[Advertisements⬇️]

Makaranta duniya Chapter29 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 Makaranta duniya  Chapter29

‘ ‘Haka abin ya kasance. Imam ya dauki nauyin‘ komai‘ na Sulaiman tun daga maganinsa zuwa nauyinsa Musamman ya aje (Pegeout’ 406) don kai shi kilink. Bayan wata biyar Asma’u ta haifo danta katon gaske, yaci sunan Idris, sunan mahaifin Mama. An sha
dabdalar suna, kamar yadda aka yi na saura. Mama kuwa ji take kamar ta goya Imam, saboda zakulo sunan mahaifinta da yayi ya dawo mata dashi
tarewa gidan, ta jima tana so ta kwana gidan, amma nauyi ta kan ji ta kasa zama, ta dawo gida. Yau kam ta fake da suna ta like. ‘ ’
Da sassafe take tashi ta yi wa Asma’u komai‘ ’ musamman aikin kicin, k0 dama shi kadai Asma’u ke yi. domin ba ta bukatar mai dafa wa mijinta abinci‘ kwana biyu Imam yana ci da hakuri.
A ra‘na ta uku ya ce wa Asma’u ya gaji da cin abinci babu dandano, saboda haka ta gaya wa Jamila Mai-gidan ya fi gane girkin da ya saba ci, ran ta ya baci kwarai da gaske.
A yammacin .wannan rana ta dauki jakar ta, ta ce za ta koma gida, ita ma Asma’u ba ta hanata ba, har da yi mata kyautar manyan turare masu kamshin alfarma. Haka ta koma gida da takaicin ba ta sami hadin kan Imam ba.
A zaton ta zai rinka sakar mata fuska ne kamar da suna wasa da dariya, sai ta ga abin ya sauya salo, tsakanin su gaisuwa ce kawai, in ya haye sama ba ta sake ganin sa, .idan ba fita zai. sake yi ba, haka Mudansir ke ji da. kansa, ko alama baya wasa da kowacce a cikin‘su. Koda ya dawo ma Asma’u ta gaya masa ta tafi, cewa ya yi ta sauka lafiya.
Jikin Sulaiman na ta ‘kara kyau, lafiya na zama jikinsa, kullum suka je kilik ci-gaba’ likitocinsa ke gani.. , Su kansu murna suke yi, don sun tabbata’Sulaiman yana samu kulawa ainun, ga shi yanzu har yana cin abinci ya zauna a cikinsa. Ramar jikinsa na raguwa, ba ka ce shi ne ba, koda yaushe Inna cikin sawa Alhaji da zuri’arsa albarka take yi. – ‘ ‘
Ba Inna, kadai ba, hatta su Raliya kannen Sulaiman suna -shi wa Imam albarka kumasuna girmama shi, ba don~yanada kudi ba, sai don yawan alherin sa da nuna kowa na shi ne, amma shi don
gogan bai taba cewa uffan ba akan abubuwan-da ake
masa. A ganin sa kankantar da kai ne, Idan ya ce wa Imam ya gode, kuma hakan‘zai sa shi Imam ya kara daukar kansa wani abu.
Yana ganin mutane na yabon sa, yana hura hanci yana bada umarni. Ai ‘shi ma ya yi‘dawainiyar dole a rama masa, koda yake an raina abinda ya yi baya, shi kam ya san ya yi kuma kowa ya ci arzikinsa taf (Akwai bahagon tunani a wasu zukatan masu illa Allah ka’ tsare mu).

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Watanni bakwai kenan da dawowar su Kaduna. Imam na ta kara matsa lamba akan zaman su JamiIa babu aure, k0 yau an yi zama na musamman, .kowacce an tambaye ta dalilin kin fidda mijin aure. ‘
Hakikanin gaskiya tsayayyu ne babu, kowa ya’ zo ya mori ganga, sai ya jefar da kwauran, ammasun kasa gane,’illar mika kan su ga kowanne kare da doki, kowa ya tofa al‘barkacn bakinsa wajen yi masu fada tare da nasihohi masu yawa. Da za’a yi sa’a su dauka su yi amfani da su, da sun ga alfanun abin.
Washe garin wannan zama da aka yi shi a falon Alhaji; Imam na tsakar aiki a ofishinsa. Lissafu ya rikice masa, kan sa ya dau zafi, ashe (Laftop) din.ce ta sami matsala, ‘ta rikirkita masa komai. Da kyar ya gano hakan, nan take ya doka wa lnjiniyan sa tarho, cikin mintoci talatin ya iso.
Babu bata lokaci ya dauke ta ya nufi ofishin Mudansir, don duba ta, koda yaushe can ya saba zuwa, idan ‘ya zoyin gyare—gyaren sa a kamfanin, saboda abokin karatun Muda ne a (Poly), kuma shi ya yi masa hanyar samun gyare—gyaren anan kamfanin su, kuma yana samun alheri mai yawa.
Fitar sa ke da wuya. Imam ya ji kamar an lallasa shi a filin dambe. Ya mike ya rage babbar rigar sa ya rataye, ya wuce firij ya dauka katon lemon kwali‘ mai
sanyi da kofi ya nufi kujerun hutawa da ke‘can wani
karshe kenan, wata kila ka yi mamaki idan na gaya maka cewar kawai ji na yi ana bikin Najeeb a Jos …….
“What? Ta ce “Babu wai a maganar da na ke gaya maka Yaya Imam .Najeeb azzalumi ne, babu tunanin da ban yi a kansa ba, don in‘dauki fansa da kashe shi na yi niyyar yi. . ‘
Amma wata zuciyar ta ce min kada in fara debo ruwan dafa kaina, haka nan na hakura, amma kullum na tuna shi ne_ Mutum na farko da ‘ya fara taba rayuwata, sai inji kamar kar in bi shawarar zuciyata.’
‘ Ya gyara zama ya dauki lemu ya kurba, ya yi dan murmushi ya ce, “Jamila kenan, ashe abin babu dadi. koda yake kurata kan so ta ci ‘ya’yan akuya, amma na ta babu mai taba su, su na killace cikin kogo tare da matakan tsaro.” ‘ ‘
Ta dago ido taf Da hawaye ta dube shi, “Ba sai
ka yi’ habaici ba. Yaya Imam, ka fito fili ka gaya min alhakinka ke bi na Wallahi ba ni da ja, kuma yadda ka san an min baki, duk wanda ya fito hakan yake min, sai na saki jiki, zai kakkabe rigarsa ya bar ni.” Ya aje kofin lemu ya dan tabe baki, ya kada kai, “Ba haka maganar take ba Jamila, ai ni tuni na yafe miki, wata kila dai akwai laifin da ki ka aikata wa Ubangiji, kuma ki ka gaza neman gafarar sa. Shi ya sa ki ke ganin ba daidai ba, ya kamataki yi tunani ki ‘gano  inda matsalar ki take.”
Ta ce “Gaskiya ne, zan yi tunani.” Ya ce, “Fine! Kin ga daga nan ki ci-gaba da addu’a sai miji ya fito.” Ta yi guntun murmushi ta ce “Yaya Imam kenan, ka na ‘ta ce wa miji ya fito, miji ya fito, wane miji zai fito, bayan daman can ina da shi? Ya ce, “K0? To me ya sa baki gabatar da shi ba?
Ta zura masa ido’ jim, ka na ta motsa ta dauki
kofin lemun da ya aje ta saita daidai inda ya sa bakinsa,
lta ma ta kurba. Gabansa ya harba ya yi sauri ya dauke Idonsa, daga kallon ta. ’
Ta yi murmushi sosai, ta mike ta dawo kujerar» da yake. “Menene na dauke ido?’Bayan kowa ya san jamila matar imam ce, tun yana mata tsarki yana share mala majinal Dif! Numfashin sa ya daUke ko kafin ya kalato shi, ya dawo jikinsa.’ Jamila .ta silalo kasa ta durkusa gabansa.
“Please Yaya Imam ka yafe min, na san ka na sona, son da babu wani da namiji da ya taba nUna min irin sa Yaya! Idan har ka tabbatar da kalaman da ka ke‘ _ gaya min tuntuni gaskiya ne, ina so ka nuna wa duniya ‘ cewa kai mijin mace hudu ne! ‘ ‘
A’fusace ya mike ya yi matsa tsaWa tare da nuna ta “Karya ne, kin’ji abinda na ce kuma, Wallahi ki‘ ka sake” bijiro. ‘min da irin wannan maganar, za ki’ fuskanci tashin hankali da ba ki taba zato ba, fitar min’ ’ daga ofis, tun kafin raina ya gama baci.”
‘ Ya ‘ wuce da Sauri ya barta nan durkushe’, ldanuwa taf Da hawaye, ‘kujerarsa da ke gaban tebir can’ya ko’ma ya zauna, yana maida numfashi, fushin sa ya hargitsa kyakkyawar fuskarsa, kafin Jamila ta yi wani motsi, wayar sa da ke kan tebur ta buga, ya jawo ta a hassale ya duba. Matar Liman ke kira, ya dan lumshe ido, ya dauka.
‘ “Nan take ya fesar da fushinsa ya danna 0k, ya kai kunne “Hello! Hello!! Liman kullin zuciyarsa ya ‘kara Warwarewa, fara’a‘ta bayyana fuskarSa. “Matar Liman, ya aka yi? Murya sanyaye ta ce. . ‘
“Kawai ji na yi gaba ‘na ya fadi, kuma babu wanda zuciya ta, ta sako min‘sai angona, shi ya sa na kira inji ya ‘ofis din? Ya yi baya ya kwanta~”sosai a kujera, tana ‘jujjuya shi a hankali. “Allah sarki Matas‘,” ‘ lafiya lau na ke, ai kin ji murya ta’ ba wata‘matsala ko?
Ta ce “Na ji Liman. Tuni sanyi ya ratsa ruhina, sai in ce a dawo lafiya ko? Ya ce “Na gode. amma kin ,san me? Kin motsa min kwadayin ganin ki, gani nan zuwa lnsha-Allahu.” ldo waje ta ce, “Ofis din fa Liman? Ya yi ‘yar dariya ya ce “Da Liman da ofis din Liman duk Karkashin mulkin matar Liman suke’, ki bada umarni Kawai Liman ba shi da zabi, in taho?
Ta rausaya kai cikin shagwaba ta amsa “Taho mana Liman.” Ya ce, “An gama’matar’Liman-‘ Ya kashe waya ya tashi da sauri ya dauki rigar sa, ya sanya ya Kwashi duk abinda yake son dauka ya fice abinsa, ba tare da ya sake kallon inda Jamila kedurkushe ba, ya tsaya gaban sakataransa,’ya ce “Ka shiga ka ce wa bakuwar nan ‘za ka rufe min ofis! ‘Ok Sir!
Ya, yi. gaba cikin hanzari, ofishin ‘Mudansir ya wuce, “Zan je in dawo yanzu, idan ya gama ya bar maka, sai ka sallame shi.” Ya ce, “To Yaya. A dawo lafiya.” Ya biyo shi yana taka masa, yana bude kofa. Jamila na kawo kai za ta wuce, “Ah Jamila.” Mudansir ya kira ta cikin mamaki, ba ta kalle shi ba ta wuce balle ta tanka masa, baki sake ya dubi Imam, “Ba Jamila bace?
Ya ce “Na fi ka sanin ita ne? Ya shafa kai ya ce, “Na ga’ ta wuce ne kamar ba ta San mu ba.” Ya ce “Ta’ jima a ofis dina, idan na dawo zan ba ka labari.’ Ya kara‘ ‘ bude ido “Me? To me ya” kawota,” Ya ce, “Me yake damunka ne? Yashafa kai.yana murmushi “0h ni Muda da tambayar tsiya.” “A dawo lafiya.” Yaya ya wuce yana amsawa “Amin.” Ya dawo ciki kan sa daure, kuma yana dauke da tambayoyi fal A zuciyarsa.
Kaf Amsoshinsa ya samu a wajen Yayansa, lokacin da suke dawowa gida daga ofis da yammacin Wannan ranar. “Wallahi ( Wallahi missed call) in dai da wannan maganar ta bullo, to wai ma Yaya in tambayeka, har ka yi kudin da za ka iya riketa?
Ya ce ‘Gane min hanya dan-uwa, ba ma haka ba. tana zaton’ zan iya yi Wa asma u kishiya ne’? Ban jin zan‘iya, sai dai wata kaddara daga Allah, ba na kuma fatan ta, zama da Jamila.” Ya ce “lnsha-Allahu ba zai taba faruwa ba, k0 a mafarkl, aure ne dai muna masu fatan Allah ya kawo masu auransu, daga can wani wuri, ba familin Alhaji Abdul-Rasheed ba.”
Yace “ldan kumasun ‘ sami mazajen, na yi alkawari komai na kayan daki da hidimar bikin.” Ya yi murmushi “Ka yi kokari Yayana.” Ya ce “Ko kuma za ka ja daya a cikin su ne? Ya dauke hannunsa daga sitiyari, ya dora bisa kai, “Ni Muda Yaya. Hamdiyya fa? Ya fara ‘ dariya, “Kai ma (Missed call) kenan? Da sauri ya amsa’ “Gaskiya gaba da “(Missed call swich off) ne, ko an kira – ba zai shiga ba.” Ya doke masa kafada, sUka ci-gaba da dariya. ‘
Al’amarin Jamila kuwa abin na ta da gaske ne, ta addabi Imam ta hana shi sukuni, ta ko’ina cikin wayoyinsa shafukansu na yanar gizo, na cikin wayarsa – da (Laftop) din sa duk inda ya duba sakwannnin ta ne,. ba dare ba rana.
Ko alama kalaman ta ba sa razana shi balle su ‘ motsa-tsohuwar soyayyarta, Wasu ma baya karantawa yake goge su, shi abinda yake mata kallo, mahaukaciya_ maras tunani, ita kanta abin na.ba ta mamaki ganin yadda ta kasa shawo kansa, abinda ba ta taba zata ba
A tunanin ta tashi guda za ta lya dawo da hasken ta cikin zuciyar Imam, duk da wani feleke da iya kissa irin na mata, sai ta ga wankin hula yana neman ya kai ta. dare ko alamar fuskar Imam ta daina gani, ko ya je duba jikin Sulaiman baya sauraranta, balle ya san da ruwan tsirarta, tun suna yi’ tsakanin su babu wanda ya sani face Mudansir, har Jamila ta wanke kafa ta tafi Kauran Juli ta roki Inna.
Wai ta rarrashi Imam, tunda ta tabbatar yana son ta, fushi kawai yayi saboda abinda aka yi masa. Inna ta watso mata harara ta ce, “Amma dai a rayuwa maras kunya ya ji dadin halin sa, ke yanzu nan har ki na tunanin Imam zai kalle ki? –
Kin yi kuskure, to k0 ni da na haifi ubanki, idan “naji Imam zai aure ki, sai inda karfina ya kare Wajen hana shi, ai mai auranki sai kalar ki Jaimila.Imam Kuwa ba kalar ki bane …… .
Ta katse ta, “Ya Isa haka Kaka, ya isa ba cewa na yi ki ci min fuska ba, don na zo neman taimakon ki, Kuma don kin hana shi, menene? Imam din wani kayan gabas ne? Ta kama haba ta ce.
“Hu’un lallai JamiIa kin cika, to don ubanki gayyato ki na, yi na ce ki zo ki nemi taimako na? Tunda ba kayan gabas bane, shin meye na bata lokacin ki? Shashashar banza maras kunya, kin ga ga hanya nan a bude, ta inda ki ka shigo, ki bi ta nan ki fice min da gani tun kafin in ci mutuncln ki.”
Ta ja dogon tsaki ta figi jaka, ta tsaya kame da kugu ta ce, “Yar bakin-ciki, ashe za ki mutu kuwa, domin sai an yi biki na da Imam, saboda haka zan fara lissafi daga’yau, da zarar lokacin bikin mu ya kusa, zan gaya wa Dadi ya tanadar miki likafani Mts ……. Ta fice ta bar Inna da matsar kwalla, saboda takaici.
Ashe duk burgar banza ma Jamila take yi, rusar kuka kawai take yi a gaban Dadin na ta tun shigowar ta gida tana mayar masa yadda suka yi da Inna. Rai bace ya ce.
“Ai maganin ki kenan, ban ce miki kar ki je gunta ba, bayan kin san cewa lnna ‘yar abi Yarima  asha kida ne. Yaushe za ta bi bayan ki, alhaIin ta san ban da komai, yaushe za ta iya tunkarar Imam, bayan yana da kudi, tana shakkarsa, ya kamataki gane bambancin.
_ Ya dan yi shiru, ka na ya ci gaba “In banda abln Inna, idan ta taimaka ya aureki, ba ci-gaban ta bane? Ammababu komai, dole a nuna min kiyayya tunda ba ni da kudi, ni kuma na sha alwashi sai kin aure shi, kuma sai na yi kudi a garin nan. Allah dai ya kara min lafiya, ku sha kallo.”
Ta gage kwalla ta ce, “Yanzu Dadi ya za’ayi? Ya yi dan shiru jim, kafin ya ce, Ki yi hakuri har zuwa lokacin da Umman ku. za ta dawo Kankiya, zan lallalabata ta jeta sami Maman mu, kin san ita suna sauraronta kuma na tabbata Baba zai;so abin, kin san shi da son zumunci.’
Ta fado jikinsa, “Yauwa Dadina, shi ya sa na ke _son ka.” Ya dago ta, ya ce “Kar ki damu, ni na fi-ki sanin fa’idar yin auran nan.” Ta mike kafa, su kai ta ._shirya manufofinsu.
s~~~s~~~ ~~~~~~~
dakyar ta dawo daga kankiyar sbd ,yanayin jikin hajia aleeya don dai ita ma ta bar wani mai
jinyar ne a gida, amma ji take a kowane lokaci za’a kira ta, ace babu mahaifiyarta. A daran wannan rana, ‘hannunta biyu ta sha tagumi tana zaune bakin gado. Sulaiman ya sahannu ya cire mata, “Hannu Marja kamar an yi mutuwa?=Tace, “Ba ka ga jikin Umma bane Baban Jamila.“
Ya ce, “Shin cuta mutuwa ce? Ashe da ciwo ke kisa da tuni kun manta da ni ai. Me ya sa za ki sanya damuwa a ran ki? Ta nisa ta ce, “Ai ganin ‘ciwo ya fi tattara duk wani tashin hankali da ‘damuwa akan . mutuwa, saboda ita. Ubangiji yana sanyawa bawansa ‘- mantuwa don? ya sami natsuwa, ~ ya ci—gaba da rayuwarsa, mai’ ciwo kuwa kullum ka‘kusanceshi “sai kaji zuciyar ka ta buga, . ‘
Kuma ai kai yanzu Allah ya taimake mu ka sami gata Wallahi duk wanda ya dube.ta, dole_ya
tausaya mata. Dubu ashirin din da Baba ya ba ni na kai’ masu, ba kaga irin farin—cikin da Yaya Mansur ya rinka yi ba, ita ba ta ma san na kawo kudin ba.”
Ta goge hawaye- ta ce, “Allah ka yaye mana masifa.’ Ya ce, “Amin, musamman ta talauci, ai shi talauci sam bai yi ba‘a rayuwa.” Ta numfas‘a ta ce, “Haka ‘ne, amma in Allah ya’ aiko da shi, babu yadda bawa ya iya, sai hamdala ga mai badawa.”
Ya kara matsota ya ce, “Akwai mafita Murja, kuma idan ki ka taimaka kowa’zai ji dadi, ba sai komai an sai mana ba.’ Ta dube shi da kyau “Me kenan? Ya ce, ‘Zan gaya miki, amma ina so ki yi wa al’amarin kyakkyawar fahimta. Kin gane? Sanin kan ki Imam yana tsananin son Jamila. ‘
Shaidan’ne kawai ya shiga zuciya ta ya zuga ni, ba’” don wai ba na son shi ba, tunda‘ yanzu na gane kuskure na, mai zai sa ba za’a rarrashe shi ba, maganar jiya ta dawo? Dauke da mamaki ta ce, “Baban Jamila ka san’ me ka ke fadi kuwa? Ka na zaton in ,maye ya ci ya manta, uwar da za ta manta‘ne? “Ah’ah…
ya katse ta “Ai ka ji, wa ya gaya miki su Baba na da rikon magana a irin son zumunci irin na su, ke ma kin san ba zasu ce ah’ah ba. Haba k0 kin manta ne? Ta yi dan shiru kafin ta ce, “Amma dai da kunya, a taso da wannan magana yanzu.”
“Ya ‘ce, “Kuma ke ce ‘za ki tada ta ba.” ido waje ta nuna kanta “Ni kuma, me zai sa ni? Ya ce ‘Saboda ke kadai za -ki yi magana ayi saurin sauraron ki. Baba na kaunar ki Murja, saboda amanar da ya ‘amso daga Abba, kafin ya rasu. Na tabbata ba zai ba ki kunya ba, ki je kawai ki same su ki nuna masu nadamar- mu da damuwar mu, za ki zo ki ba ni labari.” Ta yi shiru tana dogon tunani, hakaya raba dare yana rarrashinta.
Washe ‘gari karfe goma na‘safiya ta isa gidan, don ta .tabbatar zuwa lokacin duk sun gama komai sun
natsa, ‘yana falonsa tare da Mama inda katafariyar T.V a jikin bango ke ta aiki (Sunnah TV) ne koda yaushe dare da rana, idan sun canza. ‘
To karfe tara’ne na dare Alhajl zai kalli labaran kasa. Ta yi sallama ta shiga, suna amsawa. Mama ta ce “Oh Murja har bin biyo hanya? Yanzuna ke cewa Alhaji anjima direba zai kai ni gidan na ku. mu gaisa Inji ya mai jiki?
Ta ce, “Wallahi babu komai Mamanmu.’ ‘TO Ya jikin nata? Ta ce “To mun gode Allah don saukin na sa ne, amma har na taho ba ta san na je ba.‘ Duk suka ce Subhanallahi! Alhaji ya ci—gaba, ‘ “Kai Allah ya ba ta lafiya, ya sa kaffara ce.” Ta amsa “Amin Baba.”
Bayan sun gama gaisawa, sun tambayi har jikin sulaiman, ta yi dan . shiru,‘ da gani tana dauke da magana, amma tana jin nauyi. Alhaji ya’ gano hakan, don haka ya ce, “Ina fatan dai lafiya ko Murja? Ta ce “Eh to lafiya lau, dama wata magana ce Baban sulaiman ya turo ni in yi ma ku, saboda ya ce shi yana jin nauyi da kunya, bai ma san ta inda zai fara ba, akan maganar Jamila ce da Imam. ‘ Ya ce Ya san ya yi kuskure can baya, kuma duk sharrin shaidan ne, amma yanzu ya gane abinda ya aikata katon shirme ne, shi ne ya ce in roke ku idan har kun yafe masa, ga Jamila nan ko gobe Imam ya shirya ya zo ka daura masu aure Baba. Kunji abinda ke tafe da ni, don Allah a yafe masa.” Ta yi shiru tana share ‘ hawaye. _ Dukkan su shirun suka yi, zuwa can Alhaji ya nisa ya ce, “Mun ji jawabin ki Murja kuma mun fahimce ki, dama tuni muka yafe wannan magana, amma ina so ki gane wani abu daya. Imam shi ke da wannan hukunci a hannunsa.
Tun farko shi ya ce yana so, ba wai mu muka
hada su ba, saboda haka zan yi masa magana, idan har
ya amince. Falillahil hamdu. Ai yana sonta kuma shi so zai yi wuya ya goge duka, sai dai ya ragu. Babu komai zan ga Imam din kin ji? Karki damu.
Ta ce “To shi kenan Baba, mun gode, ni zan koma Sai a lokacin Mama ta yi magana “Har za ki koma? Ta ce, “Eh saboda Baban Jamila na ga yau Kamar ya tashi da zafin jiki.’ “To shi kenan, ki gaishe shi don Allah.” Haka suka~ fadi gaba dayan su. Ta fice fa bar gidan.
Mama ta dubi Alhaji ta ce, “K0 ka ji wata magana mai kama da almara? Ya ce “ikon Allah kenan.” Ta kada kai ta ce Ai ba ma zai yuwu ba.’ *Kamar yaya? Ta ce, “TuntUni‘ ba’a ba shi ita ba, sai da ‘ta tsofe a titi ta gama garambana daga Wancan ofis
,zuwa wannan, sannan ace Imam ya zo ya aura? Allah ya-
.tsare shi, muna dai masu addu’a Allah ya kawo masu daidaisu.”
Alhaji ya cire gilashin sa ya ce, “Haba Suwaiba, ya na ke jin magana kamar ba daga bakin ki take filowa ba? Ta ce, “Kamar yaya, ba fa zai aure ta ba Alhaji. Yaro da matarsa suna zaman lafiya, sai ace dole ya kara Ya ce, “Wa ya gaya miki dole aka ce? Kar fa ki manta irin son da lmam yake mata Ta ce “Da ne, ya kuma wuce.” ‘
Ya yi murmushi yace, “Ashe kin iya rigima, to idan ya amince fa? Da sauri ta amsa, “Ba ma zai amincan ba Yauwa ba zai yuwu ba kawai.” Ya maida gilas yana mata dariya, ‘Tsohuwa kenan, kai tsaye kin yanke hukunci, ba ki bari dan na ki ya zo ba? Ta ce “Ina nan ina jiransa.”
“Yan halas din sai gasu kamar yadda suka saba zuwa.’ Mika wa iyayensa gaisuwar safe suka yi. Suna shigowa ta dube su ranta ya yi mata fari sol! Kamar auduga. Kullum haka take ji idan ta gan su kamar tif da taya. “Maman mu.” Duk suka sanya ta tsakiya, “Ya ki ka kwana Maman mu? Ta dafa kawunan su ta ce. ‘Lafiya lau, ya iyalanku? Ya kishiyoyi na da angwaye na?
Suka ce, “Lafiya lau, duk suna gaishe ki.’ Ta ce “To madalla.” Suka juya kan Alhaji suka gaida shi. Ya amsa cike da fara’a “Baba na ga kamar ka na ta fara’a, ‘tunda muka shigo akwai labari ne? Ya ce, “Sosai kuwa, ku matso nan kuji‘.” Mama ta gyara-fuska, ta rike hannayensu. ‘
“’Ai ba- sai sun matso gun ka ba. daga “nan ma sunaji;” Ya,na dariya ya ce, “Ah ikon Allah. To shi ‘kenan, rike‘abinki Maman yara.” su dubi wannan, su ‘ dubi wancan, Wai menene? Da, alama labarin nan
fuska biyu gare shi.” Inji Imam,
Muda ya ce, “Ashe ka gane dan-uwa. Don Allah ‘ ‘ ku fada- mu ji.” Alhaji ya ce, “Ai ba wata magana bace sabuwa akan Jamila ne, yanzu Mur‘ja ta fita, wai Yayan ku ya turo ta yana neman afuwa, yana son zumunci nan dai‘ a kulla shi, kokuwa Baba na?.
lmam ‘ya kalli Muda~suka kece da dariya. Su Alhaji suka yi galala ,suna’ kallo, “Meye haka? lnji. Alhaji.” Imam ya ce, “Tanan kuma ta bullo? To ai ta makara. Imam ya riga ya yi nisa.” Wai dama ka san maganar ce? Inji Mama ya ce. .
“Tun haihuwar ldris Jamila ke bibiya ta, k0 ta ga abin ya ga gare ta ne; kwana hudu’da suka wuce ta je ta sami Inna, ita lnnar da kan ta ta kira ni ta cé akul dina, ba ta gOyi bayan aure na da Jamila ba. Na ce in ban da abin lnna yaron da ya dafa wuta ya kone, gobe in ya ganta ai sai in da mai ya kare Mama ta ce, ,
“Yauwa yanzu na ji magana, to ku tashi ku tafi ofis. Allah ya yi maku albarka! Alhaji‘ya ce‘Kai Imam ba maganar: wasa ba, menene gaskiyar-dake zuciyar ka? Ya ce. Tsakani da Allah babu Jamila-a cikin tsarina. Mata ta na ke so kuma ta isheni. Wallahi ku gaya wa Anti ta yi hakuri, za mu taya ta addu’a Insha-Allahu za su sami wasu mazajen daidai su.”
Alhaji ya numfasa ya ce, “Shi kenan, ka na iya tafiya. Allah ya yi ma ku albarka.” Suka amsa da amin. wai ina jarida ta ne? Ya ce, “Tana mota.” “Wai dama ba ka dauko ba Muda? Ya zabura ya yi waje yana fadin ooh ni Muda da mantuwa
Nan ya bar su suna masa dariya. Mama na fadin, Yaro kamar dan kama.” Jim kadan ya dawo da jaridun guda biyu, wadanda Alhaji ya” fiso, kuma ya saba Karantawa. Suka yi sallamasuka fice, iyayensu na sa masu albarka.
Shiru suke tun tafiyar Alhaji kusan minti goma kenan da Suka wuce. Kukan Jamila kawai ke tashi tana rera shi kamar ‘yar goye. Shigowar su Ummi falon su suka katse shiru, “Jama’a wai sanarwa mutuwarwa aka yi ne? Ummi ta tambaya, suna zama a kujera. Sulaiman ya kara fusata cikin fushi ya ce, “Ba’a sani ba! Duk suka dubijuna suka tabe baki, kafin Hafsat ta ce.
“Yi hakuri Dadi, kukan Anti Jamila ne ya ki karewa, shi ya sa muka tambaya.” Cikin muryar kuka ta yi masu tsawa, “To ina ruwan ku don uban ku? Murja ta
café.
“Rufe‘mana baki, kukan ai na banza ki ke yi, ba ~ ki kuma gama yin sa ba, muddin ba za ki yi hankali ba
Ga dai darasi na farko nan kin fara gani, ni dama na bi umarni ne kawai, amma na san babu abinda Imam zai yi da ke, ba tarbiyya, ba ‘natsuwa, ba komai mai mata irin Asma’u me zai ci da ke?…
Sulaiman ya mike, “To ya isa, ya ishe ki haka, ke da ‘yar cikin ki, amma ba ki kaunar ta, sau nawa za ki gaya mata irin wadannan maganganun? To kin ga idan ba kya son ta, ni ina son kaya na kuma ban yarda kowa ya daga mata yatsa ba! Don ya ce ba zai aUre ta ba, sai ya zama karshen rayuwar ta? In ‘banda kaddarar canjin lamari, ina imam ina Jamila? Har wani kudi gare shi? Ina kudin suke? ,
Murja ta mike ta ce, “Ga su kuwa ka na ci, ka na sha a cikin su, sannan har ka yi lafiyar da ka ke samu ka na barci a cikin arzikinsa! Kai idan ido da kunya Baban Jamila in an ce ka matso ma za ka ‘iya? Ga
– duniya nan, ka ci—gaba da biye wai yara abinda suke so, har abada ba za ku daina kuka ba.” ‘
‘Ta wuce da saurI’ cikin daki Sulaiman ya raka ta
: da kallo baki Sake, kafin ya dubi inda su Ummi ke zaune ya nuno ‘su, “Ku fa gayawa uwar ku ta kiyaye ni fa To. shi kenan! Suka tashi fuuuuu…. .
Suka wuce dakinsu suna tura masa baki, ya koma a hankali ya zauna, yana maida numfashi, “Kin‘ ga ke Jamila ya isa haka na ce ko? Ta taso a hankali ta rarrafo kusa da shi ta ‘dora kanta bisa jikinsa, “Wannan wulakaanci ne Dadi, don an ga ba ka da kudi yanzu shi ya sa aka rasa wanda zai yi wa Imam magana, ai k0 Baba ya isa ya tirsasa shi!
Ya ce, “Don Allah ki daina kara bata min rai, yanzu na gama karantar kowa, na san matsayin na gun su, ta yaya ma Baba da girmansa da komai ya zauna yana min habaici? Wai Imam bai yi kudin aje mata biyu ba, a cikin kamfanin ne ba fensho balle garatuti, me yake nufi?
Wadannan kalamai sun kona min rai, amma babu komai zan rama, kuma ki ba ni daga daran yau zuwa gobe, zan gaya miki hukuncin da zan yanke, tashi ki je ki wanke fuskar ki, ki kwanta.” Ta tashi ta wuce -daki tana share hawaye, tana shiga. Ummi na fadin “Sai ka ce dole ne ta aure shi.” .
Ta tsaya kame da kugu ta ce, Zan yi wa yarinyar matsiyacin duka a daran nan! Ummi ta nuna Hafsat ta ce, “Da ke take? “Ta ce “Da ke take dai.” Ta yo_ kukan
kura kowacce ta ba’ta mari a kuncin ta, haba suna
tashi.
‘ Suka rufeta da duka kamar sun sami jaka. ihunta kawai Sulaiman ya ji, kafin ya shigo ta daku ba Kadan ba, da kyar ya kwace ta, ya yi ta shari’a. Murja ma ta yi banza da su, ya dawo daki yana ta haki ta‘re da zage-zage, ba ta ce uffan ba har gari ya waye.
Haka nan gidan ya kasance kowannan ‘su da alkiblar sa. Jamila da Dadinta kawai ke wa juna magana, duk abinda yake bukata ma ita yake kira, karfe goma ya ce ta ‘zo ta fita da shi shan iska cikin gari. Suka kame a mota. Jamilar ta ja suka bar harabar gidan. Murja ta saki labulan taga ta kada kai ta ce a ranta. ‘
“Allah ka shirya. Baban Jamila ya yi nisa baya jin kira, ga babu kunya. lta motar da dawainiyar man da take sha arzikin wanene? Ta yi dan guntun tsaki ta jawo waya, ta nemo lambobin Yayan ta Mansur, suka gaisa ta tambayi jikin Umman su, shi ma tuni ya wuya ta sa ya zubda makaman, ya kinsa ya kama ‘yar-uwarsa suna zumunci ta waya.
A cikin mota kuwa bisa titin Indifendent suke.
Jamila ke fadin “Dadi‘yanzu shi kenan na rasa Yaya .
Imam? Wai me ya sa ni ba ni da sa’a ne a rayuwa? Ya ce, “Wa ya gaya miki rashin sa’a ne wannan? Shi komai ba dan lokaci bane? Kawai lokacinki ne bai yi ba.’ ‘
Ta ce “Na ji, amma wane mataki ka dauka? Ka ce in ba ka daga jiya zuwa yau.” Ya gyara zama ya ce “Babban mataki na dauka kuma tuni na yanke hukuncin abinda na shirya, don ba zai yuwu in zauna haka ba. Yaro karami yana taka ni saboda yana da kudiba
‘ Ta yi dan murmushi ta ce, “Dadi ka gaya min shirin nan na kosa inji? Ya karkato jikin kunnanta ya rada mata tsawon sakwan ashirin, ido waje ta zabura ta
dube shi. “Dadi akwai matsala, wai karma ka fara, ana ganin ka yi kudi za‘a gane shirinka ne.
Kuma ba ka jin ba za su ‘yi tunanin sa hannun ‘ ka, saboda rashin amincewar’Yayar Imam ga tayin ka ba? Ya kyalkyale da dariya, ka na ya ce, “An‘gaya miki ni mahaukaci ne? Ko kuwa irin aikin jahilai zan yi? .
Da hankalina, da wayau na, akwai lokacin da na yanke zan aiwatar da shirin, sannan akwai lokacin da na diba don yin kudin, kin gane? Saboda haka ki kwantar da hankalin ki, ni ne maganin duk abinda yake masa yawo akai, ke dai kafin zuwan ranar, ki tabbatar da kin binciko mana kwararru, ba ‘yan jagaliya ba, don kar su yi mana shirme, 0k? ‘
Bakin ta har kunne ta ce “In don wannan ne, an gama Dadi, da arziki a garin ku, ai gara a gidan ku, a gidan ma a dakin ku, cikin dakin ma bangaren da ka ke kwana.” Ya ce “Yauwa ‘yar gari, shi ya sa na ke son ki, domin na fi samun hadin kan ki, duk kin fi sauran yi min biyayya. Allah ya yi miki albarka’ ya ta! Ta girgiza jiki, – alamun rawa tace, “Amin
Kwana biyu tsakani magana ta wuce. Suleiman da kan sa ya yi wa Imam maganar cewa magana ta ‘ Wuce kuma ya roke shi, don Allah kar ya kUllaci ‘yar— uwarsa. Me zai sa ya kullace ta? ‘ ‘
Shi tuni zancan ya bi ruwa‘abinda ya sani kawai’ gaba dayan su jini daya kuma ya lashi takobin tsare-« masu komai na rayuwar duniya. Muddin yana numfashi. A haka suka tafi har ya kan tsaya ya amsa gaisuwar Jamila.
       ss~~~ss~ ~~~~~~~~
gab ake da kiran sallar azahar lokacin da alhaj ya tsinka yi sallama a kofar falonsa ta waje, ya
amsa ya kara fadin, “Shigo mana.‘ Aka dago ‘labule aka shigo tare da wata sallamar Alhajin. Ya sake amsa idanuwansa akan maishigowa.
A darare yake kayan jikinsa, sun tsufa duk da sun sha wanki, da sauri za ka iya gane kodewarsu. “Sannu Baba.’ Ya tsuguna gefe yana fadi.~ Alhajl ya tsananta Kallon sa yana amsawa, jimawa kadan ya nuna shi “Mansur ko ba shi bane?
Hawaye suka kubce masa, murya na rawa ya amsa, “Ni ne Baba! Alhaji ya taso jiki na rawa bakinsa na fadin. ‘Mansur ikon Allah, kai ne haka? Ya sa hannu ya dago shi, ya zuba masa ido, ‘Daga ina ka ke haka? Me yafaru? Ya silale ya yi kasa, ya rungume kafar Alhaji, “Zuwa na yi ka yafe min, ka yafe wa mahaifiya ta “Baba, don girman Allah, don son Manzonsa (SAW). , Baba ka yafe mata.‘ , ’ Hankalin Alhaji ya yi mugun tashi, nan take shi ma ya ji hawaye na neman su zubo masa, ya yi azama ,ya dago Mansur ya rungume shi, amma bai iya cewa komai ba, saboda murna. Mansur din ke farqan kuka yana fadin “Ka yafe mana Baba;” Mama ce ta jiyo sautin kukan ta dago labule ta shigo.
“Lafiya Alhaji? Ba su ma san ta shigo ba, har sai da ta matsa gare su sosai, “Me ke faruwa ne? Alhaji kai da wanene haka.” Sannan Alhaji ya dawo hayyacinsa, hawaye sosai ke zuba bisa kuhcinsa. Ya dago shi ya ce, -“Ba ki gane shi ba Suwaiba? Mansur ne.’ “Mansur din mu? Ta dafe kirji ta ce.
‘ “Mansur In ce dai lafiya k0? Ya dan goge hawaye yana dubanta “Na zo ku yafe mana ne Maman mu, jiya da daddare na ji wata magana a wajen Umma da ta daga min hankali, kuma ita ta turo ni inzo in nema‘mata afuwa wajen ku, don Allah ku yafe mana.”
Take lta ma ta jihawaye sun gangaro mata. Alhaji ya kama shi ya ce “Zauna Mansur, zauna Mansur ka sha ruwa ka ci abinci.” Ya zauna yana kada kai, ‘Ba zan iya cin komai ba har sai na sami tabbacin kun yafe mana, ashe duk abinda muke zargi, ba. haka bane?
Umma“ ta ce lokacin da Abba zai rasu ya. gaya mata, amma ta kasa gaya wa kowa, kuma ta rasa yadda za ta yita fuskance ka, saboda abubuwan da ta. aikata a gare ka marasa dadi. Wallahi ta yi min rantsuwa, wannan shi ne silar rashin lafiyar ta, saboda ta kasa sauke manyan kayan da ’ta daukar wa kanta. Baba, Umma na cikin wani hali, ba dole bane in koma gida in same ta.
Amma ta gaya min kunyar ka ba za ta bari ta hada ido da kai ba, shi‘ ya sa ta umarce ni da in zi’in nema mata gafara, sannan ta ce idan har ka yafe mata, to duk lokacin da’ Allah ya yi mata cikawa, kai ne take so ka sallaci gawarta koda za ta kwana biyu ne a kasa.”
Ya kara durkusawa, “Baba gani gare ka. Baba ka gafarta mana, domin Umma ta ce laifin ta mai girma ne, daga ita sai kai, sai Allah da ke tsakanin ku, kuma shi ne zai maku hisabi idan har ba ka yafe mata ba! Alhaji ya ‘sake kamo shi ya zaunar.
“Haba Mansur, wannan irin kuka ai sai ka sume. Don Allah ka sanya wa ranka salama. Wallahi ni tuntuni na yafe mata, koda ku ka ga bana zuwa Kankiya, alkawari ne na daukar mata ba don rai na ya so ba. Allah kadai ya san irin kukan- zucin da na yi, saboda rashin zuwa ta’aziyyar mahalfin ku. Aboki na kuma amini na. Duk abinda ya faru,-sharrin shaidan ne. .
Amma Alhamddllllahl, tunda Uban-giji ya bar mu da rai har ya nuna mana wannan rana, ba na s0 ka kara tada wata magana a yanzu, abinda na ke so da kai, shi ne ka natsu ka kwantar da hankalin ka. Mamanku ta
Kawo maka abinci ka ci mu tafi masallaci, idan mun dawo ma tattauna abinda ya kamata ayi, ka ji?
Ya ce “To Baba, mun gode.’ Ya dubi Mama. Maman mu mun gode.’ Ta ce “Kar ka damu Mansur- Allah dai ya ba ta lafiya, ya yaye mata wahala.” Ya ce ‘Amin.’ ‘Je ki kawo masa abinda zai sa bakinsa.’ Ta mike ta fice.
Mansur ya kara goge fuska ya ce, “Murja duk ta gaya min abubuwan da suka faru, ta ce ma yanzu Imam ke dawainiya da su.’ Ya ce ‘Ai wajibinsa ne in bar yana da karfm yin hakan, domin duk duniya ba shi da tamkar su, an ce ka na koyar wa a firamare k0? Ya amsa, ‘Shi ma da kyar na same shi, shi ne har na samu na kukuta na yi aure, yara’na biyar suna nan.”
Alhaji ya ce, “Masha-Allah, to Allah ya‘ amfana su, ni ma Murja duk ta sanar da ni, babu abinda ya fi min dadi da ta ce kun‘ shirya, hakan shi ya kamata ka rungumi ‘yar—uwarka ku yi zumunci, ita kadai ta rage maka, ka fahimce ni‘? Ya ce “Na fahimta Baba.” ‘To Allah ya yi maku albarka, ya ji kan wadanda suka riga mu.” – ‘Amin summa amin.’ Mama ta shigo da tiran
abinci. Mansur ya mike da sauri ya tarbe ta ya karbo “Sannu Maman mu, na gode.’ Ta ce, “Ka zauna ka ci sosai, ka koshi, nan gidan ku ne.‘ Ya ce, ‘To.’ Ta koma cikin gida’ta bar su da Alhaji yana ci suna hirar bayan rabuwa, yana kammalawa masallaci suka wuce, suka yi sallah, sun dawo gida kenan Mudansir ya iso. Don Alhaji ya yi masu waya ya ce su zo su ga dan-uwan su Mansur, sai dai shi Imam baya gari ya tafi Abuja. Mudansir ya mika masa hannu suka yi musabaha. Alhaji ya ce, “Rungumi dan-uwanka Muda.” Suka rungume juna, jim kadan suka dubi juna. Baba ya
ce “Mu zo mu ga dansa daga Kankiya, Yayan mu Mansur da muke jin labarinsa, to ya mai jiki?
Ya ce ‘Alhamdulillah! lna lmam Yusuf‘? Ya amsa, ‘Yaya lmam na Abuja, shi ma ya so ya ganka, amma za kakai gobe zuwa jibi? Ya kada kai ‘lnsha-Allahu yau gida zan kwana, saboda yanayin jikin Umma,” Ya ce, ‘Ayya! To Allah ya ba talafiya.’ “Amin.’
Yana rufe ‘baki, Murja ta shigo da kukanta ‘Lafiya Murja? Duk. suka tambaya ta ce “Lafiya lau, kawai  farin-cikin zuwan ka ne Yaya.’ Ya yi dan murmushi, shi ne abin kuka? Ai dama ba ki‘zo ba, zan. biya in galda mijinki.” ‘Wai yau za ka koma? Ya ce ‘Ya zama dole Murja.” Ta ce “To shi kenan. Allah ya kai ka lafiya.” . Duk suka amsa da amin, kafin Alhaji ya ce, ‘Da yardar Allah mu ma gobe muna tafe mu duba jikin na ta.” Cikin ‘jin dadi ya ce, “Allah ya kai mu goben lafiya.‘ Suka amsa da amin. Dubu goma Alhaji ya ba shi. Mama dubu‘ biyar. Mudansir goma, haka zalika lmam ya ce aba shi dubu ashirin, kudinsa dubu arba’in da biyar ya yi ta zuba godiya yana hawa’ye. Murja na taya shi.
Mudansir ya kwashe su ya aje gidan su Murjar. Mansur ya gaisa da Sulaiman tare da neman gafarar jUna. Daga nan suka wuce tasha. Muda ya sa shi a mota ya biya masa kudin, sannan ya koma ofis.
Daga sallar asuba, babu wanda ya koma barci, shirin tafiya kawai suke yi,_saboda a yau suke so su je su dawo, in Allah ya yarda. Shi ya sa karfe shida daidai suke fakin gidan Suleiman, suka dauki Murja da Hafsat suka damki hanyar katsina. Karfe takwas na safiya wayar Alhajija yi ruri.
Ya zaro ta daga ‘aljihu,’ya duba lambar Mansur – ce da ya shigar jiya, take nan‘ gabansa ya fadi, ya danna ok, ya sawa kunnan Sa, ya yi sallama cikin natsuwa, ya amsa kafin ya ce, “Kun,taso ne Baba? Ya ce, ‘Eh har
mun ba garin Dabai baya.’ Ya ce ‘Allah ya kawo ku “lfy.” ‘Umma dai Allah ya amshi abinsa
be kara komai ba, ya kashe wayar. jikinsa ya yi mugun sanyi, clkin zuciyarsa yake fadin “Inna-Lillahl’wr Inna-Ilalhir-Raju‘un! Ya dubi Malam Sadlq dake zaune Kusa da shi suka hada Ido, domin shl ma shi yake kallo. ‘Yaya dai Alhajl? A hankall yace
‘Babu Ita Zuclyarsa ta razana, amma a clkinta yake ambaton sunan Allah. Mama da Murja na can Dayan Jeep ba’ wanda yasan me ke faruwa . haka direba ya yl ta Jansu, su biyu kadai ke‘ Jujayin mutuwar.
Ammasuna Isowa taron Jama’a ya tabbatar masu akwal ablnda ya faru, wanda ba zato mutuwa ne nan take Murja ta fara kuka tuna fadin, “Shl kenan Umma Inna-LIIlahl’wa-lnna-IIalhlr-Rajl’un! Mama ta kamo ta tana ba‘ta hakur, kal tsaye suka wuce clkln glda. Mansur ya tarbesu Alhajl, . ka na Iya ganln tashln hankall clkln Idanuwansa, domln jajur! Suke babu alamar haske
Bayan sun gaisa. Alhaji ya tambaya, “An shirya ta’ne? Ya ce “An shlrya ta Babe.” “Mu je a flto da lta.” Suka shlga ciki, kokekoke mata ke ta yl, tun shlgowar Murj’a. ta yamutsa gidan, kowa ya dauki kuka. Alhajl ya tsaya ya kwantar masu da hankall, sannan ya shigo. dakln da gawar ta take. ya tsugunna ya bude fuskar ta, ya dan dube ta, ldanuwansa suka kawo kwalla.
Ya yl mata addu’a, ka na ya fadi a hankali, “Na yafe mlki Aliyaa dunlya da lahira. Allah ya gafarta mana bakl daya.” Ya dubi Mansur da ké gage kwalla, yace “Kama mun” ita
Suka kamo ta tare da Malam Sadiq, suna fitawa falo, wusu mazan suka tallafa masu aka fita da ita , Alhaji Abdurrashed ne ya jagorénci sallar Jana’izar, daga nan aka kaita makwancinta
Bayan sun natsa a gida, ana ta amsar gaisuwa. Alhaji ya kira wayar Mudansir ya shaida masa koda ma tuni Murja ta sanarwa Sulaiman shirye—shiryen tahowa suka yi da sauran yara. La’asar tagota kadan, suka iso gaba dayan su har da Muda, nan suka kwana. Washe gari Mudansir ya koma da Malam Sadiq. A ranar Imam ya dawo Abuja, gari na sake wayewa- ya debi iyalansa ad da Muda suka nufi Kankiya. ‘ ‘ ‘ ‘ ‘_ Mansur ya zuba wa Imam ido ya ‘ce, “Imam Yusuf Ya amsa. Yaya Mansur ida-nuwansa suka tara kwalla ya tuna baya, haka yake bin sa ko’ina yana kira. “Yaya Mansur Kamar shi ya rada masa sunan. ,’ Kusan ya fi shakuwa da shi fiye da sauran, ya dan kada – kai ya”rungume shi, jim kadan suka dubi juna,;‘yA hakurin mu?~Ya Ce “Mun gode Allah.’-“To Allah ya yi mata rahma.” “Amin summa amin, mun gode kwarai da dawainiya‘. Allah ya saka da alkhairi.’ Shi ma ya amsa, da amin, nan suka zauna kusa da juna suna amsar gaisuwa. Tare suka ci abincin rana, bayan sallar azahar saka sallami kowa. Imam ya kara bada dubu ashinin sadaka. ‘ Rana ta uku kafin Aihaji su baro-Kankiya, sai da ya kebe da Mansur ya’yi masa nasiha ka na ya tambaye shi, “Ina fatan maganar da ku ka yi da Umman ku babu wanda’ ka gaya ma wa, ko ka‘gaya ma wani? Ya gida kai yace “Ban gaya wa kowa ba, dama Murja na ke son ‘ gaya mawa, jira na ke mu natsa.” .Ya ce, “Ah’ah kar ka gaya mata kuma ban so wannan magana ta ci—gaba da zama sirri a wajen ka; ban lamunce maka gaya wa k0wa ba, har zuwa karshén rayuwarka. Ka ji ni da kyau? Baki sake yake kallon ‘sa. tabbas ba mamaki yake ba, don ya jima da sanin wanene Alhaji Abdul-Rasheed. Murya sanyaye yace. “Na gode Allah da ya ba Umma ikon bayyana min
gaskiya”, da ta mutu-ta bar ni cikin maraici, ba uwa ba uba.
Amma yanzun’na tabbata, ni ba maraya bane, ina da uwa ina da uba, wadanda za su kula da mu fiye da tunanin mai hankali.‘ Alhaji ya dafa kafadarsa, ‘Hakika kai ba ka zama daya daga cikin marayu ba, ban so gaya ma ka ba. ‘
Amma duk da haka ba za ka ji komai daga gare ni ba, domin ba alkawarina bane, na kanin ka ‘ne Imam. Saboda haka ka‘kwantar da hankalin ka Allah ya ji kansu.‘ Ya ce amin, zuciyarsa cike da doki, anan suka bar Murja ita sai an yi bakwai.
~ ssssssssss –
malam“ Sadiq ,ne a falon alhaj suna ta hira bayan cin abinci. Karfe tara na yi Malam Sadiq ya dauki rimot ya canza tashar (Sunnah TV) zuwa NTA don ganin labarai, kamar yadda suka saba. ‘ Tun a kanun labarum aka fadi cewar a yau ne aka sake kama tsohon dan 419 din nan da ya share shekaru ashirin da biyar a gidan yarin kasar Potugal. Don haka suka gyara zama domin jin cikakken labarin., Ba’a kawo kan sa ba, har tsakiyar lokaci, sannan ‘ya zokamar haka, “A yau ne jirgin da ya dauko tsohon dan 419 din nan da ya shafe shekaru ashirln da biyar a gidan yarin kasar Potugal, ya sauka da misalin karfe ~ daya na rana. Dan Najeriyar, Mr. Balogun Babalolo, an kama shi ne a‘ kasar ta potugal bayan, ya yi nasarar danfarar wani kamfanin harhada motoci da kudi naira miliyan ‘ dari da talati, kuma ya fuskancl shari’a a can. .’ Daga ‘bisani gwamnatin _ Najeriya ta sake gano‘ wasu laifuka bayan wani binciken su’ na tsakanin kasa da kasa, wanda ake zargin Mr. Balogun da siyar da
wasu asiran gwamnati, saboda haka jami’an ciki suka sake cafke shi.
‘Yan mintocl kadan bayan saukar sa. Mr Balogun dan shekara saba’in da biyu, zal sake fuskanta, shari’a, akwai hasashen zai yi zaman rayuwa a gidan yari da zarar abin da ake tuhumarsa ya tabbata.
Duk wannan jawabin yana tafe ne tare da abubuwan da suka wakana a filin jirgi, watau an nuno Mr. Balogun cikin ankwa, yayin da jami’ai suka tasa keyar sa cikin motarsu. Alhaji bai gaskata idanuwansa ba tambaya yake. ..“Mr. Balogun? Mr. Balogun?? Malam Sadiq ya ce, ‘Ka san shi ne Alhaji? Ya amsa’, “Abokin aiki na mataimaki na da na ba ka labari, wanda ya zama sanadin bari na aiki, kuma aka lalata min takarduna.’
Cike da mamaki ya ce, “Shi ne? “lko sai Allah.” Alhaji ya dauki tasbihi ga Allah. Malam Sadiq na taya shi, ya mike a sukwane ya daga labule ya kira Mama, ta shigo falon a razane; “Lafiya Alhaji? Ya ce “Ba ki ga Mr. Balogun ba? Mr. Balogun? ‘Waye shi? Ya ce “Mr. Balugun__ dai abokin-aiki na, yanzu aka nuno shi a filin jirgi an kama shim
‘ Ta katse shi, “Lah! Wai dama shi ne aka nuno dan 419 da ya shekara ashlrin da biyar gidan yari? Shi fa ai ban gan shi ba! “lko sai Allah ka ga karshen maci amana k0? Al shl ramin karya kurarre ne.” Ya‘ ce, Tabbas haka‘ ne. Allah ya shirye mu baki daya.” “Amin ‘
dai.
Ta juya za‘ ta tafi. Malam a gaida min Hajiya Asiya.” Ya ce “Za ta’ji.” Ta fice tana tafa hannu tana maimaita sunan Mr. Balogun, idanuwanta na kara nuna mata shi cikin ankwa. Hirar da suka rinka yi kenan, har Malam Sadiq ya tafi. Shi kuma ya kulle kofa ya kashe komai ya dawo cikin glda, nan ma zancan suka yl ta tattaunawa da Mama har barci ya kwashe su.
Washe gari cikin jaridun da su Imam suka kawo masa, hutunan Mr. Balogun ne cikin sarka a shafukan

www.littafanhausane.com.ng

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]