NADAMAR RAYUWATA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NADAMAR RAYUWATA COMPLETE

NADAMAR RAYUWATA COMPLETE

- - Post a Comment

 NADAMAR RAYUWATA COMPLETE


Kuuu! Motar taja wani wawwan birki a tsakiyar hanyar, hakan ya yi sanadiyar tashin wata karamar kura cukurkuɗaɗɗiya wadda ta tayar da karamin hadarin da bazai zubar da  ruwa ba a sararrin subhana. Gaba ɗaya idanun yan majalisar ya dawo kan abin da ya ke faruwa, ɗuuu! Tamkar sunga shugaban kasa zai wuce suka aza musu na mujiya. Cikin fitar hayyaci ya fito daga motar yana sauri tamkar zai tashi sama ya nufeta gadan-gadan.+


"Haba Malama ya inata binki kina wulakantani tun fa daga wajan biki nake biye da ke amma kina jina!".

Wani irin kugi cikinta ya yi ta juyo a kiɗime kanta ya sara ganin yadda  zauna gari banza suka zubo mata idanu. Ta cije leɓe tana dubansa tare da saɓa Ammatullah kan kafaɗarta ta gyara mata zama,

"Malam lafiya? Kake bibbiyata kai baka san abin da ya dace bane?!".

"Kamar ya ban san menene ya dace ba, sanin abin da ya dace yasa nake bibbiyarki".

"To! To!! To!!! Dakata ka kara gaba NI MATAR AURE CE!".

Wani wawwan kallo ya watsa mata, daga bisani ya kwashe da dariya ya jefa kallonsa kan ta kusa da ita.

"Idan wannan kika kira cewa MATAR AURE CE zan yadda, amma wallahi zan iya rantsewa karya kike ke ba MATAR AURE ba ce".

Cike da takaici ta sauke idonta a kan Maryam wadda ke sanye da shigar laffaya real Kanuri ta yanne ko ina na jikinta taja wani mugun tsaki saura kiris  ya ɗauke mata harshe ta furta,

"baka gani da ɗiya ba?".

"Na sani ko riko ta baki ko Auntynmu".

Ya faɗa yana sauke idonsa shanyayyu masu kama da me jin bacci a kanta tuni jikinta ya yi sanyi. Muryar Maryam ta tsinta ta yi gaba a kala tsakaninsu taku shida tana faɗin,

"tsaya dai kina yi masa bayanin ke ɗin MATAR AURE CE wankin hula da ya kaiki dare!".

Cikin hanzari ta sakaɗa ta zumbiɗa ta bi bayanta tana faɗin,

"masifafiya in ban masa bayani ba so kike muganshi a gida in cewa yayanki uban me, banza kawai?!".

Cikin takaici ta kura mata idanunta a kan fuskarta,kanana dasu suka yi ciki tsabar takaici amma data tuna hanya suke sai ta kanne.


Haka suka jera tamkar wasu kurame suna zuwa gida suka wuce maigadi yana yi musu sannu da zuwa, Maryam kai tsaye ɗakinta ta faɗa ta yi dabarar share hawayen daya zubo mata ta fito ta ɗauki Ammatullah tana shilata sama. Yarinyar dama duk a takure take bata saba ba tuni ta ɓangale baki tana kyalkkyal dariya tamkar taga ainihin mahaifiyarta. Neman waje ta yi ta zauna tana jin kwarancin da take mata a haka ta samesu ta nemi waje ta zauna.


Batun ɗazu ne yake ta cin Maryam a zuciya, amma masifar Maimuna ya hanata magana suna zaune yaro ɗan kimanin shekara tara ya shigo,

"Assalamu alaikum, wai ina sallama da wadda ta shigo me yarinya a kafaɗa, wai mutumin yace don Allah in bazata zo ba ta bashi lambar waya don  Allah".

Mutuwar zaune Maryam ta yi Maimunatu kuwa ta taso masa da masifa,

"naci uwarka na ce, kai baka faɗa masa MATAR AURE bace?".

"Yi hakuri Maman Ammatu bansan ke ce ba wallahi".

Da gudu ya fice Maryam ta rakashi da idanu tana sauke ajiyar numfashi ta dubi Maimunatu.

"Gaskiya Aunty ya kamata kiyi karatun ta nutsu, ai duk ke kika ja da kika yi shigar data saɓa addini yanzu saboda Allah ina laifin bawan Allahn nan ya san WACE CE KE!?"

Galala Maimunatu ta saki baki tana duban Maryam,

"Hmmm! Maryama ustaziyya kin gama wa azin? Hmm! Aikin ɓur inji tusa kawai, ni zaki yi wa wa azi? Fina sani kika yi ko fina zuwa makaranta kika yi? Zamani ne fa ya sauya ka yi shiga ta kece raink ka shiga taro gudun kallon wulakanci. Ke a karan kanki ban baki sha awaba don Allah?".

Maryam ta bita da kallo taga yadda ta cire gashin dokin data saka kai kamar hammatar ɗan dako, rigarta daban zani dikil dikil daban kamar ba ita bace suka fita ɗas da ita?. Ajiyar rai ta yi dariya na neman kwace mata,

"nasani Aunty amma a dinga cizawa ana furzarwa ki duba fa yadda kika fita aure fa abu ne mai kima".

"Dakata yi min shiru Maryam dan kinga ina yi miki lako-lako? Kullum batukin Aure! Aure!! Aure!!! Aikin banza in fitsari banza ne kaza ma ta yi. Naga ke kinki auran kin kibge kina samani idanu ina ruwanki dani".

Wani kududu ya tsayawa mata, hawaye ya soma zarya a idonta.

"Kin bani mamaki wallahi Aunty Maimu kullum irin haka ya haɗamu burinki kimin gori naki aure. Shin wake bada miji ne Aunty? Ko a gidanku ake saidawa?   kika siyowa kanki miji? Shifa komai lokacine. Ai nima ina burin in yi auren saboda cikar mutuncina kenan amma bafa auran rikon sakainar kashi irin naki ba.....".

Kau! Kau!! Kau!!! Ta ɗauketa da wani giggitattun mari da gudu ta bar ɗakin tana rike da kuncinta.

*****

***

Cikin kaɗuwa ta hankaɗa matashin kai ta sakaya wayar kamar yadda ya barta ya fito yana tsane ruwan jikinsa ta manna masa harara tare da mikewa ta shige ɗayan ɗakin ta dana sakata. Safa da Marwa kawai take, gumi na tsiyayo mata kamar wadda ta ƴhaɗiyi kunama. Bugun kofar ya dawo da ita daga duniyar tunanin Fawzan da take yi ta ka tsaki tare da faɗin,

"lafiya ka dameni da bugu haba Abbas nifa ka ishe ni".

Muryarsa ta sarke ransa ya gama ɓacci ya kira sunanta kasan makoshi,

"Suhaima wai meyasa kike haka nifa mijinki ne?".

"Miji!? Hmm! Miji manya to ni bana mijin da kai ai dama na faɗa maka ka tafi ka bani waje bana son ganinka".

Jiki a sanyayye yaja jiki ya bar wajan yana cizon yatsa, zuciyarsa fal NADAMA tattare da auran Suhaima. A hankali ya gaggara matattakalar benen falon ƴya zauna yana tunani.

***


STORY CONTINUES BELOW

Abbas Muhammad Dauda, shi ne cikakken sunansa abokansa yawa nakiransa da sunan Amud. Cikakken atashi ɗan kasuwa mai kimanin shekaru talatin da biyar. Ya kammala karatunsa shekaru huɗu da suka wuce kan harkar kasuwanci. Su uku mahaifinsu ya mutu ya bari wato Alhaji Muhammad Dauda tsohon ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa daya zauna da kafaffunsa ya rasu ya barmusu tarin dukiya mai yawa daga bisani mai ɗakinsa Hajiya Khadija ta bishi da wata uku. Suka tafi suka bar ƴyara uku. Abbas shi ne na farko lokacin ya kammala karatunsa da wata biyar sunji mutusar sossai. Hamza shi ne yake binsa mai shekara talatin sai kuma Ma aruf auta mai shekara ashirin ashirin da bakwai. Hamza ya daɗe da yin aure tun mahaifansa nada rai, matarsa Halima mace mai hankali da nutsuwa. Suna zaune a unguwar Sharaɗa titin Yahya Gusau a kayatacen gidansu wanda ya kasance kamar estate guda uku a jere saboda girmansa. Daya na Hamza ɗaya kuma Abbas da kuma Ma auruf auta.  Abbas wani irin  mutum ne mara son kwaramniya da ƴhayaniyya kaf harkokin kasuwancinsa yafi yinsu akadashen ketare. Ba wani kyakkyawa bane dogone sossai amma kuma yana da hanci da idanu sai dai baki ne siɗik kamar Kanuri. Mutum ne mai wadatar nutsuwa da kamewa, babban burin Abbas shi ne auran mace kyakkyawa. Lokuta da dama sukan haura da abokansa wajan wannan kuduri nasa. Cikin ikon Allah a shekarsa ta biyu da kammala karatunsa ya haɗu da Suhaima a wani bikin abokinsa ɗan ministern kuɗi. Tunda ya ɗora idonsa a kanta ya kasa nutsuwa har saida ya isar da bukatar da zuciyarsa. Da fari ta soma ja baya dashi amma daga bisani data ga uwar kuɗin sai ta amince taga wajan zama.


    Suhaima asalinsu fararan buzaye ne, ta fanin mahaifi mahaifiyarta kuma shuwa ce cikakkiya zama ya kawo su Kano unguwar Nassarawa. Mahaifinsu ya rike mukamai da dama kafin rasuwarsa sun rike dukiya ba laifi ya yin daya faɗi ya sai komai ya tsaya cak!. Maihaifiyarsu mace ce mai masifar son kuɗi su huɗu ta haifa duk ta aura dasu daga Suhaima sai auta Ajlah. Yayarsu ta farko tana auran manajan banki ta biyun kuma tana auran wani babban ɗan siyasa suna Abuja.

     Suhaima kyakkywar mace ce doguwa samɓal, tana da diri mai ɗaukar hankali. Lokacin da Abbas ya furta yana sonta tana aji ɗaya a matakin babbar makaranta ta yan mata wato _secondary school_ haka suka cigaba da soyayya kamar gaske duk wata hidimarta shi yake ɗaukar yi mata. Suna aji na biyu ne aka nemi Abbas ya turo magabatansa tashin farko suka bashi tabbacin basa son lefe amma da sharaɗi shi zai mata kayan ɗaki. Amma da dukiya bata dameshi ba ko ɗar bai yi ba dama burinsa kenan ko basu bukata ba. A haka suka yanke masa sadakin auranta naira miliyan biyu da rabi. Waliyansa da suka jagoranci abun suka dinga kananun maganganu amma hakan bai dameshi ba haka aka tattara sadakinta aka dankawa kanin mahaifinta ƴya cale ya bar garin ya barsu da baki buɗe in kin ɗauke rabin miliyan ɗin kai daya dankawa mahaifiyarta. Kwanci tashi suka tasa kuɗi da bushasha yau da gobe zara bata barin dami suka cinye kuɗi tas.

WATA SABUWA......

Wata biyu da kawo kuɗin Suhaima Abbas ya kawo mata dankareriyar waya sabuwar shugowa, a ranar data je da ita makaranta ta nunawa kawayanta nan da nan suka yi musayar numbobi. Kasancewar makarantarsu cakuɗe take da maza da mata shugaban ajin su ya yanke ya shawara ya buɗe group aka sa numbobin masu chat na aji. Harma da marasa yi suka soma sha awar buɗewa saboda yadda labarin shaɗanar da ake a group ɗin ke zuwa kunnuwansu.

Fawzan shi ne admin na wannan group, matashin saurayi ne tsaran Suhaima mai shekaru goma sha bakwai da shekara ɗaya ya ɗarata amma yana da girman jiki wasu ma ashirin suke kashi. Mahaifinsa yana da tarin dukiya shi kaɗai suka haifa wannan yasa suke sonsa sossai da ga baya ne akai masa kanne uku duk ta Zajlah, Sarrinah da kuma Sajeeda. Tun shigowar Suhaima group ɗin dashi suka fi wasa da dariya duk da shiru-shiru irin nata daga bisani alakarsu ta juye zusa murɗaɗɗiyar soyyaya mai tsanani tun suna yi a ɓoye harta fito fili. A hankali Suhaima ta soma yi wa Abbas wulakanci tun tana yi masa HANNUNKA MAI SANDA har ta fito kiri-kiri ta shaida masa cewar bata sonsa. Tashin hankali wanda ba asa masa rana, saida Abbas ya shafe sati a asibiti don fargaba. Lokacin da mahaifiyarta ta farga da abin da ke faruwa ɗan karamin haukane kawai bata yi ba a hankalce da hankalinta take auna ko barin Suhaima ta yi ta auri Fawzan tasan bame masa aure a shekarunsa duk da tasamu labarin son da mahaifiyarsa take masa amma tana da labarin burin data ɗauka a kansa na zama wani a faɗin duniya.

     A haka akaita turzawa har Abbas ya tako ya sanar da ita, amma bata sake zani ba tunaninta ya tafi kan in ya fasa ina taga kuɗin biyansa sadakinsa. Hakan yasa ta yanke shawarar bashi auran Ajlah ata bau Abbas ya dage bayasan Ajlah saboda bata kai Suhaima kyau ba.

Haka lamarin ya cigaba da kasancewa wulakanci kusufa kusufa har zagin Abbas take. Soyyayyar Fawzan ta yi kamari a ranta sossai a haka suka shiga ajin karshe wanda daga shi sai bikinta. Fawzan ya kan shiga damuwa a gaban Suhaima amma da zarar ya barta zagi kawai take sha. A hankali ya soma koya mata mummunar ɗabi arsa ya kan ɗauketa daga makaranta a motarsa zuwa wajajje da dama da sunan shan ice cream a hankali ta soma gudun islamiyya su yi waya su haɗu a keɓantacan waje ya ɗauketa su bar unguwar tun ana zuwa shan ice cream har aka soma kauce hanya domin ba iya nan ake tsayawa ba. Fawzan karamin matashi amma ya zama babban takadiri wajan sarrafa Suhaima, ya kanyi amfani da kaifin soyyayyar da take masa ya ladabtar da zuciysrta tabi a bin da yaƙke so duk iya kokarinsa sai dai kash ta gaza bari ya ketare iyarka hakan kan haifar musu da saɓani tsakaninsu daga bisani su koma su ɗinke kamar basu ɓata ba.


***

A ɓangare guda kuma maihaifiyar Fawzan babu wanda ta tsana irin Suhaima, al ammarin ya samo asaline yadda wata rana ta zageta a waya bisa rashin sani. Sanadin abun kuwa shi ne kiri kiri Suhaima ta tsiri makarantar dare wadda take bayan layinsu ana shiga ne misalin karfe takwas a tashi tara da rabi zuwa goma. Duk yadda mahaifiyarta taso dakile makarantar abun ya gaggara saboda a yanzu tafi karfinta dalili ita ce cinsu da komai nasu. Idan ta tafi makaranta wata rana taje wata rana ta bi Fawzan a rin hakan ranar wata laraba ta yi shirin makaranta ta wuce layin gabansu kai tsaye ta faɗa motarsa yaja suka gangara kasan layinsu. Sun jima suna abin da bai dace ba ganin zai kauce hanya yasa ta kwaci kanta tana faɗin,

"why Fawzan bana fa so".

Gaba ɗaya ya fice hayyacinsa ya kalleta ta tsakanin hasken daya ratso karamar hudar glass ɗin.

"Haba Suhaima bakya sona ne?".

Muryarta ta sarke ta yi rau da ido.

"Ina sonka amma bana son wannan rayuwar wallahi".

Buɗe motar ya yi yana huci.

"Suhaima fice ki barmin motata fice nace".

Da gudu ta fice tana kuka, ɗaya daga abinda ke haifar musu da saɓani kenan. Da gudu yaja motarsa ya yi gaba. Haka ta kasance har aka tashi makaranta bata da walwala ga bulala data sha. Washegari haka ta yini sukuku tsayin kwana huɗu tana kiransa baya ɗagawa duk ta shiga damuwa ta fice hayyacinta a ranar kwana na biyar ne yasata a caji ɗakinsa socket ya lallace ya jona fallon Momynsa ya fita mintuna goma da fitarsa kiranta ya shigo harta gatse shiru nacin kiran data ke yi yasa Momyn tasowa ta ɗaga da cewar,

"hello".

Wani takaici ya kasheta,ta yadda sakacinta yasa Fawzan samun wata suna holewarsu cikin ɗacin rai ta furta.

"Ke dabbar ina ce zaki ɗaukarmin wayar mijina? Waya baki izinin hakan?".

Jinkin Hajiyarsa ya kama rawa ko ina, ta sauke wayar tana duba sunan mai kiran raɗau sunan ya fito JAKA CE ta kara wayar ta furta,

"kin tabbata akan sunan daya ɗora miki ɗana ya haifu".

Daga haka ta katse kiran daidai lokacin Fawzn ya shigo ta tsareshi da ido.

"Wacece jaka ce?".

Mutuwar tsaye ya yi amma gudun rafoshi yasa ya waske,

"class meet ɗina ce".

"Mecece alakarku?".

"Freindship Momy".

"Karya ka ke!".

"Ki yarda.....".

"Dakata! Inga hotanta".

Babu musu ya haskota ta karemata kallo ta gama shaidata,

"ya yi kyau amma kasani in ma kuna da alaka wallahi bazaka aureta ba, mudun ina numfashi koda daga kai sai ita a duniya".

Fuuu! Tabar ɗakin kansa ya yi dum! Amma kome ya tuna ya zunguɗa kafaɗa ya yi gaba abinsa. Can kuma Suhaima na masifa bata ji me Momy tace da ita ba zatonta wata ce saita aje wayar tana rizgar kuka Ajlah nagefe tana yi mata dariya.


A fusace ta yi kanta tana shirin dukanta mahaifiyarsu ta shiga tsakani.

  Tsayin kwana biyar tana fama da ciwon abu ɗaya, ranar kwana na shida aka saka ranarta da Abbas tashin hankali wanda ba a samasa rana. Tun mahaifiyarta na yi wa lamarin kallon wasa harta saduda kuka Suhaima take tana haɗa kayanta zata gudu ganin babu sarki sai Allah da magarba tasa ta shirya suka nufi unguwarsu Fawzan dake jan bulo. Basu sha wuya ba wajan gano gidan kasancewar mahaifinsa fitace ne. Lokacin da suka isa gidan ba kowa yaran na gun lesson sai Hajiyar Fawzan a zaune gefanta shi ne yana daddana waya.


Tun shigowarsu take binsu da kallo har suka zauna, taso yin tijara ta lura itama Hajiya Laila yar tijara ce ta kanne. Sun gaisa a mutunce daga bisani ta dubeta,

"Hajiya baki sani ba, amma dole tasa zaki sani sunana Hajiya Laila. Wannan yata ce, soyyaya suke da ɗanki kuma gaskiya tana da wanda yake nemanta har ansa rana ta tubure sai ɗanki shiyasa na tako in bi ba asi saboda bana hangen zaki masa aure".

Ta yi jim tana dubanta, daga bisani ta dubeta shekeke.

"Bata da ubane yar taki?".

Maganar ta dakesu har Suhaima bata san lokacin data ɗago ta kafe Hajiya Naja da ido ba lokaci ɗaya su duka ukun suka mike tsaye.Cikin kaɗuwa suka mike Hajiya Naja da Suhaima da kuma Fawzan. Hajiya Naja ce ta soma magana cikin masifa,

"shegiya mayya ke kina da kunya kuwa? Ki zageni a waya kuma ki tako wai kinasan ɗana? Lallai kin cika sunanki Jaka!".

Gaba ɗaya jikin Suhaima ya kama rawa, ta yi kasa da kai a zuciyarta tana tuna muryar da inda ta santa lokaci ɗaya ta yi dogon tunani saita dafe kai ta yi waje,

"gara ki fita wallahi don mudun ina numfashi keda Fawzan sai kallo mayyu".

Da gudu ta karasa mahaifiyarta ta bita sai a waje ta sameta take tambayarta abin da ya faru bata ɓoye mata zagin da ta yi mata ba amma ta ɓoye mata ainihin abinda ya haifar da haka. Faɗa ta yi mata sossai saita kara raina wayan ɗiyartata data ga Fawzan ta lura bayan sangarta akwai kuruciya tare dashi. ƳHaka suka karasa gida kowa na saka da warwara.

***

Tun bayan tafiyar Suhaima Fawzan ƴya kasa zaune ya kasa tsaye, tunani yake bashi da ra ayin auran Suhaima amma yana kishin rasa abin da yakr kulafuci wani ya samu dan haka shaiɗan ya cigaba da kawata masa hanyar da zai gyara tsakaninsa da ita tunkan ta fahimci manufarsa. A daran bai sami bacci ba haka ya tashi sukuku mahaifiyarsa na lura da yanayinsa ta kanne haka ya kwashi su Zajlah suka nufi makaranta. Kai tsaye wajan Suhaima ya nufa tana tsaye ita da Maryam suna hira tun da ya doso wajan Maryam ta yi mata sallama ta wuce kasancewar basa ga miciji ita dashi saboda ya lura Suhaima bata kawa sama da ita kuma kullum tana yi mata nasiha kan abin da suke aikatawa a ɓoye kasancewar Fawzan nada surutu cikin abokai zuwa yanzu kowa yasan alakarsu. Da hanzarinsa ya karasa, ta ɗauke kai ya shiga furuwa kamar bashi ne Fawzan ba abinka da so tuni ta sauko suka shirya kansu. Haka suka cigaba da rayuwarsu kamar baya saima abin da ya yi gaba. Maryam na takaicin abin amma data yi magana suke samun saɓani don haka saita dage da sata cikin addu a.

***

Kwanci tashi bikinta ya karato hankalinsa da nata ya yi masifar tashi, kullum cikin kukan yaudara Fawzan ke mata na rabuwarsu haka suka kammala exam ɗinsu ta neco da waec aka soma gudanar da biki an yi shagulgula da dama daga kama daga kamu da sauransu.+


KUSKURE...SAKACI...SON ZUCIYA.......

Tunda aka fara hidimar bikin suna manne a waya, Maryam na lura da takunta tsaf a hankali take binta cikin tafiyar hawainiya. Fawzan kuwa duk ya tashi hankalinsa ganin abinda yake buri zai suɓuce. Dan haka ya kara kaimi wajan azalzalar zuciyata da kalaman kauna kuka kuwa babu magana, tun tana rarrashi harta biye masa suke yi tare zuciyarta na wani irin tururi da tukuki. Fawzan ya matsa kan lallai sai Suhaima tazo sun yi sallamar karshe hakan ya ɗaga mata hankali ta rasa mafita kullum cikin mutane take ga Maryam data raɗawa sunan ɗan kaɗafi. A ɓangare guda gabanta na tsananta faɗuwa in ta tuna zata rabu da Fawzan kuka ya zama abokin baccinta. Ana gobe ɗaurin aure misalin ƙkarfe bakwai na magarba Suhaima ta samu silallewa ta isa bayan layinsu ta kira Fawzan bugu ɗaya ya ɗauka,

"kana ina?".

"Kin fito ne?".

"Eh!".

"Ok ki sameni a Dan horonbiya hotel".

"Fawzan me zanmaka a hotel?".

Ta tambaya cikin faɗuwar gaba, cikin sauri ya gyara kwaɓars,

"gudun idon mutane kanmu".

Babu ko ɗar a cikin ranta ta amince da shirinsa ta haye ɗan sahu suka ɗauki hanya tafiyar minti talatin ta sadata da wajan ta biyashi kuɗinsa tana sauka Fawzan ya iso ya wuce ɗakinsa da ita.


Sun jima suna tattauna matsalarsu tare da alkawarori da dama, daga bisani Fawzan ya sauya akalar sallamar tasu cikin mummunar ɗabi arsa. Suhaima ta saki jiki so da shaiɗan na kiɗa mata gangarsu bata fargaba ya soma kaiwa ga gaci amma kash ta kasa aiwatar da komai, kamar a mafarki take jinta kokarin kwatar kanta take ya yi mata kyakkyawan riko,

"please! Do you love me Suhaima?".

"Yes! I love you Faw....za...n".

"So please show me how much you luve me".

Dum! Kamar ɗaukewar haske duhu ya ziyarci zuciyarta, yayin da komai ya kammala wani kuka mai karfi ya kwace mata. Komai ya kwance mata ta dinga jin faɗuwar gaba mai tsanani. Fawzan sai aikin lallashi ya ke shi ya taimaka mata ta gyara jikinta daga bisani suka wuce asibiti aka yi mata wankin mahaifa gudun shigar ciki saida ya tabbatar tayi garau ya maida ita gida misalin karfe goma da rabi na dare harda hawayansa  hakan yasa jikinta sanyi yadda ya dage yana kuka saita bi shi kan tsarinsa cewar ba a san ransa ya aikata hakan ba naira dubu ɗari biyu ya bata ta yi jagale tana dubansa,

"Fawzan kuɗin yancina kabani ko?".

Ta faɗa tana share hawaye,

"oh! Suhaima ko ɗaya gudunmawar biki ce na baki wallahi, haba ina wnn kuɗin zasu siyi mutuncinki tsada gareki?".

"Ina ka samesu?".

"Daddyne ya bani wallahi".

"Bana son yawan rantsuwa, na gode".

Bale murfin motar ta yi zata fice ya rike hannunta ta kafeshi da ido,

"Fawzan!".

Ta faɗa a kasan makoshi,

"ka rike alkawari zan dawo gareka kuma ina tare da kai".

Bata jira cewarsa ba ta ɓale murfin motar ta fice a guje, ya saki shewa tare da furta,

"Waw na yi wenning".

"Allah ya fika".

Muryar Maryam ta ratsa dodon kunnansa, cikin kaɗuwa ya juyo suka yi kallon-kallo ta yi masa wani mugun kallo kiri kiri yake hango tsanarsa a kwayar idonta. Ta cigaba,

"kabani mamaki Fawzan ka cutar da mace mafi soyuwa gareka, wadda ta ɗauki dukkan yadda ta baka.


STORY CONTINUES BELOW

"Ke munafuka! Dakatamin waima yaushe kika zo nan?".

"Yaushe zaka san nazo idonka ya rufe tun tsayuwarku nake jikin motar nan Fawzan kuma naji komai kaci amanar so wallahi kuma kana tare da NADAMAR RAYUWA kasan kuwa cin amana babban laifine?. Cin amana yana daga cikin Halayen munafurci. Manzon Allah (saww) ya lissafta wasu halaye guda uku, yace duk wanda yake dasu acikin halayensa, to hakika shi munafiki ne. Koda yayi sallah yayi Azumi, koda yayi Hajji yayi Umrah, koda yace Shi Musulmi ne (Subhanallah!!!). Cin amana yana daga cikin abubuwan da suke yauye Imanin Mutum. Mutukar mutum zai rika cin amanar Mutane, to kullum Imaninsa raguwa yake yi. Yana daga cikin halayen da suke kaskantar da darajar mutum awajen Allah. Mutukar mutum bai rike amanar bayin Allah ba, to Allah ne zai zama abokin rigimarsa aranar Alkiyamah (Subhanallah!!!). Cin amana yana sanya mutum yayi bakin jini acikin al’ummah, darajarsa da mutuncinsa su zube, sannan kuma al’ummah su rika gudunsa. Kuma yana zama sanadiyyar Dulmiyar mutum acikin wutar Jahannama. Kamar yadda yazo acikin hadisi, Allah zai sanya amanar acikin chan kasan Wutar Jahannama, sannan a umurci Maciyin amana cewa ya shiga ya dauko-ta. Sai ya dauko ya hauro wani babban Tudu, sannan sai ita kuma Amanar ta subuce ta koma chan kasan ramin Jahannama. Sai Mala’iku su daka masa Tsawa suce ya koma ya daukota. Haka zai yi ta yi har Illa ma sha’Allahu. Haka kuma yana zubar da albarkar dukiya. Domin kuwa komai yawan kudi, in dai aka cudanyashi da kudin Cin amana sai ya lalace. Fawzan me yake ruɗarka ka rasa abin ha inta sai masoyiyarka?".


"Haba Fawzan masoyi fa! Masoyi yafi makiyi wallahi".

  Jikinsa ya yi sanyi matuka, ta kaɗa kai ta yi gaba tana barin wajan ya saki dariya tare da shirya kayatacan msg ya turawa Suhaima. Suhaima kai tsaye gidan da yan matan amarya makotansu suke kwana ta yi wa tsinke takai mintuna goma da zama Ajlah ta sameta,

"amarsu akaita nemanki ɗazu ina kika shige?".

"Ke ina ruwanki dani waya ke nemana?".

"Yaya Baba ce take nemanki".

"Kice na yi bacci".

Mikewa Ajlah ta yi tabar wajan tana gunguni. Shuɗewar mintuna ashirin Maryam ta karaso gurin murya a cuɗe ta zauna,

"kin kyauta Suhaima, yau kin fito kin nunawa duniya Fawzan ne ke iko dake ba magabantanki ba!".

Kirjinta ya dinga bugawa da sauri da sauri ta ɓoye damuwarta duk alamun rashin gaskiya sun bayyana gareta.


"La.....fi...ya...Maryam..me.....?".

Kallon data watsa mata yasa jikinta mutuwa gaba ɗaya saita fashe da kuka,

"ba kuka zaki ba kuka na gaba sai sanda kika tashi sanar min ya za a ɗauramiki aure ba tare da istibira i ba!".

Das! Das!! Das!!! Gabatanta ya tsananta faɗuwa bata damu ba ta cigaba da magana zuciyarta kamar ta faɗo.

"Anya Suhaima kina tsoron Allah kuwa?".

"Waike me nayi?!".

Ta faɗa cikin dakiya,

"tsabar shari kawai dan na sami mijin aure zaki min halinku na hausawa yan bakin ciki? Saboda ke baki da ko mashinshini? Hmm lallai Maryam ashe da gaske bakya sona ana faɗa ina karyatawa yau min nunamin ainhin kalarki"....


Mamaki takaici suka haɗu suka yi wa Maryam yawa ta rasa bakin magana saita mike ta bar gidan tana mamakin halin Suhaima data sauya farat ɗaya. Bayan fitar Maryam ta yi kuka mai isarta tare da mikewa ta shiga banɗaki saida ta gyara jikinta ta fito nan ta nemi wayarta ta rasa sama da kasa haɗe da kuɗinta duk iya binciken data yi a ɗakin ta rasa su tasoma tunanin ko Maryam ce amma data tuna ko shigarta banɗaki ta barta saita janye tunanin. Washegari aka ɗaura auran Suhaima da Abbas ɗaurin auran daya tara mutane da dama, ta yi kuka ta yi takaici mai tsanani da yammaci aka sadata da ɗakinta. Gidane wadatace wanda ya wadata da dukiya da kayan alatun more rayuwa daga gidan Suhaima akan iya shiga gidan kanin minjinta. Abbas ya yi rawar gani ya wadatata da komai kayan ɗaki kansu ababban kallo ne. Tun da Suhaima ta zo gidan babu wani abun arziki da yake haɗata da Abbas rashin albarka kala kala kewar  Fawzan tafi komai damunta a haka harta share sati ɗaya. Saita soma satar wayar Abbas in ya shiga wanka suna musayar msg da Fawzan a sace ba tare da saninsa ba tun satinta na uku a gidan  har zuwa yau data cika sati biyar.

***

Maryam na shiga ɗaki ta fashe da kuka mai tsanani, mamaki da takaicin Aunty Maimu ya gama rufeta tana ta yi sukuti tana nazari kan rayuwarsu........


Maimunatu shi ne cikakken sunanta asalin mahaifanta cikakkun Kanawa ne unguwar Aisami. Gidansu mata biyu ne mai ɗauke da yara kimanin sha huɗu kaf ɗinsu an aurar dasu daga me yara biyar sai uku biyu sai sama. Maimunatu matashiya ce mai kimanin shekaru a shirin tana zaune da mijinta da ɗiyarta ɗaya Ammatullah me kimanin wata shi da da yayanta Ammar ɗan shekara biyu. Mijinta ɗan asalin maiduguri ne cikin yan gudun hijira da suka sami kuɓuta shi da kanwarsa Maryam. Haka ya dinga faɗi tashi wajan samun wajan zama har Allah ya haɗashi da mahaifin Maimuna ya saukesu a gidansa daga bisani ya kaishi kasuwa kanwarsa kuma ya sata makaranta. Hakan yafi yiwa Sulaiman daɗi fiye da komai a ransa a duniya Maryam kaɗaice ta rage masa don haka yake matukar ji da ita. Kwanci tashi har aka buɗe masa kanti nasa na kansa saboda yabawa da gaskiyarsa, a kwana a tashi soyyaya ta kulu tsakaninsa da Maimunatu tun suna ɓoyewa harta fito fili. Cikin hukuncin ubangiji aka yi bikinsu suka tare a unguwar Aisami a matsakaicin gidan da mahafinta ya kama musu zamansu masha Allah sai sambarka. Watansu biyar da aure Maimuna ta soma fito da ainihin kalarta. Da farko ya ɗauka amarci ne amma daga bisani sai ya gane haka take. Maimunatu bata kwaliya in ba biki ko suna zata ba ko gidansu, kullum a kaya daban take amma in fitace takan cancara kwaliya kamar amarya ta fice. Yasha zaunar da ita ya yi mata nasiha amma a banza a haka suka shafe shekara da rabi da ɗansu me shekara ɗaya cikin ikon  Allah, ubangiji  ya haɗashi da yan china suka fara bashi kaya nan da nan ya kuɗance ya samu kuɗi sossai a  shekarar data  ya ye Ammar da cikin Ammatullah ya siyamusu gida a unguwar Nassarawa suka koma jikin gidansu Suhaima wannan shi ne sillar amincinsu da Maryam. Ya karɓota ya sata makarantar kuɗi bashi da buri wanda ya wuce Maryam ta yi karatu a haka ta kammala secondary ɗinta tana jiran sakammako.


Zaman Maryam da Maimunatu wani irin zamane mai wuyar fassaruwa, Maryam nada hakuri amma tana da zuciya da faɗa idan ka taɓota gata mace mai tsantsani wajan kare dokokin ubangiji tare da nunawa duk wanda ya kusanceta illar abinda ƴyake aikatawa matukar ya kauce hanya. Wannan yasa basa shiri ko kaɗan ita da ita.

***

A hankali Suhaima ta buɗe kofar ɗakinta taga tabbas Abbas baya nan sai ta yi kwafa ta zaro wayarta ta dana kiran Fawzan. Cikin nishaɗi take sauraran yadda kiran yake shiga can ya ɗaga.+


"Assalamu alaikum my Fawzan".

Ya yi dum cikin sakan guda ya canki muryar mamaki ya kamashi ganin ba layinta bane ya kanne.

"Ya dai babyna?".

"Hmm! Aini kamanta dani Fawzan".

"Waya faɗa miki? Nakiraki bana samu kwanaki".

"Gashi ko kirana baka yi ba tun rabuwarmu wayata aka sace wannan ma tasa ce na ɗauke yaki siyamun waya Mama ce ta hana wai nafi zama wai kar mu dinga waya dakai".

"Kiyi hakuri to".

"Ya wuce ina labari?".

"Labari yana gunki wallahi, fatan harka ta faɗa?".

"Mtss! Faɗawa kamar ya? Ance maka ni sakarai ce? Na gaya maka zan dawo gareka ko".

Dum! Fawzan yaji saukar kalamanta kamar saukar aradu, can ya gimtse cikin sallon yaudara ya gyara zamansa,

"kai! Amma naji daɗi ina dakonki wallahi".

"Hmm! Waikai son wasa nake maka?".

Sun jima suna musayar kalamai daga bisani ta datse kiran ta faɗa kicin ta sa kuku ya dafa mata indomie ta yi wanka ta kyafe.

***

Fawzan ya sauke wayar tare da sakin wata shu umar dariya, Aisam ya dubeshi

"ya dai mutumina?".

"Barni da wannan wawuyar mana, ni banza ne tana gidan miji zan yadda ina kiranta tajamin sallalar tsiya in ta kirani dai zan ɗaga".

"Wai kana nufin Suhaima?".

"Ita mana Aisam ai tunda na yi gwajin takalmina na wuce babinta, ni nama kusa barin kasar Daddy ya ce United  zan tafi karatu".

Dariya suka yi tare da tafawa, suka mike suka bar wajan.

***

"Wai yaya Abbas me yake damunka? Duk ka lallace kai kumarin amarcin ma baka yi".

"Babu komai Hamza kawai typoid ke damuna".

"Hmm! Allah ya kyauta to Yaya".

"Amin".

Ya faɗa fuska a gimtse daga bisani suka sako wata hirar.

Ɓ  Kwanci tashi Suhaima ta share wata biyu gidan Abbas, iskanci kusufa kusufa ta iya shuka masa. Daidai da ruwan tea bata taɓa ɗora masa ba ya kawo kara Hajiyarta ta wanke kafa har gidanta tayi mata tas amma bayan tafiyarta saiya gwamace dama bai kai ba saboda abun nata karuwa ya yi. Cikin haka Ajlah ta zo gidan ta iske yanayin da suke ciki hankalinta ya yi masifar tashi ga kananun maganganun da take ji cikin unguwa yadda Fawzan ke zama majalisa yana faɗin yadda suke waya  da ita karshe kuka tasa mata saboda bakin ciki.


Suhaima ta yi sororo tana dubanta, zuciya ta tunzurota saita hauta da zagi karshe ko kuɗin mota ba ta bata ba Aljah ta fito rai ɓace a harabar gidan ta yi karo da Abbas da Ma aruf ta sunkuya har kasa ta gaisheshi ya yi jim yana NADAMA inama yabi zaɓin Mamansu ya karɓi Ajlah maimakon Suhaima tabbas ya yadda SON ZUCIYA ɓacinta bai aune ba yaga Ma aruf na jefa mata kallon kauna sai ya ɗauke kai ya bata kuɗin transport ya wuce ciki. Ma aruf ya dinga jan Ajlah da hira tana kaucewa karshe dai shi ya kaita har bakin layinsu. Yana barin wajan bata zame ko ina ba sai gidansu Maryam ta yi sa a kuwa Aunty Maimuna bata nan sai Maryam da Ammatullah da yayanta. Sai dai yadda taga Maryam ta zage tana aiki jikinta ya yi matukar sanyi, tana mamakin yadda matar yayanta ta ke bautar da ita kamar wata ɗiyarta jiki a mace ta yi sallama ta ɗago tana amsa mata fuskarta ɗauke da murmushi ta tareta da fara a,

"a a kanwa yau ke ce a gidan?".

"Ni ce yaya ina Aunty Maimu?".

"Bata nan walimar kawarta ake yi, taje can wajan gidan Suhaima".

Cikin mamaki ta gwalo ido,

"Amma tabar Ammatu ɗiyar dake shan nono?".

"Hmm! Kedai kin cika abin dariya wallahi yau kika fara gani?".

"A a yaya wallahi ni in zata shiga gidanmu bata zuwa da ita na ɗauka don kusane amma ya yi nisa wallahi".

"Hmm! Bata ɗaukarta in kinga ƙmunje da ita to tare muka fita, saboda suwagarta ce take yin kasa".

"Allah ya kyauta to amma yaya akwai matsala fa".

"Matsalama baba kanwa na rasa mai matan yanzu suka ɗauki rainon yaransu wai ki haifi ɗa ki kasa jansa jikinki. Mata da yawa na yin sakaci wajan goya yaran da suka haifa, bisa wani dalili mara tushe a cewarsu ci baya ne ki ɗauki wanka ki goya yaro. Wasu kuma kan cewa wai kar a zubar dana fulani ya takune da matsewa. Lokuta da dama nagan hangi wauta a wannan tafiya domin a dalilin rashin son goye ne ake fara ɗora karamin jariri a kafaɗa iskar duniya na baɗeshi. Sakacin da ake Ajlah shi ne a sakammakon iskar da zai shaka ba tare dake kin sani ba ya kan iya shago iska mai ɗauke da cutar data fi karfin yarintarsa. Ganganci na biyu daga ɗaukar kafaɗa zaki fara sarewa sha awar barina gida ta ɗarsu cikin ranki, ki duba Ammatu don Allah yarinya wata biyar ta koyi cin abinci ta karfin tsiya to babu nono babu kulawar uwa. An fara ajiye yaro a gida tun yana da watanni kaɗan, babbar illar ita ce may be wadda zaki barwa karamar yarinya ce daga nan ta fara yunkurin tura masa abinci tun bai isa ci ba. Na kan rasa waima meya ke ruɗarmu baki ji wuyar ɗaukar ciki ba sai ɗauka da goyawa.

Rashin goya yaro ko kulawa dashi kan kawo raunin shakuwa tsakanin mahaifiya da ɗanta.  Ya kan haifar da rashin jin kai ko tausayi.

Yakan haifar da shakuwa tsakanin mai kula dashi saɓanin mahaifiyarsa. Ki duba yadda na shaku da Ammatu ko muryata taji kuka take ko hannun wa take".


Ajiyar zuciya Ajlah ta sauke,

"Allah yaya kin ƴhuta kinma fi wata matar auran".

Murmushi ta yi tana harararta,

"lafiya na ganki a birkice?".

"Hmm! Inafa lafiya yaya, abun ne na yaya Suhaima sai Allah shiyasa naga ba wanda zan tunkara saike har Mama taje ita da yayarmu sun ƙmata faɗa amma wallahi ni dai ban gamsu da tarbiyar gidan auranta ba ki taimaka kije gareta".


Jikin Maryam yayi mugun sanyi ta dubeta cikin ɗaurewar fuska,

"ita ta tiroki wajena kanwa?".

"A a yaya gani na yi kunfi kusa da ita ke ya kamata ki nuna mata amfanin zaman taren kenan".

Hata buɗe baki zata yi magana saita fasa,

"zanje sati na sama sabida wannan satin ina ciku cikun shiga makaranta na sami gurbin karatu".

"Masha Allahu yaya Allah ya taimaka".

Da ƴhaka suka yi sallama ta wuce gida ko a fuska bata nunawa mahaifiyarsu abin da yake faruwa ba saboda tsoron faɗanta.

***

Tunda ta doso wajan idon Musa kur a kanta, shigar material ta yi mai ɗaukar ido ɗaurin nan ya tsaya kamar an kafa gwaggwaro ta zuba fassion kafarta takalmine hill ta ɗana jaka komai nata tumac. Tafiya take ɗas! Das!! Das!!! Ya dinga rakata da idanu harta giftasu Sadi ya ɗaka masa duka,

"kai Musa MATAR AURE CE fa".

"Mtss to ni ba mijin aure bane? Malam kabarni in kalla kawai".

"Kai yanzu in kayi aure kaga ana kallon matarka haka zaka ji daɗi?".

"Allah ya kiyayema matata ta yi wannan shigar Sadi, kai mugune ya kakemin bakin fata ne eyye!".


Ganin ƴyadda ya taso masa sama yasa ya kyaleshi suka kawo wata hirar daban, kai tsaye Maimunatu gidanta ta shige tun daga soro ta cika da mamakin yadda yasha gyara rike da haɓa ta shiga,

"a a Mairo yau kinsha aiki".

Murmushi ta yi,

"Aunty har kin dawo ashe?".

"Ke na dawo sannunki gida ya ɗauka, mtss! Duk yayanki ya jamiki ance ya ɗauki yar aiki yaki ai kuwa bauta yanzu kika fara tunda baki da mashinshini bale in fara tunanin aure zaki yi. Kin kime a gida duk yan year ɗinku daga me aure sai me sa rana da kawo kuɗi sai me wata biyar da aure gadai Suhaima ta isheki ishara".

"Dakata Aunty! Shiru shiru fa ba wasa bane, dan kin ga ina kyaleki bafa tsoranki nake ba keda kika yi auran me zaki nuna min? Dubarki kaxama dake gidanki kullum a datti yaranki babu kulawa bale shakuwa tsakaninku amma kece me bakin magana".

Mamaki ya kashe Maimu ta yi kan Maryam zata daketa kyam ta tsaya tana huci, tana karasowa ta ɗagata ta maka da kasa tim. Ammar ya kwashe  da dariya Maryam ta harareshi sai ya yi ɗaki da gudu nan kokawa ta sarke musu Allah ya kawo Sulaiman da kyar ya rabasu yana masifa ya dubesu.

"Meya haɗaku?".

Maimuna saita sa kuka, taki magana ya yi  juyin duniya taki magana ya dubi Maryam.

"Baki da kunya kike kokawa da matata?".

Kanta a kasa ta warware masa komai ya sauke idonsa kan Maimuna da tayi yarkace yarkace saiya samu zuciyarsa a kuntace musamman daya duba shigarta da alama dawowarta kenan.

"Maimu a haka kika je unguwar?".

Turo baki ta yi, ai kuwa ya shaka,

"kin cucceni wallahi kin zubar da duk wata tarbiya da kika samu a gida kin ari wata kin yafa. Wai Maimu me kika ɗauki aurene? Anya kina tuna ke MATAR AURE CE wallahi ko Maryam bata yin shigar da kike yi".

"Dakata! Abban Ammatu wai kai sokake a rainani cikin kawaye? Kullum mutum ya zauna a gidahumance haka ake rayuwa?. Ai wannan ma takura ce wallahi abu yazo da zamani sai ahanani rawar gaban hantsi,  Maryam kace ni kuma Maimu sunana tsarin zubin hallitarmu daban haka hallaya baga shinan rashin wayewar ya hanata auruwa ba sai gidahumanci takema mutane a gida!".

Takaici yasa ya bar mata wajan, ta yi kwafa tare da kai hannu zata ɗauki Ammatu saita canyare da kuka tilas ta barwa Maryam ɗin ita ta wuce ɗakinta tana yadda kanannun maganganu marasa tushe.Tunda Musa suka rabu da Sadi surar Maimu take masa gitso cikin idanunsa, gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa dare ya tsala amma juyi kawai yake kan shimfitarsa. Ya kula wancan ya kwance wancan har goshin asuba da kyar ya samu ya runtsa.

***

Maryam kwana ta yi tana saka da warwara kan yadda zata fuskanci Suhaima babban tadhin hankalinta yadda aka ɗaura auran Suhaima bisa rashin sani hakan ya  tsaya mata a rai matuka ta yi kuka ta yi kuka har idanunta ya tasa. Washegari Maimunatu ta tashi fuska babu walwala ba wanda ta kula a gidan babu wanda ya damu. Maryam ta shirya Ammar Abbansa ya wuce makaranta dashi.

SATI DAYA......

Cikin tsakiyar dare ne misalin karfe ɗaya da rabi sannu sannu ta riski kanta a wani wawwakeken rami mai cike da tarin wasu irin hallitu tunda take a duniya bata taɓa ganin halitu masu muni da tsoro irinsu ba. Ta duba gabas da yamma kudu da arewa amma babu wata hanya ko madafa da zata iya fidata cikin ramin. Cikin zafin nama hallitun ke kawo mata sura tana kaucewa tashin hankalinta ya karu lokacin data ɗaga kai saman ramin taga ya mammaye da wuta jajjur take ta kwala wata giggitaciyar kara daidai lokacin hallita ɗaya ta yi nasarar cizonta a idon sahunta ta dafe wajan tana gunjin kuka.

    Ta buɗe ido tarwai sai taganta akan tangameman gadonta, gumi ne ko ina yake zuba a jikinta, jikinta banda rawa babu inda baya rawa ta kuma duban ɗakin dunɗum dashi saita fashe da kuka. Kunna fitilar ɗakin ta ki ta kasa koda motsi ta zauna ta buga tagumi. Har asuba bata runtsa ba.

***

Zaune yake a office ɗinsa ya buga uban tagumi, koda wasa bai san abin da yake damun Suhaima ba yadda duk take ikirarin ta tsaneshi abin ya ɗaure masa kai a tunaninsa dukiya na siyan komai ashe dukiya bata siyan so yau Suhaima ta tsaneshi ya yin da shi kuma bashi da abin so irinta kyanta yafi komai ruɗarsa amma a ɗan tsakanin nan hallayanta na neman dakushe kaifin kyawun da yayi tasiri a zuciyarsa. Suhaima dai gata a gidansa amma babu kwanciyar hankali in kaga walwalar Abbas to kuwa a wajene cikin abokai. Yayi nisa cikin tunani Sulaiman ya turo kofar office ɗinsa ya jima a kansa ba tare daya san da zuwansa ba saida ya bubbuga bencin nasa sannan ya numfasa ya dubeshi,

"Lafiya Abbas?".

"Lafiya lau wallahi Sulaiman".

"Ban yadda ba wallahi".

Jikinsa ya yi sanyi ya gimtse tare zama,

"kowa ya ganka yasan kana da damuwa bawai na takura sai naji damuwarka ba amma karage tunani".

Abbas kansa a kasa sai ya sami kansa da duban Sulaiman ya ce,

"Sulaiman aure nake son karawa".

"Aure Abbas? Yaushe ka yi aure watanka fa uku da kwanaki".

"Hakane zai bani nutsuwa Sulaiman kayimin alfarmar bani auran Maryam".

Das! Gabansa ya faɗi ya dubeshi,

"a a Abbas ba zamu yi haka ba karka manta Suhaima kawar Maryam ce kuma a sanadin zuwa gidana ka haɗu da Suhaima gaskiya koda Maryam na sanka muka yi hakan bamu kyautaba. Balantana banajin tana ra ayinka, karatu shi ne a gabanta kuma kasan komu suwaye bamu da kowa a garin nan kowa namu sun kare banjin danginka zasu goyi bayanka".

"Daina Sulaiman kuɗi ai sune yaddarsu mudun zan sakarmusu. Kaje ka shawarci Maryam nasan bata musanta umarninka".

"Dalilan kara aure nada yawa Abbas, matarka bata da makusa burinka auran mace mai kyau kuma gata ka samu kanwata bata dace da tsarinka ba".

"Sulaiman ya isheni nace!".

Ganin ya tunzura yasa ya mike suka yi sallama ya wuce.

***

Tafe Sulaiman yake yana tunanin takadamarsu da Abbas, tabbas yana neman alfarmar da yake tunanin bazai iya yi masa musu ba Allah ne yayi nufin samun arzikinsa amma Abbas ne sanadi shiya haɗashi da yan China. A haka ya karasa gida yana tunanin mafita.


Abbas tun fitar Sulaiman ya zurfafa cikin tunani me yake damunsa kuma yake burin auran Maryam?. Haka ya tattara ya kwashe komai ya hau motarsa yana tunani, komai ya kwance masa. Ya runtse idanu yana tunanin suffarta baka ce sossai a bakin yan maiduguri ma saika tona kan kasami irinta. Idanunta kanana ne sossai sai dogon hanci da karamin baki fuskarta nada tsayi sossai tana da diri irin matan nan ne dogaye samɓal amma akwai rashin kauri daga ciki kamar ta ɓale sai dai daga kunkuminta tana da cikar hallita. Bai aune ba ya kusa bige wani tsoho da karamin yaro suna bara bakin titi ya yi ribas yana ambatar sunan Allah.

***

Kwanci tashi tsayin kwana uku kenan Sulaiman na juya maganar abokinsa a ranar na huɗune ya yanke hukunci kai tsaye ya sanar da Maimu zai aurar da Maryam. Hankalinta ya dawo jikinta daidai lokacin data zurfafa wajan dana wayarta ta dubeshi,

"Wai Maryam zaka aurar? Ina ta sami mijin?".

"Hmm! Miji Allah ne ya bata kuma zaki sanshi bada jimawa ba".

"Allah yasa da gaske kake".

Sai ya kauda hirar suka kamo wata, da haka ya fice ya bar gidan. Tun fitarsa ta batun auran ke mintsinin zuciyarta saita mike ta nufi ɗakin Maryam tana zaune tana tunanin hanyar zuwa gidan Suhaima ta dubeta,

"Amarya ashe kin kusa aure Allah ya yi aure da mara kwabo ina ce ko Musa na bayan layi zaki aura?".

Batun taji kamar almara amma bata tanka ba, ta kwashe da dariya tare da wulamata wani kwalin abu kamar makilin,

"gashi nan ki fara mutsukawa kafin lokacin don wallahi wannan bakar fuskar taki kamar kwalta ba ango ba danginsa ma sai sun tsorata".

Saroro ta yi tana dubanta harta fice tabar ɗakin kawai saita furta,

"sabon salo kuma yau tazo dashi Allah ya shirya fatata ta isheni".


STORY CONTINUES BELOW

BAYAN SATI BIYU.....

A hankali Fawzan ya soma kin ɗaga wayar Suhaima karshe ma saita ke jinta a kashe. Hankalinta ya yi mummunan tashi ta rasa nutsuwa kwata kwata. Ranar data yi nasarar samunsa na karshe ya caccaɓa mata magana san ransa tare da gargaɗinta karta kuma nemansa karshe ya yi mata albishir da ya samu gurbin karatu zai bar kasar kuma layinsa daga yau ya daina amfani dashi. Kara ta saki tare da rushewa da kuka mai tsanani tana kiran,

"Fawzan ka cucceni".

Tun daga ranar bata sake samunsa ba, kwata kwata Abbas ya fita harkarta ko magana ya daina yi mata abinci kuwa gun cin abinci yake fita yaci ko gidan Hamza. Suhaima duk ta rame ta fita hayyacinta ga mugayan mafarkai da take yi masu ban tsoro BABI NA BIYAR

Koda Sulaiman ya fita kai tsaye office ɗin Abbas ya nufa ya sanar masa ya nan da sati ɗaya su aika kuɗin neman aure Aisami da sharaɗin zata cigaba da karatu. Bai damu ba ya nuna amincewarsa daga nan Sulaiman ya wuce Aisami ya sanar da mahaifin Maimuna.


***

Maryam yini tayi tana jujjuya batun Auntynta, bata kara mamakiba saida taji tana waya tana faɗawa kawayanta hankalinta ya tashi ta soma tunanin karatunta. Har ta ɗauki waya zata kira yayanta saita fasa tajira dawowarsa. Da yamma kuwa saiga shi ya dawo saita kasa yi masa magana ya lura da rashin walwalarta sossai sai ya share. Da dadadare ya haɗasu baki ɗaya ya yi wa Maryam nasiha sossai karshe ya sanar da ita zai aurar da ita nan da wata biyu. A kiɗime ta ɗago tana dubansa, bakinta ya suɓuce

"yaya karatun fa?".

"Zai barki ki yi karatu Maryam".

Wani murmushi ya suɓuce mata, dukda bata da tsarin aure a yanzu amma taji daɗin tsarin yayanta ta tabbatar bazai maita zaɓin tumun dare ba koba komai ta ƴhuta gorin Maimu.

***

Kwanci tashi komai ya kankama batun maganar auran Maryam har zuwa kai kuɗi da sa rana amma Maryam bata san waye mijin ba.

                 ***

Gudu take tana faɗuwa gaba ɗaya jikinta ya sami raunika burinta ta gujewa mutumin dake bibbiyarta bata yi aune ba ta ruski kanta gaban wawakeken rami yana ci da wuta ganga-ganga ta juya saita ga yana binta hannunsa ɗauke da wuka mai tsananin haske ta runtse idanu tana jiran tsamani harya risketa ya ɗaga wukar zai caka mata ta  soma kuka tana rokonsa,

"kai min rai na tuba!".

Take ya ye mayafun daya rufe fuskarsa,

"baki tubaba Suhaima, kinci amanar mijinki kinci amanar iyayanki da mahalicinki".

Kwala kara ta yi sakammakon ganin fuskar mahaifinta, tana juyawa ta hango an ɗago Fawzan an wulashi ramin ta kara rikicewa ya ɗagata zai jefa ta yi firgigit ta farka a kuɗime. Sai ta fashe da kuka tana faɗin,

"na shiga uku gashi Abbas yayi tafiya sai washegari zai dawo nan da nan ta kiɗime ta janyo wayarta ta kira  layin Maryam saida ya soma shiga ta duba agogo karfe ɗayan dare sai tayi dana sanin kiran.


Lokacin da wayar ta shiga Maryam na kan dadduma tana tsaka da jan carbi ta katse ta ɗauka, shasshekar kuka ce ta yi mata sallama ta yi saurin duba numbar bata san layin ba ta furta.

"Hello".

"Mar...yam!".

Tuni ta watsake ta gano mai muryar,

"Suhaimah! Ke ce?".

"Ni ce Maryam kaicona don Allah kizo gareni".

Saida ta saisaita numfashinta sannan ta  cigaba,

"banda nutsuwa! Banda kwanciyar hankali GIDAN AURENA ya zamo ABIN TSORONA kaicona NADAMA na tattare da RAYUWATA".

"Ya isa Suhaima a kowace dakika ina tare dake".

"A a Maryam baki tare dani, yaushe raboki dani kin fice a rayuwata kin barni da hallayata wallahi nayi NADAMAR RAYUWATA bani da wani amfani".

"Koma menene ki tashi kiyi alwala kiroki ubangiji zan shigo gobe insha Allah shiya kamata ya san matsalarki fiye dani da kika kira".

Saita datse layin tana maida numfashi mai zafi zuciyarta ta cake da tunanin rayuwar Suhaima duk abin da yasa ta kirata a wannan tsohon daran mai tsananine. Suhaima na aje waya tabi umarnin Maryam ta faɗa banɗaki ta dubi gabas.

***

Washegari haka ta tashi sukuku, misalin karfe goma ta kuna labaran safe ta samu ana sanarwar haɗarin jirgin waɗanda suka bar Nigeria zuwa United a daran jiya cikin jerin sunayen ne ta tsinci sunan Fawzan  a sanarwar waɗanda suka rasa rayukansu. Kasa aikata komai ta yi  saboda tashin hankali banda kuka babu abin da take yi. Tun safe har azahar hakan ya haifar mata da matsanancin ciwon kai. Ta kasa sarrafa kanta, a haka Maryam tazo ta sameta hankalinta ba karamin tashi ya yi ba.


Da sauri takaraso ta ɗagota daga kwanciyar ta raɓata da jikinta,

"Suhaima lafiya? Menene yake damunki?".

Gaba ɗaya ta kwanto jikinta tana cigaba da razgar kukanta,

"ki faɗamun mana Suhaima, waima kinci abinci?".

"Banci ba".

Ta faɗa a takaice,

"mtss! Ki kashe kanki a banza KUKA NA MAGANI ne?".

Zameta ta yi ta faɗa kicin ta haɗa mata ruwan zafi ta dawo ta taimaka mata tasha. Bayan ta gama ta sata ta yi wanka suka yi la asar saida ta nutsu sannan ta dubeta,

"menene yake damunki Suhaima?".

Muryarta ta yi rauni, saita saki kuka. Cikin takaici ta dubeta,

"ba kukanki nazo saurara ba".

Saita haɗiye kukan ta zauna cikin kuka ta warware mata alakarta da Fawzaan da irin zaman da take cikin gidan karshe ta dire da faɗin,

"kaicona! Kaicona!! Kaicona!!! Maryam Fawzaan ya tafi ya barni acikin wannan duniya mai cike da ruɗani wai Fawzan ya rasu ya rasu Maryam!".

Mutuwar zaune Maryam ta yi gaba ɗaya ta rasa abin faɗa, mamaki da takaici ya ɗumeta saita samu kanta da faɗin,

"innalillahi wa inna ilaihirraji un! Kaico Suhaima wannan wace    irin rayuwa kika ɗaukarwa kanki?. Lallai muna cikin WATA RAYUWA da ZINA ta zama ba komai  ba a idon al ummah!".

"Maryam ki faɗamun ya zanyi, in gyara BABBAN KUSKURAN DANA TAFKA a rayuwata?".

"Duk mai saukine Suhaima bawa kan iya gyara kuskure matukar ajali bai riskeshi ba. Amma da farko dole kiyi istibira sannan ki fito ki nunawa Abbas gaskiyarki a sake ɗaura muku aure".

"Kina nufin in fito in sanar masa na taɓa aikata mummunan aiki makamancin wannan?".

"Tabbas haka zaki aikata hakan ne zai tsairar da auranki daga zaman haramci".

"Maryam Abbas bai taɓa kasancewa dani ba tsayin zamana a gidansa".

Gabanta ya faɗi ta kare mata kallo ta numfasa,

"abin naki da sauki kawai ki fito ki sanar dashi zai fi sauki tunda a zamanki a gidan nan sau nawa kikayi bako tsakaninki da Allah?".

"Sau huɗu nayi bako wallahi Maryam".

"Masha Allah istibira inki ya tabbata abin da ya rage yadda zamu tunkari Abbas da batunki ya fahimcemu".

"Waike sai batun istibira i kike ni kuma banma san ya ake yi ba".

Murmushi ta yi sannan ta dubeta ta ce,


"Isibra’i na mata wani jini ne da macen da ba tada kamun kai keyi kafin tayi aure, ko wacce aka yima fyade don gudun kada taje gidan wani da cikin wani daban. Kuma asalin sa mata bayi keyi, amma a yau abin ban mamaki sai kiga yarinyar da bakk taɓa tinanin za tayi zina ba. Idan auranta ya zo sai

kaga tana istibta’i. Ga ta dai kullun cikin shigar musulunci amma kuma abin da takeyi a ɓoye babu kyau. Don haka duk yarinyar da tayi zina

ko bazawarar da tayi zina sannan kuma maganar auren ta yazo, to dole ne fa sai tayi istibra’i kafin tayi aure. Idan kuma bata yi ba aka ɗaura auran a haka dagangan, to wannan auran babu shi, musammam ma idan ya kasance a tsakanin zinan ta na karshe da ranar ɗaurin auren ta babu nisa. Shi dai wannan jinin za ta yi shi ne sau uku(3), wato a ko wane wata zatayi jini daya, kuma ba tare da ta sake saduwa da wani ba sannan sai a ɗaura mata aure da wanda za ta aura, koda kuwa shi ne wanda yayi zinan da ita. Idan kuwa ciki ya shiga to sai ta haihu, haihuwar da za tayi shine istibra’inta, kuma da sharaɗin bayan ta haihu babu wanda ya kara saduwa da ita. Amma wasu Malamai na cewa koda jini biyu tayi ko kuma daya, za ta iya yin auren ta. Game da matar auren da tayi zina kuwa, sai tayi Istibra’i itama, wato mijin ta ba zai sadu da ita ba har sai tayi jinin al’ada a kalla sau daya ko biyu ko uku sannan mijin ta ya sadu da ita,sannan kuma akwai laifin cin amana da kuma haddin zina akan ta. Amma kikara tambayawa mazhabobi da yawa".

"Maryam yanzu ya zanyi, ina tsoron Abbas ya sani wallahi".

"Dole Abbas ƴya sani mudun zaki ɗauki mazhabar Malikiyya tunda ita muka fi tafiya akai".

"Na bani Maryam".

"Baki bani ba sai randa na koraki gidanku Suhaima kin cuceni!".

Muryar Abbas ta ratso falon cikin ammo.Gaba ɗaya sun tsorata da ganin yanayinsa, tambaya suke yaushe ya shigo ba amsa abinda basu sani ba tun fara hirarsu ya nufo ɗakin amma jin kukan Suhaima yasashi tsayawa sai ya yi karo da tashin hankalin dayake ji kamar yana kabari ne. Ya sauke  idanunsa a kanta sunyi jajjur kamar wuta ya nunata yana hawaye,

"kin cuceni Suhaima!".

Sai ya zube yana rike da kansa ta rarrafo tana gunjin kuka,

"kayafemin Abbas wallahi sharin shaiɗane bazan sake ba na tuba".

Kukanta ya dinga mintsinin zuciyarsa abu uku ya haɗe masa a kwanya so, takaicinta da kuma dumbin mamakinta kawai saiya doke hannuwanta ya wuce ɗakinsa zata bishi caraf Maryam ta riketa,

"kiyi hakuri Suhaima!".

"Ya zanyi Maryam?".

"Hakuri zakiyi babu wanda ya isa gujewa kaddararsa KOWA DA TASA KADDARAR. Babu wanda baya shiga jarrabawa dama duk wanda ya biyewa duniya yana tare da dana sani. Allah ya halicci wannan duniya a matsayin mazauni na wucin-gadi don ya jarrabi mutum, ya tsarkake shi daga munanan ayyukansa, ya sanya shi mai tsarkakakke kuma madaukakin ruhi wanda zai kai shi ga samun aljanna, sannan kuma don ya bayyana siffofin kafirai da ayyukansu. Sai dai ‘yan kalilan ne daga cikin mutane suke yin tunani da lura har su fahimci manufar Allah a cikin lamarin duniya; wadannan kuwa su ne masu imani.

Saboda haka, mutum mumini wanda ya yi imani yana kallon duniya ne ta wannan mahanga wadda Alkur’ani ya bayyana. Bambancinsu da kafirai wadanda ba su da darsashin imani tare da su shine, shi mumini ba ya damfara kansa da rayuwar wannan duniya, sai dai yana kokarin nemarwa kansa kyakkyawar makoma a gobe kiyama. Da ya ke ya san an halicce shi ne “don ya bautawa Allah shi kadai,” don haka a koda yaushe ya ke tuna ayar nan da ke fadin “Ban halicci mutum da Aljan bs sai don su bauta min.”(Sura Zariyat, aya ta 56). Kisawa ranki hakuri, ni zan wuce gida ki sameshi in ya sami nutsuwa ku tattauna matsalar dashi".


Bata jira cewarta ba ta wuce tana jin gunjin kukanta amma bazata iya karasawa. Cike da tashin hankali ta wuce gida. Tun daga bakin layinsu ta hango jama damkan anata ɗaga manyan wayoyi da alama wani abune ya faru masu rahoto suke ɗauka. Ta yi kwafa cikin ranta tana tsanani jin haushin hakan tana mamakin masu jiran abu kaɗan su yaɗa duk sai suka bata haushi. Gabanta ya ysnke ya faɗi ganin mutane damkan a kofar gidansu gefe ɗaya yayanta ne a tsaye da kuma yan sanda guda biyu ga Musa jina jina cikin jini jiki a sanyaye da kyar ta samu ta ratsa mutane ta shige cikin gida tana shiga ta hangi Aunty Maimu tsakiyar matan layin tana share hawaye.


Da sassarfa ta karasa,

"Aunty lafiya?".

Kafin ta yi magana tabawa dilalliya ta yi karaf,

"Musa ne ya hauro zai mata aika-aika Allah ya kawo yayanki".

"Subhanallah!".

Maryam ta furta kasan ranta ta cigaba da ayyana muna cikin WATA RAYUWA matar aure ma bata tsira ba ta runtse ido tana tambayar.

"Garin ya?".

Ajlah dake gefe ta yi karaf ta furta,

"da yan sanda suka tsarashi cewa yayi kwaliyar da take yi ce take wucesu ta birgeshi ko budurwa ba kowace ke yin irinta ba shiyasa yayanku yace a sakeshi tunda ai yaja mata kunne taki dainawa".

Maryam tayi murmushi kawai ta wuce ɗakinta daidai lokacin yayanta ya shigo duk ya kore matan yana mitar magulmata Aljah tayi wuf ta faɗa ɗakin Maryam suka haɗa ido saita lumshe ido tare da riko hannun Ajlah ta furta.

"Ajlah muna cikin WATA RAYUWA da tsoron Allah yayi karanci, ƘMATAR AURE ƙma bata tsiraba".

"Mtss! Aunty kidaina damuwa ai duk su suka ja".

Ajlah ta faɗa murya a cakuɗe cikin takaici Maryam ta ce,

"NI MATAR AURE CE.........Harga Allah ina mamakin matan dake yunkurin kusanta kansu da faɗin kalmar NI MATAR AURE CE.....alhali idan ka dubesu tun daga kan shigarsu, ɗabi unsu mu amalarsu da mutane kwata kwata baya nuna ainhin kalmar. Babban misali yayin gudanar da biki, suna, ko kuma fita unguwa. Matar aurece zata ƴyi shiga wadda wata budurwarma bata iya ta, ta fito ta zuba gashin doki mayafi a kafaɗa kai a waje in anci sa a ɗiyarma a kafaɗa if not kuma a ajiyeta  a gida da sunan takurawa. Bisa akasi aka samu ɗan bana bakwai ya gani ya taya sai kaji tashin jijjiyar wuya Malam baka da hankali? NI MATAR AURE CE!. Abun tambaya a nan INA AURAN YAKE?"!.


"Hmm! Kema kya faɗa Aunty, sun ajiyeshi a zaure yayin fitar".

Duka takai mata,

"ke gidan Suhaima naje tana gaidaku".

"Kin kyauta ai itama duk samma kal".

Ta sake kai mata duka ta yi waje da gudu.

***

Washe gari haka suka tashi Maimunabata da wani kuzari sai jan Maryam take da fira tana kame kame ita dai binta kawai tunanita gaba ɗaya naga Suhaima lokaci zuwa lokaci takan nemi layinta amma a kashe take samunsa.

STORY CONTINUES BELOW

Suhaima tun tafiyar Maryam ta kasa nutsuwa, abinci kasa ci ta yi ta koma ɗaki ta yi lakwas tana tunanin da nadama. Washegari kamar ko yaushe saijin tashin motarsa ta yi ya fice haka suka kasance tsayin sati guda duk ta rame ta fice hayyacinta ko mahaifiyarta data zo saida ta yi danasanin zuwanta duk iya hikimarta taki faɗa mata abin da yake damunta haka tattatara ta tafi. Abbas ya rasa yadda zai ɓulowa lamarin Suhaima dangane da abinda ya faru, har gobe yana jin santa cikin ransa dan haka ya rasa yanke tartibin hukuncin da zai mata ranar da suka kica kwana goma tana zaune tsumu a fallo ya sameta fuska babu annuri ya dubeta,

"ki shirya zamuje wani waje".

Bai jira amsarta ba ya wuce kai tsaye ta mike babu kuzari jikinta doguwar rigace jikinta ta atamfa, kawai saita ɗora katan hijab ta fito lokacin daya fito mamakine ya isheshi sai kuma yaji daɗi kamar zai yi dariya saiya fasa suka wuce zungui zungui tana biye da shi a baya har cikin mota.

      Sunyi tafiya mai nisa sossai, har suka kawo wani ɗan karamin kyauye ita dai bata iya tantance wana gari bane amma sun bar Kano sossai. A bakin wani ya sauka matsakaici, nan da nan yara suka baibaye motar cikin ɗaurewa ya yi mata magana suka fito wani dattijo ta hango cikin yara yana koya musu karatu mai cikar kammala. Basu yi minti biyar da tsayuwa ba ya tashi yaran ya karaso Abbas ya zube yana gaishe shi  itama haka daga bisani ya wuce ciki suka bishi a soron gidan suka zauna kan shimfiɗarsa inda ya yi musu nuni Abbas ya dubeshi,

"Alagafarta Malam kamar yadda na sanar dakai kwanakin baya abin da ya faru shi ne nazo da ita ta yi mata bayani da bakinta".

Ya dubeta,

"ki masa bayani yadda kika yi wa Maryam".

Gaba ɗaya ya ɗaureta da jijiyoyin jikinta kanta a kasa ta masa bayani tiryan tiryan ya yi shiru tare da nunfasawa ya ce,

"Hakika mazhabobi da yawa sunyi bayani da dama game da cuɗewar lamari irin wannan. Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini ɗaya wanda malamai suke kira Istibra’i, kafin a ɗaura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma idan har an ɗaura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba wannan auren ko da sun haifi 'ya'ya, domin suna ganin an ɗaura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana ɗaura aure a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren vatacce ne kuma rusasshe

   Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi'i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an ɗaura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka kara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka ɗaura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa yana ganin cewa mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa. A cikin magabata daga sahabbai da tabi'ai waɗanda suka tafi a kan haka akwai Abdullahi Ibn Umar da Jabir Ibn Zaid da kuma Aɗa'u da ɗawus da Salim. Wannan kuma shi ne abin da ya fi rinjaye a wurinmu saboda dalilai kamar haka:-


i. Istibra’i ga wadda ta yi zina ba idda ba ne, kuɓutar da mahaifa ne kawai.


ii. Babu wani nassi karara na hadisi da ya nuna cewa matar da ta yi zina za ta yi istibra’i ko idda. Shi istibra’i jini ɗaya ne tak, kuma asalinsa kiyasi ne a kan kuyangun da aka mallaka a fagen yaki. Kuyangu, wato mata masu aure waɗanda aka ribace su a fagen yaki sun zama mallakar Musulmi, sai dai ba a saduwa da su sai bayan sun yi istibra’i. Don haka idan mace ta yi zina, har kuma zinar ta bayyana, an fi so ta yi istibra’i domin ta kuɓutar da mahaifarta kafin ɗaura mata aure. Amma idan aka riga aka ɗaura aure ba a yi istibra’i ba, rushe wannan auren yana bukatar dalili, domin ana rushe aure ne idan aka yi shi cikin idda ko cikin takaba, ba wanda aka yi cikin istibra’i ba.


iii. Kuma Hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Umar ya ce: Manzon Allah ya ce:

Ya ku mutane! Hakika lokaci ya yi da za ku nisanci iyakokin Ubangiji. Duk wanda ya aikata wani abu daga waɗannan kazantar, to, ya yi wa kansa sutura da suturar Allah (ya ɓoye tare da tuba zuwa ga Allah), domin duk wanda laifinsa ya bayyana a gare mu, to, za mu tsayar masa da hukuncin Allah.

Don haka wanda Ubangiji ya rufa masa asiri, to, kada ya tona wa kansa asiri. Haka kuma idan mutum ya auri mace kuma ya same ta da ciki, ko cikin nasa ne ko kuma na wani ne, ko kuma ta gaya masa ta taɓa yin zina, to, kamata ya yi ya rufa mata asiri, domin rabuwa da ita a kan tana da ciki na zina ko ta taɓa yin zina, zai bazu duk duniya ta ji. Idan kuma suna da 'ya'ya, al'ummar da suke rayuwa a cikinta za su ɗauke su 'ya'yan zina ne. Saboda haka gara a rufa asiri a ci gaba da zama matukar sun tuba kafin su yi aure ko kuma bayansa.

Kuma malaman Usul sun ce, Musulunci ya zo ne domin kare abubuwa guda biyar, wanda a cikin su akwai addini da kuma mutunci. To ina kare mutunci, yayin da aka tona asirin irin waɗannan ma'aurata, aka kuma kaskantar da su tare da cin fuska ga 'ya'yan da suka haifa?.


iv. Haka kuma wasu daga cikin manyan malaman Mazhabar Malikiyya na Andalus da Magrib sun yarda cewa, irin waɗannan 'ya'yan waɗanda aka ɗaura auren iyayensu alhali ba su yi istibra’i ba, ana danganta su zuwa ga iyayensu, kuma za su ci gadonsu. Don haka zaɓi na gareku Abbas da Suhaima".


Suka yi shiru Abbas ya numfasa,

"gaskiya Malam a sake ɗauramana aure yafimin kwanciyar hankali kuma mazhabar Imam Malik ita muka fi tafiya akai don haka nafi muradin sabon auran, amma banasan ahalina danata susani zan fiso ka zama waliyinta ni kuma kasami wani babba ya wakilceni gudun a dinga yi mata gori".

"Allahu akbar yaro ɗan albarka gaskiya kayi tunani sha anin mata kam sai hakuri insha Allah bazaka taɓe ba".

Wani sanyi ne ya ratsa zuciyarta a hankali kaunar Abbas ta dinga shiga kowace gaɓa ta jikinta.


Gaba ɗaya sun tsorata da ganin yanayinsa, tambaya suke yaushe ya shigo ba amsa abinda basu sani ba tun fara hirarsu ya nufo ɗakin amma jin kukan Suhaima yasashi tsayawa sai ya yi karo da tashin hankalin dayake ji kamar yana kabari ne. Ya sauke  idanunsa a kanta sunyi jajjur kamar wuta ya nunata yana hawaye,

"kin cuceni Suhaima!".

Sai ya zube yana rike da kansa ta rarrafo tana gunjin kuka,

"kayafemin Abbas wallahi sharin shaiɗane bazan sake ba na tuba".

Kukanta ya dinga mintsinin zuciyarsa abu uku ya haɗe masa a kwanya so, takaicinta da kuma dumbin mamakinta kawai saiya doke hannuwanta ya wuce ɗakinsa zata bishi caraf Maryam ta riketa,

"kiyi hakuri Suhaima!".

"Ya zanyi Maryam?".

"Hakuri zakiyi babu wanda ya isa gujewa kaddararsa KOWA DA TASA KADDARAR. Babu wanda baya shiga jarrabawa dama duk wanda ya biyewa duniya yana tare da dana sani. Allah ya halicci wannan duniya a matsayin mazauni na wucin-gadi don ya jarrabi mutum, ya tsarkake shi daga munanan ayyukansa, ya sanya shi mai tsarkakakke kuma madaukakin ruhi wanda zai kai shi ga samun aljanna, sannan kuma don ya bayyana siffofin kafirai da ayyukansu. Sai dai ‘yan kalilan ne daga cikin mutane suke yin tunani da lura har su fahimci manufar Allah a cikin lamarin duniya; wadannan kuwa su ne masu imani.

Saboda haka, mutum mumini wanda ya yi imani yana kallon duniya ne ta wannan mahanga wadda Alkur’ani ya bayyana. Bambancinsu da kafirai wadanda ba su da darsashin imani tare da su shine, shi mumini ba ya damfara kansa da rayuwar wannan duniya, sai dai yana kokarin nemarwa kansa kyakkyawar makoma a gobe kiyama. Da ya ke ya san an halicce shi ne “don ya bautawa Allah shi kadai,” don haka a koda yaushe ya ke tuna ayar nan da ke fadin “Ban halicci mutum da Aljan bs sai don su bauta min.”(Sura Zariyat, aya ta 56). Kisawa ranki hakuri, ni zan wuce gida ki sameshi in ya sami nutsuwa ku tattauna matsalar dashi".


Bata jira cewarta ba ta wuce tana jin gunjin kukanta amma bazata iya karasawa. Cike da tashin hankali ta wuce gida. Tun daga bakin layinsu ta hango jama damkan anata ɗaga manyan wayoyi da alama wani abune ya faru masu rahoto suke ɗauka. Ta yi kwafa cikin ranta tana tsanani jin haushin hakan tana mamakin masu jiran abu kaɗan su yaɗa duk sai suka bata haushi. Gabanta ya ysnke ya faɗi ganin mutane damkan a kofar gidansu gefe ɗaya yayanta ne a tsaye da kuma yan sanda guda biyu ga Musa jina jina cikin jini jiki a sanyaye da kyar ta samu ta ratsa mutane ta shige cikin gida tana shiga ta hangi Aunty Maimu tsakiyar matan layin tana share hawaye.


Da sassarfa ta karasa,

"Aunty lafiya?".

Kafin ta yi magana tabawa dilalliya ta yi karaf,

"Musa ne ya hauro zai mata aika-aika Allah ya kawo yayanki".

"Subhanallah!".

Maryam ta furta kasan ranta ta cigaba da ayyana muna cikin WATA RAYUWA matar aure ma bata tsira ba ta runtse ido tana tambayar.

"Garin ya?".

Ajlah dake gefe ta yi karaf ta furta,

"da yan sanda suka tsarashi cewa yayi kwaliyar da take yi ce take wucesu ta birgeshi ko budurwa ba kowace ke yin irinta ba shiyasa yayanku yace a sakeshi tunda ai yaja mata kunne taki dainawa".

Maryam tayi murmushi kawai ta wuce ɗakinta daidai lokacin yayanta ya shigo duk ya kore matan yana mitar magulmata Aljah tayi wuf ta faɗa ɗakin Maryam suka haɗa ido saita lumshe ido tare da riko hannun Ajlah ta furta.

"Ajlah muna cikin WATA RAYUWA da tsoron Allah yayi karanci, ƘMATAR AURE ƙma bata tsiraba".

"Mtss! Aunty kidaina damuwa ai duk su suka ja".

Ajlah ta faɗa murya a cakuɗe cikin takaici Maryam ta ce,

"NI MATAR AURE CE.........Harga Allah ina mamakin matan dake yunkurin kusanta kansu da faɗin kalmar NI MATAR AURE CE.....alhali idan ka dubesu tun daga kan shigarsu, ɗabi unsu mu amalarsu da mutane kwata kwata baya nuna ainhin kalmar. Babban misali yayin gudanar da biki, suna, ko kuma fita unguwa. Matar aurece zata ƴyi shiga wadda wata budurwarma bata iya ta, ta fito ta zuba gashin doki mayafi a kafaɗa kai a waje in anci sa a ɗiyarma a kafaɗa if not kuma a ajiyeta  a gida da sunan takurawa. Bisa akasi aka samu ɗan bana bakwai ya gani ya taya sai kaji tashin jijjiyar wuya Malam baka da hankali? NI MATAR AURE CE!. Abun tambaya a nan INA AURAN YAKE?"!.


"Hmm! Kema kya faɗa Aunty, sun ajiyeshi a zaure yayin fitar".

Duka takai mata,

"ke gidan Suhaima naje tana gaidaku".

"Kin kyauta ai itama duk samma kal".

Ta sake kai mata duka ta yi waje da gudu.

***

Washe gari haka suka tashi Maimunabata da wani kuzari sai jan Maryam take da fira tana kame kame ita dai binta kawai tunanita gaba ɗaya naga Suhaima lokaci zuwa lokaci takan nemi layinta amma a kashe take samunsa.

STORY CONTINUES BELOW

Suhaima tun tafiyar Maryam ta kasa nutsuwa, abinci kasa ci ta yi ta koma ɗaki ta yi lakwas tana tunanin da nadama. Washegari kamar ko yaushe saijin tashin motarsa ta yi ya fice haka suka kasance tsayin sati guda duk ta rame ta fice hayyacinta ko mahaifiyarta data zo saida ta yi danasanin zuwanta duk iya hikimarta taki faɗa mata abin da yake damunta haka tattatara ta tafi. Abbas ya rasa yadda zai ɓulowa lamarin Suhaima dangane da abinda ya faru, har gobe yana jin santa cikin ransa dan haka ya rasa yanke tartibin hukuncin da zai mata ranar da suka kica kwana goma tana zaune tsumu a fallo ya sameta fuska babu annuri ya dubeta,

"ki shirya zamuje wani waje".

Bai jira amsarta ba ya wuce kai tsaye ta mike babu kuzari jikinta doguwar rigace jikinta ta atamfa, kawai saita ɗora katan hijab ta fito lokacin daya fito mamakine ya isheshi sai kuma yaji daɗi kamar zai yi dariya saiya fasa suka wuce zungui zungui tana biye da shi a baya har cikin mota.

      Sunyi tafiya mai nisa sossai, har suka kawo wani ɗan karamin kyauye ita dai bata iya tantance wana gari bane amma sun bar Kano sossai. A bakin wani ya sauka matsakaici, nan da nan yara suka baibaye motar cikin ɗaurewa ya yi mata magana suka fito wani dattijo ta hango cikin yara yana koya musu karatu mai cikar kammala. Basu yi minti biyar da tsayuwa ba ya tashi yaran ya karaso Abbas ya zube yana gaishe shi  itama haka daga bisani ya wuce ciki suka bishi a soron gidan suka zauna kan shimfiɗarsa inda ya yi musu nuni Abbas ya dubeshi,

"Alagafarta Malam kamar yadda na sanar dakai kwanakin baya abin da ya faru shi ne nazo da ita ta yi mata bayani da bakinta".

Ya dubeta,

"ki masa bayani yadda kika yi wa Maryam".

Gaba ɗaya ya ɗaureta da jijiyoyin jikinta kanta a kasa ta masa bayani tiryan tiryan ya yi shiru tare da nunfasawa ya ce,

"Hakika mazhabobi da yawa sunyi bayani da dama game da cuɗewar lamari irin wannan. Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini ɗaya wanda malamai suke kira Istibra’i, kafin a ɗaura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma idan har an ɗaura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba wannan auren ko da sun haifi 'ya'ya, domin suna ganin an ɗaura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana ɗaura aure a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren vatacce ne kuma rusasshe

   Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi'i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an ɗaura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka kara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka ɗaura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa yana ganin cewa mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa. A cikin magabata daga sahabbai da tabi'ai waɗanda suka tafi a kan haka akwai Abdullahi Ibn Umar da Jabir Ibn Zaid da kuma Aɗa'u da ɗawus da Salim. Wannan kuma shi ne abin da ya fi rinjaye a wurinmu saboda dalilai kamar haka:-


i. Istibra’i ga wadda ta yi zina ba idda ba ne, kuɓutar da mahaifa ne kawai.


ii. Babu wani nassi karara na hadisi da ya nuna cewa matar da ta yi zina za ta yi istibra’i ko idda. Shi istibra’i jini ɗaya ne tak, kuma asalinsa kiyasi ne a kan kuyangun da aka mallaka a fagen yaki. Kuyangu, wato mata masu aure waɗanda aka ribace su a fagen yaki sun zama mallakar Musulmi, sai dai ba a saduwa da su sai bayan sun yi istibra’i. Don haka idan mace ta yi zina, har kuma zinar ta bayyana, an fi so ta yi istibra’i domin ta kuɓutar da mahaifarta kafin ɗaura mata aure. Amma idan aka riga aka ɗaura aure ba a yi istibra’i ba, rushe wannan auren yana bukatar dalili, domin ana rushe aure ne idan aka yi shi cikin idda ko cikin takaba, ba wanda aka yi cikin istibra’i ba.


iii. Kuma Hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Umar ya ce: Manzon Allah ya ce:

Ya ku mutane! Hakika lokaci ya yi da za ku nisanci iyakokin Ubangiji. Duk wanda ya aikata wani abu daga waɗannan kazantar, to, ya yi wa kansa sutura da suturar Allah (ya ɓoye tare da tuba zuwa ga Allah), domin duk wanda laifinsa ya bayyana a gare mu, to, za mu tsayar masa da hukuncin Allah.

Don haka wanda Ubangiji ya rufa masa asiri, to, kada ya tona wa kansa asiri. Haka kuma idan mutum ya auri mace kuma ya same ta da ciki, ko cikin nasa ne ko kuma na wani ne, ko kuma ta gaya masa ta taɓa yin zina, to, kamata ya yi ya rufa mata asiri, domin rabuwa da ita a kan tana da ciki na zina ko ta taɓa yin zina, zai bazu duk duniya ta ji. Idan kuma suna da 'ya'ya, al'ummar da suke rayuwa a cikinta za su ɗauke su 'ya'yan zina ne. Saboda haka gara a rufa asiri a ci gaba da zama matukar sun tuba kafin su yi aure ko kuma bayansa.

Kuma malaman Usul sun ce, Musulunci ya zo ne domin kare abubuwa guda biyar, wanda a cikin su akwai addini da kuma mutunci. To ina kare mutunci, yayin da aka tona asirin irin waɗannan ma'aurata, aka kuma kaskantar da su tare da cin fuska ga 'ya'yan da suka haifa?.


STORY CONTINUES BELOW

iv. Haka kuma wasu daga cikin manyan malaman Mazhabar Malikiyya na Andalus da Magrib sun yarda cewa, irin waɗannan 'ya'yan waɗanda aka ɗaura auren iyayensu alhali ba su yi istibra’i ba, ana danganta su zuwa ga iyayensu, kuma za su ci gadonsu. Don haka zaɓi na gareku Abbas da Suhaima".


Suka yi shiru Abbas ya numfasa,

"gaskiya Malam a sake ɗauramana aure yafimin kwanciyar hankali kuma mazhabar Imam Malik ita muka fi tafiya akai don haka nafi muradin sabon auran, amma banasan ahalina danata susani zan fiso ka zama waliyinta ni kuma kasami wani babba ya wakilceni gudun a dinga yi mata gori".

"Allahu akbar yaro ɗan albarka gaskiya kayi tunani sha anin mata kam sai hakuri insha Allah bazaka taɓe ba".

Wani sanyi ne ya ratsa zuciyarta a hankali kaunar Abbas ta dinga shiga kowace gaɓa ta jikinta.


BABI NA BAKWAI.. 

Umarni ya yi wa Suhaima ta shiga cikin gidan, suka zauna shi da Abbas. Suhaima ta shiga ciki wajan matarsa ita kaɗaice bata taɓa haihuwa ba mace mai kirki da tsafta ta kama mata aiki tun safe take wajanta bata ji ɗuriyar Abbas ba har azahar.


Hankalinta ya tashi harta soma tunanin ko Abbas guduwa ya ƴyi ya barta saiga yara sun shigo suna murna an raba musu alawa da kuɗi cikin washe baki matar ƙmalam tace,

"halan ɗaurin aure aka yi?".

Gaba ɗaya suka amsa mata da,

"eh! Wai wani Alhaji Abbas".

Murmushi Suhaima ta saki, tana godiya ga ubangiji. Misalin karfe huɗu Malam ya shigo yace ta shirya zasu tafi, saida ya yi mata nasiha sossai suka ɗauki hanya har zuwa lokacin ya kasa sakar mata fuska abun na cin ranta tana danewa sai bayan magarba suka karasa gida yana direta ba magana ya juya kan motarsa ya bar gidan. Dawowarta a gajiye likis bai hanata zagewa ta gyara gidan ba bayan ta yi sallah Allah ya taimaketa kuku yayi abinci taci ta zauna a fallo shiru har tara baidawo ba ta mike a sanyaye ta wuce ɗakinta.


Washegari da safe tana zaune ya shigo cikin shirin fita, waya ya mika mata sabuwa dal,

"ga waya nan ki cire layin wayata karama da kika ɗauke kisa ciki ki bani wayata. Abu nagaba na sallami kuku yau ke zaki dinga yin girkinki da kanki ban lamunci mai girki ba. Mai aikima wanke wanke kaɗai zata dinga yi miki. Ga mukuli nan ki gyaramin sashina".

Duk saitaji kunya ashe yana sane da satar wayar data yi masa, jiki a mace ta sunkuya idonta taf hawaye,

"Abbas don Allah kayafemin!".

"Nayafe miki Suhaima ki nemi yafiyar ubangiji shi zai fimiki idan ni ne an wuce wajan".

Mika masa wayar ta yi da kansa yasa mata layin saida ya bincika yaga ba lambar kowa saita Maryam da Ajlah da kuma mamansu yasa tasa a ciki ya mika mata ya yi gaba abinsa. Yana fita ta kira Maryam ta zayyane mata komai ta lumshe ido tana jin daɗi,

"Suhaima Abbas ya cika mutum ki rike mijinki da kyau. Ki tayani da addu a nima yaya ya karɓi kuɗin aurena kuma bansan waye mijin ba amma yacemin cikin abokansa ne kuma cikin satin nan zai zo mutattauna da sharaɗin zai barni in karasa karatuna".

Haka nan taji gabanta ya faɗi a sanyaye ta furta,

"Allah ya kaimu"

Suna yin sallama Maryam ta ajiye wayar ta fito fallo abin mamaki Maimu ta gyarashi tsaf da farko bata kawo ita ta yi ba saida ta jiyo motsinta a  kicin tana gyara kantar kicin ɗin sororo ta tsaya tana juyowa suka haɗa idanu ta washe baki.

"A a Auntyn yara ya kika tsaya karaso mana".

"Hmmm Aunty mamaki nayi keda kanki".

"Hakane kam Maryam amma ni kaina sai yanzu nake takaicin abinda ya fsru dani da irin tarin zunuban dana ɗauka a baya na maida aurena kamar ba aure ba na yi masa rikon sakainar kashi karshe na kusa yin ɓatan ɓakatantan. Wallahi duk zugar kawaye ce wai ci bayane shigar wadatattun kaya yau gashi ba abinda hakan yajamin sai NADAMAR R RAYUWATA ki duba yarana babu shakuwa tsakanina dasu sabida barinsu a gida tun suna kanana menene ribar wannan rayuwar? Mijina na fushi dani mutane na zunɗena ga hakkin bayin Allah  Maryam dame zanji?".

Tausayinta ya kama Maryam ta dubeta cikin tausassawa.

"Aunty kiyi hakuri komai MUKADARI NE daga rayuwar bawa, mafita kawai a kiyaye gaba. Allah ya kawomu wani irin zamani Aunty mai cike da ruɗani kuma in kika duba babu wani abu a wannan duniya face sai ya gamu da tasirin shudewar zamani; komai inganci da kyawun gidaje, da tsala tsalan motoci masu ɗaukar ido, ko lambunan debe kewa masu kyawu, ko kuma matasa masu zalaka a wurin aiki ko sana’o’insu, babu mai iya kubuta daga tasirin shudewar zamani. Komai sabuntar abu zai koma tsoho, matasa majiya karfi da shu’urin rayuwa su zama tsofaffi. Zamani ke hallaka abubuwa masu daraja a idon dan-adam ya maida su marasa daraja da muni. Lokacin da mutum ke ganiya da holewarsa nan da nan kuma sai ya shude ya zama tarihi kamar ba a yi shi ba. Bayan wani lokaci kuma duk wani abu mai daraja ko jin dadi sukan kasance an manta da su. A wata aya Allah yana sanar da mu irin shu’urin da ke sa wa mutum son rayuwar duniya:

“An kawata wa mutum tsananin sha’awa ga mata da ‘ya’ya, da tarin (dukiya ta) zinare da azurfa, da dawakai na kawa, da dabbobi da gonaki. Wadannan jin dadi ne na rayuwar duniya. Amma ga Allah kyawun makoma yake.” (Sura Al’Imrana, aya ta 14)

Muhimmin abin da za mu fahimta a cikin wannan aya da ta gabata shine, cewa ni’imomin duniya yankakku ne ba masu dorewa ba. Don haka bai kamata ga mutum ya kallafa rayuwarsa a kan wani abin cikin wannan duniya ba, domin kuwa ma a bisa al’ada da halittar mutum ta zahiri wadda ta kunshi kashi da tsoka, har sauran abubuwan duniya marasa daraja da dorewa, babu abin da zai sa su baiwa mutum damar kallafa rayuwarsa ga wannan duniya baki daya. Irin ni’imomin da mu ke gani a wannan duniya wani dan yanki ne daga ni’imomin aljanna da a ka gutsuro mana don tuna mana ranar lahira.

Masu imani wadanda suka fahimci wannan manufa su kan ci ribar rayuwar wannan duniya. Amma akwai wani abu guda da ya bambanta su da sauran wadanda suka rudu da rudin duniya; saboda su muminai ba sa nuna hadama a kan ni’imomin duniya. A maimakon haka ma, a koda yaushe cikin godiyar Allah suke saboda baiwa da ni’imomin da ya yi musu, domin sun san cewa hakikanin mamallakin komai na duniya shine Allah.

Wadanda ke ganin wai sun mallaki dukiya, ko suna da halitta mai kyau, ko kuma suna da karfin mulki a hannunsu, to hakikanin gaskiya suna yaudarar kansu ne, tun da ba su ne suka halicci wadannan abubuwa da suke tinkaho da su ba. Hasali ma, ba su da ikon halittar koda abu guda daya daga cikinsu, haka kuma ba su da ikon kare abubuwan daga lalacewa ko halaka. Su kan su ababen halitta ne da a ka halicce su.... kuma wata rana mutuwa za ta riske su, su tafi su bar duk abubuwan duniya da suka mallaka. In muka lura da wannan aya da ke cewa “Wadannan mutane suna kaunar rayuwar wannan duniya kuma suka sanya tunanin rana mai nauyi (lahira) a bayansu,” (Suratul Insan, aya ta 27) za mu gane abin da ya bambanta muminai masu yakini da kuma wadanda suka shantake a rayuwa, domin muminai a koda yaushe a cikin shirin fuskantar rayuwar gobe kiyama suke ba ta wannan duniya ba. Alkur’ani ya kawo mana irin addu’o’in da su ke yi:

“Daga cikinsu kuma akwai masu cewa ‘Ya Ubangijinmu, ka ba mu kyakkyawa a duniya da kuma kyakkyawa a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta.” (Suratul Bakara, aya ta 201)

A sakamakon iklasinsu da addu’o’in da suke yi, sai Allah ya hada musu ni’imar duniya da ta lahira baki daya. A cikin Alkur’ani Allah ya yi albishir a kan haka:

“Saboda haka Allah ya ba su sakamako na duniya da kuma mafi kyawon sakamakon lahira. Allah yana son masu kyautatawa.” (Sura Al’Imrana, aya ta 148) kinga kenan duk wanda ya kaucewa turbar ubangiji to kuwa yana tare da dana sani".


"Haka ne Maryam na gode ubangiji yasa mu dace, anjima zaki fita ki siyomin hijabai guda huɗu mayafai manya biyu".

"Allah ya kaimu"..

***

Kwanci tashi zama tsakanin Suhaima da Abbas ya mika tun yana shareta harya bada kai bori ya hau suka zama abu ɗaya. Binsa take sau da kafa hakan yafi komai yi masa daɗi. Sau uku yana kaita ta gaishe da mahaifiyarta har gaisuwa suka jewa mahaifiyar Fawzaan taji dsɗi sossai tare da neman yafiyarta. Maimuna kam takoma kamar ba ita ba unguwa saida hijabi in ta kama sanya mayafine takesa babba ko lafayya zamansu da Maryam abin sha awa.

Tun safe suka tashi da shirin taryar bakon Maryam, ita dai jikinta lakwas tarasa abinda ke mata daɗi. Karfe huɗu suka gama komai Ajlah ta kira ta tayata karfe biyar tasamu labarin isowarsa bakin yara kai tsaye ɗakin baki aka wuce dashi saida ta ɓata mintuna sannan ta shiga tare da sallama ya ɗago tare da ansawa gabanta ya faɗi ras! Ras!! Ras!!!.


BABI NA TAKWAS.....


Gabanta ya yanke ya faɗi amma saita tafi kan tunanin Abbas data gani ba shi ne bakonta ba. Sunkuyawa ta yi ta gaisheshi ya amsa da fara a ta mike zata koma ya kada baki ya kirata.

"Maryam dawo mana ina zaki?".

"Yaya Abbas bako nayi, amma banganshi ba".

"Ni ne ai bakon Maryam".

Ya faɗa yana murmushin karfin hali  ta tsaida idonta a kansa da gaske bashi da alamun wasa ji ta yi kafaffunta na rawa ta zube tana faɗin,

"haba Yaya ya zakamin haka?".

Zuciyarta ta karye sai hawaye shi ma take zuciyarsa ta karye yana duba yadda Suhaima ke masa ladabi yanzu bai jin zai iya haɗata da wata mace amma yana kunyar ɗaga idanu ya cewa Sulaiman ya fasa auran kanwarsa saboda matarsa.

"Yaya Abbas ka rasa hanyar rabani da kawata sai kace zaka aureni?".

Kansa a kasa ya furta,

"ba haka bane Maryam in kinki aurena kinsan wazan ɗaukowa Suhaimar?".

"Yadda kake sonta nasan akwai dalilin kara auranka, nasan fa zaman da kuke tunda ta sauya mai zaisa ka kara mata abokiyar zama haba yaya wai mai yasa ku Maza kuke haka ne?".

"Is Ok shikenan Maryam na amince zan janye amma da sharaɗin ke zaki sanarwa yayanki".

"Na amince Yaya".

"Bama saikin sanar mun ba naji komai Maryam Allah ya yi miki albarka irin hangen dana yi kenan amma shi ya kasa fahimtata saboda son rai".

Muryar yayanta kenan ya karaso tare da zama, duk suka yi dariya sun jima suna hira daga bidani ya nemi ganin Maimunatu suka gaisa tasha mamaki abinda Abbas ya yi daga bisani ta bi bayan Maryam kan ba za ayi hakan ba. Haka suka jima suna hirarsu ya yi musu sallama ya wuce.


Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji Maryam ta durfafi karatunta haka mutunci da aminta babu abinda yayi ragi tsakaninta Suhaima haka matar yayanta. Wani lokacin inta tuna yadda Abbas ya nuna sha awar auranta data amince saitake hangen da tuni babu wannan amincin tsakaninsu. To shima Abbas tunaninsa kenan musamman daya fuskanci komai Suhaima zata yi sai tayi shawara da Maryam haka suka cigaba da rayuwarsu gwanin sha awa lokaci zuwa lokaci yakan ɗauki  Suhaima suje su gaida Malam da iyalansa. Shekarar daya biya wa yan uwansa saudiyya a shekarar harda sunan Maryam da Aunty Maimunatu da kuma Ajlah da mahaifiyarsu sai Malam da matarsa. Bayan dawowarsu ne aka yi bikin Ajlah da Ma arruf Maryam da wani lakcara ɗinsu Hafeez  zamansu gwanin ban sha awa. Kwatsam Hamza ya kara aure ya auro Zajla kanwar Fawzaan lokacin Suhaima nada ciki wata huɗu, tattali da kulawa wajan Abbas  kuwa ba a magana nan zumunci ya kullu tsakanin Suhaima da dangin Fawzan har gobe bata fasa sakashi cikin addu a dukda mummunan tabon da ya yi wa rayuwarta.


     Alhamdullilah.....

       Karshe.......

Taku Sanah S Matazu ke cewa,

"A duk yayin da bawa ya sami kansa cikin wani al ammari hakuri da mikawa ubangiji lamari shi ne mafita. Wayo  ko dabara basa fidda bawa a tarkon KADDARA har illa yau shi ubangiji in ka nuna masa wayau zai barka da wayanka ne karshe kuma NADAMA CE. Rayuwar duniya ba komai face ruɗi. Muminai su ne wadanda kyawu da alatun rayuwar duniya ba sa rudar su, duk kuwa da tsananin kyawu da daukar rai da suke da shi. Dalilin wannan kuwa shi ne saboda littafin Allah ya yi musu bayanin sirrin rayuwar wannan duniya filla filla. Kamar yadda Alkur’ani ya ke bayyana mana, ita rayuwar duniya “wasa ce” da “shakatawa” “da ado” “da alfahari a tsakanin mutane” “da kuma gasar tara dikiya da ‘ya’ya.” A cikin wannan aya ta Alkkur’ani, Allah ya buga mana misali wanda ya fayyacce mana matsayin wannan rayuwa ta duniya:

“Ku sani cewa rayuwar duniya wasa ce, da shantakewa, da ado, da alfahari a tsakaninku da kuma gasar tara dukiya da ‘ya’ya. Kamar misalin ruwan sama ne (wanda a sakamakonsa) yabanya ta fita kyawunta ya burge manoma, sannan sai ta bushe ka ganta ta koma ruwan dorawa sannan ta zama karmami (a warwatse). A ranar lahira akwai azaba mai tsanani da kuma gafara daga Allah da kuma yardarSa. Rayuwar wannan duniya ba komai ba ce face jin dadi na rudi.” (Suratul Hadid, aya ta 20).


Allah yasa mu dace....

Post a Comment for "NADAMAR RAYUWATA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...