MAEESHA CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MAEESHA CHAPTER A

 MAEESHA CHAPTER A


Bismillahirrah manirraheem๐ŸŽ†+

Gadiya ta tabbata ga ubangijin halittu wanda yayi mutane dakuma aljan๐Ÿ’๐Ÿ’

Ya Allah kabarmu dason annabinka muhammadu rasullilah s.a.w๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

Ya Allah kabani ikon da kwarin gwiwa na rubuta wannan littafin nawa๐ŸŽ†๐ŸŽ†๐ŸŽ†๐ŸŽ†๐ŸŽ†๐ŸŽ†๐ŸŽ†๐ŸŽ†

Godiya ta nusamman ga ma'abota karatun littafai na Allah ya bar qauna.๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜

Tana zaune a tsakar gida tana girki sai ummanta tafito rike da uniform din makaranta a hannunta.

Tace mayiesha karbi kayannan kije kisaka kiwuce islamiyya kafin kimakara.

Mayiesha tace umma nifa kawai kubarni Allah bason makarantar nan nakeyibah
Umma tace to ai yazama dole kuwa kije makaranta tunda bazaiyyu ace bakya son boko bah sannan kuma bakyason islamiyyar.

Ta karbi kayan tace to umma bari naje na shirya saina wuce.

Umma tace yawwa 'yata kuma dan Allah idan aka tadaku kawai kinufo gida kada kitsaya ko ina

Tace to umma.
Bayan tagama shiryawa ta dauki sababbin littafanta da abbanta ya siyo mata  tafito parlour tace to umma natafi saina dawo.

Yawwa yer albarka Allah ya taimaka
Tace ameen tafice warta.

Mayiesha kenan yarinya yer shekara goma sha takwas da haihuwa.
  kyakkyawa ce fara mai gashi har gadon baya komai nata dai dai ma'ana full option.tana zaune tare da iyayenta a wani dan qaramin gida sbd talakawane amma dai ahakan Allah yana hore musu nasakawa a baki.

Abbanta yanason tayi karatu amma ita kwata kwata ta tsani hakan shine kawai yake hadasu fada.

Bayan haka tana da aljannu kusan ashirin a kanta shiyasa yaran unguwa basayi mata rainin hankali sbd idan suka tashi zata iya karairaya mutum komai girmansa.shiyasa ko saurayi daya baitaba zuwa neman aurentabah kuma batada saurayi kodaya amma hakan bai dame tabah.
Wannan kenan

Cigaban labari๐ŸŽ†
Tana kan hanya zuwa islamiyya sai ta hadu da qawarta zalihat tace da ita au dama kema makarantar mu aka sakaki.

Tace eh hakane

Kenan zamu dinga zuwa makaranta tare

Tace ba lallaibah sbd nifa bason zuwama nakeyibah

Tace habadai qawas karatu fah yana da muhimmanci.
Myiesha ta harareta zulaihat na ganin hakan takama bakinta tayi shiru sbd tasan idan ta takurama saidai akaita gida summamiya.1

Suna isa makaranta zulaihat tawuce da ita office din mai makatanta bayan angama mata komai aka sakata ajin su zulaihat.

Suna shiga aji malaminsu yashigo aka fara karatu.
Bayan angama ne yafara tada su sukaranta amma acikin ajin ba wanda ya iya karatunsa anan take kuwa yayi fushi yace dasu dukansu sufito waje suyi kneel down.
Bayan kusan minti goma sannan ya dauko bulala yafara dukansu kowa aka mishi bulala biyar.
Yana kaiwa gun myiesha yace ta bada hannunta tace itafah sabuwar zuwace meyasa kawai sbd bata iya karatubah za'a daketa.
Aikuwa taki ta bata hannunta sai yaje dukanta ta gudu.
Sannan yaje yakai qararta gun malam abbas wato babban malamin makarantar.
Sukazo tare malam abbas yace kibada hannunki a dakeki kamar yadda akayiwa sauran kokuma yanxu nida kaina na dakeki.
Cikin fushi ta bada hannunta malaminsu yamata bulala biyar amma ko ajikinta.

Tana juyawa zataje aji sai tace shekarata biyu ba'a dakenibah sai yau wani qaton banza yadakeni aikuwa malam abbas najin haka ya kwala mata kira.

Ta juyo a fusace yace zonan

Tana zuwa kafin ta ankara ya watsa mata dorina a fuska aikuwa nan take aljannunta suka tashi malamin yazo zai qara kai mata wani dukan kawai tayi tsuntsu tayi sama

Dayake shima malamin ba'a barshi abayabah indai ta fannin aljannune shima nan take yayi wata adduah yayi sama
Aikuwa nan kowa na makarantar yafito domin kallon ikon Allah.

Tana ganin ya nufita ta  qara yin sama zuwa dayan bangaren makarantar cikin fushi da fusata tace idan ka karasonan kwananka ya qare.

Yana jin hakan shima ya nufeta cikin sauri.
Tana ganin hakan tayi sama sai qara sama takeyi kamar wata tsuntsuwa aikuwa kafin ka ankara ta bace basss har aka dena hangota.

Malam abbas na ganin hakan ya sauko qasa sannan yake cewa lallai ina mamakin irin qarfin wadannan aljannun yarinyarnan amma kada kudamu zata dawo kowa yaficewarsa.
Cikin surutu irin na mutane kowa ya watse.

Nana take akaje aka sanar da ummanta bayan taji wannan labarin hankalinta yatashi sosai sbd acewarta hakan bai taba faruwa da yer tata tilo bah amma  suna tsammanin idan tarage fushi zata dawo gida.

Tanata tafiya cikin gajimare sai hankalinta yadawo jikinta cikin tsoro da firgici ta kwala ihu tana dubawa taga tanata wuce garuruwa kala kala masu matukar kyau sai a hankali taga tana saukowa qasa.

Ta sauka cikin wani gari mai matukar kyau da furanni kala kala ko ina wani irin sanyi mai dadi yana tashi amma bakowa a garin sannan ba gidaje daga koramu masu ruwa sai ciyawu kala kala da tsuntsaye sai abubuwan marmari kala kala.

Bayan ta gama kallon ko ina sai tace yau nashiga uku nikuma meya kawoni nan ina umma ta wannan wani gurine haka kawai ta duka ta fasa kuka.

Tana tashi tsaye sai taga wani abu a hannunta kamar qarfe dan qarami a hannunta anyi mishi ado mai kyau na kaloli masu kyau anyi mishi zanen wata tsuntsuwa.
Ta kalle wannan abun cikin mamaki tace wannan kuma wane abune haka mai kyan kallah tana juyashi sai taga tajuya da karfi.
Cikin tsoro tace wannan wani irin qarfe ne haka ta dagashi sama kawai sai taga tayi sama cikin sauri tana saukar dashi qara sai taga tayi qasa da sauri.

Tace tabb lallai wannan karfen na tsafine watakil zai taimakamun nakoma duniyata.

Tace amma yakamata na koyi yadda ake amfani dashi kafin nayi kokarin sarrafashi.

Tana fadin haka sai tafara jin yunwa taje ta samu wani bushiya mai kayan marmari kala kala tafara ci har saida ta koshi.

Sannan ta zauna ta kalli wannan dan qaramin qarfen dake hannunta tace yakamata nayiwa wannan qarfen suna tayi tunani nadan wani lokaci sannan tace sunanshi "BAHIJ"
Tana fadar haka sai qarfen yayi dan wani haske tace laaa kenan wannan yana nufin yaji dadin sunanda nasaka mishi yanxu taya zan san yadda ake amfani dashi.

By maryam ashutrah

Tana cikin tunanin ta yadda zata fara sarrafa wannan qarfe (bahij) sai taga wani kyakkyawan saurayi dan kimanin shekara ashirin da bakwai yana nufota ta gun inda take.

Tana ganinsa bata tsoratabah saboda ita ba abunda yataba bata tsoro a rayuwarta.

Bayan ya iso gun inda take sai ya kalleta cikin mamaki yace baiwar Allah meya kawoki nan.

Ta kalleshi cikin rashin yarda sbd tana ganin kamar cutar da ita zaiyi tace nima kawai na tsinci kaina ananne.

Ya zauna dan nesa da ita kadan yace kece mutum na biyu danagani anan wannan gurin nine na farko.

Ta kallesa tace to kai bawan Allah meya kawoka nan.

Ya kalleta da damuwa a tattare dashi yace
ni sunana Munawwar abdulhakeem nidan wani attajiri ne mai suna abdulhakeem mai dala muna zama a garin kaduna.

sannan kafin mahaifana susameni sunsha matukar wahala sbd saida suka shekara goma da aure sannan suka haifeni.

bayan sunsha neman magani kala kala daga qarshe sukaje wani qauye gun wata bokanya inda tabasu magani akan zasu samu da' amma da sharadin idan suka haifeni nakai shekara goma sha biyar zasu zasu bar matani.

Cikin damuwa da tashin hankali kuma sbd iyayena sunason su haihu takowace hanya domin su samu magaji sukace zasuyi yadda tace.

bayan wata daya mahaifiyata ta samu cikina bayan an haifeni sukaci gaba da raino na cikin kulawa da lelena suka shagwabani sosai.

Shekaru na tafiya har nakai shekara goma sha biyar.

A ranar da nacika shekara sha biyar ne sai bokanyar tazo gun iyayena akan alkawarinda sukayi mata.

Sukuma har sun manta da wannan alkawarin cikin rashin amincewa mahaifina yace bazai bata nibah haka ma ummata.

Cikin fushi bokanyar tace tunda suka qarya mara alkawari to itama bazata barsu da nibah sai ta rabasu dani  haka tafadi wani abu na tsafi nan take aka namemi aka rasa.

Ina farfadowa na ganni anan cikin wannan gurin shekara ta goma sha biyu anan.

Anan na girma nikadai ba mutane nayita kokarin fita daga wannan gurin amma qarfin tsafina baikaibah sbd wannan gurin kewaye yake da qarfin tsafin aljannu.

Ta kalleshi cikin tausayi tace dama kanada tsafi ne yace eh amma da taimakon wannan dan qarfen da kike gani.

Yanuna mata cikin mamaki tace ai wannan irin qarfe nane ta nuna masa nata cikin mamaki yace tabbas nasan komai daren dadewa watarana Allah zai kawomun mafita kuma kece.
Ta kalleshi cikin mamaki tace nikuma

Yace ehh tabbas zan koya miki yadda ake amfani da tsafin wannan qarfen
Tace sunanshi "bahij"
Ya kalleta cikin mamaki yace bahij kuma

Eh nina saka masa wannan sunan
Yace kuma yayi dadi amma kafinnan inason kifadamun kekuma meya kawoki wannan gurin.

Ta bashi labarin duk abunda yafaru nan take.

Sai yace kibani wannan bahij din naki na kalla sbd da naga kamar yafi nawa qarfin tsafi.

Ta kalleshi cikin rashin yarda tace bazan bakabah
Yace nasan bazaki yarda danibah nan take amma wlhy banida niyyar chutar dake kuma inason mutaimaki juna mufita daga wannan duniyar izuwa tamu duniyar.

Tace to shikenan inshallah zan baka duk wani maimako da kake bukata daga gareni ta mika masa bahij dinta.

Ya karba sannan ya kare masa kallo yace da ita wannan bahij din naki tabbas yana dauke da tsafi kala kala kuma masu qarfin gaske sbd kinga harda wannan tsuntsuwar da take ajinkinsa babushi anawan.

Tace hakane amma yanxu yaushe zamu fara gwajin.
Ya kalleta yace yanxu dai kibari har gobe tunda kinga yanxu dare yayi tace to a ina kake bacci
Ya kalleta sannan yayi murmushi yace aduk inda naso.

Cikin mamaki tace ban ganebah

Yace to kitaso muje na gwada miki.

Suna cikin tafiya har suka isa gurinda yakeda fili sosai sannan ya kalleta yace kikalli yadda zanyi daki anan saboda kema kiyi nakin.

Tana kallonsa ya rufe idanshi ya bude sannan ya juya wannan dan qaramin qarfen hannunsa sai kawai sukaga daki a gabansu.
Cikin mamaki ta kallesa tace tabb kenan wannan abun har daki yakeyi.

Yayi murmushi sannan yace komai yanayi yanxu dai ki gwada yin naki dakin.

Tace to ai bansan yadda zanyibah

Yace kawai kirufe idanki sannan kifadi abunda kikeso sai kijuwa bahij dinki.

Nan take ta rufe idan ta sannan ta bude sai ta juya bahij dinta nan take sukaga daki mai matukar kyau a gabansu.

Tace tabdi kaga har dakina yafi naka kyau
Yayi murmushi sannan yace ehh saboda bahij dinki yana da matukar qarfi shiyasa yanxu kishiga shiki ki kwanta saida safe.
Tace to saida safe tashiga cikin dakin.
Ta kalli ko ina dakine babba sosai ta ko ina haske yana tashi da kamshi mai matukar dadi sannan an kawatashi da abubuwa na kawa kala kala har wadanda idanuwa basu taba ganibah ga wani babban gado na alfarma a ciki.

Tace lallai wannan dakin yana da matukar kyau na gaske.

Taje gun gadonta ta zauna sai ta kalli bahij dinta tare da rufe idanuwanta sai kawai tufafinta suka chanja izuwa na bacci masu matukar kyau.tace yanxu taya zanyi sallah kenan kuma gashi ba agogo ballantana nasan lokaci sannan kuma gashi ba ban daki anan.

Nan take ta tashi ta nufi kofar dakinta tana bude kofa sai taga ko ina yana haske ga farin wata sai kyalli kake gani ta ko ina sai wani kukan tsuntsaye mai dadin sauti.
Ta juya ta kalli dakin munawwar sai tanufi dakin tashiga da sallama yana zaune akan sallaya yagama sallah yana lazumi.
Taje ta samu guri ta zauna yana gamawa sai ya juyo ya kalleta nan take zuciyarshi ta buga da qarfi a cikin ransa yace bantaba ganin mace kyakkyawa mai halitta basu kyau bah irin wannan yarinyar bah.

dukda ban taso cikin duniyar mutane bah amma nasan wannan ko a cikin duniyar mutane ita ta dabance.

Yana cikin tallonta ta gane ita yake kallo nan take ta rufe idonta sai kawai ka ganta da mayafi tarufe dukkan jikinta.

Yayi murmushi ganin hakan sannan yace yana ganki a dakina keda yakamata ace kina bacci.
Tace eh hakane amma inason nayi sallah ne kuma bansan inane gabas bah sannan kuma bansan yadda zan dinga gane lokutan sallah bah.

Yayi murmushi yatashi yazo kusa da ita yace to muje na nuna miki.

Suka tashi har sunkai bakin kofa zasu fita saiga wata yer qaramar tsuntsuwa kyakkyawa tazo gunsa yana ganinta yayi murmushi yace wannan itace runat tsuntsuwa tace tana ciremun kewa sosai kuma na aminta da ita.

Myiesha ta kalli runat tayi murmushi sannan tace sunana myiesha da fatan zamu zama qawaye sai tsuntsuwar tayi wani dan sauti mai dadi.

Munawwar yace tana kuwa sonki yace da tsuntsuwar runat kijirani a dakina yanxu zanje nadawo kinji.

Runat ta fira zuwa dakinshi sukuma suka wuce zuwa dakin myiesha.

By maryam ashutrah

Suna shiga cikin dakin sai yace yanxu ki kalli yadda zanyi sai kema kiyi tace toh
Tana kallonsa ya kalli "inwak"(sunan qarfen sa)yace nunamun gabas dakuma lokaci.

Nan take qarfen ya jujjuya sannan ya kalli wani bangare na dakin sannan kuma ajikin qarfen yanuna lokaci.

Itama haka tayi sai bahij dinta yanuna mata guri daya da inda inwak ya kalla.

Ta kalli munawwar tace na gode sosai
Yace ba damuwa myiesha yanxu dai kiyi sallah sannan kuma ki kwanta da wuri sbd kitashi da wuri yadda zamu fara komai yadda ya kamata ba bata lokaci.
Tace to shikenan inshaAllah zan yi hakan

Yace saida safe sannan yafice zuwa dakinshi.
Itakuma tayi sallah sannan ta kwanta tana ta tunanin yadda al'a muranta suke faruwa kamar a mafarki.

Shikuma munawwar bayan yakoma dakinsa yaketa hira da runat har sukayi saida safe taficewarta sannan ya kwanta.

Amma a duk lokacinda ya rufe idansa sai yadinga ganin mayiesha a ciki.
Shidai baisan hakan mai yake nufibah dakyar yasamu nutsuwa sannan yayi bacci.

Washe gari da sassafe umma da abban myiesha suka nufi makarantar islamiyya din yer tasu.
Bayan sunji dukkan bayani daga bakin malam abbas sannan hankalinsu yaqara tashi sosai

umma kam sai kuka takeyi acewarta ta rasa mayiesha kenan har abada Aljannu sun dauketa.

Sai malam abbas yake cewa kada ku damu yer ku zata dawo gareku nan bada jimawabah kuma zanyi iya bincikena domin na gano inda take.
Bayan wannan bayaninne Sannan hankalinsu yadan Kwanta.

Da safe tana tashi bacci taduba lokaci taga harta makara sbd tayi baccin gajiya gakuma dadin baccin da takeji.

Da sauri ta tashi ta nufi waje domin yin alwala tayi sallah sai ta hango munawwar yanata koyon fada shikadai.
Taje gun inda yake tace ina kwana munawwar
Yace lafiya qalau yen mata da fatan kin tashi cikin koshin lafiya tace lafiya qalau.

Tace dama inason nayi alwala ne nayi sallah amma ba bandaki anan yace har kin manta yadda na koya miki kenan koh.
Ta kalleshi tace ohh hakanefah natuna to yanxu bari nayi sauri nayi sallah sai nazo gunka.

Yayi murmushi sannan yace to ina jiranki.

Tana isa gefen dakinta sai ta rufe idanta saiga ban daki a kusa.
Tashiga taga ruwa masu dumi tayi wanka tayi alwalla sannan tafito zuwa dakinta.

Nan take ta rufe idan ta sai taganta sanye da tufafi masu matukar kyau da ado tayi mamakin irin wannan kayan sosai sannan dai tayi sallah sai kuma ta gyara gashinta sannan tafito zuwa gun munawwar.

Tana fitowa daga dakinta ta nufoshi yana ganinta ya kura mata kallo har ta iso gun inda yake.
Tace munawwar kenan irin wannan kallo haka
Yace kiyi hakuri nima bansan ina kallonkibah kawai ina tsintar kainane ina kallonki tace ba damuwa yanxu dai yunwa nakeji yakamata muci abunci kafin muci gaba.

Yace hakane sukaje qarkashin wata kyakkyawar bishiya suka zauna sai yace to ke zaki hada mana abuncin sbd nasan naki sai yafi nawa qayatarwa.

Tace to shikenan ta rufe idanuwanta ta bude sai ga kayattatun abunci kala kala na alfarma a gabansu.

Tace bantaba ganin irin wadannan abuncinbah

Munawwar yayi murmushi yace to idan anan ne kuwa har ki gaji dasu.

Bayan sun gama cin abunci sai yace da ita yanxu dai da farko inason nakoya miki fada sbd ki iya kare kanki kuma kinsan fitarmu anan ba lallai yazo da sauki bah.
Ta kalleshi tace to kai waya koya maka fada

Yace ainikam tun ina gidanmu na iya fada sosai sbd ina zuwa makarantar koyan fada.

Tace to shikenan zamu iya farawa ayau yace ai dole mu fara ayau saboda bamusan mubata lokaci.

Bayan sunje cikin wani lambu mai masifar kyau
sannan yace da farko kafin nakoya miki fada zan koya miki yadda zaki iya sarrafa bahij dinki sosai.

Tace to shikenan.

Tana kallonsa sai ya kalli inwak dinshi ya dagashi sama a hankali sai taga munawwar yanayin sama a hankali a hankali har saida yayi nisa sosai sannan taga ya juyashi ta hagunsa sai munawwar yadinga zuwa hagu haka kuma idan yajuyashi ta damar sa sai yadinga yin dama.
Sai kuma ya saukar da hannunsa a hankali sai gashi yana saukowa sannu sannu.

Daga nan kuma sai ya shafi inwak dinshi saiga takobi a hannunshi mai kaifin gaske.

Yace to yanxu kitashi ki gwada duk abunda nayi.
Tace anya zan iya kuwa
Yace ai saikin gwada sannan zaki sani.

Tana tashi sai ta daga hannunta sama a hankali sai taga tadinga yi sama kadan kadan har saida tadanyi nisa sannan ta juyar da bahij dinta zuwa ta gefen dama

nan take taga tayi dama sai kuma ta juyar dashi zuwa hadu sai kuma taga tayi hagu.

Zata saukar da hannun ta kenan sai ta manta bata saukar a hankali bah kawai sai tayo qasa da sauri munawwar yana ganin zata fado cikin sauri ya yi sama sannan ya dauketa suka dinga saukowa a hankali tana kallon cikin idanuwanshi.

A cikin ranta tace amma wannan dan saurayin kyakyawane ga idanuwansa masu kyan kallo.

Tana cikin kallonsa sai kawai jin tayi ya sauketa a kasa.ya kalleta cikin kulawa yace dafatan dai lafiya kike.

Tace eh bakomai sai yace to yanxu muyi tare koh

Sukayi sama a tare sannan suka sauko a hankali.

Daganan sai yace kishafa  bahij dinki tana shafawa sai wani irin haske ya fito nan take taga wata irin kyakkyawar takobi mai kaifin gaske a hannunta.

Tace munawwar amma meyasa inwak dinka bashida wannan tsuntsuwar dake ga bahij dina.

Yayi murmushi sannan yace sbd bahij dinki yana da qarfin tsafi.
Amma yakamata kishafa tsuntsuwar sbd muga mazai faru.
Tace hakane gsky tana shafawa nan take dukkan gurin yayi haske sosai sai suka fara jin kukan wata tsuntsuwa daga sama
Suna daga kansu sai sukaga wata babbar tsunsuwa mai girman gaske tana tunkarosu.

Da farko har dukansu sun fara tsorata kawai sai sukaga tazo gabansu ta tsaya tana kallon mayiesha.
Sai munawwar yace kenan wannan yana nufin tsuntsuwar kice tunda gashi tana kama da wadda ke ga bahij dinki.
Tace hakane amma wannan tsuntsuwar tanada matukar girma mezamuyi da ita.

By maryam ashutrah

Yace daga dukkan alamu zata taimaka mana sosai a cikin tafiyar mu.
Yace kije kishafa ta manah sannan yakamata kibata suna.+

Taje gun inda tsuntsuwar take ta shafata sai tsuntsuwar ta rufe idanuwanta sai mayiesha tace inaga zankirata raunat.

Munawwar ya kalleta sannan yace kenan ni tawa tsuntsuwar runat kekuma taki raunat.

Tace eh hakane daga yanxu zandinga kiranki raunat ai kuwa kamar tsuntsuwar taji abunda tace tayi qara mai sauti sosai sannan ta tashi sama ta tafiyarta.

Tana wucewa sai munawwar yace yanxu na biyu shine na koya miki yadda zaki sarrafa takobinki.

Yana koya mata daki daki yadda zatayi itakuma tana saurin koya sbd duk abunda yakoyamata da wuri take iyawa.

Bayan sun gamane sai yace da ita kizo muje na nuna miki wani gurin.suka jera suna tafiya sai surutu take zuba mishi.

Ya kaita gun wani dutse mai girma sosai ya tsaya sai tace wai dama dutsene kakeso kanunamun to meye abun birgewa anan.

Yace kitaba dutsen tace idan na taba mezai faru
Yace to kidai taba tukunna.

Tana tabawa sai dutsen yafara tsagewa yana gama tsagewa sai ga wani guri mai kyan gaske ruwa suna zuba ta ko ina ga fulawowi masu kyau da kala kala.
tace amma wannan gurin yayi matukar birgeni sosai suna shiga ciki yace zaki iya cin komai da kika gani anan sannan kuma zaki iya taba komai amma banda wadannan koren ciyawar
Tace idan kuma nataba mezai faru yace mutuwa zakiyi
Tayi dariya sanan tace tunda nazo wannan gun bantaba ganin wani abu mai cutar wa bah to meyasa yanxu zakacemun wai wannan ciyawar tana cutarwa.

Sai yace sbd ciyawar aljannu ce.
Tace to shikenan naji bazan tababa.
Suna cikin tafiya sai tace nifa saina taba naga mezai faru.

Yana cikin tafiya saida ta tabbatar hankalinsa ya dauku sannan taje ta taba koren ciyawar
tace amma wadannan ciyawun akwai taushi da kanshi mai dadi.

Munawwar na juyowa yaganta tana taba koren ciyawun yasaki wata irin qara yaje gunda take da sauri.
Tace kada ka damu lafiyata qalau nake ba abunda yasameni.
Ya janyo hannunta cikin fushi suka fita daga gurin.
Aikuwa suna fitowa tace munawwar kaina yanamun zafi aikuwa kafinya ankara kawai saita fadi sumammiya.

Cikin firgici yayi sauri ya dauketa yayi sama da ita basu sauka a ko inabah sai cikin dakinsa.
Yayi saurin hada magani ya bude dukkan jikinta yana shafa mata.nan take yayi sauri yafita waje cikin murya mai sauti yakira sunan tsuntsuwarshi ma'ana runat.
ta iso gunsa da sauri yace taje ta samomishi ganyen furen fulawar ruwa.
Aikuwa ba bata lokaci ta kawo mishi yana karba yayi saurin jikashi da ruwa ya kunce gashinta yana zuba masa ruwan amma dukda hakan bata farfadobah.
Yatabi zuciyarta kuma sam bata bugawa.
Nan take yasaki wata irin qara ya hau kuka yana cewa haba mayiesha meyasa zaki mutu kibarni nikadai a cikin wannan duniyar da ba kowa a cikinta.

Yana ta kuka yana bubbugata.

Nan take yaji tayi ati shawa.
Yana kalonta sai yaga tana numfashi sama sama jikinta yana sakin wasu irin kuraje manya manya.
Nan take yayi sauri yaje ya dago fuskarta sannan yasaka inwak dinshi a goshinta sai wani haske yadinga fitowa daga jikin inwak din yana shiga jikinta.

Aikuwa nan take bahij dinta yadau wani irin haske sosai yama haskake dukkan jikinta.

Tare da qarfin tsafin inwak da bahij nan take kurajen suka bace gabaki daya.

Yanata kallonta yana cewa mayisha kitashi dan Allah kada kimutu kibarni cikin duniyar kadaici.
Sannu sannu sai ta bude idonta suka sauka cikin nashi ta daga hannunta sai kuma ta saukar nan take wanni bacci ya dauketa.

Sai munawwar yatashi yaje yayi alwalla yayi sallah sannan yadinga yi mata adduoi bayan kusan awa biyu sannan ta farfado.

Yana xuwa gun inda take tace dan Allah ka gafar ceni munawwar tabbas na kasance wadda batada godiya kokadan.

Sannan bayan duk taimakon da kayimun gashi inason na bijire maka.
Yayi murmushi yace ba komai mayiesha Allah dai yabaki lafiya.
Tace ameen sannan ta saukar da idanuwanta akan jikinta sai taga ba kaya a jikinta daga ita sai tajeruwar riga tasaka wani irin ihu ta lukume cikin bargo.
Munawwar yace lafiya dai mekuma ya sameki.

Tadago kanta daga cikin bargo tace meye dalilinka na ciremun tufafi yace nashafa miki maganine.

Tace kashafamun magani
Kana nufin ka shafi jikina.
Yace ai taimakonki nayi.

Sai tayi sauri ta rufe idonta nan take tufafi suka bayyana a jikinta sannan ta tashi tsaye tanajin kunyar hada ido dashi.

Tace zantafi dakina.

Yace kibari har kigama warkewa sbd ban yadda nabarki kekadaibah.

Tace to sbd me

Yace watakil ciwon zai sake tashi.

Tace kenan kana nufin a daki daya zamu dinga bacci.

Yace eh hakane

Tace to ai babu kyau mace da namiji sukwana a guri daya

Yayi murmushi sai yace ai kuma wannan larura ce.

Tayi shuri sannan tace yanxu dai kabarmun dakin nadan shirya
Yafita itakuma tashirya sanan tayi sallah.
Tana gamawa sai tafito waje ta ganshi zaune yana wasa da runat.

Yace yanxu yakike ji tace ba abunda nakeji kawai cikina yakemun zafi.

Yace to muje nadubaki

Ta harareshi sannan tace kamar ya kadubani kenan na bude maka cikina kome kake nufi.

Yayi dariya sannan yace ba haka nake nufibah.

Suna shiga daki sai ta kwanta shikuma ya aza inwak dinshi akan cikinta sai yayi haske sosai sosai.

Sai yace to shikenan nagama dubaki kuma lafiyarki qalau kawai yunwace kikeji bari na hada muna abunci.

Yana rufe idansa saiga abunci masu lafiya kala kala a gabansu.

Sukaci saida suka koshi sannan yace yanxu ki kwanta kidan huta tunda dare yayi.

Ta kalleshi sai tace to kaikuma ina zakayi bacci yace a kasa zan kwanta
Tace to shikenan nagode da kula dani da kakeyi da badan kaibah da yanxu namutu.

Yayi murmushi yace ba damuwa kawai dai kidinga yin abunda nace dan Allah sbd kinga nafiki sannan wannan gurin.

Tace kayi hakuri inshallah bazan sakebah.

Yace to saida safe suka kwanta.

Duk bayan wani dan lokaci yakan tashi yaga yatake sannan yakoma bacci.

By maryam ashutrah

Umma na zaune a bakin murhu tana girki tayi tagumi tana tunani sai taji ana kwankwasa kauren gidan.
Tayi sauri tasaka hijabinta sannan taje ta bude kofar sai taga abban mayiesha ne da malam abbas.
Tayi musu maraba sannan ta dauko tabarma ta shimfida musu.+

Bayan sun zauna sannan take gaida malamin.

Cikin sakin fuska ya amsa sannan yafara da nayi bincike na akan batar mayiesha kuma nagano tana wata duniya wadda bakowa a cikinsa sai wani dan saurayi wanda yadade a cikin ta tun yana qarami.

Amma wannan ba abun tada hankali bane sbd suna iya kokarinsu domin su kubutar da kansu daganan sbd haka suna bukatar adduah sosai sosai.

Umma tace amma kasan mace da namiji su kasance a guri daya sukadai babban hatsari ne
.
Malam abbas yace kada kidamu da izinin Allah ba abunda zai faru.

Abba yace to shikenan malam zamuyi iya kokarinmu gurin yin adduah kuma dan Allah kutayamu

Malan abbas yace inshallah zamu yi hakan to nagode zan tafi yanxu.

Umma tace nakusa qarasa abunci bazaka bari ya idar bah

Yace a'a a koshe nake wlhy na gode da karramawa.sukayi sallama yawuce warsa.

Washe gari da safe ta tashi tana waige waige sai kawai ji tayi ance ya jikin naki da fatan da sauki.

Tace kawai dai inajin kasala ne
Yace kada kidamu idan kikayi wanka kakici abunci zaki murmure.

Tace nagode sosai dan uwa yadda kake kula dani
Yace ai dole nakula dake sbd kekadai ce zaki iya fudda ni daga nan.
Tace awww sbd wannan kenan kake kula dani koh bawai sbd ka damu danibah
Yayi murmushi wanda ya fidda asalin kyansa yace ba haka bane
Yanxu kitashi kishirya muje
Tace ina zumuje

Yace training mnh

Tace laaa dama kanajin turanci

Yace eh inaji sbd lokacinda nake gida ina zuwa makaranta amma kadan kadan nakeji yanxu sbd nadade banyibah

Tace nima haka sannu sannu nakeji sbd ni kam ko a gida ma banason zuwa makaranta
kuma gaji makarantar gwamnati nakeyi sbd ni yer talakawace.

Yayi murmushi sannan ya mika mata hannunsa yace kawo hannunki na tayaki tashi.

Tana mika masa hannunta ya janyo ta tashi sannan yace to kije dakinki ki shirya nima zan shirya tace to shikenan.

Tana fitowa saita rufe idanta sannan ta bude amma bataga dakintabah.

Tayi mamaki sosai sannan ta taba bahij dinta ta rufe idanta amma duk da hakan ba daki ba alamarsa.

Tace nashiga uku kada dai ace bahij dina yadena aiki.

Tace bari dai naje nafadawa munawwar tana shiga dakinsa sai ta ganshi cikin shigar yen india yafito sak kamar salman khan ta saki baki tana ta kallonshi har saida ya lura da akwai mutum a cikin dakin.

yana juyowa sai yanufo dinda take yace lafiya baki shiryabah sannan ta dawo hankalinta.

Ta kalleshi tace kayi kyau sosai

Yayi murmushi yace to nagode meya hanaki shiryawa

Tace bahij dina yaki yayi aiki nayita kwadawa.

Yace to inaga sbd bakiji sauki bane shiyasa amma duk da hakan bai kamata ace baya aiki bah.

Amma mugani ta bashi bahij dinta ya kalleshi da kyau sannan yahada bahij dinta da inwak dinshi sai kawai ya saki wani haske.
Yace kinga yana haske yanxu.

Ya shafa bahij dinta a fuskarta tare dayin bismillah sai kawai haskenshi ya qaru.

Yace gashi yanxu inshallah zaiyi aiki.

Ta karba sannan tafita ta sake kwadawa sannan yayi aiki

Ta kalleshi tare da murmushi tace nagode bari nayi sauri nashirya yace to ina jiranki.

Tana shiga dakinta tayi sauri ta shirya tayi kyau sosai sannan tafito.

Tana fitowa daga daki ta tunkaroshi ya kalleta yace amma kinyi kyau sosai.

tayi murmushi tace ai kafini kyau.

kananan kaida runat kenan

yace eh ta kalli runat tace sannunki runat.
sai runat tayi dan wani kuka kadan alamun taji abunda mayiesha tace
sai mayiesha tayi murmushi tace yanxu dai muci abunci sai muje training.

Suna gamawa suka wuce inda suke koyan takobi.

Yaukam sosai ya koya mata tunda har gwabzawa sukayi a tsakaninsu.

(Bayan sati daya.)

Munawwar yakoya wa mayiesha fada ta iya sosai dan har tanason tafishi iyawa sbd wani lokacin idan tagama sallar asubah bata komawa bacci takan dingayin training itakadai.

Suna zaune suna cikin hira sai munawwar ya kalleta yace gobe inshallah nakeson mubar wannan wajen
Ta kalleshi tace amma fa nikam ina tsoro.

Yace kada kidamu kawai kidinga adduah shine kawai.
Tace amma zanyi kewar ka sosai idan muka rabu sbd yanxu fah kusan watan mu daya tare na shaku dakai sosai.

Yace ai bamu rabubah sbd zamu dinga kaiwa juna ziyara.
Tace kuma hakane.

Washe gari da sassafe munawwar yaje gun mayiesha sukayi plan akan yadda zasuyi tafiyar su sannan kuma ya daura mata sarka a wuyanta dakuma wasu yen hannu na gwal masu matukar kyau sai haske sukeyi.

Tace amma ina kasamu wadannan abubuwan.

yace runat ce takawomun nima bansan daga ina tasamubah shiyasa nace bari na baki a matsayin kyauta.

Ta rike hannunshi tace na gode sosai dan uwa Allah yabar zumunci.

Yace ameen ba damuwa yanxu kitashi mutafi tace to shikenan amma yazakayi da runat

yace munyi ban kwana da ita sbd bazaiyi ta biyo mubah sbd ba lallai ta iya rayuwa a duniyarmubah.
Tace hakane amma nima inason nayi maka kyau ta kafin mutafi.
Yayi murmushi yace to tame kenan

tace tsaya ka gani ta rufe idanta nadan wani lokaci sannan ta bude saiga wani abu kamar camera tace inason muyi hoto anan kafin muwuce sbd kadinga tunawa dani idan ka gani.

Yayi murmushi sannan yace to mudauka sukayi hoton sannan ta bashi tace gashi a matsayin kyauta daga gareni.

Ya karba tare dayin murmushi yasaka a cikin kayansa sannan suka fita zuwa wani babban fili.

Ya kalli ko ina sannan kawai ya tsinci kansa yana hawaye.

Ta kalleshi  tace lafiya meya sakaka kuka.
Yace kawai zanyi kewar wannan gurinne sbd anan nagirma tare da tsuntsaye nasaba da wannan gurin koda ace inason nakoma duniyarmu amma still wannan ma duniyatace.

Tace kayi hakuri ta lallasheshi sannan yace to mutafi.

By maryam ashutrah

Suka hada hannunsu tare sannan ya kalleta itama ta kalleshi tace muje na shirya.+

Sukayi bisimillah tare da tashi sama sai da sukayi nisa sosai suka kalli qasa sukaga sunyi nisa da gurin da suke sosai sannan suka nufi gabas.

Cikin sauri suke tafiya inda suke kallon qasa irin hallitunda ke cikin ta.
Har sunyi nisa kawai sai sukaga wani irin qaton tsuntsu mai mummunar halitta yana tunkarosu

Munawwar yace kishirya fah sbd idan har bamu kasheshibah to shi zai kashemu.

Tsuntsun yana isowa gun da suke sai suka rabu hanya biyu munawwar yayi hagu itakuma tayi dama.
Nan take sukayo cikin tsuntsun da zafin nama.
Suka fidda takobinsu suka kaimasa suka da qarfi.

Yayinda munawwar yaci galabar fille masa kai.

Nan take tsuntsu ya bace batt kamar ba'a taba yinsabah.

Cikin sauri mayiesha taje gunda munawwar yake tace munyi nasarar kashesa.

Munawwar yace wannan qaramine dole sai mun dage dantse sosai sbd duk wadannan aljannune sukeson halakamu.

Tace na fahimta muci gaba da tafiya kawai.
Suna ta tafiya a sana cikin gudu da sauri sunata haduwa da tsuntsaye kala kala masu cutarwa amma Allah yana basu ikon kashesu.

Har dare yayi sannan suka sauko zuwa wani dan qaramin gari wanda yakeda wasu halittu kamar na mutane amma ba mutane bane.munawwar yace zamu kafa wani tsari anan ta yadda bazasu iya cutar damubah.

Tace to shikenan amma fa yunwa nakeji sosai.
Yace kada kidamu tunda muna tare da qarfen tsafi dinmu komai zaizo mana da sauki.

Bayan sun hada daki guda daya mai tattare da qarfin tsafi sannan suka shiga ciki.

Suka hada abunci sukaci sannan tace yanxu inason nashirya yaza'ayi

Yace to nahanakine

Tace to kana nufin a gabanka zan shirya
yayi dariya yace ai saima nashirya miki dakaina.

Ta dauki filo ta jefa masa tace bakada kunya munawwar
Yayi dariya yace to ai saiki koyamun nidai ina waje inajiran kikare.
Tace taya zaka fita waje bayan kasan akwai hatsari sosai

bakajin dabbobi yadda suke wani irin kuka mai ban tsoro.

Yace kada ki damu zan iya kare kaina.

Tace to dan Allah ka kula sosai nima zanyi sauri nashirya sbd mu kwanta da wuri yadda zamu tashi da wuri yace to badamuwa.

Tana cikin shiryawa sai taji hayaniya tayi yawa sosai a waje tace nashiga uku Allah yasa ba hari aka kawo mana bah da sauri ta shirya tafito.

Tana fitowa sai ta saka ihu tace munawwar bayanka yana juyowa yaga wata irin halitta da sandar qarfe zata sara mishi cikin zafin nama yayi sama da sauri
nan take dodon shima yayi fukafukai yayi sama mayiesha na ganin haka tayi sauri tayi sama cikin zafin nama takaiwa dodon suka ta gefensa.

Nan take dodon yasaki wata irin qara ai kuwa saiga dodonni masu yawan gaske sun fito tako ina suka fara tun karo su munawwar.

Cikin tashin hankali munawwar yacewa mayiesha bazamu iya da wadannan dodannin bah kiyi sauri ki shafa tsuntsuwar ki.

Cikin sauri mayiesha ta shafa tsuntsuwar ta dake jikin bahij dinta ai kuwa nan take saiga raunat (tsuntsuwar mayiesha).

Sukayi sauri suka hauta cikin wani irin sauri ta fice daga gurinda dodannin suke aikuwa sai dodannin suka bisu.

Cikin kiftawar ido sai kawai suka nemi dodannin suka rasa sbd tsananin saurin raunat wanda har su saida sukayi mamaki.

Suna ficewa daga wannan diniyar mayiesha tajuyo ta kalli munawwar cikin farin ciki shima yasakar mata murmushi sannan suka shafa raunat.

tayi wata irin Qara sannan taci gaba da tafiya cikin wani irin sauri.
Sai mayiesha tace wlhy munawwar bacci nakeji ga yunwa sannan nagaji sosai.

Yace kenan baki shirya tafiyarbah shine kikace mufarata ai dole sai munyi hakuri yanxu bari musamu guri mai kyau sannan musauka kafin safiya ta ida wayewa.

Tace to shikenan.

Sunata tafiya har saida safiya tafara wayewa dukansu sun gaji amma kwata kwata ba alamar gajiya tattare da raunat sai tafiya take tayi.

Munawwar yana saukar da kansa qasa sai yaga har sun shigo wata duniyar wadda daga ita sai tamu duniyar sannan yace da raunat ta sauka anan su huta.

Ai kuwa nan take tafarayi qasa qasa har saida suka sauka qasa sannan suka sauka daga raunat.

mayiesha ta kalli munawwar ta dafa kafadarsa
Tace munawwar ruwa ruwa kawai saita fadi qasa.

Yayi saurin tallabarta ya taba inwak dinshi nan take sai daki ya bayyana a gabansu.

yayi sauri ya tallabeta yakaita dakin sannan ya kwantar da ita.

Yayi sauri yaje waje gun raunat yace kihuta sosai sbd inason idan muka tashi tafiya sai kin kaimu har gida tayi qara kadan ma'anar ta fahimci abunda yace sannan yakoma daki.

Yana zuwa ya kalli mayiesha sannan ya dauki hannunta dake rike da bahij dinta ya shafa mata a fuskarta nan take ta farfado ya bata ruwa tasha sosai sannan ya zauna yanata bata abunci a baki tanaci.

Bayan sun gama cin abunci sannan yace da ita kidan kwanta kihuta kinji.

Tace nagode munawwar

Yace dame kenan

Tace yadda kake kula dani

Yayi dariya sannan yace ai kamar qanwata kike dole na kula dake.

Sannan ta kwanta nan take bacci ya dauketa.

Ya gyara mata kwanciyarta sannan ya kalli kyakkyawar fuskarta yace kinada kyau.

Shima ya kwanta a qasa saida sukayi baccin kusan awa biyar sannan munawwar ya farka.

Yana tashi yaje yayi alwallah yayi sallah sannan ya tada mayiesha.

Tana tashi yace kiyi sauri kiyi sallah sai kidan huta sbd muci gaba da tafiya.

Tace to yaya munawwar.

Ya kalleta cikin mamaki yace yau kuma nine yayan.

Tace ai ka chanchanci nakiraka da hakanne shiyasa.

Yace to godiya nake sannan yafita zuwa waje.

By maryam ashutrah

Pls your votes and comments are needed and i hope you re really enjoying my short story.
Luv u all.

This page is dedicated to my beautiful family lov u all๐Ÿ˜˜+

Cigaban labari๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

Yana fitowa sai yaga raunat bata waje yasan ta tafi kiyo.
Yace amma yakamata nadan zagaya naga yadda wannan gurin yake.

Yana cikin tafiyane sai ya hango wata tsohuwar mai siffar mutane amma kunnayenta kamar na alade tana zaune agurin wata magudanar ruwa tacika tulu amma takasa dauka.

Yadan firgita kadan da ganin irin wannan halittar amma sai yanuna rashin tsoro yabi ta gurinta zai wuce sai tace dashi yakai wannan dan saurayin katemakamun na aza wannan tulun akaina.

Ya kalleta cikin rashin yarda amma sai yaga yakamata ya taimaketa sai yace idata to.

Har ya dauki tulun zai aza mata akai saikuma tace kaga inada karancin karfi a tattare dani ka taimakamun ka isar mun dashi har izuwa masaukina.

Yace to shikenan muje
Tana tafe a gaba yana biye ta ita a baya.
Suna cikin tafiya kawai sai matar tasaki wata irin gigitacciyar dariya nan take saita kidime tazama wani irin qaton dodo mai matukar girma.

Nan take munawwar ya saki tulun ganin wannan halittar.

Sai tace kai aganinka ka tausayamun kenan koh shiyasa zaka taimakamun
To nikuma wannan qarfen tsafi dake hannunka nakeso kabani.

Yace bazan bakibah saidai kikarba da karfi.
Nan kuwa tasake wata irin dariya sai kawai ta ziro dogon harsheta da niyyar zata kamashi.
Ai kuwa nan take yayi tsalle yayi sama.

Ta kalleshi sannan itama ta zira hannunta mai tsayin gaske zuwa kamashi amma yayi nasarar sarar mata hannu.
Ai kuwa sai tarabu kashi biyu wata dodonniya tafito daga jikinta sai suka zama su biyu kenan.

Munawwar bai tsorata bah sai kawai yace mata nayi niyyar yimiki alkahairi amma zaki sakamun da sharri.

Ta kalleshi tace kaine kasan wani abu alhairi nikuma bansanshibah nan take suka kaimasa hari.
Idan yasamu nasarar datsar wani ban gare na daga jikinsu sai su qara yawa.
Nan kuwa suka rikide cikin wani irin gumurzun yaki amma basu samu nasara akansabah.

Suna cikin fadar bai ankarabah sai wani dodon ya sareshi a gefen wuyanshi nan take yasaki wata irin qara ya juya sai yamaida takubbansa guda biyu.
Yafara fada dasu cikin zafin nama.

Wani dodon ya ziro harshensa kenan zai kama qafar munawwar sai kawai ji akayi fasss jini yana zuba.
Munawwar yana juyowa yaga mayiesha ce.
Ta kalleshi tace bazaka iya kaikadai bah dole saida taimakona
Cikin fushi mayiesha tayi tsalle ta sare kan daya daga cikin dodannin sai kawai ganin akayi kansa a qasa yafadi matacce.

Munawwar yace kenan takobinkice kawai zata iya kashesu.
Tace hakane sbd haka kabarni kawai dasu.
Ai kuwa haka akayi saidai kawai a dinga ganin rabin jikin dodanni da kawunansu suna faduwa a qasa.
Suna cikin gumurzun yakinne taga munawwar yana kokarin faduwa a kasalance sbd sarar da dodo yamasa a wuya jini take fitarwa sosai.

Nan kuwa hankalinta yayi matukar tashi sosai sai ta shafa qarfen tsafi dinta nan take sai ga raunat tazo gurinda suke.

Suka samu dakyar suka hau saman raunat ta tashi da sauri.

Tana tashi tayo qasa cikin sauri sai kawai ganin kake dodanni na mutuwa saida raunat ta kashesu gabaki daya sannan tayi sama sai faman gudu takeyi.
Mayiesha ta kalli munawwar dake kokarin sumewa tace dan Allah munawwar kakara hakuri yanxunnan idan muka isa duniyar mu zamu samu guri mu tsaya.

Ya kalleta yace muna sauka kihada qarfin inwak dina da bahij dinki saiki shafamun a fuskata.
Cikin kuka da tausayin halinda yake ciki tace to zanyi hakan.

Har kusan awanni biyar suna ta fanan gudu saman iska tun munawwar yana daukrewa harya sume.
Suna shiga duniyarmu nan take tafara ganin ruwa ta ko ina da ciyawu kala kala nasu kyan gaske.sai taga wani irin duhu kuma yana tunkarosu tana ganin hakan tasan aljannune suke son hakasu shiga.

Duhun yana tunkarosu sai mayiesha ta kalli raunat ta shafa gashin jikinsa tace Bismillah allahu akbar.
Aikuwa nan take raunat ta qara gudu sukayi cikin dubu dinnan da gudu.
Kafin kiftawar ido sai duhun ya watse.
Sai suka ga wani dan gari qarami ba komai a cikinsa daga dabbobi sai bishiyoyi.
Ta shafa raunat tace da ita musauka anan saboda nayiwa munawwar magani.
Ai kuwa nan take raunat tafarayi qasa qasa har saida suka sauko.
Suna saukowa nan take duka dabbobin dake gurin suka dinga guduwa sbd ganin tsabar girman raunat.

Itakuma mayiesha tana saukowa daga bayan raunat tayi  saurin rufe idanuwanta tare da shafa bahij dinta nan take sai daki ya bayyana a gabanta.

Da sauri tadinga jan munawwar a hankali sbd bazata iya daukan shibah har daki.

Tana kwantar dashi ta kalli kyakkyawar fuskarsa tace yayanna bazaka banni bah ka mutu inshallah yanzunnan zaka farfado.

Ta hada bahin dinta da inwak dinshi nan take suka bada wanj irin farin haske sai ta shafa a fuskarsa.
Nana take sai jinin dake zuba a fuskarsa ya tsotse tayi sauri ta yaga mayafinta ta daure masa wuyansa inda yaji rauni.
Sannan ta samar da ruwa  ta dinga goge masa duk inda jinin ya bushe a fuskarsa.
Ta dauki hannunsa ta dinga gogawa tana dan Allah yaya munawwar ka farka.
Amma saidai yana numfashi amma ba alamun farkawa.

Nana take ta fashe da kuka tana fadin dan Allah yayana ka farka kada ka barni bayan na cika maka burinka na dawo dakai duniyarka zakaga mahaifanka.

Amma shuru baya motsi saita kwantar da kanta kan kirjinsa tana jin bugun zuciyarsa tana kuka har bacci yayi gaba da ita cikin tsabar gajiya.

Shikuma nan take sai munawwar yaji zuciyar shi tana bugawa da qarfi sai ya dinga bude idanunsa a hankali.
Ya saukar dasu akan mayiesha dake kwance akan kirjinsa.

By maryam ashutrah

Cikin murya qasa qasa yafara kiran sunanta amma sam ta gaji ko jinsa batayi.+


Sai yayi kokarin janyeta daga jikinshi sannan a hankali ya kwantar da ita.


Ya tashi zaune cikin rashin kwarin jiki  ya taba inda yake masa ciwo.


Yana tashi tsaye sai yaji jiri yana neman faduwa yayi sauri ya zauna.


Yana zaune kusan minti talatin sai yaji motsin mayiesha tana kokarin tashi daga bacci.

Tana bude idanuwanta taganshi a zaune sai tace dashi yayana yaushe ka tashi.


Yace bandade da tashibah


Tace to ya jikin naka yanxu dafatan dai da sauki.


Yace eh kawai dai dan ji nake gani.


Tace eh wahalar tafiya ce nima ita tasakani bacci.


Yace yanxu muna inane.


Tace muna duniyar mune munawwar.

Ya kalleta cikin tsabar jin dadi ta rungumeta yace nagode miki sosai mayiesha da taimakona da kikayi.


Tace muka dai taimaki juna zakace.


Yayi dariya yace kuma hakane yanxu ai kawai sai muyi sauri muwuce zuwa garinmu sbd nasan sbd tsabar saurin wannan raunat din taki zamu iya kaiwa cikin awa daya.


Tace eh hakane amma yakamata kadan huta tukunna.


Yace kada kidamu yanxu ai naji sauki kawai yanxu mu shirya sai mukama hanya.


Tace to shikenan amma dai yau kam bazaka fitabah sbd banason wani abun yasake samunka.


Yayi dariya sannan yace kenan a gabana zaki shirya tayi murmushi sannan tace ai yau tun a cikin ban daki zan shirya.


Yace to shikenan daga nan kiyi alwala sai muyi sallah gaba daya.


Tace to tatashi tsaye sannan ta kalli wani bangare na dakin ta shafa bahij dinta tare da rufe idanta bayan tayi niyyar abunda takeso.

Nan take saiga toilet ya bayyana a gabansu.

Tashiga ciki tayi wanka sannan ta changer kayan jikinta zuwa kyakkyawar doguwar riga sannan ta gyara gashinta sannan tayi alwala tafito.


Yana zau akan gado tana fitowa ta bita da kallo.

Ta kalleshi tayi murmushi sai tace yanxunnan zaka fara mun irin wannan kallon naka koh.

Yayi murmushi yace kawai dai naga kullum sai kyau kike qarawa.


Tace a hakan muna kwata kwata ba kwanciyar hankali a tattare damu.


Yace ai yanxu kam hankalinmu a kwancene tunda saura kadan mu isa gida.


Tace hakane kam yanxu dai kayi sauri ka shirya muyi sallah.


Yace to bari na tayaki tubke gashinki.


Tace ikon Allah yaukuma kaida kanka yace eh mnh.


Tace to shikenan ta zauna yayi tsafi saiga wani irin kyakkyawan ribon dan qarami a hannunshi ya dinga nade gashinta yana sakawa a ciki.

Yana qarewa yace nagama.


Tayi tsafi saiga madubi a hannunta ta kalli gashinta tace amma kam yayi kyau sosai waya koyamaka.


Yace nima ina tubke gashina wasu lokutan.


Tace amma dai kasan idan muka isa garinmu saika rage wannan gashin naka sbd yayi tsayi dayawa harfa yakusa nawa.


Yace to shikenan naji yanxu dai bari nayi sauri na shirya.


Cikin minti goma yafito sannan yace to kitashi muyi sallah.


Tana juyowa ta kalleshi sama har qasa tace ka ganka kuwa kamar wani balarabe.


Yace kedai kullum kinason zolayata to dai nagode.


Bayan sun gama sallah sukaci abunci sannan yace yanxu ina zamu fara tafiya garina kokuma naki.


Tace duk wanda yakamata yace yakamata dai muje naku sbd ni yanxu bazan iya gane gidanmubah sbd shekaru da yawa dole sai nayi bincike.


Tace kuma hakane.


Suma cikin hira sai suka jiyo hayaniya daga dan nesa daga inda suke.


Mayiesha ta waro ido tace mun shiga uku badai wani harin bane aka sake kawo mana.


Munawwar yace muje mugani tace a'a kawai mugudu.


Ya kalleta yace mugudu kuma sai kace wasu matsorata.


Tace nibanyi kama da matsoraciyabah kawai dai sbd mu tsirane kuma kaga kai baka gama warware wabah.


Yace to muyi sauri muje.


Suna fita sai suka hango wasu mutane akan doki sunata faman gudu wasu kuma a kasa suna biye dasu suna ihu.


Nan take na saman dokim suka wuce ta inda su munawwar suke tsaye.


Mayiesha tace inaga fah barayine sukayiwa wadannan talakawan sata.

Yace kuma zai iya yuwa.


Amma dai bari mu tambayesu.

Suka isa gun inda mutanen suke sai yace dasu lafiya kuke ihu kuma gudu.


Sai daya daga cikinsu yayi wani yare wanda munawwar bai ganebah amma daga dukkan alamu yana nufin sata wadanchan suka musu.


Yayi musu alamar dasu kwantar da hankalinsu zasu kwato musu dukiyarsu.


Cikin sauri munawwar da mayiesha sukayi sama suka dingabin barayinnan da gudu.


Har saida suka isa gun inda suke sannan suka fitar da tako binsu suka sha gabansu.


Sai babba daga cikinsu ya tsayar da dokinsa ya fidda takobinsa.


Yanufo ta inda su munawwar suke cikin wani yare yayi musu alamar su barsu su wuce kukuma su kashesu.


Nan take munawwar yace mayiesha kija baya kibarni da wannan dan qaramin kwaron zanji dashi.


Ai kuwa nan take munawwar yayo cikinsa da gudu ya fillewa dokinsa kai sannan suka fara fada.

Tashin farko munawwar ya cire masa hannun hagu.


Barawon ya kurma wani ihu sannan yayiwa sauran barayin alamar su tunkaro su munawwar.

Suda yawa suka nufato inda su munawwar suke amma kawai sai dai kaji kafa da hannu suna faduwa a qasa sauran suna ganin haka suka gefawa su munawwar dukiyar talakawan sannan suka gudu.


Sukuma su munawwar suka dauki dukiyar sannan suka fice daga gurin.


Suna isa gun inda wadannan talakawan suke suka mika musu dukiyarsu.

Cikin jin dadi dukansu suka risina sukayi musu godiya.

Sannan babban cikinsu ya bude buhunsa ya dauko wani dan qaramin dutsen zinari ya basu.


Mayiesha taki ta karba hakama munawwar.

Cikin mutanen suka nuna rashin jin dadinsu akan hakan sannan mayiesha ta karba.

Tace idan bamu karbaba zasuga kamar mun rainane.

Munawwar yace kuma hakane to yanxu dai muwuce kawai.


Sukayi sallama da mutanen sannan mayiesha takira raunat suka hau kanta sannan suka cigaba da tafiyarsu.


By maryam ashutrahSunata tafiya sama cikin gajimare cikin farin ciki dajin dadi.

Haka kuwa suna isowa sannan sai kawai sukaga sun bace battt kafin su ankara sai gasu a filin makarantarsu mayiesha.


Mayiesha ta kalli munawwar cikin farin ciki ta rungumeshi.


Tace mu godewa Allah wanda da taimakon sane muka samu dawowa zuwa wannan duniyar tamu.


Taja hannunsa tace kayi sauri muje gida sbd banason kowa ya ganmu.


Shikam munawwar yayi shuru yakasa cewa komai.


Haka ta rufe fuskarta sbd kada a ganeta har saida suka isa kofar gidan sannan ta kwankwasa.


Umma kuwa na daki zaune tayi tagumi tanata tunane tunane sai taji anata kwankwasa gida.

Ta zata abban mayisha ne yadawo.


Tatashi sannan taje gun kofar tana budewa sai taga mayiesha nan take cikin farin ciki mayiesha ta rungume ummanta har da zubar da hawaye.


Umma cikin mamaki da kewar yer tata ta kalleta cikin hawaye tace mayiesha ina kika shiga  kika dauki tsawon wannan lokacin baki dawo gidabah.


Mayisha tace umma yanxu dai mushiga cikin gida.


Ta kalli munawwar tace shigo.


Suna shiga cikin gida suka wuce  parlor suna zaunawa sai umma ta kalli munawwar tace mayiesha wannan kuma waye.


Mayiesha tayi murmushi tace umma zanyi miki bayanin komai amma dai yanxu kibari mudan huta tukunna.


Sai umma tace to shikenan ki kaishi dakinki ya huta kekuma sai kije dakina nikuma bari na hada muku abunci sannan kuma nakira abbanki.


Tace to ummata.


Munawwar  yabi bayan mayiesha yana ta kallon irin gidanda suke rayuwa.


Suna shiga daki tace yanxu kashiga ga bayi nan bari na kawo maka ruwa sai kayi wanka.


Yayi murmushi sannan yace to mayiesha.


Bayan ta kawo mishi ruwa ya shiga yayi wanka yana fitowa ya shafa inwak dinsa saiga tufafi masu kyau a jikinsa.

Yana gama shiryawa.


Ya zauna akan katifar dakin yana kallon dakin yace Allah mai iko dama a irin wannan rayuwar mayiesha take zaune.


Amma kwata kwata idan mutum ya ganta zai zata daga gidan hutu take kuma yer masu kudi ce.


Tana fitowa wanka ta shafa mai a jikinta sannan ta saka hijab zuwa dakinta.


Tana shiga sai taga munawwar a zaune sai tunane tunane yake tayi.

Tashiga da sallama sannan tace nazo zan dauki kayanane.


Tana daukar tufafinta zata fita dakin saita kalli munawwar tace lafiya dai naganka a haka tunda muka iso baka ce komaibah.


Yace ba haka bane kawai gajiyace tamun yawa


Tace to kadan kwanta ka huta kafin abba ya dawo sai a zauna asan yadda za'ayi kakoma gidanku.


Yatashi yaxo gunda take yace mayiesha banason naje na barki a wannan halin.


Cikin mamaki tace wani hali kenan.


Ya kalleta sannan yayi shuru kadan yace ba komai.


Tace to bari nayi sauri naje na shirya.


Tafice tana zuwa ta shirya sai tafito ta taya ummanta girki.


Suna gamawa saiga abba yadawo daga kasuwa.

Cikin zumudin ganin mayiesha ya daga hannu sama yayiwa Allah godiya  yana shiga parlor ita kuma tana fitowa daga kitchen cikin jin dadi mayiesha ta rungume abbanta.


Cikin farin ciki abba ya kalleta yace mayiesha ke nake gani a idona


Tace abba nice mayiesha ce.


Yace mayiesha ina kika tafi kika barmu nida ummanki cikin kadaici.


Tace yanxu dai abba ka zauna zan baka labarin komai amma kafinnan ina zuwa.


Tatafi dakinta ta kira munawwar suka fito tare.


Munawwar yana isowa parlor ya durkusa qasa ya gaida abba.


Cikin mamaki abba ya amsa.


Sannan munawwar ya zauna.


Abba yace da mayiesha waye kuma wannan


Mayiesha tace abba zan baka labarin komai amma dai yanxu muci abunci.


Umma tana gama hada abuncin ta kawo parlor suka zauna dukansu sunacin abuncin.


Suna gamawa sai mayiesha ta kwashe labarin komai ta fadamusu.


Abba ya kalleta yace wannan labarin naku kamar tatsuniya umma tace a gsky nikam  ko a cikin tatsuniyoyin da nakeji ba kamar wannan sai dukansu sukayi dariya.


Abba ya kalli munawwar yace yanxu inshallah zansan yadda za'ayi kakoma gida idan naje kasuwa gobe zanyiwa aminina magana saiya nemomun inda mahaifanka suka da zama.


Munawwar yace to abba na gode.


Sai abba ya kallesu sannan yace yanxu bari naje na sanar da malam abbas cewa sun dawo.


Sai mayiesha ta kalle abba tace amma abba meye fa'idan yin hakan


Abba yace mayiesha tunda kika bata malam abbas ne yaketa kwantar mana hankali akan zaki dawo sannan kuma yana tayamu da adduah.


Tace to shikenan abba.


Abba yana isa gidan malam sai yake tarar dashi zaije masallaci bayan sun gaisane yake sanar dashi cewa mayisha ta dawo.


Cikin farin ciki malam yace to yanxu kaga masallaci zanje idan mukayi sallah sai muwuce chan gidan naka.


Abba yace to shikenan


Bayan sunyi sallah sai suka wuce.

Suna shiga cikin gidan mayisha na ganinshi sai kawai ta bata fuska sannan ta gaidashi ciki ciki.


Suna zaunawa dukansu sai malam abbas ya kalli munawwar sannan ya kalli mayiesha sai ya lura da abunda ke hannunsu.


Malam abbas ya kalli munawwar yace sannu dan saurayi wannan abun dake hannunwanku  kaida mayiesha menene.


Munawwar ya kalli inwak dinshi sai yace qarfen tsafi ne.


Malam yace karfen tsafi fa kace.

Munawwar yace eh.


Sai malam abbas ya kalli abba sannan yace mudan fita waje akwai maganarda zamuyi.


Bayan sun fito sai malam ya kalli abba yace wannan qarfen tsafin da kake gani dole fa a rabasu dashi sbd idan ba hakabah aljannu bazasu taba barinsubah.

Dole sai an salwantar dashi.


Sai abba yace to amma kasan idan ita mayiesha zatayi saurin yarda ta bada nata munawwar ba lallai ya yardabah sbd ya saba da abunshi.


Malam yace hakane gsky amma yanxu abunda za'ayi shine zan san yadda zan fahimtar dashi.


Bayan sun koma parlor sai malam abbas ya kalli munawwar yace malam munawwar nasan tabbas bakason komawa duniyarda kafito ko ba gaskiyabah.


Munawwar ya kalleshi sai yace eh tabbas hakane.


Sai malam yace to hanya dayace za'abi da zaihana kakoma idan kuma kaki ka amince to tabbas nasan bada dadewabah komawa zakayi.


Munawwar cikin tashin hankali yace wace hanya kenan


Malam yace ta hanyar salwantar da wannan abun dayake hannunku.


Munawwar ya kalli mayiesha itama ta kalleshi.


By maryam ashutrah

Sai malam yaci gaba da cewa kasan a addinance tsafi haramunne kuma kaga bazaiyu kuci gaba da amfani dashibah kenan.

Munawwar yace to malam idan dai hakane na yarda a salwantar dashi

Mayiesha itama tace ta amince.

Sai dukansu suka cireshi daga hannuwansu suka mikawa malam.
A gaban su ya ajiyesu a qasa sannan ya dauko wasu ruwa daga aljihunsa yayi musu adduah sai ya zuba nan take sai suka chanja kala zuwa baki sai hayaki suke fiddawa.

Bayan dan wani lokaci kawai sai suka bace.

Malam ya kallesu sai yace yanxu inshallah Allahu aljannun sunbar jikinku har abada.

Abba yayiwa malam godiya sosai

Sai munawwar ya kalli abba yace abba dan Allah ina rokon wata alfarma kafin nakoma garina.
Abba ya kalleshi yace to munawwar fada naji Allah yasa zan iya.

Yace inason ka rokarmun malam dana dinga zuwa gunshi yana qaramun ilimi akan addini.

Malam abbas yayi murmushi yace naji dadin wannan maganar taka munawwar kuma inshallah zandinga kara maka karatu har kayi nisa sosai sannan kuma a kyauta ba zaka biyani komaibah.

Munawwar yayi godiya sosai.

Sai umma tace kema mayiesha komawa islamiyya zakiyi
Mayiesha tayi murmushi tace to umma inshallah zan dinga zuwa.

Sukayi sallama da malam ya tafi.

Bayan kwana biyu suka fara zuwa makarantar a tare suke zuwa kullum idan mayiesha ta wuce aji shikuma yaje office din malam abbas domin karatu.

Sannan kuma yana ganewa sosai shiyasa karatun nasa yake yin sauri sosai haka ma mayiesha tana da dagewa yanxu gurin karatu sbd har malaman suna mamakin hazaka irin ta mayiesha.

Washe gari yana kwance yana baccinsa cikin kwanciyar hankali saiga mayiesha tashigo da sallama tace yayana har yanxu baka tashibah.

Taji shuru ba magana sai taje ta dauko tsintsiya kwaya daya taje dai dai kunnensa tana sakawa.
Aikuwa yanajin an tokareshi ya bude ido yana ganin mayiesha ce tace tashi muje mu karya tun dazu kai ake jira.

Yace aww dama kece kike tokarata a kunne ta tashi da sauri ta nufi kofa shikuma yabita da gudu.

Tana isowa parlour ta buya bayan umma tace umma kinga yaya Munawwar.
Yana fitowa yace umma kiyiwa yarinyar nan magana tadena damuna waifa ina bacci tazo ta sakamun tsintsiya a kunne.

Umma tace mayiesha bakida gsky meyasa zakiyi haka.

Tace umma idan bahaka nayi mishibah bazai tashibah.

Sai ga abba yashigo parlor yace waton tunda safe kunfara fadan kenan.

Sukayi murmushi sukace abba ina kwana.

Abba yace lafiya qalau yarana dafan kun tashi lafiya

Munawwar yace nikam a'a tunda mayiesha a firgice ta tadani.

Abba yace mayiesha kidena neman tsokana fah yanxu dai kuzauna muyi karin kumallo.

Mayiesha tace umma nidai yau idan akwai dimamen tuwo shi zanci bazansha kokobah.

Umma tace to kiduba a kitchen akwai saura.

Munawwar yace nima umma dimame zanci.

Umma tace to ai bazai isheku kubiyu bah
Yace nine babba kawai tabarmun

Mayiesha tace tabb bazaiyubah bari kagani tayi kitchen da sauri aikuwa yabi bayanta.

STORY CONTINUES BELOW

Abba yana kallonsu kawai yace sudai kullum sai sunyi rigima hankalinsu yake kwatawa

Umma tace ai sun shakune sosai
Abba yace nidai inason yaronnan sbd yanada hankali.

Umma yace hakane amma abban mayiesha mezai hana kudinga zuwa kasuwa tare tunda kaga kullum a gida yake sai idan yaje makaranta.

Yace kuma wannan shawara ce mai kyau amma zanyi tunani akai.

Tace to Allah yasa muji alhairi.

Yace ameen.

Tana shiga kitchen xata rufe kofa kenan saiya turo da karfi yace kuwa baza kicishi kekadai bah.

Tace haba yaya ba yawa fah yace to saimuci tare zai isa.kinsan idan mutane biyu sukaci abunci tare yana albarka sosai.

Tace to muje muci taren kuma banda loma.

Yace naji.

Suna zaune a bakin kofar kitchen sunacin dumame sai mayiesha tace yaya na

Yace na'am yer qanwata

Tace yakamata yau muyi mu gwada yin fadan takobi.

Yace fada kuma sbd me

Tace sbd banason namanta yadda akeyi kuma kaga idan katafi shikenan.

Nan take yanayinsa ya chanja yace banason naje na barki kekadai.
Tace nima haka na saba dakai sosai.

Yace mayiesha iyayenki mutanen kirkine kiduba yadda suka daukeni kamar danda suka haifa.

Yace hkn yanxu dai katashi kaje kayi wanka sai mutafi makaranta yace to.

Bayan sallar la'asar  sun dawo daga islamiyya suna zaune a parlor suna karatu sai akayi sallama har mayiesha zata tashi kenan sai munawwar yace bari naje na duba.

Ya tashi zuwa bakin kofa sai yaga wani dan yarone
Yace lafiya ya'akayi

Yaron yace wani ne yace nakira mishi mayiesha

Munawwar yace wani kuma babba ne

Yaron yace eh babba ne yace to kaje kace mishi yayanta yahanata fitowa.

Yaron kuwa yajuya yatafi.

Munawwar yana isa falo sai mayiesha tace waye yazo nemana kace bazanjebah.

Yace wai wani mutum ne

Tace to ai bakasan meyake tafe dashibah kuma zakace bazanjebah.

Yace nasan bazaiwuce yazo kunkine yanasonki

Tace to ai nikam tunda nake wani baitaba zuwa gidanmu wai da niyyar soyayya bah dukda kyau na kuwa haba dai ai daka barshi naje tunda watakila musasanta dashi.

Watakil sbd mu talakawane sosai shiyasa ba'azuwa guna kasan yanxu auren jari akeyi.

Yace to shikenan ai saiki tashi kitafi tunda ke gaki bakida jan aji kuma sarkin zumudi.
Yatashi tafice zuwa daki.

Tana kalloshi cikin mamaki tace to meye abun fushi anan sbd anzo guna

Tatashi tabi bayanshi tana shiga dakin tace dan Allah kayi hakuri ba haka nake nufibah bantaba ganin bacin rankabah kuma wlhy banaso nagani.ya kalleta yace zonan tana isa yace zauna

Bayan ta zauna yace bawai banaso kiyi saurayi bane kawai dai haryanxu ke qaramar yarinyace.

Ta kalleshi tace kasan shekaruna nawa kuwa.

Yace nawa

Tace shekarata goma sha tara fah yanxu.

Yace ai nazata kice talatin tunda dai baki kaibah to haryanxu ke qaramar yarinya ce

Ta kalleshi tace to shikenan naji yanxu dai tunda ba abunda mukeyi ka tashi muje muyi training din

Yace yazamuyi training din tunda ba takobi.

Tace yanxu zanje nan makota na aro tunda mijin matar gidan yana harkar sayarda takobi kaga bazama rasa bah.

Yace to shikenan

Tatashi taje daki ta saka hijab dinta tana fitowa tashiga gidan jummai makociyarsu da sallama.
Jummai na tsakar gida tana shara ta amsa
Bayan sun gaisa sai mayiesha tace dama takubba nakeso na ara guda biyu gunki.

Tace takubba kuma mayiesha mezakiyi dasu.

Tace wani dan abu zamuyi bazamu dadebah zan mayar

Tace bari naje na daukomiki amma dan Allah kudan hanzarta kafin mai gidana ya dawo.

Tace to badamuwa
Bayan ta dauko mata ta mika mata sannan tayi godiya tafito.
Zata shiga gida sai taji ana kiran sunanta.

By maryam ashutrah

Post a Comment for "MAEESHA CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...