auki k'awar ki ku bar min gida , san'nan kuma kema zan dawo kanki dan sai kinyi kwanan guardroom ." Ya fad'a yana ficewa daga parlourn. Cikin tashin hankali k'awar Hady ta nufi inda Hady take , d'aga ta tayi taga Sam bata numfashi ga jini yana zuba daga jikin ta. Cikin sauri ta fita ta nemi taimakon sojoji suka d'auki Hady aka sata a mota suka nufi asibiti. Shi kuwa Abdul tunda ya fita daga parlourn Hady yake kuka kamar yaro , mota ya d'auka ya nufi gidan su. Lokacin Saudala tana parlourn tana cin abinci cikin kwanciyar hankali. Babu ko sallama Abdul ya shigo parlourn yana hawaye, Mama ta mik'e tana tambayar Lafiya. Bai tsaya wani tunani ba ya nufi inda Saudat take , Saudat ganin ya nufo gunta yasa ta Mik'e tana ja da baya yana binta. Mama ce ta daka masa tsawa tace "kai kana cikin hankalin ka kuwa.!" Yana zuwa kusa da Saudat ya zube a k'asa yana hawaye yana fad'in ......... Comment and share Neat LadyπŸ‘πŸ»πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ² 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & &WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sisters*❤ *Bismillahir rahmanir rahim* 87&88 Zubewa yayi a gaban Saudat yana fad'in "ki yafe min Saudat , nasan na b'ata miki rai , Amma kiyi hak'uri ki yafe min kinji Dan Allah ki yafe min." Ya fad'a cikin kuka kamar yaro. Mama tace "wallahi Abdul ko ka tashi ka bar wajan nan ko ranka ya b'aci ," Kallan sa Saudala tayi sai taji ya bata tausayi , amma da ta tuno abinda yayi mata sai Kawai ta k'yalk'yale da dariya tana fad'in, "A rayuwa ta ina so naga k'aton gardi yana kuka , wallahi dariya yake bani Sosai , Dan Allah ka cigaba da kukan yana yi maka k'yau." Tana gama fad'ar hakan ta shige d'aki.(Saudala halin ya dawoπŸ˜‚) STORY CONTINUES BELOW Mik'ewa yayi zai bita Mama ta daka masa tsawa tace "kar ka sake ka shiga d'akin nan ," Dawowa yayi ya rik'e hannun Mama ya k'ara fashewa da kuka yana cewa "Dan Allah Mama kuyi hak'uri ku yafe min , ba laifi na bane laifin Hadiza ne Mama itace ta had'a komai gabad'aya, Dan Allah Mama kiyi hak'uri ki yafe min , wallahi idan aka hanani Saudat kamar barazana ake yi da rayuwa ta ," Akace d'a da mahaifiya nan da nan taji tausayin sa ya kamata , tana shirin magana Abba ya shigo parlourn yana fad'in , "Alhamdulilah , daman wan'nan ranar nake jira, daman na fad'a maka duk ranar da ka fara nadamar abinda ka aikata ranar zaka bani takardar sakin Saudat , to har yanzu ina nan akan baka na , maza ina jiran ka." Ya fad'a yana Mik'ewa Abdul hannu. Durk'ugewa yayi gaban Abba yana cewa "Dan Allah Abba kayi min rai , wallahi ina son Saudat bazan iya rabuwa da ita ba , duk abinda ya faru Hadiza ce ta had'a komai , Dan Allah Abba kar kace na saki Saudat wallahi ina sonta." Murmushi Abba yayi yace "k'arya kake baka sonta, ka manta lokacin da ka furta baka sonta ka tsane ta , yanzu muku shine zaka zo kace kana sonta , to baka isa ba kayi kadan ," Abdul Baba ya kalli da yake tsaye baice komai ba , Abdul yace "Baba Dan Allah kasa baki kar Abba ya raba ni da Saudat." Ajiyar xuciya Baba yayi yace "kwantar da hankalin ka kayi mana bayanin komai." Nan Abdul ya kwashe duk abinda yaji Hady ta fad'a , Baba yace "yanzu ita ina Hadizan take?", Abdul yace " nace kafin na dawo ta bar min gida Dan na sake ta ." Baba ya zaro ido Yace "ka sake ta , bayan ka gama dukan nata ," Abdul yace "wan'nan shine hukuncin da ya dace da ita , " Abba yace "haka kuma shine hukuncin da ya dace da Saudat ba , Abdul tun muna shaida juna da kai ka bani sakin Saudat , idan ba haka ba hmm." Wajan Umma yaje Yace "Dan Allah Umma ki sa baki ki bawa Abba hak'uri." Cikin tsawa Mama Tace "kai ko kunyar zuwa inda Umman Saudat take baka ji ba , ka manta lokacin da a gaban idon ta kake furta ka tsani y'ar da ta Haifa , sai Yanzu kuma zaka zo kana wani rok'on ta ,ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi Amma kasa k'afa kayi fatali da wan'nan, ka rife ido kace babu wacce ka tsana kamar Saudat, shine Yanzu zaka zo kana cewa wai kana sonta , kayi kad'an." Sai yanzu Abdul yake jin kunyar abinda ya aikata a gaban Umma da Baba , Zama Abdul yayi ya dafe kai ji yake kamar kansa zai fashe a lokacin, Iya tace "ai bara kaji mai katan kai ko kukan jini zaka yi Saudat dai baza ta dawo gidan ka ba, " ta fad'a tana yi masa gwalo. Abba yace "Abdul a matsayina na mahaifin ka ina baka umarnin ka mayar da matar Hadiza yanzu." Cikin firgici Abdul ya d'ago yana kallan Abba , Abdul yace "Amma Abba..." Abba ya katse shi da fad'in "umarni na baka ba shawara ba." A hankali Abdul yace "shikenan na mai da ita." Abba yace "to Alhamdulilah Yanzu ku tashi muje gidan gabad'aya muga halin da take ciki , itama kamar y'ar mu take ,kuma ai d'a na kowa ne." Mik'ewa sukayi suna shirin fita k'awar Hady ta shigo a firgice , Umma tace "baiwar Allah Lafiya?" STORY CONTINUES BELOW K'awar Hady tace "nice k'awar Hadiza ce mun kai Hady asibiti bata da Lafiya , kuma Dr yace yana bukatar ganin mijin ta ," Baba yace "subahanallah ai gwara mu hanzarta mu k'arasa." Abba ya kalli Abdul da ko alamun motsawa baiyi ba yace "Abdul ka tashi muje asibitin gabad'aya", Babu wadda ya iya Mik'ewa yayi jiki babu k'wari yana kallon d'akin da Saudat take , gani yake ko zata fito Amma shiru ko lek'owa bata yi ba. Gabad'aya suka tafi suka tafi asibitin aka bar Saudat da Fadila a gida. Hady kuwa tana emergency a kwance , ko Momyn Khaleed da pretty suka ganta dole su tausaya mata . Ko da suka shiga d'akin idon ta a rufe yake , zama sukayi Umma tace "sannu Hadiza ya jiki?", Da sauri ta bud'e ido tana kallan su , had'a ido sukayi da Abdul ya galla mata harara , cikin sauri ta d'auke ido daga kansa. A hankali tace " da sauk'i ". Sakkowa tayi daga kan gadon ta durk'usa a gaban Umma tace " Dan Allah kuyi hak'uri da abinda ya faru , wallahi sharrin shaid'an ne da kuma zugar da mahaifiya ta take min , wallahi nayi nadamar abinda nayiwa Saudat ," ta fad'a tana fashewa da kuka. Da k'arfi aka buga k'ofar d'akin aka shigo , Kafin su Mama suce wani Abu Momy ta fara bala'i tana fad'in "wallahi bazan yarda ba saina nayi shari'a da kai , an fad'a maka y'ata jaka ce da zaka same ta kana duka kamar baiwar ka , to wallahi bazai yu ba akan me y'ar tawa guda d'aya kake son kashe min ita , to baza ta sab'u ba wallahi." Dady yace "ki bari muji abinda yasa mana , kika sami ko wani babban laifin tayi," A hankali Hady ta tako ta zo kusa da Momy tace "komai ya faru ke kika sani ai , komai na had'awa Abdul da Saudat ke kika dinga Goya min baya kina zuga ni , kece kika bani shawarar na dinga had'a su fad'a , kece kika ce na zubawa Saudat magani a cikin lemo , banyi bacen uwa ta gari ba a rayuwa ta , banyi dace mahaifiya mai d'aura y'ar ta akan hanyar da ta dace ba , Momy ki cuce ni , kin kashe min aure , kin zubar min da mutunci a idon mijina da surikai na , " durgushewa tayi a wajan ta fashe da kuka. Jikin kowa a wajan yayi sanyi , Momy dai ta kasa cewa komai . Mama ce tayi k'arfin halin cewa "kiyi hak'uri Hadiza komai ya wuce a wajan mu , kuma auren ki yana nan domin Abdul ya mayar dake a matsayin matar sa." Dr ne ya shigo d'akin , kallan su yayi yace "da alama naga kowa d'an uwan tane anan, to abinda zan fad'a muku shine , sakamakon magungunan zubar ciki da take sha da kuma na hana d'aukar ciki yasa cikin jikinta ya zube san'nan kuma magungunan sun lallata mata mahaifa , abinda nake nufi shine baza ta kuma d'aukar ciki ba a rayuwar ta, domin tasha magungunan da yawa har sun yi mata illah , ga magunguna nan an rubuta mata zaisa jikin ta yayi k'wari , Allah ya k'ara Lafiya , zaku iya tafiya da ita." Ya fad'a yana barin d'akin. Hady ta fashe da kuka tana fad'in "Momy kinga sakamakon abinda kika saka ni na aikata ko , tunda nake dake baki tab'a cewa na daina shan maganin zubar da ciki ko na hana d'aukar ciki, kin sa na zubar da na wani gashi ni nawa ba iya zubewa ya tsaya ba harda lalacewar mahaifa ta, Momy me zaki ce min yanzu ," ta kara fashewa da kuka Babu Wanda bai tausaya mata ba , san'nan kowa a d'akin haushin Momy yake ji. Momy ta share hawayen ta tace "hak'ik'a nasan nayi kuskure a rayuwa ta , na biyewa son zuciya na d'aura y'ata akan abinda yake Mara k'yau , Dan Allah kiyi hak'uri ki yafe min daughter , duk abinda na aikata na aikata shine sabida son da nake miki, kiyi hak'uri ki yafe min ," STORY CONTINUES BELOW D'akin yayi shiru babu abinda ake ji sai sautin kukan Hady da Momy, babu Wanda yake rarrashin wani. Dak'yar Hady ta ja k'afar ta ta k'arasa inda Abdul yake ta durk'usa tana kuka tana cewa "Dan Allah kayi hak'uri ka yafe min , wallahi duk ba laifi na bane Momy ce take zuga ni , wallahi har cikin raina naso mu zauna da Saudat Lafiya Amma Momy ta dinga zuga ni , Dan Allah kayi hak'uri ka yafe min , ina Saudat itama na nemi yafiyar ta." Jikin Abdul yayi sanyi sosai , dak'yar yace "babu komai Hady na gane ba laifin ki bane , na yafe miki, kuma nasan tun kafin cikin jikin ki ya fita na mayar dake a matsayin matata ," Tace "nagode Sosai ", Dadyn Hady ne ya kalli Momy yace " Amma kin bani kunya ban tab'a tunanin son zuciya zai sa ki aikata hakan ga y'ar cikin ba ,haba wan'nan wace irin rayuwa ce, ace uwa ce yake zuga y'arta akan abinda yake Mara k'yau, kin bani mamaki wallahi. " Momy ta k'ara fashewa da kuka tace "Dan Allah kuyi hak'uri ku yafe min , nasan nayi kuskure sosai , kuyi hak'uri," Ajiyar xuciya Abba yayi yace "Alhaji Abubakar hak'uri za'ayi , kasan mata suna da rauni Sosai , kayi hak'uri ka yafe mata ," Dady yace "shikenan komai ya wuce , Allah ya yafe mana gabad'aya." Baba yace "to nima ina neman alfarmar ku yafewa Abdul laifin da yayi," Abba yace "ai tunda shima ya yafewa Hadiza nima na yafe masa, Amma sai dai yaje ya nemi yafiyar Saudat da kansa , kuma bazata koma ba har sai ta amince da kanta zata koma," Mama tace "hakan yayi nima na yafe masa ," Iya ta kalle shi tace "to nidai ban yafe ba har sai ya k'ara yin kuka irin na d'azu," ta fad'a tana had'e rai. Dariya Umma tayi tace "tab lallai iya manya," Hady tace "Abdul ina so zan bi su Momy Kano na d'an kwana biyu." Ta fad'a jiki a sanyaye Dan har Yanzu ta kasa yafewa kanta abinda tayi. Murmushi yayi yace "babu komai Allah ya dawo daku Lafiya." Suka amsa da Ameen. Sallama aka bawa Hady suka tafi , gidan ta suka je ita dasu Momy ta d'auki kayan ta suka tafi Kano, har lokacin bata kula Momy ba. Abdul kuwa gida suka koma suka zauna ana tattauna abinda ya faru. Shidai Abdul gabad'aya hankalin sa yana wajan Saudat , Tashi sukayi kowa ya tafi d'akin sa aka bar Abdul a zaune a wajan. Ganin kowa ya tashi yasa ya Mik'e ya nufi d'akin Saudat, Tana kwance tun fitar su bacci ya d'auke ta sai yanzu ta farka tayi sallah, Da sallama ya shiga parlourn, tana ganin sa ta mik'e tana fad'in, "Kar ka sake ka k'araso wajan nan , kamar yadda ka furta ka tsane ni nima na tsane ka bazan tab'a sonka ba , kaje can ka zauna da wacce kake so amma bani da , " Sosai yake jin maganganun ta suna sauka a cikin zuciyar sa , har a lokacin bai kula da cikin da yake jikin ta ba. Cikin sanyin murya yace .......... *Ko Saudala zata yafewa Abdul oho🀷🏻‍♀* Comment & share STORY CONTINUES BELOW Neat Lady✍🏻πŸ₯°πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ²πŸŒ² 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sisters*❤ *Bismillahir rahmanir rahim* 89&90 Cikin sanyin murya Yace "Dan Allah Saudat kiyi hak'uri ki yafe min , nasan nayi miki laifi Sosai Amma nima ba laifi na bane , duk abinda ya faru laifin Hady ne ,wallahi ko kad'an bani da niyar cutar dake a rayuwa ta , ina sonki Saudat kema kuma kin sani , kiyi hak'uri ki yafe min mu cigaba da zama tare ," ya fad'a kamar zaiyi kuka. Kallan sa tayi ta tab'e baki tace "amma fa ka iya dad'in baki , ni zaka zo kana fad'awa wai kana sona , bayan kalmar tsanar daka furta a kaina ,wai Hady ce mai laifi wato Dan kaga bata nan shine zaka d'aura mata laifi ko, to bara kaji ni Saudat na bar zama da kai , dole ka sake ni Dan bazan zauna da Wanda baya sona bana son sa ba," Abdul ya kwashe labarin komai ya fad'awa Saudat , duk abinda Hady tayi bai rage komai ba sai da ya fad'a mata , Allah sarki Saudat Sam bata damu da abinda Hady tayi mata ba , kawai tausaya mata take jin ance baza ta k'ara d'aukar ciki ba, Tace "Allah sarki ni na yafe Mata wallahi ," ta fad'a cikin tausayawa. Abdul yace "why ni baza ki yafe min ba , kiyi hak'uri ki yafe min kinji Saudat." Tab'e baki tayi tace "hmm nifa na gama zaman aure da kai , bazan zauna da wadda baya binkice kafin ya yanke hukunci ba ," Zuba mata ido yayi yana kallon ta , gabad'aya ya rasa abinda zai ce mata , Mik'ewa tayi zata d'auki waya ai kam idon sa ya fad'a kan cikin ta , Zaro ido yayi da sauri ya nufi inda take , rik'e ta yayi ya d'aura hannun sa akan cikin ta yana fad'in "Saudat mai nake gani haka , ciki ne dake , kenan cikin jikin bai zube ba , Alhamdulilah Allah na gode maka ," Fincike jikin ta tayi tace "naka cikin ya zube wan'nan kuma ba naka bane , na wan'nan d'an makarantar tamu ne da ya sauki ni a mota ya turo da letter cikin gida." Ta fad'a tana hararar sa. Abdul yace "wai meyasa bak'ya yafiya ne Saudat, Allah da ya hallice mu muke masa laifi ya yafe mana , kiyi hak'uri mana kodan cikin da yake jikin ki," Tausayinsa take ji tasan ta barshi ya cigaba da yi mata magiya zuciyar ta zata karaya, muka batayi niyar yafe masa yanzu ba sai ta wahalar dashi. Tace "kaga ka fita daga d'akin nan , in ba haka ba wallahi zam fad'awa Mama " Kallan ta yake kawai bai furta komai ba, Tace "nace ka fita ko" Yace "zan fita Saudat, Amma ki sani duk abinda ya faru dani *Ke ce sanadi"* ya fad'a yana fita daga d'akin. Wajan Mama ya koma , a zaune ya ganta a bedroom tana gyara kayan ta , Yace " Mama daman cikin jikin Saudat bai zube ba ?," STORY CONTINUES BELOW Mama Tace "uhum bai zuba ba , lokacin da ka bar asibitin a lokacin Dr yake sanar damu , muku bamu sanar dake ba tunda ka tsane uwar y'ar," Sunkuyar da kai yayi yana Dana sanin lokacin da ya furta ya tsane ta , A hankali ya mik'e ya fita daga d'akin, part d'insa na cikin gidan ya bud'e ya shiga , tunani kawai yake ya rasa abinda zai yiwa Saudat ta yafe masa. Washe gari Abdul ya tashi da wani irin zazzab'i mai zafi , babu Wanda ya sani a gidan tunda yana d'aki, Suna zaune a parlour ana break fast Baba yace , "wai Abdul bai fito bane ?" Fadila tace "bai fito ba gaskiya," Baba yace "maza kije ki duba shi kila ba Lafiya ba ," Fadila ta Mik'e ta nufi part d'in Abdul , A kwance ta ganshi a parlour yana faman rawar sanyi , hak'oran sa suna had'uwa da juna, Cikin tashin hankali Fadila tace " Yaya Abdul baka da Lafiya , bara naje na fad'awa su Abba, " Da gudu ta nufi main parlour , babu sallama ta fad'a cikin parlourn tana fad'in , "Baba wallahi bashi da lafiya sosai," A tare suka Mik'e suna fad'in, "Subahanallahi bara muje muga jikin nasa," Part d'insa suka shiga , yadda Fadila ta ganshi haka suma suka shigo suka ganshi, Baba ya tab'a jikin sa yaji wani irin zafi kamar wuta , Waya Abba ya d'auka ya kira Dr, babu jimawa Dr ya iso , allura yayi masa san'nan ya bashi magani , Nan da nan bacci ya d'auke Abdul , Abba ya kalli Dr yace "me yake damun sa ?" Dr yace "gaskiya ya saka damuwa a ransa shine ya haifar masa da wan'nan zazzab'in , san'nan na auna VP d'insa gaskiya jinin sa ya hau , ayi k'ok'arin ganin ya rage wan'nan damuwar , na bar ku Lafiya," ya juya ya fita. Babu Wanda yayi magana Dan kowa yasan mecece damuwar tasa , juyawa sukayi suka koma parlour , Saudala kuwa tunda ya fita jiya take jin bata kyauta ba , yanzu idan wani abun ya same shi fa , Tana zaune taji ana bashi da Lafiya , hankalin yayi bala'in tashi , kawai dai ta daure ne , Har akayi sallar la'asar Saudat bata je ta duba shi ba , Umma ce ta shigo d'akin tana fad'in "Ashe baki da hankali , tun d'azu na miki ido ne naga iya gudun ruwan ki , ace mijin ki bashi da Lafiya ki kasa zuwa ki gaishe shi , dan Kawai yayi miki laifi , to umarni nake baki kiyi maza kije ki duba shi yanzu , in ba haka ba wallahi sai na sab'a miki", ta juya ta fita Babu yadda ta iya dole ta mik'e ta saka hijjabi ta nufi part d'insa, A zaune ta ganshi yana cin abinci , A hankali yace "sannu ya jikin " D'agowa yayi ya kalle ta yace "da sauk'i." Tace "Allah ya k'ara sauk'i." Yace "Ameen" Babu Wanda ya kuma magana a cikin su, Saudala ta Mik'e tace , "Allah ya kara Lafiya, sai anjima" Bata tsaya jin mai zaice ba ta fita daga d'akin , Cikin kwana kin kullum Abdul cikin rashin lafiya yake , Saudat kuwa tunda taje duba shi bata k'ara ganin sa ba ko a hanya. Ranar laraba gabad'aya mutanen gidan sun fita , Saudat ce kawai a gidan , tana zaune sai Kawai ta mik'e ta nufi part d'in Abdul. Tunda ta shiga take jin sautin amai , cikin sauri ta k'arasa cikin d'akin, a kwance ta ganshi ya galabaita ya rame , k'arasa wajan sa tayi ta gyara wajan , duk abinda take yana kallan ta , STORY CONTINUES BELOW Dak'yar ya iya cewa "Saudat ki yafe min kar na mutu da laifin wani a kaina , kiyi hak'uri ki yafe min, nasan da sonki zan mutu ," Saudat ta fashe da kuka tace "na yafe maka wallahi , Dan Allah kar ka mutu ka bar ni , nima ina sonka wallahi, Dan Allah kar ka mutu." Abdul yace "da gaske kike kin yafe min?" Tace "wallahi da gaske nake har cikin raina na yafe maka," Nan da nan Abdul yaji cutar tana barin jikin sa , jayo ta yayi ya kwantar da ita a jikin sa yana jin sauki ciwon sa yake ji. Sun jima a haka daga baya sai Saudat ta mik'e tace "bara naje na kawo maka abinci," Babu jimawa ta dawo d'auke da flask d'in abinci , Abdul yace "ki daina d'aukar flask mana ko kin manta ba ke kad'ai bace ," Murmushi Saudat tayi bata ce komai ba. Bayan ya gama cin abincin ta d'auki kayan ta fita dasu . Koda mutan gidan suka dawo sunyi farin cikin ganin Saudat a can , Dan Kowa so yake ta sakko daga fushin, Baba yace "tunda sun shirya Kansu sai su koma gidan su, wani tsalle Iya tayi tace " babu inda zata koma har sai ta haihu." Baba yace "Iya kina nufin har wata hud'u kenan , da ta koma in yaso in cikin ya shiga watan haihuwa sai ta dawo nan ," Dak'yar aka shawo kan Iya ta amince da hakan. Da daddare Abdul da Saudat suka wuce gidan su , Koda suka koma hak'uri Abdul yake dad'a bata , ita dai bata ce komai ba , Part d'inta ta shiga yana nan harda ta barshi sai dai k'ura da yayi , Wanka tayi ta fara shirin kwanciya Abdul ya shigo, Kallan ta yake ganin yadda cikin yayi mata k'yau ,sosai yake jin farin ciki yana ratsa shi. A hankali ya tako ya rungumota ta baya yana shafa cikin ta , Tace "daman baka kwanta ba ,?" Yace "ta yaya zanyi bacci bayan nasan ina da Amarya yau," Murmushi tayi tace "Wai yaushe Hady zata dawo ?" Yace "d'azu munyi waya da ita Tace min zuwa jibi insha Allah," Saudala tace "Allah ya kaimu." Juyowa da ita yayi yana kallon cikin idon ta yace "ina so ki maimaita abinda kika fad'a d'azu , kin furta min Kalmar so ina so naku ji Yanzu," Sunkuyar da kai tayi tana jin kunyar kallon da yake mata , Tace "cewa nayi nima ina sonka," D'ago da fuskar ta yayi yace "ki kalli cikin idona ki fad'a," Cikin tsiwa Tace "indai sai na kalli cikin idonka na fad'a to na fasa, na d'azun ma Dana fad'a ka soke shi na fasa," ta murgud'a baki. Murmushi yayi yace "Ashe dai halin yana nan , to bara nayi maganin bakin da yake yin tsiwa ," ya had'e bakin su waje d'aya ya fara kissing d'inta, Ganin dai Abdul da gaske yake saina fito daga d'akin na zauna a parlour. Wai ya labarin Hady kuwa Comment & share Neat Lady✍🏻🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲 🌴🌴🌴🌴 🌳🌳 πŸŽ„ STORY CONTINUES BELOW 😜 SAUDALA πŸ₯΄ ❣❣❣❣❣❣❣ ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* { _Gaskiya Ι—aya ce daga Ζ™inta sai Ι“ata, burinmu mu faΙ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ } 🎐 '''G•W•A'''🎐 *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*πŸ‡πŸΌ *STORY & WRITTEN* *BY* *NEAT LADY*✍🏻 *Dedicated to my blood sisters*❤ *Bismillahir rahmanir rahim* 91&92 *END*✋πŸ˜₯ Hady kuwa cikin kwana kin ta nutsu sosai kamar ba ita ba , ta yafewa Momy duk abinda tasa ta aikata, Washe gari ta fara shirin dawowa Abuja. Su Saudala kuwa banda love babu abinda ake sha , duk inda tayi Abdul yana mak'ale da ita , Suna zaune a main parlour suna tattauna shirin biki Fadila da Mustapha Hady tayi sallama ta shigo parlourn. Saudala ta Mik'e taje tana yi mata sannu da zuwa , ganin ciki a jikin ta yasa Hady take mamaki , Har k'asa Hady ta durk'usa tana bawa Saudat hak'uri, tana Neman yafiyar ta, Saudala kuwa tunda taji ance bazata haihu ba take jin tausayin ta , tace "na yafe miki Hadiza Allah ya yafe mana baki d'aya," Ta kalli Abdul tace "bazan gaji da Neman gafarar ka ba , dan Allah kayi hak'uri," Shima Yace "babu komai my Hady komai ya wuce ", Cikin farin ciki ta mik'e ta shiga part d'in ta. Saudala ta kalli Abdul tace " to ango Amarya fa ta dawo sai a tashi." Murmushi yayi yace "zan kama kine ," Tace "sai dai ka kama kanka, mai hancin karas kawai." Ta fad'a tana dariya. Shima dariyar yayi ya mik'e ya wuce wajan Hady, A kwanta ya ganta tana faman kuka , d'ago ta yayi jikinsa yana shafa kanta , A hankali Tace "nayi niyar zubar da cikin wata sai gashi bai zube ba ni kuma nawa ya zube kuma har da lalacewar mahaifata , ina tausayawa masu hali irin nawa , Abdul ji nake inama kafin wan'nan ranar tazo na mutu na huta da wan'nan bakin cikin da nake ciki," Abdul yace "ki kwantar da hankalin ki tun farko Allah bai k'addara zaki haihu ba , kisa a ranki haka ya tsarawa rayuwar ki , ki kuma daina tuno abinda ya wuce ," Ajiyar xuciya take yi tana jin wani zafi a ranta, Rarrashin ta Abdul ya dinga yi har ya samu tayi shiru san'nan ya k'wantar da ita ya nufi masallaci. Bayan wata uku Zaman Saudala da Hady Alhamdulilah suna zaune Lafiya , Abdul yana k'ok'arin ganin yayi adalci a tsakanin su , ko wacce tana k'ok'arin ganin ta danne kishi don su zauna Lafiya. Cikin Saudala ya shiga wata na takwas , babu abinda Saudat takeyi a gidan komai Hady ta d'auke Mata duk ita take aikin gidan , Shirye-shiryen bikin Fadila ake dan saura sati d'aya biki, Amarya Fadila tayi k'yau sosai ta k'ara fari , ango Mustapha kuwa ba'a magana , daman su Abdul ne manyan Abokai ana ta shiri. Ranar Friday aka d'aura auren Fadila da Mustapha, Saudat da Hady duk suna gidan su Abdul ana shagalin biki. STORY CONTINUES BELOW Bayan an d'aura auren akayi kamu a cikin gidan su Abdul, Washe gari da daddare aka fara shirin tafiya dinner, babu Wanda Saudat batayi ba Amma Abdul yace bazata ba wai tayi nauyi. Tana ji tana gani aka tafi dinner aka barta, Tun daga ranar take fushi dashi , har aka kai Amarya washe gari bata kula Abdul ba , Bikin ya watse anyi lafiya an gama Lafiya , Saudala tana d'aki Abdul ya shigo yana wak'ar Nura m inuwa da yake cewa _Saudatu ce burin zuciya ta shiga b'argo har jijiya alk'awari dama na rik'a mai sona bazan bar kiba_, yana yi yana d'an taka rawa. Aikam ya taba dariya ta dinga dariya kamar me , daman abinda yake so kenan daga nan suka hau jirgin ma'aurata. Tun bayan da komai ya lafa Saudala take jin marar ta nayi mata ciwo , tun tana daurewa har ta kasa ta fara kuka , ganin halin da take ciki yasa ya kira Hady suka tafi asibiti, Direct labour room suka shiga da ita , Waya Abdul yayi ya sanar da iyayen su , Babu jimawa suka k'araso kowa hankalin sa s tashe, Kusan one hour amma babu likitan da ya fito daga cikin d'akin, Wani likita ne ya fito fuskar sa d'auke da murmushi yace "ta haihu ta sami babies mace da namiji," Tare suka ce Alhamdulilah masha Allah , Abdul yace "ya jikin ita mai jegon?" Dr yace "da sauk'i ta samu bacci ne, Dan gaskiya ta sha wahala, zaku iya shiga ku ganta," Da sauri suka Shiga cikin d'akin , tana kwance tana bacci gefeb ta kuma ga jariran nan a kwance, Da sauri Hady taje ta d'auki macen ta rumgumeta a jikin ta tana jin k'aunar Yarinyar tana ratsa ta. Namijin Abdul ya d'auka yana kallon sa , babu ta inda ya bar Abdul kamar su d'aya sak. Iya tace "to ai sai ka bamu shi mu gani ko, babu kunya ka wani d'auki yaro kana faman yin murmushi," Mik'a mata yayi Dan yasan hali , Iya ta washe baki tace "Kai wan'nan yaro babu inda yabar mai katan Kai, har kan nasu irin d'aya ne." Cikin tausayi Mama ts kalli Hady tace "to a bamu aron y'ar taki mu ganta ," ta fad'a tana.murmushi. Murmushi Hady tayi ta Mik'ewa Mama y'ar, Suna zaune ana yaba k'yaun yaran Saudala ta farka daga baccin. Sosai take jin k'wari a jikin ta , tunda ta farka kowa yake zuba mata sannu , Mik'ewa Iya tayi ta d'aura mata yaron akan cinya Tace "bashi nono yanzu ya sha." Kallan iya tayi ta zaro ido alamun mamaki, Iya tace "wallahi koki bashi kona danne ki na saka masa a baki," Babu yadda Saudala ta iya haka ta fara shayar da yaran cikin kunya. Tunda suka koma gida Hady take d'auke da macen , duk abinda ake Saudat tana kallan ta , Su Fadila sun zo gida ganin baby, Tunda akayi haihuwar nan kullum Hady tana gidan su Abdul, Ranar suna namijin yaci sunan Baba wato Ahmad , macen kuma sunan Mama inda za'a dinga kiran du da Mufty da Muftina, Suna yayi albarka sosai mutanen Adamawa sun zo anyi dasu, STORY CONTINUES BELOW A ranar Abdul yayiwa matan sa kyautar motoci , sunyi farin ciki Sosai sunyi masa godiya, Sosai Saudala take karb'ar gyara daga wajan Mama , tun Abdul yana sa ran a bashi matar sa har ya hak'ura, Ranar da Saudala tayi kwana arba'in ranar Abdul ya shirya musu yawo bud'e ido, Gabad'ayan su suka tafi, ko can kullum muftina tana wajan Hady , Watan su biyu a can suka dawo gida, Saudala ta cigaba da zuwa makaranta Dan yanzu har sun kusa barin ss1. Wata sun Mufty goma Saudala ta kuma d'aukar ciki, zo kiga farin ciki wajan Abdul da Hady, Fadila ma tana d'auke da nata cikin na wata biyar, Tunda ta samu ciki kula dasu Mufty ya koma wajan Hady, komai ita takeyi , Saudala ta haihu Lafiya ta samu y'a mace , Fadila ma an sauka an samu baby boy Wanda yaci sunan Abban ta. Ranar suna yarinya taci sunan Iya wato Amina inda ake kiran ta da Minal, Zo kuga farin ciki wajan Iya anyi mata takwara , bakin nan yaki rifuwa, Suna zaune a gidan su Abdul Saudala tace kowa yayi shaida ta mallakawa Hady Muftyna halak malak, Farin ciki wajan Hady ba'a magana, kuka take tana godiya, haka Momy ma ta dinga godiya, Su Mama sunyi farin ciki da kyautar da Saudala tayiwa Hady , ko babu komai zata rage mata rad'ad'in da yake ji a ranta. *AFTER SEVEN YEARS* Su Saudala an zama manyan hajiyoyi, Dan yanzu haihuwar ta hud'u, bayan Minal, sai wacce taci sunan Umma ake ce mata Mimi , sai Muhammad,. Shekarar Mufty da Muftyna bakwai , har zuwa lokacin Muftyna bata san ba Hady ce ta haife taba kuma sunyi alk'awarin baza ta sani ba, Anyi Bikin Khadija har tana da y'ay'a biyu, Saudat an gama diploma akan nursing yanzu take sa ran yi degree. Su Abdul an samu k'arin girma ya zama birgedia general daga general sai shi. Suna zaune a parlour gabad'ayan su Mufty da Muftyna suka shigo, Saudat tace "A'a har an dawo daga makaranta," Muftyna tace "eh wallahi Ammi mun dawo," Hady tace "to sannun ku da zuwa", Sukace yauwa Mommy. Kowa ya shiga d'akin sa. Saudat tana d'aki tana bawa Muhammad nono Abdul ya shigo yana kare mata kallo. Zama yayi a kusa da ita Yace " Ammin yara ana zaune" Murmushi tayi tace "eh ina zaune " Ya jayota jikin sa yace "ya kamata a yaye Muhammad ayi masa k'ani, " Saudala tace "hmm kaji mai hancin karas d'in nan haihuwa fa da wuya" Hancin ta yaja yace "wan'nan sunan bazai fita daga bakin kiba ko," Murmushi tayi tace "Dan ma bance brown strowman ba," ta fad'a tana dariya, Yace "zan kama kine yarinya," Tace "nima zan kama Kane yaro", Y'ar dariya yayi yace " ina sonki Saudat, kin bani farin ciki a rayuwa ta , kin haifa min yara masu albarka, Allah ya bar mu tare dake, " Murmushi tayi tace "Ameen mijin na", *ALHAMDULILAH* *Anan na kawo k'arshen wan'nan littafi mai suna SAUDALA, kuskuren dana yi a ciki Allah ya yafe.*

Post a Comment for "SAUDALA CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...