-->
 • Jelajahi

  ;ƁATACCEN YANAYI COMPLETE (1) A DALILIN MATAR UBA COMPLETE (1) A DUNIYARMU COMPLETE (2) A GIDANA COMPLETE DOC (1) A TUNANINA COMPLETE DOC (1) ABBAS COMPLETE (20) ABDULKADIR COMPLETE (4) ABDULLKADIR COMPLETE (6) ABOKIN MIJINA COMPLETE (1) ADIYYA COMPLETE (2) ADIYYAH COMPLETE (1) ADUN WASU COMPLETE (1) AGOLA COMPLETE (1) AHUMAGGAH COMPLETE (17) AJALIN SO COMPLETE (19) AKAN SO COMPLETE (1) AL (2) AL-AMARIN ZUCI COMPLETE (4) AL'KALAMINE SILA COMPLETE (2) ALMAJIRA COMPLETE DOC (2) ALMAJIRATA COMPLETE (1) AMAL COMPLETE (8) AMAREN BANA COMPLETE (8) AMARIN ZUCI COMPLETE (1) AMININ MAHAIFINA COMPLETE (17) AMJAD COMPLETE (2) ARZIQI RABO COMPLETE (3) ASHE KECE COMPLETE (1) AUREN SIRRI COMPLETE (1) AUREN SOJA COMPLETE (1) BA SONTA NAKE BA COMPLETE (16) BABBAN GIDA CHAPTER 3 MP3 (1) BABBAN GIDA COMPLETE MP3 (23) BABBAN KUSKURE COMPLETE (1) BAGIDAJIYA COMPLETE MP3 (4) BAKAR MACE COMPLETE MP3 (27) BAKIN DARE COMPLETE (5) BAƘIN DARE COMPLETE (15) BANSAN LAIFINA BA COMPLETE (2) BARIKI IYAWA COMPLETE (1) BARIKI NA FITO COMPLETE (48) BARRISTER ASAAD COMPLETE (1) BATACCEN YANAYI COMPLETE (3) BATUUL COMPLETE (24) BAYAN RAI COMPLETE DOC (1) BINTU COMPLETE DOC (1) ƁATACCEN YANAYI COMPLETE (11) CAPTAIN BILAL COMPLETE DOC (1) CIWON IDANUNA COMPLETE (1) COMPLETE (1) COMPLETE DOCUMENTS (10) CONEL AHMARD COMPLETE (6) DA'IMAN COMPLETE (1) DAMATA COMPLETE MP3 (24) DAN ADAM COMPLETE (37) DAN FASHI 🔫 COMPLETE (1) DAN MINISTER COMPLETE (1) DAWUUD CHAPTER 1 (1) DAWUUD COMPLETE (10) DIYAM COMPLETE (20) DR SALEEM COMPLETE (7) DR SAMEER AMEER COMPLETE (2) EL-MUSTAPHA COMPLETE (13) FARA YAR SHEHU COMPLETE (4) FARHA COMPLETE (21) FETTA COMPLETE (31) FIRGITA SAMARI COMPLETE (1) GAMAYYAH COMPLETE (14) GANGAR JIKINSA NA AURA COMPLETE (1) GIDAN SARAUTA COMPLETE (14) GIDAN UNCLE COMPLETE (1) GIMBIYA SA (3) GIMBIYA SA'ADIYA COMPLETE (44) GWARMAYA complete (1) H novels birnin gayu (29) HAFSAT COMPLETE (3) HARSASHEN SO COMPLETE (37) HASKE COMPLETE (27) Hausa novels (35) HIKIMA COMPLETE (10) HUTU COMPLETE (13) IGIYAR RAYUWA COMPLETE (1) IN SO YAKI NE COMPLETE (21) IT IS PART OF THE GIFT COMPLETE (6) Ita (1) ITACE QADDARATA COMPLETE (14) JALILA COMPLETE (13) JAWAHEER COMPLETE (7) JINI DAYA COMPLETE (1) JINNUL AASHIQUE COMPLETE (1) JUYIN RAYUWA COMPLETE (3) K'ADDARACE COMPLETE (14) K'ANWAR MIJINA COMPLETE (1) KADDARA KO SAKACI COMPLETE (3) KAINUWA COMPLETE (9) kANDALA COMPLETE (10) KANO TA JIDDAH COMPLETE (1) KARUWA CE COMPLETE (1) KAWU NANE COMPLETE (1) KAWUNA COMPLETE (8) KE NAKESO COMPLETE (6) KIBIYAR KADDARA COMPLETE (2) KINA RAINA COMPLETE (10) KISHIYOYINA COMPLETE (2) KIYAYYAR ZUCI COMPLETE (3) KOMA KAN MASHEKIYA COMPLETE (3) KOMAI NISAN JIFA COMPLETE (3) KUDIRI COMPLETE (9) kula da kaya (1) LOVE HER SOFTLY COMPLETE (14) MABRUKA COMPLETE DOC (1) MAEESHA COMPLETE (3) MAIRO COMPLETE (5) makaranta duniya (31) MAKIRCI KO ASIRI COMPLETE (4) MAKOTAN JUNA COMPLETE (10) MARWAN COMPLETE (3) MATACCIYAR RAYUWA COMPLETE (36) MATAR SHEIKH COMPLETE (1) MAZA {ALLURAR GUBA}💉 COMPLETE (1) MEYE ILLAR YAYA MATA COMPLETE (24) MIJIN BUZUWA COMPLETE (2) MIJIN HANEEFAH COMPLETE DOC (1) MIJIN YARINYA COMPLETE (2) MRS AMIDUD COMPLETE (12) MRS GURAJE (4) MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE (43) NANNY COMPLETE (3) NAUFAL COMPLETE (2) NAYI GUDUN GARA COMPLETE (39) NI DA PRINCE COMPLETE (19) QADDARAR SUMAYYAH COMPLETE (32) QADDARAR SUMAYYAH COMPLETE MP3 (66) RABO AJALI COMPLETE (8) RAI BIYU COMPLETE (21) RAMUWAR GAYYAH COMPLETE (6) RANA DAYA COMPLETE (3) RANAR NADAMA COMPLETE (2) RAYUWAR ASMAU COMPLETE (14) RIBAR BIYAYYAH COMPLETE (1) RIKICIN WANI GIDA COMPLETE (11) RUDI NE KO BURI COMPLETE MP3 (2) RUDINE KO BURI COMPLETE MP3 (12) RUKAYYAH YAR ALBARKA COMPLETE DOC (1) SAKAMAKO COMPLETE (10) SAMU COMPLETE (7) SAMU YAFI IYAWA COMPLETE (6) SAWUN BARAWO COMPLETE (11) SHIMFIDAR MIJINA COMPLETE (1) SILAR AJALI COMPLETE (3) SILAR GIDAN AIKI COMPLETE (30) SOORAJ COMPLETE (5) soyayyah (1) SOYAYYAH CHAPTER COMPLETE (1) SOYAYYAH COMPLETE (12) SOYAYYAR MU COMPLETE (5) TAGWAYE COMPLETE (36) TAMBARIN TALAKA COMPLETE (1) TANTIRIN NAMIJI COMPLETE (7) TARKO COMPLETE DOC (1) TARKO COMPLETE MP3 (3) TATTALINTA COMPLETE (12) TAZARAR DAKE TSAKANINMU COMPLETE (13) THE BLIND'S MONEY COMPLETE (11) THE CITY COMPLETE (6) TSANANI COMPLETE (20) TSANGAYAR MATI COMPLETE (8) TUN KAFIN AURE COMPLETE (1) TUNTUBEN HARSHE COMPLETE (4) UMARNIN SAURAYI COMPLETE (2) UMMI COMPLETE (15) UNTIL I RELLY DO COMPLETE (14) UZTAZIYA KO YAR DUNIYA COMPLETE (1) WANENE SHI COMPLETE (14) WANI AURE COMPLETE (34) Wata (1) WATA BAKWAI COMPLETE M (17) WATA FUSKA COMPLETE (15) WATA SHARI'A COMPLETE (21) YANAYIN RAYUWA COMPLETE (14) YANKAR KAUNA COMPLETE (2) YAR ALMAJIRA COMPLETE (4) YAR FULANI COMPLETE (2) YAR GWA (1) YAR MAKIYAYA CHAPTER 1 (2) YAR MAKIYAYA COMPLETE (19) YAR SADAKA COMPLETE (2) YAR SHUGABA COMPLETE (42) YAR TALLAH COMPLE (1) YARE BIYU COMPLETE DOC (1) YARIMA ASHMAN (1) YARIMA KHALEED COMPLETE (7) YARIMA SUHAIL COMPLETE DOC (1) YAZEED COMPLETE (3) ZABIN SAMHA COMPLETE (6) ZAMAN HOSTEL COMPLETE (1) ZEENAT YAR JARIDAH COMPLETE (16) ZEHRA COMPLETE (15) ZUCIYA COMPLETE (27)
  Copyright © HAUSA NOVELS
  Best Viral Premium Blogger Templates

  Iklan

  RANAR NADAMA CHAPTER A

  A/I/S
  Monday, 7 June 2021, 6/07/2021 10:21:00 pm WIB Last Updated 2021-06-08T05:21:12Z
  masukkan script iklan disini
  masukkan script iklan disini

   RANAR NADAMA CHAPTER A


  Sautin kida ne ke tashi cikin motar mai Dan karan dadi da nishadar da mai jin sa kallo daya za kayi mata ka tabbatar nishadine ya fado rayuwarta daga yanayin da take murmushi da rausayar da kai lokaci-lokaci ta na kai duban ta ga titi domin kaucewa afkuwar hadari.

  Wayarta da ke yashe cikin lokar motar ta shi ga burari da sauri ta kai duban ta kan fuskar wayar ganin sunan da yafito ya san ya ta murmusawa da sauri ta ta kai hannun ta ta dauka gami da latsa maballin amsa kira ta kara a kunne "amarya kin sha kamshi amarya bakya laifi ko kin kashe Dan mai gida" a ka fadi daga dayan Barin cikin yanayi na dariya ita ma rukayya dariya ta saki gami da cewa"ke kam kin shiga uku bunayya ke yanzu sai ki yarda ni amarya ce ai na wuce amaryar duk Wanda ki ka ji an tambata da sunan amarya to bincika zai iyayuwa ranar daurin aure ko kuma bayan an daura aure ana kokarin kai ta gidan mijin ta" shewa bunayya tayi gami da sakin guda har tafa hannu ka na iya jiyo sautin daga cikin wayar rukayya sai da taga shewarta sannan tace"ki na nufin har kun gama cin kazar amarcin?"kwalo idanu rukayya tayi sannan tace"kazar amarcin lafiya bunayya har sau nawa ake cin ta ita kazar amarcin ina sha tun daren farko da an lamushe ta an tauna kashi an kora da sanyayyan lemo an wuce wajan"shewa bunayya tayi mai sauti har sai da rukayya ta kau da wayar daga kunnan ta don ji takeyi kamar bunayya za ta dauke mata jin ta "ke kam akwai yar ban za wallahi" cewar rukayya bayan ta mai da wayar kunnan ta "wai ina angon ne ko har yanzu baki sake shi ba ne" cewar bunayya cikin dariya da sigar tsokana ba ta bata amsar tambayar da tayi mata ba illah cewa  da tayi "kin ga rabu da ni a kan hanya nake bari in na sauka zan ki raki" "ahhhh ke dai fadi gaskiya ko dai kina tare da habibi ne?" Zancen bunayya ya fara Isar ta shegen surutu kamar aku ita ko gajiya ba tayi da Dan banzan surutu caaaaa kai jama'a "kin ga sai an jima ki gaida min da habibin naki" bunayya tace"munansura kya ma fadi gaskiya kin sai an jima don na lura ba kyason hirar" rukayya tace ba haka bane wallahi Allah tuki nakeyi" "OK to shi kenan a sauka lafiya sai kin ji ni" bayan sun yi sallama rukayya ta mai da wayar ta aje ta cigaba da tukin ta tana mai cike da farin ciki a gefe daya kuma dariyar bunayya take da shegen kwakwazon ta in da tayi gigin fada mata in da zata yau da ta shiga uku dan fallasa za tayi ta iya cewa wani abin ne da ita amma Allah ya taimake ta ba tayi wannan gigin ba gwanda da ta rufawa kan ta asiri haka ta cigaba da tukin ta har ta isa wani tafkeken asibitin kudi mai suna SUNSHINE SPECIAL HOSPITAL.

  *** ***   ***

  A gajiye ya fado cikin gidan yanayin parking ya suri jakar sa mai dauki da lapton sa sauran tarkacan sa yayi hanyar falo ya na isa ya bude ya shiga gami da sallama jin ba a amsa ba ya tabbatar masa mutan gidan ba sa ciki ban damu ba don San in da aka je kuma da izinin sa ya da zango yayi cikin lumtsumemiyar kujerar da ke cikin kayataccen falon sanyi A-C da da kamshin turaran huta kawai ke tashi suka hadu suka ba da wani sanyayyan dadi gwauron numfashi ya ajiye gami da kara lumewa cikin kujerar cikin yanayi na matukar gajiya kusan mintina goma ya shafe a haka sannan ya tashi cikin jan kafa ya isa ga dining table kuloli kala biyu ajiye ya Jan yo daya ya bude shinkafa ce a ciki jallof kur yayi mata da ido yana kare mata kallo cikin yanayi na kamar bai gamsu ya tsine fuska yayi na Dan lokaci ya sauri kular gami da plant ya isa tsakiyar falon ya yada zango zaman dirshan yayi domin har ga Allah yunwa yake ji mai lasisi cikin sauri ya shiga kamata ya na dubawa a plant din sai yayi masa nak sannan ya ja kular can gefe ya shiga jiyo abincin da cigiye-cigiye a cikin  kamar mai kokarin hango wani abu a ciki bisa yanayin da yake kallon abincin kamar bai yi amanna  dashi har zuci nan ya fara kokarin kai wa bakinsa farmaki da wannan mashahurin abincin mai makon da ya kai bakin  shi maimakon  ya tau na gami da hadiyewa amma sai akasin haka wani irin furziya yayi kamar mutumin dake kokarin furzawa sumanme ruwa domin ya farfado ya shiga ya tsine fuska yayi cilli da cokalin dake hannun sa yasanya kafarshi ta hagu mai makon yayi amfani da ta dama amma sabida tsabar haushi da kiyayyar da yakewa abinci saboda rashin dadi da kuma dandano  kawai sai yayi mahagubar dashi farantin yayi sama sannan ya dire kasa ya tarwatse abinci a baje faranti yayi warwatsa wani wawan cafka yakaiwa wayarsa dake yashe gefe ya shiga latsata cikin hanzari ya kai ta kunne sakwanni kadan sai ya ja tsaki tare da kara turmushe fuskarsa "yau abin da kika aikata kenan na ta'addanci na ga alamun nan gaba yar fashi da makami zaki zama wajan gurgunta.. koma nace tarwatsa rayuwata akan rashin iya abin kirki"

  daga dayan bangaren cikin alamun na rashin bada mahimmanci kan maganar da kuma rashin fahimta tace

  "banga ne ba me kake cewa sabeer..." ya sake cewa

  "amma hala gishiri da mai da albasa ki ka hada da shinkafa kika zurkuce cikin tunkunya kika maka ruwa kawai kika daura kan wuta ruwan na tsotsewa kika sau ke"

  har zuwa wannan lokacin bata San inda zancen sabeer yake gabas ne ko kudu oho cikin nuna halin ko In kula ta sake cewa

  "wallahi shinkafarce wata iri tafiya kayan haushi da takaici  nima so tayi ta karni " a hanzarce yace"kin ga ba tatsuniya nace ina muradi ba hakkin ciki na nake magana akai na rantse da Allah in har ciwon yunwa ya ka Mani KECE SILA" ya karashe cike da karsashi da nunin alamun tsagwaron gaskiya yake sanar da ita hakan da ta fuskanta ya San ya ta dan nutsuwa dan ta San tabbas sabeer zan iya botsare mata ya ballo mata gundumemen aiki ba karamin aikin sa ba ne.

  " me ke faruwa"

  tafadi cikin nuna dai ba wani Abu

  bai wani jidadin abin da tace ba illa haushi ma da ta bashi

  " kin sa Allah rukayya bana kaunar irin wannan rainin hankalin naki wai mai yasa baki da abin a yabo ne a rayuwa kullum sai kin nemi zungurowa mutane sama da kara"

  a kausashe cikin shanyewa dan ta fuskanci cin fuskar da yasa ba yi mata shi yake shirin kinkimowa ya Dora

  "kai mai yasa ba a abin jindadi da kai ne dan Allah Malam kayi zance da hankula zasu dauka yayi musu wani amfani ba wai ka ta sauki burutsu ba..."

  da Sauri ya tare ta

  "ko ai shikenan"

  " au jirkice zancen zaka yi?"

  "to meye amfanin cigaban sa illa Karin takaici"

  rukayya tashiga lissafe lissafe kan zantukan sabeer in da samo ta saba yakamata ace izuwa yanzu ta fuskance shi

  "yi hakuri sanar dani ko abincin bai ishe ka bane"

  wani mugun takaici yashanye zuciyarsa ai in ma kishi ne  bai yi ba zai iya daukan ta annabawa amma bai ma ci ba balle yace yaji wani nauyi to ina ma abincin da zai ci wannan abincin yan bursun take so ya maka?

  " kinga tuna baya sannan ki bani amsa akan me na kira ki nayi miki magana"

  nan tashiga tunanunnuka

  "kamar kan abinci ko"

  "wai mai yasa kike haka ne ce miki fa nayi wani irin abinci kikayi"

  "dan girman Allah bari sai nadawo na rasa makama cikin maganarka bani lokaci nakusa isowa kan hanya nake"

  tsaki ya ja ya aje wayar duba da yar da take yi masa magana Sam ya rasa me take nufi wai bata gane maganarsa ba shi da yakamata ace shine da cewa haka amma sabida Neman suna da daukaka shine zata rai na masa hankali sai kace wani d'a gareta abi biyu yunwa takaici rashin makama. a zancenta yarasa irin rukayya kullum ita magana bata iya ba sabeer dake baje tsakar falo murkususu ya zame masa abin yi shi ba gwani wajan iya girki ba da ya huce haushi amma yasan ko yayi yin kurin ballo wa Kansa wannan aikin ciki zai kwana ba yarda ya iya dole ya kinkimo hakurin duniya ya yafa.

  tsayin lokaci yadauka a haka jiran rukayya kawai yake ta iso dan tsabar ma rainin hankali mutum sai kace mai tafiya a sayyadar sa har yanzu bata iso ba cikin mota fa take kuma yasan ba waje guda zata yada zango ba jarabar gantalin ta ba zai bar ta ta iso gidan yanzu ba karar bude kofa da akayi ne ya tsinke masa zarar tunanin sa dago kai yayi daga shingi Dan da yake ya shiga duban ta ita ce tashigo kallon ta yayi ya  watsar da ita gefe ya rufe idanuwansa kamar mai barci har ta iso tsakar falon ta Shiga dubansa ta mai da kallon ta wajan farantin dake yashe a tarwatse ta mai da kallonta gareshi

  "yan fashi da makami ne suka shigo sukayi maka fashin abincin naka?" ta fadi da ta tabbatar yana jinta ba barcin yake ba

  "ko duk cikin gajiyar ce hala mazgesu kayi"

  kware idanuwansa yayi ya dubeta asheke

  "kinga kiyi min shiru tunda shiga gida da mutane suke baki iya sallama acikinsa ba kila ma ta'addaci ki Shiga kowa ni gida dashi"

  a rahance tace

  "duk me yayi zafi ba wuta"

  "makera  ne a gidan"

  ya fadi a hassale gum tayi da bakin ta tasamu wajan daura kugunta tashiga dubansa cikin yanayi nason sanar dashi muhimmin abu.

  "naje asibitin ka san me ya faru?"

  "sai kin fada sannan zan Sani"

  ya fadi a rashin ba zancen nata muhimmanci ko da dai aran shi yana bukatar Karin bayani akan haka

  "bai dace ka fuskance ni irin wannan fuskar ba a turmushe sakinta zakayi muyi zance na hankali"

  "au da marar hankali kika dauke ni"

  yafadi yana wurga mata kallon na raina hankalinki

  "ni a uwa kare da gudun layya ai ba ma zan ce haka ba yanzu a yanke min hukuncin zaman gidan kaso ban shirya ba"

  yanayin fuskarta duk maganar da yake ya ba mata bata nuna jin haushin haka sai raha ma da take da alamun akwai abin da ke Sanya farin ciki Wanda ya dame haushin maganganun sabeer

  "naga dakta bello..."

  da sauri ya daga mata hannnu

  "in har kina son na ba zancen naki muhimmaci naji da nauyi a hanzar ce takai duban ta gareshi fuskarta na bayyar da alamun son Karin bayani

  "bangane ba me kake nufi da wannan zancen naka"

  a kule shima ya dubeta

  "ya kamata ki ne mi littafin Koyan girki tun kan lokaci ya shammace ki"

  in akwai abin da ke matukar bata mata rai to bai wuce korafi kan girkin sabeer ba tarasa wani irin mutum ne Allah ya halinta mai jarabar korafi wannan da ace yana cikin hukumar tace girke girke bata San yarda zata kasance ba.

  tayi ajiyar numfashi fuskarta nanu na alamun jin haushin bantun sa

  "uhmm ai sai ka sayo Mani kaga sai na koya tunda gyatumar tawa bata koya min yarda ake girki ba a kullu yau min baka rabuwa da iface iface akan girki in nayi na rasa dalili"

  cikin nuna halin ko in kula

  "nidai ba haka nake nufi ba ban gayyaci gyatumar ki cikin zance na ba dan haka kiyi saurin zareta"

  ai ji tayi kamar yakara rura wutar takaici a gareta

  "ai zancen naka kenan ka nuna ban iya kaga kenan tun gidan mahaifan nawa dama ban iya ba"

  "nifa bada fada nake Neman ki ba dan naga alamun kokarin kirbata kikeyi"

  ya fadi yana mai da komai ba komai ba tashi yayi zaune ya fuskance ta

  "ko zanci alfarmar abin da zan yafawa ciki ba ko na kori yan ta'addan da suka kawo Mani ziyarar bazata"

  duban kulolin abincin dake yashe tsakar falo tayi sannan takai dubanta gareshi da tarin zarge zarge amma bata tofa ba hakan yanuna akule take

  "kin San Allah ba zanci wannan abincin ba NO RIGA fa na sayo amma ace ta kasance haka ina!!!"

  ya kareshe cike da karsashi alamun Shifa da gaske yake ba canji

  gabadaya taji tarasa bakin magana shin me yadace tayi me Yakama tayi wa sabeer dan yayi matukar bata mata

  "in kaga nasake girka tukunya to wallahi na dare zan dorawa amma bazan sake daura wata tukunya ba ni wallahi narasa jaraba irinta taka sai kace da shnkafa a halicce ka nafa gaya ba in Kwai abin da bana muradi to dafa shinkafa"

  a gwale yace

  "yo dama duk kanwar jace wani girki ki ka iya aiko ba dafa garaugarau ba Wanda zance gwara kawai dai inayi miki adalci ne kar ace na cika korafe korafe San kace rigimanman tsoho"

  "dan girman Allah mufuskanci alkibila naji zan gyara kalas!!"

  ta fadi cikin nuna jirkitar da zancen

  ba yarda ya iya dole yayi abinda take so amma cikin sa nafa man a zalzala masa

  "na hakura naci na dare in kin girka amma in yayi min yarda nake so in kuwa ba haka ba sai nakoma take away"

  cikin nuna ba maganganunsa rashin mahimmaci da watsar dasu

  ta dubeshi "zancen zuwa na asibiti namuyi koko wani daban?"

  ta tambaya dan ita bats kaunar su fara magana ya saki layi

  "duk wannan kika zaba kiyi"

  "naje nasami dacta bello duk nayi masa ba yani ya Shiga aunani da yagama yace yana bukatar fitsarina zai kuma debi jinina..."

  wani kallo ya watsama Wanda yasa tayi gum

  "ba dai kin malala mai fitsarin da ya bukata ba?"

  yafadi cikin nuna tuhume tuhume ya kuma tsareta da idanu

  "kayya wai mai yasa kake haka ne kadai bari na karasa zance na dai ko in ma sharhi zakayi sai kayi dan ba hanaka zanyi"

  bai ce kalaba kuma bashi da niyya saida bukatarshi ta Dora masa zance dan ya matsu yaji karshen labari

  "karamar kwalba ya bani yace nashiga bayin dake cikin ofishin nasa anan nayo amsa yakai ni lab aka debi jinina sannan yace naji rashi bayan yan mintuna sai ya dawo yashiga sanar dani yayi aune aune abinda yasamu amatsayin saka mako shine..."

  da sauri ya tare ta

  "...ki dauke da maleriya ko nasan hakan zata kasance"

  sororo tashiga duban sa yarasa abin da zai danganta ta dashi sai maleriya amfa akwai alamu rai ni acikin zantukar sa

  "nidai ba haka yace Mani bai ce ina da cuta ba dan haka kadai danganta ni da ita "

  cikin son abinda zata tace masa cike da zakuwa yace

  "to me yace na gyara kalamina"

  tayi murmushi wanda haka ke bayyanar da akwai alheri cikin zancen nata tace

  "albishirin ka"

  "kinga bana son janjani a magana kawai ki sanar dani abin da nake bukata kenan ba dogon zance ba"

  duban sa tashigayi ta rasa takamaiman matsayin da zata aje shi fuskarsa dai gata nan ba yabo ba fallasa amma dai...

  ta katse tunaninta da cewa "ina dauke da ciki har na tsawon wata biyu a jiki"

  wata irin zabura yayi yaji katangar tashin hankali ta ruguzo masa ya Shiga duban cikin alamun rashin haiyaci yanayin yarda fuskarsa da gangar jikinsa ke nuni yayi matukar razana kwanyarsa tashi ga caji da lissafe lissafe akan furucin rukayya mai kama da saukar aradu ko da yake acikin rashin haiyacin da yake bazai iya banbance menene da ba menene bai da tabbacin cikin wani hali yake 'wai ciki take dauke dashi na wata biyu' yaji zuciyarsa na maimai tawa cikin sauri sauri cikin nuna shanye razanarda yashiga ya dubeta

  "shi dakta bello din yasanar da ke haka...kodai kuskure yayi"

  wani irin kallo rukayya tashiga yi masa narashin matsayin da zata aje kalamansa taimatukar mamankantuwa batayi niyar zantuwa ba amma cikin sakanni tayi jarabawar da ta bata amsar tace wani abu cikin rashin kuzari tace...

  +sabeer baka fahimci zance na bane?"

  girgiza kai yayi alamun a'a amma yana bukatar karin fashin baki

  "na dan canja tashe ne amma fahimtar dani kuma"

  zuciyarta tashiga wasi wasi akan maganarsa ta rasa masaukin aje ta zuciyar tashiga bugu kadan kadan taga alamun razana idanuwan sa a yarda ta karanceshi kamar ba ya Maraba lale da abinda take ganin na farinciki ne ga rayuka biyu koma fiye da haka cikin nuna rashin gajiya tace

  "nasan kajini sai dai matsayin da zaka aje ne yake kokarin gagarar ka karkayi kokarin nuna rashin jindadi dan allah naroke ka daga yanayin dana fuskanta maganata ta bugar maka zuciya ko Meye dalilin haka?" takare tare da Neman amsa ga tambayarta

  idanuwan da takafeshi dasune suka dan sanyashi cikin wani hali Wanda yakasa gayyato wani abin fada na azo agani yasan tabbas komai zai fito daga bakinsa adaidai wannan lokacin ba mai armashin dadi bane a hanzarce ya mike yakau da kai daga kallon tadan bayaso ta gayyace shi da wata magana Wanda yake da tabbacin baza ta samu amsar ba ciki sassarfa yafara kokarin barin wajan hakan da tagani yasanya ta sauri magantuwa

  "me kenan kake shirin yi ya muna magana zaka jirkitar da ita"..

  ko alfarmar kallo ba ta ci ba balle ta sa arai zata samu wata kalma daga bakinsa alamun kuma bazanyi  ba lokacin da ta lura har kara sauri yake a sassarfa baki ta saki tana mai duban iko daga Allah meke shirin faruwa ne da ita me sabeer ke nufi da halin ko in kula da ya nuna akan maganar shin rashin muhimmaci gareta agareshi ita dai a tata zuciyar zancen farinciki yasaka amma shi mijin nata ta so ace shima haka ne ta kasance gareshi amma sai akasi tabbas akwai alamar tambaya koma tace tambayoyi cike da kwanyarta zuciya sai faman hassafo mata abubuwa take haka tacigaba da zama cikin yanayi narashin jindadi azuci da fuska ba yarda tayi haka ta mike tanufi dakinta bawai dan tagama gasgata abinda zuciyarta ke sanar da ita bane kawai dai ta aje zancen ne kasar zuciyarta zuwa wani lokuta.

  ********* ********

  tunda sabeer ya fara kokarin turmushe mata fuska shikenan hankalinta yatashi abubuwa suka shiga riccabe mata lokaci guda ta rasa sukuni tashin hankali da yafi zauta kwanyarta shine rashin maganar sabeer ta rasa makama ta rasa meye dalilin hakan da can tadauka laifine kankani lokaci zaizo ya wuce amma mai makon haka sai ta fuskanci abin na musamman ne akwai dalili sai kuma ta rasa dalilin abinda yakara sanya rashin zaman kalau kenan haka tayi ta zarya domin Neman ba'asi amma yanayin da yake kunnan uwar shegu da ita yakara narkarda zuciyarta

  "in kana yiwa Allah sabeer ka ce ci rayuwata wallahi kokarin salwantarda ita kake"

  ta fadi a wani talatin dare ta doshi dakinsa saboda barcin da yayi mata kaura abin mamaki zaune ta taddashi shima da alamun yana cikin tashin hankali kenan dai duk gidan hankula a tashe suke. bai dubeta ba kuma bai da niyar hakan tai ajiyar numfashi mai karfi cikin raunin murya

  "na roke da kayi ma rayuwa ta adalci bazan iya jure hakan da kake yi Mani ba na rantse maka da allah"

  nan ma bai dubeta ba sai ma kara hade gira da yayi ya kau dakai

  girgixa kai tashigayi kamar wata kadangaruwa cikin yanayi na laushin murya ta sake cewa"wani bakon lamari naga yana shirin ziyartar cikin duniyarmu yake kokarin kuma ta yar mana da hankali cikin rayuka ban San dalili menene yake faruwa ba sabeer ban saba ganin haka ba kuma bana fatan ganin haka a rayuwa narantse maka da Allah"

  tashiga shashsheka tana kokarin zubda hawaye amma hakan bai sa ya dubeta ba sai  kokarin mi kewa yake da lamun ya fara gajiya da iface  iface ta kuma bashi da niyyar tanka mata in har kuwa maganarsa take bukata aiko kunnuwanta baza suji ba koma zasu ji to maras armashi da dadi ne.

  da sauri ta mike lokacin da ta lura kokarin bar mata dakin yake gabansa ta tsaya ta kallon sa  na nuna rashin fahimta.

  "wai shin me kake nufi ya fa kama ta Kasan a ina kake kuma tare da wa kake haba Malam wani irin Abu ne wannan Wanda kake kokarin tsiro dashi Wanda ban sanka dashi ko wani sabon hali ne aka ziyarce ka dashi na rashin sakin fuska da gumtse baki.

  maganganunta sun dan tabashi tabbas bata ma da kunya ta dubi tsabar idanuwansa ta dinga sakin kalamai ba ma tasan abinda tayi bakenan bazai  fada ba ita da kanta zata san menene tayi..

  "karka tsaurara fushin ka akan Wanda kake fushi dashi bai san laifin sa ba"

  dubanta yayi a wulakance

  "bana muradin jin maganganunki agareni dan girman Allah ina bukatar shiru"

  ya fadin haka yafice ya barta anan yashe tana kokarin saita kanta tabbas ta shiga uku mai yake shirin shigowa rayuwarta wani rikitaccen al'amari ne yake shirin yiwa rayuwarta k'awanya

  "ya ilahiiii"

  abinda ta furta kenan cikin rashin haiyaci da rikitar kwanya idanuwanta lokaci guda suka kada su kayi jajir zuciyarta ta fara harsaso mata abinda kwanyarta ke jarabawa akai tai matukar razana lokacin da tafara kamanta gaskiya akan zancen

  'ko dai abinda take dauke dashi ne Kodai sanar dashi datayi tana da juna biyu ne yasan yashi cikin wannan yanayi tabbas in kuwa haka ne da matsala tashiga sintiri tsakar daki tashiga lissafe lissafe ita da kwanyar ta zuciyarta na taimakawa amma komai bata gani ba Wanda za ta iya ce wa zaiyi armashi kan zancen har yataimaka mata ko dayake bai kamata ace tasanya zuciyarta damuwar da zata addabeta a  tun yanzu ba aje ko ina ba amma ba ma wannan yaushe hankali zai natsuwa ko kwanya da zuciya su huta duk haka ba ta taso  ba ya kamata ta fuskanci alkibla domin samun abinyi. zuciyarta ta sanar da ita ta aje zancen gefe ta binneshi izuwa wani kankani lokaci taga yar da wannan rigimar da ke shirin tunkaro ta yanzu.

  hakan dai ta bar dakin cike da kila wa kala akan lamarim.

  ko da ta isa falo kwance ta taddashi yayi ruf da ciki alamun shima akwai al'amura dasuke kokarin gurgunta tunanin sa gefe ta kauda kai ta ba banza ajiyarsa dan wallahi tafara zarginsa akan kokarin aikata wani mugun abun watsar dashi tayi tare da jan guntun tsaki ta wuce dakin ta.+


  Story continues below

  wannan dare dai haka suka raya cikin rashin tabbatar jindadi da kwanciyar hankali mai armashi.

  washegari karfe shida da rabi ta bar gidan saboda ba ma taso suyi gamayyar kallo dashi dan bata mukatar cewarsa kamar yarda shima ba ya bukata.

  a kowace safiya yana rigata fita wajan aiki wani lokacin ma shi ke tada ita da kar ta makara amma yau sai ga akasi ko da tafito falo anan tasameshi yashe yana barci da alamun bai rintsa ba daran jiya haka ta kare masa kallo ta rabashi ta wuce.


  abinda bata Sani ba yana ankare da ita saboda barcin da ya ribace shi ba sosai ya lula ka dashi ba ta ficewa daga falon ya mike zaune yashiga duban hanyar fitarta zuciyarsa na ta wassafo masa wasu lamura iri daban daban Wanda yake ganin rashin tabbatuwarsu anashi harsashen bai shirya tara komatsai agidan saba yana bukatar lokaci sabida sai yashirya koma ya shiryar to sai anbi tsarere tsaranshi...

  bankado kofar da akayi shiyasa shi jirkice zancen sa yashiga duba rukayya ce tashigo a hanzarce da alamun tayi mantuwar wani Abu amma dalilin ganinsa da tayi zaune yasanya gurguntar da saurin da take tashiga dubansa kamarmai shirin harsaso wani abu tana faman yatsine fuska sai da tayi masa kallon tas San ta nufi dakin ta  tana isa tsakar falon tadaskare dalilin jin furucinsa mai kama da  saukar a rudu yayi matukar gigita tata har kayan cikinta sai da taji suna harigido.

  "kin San ban shirya tarbar ko matsan 'ya'ya ba yanzu" ya fadi ne cikin isa da gadara iyakar gaskiyarsa

  jin zantukan tayi kamar wani mutum ne Wanda bakinsa da harsansa suka fara zautuwa shine ke fadin haka badan wai tasan irin azancin sabeer ba zata iya karyata kunnuwanta abinda suka jiye mata amma duk da hakan ba wai ta gasgata maganganun ba a,a lissafe lissafe take domin gano gaskiyar abin

  cikin hargitsin kwanya da zuciya tadubi inda yake girke

  "shin su wanene komatsan da kake fadin baka shirya mara ba da su ba"

  ta fadi cikin shanye farga da ta tunkaro ta tashiga dubansa kamar maikokarin gano shin shine zaune ko kuma wani daban ne amma abinda idanuwanta ke hasko mata shine din dai mijinta sabeer.

  kallan kallo suka Shiga yiwa junansu sun rasa gane madosa

  "ki saurare ni dakyau kiji abinda zance miki...ko dayake bari inyi miki wata tambaya shin yau adadin kwanakinmu nawa da zarga igiya atsakaninmu?" In akwai abin da take bakin cikin sa a duniyar nan wannan da yasa zuciyar zugi to tabbas furucin sabeer ne nan da nan ta mitsintsike idanuwan ta suka kankance alamun takaici da tarin bakincikin sabeer suka dire duniyar ta

  "ina zan Sani ba dakai limamin ya zarga ba kana wajan nikuwa ina cikin gida a tsare dan haka baza kayi min wannan tambayar ba dan bani da amsar baka"

  duk sukayi shiru ita rukayya tayi shiru ne dan taji me zai ce da ita a matsayin mai da martani.

  shikuwa maganganuntane suke yi masa yawo a kwanya yashiga shirya abin da zai ce mata in ma bata gane manufarsa ba to tagane dan shi bashi da muradin Tara komtsai tun yanzu bai gama shan sharafin sa ba.

  ya nisa San yashiga dubanta yanayin da yaga tana kallonsa yayi matukar buga masa zuciya dan alamun komai ta famjama famjam yagani yayi saurin kawar da wannan zance da cewa " au Ashe baki Sani ba ai banyi zaton haka ba na dauka zaki iya kai yade iya adadin zaman ki anan gidan"..

  rai bace ta dubeshin dan wallahi ta gama kulewa "kaga su ma ban Sani ba nafa gaji da wannan rainin hankalin naka Malam in zaka fito fili kayi magana kafito bawai kai ta shata layi ba ina da abin yi"

  ba ta jira tankawan sa ba tai saurin fadawa dakin ta mintina kadan ta fito nan ma taba banza ajiyarsa tayi ficewar ta har da bar masa tukuncin tsaki a zafafe ta isa izuwa motar ta ta balle murfin ta fada taja tayi ficewar ta bayan mai gadi ya wargamemata get yana mai cewa adawo lfy amma bata bi ta kasan ba yadaici albarkacin daga hannu.


  gudu take kan titi kamar wacce zata tashi sama fuskarta a turmushi ta dauki hanyar gidan su bunayya mai makon wajan aikinta AKTH.

  zuciyarta sai faman zugi take maganganun sabeer sukayiwa kwanyarta kawanya jin su take kamar saukar ruwan zafi ta rasa dalilin da yasa sabeer ke kokarin jirkice farincikin duniyarta ya mai da gurbin da na akasin haka shakka babu ta fara zargin sabeer wani Sabin ta'addaccin yake kokarin tunkaranta da shi Wanda zai wargaza zaman sumul kalau dasu keyi har yau she akayi. Har yaushe za'a kare Sam haka bazai yuwu ba ya kamata ace ya fuskanci alkibla tun wuri ta na ayyanawa a zuiciyarta kodai sabeer wani Abu makamancin tada gajimare ya fara ne dan yarda suka kasance jiya da yau duk ba haka suka kasance cikin watanni biyu ba acikin inuwa daya.

  haka ta cigaba da zance da zuci ita kadai har Allah yakai ta gidan bunayya.

  hon tashiga yi ba kakkautawa hankan yasa mai gadin gidan hanzarin lekowa ganin rukayya ya sanya shi saurin kokarin budewa da yake yasanta yana ida budewa ta cin na hancin motar ta ciki gidan gaf da mai gadi ta dan jinkirta tana mai dubansa yanayi na girmama dan a haihuwa yayi 'ya da ita.

  " ko uwargijiyar taka ta na nan" ta fadi bayan ta yi masa sannu da safiya.

  ya shiga kada kai yana mai cewa

  "eh ta na ciki ina ga har da Alhaji duk ba su fice wajan aiki ba"

  ta gyada kai tare da dan yamutse fuska bata so ace ta tadda mijin bunayya a gidan dan zai iya kawo mata tsaiko cikin abin da tazo yi ga bunayya da jarabar likewa miji ko ka je a matsayin kana bako bata rabuwa da shi in har yana gida hankalinta rabi na wajan miji kwata na wajan bako  wai ita mai miji kayi magana tace ita bata so taga mijinta na zaman kadaici alhalin Ku tana waje Sam haka bai dace ba kula da miji na daban ne koda dai bako shima ana karramashi shima.

  rukayya ta mai da duban ta ga mai gadi. "shi yau ba zai je aiki bane?"

  kallon ta yashiga yi yama rasa amsar da zai mata wacce zatayi daidai da tambayar da yaga ta kafeshi da ido kawai sai yace "hajiya ni ina zan Sani wajan zama na daban nashi da ban kuma bashi ga zan yi na tambayr ba"

  yard a ta lura kamar bai ji dadin tambayar da tayi masa ba yasanya ta gyada kai ta karasa tayi parking sannan ta fito hannunta rike da jaka mayafi a kafada an cukwaikuyeshi waje daya

  ta doshi cikin gidan kofar babban falon gidan ta yada zango ta shiga kwankwasa wa ajere har uku sannan ta tsagaita. shiru taji kamar ba a da niyar budewa har tayi niyar sake kwankwasawa sai taji karar alamun za a bude.bunayya ta wanzu bayan an bude kofar baki tasaki tana kallon rukayya cike da mamakin ganin ta cikin wannan safiyar abin da bata ta ba ganin tayi ba.

  yanayin fuskartar na bayyar da alamun damuwa daban tayi kamar mai shirin fuskan tar wani abu.


  "kece da wannan uwar safiyar sai kace wacce zata bar gari dafatan dai lafiya?"

  ba ta tanka mata ba illah ido data zuba mata hakan da bunayya tagani ta aiyana a ranta banza bata kai zomo kasuwa akwai abin da ke faruwa

  tq nisa sannan tasake duban ta

  "kin yi shiru ko dayake shigo daga ciki dan naga alamar in har na barki kika kara sakanni yanzu zan ganki a yashe" ta fadi cikin zolaya dan dai taga rukayya ta sauya fuska amma ko alama ba ta da niyar haka din illa dosar kofar da tayi hakan da bunayya tagani sai tq matsa mata domin wuce wa ciki.


  tana gaba tana biye da ita tana mai kokarin karantar wani Abu har suka is a tsakiyar falon rukayya ta samun guri ta zauna ita ma bunayya hannun kujerar da rukayya take zaune ta dosa na kugunta tana mai saken duban rukayya wacce da alamun bata da niyar magana kokuma ta rasa abin ce wa ne oho.


  ajiyar numfashi kawai take tsawon mintina kamar biyu sukayi ba Wanda ya tsinka bunayya ta kau da shirun da cewa "kin shigo gida kin sami waje kin kame me haka ke nufi?"

  nan ma bata tsinka ba ta sake cewa

  "wai shin me ke faruwane me ke damun ki ko sai kin gama tsinka min zuciya sannan zaki magantu nifa tsiya ta dake in har Abu na daminki sai kin gama yiwa mutun walagigi da hankali sannan zaki sanar dashi"


  rukayya ta nisa cikin sanyi murya tace "matsala nashirin ballowa cikin rayuwata"

  bunayya tadubeta cikin rashin fahimta da inda zancen nata yasanya gaba.

  "ina jinki menene matsalar"

  ta fadi batare da tasan wai kalaman nata zasuyi wani tasiri ba

  "sabeer na shirin rugurguzamin farincikin duniyata"

  nan ma dai bata fahimta ba illah kallo da tabita dashi tana gyada kai

  "ina jinki muje zuwa"

  bunayya ta fadi dan it a Sam takasa gane yarda zata fuskanci al'amarin


  tayi shiru kamar wacce ke nazartar wani Abu da take sauraro hakan da bunayyya tagani ita ma tashiga lissafe lissafe da nazartar rukayya..

  ta ja hanci kamar mai yin mura.

  "na rasa ta ina ma zan sanar da ke wannan ta'addancin da ake kokarin yi min"

  gyda kai tayi batare cewar komai ba

  hakan da rukayya tagani ta samu damar sake tsinkawa"

  "bunayya ina da ciki Allah ya albarkace ni dashii..."

  ta irin zabura bunayya tayi ta batsa gefe kamar wacce taga wuni mugun abu ajikin rukayyya cikin alamun mamaki dashi ga razana tace


  "bangane ba naji kina kiran ci shin wani irin ciki na cin abinci kowan da nasani ana haihuwa?"

  dubanta yayi cikin mamaki it a ma.

  "naga kin zabura meke faruwa cewa nayi ina da ciki na haihu in haifi da a matsayin nawa Wanda Allah ya bani cikin da zai sa na zama uwa mai reno kin fahimta yanzu kin gane abin da nake nufi"

  takare she cikin daga murya da zazzaro ido kamar mai shirin rufar wa bunayya

  tai matukar shiga mamaki tana duban rukayya jin batunta take kamar mafarki anan inda take tsaye ta fara kokarin tsinkawa..

  "kina nufin har kin mallaki ciki"

  ta gyada mata kai yanayi na tabbatuwar gaskiya

  mijin bunayya ya fito hannunsa rike da jaka dauke da kwanfuta hakan ya hana bunayya zantuwa da Sauri tayi wajansa cikin sanyin murya tace

  "haba beby ba dai harka fito ba mai makon kajira ni kaga fa wacce da zo ta rike ni"

  yanayin da tayi maganar a shagwabe

  duban ta yayi fuskarsa na bayyar da fara'a

  "ba komai kin ji beby na jeki wajan mutuniyar taki tunda ma da naji shiru nasan dai bakon naki babba ne "

  ya juya izuwa wajan da rukayya ke zaune kallon ta sosai yayi yace

  "amarya ba dai har kin ballo kin baro angon ba"


  murmushi tayi tare da kau dakai sannan tace

  "antashi lafiya"

  yayi murmushi tare da cewa "kalau"

  ba tasake duban inda suke ba tashiga nazarin abubuwa daban daban yarda taga bunayya da mijinta sai suka burgeta azuci matuka sai taji dama ace hakan zai tabbatu ita da mijin nata sai bata ganin haka zai wanzu agaresu..


  bunayya

  Bunayya ta zuba mata ido ba tare Da tace komai ba


  rukayya ta dubeta tqce

  "dama yana ciki ne ai ban Sani ba da ban shigo ba"

  ta nuna ba tasan yana ciki harara rukayya tayi ma

  "to ko kin San yana ciki hanaki zai yi kishi go...kinga mu bar wannan zancen "


  rukayya ta nisa race

  "ina tunanin sabeer bai shirya haihu dani".

  "ba zancen baishirya haihu dake ba ai duk Wanda kikaga ba yason matarsa ta haihu dashi to tabbas kila ba ya son ta kenan kin ga ai bazaki zargi sabeer da hakan ba tundashi yana sonki akwai dai dalilin yin haka nima anawa ganin bai kamata ace cikin kankalin lokaci irin wannan kin yi ciki ba har yau she akayi auren ko fa amarcin Baku gama ci ba amma ace har ciki ya samu wajan zama haba kema kiyi tunani ma rukayyya ya kamata ace kin dan dau lokaci kamar watanni haka"

  duban ta tashiga yi tana mai nazarin zantukanta shin ita ta nagoyen baya kenan to dan me akayi auren badan atara zuria ba kuma ba ma wannan ai cikin ba ita zata makawa kan taba  dan haka ita bataga abin ta da hankali ba ai ba awaje tayo ba balle ace dan gaba da fatiha neta nisa sannan tace

  "ke ma haka zaki ce mani banyi zato ba ko tsammani haba bunayya abin da Allah yake badawa baidace ace kina dankwafar dashi ciki bani nake bashi Allah ya azurtani da shi bani da iko ko wata da bara in har Allah ya tabbatar da dashi ba yarda zanyi"

  dubanta bunayya tayi tace

  "nidai ba haka nake nufi ba bacewa nayi karkiyi ciki ba"+


  "hmm haba bunayya ke fa fmda kanki kikace lokacin daukar ciki na bayyi ba kinga kenan tabbatuwar zancenki ya bayya kina goyan bayan saberr kenan to shikenam ba matsala yakamata kiyi tunani komai da kike gani ga bawa daga Allah ne"

  Rana fadin haka bata saurari zancen bunayya ba ta mike danufin wuce dan bata ga amfanin zuwanta ba Sam saii bacin rai da tashi ga hakan yasa bunayya ce mata


  "ina kuma zaki muna cikin magana"

  "Baki dauki zancen NAwa da wani mahimmaci ba shiyasa na barshi kawai naje nayi tunani dakai na na fiddo mafita"

  da sauri ta fice. kiran ta take tana nanatawa amma ina!ko takanta bata bi bata tana zuwa tashige motar ta ta fice daga cikin gidan ran ajagule.


  bata ga amfanin zuwan ta gidan bunayya ba da tasan haka ce zata kasance da bata nufo gidan da ba atunanin ta in tazo wajanta zata samu mafita ashe ba haka bane ita ta'addacin zata nuna mata tunanin da tayi aganinta ai ciwon 'ya mace na 'ya mace ce mma sai bunayya ta nuna mata akasin haka.


  tunda ta hau titi ba inda ta nufa sai AKTH saboda baza ta iya kowa gida gwanda taje can ko ta samu natsuwa ta sa marwa kan ta mafita in har da hali ita ta Mara yarda zata fuskanci al'amarin sabeer yana shirin jirkice ta ta baibai ta rasa madafa.

  ko da ta isa asibitin ba Inda ta yada zango sai masaukin ta ita kadai dan bata son kowa ya dameta dan adaidai wannan lokacin jinta take cikin wani hali narashin dadi da kwanciyar hankali

  haka ta wuni cikin asibiti ba tare da kowa ya kula ta naciki lokacin tashi da yayi haka ta kwashi tarkacen ta ta bar asibintin jiki asake.

  tashiga motar baysn ta baro cikin asibiti nan ta cilla motar bisa titi kallo daya zakai yi mata kasan ta na fuskartan rashin dadi a rai tokin kanshi da takeyi a wannan lokacin ba tabbancin zata kai gida kan lokaci dan tafiya take kamar mai kokarin yin parking sannu sannh haka take.

  ta nacikin wannan yanayi har ta isa gida bayan tashigar da motar ta ta fara kokarin fitowa ta fiddo da kafarta daya tana kokarin fiddo da dayar da ji kamar an zarge mata ita Sam ta kasa daga ta nan tashiga duban kafar tana shafata ko zata ji wani alamun na ciwo amma ba taji komai kafar a zahirince kallon kalau zakayi nata nan tashi ga kokarin fiddo da Abu kamar wasa kafar taki daguwa nan ta fara ambaton sunnan Allah hankalin ta yatashi mai ke shirin faruwa da ita ne wani irin karfin zuciya ta ji yazo mata da karfi ta fara jan karfar sai faman nishi take tana rokon Allah yasa kalau Allah yasa ba wani abin bane yasami karfar tata wani rin wawan fizga tayi wa karfar gabadaya tayo waje tazube a kasa.

  cikin yanayi na halin jijantawa

  "akwai matsala Alhaji hajiya bata da lfy jinine fa ke kwaranya ajikinta

  sabeer ya shiga dubansa cikin nuna halin ban fahimce zancen mai gadin ba


  "me kake nufi naji ka ambaci jini a jikin nata jini ke zuba ?

  ya tambaya cikin yanayi na tsareshi da ido

  gyada masa kai yayi alamun tambatuwar hakan

  yanayin da sabeer cikin sa yanuna alamun ya gamsu da zancen nasa cikin yanayi na bayyanar da tsoro da fargaba a fuskarsa nufi inda take yashe cikin yanayi na ficewa daga haiyaci


  "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"

  abin da ya ambata kenan lokacin da ya isa gareta yayi matukar firgita da razana cikin yanayi na karfin zuciya da durkushe gabanta ya tallabo kanta cikin wata irin murya mai cike da tashin hankali yashi ga ambaton sunan ta ya mai duban jinin da ke zuba a jikin ta kamar yankar damba akayi yanayin da ya ga in har banyi azaman yi taimako gareta ba wankin huta zai kai shi tsakar dare ciki gware murya da kira maigadi da zama ya iso shima cikin yanayi na tsoro ba tare da ya dubeshi ba yace

  "maza bude mun waccen motar da tashi go da ita.."

  bai kai ga karasaw mai gadi har ya isa ya wanga me motar wajan mai zaman banza sabeer ya kinkimi rukayya cikin rashin haiyaci ya watsata cikin motar yashiga wajan zaman direba da azama ya figi motar yafice daga cikin gidan bayan maigadi ya gware masa gate


  Story continues below

  tun da ya tsilla motar bi sa titi ya ke sharara gudu kamar zai tashi sama tuki kawai yake cikin yanayin rashin haiyaci lokaci lokaci yana mai duban rukayya da ke numfashi sama sama.


  asibitin Malam aminu Kano ya dosa cikin kankanin lokaci yayi masa tsinke parking kawai yayi ya balle murfin motar yafito yashiga dube dube can ya hango wata nas nesa dashi ta na kokarin shiga wani bangare daga cikin asibintin da azama ya watsamata kira yanayin da yayi kiran ya jawo hankalin wasu kadan daga cikin mutanan da ke kai komo cikin harabar asibiti ita kanta nas din kiran jinsa tayi har tsakarka


  sai da ta Kare masa kallo yanayin

  da ta fuskanta ba tatatre da nutsuwa da alamun akwai abin da ke tare dashi Wanda yayi sanadiyar shiga cikin rudu.


  cikin sauri ta ido wajansa nesa dashi kadan ta tsaya tashiga dubansa domin ta tabbatar da abin da take zantawa azuciyarta

  kallon da yaga ta kafeshi dashi kuma da alamun bata da niyar yi masa magana ya sanya shi saurin tsinkawa


  "please I need your help mata ta ce ta ke cikin wani hali"

  gyada kai tashiga yayi bayan tayi amanna da batun sa a hanzarce tace

  "me ke da munta kuma ta ina"?

  ba tare da ya iya tsinka mata da saurin yayi mata nuni da motarsa hakan yasa ta nufi motar da azama ido waje cikin matsananciyar razana tace

  "sister RUKAYYA NASEER KARAYE"

  ba ta tsaya sauraron sabeer tai cikin asibiti da gudu a firgice


  ba ta dau wasu tsayin lokaci ba sai gata ta fito tare da wasu abokan aikin nata cikin azama sabeer ya balle murfin motar su fiddo ta da sauri suka doshi cikin asibitin da ita sabeer na biye dasu hankali tashe.


  wani daki namu samman suka nufa da ita bayan sun shigar da ita nas din ta nufi ofishin likitar da sauri ta sanar shi a hanzarce yafito yana mai tambayar ta mai yasami rukayyar cikin rashin haiyaci tace

  "nima dai ban sani ba amma ga duk kan alamun akwai tambatuwar bari ne saboda yanayin da naga jini da zuba daga jikinta"

  gyada kai kawai yayi ya doshi dakin yana kokarin shiga suka ci karo da sabeer a hanzar ce sabeer ya damki hannun likita yana mai cewa

  "pleasea doctar mata ta...Dan allah ka taimaka min kar narasa ta ta na cikin hali mai matukar firgita min zuciyq bazan iya jure ganin ta cikin wannan halin ba"

  likita kawai ido ya bi sabeer dashi ssboda yanayin da yaga yashiga cikin firgici da alamun yana matukar kaunar matar tasa

  "bakomai allah zai daidai komai kuma zata samu lafiya"

  likita ya fadi tare da zare hannunsa daga na sabeer ya fada dakin tare da turo kofar.

  hakan da sabeer yagani yasan yashi jigina da kofar yana mai da numfashi a hankaki fatan shi kawai allah yasa ba wani Abu bane ya kasantu da rayuwa cikin minti na da basu gaza ashirin ba sabeer da ke yashe bakin kofar da aka aka shigar da rukayya sai faman zabga tunane tunane yake cikin duniyarsa.

  karar budar kofar da akayi ya fargar dashi da sauri ya dubi kofar likita yagani tsaye gumi ya tsattsafo masa bisa goshi da alamun tsawon lokacin da ya dauka acikine ya haifar da haka

  sabeer yayi wani irin nishi tare da duban likita

  "dafatan allah ya kawo ko manene da sauki"

  kai kawai likita ya daga masa amma yanayin da fuskarsa ke nuni akwai abin da yasan yashi rashin yalwatuwar fara'a

  "likita kai nake saurare ka ce wani Abu mana"

  sabeer yasa ke magantuwa yana mai rike da hannun likita ya mai jinjigawa sannu sannu


  likita yayi ajiyar zuciya karo na biyu tare da sharce gumin da ya tsattsafo masa sannan ya nisa

  "kayi hakuri sanadiyar zubar jinin da matarka tayi ya sanya cikin da take dauke dashi ya fice"


  wani irin duba sabeer yashiga yiwa likita kamar mai shirin gasgata abin da yake fada Dan ji yake kamar cikin mafarkinsa ya ke jin zantukan likita


  da gaske cikin jikin rukayya ya fice

  ya fadi cikin zuciyarsa cike da karsashi

  ajiyar zuciyayi yanayin fuskarsa ta sauya

  "kana nufin cikin jikin ta ya zube likita?"

  gyada masa kai yayi tare da ce masa "kayi hakuri"

  ya fadin haka ya rabashi ya wuce

  lokaci guda fuskar sabeer ta bayyanar da murmushi ma tsakaici ba alamun razana da firgici sun ziyarce fuskar sa a can ba ya

  da alamun yayi matukar jin dadi da kasantuwar wannan lamari har a zuciyarsa tsayin dakiku ya dauka tsaye a wajan ya gama shan sharafinsa sannan ya doshi cikin dakin da rukayya take yanayin da ya shiga dakin duk tausayin duniya ya kinkimo ya yafawa fuskarsa


  kwance ya tadda ta tare da sauran nas din suna kula da ita sunyi mata komai da ya dace har da gyaran jiki.

  da sallama ya isa har zuwa bakin gadon yana mai duban rukayya da ke kwance idanuwanta a rufe da alamun barci take ga ruwa na kwaranya izuwa jikinta da aka Sanya mata


  nas ta dubeshi cikin jajantawa

  fuskar ba faraa tace "yanayi matukar tausayawa sister allah ya bata wani mafiyi alheri gareta"cikiciki ya qmsa da ameen badan yaso ba ya karasa kusa da rukayyya ya zauna bakin gadon yana madubanta fusakar sa na bayyanar da tausayi amma ba har cikin rai da zuci ba sun dsuki tsawan lokaci a haka sannan rukayya ta farka daga barci da ya sure ta bashi cikin yanayi na rashin dadin jiki tafara kokarin tashi tashiga duban su daya ban yan daya lokacu guda kwanyarta tafara zayyano mata abin da yqfaru da ita cikin ki dima ta dubi sabeer muryar ta a dusashe tace ya zubeko cikina ya zubenasan haka zata faru dama ta rushe dakuka mai tsuma zuciya cikin sauri tafara kokarin sauka daga gadon hakan da sabeer yagani yasashi saurin riketa ina kuma zaki je ke da baki da lfy ...wani kallo ta watso masa kaga mallam sake ni bana bukatar wani taimako daga gateka rabu dani kawai

  jikin sabeer yayi matukar sanyi musamman da ya ji furucin Da rukayya ta tareshi da shi alamu yanuna tana zargin shi da ta'addanci kenan akan zubewar cikin jikin ta tabbas haka take nufi ajiyar zuciya yayi yasake dubanta akaro na biyu ta kau da kai daga Barin kallon sa a sanyaye ya saki hannun nata ba Dan yaso ba.

  ya juya ya dubi nas ita mashi take kallo kallo mai cike da tuhume tuhume fuskarta a ya mutse take dubansa ba tare da tace dashi komai ba amma irin kallon da take masa lokaci guda yasha jinin jikinsa da sauri ya kau da kansa daga barin kallon ta.

  rukayya da ke tsaye ta fara kokarin zama bakin gado hannunta daya dafe da kai da alamun yana sara mata hakan da sabeer ya lura dashi yafara kokarin taimaka mata tazauna da sauri ta daga masa hannu alamun bata bukata bai jidadin haka ba musamman da yalura da irin kallon da nas ke masa na tuhuma.

  tsawon minti suka dauka a haka ba Wanda ya tsinka kuma ba wanda ke kokarin tsinkawar.

  nas ce tayi kokarin tashi don zuwa kiran likita fuskarta akan sabeer Dan tabbas tana zarginsa da aikata bashi da makami a cikin sister

  haka ta fice da sauri Dan. tsoro take karkuma ya aikata wani Abu

  a tare suka shigo da likiti suka gaisa da sabeer yana tambayarsa yaya mai ciki ya amsa masa nai yasake duba bayan ya gama yace da sabeer izuwa yan a wannan za a basu sallama tunda komai ya zama normal

  haka kuwa akayi basu fi awa biyu aka sallamesu abin da ya daurewa sabeer kai yarda rukayya ta ce baza ta bishi yakai ta gida ba kawai yayi ta fiyarsa ta taho hakan bakaramin daure masa kai yayi ba yashiga gyada kai kamar mai shirin fara zubar hawaye ganin abin yake kamar almara wai rukayya ce ke yi masa haka gaban mutane take kware masa baya har an fara zarginsa da aikata ta addanci.

  juyin duniya sabeer yayi amma rukayya ta rantse bazata hau motar sa ba kawai ya wuce in kuma ya matsa mata sai ta wuce gidansu hakan da yaji tace ya sanya ya ja motarshi ba dan yaso ba yafice daga cikin asibitin yana waigenta tare da nas. zuciyarsa da kwanyarsa ga bakidaya sun gama shiga rudu yarasa mai yadace ma yayi mai rukayya take nufi dashi mai take tsammanin ya aikata tana zarginsa kenan da sanya hannun wajan ta addancin zubda ciki in kuwa haka ne batayi masa adalci ba ba yi masa zato mai kyau ba yakamata tasan ZATO ZUNUBI ko da yakasance gaskiya ko da dai shi Kansa yasan bashi da hannun cikin fashi da makamin.


  lokacin da rukayya taga sabeer yawuce tayi ajiyar numfashi ta dubi nas "sister kin ga tun da ya wuce taimaka ki kaini gida" ta karashe cikin shanyewar haushi.

  nas tayi murmushi mai kama da yake daban baza akirashi da murmushinfarinciki ba "wai shin meke faruwa be?"

  nas ta watso wa rukayya tambaya a bazata Dan batayi zaton wannan tambayar ba amma in har tayi la'akari da halin da suka shiga da sabeer dole ko wanene Wanda bai San kan dawar garin ba tambayoyi su dalsu a ransa cikin jirkitar da zancen tace "uhmm taimaka Dan Allah ki kai ni jiki ba dadi wallahi"

  nas ta dubeta domin fuskantar wani Abu amma bata ga komai ba cikin bin umarnin rukayya ta fara tafiya batare da tace wani abuba.

  a haka har suka isa motar nas taja su ka bar asibitin haka suka cigaba da tafiya ba Wanda yacewa wani Abu har suka isa gida nas tayi horn maigadi ya wangale get suka fada cikin gidan gefe guda sukayi parking su fito a daidai lokacin mai gadi ya iso ya zube yanayi wa rukayya sannun da jiki ta amsa tanayi masa godiya suka doshi cikin falon rukayya ta jabirki ta tsaya nas ta dubeta. cikin yanayi na bukatar Karin haske akan Jan burkin da tayi "menene " ta tambayeta rukayya bata kalleta kuma bata da niyar cewa wani abin na azo a gani parking  motoci tayi tana karewa wajankallo azuciyarta ta aiyana inda sabeer yayi bayan rabuwansu daga asibiti Dan bata ga alamun yashigo gidan ba cikin nuna ci da zuci tace"mushiga ciki ko"batare da nas tace mata komai ba tayi kokarin bude kofar suka shiga a tare rukayya ta zube bisa kujera zuciyar sai walagigi take kan wannan lamarin wanda take kallon kamar a mafarki bazata maradadi da armashi.

  muryar nas ce takatseta "rukayya na kasa fahimtar komai?" bata dubeta ba illah cewa da tayi"me kika gani har ya daure miki tunanin kwanyarki" tanisa sannan cikin bukatar jin wani Abu mai muhimmanci "menene silar barewar cikin jikin ki da alamun akwai wani aboye tsakaninki da mijinki Wanda ya danganci zubar cikin?"a wahale rukayya ta tashi daga shingidar da tayi tana mai maida numfashi "kiyi hakuri naja'atu bana da juriyar da zan iya sanar dake komai akan wannan lamarin kiyi hakuri" nas naja'atu bata so haka taso ace zargin da take ta kau dashi amma hakan ma ba faduwa ce akwai lokaci da zataji komai tanisa "shikenan Allah ya baki lafiya" tana fadin haka ta fara kokarin tashi don tafiya rukayya ta fara bin ta idanuwa batare da tace mata komai ba adaidai wannan lokacin sabeer ya fado cikin falon

  "uhmm takomashin barka da barewar ciki na da taya murna akayo mann"

  furucin da rukayya ta tari sabeer kenan dashi bayan tayi sallama da nas naja'atu ta wuce.

  gyada kai kawai yayi ba tare da yace mata komai ba ya dire tulun kayan dasuke hannun sa tsakar falon.

  kujerar nesa da ita ya zauna yayi shiru hakan da rukayya tagani yakara tunzura zuciyarta a hanzarce ta dubeshi "kaji na rantse tun wuri ka zo ka kwashe wannan tsummo karan naka in kuma ba haka ba..."

  bata kai ga karasa wa ya daga mata hannu a zafafe "ta'addacin da kike tun karoni dashi ya fara isa yakamata kiyi min rai ki bar zuciya da kwanya ta su samu natsuwa haba!!" yakarashe cikin daga murya

  dubansa tashiga yi kamar wacce ta shekara bata sanyashi a idanuwa ba ta mai gyada kai cikin shanye mamakin takacin sabeer bakin ta said mutsu mutsu yake da alamun tana son yin magana amma takaici ya cukuikuye mata Baki

  falon yayi tsin kamar ba rai a ciki haka suka shafe tsawon lokaci ba Wanda yayi kokarin tsinkawa hakan da rukayya tagani cikin cinye haushin da ya tunkarota ta fara kokarin shirya kalamai da zata furta

  ta nisa "ban taba zaton son da kakeyi mini na karya bane ban taba zaton kaunar da kake nuna Mani shafcin gizo bane sai a daidai wannan lokacin da muka kasance inuwa daya wallahi azim da nasan haka Zata kasance da banyi gigin hada igiyar aure da kai ba sabeer ban San kallon da kakeyi mini a matsayin kiyayya bane sai wannan lokaci tabbas zuciya da tasan haka kake da bata aminta dakai ba so banyi min adalci ba bai zaba min abokin rayuwa na gari ba SO DA RAININ.. "

  ba takai ga diga aya azsncen taba kuka yaci karfin ta tashiga rusashi kamar bazata ta daina ba kuka take mai cin rai da tsuma zuciyar mai saurare.

  baki da hanci sabeer ya saki yana ganin ikon Allah kiri kiri ana kokarin mai dashi Dan ta'adda mai salwantar da jariri abinda rukayya ke zarginsa dashi kenan wato shine silar barewar cikin ta....

  kukan da yaji Kansa ne ya dawo dashi haiyaci rukayya ce tsaye kanshi idanuwanta sun kada.. sun yi jajir sai huci kawai take kamar wacce damisa

  dubanta yashiga yi cikin rashin tsammanin abin da take kokarin aikatawa anya rukayya kanta bai samu matsala ba abin da yake ta aiyana azuciya da kwanyarsa kenan

  wawuyar ajiyar numfashi tayi cikin karsashi da nuna tsagwaron bacin rai ta fara magana

  ban yi zato a duniyata da rayuwa ta zan fuskanci kalubale azaman aure na dakai ba banyi zaton amincewar da yarda Dana dauka na baka zaka iya cutar dani ba ban taba zaton zakayi kokarin gurgurtar min da rayuwa ba na dauka yarda da aminci ya wanzu a tsakanin mu Ashe ba haka ba ne duk abin da nake ashe daukar sauna wawuya akeyi min Ashe banza BAGIDAJIYA kake kallona sabeer sai yau na kara tabbatar wa NAMIJI ba abin yarjewa bane sai yau na kara tabbar da NAMIJI ZUMA kafatanin rayuwar shi akwai tsagwaron son kai da son zuciya..."wani kululun Abu ya tokaremata makoshi takasa karasa zantukanta lokaci guda ta dauke wuta hawaye kawai ke safah da marwa a fuskarta masu tsananin zafi

  sabeer yayi matukar kaduwa da jin furucin rukayya bai taba zaton irin wannan azancin na rashin arziki zan iya fitowa daga bakinta ba ko daye zafin abin da yafaru da ita zai iya sanyawa ta aikata fiye da haka amma fa yayi matukar mamaki da zargin da takeyi masa meye nashi aciki da har zata kinkimo zargin duniya ta kakaba masa a dole shine sarkin laifi mai tarar aradu daka in kuwa tayi masa haka Sam batayi masa adalci ba a zamantakewarsu a matsayinsu na ma 'aurata...

  tunaninsa ne ya tsinke lokaci guda jin furucin da rukayya keyi.

  "yan zu mene ne abin yi tun da cikin ya salwanta kaga ai sai mukoma asibiti akarasa rufe vakin mahaifar kar nasake daukar wani cikin ko kar a dauki zunubi Dan baza a hada baki dani ai takashe rayuka ba" ta karshe cikin tsagwaron iyakar gaskiya duba da yanayin fuskarta da ta nuna Sam ba wani alamun shakka akan furucin ta

  motsa baki yashigayi alamun son tsinkawa yake amma mamaki da takaici sun hana bakinsa furta ko wani irin kalamin cikin nuna mazantaka yace. "Allah ya ganar dake bani da hannu cikin ta'addacin zubd cikin jikinki"

  abinda yace kenan ya tashi ya bar falon zuciyarsa cike da haushin abin da rukayya ta aikata masa

  tana ganin yafice ta bashi da harara da tukuicin tsaki hade da Jan kwa6a.+


  Story continues below

  *** **


  tun da abin cikin rukayya ya zube ta lankaya alhakin kan mijinta shikenan Sam su kadai na jituwa gaisuwa wannan ta fatar baki bata hadasu tun sabeer na kallon abin a matsayin haushi za ta huce har yagadai bata da niyar aikata haka cikin Neman SULHU ya tunkare domin su koma daidai amma ina ta nuna bata San zancen ba Dan haka yq rabu da ita Ib kuma Bahaka ba zata shayar dashi ruwan mamaki hakan da tafadi yasanya shi janye wa daga Barin zuwa wajanta yasan komsn Daren dadewa sai tagaji da fushe fushenta sun sulhunta amatsayin su na mata da miji

  satinta guda takoma bakin aikinta Dan Sam zaman gidan ya ishe musamman in sabeer na nan duk sai taji kamar akaya take zaune

  koma warta asibiti Sam bata ji dadinsa ba dalili kuwa shine

  nas naja'atu ta kafe da son jin abin da yafaru tsaninta da mijintq tunda har yanzu tana zargin sabeer ne silar zubewar cikin rukayya tambayar duniya tayi mata amma ta ki sanar da ita haka kullum suke kasancewa in har suka zo aiki sai tasan yarda tayi tasako maganar kozata samu abinda take amma abin yaci turu ssboda rukayya ta Riga tagane manufar naja'atu ta kance Dan Allah tayi hakuri ba za ta iya sanar da ita komai ba akan abin da yashafeta da mijinta da taga ba sarki sai Allah haka ta hakura ba Dan taso ba amma ta binne a ranta sai ta Sani ko ba yanzu ba.

  haka rayuwa tai tagara su rukayya da dadi ba dadi tun sabeeer na hakuri har ya kai bango ya sake Neman sulhu nan jiya i yau hakan da yagani ya tabbatar rain in hankali ne rukayya ke son yi masa kuma ba zai lamin ta ba yaushe rayuwa za ta yuwu a haka ace kuna mata da miji Dan kuskure yashiga tsakanin Ku shikenan kuma sai ki dauki gabar duniya ki daura wa miji Sam haka baxa ta yuwu ba gangaci ne da kuskure wai shin me ke nukurkusar duniyarka ne gabakidaya ka gama zabge wa me nene dalili?hajiyar sabeer ce ta cillo masa tambaya bayan ya kawo mata ziyara yanayin da ta ganshi ba yarda ta saba ba ta sanya ta tuhumar sa don jin dalilin sa yasa rayuwarsa ke walagigi.

  kansa akas yashi nazari yarda zai fuskar ce ta da amsar tambayar da tayi masa alal hakiki shi kanshi ya san ya sauya ga baki daya dalilin hankaki da a ka tayar masa ka hana shi kwanciya..

  tsinkawar D'a tayi ne yasake tsinke masa zaran tunanin nasa in da ta sake cillo masa wata TUHUMAR

  "wai shin an ya ba wani tashin hankali a cikin duniyarka na lura cikin yan kwanakin nan duk ka koma wani iri kamar Wanda lafiya ta gudu ta barshi"

  nan ma bai tanka ba kuma bai dago kai ya dubeta ba dsn bashi da sbin cewa jarabawar da yashirya domin samun. amsar da zai ba hajiyar tasa kwanyar tasa ta tsaya cak! taki tafiya cikin jarumtaka da nuna mazan ta ka yanisa cikin fizgo wani abin cewa

  "wallahi hajiya ba na jin dadi kuma narasa abin da ke damu na"

  yafadi kansa sunkuye Dan yasani tabbas in har ya dago ya dubeta Dan shirin da yayi duk zai tarwatse tsab.

  idanuwa tashiga zuba masa tana nazarin yanayinsa da halin da yake ciki lokaci guda yasha jinin jikinsa dalilin da yaji yasan shi take kallo cikin shanyewar damuwa yayi kokarin dago kansa ya dubeta ita ma shi take kallo murmushi yayi mai dauke da yake "hajiya wallahi bakomai kawai dai CANJIN RAYUWA kinsan komai na duniyar nan ba dadi bane gabadayansa..."

  idon da yaga tazube masa ko kyaftawa batayi shi yasanyashi cinye sauran azancin nasa yashiga sosa kai da murmushi yake ita ma murmushin tayi masa amma nata da ka kalla zaka gane akwai manufar yin sa

  shiru ya ratse cikin falon na wasu yan dakiki hakan da sabeer ya gani ya tabbata hajiya bata da abincewa cikin barin jiki ya mike yana gyara hular kansa.

  "uhmm hajiya bari na tafi naga mangaruba ta dan no kai bana so ta riske ni a hanya"

  ba tare da ta bukaci wani azancin ba tace"to shikenan a gaida mutan gidan " duban sa tayi cikin yanayi na tuhuma saboda yanayin da taga yafado mata cikin daki ba sallama bare kuma Neman izinin shigowa

  "kasan Allah bana son irin wannan...haba ai wannan shiga hakkin rai ne ha kawai Neman jawo mutane bugun zuciya kawai mutane na zaune ka fado musu daki kamar Wanda ka biyo" ta karashe cikin jan kwa6a da turmushe fuska ta shiga Jan tsaki can kasar makoshi da kun kuni kamar mai shirin tashi ta rufe shi da duka bai dubeta ba kuma bashi da karsashin tanka mata Dan lamarin nata ya fara shallake tunanin mai tunani zubewa yayi cikin kujera yana ajiyar numfashi kallo data zakai masa kayi masa kallo mai dauke da damuwa mai nukurkusar zuciya da rai "hajiyata ta ce na Gaida ne" yayi kokarin furta haka cikin nuna maganganunta basu cikarar nasa zuciya ba balle su haifar masa da wani CIWON RAI.bata amsa ba kuma da alamun bata da niyar amsawar sam hakan da yagani yasashi dubanta ganin yanayin fuskarta sai wani cin na khamsi take ta shan kamshi yasanshi murmuswa "hala kunnuwanki sun hadu da rashin jine?" yafadi shima fuskarsa a turmushe bata dubeshi ba haka zalika ba alamun zata tsinka me tagani me tagani can kuma sai ta kokarta cewa"hala ganina kayi a sahun marasa ji" ya gyada kai"gani nayi ina yi miki magana kin ba banza ajiya ta ko meye dalili"

  "ba dai gaisuwar hqjiya ba ce ai na karba hannu binbiyu ko ai shikenan"

  duban ta yashiga yi cikin alamun ta rainawa kanta hankali Dan bazai ce ta rai na masa ba "to ai banji amsawar taki bace shiyasa nayi tunani ko fitata da dawowata ki gamu da rashin magana shiyasa neyi kokarin Neman BA'ASI"

  shiru tayi Dan maganar ta fara isar ta bata bukatar dogon zan ce Mara kan gado Dan kafatanin maganar sabeer bata ji wannan da ayi jarabawa akan han ayi tunanin samun amsa ba ita fa zaman nan ma da yashigo yayi ji ranta take duk ya baci.

  kamar yashiga zuciyarta yayi sukuwa aci yasan abin da take nazari yayi murmushi "na takura miki ko bakya jin dadin zama na a nan ko" bata ce mata sa komai illa tsuke fuska. da turmushe ta da tayi hakan ta Sanya sabeer murmusawa "kin san Allah in har ki ka tsuke fuska har kyau kike karawa Dama ace fuskar taki zata tsaya a haka"ya fadi cikin zolaya da niman tura haushi

  wata harara uwar harara ta cillo masa mai cike da najin haushin abin da kake yi min "wai shin Dan Allah wani irin mutum ne kai kinkana wa Allah ka rabu Dani karabani da farinciki na ka sayo min bakin ciki Wanda zai hallaka min rayuwa amma duk haka bai ishe ka ba sai ka kara min da gyara da alamun so dai kake na bar duniya ta da rayuwartawa nakai wa lahira ziyara tun lokacin cinye rayuwa ta baiyi ba"

  ido waje yashiga dubanta maganganunta sunyi matukar tasiri wajan San yawa kwanyarsa tashin hankali musamman ganin da yayi tana kokarin bawa hawaye dama zuba a banza a wofi cikin rashin kuzarin zuci ya nisa "wai mai yasanya kike Neman salwantar mana da rayuwa be fisabilillah ya kamata kiyi abinda zai kawo farinciki rayuwar mu kisan komai yafaru da bawa daga Allah ne..." da sauri ta tsinke masa zaran zantukansa "kaga Malam ba cewa nayi kazo kasaki baki kana gayamin allah da annabi kaji ko takaicin duniya ne dai ka kinkimo ka dorawa rayuwa ta kuma na gode " sabeer yashiga duban rukayya cikin rashin haiyaci gabaki daya lamarin nata ya fara tunzurashi haba sai kace mai Wanda aljan sukayiwa tsinke aka

  mutsin tashin tayaji da Sauri ya dubeta batare da yinmagana ba Dan yasan ko yayi ba zai ji mai armashin dadi a matsayin amsa ba

  tana gyara da zaman dankwalin kanta wayarta ta fara kuwwa Neman agaji da sauri ta dubi wayar sunan da tagani yasanya murmusawa ba tare da ta shirya yin sa ba da sauri ta amsa kiran takai kunne cikin hanzarin sonyin magana taji antareta cikin tashin hankali "na Shiga uku! na shiga uku!! na shiga uku!!!..." sai kuma a ka zarce da kuka mai cike da tashin hankali rukayya dake tsaye rike da waya gabaki daya taji wata katagat tashin hankaki ta zubo mata ciikin makerketa"innalilahi...me ke faruwa ne me yasa meki"cikin shanyewar kuka daga can bangaren "kin san Allah rukayya rayuwa gaf take da karewa....kai ta ma kare..yo mai yayi saura a duniya ta daukan rai ne kawai yayi saura yanzu...da alamun cikin sakanni zaki ji ance an zuke jinin jiki na bayan na rayuka da aka hallaka ba ta re da INA da masanaiya tabbas NAYI NADAMA kasantuwa cikin wannan hali da nake ciki nayi nadamar kasancewa matar wannan azzalumin macuci maci amana ma ha'inci ma rashin imani da tausayi tabbas sai yau na kara tabbatarwa a duniya akwai mai MATCCIYAR ZUCIYA wacce bata amfanarsa dakomai sai zalunci da kashewa mutum rayuwa da ina da hali wallahi tunkafin na bar duniyar nan sai na hallakashi nasa wuta da fetir na ko neshi..."ihun kukan da tasaki yakara razana rukayya da sauri ta dauke wayar daga kunnen ta gabadaya ta gama firgicewa jikin ta rawa kawai yake gumi yashiga zubo mata lokaci guda ta zare Dan kwalin kanta tashiga fifita dashi ta sake dubana wayar hannunta har zuwa lokacin a kunne take ba a katse kiran ba jiki a sanyaye ta mai da wayar kunnena ta sannan ta nisa"kin ta yar min da hankali kin tarwatsamin tunanin Dan Girman Allah ki natsu ki sanar dani abin da ke faruwa "

  cikin shasshekar kuka mai cike da barazanar tafiya da rai yace"duk abin da kike ki zo gida na maza tun kafin a zaremin rai da karfi da yaji...ki gangauta Dan Allah rukayya INA bukatar ganinki adaidai wannan lokacin da rayuwa take gaf da karewa" da sauri rukayya ta tare Dan sambatun buhayya ma ya fara isarta "ya isa haka gani nan zuwa yanzu ki dai na ambatar rayuwarki ta zo karshe..."cikin ihu buhayya tace"lokaci fa tafiya yake rai kokarin fita yake"da sauri rukayya ta kashe wayar a firgice duk hankalin ta ya gamatashi tabbas akwai abin da ke faruwa marar dadi ga buhayya cikin a zama ta fara kokarin barin falon duk abin da ke faruwa akan idon sabeer amma bai neme jin komai ba har ta fice daga falon ta fada dakinta minti kadan ta fito hannun ta rike da mayafi da mukullin motarta sai wayar datake dubawa duk sakan har ta iso kusa da shi tana kokarin Barin cikin falon sabeer ya dakatar da ita cikin magantuwa"yakamata ki nutsu ki sawa hankalinki natsuwa kafin ki kai ga fita cikin gidan na komai da zaka aikata yakasance kana cikin kwanciyar hankali ko da kuwa abin na tashin hankali ne" cak!,ta tsaya kamar wacce aka girke a wajan zuciyarta sai harsala take jin maganar sabeer din cikin yan dakiku da suka shude ta dubeshi bata re da ta tsinka masa ba ta daga kafarta domin barin cikin falon hakan da yagani yasanyashi sake magana cikin alamun jin bacin rai"dake fa nake ko bazakiyi amfani da abin da na sanar dake a matsayi na namijinki bai dace ki fita batare da izini na ba Dan haka ban amince ki fice daga cikin gidan nan ba..."cikin harzari ta juyo tashiga dubansa cikin alamun narashin fahimtar abin da yake nufi murmushi tasaki Wanda da ka kalla zaka San zallar haushi da takaici ne "uhmm sabeer shin duk tsawon lokacin da muka dauka dakai duk fitar da nake bata tsole maka ido ba sai wannan" tana fadin haka ta juya cikin sauri ta koma dakinta mintina kadan sai ga tafito fuskarta ba yabo ba fallasa tana isowa wajansa tace"ina son zuwa gidan bunayya saboda tana cikin matsala tane mi da naje ta na son gani na "

  "me yasa me ta?" ya nemi baasi

  "wannan kuma ba da muwarka vace kawai Neman izini nayi "

  ya rangwadar dakai domin ya lura a cike take Ku yana lura ko bai barta ba zata fita

  cikin daura fuska yace"ban amin

  ce ba..."

  "nan kuma Isar da bakayi bakenan wallahi"ta tareshi a hassale


  gudu takeyi na fitar hankali kamar wacce take tseren kai wa Bagon duniya a dakiku in ka dubi fuskarta da ke dauke da tsananin Bacin rai ga tashin hankali yayi mata kawa rikicin duniya ji take kamar akanta aka sauke shi

  isar ta gidan bunayya ke da wuya ta ja burki ta tsaya a bakin get cikin hanzari ta balle murfin motar ta fice daga ciki cikin azama doshi cikin gidan gudu gudu sauri sauri tana isa tashiga kwankwasa kofar da sauri sauri.
  mai gadi dake yashe bisa guntun bencinsa hannusa rike da Rediyo yana sauraron labaran duniya yaji bugun da ake Wanda yajishi kamar za a girgide kofar da sauri ya tashi yana mai tambayar wanene cikin daga murya dagancan waje rukayya ta amsa masa cikin hanzari da ssuri ya bude kofar rukayya ta hanzarta shiga dubsnta yashiga yi yanayinda ya ganta ya tabbata ba sumulkalau ba bai tsinka illah gyada kai da yayi ya kulle kofar ya koma mazauninsa
  lokaxin da ta isa kofar falon bunayya da karfinta ta bugashi amma bai bude ba cikin karfin zuci tasake dukansa lokaci guda ya Burma ciki ta cinna kanta cikin gidan hankali tashe
  turus ta ja ta tsaya tana kwalalo idanuwa waje tashi ambaton innalillahi wa ina ilahin raji u abin da tacikaro dashi yayi matukar Dakar mata zuciya.
  bunayya ce zube magashiyan cikin halin narashin haiyaci ba alamun motsi ajikin ta
  rukayya ta ji zuciyar ta tafara sanar da ita jinkiri. da tayi har an zuke jinin bunayya da take sanar da ita Ashe da gaske ne mutuwar zatayi Ashe da gaske ne abin da take sanar da ita wasu irin zafafan hawaye suka shiga zubo mata cikin ci da zuci da fita haiyaci ta fara magana "in har ki kayi haka bakiyawa rayuwa adalci ba me yasa zaki mutu ba tare da kin jira zuwa na ba me yasa zaki tafi ki bar ni cikin wannan duniyar mai cike da rudu da tashin hankali mai yasa Baki bari Nazo me yasa me yasa.."ta ke CE da kuka mai sanya ciwon rai da razana tunani yi take kamar ita ma za a zare mata rai
  lokaci guda ta durkushe sai da tayi kukanta ma ishi San nan ta rarrafa ta isa ga bunayya Hannunta na makerketa ta ta dafa bunayya dake yashe tafara jinjigata tana mai ambaton sunan ta cikin wani irin yanayi na tashin hankali girgizata take ruwan hawaye na zuba daga kwarmin idanuwanta cikin tsananin gigita "bunayya ki farka ki sanar dani abin da yayi sanadiyyar mutuwar ki Dan allah karki tafi batare da kin sanar dani ba ina bukatar San in dalili nayi miki Alkawarin daukar fans a akan ko wanene yayi miki wannan YANKAR KAUNAR bazan kyaleshi ba har sai naga shi ma na dandana masa takaicin duniya irin Wanda ya dandana miki har ya yanke miki rayuwa tun kafin lokacin ki yayi" haka tai tasakin zan ce kamar wata zautacciya ta shafe minti kusan biyar cikin wannan hali na rashin haiyaci
  gsjiyar da tayi ta sambatu yasanya zaman dirshan gaban gawar bunayya ta zuba ta gumi hannu bibbiyu idanuwanta na kan gawar aranta ji take kamar ace bunayya ta farka ta dawo cikin duniyar nan domin tana bukatar ta tana son jin abin da ya hallaka izuwa lahira ba tare da lokacin haka yayi an kasheta ta karfi da yaji wai shin wayayi mata wannan DANYEN AIKIN ne 'mijinta'zuciyar ta bata amsa tashiga girgiza kai cikin takaici tabbas hakan ta tuno lokacin da sukayi waya abin da ta sanar da ita kenan da hannun mijinta wajan kashe mata rayuwa...
  da Sauri ta tsinke zaren tunanin ta jin da tayi ana ta bata a firgice ta dubeta bunayya ce kwalalo idanuwa tayi na dubanta kamar wacce taga gawa ta doso wajan wani iri ihu tayi tare da ambaton sunan Allah ta cakumi bunayya ta girgizata tare da ambaton sunanta da sauri sauri bunayya da idanuwanta ke rufe jikintane kawai ke motsawa bakinta yana kokarin yin furuci amma hakan ya gagari matukar jindadi da farkawar bunayya rukayya ta fara cillo mata magsnganu masu cike da tambayoyi ko lura da halin da take batayi Dan tunani take in har taja lokaci bunayya zata iya komawa lahira batare da ta sanar da ita hakika nin abinda yafaru da ita ba "ina jin ki Dan allah kiyi magana yi magana bunayya waye yayi miki haka sanar dani " ta shiga. Girgiza ta kamar wacce data zanzage mata kayan jiki bakidaya tana yi mata magana cikin ihu ihu jinjigar da takeyi mata yasanya firgita tashiga tari kamar wacce za ta tafi gabadaya hakan da rukayya tagani yasanya saurin mikewa cikin karfin zuciya ta cire mayafinta taci damara dashi mukullin motarta tasanya abaki tashiga kokarin cincibar bunayya kamar wata karamar yarinya cak ta daga ta ta sabata a kafata tayi waje cikin Sauri sauri ta isa harabar gidan tashiga kwalawa direba kira da yayi maza ya bude mata get jin kiran da mai gadi yayi ya tashi a hanzarce yana duban rukayya ya na tambayarta lafiya wani Abu ne yasami uwardakin tasa rukayya bata tsaya bashi amsa ba illah sake jandada masa da ya bude mata kofa bashi ya kware get din rukayya ta fice tana zuwa inda ta aje motarta ta bude ta Sanya bunayya aciki Wanda izuwa lokacin ta sume rukayya ta fada motar. ta fizgeta ta cilla bisa titi.
  gudu take na fitar hankali kamar wacce zata tashi sama ji take kamar ta rufe ido ta ganta cikin asibiti da wannan tunane tunane ta isa asibitin Malam aminu kano waje guda tayi parking din motarta bata tsaya gayyatar wani ma aikaci asibiti ta kinkimi bunayya da kanta tayi cikin asibitin mutanan dasu ke harabar asibitin sai bin ta suke da kallon cikin sakin Baki alamun mamaki haka tashiga wuce su cikin sauri Sauri tana shiga ta doshi wani daki na musamma bakowa aciki sai gadaje biyu da kuma komatsan kayan aiki daya daga ciki gadajen ta dosa ta kwantar da bunayya cikin alamun jinjiki ta dafe kafar gadon tana mai da numfashi gabakidaya taga ma laushi bayan ta numfasa tadubi bunayya wacce har yanzu tana sume ta Sauri ta bar cikin dakin ta doshi wani office a hanyar ta ta tafiya ne ta hadu da najaatu tashiga dubanta cikin alamu nason sanin abin da yakawo ki ita ma ana ta bangaren haka ne najaatu ta kokarta tsinkawa cikin tsare ta da idanuwa"ya haka rukayya me kuma ya kawo ki wajan aiki weekend?" bata amsa mata tambayar taba illah itama tambayar ta cillo mata. "ko dacta Basheer ya zo asibiti yau" ta fadi cikin son samun amsa a hanzarce najaatu hakan da tagani ta ai yana azuci cewa akwai abin da ke faruwa gyada mata kai tayi alamun eh da hanzari rukayya ta fara kokarin barin wajan amma jin furucin najaatu yasanya Jan burgi ta tsaya " me ke faruwa ne, hala ankuma ne...?"da sauri rukayya ta watso mata wani irin kallo Wanda yasanya ta cinye sauran maganar tata ba jira ba tayi gaba ta kyaleta tana ja. kwa6a aranta dai jinjina halin najaatu take nashegen shinshiginta da shiga zancen da bata na ta ba kai allah ya kyauta mata. cikin wannan halin ne ta isa ofishin dacta Basheer ta nemi izinin Shiva aka bata da sallama tana shiga ta gaidashi idanuwa yabita dasu alamun mamakin ganinta fuskarsa na bayyanar da murmushi da alamun al'adarsa ce haka kullum.fuskarsa bata rabuwa da fara'a ya dubeta " ya dai sister me ke faruwa ne na ganki adaiadai wannan lokaci?" nisawa rukayya tayi bayan ta ja numfashi tace "ina bukatar taimakon ka don allah yar uwa tace take ciki halin rashin lafiya mai tsanani bata ma iya gane Inda kanta yake please" ta kare maganarta a marere ce kamar wacce zatayi kuka hakan yayi matukar bashi tausayi da hanzari ya mike yana mai tambayar ta tana ina ta sanar dashi a tare suka fice saga ofishin suka doshi dakin da takai bunayya ya na shiga yafara bincikenan na tsayin minti biyu sannan ya juyo ya dubi rukayya "maza jeki office ki kiramin dacta Haruna ki ce ina bukatar sa da hanzari..." ai bata bari ya diga aya azancen sa ba tayi hanzarin Barin dakin mintina kadan sai ga ta sun dawo a tare nan dai yashiga yiwa dacta Haruna Karin akan bunayyya da abin da yake da tabbacin yasame ta shima yayi matukar tausaya mata nan suka Shiga bata taimakon gangawa domin ceto rai izuwa lokacin hankalin rukayya ya fara dawowa jikinta sabida abin da su dacta Basheer suka sanar da ita da izinin allah zata tashi su daura mata ruwa suka kara mata da allurai suka fice amma basu sanar da rukayya taka maimain abinda yake faruwa
  zaune suke suna fuskantar juna bunayya ta jingina da bango tana zaune bisa gadon da aka kwantar da ita kallo daya zakayi mata kagano zabgewar da tayi alokaci kankani duk tayi kotai kotai da ita rukayya ta ina sa "yaya jikin naki dafatan ba abin da ke damun ki" cikin yanayi na ban so abin da ya faruba bunayya tace "ban so haka ba na so ace na zarce kiyama da zan fi samun sauki da dai nasake rayuwa cikin wannan duniyar nan mai cike da tashin hankali inama ace wannan kwanciyar da nayi numfashi ya dauke INA ma ace zarcewa nayi ban dawo wannan duniyar ba..." Da sauri rukayya ta tare cikin alamun tausayawa"ki dai na ambaton irin wadannan kalaman Sam basu dace ace suna fitowa daga bakinki ba komai da kike gani na duniyar nan dan hakuri ne KOMAI YA YI ZAFI MAGANINSA ALLAH"
  Bunayya ta nisa wasu irin zafafan hawaye su gwaranyo saman fuskarta cikin murya mai rauni tace "rukayya ni nasani rayuwa a gajarce take nasani bazankara kwanaki a cikin duniyar nan ba jiki na ya bani RAI DA NUMFASHI na sun zama MALLAKI ga wani sun rigaya sun salwanta dan haka nidai nayi sallama da rayuwa..." Tai saurin cinye sauran zancen ta jin kuka na shirin kurce mata tayi matukar karyar da zuciyar rukayya nan da nan ita ma tafara kwalla tana girgiza kai"rai da numfashin ki ba wani bawa da ya isa ya rabaki da su ba wani dan Adam da iyasa yayi miki abin da allah bai yi miki kisan da wannan kisa aranki bawani ba wa da ya isa ya cutar dake"
  girgiza kai tashiga yi hawaye "ya cuce ni ya gajarce min rayuwa ya watsata cikin kwatami rukayya ki taimaka min rayuwa ta Kare..."
  cikin zakuwa ruakyya ta tareta "wai shin me ke faruwa ne ya kamata ki sanar dani wannan koke koken bazanyi miki maganin matsalar da take nukurkusar rayuwarki wai shin me yayi miki ne"
  Cikin shanyewar kuka tace "rayuka yakashe min kuma yake Neman nawa ran"
  zabura rukayya tayi alamun tsora "ban gane ba me kike nufi da zsncen yake she miki rayuks?"
  Wani dunkulanlan Abu da yayiwa makogoron bunayya kawa ta hadiyeshi Kisan rayuka biyar kenan aka salwantar min dasu batare da na sani ba ana shida ne allah yayi min gyadar doguwa na farga daga MAFARKIN IDO BIYU da nake "
  rukayya ta ja hanci cikin yanayi na tsoro tace "cigaba ina jinki"
  Bunayya ta sharce hawaye "a zahirin gaskiya naso mijina so na gaskiya ban yi zato ko tsammanin yana da wata mummnar manufa a tare dashi ba ashe fuska biyu gareshi bansani ta salihancin yanuna min ni da dangi na muguwar fuskar kuwa ya turbude ta ban san da ita ba haka ma iyaye na da suka dauke shi na kirki basu San da ita ba ashe kwallon shege ne azzalumi lamba daya ajin farko da dorawa a jarida" ta nisa tana duban rukayya da tayi kasa ke ta junta cikin ta sai kadawa yake Dan a zance na gaskiya ta fara tsorata da jin kalaman bunayya "uhm" kawai tace bayan tayi ajiyar zuciya bunayya ta cigaba da tsinkawa"mijina na kirki ne mutum arziki amma fa ada Karin wannan asirin nasa ya tonu" rukayya tasake gyada "INA jinki sanar dani"
  " shekararmu hudu da aure nasan kin san da wannan koh" ta sake gyada kai batare da tace komai
  "a cikin wadannan shekarun nasamu ciki.har sau biyar suna salwanta duk bani da masaniyar akan meke barar da cikin kawai an falwalawa allah ne cinkunan ba rayayyu bane " tayi ajiyar numafshi idanuwan ta suka fara zubar hawaye rukayya ta tare "kin ga Dan allah ki ajiye wannan kukan naki gefe na rantse da allah nafara tsorata da wannan bahagon lamarin naki zai kyautu ki cigaba da sanar dani qbin da ke faruwa zuciya ta tagama tsinkewa" murmushi tayi mata "ai tukunna na ma baki firgita ba sai kin ji yarda aka haihu a ragaya sai kin ji irin ta asar da akayi wa rayuwata da duniya" idanuwan ruakyya waje take Cuban bunayya cikin ta sai kugi yake "kinga bunayya wannan rikitaccen al'amarin naki ba zai sauraru yanzu ba abin da za ayi bari mu koma gida zaifi armashi zan fi daurewa na saurareki"
  Bunayya nakokarin tsinkawa su kaji sallamar docta basheer rukayya ce tayi kokarin amsa masa murya a sake da murmushin sa yakaraso. "ina zan nufa yanzu dake "Cewar rukayya bayan dakta basheer ya basu sallam sun fito daga ssibitin rukayya na Jan su a mota.Jan hanci bunayya tayi fuskarta a turmushe alamun bata so tambayar da rukayya tayi mata ba ba ta tsinka ba kuma bata da niyyar yi illar kau dakai da tayi izuwa bakin windo tana kallon titi rukayya tayi tunanin ko bata ji ta ba ne tasake maimai ta tambayar ta nan ma shiru tayi mata hakan ya tabbatarwa da rukayya bunayya najin ta kawai banza tayi da ita da alamar ba tason tambayar "wai shin ina alhassan ne " rukayya ta cilla mata tambayar da takusan tarwatsa mata kwanya wani kallo tayi mata bakin ta na motsi alamun ta na son cewa wani Abu amma ya gagara duk halin da tashiga rukayya na kallonta ta Dan karamin madubin dake makale a gaban motar dayake ita bunayya na kujerar baya ne ta Dan shingida amma jin furucin rukayya yasan ya ta tashi zaune sosai ta nisa" ke so kike ki hallaka ni" ta fadi cikin yanayi na ZAFIN RAI rukayya ta danyi murmushi "duk mai yakawo zancen ta'addacin cikin zance na"tsaki ta ja sannan ta CE"ai ke zancen ki ya wuce a kirashi da ta 'addacin..."da Sauri ta tsaya da zance ganin rukayya na kokarin kai ta mahalaka cikin hanzari tqce "me kike kokarin kin ji na rantse da allah bazan koma mahalaka ta ba kawai kai ni gidan iyaye na in ma mutuwa ce na mutu a hannunsu amma ba a hannun wannan Dan ta'addan ba" da sauri rukayya taja burki ta tsaya ta Shiga duban bunayya cikin rashin fahimta "duk mai yakawo wannan zancen me Nene yayi zafi ba wuta ba" bunayya tasake hassala tace" kin ga ki wuce kawai da ni gaban iyayena su nafi bukar gani in kuma bazaki iya ba ki ajiye ni nasamu Wanda zai kai ni" shiru da taji rukayya tayi mata ne yasanya ta farakokarin balle murfin motar za ta fice da sauri rukayya ta dakatar da ita "duk abin bai kai mu ga haka ba yi hakuri" ba tare da ta tsinka ta ko ma ta zauna tayi shiru rukayya ta nisa sannan ta ja motar sukayi gaba haka su ka cigaba da tafiya ba wannan yayi magana har suka isa.
  Isar su gidan alhaji adamu mahaifin bunayya ke da wuya rukkayya nayi parking bunnay ta fice dagu tayi cikin gida tana kurma ihu tana ambaton an kashe mata rayuwa da duniyar allah hallaka an rabata da farinciki an maye gurbin sa da tashin hankali da bakin ciki hannunta aka tashiga cikin falon tana zuwa ta zube ta kuka mai matukar firgita mai sauraronta hajiya zainab mahaifiyarta dake zaune cikin falon ita kadai jin kukan bunayya ya ta yar mata da hankali zumbur ta mike idanuwa warwaje tana ambaton innalillahi wa'innaaihir raji'un tana ambaton sunayen allah tana tafa hannu cikin sauri ta iso wajan bunayya zanin jikinta har yana kokarin faduwa tasa hannunta ta rike da sauri ta janyo bunayya da ke shure shure ta kware baki cikin kuka tace "momy alhassan yakashe yaka she min rayuwata tamkar GAWA DA RAI nake yanzu" momy tace"ke lafiyanki bani son sakarci mana me ke damunki kuma wanene yakashe miki rayuwa" cikin shanye kuka tace " alhassan" momy ta dubeta cikin rashin fahimta "me alhassan din yayi miki da har kike ikirarin ya kashe ki da rayuwarki" tana kokarin magana rukayya ta kwado sallama cikin yanayi na firgici momy tashiga dubanta tace "rukayya tare kuke dama da it a" ta gyada mata kai alamar eh ta karaso cikin falon tana bin bunayya da kallo "Haba Dan allah me Nene haka kikeyi wannan abin fa bana masu hankali ba ne yanzu da kika shigo kina rusar kuka basai ki tayarmusu da hankali ba su zata ko wani Abu yafaru dake.."da Sauri bumayya tadubi rukayya cikin sakin baki" meyesa zaki ce haka kinsan halin da nake ciki in kwai abin da yafi kuka wallahi zanyi sa wannan SIRADIN RAYUWAR da nake ciki ai ba kankani bane" momy da tazuba musu ido tunda suka fara maganarsu da taga alamun ba mai karewa bace tai saurin tare rukkaya da ke kokarin tsinka" wai shin mai yake faruwa ne kun sakani cikin hali na kokwanto da rashin kwanciya hankali kusanar dani abin dake faruwa" shiru sukayi ba wacce ta sake magana falon yayi shiru zuciyoyi ne kawai ke nisawa momy tace"natsuwan ku da hankalinku nake bukata ku sanar da ni abin da kefaruwa"rukayya ta nisa tana kokarin tsinkawa momy tai saurin ta tare ta"ku tashi ku hau kan kujera Ku zaune" ba tare da sun tsinka ba ko wacce ta tashi ta Dora kugunta kan kujera jikinsu duk a sabule kamar kazar da kai yafashe mata a ciki momy ta dubi rukayya sosai kamar mai son tuhumar ta hakan da rukayya tagani yasanya ta shan jinin jikin ta Momy ta juyar da kallon ta izuwa bunayya wacce gabaki daya ta fice daga haiyacinta idanuwanta sun kada sunyi jajir momy ta nisa cikin alamun tausayawa ta dubi rukayya" ke ya dace na tambaya don ki sanar dani abin da ke waka na" wata irin wawiyar ajiyar zuciya rukayya tayi ta re da nisawa "momy a gaskiya...."sauran maganar tata ta makyale dalilin jin sallamar da aka kwado cikin falon gabadayan su sukajiyo izuwa ganin wanene alhaji anas ne mahaifin bunayya yashigo momy ce tayi kokarin amsa sallamar tasa cikin fara'a yakaraso cikin falon amma yanayin da yaga fuskokinsu alamun ba lafiya yasashi saurin zare fara'ar fuskar tasa yashi tambayarsu lafiya kowa cikin su kasa magana yayi illah ido dasuka zuba masa duban bunayya yayi yace "ke menene yasa meki naga idanuwanki alamun kinyi kuka" shiru tayi masa tare da sunkuyar dakai kasa hakan da yagani ya tabbatar ba lafiya ba akwai abin da ke faruwa cikin yanayi na kaguwa da son jin abin da ke faruwa ya dubi momy yace " in kowa bazai sanar dani abin da ke faruwa yadace ace ke kin Sanar dani domin nima nashiga cikin matsalar domin a magance ta tare a matsayina na mai iko da wannan gidan da mutan gidan bakidaya" momy cikin yanayi na damuwa tace"alhaji ba haka bane al'amarin mai rikitarwa da tayar da hankula" cikin bukatar a sanar dashi komai nene yatare ta"ke dai kawai Sanar in har ina da albarkar da za a sanar dani"cikin sanyin murya momy takwashe komai da tasani ta sanar dashi lokaci guda fuskar sa ta canza izuwa damuwa "wacce irin magana ce wannan Mara makama da kangado ke bunayya shin wannan maganar. da nake ji haka take" yakareshe cikin sanyin murya mai tattare da rarrashi cikin muryar kuka idanuwanta na zubar kwalla+

  Komentar

  Tampilkan

  No comments:

  Post a Comment

  Terkini

  +
  ?orderby=published&alt=json-in-script&callback=labelthumbs\"><\/script>");