MAEESHA CHAPTER B - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MAEESHA CHAPTER B

 MAEESHA CHAPTER B


Tana juyowa sai taga audu kafinta ne wanda duk unguwarsu ba wanda yakaishi iya kafinta.+

Tace ina wuni
Yace lafiya qalau dama dazu nine na aika akiraki kuma sai yaron yake cewa wai yayanki yahana kifito.
Kuma a sanina kekadai mahaifanki suka haifa bakida yaya.

Tace inadashi mnh amma nidai abar wanchan magana dafatan dai lafiya.

Ya dan shafi keyarsa sai yace ehh to dama ina tafe da wani sakone kuma dafatan zaki amince dashi.

Tace fadi ina sauranka.

Yace wato nadade inasonki mayiesha kawai narasa yadda zan tunkarekine da maganar.

Ta kalleshi tace so kuma

Haba audu kafinta nizaka kalla kace kana sona bayan a unguwar nan ba wanda baisan halinka na biye biyen mata bah.

Yace ai wannan halinane na da amma yanxu nadena.

Tace kaga malam audu kokuma nace audu kafinta kabar kofar gidannan tun kafin na sare maka kanka da wannan takobin,dan iska kawai kawani sako turarenka mai warin tusa kazonan wai kana sona.

Yana jin haka yace Allah ya huci zuciyarki nabarki lafiya.
Ya ficewarsa.

Itakuma tashiga gida takira yayan nata yana fitowa tsakiyar gida sai ya ganta da takubba guda biyu a hannunta yace to bani daya.

Tana mika mishi tace yau zan koya maka hankali yayi murmushi yace to shikenan ai saimu kwada.

Taje daki ta saka riga da wando sannan tafito.

Yana yi mata kallo daya ya kauda fuskarsa.

Nan sai suka fara fadan aikuwa saijin qarar takobi kakeyi.

Umma na bacci a daki taji hayaniya yayi yawa tace to Wannan hayaniyar kuma ta mecece baridai naje na gani.

Tana fitowa tsakar gida sai tagansu sai faman kaiwa juna hari sukeyi.

Tasaka salati tace yau nashiga uku yaki kuma a gidan nawa.

Suna jin hakan suka tsaya sai mayiesha tace umma kawai muna gwaji ne.

Tace kinci uwaki da gwaji yanxu idan dayanku yaji ciwo aini za'abari da jinya.

Munawwar yace umma ki kwantar da hankalinki dukanmu mun kware fah ba wanda zaiji ciwo.

Tace munawwar kamamun bakinka wlhy dukansu kufita idona kada na saba muku.

Yanzunnan ki mayar da wadannan takubban inda kuka samosu kafin raina ya baci.

Suka kalleta a tare umma tace daku nake magana fah.

Sai mayiesha ta turo baki ta karbi ta munawwar ta saka hijabinta zuwa mayarwa.

Da daddare suna zaune a tsakiyar gida suna shan iska sai abba yace yawwa munawwar dama na yanke hukuncin tunda kaga zaune kake a gida yakamata mufara zuwa kasuwa tare.

Munawwar yace to nikam abba ai ban iya kasuwanci ba.

Abba ya kalleshi yace ai yauda gobe idan kana ganin yadda akeyi zaka koya.kuma sana'ata bawata babba bace ina siyar da yen kunne ne da sarkoki da kuma turaruka.amma fa ba zinare bah.

Munawwar yace to abba inshallah zan zama mai dagewa naga na koya Allah yabamu sa'a

Dukansu sukace ameen.

Abba yace kuma yanxu katashi muje gun mai aski ya rage maka wannan gashin naka kamar na mace.

Munawwar yace to abba

Mayiesha tace kenan abba nikadai za'a dinga bari a gida.

Umma tace tunda ni ba mutum bace ba koh.
Mayiesha tace ni umma ba haka nake nufibah.

Abba yace ai makarantar boko zaki koma tunda dama aji nakusa da qarshe kike a secondary yafimiki.

Tace to shikenan abbana.

Yace yanxu gobe ki shirya idan zamu wuce kasuwa sai muwuce dake na biya miki kudin makaranta kawai kici gaba da zuwa kuma wlhy idan naji bakya kokari ranki sai yayi matukar baci.

Tace inshallah abba zandinga kokari.

Washe gari da sassafe dukansu suka tashi sai shirye shirye sukeyi.bayan sun gama suka karya kumallo sannan suka nufi makarantar su mayiesha.

Bayan abba yabiya kudin makaranta ta wuce aji.

Sukuma suka wuce kasuwa.

Tana shiga aji sai taga hafsat chan qarshen benci tana zaune.
Taje gunda tace hafsat take cikin mamaki hafsat tace mayiesha yau kuma kece a makaranta.

Tace wlhy kedai nice ina sauran qawayenmu bangansu bah.

Hafsat tace suna sashen yen ss3
Tace tokekam yana ganki anan tace nima repeating abba na yasaka akamun wai tunda banida kokari sosai bazai bari naje aji na gababa.

Tace kinga kenan dagani harke yakamata mudage dantse domin muyi karatu sosai tace hakane kam gsky.Allah yabamu sa'a mayiesha tace ameen.

Bayan an tada su daga makaranta mayiesha ta tari mai adedeta yakaita gida.

Suna isa ta dauki naira dari ta mika masa tace kabani chanji.

Ya kalleta yace wani chanji zan baki ai naira dari nakawoki.

Tace kamm buu ai wlhy naira hamsin ne ake kawoni daga makarantarmu zuwa gida.

Yace to nidai a dari na kawoki har ya tada adedeta dinsa zai wuce sai ta cire hijabi taci damara.

Ta chakumo kwalar rigarsa tace wlhy kodai kabani hamsin dina kokuma nayi maka uban duka.

Yanajin haka yafito daga adedeta dinshi yace kece zakiyi fada dani to gani ki dakeni muga.

Ai kuwa yana fadan  haka kafin ya rufe baki ta kai masa uban naushi a fuska nan take hancinsa yafara jini.

Yace jar ubannan nikika fasawa hanci ai wlhy yau sai dai akwasheki sumammiya anan.
Nan take yara suka taru suna kallonsu.

Har ya daga hannu zai mareta sai tayi saurin rike hannunsa ta juyashi da qarfi sai kawai jin kayi qashin hannunsa yace qasss.

Yabuga ihu tace ai wlhy gobe bazaka qara cewa zaka dake wata macen bah ballan tanani.

Tasake kai mishi bugun naushi a ciki tace kabani hamsin dita kokuma yanxunan na karairayaka.
Ai kuwa cikin sauri ya mika mata hamsin yaja adedeta dinsa cikin mamakin qarfi irin na mayiesha ya fice.

Ta juyo ta kalli yaranda ke gurin ai kuwa kowa yakama gabansa.

Sannan tashiga gida.

Tana shiga tafice zuwa kitchen ta dibo abunci ta tarar da umma a parlor tace umma ina wuni

Umma tace lafiya qalau yana ganki kinci damara haka.

Tace umma wani dan adedeta ne fa yaso ya renamun wayo shine nakoya masa hankali.

Umma tace wato baki dena wannan halin nakibah na dukan mutane to idan abbanki yadawo saina fada mishi zakiji ajikinki yau.

Nan take tace umma dan Allah kiyi hakuri bazan sakebah.

Tace to da kin kyautawa kanki sbd ba namijinda yakeso ya auri mace masifaffiya.

Tace nifa umma kinsan niba masifaffiya mace sai idan an tabo ni.

Tace amma ai yanada kyau mutum yakasance yanada hakuri.
Nidai yanxu kigama cin abuncinnan kicire uniform sai ki kaimun markade.

Tace to umma.

By maryam ashutrah

Bayan wani lokaci.+

Abba yana zaune a shagonsa yana kirgan wasu yen kudade.

Shikuma munawwar Yana cinikin kaya da wasu yen mata.bayan sun gama sai daya daga cikinsu tace idan bazaka damubah zan iya samun number wayanka.

Yace banida waya
Tace babban yaro irinka bakada waya.

Yace ehh sai abba yataso yace yen mata wannan fah mijin aurene yana da iyali dan Allah kutafi.
Cikin mamaki suka wucewarsu suna cewa amma ai wannan baiyi kama da mai matabah.

Abba yace kadena biyewa wadannan yen matan yen iskane saisu lalatawa mutum tarbiyya.

Munawwar yace inshallah abba bazan sakebah.

Suna zaune shida abba a shago saisuka fara jin hayaniya a waje suna fitowa sai sukaga wani barawone yayi sata yanata gudu mutane nabinsa.

Cikin sauri yana isowa gefen shagon su abba,sai munawwar yabishi da sauri yarike shi.

Cikin bacin rai yakaiwa barawon wani irin naushi sai kawai ganinsa akayi kwance a kasa ya suma.

Mutane suka iso gurin sunata yiwa  munawwar godiya daya samu ikon kama barawon.

Saiga wata hajiya fara kyakkyawa mai jiki ta iso gurin itada qawayenta

Munawwar ya dauki jakar daga hannun barawon ya mika mata yace hajiya ga jakarki.

Ta kalleshi tayi masa godiya sannan tace dan saurayi ya sunanka yace sunana munawwar.

Ta dauko wasu yen kudade daga jakar ta mika mishi yaki ya karba.

Tace ka chanchanci hakanne dan Allah kada kaki karba bazanji dadibah.

Sai kawai ya karba yayi mata godiya tashiga mota itada qawayenta suka fice.
Shikuma yakoma shago.

Yana xuwa sai yake nunawa abba kudin.
Abba yace ai wannan kudine masu yawa har dubu goma.

Ya mikawa abba yace gashi sbd nikam bansan mezanyi dasubah.

Abba yace a'a munawwar wannan hakkinkane bai kamata na karbaba.

Yace to ni yanxu abba yazanyi dasu.
Yace kaga yakamata kasamu koda yer qaramar waya irin ta dubu uku saika siya sbd yakamta ace ka iya waya sannan kuma idan ina wani gun zan iya kiranka.

Yace hakane amma zansiyawa qanwata sbd itama mudinga waya.

Abba yayi murmushi yace to ba damuwa idan muka tashi aiki sai muje na rakaka kasiya har da layi da komai.

Suna tashi daga kasuwa abba ya rakashi gunda ake siyarda wayoyi suka siya guda biyu da layuka akayi musu rijista sannan suka wuce.

Suna cikin adedeta zasu koma gida sai munawwar ya hango mai kaji.

Nan take yacewa mai adedeta din daya tsaya.

Yafita yaje yasiyo kaji guda biyu gasassu da kuma lemun kwalba guda hudu dakuma abubuwan hada shayi irin madara da lipton da kuma bredi da suga duka sannan ya wuce zuwa adedeta,suka fice zuwa gida.

Suna isa gida suka shiga da sallama mayiesha na parlor itada umma tana kwance saman kafafuwan umma sai zuba mata surutu takeyi suka jiyo sallamar su.
Da sauri mayiesha ta fita tayi musu sannu da zuwa sannan ta taya munawwar karban kayan dake hannunshi.

Suna isa parlor suka zauna sai munawwar ya gaida umma

Cikin farin ciki ta amsa sai ya mika mata kayan shayi da ledar kwai yace umma gashi gobe da safe shayi zamusha  da wainar kwai.

Tace to shikenan dana Allah ya kaimu sai kuma ya mika mata ledan kaza yace wannan keda abba nikuma wannan nida qanwata.

Ta karba tace Allah yayi maka albarka munawwar dama ace inada da irinka danaji dadi.

Nan take ya bata fuska ya kalli abba yace kaji fah abunda umma take cewa kenan niba danta bane.

Umma tace ai nikam ban isa  nace haka bah wasa nake maka.

Yayi murmushi sannan tace yer qanwata akwai abunda nasiyo miki rufe idanki.

Su umma suka tashi suka fice zuwa daki dan acewarsu bazasu zauna suka kallon shiririta irin ta ya'yan nasubah.

Tana rufewa sai ya dako wayan yace to bude idanki.
Tana budewa yace surprise

Ta karbi wayar cikin jin dadi tace kaii amma natayaka jin dadi ka siya waya.
Yace ke batawa bace takice gatawanan.

Tayi tsalle ta rungumeshi yace nagode yayana.

Yace yanxu kinga koda idan ina kasuwa zan iya kira naji yakike.

Tace hakane.

Kuma kinga iri daya na yimana.

Yanxu dai yunwa nakeji ki dauko mana plate muci kazarmu.
Tace to.

Hajiya salamatu na zaune a parlor sai tunanin take tayi saiga hajiya zinaru tashigo parlor din.

Ta zauna kusa da hajiya salamatu tace hajiya lafiya tunda muka dawo kasuwa nakasa gane miki.

Hajiya salamatu ta kalleta tace wlhy hajiya zinaru tunda na kalli wannan yaron wanda ya taimakeni a kasuwa sai ya tunamun da dana wanda yabata.kuma gashi sunansu daya bayan hakan suna dan kama.

Hajiya zinaru tace tabbas hakane sbd nima dana ganshi saida naji gabana ya fadi.

Hajiya salamatu yace to kodai shine dana wanda ya bata.

Hajiya zinaru tace haba hajiya ki kalli wannan fah dan talakawane daga ganinshi kuma danki ai ba wanda yasan ko wace ma duniyar yake.

Tace hakane amma zanso naje naji tarihin sa.

Hajiya zinaru tace to kinsan mezai faru zan saka anemomuna inada suke zama idan yaso sai muje chan kinga yafi mutunci

Amma dan Allah kisaki ranki.

Tace to naji.

Washe gari da safe bayan dukansu sun shirya fita sai mayiesha tace yaya nikam bansan inda na ajiye hijabina na makarantabah kuma gashi tun jiya dana wanke uniform dina ban wankeshibah.

Yace to saiki saka wani mana
Tace uniform daya nakeda.
Amma kudan jirani bari naje nan gidansu qawata fatima idan bata wuce makarantabah saina aro mara guda daya.

Sai yace to kiyi sauri kafin abba yafito.

Tana fitowa tawuce zuwa gidansu fatima tana shiga sai tayi rashin sa'a batanan.
Sai maman fatima tace amma bari naduba miki.

Tana dauko mata ta bata sai mayiesha tayi godiya tayi saurin komawa gida.

Tana saka hijab din munawwar yace uniform dinnan na makaranta yana miki kyau.

Tace ai kai komai idan nasa haka kake cewa saiga abba yafito yace to kuwuce muje kada ki makara.

Umma tace to Allah yabada sa'a
Dukansu sukace ameen.

By maryam ashutrah

Hajiya salamatu na zaune tare da hajiya zinaru a balcony din gidan saiga kira yashigo wayan hajiya zinaru.

Tana dagawa sai tace hello umar kasamo adireshin gidanne.
Yace eh hajiya tace to katuromun ina jira.
Yace to hajiya yanxunan zan turo miki
Tace to nagode.

Ta kalli hajiya salamatu tace ansamu adireshin gidan mubari har zuwa maraice haka sannan mutafi.

Tace to Allah ya kaimh kuma Allah yasa shine dana munawwar.
Tace ameen.

Ana tashi daga makaranta sai hafsat tacewa mayiesha anjima da qarfe hudu akwai walima a gidansu ta saukar qanena ina fatandai zakixo.

Tace eh zanxo inshallah kibani number dinki idan na isa saina kiraki.
Tace aww kinyi wayane.
Tace ehh yanxu inada waya.
Tabata number din sannan tashiga adedeta tafice zuwa gida.

Tana zuwa gida take sanarwa umma tacewa zataje walima gidansu hafsat.
Umma tace to shikenan kinga bari nabaki cikon kudin tasi'u tela kikai masa saiki anso dinkinki dake gunsa.

Tace to umma.

Tana karbar kudin taje ta karbo dinkinta sai ta biya ta gidansu fatima ta kaimata hijabinta.

Tana kan hanya zata wuce gida saiga wani mai mashin yasha gabanta.

Yace yen mata sannu fah
Ta watsa masa harara tace yawwa
Yace amma ke kyakkyawace.

Tace ai nasani basaika fadabah.

Yace kinga baikamata nayi magana dakebah anan ba mutuncinki bane kiyimun kwatancen gidanku sai nazo.

Tace lafiya dai kakeson sanin gidanmu
Yace akwai maganarda nakeson muyine.

Tace malam kafadi koma menene anan kana batamun lokaci.

Ya sauko daga mashin dinsa sannan yace ina ganinki ne kawai sai naji mashin soyayyarki ya harbi zuciyata.m a'ana naji inasonki.

Ta kalleshi sama da qasa tace to nagode amma ina da wanda zan aura sbd ansaka rana.

Yace to ai wannan ba matsala bane.
Tace mekake nufi idan ba iskanci kakeso danibah yaza'ayi nace maka inada wanda zan aura sannan kacemun wannan ba matsala bane.
Kaga kawai kaja akwalan mashin dinka kafice daga nan.

Yace haba yen mata wlhy inasonki na hakika

Tace idan kakara cewa kana sona saina hada maka jini da majina .

Tace a'a basai anyi hakabah Allah ya huci zuciyarki sai anjima.

Ta fice warta shikuma yaja mashin dinsa yayi gaba.

Tana zuwa gida ta fara shiri tayi matukar kyau sosai tasala lace dinta blue riga da skirt kayan sun kwanta a jikinta sosai.

Tana gama shiryawa tafito tacewa umma to nikam natafi.

Tace Allah ya tsare munke ya'ta dan Allah banda fada.

Tace ai umma nadena saina dawo.

Tace to a sauka lafiya.

Tana fitowa saita kira munawwar yana dauka tace yayana zanje walima gidan qawata

Yace kada kidade sbd banason nadawo gida bakinan.

Tace to shikenan bazan dadebah yakashe wayar.

Qarfe biyar da rabi ta dawo gida.umma tace yanxu kitashi kije ki azamun sanwa sbd yau banajin dadin jikina sosai.
Tace to umma.

Tatashi tafice zuwa kitchen.

Umma na zaune tsakar tana hutawa sai taji ana sallama tans juyowa taga ai qawar tace abida.
Ta amsa sallamar tare dayi mata maraba.
Tana zaunawa sai tace dama naje gidan hadiza ne nayi mata barka shine nace bari nazo nan na ganki tunda mun kwan biyu bamu hadubah.

Umma tace hakane gsky Nagode sosai Allah yabar zumunci bari nakira mayiesha ta kawo miki ruwa.

Ta kwalawa mayiesha kira tana fitowa ta gaida qawar ummanta sai umma tace ki kawo mata ruwa mai sanyi nasan ta kwaso rana.

Tace to umma.

Tana wucewa sai abida tace lallai safara'u (sunan umma na ainihi)yanxu ashe mayiesha tayi irin wannan girman amma har yanxu kin zauna kina kallonta.
Kuma yakamata ace tana gidan miji ai.

Umma tace ai aure lokacine kuma idan yazo zatayi banason na dagawa ya'ta hankali nafison a duk lokacinda ta samu wanda takeso sannan muyi mata aure cikin kwanciyar hankali.

Tace to kuma hakane Allah ya kawo nagari.

Umma tace ameen.
Suka danyi hira nawani dan lokaci sannan ta fice.

Qarfe shida saiga su abba sun dawo daga kasuwa.
Dukansu suna zaune suna hira sai akayi sallama.

Suna dubawa sai sukaga wasu mata su biyu daga ganinsu kaga yen hutu.

Suka shigo da sallama.
Dukansu suka amsa sai umma ta dauko musu tabarma ta shimfida musu.

Suka zauna suka gaisa dukansu.
Sai umma tace kuyi hakuri amma ban shaidakubah.

Hajiya salamatu tace eh hakane baku sanmubah amma muna tafe da wata maganace mai muhimmanci

Umma tace muna saurarenku.
Tace wannan yaron munawwar dan Allah dankine ina nufin kekika haifeshi.

Umma ta kalli abba shima ya kalleta.
Sai abba yace meyasa kuke son sani.
Sai hajiya salamatu tace domin shekaru da yawa da suka shude akwai dana mai suna munawwar wanda yabace kuma har yanxu bamusan inda yakebah.

Abba yace tabbas munawwar ba danmu bane kuma shima ya dade rabonsa da mahaifansa.
Nan ya kwashe dukkan labarin yafada mata.

Cikin kuka mai ban tausayi hajiya salamatu tace wlhy danane munawwar.

Munawwar ya kalleta yace wace hujja kikeda akan hakan.

Itama ta kwashe labarin komai ta fada musu.

Munawwar yace tabbas sunan mahaifina alhaji abdulhakeem kuma sunan mahaifiyata hajiya salamatu.

Nan abba yace Allah mai iko ashe da rabon zaku sake haduwa.

Munawwar cikin kewar mahaifiyarsa yaje ya rungumeta suna ta kuka dukansu.
Bayan wani dan lokaci sai munawwar ya kalleta sannan yace ummata meyasa bangane kibah tace sbd watakila tun kana qarami rabonka dani sbd bana yawan zama a gida sbd ina zuwa qasashen waje kasuwanci kuma kafi sabawa da mahaifinka.

Yace to yanxu ina mahaifina meyasa bakuzo tare bah.
Nan take wasu sababbin hawaye suka fara zubo mata tace ai mahaifinka yayi shekara biyar da rasuwa sbd fama da yayi da ciwon zuciya sbd rashinka.

Munawwar yasake fashewa da kuka yace Allah yaji qanshi da rahama.
Dukansu sukace ameen.

Hajiya salamatu ta kalli umma da abba tace bansan wace irin godiya zanyi muku tare da yer ku bah sbd kunrike munawwar da amana.
Sannan kunyi mishi halacci sannan kuma kuka maidashi mutum ta hanyar kula da addininsa da kuma koya masa kasuwanci domin yarike kansa.

Abba yace ai bakomai hajiya muma sbd muna neman sakamakone daga ubangiji dakuma samun lada shiyasa.

Mayiesha tace kenan yaya munawwar qarshen zamanmu yazo tunda yanxu tafiya zakayi tare da ummanka.

Munawwar yace ai koda kuwa naje tare da ita muna tare sbd yanxu mun zama yen uwa sbd inada wasu iyayen anan.

Mayiesha ta tashi cikin kuka ta wuce daki.

Munawwar na ganin haka yabi bayanta.

Abba ya kalli hajiya salamatu yace ai wlhy sun saba sosai fiye da yadda kike tsammani bacci kawai yace rabasu.

Hajiya zinaru tace tabbas kuwa sbd munga alaman hakan yadda hankalinsa yatashi daya ganta tana kuka.

Amma inada shawara.

Hajiya salamatu tace kifada.

Tace mazai hana a hadasu aure tare.

By maryam ashutrah

Umma tace aure kuma
Ai ba soyayya a tsakaninsu.+

Hajiya salamatu tace ai nikam bama aure nakeso yayi yanxu bah sbd inason yayi karatu.

Abna yace ehj hajiya hakane karatun yana da matukar muhimmanci amma kuma namiji idan yakai irin wadannan shekarun anason ayi mishi aure sbd samun nutsuwar zuciya.

Tace hakane kan amma zanyi shawara.

Yace to badamuwa yanxu bari nakira miki shi.

Tana shiga dakin ta yaddata a kan gado tana kuka yace haba mayiesha bafa mutuwa zanyibah meyasa zaki tada hankalinki.
Tace yayana nasaba dakai bacci kawai yake shiga tsakaninmu banason kayi nisa dani dan Allah kada kaje ka barni.

Yacs kinga mayiesha yakamata naje sbd yanxu dole na zauna tare da ummata sbd mufara shakuwa sannan mu fahimci juna amma nayi miki alkawarin zan dinga xuwa ina ganinki.

Suna cikin hakane sai abba yashigo da sallama munawwar ya kalleshi yace yawwa abba dan Allah ka fahimtar da mayiesha.

Abba yace mayiesha kiyi hakuri ai bawai bazan dinga zuws yana ganinki bane kinji.
Tacw to ka dauki alkawari.

Munawwar yace nayi miki alkawari.
Tace to muje na shirya maka kayanka.

Abba yace idan kun qare kufito da wuri.suna shiga dakin ya kwashe dukkan kyansa tasaka mishi a gana must go.

Ta dauka shikuma yana biye da ita a baya.

Suna fitowa hajiya dukansu suka tashi tace to mukam zamu tafik kuma inshallah Allah zamu dinga kawo muku ziyara akai akai.ta bude jakarta ta dauko dubu dari biyu ta mikawa abba.

Tace gashi ayi cefane.
Abba yace ai abunda mukayiwa munawwar sbd musamu lada mukayi bawai sbd musamu sakayya daga gunkubah hajiya.

Tace tabbas hakane kuma nima bawai sbd hakan na baku kudinnan bah dan Allah ku karba.kuma ba kyau baida hannun kyauta baya.

Abba ya karba sannan dukansu sukayi godiya.

Suka rakasu har bakin mota suna shiga sai munawwar ya kalli umma yace nagode miki sosai da irin kula dani da kikayi Allah yabiyaki da gidan Aljanna kaima abba haka.
Yace ba komai munawwar kuma dan Allah kamar yadda nasanka da amana da kuma tarbiyya dan Allah kaje da wadannan kyawawan halayen naka a ko ina.tabbas mutane zasu soka

Yace nagode abba.

Ya kalli mayiesha yace nagode miki yer qanwata da kulawarki.

Yashiga mota yana hawaye.

Suna daukar hanya sai hajiya tace munawwar wadannan kayan naka idan muka isa gida zan baiwa mai gadi su yaci gaba da sakawa yanxu zamu biya dakai boutique ka siyo kaya iya wadanda kakeso sannan kuma muje supermarket kasiyo duk abunda kake bukata.

Yace to ummata nagode.

Tace haba godiyarme kakemun kada ka sake godemun sbd na maka wani abu.

Bayan sunje boutique da supermarket sun siyo duk abunda zai bukata sannan suka fice zuwa gida.

Nana aka bude musu gate suka shiga wani irin katafaren gida na gani na fada.wanda kallo daya zaka masa kasan lallai mutanen cikinsa attajirai ne

Suna parking din mota suka fito sannan yace akwai abunda nakeso naduba cikin kayana idan na dauka saina kawo wa mai gadi.
Umma tace to badamuwa my son.

Suna shiga cikin parlor munawwar yadinga bin ko ina da kallo sbd babban parlor ne sosai gashi anzuba mishi dukiya ta ko ina sai sheki da kamshi mai dadi ke tashi.
Yana zaunawa sai hajiya salamatu tace wannan shine gidan mahaifinka dake wannan garin na katsina.

Yanxu muje na nuna maka part dinka.
Sannan kuma dan Allah kasaki jikinka kayi duk abunda kakeso sbd wannan gidankane.

Yace to umma ta.

Tana tafe yana binta a baya suka isa wani bangare na gidan.
Tana bude kofar suka shiga wani parlor hadadde wanda idan akace za'a fadi irin kyansa zai dauki lokaci.

Tace wannan shine parlour dinka sannan kuma ga dakinka a chan.zansaka a kawo maka kayanka kuma masu aiki zasuxo su gyara maka komai sannan idan akwai wani abu wanda baiyi makabah ka sanar dani sai a chanja maka.

Yace to ummata tace ta huta sosai taficewarta.

Munawwar ya dinga bin ko ina da kallo sannan ya shiga dakinsa mai matukar kyau gashi babba sannan ga wani irin hadadden gadi a ciki ga sanyi ta ko ina.
Ya shiga toilet yayi alwala yayi sallah sannan dinga godewa Allah daya sadashi da mahaifiyarsa.

Yana cikin hakan wayarsa tayi qara yana dubawa sai yaga mayiesha ce.
Ya dauka tace dafatan kun isa gida lafia yace lafiya qalau mayiesha da fatan kinci abunci.

Tace eh yanxu muka gama cin dambu nida umma.

Yace to yayi kyau nima yanxu zanje naci abunci saina kiraki.

Tace to shikenan kakula da kanka.yace kema haka sukayi sallama yakashe.

Yana fitowa parlor ya tadda masu aiki suka gaidashi sannan sukace sunason sushiga dakinshi domin su jera mishi kayansa yayi musu izini sannan suka shiga.

Yana fitowa babban parlor ya tadda hajiya zinaru.
Ya durkusa har qasa ya gaidata sannan yake tambayarta ina umma.
Tace tana dakinta ta nuna mishi dakin.

Ya shiga dakin tarw da sallama ta taddata tana sallah.
Yasamu guri yazauna tana gamawa ya gaidata ta amsa cikin jin dadi.

Sannan tace munawwar dama inason idan kadan kwana biyu anan na maidaka makaranta kaci gaba da karatu.idan kuma qasar waje kakeso to duk wannan ba maj wahala bane.

Sannan bayan haka inason idan kagama karatu na damka maka duk dukiyar mahaifinka kaci gaba da juyawa sbd nikam kaga shekaruna karawa suke tayi.kuna qarfina yana ragewa.

Yacd hakane umma nima inason naci gaba da karatu amma banason nayi nisa da mayiesha.

Tace yawwa dama akan ita mayiesha din na yanke shawarar zaka aure ta sbd shakuwar dake tsakaninku kuma naga yarintace mai hankali kuma kaima kaga kakai munzalin yin aure.

Yace umma taya zan auri mayiesha bayan ba soyayya a tsakaninmu kuma nikam a matsayin qauna ta na dauketa.
Tace ai idanma kunyi aure zaka iya zama da ita a matsayin qanwarka kuma matarka.

Yace to shikenan umma banason nakiyi miki biyayya akan koma idan har mayiesha ta amince nima na amince.tace
Yawwa Allah yayi maka albarka.

Yace ameen.

Tace nasan kanajin yunwa muje muci abunci.

Suka tashi zuwa dinning table.

Suna gama cin abunci sai hajiya zinari tace amma hajiya yakamata nakoma abuja gobe sbd yarana zasu dawo daga dubai jibi.

Hajiya salamatu tace hakane kam gaskiya Allah ya kaimu.

Tace bari naje na fara shirye shirye.

Tace to idan nagama da munawwar zanxo nasameki.

Tace to shikenan ta tashi zuwa dakinta.

By maryam ashutrah

Munawwar yace umma wacece wannan bansantabah.+

Wannan aminiya tace tun muna yara muke tare.tazo nan ne bikin qanena ne da akayi satinda ya wuce shine takeso takoma gobe.

Yace umma meyasa kika dawo nan da zama bayan ada kaduna muke.

Tace bawai nadawo katsina da zama bane kawai nazo bikine kuma ina hada wasu takaddun filayen mahaifinkane dake nan katsina idan na qare zamu koma abuja sbd bana son zama a kaduna sbd ganin nake a yanxu kowane lokaci wannan bokanyar zata iya sake kwacemun kai sbd haka zan siyar da gidanmu na kaduna.

Yace da izinin Allah umma bazata iya yimun komaibah a yanxu sbd nafi qarfinta.

Suna cikin magana sai aka kirashi a waya yana dubawa yaga abba me yake kiranshi.

Yana dauka sai yace da fatan kana lafiya munawwar yace lafiya qalau abba .

Yasu umma
Abba yace gata ku gaisa.

Ta karbi wayan umma tace dana munawwar kana lafiya.

Munawwar yace lafiya qalau

Tace to ka kula da kanka kuma kasaki jiki da ummanka sbd zataji dadin hakan sosai.

Yace to umma nagode saida safe sukayi sallama yakashe.

Hajiya tace munawwar banason kana rika irin wannan wayar daga yau sbd haka gobe zan baka kudi kaje kaida umar sai kasiyo irin ta yayi.
Sannan kuma zai dinga koya maka mota sbd inason nasiya maka mota bayan haka kuma sai kuje banki abude maka account yanda kaima zaka dinga amfani da kudinka basaina dinga bakabah.

Yace to umma nagode.
Tace nace maka kadena godemun idan na maka abu.
Yanxu katashi kaje ka kwanta saida safe yace to umma saida safe.

Yana shiga dakinshi yaga yanda  aka gyara ko ina ya qara kyau sosai.sai yaje yayi wanka sannan yasaka kayan bacci yayi shafa'i da witr sai ya dauko gana must go dinshi ya bude ya dauko hotonda sukayi tare da mayiesha yana kallo.

Ya daga wayarsa yakirata bugu uku ta dauka.

Suka gaisa sannan suka danyi hira na wani lokaci sannan sukayi sallama ya kwanta..

Washe gari mayiesha ta gama shirinta tsaf xuwa makaranta saita daga wayanta takira wayan munawwar har kusan sau uku sannan ya dauka.

Tace ina kwana yaya
Yace lafiya qalau qanwata

Tace har yanxu bacci kakeyi baka tashibah
Yace ai gashi yanxu kintadani

Tace to katashi kaje kayi wanka sannan ka karya yace to qanwata.

Tace nidai zantafi makaranta saina dawo.

To ayi karatu dayawa sukayi sallama ya kashe.

Yana tashi yaje yayi wanka yana fitowa ya shafa tsadaddun man shafawansa ta taje gashin kansa sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu dadi sannan ta bude drawer ya dauko qananan kaya masu kyai yasaka.

Yana saukowa zuwa parlor ya tadda hajiya zinaru zata wuce.

Bayan ya gaidasu sannan yace hajiya har zaki tafi

Tace wlhy yanxu zan tafi munawwar sai kuma idan aurenka ya tashi.

Ya shafa gefen fuskarsa cikin kunya.

Hajiya salamatu tace kidena zolayarshi fah.

Bayam sun rakota har gun mota tashiga sukayi sallama sannan tafice zuwa airport.

Suna shiga parlor yawuce dinning ya dibo abunci soyayyen dankalin turawa da kwai da kuma shayi mai kauri da sausage.

Ya kalli abunci yace Allah sarki jinake kamar naje nakaiwa mayiesha sbd nasan watakila yau koko da kosai tasha tafice makaranta.

STORY CONTINUES BELOW

Hajiya tace Allah sarki ina tausayin irim rayuwarda suke ciki.

Munawwar yace hajiya mezai hana mu taimakesu mu siya musu gida sannan mu baiwa abba jari mai kauri.

Tace nima nayi tunanin yin hakan amma inshallah nan bada jimawabah zanyi hakan.

Bayan sati uku munawwar yazama dan gaye ya qara kyau da haske yazama kamar balarabe ya qara wayewa sosai.

Umma da mayiesha na zaune tsakar gida suna wanki sunata hira sai suka jiyo kukan mota daga waje.
Bayan wani dan lokaci suka jiyo sallama suna juyawa suka ga munawwar ne da hajiyarsa.
Cikin farin ciki dukansu suka tarbesu mayiesha tayita kallon munawwar tace Amma yayana kaga yadda ka chanja sosai.

Yace mayisha kenan ai kema nan bada dadewabah zaki chanja idan kikayi aure.ta durkusa har qasa ta gaida hajiya.

Hajiya ta amsa cikin sakin fuska sannan tace munawwar kudan bamu guri zamuyi magana.

Suka tashi tare suka fice zuwa parlor.
Suna zaunawa tace yayana wlhy ka chanja sosai.

Yace mayiesha kenan kina nufin nafi kyau a yanxu.

Tace sosaima kuwa.

Yace albishirinki
Tace goro
Yace mummy na tasiyamun mota mai kyau sosai idan kika ganta zata birgeki sosai.

Tace ashedai kafaso gari yanxu yen mata zasuyo chaa akanka

Yace nikam kinsan yen mata basu gabana kekadai ce.

Tace bamganebah yace zaki gane idan lokaci yayi.yace akwai sauran dimame kidibomun sbd nadade bancibah

Tayi dariya tace yanxu zaka iya cin dimame yace eh manah.tace to bari nafibo mana sai muci tare

Hajiya ta kalli umma tace ina son dan Allah idan abban mayiesha ya dawo kice masa zan turo kawunan munawwar zobe sbd sunema mishi aurenta.

Cikin mamaki umma tace hajiya kufa masu kudine mukuma bamuda komai sai wannan gidan
Taya yermu zata auri munawwar
Hajiya tace ai arziki da rashinsa duk na Allah ne kuma bawanda yafi wani ga Allah sai wanda yafi tsoronsa.

Umma tace hakane inshallah zanyi mishi magana.

Tace yawwa na gode sosai yanxu akwai inda nakeso muje nida munawwar bari na kirashi a waya.

Suna cikin cin abuncin sai kiram hajiya yashigo.
Yana dubawa ya dauka tace kafito kasan akwai inda zamuje.

Yace to ganinan zuwa.

Mayiesha ta kalli wayanshi tace wannan wani irin wayane bamtaba ganin irin shibah yace sunanta Samsung s10 idan kinaso zan siya miki irinta.

Tace a'a nidai kawai ka barni da akwalar wayata.
Yace yanxu wayarda nisiya miki kike kira akwala tace no wlhy wasa nakeyi.

Yawwa namanta nafada maka abba yace zan rubuta waec dina wannan shekarar yanxu haka na fara shirye shirye.

Yace yayi kyau sosai ya dauko dubu hamsim daga aljihunsa yace ga wannan sai kici gaba da shiryawa.

Tace to nagode yayana
Yace idan ma basu ishekibah saiki kirani.

Tace zasuma isa inshallah.

Yatashi yace to muje kirakani.

Suka rakasu har waje.
Mayiesha tace tabb nikam ban taba ganin irin wannan motarbah.

Yace nan bada dadewabah zansiya miki wadda ta fita.sukayi dariya dukansu sannan  suka  sallama suka shiga mota suka wuce.

Abba yana dawowa bayan yaci abunci umma take sanar dashi yadda sukayi da hajiya.yayi farin ciki sosai sannan yayi fatan alkhairi yace Allah ya kaimu.

Washe gari qarfe biyu na rana qanen baban munawwar da sauran manyan mutane sukazo neman auren mayiesha a gidansu mayiesha motoci suka geru a wajen gidan manyan motoci kusan guda biyar.

abba da abokanansa suka tarbesu hannu bibbiyu.
Cikin farin ciki abba ya amince ya bada auren  mayiesha.sannan aka saka rana nan da wata daya.sannan bayan anci ansha sukayi sallama sannan suka tafi.

Kawon munawwar yaje gidan hajiya yake sanar da ita yadda sukayi tayi farin ciki sosai sannan kuma takira qawarta hajiya bintu dake zama a qasar dubai cewa zata turo mata kudade ta hado musu lefe naji da fada.

Abba yakira mayiesha yasanar da ita ya baiwa munawwar aurenta kuma nan da wata daya.
Tayi matukar mamaki sannan ta rasa shin farim ciki zatayi da auren kokuma bacin rai akan ambaiwa munawwar aurenta batare da amincewar tabah.

Sai kuma tacd abba na amince Allah ya kaimu sbd nasan munawwar mutumin kwarai ne kuma bazai cutar danibah.

Nan take takowane bangare suka fara  shirye shirye yayinda mayiesha ta fidda anko sannan ta rabawa qawayenta.

Umma kuma ta dage gun siyan kayan kitchen su korai da kwanikan abunci da tabarmu.

Amma hajiya tace duka ta hutar dasu wannan.
Akwana a tashi yau saura kwana hudu auren munawwar da mayiesha.
Inda aka kawo lefen amarya akwati talatin cike da kaya masu tsada da birgewa sannan kuma zinari masu tsada sosai aka saka a ciki.

Umma tace nikam bantaba ganin lefe irin wannan bah ai yayi yawa.

Qawar umma abida tace lallai yerki mai kashin arzikice.

Kowa sai fadan albarkacin bakinsa yakeyi.

Washe gari wankin amarya sannan aka kada kalangu da kidan kwarya qawayen mayiesha sukayita chashewa.

Shikuma ango da abokansa sai shirye shirye suke tayi abun ba'a magana inda suka hada party nasu na maza suma suka chashe.

akayi kunshi da gyaran gashi  na amarya.mayiesha tayi matukar kyau sosai.

Da daddare bayan mutane sun rage sai yen uwanta kawai. tafito tsakar gida takira wayar munawwar yana dauka yace my mayiesha yakike.
Tace haba yayaba tunda aja fara shirye shiryen aurennan fa kadena kirana kuma baka zuwa ganina.

Yace haba mekikewa zumudi nan da kwana biyu fah muna tare har abada.
Taji kunya sosai sannan tace to Allah yakaimu abba nidai banason irin wannan rashin kulawar.

Yace kiyi hakuri nadena.
Suna cikin waya gwaggo saratu tafito tace lallai yaran zamani da rashin kunya waton ke kinanan kina waya da mijinki ko kunya bakyaji.
Munawwar najin haka ya katse wayar yana dariya.

Tace to nikam gwaggo saratu mekuma nayi

Tace mukam lokacinmu idan akace miki ga mijinki guduwa kikeyi sbd kunya amma ke yanxu har waya kukeyi.

Mayiesha tabata fuska taficwar ta.
Gwaggo tace iyeee lallai yer nan.

By Maryam ashutrah

Munawwar yana zaune a parlour dinsa sai wayansa ta fara ringing yana dubawa yaga faisal ne kekiransa yana dauka faisal yace mun gama hada komai akan walimar da zamuyi gobe.

Yace to yanxu zan turo maka wasu yen kudade saikayi abunda ya kamata

Faisal yace waton mukuma bayinkane tunda kai kana gida kana hutawa.

Yace eh mnh ai banason na wahala sbd kada na rame kafin amarya tazo.

Faisal yace kuma da wannan dan wannan to shikenan dai sai naji alart.

Yakashe wayar.

Munawwar yatashi yaje part din mamanshi sbd gidan duk hayaniyar mutane tayi yawa.

Yana isa yashiga da sallama hajiya tace kenan.

Ya sunkuyar da kansa yace hajiya hadda ke koh.
Tayi dariya sannan tace ya'akayi.
Yace nifa yunwa nakeji kuma banason sauka qasa sbd mutane sunyi yawa yanxunnan sai acika mutum da surutu.

Tace to yanxu ka zauna sai naje na dibo maka da kaina
Yace yawwa hajiyata.

Saida yaci ya koshi sannan yanufi part dinshi.
Ya kunna tv yana kallo.

Yau ake walima inda aka kira malamai mata da yawa sukayi wa'azi mai ratsa zuciya amarya kam taci kuka.
Ana gamawa kowa akayi masa alkhairi sannan aka watse.

Sukuma su munawwar sai qarfe hudu suka fara tasu walimar inda aka kira manya manyan malamai sukayi wa'azi akan zamantakewar aure.

Ana gamawa akaci akasha sannan aka sallami kowa ya watse.

Yau ranar jumuah ana saukowa daga masallaci aka daura auren munawwar da aminatu mayiesha da sadaki naira dubu sittin.

Farin ciki ba kamar munawwar a ranar kowa sai zolayarshi akeyi.

Mayiesha kuwa ana fada mata an daura aure tun lokacim take kukan rabuwa da ummanta har kusan qarfe biyar.

Sannan suka fara shirye shiryen daukar amarya.

Qarfe takwas motocin kai amarya suka iso.motocine nagani na fada guda goma bayan yawan nasihohi da tasha daga umma da abban ta sannan aka kwashi mutane zuwa kai amarya.

Suna isa gidan aka bude musu gate suka shiga.

Kowa sai sakin baki yakeyi suna kallon gidan wasu nacewa Allah yabamu danshenki mayiesha.suka kaita gun hajiya salamatu inda tayi mata nasiha sosai.sanan aka gwada musu part din amarya suka shiga.

Suna kaita kowa yafadi albarkacin bakinsa sannan suka fito inda hafsat tace amarya kada kimanta gobe nd zamu zana last paper dinmu ta waec mayiesha dai batace da ita komaibah sai faman kukanta takeyi.
Hak ta gaji taficewarta.

Bayan ancikasu da shatara na arziki sannan suka fice.

Sai kusan qarfe goma sannan abokanin ango suka shigo da ango.

Suna shiga cikin gidan yawuce part dim hajiya shima bayan tayi masa tasa nasihar sannan suka raka ango har kofa.

Faisal yace kunga kawai mubarshi daganan mutafi.

Kasim yace ai yakamata muga amarya

Faisal yace tunda amaryar kace dazaka wani ce kanason ganin amarya.

Haka ba yadda suka iya duk iyawarsu amma faisal ya hana kowa shiga.sannan sukayi sallama da munawwar sai suka fice.

Munawwar yashiga dakin da sallama yaji ba'a amsabah.

Sannan yaje ya ajiye kaza a gabanta sai ya cire babbar rigarsa ya ajiye.

Ya kalleta yace amaryata kuma qanwata da farko ina godiya ga Allah da yabanike a matsayin matata kuma mataimakiyata.
Kin taimake ni a lokacinda nake bukatarsa sbd haka idan ban kyautata mikibah banyi miki adalcibah.

Sbd haka ina fatan Allah yabamu zaman lafiya akan gaskiya da rikon amana.

Yace kibude fuskarki manah ohh namanta wannan ba aikinki bane.
Ya bude fuskarta a hankali sai idanunsa suka sauka cikin nata.
Yace meya sakaki kuka haka.

Tace bakomai yace wlhy saikin fadamun.

Tace kawai nima ina farin cikine nacewar zan kasance dakai har qarshen rayuwa a matsayin yayana kuma mijina sannan abokina.

Yace hakane yanxu kitashi muyi  sallah.

sallah kuma

Yace ehh mana
no kawai kai kaje kayi

meyasa
sbd ina jini

jini kuma yaushe yazo tace dazu da rana.

amma ba wanda yasani a gidanku
Tace ehh yace to shikenan nima bari naje nayi kijirani.

toh yashiga toilet yayi wanka sannan yafito ya feshe jikinsa da turaruka masu dadi yasaka jalabiya yayi shafai da witr.yagama adduoinsa sannan yace.

Yanxu dai muci kaza.

banajin yunwa

ehh dukda haka kiyi kokari muci kinji tace toh naji.

Yanaci yana bata a baki har saida sukayi rabi sannan tace takoshi.

to yanxu kije kiyi wanka sannan kishirya bacci.

Tace toh.

Tatashi tashiga toilet sai kuma ta fito.tace nikam kazo ka nunamun yadda ake amfani da wannan kayan toilet din

ayyah kinga na manta muje.

Bayan ya nuna mata komai sannan yafito itakuma tayi wanka bayan minti bakwai tafito daure da towel a jikinta.

Yana kallonta yace amma fah wannan towel din yayo miki kyai nan take kunya ta kamata ta dauko mayafi ta rufe jikinta.

kefa yanxu matata ce kuma kike hanani kallon jikinki.

nikam Allah kunya nakeji
zan cire miki ita nan bada dadewabah.

Nanta fara bude akwatunanta tana bincike bincike

me kike nema haka

bakomai
kifadamun na tayaki.

pad nake nema

meye kuma pad.

tunda baka sanibah kawai kayi shuru.

to shikenan
Tana bude qaramin akwatin ta ganshi ta dauko sai tace wannan shine pad.

me akeyi dashi tace kaikam kacika tambaya
idan ai baki fadamunbah gobe saina tambayi hajiya
Tace to zan fada maka ina zuwa dai ta dauki rigar baccinta tashiga toilet.
Cikin minti biyar ta fito sanye da wata yer qaramar rigar bacci .

Munawwar ya zuba mata kallo
Taje ta feshe jikinta da turaruka masu qanshi sannan tazo tace dashi mekake kallo.

Yayi murmushi yace matata nake kallo.

Tace to dai kallon ya isa haka.

Nidai kwantawa zanyi saida safe.
Yace yanxu bacci zakiyi ki banni.

To ai kaima saika kwanta sbd nikam wlhy a gajiye nake.

To shikenan kiyi bacci mai dadi
Bayan sun kwanta cikin dare kusan qarfe uku na dare mayiesha tafara jin cikinta yana ciwo.

Tarafa juye juye nan kuma ta farka tayi zaune saman gado ta dafe cikinta cikin tsananin ciwon da yake mata.

Nan take ta fasa kuka.

Munawwar ya farfado a firgice yace Lafiya dai mayiesha kike kuka cikin dare

Tace cikina yakemun masifar ciwo.

Yace subhanallah ciwon ciki kuma

By maryam ashutrah.

Bari nayi miki adduah inshallah zai dena.+

Tace wayyo nikam mutuwa zanyi.

Ya kalleta yace idan da mutuwa zakiyi da baki fadabah.yatashi zuwa parlor ya dauko ruwa cikin fridge da cup sannan ya dawo daki.

Ya zuba ruwam cikin cup yayi wasu adduoi sannan yabata yace kisha.
Tace bazan iya shabah.

ai kuwa kokikarbi ruwannan kisha kokuma yanxunnan nakaiki asibiti ayi miki allura.

Dajin hakan tayi saurin karba sannan ta shinye duka ta bashi kofin.

Ya ajiye sannan yazo kusa da ita yace sannu matata yanxu zai dena ciwo kinji kidan kwanta ki huta.

Ta kwanta ya rufe ta da bargo sannan yayi mata adduah sannan yaje ya kwanta.

Washe gari da safe.yatashi yayi wanka ya shirya cikin getzner mai masifar kyau yafito kamar wani balarabe sai kamshi yakeyi.
Sannan yaje gun mayiesha yace tashi kije kiyi wanka muje mu gaida hajiya.

Tace to.
Idan kin qare ina parlor ina jiranki.

Yafice Itakuma tashiga wanka.
Tana fitowa ta shafa mayukanta masu dadin kanshi ta feshe jikinta da turaruka sannan ta fiddo wata abaya mai matukar kyau ta saka.

Ta  saki gashinta wanda ya kwanta har gadon bayanta sannan ta dauki mayafinta tafito.

Tana isowa gunda yake ta gurkusa har qasa tace ina kwana mijina.

lafiya qalau matata ya jikin naki.

da sauki sosai.

kinyi kyau sosai kamar wata yer larabawa.

kaima haka yanxu dai tashi muje.

Ya tashi yana a gaba tana binsa a baya har suka iso parlor.

Nan suka tadda hajiya tare da wani mutum suna magana.

Suna qarasa maganar mutumin yaficewarsa.
Sannan suka isa gunda take suka durkusa har qasa suka gaidata.

Hajiya tace Allah yayi muku albarka yarana.
Yanxunnan nake cewa nakiraku ku karya sai gaku kun fito.

Yanxu muje dinning muci abunci.

Dukansu suka tafi dinning inda munawwar ya sakawa mayiesha naman kaza da soyayyar doya da kwai da kuma sausage a plate.da kuma shayi.

Shikuma tea kawai yasha.

Suna qarewa hajiya tace gobe nakeso mukoma abuja.

Munawwar yace tunda wuri haka.
Tace ehh sbd achan ne gidan mayiesha yake nasiya muku gida wanda zaku koma chan da zama.

Munawwar yace hajiya wai kina nufin wannan gidan wanda kika nunamun satinda yawuce.

Hajiya tace eh.

Munawwar yayi murmushi yace hajiya Allah ya biyaki da gidan aljannah

Dukansu sukace ameen.

Hajiya tace bayan haka kuma nasiyawa iyayenki gida anan yanxu haka sun koma achan da zama yau dinnan sannan nasamarwa mahaifinki aiki a wani company na dake garinnan.da kuma mota wacce zai dinga zuwa aiki.

Mayiesha nan take hawaye suka fara zubo mata tace ina matukar godiya a gareki hajiya bansan dame zan saka mikibah a duniyar nan.

Hajiya tace haba dai ai ke ba suruka ta bace kinkasance 'ya a gareni kuma kun chanchanci fiye da haka daga gareni sbd asana diyyar kune farin cikina yadawo gareni bayan shekaru dayawa.

Sannan kuma nan da wata daya inason naturaku london domin kuci gaba da karatunku achan sbd inason nayi saurin damka maka dukiyar mahaifinka kafin mahassada suyo chaa akanta.

Munawwar yace to shikenan hajiya Allah ya kaimu.

Tace ameen.

Yawwa mayiesha kitaso muje daki akwai abunda nakeso nabaki.

Munawwar yace haba hajiya kuma shine sai kunje daki.

Hajiya tace to ina ruwanka tsakanina da 'yata.

Yace to nayo shuru nidai idan kingama ina parlor ina jiranki.

Tace to.

Bayan sun shiga daki hajiya ta bude drawer dinta ta dauko wani yer qaramar jaka ta baiwa mayiesha tace gashi kyautace daga gareni.

Mayiesha ta durkusa har qasa tace nagode sosai hajiya.
Bakomai yanxu kitashi kije sai kibude a gaban mijinki sbd akwai inda nakeso naje.

Mayiesha tace to Allah ya tsare hanya.

Ameen mayiesha.

Tana shiga parlor dinta da sallama munawwar yace yawwa gwara kizo kigwadamun a bunda hajiya ta baki.

Mayiesha tace to ina ruwanka da kayana.

Ya tashi yaje gun inda take ya matso sosai jikinta yace mekika ce.

Tace bakomai

Yace ai nazata zaki maimaitane sai kiga abunda zanyi.
Tace nidai yanxu kaga ban san meye ma acikin jakarnan bah muje saimu gani.yace yawwa gwara da baki budebah.

Bayan sun zauna sai mayiesha ta bude jakar ta dauko wani dan qaramin kwali ta budeshi.

Tace wow meye wannan abun.
Munawwar ya saki dariya yace wannan wayace.

Mayiesha tace wannan wace irin wayace haka mai kyau sosai kamar madubi.

Munawwar yace iPhone 8 kenan.

Tace amma zaka koyamun yadda ake amfani da ita sbd nikam ban iyabah.

Yace ai dole na koya miki sbd kada ki dauki wannan qauyancin zuwa abuja.

Tace nadaiji.ta dauko dayan kwalin babba ta bude sai taga laptop ce mai matukar kyau.

Tace kaga wannan laptop ce
Yace to ya akayo kikasan wannan
Tace ai ina ganin irinta a office din principal dinmu.

Munawwar yace kinga koni nan banida laptop amma kinga hajiya ta siya miki.

Mayiesha tace sbd tafi sona akanka shiyasa.

Yace oho dai ai bazanji haushibah yanxu dai bude wannan kwalim muga meye.

Ta dauko kwalin shima ta bude tace woww kaga wannan qatuwar wayace.

Munawwar yace wannan ita ake kira ipad amma fa tayi kyau sosai nima zan chanja tawa na siya irin taki.

Tace nikam wadanan abubuwan duka yaushe zankoya.

Yace a hankali duka zaki koya mana kuma kinga idan mukaje london duka zaki bukacesu sbd karatu.

Tace hakane
Munawwar yace gaskiya hajiya tanasonki sosai amma nima zanyi miki kyauta wadda tafi wadannan duka.

Tace ba wata kyauta wacce takai wadannan amma zamu gani ai.

Yace hakane kam suma cikin magana wayarsa tayi ruri yana dubawa yaga faisal ne.
Yana dauka faisal yace ango kenan ya amaryar taka.

Munawwar yace gatanan lafiya qalau gobema zamu wuce abuja.
Faisal yacd haba dai kenan yakamata muzo yaj muci abuncin amarya kafin ta wuce.

Munawwar yace ba wanda zai wahalarmum da amarya sbd haka idam ma zuwa zakayi kazo da abuncinka.

Faisal yace to shikenan zanxo sbd yakamata musan juna.

Munawwar yace nifa inada kishi ko ganinta banason kuyi amma tunda ka tilasta to wlhy kazo kaikadai.
Faisal yace angama sai kum ganni.sukayi sallama.

Munawwar yace wai  faisal zaixo ya ganki  yanason musan juna kafin mutafi.

Tace ayyah ba damuwa sai yazo.

Yanxudai kitashi ki kwashe kayannan kikai daki.

By maryam ashutrah.

Mayiesha da munawwar na zaune akan gado yana koya mata sabuwar wayarta sai tace to bari nakira umma naji yasuke.
To shikenan yakamata
Tana kiran umma bayan tayi ringin uku ta dauka suka gaisa sannan take tambayarta ya munawwar tace lafiya qalau.
Suna cikin waya saiga kiran faisal yashigo a wayar munawwar.

Yana dauka faisal yace nifa ganinan a babban parlour.

Yace to ganinan zuwa yafita zuwa gunshi yabar mayiesha sai faman waya takeyi da umma
Yana saukowa ya ganshi a zaune.

Munawwar yace ashedai da gaske ne din kazo.

Faisal yace ohh waton kazata wasa nakeyi yana ganka kaikadai ina amaryar.

Munawwar yace nabarta tana waya da ummanta nasan yanxu zata sauko.

Faisal yace kaidai yanxu kazama magidanci saura ni.

Munawwar yace yakamata kam kayi aure gaskiya tunda ba abunda karasa.

Faisal yace hakane amma saina gama zabe sannan zanyi auren sbf har yanxu bansamu wacce ta kwantamunbah.

Munawwar yace to Allah yabaka.
Suna cikin hira saiga mayiesha ta sauko zuwa inda suke sanye da hijabi har qasa.

Tayi murmushi sannan tace sannu da zuwa.
Faisal yace Yawwa amarya yagajiyan biki.

Alhamdullilah bari nakawo maka abunsha tafice zuwa kitchen.

Faisal yace a gaskiya fah matarka tana da matukar kyau sosai.
Munawwar yace ai nafika sanin haka.
Faisal yayi dariya sannan yace amma wai batada qanwane sai kuhadani da ita.

Munawwar yace to itakadaice gun iyayenta.

Mayiesha tafito rike da tray a hannunta ta ajiye gabanshi.
Yace to godiya nake amarya.

Ya zuba juice a kofi yana sha sai munawwar yayi mata alamar ta tashi tawuce.
Itakuma ta gane hakan sai ta tashi tace wa faisal to nikam zanshiga ciki akwai shirye shiryen da nakeyi.

Yace to badamuwa naji gobe zaku wuce abuja to Allah ya kaiku lafiya .

Tace ameen nagode a gaida su umma duka.

Yace Zasuji inshallah
Sannan ta fice zuwa daki ta dauki wayanta sai shige shige takeyi.

Bayan minti goma saiga munawwar yashigo.
Tace har bakon naka yatafi yace ehh yawuce.

Yawwa baby na kina jina

eh ina sauraronka.

idan nayi bako bayan kun gaisa kika kawo masa abunci sai kitashi ki fice haka akeyi kinji.

to shikenan zan kiyaye inshallah.yawwa dama umma tace gobe da safe kafin muwuce yakamata muje muyi bankwana dasu.

ehh hakane kuma nima nayi tunanin haka Allah ya kaimu goben.

Tace ameen.

Washe gari tun qarfe tara suka tashi suka fara shirye shirye sbd hajiya tace jirginsu na qarfe biyu ne.

Sai qarfe sha daya sannan suka gama.

Bayan sun shirya suka je part din hajiya suka sanar da ita zasuje suga su umma.
Tacd to kugaidamun dasu sosai dan Allah.sukace to sannan suka shiga mota suka kama hanya.

Bayan kwatance basusha wuyabah suka gane gidan.

Suna shiga umma ta tarbesu cikin murna da jindadi.

Bayan sun gaisa sai umma tace yanxunnan kuwa abbanku yafita amma bajimawa zaiyibah zai dawo.

Mayiesha tace to ai saimu jirashi.

Umma tace mayiesha kinga irin alhairin da hajiya tayi mana ba  abunda zamuce sai godiya.

STORY CONTINUES BELOW

Munawwar yace haba ai kunfi wannan ma umma.

Umma tace wlhy kurike juna da amana da gaskiya da kuma yarda shizai saka aurenku yayi albarka yakuma dore.

Suna cikin magana abba yashigo.
Bayan sun gaisa shima yayi musu tashi nasihar mai ratsa zuciya sannan suka tashi sukayi sallama cikin kuka mayiesha ta shiga mota suka fice sbd tabbas tasan zatayi kewarsu sosai.

Qarfe daya da rabi suka wuce zuwa airport qarfe biyu jirginsu yatashi zuwa abuja.

Mayiesha ta kalli muna tace nida kullum saidai naga jirgi a sama yana yawo amma yau nice a ciki.

Munawwar ya rufe mata baki da hannunshi yace mutane fah suna jinki kada a daukeki baqauya.idan dai jirgine ai yanxu kika fara shiga.

Tace haka dai kace.

Bayan minti talatin suka sauka garin abuja.
Haka akazo daukan su da motoci masu kyau da tsada har izuwa maitama gidansu.

Bayan sun huta sannan hajiya tace yakamata kuwuce gidanku sbd yau achan nakeso ku kwana.
Munawwar yace amma ai yakamata a bari har gobe.

Hajiya tace idan ka zauna anan din mezakayi.

Yace bakomai tace to kagani driver na jiranku a waje.sannan kuma zan wuce italy gobe da safe akwai kasuwancin da zanje nayi achan bayan sati biyu zan dawo.

Dukansu sukayi mata fatan alkhairi sannan suka fice.

Tafiyar minti goma sukayi sannan suka isa gidan.

Ana bude musu kofa suka shiga wani irin katafaren gida mai matuqar kyau ta ko ina.

Suna fitowa daga mota mayiesha tace munawwar wannan shine gidanmu.

Yace eh shine

Tace amma kam yayi babba da yawa bazan iya zama nikadai a cikibah.

Yace haba dai saikice ba jarumabah kuma ai akwai ma aikata a ciki.

Tace to da sauki.

Yace mushiga ciki suna shiga babban parlour na qasa suka dinga kallon ko ina daga shi har ita suka koma qauyawa.

Munawwar yace to konidai bantaba ganin gidanda yayi kyan wannan bah.

Mayiesha tace ballantana ni.sukayi dariya tare sannan yace kinga wannan kenan zai kasance parlon baki wanchan part din kuma na gefen dama ya kasance na hajiya idan tazo sai kuma na hagu yazamo nash abba da umma idan sunzo.
Boys quarters din dina kuma na baki ne.
Mu haura sama.
Suna haurowa ya bude dakin farko yace kinga wannan zai kasance dakinki suka matsa kadan daga gefe yabude dakin babba ne sosai yace kinga wannan zai kasance dakina ga kuma parlor dinmu chan a gefe ga kuma kitchen ta baya.

Tace gsky yayi kyau sosai Allah yabamu zaman lafiya yace ameen.

Yace shiga kidan huta bari nasaka a hauro mana da kayan mu tace toh.

Bayan kwana biyar dukansu sun saba da gidan kuma sukan fita yawon ganin gari dakuma shakatawa cikin qanqanin lokaci mayiesha ta waye sosai sbd ba abunda yake bata wahala idan dai aka koya mata sau daya.

Tana kitchen tare da yen aiki suna tayata aiki sai kiran munawwar yashigo wayanta.

Tana dauka yace pls ki hado mun coffee kikawomun ina balcony na sama.

Tace to yanxunnan ma kuwa.
Bayan ta hada ta hausa zuwa inda yake ta ajiye masa akan table tace gashi.har zata wuce yace ina zaki kuma.

Tace bamu gama aiki bafah

Yace kibarsu suqarasa zauna kitayani hira.

Tace to gani bayan ta zauna yace rufe idanki.

Tace na rufe idona kuma
Eh kirufe.
Tana rufe idanta sai kuma yace bude.

Tana bude idonta suka sauka akan makullin mota benz

Tace makulli kuma na meye.

Yace dazu kinga ai anshigo da wata mota a gidanan kikace ta waye nace zan gaya miki.
To takice kena siyawa.

Cikin murna ta karbi makullin sannan taje ta rungumeshi tace Allah ya qara arziki mijina yakuma karemun kai a ko ina.

Yace ameen matata.yanxu zuwa gobe zan fara koya miki
Tace to Allah ya kaimu.

Data sanar da ummanta akan motarta ba qaramin dadi tajibah  sannan ta qara bata shawara akan ta kula da mijinta sosai ha hakkokinsa.

Da daddare bayan ta gama sallar isha tayi adduoin ta sannan taje gunda munawwar yake tace barka da dare mijina.

Yace yawwa matata yaushe kikayi tsarkine kuma baki sanar danibah

Tace yau ne fah bayan sallar asr.

Yace yawwa kinga kenan yau zanzama ango kinga yanzu saiki tashi muje muyi nafilah muyiwa Allah godia.

Tayi murmushi sannan tace toh.

Bayan sun gama sallah ya dafa hannunsa akan goshinta yayi mata adduoi dakuma neman tsari daga shedan.

Sannan  ya kalleta yace Allah yasa daga wannan daren muyi dacen samun baby.
Tarufe fuskarta cikin jin kunya.

Ya tashi tsaye yazo gunda take sannan ya durkusa ya tallabota ya kwantar da ita kan gado ya kashe fitila.

Nikuma ina ganin haka sai na kwashi jiki nayi waje.😎

Da safe kam tana kwance kan kafafuwanshi tana zuba mishi shagwaba yace yakamata nakira hajiya muji ya take.

Yana kiranta bata daukabah saida yakira har sau uku sannan ta daga bayan sun gaisa takecewa kakirana ina meeting ne.

Yace ayyah ai bansanibah
Tace yawwa dama inason nakiraka nasanardakai cewa yer gwaggon ka mai suna nabila tazo abuja jiya ta sauka a gidana kuma kaga baikamata ace tana zaune ita kadaibah.so inason tazo ta zauna tare daku kafin nadawo.

Yace to hajiya ba damuwa Allah yakawota.

Tace ameen ina mayiesha

Gatanan bari na baki kugaisa
Bayan sun gaisa hajiya ta kashe wayar sannan munawwar yake sanar da ita nabila zatazo gidansu kafin hajiya ta dawo.
Tace ayyah ai badamuwa kaga idan kafita dama nikadai a gidan ba dadi so kaga yanxu zan samu abokiyar hira.

Yace hakane kam.yanzu dai akwai inda nakeso naje akwai wani abokina da zanje gunsa.

Tace to adawo lafiya.

Da maraice mayiesha tana zaune a parlor tana kallo sai taji horn din mota ta leko ta window sai taga ba munawwar bane.
Tace kenan nabila ce ta iso.

By maryam ashutrah

Wata yer yarinya wacce bata wuce sha takwas bah tafito daga motar yer kyakkyawa sbd ko taka sahun kyan mayiesha batayibah gata doguwa siririya ta saka bakin madubi da kuma qananan kaya riga da wando da kuma wasu takalmi masu tsini sosai saita qara wani irin tsayi.+

Tana fitowa ta bude boot ta dauko akwatinta sannnan ta nufo kofar parlor.

Mayiesha tace tabbb wannan yarinyar sai kace ba musulmabah lallai.

Tana shigowa parlon mayiesha taje gunta tace sannunki da zuwa nabila.

Nabila ta kalleta sannan tace kece matar munawwar.

Mayiesha tace ehh tabbas nice.

Nabila ta bata hannu tace nice meeting you.

Mayiesha tace nice meeting you too.

Nabila tace ashedai dukda naji ance ke daga qauye ya kwasoki balaifi tunda kinajin turanci.

Mayiesha tayi murmushi kawai sannan tace kishigo mana.

Bayan ta shigo sannan tace muje na kaiki masaukinki.

Tana biye da mayiesha sai kallon parlon takeyi da kuma cikin gidan sbd ita kanta tasan an narka dukiya gurin hada gidan.

Suna shiga dakin mayiesha tace ga dakinki kidan huta sannan kifito kici abunci.

Ta kalli mayiesha tace kinada kirki ya sunanki.

Tace ameena amma ana kirana MAYIESHA.

Nabila tace nice name kinada suna mai dadi.

Mayiesha tace nagode sannan ta fita dakin.

Nabila ta kalli dakin sama da qasa sannan tace tabbb amma lallai wannan gidan ya hadu gashi kuma mace kyakkyawa a cikinsa.

Ta dauki wayarta takira qawarta wato aisha tace yer gari ina abuja fah yanxu kawai muhadu gobe.

Mayiesha taje parlor taci gaba da kallonda takeyi.

Bayan wasu mintuna nabila tafito sanye da qaramar riga da wando dai dai gwiwa dinta.

Mayiesha ta kalleta sannan tace har kinfito ga abunci akan dinning nabila taje ta bude abuncin taga masa da miya da kuma naman kaji.
Tace nibana cin masa sbd haka indomie zanci.

Mayiesha tayi murmushi sannan tace yanxu kuwa za'a hada miki.

Nan takira wata yer aiki ta cikin gidan tace da ita ta dafa mawa nabila indomie.

Tace to hajiya sannan ta fice.

Nabila ta zauna one sitter tana danne dannen waya.

Mayiesha kuma taci gaba da kallonta.
Bayan wani dan lokaci sai mai aikin ta kawowa nabila indomie ta ajiye a gabanta.

Nabila na bude abuncin ya tashi tsaye ta sakarwa mai aiki wani gigitaccen mari
Sai da yer aikin ta fadi

Mayiesha ta kalli nabila yace lafiya meya faru.
Nabila ta kalli yer aikin tace taya zaki kawomun indomie ba kwai kuma ba nama ko kaza ko kifi a ciki.

Mayiesha tace haba nabila ai ba'ace ta saka bane shiyasa.

Yer aikin ya durkusa tace kiyi hakuri yanxu zanje na hado miki.

Nabila tace get out kafin na ball dake
Haka ta dauki indomin ta fice.

Nabila ta koma ta zauna tasaka earpiece a kunnenta.

Mayiesha kuma taji tausayin yer aikin sosai sbd tunda tazo bata taba yimusu ko baqar maganabah ballantana duka.

Tafice zuwa kitchen ta tarar da indo tana kuka.
Ta rike hannunta tace dan Allah kiyi hakuri kawai daga yau tunda kinga yadda halinta yake sai kiyi abunda tace kawai sai azauna lafiya amma dan Allah kiyi hakuri.

Indo ta kalli hajiya tace bakomai inshallah zanyi abunda kikace

Tace yawwa yanxu kisaki ranki kidafa mata abunda tace

Indo tace yawwa hajiya.
Tana kitchen tajiyo qarar wayarta a parlo.

Nabila ta kalli wayan mayiesha tace jar ubannan wannan baqauyar iphone 8 take rikawa tabbdii.

Nan nabila tashigo parlo ta dauki wayanta sai taga munawwar ne yake kira ta dauka tare da sallama.

Ya amsa sannan yace amaryata da fatan gidan lafia
lafiya qalau

nabila ta iso

ehh ta iso tun dazu.

To nima ganinan akan hanyata ta dawowa
To Allah ya kawomun kai lafiya mijina kuma kazomun da ice cream

Yayi dariya yace ai kece ice cream din to bye zanzi miki dashi.

Tace to saika iso takashe wayar.

Nabila tace mayiesha amma wannan wayar taki ta burgeni sosai

Mayiesha tace ayyah nagode.tafice daki tayi wani wankan tasaka qananan kaya doguwar riga sannan ta gyara gashinta ta sakeshi ya kwanta akan gadan bayanta ta feshe jikinta da turaruka sannan tayi kwalliya irin ta zamani ta fito.

Tana saukowa nabila tabita da kallo tace amma fah kinyi kyau sosai.

Mayiesha tace nagode
Nabila tace amma wannan gashinkine

Mayiesha tayi murmushi sannan tace eh gashinane.

Nabila tace amma dai ke ba bahaushiya bace.

Mayiesha zata mayar mata da amsa sai taji sallamar munawwar nana take tayi sauri taje ta rungumeshi sannan ta karbi ledar dake hannunshi tace sannu da zuwa mijina.

Munawwar yace yawwa matata irin wannan kyau haka duk nikadai.

Mayiesha tace to idan ban makabah wazanwa.

Yace kuma hakane gsky.

Yana daga kanshi ya hango nabila.
Ya rike hannun mayiesha suka je suka zauna sannan yace da ita sannu nabila.

Nabila ta kalleshi sannan tace yawwa couz munawwar ya aiki

Yace alhamdulillah kinzo kintarar hajiya batanan tayi tafiya.

Tace eh hakane amma tace takusa dawowa.

Yace eh hakane kuma kafin tadawo zaki zauna anan sannan wannan itace matata mayiesha da fatan zaku fahimci juna kuzauna lafiya.

Idan kuma kina bukatar wani abu sai kiyi mata magana ta baki kokuma ta sanar dani sai nabata tabaki.

Nabila tace ba damuwa.

Yace yawwa yatashi zuwa daki mayiesha tabi bayanshi.

Nabila ta bisu da kallo sannan tace lallai ma wannan mutum waton idan inason abu saidai matarshi tabani sai wani makale mishi takeyi.wannan kuma matsalar kuce tatashi zuwa dakinta.

Suna shiga daki munawwar yace amma wannan yarinayar batada kunya kigafa irin shigar da takeyi.

kila irin kayan kawai takeda kuma ai ba dadewa zatayibah kawai mubita a hankali harta fice.

yace wani irin mubita a hankali wannan fa gidanane

Idan yanxu nace tabar gidannan dole saita fita
yer uwarkacefa

yace to sbd tana yer uwata saime sbd daga ganinta zatayi rawar kai.

Kaga fah dazu daga kawai tace a dafa mata indomie wai ita batacin masa indo ta hada mata indomie aikuwa tana kawo mata sai ta falleta da mari wai meyasa zata kawo mata abunci ba nama ba kifi ko kaza sannan ba kwai.

Munawwar yace mari fah kikace to lallai zan gyarawa wannan yarinyar zama sannan kuma da naman tazone da zata mari indo sbd bata saka mata naman bah.

Mayiesha tace ato yanxu dai katashi kayi wanka ka huta.

Bari naje na kaimata nata ice cream din.

Ai kekadai nasiyowa bada itabah

Amma ai taji lokacinda nace kasiyomun kaga kuwa yakamata nafita hakkinta.

Kyaji da wannan saikin dawo
Ta dauki ice cream ta fice.

By Maryam ashutrah

This page is dedicated to my best friends Allah yaqaro muku shekaru masu yawa.+

Sannan kuma ina godiya ya ma'abota karatun wannan littafin mai suna MAYIESHA
Da fatan kuma yana qayatar daku sosai.much luv🎆🎆🎆🎆

Tayi knocking ba'a budebah ta qar knocking harsau uku nabila bata budebah tace watakil har tayi bacci tajuya zata fice sai aka bude kofar.

Nabila tace lafiya

Dama ice cream ne nace na kawo miki
Nabila ta karba sannan tace thanks ta shige daki ta rufe.

Mayiesha tace Tabb wannan yarinyar akwai rashin kunya.

Ta haura sama munawwar yace yawwa akwai maganarda zamuyi.

Ta zauna sannan yace kinga admission dinmu na london zai dan dade kafin yafito sbd haka zamu fara karatu anan kinga idan ya fito kawai sai muwuce.

Tace kuma wannan shawarar tayi.
Sbd haka nayi magana da abokina gobe zamuje wata university nan kusa ayi duk abunda yakamata.

To Allah yakaimu goben yace ameen.

Da safe tana kitchen suan hada breakfast shikuma munawwar yana parlor yana kallon morning news itakuma nabila tana daki sai faman bacci takeyi.

Munawwar yatashi yaje kitchen yana shiga yen aikin duka suka duka suka gaidashi ya amsa sannan yace mayiesha zo kiji.

Ta iso gunshi ya janyo hannunta suka fito waje sai yace wai anya yarinyar nan tayi sallar asubah kuwa.

Tace aww wai nabila tabb inaga fah bata tashibah amma bari naje nagani.

Tafice zuwa dakin nabila ta shiga da sallama ta hangota kan gado tayi rubda ciki sai shakan bacci takeyi.

Ta isa gunta sannan tace nabila
Nabilaa!!
Tana bude idonta tace wai meye haka ina bacci zaki tadani lafiya.

Kinyi sallah
No banyibah tana fadan haka ta juya kwanciya

Mayiesha tace kitashi mana kiyi sallah idan yaso saiki koma baccin.

Nabila tatashi zaune tace wai lafiya kikeson takuramun ni ina takuramiki me kodan sbd ina gidanki.

Mayiesha tace Allah ya baki hakuri ta fita.

Ta tarar da munawwar a parlor tace taki ta tashifah wai ina takura mata.

Yace aikuwa idan har zata zauna a gidannan to wlhy sai tayi sallah ya tashi a fusace ya nufi dakinta.

Mayiesha kam kawai kallonshi tadingayi.yashiga dakin nabila yace nabilaa!! Tatashi da sauri yace kitasho kiyi sallah kina jina koh.

Tace wai meyasa kukeson takuramun kawai sbd nazo gidanku.

Yace antakura miki din dalla malama kitashi.

Tatashi cikin fushi tashiga toilet
Shikuma yafito waje ya tadda mayiesha a bakin kofa.

Mayiesha tace ai daka bita a hankali
Ai wannan yarinyar binta a hankali bazaiyi aikibah ke ai a hankali kika bita amma bai hana taki tashibah.

Suka zauna a parlor sukayi breakfast amma har suka qare nabila bata fitobah.

Mayiesha tace bari naje nakira nabila ta karya
Ki kyaleta idan taji yunwa ita da kanta zaka fito ta samu abunda taci.
Yanxu dai kitashi mu shirya muje koyan mota sbd kinga anjima kadan zan fita.

STORY CONTINUES BELOW

Tace to bayan sun shirya dukansu tace kaje mota ina zuwa

Tashiga dakin nabila da sallama
Nabila ta kalleta sannan tace waton shine kikakai qarata gun mijinki to wlhy ki tsaya matsayinki a gidannan kada kice zaki shiga harkokina

Allah ya huci zuciyarki nidai zamu fita saimun dawo zamuje koyan mota
To nikam ina ruwana Allah ya raka taki gona.

Mayiesha tafito tana Allah waddai da halin nabila.

Nabila najin qarar fitar motarsu ta dauki wayarta takira aisha tace ke wai kina inane.

Aisha tace ina gida
To zanturo miki address din gidanda nake sai kizo kuma kizo mun da kayan aiki.

Tace aha saikin ganni.
Tatashi tayi wanka tasaka leggings da top tafita zuwa kitchen.

Tana shiga tayi karo da larai(daya daga cikin masu aikin gidan)
Nabila tace jar uba waton nagane yen aikin gidannan kun rainani tass ta kwashe larai da mari tace ke qaramar yer iska baki kallon inda kike tafiyane.

Tace dan Allah kiyi hakuri ban ankara kina gun bane

Tace wlhy dukanku zan gyara muku zama a gidannan kafin natafi wuce kibani guri kokuma na babballaki

Larai tayi sauri taficewarta.

Nabila nashiga kitchen din tace tabb wannan kitchen din saikace na gidan shugaban qasa lallai wadannan mutanen.

Ta dauko juice da cake a cikin fridge ya zauna a parlor
Bayan minti goma saiga kiran aisha yashigo wayanta.
Ta dauka sannan tace kin qarasone
Tace ehh naqaraso amma mai gadi yaki ya barni nashigo tace ganinan zuwa.

Tana isa gun mai gadi tace bakuwa tace ka barta ta shigo.

Tana shigowa suka shiga cikin gidan.
Aisha ta dinga kallon gidan tace tabb lallai to ko nidai dake zama a abuja ban taba shiga gida mai irin kyan wannan bah.
Nabila tace kema kya fada nidai zo muje.

Suka shiga daki suka rufe sannan ta zauna tace nabila wannan ne dakinki.

Tace ehh mana

Aisha tace tabb wannan ai yakai girman parlon gidanmu.

Nabila tayi dariya tace nidai ina sakona.

Aisha ta bude jakarta ta dauko giya da kuma cigari da totolin da sauran kayan maye tace gasu.

Nabila tace yawwa yer gari kice yau zamu huta.

Aisha tace ke yakamata fah muje club gobe

Nabila tace gaskiya kam sbd  nadade banjebah tun ina kaduna
Aisha tace kinga kawai idan kin shirya sai kizo ki daukeni mufasa.

Tace to ba damuwa.

Bayan sun gama shaye shayen su nabila tace zan ajiye sauran anan gobe zan baki kudinki.

Aisha tace to badamuwa nidai bari natafi kafin wannan dan uwan naki ya dawo

Cikin tangadi da maye haka tabar gidan itakuma nabila ta boye sauran kayan mayen nan take bacci ya dauketa.

Har kusan qarfe uku sannan mayiesha tace nifa na gaji kawai mukoma gida.

To shikenan amma fah gobe ke zaki tuka daga gida har nan

Ba damuwa Allah yakaimu

Bayan sun shiga sahad stores sunyi yer siyayya sannan suka wuce zuwa gida.

Suna shigowa parlor suka zauna mayiesha tace yayana naga kwanannan sai kiba kake tayi kana wani qara kyau.

Yace ai dole nayi kiba tunda kina kula dani sosai matata.

Tace mijina kenan abar qaunata Allah yabarmu tare harka tunamun da rayuwar da mukayi a wata duniyar.

Yace har yanxu inaganinki lokacinda kikaje a matsayin bakuwa kafin musaba.

Dukansu sukayi dariya sannan munawwar yace wai swt hrt bakijin wani wari kamar na cigari a parlonnan tace no banjibah fah.

Yace inajin warin cigari kodai turaren wutanda aka sakane
Yau nida kaina na turare gidannan kuma ai kafin mufita ba wannan warin.

Kodai cikin yen aikinnan akwai wadanda suka fara shaye shaye ne

Haba dai taya zakace haka bafa yen mata bane dukansu sun manyanta taya zasu yi shaye shaye watakil dai sbd ka gajine muje ka huta bari nayi wa inno magana sai ta saka wani turaren.

Wai ina nabila ne kodai tafita

A'a bata fitabah ai sbd motarta nanan a gareji baridai naje ma dubota.

Ya haura sama itakuma taje dakin nabila ta tarar da ita sai shakan bacci takeyi

Da sauri ta rufe hanci wannan wani irin warine a dakinnan.

Da sauri taje dakinsu larai suna zaune suna hira tana fada musu irin cin mutuncinda nabila tayi musu.

Mayiesha tashigo da sallama dukansu suka hada baki gun gaisheta tace lafiya qalau yawwa nace yau waya gyara dakin nabila a cikinku.

Inno tace naje na gyara dazu da safe amma taki ta barni shiyasa ma ban gyarabah

Tace to shikenan amma dan Allah dayanki tatashi taje ta sake sakawa parlon qasa turare
Dukansu suka ansa da to hajiya sannan tafice.

By maryam ashutrah


Post a Comment for "MAEESHA CHAPTER B"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...