MIJIN BUZUWA CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MIJIN BUZUWA CHAPTER A

 MIJIN BUZUWA CHAPTER A
🧠MIJIN BUZUWA🧠

Hadari ne ya hade garin sosai baka ganin komai sai walkiya da kara kainan motoci a lokacin wanda suke haskawa don ganin gaban su.

   A daidai wanan lokacin ne motoci guda uku da suka karyo titin a jera wanda ke nuna wani mai akwaine tafe a lokacin yadda mutane suke ta kaucewa a titin suna basu wuri.

   Wasu daga bakin titi ke fadin yanzun haka ma ba maigidan bane tafe wanan fitsarariyar matan tashine haka da bata ganin kowa da mutunci a idon ta.

   Wani gida motocin suka shiga a lokacin gini ne na zamani motan ne suka dan tsaya da alama magana akeyi da wani a cikin gidan.

   Ba a dade ba suka wuce zuwa cikin gidan kai tsaye security ne suka fito don bude motar nan naga wata farar mata buzuwa ta fito tasha ado na fada da gani daga saman ta har kasanta kwaliya ne.

   Doguwa ce sosai ga fari sai dai idan ka kura mata ido zaka iya gano farin ne kawai ke aki yake rudin mutane don kyau akwai kyau inda bamu matan mu na Nigeria masu kyan asali da dire bayan farin da gashi da kuma tsayi babu abin da suka dara matan Nigeria dashi na fannin kyauwo.

   Tana wani tako ta shige ciki zuwa part din ta ta dan jima ciki ta fito tana kwala ma wata mata mai suna Labara kira da karfi .

  Da saurin matar ta iso gareta tana dukawa tare da fadin hajiya barka da zuwa an dawo lafiya yaya han, , , , 

  Dakata tace wa matar yaya naga witan part din can a kunne ko mara zuciyar nan ta dawo ne kuma ?

  Matar ta dago kai a hankali tace wa hajiya babba kike nufi waye hajiya baba ina nufin fatima matar wancan shiyan ta fada a fusace jin an kira uwar gidan nata da hajiya babba taji haushi.

  Eh ta dawo laraba tace ai tun ranan da kuka wuce washe gari ta dawo kutawa tayi tare da juyawa da karfi ta shige part din ta a hasale.

  Anan tabar laraba da kallon mamaki ta nisa tana fadin ikon Allah mata da mijin ta kinzo kin hana zaman lafiya a tsakanin su haka ?

   Ita kuma a daki sai faman huce takeyi ita daya nan ta dauki waya ta kira mijin nasu da suka rabu yau ya tafi waje yin wani aiki.

   Duk da tasan dare ne a duk inda yake amma bai hanata kiran shi ba a wanan lokacin saboda tsananin kishin dake damun ta a lokacin.

   Kiran farko ya tsunke bata hakkura ba ta sake kira a karo na biyu bai daga ba sai wayan na gap da katsewa ya dauka  da alaman barci yake a lokacin .

  Murya irin ta masu barci ya daga wayan tare da fadin Nafisa lafiya kira da dare haka yanzu fa kin san dare ne nan sosai a wanan lokacin.

   Bata jira ya gama magana ba tace watau munafuntana zakayi ashe kasan matar ka ta dawo shine baka fada min ba tun muna tare sai kawai in dawo in samu ta dawo gidan.

   Ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin tadawo fa ni ban san ta dawo ba don basu fada min da cewa zata dawo ba ma kit ta kashe wayan.

  Ta wurga a gefen gadon ta tana fadi a fili duk sai nayi maganin shegun tsofin don sai auren nan ya mutu inga ta bakin naci irin nasu.

  A daidai lokacin ne kuma aka turo kofan side din nata wata matace cikin dogon riga ta dora hijjab a saman rigan nata.

   Fuska da murmshi tace mutanen Abuja ashe kuna tafe yanzu ne an sauka lafiya yaya hanya fuska a daure ta juyo tana fadin eh muna tafe ko idan zan dawo sai na sanar da wani akace ko ma ?

   Ke yanzu don baki da zuciya dawowa kikayi duk da maigidan ya nuna baiyi dake saboda rashin zuciya irin naki sai da kika dawo kamar ana zama dole ne.

   Matar tadan sake murmushin dabai kai ciki ba tace nake ganin ke nan haka amma ni nasan yana yi dani har gobe ke ce dai ganin ki ke rudin ki ga hakan don ko na bar gidan shi bamu rabuba don ga diya ga zumunci a tsakanin mu.

   Fati ke nan zakiko ga abinda ba daidai ba wallahi in dan kin nace sai kin zauna min da miji don sai na rami ya fiki shan iska a gidan nan tunda haka kika zaba wa kanki sannu sugar mai iyali ko tasbi sarkin zumunci shida bakajan da daya bai biyo ka ba .

   Murmshi tayi Allah na tare da mai gaskiya dama jin kin dawo ne yasa nazo taron ki da dawowa ba wani abu ya kawo ni ba a huta lafiya bata tsanmanin ta amsa mata ta fice daga dakin .

   Zuciyar ta yana ciki da mamakin fitsara irin na Nafisa wanda sam babu kunya a cikin shi ko kadan sai zallah cin fuska da fitsara filli.

  Daki ta nufa a daidai lokacin da ruwa ya gauce sosai a garin na kaduna kamar da bakin kwarya da sauri ta isa ta rufe mirrow da sauran abinda baison walkiya a dakin saboda tsaro wanda ba kowa ke wanan ba a wanan lokacin sai masu sani da hakan a baya suka saura rufe irin wa yan nan abubuwan a daki yayin da ruwan sama ke zubuwa daga samaniya don kariya daga fitinan walkiya.

   Falo ta dawo ta zauna tare da yaranta dake cin abinci a wanan lokacin ido ta tsurawa yaran biyu sai da ba wai don tana kallon su hankalin ta yana gare ta ba ne tunane takeyi a zuciyar ta na irin rayuwan da ta tsunci kanta a ciki yanzu.

  Tun shigowan Nafisa cikin su komai na rayuwan ta da mijin nata ya sauya sallo a lokaci daya ba yadda suka saba gudanar da rayuwan su ba suda yaran su da sauran yan uwa.

   Hatta yaran yanzu a matse suke da zama gidan mahaifin nasu sun fison zama a gidan kakanin su da zaman gidan nasu saboda matsin da suke ciki a yanzu.

   Ita dai tasan aure ne a tsakanin ta da mijin ta na soyayya tun tana karama soyayyan su ta samu asali don gidajen su basu da nisa da juna shi din abokin yayan ta ne.

   Kuma akwai zumunci na makwabtaka da ya koma kaman na jini daya a tsakanin gidajen su tun kakan su zumunci ya kulu a tsakanin gidajen biyu.

  Wanda yakai bako ba zai iya banbanta tsakanin su ba sai wanda yasan tushen abin koda ta girma bai daina kulata ba cikin yan uwa haka ya kai har aure ya kullu a tsakanin su.

   Tayi haihuwan farko lafiya ga cikin na biyune ya samu aiki kano suka koma can sun koma bada dadewa ba ya hadu da Nafisa yar mutan Niger da suka shigo Nigeria neman kudi da iyayyenta ta lake mai tun bai kula ta har ya soma kulata don suna sayar masu da abinci a bakin ma,iakatar su ne.

   Yaron ta ne dayazo inda take zaune tana tunane ya katse da da fadin mama daddyn mu bai dawo bane naga anty ta dawo.

   Shafa kan yaron tayi taja sauke ajiyan zuciya tace bai dawo ba Affan da kaga ya shigo nan ai anty ce ta dawo ita kadai.

  Yaushe daddy zai dawo mama yaron ya kara jefa mata tambaya kuma tace Affan ban sani ba idan ya dawo ai zaku ganshi.

   Bai barta ta huta ba ya sake jefo mata tambaya again yace mama ai anty ce bata bari mu ganshi ko munje wurin shi sai tace mu fito muna damun shi yana hutawa.

   Murmushi tayi tace kai Affan ba yana zuwa nan ida muke kuna ganin shi ba to may kuma kake so shiru yaron yayi kamar yana tunane a zuciyar shi.

   Sai kuma yace ni mama ban ma son ya dawo saboda may Affan uwar ta tambaye shi yace saboda idan ya dawo sai ki ta kuka mama su kuma suna dariya da anty kuma su fita tare.

   Affan ban son yawan surutu fa ka faye surutu ina jin tsoron wanan bakin naka kullu naji ka kara fadawa wani matsalan mu sai na yanke ma kunne daya.

  Shiru yaron yayi yana tunanen kada uwar ta yanke mai kune kamar yadda tace din kayan da sukaci abinci ta kawar ta gyara wurin suka shige dakin kwanan su.

   Da safe bata fito ba sai da ta gyara part din nata ta nufi kitchen don dafa ma yara abincin zuwa school sai ta samu kitchen din a rufe.

   Dakin kwanan laraba mai aiki ta nufa a nan ta samay ta tace yau laraba lafiya naga kitchen a rufe  Labara tace aikin hajiya karama ne hakan.

  Nima na fito zan gyara tace na barshi taja kofa ta rufe nayi tunanen zaki fito don saboda abincin yara gashi kuma ta kulle kitchen din.

   Dan jimm tayi tana tunane a ranta  wai may Nafisa take nufi da ita ne haka abinci dai na kowa ne a gidan amma haka take mata idan ta bushi iska sai tace wai ana barnan abinci da yawa gidan.

  Bayan abinci ma da take ita daya sai ta ba wasu balle yanzu da ya samu karin girma sosai a wurin aikin shi basu da talaucin komai a rayuwan su.

  Muryan Laraba ne ke fadin sai hakkuri hajiya idan mutum ya ci gaban ka sai dai bi wallahi gama tana ganin ta samu miji a hannu sai abinda tace a gidan.

   Ba komai Laraba na gode badin tura su can cikin gida wurin hajiya su karba haka ta juya ta wuce zuwa part din ta tabar Laranba a wurin tana jin tausayin ta.

   Daki ta koma ta shirya yaran ta fito dasu da kanta ta mika wa kanin mijin su dake zaune dasu a gidan ya kaisu cikin gida wurin hajiya a basu abinci.

   Yace yau kun makara ne tace eh salis koda na tashi har gari ya haska sosai wallahi kaga idan nace zan tsaya dafa masu yanzu sai su makara.

  Ta koma ciki ya kwashe yaran zuwa gidan su dasu don duk a unguwa daya suke zaune da iyayyen nasu gida uku ne a haka kuma Nafisa ke tsula tsiyar ta a gidan.

  Don tafi son zaman kaduna saboda anan kawayen ta suka fi yawa da yan yaren su na buza da suke kara zugata tana iya shegen.

   Salis na shiga gidan kafin ya isa part din mahaifiyar mijin nasu da yaran matan gidan suka fara magana a, a su Affan ne haka yau da safe nan.

   Salis yace eh maman su ta makara ne yau bata tashi da wuri tayi masu abin karyawa ba shine zasu zo nan su dauka.

   Murmushi hajiya kubura tayi tace Fatice zata makara da safe kawai dai yar bakin halin gidan su ta dawo jiya akwai da wata a kasa.

  Ba an mayar da Fati bata san tadawo ba shine ta dawo ta samay su bakin halin nata na banza ya tashi yanzu ta soma ke nan har sai ta kure ta ta tanka mata.

   Allah dai ya sauwa dayar matar gidan ta fada daga daki tace shi kuma da yazo sai ya biyewa iya shegen nata ba daga daki suke magana.

   Sun shiga gun kakan su tana ganin su tace ai na sani ba yar iskan yarinyar nan ance ta dawo jiya ba nan yanzu tsiya zai tashi a gidan wanan karo  ko ba zan saurara mata ba wallahi.

  Salis yace cewa tayi makara tayi fa bata samu dafa masu abinci ba yau yaya maganan ku yazo daya da na mommy ne ?

   Hajiya bata iyayin magana ba sai jan yaran datayi zuwa cikin part din ta ta zuba masu abincin da tayiwa yan marayun jikokin ta da suke hannun ta.

   Bayan ta gama sallaman yaran ne ta dauki waya ta kira Fati din tace wai may ke faruwa ne yau a gidan naku cikin fara a ta fara gaida surukar nata da bata ko tsaya gaisawa da ita ba.

   Amsawa tayi sama sama dakyat tare da maimaita tambayan ta a gare ta tace hajiya makara nayi tace jinan fati na san komai walahi nasan abinda yar banzan yarinyarin nan zata iya.

   A sanyaye fati tace hajiya ba haka bane makara nayi yau din ban samu dafawa ba kashe wayan hajiya tayi badon ta yarda ba.

  Kashe wayan nata yayi daidai da shigowan hajiya kubura wurin ta tace sai gasu Affan na ga sun zo karban abinci kuma ?

  Bari hajiya Kubura duk da uwarsu ta boye min na san akwai wata a kasa wallahi bai yuyuwa haka kawai taki tanadarwa yara abin zuwa makaranta.

   Nan suka zauna suna maganan hajiya kubura tace idan ita fatin bata iya magana mu ba kyalewa zamuyi ba ai ana horo da yuwa ne kuma ?

   Kai hajiya ta dafe tace Allah ya kawo muna karshen wanan yarinyar a gidan nan hajiya kubura tace amin tana mikewa tare da fadin bari mu gani zuwa rana idan har sun dawo nan kin ga hasashen mu ya tabbata ke nan ta rufe kitchen din nasu ke nan.

   Ta fice ta bar hajiya a cikin bacin rai tana tausaya ma wanan rayuwa da yayan nasu suka tsunci kan su a ciki na bamin auren buzuwa da ya dorawa rayuwan shi yana zaune kalau da matar shi ya jajibo masu wahala haka.

  A gidan Fati kuma bata karya ba tun safe ba tunanen kanta takeyi ba a yanzu sai tunanen idan yaran sun dawo may zata basu idomie ne ya fado mata arai ta sayo ta dafa masu suci.

  Damay zaki dafa wani zuciya yace mata tsaki taja tana tausaya masu a ransu take tunanen da can baya lokacin tana ita kaida ya fado mata a rai.

   Abinci sai wanda ransu ke so zata dafa da ita da yaranta da maigidan ta har sai taba makwatab wani lokaci yau kuma gashi a sanadiyar kishi da buzuwa har horo yakai ga a rufe store da madafar abincin gidan baki daya.

  Babu wanda zata kara kai kara gareshi tunda baji mijin nasu keyi ba ko ta fada karshe ma ya dawo ya hauta da masifa gashi ita ba son masifa take ba a rayuwan ta.

  Haka ta taso da tsoro sam bata fada ko kadan saboda ruwan ciki irin na matan hausawa da ta taso a cikin shi wanda a cikin tarbiyan diyan hausa yake.

   Kamun kaina a diyan hausawa rasgin hayani da fada da mutane barkatai wanda akasarin matan hausawa hake ne ke cutar su a gidan mazaje su da gun kishiyoyin su yan bana bakwai.

  Tana tuna yadda Nafisa tazo gidan daga ita sai ghana most go din yan kayan ta a ciki amma yau ta koma kamar wata hamshikiya a gida.

   Auren ta da aka dauro ba tare da sanin iyayyen su ba can bariki suka dauro auren su da ita inda ta tare a gidan da yake a lokacin a kano.

  Sannu a hankali har ya samu iyayyen shi suka hakkura ta fara shiga cikin su inda take baiyana harin ta na zahiri a hankali.

  Da farko ta yaudari mutane inda taja yan uwan miji a jikinta duk suka yarda da ita ta gama jin sirin su kaf kafin daga baya data bunkasa ta fara fitar da kalan ta ga mutane.

   Inda yanzu kowa ya gama gane ta wasu masu zuciyar imani sun gujeta masu kwadai kuma har wanan lokacin suna tare da ita duk da abin hannun ta bai ban baruwa wasan dadi sai kayi mata bauta kafin kaci abu daga gare ta.

  Don haka take kallon kowa a wullakance sai uan uwanta dakan zo jefi jefi cin arziki wurin ta wanda ba a wuce wata daya basu zo gidan ba.

  Tazo da wata yarinya da take cewa wai kaunar tane sai da tafiya yai tafi aka gane cewa yar tace ta cikin ta yarinyar.

   Nafisa zata girmay ma Fati ga shekaru haka yasa tafi fati wayo sosai har take jin tsoron ga fin karfi ga sihiri don bata shigo haka kai tsaye ba sai da ta shirya ta shigo gidan .

  Shi kan shi maigidan ba a banza ta barshi ko yanzu kuma bawai ta fasa abinda takeyi din bane sai ma abinda yaci gaba a cikin halayen nata.ZAINAB IDRIS MAKAWA

            SEENABU

MIJIN BUZUWA🧠


2️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

           SEENABU 


NOVEL DIN NAN NA KUDI BIYA DARI UKU KO KATIN DARI UKU TA WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAN IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI KIRA TA WANAN LAYIN 09026931792 KO 08036959257 ASHA KARATU LAFIYAHayaniyar yaran da suka dawo daga makaranta ya dawo da ita ga tunen tace shike nan nawa ta samay ga Affan da dan banzan wayo kawai na shiryasu zuwa cikin gida wurin kakanin su tasan idan sunje can sa samu abinda sukaci a cikin su.

  Yaran suna shigowa suka fada mata a jiki suna fadin mama mun dawo yunwa nakeji sosai wallahi karamin ya fada take taji gabanta ya fadi don hakan halin su ne .

  Sai subar abinci a cooler makarantarsu su dawo dashi kuma suce yunwa suke ji halin yaro ke nan oya a cire uniform kuje cikin gida wurin su hajiya kwaci abinci a can banson yawan hayaniya yau.

   Acan cikin gida kuma dawowan yaran gidan makaranta yasa hajiya ta kasa kunne taji shigowan jikokin nata da take zaman jiran tsamanin su tunda safe.

  Ba afi min ashrin ba ta fara tsinkayo hayaniyar su daga kofan shigowa gidan tace a ranta nasan a rina dama tabbas hashe na ya tabbata ke nan wanan yarinyar har takai can.

  Yaran suka shigo dakin da murnan su don anan kawai suke samu su sake suyi yadda suke so batare da wani tsangwama ba.

   Suna shiga Affan ya cire rigan jikin shi ya rage daga shi sai singlet yana fadin hajiya maman mu tace muzo nan muci abinci a wurin ki wai yau bata son damuwa.

   Yar ta Aisha ta kwala wa kira tazo ta basu abinci sai gata ta fito daga daki tana saye da dogon riga a jikin ta tana ganin yaran tace a a su Affan ne yau da rana tsaka anan zakuci abincin rana ke nan ?

   Hajiya tace zuba masu Abinci don Allah ki kawo masu nan ta wuce kitchen cika umurnin mahaifiyar nata da sauri sai gata dauke da plate din abinci ta kawo masu.

   Hajiya na zaune gefe ta kurawa yaran ido tana kallon yadda suke cin abincin gwanin ban tausayi dasu tunane tayi aranta da yau babu ita fa kamar yadda babu ran kakarsu ta wajen uwa yaya Fatima zatayi da wanan ukuban haka ?

  Hajiya kubura da take matse ita tunda rana sai gata ta shigo wurin hajiyan da mamaki a fuskanta tana fadin yaya kin ga hasashen yana son ya tabbata a kan yarinyar nan ko sai ga hajiya karima uwargidan su tashigo a bayan su tace tabbas maganan mu ya zama gaskiya.

   Ya tabbata ke nan ta ki bari yarinyar nan ta girka abinda zasuci a gidan abin har ya tashi ga ta hana mai aiki yi masu girki suci ya koma ta hana masu abinci.

   Sallama ake daga kofan shigowa dayar yarinyar gidan ta leko daga kofan hajiya karima tana fadin sannu da zuwa yaya Suraj.

  Bai amsa mata gaisuwa ba sai tambaya yayi ba kowa a gidan ne ina sallama gidan shiru tace suna dakin hajiya mama ina gani can yanufa dakin don yasan idan sunyi irin wanan taron akwai abinda ke faruwa da ya shafi dayan su ne don don iyayyen nasu nada hadin kao sosai a gidan.

   In ka debe ko wanan ya kasance amaryan su Asiya bata gida ne a lokacin da su hudu zasu hade a dakin kofan ya nufa yana saye cikin uniform din shi na sojoji.

   Sallama yayi a bakin kofan daga ciki suka amsa mashi mahaifiyar shi hajiya karima tace kamar muryan suraj nake ji a kofa yace nine ummi.

  Dakin ya shiga kallo daya yayiwa iyayyen nashi alokaci guda ya gane akwai wani matsalan da suke fuskanta wanda ya shafi hajiya mama a gidan.

   Gaida su ya fara yi a cikin ladabi kamar ba soja ya samu wuri ya zauna bayan sun karba mai gaisuwa.

  Duban hajiya kubura yayi yace mommy akwai matsalane su Affan dake cin abincin su hankali kwance ta nuna mai tana fadin wanan fitinaniyar matar uban tasu ce kila ta rufe dakin girkin gidan ne yau ko da safe a nan suka dauki abincin zuwa makaranta.

  Yanzun kuma kaga uwarsu ta turo su nan su da sauri yace ita Fatin fa may zataci to ya tamnaya yana kallon fuskokin su gason jin amsan su.

   Mommy tace ai shi muke tunane a nan dafe kai yayi yace wanan mata ban san abinda take nufi ba a gidan nan tana son mayar muna da dan uwa binan.

  Kada kaga laifin ta ai shine mai babban laifi mama ta fadi a hasale sai mummy tace ba yin kanshi bane yaya bar irin shuuman matan nan wallahi.

  Suraj ya mike a hasale yana fadin yau sai naci mata mutunci idan haka gaskiya ne wallahi ko a gidan maza ana ma mutum horo da yunwa ne  balle gidan brother za a ce anyiwa mutum haka.

   Ko maigadin gida ai yana iya kyauta da abinci tunda bai rasa ba balle diyan shi ummi ta kalle shi lokacin da yake shirin fita daga dakin tana fadin ina zaka ?

   Kai tsaye yace gidan zanje wallahi idan na samu gaskiya ne yau sai tabar gidan nan wallahi ummi tayi saurin cewa dashi kaifa mahaukaci ne na sani a dai karbe key din ka bude wurin shike nan.

   Kasan yadda dan uwanka ke son ta hakan zai iya kawo matsala a tsakanin ku yace wallahi sai dai ya kawo ummi wanan wani irin bakin haline haka ?

  Ai haka suke mommy tace mashi abinda ake mai gudu ke jan tun farko bai gane ba basu son kowa sai kan su da yan uwan su kawai wanan halin su ba wai ba.

   Mama dai ta rike goshin tada hannun ta sai wanda duk yai magana cikin su ta bishi da ido kawai shine nata yayin da zuciyar ta ke mata soya a ciki tana jin wani irin ba dadi a ranta.

   Yana tsaye daga kofa mommy tace bari muje tare dakai zaifi da sauri ummi tace haka zaifi kan don wanan kin san mahaukaci ne ya shawo Alluran shi ja sojoji kar yaje ya sauke wa yar mutane a kai.

   Ai da zai sauke din haka zai fi gani take duk ta gama da kowa a gidan babu wanda bata iya takawa shiyasa take abinda taga dama inji mama.

   Yanzun dai bari mu tafi idan munje ni zan fara shiga wuri  ta inji ba asin yin hakan da tayi sai asan abinyi sukace yayi kyau hakan mikewa tayi zuwa dakin ta ta dauko hijjib din ta ta saka suka fice da suraj din a motar shi suka karasa gidan.

  Daidai lokacin Abba ya dawo shi da anty amarya daga asibiti da dan ta da bai da lafiya ganin motar suraj ya gilma ya nufi gidan dan uwan nashi yasa suke mamaki.

   Anty amarya ke fadin yau suraj ziyara zaikai gidan Abdul ne haka mahaifin nasu yace kila yazo ya samu Fati ta koma dakin ta ne zai dubuta.

  Sai da suka shiga gidan ne suke jin abinda ke faruwa karban key anty Amraya tayi bata shiga dakin taba ta bar yaron wirin uwar gidan nata ta mara masu baya.

  Sun samu kofar gidan a rufe wai taba maigadi sallahu cewa kada ya bari kowa ya shigo gidan ya damay ta don yanzu ta dawo da yarta daga makaranta zasu huta.

   Da kyat ya bude masu kofa sai da suraj yayi mashi jan ido wanan abin shiya kara harzuka suraj din rashi ya baci sosai kusan a tare suka shiga gidan da anty amarya don samun delay din shiga da sukayi.

  Bin gidan Suraj yayi da kallo daga sama har kasa kafin ya karasa fitowa daga motar shi cikin hasala mommy tace ashe kun dawo ke nan take cewa anty amarya tace mun dawo ina shiga ake fada min abinda ke faruwa nace barin biyo ku don ba mutunci ne da ita ba.

  Anty tasan ida take rashin mutunci ta ai nika yau idan tayi min wallahi balbalata zanyi in daki banza sai dai mu rufe da mijin ta ai mun saba.

  A tare suka shiga gida jin karan bude get din gida ta fito a fusace tana fadin maigadi wani dan bura, uba kabudewa, , , , , ganin su mommy yasa tayi shiru ta juya da saurin tana zaton basu ganta ba suko sun ganta.

  Kafin su iso ta wuce part din ta ko da sauri don tasan ba bakin ta bane na Fati ne don ita suke zuwa gidan su .

  Tunda ta sallamay sallah la,asar take zaune saman sallaya ta tun tana addua ta koma tunane ga tunanen ya bowayeta don yunwan da ke cin ta.

  Sun shiga da sallaman su aka gaisu tace mommy kune tafe ashe mune fati har kasa takai tana kara gaida su cikin mutunci suka amsa mata ta dago tana fadin yaya Suraj marmari daga nesa.

  Ke kin ci abinci yau ko baki ci tambayan da ya jefo mata ke nan a lokaci daya tayi murmushi tace kajika da wani magana kuma ba a gida ka samay ni ba zakai min wanan tambaya haka ?

   Mommy tace Fati ba tambaya muka zo yi ba don mun san abinda ke wakana a gidan ko yau dai bakici komai ba tunda garin Allah ya waye haka ne ko ba haka ba.

  Kai ta sadda kasa tace hakane mommy tace to akan may Fati zaki zauna ana maki horo da yunwa dake da diyan ko haka abincin nan akwaishi ba babuba kuma.

  Mommy yau fitina take ji tun jiya data dawo ta samu na dawo gidan ta fada min bakaken magana har tana ikirarin sai na rami ya fini shan iska a gidan nan.

   Shine yau da safe zan shiga kitchen na samu ta kulle komai tunda asuba wai kada a dora girki a gidan ta fadawa Laraba ni kuma ban koma ta kanta ba tunda nasan don ni tayi hakana.

  Haba Fati sai ki zauna da yunwa ai zaki kashe kanki ne idan kina haka yanzu bari muje mu samay ta muji may take nufi wai.

  Suraj bai bisu ba ya dan tsaya ganin Fati din yana kuma tambayan ta may zataci yaje ya sayo mata tace duk abinda ta samu yace kayan tea fa tace suna store acen muke ajewa fita ya yi ya mara masu baya.

  Sun shiga da sallama cikin isa ta karba masu sai suka tsaya gaisawa da ita tunda iyayye ne su bayan gama gaisuwan mommy tace munzo ne dama muji dalilin rufe kitchen da tsore din gidan da akayi wa mutanen gidan.

   Hajiya nan fa gida na ne ina da daman da zan rufe ko ina nake son don Abdul bai bar abinci da Fati a gidan nan ba tunda bai cata dawo ba ta dowo don haka sai ta jira idan ya dawo ya bata abinci ita da diyan ta suci.

  Karya kike yi munafukar Allah kuma baki isa ba wallahi muryan Suraj ne da batayi tsamani ba ya fado dakin yana zazzare mata ido a cikin hasala yake magana yana huci.

   Tare da daka mata tsayawa yana fadin ban makulin nan tun ban balbalaki yanzu a wurin nan in kuma sa sojoji suzo su kwashe ki sukaiki barikin mu su daure har ranan da miji ku ya dawo inji shiku idan shiya ai horo da yunwa haka.

 Kallo da tayi wa Suraj raga fuskan nan nashi ba imani a cikin sa zai iya aikata abinda yace a kanta tsoran ta Allah tsoran ta soja da sauri ta mike ta shige dakin ta yabi ta da harara.

  Yadawo da fuskan shi kan yar ta dake cin abincin da tayo masu take away a hanyan dawowanta gida ya watsa ma yarinyar harara da sauri ta noke kanta kasa ta kasa cin abincin da tun shigowan su dacin abincin ta take yi bata ko gaida su ba.

  Da sauri tafito daga dakin dauke da key din a hannun ta tana mika mashi cikin ladabi ya fisge a hannun ta har ya fara tafiya su mommy zasu bishi sai kuma ya juyo yana fadin.

  Ina ne kitchen din da tsore suke ki taso muje yau za a yi ta ta kare and idan bayan tafiya ko harara naji kin ma yar uwa wallahi yau ba ubanda zai hanani daureki a garin nan jiki na rawa ta bi bayan shi zuwa tsore din yace ta bude da kanta ta bude.

   Laraba da mai masu aikin gida namiji da ta dauko dan kabilar su can garin su wanda ya zama kamar CID din ta ga komi a gidan ko tana nan ko bata nan ya kira.

  Komai na tsore din aka fito dashi waje aka kasa uku yace Fati ta kwashi kashi biyu ita da diyan ta kashi daya ta dauka nata ne.

   Ga abin magana ba halin yi don tsoron soja da ke zuciyan ta tun da zasu shigo Nigeria sojoji suka latsu a hanya take tsoran soja inda duk ta ganshi.

   Yana tsaye a rike kunkurun shi da hannayen shi biyu yake tambayan fati akwai wani tsore da kitchen a gidan tace eh akwaishi a part din ta wanan nata ne ita fatin suke amfani dashi in generar.

  Kwashi naki kikai part din ki da sauri taja wani kwali da kyat tana fadin kasiye dauko mun sauran ta matsu tabar wiein wanan dan banzan soja mara hankali dake gabanta.

  Dama tun zuwan ta gida da ta fara ganin shi aka nuna mashi ita a matsayin sabuwar matar wan shi bai yi murna da ganin ta ba a fili ya nuna hakan kowa ya gani.

  Don shi kyamar irin su yake yi bai dauke su wasu cikakkun mutane ba a idon shi,  yafi daukan mayaudara aduk inda ya gasu haka yake kallon su a yatsune.

  Shine dan uwan shi ja jini ya auro ya kawo ta cikin zurian su take juya mutane yadda ta ga dama a gidan da takaicin ta ya juya tafi bai shiga gidan nasu ba a lokacin mommy tare da anty Amarya suka koma gida bayan sun yiwa Fati nasiha kadan.

  Nan suka tafi suka bar Fati da tsoro a zuciyar ta fam sai dai abinda bata sani ba a halin yanzu Nafisa tafita shiga tashin hankali don tsoranta Allah tsoron ta Suraj soja.

  Wanda ta hango mugunta zalla cikin kwanyan idon shi abinda ya fadi tasan karamin aikin soja ne yayi shi ya aiwatar da abinda ya fada din dole ga magana nacin ta da zata fadawa Fati a yau sai dai babu halin yin hakan gare ta dole ta kawo ido ta saka mata a gidan tana jiran dawowan mijin nasu wanda zata sa ya ci fuskan Fati din a gidan.

  Ai idan sun san wata basu san wata da makirici zataci galaban su gaba daya don ta gane yan uwan mijin da iyayyen shi duk munafukai ne a kanta.

  Can gidan su hajiya sun koma kumshe da dariya a cikin su sai da suka shiga mota suka fara dariyan abinda suraj din yayi wa Nafisa .

   Yanzu sun gano takon ta Suraj ne zai dinga mata hukunci irin nasu na sojoji na rashin imani sun shiga gida nan suke bada labarin abinda ya wakana a gidan.

  Mama taji dadin har cikin ranta ko banza Suraj ya kwantarwa Fati incin ta yau wanda inba shi din ba,  ba wanda ya isa yayi haka a zauna lafiya da ita tunda tayi niya.

  Maganan mommy ne ya dakatar da ita da taji abinda Nafisan ke fadi a lokacin shigan su gida da take fadin wai babu rabon su Fati da yayan ta ga abinda maigidan ya bari a gidan.

  Lalaima wanan matar tantiriya danta ya dauko mata ba kwai ba donge amma har take ikirarin cewa wai ba abincin su a gidan.

  Wani zafi na bakin ciki irin wanda iyayye ke ji a gamay da diyan su idan sun yi abu ba daidai a cikin alumma wanda sai uwa ko mahaifi suka san da irin zafin da mama taji a lokacin.

   Haka dai ta shige daki a dadafe bakin ciki da takaicin da matan dan nata ke kumsa mata a zuciyar ta yayi yawa kuma dan nata ya sani amma bai iya daukan wani mataki akan hakan.

   Wunin ranan haka suka kare shi da maganan Nafisa wanda hakan ba bakon abu bane agurin anyi sau tari da yawa sai dai na yau din ya banbanta da sauri don ta fito ta nuna masu karfin iko da izan da take dashi a cikin kan dan nasu .

  Wanda suka haifa suka tarbiyartar da hannun su kuma ya tashi da tarbiya suke saka ran samun farin ciki a wurin shi kamar yadda duk wasu iyayyen ke fata ga diyan su idan su samu

   Amma lokaci guda Nasifa ta shiga rayuwan dan nasu wanda ya watsar da duk wani rayuwan farin ciki da suke hasashen samu daga gare shi.

   Gashi a yanzu yana a cikin ganiyan samun duniyan shi wanda bai zauna ba tsaye yake wurin neman na kanshi a rayuwan wanda ba komai yakawo hakan ba sai addun mahaifa da yawaita ta sadaka akan diya yake bibiyan shi a yanzu.

  Don a baya in zata iya tunawa bata da aiki sai yawai ta sadaka fiye da kowa a gidan in anyi magana sai tace ba neman duniya nake wa kaina nemawa na baya nake madogara.

  Ga yawan taimakon na kasa da ita tundai idan ance yaro maraya ne sai mama tasan yadda takai alherin ta ga yaron ko ta saka yayan ta suyi mai alheri daga abinda suke dashi na jikin su mai kyau wanda zai farauta ran yaron da za a ba abin.

  Don Allah iyayye mata mu kula kada muyi sakaci da wanan dama akan marayu da muke gani zaki iya dafa kan yaro maraye zai ji dadin hakan da kikai mai har a cikin ranshi.

   Bawai duka maraye bane zai bukaci taimako wasa ma da dariya a gare su sadaka ce dan abinda zai farauta masu rai sadaka ne Allah ya bamu ikon yi ga maratun dake a kusa damu.

  


ZAINAB IDRIS MAKAWA

            SEENABU

MIJIN BUZUWA🧠


3️⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA

          SEENABU


NOVEL DIN NAN NA KUDI NE BIYA DARI UKU KO KATIN DARI UKU TA WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI KIRA TA WANAN LAYIN 09026931792 KO 08036959257 ASHA KARATU LAFIYA YAN UWA.Tsaye take gaban mirrow tana gyara rigar da ta sa a jikin ta na tampha wanda akai mata dogon riga dashi mai wani launi kamar jikin damisa brown colour.

  Dinkin mai dan kwala sai da wuyan rigan V neck akayishi wanda yasa gaban ta ya fito dakyau daga cikin rigar kasan rigan ma an bude shi free yadda zata iya walla kafafuwan ta ba cikin matsuwa ba.

   Turare ta dauka ta feshe jikin ta dashi ta juya ta dauko gyalen ta dake saman godo gefe ta fesa mashi turare ta mayar a hand bag din ta dan kwali ta dauko ta dan daki lokaci tana daurawa take fuskanta ya fito tsonen a jikin mudubin.

  Duk wanan shirin da take yi ranta ba dadi don bata son zancen zuwa kaduna a zuciyar ta tafi son tayi rayuwan ta a gidan ubanta dake a cikin garin Minna.

  Inda gidan su yake a kwangila road asalin su su hausawa ne zamane na kakan ni ya kawo su garin minna har suka zama yan ainihin gari baza kace su bakin gari bane yanzu don kowa nasu anan aka haifeshi.

   Daga wajen gidan wanda irin ginan da can bayane na siminti wani murya ya kirata da fadin Khadija kina makara fa a cikin irin hausan mutane Niger shiba kananci kuma ba hausa pure ba do  ya dan hade da surkin harshe.

  Muryan Khadija ne ke fadin mama shiri nakeyi gani fitowa yanzu da sauri ta karasa shirin ta jawo dan trolley din da ta sa tufafin ta a ciki tare da rataya handbag din ta a kafada ta fito waje.

   Kallon ta mama tayi wace zance a wurin ta khadija ta debo kyau da na saba kafin in ga mahaifin ta farar mace ce doguwa yar kabilan gwarin may kunkele dake a cikin minna din.

  Kallon yar nata tayi tace kin fi son ko yaushe kiyi tafiyan marance mama nina fison in shiga da yamma yafi ba wanda yasan zuwan ka sai dai a ganka.

   Maimakon tayi haraman tafiya sai ta ja kujera roban dake gefenta ta zauna kallon ta uwar tayi tare da fadin yaya haka kuma ?

  Banbara nake jira na aika a sayo dashi zan tafi bana son in mising din shine idan naje ke dai yanzu na gane baki son zuwa wurin yar uwan naki tunda kika girma kika fara karatun jamia .

  Ta dan ya motsa fuska mai kama da sallo ko yanga wanda ba haka bane kusan yanayin yan garin ne haka suke maganan su da kamar sallo da yanga tace ni nafison in yi hutu na a gida.

  Amma ita ya Amina kullun sai tace sai mutum tafi wurin ta hutu yanzu kuma ba da bane ban son ina missing din gida sosai murmushi kawai uwar tayi don tasan halin yar nata.

  Ba ajima ba mahaifinta ya shigo gidan yana ganin ta yace a Khadija an fito ke nan eh baba zan tafi hannu yasa ya fara laluban aljihun shi sai ya fito da dubu biyu ya cire guda ya miko mata.

  Kai ta girgiza mai tace baba ka barshi kawai kudin da anty ta turo min zai ishe ni na gadone a daidai lokacin yaron da ta aika ya sawo mata banbara ya iso da leda a hannun shi yana mika mata da canjin karike canjin tana bude ledan ta debo banbaran ta mika mai ta mike tana gyara jakkan ta yaron ya taima ya fita mata da kaya ida ta tare Napep zuwa Abdulsalam garej .

  Tana isa saura mutum daya ta biya suka shiga suka kama hanyan garin kaduna yamma lis suka shiga gari lokacin kuma akai hadarin marancen nan da Nafisa ta dawo ta samu Napep din da zai kaita unguwar da yar uwar nata ke aure wanda kusan rabin zaman ta a baya a nan tayi shi sai data girma ta koma gida karutun da take yi Abuja yanzu shine silar mayar da rayuwan Khadija gida Niger state.

  Tun ranan da khadija tazo kaduna bata fita ba tana daga daki sai falo indan ta fito ko kuma ta shiga kitchen tayi masu girki a gidan.

   Yau da yamma ya Amina ne ke kwala mata kira tana zaune tana cin banbara da tayi worming din shi kamar yanzu akayi shi bai kwana ba.

   Ya Amina gani ta fito tana fadi cikin ranshin kallon fuskanta don Allah zo ki shiga gidan su mommy ki karbo min sako tace yanzu in tura a karbo min.

   Fuska khadija ta ya motsa tace ni ban shiga ba tunda nazo banje na gaidasu ba Amina tace wai khadija may ke damun ki ne haka ?

  Ke a rayuwan ki sam baki son shiga jamma a ban san inda kike dauko wanan rayuwa naki ba haka cikin bacin rai ta juya dauko gyalen ta kayan da tazo dasu garin ta kara sakawa a jikin ta.

   Yaran anty nata biyu ta, ta kira su rakata gidan da aka aike ta din fitowan su bakin get din gidan yayi dai da zuwan wata mota a guje ta watso masu ruwan dake kwance a wani dan rami saman hanya.

  Cikin bacin rai Khadija ta dago kai tana fadin you are very stupeid bakya gani ne kika watso ma mutane ruwa haka.

   Horn kawai Nafisa tayi masu ba tare da ta tsaya khadija tabi motar da hararan takaici tana dan kakabe riganta da ruwan ya dan taba a lokacin.

  Raina yayi matukar baci haka muka doshi gidan mutane ina mita wani saurayi dake tafe a bayan mu naji yace yar iskan buzuwan nan ne haka take tuki kamar mahaukaciya wallahi.

  Dan juyawa nayi na kalli mai maganan nace sannu yace yawa bata dai zuba maku ruwan sosai ba ko nace kadan ya taba mu inayi har lokacin ina kakaban ruwa a jikina.

  Gidan muka shiga wanda har lokacin raina a bace yake da buzuwar da naji saurayin nan yace min da sallama muka shiga gidan.

  Wanda sai kawuce kofan falon gidan kabi wani dan siririn hanya da zai sadaka da cikin gidan da muka shiga wanda babban gida na ba yau bane farkon shigana gidan don duk zuwa nayi sai anty ta aike da gidan ina shiga akai akai yanzu tunda na girma bani shiga idan nazo sai da wani dalili.

  Sallama mukayi inda kofan uwargidan ne fara isa sai na mama daga can ciki sai kuma wasu biyu dake kallon nasu din na mommy dana anty Amarya ke facing din su.

  Hajiya ummi da yaranta nake jiyo hayaniyar su daga kofan part din ta na dan matsa daga kofan dakin ina gaida su dakyat aka amsa min ban tsaya ba na wuce.

   Lekowa akayi daga dakin ummi don ganin mai gaidasu din da bai shigo ba bata gane ni ba alokacin har nakai kofan mama shiyasa ban son shiga wanan gidan don yawan dake garesu kuma sai kabi kowa kagaida shi dole don hadin kai irin na matan gidan.

  Koda baka gaida mutum ba wanda kaje wurin shi zaice dakai ka ko gaida mutanen gidan sanin haka danayi yasa na fara binsu daga daga ina gaida su.

  Dakin mama ma a kofa naja na tsaya ina fadin ina kwana mama ta amsa min daga ciki tana fadin waye shigo mana ciki.

  Dole na shiga daga cikin dakin tare da kara gaida ita inda nakai gwiwana duka biyu a kasa irin gaisuwan mu na mutanen Niger.

  Daga kuryan dakin ta aka fadin muryan wa nake ji kamar khadija Adamu da sauri mai maganan ta fito falon ida nake wani irin ihu ta sake a lokaci daya tare da kwalawa binta kira tana fadin ga khadija Adamu ashe tana garin nan mukayi maganan ta jiya.

   Murmushi nayi ina dagowa daga gaida mama da nake nan suka shiritar dani nace anty ta aiko ni wurin mommy.

  Bayan nagaida amaryan su ne na wuce zuwa dakin mommy ta tareni da fara anta mun dade tana jana da hira wanda ni ban iya sake jiki dasu muyi hiran sosai saboda mutunci da girma da nake gani a idona.

  Sakon ta dauko min na fita mukai sallama dasu nan suka rakoni suna dan taka min in baki mantaba mai karatu na fada maki a nan kaduna nayi rabin rayuwa na.

  Kamar abin tsokana wanan motar dai ne na dazun ta dawo a guje ta kara yin facali da ruwa a take nace wanan wani irin iskanci ne wai haka ?

  Har motar ta wuce sai ta dawo baya a hankali zuwa gare mu a lokacin zainab ke fadin Nafisa ce fa ta dawo zai tai muna cin mutunci kila taji zagin da khadija tayi ne.

   Gab damu ta tsaya tare da sauke glass din motar  wata farar mata nagani ciki tare da wata zaune a gefen mai zaman banza.

  Tace wace yar iska ce cikin ku take zagina shiru naji sunyi suna soke kai kasa nan san lokacin da nace mata kece dai yar iskan da baki san darajan mutane ba kika gudu da mota haka a wulkance cikin gari kamar yar koyo.

   Ke tafadi a zafafe tana kokarin bude kofan motan da sauri naji su Binta da zainab na fadin yi hakkuri anty bata san ke bace .

  Cikin zafin rai nace ke wacece da zaki watsa ma mutane ruwa kice kada ayi maki magana wallahi ko diyar shugaban kasa kike sai nayi maki magana .

  Karasa fitowa tayi daga motan tana fadin ke yar gidan uban waye a garin nan take raina ya kara baci nace kedin yar gidan uban waye da baki da tarbiya fada min naki in fada maki nawa.

  Fisgan hannu na Zainab keyi ni kuma ina turjewa don ban ga wani kimar ta da suke gani ba idons a lokacin   don sam ban da tsoro akan gaskiya na.

  Ke yar waye da zaki tsaya kina fada min magana son ranki nace ni yar gidan ubane ke kuma cewa akai titin na gidan ubanki ne da zaki dinga gudu kina watsa ma mutane kura da ruwan titi.

   Yadda taga ina yi sai ta tsaya tana kallo na kafin ta mayar da fadan akan su Binta da zainab din tana fadin zamu hadu da kune wallahi don nasan da sanin ku take min hakan.

   Nace wai kun san wanan banzan ce da kuka tsaya tana fada maku maganan banza saman hanya haka ?

   A harzuke tace nice banza nace an fada maki idan ba banza kike ba may kike zaki tsaya kina ma mutane son raki ke gaki mai kudi ki takamu ki wuce lafiya kin taki banza ko ?

  Zaki gane kurenki wallahi wani kallon banza na watsa mata nace sai dai mu gane kuren mu amfada maki don kina da kudi zanji tsoron ki ne ko may kudin ki bai damay ni ba tunda ban taba zuwa wurin ki neman wani abu ba.

  Matar da take cikin mota ne taji abin yayi yawa kuma dukkan mu munki bari ta bude mota ta fito tana jan ta tana fadin haba Nafisa zaki tsaya kan wanan karamar mara kunya kuna raba hali a saman hanya ai sai ta ja maki raini ga jama, a.

  Kuta tayi ta watsa min harara na mayar mats ta shiga mota tana fadin zaki san kin shiga hurumi  na nace inga alheri .

   Fisgan mota tayi sai da yayi wani irin kugi suka nufi hanyan cikin gari zainab tace wai Khadija kin san kowacece ita din ?

   Wacece kuwa banda kila matar wani ko wata kusan gwaunati shike nan don muna kasa sai ta rena mu Binta ce ta katse ni da fadin matar yayan mi ne kishiyar anty Fati.

   Inda motar yabi nabi da kallo nace yanzu wanan matar matar dan uwan ku ne wallahi na dauka irin matan bariki din nan ne masu zaman kasu nima ban san yaya akayi idona ya rufe haka ba naci mata mutunci.

   Nan nake fada masu abinda tayi muna da zamu shiga gidan su yanzu kuma ta sake maimaita muna shiyasa raina ya baci don naga kamar da gaiyya tayi hakan amma kuyi hakkuri don Allah.

  Binta tace ai mu yau kin muna daidai wallahi don ba karamin dadi naji ba da kikaci mata mutunci nan a gaban mu.

  Mun da jima a tsaye dasu karshe mukai sallama muka shige gidajen mu har lokacin ina da zafin matar nan a raina.

   Nafisa ko sai fada take kawar ta na bata hakkuri tana fadin ban son ki biye mata ba tunda kinga kannen mijin ki a wurin may yuyuwa tasan ki ke baki santa ba.

   Zanyi maganin ta wallahi sai ta rena kanta zata san ba a taba ni a zauna lafiya ko wacci tuwo dani miya ya sha na san dai ba yar gidan uban kowa bane ita.  Su zainab na shiga gidan su suka fara bada labarin arangaman mu da matar yayan nasu nan mutanen gidan suka fito suna sauraren su.

  Mommy tace kai amma wanan yarinyar wallahi ta burge ni sosai yau da haka Fati ke daurewa ta mayar mata da martani da abin nata ya rage.

   Anty amarya tace ai ba zata iya ba ne don ta riga tasa mata tsoron ta a zuciya kuna ganin a banza ta bar mutane ne haka da kowa ke shayin ta.

  Ummi tace kwarai ai irin su ba a banza suke barin gida ba sai sun kama bakin kowa sun daure yadda ba mai iya motsawa a kan su.

  Sai lokacin mama tayi magana tace aini wanan yarinyar ta gama shereni wallahi tayi min daidai yanzu zata san in ta daure bakin wasu bata iya daure na wasu.

   Nikan da muka shiga gida ya Amina tana daki mika mata sakon nayi a cikin wani dan leda wanda ban san abinda ke ciki ba dakina nakoma na fara rage kayan jikina.

   Na mayar da dan riga mai karamin hannu da bujen body hook dana cire sai hula dana dora a kaina kitchen na nufa don dora abincin dare saboda yamma yayi.

  Kafin wani lokaci har na kammala na gyara wurin na mayar da kauan da nayi aiki a inda suke daki na kofa nayi wanka kafin a kira sallah na fito na canza kayan jikina.

   Kananan kaya na kara sawa a jikina don idan ina gida sune kayan sawa na wayata na jawo ina duba sakon dana samu daga abokaina da muke karatu dasu.

   Lokacin sallah yayi na mike na gabatar da sallah ban daga ba sai da na yi har isha,i na nike abin sallah na fito din in ba yaran anty na abinci.

   Anty ce ta fito daga dakin kwanan ta muryan ta naji daga baya na tana fadin har kin fito eh kawai nace mata ba tare da na juya ba ina zuba abincin a plate na mika ma yaran dake zaune suna jirana.

   Juyowa nayi inda nake tsanmanin take zaune nace in zuba mata abincin yanzu ne kallo na naga tanayi cikin mamaki tambayan da ta jefo min a lokacin ban zaci ji ba.

  Khadija may ya hada ki da buzuwa yau kin ko san waye buzu kin san ko matar waye don Allah ki rufa min asiri tunda nake unguwan nan ban taba fada da wani ko wata ba ina jin tsoron rashin tsoran nan naki wallahi.

   Kara daure fuska nayi nace ina ruwa da wata buzuwa ko baturiya take ba zan yarda ta wullakantani ba ga banza don tana takama tana da kudi tunda ba kudin ta nace ta bani ba.

  Don Allah dai ki bari ban son irin haka ni na dauka kin bar halin nan naki yanzu da kika girma ashe halin na nan baije ko ina ba.

  Mijin ta fa na iya sakawa a kore mu a unguwan nan wallahi don suke fada aji yanzu a garin don Allah dai ki bari.

  Kamar zan yi magana sai nayi shiru ranan banci abinci ba saboda haushin buzuwan nan dake ci min rai haka na kwana da tunane kala kala a raina.

  Hajiya mama haka ranan itama ta kwana tana tunane a ranta kan yadda zatayi da danta akan buzuwan da ta zama masu fitina da masifa a cikin zuri,an su.

  Dan ta ya zubar mata da mutunci da kimar da mutane ge gani nata duk a kan auren wanan matar da bata darajja mutane da halin ta.

  Da safe nafito na hada breakfast har na gama ya Amina bata fito ba tana daki na gyara ko ina na gidan sai na koma na shiga wanka na fito na shirya tare da hayewa gado in dan huta.

  Sai lokacin na fara jin hayaniyar su a falon gida alaman sun tashi ke nan daga barci hakan baisa na fito ba sai kara lafewa danayi saman gadon barci ne ke son dauka na a lokacin.

  Muryan ya Amina naji na bude idona a hankali ina kallan ta daga inda nake kwance nake mata ina kwana murshi tayi ta karaso gare ni tana fadin.

  Har kin gama kin kwanta yau barci ne ya dauke ni tana fadi tana kaiwa zaune a saman gadon da nake kwance jin banyi magana sai naji tayi murmushi .

  Tace khadija fushi kike yi akan maganan da nayi maki jiya akan buzuwan nan bata da mutunci ne khadija shiyasa kowa ke tsoron shiga tsabganta don mijin ta zai iya keta ma kowa a kanta yadda yake son ta.

   Dagowa nayi nace OK shike nan don mijin ta na da kudi ko mulki ba zanyi  fada akan dama na na dan adam ba murmushi naji tasake yi tace khadija ina raba ki da shiga tsabgan irin mutanen nan.

  Kai na kawar gefe ina hade miyau takaici da yazo min a lokacin haka abin yai ta cina har na gaji na sake na manta da wata can a zuciya.

   Jin shiru da su Binta sukayi yasa su ranan biyo ni gida a falo suka samay mu dukkan mu nan muka zauna har anty muna hira suna min korafi wai kullun ina gida kumshe ban fita.

 Zainab tace kodai kina tsoron haduwan ki da Nafisa ce nace waye Nafisa kuma tace matar yayan mu mana da kuka kwasa ranan .

  Oh kuce mi  buzuwa mana ai sai in gane ba Nafisa ashe sunan ta ke nan ni na fi gane ma buzuwa ai Binta tace ai bata son a kira da buzuwa shiya sunan ya mutu a bakin mu.

  Ranan da ra kai kara wajen yayan a gidan bakiga irin fadan da yai muna ba ni tun lokacin gidan ya fita raina wallahi.

  Ashe ya zama mijin buzuwa ke nan yar sani in fika wai agola da rabon gida ina kika san yar sani in fika ne ai sai kin ga yadda ta mayar da anty Fati a gidan.

   Ita da mijin ta yanzu ta koma yar kallo a gidan ko dan aikin gidan yafi ta daraja a gidan kwanan fa sai da ta fito aka maida ita kin san may ?

  Da ta koma bata gidan tana dawowa sai cewa tayi wai uban wa yace ta dawo gidan sai ta kama kitchen da komai tarufe na gidan ta hana ma anty Fati da yaranta.

  Sai lokacin anty dake gefe ta saka baki a hiran da mukeyi a falon tace amma samun wurin nata yayi yawa wallahi nace wai wace anty fati kuke magana haka ?

  Wanan da ta taba haihuwa har mukai fati daku a baya dan tunane nayi nace nagane ta itace mijin ta ya auri wanan matar wallahi itace inji Binta zainab dai sai dakilan wayanta takeyi tana charting.

  Anty ce tace yanzun yaya akayi akan abincin nan dai take fada muna yadda suka kwashe da suraj anty ce ke dariya ni banga abin dariya ba tunda ba dukan ta naji yayi ba.

  Sun kai wani lokaci suka ce zasu tafi na mike  na dan taka masu har bakin get din gidan anty na na dawo ciki.

  


ZAINAB IDRIS MAKAWA

            SEENABU

 Yau ta tashi tana ta farin ciki maigida yace zai dawo garin sai abubuwan taron shi akayi ita da kawayen ta a gidan.

  Fati bata san abinda ke wakana ba sai dai gani tayi mata da maza suna ta shige da fice a cikin gidan nasu wanda duk girman shi bai hana a jiyo ihun da suke yi ba a lokacin wai duk cikin murna ne hakan.

  Hajiya ce ta aiko gidan a tambayi Fati mai ke faruwa ne gidan nasu amce anga mutane na ta shige da fice a gidan.

  Fati tace itama ba ta sani ba itama dai haka ta gani suna shiga suna fita kawai a gidan amma bari ta tambayi laraba taji ko ta sani zuwa tayi ta kira Laraba take tambayan ta abinda ke faruwa tace wai maigidan ne zai dawo shine ake shirin taron shi.

   Mamaki Fati taji a lokacin tace yanzu dawowan na yaya Abdul shine shine akewa wanan hiddimar haka ikon Allah ikon gaskiya.

   Hajiya mama ma da taji fada tai tayi tana zage zage sai da hajiya ummi da mommy suka ce ta sa masu ido ga duk abinda take yi wani abin saboda neman baki take yin shi.

  Ran hajiya ya baci sosai daki ta shige saboda bata son yawan surutu abin kunya abin takaici wai dan da ta haifa da cikin ta a gaban idon su tantirai ke wanan wasan a gidan shi.

  Yau ina tarbiyan da tai mai a matsayin dan ta na fari a matsayin shi na jikokin malaimai bu sanadin mace ya samu raini a rayuwan shi macen ma shu,umar mace da tafito yawon barki.

 Muryan mommy ya katse ma mama tunane tace nazo ne in ji haka zamu kyale Fati ita kadai a cikin tantiran matan nan.

  Mama ta nisa tace may zanyi hajiya karima mommy tace ni a gani na yaran nan suje suma su zauna a dakin Fati din kin ga ko suna da niyar mata wani abinda ba daidai ganin idon su zai sa su fasa.

   Abinda kuka yi shawara akai sai ayi ni banda abincewa don wanan yaron ya gama bada tako ina mommy tace kada kice haka yaya kowa yasan ba halin shi bane juya shi akayi ya koma haka.

  Murmushin takaici mama tayi tace haka dai kuke cewa amma har da raayi kin san shi tun farko da son farar mace ai doguwa.

   Shine dai abinda ke rudin dan naki kawai ba wani asiri wallahi yaya mudai bishi sannu har a samu ma fita yaran ta kwala ma kira duk suka hadu nan take fada masu tana son su shirya gobe idan yayan su zai dawo su je su zauna da Fati a part din ta sai ta sake cewa ina ganin zamu biku ni da antyn ku amarya zan buga waya sauran uan uwanku suzo ba zata zamuyi mata kamar yadda tai muna bazata itama bata fada wa kowa da shafe shi ba.

   Nan dai suka taru sukai ta shawaran abinda zasu yi bada sanin buzuwa ba don su rama abinda take shirin masu din na iza masu takaici ta nuna masu su ba kowa suke gare shi ba yanzu.

   Muna falon antyna zaune karatu muke da yaranta ita kuma tana duba littafinta na islamiya don tana hadda a wata makarantar matan aure dake unguwar su.

  Wayan ta ne yai kara tace dan ta dake kusa da wayan ya miko mata jin ta ce hajiya karima mun wuni lafiya yasa na gane da mommy take waya don aminiyar ta ne sosai mama kuma a uwa ta dauke ta a gidan tafi shiri dasu su biyun.

   Bandai ji may suke fadi ba bayan gaisuwa da sukayi sai ji nayi antyna tana fadin kwarai kuwa hakan yana da kyau sosai mommy in Allah ya yarda goben zan shigo dani da khadi tunda tana nan sai muzo a cika taro da mu muma.

  Dagowa nayi na kalli antyn nawa don jin abinda tace bayan sun gama waya ne take ce min ikon Allah wai dan gidan hajiya mama ne ya samu karin girma bai fadawa yan uwan shi ba sai gani sukayi matar shi tana ta shirin buki ita da kawayen ta.

   Haushi naji a raina nace shiya sani mana duk wanda ya wullakanta iyayyen shi ai kan shi yai wa wasu ma suna can suna neman iyayyen ido rufe basu samu ba.

  Shi ya samu Allah ya bar mashi nasa a raye shine zai wullakanta su antyna tace ai shi na gani nima wallahi.

   Shi fa dama haka yake kamar mai tsoron mutane yake hadewa da buzuwan nan da yayi sai abin ya kara bulakucewa mai.

   Yanzu hajiya karima ta kirani ne tana fada min wai gobe tana gayyatan mu zuwa gidan nashi don suma zasuyi nasu taron a part din Fati.

   Kai amma suma dai basu da zuciya wallahi akan may ba zasu saka mashi ido suga iya gudun su ba ai mutum baiyi sai da nasa.

  Ni dai ba zan je sai kun dawo don babu komai wurin nan sai tarin takaici tace a a don may bazaki ba ba gaiyyatan mu sukayi ba muje mu mara masu baya a cika taro da mu muma.

   Ban iya bata amsa ba sai ma cewa da nayi da yaron ta kana jina ko muci gaba da karatun mu dajin wanan abin takaicin.

   Duk abinda muke sai na gaza yi sai cewa nayi da ita wai mashi wani irin mutum ne haka wai tace ai zaki ganshi gobe idan munje gidan.

   Washe gari ko da wuri anty tasa muyi aiyukan da muka saba a gida muka gama komai akan lokaci.

   Tace mu shirya zuwa karfe uku mushiga gidan su mommy din raina bai so ba haka na shirya dole cikin wani buje dariga na atampha da nayi dinki shi a abuja atamphan pink ce don haka shirgan pink colour nayi na ni kaina nasan kayan sun karbe sosai don sun fitar min da sura na fili.

   Muka fito muka rufe gidan muka nufi gidan da kafa saboda ba nisa sosai abin mamaki sai samu mukayi duk yan uwa da abokan arziki sun hadu a family house din nasu.

   Mun dan shiga dakin mommy ita kirjin abin nikan ganin duk matan aure ne a ciki yasa naja yaran anty muka wuce dakin mama wurin su zainab.

  Ba wasu mutane a dakin sosai sai ita da yaran ta kuma da alama kamar wani magana mai muhiamci suke a lokacin sai naji na tsargu ga yadda na gansu din a lokacin saboda kar na takura masu dana gaida su sai na mike zan fice daga dakin.

  Muryan mama din naji tana cewa a a dawo abinki ki zauna ai ba wani magana muke yi ba cikin muryana da yake kamar sallo da yanga nace No bari kawai na tafi daga waje ai.

  Binta ne ta fito daga cikin daki tace muryan ki naji yasa ni fitowa yanzu wai rangas wanan irin kwalliya haka ai sai ki sa kallo ya koma kan ki.

  Guntun murmushi nayi nace da ita silly girl ina zainab ashe tana kusa da mama zaune saboda cika min ido da sukayi ne banganta ba tace gani nan bakiji ina cewa khady ba da kika shigo.

  Binta ne tace mu shiga daga ciki mu zauna sai maman tace a a tazo nan ta zauna abinta ki sakata ciki kamar kunshi matsa min take yi wai nazo na zauna a kusa da ita ban hau kujeran ba sai na zauna a kasa kusa da kafafuwan ta.

   Ina zama tace da yaranta masu aure mutum biyu kun ganta nan ranan ta burge ni da ta tsaya taci wa yar iskan yarinyar nan mutunci ido rufe akan titi taso ta kawo masu rainin hankali  a saman hanya ita ko ta wanke ta tas wallahi.

   Anti fauziya tace kin min daidai wallahi dama ai ganin ana daga mata kafa ne yasa takewa mutane iskanci wai ita a dole matar mai kudi.

   Nan dai suke ta maganganun su a wurin kamar daga sama muke jiyo haya niya wata ta leko tana fadin ga yaya Abdul nan ya iso kuma nan ya fara shigowa.

   Fita suka kama yi a raina nace ashe shiyasa yake maku abinda yaga dama saboda hakan da kuke mai nidai ina zaune a kusa da hajiyan tasu.

   Ganin yaran nata sun fita yasa ta mayar da hankalin ta a kaina tana fadin dada dai yanzu khadija gudun mu kikeyi baki ko son shigowa gidan nan in kin zo na dan yi murmushi nace no mama ba haka na bane kawai dai daurowa ne.

  Nan take dan jana da hira cikin rashin sakin jiki nake dan bata amsa a hankali ganin dandazon mutane sun nufo dakin nata ne yasa na mike zan bar wurin tace dani koma ki zauna abinki yanzu fita zasuyi idan mun gaisa.

   Wani farin mutum ne ya dumfaro kofan zai shigo kamshin turaren shi kawai ya isa ka dago kai kaga ko waye maishi nan dandazon yan uwa suka dare a kofan dashi da wani suka shigo dakin kawai ba wanda ya shigo bayan su sai ni da mama da yaron anty na da muke zaune a dakin a lokacin.

  Mayar da hankali na na nayi ga wayana dake hannu na a lokacin ban daga na kallesu ba suka zube kasa suna gaida mama din cikin girmamawa.

   Tace dashi bayan sun gaisa ashe kana tafe baka fadawa kowa ba harda samun abin arzikin da kayi bamu kai girman da zaka sanar damu hakan ba a yanzu sai dai muji ga shanun talla ana fadin wai ka samu karin girma a ma aikatar ku.

   Yace ba hakkana bane mama bari nayi sai nazo in fada maku dama ashe ma kun riga da kunji abinda ba a ko rantsar dani ba tukun .

  Daidai lokacin na dago kai cikin jin haushi na watsa mashi wani irin harara ban sani ba ashe idon shi yana kaina a lokacin cikin rashin sani na nayi saurin dukar da kainanajigina da kujeran da mamake zaune tare da mayar da kaina ga wayana da nake duba.

   Wanan wata yarinyace haka miskila har da zata iya hararana da nuna min ko in kula yace a ranshi in dai zaka sake hali wallahi kasake mudin dai mune iyayyen ka ba wasu ba.

  Yanzu ka duba fadin gidan nan kaf yan uwa ne da abokan arziki da mommyn ku ta gaiyato suka zo don ka idan  ba a zumunci waza ka gani a nan yanzu kai hakan ma da sukai maka bakaji dadin shi ba.

  Ace mutum babu nashi wanda ya ja a jiki sai dai yan duniya masu maka rudi da duniya kaina na kada alaman fada mashi dai mama na tabe baki na.

   Wayana ne yai kara a lokacin baba nane ya kirani da sauri na dauka cikin kashe murya nace daddy yau kaji ban kiraku ba ka kirani yanzu nake son kiran ka a yanda nake magana da mahaifina cikin sakewa da walwala kamar ina magana da wani sa a na sai mutum ya saurara zai iya jina don kada in damay su in hana su maganan da suke yi din.

   Muryan su naji yana fadin mama zan shiga gida in huta don ban isa can ba nan na fara shigowa in gaida ku.

  Har lokacin yanayin ta ba dadi Allah ya sauwaka naji ta fada masu tace Yusuf ashe kuna tare yusuf din da ya dukar da kan shi tunda mama ta fara mai fada sai a lokacin yayi magana yace eh mama tun da ya bugo min zai dawo ai naje abujan taron shi.

   Mikewa sukayi zasu bar dakin tace kaji an mayar da Fati dakin ta ko   hakan yasa shi tsaya yace naji mama.

  Wani sabon hararan na dago in aika mai still muka kara hada ido yasha toka a lokacin yace zamu tafi Allah ya tsare ta kara maimaita mai suka fita dakin.

  Ajiyan zuciya na sauke bayan fitan su mama din tace kin ga yayan ku ko yau khadija nasan kila baki san shi ba.

   Murmushi kawai nayi mata nan sauran diyan suka shigo suna fadin su mommy sun fita ance gidan ya cika da mutanen Nafisa don haka mu zamu wuce can.

   Kafin ya gama ganawa da baba su zainab suka fito suka ce in tashi mu tafi Allah ya gani da zasu bar ni in zauna wurin mama da zai fi mun dadi don ban son hayaniya da yawa ga matar gidan da mai gidan da nake kule dasu a raina.

  Ganin mota zamu shiga yasa na dauka gidan yana da nisa sosai ashe ma ba wani nisa muna shiga mata yan duniya ne birjit a farfajiyan gidan zazaune saman kujeru farare sai kidan dj dake tashi kamar wani buki akeyi mai muhinmanci a gidan.

  A raina nace kudin banza a bazan suke tafiya mommy na gaba ita da anty amarya muna biye da yawan mu a bayan ta muka shige gidan.

  Nan naga duniya a cikin gidan sai kace ba a garin kaduna muke ba part din Gatin muka shiga a sama suke dukan su mun samu tayi kwalliyanta ba laifi nikan a nan falon ta na zauna zainab ma da namu yazo daya sai ta zauna a wurin.

  Anan wasu suka zauna basu shiga dakin ta ba su anty na kan an shige daki nace magulmata a raina jefi jefi muke hira da zainab muna dan dariya .

   Sai gasu sun fito suka ce a sauka kasa a falon kasa zamu jira shi koda muka fito ba kowa a falon sai zuwa can Nafisa da mutanen ta suka fito cikin mamakin ganin yan uwan shi da na Fati wanda bata zaci haka ba yasata daure fuska atake ta nuna kinshin ta karara a wurin.

  Gashi kuma har ya iso gida a lokacin nan su mommy suka ja Fatin zuwa taron shi daidai kofan shigowa falon gidan mai dan karen girma da tsaruwa.

   Duk abinda su mommy suka ce tayi shi tayi a wurin aka dauki ihu da tafin yan uwa itama tazo da nata tawagan sukayi iskancin su da sowace sowace irin na yan duniyan mata shiko yana wani washe baki yana runguman matan nashi.

  Ranan dai naga kishi kara don buzuwa a gaban kowa ta kwace hannun mijin su daga gefen Fati din ta rungumay shi ita kadai.

   Juyawa nayi wurin zainab nace wanan tsohuwar may take nufi ne haka wai tsuhuwar da nace yaba sauran yan matan da muke tare dariya duk aka kwashe da dariya.

  Ido rufe ta kallo mu tana rugumay dashi a jikin ta kamar wani soko sai lumshe ido yake yi tace kada ku kawo min iskaci a gida na don ban gaiyace ku ba.

   Ai ba gaiyyan ki muka zo ba mu wane mu da gaiyan ki kin ga mun yi maki kama da mutanen banza ne duk wurin akayi tsit ana kallon mu .

  Wai wanan yarinyar yar gidan uban waye a garin nan nace yar gidan ubanki ne a garin nan tsaye kowa yayi yana kallon mu ta fara fisge fisge wai zata zo ta dake ni a wurin .

   Ko dar banji ba na ce da turanci too hell with you wallahi don ba don ki muka zo gida idan kikayi gigin tabani yau sai kin raina kanki wallahi .

  Anty Fauziya tazo ta jani da mommy suka hau sama dani shi kuma sai cewa yake ta bari bai son fitina ita fa ta tara mutane tace ba gaiyyaci kowa naka ba don nasan halin su ba sona sukeyi ba.

   Saman yabi da kallon mamaki yadda karama dani na iya tsayawa a gaban su nayi wa yar lalai matar shi tas na barta nan tana hargowa.

  Anty na duk ta tsure sai fadi take ku bari mu tafi gida khady dama nasan halin ta bata daukan wulakanci tun tana karama.

   Kowa a wurin fadin albarkacin baki  shi yake yi mun dade a dakin kagin mu fito zuwa gida muka bar wasu anan sai da su Binta sun fito tare damu sai nuna ni abokanta sukeyi da muka fito.

  Niko ko a jikina don ban damu ba ban biya gidan su ba gida muka wuce mommy taba anty wani leda dake da kaya a ciki ni har nayi gaba a lokacin har muka kai gida ba wanda yayi magana a cikin mu.

  Sai bayan mun yi sallah magariba da ishai muka fito falon har lokacin ban sake ba raina a bace yake da abinda ya faru dani.

  Zaman mu shigowan su zainab da Binta da Amira suna shigowa suka saka dariya gaba dayan su anty tace dasu yau ai ni naga abin mamaki gun khady mata da gidan ta ki ce zaki fadan karfin hali.

  Nace anty wallahi ko ba yau ba wanan matar tai min ramawa zan yi haka kawai zan tsaya tana zagina akan may wata tafi asali.

   Ni dai don Allah ki rufa min asiri a garin mutane khady ki koma gida lafiya  wanan abin da may yayi kama Binta tace anty mu ai tayi muna daidai wallahi.

  Baba ma da yaji cewa yayi wai waye khadija din nan har cewa yayi a kiraki mukace kin tafi gida.

   Anty tace kinji ko wallahi khadija ki rage wanan girman kan naki don ba zai kaiki ko ina ba wallahi tace ai bayan dawowan mu ayin fitina sosai a gidan dasu anty Fauziya da suka tsaya suma sai da akai rashin mutunci dasu yau.

  Wuri ta samu mana shiyasa takewa mutane rashin mutunci son ranta inji zainab ai yau naji mamaki da bai biye mata ba da dane ai rama mata zaiyi.

  Sai lokacin nayi magana nace ashe na manajo ne yayan naku cabdi dako yau yaji magana wallahi binta tace da zaki iya ramawa nace mai zai hana iyaka dai yasa a kama ni ko zainab tace wane shi.

[10/12, 3:46 PM] Khadeejah🥰: A raina sai mamaki nake wai wanan matashin da nagani wanda bai wuce ace yanzu zaiyi auren farko ba ke da mata har biyu haka.

  Buzuwan nan dai da za a zauna a fadi gaskiya tana iya girmay mashi daga shi har matar shi sai idan ance yanayin jikin su kawai da ba a gane hakan.

  Ita kuma Fatin baka ce sai dai da zata zauna ta gyara jikin ta banga abinda buzuwan nan zata gwada mata ba sai dai kasshh yanayi irin namu na matan hausawa yana cin rayuwan ta da haka nake hango buzuwa ta kwace mata miji .

   Yau da gobe sai Allah dama sati uku zanyi don hutun ba yawa shiyasa ban so zuwa kaduna ba a wanan lokacin amma anty na ta dage sai nazo ita kadai ne a gida mijin ta yayi tafiya.

  Ashe kuma da rabon mu kwasa da matar mulki ne a garin ya kawoni don haka shiri nake inda ba komai nake shiryawa sai kayana don ban daukan provition da ga gida sai na tafi can nake saya.

   School zan wuce direct sai nakwana biyu zan shigo mina in masu weekend in kwashi abinda na samu in koma bayan kwana biyu don haka nake ta shirin komawa makaranta a lokacin.

  Kwatsan da safe muna karyawa saura kwana biyu tafiyana sai ga wayan mommy ta bugo ma anty wai Fati ta dawo gida yanzu haka tana nan gidan su naji anty na fadin o o Allah yanzu matan nan da karfi da yaji sai ta raba wanan auren take nufi.

  Banji may mommy ta fada mata ba nadaiji tana fadin gaskiya haka nane idan abu yaki sai ayi hakkuri kada zumunci ya baci idan abin ya sake shi inda rabon komawan ta gidan sai ta koma.

   Bayan ta kashe waya tace mummy tace ki shiga kafin ki wuce kada ki tafi baki sallamay su ba nace haba anty may yasa kika fada mata zan wuce ai sai yazama kamar roko idan naje sallaman su.

  Kai ta girgiza min tace ba haka halin su yake ba dauka na sukeyi kamar wata ta gida a gurin du duk zuwa kikayi kika wuce sai sunyi min korafin hakan.

   Shiru nayi sai tace o Allah sarki wanan buzuwan dai ta hana Fati zama gidan mijin wai yanzu kuma ta kara fitowa tace bazata koma ba.

   Dudufa baifi wata da ta koma gidan na yanzun kuma ta kara fitowa jiya wai sai dai na shiga inji may kuma ya hadasu fada yanzu.

   Takaici bai barni nayi magana ba sai dai a zuciyana nake bankawa mijin zagi da rana su binta suka shigo gidan mu anan muke jin labari wai tunda ya dawo buzuwa taki bari ya ke be da fati hakan bai isheta taja Fatin da fada har tana fadin sai ta kashe ta.

  Shiya ba Fati  tsoro tace barin gidan yafi mata nace shike nan ta samu galabanta ai ta kashe ta din idan ta isa mana.

   Gaskiya matan nan ta samu wuri da yawa wallahi nace shiko sokon yayan naku fa may yayi a kai tace jiya baban mu ya kirashi sai cewa yayi shi yagaji da halin fati tana bata mashi suna.

   Ai wallahi idan da nice tace sai ta kashe ni da na nuna mata hauka ke matsorata ne fa iskancin abaki yake masu kawai Fatin dai ne wallahi she is to slow .

  Anty tace khadija baki san aure ba fa shi wanda ake abin a kansa bai nuna wani feeling din shi akan ta gara dai da ta hakkura ta basu wuri.

   Zata tafi nace barin bisu daganan in masu mommy sallama tun ranan da mukai fada da buzuwa ban sake shiga sai yau da zan tafi sallaman su da anty ta matsa min.

   Tsab na shirya na fito cikin wani dogon riga mai hannu shara shara shara da gyalen shi na yafa akaina sai turaren da na fesa a jikina.

   Mun shiga gida inda na fara zuwa dakin mama na gaida ita sai na fito naga anty amarya a waje anan na gaida ita har zan wuce tace khadija ashe haka kike ina ganin ki shuru shiru dake ashe ke ma jaruma ce ban sani ba.

  Dan guntun murmushi nayi nayi kasa da kaina kawai dakin mama na nufa ina jin suna maganan a waje da mai masu aiki na shige wurin mama in gaida ita.

  Tana zaune a falon ta tana waya haka yasa na samu wuri a kasa gefeta na zauna ta gama wayan ta dago kai cikin fara a tana fadin yau khadija ne gidan nace mama ina kwana.

  Ta amsa min fuska a sake nace mama nazo in sallamay ku gobe zan koma school tace a a har hutun ya kare wanan karon nace eh mama.

  Ta sake cewa gida zaki ko Abujan zaki wuce aa zan wuce school ne daga nan tace barin baki tsaraban yan makaranta ko nace mama da ki  barshi ai ba zan dauki kaya daga nan ba sai naje can saya.

  Tace a a wanan kan zaki so dambu ne da akai ma yayan zai tafi dashi kin san yana son dambun nama sosai shine na aikai mashi shima gobe zasu tafi.

   Ta mike ta shiga daga ciki sai gata da roba dan madaidaici ta fito da kudi a hannun ta ta miko min nayi godiya namike zan fita ko ba a fada ba yanzu na sheda wanan kamshi ba kowa bane sai dan ta Abdulsamad mijin buzuwa.

  Zai shigo ni kuma zan fita ban yi tunanen in kauce mashi ba a lokacin dole suka jaye a hanyan na fita ashe da buzuwa suke tana bayan shi.

   Mama ce naji ta kwala min kira sai na dawo wanan karon sai da na bari sun gama shiga na shiga dakin nima na karasa wurin ta gwiwa na biyu a kasa na zube ina fadin mama gani.

   Buzuwa ke gaida ita ta tsaya amsawa ta dago tana cewa dan ta gobe ne zaku tafi din ko yace insha Allahu mama yanzu ma mun zo mu sallama ku ne don goben sakko muke son yi dan zan shiga office.

  Ta juya gare ni tana fadin gobe sai ki shirya su tafi dake indan zasu wuce gaba na ya ba da damm da sauri nace a a mama ba tafiyan safe zanyi ba ni.

   Khadija yayan ku ne fa ki shirya ki bishi yafi shiga motar kasuwa su wuce da ke shidai baiyi magana ba ya rike goshin shin da hannu guda .

   Sai buzuwa ne tace motar tamu ai a cike take  dayan ni dashi ne sai driver dayan kuma na masu aiki mun ne su larba sai na security din mu .

  Naku zata shiga don ita din ba bare bace yar gida ne kaji na fada maka tau mama yace ta shirya da safe din kada ta makara sukuku na mike tare da fadin mama na gode.

   Fitana dakin mommy na tafi ina nuna mata abinda hajiya mama ta bani tace ai yaya tafi danan ban fada mata zancen bin mijin buzuwa da tace in yi ba a lokacin itama daki ta shiga sai gata ta fito min da wani bakin dogon riga da takalma cikin na sayarwanta tace ga wanan a samu na sakawa.

   Binta ce ta shigo dakin tana dariya mommy tace maynene kuma tace khady nakewa dariya mommy mama tace da yaya gobe su tafi da ita.

   Ga buzuwa can tana fada bayan fitar mama daki  wai bata yarda ba bata san mama ta jita ba shine mama ta fito tana fadin har ta isa tace ga abinda take so tace ita bata yarda ba yaya ce shi baice ba zata bisu ba ai.

  Juyowa mommy tayi ta kalle ni nace nifa ban iya bin su gaskiya don idan tayi min wallahi nima yi mata zanyi gara ko kada in bisu din.

   Dariya take min mommy tace akan may kin samu sauki bazaki bisu ba ai shi Abdulsamad baida hakana tunda har yaya tayi mai magana da bai daukan ki tun a nan zaiyi magana balle yanzu da yasan yaya tana hake dashi ai ba zai so ya bata  mata rai ba kuma.

  Daga cikin dakin mommy anty Fatine ta fito tana saye da wani hijjab har kasa fuskan ta duk ya kode alaman tasha kuka har ta gaji.

  Gaida ita nayi ta amsa kasa kasa ta zauna a daya daga cikin kujerun falon mommy tace kin tashi tace eh mommy tace ga mutanen ki can sun shigo sallaman mu zasu koma gobe wai.

  Shiru tayi batayi magana ba sai mommy ta kara cewa kin san yaya da son jan magana wai cewa tayi gobe su wuce da khadija da zata koma makaranta goben.

  Wai ai ba zata bari ba wallahi bata son kowa ya rabe shi balle wanan da take gani mace haka maikyau kuma gasu da wata a kasa daman.

  Aiko banyi niyan binsu ba da amma yanzu sai na bisu tunda abin haka inga yadda zatayi a motan dani idan na shiga.

   Murmshi mommy tayi tace ki shirya da wuri don shi da wuri yake tafiyan shi idan zai tafi tashi nayi  nayiwa mommy sallama muka fita da binta ta rakani.

  Naje gida na nuna ma ya Amina tsaraban da suka bani don da zanfito anty amarya taji zan wuce ta dauko min wani set din turare mai kamshi ummi ce bata ban komai ba a cikin su.

  Sai can muna hira nace ya Amina kinsan wai mama cewa tayi in shirya gobe in bi mijin buzuwa da buzuwa idan zasu koma.

               Da sauri tace may ne ?

  Nace wallahi da banyi niyan binsu ba amma tunda ta nuna bata son haka zan bisu din inga yadda zatayi dani a hanya .

  Nidai wanan zuwan wai damay yazo muna haka ne da tarihin buzuwa ko damay yanzu ke binsu din zakiyi,  ba zaki hakkura kibi motar kasuwa ba.

   Don mama ne kawai zan bisu kada in bata kunya tunda tana sin gwada masu ikon ta ne a kan su da kuma ita buzuwan zantafi.

  Da yamma sosai na fito zan shiga gari in karbo dinkina da nakai ina fitowa bakin get sai ga motan shi tundaga nisa na kawar da kaina don ban san wanda ke cikin motar ba sun kawo kusa dani na gane su ne na watsa mai harara na kawar dakai.

  Yusuf wacece wanan yarinyar wai da nake gani a gurin mama yarinyar bata da kunya ko yanzu baka ga wanj harara da ta watsa muna ba kullun shi take min fa har a falon mama da muke haduwa.

  Dariya Yusuf din yayi yace amma kuma tana da kyau gaskiya koda yake kai yanzu baka ganin kyaun mace gaka da buzuwa a gidan ka.

   Wai Yusuf may ya kawo wanan magana haka daga tambayan ka yarinya idan baka santaba kace kawai baka santa ba period.

   Dariya Yusuf din yayi  yace kai ke nan da anga mace mai kyau kace kada ayi magana wallahi yarinyar ta hadu sosai shiya take da jan aji da yawa.

   Nafisa fa tayiwa rashin kunya a gida na ka sani kuma kake wanan magana yace a a suka dai yiwa juna ta zage ta ta rama don uba baifi uba ba.

  Matsalan Nafisa tace kowa zata juya don tana takama mijin ta na da kudi kaji dai abinda yarinyar tace mata ai batazo roko wurin ku ba zumunci ya kawo ta.

 So tayi ka kama mata kuyi wa yar mutane cin mutunci a banza.

  Yace ai don na ganta a wurin mama ne yasa na kyale ta amma da ba zan yarda ta shigo min gida tayi min tujara ba for what ?

   Matar ka ce yar cin mutunci ai ya furzo iska daga bakin shi yace matsalan ta ke nan wallahi cikin ina tsawata mata ta bari ke nan ma.

  Yanzu dai kun kori Fati kun huta tabar maku gidan yace ta dai kori kanta amma ni ban kore ta ba ai ban san irin Fati ba wallahi .

  Bandai san irin ka ba malam buzuwa ta hanaka ka ba Fati da yara hakkin su kai kuma ka biye mata ranan fa a gaban kowa ta banbare hannun Fati a jikin ka kuma ka yarda.

  Wallahi idan zakai ma kan ka fada kayi tun baka makara ba kana ganin su Affan idan suka girma sukaga kanawa uwar su haka zakaji dadin su ne.

 Kai wa kan ka fada wallahi akan buzuwan nan kada ka tashi ranan lahira da bari shayaye .

  Bugu yakai ma abokin nashi yace Allah man abinda akace yana samun masu karkata gin mace daya ke nan na fada ma tun farko ban yarda da ita ba yanzu kaji abinda hajiya ta fada muna ranan.

   Nisawa yayi yace ai Fati ta riga da ta hadani dasu har baba fushi yake dani a gidan da sauran yan uwa.

  Yusuf yace buzuwan ka kuma tana jin dadi ba ta kori yar masu gida an bar mata gida tana yadda take so ita kadai tayi hankali wallahi da iyayyen nan namu.

  Shiru yayi yana nazarin maganan abokin nashi baice komai ba san cen yace kasan hajiya don jan magana cewa tayi gobe da wanan yarinyar zamuyi tafiya.

  Ina Yusuf ya tambaya da sauri yace wai Abuja zamu tafi a can take tace nowarder idon ta yake a bude haka bata da tsoro da ganin ta ai.

   Na karbo dinki na dawo na shirya kaya na bayan na gama komai na zauna ina tunanen yadda tafiyan mu zai kaya a goben.

   Ya Amina ta ban abinda zata bani taja min kunne don Allah kada in kula buzuwa har mu isa nace ni ina ruwana da ita su dai kaini su sauke kawai.

   Da safe ya Amina ta tana dani da wuri na shirya jiran kawai nake ace in fito mu tafi ya Amina tace in dauki jakkana da sauran kayana inje dasu gidan su mommy nace ai wanan ya zama tonon asiri haka .

  Ni madai su wuce idan haka ne dole ta kyaleni don ba yadda zatayi dani na gama komai har da karyawa ya Amina ta sani yi da safe don tafiyan da zamuyi din.

   Can sai ga su Binta sun shigo wai in fito da kayana ga su buzuwa nan sun fito suna ciki suna sallaman su mama zasu biyo nan su dauke ni inji mama.

   Tashi nayi na fara fito da kaya na waje suna tayani fitarwa kofan gida sai ko ga motan su ya tsaya suna baya dashi da buzuwa gaba zan zauna dani da driver su.

  Ina jin ya Amina tana gaida su binta ta bude min na shiga duk da kamshin turen su amma nawa ya karade motar har na shiga na zauna ban yi masu magana ba  ina daga wa su ya Amina hannu muka tafi.

  Tsayawa sukayi suna bin motar da kallo Binta tace yau akwai tafiya a wurin nan jifa yadda anty Nafisa ke cika tana batsewa kamar ta fashe.

  Zainab tace suna daidai da khady ai ta fita iskanci    daidai zasuyi a motar niko saida aka fara tafiya na dan juyo nace dasu ina kwanan ku murya can ciki bai fita.

  Ina kokarin cire airpies dina na  sa a kunnuwa na  tare da sake kira, a a wayan na lumshe idanuwa a hankali ban kara bi ta kansu ba kuma.

  Tun ina bi sai dan barci ya dauke ni ina yi ina falkawa na gyara zama tare da dan satan kallon su ta karkashin idanuna na naga yadda suka zauna manne da junan su sai dai aiki yake a laptop din shi.

   Ita kuma tana gyangyadi daga zaune  da yake lafiyayun motoci ne kafin wani lokacin har mun kusa isa Abuja driver yaiwa magana yatambaye ni ina za a sauke ni .

   Ya juyo idanuwa suna lumshe ya dan taba sit din na bude ido tare da cire airpies din dake a kunne na yace yallabai yace a ina za a sauke ki ne ?

   A hostel nake zaune na bashi amsa ya juya gun ogan nashi yana fadamai abinda nace mai bai kara magana ba har muka shiga gari.

   Ban ankara ba sai naga suna shiga jerin gidajen dake asorock a wani gida motar ta danna kai suka shiga katon gida ne mai wani babban get ginin gidan sai mutum yace a turai yake sai lokacin na cire airpies din kunne na naji buzuwa na fadin ita a ina za a sauke ta banji may mijin ya fada mata ba nidai ban fita motar ba su kuma sun shige ko godiya ban masu ba.

   Driver ya shiga masu da kaya ciki ni dai sai bin gidan nake da kallo a raina nace shiyasa yake abinda ya ga dama ashe yasan abinda ya taka, 

  Ga wasu manyan motoci gudu uku a fake wata katuwar jeep ta dauke min hankali har ina satan kallon ta a wurin motar sai sheki take tana daukan ido da gabin ta sabuwace.

  Sai dai ga daular duniya matashi dashi amma ya kasa auren yar kasamu suci arziki a tare sai wata bare ce buzaye ne gidan naga suna fitowa daganin su kasan yan uwan buzuwa ce ba sai an fadi ba nace mijin hausa ke nan inwar giginya na nisa ka more ka.

   Driver ne ya fito tare da wani dan saurayi buzu a baya shi yana dauke da tire da drinks yace gashi mai gida yace a kawo maki No na gode na fada  tare da juyawa da kaina gefe a can cikin gida kuwa fitina na tsakanin buzuwa da mijin ta.

   Wai sai dai in shiga motar haya akaini hostel bata yarda ya wuce su sauke ni ba dole yasa driver yakai ni sai ya dawo ya kai shi office daga baya.

  Mun kama hanya driver ke cewa kai matar oga akwai kishi yanzun haka ta rike shine ciki wai bata yarda ya fito atafi kai ki dashi ba.

  Murmushi nayi nace mahaukaciyar banza kawai itake nata haukan ni ko a jikina yace nayi mamakin yadda ta yarda aka dauki ai nasan shi take ma fushi har muka zo ba shiri a tsakanin su.

   Surutun nashi ya isheni don haka nakawar da kaina gefe kamar ina kallon titi don abokin gulma yake nema da alama ganin na kyale shi shima yaja bakin kishi yai shiru har muka isa gidan da nake ba a cikin hostel sai dai gidane na haya da yan makaranta ke kamawa.

  Driver shi ya taimaka min da kayana har zuwa bakin gidan namu ya shiga min dasu sai dai bai shiga ciki ba kudi ya miko min yace gashi oga yace idan na sauke ki in baki.

  Dan jimm nayi kamar bazan karba ba sai dai nasa hannu na karba tare da fadin kace nagode sai dai ban faye karban irin kyautar nan ba kallo na yayi ganin na fara jan trolley dina yasa shi wuce yana mamaki na a ran shi.

  Dakina na bude wanda mijin ya Amina ne ya kama min hanyan shi dakine ciki da falo da bandaki a cikin sa sai inda mutum zai danyi girki daga waje haka dakunan suka a jere har dari da wani abu.

   Dakin yayi kura dan sati biyar din da nayi ban ciki daga kofa na aje kayan da na dawo dashi na fara gyara dakin tukun sai da na sharo ko ina na dakin.

  Na mayar da komai yadda nake son shi na fito ba zan iya fita ba haka yasa na kwanta don in sauke gajiyan dake jiki na a lokacin.

  Ba wanda yasan na dawo do  haka na rufe kofa na kwanta abina sai barci mai nauyi ya dauke ni a cikin barci sai gashi wai muyi mumunan fada da buzuwa mijin kuma na tsaye yana kallon mu baiyi magana ba.

  Falkawa nayi don kiran wayana da akeyi na lalubu wayan da kyat saboda barci da yaci idona ya Amina takirani.

  Ina dauka naji muryanta tana cewa ina kika shiga ne haka waya nata kara baki dauka ba cikin muryan mai barci nace wallahi barci nakeyi anty.

  Tace yaya kuka sauka shine koki kirani hankalina ya kwanta nace wallahi lafiya kalau muka sauka tace badai wani matsala ko ke da buzuwan ki ?

  Naja guntun tsaki nace suna can gidan su muka sauke su driver su ya kawo ni hostel ni komai bai hada mu ba a motan bayan gaisuwa.

  Tace to barin barki ki huta an jima zan kira son naga yanzu barci yaci karfin ki nace ai na tashi yunwa ma nake ji yanzu tace to ki samu abinda kikaci kin san kina da ulcer nace yanzu zan tashi.

   Baki sayo komai ba ma ke nan nace yau na gaji ne anty ba zan iya zuwa ko ina ba sai dai gobe idan na fito lecture.

  Allah yakai mu tace muka kashe waya ina jin dadin yar uwa ta sosai saboda kulawan da take bani na musanman shiyasa nima nake mata komai kamar ita ta haife ni.

   Mafalkin da nayi ne ya fado min a raina lokaci guda yake dawo min dan dariya nayi nace ikon Allah wanan buzuwar kamar manya ta tsaya min a rai haka ?

   Sai a lokacin kudin da driver nan ya bani ya fado min a rai na jawo jakka na daga kwance na kirga kudin ido na zaro ganin har dubu hamsi ya bani nace wanan yasan zafin kudi kuwa ?


ZAINAB IDRIS MAKWA

            SEENABU

Bai yi mamaki shigowa ya samu abinda ya gani ba a gidan don ba yau bane farkon yin haka gare ta don a duk lokacin da ta ganshi ya rabi wata mace ba aita ba ko kannen sa da suke uwa daya ko uba daya ba hakan take mashi wannan haukan a gida.

  Don sani yadda suka rabu da ita kafin yaje office akan kawai mahaifiyar shi ta bashi umurni ya bi na su rage min hanya zuwa abuja kuma a motar shigan su.

   A hankali ya kusa kai cikin falon su na sama ga tarin gajiya a jikin shi daya kwaso yau ga na tafiyan da sukayi ga ya zo ya samu aiki a office.

  Hankalinshi yayi matukar tashi saboda ganin yadda tayi kaca kaca da falon komai ta har gitse ta fasa na fasawa ta watsar dana watsarwa a kasa.

  Hatta tv bango ta tarwatsashi ga crystal glass da aka aje don decoration din falon a folon a kasa ta tarwatsa duk komai na falon a har gitse kamar ta haukace.

  Tsayawa yayi a daga kofa yana bin ko ina da kallon mamaki a ranshi kuma yana mamakin irin zafin kishin Nafisa.

   Wanan wani irin kishine haka shi bai da dama ya sake da wata mace a rayuwan shi sai ita duk da tasan neman mata ba halin shi bane.

  Wanan wani irin rashin hankali ne ko kishi haukane kinshi Nafisa ba ba bai san yadda zai fasarashi ba don abin baiyi kama dana mai hankali ba.

  Shi dai tun farko bai fada mata da ita kade zai zauna ba a rayuwan shi kuma tasan yana da mata tayi ta nacin sai da ya yarda ya aure ta.

  Amma kuma shigowan ta ta hana shi zaman lafiya da iyalin shi da mahaifan shi gaba daya halin Nafisa idan ya motsa sai yaji nadaman auren ta dayayi.

  Amma kuma idan komai ya wuce sai ta koma kamar ba ita ba shi dai wanan abin yana matukar damun shi wallahi.

  Dakin barcin su ya nufa inda ya hangota takure a wuri daya tayi kuka tagaji ta ba kanta hakkuri jin an shigo dakin yasa ta dago kai cikin fushi don taga ko waye ya shigo mata daki.

  Daga kofa ya tsaya ya kare mata kallo da kyat ya bude bakin shi yace wanan wani irin rashin hankali ne ko kishi haukani a garin ku ko kwakwalwan ki ya tabo ne da zaki min hassara irin haka don bake ke saye ba ko ?

  Ya ka maganan cikin fushi yana hararanta a harzuke ta dago tana huci tana fadin eh hauka nake kuma a kan ka wallahi kadan ka gani duk kace zaka hadani da wata mace a duniyan nan abinda zan ma sai yafi wanan.

  Yace oh ashe kina da aiki kuwa don dai ni namiji ne mijin macd hudu so zan iya aure a duk sanda nayi raayin hakan.

  Cikin wani murya tace wallahi karya kake baka isa kace zaka hadani da wata kishiya can ba ni ni kadai ne matar ka,  ka sani.

   Oh dama tunanen ki ke nan amma kafin ki shigo kin samay ni da wata matar ko amma sabods zafin kishi irin naki ki  hana mu zauna lafiya da ita.

  Kaima kasan abinda ba zai yuyu ba ke nan ka hadani da wata mace may na rage ka dashi a duniyan nan wani irin kulawane baka samu a gare ni da sai ka hango wata a waje.

  Cikin mamaki yace wana na hango a yanzu din kuma wa kika gana kula haukan ki dai ke nuna maki hakan mahaukaciyar banza kawai.

  Indan kai ba baka hango ba ai mahaifiyar ka ta hango maka ita in bashi ba may ye nace wa sai wata ta biyomu a motar mo inba son hada fitina ba.

  Yace Nafisa rashin hankalin naki har yakai ga mahaifiyata haka  tanan kika biyo kuma Nafisa kan mahaifana tace in ba haka ba ne may take nufi  yasa ta hado mu da ita ?

  Yace cikin daka tsawa karki kuskura ki kara fadin wani maganan banza akan haka rakin zai baci sosai a gidan nan daga haka ya juya zaj bar dakin sai kuma ya juyo yace.

  Ki tabbatar da kin gyara dakin nan da kan ki kuma ki mai da komai da kika fasa in ba haka ba wallahi zaki ga bacin rai na a yau din nan.

  Sannan wani magana guda kada ki kuskura ki kira wani dan aiki yazo ya kwashe wanan barnan da kikayi ke da kan ki nake son ki kwashe shi daga haka ya fice ya shige wani daki a gidan.

   Bin shi tayi da kallo don tasan ya hau sosai ga abinda tayi din sai yanzu nadama yazo mata a rai ga abinda ta aikata don tasan gaskiya ya fada mata kuma zuciyar tane kawai ya bata hakan ta hau ta zauna akai.

  Gashi ta jawa kanta aiki don abinda ya fada har cikin ranshi ya fada duk dan aikin da takira ya gyara mata tasan abakin aikin maishi yake.

  Gashi duk yan uwanta ne na jini babu wanda zata so a kora a cikin su haka yasa ta mike dole a cikin daren nan ta fara gyaran duk inda ta bata din.

  Dakin yake yayi wanka ya sauya kayan shi zama yayi tare da dauko laptop din shi ya duba sai dai ya kasa aikin da yake son yi a lokacin tunane halin Nafisa yake yi.

  May take nufi dashine ya tun haduwan su na farko da ita a bakin ma aikatasu yazo shigewa ta miko mai hannu tana fadin baba bani kuddi.

  Kallon mamaki ya tsaya yana mata tare da waigawa baya ko da wani take magana bashi ba sai yaga babu kowa a wurin sai shi kadai tsakanin shi da mutane akwai nisa ta sake mika hannu tana fadin baba bani kuddi.

   Yace kudin may zan baki tayi mashi alama da hannu abinci zataci alhalin su ke sai da abincin dayake shi mai tausayi ne kamar yadda mama ta koyar dasu na taimaka ma nakasa dasu sai ya ciro dari biyar ya mika mata da sauri ta karba har kasa tana mai godiya.

  Ta nufi rufan sai da abincin nasu ta mika kudi yana kallo aka bata abinci ta koma gede tana ci a haukace kamar mai yunwa.

  Tun wanan ranan idan yazo zai shige zata taso tana fadin baba bani kuddi sai ya mika mata dari biyar taje ta karya dashi.

  Har shakuwa ya shiga tsakanin su mai karfi ko bai ganta ba zai aje mata dari biyar din nan kudin karyawanta yakawo mata yace ga kudin abinci nan.

   Tsaki yaja ya rufe laptop din tare da kai kafadan shi saman gado ya kwanta rigingine yana ci gaba da tunane shi mutum na farko da ya fara warning din shi akanta shine Yusuf.

  Yace kasan fa irin mutanen nan kudi suka fito nema ido rufe da maza ya kamata ka daina bata kudin nan kar mutane suyi zargin ka akanta.

  Shiko tausayi  take bashi baiga zai iya kin taimaka mata ba don taba bukatan taimako aa lokacin har yakai sun fara kyaabewa da ita.

  Alokacin kallon yarinya yake mata don bai dauka ta haihu ba ma sai da yaje da zancen ta gida wurin su mama nason ya taimaka mata.

  Mama ta kafe ba  zai dauko mata fitina cikin zuri,anta ba anyi anyi da mama tace ba zata yarda ya dauko buzuwa ba yadda take ganin a na kwashewa dasu a gidaje da suke.

   Ga fati bata rage shi da komai  ba tana mishi biyayya don auren gata akai masu shida ita tun yana karami sosai saboda an ga taso yazo daya da ita aka dauka soyayya suke yi dashi aka hadasu aure tare.

   Ido ya runtse a haka barci ya dauke shi cikin barcin ne yaji ta a jikin shi don bata zuciya dashi duk yadda ya iya fushi da ita bata yarda fushin nasu yai nisa.

  

Tea na tashi na hada don yunwa ke damu na na debo danbun da mama ta bani ina hadawa dashi ina jin kida na tashi a gidan alaman adawo da yawa ke nan hakan bai sa na fito ba don har na rufe kofana a lokacin.

   Na gama nayi shirin kwanciya na don kada in makara da safe ina son shiga school tunda safe in gama komai don zan tafi shopping da yamma.

  Washe gari bakwai na gama komai na fito don zuwa cikin makaranta ina rufe daki ne makwaciya na ta gani tace ashe kin dawo dama naga haske jiya a dakin ki sai kuma ba sake gani ba nayi zaton idona ne ke gizo kawai.

  Nace eh nadawo jiya nan dai na tsaya muka gaisa sama sama da ita don ina sauri a lokacin na samu napep da zai karasa dani cikin school tunda ajike nake da kudi yanzu.

   Naje na gama komai har na samu shiga lecture a lokacin sai karfe uku na juyo zuwa gidan mu a hanya na tsaya sai da na sai abinda zanci na wuce zuwa gida.

   Sallah na fara yi don lokaci ya shige sosai koda na dawo wanka nayi na dan huta sai na shirya don zuwa sayo abincin da zanyi amfani dashi na wanan time din tunda ina da waddatacen kudi a hannu na saboda wanan tafiyan a saa nayi shi nake gani.

  Don ga kudin da ya Amina ta bani wanda dama ita ke sallama na idan zan dawo sai dai kudin bai kan isheni sai na je gida na dan kara roro abinda ke akwai in kara kafin time ya kare.

  Sai gashi wanan karon na samu a wurin mama da kuma dan su mijin buzuwa da ya driver ya bani dariya nayi don tuna sun da nayi nace jamgwangwan ke nan.

  Ai sune maganin mazan dake ketare matan kasan mu su auro su don kawai ace buzuwa mutum ke aure ko may ko kuwa jaraba ne irin na mazan Nigeria oho ?

  Na watsar da maganan su na mike na sabala jakata na rufe kofana na nufi bakin titi don samun abin hauwa a lokacin sahad yana tashe sosai a cikin abuja do  haka na yanke shawaran zuwa can in sayo komai da nake so a saukake.

  Ban samu wani matsala samun abin hawa ba ni kadai na dauki shata har can bakin sahad mai Napep ya aje ni na karasa shiga ciki.

  Ban tsaya wani feleke ba abinda ya kawo ni na fara yi inda na dauki basket na fara zagayawa ban gare su indomie da taliya wanda shine abincin dan makaranta.

  Sai shikafa karamin buhu dana dauka da su kayan miya yadda zai kai min time kada yazo ya kare in rasa mai taimaka min.

   Bayan na gama da wayan nan sai na nufi bangaren kayan tea madaran Nidor na dauka na gari dan madaidacin gwagwani na juya zan sa a basket din da nake tara kayan a ciki .

  Kamshin turaren mijin buzuwa ne ya daki hanci na kaina na kasa ban dago ba sai takalman mutumin da na gani bakake a kafan shi hakaya na dago kai na dan kalle shi.

   Mijin buzuwa ne tare da Yusuf suke sayayya a shagon su ma dan daburcewa nayi da ganin su kamar ba zan gaida su ba sai wata zuciya tace min ko dan kudin da ya baki ai kya gaida su.

  Sannu ku nace dasu tare da juyawa na fara tura keken kayana Yusuf din ne ya amsa min tare da fadin a a yar garin mu ke ce.

  Ummm kawai nace dasu na wuce abina na karasa saura sayayyana na dungura keken zuwa wurin biyan kudi na aje a gaban wanda ke lissafi ina jiran inji ko nawa na kashe a cikin shagon in biya.

   Ya gama lissafi kaina yana akan wayana ya dago yace thirtythree thousand five hundred nace OK na bude jakkan dake makale a kafada na zan biya kudin yace ai an biya maki kudin ga canjin ki ma ya rage yana miko min kudin.

Yana kokarin miko min ledojin yaron shagon ya mike da sauri yana karba da mamaki nake kallon shi ina kallon kudin da yake miko min din.

  Waya biya nace mai duk da nasan ba wanda ya sani in ba mijin buzuwa da Yusuf dana hadu dasu yanzu ba a ciki.

  Yace gasu can suna fita su suka bada kudin sukace indan kin gama sayayya a biya maki suka tafi da sauri nabi bayan su har na samu sun tayar da motan su suna ribas a lokacin.

   Ganina Yusuf ya tsaya na dago da zuman fadar wani magana kuma sai na kasa yaya akayi yar garin mu nagan ki a sukwane ko hanya zamu rage maki ne ?

   Nace murya a tausashe aa nazo inyi godiya ne mai shago yace kun biya min kudin kayan na mika mai canji nace ga sauran kudin daya rage nan.

  Nuna min mijin bazuwa yaya yace bani na biya ba ogana ne ya biya maki albarkacin ki na yar mama mun yasa ya biya maki ban san sanda nace mijin buzuwa na gode ba.

  Ido ya waro waje jin abinda na kirashi dashi shiko Yusuf dariya abin ya bashi yace kwarai kuwa mijin buzuwa ne abokiyar fadan ki ko ?

  Sai nayi kasa da kai kunya ya kamani nace ga sauran canji ina mikawa Yusuf din kudin kai ya girgiza min yace ai shi bai kyauta ya karba jeki dashi Allah ne ya baki sai a kara ayi provition ko don naga alaman sayayyan yan makaranta kikayi.

  Kallon ledan da yaron ke biye dani dasu nayi nadan yi murmushi nace na to gode kai mun godiya wurin mijin buzuwa zai ji yace dani.

  Ai da kizo mu sauke ki don naga gaki da kaya dayawa abin hawa zai maki wuyan samu a nan da sauri mijin buzuwa yace amma dai kasan sauri nakeyi ko ?

   Haba baka gani  marance yayi ina zata samu abin hawa mu sauke ta mana sai mu tafi aiba dadewa zamuyi ba a can ko may kace yana bukatan jin ra ayin shi.

   Da sauri nace a a zan hau napep a bakin titi zaku iya tafiya na gode yana kokari bude mota yace a a ai ba zamu bar yar mama a nan na shiga kawai mu sauke ki kada ki fada ma mama mun ganki muki rage maki hanya tayi muna fada.

  Ya fito ya bude booth din motan yake magana ban da yadda na iya dole ina kallo yasa mun kayan a booth din su ya bude min bayan hangamaymay jeep din su na shiga sanyi da kamshi kawai ke tashi a cikin motar.

   Ya shigo ya tayar da motar muka fara hanya shiko mijin buzuwa ko ta kan mu bai yi ba sai faman aiki yake a sytem din shi saman jukin shi.

  A hankali yake tukin motar mun dan bar sahada din Yusuf yace mijin buzuwa sorry fa mun bata maka lokaci ko ?

  Ban son iskanci yace a harzuke sai kuma ya juyo gare ni yana fuskanta yace and ke kuma duk na kara jin kin kirani da wanan sunan sai na bata maki rai wallahi.

  Da sauri nace ni kada kaga laifi na haka naji kowa na kiran ka da mijin buzuwa bani na fara fada  ba ina magana ina jujuya idanuwa na manya.

  Dariya Yusuf keyi muna yace a a mijin buzuwa da haka kowa ya sanka a layin mu don ta fada yanzu shine zakaji haushin ta nace ai shi nagani nima.

  Yace dakyau yar mama har lokacin wani kallon takaici yake min yaja tsuki ya mayar da kan shi ga abinda yake yi ya fita batun mu da Yusuf din.

   Yace yar mama ke may sunan ki sai naji mijin buzuwa yaja wani uban tsuki yace kai malam kafa san aiki nake yi ka samu yarinya kana biye mata don wauta.

  Kasa kasa nace wai yarinya yarinyar dai tafi buzuwan matarka yasin ban dauka maganan duk sun jini ba a motan sai gani nayi ya rufe laptop din ya dafe kan shi da hannu daya.

  Shiko Yusuf cewa yayi a sosai ma yasani ai gashi yana gani a gaban shi yace kai Yusuf tsaya in fita motar nan don Allah kun isheni wallahi ban son damuwa kasani.

  Maimakon ya tsaya kamar yadda yace sai ya kara ma motan wuta ya harba saman titi da sauri shi yana dariya ya sake cewa baki fada min sunan ki ba mana.

   Khadija nake yace suna mai kyau a uni ke karatu ko ina nace eh anan nake yace dakyau aji nawa yanzu nace ban dade da farawa ba biyu muka shiga yanzu.

   Kai amma kinyi kokari nake ganin ki yarinya ashe yarinyar da kwazon ta yace may kike karantawa anan ?

  Ban kai ga bashi amsa ba yace yaushe ne kazama dan jarida haka Yusuf ban sani ba wanan tambaya ai yayi yawa haka yace ai ba zaka san na zama dan jarida ba sai na karasa tambaya na tukun.

  Kawar da kai yayi gefen window motar yana kallon titi Yusuf din yace baki bani amsa ba nace bari in ogan ka ya fita bai san ni nafishi rashin son magana ba ma .

  Yace aini naga alama shi ne dai  kamar bai ga hakan ba ke nan zan bari sai next haduwa mu sai mu dora a ida muka tsaya tunda ku dukan baku son hayaniya jin nayi shiru yasa ya dan juyo yana satan kallo don jin banyi magana niko ina kokarin ciro wayana daga ciki  jakkata da ake  kirana.

  Bayan na dauko naga baba nane ke kira da sauri na dauko ina fadin daddy i miss you ina mama yace gata kusa dani jiya anty ki tace kin dawo makaranta nace eh daddy amma ban zan zo minna yanzu ba sai dai hutu ina gani.

    Mun gama watan da  naji  Yusuf yace ashe ke yar Niger state ne nace eh ni yar minna ce yace a cikin garin minna kuke da zama ?

  Ohh god wanan wani irin abune haka for god sake in kana son jin kwab ne basai kuje gidan redio ba kuyi wannan abi damay yai kama don Allah.

   Ku ajeni daga nan don Allah zann karasa da napep don ma mun kawo kusa da inda nake ai a haba ke ko baki son muga a inda kike ne don watarna idan za a bamu sako mu baki.

   No I no wan  wahala ne ji yadda yake ma fada  ban son in ja maka matsala gun ogon ka ne don naga kamar bai so dauka na da kayi ba beside nima din ban son shiga mota dashi don takurawa.

  Ke yace yana kallo na a zurke yace ka neman min rai ni a wurin wanan yarinyar Yusuf harta kalli idona tace ina takura mata.

  Ya kara yana jan tsaki don Allah yaya Yusuf ka tsaya in sauka anan tun bai yi ball dani waje ba don  ban daukan irin wanan na karasa fadi a hankali.

  Ina zamu bi don mun kawo unguwar Yusuf ya ke tambayana nace wancan layin zaka bi anan gida jen namu suke ya dan gangara kadan sai nace wancan get din zaka tsaya nagode ina kokarin mikewa ya ja ya tsaya get din a wagale yake a lokacin.

   Bai bode motar ba sai yace a nan kike da zama ke nan eh kawai na bashi amsa yana sake bin gidan da kallo sai can ya bude mota nima na bude gefen da nake na fito.

  Ya fito ya fara fitar min da kayana daga cikin motar ina tsaye gefe har ya gama ya dago yana cewa kona shigar maki dashi ne ciki.

  Abinda yasa ni murmushi ke nan har dimple dina ya dan lutsa kadan yace ko maza basu shi nace ko haka na gode Allah ya saka da alheri kai min godiya wurin mijin buzuwa.

  Dariya ya kwashe dashi ya shige mota yana dariya ina tsaye a wurin suka ja motar suka wuce na sauke ajiyan zuciya a hankali na duba tarin kayan dake gaba na a lokaci.

   Shiko yana shiga motar ya sauke ajiyan zuciya yana fadin kai yarinyar ta hadu wallahi ga kyau ga zakin murya kamar dai ita tai kanta ji idanuwa karmar ita ta tsaya ta halici kanta wallahi.

  Tsakiya yaja yace wai yaushe ka koma haka ne don Allah ka koma kamar wani sabon shiga a ganin mace mai kyau.

   Wanan din kyaunta na daban ne ai dole ne a yabata wallahi don komai akwai zamzam wanan sai irin gidajen ku ai.

   Gidan wa ya juyo da sauri yana fuskantan shi cikin alaman tabaya a fuskan shi yace ban ga laifin Nafisa ba da ta haukace min  jiya a gida.

  Hauka fa kace yace hauka mana don kawai mama tasa mun rage ma yarinyar nan hanya take ta hauka wai mama na son shirya wani abune akai.

   Jiya koda na koma gida gaba daya duk ta hargitsa komai na falon sama da daki wai tana kishin wanan din.

  Kaji ba Nafisa tasan abinda ta gani anan ita ke nan ma mace taga inda kyau da fari ke aiki ba farin bane kawai irin nata.

  Yace cikin gatse gashi fa in akwai kyau ba gashi may akayi yace kasani ko duk ta hada kai dai ka kwantar da hankalin kasha kallo kawai a nan.

  No warnder Nafisa take fadin bata yarda dakai ba ashe tana da gaskiya yau kaine da bakin ka kake fadin inso wata bayan ta ni wata mace kuma zan so yanzu nidake da Nafisa a gida na.

  Baki Yusuf ya tabe yace ai ko baka kai namiji ba idan ka buge ga wanan buzuwa ke nan ka zama mijin buzuwa da gaske.

  Lumshe ido yayi da Yusuf ya fadi hakan yace yarinyar nan ma ta raina ni wallahi da ganin ta bata da kunya dama don dashi ta tare ni.

  Wallahi yarinyar ta hadu ne kai dai kawai ka mace ga son yar buzuwa baka ganin sauran mata da gashi yanzu.

   Ina mukayi yace mashi yana kallon shi don son ji yace kaini gida kawai murmushi yayi tare da fadin buzuwa tayi kira ke nan ?

  Bai ce dashi komai ba sai lumshe idon da yayi mai kawai yana sauka yace to mijin buzuwa sai gobe ke nan ko don nasan in kashiga ka shige ke nan .

  Harara ya watsa mai yana tafiya yana gyara jakkar laptop din shi cikin hasala da abokin mashi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

            SEENABU

Agidan su kuma Nafisa ne ke waya da kawar ta da ta baro kaduna wace suke kira da madam a cikin su tantiriyace ta kwarai na fada.

  Da mijin ta sai dai kamar itace mijin ba mata ba don sai yadda tayi da mijin a gidan idan tace kada ya zauna bai isa ya zauna ba.

  Atakaice dai ya zama mijin tace ga madam ko kawayen nata zasu iya aiken shi ya tafi komai nisan wuri koda da kafane sai yatafi yadawo.

   Itace Nafisa ta kira tana son fada mata abinda ya faru da ita bayan barin su kaduna ta dauko wayan ta madam ta soma nema a wayan sai dai wayan nata ringing ba a daga wayan ba takaici ne ya kama Nafisa.

  Ta ja tsaki ta na fadin yar iskan ko gidan uban wa ta shiga waya nata ringing haka bata dauka ba har ya katse bata dauka ba kin sake kiran layin tayi a lokacin sai taci gaba da tunanen ta tanayi tana kada kafan ta daya dake har de.

  Babu abin da take tunawa sai irin shirmay da ta tafka jiya din akan bakin kishin dake damun zuciyar ta akan mijin ta wanda take mashi son daba taba yi ma wani abu ba sai dai kuma a kasan zuciyar ta ba so bane can na har abandan don da zai iya shiga wani halin jarabtan rayuwa a yanzu tsaba zata iya gudun shi ta koma wa mai maski.

  Wayan nata aka kira ya hanata karasa muna jin birnin zuciyar sai ta dan sake guntun murmushi tana daukan wayan nata tare da fadin Aloh ina kika shiga nake ta kiranki   baki daga waya ba.

  Cikin muryan barci madam din tace tana hamma baki hangale bata fasa magana duk da tana hamman tace wallahi barci nakeyi tunda rana.

  Tsuki Nafisa taja tare da fadin barci sai kace wata mai ciki ko kasa ni don Allah watseke fuskan ki kiji ni magana nake son muyi dake ki ban shawara.

    Madam tace ina jin ki matar manya dadi Nafisa take ji idan su madam na fada mata wanan sunan madam din ne tace ke nake sauraro fa.

  Wallahi ke dai madam kin san ko sai da munafukar tsohonwan nan ta hadamu da yarinyar da nake fada maku tace mu rage mata hanya ?

  Don Allah ki bari madam ta fada itako tace sosai kuwa ai saida muka dauke ta a mota daya mukai tafiyan.

  Tace yaya kika bari haka ya faru don Allah kin ko san iein mijin ki neman su mata keyi ido a rufe nasha fada maki ki nisanta shi daga ko wace  mace in ba muraharamin sa bace har kika yarda hakan yafaru dake.

  Ke dai bari madam nanu mashi rashin yarda na ga hakan amma ya rufe ido yace shi yace umurnin mahaifiyar shi ce dole ya bi.

  Madam tace yaya kukayi a motar injin baki basu daman sakewa da juna ba a motan ?

  Tace ai in fada maki ban yarda ko daga kai yayi ya kalle ta ba kuma nima ban sake ayi hakan ba sai dai mun kwashi rikici dashi sosai da muka iso gida wai zai tafi office a sauke shi sai a wuce da ita.

  Bude mashi wuta nayi sosai in fada maki sai da mukayi kaca kaca dashi na kuma hana shi fita sai da aka kaita a ka dawo san nan ya tafi.

  Da haushi da bakin ciki ya kamani duk na farfasa kayan falon nan gaba daya don in nuna mashi bacin raina don gobe kada ya kara min haka.

  Madam tace kash aike kinji matsalan ki ke da zaki bishi da lalama ki nuna mai ba wata mace sai ke a duniya daga baya sai mu sake shirya wa tace.

  Madam idona ya rufe a lokacin da kishin ganin wanan yarinyar a kusa dashi amma da ya fahintar dani shi irin su ba su gaban shi shi yanzu wace mace zai kalla ta bashi sha,awa sai naji hankalina ya dan kwanta a lokacin.

  Madam tace amma kin so ki bada mu wallahi kai kin ma dai kwafasa wallahi yanzu ke ko irin matan abujan  nan ya lalubu maki har ki ta da hankalin ki haka mudake da wuka a hannun mu nama kawai muke jira.

  Kawai yanzu idan ya dawo kije ki bashi hakkuri akan abinda kikai mai din don kada ya zarge wani abu a gare ki.

  Kin ga zaki ji a bakin shi ko ita wanan yarinyar wacece a garesu kin dai san yadda zaki bugi cikin shi ai muji komai a saukake.

  Tace zanyi kamar yadda kika ce din amma ba yanzu ba zan dai saka ido in gani idan suna tare ko basu tare sai musan abinda zamuyi daga baya.

  Sun dauki lokaci suna maganan akaina ana ta kulla sheri da tugu akan mazajen su kafin suyi sallama madam tace zata kira zuwa gobe taji indan da wani matsala kuma.

  

   Na gama shiga da komai daki na da taimakon wata yar gidan namu da ta dawo tagan ni da kaya ta tsaya taimaka min.

  Kayan jikina na fara cirewa san nan na fara gyara kayan ina aje komai a inda nake bukatan shi na gama na zauna ina tunane a raina.

  Bakomai nake tunane ba sai mijin buzuwa da Allah ya jefo a rayuwana a dan lokaci ya taimaka min yau gani da kudi a hannu na wanda yakai dubu dari ta dalilin mijin buxuwa da iyayyen shi duk na samay su.

  Waya na dako a cikin handbag dina ina neman layin ya Amina don in fada mata abinda ya faru don komai ya faru dama nakan kirata in fada mata.

  Kira uku ta daga wayan ina ji bata kusa da wayan ne a lokacin mun gaisa nake tambayan yaranta tace suna lafiya sun tafi islamiya.

  Nace anty kin san wani abu da ya faru yau tace ina zan sani Khady nidake kaduna zaune kina abuja ke.

  Nace anty yau na hadu da mijin buzuwa danaje sayayya tace kun sake haduwa kuma again nace wallahi anty wai duk wanan uban kayan da na sawo nazo biya sai ake ce min ai ya biya bayan da suka sauke ni ranan ya ba driver dubu hamsim ya bani.

   Kai da gaske khadija nace wallahi anty kuma su suka kaini gida sai dai shi bai so su dauke ni ba sai abukin shi ne yace saboda mama ne suke min haka.

  Dariya tayi tace to Allah ya saka da alheri ki dai bi a hankali inda duk kuka hadu don buzuwan nan ba imani ke gare ta tana iya komai akan mijin ta.

  Ya Amina ni inama zan kara ganin shi kuma Allah dai ya tsaga rabona daga Aljihun shi wanan karon mutumin da ko yaushe take a cikin hade fuska banda gaisuwa may zai hada ni dashi kuma.

  Daga haka muka kawar da zancen shi muka dauko na iyayyen take fada min cewa sunyi waya da baba yana fada mata kudin su na ritaya ya kusa fitowa kwanan nan.

  Ihun jin dadi nayi don murnan iyayyen mu zasu fita acikin hali talaucin da suka shiga na ritayan da mahaifin namu yayi muke cikin halin kaka nakayi.

  Tace ai zan riga ki ji idan kudin sun sauka don haka sai abinda kika samu daga baya nace ai ni indai daddy zai samu bukata na ya biya ke nan.

  Yanzun ma shawara nakeyi inje banki gobe in tura mai kudin da mijin buzuwa ya bani don akwai kudaden da zasu isheni a hannu na tunda ina da abinci waddatace .

  Tace haka akeso mutum idan ya samu ya tuna da iyayyen shi dama dako kin kyauta wallahi dama sallaman ki ya hanani tura mashi kudi wanan watan.

  Haka dai mukai ta hira da ita daga karshe mukayi sallama na kashe wayan tare da mikewa na jona electric dina don in dafa dan abinda zanci da dare.

   Kira, a na saka a wayana ina aiki ina bin kira a don ni gwanace a wurin iya hadda tun ina yar shekara sha hudu na sauke alkurani mai girma  na sake maimaitawa yakai kashi uku yanzu don duk wanda yasan yaran minna ya sansu da ibada da kamun kai ga girmama na gaba dasu a duk inda suke.

   Da wanan halin namu nake shiga ran mutane farat daya kowa tsakani na dashi gaisuwa ne na mutunci da sani girman wanda ya girmay mun.

   Na gama na zuba a plate na dauko ledan ruwa guda cikin wanda na sayo na aje a dakin na zauna don in fara cin abincin sai ga kiran waya ya shigo min.

   Binta ce ta kirani a lokacin na dauka kafin wayan ya tsunke hiran mukayi sosai ranan da ita har nake mamakin ko nawa ta sa awayan ta haka don da mun sake wanan hiran take dauko min wani.

  Har take fada min yadda akayi ranan da zamu wuto da buzuwar yayan su tace bazata shiga mota dani ba mama ta dage daya zo mata da maganan kan lalai sai sun tafi dani.

   Nace kin ko ga tunda muka kama hanya batai min magana ba nima ban masu ba daga ita har mijin ta.

   Tace wanan ai dama shi miskili ne magana kamar aiki yake ganin sa a gare shi zai iya zama da kai kuyi awa daya baice uffan ba haka kuma matar shi anty fati itama take shiru shiru bata magana.

  Nace aiyanzu sun samu mai magana a tsakanin su haka yasa ta samu daman musguna mata yadda take so ai.

  Tace ke kin ko san halin wanan matar shu,uma ce wallahi ta karshi da farko da tazo boye halin ta tayi kamar wata mutumiyar kwarai da ita.

  Sai daga bayane ta fitar da kalar ta kowa ya sani bata kaunan ko dan uwan yaya ta ganshi a gidan nan wallahi.

   Nace wuri ta samu wallahi ni kar nake kallon ta don banga abin tsoro ba anan ku dai na fahince ku kuna bata girma ne don mijin ta yana da hali a cikin ku.

 Tace ga tsiya nace eh mana haka din ne amma in bashi ba ta yaya zaku zauna wanan matar ta dinga raina maku hakali har tace wai idan tana wuri kada ayi dariya .

   Tace ina ma kika sani khadija ai sai wani lokaci da mukaje hutu wurin su a abuja ba girma muka dawo gida kwanan mu biyar ko sati bamu kai ba matsi yai muna yawa a gidan.

  Muka matsa ma yaya zamu dawo ga yan uwanta nan muna ganin yadda take ji dasu amma mu ko falo ta hana mu fito muka koma kamar wasu bare ba yan uwan maigidan ba.

   Dariya nake mata sosai tace Allah ko magana mai karfi wai ba ai mata a gida tace ba kallo ba komai sai zagi da hattara ga anty Fati damu da ita duk muka koma daya.

   Bayan mun dawo sai ga anty Fati ma ta dawo wai a kaduna zata zauna bata iya zama da buzuwa a abuja bata bari ko miji ta gani idan yana gida.

  Nace ke ki bari don Allah ashe ba karamar shuuma bace tace baki santa bane Khady wanan fa ko kashe mutu tana iyawa fa.

  Nace wanda Allah yabata ikon kashewa ba wani kan ai yafi karfin ta wallahi ba abinda zata iya wanda Allah bai tashi yi da bawan shi ba.

  Ni don Allah har kin ban haushi da wanan maganan naki don ba a gidan ku nake ba wallahi da taga tsiya a guri na nifa irin matan barikin nan haushi irin su nake ji.

 Zako kiji nata don bata da hali mai kyau ko kadan akan mijin ta zata iya yiwa mutum komai musan man ma ce ko waya tayi da wata ranan sai sunyi jidali sosai da ita ke ta zama mai kaya ko shi yanzu bai da yadda zaiyi da ita ne kawai wallahi.

  Nace ya dai ga dama ne Binta idan ka ganshi ga mutum har mutum amma baida kuzari gun mace tir yayan ku ya zama mijin hajiya wallahi.

  Haushin abinda na fadi taji da fada muka karasa wayan a rana na kashe ina mata dariyan shakiyanci na gama na wanke kayan na samu wuri na kwanta.

   Washe gari da wuri na fita don ban yarda in makara in ba wani dalili ya tsayar dani ba mai karfi shi kadai zai sani makara kawai.

   Ban da yawan kawaye sai mutum biyu yan department din mu kosu shirin mu dasu don sun ga nafisu kawo wuta sosai a class din shine likewan su dani.

  Banda wasa ga abinda ya kaini abujan daga school sai gidan mu sai ko idan wani dalili zai sa na fita a ranan zan fita.

  

   Yau ya dawo a gajiye don daga wurin aiki ya wuce wuri wasan polo da suke yi don dan wasan ni ne sosai wanda yana daya daga cikin abinda ke kawo mashi kudi a lokacin bai dogara ga aikin shi ba yana buga buga irin na maza gida da waje shike sa yana samun mahaukacin kudin da yake riko.

  Wanka yayi yana saka kaya a jikin shi ta shigo dakin dan juyawa yayi ya kalle ta ya kawar da kan shi yaci gaba da abinda yake yi.

  Karaso wa tayi gare shi tana wani rangaji na daukan hankalin shi ta sake abinda yake so ya sauko mata har mazaunan ta.

   Cike da sallo ta iso gare shi sai dai tsiyan shi da ita duk gayun ta bata damu da saka kamshi ba kuma har yanzu ba gwanewa tayi ba da iya kwalliya shine ma yake kokarin wurin gyara mata idan tayi wani kwaliyan zasu fita.

  Gata da son karya sai dai ko bokon kasar su bata samu ba kuma babu na Allah a tare da ita abin ya taru yai mata yawa amma hakan bai hana shi son abin shi ba.

  Rungumoshi tayi ta bayan shi ya sauke wani ajiyan zuciya yana dan murmushin jin dadin ganin ta tace yau ina ka shige haka ne ta dawo ta gaban shi suna fuskantar juna.

   Bai ce komai ba yadan jajeyeta ya dauko turare yana fesa ma jikin shi tace har da daren ma sai an feshe jiki da turare ko fita zakayi ne haka  ?

  Sai lokacin yayi magana yace sai zan fita ne zan saka kamshi a jiki na ke baki son kamshine ashe yasa baki sakawa .

  Taji zafin maganan amma ta daure don in da sabo ta saba da gorin saka kamshin da yake mata din ko yaushe kuma hakan bai sa ta saba da sakawa ba.

  Tace muje kaci abinci yace na koshi ta dubeshi da sauri tace tare da fadin ban gane ba yace mun ci abinci da Yusuf kafin in dawo.

  Juyawa yayi ya nufi saman gadon su yana jawo laptop din shi tasan idan ya fara dakilan laptop sai ranta ya baci kafin ya gama.

  Idan tayi magana kuma yace business yake a ciki shi ko wani abin dariya tayi ya dago yana duban ta na lafiyan ki kalau kuwa ?

  Sai yaji tace maganan turaren da kayi ne dai yaban dariya har na tuna da yarinyar da mama ta saka mu dauko ranan.

  Bakaji wani irin kamshi tiraren da takeyi ba kamar tayi wanka dashi yace tasan kan ta ne yasa ta saka turaren haka don kada a raina ta.

  Tace shi saka turare kuma har wani sanin kai ne dashi wai ma may ye alakan ta da mama ne data nace sai mu dauko ta wai ?

  Yana bude laptop din yace sai yanzu kike son jin halakan su da mama da kishi ya rufe maki ido baki tsaya tambayan ta ba da farko.

  Tace kayi hakkuri cikin yanayin tausasa harshe tace nasan ban kyauta ba kishin ganin ka kusa da wata mace nakeyi tundai irin wanan yarinyar dake cikin ganuwan kurciyan ta ga kyau kuma da gani tana kuri da ilimin ta.

  Ina tsoron ka hango kyawon tane wallahi kazo kace zaka dauko min ita a gidan nan wata rana son ka nake har karshen zuciya ta ka sani.

  Ya tsaya yana mata wani irin kallo yace don kina kishina sai ki min hauka mata nawa nake gani a rana da ina raayin mata ne zaki san lokacin da zan nemay su ne.

  Har kina fada min cewa mahaifiya ta da biyu ta hadamu tafiya da yarinyar don in so ta kika haukace har kina fashe fashe a gida.

  Kwantowa tayi a jikin shi ta dan shafi kan shi tace kai min afuwa don Allah haka ba zai sake faruwa ba a tsakanin mu.

   Yaji hakkurin da ta bashi har cikin ranshi yace ki rage kishin nan nake don ni din mijin mace hudu ne watarana.

  Da sauri ta rufe mai baki tana fadin don Allah ka daina fadin haka don kana sa zuciya ta tana bugawa da wanan zancen kishiyar da kake min.

  Yace idan lokaci yayi ai yi zanyi sai dai ki tausasa zuciyar nan naki bakiga mahaifina matan shi hudu ba kin sani ko in gado shi nima ?

   Kuka ta soma mashi tana fitar da hawayen munafunci a idon ta dariya yayi mata yace akan kishiya kike wanan kukan haka fati fa ba kishiyar ki bace kin ga ai ko yanzu kina da ita ke nan.

   A bar maganan Fati tace don ni kaina ma kunya nakeji ace wai ita din kishiya ta ce balle kai ace matar ka ce Fati ta sunna.

  Ohh kin fison indan zai ne ma yanzu in nemo wace idon ta ya bude sosai don itace ta dace dani tace ba haka nake nufi ba don Allah mu bar zancen kishiyan nan haka na.

   Tambayan ka nayi cewa wacece wanan yarinyar ne sai ka dauko min wani dogon zance kuma akan kishiya ?

  Yace nima ban san ta ba a gurin mama wanan zuwan da nayi na fara gani  ta koma waye dai ita nasan alakar ta da mama mai muhinmaci ne sosai.

   Shiru tayi tana nazarin maganan shi daga karshe dai data ga ya fara aikin shi ta kwanta tana ci gaba da tunane kala kala a zuciyar ta.ZAINAB IDRIS MAKAWA

            SEENABU

Bayan mun gama waya da ita naji raina ya baci sai a lokacin na gode ma Allah da ban goge number shi ba a wayana kira nayi har sau biyu bai daga ba sai na tura mashi sako masu zafi na kashe wayan.

  Don nasan zai gani da safe in ma kwanciya yayi a lokacin haka yasa na danji zafin da nake ji ya rage min da kyat barci ya dauke ni a ranan.

  Har na rufe ido sai nayi wayana yana kara na dauka a zatona shine yaga sakona ya kira wayan sai dai ba number daya kirani daya kira dashi bane.

   Nace ummhumm ina jin ka naji ance haka ake karba kiran wanda baka sani ba na sheda muryan Yusuf din nace yayana kaine a na dauka wani ne.

   Yace nice injin ruwa bai saki jin zazzabi ba dariya nayi nace ai na watsa ruwan zafi a jikina yace good dama na kiraki ne don mutumin ki ya karbi number ki a hannu na nasan zai iya kiranki kada ki biye ma halinshi don Allah don bansan abinda zai kiraki ya fada maki ba koda yake yace akan maganan hajiya mama zai kiraki yaji don Allah , , , 

  Na katse shi da fadin ai ya kirani ko har munyi tsiyan shi ya dauka kowa nema yake a gare shi ko yaushe ni kuma na wanke shi tass.

  Da karfi naji yace haba don Allah nace wallahi na kwashe komai na fada mai har text din da na tura mai mai zafi yace amma baki kyauta ba wallahi.

  Nace saboda may zai mun hadi yace khadija kin san kuwa kece mukee son kizama weapon din mu wurin yakan buzuwa nan gaba.

   Don Allah ki dinga sausautar harshen ki gare shi nace wa ni ni ina ruwa da shi da zan zama muku makami a gare shi da buzuwan shi.

  Dariya yayi yace ke ko ke dashi khadija ke da komai da zaki yakar muna buzuwa don kin cancanci yin hakan.

   Ni din yayana yace kwarai kuwa kauna na sai dai idan mun hadu zan maki bayani yadda zaki gane nace to shike nan tunda haka ka fada yace bani na fada ba umurni nima aka bani kan hakan .

  Yace sai dai idan mun hadu din zan maki bayanin komai nace Allah ya kaimu ina saurarenka da haka muka yi sallama dashi ya barni da tulin tunane a zuciyana.

   Da safe zarah ce take buga min kofa jin bugun kofan na tashi na bude daki tana tsaye kofan dakin nawa ganin tana son shigowa na bata hanya ta shiga daga ciki.

   Tambaya na tayi ko da safe zan fita nace ai kemakin sani yanzu haka shiri nakeyi kada in makara take cewa dani zata fita amma wai za a kawo mata sako shine take son in karba.

  Nace zarah fitan kuma zakiyi yanzu tayi dan guntun tsaki tana fadin eh wani friend dina zaiyi tafiya nake son inje muyi sallama dashi.

  Zarah ba zaki wankan ki fada ki zauna ki abinda iyayyenn mu suka kawo mu yi ba wanan dabiar da kika dauko bai da amfani gare ki nan gaba.

  Ta dan yi murmushi ta nufi wurin da taga na aje plate din abin ci da tukunya tana bude bayan ta bude ta dago tana dariya tace an fada maki yadda bakin san wayen kai ba haka kowa yake yanzu da anganki kamar may wayayen kai .

  Nace in dai irin wanan wayen wane kada Allah ya nufe ni da yin shi ina neman tsarin Allah ga irin wanan dabian naku Allah kuma ya shirye ku ku gane gaskiya.

  Ta juya ta debi arish a plate ta zauna ta fara ci ni kuma ina ta shirina nace kiyi ki gama gada ki makarar dani anan don banson in makara.

  Tayi murmushi tana kai abinci a bakin ta sai da ta hade tace wanan halin naki na ina kika fito karatu ina zaki karatu sai ke khadija.

  Khady look at you me kika rasa ke kanki jarin kanki ne amma kin tsaya kina wahal da kanki haka har kina wani girki tunda safe kamar wata matar aure amma waike nacin karatu sai wahala kike haka.

  Wallahi da zaki yarda akwai wanda zan hada ki dashi cikin kwana biyu kiyi clean ke baki daukan misali a kwaina khady da haka nake ?

  Amma yanzu gani tunda hanya ya bude min mai na rasa na rayuwa atare da ni amma ke gaki da abin kawo kudi kina ta faman kumshe shi a jikin ki ta fada tana dariyan shakiyanci.

  Ni dai ina tsaye ina mata kallon mamaki da huduban shedan da take min har kuryan dakina ta dauka nasihan ta ya na shigana ne ganin yadda na tsaya ina kallon ta.

  Tace ina son ki fahimci wani abu tsarin rayuwa yanzu ya canza ki shigo kawai a dama dake yarinya.

   Nace cikin murmushi zarah baki fance ni batsarin rayuwa ta daban yake da naki ban sanya ma zuciyana kwadayi ko son jin dadi a ko wani irin yanayi ba don haka kada kiyi tsammanin guntun huduban ki zaiyi tasiri a raina .

  Ni da kika ganin nan ina da mutunci na kuma nasan ciwon kaina dana iyayyena kada kiyi tsammanin kananan kwarin da kike bi zasu iya rudana da wani abu.

  Shi jin dadi lokaci indan lokaci yayi sai inji amma ba ta hanyar wullakata kai yadda kukeyi din nan ba kema idan da zakiji sharata da kin watsar da wanan rayuwan ki rungumi abinda ya kawo ki Abuja.

  Su kansu mazan da kuke bi aida karatun suke amfana yanzu bance maki ban saurayi ko rayuwa ba sai dai in gajarce maki ni indan zanyi mai tsabta da sanin ciwon kai zanyi amma bana kwanan gida irin naku ba.

  Baki zarah ta tabe min tana dariya ta saba da nasihana kullun wanda ita a ganin ta ni har yanzu ban waye ba ban san ciwon kaina ba bansan ta kan duniya ba kuma.

  Nace keyi dariya amma ni idan zan faso gari ba irin wa yan nan kanana kwari masu gurbata rayuwa zan tsaya dububa ba sai wanda ya san kanshi da mutuncin kanshi.

  Ta mike bayan ta gama ci dama ina magana ina kallon agogona ne kada in makara tace ina son ki fahince ni a yanzu ba a samun irin wa yan nan mazan da kike hasashe kinga ko zaki shawa wuya wurin neman su.

  A naki ganin ke nan zarah amma muna nan dake zakice na fada maki watarana ta miko min key din ta nace kenan yauma till down zakiyi tace yo may za a fasa kuma.

  Ta fita na rufo kofana muka fito tare da ita a titi muka raba hanya tana neman lift ni kuma na nufi cikin makaranta ina mamakin wanan rayuwa da zarah ta daukan ma kanta.

  Itama yar minna ce kama na dalilin haduwan mu ke nan da ita don ko a minnan ba unguwa daya muke ba su suna zama a cancaga ne ni kuma muna tsakiyan gari.

   Kasancewar mu yan gari daya yasa muka zama kamar yan uwa da ita da farko halin ta mai kyaune kafin idon ta ya bude da bin mazan abuja.

  Sai lokacin muka raba hannu da ita amma hakan baisa mun daina kula junan mu ba kamar baya sai dai ban taba yarda naci abinda take samuwa ba daga wurin yawon banzanta ba.

  Tun abin na damun ta har yazo ya daina damun ta ta daina ba sai wanan da iyayyen ta suka kulla suka aiko mata yanzun tana ganin tafi karfin shi ita shine ta kawo min inyi amfani dashi.

   

Tun asuba yake tayar da ita ta tashi tayi sallah amma tana kwance tana barcin ta har yagaji yatayar da ita da karfin tsiya ta zauna tana mustsukan ido alaman barcin bai isheta ba har lokacin yana ganin ta tashine yasa shi fita daga dakin azaton shi zata tashi tayi sallah.

  Ya fita zuwa dakin motsa jikin shi da yakeyi duk safe inda kuma yake aje wasu kayan amfanin shi jiya anan yabar wayan shi yana canji ya je ya kwanta yana tunanen rashin son ibadan da batayi.

  Ya gama komai na motsa jiki da yakanyi da safe ya wuce zuwa inda wayan shi yake jone ya dauko din ka idan shine sai takwas yake bude waya da safe.

   Budan wayan yasa sakon da suka taru mai shigowa ya gane su wanda farko budewa nawa ne ya shigo da farkon.

   Mamaki yayi don ba suna sai lamba ga dogon sako kuma da maishi ya turo mashi kamar kada ya karanta tunda baisan mai sakon ba sai kuma wata zuciya tace dashi karanta kaji mana abinda sakon ya kumsa kila mai amfani ne gare ka.

   Fara karanta sakon ne yaji ranshi ya baci don ya fahinci inda sakon ya fito don ganin farkon rubutun nawa kamar haka

  Mijin buzuwa a zaton ka zaka iya rabani da hajiya mamane ko ka zubar min da mutucina da take gani  kayi kuskure wallahi kuma kayi karya don bakina da naka ban fada ma hajiya mama tana gida an mata rasuwa ba.

  Ga wanda yasan mutuncinta yasan darajan ta na fadawa shida ya tambaye ni ko ina da labarin su bakai da buzuwa wace bata da daraja da galihu tasa ka zubar da matan ka da yayan ka da kowa naka kana ganin tsohuwar buzuwa tana maka rudi da huduban shedan kullun.

  Kai bari ma kaji wallahi wanan buzuwar ta zubar ma da kima da komai naka a idon duniya tunda kiri kiri ta mai dakai mijin hajiya.

  Ga mutum har mutum amma baida ta cewa saboda mace macen kuma buzuwa wace bata san Allah how dear you kaida mace bata bari ka zauna dako matar sunnan ka har kake da bakin yi mun hadi a wurin mama, , , , 

   Jikin shi har rawa yakeyi da yake karata text din kasa kai kashen rubutun daki ya nufa da sauri da zuman ya shiga yai wanka ya fita ya samu Yusuf shida yaja mashi rene da wullakanci wurin yar karamar yarinya harta iya turo mashi text din banza haka.

   Sai yayi magani na a garin sai yasa na raina kaina may nike dashi may nake takama dashi da zan iya yimai cin fuska haka ina aibanta shi shi da matar shi.

  Waya ya fada min maganan da sukayi da hajiyan su hajiyan ne zata fada min kowa komai dai may nene sai ya rena min wayo sai na gane banda wayo yau a garin nan duk inda na shige sai ya tononi a cikin garin nan yayi min wulkanci

  Sai dai yana shiga dakin su kuma sai bacin ran nashi ya karu ganin Nafisa kwance tana barcin ta hankali kwace rashi ne ya kara baci ya tuna abinda nace a text dina.

   Bai san lokacin da ya isa wurin ta yakai mata mugun maka a tsakar bayan ta ba ta mike firgigit tana fadin Samad may nayi maka ?

   Tsawa ya daka mata yace wanan abin zai hada ni dake ke sai yaushe ne zaki rike ibada a zuciyar ki ne  yaja tsuki ya shige wanka.

  Da sauri ya watsa ya fito ranan ya fito bai wani dauki dogon lokaci ba ya shirya ya fita daga gidan koda ta fito ta samu baya gidan.

             Tun a mota ya kira Yusuf yana fadin kana inane yanzu?

   Gani gidana ya bashi amsa OK kajirani ganin zuwa yanzu gidan yace eh mamaki Yusuf yaji yana tunanen mai zai kawo Samad gidan shi wanan lokacin haka.

  Don ka idar shine sai takwas yake fitowa ko takwas da rabi ware hannu yayi alaman shi ya sani ya mike ya shiga wanka kada yai mashi girshi.

   Yana shiri ya sake bugo mai waya gashi kofa gidan shi ya fito ya karasa ya fito ya samay shi don ko driver bai fito dashi ba Yusuf din na gani haka ya rufo gidan nashi ya fito ya samay shi.

   Anan ya bude mai mota ya shiga yarufe sai ya dauki hanya batare da yasan inda zasu nufa ba sai yaga ya miki mashi wayan shi duban wayan yake da mamaki yake fadin na maye wanan kuma ?

   Ka duba mana cewa fuska a daure ya karbi wayan ya fara karantawa a hankali yana sake murmushi ya gaba yana mika mai wayan yace kai amma wanan yarinyar takai jaruma wallahi haduwan zai zama abin shaawa ga mai kallo.

   May ne kace yanzun kai baka ga abin jin haushi ba a nan yace ban gani ba sai ma wani abin da na hango na daban tsakanin ka da beauty din.

   Yau sai nanu namata ita ba kowa bane a garin nan sai na wullakanta ta a garin nan dariya yayi sosai yace da kaima kan ka wallahi da ka tozarta kan kuwa.

  Wai kaiko kaga yadda kukai balain dacewa da yarinyar nan kuwa wallahi ni abin naku burgeni yake yi idan kuna yi har wani dadi nake ji.

  May kake nufi ne wai yace abinda idona ya hango min mana a kai saidai fatan alheri amma zancen ka ci mata mutunci bai taso ba ko kaje ka tozartata duk ba wanan a tsakanin ku ko kamanta da hikimar hajiya na hada ka da wanan yarinyar ne ko kana nufin kai baka gane hakan ba.

  To bari kaji Khadija itace zata iya fitar dakai  daga zargin da ake maka na cewa Nafisa ta gama dakai da cewan da ake saboda ita ka kasa zama da Fati.

   Akan wani dalili zata fitar dani ta yaya din zata fitar dani yace muje zuwa nan gaba zaka sani idan lokacin hakan yayi yanzo ina zamu ne kadauko ni tunda safe haka.

   Wurin ta zamu in gwada mata ita din ba kowa bace ya kwashe mai da dariya yace ta zama kowan ke nan tunda har zaka iya biye ma shirmay ta na mata.

 Bai kara magana ba sai juya kan motar yayi zuwa office din su ya shige bai tsaya jiran Yusuf din ba.

   Anan malam musa driver ya tsayar dashi yana fadin yana da magana dashi na siri da yake son suyi a tsakanin su yace da malam sani din wani abu ya faru ne yace eh to sai dai maganan nason siri gaskiya yace dashi babu damuwa kasa may ni a gida da yamma idan mun tashi.

  Ga haka suka bar zancen da malam sani din sai dai ya barshi da tunane a zuciyar shi ko akan may yake bukatan kebewa dashi bai sani ba ya san dai abune mai muhinmanci sosai.

   Shiko gogan acikin office maganan da sukayi da Yusuf ne yake ta mashi yawo arai wai zata zama mai garkuwa a kan matsalan shi da Fati da Nafisa ta yaya ma haka zai faru .

   Nan dai ya watsar da maganan ya ci gaba da aikin dake gaban shi sai dai yanayi yana tuna zancen a zuciyar shi.

   

Kai tsaye da na fito kamar yadda na saba gidan da muke na nufa yau yawan ci basu da lectures sai karan gida ke tashi ko ina a cikin gida.

  Yunwa nake ji don ban tsaya nayi karin kwarai ba da safe sallah nayi sana fara hada tea na  nasha sai da na dan huta a wurin na mike ina sauya kayan jikina.

  Na saka dan guntun rigan da nake zama a daki dashi gyaran dakin nayi na gyaro ko ina na dakin sai na dora girkin dare don shinkafa da miya nake son yi irin na yan makaranta.

  Bayan na gama miya na dora shinkafan na koma na zauna a bakin katifa ina tunane zarah ne ta fado min a rai yau in zan lissafa kwananta biyar bata dawo ba.

  Zarah tana daya daga cikin "ya"ya dake cin amanan iyayyen su don babu inda suka rageta don koba a fada ba zarah tafi gata don sati biyu bai shigewa iyayyen ta basu turo mata da sako ba.

  Amma duk ta watsar da wanan gatan nata tabi ra,ayin kwadan abin hannun samari wanda ya rufe mata ido a yanzu har yakai ga ta watsar da karatun ta.

 Ido na lumshe tare da girgiza kaina ina cewa ubangiji katsare mu ka karemu ya Allah kasa mufi karfin zuciyar mu don yanzu rayuwa abin tsorone .

   Sai gata washe gari ta dawo dakina ta nufa don karban key din ta koda ta shige ban sake mata fuska ba daga inda nake kwance ta tambayi key din ta na nuna mata da hannu kawai ta nufi wurin ta dauka.

  Harara na bita dashi tana ficewa daga dakin andan jima kadan sai gata ta dawo dakin daga ita sai wani dan guntun tawul da ta daura iya cinyan ta tana tambayana wai ban rage abinci ba in bata.

  Wani kallo nayi mata nace inda kika fito gantalin ki kwana da kwanaki baki kici abinci bane acan ?

   Tace kin san yanzu wata yayi nisa ba wani abin kirki ake samu ba sai maneji nace sai ki je gaba ki nema ni banyi abinci ba yau.

   Ta ce khady yaushe kika fara rowa haka ba halinki bane  rowa nace ban dafa ba nace maki ashe karyan iskanci kike yi da zaki dawo kwana da kwanaki hannu empty.

  Ta dan tsaya jin ganin ban kulataba ina karatuna sai ta fice min daga dakin dagowa nayi nabita da kallon mai kama da harara har tafice daga dakin.

   

Bayan ya gama saurare abinda malam sani ya gaya mashi jikin shi ne yayi sanyi karshe yayi mai godiya tare da jaddada mashi kan kada ya fada ma Nafisa komai ya dai saka ido ga alamarin ta kawai.

  Bayan fitan shi gidan nine na fado mashi a rai wayana ya kira mun gaisa dayake shi mai son wasa ne nan yajani da wasa wanda bai wuce hiran mijin buzuwa.

   Yace gobe dai weekend  ne ba shiga aji ke nan nace eh sai dai ina son zan fita zuwa wurin wankin kai don ina son gyaran jiki gobe dai.

  Yace ashe shi gyaran ma sai anje wani guri yin shi dariya yaban don irin zolayar shi nace ana mace ba gyara ne yace kwarai kuwa har in ta san kanta.

  Karfe nawa zaki ya tambaya nace wuraren goma zan tafi nasan zuwa karfe sha biyu ko da rabi na gama yace da safe banda time da nazo na kaiki sai dai ki fada min sallin din da kike zuwa in duba ki idan na rarage abinda nake yi.

  Nace No kabarshi kawai ba wani nisa yake dashi da inda muke ba nagode yace aini nace ki fada min ko nace beauty hair drasses na fada mai layin da yake a saman babban titi.

   Munyi sallama ina mamikin halin shi da saurin sabo irin nashi na zauna na tsefe kaina a cikin daren nan don kada in makara in samu mutane a wurin.

  Washegari da safe na shirya na isa sallon din ba wasu mutane dayawa don haka nabi layi sai da akawanke min akai min drying din shi kafin su fara min kitso.

 Ranan nasha gyara sosai na jiki daidai zan fito sai ga wayan Yusuf shigo yana tambayana ina wurin ko wuce nace an kusa gamawa nan da minti talatin zanbar wurin .

   Nakashe wayan akaci gaba da min gyara sai yaba yawan gashina da tsayi suke yi nidai murmushi kawai nake masu ban wani dogon magana da kowa a wurin.

   Sun fito daga kubuwa duban fili da sukaje gani a hanyansu na komawa gida yaga Yusuf ya dauki hanya bai iya magana ba yana aiki a system din shi kan shi a duke yake.

  Sai dai yasan ba hanyan gida Yusuf ya nufa dasu ba aikin da yakeyi ya dauke mashi hankali a lokacin ganin ya tsaya a bakin wani gyaran jiki na mata yasa shi dago kai yana tambayan shi ina ne nan kuma ?

  Kafin ya bashi amsa yaji yana fadi a wayan shi fito gamu a kofa idan an gama maki nace gani tafe na fito tun fitowa na ya hango nice tafe kallon mamaki yake wa Yusuf din.

   Har na karaso bakin motar nasu sai a lokacin nasan tare suke dashi fadi yusuf ke yi da na karaso wai wanan haduwa haka fa kanwata .

  Kaike kara zuzuta yayi maganar kamar bashi ya fada ba yace ba dole ba in zuzuta kanwata yar gidan mama wanan ai kyasa ayi karo a hanya nidai murmushi kawai nayi mashi.

   Na fara gaida su yace shigo mu sauke ki mana ba hostel zaki koma ba nace a a nagode yayana ku tafi abinku kawai dakai dayane zan shiga amma dai ku tafi kawai.

  Yace au don wanan miin buzuwan da kika gani ai bashi ke jan motar ba ko shiga muje don ki kawai muka biyo nan fa.

  Jin haka yasa na bude motar na shiga batare da na sake wani magana ba shiko sai aikin shi yake yi kawai ana tafiya mun kai wurin wani babban shago yace don Allah ku bani minti biyu in dawo   Ya faka motar yafita sai mu biyu a cikin motar kowa da abinda yake yi a lokacin sai can naji yaja tsuki yana kallon shagon na dauka dani yake yi nace dakata malam bafa kai ka dauko ni ba da zaka ja min tsuki haka.

   Da mamaki ya dago kai yana kallo yace ke dani kike nace da wani nake haka kawai zaka kama jamin tsuki a mota da mamaki yake kallo na yace ke wata irin yarinya ce da bata da tarbiya.

   Kadai gyara maganan ka malam tarbiya ai ko makaho yasan akwaishi nan sai dai a lalaba a gani ai ba bace marasa tarbiya suke ba.

  Bai kai karshen magana ba cikin zafin nama da kunar zuciya ya juyo inda nake yace wa kike nufi baida tarbiya cikin muryan nan nashi mai dadin saurare da yake rowan ta.

  Tsoro naji ganin irin kallon da yake bina dashi  mai kama da harara ko tsana sai nayi kasa da kaina na kasa furta komai don kwarjin da yai min a idona

   Ya nuno yatsan shi daidai saitin fuska na tare da tsure ni da idanuwan shi lumsarsu yana fadin ke in badan Yusuf da bai san ciwon kan shi ba har kucaka irin ki ta isa ta shiga min mota na a tare dani.

  Yace kallani nan ko a hanya nagan ki baki isheni kallo ba a cikin mata don banga abin gani a wurin irin ki ba  cikin dakiya da dauriya nake kallan shi ina jin kalamin shi har cikin raina sai dai ina tara abinda zan mayar mashi ne a zuciya ta duk da naji tsoran yanayin shi.

 Yaci gaba da fadin idan baki hankali da ni ba watarana sai na balbala ki wallahi don ni mace bata kawo min raini nace dashi.

  Don Allah malam matsamin bakumayi mamaki  jin haka don ba abin mamaki bane don ka fadi hakan tunda dama kai irin maza nan ne dake raina jinsin su sai kai ido ga mata ketere saboda zalama irin na rashin sanin ciwon kai.

  Don wanan matar taka abin kyama ga jamma a da kai ka mayar mutum har kake ganin tafi ko wace macen kasan nan dadin abin dai kaima macen kasan nan ta haife , , , , 

   Fat naji yakai min bugu a baki don zafi sai da na dafe baki na ina dubawa ko jini yake min ban san lokacin da idona ya fara fitar da hawaye ba na yun kura zan fita daga motar yasa hannu ya danna lock mutar ta rufe kit yace kuma ki saurare ni.

  Duk kika sake ganina a mota kikayi gigin shigan shi sai ya jefar dake a waje mota ya take ki kin mutum in kashe ki in kashe bazan .

   Nace ni wallahi ba banzan bace sai dai in kaine yace bakin naki bai mutu bako yana kokarin kai hannun shi ya kamo baki na na noke kaina a kafana sai bai samu kama bakin nawa ba.

  A daidai lokacin Yusuf ya iso wurin da manyan ledoji a hannun shi yana bude motan zai sa ganin mu haka yasa shi ya sake murmushi.

  Ina jin shi nayi saurin dago kai nace mugu kawai azzalumi yace kai yaya haka may kai mata don Allah take kuka kuma ya waigo zai kara jamin baki na noke ina son fita a motan Yusuf ya tare ni yana fadin haba dai yaya zakaci zalun ta kuma haka ?

  May tayi maka haka wai kasa ta kuka ya juya yana cewa bakin nan mai rashin kunya na daka ido ya zaro yana cewa ka dake ta Abdul ?

   Kadan ma ke nan nayi mata ai fita nake son yi ba hanya don Yusuf dake wurin yayi rufe kofan ya zagaya ya shigo motar sai da muka fara tafiya yace ka bata hakkuri Abdul.

  Ina baya ina kuka naji ya fada mai hakan yace nace ka bata hakkuri yace wani zanba wanan yariyar hakuri ko wa yace bakai ka zalunce ta don may bazaka bata hakkuri ba ko kafin ka tafi da hakkin ta ne a kanka ?

  Baiyi magana ba sai aikin shi dayaci gaba dayi yace wai may ya hada kune haka da sauri nace zagina yayi na rama.

   Motar ya tsaya a kofa  gidajen mu na fita da sauri ya biyo ni yana kirana ban tsaya ba wata yar gidan yaba kayan ta shigo min dasu suka tafi ban san yadda suka karata ba.ZAINAB IDRIS MAKAWA

           SEENABU

Ina shiga ruwa na saukowa daga sama da karfi dama hadarin da ya gama haduwa a lokacin kiris yake jira ya fara zuban ruwa.

   Ruwa ake sosai a lokacin na kuma san basu kai gidajen su ba duk da ba zan iya cewa ga nisan gidajen su ba a lokacin.

   Na fara cire kayan jikina aka turo kofan dakin nawa da na saya da sauri na juya don ganin wanda ya shigo min a wanan lokacin haka.

  Maryam yace sabuwar kawar da nayi a cikin hostel din namu tana rike da wani warmer dain abinci na silver mai marika tashigo tana dauke da murmushi a fuskanta nima murmushin na mayar mata a lokacin nace cikin ruwan nan kika fito.

  Tana aje kulan tace tun dazun nake dakon dawowar ki ai sai yanzu na ga wuta a dakin ki na san kin dawo gami da yi min sannu da dawowa na amsa ta.

   Na karasa cire kayan na daura zani a jikina tace abinci na kawo muci don yanzu na samu yar uwa na huta zaman kadaici hakana murmushi nayi ina zama a saman katifan nace fitan nan nawa har kikai girki haka ?

   Tace dama akwai miyan a fridge sai shinkafa ne kawai na girka muna yanzu nayi mamakin jin har da fridge a dakin ta don ban taba shiga ba sai ita ce mai zuwa dakin nawa.

   Ido na ta kai ga ledan da na shigo dasu dakin yanzu na dauko na fara budewa kayan mata ne a ciki irin doganyen rigunan nan har kala biyar sai takalma da jakka biyu.

   Sai dayan ledan mai dauke da kayan drinks da su packed din sweet irin mai tsadan nan tace woow duk wanda yayi sayayan nan yasa kansa wanan rigunan duk letes ne fa don anty na business din da take yi ke nan wanan dawowan da tayi daga dubai naga ta dawo dasu har nace taban guda daga ciki tace sai dai in saya.

  Nace uhmm kyautar maya ne haka maryam wasu yan yan gari mu ne da suka zo yanzu muka fita tare suka saya min su.

  Maryam tayi dariya tace manya ko ba nawa sa ba nerbough don wanan wawan kyautar sai da wata a kasa kin san ko ba karamin kudi aka kashe wurin nan ba.

  Nace kuma kin ga ba wani abu a tsakanin mu sun dai ce ne mudan fita in rakasu wani wuri ni ban ma shiga shagon ba Yusuf kadai ya shiga sai gashi da wa yan nan kayan haka ya fito.

  Tace haka abin yake ai don masu kudi basu jin zafin fitar da kudin su,  ga abinda suke so don wanan kyauta ai ta maya ne daganin su duniya na damawa dasu Allah.

  Nace sam ban san yayi min wanan mahaukacin sayayya ba da na dakatar dashi wallahi ni na dauka ko irin dan drink's din nane da sweet fa.

  Maryam tace may ye na damuwan kan ki tunda bake kikace su saya maki ba sai dai gaskiya kyauta yana nuna alama ga abinda ake so ne.

   Nace so kuma ai sun san ban da lokacin wani so a yanzu kawai dai raayin su ne yin hakan sai dai zan dakatar dashi ga yi min haka nan gaba.

   Abinci ta fara zuba muna muna hira na kwashe kayan na kawar gefe guda ina ce mata kinga yanzu sai dai mu canza tsari ba wai kullun kita dafawa kina kawo min muna ci ba haka.

  Dariya tayi tace kin manta da rana naki mukaci shiyasa nima na dafa muna yanzu muci ai ko hakan kuma laifi ne nerbough ?

  Muna ci muna hiran makaranta da ita har mun kusa gamawa wayana dake gefe yayi kara da sauri na mika hannu na dauko don kada ya tsunke.

  Daddyn mune akan layin na dauka da sauri ina hadiye abincin da ke a bakina yace may kike ci haka khadja ko dadi kuke ci a makarantar mu muna nan gida muna hadiyan shikafa da mai ya fada cikin zolaya .

  Nace daddy Allah ya nuna muna mun samu kuma kuji dadin da iyayye ke ji ga diyan su watarana indai zakuyi farin ciki da hakan.

  Yace ko yanzun ma mun gode maku don muna cin moriyan ku a haka yaushe yaushe kika turo muna da kudin hannun ki wai mu kara nayi fada ai da yar uwarki nace ke da kike makaranta kin fimu bukata a yanzu ai.

  Burin mu daya shine muga kin tsayar da miji da wuri kiyi koyi da yar uwar ki kema kiyi aure basai kin yi dogon karatun nan dakike so ba.

   Dariya nayi nace kai daddy aure yanzu kuma nida nake son in zama babban lauya kafin in aure amma tunda naga raayin ka ke nan ba damuwa .

  Daddy da izzinin Allah zan cika maku burin ku daddy na karasa fadi cikin sanyin murya daddy yace da sauri .

  Dear kada ki sa wanan a rai yanzu buri na fada maki kawai shi aure ai dan lokaci ne indan lokacin yayi ko da shiri ko ba shiri zakiyi ne ai nafison in ganku cikin farin ciki a koda yaushe bana son bacin ranku kada magana na ya kara maki zuciyar ki akan karatun ki.

  Ya kara da fadin Allah dai yayi maku albarka dake da yan uwanki don baku taba bata muna rai ba da halin ku.

  A hankali na goge hawayen da ya zubo min a idona nace mukai sallama dashi bayan ya gama kwatar min da hankali na.

  Maryam ido ta tsura min ina aje wayan tace dani ina son nima inga ina haka da iyayyena wallahi sai dai hakan bai samu ba a gare ni don na taso ne ba tare da iyayyena a wuri daya ba.

  Mahaifiyar mu sun rabu da babban tun muna kanana sai dai idan naje inkai masu ziyara dukkan su tunda riko na yadawo hannun yayata.

  Nace Allah sarki lalai dole kiji sha, awan hakan gaskiya don iri haka babu daddy ni kinga iyayyena sun fi son suga nayi aure ko yaushe maganan su ke nan a kaina.

  Sai dai ko yaushe auren nawa zai zo ban sani ba tunda ko sauriyi tsayayye ban kai ga tsayarwa ba a yanzu haka.

  Tace to ina ga dai yazo din ne tunda ga wanan yanzu da ya fito ya fara nuna maki son shi dariya nayi nace maryam ke nan baki ganewa ne ke.

   Bandai fada mata komai ba mukaci gaba da hiran mu sai goma ta koma dakin ta nima na gama abinda nakeyi na kwata.

  Har na kawanta naji wayana na verviration a gefena nasa hannu na dauko wayar nace salamu alaikum.

         Yar mama kina lafiya yaya ruwa , ?

   Na sauke lafiyayyen murmushi nace lafiya kalau yaya Yusuf yace kina kara fasa min kai fa da yayan nan da kike kirana dashi nace kai ka saya a kira ka da sunan.

  Nace yaya kuka isa gida kuma yace lafiya kalau sai yanzu na kai mutumin ki gida yanzu haka ina hanyan gidana ne na kiraki mu gaisa.

   Yace bayan mun rabu dazu mun dade muna maganan ki da mutumi na nasan zai kiraki yau din na shiya na kira ki in fada maki don naga ya yarda sosai da shawarana.

  Nace anya kuwa zan iya cika maka alkawarin da na dauka don mutumin naka akwai zuciya sosai wallahi ni kuma ban iya daukan haka don nice zan taimake shi ba shi zai taimake ni ba.

   Dariya yayi yace a yadds kuke yi din nan shakuwa zaizo ya shiga tsakanin ku sosai zakice na fada maki watarana bagashi yanzu ya fara saukowa ba.

   Idan ba ta haka na fito mashi ba da wuya yayarda mu aiwatar da komai yadda muke so amma ki daure don Allah mubi abin sannu ni dai buri na shine ki san yadda kikayi kika kara ma wanan buzuwar kadarin ta a gurin jamma,a.

  Abin ne da kamar wuya yaya na sai dai zan yi kokari inga nayi yadda kuke so din yace good girl Allah ya taimaka ya bada sa,a nace amin.

  Shine kuma ka yi min dawainiya haka mai yawa don Allah nan gaba kada ka kara min irin haka don hakan zai yi maida ni cikin wani yanayi daba shi nazo yi a gatin ba.

  Dariya yayi yace Khadija kin san dai sutura shine mutum yanzu don haka farawa akayi don ina son ki goge sosai ki fito a cikin classes ladies ta yadda zamuji dadin aiwatar da komai a cikin sauki nace to na gode sai dai a rage don Allah.

  Kada kiji komai mana lokacin kine yayi kawai ki kwantar da hankaki kici arzikin ki a saukake wanan ba komai ba kada ki damu da hakan don har motan shiga ba dadewan nan ba zaki samu in komai ya tafi daidai.

  Zanyi magana ya katse ni da cewa na iso gida zan shi sai dai indan mun kara waya don yanzu zamu rage haduwa sosai kada a zargi wani abu a gare ni.

   Mun gama wayan ina mamakin su kudi kamar na sata haka nikan ban cika amincewa da irin haka ba azo ba a daidaita ba shirin mu ya watse abarni cikin wahala daga baya.

  

A hankali ya shigo gidan babban falon su ya samu su hidaya da sauran yan su zaune suna shan bakin shayin su na buzaye.

   Gaisuwa sukayi bai tsaya ta kansu ba ya shige ciki bai jin dadin yadda suke cika mashi gida a ko wani lokaci haka.

   Duk da wani lokaci abin yana taba mashi zuciya ganin yanzu babu wani nashi da yake zuwa wurin shi kamar lokacin da suke zaune kano da fati .

  Yan uwan shi na yawan ziyarar su maza da mata amma tunda abin ya juye haka sai dai kulun idan ya dawo gidan ace mai akwai bakin da suka zo daga kauyen maradi.

   Dakin ya nufa ya tura kofa a hankali dakin na nan a yarda ya barshi da safe ba a gyara shi ba in zai iya tunawa yau kwana uku ke nan bai samu lokacin da zai tsaya ya gyara dakin ba.

  Don cikin yan kwana kin nan suna zirga zirgan filin da suke son saya a kubuwa ga kuma wanan shirin da Yusuf yake son yi a kan shi.

   Rigar shi ta sama ya jefar a saman gado ya kara bin dakin da kallo ya ja tsuki ya nufi yanyar bathroom din shi wani zarni ne ya daki hancin shi da sauri ya fito ya nufi hanya wajen dakin.

   Dakin Nafisa ya shiga don yana kyautata zoton tana ciki tunda bai ganta falo ba kuma bai ganta a nan dakin shi ba.

  Yana shiga nan  ma wani tsami ya tare shi mai kama da karni karni yabi dakin da kallo ga kaya a ko ina watse a dakin tana kwance saman godon dake tule da kayan da bai san ko na maynene ba.

   Nafisa na ganin shi tace ka dawo ashe yanzu nake tunanen ka fa a raina nace ko ina ka shiga tunda ka fita da safe baku dawo ba.

   Haushine ya kamashi yadda take kwance ta mike kafa sai kadasu take yi tana magana kamar wata basaraka da ita.

   Kallon da yake mata ne yasa ta tsargu yace Nafisa wai ke dadin may kike ji ga kazantar nan naki ne haka don Allah dubi dakin da mutun ke rayuwa wai a cikin sa.

  Kina mace kice ba zaki iya gyaran muhalin ki ba sai wasu sunyi maki wai ma ina masu aikin da kikace kin dauka ban ga wani abinda suke a yi a gidan nan ba.

   Tace Samad yan uwana ne fa ko kuma yanzu kana bakin ciki da zaman su ne a gidan ko suyi aiki ko kada suyi zasu dai zauna anan tare dani ne ko ?

   Nasan wanan munufakin kila yaka su hadiye a falo ya zuga kwanan nan sai nayi maganin shi wallahi ni banga dalili da zai sa yayi ta shigo min gida ba haka ba gaira ba dalili yana sa muna ido.

   Ke na fada maki duk abinda zakiyi idon ki ya fita ga Yusuf don idan kikace zakiyi kokarin raba ni dashi kan ki zakiyi wa kin dai san halina and kuma ki tashi kije ki pulloshing din rubish din da kikayi min a bandaki tunda ba dakin ki bane.

   May nayi kuma kewayawa fa kawai nayi a ciki na fito yace zaki tashi ko sai na bata maki rai yanzu ya fadi yana dan zare mata idon shi.

  Mikewa tayi da kyar tazo ta wuce shi zuwa dakin ya bita da harara ya mara mata baya yana sa kai warin bayin ya ji har cikin dakin da sauri yafita zuwa dakin hutun shi tare da rufo kofan da key don bai son damuwa.

  Anan ya cire kayan shi ya yi wanka ya fito sallah ya gabatar ya dade zaune a wurin yana tunanen halin Nafisa ga gida da ta cika mai da yan uwanta babu halin ya zauna a tsararen falon shi ya sha iska a ciki.

  Tsuki yaja ya mike don ya kwanta nan yaga wayan shi da ya jefar saman gadon daya shigo dakin kafin ya kewaya dauko wayan yayi yana duba lokacin maganan Yusuf ya fado mashi a rai.

  Da yake ce mashi kabi yarinyar nan a sanun har mu cin ma manufar mu a kan hajiya ba wai nace kaso ta bane dole a a wanan wani dama ne da muka samu zamuyi amfani dashi.

   Nomba na ya bida a wayan da ya rubuta ma tsoturburn girl ya danna kira sai ko kiran ya shiga tunanen ya fara yi idan na dauka may zai ce min sai yaji na dauki wayan da sallama a bakina.

   Queen yar matsala yaya kika shiga gida yaya kuma ruwa i hope bai taba ki ba dai ?

   Murmushi nayi sai da yaji shi cikin zuciyar shi nace au mijin buzuwa ne a layi lallai kana son aikin nan da zan maka ke nan ?

  Yace to yaya na iya tunda Yusuf yace ke ce maganin matsalata yanzu indai har zaki min hakan ai ya zama dole in koyi zama dake da halin ki .

   Nace ashe shiyasa na samu queen din yan matsala yace idan akwai abinda yafi queen din su kinci a baki wanan muka min.

  Murmushi na sake yi nace nace nako gode da wanan sunan da aka rada min sai dai ina ganin bada ni sunan ya dace ba yanzu ai.

  Da sauri yace dawa ya dace nace kaida buzuwar matarka mana fara yar dagwas mai gashi har baya sai dai kassh kuma gashin sai naga kamar bai samun gyaran da ya dace dashi balle har kaji dadin shakan shi dakyau.

   Ke kada fa kiga na kiraki ki nemi tozarta min matata don kin san tafi komai da kike takama don wanan banzan dalilin na Yusuf da yakawo bashi ne zai sa ki samu daman fada min maganan banza ba.

   Wanan kuma fadi kayi mijin buzuwa don yanzun haka ma nasan tunanen yar asaline ya hana ka shakat sai da ka kirani kaji yaya nake sai dai kana tsoron buzuwar ka nasan ma yanzu haka wani wuri ka samu ka labe kake wanan waya dani.

   Idiout stupied girl kawai ya fada ya ja tsuki ya kashe wayan yana huci wai may yarinyar nan take takama dashi ne wai zuciyar shi tace kyau ilimi tsabta da fadin gaskiya.

  Idon shi ya lumshe yana tunane sai kuma ya sake guntun murmshi a yadda yake rigingine a kwace taba kofan da Nafisa keyi yasa shi bude idon yana jin ta har ta soma bugun kofan bai tashi ya bude mata ba sai gyara kwanciyar shi yayi dakyau ya fara adduan barci haka har barcin ya dauke shi yana tunane.ZAINAB IDRIS MAKAWA 

            SEENABU

Ina isa na fara bude kofana na lokacin yarinyar ta iso da kayan da Yusuf ya bata tana mika min kallon kayan nayi sai na karba ta karasa min da sauran a cikin daki na.

  Godiya nayi mata tace babu komai ai ana tare bayan na aje kayan na fada saman katifa na wasu hawaye masu zafi ne suke silalo min a fuska na.

   Idan na tunana da maganganun da ya fada min masu zafi duk da nima din nayi karfin halin ramawa a lokacin sai nake ganin ya kwaraini da yawa.

   Na dade a wurin ina neman hanyan da zan rama abinda yayi mun din don yaji zafin da naji  ban kai ga samun mafita ba wayana yayi kara a lokacin.

 Yusuf ne ya kirani sai da ta kusa tsukewa na dauka na kara a kunne na ina sauraron shi yace har yanzu kina fushi ne yar mama.

   Daurewa nayi nace ai ban fushi dakai don bakai min komai ba yaya na yace dakyau ina son ki saurare ni dakyau magana nake so  muyi dake yanzu.

    Ina jinka nace mai.

Khadija don Allah ina son ki bani hankalin ki ki fahinci abinda zan fada maki yanzu naji na kara furtawa.

   Don Allah ina son in rokeki wata alfarma wani aiki zaki nake son ki min a kan aboki na amma aikin yana da wahala sosai sai dai indan kin daure ba  wani wahala a cikin sa.

  To ina jinka Allah yasa zan iya kuma Allah yasa dai  aikin bai fi karfina ba,  murmushi yayi yana fadin bai fi karfin ki ba ma insha Allahu don zaki iya.

   Nace fada min inji aikin idan ba zai shafe karatuna ba da rayuwa na zan iya insha Allahu yace good girl dama na dade ina neman mace irin ki mai gaskiya da zan saka.

  Ba wani abu zan saki ba sai taimako rayuwan abakina Samad nake son in danka a hannun ki don kice a yanzu kadai nake da ita da zatayi min wanan kokari.

  Nace ni kuma yayana yace kwarai kuwa ke khadija don ko zaki iya idan munyi laakari da irin halin ki na san zaki iya shiyasa na zabo ki.

  Tun ranan da muka shiga dakin hajiya mama na fara ganin ki da kuma abinda yafaru dake da Nafisa matar shi kika tsaya min a rai.

  Ban kuma gaskanta hakan ba sai da naga kin iya biyu su a motar su zuwa nan Abuja kuma komai bai faru ba yasa na kara yarda da abinda nake shirin yi din .

  Sai gashi kuma yanzu abubuwa suna wakana a yadda nake son su tafi a tsakanin ku cikin hukuncin Allah komai yana tafiya daidai.

   Khadija ko kin san ba macen da ta isa ta tsaya kusa da Samad tun lokacin da ya auri Nafisa buzuwar matar shi kuwa.

   Nasan kin san matar shi Fati da akai masu auren gida har suka haifi yaya biyu shigowan buzuwa gidan ya sa suka rabu da ita badon basu son junan su ba.

   Khadija kin san abinda ya daure min kai nace a a  yace yadda Yusuf ya aminta dake a lokaci daya duk da nasan ba abu bane mai wuya a wurin Allah idan ya tashi yin ikon sa akan abu.

   Don haka nake son ki taimaka muna ki sake jiki da shi tayadda zai aminta dake idan haka ya samu gare mu na tabbatar da sheri buzuwa  yana gap da karyewa.

   Da sauri nace ba zan iya ba gaskiya ku nemi wata wanan miskilin mara mutunci ai buzuwar ne daidai dashi yace khadija zaki iya zaki iya komai.

  Kyau dai Allah ya baki shi ilimin addini da na boko duk kina dasu a wadace to may zai saki ce bazaki iya ba ai ko ba don niba ko don hajiya mama da fati da yaran ta zaki iya.

   Nace yanzu may kaka son in yi wai yace shina ke son in fada maki da farko dai idan ki  bi labari na zaki gane Samad bai iya ssoyayya ba shine matsalaan farko da aka samu gare shi.

   Murmushi nayi nace bai iya soyayya ba ta yaya ya auri matan shi har suka zauna Fati har ta haihu dashi biyu shima din murmushi naji ya dan yi yace.

   Bamu tare ke nan kin manta na fada maki ita fadi hadin iyayyene auren su ita kuma buzuwa abu biyu muke zaton shine silar auren su na farko dai ta rude shi da kyaun ta na biyu kuma ta hanyar sihiri da sauri nace sihiri kuma bada ni ba gaskiya.

   Yace da zata iya maki komai da tayi tuntuni ai shine ya bani daman sakaki wanan aiki a yanzu.

  Nace a takaice dai kana son in bata lokaci na a kan shi abinda ya kawo ni in barshi inje taimakon wani wanin ma wanda bai san darajan mutane ba.

   Aikin da zaki muna ke nan dama ki koya mashi zama da mutane da sauran abubuwan da ya watsar a baya ki dawo muna dashi Abdulsamad din shi na baya.

   Babban magana ke nan yayana yace ba wani babba bane a matsayin ki na mace zaki amfani da daman ki taimaka muna ki tai maki hajiya dake cikin halin bakin ciki a kashi.

  Shiru nayi ina tunane ko badon Yusuf ba ko don hajiya da yaran Fati zan iya kasadan yin wanan gwajin da suke sona dashi yanzu.

   Nace to shike nan naji zan yi matukar hakan ba zai shafi mutunci na ba dai yayi saurin cewa idan nasan zai zubar maki da kiman ki ba zan saka ki ba ai.

   Nace amma fa in ya nemi keta min mutunci ba zan kyale shi ba zan dauki mataki da kaina yace wanan ba halin shi bane don nasan halin shi tare muka taso tun muna yara dashi.

   Nace Allah bamu sa,a yace amin na godd da kika fahince ni yanzu zan samu lokaci in shigo inji mai kike bukata don kin san dole sai kin koma ke ma babban yarinya sosai.

   Kada ka damu zanyi amfani da wanda nake dashi yace kin wuce wanan yanzu khadija zaki zama budurwan mayan garin abuja ne fa.

  Yace ina son ki fara daga yau  nace yau din nan ina zanganshi yace zai bugo maki waya ba yana da layin ki ba nace eh zaki kaga ya kiraki kan abinda yayi maki.

  Amma sai dai please ki bishi a hankali yana da izza da saurin fushi da zuciya bai son yawan magana idan ba yaso ba amma banda wanan baida komai da zaki damu.

  Ni kuwa nasan haka nida ya fada ma magana yau sun ranshi sai dai zan  jure kamar yadda kuke so inyi din.

  Ajiyan zuciya naji ya sauke yace ban san irun godiyan da zanma maki ba ga wanan haracin da kikai muna wanda nasan insha Allahu zai zamo maki alheri ke ma nan gaba.

  To Allah yasa hakan alheri ne a gare ni dai fatana in ga ya koma da iyalin shi normal  sai naji ya sauke ajiyan zuciya yace final shine dama bukatan mu .

   Mukai sallama ya barni ina tunanen yadda abin namu zai kaya tsakanina da miskilin  mijin buzuwa ta ina zamu fara nace anya ban daukar wa kaina abinda ba zan iya ba kuwa.

  Gashi kuma Yusuf yace sirine ne tsakani na dashi sai Allah sai ko nan gaba da zai fada ma hajiya mama shirin shi.

  A raina nace zan iya insha Allahu indai iyalin shi zasu dawo gare shi sai dai ban taba zaton abin zai zo a kaina haka ba amma ba komai wahala bata kissa ai.

  Nan dai nayi ta tunanen ta yadda zan fara deal din akan shi amma dai Yusuf yace shi zai fara aiwatar da komai kamar yadda yake yi da farko.

  Safiyan lahadi wanki nayi sai wanan bakuwar yarinyar da ta shigo min da kaya don dai han san ta a gidan ba tazo min hira dakina ina gugan kayan da suka bushe min.

  Nan take fada min ai ita yar jos ne amma tana zaune ne da yayanta a nan cikin gari ta dawo hostel ne don ta samu yin karatu da kyau naji dasin haduwa na da ita ko banza zan rage zaman kadaici ni kadai da nakeyi ni kadai.

   Waya na yai kara na daga Yusuf ne bayan mun gaisa yace fito gamu kofan hostel din ku dam naji gaba ya bada na kalli maryam dake gefe na nace ina zuwa ta mike ita tace zata je ta gyara daki don gobe akwai classes.

   Ba wani dogon kwalliya nayi na dan yafa gyale na na fito tun fitowa idon su yana kaina har na iso inda suke a cikin motar su.

  Na gaida Yusuf din yace ga abokina ogana baki gaida shi ba na dan juya wurin shi a yatsune nace oh ashe tare kuke ina wuni.

  Haushi da takaici ya kama shi ya rasa ma zai yi sai da Yusuf yace khadija na gaishe ka fa cikin yanayi da alama na ko in kula yace lafiya kawai ya kawar da kanshi gefe.

   A ranshi yace i hate dis girl wallahi Yusuf ya katse shi da cewa oga gata nan ta fito fa ya fada cikin tsigar tsokana ya juyo da sauri yace wa wurin na tazo dama.

  Yace bakai kace muzo kabata hakkuri ba abinda kai mata jiya kasa ta kuka ya damay ka da sauri na tare Yusuf da cewa ai nice zan bashi hakuri nida na bata mashi rai jiya.

  Don fadin gaskiya ni kuma nasan gaskiya na fada duk cikkaken namiji da yasan ciwon kanshi ba zai tsaya mace na juya shi macen ma kuma buzuwa wai.

  Yusuf dama ka kawo ni nan ne don ta kara ci min mutunci ko may haushi ya ishe shi yarasa may zai ce min wallahi na tsani wanan yarinyar ya fada a hasale .

  Cikin ko in kula nace i hate you too dama abinda yasa kuka zo ke nan daga ganin ka nasan ba yin kanka bane buzuwa ta hasala ka ka koma ma matar ka kawai  ta asali ko mutuncin ka zai dawo ga idon jamma, a.

  Yusuf yace kai oga fitina khadija ko rigima nace bai son gaskiya ne gadai mutum har mutum amma bai kai ga cikan kamala ba har yanzu ga idon jamma a.

   Oh stop it gara ku fito fili kununa ma duniya soyayyan ku da wanan sallon soyayyan naku da kuke yi kullun u don't need to pretend garama ku fara tun yau.

   Wai Yusuf may kake nufi dani akan wanan yarinyar ne da kullun kake kawo ni wurin ta taci min mutunci hakane.

   Ni dramar kuce take burgeni wallahi don naga idan na kawo ka wurin khadija tana saka magana kana rage damuwa ko yaushe kuma tana ma tuni da abinda ka manta.

  Gyara zama yayi a motar ya kwantar da kai tare da harde hanaye shi wuri daya yana kallon bakin hostel din mu yadda mutane ke ta shiga da fita ciki.

  Nima kallon Yusuf nayi nace yayana wani wuri zaku ne yace muna dan yawata wane muka zo duba ki kin san ke amanan hajiyan mu ce gare mu yajuya wurin shi yana fadin ko ba haka ba aboki na ?

  Tsaki yaja ya kara kawar da kanshi gefe nace sai dai tsiyan abin indan yayi fushi fushin bai mashi kyau sai ma ya kara mai muni sosai.

  Murmushin dole ya sake yace kai Yusuf muje don Allah wanan na gane zata iya haukatani in banyi da gaske ba.

   Kaiko daukanta zamuyi mutafi da ita adan sawo mata wani abin mana kaga sai ta kara hucewa ko tunda gashi har ta baka hakkuri yanzu ai komai ya wuce kenan.

  Kinga ba sai kin fada ma hajiya mama dukan bakin ki da yayi ba jiya ai yanzu kun zama friends kuma ko fada ya kare ke khadija ba yayaki hakkuri don Allah.

Da sauri ya juyo inda nake sai na dan durkusa nace ya Samad kayi hakkuri don Allah idan na maka laifi.

  Oh baki san ma kin min laifi ba ke nan Yusuf yace shigo mota sai mu karasa magana a hanya yamma nayi kwarai.

  Banki ba tunda nasan plain ne na shiga motar a hankali ya harba titi ina harara dan iska a inda nake zaune Yusuf ne ya shiga aiwatar da nashi shirin a lokacin cikin motar yana dan muna nasiha.

   Yace kar kuji komai indan nine take a deep breath and confess your love to each other wani irin dogon nunfashi yaja tare da lumshe idanuwan shi.

  Da sauri nace yayana love kuma a ina kataba jin anyiwa mutum dole haka akan abinda yaki jini yace don't say dat again just say yes to each other don kuna bukatan hakan.

  Khadija ina son ki rike min oga na tsakani da Allah ko babu soyayya ku zama aminan juna muna son ki gyara tsakanin shi da hajiyan mu ta fahince shi ta bar hushi dashi.

   Sai lokacin ya kallo Yusuf ya sauke wani ajiyan zuciya don ya zaci Yusuf yana son hakane don gyara tsakanin shi da mahaifiyar shi.

   Nace yaya zanyi in gyara mashi laifin dashi yayi da kan shi har kake tunanen nice zan gyara hakan yace yes idan hajiya taji kuna tare nasan zata ji dadin yin hakan da kuka kin ga zata fitar ma abokina da zargin da suke mashi na buzuwa bata bari ya rabi wata mace sai ita.

   Sai yanzu na gane nufin ka abokina ya danyi gyaran murya sai kuma yayi shiru can yace da farko dai na gane manufan ka yanzu Yusuf .

   Yace zamu shirya dake idan har zakiyi min wanan taimakon iyayyena su fahince ni a hankali nace idan ka shirya yin hakan a shirye nake in taimaka ma in har zaka koma masu da zuciya daya.

   Maganan ta dan soshi ranshi amma haka ya dake yace na gode a hankali ai lokacin gode min baiyi ba nace mashi.

  Tsayar da motar yayi a bakin wani babban sai da kayan sawa irin na mata da maza ga motoci birjit a wurin an paka su a haraban wurin.

  Bissimilah yace muna kallon shi yayi yace wa wai ni kake nufi kowa yace daku duka nake magana ai yace may zanyi a wanan gurin yace kaunar mu zamu ma sayayya mana.

  No kuje kawai yace yana gyara zaman shi a yadda yake nace da ka barshi ma ban bukatan komai a yanzu yace tunda nayi niyar yin haka barin in fita induba zaku iya jira a mota yana bude motar zai fita yake wannan magana.

  Da sauri nace dashi barin fito mu shiga tare yace No ki zauna abinki yanzu zan fito ba dadewa zanyi a ciki ba.

   Yana wuce na koma na zauna bayan na bishi da kallo wayana na dauko ina dubawa shiru motar babu mai maga a cikin mu sai can naji yaja guntun tsuki wai da bai harka da kananan mata sai manya masu aji ko su sai a waje idan yafita duk da ba wai yana yawan hurda dasu bane yanzun ga Yusuf yana son ya dauko mashi wani aiki ga wanan yar karamar yarinyar dako sa,an kannen shi batakai ba sosai.

    Nima tsakin naja ina gyara zama cikin tunanen da nakeyi nashi.

  Ga dai mutum har mutum kudi kwaliya kwarjini duk Allah ya bashi sai dai yawan miskilanci da girman kai da jan aji din yayi yawa kamar ba mace ce ke juta shi ba a gida.

  Ke ni kike wa tsuki ko kowa ya juyo tare da zuba min kyawawan idanuwan shi a kaina na ma mance kana cikin motar nan murmushi mai kama da takaici yayi yaci gaba da zuba min kyawawan idanuwan shi can ya koma ya lumshe su tare da komawa saman kujera ya zauna.

   Ya sake cewa kina aji nawa ne yanzu ba tare da ya juyo ya kalle ni ba shiru nayi ina game da wayana batare da na nuna mai dani yake magana ba.

  Dake nake magana ko bakiji bane nace wa ni ai na dauka da kurma nake a motar a hankali ya kada kanshi ta dan sake murmushi yace ke dai ba zaki bar wanan halin naki ba ke nan.

  Nace ba halina bane hakan a ra nayi don in kare kai na daga masu raina ma tallaka hankali ya fido ido waje yace haka kika dauke ni ke nan .

  Hakan na gani kamar kana tsoron talaka a kusa da kai sai dai ba abun mamaki bane don ko a gida haka naga kanayi masu wanan daure fuskan.

  Kin san nayi ma aboki na alkawarin ban kara fada dake yanzu don haka ki kama min bakin ki tunkan in hasala da wa yan nan maganganun naki.

  Kai ashe kasan girman alkawari haka ne nakoji dadin jin hakan saidai kamar yadda kai mashi alkawari ka cika nima ada hakana naiwa kaina alkawarin ba zan tsaya da wani namiji ba sai gashi a sanidin taimako ina son karya alkawarin da na dauka ma kaina.

   Yaja numfashi tare da cewa wanan deal ne a tsakanin na dan wani lokaci banga abinda zai sa ki dauke shi kamar serious ba.

  Nayi dariya tare da cewa wasa mai kamar wahala ba indan buzuwa ta sanda hakan akwai matsala babba ashe sai na kwashe da wanni irin dariya mai ban haushi dake wa yayi bai ce komai ba cikin kuluwa.

  Yusuf ya fito da manyan jakkuna a hannun shi yana kokarin bude motar ta kofar baya ya saka jin dariya yasa shi cewa abin ya fara tafiya ke nan dai.

   Ya dai kusa na bashi amsa a takaice kai a fasa wanan deal din nace a fasa gaskiya zai fi don wanan ba zai kai ko ina ba.

  Zai kai mana yace yana rufe kofan motan ya zagaya ya shiga kallon Samad dake dafe da kan shi yayi muka kama hanya a lokacin hadari ya hadu sosai a garin ruwa na iya zuba a ko wani lokaci.

  Mun iso Yusuf ya tsayar  da motar yace khadija mun gode sai mun kara haduwa yanzun ba time hadari ya hade gari ta ko ina nace nagode kwarai.

   Ka kula min da mijin buzuwa don Allah na bude motar zan fita yace ga kayan ki nan ki kwasa duka naki ne godiya na sake mai karo na biyu na fice daga motar.ZAINAB IDRIS MAKAWA

            SEENABU

 Zaman da maryam yana min dadi sosai don itama bata da wasa da karatun ta gashi musan mutuncin junar mu kamar mun dade da haduwa da ita.

  Ita ta tilasta min fara amfani da kayan da Yusuf ya saya min tace may ye amfanin ajesu da nakeyi gara dai a fara gani a jikina zai fi.

   Ban sake bi takan su Yusuf din ba na mayar da hankalina ga abinda ya kawo ni garin sosai sai dai muna waya da kowanin su har yanzu wanda wayana da Samad duk ya kira fada ne da zolayan junan mu har ai fada a kai ga kashe wayan.

   Munyi jerabawan karshen zango na farko inda muna gap da gamawa Yusuf ya kirani nake ce mai sati mai zuwa zan tafi minna don ba zan leka kaduna ba wanan hutun saboda hutun ba mai yawa bane .

  Nan yake ce min suna tafe gurina kafin in wuce gida don suma zasu shiga kaduna don Samad ya dade bai je gida yana kokari yaga ya shawo kan shi su tafi.

  Nace ka barni dashi in gwada in gani idan zamuyi sa, a da nawa dabaran yace ya gode muka kashe wayan suna zaune tare aiki suke a wani file.

   Yusuf yayi mamakin jin ya tambaye shi khadija yace tana nan lafiya kasan jerabawa suke yi kwanan nan wayan shi ne yai kara baiyi saurin dubawa sai da ya gama abinda yake ya dago wayan.

  Kallon Yusuf yayi da mamaki tare da fadin Yusuf yarinyar nan ko mutum ce jifa itace ke kirana yanzu muna maganan ta.

   Yusuf ya kalle shi yace mutum ce mana kamar kowa kaima kana ranta kamar yadda take a ranka ke nan .

   Ya dauka ciki daure fuska kafin in magana ya fara fadin lafiyan kirana ina aikina nace lafiyan ya kawo haka ai .

   Ya sake kiran suna na a zuce da karfi yace matsala na amsa mai da cewa may ye ne haka zaka fasa min kunne da kira haka kamar makaho.

  Kai na tsani wanan yarinya ya fada a hasale na amsa mai da nima haka wallahi cikin yanayin na bashi amsa.

   Nace dama abinda yasa na kiraka don in fada ma ya kamata kaje gida ka duba tsofin ka don gudun su da kakeyi ba shine mafita ba gare ka.

   Yace what da karfi don bai yi tsammanin jin wanan magana haka ba a baki na

  Duk wani da mai neman albarkan iyayyen shi yana tare da su a kullun suna saka mai albarka da fatan gamawa da duniya lafiya don samun haske a gare shi.

  Kai kana ganin kudi da girman kai da suke rudin ka zasu iya sama ma farin ciki haka ne a gare su,  sunyi ciwo sun yi rashi amma bakai tunanen zuwa ka duba su ba har yau.

  Who dear you are da zaki fada min abinda zanyi akan iyayyena, nace  ni bakowa bace sai mai neman albarka iyayyena don haka kai ma na tunar  da kai akan hakan.

   Kuma kada ka manta da su Affan don sun fi kowa bukatan ka a wanan lokacin don nasan zaka iya zuwa masu hannu sake kai ba abin kunya bane a wurin ka.

  Don haka oga aje a duba su kada a shagala da yawa wataran sune masu duba mu you are stupid kece zaki tunatar dani komai kike nufi wai ke wacece wai waya baki wanan right din da zaki min wanan magana haka.

  Nace gani kamar kowa na tsoron fada maka gaskiya don suna ganin kana da kudi niko kudin ka ba damuna sukayi ba wallahi gaskiya komai dacin ta dole ne in fada ma mutum shi.

    Amma gani nayi buzuwan ka kamar kanta kawai ta sani  sai yan uwanta ai don haka nima dan uwa na na sani a yanzu.

   Kit na kashe wayan ina dariyan keta shima Yusuf dake zaune yana jin yadda mukayi dashi sai murmushi yake yi yana huci yabi wayan da kallo.

   You see abinda nake fada maka kenan gashi yarinyar nan har ta hango tunda kaji ta fadi haka akwai abinda taji ya faru a gida may be.

   May yarinyar nan ta dauki kanta ne wai zanyi fa maganin ta a garin nan Yusuf da sauri Yusuf din yace kunfi kusa ai ni dan kallo ne a tsakanin ku sai dai ya kamata ka bincika idan ba wani taji bai da lafiya a gidan ba.

    Tsaki yaja yana rufe file din da suke aiki akai alaman rashi ya baci sosai ya dafe kai da hannun shi daya tunane ya shiga yi yaya akayi yayi sake rainin da bai taba shiga tsakanin shi da kowa ba har shiga tsakanin mu haka wai abinda nake mai zakace ko mu din cousin ne.

  Kan shi yana dafe da hannu shi daya Yusuf yace muci gaba mana yace kana iya tafiya yanzu makarasa next yanzu matsala ya shiga .

  Dariya yayi yana mikewa yace matsalan khadija ke nan ko hararan shi yayi da idanuwan shi da sukai mashi ja shidai ya fice bai yi magana ba.

   Ya dade zaune a gurin a karshe ya jawo wayan shi yana neman layin mommy don ita kadai ce zai tsaya yayi magana na fahinta da ita ya gane komay ke guda.

   Kira biyu ta dauki wayan da sallama a bakin ta ya amsa mata tare da fadin mommy kowa na lafiya ko kwana biyu ban kira waya ba.

   Tace lafiya kalau muke sai dai Alhaji ne jikin nasa ba dadi wallahi wanan matsalar tashi dai ta kwanaki ke damu shi kuma sai kuma Affan da suka kwanta asibiti amma dai yaji sauki sosai yanzu.

   Wanan yarinyar takai shu,uma wallahi mommu tace wace yarinyar ke nan kuma yace da sauri No magana mukeyi a nan bayan ya gama waya da mommy sai ya kira hajiya mama.

   Sun gaisa ta fara mai korafin rashin kula da kyautatawan da bai yi take mai fadan ga mahaifin shi nan ba lafiya yan uwan shi na kai da komo akan sa amma ace shi yayi biris dasu badon suraj da yazo ya kai shi asibiti ba may yake son mutane su fada a kan shi.

   Hakkuri ya fara bata yana fadin in Allah ya yarda jumma,an nan mai zuwa zai shigo ya tabayi jikin Affan sai bata bashi amsa ba.

   Bayan sun gama waya ya dade zaune a wurin kafin ya mike ya nufi hanyar fita office din ya rasa abinda ke yawan shagaltar dashi yanzu gamay da iyayyen shi haka.

   Zuciyar shi ne tayi mashi zafi don haka ya nufi gidan shi dan ya dan sarara batare da ya sanar da kowa ba ya fice a ma,aikatar nasu sai gida.

   Tun a kofa yake jin suruntun yana shiga Nafisa tana zaune a tsakiyan falon tana shan bakin shayi a dan karamin cup tana lumshe idanuwanta.

   Ganin shi a wanan lokacin tayi mamakin dawowan shi gida yanzu rigar da ya barta dashi na barci ne saye a jikin ta har wanan lokacin ga su hadiye na busa shisha duk falon ya gauraye ta ko ina kamar ba falon da ya narka ma makudan kudi ba haka.

   Batare da yabi ta kansu ba ya haye sama zuwa part din shi har ya kama hanyan da zai kaishi dakin shi sai kuma ya juys ya shige dakin hutun shi ya rufo kofan.

   Sai da ta gama shan attayen ta ta mike zuwa wurin mijin nata ba tare da damuwa da irin shigar dake jikin ta ba bata samay shi a dakin ba don haka tasan yana dayan dakin da yakan kebe kan shi wani lokaci.

   Can ta nufa duk da tasan ba lalle bane ta samu kofan a bude sai dai tayi mamakin da ta tura taji kofan a bude ta sa kai ta shiga yana kwance yayi rub da ciki a saman gado ta iso gare shi tana fadin.

   Samad yau lafiya ka dawo irin wanan lokacin tana kokarin hawa saman gadon ta zauna a kusa dashi juyowa yayi yana fuskantar ta wani irin karni da bashi kanta da jikin ta ke sakewa da kyat ya daure yace banjin dadi jikina ne tace oho ba sannu ba Allah sauwaka.

   Samad dama ina son in fada maka satin nan akwai bukin da zamu maradi sai kuma wayan nan kannen nawa maza da suka zo zasu koma gida.

   Gashi kuma ina son ka canza min mato don wanan naje dashi har sau biyu an sani dashi sai kuma su hadiye da nake son inyi wa sayayya kafin mu tafi dakuma, , , , 

   Ke enough ya ishe ni don Allah duk wanan abin a cikin sati daya kike son inyishi ko kay wai may yasa ke baki da tunane ne wai ?

   Tsayawa tayi tana kallon shi galala tana mamaki yadda a dan lokaci yake son juya mata baya haka a lokaci guda tace Samad ni kake dakawa tsawa haka.

  Kallon ta yayi yace an daka maki ke baki da aiki sai na abaki dai a naki ai ma yan uwanki kaza ai masu kaza sam baki damu da na wa yan uwan ba da damuwar su.

  Tace amma kasan ina da yan uwa da ka aure ni ko yace wa kika fi yan uwa da bukatu ni nawa yan uwan basu son ai masu ne komay.

   Tace wanan kai ya shafa matsalar kace kuma ni dai nawa yan uwan na sani kuma dole kai masu don dani sula dagora.

   Mamaki da karfin halinta yaji yadda take fadin magana son ranta kai tsaye ta nuna mashi nata kawai ta sani shi yaji da nashi.

  Queen matsala kinyi gaskiya yace a ranshi ya ta tunar dani wani abu mai nauyi da na manta a rayuwana shiru yayi taci gaba da masifan ta akan shi bai iya furta komai ba a lokacin.

   Tashi yayi ya fada bathroom ya rufo kofan da karfi ruwa ya watsa a jikin shi yai wanka tare da yin alwala don yayi sallah la,asar don har lokaci ya dan gwauta da mintoci.

   Har ya fito tana zaune a wirin inda ya barta ya dauki room fresh ya fesa a dakin don bashin da dakin ya dauka ganin zai ta da sallah ya sa ta fita daga dakin ta barshi.


   Gyaran kai da jiki mukayi na zuwa gida don haka agajiye muka shigo hostel din mu maryam ta zauna dafa muna abinci ni wanka nashiga don zafi nake ji jikina ina ganin yayi min dauda.

   Tsab na fito nayi sallah a wirin na jawo ledan ice cream din da maryam ta sayo muna na fara sha a hankali maryam tace wallahi ji jake kamar kada ai hutun nan da za ayi.

  Da sauri na juyo ina ce mata saboda may maryam kika fadi haka tace ban son rabuwar mu wallahi yanzu ko ja koma gida banda wata abokiyar hira a kusa dani don anty na ba zama takeyi ba tana da yawan tafiye tafiye kullon don ita business woman ce .

   Nace ko dai ai koya nene kyayi kewan gida mana ni banki ba yanzun haka in bude ido in gani a cikin garin minna ma.

  Tace kin ji dadin ki wallahi khadija na yarda ba jin dadi bane farin ciki don ko dashi ne da bazan fadi haka ba farin ciki yana ga inda kake da sukunin aiwatar da komai.

   Kafin in magana wayana yayi kara na dauka kina ina nace maynene yace ki ban amsa kada ki min halin ku na yan African don Allah .

  Katambayi mutum ya mayar ma da tambaya shi kuma nace ina hostel mana yace ok kawai ya kashe wayan shi dip bin wayan nayi da kallo nace miskilin banza kawai.

   Maryam ta gama abinci wanda indomei da kwai ta dafa muna wanda yaji danyen attarudu mai yaji a ciki zubawa tayi a plate guda ta dauko muna lemon kwali a cikin fridge din ta wanda muke ajewa yanzu a ciki ida mun samu.

   Na fara cin abincin ke nan cibi biyu kawai nayi wayana yayi ringing na duba yaya Samad nagani a layin kamar kada in dauka dai na dauka kuma gani a kofan ku ya fada kawai.

  Kofan mu na maimaita da mamaki nace may kazo yi a nan kuma ban sani ba yace idan zaki fito ki fito sai ya kashe wayan kawai.

  Tsaki nayi na wurgar da wayan tare da fadin dan wahala kawai maryam dake zaune ta tsura min ido tana kallo na murmushi tayi tace.

  Uhm wani lucky guy din ne yazo haka ake ja mashi aji kuma abinda wasu ke nema ido rufe a zo gurin su anzo kike wanan masifa haka ?

   Nace sister kin faye bin kwakwafi wanan fa ba masoyi na bane zuwa kawai yayi ya bata min lokaci na ina zaune kalau.

  Don Allah ko may ya kawo shi kije ki saurare shi ba dadi mutum yazo wurin don ka ka wullakanta shi haka muje in zaba maki kayan da zaki saka in maki rakiya.

   Dole na mike muka tafi dakina ita da kanta ta zaba mi  wani dogon riga mai ruwan ganye da dan karamin gyale shi sai da na shirya tsab a cikin rigan tabi jikina ta feshe da turararuka masu kamshi muka rufo kofan muka fito tare.

   Yana zaune a cikin motar shi riga da wandon shadace mai guntun hannu rigar ma iya ciya dinkin yake light green kayan su matukar karban jikin shi da dinkin .

  Wurin dirkekiyar motar shi da ke fake a kofan can dan nesa kadan damu muka nufa ko ganin maryam ya hana shi fada ban sani ba sai cewan da yayi.

  Ita ko maryam tunane take a ranta ina tasan fuskan nan nashi ne ya katse mu da cewa kin san ina waje zaki shanyani a wanan wurin naku mai kazantar tsiya haka ?

  Nayi dan dariya tare da cewa cikin wayance abinda yafa da nace ga kawata maryam tazo gaida kai don ma ita ta matsa min in fito yanzun haka.

 Anyway maryam ga yayan mu Abdulsamad Abdulrahim nan ku gaisa tace dama nace kamar nasan fuskan nan ai tace ina wuni yayan mu anzo lafiya yaya iyali.

  Yace lafiya kalau yaya karatu koda yake exam kukeyi yanzu ko yana wani kauda kai yana basarwa .

  Tace karatu Alhamdullahi mun kusa cin ma karshen shi da yardan Allah ai a huta gajiya dama nace barin zo mu gaisa ne kawai yace to na gode kwarai da alama kin fi kawar taki kirki sosai.

  Dariya tayi tace a a wallahi ai kirkin khadija na daban ne wallahi tana da kiki matuka shiyasa ma nake jin dadin zama da ita wallahi.

   Baki ya tabe ta juya ta tafi tana mashi a huta gajiya ta nufi hanyan shiga hostel din namu sai lokacin na sauke ajiyan zuciya bayan tafiyan ta.

  Katse ni yayi da fadin tsaye zaki min sai kace wanda tazo tadi da buduruwar shi haka bude  kofan motar shi yayi na zagaya na shiga sai naji ya rufe motar.

  Shiru daga ni harshi ba wanda ya iya magana a lokacin sai ma gyara kwanciya yayi a motar bansan lokacin da nace dashi baka da lafiya ne Yaya Samad.

   Shiru yayi kamar baiji ni ba sai can yace may kika gani a tare da ni nace yau na ganka so weak ne ba miskilancin nan naka yasa na gane bakajin dadi ko baka cikin good mode.

  Wai ke aljana ce ko may dazun kin fada min magana akan ahalina ya zama gaskiya yanzu kuma waya fada maki banjin dadin jikina ?

  Nace yanayin ka ya nuna min haka sai ya dago da sauri ya na kallo na nima kallon shi nake yi sai dai ba zan iya jimirin kallon nashi ba a lokacin saboda kwarjin shi da ya cika min fuska a lokaci daya dukar da kaina nayi kasa ina wasa da yan tsun hannu na.

  Yau ina bakin naki ya shiga nace ko don Yusuf ne dama kike da bakin a gaban shi nace da sauri ko daya wallahi gani nayi yau kana bukatan kulawa don baka cikin hayacin ka sosai.

  Don jikina ya bani baka da lafiya sai naga ya koma ya kwanta kamar yadda yake da farko ya fadi a kasalance cewa kaina kamar zai rabe biyu nake jin shi khadija.

  Kasha magani na tambaye shi da sauri yace ban sha ba wani magani kake sha yace panadol extra nakan sha wani lokaci.

  Wayana na fara dannawa ina neman layin  maryam ta dauka nace fito min da panadol extra din nan da goran ruwa don Allah yaya Samad bai jin dadin jikin shi tace to da sauri na kashe wayan.

   Motar shiru ba a dauki lokaci ba sai ga maryam ta iso da maganin ta kwankwasa glass din motar ya bude mata karba nayi ina mata godiya tace babu komai mana Allah ya bashi lafiya.

   Maida marfin motar nayi na rufe na fara kokarin bare mashi maganin tare da bude goran ruwan nace mai gashi ka sha.

   Ya dago kanshi da kyat ya kalleni ya kalli maganin da ruwan da nake mika mai sai naga ya bude min bakin shi alaman in bashi da kaina .

  Dan rankwafawa nayi ina saka mashi maganin a baki na kawo goran ruwan na bashi ya hadiye da kyat yana wani lumshe idonun shi yana bata fuska.

   Komawa yayi ya kwanta tare da fadin thanks nace Allah ya baka lafiya amin yace da kyat ni dai komawa nayi na zauna na zuba mai ido.

   Wasu irin jijiyoyi naga sun fito rada rada saman goshin nashi wanda ban taba kula ko yana dasu bane dama tsoro ne ya kamani kada wani abu yazo ya samay shi fa a nan wurina nawa ya samay ni kuma.

   Shiru daga ni har shi ba wanda yayi magana a cikin mu har mintina na shudewa a hakan suna batun zama awa daya muna nan a hakan dashi kamar mai barci.

   Abu daya ne yasa hankalina dan kwantawa ganin yana numfashin shi normal a lokacin yasa nayi shiru tare da zuba mashi ido kawai ina kallon ikon Allah.

  Wayan shi dake aje a motan ne ke ringing ganin anata kira bai dauka ba yasa na daga kiran don ba suna batare da na saurari mai magana ba nace mai wayan bai da lafiya please.

  Naji muryan mace tana fadin ke wacece da sauri ya dago ya kwace wayan a hannu na ya katse kiran  yace akan may zaki daga min waya waya baki wanan damar da ikon daga min kira a wayana.

  Zanyi magana yace get out tunda ka samu lafiya yanzu zaka iya ci min mutunci sai dai ka sani ba zan ce ma komai a yanzu ba don yanayin da kake ciki na bukatan natsuwa.

   Get out i said na bude motar na fita ba tare da na juya na kalle shi ba naji ya tayar da motar ya jata da karfi yabar gurin nashige ciki abina.

   Dakina na shiga na wurgar da sauran maganin saman katifana na fara kokarin cire kaya a jikina sai ga maryam ta shigo tace ashe kin dawo.

  Eh ya tafi ya samu lafiya ai nace mata ina daura zanin a jikina na  nike kayan na za saman jakkunan kayana dake gefe daya a dakin.

   Shiko tunda ya kama hanya yake jin wani bacin rai da bakin ciki a ranshi yana fadin wanan aljanan yarinyar sai ta kasheni wata rana.

  Yarinya yanzu ta sauke min bacin raina yanzu kuma ta kara sakani a wani anya ma mutnce kuwa dai , ?

   Yana shiga gidan a hargitse ya samay su duk kan su Nafisa ta haukace masu daga ita sai dan buje a jikin ta tana fadin yaushe samad ya fara cin amana na haka ?

  Yaushe samad ya canza ban sani ba nayi sakaci da yawa har na bari haka ya faru a yau da ban dauki mataki ba.

  Haka ya shigo ya samay ta tana wanan sambatun a cikin yan uwanta da suke ririke da ita kamar sabuwar mahaukaciya.

  Nan ya shigo baice da kowa kalaba cikin fushi ya shigo gidan don haka basu ga fuskan wani magana a gareshi ba.

  Tayo cikin shi da zagi tana fadin macuci mayaudari sai Allah ya isar min a gare ka har zaka dauki waya kabawa wata mace ta fada min wai baka da lafiya a wurin ta.

   Da karfi ya banbare hannun ta da ta rike mai wuyan rigar jikin shi ya fisge ya shige dakin shi a hasale.ZAINAB IDRIS MAKAWA

            SEENABU

Maryam kamar jirana take in gama debe kayan a jikina ina zama tace amma friend zurinfin cikin ki yayi maki yawa wallahi.

   Ashe wanan guy din da ake nema ruwa a jallo dan uwan ki ne ban sani ba saurin kallon Maryam nayi nace ruwa a jallo ake nemas may yayi.

  Tace tsadan ganin gare shi mana gashi dai matashi ne amma Allah ya kai shi ga babban matsayi nace wani matsayi ne gare shi wanda kike zuzutawa haka wai ?

  Kai haba friend zakice baki san koshi waye ba kina tare dashi haka mutumin nan fa na hango tsatsan son ki a kwayar idon shi.

   Nace baki hango gaskiya ba idon ki bai hango maki gaskiyan alamarin ba kuma koda kin hango ma bai taba zama gaskiyan magana.

   Mutumin da gidan shi yafi karfin shi a karskashin mulkin ki mace yake wanda baida mutucin duban yan uwan shi tunda na fara magana ta kafe ni da idanuwan ta.

  Shiru nayi don na farga na fara sakin layi dariya tayi tace min kin dakata kuma mana nace barni da abin haushi don Allah kwantawa nayi rigingine ina tune a raina sai kuma na bushe da dariya ni kadai.

   Kallo na tayi tana mamakin abinda nakewa dariya haka ni kadai nace yau akwai bura uba a gida Samad tace akan may kuma nace ke dai bari.

  Buzuwar matarshi ta bugo waya tana tambayan shi na dauki wayan nace mata gashi nan wuri na baida lafiya.

  Ido ta zaro waje tace kika amsa kiran matar tashi khadija nace kwarai kuwa ina dariya nace zata gane shayi ruwa ne maryam.

   Ba gani take ta mallake shi ba ba macen da ta isa tazo kusa da shi hatta uwar shi ta raba shi dasu duk yan uwa ganin su take muggaine bata yarda dasu ba.

  Kirikiri ta hana matar shi zama a dakin ta dole yanzu saida ta koma gida take zaune ba ruwan shi da yaran da ya haifa da cikin shi.

  Tace khadija kina nufin wanan guy din yana da iyali haka dama idan ka ganshi sai ka dauka ko auren farko baiyi ba a rayuwan shi.

  Nace wa mai iyali ne da kike ganin shi wurin nan auren gata ya samu ga iyayyen su shine kuma bai iya riko ba saboda buzuwar matar shi.

  Nace Wasa farin girki yanzu muka fara wasan da ita sai na manna mata karamin hauka a zuciyar ta tunda tace bata son hurdan shi da ko wace mace.

   Haduwa goma zamuyi dashi sako goma zan tura mata muje zuwa indai nice ko wace mace da dabaranta ake haihuwan ta sai dai na wata yafi na wata kissan.

  Khadija kin ko san kisan macen buzuwa macen buzuwa fa duk inda take shu,uma ce bata bari miji ya zauna da matar shi lafiya sai ita.

   Nace maryam kin san ko matan minna ko waye su ba buzuwa ba ko tsakiyan matan maradi za a kaini na shirya mata indai akwai ayar Allah.

   Zan bi dare in bi rana sai na nuna mata muma matan Nigeria akwai shu,umai cikin mu ai banda matsala tunda na san lagonta ta .

   Allah ya bamu saa tace nace amin sai na girgiza kai nace bawai da manufar yaso ni har cikin ranshi nake wanan abin ba yi dai nake in nuna mata boka da malam karya ne.

   Tace yanzu yaya kuka kare dashi nace korata yayi daga motar shi kai tsaye dariya ta kwashe dashi tace ai ba zaki kara ganin shi ba ko.

  Nace gobe ma yayi nesa ki gan shi nan ai ni abin har mamaki nake ji wallahi tace don dai kince buzuwa ce matar shi amma da sai in ce wani namiji zai samay ki ya bari ki kufce mashi khadija.

  Kyau Allah ya baki tsayi da gashi ga ilimi addini dana boko kin tara ranan da naji kina karatu wallahi har rudewa nayi na raya a raina da naje gida komawa zanyi makaranta ni ma na samu in sauke.

  Tun ina karama fa na sauke maryam yanzun haka ban bar karatu ba don ina nan ne bana zuwa amma a gida ban wasa da karatu ko kadan kinga yayata malama ce sosai wallahi.

   Tace ai naga alama tun haduwa na dake idan kuna waya da ita zata tana makaranta ko gata tana shiri fita makaranta may yafi wanan dadi ga mace.

   Nace kinga mu zama yakawo kakannin mu zama garin minna amma aslin mu yan wani gari ne da ake kira ka,oje tun ana hade da sokoto da Niger yanzun haka mu bamu san gida ba mu filani ne na asali wallahi.

  Mahaifiyar mu ce kwarin minna amma saboda zama muka juye muka zama mutanen minna baki sanin mu baki ne idan ba mun fada ma ba.

   Haba nature din ki yayi kama sosai da na fulani ashe ma ke ruwan su ne nace ada ke nan ina so  zuwa garin mu sosai inga yan uwana wallahi.

  Don ance har yanzu yan uwan mu suna garin don daddy din mu shi yasan gari har yakan je lokacin da bai tara iyali haka ba.

   Tace ya kamata ku nemi gida su san ku fa nace muna da burin haka nida ya Amina ai sai dai kin san abin sai an shirya ne .

   

Dakin shi ya nufa ya fara cire kayan shi zuciyar shi yana mai soya yana jin kamar ya ganin a gaban shi ya shake ni don haushi da takaicina da yake ji.

  Nafisa ce tazo dakin har lokacin a hasale take daidai ya fito daga wanka ta yi mai wani mugun kallo tace yau sai ka fada min gurin wace kaje har ta dauki wayan ka ta kirani dashi.

   Baiyi magana ba sai kokarin saka jallabiyan da yake yi a jikin shi ta karaso tana ce mai wata yar iska yar kasada ke son shiga rayuwan ka Samad ?

   Ido kawai ya tsura mata yana kallon ta batare da yayi mata magana ba ta sake maimaita tambayan shi samad ka fada min wa cece kaje wurin ta har ta dauki wayan ka ?

   Ta karaso tana rike mai kwalar dogon rigan da ya a jikin shi yanzu kama hannuwan nata yayi ya murde ya wurgata saman goda ya nufi inda turaren shi suke ya dauko yana fesawa jikin shi.

  Ta kara juyowa ta nufo shi a hasale tana cewa kunji kun gama iskancin ku shine ka dawo gidana kana min wankan tsarki anan.

  Da mamaki yake kallon ta ya bude baki da kyar yace Nafisa yau ni kike wa zargin aikata zina da wata kace tace dole in maka samad may ye hadin ka da wata mace , ?

   Yace dani mazanaci da akan ki zan fara tunda dashi kika gabatar min da soyayyan ki farkon haduwan mu dake.

  Haushin maganan shi taji sai ko ta haushi da duka da yakusa tana ture shi tsayawa yayi yana kallon ta da mamaki.

   Jayeta ya kara yi ya hakadata gefe ya fice daga dakin ta biyo shi tana zagi ta uwa ta uba ya shige dayan dakin ya kyale ta.

  Yana shiga wayan shi na kara ya dauka Yusuf ne yake son fada mashi ya gama tsara masu tafiyan da zasuyi kaduna.

   Yace sai dai abinda zamu saya wa yaran nake son mu dauko khadija ta zaba muna abinda ya dace dasu tunda mu ba zaben kayan yara muka iya ba.

  Yusuf ya ambaci sunan shi a kasalance Yusuf din ya amsa mai yace don Allah ka rabani da wanan yarinyar dake batun tarwatsa min gida da rayuwa na.

   Cikin mamaki Yusuf din yace tayi ma wani abune kuma ban sani ba yace may ne ma batai min ba yanzun haka in ka saurara zaka iya jiyo hargowan Nafisa akan khadija.

   Da sauri Yusuf din yace dashi kai haba sun hadu ne komai ko ta samu labarin khadija din ne yace basu hadu ba sai dai yau kaddara ya hadasu a wayana.

  Nan ya koro mai abinda ya faru yau din dariya sosai Yusuf ya kwashe dashi lokaci guda yace kai khadija akwai jan magana da rashin tsoro.

  Yace ni yau taja min masifa da fushin Nafisa a gidan nan ban son wanan bakin kishin na Nafisa wallahi idan ya tashi bataji bata gani imagine wai har ni Nafisa ke ma zargin zina yau.

  Intrested ashe yau tasan zaka iya kara aure ko wani lokaci ke nan wow i am impress da jin wanan labarin Allah yasa haka yasa ta fara gyara halin ta.

   Rikici kake son jawo min Yusuf da ka hada ni wanan aljanan yarinyar mai shegen rigima wai dole sai itace zatai min wanan aikin ne ?

  Kana son mu canza wata ce ya tambaya shi a cikin gatse yace No da sauri yace ta faye matsala ne wallahi.

  Yace da matsalan nata za a gyara komai kai dai ka kara hakuri don Allah yace wallahi yarinyar ta fara shiga raina amma kuma ta faye matsala ne ai.

  Yanzu yaya zan iya shawo kan Nafisa a gidan nan gaba daya ta birkice min yau kan kishin wace ma bata sani ba har da duka na fa takeyi.

   Duka kuma subbahanallahi kai kuma sai kai tsaye tana dukan ka ko mai yace to may zan mata Yusuf kit Yusuf din ya kashe waya alaman yaji haushin maganan abokin nashi.

   Dariya ya soma yi bayan ya kashe ma Samad waya yace komai na zuwa yadda nake so da alama samad ya fara son khadija.

  Wayana ya kira bayan mun gaisa yake tambayana ashe yau mutumin yazo gurin ki shi kadai nace eh dan matsalan yazo min wai bashi da lafiya.

  Sai bayan na taimaka mai da magani yaji sauki ya soma karanta min haukan shi wai na fita mai a motar shi tunbai balbalani ba.

  Dariya yayi yace may ya hada ku har haka nace bakin rigima na yasani daukar mai wayan matarshi da take neman shi ganin kamar barci yake wayan nata ruri nikuma sai na dauka.

  Dariya yayi sosai a lokacin yace aiko nasan yau suna can suna tafka fitina a tsakanin su kin ja mashi aiki yau

  Nace shi ta sha matsoracin namiji kawai wanan ma ko ga maza yan uwan shi nasan matsoracine wallahi dariya Yusuf yayi sosai.

   Yace to yanzu na kiraki ne don Allah gobe indan kina free zaki taimaka muna da sayen kayan yaran samad don Friday zamu shiga kaduna insha Allahu.

   Nace idan dashi ne gaskiya ba zan tafi ba yace saboda may khadija kefa kika kawo wanan idea din zaki ce kuma bazaki tafi ba.

  Ki daure ki karasa ladan ki don Allah ai ba don shi zakiyi ba yaran fa kika dauki alkawarin taimakawa saboda Allah shiru nayi yace may kikace nace a hankali naji sai dai idan ya wuce gobe ba zan  samu fita ba don ina da exam talata kuma zan wuce gida.

   Yace nagode khadija Allah ya biyaki da alherin sa yadda kike muna Allah ne kadai zai saka miki sai mun hadu goben zamuyi magana Allah ya kai mu nace dashi.

   Na kwanta cike da tunane a raina wai dama da gaske akwai mazan da suke irin wanan rayuwan a gidajen su don dai ni nasan mahaifin mu zaki ne a gidan shi akan iyalin shi.

  Wai duk gidajen masu kudi haka yake ne rayuwan su sai mata ke juya su yadda suka ga dama idan ka gansu awaje sai kai masu kallon isa da izza amma a gidajen su sai ka raina su.

   Yaya matashi kamar Samad zai zauna mace tana juya shi haka yadda take so wai kuma yana sunan miji a gidan shi gashi da ilimi daya dace yayi amfani dashi ako ina ya kama amma mace ta na juya shi son ranta.

  Kwafa nayi nace wallahi gobe zasu ga tsiya don sayayya zanyi masu kamar na hauka inta gani ta haukace da tushe.

   Washe gari nace ma maryam ta shirya zamu fita da su yaya Samad zasu zo mu muyi wa iyalin shi sayayya tace tau da murnan ta.

   Mun shirya tsab don Yusuf ya bugo min waya suna kan hanya zuwa wani dan abu ne ya tsayar dasu yanzu.

   Sun iso wayan Yusuf ya shigo min gasu a kofan mu nace gamu tafe yace keda wa khadija nace da kawata maryam zata tayani zaben kayan ne sai kun fito yace min.

   Mun fito daga gidan kwanan namu na dalibai muka hango su can nesa kadan inda suka aje motar su muka karaso wurin .

  Motar Yusuf ya fito ya bude muna muka shiga ya rufe sai da muka zauna muka fara gaida su wanda nidai kusan Yusuf kawai na gayar maryam ne tace da Samad yaya jikin shi yace cikin daga hannu da  sauki.

   Sai looacin ciwon kan da yazo dashi jiya ya fado mashi a rai don fitinan da suka kwana sunayi da Nafisa yasa ya manta da komai nashi.

  Kawar ki bata magana ne Yusuf ya kawar dashirun da motar yayi a lokacin  maryam ne ta bashi amsa da fadin ai itace dai magana ya zama aiki a gare ta nikan ko aku ya ganeni ya kauce min wurin zuba.

  Ashe kuna da aiki shi yasa abin yazo maku daidai naji mamakin da kika iya zama da wanan mai zubin yan ruwan dariya ta danyi tana cewa ashe kaima kyaunta na ruda ka haka.

   Haka take ruda maza a cikin makarantar dama wajen makarantar  amma kunsan may wai duk wanan bata ga may mata ba har yanzu ga kyau yana tafiya a banza a gurin maza.

  Tsuki yaja tare da juyowa ya dan watsa mata harara lokacin da take fadin ni wallahi ina son ganin lucky man din zai iya sace zuciyar wanan yar kwalisan yarinyar.

   Zaki ko sha zaman jira don maza basu son zuben mace irin wanan da ko ina tabi surar ta na rawa sun fi son mace mai natsuwa da kamala.

   Yusuf yace har kin sa yau na fahinci wani abu da kika kawo wanan maganan haka nayi real sign ba karamin kyau ki ga khadija ba da har na kasa fahintar abinda yasa abokina yake yawan rudewa idan ya hadu da khadija ashe kyawon tane yake yawan tsorata shi yana mata kallo mai kama da tsoro but still yanzu da yai maganan nan sai na gane kyauta ne yake yawan ruda shi.

  Da na dan shiga rudanin wanan abin amma yanzu maganan nan da kikayi yasani a hanya  watau a takaice aboki na yana rudewa idan yaga khadija sai take mashi zubin yan ruwa idan ya kalle ta.

  Tayi saurin fadin ya gano sirin da Allah ya boye ne anan ai khadija matar manya ce wallahi duk namijin da yai saa ta kalleshi da manyan idanun nan nata yakan shiga rudu ne ya rasa inda yake ina ga shiya take tsoron fita wallahi.

  Don Allah malam idan kun gama kaja mota kakai mu inda zamu ko ka mayar damu inda ka dauko mu zaifi ya fada batare da ya juyo gare shi ba

Yi hakkuri malam abinda na gani na fada yasin khadija ta hadu ba karya a gurin nan kai mai dani inda ka dauko ni ya fada a dake.

  Nidai nayi kamar badani suke yi ba kaina yana duke ina danna wayana dake hannu na muna charting da zarah.

  Yusuf yace karkai fushi dani abokina gaskiya muka fada anan take a deep breath and confess khadija ta fi matan da kake gani haduwa.

  Bude baki yayi  ya zaro ido yana kallon yusuf da mamaki kalaman shi dayaji na bazata yasan Yusuf ne kadai duk duniya yake iya fahintar shi lokaci daya.

   Yusuf ya sake kallo shi ya dan lagabe kai tare da girgiza mashi kai yace dont give me that look just say yes to your mind she is realy beautiful as you see.

  Take ya daure fuskan shi tamau tankar bai taba dariya ba yace Yusuf kayi kuskuren furtan hakan a gare ni don kafi kowa sanin banda lokacin yin hakan .

  Nace kunyi babban kuskure Yusuf da kuke son kamanta da wanan mutum matsoraci ko kuna zaton sakewan da nayi daku kun dauke shi da wani manufane ?

  Ba so ko wani abu makamancin haka cikin zuciyana don ban taba daukan haka ba a tsakanina dakai sai mutunci da niyar taimakon ka a zuciyata don rayuwan ka na bukatan taimako da agaji ga wanda yasan shi.

  Tsakanina daku kuma sai dangantarkar irin na zumunci na an fito wuri daya da biye min da kukeyi da kyautatawa .

   Da ka sani da baka dauki haka ba da zafi don zuciyar ka ta baka ba daidai ba me yasa zakayi zaton soyayye zai yuyu a tsakanin mu don kana kyakyawa mai kudi maiji da ilimi da wayewa ko may ?

   To ni duk wanan nasaban naka baya burge ni don ni ina fatan samun miji ne wanda yasan kanshi yake iya mulkata ba in mulkeshi ba ko wata tana mulkanshi.

  Barin fada maka ban taba jin son ka wallahi a raina don halinka bai mun ba bai kuma taba burgeni ba tausayi ne da fatan alheri ka shirya da iyayyen ka takowani hali .

  Don halinka da dabiar ka yanayin rayuwan da ka shiga da komai naka yana bukatan gyara a yanzu.

  Ya isa yace da karfi ya fada cikin kuna rai,  yayin da maryam tunda na fara magana take rufe min baki waina bar maganan .

  Idon shi yayi mai jawur hankalin shi yana neman barin jikin shi zuciyar shi yana son tarwatse mai yace ba laifin ki ba ne.

   Yaja wani irin huci ya furzar a bakin shi yace Yusuf ka juya mu sauke su inda ka dauko su don Allah.

  Bana son inkara ganin fuskan yarinyar nan na tsane ta wallahi bana son kara haduwa da ita a rayuwa na .

  Shiko Yusuf a ranshi ya gigice da fadan mu sosai yana rayawa yaushe ne zai samu cin ma manufar shi a kan mu yaushe zasu bar wanan halin may yasa Samad ke biye mata suna haka kamar wasu yara kanana.

   Ya zama mai dole ya shiri mu tun yanzu tun kan mu rabu a hakan ba wani ci gaba gashi ya fara ganin hasken alamarin tun ba a je ko ina ba.

  Ya zama dole ya gyara wanan abin tun anan don ba zai yarda abokin nashi yaci gaba da zama haka ba yanzu in ya bari muka watse a hakan abin bayi ba wallahi.

  Naji Yusuf din yace  Khadija ba nufin abokina ke nan ba baki fahince shi bane tun farko kin san tun jiya fa yana da haushin ki a ranshi don haka don Allah bashi hakkuri ya huce dake haka please.

   Yadan juyo yana kashe min ido sai na gane manufarshi da sauri sai da na hade wani bakin ciki na iya furta to kayi hakkuri don Allah ban fahince ka bane na fada a sanyaye.

   Da kyau Khadija matar na tuba ko bata laifi komai rintsi ya juya gurin shi yace kayi tsamanin jin hakan daga bakin ta yanzu a yadda tahau din nan.

   Wani iri yaji yace a ranshi may yasa na kasa fahintar wanan yarinyar ne wai me yasa na fadi wanan maganganun masu zafi gareta yanzu bayan nasan gaskiya Yusuf suka fada.

  Halinta daban ne da na sauran matan dake bina suna ribibin in so su kai tsaye zata iya fada ma gaskiya batare da tsoron komai ba kuma ya amfane ka.

  A sanyaye yace Yusuf ban san may yasa  take son bata min rai ko da yaushe muka hadu ba zan bata dama taci gaba da min yadda take so ko yaushe.

  Motar ta tsaya a bakin wani plaza babba ba wanda yayi magana Yusuf ne yace bissimila mun iso mu shiga mu fito tukun.

   Fita mukayi a motan har lokacin jikina a sanyaye nake jin shi don abinda ya faru a motan Yusuf ne yazo daidai inda nake yace khadija na gode da kika fahince ni ba komai nace dashi cikin yake.

   Muna shiga shi yana bayan mu yana tako a cikin izza da kamala maryam tazo daidai kunne na tace dan dakata mai ku jera mana.

   Hara na aika mata nace sai dai ya mutu idan sai na jera dashi din ya dai ci albarkacin Yusuf da kuma na iyayye wallahi.

   Ban garen kayan yara muka nufa inda maryam ta fara duba kayan ina tayata har lokacin ban sake ba nan muka shiga jidan ma yaran kayan sawa da sauran abubwan yara.

  Mu koma bangaren takalma da dasu sauran abin bukatan yara harda su tawul da sabule da su kulan zuwa school muka hado dashi a hankali na taka wurin kayan mata na zaba ma anty fati kusan kala goma masu kyau da tsada.

  Su dai ido kawai suka saka min har lokacin da muka gama Yusuf yace mu zabi abinda muke so ni wani jakka da takalma kawai na dauka maryam kuma ta dauki wani dogon riga da jakka.

   Munje gun biya muka da ja baya naga ya ciro katin shi na bakin ya basu suka debe kudin su suka miko mai mun shiga motar mun zauna.

   Yace kina ganin mun sai komai da zasu buta nace insha Allahu har maman su ma da sauri ya juyo yadan kalle ni kamzaiyi magana sai kuma ya fasa yusuf yaja motan muka tafi.

       SEENABU
Hutun sati uku kacal muka samu wanan karshen zangon don haka naji dadi sosai da bai kasance dogon hutu bane don zan samu zama a minna tare da iyayyena in yi hutu.
  Wanda rabo da in samu kasancewa dasu haka a wadace har na manta yanzun haka na fito daga zana jerabawan karshe na wanan zangon da mukayi da yazo min da rikicin haduwa da Abdulsamad da abokin shi Yusuf.
  Ba ranan zan tafi ba sai washe gari don haka maryam ta tsaya jirana don taso muje gidan yayar ta na nuna mata ban son zuwa can din.
  Komai na gama shiryawa a dakin sai kayan da zan saka ne da katifa ban samu daga wa sama ba don kwantawa da zanyi na yau kawai da safe in dage shi sama in tafi gida.
  Bayan mun rabu dasu yusuf ya kirani yana tanbaya na ya muka isa hostel din mu tare da kara yi min godiya .
  Bayan mun kashe wayan gidan Abdulsamad suka nufa sun kusa shiga gidan ne  Abdulsamad din yace dashi idan sun tafi kada a sauke kaya da aka sayo a gidan shi abar kayan acikin mota kawai idan sun isa Yusuf yagane manufan shi na fadin haka.
  Sai dai bai ma abokin nashi magana ba gamay da abinda ya fahinta na son kada a sauke kayan dayace kada ayi har lokacin gidan ba dadi tsakanin su da Nafisa.
   Wanka ya fito yana goge ruwa akanshi ta shigo dakin har lokacin tana nan cikin fushinta da shi zuwa tayi tambayan shi kudin da tayi requesting wana zata yi tafiya zuwa gida.
   Tace Samad kwanaki na ta matsowa har yanzu bakai magana kan abinda na bukaci ka bani ba wanda zan je gida dashi indan zan tafi sai in wuce dashi.
   Yadda take magana bai sa ya daga kai ya kalle ta ba Samad dakai fa nake magana ya dan wuce ta zuwa bakin gado ya zauna .
  Ta juyo gareshi tace magana fa nakeyi maka kana ji kuma ta fadi a hasale sai lokacin ya dago yace kada ki kara yi min maganan nan.
  Don bashi ke gaba na ba gobe kaduna zan tafi in daba iyayye da iyali na wani irin gumzi tayi tayo kan shi tana fadin wallahi baka isa ba.
  Ba kuma inda zaka kaje na fada ma don baka fada min zancen tafiya ka ba don haka ban shirya ma tafiyan ka yanzu.
  Murmushi yayi yace kice ma mai shirya min tafiyan don kece zaki sallamay ke nan ko ?
   May kake nufi da wanan maganan haka ban ci na sani bane idan za kai tafiya yanzu koma ko da da kake fada min ni nake sa ka fada min .
  Yace shine kuskuren da na aikata a baya yanzun kuma a shirye nake da na gyara komai da ya faru ido ta zuba mai cikin firgici take.
   Ganin zata damay shi yasa ya fice ya bar mata dakin don da dakin yaso ya gyara kafin ya kwanta don ya kwana biyu ba samu tsayawa ya gyara ba.
  Don yanzu gyaran dakin kwanan nashi ya dawo kan shi saboda indan yan uwan nata sun mashi gyara sai abubuwan da dama suyi ta bacewa a dakin.
  Wanan yasa ya daina bari su shiga mai daki suyi mashi gyara sai shi ya ke gyaran dakin nashi da kanshi ya don yafi mai sauki idan bai gyara ba ita bata da lokacin gyaran .
   Haka kuma zata shigo ta kwanta a cikin dakin ba kunya ba tsoron Allah haka dai ake rayuwan a dunkule ba wani jin dadin irin na aure tsakanin  mata da miji.
   Laptop din shi ya dauko ya na dubawa sai dai tunane ya hana shi yin wani aiki a ciki bakomai yake tunane ba sai irin maganan da nake fada mai, mai kama da shagube yana jin haushi na ashe gaskiya nake fada mashi.
  Yaushe rabon shi da yaran shi suzo kusa dashi su zauna a matsayin shi na mahaifin su suji dadi babu.
  Ya tanbatar da ya tafka babban kuskure da Allah zai iya kama shi da laifin da ba zai iya amsawa ba gobe kiyama.
  Khadija khadija ya furta a hankali kin taimake kin ceci rayuwana ta yadda ban taba zato ba wanan wace irin yarinya ce mai hikimà da basira.
   Ya dade a wurin zaune har ya kai kwance sai da wayan shi yayi ringing ya daga wani yaron shi na wurin aiki ke gaya mai an samu wasu filaye ns gwaunati a gwagwalada da wasu mutane ke son ci.
   Yace da yaron nashi ya bari sai next week za a duba case din idan Allah ya kaimu sun gama waya kiran Yusuf ya sake shigo mai inda yake fada mai gashi a kofan gidan shi sin dawo da motaci an gama duba su .
  Yace gaya nan fito mikewa yayi ya zura santala santalan kafan shi cikin wasu budaddun takalma ya sauko zuwa kasa inda ya samu falon cike da yan uwan Nafisa kamar suna shawara.
   Ganin yadda ya fito yasa ta dago kai tana kallon shi ya fito ya samu Yusuf din zaune a saman dan wani dakali yana jiran fitowan shi.
  Ya fito ya fara mai baiyanin komai basuyi aune ba sai ganin Nafisa sukayi a gaban su tana huci ba bata lokaci ta shiga dura ma Yusuf din zagi tana ai banta shi.
  Bai tanka ta ba sai faman kururuwa take masu a kai tana kiran da munafuki dan bakin ciki ko bai so sai ya gansu da  Samad agidan shi.
 Dama tasan duk wani munafuncin da ga wurin shi yake fitowa daga shi har samad din sai ta dauki mataki a kansu.
  Amma dai karki manta bakece Allah ba ko don haka babu wani abin da zaki iya muna sai Allah don in da sabo ya saba da wanan halin na Nafisa.
  Sau da yawa idan sun kwaso rikici da mijin ta a  kanshi take saukewa don tana ganin shine mai zuga shi sai taga ta kamo shi da kyau dan lokaci kadan kuma sai abin ya juye mata.
   Wanda take ganin Yusuf din ne ke mata zagon kasa a hakan sai dai bai nasaran rabata da Yusuf din da yake son yi ko yaushe.
 Da kyat yan uwanta suka samu takoma ciki bayan sun kare masu kallon banza suka shige da ita cikin gida tana ta haure hauren rashin mutunci.
   Washe gari tun da safe ya shirya Yusuf yazo zasu tafi kamar yadda ya saba motoci uku zasuyi tafiyan da shi sai dai wanan karon tafiyan ya canza masu sallo.
  Na farko su kadai ne ba tare da buzuwa ba na biyu kuma tare da a abin arzikin da bai saba tafiya dashi ba zasu dunfari gidan.
   Ana kara gyara kaya kamar daga sama sai ganin ta sukayi a wurin motacin tana ganin kayan ta shiga tonawa har ta gano abinda ke cikin buhuhunan da akayi siling din su din.
  Ranan sun ga masifa haka sukaja mota suka tafi ransu bace da halin da Nafisa ta nuna masu din sun isa a cikin lokaci gari bai je gidan ba sai da ya karasa gidan shi ya huta don sun iso kan shi yana mashi ciwo sosai saboda hayaniyar da baiso.
   Tunda Yusuf ya sauke shi yanufo gidan nasu da abinda suka zo inda sai gani motane keyi anata shiga da kaya a cikin gidan ana jibgeasu a kofan hajiya mama kamar yadda ya umurce shi da yi.
   Sun kasa boye mamakin su anty amarya ce ta fara tambaya anya wanan abin da Nafisa ko aka zo wanan karon dariya Yusuf yayi yace bada ita bace anty muka dai muka zo.
   Mommu tace abin kan da mamaki gaskiya Allah yasa babangida ya canza daga wanan karon dariya Yusuf yayi yace insha Allahu mommy kudai taya mu da addua.
   Ya shiga dakin hajiya mama don ya gai da ita ya samay ta da yan matan ta suna mamakin wanan sayyayan da suka gani haka wai daga gun Abdulsamad ya fito haka ?
    Ya shiga dakin sai da ya zube kasa ya fara gaida ita sai faman murmushi take yi har lokacin ta kasa boye mamakin ta bayan sun gama gaisawa dakin take tambayan shi wanan sauyin yanan Abdul din data gani.
   Yace hajiya adai taya mu da addua kusan kece sillar canzawan nan nashi lokacin fada maki komai baiyi ba amma nan gaba insha Allahu zan sanar dake komai so nake komai ya tafi haka yadda muke so dashi .
  Don yanzu insha Allahu akwai canji sosai wallahi nan dai suka dan taba hira yace Abdulsamad na tafe zamuyi bayananin komai idan ya shigo.
  Duk da zaman lafiyan da akeyi gidan bai hana a kebe gefe ba ana gulman wanan sabon yanayin da aka hango a gare shi.
   Sai dai kowa ya matsu yaga abinda ke cikin buhuhunan wanda ba wanda ya iya gane komau ye a cikin su su indan gaiyan aikin nasu ya shigo.
    Saida suka sauko sallah jumma a ya shiga gidan iyayyen nashi a falon Alhajin su ya fara shiga ya gaida shi da mashi yaya jiki ranan yaga sauyi sosai na sakin fuska a wurin mahaifin nashi wanda ya dade bai gani ba.
  Bayan sun gama da mahaifin nashi ne ya shiga ciki ya fara gaida ummi sai mommy sai anty amarya ya wuce dakin hajiya mama wanda dama kullun itace karshen shiga da yafito kuma sai ya bar gidan.
   Sun gaisa da ita acikin sakin fuska ya dubi Affan dake zaune gefenta yana cin abinci ya kira yaron saboda rashin sabon da basuyi ba dashi ya dago ya kalle shi kawai ya gaida shi.
  Sai baiji dadin yadda yaron yayi mashi ba shiru ya dan biyo dakin take tambayan shi iyali ya amsa da duk sina lafiya hajiya tace dole ita da yan uwanta zamu tambaye ka don sune yanzu iyalin naka.
   Babangida yanzu kana ganin abinda kakeyi kana aikata daidai a rayuwanka mutum ya watsar da iyalin shi ya rugumi wasu bare can.
   Shiru yayi ya dukar da kanshi tace kaima kanka fada kada ka mutu a cikin wanan halin kasan Allah na zai barka ba Yusuf ne yace ayi hakkuri hajiya komai zai zo daidai in Allah ya yarda adai tayamu da addua.
   Nan ya fara mata bayanin kayan da suka zo dashi inda ta fahinci komai yace saura kayan abinci muyi magana ko za a kawo zuwa yamma sai a raba yadda ya kamata.
   Yayi mamakin yadda yaji mahaifiyar tashi tana kwararo mashi addua yau da saka mashi albarka wanda ya dade baiji ba daga gare ta duk zuwan da yake yi da fada sukan kare ya fita rai a bace.
  Yau sai gashi sanadin yarinyar da yake gani mai matsala a gare shi yaja mai samun addua irin haka a gurin mahaifan shi bai fita gidan ba sai da yayi masu alheri yakuma mata alkawari zai je zaria yayi masu taaziyan rashin da akayi can.
  Taji dadin jin hakan sosai na ya fito ya barsu a cikin farin ciki ya koma gidan shi don yana bukatan hutu a lokacin bayan fitar shine hajiya ta kira su mommy tana masu bayani aka shiga bude kayan da ta nuna masu din.
  Kowa yayi mamakin ganin hakan don basu zaci haka ba yanzu a gare shi sai addua suke mashi da fatan gamawa lafiya kowa aka cire mai nasa cikin farin ciki da jin dadi.
   Tunda ya koma wake kwance a dakin shi na gidan ba abinda yake tunane sai irin yadda na fada mai magana mai amfani acikin gatse kuma yayi mai tasiri.
   Yani yace a ranshi lalai ya zama dole in san yadda zan gyara alamarina da yarinyar nan don ita din ba abin yar wa bace .
  Cikin dan lokacin kadan tayi min sanadin dawo min da farin ciki tsakani na da iyayyen har da yan uwa wanda wanan tunanen bai taba zuwa min ba ko wani ya tsayar dani ya fada min gaskiya yadda take fada min kai tsaye.
  Tayi namijin kokari wurin ganin ta tsaya ta fada min maganna irin haka kai tsaye bataji shakka ko nauyin fada min yadda kowa ke shayi na ba.
   Wayan shi aka kira ya daga Faiza ce take mai godiyan abinda aka kawo masu yace babu komai ta kashe kuma Lawisa yar wurin ummi ma ta kirashi tana mashi godiya haka suka dinga kiran shi sai da yagaji ya kashe wayan shi ranan.
   Wani irin farin ciki yake jin kanshi ciki mara misaltuwa da wanan kiran da yan uwan shi suke mai a lokacin don ba zai ce ga ranan da suka kirashi karshe ba.
  Ya zama dole gare shi ya san yadda ya gyara mu,amulan shi da duk wani dan uwa nashi da ya watsar da farko.
   Sai yaji yana sha, awan ya kira layin khadija a lokacin yayi mata godiya haka yasa ya jawo wayan shi ya kira layin ta.
  Ina fitowa cikin makaranta na samu guri na zauna ina jiran maryam tafito mu wuce cikin gidajen mu don an kara muna kwana daya yanzu.
  Kiran shine ya shigo min wanda tun bayan rabuwar mu ranan ban kara ji daga gare ba sai yanzun da ya kirani din na tuna dashi.
  A hasale na dauki wayan ba tare da nayi magana ba don na gane shine jin shiru ya danyi yawa banyan na dauki wayan sai nace
 A hasale nake fadin lafiya ka kirani ko ka kirane ka fada min ka tsane ni din da kake fada min ko yaushe ?.
  Murmushi naji yayi kasa kasa sai ya sake kiran suna full yace khadija a zuciye nace ina jinka ai yace ba wanan kiran nayi maki ba yanzu.
  Nace may ye ka kira malam ni kada ka bata min lokaci haushi ne ya ishe shi a lokacin yana rayawa a ranshi yaya zai yi dani ne wai ?
   Cikin sanyi murya yace min thanks khadija na gode kwarai da taimakon ki gare ni sai dai don Allah, , , , 
   Dama abinda yasa ka kirani ke nan don ka samu wani sabon yaudara ka zageni kuma dashi na fahince ka don haka banda lokacin ka ni yanzu.
   Na fadi a cikin tsigar tsokana tare da saurin kashe wayan sai dai a zahiri jikina yayi sanyi da yadda naju yana maganan cikin wani yanayi.
  Shiko ina kashe wayan yabi wayan da kallo kamar nice wayar ya sauke wani irin ajiyan zuciya yana fadi a fili shi kadai a daki.
  Wanan yarinyar ni yaya zanyi da ita ne wai ta fahince ni yanzu ya girgiza kai yace kina da matsala khadija yarinya haka bata da kwaciyar hankalin fahinta.
   Why why khadija baki so na da kwanciyan hankali a tare dani yanzu ne mikewa yayi daga kwancen da yake ya nufi fridge ya dauko goran ruwa mai sanyi a ciki ya kwankwada tare da wurgi da goran ya fito falon shi.
  Mutane ya samu sunzo gaida shi inda ya bisu da alheri sai yamma lis ya samu suka rage nan ya nufi bathroom din shi don ya dan watsa ma jikin shi ruwa ko zai ji sanyi.
  Dan ruwan dumi ya hada saboda yanayin garin na kaduna ya shige jacuzzi ya dan dauki lokaci yana tunane kafin ya fito ya sa kaya a jikin shi ranan a maslcin uguwan su yayi sallah magariba tare da jamma, an unguwa da mahaifin shi aciki.
   Ba abinda yake tunane sai yadda zai samu mu shirya a tsakanin mu  gashi dan lokaci kadan yarinyar ta shiga zuciyana ta samu wuri a ciki.
   Tunanin yadda zai shawo kaina amma ya kasa samun mafita har wanan lokacin shigowan suraj soja wurin shi yasa ya matan halin da yake ciki don sun dauki lokaci dashi suna fira kafin Yusuf ya shigo mai da abincin da mommy ta girka masu.
  A tare da Suraj da Yusuf   din sukaci abincin suna hira a tsakanin su bayan fitan Suraj ne suka samu kebewa da Yusuf wanda tun bayan zuwan su basu samu zama a tare ba.
  Nan yake kara mai godiyan kokarin da yake mashi inda yake sanar dashi ya kira ni don yai min godiya amma naki fahintar shi Yusuf din yace ya sake kirana zan fahince a hankali.
  Ba laifi yace dashi sun dan dauki lokaci sukayi sallama akan da safe zai shigo su tafi zaria idan sun dawo yana son kuma ya dan je wurare masu muhinmanci a kaduna daya dade bai tafi ba.
  Yusuf na fita ya kira waya maryam ta dauka ta miko min bayan ta dana recieve na dauka da sallama na kara a kunne na.
  Bayan mun gaisa ne yake rokona da in karba wayan abokin shi inji may zai fada min dariya nayi tare da fadin abokin nan naka ne ai sai a solo baida mutunci.
  Yace kada kice haka Khadija  baki fahince shi bane amma abokina mutumin kirki ne wallahi ki bashi dama ku fahinci juna yanzu zai bugo waya godiya yake son yi maki akan taimakon da kikai mashi na bashi shara kuma yabi yaji dadin shawaran ki shine zai maki godiya akai.
   Munyi sallama dashi ranan maryam tazo dakina wai a nan zata kwana saboda exam din da zatayi washegari yana da zafi ita kuma tana son tayi karatu a daren ranan.
  Muna tsaka ga karatu wayana yayi kara na daga tare da karawa a kunne na muryan shi naji yana tambayana har yanzu baki barci bane.
   Karatu mukeyi na bashi amsa yace OK dazun na kiraki in maki godiya kika kashe waya nace  ina busy ne a lokacin.
  Khadija ya kira sunana amsawa nayi ciki ciki yace please ki bani dama in maki godiya akan abinda kikai min shiru nayi na kasa magana.
   Khadija kina jina nace ina jin ka mana sai naji tayi wani kasalalen murmushi yace in tambaye ke zaki ban amsa tsakani da Allah ?
   Nace sosai makuwa idan har na sani may zai sa in boye maka tunda ba rike min baki zakayi ba.
  Ajiyan zuciya naji ya sauke sai can yace may yasa kike son yawan bata min kina son ganin hasalana ni koda ban tashi hasala ba ?
  Kin tsane ni kin ki jini baki kaunar ki ganin a cikin farin ciki why khadija why kika zabi wanan rayuwan a tsakanin mu.
   Shiru nayi na kasa magana nauyin shi da kunyanshine suka kamani a lokaci daya na rasa may zance dashi don yadda yake magana bazakace shi din bane mai izza da jiji da kai.
  Nasan kin san bawai son soyayya ne a tsakanin mu ba amma kuma kika zabi yin haka a gare ni  ki fada min may ke sakina tsana na haka da yawa.
  Dan murmushi nayi tare da fadin yaya Abdulsamad ke nan ni nasan babu dingo soyayya ma a tsakani mu tun farko sanan kuma ni ko in so ka ko da so ka ba abinda zai ragaka dashi duk dayane a wurin ka.
   Ni dama ba kai na tsana halin ka na tsana da matar ka da bata san mutucin yan uwanka ba har hali ku ya juye iri daya da ita.
   A yau in rayuka zai sauya kasan mutucin kan ka dana yan uwanka ka farga ka dawo yadda mahaifan ka suke son ganin ka da yan uwanka ka san darajan su da mutuncin su fiye da kowa.
  Amma ni may zai sa na tsane ka kana a matsayin yayana aiko don mama zan so ka zanyi muamula dakai kamar kowa.
  Don dama ba kinka nayi bani halin ka dai na tsana bani ba kowa ma zai so ya kulla halaka dakai ta yadda baka zata ba.
  Murmushin da naji yayi yasani shiru yace khadija idan nace maki ashiri nake da in caza yanzun zaki yarda koma in ce dake din na canza a sanadiya ki.
  Jin shi kawai nakeyi ta yaya ni zan iya canza mutum kamar Abdulsamad a lokaci daya haka.
   Muryan shi naji yana fadin kina mamaki abinda na fada ne yanzu yace yes ke khadija kin tunatar dani abinda na manta acikin abinda nake dauka shirmay kukeyi ke da Yusuf a lokacin.
  Nace ba abinda mukayi da har zai kawo sauyi gare ka haka da wuri sai dai idan dama Allah ya kaddara tamu din abin zai fito ma.
  Kuma ina mai farin ciki da jin haka idan ya kasance gaskiya ne maganar ka da sai nafi kowa farin cikin haka a duniya.
  Yace to ki fara farin ciki daga yau don ko kin sa iyayyena sun min abinda suka dade basu min ba a yau don haka khadija ban san ta yaya zan gode maki ba da tunatar dani da ki kayi ga abinda na manta hakki na ne yinsa a baya.
  Koda da wasa ko gatse kika fada min wanan magana to ki sani your words inspired me har nakai ga samun kalmar albarka a bakin iyayyena yau abinda na dade baji ba a gun su.
   Yau kin dawo min da farin cikin dana rasa da dadewa a tare dani kalman ki na ranan gare ni sun sa na dawo da natsuwana.
   Ya kuma fara dawo min da respect da power na ga idon mutane dana rasa a baya wa yanda ya kamata ace komai wuya komai dadi ina tare dasu.
  Ba zan iya kwantata maki dadin da naji ba yadda na kasance da yan uwana da abokai kai har ma da makwabta na ayau suna murna da zuwa gare su.
  Don haka yazama dole in gode maki please khadija kada kiki fada min gaskiya a duk lokacin da kika ga na kauce ma hanya.
  Murmushi nayi nace naji dadi kuma na tayaka murnan dawowa farin cikin ka gare ka don ko  yau ranan kace ranan farin cikin ka.
  Ka kuma gode ma Allah da bai sa ranan ya kasance ranan nadamar ka bace ya fargar dakai da wuri haka.
  Allah ya kars shirya zukatan mu ni zan kashe karatu nakeyi ka tsayar dani don gobe zamu gama exam jibi gida zamu.
  Da sauri yace jibi wata rana nace talata inda Allah ya kaimu da safe zan tafi gida don yin hutu a can.
  Yace No kada ki tafi don Allah ranan ki jira in dawo akwai abinda nake son in shirya akan tafiyan ki nace Allah sarki dama ka hutar da kan ka don ni a shirye nake yanzun haka.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
           SEENABU
A zoto na shika dai ne a cikin motar sai da na isa kusa ne naga sabanin haka ashe tare suke da dan baiwa yana zaune kamar kullun ya aza Laptop a cinyar shi yana dubawa.
   A sanyaye nake nace dasu sannu ku da zuwa yaya hanya yaya mutanen gida kun barsu lafiya ?
   Yusuf yace ke ce African ta gidi khadija tambaya haka a jere lokaci guda wani zamu fara amsa maki daga cikin wanda kika jero muna a lokaci daya ?
   Nace amsa daya ya wadata gareni wanda nake fatan alheri a cikin shi yace to duka amsan ki alheri ne don duk Alhamdullahi gaba daya kowa na lafiya kuma hanya lafiya.
  Murmushi nayi sai yace baki gaisa da oga na ba kuma aboki na dan satan kallon shi nayi nace ai bugu daya nayi maku gaba daya nashi gaisuwan daban ne kuma ?
   Yace oga ne fa khadija kema kin sani ai dole gaisuwan manya ya zama daban da na saura nace a wurin ka yake daban don kace shi din ogan ka ne amma ni a wuri na duk daya kuke gare ni.
   Eh to kya iya fadin haka yanzu amma dai nasan nan gaba bazaki fadi hakan ba dariya nayi nace saboda may kana ganin zanyi aiki a karkashin shi ne ko may , ?
   In wanan kake tunane may zai kai lawya aiki a FCDI kuma sai in dai bukatan haka yataso mu a bukace mu a wurin muyi aikin mu mu bar wurin.
   A a a ashe da babban lauya muke bamu sani ba haka nace cikin murmushi lawyer to be insha Allah ba ya juya gare shi yace kai kaji ashe da Barister muke bamu sani ba shike nan yanzu muyi abin mu ba kwabo muna da mai kare mu.
  Nace wa ni ai nice ma zan tsaya sai na kama masu cinye ma gwaunati kudin filayen ta in daure mutum inga tsiyan kwashe kudi ana tura ma yan Niger suna cinyewa dama yan Nigeria kuke ba sai in maku sausaci a kai.
  Sai lokacin ya dan sake murmushi yace ashe har kin fara hada evendece a kaina ban sani ba nace tun yaushe na fara hadawa zan tura babban kotun mu.
  Dariya sukayi sosai gaba dayan su yace dama karatun da kike yi ke nan ashe nace kwarai don kama manyan bariyin gwaunati ba.
   Yace ashe aiki ya ganki magana yake ba tare da ya dago kai ya kalle ni ba sai dakilan laptop da yake yi hankali kwance da gani abin ya zama mai jiki hakan.
   Yusuf yace wai kin san ban taba sanin abinda kike karantawa bs ke nan sai yanzu na dan natsu nace shi nake karantawa ai Allah ya bada saa yace nace amin nagode.
  Still bai dago kai ba yace wace zata kama ka kakewa addua haka kuma yace ai addua ya zama dole muyi mata shi fadi take yi kawai mutum ya taba kama kanshi da laifi ne.
    To wai ni fa kun barni a cikin duhu yakamata ace yanzu ina gida kun tsayar dani a nan aikin oga ne haka khadija bai son ki bar garin nan yanzu ne yasa ya tsayar dake.
   Kallon shi nayi sai faman aikin shi yake yi hankali a kwance bai dago ya kalle mu ba nace  ni ai ba yar Niger bane da yake tarawa a gidan shi kamar almajirai.
   Dama titi yake bi yana ba mabukata alheri da zai fi samun lada ga Allah da wanan ciyar da mayaudaran dayake yi zai fi mai Alheri sosai.
   Rufe Laptop yayi tare da fadin wai ke maye matsalan ki da yan Niger ne cikin rashin sani nayi subul da baka nace kishi mana lokaci daya suka ce kishi nace wallahi.
 Murmushi naga yayi yana lumshe ido Yusuf ko sai kallo na yake yana dariya shi ya bude idon shi yace kishi yana jijiga kai nace na kasata ba .
  Sun zo suna kwashe muna dukiya suna raya kasan su da sunan aure nan ko barayi ne na zaune Yusuf yace a a kada ki gyara zancen kuma mana khadija yar mama.
   Nace a in ba kishin kasata ba kishin may zanyi kuma Yusuf yace gashi a gaban ki kishin dai kike yi amma kada ki gyara kice kuma wai kasan ki.
  Ikon Allah akan may zanyi kishin shi shi mijina ne ko wani nawa ba hadin kifi da kaska ai Yusuf yace waye kifin waye kasa yanzu.
   Yace itace kaskan mana nine kifin ba ita ta lake min ba kana gani kuwa ido na waro waje nace ni din yace Yes kamar zanyi magana sai kuma na kalle su tare da fadin sai anjiman ku.
   Ina juyawa da sauri Yusuf yake kirana ban tsaya ba ya fito daga motan ya sha gabana shiko yana ciki sai murmushi yake ba abinda ke mai yawo a rai sai kallaman kishin da nace.
   Ya samu na tsaya yace ke ko daga wasa zaki mai da abin wani magana nace ina nuna shi bakiji may ya fada min bane yanzu wai ina like mai.
   Yace ai wasa ne ko shima yasan baki like mai shiyasa ya juye maganan yace ke ce mai like mai yanzun bamu muka zo wuri ki ba wake nan kaskan a cikin mu ?
   Bude motar yayi ya fito yana mika tare da nufo inda muke tsaye yana fadin wai may kaskan nan take fadi ne haka ka tsaya wani bata magana can.
   Yusuf yace kin gani ba har ya kai ga fitowa a mota don ki yace ai ita ma ta fito don ni ko,  kallon shi nayi na kauda kai na gefe daya.
   Ya karasa takowa zuwa inda nake yace wai yaushe ne zaki tafi in samu in huta da wanan matsalar taki.
  Nace nice yar matsalar yace gashi ko kina muns ko yanzu kai na girgiza kawai nace ba komai baka da laifi fito war maryam ya tsayar damu daga maganan .
  Ta fito tana gaishe tare da masu yaya hanya da mutanen gida yusuf yace suna gaida ku tace kuna nan da miss barister ne yace wallahi kuwa kauna a kwai rigima ai.
  Tace da kyat na shawo kan ta ta tsaya da yanzu tana gida baku samay ta ba Yusuf yace kin kyauta shi dai tunda ta fito bai mata magana ba ko gaisuwan da tayi bai karba ta ba sai ma daure fuska da ya kara yi yanzu.
  Yaushe ne zata wuce Yusuf ya tambayi maryam tace bataki ko yanzu wanan ta bar gari ba ta isa da dare da sauri shi yayi magana da fadin No bako a cikin daren nan ba kan gaskiya.
  Nace may ye a hanya da zaka ce ba da daren nan ba zan isa ko lafiya yace No sai gobe za a zo a kai ki har gida.
   Nace a a kada ku wahal da kan ku motar kasuwa 
nake shiga yanzun ma shi zan bi in Allah ya yarda bani kadai ba kowa dake wurin yayi mamakin maganan shi da yace.
  Ba zan yardan ba ki bi motar haya ke kadai idan wani abu yaje ya samay ki fa a hanya ki sani a wani hali don haka ki shirya gobe zan turo malam sani ya kaiki gida da safe.
  Ido gaba dayan mu muka tsura mashi da yake maganan kamar wani uba da yar shi ko miji da matar shi yadda ya hakikance yana fada a hasale dani.
  Zan yi magana Yusuf yace ya gama yanke hukunci akai Allah ya kai mu gobe din ai yau da gobe duk na Allah ne ko amma ki bi motar haya wani abu yaje ya samar mashi ke a hanya kuma ?
   Maryam ne tayi dariya nikan hararan shi nayi mai dani gida yace a dake Yusuf yace to bissimillah muje in sauke ka ko ya juya ya fara tafiya ba tare da yayi magana ba kuma.
    Sai Yusuf ne ya tsaya yana ce muna yar mama ni zan tafi ban sani ba ko zamu sake haduwa ga wanan ayi ma kanne tsara ba dashi ya mika ma maryam sai kuma ya sake ciro wasu yana miko min wai na karba.
  Kai na girgiza mai nace daka barshi don ni ina da kudin mota a hannu na tsaraba kuma ai kowa yasan makaran ta naje basu expecting din tsaraba a wuri na.
  Yace daga wanan time din sai ki fara masu tsaraba baki san tsaraba ko ga babba yana da muhinmanci ba ne mutuka kauna na.
  Dole ya mika min na karba tare da mashi godiya har dan Baiwa ya fara mashi horn a mota yace Allah sada mu da alherin sa nace amin yaya Yusuf ya juya ya tafi sai da suka shige muka koma ciki.
    Maryam bata shigo daki ba don haka ni kadai na shiga na adana kudin tare da cire rigar da nasaka a jikina.
  Can ta shigo ta hada muna abinda zamu ci ina kwance a wurin tunane ya addabe ni a raina har ta gama tace inzo muci don na idar da sallah a lokaci.
  Sai da muka zauna cin abincin ne muka fara hira da ita take tuna min maganan shi da yayi dazun tare da fadin guy din ya hadu wallahi
  Daure fuska nayi nace a naki ganin kike ganin haka amma ni mai zaisa in sawa raina abinda nasan ba mai yuyuwa bane gare ni ai ko a mafalki wallahi.
  Ko dai baki san ko shi waye bane yasa kike wanan magana haka shima dai Yusuf ai yanayi ne don wasa kawai amma ba gaskiya bane so kima daina wanan zancen don Allah.
   Wayana dake gefe ne yayi kara ban gani don wayan a silent take lokacin sai maryam ne ta gani take ce kamar kiran ki ake a waya fa sai nayi saurin juya don in duba.
  Tashi nayi na dauko wayan mai kiranane yaban mamaki tunda basu dade da barin wuri na ba, daukan wayan nayi na kara a kunne na da sallama yace fito gani waje.
   Da mamaki nabi wayan da kallo muryan shi naji yana fadin kin ji abinda nace nace eh maryam na kalla da ta tsareni da idanuwan ta nace a sanyaya wai shine a waje .
   Ta kwashe da wanin irin dariya bance da ita kala ba komai ba na zura rigana na fita zuwa jin may ya kawo shi kuma.
   Ina fita na hango motan shi dan nisa kadan damu na karasa wurin na samu ya fito da kafa daya a waje yana duba abu a cikin motar na iso wurin.
   Ina wuni ya dan juyo ya kalle ni yace zagaya ki shiga dan jin nayi bai zagaya ba kamar yadda ya umurce ni dayi ya sake dagowa bayan ya rufe cabinet din motar yana fadin baki ba ne dole na zagaya kamar yadda ya umurce ni din dayi.
   Bayan na shiga naga ya tayar da motar ya bar gurin down hostel din ya halba motan muka hau expresse ba wanda yayi magana a motan sai dai gaba na yana dan fadi don ban san ina muka nufa dashi ba.
   Mun dan yi nisa da gurin ya juyo ya kalle ni yana fadin maman ki ita kadai ne a gurin mahaifin ki ?
   Mamakin tambayan nashi nayi sai ban iya bashi amsa ba na kawar da kaina gefe yace ina magana kin kyale ni nace akan may zakai mun wanan tambayan haka.
   Yace don na isa na tambaya yasa na tambaye ki OK idan kana son sani sai kaje ka gani da idon ka ai.
   Kan nen ki nawane dariya tambayan ya bani sosai nace yau ni naga ikon Allah to kannen na biyar ne na bashi amsa tare da kawar da kaina.
   Ok kawai yace mukaci gaba da tafiya sai wani katon Plaza muka tsaya ya juyo yana fadin bissimillah fito mu shiga yace.
  Ban ki ba na fito muka shiga shagon sai faman gaida shi masu shagon keyi layin kayan sawa muka nufa yana gaba ina bayan shi.
   Abin ya ban mamaki yadda naga yana jidan kaya a wurin ya ban mamaki ya koma layin kayan yara sai lokacin ya juyo ya tambaye ni shekarun su nawa ne kallon shi nayi nace a kwai sha uku da sha daya sai takwas da shidda mutum biyu.
   Maza da mata ne ya kara tambaya nace maza uku mata biyu sai yaran yaya na biyu yan she kara takwas da shidda maza.
   Bayan mun gama wurin takalma muka nufa muka zaba sai layin zanuwa nan ya zaba da dama ya zaba sai ya duba kudi ya gani yake daukan mafi tsada a wurin.
   Ya sa yaron shagon ya tura yakai yace a samu trolley masu kyau a saka mai kayan a ciki muka bar shagon hanyar down hostel muka nufa sai lokacin hankalina ya kwanta.
   Bayan ya tsaya da motar nayi kokarin budewa naji ta a rufe gam na juyo na dan kalle shi naga shima ni yake kallo a lokacin sai na kawar da kaina gefe daga kallon shi.
   Ina son in maki godiya amma kin kasa tsaya ki bani daman yin hakan gare ki nace godiya akan may fa ?
   Au baki ma san abinda kikayi ba ke nan nace ban sani ba sai ka fada min iska ya dan furzu daga bakin shi yace OK you can go zamuyi waya idan kin isa ki gaida gida na gode kawai nace na fita.
  Banji yace dauki kayan ko wani abu ba nikan na shige abina ina fadin dan rainin wayo kawai dama sayayya zan rakashi shine yake min tambayan bazan a hanya.
   Har yasa gaba na faduwa ina zan kai wanan uban kayan danaga ya jida a shagon sai yanzu hankalina ya kwanta.
   Koda takwas na safe yayi mun gama shirya komai muna zaman jiran su sai na tafi maryam tace zata wuce itama takwas da wani abu ya bugo min yana fafin in fito da kayana ga mota a waje ana jirana.
   Fitowa nayi da kayan maryam ce mai karasa min su a wurin motar har aka gama na rufo kofana na saka key din a jakka ta mukai sallama tace za a zo yanzu a dauke ta ta buga waya gida itama.
   Driver ya bude min baya na shiga muka dauki hanyan minna shigan wuri zan ma minna wanan karon ba yadda na saba ba da dare nake shiga garin.
   Tunda muka kama hanya barci ya dauke don sanyin motar da lafiyar ta sai faman gudu driver ke shararawa dani ina barci na hankali kwance.
  Barci nayi sosai driver naji ya tsaya a wani gari na bude ido fita naga yayi zuwa gun masu sai da manja da doya a hanya ya saya aka loda mashi a motar muka kama hanya kuma.
   Tun ina duban waya sai na koma barci abina muryan driver ne ya tayar dani yana fadin hajiya wani unguwa zamu je na bude ido ina kallo har mun isa deport din mai zamu shiga cancaga .
   Nace a cikin gari kwagila road, zaka kaini yace ban san wurin ba don ni bakon garin ne nace OK mushiga sai in nuna maka.
   Miko min envelop yayi yace oga yace idan mun iso in baki wanan sako wai sai kin shiga gida ki bude nace OK
   Mun wuto ina mashi kwatance har kofan gidan mu motar ya tsaya duk da rana ne kowa na zirga zirgan gaban shi nai hana masu zama layin namu zama suna ganin motar ya tsaya kofan mu suka sako ido caa suga waye a motar yazo gidan mu.
  Driver ya fito ya bude min motar na fito can naji wani classmates dina na primary yana fadin yau Khadija ce a garin namu.
   Murmushi nayi mai nace Faisal mun samay ku lafiya ya karaso muna gaisawa dashi na shiga yace bari ya taimaka min da saka kaya a gida.
   Da sallama na shiga inda kanne na dake daki suka fito da gudu taro na suna ihu na rungumay su tsayawa nayi ina kallon kayan da su Fesal ke shigowa dashi gidan namu.
  Na kasa furta komai mama ma kallon kayan take da mamaki yaran suka fita sai gasu suna shigowa da ba adadi nace wai duk mu muka zo da wanan kayan haka wai ?
   Mama tace waya zo dashi in ba ke ba bagashi kin ga ana shigo dasu ba tare da kayan ki ko kina nufin baki san da su bane wai ?
  Wallahi mama ban sani ba sai yanzu nima nake ganin su anan kamar kowa yadda ya gansu mama ta katse nu da cewa motar wa kika shigo ne naji yara na fadin kin zo a mota mai kyau.
  Shiru nayi na dukar da kaina ba tare da magana ba har suka gama shigo da kayan mama tace ku dauki ruwa kusa a plate kukai ma mai motar kafin ya tafi.
  Yaran suka ruga da gudu suka dauki ruwan leda suka sa a plate suka fita dashi waje kamar yadda mama tace dasu ta wuce tabar ni tsaye a gurin.
   Dakina na nufa tare da dan hand bag dina dake rike a hannu na rai na babu dadi ko kadan a tare dani ina fadin yaya wanan mutumin zai min haka ya hadani fada da iyayyena su fara zargina.
   Anty khadija wai yace a fada maki zai wuce nace ya kice Allah ya kaishi lafiya nace a hasale yaron ya fita da gudu daga dakin zuwa fada mashi.
  Daddy ya shigo gida yana fadin ance baby na ta dawo sai kuma yaja ya tsaya yana kallon kayan da mamaki dake zube a tsakar gida.
  Mama tace kai nake jira dama kazo ka gani ko zata fada ma inda kaya ya fito haka don wai ita ma bata sani ba tace kuma su sukazo da kayan.
   A sanyayye na dago labule dakin na fito ina fadin daddy sannu da dawo wa mun samay ku lafiya ?
 Lafiya baby na sai dai wanan kayan kuma fa ina suka fito haka nace wallahi daddy ban san da su ba sai da muka iso na gansu.
 Kamar yaya bakin san dasu ba bake kika zo dasu ba sai nayi kasa da kaina ban yi magana ba kuma kayan yake bi da kallo tiryan tiryan yace ikon Allah.
  Shiga ciki ki huta zamuyi magana anji yanzu zan tafi inyi sallah ne ya wuce gurin da buta yake yana dauka ni kuma na sake labule na koma ciki jiki a sanyayye.
  Na fada saman gadon dakin duk da kuran da yake ciki don ba gyara ake ba a kai akai tunda ba kowa a cikin sa ina zaune kamal kanina ya dawo shiya fara shigo min da kaya yana min sannu da zuwa.
  A dadafe na amsa mai ina kallon akwatinan daya shigo min dasu akwatunan da muka sayo a daren jiya ne dashi inba idona ke min gizo ba.
  Watau kayan de na yan gidan mu ne kenan ba wasu ya saya wa ba mikewa nayi don in yo alwala ina shiga banda ki sai na samu ai period dina yazo min ba daman inyi sallah ke nan haka na fito jiki a sabule na aje butan.
   Sai mama ta aiko da abinci a kawo min ban kali abincin ba nace kaunata ta aje min a nan kawai ina jiran dawowan daddy daga wurin sallah.
   Envelop din da driver yaban na tuna dashi na dauko a cikin jakata na bude a hankali kudine a ciki sabbi ful din su anyi rubutu kamar haka a wrafer farko daddy sai na biyun mama.
  Na ukun ne bai rubuta komai ba na shiga uku nace tare da yin nadama da haduwa da shi karo na farko a rayuwana don ban san yadda daddy da mama zasu fahince ni ba.
  Nayi dana sanin tsaya jiran shi da yace inyi har na tsaya din sam ban kawo komai a raina ba irin haka don ban taba zaton hakan ba dayayi min.
   Muryan daddy daya shigo naji ana gaida shi yasa ni kaduwa bai min magana ba har yaci abincin shi ya fita haka na tashi na gyara dakin tsab na fita da na wankewa na wanke a ranan.
  Na dawo na sa kamshi a dakin tare da gyara komai a yadda nake bukatan shi a dakin na koma na zauna wayan maryam ne ya shigo tana tambayana yaya muka isa ?
   Nace wai kin san abinda mutumin nan yayi mun kuwa maryam nan dai na koro mata labarin abinda ya faru bayan isowar mu gida da driver.
  Tace ikon Allah sakayyan da yai maki ke nan ashe kai lallai mutumin nan yaci sunan sa dan Baiwa ne shi din.
  Nace ke maryam har kin samu bakin yabashi ko may may kike son in fada ma iyayyena yanzu don Allah wa zance yake gare ni da yai min wanan kyauta haka.
  Tace ki fada masu gaskiya taimakon shi kikayi ya saka maki da alheri haka nace ban sin su san ko shi waye tundai Ya Amina .
  Dariya tayi tace komai dadewa ai zata sani ne nace amma fa ba yanzu ba koda zata sani din don ban son ta fasara ni da wata manufa.
   Har dai dare banji daddy yayi min magana ba haka yasa na dan sake jiki naji shigowan daddy gidan sai na sha jini  jikina a daki ban fito yadda na saba muyi hira ba dashi.
  Ina nan kwance wayana yayi kara na dauka kamar yadda na rubuta a sunan shi dan Baiwa shi ya baiyana a wayan.
  Kamar ba zan dauka ba dai na daga maimakon inyi magana sai na kama kuka nace may yasa zakai min haka don Allah ?
  May kake son in fada ma iyayyena yanzu a kan kayan nan yace daddy na gida nace yana nan yace dama shina ke son magana dashi na kira ki yanzu.
  Da sauri nace may zaka fada ma daddy din yace gaisawa nake son muyi dasu in masu bayanin kayan ba shike nan ba.
  Yasir na kira nace ya kaiwa daddy waya ana magana dashi ban san yadda sukayi ba a wayan har mama naji suna gaisawa da ita.


ZAINAB IDRIS MAKAWA 
            SEENABU
Washe gari muka shirya zuwa beji duba wani kakan mu dake zaune acan kanin mahaifin maman mu ni da ya Amina da yaran su.
   Bayan Nkwa bamu iya wani gaisuwan kirki ba sai habalu da sauran kananin kalma irin na gwarawa da muka rike a bakin mu.
   Tsohon yaji dadin ganin mu yana ta murna da zuwan mu gidan duba su anan muka wuni tare da su sai yamma muke son mu dawo mu biya maikunkele gidan iyayyen mama din.
   Tsohon bagwaren yana waje zaune da bakon shi muka fito zamu wuce muna masu sallama bakon nashi ne yayi yare sai naga tsoho yayi dariya tare da fadin yaki nan amarya na.
  Nazo na duka a gaban shi yace bako na ne ke son ganin ki sai na gaida dattijo ya mika min hannu alaman in bashi nawa hannun.
  Ban ki ba nayi kamar yadda yace min sai da ya kalli tafin hannu na da kyau yayi murmushi yace Allahu akabar akwai tarin alheri ga wanan hannun naki sosai zan ba kaka ku wani abu ya baki gobe  ba mai wuya bane abin inda zaku tsaya na awa daya zan iya hada maki ko anan ma.
  Don tsari juyawa nayi na kalli ya Amina tace ai zamu iya tsayawa mu karba nan saman tabarman muka zauna ya bude jakkar shi ya ciro wani dan farin abu a wani kwanko yayi ta abinda zaiyi a abin sai ya miko min hannu na mika mashi nawa.
  Ya fara murza min abin a tsakiyar tafin hannu na har saida abin ya bace bat a hannu na ya dan dade rike da hannu na yana min tofi har kaina sai daya dafa yayi min yadda yayi a hannun ya sake ni dama tsamin jikin shi duk ya isheni sosai.
   Ya Amina ma tace aiwa yaranta da ita ba irin wanda yayi min yayi mata ba zamu tafi na bude jakka na fido dubu daya na bashi ya girgiza kai.
   Yace idan ina da dari biyu in bashi kawai yaci goro dashi na duba naga wani sabon dari biyo na dauko na bashi nayi mai godiya muka tafi.
  Muna cikin mota ya Amina tace na rasa may sa tun kina karama idan mun fita ke kawai mutane ke taimakawa wanan karo na biyu ke nan da haka ya faru dake.
  Nace su suka san abinda idon su ke gani a kaina wanda mu bamu gani hakan dariya tayi tace kila ya hango maki buzuwan ku ne .
   Kai ya Amina may yasa kuke fadar haka ne karfa maganan nan yakai kunnen su mommy da yan gidan su fa.
  Tace indan ya kama suji ai ji zasuyi khadija lokacin jin su ne baiyi ba kawai amma duk wanda yaji mamaki zai yi wallahi.
  Sai dare muka isa gida don mun bata lokaci a maikunkele wurin yan uwa da abokan aarziki ko da muka dawo wanka kawai nayi na samu wuri na kwanta abina.
   Da safe muka tashi da labarin haihuwan antyn mu Anty Hauwa dake aure a pilamigo easther wanka mukayi muka nufi gidan ta acan muka wuni sai four muka baro gidan ta.
   Koda muka dawo gida mama tana dora girkin dare sakwara zatai muna da miyan egushi tubewa nayi na fara taya mama aikin dakan sakwara don doyan ya dahu ko.
  Ya Amina data fito dakin ta tsaya tana kallon yadda nake dakan sakwaran ta kwashe da dariya tace ashe kin iya idan nace muyi sai kice bakya son ci.
  Sallaman da muka jiyo a kofan shigowa gidan mu ya hana ni bata amsa naci gaba da dakan sakwarana.
  Anty Amina ce ta dan leka raga mai sallaman sukai kicibis da Yusuf a tsaye yana gyara rigar shi da ya dan takure ga zaman mota.
  Kamar daga sama ta san shi a gidan su mommy shine dai bai santa ba tace cikin mamaki Yusuf kune tafe haka da yamman nan ?
  Yayi mamakin sanin shi da tayi haka shi bai santa ba sai dai ya gane muna da kama da ita sosai sai dai tsayin da nafita da kuma hasken fata don ni daddy na fadin gidan mu na debo sosai ina da zubin fulanin su na ka,aje ne.
   Ta juya tana fadin barin sanar da Khadija gata can yau sakwara take daka muna a gidan yayi dariya ta wuce ciki ina ganin ta shigo tana dariya ina rike da tabarya mama na duke tana saka wanda na daka a leda tace khadija ga ki da baki fa a kofan gida.
  Da sauri nace da ita su waye ya Amina tace wa kike tsamani zai zo maki yanzu banda su Yusuf da abokin shi nace kai haba dai ya Amina may zai kawo su nan in ba gulma ba.
   Tace to gulman ko ya kawo su gasu can a waje dai nace wai da gaske tace ina wasan haka dake ne dama tabarya na aje ina fadin yau na shiga uku.
   May suka zo yi yanzu kuma don Allah tace kyaji idan kin fita ai ni wallahi sai naci masu mutunci don may kuma zasu biyo ni har gida haka ?
   Harara mama ta watsa min tace idan zaki natsu ki natsu kije ki gan su falo ya Amina ta shiga ta fara gyara wurin inda zasu zauna ko kafin in fita na samay su da daddy suna gaisawa a waje na juyo na dawo ciki abina.
   Har ciki daddy ya shigo dasu ina labe a dakin mu ina kallon su sai da suka shiga sun dade ciki da daddy da ya Amina kafin ta fito ta kwala min kira ban fito ba ta samay ni a dakin tana dariya.
  Ya Amina may wanan mutumin ke nufi da nine wai for god sake may ya kawo su har gidan mu ne don bata min suna.
   Kallona tayi da mamaki tace  zuwa gidan ku shine barnan suna khadija ai gara da suka zo zai fi hankali mama ya kwanta.
  Ni kan na shige su wallahi tace don Allah ki natsu kije ku gaisa sunce hanya ne ya biyo dasu nan suka ratso su gan mu.
   Ina shiga na samu har da abinci aka aje masuz sai hira Yusuf keyi da daddyn mu shiko sarkin miskilanci ido kawai ya zuba ma kofan shigowa falo.
  Da sallama nashiga tare da samun wuri gefe na zube gwaiwa na a kasa ina gaida su Yusuf ne ya amsa min shiko ido kawai ya zuba min kamar yadda na samay shi zaune.
   Daddy ya fita falon yana cewa dasu yana zuwa ya fita daga falon bayan fitan daddy ban daga a yadda nake na dago ina kallon su nace may ya kawo ku may kuka zo yi gidan mu ?
  Baiyi magana ba sai bude kula  abincin yayi yana kallon sakwaran tare da fadin ke kika yi wanan abincin wai ?
   Yaya akayi suka san haka nake tambaya kaina a zuciyana Yusuf ma budan abincin yake yana faadin yar mama ashe kin iya girki ne haka ?
   Yayana may kuka zo yi nan yace gashi kinga munayi kawai dai mun yi marmarin cin girkin gidan ku ne mukazo muci dan harara na aika masu.
   Abdulsamad din ne yace kina ganin zaki iya kashe min waya don kada na kiraki da sauri nace ni ba kashe ma waya nayi ba.
  May yasa baki kuna wayan naki ya tambaya cikin kura min idanuwan shi dake ban tsoro yanzu nace wayar ce bata da lafiya.
 Baiyi magana ba ya fara cin abincin ba ko kunya hankali a kwace nace baku da kunya ne zaku ci a binci a gidan mu ku wai wasu irin mutane wai ?
  Ruwan abincin gidan ku zaki muna ya fada nace ni naci na gidan ku ne to yace wayasan iyaka wallahi ban taba shan ko ruwan gidan ku ba ni.
  Yusuf yace saboda may yar mama yana kai lomar sakwara a bakin shi kunya su nake ji ban iya shan ko ruwa a gidan don nauyi.
   Ashe ko kin cuci kan ki don ni dai a sani na gidan mu bako bai shiga ba a tare shi da abin sha ko na ci ba daddy ya kwala min kira daga cikin gida na mike na fita da sauri ya daga kai ya bini baya na da kallo.
 Saurin kawar da kanshi yayi yana cin abincin da yaji dasin dan danon shi har cikin ranshi ina fita naga baba da leda ya sawo drinks.
 Yace in kai wa baki a falo a tire na saka nakai na dire masu a gaban su nace gashi kun sa baba kashin kudi bai shirya ba.
   Murmushi magana na yadan yi sun ci abincin sosai suka wanke hannu na fita da kayan bayan sun gama ne suka ce inyi masu iso su gaida mama zasu tafi.
   Fita nayi na kira ya Amina ina fada masu abinda suka ce man ita ta fada ma mama zasu shigo su gaida da ta nan mama ta gyagyara suka a kofan daki aka shimfida masu tabarma suka zauna.
  Bayan fitar sune na samay su a waje har sun shiga mota ina isowa Yusuf ya miko min waya kallon wayan nayi ina tambayan shi ta may yace ogana yace a baki tunda naki ta lalace kiyi maneji da wanan kafin ki dawo Abuja a sai maki wani.
  Amma don Allah kada ki kara kashe muna waya mu kira bamu samay ki ba ran mu baya dadi rashin jin ki da bama yi a koda yaushe.
   Kai na girgiza tare da fadin kubar wayan ku ni wayata lafiya take kashewa nayi kawai don, , , 
   Ban karasa ba naji yace don kada kiji muryan mu ko may khadija nace kawai abubuwa ne sukai min yawa a nan bata waya nakeyi ba.
   Yaushe zaki dawo school don hutu ya kara nake gani nace sai anyi sunar yayan mu data haihu zan dawo uffer week may zaki zauna yi har uffer week Abdulsamad ya tambaya.
  Ba a gida nake ba tare da iyayyena na bashi amsa da hakan yace ranan tuesday zan turo a dauke ki yana fadin haka ya rufo kofan motar Yusuf yayi min sallama tare da kara mika min wayan suka tafi.
  Azato sun tafi ne sai ga yara suna shigo da drinks da wasu abubuwa a kwali wai i  ji su ina daki ina kallon wayan daya ba babban wayace mai tsada fara kwal da ita.
   Ya Amina ne ta shigo dakin tana kallo na tare da fadin wai shi baya gajiya da wanan daiwaniyar da yake haka ne kuma kin ce ba soyayya kuke dashi ba.
  Wayan da ya bani ne na miko mata ta karba tana fadin ta maye wanan kuma nace shiya bani do  kawai nace tawa ta samu matsala ne yasa basu samu na .
  Abin nayi ne ashe yanzu a ka fara wasan da ba ansan maci tuwo ba sai miya ta kare nace ba wani wasan da aka fara indai nice da na koma zan kakabe shi in huta da  zancen su gaba daya.
  Tace ai wanan da alama kin samu kaska baya kakabuwa wasan dadi don ko ya fiki dabara yanzu gashi ya gama daure ki a gurin daddy da mama ko.
  No way to exscape daga tarkon shi a kwai game da na sani kan nan gaba din ba karamin aiki kika banbaro muna ba yarinya.
   Kai ke ya Amina ke kekara ma abin wuta wallahi ni may zanyi da mijin da wata ke juyawa a gidan shi kina so in shiga nima in koma yar bi ce kamar fati ?
   Ke zaki tsayane ki zauna kamar ita a wirin shi ta kai zaune tana fadin da farko ina tsoron abinda ke shirin faruwa tsakanin ku da shi.
  Amma yanzu zuwa na gida da daddy ya wayar min dakai sai hankali na ya kwanta da zance nake ganin kece haske da zai yaye duhun da Abdulsamad din ya shiga.
   Ya Amina ki bar wanan magana kimun fatan alheri a rayuwana ba irin wanan fatan ba na shiga wurin da fitina ta nuna kan ta a fili.
   Khadija kin taba ji ko ganin Abdulsamad ya taba bata lokacin shi ga wata mace irin haka amma sai gashi a kanki abubuwa na ta shirin faruwa a tsakanin ku.
  Na tabbatar da su hajiya mama zasuyi fari ciki da jin wanan labarin don wata kila adduan su ne ya fada kan ki.
  Shiru nayi ina sauraren ta tace abu daya zuwa biyu ne na farko gaba dayan mu sai mu dage da addua gaba dayan mu na biyu kuma kiyi kokari ki cusa mashi so da kaunar ki ta yadda buzuwa ba zata iya mashi gibi ba.
   Har muka gama magana ta fita ban iya cewa komai ba ta barni ina cike da tunane a raina na yadda abubuwa ke zo min a haka.
   
Sai dare sosai suka shiga Abuja inda Yusuf ya aje shi gida ya nufi nashi gidan da motar shi da ya bari gidan don tafiya da ba shiri sukayi.
   Ko da yashigo gidan shiru yaji kamar yau mutanen gidan nashi basu ciki bai tsaya falon ba ya haura sama inda dakunan kwanan su yake. 
   Ga kaya nan ko ina a warwatse ko ina agidan anyi amfani dasu an kasa kawar dasu don tsabagen kiuya da lalaci har ya kai kofan dakin ya tura a hankali ya shiga.
  Baiyi mamakin ganin ta a yanayin da ya samay ta ba don duk kwanankin nan a yamutse take a gidan ba wani gyara ko kwaliya da take samun yi .
   Tana zaune saman gado gashin kanta a wawatse ba gyara ta dago ido ta kalle shi tare da kallon agogon bangon dake dakin tace Samad ina kafito a wanan lokacin.
  Aikena kikayi da kike tambayana ya bata amsa tare da wuce wa wurin wardrobe din shi yana rage kayan jikin shi.
  Samad neman mata kafara ko mai yace idan na nemay su ba namiji nake ba wallahi baka isa ba ta fadi da karfi ya juyo gare ta yace ban isa ba fa ki ka ce Nafisa.
  Tace baka isa ba wallahi may na rage ka dashi a wanda ban baka da har zaka lakanci neman mata a yanzu daga sama.
  Ya ciro wani dogon jallabiya baka yana fadin waya san iyaka Nafisa baki san komai ba banda son kan ki da kashin kudi abaki kuma baki godiya.
   Kudi dole ne ka bani don kasan sune buri na kuma akwaisu bathroom ya shiga ya barta ta ta fadin bakaken maganganu gare shi har ya fito bata fasa magana ba.
  Gadon ya duba yace duba don Allah wai a inda mutum zai kwanta ke nan ya fara kakabe shimfidar da wani dan karamin towel daya fito dashi daga ban dakin.
   Yace mace sai tarin kazanta na fada maki bani son wanan kazantar taki amma ke abin sai gaba yake yi gare ki.
   Ai kasan a haka nake kuma ka aure ni na dauka idan kin shigo cikin daula zaki canza ne ashe ni ban san abin a jinin ki yake ba.
  Kazantar ne a jina na yake Samad yace in ba ajiin ki yake ba za a ce duk yawan ku baku iya gyaran wuri tace samad wa kake so  in sa aiki a cikin gidan nan.
  Kafa san daga kanne na sai yayyena anan sai kuma kawu naina da gwago na yace may yasa kika boye min hakan da farko kin fada min yan aiki ne kika samo min kuma biyan su nake duk wata.
   Sai yanzu zaki ce min wai yan uwan ki ne na jini baki iya saka su aiki a gidan nan kin zo gidan nan kin samu masu aiki kika ce baki yarda dasu ba.
  Na baki go ahead da zaki kawo wanda kika yarda su suyi mana aiki ashe ke yaudarana kikayi ki kwaso yan uwanki kika cika min gida dasu.
  Samad ta fada da karfi kawo yan uwana danayi a gidan shi ne kake kira da yaudara yace yaudara ne mana mutum da gidan shi ba dama ya shigo ya huta a ciki yaji dadin ranshi.
   Samad yau ni kake fada ma haka don ka gani da ciki kake kokarin ka wulakantani yanzu ko may babu zancen wullakanci sai maganar gaskiya.
   Haukace mai tayi ranan tana fadin bai isa ya rabata da yan uwanta ba don tare ya gansu ya kuma yarda ya aureta a hakan.
   Haka ya kwana da tarin bakin ciki babu kunya washe gari kuma sai gata ta neman sulhu dashi don dai kawai ya biya mata bukatan ta don bata iya hakkuri dashi duk yadda ranta ya baci dashi ga wasu kudi da take son karba a wurin shi masu yawa don ai mata aiki a kan shi.
  Bata samu ko daya ba ranan don asubanci yayi ya fita wirin aiki da wuri koda yaje gurin aikin bai iya aiwatar da komai ba.
  Yusuf ya shigo ya samay shi a haka yake tambayan shi wai may ke faruwa dashi ne bai tsaya boye mashi ba ya sanar dashi halin da yake ciki da nafisa a gidan shi.
  Da yan uwanta da suka cika maigida da sunan yan aiki ta kwaso yana biyan su a wata ashe ba haka abin yake ba.
  Kai inji Yusuf lamarin Nafisa akwai daure kai wallahi Abdul yace nima bashi ba kazantar nan ke damuna Yusuf.
  Ka san dai halina da kyakyami wallahi komai na gidan nan yanzu kazantar shi nake ji in ba ruwan gora ba ban iya cin komai a gida na .
  Yusuf yaya zanyi da wanan masifa dana dauko ma kaina nasan ina son nafisa sosai why da ba zata gyara halin ta ba may ye ban ma Nafisa a rayuwan ta.
  Kamar karta samu cikin nan yanzu abin ya karkare jagule mata mace ba wanka ba saka sutura a jiki idan anyi magana sai tace wai lalurar cikine haka take cikin ta.
  Au dama ta taba ciki ke nan naga auren budurwa mukai mata wani kallo ya jefe shi dashi yace Nenan yar waye idan bata taba haihuwa ba nima daga bayan nan na fahinci yar tace ashe.
  Yanzun haka zan kare ga yawon restaurant ina cin abinci a garin nan kamar wani mara galihu dani.
   Kai innalillahi abin nakune akwai daure kai wallahi saukin abin khadija zata dawo next week zaka dan samu sauki a awurin ta.
   Saukin may zan samu a gurin ta ya tambayi Yusuf a yanayin rashin fahintar maganan shi Yusuf yace koba komai tunda ta iya girki naga ai zata dan dinga maka idan tana da time.
  No ban san in jefa rayuwan yarinyar ga halaka ko kadan nafi son ayi komai a kaidance yace kana nufin auren ta zakayi.
  Shiru yayi ya dafe kanshi bai sake magana ba ya fahinci bai son maganan don haka ya kyale shi tare da canza topic.
   Yusuf na fita ya jawo wayan shi ya kira layina muna gida ya Hauwa mai jego ya kira wayana ina wanke kayan miya a kitchen aka kawo min wayan.
   Sai da ya kusa katsewa na dauka tare da sallama yace ina kika shiga kika bar waya na ruri haka nace ina kitchen ina girki wa ya hauwa da ta haihu.
  Kuna gidan ta ke nan ya tambaya nace eh may kike girka mata nace miyar shuwaka zanyi mata da tuwon shikafa.
    Ke wa ya koya maki girki haka ne wai nace girkin ma har sai an koya ma mutum yin shi idai kana mace ai zaka iya girki ko wani iri dole.
  Aranshi yace ga macen da ta san kanta ba sai kuma yace ke wace irin yarinyace da baki iya kiran mutane kiji ko sun sauka lafiya ?
  Na aiku tafiyan dare ne ko ni na saka ku yin tafiyan da kuyi din yace OK haka zaki ce ma nace haka din ne ma ai.
  Sai naji ya kashe wayan dariya nayi nace zaka kaji ai ka daina in yar da magoro in huta da kuda har dare muna gidan sai tara muka dawo gida a gajiye .
   Ban kara bi ta kanshi ba har akai bukin suna aka watse lafiya drinks din da suka kawo muna yayi muna rana do  shi mukai amfani dashi wurin taron sunan.
  Mun fara shiri don tare da yaAmina zamuyi tafiyan kamar yadda na fada mata yace zai turo mota hakan ne ya faru sai ga mota zuwa sha biyun rana ya tsaya a kofan gidan mu.
  Nan muka fito mukayi haraman tafiya  nasha nashi ha a wurin mama da daddy kafin mu wuce muka dauki hanyar Abuja tare da ita don zata kwana a wurin mu.
   

Washegari da safe ban tashi da wuri ba don fashin sallah da nakeyi sai da naji motsin daddy ya dawo na fito don in gaida su har lokacin a cikin damuwa nake.
  Daddy yana zaune a cikin dan karamin falon mu ga abin karyawa a gaban shi mama tana gefen shi ta motsa mashi kunun da ta aje mai a gaban shi sai kamshi kosai ke tashi a falon.
  Daga kofa na tsuguna ina gaida su daddy yace a a baby na shigo mana daga ciki na tashi na karasa shigowa cikin falo har lokacin na kasa sakin jiki dasu kamar kullun.
  Daddy yace ya karatu nace daddy Alhamdullah yace babu matsalan komai ko nace daddy ba matsalan komai na fada tare da sunkuyar da kaina kasa.
  Ina kokarin mai da hawayen da ya ke shirin silalowa a idona nace daddy sai dai wanan mutumin da ya hado ni da kayan nan wallahi ban san ya sakasu a mota ba sai da muka zo nan taimakon shi nayi shine ya saka min da haka.
  Ido duk kan su suka tsura min da nake masu bayanin daddy yana kallona yana yaba hankalina don yasan ba zan boye masu komai dake faruwa ba.
  Saboda karya ba halina bane kai tsaye nake fadin gaskiya ga mutum yace dakata khadija kin mashi alheri kin shirya shi da iyayyen shi.
  Shi kuma yaji dadin hakan ya saka maki da alheri ko kamar yadda yace na gyada kai nace hakane  daddy.
  Mama tace ina kika hadu dashi haka khadija nace mama a wurin da aka tura mu aiki ne na hadu dashi ya samu matsala da iyayyen shi da yan uwanshi.
  Shine na basu shawara ya nemi shiri da yan uwanshi da mahaifar shi ta hanyar aikata masu alheri daya jaraba hakan sai suka shirya dashi.
  Shine yazo yace zai saka min da alheri akan abinda nayi mashi tace khadija shine ya kashe maki wanan uban kudin daga taimako kawai irin haka ?
   Nace mama wallahi ni ban san haka zai min ba daga ta Hussai yace ma mama kin san ni ya kamata in dauki zafi akan maganan nan fiye da kowa.
  Amma sanin halin ya ta danayi yasa na yarda da bayanin mutumin nan tunda ya rantse min da bata roke shi ba kuma ba da wani manufa yayi mata haka ba.
  Yai min bayanin da hankalina ya sa na yarda dashi da ita sai dai yanzu ba yadda muka iya tunda kayan nan sun riga sun shigo gidan nan.
  Kiga ba komawa zasu yi ba tunda dai ba rokon shi tayi ba sai dai khadija a gaskiya nayi mamaki da wanan abin don ba karamin kudi ya kashe ba  ga kayan abincin nan.
   Da sauri nace daddy ba kayan abinci bane kawai har da na sakawa da kudi sune a cikin wanan akwatin da ga gani jiya.
  Ido maman mu ta fitar waje tace khadija anya ba dan yankan kai bane kika hadu dashi kada fa watarana ya gama zolayar ki da abinduniya mu nemiki mu rasa.
   Dariya maganan ta yaso bani sai na dake nace mama ba dan yankar kai bane don nasan kowa nasa na kuma san matar shi.
   Share kawai duk wanan tunanen nayi shi a daren jiya har nafila sai da nayi akai banga wani abin cuta ba daga gare shi sai tarin alheri da na hango ga wanan alamarin.
  Shiyasa kika ga ban wani damu ba da hakan sai da ita din ta kula da kanta da mutuncin ta da irin tarbiyar da mukai mata zan sake yin yau na gani don ni kaina abin ya daure min kai sosai.
  Mikewa nayi na dauko kudin da kayan na turo zuwa dakin nan na fara fitarwa ina masu bayani yadda kayan suke nima mamakin yawan kayan nake yi a cikin macewa jiki.
   Daddy yace aje kayan zamuyi sai na nemi yar uwarki a waya naji shawaranta akai da yadda za ayi da kayan.
   Zan dage da rokon Allah don ina jiba jikina kamar akwai alheri ga haduwan khadija da wanan mutumin sai dai mu bar ma Allah sanin shi.
    Koda yakira ya Amina yayi mata bayanin abinda na dawo dashi wanan karon tare da fadin ta sake binkice na tsakani na da wanan mutumin don a gono gaskiyar maganan.
   Ta kira ni lokacin ina kwance mara na yana damu na da ciwo na dauki wayan ina gaida ita bata tsaya amsawa ba sai cewa tayi Deeda make faruwa ne daddy ya kirani yana fada min wani magana da safen nan.
  Shiru nayi sai da ta kara maimaita maganan ta nace cikin kuka wallahi ya Amina ba halina da kuka sani da na canza yanzu.
  Nima ban san da kayan nan ba sai da muka shigo garin nan na gani nan dai na koro mata bayanin komai don ba zan iya boye mata ba ita.
  Tace khadija kina nufin dama Abdulsamad ne ya yi maki wanan alherin ban sani ba khadija baki jin tsoron buzuwa ta san wanan labarin ta yi maki illar nace ya Amina yaya zanyi ni ban roke shi ba shiya bani.
   Tace dama khadija kece kika saka yayi wanan alherin da yayiwa iyayyen shi ashe dama duk kece sanadi ni ba komai nake ji wa ba sai buzuwan matar nan tashi wallahi.
  Takira daddy tayi mai bayanin komai yace shi zancen buzuwan matar shi bai damay su ba tunda ta sheda ba mugu bane.
   Nema ne idan naga zan iya sai in yi dashi wanan ba komai bane Allah yasan abinda ya hada a tsakanin mu ya kawo hakan sai dai mu saka ido a kan yar mu don har yanzu khadija yarinyar ce karama.
  Ya Amina tace gaskiya ne daddy zan shigo kafin ta koma dayardan Allah anan suka rufe maganan  tare da taya ni addua ga wanan lamari tunda daddy yace abarwa Allah sanin shi a tsakanin mu.
   Maryam ta kirani nake mata bayanin abinda ya faru dani maimakon ta tayani jimamay sai naji tana min dariyan shakiyancin da ta saba min tace shike nan ya nuna maki wayon manya ya gabatar da kan shi ke nan gare su.
   Nace wai ke maryam don Allah may yasa kike irin haka ne sai a na maganan gaskiya sai ki dauko wani zance daban tace shike nan yanzu mubar zancen a haka dai.
  Nace zai fi sauki muka dauko maganan karatu bayan mun gama wayan ne barci ya dauke ni a wurin wanda nasan barcin da ban samu bane a daren jiya.
   Nan dai na kwashi barci na sosai a ranan sai wani lokaci na tashi don mama taki sake min fuska yasa ban son fita a tsakar gidan sam.
  Wayana yayi kara na dauka Dan Baiwa nagani a rubuce wani haushin shine ya kamani a raina nayi banza da wayan nashi bandaga ba har kiran ya katse.
  Ya sake kirana da kyat na iya daga wayan don har yanzu ina fama da ciwon mara dake cina jin murya na da yayi yasa shi saurin fadin.
  May ya samay ki baki da lafiya ne may ke damun ki ne khadija haka yadda naga ya rude ne nace banda lafiya ne .
  Tun yaushe nace tunda safe daddy na gida naji ya tambaya nace yana waje turo min da layin shi  may zakayi da layin shi nace dashi.
  Ban number shi nace maki ya fada a dake nace ban san number shi OK zan kira a bani number yar ki in karba a gurin ta yace da sauri nace a a din Allah ni dai kada ka kirata naji sauki.
   Dole na bashi layin daddy din don naga yana niyar kashe wayan bayan na bashine ya kashe wayan bai fi minti goma ba sai ga daddy ya shigo gidan yana fadin ina khadijan take ne wai ashe bata da lafiya bamu sani ba.
  Sai da wanan yaron ya kirani yanzu yake fada min khadija bata da lafiya a kaita asibiti wai zai turo da kudi kamar shine ya haife ta.
  Mama tace ni tunda jiya da ta dawo na ganta kwance ban san may ke damun ta ba, har dakina daddy ya shigo ya samay ni kwance sai dai ba barci nake yi ba.
   Zama yayi saman tsohowar kujeran dake falon yana fuskanta na yaga yar raman da nayi yace baby na may ke damun ki ne yanzu wanan mutumin ya kirani wai baki da lafiya.
   Sai dai ban san ida ma yasamo lambata ba ya kira nace niyace in bashi na tura mai yanzu amma ban san kiranka zai yi bz ai daddy yace zai turo da kudi wai kije asibiti nace ya barshi bayan kudin da ya turo muna zai kara dawainiya kuma.
   Daddy yayi murmushi yace kin san may yace dani na girgiza kai cewa yayi wai dawainiyar ki yanzu akan shi yake.
   Nace daddy kada ka yarda da maganan shi wallahi ni ba komai a tsakanin mu yace naji sai dai yadda yake ya nuna min da fuskan gaskiya yazo maki don bai bar abin a tsakanin ku ba ku biyu ya sakomu mu iyayyen ki a ciki bai boye muna ba.
   Yanzun dai yace a tura mashi da account number da zai turo kudi kije asibiti nace daddy nifa ba komai a tsakanin sai mutunci kawai yace yaji.
   Sai ga daddy ya shigo zuwa sha biyu yana fadin ya turo dubu hamsin in tafi asibiti nace nasha magani naji sauki daddy dama ciwon mara ne kawai ke damu na.
  Yanzu yaya kike son ayi da kudin da ya turo maki kasa kasa da murya nace kayi amfani dashi kawai daddy.
  Sai yamma ya kira yana tambaya ko naje asibitin nace eh yace sun baki magani nace eh nasha har naji sauki sosai yace ashe period kike yi kike wanan raki haka ?
   Shiru nayi banyi magana ba yace duk wata haka yake maki nace ban sani ba yace kan ki ga Yusuf ku gaisa.
   Kunya naji sosai jin har da Yusuf yasan ina period yanzu muka gaisa yayi min yaya jiki nace da sauki yace ki sha magani kin ji sauki ko nace eh yayana .
   Sai shiru ya biyo nace Yusuf batare da fadin yayan da na saba kiran shi dashi ba yayi makin jin hakan daga bakina sai ya dake yace yaya akayi yar mama ?
  Nace kayiwa mutumin nan fada mijin buzuwa akan abinda yayi min bai kyauta min ba don may yake son saka iyayyena su zarge ni.
  Yace zargi kuma khadija  akan may nace yanzu haka tunda na dawo mama sai fushi take yi dani akan abin da ya saka a motar da naje gida dashi.
   Saboda shi take fushi dake nace wallahi ni na rasa may zanyi akai suna ganin kamar ban kama kaina bane a Abuja ina hurda da mazan banza ne a can.
   Sai daddy ne kawai daya fahinci komai da taimakon ya Amina na samu ya dan sausauta min bai fishi dani muryan shi naji yana fadin why mama zata yi fushi dake akan dan abinda na tura masu.
   Mama bata yarda da tarbiyan da sukai maki bane ko may in haka ne kuwa zan shigo da kaina in mata magana da zata fahince ni ita ma.
   Ban saka ba haka ka hadani dasu dazun daga na fada ma banda lafiya ka fadawa daddy yazo yana yi min fada balle maman mu da ta hau dani.
  Ba matsalan ki bane nasan abinda zance da ita idan nazo nayi saurin fadin bansaka ba dai ka barni da ita zamu shirya wataran.
   Bayan na kashe wayan na mike na shiga wanka na fito na canza kaya jikina zuwa dogon riga nayi kyau sosai a cikin rigar lokacin yamma yayi sosai nace zan je gidan su hafsat kawata da tai aure ta haihu bani gari.
  Kallon da mamaki min ne yasani tsarguwa sai daga baya na fahinci rigar da na saka ajikina ne yasa take min wani kallo da bashi ba.
   Sai na dawo tace min batare da ta kalle ni ba na fita jiki a sanyayye zuwa gidan hafsa din dake bayan minna minicipla coucil.
  Hafsa kawa ta ce tare muka taso da ita kasancewar unguwar mu ba nisa da karatuna ya dawo minna na hadu da ita muna zuwa girl day dake a bayan old airport tare kusa da tsohon makarantar wtc na mata.
   Bayan mun gama ta samu wani guy ta aura dan kabilar Nufe dake tashen kudi a lokacin .
  Na fito gida a hankali nake takawa iskan marance yana kadawa inda nake ganin fuskokin wa yan da na sani muna gaisawa jefi jefi dasu a hanyan.
  Har na isa gidan na samay ta tana girkin abincin dare tana gani na ta tare ni da murna muka gaisa ta nufi falon su dani ina biye a bayan ta.
  Sai bayan na zauna ne ta dauko min baby ta har yaron ya fara wayo sosai ta miko min shi sai bina take da kallo wai na sauya gaba daya na zama wata big girl dake nace kai haba dai hafsat har dake cikin fadin haka.
   Tace wallahi gaba daya kin sauya ma sani na ne khadija nace yanayi ne kawai wallahi yazo a haka ba wani abu may ye sunan yaron na tambaye shi.
  Muna hira tana duba girkin da takeyi har ta karasa takawo min nace wallahi hafsat a koshe nazo gidan nan watarana  zanci.
   Mikewa nayi saboda magariba daya kawo jiki sosai na bata asai ma yaro takalma ina shirin fitane mijin ta ya shigo gidan.
  Allah ya gani jini na bai hadu da mijin ta ba tun farko asali ma nice ya fara cewa yana so sanin shi da nayi dan duniya mai wayan yan mata da kyale kyali yasa ban bashi fuska ba.
  Naje hutu kaduna kafin in dawo na samu sun dinke da hafsa har sukai aure yanzun ma da ya shigo gidan ya samay ni sai da ya daga min gira ba tare da sanin hafsa ba.
  Harara na watsa mai na fice gidan tare da yi mata sallama nadan yi nisa naji muryan shi a baya na  yana fadin khadija ji mana.
  Juyowa nayi fuska a daure ina kallon shi nace lafiya dai ko ya washe baki yace don Allah sorry to distub you kin boye fa da yawa ban san kin zo garin ba ai dana kawo maki gaisuwa.
  Dan murmushi nayi nace ba komai ai gashi mun gaisa yanzu dama boye nazo gani na ganshi har yayi wayo.
   Yace in ba laifi ki bani layin ki akwai maganan da zamuyi kin san dai yanzu ba da bane zaki iya fahinta na har yanzu ba kin fita raina bane.
   Auren hafsa Allah ya nufa sai munyi da ita amma ni ke ce choice dina tun farko hafsa dai ta shishige min har na aure ta.
   Dakata Adam kada ka kara taro na da irin wanan maganan ko da hafsat bata gidan ka kai ba choice dina bane ka sani ban hurda da maza irin ku da kafan su bai tsayo a guri daya ba.
  Ke kizo kici arziki kibar arziki kawai don yanzu arzikin bana yaci uban na da zan iya daukan lalurar ki da komai naki wallahi.
  Wani kallo na watsa mai na up and down nace a haka din kake tunanen zan iya cin amanar kawata aminiya ta nace Allah ya tsare ni da masu irin halinka.
   Na wuce na barshi tsaye a gurin yana bina da kallon zalama irin ta yan iskan maza yana sosa kan shi baida mu da mutanen dake wuce ba a saman titin.
   Na shigo gida ana kiran sallah magariba dakina na nufa sai da mama ta gama alwala ta kwada min kira na fito inyi sallah lokacin sallah yayi.
  Nace mama kin manta bana sallah ne ta ce oho ta shige dakin ta sai bayan sallah isha,i daddy ya dawo gidan suka zauna a dan falon mu har kanne na ciki suna kallon NTA dake labaran marance.
  Daddy ya duba bai ga na shigo ba yake tambayan ina nake mama tace ina dakina kafin yace wani abu wayan shi ne yayi kara ya dauka bayan sun gaisa ne yayi mai magana yana son magana da mama ne daddy yasa handfree din wayan yadda zai ji abinda yake fadi.
  Sun gaisa yace mama don Allah a dan sasauta ma khadija da takurawa tace na saka kuna zargin ta da aikata ba daidai ba ni kuma nasan idan har kun yarda da tarbiyan da kukai mata ba abinda zaisa ta canza daga baya kuma.
  Mama kiyi hakkuri khadija na nan a yadda kika santa alheri kuma yanzu na fara maku kuda ita muddin ina raye sai abinda yafi karfina ne bazan maku ba.
  Alherin yar ku gare ni ne ya jawo maku hakan ba ina nufin Khadija da wata manufa bane sai alheri don ta cancanci haka a gare ni so kuyi hakkuri a sake mata fuska babu komai sai alheri ga haduwana da khadija.
  Bayan sun gama waya da mama ya gama daure ni a gaban su da ban gane manufar maganan shi ba daddy ya kwala min kira daga falon.
  Da sauri na shigo dakin har lokacin shigan da na fita gidan hafsat ne a jikina ban cire ba na samay su a zaune falon.
  Gaidasu na fara yi tare da samun wuri na zauna mama tace khadija yaushe ne kika canza haka wai ?
  Nace cikin dago kai da mata kallon mamaki nace mama wanin abin nayi kuma again tace yanzu bamu da shakat a gidan nan dan abu kadan sai ki kai karan mu ga saurayin ki.
  Da sauri nace mama wane saurayina kuma danakai karan ku gare shi tace wanda kika jajibo a Abuja mana wanda ya fimu sanin zafin ki a yanzu.
  Mama ni ba saurayina bane wallahi ba wani abinda ya taba shiga tsakanin mu na soyayya har yau tace in babu yaya kika kai karana wurin shi wai na saki gaba a gidan nan tunda kika dawo.
  Kai kai innalillahi haka yace maku mama fada nayi mai fa akan abinda yayi min nace kina zargina ga abinda kika gani ya bari ban so.
   Daddy sai dariya yake muna ni da mama don yasan duk iya binciken shi bai gano wani abu da nake aikatawa a bayan su.
   Tun daga wanan ranan mama bata kara daure min fuska ba muka koma daidai a gidan kamar yadda muke a baya.
   Wayana gaba daya na kashe sai zan kira nake kunna wa don ban son wani abinda zai haifar min da matsala kuma tsakani na da iyayyena a gida.
   Ya rage saura kwana biyar mu koma makaranta sai ga kamal mai bi mun ya shigo da kaya wai ya Amina ta shigo gari.
   Da gudu na kwasa nayi waje ina masu sannu da zuwa tana sallaman driver da ya kawo ta gida na rungumay ta na sake ta naja hannun yaran na rungume su a jikina.
   Ciki muka shiga gaba dayan mu bayan ya Amina ta huta taci abinci tana zaune a falo na shigo da karamin dan ta a hannu na tace dada hutu ya kusa karewa dai nace wallahi ya Amina.
   Nakai zaune kusa da ita tace dama ina son in zo gida in samay ki kafin ki koma ne nace tau wani abin nayi ya Amina ?
   May ye ma baki yi ba khadija ina ke ina Abdulsamad mijin buzuwa fati da mijin ta ta barshi dole don wanan buzuwa ke yanzu kike kokarin jefe kan ki ciki.
  Kai ya Amina kuna bani mamaki wallahi wai ya fada maku muna soyayya dashi ne halan na san dai shi ba zai fada ba.
  In kuma don wanan abinda yayi ne kuke zaton muna tare ne da bakin shi ya fada ma daddy gaskiya ba sona yake ba.
   Haka kike tsamani ke ko azaton ki duk wanan alaman da yake gwada maki ba so bane hakan wani namiji zai samay ki yace bai so  ki.
  Kin fi buzuwa durin na ya mace sai dai fari da gashi zata gwada maki ko farin ma ba wani can ba don ke ma ba baya ba.
  Sai yanzu nake gane maganan baban boy da yake cewa ke din matar manya ce watarana ina ganin kamar fadi dai yake yi.
  Abin mamaki ne yadda har Abdulsamad ya fada tarkon ki abinda ba wanda ya taba tsammani zai iya sai gashi lokaci guda har kin fara canza shi da naki sallon soyayyan.
   Mama da ta shigo dakin dauke da kwanon da ta tuka muna tawaska ta aje tana cewa ke ma dai kya fada idan anyi magana tace an matsa mata ba soyayya suke da shi ba ko takai karan guri shi.
  Shi ko ba kunya gare shi ba ya kira mutane yana rokon su akan a daina matsa mata don Allah ni daddy ku har mamaki yake bani yarda ya yarda da mutumin nan a lokaci daya.
  Da ban san halin shi ba sai ince ko don kudin shine yake son shi ya Amina tayi sauri cewa a a mama ba halin daddy bane haka da yana bin kudi da ba zan auri Abban su boy ba.
   Mama tace nasani ai shine abin ke ban mamaki yanzu ai tace yarda ne kawai wallahi in badon buzuwar matar shi ba ai Abdulsamad mijin aure ne ga ko wace mace ta samay shi.
  Nan ya Amina ta fara ba mama labarin shi da rayuwan su har karshe nace wai ku may yasa kuka damu da wata buzuwa can ne.
   Kowa tashi tafishe shi amma ni bata cikin tsarina ni dai kawai bai min bane ina zan jefa kaina ga family man mai iyali da yawa haka.
   Wanan duk ba matsala bane tunda yana da abin kula da koda mata nawa yayi niyar yi abin damuwa shine kishi da wanan buzuwan da bata da imani ko kadan.
  Balle idan taji ba barin shi zatayi ya aure ki ba kuna tana iya yima rayuwan ki illar yada taiwa fati ko sunan ta baya son ji yanzu.
   Allah bai bata iko a kaina nace ke don Allah rufawa mutane baki ana baki kina roko may kika taka da kike fadan haka nace mama Allah.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Alhamdullahi mun sauka lafiya inda na samu maryam ta dawo ko saboda kwanakin da na kara ta rigani shigowa na samu har ta gyara min daki ko.
   Anan driver ya zube mu ya wuce abinshi ko ba a fada min ba nasan anty ta biyoni ne don taga yanayin zaman da nake a Abuja inda tazo da sunan kwana daya sai gashi ta share biyu kuma muna tare da ita ban je ko ina ba.
   Washe gari da safe na rakasu tasha suka shiga motar kaduna suka tafi bayan yan nasihohin da taimin na in kula da kaina in maida hankali ga abinda ya kawo ni.
   Muka rakata garage ta shiga motan kaduna wanda ta dauka ita kadai sai yaranta har kaduna mun dawo hotel a gajiye don haka na kwanta barci don nadan ji dama jikina.
   Tun da na kwanta ban tashi ba sai bayan sallah la,asar na tashi nayi wanka na tare da gabatar da sallolina ban dade ba maryam ta shigo tana fadin kin tashi ?
  Nace wallahi tace ga abinci nan ki cikin kula idan kin tashi ci ni na koshi sauran kayan bukin da ya rage na zauna ina ci nace abinci sai da dare.
   Ina zaune kamar daga sama zara ta shigo dakin    nace mutumiyar ashe ke ma kin dawo ke nan tace dazu fa na gama tunanen ki.
  Zarah tayi dariya tace ai ni na riga ku dawowa tun wancan satin daya wuce na dawo school da sauri nace ai lokacin ba ai resuming ba.
  Ta wallahi gajiya nayi da zaman gidan shine nace hutumu ya kare aka shiryani na dawo school  kaina jinjina nace Allah ya kyauta da halinki zarah tunda har kin san ki aikata haka.
  Dariya ta sake min tana fadin gidan ne babu dadi yanzu da na saba da ruyuwan independent din kaina .
   Sai da taci abinci a dakin ta koshi tana bani labarin tafiya sukayi da saurayin ta ta raka shi kano shiyasa ban ganta ba maryam baya ta bamu tana diban takardun da take hadawa har zarah tabar dakin.
  Sai lokacin ta juyo take ce min irin wa yan nan bai kamata mutum yana hurda dasu ba ai kada su bata ma mutum suna a banza.
   Nace yaya zanyi mun fito gari guda da ita bazan iya kyale ta ba ai kin ji dai ina bata shawara ko zata daina halin nan da tasawa kanta.
  Allah ya kyauta tace muka canza hiran kada muci namanta bamu sake fita ba har gari ya waye muka shiga school.

Wanan karon Nafisa bata yar da ba dakanta ta shirya tafiya zuwa kaduna bayan ta dawo Niger don an bata labarin wani sabon malami a Kusfa.
   Abdulsamad bai hanata zuwa ba don tace kaduna zata leka don ta kwana biyu da zuwa shiri sosai yayi mata don zuwa kadunan a ganin shi ai gida zata.
   Ranan da ta isa kaduna bata samu zuwa ko ina ba sai washegari suka tafi ita da Auta yar take ga su Abdul din sai dai halin kwadai irin nata zata iyayin komai akan kudi.
  Haka yasa suka kule sosai da Nafisa har aminci ya shiga tsakanin su tana mata shige shige dama Auta irin yan duniyan matan nan ne tunda ta fito gidan mijin ta bata sake aure ba tana zaman rayuwa kawai a gida.
  Su biyu sukai tafiyan sai driver daya kaisu bayan sun gama yi ma malamin bayanin komai ne malamin yayi dariya yace    kamar yadda take zargi gaskiyan maganan ke nan ya fada tarkon son wata yarinya a yanzu sai dai abin bai wani yi nisa sosai ba.
  Idan kuma bata bi alamarin a hankali ba zafin kishin da take nunawa ne zai sa komai ya iya faruwa da ita.
  Hakalin ta ya tashi sosai wanan ne mutum na biyu daya fada mata haka malamin yace alamarin yarinyar yana da karfi sosai.
   Don asiri baya kamata kai tsaye da zaran zamcen yakai ga iyayyen shi komai zai iya faruwa a tsakanin su a yadda bata zata ba.
   Don haka sai kin natsu aiki zamuyi maki wanda zaki kama mijin ki a hannun ki indan shi ya kamu yadda muke so komai zai iya zo maki da sauki.
  Amma koda zakici nasara akan hakan sai kin bi a sannu don yarinyar tafiki komai da kike tunanen kina dashi abune wanda sai an aiwatar dashi a sannu saboda mijin ki yana mata mugun son da bai san yana mata ba.
  Nashiga uku tace malam tafini komai fa kace yace kwarai da gaske don gata nan a gaban mu kina gani ta shige maki gaba ko a wurin shi.
   Kuka ta fara tana fadin don Allah malam kai min rai ka taimake ni ko nawane zan iya baka indai zaka min aikin da za a raba su hayatan hayatan ya ji bai kaunar ta ko kadan.
  Gaba daya yanzu na daina gane kan shi ada komai yana min kai tsaye yanzu sai yaja min rai yake min abu da na dauka ko cikin dake gare ni ne yasa yake min hakan.
  Yace magana dai guda ce ga yarinyar nan kina gani taurarin ta na da matukar haske sosai duk abinda ta sama gaba takan cin ma nasara a kan shi lokaci daya.
  Yana nuna masu zanen da yayi a kasa wanda su basu fahintar abinda ya zana sai dai bayanin da yake masu wanda ke matukar tayar wa Nafisa da hankali.
  Yace saukin abin daya ne yarinyar mijin ki baya gabanta don wani dalili nata amma shi yana kokarin cusa kanshi ko yaushe a wurin ta ne.
   Tace da karfi shi samad din malam yace kwarai kuwa muddin muka ce zamuyi aiki na gagawa komai zai iya faruwa na fada maki.
  Idan baki yarda ba zaki iya zuwa gurin wani kiji nasan duk wanda zai fada maki tsakani da Allah ba zai fada maki sabanin abinda na fada maki ba.
   Tana share hawayen dake zubo mata take fadin malam yanzu may ye abin yi don ko yanzu da dabara na samu nazo nan din.
  Wanan ba wani matsala bane aiki zamuyi mashi wanda hankalin shi zai fita a kan wata mace baki daya sai mu cus mashi kaunar ki ke kadai.
  Ta gyara zama tana fadin in hakan zai samu malam shi nafi bukatan ai min a kan shi a raba shi da ko wace yar iska ce kison tayi min kutse a gidana.
  Ya zayyana masu aikin da zai masu din ta yarda ta amince zata biya makam din abinda ya bukata a wurin ta suka biya shi ba tare da taji komai ba sukai mashi sallama.
  Tun a mota take zazaga balai tana zaginshi da iyayyen shi Auta tana kara zugata da fadin wanan wata irin yarinyar ce da za a ce ta fiki komai har kyau ke nan malam yake nufi ko may.
  Don banda kyau babu wani abu da Nafisa ke kadagi dashi don ba arabi ba boko haka take dip dinta bakauya kuma.
  Koda ta dawo kaduna bata biya gidan su Abdul din ba bata mayi tunanen shiga gurin su ba don daukan su take a makiyan ta dama balle yanzu da sunan su ya fito ga zancen.
  Kwanata uku a kaduna bayan Auta ta koma ta koma ta karbo abinda zasuyi amfani dashi idan ta koma sauran sai ya hada yace zai kira Auta ta karban mata don sai ya nemi abin hadi.
   Haka ta shirya sai da zata wuce ne ta dan shiga tsatsaye ta gaida su hajiyan shi da sauran mutanen gidan ta juya suka tafi.
  
Almarina kuwa tunda na dawo sau daya muka hadu dashi koshi a tsatsaye don ina sauri zan tafi class karatu don muna da test din da zamuyi washe gari.
  Yazo min da provition mai yawa kamar ba gobe har sai danace kayan suyi min yawa yace naci da kawayena.
  Sun tafi abisa alkawrin zamuyi waya amma har wani lokaci bai kirani ba Yusuf ma haka bai kira ba nikan haka yafi min nono fari.
  Don dama neman mafita nake dashi kuma na samu yanzu sun sarara min ranan muna hira da maryam take tambaya na su.
  Nace banji komai daga gare su ba na nuna mata ni basu gabana yanzu abinda ya kawo ni nakeyi.
  Tace kai amna abin mamaki ne khadija ace sun share ki haka ba labarin komai daga wurin su ko yusuf ai ya kamata ace ya kira musan halin da suke ciki.
  Ke kuma baki neme su ba halarci baice haka ba fa khadija shiru nayi mata don mu kawar da zancen su da ta dauko min ina zaune kalau.
  Sai bayan da na kwanta sai kuma maganan ya damay ni a rai gaskiya maryam ta fada min ya kamata ka kula mai kula ka koba komai zai san ka damu dashi ai.
  Ranan da kyat na samu nayi barci da tunanen su a raina sai dai ni ba zan iya kiran shi ba sai dai dan dama dama Yusuf din.
   Washe gari haka na tashi da jin bakin rai a zuciyata sai dai kawai na danne abin a raina don na kudurta a raina ba zan taba kiranshi ba indai nice zakira inji ko lafiya suke.
  Tunda dama ba wani soyayya ko wani abu ke tsakanin mu haka ba mai karfi kawai dai ya gaji danine shima ya hutar da kan shi.
  Na share kawai kada maryam ta fahince ni na shirya muka nufi cikin school don daukan lectures na watsar da maganan su a raina kada in sa wa kaina damuwa a banza.
   Alamarin gidan shi kuwa yanzu tun dawowan Nafisa daga kaduna sallon zaman su ya sauya don yana dan samun kulan daya kamata daga gareta duk da ba wani dadin yake ji ga hakan ba don baya samun sakewa har yanzu a gidan shi yadda yake so.
  Shima Abdulsamad din ina a ranshi yakan so ya kirani yaji lafiyata sai dai yanzu duk lokacin shi na aiki ne dana Nafisa a haka har yayi tafiya tare suka ketara da nafisa zuwa wanan tafiyan.
  Satin su biyu suka dawo Nigeria koda suka dawo abuja bai samu kafan kiran na ba don Nafisa ta mamaye komai a lokacin.
  Yau suna tare da Yusuf a office din shi Yusuf ma wanda yayi tafiya yake tambayan shi labarina ya yamutsa fuska yana fadin wallahi banda labarin ta itama bata neme ni ba.
  Yusuf yace haba kai ma kasan bazata nemay ka ai, amma hakan bai mun dadi ba wallahi dakace baka kirata ba waya ya dauko daga Aljihun shi ya fara neman layina a lokacin.
  Ban shiga school ba ranan don na tashi da ciwon mara ina kwance a dakin mu ko karyawa ban yi ba har lokacin don haka ina cikin barci mai nauyi daya dauke ni naji kira a wayana.
  Da kyat na lalubo wayan dake gefe na ina jan tsakin wanda ya tayar dani a wanan lokacin dana dan samu sa,ida na samu barci ya dauke ni.
  Koda na dauko har kiran ya katse sunan Yusuf na gani akan wayan ban kai ga tunane ba wani kiran ya sake shigowa again.
  Tunane nake a raina may kuma zai fada min yanzu mutanen da suka shareni kusan wata daya ke nan yanzu kuma zai kirani yace min may ?
   Kamar in share shi kiran ya katse sai dai na danna recieve inji abinda zai fada min a lokacin na amsa da sallama cikin muryan barci da yanayin ciwo a tare dani.
  Naji yace subbahanallahi khadija baki da lafiya ne may ya samay ki naji muryan ki a haka ?
  Da sauri ya dago kai yana kallon Yusuf dake magana a waya yaji yace ayya sorry sannu ko kin je asibiti ne nace nasha magani ai ba sai naje asibiti ba.
  Idon shi har lokacin yana akan Yusuf din yace may ke damun ta ne naji Yusuf din na fada mai wai banda lafiya ne a kwance nake ma.
  Taje asibiti Yusuf yace tace ba sai taje asibiti ba wai karban wayan yayi daga hannun Yusuf din naji muryan shi yana fadin ki shirya yanzu gani nan zuwa nakai ki asibiti ya fada kai tsaye.
  Nace naji sauki ba sai kazo ba na kashe wayan wayan ya kalla tare da mikewa tsaye yana rufe file din dake gaban shi ya fara tafiya.
   Yisuf dake zaune ya mike juyowa yayi yana fadin ka zauna ka karasa aikin barin je na ganta in dawo Yusuf yace amma kana ganin zata saurare ka idan kaje kai kadai.
  Wani kallo yayiwa Yusuf din kamar zaiyi magana sai kuma ya juya ya fita Yusuf ta girgiza kai yana murmushi halin abikin nashi na bashi mamaki ace mutum haka da girman kai.
  Nikan ina kashe wayan naja tsuki nace mayaudari kawai naja filo na gyara kwanciya na barcin da ban koma ba kenan idona a rufe nake tunane nace yanzu na tabbatar da karkashin mace yake.
   Wata kila matan shi tasamu labari ne ta hana shi kula kowa yanzu ya dawo zai yaudare ni kuma ya bata min lokacina a banza.
  Dama ban sa zancen ko kadan a raina ba balle ya damay ni in ma junin shi iya yaudaran mata ne ya bata masu lokaci Allah ba zai bashi saa ba anan naja tsuki na gyara kwanciyana.
  Na samu barci ya fara dauka na naji wayan shi ya shigo min na duba na bar wayan nata ruri har ya katse kira uku yai min ban daga ba .
   Ranshi ne ya baci sosai yana shirin juyawa sai ga maryam kamar daga sama ta dawo don hankalin ta bai kwanta a yadda ta barni ta dawo ta dubani.
  Sai ganin shi tayi yana shirin juyawa da sauri ta karsa wurin shi tana gaidashi tare da fadin wallahi tana ciki bata da lafiya ne tun jiya nima yanzu na dawo in dubatane.
  Yace shi yakawo ni yazu asibiti nake son zuwa da ita a ranta tace boye min khadija ke nan rayi ashe suna waya dashi shine take boye min.
   Taji yace nakira wayan ta taki ta ga bayan yanzu Yusuf ya gama waya da ita ta fada mai bata da lafiya tace barin shiga in fito maka da ita nasan fushi take daku.
  Fushi ya tambaya da mamaki dariya tayi tace ina zuwa don Allah ta wuce ya bita da kallo har tabace yana mamakin kalamin ta wai fushi take da ku fushi akan may ?
    Tana shiga dakina ta nufa ta samay ni a kwance zama tayi a gefe na tana min sannu tare da fadin ga mutumin ki nan a bakin get yana jiran ki wai kuje asibiti yanzu.
   Wani kallo mai kama da harara na watsa mata nace rabu da mayaudari nine zai kai asibiti akan may zai zo min a yanzu da bana son ganin shi.
  Haba khadija kin san uzurin da ya tsayar dasu basu nemay ki ba tunda har yanzu ya iya zuwa da jin baki da lafiya ai ya kamata ki saurare shi.
   Haba maryam abinda kika sani ne nafi jin dadin zaman da nake yanzu babu takuran kowa a kaina akan may kuma kike son in kara fadawa tarkon mayaudari irin wanan mutumin da matar shi tafi karfin shi kuma.
   Kada kice haka khadija ko ba komai ya nuna kulawan shi a kan ki yanzu ina laifin wanda ya nuna maka haka a lokacin da kake cikin halin ciwo.
  Don Allah ki tashi ki daure badon ni ba sai don Allah ki tafi ki ganshi ko ba komai zakiji abinda ya tsayar dasu kwanaki mai tsawo haka baki ji su ba.
  Allah da kika hadani dashi ne zai sa in tafi badon wani abu ba can nasa, don ina son inyi nisa da shuumancin su yanzu tace daure kiwa Allah da kika ce zato kike yanzu kila ma ba matar shi bace ta hana ya kulaki.
  Kalaman ta yayi tasiri sosai a raina koba komai ina son jin abinda ya hana injisu kwana biyu don ban sin jawa kaina wulakanci ko kadan.
   Ita ta taimaka min na shirya atamfa na daura don yanayin da nake ciki tare muka fito zuwa ida yake zaune a motar shi.
  Yana yi yana kallon agogon hannunshi can ya ga fitowan mu tare da maryam ina tafiya da kyat yanayin ina jin jikin nawa sosai.
  Har muka karaso bai dauke idon shi a kan mu ba  yi hakkuri mun barka kana jira wallahi barci na samu tanayi yanzu na tayar da ita.
   Bai yi magana ba sai kallona yayi yana fadin shiga mota mu tafi nace basai naje asibiti ba na sha magani naji sauki ina magana da kyat cikin daure fuska.
   Shiga muje nace maki da sauri maryam ta riko min hannu ta nufi gefen mai zaman banza tana bude min motar tare da fadin sai kun dawo Allah ya sauwaka.
   Sai da na zauna da kyau ya tayar da motan muka hau dogon titin da zai kaimu cikin gari sai da mukai nisa kaina da duke na dafe goshina da hannu na daya naji yace.
  May damun ki ne haka ban bashi amsa ba sai gyara zama da nayi ina cije baki don dan motsawan da nayi maran yana min ciwo yanzu.
   May damun ki ya sake maimaitawa shiru nayi can nadan sauke nufashi nace da kyar banda lafiya ne kawai tare da dan dafe mara na.
   Au ko abin ne yazo maki na manta yanzu kike cikin time din period din ki ko hararan shi nayi tare da kawar da kai ina cewa a raina kaji min mutum da bin didigi haka ?
   Kwana nawa yakeyi halan sake dago kai nayi na kalle shi kamar bashi yake maganan ba nayi saurin kawar da kaina daga kallon shi.
   Yace bakiji bane kwana nawa kike dauka kina period din nace ya fada tare da dan kallo na nace ban sani ba kada ka wuce hurumin da ba naka ba mana na fada ina kwantar da kaina.
  Murmushi yayi yace haka kike ce ko nace na fada din ni banga dalilin tambayana haka ba kai ba likita ba wani sai nayi shiru.
  Yace go ahead you say your words out, shiru nayi tare da kawar da kaina gareshi gaba daya ya sake fadin you free to say komai zaki iya fada don ance fushi kike damu.
  Da sauri na jiyo ina kallon shi nace fushi fa akan may zanyi fushi daku in ba ina son sama kaina nauyin da bai hauni ba ?
   Murmushi yayi da sai ka saurara zakaji shi yace kwana biyu bamu kasan ne daga ni har Yusuf na fita da madam dina ne mun tafi check up ciki ke bata matsala.
   Don Allah malam ni ban tambaye ka ba in zaku iya ma ku tare a can ba damuwa na bane wanan ciki kuma Allah ya bata lafiya ya sauketa lafiya amma mi ya hadani da tafiyan ku kuma.
   Kwana yasha muka shiga wani clinic inda yasa na fito muka shiga guri ya sama min na zauna ya nufi gurin tankan kati ba mu dade ba duk da mun samu mutane a gurin yace in taso mushiga gurin likita.
  Mun shi likitan yare ne don turanci suke dashi sun gaisa naji likita na cewa kayi sabin aure ne ashe yace mashi eh yace madam ta kwana biyu bata shigo ciki ya zaunu ko yace eh a gadarance yake ma mashi magana yace ina son ka duba min ita tana fama da mesturalpain ne.
  Yace ayya sorry madam  yakamata ace ya rage maki ciwo yanzu da kiyi aure ya kamata ace kin rage jinshi haka indan zakiyi period don agana kawai matsalan hakan.
  Nauyi kunya ya rufe ni a wurin na kasa daga kaina shima wayan shi yake dakila baibi ta kan likitan ba sai da likitan ya fara tambayana ina mashi bayanin ya dago yana kallo na.
   Tashi nayi zuwa inda likitan yace in kwanta ya dan dadana cikin nawa na dan sake kara daidai kasan mara na daya tausa da dan karfi yace in tashi ya dawo ya zauna yana rubutu a wani farin takarda ya mika mai lokacin na dawo na zauna dakyat dafe da marana dake min tsananin ciwo sosai.
   Bayan ya mika mai yayi mai bayanin anemi wanan maganin in sha zasuyi min allura kuma zan samu sauki da yardan Allah ya mika mai hannu tare da fada mai inda zamu kai takardan a duba ni.
   Sai da muka gama komai muka fito yana min sannu muka dauki hanya wani shago ya tsaya yace min yana zuwa ya shiga ciki yadan jima sai gashi ya fito yaron shagon na binshi a baya dauke da wasu manyan ledoji biyu a hannun shi.
  Ya saka bayan motar ya shiga muka tafi bayan ya mikawa yaron kudi yana mashi godiya kaina na duke yace sannu likita yace zaki samu sauki dan anjima kadan amma zaki barci sosai ki ci wani abu don kince baki karya ba.
   Bana jin shi do  murdan da mara na keyi ina dan cije baki ina jijiga kafa na da matse hannaye na duk yadda na so in daure na kasa sai da na yi ya gani a bakin down hostel din mu ya tsaya da motar shi.
  Zaki kara kawar ki ta taimaka maki ne ko in taimaka maki ki fita duk da ciwon da nake ji sai dana harare shi na bude motan na fita ko godiya ban mashi ba.
  Ina fita yace  turo min kawar ki ta daukan maki magani kai na iya dagawa na shige ciki na samu maryam na girki a dakina din bata da kiuyar girki ita tana gani na tace har kun dawo kaina gyada mata na fada saman katifa nace yana kiranki a waje.
   A saka hijab da sauri ta fita daga dakin zuwa wurin shi bata jima ba ta dawo dauke da ledojin nan da ya sayo tace yana maki sannu wai sai kunyi waya yace kici wani abu kafin ki kwanta.
   Itace ta zauna ta bude ledan kayan ciyeciye ne a cikin dana sha tarkace dai gasu nan sai dayan ledan dake dauke da pad din mata always kamar mai bude shago dashi ban san ranan da zai kare ba.
   Abinci ta debo min na dan ci kadan na kwanta sai barci mai nauyi ya dauke ni a gurin ban kara sanin inda nake ba kuma.
   Yana fita ya daga wayan shi six miscall ya gani na Nafisa da sauri ya danna wayan ya kirata yana fadin sorry ina wani abune yasa banga kiran ki ba.
  Tace Samad ina kaje wacece akace mi  an ganku tare a asibitin doctor Bisi yanzu waka kai asibiti wata macs ce aka gan ku tare tare ta fada cikin tashin hankali.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
            SEENABU

Bai iya bata amsa ba sai kokatin wuceta da yake yi ya karasa cikin dakin rigar shi ta riko ta baya da mamaki ya juyo yana kallon ta.
  Shi da magana take mai wuya ina shi ina tsayawa fada irin haka da mace sau da yawa nafisa takan tunkare shi da irin wanan fita tana kokarin kama mai kaya ko ta sha mai kwala sai dai bai biye mata sai dai ya shige ya kyale ta tayi ta masifanta har ta gaji.
  Inda ita kuma a nata ban garen take ganin tafi karfin shi ne, dan bai da yadda zaiyi da ita dole ya zauna da ita take gani yau da ta cakuma rigar shi ta baya tana kokarin kaimai duka ya juyo da sauri yana fadin Nafisa ki na da hankali kuwa ?
  Cikin shi tayi tana banda hankali sai ka fada min wacce aka ganka da ita a asibiti dazun hannu yasa ya banbare hannun ta da karfi ya jefar da ita gefen kujera.
  Zafin kishi sosai ya rufe mata ido nan ta fara ja mai Allah ya isa ya ci amanan ta ya cuce ta sai taga bayan ko wacece ke son mata katsalandan a rayuwan ta.
  Yan uwanta suna tsaye cirko cirko suna kallon ikon Allah sai yare ne ke tashi suna magana rai a bace suna nuna goyon bayan yar uwan su.
  Harara ya watsa masu sai suka fara sulalewa daga falon kowa yana barin gurin don yanayin kallon da yayi masu din .
  Sama ya hau a hankali inda yake tafiya yana jin sautin kukan Nafisa yana isa inda yake.
   Tsaye yake yana balle bottom din rigar shi a hankali sai dai zuciyar shi cike yake da mamakin waya gan shi ya fada ma Nafisa cewa ya ganshi tare da wata mace a asibitin doctor Bisi.Doctor Bisi ne ya fada a ranshi sai kuma yace No it can't be doctor bisi is a man he can do such full to me.
  Beside, ma nine na hadasu da doctor bisi din  anan don bata san kowa ba a Abuja sai zuwan da yayi da ita ne tasan kan garin.
Bayan wucewan mijin nata ciki ne ta watsa ma yan matan uku da suga rage a falon harara tace a cikin yaren su na buzaye.
  Simi simi suka mike suka bar gurin itama mikewa tayi ta bishi ciki su karasa a can sai dai ta samay shi har ya shiga wanka ko.
  Zama tayi a bakin gadon cike da masifa tana jiran fitowan shi daga wanka su aza a inda suka tsaya.
  Zancen malaman ta ne ya fado mata a rai da kyat ta yaki zuciyar ta ta dan sasauta zafin da take ji nashi koda ya fito anan ya samay ta zaune cikin masifa bai kula ta ba ya fara gyaran jikin shi kamar yadda ya saba yi idan ya fito daga wanka.
  Kallo daya yayi mata fuska a daure ya kawar da kan shi gare ta ta mike ta tako gare shi tace samad ka daina ganin laifina.
   Ni kadai ce macen da ta dace kai a duniya da ina da iko ko macen kudi ba zan bari ta sauka a akan ka ba balle macen mutum.
  Ta hade wani miyaun fitina da yazo mata a makoshi tare da fadin nasha alwashin duk macen da tayi gigin shiga gonar ka sai naga bayan ta a duniyan nan.
   Kallonta yake da mamakin abinda ta fada yaga kuma gaskiyar maganan nata har cikin kwayan idon ta da gaskiya take maganan.
    Kuma ko wacece wanan macen sai na tono ta a garin nan na nuna mata ruwa ba sa, an kwando bane.
  Juyawa tayi ta fita daga dakin a fusace bayan taja wani uban tsuki tare da rufo kofan da karfi,   binta yayi da kallo bayan ta fita ya girgiza kan shi ya tabe bakin shi gami da daga kafadan shi yace mahaukaciyar banza kawai.
  Karasa shirin shi yayi ya fara gyara gadon shi don yana bukatan ya huta don ya gaji yau sosai ga maganan Nafisa da ke ci mashi rai kishi kamar wace bata da hankali.
   Gadon ya hau ya kwanta bayan ya gama gyara yana sauke ajiyan zuciya a hankali may Nafisa take nufi da kalamin ta na sai taga bayan khadija.
  Yasan zata iya abinda ta fada mashi a yanzu karfa ya ja ma yarinyar mutane matsala a rayuwan ta don bai san abinda Nafisa zata aikata mata ba.
  Tunane yayi kada ya sare Nafisa ta samu daman da zats yi mai abinda taga dama a rayuwan shi don haka zuciyar shi ta bashi shawaran gwada Sa,an shi akan khadija ko zai yi nasara akai.
    Bai koma ta kanta ba yadda ya saba binta yana bata hakkuri har sai yaga ta hakkura yake samun saida a ranshi wanan karon sai yaji ba zai iya tunkaranta ya bata hakuri ba akan kuskuren da take tuhumar shi da aikawa ba.
  Kamar yadda Nafisa itama a dakin ta take zaune abin duniya duk ya damay ta ji take tankar tayi hauka don bacin rai wai yau samad din tane yakai wata mace asibiti ba ita ba.
  Wai wacece wanan da samad har ya iya tunkara da sunan so may take dashi may take tunkaho dashi a duniya wanda ake cewa tafi ta komai.
  Zubur ta mike ta fara zagaya dakin duk da dan cikin ta dake mata motsi a lokacin bai sa ta damu ta tuna da yadda take kaunar cikin nan ba.
   Kishi ne zalla a rayuwan ta kawai so take tasan wacece wanan yarinyar don tasan ta inda zata iya fito mata da shirin ta.
   Tana yi nata kallon lokaci don tasan dole yazo gare ta idan ta yi mai irin wanan boren nata sai dai a yan watanin nan tana ganin abubuwa suna son sauya mata sallo ga aikin ta.
   Shiko Abdul a dakin shi yana kwance barci yaki zuwa mai a lokacin tunane kala kala yayi shi a wurin Yusuf ya kirashi yana tambayan shi ko yaji yaya jikin nawa don ya kira wayana yana a kashe.
   Yace ban kirata ba don likita yace zatayi barci sosai a idan maganin ya fara mata aiki a jiki wata kila ta samu barci ne ta kashe wayan.
  Nan yake labarta mashi yadda suka kwashe da Nafisa da ya dawo gida hankalin Yusuf ya tashi yace sai nake zaton doctor ne ya fada mata tunda kace baku hadu da kowa ba a gurin.
  Yace idan shine ya fada mata kuwa yayi kuskure don cikin shi tayi don zan can za wani likita ke nan yanzu.
  Yusuf yace baka tunanen kada Nafisa ta gano a inda khadija take tayi mata wani abin yace haka ma ba zai faru ba zanyi tunane mafita akan hakan.
  Sukai sallama bayan sun gama tataunawa ga maganan ya kashe wayan yana gyara kwanciyar shi a hankali.
   Bai dade da gama wayan ba yaji an turo kofan an shigo dakin yasan ita ce don ita kadai ce mai shigo mashi daki.
  Ta karo gaban gadon ciki da mamakin ganin shi a kwance da tayi cikin rashin damuwa da ita har ta iso a gadon ta zauna tana fadin nasan ba barci kakeyi ba.
   Ya dago ido ya dan kalle ta yace banyi barci ba kuma hutu nake so a yanzu ta gyara zama tana kallon shi tace samad cikin sanyayar murya.
   Wai may na rage ka dashi a duniya may ye wanda ban maka har kake kokarin hadani da wata mace a duniya bayan kasan irin son da nake maka ba na wasa bane.
   Ta kamo hannun shi tana fadin gaba daya ka canza min a yan watannin nan ko dan ka gani da ciki ne ka dauko yimin hakan.
  Ka hana mu kwanciyar hankali gaba daya a gidan nan sai faman takura min kake yi ko yaushe.
  Sai ga hawayen da yaki zubu mata a daki yazubo mata a lokacin tace ko wacece sai na kashe ta a garin nan idan na gane ta.
   Cike da jin haushinta yace ashe ko ke ma za a kashe ki ke nan kinga matsalar ki ko meyasa ne har kullun ke baki tunane a rayuwan ki sai bakin kishi .
  Ni ina kokarin ganin ko yaushe inga lafiyan ki ke ko sai wani banzan kishi ke a gaban ki ban tsamaci haka daga gare ki ba na dauka kece mutum ta farko da zata shedi rayuwana a idon jamma,a.
    Yarinyace na kadai ta zan dawo gida in dubaki dole na dauke ta na kai asibiti doctor Bisi ya dubata ashe yariyar bata da lafiya shine ya taimaka mata.
  A rashin wayo na Nafisa  sai cewa tayi ashe wanan likitan munafuki ne shine ta kirani yana fada min wai yaga ka kawo amaryan ka asibitin shi yanzu.
  Kawai may yake nufi don ya hada mu fada yayi min wanan maganan ko may yace da yake ke baki da tunane sai ki biyewa zancen shi ko ?
  Ace  kulun mutum ba zai saka ma zuciyar shi salama ba koda yaushe sai bakin kishi ke baki hangen nesa akan ki fa duk yan uwana suke fushi dani.
  Hakan bai maki dadi ba sai kin tayar min da hankali kuuma har na tunzura na aikata abinda ban tashi yi ba.
  Tace da sauri don Allah samad kayi hakuri sherin shedan ne wallahi dana doctor Bisi sai da ta san yadda ta bashi hakkuri har ya hakura suka koma dai dai suka sulhunta kan su.
  Bai fita ba sai washegari bayan ya gama abinda yakeyi ya fice a gidan kiran Auta tayi ta fada mata ta koma kusfa ta fada ma malamin ta ya duba mata idan akwai matsala.
  Sai da ya duba wasu file ya dan huta tare da kiran layina maryam ce ta dauki wayan tana fada mashi ina bandaki amma  naji sauki.
  Bai kai ga magana ba tace gani nan ma na fito tana mika min wayan tayi tana fadin yaya Abdulsamad ne a layin.
   Karba nayi tare da kara wayan a kunne nace hello cikin murya kasa kasa yace yaya jikin naki nace da sauki baki je class ba ke nan nace sai anjima zan shiga.
  Kin karya ko nace yanzu zan karya dai to idan kin karya kisha maganin ki zan shigo idan na rage aiki zuwa yamma in dubaki.
  Nagode na tsunci kaina da fadi Allah ya sauwaka ya fadi yana kashe wayan maryam tana gefe tana sauraren mu bayan ya kashe wayan na zauna saman katifa tare da kaiwa kwance.
   Tashi kisha tea din kada yayi sanyi gashinan na hada maki yamutsa fuska nayi nace miko min in sha bakinane bana jin dadin shi har yanzu.
  Daure dai kisha ko kadan ne sai kisha maganin ki gashi ta mike tana dauko min ledan maganin dake aje a gafen kayana.
   Tea din nasha tare da hade magani na koma na dan kwanta wayan daddy ne ya sake shigo min yana tambaya na ko lafiya jiya tanemi wayana yaji ta a kashe.
   Daddy iam sick yace may ke damun ki khadija murmushi nayi nace naji sauki ai period time dinane yake damu na amma kin je asibiti yace ?
  Naje daddy wanan mutumin ya kaini asibiti jiya yace good zan buga inyi mashi godiya don kwana biyu bai kirani ba yace nace bai kasan ne daddy ya kara da Allah ya sawaka ki kula da kanki ki abinda kika je yi khadija insha Allahu daddy na gode ka gaida mama.

Madam ranan a gidan Nafisa ta wuni sun kule a dakinta suna jiran kiran Auta daga zaria suji abinda malam zai fada masu.
   Madam ta kawar da shirun da cewa wai shi wanan mijin naki wani irin mutum ne da baijin magani haka sai anyi kamar an samu kanshi sai abu ya zo daga baya ya can baki daya.
  Tace shike damu na madam dubi irin kudin da nake zubawa akan bawan Allah nan sai naga nasara daga baya sai komai ya lalace.
   Komai zan iya yi akan Samad din in dsi zan samu ya kawar da ido akan ko wace mace a dunuyan nan.
  Madam tace idan shiya kawar da idon shi a kan mata su matan kina tsamani zasu kawar da ido su ne akan shi dole suma dole da tasu shirin da suke don suga sun kamo shi.
  Don shegen kyau da daukan hankalina da wanan mijin naki ga abinda mata keso a tare dashi kudi da kyawo da hali.
  Hankalin Nafisa ne ya tashi sosai da maganan madam tace wallahi da ina da hali da boye shi zan dinga yi a gida.
  Dariya madam tayi tace idan kika boye shi kuce may ke da yan uwan ki Nafisa karki matanta shine hannu da kafar ku kaf zurian ku.
  Yanzun dai zan tafi Ondo ance akwai wani boka acan may aiki kamar yanka yuka wata kawatace ta gano hakan.
  Nikan ina can na dan samu karfin jikina shiryawa nayi zan leka cikin makaranta don kada a wuce ni da karatu da nazo yi.
  Daddy ya kira Abdul yana mashi godiyan kaini asibitin dayayi yace ba komai insha Allahu zai kula dani kamar yadda zai kula da kaunar shi.
   Bayan ya gama abinda yake ya kira Yusuf don su leka wurina kafin yaje gida Yusuf din yabar abinda yakeyi yazo suka tafi.
   Sun samu na dawo ke nan ya kirani a waya na fito na samay su a waje lokacin da na karaso wurin su na samu suna magana suna kallon laptop din dake a saman kafan Abdul din nasan wani abu suke duba a ciki.
   Karasowana suka bar abinda sukeyi din tare da maida hankalin su a gareni Yusuf ke fadin lalai jiki yayi sauki kauna na sai dai har kin dan fada kadan wallahi.
  Murmushi nayi na dan jingina jikina ga motar su nace naji sauki sosai yusuf yace barin in dan je can inga shagon yan makaranta indawo ina son duba wani abu a gurin.
  Nasan yayi haka ne don ya bamu wuri mu gana dashi wuce wanshi yace dan gyara zama yana fadin abin ya daina zuba ke nan ko ?
   Harara na aika mai tare da fadin ban sani ba sai ka fito ka duba ai tunda kana son sani ne sai yau naga dariyan shi yace kin dai ji abinda likita ya fada saukin abin ai.
  Banji ba kuma bana son naji tunda ba kai ke da lalurar ba au yanzu tunda kinji sauki kina da bakin magana ashe jiya fa nan kike ta murdemurde ina tausaya maki.
   Kawar da kainayi gefe guda ban bashi amsa ba na share shi yace na tambaye ki jiya ciwo ya hana ki ban amsa na.
   Nace may ka tambaye ni jiya din yace kwana nawa kike dauka kina off shiru nayi tare da bashi ba a raina ina fadin wai shi baisan ina matukar jin kunyanshi bane da yasan abin dake damu na.
  Gashi kuma ya tsare ni da tambaya irin haka da zai sani jin kunya da nauyin shi ai wanan kamar kamar yar iska ya dauke ni.
   Niko gidan mu in badon ciwon mara ba har zanyi in gama basu sani ba ji nayi yace may nene abin jin kuya kibani amsa na kawai don ya kama ne in sani.
  Nace don Allah yaya Abdul ka daina wanan zancen naji yace na daina tunda baki son zancen yanzu.
  Badai kina shan maganin ki ba akai akai nace ina sha na gode daddy ma ya bugo waya nake fada mai ka kaini asibiti yace zai kiraka yayi ma godiya.
  Yace ya kirani ai dazun sai danace mai kaina nayiwa aiki ba sai ya godd min ba nace ka fada ma daddy hakan ?
  Yes ya dace ne in fada mai don lokaci yayi da zai fahinci hakan daga inda Yusuf yake tsaye yake kallon mu yana jin farin ciki a ranshi.
  Hikimar yin haka da yayi ke nan a gusa daga wurin don mu samu daman sakewa da junan mu don idan yana wurin komai bazai wakana ba a tsakani karshe ma muna iya yin abinda muka saba fada ke nan.
  Ka samu zuwa duban su Affan kuwa na kawar da zancen da wanan tambayan murmushi yayi yace ban samu komawa ba sai dai na fara shirin komawa.
   Sai dai wanan karon ban san wani shiri kikai ma tafiyan nawa ba idan zan koma nace dama idan zaka nike shirya maka tafiyan.
  Yanzu shirin ya dawo kan ki don haka kece mai shirya komai ta wanan bangaren ya kamata ace na fara maki albashi a wanan bangaren don kin ci hakan a gare ni .
   So ki fara shirya min nan da two weeks zan tafi ina jira inji shirin da kai ma tafiyan nawa da abubuwan da zan yi a can.
   Yusuf ne ya iso gurin yana fadin mu tafi ko kada lokaci ya kure maka anan tunda munga lafiyan kaunar tawa sauki ya samu.
   Har kagama duba shagon nace mai yace ko dai in koma ne kada in takura maku kuna hiran ku na jin dadi zan katse ku kai haba yayana wani hira kuma a haka ?
   Ni dai daukar shi ku tafi kada yar buzaye tace ina shigewa mijin ta yanzu Abdul yace kina tsoron ta ke nan ?
  Nayi saurin fadin tsoro fa tsoron mace yar uwana kuma macen ma kuma buzuwa da kyau kauna ta haka nake son naji mace jaruma wallahi.
  Kai kaji ya juya wurin Abdul din yana fuskantar shi tare da fadin na fada ma kauna ta jaruma ce ba irin ka ba mai tsoron buzaye yan haure.
   Idan bata tsoro ai sai mu gani a kasa ba cika baki a nan ba nace ko agaban ta wallahi zan cika baki idan ya kama in cika akan may zanji tsoronta ne wai ?
  Mace ce fa yar uwata kowa sai ya gwada sa an shi yayi mai fishe shi duk abinda take takama dashi wallahi ni khadija ina dashi fari kyau da tsayi kagako ba zanji wani shakkata ba.
  Irin kallon da yake jifana dashi daga cikin motar yasa nayi shiru dole don kallone da ke dauke da fassara irin mai nuna feeling ga mutum din nan.
   Mun gama shan matan juna suka ja motar su suka tafi ni kuma na koma ciki tare da tunanen da yawa a raina na canjin yanayin da na hango a kwayar idon shi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
          SEENABU

Kamar yadda yace nice mai tsara mashi tafiyan haka yasani a gaba dole sai dana tsara mashi zuwa gidan da zai yi da abinda zai kai gida.
   Da farko na dauka zolayane sai da naga abin nasa da gaske ne na tsaya na tsara da taimakon maryam nayi komai.
   Wanan karon bai sai kayan tsaraba ba kudi muka tsara zai bayar idan yaje sai abincin da zai sai ma iyayyen shi don rage ma mahaifin shi nauyi.
  Da yamma lis suka isa kaduna don haka ya wuce gidan shi bai shigo wurin su hajiya ba sai da safe bayan ya karya ya shiga gaida su.
  Sai da yagama gaida abokan zaman hajiya suka wuce nata part din dake daga can ciki yana fuskantar part din mommy.
   Sai dai tsakanin su akwai dan filin tsakar gida da shuke shuken filawoyi a gurin da wani babban icen ambrale dake basu innuwa a gidan.
  A kofa su kai sallama ta amsa masu daga ciki suka shigo ko ina na falon tsab yake sai kamshin turen wuta dake tashi a falon.
  Tana zaune tare da kannen shi Binta da zainab su uku a falon gaida shi kannen nasa keyi ya amsa masu a tsatsaye tare da zama saman center capet din falon shi da Yusuf.
  Gaida hajiyan sula farayi a cikin ladabi inda hajiyan ke nuna farin ciki da ganin su tare da fara,a a fuskanta.
   Tana man kamar yadda take a cikin gyaran ta ko yaushe atamphar super ne ja a jikin ta babu wani alamar tsufa ko girma a tare da ita hutu da jin dadin da mijin su ke basu ya kama ta.
  Cike da kula take amsa masu tare da tambayan da Nafisa suka zo ne Yusuf yace su kadai suka zo don Nafisa cikin ta ya fara girma yanzu.
  Tace cikin mamaki ciki ke ga Nafisan bamu sani ba mu tana kallon su cike da kulawa Yusuf yace wallahi hajiya ai cikin ma yanzu zai kai wata shida ko bakwai.
  Ikon Allah to Allah ya raba lafiya ashe da baka fada yanzu ba da sai dai muji haihuwa kawai.
  Yace ba akai ga haka ba ai hajiya zakuji ne don dai ba a tare ne Affan ne ya shigo falon bai mai da hankali shi wurin su ba sai fada ma hajiyan dayayi a jiki yana fadin wai yaji ciwo a waje.
   Tace baka ga Abban ku bane Affan daba gaida su ba yaron ya dan kara lafewa a jikin kakan nashi Yusuf yace malam Affan kuna lafiya ina daddy yake ?
   Hajiya ke fadin maza ka gaida Abban ka da baban ku daga jikin kakan yace ina wuni bazakaje kusa dasu ka gaida su ba in ji Binta dake dagawa daga inda take zaune zainab ko sai charting take a wayan ta.
  A dadare yaron ya isa gurin su yana kara gaida su Yusuf ya jawo yaron a jikinshi yana tambayan shi dan uwan shi yace yana gurin mommy su.
  Hajiya tace ai shi wanan dan lake ne tunda uwar tabar gidan ga ta koma gidan su kullun yana can like da ita.
   Da sauri Yusuf din yace hajiya Fati ta koma gida ne kuma tace to mu rike ta ne nan tunda abin yaki ci yaki karewa haka.
  Ai gara dai ta koma gida ko hankalinta zai kwanta a can anan taki ta sake sai rama da takeyi kullun Abdul ya mika hannu yana tambayan yaron labarin makaranta.
  Yayin da Yusuf da hajiya ke magana akan komawan fati din gidan su yace zamu lekata kagin mu koma abin ne sai an hada da hakkuri.
   Don Fati taki tayi hakkuri da yanayin Nafisa amma ai ita ta zabi ta zauna nan kaduna cewan ta hankalin ta yafi kwanciya da nan din.
   Wayan zainab dake gefe ne yayi kara ta dauka tana fadin Khadija Adamu wallahi nayi fushi dake ai tana mikewa ta shige dakin su.
   May wanan yarinyar ta bugo ta fada ma zainab yanzu ko dai komai da sanin su take aiwatar wa yace a zuciyar shi sai ga khadijan ta fito tana hajiya ga khadija na son gaida ke.
  Ta amshi wayan da faraa a fuskan ta muka fara gaiswa da ita ba wani dogon magana bane gaida ita kawai nayi tana sa min albarka.
  Ta mikama zainab wayan ta ta sake shigewa ciki shiru falon yayi sai hajiyan ne ke fadin yar albarka yariyar na da hankali sosai wallahi.
   Ta juya tana fadin yarinyar nan da nasa ku rage ma hanya wani lokaci da zaku koma abujane Yusuf yace oh khadija tana da kirki sosao wallahi.
  Ai nikan dan leka ta wani lokaci mu gaisa idan na samu lokaci tace ka kyauta haka ake son mutum ya zaba ma kanshi abu na gari.
   Yace hajiya babu komai a tsakanin na da ita wani dai ma yake raayin ta yanzu haka don yabawa da hankalin ta da yayi har lokacin hira yake da dan shi dabai sake jiki dashi ba.
  Ya dago kai yana fadin hajiya ko Abba ya fito yanzu mu gaisa dashi kafin ya fita tayi murmushi tace ai yanzu Alhaji ya rage fita kasuwa don yanayin girma da kuma jikin shi yana gida koda yaushe.
  Binta ta kwala wa kira tazo ta kira mata mommy a dakin ta don tai masu iso gurin Alhajin mommy ta shigo tare da Binta dataje kiran ta hajiya ke fadin dan ki zaki wa iso gurin Alhaji wai.
   Mommy tana murmushi tace kai hajiya sai kace wani bako a gidan Alhajin yana nan falo ya fito yanzu ma na baro wirin sa ta juya ta fita zuwa fada ma Alhajin zuwan su.
   Sai lokacin ya dubi hajiya yace wanan karon ban riko komai ba yana sa hannu a cikin aljihun shi yace ga dai kudi a kasa fa aba su mommy dubu daridari sai yaran nan a raba masu dari biyu ke kuma ki dauki sauran ya zube kudin a gefen mahaifiyar sai kuma abinci da anjima za a shigo dashi.
  Ta kasa boye farin cikin ta nan ta shiga saka mai albarka mommy ne ta dawo dakin tana fada masu su shiga yana jiran su har mommy ta juya hajiya tace .
  Mommu yara da alama adduan mu ya fara kana dan ki yanzu ga kudi ya kawo a raba ga kuma kayan abinci a tafe.
  Komawa mommy tayi dakin tana fadin kai madallah Allah mun gode maka da dan mu ya fara dawowa gare mu.
   Haka ake so wallahi amma da babangida kamar wanda baida kowa a duniya da gatan ka zaka bari shedan yana rudin ka.
  Ga dan uwaka nan Suraj sai shine ke bamu talafi bawai don bamu dashi ba don nemawa kansa albarkan mahaifa kawai don Allah aci gaba da kula da hakkin mahaifa dana.
   A da ya tsani mommy sosai don yana ganin nuna mashi kulawan da take kamar duk a munafunci ne sai yanzu yake fahintar halinta ne kawai a hakan ga yaran gida musanman na hajiyan su da takan nuna nata ne.
  Ita mommy Allah bai bata haihuwa da yawa a gidan ba daga Sadiq danta na fari sai salma kuma ba wasu manya bane sosai yanzu ma suke a secondary.
   Yace mommy in sha Allahu za a gyara kwanan nan ma zaki tafi abuja wurin mu don Nafisa ta kusa haihuwa ke nake son kije tare da iya na zaria ku zauna a gidan.
  Ba mommy ba har hajiya sai da tayi mamakin jin wai yau Abdul ne da kansa ke fadin wani nasa yaje gidan shi ya zauna don matar shi da zata haihu.
  Kirikiri a baya tace bai yarda kowa nasa yaje gidan shi ba don suna zuwa suna tayar kashi da hankali a gidan shi haka Nafisa ta fada mai a baya.
  Hajiyan su ce tace yar ikon naka tasan da haka kuwa yace haba hajiya sai ta san da hakan mahaifana da yan uwana zasu zo gidana.
  Idan na gama shiri zan aiko a dauke su yanzu idan na shiga gurin Abba zan sanar dashi bukatan hakan don ba zan so ta haihu babu wani dan uwana a kusa ba.
  Allah ya kaimu mommy tace da murnan ta fita daga dakin cikin farin cikin canjin da suka gani gareshi.
  Wayan shine yayi kara ya mike yana amsawa ya bar Yusuf a gurin hajiyan Yusuf yace hajiya muna bukatar adduan ki kamar kulun yanzu haka akwai yarinyar da Abdul ya fara so ina ganin zata iya zama da Nafisa.
   Duk wanan shiri nane don ba mace matsoraciya bane zata iya gwabzawa da halin nafisa ba don haka a tayamu da addua akan zancen in lokaci yayi nasan zakifi kowa farin ciki da zancen.
   Hajiya tace ashe ba batun mayar da Fati kuke yi ba ku wani tashin hankalin kuke shiri daukowa yace hajiya wanan shi kadai ne nake ganin mafita ga alamarin.
  Tace to shike nan addua dama kulun munayi Allah yasa hakan shine saukin abin amma dai wanan yarinyar ta cuta muna da yawa a rayuwan mu.
  Babu komai hajiya komai ya kusa zuwa karshe insha Allahu Allah yasa tace ya mike tana mashi godiya ya fita ya samu Abdul din a waje suka wuce wurin alhajin shi.
   Da sallama suka shiga dakin na Abba yana zaune saman kujera yana duba wayan shi ya dago kai yana amsa sallama tare da kallon su ta cikin farin glass din shi idon na medical.
   Kasa suka zube suna mika gaisuwa ga Abban girma da kuma ciwo ya ramar da Abban don mutum ne mai jiki a da yanzu ko girma da ciwo yasa duk ya zube.
  Sun gaisa sosai sabanin da da in yazo gaida Abban yake amsa mai a dadafe ba wani saki a fuskan shi.
   Ya aje wayan tare da mayar da hankalin shi gare su magana yake irin na dattako yana tambayan su yaya aiki da iyali suka amsa da lafiya kalau Abba Alhamdullahi.
  Kallon da yake masu ne yasa suka san da magana a bakin Abba din jikin Abdul yayi sanyi yana tunane a ran shi may kuma yayiwa Abba din yake mashi kallon tuhuma a yanzu.
   Yasan dai ba wuce maganar yar aminin shi ba da yake ganin yayi mata ba daidai ba shi dai Fati taja mashi kiyayya a gun mahaifan shi yanzu komai yake masu baya fari a gare su.
  Gyara zama yayi yana kallon Abba din don jin abinda zai fada masu Abba yace Yusuf zan iya cewa yanzu Alhamdullahi    a yadda naga abokin ka yana waiwayan mu akai akai.
  Ko ba a fada ba alama ya nuna cewa yanzu ya fara samun kwanciyar hankali a tare dashi shidai Abdulsamad ya zuba ido yaji karasan magana shi.
  Abba yace ya na dade ina jiran wanan ranan tun ban mutu ba ranan da zaka gano gaskiya ka dawo a cikin hankalin ka irin haka.
  Wanda nasan ba yin kan ka bane don ba haka muka tarbiyarta da kai ba da farko don haka nake son ka kara natsu ka tsayar da ibadan ka duk wani abinda zakayi kada ka manta da yawan addua a tare da kai don shine jagoran rayuwa ko ba haka ba ya tambaye su.
  Lokaci guda suke kada ma Abban kai tare da fafin hakane Abba , murmushi Abban yayi masu yace to yanzu saura maganan iyalin ka zan so inga ka hada kan iyalin ka a wuri daya.
  Kamar yadda ka taso ka gani a gidan nan kasan hakan shine cikar kamalan ko wani magidanci aga yana ba ko wace mace hakkin ta daidai gwargwado.
  Suka ce hakane Abba, Abban ya dan tsura masu ido yayin da kanun su yake a kasa suna sauraren shi Abban yace kai kuma Yusuf na dawo gare ka mai kake jira har yanzu baka maye gurin matar ka da ta rasu ba shikenan kana nufin ba zaka sake aure ba a rayuwan ka ko may.
   Yusuf din ya dago da sauri yana fafin ba haka bane Abba zan sake insha Allahu da zaran an gama na Abdulsamad dake tafe.
   Au Abdul din aure zai karane kuma Abba ya tambaya sai Yusuf yayi kasa da kai yana fadin insha Allahu Abba basu gama daidaitawa bane da yarinyar shi yasa bamu gabatar maku ba tukun.
  To madalla ka nuna ka gado gida ke nan to yaya maganan Fati kuma fa may ake ciki game da alamarin ta ?
  Abba insha Allah zata koma daki ta ba da dadewan nan ba akwai abinda muke tsarawa a kai ne yanzu to Allah ya bada sa a sukace amin ya kara da fadin a kula da hakkin akai dai.
   Insha Allahu suka fadi suna mikewa ta  ciro kudin da ya ware na Abba ya nufe shi yana aje mai a gefen kujeran da yake zaune a sama.
  Suna fita dakin Abba suka sallami mutanen gidan suka fice a gidan Abdul yace Yusuf yaya zakai min haka kace wa Abba wai aure zan kara kwanan nan ?
   Idan ba haka na fada mai ba kana ganin iya abinda zai fada muna ke nan a yadda yake kallon mu din nan shine kawai mafita ai kai kasan ba auren zaka kara yanzu.
  Bai yi magana ba ya bi bayan shi yana murmushi don yasan ya kulu dashi sosai da yamma motar kaya ya tsaya a kofan gidan Yusuf yasa akai ta shiga da kayan cikin gida.
   Kowa na gidan sai farin ciki duk da zaman kishi dole na ciki na ciki a ransu ganin sauyin da yayi hakan bai hana a kebe gefe ai gulma ba tsakanin ummi da anty Amarya.
  
Nafisa da madam murnan tafiyan shi kaduna a satin  sukayi don dama kafan zuwa ondo take nema don Abdulsamad ya hanata tafiya yanzu ko ina.
   Tafiya sukayi sosai tun suna na dadin rai har ta fara galabaita ga tafiya don dan karan nisan da garin ke da tsakanin shi da Abuja.
  Bata dauka nisan shi yakai haka ba sai da suka fara hanya duk wanan bakar wahalan bai sa ta janye kudirinta na zuwa wurin wanan bokan dataji ana yabon aikin sa ba.
  Ko da suka isa ondo da safe wani motar suka kara bi zuwa kauyen da bokan bayaeraben yake zaune  sun isa a wahalce don har amai da zazzabi sai da tayi a hanya.
   Sun isa dajin mai kama da gari da baifi yan gidaje a kirga ba sai da suka huta kafin su samu ganin bokan don ranan suke son su koma Akure su shiga motan dare su koma abuja.
  Bayan ta gama fadin abinda take son yai mata  nan boka ya fara surukule shi ya dago yana kallon ta na dan lokaci.
  Sai duk suka tsargu da irin kallon da yake masu wanda ke nuna akwai magana kai ya girgiza sanan yace aikin ta akwai dan wahala a cikin sa.
  Don yanzu haka mijin ta yana tare da wata yarinya sai dai bai hango soyayya tsakanin su ba amma akwai aure har da haihuwa a ciki.
Kirjin ta ta doka tana fadin ta shiga uku ita samad zaiwa kishiya wacece zai aura har su haihu ?
  Sam ta mace da Fati ma mallakin mijin ta ne har da diya shi boka Allah bai bashi ikon tsafin shi ya hasko ni ba nan tasa ai mata aikin da za a raba tsakanin shi da ko wacece .
  Akuma fitar da ranshi ga ko wace mace a rayuwan shi sai ita kadai ya kara yin saddabarun shi na bokayen da suka gwane da tsafi yace ya ga wata mace sai dai baiga gaban ta sai bayan ta kamar tana son shiga rayuwar mijin ta amma dai bari ya mata aiki akan wace ta baiyana in yaso daga baya aikin da zaiyi zai gusar da waccan matar da yaga bayanta din.
  Tace tana son koda kashewa ne a kashe mata wace aka gani ko a haukatata gaba daya kowa ya huta.
  Yace an gama sai dai aikin ta na da tsada sosai tace kada yaji komai indai aikin zaiyi kyau nan ya shiga hada mata irin nashi surukulle da bayanun yadda zatai amfani dashi ba tare da kuskure ba.
   Yace ba mijin ta ba wata mace da zai duba a duniya muddin tayi abinda ya fada mata daidai suka kama hanya komawa gida bayan ta cika shi da kudi.
  Sam bata san Abdul kwana biyu zaiyi a kaduna ba lokacin da Abdul ya iso gida ya neme ta sai cewa sukayi ta tafi unguwane.
  Har ya shiga ya huta ya dan kwanta bata dawo ba ran shi ne ya baci sosai da ita yaji yana son fita don haka ya shirya ya fito dan yasan kafin ya dawo ta dawo gida a lokacin.
  Sai dai abinda ke bashi mamaki baifi ganin motocin shi duka dayayi ba a gidan yana tambayan kan shi da wace mota nafisa ta fita ?
  Yana fita batare da sanin inda zai tafi ba har ya yanke shawaran zuwa wurin Yusuf sai ya fasa don ya san yanzu shima hutawa yake a gidan shi kada yaje ya damay shi.
  Sai kawai ya yanke shawaran ya leka khadija don ya kwana biyu da ganin ta hanyar hostel din mu ya dauka sai da ya iso ya kira waya gashi abakin hostel.
   Nace da yamman nan yace na koma ne nace gani fitowa yaja iska ya kashe wayan na fito ina tako dadaya wanda ni ban san inayi ba ma.
   Na karaso wurin motar cikin yar murya na nace dashi sannu da zuwa baki maraba da zuwa na bane ko may ?
   Murmushi nayi tare da fadin naga baka fita a wanan lokacin ne kawai har ina da lokacin fitane na daban da ban sani ba yace shigo mota mana.
  Ina shiga sai kawai ya tayar da motar nace da sauri sata na zakayi ko may ?
   Bai bani amsa ba yaci gaba da kallon titi may zan sata anan, nace mutum, dariya yayi yace kan nan naki kuwa zaiyi kudi sosai nace ai kafin ka sai da nawa ka fara sayar da na buzuwar ka ita bakuwar haure,
  Kuff naji yake ma bakina dan bugu da sauri na dafe bakin nace saboda buzuwa ka dukar min baki ?
  Yace ban san hadinki da wanan buzuwar ba nace halinta halinta bai mun bane don tana da ji da kai da son wullakanta mutane.
  Ita abi kyama ba a kyamace ta ba sai itace zata kyamace mutane matar tawa ce abin kyama khadija ?
   Ba ita duk buzaye abin kyama ne gare mu yan Nigeria sai iri kune dake mai dasu mutane kawai baku kyaman su don su din ba abin yarda bane mazan su da matan su.
   Sai mutum ya yarda dasu daga baya su zo su yaudare shi yaudara a wurin su ba abin kunya bane don su din basu da kunya ko kadan.
   Shiru yayi yana tunane a ran shi bai bani amsan magana na ba nace kuma gasu da son raba mutum da yan uwan shi su cika gida da nasu yan uwan.
   Ga kazatar tsiya da son mamaye komai ya koma nasu su kadai koda kuwa  sun samu wasu mata ne a gidan shiru nayi don na dauka bai saurare na a lokacin.
   Sai naji yace uhmm go on yaya kikai shiru ba labari kike bani ba nace au na dauka baka sauraro na ai gasu da dan banzan bin malamai da bokaye basu yarda da kowa ba sai kan su suna iya yiwa yan uwan su yankar baya su zauna da mijin yar uwar su.
   Zasu iya ketarowa da auren su suzo su auri wani anan alhalin duna da mazan da suka baro a gida sai lokaci lokaci suke lekasu.
   Kai bazaye muggan mutane ne sosai wallahi duk wayon ka zasu san yadda suka juya ka indai na miji ne ji nayi ya tsayar da motar da karfi yace bari inyi sallah please sai kici gaba da bani labarin ki.
  Fita yayi a motar ya nufi wani gu sai yanzu na duba naga ashe massalaci ne a wurin shiga yayi a ciki na mayar da kaina akan sit din motar ina kallon mutanen da ke gurin.
    Ya dan jima a ciki ya fito ya shiga motar ya kama hanya mun dan taba tafiya ba tare da nasan ida zamu nufa ba.
   Yace bissimila cigaba da labarin ki nace labarin yai ma dadi ke nan kwarai kuwa ina jin dadin labarin sosai nace toba zan kara fada ba.
  Don may ko don kar naji  halin buzaye nace ba wanda baka sani ba a cikin wanan kai da ke da ita a gida may ya rage da baka sani ba.
  Ina ga saura bani kuddi baba ko a yaye ka kafa ka wayi gari ka samu ta ketara kasan su da dukiyar ka.
  Yace da taci rabon ta ashe idan ta iya ketara kasa da dukiyana duka eh tunda a banza kake samun kudin yace haka kike zato ashe ?
   Ni ba ragon namiji bane ko da yaushe ina tsaye da kafana wurin neman na kaina zaune a office din nace mai.
   Au haka kike dauka na ni ko a gidana nake ina neman na kai na nace gun buzuwa ke nan kai ya girgiza min.
    Koda yake dama abinda kuke nema a wurin su na daban ne da sauri ya juyo yace may muke nema a gun su nayi shiru tare da kawar da kai gefe.
Fada min may muke name muka aure su nace su mana tunda irin su ne ku din jara, , , , shiru nayi karasa mana ina jin ki.
   Hannu yakai yana kamo min baki nayi saurin rike hannun nashi a karo na farko dana taba taba jikin shi da sauri na sake hannun nashi.
   Na kawar da kai na gefe hannun nashi ya duba a hankali sai naga ya sauke murmushi a fuskan shi yace how lucky you're ?
   Ke ce mace ta uku da na taba hada jiki da ita a duniya nace nima ina regreting din hakan da nayi wallahi.
   Shiru mukayi yaci gaba da tuki wani guri ya shiga  da motar mai yawan ginene gine da sasa da yawa yace kin san wanan gurin tsoro ne ya kama ni dana kalli gurin sai na dauka ko hotel ne.
   Kai na girgiza alaman tsoro ya kamani sai naji yace nan ne ma,aikatar mu wanda daga MD din mu sai ni a gurin.
   Da sauri na kalle shi yace ko kina bukatan shiga kiga gurin da sauri na girgiza kaina nace a,a don Allah ka mayar dani hostel inda ka dauko ni.
   Ai bamu gama ba don baki ban amsata ba da sauri nace tamay yace irin mu da kika fara fadi baki karasa ba nace maganar yawuce ai.
  Yace a gunki ya wuce ni a wurina bai wuce ba sai naji karasan maganan ki ko mu kwana a nan da sauri na dago ina kallon shi don Allah dai kayi hakkuri ka mayar dani inda ka dauko.
  Maimakon yayi abinda na nace sai naga ya gyara set din motar ya kwantar dashi tare da sa hannayen shi yayi matashi dashi yakai kwance.
   Muna wurin shiru ba wanda yai magana a cikin mu sai tsukin da nake ja can yace a kasalance kada ki kara jamin tsuki a mota yanzu na fitar dake na wuce.
   Kayi hakkuri don Allah ka maidani hostel ina da exam next tomorrow ban son in fadi wani mutum ne ya dun faro inda muke yana haska toci a hannun shi.
   Ni dake zaune nake iya ganin mitumin dake tafe nace ga wani nan yana zuwa gurin nan fa bai damu da abinda nace ba yana kwance abinshi yadda yake.
   Har mutumin ya karaso ko ya sheda motar shine sai naga ya dan tsaya daga nesa damu yana fadin barka da dare yallabai an wuni lafiya cikin harshen turanci.
   Ya dago yana amsa mashi da lafiya kawai sai mutumin ya juya ya koma ciki ban san na firgice ba sai bayan wucewan mutumin yace lafiya kika shige min a jiki haka ?
   Ko kina son jin abinda buzuwa ke ji ne ajikina ta leke min da sauri nayi kokarin jaye jikina dana dan manna da nashi sai naji ya riko ni.
  Ta yadda har muke iyajin saukar numfashin junan mu a lokacin ka sake ni don Allah wai may kake nufi da nine haka wai ?
   Fada min amsan tambayana mubar aurin nan kada masu gadin nan su dauke ni dan iska nace sake ni in fada ma to yace sai kin fada jin irin rikon da yaimin yana kara manna ni a jikin shi nace jarabbabu irin su mana.
   Sake ni yayi ya daga bai ce komai ba ya tayar da motar muka bar gurin sai da naga mun hau titin da zai sada mu da hostel din mu hankalina ya kwanta dashi.
  Don yadda a lokaci daya naga canjin yanayi a gare shi ya firgitani ainun sai da muka dauki hanyar hostel din yace ki shirya shiga cikin jarababbun mutane daga yanzu.
   Ban iya magana ba bukata na shine inga kafata a kasa yanzu a wani shago ya tsaya ya shiga har ya dan dade sai gashi ya fito ina hangen shi tun daga nesa na raya a raina Allah yayi halitan namiji a nan .
   Baya ya bude aka saka mai kayan a ciki ya sallami yaron ya shiga muka tafi bakin hostel din mu ya tsaya bai bude motar ba niko a kage nake da in fita daga motar.
   Yace zan yi tafiya may yuyuwa baza mu hadu ba sai idan na dawo Allah ya tsare hanya nace dashi tare da kallon shi ya bude min motar.
   Kina level nawa yanzu a karatun ki nace two a takaice yace yayi nisa da yawa gaskiya nace ai ni ke yi ba wani ba ban ga amfanin karatun ba a guna amma ai naga su Binta da zainab sunayi suma ?
   Wanan matsalar su ne ni nawa matsalar na sani  bata wani ba su ya shafa wanan bani ba amma kai mugu ne ko ?
  Zaki iya ba kan ki amsa idan kin so ko wani kalar nake ya bude min motar tare da miko min ledojin dake bayan motar ina karba na fice ina fadin mugu kawai da karfi.
  Girgiza kan shi yayi ya tayar da motar ya tafi sai da ya fara tafiyane tunanen Nafisa ya zo mashi a rai yana tunanen ko ina taje dazun ya dawo bai samay ta a gida ba.
   Ya iso gidan ya shiga a falo ya samu su Hadiye zaine suna hira suna ciye ciye gaishe suke da dawowa yace Nafisa ta dawo sukace bata dawo ba ya shige ya barsu a gurin zaune.
  Ya shiga ran shi a bace ya dubi lokaci yaga tara da wani abu na dare goma saura kadan wanka ya shiga yana tunanen Nafisa a ranshi har ya fito ya kwanta shiru ba Nafisa.
    Ni na fado mashi a rai jarababu irin ku murmushi ya danyi yana rufe idon shi kamshin turen oud dina yake tunowa daya shaka.
  Ya lumshe idon shi tare da gyara kwanciyar shi yana lumshe ido yaji dadin kasancewa mu a tare yau hiran da nake mai na buzaye ne ya dawo mashi a rai.
   Ba abinda na raga daga halin da yasan Nafisa dashi zai iya cewa kila wani ya fada min kadan daga cikin halinta daya fahinta.
   Sai dai abinda ya tuno inda nace suna barin mazan su a gida su zo duniya su auri wani mijin na daban sunayi suna zuwa ziyarar mazan nasu.
  May wanan maganan yake nufi kodai shiyasa Nafisa take yawan ziyaran gida akai akai bai sani ba da sauri ya kawar da wanan zancen kada zargi abinda bashi ba yashiga zuciyar shi.
   To wai ma ina Nafisa taje ne uban may tafitayi da tun safe har wanan lokacin bai ta dawo ba yaja tsuki yace zan gwada ma Nafisa matsayin ta na mace a gidan nan.
   Goma, sha daya shabiyu saura ya mike zubur hankali a tashe ya mike yana zura riga a jikin shi ya sauko zuwa kasa komai na falon a kashe yake .
  Su hadiye sun shige dakunan kwanan su kayan da sukaci abinci gurin babu kowa a wurin tsuki yaja ya fita waje ya nufi gurin maigadi yana tambayan shi ko yaushe nafisa tafita a gidan.
  Maigadi yace rabon shi da ita tun shekarajiya da kawar ta tazo suka fita komawa yayi ciki yana tunanen tun shekaran jiya da kenan Nafisa dama bata gidan tun lokacin da shima yayi tafiya ko may ?
   Kamar zai tayar dasu hadiye ya tambaye su sai kuma ya fasa ya koma ya kwanta suna barin mazan su a gida su je wani guri su kara aure suna yi suna ziyarar su.
  Abinda ya fado mashi a rai ke nan karfe daya agogon da ya kalla ya nuna mai da sauri ya mike zaune biyu saura na dare yaji ana buga gidan maigadi ya bude kofa motar ta shigo sai ganin nafisa yayi ta fito daga motar ta dan tsaya suna magana da ta cikin motan.
   Ta shigo gidan a gajiye take kafafuwan ta har sun dan kunbura saboda zaman motan da tayi mai tsawo dakin su hadiye ta fara zuwa.
   Ta samu suna barcin su hankali kwance ta ta da ita a cikin magagin barci tace kin dawo da yare tace na dawo bata gane komai a guta ba ta juya zata shige tace Alhaji ma ya dawo dazu da safe.
  Dam taji gaban ta ya fadi da sauri ta fita zuwa dakinta ta kayan sihirin da ta dawo take kokari boyewa a wardrobe din ta sai taga an kuna wutan dakin ta.
   A fusace ta juyo sai ganin Abdulsamad tayi tsaye yana kallon ta da sauri ta kara gare shi sai yayi saurin juyawa ya fice daga dakin .
   Boye kayan ta karasa yi ta rufa mai baya ta murda kofan dakin a rufe taji shi gam ta juya zuwa dakin ta ciki da fargaba da tsoro a ranta.
   Washe gari ta samay alokacin ya gama shiri zai fita yana daura agogo a hannun shi yana gani ta ya daure fuska tankar bai taba dariya ba a rayuwan shi.
  Rudewa tayi tama rasa may ta fada mashi can dai tace Samad kayi hakkuri na san ban kyauta ba na fita ba da sani  ka ba.
  Jakar laptop din shi ya dauka zai wuce ta zube kasa gaban shi tana fadi  ka yafe min gurin buki naje shine naka wanan lokacin ban dawo ba.
  Nasan nayi laifi  fita in dade baka nan amma kayi hakkuri haka ba zai sake faruwa ba insha Allahu.
  Yace don gani saunar na miji ki fita gida na kwana da kwanaki yanzu kizo kice inyi hakkuri haka kai tsaye bayan kin gama yawon gantalin ki a can.
  Kin kwaso kafan ki kin dawo min gida ki koma inda kika fito zai fi maki sauki na baki minti awa daya ki fice a gidan nan da kowa naki.
  Samad kayi hakkuri ka yafe min ba zan sake ba yace rufa min baki munafuka wace bata san ciwon kan ta da darajan aure.
  Ya sure jakkar shi ya fice a dakin da kyat ta iya mikewa tsaye daidai lokacin ya dawo yana fadin fita min daga daki zan rufe abina ne .
Ta bishi da kallon mamaki a kofan tana tsaye ya rufo dakin shi karo na farko a gidan abin ya mata zafi saidai cikin ranta tana fadin yi abin ka a hannu na zaka dawo kwanan nan.
   Ya fice ta bishi da kallo tare da juyawa ta wuce zuwa dakin ta tana mai jin haushin shi.


Post a Comment for "MIJIN BUZUWA CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...