Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SARAUNIYA ZAJLAT COMPLETE

SARAUNIYA ZAJLAT COMPLETE

- - Post a Comment

 SARAUNIYA ZAJLAT COMPLETE


Gaba ɗaya garin ya yi wani irin yin baki kirin da shi da kyar mazauna garin ke ganun tafin hannuwansu, a hankali duhun ya yayye sai wata irin gugguwa ta taso jajjur da ita ta soma shawagi da mutane tana makawa a bango. Duk wanda hakan ya kasance a kansa to kuwa baya faɗowa da rai sai ya sheka barzahu, shekaru goma sha uku kenan wannan annoba na adabar ɗaucin mazauna birnin bisa wani gaggarumin laifi da suka aikata babban tashin hankaƙin Sarkin garin duk sanda hakan ya kasance ya kan rasa dakaru da yawa abu mafi muni ya kan rasa ɗan da ya haifa a cikinsa yau kimanin shekara goma sha uku kenan wanda ya yi daidai da rasa yaransa guda goma. *ZAJLAT* Ita ce yar da yafi so fiye da sauran yaransa shi yasa yake takaicin rasata a wannan *GUGGUWAR ANNOBAR*. A yau da wannan iska ke kaɗawa gaba ɗaya hankalinsa ya yi masifar tashi jikinsa ko ina rawa yake tamkar mazari zuciyarsa ta cunkushe tamkar bakar kwalta idanunsa sun kaɗa sunyi jajjur kamar ɗan buda a cikin ruwan barkono.+


Bayan kurar ta lafa ne, kuma katangun birnin suka fara girgiza kamar zasu rufta inda sabo sun saba da hakan sai iface-iface ke tashi da guje-guje tare da kukkan kanannu yara da sauri ya faɗa cikin gida ga mammakinsa Zajlaht zaune tana karanta wasu surutai da kunnuwansa suka juyo masa tamkar na makiyansa tabbas kunnuwansa basu suka jiyo masa karya ba ya shiga tunani yaushe ne Zajlah ta samu keɓewa da makiyansa?. Bai bi takanta ba ya sureta bai zame ko ina ba sai ɗakin mahaifiyarsa bokanya Sharmila ya direta tare da juyo wa a fusace ya bar gidan sarautar.

Nan ne ya zama wajan ɓoyan Gimbiya Zaljah duk shekarar da hakan ƴya kasance sabida hakane take kuɓuta daga wannan gugguwar annoba.


***

Fuskarta ɗauke da matsanancin fushi, tamkar wadda aka aikowa sakon mutuwa take duban dakarun dake zagaye da ita wanda babu komai a jikinsu sai shigar silken yaki baki yana walwali. Kowa ne daga saman kansa akwai hular karfe baka an mata ado da zaiba mai kyau tare da ɗamarar adon wani gunki a rike da mashi. Ta cigaba da zazzare idanu tana muzurai.

"Na rantse da abin bauta bazan ɗauki wannan ba, a haifi ya a a gabana a tafin hannuna tazo ta na neman gaggarata ina karya ne! Abin bauta! Abin bauta!!".

Haka muryarta ta cigaba da amo da amsa kuwa har zuwa lokacin da wasu dakaru suka gurfanar da wata matashiya yar shekaru kimanin goma sha biyu zuwa sha uku a gabanta. Suturarta ta bambanta da tasu sossai doguwar riga ce a jikinta fara mai faɗi an mata adon da koron launi da kuma zaiba mai daukar idanu kanta sanye da wani kambu na sarauta mai ɗaukar idanu gashinta ya zubo baki siɗik da shi tana da idanu manya sossai a kwai kyawu tare da ita duk da karancin shekarunta tana da girman jiki sossai.


A hankali ta sauke idanunta a kan kakkaurar matar wadda sabida muni in a ka ce ka yankata hatta wukar saika ɓoyeta, hancinta kato idanunta kulu-kulu jajjaye kamar idanun ɗan buda a cikin ruwan barkono. Ta sunkuyar da kai,

"Zajlat!".

Bata ɗago ba ta cigaba,

"me kike zuwa yi wajan waɗancan ɓatattun mutanan? Ko kin manta fushin da abar bauta ta yi damu a zuwanki na wancan karon?".

"Kiyi hakuri ya ke Kakata bazan kuma ba".

"Karya ki ke, indai waɗancan mutanan ne ba zaki barsu ba sau nawa kina faɗa?. Ta karasa tare da sunkuyowa ta ɗago fuskarta suna jin numfashin juna,

"ba zaki gane ba amma zan koya miki hankali ku tafi da ita ɗakin azaba!".

Ta faɗa da matsananciyar tsawa mai firgitarwa, kafin kiftawar idanu sun kwasheta sun tafi da ita ta kyalkkyale da dariya tare da ɗaukar tambulan giya dake kusa da ita ta soma kafa kai tana sha tana yi wa kanta kirari.


2


MASARAUTAR SAMBASU


Birnin *SAMBASU* babban birnine dake ɗauke da mutane kimanun miliyan dubu goma. Birnin  kewaye yake  da kayan jin daɗi da more rayuwa, gari ne daya shafe shekaru sama da shekara ɗari da ashirin da tara ana mulki a cikinsa mulki irin na bakin zallunci. Sarkin dake mulkar wannan gari ya kasance takadiri kuma gawurtacan sadauki wanda ake matukar tsoronsa halima asalin sarautar kwacanta ya yi ba gada ba, babu abinda ya tsana a duniya irin musulmi da musulunci.

Asalin Sarkin garin sunansa Sarki Markahu yana da matar aure mai suna Sharmila tare da yara goma sha biyu dukkaninsu maza kuma babu wanda ba gawurtacan sadauki ba cikinsu daga mafarauta sai mayaka yana alfahari dasu sossai. Matarsa kuwa gawurtaciyar matsafiya ce wadda ta amsa sunanta asalinta ɗiya ce ga sarkin sarakunan bokayan garin kafin ya rasu ta haye kujerarsa, Sarki Markahu ya aureta ne sabida ita jaruma ce kuma da taimakonta ya kwaci sarauta yana matukar ji da ita kuma baya tsallake duk abin da ta gindaya masa. Tsanar da ya yi wa musulnci ta shahara matuka hakan yasa bida shawarar mai ɗakinsa ya gidana *GIDAN AZABA* kawai sabida azabtar da musulmi.  Mutanan masarautar Sambusa basu da abin bauta face wani katon taswirar suffar wani gunki ne da aka kera wato JARBUBA. Duk wata bukata tasu idan ba ranar bauta ba sukan kawota ne ga SHARMILA ita kuma ta mikata gareshi ko kuma mutum ya hakura sai ranar bauta wato kowace Talata.


Story continues below

Al adar mutanan Sarki Sharmil shi ne, duk Talata suke halartar ɗakin abin bauta don mika bukatunsu, a irin wannan rana sukan yi shigar data bambanta da shigar kasarsu maza da mata akan sha giya a kuma bada yara jarirai masu ciki da dama kuma kan yi ɓarinsa mudun sun hallata. Hakan yasa masu ciki da dama kan kaƴracewa ɗakin bauta a asurce domin mudun Sarki ya samu labari to kuwa hukuncin kissa ne ga matar mijin kuwa korarsa ake daga garin. Yan mata kan yi shiga ta fitar da tsuraici wanda da damarsu a ɗakunan samari suke kwana, da dare kuma akan kunna wuta a tsakiyar gari a zagayeta ana tikar rawa har zuwa wayewar gari.


Asalin suffar gunki JARBUBA ta mahaifin  Sharmila ce wato Boka Jarbuba bayan mutuwarsa suka sassaka suke bauta masa aka yi katari wani aljani cikin hadimansa ya shiga jikin gunki yana kara dulmiyar da su.


*GIDAN AZABA*


Babban waje ne  dake ɗauke da ɗakuna a kala sama da guda ɗari da hamsin, kowa ne ɗauki nau in azabar da ake yi wa laifi daban daban cikin kowane ɗaki akwai ɗakuna guda huɗu a ciki masu tsaninin duhu sai itacen da suke ajiyewa wanda ya zamo shi ne abun haske ko wane ɗaki. A ciki akwai ɓangaran mata dama maza, sai kuma banɗakuna wanda suka kasance a cikin kowa ne ɗaki a kwai. Akwai   babbar magirkar abincin masu laifi wadda keda ma aikata sama da mutun dubu suna aikin shige da ficen rarraba abinci.

Sai da Sarki Markahu ya shafe shekaru tamanin yana mulki sannan matarsa ta ci amanarsa ta kashe shi ta hanyar sa masa guba a abinci ya mutu, bayan kwana arba in ta ɗora babban ɗanta mai suna *SHAMFALI* kwanansa goma ƴya mutu aka ɗora kaninsa  shi ma haka a haka sai da kaf yaranta suka kare ciki shekara goma ya rage saura autansu mai kimanin shekaru ashirin da tara wanda ya kasance sadauki na gaske. Hankalinta ba karamin ta shi ya yi ba da wannan al ammari nan da nan ta shirya ta shiga halwar tsafi wanda sai da ta shafe kwana arba in cif sannan ta fito cike da tashin hankali domin abin da ta yo karo dashi babban al ammari ne.


MASARAUTAR SAMUWARU


Daga hagu cikin birnin akwai wasu mutane cikin wani ɗan karamin gari mai suna *SAMUWARU*. Garin samuwaru mazauna cikinsa sun kasance suna bautar JARBUBA ne kamar yadda mazauna *SAMBUSA* ke bautawa *JARBUBA* shi dai wannan abin bauta duk shekara ka ida yana shan jinin ma abota addinin musulci kimanin mutu ɗari da goma sha biyu da sunan *SADAUKARWA*. Sarkin dake shugabantar wannam gari aminine ga Sarki Markahu matansa huɗu ya tsufa sossai duk da Markahu ya girmeshi bai taɓa haihuwa ba sai shekarar da aka haifawa Markahu autan ɗansa wato Sharmil a shekarar matarsa ta haihu aka sawa yaron Sharbusa. Sharmil da Sharbusa sun taso jarumain kuma aminan juna har zuwa mutuwar mahaifin Sharbusa ya ɗare karagar mulkin mahaifinsa yana shimfiɗa mulki cike da umarnin Sarki Markahu har zuwa mutuwarsa. Komai nasu irin na mutanan Sarki Markahu ne har shiga zuwa horan yaki da cima. A shkekarar Sharbusa ya yi aure ya auri yar sarkin yakin garinsu, wata tara ta haifi ɗa Namiji ya ci sunan *SHAM UNU* shekara biyar tsakani Sarki Markahu ya mutu. Yaran ya taso da tsagwaran jarumta sossai.


GARIN BAITUL NUR

Daga damansu kimanin tafiya kilomita ɗari da saba in, akwai karamin kyauye wanda ya kasance mutanan cikinsa rumawa ne, kyakkyawa dasu masu tsayi da kirar sadaukantaka ma abota zama a wannan kyauye mai suna *BAITUL NUR* ma biya addinin musulunci ne. Masu tsantsani tare da bautar Allah, sukan fita gari-gari don yaɗa addinnin Allah. Shugabansu mai suna Malam Tahir yana da mace ɗaya da yara tagwaye guda biyu maza, Hassan da Hussaini sai mahaifiyarsu Khadijatul Kubrah. A kwai alakar siye da siyarwa tsakaninsu da mutanan Sarki Sharbusa da kuma kuma na Sarki Sharmil kafin daga bisani su haramta hakan sabida yadda suke yi wa yaransu mata aika-aika kuma i sun kai kara babu wani kwakkwaran matakin ɗauka.


Garin Baitul nur garine da ake shimfiɗa adalci kowa na jin daɗin yadda suke zamansu,babutsangwama bare kyara babban tashin hankalinsu shi ne cikar shekarar garin dake makwabtaka dasu wato masarautu guda biyu. Domin suna asarar rayukan mutaneda daa kama daga kan  yaransu musamman jarirai sai da takai ta kawo ko cikine da mace in dai ya shigo shekarar cikar shekara sai ta yi ɓarinsa sabida mugun tsafinsu da suke aikowa da shi. Malam Tahir ne ya yi tsaye wajan kauda wannan cuta da karfin addu a hakan yasa sai dai su dinga farautarsu idan shekarar ta tunkaro sabida basu da damar shiga garin basa samun nasara sabida karfin addu'a . Malam Tahir babban Malamine dake da almajirai sama da mutum ɗari, bayan karatu yana basu horon yaki ta fanni daban-daban kasancewar mahaifinsa shi ne asalin Sarkin yakin garinsu karɓar addinin musulunci yasa aka kashe shi su kuma suka samu suka tsere suka kafa karamin gari. Bayan haka suna yin sana o i na hannu da dama, noma da kira da kuma kiwo a cikinsu ma akwai mafarauta da maɗinka. Malam Tahir gwanine kuma hafizin alkur ani mai ruko da addinni sossai ya sha kawo wa birane da  dama dake makwaftaka dasu  tallar addininsa suna watsa masa kasa a ido, suna matukar jin haushinsa gashi kuma sun rasa yadda zasu yi da shi sun sha kai masa hari basa samunsa ko kuma su iske garin ya zama daji ko ruwa haka suke hakura su juya. Kullum muradinsu shi ne ta ya ya zasu kauda shi a doron kasa su mulki mutanansa?.


Tunda Sharmila ta fito daga halwa babu wanda ta sake yi wa magana tsayin kwana ki goma lamarin daya dugunzuma hankalin Sharmil sossai kenan yasan tabbas a kwai matsala gaggaruma, sai ranar kwana na sha biyu ne ta kaɗaice dashi cikin sirri fuskarta babu annuri ta dube shi,
“Yaƙkai Sharmil ka sani abin bauta JARBUBA ya nemi mu yi masa gaggarumar SADAUKARWAƁwadda zai yi alfahari da ita, ba komai ya bukata ba face yana son ya sha jinnin wancan mai taurin kan na birinin *BAITUL NUR*”.
Koda ta zauna a zancanta, sai gabansa ya yanke ya faɗi, kansa ya sara idanunsa suka yi jajjur kamar gauta jijjiyoyin kansa suka mummurɗe suka ɗago raɗa-raɗa ya dinga huci kamar mesa.
“Ya kike gani ya ke mahaifiya ta?”.
.
ƘKunnuwansa ta rankwafa ta yi masa raɗa koda ta zauna a zancenta bai san lokacin da ya takarkare yana ɓaɓɓaka dariya ba, ita ma ta soma kyalkkyalawa tana mai taya shi. Hakan yasa ɗakin ya dinga girgiza daga bisan ta tsagaita tare da daka masa tsawa ya daina. A ranar an yi busha-busha da yawa an sha giya an yi wa kananan yara fyaɗe da yawa da sunan murna tun daga ranar suka soma shirin tunkarar birnin baitul nur da mutanansa. Ya rage saura kwanaki bakwai su je, suka aika masa da takarda ɗauke da bayanin suna son ƙshiga musulunci, lokacin da ɗan aiken ya iske shi sun fito sallahr la asar ne suna zaune a kofar bukarsa yana yi musu wa’azi ya karaso ya isar da sakon, Hassan lokacin yana da shekaru goma shi ya mike ya karantawa mahaifinsa takardar kasancewar Allah ya yi masa baiwar jin yare kala-kala ciki kuwa hadda larabci. Bayan ya gama jawabin ne Malam ya yi shiru, wani dattijo wanda ya fisu yawan shekaru ya numfasa tare da furta,
“bamu yarda ba yaudara ce kawai Malam!”.
Murmushi ya yi masa ya ce,
“babu komai Baba, Allah ne kaɗai yasan gaskiya abun alfaharine ace birni kamar wannan zasu karɓi addinin musulunci”.
Take yasa aka rubuta musu martani kan cewar suna maraba da su, ɗan aike kuwa aka haɗa masa sha tara ta arziki ya koma garinsu. Tafiya mai tsayi ya yi sai cikin dare ya isa gari ya samu fada dankam shi ake jira bai wata-wata ba ya bayyana musu komai sun ji daɗin yadda Malam Tahir ya amince sossai. Bayan ƙkwanaki goma da faruwar hakan su Sharmil suka karɓi addinin Musulunci sai da Malam Tahir ya shafe kwanaki ashirin yana koya musu ibada da sauran abubuwan da suka danganci musulunci sannan suka yi sallama ya dawo gida. Matarsa Khadija kwata-kwata ta kasa yarda da abinda suke faɗa kawai dai ta zuba idanune sabida wasu mugayan mafarkai take marasa kan kyau.
*** *** ***
Kwanaki ɗari da ashirin da musuluntarsu, suka aiko musu da katin gayyata na murnar cika kwanakinsu da musulunta. Malam ya yi jim yana tunanin wannan sabuwar bidi’a amma daya tuna basu gama sannin addinin ba sai yasa a ka shirya tafiya da zumar zai daɗa wayar musu da kai. Ana gobe zasu tafi ne da dare Khadija ta sameshi da batun da yake damunta,
“Malam ina hango matsala a tafiyarmu da waɗanan mutane, mai zai hana kaki amsa wannan gayyata tasu”.
Sai da ya dade sannan ya dubeta,
“Khadija kyautatta zato abune mai muhimmanci kuma duk abin da ya faru da bawa kaddararsa ce bazai kauce mata ba, imani da cewar komai kika ya samu bawa daga ƴubangiji ne abin alfahari ne garemu ace mun jagoranci wata runduna masu yawa zuwa tafarkin gaskiya”.
Koda ya zauna a zancansa jikinta ƴya yi matukar sanyi harta gaza bakin magana ya numfasa,
“ki kasance mai addu a garemu ki zamo mai karfafa guiwa kamar mai sunanki mana, kinsan fa ta yi wa addinnin Allah hidima fiye da tunaninki Sayyada Khadijatul Kubra ita ce wadda ta hudimtawa addinni da dukiyarta da lafiyarta kuma alhamdullilahi tabbas ta yi rawar gani”.
“Malam ya kayi shiru ka cigaba mana da yi min tarihinta ai zan karu”. Cikin murmushi ya ce,
“ki bari sai ubangiji ya bani ikon dawowa”.
Saida suka raba dare suna hira mai tsayi basu gushe ba har ketowar alfijir daga bisani suka yi alwala tare da yin salollinsu suka zauna har zuwa huɗowar rana wato gari ya yi haske sossai. Ayarin da Malam ya zaɓa a tafiyar mutum goma sha biyu ne wanda suka kasance jarumai na gaske sai yaransa guda biyu Alhassan da Alhussain amma kash lokacin da za a fita sama da kasa suka nemi shi suka rasa tilas aka yi tafiyar babu shi.
Kwana ɗaya ɗa yini ya kaisu garin, sai dai tun daga bakin ganuwar garin suka cika da tsantsar mamaki ba komai  yaja hakan ba face ganin kofar garin an saketa an yi katuwa ta bakin karfe a jikinta an yi suffar abin bautarsu JARBUBA da kuma hotan sarkinsu MARKAHU. Suna shiga kuma kofar garin suka riski dakaru sama da mutum ɗari biyar ko wane sanye da silke baki da kuma dogayan masu a hannunwansu, jikkunansu sun yi sanyi matuka ga mamakinsu maraba aka yi musu aka wuce da su cikin gidan sarauta wanda aketa kiɗe-kiɗe shi dai Mallam Tahir bai magana ba amma abun yana sossa ransa a haka suka isa har masaukinsu bayan sun huta sun rama sallolinsu aka kawo musu abinci kala-kala babu wanda ya yi yunkurin ci. Sharmil ya dubesu cike da damuwa,
“ya kai babban Malami ya an kawo abinci amma ka kauda kai?”.
Koda ya zauna a batunsa sai ya yi murmushi,
“naga kuna wasu ɗabi u wanda suka saɓawa addinnin da kuka karɓa ya kai Shamsudeen”.
Cikin hanzari ya tareshi “haryanzu bamu gama sanin addninku ba sai an mana afuwa”.
Kur ya yi masa a ido daga bisani ya yi basmallah ya soma cin abincinsa suma mabiyansa suka aikata hakan tas suka cinye abinci karfin basmallar da suka yi ya hana gubar tasiri a kansu lamarin daya dugunzuma hankalin Sharmil kenan haka ma abincin dare babu abinda gubar ta yi musu wannan yasa suka haɗa dakaru ana gobe zasu tafi a daran suka far musu bayan dogon artabu suka yi nasarar kashe Malam da mutanansa amma basu sami ganin Hassan ba wanda ya shiga cikin gari ne yana zazzagawa.
Kafin kace kwabo gari ya cika da raye-raye dai-dai wannan lokacin Hassan ya dawo ba karamin tashin hankali ƴya shiga ba duk da yana da karancin shekaru a lokacin shekarunsa goma amma jarumi ne, nan ya soma yunkurin guduwa amma kash Sharmil yasa aka kamashi aka kai shi gidan azaba aka rufeshi a washegari ya haye karagara mulki bayan sun ba wa Jarbuba jinnin aka ci aka sha aka yi wadaka da giya.
***
  Acan gida kuwa bayan tafiyar su Malam da sa a huɗu Hussain ya dawo ɗauke da katuwar barewar da ya harbo mahaifiyarsa ta tare shi da faɗa buɗar bakinsa sai cewa ya yi,
“yake Ummina tafiyar ce bata kwantamin ba”.
Koda ya zauna a zancansa sai idanunta suka ciko da hawaye basu gushe ba gar saida ta kasance tana mai kuka, da kyar ya lallasheta kwana huɗu suka wuce basu dawo ba hankalin mazauna garin ya yi masifar tashi aranar kwana na huɗu ne suka shirya tafiya don gano ko lafiya amma Hussain ya dage kan shi zai je. Tafiyarsa da sa a biyu mahaifiyarsa ta tafi farauta, bata wuce sa a ɗaya da tafiya ba dakarun Sarki Sharmil suka hayo garin suka far musu babu wanda suka bari sai wata kyakkyawar matashiya da bata wuce shekara sha takwas ba a bisa umarnin Sharmil ita ma suka barta. Khadija bata dawo ba sai wucewar sa a biyar anan ta riski gawawwaki fafful wannan ya tabbatar mata an kashe mata maigidanta da yaronta bata gushe ba tana kuka mai cin rai kwatsam Hussain ƴya bayyana a gabanta yana zubda hawaye. Ya gurfana yana rike da hannunta.
“Yake Ummina ina cikin tafiya ne na riski ihun makiya Allah tare da hanninniyar dawakansu hakan yasa na samu waje na ƙlaɓe, ina kallon sun nufo birninmu nasan babu alkhairi tare da su ina bin bayansu har zuwa nan cikin tsarewar Allah amma kash banda karfin tunkararsu a yanzu sun kashe kowa Zahra ɗiyar Liman kawai suka tafi da ita wai zata zamo matar Sarkinsu!”.
Koda ya kawo karshe a batunsa sai ta fashe da matsanancin kuka,
“kaico makiya Allah”.
Shi ne abin da take iya furtawa, basu gushe ba suka tattara manyan littatafan Malam suka hau rakumi ɗaya da guzuri suka nannaɗe fuskokinsu suka rufe sai idanunsu ake gani suka nausa cikin daji gabas da garinsu. A hanya ne suka tsinci kanwar Zahra mai suna Aisha yar kimanin shekaru biyar suka tafi da ita. A ranar da dakarun Sarki Sharmil suka je da Zahra a ranar ya aureta ta zama matarsa ya cigaba da gudanar da bakin mulki son ransa. Sai dai babban tashin hankalinsu duk randa sati ya zagayo na kashe Malam Tahir garin na afkawa wata irin mummunar masifa wadda kwata-kwata duk iya bincikensu sun rasa maganinta.
Ba komai bane face wata irin gugguwa dake tashi tana hallaka mutane kuma bayan ta lafa akan rasa ruwa a garin tsayin kwana uku wanda wasu in basu mutu a guggurwa sukann rasa ransu a matsananciyar kishirwa mai soye makwogwaro.Bokanya Sharmila ita ta shiga ta fita wajan bincike da gano matsalar karshe suka samu nasarar kauda ita bayan sun sadaukar da jinnin Hassan hakan yasa sai shekara shekara annobar take tashi.
Sarki Sharmil yana tsananin san matarsa Zarha baya son abinda zai ɓata mata rai, hakanya asasa tsanarta a zuciyar bokanya Sharmila tasoma yunkurin hallakata amma bata samunasara saboda Zahra bata bar ibadarta ba. Hakan ya zamo barazana ga gunki JARBUBA kullum cikin gargaɗinsu yake tare da nuna musu spn shan jinin ahra amma hakan ya gaggara.
Shekara ɗaya da auran Sarki Sharmil aka haifa masa ɗa ɗaya mai suna Zajlat, wadda mahaifiyarta ce ta nemi asa mata sunan babu musu mahaifinta ya amince bokanya Sharmila ta fusata sossai domin sunanta taso asaka mata. Cikin kankanin lokaci ta soma yunkurin kauda Zahra sabida abin bautarsu ya bata tabbacin yin nasara akanta sabida bata da damar yin ibada.
Allah bai basu nasara ba,bayan shekara ɗaya da haihuwar Zajlat mahaifiyarta Zahra ta rasa rayuwarta hakan yasa sarki ya kwalafa rai kanta yana matukar sonta, a shekarar mahaifiyarsa ta samo masa wata matar wadda ta kasance jinninn sarauta ce can gabashinsu ya aura.
Matar tasa mai suna Samaratu muguwa ce bata da imani ko kaɗan ita takekara ɗoa sarki Sharml a kan akidarsa takin musulunci. Shekarata ɗaya ta haifa masa yara tagwaye guda biyu, sai da ya zama duk shekara take haihuwa tsayin shekara goma amma duk randa aka yi gugguwar annoba to kuwa takan rasa ɗanta ɗaya amma abun da ya ɗaure musu kau gugguwar bata taɓa ɗaukar Zajlat ba, lamarin daya haddasa kiyyayarta a zuciyar Samaratu kenan matar mahaifinta take kokarin hallakata ta kowa ce hanya.
Zajlaht ta taso yarinya mai wayau da saurin shiga rai ga saurin rike abu, tana da som bincikeda zaga arurruwa amma mahaifinta baya barinta sabida gargaɗi da bokanya Sharmila ke masa a kodayaushe kan kula da ita. A wata rana Sarki ya shirya mata fita randagi a tare da ita dakaru goma ne, lokacin tana da shekara goma sha huɗu a duniya a wannan tafiya ya shirya ta ne don zuwa ta gaishe da amininsa Sarki Sharbusa amma sai Zajlat ta ɗauke hanya bisa umarnin data bawa umarnin da ta bawa dakarunta, koda wasa ta tsani zuwa MASARAUTAR SAMUWARU sabida mutanan garin basa tausayin matansu ko kaɗan har sunfi masarautarsu bakin mulki tana yawan kawowa mahaifinta korafi kan hakan amma ba wani mataki da ya ke ɗauka. Babbar damuwarta yadda karfi da ya ji Yarima  Sham’ unu ke sa a ɗauko masa matasan yan mata ya yi lallata da su da sanin mahaifinsa kuma babu wanda yake da karfin ikon tsawatar masa, sunyi nisa da garinsu sossai suka riski kansu a wata alkarya mai cike da yayyan itattuwa da buka guda biyu. Zaljaht ta yi umarni ga dakaru kan tana so ta shiga babu musu suka amince da umarninta su kansu sun yi mamaki kuma al’amarin ya burgesu har suka soma sha’awar shiga wannan waje harma suna ayyana yin rayuwa a cikinsa.+

Story continues below

4

Lokacin da suka shiga wajan sai suka cika da mamaki ganin koramu da shuke-shuke. Daga gefe ga wani matashi mai sufar sadaukantaka sunkuye a gefansa matane guda biyu suna lullube da farin mayani ba a ganin komai sai fuskarsu Zaljat ta zubamusu idanu tana tunanin mai suke yi ta rasa mai bata amsa?.

Basu kai rabin sa a da tsayuwa ba, suka juyo zuba garesu namijin mai kirar sadaukantaka ya furta,
"ya ku waɗanan mutane meke tafe da ku?".
Koda ya yi shiru sai dakaru biyu suka nufi hanyar da wata itaciya take babu magana suka hau tsinka, lamarin daya fusatashi kenan ya daka musu tsawa take jijjiyoyin hannuwansa suka murɗe suka kumbura har tufafinsa suka soma yayyagewa cikin fushi ya ɗaga hannnunsa ya gabzawa badakare ɗaya naushi take ya faɗi sumamme koda ganin hakan sai wasu mutum goma suka yo kansa take ya dinga watsi dasu kamar kararre na shawagi kan iska cikin dakika kadan ya gama dasu. Ganin hakan wasu suka sake kukan kura suka yi kansa take Zajlat ta daka musu tsawa suka dakata ta dubeshi,
"ya kai wannan ma abocin karfi wanene kai, kuma menene addininnka?".
"Ni bawan Allah ne, kuma addinni na addinnin musulunci ne".
Koda ya zauna a zancansa sai ta yi jim tana mamaki, ta ɗauke idanunta daga kan dakarunta da suke kwance magashiyan cikin raunka ta furta,
"sunan Gimbiya Zajlat Sharmil bin Markah ni yar sarki Sharmil ce, na futo zagaye ne na hangeku alkaryarku ta birgeni shi ne na shigo don ɗebe kewa".
Koda ta zauna a zancanta sai ya yi murmushi ya basu dama suka ɗibi abinda suke bukata suka yi nufin fita har sun kai bakin kofa ta juyo tana mai tambayar sunayansu kamar ba zai tanka ba ya dubeta,
"sunana Alhussain ibn Tahir wannan kanwata ce Zahra wannan kuma mahaifiyata ce".
   Koda ya zauna a batunsa take dakarunta suka tsorata matuka, harda masu fitsarin wahala juyawa ta yi suka fice daga wajan. Sinyi nisa sossai ta dubi amintacan badakaranta,
"ya kai Lamrisu ina dalilin tsoratar ku yayin da kuka ji sunan wannan jarumi?".
Koda ta zauna a tambayarta sai ya buɗa baki ya bayyana mata waye Alhussain lokacin daya kare a batunsa saita fashe da kuka tana mai la antar mahaifinta da mummunar manufarsa.
***
Tun daga wannan lokacin Zajlat ta soma zuwa tana kaiwa Alhusain ziyara, sun shaku da su Aisha sossai mahaifinta bai taɓa sanin abin da ya ke faruwa ba sabida ta gargaɗi dakarun rakiyarta kan duk wanda ya tona zata kashe shi.
     A haka aka ɗauki lokaci tana zuwa wajan, mu amalasu da yadda suke bautarsu ya burgeta sossai wata rana ta kawo musu ziyara ta samu suna sallah bayansun idar ta kasa jurewa ta tambayi Alhussain,
"ya kai wanna jarumi me nene wannan kuke yi haka?".
   "Ya ke Gimbiya wannan ita ce ibadat wato sallah".
Koda ya zauna a batunsa sai ta dubeshi da alamun mamaki,
"Sallah? Ya kai wannan jarumi mecece sallah kuma menene dalilinku na yinta?".

Jim ya yi daga bisani ya dubeta.
   "Gimbiya sallah da kike gani aba ce mai matukar muhimmanci ga musulmi. Ita Daya ce daga cikin rukunnan musulunci guda biyar, wanda Allah maɗuakakin sarki ya wajabtata guda hamsin a kan bayinsa yayin da Manzan Allah S.A.W yaje mi'iraaji (wato Sama) ya karɓo ta yayi ta neman ubangiji da ya ragemana ita har aka rageta zuwa guda biyar.
    Kamar yadda take a yau saboda tausayin Manzan Allah S.A.W. Kuma Manzan Allah S.A.W ya ce,
"Itace farkon abinda za'ayi wa bawa sakamako (hisabi) da ita ranar k'iyama. Idan ta yi kyau dukkan sauran aiki zasu yi kyau bawa ya samu tsira kuma idan ta yi muni to dukkan sauran kafin Sallar da bawa yake yi ta sami karɓuwa sai idan tadace da yadda Manzan Allah S.A.W ya yi ta kuma ya karantar domin fadar Ma'aiki "Kuyi sallah kamar yadda kuka ina yin Sallah".
      Sannan an wajabta yinta acikin jama'a (wato Jam'i a masallaci ga maza mata kuma suyi ta a gida a ɗakunansu). Kuma wanda duk yabarta to yabar musulunci kamar yadda ma'aiki tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi yace " Alkawarin dake tsakaninmu dasu shi ne Sallah duk wanda yabarta to ya kafirta".

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “An gina musulunci a bisa ginshiqai guda biyar, shaida wa babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, kuma Muhammad bawansa ne Manzonsa ne, da tsayar da sallah…..” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] .

Story continues below

Manzon Allah (S.A.W) ya ce,
“Mafi falalar ayyuka sallah a farkon lokacinta” [ Tirmizi ne ya rawaito shi] .
    Annabi (S.A.W) ya ce, “hakikaa tsakanin mutum da shirka da kafirci barin sallah” [Muslim ne ya rawaito shi] .
    Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku bani labari da ace akwai qorama a qofar xayanku, yana wanka a cikinta a kowace rana sau biyar, shin wani abu zai ragu na dattinsa, sai suka ce “Babu wani dattinsa da zai ragu” sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Hakanan misalin salloli biyar suke, Allah yana goge zunubai da su” [Bukhari ne da Muslim ne suka rawaito shi]".

Koda yazauna a batunsa sai ta dubeshi cikin mamaki ta furta.
"Ya kai wannan jarumi me yasa mu bama yi, kenan muma mun kafurta?".

5

"Mu me yasa bama yi?".
"Ba kwa bautawa ubangiji waninsa kuke bautawa....".
Take dakaru biyar suka zuciya suka zuciya suka saken yo kansa a fusace ya mike ya buɗe hannunwansa wasu murɗa-murɗan jijjiyoyi ne suka bayyana a dantsan hannunsa har saida tufaffinsa suka soma tsattsagewa ya dunkule hannu ya kai musu naushi take ya sumar da mutane shida huɗun suka yi baya suna makyarkyarta sai abin ya birge Zajlaht ta gyara zamanta a kan doki,
"ya kai wannan ma abocin karfi kaimin bayanin wannan kalma yadda zan fahimta".
Ya zuba mata idanu yana kisima shekarunta bazata kai sa ar  Aisha ba amma a kiyasinsa Aishan ta girmeta sai dai girman jiki sai ya sami kansa da jin wani nishaɗi mara tushe ya dubeta,
""Hakkin salla shi ne ka san cewa ita salla neman kusaci ce da Allah Mai Girma da Daukaka, kuma yayin da kake yinta kana tsayuwa ne gaban Allah Mai Girma da Daukaka. Idan ka san haka to zaka yi tsayuwa irin ta makaskancin bawa mai tsammani, mai tsoro da kaskantar da kai, mai natsuwa domin girmama wanda yake tsaye a gabansa (wato Allah), kuma zaka fustantar da zuciyarka gareta sannan zaka kiyaye iyakokinta ka bata hakkokinta"Karkata zuwa ga ibada lamari ne da ya samo asali daga fidirar mutum wato dabi'ar da Allah ya halicce shi da ita tun fil azal. Wasu mutane da dama  wurare sun kasu daban daban dan Adam ya kasance yana bautawa ababen bauta daban daban, ko dai Ubangiji makadaici ko kuma gumaka da halittun da suke cikin sararin samaniya kamar rana da wata da taurari. Wannan yana nuna mana cewa dan Adam, bisa dabi'arsa, yana bukatar abin bauta kuma Alkur'ani mai girma ya yi baiyana cewa mutane gaba dayansu suna tareda wannan dabi'a kuma an haliccesu ne da ita. Allah madaukakin sarki yana cewa: "Sannan kuma ka tsayar da fuskar ka ga addini ɗoɗar, wannan addini dabi'a ce da Allah ya halicci mutane a kanta, ba wani canji ga halittar Allah. Wannan shi ne addinin mikakke, sai dai kuma yawaicin mutane basu san haka ba." Suratu Rum aya ta 30.Manufar addinin Musulunci shi ne mutane su gane wane ne abin bauta na gaskiya, kuma su san shi gwargwadon iko, ta yadda zasu biya bukatar su ta yin bauta ba tareda sun fada tarkon ababen bauta na boge ba.
Addinin Musulunci yana sifanta Ubangiji wanda ya cancanci ibada da cewa shi rayayye ne, mai dukkan daukaka, mai hikima, masani, mai ji da gani da kudura. Shi ne mai gudanarda lamuran dukkan talikai kuma shi ne mai taimakon bawa idan ya fada halin kaka ni kayi. Addinin Musulunci ya baiyana cewa hanyar da bawa zai iya kulla alaka da mahaliccinsa ita ce ya yi masa ibada, wanda kuma salla ce mafi girma daga cikin ibadu. Mafificin tafarkin da zai sada mutum da Allah shi ne salla, domin salla wata irin ibada ce mai game dukkan sassan mutum, jikinsa da tunaninsa da kuma ruhinsa. Dukkan wadannan suna gurfana gaban girman Allah, tareda hushu'i da kankan da kai. Manzon rahama Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) yana cewa: "Ko wani abu yana da fuska, fuskar addini ita ce salla, saboda haka ku yi kokarin kiyayeta." A wani hadisi kuma Ma'aikin Allah yana cewa salla ita ce ginshikin addini, duk wanda ya tsai da ita ya tsai da addini, duk kuma wanda ya wulakanta to ya wulakanta addini.
Wato idan mutum ya kasa tsai da salla alakarsa da Ubangiji zata yi rauni, idan kuwa alakar mutum da mahaliccinsa bata da karfi to imaninsa zai raunana, shi kuwa raunin imani yana sa sauran aiyukan ibada su kasa bayar da tasirin da suke da shi. Salla ce take tallafawa sauran ibadu take basu kima, domin ita salla ta kunshi aiki da fadi da tsarkin niya, ta yadda idan mutum ya doge kanta dare da rana zata dasa masa son kyautatawa a zuciyarsa, sannan kuma ta tsarkake masa ruhinsa.Imam Sajjad (a.s.) yana kiran masallata da su kula saboda girman wanda suke tsayawa gaba gare shi, sannan kuma su yi kokarin amfana da falalar da Allah (swt) yake lullube mai salla da ita, saboda su kyautata aiyukansu na kwarai su kuma bar ta aikin assha. Imam din yana fadakar da mu cewa idan mutum bai yi sallarsa kamar yadda ya kamata ba, kuma yayinda yake tsaye gaban Ubangiji masani mai iko, bai ji kaskancin kansa ba, sallarsa ba ta wuce sunkuyawa da tsayuwa ba, wanda kuma ba shi da wani tasiri a rayuwar mutum ta yau da kullum. Sai dai ya kamata mu sani cewa mai salla yana kula da hushu'i da tawalu'u da kankan da kai gaba ga Ubangiji yayin salla ne saboda ya fahimci girman Allah mahalicci, amma ba wai Allah yana bukatan hakan ba, domin kuwa shi Ubangiji baya bukatan komai daga bayinsa. Yayin da mutum ya fahimci cewa a cikin salla, yana magana ne da Allah mamallakin dukkan iko da hikima, to zai sami dammar sha daga tafkin falalar Ubangiji (swt). Saboda haka ne ruhin salla da kashin bayanta shi ne tara hankali da natsuwar zuciya yayin munajati da Ubangiji.

Tasirin wannan tara hankali a lokacin da mutum yake ibada shi ne samun kariya daga aikata munanan aiyuka da kuma samun karfin aikata kyawawa. Allah madaukakin sarki ya baiyana wannan lamari a cikin littafinsa inda yake cewa: "Ka karanta abinda ake yo maka wahayinsa na Alkur'ani, ka kuma tsai da salla; hakika salla tana hana alfasha da kuma abin ki. Kuma hakika ambaton Allah shi ne mafi girma, kuma Allah yana sane da abin da kuke aikatawa." Suratul Ankabut aya ta 45."
Koda ya zauna a zancansa sai jikinsu gaba ɗaya ya yi sanyi bakinsu ya yi nauyi zuciyarsu ta cika da imani, take suka nemi karin haske kan addinin musulunci babu jimawa ya yi musu basu gushe ba dukansu su goma sha ɗayan suka nemi shiga addinin musulunci, take ya biya musu kalma shahada suka maimaita, ya yi musu bayanin muhimman abubuwa kan addinni suka yi masa godiya Zaljat ce ta cire sarkar wuyanta wadda ta kasance ta zinare ta mika masa ya ki karɓa ya girgiza kai,
"ya na baka abu ka ki karɓa".
"Kin fini bukata yake ma abociyar rauni".
Jinjina kai ta yi suka juya suka tafi.
   Tun daga wannan lokaci Zajlata ta karɓiadddinin musulunci, haskensa ya ratsata take gudaar dashi a asurce a gidan mahaifinta cikin fadarta kuma cikin kariyar ubangiji babu wanda ya taɓa fuskanta har mahaifinta. Haka Zaljah ta kasance tsayin shekara ɗaya tana ziyartar Alhussain sun saba sossai da dattijuwa Khadija da kuma Aisha haka Alhussain tare da amintattun dakarunta sunyi zurfi cikin sannin addinnin Allah tare da sannin ilmi mai yawa musamman ita tamkar wata Malama haka ta kasance cikin dakarun. Mahaifinta bai san badakalar da ake yi ba sai a wata safiya da bokanya Sharmila ta fito cikin halwar tsafi cikin matsanancin tashin hankali, ga wani ammo mai karfi yana fitowa daga ɗakin abin bauta JARBUBAmai barazanar fasa kunnuwa, fuskata bau annuri ko kaɗan  ta shigo kamar an jehota. A lokacin  bai fi sa a biyar da tafiyar Zaljay rangadi ba.

A ɓangare guda bayan fitarsu Zajlat da sa a biyu sai garin ya haɗe ya yi wani irin ja mai ban mammaki ga wata kara da take tashi mai firgitarwa nan mutan garin suka soma guje-guje da iface-iface lamarin daya ɗaga hankalin sarki Sharmil kenan ya soma tunanin in da Zajlat ta ke. Harya janyo mudubin tsafinsa zai fara dubawa sai ga bokanya Sharmila kamar an jehota tana huci idanunta kamar zasu zazzago sai huci take bakinta na fida wani irin tururi mai koran launi.

Lokacin da bokanya Sharmila ta shigo faɗar ɗanta Sarki Sharmil bin Markahu ba karamin kaɗuwa ya yi ba, domin a iya saninsa ta shiga halwar zafinta kuma kwana casa in take sai gata ta fito a kwana goma yasan tabbas da walakin. Gaba ɗaya aka mike alamun girmammawa ta dumfaro wajan tana hucci idanunta sun yi gwalo-gwalo sun yi ja ga wani hayakin sihiri da ya ke fita ta kofoffin kunnuwanta da kafar sadarwar numfashinta.
Zama ta yi tare da takarkarewa ta kwarma ihun da ya hadasawa masu nakuda haihuwa, masu karamin ciki kuwa suka hau yin ɓarin da basu shirya ba daga bisani ta kyalkkyale da wata shu umar dariya irin ta takadirai makiya Allah dariya mai cike da kekashe zuciyar imani. A fusace ta juyo ta daka masa tsawa,
"kaicon ka ya kai Sharmil, ka yi wauta mai girma wadda zata kai kai ga nadama!".
Koda ta zauna a zancenta sai ya ɗago a razane yana dubanta fuskarsa cike da tsananin mamakin furucinta,
"yake Ummina ina dalilinki na yin wannan batu?".
"Ina Zajlat ta ke?".
Ta faɗa murya a kausashe, sai ya dirirrice ya hau kame-kame ta daka masa tsawa,
"ina take!".
"Ta ta fi faɗar Sarki Sharbusa".
Koda ya kai karshe a batunsa sai ta wanka masa mari, lamarin daya girgiza ɗaukacin fadawansa kennan bata tanka ba ta yi nuni da hannunta sai ga wani haske mai launin rawaya ya bayyana a jikin bango wani duhu ya rufeshi daga bisani kuma ya yi haske, tiryan-tiryan sai ga farkon zuwan Zajlat wajan da kuma yadda komai ya gudana. Sai ya ɗauke wani ƴya kawo sai ga inda ta dinga kai musu ziyara duk fitar da zata yi harda wajan koya mata karatu take ya kwala kara yana gurnani kamar wani tsohon zaki.
"Yake Ummina ya aka yi hakan ya faru?".
Kallon data watsa masa ne ya sa ya yi shiru daga nan ta dinga zazzaga faɗa fadar ta yi tsit, sai da ya tabbatar ta gama sannan ya buɗe baki ya yi magana.
"Ya ke Ummina yanzu menene abin yi?".
Koda ta ji batunsa sai ta kyalkkyale da dariya ta mike ta yi tafiyar rabin sa a sannan ta juyo,
"zamu hallaka waɗanan mabiya addinni domin fanshe fushin abin bauta, zamu bada jinninsu su sha".
Koda ta kai karshe sai ta sake nuni hotan su Alhussain ya bayyana, koda ya yi arba da hotan idonsa ya sauka kan Aisha kanwar Zahra take gaban Sarki Sharmil ya faɗi sabida karo da ya ƴyi da fuskarta take fuskar tsohuwar matarsa ta faɗo masa sai kuma ya rikice yadda ya gansu jere da Zajlat tamkar wasu tagwaye kafin ya yi wani yunkuri bokayan Sharmila ta ɗauke hotan tana ɓaɓɓaka dariya.
Gaba ɗaya gumi ya gama jikashi, hannunta ta runtse katamau tana karanta wasu dalamusan zafi take faɗar ta fara girgixa cikin gari aka soma iface-iface da guje-guje bata gushe ba wasu manyan hallitu masu kama da ɓatoyi suka dinga bayyana ta karkashin kasa, girman hallitun ya kai girman bishiyar kuka katuwa suna da kafaffu guda hudu da doguwar jela jikinsu kuwa wasu kayoyyine masu tsananin kaifi da tsini bakinsu wakekkene zasu iya haɗiye mutum uku lokaci guda suna da fuka-fukai masu tsayi da idanu kwala-kwala suna fitar da feshin wuta. Su goma sha biyu ne suka yi jerin gwano tare da sirrina a gabanta alamun girmamawa.
Daya bayan ɗaya ta bisu tana shafa wuyansu daga bisani ta yi wani irin yare da ita kaɗai tasan abin da take nufi, take suka yi juyi da wani irin gurnani suka ɗaga fuka-fukansu suka tsaga ginnin masarautar suka wuce ɓat, take ginnin masarautar ya koma kamar ba shi ne ya dare ba ya koma man ya manne.+

Koda ɓacewarsu basu bayyana ko ina ba sai anahiyar su Alhussain bayanarsu keda wuya kasa ta soma girgiza koramar wajan ta kafe kaf bishiyu suka soma zubewa kamar lokacin hamada babu wanda bai tsorata ba cikinsu sai Alhussan jarumin maza da ya tsaya kyam yana hucci.Gaba ɗaya jijjiyoyin jikinsa sun mummurde a sukwane wata hallita cikin hallitun ta kawo masa bahagon sara ya sunkuya cikin gwanintar iya salon yaki ya kauce ta karci kasa take wajan ya bada wani wawwakeken rai tamkar rijiya gaba biyu hucin giftawar halitar ya hada karamar gugguwar data turnuke wajan ya yi bakikkirin. Sai bayan lafawar iskarne Alhussain ya hangi gawar mahaifiyarsa yashe a kasa cikin jinni hankalinsa ya yi matukar tashi ya daddage ya kwarara kabara take tsuntsaye suka soma shawagi suna faɗowa kasa ya yi kukan kura ya fada cikin hallitun suka soma gabzawa yaki yake yana kukan rashin mahaifiyarsa shikenan ahalin ƁMarkahu sun yi nasarar watsa ahalinsu sunyi nasarar watsa a halinsu?.
Bai gama dawowa tunaninsa ba wani cikin hallitun ya shamace shi ya laftamasa ya kushi a kaucin cikinsa ta ke ya kwalla kabara ya zube kasa yana numfarfashi tuni suka suri Zajlat suka yi sama da ita.Duk abinda yake faruwa Sharmila da Sarki Sharimil na kallo ta madubin tsafi koda faruwar hakan sai suka takarkare suka kece da dariya dakaru da fadawan Sarkin suna masu tayasu kafin kiftawar ido sai gasu a gaban gidan sarautar dauke da Zajlat tana kuka.
7

Story continues below

Da gudu Aisha ta karaso daga maɓuyar da ta boye tun sa ada aka fara gwabza yakin ta yi yunkurin ɗaga Alhussain duk da kasancewarta jaruma kuma gwana a fagen yaki amma ya hakan ya gaggara . Ruwa ta ɗebo ta yi bisimillah ta shafa masa a jikinsa da ikon Allah sai ya yi zumbur ya mike yana layi kamar wanda yasha banju rike shi ta yi suka som tafiya fahimtar inda yake son nufa wato kan gawar mahaifiyarsa. Hakan yasa ta nufi can, koda zuwansu sai ya fashe da kuka sun jima sua kuka daga bisani ya mike shi ya yi mata wanka ya sallaceta ya buneta sai bayan komai ya lafa ciwan kuiɓin cikinsa ya soma uzura masa da kansa ya ɗinke ya shafa wani koran magani haɗe da zuma bayan ya yi basmallah kafa tara. Zuciyarsa ta dinga zafi musamman da ya kali Aisha ya ga ita kaɗai ta rage masa a duniya zuciyarsa ta yi zafi bai aune ba ya tsinkayi muryar Aisha tana fadin:-
"Hakika duk abinda ubangiji zai kaddarowa bawansa, to hakika yana cikin kaddarar rayuwarsa idan kuma ya yi hakuri yana da lada ma dumbin yawa".

Koda ta zauna a zancanta sai idanunsa suka ciko da kwalla mai zafi ya share yana mai tasbihi ga ubangiji.

Lokacin da waɗanan hallitu suka kai Zajlat fadar mahaifinta sai gaba daya fadar ta yi tsit take a wajan kakarta Sharmila ta hukunta ta tare da sa a kaita gidan a zaba mahaifinta yana ji yana gani ya kasa hana aikata hakan. Tun daga ranar duk lokacin da aka je kai wa su Alhussain hari ba a ganinsu sai dai sautin muryoyinsu hakan ya dagulawa Sarki da bokanya hankali. Haka aka cigaba da azabtar da Zajlat duk sanda ta saci jiki ta je wajansu Alhussain.
A bangare guda kuma matar Sarki Sharmil bata da burin da ya wuce kashe Zajlat, yayin da soyayyar Zajlat ta yi wa dan Sarki Sharbusa wato Sham unu kamun kazar kuku. Daga wannan ranar ya zama ansawa Zajla takunkumin fita babu inda take zuwa kwatsam ranar Talata an shiga ɗakin bauta ta saci jiki ta tafi basu ankara ba sai da abin bautasu ya fusata ya soma haufar datsawa da girgiza katangun birnin hakan ya fusata Bokanya Sharmila tasa aka bi sahunta aka kawota shi ne dalilkin kaita ɗakin azaba.
CIGABAN LABARIN

Dakin da aka kai Zajlat kuntattacan dakine mara yalwa gashi mai tsaanin duhu, ko mikewa gaba daya bata iya yi a gefan dakin an yi wani rami da aka hura wuta a cikinsa wadda ta kasance ta zafi ce tana ci kodayaushe bata yankewa gata jajjur tana fitar da shud shudin haske mai tsoratarwa.1

Tsayin kwanakinta biyu da ta yi a dakin cikin mawuyacin hali ta yi su. Domunzafin wutar yabfara y mata illa sossai a ranar kwana na uku ne ta shiga mawuyacin hali sabida galabaita harta kaita ga faduwa magashiyan a hankali bacci ya ɗauketa ta yi mafarki da Alhussain yana karanta mata kalmar, innalillahi wa inna ilaihirraji un tare da la ilaha ila antassubhanaka inikuntuminazalimun take ta mike a firgice tana maimaita kalmar take wutar ɗakin ta mutu wani haske ya gauraye ɗakin saɓanin duhu mai tsanani ta rarrafa ta sami kasa ta yi taimama kamar yadda Alhussain ya koyar da ita a wani zuwa da ta yi, ta yi jim tana tunanin yadda lamarin ya kasance.
Wani yammaci ne mai cike da ni ima Zajlat ta kaiwa su Alhussain ziyara koda ta je sai ta samu basu da ruwa gashi lokacin ibada ya karato sai ta ga duk sun tsuguna sun ɗora hannuwansu kan kasa ta zuba musu idanu tana kallo bata gaza ba ta furta,
"ya ku ma abota karamci menene wanan ku ke aikatawa?".
Koda ta zauna a zancanta sai Aisha tace,
"wannan ita ce taimama".
Cike da mamaki take maimaita kalmar ta sake furta,
"ki gafarce ni ya ake yin wannan ibada kuma baku koyamin ba?".
Murmushi suka yi dukkasu daga bisani Khadija ta furta,
"yadda ake gabatar da taimama shine; zaki wara yatsun hannayanki biyu ne sai ki buga a kasa, sannan sai ki shafi fuskarki da cikin tafikan hannunki, sai kuma ki shafi hannayanki zuwa wuyan hannu (Ku'i), zaki yi ko kari ya tabbata ya game ko'ina na fuskarki a lokacin da kike shafar kar ki manta da karkashin haɓarki da kuma hannayanki idan kina da zobe sai kin cire domin shafar ta game ko ina, idan lokacin da kika shafo kasar ba'ace dole sai mutum ya sa kasa a fuskarsa ba.
Idan kuma ya ga dama sai ya yi shafar sau biyu to tafarko sai ya shafi fuska da ita ta biyun kuma ya shafi hannuwa zuwa gwuiwar hannu.
Cikin mamaki Zajlat ta ce,
"shin ita ma tana ɓacci kamar yadda kuka yimin bayanin alwala?".

Story continues below

Alhussain ne ya amshe batun,
"Zajlat hakane taimama tana baci da duk abinda yake bata alwala babbane ko karami, kamar tusa fitsari. Fitar maniyyi, jinin al'ada, sannan kuma idan uzurin da ya sa aka yi taimama ya gushe to taimama ta gushe.

Duk wanda ya yi taimama domin ya yi sallar farillah to ya halatta ya yi nafila da wannan taimamar. Idan mutum ya yi taimama ya yi sallah da ita sai kuma lokacin wata sallar ya yi kuma gashi ba abinda ya karya mishi taimama to sai ya sake wata taimamar kafin ya yi sallar, domin abin nufi anan sai ya sake neman ruwa idan bai samu ba to sai ya yi taimama.

Koda ya zauna a batusa sai ta yi murmushi ta ce,
"Yakai wannan jarumi mai cikar kamala me ya ke kawo ayi wannan ibada ta taimama?".
A wannan karon Aisha ce ta amsa da cewa:-
Rashin ruwa, idan ya kasance matafiya suna cikin tafiya ko suna zaune a gida sai suka rasa ruwa sun nema iya yadda za su iya basu sami ruwan ba, to anan tunda sun nema basu samu ba ba za su bari lokaci ya wuce ba su ce sai sun je gida sai su gabatar da taimama su yi sallar su, ko da a cikin su akwai masu janaba, ko matan da al'adar su ta dauke. Kuma da zarar sun gabatar da wannan taimama to sun sauke wajibinsu ko da an sami ruwa ba za su sakeba. Wato shi addinin musulunci gwargwadon yadda ka gane shi a yadda yake gwargwadon yadda yake da sauki a gareka.

Rashin wadatar ruwa Idan kuma a tare da ku akwai ruwan amma kuna da matukar bukata domin shi zaku sha da shi zaku yi girki ko shi za ku ba dabbobi yadda idan ku ka yi alwala da shi ba zai ishe ku wadancan bukatuba, asalima za'a iya tagayyara, ko kuma ga ruwancan kuna hangowa to amma miyagun namun dajine a wurin ko kuma matattarar barayine wurin to anan fa hukunciku duka shine wadanda basu da ruwa, saboda haka wadanda suke dashi kadan domin bukatunsu sai su sha su yi taimama. Idan ga ruwan, amma ka ji tsoron cuta a jikinka ko kuma ciwon zai sami jinkirin warkewa, sai ka yi taimama. Idan ya zamana yana fama da rashin lafiya amma zai iya alwala sai dai ba zai iya motsawaba domin ya debo ruwan alwalar kuma bai sami wanda zai debo mai ruwanba ko babu wanda zai yi mishi alwalar kai tsaye sai ya yi taimama. Idan yana matukar jin tsoron sanyi idan ya yi amfani da ruwa, kuma ga shi yana son yin alwala ko wankan tsarki ga shi bai sami abinda zai dumama ruwanba to kai tsaye sai ya yi taimama.
Wadannan bayanan suna nuna mana cewa rashin lafiya bata dauke sallah, domin koda ba zai iya alwalaba saboda tsoron sanyi ko jinkirin warkewa ko dai daya daga cikin abubuwan da aka ambata to sai ya yi taimama, abin takaici shine sai ka ga dazarar mutum bashi da lafiya to abu na farko da zai ajiye shine sallah.
Hakanan inda mutum za'a tsare shi, ba zai bada hanzarin ai lokacin da suke a tsare ba'a barinsu su yi alwala to ba sai ya yi taimamaba. Idan mutum yana da ciwo a gabban alwalarsa kuma ba zai cutuba idan ya shafa hannunsa a kan ciwon to sai ya yi alwalar idan ya zo wurin sai ya shafa kawai ba sai ya wankeba.
Idan galibin jiki ya zama ba lafiya kamar ya zama ba inda ya raje sai hannu ko kafa to anan kai tsaye sai ya wuce zuwa taimama. Shi bayani akan abinda ya shafi wanke wasu gabobi sannan ayi shafa akan wasu gabobi sabo matsanancin rashin lafiya daya shafi gabban alwala ko taimama darasine mai zaman kansa, a littafin Iziyyah shine fasali na gwoma sha-daya, malamin ya ware fasalinne domin bayanin cututtuka da zasu sami gabban alwala, kuma ya kawo fasalinne bayan ya kammala bayani akan taimama a fasali na goma, Allah ya saka masa da alkhairi.
Ya halatta ka yi taimama a duk inda yake doron kasa kamar inda yake; rairayi ko jangargari ko dutse ko kamfa ko kasar gishiri ko ta kanwa ko inda yake dusar-kankarace.
: Allah ya yi bayanini shar'antuwar taimama a cikin Alkur'ani mai girma a Suratun Nisa'I, aya ta 43, da kuma Suratul Ma'idah aya ta: 6. amma ayanzu zamu kawo bayani akan ayar suratul ma'idah, wato aya ta shida kenan, Allah madaukakin sarki yana cewa:

''Ya ku dukkanin wadanda su ka yi imani! Idan kun tashi za ku yi sallah to ku wanke fuskokinku da kuma hannayanku zuwa gwiwar hannu, ku kuma shafi kawunanku kuma ku (wanke) kafafuwanku zuwa idon sawu, idan kun kasance masu janaba to ku tsarkaka (ku yi wanka), idan kuma kun kasance marasa lafiya ko kuna kan tafiya ko kuma daya daga cikinku ya yi bayan gida, ko kuma kun taba mata (janaba) baku sami ruwa ba to sai ku yi taimama a wuri mai tsarki sai ku sahfi fuskokinku da kuma hannayanku daga wurin, Allah baya nufin ya sanya mukun kunci ko kaka, saidai yanason ya tsarkake ku kuma domin ya cika ni'imarsa a gareku domin ku gode masa. (Ma'idah, aya ta:6).
Wannan ayar babbar ayace, ta kunshi hukunce-hukuncen Alwala da abinda yake karyata, da kuma janaba da yadda ake wankan tsarki, da kuma taimama da abinda ke sawa ayi taimamar da kuma yadda ake yenta, sannan da manufar da tasa Allah ya shar'anta taimamar.

Story continues below

Ma'aikin Allah -Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- yace: ''An bani abubuwa biyar da ba'a ba wani ba kafin ni; An taimakamin da tsoro (ma'ana sanya tsoronsa a zukatan makiya) na tafira tsawan wata guda, kuma an sanya min kasa ta zama wurin sallah da kuma tsarki, duk inda wani mutum daga cikin al'ummata sallah ta riskeshi to ya yi sallar shi'' a wata riwayar ''To anan inda yake masallacinsa yake da kuma abin tsarkinsa''.
Bukhari, Hadisi na: 335 , Muslim Hadisi na: 521.
Wannan hadisin ba karamin hadisi bane, domin ya yi bayanin gatan da Allah ya yi wa wannan al'ummar gatan da bai yiwa wata al'ummaba, a ciki ya ambaci cewa an sanya masa kasa ta zama wurin sallah, al'ummomi da suka gabata basa sallah a ko ina sai a inda aka kebe musu, amma mu ko atsakar da ji ne sai ka tsaya ka kallaci alkibla ka yi sallar ka, kuma yace an sanya masa kasa ta zama wurin tsarki, za ka yi tsarki da ita.
Taimama matsayine na musamman da wannan al'umma ta kebantu da ita, Allah bai sanya taimama ga wata al'ummaba kafin wannan al'ummar domin yalwatawa ga wannan al'ummar. I jima'i: Malamai duk sun yi ijima'i akan tabbatuwar taimama. Ita taimama tana tsayawane matsayin ruwa a shar'ance lokacin da rowan ya faskara, dukkan abinda kasan ba'a yi said a ruwa to ana yi da taimama, kamar sallah, dawafi, karatun Alkur'ani da dai sauransu......".
Koda ta zauna a tunaninta sai ta fashe da kuka tana mai yi wa mahaifiyar Alhussain fatan dacewa a lahira.

SHIN DAN SARKI SHARBUSA YANA SAMUN SOYAYYAR ZAJLAT?.
SAMARATU NA SAMUN NASARAR KAWAR DA ZAJLAT?.
SARKI SHARMIL DA BOKANYA SHARMILA NA SAMUN NASARAR KAUDA ALHUSSAIN?.
INA BURIN AISHA DA ALHUSSAIN KE TSAYAWA NA KAFA DAULAR BAITUL NUR A DORAN KASA?.

8

Cikin tashin hankali ta kai mari ta kai gwauro, fuskarta ta yi jajjur har wani jajja ta ke yi ga wani gumi da ke keto mata tamkar fanfo ta numfasa kanan ta sauke idanunta a kan amintaciyar Baiwar tata,
"ya ke Juda ki sani bani da burin da ya wuce in kauda Zajlat a doran kasa amma hakan ya ci gagara, ina son in saki wani aiki mai matukar haɗari amma an tabbatarmin ke ce kaɗai zaki iya aiwatar dashi amma kain nan zan fara ganawa da boka Samus".

Koda Samaratu ta zauna a zacanta, sai ta kyalkkyale da wata shu umar dariya lamarnin kenan daya haifar da kaɗuwar karamar iska, ta ke ta jawo wata kwataniyya ta runtse idanunta tana karanta waɗansu dalamusan tsafi faruwar hakan keda wuya wani hayaki mai launin ɗorawa da fari ya dinga fitowa daga kwatanniyar a hankali ya cuɗe waje ɗaya ya zama wani launi mai kala-kala sai ya zama wata irin hallita akan kwataniyar shi ba mutum ba ba aljani ba yana da motsewar fuska da katon kai ga idanunsa manya da sirarran hannuwa.Hancinsa katoto a bayansa akwa fuka-fukai kamar Malam buɗa mana littafi ya risina yana mai alamun girmamawa.
"Me ki ke so ya shugabata?".
Ya.yi furucin da wata murya mai firgitarwa, cikin ɗaurewar fuska ta furta,
"ina son abinda zan nakasa rayuwar Gimbiya Zajlat ta daina amfanuwa daga nan gaba ɗaya a rasata sai dai inasan komai cikn tsari yadda Sarki da bokanya Sharmila ba zasu fuskanta ba".

Koda ta zauna a zancanta sai ya kyalkkyale da dariya ya yi nuni da hannunsa take hotan Zajlat ya bayyana tana kwance tana bacci hannu yasa ta yi nuni zuwa gareta take wani haske baki ya fito ta yatsansa manuni ya daki kafaffunta faruwar hakan keda wuya ta kwalla giggitaciyar karar data karade gidan azaba gaba ɗaya a hankali kafaffunta suka hau nannaɗewa tamkar roba tun tana ihu da karfinta har ta hau shure-shure gaba ɗaya dakarun gidan na zagaye da ita sun zare makamai suna muzurai sun kasa kataɓus har ta daina motsi. Yana sauke hannunsa ya kyalkyale da dariya mai karfi tare da furta,
"daga yau ba ita ba taka doron kasa, kuma baza a taɓa samun maganin warkewarta ba har sai anje dutsan darul ukub shi kuma wannan gida shigasa babban haɗarine dai-dai yake da nemo jaki mai kaho a doron duniya".
"Godiya na ke ya shugabana".
Bat ya ɓace suka hau kyalkkyala dariya mai karfin gaske.

Boka Samus amintacen bokan Samaratu ne a ɓoye, babu wanda yasan yana yi mata aiki daga ita sai amintaciyar baiwarta Juda.

***
Lokacin da Zajlat ta kwala kara mai firgitarwa a firgice dakaru suka rugo suka zagayeta suna mazurai duk sun zare makamansu amma basu ga kowa ba sai shure-shure da take yi tana fitar da wata kumfa mai yauki take suka ruga aka sanar da Sarki abinda ke faruwa a kidime ya taho yana huci karan farko a rayuwarsa daya taka gidan Azaba da kafaffunsa halin daya sameta ya yi matukar daga masa hankali kai tsaye aka sureta sai fadar bokanya Sharmila suna shiga Sarki ya shimfiɗeta tare da zubewa yana rokonta wata mahaukaciyar tsawa ta daka masa tare da yi masa nuni daya fita ya bata waje yana ji yana gani ya fito yana kallon yadda kwalin ɗiyarsa ta koma tashi ɗaya. Fitarsu keda wuya ta kule fadarta tare da bada umarnin kada wanda ya sake shigowa sai nan da kwanaki uku, lokacin da labari ya kai kunnan Sarki Sharmil ba karamin tashin hankali ya shiga ba.

Story continues below

Al' amarin ciwon Zajlat ya damu kowa a gidan sarautar kasanewarta mai tausayin na kasa da ita ba iya masarautar ba har ilahin mutanan garin kullum cikin bauta suke suna nema mata lafiya sai ya zamana ɗakin bauta bashi da shamaki da kowa kulum cikinta suke yi.

***
Kwana biyu tsakani Sarki ya shiga matsananciyar damuwa ga Sharmila ta hana a ganta bai san halin da take ciki ba, hakan yasa ya rame ya fita hayyacinsa ko abinci baya ci bashi da cikakkiyar nutsuwa. Al' amarin Samaratu kuwa komai da yake faruwa tana hangensa ta madubin tsafinta komai na tafiya yadda take so. Ranar da Zajlat ta cika kwanaki uku a wajan bokanya Sharmila a ranar garin ya tashi da wani rin bakon al amari. Garin ya yi jajjur sossai daga yamma daga gabas kuma ya yi wani irn duhu ga zafin rana tamkar zai fasa kwanyarsu ga rijiyoyi duk sun kafe al' amarin daya dugunzuma hankulan mazauna garin kenan suka fara iface-iface ana haka bokanya Sharmila bude fadarta tare da bada sanarwar tana son ganin kowa na garin manya da yara.
9

Koda fitowata sai daukacin mutanan garin suka sunkuyar da kai alamun girmamawa, ta bude baki cikin izza da takama,
"ya ku jama ar wannan gari a halin yanzu gimbiyarku na cikin mawuyancin hali wanda take bukatar magani a gaggauce. Sabida haka zamu sa gasar nemo mata magani bisa sharaɗin duk wando ya kawo maganin shi zai aureta.....".
Koda ta zauna a zancenta sai mahaifinta ya yi zumbur ya mike yana muzurai, zuciyar Samaratu kuwa ta cika da bakin ciki, mahaifinta kuwa hankalinsa ta she ya buɗe baki zai yi magana sai suka yi arba da Zajlat cikin wani abu ana turata kafaffunta sun sirrance kamar na jariri koda suka yi arba da ita sai jikinsu ya yi sanyi masu kuka na yi masu hawaye na yi mahaifinta ma jiki a mace ya koma ya koma ya zauna yana maida numfashi da kyar. Kamar an tsikare shi zumbur ya mike,
"ni zan nemo mata magani!".
Koda ya zauna a zancansa sai wajan ya i tsit, Samaratu kuwa ta cika da farin ciki ta sami hanyar kauda Sarki da Zajat cikin sauki. Tsawa mai karfi bokanya Sharmila ta daka masa, shi ma ya maida mata martanin tsawa karan farko kenan a masarautar ganin sa insa tsalaninsa da mahaifiyarsa.

Haka taran ya watse, tsayin kwana uku ana bada sanarwar samowa Zajlat magani ga garurruwan dake kusa dana nesa dasu a ranar kwana na hudu ne aka gama haɗuwa harabar masarautar ta cika makil yayan sarakuna da wazirai da sauran masu mukamai da dama ciki hada SHAM UNU da tawagarsa. Lokacin da aka bada sanarwar isowar bokanya Sharmila sai suka sake nutsuwa ta fito ɗaya bayan ɗaya take dubansu daga bisani ta buɗe baki zata yi magana.

Kamar daga sama suka hango wani ingarman doki fari tas yana haninniya ya nufo taron mutanan bayansa mutum ne a goye mahaya dokin dukansu fuskarsu a rufe take da wani mayani baki dashi suturarsu ta bambanta da ta mutanan gari take dakaru sama da hamsin suka yo kansu cikin gwanan cewar yaki kafin kiftawar ido dukkansu mahaya dokin suka diro tare da zare takubansu suka soma artabun yaki cikin gwaninta da tsagwaran jarumta kafin cikar sa a daya sn karar da dasu a haka saida suka karar da dakaru dari da hamsin a sanan bokanya Sharmila ta yi wa dakarunsu tsawa suka tsakaita dai-dai lokacin ne mayanin fuskokunsu ya zame suka bayyana tsananin mammaki y bayyana ga daukacun fuskokin mutanan wajan sabida ganin mace da namiji ga macen karama bata fi sa ar Zajlat ba take wajan ya kaure da hayaniya Sharmila ta yi tsawa aka dakata daga bisani ta bude baki kamar haka.

"Yaku waɗanan ma abota karfin meke tafe da ku?".
Koda ta zauna a zancenta sai matashin ya buɗe baki ya ce,
"mun zo ne shiga sahun masu bawa Gimbiya taimakon magani amma da sharadi ni ba auranta ne muradina ba muradina shi ne ku karɓi addinina bayan na samo maganin idan kuka saɓa alkawari zan yake ku!".
Koda ya tsaya da batunsa sai akai kalon kalo tsakanin Sarki da bokanya,
"menene addinin naka?".
"Addinn gaskiya wato musulunci".
Take zuciyarsu ta tsinke amma Sharmila ta dake,
"an yarje maka ku shiga sahu".
Take suka shiga layi Sharimila ta kara nanata gasar da dalilinta ta ɗora da bayanin inda za a samo maganin.

10
Daya bayan ɗaya tadubesutare da furta,
"Darul ukub shi ne inda za a samo maganin gimbiya, daga nan zuwa darul ukub a binciken alkalumana tafiya ce ta tsawan sati biyu tae da tsayawa da hutawa idan kuma babu tsayawa tafiyar lwana tara ce. Daki ne da ke da nau in abubuwa kala-kala akwai haɗarurruka da masifu masu tarin yawa a wannan hanya. Hanya ce mai cike da sarkakiy an tabbatar babu hallitar data taɓa shiga wannan daji ta fito da ranta face ta mutu maganin da gimbiya take bukata yana tsakiyar wannan daji na darul ukub a wani kogo mai suna kogon mutuwa".
Koda ta zauna a zancanta sai mahalata wajan suka soma zarewa a hankali a hankali har gun ya rage daga Sham unu sai wannan matashi da matashiyar budurwa da wasu jarumai uku Samu da Hamu da kuma Jurdas al'amarin daya bawa kowa mamaki kenann bokanya Sharmila kuwa dariya ta hau kyalkkyalawa take aka sallami mutan gari gaba ɗaya ta karasa yi musu bayanin garin ta sallamesu har sun juya zasu tafi matashin ya sake juyowa ya yi murmushin daya sa gaban sarki da bokanya cikin dakiyar zuciya ya sake maimata sharadinsa suka wuce, Sarki Sharbusa yana kuka ya yi sallama da ɗansa suka nausa suka soma tafiya.
***
Haka aka tura Zajlat cikin kekenta zuwa cikin gidan sarautar bata ko motsi, al amarin mahaifinta kuwa yana shiga ya nufi bokanya Sharmila yana huci,
"haba ya Ummina ya zaki min haka ki amince da sharadinsa?".
Koda ya zauna a zancansa sai ta tuntsure da dariya lamarin daya bashi mamaki kenan daga bisani ta furta,
"nasan abinda kai baka sani ba ina so a yau ba gobe ba kasa a kashe matarka Samaratu".
Cikin firgici ya soma motsa baki, bai samu damar tankawaba ta yi masa nuni da bango take komai ya bayyana jikinsa har tsuma yake ya suri takobi tsirara ya nufi cikin gidan sarautar yana huci bai yi wata-wata ba ya sare kan Samaratu ga mamakinsa sai kan ya koma daidai ta mike tare da nunashi da izgar hannunta ya yi sama ya daki bango ya faɗo a sume ta kyalkkyale da dariya ta bace ɓat daga gidan sarautar.
Hankalin Sharmila ba karamin tashi ya yi ba ta soma buga bincike don gano ina Samaratu ta nufa amma duk iyakar kokarinta ta kasa gano komai karshe ma madubin tsafinta bunduga yayi ya tarwase gaba ɗaya. Nan da nan ta baza dakaru nemanta amma tsayin kwana bakwai babu labarinta.
Lokacin da sarki Sharmil ya farfaɗo ba karamar buguwa ya yi ba, saida Sharmila ta gyara masa kashin guiwarsa nan hankalinsa ya tashi ya shiga neman mafita.
***
Al'amarin Samaratu kuwa bata bayyana a ko'ina ba sai gaban boka Samus a galabaice cikin dugunzuma take faɗin,
"ya kai amintacen bokana menene abin yi?".
Koda ta zauna a zancanta sai ya sheke da dariya mai amo ya furta.
"Mafita ɗaya ce zaki bibbiyi sahun waɗancan jarumai yayin da suka yi nasarar ɗauko magain gimbiya ki karɓa da karfin jarumtarki ki shanye maganin ta nan kaɗai zaki sami tsagwaran karfin jarumtar bokanya Sharmila ki kwace masarautarsu".
Koda ya zauna a batunsa sai tsoro ya bayyana a fuskarta, amma data tuna kudurinta saita hau shirin binsu hanya cike da muguwar manufa a ranta.

***
Lamarin su jarumi Sham unu wucewar sa a biyu suna tafiya wannan matashi yaja dokinsa ya tsaya koda ganin haka sai sauran suka dube shi ware mayaninsa ya yi tare da furta,
"lokacin ibadarmu ya yi zamu bautawa ubangijinmu".
Koda jin hakan sai Samu da Hamu da Jardus suka kaɗa kawunansu suka yi gaba abinsu Shamunu kuwa sai ya sami waje ya sauke dokinsa ya tsaya yana kalo suka gabatar da ibadarsu. Ya dinga kallonsu cike da sha'awa har suka kammala suka mike suka cigaba da tafiya, babu mai kula wani a haka suka yi ta tafiya har kwana hudu amma basu hadu da kowa ba. Idan lokaci yayi Sham unu kan tsayasu suyi ibadarsu sossai babu abinda ke burgeshi face kyawun matashiyar yana son ganin fuskarta wadda ta kadance kullum a rufe cikin mayani bata buɗeta sai zata yi ibadarta.
A ranar kwana na tara ne ya kasa jurewa ya tambayi sunayansu babu jinkiri suka bayyana masa sunayansu na ainihi sossai ya yi mamaki da jin sunayansu ya tabbatar suna da manufa kan samowa gimbiya magani da kuma sharaɗinsu domin yana da tarihin yadda aka kashe mahaifansu ta hanyar haɗin bakin mahaifansu.
A ranar kwana na goma ne suka shigo wani daji mai tsananin sahara tafiyar sa a ɗaya suka riski su Samu kwance magashiyan koda suka karasa sai Sham unu ya kada kai zai wuce amma ga mamakinsa sai ya abokan tafiyarsa sun tsaya tare da basu taimakom ruwa suka sha suka dawo hayyacinsu cikin mamaki ya ce,
"yana ga ya kai wannan jarumi ma abocin karfi ko ka manta baro mu suka yi a baya basu tsaya mu ba?".
Koda ya zauna a zancansa sai ya yi murmushi tare da furta,
"musulmi mutane ne masu tsarkin zuciya da kyakkyawan tunani. Daya daga cikin halayen musulmi shine ba sa kallon sauran mutane ta mahangar jinsi ko al'ada, addinnina ya yadda in taimaki wanda ya ke cikin halin neman taimako".
Koda ya zauna a zancansa sai suka cika da mamaki a zukatansu haka suka cigaba da tafiya babu mai cewa ufan har tsawa sa a ɗaya. Sunyi tafiya mai yawa Sham un ya kasa jurewa ya dubeshi,
"wai menene addininka?".
"Addinnina shi ne addinnin musulunci. Asalin addini a duniya shi ne musulunci. Mutum na farko da Allah ya halitta, Annabi Adam (alaihis salam), ya rayu ne bisa tafarkin musulunci. Dukkanin manzanni tun daga Annabi Nuhu (alaihis salam), zuwa Annabi Ibrahim, da Annabi Musa , da Annabi Isa , alaihimus salam, musulmai ne ma su kadaita Allah. Sai dai gaba dayansu Allah ya aikosu ne zuwa ga al'ummominsu kadai. Annabi na karshe kuma cikamakin tsarin annabawa shi ne Annabi Muhammadu (yabo da amincin Allah su tabbata a gareshi). Allah ya aiko Annabi
Muhammadu (SAW) da sako zuwa ga daukacin al'ummar duniya, mutane da aljannu. An haifeshi a birnin Makkah da a yanzu ke kasar Saudi Arabia. Annabi Muhammadu (SAW), bakureishe ne, dan Abdullahi da Amina daga tsatson Annabi Isma'ila (AS) dan Annabi Ibrahim (AS).
"Shi ya ake shiga wannan addinni naka?"
Koda ya zauna a batunsa sai ya dubeshi,
"ana shigasa ne ta hanyar kalma shahada ita kuma kalma shahada na cikin sharaɗan musulunci".
"Ko zaka iya bayyana min su?".
"Kwarai kuwa dan uwa. Shika shikan musulunci guda biyar sune ne kamar haka :- Kalmar shahada (TAUHIDI), Sallah, Azumi, Zakkah, da Aikin hajji ga wanda ke da iko. Kalmar Shahada
ma'anarsa shine shaidawa babu abun bauta bisa cancanta sai ALLAH (SWT), sa'annan Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne.
Sallah sallah na daga cikin shika shikan Musulunci mai mahimmanci matuka bayan Tauhidi, ana bukatar kowanne musulmi yayi Sallah sau biyar a rana, yana mai fuskantar Ka'aba dake kasar Saudiya . A kasashen Musulmai, za'a ke jin kiran Sallah daga Masallaci mafi kusa a yayin da lokacin Sallah yayi.

Sallah ana yinta ne cikin Natsuwa, domin a samu kyakkyawan lada. Azumi : Wannan rukuni ne wanda ake nufin barin ci, da sha, da yin jima'i daga fitowan alfijir har zuwa faduwan rana. Dukkan musulmi tilas ne da ya/ta azimci watan Ramalana (watau wata na tara a kalandar musulunci).
Zakka shi ne cire wani kayyadadden kaso, daga cikin wasu kayyadaddun dukiyoyi, a cikin wani kayyadadden lokaci ga wasu kayyadaddun mutane, domin Allah (SWT). Hajji shi ne zuwa ziyartan dakin Allah Mai Alfarma ga wanda keda iko da nufin Ibada. Imani ma'anan Imani shi ne : abun da zuciya ta kudurta, harshe yayi furuci da shi, sa'annan gabban jiki suka yi aiki da shi. Imani yana da shika-shikai guda shida (6) kamar haka : Imani da Allah, da Mala'ikunsa, da littafansa, da Manzanninsa, da Ranar karshe, da Imani da kaddara mai dadi ko marar dadi".

Koda ya zauna a zancansa sai jikinsa ya yi sanyi dai-dai lokacin suka kawo hanyar data rabu gida uku wadda daga itane za su shiga dajin darul ukub bayan sunyi tafiyar sa a huɗu cif. tsayawa suka yi suna shawarwarin abin yi.....

8

Cikin tashin hankali ta kai mari ta kai gwauro, fuskarta ta yi jajjur har wani jajja ta ke yi ga wani gumi da ke keto mata tamkar fanfo ta numfasa kanan ta sauke idanunta a kan amintaciyar Baiwar tata,
"ya ke Juda ki sani bani da burin da ya wuce in kauda Zajlat a doran kasa amma hakan ya ci gagara, ina son in saki wani aiki mai matukar haɗari amma an tabbatarmin ke ce kaɗai zaki iya aiwatar dashi amma kain nan zan fara ganawa da boka Samus".+

Koda Samaratu ta zauna a zacanta, sai ta kyalkkyale da wata shu umar dariya lamarnin kenan daya haifar da kaɗuwar karamar iska, ta ke ta jawo wata kwataniyya ta runtse idanunta tana karanta waɗansu dalamusan tsafi faruwar hakan keda wuya wani hayaki mai launin ɗorawa da fari ya dinga fitowa daga kwatanniyar a hankali ya cuɗe waje ɗaya ya zama wani launi mai kala-kala sai ya zama wata irin hallita akan kwataniyar shi ba mutum ba ba aljani ba yana da motsewar fuska da katon kai ga idanunsa manya da sirarran hannuwa.Hancinsa katoto a bayansa akwa fuka-fukai kamar Malam buɗa mana littafi ya risina yana mai alamun girmamawa.
"Me ki ke so ya shugabata?".
Ya.yi furucin da wata murya mai firgitarwa, cikin ɗaurewar fuska ta furta,
"ina son abinda zan nakasa rayuwar Gimbiya Zajlat ta daina amfanuwa daga nan gaba ɗaya a rasata sai dai inasan komai cikn tsari yadda Sarki da bokanya Sharmila ba zasu fuskanta ba".

Koda ta zauna a zancanta sai ya kyalkkyale da dariya ya yi nuni da hannunsa take hotan Zajlat ya bayyana tana kwance tana bacci hannu yasa ta yi nuni zuwa gareta take wani haske baki ya fito ta yatsansa manuni ya daki kafaffunta faruwar hakan keda wuya ta kwalla giggitaciyar karar data karade gidan azaba gaba ɗaya a hankali kafaffunta suka hau nannaɗewa tamkar roba tun tana ihu da karfinta har ta hau shure-shure gaba ɗaya dakarun gidan na zagaye da ita sun zare makamai suna muzurai sun kasa kataɓus har ta daina motsi. Yana sauke hannunsa ya kyalkyale da dariya mai karfi tare da furta,
"daga yau ba ita ba taka doron kasa, kuma baza a taɓa samun maganin warkewarta ba har sai anje dutsan darul ukub shi kuma wannan gida shigasa babban haɗarine dai-dai yake da nemo jaki mai kaho a doron duniya".
"Godiya na ke ya shugabana".
Bat ya ɓace suka hau  kyalkkyala dariya mai karfin gaske.

Boka Samus amintacen bokan Samaratu ne a ɓoye, babu wanda yasan yana yi mata aiki daga ita sai amintaciyar baiwarta Juda.

***
Lokacin da Zajlat ta kwala kara mai firgitarwa a firgice dakaru suka rugo suka zagayeta suna mazurai duk sun zare makamansu amma basu ga kowa ba sai shure-shure da take yi tana fitar da wata kumfa mai yauki take suka ruga aka sanar da Sarki abinda ke faruwa a kidime ya taho yana huci karan farko a rayuwarsa daya taka gidan Azaba da kafaffunsa halin daya sameta ya yi matukar daga masa hankali kai tsaye aka sureta sai fadar bokanya Sharmila suna shiga Sarki ya shimfiɗeta tare da zubewa yana rokonta wata mahaukaciyar tsawa ta daka masa tare da yi masa nuni daya fita ya bata waje yana ji yana gani ya fito yana kallon yadda kwalin ɗiyarsa ta koma tashi ɗaya. Fitarsu keda wuya ta kule fadarta tare da bada umarnin kada wanda ya sake shigowa sai nan da kwanaki uku, lokacin da labari ya kai kunnan Sarki Sharmil ba karamin tashin hankali ya shiga ba.

    Al' amarin ciwon Zajlat ya damu kowa a gidan sarautar kasanewarta mai tausayin na kasa da ita ba iya masarautar ba har ilahin mutanan garin kullum cikin bauta suke suna nema mata lafiya sai ya zamana ɗakin bauta bashi da shamaki da kowa kulum cikinta suke yi.

              ***
Kwana biyu tsakani Sarki ya shiga matsananciyar damuwa ga Sharmila ta hana a ganta bai san halin da take ciki ba, hakan yasa ya rame ya fita hayyacinsa ko abinci baya ci bashi da cikakkiyar nutsuwa. Al' amarin Samaratu kuwa komai da yake faruwa tana hangensa ta madubin tsafinta komai na tafiya yadda take so. Ranar da Zajlat ta cika kwanaki uku a wajan bokanya Sharmila a ranar garin ya tashi da wani rin bakon al amari. Garin ya yi jajjur sossai daga yamma daga gabas kuma ya yi wani irn duhu ga zafin rana tamkar zai fasa kwanyarsu ga rijiyoyi duk sun kafe al' amarin daya dugunzuma hankulan mazauna garin kenan suka fara iface-iface ana haka bokanya Sharmila bude fadarta tare da bada sanarwar tana son ganin kowa na garin manya da yara.
9

Story continues below

Koda fitowata sai daukacin mutanan garin suka sunkuyar da kai alamun girmamawa, ta bude baki cikin izza da takama,
"ya ku jama ar wannan gari a halin yanzu gimbiyarku na cikin mawuyancin hali wanda take bukatar magani a gaggauce. Sabida haka zamu sa gasar nemo mata magani bisa sharaɗin duk wando ya kawo maganin shi zai aureta.....".
Koda ta zauna a zancenta sai mahaifinta ya yi zumbur ya mike yana muzurai, zuciyar Samaratu kuwa ta cika da bakin ciki, mahaifinta kuwa hankalinsa ta she ya buɗe baki  zai yi magana sai suka yi arba da Zajlat cikin wani abu ana turata kafaffunta sun sirrance kamar na jariri koda suka yi arba da ita sai jikinsu ya yi sanyi masu kuka na yi masu hawaye na yi mahaifinta ma jiki a mace ya koma ya koma ya zauna yana maida numfashi da kyar. Kamar an tsikare shi zumbur ya mike,
"ni zan nemo mata magani!".
Koda ya zauna a zancansa sai wajan ya i tsit, Samaratu kuwa ta cika da farin ciki ta sami hanyar kauda Sarki da Zajat cikin sauki. Tsawa mai karfi bokanya Sharmila ta daka masa, shi ma ya maida mata martanin tsawa karan farko kenan a masarautar ganin sa insa tsalaninsa da mahaifiyarsa.

      Haka taran ya watse, tsayin kwana uku ana bada sanarwar samowa Zajlat magani ga garurruwan dake kusa dana nesa dasu a ranar kwana na hudu ne aka gama haɗuwa harabar masarautar ta cika makil yayan sarakuna da wazirai da sauran masu mukamai da dama ciki hada SHAM UNU da tawagarsa. Lokacin da aka bada sanarwar isowar bokanya Sharmila sai suka sake nutsuwa ta fito ɗaya bayan ɗaya take dubansu daga bisani ta buɗe baki zata yi magana.

Kamar daga sama suka hango wani ingarman doki fari tas yana haninniya ya nufo taron mutanan bayansa mutum ne a goye mahaya dokin dukansu fuskarsu a rufe take da wani mayani baki dashi suturarsu ta bambanta da ta mutanan gari take dakaru sama da hamsin suka yo kansu cikin gwanan cewar yaki kafin kiftawar ido dukkansu mahaya dokin suka diro tare da zare takubansu suka soma artabun yaki cikin gwaninta da tsagwaran jarumta kafin cikar sa a daya sn karar da dasu a haka saida suka karar da dakaru dari da hamsin a sanan bokanya Sharmila ta yi wa dakarunsu tsawa suka tsakaita dai-dai lokacin ne mayanin fuskokunsu ya zame suka bayyana tsananin mammaki y bayyana ga daukacun fuskokin mutanan wajan sabida ganin mace da namiji ga macen karama bata fi sa ar Zajlat ba take wajan ya kaure da hayaniya Sharmila ta yi tsawa aka dakata daga bisani ta bude baki kamar haka.

"Yaku waɗanan ma abota karfin meke tafe da ku?".
Koda ta zauna a zancenta sai matashin ya buɗe baki ya ce,
"mun zo ne shiga sahun masu bawa Gimbiya taimakon magani amma da sharadi ni ba auranta ne muradina ba muradina shi ne ku karɓi addinina bayan na samo maganin idan kuka saɓa alkawari zan yake ku!".
Koda ya tsaya da batunsa sai akai kalon kalo tsakanin Sarki da bokanya,
"menene addinin naka?".
"Addinn gaskiya wato musulunci".
Take zuciyarsu ta tsinke amma Sharmila ta dake,
"an yarje maka ku shiga sahu".
Take suka shiga layi Sharimila ta kara nanata gasar da dalilinta ta ɗora da bayanin inda za a samo maganin.

10
Daya bayan ɗaya tadubesutare da furta,
"Darul ukub shi ne inda za a samo maganin gimbiya, daga nan zuwa darul ukub a binciken alkalumana tafiya ce ta tsawan sati biyu tae da tsayawa da hutawa idan kuma babu tsayawa tafiyar lwana tara ce. Daki ne da ke da nau in abubuwa kala-kala akwai haɗarurruka da masifu masu tarin yawa a wannan hanya. Hanya ce mai cike da sarkakiy an tabbatar babu hallitar data taɓa shiga wannan daji ta fito da ranta face ta mutu maganin da gimbiya take bukata yana tsakiyar wannan daji na darul ukub a wani kogo mai suna kogon mutuwa".
Koda ta zauna a zancanta sai mahalata wajan suka soma zarewa a hankali a hankali har gun ya rage daga Sham unu sai wannan matashi da matashiyar budurwa da wasu jarumai uku Samu da Hamu da kuma Jurdas al'amarin daya bawa kowa mamaki kenann bokanya Sharmila kuwa dariya ta hau kyalkkyalawa take aka sallami mutan gari gaba ɗaya ta karasa yi musu bayanin garin ta sallamesu har sun juya zasu tafi matashin ya sake juyowa ya yi murmushin daya sa gaban sarki da bokanya cikin dakiyar zuciya ya sake maimata sharadinsa suka wuce, Sarki Sharbusa yana kuka ya yi sallama da ɗansa suka nausa suka soma tafiya.
***
Haka aka tura Zajlat cikin kekenta zuwa cikin gidan sarautar bata ko motsi, al amarin mahaifinta kuwa yana shiga ya nufi bokanya Sharmila yana huci,
"haba ya Ummina ya zaki min haka ki amince da sharadinsa?".
Koda ya zauna a zancansa sai ta tuntsure da dariya lamarin daya bashi mamaki kenan daga bisani ta furta,
"nasan abinda kai baka sani ba ina so a yau ba gobe ba kasa a kashe matarka Samaratu".
Cikin firgici ya soma motsa baki, bai samu damar tankawaba ta yi masa nuni da bango take komai ya bayyana jikinsa har tsuma yake ya suri takobi tsirara ya nufi cikin gidan sarautar yana huci bai yi wata-wata ba ya sare kan Samaratu ga mamakinsa sai kan ya koma daidai ta mike tare da nunashi da izgar hannunta ya yi sama ya daki bango ya faɗo a sume ta kyalkkyale da dariya ta bace ɓat daga gidan sarautar.
Hankalin Sharmila ba karamin tashi ya yi ba ta soma buga bincike don gano ina Samaratu ta nufa amma duk iyakar kokarinta ta kasa gano komai karshe ma madubin tsafinta bunduga yayi ya tarwase gaba ɗaya. Nan da nan ta baza dakaru nemanta amma tsayin kwana bakwai babu labarinta.
Lokacin da sarki Sharmil ya farfaɗo ba karamar buguwa ya yi ba, saida Sharmila ta gyara masa kashin guiwarsa nan hankalinsa ya tashi ya shiga neman mafita.
***
Al'amarin Samaratu kuwa bata bayyana a ko'ina ba sai gaban boka Samus a galabaice cikin dugunzuma take faɗin,
"ya kai amintacen bokana menene abin yi?".
Koda ta zauna a zancanta sai ya sheke da dariya mai amo ya furta.
"Mafita ɗaya ce zaki bibbiyi sahun waɗancan jarumai yayin da suka yi nasarar ɗauko magain gimbiya ki karɓa da karfin jarumtarki ki shanye maganin ta nan kaɗai zaki sami tsagwaran karfin jarumtar bokanya Sharmila ki kwace masarautarsu".
Koda ya zauna a batunsa sai tsoro ya bayyana a fuskarta, amma data tuna kudurinta saita hau shirin binsu hanya cike da muguwar manufa a ranta.

               ***
Lamarin su jarumi Sham unu wucewar sa a biyu suna tafiya wannan matashi yaja dokinsa ya tsaya koda ganin haka sai sauran suka dube shi ware mayaninsa ya yi tare da furta,
"lokacin ibadarmu ya yi zamu bautawa ubangijinmu".
Koda jin hakan sai Samu da Hamu da Jardus suka kaɗa kawunansu suka yi gaba abinsu Shamunu kuwa sai ya sami waje ya sauke dokinsa ya tsaya yana kalo suka gabatar da ibadarsu. Ya dinga kallonsu cike da sha'awa har suka kammala suka mike suka cigaba da tafiya, babu mai kula wani a haka suka yi ta tafiya har kwana hudu amma basu hadu da kowa ba. Idan lokaci yayi Sham unu kan tsayasu suyi ibadarsu sossai babu abinda ke burgeshi face kyawun matashiyar yana son ganin fuskarta wadda ta kadance kullum a rufe cikin mayani bata buɗeta sai zata yi ibadarta.
     A ranar kwana na tara ne ya kasa jurewa ya tambayi sunayansu babu jinkiri suka bayyana masa sunayansu na ainihi sossai ya yi mamaki da jin sunayansu ya tabbatar suna da manufa kan samowa gimbiya magani da kuma sharaɗinsu domin yana da tarihin yadda aka kashe mahaifansu ta hanyar haɗin bakin mahaifansu.
Story continues below

A ranar kwana na goma ne suka shigo wani daji mai tsananin sahara tafiyar sa a ɗaya suka riski su Samu kwance magashiyan koda suka karasa sai Sham unu ya kada kai zai wuce amma ga mamakinsa sai ya abokan tafiyarsa sun tsaya tare da basu taimakom ruwa suka sha suka dawo hayyacinsu cikin mamaki ya ce,
"yana ga ya kai wannan jarumi ma abocin karfi ko ka manta baro mu suka yi a baya basu tsaya mu ba?".
Koda ya zauna a zancansa sai ya yi murmushi tare da furta,
"musulmi mutane ne masu tsarkin zuciya da kyakkyawan tunani. Daya daga cikin halayen musulmi shine ba sa kallon sauran mutane ta mahangar jinsi ko al’ada, addinnina ya yadda in taimaki wanda ya ke cikin halin neman taimako".
Koda ya zauna a zancansa sai suka cika da mamaki a zukatansu haka suka cigaba da tafiya babu mai cewa ufan har tsawa sa a ɗaya. Sunyi tafiya mai yawa Sham un ya kasa jurewa ya dubeshi,
"wai menene addininka?".
"Addinnina shi ne addinnin musulunci. Asalin addini a duniya shi ne musulunci. Mutum na farko da Allah ya halitta, Annabi Adam (alaihis salam), ya rayu ne bisa tafarkin musulunci. Dukkanin manzanni tun daga Annabi Nuhu (alaihis salam), zuwa Annabi Ibrahim, da Annabi Musa , da Annabi Isa , alaihimus salam, musulmai ne ma su kadaita Allah. Sai dai gaba dayansu Allah ya aikosu ne zuwa ga al'ummominsu kadai. Annabi na karshe kuma cikamakin tsarin annabawa shi ne Annabi Muhammadu (yabo da amincin Allah su tabbata a gareshi). Allah ya aiko Annabi
Muhammadu (SAW) da sako zuwa ga daukacin al'ummar duniya, mutane da aljannu. An haifeshi a birnin Makkah da a yanzu ke kasar Saudi Arabia. Annabi Muhammadu (SAW), bakureishe ne, dan Abdullahi da Amina daga tsatson Annabi Isma'ila (AS) dan Annabi Ibrahim (AS).
"Shi ya ake shiga wannan addinni naka?"
Koda ya zauna a batunsa sai ya dubeshi,
"ana shigasa ne ta hanyar kalma shahada ita kuma kalma shahada na cikin sharaɗan musulunci".
"Ko zaka iya bayyana min su?".
"Kwarai kuwa dan uwa. Shika shikan musulunci guda biyar sune  ne kamar haka :- Kalmar shahada (TAUHIDI), Sallah, Azumi, Zakkah, da Aikin hajji ga wanda ke da iko. Kalmar Shahada
ma'anarsa shine shaidawa babu abun bauta bisa cancanta sai ALLAH (SWT), sa'annan Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne.
Sallah sallah na daga cikin shika shikan Musulunci mai mahimmanci matuka bayan Tauhidi, ana bukatar kowanne musulmi yayi Sallah sau biyar a rana, yana mai fuskantar Ka'aba dake kasar Saudiya . A kasashen Musulmai, za'a ke jin kiran Sallah daga Masallaci mafi kusa a yayin da lokacin Sallah yayi.

Sallah ana yinta ne cikin Natsuwa, domin a samu kyakkyawan lada. Azumi : Wannan rukuni ne wanda ake nufin barin ci, da sha, da yin jima'i daga fitowan alfijir har zuwa faduwan rana. Dukkan musulmi tilas ne da ya/ta azimci watan Ramalana (watau wata na tara a kalandar musulunci).
    Zakka shi ne cire wani kayyadadden kaso, daga cikin wasu kayyadaddun dukiyoyi, a cikin wani kayyadadden lokaci ga wasu kayyadaddun mutane, domin Allah (SWT).  Hajji shi ne zuwa ziyartan dakin Allah Mai Alfarma ga wanda keda iko da nufin Ibada. Imani ma'anan Imani shi ne : abun da zuciya ta kudurta, harshe yayi furuci da shi, sa'annan gabban jiki suka yi aiki da shi. Imani yana da shika-shikai guda shida (6) kamar haka : Imani da Allah, da Mala'ikunsa, da littafansa, da Manzanninsa, da Ranar karshe, da Imani da kaddara mai dadi ko marar dadi".

Koda ya zauna a zancansa sai jikinsa ya yi sanyi dai-dai lokacin suka kawo hanyar data rabu gida uku wadda daga itane za su shiga dajin darul ukub bayan sunyi tafiyar sa a huɗu cif. tsayawa suka yi suna shawarwarin abin yi......
GIMBIYA ZAJLAT
BABI NA SHA DAYA

Koda suka tsaya sai Samu ya kama hannun Hamu suka nufi hanyar da ta yi yamma da ganin haka sai Jardus ya kama Sham'unu suka nufi hanyar kudu take Alhussain da Aisha suka nufi hanyar da ta yi gabas suka nausa. Sham'unu yana ta waigensu har suka ɓacewa ganinsa gaba ɗaya tafiya suke cikin tsanain sahara ga zafin rana takai gaba ɗaya ababan hawansu sun galabaita sun faɗi haka suka barsu suka cigaba da tafiya.
***
Lokacin da Hamu da Samu suka nausa cikin dajin tafiyar sa a daya suka riski kansu a wata faffaaɗar hanya mai cike da kwazazzabai ga duwarwatsu, haka suka dinga bi har suka wuce duwatsun. Cikin hanyar suka dinga gamuwa da namun daji masu haɗarin gaske suna artabu. Kwatsam ranar kwana na ukun gab da za su shiga dajin suka soma jiyo gurnani mai tsanani a kunnuwansu nan suka soma waige-waige, shiru na yan da'ki'ku can wani duhu a wata irin iska mai tsanani ya mammaye saman dajin, ba su yi aune ba sai ga wata hallita mai fuka-fukai ta bayyana suffarta abun tsoro. Ta dinga nufosu tana da kai guda huɗu da jela a bayanta nan suka soma artab babu ji babu gani cikin shammata ta wage bakinta ta suri Hamu ta jefa shi a baki ta la'kume kamar mage da ɓera. Al'amarindaya ɗaga hankalin abokin tafiyarsa kenan ya kuma fusata shi koda ganin hakan sai Samu somankai mata sara da suka ya kuntatta ta al'amain daya usatata kenan ta yi kansa  ya kwasa da matsanancin gudu yana mai falfalawa kamar zai taɓo keyarsa da kafarsa don tsananin gudu. Nan fa suka kasa gudu yake ya galabaita ya sadaka mutuwa kawai zai yi tuntuɓe ya yi ya kifa ta bishi ta dakeshi da jelarta take hannunsa ya karye ya kwala kara mai amo ta wage baki zata hadiyeshi cak ya ga ta tsaya tare da sakin wata kara mai karfi data haddasawa jejjn girgiza duk da radadin da yake ji saida ya ya ɗago yaga daliin tsayawarta take ya yi arba da Alhussain takobinsa na digar da jini ga kuma fuskarsa duk jinin ya falatsa.
Rikica ta fadi gefe wajan ya zurma rabinta ya rufta da hannu daya ya ɗagoshi suka 'karasa ya zauna Aisha ta tsaya tana shawagi da takobinta, tambayarsa ya yi ina abokin tafiyarsa ya bashi tabbacin ya rasa rayuwarsa, jim ya yi daga bisan ya gyara masa karayar suka mike da niyyar tafiya ya bisu da idanu,
"yanzu tafiya zaku yi ku barn wata hallitar ta cinyeni kai kaicona dana sani banyo wannan tafiyarba".
Cikin tausayi Alhussain ya kamo hannunsa suka cigaba da tafiya tafiyar sa a daya suka soma jiyo ihu da kida kide na tashi nan fa hankalinsu ya dugunzuma domin suna da tabbac suna gab da shiga garin tafiya suke cikin taka tsantsan koda suka kara gaba sai suka hangi mutane biyu daure jikin itace kimanin mutum dubu zagaye dasu suna kida take suka gano ko suwaye komawa da baya suka yi suka sami mafaka suka zauna tunanin abin yi.
               ***
Al amarin Sarki Sharmil kuwa kullum cikin tunan yake ga Zajlat jiki kara rikicewa ya ke yi sossai kulum Sharmila bashi baki take takai ta kawo dakin bauta ya yi kaura ya daina zuwa al ammuran masarautar duk sun lallace a ɓangare guda kuma sarki Sharbusa na masa barazanar ɗaukar fansa mudun ya rasa tilon ɗansa ga yawan mafarkai da yake yi masu ban tsoro da firgtarwa. Ga yawan mafarki da yake da Samaratu tana barazanar ɗaukar ran Zajlat.
***
Cikn dare Alhussain ya faki ido ya shiga cikin garin suna bacci ya kashe mutum uku ya dauko kayansu bayan ya binnesu suka saka kayan awashegari suka shiga garin gefin asuba suka saje da mutanan komai iri daya.

Story continues below

Mazauna garin arnan daji ne masu cin naman mutane, a tarhin garin shekaru hamsin kenan raban da su sami naman mutum sai tarkon da suka kafawa su Sham unu shi yasa suketa murna da tsale da kude-kide safiyar ranar ita ce safiyar da zasu yanka su daya aba sarkisu daya su kacaccala. Sarkinsu wani basamude ne mai katon tumbi ga katon hanci da idanu manya kofar hancinsa a zura irinsu Rash da Avv guda biyu ko huɗu, iin su Kamala ɗaya n kawai zasu iya shiga ba sauran waje Dr Mubara kuwa sai asa shi sau uku. Bakinsa kuwa tamkar kofar gari guda haka take.

Lokacin da aka soma hararramin yankasu sai hankalin Alhussain ya tashi zuciyarsa ta dugun zuma ya soma huci gashin jikinsa duk ya mimmike ya mummurde kamar wani gawurtacan zaki bai aune ba ya afka musu dasara da suka Samu na saman bishiya yana tayashi da kibau a daya bangaran Aisha na tayashi da zarge musu wuya da igiyoyi nan da nan waje ya hautsine suka rikatasu kadin sa a daya sub karar da rabin mutanan al amarin daya dugunzuma hankalin shugabansu kenan ya shammace Alhussain ya lafta masa wani kashin kwarangwal a tsakiyar ka take ya fadi bab numfashi Aisha data hango ta kwala wata giggitaciyar kara ta yo cikinsu tana sararsu da iya karfinta sarkin yawa yafi sarkin karfi dukda asarar data yi musu sun sami nasarar cafketa sanan suka kama Sam suka hadasu suka daure acikin keji su biyar har zuwa lokacin Alhussain baya numfashi...

ku biyoni dojin Alhussain ya mutu ne ya makomarsu masarautar sarki sharmil? Shin Zajlat na samun lafiya ne? Ina burin Sarki Sharbusa na daukar mataki idon ya rasa yaronsa? Shin yana rasawa da gaske?.
BABI NA SHA BIYU

Lokacin da aka kwashi su Alhussain basu riskikansu ko ina ba sai cikin wani wawwakekken keji mai faɗi da tsayi. Babban tashin hankalinsu yadda Alhussain bai farfaɗo ba har tsawan rabin sa a hakan ya dugunzuma hankalinsu. Hamu ne ya dubi  Jardus da tsananin takaici,
"ya aka yi suka kamaku".
Koda ya zauna a zancansa sai takaici yasa ya ki tanka masa al'amarin daya fusata shi kenan ya soma huci, kamar daga sama suka hango tahowar wani katon basamuden gwaggwon biri cikin hanzari Aisha ta mike ta jijjiga kejin ya juyo sabida jin mitsi. Da hannu Aisha ta yafito shi  ganin mace ce yasa ya taho hada tsale-tsalensa ganinta cikin keji yasa ya dinga tamola da kejin kenan al'amarin daya farkar da Alhussain kenan daga dogon suman da ya yi, jikisa duk ya yi tsami koda ya yi arba da abinda yake faruwa sai hankalinsa ya ta shi kafin ya yi wani yunkuri birin ya hankaɗa kejin ya tafi ya gangara nan suka soma gware da juna, bai faɗa ko ina ba sai gasu a wata alkarya suna faɗawa bamuɗin yana buɗewa sai gasu ga wasu wadannin mutane masu katon kai da ido ɗaya kunuwansu kuwa falka-falka kamar na Dr.
    Karfin dakuwar da kejin ya yi yasa ya buɗe suka yo waje, kamar an watsosu.   Koda birin ya yi aba da Aisha sai ya kwarara ihun murna yana tsale yana buga kirjinsa cike da iza. Kamar daga sama suka yi arba da wadannin nan suna fiffitowa da wasu irin makamai suka yi wa birin k'awanya nan kallo ya koma kansu aka soma artabun gumurzu.
   Cikin matsanancin artabun yaki,birin ya dinga makasu da kasa ya dakewa suna ɓalewa, cikn shammata wani wada ya yi tsale tare da caka masa wani kakkauran itace mai tsini a idanu take ya ɓingire yana mata gugu yana kai duka ko ina al'amarin daya haifar da cakuɗewar wajan kenan su Alhussain suka sulale suka nausa cikin daji.
   Tafiya kwana ɗaya da yini suka riski kansu a kofar kogon darl ukub, nan fa zuciyar 'yan maza ta motsa kowa na neman ace shi ne gwanin iyawa lokacin da suka kutsa kai cikin kogon sai hankalinsu ya tashiwasu 'kayoyine suke sukar 'kafafunsu suna hudowa ta saman 'kafar da 'kyar da siɗin goshi suka 'karasa akingaɓar kogon suka zauna da niyyar hutawa. Zamansu keda wuya waubirin hallitu masu suffar doddani suka dinga fitowa suna kewayesu, al'amarin daya ɗaga hankalinsu kenan suka shiga damuwa mai tsanani, nan suko soma yunkurin kai musu hari da faratansu masu tsananin tsini kama mashi. Duk wanda suka tsira sai ya kwala kara sabida tsananin zafi sai da suka shafe sa a shida sanan suka sami nasarar kashe hallitun suka shiga kogon. Koda shigarsu  sai suka cika da tsananin mamaki ganin sa faffaɗa mai haske ga wani kwantacan yanayi a shimfiɗe a kasansa, daga nesa da shi akwai wani tudu mai kama da rijiya a samansa a kwai wata wuta tana ci ga ruwa na zirarowa ta samansa amma ruwa bai kashe wutar ba. A gefan rigiyar akwai wata kwalba ta dinare tana ta kyalkkyali da ɗaukar idanu a cikinta koda suka yi arba da ita sai Jardus ya zabura da karfin gaske ya nufi wajan, takunsa ɗaya biyu wasu kibau suka dinga fitowa ta wasu sirarran kofofi suna sukarsa take ya faɗi matace.
   Al'amarn daya ɗaga hankulansu kennan, koda ganin haka sai Alhussain ya yi bisimillah ya yi taku ɗaya sai ya lura duk inda ake s ka taka ga shatin 'kafa nan amma ba a ganinta sossai cikin sauri-sauri  ya dinga bi, koda ganin haka sai Sham'unu da Aisha da Hamu suka bi ta sauran rukunnan hanyoyin guda uku suna bin yadda ya ke fi, al'amarn daya haifar musu da ruɗani kenan cikin ci da zuci kowane keson kai wa ga gaci, da karfn sihiri Hamu ya fara isa karshan wajan al'amarin daya dugunzuma hankulansu kennan suka tsaya cak! Cikin keta da nuna iya wa ya furta,
"dama nasai ni zanyi nasara",
ya dubi Alhussain,
"ina bin dogaran naka? Yau ya gaza taimakonka ne?".
Koda ya zauna a batusa sai Alhussain ya yi murmushi,
"ubangijina mai jarrabtar bayinsa ne".
Dariya ya kyalkkyale da ita tare da juyawa ya ɗora hannu da niyyar ɗaukar kwalbar take hannunsa ya daskare ya soma komaa dusar 'kan'kara a hankali har zuwa gaɓar hannun, ya cika da tsoro ya soma kwarara ihu, suka yi zugum suna dubansa har ya gama zama dusar 'kan'karar baki ɗaya jikinsa daga nan ya tarwatse a wajan ya bi iska. Gaba ɗaya suka tsaya cike da mamaki cikin azama Aisha ta 'karasa ta yi basmallah ta sa hannu ta ɗauka tare da juyowa ta soma tafiya murmushi ɗauke a fuskarta.
     Shu! Wata macijiya ta taso sama bakikirn da ita, bakinta yana zubar da wani bakin dafi mai tsananin tururi ta nufi Aishan gadan-gadan.
Story continues below

*BABI NA SHA UKU*

Cikin tsananin tashin hankali da damuwa suka maida dubans kan macijiyar, gaba ɗaya ta wage bakinta tana neman haɗiye Aisha cikin sufa Alhussain ya daka wani wawwan tsale ya ɗare bisa wuyanta ta yi matagugu ta wurgar da shi gefe ta sa jelarta ta fyaɗeshi take ya faɗi magashiyan ganin haka sai Aisha ta kara tsorata hankalinta ya yi mugun ta shi, gata ta nufota da karfinta kafin ta karaso Alhussain ya sake sufa  ya makyalkyale wuyanta suka soma artabun gumuzu hohoho in baka yi bani waje,  waniaikin sai Jarumai masu tsagwaran karfin damtse da jarumtar nunawa sa a. Haka sukaita gumurzu Aisha da Sham'unu suna kallo.
     ***
A can birninsu Gimbiya kuwa duk abin da ke faruwa suna kallo ta madubin tsafin bokanya Sharmila kamar wani majigi, kofar fada cike dam'kan da jama'a suna kallon avɓbin mamaki sananin jarumtar Alhussain ya fi komai birgesu har sun soma yi masa al'kakancin cin gasar, al'amarin daya fusata bokanya kenant janye hoton tare da korar kowa ta shige fadarta koda ganin hakan sai Sarki Sharmil ya bi bayanta fuskarsa cike da damuwar da ya kasa tantance ko damuwar mececce. Samun waje ya yi ya zauna a gefe tare da dubanta,
"ya ke abar dogaranmu me kike tunani akan wannan al'amari?".
Koda ya zauna a batunsa sai ta yi shiru ta shiga dogon tunani mai zurfi.
                 ***
Lokacin da gumurzu ya yi gumurzu, gumu ta gumu harta kai ga macijiyar ta ciji Ahussain a sassa biyu a hannunsa sai lamarin ya tsananta ya zama baya iya kai hari sai dai 'ko'karin kare kansa da yake yi. Ana haka kwatsam wani haske ya ratso cikin kogon a hankali ya cur guri ɗaya ya rikiɗe ya koma Sarauniya Samaratu cikin mununar shiga ta yaki.
    Dariya ta soma kyalkkyalawa ta nufi Aisha gadan-gadan. Nan da nan Aisha ta bude batar jikinta ta saka kwabar maganin ta nufeta suka soma gwabza yaki cikin tsananin gwanancewa. Sham'unu sai ya zama ɗan kallo ya rasa tantance waye yafi wani tsananin jarumta tsakanin Aisha da Alhussain.
   Cikin shammata Alhussan ya faki idon macijiyar ya caka mata wuka a ciki take ta saki 'kara ya 'kara cakawa ɗayan idon take wani tafashasshan ruwa ya soma ambaliya a tsakar wajan yana ɓulɓulowa ta idanunta kamar famfo cikin tsananin zafin nama Alhussain ya finciki hannun Aisha daga ri'kon da Samaratu ta yi mata suka yi gefe kusa da Sham'unu faruwar hakan keda wuya ruwan ya gangaro inda ta ke take ta kwala kara ta soma zagwanyewa a wajan kamar darma suna kallo harta gama zagwanyewar ɗif  kogon ya ɗauke tsit! Sai kuma ya soma 'kara yana girgiza kamar ana jijjigashi wani fanni na kogon ya soma zaftarewa yana faɗowa cikin kicima suka nufi hanyar fita duk inda suka ɗauke 'kafa sai ya zurma ya yi wawakekken rami da 'kyar da siɗin goshi suka fito 'kofar kogon suna maida numfashi.
   Kwanansu bakwai suna tafiya basu haɗu da komai ba na mugun abu, kwanci tashi suka shafe kwanaki goma cif suna tafiya, ɓangaran Sham'unu ya gama cika da mamakin su Aisha kwaɗayin shiga addinnin musulunci ya ɗarsu a zuciyarsa amma ya yi shiru bai nuna ba. A ranar kwana na sha biyar ne suka iso birnin Sambusa cike da farin ciki ga mamakinsu tn daga harabar ganuwar garin suka hango dandazon dakaru an zo taryarsu cike da farin ciki aka wuce dasu fada, bayan komai ya lafa Alhussain ya fito da maganin ya mikawa Sarki Sharmil shi kuma ya mika wa Sharmila ta buɗe tare da kura masa idanu, koda faruwar hakan sai ta turɓne fuska ta furta,
"wannan ba tsumin dodo kiryanu ba ne, da alama ba can kuka je ba".
Gaba ɗaya fadar ta hautsine da maganganu kowa na faɗin albarkacin bakinsa, al'amarin daya dugunzuma hankalin Aisha kenan ga mamakinta sai taga Alhussain ya mi'ke yana dubanta,
"ta shi mu tafi Aisha".
Babu musu ta mi'ke ta na mai bin bayansa, tun mutana garin na hangosu har suka 'kulle aka daina ganinsu. Fuskar Sharmila ta washe ta mi'ke tare da sallamar mutanan garin gaba ɗaya.
    Koda ta shiga ciki sai ta haɗa maganin ta bawa Zajlat, ta dubi Sarki Sharmil,
"nan da kwana uku zata koma dai-dai".
              ***
Tsayin kwanaki huɗu kenan da faruwar al'amarin, amma *GIMBIYA ZAJLAT* ko motsi bata yi bale asa ran tashinta. Lamarin daya ɗaga hankalinsu kenan.

SHIN DA GASKE NE ZAJLAT BATA WARKEWA?.
INA LABARIN ALHUSSAIN DA KUMA JARUMA AISHA?.
SHIN SHAM'UNU YANA KAR'NBAR MUSULUNCI?.
WAYE YA KE SAMUN NASARAR WARKAR DA GIMBYA ZAJLAT?.

Story continues below
Dukkanin amsoshin ku naga ɗiyar Katsinawa jikar Katsinawa 'yar asalin garin Matazu, Mata kuɗi Mata imani Mata gasu da albarka, Matanmu namu abincinmu da gonakinmu na ba'kinmu.Rainan ta dikko ɗakin kara kunya garesu badai.......lol😜

BABI NA SHA HU'DU

Gaba ɗaya Sharmila ta shiga damuwa da tashin hankali mai tsanani game da rashin mik'ewar Zajlata. Hakama mahaifinta.
***
Al'amarin Sham'unu kuwa tunda ya koma gida ya kasa taɓuka komai, hatta horan yaki da yake ba wa mayak'an garinsu ya yi sanyi. Hakan ya ɗaga hankalin mahaifinsa sossai ya zaunar da shi yana tambayarsa dalilin damuwarsa. Bai ɓoye masa ba ya nuna masa yana sin karɓar musulunci ne, koda ya zauna a batunsa sai ya bushe da dariya daga bisani ya furta,
"ya kai ɗana menene ya baka sha'awa da wannsn addinni?".
Koda ya zauna a tambayarsa, sai ya gyara zama ya bayyana masa komai daya faru kama daga tafiyarsu zuwa dawowarsu.

     Koda ya zauna a batunsa sai ya cika da mamaki zuciyarsa ta cika da farin ciki, nan da nan ya amince da bu'katar ɗansa ya tashi dakaru bisa jagorancin ɗansa aka shiga daji neman su Alhussain.
           ***
Al'amarin su Alhussain nuwa tunda suka nausa cikin daji, sai suka sami gari nesa da birnin Sambusa kaɗan da tafiyar sa a biyu suka yadda zango. Kwanansu ukuba wajan babu wanda ya sake magana game da batun su Sharmila, bayan sun yi sallahr la asar ne Aisha ta dubeshi.
   "ya kai ɗan uwana, wana mataki ka ke ganin zamu ɗauka game da wannan cin amana da aka yi mana?".
Koda ta zauna a batunta sai ya yi murmushi ya buɗa baki zai yi magana kenan suka ga wani tsoho ya bayyana a gabansu yana nishi da 'kyar. Da sauri Alhussain ya ɗagoshi tare da bashi ruwa ya sha baya sha ne ya dube Aisha da ido ya yi mata nuni ta bashi gurasa tana mi'ka masa ya bashi ya soma ci. Yun'kurawa Alhussain ya yi zai mik'e ya hango tashin 'kurar dawakai tuni ya mi'ke tare da zare takobinsa yana jiran kota kwana.Koda isowarsu sai ya hangi tawagar su Sham'unu nan ya maidata kufenta ya nufi Sham'unu suka rungume juna.
     Bayan ya janye ne ya dubeshi,
"ya kai Jarumi Sham'unu menene ke tafe da kai?".
Koda ya zauna a batunsa sai ya sanar masa da yadda suka yi da mahaifinsa take fuskarsa ta washe ya yi kabara yana mai nuna godiyarsa ga ubangiji. Aisha kuwa jikinta ya yi sanyi sossai. Tare da su suka koma garin Samuwaru a ranar suka karɓi addinnin musulunci Alhussain ya soma koyar dasu yadda addinnin gaskiya ya ke cike da 'kwarin guiwa, da fari Aisha ta'ki sakin jiki dasu tsoranta kar a aha'ince su daga bisani saita saki jiki sossai ita take koyawa mata ababban da suka shige musu duhu. Kwananki kaɗan suka rushe ganuwar garin aka sake sabuwa mai ɗauke da kalimatushahada suka rushe duk wasu ɗakunan bautar gumaka. Sham'unu aka sauya masa suna da Muhammad mahaifinsa kuma Abdallah mahaifiyarsa Khadija.
      ***
Lokacin da Sarki Sharmil da bokanya Sharmila suka sami labarin abin da ya wakana ba 'karamar kaɗuwa suka yi ba. A ranar suka tura da Manzo kan mutanan Sarki Abdallah su bar addinnin gaskiya, Alhussain ne ya sa aka yi musu martani da cewa su ya kamata su dawo addinnin gaskiya ko kuma su ya'kesu nan da tsawan kwanaki bakwai masu zuwa, lokacin da sa'kon ya isa fadar Sarki Sharmil take ya harzu'ka yasa aka soma shirin ya'ki ganga-ganga.

    ***
Lamarin masarautar Sarki Abdalla kuwa bayan tafiyar Manzo birnin Samuwaru sai Muhammad ya dubi Alhussain,
"ya kai wannan Jarumi ina so kasani har yanzu ina mamanin rashin warkewar Zajlat bayan kuma zahiri maganin ka ɗauko".
Koda ya zauna a zancansa sai ya ga ya bushe da dariya, al'amarin daya ba shi mamaki kennan wannan ne karon farko daya ga dariyarsa kodayaushe murmushi ya ke yi.
"Muhammad kasani cewa, banyi mamaki ba da maganin bai ba domin har abada ɓata-ɓata ne. Dana so zan zauna a garin Sambusa in ro'ki ubangijina ya bata lafiya kuma cikin amincewarsa zai bata lafiya amma don in nuna musu ubangijina mai iyawa ne mai taimakon bayinsa ne a kowane yanayi sai naje na samo maganin da suka yi imani shi zai warkar da ita kuma ya 'ki yi musu aikin".
Koda ya zauna a batunsa sai ya cika da mamaki ya 'kara gasgata hikimar ubangiji.
   Cikin kwanaki uku masarautar Satki Abdallah cikin shirin ya'ki suke da horo na musamman daga Jatumi Alhussain bisa ɗabarun ya'ki kala-kala don jiran kotaɓkwana. Haka Aisha ta dage tana koyawa mata tsagwaran jarumta da juriyar ya'ki.  A gefe guda kuma soyayya ce ta 'kulu tsakanin ɗan Sarki Abdallah da Jaruma Aisha.
  Ranar kwana na biyar ne kwatsam suka soma jiyo karar sukuwat dawakai, da busa alamun zuwan dakarun Sarki Sharmil nan da nan suka hau shiri. Kamar wucewar sa a ɗaya suka yadda zango a bayan gari suka aiko da Manzo zuwa cikin gari. Koda isarsa sai ya mi'ka sa'kon Sarkinsu take maga takarda ya mi'ke ya soma karantawa.

_"Sa'ko daga Sarki mai daraja Sarki Sharmil bin Markahu, na birnin Sambusa. Mun gargaɗinku da komawa addinnin iyaye da kakkani, ko kuma fushin abin bauta JARBUBA ya hau kanku. Mu shigo mu ya'ke ku mu kama matayanku da dukiyoyinku_".
  Koda ya zauna a karatunsa take Alhussain ya rubuta martani ya tashi Manzo da sa'kon martani,
_"Sa'ko daga maɗaukakkiyat masarauta, masarautar Sarki Abdallah mun ga sa'konku mun kuma karɓa amma kusani cewar. Ha'kika addinnin musulunci shi ne addinnin gaskiya kuma muna kan turbarsa baza mu sauka ba, mun amince zamu fito mu ya'ki juna amma da sharaɗin idan muka yi nasara zaku karɓi addinninmu"._
  Koda ya zauna a batunsa sai Sarki Sharmil ya kwarara ihu mai firgitarwa. Take suka rubuta radin amincewa aka hau kafa tantuna.
👑

Washegari aka shiga gabza ya'ki, tsayin kwanaki uku ana ya'ki babu hutawa a ranar kwana na huɗu ne su Alhussain suka yi nasarar kama Sarki Sharmil hannu-da hannu bayan aɓ kadhe mutane da dama ciki hada bokanya Sharmila.
  Cikin murmushi Alhussain ya dubeshi,
"ka amince addnnin musulunci ne addinnin gaskiya?".
Take ya zube yana kuka yana neman yafiyar su Alhussain, bayan komai ya lafa suka yi masa rakiya masarautarsa a washegari birnin Sambusa suka sake karɓar addinnin musulunci karo na biyu cike da 'karfin guiwa da kyautattawa. Tsahin kwanaki bakwai Alhussain yana yi wa Zajlat tofi a ruwa ana bata a ranar kwana na takwas ne ta mi'ke 'kyam da 'kafaffunta babu wanda ya sani sai Alhussain ya gargaɗeta kada ta fito sai an zauna fada. Kaya ya sa aka kawo mata mai mata hidima ta yi mata wanka kamar yadda aka saba.
     Da yammaci fada ta cika ma'kil ana zaune saiga Gimbiya cikin shigarta ta alfarma take mahaifinta ya mi'ke yana faɗin,
"tsarki ya tabbata ga ubangijin addinnin gaskiya".
Suka rungume juna cike da farin ciki suna godiya ga Allah. Bayan wasu kwanaki aka ɗaura auran Aisha da Muhammad Gimbiya Zajlat da Alhussain, kwanaki huɗu tsakani aka naɗa Alhussain Yariman birnin Samuwaru. Burinsu Alhussain ya cika ya 'kaddamar da burin mahaifinsa daular musulunci ta kafu a birnin  Sanbusa wanda ya maye gurbin sunan Baitul ƁNur.
         Masha Allah.
TAMMAT BI HAMDULLAH!.

Godiya ga ubangijin daya bani ikon farawa da 'karewa cikin iko da hikimarsa, abinda muka yi dai-dai da kuskure ubangiji ya gyara yasa mu amfana da abinda muka ji mai kyau mu watsar da marasa kyan


Post a Comment for "SARAUNIYA ZAJLAT COMPLETE"