SAMARIN BANA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SAMARIN BANA COMPLETE

SAMARIN BANA COMPLETE

- - Post a Comment

 SAMARIN BANA COMPLETE


*S*anye take da atamfa mai matsakaicin kud'i d'in kin riga da skirt ne kalan orange da lemon green ne a jikin atamfar, yayin da ta yane kanta da mayafi orange mai dan kauri, jakar porse ne kawai riqe a hannunta sai wayarta riqe a dayan hannun. Matashiyar budurwa ce wadda a qalla ba zata wuce shekara sha takwas ba, bata da muni ko kad'an, tana da madai-daicin kyau irin namu na hausa fulani_,


+

_Ta sake wai gawa don jin muryarsa tamkar yana biye da ita, shi d'in ne kuma yana biye da ita d'in still, sab'anin d'azu da yake cikin motarsa qirar benz yan zun a qafa yake bin ta. kusan ya biyota ne tun daga bakin titin unguwarsu har zuwa yanzun da ta iso gidan yayarta bai bar bibiyarta ba, ganin bata da niyyar tsayawa ne yasa matashin saurayin saurin shan gabanta wadda yasa tilas ita d'in ma taci burki don ta riga data iso qofar gidan da zata je._


_Ajiyar zuciya ya sauke cike da salon iya d'aukar hankali irin na *samarin bana* 'yan bana bakwai yace_

_"Haba gimbiya a cikin mata, kin wahalar da zuciyata da yawa fa! irin wannan horo haka ai sai kisa na shiga wani hali."_

_Duk yadda taso qin saurararsa sai da ta gaza hakan, satar kallonsa ta dinga yi da salon yadda yake maganarsa wadda ta tafiyar da ita tashin farko ba tare da tayi zato ko tsammani ba_.


_Sake dai-daita tsaiwarsa yayi yana sake qare mata kallo ya kuma cewa_

  _"Kinyi shuru tun d'azu ko sallamata ma kin gaza amsawa meye dalili uhm?!"_

_D'auke kanta tayi cikin kauda abinda take jin na shirin tasowa daga zuciyarta ta daure dai tace mai_,

  _"Ka riga da ka karya bin qa'ida don bana tsayawa da kowa kan hanya, tunda a zahiri dai ni ba motar haya bace balle na tsaya ga duk wanda ya tsaida ni a bakin titi"._


_Ba qaramin dariya maganar tata ta bashi ba, hakan ne ya sanya shi tsayawa ya dara sosai sai dai duka cikin wata iriyar kisisina ta jan hankali kafin ya tsagaita da dariyar sannan yace..._

   _kallo d'aya nayi miki nasan cewa kinfi gaban haka, dalili kenan da ya sanya na ajjiye abun hawa na na tako har nan don na iskeki nima da tawa kafar kamar yadda kikeyin tattaki, ayimin afuwa kan karya miki qa'ida da nayi kaina bisa wuyana."_

_Ya fad'a yana had'e tafukan hannayensa guri d'aya gami da d'an duqar da kansa. sassanyar ajiyar zuciya ta saki, salonsa ya gama burgeta sai dai duk da haka bata ce komai ba, hakanan shima bai d'aga kansa ba sai da ya tambayeta sau uku ta tabbatar masa da tayi masa afuwan sannan daga bisani ya sake dai-daita tsaiwarsa yana binta da wani irin shu'umin kallo_.


_Kusan minti talatin ya kwasa yana bayyana mata manufarsa game da ita da kuma shi d'in ko wane ne, hakanan taji zuciyarta nason zab'arsa a matsayin masoyi. duk yadda taso tujewa hakan amman abin ya faskara, abu guda ta samu nasara a kansa shine taqi amsa tayinsa da zummar sai tayi tunani, bai matsanta mata ba yace ya yarda, shawara abace mai alfanu ya bata lokaci taje tayi shawara zai dawo nan bada wani tsawon lokaci ba da haka suka yi sallama ya tafi ita kuma ta shiga gidan yayar tata..._

_Har yayi nisa ya tuna be amshi numbern wayan ta ba wanda ita kad'ai ce zata sada shi da ita sai kawai ya juyo ya dawo gida. Knocking yayi daga nan zaure ita kuma har ta zauna yayar tata tace tad'an lek'a ta gano ko waye tamik'e tana kunkuni tana fita sai taga bakwanta yayi murmushi tare da cewa_+


_sorry fa kinga na dawo ko?!"_


_Ya d'ora da cewa "amma ina ganin ya kamata ace munyi musayar number waya ko? koda zanzo gida, tunda kince min nan d'in gidan yayarmu ce"_

_Kanta kawai ta rausayar ta miqa hannu ta amshi tsaleliyar wayarsa da yake miqo mata ta zuba masa number d'inta nan take ya karb'a ya kira wayarta dake riqe a dayan hannunta ta d'auki ringing. Murmushi ya saki sannan ya mata godiya bayan ya cusa hannunshi cikin aljihun wandoshi ya fiddo da rafa na dubu dubu sababbi kar a miqe ya miqa mata. fad'uwa taji gabanta yayi sannan ta girgiza kai cikin nuna masa sam bata da ra'ayin amsar kyautarsa, ganin ya soma matsantawa ya sanyata ta shige gidan sannan ta karo qofar._


_A tsakar gida kusa da qofar kitchen ta tarad da yaya Rahama tana gyaran kayan miya, kanta ta d'ago tana amsa sallamar tare da cewa.._

_"kudai kuna son fitar yamma wallahi, ba zaku tashi zuwa guri ba sai yammaci don masifa. Toh yanzu waye yake salkama?"


_ASY bata tanka mata ba har sai da ta qarasa gefe inda botikan tara ruwan yaya rahama yake a jere gefensu kuma kujerunta ne 'yar tsuguno wata kan wata ta d'auki guda d'aya ta qaraso gabanta ta zauna tare da cewa..._


_"Fitar yamman ce ai tafi dadi, babu zafin rana ba kuma go slow"_


_Tab'e baki tayi tace "Haka dai kika ce....ya mutan gidan kuma"_


_"Suna lafiya suna gaidaki...ya naji gidan yau shiru haka?"_


_"Duk suna gidan baaba, sai dare zasu dawo."_


_Basu kai ga sake cewa komai ba yaro yayi sallama ya shigo gidan hanunshi riqe da nannadaddiyar baqar leda yace_

_"Wai gashi a bawa Anty Asy inji yasir" ya fad'a yana miqawa Asy don ya santa yaron maqota ne, hannu tasa ta karba tana bud'e baqar ledar, kud'adden dazun ne da tak'i karba daga gunsa, da sauri ta miqe a firgice ta fice daga gidan, isarta kofar gida ta hau dube dube sai dai babu yasir din babu alamunsa haka ta dawo cikin gidan jiki a salule._


_Yaya Rahama ce ta kalle ta tare da tambayarta lafiya kuwa?_


_Saida ta koma kan kujerar ta zauna sannan ta gaya mata haduwarta da yasir din, har take sanar da ita cewar shine ya buga gidan. tsaki yaya Rahama ta ja sannan tace.._


_"Banza shashasha, shine kika bi duk kika wani firgice kamar wadda ta yiwa sarki qarya, kanki aka fara yiwa budurwa kyautar kudi?" Asy tace_

_"Amma yaaya kallo daya zaki yiwa kudin nan kisan cewa ba kad'an bane ba fa ni tsoro nake ji gsky."_


_"To ai sai ki cillar tunda baki so, bansan yaushe kanki zai bud'e ba wallahi"_


_Asy bata tankawa yaaya Rahaman ba ta sake fidda kudin ta fara lissafasu, naira dubu dari ne cif cif, idanunta suka sake fitowa waje tana sanar da yaaya Rahaman, mai makon taga damuwa kamr yadda ita ta damu sai tab'anin haka_


_"Allah ya kashe ya baki Asy, wata qila ke mai qashin arziqi ce wallahi, Allah ya ba ki sai ki gode mai,tashin farko kyautar dubu dari?,gaba kuma sai nawa kenan?" ta fad'a farin cikin kwance a fuskarta_


_Asy ta gyada kai gefe tana fad'in "Barni kawai yaya Rahama, *samarin bana* tsoronsu nake, babu wuya sun kaika sun baroka shi yasa na tsorata da kyautarsa."_


_Ta k'arasa maganar da tsananin damuwa a fusakarta_


_"Kinga ki kwantar da hankalinki, wannan dai da alamu babu yaudara tattare da shi, da bakinki fa kika gayan tashin farko maganar aure ya fara zuwa miki da ita ko?,to kuma meye abun tsoro gunsa..?"_


_Bayan d'an gajeran nazari da tayi zuciyarta ta aminta da zan can yaya Rahama, don ita kanta bata hangi wata alama ta yaudara ko son zuciya a gun yasir ba_.


_Sai bayan magariba ta shirya komawa gida, duka kudin ta miqawa yaya Rahama sannan tace..._


_"Ki ajjiyen kud'in a gunki don ba zanje gida dasu ba, ki ciri abinda zaki cira a ciki, ban san yadda zan amsawa mama tambayar wanda ya bani kudin ba, sai magana taje gaba tukun idan yaso na nuna mata ko kuwa?"_


_"Shike nan hakan ma yayi" cewar yaya rahama sannan Asy ta fits._


************


_Su biyu ne a d'akin sun baje saman katifar dake shimfid'e gefan d'akin, 'yan mata ne guda biyu wad'anda a qimance ba zasu haura shekara goma sha takwas ko sha tara ba, d'aya daga cikinsu wadda ke tallafe da hab'arta sanye take da unifoarm na islamiyya ruwan qasa doguwar riga da hijabi ga qur'aninta ajjiye a gefanta, yayin da d'ayar ke saye da rigar material d'inkin buba, baqaqen ledojine a gabansu guda biyu mai d'auke da leshi atamfa jaka takalmi da tarkacen kayan kwalliya irin na mata nau'ika daban daban_.


_Mai kayan gidan wadda ke da mallakin sunan SAJIDA taci gaba da fiddo da kayan tana kallon fuskar RUQAYYA tare da yin dariya qasa-qasa, ruqayyan ta numfasa bayan sajida ta gama fitar da kayan ta dubeta tace...._


_"Yanzu duka wannan Nuraddin din ne ya siya miki lokaci guda?, sai kace wanda bai san ciwon kud'i ba?"_


_Dariya sajida ta saki tana fad'in "lallai ruky na yarda har yau baki san waye Nuraddin ba, to wallahi duk abinda zan tambaye shi komai tsadarsa bai taba bud'an bakinsa yace min a'a ko babu ba, wuyarta na tambayeshi to kuwa in sha Allahu a washegari ke wani zubin ma a ranar zai kawo min, kudi ne da shi fa ruky, shiyasa nake ta so ki amincewa zaharadden abokinsa wallahi idan har kika yarda da soyyyar shi sai mun kerewa sa'a cikin sa'annin mu dama wadanda suka girme mana"._


_Tabe baki Ruqayya tayi tana janye taguminta tace "nikam qyaleni kawai sajida, don haduwa zahradden ya hadu, amma gaskiya kallon mai budadden ido kawai nake yi masa"._


_Murmushi sajida ta saka "wallahil azim kin san Allah daya ko? ,tunda muke da Nuradden kallon banza bai tab'a yimin ba bare akai ga yace zai tabani, kawai sunyi karatu ne kansu a waye yake shi yasa kike musu kallon haka, kinsan dai bazan baki shawarar banza ba dai Ruqayya"_


_"Uhmmm, ai shike nan zanyi shawara duk abinda na yanke zan sanar da ke sai ki gaya masa." cewar Rukayya da alamun d'an damuwa a fuskarta_.


_"Shike nan, amma wallahi kada ki bari zaharadden ya qwace miki don ba qaramin so yake miki ba, don ko d'azu da suka zo maganarki ya dinga yimin." cewar sajida murmushi kwance kan fuskarta_.


_miqewa Ruqayyan tayi tana d'aukar qur'aninta "bari na wuce gida kuma sai mun had'u."_


_"Mai makon ki bari kiyi sallar magariba kafin ki qarasa ai anyi kira."_

_"Gwara na tafi, yanzun zakiji umma ta fara cigiya ta wallahi." Sajida bata sake cewa komai ba ta miqe ta bud'e wardrobe dinta dake shaqe da suturu wanda fiye da rabi duka Nuradden ne ya d'inka mata ta ciro hijabi ruwan madara yasha guga ta ware tana sanyawa tare da fadin "muje na rakaki ko qofar gida ne, gwanda nasa hijabin kada muyi karo da wannan dan takurar"_.


_Ruqayya ta matso kusa da Sajida tadan kama gefan hijabin tana cewa.._

_"kinga irin hijabin da na je siya shekaran jiya a kasuwa sai dawowa nayi kudina bai kai ba, gashi ina masifar son irin yadin wallahi."_


_Dariya sajida tayi tace "kinga da kina da zahradden ai da kin wuce wannan ajin wallahi, sai dai kisa ma ya siyawa wasu bake ba, ni kaina ganin irinsa nayi jikin wata na nuna sha'awata kawai sai ga nuradden da shi washegari" cewar sajida_


_Sai abun ya qayatar da Ruqayya har ta fara canki cankin yanke hukunci kan zaharadden._


_Tafe suke amma duka tunaninta na kan ta bawa zaharadden soyayyarta ko ko a'a? ta riga data sani sajida ta fita wayewa nesa ba kusa ba amma sam ba 'yar iska bace, hakan yasa ta bawa kanta yaqinin lallai ba zata taba zabar mata wanda zai ci mutuncinta ba.....!_

Dnt 4gt to Vote n ff me on wattpad@asykhaleel

*Muje Zuwa.....Its king Asy Khaleel* 👌_Zaune take a gaban mirrow tana tsara kwalliya kafin ta mik'e, sai da ta qara kallon kanta a madubi na tsawon mintina biyu ta tabbatar komai cikin kwalliyarta yayi babu makusa sannan ta yafa gyalenta_.


+

_Kai tsaye ta fito ta shiga kitchen d'in gidan su dake tsakar gidan tana kwad'awa qanwarta kira kan ta kawo mata aiken ruwan roba da lemon gwangwanin da tayi mata shagon kusa da gidansu. hajara ta fito da ledar daga d'akin mamansu ta miqa mata da canjin naira hamsin, kan d'an madaidaicin faranti ta shiryasu ta d'ora cups guda biyu sannan ta d'auki farantin ta leqa d'akin maman su ta sanar mata sannan ta fice zauren gidansu._


_Zaune yake kan tabarma wadda samanta darduma ce, ya had'e yayi kyau cikin shadda fara qal mai azabar tsada. Yasir kam ba baya bane gun kwalliya yasan sirrin adon dake tafiyar da zuciyar 'yan mata. sallama ta masa da sauri ya miqe ya amshi farantin hannunta yana amsawa game da kasheta da murmushin shi mai matukar kyau._


1

_Cikin salo na masoya cike da qaunar juna suka shiga hirarsu bayan sun gaisa da farko. hira ce mai dad'i wadda babu komai cikinta face nuna tsantsar qauna daga Yasir d'in har zuwa Asy, sai da suka shafe a qalla awa biyu sannan yakai duba ga tsadadden agogonsa ganin duhun magariba ya fara sawo kai yana fad'in "kai kai kai! haka muka cinye awanni bamu sani ba? ya kamata na kama hanyar garinmu hakan nan fa."._

_Murmushi Asy kawai tayi tana duban sa amma bata yi magana ba._


_miqewa tsaye tayi bayan shima ya miqe d'in ya sanya hannu a aljihunsa ya fidda bandir na dubu d'aya-d'aya sababbi kamar wancan karon ya miqa mata. kudin ta kalla kana ta kalleshi ta noqe kafad'a alamun ba zata karb'a ba_.


_Fuska ya d'an had'e kad'an alamun baiji dad'i ba sannan  yace "me yasa kike qyamar duk wata kyauta da zan miki ne Asy?bayan so da qauna ne ya had'a mu? kin san muhimmanci k'arb'ar kyautar saurayi kuwa?"_


_Kai ta kad'a sannan tace "ba qyamar karb'a nake ba, hasalima na gode da duk wata kyauta da zaka min nan gaba ma, kyautar ce yasir tayi yawa gaskiya tana yin yawa."_

_"A'ah Kodai tayi kad'an na qara miki?"_


_Ya fad'a yana kallon idonta,_


_murmushi tayi ta sunkuyar da kanta tana cewa "Da kuwa babu na biyu na a cikin sahun hadamam mu."_


_"Babu zan can had'ama, cikin abinda Allah ya bani wannan da na baki ba komai bane, ke da nake saka ran zaki zama matata nan gaba kad'an Asy."_

_Ganin da gaske yake sai tak'i k'arba yasa ta faki idonsa ta shige gida da saurinta_.


_Ratar kusan minti goma ta bada sannan ta aiko hajara ta d'auko mata tabarma da cups d'in data bari, saiga hajaran na kiranta tana miqa mata d'aurin kud'in ta saci kallon kud'in sannan ta kalli Mamanta da sauran 'yan uwanta dake zaune a tsakar gidan nasu sunyi shiru._


_"Yaya yasir ne yace na baki duk da kinqi tsayawa ki karba toh shi yayi niya."_


_Kafin ta amsa d'aya daga cikin qannenta mai bi mata tayi hanzarin k'arba tana wara idanuwa tace "yaya Asy wannan wanne DON ne kika had'u da shi haka? rafar dubu d'aya-d'ayq fa dubu dari ne a ciki, kyautar dubu dari lokaci guda?!" fuska ta marairaice tace "waccan karon ma da muka hadu fa hafsa haka ya bani su."_


_Ihu dukkansu suka sa cike da farin ciki, kowan ne na nuna goyon bayansa kan soyayyarta da yasir, hafsa ce tace "mukam wallahi yayi mana yaya asy Allah ya nuna mana ranar biki kawai zamu b'argaje kan sha'ani, dinner ba kama hannun yaro." laurat tace "gaskiya yaya Asy kinyi goshi, Allah ya bamu ya taku muma." a hankali Asy ta maida kallonta ga Mama sai taga tayi murmushi kawai ta tashi ta basu gurin, Se a sannan hankalinta taji ya d'an kwanta tunda taga alamun yarda kan fuskan Maman, ta amshi kud'in ta fidda dubu goma ta  raba masu ta ajjiye sauran, kiran wayar yasir da ya shigo wayarta shi ya rabata da 'yan gidan nasu dake ta lissafin hidimar da zasu sha a biki tun yanzun ta shige d'akin su don amsa wayar._


**********


_Tun bayan ta idar da sallar la'asar ta yi azkar d'inta a daddafe ta fita ta qarasa had'awa ummanta tuwon dare wanda ya kaita har biyar na yamma. ban d'aki ta shiga tayi wanka bayan ta fito ta shiga d'akin su ta fara shiryawa._


_Tun d'azu sajida ce a ranta gidansu take son zuwa kasancewar yau alhamis babu islamiyya, wayarta qirar nokia mai keypad ta d'auko dake gefan filon katifarta ta d'auko ta nemo lambar sajida ta kirata_.


_Babu dad'ewa ta d'aga wayar sai dai kafin takai ga cewa komai kud'in wayar ya qare, tsaki taja ta ajjiye wayar, sai dai kafin takai ga ci gaba da shafa man kiran sajidan ya shigo wayarta._


_"Gaskiya kina bada mu, daga kira kawai saiki wani katse ko flashing ne dama?"_


_"Mtswee kefa baki da mutunci, wanne flashing! kud'i nane suka qare wallahi nima bansani ba."_

_Dariya sajida ta saka sannan tace..._


_"ke kika so wallahi, inda kin amince da soyayyar zahradden wallahi kinfi qarfin credit sai dai kice ya turawa wasu ma ke bama credit ba wannan takurarriyar wayar taki ma sai ya rabaki da ita, mutumin nan ba dan iska ba ba komai ba kawai soyayyarki yake nema wadda daga qarashe zaku yi aure amma kin wani qi."_


_"Lallai credit yayi miki yawa, to taqaita zan canki idan kina gida gani nan zuwa."_


_"Dama ko baki zo ba ni zanzo in nuna miki sabuwar IPHONE 8 d'ina da nuradden ya siya min jiya.", ido ruqayya ta zaro don batun ya girmi hankalinta, iphone 8 fa sajida ke magana turk'ashi._

_"kinga bana son zuqi ta malle sajida, sai kace bawan gidanku."_


_"Bazan bata yawun baki na wajen rantse miki ba, abinda yanzu zaki zo ai gani ya kori ji sai kin k'araso." bata samu damar amsa mata ba ta kashe nokia d'inta ta hau shiryawa da sauri don ta qure qaryar sajida_.

*************


_A hankali Asy ta kutsa kai cikin gidansu aminiyarta sumayya, sallama tayi kafin ta shige tsakar gidan nasu, cikin sa'a ta tarar da sumayyan tana daka a tsakar gidan nasu. gidan shiru da alama duk mutan gidan basa nan sai ita kadai..._


   _"Yar halak kinqi ambato, kinsan yanzu haka zan canki nake cikin raina?" Ta fad'a tana miqa mata kujera 'yar tsuguno dan ta zauna._


_"Kedai bari 'yar uwa, had'uwar tayi wuya, karatu ya b'oye mu kamar wannan lokacin bazai zo ba, mu da bamu kwana guda tak bamu had'u ba sai gashi yanzu sai muyi kwana uku ma." ta fad'a tana dariya cikin salon tuna baya._


_"Ina su umma ne naga gidan sai ke d'aya?!". cewar Asy_


_"Su haidar duka suna islamiyya umma kuma sun tafi dubiyar qanin abba a asibitin murtala." ta fad'a tana yin gaba bayan ta saki daka d'in dan samo mata ruwan sha, a kanta ta tsaya tana fad'in._


_"Tashi to mu shiga daga ciki mana kawas." harararta Asy tayi cikin wasa tace "naga alama baquwa kike son mai dani ko? bayan layi zuwa nan sai kin wani kawon ruwa harda mu shiga d'aki, dakin da nake zuwa takanas musha wasan mu na kwashi bacci na natah." dariya sumayya tayi tana dire mata ruwan a gabanta tace "ai saura qiris ki zama baquwar, yau kwananmu nawa bamu hadu ba? koma ba haka ba ai baqonka annabinka ko?" dariyar itama tayi ta d'auki ledar ruwa d'aya ta bula ta d'an zuqa_.


_Hirarsu suka shiga yi irin ta aminai har suka gangaro batun daya kawo Asy gidan, a nutse ta fayyace wa sumayya abinda ke tafe da ita sannan tad'ora da cewa_


_"Nifa a gaskiya sumayya tsoro nake ji, kud'in sunyi yawa zuwansa uku amma kowan ne kyautar dubu d'ari sai kace d'an gidan buhari? kuma na yiwa yaya rahama maganar har sau uku fa tana cemin naga wani alamun aibu ne tattare da shi nace mata a'a, tace wai kada na wani d'aga hankali na cemin akayi mai kud'i bazai ce yana sona da aure bane, ko ko talaka nake nema bayan Allah yayimin baiwa da samun mai arziqi? sai dai sam sumayya hankalina bai kwanta ba har yau zuciyata ta kasa natsuwa da Yasir d'in kwata-kwata..._

*A*jiyar zuciya sumayya ta sauke sannnan tace "duk naji bayanan ki, maganar gaskiya Asy samarin yanzu kaso casa'in cikin d'ari abin tsoro ne. gani da ido kawai bai isa ya zama hujjar da zaka shaidi halin su ba sanin gaibu sai Allah, hakan nan su ba tukwa ne bane balle kace zaka qwan-qwasa ka ji wanne yafi qwari, ina ganin abu mafi kyau shine kici gaba da takatsantsan da yasir, kada ki yadda ya b'ullo miki da wani baqon lamari duk lokacin da kika ga wani abu tattare da shi wanda zuciyarki bata kwanta da shi ba ki sanar da ni, sannan kudi kuma ki amsa amma ki ajjiye kada ki tab'a saboda ba'a san me gaba zata haifar ba. muci gaba da addu'a baki d'ayan mu, Allah ya zab'a mana abinda yafi alkhairi, idan da alheri yasir yazo Allah ya dai-daita tsakaninku, idan kuma da akasin haka ne Allah ya tsareki ya raba tsakaninku cikin sauk'i."_

+

_Ajiyar zuciyar itama Asy tayi sannan tace "ameen ya Allah na gode sumayya, haqiqa shawararki tafi kwanta min fiye da ta yaya Rahama, na gode Allah ya bar qauna tsakanin Mu." murmushi sumayya tayi tace "ameen qawata." nan suka ci gaba da hirarrakin su Asy na taya sumayya 'yan ragowar aikace aikacen da suka ragewa sumayya sannan daga bisani suka yi sallama ta koma gida_.


************


_Ko kad'an bata ruwa pure water guda biyun da sajida ta ajjiye mata take yi ba, burinta kawai Sajida ta nuna mata iphone 8 da take maganar nuraddeen ya siya mata, tuni sajidan ta fahimci hakan sai ta qyalqyale da dariya ta miqa hannunta saman d'an qaramin mirrow dake d'akin ta jawota ta cillawa ruqayya kan cinyarta, ba bata lokaci ta cafe ta soma kallon wayar tana jujjuyata gami da zare idanuwa cikin mamaki tace._


_"Da gaske sajida taki ce iphone 8 ce da gaske?", tsaki sajidan tayi fuskarta d'auke da murmushi tace mata "ki bud'e ki duba mana gani ai ya kori ji, ke kika yi wasa da damarki da tuni kema yanzu kin mallaki taki irinta." Ta fad'a hankali kwance tana kwanciya ruf da ciki kan katifarta fuskarta na fuskantar ruqayya da tuni ta soma danne danne a wayar._


_D'akin yayi shiru har ruqayya ta gama danne dannenta sannan ta dubi sajida bayan ta saki ajiyar zuciya "gaskiya na tayaki murna qawata, haqiqa kin kere sa'a, na tabbata cikin qawayenmu kece ta farko da kika fara mallakar wannan wayar, hatta da su Maamaa dake faman bawa maza kansu har yau basu kai ga cimma wannan gashin ba." ido sajida ta kad'a ta ja tsaki sanna tace "banzayen ba." gyara zama ruqayya tayi sannan ta sake duban sajida tace "to yanzu ya za'ayi ki hadu da Zaraddin din, ni kam na amince na amshi soyayyarsa." dariya sajidan ta dinga qyalqyalawa sannan tace "dama abinda zahradden keson ji kenan ke kika qi amincewa tun tuni."_


_Tayi maganar tana miqa hannu ta amshi wayarta dake hannunta tana neman layin nuradden, flashing kawai tayi masa duk da yawan kud'in dake wayarta babu dad'ewa kuwa ya kira ta._


_Sakin baki kawai ruqayya tayi tana kallon yadda sajidan keta fama maqale murya da marairaicewa, sam bata jin ma abinda take fad'a duk da tana kusa da ita, daga qarshe suka yi sallama._


_Kallon ruqayya tayi tana dariya tace "kin daki sa'a kuwa don suna tare da zahradden d'in ma, yanzu haka ma anjima zasu zo tare bayan magariba uban zumudi."_


_"Ni da zan koma gida kafin magaribar kuma sajida? ban cewa mama zanyi dare bafa." ta karasa maganar da alamun damuwa k'arara kwance a fuskar ta_.


_Tsaki tayi tace "sai ki kirata kice kin rakani unguwa da mun dawo zan rakoki har gida nasan babu abinda zata ce miki."_


_"Haka za'ayi, amma babu credit a wayata, sannan kuma kayan jiki na kina nufin da su zan fita?"._


_Waya Sajida ta cilla mata tace "ki kira ta awaya ta, kaya kuma akwai nawa sai in baki ki saka duk ba damuwa bace." take rukayya ta kira maman ta tsarata, mama bata ce komai ba sai fatan Allah ya tsare, "kuyi qoqari ku dawo akan kari." rukayya ta amsa da "to." tare da katse wayar. hakan kuwa ya musu dad'i gaba d'aya ganin sun cimma tsara maman da suka yi._


_Ido kawai ruqayyan kebin sajida da shi sanda take zuba kwalliya, kwalliyar da tunda suka idar da sallar magariba take yinta har yanzu taqi ta qarewa, sai da ta tabbatar komai yayi mata dai-dai sannan ta juyo suka had'a ido da ruqayyan_.


_"Kina ta kallo na kamar baki sanni ba?"_


_"Ai dole ne na kalleki, sai zuba kwalliya kike kamar wadda zata je dinner?"_

_murmushi ta saki "ya za'ayi mutum yana miki hidima kuma yaqi gani a jikinki, haka zaki dinga yiwa zahradden kenan? bugu da qari ma dole ki nuna masa kefa 'yar ado ce 'yar gayu ce, hakan ne zai sanya duk wani abun ado da kika buqata daga gareshi zai siya miki saboda yasan ba qaramar mace bace ke......kinga kada su qaraso bamu shirya ba d'auki kayan ki saka don Allah"._


_Dariya kawai rukayya tayi tana d'aga kayan da sajidan ta fito mata da su, lace ne swiss mai kyau d'in kin riga da skirt, ba qaramin amsarta kayan suka yi ba, hakanan sun burge ruqayyan har ta dinga kallon kanta, sajida ta lura da hakan sannan tace "kwantar da hankalinki, indai kina da zahradden a matsayin masoyinki toh kuwa babu shakka irin wad'an nan laces d'in sai kinyi kyautarsu wallahi."_


_Jin-jina kai rukayya tayi ta shiga gyara fuskarta cike da mamakin irin kud'i da kyauta da wad'an nan samari ke dashi_


_Cikin hadadd'iya kuma tsadaddiyar motarsu ake zancan, sajida da nuradden na gidan gaba, ruqayya da zahradden na baya, tun rukayya tana d'ari d'ari na rashin sabo har ta d'an saki jikinta ganin cewa zahradden d'in a kame yake, yana zaune can nesa da ita babu wani alamu na rawar kai a tattare da shi. kusan awa guda suka kwashe suna hirar sai da ruqayya ta soma qorafin zata tafi gida sannan suka an kare da lokacin da suka ata.6_


_"Amma ina ganin ku d'an fara raka mu wata unguwa tukun ko?"_


_Da sauri ruqayya ta d'an had'e rai tare da girgiza kai tace "a'ah gida gaskiya zan tafi dare nayi fa." sajida ta karb'e zancan da sauri "haba ruqayya nace miki har gida zan rakaki kuma du..du..du qarfe nawa yanzu, takwas ma fa saura minti goma."_


_"To ki daure ki ara mana minti goman kacal yanzu zamu dawo gimbiya Rukayya." cewar zahradden cikin salo irin na ma'abota qauna, tilas rukayya tayi shiru don sun rinjayeta, sannan nuradden ya ja motar suka bar layin._


_wani katafaran Mall suka nufa, kallon d'aya zakayiwa Mall d'in kasan cewa manyan masu bugun Abuja ke nufar Mall d'in. Ba qaramin kad'uwa rukayya tayi ba ganin irin kud'ad'en da zahradden ke b'atar mata ba cikin qaton shopping mall din ba, binsa kawai take da kallo tana son taga qurewar qaryarsa don gani take sam baze iya biyan kud'ad'en ba. manyan atamfofi shaddodi da laceses yake d'auka hakanan takalmi jaka da kayan cosmetics_.


_Bata tsinke da lamarin ba sai da suka zo gun biyan kudi taga sajida da kwatankwacin tata siyayyar har tana qarawa da wasu kayan ma nuradden din na taya ta sannan taga zahradden ya d'auko kudaden daga aljihunsa ya had'a duka ya biya nata da na sajidan ba tare da yaji ko d'ar a jikinsa ba_.


_Jikinta a sanyaye har suka dawo da su suka sauke su sajida ta saka yara suka jidi kayan suka shigar musu da su gida, tunaninta daya ta yaya zata doshi gidansu da wannan kayan, tace uban wa ya bata su? ga mamakinta da suka shiga gidan maman sajidan ko ajikinta sai sannu da zuwa ma da tayi musu abinta taci gaba da sab goginta._


_Sajida ta fuskanci yadda jikin ruqayyan yayi sanyi don haka tace "wai lafiya kike kuwa qawa?, ko zahradden d'in bai miki ba kya son shi?!" kai ta girgiza don batun zahradden bai mata ba ma bata taso ba "a'a ko d'aya, kawai ina tunanin ta ina zan shiga da kayan nan cikin gida? kuma nace waye ya bani?"_


_Kafad'a sajida ta d'aga tace "idan don wannan ne ai baki da damuwa, saiki barsu kawai a gidan nan, umma bata da matsala duk lokacin da kike da buqatar amfani da su saiki biyo ta nan ki dauki abinki kiyi amfani da shi kawai ko kuwa?" tabbas hakane dan kuwa rukayya bata hango wata mafita da ta wuce wannan ba don haka ta aminta da shawarar, sai da ta shiga ta sauya kayanta da tazo da su sannan suka fito sajidan ta rakata gida tana sake jaddada mata ayanzu bata da wata matsala fa, duk abinda take da buqata ta sanar da zahradden kawai ta gama mallakarsa, duk da taji shi din ma yana gaya mata, sannan kuma "kada kice zaki yi kawaici ko zaki ji kunya." a san yayaye rukayya ta gyad'a mata kai_.


************


_A sanyaye ta sake kallonsa sannan ta ambaci sunan shi,_

"Yasir wai me yake damunka ne cikin kwanakin nan, gaba d'aya ka koma wani sukuku da kai? na tambayeka har sau biyu kace min babu komai? ka tab'a ganin inda babu ta saka mutum a damuwa, ai hausawa sunce gaida me gaidaka koda baxai amsa ba?"_


_D'an murmushi ya saki sannan ya gyara zamansa kan tabarmar "Asy sai a yanzu na tabbatar da cewa haqiqa nayi dacen masoyiya ta gari, wadda ta damu da damuwata, wadda ke sona don Allah ba don wani abu da na mallaka ba, kuma ina fatan zaki cike siffofin nan naki ta hanyar share min hawaye na."_


_Shiru suka yi dukkan su kowa da abinda ke cikin ransa._

_Sake numfasawa yasir yayi yace "haqiqa Asy akwai abinda ke damuna wato cikin watannin nan gaba d'aya harkokin kasuwancina sun tsaya, na rasa gane kansu da gindin su, komai na tab'a sai ya zama asara, komai ya tsaya cak samuna ya fara rawa, na rasa meke faruwa, ana cikin haka d'aya daga cikin abokaina ya shawarceni da muje zai rakani gurin wani malami ko da taimakon da zai iya yimin, muna zuwa kuwa kin san abun mamaki?" Asy da ta saki hanci baki da kunne tana kallon yasir ta girgiza kanta, don tun lokacin da yazo da batun gidan malami taji tamkar an saka guduma an sare mata gwiwoyinta, jikinta yayi sanyi qalau._


_Ya sake gyara zamansa yace_


_"Wallahi Asy ashe hannu aka samin, abokan kasuwanci na ne suka saka min hannu." ya k'arasa maganar alamun abun tausayawa_

_"Subhanallah" Asy ta fad'a cike da mamakin yasir d'in da sauri ya dora ganin yadda yanayin fuskarta ya sauya "wallahi Asy amma malamin ya taimakamin sosai, fata na d'aya kema zaki shiga cikin sahun wad'anda zasu taimaka min din don ci gaba na naki ne Asy, tunda ke nake da burin ki zama mata a gareni." ya fad'a yana tsatstsare ta da ido_.


_Murmushi ta saki bayan 'yar gajeriyar shawarar da zuciyarta tayi saurin bata cikin sakan uku "me zai hana yasir ai duka yiwa kai ne."_

_Fuskarsa ta fad'ad'a da murmushi sanan ya d'an karkata kad'an ya cusa hannunshi cikin aljihun rigar shaddarsa._


_Qyalle ne fari qaal ya fito da shi ya riqeshi a hannunsa yana duban Asy da take kallon qyallen "kinga abinda ya bani, kin san me za'ayi da shi?" kai ta girgiza "cewa yayi na samu mace mai jinin al'ada idan ta fara ta shimfid'a qyallen a matsayin pad dinta tayi jinin a kai, to in sha Allahu da tayi shikenan dukkan al'amura na zasu dai-daita" kai take jinjinawa shi kuma yaci gaba da kallonta "ai babu komai don wannan ai ba damuwa bane yasir" ta fad'a tana murmushi, cike da jin dadi yace "na gode na gode My Asy, Allah ya barmu tare, "yanzu saura kwana nawa kenan ki fara?" d'an jim tayi sannan tace "saura kwana uku ko hud'u."_

_"Alhamdulillahi! to gashi don Allah kada ki manta my dear, da kin fara ki shimfid'a don Allah." hannu ta saka ta amsa tana cewa "kada kaji komai in sha Allah bazan manta ba"_

_Jikinta har rawa yake lokacin da suka rabu ta soma neman layin wayar sumayya, abu na farko da ta fara cewa bayan ta daga shine "kina ina, kina gida?"_


_"A'ah kin manta ina gidan yaya sadiya, ba shekaran jiya nake gaya miki ta haihu ba gata ma suna, amma lafiya kike kuwa Asy?" Kai ta girgiza sannan ta zayyanewa sumayyan yadda suka yi yanzu da yasir din, ajiyar zuciya sumaiyan ta saki sannan tace "ki kwantar da hankalinki abinda nakeso dake kawai shine ki ajjiye qyallen kada ki soma amfani da shi, ranar sunan in sha Allah zan dawo sai musan abinyi." sai da tabbatar ta kwantar ma da Asy hankalinta sannan suka yi sallama_.

************

_Cikin kwanaki qalilan ruqayya ta yadda da zancan sajida, sai a lokacin ta sake tabbatarwa da zancan sajidan, wautarta take gani da tun asali bata amincewa zahradden ba'a yanzu kam bata da duk wata matsala data danganci kud'i, a boye take bushasharta, waya zaraddin yaso canza mata irinta sajida ta qiya tace ba yanzu ba saboda gida._


_Kusan shopping har ya fara zame mata jiki, wani lokacin idan taje da wasu abubuwan gidan sai tayi qarya maman fadila maqociyarsu ce ta bata musamman kayan ciye ciye haka kona qyale qyale, tasan maman ba zata bi ba'asi ba saboda mutuncin dake tsakaninsu, haka nan matar akwai kyauta kuma babu laifi mijinta mai wadata ne_.


***********

_Qarfe biyar da mintina ne na la'asar, tana zaune kan kujera 'yar tsuguno tana yankan kub'ewa da zasuyi miyar dare da shi wayarta ta d'auki ruri, tana kan cinyarta don haka hannunta kawai ta cire ta daga wayar da sauri ganin sunan sumayya_

_"Kin dawo ne sumayya?" Asy ta fara tambayarta, dariya sumayya ta d'an saki tace "haba malamarsu ai sai gobe ake sunan ma ko?"_

_Murmushi tayi! "ayyah ai na manta wallahi na qagauta ne ki dawo, kira na yake yana ta tunamin zancan qyallen fa, tunda kinga alissafe gobe nace masa zan fara." Ta fad'a cikin yin qasa da muryarta duk da tasan da wuya ma maman ta ji kasancewar hayaniyar yara dake wasa a soron gidan ta karad'e tsakar gidan._

_"Kwantar da hankalinki na samo mana mafita ai karki damu...."_


_"Hmmmm Mafitar me sumayya ta nemo masu?" Ku biyo ni dan jin wanana lbr domin babu karya ko k'age a lbrn, Tabbas ya faru da gaske_

C*ike da zumud'i da son jin mafitar da suka samu Asy ta tambaya.+

"Meye mafitar kenan?"
"Cool down friend, kinga gobe sunan yaya sadiya kuma za'a yanka ragon haqiqa amma da safe, shine nace mai zai hana ki taho da qyallen nan mu tari jinin ragon kawai mu zaba kan qyallen sai ki bawa yasir d'in?".
1
Wani farin ciki ya mamayi Asy da sauri tace,
"faqat!, wannan shawarar tayi wallahi kamar qarfe nawa kike ganin zanzo d'in?"

"Kamar takwas haka ko ina ganin yayi."
"Shike nan babu damuwa Allah ya kaimu zanzo."

"Ameen ameen ki gaida mamah"

Da haka suka yi sallama.

***********
Kamar kowan ne lokaci qarfe tara na dare suka sauke su qofar gidan su sajida, suna shirin fita suka dakatar da su Zahraddin ya bud'e aljihun gaban motarsa ya ciro wata leda kana ya dubesu yace.

"Yammata d'an wani aiki zamu baku don Allah."
"Ok Wanne irin aiki ne haka dear da har sai ka roqemu ma? ai umarni kawai zaka bada"
Inji sajida wadda tayi maganar tana fari da idanuwa. murmushi ya saki yana duban ta yace,
"Ni na sani bani da case dake ai, qawarki ce nake ganin ba zata iya ba".
1
Da sauri zahradden ya amshe zancen ta hanyar cewa.
"kaga malam, nima banda matsala da princess d'ita, yadda kuke da fahimta da taka gimbiyar haka yake tsakani na da tawa, ko ba haka ba tawan?"
Ya fad'a yana kashe ma ruqayya ido, kunya da farin ciki ya kamara mata tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta tana murmushi game da gyada mai kai.
Dariya Nuradden yad'an saka yana fadin,

"Well dama haka ake so ai."

Ya d'auki ledar da ya fito da ita d'in ya kunceta, goro ne 'yan madai-daita guda biyu farare, ya miqawa sajida d'aya sannan ya miqawa zahradden shi kuma ya bawa ruqayya,

"Na meye wannan?"

Sajida ta tambaya tana jujuya shi.
"Wannan shine aikin da zamu baku da daddare zaku sanya shi a mafitsararku ku d'an tura shi ciki kad'an kada ku tambayi amfaninsa, da kanku zaku gani."

Ya fad'a fuskarsa qunshe da faffad'an murmushi.
Itama murmushi sajidan tayi ta zuge jakarta ta jefa shi tana fadin.

"Ok dear."

Zahradden ya dubi ruqayya ya d'age mata gira.

"Kin gane princess?"
Ta d'an sadda kai kana tace "eh." hira suka sake tab'awa kad'an sannan suka yi sallama kowacce dauke niqi-niqi da ledojin shopping d'inta. suna shiga ruqayya ta bud'a kayanta ta debi wasu daga ciki ta bawa sajidan ajiya kamar yadda suka saba tana fad'in gida zata wuce sai sunyi waya.

*************

Qarfe takwas ta isa gidan yaya sadiya, barka kawai tayi mata sumayya ta janyeta can bayan gidan inda aka ajjiye ragunan ana jiran mahaucin da zai yanka yazo.
Suna zaune suna tab'a hira sama-sama har ya qaraso d'auke da wuqaqensa da yaronshi qwaya d'aya da yake tayashi tare da mai gidan suka shigo gurin ya nuna musu komai kana ya fice yabar bayan gidan.

Yana gama yanka ragon ya janye shi can gefe ya d'ora kan wani buhu ya fara fid'a. qarasowa suka yi suka d'ebi jinin cikin wani dan mazubi kana suka fice daga gidan.
Gidansu sumayya suka nufa don sun san babu kowa duk suna gidan sunan, d'akinta ta bud'e suka shiga duka suka zube kan katifarta.
Asy ta fidda qyallen ta shimfid'a sannan sumayya ta ninka shi irin ninkin pad ta kwarara jinin a jiki, nan take ya tsotse kuwa, dariya Asy tayi tace.
"Gaskiya qawalli kina da dabara, yanzu wannan waye zaice ba jinin bane, harda dan guda gudan nan fa"
"ke dai rabu da shi, saima goben kafin nan ya dad'a turuwa sosai ki d'auke ki samu baqar leda kawai ki qulle muyi mu koma gidan sunan."

Ta fada tana miqo mata ledar.

*******

A cike suka tadda qofar gidan gefe kuma ga jami'an 'yan sanda ne a tsaye anata cece kuce. ganin basu fahimci abinda ke faruwa ba sai kawai suke shige cikin gidan nan ma kamar wajen ana tsaye ana ta maida magana, sumayya ce ta dubi mai jegon tana ambays.

"Wai yaya sadiya me ya faru ne?"
"Hmmm wani abun al'ajabi ne ya faru, mahaucin dake yanka ragon suna ne wai yana cikin fid'a ragon ya bace bat! sama ko qasa kiji fa wani rainin hankali, shi kuma abbansu Saddam yace bai yadda ba shine ya d'auko masa 'yan sanda".
Had'a ido a kayi tsakanin sumayya da Asy, dukkan su abu guda ne ya ziyarci zuciyar su, take jikin Asy ya fara rawa tsoro da tausayin mahaucin ya kamata.tabbas babu tantama da tuni yanzu ita ake cigiya ba ragon ba, da tuni itace kenan ta b'ace..!5

"Kamar yaya Asy?"
Taji yaya sadiya na tambayarta, bata sani ba ashe zan can b'oye ne ya fito fili, hannun sadiyan ta kama ta jata can uwar d'akinta inda ba kowa sumayya tabi bayansu.

Basu b'oye mata komai ba suka sanar da ita, ita kanta jikinta ba qaramin sanyi yayi ba. babu shakka yasir kodai dan qungiyar asiri ne ko ta mashaya jini. take ta d'auki wayarta ta kira mai gidan nata cikin lokaci qanqani ya iso, yadda suka sanar mata haka suka gaya masa.

Ya dad'e shi kansa bai iya magana ba gumi na yanko masa daga bisani ya miqe yace yana zuwa ya koma qofar gidan ya bawa 'yan sandan umarnin su saki mahaucin bai da laifi.
**********
Ruqayya na shiga gida d'akin ta kawai ta wuce sannan ta dawo tsakar gida ta d'aura alwalar sallar isha'i da bata samu tayi ba don ta gaji sosai shi yasa ko abincin dare bata nema ba duk da dama a qoshe take don sunyi ciye-ciye da maqulaashe a fitarsu.

Tana gama idar da sallar ta dora kanta gefan kujerar dake d'akin da niyyar yin azkar idan ta kammala sai ta sanya goron da zahradden ya bata idan yaso sai ta kwanta ta huce gajiyarta. bata kai ga kammala azkar d'in ba wani qaqqarfan bacci yayi awon gaba da ita a gurin.
2
**********

I iPhone 8 d'in sajida ce a hannunta take ta faman kiran ruqayyan babu qaqqautawa sai dai bata d'aga ba, tilas ta ja tsaki ta haqura tana fad'in "hala wannan kasar tayi bacci dama tana son gaya mata ya bar ice cream guda d'aya a kayanta kuma zai iya narkewa tunda ba fridge garesu ba balle ta saka mata, sai ta koma ta kwanta rigingine ta bud'e data d'inta ta hau WhatsApp.

Kusan awanni biyu ta shafe tana online kana daga bisani ta kashe ta sauka jin bacci na rinjayarta, jakarta ta janyo ta d'auko goron gun nuradden ba b'ata lokaci ta gyara zama ta cusa shi cikin matucinta kana ta gyara kwanciyarta, cikin qanqanin lokaci bacci yayi gaba da ita.
*******
A firgice ta farka tana salati saboda tunawa cewa bata saka goron da zahradden ya bata ba, sai dai tana duba agogo ta tarar bakwai saura na safe, baqin ciki ya kamata ganin babu damar saka goron tunda gari ya waye dole sai wani daren, lallab'awa tayi ta fito tsakar gida a sace ta d'aura alwala ta koma don kada innarta ko babanta su ganta tasha fad'an makararta sallah.
3
Tana idarwa ta janyo wayarta, missed call din sajida ta fara cin karo da shi, ba b'ata lokaci tabi kiran.
Maimakon muryar sajida sai taji muryar mamanta cikin sautin kuka.
"Lafiya Mama? me ya faru? ina sajidan?"
"Sajida muna asibiti da ita ruqayya tun asuba."
Ido ta zaro cikin fad'uwar gaba take tambayar me ya faru.
"Bamu sani ba muma, mun fito sallar asuba kawai muka jiyo ihunta mun zuwa muka tadda ta male male cikin jini yanzu haka tana nan rai a hannun Allah."
Ba qaramin gigicewa ruqayya tayi dajin jawabin, kai tsaye ta sanar da mahaifanta suka yarje mata taje kafin anjima suma suje, ba b'ata lokaci ta fice tayi asibitin.

Yanayin yadda taga sajidan ya d'aga mata hankali matuqa, sam bata san waye a kanta ba jini kuma bai fasa zuba ba ana dura mata wani yana ficewa, cikin dabara tabi qannen sajidan da zasu koma gida su sake d'auko zannuwa sabida jinin dake zuba yati yawa,jakar da suka fita jiya ta duba bata ga goron da aka basu tare ba, take ta yankewa ranta anya ba shi sajidan tayi amfani da shi ba? wayarta na hannunta don haka ta hau bincika chart d'insu da nuradden kafin ta kwanta take taci karo da inda yake sake jaddada mata maganar saka goron ta sanar masa yanzu nnan suna sallama zata saka.

A rud'e ta sauka ta fara kiran layin nuradden d'in don ta gaya masa b'ar nar da goron ya yiwa sajida sai dai duk kiran data dinga faman yi layin is switches off, take tasha jinin jikinta.

4
Wuni guda tana kiran layin amma yaqi shiga, take tsoronsu nuradden ya kamata don hatta layin zahradden ma tun safen ba shiga yake ba.

Wunin gabaki d'aya a firgice ta yishi musamman duk lokacin data dubu qawartata ta ganta kwance rai a hannun Allah. Har ta koma gida bata fasa kiran layukan wayar Nuraddin da zahraddin ba sai dai har yanzu dai amsar d'aya ce layukan a kashe suke..

+

*******

Qarfe bakwai na safe ta gama k'intsawa tsaf don tafiya asibitin zata iya cewa kwanan zaune tayi ranta cike fal da fargaba da tsoro. burinta kawai taga yadda jikin qawar tata ya kwana.


D'aki ta leqa ta samu maman su na shirya qannanta da zasu wuce makaranta ta sanar mata zata tafi asibitin, duban ta maman nata tayi tana sakawa qaramar qanwarsu safa tace.


"Amma ko karyawa kya tsaya kiyi ai ko?"

Kai ta girgiza idonta cike da qwallar dake son zubowa tace.


"A'ah mama ba zan iya ba na karya kawai a can."

Shiru tayi tana sake jin tausayin yadda jikin sajidan yayi don ko ita d'in ma jiya da ta ganta ta sare da lamarin, jini na fita daga jikin d'an adam kamar koroshi ake yi.

"Shike nan ki gaishe su, ki sake yi mata sannu da jiki Allah ya sawwaqe, babanku ya d'an fita amma gashi."

Ta fad'a tana miqa mata d'ari biyu kud'in mota tana cewa.


"Idan ya dawo na sanar masa kin tafi."


Duk da kud'i a jikinta irin ragowar kud'in da su Nuraddin ke basu amma bazata bar suba kuma hakan bai hanata amsa ba don yanzu tsoron tab'a duk wani abu da ta san daga hannunsu ya fito take yi. Domin tana da zargi mai qarfi akan su.


   Cikin abun hawan ma saqe-saqe tayi ta yi har suka isa asibitin, abakin qofar d'akin da sajidan take ta hango maman su tsaye ita da qannanta mata su biyu, cikin hanzari ta qarasa gwiwarta ta qarasa sabulewa ganin idanun kowannen su jage-jage da hawaye, sai ta kasa tambayarsu abinda ke faruwa ta shiga bin su da ido.

Maman ce tayi qarfin halin cewa.


"Sannu ruqayya har kin iso? jikin qawartaki ne ya motsa sai dai addu'a kawai."


Bata san hawaye take ba sai da taji sun fara shigar mata cikin baki taji gishiri-gishir.


    Tsawan kimanin minti goma suna tsaye kafin qofar d'akin ta motsa, likitoci biyu ne da nurses biyu suka fito da sauri suka tare su, d'ayan likitan gaba yayi sauran suka tsaya kallonsu likitan ya d'an yi kamar bazai yi magana ba sannan yace.


"kuyi mata addu'a kawai hajiya, wanda ya fiku sonta ya karbi abarsa, Allah ya sanya iya bakin wahalarta kenan."

7

Kuka qannan sajidan suka saka tare da d'ora hannu aka, Ruqayya kuwa ji tayi kamar ana jij-jigata sai ta sulale kawai qasa tayi zaman dirshan sai ta rasa inda take duniya ce ko wani sashi na daban?amon muryar kukan qannan sajidan ne kawai ke mata amsa kuwwa cikin kunnenta cakud'e da maganar da likitan ya fad'a.


Bata sake fahintar komai ba, bata kuma san tsawon awannin data d'auka zaune a haka ba sai data ji an dafata ana qoqarin d'aga ta. Maman sajida ce wadda idanunta suka rine sabida kuka tace.

"Tashi ruqayya mu tafi an saka gawar cikin mota"


Binsu kawai take har zuwa bakin titi inda suka tsaida adai-daita suka shiga ita da qannan sajidan suka bi bayan motar gawar.


   Gani take kamar ba gaske ba, meke shirin faruwa da su ne? su Nuraddin su waye? goron me suka basu?, dama jinin su suke nema?, dama duk bautar da suka musu jininsu suke da buqata?"


1

Tambayoyin da suka had'u suka dinga dukan ruqayya kenan, su suka sata ta sake susucewa har tafi 'yan uwam sajidan shiga tashin hankali.


Ta kasa mance abun ta kasa shafeshi daga ranta, kamar almara ta rasa sajida wa zata gayawa sanadiyyar rasa qawarta aminiyarta?, sosai tsoro ke shigarta ko baccin arziqi rasashi tayi daga wayarta harta sajidan duka ta cire layukansu ta musu mugun b'oyo, tana gani aka dinga fidda kayan da sajidan ta bari da wanda ita ke bata ajiya cikin irin siyayyar da su nuraddin ke musu ana rabarwa. bata ko d'aga kai ta dube su ba balle tace da nata don ko rab'arsu bata sanyi.


*************


  Kuka ta sake fashewa da shi bayan ta kammala bawa maman sajidan labarin abinda take da yaqinin shine silar mutuwar qawarta ta.

Hawaye ne kawai ke biyo kuncin maman tana sharewa tare sa cewa.


"kaico na, kaico na da na zubawa tarbiyyar d'iya ta ido. kaico na da kwad'ayi yasa na kasa yiwa 'yata waigi daga kwashe kwashen samarin da take yi wanda ni a ganina duka farin jini ne ashe ina turata ne ga mahallakarta, gaskiyar hausawa da suke cewa k'uda wajen kwadayi yakan mutu, gashi naga zahiri haqiqa ruqayya ko da kuna da laifi nima na taka rawar gani matuqa, tunda agabana kuke komai na kasa tsawatar muku, yanzu da akanki hakan ta faru me zance da iyayen ki?, naci amanar su wwyyo Allah dama ana iya maida hannun agogo baya."


Ta fad'a itama tana rushewa da wani sabon kukan.


***********


Cikin qaramin lokaci rayuwar Ruqayya data Asy ta sauya, samari suka zamto musu tamkar dodanni basa tab'a yarda su kulaka duk inda kakai ga na cinka matuqar baka gabatar da kanka ga magabatansu ba kuma sunyi kyakkyawan bin cike a kanka ba, ko da hakan ta faru ma babu batun su kulaka sai sun samu izini daga garesu. tuni suka fahimci cewa ba tarin samari ne farinjini ga d'iya mace ba, haka nan ba siye-siye da kashe kud'i ko kyautar maqudan kud'i ke nuna nagartar saurayi ko arziqinsa ba. A'a mutunci, ilimi, kyakkyawar nasaba da kyakkyawar mu'amala shine gaba da komai, a yanzun sun ga izina kuma su zasu bawa wata labari, sun sake yarda cewa rayuwa ta zama abar tsoro haka nan ta sauya baki d'ayan ta darajar d'iya mace na tafin hannunta, ruwanki ne ki sai wa kanki daraja da qima da tsoron mutunci, ruwanki ne ki watsar lah shakka kuwa a guje zaki samu masu ta yaki tattakawa.

    Sai addu'arsu ko da yaushe ta koma ta Allah ya basu mazaje na gari salihai masu kyakkyawan hali kamar yadda suka kasan ce haka. Allah ya kyautata zuciyar mu yasa Mufi karfinta, ya kuma tsare mun dg sharrin *SAMARIN BANA*


    *Tammat bi hamdillah*


*Duka duka anan na ajiye alkalamina, abunda nayi daidai Allah ya bamu ladansa, kurakuran ck Allah ya yafe mana baki daya*


_Godia ga dukkan masoyana_ 😍

Post a Comment for "SAMARIN BANA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...