SABON AL'AMAREE CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SABON AL'AMAREE CHAPTER A

SABON AL'AMAREE CHAPTER A

- - Post a Comment

 SABON AL'AMAREE CHAPTER A


SABON AL'AMAREE
                                         


NA BILKISA IBRAHIMDa sunan ALLAH mai rahma mai jin'kai, ya ALLAH kabani ikon fa─Ćin abinda zai amfanar da al'ummarka, ka tsare harshena daga fa─Ćar abinda zai cutar da al'ummarka.AMIN

Ina mai farin cikin sake ha─Ćuwa daku asabon littafina mai suna SABON AL'AMAREE, ALLAH yasa mu amfani abinda zaizo aciki. AMIN.

NA sadaukar da wannan littafi ga dukkan masoyana, aduk inda suke.
    Duk wanda yacanja mini wani abu aciki ban yafe masaba wlhy.

YABO DA JINJINA
    Ga gareku writers gaba ─Ćaya, musamman.

☆ Abba gana.    
☆ Ayusher muh'd.
☆ Rayfat yahaya.
☆ billy galadanci.
☆ leemcy.
☆ ummiee khaleel.
☆ ummiee jafar.
☆ xoxo
☆ safiyya galadanci
☆ Mrs JH
☆ cwtjiddah.
   Dama sauran wa─Ćanda ban ambataba,  ALLAH ya'kara basira
               
                                
                                          

Da gudu suka shigo ─Ćakin kowa yana maida numfashi, mama dake zaune abakin gado tana ninke kaya tadaka musu tsawa, kai wai lafiyarku!!!!.???
     Bathroom suka shige batareda sunbawa mama amsaba.
   Mama ta maida kallonta ga 'kofa da ake 'ko'karin bu─Ćewa, tasan tabbas wani suka takalo daga cikin yayyensu, ilai kuwa hasashen mama gsky ne, wani 'kya'ky'kyawan saurayi ba'ki yashigo yana hura hanci, hannunsa ri'ke da belt .
   Ganin mama a tsaye yasa yay 'kasa da kai, ya rissina yana gaisheta, mama ta amsa tana kauda kai gefe, tashi yayi ya fice dan bazai iya cigaba da ─Ćaukar matakin dayay niyyaba.


    Bayan kamar minti goma da fitarsa mama ta ce, "marasa kunya saiku fito!!.
   Saida suka ─Ćan le'ko suka tabbatar yafita sannan suka fito kowa fuskarsa tana nuna alamun tsoro.
   Mama ta hararesu mikuka yimasa?? Marasa kunya!.
   Matasan 'yammatan biyu masu matu'kar kama da juna suka shiga kallon kallo, kowa bayaso yafa─Ći laifin dasukayi, mama tasake daka musu tsawa, wai badaku nakeyi bane??,.
   Cikin rawar baki Nurr ta ce, "mama dama yayane yasakamu gyaran...........saikuma tayi shiru tana sosa 'keya,, mama ta hararesu kunsan ALLAH zan aika akirashi yazo yaci ubanku.
   Da sauri deena ta ce, "gyaran ─Ćaki yasakamu shine muka zauna duba wasu takardu daya ajiye, harya dawo bamu gyaraba, shine yabiyomu zai zanemu.
   Mama taja tsaki kudai kuka sani mara mutunci, kunfison kullum ayita dukanku kamar jakuna ko??, kune zakuyita shan wahala abanza, ni ku fice kubani waje masu kunnen 'kashi kawai.
     sum sum suka fice kamar munafukai, afalo sai la6e2 sukeyi, dan suna tsoron yin gamo dashi.
   Saif dake cin abinci afalon ya bushe da dariyar mugunta harda buga kai da kujera, ya ce, "matsoratan banza, aii wlhy dama na ri'ke masa ku........Nurr ta harareshi to ─Ćan ha─Ći basai ka ri'kemuba yanzuma aii baka makaraba mtsoooow.
   Saif ya harareta kwacika bakifa yanzu tunda kunga ya koma ─Ćaki, wlhy yau daba ─Ćakin mama kukajeba da kun daku, dan nasan da mami ce da badaku zatayi........, deena taja tsaki yanzuma kaje ka sanar dashi mun fito mana.
   A'a mikukeci nabaka na zuba, aii wlhy nasan ba 'kyaleku yayi ba............kafin yarufe baki wani saurayi mai tsananin kama dana ─Ćazu yashigo falon, 'yammatan suka sake ranta ana kare zasu afka ─Ćakin mama.
   Da sauri saurayin ya ce, "ku kuma lafiyarku????, sukaja birki danjin ba muryar na ─Ćazu bane, Saif yasake tun tsurewa da dariyar mugunta, cikin dariya ya ce, "yaya Fahad sun zatafa yaya Mahmud ne, matsorata kawai.
    Yaya Fahad yazauna yana fa─Ćin hala laifi sukai masa?, eh mana laifi sukai masa yabiyosu zai laka─Ća suka sha a ─Ćakin mama, shine dasukaga ya koma ─Ćaki suka fito zasuyi mana salo.
   Yaya fahad ya maida kallonsa ga matasan 'yammatan yana murmushi, ya ce, "autara's bakwajin magana ko ka─Ćan wlhy, aii yaya Mahamud ─Ćinne maganinku, saikuzo ku zauna tunda baya nan, danna ha─Ću dashi a gate zai fita.
   Nurr ta ce, "dan ALLAH yaya Fahad da gsk kakeyi??, kar sai mun zauna ya shigo fa."
  Yaya Fahad yay dariya to kuce yau atsaye zaku wuni kenan?..........mami dake sakkowa daga saman daddy ta kalli su Nurr dake tsaye cirko2 kamar kaji, ta ce, "kukuma lafiya???.
    Saiff yashiga zayyano mata yanda akayi,, mami ta hararesu wlhy tun kafin na aika akira mishi ku wuce ku gyara masa ─Ćakin, inkuwa ba hakaba zaku gane kurenku, aini mama bata 'kyauta miniba dabata bari ya jibgekuba, marasa kunya kawai, oya kuwuce mana tafa─Ća tana nuna musu hanyar fita...
    Jiki a sanyaye suka fice dan sunsan ba 'karamin aikin mami bane ta─Ćaukesu da kanta takai masa.
   Awaje suka tsaya suna kallon kalo, Nurr ta ce, "deena mun shiga uku wlhy tsoro nakeji, kinsan dai dukan yaya Mahamud sarai babu sau'ki, ta 'kare maganar da zubo da hawaye.
    Deena takamo hannunta kinga muje kafin yadawo mu gyara masa tunda yaya Fahad ya ce, "baya nan.
   ─Ćakin suka nufa zuciyarsu tana dukan uku uku dan tsoro..................

Kubiyoni masoyana,, cikakken littafin yana nan tafe insha ALLAHU. 
    KUKAN KURCIYA MA yana nan zuwa gareku, muna wasu 'yan gyararrakine,, mungode da 'kaunarku garemu
   Luv u oll.


   Bilyn Abdul
                                         
    luv u oll my fan's
                                          
[12/02 15:10] bilyn Abdul: ------------©2017-------------- 
------SABON AL'AMAREE----
   

NA BILKISA IBRAHIM


BAN MANTA DAKUBA.
☆Ayusha ilyasu.
☆Ummiee Garkuwa.
☆Maman usseey.
☆Maryam G.
☆Rabi'atu sk/mash.
☆Abdul'azez AJJ.
Kuma ALLAH ya'kara muku basira.

            
                                 
                                          
2

...........Atare suka shiga ─Ćakin gsky ─Ćakin ya ha─Ću, tamkar da mace aciki, Nurr ta ce, "mu raba aikin wani yayi bedroom wani yayi falo, yanda zamuyi mu gama da wuri.
    Deena ta ce, "to jekiyi bedroom ─Ćin, amma dan ALLAH karki zauna wasa, dan nasan kin iya shiririta, Nurr ta ce, "matsalarkice kuma wannan, tafa─Ća tana shiga cikin bedroom ─Ćin daya 'kawatu da 'kyawu.
               Dagewa sukayi suna aiki cikin hanzari, burinsu suyi sugama kafin mai ─Ćakin ya dawo, sunkuwa yi saurin gamawa, Nurr ce kawai bata 'karasa wanke bayiba, deena tashiga tana tayata dansu gama da wuri.
    Batareda sun saniba ya dawo, 'kofar yasakama key yadawo saman kujera ya zauna, 'kafa ya ─Ćora ─Ćaya kan ─Ćaya yana jiran fitowarsu.
   Cikin hanzari suka fito Nurr ta kwalla 'kara dan ganin wanda suke tsoron ha─Ćuwa dashi a zaune, da gudu suka isa bakin 'kofar da zummar guduwa, amma sai sukaji 'kofar gam da key, yadaka musu tsawa data sakasu durkushewa awajen suna rawar jiki, tamkar wan─Ćanda suke cikin dusar 'kan'kara.
   Belt ─Ćin jikin wandonsa yaxare yanufi inda suke, tuni suka 'kara tsurewa, Nurr uwar 'yan tsoro harta fara fitsari awando, tuni hawaye sun wanke mata kumatu, dama akwaita da tsoron duka, saikuma rashin kunya fal cikinta, deena tafi Nurr dauriya sosai.
   Ya zazzare musu manyan idanunsa, cikin 'karaji ya ce, "ku bakwajin magana ko,, kun manta da garga─Ćin danayi muku wancan weekend ─Ćin ko??, kun raina kowa agidan nan, saboda kunnen 'kashi.
  Nurr zata fara rantse2 ya zura mata ─Ćaya a baya, ta kwala wani uban ihu kamar wadda aka kashe, itama deena aka bata ─Ćaya, saida yay musu uku2 sanana yabarsu, zuwa lokacin sun cika gidan da ihu.
   Yaya fahad yazo yana bashi ha'kuri sannan yabu─Će 'kofar yafito yana huci.  ALLAH sarki yaya Fahad sarkin tausayi, shigowa yayi yatadasu yana lallashi, yakamo hannunsu zuwa babban falon kowa yana kwasar kuka, suna shiga sukayi arangama dashi a babban falo zaune, da gudu suka shiga ─Ćakin mama, tabisu da kallo rai a 6ace, baki kawai ta cije tafito falon.
    Cikin fa─Ća ta ce, "kai yanzu nan saida kadoki yarannan akan abinda bai taka kara ya karyaba  ko??.
    Yay 'kasa da kai, ALLAH mama yaran nan basa jin magana kwata2, yanzu idan na 'kyalesu gobe zasu yimin abinda yafi haka, tunda kunnen 'kashi garesu.
   Mama ta ce, "ai ka 'kyauta, nakuma gode,, ayi ha'ku yafa─Ća yana 'kara rissinar da kai 'kasa, mami tafito daga ─Ćaki tana fa─Ćin aini yaymin dai2 wlhy, suba sun raina kowaba agidannan??, gobema idan suka 'kara yaymusu wanda yafi haka.
    Mama ta ce, "ALLAH mami kibar zugashi, dan bazan yarda ya illata min yara abanzaba.
   Babu wani illatawa mama, kema kinsan halinsu sarai, inda basuyi masa laifinba ai bazai dakesu ba ko.
   Mama tajuya cikin ─Ĺaki tana fa─Ćin ai dama mami kekike goya masa baya.
   Babu wani goya baya anan, gadai gsky sai a'kita, saboda shi babba an maidashi juji, kuma ba'kya son laifinsu deena agidan nan.
   Ya Mahmud ya ce, "ALLAH mami yaran nan basuda mutunci, kuma ita mama bataso a hukuntasu idan sunyi laifi, karka damu My son daga yanzu suka 'kara yimaka laifi ka zanesu karka ─Ćaga musu 'kafa.
    Mama tana jinsu tayi shiru dan tasan harda halin yaran, yaya Mahmud yanada zafi sosai amma bashida saurin duka, dan bakomai yake saka musu bakiba saboda bashida yawan magana, idan kaga yayi duka to an kaisa ma'kura kenan.

ASALIN LABARIN.
    Sardauna family shine sunan da'ake kiran ahalin dangin.
    Dangine na 'yan boko kuma 'yan kasuwa, dan 'kalilanne acikinsu suke aikin gwamnati, kan mutanan family ─Ćin  aha─Će yake babu wani bare daya isa yaji sirrinsu, ko auratayyama atsaka ninsu sukeyi, kusan family ─Ćin duk auren dangine.
   Basa yarda ─Ćansu ko 'yarsu ya auri bare saidai idan ALLAH ne ya 'kaddara hakan, ko kuma zaka ajiye matar data wuce ─Ćaya, tofa wannan kanada damar auren bare idan kaso.
     Awannan familyne aka samar da Alhji Abdul'malik, wanda ─Ćane na goma awaje Alhaji mutallaf Sardauna.
    Alh Abdul'malik yanada mata biyu da yara tara.
   Hajiya suwaiba itace uwar gidansa, suna kiranta da mama, itama tafito daga tsatson Sardauna family, dan ─Ćiyace ga 'kanin Alh mutallaf, yaranta shidda dashi, Mahmud shine ─Ćanta na fari, dan batama fa─Ćar sunansa, akwai kunya tsakaninta dashi, babu wata sha'kuwa mai yawa tsakaninsu, ko hira bata shiga tsaka ninsu saidai idan ya zama dole, bata shiga harkarsa ko ka─Ćan, bama tafiya sakashi a al'amurantaba, wannan dalilin yasa yafi sha'kuwa da daddyn sa Alh Abdul'malik, dakuma mami.
    Ya kammala karatunsa tuni a fannin kasuwanci, yanzu haka yana kulada kamfanin fahaifinsa mai amsa sunan (SARDAUNA FAMILY CARPETS & RUGS NLM)...................

Kubiyoni a page nagaba danjin 'karshen tarihin.


bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam
          luv u my fan's
[12/02 15:10] bilyn Abdul:
SABON AL'AMAREE
                       

NA BILKISA IBRAHIM

KUNA RAINA.
☆zarah bukar.
☆Manshat.
☆Deedo 'yar ficika.
☆online Hausa writer's.
☆Exquisite online writer's .
ALLAH ya'kara sibirbi─Ća muku basira.

  
              
                                                                                3........Yaya Fahad shine ─Ća na biyu a wajen mama, shine ─Ćan lelen mama dan shikam komai anayi dashi, shima ya kammala karatunsa a fannin kasuwancin, yana tareda yaya Mahmud a kafanin mahaifinsu, wanda yaya Mahmud yake shugabanta.
     Sai Ru'kayya itama tayi karatu yanzu haka tanada aure, tana auren wani muhseen acikin family nasu, yaransu biyu mace da namiji.
   Sai yaya Mustapha shine ke binta, shikan yanzu yake nasa karatun acikin (BUK) zai kammala a wannan shekarar.
    Sai 'yan biyu Saifullahi da maryam, wa─Ćanda suke kira Saiff da Nurr, sukam ko secondary basu gamaba, yanzu suna  (ss 1) dan yaya mustapha yabasu tazara sosai.

   Hajiya wasila itace amarya, wadda suke kira mami,  itama cikakkiyar 'yar family ─Ćince, yaranta uku, Suhaila itace babba, sa'ar Rukayya ce, komai na rayuwarsu tare sukayi, itama tana auren ─Ćan family ─Ćin, yaranta biyu duk maza.
   Sai yaya mubarak shima sa'an mustapha ne, suna makaranta tare yanzu haka, dan komai nasu tarene, idanma baka saniba saikace tagwayene, sai auta madeena, wadda suke kira deena, itama sa'ar su Nurr ce, dan haka komai nasu tarene kamar 'yan uku.
    Nurr da deena ko ka─Ćan basajin magana, akwaisu da jan fa─Ća, dan haka kowa yasansu a makarantar su, tundaga malamai har ─Ćalibai, kowa yasan 'yan biyu,, ba'a ha─Ća sati biyu ba'akawo takardar laifinsuba daga makaranta,, tun malamai na dukansu harma suka ha'kura saidai a aiko gida,, suna tsoron yayyensu sosai dan basa ─Ćaga musu 'kafa,, yaya Fahad ne kawai baya dukansu danshi yanada ha'kuri da tausayi sosai.
   Amma sunfi tsoron yaya Mahmud dan ko ka─Ćan baya shiga harkarsu, yaya Mahmud bayida hayaniya sosai dan bai fiya yawan maganaba, dan ba komai yake saka musu bakiba, idan kaga yana hira sosai to daddyne ko yaya Fahad, saiko mami, dama ita mama 'yar kunya sukeyi da juna, daga gaisuwa babu abinda yake shiga tsakaninsu.
   Yaya fahad ne suke tsananin kama da yaya Mahmud amma muryarsu ta bammanta, hakama hali,, ya fahad yanada sau'kin kai, dan mutumne mai barkwanci, dan idan kaganshi cikin yaran yana hira bazaka ta6a ─Ćaukar yayansu bane.
      Akwai sha'kuwa da zaman lafiya da girmama juna a gidan Alh Abdul'malik, ko ka─Ćan ba'a kishi dan kuwa ana zama irin na yaya da 'kanwa, a gidan akwai fahimtar juna dayima juna uzuri, azukatan ahalin gidan akwai tsantsar soyayyar juna, baka isa ka bambanta yaran gidanba duk suna kama da juna, gaba ─Ćaya a ─Ćakin mama suke, ya Mahmud ne kawai ─Ćan ─Ćakin mami.
   Wannan kenan.

Mun dawo labari.
    Tun daga randa yaya Mahmud ya laka─Ći su Nurr sukayi karatun tanutsu, duk rashinjinsu sai suka rage idan ya Mahmud yana nan,, gyaran ─Ćakinsa kuwa aii basai ya sakasuba, kullum safiya kafin su tafi makaranta suke zuwa su gyara masa, dama sune suke gyara nasu mama da daddy, sauran gurare kuma 'yan aiki su gyara.
   Yau ta kasance juma'a da wuri aka taso daga makaranta, hakama su ya Mahmud masu aiki sun taso da wuri, harsu yaya Mubarak suna gida kowa yana shirin zuwa madallaci,, kasancewar da sauran lokaci duk suna family falo zaune.
  Tunda su Nurr suka sauka daga motar da ake kaisu makaranta 'kirjinsu ke dukan uku2 dan ganinin takalman yayyen nasu reras a 'kofar falon,, deena ta ce, "Saiff da ALLAH kayi ha'kuri karka nuna takardar nan, wlhy zamu baka ku─Ćin makarantarmu na ranar monday.
   Saiff ya ce, "wlhy ban yardaba  ai dama kunsha yin laifi a makaranta dakunga an bani takardar laifinku saiku cikani da da─Ćin baki da al'kawarin bani ku─Ćin makarantarku, amma dakunga na yaga saiku hanani, to wlhy yau saina kai, kuma ya Mahmud zan bamawa ko ya Mubarak dan nasan kunfi jin tsoronsu.
    Nurr harda tsugunnawa tana bama Saiff ha'kuri da ro'konsa karya bayar.
   Ya ce, "wlhy dama kin tashi dan babu ─Ćaga 'kafa wannan karon, ai bani nace kuje ku aikata laifinba,, yana gama fa─Ća yashige falon da sauri, dan zasu iya mur─Ćesa su kwace, da sauri suka take masa baya.
   Da ya Mahmud ya fara cin karo a kujerar farko yana karatun jarida, yayinda sauran kowa ke harkar gabansa, Saiff ya mi'kawa ya Mahmud zungureriyar takardar.
   Ya Mahmud ya'kar6a yana tambayar Saiff tamicece???, saiff ya ce, "ta laifice su deena sukayi amakaranta, hakan yayi dai2 da shigowar su deena falon,, ya Mahmud ya ajiye jaridar hannunsa yana 'ko'karin bu─Će takardar, cikin tsoro su Nurr suke gaida yayyen nasu, ya Fahad ya ce, "autara's lafiya na ganku kamar marasa gsky???.
   Da sauri ya Mahmud ya ce, "inafa sukaga gsky 'yan iska kuzo nan,, jiki na 6ari sukazo suka durkusa gabansa,, ya Mubarak dayake tsaye yana na─Će dutsen guga daya gama guga yanzu, yazo ya rankwashi kawunansu yana fa─Ćin muna fukai, aii ni tunda suka shigo nasan basu aikata alkairiba.
   Ya Mustapha ya hararesu aii wa─Ćan nan yaran su ka─Ćaine suke bamu ciwon kai agidannan shima yabasu rankwashi ─Ćai2.
  ALLAH sarki ya Fahad sarkin ha'kuri shine kawai ya ce, "to kuyi ha'ku dai, ya Mahmud misukayi???.
    Ya Mahmud ya mi'ka masa takardar yana fa─Ćin A'a 'yar wani suka laka─Ća a makaranta kamar sune suka haifeta, shine akace ana neman daddy ranar monday, dan baban yarinyar ya ce, "bazai yardaba.
   Ya Mustapha ya ce, "marasa mutunci nida Mubarak zamuje, dama ranar bamuda lectures ─Ćin safe,, wlhy agaban asambili zamusa a tu6eku a zane,  masu kunnen kashi kawai.
   Cikin rawar murya deena ta ce, "wlhy ita tajamu kuma harda kairat da farhan ─Ćin gidan abba 'karami, wlhy bamu ka─Ćai bane.
   Ya Mahmud ya daka mata tsawa dallah kiyima mutane shiru!!, idanma hardasu ai kune shugabanni, bari mu dawo masallaci jikinku saiya gaya muku, hardasu farhan ─Ćin zan ha─Ća na lallasaku, yana gama fa─Ća ya ─Ćauki jaridarsa ya fice, ya mubarak da ya mustapha ma suka fice suna harararsu.
   Ya fahad dayake zaune yadawo kujerar da ya Mahmud yatashi, cikin sau'kin murya ya ce, "wai miyasa ku bakwa jin maganane??, kun fison kullum ayita dukanku dayi muku fa─Ća agidannan??, har kun manta da dukan da ya Mahmud yay muku ranar ko??.
   Cikin zubarda hawaye suka ce ALLAH ya Fahad yarinyarce ta jamu, kuma atanbayi 'yan class ─Ćinmu.
   Ya Fahad ya ce, "A'a nikam yanzu babu ruwana tunda ku ba'a gaya muku magana sau ─Ćaya kuji, kofa wata ─Ćaya ba'ayi dakawo takardar laifinkuba a gidannan, naje nabada ha'kuri da al'kawarin bazaku sakeba, amma shine kuka ba─Ća min 'kasa a ido kuka 'kara, kunga kuwa yanzu da kunya na koma, shima yatashi yafice daga falon.
    Deena da Nurr suka zauna suna kwasar kuka kashir6an, saida sukayi mai isarsu sannan suka tashi dan babu mai lallashi,, mama mai goya musu baya tana sama wajen daddy tana taimaka masa wajen shirin masallaci.
   Mami kuma tana kichin suna girki da 'yan aiki, dan dama haka sukeyi mara girki itace ke tsayawa akan 'yan aiki ayi girki, ke kuma mai girki kina tareda mijinki kina bashi kulawa.
   To dama sun san mami saidai ta zuga azanesu, dan haka idanma suka kwaso laifinsu bamasa tunkarar inda take ko ka─Ćan.
   ─Ćaki suka shige suka kulle kansu,, na ce, "haba 'yammata yunwama ta isheku aii......................

bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam
          luv u oll my fan's

[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE
NA BILKISA IBRAHIM

4
            
          
                                        


..........Har aka sakko masallaci basu fitoba, saida daddy yafara cigiyarsu sannan, da'kar mama ta lallashesu suka fito, aiiko dagudu suka haye saman daddy dan yayyen nasu duk suna falo suna cin abinci, ya Mahmud ne kawai babu.
   Agaban daddy sukaja birki, yabisu da kallo yana murmushi, yarana sarakan tsoro, gaku da iya laifi gakuma tsoro kamar fararen kuraye.
   Suka gaidashi suna murmushi suma, ya ce, "to kuzo muci abinci kunji, dan naji ance saboda tsoro yau bakuci komaiba, gashi kuma wannan bazai hana ya Mahmud zanekuba, garama kuci kuyi ─Ćan 'karfi,, Nurr tayi kwal2 da idanu kamar zatayi kuka,, daddy dan ALLAH kabashi ha'kuri karya dakemu, ALLAH bazamu 'karaba,, murmushi daddy yasakeyi,, to mamana bar kuka, kunga kuzo kuci abinci,, tare sukaci abinci da daddy dan dama wata sa'in haka yake musu, saiya sakasu gaba suci abinci tare harda Saiff.
   Bayan sun kammala sukayi zamansu afalon daddy har dare sunki sakkowa 'kasa, sabida tsoron gamo da ya Mahmud kosu ya mubarak.
    Saida suka tafi sallar isha'i sannan suka sakko, ─Ćaki suka shige suka kulle kansu, har safiya basu fitoba,, suna kwance suna barcinsu bayan sun gama sallar asuba suka koma, kamar daga sama sukaji an daka musu tsawa,, afirgice suka farka, ya Mustapha suka gani tsaye akansu, ya ce, "'yan iska kutashi ku fito falo, wlhy minti 5 nabaku in kuwa ba hakaba jiki magayi kunne boka.
    Cikin hanzari suka tashi, hijjabai kaiwai suka xira suka fito, babban  falo suka nufa sunyu matu'kar razana daganin yayyen nasu gaba ─Ćaya, gakuma farhan da khairat zaune A'kasa,, kusadasu kairat sukaje suka zauna,, cikin tsoro suka gaishesu ya Fahad ne kawai ya amsa musu.
   Ya Mahmud yay gyaran murya, tareda gyara zama, ya ce, "iskancinku ya ishemu, dan haka hukuncin laifin dakuka aikata jiya shine aikin gidannan gaba ─Ćaya da gidan abba 'karami,, daga yau har monday kune zaku ringa yi, duk wani aikin da 'yan aiki sukeyi,, nasallami 'yan aikinmu suje su huta na kwana biyu,, cikin tsoro suke kallonjuna,, sukam sun shiga uku, aikingidannan aiba 'karamin aiki bane garama adakesu gurinya huce, Nurr tabu─Će baki zatayimagana ya Mahmud ya daka mata tsawa, gam ta kulle bakinta.
   Ya mustapha ya ─Ćora da fa─Ćin sannan hukunci nagaba shine da Khairat da deena da Nurr duk zaku koma bodin, kuma ranar talata za'a kaiku.
   Atare suka kwallah ihun kuka, yaya mubarak ya mi'ke da belt a hannunsa, wlhy kokuyimana shiru kokuma yanzu ku daku.
   Hannu kowa tasaka tana toshe baki, amma idanunsu yana zubar da hawaye, ya mustapha ya ce, "kaiko farhan dakake biye musu kaima hukuncinka yana nan zuwa,, kuma wlhy babu fashi saikunje bodin kuma ta 'kauye za'a kaiku, government school.
   Yanzu kutashi kufara aikinku, sannan muna jiran break daganan zuwa 'karfe 10 na safe.
   Tashisukayi suka fice suna kuka kamar wa─Ćanda aka aikoma sa'kon mutuwa, su biyu suka ha─Ća break ─Ćin gidan, danma iyayensu suna koya musu girki, tunda su aunty suhaila sukayi aure ake ─Ćan basu girki suna jagulawa hargashi yanzu sun iya,  farhan da khairat ma suna gidansu suna cin aiki.
    Yaukam 'yammatan mama sun aikatu saikace 'ya'yan bayi,, gashi daddy ya hana mama magana, ya ce, "babu ruwanta ta saka musu ido.
    duk wanda ya kallesu yasan sunyi laushi, sune girkin rana, dare sharan kowane ─Ćaki, wanke2, komai na gidan yau sune sukayi,, aifa dazasu kwanta dole suka gasa jikinsu da ruwan zafi sosai.
   Washe garima haka sukaci uban aiki kamar jakuna,, sun bani tausayi gsky.
   Ranar monday su ya Mubarak sukai musu rakkiya makaranta,, babu tausayi sukasa aka zanesu, suma suka kar6a suka yimusu uku2, daga nan sukayi shigi da fici aka basu taransifa zuwa (G,G,A,S,S DAN ZABUWA).
   ALLAH sarki sunsha kuka dan suna son nakarantarsu, suma malaman basu so hakaba, 'kawayensu sai kuka sukeyi na rabuwa dasu,, shima Saiff baiji da─Ćin rabuwa da 'yan uwansaba, dukda kullum sai sunyi fa─Ća amma yau saiyaji wani iri.

BAYAN KWANA BIYU.
   aka gama yimusu shirin tafiya bodin, babu irin ha'kurin dabasu bama yayyen nasuba amma sukayi burus dasu,, dama ya Fahad ne mai ─Ćan raga musu, shima yau yayi kunnen uwar shegu dasu,, sunje wajen daddy domin neman ─Ćauki, amma ya ce, "babu ruwansa, haka aka tarkata 'yammatan uku zuwa bodin dake ─Ćan zabuwa,, mama harda 'yan hawayenta,, amma babu yanda zatayi tunda daddy ya saka mata gate, ya Mahmud da ya fahad ne zasu kaisu makarantar.
    Tunda suka shiga cikin garin ─Ćan zabuwa su Nurr suketa yatsine fuska, dan ganin 'kauyen da'aka kawosu,, wai duk eriyar kaduna arasa makarantar daza a kawosu sai wannan 'kauyen, suna cikin zance zuci aka iso gate ─Ćin makarantar mai fentin tutar Najeria, wasu tsofafin masu gadi guda biyu suka wangale gate ─Ćin suna ─Ćaga musu hannu.
   Ya mahmud ya danna kai cikin makarantar,, adaidai kuma wannan lokacinne ─Ćalibai suke tururuwar zuwa karatun yamma cikin uniform mai gida2 amma kala2 ne, kowane aji da kalar nasu.
    Tunda suka fito ─Ćalibai suke kallonsu, sumadai baza ido suke suna kallon ─Ćaliban,, ya Fahad ya ce, "kumuje ko,, Nurr ta yatsine fuska ya Fahad yanzu nan awannan dajin zaku barmu,, ya Mahmud ya watso mata harara, da sauri ta kulle bakinta.
    Office ─Ćin principal aka kaisu dan dama ansan da zuwansu, wani abokin yaya Mahmud ne yay musu hanya, akwai wani ─Ćan uwansa dake aiki a makarantar.
   Bayan angama shiga da fita dakuma cike form daduk abinda yadace, aka kaisu aji hu─Ću, (ss 1a) amma sai gobe zasu fara zuwa aji, an gaya musu dukkan dokokin makarantar.
    Principal da kanta tasa aka kira mata shugabar ─Ćalibai ta dan'ka su Nurr ahannunta.
   Su ya Mahmud sunji da─Ći sosai, dan haka sukaita godiya..     bayan sun fito daga office ─Ćin pc ya mahmud da ya fahad suka shiga yimusu nasiha, da nuna musu nanfa ba gida bane, dan haka su dage da karatu, banda rashin kunya, da rashin mutuncin dasuka sabayi agida,, nasiha sosai sukayi musu,, suka basu ku─Ćin kashewa dubu biyar2, shugabar ─Ćalibai mai amsa sunan  Badiyya yusif Ahmad ita tasaka ─Ćalibai suka kwashi akwatina da katifu da botikai nasu deena zuwa hostel.
    Bayan su ya mahmud sunyimata alkairi suka tafi suka bar su khairat da kuka,, ALLAH sarku ya Fahad jiyayi kamar karya tafi yabarsu, gaba ─Ćaya fuskarsa ta nuna alamun tausayi,, shiko ya Mahmud ko'a kwalar rigarsa.
   Badiyya tashiga lallashinsu taja hannuwansu suka nufi hostel.........................

SABON AL'AMAREE


NA BILKISA IBRAHIM
              
                                      
                                              

5

.........Tunda suka shiga 6angaren kwanan ─Ćaliban suke baza idanu, ─Ćalibai sunata harkokinsu, wasu suna ─Ćibar ruwa wasu kuma ri'ke da robobi irin na al'majirai suna nufar wani 'katon gini, wasu kuma wanki wasu kuwa suna zaune suna hira, sun wuce wasu ─Ćakuna kamar uku sannan suka nufi wani dake gefe, an rubuta Hostel F, agaban ─Ćakin,, wasu ─Ćalibaine zaune agaban ─Ćakin saman katifu, gawasu kuma suna kamun kunne agefe, wata farar budurwa tsaye kansu da manyan bulalai na dalbejiya.
    Badiyya ta 'karasa inda nakan katifar suke, wata acikinsu ta ce, badee wa─Ćannanfa??? tafa─Ća tana nuna su Nurr dake tsaye suna kallon ikon ALLAH, badiyya ta ce, " 'kannenane aka kawo, wata takuma fa─Ćin kai amma gasu 'kyawawa dama kiran da pc tayi miki kenan??, eh wlhy kiran kenan,, wata kuma ta ce, " badee kudai nakula duk danginku 'kyawawane, 'kannenmu kuzonan ku zauna.
    Su khairat suka 'karasa saman katifar suka zauna, batare dasunyi maganaba, badiyya ta ce, "kunga bari na canja kaya na dawo.
   Bayan shigewar badiyya suka tanbayi su Deena sunayensu, khairat ta ce, sunana Aysha Sadiq mutallaf sardauna (khairat),, Madeena Abdul'malik mutallaf sardauna (deena), Maryam Abdul'malik Mutallaf sardauna. (Nurr), wow!! Nice name, 'yammata aji nawa aka kawoku?, (S's 1).
   Masha ALLAHU, ku 'yan wane garine??, Kaduna, wata ta gwalalo idanu kai!!! Tundaga kaduna aka kawoku nan yanzu??, sukace eh, taf lalai sannunku da zuwa, suka ce yauwa.
   Wadda take tambayarsu ta ce, "to mukuma sunayenmu, Salma bashir tana fa─Ća tana nunawa, shamsiyya kabeer, Ni'ima muh'd, Nazeefa sani, Sadiya sani, sai badiyya yayarku, munan 'kawayen junane komai namu aha─Će yake, muduka firifet ne, sai ahankali zaku ida fahimta.
    Badiyya tafito sanye da wando da riga matsatstsu, kai babu ─Ćankwali, gsky tanada gashi sosai, tatsaya kan masu kamun kunne tana tambayar wai wa─Ćannan misukayine Nazee???, Nazee ta yatsine fuska wa─Ćanda basu bada ruwan wankin tolet bane jiya, badiyya ta ─Ćirkama takusada ita dundu 'yan iska dukkutashi naganku,, 'yan kutumar uba, wlhy yau saikun kawo 2 boket2, suka tattashi tsaye wasuma kuka sukeyi, wata acikinsu ta ce, "wlhy aunty badiyya nidai botiki nane yafashe, kuma nafa─Ća miki tun shekaranjiya, nama gayama aunty salma, salma dake zaune kusada Nurr ta ce, "eh gsky ne wlhy na mantane, k tashi ki tafi kukuma ku koma kamun kunne.
   Bulalai badiyya ta─Ćiba tafara lafka musu abaya, duk wadda ta motsa tata tazube sai an sake, tayi musu uku2, suma sauran  duk saida suka yimusu uku2, kuma su biyarne.
   Bayan angama dukansu akace suje su kawo ruwan kuma,, sudai su deena suna zaune suna kallon ikon ALLAH, dama haka akeyi a makarantar kwana ─Ćin??, suna nan zaune wasu gayya suka zo wajensu, suduka babu mai shigar arzi'ki acikinsu, wasu suka zauna kan katifun wasu kuma saman botikai, suka ce, "wa─Ćannan 'kyawawan fa??,, su salam sukace 'kannenmune,, ─Ćaya cikin wa─Ćanda sukazo ta ce, "kai amma yau aka kawosu??, shamsiyya ta ce, "yanzuma,, ya sunansu?, Nurr khairat deena, kai amma sunayen sunyi da─Ći, niharma nasamu dota ta nuna Nurr.
   Badiyya ta ce, "k ni 'kannena ba haka sukeba, wadda tace tana son Nurr ─Ćin ta ce, "kai badee tunda kema haka kike ai dole 'kannenki suma su zama haka,, badee ta ha─Će fuska kinsan ALLAH jamcy zamu hau jirgin durin uwa mu sakko na kutumar uba, jamcy ta ce, "A'a yi ha'kuri badee tsokanarki nakeyi.
   Ni'ima ta mi'ke tana kama hannun su Nurr kunga kutashi muje ku canja kaya kunji.
   Sai yanzu su deena suka shiga 'katon ─Ćakin da aka layanta gadaje tamkar asibiti, gadajen farko suka shiga, anha─Ća rukunin gadajen wajen guda shidda, salma ta ce, to kunga kwanarmu nan kunji, kuma nan zaku zauna, gama kayanku nan, suka kalli inda aka nuna musu harma an saka musu katifunsu saman gado, an tura akwatinansu 'kar'kashin gado,, jakarsu takaya suka bu─Će suka ─Ćauki kaya na gida suka saka kamar yanda sukaga ─Ćalibai sun saka,, to dama su Nurr ─Ćin gwanayen saka 'kananun kayane, dan hakama yanzu su suka saka.
    Tunda suka fito aketa kallonsu dan ainahin 'kyawunsu ya 'kara fitowa fili, kusada auntys ─Ćin nasu sukaje suka zauna,, anan sukai sallar magriba kamar yanda sukaga sunyi har isha'i,, daga nan suka tafi dasu wajen rabon abincin dare,, kai sudai yau sunata ganin abubuwan mamaki.
    Tofa saida akazo wajen kwanciya suka kasa barci saboda tsoro,, sukaita juye2, Nurr harda kukanta, ta tuna 'katon gadonsu na gida daga ita sai deena, afili ta furta ya Mahmud wlhy ka cucemu, sai wajen asuba barci ya ─Ćaukesu.
    Dasafe akasa ─Ćalibai suka kai musu ruwan wanka, saidai sunata 'kyan'kyamin bayin, haka suka daure sukayi suka fito,, shiri sukayi cikin kayan makaranta,, dawasu yara aka ha─Ćasu sukaje suka amso shayi da biredi, tunda suka kar6o suketa kallon shayin kamar ruwan wanke kai, Nurr ta ce, "kai 'yan uwa nifa 'kyan'kyamin shayinnan nikefa wlhy, kairat ta ce, "ashe bani ka─Ćaiba, deena ta ce, "ai inagama ni zubarwa zanyi,, Fateema ibrahim da aka ha─Ćasu ta ce, "karku zubar, yanzu zuwa zakuyi ku 'kara madararku da sukari, saikuga yayi muku yanda kukeso.
   Khairat ta ce, "eto yanzu naji batu,, madara da sukari suka 'kara sannan suka iya sha, amma kasa cin biredin sukayi saboda basu sababa.
   Bayan sun gama aka tafi aji dasu,, 'yan ajin sun tarbesu da mutunci bare dasuka gansu 'kyawawa, aiko kujerun gaban aji aka basu suka zauna, 'yan ajin suka fara iyayi sunaso suyi 'kawance dasu, tosu dukma basu wani burgesuba, garama wata khadija umar, da safiyya hashim da muneera lukman, sukam sun─Ćan burgesu dan sunga sune wayayyun ajin ma, kuma kamarma zasufi kowa 'ko'kari,, dama sune suka nema musu kujerun zama.
    Wannan kenana......................


Bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
         Luv u oll my fan's©2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

NA BILKISA IBRAHIM
   {♡bilyn Abdul♡}

   6          
                                   
                                    
.........Su ya Mahmud kuwa tunda suka tafi kewar 'yan 'kannen nasu tafara gallabar zuciyarsu, musamman ma ya Fahad, jiyake kamar yakoma ya ─Ćakkosu.
   Haka suka iso gida kowa yana sa'ka wasi'kar jakuna,, dayake dare yafarayi abinci kawai sukaci suka kwanta, gidan shiru yau babu sarakan 6arna, Saiff harda zazza6i yayi saboda kewa,, an ─Ćauke masa abokan fa─Ćansa.
   Hakadai rayuwar taketa gudu da sauri,, gidan basuda labari sainasu Nurr,, komai akayi sai ace dasu deena nanan dayanzu kaza yafaru, kullum sai a ambaci sunansu samada sau talatin agidan,, itako mama idan kanaso kaga farincikinta kayi mata hirarsu Nurr, shi kansa daddy yayi kewar 'yan yaransa.
   Yaudai naga gidan antashi da yawan jama'a,, dukkan family ─Ćin sardauna family manya sun taru agidan su Nurr,, araina na ce, "tokomi akeyi??, gashi 'kakwayena basa nan bare na tambayesu,, ina nan zaune aharabar gidan inata raba idanuwa dan nema hanyar dazan ─Ćakko muku rahoto,, can na hango saiff xai shiga falonsu,, da sauri na kwala masa kira,, yajuyo yana neman mai kiransa,, ganina yasashi nufoni da sauri yana washe baki kamar gonar auduga.
    Ya 'karaso yana fa─Ćin aunty Bily dama kina nan?, tundasu deena suka tafi makaranta kika daina zuwa gidannan.
   Nayi murmushi ina fa─Ćin A'a saiff bahaka bane,, lamurane sukayi mini yawa wlhy, ga islamiyya ga hidimar my sweet Abdul ─Ćina,, dariya yayi ya ce,, "to uncle Abdul yana lafiya kuwa??, na ce, "lafiyarsa 'kalao wlhy, ykk ya makaranta??, Alhmdllh Saiff yafa─Ća.
   Saiff mi akeyi agidan naku haka nagansa cike da mutane??, aunty bily ansaka ranar auren ya Mahmud ne da ya Fahad.
   Na zaro idanu waje kai dama aure zasuyi??, eh aure zasuyi dama su Nurr basu fa─Ća mikiba,, na girgiza kai A'a wlhy bamu ta6a maganarba,, wazasu aura??, duk auntys ─Ćinmune, suma 'yan cikin family ─Ćinmune,, ya Mahmud zai auri aunty Bilkisu ─Ćiyar daddy habeb, ya Fahad kuma aunty Ikileema ─Ćiyar abba Umar.
   Na jinjina kai ina fa─Ćin ALLAH yasanya alkairi, yaushene bikin,, yay ─Ćan shiru alamar tunani eh naji su mami suna cewa nanda wata hu─Ću,, to ALLAH Yakaimu sannan su deena sunzo hutuma,, ya ce, "eh hakane suna gida.
Mun─Ćan da─Će muna hira da Saiff daga baya natashi na nufo gida abina.

D/ZABUWA.
      su Nurr ana ─Ćan zabuwa,, zuwa yanzu sun gama fahimtar makarantar,, saidai su 'yan gatane, su aunty badee basa bari adokesu bare aike,, hasalima saka wasu akeyi suyi musu abu,, su badee suna shanawa a makarantar dan har 'yan aji shiddamma tsoronsu sukeyi, kai harma wasu malaman,, kwata2 basuda mutunci, group ─Ćinsu yayi suna sosai,, 'yan iskane nafa─Ća aji,, idan suna zaune jiniyos basa son bi tawajensu dan zaka iya wucewa tsautsayi ya fa─Ća kanka, kosu aikeka kosu saka aiki,, har tausa sakawa suke ayi musu,, to sudai su khairat sun shigo da 'kafar dama, dan 'yan gatansu badee ne, koda yaushe suna nane dasu.
     Suna kewar gida dan kullum sai Nurr tayi kuka saboda bata iya barci sosai.
    Yau takama 'karshen sati, tunda aka ka─Ća sallar asuba ─Ćalibai basu samu damar komawa ─Ćakinsu ba,, sunacan gaban ─Ćakin hostel F zazzaune,, cikin sanyi,, saida su badee suka tashi daga barcin safe sannan sukaje inda yaran suke, su deena suna ─Ćaki kwance, ta Window suke le'ken hidimar da akeyi agurin, wata ba'ka doguwa ta hau saman birandar kaidaka ganta saika ─Ćauka namiji ne,, tana hawa ta ─Ćanna uwar ashariya, kai dan kutumar ubanku kowa tayi 'kasa da kanta,, gaba ─Ćaya yaran sukayi 'kasa da kai cikin tsoro,, wata dake gefe tace 'yan iska suyita gwalo mana idanu kamarna mujiya, duk wadda tasake ─Ćagowa saidai uwarta ta haifi wata,, azuciyata nace rigiji gabji, anya kuwa hakan zata faru 'yammata??.
    Babu abinda kakeji asaman barandar sai ruwan zagi kala2 wanima bansansaba ni sai a yau,, sudai su deena sunadaga ─Ćaki suna kallon SABON AL'AMAREE, haka 'yan aji shiddan nan sukaita bayani ─Ćai ─Ćai yawancin bayaninma dai duk babu ma'ana, bayan sun gama girgije2n su aka kira 'yan aji biyar saman baranda,, ALLAH sarki dukansu akaitayi kamar jakuna saboda dama ba'a shiri 'yan aji shida da biyar, bayan angama loda musu duka aka raba musu aiki, kowacce firifet taja zugarta.
   Haka rayuwar makarantar tacigaba da tafiya su khairat suna kallon SABABBUN AL'AMURA, tamkar al'amara, wasu subaka haushi wasu kuma dariya.

KADUNA
   Ya Mahmud ne yafito cikin kwalliya ta kasaita, sai zabga 'kamshi yake, araina na ce, "kai gsky guy ─Ćinnan yaha─Ću wannan irin ─Ćaukar wanka haka, ya Mahmud matashin saurayine 'kya'kya'kyawa dukda dai baza'a kirashi alayin masu tsananin 'kyawuba, ammafa ko makaho bazai kirashi mummunaba, shekarunsa bazasu wuce 30/31 ba, dogone babu laifi, kuma 'ka'k'karfane, ba'kine babu 'karya kuma ba'kinsa mai duhune, saidai kawai saboda jin da─Ći fatarsa a goge take kuma tana bada kalar she'ki,, yanada ─Ćan jiki ka─Ćan amma ba sosaiba, fuskarsa zagaye take da 'kasumba wadda take lashe nairorin ku─Ĺi wajen gyaranta, hakama kansa akwai yalwatacciyar suma irin wadda gayun zamani suke tarawa,, yanada wushirya mai 'kyayatarwa yayinda yayi murmushinsa mai ─Ćaukar hankali, baza'a kira ya Mahmud muskiliba amma bashida yawan magana, saidai mutumne mai saurin fushi, kuma yanada fa─Ća sosai dan fuskarsa tana nuwama,, bai cikayin dariyaba gsky, ko murmushi sai yagadama yakeyinsa kodan yaga yana masa 'kyaune idan yayi oho.
   Ya Mahmud baita6a yin budurwaba saboda jin kansa, sai akan bilkeesu, itama itace ta ce, "tana sonsa, aiko da'kyar ya kar6i soyayyarta, bilkeesu ─Ćiyace ta 6 awajen Alh habibu yayan Alh Abdul'malik, yarinyace mai ha'kuri da hankali, gata 'kya'ky'kyawa dirarriya, komai nata yayi, 'kyawawan halayentane suka bata nasara wajen jawo hankalin ya Mahmud kanta,, tun yana basarwa har shima yafara bata kulawa irinta masoya masu matu'kar sha'kuwa, har gashi ALLAH yakaisu da nasarar yin aure yanzu, dan nanda wata hu─Ću sun zama mallkin juna, lol.
       Babban falo yanufa, yashiga da sallamarsa, afalo ya iske Ya mubarak da ya mustapha, suka gaisheshi cikin girmamawa dan gidan ana girmama juna kamarba gidan 'yan bokoba, cikin tsokana mubarak ya ce, "ya Mahmud irin wannan ─Ćaukar wanka haka kodai wajen auntyn mu zaka??.
   Murmushi ya Mahmud kawai yayi tareda kama kunnen ya Mubarak ya mur─Ća, cikin muryarsa mai da─Ći ya ce, "mubarak karainani ko??, mubarak yari'ke hannun ya Mahmud yana fa─Ćin sorry babban yaya magajin daddy.
   Ya Mahmud yasaki kunnen yana dariya,, Mustapha dake zaune agefe ya tuntsure da dariyar mugunta, cikin dariya ya ce, "kai amma ya Mahmud ya iya mashar kunne,, ya Mahmud yashige ─Ćakin mama yana fa─Ćin kaima zanzo kanka aii.
    Da sallam yashiga mama tana zaune itada mami suna hira, ya rissina yana gaishesu,, mami ta amsa cikin fara'a, yayinda mama ta kauda kai gefe,, mami ta ce, "yaya sai ina haka??, yay 'kasa dakai yana murmushi mami zanje gidan abba habeb ne,, okey kace za'aje wajen ─Ćiyata bilkeesu.
   Yajinjina kai cikin jin kunya,, mami ta ce, "to agaida mana ita da 'kyau.
   Ya mi'ke yana fa─Ćin to zataji, mama najinsu amma ko tari batayiba,, bayan fitarsa mami ta ce, "kai mama ko addu'ar baza'ayimanaba??, mama ta yatsine fuska ta ce, "bakin yimasaba, ai ya wadatar.
    Mami tayi dariya,, kai mama mudai gsky abunnan dakike mana yafara isarmu.
   Mama tami'ke tana fa─Ćin kudai kuka sani, nikam badaniba.......................bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
        luv u oll my fan's


©2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

BILKISA IBRAHIM
      {♡Bilyn Abdul♡}

8
              
                                   
                                         
..........BAYAN WANI LOKACI.
   yau muta nene gidansu Nurr sunata shirin zuwa D/Z bistin, shiri sukayi sosai domin zuwa ganin 'yan gata, harda daddy, tunda safe suka tafi, cikin amincin ubangiji suka isa da wuri, a office ─Ćin pc akayi musu masauki, sannan aka aika kirasu Nurr,, aiko babu 6ata lokaci suka iso, wayyo zokaga murna wajen 'yan uku, harda kukan shagwa6a su sunga 'yan gida,, daddy ya ce, "yaran mama duk kun rame kunyi ba'ki, Nurr tafara hawaye daddy dan ALLAH kace da ya Mahmud mun shiryu ya taimaka ya maidamu school ─Ćinmu nada, wlhy anan akwai wahala gashi abincin babu da─Ći.
   Dariya daddy yayi ya ce, "nikam babu ruwana kubari idan kunje hutu saiku bashi ha'kuri, deena ta zaro ido waje, tab daddy wlhy zai bibbigemu ne kawai garama mu ha'kura kawai,, mama ta ce, "karku damu, aiikoni bazan juri ganinku a wannan makarantar ba, dolensa yasan yanda zaiyi daku,, mami ta ce, "haba yara garama idan zaku zauna ku zauna, dan babban yaya babu abinda zaiyi muku, khairat ta langwa6e kai, mami plz kisa baki,, ALLAH ya Mahmud yana saurin jin maganarki,, mami tayi dariya, kukam kuncika raki, kofa hutu ─Ćaya bakujeba.
   Hakadai sukaita hira, suna bama su daddy labarin makarantar, suka kira su aunty badee daddy yay musu al'kairi tareda godiyar ─Ćawauniyar dasukeyi da 'ya'yansa,, dazasu tafi kuka su Nurr sukeyi sosai, da 'kyar su Nazee suka 6an6aresu daga jikin daddy da mama,, suma haka suka tafi cike da kewar 'ya'yansu, mama harda 'yan kwallanta.

BAYAN WATA BIYU.
   su deena suka sami hutu,, sunyi farincikin wannan hutu kamarsu tashi sama,, ya Mahmudne da ya Fahad sukazo ─Ćaukarsu, babu kunya Nurr taje ta rungume ya Mahmud danshi tafara gani kuma ita tafara ganinsa, ─Ćalibai sai kallonsu sukeyi, ya cirota daga jikinsa yana murmushi, Nurr haryanzu ba'a fara hankaliba KENAN??, ta rufe fuska tana dariya wlhy yaya munyi missing nakune, kai ka─Ćai kazo??, da hannu ya nuna mata ya Fahad dake waya a bayan mota,, da gudu ta 'karasa shima ta rungumeshi sai asannan su deena sukaji labari, suma ya Fahad suka rungume dan sunsan ya Mahmud baya son wargi, ya Fahad ya rungumesu yana dariya, cikin sanyinsa ya ce, "i missing u autara's, suma sukace muma munyi kewarku yaya, ya Mahmud ya 'karaso shima, su deena suka daure suka rungunesa amamakinsu sai sukaga baiyi musu fa─Ćaba, saima shafa kansu dayayi yana musu musrmushi,, lallai sun yarda ya Mahmud yayi missing nasu shima,, dan saisuce sukan da─Će basuga dariyarsaba amma gashi yau yana musu, kodan karya badasu gaban ─Ćalibaine oho.
    Ya fahad ya ce, "ina wadda muka ha─Ćaku ─Ćinnan??, khairat ta ce, "yaya bari nakirasu,, babu da─Ćewa taje takirasu sanan su Nurr suna basu labarin al'kairin da su badee suke musu, su badee suka gaida su ya fahad,, sudukansu saida suka 'kyasa matasan samarin masu matu'kar kama da juna,, Nazee ta ce,, "inama ya ce, "yana sona, shamsiyya dake kusada ita ta ce, "wanne aciki??, da ido ta nuna ya Mahmud,, salma ta ce, "ai guys ─Ćin duk sun ha─Ću babu na yarwa, saidai wanda kika nuna yafi aji, daganinsa zaiyi girman kai,, Nazee ta ce, "ai wanan shine halin 'yan mazan,, ya fahad yay musu alkairi sanan yace suyi sallama dan garinsu da nisa, shikam ya mahmud tundaga gaisuwa bai sake kula inda sukeba,, Nurr tana kusadashi tana zuba masa surutu, amma iyakarsa murmushi dan tasanma ba amsata zaiyiba,, tama gode dayake saurarenta.
  Bayan sun gama sallama ya Fahad ya ce, "sushiga mota, deena ta ce, "ya fahad hardasu aunty Nazee da aunty sadiya zamu tafi saimu ajiyesu a malumfashi, ya fahad ya ce, "okey babu damuwa, ai wajen zai isheku, kokuma Nurr tadawo kusada ya Mahmud tunda itace 'yar 'karama,, Nurr ta─Ćan zare ido dan tsoro, ya mahmud ya harareta, kinafa 6ata mana lokaci,, jiki a sanyaye tashiga ta zauna kusadashi, dukma rabin jikinta yana jikinsa.
   Suma Mota suka shiga ya fahad yaja suka fice daga gate ─Ćin su aunty badee suna ─Ćaga musu hannu.
     Tunda suka fice daga cikin makarantar bakin kowa yay gum musamman ma Nurr dan batada damar yin surutu kusada saraki,, garama su deena suna hira 'kasa2 sudasu aunty Nazee.
   Nurr ta ce, "ya Fahad ALLAH yunwa nakeji sosai,, ya Mahmud ya harareta to acici saiki bari saimunje wani garin, ya fahad yay dariya, ya mahmud kasan 'yan bodin  kamar almajirai suke nasan yanzu dole a'kara mudun abinci agidannan sabida su autaras sun dawo,, khairat ta ce, "yaya ALLAH jinake kamar naci babu,, dariya sosai ya fahad yakeyi, ya ce, "lallai kuce ci kuka koyo a school ─Ćin??, humm ALLAH ya fahad abincin makarantar babu da─Ći, tunda mukaje mun kasa ci, deena tafa─Ća tana hawaye.
   Tofa yanzunan kuna nufin tunda kukaje bakucin abincin school ─Ćin??, eh wlhy yaya bamaci kuma katanbayi su aunty sadiya kaji, tab─Ći to mikukeci??, yo abincin akwatinmu dakuma ku─Ćin dakuka bamu, saikuma wanda su daddy sukazo suka bamu.
   Ya mahmud da tun ─Ćazu yanajinsu bai tankaba hasalima wayarsa yaketa dannawa,  ahankali ya furta lallai yara kuna tare da wahala kuwa,, ya fahad yay dariya ya ce, "gsky kam.
   Dahakadai suka iso gidan mutum ─Ćaya, kasancewar safiyane babu wani abinci mai─Ćan da─Ći, saidai 'yan kayan kwa─Ćayi aka sai musu daganan suka 'kara ─Ćaukar hanya,, ya mahmud yana lura da irin kallon da Nazee take masa, dan duk ─Ćagowar dazaiyi saisun ha─Ća ido ta madubi, aiko ya'kara tamke fuska tamau,, sanda suka isa marabar musawa Nurr tayi barci, ya Mahmud ya kwanto da ita jikinsa yana fa─Ćin raguwar banza hartayi barci.
   Khairat ta ce, yaya aidole tayi barci jiyafa batayi barciba saboda murna zataje gida,, ya Mahmud ya ce, "zaku iya tunda hankali bai gama isarkuba.
   A malunfashi har 'kofar gida suka kai su Aunty Naxee, daganan suka nufi kaduna,, cikin amincin ALLAH karfe shabiyu a akudana tayi musu................
luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul SABON AL'AMAREE

BILKISA IBRAHIM
     {♡bilyn Abdul♡}               
                                                                       
7

............koda ya Mahmud yafita gidansu bilkeesu yanufa, dayake babu nisa tsakaninsu akafa yaje,, zan iya cemuku yawancin gidajen anguwar duk na 'yan Sardauna family ne, shiyyasama ake kiran anguwar da suna Sardauna.
   Ya tura 'kofar gate ─Ćin gidan yashiga, maigadi dake zaune agefe yanajin redio yay saurin mi'kewa ganin ya Mahmud saiya washe baki, ya rissina yana gaisheshi,, ya Mahmud ya amsa cikin fara'a yana fa─Ćin sarkin gate da cakake 6arayine??,, mai gadi yayi dariya, A'a yalla6ai kawai dai abinne yabani mamaki.
   Ya Mahmud yay 'yar dariya tareda zaro ku─Ći a aljihunsa ya mi'kawa mai gadi, jiki na rawa ya amsa yayita masa godiya da zuba masa addu'oi, ALLAH yabaka 'ya'aya nagari masu amfani yalla6ai, ALLAH yasa kagama da duniya lafiya, ALLAH yasa kagama da iyayenka lafiya......haka dai yayta suburbu─Ća masa addu'a.
   Ya Mahmud yashige ciki yana mai jin da─Ćin addu'ar ta mai gadi,, yanason yara sosai harma baisan iya adadin dayake addu'a ALLAH yabashiba,, yana fatan ace Bilkeesu tana zuwa gudansa tasamu ciki, idan duk shekara zata haihu zayi farinciki,, akan la66ansa ya furta ya ALLAH kacika min burina na mallakar 'ya'ya masu tarin yawa,, nace amin ya Mahmud.
   Ya tura 'kofar falon yashiga da sallama,, ummy mahaifiyar bilkeesu ta amsa da fara'a, tareda fa─Ćin Mahmud kaine tafe??, ya'karasa gabanta yana fa─Ćin nine ummy ina yini yafa─Ća bayan ya durkusa, lfy lau ummy ta amsa, yasu mama dasu mami??, duk suna nan lafiya ummy suna gaisheki, ina amsawa yawajensu Nurr 'yan bodin??, yay ─Ćan murmushi suna lfy wlhy,, to masha ALLAH ai haka akeso, tunda ka kwashema su mama autoci kakai su bodin.
  Ya mi'ke yana dariya, ummy ai gara haka, yaranne basa jin magana ko ka─Ćan,, aii dama yara sai ha'kuri Mahmud, bakaji masu iya magana sunce 'kuruci dangin hauka ba, kumafa duk kunyi irin wanan rashinjin,, kansa ya sosa yana dariya, ummy tami'ke tana fa─Ćin bari na turo maka bilkeesun tana ─Ćaki yanzu haka tana barci, aii kana da aiiki sosai a gabanka Mahmud, saikayi dagaske zaka iya control ─Ćin yawan barcin bilkeesu ,, murmushi kawai yayi batareda yace komaiba.
   Bayan kamar minti biyar bilkeesu tafito, ya Mahmud ya─Ćago yana kallonta fuskarsa cike da murmushi, itamadai murmushin takeyi,, harta nufoshi saikuma ta ce, "ina zuwa yaya, kichin takoma ta ha─Ćo abubuwan motsa baki, a gabansa ta dire, saida ta zuba masa lemo a kofi sanan ta gaishesa,, ya amsa yana kallonta ummy ta ce, "barci kikeyi??, hummm ummy kenan, itafa dataga nayi shiru a─Ćaki saitace barci nakeyi, wlhy ina karatun novels ne a waya, ya─Ćan murmusa, karki damu nasan ka─Ćaici yana damunki, insha ALLAHU nanda wata hu─Ću kina tareda mai ─Ćebe miki kewa ya'kare maganar da kanne mata ido ─Ćaya ,, hannu tasa ta rufe fuskarta saboda kunya, ya kur6i lemo yana murmushi,, ta ce,, "ya Mahmud wai dan ALLAH miyasa kakai su deena bodin ne??, saida ya ha─Ćiye lemon daya kur6a sannan ya ce, "saboda inaso a hora mini su, yaran basajin magana, idan aka cigaba da tafiya ahaka za'a ha─Ća mazajensu da aikine kawai.
   Dariya bilkeesu tayi, ta ce, "humm yaya kenan, to aii daka barsu agidama sai'a hirasu, amma bodin akwai wahala ballesu ankaisu mai nisa kuma ya Fahad ya ce, "min school ─Ćin 'kauyece, humm ai dama nakula bada sonsa aka kaisuba, tundafa muka kaisu muka taho baiyimin maganaba, dana kalleshi sainagama kamar zaiyi kuka, kinsan Fahad akwai tausayi,, bilkeesu tayi dariya, aini burgeni yakeyi saboda yanada matu'kar ha'kuri wlhy, ya Mahmud yaymata hararar wasa okey mukuma bamuda ha'kuri kenan??, cikin dariya ta ce, "A'a ni na isa na fa─Ća, yayi dariya gashima kin fa─Ća, hakadai sukaita hirarsu cikin so da 'kaunar juna, har saida akayi kiran sallar magriba sanan yataho gida.

D/Z.
   A D/Z.... kam su khairat anatashan karatu, saidai matsala ─Ćaya suke fuskanta shine gatanda su Naxee suke musu, dankuwa kamar suna 'kara musu ba'kinjini agun ─Ćalibai. musamman ma 'yan aji biyar, babu abinda yake ha─Ćasu da juna sai 'yar harara, wani lokacinma har zaginsu sukeyi, dayawa ana ─Ćaukar su Nurr ne amatsayin 'kannensu badee, dan haka duk muguntar dasu badee keyi akaci burin ramawa akasu deena, matsala ta biyu kuwa itace basa iya cin abincin makarantar saidai kayan kwa─Ćayi dasukazo dasu, saiko ku─Ćin da'aka Basu suketa faman kashewa, damma su dukansu basuda yawan cin abinci.
    Yauma kamar kullum bayan an taso daga makaranta suka iso hostel agajiye dan akwai 'yar tazara tsakanin hostel ─Ćin da classis ─Ćinsu, suka yada zango akwanar su, suna zama su aunty sadiya suka dawo,, suka gaishesu, aunty shamsiyya ta ce, "kutashi kuyi wanka sanan saiku huta gaba ─Ćaya dan yau an shiraya yin wani gagarumin tare, kuma wlhy babu sau'ki,, salma ta ce, "dakin barsu yau an─Ćan ta6a lafiyar jikinsu, tunda tundasuka zo ba'a dakesuba,, Nurr ta ce, "kai aunty salma yanzunan kina fata adokemu wlhy inada tsoron duka sosai.
   Badee tayi murmushi ke 'kaleta kinji Nurr ─Ćin yaya babu mai dukar minku indai ina makarantar nan, saidai idan munbar makarantar, suduka dariya sukayi tareda mi'kewa suna murna,, babu da─Ćewa sukayi wanka suka fito, agurguje suka shirya,, kwanciya sukayi tunda dama basa zuwa kar6o abinci,, amma kullum saisu badee sun ─Ćebo musu nama ko kifi da'ake rabawa.
   Aiiko maganarsu Nazee dutse tunkafin agama rabon abinci akaje gaban gate ─Ćin hostel aka jibge manya2n bulalai,, ALLAH sarki sukam yaran sunsani, dan haka sukaita himmar tafiya wasuma ko abinci basu tsaya ciba suka tafi, 'karfe uku da rabi aka rufe gate, wa─Ćanda aka tare sunci duka musamman ma 'yan aji biyar, dama dansu aka shirya yin taren,, shiyyasa aka  'ki basu abinci da wuri,, awajen tarenma sunfi kowa yawa,, humm mugudai baji da─Ćin halinsaba wlhy,, ALLAH ka shiryamu........................

SABON AL'AMAREE

BILKISA IBRAHIM
    {♡bilyn Abdul♡}

Kuyi ha'kuri da typing ─Ćin danakeyi yanzu ka─Ćan2, wlhy ayukane sukayimin yawa.
    Kucigaba da kasancewa dani A SABON AL'AMAREE, dan har yanzu shimfi─Ća mukeyi bamu shiga cikin Novel ba,, akwaifa SABON AL'AMAREE agaba mai ban mamaki da al'ajabi,, karna cikaku da surutu kudai kubiyoni.
    Ina mi'ko ─Ćunbin gaisuwa da fatan al'kairi ga masiyana aduk inda kuke,, luv u oll.

             
    9                                 
                                             

........Tun kafin ya fahad yagama fakin su deena suka fice da gudu, sunaji ya Mahmud yana daka musu tsawa amma basu saurareshiba ko ka─Ćan, ya fahad kam dariya suka bashi sosai,, a babban falo sukaci karo da mama suka cikuykyeta suna ihun murna, cikin farin ciki mama ta rungumesu tana mai jin da─Ćin ganinsu,, Saiff yafito dagudu daga ─Ćakinsa, shima cikin farinciki ya ringumesu, dan danan gidan yakacame da ihun murnar ganinsu, kowa kagani yana cikin walwalar ganin su auta.
    Bayan gama murna sukaje sukayi wanka, cikin 'kananun kayan nasu nafama sukayi kwalliya,, ha─Ća─Ć─Ćen abincin da mama ta ha─Ća musu dakanta sukaci suka 'koshi, daga nan akashiga bawa su mama labarin D/Z, har daddy saida yasha labari,, ranar kunnen kowa bai hutaba agidan saida dare yayi,, suna ─Ćakimsu daniyar kwanciya, deena taha─Ća uniform ─Ćinsu tana ninkeke dasuka baza akan gadon, ta shinshina kayan Nurr ta lumshe idanu, Nurr tabita da kallon mama ki, kekuma lafiya??, batareda tayi maganaba ta mi'kawa Nurr kayan saitin hancinta, Nurr ma ta sha'ka, ta ce, "turaren ya Mahmud ne, inason turarennan wlhy, amma munnemesa mun rasa, narasa inda yake sayosa.
   Deena ta ce, "gsky turaren ya ha─Ću jibafa kigani wai ─Ćan zaman dakikayi kusadashine yasa turaren ya manne akayanki,, Nurr tayi dariya k 'yar uwa aina manta nabaki labari ─Ćazufa a cinyar ya Mahmud nayi barci,, deena tayi dariya wlhy naganku nima nasha mamaki, ya Mahmud ─Ćin dabaka isa ko kusadashi kazaunaba, amma harda kwantar dake ajikinsa.
   Nurr tayi far da idanu kinsan ni 'yar baiwace,, deena ta hawo gadon tana fa─Ćin to sannu 'yar baiwa, kedai kawai ya gadamane, kuma danyaga su aunty Naxee ne,, k kinga irin kallon da aunty Naxee takema ya Mahmud inagafa ta fa─Ća tarkon so,, dariya sosai Nurr takeyi, aiiko ta ─Ćakko dazafi dan batasan halinsa bane.
   Deena taja filo tana kwanciya, ai wlhy nasan koda mata sun 'kare ya mahmud bazai auri aunty Nazee ba, 'yar uwa ashe kingane Nurr tafa─Ća tana lullu6a da bargo,, kai ALLAH mungode maka gadon nan kaima kayi missing namu,, kwana nawa bamuyi kokawa akankaba,, deena ta ce, "kai bodin gidan bala'i jiya iyanzu munacan anayimana 'kunshi ko??, Nurr takalli agogo hakane kam,, yanzu ko khairat tayi barci??, 'kila tayi kinsanta dai kamar kasa take, haka sukaita hirarsu har barci ya ─Ćaukesu.
     Washe gari dakansu suka ha─Ća break ─Ćin gidan gaba ─Ćaya, su mama sunji da─Ći sosai lallai sun yarda yaransu sun fara hankali kam.
  Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, Sardauna family sunata shirin bikin 'ya'yansu maza da mata, hakama su ya mahmud anata shirin ─Ćaukar amare.
    Dahakadai aka shiga shagalin biki,, duk wata bidi'a za'ayita kafin aure da'an ─Ćaura aure za'a kai amare ─Ćakinsu shikenan biki yatashi, su Nurr anata iyayi, dama anyimusu ─Ćunkunansu tunkafin su dawo,, gashi aunty rukayya da aunty suhaila suma sunyi musu, dadyma ya burgesu da nasa,, hakama mama da mami, kai autaras dai sunfito gari kam.
    Yaune akayi loncin gurin yayi matu'kar ha─Ćuwa dukkan amare da angwayen sun hallara awaje, kuma kowa yabada ma'ana, karkuga yanda ya Mahmud da ya fahad sukayi 'kyau abin saiwanda yagani,, hakama amarensu sunyi 'kyau bilkeesu da ikileema, sai she'kin amarci sukeyi,, yayinda autoci suka fito sai kallo ya koma sama domin kuwa yaran sunyi 'kyau,, sunci adonsu cikin jar doguwar riga ta matiriyal sun na─Će kansu da blue ─Ćin gwagwgwaro, sar'ka da 'yankunnesu da gale da takalmi duk blue yaran sun bada ma'ana dan sun ─Ćau wanka mai 'kayatarwa,, su kansu su ya Mahmud sun birgesu, kai kowama sun birgesa,, yayinda akazo fagen rawa kuwa aisai kallo ya koma sama, sai suka ware suna bama jiki hakkinsa yaran sun iya taka kowacce irin salon rawa,, aituni li'ki yatashi daga kan angwaye da amare yakoma kansu Nurr, mawa'ka kuwa suka shiga ko─Ćasu,, 'yan uwansu sai hotina da bidiyo suke musu,, tuni wani abokin ya Mahmud ya 'kyasa Nurr amma shi ba ─Ćan family ─Ćin Sardauna bane,, yazone daga abuja, tare sukayi karatu da ya mahmud a jami'ar abuja.
    Hotuna sosai yaran sukayi, yanda suke rawa abin duk ya 6atawa ya Mahmud rai,, amma babu damar magana, dasun ha─Ća ido dashi saiya sakar musu harara,, aiko ko a kwalar rigarsu, tunda sunsan bazai dakesuba cikin taron jama'a,, shikam ya fahad dasun ha─Ća ido saiya jinjina musu tareda yimusu murmushi,, sunsha rawa kafin daga bisani taro yatashi.
     Washe gari kuma akayi kamu, nanma su Nurr sun cashe damma ya Mahmud baijeba,, amma ana gobe ─Ćaurin aure da'akayi dina da daddare suna fara rawa ya mahmud yakirasu, da har sun'ki zuwa sai sukaga ya mi'ke da'alama wajensu zai nufo,  dasauri sukazo,, ya galla musu harara waiy ku bakuda hankaline?, kuzauna kuyita rawa kamar mazari,, wlhy duk wadda nasake gani afincan tana rawa acikinku sainaci 'kaniyarta,, kunemi waje ku zauna kamar yanda kowa yazauna,, Nurr ta ce, "yaya muna murnanefa,, ya sake hararar ta to shikenan kuci gaba zakuga murna ajikinku, marasa kunya ku 6ace min dagani,, jiki a sanyaye suka shige.
    Aunty bilkeesu ta ce, "yaya daka 'kyalesu daga yaufa shikenan,, ya girgiza kai bazaki ganeba my bily yanzu haka wani abokina saboda wannan iya shegen dasukeyi yaga Nurr wai yanaso nayi masa hanya wajen daddy, ni nama rasa mizan cemasa, saboda inajin kunyarsa,, nasan kuma family ─Ćinmu ba'a bada aure ga bare saidai idan ALLAH ya 'kaddara.
   Kuma Nurr yarinya ce banaso ta lalace da soyayya tun yanzu, karatu nakeso suyi,, bily ta ce, " shikenan saimuyita mata addu'a ALLAH yaxa6a abinda yafi alkairi,, ya mahmud ya ce, "amin ya rabbi.
   dahaka taro yatashi,, washe gari aka ─Ćaura aurensu ya mahmud da amarensu,, zokaga farinciki awanana family,, to ya Mahmud & ya fahad ALLAH yasanya alkairi,, yabaku zuri'a tagari,, ALLAH ya kore fitina acikin auren............................


luv u oll my fan's
©2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE


BILKISA IBRAHIM
    {♡bilyn Abdul♡}

              
   10                                 
                                            
........Kowa ka kalla yana cikin farinciki, da daddare aka kai amare ─Ćakinsu, suma anan anguwar zasu zauna amma daga can sama, jerin gidajen matasan family ─Ćin,, ana kai amare kowa ya koma gidansa domin ya huta, shikenan kuma sai wani ya taso.
     Su Nurr suna zaune a harabar gidan suna hira itada deena dama basuje kai amaryaba, ya Mahmud ne yafito cikin kwalliya, farar shaddace ya ─Ćora 'yar gaske sai mai'ko takeyi,, ─Ćinkin ma ya amsa sunansa dan yazauna dai2 da tsarin halittarsa,, ya ─Ćora farin gilas a idanunsa sai zabga 'kamshin turarensa yakeyi mai da─Ći 'kamshi da saka ma'abocin sha'karsa nisha─Ći, Nurr ta tunture da dariya tana kallon ya Mahmud,, cikin tuhuma deena take kallonta k wai lfyarki kuwa??, cikin dariya Nurr ta ce, "wlhy ya mahmud ne yabani dariya, kina ganin yanda ya kwama gilas a idonsa.
   Deena ta juyya tana kallonsa itama dariya tayi ta ce, "wlhy kuma yayi masa 'kyau sosai fa,, abokin ya Mahmud dayace yana son Nurr ya ta6a ya Mahmud, Mahmud kaga 'kannenka can tun ─Ĺazu daka fito suke kalloka kodai kayi musu 'kyaune?.
   Ya Mahmud ya ─Ćago dara2n idanunsa yana kallonsu deena dake ta dariyarsu, ya ce, wa─Ćancan yaran dakake ji da gani bafa mutuncine dasuba, bari kaga ina zuwa, batareda yajira amsar abokansaba ya nufi su Nurr, suna ganin yanufosu suka shiga gimtse dariyar dasukeyi, yana zuwa suka ha─Ća baki wajen gai sheshi, bai amsasu ba saima tambaya daya jeho musu, kai mukukeyi anan wajen??, deena ta ce, "yaya muna shan iskane ciki hayaniya tayi yawa,, yaja ─Ćan tsaki aransa ya ce, "wai har wa─Ćannan 'yan yaran sunsan wata hayaniya, afili kuma saiya ce, "to kallon mikuke mana kamar wasu ba'kinku???.
   Da sauri Nurr ta ce, "yaya wlhy kwalliyarka tayi 'kyau baka ta6a cin gayuba irinna yau ba, jibafa harda gilas,, yaji da─Ćin kalaminnata amma saiya basar ya harareta Nurr kin rainani ko??, da sauri ta ce, "wlhy yaya A'a nidai nafa─Ćane kawai saboda kamana 'kyau, dan ALLAH kayi ha'kuri bazan sakeba, juyawa yayi yatafi batareda ya sake maganaba, amma fuskarsa ─Ćaukeda murmushi, afili ya furta matsoraciya.
   Ya 'karaso wajen abokan nasa yana fa─Ćin kumuje ko,, mai son Nurr ya ce,, "gsky Mahmud nidai 'kanwar can taka kullum 'kara shiga raina takeyi yakamata kayi wani abu,, ya Mahmud ya─Ćan Ta6e baki kukam kuna bani haushi, kurasa dawa zakuyi soyayya sai yara 'kanana,, har nawa Nurr take daza awani sota, dan ALLAH kabar wanan zance, dan yarannan dama sun iya raini bare ace ana sonsu ai sai su ringa ganinmu dai dai dasu ma.
    Mujaheed yay dariya, Mahmud kana bani mamaki, har yanzu nagaza gane kai wane irin mutumne wlhy???, kacika son girma dayawa, miye abin raini danka auri yarinya 'karama ai sannannema zaka more sadakinka,, ya Mahmud yay ─Ćan tsaki aidama duk jirgi ─Ćaya ya kwasoku kaida kamal ─Ćin, ni kunga kuna 'kara 6ata min lokaci, idan zaku rakani kumuje, idan kuma surutu mara amfani zaku tsaya nakama hanya.
   Dariya sukayi su duka, Sadam ya ce, "lallai ka nuna mana ka 'kagara, to guy adaiyi ahankali awajen harka karkaje kayi gagarumar 6arna, duka ya Mahmud ya kai masa yana fa─Ćin kaidai ─Ćan iskane wlhy sadam, sadam ya kauce yana dariya babu wani iskanci alaramma gsky nafa─Ća ko 'yan uwa, suma sauran dariya sukeyi sosai, kaseem ya ce, "kunsan dai tuzuru idan yasamu dama sai ahankali, ya Mahmud yay gaba yana dariya, kudai kun bani 'yan iska kawai, niba ─Ćan iska bane, kuma gasu Nurr can zaune sunajin duk iskancin dakukeyi, mota suka shishshiga suna dariya, sukatafi raka ya Mahmud gidansa.
     babu da─Ćewa tawagar ya Fahad tafito, shimadai yaci gayu abinsa, Nurr ta ce, "lallai aure dabanne, zamuyi kewar ya fahad, amma wlhy murna nake da barin ya Mahmud gidanan, dan yanzu zamu shana sosai,, damma gasu ya mubarak nan, dan suma halinsu ─Ćaya da ya Mahmud, ALLAH yasa suma daddy ya ce, "suna gama karatu sufito da matansu ai musu aure,, deena tabawa Nurr hannu suka tafa, kai 'yar uwa dakuwa mun shana awannan lokaci wlhy, dagamu saimu kenan.
  Araina na ce, "dayake kukuma agidan zaku dawwama.

Acan  kuwa su mujaheed sun raka ya Mahmud bayan nasiha da ─Ćan barkwanci na abokai suka taho, akabar ango da amaryarsa,, lallai yau su ya Mahmud za'a shanakai babu ruwanalol.
   Shima ya fahad ya isa ga tashi amaryar, nanma nasan babu sau'ki, dan ajiye wannan ha'kurin nasa zaiyi agefe ya murji amarci, lol.

Washe gari mami taha─Ća break mai rai da lafiya su deena suka shirya suka tafi kaiwa, gidan ya fahad suka fara shiga, afalo sukaci karo dashi, suka gaisheshi tareda tambayar aunty ikilee, ya ce, "autaras auntynku tana barcin gajiyar bikine, sukace to idan ta tashi ace muna gaisheta ga break nan inji mami, yauwa yaran mama sannunku kunji,, kuce munama mami sannu da 'ko'kari,, ALLAH ya 'kara musu tsawon rai,, su deena sukace amin tareda yimasa sallama suka fito, suna 'yar gulmarsu.
    Daganan sai gidan ya Mahmud,shikam sunkai minta 15 suna kwankwasa 'kofar falon ba'a bu─Ćeba,, Nurr ta ce, "deena kodai mu koma dan nikam nagaji da tsayuwa wlhy, kafin deena ta ce wani abu an bu─Će 'kofar,, ya Mahmud ne ya bu─Će musu,, yaja gefe suka shigo sannan ya rufe,, saman kujera suka zauna suna gaisheshi ya amsa yana zama saman hannun kujera shima, sukace yaya ina aunty bilkee, ya ce, "tana ─Ćaki tana barci nima wanan buga 'kor nakune ya tasheni, kunata bugama mutane 'kofa kamar zaku cireta, bakusan idan kunyi ─Ćaya biyuba ku hakura.
   Deena ta ce, "kai yaya break fa muka kawo maku, ya yatsine fuska shine kuma zakuyi mana tashin 'yan birsin,, shuru sukayi dan sunsan shidama ba'ayi masa gwaninta, suka mi'ke suna fa─Ćin yaya sai anjima, ka gaida mana da aunty bilkee idan ta tashi, binsu kawai yayi da ido batareda ya amsaba, suma basu jira amsarsaba suka fice.
   Nurr ta ce, "kai shidai ya Mahmud halinsa dabanne dana kowa agidanmu, kiga yanda ya fahad ya tarbemu amma shi sai wani cin magani yakeyi, yayi aurenma bai canjaba, ai aunty bilkee taga takanta wlhy, tayi za6en tumun dare.
   Deena ta ce, "k ai bakisan irinsu ya Mahmud sunfi kowa iya soyayyaba, wlhy saikiga ita baiyi mataba tunda yana sonta.
   Nurr ta ta6e baki to ALLAH yasa haka......... ...........


luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE


BILKISA IBRAHIM
    {♡bilyn Abdul♡}

           
                                                             
                                             
11
.........Haka su Nurr sukayita shan hutu cikin farinciki, jisukeyi kamar karsu koma,, yauma suka ─Ćau wanka cikin dogayen jallabiya ba'ka, suka na─Će kansu da farin mayafi sunyi 'kyau sosai,, ─Ćakin mama suka fara shiga sukace mata sai sun dawo,, ta ce, adawo lafiya 'yammatana, bayan sun fito sukaje ─Ćakin mami sukayi mata sallama itama sannan suka nufo waje sai gidan aunty rukky.
   Suma anan anguwar suke basuda nisa dasu ya Mahmud, cikin farinciki ta tarbesu,, ma'aruf yaronta yazo ya rungumesu yana mai farin cikin ganinsu, suma cikin farinciki suke ─Ćagashi sama,, deena ta ─Ćauki khursum dake wasa cikin 'yar motarta, tashiga ─Ćagata sama tana wangale baki.
   Aunty ruky ta ce, "autaras ─Ćin mama kunyi 'kyau saidai bodin tasa kun rame kunyi ba'ki, deena ta ce, "himmm aunty badole mu rameba, kinga 'kyauyen kuwa da ya Mahmud yakaimu,, wlhy munsha wahala sosai, danma ALLAH yaha─Ćamu da wasu 'yan aji shida sunata gatantamu.
   Ayya to ALLAH yabiyasu da mafificin al'kairi,, ai kune bakwajin magana ko ka─Ćan, inda kun nutsu kundaina ─Ćakko musu magana aida ba'a kaiku bodin ba,, Nurr  tayi dariya haba aunty kema haka zakice bama jin maganar??, eh mana ina kuke jinta, kune dukanyaran mutane kune barna kamar 6eraye,, dariya sosai sukeyi wai su aunty ruky takecema kamar 6eraye, sallamar mijin aunty rukyne ya katse musu dariyar, ya 'karaso yana murmushi kai lallai yau 'yan bodin ne agidanmu,, ina sauran 'kanzon da kwaki???
   Suka tuntsure da dariya,, yaya aimu bama cin 'kanzo da kwaki, ya ce, "kai haba kufa─Ći gsky dai?,ALLAH kuwa yaya mu  abincin makarantarma bamu ciba bare 'kanzo da kwaki, yay dariya to shikenan 'yan 'kannena, ya gajiyar biki?, kunsha rawa ko?,hannu sukasa suna rufe fuska waisu kunya, aunty ruky ta ce, "lalai sanda kuka cashe ai kun manta da kunyar ko, sai yanzu?, dady ma'aruf ya ce, "ato aisuna da gsky ranar murna sukeyi da farin cikin auresu ya Mahmud ko??, kai suka ─Ĺaga suna dariya.
   Sun da─Će agidan suna hira saida aka kira sallar azuhur sanan suka tafi gidan aunty suhaila,, nanma dai tayi farin cikin ganinsu, nanma hira sukai mata sosai sai gabda magriba suka tafi gida.

------------------------------------------------
                   Suna falo zaune suda Saiff wani American film suke kallo, gaba ─Ćaya hankalinsu yana kan tv, saidai lokaci2 sukanyi ─Ćan ihu saboda film ─Ćin na fa─Ćane, ya mustapha da ya mubarak suka shigo falon da sallama, babu wanda ya amsa dan hankalinsu yana kan tv, ya mubarak ne yadaka musu tsawa, afirgice suka ─Ćago suna kallonsa, ya ce, "wane irin iskancine kunaji ana sallama amma kunyima mutane shiru??, cikin rawar murya Nurr ta ce, "sorry yaya wlhy bamujiba, ya mustapha ya ce, "yaza'ayi kujimu bayan hankalinku yana kan tv ku idan kuna kallo film bakwa tunawa da kawa da komai.
   Sudai ha'kuri suke basu, suma zama sukayi, ya mustapha ya ce, "kai kubamu abinci, deena da Nurr suka mi'ke agaggauce suka kawo abincin dabasa so awucesu a film ─Ćin.
         Rayuwa mai gudu da sauri yau gashi saura kwana biyar su deena su koma makaranta,, amma basu ta6a addu'ar komawaba, da yamma suka shirya sai gidan ya Fahad, sun da─Će acan suna hira, aunty ikilee taji da─Ćin zuwansu sosai dama ka─Ćaici ya isheta sabida ya Fahad yana office bai dawoba, saida suka tayata tayi abinci suka gyara mata gidan fes sanan suka taho gidan ya Mahmud, itama aunty bilkee ita ka─Ćai suka tarar harma tagama aikinta, ta tarbesu da murna itama, dan danan tacika musu gaba da abinci da abinsha,, ka─Ćan sukaci dansunci abinci gidan ya fahad, daganan suka shiga hira abinsu da labarin shagalin biki, sai wajen 'karfe biyar da rabi ya mahmud yadawo, da sauri aunty bilkee ta tarosa, ya─Ćan rungumota jikinsa yay mata kiss a kumatu, su Nurr suka kalli juna itada deena, hannunta yakamo suka 'karaso cikinfalon shi sai yanzuma ya gansu,, suka rissana suna gaisheshi, sau ─Ćaya ya amsa ya ─Ćora da fa─Ćin yasu mami, lfy lao suke suka amsa, yaja hannun matarsa yana fa─Ćin ina zuwa dama ina son ganinku,, to kawai sukace suna binsu da kallo suna hayewa saman bene, saida suka shige ─Ćakin sa sannan su Nurr suka tuntsure da dariya suka ha─Ća baki wajen fa─Ćin soyayya ruwan zuma. suka tafa, Nurr ta ce, " 'yar uwa kinga wani SABON AL'AMAREE???, deena ta gyara zama tana dariya, kai sis... dama haka ya mahmud yake??, Nurr ta ce, "ga dahir kin gani, kofa kunyarmu baijiba ya mannawa matarsa kiss.
   Deena ta ri'ke ha6a mumadai ALLAH yabamu masu yimana,, dama ance masu shiru2 sun iya soyayya.......
      A─Ćakin ya mahmud kuwa suna shiga yazube a kangado yana fa─Ćin wash ALLAH na nagaji,, aunty bilkee ta ce, "sannu my handsome nasan ka gaji dayawa, ya─Ćan lumshe idanu wlhy kuwa kamar kin sani, yaushe yarannan sukazo??, zasukai awa ─Ćaya da zuwa aunty bilkee tafa─Ća tana zame masa kayan jikinsa, baice komaiba saima ta6e baki dayayi, tagama tabarshi dagashi sai gajeren wando, ya mi'ke yana fa─Ćin bilyna saura  wankan mana, saida tayi ─Ćan fari sannan ta ce, "sorry my handsome kaga bamu ka─Ćai bane, kadaure kayi da kanka yau sai nikuma naje na ha─Ća maka abinci ko??.
   Okey no wahala yafa─Ća yana nufar bayi, itakuma ta tattare kayan ta kaisu inda ya dace, falo tafito ta ha─Ća masa abinci a dani, su Nurr suna zaune suna kallon ikon ALLAH.
   Bayan ta kammala saman ta koma itama, sanda ta dawo harya fito, dakanta ta shafa masa mai ta kawo masa kayan dazaisaka,, bayan yagama shiryawa suka sakko falon, dani ya wuce abinsa, itama ta take masa baya, ta ha─Ća masa abinci sanan tadawo wajensu deena suka cigaba dayin hira.
    Yana gama cin abinci yatafi masallaci, suma dole suka mi'ke suka gabatar da tasu, saida akayi isha'i yadawo, su Nurr suka sake gaishe shi ya amsa yana zama, ya─Ćan kallesu ince dai kuna lissafin hutunku??, gaba ─Ćayansu saida gabansu yafa─Ći, murya na rawa suka ce, "ee, ya ce, "okey!!, tokuyi shiri dan ranar da'aka koma zaku koma.
    Tuni hawaye sun wanke fuskar Nurr ta ce, "yaya dan ALLAH kayi ha'ku ALLAH bamason makarantar nan, a─Ćage yake kallonta, to idan bakwaso ina kukeso,, da sauri deena ta ce, "school ─Ćinmu tada, ya Mahmud!!,  yaja tsaki ashe bakuda hankali, kunsandai magana ─Ćaya nakeyi ko??, banason yawan gardama dan haka ku shirya ranar lahadi zaku koma, gobe idan ALLAH yakaimu zan ha─Ćo muku provision ─Ćinku, idan kuna bu'katar wani abu daban saiku rubuto mini yanzu, ko idan kun koma gida, idan nazo gidan da safe saina kar6a.
   Shiru sukayi dan jisuke tamkar su kwala ihu, gashi babu damar gardama dan ya ha─Će girar sama data 'kasa,, yadaka musu tsawa wai bakwa jinane??, cikin tsoro su ka ce, "munaji, "o,! Da iskancin nakune ya motsa, idanma zaku kwantar da hankalinku ku kwanta dan wlhy makaranta babu fashi bare ─Ćaga 'kafa, kuma daina tunanin wataran zaku barta, idan kunga kun barta tofa kun gama, kutashi ku tafi gida dare yafarayi.
   Jiki a sanyaye suka mi'ke,, sallama sukayi musu suka fice suna gunguni........................


Luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

BILKISA IBRAHIM
    {♡bilyn Abdul♡}

             
12                       
                                                                
........Tunda suka fita basuyima juna maganaba kowa da abinda yake sa'kama zuciyarsa, gidansu khairat suka wuce suka kaimata labarin abin haushi,, itakam harda kuka, amma yazasuyi dolene su koma tunda oga ya 'karrafa, daga nan gida suka wuce, tunda mama tagansu tasan da akwai wani abu a'kasa, kiransu tayi tana tambayarsu cikin lallashi,, ganin ana lallashinsu sai suka saka kuka, suka gaya mata yanda sukayi da ya Mahmud, lallashinsu tashiga yi, ta ce, "suyi ha"kuri su koma tunda yariga ya kafe saisun koma.
   Haka suka ha'kura suna shiri tafiya cikin damuwa, Nurr har wata ramar wahala tayi cikin kwana biyu.
   Ana gobe zasu koma ya ha─Ćo musu duk abinda ya dace,, sayayya yay musu irinta 'ya'yan gata, ranar a ─Ćakin mama suka kwana dayake itace da daddy yau,, har gari yafara haske basu tashiba, ya Mahmud yashigo falon da sallama, ─Ĺakin mami yafara zuwa ya gaisheta sanan yanufi ─Ćakin mama.
     Cikin takunsa na sarauta ya 'karasa gaban gadon, ya─Ćora 'kafarsa ─Ćaya saman gadon ─Ćaya kuma tana 'kasa, hannu yasaka ya yaye bargon dasuka lilli6a dashi, ya cije le6ensa na 'kasa tareda kauda kai gefe dan dagasu sai vest da wandonta, bargon ya maida ya lilli6a musu tareda daka musu tsawa, a firgice suka farka, ganin ya Mahmud tsaye akansu yana huci suka tashi da sauri suna kudundune jikinsu da bargo.
   Fuskarsa a murtuke yake kallonsu,, ya ce, "yanzunan saboda rashin mutunci bama ku tashiba,, nidanake da mata tuni natashi na shirya hakama fahad, wlhy tunkafin na sakko daga gaida daddy natarar daku kun shirya inko ba hakaba wlhy jikinku zai gaya muku marasa mutunci, 'kafarsa ya sauke 'kasa yanufi hanyar fita, haryaje 'kofa yajuyo ya'kara daka musu tsawa wai bazaku tashiba saina laka─Ćeku!!!!!.
   Har rige2n sakkowa sukeyi daga gado, Nurr tafa─Ća bayin mama da sauri, ita kuma deena tanufi ─Ćakinsu domin yin wankan.
   Daga nan saman daddy ya haye afalo ya iske daddy da mama daddy yana break mama tana gefensa,, ya tsugunna yana gaishesu daddyne kawai ya amsa amma mama ko motsi batayiba,, daddy ya ce, "Mahmud za'a amaida 'yan makaranta yau kenan??, eh wlhy daddy zasu koma tunda hutunsu ya 'kare, to shikenan ALLAH yay muku albarka gaba ─Ćaya, amin daddy Ya Mahmud yafa─Ća, daddy ya ─Ćora dafa─Ćin yauwa idan kun dawo kuwa inason ganinka, akwai wani taro danakeso ka halarta a TURKI, an gayyace nine nikuma inada wasu uzuri sosai agabana, dan gobe idan ALLAH yakaimu zan wuce KORIA insha ALLAHU.
   to daddy ALLAH yakaimu,, idan muka dawo sainazo da daddare muyi maganar aii.
   Okey ALLAH yakaimu,, saikun dawo, ina Fahad ─Ćin??, daddy bai kai ga 'karasowaba, amma inaga yana hanya.
  To shikenan ALLAH yakawoshi lafiya, amin ya Mahmud yafa─Ća yana mi'kewa, bayan yafito daddy yakalli mama datayi burus dasu,, murmushi yayi yana fa─Ćin nasan duk cikin 'ya'yanki kinfison Mahmud amma kike nuna ba'kyayi dashi,, mama ta kauda kai gefe tana fa─Ćin nikam Alhaji dan ALLAH kabar fa─Ća karma wani yaji,, aini bani na haifeshiba ga uwarsa can mami.
   Daddy ya ha─Ćiye dankalin dake bakinsa yana dariya, wa─Ćannan halayen yasa yake matu'kar 'kaunar matan nasa sosai, ya ce, "shikenan maman fahad,, mama tayi murmushi to kaji nawa ─Ćan kenan,, haka daddy yayta tsokanar mama suna dariya.
    Suko su Nurr sanin halin ya Mahmud yasasu saurin shiyawa cikin uniform blue da farin hijjabi kayan makarantar ─Ćan zabuwa kenan, jiki asanyaye suka hau saman daddy, sukaje jikinsa suna zauna suna gaidashi, ya amsa yana shafa kansu, ya ce, "yarana yau sai makaranta ko??, suka ─Ćaga kai suna hawaye,, daddy yashiga lallashinsu dayi musu nasiha saida ya Fahad ya iso sanan suka fito suka shiga mota sunata kuka, yau harda ya mubarak da ya mustapha harda Saiff sai sadiq da Nasir yayun khairat, haka suka ─Ćaga zuwa ─Ćanzabuwa.
   Tunda suka tafi babu mai magana, saida ya Fahad yaga shurun yayi yawa sanan yafara jansu da hira, tunsuna bashi amsa ─Ćai2 harsuka fara sakin jikinsu suna hira, suma su saiff motarsu daban.
   Sun isa ─Ćanzabuwa dayawan ─Ćalibai sun dawo, saida aka dam'kasu hannun malaman su sanan su ka shiga yimusu nasiha, alkairi sukai musu mai yawa sanan suka taho suka barsu suna kukan.

Bayan wani lokaci,, matansu ya Mahmud suka fara kwaikwan ciki suduka,, wayyo zokaga murna wajen ya mahmud jiyake kamar ya aha─Ćiye matarsa bilkisu,, aiko tanashan tattali kamar jaririya, duk wani motsinta akan idonsa,, hakama matar ya Fahad itama tana rainon nata cikin cikin nasara, tana shan tattali itama wajen nata mijin.
   Su Nurr ana ─Ćanzabuwa anashan gwagwarmaya, gata kuwa sai abinda yay gaba awajensu aunty badee, komai sukeso ana yimusu, bare yanzu dasu badee keson cusa kansu wajensu ya mahmud,, dansufa sunanan suna haukan sonsu batareda sunsaniba,, kuma kowa yana 6oyema ─Ćan uwansa sirrinsa.
   Yaudai akai kora zuwa masallaci sallar isha'i su Nurr suna ─Ćaki basu fitaba saboda su badee ne masu korar,, Nurr tafito daga ─Ćaki zatayi fitsari saboda tana fashin sallah, gullewa tayi tafa─Ći tareda kwalla wata razananniya 'kara mai firgitarwa.....................
luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

  BILKISA IBRAHIM
     {♡bilyn Abdul♡}

13
           
                            
      ......da gudu su khairat suka fito, yayinda 'yan aji shiddan dake gurin suka bata taimakon gaggawa, asan'kame suka ─Ćauketa tamkar matatta, ─Ćaki suka nufa da ita aka kwantar da ita saman katifa a'kasa, su deena sai kuka sukeyi, ruwa sadiya tashiga yayyafa mata amma ko motsi batayiba, babu dabarun dabasuyi mataba amma ta'ki ko motsawa,, aunty salma ta ce, "anya kuwa ba aljanu bane??, Naxee ta ce, "nima nafara tunanin haka,, inaga mufita daita gaban ─Ćaki sai ayimata karatu,, haka suka 'kara ─Ćaukarta asan'kare zuwa gaban ─Ćaki zuwa sanan anfara dawowa daga masallaci, shamsiyya tafara karatun alkur'ani cikin suratul ba'kara,, takai minti goma tanayi sanan Nurr tafara fisge2 tana wata irin kuwwa,, su Nazee suka rirri'keta, anuty badee ta'karaso aru─Će dan labari yajemata wai Nurr tafa─Ći babu rai.
Shamsiyya ta ce, "wanene??.
      Cikin wata irin murya mara da─Ćinji akace basai kinjiba.
  Shamsiyya takuma cewa shikenan tunda basai najiba, karatun tacigaba dayi, Nurr kafara harbe2 tana cewa zan fa─Ća kidaina 'konani zan fa─Ća,, banza shamsiyya tayi mata tacigaba da karatunta,, saida Nurr tafara kuka konace aljanin sanan shamsiyya ta tsaya.
   Ta ce, "to wanene",
    ya ce, "sunan jantile!!,
   To jantile miyasa kashiga jikinta??.
   Ya kece da wata irin mahaukaciyar dariya, saida yayi kamar minti biyu yanayi sanan ya ce, "tana burgemune danba ni ka─Ćai bane, tun ranar da'aka kawota makarantar nan muke binta, amma bamu samu damar shiga jikintaba sai yau,, har gida muka bita.
   Badee ta ce, "anya kuwa kai musulmine??.
  Nanma saida yayi dariya sanan ya ce, "niba musulmi bane, amma sauran musulmaine.
   To ina ro'konka dan girman ALLAH kafita daga jikin yarinyarnan tunkafin mufara kai ruwa rana,, kaga batayimuku laifin komaiba bare kuce, dan haka kawai ku fita daga jikinta.
   Ya 'kara kecewa da dariya, saikuma ya murtike fuska, k wlhy babu inda zamu domin minga gurin zama, dan jikinta yanada da─Ćin zama gata mai'kyau da'ita 'yar falai2, dan hakama kidaina tunanin zamu fita........ kafin ya'karasa badee ta wanka masa mari, ya dafe kunci yana kallonta,, wlhy karku 'kara kuskuren dukana, idan ba hakaba zan kauce kiyita dukanta babu abinda ya dameni,, shamsiyya taja tsaki ai idan ba'a dokekaba za'a 'konaka wlhy,, batareda tajira amasarsaba tacigaba da karatunta,, ihu yayta kwa─Ćawa yana bada ha'kuri amma sun'ki saurarensa saima 'yan karatun suka 'karu,, yara suna tsaitsaye suna kallo daga nesa,, yayinda 'yan aji shida suka cika wajen,, su khairat ne kawai 'kanana awajen,  suna gefe sunata kuka.
   Saida sukayima al'janinnan ligif da ayar ALLAH sanan suka sakeshi yafice.
   Nurr tabu─Će ido tana yatsine fuska, ganin mutane akanta saita fara tambayar lafiya??, babu wanda yabata amsa saima Badee ce ta jeho mata tambaya,, Nurr inane yake miki ciwo ajikinki??"
  Nurr takalli kanta, aunty duk jikina ciwo yakeyi gashi inajin fitsari, sannu suka shiga yimata, aunty badee tarakata tayi fitsari sanan tazo ta kwanta sai barci.
  Wanan kenan

KADUNA.
   a kd kuwa matar ya Mahmud ce babu lafiya, tanata fama da ciwon mara, a gaggauce ya ─Ćauketa suka tafi asibiti, suna zuwa aka shiga bata taimakon gaggawa dan jinine yafara zuba ta 'kasanta,, tunda aka shiga da'ita ─Ćakin ya Mahmud yake safa da marwa a "kofar ─Ćakin, gaba ─Ćaya hankalinsa atashe yake, yana addu'ar ALLAH yabata lafiya ya kare masa jaririnsa.
    Bayan kamar awa ─Ćaya doctor ya fito yana cire safar dake hannunsa wadda ta 6aci da jini, Nos ─Ćin dake biye dashi ta mi'ka masa wata tasa ya jefa safar aciki, aki─Ćime ya Mahmud yataresa da jerin tambayoyi, doctor yaya matata??, ya cikin jikinta??, incedai kun cetomin matata??........, da sauri dector ya katse ya Mahmud, karka damu Alhaji muje office muyi magana.
   Ya mahmud ya takema doctor baya suka nufi office ─Ćinsa,, kujera ya nuna masa suka zauna,, saida yabashi hannu sukayi musabaha sannan ya ce, "kayi ha'kuri Alhaji mahmud munyi iyakar 'ko'karinmu domin ceto cikin jikin matarka amma hakan ya gagara, cikin dake jikinta yazube saidai mutayaku da Addu'a ALLAH yabaku wani mai amfani.
   Ya mahmud ya dafe kai yana jujuyawa ALLAH ka─Ćai yasan irin burin daya ─Ćauka akan cikinnan, amma babu komai ALLAH daya basu ya kar6a shine zai sake basu wani akaro na biyu,   ya ─Ćago kai yana fa─Ćin doctor matatafa??".
   Doctor ya ce, "itakam alhmdullah munyi mata allurar barcine dan ta huta, zamaka iya shiga kaganta Dan yanzu nasan angama gyarata..........jiki asanyaye ya mi'ke yafice, ─Ćakin da'aka kai Aunty bilkee yanufa,, itaka─Ćaice a─Ćakin, tana kwance agado idonta arufe, ansaka mata ledar 'karin ruwa a hannu ─Ĺaya, ahankali ya dur'kusa gabanta yakamo ─Ćayan hannunta daba'a saka 'karin ruwaba, ahankali yake murzashi yana magana 'kasa2 kamar mai ra─Ća,, karki damu bilyna ubangiji yana sane damu insha ALLAHU zai bamu wani, kekuma ALLAH yabaki lafiya, ya 'kare maganar da sumbatar kumatunta, mi'kewa yayi yazaro wayarsa daga aljihu yashiga laluben mami, bugu ─Ćaya ta ─Ćauka.....saida ya─Ćan rissina wajen gaisheta, ya ce, "mami muna asibiti.
   Arikice mami ta ce, "waye baida lfy mahmud!!, cikin sar'kewar murya ya ce, "bilkeesu ce tayi 6ari.
   Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un mami tashiga fa─Ća ta ce, "ganinan zuwa yanzu,, wayar takatse tanufi ─Ĺakin mama aru─Će,, mama tana zaune tana lazumi dan ba'a da─Će dagama sallar azuhurba, ta ce, "mami injidai lafiya??.
   Mami ta ce, "dadai sau'ki wlhy yanzu mahmud yakirani wai bilkeesu ce tayi 6ari sunama asibiti, mama ta ce, "Hasbinallahu wani'imal wakil,, ALLAH yabata lafiya,, amin mami tafa─Ĺa tana mi'kewa mama bari naje asibitin naga halin da suke ciki dannaji kamar shi ka─Ćainema.
   To saikin dawo ayi mata sannu, to mama saina dawo.

Mama na fita asibiti tanufa, sanda taje har yayar aunty bilkee ta je dan ya Mahmud yakirasu,, ta gaisheda mami sanan mami ta tambayeta yamai jikin,, aunty hajarah ta ce, "da sau'ki mami aitanama barcine.
   ─Ćakin suka shiga, mami tanata jinjina abin da addu'ar samun sau'ki ga bilkeesun, ta ce, "ina Mahmud ─Ćin??, aunty hajara ta ce, "yaje sallah yanzu zai dawo.
   Babu da─Ćewa ya Mahmud yadawo, ya gaida mami,, itama tayi masa jaje,, sun─Ćan da─Će suna jajanta abin,, mami ta ce, "wai ya akayi haka tafaru Mahmud??.
   Wlhy mami tun jiya nake lura da'ita kamar batada lafiya,, na tambayeta ta ce, "lafiyarta 'kyalau, sabodama karna dameta da tambaya saita dunga dakewa tana nuna lafiyarta lao,, yau hakadai nafita aiki cikin zullumi, wajen shabiyu saina kirata jin muryarta asar'ke nashiga tambayarta lafiya dai kuwa??, ta ce, "babu komai cikintane ke─Ćan mur─Ćawa, na ce, "shikenan ALLAH yabata lafiya,, harna cigaba da aiki sai zuciyata takasa nutsuwa da yanda naji muryarta shine nabawa Fahad sauran aikin daban gamaba na nufi gida, a tsakiyyar falo na tarar da'ita tanata juye juye, shine na ─Ćakkota muka taho asibiti, sanda muka iso har jini yafara zuba.
            Mami ta ce, "ALLAH sarki, to ubangiji ALLAH yabata lafiya,, amma zurfin cikin bilkeesu yayi yawa, kaida mijinka bazaka fa─Ća masa bakada lafiya ba.
   Aunty Hajarah ta ce, "wlhy mami haka bilkeesu take ko'a gida bakowa yake saurin gane batada lafiya ba.
      kai amma wanan aisaita cutar dakanta gashi gida kai ka─Ćai, hakadai sukaita ─Ćan tattaunawa, kafin kace mi asibitin yacika da dangi sunata zuwa dubata.
   Anan mami ta kwana dan an kwantar dasu,, da daddare daddy da mama sukazo suka dubata, da 'kyar aka lalla6a ya mahmud yatafi gida,, da ya ce, "shifa anan zai kwana, to aunty bilkeesu ALLAH yabaki lafiya,, yakuma azurtaku da wani ─Ćan mai amfani..

D/Z
  Amakaranta ma su Deena suncigaba da harkokinsu kamar yanda suka saba, saidai lokaci2 aljanun Nurr sukan ─Ćan motsa kuma suna bata wahala, dan wataran 'kafa suke ri'kemata su hanata tafiya, wani lokacin kuma susakata ta zauna tayita kuka,, suma su khairat dasunga tana kuka saisu zauna suna tayata, to Nurr kema ALLAH yabaki lafiya.

Itama aunty bilkeesu an sallamota, tacigaba dayin dukkan harkokinta na rayuwa,, matar ya Fahad kuwa aunty ikilee tananan tana jan nata cikin dahar yafara fitowa masha ALLAHU.
   Dahakaidai lokacin bistin yayi, ya Mahmud ne da aunty bilkee sukaje musu,, sunkoyi murna da ganinsu,, ya Mahmud yashiga tuhumar Nurr akan ramar datakeyi, dasauri ta ce, "karatune yaya da tunanin gida amma lafiyata 'kalau,, su deena sunason fa─Ćar gsky amma tahanasu.
   Ya mahmud ya ce, "to ALLAH yataimaka, idan kunyi ha'kuri kamar yaune zakuga kun kammala,, aunty bilkee ta ce, "gsky ne.
    Sun da─Će suna hira daga bisani suka taho,, kamar yanda suka saba idan sunga 'yan gida sai sunyi kuka yauma hakance ta kasance saida suka─Ćan matse hawaye....... ....... 

SABON AL'AMAREE

BILKISA IBRAHIM
   {♡bilyn Abdul♡}

           14
                           
                                             
.......Yauda gobe sai ALLAH,, akwana atashi bayida wahala su Nurr sunshiga aji biyar amakaranta, ranarda su aunty badee zasuyi candy kuwa sunsha kuka kamar ransu zai fita,, suma har kuka sukayi amma yazasuyi haka rayuwar makaranta tagada, wasu sutafi wasu su shigo,, hakadai suka dangana suka barma ALLAH komai,, yanzukam rayuwa ta canja musu domin basuda wani gata a makarantar kuma dama 'yan aji biyar haushinsu sukeji saboda dukanda su badee sukai musu sun ─Ćau alwashin ramawa akansu deena, gakuma 'kiyayyar dake tsakanin 'yan ss 3 da ss 2,.
   Duk tsoron dukan Nurr saita dake yanzu domin idan ta nuna tsoro rainasu za'ayi, babu 'karya suna dakuwa kamar jakuna, komai aka yayo sai kansu,, kodukan 'yan ss 2 za'ayi sainasu khairat yafi yawa, ranar kuwa akayi musu wani duka wanda yay sanadi tashin aljanun Nurr.
   Nurr ta sha'ke wuyan 'yar aji shiddan dake dukansu taita jibga kamar ALLAH ya aikota,, 'yan ss 3 suka rufu akanta suna duka,, datai kukan kura saita zubar dasu 'kasa suduka, dukan kan mai uwa da wabi tashiga yimusu,, aiko sun lallasu da'yar su deena suka shawo kanta ta ha'kura,, aljanin ya ce, "wlhy duk ranar dasuka sake dukansu Nurr saiya koya musu hankali fiye da yanda basa zato.
   Wanan lamari har gaban pc yakaisu,, pc tabawa 'yan ss 3 rashin gsky takuma gaya musu su Nurr ba 'kannen su badee bane, itace dakanta ta ha─Ćasu dasu,, daga yau aka 'kara dukansu Nurr batareda sunyi laifiba to wlhy mutum saiya gane kurensa.
   Tundaga ranar su deena suka samu 'yancin kansu indai kaga an dokesu to za'a doki kowane, wanana ne yabasu damar tsula tsiyarsu suma amakatantar duk 'yan ss 2 babu masu ajinsu Nurr,, sune manya masu aji gakuma 'ko'kari, komai nasu na girmane, su kansu wasu 'yan aji shiddan tsoronsu sukeji musammanma na ─Ćakinsu.
   Yaranfa suna shanawa wlhy.

KADUNA
  A kd kuwa lamura sai ahankali,, ya Mahmud yana cikin damuwa dominkuwa har yanzu idan aunty bilkee tasamu ciki saiya zube dayakai wata uku,, kwata2 cikin ya'ki zama, har matar ya fahad ta haihu sarga─Će─Ćen ─Ĺa namiji,, sunan daddy suka saka masa suna kiransa da Abdul.
   Tun ya Mahmud yana nuna rashin damuwa da lamarin har abin yafara caccakar zuciyarsa,, to ayanzu dai tana ─Ćaukeda ciki na hu─Ću muna kuma addu'ar ALLAH ya inganta.
   Wannan hutun su ya mubarak ne sukaje ─Ćaukar su Khairat daga makaranta, sundawo sunsha hutunsu kamar yanda suka saba, sunyi ziyara gidajen dangi dahaka hutunsu ya 'kare suka koma dan yanzu sun dake harma wani son makarantar sukeyi.
         To awanan karonma bata canja zaniba domin aunty bilkee ta'kara yin 6ari harma na 'yan biyu,, ya Mahmud harda kuka yayi,, yabani tausayi kwarai da gsk amma yaza'ayi haka ALLAH ya 'kadarto masa,, yana matu'kar son 'ya'ya amma ALLAH bai hukunta su iso duniyaba bama sukai wata hu─Ĺu aciki,, wanan karon doctor yabashi shawarar ayimata wankin ciki ko ALLAH zaisa adace,, ya Mahmud baiyi gardamaba yabada umarnin ayi mata, likitoci sunyi mata wankin ciki suka bata kuma maginguna.
   Haka ya Mahmud yacigaba da tattalinta batareda yarage ko kwayar zarra asontaba saima 'karuwa da sonnata yakeyi acikin zuciyarsa, itama tana son mijinta sosai shiyyasa take bashi nagartacciyar kulawa ta musamman, ya Mahmud yana 'ko'kari wajen danne damuwarsa ta rashin ─Ća dukda wani lokacin aunty bilkee tana harbo jirginsa saidai tayita kwantar masa da hankali da bashi labaru masu da─Ći dahaka harya saki jikinsa.
    Hakama mama tana damuwa da al'amarin na ─Ćan nata, dan tasanshi da son yara tunyana 'karami,, takan ware dare guda wajen ro'ka masa ubangiji akan samun haihuwa, takanyi azumin alhamis da litinin domin yi masa addu'a da mi'ka 'ko'kon bararsu ga ubangiji,, tasan duk cikin 'ya'yanta tafison Ya Mahmud tanayin kawaicine kawai irinna al'ada.
   Awanan karon kusan tare suka 'kara samun ciki da aunty ikilee matar ya Fahad,, ya mahmud yayi murna dukda zuciyarsa tana rawa,, yayita addu'a ALLAH ya inganta masa wanan,, cikin amincin ALLAH tawuce wata uku harta shiga na hu─Ću,, na hu─Ćuma ya shu─Će aka shiga na biyar dangi sunata murna dan ganin wannan karon da alamar nasara.
   Wani daren juma'a ta tashi da matsananncin ciwon ciki,, arikice ya Mahmud yafarka,, tallafota yayi zuwa jikinsa yana mata sannu,, ya ce,, "bilyna miyake miki ciwone??, cikin kuka tanuna masa cikinta,, ya shiga ru─Ćani sosai gashi dare yayi,, jiki na rawa yakira doctor ─Ćinsu cikin sa'a yasameshi, cikin ru─Ćewa yake masa bayanin damuwarsa, doctor ya ce, "karka damu ina zuwa.
   Minti ka─Ćan doctor ya iso, sanda yazo har jini yafara zuba ajikin aunty bily,, taimakon gaggawa likita yashiga bata amma ina yauma antaki rashin sa'a domin cikin yazube,, ya Mahmud yadafe kai yana hawaye amma ya zaiyi,, likita yashiga lallashinsa da bashi baki,, da'kyar yayi shiru daga kukan dayakeyi,, ya taimakawa likita suka gyara aunty bily dabatasan inda kanta yakeba,, 'karin ruwa yasaka mata sanan doctor yanufi gida,, shikuma ya Mahmud yayo alwala yashiga mi'ka kukansa ga ALLAH subahanahu wata ala.

Awanan karonma su Nurr sunzo hutu saidai bashida yawa,, suka gama kwanakinsu suka koma, daga wanan hutun sune zasu shiga aji shida.
   Tafiyarsu babu da─Ćewa matar ya Fahad ta haihu mace, aka saka mata sunan mama suna kiranta da Farha,, anyi shagalin suna babu laifi Alhamdllh.
   Ya mahmud yataka rawar gani awajen sunan,, kusan kullum Abdul yana gidansu, gata sosai ya Mahmud yakema yaron jiyake kamar shine ya haifeshi acikinsa,, shima yaron yasaba dasu sosai.
   Haka rayuwar take gudu, bayan cikin daya zube aunty bilkee tasake samunciki sau biyu yana zubewa zuwa sanan ya mahmud yama gama fidda rai.
    Lokacin dana takwas yazube sai likita yakirashi suka zauna,  doctor ya ce, "Alhaji mahmud gawata shawara mana.
   Ya mahmud ya ce, "inajinka doctor karkaji komai kasanar mini,, likita yacire gilas ─Ćin idonsa yana kallon ya Mahmud,, Alh Mahmud kayi ha'kuri inaga yakamata mu ─Ćaure mahaifar matarka ta huta,, bincike ya nuna mana mahaifarta batada 'karfin dazataa ri'ke ─Ća, shiyyasa da cikinta yafara girma saiya zube saboda yafara nauyi,, gashi kuma kana yawan takura mata a 6angaren auratayya.
   Shawarata kuwa itace yakamata ka 'kara aure, arikice ya mahmud ya─Ćago yana kallon doctor, doctor ya jinjina kai haka nake nufi ka 'kara aure domin naga kana matu'kar son 'ya'ya,, kuma hakan zai taimakawa matarka wajan samun hutu,, kaima zai taimaka maka wajen samun mai biya maka bu'kata yanda yakamata, idan kanada mata biyu zaka ringa raba musu kwana kaga karage mata nauyi kenan,, kuma idan da rabo ita zatazo ta haihu maka, dan haka ina mai baka shawara dakayi nazarin maganganuna insha ALLAHU zakaga fa'idarsu,, itama  bamu fidda ran wataran zata haihuba amma gsky zamu barta tahuta sosai.
      nariga nayima mahaifinka bayanin komai ─Ćazu, domin kai kana cikin ru─Ćani sanan.
    Ya Mahmud ya zaro ido doctor miyasa ka gayawa daddyne??, doctor yay murmushi saboda hakan yadace aii.
   Shiru ya Mahmud yayi yana juya maganganun doctor shikam gsky babu maganar 'kara aure acikin tsarinsa,, baima ta6a mafarkin hakaba,, toshi idanma zai 'kara auren wazai aura?????????????.......................

luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

BILKEESA IBRAHEEM
    {♡Bilyn Abdul♡}

WANAN page ─Ćin nakune sweet sister's Reefat yahya & maman usseey, AL'KAIREEN ALLAH ya kaimuku har gadon barcinku, nagoda da 'kaunarku gareni ALLAH ya 'kara mumu baseeeeeera my darling's .

              1⃣5⃣
               
.....Tunda aka sallamosu daga asibiti suka dawo gida ya Mahmud yakasa nutsuwa da magamganun doctor,, abu ─Ćayane yake sakashi fargaba shine daddy da doctor ya ce, "yafa─Ćamawa,, dukda har yanzu daddy baita6a yimasa maganarba amma tabbas yasan yana sane kuma duk daren da─Ćewa saiyayimasa,, yasan halin daddy sarai akwai basar da'abu,, saiyayi kamar basan kana cikin wani haliba sai rana─Ćaya yabaka umarni kuma dole kabishi, dan mutumne mai magana ─Ćaya maikuma tsayawa akan ra'ayinsa.
   Aunty bilkee dake zaume tun ─Ćazu agefen ya Mahmud amma bai saniba saboda yana cikin duniyar tunani,, ya ─Ćago da sauri yana kallonta, ta ─Ćan langwa6e kanta gefe itama tana kallonsa cikin taushin murya ta ce, "haba my handsome mikake tunani haka??, miye damuwarka??, saida yaja numfashi tareda juyowa yana fuskantar ta sosai, ya─Ćanja hancinta yana murmushin ya'ke babu komai bilyna kawai dai ina tunanine akan office wani─Ĺan aikine yashamin kai shine nake tunanin mafita.
    Hannunsa takamo tana murzawa ahankali, ayya my handsome ka kwantar da hankalinka kaji,, nasan insha ALLAHU komai zai warware, kaifa gwarzone a 6angaren komai na rayuwa, dayawa ana alfahari dakai acikin family ─Ćinmu saboda kwazonka da dauriya.
    Ya sumbaci hannunta data ri'ke nasa,, ngd my bily nagode da irin kulawar dakike bani ALLAH ya tsawaita rayuwarmu harmuga jininmu muma a duniya,, amin tafa─Ća tareda kwanciya saman cinyarsa, my handsome!!.
   Na'am bilyna yaya akayi ne??, dan ALLAH yaushe zamuje ganinsu Nurr makarantane?? Wlhy ina sha'awar sake zuwa school ─Ćinnan dan tana burgeni, kanta yashafa tareda fa─Ćin nidai inson zuwa kano ranar litinin inaga dagacan zan biya nagansu tunda tafiyar mota zanyi,  kekuma kiyi ha'kuri sai wani hutun tunda kinga dasun dawo sai kuma candy kenan,, murmushi tayi ta ce, "ALLAH yakaimu darai da lfy,, kai gsky duniya tana gudu yanzunan harsu khairat sun shekara uku amakaranta, kenanfa aurenmu shekara uku kenan??, ya Mahmud ya ce, "hakane gashi har Fahad yanada yara biyu, ai abun kamar yaune.
   Hakane kam ALLAH dai yasa mucika da imani,, amin my bilyna ya mahmud yafa─Ća yana sumbatar kumatunta.

D/Z
     Su Deena ana makaranta yanzukam sune suke shanawa, Nurr itace shugabar ─Ćalibai tayanzu, suma su khairat duk anbasu ─Ćankwali,, sumafa suna tsula tsiyarsu gsky,, dan sun maye gurbin su badee nada,, su harma malaman shakkarsu sukeyi, gashi yawancinsu duk so sukeyi suyi soyayya dasu musamman ma Nurr dantafi su khairat 'kyau dukda suna matu'kar kama dajuna.
    Yau monday gaba ─Ćaya Nurr sukuku ta tashi, ko wajen tare bata tsayaba, dan yau batajin  dukan kowa, tawuce aji ta kwanta,, malam Mahfuz 'kya'ky'kyawan saurayi mai kwarjini yada─Će yanason Nurr kuma bai 6oye mataba yafito fili yasanar mata, itakam ko kallo bai ishetaba dan haushima yake bata,, ya 'karaso gate ─Ćin 'yan ss3 suka shiga gaisheshi wasukuma suna masa kwarkwasa kamar yanda suka saba,, ya kai dubansa ga khairat yana fa─Ćin yau banga shugabar ─Ćalibaiba kota manta yau duti namune nida ita??, khairat ta ce, "malam bata mantaba dan tare muka fito inaga batajin da─Ći shiyyasa ta wuce aji,, amma karka damu zamu wakilceta.
   Okey babu damuwa amma kusanar da'ita ta daure tafito anjima dan bazaiyuwu ace ba'a ganin mai duti ba,, to malam za'a sanar mata deena tafa─Ća tana binsa da harara, dan sunsan shishshiginsa ne yasa aka ha─Ćashi duti da Nurr.
   Koda aka fito break Nurr bata fitoba tana zaune a aji abinta saidai daka kalleta kasan batada walwala, tana zaune saiga Sajeeda marwan,, Sajeeda marwan itama 'yar ss3 ce, tana bala'in son malam Mahfuz kamar ta kashe kanta, tun tana 6oyewa harta kasa, tafito fili ta nuna masa amma saiya nuna mata shifa Nurr yakeso,, wannan dalilin yasa take matu'kar jin haushin Nurr jitake kamar ta ha─Ća wuta ta jefa Nurr,, tasan Nurr tafita komai 'kyau, ilimi, gata, gayi itace shugabar makarantar kuma pc da malamai suna matu'kar jida ita dan hazi'kar ─Ćalibace mai hankali da Nutsuwa.
    Tayi tsaye kyam akan Nurr dake zaune takifa kanta akan desks,, amma ba barci takeyiba, jin kamar mutum akanta yasata ─Ćago,, ganin sajeeda tsaye saita yatsine fuska tana fa─Ćin kekuma kafiya zakizo ki tsaya min akai kamar naci miki bashi???,, Sajeeda ta 'kara tamke fuska saikuma ta tsartar da yawu tana wani jijjige2n jiki kamar wadda take afilin gasar rawa,, Nurr ta ta6e baki tareda maida kanta takwanta,, dasauri Sajeeda ta finciko hijjabin Nurr,, Nurr tayi mata banza dan batajin yin hayaniya yau,  itama sajeedar tasan Nurr sarai ba kanwar lasa bace.
    Ganin Nurr ta'ki kulata saita dan'kara mata KULLI abaya (dundu)jikake tiiiimmmmm!!!!!!.
   Da sauri Nurr ta─Ćago idanunta da sukayi jajur saboda 6acinrai,, zuwa sanan 'yan ajin sun fara dawowa,, jikin Nurr yafara rawa, ita kanta Sajeeda ta tsorata kwarai da gske, su khairat suna gefe suna kallo dan suma shigowarsu kenan, tabbas sunsan aljanun Nurr sai suntashi dan tun ─Ćazu ranta yake a6ace,, wata muguwar sha'ka tayima Sajeeda ta ─Ćagata sama ta fa─Ća da bangon class ─Ćin, saman cikinta ta haye tashiga jib─Ća,, duk wanda yakalli Nurr yasan ba'ita take wanan aikin ba dan Sajeeda tafi Nurr girma sosai,, Nurr yar karamace kodayake ance fa─Ća azuciya yake ba'a jikiba.
     Adai2  wanana lokacin kuma ya mahmud ya iso cikin makarantar,, sunata gaisawa da malamai dayake sun sanshi sosai saboda yawan zuwan dayakeyi, gashi kuma indai yazo saiya yimusu alkairi sosai.
   Dukanta take sosai kamar uwarta dama anfa─Ćawa su Nurr iya dambe ne,, dagudu wasu 'yan ajin sukaje kiran malamai , dagudu suka 'karasa staffroom suna  hakki,, malamai suka fara tambayar lafiya,, cikin hakki Fadeela Ahmad ta ce, "malam Nurr ce suke fa─Ća da sajeeda kuma da alama ba Nurr bace dan gatacan tasha'keta zata kashe...... .aii kafin su'karasa fa─Ća malaman sun rufo da gudu sai ss3a.
    malam Mahfuz ne yashigo shida ya mahmud saikuma malam Faruq da malam shazali,, ya Mahmud yashiga 'ko'karin fincike Nurr daga kan sajeeda danta mata wata muguwar sha'ka sai kakarin mutuwa takeyi nakula tafarajin kamshin lahirama........................

luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

BILKEESA IBRAHEEM
     {♡bilyn Abdul♡}

16
          
                             
                                               
...........Duk 'karfi irin na namiji amma ya mahmud yakasa fincike Nurr daga kan Sajeeda,, ya daddage ya wanka mata mari, da sauri ta saki sajeedar takoma ta sassan'kame kamar gawa,, da hanzari ya mahmud yatarota tafa─Ćo jikinsa, ya rungumeta yana girgizata ahankali yake ambara Nurr! Nurr!!!, amma Nurr ko motsi tagaza yi, malam Mahfuz ya ce, "inaga a─Ćauketa zuwa staffroom kawai.
   Wasu daga cikin ─Ćaliban sukazo zasu ─Ćauki Nurr amma sai ya mahmud ya─Ćaga musu hannu batareda yayi maganaba, cak ya─Ćauketa kamar wata jaririya to dama Nurr ─Ćin 'yar fit ce,, su khairat suka take musu baya,, itama sajeeda saita mi'ke jiki asanyaye tana shafa fuskarta data kumbura tayi dam saboda duka, malam shazali yadaka mata tsawa kiwuce akace mara mutunci kawai wlhy nasan ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba kece kika jata, Sajeeda tawuce tana shar6ar hawaye.
   Barandar staffroom suka nufa,, tabarma aka shimfi─Ća ya mahmud yakwantar da ita sanan yanemi gefenta yazauna,, malam faruq ya ─Ćakko alkur'ani yafara karatu, yada─Će yanayi kafin ta motsa, tafara fisge2 kamar yanda tasaba, ya mahmud yari'keta yana tofa mata addu'oi shima,, zuwacan tasaki wata 'kara tareda yin atshawa mai 'karfin gask, saikuma jikinta yayi sanyi tayi wani lagwaf, ya mahmud yasake jawota sosai zuwa jikinsa yacigaba dayimata addu'a,, bayan kamar minti 30 saita bu─Će idanu akan ya Mahmud,, da sauri ta rungumeshi tana rusar kuka mai tsuma rai,, shiru yayi yana kallonta batareda ya ce, "komaiba suma su deena suna tsaye suna hawaye, ya Mahmud ya─Ćagota yana share mata hawaye to kukan ya isa hakako??, ahankali tashiga sassauta kukan, su deena sukazo suma suka zauna kusada ya mahmud suna gaisheshi,, ya amsa yana tambayarsu ya karatu sukace alhamdullah, ya kalli Nurr da fuskarta ta─Ćan kumbura anya Nurr kina amfani da magungunanki kuwa??, kai ta─Ćaga eh yaya ina amfani dashi wlhy, amma yaya yaushe kazone wai??,, yanzu nazo natarar kina jibgar 'yar mutane wato a bodin ─Ćimma bakubar halinkuba ko??.
   Cikin rashin fahimta take kallonsa ta ce, "yaya aimu bama fa─Ća dakowa  yanzu,, ya mahmud ya harareta bayanzu kika gama fa─Ća da wataba,, kai ta girgiza masa wlhy yaya banyi fa─Ća dakowa ba, nifa ina ajima ina barci saiyanzu nafarka naganni awajenka.
    Shiru yayi domin yagano bama da'ita akayi fa─Ćanba kenan, ALLAH dai yabama 'yar 'kanwar tasu lafiya kawai zaice, nan sukayi 'yar hira sanan yabasu abinda yakawo musu sukaita masa godiya danshidai baya zuwa wajensu hannu rabbana,, shiyyasa basu ta6a tashi basuda abunda zasuciba, abincin makaranta kuwa saisun gadama sukeci, idan aka kusa hutu har 'kyautar kayan abincinsu sukeyi.
   Yabasu ku─Ću masu yawa kuma sanan ya ce, "bari yatafi dan yanada mitin akano 'karfe uku,, yanafata karfe biyu da ravi tayi masa akano saiya huta na rabin awa kafin sushiga mitin ─Ćin.
    Hannu suka shiga ─Ćaga masa bayan yayima malaman sallama tareda yimasa fatan alkairi da sauka lafiya.

Bayan tafiyar ya Mahmud aka kira 'yan ajinsu Nurr suka fa─Ći abinda suka sani,, har malamai suka gano laifin Sajeeda ne,, malam Mahfuz dakansa yayma sajeeda bulala goma,, tareda gaya mata maganganu masu zafi akan Nurr, daganan aka sallamesu suka dawo aji, dama ita sajida 'yar ss3b ce danhaka saita wuce ajinsu.

Haka akacigaba da damawa yau fari gobe tsumma har hutu yazo kowa yakama gabansa,, wanan karonma su ya Mustapha ne sukazo ─Ćaukarsu, sunyi farinciki da ganinsu, bayan gaisuwa da murnar ganin juna suka ─Ćauki hanyar Kaduna,, cikin nasara suka isa da wuri kuwa.

WASHE GARI.
     Tunda suka shiga gaida daddy yake binsu da kallo tabbas lokaci yayi dazai zartar da hukuncin dake zuciyarsa, saidai yana fargabar abinda zaije yadawo,, amma tabbas zai aikata umarnin marigayi mahaifinsu Alh mutallaf,, yasan akwai gagarumin tarna'ki dazai biyo baya amma yazaiyi dolene yacika al'kawarin daya ─Ćauka kodan samun alkairi daga albarkar iyayensa,  yafitar da numfashi mai 'kargi daga hancinsa, insha ALLAHU zai zauna mitin da sauran 'yan uwansa guda goma sha uku danjin abinda yadace akan SABON AL'AMAREEn dake shirin faruwa a family ─Ćin nasu,, yana fata ALLAH ya yayyafama abin ruwan sanyi kawai......
    Nurr ta katse masa tunani dafa─Ćin daddy lafiya tunanin mikakeyine haka??, murmushin ya'ke daddy yayi, ya ce,, "ina tunanin yanda naga yarana sun girma, kamar basu bane aka kai makaranta suna kuka dafa─Ćin basaso.
   Fuska suka rufe suna dariya , ahaka mama tashigo falon tasamesu, bayan sun gaisheda daddy itama suka gaisheta sanan suka mike suka fice, mama tabisu da kallo itama yana murmushi kamar yanda daddy yake binsu danasa kallon.
   Bayan shige warsu daddy yaja ajiyar zuciya tareda fa─Ćin hajiya lokaci yayifa da komai zai fito fili, "lokaci yayi da za'a bu─Će wani sirri a family ─Ćinnan, lokaci yayi da SABON AL'AMAREE zai bayyana.
   Arazane mama take kallonsa, tuni hawaye sun wanke mata fuska cikin sanyin jiki tanemi guri tazauna,, ta─Ćago kai tana kallon daday idonta cike da kwalla, niko wlhy Alhaji saza'abar abunan danayi farinci mai yawan gsk,, banason tone2nan wlhy,, dan ALLAH kubar zancennan karku bari wani SABON AL'AMAREE ya 6ullo acikin family ─Ćinana, tunda manyan 'ya'aynku ma basu san komaiba akai,, ta'kare maganar da sakin kuka mai tsuma rai.
   Rungumeta daddy yazo yayi yana share mata hawaye,  gsky kika fa─Ća amma yazama dole sirrin 6oye yafito fili,, dolene SABON AL'AMAREE ya bayyana kodan cikar burin mahaifinmu danakeson yi,, ina son cika al'kawari nawasu shekaru abaya dana ─Ćauka,, kedai kitayamu da addu"ar samun sau'ki akan 'kurara dazata tashi awanan family. Koni banason faruwar wani SABON AL'AMAREE amma hakan yazama dole kodan 'kyautata rayuwar wa─Ćanda abin yashafa.
    Fa─Ćawa jikinsa mama tayi tana cigaba da kukanta shikuma yana aikin lalashi.

Haka su Nurr suka gama hutunsu suka koma,, amma har yanzu babu abinda yafaru a family ─Ćin dan daddy yakasa bu─Će sirrin komai,, yama kasa 'kir'kirar mitin─Ćin dazaisa komai yafito fili, itama mama dayake bataso bata ta6a ─Ćaga masa maganarba bare ta 'karfafa masa gwuywar fallasa SABON AL'AMAREE.
   dahaka rayuwa taci gaba da shurawa su deena suka fara zana jarabawar ssce ─Ćinsu,, cikin hukuncin ubangiji suka gama cikin nasara,, ranar mota biyar dangi sukayi wajen ─Ćakkosu domin kuwa daga kansu aka fara bodi, sadda suka iso gida kuma suka tarar da gagarumin farty da yayunsu suka ha─Ća musu,, lalai gurin ya 'kayatar anci ansha ankuma 6ararraje dan 'yammatan uku sunci rawa sosai,, babu wanda ya hanasu domin ranar farin cikinsune da dukkan masoyansu.
      Saida sukai kwana biyu suna hutun gajiya kuwa,, daga baya suka warware suka cigaba da harkokinsu nayau da kullum tunda yanzu suna a free, zan iya cewa kusan har yazu akwai sauran rawar kai atareda su Nurr, amma sun─Ćan sasaauta bakamar daba,, sunkoma islamiyyarsu tunda yanzu babu boko, komai yana tafiya normal saidai daddy abubuwa da dama sunacin zuciyarsa ga damuwar ya mahmud gakuma babban al'kawarin dake kansa na fallasa asirin dake 6oye, har wani ─Ćan ciwo yayi na kwana bakwai dole yaje yaga likitansa dake 'kasar india.
       A6angaren ya Mahmud kuwa yana cikin damuwa tun yana 6oyewa har matarsa tagano shi,, itama tabbas abin yafara damunta dan haka taje tayi bincike agurin likitansu,, bai 6oye mata komaiba gameda bayanin dayayima ya mahmud ashekaru uku dasuka wuce,, tayi mamaki kwarai da gsk dan bai ta6a gaya mataba koma nuna mata bai ta6ayiba saidai talura yana cikin damuwar rashin samun haihuwa,, ashe angayamasa hanyar dazaibi yamagance matsalarsa yaki yabi,, tabbas yanzu zata koma gida saidai komai tafanjama fanjan dan bazata iya dawwama cikin 'kunci da damuwar rashin 'ya'yaba dolene yanema musu mafita tunkafin guru ya kure musu kowa yasan matsayinsa tofa akwai matsala kenan aunty bilkee kardai kiyi mana butulciiiiiiiii!!!!!!!!!!......................luv u oll my fan's
©2017
[12/02 18:35] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

BILKEESA IBRAHEEM
     {♡bilyn Abdul♡}

WANAN page nakine dear manshat ALLAH ya inganta miki abin farincikin daya samemu, ALLAH yakaimu da rai musha shagali

17
          
                            
                                              
..........Tunda taturo 'kofar falon tashigo yake binta da kallo tamkar yau yafara ganinta,, itako ta 'kara ─Ćaure fuska kamar wadda taha─Ću da ma'kiyinta,, ko kallo bai ishetaba tawuce bedroom ─Ćinta,, harta 6acema ganinsa yana binta da kallo ya tsurama 'kofar ido yana mai mamakin canjawar da bilkeesu tayi a yau, kodai wani abu akayimata??, ya mi'ke jiki a sanayaye ya rufa mata baya zuwa ─Ćakin.
   Yatura 'kofar bedroom ─Ćin yashiga tana tsaye tana cire kaya, bayanta yatsaya tana 'ko'karin cire brah ─Ćinta, ya─Ćora hannunsa akan nata ya cire mata,, bata cemasa komaiba taja zani ta ─Ćaura ko kallon inda yake batayiba tashige bayi abinta tabarsa tsaye zororo.
    Bakin gado yazauna yana jiran fitowarta dukda lamarin nata yafara 6ata masa rai amma saiya danne tunda bata ta6a yimasa irin hakaba,, yanada tabbacin akwai abinda ya 6ata mata rai,, yazame yakwanta idonsa yana kallon fankar dake juyawa a─Ćakin,, tafito daga wankan tahau shiri bataredata tuna akwai mutum a─Ćakinba,, saida tagama shirinta sanan yatashi zaune yana kallonta, cikin muryarsa mai da─Ći ya ce, "bilyna minene matsalarki ne??, ta ─Ćago daniyyar yimasa bore amma saitaga yayi mata wani kwarjini na musamman,, ya Mahmud yanada kwarjini fuskarsa tana nuna alamun tsoratarwa.
   Ta ha─Ćiye maganar datayi niyyar fa─Ća, tasowa yayi ahankali ya kama hannunta suka nufi bakin gadon, batayi yun'kurin kwacewaba saima wasu 'yan kwalla dasuka taru mata a gefen idonta, ya juyo da'ita suna fuskantar juna, bilyna minene yake faruwa? kifa─Ćamin kinsan banason irin wa─Ćannan halayen suna sauri fusatani cikin sigar lallashi yake wanan furucin.
   Ta matso hawayen dake idonta cikin rawar murya ta ce, "my handsome dama haka kukayi da doctor ashir amma shine ka 6oyemin, kafiso muyita rayuwa ahaka babu yara kenan??, nida kai duk munsan muna cikin damuwar rashin samun haihuwa amma kasan mafita ka 6oye min?, ya mahmud kana sona kuwa???.
        A tsanake yake kallonta dan yarasa gane inda maganganun nata suka dosa shin na amincewane??, kokuwa na bujirewane??, ta'kara jeho masa tambayar????
     baka sona ko???,
da sauri yake girgiza kai alamar A'a,
   Ta ce, "to miyasa ka 6oyemin sirrinka??.
   Ya─Ćan gyara zamansa sanan ya ce, "ba 6oyemiki nakeyiba bily kawaidai bazan iya aikata abinda yace bane.
   Bily ta─Ćan murmisa to aiko indai kana bu'katar zama dani dolene ka 'kara aure.
  Cikin mamaki yake kollonta domin jin furicin bakinta, ya ─Ćan cije le6ensa na 'kasa bily kinsan abinda kike fa─Ća kuwa??,
     nasani my handsome kuma kaima kasan hakan shine dai2 kuma shine yadace.
  Shiru yayi yana kallonta, shiba wani abu bane yasa baya son 'kara aurennan ba, ila ita yake tausayi,, yaje ya auro wata ta haihu tazo tana mata wula 'kanci shikuma bazai juri hakaba.........ta katse masa tunani dafa─Ćin mika yanke yanzu akan lamarin???
   Huci ya fidda daga bakinsa sanan ya ce, "toni bily idanma hakan ta kasance wazan aura??, kinsandai ba kula wata yarinya nakeyiba a family ─Ĺinnan namu???.
         murmushi tasaki karka damu indai dan wanan ne mun gama magana da daddy nagidan ku, yasanar min yanada matar dazai baka ka aura!!, arazane yake kallonta ya ce, "bily yaushe kukayi wanan maganar da daddy??.
     ta─Ćan huro hanci tana fa─Ćin yau─Ćinnan mana ganin dakayimin daga can gidan nake bayan naje wajen doctor saina wuce can, yafara girgiza kai yana─Ćan ja baya dajikinsa saikuma yay saurin dam'ke hannunta haba bilkeesu yazakiyi min haka danmi zakisaka daddy acikin wanan maganar?????!!!!!!,  ya'kare maganar cikin 'karaji tareda gitgiza hannunta da 'karfin tsiya, har saida ta rumtse idanu saboda zafi, ya wurga hannunta zuwa baya sanan yasake daka mata tsawa tunda kece zaki zaunamin da matar saikiyi saurin auromin ita aikin banza kawai!!!!!!!!.....yana kaiwa nan yafice afusace..
    Saman benen ya haura zuwa ─Ćakinsa, saida yasakama 'kofar key sanan yafa─Ća saman gadon yana huci, (na ce, "lallai yau ran 'yan maza ya 6aci) kansa yadafe danjin yana shirin tsagewa wacece daddy yaza6a masa amatsayin mata??, shinwai mike damun bilkeesu ne??, ance mata suna gudun kishiya amma gatashi matar dakanta taje ta rakitoma kanta, yaja wani wawan tsaki jikake mtsoooow!!!!!!!!!,  yakula yarinyarnan batada hankali wlhy,, to inbanda hauka dakanki zakije kice asaka mijinki yayi miki kishiya wannan wane irin tunanine da ita????, (na ce, "tanada tawakkaline, sanan kuma kishiya aiba bala'i bace ga macen data gane).

Itako yana fita ta rushe da kuka dama kamar jira takeyi, saida tayi mai isarta sanan ta lallashi kanta tayi shiru,, mi'kewa tayi tanufi ─Ćakinsa domin basa ha'kuri, tasan ya Mahmud yanada zafi sosai amma bai ta6a nuna mata 6acin ransa irin yauba, lallai yau tasan ta ta6oshi amma yazatayi hakan datayi shine dai2, shima wataran saiyayi alfahari da abinda ta aikata, idan ta ce, "bazai'kara aureba aita cutar dashi sosai,, domin shi mutumne maison yara, tunkafin suyi aure bashida hirar data wuce idan sunhaifi yara zayi musu kaza zai musu kaza,, hakama dasukayi aure,, to itako yazata tauye masa hakki tunda ALLAH bai bata nataba, ahankali ta 'karasa jikin 'kofar tashiga bugawa amma yayi burus da ita,, daga 'karshema saiya buga mata tsawa wai karta sake buga masa 'kofa idan bahakaba zai matu'kar bata mamaki.
   Zamewa tayi jikin 'kofar tana kuka, yanajinta, dayaga zata damesa saiya kunna tv yasa 'kara dayawa.
      Saida tayi kuka mai isarta sannan tami'ke takoma ─Ćakin,, haka akacigaba da zaman doya da manja har kwana biyu, dayake weekend ne baya fita aiki,, babu abinda yake sakko dashi sai sallah,, baya cin abincinta baya shiga ─Ćakinta, idan yashigo yaganta afalo saiya ─Ćauke kai gefe,, itako harta sakko daga nata fushin,, fatantadai ALLAH yaganar da mijinta yafahimceta su daidaita da juna.
                   Nurr da deena suna ─Ćakinsu Nurr tana kwance yayida deena ke gefenta tana karantamusu Novel mai suna "NAWAFF  NA bilyn Abdul" cikin waya,  deena tadasa aya ayayinda ta je 'karshen page, Nurr takalleta da sauri kai deena yakika tsaya kuma Novel ─Ćinfa yafara sweet wlhy,, deena tayi dariya kai 'yammata maida wu'kar mana zan ─Ćan sha ruwane, nikaina yanda nakejin da─Ćin buk ─Ćinan bazanso na tsayaba amma bani minti ─Ćaya naje na ─Ćakko mana fanta a firij, da sauri Nurr tami'ke tana fa─Ćin A'a yizamanki naje na ─Ćakko mana.
   Kichin tanufa dan ita harma yunwa takeji, taduba babu abincin saita nufo saman daddy dantasan anan zata samu tabbas,, babu kowa a falon tagama waige2nta bataga kular abincin daddy ba, ta─Ćanja tsaki ita saima yanzu ta tuna baya 'kasar, da gudunta ta sakko,, jikake gafffff sunyi karo da mutum, ta─Ćago kai dasauri saitaga ya Mahmud fuskarsa tamkar baita6a dariyaba.....................


luv u oll my fan's
2017
[12/02 21:54] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

BILKEESA IBRAHEEM
    {♡bilyn Abdul♡}

18
           
                           
                                             
...........Tai saurin jabaya tana rawar jiki dan tsoro, cikin matu'kar ─Ćaurewar fuska yake kallonta, ta dur'kusa tana bashi ha'kuri,, wani wawan tsaki yaja cikin fa─Ća ya ce, "yaza'ayi kiganni tunda kina tafiya daka, useless kawai, kuma ban haku saka 'kananun kayaba anan gidan yafa─Ća yana zare belt ─Ćin jikin wandosa,, tsale Nurr tafara tana yarfe hannu kamar wata yarinyar goye, yaya dan ALLAH kayi ha'kuri badan niba,, wlhy damuka saka bamu fitoba muna ─Ćaki zaune,  yanzuma nazo ─Ĺaukar abincine,, plzzzz karka dakeni dangirman ALLAH,, bai sauraretaba ya lafka mata ─Ćaya a'kafafu, gashi wandon iyakarsa gwuywa saikuma 'yar mitsistiyar riga mai 'karamin hannu komai najikinta abayyane yake, ya 'kara lafka mata tabiyu saita ru'kun'kuneshi tana 'kara ihunta,, da sauri mama tafito dan da barci takeyi, ta 'karaso wajen tana daka masa tsawa,, "*k!!!!!! Mitayi maka zaka baro gidanka kazo kana dukar mini yarinya???, da sauri tabar jikinsa taje tafa─Ća jikin mama,, shiko du'kar da kai 'kasa yayi yana bawa mama ha'kuri.
   Ta kuma cewa wlhy ka kiyayeni dammi zaka tasamin yarinya gabane wai???, mitayi maka daga zuwanka gidan??, mama jibifa shigar dake jikinta,, kuma tuni na hanasu amma dan iskanci shine suka 'ki bari,, jibarta kamar ─Ćiyar yahudawa..
    Toba ahankali akebiba, idan kana binsu da nasiha da lallashi aizasu bari ko??,, amma haka kawai da ranarnan tsaka kazo kana dukanta haba wace irin rayuwace wannan????.
    Har 'kasa ya rissina yana bata ha'kuri, yatashi yafice yana gallawa Nurr harara.
   Mama taja hannunta suka shige ─Ćakinta tana mita.
   Su Nurr kam abin nema yasamu wai an cuci matar baqauye, tashiga rusa uban kuka mama tana lallashinta, daga lallashi barcin wahala yay gaba da'ita.
   Itako deena tana ─Ćaki ta kulle kanta, tasan yana gamawa da Nurr kanta zai dawo, da sauri tashiga cire kayan jikinta itama ta canja da jallabiya ba'ka,, (na ce, "lallai wannandai badan ALLAH bane).
      Ya mahmud kam yana fita motarsa ya shige ya kifa kansa saman sitiyari, lallai yana cikin matsala, itadai Nurr ta taka sahun 6arawone kawai, ya huce haushinsane kawai akanta, motar yasakama key yabar anguwar. (Na ce, "ALLAH yatsare).
       Aunty bilkee zaune ta zabga uban tagumi itafa tagaji da fushin da ya mahmud yake da'ita, miyakamata tayine? dansu shirya tabashi ha'kuri amma ya'ki saurarenta, kozata koma tasanar da daddyne??, kai A'a wanan sirrinsune itada mijinta.
      da sauri ta─Ćago danjin an ta6a 'kofar, ya mahmud ne ya shigo, fuskarsa ta fara kallo amamakinta saitaga fuskarsa asake take, ta taso da sauri ta kar6i ledar hannunsa, saida ya rungumota jikinsa ya manna mata kiss akumatu sanan ya ce, "i luv u my bily, ta ce, luv u too my handsome.
   Saman kujera suka 'karasa ta zaunar dashi sanan ta ajiye ledar tanufi firij, ruwa tabashi dan tasan bai cika shan kayan dreks ─Ćinnanba, ya kar6a yana murmushi, saida ya shanye duka sanan ya dire kofin saman tebir ─Ćin gabansa, jawo bily yayi saman cinyatsa yana fa─Ćin i miss u bilyna.
   Tai far da idanu tana fa─Ćin da gske handsome??, ya jinjina kai yana lumshe idanu, ta sumbaci 'kirjinsa ta ce, "ngd sosai handsome, kenan kadaina fushin dani??, murmushi yayi ya ce, "aii yanzu na fahimceki dan fitata 'kaddara tasani zuwa gida na sauke fushin akan Nurr.
   Ido ta zaro kai my handsome mitayi makane??, kibari kawai haushi tabani wlhy,, na hanasu saka 'kananun kaya amma sun'ki subari, to nikuma yau zuciyar akusa take shiyyasa na zaneta.
   Bily ta langwa6ar dakai gefe tana shafa sajen sa, ALLAH sarki Nurr ─Ćin mama yau mijina ya ta6a lafiyar jikinki, amma mama bata nan ko??
  Tananan wlhy, aiko nasha masifa gashi mami bata nan bare ta karemini,, aikaima dai dabaka daketaba wlhy,, ya ─Ćan ta6e baki kibari kawai gara dataji ajikinta gobe aii bazata sake sakawaba.
    Daga gurin aka fara soyayya (na ce, "bari nayi nan.).

Bayan kwana biyu daddy yadawo, daga tafiyar dayayi, awanan karon ya ─Ćau alwashin fitar komai fili,, dan haka yabi dukkan dangi yasanar musu akan mitin─Ćin dazasuyi sati mai zuwa.
      Su Nurr kam basu san hidimar da akeyiba.
   A 6angaren mama kuwa hankalinta atashe yake, nakula bata so a bayyana SABON AL'AMAREE da ake shirin fallasawa, amma babu yanda zatayi dolene gsky tafito kodan wasiyyar da ALH MUTALLAF yabari.

A yaune sati guda yacika,, gaba─Ćaya manyan dangin sun hallara a tsohon gidan alh mutallaf inda yazauna sanda yanada rai,, duk shekara sai sun sake masa fenti dan anan suke mitin idan yataso kokuma wani taro .
     Falon yayi tsit kamar babu kowa,, Alh Usman ne yafara mi'kewa domin shine babba saida yayi musu addu'oi sanan yayma iyayensu da 'kannensu, ya'kara bin fukokin 'yan uwansa da kallo ─Ćaya bayan ─Ćaya suma shi suke lallo, yaja numfashi,, kuyi ha'kuri 'yan uwana domin yaune za'a taso da tsohuwar magana wadda tafaru abaya,, yaune SABON AL'AMAREE zai bayyana a zukatan 'ya'yanmu domin su basu san dashiba,, bakomai bane yasa hakan sai faruwar wani SABON AL'AMAREE dakuma son cika wasiyyar da mahaifinmu ya bari kafin yabar duniya,, bayyanar komai yanada amfani domin hakane zai bada ma'anar warware wasiyyar daya bari,, kowa yasan waye ALH MUSBAHU acikinmu? ???? Dan danan fuskokin kowa ya canja zuwa 6acin rai mai tsananin gsk...................tofa komiye dalilin hakan????,, kubiyoni kawai....... .................

SABON AL'AMAREE

BILKEESA IBRAHEEM
     {♡bilyn Abdul♡}

                            
                        19                        
......Alh usman yaja nunfashi tarda furzarda huci mai zafin gaske, kuyi ha'kuri 'yan uwana yakamata mu bu─Će sirrin dake cin zuciyarmu domin samun nutsuwar zukatanmu...............da sauri Alh habib ya katseshi yaya nikam daza'abi tatawa dakawai anzartar da wasiyyar baba batareda an tono sirrin daya wuceba a baya,, bayyanar wanan sirrin zaisa wasu suji wani SABON AL'AMAREE a rayuwarsu, koya kuka gani 'yan uwa???, yafa─Ća yanamai kallon fuskokin 'yan uwannasa.
    Gaba ─Ćaya suka amsa da eh hakanma yayi, basai antuna bayaba, alh usman ya jinjina kai to shikenan hakanma yayi nima nayarda da shawarar ku.
   Wani littafi yajawo yashiga bu─Ćewa sanan yay gyaran murya, ina bu'katar nutsuwarku da hankalinku,, gaba ─Ćaya suka maida hankalinsu gareshi, yajawo farin gilas ─Ćinsa yasaka yafara karanta takardar kamar haka.....
       ASSALAMU ALAIKUM. Yaku 'ya'yana, inafatan takardarnan tawa zata riskeku alokacin dakuke cikin farinci dakuma ha─Ćinkai,, ina addu'ar ALLAH ya ha─Ćamin kanku har bayan raina.
    ALLAH yasaukar da farinciki da 'kaunar juna da zuminci arayuwarku,, ni Alh mutallaf ina maimuku wasiyya akan na aurar da ─Ćiyar MUSBAHU ga yaron ABDUL'MALIK wato MAHMUD, nayanke wanan hukuncine domin yabawa da hankalin yaron inada tabbacin bazai ta6a 'kyamartaba bare watarana ya goranta mata.
   Kukuma karkusaka wani abu azuviyarku, karku ─Ćauka na fifita Abdul'malik ne akanku, karku ─Ćauka nafiyarda da tarbiyyar 'ya'yansane fiye da naku,, A'a nayi hakane saboda aranar da ASMA'U zata rasu tayi al'kawarin mallakawa mahmud ─Ćiyarta inhar ta girma saboda son dayakema yarinyar.
   Saikuma ALLAH ya amshi rayuwarta awanan ranar tatafi batareda cika alkawarin data ─Ćaukaba,, to dan haka nina cika mata kafin nabar duniyar nima,, dan banida tabbacin kaiwa lokacin da yarinyar zata mallaki hankalinta ta isa aure,
    inafata ko bayan raina ku ida cika wanan al'kawarin ku mallaka masa matarsa alokacin bu'katar hakan ta taso, ALLAH yayimuku al'barka ya 'kyautata rayuwarku data 'ya'yanku data 'ya'yan 'ya'yanku.

                   Alhji mutallaf mahaifinku....

Kowa ka kalla fuskarsa tana zubar da hawaye, lalai yau ansosowa wanan family inda yake musu 'kay'kayi,, da'alama kuma akwai wani 6oyayyen al'amaree dabasu bayyanaba, basaso 'ya'yansu suji wani SABON AL'AMAREE dayake arufe kuma sirrin wanana family,, tokomadai miye idan tayi wari aizamuji.
   Daga nan suyi addu'a da tattaunawa akan abinda yashige musu duhu, aka kuma tsaida ranar biki kowa yakama gabansa. (Tofa kowacece wanan amaryar ta ya mahmud,, kudai kubiyoni kawai).
      Tunda daddy yadawo gidan baibi takan kowaba ya haye samansa ya kwanta, sai gabda azhur yatashi yay wanka yasakko zuwa masallaci, koda yadawo saiya zauna a falon 'kasa, tabbas muhimmin abune yake zaunar da daddy falon 'kasa, dan haka kodasu Nurr suka fito suka ganshi sai tsoro yakamasu, gashi fuskarsa babu walwala sosai, ya ce, "suje su kira masa mama da mami, to suka amsa cikin girmamawa,, babu da─Ćewa suka fito sudasu mama, saidai suma idan ka kalli fuskokinsu zakaga basuda walwala, lalai akwai damuwa tattareda wannan family ayau saidai basusan wane SABON AL'AMAREE bane ya kunno kai acikin family ─Ćin nasa, su mama suka nemi guri suka zauna,, babu da─Ćewa saiga ya Mahmud da ya faisal, suma suka nemi guri suka zauna bayan sun gaida iyayen nasu,, su ya Mustapha ma suka shigo suma gaisuwa sukayi suka zauna,, su deena dai suna kallon ikon ALLAH, saiff yafito shima ya zauna, saida daddy ya gama binsu da kallo sanan yay gyaran murya, tareda yin sallama, gaba ─Ćaya suka amsa akasalance.
   Ya gyara zamansa ya share kwalla, sukam cikin tsoro suke kallonsa dan ganin yana matse hawaye, dama mama da mami tun ─Ćazu suke nasu kukan.
   Cikin sar'kewar murya daddy ya ce, yau zan fa─Ća muku wani abu game da kanku ammafa kuyi ha'kuri ba komaine zan iya warware mukuba,, maganata tafi 'karfi akanka kai Mahmud, dan adalilinkane komai zai fito fili,, cikin tsoro ya Mahmud yake kallon daddy, daddy ya jin jina kai, eh akankane, kwanaki likita yayimin bayani akanka da matarka saikuma abinda yadace kayi, amma sainayi burus dakai inga kozakazo min da zancen kaima, to amma sai bakayi maganarba har gashi tsawon shekara biyu,, shekaran jiya waccan matarka tazomin aki─Ćeme takuma sanar dani itama batasan komai gameda shawarar da likita yabakaba sai aranar dataji a wajen doctor, taro'keni akan nasaka ka 'kara aure.
   To zan iya cewa fa─Ĺuwace tazo dai2 da zama, damancan kanada matar aure ahannu, abinda yasa ba'a baka itaba saboda bata isa aureba sai yanzu..... arikice dukkan ahalin gidan suke kallonsa musammanma ya mahmud.
   Daddy ya─Ćora da fa─Ćin matarka tana nan gidan!!!,  kuma munyanke hukunci baka ita a 'karshen wannan shekarar,, bazan fa─Ći kowaceceba saboda banason tashiga ru─Ćani tun yanzu dan zataji wani SABON AL'AMAREE daban....... yana kaiwa nan yami'ke da sauri ya haye samansa yana hawaye.....................tab ─Ćijan nifa nagaza gane wanan lamari,, wane irin SABON AL'AMAREE ne yake shirin faruwa a gidananne???????, to komadai miye muna biye daku su daddy........................

luv u oll my fan's
2017
[13/02 16:21] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

BILKEESA IBRAHEEM
   {♡bilyn Abdul♡}

       
                      20                                       
.........cikin tsoro deena da Nurr suke kallon juna, tabbas akan ─Ćaya daga cikinsu ake magana, kenan akwai wadda ba 'yar gidanba acikinsu, hawayene suka shiga silalomusu akumatu, lallai suna cikin ru─Ćani,, wannan wane irin SABON AL'AMAREE ne mara da─Ćin ji??????.
   To a 6angarensu ya Mahmud ma hakane, tunda daddy yabar gurin zufa ta wanke dukkan sassan jikinsa, jiyake kansa yana sara masa tamkar zai rabe gida biyu yadafe kai yana fidda numfashi da'kyar wanan wane irin SABON AL'AMAREE ne mai rikitarwa dasaka ru─Ćani, ahankali mama ta mi'ke ta bar gurin tana kwararar da hawaye hakama mami kuka take, ganin haka sai suma sauran yaran suka shiga nasu raira kukan, amma babu mai lallashi.
    Sunkai tsawon awa ─Ćaya suna abu ─Ćaya daga baya ya mahmud yamike yana tanga─Ći yafice, shima ya fahad baya yatake masa, ahankali kowa ya fice amma banda deena da Nurr dasuka shiga cikin ru─Ćani, daga 'karshema saisuka zame suka kwanta a falon suna cigaba da kuka mai bantausayi, (gsky koni na tausaya musu, saboda basusan wacece acikinsuba????, to ALLAH yabaku ha'urin jurewa)

Har tsawon kwana biyu gidan bai dawo dai2ba kowa kagani yana cikin wani yanayi lallai SABON AL'AMAREE ya shigo wanan gida.
    Ya mahmud kuwa aiko office baya fita, saidama yayi ─Ćan zazza6i saboda damuwa, daga baya kuma saiya dake,, kunsan maza akwai juriya.
   Tundaga ranar babu wanda yasake tada maganar nan, ahankali kowa yafara komawa kan harkokinsa, rayuwar tafara komawa dai2, amma a 6angaten Nurr da deena bahaka baneba,, sukam babu abinda yacanja musu saima 'kara ta6ar6arewa da al'amura suke musu, dan danan suka shiga rama mara 'kyau, garama deena tanada 'yar 'kiba amma Nurr sai ahankali.
   Nurr farace tas amma zamu iya kiranta gajera gsky, gata 'yar fit dan batada jiki ko ka─Ćan idan kaganta zaka iya cewa batakai shekara sha bakwai ba saboda rashin girman jiki,, tanada idanuwa dai2 wadaida suba 'kananaba kuma ba manyaba, tanada ─Ćan gashinta dai2 musali amma bai cika tsawoba,, tabbas Nurr 'kya'kyawace sosai dan duk namiji mai lafiya yaganta saiya 'kyasa, idan tayi dariya kumatunta sai sun lotsa akwai ilimi saidai akwai rashinji.
    Deenama dai farace zan iya cemuku tana matu'ar kama da Nurr saidai ita tafita tsayi da 'kiba, ita idan kagantama akace kabata shekaru to ashirin zakace amma shekararta sha bakwai itama harda wata biyar asama dan tagirmisu Nurr da Saiff.
    Ko tsakar guda basa fitowa abincima sai an tilasta musu sukecinshi, idan kazo gidan saikace babukowa saboda sarakan hidima sunyi laushi suna cikin yanayin SABON AL'AMAREE, dahaka komai yayta tafiya rana tana gudu bikin su Nurr yana isowa, sukuma suna 'kara shiga ru─Ćani, dan har yanzu basusan wacece matar ya mahmud ba,, shiko ko gidan yazo baya nemansu kwata2, saidai nakula shifa kamar yasan matar tashi yana basarwane kawai kokuwa baisaniba oho dai.
    Ana cikin haka sa'ko ya isowa family ─Ćin Sardauna Alh musbahu yarasu,, kunsan abinda yabani mamaki kuwa???, amsar itace babu wanda yadamu ko jimamin rasuwarsa, kai bammaji wanda ya ce, "ALLAH yaji'kansaba,, toko miyayi musu dazafi hakane?????.

NOVEMBER/25/2016.
    A yawune daddy yadawo daga 'kasar London, cikin murna su deena suka taroshi dan sun─Ćan fara sakin jikinsu yanzu,, ayayinda aka shigo da akwatina gidan sai tsoro da fargaba yashihesu tabbas akwatinan aurensune dan yanzu ance suduka za ayima auren zasu cigaba da karatunsu agidan mijinsu,, babu wanda yatambayi daddy akwatinan waye dan kowa yasan konasu waye.
   Da daddare ya Mahmud ya amsa kiran daddy bayan sun gaisa daddy ya nuna masa akwatina, gasunan na matarka shidda na matar Suraj shida, saika za6i ─Ćaya tunda kaine babba, ya mahmud ya langwa6e kai yana fa─Ćin daddy duk wanda aka bata ai yayi ALLAH yasaka da alkairi ya ji'kan mahaifa.
  To amin shikenan,, amma daka duba kayan ko kana bu'katar 'kara wani abun??, kai ya girgiza daddy koban ganiba nasan sunyi, idanma tana bu'katar wani abu, idan taje gidan saina saya mata,, okey shikenan,, yanzu yamaganar ─Ćaurin auren ─Ćayar 'kanwar taka, dan komai kasandai kaine zakayi amatsayinka na babba, wanan shine zaisa su ji'kanka wataran, kuma ko babu ranka zasu tallafi 'ya'yanku,, shiyyasa muke ─Ćora muku nauyinsu tun yanzu.
   Saida ya sosa 'keya sanan ya ce, "babu damuwa daddy insha ALLAHU komai ashirye yake rana kawai mike jira,, daddy ya ji jina kai yana murmushi to ALLAH dai yakaimu darai da lafiya,, amin ya Mahmud yafa─Ća yana mi'keawa, daddy bari nawuce gida naga rana tafara yi.
   To saida safe agaida min da bilkeesun, to daddy zataji,, harya fice daddy na binsa da kallo afili ya furta Mahmud yaron kirki kenan, kaima ALLAH yabaka masu yimaka addu'a kaji,, kullum addu'ata ALLAH ya nuna mini 'ya'yanka a duniya, tabbas zanyi farincikin samun jika daga tsatsaonka.
   Yana sakkowa yaci karo da deena da Nurr suna zagaye falon, dagasu sai best da zani saboda yanayin zafin garin,, deena ta ce, "ALLAH kinga Nurr kibani banason wula'kanci, Nurr ta ta6e baki karkiso wula'kancin mana aibani nace ki ajiyeba ko???, kumani ita zan saka wlhy.
   Ya Mahmud yay gyaran murya da hanzari suka juyo suna kallonshi gaba ─Ćaya suka shiga ru─Ćani, ya bisu da kallo fuska a ─Ćaure, agurin suka dur 'kushe suna gaisheshi, batarda ya amsaba ya ce, "waiku bazakuyi hankaliba ko??, ya wurgama Nurr harara uban miye kika ─Ćaukar mata, Nurr ta buntsuro baki gaba yaya rigacefa kuma saida taga na ─Ćauka zan saka sanan ta ce, "itama shi zata saka,, hannu ya 'mi'ka mata batareda yace komai ba, tasan miyake nufi dan haka ta mi'ka masa rigar kawai, kar6a yayi yay ficewarsa batareda yatanka musuba.
   Suka bishi da kallo kowa tana 'kyafta idanu...................

luv u oll my fan's
2017
[13/02 18:46] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

BILKEESA IBRAHEEM
       {♡bilyn Abdul♡}

        
                           
      21                                        
........Nurr ta harari deena aikinga kinja ya kwace ko??, sai kowa ya huta aii,, deena ta tuntsure da dariya aigarama daya kwace ni wlhy banji haushiba,, tsaki Nurr taja tawuce ─Ćaki tana fa─Ćin matsalarkice kuma wannan,, hhhhhh 'yammata kodai matsalarmu deena tabi Nurr tana dariya.
    Shiko koda yafita mota yashige, kai tsaye gidansa yanufa abinsa, yay fakin a yalwatacciyar harabar gidan, ya fito zuwa cikin gidan hannunsa ri'ke da rigarsu Nurr wadda ya kwave,, babu kowa a falon dan haka kai tsaye yanufi saman sa, dirowa ya bu─Će ya jefa rigar ciki, sanan yacire kayan jikinshi yashiga wanka,, sai asannan aunty bily tashigo, ganin yashiga wanka sai kawai tashiga tattare kayansa daya zube akan gado, inda yadace ta ajiyesu sanan tafito masa da farar jallabiya tas, tananan zaune yafito daga bayi saidai fuskarsa babu walwala,, tasan halin kayanta dan hakama bata cika damuwa da ─Ćaurewar fuskarsaba, dan hakan ajininsa yake, ta ce, "sannu da zuwa my handsome,, yauwa sannuki yafa─Ća shima yana goge jikinsa da 'karamin tawul dake hannunsa,, ta 'karaso gareshi hannunta ri'keda man shafawa, tawul ─Ćin ta kar6a ta 'karasa goge masa jikin, sannan ta shafa masa man, ya zura jallabiyar data fiddo masa suka sakko falon 'kasa.
   Saman doguwar kujera ya kwanta tabishi da kallo tana fa─Ćin yaya abincinfa??, ya─Ćan yatsine fuska saika ce mace, bayanzu zanciba yafa─Ća yana gyara kwanciyarsa, okey tafa─Ća tana zama kujerar dake kallonsa.
   Ta ce, "yauwa na manta ya mujaheed yazo nemanka ─Ćazu bayan kafita.
  Okey miya cemiki??.
  Baice komaiba ya ce da daddare zai dawo.
      Okey ALLAH yakaimu.
  Amin tafa─Ća tana jawo wayarta,, garama tayi catin da 'yan uwa dan idan bai gadamaba saisuyi zaman awa ─Ćaya batareda ya tankaba, sabodashi mutumne bamai yawan surutuba, ilai kuwa remote ya ─Ćauka yafara canja tashoshi, idonsa ya tsaya akan tashar MAX TV, suna wani American film mai 'kyau.
   Haka sukayita zaman kurame har la'asar daga nan yatafi masallaci domin sauke farali.
  Itama ─Ćaki tanufa tayi tata, tana zaune tana lazumi taji 'kiriniyar Abdul, tashafa addu'ar sanan tafito ilaiko shine shida ya Mahmud 'kila gidan yaje ya ─Ćakkoshi dan idan ba'a kawoshiba saiyaje dakansa ya ─Ĺakkoshi,, dagudu yazo ya rungume aunty bily yana kiran momy oyoyo,, ta ─Ćagashi sama tana fa─Ćin my boy yaushe kazone??
   Cikin muryarsa dabata fita ya ce, "yanju dad ya tacconi.
  Ayya ykk my boy??.
    Yaron yay 'yar dariyarsa mai 'kayatarwa ya ce, "lfy momyna.
Yauwa yaron dad tafa─Ća tana saukeshi akan cinyar ya Mahmud,, abinci tazo ta shirya masa akan tebir ─Ćin dake tsakkiyar falon,, yanata wasa da Abdul suna dariya kamar bashiba,, dama idan kanaso kaga yana tuntsura dariya to ka kawo masa yaro.
   Tare sukaci abincin yanaci yana bashi harsuka gama sukaci gaba da wasa shima yana biye masa kamar yaron lol.

Bikifa yazo anata shirye2n hidima kowa kagani yana cikin farin cikin,, duk wata al'ada dama sunayinta ne kafin ─Ćaurin aure, dan haka akayi kamu yau,, saidai amaren duk suna cikin damuwa kowa yana fargabar mijin dazai tarrar musamman ma wadda ta kasance matar ya Mahmud, washe gari akayi 'qauyawa, saikuma Arabiyan day, komai ya 'kayatar amare sunata shan 'kamshi da gyara, sunyi 'kyau harsun gaji,, yaune akayi Loncin amma ya mahmud bai jeba ya Suraj ne kawai yaje, saiya shiga tsakkiyarsu sukuma suna gefenshi na haggu da dama,, hakama wajen dina ya mahmud baijeba zama sukayi kamar a wajen loncin, washe gari aka tashi da shirin ─Ćaurin aure.
    Saidai abin haushi har aka ─Ćaura my Abdul bai barni na fitaba, wai yau agida zai wuni, gsky naji haushi sosai naso ace naje naji wacece amaryar ya mahmud tunda banda ita za'a ─Ćaura dan tuni ita da aurenta akanta,, yazanyi dole na ha'kura da ─Ćakko muku rahoto sai yamma daya fita ya ce, "naje.
   Ammafa badan kuba dabazanjeba lol.

Sanda na iso su Nurr suna harabar gidan sunci kwalliya dawani ─Ćan ubasu less skyblue doguwar rigace  an na─Će musu kai da darkblue ─Ćin ─Ćankwali, sarkar wuyansu ma darkblue ce ta zallar duwatsu atsakkiya an ratsa skyblue ─Ćin bit, hannunsu yasha bangus da zobuna masu matu'kar 'kyau fuskarnan tasha kwalliya irin wanda amaren zamani suke yayi, kai masu karatu abin sai wanda yagani dai,, ga wani ─Ćan ubansu takalmi sun kwama mai shegen tsini,,  'yan uwa sai ─Ćaukar hutuna suke dasu,, ana cikin ─Ćaukar hoto saiga ya muhsin ri'keda ya mahmud wow!! Mutumin nakufa ya kashe kala wlhy,, shima yaci ado cikin wata farar shadda mai shegen mai'ko da 'kyawu tasha sirfani na alfarma ya murza ba'kar hula akansa mai suna (president) hannunsa ─Ćaure da ba'kin agogo mai 'kyau hakama 'kafarsa,, tunda yashigo su Nurr yake kallo dansunyi matu'kar burgeshi yaran sun 'kayatu da kyawu.......... ya Sultan ya 'katse masa tunani da fa─Ćin ango shiga a ─Ćauka dakai dama tun ─Ćazu kai muke nema, ─Ćan murmushi ya Mahmud yayi ya 'karasa wajen 'kannen nasa dake tsaye ya Suraj yana gefensu shima yatsaya a─Ćayan gefen suka sakasu tsakkiya, bayan an─Ćaukesu saikuma aka ─Ćaukesu su biyu, shida deena dakuma shida Nurr daganan dai akaita ─Ćaukar hotunan,, nima danaga ba'ada niyyar kirana saina lalla6a tabayan aunty bily na─Ćan le'ko da kaina, lol, itama tayi matu'kar 'kayatuwa cikin kwalliya ta alfarma.
    Inama duk wadda za'yima kishiya ta─Ćau 'kya'ky'kyawan hali irinna aunty bily,, tabbas data more, da mijinta ya girmamata yakumayi alfahari da'ita,, ALLAH yasa mudace amin.
      Bayan angama hidimar ─Ćaukar hoto akacigaba da shagali har zuwa dare,, 'karfe takwas aka shirya amare tsaf cikin jar lifaya sai zabga 'kamshi sukeyi maida─Ći, gakuma uban kuka suna shar6a tunda suke basu ta6a rabuwa da junaba kodana wuni ─Ćayane,, tunda suka girma sukai wayau suna tare har yau da aure zai rabasu,, sau'kinsuma suna kusada juna sosai suke,, gefe guda kuma kowa tana fargabar kasancewar ta matar ya Mahmud,, falon daddy aka kaisu inda dukkan iyaye maza da mata suke zaune, dayake falon babbane kuma duk yarinyar daza'a aurar sai ammata wanan taron dagi wajen fa─Ća da nasiha,, tunda aka farayimusu fa─Ćan suke kuka kamar ransu zai fita,, wasuma dayawa a falon kuka sukeyi saboda tuna abubuwa masu yawa abaya, hakadai akai musu nasiha sanna aka dan'kasu ga iyaye mata domin kaisu gidajensu..
     Da'aka kaisu wajen mama kasa magana tayi saboda kuka,  dole akayi mata uzuri aka fito dasu zuwa ─Ćakin mami,, itadai ta─Ćan yimusu ka─Ćan itama kuka yaci 'karfinta, daganan aka fito dasu sai mota sunata kuka dafa─Ćin sufa bazasujeba sun fasa abarsu taredasu mama zasu zauna anan basa son auren,, haka sukaita sambatu da kuka mai ban tausayi bayanda za'ayi afasa dan haka aka dannasu mota sai gidan mazajensu dake nan cikin anguwar, (nima bari na─Ćan matse hawayen)

Kowa gidanta aka kaita bayan wasu 'yan muntuna gidajen sukayi tsit, garama wadda aka kaima ya Mahmud an ha─Ćasune da aunty bily,, amma dukda haka gidan tsit kamar babu kowa.
    Daga deena har Nurr sun kasa motsi daga gadon da'a ajiyeshi,, kowacce tana fargabar abinda zai biyo baya, shiyyasa sukayi zaune akan gadajen nasu suna cigaba da kuka..
    Ku kasance dani danjin wadda zata kasance agidan ya Mahmuddddddd!!!!!!!!!!!!!..................

luv u oll my fan's
2017
[16/02 12:49] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

BILKEESA IBRAHEEM
      {♡Bilyn Abdul♡}

   
       22                  
                                              
........A hanakali aka turo 'kofar aka shigo batareda yayi ko sallamaba, tana lilli6e cikin lafayar tana rusar kuka, jigina yayi da 'kofar ya har─Će hannayensa a 'kirji idanunsa 'kyam akanta, zuciyarsa cike da fargaba, bayason hankalin yarinyar nan yatashi, yakuma san tabbas tana ganinsa komai zai dagule, zataga SABON AL'AMAREE mai ban mamaki.
   Tun─Ćazu taji motsin bu─Će 'kofa amma firgici da ru─Ćani sun hanata ─Ćagowa jikinta sai rawa yakeyi, gabanta kam dukan tara2 yakeyi bama uku2ba, sunkai minti talatin ahaka babu wanda yayi wani yin'kuri ga ─Ćan uwansa, harya bu─Će 'kofar zai fice saiya tuna dawani furici na daddy, ya fitar da huci mai zafi daga bakinsa tareda cije le6ensa na 'kasa, ahankali yataka zuwa bakin gadon, yazauna kamar mai zama akan wuta, nanma shiru yayi baiyi maganaba, itako amarya wani sabon ru─Ćani tashiga danjin angon nata zaune kusada ita, sai hawaye ke zurara akuma tunta.
    Ahankali ya furta kicire wanan abun kisha iska mana.........arikice ta ─Ćago danjin muryar ya Mahmud, jadabaya tafarayi tana girgiza kai ga hawaye share2, innalillah wa inna ilaihirraji'un kawai take ambata, kafin ya farga ta sassan'kame agurin, da sauri ya tallafota dan tana niyyar fa─Ĺuwa daga gado,, girgizata yafarayi yana kiran Nurr! Nurr!! Nurr!!!, ina Nurr tayi nisa batajin kira, da sauri yaciro wayarsa daga aljihu yafara kiran bily, minti biyar ta'iso ─Ćakin aru─Će, ganin Nurr a sassan'kame ajikinsa saita 'kara firgicewa tashiga tambayar lafiya.
        Bai bata amsaba ya ce, "─Ćakkomin alkur'ani, da hanzari takoma ─Ćaki ta ─Ćakko masa, ya kwantar da Nirr saman gado, ya kar6i alkur'anin yafara karatu, fisge2 tafara ya mi'kawa aunty bily alkur'anin cigaba da karatun tayi shikuma yari'ke Nurr.
      Tafara magana cikin wata irin muraya, kudaina 'konamu munzo tayata murmane da samun gwarzon namiji irinka, lallai tayi dace dasamun miji nagari, ya Mahmud yay tsaki to haka ake taya murna saikuzo ku sassan'kame yarinya, waiku baza kubar jikinta bane, shuru sukayi basu bashi amsaba, ya mi'ka hannu ya kar6i alkur'anin zai cigaba da karatun, da sauri tayi atshawa sun fita kenan.
    Ya mahmud yay tsaki yana fa─Ĺin daku tsaya mana, koda Nurra tadawo saita ganta ajikin ya Mahmud da sauri tatashi taje ta 'kan'kame aunty bily tana kuka.
    Aunty dan ALLAH ki rufa min asiri nashiga uku ni Maryam dan ALLAH kice mafarki nakeyi ba gsk baneba, ya za'ayi na auri ya mahmud bayan duk mamace ta haifemu, dan ALLAH kigaya min gsky ta 'kara fashewa da kuka mai ban tausayi.
   Itama aunty bily kuka takeyi yayin da ya mahmud ke zaune kamar gunki gaba ─Ćaya kansa acunkushe yake, inama su daddy sun ha'kura sun binne wanan sirrin??, afirgice yadawo da hankalinsa akan Nurr danjin ta kwalla wata 'kara mai firgitarwa, jikinta sai rawa yakeyi, aunty bily nari'ke da ita tana kuka, ya Mahmud ya 'kar6eta yana cigaba damata addu'oi, ahanlai zufa tafara keto mata adukkan sassan jikinta, sai kuma jikinta yay lakwas, aunty bily ta fashe da kuka tana fa─Ćin yaya ta mutu mun shiga uku.
   Bai cemata komaiba danshima nasa hankalin atashe yake yama rasa wane mataki yakamata ya─Ćauka, dabara ta fa─Ćoma aunty bily ta tashi tafita da hanzari, waya ta ─Ćauka takira ya fahad, cikin ru─Ćewa ta ce, "yazo.
    Babu 6ata lokaci ya iso gidan dama shima hankalinsa atashe yake, yasan dole Nurr tashiga ru─Ćani da SABON AL'AMAREEn dazata gani, shine yay kokarin kiran likita, lokaci kalilan doctor ya iso, har sanan Nurr tana jikin Ya Mahmud a sume, babu 6ata lokaci yasaka mata abinda zai taimaka mata wajen jawo numfashi, sanan yay mata wata allura ya li'ka mata 'karin ruwa.
   Ya Mahmud ya ce, "yaya dai?? Doctor!!, doctor ashir ya ce, "karka damu mubata awa ─Ćaya insha ALLAHU zata dawo daidai, tashiga ru─Ćanine ma yanzu shiyya kawo bugawar zuciyarta da 'karfin gsk amma komai zai dai2ta insha ALLAHU.
     Haka sukayi zaune jigum2 saikace gidan mutuwa, awa ─Ćaya tana cika Nurr tafara numfashi sama2, doctor yasake yimata wata allurar, ahankali kuma sai numfashinta yafara dai2ta, barci yay awon gaba da'ita, doctor ya ce, "Alhmdllh yanzu komai normal tana barcine, zuwa lokacin da ruwan ya 'kare saika cire mata, nibari na wuce saida safenku.
  To ALLAH yakaimu doctor mungodefa sosai sannu da 'ko'kari, saida suka rakashi yashiga mota daganan ya fahad shima yashige gidansa, ya Mahmud kuma yadawo.
    ─Äakinsa ya wuce yay shirin barci sanan ya sakko 'kasa ─Ćakin Nurr, aunty bily tana zaune a bakin gadon, yana shigowa ta mi'ke tsaye, ya bita da kallo yana fa─Ćin ina zuwa kuma??, ta─Ćan marairaice fuska zanje na kwanta mana my handsome tunda naga itama tasamu barci.
   Ya─Ćan matso kusada ita haba bilyna ince anan kema zaki kwana??, ido ta zaro waje, kai idan nace zan kwana saika yarda???.
         Cikin mamaki yake kallonta, miyasa zan'ki yarda to??,  'yar dariya tayi tana tafiya saboda bai daceba mana ta 'kare maganar da ficewa daga ─Ćakin.
      Murmushi kawai yayi yana girgiza kai, bayan wasu 'yan mintina yabi bayanta, yata6a kofarta yaji akulle gam, dawowa yayi ─Ćakin Nurr, tsaye yayi yana bin Nurr da kallo, duk ta 'kara ramewa dama gata kamar sillen kara, idanunta duk sunshige ciki, ya─Ćan share zufar data taru mata agoshi, yaje ya'karama AC 'karfi sannan yadawo gefen gadon ya kwanta (na ce, "asuba tagari ya mahmud).

WASHR GARI.
       da asuba yatashi yatafi masallaci, bai tadata ba itakam, dama tunda yacire mata 'karin ruwan tasake canja salon kwanciyarta alamun barcin yana mata da─Ći kenan, koda yadawo daga sallah bai koma ─Ćakintaba saiya wuce ─Ćakinsa.
    Sai wajen 7:12am Nurr ta farka, ta tashi tayi wanka sanan tayi sallar asuba, tana idarwa ta shirya cikin siket da riga ta zura dogon hijjabi, saida tafara le'kowa taga falon babu kowa sanan tafito cikin san─Ća tabar gidan sai gidan daddy, koda ta isa canma duk suna ─Ćaki suna barci, kai tsaye ─Ćakinsu nada tawuce takwanta, barci ne yakwasheta dama bai ishetaba ta tashi.
               Aunty bily tagama ha─Ća breakfast tsaf, laure mai aikinta ta gyara gidan aka ba─Ćeshi da 'kamshi, ─Ćakin ya Mahmud ta nufa da nufin gyarawa tayi turus dan ganinsa kwance yana barci, badai mutiminnan anan yakwanaba??, tafa─Ĺa tana 'karasawa  bakin gadon, tasan halinsa sarai bayason katasheshi da hayaniya, dan haka saita ─Ćan ja hancinsa ya motsa ka─Ćan, ta sake ja sannan ya bu─Će ido yana kallonta 'kasa2, agogo ta nuna masa, yatashi zaune yana mi'ka sanan ya ce, "wai lokaci har yakai haka??, ehmana yakai, katashi kayi wanka.
    'Kafafunsa yazuro 'kasa tareda sakkowa, haryakai 'kofar bayi aunty bily ta ce, "wai anan ka kwanane??, juyowa yayi yana kallonta baice mata komaiba yashigewarsa bayi, kai ta girgiza kawai itakam batasan ranarda ya Mahmud zai fara baka amsoshin dukkan tanbayoyo yin da kamasaba, ko magana dakayi masaba, gadon tafara gyarawa, daganan tagyara ─Ćakin tsaf, ta ajiye masa kayan dazaisa tafice domin tada Nurr itama.
    ─Äakin ta tura tashiga saidai babu wakowa a─Ćakin, azatonta bayi tashiga dan haka tafara kakka6e mata gadon, hartagama gyaran ─Ćakin bata fitoba, bakin bayi taje tana fa─Ćin Nurr wai wanka kikeyine???, shiru babu amasa, ta 'kara kiran Nurr! Nurr!!!, shiru babu amasa da sauri ta tura 'kofar bayin wayam babu kowa, da gudu tafita sai ─Ćakin ya Mahmud, yana tsaye gaban madubi yana gyara kwalar rigarsa, aunty bily ta ce, "ya Mahmud Nurr fa bata cikin gidannan, bai fasa abinda yajeyiba, idinsa nakan madubi ya ce, "kamarya bata cikin gidannan??, ba tana ─Ćakinta ba??.
      A'a gsky babu kowa ─Ĺakinta, nakuma duba duk inda yadace amma bata nan, sai asannan ya juyo to ina tashiga??, ina zan sani yaya kasan Nurr zata iya fitafa sarai........kafin ta 'karasa ya fito, itama baya ta take masa, lungu da sa'ko na gidan suka shiga dubawa amma babu Nurr babu alamarta, hankali tashe ya Mahmud ya ce, "ina yarinyar nan tashiga ne??, aunty bily ta ce, "kodai gidan daddy zakaje kotaje can.
    Okey ina zuwa yafa─Ća yana fita..........................

SABON AL'AMAREE

BILKEESA IBRAHEEM
      {♡bilyn Abdul♡}

23
  

..........Kai tsaye gidan daddy yanufa, tun a gate yafara karo dasu Mubarak zasu tafi wajen aiki, suka gaisheshi, bai amsaba ya ce, "musu Nurr tazo gidannan??.
    Saida suka kalli juna sanan suka dawo da kallonsu gareshi, mustapha ya ce, "ya mahmud Nurr kuma??, mizai kawo Nurr nan gidan??.
    Ya ha─Će fuska, ya ina tambayarku kuma kuna tambayata??, sunsan halinsa sarai dan haka sukace wlhy basu saniba saidai sukoma ciki su tambaya??, baibi takansuba yayi gaba, suma baya suka take masa, falon babu kowa sai masu aiki suna gyarawa, suka dur'kusa suna gaida ya mahmud sau ─Ćaya ya amsa ya ce, "Nurr tashigo gidannan??, A'a suka fa─Ća kansu a'kasa.
    Mama tafito daga ─Ćaki da sauri danjin ankira Nurr, ya Mahmud ya rissina yana gaisheta, ta amsa kai agefe, ta ─Ćora da tambayar lafiya kaikuma da sassafenan???, ya Mahmud ya─Ćan shafa kansa mama nazo neman Nurr ne.
   Nurr kuma??, bangane kazo neman Nurr ba??, Nurr ─Ćin ba'a gidanka ta kwanaba???.
    Acan ta kwana bamatada lafiya, dan saida doctor yazo yabata taimako, amma da safenan mun nemeta mun rasa acikin gidan, nama zata kotazo nan ne shiyyasa nazo???.
   Daddy da mami ma suka sakko daga sama dayake yau itace dashi,, neman Nurr aka shigayi acikin gidan amma sama da 'kasa babu ita, saidaga baya Saiff ya ce, "bari na duba ─Ćakinsu kotanacan.
    Yana shiga yaganta kwance tana barci, da 'karfi ya ce, "ya Mahmud gata anan tana barci, hakan yayi dai2 da farkawar Nurr, suma suka 'karaso ─Ćakin, da gudu Nurr taje ta rungume mama tana kuka, mama tashiga lallashinta tana shafa kanta, daganan falon daddy suka koma, kowa yasamu muhalli ya zauna.
       Falon yayi shiru bakajin komai sai shashshekar kukan Nurr, daddy yagyaran murya tareda kiran Nurr!!, Nurr ta─Ćago kai tana kallon daddy batareda ta amsaba, daddy ya ce, "zonan!!.
     jiki a sanyaye tatashi taje gaban daddy ta dur'kusa, hannunta daddy yakamo ya matsoda ita sosai kusadashi.
    Cikin taushin murya ya ce, "haba ─Ćiyata Nurr kukan ya isa haka ko??, kinga share hawayenki.
   Babu musu ta share hawayenta"".
  Daddy ya ce, "yauwa ─Ćiyar albarka, yanzu in tanbayeki mana??,, kai ta jinjina batareda tayi maganaba, saboda datayi magana kukane zai taho mata.
   Yauwa miyasa kika baro gidan mijinki da sassafennan??.
   Jajayen idanuwanta ta─Ćago tana kallon daddy cikin raunin murya ta ce, "daddy bazan iya zamaba ina kallon ya Mahmud amatsayin wanda muka fito ciki ─Ćaya, har yanzu inaji ajikina mama ce mahaigiyata, dan haka ALLAH daddy bazan iyaba, tafa─Ća cikin raunin murya, inko kunaso na zauna dashi to sai kunmin bayani akan iyayena, miyasa basa taredani??, miyasa suka barni??, kuma yanzu suna inane??, sun rasune kokuwa suna raye???.
    ─Äan murmushin takaici daddy yayi, yashafa kan Nurr, karki damu ─Ćiyata nanbada da─Ćewaba za'a amsa miki dukkan tanbayoyinki, kije kizauna gidan mijinki kamar yanda 'yar uwarki deena ta zauna,, yau zansanar da family bu'katarki, insha ALLAHU zuwa gobe idan ALLAH yakaimu zakiji ranar damuka tsaida dominjin amsoshin tanbayoyinki kinji..??
   To daddy zanyi kamar yanda kace insha ALLAHU.
   Yauwa Nurri na ALLAH yayi miki al'barka kinji, yanzu tashi kibi mijinki ku koma gida.
   To, tafa─Ća tana mi'kewa, ya Mahmud ma yami'ke suka fice, yayinda su mama suka bisu da kallo,, mamakam kuka takeyi.
  
Koda suka fita babu wanda ya tankama wani, Nurr tana gaba ya Mahmud yana biye da ita, tafiya ka─Ćan takaisu cikin gidan, da sauri aunty bily tazo ta rungume Nurr tana fa─Ćin haba Nurr ina kika tafi da sassafen nan?, kin tayar mana da hankali gsky.
    Nurr ta share hawaye ta ce, "kuyi ha'kuri aunty bazan sakeba.
      yauwa Nurr karki sake kinji, ta ─Ćagota tana share mata hawaye, to kukan ya isa haka kinji zomuje kici abinci kinga bakida cikakkiyar lafiya.
  Duk abinda sukeyi ya Mahmud yana zaune a dani yana hidimar ha─Ćama kansa breakfast, suma zuwa sukayi suka zauna aunty bily ta kar6a ta 'karasa ha─Ćama ya Mahmud abincinsa, tagama tazubawa Nurr nata sanan tazuba itama.
     Shikam ya Mahmud sai dannama cikinsa abinci yakeyi babu ruwansa, hakama aunty bily, amma Nurr sai juya cokalo takeyi acikin kofin shayi har yanzu ko lauma ─Ćaya batakai bakintaba, aunty bily ta─Ćan ta6ata haba Nurr kici abincin mana.
   ALLAH aunty banajin cin komai,,.
     aiko bazai yuwu kizauna da yunwaba, kidaure ko ka─Ćan kici kinji, to aunty Nurr tafa─Ća tana kur6ar shayin.
   Ya mahmud yana jinsu amma bai tanka ba, yadai ─Ćago ido ya kallesu har suka ha─Ća ido da Nurr, tai saurin yin 'kasa da idanunta.
   Aunty bily tayita lalla6a Nurr harta ─Ĺanci abincin sanan ta 'kyaleta, suna gamawa Nurr takoma ─Ćakinta ta kwanta, shikam ficewa ma yayi daga gidan, suka bar aunty bily ita ka─Ćai afalon.

DEENA.
      a6angaren deena kuwa, tunda taga ya Suraj amatsayin mijinta sai tausayin Nurr yakamata tasan Nurr tanada rauni, gashi kuma rayuwar ta tazo da SABON AL'AMAREE lallai tana tausayin wanan baiwa, da'kyar ya Suraj ya lallasheta tayi shiru daga kukan tausayin datakeyi a kan Nurr.
     Shikam bai ─Ćaga mata 'kafaba aranar ya more sadakinsa, saidai tasha kuka sosai, daga baya yayta lallashin matarsa da saka mata albarka.

Sai 'karfe ─Ćaya ya mahmud yadawo gidan lokacin Nurr ta tashi tayi wanka dukda bawata kwalliya tayiba amma tayi 'kyau, wando da riga tasaka rigar yar mitsila sunyi mugun fitar mata da surarta, tariga tasaba da saka 'kananun kaya sosai, dan haka idan basu tasakaba batajin da─Ći, gashi garin kuma akwai zafi, duk yawancin kayansu 'kanane itada deena.
    Tun ─Ćazu tanajin motsin da aunty bily takeyi a babban falo amma takasa fita, har yanzu batajin da─Ćin jikinta dan haka tayi zamanta a─Ćaki, batasan inda wayarta takeba data kira deena sun gaisa, kwana ─Ćaya kacal harta fara kewarta, ALLAH sarki 'yar uwa deena muyi fa─Ća mu shirya kullum sai munyi ashe wata rana aure zai rabamu munaji muna gani, ta goge hawayen dasuka sulalo mata.
     Ahankali ya turo 'kofar yashigo da sallama, Nurr ta amsa can "kasan ma'koshinta, ya 'karaso tsakar ─Ćakin idonsa akanta, tashi tayi zaune da sauri tana rarumar gyale danta lullu6e jikinta,  dan bata manta da dukan dayayi mata ranarba akan saka 'kananun kayaba, cikin rawar murya take gaisheshi, bai amsaba saima zama dayayi a bakin gado, ya ce, "yajikinki??.
    Da sau'ki ta amsa kai a 'kasa, leda ya mi'ko mata, hannu biyu tasaka ta 'kar6a, ki ajiye anjima zanyi miki bayani yafa─Ća yana mi'kewa.
    "Ta ce, "ALLAH yakaimu.
   Amin yafa─Ća kan la66ansa ya fice.
     Binsa tayi da kallo a zuciyarta ta ce, "lallai aunty bily tana fama da wanan ─Ćan bala'in, wanda babu abinda ya iya arayuwarsa sai muguntar tsiya, ledar tabu─Će ta le'ka saitaga magunguna, baki ta ta6e ta ce, "kona miye??, oho masa.
     Ma'ajiya maikyau ta ajiye tadawo saman kujerar tayi kwanciyarta.
    Bata fitaba saida aunty bily tazo takirata dansuci abinci, after dress ta ─Ćora akan kayanta sanan tafice,, koda suka gama cin abinci saita dawo ─Ćaki abinta tabarosu afalon suna hira, konace aunty bily tana hira danshi sarakin sai'ayi magana sama da ashirin baifi yabada amasar biyu ba..................

luv u oll my fan's
©2017
[20/02 17:09] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE


BILKEESA IBRAHEEM
      {♡bilyn Abdul♡}

Assalamu alaikum
  'Yan uwa kuyi ha'kuri da rashin posting ─Ćina, murace tayimin kamun kazar kuku,, dan haka ina jiran kaji masu yaji awajanku, gashin gida, ga wanna ku─Ćanyi manage kafin gobe idan ALLAH yakaimu, ko anjima I dan nasamu dama.
Luv u oll

24
  

.........Tana zaune abakin gado bayan ta kammala shirin barci, sotake ta kwanta amma tanajin tsoro, bata saba kwana ita ka─Ćaiba, to kodai ─Ćakin aunty bily zatane saisu kwana??, ta─Ćanja tsaki kai amma saitaga kamar bai daceba, to amma idan ba haka tayiba aibatada wata mafita bayan wanan, ta mi'ke tsaye tana gyara ─Ćaurin ─Ćankwalinta, itakam wlhy can zata tasandai babu mai cemata dammi, fitilar ─Ćakin takashe tafito, 'akofar ─Ćaki sukai karo ita tana 'ko'karin fita shikuma yana 'ko'karin shigowa, abisa tsaushayi 'kafarta tabigi 'kofa zafi yasa ta tuzgu─Će zata fa─Ći, da sauri ya ri'ko 'kugunta zuwa jikinsa, sorry yafa─Ća ata'kaice.
    Ajiyar zuciya tasaki tareda zame jikinta daga nasa, baibi takantaba ya tura 'kofar ya shige ─Ćakin.
   Nurr ta ce, "yau naga 'karfin hali mai ─Ćaki tana fita kai kana tura kai ciki, babu yanda zatayi dole tabishi zuwa ciki, a bakin gado ta tarar dashi zaune, jiki asanayaye ta 'karasa saman kujera ta zauna.
  "To da ina zakije???.".
  " kai ta─Ćago ta─Ćan kalleshi, saikuma tamaida kasa dan ganin ya kafeta da idanuwansa, cikin rawar murya ta ce, "wajen aunty bilkee zanje.
   Baki ya─Ćan ta6e ya ce, "yanzu a darennan??.
   Shiru tayi bata bashi amsaba, dan batasan mizata fa─Ća masaba..
    Bani ledar ─Ćazu yafa─Ća yana sauka saman carpet ─Ćin dake gaban gadon, mi'kewa tayi ta ─Ćako masa, har zata koma saman kujera ta zauna, sai ya ce, "dawo nan.
    Zuwa tayi ta zauna inda ya nuna mata, ya bu─Će ledar yana fito da magungunan, bayan yagama yashiga yimata bayanin yanda zatayi dasu, wato dai idan ta fahimta saboda Aljanunta yaje ya kar6o mata magani.. 
    Saida yagama yimata bayani dalla2 sanan ya ce, "gashi nan idan kin gadama ki ajiye, idankuma kinyi tofa kanki kika taimaka, yana gama fa─Ĺa yatashi ya fice.
    Binsa kawai tayi da kallo, azuciyarta ta ce, "saiikace wani ─Ćan sarauta.

Koda yafita ─Ćakin aunty bily yanufa, baiwar ALLAH harma tayi barci abinta, bargon ya─Ćaga yashiga, cikin barci taji ana shafata ta mi'ke afirgice, shikam ko motsi baiyiba saidai binta da kallo fayakeyi.
     Cikin rawar murya ta ce, my handsome baka kwantaba ne??,         eh", yafa─Ća ata'kaice.
  To miya faru naganka anan??, fuska ya ha─Će tamau, sai wani abu yafaru nake zuwa ─Ćakinki??, bahaka nake nufiba my handsome, ina tuna makane banan yadace agankaba, yakamata ace kana ─Ćakin Nurr dan baka gama mata kwana bakwai na al'ada ba, daga baya saika raba mana kwana ko??.
    Harararta yayi tareda jan tsaki, ta marairaice fuska plzz ya Mahmud gsky nake fa─Ća maka, jiyafa aka kawo yarinyar nan gashi kuma batada isashiyar lafiyama..
   Mi'kewa yayi tsam yabar ─Ćakin, tabishi da kallo tana girgiza kai, wai har sai yaushe zata gane mijinta wane irin mutumne??, kanta tamaida ta kwanta, tasan kodata bishi saidai ta 'kara tunzurashi ya hau sama, dan haka garama tayi kwanciyarta.

Shikam ─Ćakinsa yatafi yayi kwanciyarsa, sai mita yakeyi wai ya za'ayi ya ha─Ća makwanci da Nurr ta rainashi wanan yarinyar daba kunya garesuba ahakama yasuka 'kare bare taga gadon barcinsa, hakadai yayta mitarsa har barci ya kwasheshi.

Itako Nurr takasa barci, har wajen 'karfe ─Ćaya na dare, mi'kewa tayi dan tsoro sake shigarta yakeyi, rufo ─Ćakinta tayi tashiga ─Ćakin aunty bily, itakam zuwa sanan barcinta yayi nisa, saman kujera tayi kwanciyarta.
     Da asuba aunty bily ta tashi zatayi sallah saitaga Nurr saman kujera tana barci, kai ta girgiza dan yarinyar tabata matu'kar tausayi, saida tayo alwala sanan ta tada ita, Nur ta mi'ke bakinta da addu'ar tashi barci, aunty bily ta ce, "haba Nurr miyasa baki hau hadoba kika kwanta anan?? aisai wuyanki yayi ciwo kowani sashe najikinki.
    Murmushi Nurr tayi tana mi'kewa babu komai aunty bana son na tadakine shiyyasa na kwanta anan,, to shikenan jekiyi sallah, ─Ćakinta tawuce tayi sallah daganan tahaye gado sai barci.
    Yauma bata tashiba saida aka tadata, tana mamakin yanda take barci kwana biyunnan kodan tada─Će batayi barcin daya isheta bane????, tunda aka tsira maganarta da ya Mahmud barci ya 'kauracema idanunta saifa akwana biyunnan datake yinsa baji babu gani, bayi tashiga tayo wanka, kwalliya tayi cikin shadda mai ruwan kasa tayi "kyau sosai dukda yanzu ta daina kwalliya, falo tafito kamar yanda aunty bily tafa─Ća mata, kusan tare suka fito da ya Mahmud, rissinawa tai ta gaidashi sau ─Ĺaya ya amsa yayi gaba itakuma tarakasa da harara.
    Kai tsaye saman dani yanufa ya zauna, aunty bily tafito daga kichin itama gaidashi tayi cikin girmamawa, ya amsa fuska acunkushe hakan bai dametaba dan idan da sabo sun saba, abincin ta zuba masa kamar yanda ta saba.
   Itama Nurr ta ha─Ća abinda take bu'kata, daganan kowa yacigaba da cin abincinsa, aunty bily ta ce,  "yaya yaufane zanje gurinnan.
    Batareda ya kalletaba ya ce, "ina kenan??.
    Cikin mamaki take kallonsa, ta daure ta ce, "kamanta nagaya maka Ramla ta haihu,, okey yafa─Ća yana Kur6ar lemo, ki shirya sai direba ya kaiki kokuma idan zaki iya kije da kanki, babu damuwa zanma iya zuwa da kainan, nandai da Marafa ai bawani nisa bane.
   Shiru yayi bai sake cewa komaiba,, Nurr ta ce, "aunty dan ALLAH nima zanje, jinjina kai tayi tareda nuna mata ya Mahmud da idanu, Nurr ta ─Ćan ta6e baki dan tagane mi aunty bily take nufi, ta ─Ćan kalli fuskar ya mahmud ya 'kara wani ─Ćaure fuska dan yana kallon duk abinda sukeyi, itama fuskar ta ─Ĺaure ta ce, "yaya zanbi aunty bily.
    Banza yay mata yacigaba da cin abincin sa, ya gama ya mi'ke tsam yabar wajen, Nurr ta kalli aunty bily ido cike da hawaye, aunty kina ganifa bai amsaniba.
   ─Äan murmushi tayi, Nurr kenan kemafa kinsan halinsa, mi'kewa zakiyi ki bishi, aii kinsan saida lallashi, nima bakiga da buyagi zaiminba, kinga tashi kije ki sake lalla6arsa nasan zai barki.
    To Nurr tafa─Ća tana mi'kewa jiki a sanyaye, samansa tanufa, yauce rana ta farko data fara zuwa ─Ćakinsa, 'kofar falon ta tura tashiga wani 'kamshi ya bugi hancinta, tabbas tasan dama ya Mahmud mutumne mai tsafta da gwalli tamkar mace, bayason hu─Ĺa da kazamin mutum ko ka─Ĺan.
   Saman doguwar kujera ta iskeshi kwance, hannunsa ri'ke da remote, tunda tashigo yana kallonta ta gefen ido amma sai yayi fuska tamkar bai gantaba, takai minti goma atsaye tana tunanin yanda zata tunkareshi.........jitayi kamar daga sama ance mikike sone???, da sauri take kallonsa jikinta sai rawa yakeyi, itafa azatonta baimasan ta shigoba, kai wanan mutumi sai abarshi kawai,, murya na rawa ta ce, "wajenka nazo.
    Tashi yayi zaune batareda ya tanka mataba, saima nuna mata kujerar datake kallonsa yayi da hannu, babu musu tanufa ta zauna, idonshi nakan tv ya ce, "ina sauraraenki fa─Ći bu'katarki dan inada aikin yi.
    Yatsun hannunta ta lan'kwasa yayi 'kara cikin in ina ta ce  "dan ALLAH kabarni nabi aunty nace, ─Ćan tsaki yaja sanan ya ─Ćago idanu yana kallonta, itama ta ─Ĺago suka ha─Ĺa ido  da sauri ta maida nata dan bazata iya jurar kallonsaba.
   Ya ce, "k idan an barki saikije??.
Nurr batasan gatseba ta ce, "eh mana da 'karfin gwuywarta tafa─Ća, saida ya hararaeta sanan ya ce, "to bazakijeba, idan kin bita waye zaiyi abincin rana???.
    Baga masu aiki nanba, Nurr tafa─Ća tana turo baki .
    Banxa yay mata yakoma ya kwanta, dandanan idanunta suka cika da hawaye, aunty bily tashigo falon da sallama, suduka suka amsa taje gabansa tana fa─Ĺin yaya kabarta mu tafi ─Ćin, bai bata amsaba saiya zaro ku─Ći a aljihunsa ya mi'ka mata, saura kuma ki yuce 'karfe biyar yafa─Ća yana kwanciya, wannan amsarma ta wadatar da ita dan haka tayi musu sallama ta fice....................

luv oll my fan's
©2017
[21/02 11:39] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE

BILKEESA IBRAHEEM
     {♡bilyn Abdul♡}

25
  

..........Tunda aunty bily ta fice sai hawaye suka fara zirara a kumatun Nurr,, yana kallonta ta gefen ido amma ko kallo bata isheshiba ma, ahankali ta 'mi'ke tabar ─Ćakin, falon 'kasa tadawo ta zauna, saikuma ta tashi tashige ─Ćakinta ta kwanta tanata kuka.
      Saida tayi mai isarta daga baya barci yay gaba da'ita.
   Tunda tabar ─Ćakin bai motsa daga inda tabarshiba, yana kwance yana kallon kwallo, saida aka kira sallar azuhur sanan yami'ke yay alwala yafito, al'adarsa ce ko masallaci zaije saiya sanarwa matarsa, dan haka yafara le'ka kicin, a irin wannan lokacin yakan samu aunty bily ne akicin, tsayawa yayi yana bin ko'ina na kichin ─Ćin da kallo dan babu alamar anyi girki aciki bare ya ce har angama.
    Fitowa yayi zuwa ─Ćakin Nurr, tana kwance saman gado tayi ─Ćai2 iskar AC tana ratsata, ya─Ćan runtse ido tareda cije le6ensa na 'kasa lallai yarinyarnan 'yar rainin hankalice, watoma barci takeyi.
    Bakin gadon ya 'karasa cikin fa─Ća ya ke kiran Nurr! Nurr!!, ta─Ćan bu─Će ido saikuma tamaida ta lumshe abinta ya daka mata tsawa 'k!!!! Wai wane irin iskancine wanan.
     Agirgice ta tashi tana murza idanu ta waresu akan ya Mahmud dake tsaye tamkar dogari.
    Ya 'kara tsare gida yana fa─Ćin incedai kin mana girki kafin kizo ki kwanta?.
   Girki kuma?? Nurr tafa─Ća tana 6ata fuska, nifa banyi wani girkiba dan barci nakeyi tun ─Ćazu, wata uwar harara yake watsa mata wadda tunda tafara magana yake mata ita, jiyake tamkar ya bugeta, dan haushi saikawai ya juya zai fita, Nurr kuma tana binsa da kallo, saida yaje hanyar fita sanan ya juyo nabaki nanda kafin indawo wlhy natarar kin girka abinci yafice abinsa.
    Tab─Ćijan kajimun mutum saikace wata inji?, zaka wanice daganan kafin kadawo na girka abinci, munti nawa ake idar da sallah, kaini wlhy katakura min gida zankoma danni ba matarka bace daka raina kake juyata yanda kakakeso, ita sonka take niko banta6a jin sonka ko ka─Ćanba azuciyata wlhy, hasalima haushi kake bani masifaffe kawai mtsowwwwww!!! Ta 'karashe maganar da tsaki.
    Bayi tashiga tayo alwala saida tayi sallah sanan tanufi kicin ─Ćin tana tunanin mizata dafa dazaiyi saurin dahuwa???, murmushi tayi dan tagano muguntar dazayimasa, afili ta furta idan kasan wata aibakasan wataba Alhaji, badai girki kake bu'kataba kafin kadawo? zaka kuwa samu.
    Kayan miya ta gyara ta wankesu sanan ta marka─Ća, ta ─Ćaura kifi awuta, tashiga yanke2n su karas da sauran kayan ha─Ćinsa, tanata hidimar girkinta yadawo yawuce ─Ćaki yay wanka sanan yadawo falon 'kasa, zuwa sanan tagama girkin harma tajereshi a dani tatafi ─Ćaki yin wanka.
   Yana nan zaune tafito cikin 'kananun kaya, siket daka─Ćan yawuce gwuywarta sai 'yar riga mara nauyi kanta ko ─Ćankwali babu.
    Saida gabansa yafa─Ći yayinda ya─Ćago yana kallonta dan tunkafin ta iso 'kamshinta ya iso, kayan sunyi mugun zauna mata ajiki saikace ajikinta aka haliccesu, ka─Ćan yarage ta harbo jirginsa saboda ru─Ćani daya─Ćan shiga, yarinyar tanada 'kira mai 'kyawun gani, da burgewa, amma saiyayi saurin kama kansa, ya gimtse fuska 'k wane irin iskancine wanan?, koma ki ─Ćakko ─Ćankwali, zakiwani fitowa mutane da wanan daddagaggen gashin naki abin amai.
    Nurr ta 6ata fuska danjin ankushe mata gashinta datakeji dashi (tasan dai gashinta yafi na Sadiya sulaiman tyw) amma zai wani kushe mata gashi, saidai ta─Ćan murgu─Ća baki tace aidai yafi naka acan 'kasan makoshi tafa─Ĺa.
    Ya ce, "mikikace??.
    Da sauri ta ce, "nifa bance komaiba.
  Kedai kika sani kuma ki 6acemin da gani anan, ─Ćaki ta koma amma koda ta ─Ćaura ─Ćankwalin saitayi zamanta a ─Ćakin, shikam yana zaune yana jiranta, baifargaba har minti talatin tacika da tafiyarta, afusace yami'ke yanufi ─Ćakin, rainin hankali yafa─Ća zuciyarsa yayinda yaga Nurr zaune a kujera tana duban hotuna, mima yakamata yay wa yarinyar nane danta shiga hankalinta yagafa raini yana niyyar shiga tsakaninsu.
    Gabanta ya'karasa yayinda itakuma ta─Ćago arikice tana kallonsa (na ce, "garashin kunya gakuma tsoro Nurr ─Ćin mama kenan), albom ─Ćin yakwace ya wurgar gefe, tuni ta tashi tana rawar jiki taje jikin dirowa ta ma'kale, yazazzare mata idanu waini sa'ankine??, cikin rawar jiki ta ce, "A'a.
   Okey rainine yakeson shiga tskaninmu?, yafa─Ća yana zare belt ─Ćin wandonsa, tuni mutuniyar taku tafara kuka tana fa─Ćin ALLAH niban rainakaba, dan ALLAH karka dakeni natuba.
    Ai yau sakin gayamin rainin dake shirin shiga tsakaninmu, inbanda iskanci kinsan inacan ina jiranki kizo ki bani abinci shine zakizo kiyi zamanki, watoma kin manta akwai mai jiranki??.
    Kaifa kace natashi maka dagani.
    Haushi ya'kara kamashi ya ─Ćaga belt ─Ćin zai bata ─Ćaya ai dagudu tafice tayo falo shikuma yadaki dirowa, yadafe kai oh ni Mahmud wauy sai yaushe Nurr zata bar shiriritane??, ahaka zata haifamini yaran danake buri daga gareta?, yarinya kamar ─Ćiyar goye?, ALLAH ya shiryaki yafa─Ća yana maida belt ─Ćinsa ajikin wandonsa.
   Falon yafito, tana ganinsa tasake ranta anakare, ko inda take bai kallaba yanufi dani yazauna, dakansa yabu─Će abincin zai zuba, "innalillihi" ya fa─Ća tareda maida kallonsa ga Nurr dake tsaye tana kallonsa, zonan ya ce, "tareda tamke fuska.
    Tayi burus dashi dan tasan laifinta, tsawa yadaka mata wlhy idan bakizoba saina zaneki yau agidanan, da sauri ta'iso wajen amma 'kirjinta na dukan uku2 na tsoro, kujera ya nuna mata ya ce, "zauna, babu yanda zatayi dole tajawo kujerar ta zauna, ya tura mata kular abinci yana nunawa 'k! Tunda kika tashi kinga nata6a cin kus2?, kuma da ubawa da ubanwa zasuci wanan uban abincin dakika dafa??, komu ashirinne agidan??, shiru tayi masa tana kallon kus kus ─Ćin, yasake daka mata tsawa badake nakeyiba???.
   Tai saurin cewa ainazata yanzu kafara ci tunda kayi aure, ta'kare maganar da zum6ura baki, dukda yana cikin jin haushinta tabbas tabashi dariya amma saiya gimtse, ya watsa mata harara, k wai yaushe zakiyi hankaline??.
     Ta ce, "ai mama tace sainan gaba.
   Tsaki yaja okey zaki gane sainan gaba, oya ─Ćauki cokali yau saikin cinye abincin nan duka, zakiga asalin rainin hankali.....................

Luv u oll my fan's
©2017
[21/02 11:50] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE.

®BILKEESA IBRAHEEM
      {♡Bilyn Abdul♡}
26

.......Tazaro ido haba yaya yaza'ayi na iya cinye wanan abincin sokake nazama mai 'katon ciki??.
     Kizama mana ubanwa yace kidafa??, wlhy koki faraci kokuma yanzu jikinki yagaya miki, jan kular tayi zuwa gabanta tana hawaye tanaci, shikam yana zaune da caja ahannunsa, tun tanaci da dauriya harta kasa tafara yun'kurin amai,, kinsan ALLAH kikayi min amai anan saina baki mamaki garama ki ri'ke abinki, dan ALLAH yaya kayi ha'kuri wlhy na 'koshi jinake tamkar na mutu ka tausaya min plzzzzz.
       Haba yarinya aisai kin cinyeshi tas, keba 'yar rainin hankaliba?, kinga gobe aii saiki sake dafa abinda banaci ko??, ta fashe da kuka tana ri'ke ciki wayyo mama nashiga ukku kinacan ana ana za'a kashe miki ─Ćiya, ni wlhy gida zan koma bazan iya da wanan bala'inba........kafin ta'karasa ya mi'ke yana fa─Ćin nine bala'in kenan??, ya tsula mata caja ajiki, da sauri ta ru'kun'kumeshi tana kuka, tari'keshi tsam harya kasa wani motsi bare yasamu damar sake dukanta, sai kuka takeyi tana jijjigashi wajan ─Ća─Ća─Ćaga 'kafafu.
    Tsaye yake kamar gunki yakasa koda motsi dan gaba─Ćaya tatafi da imaninsa, ana cikin haka aunty bilkee tayi sallama da sauri Nurr tasakeahi taje ta ru'kun'kume ta tana kuka, aunty wlhy ni gida zani, bazan zauna ayita dukanaba, nidai bazan zaunaba.
    Aunty bilkee ta ─Ćagota tana lallashi kinga yi shiru to ya isa haka, hannu ta ri'ke mata suka 'karasa inda ya Mahmud yake tsaye, ta ce, "my handaome miyake faruwane??.
    Kular abincin kawai ya nuna mata batareda yayi magana ba, gaban dani ta 'karasa ta kalli kus2 ─Ćin dake ciki ta─Ćan zaro ido, Nurr kece kika dafa??,.
   Bkai Nurr ta─Ćaga tana hawaye.
    oh ke Nurr yanzu nan yazamuyi da wanan abincin??, kinsan kuma yaya baya cin kus2?, yanzu dan ALLAH ina zamu da wanan uban abincin kamar mu ashirin ne agidan?.
       aunty nifa bansan yanda ake zuba yawan abincin gidanananba, shiyyasa nayi kamar yanda mukeyi agida.
    Dariya sosai ta tahoma aunty bily tasaka hannu tana gimtsewa dan karta tunzura ogan nasu, dataga zata fito fili saita ─Ćauki kular abincin tanufi kichin, tashiga bin ledojin kus2 da Nurr tabu─Ĺe wato biyar tadafa kenan?, kai ALLAH yashirya kuruci dangin hauka. agurguje tayi wani girkin dan tasan tabbas yanajin yunwa, kamar tasani tabaro gidan sunan badan angama shagalinba.
    Zuwa tayi ta jere abincin sanan ta ce, "yaya ga abinci nasan kanajin yunwa, mi'kewa yayi yanufota ai wlhy bily idanma kinji yinwa ─Ćaya, yarinyar nan tunda kika bar gidanan take bani hauka, ni kainama harya fara ciwo, dariya aunty bily tayi my handsome ai saidai ha'kuri kasan har yanzu akwai kuruciya atattare da Nurr, sai munringa lalla6ata da sakata a hanya, nasan wataran komai zai daidaita.
       hummm to ALLAH yasa amma nidai banhango ranar hankalin Nurr ba anan kusa.
    Haba yaya zatayi wlhy, bari kaga tafara haihuwa.
   tab─Ći jana wace zata haihu yanzu??.
    Nurr mana.
  Lallai to idan ta haihu wazai raini wani itada ─Ćan??, itama kanta ba'agama rainontaba bare tahaifi wanda zata raina.
   Dariya aunty bily tayi ta ce, "yaya kenan ai abun ba'anan yakeba, mudai kasan 'ya'ya muke bu'kata.
    Baice mata komaiba illa murmushi kawai dayayi, bayan yagama cin abincin yatafi sallar la'ar.

Haka rayuwa taci gaba datafiya, yauda gobe sai ALLAH inji masu iya magana, yau satinsu Nurr biyu da aure, shiririta awajenta sai abinda yay gaba, tun ya Mahmud yana mata magana harya tattaraeta ya watsar, saidai aunty bily tana 'ko'kari wajen bambance mata gabas da yamma.

Deena kuwa anacin amarci yanda yakamata, soyayya sosai akeyi agidan kamar babu gobe, idanma da rabo akusa tofa ansamu ciki kila, yauma suna falo itada mijin sunatashan sharafin siyayyarsu, ta kwantar da kanta ajikin kafa─Ćar ya suraj, ta ce, "my D!, na'am babyna yafa─Ća yana shafa kumatunta.
   Dan ALLAH yaushe zaka kaini nagano Nurr??, wlhy duk kewarta ta isheni.
   Kumatunta ya sumbata, karki damu babyna insha ALLAHU weekend ─Ćinnan zamuje saiki wuni acan, murmushi tayi tareda bashi kiss mai zafi awuya, ta ce, "ngd my D ALLAH yabarmu tare, amin babyna, nan suka cigaba da hirarrsu cikin nisha─Ći.

Agidan Nurr kam yau ta tashi batajin da─Ćin jikinta, gashi itace da girki dukda ba kwana take da mijinba ma, gashi bata iya barci saboda ─Ćan karen tsoro datakeji, aunty bily kuma duk ranar girkinta ─Ćakin ya mahmud take kwana.
    Bayan ta idar da sallar isha'i ta rarrafa ta kwanta a kan gado.
    Acan kuma aunty bily tana can tana ro'kon ya Mahmud akan yarin'ka kwana ─Ćakin Nurr tunda ita batason zuwa ─Ćakinsa, gashi duk ranar girkinta bata barci saboda tsoro.
    ─Äan tsaki yaja yana fa─Ćin bily bazaki ganebane, Yarinyar nan batada kunya, yanzuma yaya muka 'kare bare taga gadon barcina.
   Hummm yaya kenan, katuna Nurr tanada ha'kki akanka domin itama matarkace, yarinyar nan watarana zata bar duk abinda takeyi kuma zakace nina gaya maka, dan ALLAH kaje can ka kwana.
   Hummm bily kenan shike nan tunda kin matsa, ammafa gsky dole kicigaba da ─Ćaukar nauyina zuwa wani lokaci.
   Murmushi tayi dan tagane inda yanufa, karka damu na yarda, to shike nan malama bilkisu.
    kai yaya yau kuma nice malamar??.
   eh mana gashi anzo an tsareni da wa'azi, mi'kewa tayi tana dariya to saida safe nidai.
      ALLAH yakaimu yafa─Ća yana binta da kallo harta 6acema ganinsa.
      Sai wajen 'karge goma yashiga ─Ćakin Nurr, tana kwance zazza6i ya lullu6eta, ya'karasa gefen gadon ya zauna danshi azatonsa ta kwantane kawai, jiyayi tana fidda numfashi da 'kyar, "k lfy kuwa yafa─Ća yana yaye bargon data lullu6a dashi, ya salam bakida lafiya dama??.
    ─Äagota yayi zuwa jikinsa, tabu─Će ido ahanlali tana kallonsa, bakida lafiya amma shine baki fa─Ćaba??, ahankali ta ce, "naje zanfa─Ća ma aunty bily natarar bata ─Ćaki, miyasa ni bazakije ki sanar minbane??, babu komai tafa─Ĺa tana lumshe idanu.
    Goshinta yashafa ya ce, "sorry, tashi kisha magani, jinginata yayi ajikin gado yaje ya ─Ćakko mata magani, dakansa yabata tasha, ita abin ma mamaki yake bata ammafa duk abinda yake mata baya burgeta dan ahushi yake batama, itafa ba sonsa takeyiba.
    Komawa tayi yakwanta, shikuma yaja bargo ya lullu6eta, barci yafara ─Ćibarta taji ya nutsata ajikinsa, shiru tayi dan barci yafara cin "karfinta................

SABON AL'AMAREE》》

®BILKEESA IBRAHEEM
         {♡Bilyn Abdul♡}

Kuyi ha'kuri masoyana yanzu nazama lazy wlhy.
Luv u oll

27
......Da asuba tarigashi farkawa, wani haushi ya turni'keta dan ganin yanda ya wani kanainayeta ajikinsa, wannan ai iskancine tafa─Ća a zuciyarta tana hararar sa, shikam baimasan tanayiba dan barcinsa yakeyi, jikinta tayi 'kokarin zamewa daga nasa amma saiya farka, ya ce' "lafiya?, ko zazza6inne??, kai ta girgiza batareda tayi magana ba, ya ce, "to ina zakije??.
    Sallah zanyi".
Juyawa yayi yana kallon agogon dake manne a jikin bangon ─Ćakin 5:11am mi'kewa yayi shima dan tuni Nurr ta tashi harma tashige bayi, shima tashi yayi yanufi ─Ćakinsa domin yin alwalar.
    Koda tafito daga bayin saita sama 'kofarta key tana mita, nikamdai wlhy bazan sake yarda ka kwanarmin a ─Ćakiba, wannan ma aii zubar da girmane, 'kato dakai kazo kana kwana a─Ćakin 'kanwarka, aiko Saiff bazaiyi abinda kayiba wlhy mtsooowwww ta'kare maganar da tsaki mai 'karfi, (nace lallai yarinya zakiyi bayani, zakiga ainahin 'kato a─Ĺakinki nan gaba).
     Koda yadawo daga masallaci ─Ćakinsa yawuce domin yin shirin office, dan yakoma aiki.
     Anty bily ce kawai da 'yan aiki suketa hada hadar ha─Ća breakfast, itakam 'yargatan mai mijin tana gado tana sharar barcin safe, bayan sun gama komai 'yan aikin suka ida gyara gidan tsaf, 'karfe takwas dai2 ya mahmud yasakko anty bily ce ka─Ćai afalon, taje ta tarbosa, jakkar hannunsa ta amso tareda gaisheshi, ya amsa yana 'kayataccen murmushinsa wanda har wushiryarsa ta bayyana, dinning suka 'karasa kamar yanda suka saba, ta ha─Ća masa komai zuwa gabansa dukda bawani ci yakeba sosai, kofin shayi ya─Ćauka yana juya cokali aciki, ya─Ćago yana kallonta my bily wai ina Nurr ne??.
     Tayi ─Ćan murmushi yaya aikai zan tanbaya Nurr tunda ─Ćaki ─Ćaya kuka kwana, amma inaga bata tashiba.
   Baice komaiba yacigaba dacin abincinsa, (azuciyarsa ya ce, "dolene na saitama Nurr zama agidannan, dan nakula har yanzu kanta yana rawa).
   Bayan ya kammala break yale'ka ─Ćakin Nurr domin yay mata sallama, saiyaji ─Ćakin akulle, dawowa yayi anty bily tarakashi har wajen motarsa saida taga fitarsa sannan tadawo, itama ─Ćakinta takoma danta ─Ćan runtsa.

Sai 'karfe goma Nurr ta tashi, bayan tayi wanka tashirya  tsaf sannan tafito, afalon ta iske anty bily itama ta tashi, ta 'karasa suka gaisa, anty bily ta ce, "kinga tashi kiyi break zama da yunwa babu 'kyau.
    To aunty na,  tafa─Ća tana mi'kewa.
Bayan ta kammala tadawo falon suka cigaba da hira da aunty bily, idan kagansu saika ─Ćauka yaya da 'kanwane zuciyarsu fas babu irin ─Ćan banzan kishinnan aransu, dan ita Nurr har yanzu tanama ─Ćaukar kanta tamkar 'yar shekara gomane, bama takawoma kanta cewa zaman aure takeyi, itadai inbanda shirme babu abunda ta'iya, ALLAH dai ya shirya.
    Sai wajen 'karfe shabiyu aunty bily tashiga kicin tareda masu aiki, amma Nurr saima ta'kara gyara zama wajen kallon film ─Ćin datakeyi.
   Anty bily tana kicin wayarta tashiga 'kara, Nurr dake kusada wayar ta ─Ćauka ta duba, my handsome tagani an rubuta, baki ta ta6e tana fa─Ćin lallai anty bily bama kisan handsome ba, wannan mai 'katuwar fuskar kike cema handsome, (na ce kai Nurr akwai ita sheri dai), bata ─Ćagaba saima tami'ke takai mata wayar, da sauri aunty bily ta ─Ćaga dan ganin ya mahmud ne, ta ce, "my handaome yaya office??, Alhmdllh yafa─Ća, mikikeyine??, ina kichin mana domin 'ko'karin ha─Ća maka abincin rana.
   Ajiyar zuciya yaja, sannan ya ce, "Nurr fa??, tana falo yaya yanzu nabarota tana kallo, baice komaiba yayi mata sallama, itama saita cigaba da aikinta batareda tunanin komaiba.
            Sai 'karfe biyar yadawo kamar yanda yasaba, zuwa sannan duk sun sake wanka, yaudai su Nurr anyi abinkai ansaka atanfa siket dariga sunyi ba'in kama jikinta saikace fenti, anty bily ce kawai tayi masa sannu da zuwa, amma Nurr ko kallo bai ishetaba, shima baibi takantaba ya haye samansa, anty bily ta ce, "Nurr tashi kikaima yaya ruwansha daganan ki ha─Ća masa ruwan wanka.
     Nurr ta 6ata fuska kai anty ki 'kyaleshi kinsanfa shi ba ayimasa gwaninta, yanzu zaka masa abu ya kusheka nikam bazan iyaba, daka masa kuskure yace zai dakeka saikace wani ─Ćan doka.
    Anty bily tari'ke kai, kai Nurr akwai gyara sosai a al'amuranki kinga tashi kije bazai kushekiba, nidai anty 'kyaleshi kawai indai wancan masifaffenne, garama na kalli film ─Ćina wlhy, anty bily bata sake cemata komaiba tatashi tanufi ─Ćakinsa, tana mai jinjina wautar Nurr azuciyarta.
  (Nace ka─Ćanma kika gani indai 'yar mamace.
      
   Akwance ta iskeshi yacika yayi fam da haushi, ta ajiye tiren data ─Ćoro ruwan a saman tebir ─Ćin dake gaban gadon, ta ce, "sannu ya aiki?, banza yay da ita koma motsi baiyiba balle yabata amsa, batayi zuciyaba ta tsiyaya ruwa akofi taje bakin gadon tazauna kusadashi, yaya tashi ga ruwa kasha, ahankali yabu─Će idanunsa cikin masifa ya ce, "saiyanzu kuka tuna dani??.
     A'a waya isa yamanta dakai yi ha'kuri dan ALLAH kar6i ruwan kasha, nakoshi yafa─Ća yana lumshe idanunsa dasuka nuna alamun gajiya, ruwan ta ajiye cikin sanyin murya ta ce, "kayi ha'kuri dan ALLAH my handsome, kasandai babu yanda za'ayi mu manta dakai.
    Zaki fa─Ći haka kuwa, mintina nawa dashigowa gidan amma babu wanda yanemi inda nake, idan ita batada hankali "k saiki biye mata?, shiru tayi dantasan halin kayanta sarai, da'kyar ta lalla6ashi yasha ruwan sannan ta ha─Ća masa ruwan wanka, itama ta taimaka masa wajen wankan, ta shafa masa mai ya shirya cikin farar jallabiyya suka sakko falon............


Luv u oll my fan's.
©2017
[24/02 18:11] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》

®BILKEESA IBRAHEEM
     {♡Bilyn Abdul♡}

28

.....Sanda suka sakko tuni Nurr tabar falon, shima masallaci yatafi domin yin sallar magriba, dama sai anyi isha'i yake dawowa, har sannan Nurr bata fitoba, anty bily ta ha─Ća masa abinci ta ce, "bismillah bari nakira Nurr.
    Hannu ya─Ćaga mata yana fa─Ćin yi zamanki, ita dan iskanci kullum sai ankirata wajen cin abinci, karta fito tayita zama aii cikinta zatakai bana waniba.
   Badan aunty bily tasoba takoma ta zauna sukaci abincin, har suka gama Nurr bata fitoba, tana ─Ćaki abinta kwance kuma ba barci takeyiba idonta biyu badai tayi niyyar fitowa bane.
    Bayan sun gama anty bily ta ce, "yaya dan ALLAH bari naje nayima abba sannu da zuwa, dan inaso muyi wata magana dashi kafin yasake barin 'kasar.
   Okey, amma kibari sai gobe mana.
    A'a yaya gara naje yanzu kasansa dai zai iya wata tafiyar gobe.
   Okey to kigaida manasu, ─Ćazun nashiga ni mungaisa, mi'kewa tayi tana fa─Ćin zasuji, ya ce, "o, dama kice saida kika shirya sannan kika nemi izini, dariya tayi tana fa─Ći afuwan my prince, shima dariyar yayi ya ce, nayi my dear.
   Mi'kewa yayi bayan tafiyarta yanufi ─Ćakin Nurr, tana kwance a saman kujera idanunta suna kallon sama, da alama tana duniyar tunani, harya shigo yazauna bakin gadon bata saniba.
    Yasan tana tunanin iyayentane, yana ganin yakamata su dady sanar da'ita kodan tasamu nutsuwar zuciya, koba komai zata yima iyayenta addu, gyaran murya yayi sannan tasan da shigowarsa, ta tashi zaune amma bata kalli inda yakeba, shikam sai binta da kallo yakeyi dan ganin yanda taketa cin magani, ya girgiza kai tareda 'kara tsare gida dan soyake yakafa mata dokoki.
   Ya ce, "k".
   A 'kasan ma'koshi ta ce, "na'am.
Bai damu da yanda ta amsa masaba yacigaba da fa─Ćin waye sa'anki agidannan?.
      Saida ta kalleshi sannan ta ce, "babu.
   Mikike nufi dazaman ─Ćaki kullum sai anzo ankiraki wajen cin abinci?.
   Baki ta zum6ura ta ce, "nifa bance dole idan zakuci abinci saikun kiraniba, le6ensa ya cije dan yalura saiya bu─Će mata wuta tunda lallami baya mata.
    Cikin tsawa ya ce, "kishiga hankalinki dan wlhy yanzu xan ─Ćumamamiki jiki, dan rashin mutunci ina miki magana kina maidamin yanda kika gadama ko?, daga yau yazama nafarko na 'karshe dazan miki magana ki mayarmin, nakula duk aikin gidannan bilkeesu ce takeyi saboda "k bakida kunya, kullum kina kwance saidai a tasoki kici  ki koma gado, bakisan idan nadawo gidan nan kimin sannu dazuwaba, bakisan ki ─Ćebo ruwa kibani nashaba, bakisan gari yawaye ranar girkin ki kije ki gyaramin ─Ćakiba, a'a "k abinda kika sani shine kici ki kwanta kiyi barci kitashi kiyi kallo ko??.
    Haka kikaga su mama sunayi agida?, haka zakiyita rayuwa kina ─Ćaukar kanki amatsayin 'karamar yarinya, duk wannan ayyukan babu wanda bakwayi agida, amma nan saboda kin samu maiyimiki shine zaki 'kiyi, ─Ćazufa saboda raini kina kallo nadawo bily tayimini sannu amma "k ko kallo ban ishekiba saboda raini, daga 'karshema saikika baro falon kika dawo ─Ćaki saboda ma'kiyinki yadawo gidan?, sai bily ce takawo min ruwansha ─Ćaki.
   Tunda yafara maganar take kuka amma saboda ta─Ĺan karkatar da fuskarta bai kulaba.
   Yacigaba da fa─Ćin kinsan halina sarai dan haka wlhy kishiga hankalinki niba sakaren miji bane da zan zauna mace tafi 'karfina, inhar kinaso mu zauna lafiya dolene kiyi abinda nake bu'kata, tunda na auri bily bata ta6a tsallake umar nina ba, duk abinda nakeso shitake so kafinma nace taimin tatashi tayinshi.
    Daga yau duk safiya kitashi aringa ha─Ća break dake kafin natafi office, dolene idan ranar girkinkine ki ha─Ća min ruwan wanka, kibani break naci, idan nagama kirakani har wajen mota, kidawo ki gyaramin ─Ćaki, dolene ki girka abincin rana akaimini office, idan nadawo ki tarbeni kirakani har ─Ćakina, kibani ruwan sha, ki ha─Ća min ruwan wanka, "k wankanma idan takama kece zakimin, da sauri tajuyo tana kallonsa, yasake tsare gida.
    Daga yau karna sakejin sai ankiraki wajen cin abinci tunda ita ba sa'ar ki bace, inko hakan tasake faruwa ranki sai yayi matu'kar 6aci, kinsanni kinsan halina duk abinda na lissafo miki babu ba'konki aciki.
   Nurr ta ce, "har yimaka wankan?.
   Fuska ya'kara tamkewa ya ce, "eh, Nurr tafashe da kuka tana fa─Ćin ni wlhy ba 'yar iska bace,
Da sauri ya mi'ke yanufi inda take ubanwaye ─Ćan iskan to??, filon kujera ta ─Ćauka ta kare fuskarta dan gudun kartaji saukar mari, ga kuka tanayi, ya ce, "wlhy ki ha─Ćiye wannan kukan kafin nakashe fuskarki da mari, ubanmi aka yimiki dazaki tasa mutane gaba kina faman rusar kuka yafa─Ća yana fisgo filon data kare fuskarta dashi.
   'Kuuttt ta ha─Ćiye kukan dan tasan yanda ya fusata ─Ćinnan ba 'karamin aikinsa bane ya saukema fuskarta marin.
   Ya ce, "maza tashi nabaki minti uku kishiga bayi ki wanke fuskarki.........kafin ya 'karasa harta kai hanyar bayi, dama hanyar guduwa take nema, yana nan tsaye tafito, amma saita dogare a 'kofar bayin, hanya yanuna mata batareda yayi maganaba, sum2 tafice falo shima yatake mata baya, ya ce, "wuce kici abinci.
   nifa na 'koshi tafa─Ća cikin rawar murya.
   inda take yanufo tako zura da gudu hanyar fita, a'kofa sukaci karo da anty bily da sauri tari'ke Nurr dasuke 'kokarin yin karo, Nurr lafiya dai??, hawaye suka zubo mata ta ce, "ya Mahmud ne, bily tamaida kallonta gareshi yayi kicin2 da fuska babu alamar wasa, taja hannunta suka 'karasa cikin falon, tsawa yadaka ma Nurr wanda tasakata dur'kushewa ita kantta anty bily ─Ćin saida ta tsorata, ya mi'ka mata filet ─Ćin abinci daya zuba, ya dangwarar agaban ta minti goma nabaki kicinyeshi tas, Nurr dake kusada anty bily ta fashe da kuka ni wlhy bazan iya cinye wannan avincin ba, karki iya yafa─Ća yana nifota da cajar fitila ahannusa, ta ko 'kadandane aunty bily tana kuka, aunty bily tashiga ro'konsa akan yayi ha'kuri ya 'kyaleta karya daketa.
    Ki bari bily gara na koyama yarinyar nan hankali iskancinta yafara isata, dukda hakadai kayi ha'kuri aizataci, tsaki yaja yakoma saman kujera yana kallon labarai.......................

Luv u oll my fan's
©2017
[26/02 11:21] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》

®BILKEESA IBRAHEEM
       {♡Bilyn Abdul♡}

29

......itama anty bily taja hannunta suka zauna tabata tahau ci, data tsaya dacin abinci alamar ta 'koshi sai aunty bily ta nuna mata ya Mahmud da idanu, haka tayita tura abincin harta cinye, dama yunwa takeji kuma abincin daya zuba mata baifi 'karfin cikintaba, kawaidai 'yan rashin arzi'kinne akanta, bayan tagama takai filet ─Ćin kichin tadawo zata wuce ─Ćaki.
   Ya ce, "dawo nan ki zauna.
    Ta ce, "barcifa nakeji.
  Kidawo kizauna nace, duk maganar dayakeyi idonsa nakan tv, anty bily ta nuna mata da hannu tadawo ta tazauna, dawowa tayi tazauna tana kunkunai.
   Bayanda zatayi dole ta zauna harya gama kallon labairai yatashi sannan suma kowacce tanufi ─Ćakinta.
    Tana shiga tasakama 'kofarta key tana fa─Ćin wlhy bazan sake kwana da 'katon gardi a ─Ćakinaba gara tsoron yakasheni, koda yake dije mai aiki zan kira taringa tayani kwana naga tsiyarka masifaffe kawai, wanda idan ba bala'i yayiba baya jin da─Ći.
    Shikam koda yaje ─Ćakinsa shirin barci yayi yanufo ─Ćakin Nurr amma saiyajishi akulle, kai kawai ya girgiza yakoma ─Ĺakinsa.
   Andaiyi sa'a yau tatashi ta ha─Ća masa break da taimakon aunty bily, amma ko saving nasa bata tsaya tayiba takoma ─Ĺaki tai kwanciyarta, sai anty bilyce tabashi abincin amma ita tuni ta tsufa a─Ćaki, baice komaiba yazauna yaci abincinsa yatafi office, yasan dolene saiya 'kara ha'kuri da Nurr akwai sauran lokaci dazata bambance fari da 'ba"ki, shekara sha shidda aiko da sauran 'kuruciya.
 
Haka rayuwar tacigaba da tafiya, balaifi Nurr tana rage wasu abubuwan na rashin hankali saboda tsoron ya mahmud datakeyi.
   Yauma takasance weekend ranar kuma girkin Nurr ne, amma ko ka─Ćan bata farin ciki da hakan, tana shiga matu'kar damuwa duk ranar dayake ─Ćakinta, bata iya barci ko ka─Ćan saboda fargaba, har yanzu kuma takasa kiran dije mai aiki ta tayata kwana, amma yau ta─Ćauki aniyar kiranta komai tafanjama fanjam.
       Suna zaune afalo itada aunty bily suna hira, shikuma mai gidan yana ─Ĺakinsa dan yanzu ya fahad yafita bayan sungama tattaunawa, mai wankinsu yay salkama suka amsa tareda bashi izinin shigowa,  yashigo hannunsa rungume da kayan wankin ya Mahmud dayayi yau, saida ya gaishesu sannan ya ce, "ga kayan oga hajiya, anty bily ta ce, "to ─Ćanliti sannu da 'ko'kari, Nurr tashi ki kar6a ki kaimasa ─Ćaki.
    Nurr jitayi kamar ta fasa ihu amma yazatayi tanajin kunyar aunty bily kodan hidimar datakeyi da'ita.
   Tashi tayi takar6a tana fa─Ći ─Ćanliti ai kayan da nauyi, dariya yayi eh hajiya akwai nauyi amma ai zaki iya, hakadai kace tanufi saman ya Mahmud tana fa─Ći, tana mama kin irin turaren da ya Mahmud yake amfani dashi, dukda wankin da kayan suka sha amma sai zabga ─Ćan karen kamshin turaren sukeyi, kamar yanzu aka saka, taja birki a 'kofar falon dan fargabar abinda zata tarar, tana tunanin ta kwan kwasa kota juya, to amma idan tajuya yazatayi da wa─Ćannan kayan??, tasan aunty bily tana falo a zaune.
    Ahankali ta kwankwasa 'kofar dan batayima zaton zaijiba, ta 'kara tabiyu, takai tsawon minti biyar agurin ba'a bu─Ćeba, harta ─Ĺaga 'kafa zata juya aka bu─Će kofar, da sauri ta kalli wajen, gogan nakune tsaye dagashi sai guntun tawul ─Ćaure a 'kugunsa da alama wanka zaishiga, tayi saurin yin 'kasa da kai, dan bata ta6a ganin namiji ahakaba tunda take, koda suna gida yayyen nasu basa zama haka, ko gajeren wando basa fitowa dashi garama jallabiya da wando iya gwuywa.
   Yalura da kunya takeji amma saiya basar ya matsa mata alamar ta shigo, kanta sunkuye ta shigo falon shikuma yamaida ─Ćakin yakule.
   Saman kujera tayi yun'kurin ajiyewa, yay saurin fa─Ćin karki sake ki ajiye min kaya anan gurin.
    Cikin dauriya ta ce, "ina zankai to, yanda tayi maganar muryarta babu tsoro saida tabashi mamaki harya ─Ćago yana kallonta, amma saiya danne mamakinsa ya ce, "a ina kike kai kayanki, ta ce, "bedroom acikin dirowa, baice da ita komai ba yay gaba zuwa cikin bedroom.
    Kular datayi bashida lokacinta yasa ta take masa baya, sanda tashiga ya cire tawul ─Ĺin yana kokarin saka gajeren wando, da sauri ta watsa kayan saman gado zata gudu, yay saurin daka mata tsawa "k wanne irin shirmene wannan kobakiga yanda kika yimin da kayabane??, tsayawa tayi jiki narawa ta ce, "sorry kuskurene, tsaki yayi yace dawo ki gyarasu kuma adirowa nake son ganinsu yafa─Ća yana zura jallabiya, dan yakula ganinsa datayi ahaka yasakata tsorata,.
   Zuwa tayi tana tattara kayan, tabbas ya Mahmud yana burgeta awajen tsafta, mutumne mai tsafta da son gayu, ko 'kafarsa ka kallah kasan ya ha─Ću wajen tsafta dajin da─Ći, saidai zuciyace babu 'kyau sai ba'kar mugunta dason girman tsiya, tagama gyarawa ta ─Ćiba zuwa dirowa, ya ce, "ai nan zaki ajiyesu kiringa ─Ćauka da ─Ćai2.
     Saida ta murgu─Ća baki sannan ta ajiye amma bai ganiba, dirowar tabu─Će tana kallon ikon ALLAH, komai na dirowar atsare yake, shaddoji wajensu daban, sut wajensu daban, 'kananun kaya wajensu daban, jallabiyoyima haka, kai komaidai atsare kuma ajikin hanga, gawani 'kamshi na musamman mai da─Ći yana fita acikin dirowar, hankalinta nawajen kallon dirowa yashigo, dan da yafita, kamar daga sama taji yace aikin dana sakaki kenan?.
    Da sauri tajuyo tana kallonsa cikin rawar murya ta ce, "yi ha'kuri ina duba inda zansakane, ya ce, "kodai kina kallemin sirrin dirowane??, kai ta girgiza tana fa─Ćin a'a wlhy, ya─Ćan ta6e baki to kiyi aikinki.
    Kayan ta ─Ćauka zuwa dirowa amma tarasa yanda zatayi tasakasu, karasowa yayi wajen dirowar ya tsaya bayanta tamkar zai rungumeta, yami'ka hannu ya─Ćau hanga ─Ćaya ya nuna mata yanda zatayi, batace komaiba tacigaba dayi yanda ya nuna mata, saida tagama lodasu tas sannan.
   Tana cikin ─Ćan gyara musu zama idonta yakai kan rigar daya kwace kwanaki ahannunta randa yatarar suna fa─Ća ita da deena, rufewa tayi dan yana tsaye yana kallonta, amma ta─Ĺau alwashin wataran saita sace rigarnan dan tana sonta sosai.
    Bayan ta kammala ya ce, "shiga bayi ki ha─Ćamin ruwan wanka, ido ta─Ćago tana kallonsa ya─Ćan ─Ćaure fuska, da sauri tawuce bayi shikuma yafara zame kayan jikinsa, ruwan taha─Ća masa agurguje tafito a'kofar bayin taci karo dashi, dagashi sai guntun tawul iya cinya na ─Ćazunnema ya mayar, 'kasa tayi da kanta tawuce sum2 tamkar mara gsky.
    Yabita da kallo kayan sunmata 'kyau amma sun matseta sosai, yarinyar akwai jikin mata. (kwalelenka ya Mahmud)..............Luv u oll my fan's
©2017
[26/02 11:31] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》

®BILKEESA IBRAHEEM
       {♡bilyn Abdul♡}

30

........da daddare bayan sun gama kallon labarai kowa yanufi ─Ćaki, dama ita Nurr ko hira suke bata saka musu baki, shima─Ćin bakomai yake fa─Ća kai tsayeba saidai ata'kaice, wani sa'in har soyayya sukeyi agabanta amma ko kallo basu ishetaba, idan tagama suna abinda yafi 'karfin tunaninta tashi take tabar wajen, ita kallonma 'yan iska take musu.
   Tagama shirin barcinta tsaf, sannan taje kiran dije mai aiki danta tayata kwana, duk da dije mai aiki tana tsoron abinda zaije yadawo wannan bai hanata cika umarnin Nurr ba, katifa tasaka atsakar ─Ćakin ta kwanta, itakuma Nurr ta haye gado, babu da─Ćewa barci yay gaba dasu.
     Wajen 'karge goma nadare ya Mahmud yakammala duk abinda yazamana na al'adar rayuwarsa, yay shirin barci, yakashe komai yanufi ─Ćakin Nurr, key yasa yabu─Će, dan tunda tafara kulle masa 'kofa saiya nemi wani key ─Ćin, dayazo saidai yabu─Će yashige batareda ya kwankwasa ba, saidai tafarka taganshi kokuma da asubahi, turus yayi danganin mutum kwance atsakar ─Ćaki, yaja numfashi tareda cije le6e, 'karasawa yayi jikin gadon yazauna gefen ta, yana mai mamakin mike damun yarinyar nanne??, Nurr! 'k Nurr!!, maimakon Nurr tafarka sai dije tafarka,  afirgice take kallon ya Mahmud.
    Cikin rawar murya ta ce, "sannu alhaji.
   Yauwa ya Mahmud yafa─Ća tareda fa─Ćin dije lafiya naganki anan?.
   Ta─Ćan sosa gefen wuyanta ta ce, "anty ce tace nazo natayata kwana wai tanajin tsoro........kafin tarufe baki Nurr ta tashi, dama indai ana magana akusa da ita komin nisan barcinta saita tashi, cikin mamaki take kallonsa, ta maida kallonta ga dije datake na─Će kayan shimfi─Ĺarta, a'a dije ina zakije??.
    Anty zan koma ─Ćakinmu dije tafa─Ća..
   Kamar ya xaki koma ─Ćakinku?, bani na ce, "kizo kitayani kwana ba?.
   Harara ya Mahmud ya watsa mata......gum tayi dabakinta, ya maida kallonsa ga dije kinga yitafiyarki, to Alhaji saida safe dije tarissina sannan tafice, tashi yayi yarufe ─Ćakin yadawo saman gadon yakwanta batareda yabi takan Nurr ─Ćinba dake zaune tana binsa da kallo tamkar gunki, addu'a yayi tareda jan bargo ya lullu6e jikinsa, Nurr ta watsa masa harara amma bai ganiba, sakkowa tayi takoma saman kujera ta kwanta.
    Ya Mahmud ya ce, "k dawonan.
   Ta tashi daga kwanciyar datayi tana zum6ura baki nidai kabarni na kwanta anan, ya za'ayi muringa kwana waje ─Ćaya.
   Tashi yayi zaune kinsan ALLAH idan baki tasoba nazonan saikin raina kanki, "k wai miki ─Ćau kankine?, yafa─Ća cikin matu'kar masifa, tashi tayi takoma kangadon, ya fusgota jikinsa yafatse sosai, "k kina ganin idan kinyi hakan shine zaisa na 'kyaleki??, idan nayi niyyar kusantarki kota 'karfine zan aikata hakan, matata kike inada hakkin dazan kar6i hakkina najikinki kota halin 'ka'ka, bawai na 'kyaleki bane saboda wayonki, ya─Ćan sassauta mata ri'kon dayayi mata, wlhy daga yau kika 'kara kawo mini wata daniyyar ta tayaki kwana saina kacaccalaki a wannan daren, idankuma kinji 'karya kisake aikatawa ya hanka─Ćata saman filo yana fa─Ćin iskancin banza kawai!!!!!.
     Ya koma ya kwanta.
  Kifewa tayi tana garshe'kar kuka, juyowa yayi yana fa─Ćin wlhy kiyi maza ki ha─Ćiye wannan kukan kafin jikinki yayi tsami a wannan daren.
    Ai dawuri ta ha─Ćiye kukan tasan zai iya bubbugeta, ya ce, "oya kwanta, filo tajawo ta kwanta yaja bargo ya lillu6esu yana fa─Ćin ko shashsheka banasonji danhaka kiyi barci kokuma yanzu kisha mamaki, dama yara nakeso kinga adarennan da izinin ALLAH saina baki cikin ─Ćana.
    Gabantane yafa─Ći rass plzzz yaya kayi ha'kuri zanyi wlhy, ya ce, "ato kidaiyi mai yuwwuwa, dole tabi abinda yakeso dan bata fatan abinda zai shiga tsakaninsu, jira take kawai daddy yadawo daga tafiya taje yaymata bayani akan iyayenta.
   Tana gama jin tushenta zata mi'ka bukatarta asa yasaketa, dan wlhy bata sonsa bakuma zata iya zama dashiba.
                          Tuni barci ya kwasheta, amma shi yakasa barcin tuni yafa─Ća duniyar tunani, shi yanzu wace hanya yakamata yabi wajen kwantarma da Nurr hankali, bai ta6a soyayyaba sai akan Nurr, tun tana 'yar 'karamarta yake 'kyaunarta, ita ka─Ćai yabama dukkanin soyayyarsa, tuni zuciyarsa take mata 'kauna mai zafi yana dannewane saboda gudun tashin hankalinta, domin sannan tana masa kallon wanda suka fito ciki ─Ćaya, yarinyar tana bashi matu'kar tausayi saboda hali irinna mahaifinta, yana burin nuna mata soyayya nagartacciya maikuma tsafta, saidai shirmen yarinyar yayi yawa, har yanzu 'kuruciya tana ─Ćawainiya da ita, yasan yanason bilkeesu amma bakamar Nurr ba, yana yima yarinyar wata irin zazzafar soyayya, yana kwa─Ćayin ─Ćan ─Ćana mata zumar irin son dayake mata, ya kalli yanda takoma can 'karshen gado tawani takure jinta, ya rungumota zuwa jikinsa, ajiyar zuciya yasaki danji lallausar fatarta ajikinkinsa, azuciyarsa ya ce, "ALLAH yakaimu randa zakiyi hankali my love! Burina nabaki cikin baby na ki haifa min, wannan shine cikon farincikina Nana maryam.
   Itadai batamasan yanayiba dan barcinta takeyi.
  Da asuba yarigata tashi saida yayi alwala sannan yatada ita yafice masallaci, bayan ta idar da sallah haka ta daure tafito ta─Ćora breakfast ─Ćin safe, anty bily tafito ta tayata kamar yanda tasaba, bayan sun kammala kowa tanufi ─Ćakinta, barci suka koma tunda weekend ne.
    Sai wajen 'karfe tara da rabi suka tashi, ya Mahmud ya─Ćauki waya yana kiran Nurr wai tazo ta ha─Ća masa ruwan wanka, saidai wayar bata shigaba, har yafarajin haushi saikuma yayi wani tunani, ai tunda aka kawota gidan baiga waya ahannuntaba ma, toko ta 6atarne?, yafa─Ća yana sakkowa, dakansa yaha─Ća ruwan wankan yayi sanan ya sakko 'kasa.
   ─Äakin aunty bily yafara shiga ya rungumeta tsaf yana fa─Ćin i miss u my bily, murmushi tayi tareda fa─Ćin miss u too my handsome, janta yayi bakin gado suka zauna, ya manne bakinsa da nata yana nuna mata soyayyarsa mai tsafta da nagarta, adai dai wannan lokacin kuma Nurr tashigo ─Ćakin daniyyar tada aunty bily daga barci idan bata tashiba, hazbinannahu wa'nimal wakil tafa─Ća kamar wadda taga wani abu, ya Mahmud ya─Ćago idanunsa dasukayi jaa yana kallonta, dagudu tabu─Će ─Ĺakin tafice.
   Aunty bily ta ce, "my handsome kaga abinda nake gudu ko??, bai tanka mataba saima maida bakinsa dayayi kan nata yacigaba da abinda yakeyi, babu yanda zatayi mijintane dolene ta taimaka masa dan tasan yana matu'kar bu'katar hakan, tundashi mabu 'kacine, saida yagama lugiyguytata san ransa sannan ya'kyaleta.
      Nurr kam tuni taje ─Ćakinta, saman gado ta haye ta rufe fuska wai yau taga iskanci, itakam wlhy yau gida zataje sai kuka takeyi, tana nan zaune ya Mahmud yashigo, ta'kara 'kudundune kanta acikin gyalen data yane kanta, gadon yahawo yana fa─Ćin "k suwaye 'yan iskan???.
    Bakinta bai mutuba ta ce, "kumana, wlhy ni gida zani bazan zauna aringa iskanci agabanaba.
   Janyota yayi jikinsa ya manneta sosai...............

SABON AL'AMREE》》NA BILKEESA IBRAHEEM
       {♡Bilyn Abdul♡}

31

............munedai 'yan iska ko?, to kema yau zanyi iskancin dake, rigarta yashiga 'ko'karin cirewa, itako sai tureshi take tana kuka dakiran tashiga uku mama kizo ki ceceni, abubuwa yashiga yimata masu matu'kar tsoratar da bakonsu, yafara 'ko'karin cire dogon wandon dake jikinta, cizo ta galla masa a 'kirji, dukda yaji zafi amma ya daure yacigaba da abinda yake, kawai jiyayi tafara shi─Ćewa dannan ta sassan 'kame awajen bayan tasaki wata razananniyar 'kara, ─Ćagata yayi yakoma gefe yana kwafa tareda harararta, ya sakko daga saman gadon yafara neman magungunan daya kawo mata kwanaki, da'kyar yagansu batayi amfani da ko ─Ćayaba, rintse idanu yayi yana fa─Ćin halinki saike maryam, abin turare yajona ajikin soket yazuba turaren maganin babu da─Ćewa tafara tari, ta tashi arazane zata gudu dan ganinsa tsaye akanta, ya ce, "mu sa'anninkine???.
     Kai ta girgiza da sauri.
    Zaki 'kara cemana 'yan iska?.
  Nannma kai tagirgiza, ta ─Ćora dafa─Ćin yaya dan ALLAH kayi ha'kuri bazan sakeba dan ALLAH karkayi iskancin nan dani natuba wlhy bazan sakeba kaji na rantse, yanda ta ru─Će sosai tabashi matu'kar dariya amma saiya gimtse ya ce, " ba nace karna sakejin kince iskanciba, hannu tasa tarufe bakinta tana hawaye, jikinta sai rawa yakeyi, ya watsa mata harara maza ─Ćauki rigarki ki saka..........kafin yarufe baki ta rarumo rigar tana kare 'kirjinta saiyanzu talura yacire mata har bra ─Ćinta, taja bargo ta lullu6e jikin, ya ce, "riga nace ki sakafa.
    Ta ce, "dan ALLAH to kajuya baya koka fita plzzzz.
   harararta yayi babu inda zanje, idan zaki saka ahaka ki saka, kitashi muje wajen break bily tana jiranmu, kuma wlhy ki daidaita nutsuwarki, idan kika bari tagane kina cikin wani yanayi zakisha mamaki.
    Wlhy bazan bariba barima kaga nawanke fuskata, rigarta bra ─Ćin ta ─Ćauka dagudu tashige bathroom, ya Mahmud ya tuntsure da dariya harda zama, kai matsoracima baiji da─Ćin halinsaba, yarinya sai tsiwar tsiya amma tsoro fal cikinta, magungunan yagyara yamaidasu inda ya─Ćakkosu, yakarasa gaban 'kofar yana bugawa kefa nake jira kina 6ata mini lokaci.
    Burum tabu─Će tafito, ya ce, "maza jeki shafa fauda da kwalli, babu musu tayi abinda yace (nace o, su Nurr akwai tsoro), ya ce, "ki daidaita nutsuwarki sosai banason shirme, tayi kwal2 da idanu hawaye suka cika idon taf, ya ce, "o, kukan zaki 'kara???, da sauri ta maidasu tana girgixa kai, gaba yatasata har falo inda aunty bily take, takamo hannunta tana fa─Ćin haba Nurr ─Ćin mama badai kuka kikayiba???.
    Saida takalli ya Mahmud sannan ta girgiza kai tana murmushin ya'ke, ya ce, "sakarta tazuba min abinci dan inada gurin zuwa, anty bily tasaki hannun Nurr, itakuma jiki asanyaye ta ha─Ća masa dukkan kayan abincin agabansa, bai sake bi takansuba yashiga cin abincinsa, yana gani aunty bily tana ta lallashinta, yagama ya mi'ke samansa yakoma domin canjo kaya, wajen kokawa da Nurr duk kayansa sun yamutse gata shadda, yasakko cikin wata sabuwar shigar ta farin yadi mai shara2, saina dawo yafa─Ća yana ficewa batareda yajira amsar suba.
    Da 'kyar aunty bily ta lallasheta ta─Ćanci abincin, tana gamawa takoma ─Ćaki tadasa sabon kuka.
 
Da gudu deena tashigo gidan tana ihun kiran Nurr aunty bily!!!, ta ─Ćane wuyan aunty bily tana murna, ohni deena haryanzu ba'ayi hankalinba??, dariya tayi ta ce, "aunty da sauran lokaci ina Nurr??, tana ─Ćaki aunty bily tafa─Ća.
    Dagudu tanufi ─Ćakin Nurr, tana shiga suka rungume juna, deena tana murna Nurr tana kuka, sunkai minti biyar ahaka sanan suka saki juna, deena tafara share ma Nurr hawaye haba sis......miya sakaki kuka haka??, da nazata na murnar ganinane??, miyake faruwa??.
     Nurr ta zauna tana share hawaye deena wlhy bazan iya zama da ya Mahmud ba, bana sonsa shi ─Ćan iskane, wlhy bana sonsa.
    Deena ta ce, "ban gane ─Ćan iskaba??, kin ta6a ganinsa da karuwane??, kai ta girgiza, to giya yakesha??, nanma kai ta girgiza.
    To miyayi miki???.
Hawaye Nurr ta share ta zayyanama deena komai, dariya sosai deena takeyi harda kwallah,, saida taga Nurr ta sake fashewa da kuka sanan ta tsagaita da dariyar datakeyi tana fa─Ćin sorry my dear wasa nakemiki.
     Yanzu waye yayima gadonnan haka?? deena ta tambaya tana gimtse dariya, Nurr takalli gadon tana hawaye, shine yay masa haka yanzunnan kafin muyi breakfast, deena tami'ke tana dariyarta ciki2, gadon tagyara tsaf sannan tadawo tana lallashin Nurr, saida taga ta nutsu tafara sakinjikinta sanan ta ce, "Nurr abinda kikagafa ya Mahmud yanayi da aunty bily ba iskanci bane, matarshicefa yana da hakkin aikata hakan agareta, kuma kema ba iskanci yay mikiba tunda "k matarsace, aii yamayi 'ko'kari da har yau baiyimiki komaiba, wlhy ni randa aka kaini ya Suraj bai barniba, gashi ina cikin kukan rabuwa dake da iyayenmu amma ko ka─Ćan bai saurara miniba, "k yanzu hakafa ciki gareni.
    Idanu Nurr tazaro saikuma ta bushe da dariya tana fa─Ćin kai deena ciki kuma??, ta 'kara tuntsurwa da dariya.. 
   Deena ta ce, "bakuna nason iskanci malama, dan nace miki inada ciki shine zaki tasani gaba da dariya, Nurr takai hannunta kan cikin deena tana fa─Ćin sorry mai ciki, ashe nakusa zama momy babyna ykk??.
    Deena ta ce, "yar iska saura "k, tunda aka fara gwadaki yau aiko ana hanyar baki ciki, duka Nurr takaima deena deena takauce tana dariya.
    Aunty bily tashigo tana fa─Ćin lafiyarku kuwa??, Nurr ta tuntsure da dariya aunty wai kinji deena ciki gareta, hhhhhhh takuma kecewa da dariya, anty bily ta ce, "ALLAH yashiryaki Nurr kinji, cikin shine abin dariya saurake aii, ta gwalalo ido waje ALLAH yakiyaye aunty nayo ciki??? haba.
     Da'kyar ta daina dariyar suka zauna suna hira.
   Deena tami'ka mata wayarta Nurr ga phone ─Ćinki.
   Lah dama tana wajenki??, inata tunanin kona yarda, a'a tana wajena, saidaga baya naganta acikin akwatina ashe nan muka sakasu, ALLAH sarki my phone i miss u, tafa─Ća tana summbatar wayar.
    Aunty bily tami'ke kunga kuci gaba da hirar bari naje na ha─Ća mana abincin rana, yanzu zakiga yaya yadawo.
    Suna ─Ćaki ya Mahmud yadawo, baiyi zaton aunty bily tana kicinba, yazata suna tare dan yaji hirar mutun biyu tunda baison deena tazoba.
    Yaturo 'kofar yashigo, deena ta ce, "yaya sannu dazuwa.
   A'a deena kece agidan namu?.
  Eh yaya nice nazo muku yini.
To lallai mungode dayawa, amma ba mijinki yace mini bakida lafiya ba??, eh yaya amma naji sau'ki aii.
   To ALLAH ya'kara sau'ki.
Ameen yaya.
   Nurr tace sannu da zuwa, bayan taga ya watsa mata wata uwar harara, sai yanzu kika gani yafa─Ća yana fita.
    Baki ta murgu─Ća ta ce, "mugu kawai.
  Deena ta zaro ido lallai yarinya wuyanki ya isa yanka, yaushe kika raina ya Mahmud haka?, yanzunan idan yajikifa??.
    To yaji mana, zai kashenine.......salamu ailaikum, sukaji sallamar ya Mahmud yadawo.....................Luv u oll my fan's
©2017
[27/02 17:23] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》


NA BILKEESA IBRAHEEM
       {♡bilyn Abdul♡}


32

.......A tsorace suka amsa masa azatonsu yaji, shima ya fahimci kamar sun─Ćan razana da dawowarsa, ya ce, "k bani magungunan nan, Nurr ta 6ata fuska dan tanajin haushin ''k ─Ćinnan saikace baisan sunantaba, ya ce, "ba'kya jinane??, mi'kewa tayi ta ─Ćakko masa, ya kar6a yafice.
     Deena ta ce, "maganin miye Nurr?.
   Oh masa ranar yakawoshi tun ana kwana ─Ćaya da kawoni, nikuma banyiba.
   To saboda mi??".
Babu komai wlhy nina ma mantane, ALLAH ya shiryeki Nurr, amin 'yar uwa Nurr tafa─Ća suna tafawa da deena.
   Haka sukaita hirarsu kamar karsu rabu, bayan aunty bily ta kammala abinci takirawosu, kusan tare sukafito da ya mahmud, suka 'karasa dani kowa yanemi gurin zama.
   Aunty bily batayi yin'kurin ha─Ćama ya Mahmud abinciba dan tasan girkin Nurr ne, itama tayi burus dashi, saida anty bily ta ce, "Nurr yayafa ''k yake jira, Nurr ta─Ćan zum6ura baki ta─Ćago tana kallonsa, ya harareta, tai saurin kauda idonta daga kallonsa, tashi tayi tana saving nasa, tako ta'ke filet da abinci kamar mutum uku zasuci, aunty bily tabu─Će baki zatayi mata magana ya Mahmud ya─Ćaga mata hannu alamar tayi shiru, itamadai deena kallon abin mamaki takeyi, tasan Nurr da iya tsokanar fa─Ća kosanda suna makaranta itake fara jawo musu fa─Ća, saikuma tsoro kamar farra kura, tasan kuma tabbas ya Mahmud ba 'kyaleta zaiyiba.
   Tajuya tazubama su aunty bily suma, amma su daidai cikinsu, yagane wato shine abokin wasanta, wani filet ─Ćin ta─Ćakko dazummar zuba nata amma saiya dakatar da ita tahanyar fa─Ćin aibama saikin zuba waniba, tsayawa tayi tana kallonsa da mamaki, ya ce, "─Ćakko cokali kidawo nan yanauna mata kujerar kusadashi, ta zun6ura baki toni idan nadawo mizan maka anan??.
    Harara ya watsa mata ya ce, "bansaniba, zakiyi abinda nace kosaina 'kara ─Ćaukar irin matakin ─Ćazu da safe akanki??, kafin yarufe baki tazo ta zauna, oya sakahannu muci, ta zaro ido waje yaya nifa ba shinkafa zanciba taliya zanci, ya ce, "wannan kuma abinda yashafekine ba damuwata bace, ubanwaye yace kizuba wannan uban abincin anan??.
   Idonta yaciko da hawaye ta ce, "aii canike zaka iya cinyewa, ya ce, "kwarai zan iya tunda ga mahmud jaki, kina 6ata min lokacifa.
   Yaya dan ALLAH tunda anty bily shinkafa zataci tazo kuci tare, kokuma na rage tunda baka fara ciba? Nurr tafa─Ća cikin muryar tausayi, aiba ita tace kizubaba, kuma tunda kika fito dashi bazai komaba, daga nan yafara cin abincinsa batareda yasake bi takantaba, saida yakai lauma ta uku sannan ya ce, "kinsan ALLAH idan kika bari nagama cin abincinnan bakiciba yau zakisha mamaki, tunowa tayi da abinda yafaru ─Ćazu da safe dan haka sauri tasaka cokali suka cigaba daci.
    Deena da aunty bily sai gimtse dariya suke amma bai kulaba.
   Baifi lauma goma shabiyarba ya ajiye cokalin damashi bacika cin abinci dayawaba, (nace ance maza sunada cin abinci amma banda ya Mahmud wata macenma tafishi cin abinci).
    Tunda ya ajiye cokalin itama Nurr saita ajiye, baice mata 'kalaba ya─Ćauki ruwa yana sha, saida ya kammala ya─Ćauki tishu yagoge bakinsa, sannan ya ─Ćauki cokalin dayaci abincin dashi, ya kalli deena ya ce, "deena ─Ćakkomin caja ─Ćincan, deena tami'ke tana fa─Ćin to.
    Tuni cikin Nurr ya ─Ćuri ruwa, ya ciko cokali da abinci yakai saitin bakinta, ta waro ido tana tamke baki, cajan ya─Ĺaga kamar zai zura mata ya ce, "bu─Će bakin.......da sauri tabu─Će yajuye mata abinci, kafin ta ha─Ćiye ya ─Ćebo wani kuma saiya cika cokalin taf, datayi 'kokarin yin gardama saiya ─Ćaga bulala saita amsa da sauri kunsandai Nurr da tsoron duka.
    Cikinta yayi bala'in cika jitake kamar zai fashe amma shi sai ─Ćura mata yakeyi, tanaci tana hawaye, tunsu deena suna gimtse dariya harta fara fitowa fili, harararsu kawai yayi batareda yayi maganaba, suka saka hannu suna toshe baki, Nurr ta fashe da kuka saboda tayi bala'in 'koshi bana wasaba, ta marairaice yaya dan ALLAH ka tausaya min wlhy zan mutu, banza yay mata yacigaba da bata abincin, ina dataga babu ala aii saita shammacesa ta arce da gudu ─Ćaki tasakam 'kofar key, su aunty bily suka kece da dariya dan bazasu iya ri'ketaba, shima mi'kewa yayi ya haye samansa dan dariyar neman kufce masa takeyi, dayaje falonsa saiya zube saman kujera yana she'ka dariya harda hawaye, walhy gudun yarinyar nan yayi bala'in bashi dariya saikace wadda tayo sata, saida yayi mai isarsa sannan yay shiru amma daya tuna saiya murmusa.
   A 6angaren su aunty ma haka saida sukayi dariya mai isarsu sanan suka shirya tsokanar Nurr, wadda tunda ta fece saita zube ajikin 'kofar bayan ta kulle, sai maida numfashi take da 'kyar, tunda tayi girma bata ta6a cin abinci mai yawan na yauba, jitake tayi nauyi ga cikinta tamkar zai fashe, aunty bily tayi bala'in iya muryar ya Mahmud danhaka suka nufi 'kofar Nurr da niyyar tsokanarta.
     'Kofar ─Ćakin sukaje suna bugawa, Nurr tanaji tayi shiru dan tasan ya mahmud ne ya biyota aii wlhy kizasu kwana ahaka bazata bu─Ćeba, ya daketa abanza, anty bily ta ce, "wai bazaki bu─Će bane?, tafa─Ća cikin irin muryar ya mahmud..         daga can Nurr ta ce, "ai wlhy kozaka kasheni bazan bu─Ćeba, anty bily ta ce, "haka kikace ko?, Nurr ta ce, "eh haka nace, kuma wlhy kamatsamin yau agidan daddy zan kwana naje na ha─Ćaka da mama, anty bily ta ce, "to ki bu─Će 'kofar nace, aff zancen kakeso ashe zamu kwana ahaka yaya.
     Suka tuntsure da dariya dansun kasa riketa, data gane bashi bane su aunty bilyne suka tsokanarta saita bu─Će 'kofar, suka shiga suna mata dariya, deena ta ce, "o, ''k Nurr yaushe zakidaina wannan tsoron ga jan fa─Ća kin iya amma sai tsoron tsiya.
    Zama tayi a'kasa tana dafe ciki ta ce, "wlhy ya Mahmud mugune original, not photo  start copy, dan ALLAH kugafa yanda yake neman kasheni da raina, gashi kukuma sai dariya kukemin, ALLAH yasoku bai sauke muku bala'in nasaba, waima yana inane??.
    Anty bily ta ce, "kina zurowa da gudu shikuma yatafi ─Ćakinsa, kai Nurr kin iya gudu fijo!!!! Sunan wata mota.....suka tuntsure da dariya harda Nurr, tanayi tana dafe ciki ita adole kar cikinta yafashe, deena ta ce, "to bakiji tsoron sanda kaika arto yabiyokiba??.
    Nurr ta ce, "ainasan duk bala'insa idan ka gudu ka tsira, aunty bily ta ce, "ALLAH nurr kirage abinda kikeyi kinfison keda yaya kuyta wasan 6uya agidannan kamar 6era da mage, ALLAH anty ya mahmud ─Ćinne yacika muguntar tsiya saikanayi kana ─Ćan ramawa, hakadai sukata hirarsa suna dariya..................
Luv u oll my fan's
©2017
[01/03 13:57] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》


NA BILKEESA IBRAHEEM
      {♡Bilyn Abdul♡}


33

......Har yamma Nurr ta'ki fitowa, koda ya Suraj yazo ─Ćaukar deena da 'kyar tafito suka gaisa, ya mahmud yana fitowa ta arce ─Ćaki, har suka tafi bata fitoba sai deenace tazo tayi mata sallama.
    Da daddare bata fito cin abinciba, da aunty bily ta ce, "bari ta kirata sai ya mahmud ya ce, "ta 'kyaleta, wannan cikin nata bazata iya cin abinciba, idanma tayi wasa bazata iya barciba dan ba 'karamin abinci taciba, saidai ki ha─Ća mata furut tasha, shine zai taimaka mata abinda taci yayi 'kasa.
   Anty bily ta ce, "kai yaya kasan dalon mugunta iri2 saikace wani soja, murmushi yayi ya ce, "wlhy bily Nurr batajin magana ko ka─Ćan, du ha'kurinka saita 'kureka, saikuma taga za'a hukuntata duk saita ru─Će saboda shegen tsoronta.
    Aini zangaya maka Nurr akwai tsoro ─Ćazufa tsokanarta mukayi.......aunty bily tashiga zayyane masa yanda sukayi.
   Dariya sosai yakeyi ya ce, "aibatada kunya yarinyarnan wlhy ni nama rasa yanda zanyi da'ita, nema ma take ta rainani, anty bily ta ce, "kuruciyace kawai ke damunta bari kaga takai irin shekara ashirin ─Ćinnan zata rage abinda takeyi.
    Ya ce, "ta6 ashe da sauran aiki wajen shekara ukufa nan gaba, kafin sanan aina gama jigata da halin Nurr, dariya anty bily tayi, kuma dayake tanajin tsoronka zata rage wasu abubuwan kafin sanan, to ALLAH yasa yafa─Ća yana ajiye cokalin hannunsa alamar ya 'koshi kenan.
    Bayan sun kammala aunty bily ta ha─Ća kayan furut takaima Nurr, Nurr ta ce, "yauwa anty bily wlhy kin taimakeni dama cikina tun ─Ćazu narasa yadda zanyi saboda ya cinkushe.
   To aiga furut nan saiki sha insha ALLAHU zai sauka yanzunnan.
   Acan kuwa Deena tunda suka koma take bama ya suraj labarin ya Mahmud da Nurr, sai tuntsura dariya yake, ya ce, "sukuma tasu salon soyayyar kenan??, deena ta ce, wlhy kuwa kaima ka fa─Ća ai da gidan nake danaci dariya wlhy.
   Ya ce, "gsky kam saikace wasu tom & jerry, ai sunfima tom & jerry, haka taita bashi labari shikuma yana she"ka dariya.
      Da lokacin kwanciya yayi sai ya Mahmud yay kwanciyarsa a ─Ćakinsa, dan yanaso yabar Nurr tasamu Nutsuwa tunda a tsorace take dashi, ga abinda yay mata da safe gakuma laifin datayi masa.
    Itakam addu'a taketayi ALLAH yasa kar ya mahmud yazo dan yau koma tsoron bataji, idanma tanajin tsoron saidai na ha─Ćuwarta da ya mahmud, tada─Će batayi barciba saboda fargabar kada yayi amafani dawani key ─Ćin yashigo kamar yanda yakeyi, to hardai barci ya saceta bai shigoba.
  
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, yauda gobe sai ALLAH inji masu iya magana, Nurr tanata hidimarta dan yanzu ya Mahmud yadaina kwana ─Ćakinta, iyakarta ranar girkinta tayi masa abinci, tana gyara masa ─Ćakinsa amma ruwan wanka saidai ya ha─Ća da kansa, haka fira bakoda yaushe take zama ayi da itaba, tafi maida hankali wajen karatun novel awa, duk lungu dasakon dazata tasamo novel tasani, dan haka tarage wanima shirmen dan tana ganin yanda ake wasa 'yammatan littafi ko matan aure, shiyyasa itama takeso ta koyi wasu abubuwan badan ta burgr mijintaba saidan itama aringa ─Ĺaukarta a babba ba yarinya ba, har yanzu bata ta6a jin son ya Mahmud ko kwayar zarra azuciyartaba, hasalima komai yayi haushi yake bata, tana masa kallo na mugun mutum masifaffe, kullum burinta ALLAH yasa yasaketa takoma makaranta kamar yanda khairat taci gaba da karatunta, itama tana burin haka, koda yake deena ta ce, "mata suma ana nema musu makaranta to ALLAH yasa hakane.
 
Yauma dai aikin aunty bilyne suna gama breakfast ya mahmud yafice gidan dady, da sallama yashiga falon babu kowa dan haka kai tsaye yanufi ─Ćakin mama tunda su dady basu dawoba shida mami, nanma da sallama yashiga, Saiff dake zaune saman kujerar ─Ćakin yana break ya amasa tareda sakkowa 'kasa yabama ya Mahmud kujerar, saida ya zauna sanan saiff ya gaidashi, ya amsa yana tambayar ina maman??.
    Saiff ya ce, "tana bathroom amma yanzu zata fito, yaya Ina Nurr??, tana gida saiff tunda ka'ki zuwa, zanzo wlhy yaya makarantace take hanani wani motsi amma zanzo gaishesu itada aunty bilkee harma da deena da aunty ikileema, to shikenan sai munganka.........mama ta katse musu zancen saboda fitowarta daga bayi, ─Ćan zamowa yayi daga kujerar yana gaisheta, ta amsa tana zama gefen gadon ta ce, "ya iyali??, lafiya lau suke suna gaidaku yafa─Ća yana sunkuyar da kai kamar mara gsky, mama batace komaiba dan tanajin nauyin yin doguwar magana dashi, tsawon minti biyar babu wanda yasake magana, saiff yami'ke yana fa─Ćin mama bari naje wajen su Farhan, to saiff adawo lafiya, yafice yana fa─Ćin yaya ka gaidamin Nurr, to zataji saiff.
    Bayan fitarsa ya Mahmud yadaure ya ce, "mama dama nazo akan maganar Nurr ne.
   Mama ta ce, "incedai lafiya?, ko Nurr ─Ćin batada lafiyane??.
    A'a lafiyarta 'kyalao akandai son sanin maganar iyayentane.
          , har yanzu tana cikin damuwa kenan bata kwantar da hankalintaba?, mama ta tambaya tana kallonsa, eto dadai sau'ki amma wani sa'in takan zurfafa tunaninta.
   Mama taja numfashi aii wanan kuma laifinkane, kaikeda alhakin lallashinta da kwantar mata da hankali, nasanka da zarni amma kuma duk zarnin mutum yakamata ya sassautama iyalinsa tahakane zakasan matsalarsu harka iya maganinta, kasan Nurr har yanzu akwai kuruciya atare da ita, idan ka bita ahankali kana kwantar mata da hankali saikaga ahankali taringa rage damuwarta harma tacigaba da rayuwarta kamar da, kasan ba'ason tada zancenan a family saboda nemawa yarinyar nan daraja, iyayenku basa son aringa kallonta da laifin mahaifinta, dan haka kaima karna sakejin makamanciyar maganarnan abakinka.
   To mama insha ALLAHU ya wuce kenan ayi ha'kuri,, shiru tayi saikuma ta ce, "ya ciwonnata basadai matsa mata ko??, a'a da sau'ki tundama taje sau ─Ćaya tayi, kuma dayake an kar6o mata magani.
    To shikenan ALLAH ya 'kara karewa, amin yafa─Ća akan la66ansa daganan shiru yabiyo baya, ya Mahmud yanaso yaga sun zauna da mama haka suna hira, amma ita bata sakar masa fuska saboda kunya da kawaici, yauma saboda mami bata nanne shiyyasa har firar tasu tayi tsawo haka, haka zai dage yayta cusa kansa harta fara sakewa dashi.
   Mamafa ko gidansa bata ta6a zuwaba saida bily tayi 6ari kusan na 'karshe sanan tadaure taje abisa tursasawar dady, yanzukam ai yasan dole taje kodan Nurr, yasan yanda take 'kaunar Nurr kosu 'ya'yanta bata musu haka, shiyyasa mutane dayawa suka gaza gane ba itace ta haifi Nurr ba........mama ta katse masa tunanin dafa─Ćin akawo maka breakfast ne??, kai ya girgiza cike da jin da─Ći ya ce, "a'a mama saida nayi break nafito, to shikenan mama tafa─Ća.
    Haka  suka zauna tamkar surukai lokaci2 su─Ćan ta6a hira saikuma ayi shiru na tsawon lokaci, yada─Će agidan daga baya yay mata sallama yataho gida.

Daga nan gidan ya fahad yashiga, suna falo shida iyalinsa suna hira, Abdul da rauda sukazo suka taresa suna fa─Ćin oyoyo dady, ─Ćagasu yashiga yi yana fa─Ćin oyoyo yaran daddy, ya zauna saman kujera yana fa─Ćin school ya 6oyemin ku yarana, Rauda dake cinyarsa ta ce, "dady jiyama na iya alifun, ya ce, wow!! Babyna da gsk??, ta ─Ćaga kai cikin farinciki, Abdul ya ce, "dady aini na'iya tuni uncle ma ya ce, "nafita 'kokali, ya mahmud yaja hancin abdul aikai dabanne babammu.
   Anty ikileema ta ce, "yaya ina kwana wa─Ćannan maganannun sun hanamu ko gaisuwa ayi, ya amsa yana dariya to aini dama danna gansu nazo badan kuba.
   Yaya fahad ya ce, "haba yaya wasa kakeyi.
   Babu wani wasa gsky ce nafa─Ća, okey ikileema to tashi mubar musu falon ya fahad yafa─Ća yana dariya, hanya ya mahmud yanuna musu ya ce, "kuyi maza ga hanya, dariya sosai sukeyi, yami'ke tareda sa6ar Rauda akafa─Ća yakama hanun Abdul suka fice.
    Suka bishi da kallo da addu'ar shima ALLAH ya azurtashi danasa 'ya'yan.
   Daga nan gida yanufa, Nurr ka─Ćaice a falon, tana kwance saman doguwar kujera, jikinta sanye da wando pink iya gwuywa tasa farar best ta─Ćora pink ─Ćin jaket mai mannewa ajiki, kanta ko ─Ćankwali babu dama batacika sonshiba, kunnenta manne da iya fis, tanajin wanka, yashigo da sallama hannunsa ri'ke dasu abdul, kwata2 Nurr batasan da shigowarsuba dan idanunta alumshe suke da alama tanjin da─Ćin wa'kar.................


Post a Comment for "SABON AL'AMAREE CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...