KWAI CIKIN KAYA CHAPTER C KARSHE BOOK2 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KWAI CIKIN KAYA CHAPTER C KARSHE BOOK2

KWAI CIKIN KAYA CHAPTER C KARSHE BOOK2

- - Post a Comment

 KWAI CIKIN KAYA CHAPTER C KARSHE

                   BOOK2


Page 43

.....................A take salon wasan ya canja, bily da batai tunanin hakan daga garesaba a wannan daren duk da dai yau jinta take wani sakayau kamar an sauke mata kaya tuni jikinta ya fara tsuma, zuciyarta da jininta na wani irin tsitstsinkewa, gashi ya hanata dukkan damar da zatai ƙorafi ko magiya, juyata yake duk yanda yaso da zafafan salonsa masu rikita ƙwanya da zuciyar duk macen data mallakesa matsayin mahaɗin rayuwarta, ta rumtse idanunta da ƙarfi lokacin da yake karanto___
بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.
         (Da sunan ALLAH. Ya ALLAH! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi).
        Ƙanƙamesa tai da sauri jikinta na wani irin rawa cikin gigitar data risketa batare datayi hasashe ko shiyaryama zuwan wannan daren ba.


          Abinda yay matuƙar birge Jay da mamakin matar tasa shine Jarumtar da bai zatoba daga gareta, ko sau ɗaya batai yunƙurin hanashi yin yanda yaso da ita ba, ta miƙa masa dukkan ragama baki ɗaya cike da juriya da dauriya da sadaukarwa, sai saukar ɗumin hawayenta kawai yake ji da ajiyar zuciyarta tamkar zata shiɗe. (Uhumm) baiji daga garetaba dangane da ɗaga murya balle akai ga kwakwazon da duniya zata fahimci ana dai-dai wajen. duk yanda yaso yin juriya wajen binta a hankali shima dan nuna tausayinta hakan ya gagara, komai ya ƙwace masa a lissafi itaɗin kawai yake gani abu mafi daraja da martaba a garesa a wannan daren dama cikin duniyar baki ɗayanta. Ƙaunarta da tausayinta na ratsa dukannin tsoka da ɓargon jikinsa da jijiyoyi yana gaurayewa da jininsa, bashi da bakin musaltawa, bashi da kalaman kwatantawa, bashi da ƙarfin shelantawa, abinda kawai ya sani shine itaɗin tadabance, idan yace tadaban yana nufin tadaban har ƙarƙashin ruhinsa. Nutsuwar da ya daɗe yana hasashenta a zahiri da mafarkinsa daga gareta yama riski fiye da hakan.......
        A zahiri Bilkisu ta hana kanta kuka mai sauti, amma wahala iya wahala shanta take a hannun Jay, yanda kawai take fitar da numfashi ɗai-ɗai zai baka tabbacin baije da wasaba. Hawaye kam ai wasu basa direwa wasu ke gangarowa. shi kansa bai fahimci ya tafka ɓarnaba sai da komai ya lafa, Sosai tausayinta ya sake mamayesa, taimakon gaggawa ya shiga bata ta kowace hanya data dace. Yanda take kuka sosai sai hankalinsa ya sake tashi, amma haka ya daure ya gasa mata jiki dan yasan shine babban gatan dazai mata a yanzun. Sai da ya tabbatar ta samu ƴar nutsuwa sannan ya barta ta ƙarisa gyara jikinta shi kuma ya fito ya cire bedsheet ɗin da duk yaɗan ɓaci, tunani yake anya kuwa baiji mata ciwo ba?....... Da sauri ya waiga bayansa jin kukanta, zanin gadon daya fara jawowa ya saki ya nufeta dan bai zaton zata fito ba, tarota yay jikinsa yana magana a hankali dan shi kansa muryarsa gaba ɗaya ta wani dadushe kamar mai mura, “Miyasa zaki fito kinsan bazaki iya tafiya ba?” Yay maganar yana kwantar da ita akan sofa.
         Hawayen dake ziraromin na share, dan ni kaɗai nasan azabar da nakeji, babu inda kemin daɗi a dukan jikina, dai-dai da bakina ɗaci yakemin sam babu ɗanɗano, tausayin dukkan matan da aka kusancesu ta ƙarfin fyaɗe ya kuma mamayemin zuciya, shiyyasa Amina ta koma kamar wata ƙaramar mahaukaciya a lokacin.......
     “Ya isa haka kukan mana uhmyim, kinga jikinki harya ɗauki zafin zazzaɓi, ina cewa matar tawa jarumace ashe raguwace?”. Haushi maganarsa ta bani, dan haka nasa hannayena biyu ina kai masa ƙananun duka a ƙirji. Hannayen nawa ya riƙe yana ƙaramar dariya, “Oh to yi haƙuri jarumace, giwar mata, bara na duba wajen nagani bakiji ciwo ba”. Ƙanƙamesa nai ina sake fashewa da kuka, nace, “Ni dai a'a, banji wani ciwoba”.
       Jay yay murmushi kawai yana girgiza kansa, miƙewa yay ya ƙarisa cire zanin gadon ya shimfiɗa wani, rigarsa mai ɗan kauri data kai mata har cinya ya saka mata, yasa towel ya tsane mata kanta sosai gudun kar mura ta kamata, dama ga jikinta yay mugun ɗaukar zafin zazzaɓi, tausayinta duk ya gallabi ransa, cak ya ɗauketa dan harta fara barci ya maidata saman gadon ya kwantar, so yake tasha magani amma baison tadata, dan haka ya ɗakko man zafi kawai ya shafa mata a jiki kozataji ƴar nutsuwa.
            Gaba ɗaya a hidimar Bilkisu Jawaad ya kusa cinye wannan dare, sai da ya tabbatar komai yayi masa yanda yake buƙata sannan ya samu shima ya kwanta, wani irin zafi yaji jikinta ya ɗauka, sai sauke ajiyar zuciya take a jajjere cikin barci, fuskarta ya ƙurama idanu yana kallon yanda ta ɓata fuska alamar dai bata jin daɗi har a cikin barcin. Yaɗan lumshe udanunsa ya sake buɗewa akan fuskarta yana wani ɗan murmushi, ƴar yarinyar nan itace ta nema zautar masa da tunani, “UBANGIJI mai hikima, UBANGIJI mai rahama da jinƙan bayinsa” yay maganar a fili tare da sumbatar goshinta da laɓɓanta da sukai jazur sosai saboda wahalar da sukasha a hannunsa. ‘Yanda take mai sanyi haka komanta yake mai sanyi’ ya ayyana a ransa yana rungumeta tsam cikin jikinsa har saida ta motsa sannan ya sassauta mata. A haka shima barci ɓarawo yay awon gaba dashi.31

STORY CONTINUES BELOW

★★★★★★

          DARE MAIBAN MAMAKI.

        Dolene mutane masu yawan gaske su kira wannan dare  da sunan dare maiban mamaki da ruɗani tare da tashin hankali ga wasuma maybe. Dan kuwa lokacin da Jawaad ke angwancewa a lokacin wasu cikin matsanancin ruɗani suke, dan duk wani azzalumi dake da alaƙa da wani ɓoyayyan sirri daya shafi waɗanan ma'aurata da hikimar UBANGIJI ta dunƙule waje guda wannan shine mafarkin da suka tsinci kansu a ciki a wannan dare.
       (Ƙudirar UBANGIJI ta tabbata, rahamarsa ta yalwata, izzar mulkinsa ta Ƙaddara haɗewar jini dake cikin  jinin da kuka salwantar, azzalumai lokaci yayi, UBANGIJI ya ƙulla rugujewar zaluncinku ta inda bakuyi zato ko tsammani ba, wannan ruɗanin shine nai muku hasashe, kuma gashi ALLAH ya tabbatar dashi, dama na faɗa muku wannan shukar saita fito da izinin UBANGIJI tai yaɗon da zata zamewa rayukanku barazana, nakuma tabbatar muku kafin kubar duniya sai kun wulaƙanta, duk wanda yaci amana dolene amana ta cisa shima, gashi kuwa ALLAH ya tabbatar da hakan, ku fara gudu maƙiya ALLAH, na ce ku fara gudu tun yanzu.......”  
            Dukkanin wanda keda alaƙa da wannan mummunan kalamai a cikin mafarkin a wannan dare hankalinsa a tashe ya wayi gari, domin dai wata shukace da suka binne a wasu shuɗaɗɗun shekaru take nuni da tayi tsiro da yaɗo harta saki ƴaƴa, suwaye ƴaƴan? A ina suke? Tayaya aka samesu bayan irin da suka shuka sunada tabbacin basu bar ko fure ajikin itaciyarsa ba, itaciyar kanta saida suka busar da ita balle ai tunani tayi yaɗon ɗa? Mike shirin faruwa dasune? A ina kuskuren yake? Ya akai mai gidauniya bai taɓa gano musu hakanba? Shima bai gani bane? Kokuwa ya gani ya ɓoye musu?.15

      Lokacine zai basu wannan amasar damu kanmu masu bibiyar labarin😵.

★★★★★★★

             Rashin yin barci da wuri ya sakasu makara da asuba, dan sanda Jawaad ya farka wasu masallatan ma harsun kusa idar da salla, akan fuskar bily ya sauke idanunsa dake cike da barci, ya sauke siririyar ajiyar zuciya tare da tashi zaune da ita a jikinsa, idanu itama ta buɗe a hankali, sai dai suna haɗa ido tai saurin maidawa ta rufe tana ɓata fuska. Murmushin da bai niyyaba ne ya suɓuce masa, a zuciyarsa yake ayyana ‘sai shagwaɓan tsiya’ A fili kuwa sumbatar laɓɓanta yay, cikin raɗa-raɗa yace, “Good morning my Heartbeat”. Saurin cusa kanta tayi cikin ƙirjinsa. Iska ya hura mata cikin kunnenta yana murmushi, “Ko a ɗan ƙarane” yay maganar yana ƙoƙarin cusa hannaunsa cikin rigarta. kukan taɓara ta sakar masa da sauri jan jikinta baya. “Matsoraciya” ya faɗa yana sauka daga gadon gaba ɗaya.
                Lamo nayi kwance zuciyata na tariyomin dukkan abinda ya wanzu a daren na jiya daya tara abubuwa masu yawa a cikinsa, darene da zuciya bazata iya mantashiba ta kowacce irin siga, dan yazo da abubuwa kala-kala a cikinsa. Har yanzu jikina akwai zazzɓi, ga ciwon kai da bala'in ciwon jiki, babu inda bayamin ciwo a jikin nan nawa wlhy. Ina jin motsin fitowarsa amma nakasa motsawa, tunanima nake tayaya zanyi tafiya ni balki........? Cak aka ɗagani sama, wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke ina ɓoye kaina a ƙirjinsa dan banaso ko ido mu haɗa, wata irin matsananciyar kunyarsa nakeji fiye da da. jina kawai nai cikin ruwan zafi, hakan yasa na ƙanƙamesa sosai. A cikin kunnena yace, “Sorry daure, kaɗan za'ayi”. Kaina na ɗaga masa ina haɗiye kukan dake neman tahomin. Yanda ruwan yaɗanyi zafi sosai sai naji daɗi dan har jikina ya gasamin gaba ɗaya dukda inata noƙewa,  har aka gama hannayena suna naɗe a ƙirjina. Saida ya bani towel na ɗaura sannan na samu nutsuwa duk da dai shima bawani babba bane amma yafi dai babu. Matsowa yay zai ɗaukeni bayan na kammala alwala. kaina a ƙasa cikin dakusashiyar muryata nace, “Zan iya tafiya da kaina”. Baice komaiba ya ɗan matsa baya ya bani hanya. Cikin dauriya na fara tafiya a hankali ina matse idanu, dan  zafin nakeji, sai dai ba sosai dazai cutarba,  bakamar na daren jiya dana ringajin tamkar ana yayyankani da wuƙa ba.
       Kallonta Jawaad yake cike da nazari harta fice, yanda take tafiyan batason haɗa ƙafafunta sosai ya sakashi jin dolene ya dubata kodai ya jimata ciwon da gaske?. bayanta yabi  shima. taimaka mata yay ta saka doguwar riga da hijjab shima ya saka jallabiya ya jasu jam'i duk da garima harya waye.

STORY CONTINUES BELOW

            Bayan sun idar fita yay daga ɗakin, babu jimawa sai gashi ya dawo ɗauke da madaidaicin kofi daketa fidda turiri. Kwance ya sameta a inda tai sallar ta ƙudundune da hijjab, tea ɗin ya ajiye ya ɗakko magunguna ya ajiye sannan ya ɗagota jikinsa harma ta fara barci, “Sorry, tashi kisha tea da magani saiki kwanta”.
         Duk yanda na marairaice masa akan na ƙoshi bai saurareniba, sai da ya tabbatar nashaye tas sannan ya bani maganin nasha. Da taimakonsa na koma saman gado, harna fara lumshe idanu naji yana buɗemin jiki, sauri buɗe ido nayi da riƙe masa hannunsa ina ɓata fuska, dan nazata ƙarawar zaice zaiyi. “Na shiga uku, dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy ka maimaita mutuwa zanyi”.
      Dukda ta bashi tausayi saida yaji dariya na neman kufce masa, ya dai daure ya haɗiye kayansa yana wani binta da kallon ƙasan ido, harta fara hawaye. Ɗauke idonsa yay daga fuskarta batare da yace komaiba ya maida inda yake son ganin.Ya kuwa ji mata ciwon da yay hasashe, sai dai bamai ɗaga hankali bane, amma zaiso a dubata gudun kuskure, tsabar son ya tsokane saiya ranƙwafo kanta kamar da gaske abinda take gudun zaiyi. jiyay kawai ta fashe masa da kuka jikinta ya fara rawa kamar wadda ta hango dodo. Dole ya danne dariyar da keson ƙwace masa ya rungumta. “Wasa nake miki niba ƙarawa zanba yi haƙuri”. Da ƙyar ya samu tai shiru har barci yay awon gaba da ita saboda maganin daya bata yana saka barci, ga kuma dama bawani isashen barci sukaiba. Sai da ya tabbatar barcinta yay nisa sannan ya gyara mata kwanciya ya sauka daga gadon bayan ya lulluɓeta da bargo. Dukda shima barcin yake buƙatar yi bai kwanta ba, wayarsa dake a drowan gefen gadon ya ɗauka ya fita falo.

10:30am

            Ring ɗin wayarsa ne ya sakashi farkawa daga barcin daya ɗaukesa anan falon bisa doguwar kujera, kwance yake a rubda ciki, hakan ya sakashi miƙa hannu bisa centre table ɗin dake gab dashi ya lalubi wayar batare da ya buɗe idanunsa ba, guntun tsaki yayi sannan ya buɗe idonun da ƙyar ya kalli wayar. Ganin Jabeer ne ya sakashi ɗagawa yasa wayar a kunne, cikin muryar barci ya amsa masa sallama suka gaisa. Daga can Jabeer ya sanya dariyar shaƙiyanci, “A lallai boss Mamin mu batazo da wasaba, ka kalli agogo kuwa? Kaine da barcin safe har goma da rabi?”. Idanu Jay ya lumshe ya sake buɗewa akan agogon falon, kafin yace, “Kai ka sani dai ɗan sa ido” yay maganar yana tashi zaune da ƙyar. Dariya Jabeer yayi daga can, “Bari nakira anjima, dama akan maganar da mukai dakai jiya ne”. Jawaad ya ɗan sauke numfashi a hankali, “Karka damu gani nan zuwa station ɗinma”. Kafin Jabeer yace wani abu ya yanke wayar.
      Ɗakinsa ya nufa inda ya tarar bily na barcinta har yanzu, sai da yaje gareta ya taɓa goshinta, zazzaɓin yaɗan sauka amma ba duka ba. Baice komaiba ya ƙarisa bayi domin yin wanka.
          Shiri yayi cikin ƙananun kaya da sukai masa ƙyau, yana fesa turare ya jiyo ana knocking turaren ya ajiye ya fita, yasan bazai wuce Nabeelah ba, dan ya kira Ummah yace ta turo masa ita, Ilai kuwa itace ɗin tsaye a bakin ƙofar, Nabeelah da Ummah ta sakata zuwa akan dole kawo breakfast taja baya ganin Yah Jay ne ya buɗe ƙofar yau da kansa, saurin durƙusawa tai ƙasa tana faɗin, “Yayanmu dan ALLAH kayi haƙuri, na tuba wlhy bazan sakeba, ranarma suɓutar bakine”. Shi dai baice mata komaiba ya bata hanya ta shigo, juyawa yay ya koma ɗakinsa. Ta sauke ajiyar zuciya da ƙarisa takowa cikin falon sosai, basket ɗin hannunta ta ajiye saman centre table ta zauna tana waige-waigen ta inda Bilkisu zata fito, zamanta babu jimawa ya fito daga ɗakin yana waya, basket ɗi  data ajiye ya yaye ɗan ƙyallen da aka rufo a kansa, kulolin ya buɗe duka, baice komaiba ya zauna a kujera da faɗin, “Tashi Ki haɗa min coffee”.
       Nabeelah da aka nutsu kamar ba itaba tace, “to” tana miƙewa, tasan wannan ƙyaletan da yay ba yana nufin ya bartaba, akwai abinda yake shiryawa, Ummah ce dukta jamata, tayi alƙawarin bazata bari su sake haɗuwaba har sai bayan wata biyu, amma aunty Batool ita da Ummah yau suka zuga Abbah yace itace zata kawo breakfast. Ummah bata wasa wa yaranta akan aikin gida da girki, duk taɓarar Nabeelah da shegen surutu komai ta iya na mata, sai dai son jikin jaraba, wani lokacin sai Ummah tai mata wuju-wuju akan aiki take tashi tayisa. Kitchen ta nufa ta haɗa masa coffee mai daɗi kamar yanda tasan yanaso sannan ta kawo masa. Har yanzu wayar yakeyi, dan haka yaymata nuni da abincin da hannu. Komawa ta sakeyi ta ɗakko filet tazo ta haɗa masa abincin shima ta koma gefe ta zauna, tana son tambayar Bilkisu tana tsoron sake yin laifi a garesa.
         Abincinsa ya cigaba da ci yana wayar har zuwa wani lokaci, kafin ya ajiye ya maida hankali ga cin abinci kaɗai. Ita dai tana zaune ne tanata satar kallonsa da gulmarsa a zuciya harya kammala ya miƙe yana goge baki da tissue, yay magana batare da ya kalleta ba. “ki tabbatar kin gyara gidan nan, idan kin tashi karki nutsu kiyi da ƙyau kinji, ki kuma tasheta da rawar kankin nan kiga yanda zan sauya miki kamanni”. Fuska Nabeelah ta kumbura tana faɗin, “ALLAH kuwa yayanmu ni yanzu na daina rawar kai”. Juyawa yay ya zuba mata harara ya nufi hanyar fita, harya kama handle ɗin ƙofar kuma sai ya juyo, “Idan ta tashi ki kirani”. “To yayanmu”.
 
         Sadiq da tun ɗazun yazo gidan saboda kiran da Jawaad yay masa akan yazo zasu fita, ya taso daga wajen maigadi da yake zaune suna hira ganin Jawaad ya fito, sai da suka gaisa sannan ya buɗe masa ƙofar ya shiga ya zauna. Zagayawa yay shima ya tada motar suka fice a gidan bayan sun gaisa da maigadi daya buɗe musu gate.
      Duk da ba aikine ya kawosa office ɗinba saida ya shiga suka gaisa da Sir Ahmad da yayta tsokanarsa. Office ɗinya ya buɗe ya shiga, komai tsaf babu wani datti sai ƴar ƙurar da ba'a rasaba. Yana zama babu jimawa su Aliyu na shigowa.
        Yanda suke wani binsa da kallon shaƙiyanci ya sakashi haɗe fuska yana harararsu. “Malamai miye namin wannan kallon ƙurullar?”. Dariya duk suka sanya masa hatta Aliyu da bai cika tsokana ba. Jabeer yace, “Kuji kama kaifa jama'a, waya ce da kai wani abu anan dan ALLAH?”. Jay ya sake zuba masa harara yana ɗauke kansa, “Ai nasan zakuce ɗinne musamman ma kai da babu abinda ka iya sai shegen gulma ko mace ta shafa maka lafiya”. Yanzunma dai dariyar suka sanya suna cigaba da masa sherin wai ƙyallin angwaci yake kamar wata ɗan daren sha biyar.
       Shiru yay musu sukai sherinsu suka gama sannan suka zauna.
          Hafiz ya maida dubansa ga Jay dake duba file ɗin da Jabeer ya basa, “Boss wai mike faruwane haka? Gaba ɗaya mun kasa banbance komai tun daga yinin jiya har safiyar yau ɗin nan? Gashi kuma kazo office bayan munsan kana hutu?”.
           Jawaad ya ajiye takardun yana sauke nannauyan numfashi, miƙewa yay ya ɗakko wani file a drawer bayansa, yana daga tsaye ya ranƙwafo ya dafe tebirinsa da duka hannayensa, dara-daran idanunsa da tun daren jiya haskensu bai gama dawowa ba ya zubamasu Aliyun, cikin ɗacin murya yace,“Hafiz nima wannan amsar nake nema, nakasa fahimtar komai, komai sake ruɗar dani yake da dilmiyani a kogin ruɗani..... a daren jiya wani ya shigar min gida domin cutar da Miemaa, lokacin inacan wajen kama ɓaleru”.
       A tare suka ɗago suna kallonsa fuska cike da tashin hankali. Har haɗa baki suke wajen tambayar baidai cutar da itaba ko?.
      Kansa ya girgiza musu yana miƙewa tsaye sasai, “Babu abinda yay mata, sai itacema ta jijji masa ciwo, ta faɗamin a bubuwa da yawa masu kamanceceniya da yanda akaima matar Jabeer fyaɗe.
      Jabeer yace, “Boss da gaske?”. Kansa ya sake jinjinawa kawai yana mai datse haƙwaransa waje guda saboda azabar zafin da zuciyarsa ke masa.
      Su duka ukun tsaye suka miƙe, suma cikin zafin ran da akan daɗe ba'aga Jabeer da shi ba yace, “Boss anya ba Qaseem bane?”.
      Kafeshi da idanu Jay yayi kafin ya janye yana wani ɗan murmushi mai ƙona zuciya,  “Jabeer! Ba Qaseem bane, a yanzu bashi nake zargiba sam, tako wace siga na auna Qaseem bai hau mizanin bincikena ba, Idan har wanda nake zargi ya zama shiɗinne da gaske to lallai ƙungiyace dasu, dan adaren jiyan Miemaa ta samu nasarar cirar zobe daga hanun wanda ya shigo gidannan, kuma zoben tabbas na taɓa ganinsa a hannun kusan mutum huɗu, abinda ya kuma ɗauremin kai basuda wata alaƙar zahiri dake a bayyane su duka huɗun kuma”.
         Aliyu ne yay ƙarfin halin cewa, “To boss indai basu da alaƙar zahiri tayaya zamuyi tunanin haɗasu a kamanceceniyar laifi?”.
        “Ƙyaƙyƙyawar tambaya Aliy” Jawaad ya faɗa yana fuskantarsa da ƙyau, hannayensa duka biyu ya zura cikin aljihun wandon sa ya zagayo ya sake zama a kujerarsa. suma duk komawa sukai suka zauna.
      Jay ya ɗauki coffee ɗin da Hafiz ya ajiye masa yakai baki yana faɗin, “Akwai kamanceceniya mai yawa Aliy, musamman idan muka saka abubuwa da yawa da suka faru a tsakanin nan a mizani guda, babu abinda yafi ɗaukar hankalina wajen kamantasu sai maganar fyaɗen nan, dan haka zamuyi amfani da wannan damar mu canja salon bincikenmu. Fyaɗen da akaima Amina, Matar Jabeer, Nazifa, yayar Ummie, da ƴar mai aikin gidansu Nazifa daya faru kwanannan duk basu da banbanci, a tunani na hankali da yazo a zahirance zai bama mai nazari wahala wajen fahimta musamman daya kasance ba'a guri ɗaya al'amarin ya faruba, hasalima ba lokaci gudaba, idan har zamuyi aki da hankali kuma amsar ƙarshe itace ba mutum ɗaya ke aikatawa ba kenan. Da akwai aikin dana shirya dunƙule yaran suyi da, dan a jiya harma na sakasu zuwa gidana zamuyi magana sai ban koma gida akan lokaciba, to yanzu zamuyi amfani da wannan damarne, saboda su abin ya faru da wasunsu, sunsan zafi da raɗaɗin da akeji”.
           Cikin farin ciki Hafiz yace, “Wannan tsarin yayi wlhy Boss, amma nima ga tawa shawaran”. Gaba ɗayansu hankalinsu suka maida ga Hafiz ɗin, ya gyara zamansa sosai yanda zai faɗi komai dalla-dalla. “Kunsan a yanzu bazai yuwu kai tsaye mu iya binciko waɗanda akaima fyaɗe irin nasu ba, fitowarma fili zaisa masu aikatawar su ɗauki mataki suma, haka bayyanar yaran kai tsaye zai dawo da hankalin masu aikatawar kansu”.
      “Ƙwarai kuwa hakane Hafiz”.
“Yauwa to mizai hana mu taimakama yaran su buɗe wata ƙungiya haka ta ƙarɓar ƙorafin waɗanda akaima fyaɗen koma a wane yanayine, matanmu su zama sune masu ƙungiyar a bayyane, mukuma mu koma ta bayan fage wajen tsayawa tsayin daka ga masu shari'a su ringa yanke hukuncin daya dace cikin ƙanƙanin lokaci, na tabbata hakan zaisa mu sami dukkan damar da muke buƙata kodan sakacinma da kotuna keyi akan wannan matsalar, kunga mun jefi tsuntsu biyu da dutse guda, zamu sami abinda muke buƙata, zakuma mu taimaki yaran da ake zalinta musamman waɗanda iyayensu basu da ƙarfi akan tsaya masu bayan an cutar musu da ƴaƴansu”.
        Tafama Hafiz suka shigayi dan shawarar tashi tamusu yanda suke buƙata. A take kuma suka tsara komai yanda ya kamata. Suna cikin tattaunawar su Zuhrah suka iso office ɗin kamar yanda Jay yay kirasu tunkan ya baro gida akan su samesa nan.
       Ummie ce tai musu jagora har office ɗin na Jay, Sai da suka gaishesu duk cikin girmamawa kafin su basu izinin zama. Shine ya fara magana cikin dakewar nan tasa da kowa ya sani musamman akan abinda ya shafi aiki, “Inason ku bani dukkan hankalinku nan”. A take duk suka sake nutsuwa garesa fiye ma da yanda yake buƙata.
         “Ku dukanku a yanzu zaku kasance wajen aiki ɗayane, ina mai gargaɗarku da bama buƙatar wasa, daga yau zaku ajiye wani ƙawancenku gefe kuyi aiki tamkar bakusan kankuba, zaku fito a ƙungiyance domin karɓar kukan iyayen da akaima ƴaƴansu fyaɗe. Wannan itace hanya ta farko da zaku iya fahimtar dukkan abinda kukai buri. Sunan ƙungiyarku, lauyoyin da zasu taimaka muku, harma da alƙalai mun tanada, ku naku kawai sauraren duk waɗanda matsalar ta shafa. Baku kaɗai bane a ƙungiyar, akwai matan su Jabeer, dan irin matsalar data faru da ke Nazifa da sister ɗin Ummie data rasu da Amina itace irin hanyar da akabi akaima matar Jabeer fyaɗe kafin aurensu da wasu ƙawayenta biyu data sani”.
        Duk kallonsa sukai cike da ɗunbin mamaki, Nazifa dake sharar hawaye tace, “Yaya kuma suma ba'a gane wanda yay musunba har yanzun?”.
       Cikin tsananin takaici Jay yace, “Ba'a ganeba, hasalima daga ƙarshe a lalace shari'ar ta ƙare tunda babu wasu hujjoji da zasu tabbatar da wanda ya aikata ɗin. Abinda yasa mukai tunanin kufito a ƙungiyancan dan bazai yuwu mu iya gane waɗanda akaima irin wannan kalar fyaɗen ba saita siyasa, suma waɗanda akayima ɗin ta wasu hanyoyi wasu rashin gata ya sakasu sunyi shiru, wasu kuwa sakacin shari'a yasaka zancen wucewa tamkar ba'ayiba. Ku jami'an tsarone shiyyasa muke fatan ƙungiyar da zata fito daga ƙarƙashinku ta banbanta da sauran ƙungiyoyin, mukuma zamu tsaya a bayanku mu baku dukkan gudunmawa ta ɓangaren shari'a dan acanne ake ruguza komi da make ƙwarin gwiwar ƙungiyoyin dake faɗi tashi akan wannan matsalar. Dan haka aikinku zai kasance da manufa biyu....”
            Kasancewar hakan burinsune sai duk suka amsa cike da farin ciki da zumuɗi.
       A nutse Jay ya ƙarayi musu bayani suma su Aliyu suka ƙara musu da nasu.
      
STORY CONTINUES BELOW

★★★★★★★

           Ring ɗin wayatane yasa na farka, na buɗe idanuna da ƙyar ina tashi zaune, saman mirror ɗinsa na hango wayar, dan haka na sauka a kan gadon ina cije baki, duk da Alhmdllh naji daɗin jikina bakamar a daren jiya ba da ɗazun da safe, ganin Ummu ce da kanta tai kirana na ɗan zaro ido waje na ɗauki wayar da har ta katse, ina ƙoƙarin kiranta kiran ya ƙara shigowa, cikin ladabi na ɗaga tamkar ina a gabanta na gaisheta Ina hawaye.
     Daga can gimbiya tai murmushi tana gyara kishingiɗar da tayi jikin mai martaba, “Haba ɗiyata, miye kuma abin kukan, baki da lafiyane naji muryarki haka? Ayi haƙuri to, shiyyasa naƙi kiranki ai sai yau, duk kuna lafiya ko?”. Kaina na ɗaga tamkar ina gabanta nace, “Lafiya lau Ummu, barci na tashi ne, sai kaina dake ciwo kaɗan, inasu Safah? Tun jiya naketa zuba idon zuwansu amma shiru”. “kisha magani to, ALLAH ya ƙara sauƙi, Karki damu zasuzo insha ALLAHU, yanzuma na kirakine akan zuwansu Anuwar anjima kaɗan dan zasu wuce gobe idan ALLAH ya kaimu”. Cikin jin daɗi na share hawayena Ina faɗin, “ALLAH ya kawosu lafiya Ummu, to suzonan su kwana dan ALLAH”. “A'a babu batun kwana ɗiyata, ai ba'a kwana gidan amarya, zasuzo dai zuwa dare su dawo, ki tabbatar mijinki da Anuwar sun haɗu dan munyi waya dashi ɗazun yace baya gida”. “Insha ALLAHU Ummu zanyi ƙoƙari”. “To shikenan, sai anjima na kiraki kinji, kidage da shiga ruwan zafi karkiyi son jiki”. Kunyace ta kamani, a raina ina tunanin kodai shine ya sanar mata..... “Kina jina” magarta ta maidoni hankalina. “Eh Ummu”. “Bawai ina nufin ki shiga ruwan zafi idan babu abinda ya faru ba, tunda nasan kina fashin salla, bakuma saina buɗe miki abinda nake nufiba, ayita haƙuri danshi zaman aure haƙurine, allah yay miki albarka”. Hawayena na share nace, “Amin Ummu nagode”.
           Rashin ganinsa a ɗakin ya sakani jin daɗi bayan na ajiye wayar, cikin dauriya na gyara ɗakin tsaf, na fito ɗaukar kayan shara naga Nabeelah, sosai naji daɗin ganin nata, itace tace nabar sharar ita zatayi, ban musa mataba na shiga nai wanka da sake gasa jikina sosai, hakan ba karamin nutsuwa ya ƙaraminba. Koda na fito saina koma ɗakina nai shiri, ina cikin shirin Nabeelah ta kawomin abinci, dan tunda taga yanayina ta tambayeni lafiya nace mata banida lafiya duk sai naga jikinta yayi sanyi. Yunwa nakeji sosai shiyyasa na zauna naci abincin. ɗakinsa na sake komawa ɗaukar maganin dan naji daɗinsa, ina buɗe box ɗinne Nabeelah ta shigo da sallama da waya a hannu, a kunne kawai ta sakamin batare da tayi maganaba. Ɗagowa nai zan tambayeta wanene? Muryarsa ta shiga dodon kunnena.
       Saida na lumshe idanu na buɗe sannan na amsa masa sallamar tasa,
          “Amarsu kin tashi?”. Ya faɗa cikin zolaya.
       Jinai tamkar na nutse dan kunya, dukda bana gabansa, nai saurin saka hannuna na rufe fuskata ina murmushi da faɗin, “Nidai ALLAH a'a”. Ina jiyo sautin murmushinsa shima, yace, “Nidai nasan amaryata amaryace ƴar gaske, yaya jikin naki?”. Batare dana buɗe fuskarba nace, “Da sauƙi”. “Alhmdllh ai haka akeso, kinci abinci ko?”.
     “Uhm naci”.
  “Tom kisha magani ki sake kwanciya ki huta karki biyema surutun Nabeelah, Gimbiya ta kirani akan baƙi zasuzo kuyi sallama, zanyi ƙoƙari na dawo da wuri nima insha ALLAH. ga Sadiq nan zai kawo cefane Nabeelah tayi girki”.
        “ALLAH ya dawo dakai lafiya to”.
“To nagode, amma mizan ɗan samune Noor-Jahan?”. A marairaice nace, “Mi kake so?”. yace, “Komai aka bani inaso mana”. Duk da ina tsananin jin kunya nace, “To rufe idonka”. “Na rufe ruf Matar Jay”. Yay maganar cikin sanyin murya kamar ba shiba.  da saurin na yanke kiran ina dariya, ina gani ya sake kira naƙi ɗagawa, saima maganin na ɗauka na fita falo wajen Nabeelah.

       Babu jimawa da zamanmu Sadiq ya kawo cefanan da yace, karon farko da zan fara girki a gidana dukda Nabeelah tace na barmata zatayi kar yazo ya gani yay faɗa, ban sauraretaba dan nima inason ƙarfafa jikina ai. Tare mukai girkin cikin nutsuwa da salon da Umm-Anum ta sake koyar dani, dan danan gidan ya kaure da ƙamshi, muka kammala tsaf muka gyara kitchen ɗin sannan.
     Kusan ƙarfe uku na rana saiga su Anum, Anuwar, Abdul-Rahman, Abdur-raheem, Ameen, Meenal, Amaturrahman, Amatullah. Tuni muka rungume juna dasu Amaturrahman kamar mun shekara da rabuwa, su dai su Abdur-raheem dariya suketa mana.............✍1

Inacan ina muku dogon page, kunanan kuna ƙwalama sunana kira😣😫, ku baku ganeba ne, duk randa nai posting da wuri to nayi typing ɗin dare ne ya kwana, idan kuma ban samu damar yiba dole sai randa zan tura nakeyi, ga aikin gida ga uzurorin rayuwa🤦🏻😓, gashi yanzu anzo gangara typing ɗin na buƙatar nutsuwata sosai, amma idan naga wani Comments ɗin har mamakin mai rubutashi nakeyi wlhy. ALLAH dai ya dafa mana kawai, duk ƙoƙarinka baka isa yima kowa yanda ya dace ba, ALLAH kaɗai ka iyama ɗan adam da halinsa wlhy😂🚶🏻🚴🏼.
26
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.10

Page 44
Auntyn Alfindiki saƙonki ya iso gareni, alkairin ALLAH ya kai gareki a duk duniyar da kike, kema ALLAH ya tabbatar da addu'arnan da kikaimin a gareki, yanda kika soni domin ALLAH, kema ina roƙon ALLAH ya soki haka dear.
          Godiya irin trillions dinan 😍😍😍😘😘😘😘

....................Duk yanda zan musalta muku kalar daɗin da naji na zuwansu bazaku fahimtaba, irina da suke gararanbar rayuwane kawai zasu fahimci kalar jin daɗin da mukanji idan mutane irin haka da baka haɗa komai da suba suna nuna maka soyayyar da naka dangin basa nuna maka irinta, abinda ya ƙarama farin cikin nawa armashi kuwa ganin harda matasan samarin ƴaƴan sarki masu zamani da lokacinsu a cikin gidana, kuma sun sake dani tamkar jininsu kona rayu a cikinsu ne. Abdul-raheem ne dai baida yawan fara'a da magana, amma shima bashi da wulaƙanci. Abincin kuma da aka jera musu zama sukai sukaci sosai har ana santi, Abdur-Rahaman harda cewa dama yunwarsa ya tara dan yazo yaci girkin amarya. Amaturrahman ta ɗauki filo ta saka masa waiji wai santi yakeyi. Nan take faɗa ya kaure tsakaninsu, ni wlhy dariyama suka bani, idan kana tare da triple ɗin Ummu dolene drama ɗinsu take baka dariya, shi Abdul-raheem baya magana, amma idan ya mulmulo baƙar magana ɗaya sai tayi kamar ta kar mutum dan takaici, shikuma Abdur-raham babu haƙuri saiya rama, Amaturrahman kuma zuga. Gefe kuma Ameenullah da Meenal ma cashewa akeyi, hakama Anum da Anuwar. Wannan caskalen nasu ne ya sake ƙara armashin hirar tamu da nishaɗi sosai. Kiran sallar la'asar ya saka samarin fita salla, mukuma mukayi a gida.+

★★★★★★

         Ana idar da sallar la'asar Jawaad ya baro station, kai tsaye anguwar su Hudah ya nufa, sadiq yay fakin dai-dai ƙofar gidansu Amina inda Jay ya bashi umarnin tsayawa. Jay daketa rubuce-rubuce batare da ya ɗagoba yace, “Sadiq yimin sallama a gidan nan”. “To Oga” Sadiq ya faɗa yana buɗe motar ya fita. Ƙofar gidan su Amina ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama. Kusan mintuna uku Aminar ta fito sanye da hijjab tana amsa masa. “Assalamu alikum. Malam lafiya kuwa?”. Amsa mata sallamar Sadiq yayi, sannan ya nuna motar, “Dama oga ne yace aimasa sallama”. Cikin rashin fahimta Amina tace, “Oga kuma? Wanene kuma oga?”. Batajira amsar Sadiq ba ta fito zuwa motar, knocking glass ɗin tayi har sau uku, Jawaad da har yanzun hankalinsa na akan rubuce-rubucensa ya saka hannu ya sauke glass ɗin batare da ya ɗagoba. Amina taɗan zaro ido da ɗora hannunta saman baki, “Oh wlhy bansan kai bane Yaya Jawaad, ina yini?”. Ɗagowa yay ya kalleta da amsa mata, duk da fuskar dai babu walwala bai ɗaureta tamauba, “Mama na nan?”. Kanta ta jinjina masa, “Eh tana nan ka shigo”. “Okey” ya faɗa yana maida kansa ga abinda yakeyi. Juyawa tayi ciki ita kuma domin sanarma maman.
       Sai da Jay yaja kusan mintuna huɗu sannan Sadiq ya buɗe masa motar ya fito. yana fitowa Amina na leƙowa dan sunji shiru, itace tai masa iso har cikin gidan, mama na zaune daga ƙofar ɗaki gefenta da tabarmar da aka shinfiɗa masa.
         “Lale marhabin, yau angone a gidanmu?”. Ɗan murmushi Jawaad yay ya zauna a tabarmar yana faɗin, “Ayi haƙuri Mama bamuzo mun muki ya gajiya ba”. “A'a nikam ku riƙe ban gajiyar ku, dan an mana babban ya gajiya, ɗawainiya kan ɗawainiya Jawaad baka gajiya? Anyi hidimar azumi akayi ta salla shekaranjiya kuma saiga saƙo, ALLAH ya saka da alkairi ya jiƙan mahaifa kaji, ALLAH ya azurtaku da zuri'a tagari mai albarka”. Kan Jay a ƙasa yana ɗan murmushi yace, ”Amin mama”. Amina ta ajiye masa kunun ayar da sukayi ta sake gaishesa da tambayar Bilkisu.
            Zama Jawaad ya gyara ya fuskanci mama sosai, “Mama wani taimako nazo kimin Please”. “Inajinka Jawaad, ka faɗa kanka tsaye, inhar baifi ƙarfinaba zan maka da izinin ALLAH”. “To nagode sosai Mama, nasan tun dawowar su Hudah ƙasarnan kike aiki a gidansu bayan rasuwar mijinki, sannan kaf anguwarnan da ƴan gidan nan suke mu'amularsu kawai, a zaman da kikai dasu nasan dolene zaki san abubuwa masu yawa dangane dasu, musanman ma akan duk wani ma'aikaci da yake aiki a gidan”. “Wannan gaskiyane Jawaad, dan mijina kansa kafin ya kwanta jiyyar ajali Alhaji Ali ne ya koma masa kamar amini”. “Alhmdllh, inason sanin maigadin nan nasu ke da shi waye ya riga wani fara aiki?”. “Ya rigani farawa, danshi tunma ana gina gidan shine maigadinsa har aka gama suka tare”. “Okey, yanada mata ne?”. “Tunda nake da shi ban taɓa ganin iyalinsa ba, sannan ban taɓa jin ance yau ya tafi ganin gidaba, dan har tambayarsa nama taɓayi game da hakan lokacin inason bada wasu kaya sai nake tuntuɓarsa ko yanada iyali na haɗasu ya kai musu?. Sai cayaymin ai suna gida, daga wannan amsar ya shiriritar da zancenma gaba ɗaya. Nikuma ban sake tuntuɓarsa game da suba gaskiya”. Shiru Jawaad yayi yana nazarin maganganun Mama, kafin yaɗan huro iska da gyara zamansa. “Amma mama kin taɓa ganin wani abu dangane dashi na rashin gaskiya haka”. “Gaskiya ban taɓa ganiba, saboda shifa mutumne ma da baida yawan magana sam, kafin kaga firarsa da mutum tai tsawo akan daɗe, kodan ba abokina hirar nawa bane oho”. “Kukun gidanfa, yakai shekara nawa shikuma yana aiki dasu?”. “Shima tunda suka tare yake, a gidan na sanshi”. “Mai bayin fulawa fa?”. “Eto shine dai kafin shi kusan mutum uku sukai aiki”. “Miyasa suka bari to? Ko ba'a baku albashin daya dace ne?”. “Ai Jawaad idan ta yawan albashine babu wani mai aiki da zaiso barin aiki gidan Alhaji Ali, zan iya rantse maka a cikin dubu irinsa dake fita haƙƙin ma'aikacin gidansa da albashi mai tsoka sai an tona, sannan duk abinda masu gida zasuci kaima mai aiki zakaci, wulaƙanci da rashin tarbiyyar ƴaƴansa ne kawai matsalar ma'aikatan gidan, amma masu bayin fulawarnan da suka taɓa ajiye aiki wlhy bansan dalilinsu ba, dan daina ganinsu kawai mukai mudai koma sallama basuyi damuba”. “To amma baƙwa zaman mutuncine dasu har zasu ajiye aiki baku saniba?”. “Sosai ake zaman mutunci wlhy, dan wanda na tararma a gidan idan kaga yanda ya ɗaukeni tamkar uwa, amma daga zuwa ganin gida bamu sake ganinsaba sai wani mukaga an kawo”. “Zan iya sanin garinsu su duka biyun?”. “To gaskiya anan gizo ke saƙar dan na manta, amma zanyi ƙoƙari na tinano insha ALLAH”.  “ALLAH ya bada iko to, drivern su fa?”. “Shima basu taɓa canjawaba”. “Kafin ku wasu sun taɓa musu aiki ne?”. “Akwai ƴammata biyu da suka fara musu aiki kafin mai gidana ya rasu mu fara”. “Miyasa suka bari? Kodan an sameku?”. “Wannan bansaniba kam Jawaad, nidai kawai nasan kafinmu wasu sunyi musu aiki, amma ai nasan kaima kasan duk waɗanan abubuwan tunda kana zuwa gidan”. Murmushi Jawaad yayi, “Sanin dazan musu bazai kai na wanda yake rayuwa dasu yini da kwana ba, Mama inason naji wani abu dangane da fyaɗen Amina, tana ina?”. Mama tai ɗan murmushi, “Oh ni, yanzunan Bilkisu bazata haƙura da maganarnanba? Abinda ya faru ya riga ya faru ai sai haƙuri kuma”. “Karki damu Mama, binciken yanada amfani, dan inma ba'aiba haka za'a cigaba da wulaƙanta rayuwar yara cike da zalunci, ita kanta Miemaa ɗin a zaman datai gidan anshayin farautar rayuwarta akan hakan ai”. Cikin tsagwaron mamaki Mama tace, “Bilkisun?”. “Eh wlhy Mama”. Mama tai sagade al'ajabi na neman kasheta, ta sauke nannauyan numfashi da faɗin, “Bilkisu akwai zurfin cikin tsiya, koda wasa bata taɓa faɗiba wlhy. Saima dagewa datai akan gano wanda yay ma Amina, to ALLAH ya ƙara tsarewa, tunda dai kuma basuci galaba a kantaba ai Alhmdllh”. Ta ƙare maganar da ƙwala kiran Amina.
      Amina ta fito daga ɗakin tana amsa mata. Gurin da Mama ta nuna mata ta zauna, Jawaad ya kalleta da ƙyau. “Amina! Randa akai miki fyaɗe suwaye a cikin gidan can?”. “Yaya daga maigadi sai kuku”. “Ina mutanen gidan sukaje?”. “Yah Qaseem da Salman dai sun fita aiki, Momy kuma itada Aamilah ne suka fita, sannan Bilkisu tana makaranta ita”. “Wanene ƙarshen fita a gidan?”. Shiru Amina tayi alamar nazari, kafin tace, “Kamar Aamilah ce”. “Waye ya fara fita kuma?”. “Yah Qaseem”. “Waye ya fara dawowa?”. “Momy da Aamilah nidai na farka na gani bayan na farfaɗo” “Toke dama kina barcin rana a gidanne? Kokuwa a ranar kika fara?”. “Wani lokaci nakanyi idan nasan Mama ta fita dan karna dawo gida ni kaɗai. Da yake akwai ɗakin masu aiki sai nake shiga ciki na kwanta”. “Kafin ranar wani yataɓa miki maganar banza a gidan ne?”. “A'a babu wanda ya taɓa”. “Mikikaci ranar a gidan? Ina nufin Abinci ko abinsha?”. “Banci komaiba bayan abincin safe, dana kammala aiki kuma saina zauna zanɗan huta, tunawa da wani sauran lemo dana ganine lokacin da zan saka wasu a fridge yasa na miƙe na ɗakkosa na shanye, daga haka ban sake sanin ina kaina yakeba sai farkawa nai na ganni cikin mummunar ƙaddara ”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka. Shiru Jawaad yay yana kallonta da nazarin maganarta. “Dama kina shan lemo a gidan kenan?”. “Eh inasha Yaya, dan indai ɓangaren Abincine ba'ai mana shamaki da komai, abinda sukaci muma shi mukeci babu hantara kuma ”. “Alamu sun nuna Dad baya gidan, lokacin kwanakinsa nawa da tafiya?”. “Eh kamar dai zai kai kwana goma inaga”. “Da yaushe ya dawo?”. “Kwana biyu dayin abun”. “Wane mataki ya ɗauka?”. “Da farko ya nuna damuwarsa, har ya bada kuɗi a kaini asibiti, amma daga baya daya fahimci yaransa ake zargi saima yayta faɗa ya kuma ja baya da al'amarin, yay mana korar kare da ƴan sandan da Yaya Sule ya ɗakko dan bincike”. “ALLAH ya ƙyauta to, ai kinyi karatu ko?”. “Eh nagama secondary school”. “Kin amshi result ɗinki? Kuma yayi ƙyau”. “Eh Yaya, credit ɗina taƙwas”. “Masha ALLAH, ki shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Sadiq zaizo ya kaiki wani waje, saiki tafi da takardun, jeki abinki”. Tashi amina tayi tana masa godiya da addu'oin gamawa da rayuwa lafiya ta koma ɗaki.
     Jay ya maida hankalinsa ga Mama, “Mama bara na wuce, zata iya yuwuwa kiga na sake dawowa. nagode sosai”. “Babu komai wlhy Jawaad, ALLAH ya saka maka da alkairi, bara kaga na ɗakko maka ɗanyar awara da nayi ɗazun da safe ka kaima ɗiyata dan tana sonta sosai”. “To mama ALLAH ya saka da alkairi, ita Amina yaushe zataje mata ne?”. Mama dake murmushi tace, “zuwa satin sama zatazo insha ALLAH, kusamu yanzu kuma ku huce gajiya basai an dameku da hayaniya ba”. Murmushi kawai Jay yayi baice komaiba.

STORY CONTINUES BELOW

         Koda Jay ya baro gidansu Amina family House ɗinsu ya nufa, yay ƙoƙarin shishshiga ko ina ya gaishesu da musu godiyar hidima har wajen Mama Atika data amsashi sama-sama, daga baya kuma ta koma lallashinsa akan ya saka ɗan-fir'auna ya saki Shahudah kodan son da take masa ya maidata ɗakinta. Yana wannan murmushin nasa na rainin hankali yace to zaiyi hakan tai musu addu'a. Daga haka ya baro sashen nata ya leƙa yaga jikin Mama Badiyya da sai godiyar ALLAH kawai, zaman asibitin ne anyi har angaji an maidota gida, amma kullum lkitanta na zuwa dubata, su Uncle Sulaiman kuma tsaye suke akan al'amuranta basa wasa da ciwon mahaifiyar tasu da aka rasa kansa. Daga nan ya shiga sashensa ya ɗauki wani akwati ya fito suka fice daga gidan.
            Hankalinsa kuma yay gida gaba ɗaya, duk da yaso zuwa ya duba ɓaleru sai wani gefe na zuciyarsa yafi ƙwaɗaita masa wucewa gidan, koba komai yana da ƙyau yaje yaga halin da ƴar mutane take ciki, ya kamatama ace yau a gidan ya yini ya bata dukkan kulawa da tattali, amma muhimmancin aikin nan daya saka gaba dole ya daure ya fito ɗin.
       Bayan sun iso gidan Sadiq ne ya kwasar masa kayan ya bisa dasu a baya, suna zuwa ƙofar falon ya amsa, duk da yasan suwaye sukazo gidan hakan bai hanashi jin kishi ba saboda jin dariyar maza. Ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga falon da sallama ciki-ciki. Su Abdul-Raheem duk suka amsa masa suna miƙewa tsaye domin girmamawa a garesa, Ameen yazo ya amshi kayan hannunsa duk suna jera masa sannu da zuwa banda Anuwar da tun shigowar Jay yay mutuwar tsaye, su kansu su Abdur-rahman duk baki suka saki suna kallon Jawaad sai kuma su koma su kalli Anuwar dan yau suka fara ganin Jay su. Jin yanda falon yay wani irin tsitt lokaci gudane ya saka Jawaad da tun shigowarsa gabansa ke wata irin faɗuwa ɗagowa ya kallesu. Idonsa ƙyam ya sauka akan Anuwar tamkar wanda magana ɗisu ya janyo. A take kansa ya shiga wata irin juyawa tamkar mai ganin hajijiya. Amma kasancewarsa gwanin dakiya sai ya dake ɗin ya kafe Anuwar kawai da kallo kamar zai haɗiyesa da idanun.
          Anuwar da bazai iya jurewaba kansa ya riƙe da hannu biyu ya koma zaune daɓar saman kujera. Cikin rawar jiki Anum ta ƙarasa gabansa tana faɗin, “Bana faɗa makaba kace ƙarya nakeyi, kagani ko tamkar kai, Anuwar wlhy bari kaji yay bagana muryarku iri ɗaya ne shima. Anuwar da ya kasa bama Anum amsa ya wani rinƙa fisgar numfashi da ƙyar yana sake matse kansa cikin hannayensa yana jujjuyashi. “Anum kaina zai fashe, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wash ALLAH kaina......”      
           Yanda yay maganar tamkar numfashinsa zai ɗauke baki ɗayane ya kuma tadamana hankali mukai kansa mu duka. Duk yanda nake zumuɗin son ganin yanayin dazasu shiga idan sun haɗu da juna sai hankalina ya tashi.
       Ƙarar da Anum ta ƙwalla ce ta maido Jawaad da shima yake riƙe da kansa hayacinsa yay kan Anuwar jiki na rawa. Karɓarsa yay daga cinyar Anum ya maidosa jikinsa yana girgizashi. Sai dai ina numfashin Anuwar ya ɗauke ɗaf, Nabeelah da tun zuwan su Anuwar ta shiga ruɗani hartai masa video cikin hikima batare da kowa ya saniba ta matso tana faɗin, “Yayanmu a kawo ruwa ka zuba masa?”. Kansa kawai ya jinjina mata yana cigaba da ɗan bubbuga fuskar Anuwar da girgizasa. Nabeelah na kawo ruwar Abdul-raheem ya amsa, shine ya shafama Anuwar a fuska, wani irin nannauyan numfashi ya sauke. Jawaad ma ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana lumshe idanunsa ya buɗewa akan Anuwar da shima ya buɗe nasa a hankali, kallon juna suke kallo irin na ruɗani da al'ajabi, basu da suke ganin kamainin nasu da junaba hatta su Bilkisu al'amarin ya kuma ruɗar dasu, dan ita saima yanzun data gansu a waje ɗaya ta sake tabbatar da hukuncin ubangiji, dai-dai da wani ɗan ɗigon baƙi dake gab da kunnen Jay akwaishi a jikin Anuwar shima exactly yanda na Jawaad ɗin yake.......
      Jawaad ya kwantar da Anuwar jikin Ameen a hankali ya miƙe yabar wajen dan jikinsa wani irin tsuma yakeyi, idan kuma yay wasa shima hajijiyar zata iya kwasarsa ne takai ƙasa kamar yanda taima Anuwar.1

       Ruwa na ɗauka da sauri nabi bayansa dan tafiya yake yana haɗa hanya, Zaune na samesa a saman gado ya riƙe kansa da dukan hannayensa biyu, saurin ƙarasawa inda yake nayi ina faɗin, “Boss lafiya?”. hannuna ya riƙo cikin nashi tare da fisgoni na faɗa jikinsa, wata runguma data nema saka ƙirjina buɗewa yay min, ƙaramar ƙarar da nai ta sakashi sassautamin, muduka muka shiga sauke numfashi, munkai tsahon mintuna biyar a haka kafin ya miƙe dani zaune sosai a bakin gadon ya zauna tare da riƙo hannuna ya zaunar dani a kusa da shi. “Wanene wannan Miemaa? A ina kika sanshi?”. ƙasa nai da kaina dan gujema kallon daya kafeni da shi. saurin ɗago fuskata yayi muna kallon juna sosai, “Please Miemaa ba batun kunya mukeba, ki faɗamin wanene shi?”. “Bansan wanene shiba nima, sai dai nasan shiɗin ɗan Umm-Anum dana zauna a wajen tane, mamarsa itace na zauna wajenta a saudiyya sati biyun nan”. “Saudia?, kina nufin daga can yazo nan?”. “ƙwaraima kuwa harda ƙanwarsa ma Anum”.
     Yace, “Innalillahi... mi hakan ke nufi? Wane irin kamannine wannan? Babu ta indafa yaron nan baya kama dani Miemaa?”. “Irin wannan ruɗanin nima na shiga a randa muka fara haɗuwa dasu, da yay magana wlhy nazata kaine, sai daga baya na iya fahimtar ba haka baneba, amma boss kafin Mamah ta rasu bata haifa maka ƙani bane?”. Yanda ya kafeni da idanunsa ya sakani yin ƙasa da nawa gabana na faɗuwa. Ya ɗora duka hannayensa saman fuskata ya ɗago, “Bilkisu Mamata ba rasuwa tayiba”. Yay maganar yana sakin fuskata ya miƙe zumbur yana girgiza kansa. saurin riƙo hannunsa nayi nima ganin zai fita a ɗakin, “Miya faru?”. Saurin dawowa yay ya sake zama. Muryarsa har sarƙewa take yace, “Inason ganin mamar yaran nan”. Bansan lokacin danai wata zabura ba nima ina faɗin, “Ganinta ba matsala bane, amma dan ALLAH da gaske kakeyi mama ba rasuwa tayi ba? To tana inane?”. Yanda nai masifar rikicewane ya sakashi kamo hannuna ya maidani inda nake ya zaunar shima yana wani kafeni da idanu fiye da ko yaushe, “Labarina mai tsahone, namiki alƙawarin a yau zakiji komai daya shafi mijinki, dan kema a yanzu kin zama ɗaya daga cikin family na, kobabu alaƙar jini a tsakaninmu ke matata ce, amma tabbas kamar yanda baba ƙaura ya faɗa Ƙaddarata tana tare da taki”. Cike da mamakin kalamansa nake kallonsa, amma fahimtar danai baya cikin hayyacinsa, shiyyasa nai tunanin yana buƙatar yafara yin wanka yaci abinci sannan. nace, “Kayi haƙuri to ka fara yin wanka kaci abinci sannan dan magriba na gab”. Baice dani komaiba sai kallona da yakeyi har yanzun, hakan yasa na miƙe na shiga bayi. Ruwan wanka na haɗa masa, inda na barsa anan nazo na sake samunsa. Sai dai yanzu riƙe yake da kofi a hannu alamar yana shan ruwa. “Ga ruwan can?”. Idanunsa ya ɗago ya kalleni da miƙomin hanunsa na haggu. Baya naja ina maƙe kafaɗa nace, “Kaje kayi wanka bara na duba su Anuwar ɗin”. Muryarsa ƙasa-ƙasa yace, “Dama ɗazun kin kashemin waya, yanzu kuma nace kizo zaki gudu, laifi biyu kenan nasan maganinki ai, zaki biya bashinsune”.
       Saida na kusa zuwa ƙofa sannan na juyo ina faɗin, “To nima idan na kiraka a waya ka kashe shikenan ai ka rama ko?”. Miƙewa yay yana ɓalle maɓallan rigarsa, “Ai nafi ƙarfin ramawa ta haka yarinya”. Tsayawa nai ina kallonsa fuskata a marairaice, “To gani na dawo ai, amma dan ALLAH faɗamin ta yaya zaka rama? Nifa ɗazun wlhy bansan mizan baka bane shiyyasa na kashe”. “Kin tabbatar?”. Kaina na ɗaga masa. Yay murmushi kawai batare da ya sake cewa komaiba. Hakan yasa nace, “Naje dan ALLAH? Kaga an barsu su kaɗai”. Kansa kawai ya ɗagamin. Nikam tuni nai waje. Mamakine ya kamani ganin falon wayam, na leƙa ɗayan falon har zuwa ɗakina nanma babu kowa, a rikice na fito harabar gidan saina iske babu motarsu, abinda ya sake ɗaure kaina har Nabeelah babu itama. Dawowa nai ɗakinsa danna sanar masa saina iske harya shiga wankan, da sauri na ɗauki wayarsa dan tawa babu kuɗi ciki na shiga laluben sunan Ummu. Bugu biyu kuwa ta ɗaga tamkar dama jira take. Kafin tai magana nai sallama dan karta ɗauka ko shine, ko gaisheta ban tsaya yiba nace, “Ummu.......” katseni tai itama da faɗin nasan mizaki tambaya kwantar da hankalinki, Anuwar ne ya sake suma shiyyasa nace su taho gida, yana da Asthma shiyyasa gashi basu taho dako inhaler ɗinsa ba ma, sun faɗamin komai daya faru yanzu ina mijin naki shi?”. Ya shiga wanka Ummu, ya kumace zai sanarmin da komai daya shafesa”. “Alhmdllh mu dama wannan muke jira ai, saiki nutsu sosai ki fahimci komai yanda yake, ta hakane zamu tabbatar da abinda yake gaskiya, sannan nasan zai iya cewa zai biyosu idan ya fito yaji sun taho, karki faɗa masa Anuwar ɗin yana cikin wani haline, nafiso sai zuwa da safe idan ALLAH ya kaimu inma zaizo ɗin kuzo tare”. “To Ummu insha ALLAHU zanyi hakan, amma inaji a raina wlhy abinda muke zargin gaskiyane, dan yace mamarsa bata rasuba”. “Da gaske?”. “Wlhy kuwa Ummu”. “To shikenan bara na barki karya fito”.
       Ummu na yanke wayar kuwa na goge kiran na dawo ɗakin na ajiye masa wayarsa, fita na sakeyi domin yin salla nima dan anata kira.

     Koda Jawaad ya fito a gaggauce yay shiri ya fita massallaci, bai kawo komai a ransa game da rashin ganinsuba a falon, yayi zaton sun tafi salla matan kuma sun shige ciki, yanayin da yake ciki kuma ya saka bai kula da babu motarsu a harabar gidanba.
     Ana idar da salla gida ya nufo, dai-dai Bilkisu itama ta fito daga kicin tana haɗa masa abinci a d/table. Tsayawa yay kawai yana kallonta daga cikin falon...
     Jin idanu na yawo kaina ya sakani ɗagowa nima, cikin sanyin murya nace, “Ga abinci”.
     Ɗauke kansa yay daga gareni, ya tako zuwa dani ɗin yaja kujera ya zauna, “Su suna ina?”. “Sun tafi”. Na faɗa ina ƙoƙarin zuba masa abincin, Da sauri ya ɗago ya kalleni, “Bangane sun tafi ba, miyasa?”. “Takawane ya kira yace su koma gida hakanan”.
       “Aiko dolene na nabi bayansu dan zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason yima yaronan  tambayoyi”. Saurin zuwa nai gabansa murya a sanyaye nace, “Kayi haƙuri zuwa safiya mana, nima akwai abubuwa da yawa dazan faɗa maka game dasu wanda tunda naga kamaninka dasu naita samowa dama dan na kawosu gareka”. Murmushi yayi ya jawoni kawai ya rungume a jikinsa batare da yace komaiba.............✍14

Maganar gaskiya man kaina ya gama tsiyayewa antafi yajin aiki daga yau😓😫🚶🏻.
104
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
16

Page 45

..................Ganin ya nata juya spoon a abincin ya kasa kai ko lauma ɗaya yasa tausayinsa kamani. nasan yana cikin yanayin ruɗani da shikaɗai yasan yanda yakeji, sai dai jarumtar ƴan mazan ta ɓoye komai daga fuskarsa harma da kuzarinsa. naɗan rumtse idanuna ina tariyo kalamun Umm-Anum. ‘Anya zan iya kuwa?’ na ayyana a cikin raina, daga can gefen zuciyata tace zaki iya ki daure, ruɗanin da yake ciki yana buƙatar kulawarki, hakan zai bashi nutsuwa. Kaina naɗan jinjina ina danne fargabata da matsananciyar kunyar da nakeyi na ɗaura hannuna akan nasa dake riƙe da cokalin.
     Ɗago lumsassun idanunsa yay yana kallona batare da yace komaiba. daƙyar na iya danne zuciyata nabar idanuna cikin nashi daya tsareni dasu, na langaɓe kaina cikin tsananin nuna kulawa nace, “Dan ALLAH ka kwantar da hankalinka kaci abincin karya huce, kagafa harka rame, kanaso Ummah tace bana kula mata da kai duk farfesun da take sawa kullum Nabeelah tana kawowa”.      
             Lallausan murmushi na musamman ya saki har dimples ɗinsa guda biyu na loɓawa, haƙwaransa suka fito kaɗan, yaɗan lumshe idanu ya buɗe a kaina yana faɗin, “Yarinyarnan na kula wayo kawai kikeson min dan karna fita”. Ya ƙare maganar a hankali yana wani kashemin ido ɗaya da ɗage gira sama.
           Hannu na saka na rufe fuskata ina murmushi, ba ƙaramin kasheni murmushinsa yayiba, dan nikam zan iya rantsewa ban taɓa ganin kalarsa daga garesaba sai yau, fuskata a rufe cikin tafukan hannuna nace, “Ni ƴar ƙaramarnan da nice zan maka wayo?”.
          “Ba gashi ba kinamin”. Yay maganar da kamo hannuna ya miƙar dani tare da zagayo dani inda yake ya ɗaurani saman cinyarsa, ya zagayo hanayensa duka biyu kan cikina, kansa kuma na bisa kafaɗata. Jinai kamar na nutse dan kunya amma na daure kaina a ƙasa nace, “karfa kasa wani yaji ya ɗauka da gaske ne, ina ni ina yima boss wayo, bayan kai ɗin wayon ne da kansa”.
       Kansa ya ɗaura saman wuyana yana huramin iskar numfashinsa, hakanne ya saka tsigar jikina tashi lokaci guda, naɗan ƙanƙame jikina ina haɗiye yawu daƙyar. Dai-dai saitin kunnena ya ɗora bakinsa yana magana a hankali kamar mai tsoron a jisa, “Ni ina naga wani wayo tunda gashi kinamin kuwa, a wajene Jay yake boss, amma a gaban Zinaran bawane, kece boss ɗin. buɗe idonki kiga wani abu”. Sosai maganarsa ta nema fasan kai, ashe mutumnan haka yake yana magana raɗam abinsa, amma yayta mana mazurai a office. Janye hanayen nawa nayi daga kan fuska a hankali harna kaisu ƙasa sannan na buɗe idanuna dake rufe. Ina buɗewa yana ɗaura laɓɓansa akan nawa. Na zaro idanu sosai dan ba haka na zataba. Shima idanun nasa dake cikin nawa yaɗan zaro yana cigaba da abinda yakeyi.
       Nasan banida ƙarfin dazan ƙwace, kuma ma nayi alƙawarin insha ALLAH bazan taɓa zama mai bijirewa a garesaba a komai da zaizo min dashi inhar bai taka dokar ALLAH ba. Ballantana a yanzu da nake hango tsagwaron damuwa akan fuskarsa, dannewa kawai yake dankar na fahimta. Mun kwashi tsahon mintuna biyar ahaka kafin ya barni, ya rungumeni muna sauke ajiyar zuciya a tare, ya sumbaci kuncina da wuyana, acan ƙasan maƙoshi yace, “Idan nace tadaban ina nufin keɗin tadabance har ƙasan ruhina Miemaa, a kwana biyu kacal da mukai dake na fahimci ƙyawawan abubuwa masu yawa daga gareki, inason mace mai juriya da biyayya akan abu koda bai mata ba, inason mace mai tsafta da ƙamshi, inason mace mai kawaici, kunyarki tana a farkon abinda ke ƙara miki daraja da girma, inason mace mai aji, mai addini, mai kamun kai, na tsani ballagazar mace mai rawar kai, da ace ƴammata da yawa zasu zama irinki da sun zama masu darajar daraja bisa daraja a wajen maza......” ya ɗagoni daga ƙirjinsa, muna haɗa idanun nai azamar maida kaina a ƙirjin nasa.
       “Ka daina huramin kai da yawa irin haka, yanda kake lissafin nan bankai haka ba, ni macece mai rauni, maison kulawa, waɗanan makaman suna saurin sakani bama mutum yarda, ada kallon bahagon mutum nima nake maka, wanda ba damu da damuwar kowaba sai abinda ya shafesa, amma a tsakanin jiya da yau na kula kai adaline mai sauƙi ga iyalanka, ka yafemin akan gurɓataccen tunanina, idan nace kai na dabanne ko a cikin mazan ina nufin nadaban a cikin miliyoyi, ba dan kafi sauran maza bane dan dukiya, ba dan kafi sauran maza bane dan ƙyau, ba dan kafi sauran maza bane dan darajar da ALLAH ya baka, kafi sauran mazan dan kai ɗin mai ƙyaƙyƙyawar ZUCIYA ne”. Na ƙare maganar da ɗora yatsana akan saitin zuciyarsa ina hawaye”.
        Bilkisu ko duniya zatace ƙarya nake saina faɗa, keɗin tadabance ko acikin nadaban ɗin kinzo da banbanci mai tazarar nisa. 
        “Karfa kasa mata sumin bugun kayan wanki”. Ɗagoni ya sakeyi yana murmushi, “Su sun isa ko kallon banza ga matar Jay ma”. Dariya muka ƙyalƙyale da ita a tare saboda yanda yay da fuska kicin-kicin kamar mai shirin shiga filin daga. Na yunƙura zan sauka daga jikinsa ya sake riƙeni. Naɗan marairaice masa batare da nabari mun haɗa idanu ba, “Yanzufa za'a kira sallar isha'i, ga abincin zai huce kuma”. Siririyar ajiyar zuciya ya sauke yana sakina, “Idan bakiso na fita akwai sharaɗi”. Kallonsa nai alamar ina sauratensa. tattausan hannunsa ya ɗaura akan haɓata ya matso da fuskata gab da tashi. “Idan har bakiso na fita sai dai ki ciyar dani da hannun nan naki, inba hakaba bazanci abincin nanba, kuma saina fita, kuma yunwa nakeji, kuma nagaji barci nakeji”. Ƙoƙarin juyar da fuskata nayi dan kunya da dariyar dake tahomin dan a narke yay maganar, amma ya hanani damar hakan, saima wani sake narke fuska da yayi irin na (Aji tausayina ɗinnan😔).
          Da sauri na jinjina masa kai danya barni na tashi nidai, zuciyata sai wani zallo take cikin ƙirjina tamkar zata fito, ga kunya kamar ƙasa ta buɗe na shige ciki, dan kusani ALLAH ba ƙaramar dauriya nakeyiba yasin.
      Ɗauke hannunsa yay ya gyara zamansa, hakan ya bani damar tashi tsaye, kujerar kusa da shi ya zaunar dani da juya kujerar yanda zanyi facing ɗinsa sosai. Ya zanyi, nina taroma kaina match ɗinan ai. Abincin na fara basa idanuna a ƙasa ban yarda na kallesa ba, amma shi inajin yanda idanunsa kemin yawo a zahiri da baɗini na, koda naɗan saci kallonsa sai muka haɗa idanu. Saurin maidasu nai ƙasa, daga haka ban sake ɗagowarba harna tabbatar ya ƙoshi. Ina murnar an gama zan tashi ya riƙe hannuna, kallonsa nai ya ɗagan gira, “Malama saura ke dan baza'amin ɗuraba ni kaɗai”. Dukda da gaske yunwar nakeji saina ɗan ɓata fuska nace, “Nifa na ƙoshi”. “Idan na yarda kenan”. Yay maganar yana ɗebo abincin ya kai bakina. Dole nima na haƙura na karɓa, yana bani yana addabata da kallo, hakan yasa duk naji na takura matuƙa. Sai da ya tabbatar na ƙoshi sannan ya barni.
          Naɗan kallesa ina tattare kayan ganin bai tashiba, kuma salla akeyi. Nace “Sallafa akeyi”. “Kin karyamin alwalata ai?”. Yanda yay maganarne ya sakani barin wajen da sauri na nufi kitchen. Bayan na kammala ɗauraye kayan na fito, ban iskesaba ya tashi, ɗakina na nufa nima domin gabatar da sallar isha'i.11
STORY CONTINUES BELOW

            Sai da nai wanka na saka doguwar riga mara nauyi sannan na fito falon dan banji motsinsa ba, zaune na iskesa cikin kujera yana waya, ga takardu ya baza saman centre table. ‘Agogo sarkin aiki kenan’ na faɗa a zuciyata ina ƙarasawa. Kitchen na wuce domin ɗakko masa ko ruwa ne. Inaji a jikina kallona yake amma ban juyaba. Harna dawo ɗauke da ruwa da lemo bai gama wayarba, naja ƙaramin copy table na ajiye tiren sannan na ɗago na kallesa, ganin ni yake kallo na ɗauke kaina, “Wanne zan zuba?”. Maimakon ya bani amsa sai ya amshi kofin ya ajiye ya kamo hannuna, zaunar dani yayi a gefensa tare da kwantar da kaina a kafaɗarsa ya cigaba da wayarsa.
        Bai jimaba sukai sallama ya ajiye yana ɗan guntun tsaki, ɗago kaina nayi na kallesa, kafinma na tambayesa yacemin, “Inaga yarinyarnan zan taka mata birki, iskancinta sake gawurta yakeyi, aikin nan kusan sati ɗaya kenan na batashi amma sai yawo takemin da hankali”. Tsaf na fahimci da Rose yake, dan naji muryarta ta cikin wayar, amma sai nai kamar ban fahimtaba nace, “Wacece?”. Tsakin ya kuma ja da ɗaukar wata takarda yana dubawa, harma na fidda rai da samun amsa sannan yace, “Rose” a taƙaice. Ƙin cewa komai nayi dan naga kamar ya hau sama.  Sai da ya gama shan ƙamshinsa niko nai kamarma na manta da shi a falon sannan ya juyo ya fara sakani wani aikin muka cigaba dayi tare, sai kusan goma da rabi sannan muka kammala, munayi yanamin bayani akan abinda suka tattauna yau da yaje office, da yanda suka tsara yanda abubuwan zasu kasance, tsarin yayimin, nakuma ƙara da shawarata dana fuskanci yaji daɗinta sosai.1

________________________________

              Su Abdul-raheem kuwa suna isa masarauta clinic aka wuce da Anuwar, likitan da yay aiki da rana ma har yana shirin tashine na dare kuma zaizo ƙarfe tara, dole ya dakata, taimakon gaggawa ya shiga bashi, cikin amincin ALLAH ba'a wani ɗauki lokaci ba numfashinsa ya dawo dai-dai. Hannun Abdur-raham dake kusa dashi ya riƙe yana hawaye, “Abdull  kamarmu ɗaya fa da shi, komaifa iri ɗayane, Wlhy ina cikin ruɗani Abdull, ko ku baƙwa irin wannan mugun kamar dasu Abdul-Raheem ai, inason ku maidani wajensa naji wanene shi? Idan kuma kun sani ku faɗamin Please, karkuce na rasa hankalina wlhy a rikice nake, jinake zuciyata na wani irin tsitstsinkewar da bantaɓa jin tayi ba.....”
     Abdur-raham bai samu damar bama Anuwar amsaba aka sanar da zuwan gimbiya. Kanta tsaye kan Anuwar tayi, tashi Abdur-raham yayi ya bata wajen zama, ta zauna tanama Anuwar sannu. Hawaye na shatata a kumatunsa yace, “Ummu yau naga mai kama dani kama mai ban al'ajabi da saka zukata ruɗani”. Murmushi Ummu tai masa cikin sigar lallashi tace, “Nasan da hakan Anuwar....” “Kin sani? Kenan kema kinsan shi? Kuma kinsan muna kama Ummu?”. Kanta ta jinjina masa tana sake faɗaɗa murmushinta, “Anuwar muma kamanninku ba ƙaramin sakamu a ruɗani sukai ba alokacin da muka gansa, hakanne ya saka muka tura Bilkisu wajenku, muka kuma ƙirƙiri hanyar da zakuzo ƙasarnan danmu sake tabbatarwa...”. “Ummu kin sake sakani a duhu wlhy”. “Zaka fita insha ALLAH Anuwar, amma lokacin hakan baiyi ba. abinda dai nakeso shine ka kwantarmin da hankalinka kaji, komai zai warware fiyema da abinda muke hasashe”. “To Ummu, amma inason na sake ganinsa dan ALLAH”. “Eh to banƙi ta takaban ba, amma ina ganin mubarshi basai ka koma ba, hakan zai saka ya sake zaƙuwa da ganinka kaima, dan inason ku wuce saudia goben idan ALLAH ya kaimu, lokacin da zai biyo sawunku nan ku kuma kun wuce, hakan zaisa yaso zuwa saudia ɗin, mukuma dama wannan damar muke buƙata ai”. Kansa kawai ya iya ɗaga mata danshi ta sake dulmiyasa a ruɗani, amma sai yay shiru bai sake tambayar komaiba. A take ma Doctor ya shigo ya bashi sallama suka tafi sashensu Abdul-Raheem.
           A wannan dare inhar Anuwar yayi barci to ragaggene, gashi Ummu ta gargaɗesa karya kira Umm-Anum balle sukai ga tunanin sanar mata wani abun, kuma koda komawa sukai karsu sanar mata komai har sai Jay yaje saudia da kansa.
       Washe gari jirgin safe suka bi shi da Anum cike da tsarabar biki daga Ummu, daka kallesu kasan basa son tafiyar dan ransu duk a cinkushe yake musamman ma Anuwar, har jiyake kamar ya zauna yayta kuka, sam bayason tafiya bai sake ganin Jawaad ba, baiji wani abu daga garesaba kuma.

STORY CONTINUES BELOW

_________________________________

                Ɓangaren Shahudah kam an sallamota itama sun dawo gida, taji sauƙi amma dukta rame ta ƙara wani irin haske maiban tsoro kamar wadda bata da jini a jiki, gashi yanzu ko yawan magana batayi sai dai ka ganta tayi zugum kamar wadda abin duniya ya dama. Koda yake ya dametan, dan Shahudah tanama Jay so mai tsananin gaske, sai dai tanaji a ranta bazata taɓa iya shearing ɗinsa da kowacce maceba ballema Bilkisu ƙasƙantacciya da tazo ƙarƙashin inuwarsu cin arziƙi. Har yanzu zatonsu na akan bilkisu asiri taima Jay ya aureta wai.
        Shi Dad harya bar ƙasar ma yau kwana biyu kenan, dan wani business ne na gaggawa yace ya taso masa, ko sallama saita waya yayma Momy ma, da yake ta rigada ta saba da irin wannan halin nasan sam sai bata damuba bakuma ta kawo komai a ranta ba.5

_____________________________

              Koda na kammala shirin barcina ban nema inda ya keba nai kwanciyata a ɗakina, har barci ya fara figata naji shigowarsa ɗakin, banko motsaba balle yay tunanin idanuna biyuma, gadon ya hawo yana faɗin “Wannan amaryar dai matsoraciya ce, nasan idanunki biyu ai”. Guntun murmushi nayi kawai batare dana motsa ɗinba. Mannani da yay da jikinsa ya sakamu sauke ajiyar zuciya a tare, ya busomin numfashi a saman wuyana zuwa kunne yana sake ƙanƙameni. “Kin fasa jin labarin kenan?”. Da sauri na girgiza kai, “Naga kamar ka gaji ne shiyyasa nai shiru, amma cike dake da zaƙuwa wlhy”. Murmushi ya saki mai sanyi yana matsa yatsun hannuna daya riƙe, “To aike miskilancinki bai bari asan kinason abu”. Sosai maganarsa taso bani dariya, amma saina dake nai murmushi kawai, wai ni yake kira miskila, ai shinema ya dace da wannan sunan bawai niba. Yanzunma bance komaiba ina dai saurarensa, saida ya gama jan ajinsa da shan ƙamshi sannan ya juyo dani muna fuskantar juna, idanunsa a kaina yace, “Idan kuma na fara kikace zakimin barci saina ƙarya ƙasusuwanki”. A zuciyata nace, ‘Ai tun daren jiya ka kakkarya ƙasusuwan nawa da sauyamin kamanni Alhaji’. Dariyarsa da naji ciki-ciki ya sakani fahimtar maganar zuci ce ta fito fili. Baya nai zan juya yay saurin riƙoni ya maidoni, dole na haƙura tunda dai nariga nayi katoɓarar.
      Yaɗanja hancina kaɗan, “Wato tun daren jiya na sauya miki kamanni da karya ƙasusuwan ki? To a yafeni bazan sakeba Zinaraina”.
         Bance masa komaiba dan naji kunya. Ya fara shafa bayana a hakali da gyara kwanciya, “Jawaad Abdul-Azez Yuseef ɗane da ga. zuri'ar Alhaji Yuseef Tafida. Alhaji Yusif talaka ne mai rufin asirin ALLAH, domin kuwa manomine kuma makiyayi, duk dai a birni yake rayuwarsa da iyalansa to dukkan wani sabgoginsa na ƙauyensu, acan yake nomansa da kiwo, hakan yasa hankalinsa rabuwa biyu, harma zamansa a ƙauyensu ya so ya rinjayi zaman birnin. Matan Alhaji Yusif uku ne cif, kuma kowacce a cikinsu ALLAH ya azurtata da haihuwa, matarsa ta farko hajiya Atika yaranta shida huɗu duk maza biyu mata, sai ta biyu badiyya yaranta huɗu itama, mata uku namiji ɗaya, sai amarya Rahina ke da uku maza biyu mace ɗaya...............
  
           Tunda ya fara nake hawaye, sanda ya dire ƙarshe tuni kuka yaci ƙarfina har ina shashasha, ya jani jikinsa ya rungume yana lallashi, “To kuka ya isa haka mana uhmyim, haka rayuwa take, ganin wani a cikin ni'imar rayuwa bashine yake nufi ya samu komai ba, kowacce irin rayuwa zaki samu akwai rauni da jarawa a cikinta, da yawan dariyar da mutane keyi idanda zaki zauna dasu kiji suwayesu zaki fahimci iyakarta haƙori ne kawai, Haƙuri rahamane, duk wanda yay haƙuri baya yin asara, idan kayi haƙuri kaga babu riba a cikinsa to ɗan kaɗan kayi, sannan ka binciki kanka maybe kana zaluntar waninka ne, dan bakowacce jarabawa bace ga ɗan adam take zama daga ƙaddararsa, wasu mutanen sune da kansu suke shuka sharri sai kiga suna ta naɗar sakamakonsa da sharrika suma. Duk sanda na samu wani bakin zare na binciken mahaifiyata koxan dace da samunta sai kaina ya kulle Miemaa, kiga hankalina ma da tunanina sun gushe daga wajen, bansan miyasa hakanba?”.
           “Al'amarinta kamar akwai sihiri a ciki boss”.
     Saurin ɗagoni yay daga jikinsa, yace, “Miyasa kikace haka?”. Hawayena na share ina ɗan jan hanci kaɗan, “Duk musulmin ƙwarai ya yarda akwai ƙaddarar mutuwa, kuma wajibice ga kowa babu fashi, a ganina rasuwar Abba bazata gusarma Mamah hankali ba, koda zata shiga ruɗani bazai yuwu ace na gushewar hankaliba har akai gayin haukan da za'a bar gida ma gaba ɗaya. Matar dana zauna da ita a saudia bansan asalin sunanta ba, amma haka kawai tun ganina da ita na farko naji ƙaunarta mai tsanani ta shigeni har nakanyi mamaki, itace mahaifiyar Anum da Anuwar, aɗan zamana da ita na fahimci abubuwa da yawa daga gareta waɗanda suka sakani a ruɗani,  bazan yanke hukunci akan gaibu ba, dan ALLAH shi kaɗaine masanin gaibu, saidai ga shawara”.
        “Wace irin shawara?”. “Mizai hana muje Saudia a zuwan kamar na kai mata kai ku gaisa, dan dama ta roƙeni akan wataran na kai mata kai, haka kawai a ranta takejin son ganin mij.......”
         “Ƙarasa mana to”.
Fuskata na ɓoye cikin ƙirjinsa ina murmushi. Murmushin shima na jiyo yanayi, ya tura hannunsa cikin sumata yana yamutsawa kamar maimin susu. Tsawon lokaci muka ɗauka a haka babu wanda ya sake magana, daɗin yanda yakemin a cikin kai ya sakani fara lumshe idanun barci, cikin mintuna ƙalilan kuwa barcin yay gaba dani.5

STORY CONTINUES BELOW

               Tunda Bilkisu tai barci sai idanun Jawaad suka sake bushewa, kalamanta kawai yakema fashin baƙi dalla-dalla, daga ƙarshema zameta yay daga jikinsa a hankali ya kwantar, bayi ya shiga ya ɗauro alwala yazo yayta nafilfili, ya jima yana miƙama ALLAH kukansa cikin ƙanƙan da kai da ƙasƙantarwa, harda hawayensa shaɓe-shaɓe, fatansa ALLAH ya buɗa masa haske akan al'amarin nan ya fahimci sirrin dake ɓoye, duhun dake lulluɓe da shi da matarsa ALLAH ya yaye musu shi ya zama haske. Bai kwantaba sai kusan ƙarfe uku. Yana kwanciya barcin yay gaba dashi dan idanunsa dama har zafi suke saboda barcin.

          Kiran sallar asuba da aka ƙwalane ya sakashi farkawa a ɗan firgice hannunsa dafe da kansa, sai da ya jero addu'ar tashi barci kafin ya iya furta Aunty Mah-mah, yau kam ya sake mafarkinsa daya saba na ƙaddarar jini a cikin jini, sai dai yau ya farka bai manta fuskar matar dake masa kalaminba, Gwaggonsa ce Rahma wadda suke kira da Aunty Mah-mah. Juyawa yay ya kalli Bilkisu data cure waje guda cikin bargo ta rufe har rabin fuskarta. Yaɗan lumshe idanu ya buɗe yana sauke ajiyar zuciya, tsahon lokaci yana kallon Bilkisun da nazarin abubuwa masu yawa har aka fara kiraye-kirayen sallar shiga masallaci. Nannauyan numfashi ya sauke sannan ya sauka a kan gadon da ƙyar dan jikinsa ko ina ciwo yake masa alamar barcin bai ishasa ba.
      Alwala yayo, ya fito a gaggauce ya tada Bilkisu sannan ya fice masallaci.

        Sukuku na tashi da ƙyar nai alwala, raina cike da wasuwasi akan mafarkin da nayi maiban mamaki da al'ajabi, gashi komai dalla-dalla a zuciyata ban manceba kamar azahiri komai ya farumin ba'a mafarkiba. Bayan na idan da sallar ina cikin yin azkar ya dawo, baimin maganaba ya cire jallabiyar jikinsa kawai ya haye gadon ya kwanta daga shi sai boxer. Kallo kawai na iya binsa dashi haryaja bargo ya lulluɓa sannan ya miƙomin hannu alamar nazo. Janye idanuna nai daga garesa ina faɗin, “Ban kammala azkar ba fa”. Baice komaiba ya maida hannunsa a bargon ya lumshe idanu.
      Lokacin dana kammala azkar haryay barci, dan saukar numfashinsa kawai nake jiyowa a hankali. Lallaɓawa nai na fice daga ɗakin danni idanun nawama sun bushe banajin barcin kuma. Ɗakinsa na nufa na fara gyarowa dukda babu wani datti tunda bawai zama akeba, kuma yau ba'a nan muka kwanaba, daga nan na dawo falonsa sai babban falo kuma har zuwa nawa falon tunda dama ƙananane su, turaren wuta da air fresheners na baza ko ina, nan take gidan ya ɗau ƙamshi. Jina nai tiɓis da gajiya, nifa dama can na tsani mopping yasin, babu abinda nake kallo mai wahala a aikin gida irin mopping da wanke-wanke, na tsani wanke-wanke fiye da zato, to amma yaya na iya haka zankeyi dole, idan wahalarce dama mun riga mun saba da ita ai tun ƙuruciya, to yanzukam data kasance dole kuma mai muhimmanci a gareni ai dole na zage nayi, sai dai harna fara tausayin kaina idan na koma aiki, lallai zanci ƙaniyata da ayyuka.
      Agogo na kalla ƙarfe tara harda wasu mintuna, cikin jan jiki na nufi kitchen, ina tsaye da tunanin miya dace nayi mai sauƙi da bazan sake jigata kainaba naji ana knocking ƙofar falo. Fita nai kasancewar jikina da hijjab, na buɗe ƙofar. Drivern gidan Ummah ne ɗauke da kwando. Ya gaisheni sannan ya miƙamin basket ɗin, amsa nai da masa godiya, nakumace ya miƙa mana godiyarmu ga Ummah kafin muyi kiranta.
     Sauƙi dana samu bazanyi girkiba kenan, sai kawai na shirya komai a D/table ɗin. Nagama zubama maigadi abinci a kularsa ya fito. Ɗagowa nai na kalli sashen da nakejin motsi, yana daga tsaye jikin glass ɗin daya raba falona da babban falon hannayensa duka a harɗe saman ƙirji. “Barka da tashi”. Na faɗa kaina a ƙasa ina ɗan murmushi.
       Baice dani komaiba ya tako zuwa Dining ɗin yana wani yamutse fuska na alamun bai jima a tashi barci ba. Hannuna da nake rufe kulan ya kamo cikin nashi, cikin yanayin muryan wanda ya tsashi a barci yace, “Haka ake gaida miji dama hajjaju?”. Ɗagowa nai naɗan kallesa na ɗauke idanuna, “Nifa idan aka cigaba da takalata faɗa zan maida murtani”. Yay maganar da ɗora bakinsa saman goshina ya sumbata sannan ya ɗago haɓata ya haɗe ba....🙄😏2

            Da ƙyar na samu ya barni mukai zaman yin breakfast, a hakanma ba tsira naiba dan kallonsa kawai ya isheni. Muna tsaka dacin abincin kira ya shigo wayarsa, ɗauka yayi, yanda naji yana amsawa da girmamawa ya sakani fahimtar da Umman su Nabeelah yake. Har muka kammala cin abincin basu kammalaba, na fahimci maganar tasu duk akan Anuwar ne, Nabeelah takai bayani kenan, nidai kwashe kayan nai na nufi kitchen domin wankewa, shi kuma ya ɗauka abincin maigadi ya fita.
          Na kammala wanke-wanken na nufi ɗakina zanyi wanka, ina gama cire kaya na ɗaura towel sai gashi ya shigo tsulum babu zato. Kunya naji kamar in nutse, shiko ya wani fuske abinsa saima jallabiyar sa shima ya cire, sama kawai naji anyi dani, hakan ya sakani tsorata nai saurin zagaye hannayena a wuyansa. Ƙaramar dariya yayi da ranƙwafowa ya sumbaci gashina yana faɗin, “Ki rage tsoro yarinyarnan wlhy”.
      Ban iya bashi amsaba muka shige bathroom. tunda na fahimci yana nufin muyi wanka tare na shiga zare idanu, ‘kutt inani ina wanka da sangamemen ƙaton nan’. Cikin marairaicewa na shiga roƙonsa akan ya barni na fita idan ya gama sai nayi nima.
        Towel ɗin jikina ya sunce yana faɗin, “Barma wahal da kanki Zinaran”. Saurin juya masa baya nai ina rumtse idanu da ƙarfi, sai kawai jinsa nai ya sakani jikinsa da saukar ruwa a kanmu lokaci guda. Sassanyar ajiyar zuciya na saki.
       Duk wani noƙe-noƙena akan wankan nan dole na sake mukai wankan nan tare yanda ya keso, dan hanyoyin da ya ringabi dani bazasu yuwu na iya cigaba da bijirewanba. duk yanda zan fassara muku dodon nan nawa da wahala ku yarda dani, dan haka bara kawai nai zipping🤐 bakina kamar zaifi sauƙi.
           Man ma tare muka shafa, yaymin drying kaina da yake wuta ta kwana har yanzu akwai, tsaf ya gyaramin shi tamkar wani mai'aikacin gidan saloon. Kayan sawama shine ya zaɓamin zani da riga na wani lass mara nauyi, sai dai ya haɗu harma ya gaji da haɗuwar, zaunar dani yay wai zai ɗauran ɗan kwali, nikam yau naga idi an maidani kamar wata doll. Tunda aka fara ɗaura ɗan kwalin nake gumtse dariya, sai kace irin yadikkon nan na cikin ruga, kasa jurewa nai na ƙyalƙyale da dariya, ya dunguremin kai shima yanayi da faɗin, “Ai dai nayi ƙoƙari”.
       Nace, “To dama waye zaice bakayiba ya kwana a call”. “Ashe kin gane karatun ta wajena, muje a ramawa kura aniyarta nima a shiryani yanda Ummah zatazo ta tabbatar ɗanta ya gama dacewa a duniya sai fatan lahira”.
       Murmushi nayi ina rufe fuska. sai kuma na buɗe da tambayarsa zuwa zasuyi?. Kansa ya ɗagamin, “Nabeelah takai gulma ta kasa haƙuri sai tazo taji bayani, dama kuma akwai wani abun a ƙasa, zasuzo itada Ummah ƙarama”. Daɗi naji ya sake kamani dan ƙaunarsu nake bayin ALLAHn nan, yaja hannuna muka tafi ɗakinsa, tsareni yay na zaɓo masa kayan shima, ya kuma rantse nice zan shiryashi babu ɗaga ƙafa. Jama'a yau nasha kunya fiye da hasashe, shi dai wannan boss ɗin ku gansa kawai ku barsa inda yake, sanin wanene shi saini matarsa😉 (karfa aimin snatching ƴammatan Bilyn Abdull😝. Lol😂).
               Tsaf na shirya abuna ina ƙuƙƙumshe fuska na feshesa da kalolin turarensa masu daɗin ƙamshi, kiransa da akai a wayane ya bani damar gudowa nawa ɗakin na gyara nai zaman ɗaura ɗan kwali, sai da na tabbatar nayi dai-dai buƙatar mai kallo sannan na ƙara turare na fito ina tunanin abinda zan girkama baƙina da rana.
      Na shiga kitchen ɗin ina nazari da duba abinda muke dashi ya shigo. “Ki rubuta abinda zaki buƙata ga Sadiq nan yazo zaiyo cefane”. Kaina na jinjina masa.
            Ina gama rubuta abinda zan buƙata na dawo kitchen ɗin na fara ɗaura abinda ke a hannu, a mamakina sai gani nai shima ya shigo, riga ya ɗauka ya miƙamin wai na ɗaura masa. Na ɗan waro idanu waje da faɗin, “Namiji da girki?”. Ido ɗaya ya kannemin da faɗin, “Bakiso nai koyi da ƙyawawan halayen MANZON ALLAH (S.A.W)? Miemaa insha ALLAH zaki sami mijinki a cikin gidanki fiye da yanda kike zato, zan riritaki na shagwaɓaki na gatantaki, idan saɓani ya shigo a tsakaninmu muyi haƙuri da juna mu daure wajen yima juna uzuri da ƙyaƙyƙyawan zato, bance dake niɗin na daban bane, bankuma miki alƙawarin zama na daban ba, sai dai insha ALLAH zan kasance miki mai sauƙi da rangwame kamar yanda nake fata daga gareki, randa kuma zan ƙara aure ki kwantarmin da hankalinki kamar kinyi baƙo ya mutu”. Harara na zuba masa batare da nayi zatoba ina mai zumɓura baki da juya masa baya. Ya ƙyalƙyale da dariya yana rungumoni jikinsa, “Oh gulmammiyar matata ashe tana sona take basarwa, garama ki shirya yarinya mata huɗu zanyi gangariya”. Ƙin tanka masa nayi, dan jinai zuciyata ta kumbura, har nai mamaki dan bansan dalilin hakanba.
      Bai fasa tsokanata ba har Sadiq ya kawo cefanen muka shiga yin aikin girkin ni da shi, yanda yake komai a nutse ya sani fahimtar ya iya girki shima, ban tambayesa ba dai har muka kammala komai, sai dai lokaci-lokaci yakan fita Dining ya amsa wayarsa daya bari a can sai ya dawo................✍8

😵kuttt addu'arkufa ta cini da yawa words 4412😫🤒
22
         Barka da juma'a😍😍😘😘.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

9Page 46

..................Tsaf muka kammala komai tare da shi, kiran sallar zuhur da akayine ya sakashi fita ya barni ina ƙarasa sauran abubuwan. Nima a gurguje na ƙarasa komai na fito yin sallar. Na idar kenan ina addu'a naji ana sallama, kafin na miƙe na fita ganin wanene Nabeelah ta shigo ɗakin.
Murmushi mukaima juna, ta ƙaraso ta rungumeni tana faɗin "Amarsu ta ango mai daɗin suna, bara na faɗa a hankali kar yauma nai suɓutar baki ya jini ya markaɗa". Dariya ta bani sosai, dan haka na shiga yi. "Hum ke dariyama abin ya baki, wlhy kaɗan daga aikinsa yamin casar gyaɗa indai yayanmu ne. Ina fata baya nan?". Toilet na nuna mata da ahannu ina faɗin, "Yana ciki kuwa". Sosai ta waro idanu waje da faɗin, "Na shiga Uku dan ALLAH da gaske kikeyi?". Yanda ta rikice ɗinne ya sakani sakeyin murmushi, na ajiye abin sallar dana linke, "Wai ke kaɗai kikazo ne?". "A'a ni da su Ummah ne fa, suna falo". Ban bata amsaba na fito batare dana cire hijjabin ba.
Tunda na fito suka zubamin idanu har abin ya bani kunya, na ƙarasa inda suke kaina a ƙasa, har ƙasa na durƙusa inai musu sannu da zuwa. Cikin fara'a suka amsamin har suna haɗa baki wajan faɗin nazo garesu. A kunyace na kuma tashi naje gabansu dab zan sake tsugunnawa Ummah babba ta riƙoni, tsakkiyarsu ta zaunar dani tare da rungumeni jikinta tana sauke wani nannauyan numfashi daya bani mamaki matuƙar gaya, itama Ummah ƙarama saita riƙo hannuna da faɗin, "ALLAH yaymiki albarka kinji, lallai ƙaunar da muke miki da gaske ta wuce ta surukuta kawai". Ban fahimci zancen nataba nidai, na ɗago daɗan satar kallon Ummah babba da naga kamar tana hawaye. Kaina na maida a ƙasa nace, "Bara na kawo muku ruwa".
Ummah ƙarama da itama na ga tana share hawayen tace, "Bara mu fara yin salla ɗiyata, dan ta riskemu a hanya saboda go-slow ɗin garin nan da baya ƙarewa". Kaina na jinjina musu tare da miƙewa nai musu jagora har cikin ɗakina. Sai da na saka musu abin salla sannan na fito dan na basu waje suyi.
Kwance na iske Nabeelah na danna waya, na zauna kujerar dake kallonta, "K bazakiyi sallarba madam?". Wayar ta janye daga fuskarta tana tashi zaune, "Aini shehi yamin". Nace, "Okay to acigaba da gashi". Dariya ta sanya tana ƙoƙarin komawa ta kwanta, ni kuma na miƙe dan naje na shirya abincin a dining, harna miƙe na dawo na sake zama. "Nabeelah niko kinga abinda na gani kuwa? Saifa naga kamar su Ummah kuka sukai?". Kallona tai tana murmushi, "Nima dai ba komai na saniba akai, amma tabbas akwai wani abu da suka sani game dake wanda na lura shine dalilin kukan nasu". Babu shiri na koma na zauna a kujerar sosai ina faɗin, "Game dani kuma Nabeelah?". "Lah bafa wani abu mara ƙyau bane naga kamar kin ruɗe". Ajiyar zuciya naɗan sauke duk da bawai na gamsu da amsar tata bane, na sake miƙewa na nufi kitchen. Abincin dana shirya a kuloli na fara fiddowa, ganin hakan Nabeelah ta taso ta tayani muka shirya komai. Falon muka sake dawowa muka zauna, Nabeelah ta fara zubamin surutu, nidai nawa murmushi ne, wani gurin kuma nakan jinjina wautarta sosai. zamanmu baifi da mintuna goma ba su Ummah suka fito, miƙewa nai ina musu sannu. Fuskokinsu ɗauke da murmushi suka amsamin suna zama. Ina fara zuba musu ruwan dana ajiye ya shigo falon da sallama.
Tsokanarsa suka shigayi da faɗin ga ango ga ango. Yay murmushi mai sauti cike da girmamawa yace, "Sannunku da zuwa Ummahs, har ina tunanin kiranku a waya sai kuma na duba naga nama bar wayar a gida".
Ummah ƙarama tace, "Wlhy Go-slow ne ya riƙemu Son, amma da tuni mun iso ai". Ledar hannunsa na amsa ina masa sannu murya ƙasa-ƙasa, ban jira amsarsaba ko kallonsa nabar wajen.+

Jay daya ɗan bita da kallo ya zauna yana amsa gaisuwar da Nabeelah ke masa, kafin ya gaida iyayen nasa da keta tsokanarsa yayi ƙiba a kwana uku kacal. Shidai murmushi kawai yake musu bai iya cewa komai.
Nabeelah data san halin kayanta kuwa tuni ta miƙe tabi bayan Bilkisu dake kitchen tana wanke fruits ɗin daya shigo dashi. Tare suka ƙarasa suka fito.

Koda nazo na sanar musu cewar ga abinci sai Ummah babba ta hau faɗa akan miyasa zan fara girki, ai sai nayi sati biyu sannan. Murmushi nidai nakeyi kawai kaina a ƙasa, shima dai banji yace wani abu ba. Sai da ta gama faɗanne sannan naji ya bata haƙuri da cewar, "Ummah karki damu ai gara tayi, dan bazai yuwu muyita wahal dake ba". Ummah tace, "Minene wani abin wahala anan, aida nasan zatai girkin dana kira nace karma ta fara".
Shidai ya lallaɓasu akan suzo suci abinci, daga baya saita cigaba da faɗan. Dariya Ummah ƙarama da Nabeelah sukayi jin furcinsa, nima dai saida na murmusa. Ni da Nabeelah muka zuzzuba musu abincin yanda kowa yake buƙata, Nabeelah ma ta zuba nata ta zauna, niko sai nai ƙoƙarin barin wajen, hannuna Ummah ta kamo ta zaunar dani a kujerar kusa da ita, "Maza zauna kici abinci, kina nufin mu kaɗai zakima wannan wahalar". Kaina a ƙasa nace, "Ummah ai na ƙoshi, in ALLAH ya kaimu anjima zanci". Bata saurareni ba ta hau ɗiba da cokalinta ta fara bani, bazan iya mata musu ba, dan haka dole na ringa amsa a kunyace, Nabeelah nata mana dariya ƙasa-ƙasa dan tana tsoron yi yaci ƙaniyarta. Dana ɗago saina kamashi yana kallonmu, hakan yasa na ƙara takura sosai. Ummah bata barniba saida ta tabbatar cikina yayi ƙat da abincin nan, suma sukaci sosai suna santi da sakamin albarka da yaba ƙoƙari na.
Bayan mun kammala Nabeelah ta tayani gyara wajen, shi kuma ya zagaya dasu lungu da saƙo na gidan, inajin yanda suketa yaba gidan da jinjina halin girma irin nasu Ummu, a yanda suka hidimtamin babu dangin iya babu na baba sun cancanci yabawa mai girman gaske da ƙyaƙyƙyawar addu'a.
STORY CONTINUES BELOW

A falon Jawaad su Umma suka yada zango, inda suka shiga tattaunawa akan batun Bilkisu da kuma kamannin Anuwar dana Jay. su Ummah sun dage akan cikin satin nan zasuje saudia domin ganin Umm-Anum, dan sunce lallai sunaji a jikinsu kamaninsa da Anuwar yafi ƙarfin kamanni, sunce zasu sanarma Alhaji babba dan su ɗunguma gaba ɗaya su tafi.
Murmushi Jay yay yana gyara zama da fuskantar iyayen nasa. "Ummah banƙi ta takuba kam, amma sai nake ganin kamar dai kubari na fara zuwa tukunna, dan kunga bamu da tabbas hasashe kawai mukeyi, shima baba karmu sanar masa tukunna, yana a shekarun da baya buƙatar irin wannan ruɗanin a halin yanzun, yanzu haka da kunga yanda hankalinsa ke a tashe akan zancen Miemaa da zakusha mamaki, yana dannewane kawai, to kunga abin zai haɗe masa biyu. Insha ALLAH zanje masarauta nima anjima domin sakejin bayani dangane dasu yaran, duk da dai Miemaa tamin bayanin abubuwa da dama game da mamansun".
Duk sun gamsu da jawabinsa, sun kuma yi masa addu'ar fatan nasara, amma ita Ummah babba ma tariga ta tabbatar musu da tanaji a ranta kamanin nan bazasu zama kamanni na haka nanba, ita wlhy jima take kamar tai tsuntsuwa ta ganta a saudia. Shi dai Jay ya cigaba da lallaɓasu dan yanason abi komai a sannu kodan maganar Bilkisu data sanar masa tana zargin akwai sihiri a cikin al'amarin.
Sun cigaba da tattanawa har zuwa la'asar, Jay ya fita salla su kuma sukai tasu a gida. Ƙyaututtukan da duk suka kawoma Bilkisu duk suka bata, kafin suyi shirin komawa.
Godiya naita musu dukda bansan mike a cikiba har sai da Ummah tace ya isa haka nan, da ya dawo daga salla shima na sanar masa, shima dai godiyar yayi.
Har bakin mota nai musu rakkiya da bama fadila nima tsarabar dana haɗa musu ta turaren wuta da fruits ɗin da basu sha ba sai kajin dana gasa guda uku na naɗesu batare da shima ya sani ba. Sai da suka fice daga gidan sannan muka koma cikin gida. Hannuna ya kama ya zaunar dani a kusa da shi yana faɗin, "Sannu da ƙoƙari Miemaa, nagode sosai da yanda kika karrama ahalina". Murmushi nai masa, nace, "Nima ai ahalina ne yanzun, dan ƴan uwanka nawane, iyayena ne yazama dole a gareni na girmamasu, dan haka ka dainamin godiya dan ALLAH". Baice komaiba sai jawoni da yay na haye saman jikinsa, ya sauke siririyar ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa. luf na kwanta nima ina shaƙar ƙamshinsa, gashi daman barci nakeji sosai, ai tuni na fara lumshe idanu.
Ɗagoni yay yana kallon fuskata, ya saka hannunsa ya shafi kumatuna, "Badai barciba ko?". Buɗe idanun nawa nayi kaɗan na kallesa, ganin ni yake kallo saina maidasu ƙasa da yunƙurin tashi daga jikin nasa, "ALLAH barci nakeji". Zamansa ya gyara sosai yana kallona, sai dai yaƙi cewa komai, jinai idanun nasa sunmin yawa, dan haka nace, "Ko zaka ƙara cin abinci ne". "Uhm, amma ba wancan ba" ya faɗa yana nuna Dining. Da mamaki na kallesa sosai, "To wanne? Ko wani za'a dafa maka?". Hannuna ya kamo ya matso dani jikinsa sosai, a hankali kamar baya son yin magana yace, "Zona faɗa miki wanda nake so". Yay maganar yana ɗaura kansa saman wuyana, yanda yake busan iskar numfashinsa a saman wuyan ya saka tsigar jikina tashi, na cije bakina da haɗiye yawu da ƙyar, abinda ya gwargwaɗa min a cikin kune ne ya sakani zabura naɗan kallesa, sai kawai na miƙe nabar wajen da ɗan gudu.
Lumshe idanu Jay yay yana wani sassanyan murmushi, yabi hanyar falonta da kallo yana sauke ajiyar zuciya, ganin idan ya cigaba da zama a gidan jikinsa zai cigaba da mutuwa sai ya miƙe, ɗakinsa ya shiga, mintuna kusan goma ya fito ya nufi nata.

Ina zaune a sofa ɗin dake ɗakin ina duba abinda su Ummah suka kawomin ya shigo, ban yarda mun haɗa idoba nace, "Yayanmu kaga abinda su Ummah suka kawomin". Muryarsa a sanyaye yace, "Kin gode, ALLAH ya saka da alkairi". Ɗagowa nai naɗan kallesa na janye idanuna. "Baka da lafiya ne?". "Mi kika gani?" ya faɗa yana ɗaukar agogonsa dake kan mirror na. "Naji muryarka a sanyaye ne".
Murmusa yayi ya miƙomin hannun da zaisa agogon, babu musu na fara ɗaura masa. Harma na fidda rai ga samun amsa nikam, sai da na kammala ɗaura masanne ya ranƙwafo tare da sumbatar laɓɓana, cikin ƙaramin sauti yace, "Bazaki ganeba Miemaa". Idanuna na ɗago na kallesa, ya ɗagemin gira ɗaya yana cije leɓensa na ƙasa. "Kimin addu'a zan fita". Duk da banason fitar haka na daure nai masa fatan alkairi da dawowa lafiya, sake ranƙwafowa yay ya sumbaci laɓɓana da cewa "Amin" sannan ya fice.
Na sauke ajiyar zuciya da tattare kayan na maidasu inda suke sannan na miƙe, gidan duk sai yamin babu daɗi, dan haka na saka silifas tare da hijjab na fito harabar gidan dan inɗan rage kaɗaici, na ɗan zazzagaya ina tsinkar flowers ɗin da aka ƙawata gidan dasu masu ƙamshi, sai gab da magriba na shige ciki, falonsa na nufa kai tsaye domin tunawa da kofunan dasu Ummah sukasha lemo ban kwasosu ba, na gama tattarewa zan fito idona ya sauka akan file daya ajiye a kan hannun kujera, ajiye kofunan nai na ɗaukesa da nufin kaimasa ɗaki dan nasan mantashi yay anan. Takardun dake ciki suka zubo ƙasa a mistake, 'Ya salam' na faɗa ina duƙawa na tattaro su, ido na tsirama ɗaya daga cikin takardar domin ganin sunan Dad ɓaro-ɓaro, mamaki yay matuƙar kamani, na koma na zauna a kujera ina dubawa daki-daki. Kai nane ya nema kullewa, daga gefe kuma zuciyata najin wani irin takaicinsa, waishi mutumin nan mi ya ke nufi da ƴan gidanmu ne? Na kula gaba ɗaya bayanan dake a file ɗin akan ƴan gidanne, sunan Dad, mom da yah Qaseem yafi na kowa fitowa ma, maidawa nai na dangwarar da file ɗin na ɗauka kofinan na fita ina ƙunƙuni, ko wankesu ban tsaya yiba na ajiyesu a kicin ɗin na fito. Ɗakina na shiga raina duk babu daɗi, Dad ya wuce duk yanda yake zato a gareni daga shi har zuri'arsa baki ɗaya, Dad yaymin abinda sauran dangina suka gaza yimin, Dad ya tallafi maraicina a lokacin da rayuwata ke walagigin ƙila wakala, ta sanadin gatan da Dad yay minne har shiɗin ya sameni ya aura, lokaci yayi da yakamata nasan komai dangane da aurenmu da shi da yanda akai na koma hannunsa ba Yah Qaseem ba, inason sanin ina Yah Qaseem yake ne shin? Miya faru ne ranar ɗaurin aurenmu har aka ɗauramin aure da boss?'. da wannan tunane-tunanen na shiga bayi, wanka nayo da alwala raina duk a dagule, na shafa mai sama-sama tare da zira siket da riga marasa nauyi a jikina waɗanda sam basu kamamin jiki ba. Hoda naɗan shafa kaɗan da lipsgloss na saka turare sannan na tada salla, bayan an idar ban tashi daga saman abin sallar ba na ɗauka Al-Qurani nahau karatu, har saida aka kira sallar isha'i sannan na tashi nayi har shafa'i da wutiri dan yanda nakejin idanuna na bauri nasan kwanciyar wuri zanyi yau.

STORY CONTINUES BELOW

Koda na fito saina shiga kicin na ɗauraye kofunan sannan nai zaman gyara masa fruit duk da raina a dagule yake, na shirya tambayoyi fal ina jiran ya dawo na shiga yi masa su. Nayi nisa a tunani har bansan ya shigo kicin ɗinba, ƙamshinsa da alamar mutum da najine ya sakani ɗagowa da sauri. Ajiyar zuciya naɗan sauke dan baƙaramin tsorata naiba da farko, nace, "Ni ALLAH kaban tsoro".
"Ai ke komai abin tsorone a wajenki daman" ya faɗa yana juyawa ya fita a kicin ɗin. Ɓata fuska nayi na cigaba da aikina, sai da na kammala tsaf na ɗoro akan tray tare da ruwa da lemo sannan na fito. Ganin baya babban falo saina nufi parlorn sa. Nanma baya nan, na ajiye tray ɗin na nema waje na zauna jiransa ya fito danna amayar da abinda ke a raina, duk da tsoron da nakeji kuwa. Kusan zaman mintuna talatin nayi sannan ya fito, ya canja kayansa zuwa wando da riga farare tas masu taushi alamar yayi wanka. Yanda ya kalleni na kula baiyi tunanin ganina a nanba, amma sai ya basar ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya kamar wani saraki. "Bani remote ɗin can". Miƙewa nai na ɗakko masa. Inata dai danne abinda ke raina dan son yin koyi da nasiha da dabarun da Umm-Anum ta koyamin. Sai da ya kunna television ɗin sannan yace, "Sun wuce".
Kallonsa nayi nace, "Su wanene?". Kamar bazai tankaba ya maida hankalinsa ga labaran, harma na fidda rai sai naji yace, "Daga masarauta nake". Duk da na fahimci waɗanda yake nufin sai nace, "Wai kana nufin su Anuwar?". Kansa kawai ya ɗagamin. Na fahimci ransa a jagule yake, amma duk da haka banji zan iya haƙuri ban masa maganar su Dad ba. Ruwan dana tsiyaya na miƙa masa, ya amsa tare da haɗewa da hannuna, ɗagowa nai mukaima juna kallon ido cikin ido, murya a sanyaye yace, "Jibi idan ALLAH ya kaimu zan wuce saudia". "Nidai dan ALLAH mu tafi tare, kuma ma ai ni ta sani ba kaiba". Karon farko datun shigowarsa naga yayi fra'a, ya ɗan murmusa da zare kofin daga hannuna ya kai bakinsa, sai da yasha ruwan sosai ya ajiye kofin sannan ya sake dubana, "Kinada kuɗin jirgine?". Da sauri nace, "Eh" cikin karsashi da ƙarfin gwiwa. Yace, "Yayi ƙyau hajjaju". Yay maganar da buɗe plate ɗin dana rufe fruit dana yayyanko a cikin bowl ɗin glass. Cokali mai yatsu dana haɗo da shi ya ɗauka ya fara sha hankalin kwance kamar nace nasane🙄😒.
Shiru falon yayi sai tv daketa subaɗi, saida ya sha kusan quarter sannan ya juyo ya kalleni, "Zo nan naji mike damunki ne?". Mamaki ya kamani, ya akai ya fahimta? Saurin gyara yanayina nai da cewa, "Babu abinda ke damuna sai barci". yaɗan tsuramin idanu sannan ya janye, "Tunda yau na fara saninki ko?. Taso nace". Tashi nai zuwa inda yake ina kumbura fuska, ya fisgoni da ƙarfi na faɗa saman cinyarsa, ƴar ƙara na saki wadda ni kaina nasan ta shagwaɓace, "Shiiii" ya faɗa yana saka kankana a baki, bakinsa ya ɗora kan nawa ya sakamin kankanar dake bakin nasa cikin nawa. Na yamutse fuska kaɗan a raina ina faɗin 'ƙazanta'. Ɗallar bakina da yay ya sakani sake ɓata fuska dan naji zafi, ya ɗage gira ɗaya da faɗin, "Nasan ai gulmata kikai a zuciyarki". Saida na shanye sannan nace, "Nidai nasan banyiba ai". Bai tanka minba ya cigaba da bani fruit ɗin shima yana sha, saida nace masa na ƙoshi sannan ya barni. Zameni yay na kwanta a kujerar kaina na saman cinyarsa, wannan damar dana samuce ta bani damar faɗin, "boss wai dan ALLAH wane laifi Dad yay makane?". Kallona yay cikin ido ya watsar, ya maidama hankakinsa ga kallon labaransa hankali kwance. Iya kaiwa ƙarshe nakai da haushi, hakan yasa na sake maimaita tambayar kozai fusata ya bani amsa, amma nanma saiya shareni, aifa nakai ƙarshen harzuƙa, na fashe masa da kuka, "Wai miye laifin Dad ne da Yah Qaseem a gareka? Bayan tarin ƙauna da kulawa da suka nuna maka dagasu har Momy, ƴa fa suka ɗauka sukutum suka baka ka aura, basu ji komaiba suka sake bakani duk da kuwa ɗansu jininsune ya dace na aura, sannan ƴarsu da ke tsananin sonka ya dace ka aura kaima, boss bai kamata ace ka maida alkairi ta wannan sigarba, suɗin ƴan uwanane fa waɗanda sukaimin gatan da kowa ya gaza yimin, sune suka maidani mutum harna zama abin sha'awa ga irink......." ruf ya rufemin baki da nashi, ya ɗagani cak batare daya sakimin bakiba yay bedroom dani, duk ƙoƙarin son ƙwacewar da nake ko gezau baiyi ba, dama ya kashe fitilar ɗakin sai na gefen gado kawai, dan haka sai kawai jina nai bisa gado, babu wani ɓata lokaci ya shiga juyani da zafi-zafi yanda yake so, gashi ya hana bakina damar neman ɗauki, yanda yake bi danine ya tadamin hankali, dan sam babu wani bi a hankali kamar ranar, sai dai kuma hakan bai hanashi kasancewa cikin nutsuwaba da min abinda zai gusarmin da hankali. Idan nace muku na gurzu fiye da ranar farko to ku ɗauka gurzuwa nai irin ta ƙarshen nan da faɗarta kawai takai a tausayamin, dan al'amarin ya zama kamar famine daga baƙar azabar dana sha a daren shekaranjiya. Muryata harta dasashe saboda kuka, ya kuma ƙi lallashina kosau ɗaya.
Kamar ranar yauma shine ya taimakamin na gyara jikina, ya kuma sakani a ruwan zafi sosai sannan ya maidoni saman gadon ya kwantar batare da yace dani uffan ba, yamayi tamkar baijin kukan nawa, komawa yay bayin yaje yayo wanka shima, har lokacin ina shashshekar kuka na, muryarsa a dadushe kamar mai mura yace, "ALLAH idan bakimin shiruba na hawo gadon nan saina sake banbance miki aya da tsakkuwa, daga yau kuma dan ALLAH ki sake ahiga abinda babu ruwanki kinji ko". Yana gama faɗa ya ficewarsa a ɗakin.
Kukan na sake fashewa dashi ina danna kaina cikin filos dan karya ji, kusan mintuna goma da fitarsa naji ya dawo ɗakin, haɗiye kukan nayi na koma sauke ajiyar zuciya, bai tankaminba naji dai yanata kai kawonsa har na wasu mintuna kafin ya hawo gadon. A jikinsa ya sakani ya rungume batare da yace ƙala ba, mintuna kaɗan barci yay gaba dashi bayan yaymana addu'a, nima ajiyar zuciyata na cigaba da saukewa har barcin yay awon gaba dani.3

STORY CONTINUES BELOW

★★★★★

Da asuba shine ya tadani, kafinma na sakko a gadon yayi ficewarsa, na rakasa da harara sannan na sakko da ƙyar, wani irin zafi naji ya ratsani a wajen, sai ga hawaye shar, nasa hannuna na share ina jinjina muguntar maza a raina, idan dai haka za'a dingaji to miye abin daɗi anan da har mata suke zuwa suyi iskanci dan ALLAH?. Sai da na shiga ruwan zafi yanzunma sannan nai alwala na fito, naji daɗi sosai yanzun kam harda nutsuwa, ficewa nai daga ɗakin na koma nawa, sai fitilar waya na kunna dan sun ɗauke wutarsu. Ina idar da salla gado na haye nai kwanciyata ko azkar banyiba, banason yazo ya iskeni zaune, barci yaɗan fara fisgata naji ya buɗe ƙofar, ban motsaba balle yasan idanuna biyu, sai da ya maida ya rufe sannan naɗan buɗe kaɗan naga bayanan, ajiyar zuciya na sauke na gyara kwanciya abina.1

Taƙwas saura na farka, na sakko daga saman gadon ina matse fuska saboda ciwon da jikina kemin ta ko ina, bama dole nai ciwon jikiba kodan muguntar da akaimin, wanka nayi na fito nai shiri cikin wando da riga na parkistan da sukaimin ƙyau, nai ƴar kwalliya dai-dai misali sannan nasa turare da yafa ɗan gyalen kamar yanda sukeyi. Fitowa nai dan nema mana breakfast tunda ya roƙi Ummah akan a daina kawo abinci, a bazata na iskesa a babban falo zaune yana aiki. 'Agogo sarkin aiki' na faɗa a zuciyata cike da gulma. Ɗagowa yay ya tsatstsareni da mayun idanunsa, hakan yasa nai ƙasa da nawa, saida na rissina ina gaishesa sannan ya ɗauke kansa daga kallona, amsamin yay da tambayata wai ya jiki. "Ni lafiyata lau". Na faɗa ina ɓata fuska "Haka akeso ai". ya bani amsa a taƙaice. Miƙewa nai ina satar kallon kofin dake a centre table ɗin alamar coffee ya haɗa da kansa yasha kenan? Bance komaiba na nufi kicin, inaji a jikina kallona yake harna shige.
Idanunsa ya lumshe da sakin murmushi yana ɗauke kansa daga binta da kallo da yayi, a fili ya furta, "Masu dangi, yauma ki ƙaramin maganarsu kiga yanda zamu kwashe anan gidan sarkin son ƴan uwa".
Gyaɗar dana jiƙa da farar shinkafa tun da daddare na wanke, na ɗakko farar kwakwa da dama na fasa na yayyankata itama na haɗesu waje guda da citta ɗanya da kayan ƙamshi dai-dai buƙatata na markaɗesu kasancewar akwai wutar da naita addu'a da fatan su kawo tunda nai sallar asuba, sai da sukai laushi sosai sannan na tace tsaf na ɗauraye tukunya na zuba, ban kunna gas ɗinba tukunna na ɗiba wake gwangwani biyu da rabi shima nai zaman dakawa aɗan turmina, sai da yaymin yanda nakeso sannan na cire na wanke shima nai markaɗan ƙosai, saida na tabbatar na haɗa komai sannan na kunna gas, ban rufeba tukunyar kunun ba gudun karya taso ya zube saboda gafin gyaɗa, na saka ludayi ina motsawa a hankali har yay zafi ya fara kauri, cikin amincin ALLAH baiyi ƙurnu ba yay ƙyau abinsa sai ƙamshin gyaɗa da kwakwa ke tashi, na sauke tukunyar a ƙasa danya ɗan huce kafin na saka madarar dana dama. Suyar ƙosan na fara wanda dandanan na gama kasancewar bawani yawane da shiba, na zuba madarar a kunun sannan na zuba ma maigadi muma na juye mana namu, saida na gyara komai tsaf sannan na fito da namu a Dining na maigadi ma na fito dashi na ajiye gefe. Baya a falon, dan haka naɗan gyara tunda babu wani datti na azo a gani na saka turaren wuta. Ina kammalawa yana fitowa, yay tsaf cikin ƙananun kaya sai baza ƙamshi yakeyi.
Baice dani komaiba ya ɗauki abincin maigadi ya fita, babu jimawa sai gashi ya dawo, lokacin ina a Dining ɗin ina ƙoƙarin haɗa masa nasa, kujera yaja ya zauna idonsa akan hannuna da har yanzu yake raɗam da ƙunshi.
"Duk a yaushe kikai wannan?" na tsinkayi muryarsa a bazata. Kallonsa nai na janye idanuna, nace, "Yanzun". "Kinyi ƙoƙari, ALLAH yay miki albarka". Murmushin daban niyyaba na saki sai naji duk fushin nawa yay ƙasa, a hankali nace, "Nagode". Shima murmusawa yayi kaɗan da ɗaukar ƙosan yakai bakinsa, ya lumshe idanu da faɗin, "Uhhhmm". Kallonsa nai dariya na cina, na ɗauki cokali nasa gefensa alamar waiji. "Yarinya ai ba santi nakeba" ya faɗa yana jan kofin kunun dana ajiye masa a gabansa sosai. "Nima ai bance santi kake ba". "Kin taimaki kanki to".
Murmushin na sakeyi ina ƙoƙarin haɗa nawa nima.
Nayi mamakin yanda yaci sosai, ya ɗauki tissue yana goge bakinsa damin almar komai zamm da hannu👌🏼. "Nagode to" nafaɗa ina murmushi. Zagayowa yay ta bayan kujerar da nake ya ranƙwafo ya sumbaci kumatuna duka biyu sannan yace, "Kin gama mallake Jay da komansa Miemaa".
Hannu nakai na shafi fuskarsa ina faɗaɗa murmushina, dan naji yanda ya nuna jin daɗinsa da abincin.
ya zagayo ta gabana ya nunamin kuncinsa alamar na sumbata. Dukda inajin kunya haka na daure na sumbacesan kamar yanda yake buƙata. Sassanyan numfashi ya sauke da juyamin ɗayan, nanma dai yi nayi ina mamakin rashin kunyarsa. "Jazakhillah bi jannah" ya faɗa yana kamo fuskata cikin tafukan hannayensa, kafin nace wani abu ya manne bakinsa da nawa.
Yana saki na saka hannu na rufe fuska. yace, "Daga baya kenan. Bara naje Alhaji Babba na jirana zamuje wani waje".
Miƙewa nai tsaye nima, "To dan ALLAH ka kira Nabeelah tazo ta tayani zama, ALLAH babu daɗi kaɗaicin". "Baga wuta ba, kuma nima aiba daɗewa zanyiba". Cikin marairaicewa nace, "Idan suka ɗauke fa, kumafa ni tsoro nakeji". "Jami'ar tsaro da tsoro". Ya faɗa yana jan hancina. Bai jira amsataba ya fice yana faɗin "Aimana addu'a".
Da "ALLAH ya tsare" na rakasa inajin duk babu daɗi...................✍
2
Jiya kam Wattpad yay muku buƙulu, nayi typing tun dare zan baku na nemesa na rasa, wlhy sai sake wannan page ɗin nai cike da haushi, gashi dai sai dai kuyi maneji da shi😥.

6
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.4

Page 471

..................A harabar gidan suka iske Alhaji babba zaune alamar isowarsu daman yake jira, kafin ma Sadiq ya fito ya buɗema Jay shi harya buɗe da kansa ya fita, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙarisa ga kakan nasa da tun shigowar motar gidan ya ajiye jaridar dake hannunsa. Cike da zolaya Alhaji babba yace, “Kai angon nanfa kamin wayo, gaskiya nima azo a nomin ƴar bana bakwai auren nan zanyi ko kaurin wuya na ƙara da jar fata”. Sosai Jay ya ƙyalƙyale da dariya, ya zauna akujerar robar dake gefen Alhaji babba yana faɗin, “Duk gasarka dai ba zaka samo cancaɗeɗiya kamar tawaba Alhaji, domin tawa fa ta musamman ce”. “Ni dai banason cika baki, kar nan da wata biyu inga ka faramin zarya a gida ehe”. “Ai bama zanyin ba, sai dai kai ka ringa mana saboda zuwa cin tuwo”. Dariya suka sanya a tare, Jay ya rissina ya gaidashi cikin girmamawa, kafin su miƙe cike da farin ciki. Sadiq da shima tuni ya fito a motar ya rissina ya gaida Alhaji babba. Cike da kulawa ya amsa masa tare da sanya masa albarka. Jawaad ya buɗema kakansa mota da kansa, sai da ya shiga ya maida ya rufe sannan ya zagaya inda Sadiq shima ya buɗe masa. Kasancewar tun fitowarsu Jay ya bama Sadiq address ɗin inda suka nufa sai kawai kaka da jika suka cigaba da hirarsu, yayinda Sadiq keta aikin tuƙi abinsa.
          Tun a farkon shigowa layin Sadiq yay tambayar gidan Malam ɗan inna. Kasancewar sanannen gidane kuma anga mota mai ƙyau dan danan suka samu rakkiya har ƙofar gidan. Gidane irin da ɗin nan, dan daga ƙofar gidan zaka iya kallon babban zaure dake da ƙatan murfi ja wanda wahaka ta sakashi komawa mai roɗi-roɗin baƙi. Sadiq ne kawai ya fita, cikin alnajiran dake zazzaune bisa dakalin gidan wasu na karatu wasu na rubutu a alluna wasuma hirarsu sukeyi ya ƙarisa. Duk idanu suka zuro masa, ya ɗaga musu hannu alamar sannu sannan yace, “Ƙannena dan ALLAH ko malam ɗan inna na nan?”. Babban gardi dake karatu da sauri-sauri tamkar zai haɗiye harshensa ya dakata yana kallon Sadiq ɗin. “Malam baya nan, amma ba nisa yayiba”. Sadiq dake saurarensa yace, “To masha ALLAH, dama baƙine muke tare dasu gasu a mota, idan babu damuwa ko za'a aika wani ya kira mana shi ne?”. Gardin baice komaiba ya gyara zaman allonsa ya sakko daga dakalin, zauren gidan ya shiga, babu jimawa sai gashi ya dawo. “Ku shigo” ya faɗa kawai yana kallon Sadiq. Sadiq baice komaiba ya juya ga motar, a saitin Jay yay knocking glass ɗin, Jawaad da gaba ɗaya hankalinsa na'a tattaunawa da Alhaji babba ya juyi tare da sauke gilashin motar. “Oga yaronsa yace baya nan amma bai nisaba, yace kushiga ciki inaga zaije ya kirashi ne”. “Okay” Jawaad ya faɗa a taƙaice yana maida kallonsa ga Alhaji babba dake saurarensu.
     Kusan a tare suka fito, a take dukkan almajiran dake wajen suka zubo musu idanu, sannu kawai suke musu babu batun gaisuwa, su dai suka shige cikin zauren dake ƙaton gaske, sai dai ko'ina mulmule yake da suminti, sai alluna masu yawan gaske dake jijjingine da kowacce kusurwa ta bangon zauren. Zama sukai a tabarmar da aka shinfiɗa, Sadiq dai dama bai biyosu ba sai Gaddin nan kawai. Saida yaga sun zauna sannan ya shige wata ƙofa alamar cikin gidanne, babu jimawa sai gashi ɗauke da kofin silba babba. ya ajiye a gabansu sannan ya gaishesu. “Bara naje na kirashi yana nan ƙasan layi suba wata mata mara lafiya”. Alhaji babba ne kawai ya amsa masa, ahi Jay ma dai kallon Gaddin yake cike da nazari.
       Kusan mintuna talatin da fitar gaddin nan sai gashi ya dawo tare da Dattijo, daka gansa kasan akwai wahalar rayuwa tattare da shi, dan tsufan nasa yafi shekarun yawa a zahiri. Tun shigowarsa Alhaji babba ya shaidashi tsaf, dan kamanninsa na ƙuruciya duk suna a tare dashi, ya ɗan murmusa yana sake girmama buwayar UBANGIJI.
       Sannu da zuwa shi dai malam ɗan inna keta zuba musu, ya zauna saman buzunsa dake fuskantar su Jawaad, shima dai kallon sani yakema Alhaji babba, sai dai ya rasa a ina yasan fuskar ne?. Hannu ya fara bama Alhaji babba suka far gaisawa, sannan ya miƙama Jawaad shima suka gaisa. Cikin ɗan tsantseni yace, “Sai dai kuma ban gane baƙin nawa ba duk da ina musu kallon sani sai dai na rasa a ina?”.
          Murmushi Alhaji babba yayi yana gyara zamansa, yace, “To bazan musa makaba, sai dai nasan ƙila kamanni kake gani kawai. Da farko dai sunana Nuhu. wannan jikanane sunansa Jawaad, munzo neman wani bawan ALLAH ne mai suna Adamu”.
     Malam ɗan inna ya kafe Alhaji babba da kallo, dan yanzukam ya gano ta inda ya kema Alhaji babban kallon sani, to amma abin tambaya shi wanene? Haɗiye wannan tambayar yayi a ransa, a fili yace, “To Adamu dai biyu ke garemu, ɗaya muna kiransa Ado, yanzu haka yana can balaguro kudu damu, shiɗin babban ɗanane, yanada iyalinsa duk suna man cikin gida tare damu, sai kuma ɗan ƴar uwata shima sunansa Adamu, amma ana kiransa Adamu makaho, shikam dai ALLAH yay masa rasuwa shekara kusan ta takwas kenan, matarsa ma ta rasu kafin shi”.
      Su jay suna jira suji yace yana da ƴa sai sukaji yay shiru.
      Alhaji babba daya haɗiye mamakinsa ya gyara zama yana faɗin, “Masha ALLAH, mu munzo neman Adamu makahon ne, ashema ALLAH yay masa rasuwa?”. “Tabbas ya rasu dalilin mota data bigesa”. Ƙwallar data cika idon Alhaji babba yasa bakin rigarsa ya share yana ɗan murmushi, “ALLAH ya gafarta masa shi da matar tasa”. Amin ya rabbi, da Alhaji ɗan inna suka faɗa a tare.
       “Mahaifiyarsa fa ko ita tana raye? Sannan shi baibar zuri'a ba ne?”. Alhaji babba ya faɗa cikin ƙarfin hali.
    Alhaji ɗan inna ya jinjina kansa, “Mahaifiyarsa ta jima da rasuwa, dan dalilin jinyane ma ya maidota gida saboda shekaru da dama ba'asan inda takeba ita da ɗan nata, sai kawai rana tsaka muka ganta tare dashi, adalilin jinya ya matsa suka dawo gida, dan shi makanta ta samesa ta idi ɗaya tun ƙuruciya dalilin ƙyanda, to ganin inda suke babu mataimaki sai ALLAH ya matsa mata harta faɗa masa tushenta suka dawo, kowa ƙin yarda ta raɓesa yay a cikin dangi, sai nine na bata masauki a gidana, na kuma riƙe shi Adamun tamkar sauran ƴaƴana har nai masa aure, bayan aurensa da shekara kusan huɗu ALLAH yay ma yaya Sa'a rasuwa. Shi adamun da anan cikin gidan nawa suke zaune shi da matar tasa mai suna Asiya, itama tanada nakasar ƙafa dan gurguwa ce. Daga baya kuma sai suka tashi”.
    Kafin Alhaji babba yay magana Jay yay saurin faɗan, “Miye dalilin tashin nashi? Sannan kuma basu da yarane? Naji baka amsa wannan tambayarba”.
      Malam ɗan inna yaja fasali yana sake gyara zamansa a karo na babu adadi. “Mudai a saninmu Adamu baida wasu ƴaƴa, amma kuma al'amarinsu dalilin wata ƴa ƙwallin ƙwal yazo ma mutane da ruɗani musamman lokacin da tai girma kamanninta da nashi suka fita. Tun aurensa da Asiya bata taɓa ko ɓatan wata ba a gidanan, danni da kaina nan nasha basu taimako akan hakan ko za'a dace, amma har bayan rasuwa yaya Sa'a da kusan shekaru uku babu wani bayani daga matarsa, hakanne ya saka muka fara masa kwaɗayin kozai ƙara aure. Amma ya murje idonsa yace baisan wannan zanceba shi yana son matarsa. Munta lallaɓashi akan inma kuɗin auren yakeji karya damu zamu haɗa muyi masa, tunda dai maganar ciyarwa daga iyalina ake basu abincin dare da rana, na safe kawai yake samowa da yake yana ƴar sana'arsa ta gyran tsummokara. Sam bai saurari kowaba, dama yaga an takura masa da zancen sai kawai rana tsaka yazo mana da maganar zai tashi ya samu ɗakin haya a wata anguwa dalilin abokinsa. Munsha mamaki sosai da al'ajabi, dan bamuyi zaton gatan da muke masa har yakai abin zafin da zaiyi tunanin yin nesa damu ba. Hakan ba ƙaramin sqkamu ɓacin rai yayiba ainun, musamman ma ni da nake ganin na taimakesu shiga mahaifiyarsa a lokacin da kowa ya gujesu. Cikin fushi nace yaje abinsa, amma karya sake tunawa dani matsayin ƙanan mahaiyarsa tunda ya zaɓi mace sama damu. Suma sauran dangi duk sukai masa wannan furucin.
        Baiko nuna yaji ko ɗarba ya tattara matarsa daƴan komatsansu sukabarmu zuwa can nesa damu sosai. Tunda suka tafi bamu sakejin ɗuriyarsu ba sai bayan shekara biyu sukazo mana nan matar tasa da ciki ƙarami, da farko kowa yaƙi saurarensa, amma ni saina sauraresa ganin abin farin cikin da matarsa ke tare dashi, shima ya nema gafararmu dukda wasu a cikinmu basuce dashi sun yafe ɗin ba. Matarsa ta cigaba da rainon ciki lokaci-lokaci sukanzo gaishemu, hakama yaranmu sukan ɗanje musu, idan kuma sabga ta tashi matarsa na zuwa har cikinta ya shiga wata takwas. Rana tsaka yazo ya sanar mana wai tana asibiti babu lafiya, likitoci sunce ɗan cikinta ya samu matsala cireshi zasuyi dan rabin jikinsa a ruɓe yake, ma'ana dai bamashi da rai kenan, suna buƙatar kuɗaɗen da za'ai mata tiyatar, shi kuma na wajensa basu kaiba amma dan ALLAH mu ranta masa a hankali zai biyamu idan komai yay dai-dai. To mudai bai samu ko sisiba daga garemu, dan bamu dashi saboda kuɗin sunda yawa gaskiya, haka ya tafi. Mukuma anan mukai shiri domin zuwa mu duba matar tasa sai dai kuma mun manta bamu tambayesa asibitinba. Haƙura mukai muka zauna zaman jiransa kozai sauyo saiya kaimu. To adai ranar bai dawo ba sai washe gari mu mukaje can gidan da yake hayar muka tambaya, daga can akai mana rakkiya asibitin, tun kuma kafin muje an sanar mana ai anmata aikin an cire ɗan babu rai. Amma abin mamaki sai muka isketa da jaririyar yarinya a hannu. Babu wanda ɗunbin mamaki bai kamaba a cikinmu, har muka kasa haƙuri mukai magana tunda ita amma ce ɗa namiji aka cire mata kuma baizo da raiba. Amma sai cewa sukai ai jaririyar dake wajenau itace ƴar tasu, yaran ƴan biyu ne, ɗayane babu rai ɗaya da rai. Sam bamu yarda dasu ba, hakan yasa mukai fushimuka bar musu asibitin, munta sauraren muga Adamu ya biyi bayanmu yay mana cikakken bayani akan gaskiyar al'amari sai mukaji shiru, a haka har shekaru suka shuɗa yarinya ta fara girma, kowa dai yasan tabbas ƴarnan ba ɗiyar Adamu bace akwai abinda suka ɓoye dangane da samuwarta, amma kuma a zahiri ga wasu abu na kamanninsa na bayyana ga yarinyar, sannan idan ka nutsu da kallon yarinyar lallai zakaga wasu abubuwan na Asiya tattare da ita dukda sam batayo asalin fuskarta ta fulaniba dan Asiya farace tas kuma ƙyaƙyƙyawar gaske, wahalhalun rayuwane kawai suka ɓoye kaso mafi yawa daga ƙyawunta, wannan abu shine ya kawo mana ruɗani maiban mamaki wanda har a yanzu da kuke a gabana bamu fita daga cikinsaba, kuma har Adamu ya rasu shida matarsa basu taɓa faɗa mana komai daya shafi yarinyarba”.
     Alhaji babba daketa sauke tagwayen ajiyar zuciya na tausayin gudan jinin nasa da son zuciya ya saka mahaifiyarsa nisantasu ya share ƙwallarsa, muryarsa a raunane yace, “Tabbas bakai dake bamu labarin nanba, hatta dani nan ka sake dulmiyani a ruɗani, taya za'ai kuna zargin ba ƴarsu bace amma kuma take kamanni dasu ta wasu abubuwan? Koni dana kalli hotonsa da yarinyar naga tabbataccen jini na haƙiƙa tattare da junansu, na tabbatar koda kutu akaje wannan yarinya za'a iya tabbatar da tasuce babu wani haufi a cikin hakan”. “Tabbas hakane Baba, sai dai mai warware ainahin gaskiyar lamari sai ALLAH sai kuma su da suka kasance da yarinyar, gashi kuma a yanzu duk basa a raye”.
     Jawaad da baice ƙalaba, saima latsa waya da yakeyi, batare da ya ɗagoba yace, “Yanzu Kunsan inda yarinyar take ku?”. Yanda yay maganar babu wasane ya saka Alhaji babba da Malam ɗan inna kallonsa, dukda yasan kallon nasa suke bai ɗagoba, baikuma gyara fuskarsa dake a ɗaureba. Malam ɗan inna da duk ya daburce yace, “E.. e eto saurayi yarinyar dai tana gidan da ayka zauna”. Ɗago idanu Jay yay ya kallesa, “Kenan babu wanda ya ɗauketa a cikinku bayan rasuwar mahaifinta saboda kunaji a ita ba jininku bace bayan kuma UBANGIJI ya baku komai a bayyane tunda ya fidda kamanin iyayenta a jikinta?”. “Saurayi ba haka bane ba”. “To yayane?”. Kasa cewa komai malam ɗan inna yayi, sai zufa data jiƙe ta cikin babbar riga, shi dama tun shigowarsa bai hangi sauƙi da ga yaron nanba sam.
      Ajiye wayar Jawaad yayi yana fuskantarsa sosai, “Malam da farko dai yanzun bara na fito maka a mutum, wannan da kake gani dai shine mahaifin Adamu makahon, mijin ƴar uwarka Sa'a wanda ta gudar masa da ɗa bisa son zuciyarta, ina fatan ka gane”..
      Sallalami malam ɗan inna ya kwaso daga samaniya ya dire bisa ƙasa yana zare idanu jikinsa na ɓari, “Wai dan ALLAH da gaske kana nufin Mati ne? Dama kana raye? Adamu yayta nemanka ruwa a jallo amma ko labarinka bai taɓa samuba daga wani, dangi da duk muka sani a baya mun sakashi ya abi amma duk sun rasu bai samu ko guda ba a ciki”.
        “Hakane Hamza, kasan idan UBANGIJI nason saukar da wata aya ga bayi saiya datse al'amarinsu ya ɓoyesa a rasa bakin zaren a dalilin ƙaddara, muduka ƙaddarace ta ɓoyemu dukda muna a cikin gari ɗaya, nima nasha bibiyar ahalinku dalilin son ganin ɗana ya dawo gareni, sai dai hakan bata kasanceba har gashi ƙasa ta rufe idanunsa, hakan jarabawace, dan tabbas tun daga Zazzafar soyayyar danaima Sa'a har zuwa zaman aurenmu da guduwarta da yarona duk jarabawace a garemu da wata hikima ta UBANGIJI, naso ace na sake ganinsa, naso ace na kwatanta sauke haƙƙinsa dake kaina matsayin mahaifi a garesa, naso ace shima ya tashi cikin ƴan uwansa da a yanzu sune suka zamema rayuwata haske, ALLAH ne yaymin komai da kaini matsayin da nake a yanzu amma ta dalilinsu ne, na yarda abinda kakeso bai zama lallai ya kasancema rayuwarka alkairiba, wanda kake ganin yay kutse ma rayuwarka sai kaga shine alkairin, naso Sa'a so mai tsanani, harnaso bijirema iyayena a kanta, sai dai itaɗin ashe ba itace abinda nake ma hasashenba, wadda iyayena suka auramin ina baƙin ciki da takaici, na ƙuntata rayuwarta a zamanmu sai tazama ashe itace abinda banyi zatonba, dan gashi yanzun albarkacin zuri'arta nakeci ita bata raye, wannan aya ce ga masu ZUCIYA irin tawa, ɗan adam shidai abinda akeso ya nema zaɓin ALLAH akan dukkan al'amarin sa ba wai son zuciyarsa ba”.
         Sosai Malam ɗan inna keta faman jinjina kansa, Jawaad dai yana saurarensu amma bazaka taɓa fahintar yanayinsa ba sam, saida Alhaji babba ya gama share-sharen hawayensa sannan Jawaad ya ɗago ya sake kallon Malam ɗan inna, “Na biyu kuma zamuje da kai gidanda suka zauna danka nuna mana yarinyar, mu zamu ɗauketa mu riƙe, basai munsan gaskiyar yanda suka sametanba”.
      Sosai ruɗani ya bayyana ga Malam ɗan inna, ya shiga matsar hawaye yana bada haƙuri da musu bayani akan suma basusan inda Bilkisu take zaune ba, amma kwanaki taɗan zazzo gaishesu, sai dai maganar gaskiya ko tazo ɗin basu wani sake mata fuska, danshi sau ɗayama ya taɓa ganinta, kusan shekara uku kenan ya kuma ja mata gargaɗi akan karta sake zuwa masa gida tunda basu da alaƙa da ita, dan saida ya titsiyetama yaji wanene ya nuna mata gidan kafin yaymata korar rashin arziƙi. to amma yaji kwanaki iyalinsa suna gulma wai tana zuwa wajen Ramatu, kuma ma har tayi aure kwana nannan ita Ramatun taje.
     Kafesa kawai da kallo Jawaad yay ransa a matuƙar ɓace, ganin hakanne ya saka Alhaji babba riƙe hannunsa yana murzawa alamar lallashi, hannunsa ya zame ya tashi ya fice daga zauren.
        Alhaji babba yay murmushi yana girgiza kansa, sannan ya maido kallonsa ga Malam ɗan inna da shima yabi Jawaad ɗin da kallo, “Haka yake yana da matuƙar zuciya, sai dai yanada kirki sosai, shine jikana na farko da ƙanwar Adamu mai suna Bilkisu ta wajen Amina kenan ta haifa, ɗan tsohon shugaban ƙasa da ALLAH yayma rasuwa Alhaji Abdul'aziz yusif tafida”. Idanu sosai malam ɗan inna ya zaro, cikin ɗan rawar baki yace, “Dama yarinyar wajenka ce matar marigayi A.Y tafida?”. “Hakane, gama yaronsu da ya bari nan”. “ALLAH maiyin yanda yaso, ALLAH mai hikima, lallai zaɓin ALLAH shine zaɓi kam bawai son zuciya ba, wanene zai iya mantawa da tsohon shugaban ƙasa Abdul-aziz Yusif Tafida a ƙasarnan ai saida azzalumi, adalin shugaba da har yanzu ba'a ƙara samun makamancinsa ba ma”. Murmushi Alhaji Babba ya dingayi jin ba'a manta da ɗan matarsa ba, surikinsa kuma uba ga babban jikansa. A take ya warwarema Malam ɗan inna gaskiyar al'amari dan gane da bilkisu harma aurenta da jikansa Jawaad, wanda a dalilin hakanne kuma yasaka su ma bincike har suka ganosu ta dalilin kamannin bilkisu da Adomu daya gani, da kuma ƴarsa data rasu Rahmah, wanda yake ganin bilkisu ta ɗakko kamanin Rahama ne saboda ƙarfin jini, to gashi sukuma sunmace basu yarda ADamun ta haifi bilkisu ba, to shi ina zasu kama su fahimci gaskiyar wannan ruɗanin ne. Al'ajabi ya sake kama Malam ɗan Inna har takaisa ga sharar hawaye, yayta ban haƙuri da neman afuwa ga alhaji Babba tundaga laifin da ƴar uwarsu ta zama sila har wanda suma suka tafka. Tarr syka fito har wajen mota yana bama Jawad da yay kicin-kicin da fuska haƙuri shima. Hannu kawai ya ɗaga masa da jinjina kansa, dan ransa a ɓace yake, kuma bayaso kosau ɗaya fushinsa yakaisa ga aikata abinda bai daceba ga dattijon da zaiyi sa'a da mahaifinsa, gashi koba komai akwai alaƙa.
     Sun rabu akan zai faɗama sauran ƴan uwansa komai auzo kuma har gida su ƙara bada haƙuri.+

STORY CONTINUES BELOW

           Lallashin Jawaad Alhaji babba yay tayi cikin hikima, tun yana baɓɓata fuska na shagwaɓa harya sake yana masa murmushi, gida suka maida Alhaji babba, batare da sun shigaba Sadiq yay reverse suka sake barin anguwar. Daga nan inda ya ajiye ɓaleru suka nufa kuma. 
           Tun shigar Jay ɗakin da ɓaleru yake jikinsa ya fara ɓari, ya ajiye abincin da yake ci gefe yana zazzare idanu, da hannu Jawaad yay masa nuni da abincin alamar ya ɗauka ya cigaba da ci. Babu musu ɓaleru ya ɗauka teakaway ɗin yana cusawa kamar yanacin maɗaci saɓanin yanda abincin ya fara masa daɗi da farko.
      Ɗauke kai Jawaad yay daga garesa, saida ɓaleru ya cinye abincin tas ya ajiye batare da yaci kifin cikiba, ”Shikuma wannan waka barwa?”. Jawaad ya faɗa yana tsatstsaresa da idanu murya a kausashe. Ɗauka ɓaleru yay da sauri ya hau ci, ALLAH dai ya taimakesa ƙaya bata maƙale masaba ya gama lafiya. Hannu yaje ya wanko ya dawo, ya maƙure jikin bango hantar cikinsa na kaɗawar tsoro, dan har yanzu baibar jin ciwon jikin dukan daya shaba ranar. Jawaad ya ajiye wayarsa yana kallon ɓaleru da ƙyau. “Ka shirya faɗamin gaskiya ko sai mun sake kalar wasan ranar?”. “Wlhy duk abinda kake buƙata inhar na sanshi zan faɗa maka oga”. “Tunani mai ƙyai” Jay ya faɗa yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. “A gidan wa kake aiki?”. “Mr Gebrail”. “Waya sakaka ka ɗauki Gimba a mota?”. Inda inda ɓaleru ya nema farawa Jay ya daka masa tsawa, “Wlhy ko sau ɗaya kamin ƙarya saina karyaka a wajenan na ɗauraka”. Sanin Jay zai iya aikatawa yasa ɓaleru haɗiyar yawu muƙutt, “Uh.. Uh... Uhmm ni dai kawai wata safiya ne aka kirani da kwatanta mini shi, bammayi zaton shi bane saida naje zan ɗaukesa”. “Waye ya kirakan?”. “Mr Gebrail ɗin”. “Ina ka kaishi?”. “Wlhy acan titin ƙatshen gari ya tareni ya amshesa?”. “Kenan dama ka saba musu irin wannan aikin? Koma shi kake musu?”. “Oga Wlhy.....” “Amsa kawai nake buƙata, duk abinda yazo a saɓaninta kai kuka da kanka”. Kansa ya ɗaga da sauri yana karkarwa. “Shi da waye suke sakaka? Kuma wanene ya kaika aiki gidansa?”. “Ɓaleru ya share hawayen da suka cika masa idanu, “A anguwar da gidan drama ɗin nan yake yake gini, wataran yazo wajen shine ya ganni”. “Sai kawai yace zoga aiki na baka?”. “A'a nine da kaina naje na tambayesa saboda a lokacin aikin nake mema, to da yake ina ɗibo yashi daga can wani rafin dake ƙasan anguwar ina kawoma masu gini na saya, lokacin ana aikin gininsa kuma nine mai ɗebo musu yashin, sai naji yana tambayar Engineer ɗin ko yasan wani driver? Dan yanason ɗaukar driver, drivernsa ya ajiye aiki saboda tsufa, to ahinefa nace zanyi da yake na iya mota. Da farko yayi kamar bazai ɗaukeniba sai kuma ya bani key yace na gwada ya gani, a take na amsa na shiga motarsa naɗan zagaya wajen, a lokacinma bai amsa zai ɗaukeniba ya tafi, sai bayan kwanaki biyu harma na fidda rai sannan yazo yace ya ɗaukeni”. “Daga nan sai ya maidaka kidnapper ko? Har takai kuɗi ya rufe idonka aka haɗa baki dakai aka kashe abokinka ɗan garinku?”. “Wlhy oga bada ni aka haɗa baki aka kashesa ba, hasalima nima mutuwarsa kawai naji, wlhy tunda gimba ya rasu ban sake samun kwanciyar hankaliba, oga ina tsaka mai wuya”. “Ai bama ka shigaba tukkunna indai tsaka mai wuya ce. Ya akai ka tuƙa Alhaji Kokino ranar kuma?”. “Alhaji Kokino kuma? Wlhy ni bamma sanshi ba”. “Humm kana wasa dani ko?”. “Wlhy oga da gaske nake maka”. Jay baice komaiba ya ɗauka wayarsa, hoton da yay musu lokacin da traffic light ya tsaidasu ya nuna masa, ɓaleru yace, “Aiho, ai yaje office ɗin Mr Gebrail ne sakan kasuwanci sai motarsa ta samu matsa, shine drivernsa ya ɗauka ya kai wajen gyara, to bai dawo da wuriba shi kuma ya gaji da jiransa shine yace na kaisa gida, wannan shine dalilin da yasa ka ganmu tare”.
     Kafesa da kallo Jay yayi cike da nazarin maganarsa, bai sake cewa komaiba ya miƙe, fitowa yay abinsa. Ɓaleru ya bisa da kallo, daka ganshi kasan a tsorace yake. Securitys ɗin dake kula da ɓaleru ya korama winning akan su kula dashi da ƙyau, duk kuskuren da aka samu sune zai fara hukuntawa. Daga haka ya shiga mota suka bar gidan.

           Ganin lokacin sallar la'asar yayi saiya saka Sadiq tsayawa sukayi sannan suka ƙarasa gida.

★★★★

       Bily na zaune da ƴammatan maƙwafta da suka shigo mata dan a gaisa asan juna ya shigo. Sannu da zuwa tai masa, suma suka shiga gaisheaa suna binsa da kallo tamkar wasu mayu. Kallo ɗaya yay musu ya amsa Sau ɗaya yay shigewar, miƙewa nayi, dan haka suma duk suka miƙe, sallama sukai man suka tafi, nai musu godiya nima sannan naje kicin na ɗauki kunun ayar da nayi na nufi ɗakin nasa. A bakin gado na iskesa zaune ya dafe kai, koda nai sallama bai ɗagoba yadai amsa mani. Naja ƙaramin table ɗin na ajiye. “Su wanene waɗanan?”. Ya faɗa batare da ya ɗago ba. “Nima ban sansuba, basu fi mintuna talatin da shigowaba, sunce min nan gidan maƙwaftan nan namu suke”. Amsar kofin dana miƙa masan yayi, yaɗa lumshe idanu sannan yasaka a bakinsa ya shanye gaba ɗaya alamar yanajin ƙishi sosai, kofin ya ajiye yana miƙewa, “Kidaiyi a hankali”. Ya faɗa yana cire maɓallan rigarsa. “Insha ALLAH zan kiyaye”. Na faɗa ina miƙewa.
              Hannunsa ya miƙomin yana min nuni da rigar, dukda dai inajin nauyinsa haka na kama na taimaka masa muka cire, dan na lura shifa komai yafison ai masa. Na juya zan ajiye rigar naji kawai an kwasheni anyi sama dani, ina mamakin yanda ya ƙware da iya ɗaukar mutum babu ko ɗar, shi ko nauyina bayaji ma.
      Ganin ya nufihanyar bayi nai saurin cewa, “Bandaɗe da yin wankaba fa ALLAH”. “Ke kika san wannan”. Ya shige toilet ɗin yana faɗa. Nidai balki naga ta kaina, inaji ina gani dole akai wankan nan, ni gaba ɗayama ya fara busarmin ido da salonsa. Haka mukai wankan muka fito, bayan mun kimtsa muka fita domin cin abinci.

             ★★★★★★★★

  
Yau kwanakinmu shida kenan da tarewa, zuwa yanzun bansan yanda zan lissafo muku abubuwan da boss ya koya minba, gaba ɗaya ya fetsarar dani, duk da dau bana fiddo zaƙewat dan akwai sauran lokaci, kunyarsa kuwa inajinta tamkar babu gobe, dan duk abinda zai sakani na masa inayi ina rufe idanu, mu'amular gadoce fa na kasa sabawa, dan duk sanda zaizo min babu fashi sai nayi kuka, har fargaba nake ya nuna buƙatarsa, duk da hutun amarci da aka bamu hakan bai hana boss aiki tuƙuruba a gida, ni kaina bai barni na hutaba, matan su Jabeer sunzo sun yinarmin, hakama su Safah an kawosu, Amina ma tazo ta yini randa matan su Jabeer sukazo, da yamma sai ga su Nazifa ma, maganar da muka tattauna ta sakani fahimtar sun shirya zuwanne dama, nayi farinciki sosai ganin maganar ƙungiya ta kankama, komai an kammala na shirye-shirye a satinan za'a fara fidda komi ta kafafen yaɗa labarai da yanar gizo kamar yanda aka tsara, dan aomuke mu fito da zafinmu, ga bikin Nazifa nata matsowa ita, dan ƙarshen wata mai kamawa ne.

     Bayan tafiyarsu na gaji liɓis dan dan suma su Aliyun anan suka kusan yinar mana tare da boss, sauƙina ma basu bar gidanba saida suka tayani na gama komai tsaf gidan ya dawo normal, sanin ko nayi wanka idan ya dawo saina sake dole tare da shi dan kullum tare muke wankan dare sai kawai naƙiyi na dafa masa shayi na gyara fruit. Falonsa nakai komai sannan na shiga haɗa ruwan wanka, ina ciki kuwa ya shigo, sai kawai jinai an ringumeni ta baya. Murmushi kawai nayi na juyo muna kallon juna, murmushin shima yamin da kai hannu a.................🙄😣✍

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.5

Page 48

..............Murmushi shima yaymin da kai hannu a ƙuguna ya kuma matsoni sosai jikinsa, cikin raɗa yace, “Are you ready?”. Ɓata fuska nayi ƙwalla na cikamin ido na girgiza masa kai dan nasan inda ya dosa. Wata shaƙiyyar dariya yayi dajan hancina yace, “Kedai raguwa ce yarinyarnan”. “Ni dai wlhy naji koma miye ace ba raguwaba, kai dan bakasan wahalar da ake sha bane ai”. Bakinsa ya ɗaura a saman kunnena ya ɗan ciza yana dariya da faɗin, “Shiyyasa nake son maidaki jaruma”. Nai saurin ƙanƙamesa saboda tsigar jikina dake tashi, da sauri na mintsini damtsan hannunsa “Ai na fika jarumta”.
       Saurin sakina yay da faɗin, “Ouch!. Ke dai muguwace wani lokacin”. Gwalo na masa na shige cikin ruwan. biyoni yay ciki, “Yarinya kin taro match kuwa”. Saurin ɗaukar soso nai dana haɗama kumfa na saka masa a fuska, yay ƙoƙarin riƙe hannuna naƙi bashi dama, hakan yasa mukaita facal-facal da ruwan kamar wasu ƙananun yara.
     Sai da muka gama shiriritarmu sannan muka fito. Zama nai a kujerar mirror ina goge fuska yazo ta bayana ya tsaya yana miƙamin hannunsa.
        Cike da mamaki na kalli hannun nasa, wani ɗan ƙyaƙyƙyawan akwatine mai kama da diamond amma farine shi tas wannan, sai ɗaukar ido yake da ƙyalƙyali, ɗaga kai nayi na kallesa ta cikin mirror ɗin ya ɗaga min kai da lumshe ido. Yawu na haɗiye da ƙyar nasa hannu na ɗauki ɗan box ɗin inayi ina kallonsa, ganin idonsa a kaina yake har sannan sai na nutsu waje guda, jiki a sanyaye na buɗesa. Na waro idanu sosai waje da faɗin, “Woow!” dan ƴan kune ne masu ƙyau a ciki da zobe. Bansan sanda na juya na daka tsale na ɗanesa bama ni, ya riƙeni da hannu biyu yana dariya muka faɗa saman gadon, tattare kunya nai na ajiye gefe, cikin salonsa daya koyar dani na shiga sumbatarsa fiye da yanda ya koyamin nasa karatun. A take ya rikicemin, nima dai nasan na taro match ai dama, tunda a hannu yake, dan wannan boss ɗin da kuke gani hummm, baisan wasaba ta wannan fannin.
         Duk yanda na dawo kuma ina roƙo da magiya daga ƙarshe bai saurareni ba, sai da ya samu abinda dama yakema ƙulafucin. Daga ƙarshe ya barni da kuka😒 (Kinada matsala ɗiyarga🚴🏼. Lol)
         “Haba my sweet Miemaa na Mai gadon zinarina, kukan ya isa haka Uhimyim, kece kinzo da salon da ban taɓa zaton kin iyaba, ashe kina ɗaukar karatun dai-dai gwargwado”. Cusa kaina nai jikinsa ina ɗan kai masa duka. Ya riƙe hannayen duka yana sakin murmushi mai sauti, “To shikenan nama fasa zuwa dake ni kaɗai zan tafiyata saudian gobe idan ALLAH ya kaimu”. Da sauri na ɗago na kallesa hawaye shaɓe-shaɓe, “Dan ALLAH da gaske kake?”. Goshina ya sumbata yana murmushi, “Idan kin barmin kuka ba”. Saurin share hawayena nayi, yaymin raɗa a cikin kunne. Zabura nai da sauri inaja da baya, “Dan ALLAH ka tausayamin wlhy bazan iyaba”.  Jawoni ya sakeyi jikin nasa yana murmushi, ya sake min raɗa a acikin kunne, hakkane ya sakani yin luff a jikin nasa ina sauke tagwayen ajiyar zuciya, shiko yana aikin shafa bayana alamar lallashi.
        Saida ya tabbatar nabar kukan sannan muka je muka sake wankan, shirin barci mukai muka koma falo, gaba ɗaya ya sake rugurguzar dani da gajiya, ko iya zaman shan fruit ɗin banyiba na kwanta da ɗora kaina a cinyarsa sai barci. Buɗe ido kawai nai da asuba na gammu a kan gadon ɗakinsa.10

            Kamar yanda ya faɗa bayan dawowarsa sallar asuba ya sakani muka shirya kaya akwati ɗaya kacal, da dukna ɗauka wasa yake wlhy, sai da naga dai da gaske yake sannan na yarda. Da taimakonsa na gyara gidan, na killace duk abinda ya dace da ya zam a kilkacen, abinda nasan zai iya lalacewa naci na tattaresa ya kaima maigadi da Sadiq da yazo zai kaimu airport. Mamaki bai nema kasheniba sai da muka fito zamu tafi, securitys ɗin hukumarmu na gani nata kaikawo, na kallesa amma sai ya ɗauke kansa alamar baya buƙatar kowace iriyar tambaya, dole naja bakina na tsuke dan a zauna lafiya tunda baya buƙata.
      Wani gida muka fara zuwa, saida muka shiga naga dattijon tsoho da naita son tunano inda na san fuskar amma na kasa hakan, ga kallon da ya kemin shima tsigar jikina har tashi take. Har ƙasa na tsugunna na gaidashi cike da girmamawa.
        Yanda ya amsamin da tsantsar kulawane ya sakani kallonsa, ya sakarmin ƙyaƙyƙyawan murmushi wanda a wajen Mahaifina kawai nasan irinsa, gabana yay wata irin yankewa ya faɗi har ina ɗan dafe ƙirji, “Babana”. Na faɗa a zuciya batare dana san maganar ta fito fili ba. Daga Alhaji babba har Jay kallon Bilkisu sukai.
    Nai saurin zama ƙasa danjin ƙafafuna suna neman gaza ɗaukata, wlhy da tsohon nan yay murmushi sai naga kamar babana ne, sake ɗagowa nai na kalleaa sai naga duk idanunsu a kaina suke. Boss yace “Yaya dai?”. Kai na girgiza masa da sauri alamar babu komai ina sake satar kallon tsohon ta gefen ido.
          “Tashi ki koma saman kujera”. Muryar tsohon ta daki dodon kunnena. “Nanma Yayi Baba” na faɗa muryata naɗan rawa.
     Murmushi yayi da har na iya jinsa daga inda nake, yace, “Amarya lallai kin iya tuwo, naga wannan ɗan dokar ya washe harda kaurin wuya ya ƙara”. Murmushi nayi kaina a ƙasa, sai boss naji yana basa amsa. “Idan yaji haushi gobe muje ɗaurin aurensa Miemaa, idan ya auro matarsa shima saita ringa masa yayi kaurin wuyan”. Dariya naji ya ƙyalƙyale da ita. Haka suka cigaba da tsokanar juna cike da birgewa, kafin suɗan tattauna. Banji ya faɗa masa ainahin mi zamuje yiba, hakan sai ya bani mamaki sosai. Kusan awar mu ɗaya da rabi a gidan sannan muka fito, daga nan sai airport.
                Farin cikine mara misali ya kamani lokacin da nai tozali da Ummu, ashe tare da ita zamu tafi harda takawa, ta rungumeni a jikinta tana yaba yanda nai ɓulɓul kamar yanda ta faɗa. Amintacciyar baiwarta nata mana dariya, banga takawa ba saida zamu shiga jirgi, ‘Masha ALLAH’ na faɗa a raina dan ganin cikakken mutum mai haiba da kwarjinin mulki, lallai sarauta ba ƙarya bace. Har ƙasa na tsugunna na gaidashi, ya amsa min da kulawa tare da sakamin albarka.
     Sai da suka fara shiga shi da boss da ya riƙema hannu da dogaransa biyu kacal sannan muma muka shiga. Da yake waje na musamman aka bamu sai naji kamar mu kaɗaine a jirgin, acan ƙasan raina cike nake da ɗoki da fatan dacewa akan abinda zamuje dominsa.1

STORY CONTINUES BELOW

____________________________________

               Gaba ɗaya hankalin Momy a tashe yake da duk wanda yake cikin gidan Dad a yau, ba komaine sanadin wannan tashin hankalinba kuwa sai zuwan ɗan fir'auna gidan da far1ar safiya ya tafi da Shahudah. Kusan ƙarfe takwas yazo gidan, lokacinma babu wanda ya tashi sai ma'aikatan gidan kawai, daga Shahudah harsu Momyn ma babu wanda nake tunanin yayi sallar asubahi, sabuwar mai aikinsu na tsaka da sharar falonsu ya shigo. Da ɓacin rai ta kallesa zatai magana, sai dai yanayinsa ya sakata haɗiye abinta a cikin rai ta koma zare idanu. Ya zabga mata harara cike da gadararsa yace, “K rakani ɗakin matata”. Cikin ƙarfin hali tace, “Matarka kuma? Anan gidan?”. yay mata kallon tara saura kwata ya ɗauke kansa, “Baki da labari kenan?”. Kafin ta bashi amsa sai ga Aamilah da muryar ɗan fir'auna ta sakata tashi a firgice, dan sam shi baya magana a hankali.
         Idanu ta zaro zata koma da gudu ya daka mata tsawa, “K dan tsohonki dawo nan!!”. Bata da ikon jayayya, dan haka ta dawo ta tsaya tana rurrufe ƙirji da hannu kasancewar rigar barcin jikinta bata kirki baceba. Yi yay kamar bai fahimci abinda takeba, yace, “Ina matata?”. “T.. Tan tana barci a ciki”. tai maganar tana nuna masa saman benen. “Kaini”. Yay maganar yana yin gaba. Binsa ta farayi a baya tana hararsa, tai wata zabura daya juyo, baibi takanta ba yace, “Wuce gaba”. Kamar zata fasa ihu haka taji, amma dole ta haɗiye abinta a rai tai masa rakkiya har ƙofar ɗakin Shahudah.
     Tana kwance ɗai-ɗai tana barcinta ac na kaɗata suka shiga. “Tasheta” ya faɗa yana kallon Aamilah. Jikinta na rawa ta shiga tashin Shahudah, daƙyar ta tashi, tana ganin Aamilah ta hau hararta, sai dai ganin ɗan fir'auna tsaye ya sakata watsakkewa.
         “Sannu da tashi ƴar hutu. Ke shirya mata kayanta”. Idanu Aamilah ta zaro, ya daka mata wata mahaukaciyar tsawa da ta sakata fashewa da kuka tana bashi haƙuri, a take ta buɗe Wadrobe ɗin Shahudah ta fara zuba kayanta a cikin a kwati, shikuma yahau tattare kayan kwalliyar saman mirror. Ita dai Shahudah tayi mutuwar zaune, dan binsu kawai take da kallo ko sau ɗaya ta kasa magana.
      Momy da mai aikinsu taje ta kirawo tana fitowa falo ɗan-fir'auna na fitowa daga ɗakin Shahudah riƙe da hannunta tana tirjewa da kuka tana kiran Dady da Momy, Aamilah na biye dasu da akwati. “Kai wai wane irin mahaikacine ne? Gidan ubanwa zaka kaimin yarinya? Sakarta dan ubanka!!”. Ko kallon Momy baiyiba yaja Shahudah ƙeeyyy!! sukai waje, Aamilah na biye dasu tana hawaye. Binsu momy tayi takai hannu zata riƙe Shahudah ya zaro bindiga a ƙugunsa, “Wlhy kina taɓata saina tsiyayar miki da jinin hannu, inbanda rashin mutunci da raini, an ɗauramin aure amma kun maidani ɗan iska kamar wani gwauro, ke lokacin da aka ɗaura aurenki da surukina ba ranar aka kaiki kika tareba ya kwashi gararsa, saini dan an maidani wani sha ka tafi sai safa da marwa nake tsakanin titi da gida, to daga yau ta ƙare, kwa biyota da sauran kayanta, ga oga can an basa matarsa shi yanata watayawa ƙilama mun samu ɗa, amma ni ambarni hagaga da baki kamar tsohon amalen raƙumi. Motsoow, aikin banza kawai. Ke muje ƴar farata yau nima ango nake mai lokaci”.
      Sunaji suna gani ɗan-fir'auna ya tura Shahudah a motar da yazo da ita bus, ya shige abinsa ya tada yabar anguwar. Kuka momy da Aamilah keyi kamar ransu zai fita, Salman yana daga jikin Window ɗakinsa duk abinda akeyi yana gani amma yaƙi fitowa, saida ɗan fir'auna ya wuce da Shahudah sannan ya fito yana murza ido da tambayar abinda ya faru shi a dole barci yake baiji komaiba.
   Kuku ne ya masa bayani dan sun ɗauka da gasken barcin yake bai jiba.
     
      Daƙyar momy ta iya samun Number Dad ta faɗa masa komai, hankalinsa yay masifar tashi, yay kiran commissioner of police dan yayi report amma bai ɗauka ba, ya kira I.G shima wayarsa switch up, duk ya rikice ya rasa wazai kira, daga ƙarshe ya yanke shawarar kiran Jay, amma shima wayar tasa dai switch up. Tashin hankali kenan wanda ba'a saka masa rana, karan farko da yaji nadamar barin Qaseem barin ƙasarsa. Haka yayta bige-bige waya bai dace ba, wasu aƙi ɗauka, wasu suƙi shiga. kansa gaba ɗaya ya kulle ya kasa fahimtar wannan ruɗaɗɗen al'amari, yama za'ai ace shi kamarsa yana kiran wayoyin waɗanan mutanen amma babu mai wucewa, wasu kuma sunƙi su ɗaga masa ma. ‘Mi hakan ke nufi?’.6

STORY CONTINUES BELOW

Muma wannan amsar muke buƙatar ji Dad😥.

__________________________________

           Mun sauka Saudia lafiya, inda akazo da zuƙa-zuƙan motoci akai mana tarba ta girmamawa, Aunty Mahfuzah da mijinta da ƴaƴansu biyu. Nazata wannan karonma gidansu Aunty Mahfuzah zamuje, sai naga an kaimu wani wajen daban.
    Ba boss ba koni a ƙage nake da son ganin Umm-Anum wlhy, sai dai shi jarumin naku ya dake kamar babu komai a ransa. Ni kaina ta yadda yake komai a sanyaye na fahimci komai ya kwance masa, hatta da wanka da ƙyar na samu yayi sannan mukaci abinci, kasancewarsa maicin abinci sosai sai gashi ya tsakura kaɗan ya tashi, nata marairaice masa da lallashi akan ya ƙara amma ya girgiza min kai, daga ƙarshe ma sai ya tashi ya shige bedroom ɗin ya barni a falon.
      Raina gaba ɗaya sai ya sake jagulewa, na ajiye abincin nima na tashi na bisa ciki, kwance na iskesa saman gado a rigingine yana kallon p.o.p ɗin da aka ƙawata saman ɗakin dashi, ga fitulu masu ƙyau da ɗaukar hankaki, na daɗe tsaye a bakin ƙofa amma baiko motsaba balle nasan yasan na shigo, kaina na girgiza inaji a raina dolene nayi wani abu koyaya na dawo da kuzarinsa koda ba dukaba, dukda nasan ba sauƙi zan samoba haka na cije na ƙarisa gaban gadon, kwanciya nayi a gefensa na ɗaura kaina saman ƙirjinsa ina kallonsa, abin mamaki baiko motsaba fa, yatsana manuniya na ɗaura saman lips ɗinsa na fara zagayawa a hankali. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya da buɗe lumsassun idanunsa a kaina, gira na ɗage masa, na ɗan juya ƙwayoyin idona alamar “Yaya dai?”.
        Murmushi ya ɗanyi da gyara kwanciya ya juyo sosai muna fuskantar juna, hannunsa ya ɗaura saman gefen fuskata muna kallon juna cikin ido, sai dai yaƙi cewa komai, sai busamin numfashinsa kawai yake saman fuska kamar yanda nima nawa ke sauka akan nasa.
         “In baka wani labari”. Guntun murmushi ya ɗanyi, ya buɗe baki daƙyar yace, “A kanki kawai”. Murmushi nayi har haƙwarana na fitowa, na ɗaura hannuna nima akan fuskarsa ina ɗan murza gashin sajensa daya fito kaɗan da ƴan yatsun. “Bara na baka labarin farkon girkina”. Kansa ya ɗagamin yana lumshe ido. Na gyara kwanciyata sosai ina sake shigewa jikinsa, “Innata zataje anguwa sai ta barmin girki tace nayi kafin ta dawo, amma komai zan zuba na tabatar Innar Firdausi na a wajen, dan bata taɓa barina nayi girki ba, sai dai idan tanayi ta dinga sani na zuba abu harmu gama. Ni sarkin rawan kai inason na bama Inna mamaki tasan na iya girkin nima, sai kawai nahau hidima batare danama innar firdausi magana ba, da yake ita kuma tana ɗaki sai batasan hidimar da nake ba. Shinkafa da wake aka barmin nayi, kasan mina fara zubawa bayan na saka kayan miya, mai?”. Kansa ya girgizamin alamar a'a. Nai ƴar dariya, “Karfa kace zakamin dariya to”. “Ɗan kaɗan zanyi” ya faɗa a hankali. “Tab to na fasa gaskiya”. Da sauri yace, “Yi haƙuri wasa nake bazanyiba”. “Tam, in gaya maka na tsaida ruwan abinci bayan nayi komai dai-dai ɓangaren soya mai, kayan miya, da tsaida ruwa, na kawo magi da gishiri duk na zuba, saida ya tafasa saina zuba shinkafa...” cikin ɗan zaro ido yace, “Waken fa?”. Ƙaramar dariya nayi, “Yo waken sai da shinkafar tai rabin dahuwa sannan na wankesa na zuba na saka albasa na rufe inata murmushi ni na kammala komai, har wani imagine yanda Inna da Babana zasu kwashi girki nake a raina.
      Kasa daurewa Jawaad yayi ya shiga ƙyalƙyala dariya sosai, dukda naji daɗin ganin yana dariya saina saka hannuna kan bakinsa zan rufe ina kumbura fuska ni a dole naji haushi. Hannuna ya riƙe zai janye naƙi, nai azamar hayewa kansa na danne da ƙyau yanda bazai cireba, “Kafayi alƙawarin bazakayi dariya ba?”. Dagewa yay ya cijemin hannun, nai saurin janyewa ina fashe masa da kukan taɓara duk da dai da gaske naji zafin. “Ni ALLAH saina rama” na faɗa ina kai bakina kan hannunsa daya riƙe ɗayan hannuna. Take muka fara kokawa, shi yana dariya ni kuma ina saina rama da kukan da babu hawaye. Ba'akai dogon zangoba lissafin ya canja salo, duk kuma yanda naso ƙwatar kaina a hannunsa sai hakan ta gagara, yayi yanda yakeso daga ƙarshe ya koma lallashina kamar yanda ya saba.
            “Wai har yanzu fushin ne?”. Ya faɗa yana jawoni jikinsa. Sake tura baki nayi, nace, “Kuma indai mukaje gidan Umm-Anum bazan dawo nanba”. “Sai mu kwana tare a can ai”. Yay maganar yana ɗauremin gashi na daya gama gyarawa. Ɗagowa nai na kallesa, nace, “Dawa ɗin?”. Ya nuna kansa da ɗan yatsa. “Tab kayi ƙato da yawa bazaka kwanar mata a gida ba”. Ranƙwashi ya bani a kai mai zafi. Na dafe wajen idanuna na cika da ƙwalla. Ɗauke kansa yay tamkar baiganiba.

STORY CONTINUES BELOW

★★★★★★

               Duk yanda muka kai da zumuɗin ganin Umm-Anum a ranar dai bata yuwu ba, sai washe gari wajen goma na safe. Ni da Ummu da amintacciyar baiwarta muka farayin gaba akan su boss sai daga baya zasu biyomu shi da Takawa da mijin aunty Mahfuzah. Duk da bansan yaya manufar tsarin nasu yakeba hakan yamun.
        Tarbar da akai mana kawai zai tabbatar maka da ansan da zuwanmu, sai dai bawai da tunanin har dani ba, dan bayan Umm-Anum sun rungume juna da Ummu irin gaisuwar larabawa tana ɗagowa ta ganni, baki ta saki da mamaki, “Amaryan kwana takwas ne a saudia kuma?”. Kaina a ƙasa nidai ina murmushi ban iya bata amsaba, sai Ummu ce ta bata amsa ƙasa-ƙasa, bansan mitace mataba naga dai sunyi dariya.
       Yanda Anum ta rikice da ihun murna zai tabbatar maka itama batayi tunanin dani a zuwan ba, ta rasa inda zata saka ranta dan daɗi, tabi dukta katantaneni da labarai, ganin banga Anuwar ba nace mata, “Ina Yah Anuwar?”. Ɗakinsa ta nuna da hannu. “Tunda muka dawo ai baida lafiya, dafa jiya zai kona ƙasarku wai yayi mantuwa, shinefa Umm-Anum tace masa ai Ummu ma zatazo ya faɗa abinda ya manta ɗin tazo masa da shi. Ni nasan bawani mantuwa da yayi, so yake yaje ya ƙara ganin mijinki kawai Umm-Anum ta ɓata masa shiri, shinefa yaketa fushi da kowa a gidan tun jiya, yau ko makaranta yaƙi yaje”. Tausayinsane ya kamani, sai dai bancema Anum komaiba game da zuwan boss.
      Munyi kusan zaman awa biyu sannan Anuwar ya fito, wani irin taka burki yayi yana waro idanu waje. muryarsa har rawa take wajen faɗin, “Wai dama dake akazo?” ya ƙare maganar yana murza idanunsa da hannu. Murmushi nai masa hakama Ummu, cikin tsokana tace, “Dama kana gidan amma ko tarba babu Anuwar?”. Kafin yace wani abu Umm-Anum tace, “Fushi yake dan ya shirya ƙaryan komawa ƙasanku na ganosa na hana”. Kallonsa mukai da ga ni har Ummu, ya wani ɓata fuska da narketa a shagwaɓe. Dariya nayi kaɗan ina ɗauke kaina. Ummu tace, “Kaga manta dasu Anuwar kaji, lokacin da zamu rama yana zuwa ai”. “Yauwa Ummuna” ya faɗa yana zama kusa da ita ya gaisheta. Nima gaishesa nayi. Cikin hikima yaketa tambayata ina mijina? Da tsokana nikuma nake bashi amsar yana can mun baro. Da nace haka sai ya ɓata fuska ya ɗauke kai. Har raina sai nakejin tausayinsa, dan bamusan mi ALLAH ya ɓoyeba a al'amarin nasu da har suke masifar ƙulafucin juna irin haka.
           Bayan sallar zuhur Abbun su Anum ɗin ya dawo gidan, sai da ya zauna suka gaisa da Ummu sannan yake sanar da Umm-Anum gasu takawa nan a falon baƙi a shirya musu abinci akai. Da yake dama tasan da zuwan nasu saita hau shirya komai yanda ya dace, sai dai kallo guda zakai mata ka fahimci kamar a rikice take. Daga ƙarshe ma saita zauna tana mai dafe kanta. Aunty Mahfuzah ce tai azamar ƙarisawa gareta ta dafa ta, “Umm-Anum lafiya kuwa?. Kanta ta nuna mata da hannu alamar yana mata ciwo, Ummu da Aunty Mahfuzah suka kalli juna dansu su Ummu sun sanar dasu komai dama. Addu'a Aunty Mahfuzah tai mata sannan taɗanji ya sassauta mata, amma data miƙe sai tace jiri take gani.
      Anuwar ya fita salla bai dawoba, Anum da Bilkisu kuma suna ɗaki suma tunda suka idar da sallar basu fitoba, dan haka basu san wainar da ake toyawaba su.

            A falon baƙi Takawa ne zaune da mijin Aunty Mahfuzah abokinsa, sai Jawaad dake zaune a wani irin yanayi mai wahalar fassara, idanunsa sun kaɗa sunyi jazur, ya jingina da kujera saboda jin yanda ƙirjinsa ke wani irin mahaukacin bugu, ga jinin jikinsa sai tsitstsinkewa yake. Takawa ya kafesa da idanu na wasu ƴan mintuna cike da nazari kafin ya sauke gajeren numfashi yana maida dubansa ga Abu-Siddiq, shima ɗin dai kallon Jay yakeyi tun ɗazun cike da nazari, dan tun haɗuwarsu da Abunsu Anuwar gaba ɗaya yanayin Jawaad ɗin ya sake canjawa, shi kansa Abbun su Anuwar ɗin rikicewa yay jikinsa ya hau rawa saboda ganin tsananin kamar Jawaad da Anuwar ɗin, farine kawai Anuwar ya ɗara Jawaad. Duk da daman Takawa yay masa bayanin komai tunma kan suzo ƙasar hakan bai hanashi shiga gigita da ruɗani ba, sai dai baice komaiba bayan gaisuwar daya zauna sukayi, shine ya fita ya sanarma Umm-Anum ɗin da zuwansu shi kuma ya sake dawowa.
       Sam ya kasa haƙurin daina kallon Jawaad dake kwance cikin kujera idanunsa rufe, ba barci yakeba amma sam tunaninsa da hankalinsa basa tare da duniyar mutane, da za'a tambayesa wanene shi a wannan lokacin, bazai iya bada amsar komaiba. A wannan yanayin Aunty Mahfuzah da ma'aikatan gidan suka shigo suka shirya abinci gasu takawa.
          Duk yanda sukaso Jawaad yaci abinci sam ya kasa, daga ƙarshema yace musu kansa ke masa ciwo, kuma yana ganin jiri, wannan magana ta sake rikita Abbun su Anuwar, dan a irin halin daya baro Umm-Anum kenan itama a cikin gida. Shine yayma Jawaad addu'a, kafin ya sakashi dole cin abincin, gurasa ɗaya yaci da ƙyar ya tsame hannunsa. basu sake tilasta masaba dan sun fahimci bayama cikin hayyacinsa kamar.............✍4

Ku lallaɓa da wannan, yau na tashi banajin garin dai-dai nima😩
            
     Gaskiya a rage sakama Jay ido da yawafa ƴan Wattpad😂, dan kunfi kowa iya gulmar Jay na kula, su ƴan Telegram ƴan blue House ne, Yah Qaseem ɗinmu sukafi sama ido da Aunty Hudah🙄😣.6

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.7

Page 49

..............Kamar yanda Umm-Anum ta saba duk sanda takawa yazo Saudia ya kanzo har gidan su gaisa, domin dai a halin da take ciki su kaɗai takema kallon ƴan uwa, su kaɗai ta sani a yanzu sai mijinta sai ƴaƴan guda biyu, ta mance ita wacece? Ƴar wacece? Daga ina take? Daga ina ta fito?. Wani lokaci hikimar UBANGIJI kan sakata kawo wannan tunanin a zuciyarta, musamman ida tunaninta ya karaɗe ko ina a cikin duniya ta ga babu wanda ta sani sai ƴan Masarautar gagara badau, sai mijinta da danginsa dake anan, hakan kan ɗaure mata kai, sai dai duk yanda taso ta furta da baki kota tambaya bata iyawa. Idan hakan ta kasance takan zauna tasha kukanta ta share hawayenta.

    Yauma kamar yanda ta saba ɗin haka ta ƙimtsa ta fito cikin shirin zuwa gaida takawa, idan da Ummu yazo sukanje tare, idan kuma da amaryarsa ne tare itama suke zuwa, sai idan shi kaɗaine yazo sai taje tare da Anum su gaida shi ko Aunty Mahfuzah idan ta shigo. Yau kam sai suka ɗunguma gaba ɗaya, ita, Anum, Ummu, Bilkisu, sai Anuwar daya shigo gidan babu jimawa shima, dan tunda ya fita salla sai yanzu yake dawowa saboda baisan da Takawa sukazo ba balle yay tunanin harda Jawaad.
      Sallama sukai a ƙofar ɗakin aka amsa musu da ga ciki, tare da basu izinin shiga, jikin Umm-Anum sai tsuma yake tanata dai ƙoƙarin dannewa da karanto addu'a a zuciyarta. Anum da Bilkisu ne suka fara shiga, sai Ummu sai Umm-Anum, sai Anuwar a ƙarshe. Jay na kwance a kujera idanunsa a lumshe tamkar mai barci, sai dai shigowarsu falon ya saka ƙirjinsa wani irin mahaukacin bugu irin wanda tunda yake a rayuwarsa zai iya rantsuwa bai taɓa jiba, ya buɗe idanunsa a hankali zuciyarsa na wani irin masifaffen tsitstsinkewa. Akan Bilkisu da Anum da suka zauna gefen Abbun su Anuwar ya fara saukewa, ya maida kan Ummu da itama ta zauna a kujerar da takawa yake zaune, sai Anuwar dake tsaye tamkar gunki idanu a ware yana kallon Jawaad, da alama dai yayi sumar tsayene na bazata. Ya maida kallonsa ga dattijuwar mace data juya masa baya suna gaisawa da takawa, tana sanye da baƙar abaya ta naɗe kanta irin naɗin larabawa. Jiyay gaba ɗaya jinin jikinsa na wani bada zuuuu!! Zuuuu! Zuuuu, bazai iya daurewa har saita juyo garesa ba, a matuƙar ɗokance yake da son ganinta duk da cike yake da fargaba da tsoron kar hasashensu ya zama kuskurene kuma ba itaɗin bace ba. Ya miƙe a hankali ƙafafunsa na harharɗewa, yayinda bugun zuciyarsa da fitar numfarfashisa ke fita a matuƙar guje. Miƙewarsa tai daidai da miƙewar Umm-Anum itama fuskarta ɗauke da murmushi sun gama gaisawa da takawa tanason komawa kusa da mijinta ta zauna sai a ɗora firar, dauriya kawai take itama tana danne halin da take ciki. Lokaci ɗaya sukai tsaiii! Suna kallon juna, kallo mai wahalar fassara ga ma'abocin yinsa da wanda ke kallo, kallo mai saka razani da firgici da ban mamaki, kallo mai ɗarsa tausayi ga duk wanda idanunsa zai iya sauka a kansu shima.
          Ƙafafun Jawaad sun kasa ɗaukar gangar jikinsa, Mahaifiya ta wuce gaban wasa, jini ba ƙarya bane musamman irin na uwa da ƴaƴa, ko shekara dubu yay baigantaba saiya gane, shekarun data barsa bazai yuwu ya iya manta fuskartaba musamman da ya zam yana kallonta a hoto a koda yaushe, manyanta kawai da ƙiba da haske ta ƙara na alamun girma da jin daɗi. Ƙasa ya zube bisa gwiwoyinsa jikinsa na rawa, kansa na wani irin Masifaffen sara masa tamkar zai tsage gida biyu, cikin rawar harshe da kwararowar hawaye bisa kumatunsa yace, “Ummuna!”.
           Umm-Anum dake tsaye cikin mawuyacin hali da ruɗanin zuciya da gangar jiki idanunta kafe akan Jawaad ko ƙyaftawa batayi ta ɗaga hannu da ƙyar tana mai nuna shi da yatsanta manuniya jikinta na wani irin rawa, mai kama da Anuwar ɗinta! Wanene shi? Da ga ina yake? Ya akai kamaninsa da Anuwar ɗinta?! Mutum ɗaya tasan duk duniya yana kiranta da wannan sunan, sai dai wanene? A ina yake? A yaushe ne kuma?. Bakinta rawa yake amma ta gaza furta komai, sai tai luuuu baya zata faɗi.
      Wani irin wawan miƙewa Jawaad yayi ya tarota jikinsa, dai dai da zaburowar Anuwar shima yana ƙoƙarin tarota, sai kawai hanunsu ya haɗe waje guda suka tallafota a tare......
       Zumbur suma ƴan falon duk suka miƙe tsaye, banda Takawa kawai da ya dake abinsa duk da shima jikin nasa duk yay saƙwat. Da ga can Anum ta ƙwala kiran sunanta cikin kukan da takeyi tun farkon durƙushewar Jay a gaban Umm-Anum. Bilkisu ma hawayen takeyi.
      Abin tausayi da tashin hankali daga Jawaad har Anuwar kuka suke suna faman girgiza Umm-Anum da kiranta, Jay na faɗin, “Ummuna! Ummuna Please, Ummuna ki buɗe idanunki ki ganni, nine Jay-p ɗinku ke da Abbah, karkice ba hakaba dan ALLAH, dan ALLAH Ummuna zuciyata zata buga ki tashi ki ganni kicemin da gaske kece ba gizo idanuna keyiba, ba mafarkin dana sabayi bane, ba tunain danake dulmiyawa bane, ki tabbatarmin a zahirance kece tare dani Ummuna, kitashi kiga Jay-p ɗinku yazam Jay-p ɗin gaskiya, Dan ALLAH Ummuna karkice baki ganeniba  karkice baki sanibaaaaa”. Yaja (a) ɗin ƙarshe da  fashe da wanu irin kuka maiban tausayi da tsuma zuciya yana mai kife fuskarsa saman tata.
       Anuwar shima kukan yake yana faɗin, “Umm-Anum ki tashi da ALLAH, ki tashi ki faɗamin shiɗin ɗan uwanmu ne da gaske, wlhy inajin ƙaunarsa mai zafi a raina irin wadda ban taɓama wani mahaluki irinta ba, jinake tamkar zan iya rasa numfashina sabida shi, Umm-Anum dan ALLAH kice shiɗin jininmu ne Ummu”.
         Duk wanda yace baiyi hawayeba a parlorn nan ƙarya yake, hatta da Takawa saida yasa handkherchief ya tsane hawaye, Abbun su Anuwar ya saka gefen mayafinsa da larabawa ke sakawa saman kai ya share nasa hawayen, kafin ya taka a hankali shima ya durƙusa a gabansu ya ɗago kawunansu ya rungume a ƙirjinsa yana shafa kansu, fuskarsa ɗauke daɗan murmushi ga ƙwalla da suka sake cika idanunsa, a hankali yakai bakinsa saman kan Jawaad ya sumbata, kafin ya maida akan Anuwar shima ya sumbata. Cikin harshen turanci ya shiga lallashinsu da kalamai masu sanyi. Suna cikin haka Ambulance ɗin da Abbu-Siddiq ya kira asibiti ta iso, mata ma'aikatan asibitine suka shigo su huɗu, da taimakon su Jawaad da har yanzu jikinsa ke a sanyaye suka kamata aka ɗaura a gadon gungura mara lafiya, ma'aikatan asibitinne suka fita da ita, Jawaad da Anuwar suka take musu baya suma. Bilkisu da Anum ma miƙewa sukai da sauri sukabi bayansu. Duk miƙewa suma sukai domin binsu, amma sai Abbun Anuwar yace Abu-Siddiq ya maida su Takawa masauki su huta. Noƙewa Ummu tayi akan ita dai zatabi bayansu itama. Takawa baice komaiba suka fito gaba ɗaya, su Jawaad harsun wuce, su Bilkisu ma basu iskesu ba suna tsaye suna jiran fitowarsu Ummu, Ummu, Aunty Mahfuzah, Bilkisu, Anum suka shiga mota ɗaya suka bisu. Abbunsu Anuwar kuma dasu Takawa suma suka tafi a mota guda.3

STORY CONTINUES BELOW

        Da taimakon su Jay da suma suke a motar Ambulance ɗin aka fidda Umm-Anum zuwa cikin asibitin, abinka da inda kasan darajar ɗan adam, dan danan likitoci sukai mata caa da taimakon gaggawa, yayinda Anuwar da Jawaad ke tsaye aƙofar ɗakin da aka shiga da ita kowanne cike da tsantsar damuwa, kaɗan-kaɗan saisu ɗago su kalli juna, sai dai kowanne ya kasa magana ma ɗan uwansa ko sau ɗaya, dan harsunansu sun musu nauyi, burinsu kawai suga farfaɗowar rabin numfashinsu masoyiyar zuciyarsu mahaifiyarsu abin alfaharin kowa da tinƙaho.
      A wannan halin su Bilkisu suka ƙariso suka iskesu, da ga ita har Anum idanunsu sunyi luhu-luhu saboda kuka, Ummu duk tana riƙe da hannayensu. Idanu kawai Jay ya zuba musu amma bai iya cewa komaiba, sai Anuwar ne ya bama Ummu amsar tambayar da tayi akan ina Umm-Anum ɗin. Isowar su Abbu suma ya saka aka basu wajen zama, domin su Abbu sun kasance zuri'a sananniya mai daraja a ƙasar saudia musamman cikin birnin makka, nagartattun malamaine hafizan Al-Qur'ani mai girma, sunada manyan makarantu na addini da cibiyoyin magunan musulunci da suke badawa da sunansu ya zagaye lungu da saƙon birnin na makka da kewaye da saudia ke alfahari dasu a ɓangarori da dama na ƙasar.
      Anuwar da Jawaad dai sun kasa zama, sai da Abbu ya kamosu duk ya zaunar tare da zama tsakkiyarsu. Jawaad shi kaɗai yasan irin matsanancin ciwon da kansa ke masa, amma ya daure ya jure, sai dai ta jijiyar kansa data mimmiƙene kawai zaka iya fahimtar yana cikin mawuyacin hali. Hannu Abbu ya ɗaura akan Jawaad ɗin daya kwantar da bayansa jikin kujera ya lumshe idanunsa, hakan ya saka shi buɗe idanun da suke jajur ainun, addu'a ya fara karantowa yana tofa masa a kan nasa, Jay ya maida idanunsa ya lumshe jirin da yakeji na ƙara ƙarfi a cikin idanunsa. Luuuu ya kwanto jikin Abbu alamar shima dai koya suman kokuma wani abun dai daban, saurin ɗagosa Abbu yay yana girgizashi, amma ina numfashinsa yay ɗaf daga ƙirjinsa. Saurin miƙewa Anuwar yay shima jiki na rawa, hakanne ya jawo hankalin sauran suka fahimci abinda ke faruwa. Bilkisu ta cusa kanta cikin cinyoyinta ta sake fashewa da kuka mai tsuma rai. Hakama Anum ƙanƙame Ummu tai ta fashe da kuka tana faɗin, “Ummu shima yayi kamar na Umm-Anum”. Rungumesu Ummu tayi a jikinta daga ita har Bilkisu itama tana ƙoƙarin haɗiye hawayenta, ‘wannan wane irin tashin hankaline haka?’. Ta faɗa a ranta cike da tausayin wannan ahali.
      A take shima Jawaad aka ɗaukesa zuwa ɗakin kusa da Umm-Anum aka shiga bashi taimakon gaggawa domin ceto numfashinsa.

★★★★★★

           Saida sukai zaman awanni biyu cikin kuka da tashin hankaki sannan suka sami labarin farfaɗowar su, atake duk murmushi ya suɓuce musu, Bily ta saka gyalenta itama tana share hawaye kamar yanda Anum keta faman yi. Ba'a basu damar shiga ba dan duk ance suna buƙatar samun hutu musamman ma Umm-Anum da jikinta ya manyanta.
     Da wannan albishir ɗin suka sami ƙwarin gwiwar tafiya yin sallar la'asar da lokacinta yayi, kowa ya shiga miƙama UBANGIJIN al'arshi kukansa dan shine masanin duk wani sirri dake a binne tare da rahama ga bayin da aka zalunta kuma suka jurema jarabawar rayuwa batare da nuna ƙosawarsu ba. Sosai yin sallar ya ɗan basu ƙwarin gwiwa suka dawo asibitin, Abbu ya roƙa takawa akan suje su huta haka nan tunda ance sun farfaɗo ai. Daƙyar Ummu ta yarda, Bilkisu kam ƙasa tai da kai tana hawaye alamar batason tafiya. Takawa yay murmushi da yima Ummu alamar a barta anan ɗin da ido.
    Hakan kuwa akayi, bayan sun shiga sun duba su Jawaad da Umm-Anum suka tafi akabar Bilkisu da Anum da Anuwar anan, sai Aunty Mahfuzah, takawa kuma da Ummu da Amintacciyar baiwar Ummu da Abu-Siddiq suka tafi, sai Anuwar da Abbu suma suna nan. Suma dai bayan wucewar su takawan duk sai suka shiga suka dubasu suka sake fitowa suka zauna zaman jiran farkawarsu da musu addu'oi.
      Kasa haƙuri Abbun su Anuwar yayi yaɗan farama Bilkisu wasu tambayiyi game da Jawaad da ita kanta, danshi tabbas yana kallon wasu abubuwan na Bilkisu masu mugun kamanceceniya da Umm-Anum, tafiya, murmushi dama abubuwa da dama tun a wancan zuwan nata, hakan sai yasa kansa ya ƙara kullewa ya shiga tambayarta ko auren zuminci akai musu ita da Jawaad?. kanta a ƙasa ta bashi amsa da “A'a”. Ya tisa (a'a) ɗin nan ta bilkisu a ransa yafi sau dubu, dan shidai gaskiya bai yardaba akwai abinda ita Bilkisun bata saniba maybe, musamman yanda yake mata tambayoyin da amsoshin da take bashi. Anuwar dai da Anum da Aunty Mahfuzah na binsu da kallone da saurarensu.
        A haka lokacin sallar magriba yayi itama suka tashi suka gabarta, sun dawone suka iske Jawaad ya tashi, Abbu ne yace Bilkisu kawai ce zata shiga, badan Anuwar da Anum sunso ba suka haƙura.

STORY CONTINUES BELOW

         Tunda na shigo ɗakin idanuna a kansa suke, shiko nasa a lumshe tamkar mai barci har yanzun, yana kwance ne, amma yanzu an ɗago gadon sama ta wajen kanshi yanda kwanciyar ta bada style kamar yana a zaune. Na cigaba da takawa a hankali na ƙarasa garesa, Zama nayi dai-dai saitin fuskarsa tare da ranƙwafawa na sumbaci goshinsa, hawayen da suka cikamin ido suka ziraro suka ɗiga akan fuskarsa. Buɗe idanun yayi a hankali tare da riƙo hannuna cikin nashi, kallon cikin ido mukaima juna, wasu hawayen suka sake silalo mani na tausayinsa, abinda ban taɓa gani daga garesaba sai yau, (kuka) Boss ne gwanin dauriya da shanye abu yay kuka, kai mahaifiya dabance a rayuwar kowanne ɗan adam, mahaifiya tafi gaban wasa, mahaifiya mutum mafi daraja sama ga komai ga ƴaƴa. Na ayyana a raina ina matsawa jikinsa na kwantar da kaina a ƙirjinsa ina fashewa da kuka, dan nima haka kawai sai naji ƙaunar tawa mahaifiyar da kewarta, Innata gatana, innata abar alfaharina da tinƙahona harma da taƙama a dukkan daƙiƙa ta rayuwata.
       Jawaad da shima wasu zafafan hawayen da babu zato suka silalo masa ya ɗaura duka hannayensa saman bayanta ya rungumeta a jikinsa. Sunkai tsahon lokaci Bilkisu na kukan da shashsheka ta kasa ɓoyesa, Jawaad na kukan zuci da hawaye masu zafi da raɗaɗi. Buɗe ƙofar da akaine ya saka Bilkisu saurin ɗagowa dan ta zata su Abbu ne, shima babu musu ya saketa ta miƙe yana share hawayensa, itama nata ta shiga sharewa da bakin mayafin jallabiyar. Nurse ɗin daya shigo ya nema afuwarsu, dan ya jima yana sallama da knocking babu amsa, hakanne ya sakashi shigowa direct, dan tun daga can waje ta cctv'n da suke amfani dashi na ganin duk wanda ke a sashen da suke kula da shi ya gano ruwan da suka sakama Jay ya ƙare har jininsa ya fara zuƙa yana komawa cikin robar ruwan, shikam sam baima luraba saida Nurse ɗin ya kama hannunsa yana cirewa sannan suka gani shi da Bilkisu. Idanu taɗan ware waje na alamar mamaki, shikam sai ya lumshe nasa idanun ya maida bayansa ya jinginar kamar yanda yake da.
      Nurse ya kammala komai sannan ya fita su Abbu suka shigo duba Jawaad ɗin. Sannu sukaita jera masa da addu'oi, shi kuma yana amsa musu da kai dan harshensa ya masa nauyi sosai har yanzu baijin zai iya furta wata kalma ga kowa idan ba Umm-Anun ba. A rikice Nurse ɗin dake tare da Umm-Anun ta shigo tana sanar musu ta farka itama amma bata cikin hayyacinta.
    Rige-rigen fita aka dingayi a tsakaninsu, dan hatta da Jay ba'a barsa a baya ba shima. Tashin hankali kenan, yanda Nurse kusan biyar ke riƙe da Umm-Anum zai baka matuƙar tausayi, a take duk suka rufu a kanta banda Abbu dake tsaye kawai yana kallon yanayin nata cike da nazari, ajiyar zuciya ya sauke kafin yayma Nurse ɗin Umarni akan su sallamesu zasu koma gidan ciwon nata addu'a yake buƙata. Basu musaba dan sunsan shiɗin babban likitane mai bada magungunan musulunci wanda akema ɗakko marasa lafiya daga wata ƙasa mai nisa a kawo garesa balle matarsa kuma.
       A take aka shirya musu maidata gida. Hankalin Jawaad yay matuƙar sake tashi ganin mahaifiyarsa ta koma cikin asalin halin hauka kamar yanda tabar gida a wancan lokacin, su kansu su Anuwar ɗin hankalinsu a tashe yake dan basu taɓa ganin Ummunsu a wannan irin halinba, sundai san tanada wani rashin lafiya da takan fita hayyacinta lokaci-lokaci amma basu taɓa sanin dalilin motsawar ciwon nataba suma, da kuma Abbu ya dage kanta saita dawo normal kamilar mace. Anuwar yasha tambayar Abbu amma bai taɓa sanar masa komaiba sai yace lokaci na zuwa da zai sani.1

           Da isarsu gida Abu-Siddiq da Abbu suka rufi kan Umm-Anum da karatun Al-Qur'ani mai tsarki, hakanne ya ja hankali su Jawaad suma duk sai suka ɗaura al'awa suka zauna sunayi su duka har Bilkisu da Anum, kai harma da ama'aikatan gidan da Aunty Mahfuzah da yaranta itama dukda ƙanana ne ba'a barsu a baya ba. A hankali Umm-Anum ta fara lafawa daga bige-bigen da takeyi, ta buɗe idanunta dake jajur tamkar garwashin wutane a cikinsu tana binsu da kallo. Ba ƙaramin tsorata idanunta suka basu ba, amma hakan baisa sun dakataba suka cigaba, maidawa tai ta sake lumshewa tare da kwanciya jikinta na wani irin masifar rawa, sai kuma ta fashe da matsanancin kuka. Turaren magani Abbu ya tashi ya kunna, hayaƙi ya fara fita yana baje ɗakin. Wani irin gunjin kuka ta fara maiban tsoro tana magana cikin muryar da dagaji kasan ba tata bace. “Ku daina ƙonamu, dan ko zaku shekara dubu kuna ƙonamu bazamu bartaba, zamu gama jiyyane a jikinta batare da mun bar aikinmu ba, alƙawarine rubutacce zamu kasance da ita har ƙarshen rayuwarta, dan haka kuma bar wahalar da kanku babu inda zamuje, bazamu taɓa saɓama shugabanmu ba har abada dan shima bai taɓa saɓa manaba bisa umarninmu...!!”. Sam su Abbu basu sauraresuba suka cigaba da abinda sukeyi, hakama su Anuwar basu fasa nasu karatunba, yayinda Abbu ya cigaba da zuba magani kala-kala na hayaƙi a cikin Burne. Tun suna ihu har suka koma kuka da magiyar a daina ƙonasu kar'a halakasu suba laifinsu bane sakasu akayi. Zuwa wani lokaci kuma sai tayi shiru sai uwar zufa take tamkar an jiƙeta da ruwan zafi. Abbu bai dakata da abinda yakeba har saida yaji ta kirayi sunansa cikin sanyin murya. Ajiye abinda ke hannunsa yayi ya ƙarasa gareta ya ɗago, faɗawa tai jikinsa ta fashe da kuka mai ban tausayi. “Abu-Anuwar yau cikin mafarki naga wani abu maiban mamaki da al'ajabi, naga mai kama da Anuwar wanda tabbas inada alaƙa dashi”.
     Tashi Abu-Siddiq yay ya fita dan ya basu waje.
        Abbu dake shafa bayan Umm-Anum yana murmushi yace, “Ba mafarki kikeba zahiri ne”. Zumbur ta miƙe zaune tana kallonsa, sai kuma tai saurin dafe kanta da taji ya sara mata. Kamata yay ya kwantar yana faɗin, “Kiyi haƙuri ki kwanta ki huta zuwa anjima ko da safe idan ALLAH ya kaimu sai muyi magana, Alhmdllh nafahimci mun samu wani haske saɓanin da da bama ki taɓa makamancin wannan maganarba”. Umm-Anum dai batace komaiba hannunta na dafe da kanta, ahaka barci mai nauyi yay awon gaba da ita, dukda anata kiraye-kirayen sallar magriba bai hanataba.
       Sai da ya tabbatar barcin ya ɗauketa sosai sannan ya fito falo, Bilkisu da Anum yace su shiga suyi salla a ɗakin dansu dinga kula da ita, shi kuma suka fita tare da su  Abu-Siddiq salla masallaci. Tunda suka fita salla Abbu ya fahimci Jawaad bayajin daɗi, dan daya kama hannunsa sai yaji zafi alamar zazzaɓi na neman rufesa. Baice komaiba sukai salla suka zauna har isha'i itama suka gabatar sannan suka koma gida. Har lokacin Umm-Anum nata barci, su Bilkisu da suma suka idar da salla suna zaune sun zuba mata idanu cike da damuwa.
       Sashin baƙi Abbu yasa aka gyara, aka kaima su Jawaad abincinsu can, Abbu yace Anuwar yaje ya raka Jawaad itama Bilkisu Anum zata rakota.

STORY CONTINUES BELOW

____________________________________
★★★★★★★★★★★★★★★★★★★
____________________________________

               Duk wani masoyin su Momy hankalinsa a tashe yake akan ɗauke Shahudah da ɗan fir'auna yayi, abin ɗaure kai da ban mamaki shine duk yanda ƴan sanda suka bazu nemansa basu samu koda mai kama da shiba, dai-dai da wayarsa an kasa samunta ta kowanne yanayi, dama ita Shahudah tata wayar na nan bai bari ta ɗauka ba, duk kuma inda ake tunanin samun ɗan fir'auna anje babu shi babu abokansa.
     Hankalin kowa ya ƙara tashi, Momy kuka take kawai tana zazzagama Dad masifa ta waya akan ya dawo ita tashin hankalin nan yamata yawa, sannan ya saka Qaseem ya taho shima. Shidai lallashinta kawai yakeyi dan shima hankalin nasa aiba a ƙwance yakeba, yana matuƙar ƙaunar Shahudah fiye da zaton mai hasashe, shi da yake nesama dasu ya fisu tashin hankalin. A ranar ya sanarma Qaseem ya shirya ya koma gida zuwa gobe saboda halin da ake ciki. Qaseem dai ya amsa da “to” dan zuwa yanzun bai iyama Dad musu akan komai, duk abinda yace yayi shi yakeyi koda bai masaba. Tun a daren ya fara shirin komawa ƙasarsa ta haihuwa, dan dama hankalinsa bama a kwance yakeba a China'r saboda wata cuta da aketa raɗe raɗin ta ɓillo a wani yanki na ƙasar chain mai suna Corona virus, mutane duk a tsorace suke, daƙyar ya iya danne ransa yaje yayo wata ƴar sayayya da yake buƙata ya dawo hotel ɗin da yake ya kimtsa kayansa, insha ALLAH jirgin farko na gobe dashi zai tashi zuwa ƙasar Dubai cikin birin Abu-dabi, daga nan zai hau jirgin da zai sadashi ƙasarsa.

Ɗan-fir'auna ka sakamu a cakwalkwali😣🙄😏😒😠🚶🏻.

______________________________________
((°•°))((•°•))((°•°))(())(())((°•°))((•°•))((°•°))
______________________________________

                    Iya ƙofar ɗaki Anum ta tsaya tai min saida safe, kaina kawai na iya ɗaga mata batare da nace komaiba. Ƙofar na tura na shiga da sallama a bakina, falone madaidaici da aka zuba komai cikinsa, sai ƙamshi mai daɗi ke tashi a ciki. Na sauke kumburarrun idanuna akan boss dake kwance cikin doguwar kujera idanunsa rufe, nai masa kusan kallon mintuna biyu kafin na ƙarasa inda yake, durƙusawa nai gaban kujerar na ɗaura hannuna saman goshinsa, wani irin zafi naji zauu dan haka na rimtse idanu da sauri. Jin ya ɗaura hannunsa saman nawa na buɗe idonuna, hannunma akwai zafi shima, a rufe idanunsa suke har yanzu, “Yayanmu baka da lafiya ne?”. Baice min komaiba sai idanunsa dake jajur ya buɗe yana kallona. Hawaye naji sun cikamin idanu, yaɗan lumshe nasa idanun ya sake buɗewa a kaina da girgiza min kansa alamar kar nayi kuka. ban ankaraba naji sun silalo kawai, hannunsa ya ɗaura saman kumatuna ya shiga sharemin batare da yayi magana ba. Kusan mintuna biyar muna a haka kafin ya buɗe baki da ƙyar yace, “Kukan ya isa mana, haɗamin ruwa maiɗan zafi nayi wanka kozanji ƙarfin jikina”. Kaina na jinjina masa sannan na yunƙura na miƙe. Ƙofar dana gani a falon ya sakani tunanin itace bedroom, can na nufa kaina tsaye, koda na tura sai naga ƙaramin kicin ne, rufewa nai na nufi ɗayar ƙofar, itakam ina buɗewa nai tozali da bedroom babba. Numfashi naɗan sauke na shiga, ban wani zauna ɓata lokacin kalle-kalleba na shiga bathroom ɗin da shima ya kasance babba, komai tsaf an gyarashi, sai ƙamshin fresheners masu daɗi. Dai-daita ɗumin ruwan nayi yanda zai masa daɗi sannan na tara masa, komawa falon nayi na taimaka masa ya tashi zaune, dan da gaske bayajin ƙarfin jikinsa, amma duk da haka yamin nauyi sosai, haka dai na daure har muka isa bedroom ɗin, taimaka masa nayi ya cire kayan, ya rage daga shi sai singlet da boxer kawai, a haka na sake taimaka masa zuwa bayin. Duk yanda naso na zame na barsa yay wankan shi kaɗai bai yarda ba, yace na taimaka masa jikinsa sam babu wani ƙarfi, gashi yanajin jiri. Dole na daure nai masa yanda yakeso sannan na sake taimaka masa muka fito, har kayan barci an kawo mana dan haka na taimaka masa ya kimtsa yasha shayi da magani ya kwanta, bargo naja masa na rufesa na zauna gefen gadon ina kallonsa, shima dai idanunsa a kaina, bamu jima a hakaba barci ya kwashesa, ajiyar zuciya na sauke a hankali ina share ƙwallar da suka cikamin ido, duk wanda ya aikata al'amarin nan yacika baƙin azzalumi mai busashshiyar zuciya. Nima shayin kawai nasha, na ɗauki abincin na maida sashensu Umm-Anum sannan na dawo na shiga wankan nima. Gasa jikina nai sosai sannan na ɗauro alwala na fito, nima nai shirin barcin na haye gadon na kwanta tare da shigewa jikinsa da har yanzu yake zafi zau. Lumshe idanuna nayi ina sauraren yanda bugun zuciyarsa ke harbawa, a haka nima barci ɓarawa ya saceni.

WASHE GARI

                  
                Bayan mun tashi daga barcin da muka koma na safe wanka mukai, muna cikin tunani da zullumin kayan da zamu saka saiga sallamar Anuwar, boss ne ya amsa masa tare da zira jallabiya ya fita falon, babu jimawa sai gashi ya shigo da akwatinmu. Kallonsa nai da alamar tambaya, sai dai baice komaiba ya ɗora akwatin saman gadon tare da buɗewa ya ɗauka kayansa nima ya fiddomin nawa. “Kitashi ki shirya suna jiranmu, su Takawa ma sunzo”  yay maganar cikin dasashshiyar muryarsa da tun jiya bata dawo dai-dai ba. Kaina na ɗaga masa na miƙe.

        Tsaf muka fito cikin shiga ta kamala munata zabga ƙamshi, mun iske Anum a fallon su Umm-Anum zaune ita kaɗai da alama mu take jira, da girmamawa ta gaida Boss daketa faman kallonta ko ƙyafta ido bayayi. Nima muka gaisa sannan ta sanar mana duk suna falon baƙi mu ake jira.
        Duk suna zaune an baje abinci kala-kala a tsakkiyar falon, yanda muka samu Umm-Anum zaune cikin kamala ya sakamu sauke ajiyar zuciyar jin daɗi muka bisu ɗai-ɗai muka gaisar.
      Gaba ɗaya hankalin Jay akan Umm--Anum yake, kamar yanda itama nata hankalin na agaresu shi da Bilkisu, sai dai batace komaiba dan an bari sai anci abinci sannan ai zama akan hakan. Lafiyayyen breakfast ne da kowa ya tsinci kansa cikin jin daɗin cinsa, sai dai boss tsakura kawai yakeyi. hakama Umm-Anum bata wani ci sai kallon Jay take.
      Bayan an kammala aka gyara wajen tsaf sannan kowa ya nutsu waje guda..............✍😓1

wayyo idona wayyo yatsuna😢🚶🏻

16
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
7Page 5010


.................Shiru kakeji falon ya ɗauka bakaji motsin komai saina ajiyar zuciyoyi dana AC dake aiki. Sai da Abu-Siddiq yay doguwar addu'a kafin kowa ya sake maida hankalinsa ga takawa da yay gyaran murya alamar zai fara magana. Wata gyaran muryar ya sakeyi kafin yay sallama a garesu duk suka amsa, Cikin nutsuwa Takawa ya sake gyara zamansa.

         “Alhamdulillahi ala kulli halin, duk da dai bamu da tabbacin har yanzu Umm-Anum ta gane Jawaad matsayin jininta ina ganin ya kamata na fara warware abinda mu muka sani game da ita kafin muji abinda zai fito daga nata bakin yanzun”. Jinjina kai kowa ya shigayi cikin gamsuwa da jawabinsa.

         “Mun tsinci Umm-Anum a wasu shekaru da zan iya ƙiyastasu da kusan shekaru ashirin da takwas idan ban mantaba, a lokacin nazo gida daga india domin halartar bikin salla babba kamar yanda na saba a duk shekara, saukar dare nayi a ranar, dan sai kusan tara na dare ma na iso, amma kamar ko yaushe na iske sarkin mota na jiran isowata a airport ɗin. A gajiye nake matuƙa gaya dan haka bamu ɗau lokaciba muka bar airport ɗin, tafiyar mu bata wuci ta mintuna goma ba akan titi sarkin mota yaja wani wawan birki. Sosai gabana ya faɗi saboda ƙarar da aka ƙwalla mai nuna tabbacin mun bige wani, daga ni har shi fita mukai cike da tashin hankali. hakama mutane dake ɗan kai kawo a titin harsun fara taruwa a wajen. Ganin mace ce kuma cikin shiga ta kamala duk da babu lulluɓi tare da ita sai muka fara bincikar mutane ko akwai wani nata a wajen?, amma babu wani mai alaƙa da ita. Mun ɗauketa zuwa asibiti, duk da gajiyar da nake ciki bamu bar asibitinnan ba sai da muka tabbatar ta samu dukkan kulawar da ake buƙata a daren sannan muka wuce raina duk a dagule. A dalilin bige baiwar ALLAHr nan gaba ɗaya bikin sallar nan baimin daɗi ba, dan tun bayan farkowarta daga magagin ciwon bugetan da mukai sai muka fuskanci tanada taɓin hankali ma, taɓin hankali irin mai ban tashin hankali, dan duk da cikin halin ciwo da take ƙoƙarinta kawai ta gudu daga asibitin ita dai, dalilin hakan takai har sai da aka saka mata hand corps a hannu da ƙafa sannan aka samu ɗan kwanciyar hankalin ta, a hakanma fisge-fisge take ita kawai a barta ta tafi duk ta jima hannayenta ciwo da ƙarfen ankwa dana gado. Doctor ɗin shine ya faɗamin gaskiya da tabbatar mana cewar matarnan akwai wani babban al'amari tattare da ita, mizai hana mu haɗata da malaman musulinci. Wannan shawara tasa itace ta zame mana haske a kanta, sai kuwa na samu abokina Muftahu akan ya bincika min malamin da zamu kaita wajensa, shine kawai ya bani shawarar mizai hana mukaita Saudia wajensu Abu-Siddiq. Na amshi shawarsa da hannu biyu babu ɓata lokaci mukai duk wani ciku-ciku dagyar muka samu damar fita da ita zuwa nan saudia. A ganin farko dasu Abu-Sufyan sukai mata suka tabbatar mana akwai sihiri tattare da ita, dan kuwa tunda ta buɗe ido daga barcin da take dan allurar barci a kai mata tun da ga can kafin mu taho saboda gudun matsala, sai muka sameta a nutse babu wani bige-bige da takeyi sai dai alamar rashin lafiya na haukan yana tare da ita, alamun hakan na nufin can ƙasarne ba'ason ta zauna kenan ko wani abun daban da bamu da ilimi a kansa. Bayanin da mukaima Abu-Sufyan akanta ne yasa yace mubarta a wajensa na wani lokaci zasu cigaba da kula da ita. Nai masa godiya sosai bayan kwana biyu na koma india nabar Muftahu anan saudia. shima kuma bayan wani lokaci saiya koma. A koda yaushe muna magana da Abu-Sufyan ko Abu-Siddiq akanta da yanayin jikinta, sannan Muftahu nata ƙoƙarin bincike game da ahalinta acan gida, sai dai babu wani haske da muka samu game da samunsu. Bayan wani lokaci jikinta yay sauƙi sosai ta koma normal Alhmdllh, sai dai kuma ta manta komai dangane da kanta, batasan ko itaɗin wacece ba, daga ina ta fito? duk ta manta har sunanta, wannan shine ya ɗarsa tausayinta a zuciyar Abu-Sufyan yace shikam zai aureta har ALLAH ya kawo iyakar komai ta gane ahalinta. Tunda yaymin bayani sai ban musaba, dan uba nike kallonsa bawai yayan aboki kawai ba, na kuma tabbata shine kawai zai iya riƙe amanar baiwar ALLAHr da bata da kowa tunda hatta kanta da sunanta tama manta, ya bada gudunmawa sosai gameda jiyyar mahaifina shima, har kawo yanzu kuma yana badawa a dukkanin al'amurana dana zuri'ata, babu abinda zance a garesu sai addu'ar fatan gamawa da wannan rayuwar lafiya su samu sakamakon aljanna a ranar sakamako”.

       Tunda Takawa ya fara magana hawaye kawai kowa ke faman sharewa, Abbu yace, “Tabbas duk abinda ya faɗa hakane, abinda kawai ya manta bai faɗaba shine ciki dake tare da ita, sun kawota da ciki kwantacce da bamusan adadin wataninsa ba, kamar yanda ya nuna, dan sai da muka dage da addu'oi da magani matuƙa sannan ya fara motsi alamar abinda ke cikin yana raye, da alama dai akwai sharrin jinnu a al'amarin kokuma wata hikimar UBANGIJI daya ɓoye game da cikin wadda zuwa yanzu munga ƙalilan daga ciki shiyyasa ya ɓuya a jikinta, tashin da cikin yayi sai yazam watanninsa ya koma baya, dan saiya koma wata uku, sai da tai wata shida sannan ta haihu Namiji, shine yaci suna Muhammad Anuwar gashi nan, bayan haihuwarsa ne mukai aure da ita ta haifi Anum kuma, ga tanan tana da shekaru ashirin da uku, daga ita dai bata sakeba har zuwa yanzun”.

     Cikin rawar jiki Anuwar ke kallon Jawaad, sai kuma ya kalli Abbu ya kalli Umm-Anum da ke zaune shiru ta zabga tagumi tana hawaye, dan abubuwa da dama ne keta dawo mata cikin rai tun a daren jiya, hatta da sunanta ta manta sai a daren jiya ta tuna shi. Hannunta dake rawa ta miƙama Jay dake kallonta ko ƙyafta idanunsa bayayi,  a hankali ya miƙe ƙafafunsa tamkar an dokesu ya nufota, ta riƙe hannunsa ta zaunar da shi kusa da ita tare da rungumesa ta fashe da kuka, shima Jawaad hawayen yakeyi. A take falon ya ɗauki sabon koke-koke har saida Abbu ya fara musu nasiha akan hakan sannan suka tsagaita. Anuwar ya taso shima ya zauna kusa da Ummu, kafin ya tashi ya koma jikin Jay yana sharɓar kukansa, Jawaad ya rungumesa da ƙyau yana murmushin farin cikin samun ƙanne. Tasowa itama Anum tayi tazo ta zauna ƙasa ta ɗaura kanta saman ƙafar Jawaad, ya sake murmushi da shafa kanta yana lumshe idanunsa da kai hannu ya share mata hawaye itama. Wata irin ƙaunarsu mai tsananice ke ratsa dukkan ɓargonsa da jini, ji yake a duk duniya yau babu kamarsa a cikin masu nasara, jinsa yake tamkarma su kaɗaine a cikin duniyar babu wani mahaluki mai numfashi da ya rage bayansu ɗin, wani sanyi mai sanyaya kuzari na shiga cikin tsokar jikinsa tana ratsa dukkan ɓargonsa da jijiya.

       Cikin dasashshiyar murya Umm-Anum tace, “Tabbas niɗin na taɓa aure, bankuma taɓa tuna hakanba sai a daren jiya, na auri wanda yake matsayin yayana a gidanmu dukda ba iyayenmu ɗaya ba, matar babanmu ce da ya aura bayan rasuwar innarmu ce mahaifiyarsa, itama kuma mijinta ya rasune, shine iyayenmu sukai aure, suka kuma haɗemu suka riƙe tamkar tare suka haifemu, Auren soyayya mukayi da Abdul-aziz, shiɗin mutumne mai himma wajen neman nakansa, sannan mutumne mara hayaniya da damuwa da gudun ƙyale-ƙyalen duniya, mutum ne ma'abocin son noma da kiwo, mai tsananin son ƴan uwa da zuminci, shine auta a gidansu kaf, shi kaɗai kuma mama maryam ta haifa a gidan, baida wa baida ƙani dan haka yay mana gata sosai ni da ƙannena lokacin da mahaifiyarsa ta dawo aure gidanmu. Bayan aurenmu mun samu jarabawar rashin samun haihuwa na tsahon wasu shekaru harma dana abubuwan more rayuwa, kafin na fara haihuwar kuma yaran su rasu, sai daga baya harma mun fidda rai da wata haihuwar sannan ALLAH ya azurtamu da samunsa (ta nuna Jawaad) lokacin da muka samesa Abdu-aziz ya bunƙasa, dan harkokinsa na noma da kiwo sun kaisa har ƙasar turai dalilin zaman mutunci da wasu turawa da sukai aikin dam ɗin ƙauyen garinsu, abinda kawai zan iya tunawa bayan wannan game da rayuwata shine, sunana BILKEESU, sai mahaifina, sai ƙannena uku mata, Mariya, Rahmah, Wasila, sai Mama maryam, saiko shi dana bari, sai Abbansa dana tabbatar ya rasu, wannan shine kaɗai abinda zan iya tunawa game dani da rayuwata ta baya kafin gushewar komai”. Ta ƙare maganar hawaye na ziraro mata.

     Jawaad da shima ke hawayen ya saka hannu ya share mata yana girgiza mata kai alamar ta bari, muryarsa a ɗashe yace, “Na godema ALLAH da yasa kika tunani Ummuna, na kwana da tsananin fargabar kar kice baki tunani ba koma baki sanni ba gaba ɗaya, da hakan ta kasance na tabbata sai dai ku binne gawata a yau Ummuna, na godema ALLAH da yasa kina raye, na godema ALLAH da ya ƙaddara sake haɗuwarmu a duniyar nan, na godema ALLAH daya jarabceni da son wadda ta silarta yau nake a jikinki Ummuna, (yay maganar yana nuna Bilkisu) na godema ALLAH daya haɗa dangantakarta da zuri'ar Takawa har nima nakai ga zuwa garesu, su ɗin shugabannine da adalcinsu yakai kowanne yanki, kowacce ƙabila, suyi fatan zamowa masu mulkinsu Ummuna, mutanen nan uku haskene babba a gareni da suka haskamin hanyata zuwa gareki”.

         Share masa hawayen shima tayi tana miƙama Bilkisu dake kuka hannu alamar itama tazo, da ƙyar BILKEESU ta miƙe zuwa garesu tana haɗa hanya, Umm-Anum ta sakata a jikinta tana maijin ƙaunarta har ƙarƙashin ruhinta, “Ɗiyata ashe ƙaunar da nake miki tun ganinki na farko bata wasa bace, ALLAH yay miki albarka kinji, ALLAH ya ɗaukaka rayuwarki ya saka mata albarka ya baibaiyeki da alkairi da rahamarsa mai tarin yawa”. Gaba ɗaya falon aka amsa da amin.

     Ummu dake murmushi tace, “Haka rayuwa take, ƙanƙanin abu sai yazama silar warware babba, kunga dai yanda aka ɗauki tsahon shekaru wajen addu'oi da neman ahalin Umm-Anum, amma sai gashi cikin sauƙi Wallet ta zama silar komai......” Ta shiga bama su Umm-Anum labarin komai game da haɗuwar Bilkisu da su Safah a Ladies mirror, da dagewar Safah akan saita tafi da Wallet ɗin bilkisu masarauta, har silar komawarta hannunsu...

        Sosai al'ajabi ya kama su Umm-Anum sukaita sake jinjina al'amarin da girmama hukuncin UBANGIJI mai shirya yanda yaso a lokacin da yaso ga wanda yaso cikin hikimarsa.

       Duk godiya suka shiga sake jera ma su takawa da addu'oin fatan alkairi, dasu Abbu ma kansu suma har saida takawa da Abbu sukace ya isa haka sannan. Akwai sauran magana sosai a bakin Takawa dan ya fahimci akwai wasu abubuwan da yawa dake a ɓoye wanda Umm-Anum bata iya tunawa ba, shima kansa Jawaad dai akwai magana a bakinsa musamman game da haukar mahaifiyarsa da abubuwa ma da dama, sai dai yayi shiru ya barma ransa, so yake ya samu nutsuwar zama sake nazari da fashin baƙi akan komai, su kuma keɓe da matarsa su tattauna kozai ƙara samun haske daga gareta dan kowa da irin baiwarsa. To yanda duk tunaninsu yake hakama na Abbu da Abu-Siddiq yake, su kuma sunason su keɓe ne da Jawaad sumasa tambayoyi game da family ɗinsa, dan sunji Umm-Anum bata tambayi komaiba akan komai ma, alamomi da yawa kuma sun nuna akwai abinda ke binne, bazasu fahimci hakanba sai sun sami sanin ainahin tarihin komai tun daga tushe sannan.1


STORY CONTINUES BELOW

         Kiran sallar zuhur ne ya tashesu daga wannan zama, matan suka shige cikin gida sukuma mazan suka fita massallaci.

       Bayan an idar suka dawo akaci abincin rana, Jawaad dai tsakura yay tayi yanzun ma, baici na kirki ba, hakama Bilkisu, Umm-Anum da take jinta sakayau yau tanata lura dasu sai dai batace komaiba har aka kammala aka tashi.

        Takawa, Abbu, Abu-Siddiq suka fice masaukin su takawa dan su masa rakkiya yaje ya huta. Bilkisu kuma Umm-Anum ta tsareta ta kwanta barci, acewarta yanayin bily ya nuna barci takeji, kasa mata musu tayi ta kwanta, itako ta ɗaura kan bily saman cinyarta tana shafa mata kai har barcin mai nauyi kuwa yay awan gaba da Bilkisun, Anum dake ta tsegumi Umm-Anum tabar yayinta itama tazo ta raɓa bayan Bilkisun ta kwanta da yake a ɗakin Umm-Anum ɗinne. Ummu da Aunty Mahfuzah kuwa sun tafi can gidan aunty Mahfuzah ɗin suma.

        Anuwar da Jawaad kuwa suna can sashen baƙi suma, Anuwar ya tsare Jay akan ya bashi labarin Abban su, sai shagwaɓa yake masa. Jawaad dake kwance cikin doguwar kujera yay murmushi idanunsa akan Anuwar dake zaune a ƙasan darduma jikin kujerar da yake a kwance hannunsu sarƙe dana juna. Cikin muryarsa dake a sanyaye yace, “Dear nima bansan Abba ba sosai, abubuwan da zan iya tunawa game da shi basu da yawa, dan banfi shekara bakwai ba ya rasu, sai dai kakanrmu mama maryam bata gusaba sai da ta maidamin tarihinsa tamkar karatu, dan sai da na haddacesa a cikin kaina tsaf, daga ni har kai da shi muke tsananin kama, musamman ma kai daka biyo har hasken sa, abubuwa ƙalilanne muka ɗakko Ummuna. Inada videos da dama da akayi lokacin da yake shugabancin ƙasarmu, ta hakane nakejin kamar na rayu da shi rayuwa mai tsaho...........”

        Da sauri Anuwar ya ƙara ƙanƙame hannun Jawaad dake a cikin nashi yana faɗin, “Suna tare da kai yanzu?”. Murmushi Jawaad yayi ya kai hannu ya shafi kan Anuwar, “Da ganinka ɗan karan gaggawa ne da kai da rashin haƙuri yaron nan”. Yanda yay maganar da jan hancin Anuwar a ƙarshe ya saka Anuwar ɗin ƙyalƙyalewa da dariya, shima Jay murmushin sa ya sake faɗaɗawa yana maijin daɗin ganin Anuwar ɗin cikin nishaɗi. Wayarsa ya ɗauka ya lalubo folder da ta kasance duk hotunan Umm-Anum ne da Abban su sai shi. Miƙama Anuwar yay, jikinsa har ɓari yake wajen son amsar wayar abin tausayi, kallo ya shigayi yana hawaye sosai, hakan yasa Jawaad lumshe idonsa yana haɗiye abinda ya tarar masa a ƙirji na tausayinsu musamman ma Anuwar ɗin. Saurin buɗe idanu Jay yayi danjin yanda Anuwar ya fashe da kuka, ya kafesa da ido shima yana ƙoƙarin danne tasa zuciyar, “Haba my sweet Darling kamar ba namiji ba, kukan ya isa haka kaji lilly na”. Yay maganar da tashi zaune ya rungume Anuwar ɗin yana mai shafa masa baya, har saida yaji yayi shiru ya koma sauke ajiyar zuciya sannan ya barsa. Labarin ahalinsu da mahaifinsu ya cigaba da bashi cikin kulawa, wani gurin Anuwar yay kuka wani gurin yay dariya, haka suka kasance har akai kiran sallar la'asar, wanka Jawaad ya sakeyi da gaggawa suka fita massallaci.


         Umm-Anum ma ta tada su Bilkisu sukayi tasu, bayan sun idarne ta saka mai aikinsu ta kawo abinci, zaunar da Bilkisu tayi tana faɗin, “Zauna na baki abincin nan da kaina, kwana biyu da zuwanku duk kun fara ramewa ke da mijin naki saboda rashin cin abinci, ina dalili”. Murmushi nayi cike dajin kunyarta, yanda take ƙoƙarin yin hausa sai abin keban dariya dan hausar kamar bata bahaushiya ba, wani wajenma kakarewa take ta kasa faɗa.

      Duk yanda nakejin kunyarta haka na ringa amsar abincin da take bani da hannunta, sallamar su boss ta sakamu maida hankalinmu garesu, idanunsa a kaina dan haka nai azamar ɗauke nawa na maida ƙasa. “Kaima zo ka zauna” Umm-Anum ta faɗa idanunta akan Jawaad dake kallonsu cike da sha'awa dajin daɗi. Hannunsa ta riƙo ta zaunar ɗayan gefenta, ta ɗiba abincin takai bakinsa, “Haa!” ta faɗa kamar yanda akema yara. Ƙwallane suka cika idanun Jawaad ya buɗe bakinsa a hankali ta zuba masa, taunawa ya shigayi yana kallon yanda take sakama Bilkisu itama, gabansu Anuwar yazo ya durƙusa shima ya buɗe baki wai a basa. Umm-Anum ta zuba masa tare da dungure kansa. Anum ma zuwa tai ta tsugunna tana faɗin, “ALLAH nima sai an bani to, anma manta dani kamar banice autar ba”. Sosai abin ya bama Jawaad nishaɗi, su Bilkisu suka shiga yima Anum dariyar tsokana.

    Hannunsa Jay ya ɗauraye, shima ya ɗiba ya kai bakin Umm-Anum, amsa tai tana murmushi ta shafa kansa da ƙoƙarin haɗiye hawayen da suke neman taho mata, murmushi Jay yayi ya ɗiba ya bama Anuwar shima, sannan ya bama Bilkisu da kunya ta kusan halakawa, Anum itace ƙarshe. Daka gansu kasan suna cikin farin ciki mai tsanani.

      Haka suka ƙarasa wannan yini tare, har zuwa dare dan Abbu yau a gidan Uwargidansa ma yake ba nanba, hakan ne ya ƙara bama Umm-Anum damar sakewa da ƴaƴanta har dare ya farayi, daƙyar ta daure tace suje su kwanta haka nan gobe idan ALLAH ya kaimuma ranace ai. Da wannan kowa ya nufi makwancinsa badan sun gaji da kasancewa tare ba.


STORY CONTINUES BELOW

          Sai da muka gama shirin barci muka kwanta, ina jikinsa a lafe kamar wata mage yana shafa bayana a hankali, fitar numfashinmu yana dai-daitane da sautin bugun zuciyarmu, “Miema kinyi barci?” ya faɗa a hankali cikin kunne na. Kaina na girgiza masa da ɗago fuskata dake cikin ƙirjinsa na kalli fuskarsa, shima kallona yakeyi. Murmushi mukaima juna, ya ɗan sumbaci goshina kafin ya sake maida idanunsa cikin nawa. Maida nawa nai na lumshe dan nakasa jurar cigaba da kallon cikin idanun nasa. Baice komaiba sai sake turani da yay jikinsa ya rungume da ƙyau. A haka barci yay awon gaba damu.

★★★★★★★


           Mun cigaba da kasancewa a cikin Saudia tare dasu Umm-Anum cike da tsaftatacciyar soyayya da tarin ƙauna mai daraja daga garesu, tattalinmu take tamkar wasu ƙananun yara ni da boss, yayinda a koda yaushe ƙannensa ke nane da shi, yanayin waya sosai dasu Oga Hafiz musamman akan aikin da a yanzu mukasa gaba na ƴan fyaɗe, a yanzu haka dai su Jabeer suna ƙoƙarin miƙa wasu samari kusan goma sha uku kotu akan case ɗin fyaɗen, sannan sunce sun samu case huɗu masu kamanceceniya da nasu Amina. Duk da muna nan saudia muma aikin mukeyi musamman ma boss, danni wataranma A wajen Umm-Anum nake yini komu tafi makarantarta. Har gidan Uwargidanta an kaimu, abin ya birgeni sosai yanda aka tarbemu tamkar ba kishiyoyi ba, a raina nace ‘kaga inda ake kishin ilimi, ba irin na ƴan ƙasarmu ba na hauka’.


        Randa muka cika kwanaki bakwai a saudiya boss ya fara samun kira daga wajen aiki, dan mun wuce ƙa'idar kwanakin da aka bamu na hutu, duk yanda yake da son aiki da ƙwazo saina fahimci bayason komawa yanzun, nima dai bason komawar nakeba sam, amma yaya zamuyi hakan tilasne a garemu kodan ɗunbin ayyukan da muka baro.

       A ranar yayma Umm-Anum magana akan binmu, sai dai abin mamaki da al'ajabi a take ta nuna ɓacin ranta akan bazataje ba, shiru mukai kawai duk muna kallonta, yayinda fuskar Boss da Anuwar ta nuna tsantsar ɓacin rai akan hakan. Kafin suce wani abu akan hakan Abbu yaja hannunsu suka fice daga gidanma gaba ɗaya.

      Wannan al'amari ya tsaya min a zuciya, dan yinin ranar gaba ɗaya wuni Umm-Anum tai cikin ɓacin rai, yayinda na yini nikuma cikin nazarin komai da fashin baƙi a kai.

     ★•°•★°•°★•°•★°•°★•°•★

                 A ɓangare su Jawaad suna fita daga nan wucewa Abbu yay dasu masaukin takawa, tattaunawa suka shigayi game da abubuwa masu dama, Abbu yace, “kuyi haƙuri kubar ɓacin rai kunji, itama ba laifinta bane, babu yanda za'ai taƙi son zuwa ƙasarta kodan shekarun data ɗauka bata cikinta, al'amarin bai baku mamakiba yanda har yanzu bata iya tambayar kowa daga ahalin nata ba, tunfa washe garin zuwanku har yanzu bamu sake zaman tattauna komaiba, tama ƙi ƙara nuna tana buƙatar jin komai, hatta da yanda ka rayuwu bayan barinta gida bata tambayeka ba Jawaad. Wannan babban al'amarine daya dace ace an zauna anyi dogon nazari a kansa. Shi sihiri a jikin ɗan adam abune mai wahalar yakicewa, musamman irin nata da ba'asan dalilinsa ba ma da sarƙaƙiyar sa, shifa mai sihiri baya gajiyawa da ƙoƙarin ɗaura wani akan wani, dan ya riga yayi imani da yin wannan shirkar itace ƙarfin ikonsa, har yanzu akwai sihiri tattare da mahaifiyarku, wanda inaji a raina akwai wani abu da aka binne wanda saimun tonosane komai dake jikinta zai iya warwarewa harmu fuskanci matsalar gaba ɗaya, bakuma wai dan addu'oin da muke basa ƙarɓuwa bane, ita rahamar UBANGIJI da kariyarsa bata taɓa gushewa ga wanda ya dogara da shi kuma yayi imani ya riƙe gaskiya, gaskiyar ɗan adam bata taɓa ƙarewa sai dai ace ƙaryar wane ta ƙare, dan haka mucigaba da bin komai mataki-mataki insha ALLAHU komai zai zama labari ne, Jawaad idan babu damuwa ka bamu haske dangane da family ɗinku ko zamu samu wani haske”.

          Duk sun gamsu da maganar Abbu, dan haka Jay ya shiga basu tarihin rayuwar mahaifinsa da Umm-Anum kamar yanda kakarsa mama maryam ta shaida masa komai bata ɓoye masa ba. Ya cigaba da faɗin, “Ban taɓa zargin kowa a zuri'ata game da iyayena ba, dan babu wani alamun cutarwa dana taɓaji ya shiga tsakaninsu da mahaifina harya bar duniya, sai dai maganar gaskiya lalurar hauka da Ummuna ta gamu da shi a ranar rasuwarsa abin tambaya ce, ada ban taɓa ɗaukar hakan komaiba sai kwanannan da matata tai wata magana data kasa barin raina, na cewar a al'amarin Ummuna akwai alamomin sihiri, dan mutuwar Abba bai kai ace ta kasa jure ƙaddara ba har ta kaita da ciwon hauka, ciwo ma irin wanda mutum baison zaman gida, bayan duk musulmi yasan mutuwa wajibine ga mai rai. Abinda kuma naji daga gareku a yau da wanda ya faru ranar ya tabbatar min akwai abinda bamu saniba dake a ɓoye tabbas”.

        Abbu ne ya sauke ajiyar zuciya yana gyara zamansa, yace, “Tabbas kamar yanda ka faɗa Muhammad akwai ababen tambaya masu yawan gaske akan al'amarin, ko sunanta sai a jiya na taɓaji, kai tsaye bamu da damar zarigin kowa akan wannan al'amarin, musamman idan mukai dubu da marigayi yayi shugabanci na ƙasa, ƙasarma babba irin taku, bazai yuwu ace baida maƙiyaba koda kuwa suna a kusa da shine. Sihiri gaskiyane, hakama addu'a waraka ce, sai dai wani lokacin sai kaga kamar ka ɗauki lokaci kana addu'ar babu biyan buƙata, ba haka bane, UBANGIJI maijin kukanmune a koda yaushe, mai kuma magance mana damuwarmu ne a koda yaushe, wani lokacin ita addu'a idan kayita takan jinkirta da ga abinda ka roƙo a kansa, saita zama kariyane ga wani al'amarinka ɓoyayye da kai kanka baka san da shi ba, mahaifiyarku ta jima cikin wani hali na jarabawa, mun kuma ɗauki lokaci muna gayama UBANGIJI, bamu taɓajin mun ƙosa ba, domin mun tabbatar shi kaɗaine mai badawa, yana jinmu, kuma yana ganinmu, yana kuma sane damu, jinkirtawar warwarewar komai ba yana nufin bai karɓi kukanmu ba. a yanda kuma nakeji a raina addu'armu ta kasance da kai, kai kanka, dan duk waɗanda suka iya tauyeta kaima abune mai sauƙi su ɓaddaka, inaga damuwa akan saita biku ba shine ya kamata ba, bincike akan ainahin miya faru shine ya dace domin mu samu bakin zaren, dan ko Anuwar bai kamata ya biku ba”.

       Kallon Abbu Anuwar yayi cikin tsagwaron tashin hankali, kafin yace wani abu Takawa yace, “Wannan tunanin shine a raina nima Abu-Sufyan, Anuwar kayi haƙuri kaji, indai ƙasarmu ce zakaje ka rayu har saika gaji ma, amma ba a irin wannan lokacin ya dace ba, dan abubuwa da yawan gaske na zuwarmin a zuciya game da al'amarin nan, sai dai banason furta komai nafison matsayin Jawaad na jami'in tsaro shi yay wannan tunani, zuwan Umm-Anum da Anuwar ba shine abu mai muhimmanci ba a yanzu ƙwarai da gaske, dan komai ma zai iya faruwa inhar azzaluman da suka ƙulla al'amarin suna tare dasu ne, kai koma nesa da su suke suna bibiyar al'amarin komai dan nima nayi makamancin wannan rayuwar nasan sarƙaƙiyar cikinta, amma kai Jawaad minene a ranka?”.

       Zama Jawaad ya gyara cike da kaifin basirar da ALLAH ya azurtashi da ita shima yace, “Na gamsu da duk abinda kuka faɗa, dan nima a kwanakin nan sune suka zama abin nazarina, rashin tambaya ta komai da Ummuna batai ba yafi komai tsayawa a raina sosai, ni a yanzu shirina na farko shine lallaɓata naji waɗanda sukai rayuwa dasu kamar ma'aikatan gidan da sauransu”.

     “Tunani mai ƙyau” cewar Takawa da Abu-Siddiq. Jawaad ya cigaba da faɗin, “Sai abokai makusanta da Abbah ya rayu da su kafin shigarsa siyasa da hawansa mulki, abu na uku ne bamu da dama a kansa, dan a wajen Ummuna ne kawai zamu iya jin wasu sirrika game da rayuwar Abba da ƴan uwansa a lokacin da yake mulki, dan haka wannan na ajiyesa gefe zanyi anfani da waɗancan damar guda biyu mugani ko za'a dace, amma nima na gamsu da basai sun bimu ɗinba kam yanzun”.

        “ALLAH yay maka albarka” cewar Abbu yana dafa kafaɗar Jawaad dake a kusa da shi. A tare suka amsa da amin. Abbu ya cigaba da faɗin, “Nima nanda sati guda zan biyo bayanku dan inason ganawa da Abba (Alhaji Babba). Kai Jawaad ya jinjina masa yana ɗan murmushi da faɗin, “ALLAH ya tabbatar Abbu”. Da Amin duk suka amsa..

       Akan wannan shawarar taron ya tsashi, shi dai Anuwar badan yasoba ya haƙura akan binsu Jawaad, dan yay masifar ƙwallafa ransa da zumuɗin son ganin ahalinsu.


       

★★★★★★★★


           Cikin hikima Abbu ya samo sunayen ma'aikatan da su Umm-Anum sukai rayuwa dasu a gidan gwamnati da kafin hakan, harma da sunayen abokan Abban Jawaad ɗin data iya tunawa da ƙyar.

        Sai kuma ta nema tada hankalinta akan komawar su Jawaad ɗin, ta kafe akan ita bazata barsu su koma ko inaba sunzo kenan. Duk yanda Jawaad dake cikin damuwa shima yake ƙoƙarin mata bayani akan aikinsu da buƙatarsu da akeyi taƙi fahimta, tamaƙi sauraren komai, saima ta saka masa kuka daga ƙarshe. Wannan abu ya sake tada hankalin Jawaad sosai, dama dauriya kawai yakeyi. Da ƙyar aka shawo kanta da lallashi akan Jawaad da Bilkisu zasuje su ajiye aikinsu ne su dawo nan da zama gaba ɗaya wajenta.

        Wannan batu ya sakata yarda, amma sunsha gargaɗi akan karsu daɗe basu dawo ba, dan da farko ma catai Jawaad yaje shi kaɗai yabar bilkisu ita anan, sai da Abbu ya sake wata sabuwar dabarar ya lallaɓata sannan tadai barsu suje ɗin, sukuma dawo akan lokaci kamar yanda ta faɗa, inba hakaba zata aika a ɗakkosu koda basu gama shiryawaba.


       Da wannan yarjejeniya daba tabbatacciya ba muka baro ƙasar saudia cike da kewa ni da boss. su Ummu kam can muka barosu dansu sati biyu zasuyi.

         Saukar yamma mukayi ƙasarmu ta haihuwa, inda muka iske Sadiq yazo tarbarmu, dan shikaɗai yasan da dawowar tamu, dama tunda muka tafi boss bai yarda munyi waya da kowaba bayan su oga Aliyu, su Ummah duk yaƙi yarda yay waya da su, dan baiso suji komai da wuri harsu kasa daurewa su sanarma Alhaji babba, a yanzunma da muka dawo bazai faɗa musu komaiba gudun matsala.............✍


Asha sauran weekend lafiya🤒😣🚶🏻🚴🏼

*_Shin kina ko kana sa sha'awar koyon ilimin ICT?_*


*_Ko kuna da sha'awar yadda ake hada cartoon?_*


*_Ko kana da sha'awar yadda zaka bunqasa kasuwancinka ta hanyar online?_*


*_Matsalarki ko matsalarka rashin makarantun da zasu koyar dake/kai ilimin computer ta fannnin larabci?_*


*ALBISHIRINKU KANAWA*


*_Kukanku ya qare,matsalarku tazo qarshe,shahararren kantin nan na yanar gizo wato RAHAMALLS yazo muku da makarantar koyon sarrafa computer a sauqaqe wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI)_*

_Sun tanadarmuku qwararrun malamai wanda zasu koyar daku bisa tsarin da kuma cikakkiyar qwarewa ta yadda zaki fahimta fiye da yadda kuke zato_


*ga masu buqatar aji na musamman har cikin gidajensu,makarantar ta shirya tsaf don baku darussa har cikin gida*


*sannan akwai tsarin ajujuwa na musamman bisa yanar gizo wato(online classes)*


*kaidai maza garxaya ka tuntubesu akan wanannan lambar waya*


08033990209

*_akwai ragin kaso hamsin cikin dari na kudin registration ga kowanne dalibi_*👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

6*_Shin kina ko kana sa sha'awar koyon ilimin ICT?_*


*_Ko kuna da sha'awar yadda ake hada cartoon?_*


*_Ko kana da sha'awar yadda zaka bunqasa kasuwancinka ta hanyar online?_*


*_Matsalarki ko matsalarka rashin makarantun da zasu koyar dake/kai ilimin computer ta fannnin larabci?_*


*ALBISHIRINKU KANAWA*


*_Kukanku ya qare,matsalarku tazo qarshe,shahararren kantin nan na yanar gizo wato RAHAMALLS yazo muku da makarantar koyon sarrafa computer a sauqaqe wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI)_*

+

_Sun tanadarmuku qwararrun malamai wanda zasu koyar daku bisa tsarin da kuma cikakkiyar qwarewa ta yadda zaki fahimta fiye da yadda kuke zato_


*ga masu buqatar aji na musamman har cikin gidajensu,makarantar ta shirya tsaf don baku darussa har cikin gida*


*sannan akwai tsarin ajujuwa na musamman bisa yanar gizo wato(online classes)*


*kaidai maza garxaya ka tuntubesu akan wanannan lambar waya*


08033990209

*_akwai ragin kaso hamsin cikin dari na kudin registration ga kowanne dalibi_*👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽Page 5116


..................Gidan duk ya ajiye ƙananun ƙura, duk da ko'ina a rufe yake, haka na daure naɗan gyara ɗakinsa dan mu samu inda zamu kwanta, kafin a kira sallar magriba na kammala, shikam wanka ma yayi ya fita tun fara aikin nawa. Bai dawo gidanba har saida akai sallar isha'i, kusan tara sai gashi ya dawo mana da abinda zamuci. Gaba ɗaya banajin daɗin yanayinsa, ya koma min Boss ɗin dana sani a office mara walwala da yawan magana, komai nake sai dai yayta bina da ido kawai, abincinma da ƙyar na samu yaɗan ci yace ya ishesa, nima cire hannuna nai a ciki na ɗauke kaina gefe. “Miye hakan?”. Ya faɗa muryarsa can ƙasan maƙoshi. Ƙoƙarin miƙewa nai tsaye nace, “Na ƙoshi nima...” kafinma na gama rufe bakina naji caraf ya cafko hannuna ya maidoni ya zaunar, kallonsa nai ina kumbura fuska, ya zabgamin harara tamakar idanunsa zasu faɗo ƙasa, “Ina wasa da ke ko?”. Ƙasa nai da kaina dan bazan juri kallon nasaba, “ALLAH nima na ƙoshi to”. Banza yaymin bai tanka ba, ya ɗebo ya kawo bakina, zan ɗauke kaina yay saurin faɗin, “Kinsan ALLAH idan baki shiga hankalinki ba sai na sauya miki kamanin wannan fuskar taki, malama haa”. Idanuna cike da ƙwala na buɗe bakin, ya ko zubamin yana sake zabgamin harara da yin ƙwafa, inaji ina gani yaymin ɗurar dole, shiko yaƙi ya ci, sai yogurt yaɗan sha, hakanne yasa naɗan samu kwanciyar hankali. Kasancewar a gajiye muke ga mai gayya mai aikin baya tare da walwala, gashi zamu koma aiki gobe idan ALLAH ya kaimu sai mukai kwanciyarmu da wuri.2


WASHE GARI


           Tun kiran sallar farko na tashi, cikin sanɗa na fita daga ɗakin nasa, kasancewar barcin da muka kwanta da wuri sai na tashi jikina babu nauyi sosai, da wannan damar na fara rage aiki. Koda ya fito zai tafi massallaci ya ga ina aikin gyaran babban falo baice dani komaiba ya fice abinsa, ajiyewa nai nima na koma ɗaki nai salla, ina idarwa ban hutaba na sake fitowa na cigaba, ana idar da salla shima bayan wasu ƴan mintuna sai gashi ya dawo, bayan mun gaisa shima sai ya cire jallabiyar jikinsa ya shiga tayani aikin. Duk da na roƙesa ya bari zan ƙarasa tunda na kusa bai saurareni ba, sai da yaga ya rage bedroom ɗina kawai sannan ya barni na ƙarasa.

          Ƙurar dana gani tasa nake sharo har ƙarƙashin gado kamar yanda nayi a ɗakinsa da ƙarƙashin kujerun falo ma, abu na sharo a ƙarƙashin gadon, wanda ya sakani dakatawa da sharan nasaka hannu na ida jawosa dan naga minene, wallet ce ƴar karama dan bata kai girman normal wallet dana sani ba, kamar zan buɗe sai kuma na ajiye da tunanin ko tashice, saman mirror na ɗaurata na cigaba da sharan harna kammala komai, ganin lokaci yaja na shiga bayi dan yin wanka sauri-sauri, ban wani ɓata lokaciba na fito. Idanuna ne suka sake sauka akan wallet ɗin nan, duk yanda naso na share a yanzun sai na kasa hakan, na matsa gaban mirror ɗin ina goge fuskata da ƙaramin towel dake a hannuna da hannun haggu, na damar kuma sai na fara ƙoƙarin buɗe wallet ɗin, ɗan ƙaramin hoton dana fara cin karo da shine ya sakani shiga mamaki, na fara fiddo abubuwan cikin wallet ɗin gaba ɗaya, ƙirjina sai wani irin mahaukacin bugawa ya keyi, banma san lokacin dana saki towel ɗin hannun nawa ba jiki na rawa, harda zufa ta fara tararmin a goshi, nagama zazzage komai a ciki, abubuwane masu muhimmanci da daraja dana san maisu bazai taɓa sakaci dasu ba da har zan gansu anan, to wama ya kawosu? Ni dai babu wanda ya taɓa zuwamin nan gidan a kaf mutanen gidan balle nace a mistake wani yazo da su. A fili nace, “To kodai boss ne ya kawo?”. Wannan tambaya na yitane badan zuciyata ta gamsu da ita ba, Duk da sallamarsa da naji a bayana ban iya na waiga ba.

       Ƙarasowa yay yana ɓata fuska ganin bama ta shirya ba, ya ajiye ƙaramin tiren da ya ɗoro musu tea a saman table kafin ya ƙaraso inda take yana jan tsaki. Ganin ko motsi bataiba har yanzu tanata juya abu a hannu sai kansa ya sake ɗaurewa, “Wai kina kallon agogo kuwa Miemaa!?”. Ya faɗa a ƙausashe. Ɗagowa nai ina kallonsa, cikin rawar baki da fargabar amsar dazan iya samu nace, “Dan ALLAH kaine ka kawo wallet ɗin nan ɗakin nan?”.

        Baice komaiba ya tako gabana tare da riƙo hannuna duka biyu yana kallon abinda ke ciki, cards ne masu muhimmancin gaske, ga sunan maisu kuma ɓaro-ɓaro a jiki da hotunan sa, “Ina kika ganta ke?”. Gado na nuna masa batare da nayi magana ba, ya kafe hannayena da nake sake jujjuya cards ɗin ƙo ƙyaftawa bayayi, nikam ƙirjina sake bugawa ya keyi da sauri-sauri, jira kawai nakeyi yace wani abu, amma yaƙi cewar. Hawaye suka sulalomin ina mai fatan kar abinda keta zomin arai ya kasance hakane, kai banama fatan hakan, sai dai idan anason min yawo da hankaline dan a ɓata masa suna. Muryata na rawar kuka nace, “Kace wani abu dan ALLAH boss”. Kansa kawai ya girgizamin yana mai cije leɓensa na ƙasa, ya saka hannu ya amshi komai dake hannuna ya maida a wallet ɗin ya sakata aljihu, taimakamin yay na shirya ina hawaye, wata gigitacciyar tsawa data nema haukatani ya dakamin, “Ke komai kuku! kuka!! kuka!!!, komai abin kukane a gareki, ya isheni haka banason ji kuma, malama ki sharemin waɗanan banzayen hawayen kafin nai miki bugun kayan wanki wlhy a gidan nan!!!”. Na matuƙar tsorata da yanayinsa, na koma jikin madubi na maƙure ina ƙoƙarin haɗiye kukan, gaba ɗaya kamanninsa sun masifar sauyawa, idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, baice dani komaiba ya juya ya fice daga ɗakin. Sake fashewa nai da kuka ina faɗin, “Ya ALLAH ka bani haske akan wannan al'amarin”. ƙarar takunsa dana jiyo ya sakani saurin goge hawayen na juya ina saurin ɗaukar soson hoda nahau shafawa. Bayana yazo ya tsaya yace, “Agogon wanene wannan?”. Da sauri na juyo gabana na faɗuwa na zubama hannunsa idanu, kusan mintuna biyu na ɗago na kallesa, Kaina na girgiza masa alamar ban sani ba. “Kin tabbata?”. Na ƙara ɗaga masa kaina. Bai sake cewa komai ba ya koma bakin gado ya zauna tare da ɗaukar kofin tea ɗaya ya fara sha yana cigaba da kallon agogon kafin ya ajiyesa gefensa. Ganin ya kafeni da idanu nai sourin ƙarasa kimtsawa zuciyata nata kaikawo da tunane-tunane kala-kala waɗanda gaba ɗaya sake zurma zuciyata suke a firgici. Tea ɗin ya ɗauka ya miƙamin, babu musu na amsa dan a yanda yake ɗinnan zai iya mammakeni idan nai masa gardama. Ni nafara fita daga ɗakin nakai kofunan kicin na ɗauraye da sauri-sauri na fito, a falo na iskesa jikkata na gefensa ajiye. Ɗauka nai tare da briefcase ɗinsa, baice dani komaiba nai gaba ya bini a baya, shine ya kulle ƙofar sannan muka ƙarisa inda Sadiq ya goge motar ƙal yana jiran fitowarmu shi da maigadi, mun gaisa dasu cike da girmamawa, suka buɗe mana motar muka shiga bayan kowannenmu ya karanto addu'ar fita daga gida.


STORY CONTINUES BELOW

             Tunda muka fice daga gidan hankalinsa nakan wayarsa, yayin da ni kuma na afka kogin ruɗaɗen tunanin da gaba ɗaya kwanyar kaina ta gaza ɗauka. Jinai kawai an riƙo hannuna, na juyo na kallesa, baice dani komaiba ya matsoni jikinsa tare da aza kaina bisa damtsen hannunsa yana shafa bayana. Shiru nai ina haɗiyar zuciya da hawayen dake taho mani.

        Tunda Sadiq ya tsaida motar muke ta yima station ɗin kallon mamaki, duk da dai safiyace sosai baici ace babu mutane haka ba, sai securitys da keta kai kawo, Sadiq ya buɗe masa ya fita, kafinma ya zagayo ta wajena nidai na buɗe da kaina. Na ƙara ɗan wawwaigawa na kalli ko ina, station ɗin tsit kamar babu kowa a ciki.

       Shima kansa kallon ko ina yake da mamaki, amma baice komaiba, ganin bai amsa jikkarsa ba nasan so ya ke saina kai har office ɗinsa kenan? Tare muka jera, baya bari ya tseremin da ko step ɗaya. Shine ya buɗe ƙofar, muna shiga kawai sai mukaji abu kanmu ana mana wanka da shi. Saurin ƙoƙarin fara share fuskkokinmu mukayi, amma abin yaƙi daina zubowa, sai ma ihun ma'aikatanmu da tafi daya karaɗe wajen. A sannan ne abun ya daina zubowa, muka share na fuskarmu sannan muka kalli juna kafin mu maida ga kallansu. A take kunya ta kamani kuma, dan gaba ɗayansu sukayo mana caa a ka da kalmar “Muna tayaku murnar aure!”.

      Murmushi Jawaad ya daure ya saki duk da iya fuskarsa ne, kafin ya maida dubansa ga Bilkisu datai ƙas da kanta, ya kamo hannunta cikin nasa yana faɗin, “Mun gode sosai, ALLAH yabar zuminci”. Ya ƙare maganar da kai hannun Bilkisu saitin bakinsa ya  sumbata. tafi aka sakeyi, sannan kowa ya nufosu da ƙyautar dake hannunsa, tun jay na amsa har hannunsa ya cika bilkisu ma ta fara amsa, jabeer ne ya matso ya taimaka musu aka tarasu waje guda ya sake musu godiya itama bilkisu tai musu ranta fal mamaki.

        Gaban ƙaton cake ɗin da akai da hotonsu aka jasu, daga bilkisu har jawaad ɗin dai murmushine shinfiɗe a fuskarsu, bazaka taɓa gane sunada damuwa ba, bily ta fara ɗaura hannun ta saman wuƙar kafin Jay ya ɗaura nasa saman nata suka yanka. Ita ta fara cirar ɗan guntu ta saka masa a baki, yay mata murmushi mai sanyi ya ciro kaɗan itama ya saka mata yana jawota jikinsa ya rungume, saboda ganin yanda Rose take musu wani irin mugun kallo mai cike da tsana da takaici yay hakan, da farko baiyi niyyar bama Bilkisu cake ɗinba, amma saboda Rose yayi dan yana lure da ita ko kalma ɗaya bata togaba na tayasu murna, hakama wasu daga cikin matan gurin sai baƙin rai suke da bankama bilkisu harara..

     Nanma tafin akayi, kafin Sir Ahmad ya farayin jawabin taya murna a garesu kasancewarsa head of department nasu, daga nan sauranma suka sake tayasu murna da fatan alkairi da bama Jay hannu suna musabaha, matan kuwa Bilkisu suke bama hannu itama suna mata, shikam Jay sai dai su ɗaga masa dan sunsan ƙa'idarsa ce baya hannu da mace ko wacece ita a station ɗin nan ko tana a gaba da shi kuwa sai dai a kuskure. Suma mazan duk da Bilkisu na ƙasansu hakan bai hanasu mata murna ba, tanata amsawa a kunyace dan wasuma ko magana ita bai taɓa haɗata da suba sai yau.

          Sai da aka gama ɗan kace nace sannan suka wuce office ɗinsa, ƙyaututtukan da suka samu kuwa tuni Jabeer ya saka an kaisu ciki dama.

              Jikkarsa na ajiye masa saman table ɗinsa na ɗan kallesa, ganin hankalinsa nakan files ɗin saman table ɗin ya ɗauki ɗaya yana dubawa saina ce “Sai anjima” kawai na juya zan fita. Caraf naji an riƙoni, kafinma na juyo ya maidoni baya ya jingina da table ɗin, kallonsa nai da mamaki, ya ɗan harareni batare da yace komaiba naji saukar laɓɓansa kawai saman nawa babu zato.

       Idanuna na lumshe kawai ban masa wani musuba ko sau ɗaya, dan inhar zai huce ta hakan to Alhmdllh, rabonsa dako kissing ɗina tun randa mukaje Saudia. Ganin da gaske yake sai kawai na shiga bashi gunmawa, nidai fatana ya samu nutsuwa wannan fushin da fusatar dana gani tattare dashi ya gushe. Burrum aka turo ƙofa babu ko neman izini, ƙoƙarin janye kaina nayi amma ya hanani kowacce dama, saima sake turani jikinsa yayi sosai da sake sauya salon sumbatar, ƙamshin turaren rose da naji ya sakani nima canja salo dan ta bani haushi ɗazun, dan batamin magana ba sam, nakuma gaisheta taƙi amsamin. Jin ta fita da gudu tana kuka ya janye kansa da ƙyar yana jan tsaki da harar ƙofar. Kallonsa ya maido gareni yana hararata, hakan ya sakani sakin murmushi dan harga ALLAH dariya ya bani, to ni miye laifina kuma?.

      Kaina ya dunguremin da faɗin, “Idan kika cigaba da wannan noƙe-noƙen da sanyi saita cigaba da raina miki ai, ki kwana da shirin cewar ke matar Jay ce a station ɗin nan yanzun ba budurwarsa ba”. Ya ƙare maganar a hankali cikin kunnene kamar mai raɗa. Lumshe idanuna nayi ina murmushi, bance komaiba na ɗauka jikkata nasa a kafaɗa sannan na kallesa, shima kallona yake, murmushi na sake sakar masa da ɗaga masa yatsun hannuna biyu alamar bye-bye. Kafin ya samu damar cewa wani abu harna fice abina daga office ɗin.

          A jikin ƙarfen lifter na iske Rose tsaye sai cika take da batsewa, kallo ɗaya nai mata na ɗauke kaina, “K!!” ta faɗa a daƙile, banza nai mata tamkar banjiba na haye lifter ɗin abuna, wani tsalle tayi zata cakumoni naji muryarsa a bazata kanmu, “Koda kuskure karki sake wlhy hannunki ya taɓamin mata”. Ya faɗa a kausashe. Murmushi nayi da ɗage masa gira na ɗauke kaina, banajin amsar da take bashi dan nayi nisa da su, ina sauka kuma na sake ɗaga masa yatsun hannuna, shima ɗagomin yay, nai gaba abina na barsu bansan yaya suka kwashe ba.1


STORY CONTINUES BELOW

        Bily na ɓacema ganinsa ya juya office batare da ya sake ko kallon inda rose take ba, ta cika tayi fam da baƙin ciki tamkar zatai bindiga a wajen. Ganin zai shige sai tabi bayansa a guje. Tana shiga office ɗin yana zama a kujerarsa, tsabar wulaƙanci sai yay kamar baisan ta shigo ba ya fara ƙoƙarin haɗa Computer ɗin saman table ɗinsa.

     Kuka maicin rai Rose ta fashe da shi tana dafe tebirin da hannu biyu, “Boss! Ni zaka wulaƙanta akan yarinyar da tazo station ɗin nan jiya-jiya? Ni zakaci amana ka yaudara saboda waccan ƴar tatsitsiyar yarinyar da bata wuce ɗiyar cikinka ba?, ko kunya bakaji kake iya nuna ƙaramar yarinya matsayin matarka wai?”.

          Jawaad ya ɗan lumshe ido yana buɗewa akan Computer ɗin da ya kunna, jikkarsa da bily ta ajiye masa ya ɗauka ya buɗe batare da yama rose ko kallo ɗaya bama balle tai tunanin samun amsa.

       Rose dake binsa da kallo ta sake fashewa da kuka tana faɗin, “Yanzu nan boss ina maka magana kana sakemin wani wulaƙancin?”. Sake yimata banza yay yama fara aikin gabansa. A wannan yanayin su Jabeer suka shigo office ɗin dan sunyi knocking har kusan uku yanaji ya share, shigowar tasuma baisa ya ɗago ya kallesu ɗin ba, su dai suka zauna a kujerun gaban tebirin suna kallonsa suna kallon Rose dake kuka. Hafiz ya jawo kujerar dake can gefe shima ya zauna yana jan ƙaramin tsaki dan shifa Rose takaici take bashi da halintan nan.

         Ganin yamaƙi kallonsu Jabeer yace, “Boss wai mike faruwa ne?”. Bai tankaba bai kuma kallesun ba yanzuma, dama cikin damuwa yake, ya fito gida da fushi, ita kuma yanzu sake kunna zuciyarsa take tana cikowa saman ƙirji, idan kuma har ta bari takai masa wuya to lallai zatayi nadamar biyosa office ɗinsa tana masa ihu a kai.

       Jabeer zai sake magana Aliyu ya girgiza masa kai alamar kar yayi, Rose ɗin ya kalla da take kallon Jay tamkar zata haɗiyesa, kuma har yanzu kukan take, “Rose miya faru?”. Juyawa tai ta kalli Aliyu hawaye na sake ziraro mata, “Aliy na gaji wlhy, na gaji da wulaƙancin da boss yake min, dan na soshi shine ya zama laifi? Shekara nawa na ɗauka tare da ku, kuma ban gazaba wajen nuna masa ina sonsa tun yana tare da wancan matar tasa, ya cemin shi bashi da ra'ayin yin mace fiye da ɗaya, karka manta har suspension yasa aka bani lokacin da matsalarnan taku ta faru, saboda ina sonshi na haƙura na mance da komai kamar bai faruba, yazo suka rabu da matansa muka tafi U.S ɗin nan, babu roƙon da ban masaba muyi aure a lokacin tunda dai ai baida mata, amma ya dinga shareni da zancen har muka dawo, yanzu duk ƙoƙarin nan da nai masa bai ganiba sai daga ƙarshe ya auri wannan yarinyar da tazo jiya-jiya cikinmu, bakuga yanda ya yarfani a gabanta ba yanzun, mi take da shi da har zai wulaƙantani a kanta?”.

       Kasa magana duk sukai, dan wannan faɗan kam dai yafi ƙarfinsu, duk da sunsan komai, amma ita rose banda haukarta ai ba lallaine ka SO a SOKA ba ko? Su shaida ne boss bai taɓa cewa yana sonta ba, sannan bai taɓa wulaƙantata ba. Hafiz ya taɓe baki cikin takaici yace, “Ikon ALLAH, so kike ya wulaƙanta matarsa a kanki kenan komi? Mtsoww! Lallai aiki ya sameki, kuka kuwa yanzu kika fara s.....” hannunsa Aliyu ya riƙe da sauri yana murmushi, yasan hafiz da iya yaɓowa mutum zafafan magana, yanzu sai ya sake birkitata. Duk da hakan kuwa sai da Rose ta hayayyaƙo ma Hafiz akan dama ta lura ita tuni ya tsaneta.

       Da sauri Jay ya bugi tebirinsa, cikin tsananin ɓacin rai ya nuna mata ƙofa yana faɗin, “Rose fitarmin a office!!”. Rose ta nuna kanta tana faɗin, “boss ni ka.......” cikin ƙaraji ya katseta ta hanyar sake doka tebir ɗin, “Nace! Ki fitarmin daga Office”. Yanda taga idanunsa sun masifar kaɗawa ya sakata firgita, tasan shi tasan shiɗin wanene idan yay fushi, ta kuma san abinda zai iya aikatawa bayan hakan, ta kalli su Jabeer ta sake kallonsa.

     Tashi Jabeer yay ya kama hannunta ya fitar da ita dan ya tabbata wlhy idan har ta sake wasu mintuna bata fitaba komai yazo masa rai zai aikata mata, sai da ya kaita har waje sannan yace, “Rose miyasa kikai haka? Kinfa san wanene boss?”. Zatai magana yace, “Kinga kije zanzo na sameki muyi magana, amma Please ki daina masa haka babu ƙyau, wlhy na tabbatar yana ɗaga miki ƙafane darajar kina cikinmu, kinsan fa yana gaba dake, sannan boss bayason raini, kije zanzo ni da Aliyu mu sameki”.

     Badan taso ba ta tafi tana sharar hawaye da kissima irin tashin hankalin da zata saka Bilkisu a station ɗin nan.1


STORY CONTINUES BELOW

(🤔Rose mi kike ƙullawa kuma?).1


★★★★★★★


         Tana fita Jawaad ya daki kujerarsa daya tashi akai yana faɗin, “Wlhy yarinyar can saita bar aiki a cikinmu, kai ama station ɗin nan gaba ɗayansa”. Da sauri Aliyu ya taso yana faɗin, “Please Boss! calm down, don't waste your time for her, ba yanzu ya kamata ai wannan ba”. Hafiz yace, “Gaskiyane maganar Aliyu boss, micece rose da har haukarta zai dameka, nifa dama can bataimin ba, duk da tana da ƙwazo tana da siffofin mutane masu bala'in son kansu, ka barta saita gama shagala bazaka ɗauki matakin komai a kanta ba sannan ka ɗauka. Amma idan aka maida mata murtani a yanzu anma damu da ita kenan, abinda kawai za'ai mata shine winning, ayi bala'i bala'in winning ɗinta akan Mami, idan tace zata shigar mata hanci kacimin ubanta iyakar iyawa”.

        Ƴar dariya Jabeer da ya shigo yayi jin furucin Hafiz ɗin, ya zauna yana faɗin, “ALLAH kai mugune Hafeez”. Zama duk sukayi suma, Hafiz yace, “ALLAH kuwa jabeer haukar yarinyar baimin ba, haka ake so ne banda hauka?, ni dama ni tace tana so ALLAH kuwa ko, hummm”. ya ƙare maganar da cije leɓe irin na tsantsar mugunta. Basu Jabeer ba hatta Jay sai da ya murmusa yana mai girgiza kansa, dan yasan Hafiz shegen kansane a iya mugunta.

     Ya sauke ajiyar zuya da jan guntun tsaki. Aliyu yace, “Kayi haƙuri boss, mu munzo musha labarin Honeymoon shashashar ta wargaza komai”. Harara ya balla musu, dan haka suka kwashe da dariya suna tafawa. Jabeer yace, “Wlhy Jay kayi wani ɓul-ɓul da kai fa, ka kuma ƙara haske”. “Kana baƙin ciki ne ɗan sa ido?”. Jay ya faɗa yana jefa masa biron hannunsa. Dariya suka sake kwashewa da ita.

            “Mtsoww, kufa wataran shashashancinku yawane da shi wlhy, ku ajiye wannan shiriritan muyi abu mai muhimmanci, kosu sir Ahmad banje na gaida ba, so nake mu gama sannan, dan na dawo da ayyuka masu yawan gaske, amma inason na fara jin mike tafiya daga wajenku?”.

          “Akwai nasarori masu yawa da zasu sakaka farin ciki kuwa, dama mun barsu ne harka dawo muyi maka surprise”. Murmushi Jay yayi mai sanyi da jin duk ɓacin ran daya toshe masa ƙofar zuciya yana faɗawa. Aliyu ya ajiye masa files ɗin hannunsa. Ɗauka Jay yayi ya fara dubawa, a take fuskarsa ta bayyanar da annuri, sai da ya gama dubasu duka sannan ya ɗago yana kallonsu, “Woow! Ina alfahari daku sosai da sosai wlhy, gaskiya kunmin babban albishir mai darajar gaske, yanzu kuna nufin waɗanan duk sunzo hannu? Kun gama mana da waɗan nan ayyukan?”. Jabeer yace, “Ƙwarai ma kuwa, dan wanda yasa aka kashe jami'inmun ma yanzu haka gobe za'a miƙasa kotu”.

           “Masha ALLAH, gaskiya naji daɗi wlhy, kuma nayi farin ciki sosai, maganar yaran canfa?”. Jawaad ya faɗa yana miƙewa ya ɗakko wani file a drawer ɗin bayansa.

      Yanzunkam hafiz ne ya bashi amsa, “Ai boss maganar ƙungiya ta wuce duk yanda mukai zatonta, lokaci kawai zamu samu ko zuwa anjima sai muje office ɗin nasu kaga komai da idanunka zaifi, ko zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”.

      “Hakan yayi Hafiz, mu barsa kawai zuwa gobe sai muje, kuma sannunku da ƙoƙari, Jabeer maganar matar nan fa, har yau baka kammala ba ne?”. Na kammala komai, sai dai abinda ba'a rasaba, shima akan binciken mitaje yi inda take ne, inason binciko ƴan uwanta ne kokuwa? Gashi yanzu ma na daina samun wayarta gaba ɗaya kuma”.

         Saurin kallonsa Jay yayi “Bata aiki wayar kokuwa?”. “An kasheta dai kusan kwana uku kenan, nafi kawoma raina matsalar caji ne”. Numfashi Jawaad ya ɗan sauke da faɗin, “Okay to ALLAH ya dafa mana, yanzu dai bara na leƙa na gaida su sir Ahmad, idan na fito zan ɗan fita wani waje, dana dawo saimu zauna akan wasu cases ɗin da muke dasu a ƙasa tunda kun kammala waɗannan”.

       Duk kai suka ɗaga masa, kafin duk su miƙe su fito, shi ya hau lifter yay sama su kuma kowa ya nufi office.

     

          Sai da ya shiga suka gaggaisa da oganninsa, office ɗin sir Ahmad ne ya zama ƙarshe, bayan sun gaisa shima da tattauna abinda ya shafi aiki Sir Ahmad ke cewa, “Nasan kasan Qaseem ya dawo ai?”. Da mamaki Jay yace, “Qaseem kuma sir!? Wlhy ban sani ba. Yaushe ya dawo?”. “Ya dawo kwana uku kenan, sai dai kuma yanzu haka sun killacesa, duk da shi ya dage akan shifa lafiyarsa ƙalau, shima Alhaji Ali ya kirani akan maganar wai ya kamata muyi wani abu a sakar masa ɗa dan baida wata corona”. Jawaad ya gyara zama yana ɗan murmushi da mamaki, yace, “To ALLAH ya kiyaye, amma kunje ɗin ku?”. “To Jay mu zamu biye musu ne, wannan hurumine na hukumar lafiya ai, kuma sunce nan da sati biyu idan bata basuga komai ba zasu sakesa ai”. “To ALLAH ya kaimu lokacin”. “Amin” sir Ahmad ya faɗa sannan sukai sallama ya fito.

      Bai koma office ba ya nufi inda Sadiq ke jiransa, buɗe masa mota yay ya shiga sannan suka fice.2

★★★★


       Cikin Barrack sukaje wajen baba ƙaura, baba ƙaura na zaune yanata fiƙar tsinkayen iccen ƙwari Jawaad ya shiga da sallama shi da sojan da yay masa rakkiya. Ɗagowa baba ƙaura yay yana amsa musu da musu sannu da zuwa, ya nunama Jawaad wajen zama shi kuma wancan sojan ya fice. Sai da suka gaisa da tambayar ya kwana biyu sannan baba ƙaura ya kalli Jay yay murmushi da ɗauke kai. “Malam Jawaad kenan, mi kuma ya faru?”. Jawaad yaɗan murmusa yana kallon ƙwarin da baba ƙauran ya feƙe ya zube gefe kusan ashirin, “Baba na zone akan wata magana daka faɗa ranar a dajin nan”. “Tofa wace magana ce?”. Hannu Jay ya saka aljihun wandonsa ya ciro wuri da gurun nan na hannu sai zobe ya ajiye gaban baba ƙaura”. Kallon kayan baba ƙaura yay ya ɗauke kansa yana murmushi, “Kun sami huɗu kenan?”. Kai Jay ya jinjina masa. Cigaba baba ƙaura yay da aikin gabansa kamar ba zaice komai ba, kusan mintuna biyu sannan ya sake duban Jawaad ɗin da maida dukkan hankalinsa ga resa, “Yanzu ina ɗayan yake?”. “Bamu ɗakkosa ba, yana acan gidan data zauna ɗin”. Baba ƙaura ya ɗauki zoben ya jujjuyashi sosai a hannunsa sannan ya ajiye, “Lallai kun samu damar amsar babban makaminsu, amma yaya akai kuka iya samun zoben nan? dan abune mai daraja ga mai shi”. Muryar Jay cike da ɗaci ya zayyane ma baba ƙaura komai da ya faru, harma da maganar fyaɗen da aketa bibiyar Bilkisu da shi da sai a randa ta cire zoben ta iya tunawa. Nannauyan numfashi baba ƙaura ya sauke, yace, “Ai dama na faɗa maka yarinyar akwai duhu dake biye da ita, wannan yana ɗaya daga ciki, amma akwai wanda ya fisa girma ma sai dai bansan minene ba,  ku cigaba da gayama ALLAH shi mai komai da kowa ne, ba ita kaɗai ba abubuwa da yawa zasu fito dalilin wannan zoben, dan duk inda maishi yake hankalinsa baya a kwance yanzu, har dama duk wanda ke zagaye a ƙungiyar shaiɗancin, ka turata gidan ta ɗakko wancan ɗayan wurin, idan har ta tarar an hargitsa ɗakin data ajiye to lallai mai bibiyarta da wannan sheɗancin na fyaɗe yana cikin wannan gidan, kuma shaiɗaninsu sun tabbatar masa wurin data cira a farko yana a gidan, an basa damar ya nemosa gudun karku haɗasu kamar yanda muke buƙata, dan inda tace maka ta ajiyesa babu wani shaiɗani da ya isa ɗaukarsa saboda darajar Al-Qur'ani, shiyyasa shi akace ya ɗakko, inaji a raina kuma bazai gansaba insha ALLAHU, dan daya gansa komaima zasu iya aikatawa a kanku domin halakaku baki ɗaya musamman ma ita, suma kansu basusan taka mai mai inda ya keba bayan sanin yana cikin ɗakin kawai”. Jay dake ta tauna lip ɗinsa na ƙasa sai jinjina kai kawai ya keyi, ya furzar da huci mai zafi a bakinsa yana sake jinjina kansa. Baba ƙaura yace, “Idan ta ɗakko ku yanka wannan gurun, ku zira zoben da wurin guda biyu cikin gurin, zoben ya zama shine a tsakkiyar wurin, sai ku ƙulle gurun ku ajiye. wannan ba tsafi bane, ba kuma wani shaiɗanci bane, zakuga abinda zai biyo baya insha ALLAHU, dan cikin sauƙi zakuyita gano abubuwa masu ban mamaki da al'ajabi insha ALLAH..............✍
5

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.12

*_Shin kina ko kana sa sha'awar koyon ilimin ICT?_*

*_Ko kuna da sha'awar yadda ake hada cartoon?_*

*_Ko kana da sha'awar yadda zaka bunqasa kasuwancinka ta hanyar online?_*

*_Matsalarki ko matsalarka rashin makarantun da zasu koyar dake/kai ilimin computer ta fannnin larabci?_*

*ALBISHIRINKU KANAWA*

*_Kukanku ya qare,matsalarku tazo qarshe,shahararren kantin nan na yanar gizo wato RAHAMALLS yazo muku da makarantar koyon sarrafa computer a sauqaqe wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI)_*

_Sun tanadarmuku qwararrun malamai wanda zasu koyar daku bisa tsarin da kuma cikakkiyar qwarewa ta yadda zaki fahimta fiye da yadda kuke zato_

*ga masu buqatar aji na musamman har cikin gidajensu,makarantar ta shirya tsaf don baku darussa har cikin gida*

*sannan akwai tsarin ajujuwa na musamman bisa yanar gizo wato(online classes)*

*kaidai maza garxaya ka tuntubesu akan wanannan lambar waya*

08033990209+

*_akwai ragin kaso hamsin cikin dari na kudin registration ga kowanne dalibi_*👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽

4
Page 52

................Wata tarbar karramawar na sake iskewa wajen ƴan office ɗinmu nima, suka baibayeni mazansu da matansu suna mai tayani murnar aure da samun boss matsayin miji, su Ada iyayen gulma harda cewa na musu wayo nai wuf da boss. Ni dariyama suka bani wlhy. Na musu godiya da fatan suma ALLAH ya basu nasu musha biki. Fassara muku farin cikin dana tsinci kaina a ciki saboda dawowar su Nazifa station ɗinmu ɓata lokacine, muka sake rungume junanmu daɗi na ratsamu, a karo na uku mun sake kasancewa tare, ALLAH dai yasa muci amfanin wannan ƙawance har a gidan aljanna. Gaba suka tasani da sheri wai nayi ɓul dani kodai an samar musu baby?. Yinai kamar banjisu ba, da suka isheni sai nace suje su tambayo boss ɗin. Dariya suka sanya kowa na miƙewa duk suka koma mazauninsu da aka basu suma a office ɗin namu. Daga haka na samu lafiya daga iskancinsu.
Ban tarar da kowanne aikiba, Ummie ta sanarmin ai duk oga Jabeer ya bata ta ƙarasa ayyukan dana bari, naji daɗin hakan sosai, saina miƙe ƙafa ina hutawata, da wannan lokacin nai amfani wajen zurmawa duniyar tunane-tunane kala-kala, ciki harda neman amsar yanda akai aurena da Yah Qaseem ya fasu aka maida shi kan boss, sai abinda na gani yau a ɗakina da duk nama rasa wane tunani ya dace nayi akan hakan, dan duk wanda nayi mai ƙyau sai naga bai zauna da al-amarin ba sam, sai marasa ƙyawunne keyin dai-dai. Ban sakejin ɗuriyar boss ba har muka fita sallar zuhur, bayan an idar mun fito su Nazifa ke faɗin ya kamata muje muci abinci, dan wasu a cikinsu ma basu ko karya ba suka baro gida, nima ɗin sai yanzun na tuna ban karyaba, ruwan tea ne kawai a cikin nan nawa. Shiru nai ina tunani, ni dai banda damar cewa zan bisu wajen cin abincin nan boss bai saniba, ni kuma bana wani son zuwa Office ɗinsa.... Taɓanin da akai ne ya katse tunanina, na sauke numfashi da kallon Rebecca da hannunta ke a kafaɗata, "Matar nan ina kika tafine? anata magana". Murmushi na mata ina tura hannayena cikin aljihun wandona, "Ba komai, kinsan zuciya da tone-tone, inaga kuje kawai banajin wani yinwa nikam". Har Ummie ta buɗe baki zatai magana sai Zuhrah ta katseta, "Kai inagama fa bai kamata ta bimu ba mijinta bai saniba gaskiya, tunda yana cikin station ɗin shima ta fara sanar masa, yanzufa ba da bace da muka saba shirmen mu kai tsaye". "Hakane kuma gaskiya" cewar Nazifa tana komawa kalar tausayi. Fahimtar inda ta dosa yasa muka kwashe da dariya mu dukanmu, dan itama dai bai wuce nata auren da ya rage six weeks ta tuno ba. Office muka koma bisa shawar Zuhrah, ita da Ummie kuma suka tafi sayo mana abincin..12

★★★★★★

Tunda suka baro cikin Barrack ɗin Jay ke ƙullawa da kwancewa, lumsassun idanunsa da launinsu ya gushe da ga farare zuwa ɗan jaa ya buɗe a hankali yana furzar da nannauyan numfashin da har sadiq sai da ya saci kallonsa ta mirror. Wayarsa ya ɗauka ya shiga daddanawa kafin ya saka a kunne dayin sallama, Munkaila na amsawa bai tsaya bi takan gaisuwar da yake masaba yace, "Zan tura maka wasu sunaye guda huɗu, inason daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu a nemomin inda suke, sana'arsu ko aikinsu, abokan mu'amularsu na rayuwa dana kasuwanci". "Okay sir insha ALLAHU zanyi ƙoƙari, akwai ma waɗan can ayyukan na wajena guda biyu suma duk na kammala". "Saika haɗosu kawai". "Okay Sir" Munkaila ya faɗa cike da girmamawa.
Suna isowa cikin station ɗin baima jira Sadiq ya buɗe masaba ya buɗe da kansa ya fita, sallamar Sadiq ɗin yay akan yaje zuwa biyar sai ya dawo, shi kuma kai tsaye massallaci ya nufa saboda lokacin salla yayi.
Bayan an idarne ya fito zai koma office yaga su Bilkisu, sai dai su sam basu ganshiba dan hankalinsu baya ta wajen, yazo zai ɗan gittasu yaji hirar da sukeyi, ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yaba hankalinsu, yanda yake musu kallon yara ƙanana bai zaton sunada zurfin tunani irin hakaba, dan daidai zai wucene maganar zuhura ke shiga kunnensa akan bilkisu bai kamata ta bisuba mijinta bai saniba. Sai da ya shiga office ya zauna sannan yay kiran gidan abincin da yaji su Ummie zasuje, umarni ya bada akan a basu duk abinda suke buƙata kar kuma a amshi kuɗinsu shi zai biya. Kasancewar sa babban Customer babu ɓata lokaci aka haɗa musu komai.
Su Ummi basu san wainar da ake toyawaba, sudai sukaga an haɗa musu abinci kala-kala harma da wanda basuce ɗinba, amma dai-dai abinda zasu iya cinyewa ba almabazaranci ba, sannan akaƙi amsar kuɗinsu, da suka matsa da tambaya aka basu amsa akan an biya. Sosai sukaita mamakin da tambayar waye ya biya ɗin?, babu wani ɓoye-ɓoye aka sanar musu.
Tunda suka dawo suka sanarmin yanda akai wajen sayen abincin sai naita mamaki akan yaya akai yasan zasuje? Shin kodai idanu ma yasa a sakamin ne? Kai bana tunanin hakan daga garesa, sai kace wanda bai yarda dani ba. waya na ɗauka na tura masa saƙon godiya da fatan alkairi.1

STORY CONTINUES BELOW

Jawaad na zaune ya duƙufa aiki saƙo ya shigo masa, kasancewar Number da kowa ya sansa da itace ya zata akan wani aiki ne, dan ya kashe wayarsa da mutane masu muhimmanci kaɗai ke ciki, gudun kar Alhaji babba kosu Ummah su kirashi susan ya dawo, baiyi tunanin bily bace tunda bai saka Numbar ta anan ba, ɗauka yay ya duba, a mamakinsa sai yaga itaɗin ce ashe, yay murmushi da ɗan lumshe idanu ganin abinda ta rubuto, ajiye wayar yay kawai ya cigaba da aikin gabansa. Cak ya tsaya daga abinda yakeyi yana mai ƙure takardar daya saka sunayen da suka samo wajen Umm-Anum da ido, waya ya ɗauka da hanzari yay kiran Jabeer, yana ɗagawa yace, "Jabeer bama wani ya kawo min file ɗin matarnan".
Daga can Jabeer ya amsa masa da "to". babu jimawa kuwa sai gashi ɗan aike daga jabeer yay knocking, damar shigowa ya bashi.
Cikin girmamawa ya ƙame da sarama Jay kafin ya gaida shi, sannan ya ajiye file ɗin hannunsa. Ɗaga masa hannu Jay yayi alamar ya tafi kawai. Yana fita ya ɗauki takardar dake da sunayen bayan ya zagaye sunan macen dake a ƙarshe da jan biro, sannan ya buɗe file ɗin wajen Jabeer. tsai Jay yayi a zaune yana ƙarema sunayen kallo, sam babu wani banbanci hatta da sunan gari, waya ya ɗauka ya shiga dannawa. Kira yayi, bugu biyu aka ɗauka, bayan sun gaisa yace, "Malam Rabo, yanzun nan inason Ka binciko min Hajiya Safara'u a cikin ƙauyen nan naku, gashi nan zan turo maka cikakken sunanta da sunan mahaifinta nasan zaka gane, banason ɓata lokaci, yanzun nan nakeson kabar tasharnan ka tafi". "Insha ALLAHU kuwa oga yanzun nan zanbi motar datai lodi kuwa, koma na amshi mashin ɗin Madu naje yanda zanfi sauri". "Hakan yayi, ka zuba mai idan ka dawo sai a bashi wani abu shima". "To oga babu damuwa, sai ka jini".
Jay na ajiye wayar ya maida dubansa ga file ɗin yana bin komai dalla-dalla, dogon nazari ya shiga akan abinda ke cikin file ɗin da wanda ke a ƙwalwar kansa, 'Wato na fahimci akwai wani kuskure da nayi ƙwarai da gaske' yay maganar a fili yana dafe kansa, takarda ya ɗauka ya hau rubutu, sai kuma ya ajiye biron ya kwanta jikin kujera da faɗawa duniyar tunani.
Rasuwar gimba ta rikitashi ainun har yama manta abubuwan da ya kamata ace ya bibiyesu. Akwai Number ƙarshe da gimba yay waya da ita ya kamata yasan wanene ma? da wuri, sannan matarnan da gimba ya ambata ta gidan Alhaji kokino tabbas da itane suka taɓa haɗuwa a gidan Alhaji Kokinon, kuma itace tai aiki a gidansu kenan? Idan binciken ya zama dai-dai. Yaya akai hakan ta faru bai taɓa fahimtaba kai tsaye, kalamanta na wancan karon sun isa su bashi dukkanin amsar da yake buƙata. tabbas wani baƙon al'amarine da bai taɓa sakashi a lissafisa bane ya shigo masa kai yanzun nan musamman akan kashe Gimba da akayi yake tunanin da babu gaira babu dalili. Abinda yake tunanin ya faru akan kisan gimba ba shi bane ashe. Alhaji kokino sunyi abotar siyasa da Abba kamar yanda Ummuna ta faɗa, sun kumayi ta kasuwanci, indai har matarnan tayi aiki a gidanmu mizaisa ta koma can gidan tana aiki? Lokacin da aka sace Alhaji kokino itace ta bani dukkan sirrikan da nabi na samosa a hannun ƙaninsa, maganar gimba a al'amarin, yace akwai dalilinsa na zuwa aiki ƙarƙashina, na kuma nemeta zanji abubuwa masu muhimmanci. Idan har zan haɗa wannan maganar tashi da maganganunta na waccan ranar da muka taɓayi to lallai tamin farin sani kenan?. Miƙewa Jay yayi yana ɗan dukan tabirinsa da faɗin, "Yah ALLAH ". Ya sassauta tie.. ɗinsa yay ƙasa da shi, saima ya fincikesa gaba ɗaya ya jefa saman kujera ya shiga safa da marwa a office ɗin, duk da ac dake aiki hakan bai hanashi haɗa gumi ba, tun randa yasan akwai alaƙa tsakanin Alhaji kokino da Mr Gebrail ya saka ake bibiyar masa Mr Gebrail, ta hakane ya gano kuma alaƙar Mr Gebrail da ɗaya a cikin Uncle ɗinsa, idan ya dunƙule maganar waje guda hakan na nufin, Uncle ɗinsa, Mr Gebrail, Alhaji Kokino duk sunada a laƙa ta baɗini, dan a zahirance babu wannan alaƙar kota gaisuwa a tsakaninsu sai a ɓoye. dolene a daren nan a sato masa wayoyin Alhaji kokino, sai dai waye zai masa aikin? 'Dan dole ya kasance ɗan cikin gidanne zaiyi hakan' ya ƙare maganar a fili yana dafe kansa da furzar da huci mai azabar zafi.
Tunanin kiran bilkisu ne yazo masa a rai, dan kosu Hafiz bayason sakasu a wannan case ɗin yanzu, saboda ya haɗa da family nashi, sannan yanada sarƙaƙiyar yarda da wani, kai tsaye zai iya zama ganganci, bawai dan bai yarda dasu bane, dan su Jabeer sun wuce duk hasashen mai karatu a garesa, amma ciki ba'a yisa dan abinciba kawai ai. Bilkisu na ɗagawa yace, "Ina jiranki a office". Ya yanke wayar.
Kallon wayar kawai na tsaya yi da mamaki, to amma yanda naji muryarsa tamin kama da ta mai damuwa, miƙewa nai na fice, inajin Nazifa na tambayata ina zuwa? Ban sauraretaba na ɗaga mata hannu kawai. Koda nai knocking ba'a amsamin ba, dan haka kawai na shiga kaina tsaye. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ganinsa ba yanda nai zatoba, ya ɗago ido ya kalleni sannan ya maida ga abinda yakeyi. Takawa nai na ƙarasa garesa, murya a sanyaye nace, "Wlhy nazata ko baka da lafiya, ya aikin?". Baice dani komaiba ya nunamin wajen zama, shima zagayawa yay ya zauna a kujerarsa, yanda ya tsatstsareni da idanu duk sai naji na takura, na risinar da nawa ƙasa ina kallon yatsun hannuna. Numfashi naji ya sauke mai ƙarfin, kafin nace wani abu ya fara min bayani akan kiran, ya ƙare maganar da faɗin, "Dole ne musami wayar a daren nan, dan itace zata bamu haske akan komai da gaggawa, aikin nan kuma dole mu biyu kawai zamuyisa ni da ke kawai, ko su Aliyu banason na saka sai na gama fahimtar komai".
Naji daɗin karrawarsa gareni sosai, dan banyi zaton hakanba, na gyara zamana, "To ina ganin mizai hana muyi amfani da cikin ƴaƴansa ko ma'aikatan gidan?". Shiru yay yana kallona da goga ƙasan biro akan laɓɓansa, kusan sakan goma ya janye ya maida kan takardar gabansa, ɗan rubutu yayi sannan ya sake ɗagowa ya kalleni, "Wannan shawarar taki tayi, amma babu wani ƙarin bayani a kanta?". Tsai na ɗan ƙarayi na tunani kafin nace, "Akwai, ya kamata wadda zamu saka ɗin cikin ƴaƴan nasa ta kasance mace, sannan mu nuna mata za'a cutar da shine shiyyasa muke son wayoyin na wasu awanni kawai za'a maido mata ta maida masa bayan mun saka matakan tsaro. Ko baiyi ba?". "Ihum inajinki cigaba" ya faɗa cikin lumshe idanu. Naɗan sauke ajiyar zuciya da cigaba da faɗin, "Idan muka amsa maimakon mu ajiye wayoyin a hannunmu kawai muyi copy ɗin komai na ciki sai a maida mata ta maida masa zuwa safiya". Lallausan murmushi ya saki yana ɗagemin gira ɗaya, "Ashe matar tawa ƙwaruwa ce?". Yanda yay maganar cikin zolaya yasa na rufe idanuna da tafin hannu ina murmushi. Yace, "Thanks Miemaa, da duk kaina ya kulle". Nace, "Haba dai, kaine kanka ke kullewa?". "Oh ni ba mutum bane? Duk ma ba kece kika rabamin hankali biyu ba". "Nidai babu ruwana". "Humm", ya faɗa kawai yana miƙewa. "Kinga tashi muje, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe".
Koda muka fito sai da ya shiga office ɗin Aliyu, babu jimawa ya fito riƙe da key ɗin mota, da kansa ya buɗemin na shiga sannan shima ya zagaya ya shiga, nidai addu'a nake a raina karyay gudu damu, yanda naci abincin nan na ƙoshi matsala za'a samu ai. Kasa daurewa nai na roƙesa karyay gudu dan ALLAH, ƙin tankamin yayi, sai ma waya daya ɗauka yay kira, kasancewar a Hans free ya sakata sai naji duk abinda suke faɗa, na fahimci da wani ma'aikacin gidan Alhaji kokinon yay magana, dan ya faɗa masa gamu mun taho ya fito mu haɗu a bayan layin. Dai-dai saitin wani shagon saida kayan abinci dake farkon layin muka tsaya, wani dattijon tsoho ya fito daga shahon, kallo ɗaya naga yayma motar ya ɗauke kansa, sai kuma naga ya buɗe ya shigo baya. Motar boss ya harba gaba batare da yayi magana ba. Nidai mamaki nake tayi a raina, wannan aikin namu gaskiya saida jajircewa da cire tsoro, sai kuma ka iya kowanne irin salo na mutane masu wayo. Gaba ɗaya muka fita daga layin muka shiga wani, shima muka fita muka shiga na gaba, yana tuƙin yana kallon mirror, na fahimci dubawa yake yaga ko ana binmu, ganin babu wani mai bibiyarmu sai yay fakin gefen babban titi da muka fito. Sai lokacin ne dattijon yay magana. "Na tabbata babu wani mai binmu insha ALLAH". Kashe motar yayi ba tare da yace komaiba, ya ɗan kalleni sannan ya juya yana kallon dattijon. "Wannan itace matata, sunanta Bilkisu". "Masha ALLAH, kai ALLAH ya sanya albarka ya bada zuri'a tagari". "Amin" ya faɗa, ni kuma na juya muka gaisa da shi yanata sakamin albarka.
"Baba wannan karonma aiki ya sake kawoni gidanku, kuma ina buƙatar taimakonka kamar wancan karon". "Karka damu ɗana, zan baka dukkan taimakon da kake buƙata insha ALLAHU". "Nagode baba, akwai dattijuwar mai aikin nan da naji kuna kira maman yara ko tana gidan har yanzun?". Jimmm mai gadi yayi kafin ya sauke numfashi, "Gaskiya bata nan, a ƙalla zata kai kusan wata biyu ma kenan bata gidan nan". "Aiki ta ajiye kenan?". "A'a bata ajiyeba, mudai bamusan miya faruba, rana tsaka ɗanta yazo yana nemanta wai kwana uku bai samunta a waya" kallonsa Jawaad yake cikin nazari, "Kana nufin Yazeed?". "Ƙwarai shi kuwa, to dalilin zuwan nasane muka fahimci muma bata gidan, ita dai Uwargida tace ta tambayeta zataje gida wajen rasuwar ɗan yayarta, to nidai ALLAH shine shaida ranar data cika kwana uku da tafiya naganta da idanuna ta dawo gidan lokacin ina sallar isha'i, to amma abin mamaki sai naji ana cigiyarta bayan kwana biyu wai bata gidan". "Ban gane bata gidanba? Kai kuma bakaga fitarta ba?". "Wlhy ban ganiba yarona, dan ita macece mai yawan barkwanci inhar zata fita a gidan nan kota shiga saimun tsokani juna, to a randa ta dawo da yake salla nakeyi sai ban kawo komai a rainaba, abinda ma ya ɗauremin kai da sukace su basu gantaba randa ta dawo ɗin". Shiru boss yayi alamar tunani, dan haka nikuma nace, "To amma baba a wannan daren kana tunanin zata iya fita?". "Gaskiya bazata iyaba ƴata, dan maman yara ma tana da ciwon ƙafa bata cikason yawan kai kawoba". "Hakan na nufin tana cikin gidan kenan kokuma an fita da ita a daren, ko kaine idonka bai nuna maka dai-dai ba?". "Wlhy bana ko tantama itace ta dawo da mangaribar nan, to ƴata wazai fita da ita kuma sai kace wata kaya batare da an gani ba?, shaiɗanin daya taɓa kwatanta hakama mijinki yasa an kaisa gidan maza ai". Murmushi nayi kawai, na ɗan juya na kalla boss ɗin dake saurarnmu sannan na maida ga baba, "Baba a wannan ranar mota nawa ta shiga gidan ta kuma fita bayan dawowar maman yara?". "Babu wanda yazo tunda Alhaji baya gari ma, sai wani yaro ɗan dogo baƙi mai dogon hanci da ya kanzo lokaci-lokaci idan Alhaji na nan, to ni a ranarma da yazo ɗin saida na sanar masa baya nan ai Alhaji, sai yace ai ya sani saƙo zai bama hajiya inji Alhajin. Daga haka ban sake tofa komaiba na barshi ya shiga ni kuma na shige ɗakina, to baifi mintuna goma sha biyar da shigaba ma naji yana horn nazo na buɗe masa ya fice". "Kasan sunansa baba?" "A'a gaskiya ƴata, ban saniba wlhy".
Waya boss dake saurarenmu ya ɗauka ya shiga daddanawa, kafin ya miƙama baba wayar yana faɗin, "Shine wannan?". Amsa baba yay ya kalli hoton, cikin jinjina kai da murmushi yace, "Tabbas shine kuwa ɗana". "Baba ka tabbata?". "Babu tantama a zancena". "Shikenan mun gode, bara mu maida kai, sai dai zamu iya dawowa gareka a ko wane irin lokaci". "Babu damuwa wlhy ɗana duk sanda kake buƙatar wani abu ka kirani". Godiya muka sake masa, ya tada motar yay reverse, a wani wajen muka saukesa saɓanin inda muka ɗaukesa.
Jin yayi shiru sai na ɗan kallesa, "Hoton wanene ka nuna masa dan ALLAH?". "Zaki gani yanzun" ya faɗa yana karya kan motar muka shiga wani layi. A ƙofar wani gida madaidaici yay fakin, ganin zai fita nima sai na buɗe na fita. Mun gaisa da samari uku da alama ta nuna suke tsaron gidan, yanda suke gaishemu cikin girmamawa nasan lallai shine ya ajiyesu. Ɗakin farko dake a gidan muka shiga, inda muka iske matashin saurayi zaune, shigowarmu ta sakashi miƙewa yana murmushi da mana sannu da zuwa. Na buɗe baki zan amsa kawai naji tass!!!.
Idanu na zaro baki a hangame ina kallon boss da ya saukema saurayin mari, ban gama fita a mamakinba naga ya hau dukansa. Dukansa yake ta ko ina, a take jikina ya fara rawar tsoro, nasa hannu na rufe fuskata ina ambaton "innalillahi....." da sauri na buɗe fuskata jin ƙarar ɗana kunamar bindiga, nai masifar sake zazzaro idanu waje ina faɗin, "Boss badai kashesa zakai ba?". Harara ya balla min ya ɗauke kansa yana huci.
A tare muka saki ƙara ni da saurayin saboda harbinsa da yay a ƙafa, zufa ta shiga rige-rigen karyo masa, jikinsa na wani irin rawa, ko kallon inda nake baiba ya ranƙwafa kan saurayin yana hure bakin bindigar dake ɗan hayaƙi da faɗin, "Kaga bindigar nan cike take taf da alburusai, kuma idan zan ƙarar dasu tas a sassan jikinka babu mai tambayata yaya nai da su?, wannan harbin danai maka na ƙaryar daka mince, idan wata ta biyo bayanta yanzun kuma wlhy saina faffasa gaɓɓanka ɗaya bayan ɗaya da alburusan nan kafin na aikaka lahira dan ubanka. Ina kakaita itama?". Jikin ɓaleru na rawa ga jini na malala a ƙasa cikin hakkin kuka da azabar shigar harsashi yace, "Bansan wacce kake maganaba oga, dan ALLAH karka kasheni, nayi kuskure a farko amma wlhy bazan sake kwatantashi ba". "wani rainin hankalin zaka sakemin?" ya faɗa a taƙaice yana sake ɗaure fuska da ɗana kunamar bindigarsa.
"A'a wlhy oga ba haka bane ba, na tuba dan ALLAH zan faɗa maka komai, bata a garin nan". "Amma ranar ca kaimin baka da alaƙa da Alhaji kokino, bama ka sanshiba ko?" ya faɗa yana ɗora masa bindigar a saman kai. a take jikin ɓaleru ya ƙara ƙarfin mazari, harya jiƙe wandonsa da fitsari, "Oga kawa ALLAH da MANZONSA karka kasheni, ka yafeni, komi kake buƙata yanzu wlhy zan makashi, harma abinda baka saniba zan faɗa maka". Ƙafa Jay ya saka ya danna ƙafar ɓaleru daya harba. Ya sake sakin wata wahalalliyar ƙara jikinsa na karkarwa.
Da sauri nazo na riƙe hannunsa ina hawaye. Janye ƙafar tasa yay ya juyo yana kallona da wani murmushi irin na tsagwaron muguntarnan, ya lakacemin hanci da faɗin, "Ki rage wannan tausayin malama". Rungumesa nai da sauri ina faɗin, "To dan ALLAH kayi haƙuri ka barshi haka tunda yace zai faɗa mana".
"To na barsa" Jay ya faɗa yana ballama Ɓaleru da keta kukan wahala harara da shafa bayan bily data lafe a jikinsa. Sai da ya tabbatar tayi shiru sannan ya ɗagota ya share mata hawayen tas da sumbatar goshinta.
Jikkata ya amsa ya buɗe, ya fiddo biro da ɗan littafi dake ciki ya jefama ɓaleru, duk da halin da yake ciki haka ya ɗauka ya rubuta masa address ɗin. Yana sharar hawaye da sauke numfarfashi yace, "Oga gidan akwai matakan tsaro sosai, hanyar da zaku iya fiddota cikin sauƙi itace kiran masu tsaronta da wayar Alhaji kokino". Uffan baice masaba, saima waya daya kira, mintuna kaɗan saiga ɗaya daga cikin masu tsaron gidan ya shigo. A daƙile yace, "A cire masa wannan bullet ɗin a tsaida jinin". Da girmamawa ya amsa da "Yes Sir" hannuna ya kama kawai muka fice, sai binsa nake da kallo da ɗunbin mamaki, ban taɓa zaton tsaurinsa ya kai hakaba, nikam tsoroma yake ƙara bani yanzun.
Sai da muka fara tafiya sannan yay magana hankalinsa nakan tuƙi, "Tunaninmu na samun wayar kokino yana a kan hanya, wannan tsoron da tausayin naki kuma dole ki cireshi dan aikinmu baya buƙatarsa". Kallonsa nayi sai naga bani yake kallo ba, yama fuske abinsa tamkar bashine yay maganarba. Nima bance komanba amma sai juya lamarin nake a rai, 'sai kace a cikin film? kai anya kuwa ban sako kaina inda yafi ƙarfina ba? Wani ƙarfin zuciyar ai sai maza dole'.
Da wannan tunanin a raina muka iso wani waje saɓanin station da nai tunanin zamu koma. Fakin yay sannan ya ɗauka waya yay kira. Yanda ya kwantar da murya tamkar ba shine ya gama hargagi yanzunba sai ya bani mamaki, jin kuma da mace yake maganar dan a hans free yasa sai naji wani abu ya dunƙulemin a ƙirji na takaici. Ƙin kallona yay ya cigaba da wayarsa, "Kiran da nai miki yanzu ai ya tabbatar miki ban manta da ke ɗinba". Cike da yanga daga cikin wayar akace, "Kai dai kanason kare kanka, shekara biyar ai ba kwana biyar bace". Baki naga ya wani taɓe da ɗauke kai kamar yana a gabanta, a zahiri kuma sai ya sake kwantar da murya da faɗin, "Tom nayi laifi, amma nima bana ƙasar ai, yanzu ma dai akwai wani taimako da zakimin akan Dadynki". tace, "To yanzu na fahimci dalilin kiran, tunda ba taɓa kirana kayiba, inma na kira baka ɗagawa" "Humm" ya faɗa batare da ya bata amsar zancen nata ba, "Yanzu dai bazakimin taimakonba na nema wani?" "Ah haba, kaima kasan bazan iyaba ai, ko karan gidanka ka aiko da buƙata ai zan biya masa balle kai ɗin da kanka" "Yayi" ya faɗa a taƙaice, sannan ya cigaba da faɗin, "Wani ƙulli da ake sonma Dadynki mukeson kwancewa batare da ya saniba, dan haka mukeson ki ɗebo mana dukkan phones nashi a daren yau zuwa safiya insha ALLAH za'a dawo dasu ki maida masa batare da ya saniba". Jimmm tai alamar tunani, kafin ta sauke numfashi da faɗin, "Tab wannan aikin baiyi girmaba kuwa Jay, Dady fa ko Momy bai bari ta taɓa masa waya balle mu, to ta inama zan fara hakan?". "Yanda za'ai ɗin ke ya kamata kiyi tunani, inba hakaba komai zai iya faruwa da shi, idan kuma kin zaɓi komai ya farun akan ki bada haɗin kai a taimakesa kafin ya farun to babu damuwa sai anjima....." da sauri tace, "A'a tsaya-tsaya, ka bani lokaci zanje nayi tunani, nanda magriba idan da yuwuwar hakan zan turo maka saƙo, dan matsalar shine kasan shi business yake, komai dare kuma amsa waya yakeyi, to tayaya za'a ɗauka har sai zuwa safiya a maido bai fahimta ba?". "Kidaiyi ƙoƙari mugani". "Shikenan sai ka jini" ƙitt ya yanke wayar tare da juyowa ya kalleni. ɗauke kaina nai gefe batare da nace komaiba. Shima ɗin baice min ɗinba, saima sallama da naji ya sakeyi alamar wata wayar.
kiran oga Hafiz yay aka yayma su Jabeer magana su zo su samemu a office ɗin da aka buɗe na karɓar cases ɗin masu fyaɗen nan, dan yanada buƙatar sanin komai a yau ya fasa gobe, amma kafin sannan su fara turo su Ummie sannan, kafin su su biyo bayansu nanda mintuna talatin.
Duk da abin ya bama Hafeez ɗunbin mamaki sai bai tambayi dalili ba ya amsa masa da to kawai, dan yasan zai musu bayani. Wayar ya ajiye yana sauke numfashi, ya kamo hannuna cikin nashi tare da saka ɗayan hannunsa ya juyo da fuskata garesa. "Na matan ne ya motsa?". Yay maganar gab da fuskata yana wani ɗagemin gira. Fuska naɗan ɓata nace, "Miye na mata?". "Kishi mana" ya bani amsa da lakacemin hanci. Bansan sanda murmushi ya suɓucemin ba nace, "Nidai ai ban faɗaba". "Ai shi ba sai an faɗaba, a fuska ake ganoku". Mintsininsa nai a hannun da yake murzamin cinya. Ya ɗauke da sauri yana faɗin, "Ouch!, muguwa". Dariya na ƙyalƙyale da ita, dan yanda yay da fuska kamar wani ƙaramin yaro.
Murmushi Jay yay yana kwantar da kansa a kafaɗarta da lumshe idanu dan dama soyake yaga ta dawo cikin walwalarta.
Babu jimawa sai gasu Zuhrah sun iso, cayay na fita na samesu mu shiga wajen tare, shi zai jira su Oga Aliyu.
"Anacan anashan soyayya an barmu" cewar Ummie sanda na iso inda suke. "Ya ranki ne?" na faɗa ina mata gwalo. Dariya su Zuhrah suka sanya mana, Ummie kuma tace, "Fari ƙal, muma ai tana tafe garemu, a lokacin wasu sun tsufa". "Ko kuma mun zama gwanaye ba" na bata amsa ina mangare ƙeyarta.
Yanayin yanda aka tsara wajen ya birgeni sosai wlhy, ga matansu Oga Jabeer sunata aiki tuƙuru, gaisuwa mukai cikin girmama juna suna tsokanata wai har mun dawo daga Honeymoon ɗin. Dariya kawai nayi bance komaiba. Muka rungume juna da Amina ina tambayarta ya mama da yaya sule?.
Babu jimawa da zamanmu su boss suma suka shigo, bayan anyi ɗan gaishe-gaishen juna matar Jabeer data kasance shugaba ta fara mana jawabin cigaban da aka samu musamman ma ni da Boss da bamusan yanda ake ciki ba.
"Ƙasarnan danƙare take da cases na matsalolin fyaɗe, wasu sunma kai kotun amma rashin gata yasa an watsar da shari'oinsu, daga baya an saki waɗanda suka aikata laifin, wasu ko tsoro yama hanasu fitowa su faɗa. A yanzu haka dai munada ƙararraki kusan saba'in da uku a cikin kwanaki goma sha shidda kacal da shelanta ƙunyar, mun gama bincike akan ashirin da ɗaya kamar yanda muka sanar maka, mun tabbatar da gaskiyarsu kuma harma munsa an kama wasu daga cikin masu laifin, wasu kuma muna kan fakonsu, sai cases Goma sha huɗu masu kamanceceniya da irin wanda muke nema".
Kai Jawaad keta jinjinawa yanajin daɗi da ƙaunar abokan nasa, ya ajiye file ɗin hannun nasa da matar Hafiz ta bashi yana gyara zama, "Wace shawarace da ku yanzu akan goma sha huɗun da muka samu? Dan kunga idan muka haɗa da baƙwai ɗin dake ƙasa sun zama ashin da ɗaya kenan".
Aliyu yace, "Hakane, ni dai a nawa ganin shine mu fara bincike akan gidajen da duk abin ya faru, dan abinda zai baka mamaki da ɗaure kai waɗanda abin ya faru dasu dak ƴaƴan masu gidan ne, ko ƴaƴan ƴan uwa, kuma babu gidan talaka, ƴaƴan talakawan da tsautsayin ya hau kansu duk masu aikine a gidajen".
"Shawararka tayi Aliyu, yanzu zamu rarraba yaranan cikin ofisoshin waɗanda abin ya faru a gidansu a gobe idan ALLAH ya kaimu, kowacce zata lurar mana da abu biyu, na farko zobe, na biyu sana'ar mutumin ko aikinsa".
Duk kai muka jinjina masa na gamsuwa, daga haka aka ƙara ɗan tattaunawa muka fito bayan an damƙama kowa aikin da zaiyi.............✍17

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.2

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.4

Page 536


.................Bayanan da Dattijon nan na tashar garinsu gimba ya kawo masa yay dai-dai da dukkanin hasashen Jay, abin sosai ya ƙara bashi mamaki da tsoro, babban mamakin shine minene alaƙar Hajiya Safara'u (Maman yara) da gidan Alhaji kokino tunda a gidansu ta fara aiki? Sannan minene dalilin da yasa ta turo masa gimba?. Bibiyar rayuwarsa take bisa umarnin wasu ko kuwa umarnin kanta ne?. Malam shehu shine ya haɗashi da gimba lokacin yana neman driver, dan malam shehun shine drivern da aka fara nemo masa kasancewar shi mutumne da baison tuƙi, kasancewar ya gansa babba yace a canja masa da yaro, dan bayason yaga babban mutum mai shekaru kamar na mahaifinsa ace yana aiki a ƙarƙashinsa gudun watarana kar wani dalilin ɓacin rai ya shigo ya aikata abinda bai daceba a garesa. Haka malam shehu ya kawo masa gimba a cewarsa ɗan garinsu ne, shikuma sai ya samawa malam shehu wani aikin a gidan gonarsa wanda bazai wahala ba, to a yanzu dai shekarun malam shehu kusan huɗu kenan da rasuwa, dan shekara uku da wasu watanni kaɗai yay yana aiki a gidan gonar ALLAH yay masa rasuwa dama yana da hanta.

         Hannun da ya tallafe kansa da shi ya janye yana furzar da huci. Yanzu idan yace zaije garin su gimba yamma tayi, ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa yaɗan lumshe idanu, lokacin ma tashi yayi, yanason su wuce gida da wuri kodan Bilkisu, ga kuma aikin da yake son suyi ma a gidan. Yaɗan fara tattare kayansa akai knocking ƙofar. Batare da ya kalli wanene ba ya bada izinin shigowa.

       Ƙamshin turarenta da yajine ya sakashi ɗagowa ya kalli ƙofar, kallo ɗaya zakai mata ka fahimci a matuƙar gajiye take, ya ɗauke idanunsa yana murmushi a ransa. Takardun hannunta ta ajiye bisa tebirin nasa tana faɗin, “Barka da yamma Sir”. “Yarinyar nan kin fara rainani wlhy” ya faɗa yana tura takardun daya haɗe cikin briefcase ɗinsa.

        Bily dake ɗan murmushi tace, “Rufamin asiri, ina ni ina raina shugabana”. Baice komai ba ya ɗauki takardun data ajiye ɗin, “Na minene?”. “Oga Hafeez ne yace na kawo maka ka saka hannu, yace dan ALLAH yanzun”. Rufe file ɗin yay ya ture gefe, “Ku wlhy ku barni na gaji, sai dai ya bari sai idan ALLAH ya kaimu gobe danni kam nama tashi”. Agogon hannuna na kalla sannan na kallesa, biyar da minti tara fa”. “Koma babu minti tara ne bazanyi ba, kije ki shirya mu wuce, idan kuma na barki anan to?”. Ɓata fuska nai batare dana ce da shi komai ba na juya zan fita, harna kama ƙofar zan buɗe na tsinkayi muryarsa yana faɗin, “Habawa yarinya badai gida zamu ba, zakiyi min bayani ai”. Idanu na lumshe da buɗewa a lokaci guda, kafin naɗan juya na kallesa, “To nama fasa binka, gidan Ummah zanje na kwana”. Da hanzari na buɗe ƙofar na fice ganin ya taso, sai da na tabbatar na sauka ƙasa sannan na dafe ƙirjina dake bugawa da sauri-sauri ina murmushi, juyawa nai na kalli saman sannan nabar wajen zuwa office ɗin oga Hafiz dan na sanar masa abinda yace.+


        

★★★★★★★★


           Muna shigowa gida ana kiran sallar magriba, ɗakinsa ya nufa nima na nufi nawa, wanka na farayi sannan nai sallar magriba, bayan na idan na zura doguwar riga kawai na fito, kitchen na nufa dan na duba abinda zan samar mana muci kasancewar ya faɗamin Sadiq yayo cefane da rana. Ina fara ƙoƙarin ɗaura abu mai sauƙi da bazai takura mana ba ya shigo kicin ɗin, kallonsa nai da masa sannu, ya amsa yana mai kallon agogon hannunsa, “Miemaa bara naje yarinyar nan ta kirani inaga an dace”. Nace, “To ALLAH ya tabbatar da hakan, sai ka dawo”. Matsowa yay ya sumbaci goshina da faɗin “Amin nagode, sai na dawo”. “ALLAH ya tsare” na ƙara faɗa ina maida hankalina ga aikina shi kuma ya fice.

      Dawowarmu gidan sai tunanin ganin wallet ɗin ɗazun ta sake dawomin cikin rai, ina aiki ina sake juya al'amarin, da yake aikin ba wani mai yawa bane dan danan na kammala, na tanaji abinda zamuyi breakfast da shi dana tashi sai haɗawa. Shirya namu abincin nai a dining na saka hijjab na fita na kaima maigadi nashi. Sannan na dawo nai sallar isha'i, na gaji hutu kawai nake buƙata, amma yaya na iya, gaskiya a kwai wahala ga mace mai aure ace kuma tana aiki, yanzu mu biyu ne kawai fa, to inaga nan gaba ƴaƴa sun ƙaru kuma fa? Mace daban ce a rayuwa, na tabbatar ba kowanne namiji bane zai iya juriyar da mu mata mukeyi wlhy, ki duba dasun dawo aiki wanka kawai zasuyi suci abinci su huta, mace ko kota dawo ɗin wani sabon aikinma zata taras, harma shi kansa ya ƙara mata da wani a bayan fage, hakan kuma bazai hanata tayi sammakon tashi ba da safe. (Mata kuɗin na dabanne, idan nace na daban ina nufin nadaban aduk lungu da saƙo na duniya, ALLAH ya ƙara muku martaba da kwanciyar hankali a duk duniyar da kuke. “Maza banda jealous kuma👻dan gaskiya na faɗa🙈”. lol😂).

        Bai shigo gidan ba har tara saura, lokacin harma naɗanyi barcin wasu mintuna a falon. Jin ana shafa min kai na buɗe idanuna a hankali, cikin nasa suka shige, yana tsugunne gaban kujerar da nake kwance, hannunsa ɗaya a sumar kaina ɗaya ya riƙe hannuna dana ɗaura saman ciki yana murzashi. Murmushi yay min nima na maida masa murtani, cikin muryata da taɗan sirka nace, “Sannu da dawowa”. Kansa ya ɗagamin yana mai lumshe idanusa, kafin ya tura yatsunsa cikin gashin kaina da faɗin, “Ya kamata aima kan nan kitso Zinaraina, kar yazo ya lalace aimin asara”. Na ɗan jinjina kaina ina murmushi da yunƙurawa zan tashi, taimakamin yay na tashi zaune sosai, sai da na zauna da ƙyau sannan nace, “An dace?”. Ni kaina yanda nai maganar cikin kalar tausayi sai da na bama kaina dariya, yay murmushi shima yana miƙewa tsaye da zama a kusa dani, “Idan kika koma kalar tausayi sai ki zama wata saliha dake”. “Lah!, to ni ina da tsiwane?”. “Eh mana, sai mutum ya zauna dake yake ganewa ai, a nesa ba'a gane Fitsararriyace”. Nace, “ALLAH kana gani”. “Nima ALLAH kana gani” ya faɗa da dungure kaina da ɗoramin ƴar ƙaramar jikka saman cinyata. leƙa jikkar nai, ganin wayoyi huɗu a ciki ya sakani jin wani ɗanyan farin ciki, bansan sanda na rungumesa ba ina dariyar jin daɗi. Shima rungumeni yay yana dariyar. Ɗagowa nai da sauri, cike da farin ciki nace, “Kai amma tayi ƙoƙari wlhy, yaya akai ta samo mana?”. “Ai dama nasan zata ɗakkosu, yanda yarinyar nan ta mutu a kaina ko Alhaji kokinon nace ta sato ai zata sato min”. “Uban nata?”. “Sa wasa yarinya, nifa nan farin jinine dani garama ki ringa lallaɓani”. Yay maganar yana miƙewa, sai da yaje dining sannan ya juyi ya kalleni, “ƴammata ko dai kina jealous ne?”. Baki na taɓe ina miƙewa nima bayan na maida wayoyin a jikkar. Ganin na basar shima sai ya basar da zancen.

         2

STORY CONTINUES BELOW

★★★


        Tunda muka kammala cin abincin muka koma falonsa, a ƙasa muka baje, shine yake binciken wayoyin ɗaya baya ɗaya ni kuma ina copy ɗin komai na ciki zuwa lap-top ɗinsa, yanayi yana rubuce-rubuce, kasancewa dama tun daga can ta saka wayoyin a Airplane mode sai babu wani kira da yake shigowa ciki.

      Ɗan kallonsa nai na ɗauke kai, “Boss!”. “Uhmyim”  ya amsa min batare da ya ɗago ba. “Wai baka tsoron yasa a bibiyi wayoyin nan ne? Naga fa komai yinsa kake hankali kwance”. Shiru bai amsa minba sai kusan mintuna biyu sannan ya ajiye biron da yake rubutun yana miƙomin flash, “Basai idan mai wayoyin yana duniyar da kike ba zaisa a bibiyesun?”. A tsorace nace “kamar ya? Kashesa kukayi?”. Yanzun kam saida ya kalleni sannan ya ɗauke kansa, “Kefa wani lokacin mashiririciyace, miye na kisa anan?. Gani nai zata bamu matsala dan ta kirani akan ita dai tarasa ta yanda zatai tunanin ɗauka, shine na ɗaurata bisa keken ɓera, na saka aka kai mata maganin barci mai ƙarfi ta saka masa a drink ɗin da yake fara sha kullum idan ya shiga gida, na kuma ƙara mataa da allura”. kasa janye idanuna nai daga garesa, hatsabibancinsa kawai nake jinjinawa a raina, boss dabanne akan dabaru da ƙwazon aiki, dolene kana tare da shi ka rinƙa koya kaima....... “Kallon fa?”. Ɗauke kaina nayi na cigaba da abinda nakeyi.

      Muna tsaka da aikin wayarsa tai ring, yanda naga ya ɗauki wayar a ring ɗaya babu wani ɓata lokaci, ya sakani kallonsa da mamaki, wani lokacinma da zakaga anata kiransa ya share wayar.

         “Munkaila kun isa ne?”. “Eh boss gamu a cikin anguwar kusa da gidan ma”. “Okay ku saka masa wannan rigar bomb ɗin. bashi wayar”. “Okay sir, gashi”. Ɓaleru da duk ya zama wani kalar tausayi ya amshi wayar, cike da ladabi yay sallama. Cikin Kakkausar murya Jay yace, “Idan ka gadama kaci amanarmu, idan ka gadama kayi aikin da zaka ceci ranka, wannan bomb ɗin da kake gani a tashi ɗaya zai tarwatsa naman jikinka ko kalar ƙashinka baza'a gani ba ma balle kaiɗin”. “Oga dan ALLAH kaimin rai, komai kake buƙata zanyishi”. “Ya rage naka”. Jawaad ya faɗa yana yanke kiran.

         Computer ɗin da ya haɗa a saman centre table tun ɗazun ya kunna, ya koma saman kujera ya zauna, ya jona wayarsa jikin USB sannan ya daidaita muryar Alhaji kokino da maigadin gidansa yay mana recording. cikin wayoyin da yazo da su ya ɗauki ɗaya, itama ya haɗata da Computer ɗin sannan yay kira. Nidai inata aikina ina kuma kallonsa lokaci-lokaci, da hannu yaymin nuni dana zo, matsowa nai garesa, ya miƙamin mouse ɗin Computer da faɗamin yanda zanyi da zaran an ɗaga wayar, saboda muryar Alhaji kokino yazam ita suke ji. Kaina na jinjina masa, ya saka abu a kunne sannan yay kiran wayar. Bugu biyu aka ɗaga, cikin wata buɗaɗɗiyar murya aka fara gaisuwa da tsantsar ladabi. Amsawa naji yanayi da salon da ba nasa ba, kafin ya fara magana cike da tsumewa, “Yaron da ya kawo matar nan gashi nan na turosa shi da wasu yara su uku zasu ɗauketa”. “To amma oga ya kuma zaka canja shawara? Ɗazunfa ba haka mukai da kai ba, wai miyasa kuketa canja mana aiki bakamar yanda yake a baya ba?. Kawai saboda sakacin mutum ɗaya, gaba ɗaya gazawarsa tasa komai sai rushe mana yake nemanyi a ƙungiya, a kaudashi mana”. Kallon juna mukai ni da boss, ya ƙara tsaurara muryarsa da gyara zaman abinda ya ɗaure wuya dashi, “Sabon yanka kaima kasan muhimmancinsa ai a garemu, amma ka ajiye wannan maganar zamuyita wajen taron ƙungiya na ranar bauta, a basu matar dai dan akwai matsalane zasu canja mata wajen zamane”. “To babu damuwa oga, saisun ƙaraso”. Ya yanke wayar da sauri yana kunce ƙyallen wuyansa da sauke nannauyan numfashi, saurin miƙa masa ruwa nai, ya amsa yasha yana lumshe ido da murza wuyansa. sai kuma ya ɗauka wayarsa ya turama su Munkaila saƙo akan suje komai yayi.

          Daga ni har shi kowa juya zancen ƙungiyarnan da sabon yanka ya faɗa mukeyi a ranmu, ya kalleni yana miƙewa “Mikika fahimta a zancensa Miemaa?”. “Sunada wata ƙungiya, da gaji kuma bata alkairi bane, to amma wanene ya ɓata musu aikin?”. “Nima wannan shine tambayata, maganar gayen nan ta sake ɗarsamin abubuwa a cikin raina da yawan gaske, kuma insha ALLAHU saimun bincikosu. Inada tabbacin duk wani wanda muke buƙatar samu a dalilin bibiyar numbers ɗin dake cikin wayarnan zamu samesa, tsabar munafurci babu wadda akai saving nata da sunan mai ita, yanzu dai mu jira dawowarsu da maman yara, insha ALLAHU daga nan zuwa asuba nasan zasu shigo”. Kaina na ɗaga masa jikina duk a sanyaye.

    Dawowa yay ya zauna muka ƙarisa aikin, kusan sha ɗaya muka kammala, muna cikin tattare komai Munkaila ya kira ya sanar masa yanzu haka sun ɗakko hanyar dawowa, amma gaskiya maman yara na cikin mawuyacin hali sosai, dan a yanayin da take ciki su da farko ma sun zata bata numfashi, sai daga baya suka fahimci tsabar wahala ce da azabar da ake gana mata.

         Hankalinsa tashe ya basu Umarni akan su gaggauta tahowa kawai, su kuma ringa mata addu'a suna tofa mata.


STORY CONTINUES BELOW

            Mun kwanta ne kawai badan muna tare da nutsuwa ba, duk bayan wasu mintuna sai ya kirasu yaji suna a ina ne? Barci gaba ɗaya ya ƙauracema idanunmu. Bamu sami ƴar nutsuwa ba sai da suka iso kusan ƙarfe uku na dare. Likitan da zai dubata isowarsu kawai yake jira, dan haka suna isowa ya duƙufa kanta kamar yanda suka kirasa video call mukaga komai.

       Mawuyacin da take ciki saida nai kuka dan tausayi duk da a yaune na fara ganinta, shi kansa ajiyar zuciya kawai yake saukewa a jajjere. Barci ya sacemune kawai kasancewarsa gwanin iya sata, amma badan mun shirya kwanciyarba.


              ★★★★


    Da asuba kiran sallar farko yay alwala ya fice gidan, na zata massallaci ya nufa, sai da najiyo ƙarar tada mota da buɗe gate na fahimci fita yay. Addu'a na bisa da ita na tashi nai alwala nazo nai zaman yin nafilfili nima har aka kira sallar shiga.


         Koda Jawaad ya fito kansa tsaye gidan Alhaji kokino ya fara isa, ya bama baba maigadi wayoyin sannan ya wuce inda aka ajiye maman yara. Ba ƙaramin tashi hankalinsa yayi ba ganin mawuyacin halin da baiwar ALLAHr nan ke a ciki, a hakama Munkaila ya tabbatar masa tayi fasali fiye da yanda suka ɗakkota, Jawaad ji yay kamar yayta dukan ɓaleru har sai ya daina numfashi, amma ya danne ransa suka fita salla. Bayan an idar baro gidan yayi akan zai dawo zuwa anjima tare da wadda zata kula da ita.

      Ina kitchen ya shigo gidan, na leƙo nai masa sannu tare da gaisheshi, a yanda ya amsa min kawai nasan zuciyar ƴan mazan a kusa take, ɗakinsa ya wuce, nikuma na cigaba da aikina dan na samu na kammala da wuri ba sai na makarar damu kamar jiya ba.

       Bayan na kammala sai da na fara leƙe ɗakinsa, wanka yake, dan haka nima na fito zuwa nawa ɗakin na shiga wankan. Harna fito nai shiri bai shigoba yau, ban damuba na kammala abinda zanyi sannan na fito gaba ɗaya, ɗaura bag ɗina nayi a dani na kuma nufar ɗakinsa inajin duk babu daɗi, shi indai yanada damuwa to shikenan sai kiga duk ya ƙuntata, duk wani walwalarsa gushewa take ya koma miskilin gaske, nikam a ɗan zamana da shi ɗin nan na fahimci ga iyalinsa shi mai sauƙine, miskilancin sa sai a waje yake zubashi kamar ba shiba. A shirye na iskesa, rigar saman suit ɗinsace kawai bai sakaba sai tie...,  zaune yake a bakin gado da waya a kunne alamar waya ya keyi. Ƙarasowa nai na gyara saman mirror ɗin da ya gama hargitsawa, ya riƙo hannuna ya ɗaurani bisa cinyarsa yana faɗin “Gata Ummuna, amma ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, muna nan munata shirin dawowar ai”. Sai yanzu na fahimci da ƴan saudia yake wayar, kafin nace wani abu ya ɗauran wayar a kunnena. Cikin girmamawa da ɗoki nai sallama, daga can Umm-Anum ta amsa min cike da kulawa, sai dai yanda naji muryarta na sake fahimtar tana tare da damuwa. Bayan mun gaisa tace, “Ɗiyata wai da gaske yake kuna shirin dawowa?”. Murmushi nayi ina kallon fuskarsa, ya wani narkemin idanu da fuska, na sake murmusawa sannan nace, “Eh Ummu da gaske ya keyi”. Wata sassanyar ajiyar zuciya naji ta sauke, sai tausayinta ya kamani har ƙwalla suka cikamin ido, munyi ƴar hira kaɗan ta bama Anuwar wayan shima muka gaisa, sannan Anum ta amsa itama, ganin mun fara nisa a fira dan Anum ma dai babu laifi akwai magana tamkar Nabeelah, ƙwace wayar yay, “K sai anjima aiki zamu fita”. Ina jiyota tana kukan shagwaɓa ya kashe wayarsa bai saurareta ba. Kai ya dunguremin, “Idan kina biyema Nabeelah da Anum sai kin zama parrot irinsu, nidai nafison matata haka mara son hayaniya”. Murmushi nayi tare da miƙewa daga cinyar tasa batare da nace komaiba. Shima bai sake cewa komaiba ya miƙomin tie.. Ɗinsa, “Nifa ban iya sakawa ba”. “Sai ki fara koya daga yau” ya faɗa yana miƙewa. Ya fini tsawo, dan haka na ɗauki filon dake saman sofa na ajiye ƙasa na taka, duk da hakan ma dai ban kaiba, amma nafi ɗazun, shine ya rinƙa nunamin yanda zanyi har muka kammala, yace, “Woow kinyi ƙoƙari”. Daɗi naji sosai, nace, “Da gaske?”. “Ehum” ya faɗa da ɗan lumshe ido. “Thanks” na faɗa nima ina murmushi.

          Tare muka fito daga ɗakin, ya ɗauka abincin maigadi da Sadiq tunda yana nan da safe ya kai musu, nikuma na zuba mana namu a plate ɗaya, sai tea dana haɗama kowa dan nasan shikam in bai sha tea ba akwai damuwa, ina mamakin yanda yakema tea so na masifa haka. Koda ya dawo muka zauna cin abincin sai naga bayaci sosai, ya raba hankalinsa biyu, ɗaya a aiki a tab... ɗaya ga abincin, cire nauyinsa da nakeji nayi na amsa cokalin na fara bashi da kaina, baice dani komaiba ya fara amsa, da yake hankalinsa nakan wayar sai yaci abincin sosai batare da ya fargaba. “Miemaa Please barni haka karnaje office na kasa aiki, ashe wayo kikemin kinata nausamin abinci a ciki”. Ƴar dariya nai kawai na tattare kayan zuwa kitchen, sauri-sauri na ɗaurayesu na fito, tsaye na iskesa riƙe da bags ɗinmu alamar ni yake jira. “Anya kuwa bazaki ajiye wannan aikinba ki zama matar gida kawai?”. Gabana ne yay masifar faɗuwa da jin wannan furuci nashi, dama kullum cikin addu'a nake kar wannan tunanin yazo masa a kai, dan na kula shi mutum ne mai tsananin kishi. Yinai kamar banjisa ba na hau gyaran agogon ƙarya, “Nasan kin jini ai”. Yay maganar daɗan kallona. “Nifa banji komai ba, yi haƙuri mikace?”. Shareni yay muka ƙarisa, bayan mun gaisa da su Sadiq ya buɗe mana mota muka shiga.

               A motarma bai hutaba, aiki ya keta faman yi har muka iso office, nazata zamu biya ta wajen maman Yara, amma jin baiyi maganarba saina share abina. Yauma sai da na masa rakkiya har office sannan na koma namu inda na tarar da Rebecca kawaice tazo a cikinmu, itama ta cemin nanda goma zata fita saboda aikin da boss ya raba musu jiya, akwai abinda tazo yi shiyyasa amma da sai ta kammala zata shigo kamar su Ummie, ni dama bandani ya ba shugaban ƴan kishin, dana tambayesa bayan mun fito amsar daya bani itace, yanzu duk inda nasa ƙafa yana wajen ai, duk aikina zai kasance tare da shine insha ALLAH, nidai najisane kawai, watarana ai za'a iya canjama wani wajen aiki a cikinmu ko wani abun daban, naga yanda zaiyi kuma. Tana aikin muna hira danni aikin gabana mai sauƙine, jiya nema oga Hafiz ya banishi da yamma. Goma nayi ta fice, saina maida hankali ga nawa aikin. Yau bamu da yawa a office ɗin, mafi yawansu sun fita operation, wasuma ko office ɗin basu zoba.

             Wajen sha biyu na amsa kiran boss da yaymin, na iskesa shi da Jabeer, na gaishesu sannan nace masa gani. “Na ganki ai” ya faɗa yana cigaba da aikinsa a Computer batare da ya kalleni ba. Ina daga tsayen ban zauna ba, dan baibani izinin yin hakanba, yanzu a matsayin shugaba yake wajen aiki ba miji ba. Kusan mintuna huɗu sannan ya juyo gareni yana tattare takardun gabansa da yake aiki akansu. Miƙomin yay fuskarsa dai babu walwala sam, a boss ɗinsa dana sani yake. abinda zanyi ya faɗamin, na amsa ina jinjina masa kai, kafin na juya na fita.

           Aikin nan daya bani shine ya jani lokaci daƙyar na turesa naje nai salla na dawo na sake cigaba, a lokacin ne su Zuhrah suma suka dawo, sam banajin yunwa, koda ya kirani akan miza'a kawomin nace masa ni banama jin yunwa, baice komaiba ya yanke wayar, bayan wasu mintuna saiga doughnut da fresh milk an kawomin. Murmushi kawai nayi nama wanda ya kawo godiya na cigaba da aikina, shine su Nazifa suka iske inaci, ƙarshe ma tare da su muka ƙarisa.

       

★★★★★


            Ƙarfe biyar muka bar office, barci nakeji sosai a idona, dan haka naɗan jingina kaina da kafaɗarsa. Ɗan kallona yay ya ɗauke kansa yana murmushi, tun ina kallon aikin da yake a lap-top har barci ya ɗaukeni a haka. A hankali na buɗe idona jin an jamin hanci. “Sorry kin gaji ko?” yay maganar yana shafamin gefen fuska. Kaina na ɗan ɗaga masa da lumshe idanu na sake buɗewa a kansa. “Daure mu shiga, bazamu jimaba, sai mu tafi gida kinji”. A hankali nace to ina tashi.

     Koda muka fito da mamaki na kallesa, “Lah! Dama nan mukazo?” na faɗa cike da zumuɗi. Ƙin tankamin yayi, sai ma nunamin gidan su Amina da yay da hannu alamar muje. A tunanina nan zamu fara shiga kafin gidan Dad, dan haka nai gaba raina fari ƙal.

           Cikin farin ciki Mama ta tarbemu, sai faɗi take, “Kai masha ALLAH, lallai Jawaad kana kularmin da yarinya sosai, kaga duk ta sake canjawa, kai Alhmdllh”. Murmushi mukaita yi mudai, inata ɓoye fusaka dan naji kunya kuma ALLAH. Tunda naga banga Amina ba nasan basu taso aikiba, mama ta nuna mana ɗakin kusa da nata, “Ku shiga to, dama yanzu na gama kimtsata, mun samu yanzu taci abincin Alhmdllh”. Shine ya amsama mama da Alhmdllh, ni dai da ba fahimtarsu nai ba sai nabi bayansa kawai.

         Babbar mace muka tarar a ɗakin kwance, kallo ɗaya nai mata na gane maman yara ce da nagani jiya a video call, kenan nan aka kawota ashe? Shine koma faɗamin baiyiba. Kallonsa nai irin na tuhuma ina kumbura fuska, ya ɗan waro idanu da ɗage kafaɗatsa alamar “shima babu ruwansa”. sake tura bakin nai, yaymin gwalo da ɗauke kansa daga gareni.. 

     Shigowar mama tasa na ƙyalesa, yace, “Mama barci take ne?”. “Eh to inaga ta koma, dan tun allurar da sukai mata jiya da daddare bata gama sakinta ba, likita yace da gani ko barci bata samu a can shiyyasa ta jigata sosai”. “Humm” ya faɗa cikin ƙunar rai tare da matsawa gaban katifar da take ya durƙusa saitin fuskarta.

        Jin motsin mutum gab da ita yasa ta buɗe idanu a hankali, ƙure boss tayi da kallo ko ƙyaftawa batayi, har zuwa wasu sakanni, sai kuma ta saki murmushi cike da ƙarfin hali, hanunta dake rawa ta ɗaga da ƙyar ta miƙo masa, babu musu ya miƙa mata nasa shima ta riƙe, murmushin ta sakeyi hawaye na ziraro mata akan kumatu.

       Hawayen ba ƙaramin sake tunzura zuciyar Jay sukayi ba, ya risinar da kansa ƙasa yana haɗiyar zuciya, jijiyoyin kansa harsun fara mimmiƙewa, cikin muryarta da bata fita sosai tace, “Jawaad”. Da sauri ya ɗago idanunsa da sukai jazur ya zuba mata. “Na godema ALLAH da ya ƙaddara haɗuwarmu kafin nabar duniya, nagode ma ALLAH dana samu hanyar da zan ƙarasa abinda na fara kafin nabar duniya. Babu isashen lokaci Jawaad, kayi ƙoƙari a kwanaki biyun nan daga daren yau zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu kaje gidan Alhaji kokino, akwai wata tukunya na nan a tsakkiyar ƙarƙashin gadonsa, ka tabbatar an ɗakko maka ita, karkayi wasa da an fiddota daga gidan ka fasata, sannan ka ƙona abinda ke ciki koma minene, itace makarin........” tari ya sarƙeta.

     A take hankalinmu duk ya tashi, ya tallafota jikinsa yana girgizata da kiran sunanta duk ya ruɗe. Da ƙyar aka samu tarin ya lafa, yanda ta jigata yasa bai nema jin abinda take son faɗarba tunda ta faɗi mai muhimmancin, mama ta gyara mata kwanciya dan danan sai barci yay gaba da ita. Fitowa mukai a ɗakin jikinmu duk a sanyaye.

     Mama ce ta fara magana cikin damuwa, “Tunda ta farka maganar da taketa maimaitawa kenan Jawaad, na rasa wace irin tukunyace wannan?”. Nannauyan numfashi ya sauke yana gyara tsaiwarsa, muryarsa cike da ɗaci yace, “Koma wace irice, kuma kota micece insha ALLAHU zan ɗakkota mama. Bara muje gida Doctor yace zai zo anjima ya ida kawo mata sauran maganinta sai ya ƙara duba jikin nata”. “Eh haka yace mana, ALLAH ya bada nasara to amma banda ganganci dan ALLAH, karkuma a manta da addu'a kunji ko?..............✍

4

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻1Page 54


................Kanmu duk muka ɗaga mata, da amsawa da “Insha ALLAHU mama zamuyi ƙoƙari, a cigaba da tayamu dai”.  rakkiya tai mana har soro. Ganin ya nufi mota na dubesa cikin rawar murya nace, “Yayanmu gidan Dad ɗin fa?”. Bai tankaminba yaja hannuna ya turani mota shima ya shiga, Sadiq ya tayar muka bar anguwar.

         Kallonsa nake idanuna cike da ƙwalla, ya juyo shima ya kalleni fuska a cinkushe. “Kinsan idan kika bari hawayen nan suka zubo sai ranki yay matuƙar ɓaci wlhy!”. Ƙasa na maida kaina ina ƙoƙarin haɗiye kukan dake neman ƙwace mani, bai sake kulaniba har mukaje gida, kowa ɗakinsa ya nufa zukatanmu duk babu daɗi, sai da na rufe ƙofar sannan na saki kukan da ya hanani yi amota irin mai cin rai ɗin nan kuwa. Harnai wanka na fito hawaye basu daina min gudu a kumatuba, a haka na saka wando da riga marasa nauyi nai sallar magriba, ina idarwa na fita kitchen, banji motsinsa ba harna kammala girka abinda zamuci, na ɗauki na maigadi zan fita na kai masa mukaci karo a ƙofa zai shigo. Uffan baice mani ba ya miƙamin hannu alamar na bashi. Bashi nayi na juya ciki shi kuma ya tafi kai masa. Ɗakina na nufa dan banyi sallar isha'i ba, ina farawa ya shigo. Ganin ina salla sai ya juya yana faɗin, “Idan kin idan ki sameni falon baƙi”.

              Koda na idar ban cire hijjabin ba na fita, ruwa na ɗauka sannan na nufi falon baƙin, nai sallama suka amsamin da bani izinin shiga. Dattijon tsohon nanne da muka haɗu da shi ranar akan zancen maman yara, na ajiye ruwa na zuba musu sannan na zauna muka gaisa. Miƙewa na sakeyi dan na kawo masa abinci, ban jimaba na koma da abincin, sakamin albarka baba yay tayi, shi kansa boss na fahimci yaji daɗin hakan da nayi. Abincin ya faraci, boss kuma yana cigaba da latsa wayarsa ta fama, tashi nai zan barsu yace, “Dawo ki zauna, magana zamuyi da shi yanason komawa da wuri”. Na amsa masa da “to” na koma na zauna. Cikin ƴan mintuna Baba ya kammala cin abincinsa yana sake sanya mana albaka, sai da ya sha ruwa sannan ya maida hankalinsa ga boss. “Yauwa ɗana ina saurarenka”. Ajiye wayar boss yay yana furzar da huci. “Baba kamar yanda na fara maka bayani shine ta wace hanya kake gani zan iya shiga gidan domin ɗakko abinda tace? Matsalar shine a ɗakinsa tace abin yake, ɗakinma a tsakkiyar ƙarƙashin gado”. Baba ya jinjina kansa yana gyara zama, “Wato ɗana, ba wai ɗaukar ko shigar bace matsala ma, dole al'amarin sai da lura, su shaiɗanun mutane irin waɗan nan al'amarinsu baya buƙatar fuska da fuska, kamar yanda suke ƴan yaƙin sunƙuru haka masu cinsu da yaƙi ya kamata su kasance suma”. “Hakane baba”. “Yauwa to kagani ni a nawama tunanin wannan aikin kam da mace yafi dacewa ta wani ɓangaren, wani ɓangaren kuma namijinne, ɗakinsa dai bazai shigu gareka matsayin namijiba cikin sauƙi”.

      “Baba to mizai hana ni kawai naje”. Na faɗa kaina tsaye babu ko ɗar a raina. Shiru duk sukai suka zubamin ido. Cikin jinjina kai baba yace, “Shawararki kam abar dubawace, sai dai kuma ai bazai yuwu kije kai tsaye ba, sai dai mu duba wasu ƴan dabaru haka?”.

       Kafin nayi magana boss yace, “Baba bazai yuwu taje ba, mudai sake wata shawarar”. Murmushi naga baba yayi kawai, cikin rawar murya nace, “Miyasa to? Yanzu idan bajeba wa zamuce zamu saka wannan aiki? Ni a ganina baba zai iya ya kaini gidan matsayin jikarsa, insha ALLAHU ni kuma zan ƙarasa sauran aikin inhar na shiga gidan dai da matsayin da zan iya shiga wasu ɓangarori shikenan”.

       Shiru yay bai tankaba, baba yace, “ƴata idan mijinki baya so karki matsa, dan gaskiya wannan aikine mai haɗarin gaske, inaga zanje na ƙara tunanin wata hanyar, kuma sai ku sakeyi, yazam dai kafin safiya idan ALLAH ya kaimu ya muna da abinda muka riƙe, dan na tabbata nan da kwana biyu zai dawo daga tafiyar da yayi yau da safe. zan koma dan banason a farga da bani bane a gate ɗin”. Godiya mukai masa ya tashi yay masa rakkiya, ni kuma na koma ciki ina ƙunƙuni, dan insha ALLAH zanta lallaɓasa nikam harya amince naje nai wannan aikin da kaina. Ganin halin da maman yara take ba ƙaramin zaburar da zuciyata yayiba, na fahimci al'ummata na buƙatar jajurtattun mata irin su maman yara, wayasan shekarun data ɓata domin bibiyar wannan tukunyar? Amma gashi har tana a cikin magagin wahalar da aka bata bataji ta gajiyaba da son cimma ƙyaƙyƙyawar manufarta ba.

      Jin an taɓani na sauke sassanyar ajiyar zuciya, kujera yaja ya zauna idonsa a kaina har lokacin. Kallonsa nai cikin ido ko gezau babu a karo farko na tarihin rayuwata, dukda bugun ɗari-ɗari da zuciyata keyi haka na daure na dake ban cire idanuna ba, “Kar kace a'a, dan ALLAH, mune ya dace muyi aikin nan basai mun saka kowa a ciki ba, sannan bamu da isashen lokacin zaman yin tunni ko binciken wanda zaiyi mana ma.  ɗiyarsa ta ɗakko mana wayoyi ba shine ke nufin zata ɗakko mana wannan ba kuma”.

           Gani kawai nai idanunsa na ƙyalli tamkar hawaye sun taru a ciki, ya girgizamin kai a hankali yana kauda kansa, hannunsa nai saurin kamowa cikin nawa, ya sake juyowa ya kalleni, nawa hawayen ne suka silalo a hankali saman kumatu, “Please yayanmu karkace a'a, nima ka barni nai hidima ga Umm-Anum kamar yanda tayi a gareni tun batasan wacece ni a gareta ba, har raina jin ahalinka nake a zuciyata da ɓargo, idan ka hanani yin wannan aikin zanji matuƙar zafi a raina bakuma zan daina jiba har na koma ga ALLAH, dan zanke ganin kamar ni ɗin dan ba ahalink.....”

      Jawoni kawai yayi jikinsa ya rungumeni batare da ya barni na ƙarasa faɗa ba, da sauri-sauri zuciyarsa ke harbawa a ƙirjinsa, kamar yanda nima tawa keyi, cikin kuka na sake cewa, “Please Yah Jayyyy”.

       Jawaad ya lumshe idanunsa a hankali yana wani cije lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi, “Jay” sunane da mafi yawan mutane ke kiransa da shi, bai taɓajin ambatar sunan da wani banbanci na daban ba ga mai faɗarsa sai yau a bakinta, musamman ma data ja “y” ɗin ƙarshe sai yaji gaba ɗaya tsigar jikinsa ta tashi.

      Ɗagoni yay a hankali na sake zama sosai a kujerar dining ɗin, ya riƙe fuskata a cikin tafukan hannunsa yana sharemin hawayen da babban yatsansa, muryarsa a shaƙe yace, “Miyasa kema kin iya rigima ne Miemaa?, aini Kin riga kin gamai min komai a rayuwa tunda kika zama sanadin haɗuwata da mahaifiyata”. Sake ɓata fuska nai alamar tahowar wani kukan, nace, “To dan ALLAH ka barni na cika ladana”. Murmushi ya ɗanyi mai ciwo yana sake turani cikin jikinsa, “Shike nan bar kukan haka, zanyi tunani daga nan zuwa safiyar da yace insha ALLAHU, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. “Amin” na faɗa ina murmushi.

          Yau shine ya bani abincin da kansa, bayan mun kammala ya taimaka min muka tattare kwanikan zuwa kicin, ina wankewa yana ɗaurayewa har muka kammala sannan muka fito bayan na kammala tanadar abinda zan haɗa mana breakfast insha ALLAHU da safe. Yau kam bamuyi zaman wani aiki ba, brush kurum mukai da yin shirin barci muka kwanta. Babu jimawa barci yay awon gaba damu kuwa. Kusan ƙarfe uku na dare ya tadani, alwala mukai muka shiga yin nafilfili domin miƙa buƙatarmu wajen mahaliccin kowa da komai, mai rahama da ƙari ga bayinsa. Bamu sake kwanciya ba sai da mukai sallar asubahi, da yake a gida yayi shima muna idarwa ya jani muka haye gado, zanyi magana yasa tafin hannunsa ya rufemin baki ruf. Dole na haƙura muka kwanta, barci kuwa yay cak damu zuwa duniyarsa.+


STORY CONTINUES BELOW

       Bamu farkaba sai 8:11am, nice ma na fara farkawar, na waro idanu a waje dan ganin makarar da nake gudu dai ta tabbata, jawoni yay zai maida ya sake kwantarwa nace, “takwas fa ta wuce boss”. Buɗe idanunsa yayi yana ɓata fuska, da alama ba haka ya soba. Da ƙyar ya iya tashi muka shiga wanka tare, a gaggauce mukai muka fito, batare da mun tsaya neman abinci ba muka shirya, tea ɗin dana haɗa manama cayay muje masha a mota, shi dai maigadi ya miƙa masa nasa tare da kuɗi akan ya sayo bread mun makara yau. A motar kuwa muka sha tea ɗin abin dariya da tausayi (lol😂😜). Aiko yau ina rakasa office na fito dan ban kammala aikin jiyaba nima, a ƙofar office ɗin naci karo da rose, ko kallonta banyiba nai gaba abina, harna sauka ƙasa ina jiyo idanunta dake yawo a jikina, nidai ban fasa neman tsarin ALLAH da ga sharrinta ba harna ɓace abina.

  

     Kusan sha biyu da wasu mintuna ya kirani akan idan anfito salla nazo na samesa. Amsa masa nai da to ana idarwa kuwa can na nufa, shi kaɗaine a office ɗin yanata ayyuka, duk da da alama shima yanzu ya shigo ɗin, ban zaunaba har sai da ya bani izinin zama. Tasowa yay daga kujerarsa ya dawo ɗayar dake kallon wadda na zauna, ya kamo hannayena cikin nasa yana mai tsareni da idanunsa nan masu takurani. “Miemaa na amince kije gidan Alhaji kokino, amma da sharaɗi”. Cike da ɗoki nace, “Minene shaɗarin?”. “Sharaɗin shine kwana ɗaya kacal da yini biyu zakiyi, idan yayi tsaurine kikai biyu, sannan tare zamuyi aikin dan bazan taɓa barinki ki shiga wannan aikin mai haɗari ke kaɗai ba”. Rungumesa nai saboda jin daɗi, hannu biyu ya amsheni yana murmushi, nace, “Na yarda da duka sharaɗin, ALLAH ya bamu sa'a da nasara”. Yace, “Amin Beejay, yanzu zaki tashi Sadiq ya kaiki gida kiɗan shirya, shine zai kaiki inda zaku haɗu da baba, sai ya ƙarasa da ke”. “Wow da wuri haka?, insha ALLAHU zaka sameni fiye da yanda kai tunani, kaida kaitamin addu'a boss ɗinmu abin alfaharinmu”. Ɓata fuska yay cikin wasa yace, “ke da wa?”. Ganin yanda yay da fuska ya sakani ƙyaƙyƙyawa da dariya, “Ni kaɗai mana, sai su oga Jabeer ”. Hararata yay, “K nifa kibarma kirana da wani boss na gaji da ji”. Kunya naji sosai, dan haka na ɓoye fuskata a ƙirjinsa ina dariya.


★★★★


       Duk yanda muka tsara hakance ta kasance, bayan sallar la'asar muka isa gidan Alhaji kokino, cikin shiri nake irin na ainahin garorin yaran nan na ƙauye da ko karatu basu taɓa samu ba, ga matarsa kam mun samu tarbar mutuntawa, ƴaƴan gidanne dai sai a hankali, dan gaba ɗaya halayensu baimin ba, sai wani famar min kallon banza suke, musamman mai son boss ɗin nan. Shiru nai na maƙure jikin kuje alamar tsorata ta baƙunta. Baba mai gadi da suka gama gaisawa da hajiya ya juyo ya kalleni, “K Larai! Baki iya gaisuwa bane? nifa banason wannan ɗabi'ar banzar kin sani”. Muryata na rawa nace, “Ina wuni hajiya, mun sameku lahiya?”. Dariya yaran suka bushe da ita duka falon, irin wai ƙauyancina ne ya basu dariyar. Ita dai hajiyar Murmushi tayi tana cigaba da kallona, tace, “Lafiya lau Larai, yasu mamar taku?”. “Lahiya lumi suke aradu hajiya, tace tana gaiheki”. Saboda dariya har ƙasa suke faɗuwa daga saman kujerun. A raina nace, ‘Wawaye kawai’.

      Baba ne da yake ɗan murmushi shima yace, “Hajiya dama tazo daga ƙauye ne can anguwar tudun birji wajen ƴar uwar mahaifiyarta, to saita iske wai sunje suna ko ina, kuma sai jibi zasu dawo, shine nace data koma kuma ai wahala goma da ashirin tazo nan saita kwana idan suka dawo sai taje, ALLAH yasa dai ban wuce gona da iriba?”. “A'a Malam baka wuceba kam, ai kaga anyi zuminci tunda dama kaƙi kawo mana iyalanka shekara da shekaru, ni nagode sosai da wannan ziyara”. “Nima nagode hajiya, bara na koma bakin aiki to ga tanan”.

      Ganin zai fita nai ƙwalƙwal da idanuna alamar kuka, “Kaka anan zaka barni?”. Juyowa yay da ɗan faɗa yana min daƙƙuwa, “Kinci gidanku Larai, nanɗin cin mutane ake bare kice za'a cinyeki? To idan hakan bai mikiba tashi ki kama hanyar ƙauye idan su Rakkiyar sun dawo sai ki dawo”. Baki na tura ina maƙe kafaɗa, “Ni alkur'an a'a”. “Ke kuma kika sani ja'ira kawai” ya faɗa yana ƙarasa ficewarsa. Yana fita suka fara jana da hira wai na basu labarin garinmu, nasan sosuke kawai su ringajin yanda nake magana suna dariya. Abinci aka kawomin, inaci ina basu labari kamar wata sakara, suko sai kwasar dariya sukeyi da zagina a kaikaice.

        

              Haka na maida kaina ƴar cali-calin ƙarfi da yaji a gidan Alhaji kokino, sannan aiki duk dana gani zan tashi nayi kamar bansan ciwon kaina ba, bansan inajin kewar mijina ba sai da dare yayi nazo zan kwanta a tabarmar ɗakin masu aiki, hakan bai dameni ba, dan wannan ba sabo bane a gareni, kewar tasace dai kawai naji, sai tunani nake yanzu koshi mi yakeyi? Oho.


STORY CONTINUES BELOW

★★★★


         Yanda Bily ke cikin kewa a gidan Alhaji kokino haka Jawaad yake a gidansa, tun da ya dawo daga wajen aiki duk sai yaga gidan yay masa wani faɗi da baƙi, yay zaune a babban falo yanata kallon sashenta, da ƙyar ya iya tashi yaje yay salla, koda ya dawo yaga zuciyarsa na ƙara ƙuntata sai ya fice daga gidan zuwa gidansu Amina, baisan yawan zuwa gidan dan kar a fahimci akwai wani abu duk da yasan Dad baya a garin, sannan ma ƴan gidan hankalinsu baya aƙwance saboda rashin ganin Shahudah, shiko akan hakan yamaƙi zuwa ko family house ɗinsu tunda suka dawo, ya kuma kashe wayar da kowa zai iya samunsa.

     A gidan su Amina ya ɗan rage kewa,  maman yara tace ya kwantar da hankalinsa tanaji a ranta insha ALLAH bilkisu zata iya, dan a zuwan da sukayi jiya ta fahimci tana da hankali da wayo. Kai kawai Jawaad shi dai ya ɗaga, zuwa tara ya baro gidan, rasa mizaiyi yayi, haka dai ya koma gidan ransa duk a jagule. Tea kawai yasha yay shirin barci ya kwanta a ɗakinta, jin zuciyarsa ta sake ƙuntata ya ɗauki waya akan bara ya kirata ko muryarta yaji, sai da yaji switch up sannan ya tuna cewar bama ta tafi da waya ba. Tsaki ya buga yana jefar da wayar a kan gadon, waishi mima yasa ya barta taje ne?. haka yayta takaicinsa hardai daga ƙarshe ya sake ɗaukar wayar, Anuwar ya kira, bugu ɗaya kuwa ya ɗauka cike da ɗoki. Wannan kiran Anuwar shine ya rage masa kewar Bilkisu a ransa, sunsha hira sosai dai sai kusan ɗaya da rabi na dare sukai sallama, sai kawai yayo alwala ya hau salloli ma. Sai kusan uku ya kwanta sai barci.


WASHE GARI


        Washe gari ma haka na tashi cikin ƴan aikin nan duk abinda sukeyi dani akayisa, babu wanda yace nabari a gidan, saima faɗa suke wai nafi masu aikin iya aiki. Nidai bance komaiba, sai lokacin da hajiya ke faɗa akan mai gyara mata ɗaki batayi da ƙyau ba, idan bazata iyaba a canja da wata. Murmushi nayi domin wata damace ni a gareni hakan, dan haka nai caraf nace ni bara na gyara mata yau. “A'a Larai, daga zuwa sai kita aiki? Aiba haka akeyiba”. “Lah hajiya karki damu, yo mufa mun saba alkur'an, dafa a ƙauyene da yanzu inacan ina sirhe, yo ni ina zan iya da wanga lalaci naku na mutan burni hajiya, ke dai bani aiki kiga aikin mata aradun ALLAH yanzu na ƙalƙale miki ɗaki ko fadar mai garin garinmu bata nuna masa fita ba”. Sunata dariyarsu niko na fuske abuna.

       Zagewa nai naima ɗakin gyara na sosai, sai gashi hajiya na santi ita da yaran nata, aiko ranar na aikatu, dan ɗakunansu sukaita sakani na gyara musu suma yaran, duk da na gaji haka na daure dan fatana nidai a ƙarshe a turani ɗakin mai gidan, amma sai naji tsit. Washe gari babu wanda ya sakani wani aiki, har yamma, abin duk ya dameni inata addu'a da fatan samun hanyar da zan shiga ɗakin, dan a yinin da nai jiya na aiki nazarin gidan naitayi da hanyoyin cikinsa. Kusan ƙarfe huɗu da rabi ina zaune a can baya ni da ɗaya daga masu aikin gidan sai ga hajiya ta fito, sannu duk mukai mata da gaisheta dan duk yau ban gantaba bata yini a gida ba. Tace, “Larai Please zoki min wani ɗan aiki nan na dawo a makare”. “To” nace ina miƙewa, wani irin farin ciki ya kamani ganin mun nufi sama, inda nake da tabbacin turakar mai gidance anan. Fasalta muku yanda tsarin yakema ɓata lokacine, kowa ta ƙiyasta tsaruwarsa kawai. Kallona tai tana ɗan murmushi, “Larai nan zaki gyaramin, babu wata mai aiki dake shigowa ni nake gyarawa, to naje saloon da gyaran jiki sai yanzu na dawo gashi lokaci ya ƙure, kuma Alhaji nanda takwas na dare zai iso yayi tafiyane, na yarda da kene saboda kinada nutsuwa, dan ALLAH ki gyara komai ƙal kinji, ni kuma zanje mu ɗaura masa abinci”.

       Farin cikin da ke cin raina na danne, na amsa mata da “Insha ALLAH hajiya zaki samu fiye da yanda kikeso” “Yauwa ƴar albarka nakuwa gode, bara na turo miki Laila ta tayaki. Ɗaf ɗokina ya gudu, kamar zanyi magana sai kuma nai shiru harta fice. aikin na fara ina tunanin yanda abin zai kasance, dan insha ALLAHU bazan fita daga ɗakin nanba yau sai da abun nan.

     Laila ɗaya daga cikin yaran gidan ta shigo ko sallama babu, bataimin magana ba ta nema waje ta kwanta a cikin kujera tana danna waya, nima bance da ita komaiba na cigaba da aikin, tsaf na kammala falon na saka fresheners dana gani da turaren wuta, sannan na nufi bedroom ɗin. Ƙaton gaske ne shima kuma ya haɗu, sai dai gadon irin gajere ɗin nanne wanda babu yanda za'ai ka iya leƙa ƙarƙashin gado balle harka jawo abu. Wucewa nai toilet ina ƙullawa da kwancewa a raina, gabana sai faɗuwa yake amma inata addu'a. Bayan na gama sai na ɗan fito falon dan naga mi laila keyi. Tsaye na taddata ta tashi, ta kalleni tana faɗin, “Nazo na baki bedsheet ko?”. Kaina na ɗaga mata alamar eh. Tare muka koma cikin ɗakin, ta buɗe haɗaɗiyar Wadrobe ɗin ta ciro zanin gado mai ƙyau ta ajiyemin a ledarsa. Murmushi kawai nai mata, a raina ina addu'ar ALLAH yasa ta fita, sai kawai naga ta ɗane sofa ta kwanta. Kaina na dafe ina cije leɓe, wannan itace damar da nake da ita ta ƙarshe, gashi kuma tana neman kufcemin. Jiki a sanyaye na fara yaye zanin gadon dake a gadon, na ajiyesa gefe suma filolin na fara cire rigarsu, harna gama na saka na wanda ta fiddomin, na ɗauki zanin gadon na fara shimfiɗawa, ina gab da gamawa akai kiran wayarta, gani nai ta tashi tana murmushi, ta kalle ni tana faɗin, “Larai banda aikin mugunta fa, ki tabbatar komai tsaf bara na amsa waya”. Kaina na ɗaga mata ina murmushi, ta zare keys ɗin duka drawer ɗin ɗakin ta fita da su, bakina na taɓe dan inda take bama tsaron ni bashine abin harina ba. Wata ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi jin ƙarar rufe ƙofa alamar tama fita daga falon. Ban ɓata lokaciba na yaye zanin gadon gaba ɗaya jikina na rawa, katifar na kama na ɗaga, bana ganin abinda ke ƙasan gadon saboda an saka kwali bisa katakon shimfiɗar gadon, maida katifar nai na ɗan fito falo na sake lalleƙawa, ganin babu kowa nai azamar dawowa na sake ɗagawa, shima kwalin ɗagashi nai, addu'a naketa yi a raina nidai, ina ɗaga kwalin wani hayaƙi ya taso ya bulemin ido, tari na farayi kamar zan mutu, na saka hannu na toshe bakina dan kar wani ya jiyoni, saurin maida katifar nai saboda jin kamar motsin tafiya, na cigaba da ƙoƙarin gyara gadon kamar dama shi nakeyi, hajiyace ta shigo, ɗagowa nai naimata murmushi, itama dai fuskarta da murmushin take faɗin, “Kai sannu da ƙoƙari larai, falon yayi ƙyau kuwa, an wanko bayi ko?”. “Eh na wanke hajiya, yanzu nan zan ƙarasa kawai”. “Yauwa to sannu da aiki kinji, ina Lailan?”. “Yanzun nan tafita inaga abu zata ɗakko”. “Okay to bara naje mu cigaba da namu aikin muma, dama dan naga yaya aikin ke tafiyane shiyyasa”.

    Ficewa tai, ni kuma na sauke ajiyar zuciya da lumshe idanu na buɗe lokaci guda, hannuna dafe da ƙirjina. Yanzu kam a fili na fara karatun alkur'ani mai girma cikin suratul baƙara, na sake ɗaga katifar da kwalin, baƙin maciji na gani kwance idanunsa jajur, sai tukunyar ƙasa a gefensa an ƙulle bakinta da jan ƙyale. UBANGIJI mai rahama da ƙari, sai ya sakamin dakiyar zuciya da ganin nasa, nama cigaba da karatuna ina sake danne al'ajabi na, baya ya ringa ja daga gaban tukunyar, ganin haka sai na cigaba da karatun nima, sai kawai naga ya sulala ya shige wani rami a jikin bangon wanda bansan tayaya aka ƙirƙiresa ba. Cikin rawar jiki na ɗauka tukunyar na fiddo, ina cigaba da addu'a, sai dai ƙirjina wani irin mahaikacin bugawa ya keyi tamakar zuciyata zata faso ta fito, maida kwalin da katifar nayi, na fito falo da tukunyar jikina har yanzu rawa yake, sai da na leƙa falon ƙasa na tabbatar babu kowa sai tv kawai dake magana sannan na fito cikin sanɗa, addu'a nake jikina kuma na wani irin tsumar rawa, ina ficewa a falon naji muryar cikin masu aikin na faɗin, “wanene ya fita?”. Innalillahi na faɗa ina ƙara sauri, baba maigadi yana hangoni ya taso, na tsaya bayan wata mota inata waige-waige, isowa yayi gareni cikin sassarfa, na miƙa masa tukunyar ina magana da rawar murya matuƙa, “Baba, ka kirashi yazo ya amsa yanzun, bara naje na ƙarasa aikin da aka sani karsu fahimci wani abu”. Kansa ya ɗagamin kawai, na juya da gudu na koma, nai saurin daidaita yanayina lokacin dana shiga falon, hajiya na iske tsaye, ta zubamin ido cike da kallon tuhuma. “Keda kike aiki a sama mi kuma ya sakko dake ƙasa larai?”. Da ƙyar na iya ƙaƙalo yawu na haɗiye ina murmushin ƙarfin hali, “Hajiya wani yana na gani ta tagan ɗakin (Window) shine fa na zagaya dan na share sai naga ashe da nisa ta waje”. Dariya naga ta tuntsure dashi tana girgiza kanta, “Banda abinki larai ba a sama kikeba? Ki barsa akwai yaron dake sharewa zaizo ya share ranar weekend”. Kaina na ɗaga mata, ta juya kicin ɗin ni kuna na nufi saman benen ina godema ALLAH da ya rufamin asiri. Sai dai jikinafa har yanzu wani irin tsuma yakeyi, ga Masifaffen ciwon kai da alokaci ɗaya ya saukarmin. Haka na daure na koma ɗakin, canma na iske laila tsaye tana ƙarema ɗakin kallo, da masifa ta hauni akan ina naje? Kenanma tana fita nima na fita tunda ga shi nan ko gadon ban kammala gyarawa ba. Haƙuri na bata duk da zamuyi sa'anni da ita, na faɗa mata kamar yanda naima hajiya bayanin share yana. Tsaki taja min tana faɗin, “Malama kiyi sauri ki gama inada wajen zuwa”. Kaina na ɗaga mata kawai a sanyaye na hau gyaran gadon, yanzunkam tsaye tayi a kaina harna kammala aikin, hakan bai dameniba tunda naci nasara, na saka turaren wuta muka fito tare ina dafe kai saboda ciwon da yakemin.


★★★★★


         Jawaad na tsaka da aiki a office, sai dai rabin hankalinsa duk yana ga Bilkisu, tunda ta tafi basuyi ko waya ba, sai dai baba na faɗa masa tana cikin ƙoshin lafiya ya cigaba da mata addu'ar nasara. Wayarsa da tai ring ya duba, ganin baba ne yay saurin ɗagawa babu ɓata lokaci. Ko gaisuwa baba bai jira sunyiba yace, “Duk inda kake ka taho nan yanzun, yarinyarnan ƴar albarka tayi nasarar ɗakko tukunyarnan gata a hannuna ma”. Zaram Jawaad ya miƙe tare da wancakalar da takardun gabansa, bai saurari ɗaukar komaiba ya fice, key ɗin motar ya amsa a hannun Sadiq yace ya zauna ya jirashi dan da kansa zai tuƙa motar.

     Gudu yake na tashin hankali kamar titin nasane shi kaɗai, tsabar karya samu cinkoso ma sai ya ringabi ta wasu hanyiyin daban yana ratsema duk titin da yasan zai iske go-slow. Acan bayan layin suka haɗu da baba maigadi daya fito daga gidan akan yaje salla, da yake anata kiraye-kirayen sallar magriba ne. Miƙa masa kawai yayi batare da sun tsaya doguwar magana ba, “Maza kaje ka fasata Jawaad, karka tsaya ɓata lokaci”. “To baba, amma matata fa?”. “Kaje itama zan fiddota yanzu dana koma, dan tabbas akwai haɗari babba Alhaji ƙarfe takwas zai sauka ƙasarnan, duk inda yake a halin yanzun kuma nasan yaji a jikinsa an ɗauka tukunyar nan.............✍


3

ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻Page 55


.................“Baba bazan iya barin anguwarnan ba sai da ita”. “Bazai yuwuba Jawaad, kaje itama insha ALLAH lafiya zata fito, dana koma yanzu zan fiddotane itama”. “Baba kaima fa bazai yuwu ka zaunaba, dan zamanka akwai haɗari Sadiq zaizo ya ɗaukeku tare, kaje ka haɗa duk wani abunka mai muhimmanci”. “To shikenan ɗana, ALLAH yay maka albarka sai ya zo”.

             

CIKIN JIRGI


           Tun ɗaga gadon farko da Bilkisu tayi jikin Alhaji kokino ya bashi, to amma yasan akwai mai tsaron wajen koma waye tsautsayi ya kaisa sai dai gawarsa. Sai dai kuma ƙarfin gwiwarsa ta sare lokacin da yaga zoben dake a hannunsa yana canja kala zuwa baƙi, gabansa yay matuƙar faɗuwa, gashi babu damar kiran waya, a take komai nasa ya fara kwancewa lokacin da zobe tsafinsu ya shiga hasko masa abinda bilkisu keyi, sai dai ALLAH ya hanashi ganin fuskarta sam sai duhun inuwarta kawai yake gani harta ɗauki tukunyar data ɗauki tsawon shekaru a jiye babu wani mahaluki da ko yatsansa ya taɓa taɓata, sai maman yara da idanunta suka gani itama kuma saida ya sakata tai nadamar hakan, tanama can cikin nadamar ma (Masu karatu Alhaji kokino fa baisan yanzu maman yara bata wajen yaransa ba, dan randa ƴarsa ta saka masa maganin barci koda ya farka a washe gari har an maida masa wayoyinsa, babu wata kuma alama da Jawaad ya bari dazai iya zarga, shikuma da yasan babu wani mahaluki da zai iya masa makamancin haka sai bai kawo komai a ransaba, a washe garin ya bar ƙasar batare da yayi waya da yaransa akan komaiba. ALLAH kuma ya hana shaiɗanun dake taimaka musu fahimtar komai balle shugaban nasu na dodon tsafi damar sanar masa.

         Gaba ɗaya ya jiƙe da uwar zufa sharkaf kamar ana masa wanka da ruwan zafi, jiyake tamkar ya rikito jirgin ƙasa dan tsabagen tashin hankalin da yake a ciki, gashi sauransu kusan awa ɗaya da rabi kafin ma su sauka. Lallai wannan ko wanene a cikin gidansa sai ya ƙarar da dukan ahalinsa bama shi kaɗaiba.

          Jawaad kam kai tsaye gidan Alhaji babba ya nufa, sun fito masallaci kenan sai ganin Jawaad ɗin yayi ya fito a mota, sai dai yanayinsa yay masifar ɗaga hankalinsa. Tambayoyi ya shiga jera masa, Jay dai bai amsa masa ko gudaba a ciki ba, “Baba wannan ba lokacin amsa tambayoyi bane”. Ya faɗa yana nufar cikin gidan da tukunyar a hannunsa dan da duk a wajen gate suke inda Jawaad ɗin ya faka motarsa. Alhaji babba da ciwon ƙafa ya matsamawa a kwanakin nan ga yawan mafarke-mafarke da faɗuwar gaba da yake yawanyi yabi bayan Jawaad jiki a sanyaye, iskesa yay tsaye tacan bayan ɗakunansu ya ɗaga tukunyar zai fasa bakinsa ɗauke da addu'a. “Kai wai minene kake haka? sai kace wani matsafi?”. Jikake “Tassss!” Jawaad ya buga tukunya da ƙasa.

       Fashewarta tayi dai-dai da faruwar abu uku a zahiri, biyu a ɓoye.+


       Na farko shine saukar jirgin da alhaji kokino ke a ciki bisa ƙasa. Na biyu mummunar faɗuwar gaba ga duk masu alaƙa da tukunyar, na uku faɗuwar Umm-Anum dake a kicin tana dafama Abbu shayi da yake a gidanta yake yau. Na baɗinin kuwa daga can fadar shaiɗancinsu ya faru.

        Wasu irin mugayen layune manya-manya guda uku a ciki, sai ƙananun allurai da wasu irin abubuwan surkulle da baisan minene ba shima, sai ruwan kuwa da suke ciki na jini ne sai wani uban wari ya keyi maiban tashin hankali, Alhaji Babba ya waro idanu waje jikinsa na rawa da toshe hancinsa da hannu yace, “Muhammad minene wannan? A ina ka samoshi ni Nuhu?”. Taga-taga Jawaad yay zai faɗi idanunsa a matuƙar jazur, Alhaji babba yay saurin riƙosa. Atare suka sauke ajiyar zuciya, da sauri Jawaad ya zare hanunsa daga na Alhaji babba ya nufi cikin gidan, hankalin Alhaji babba sake tashi yayi, ya kalli tukunyar da kayan ciki ya kalli hanyar da Jawaad yabi, ya juya zai bishi sai gashi ya fito ɗauke da ashana da gallon ɗin fetur na Genretor. Akan kayan ya zuba ya ƙyasta musu wuta. A take gidan ya ɗauki wani irin mahaukacin ƙauri mara daɗin shaƙa, sai ƙananun motsi kamar ana guje-guje, suka hau waige-waige suna dafe kunnuwansu da hannu da sauri, sai kuma aka fasa kuka da wata irin murya mara daɗin saurare. Ana ƙwalla kiran sallar isha'i gidan kuma yay tsitt dan masallacin idan aka kira salla kakanji tamkar a cikin gidan akeyi tsabar kusancin da suke dashi. Jagwab Jawaad ya zauna a ɗan dakalin da aka shuka fulawoyin gidan, ya dafe kansa yana karanto hasbinallahu wani'imal wakil. Sai kuma ya miƙe zumbur saboda tunawa da bilkisu da baba, lallai duk inda Alhaji kokino yake yanzu jirginsu ya isa sauka ƙasarnan. “Baba ina zuwa ya faɗa yana nufar gate cikin zafin nama. Sake binsa da kallo Alhaji babba yayi harya fice.

      Jay ya buɗe mota zai shiga saiga drivern gidan Ummah babba ya kawo Batool, baiko kallesu ba duk da ɗaga masa hannu da takeyi ya buɗe motarsa ya shiga tare da yin reverse yabar anguwar da mahaukacin gudu kamar zai tashi sama.


STORY CONTINUES BELOW

★★★★


          Tun ina ɗaukar ciwon kai wasa har ya fara neman fin ƙarfina, dan idanuna sun fara rufewa bana ganin abu da ƙyau, innalillahi wainna'ilairraji'un naketa ambata da sauran addu'oi. A wannan halin lariya ta shigo ta sameni ɗaya daga masu akin gidan. “Larai kije inji hajiya”. Gabana ne ya faɗi, dan a tunanina kodai ta gane wani abune?.

      A babban falo na iskesa tsuggune ita kuma tana daga tsaye da hijjab jikinta alamar salla tayi, “Haba dai baba, ai bai kamata ace a darennan zata wuceba, gashi bamu tanadar mata komai ba, kacema wanda yazo ɗaukar nata yayi haƙuri sai da safe sai ya dawo su tafi”. Baba da gabansa ke faɗuwa yace, “To hajiya banƙi ta takiba, amma da anyi haƙuri sun tafin dai babu damuwa, idan ta gama kwanakinta a can ɗin saita dawo nan ta ƙara miki kwana ɗaya daga nan saita wuce”. Shiru tai kamar bazata amsaba, sai kuma tace, “To shikenan na amince da wannan shawarar taka, bara na basu ko kuɗin motane, amma dan ALLAH fa kartaƙi dawowa”. “Insha ALLAHU zata dawo Hajiya”. Kallona tai da ɗan murmushi, “To larai kije ki ɗakko kayanki anzo ɗaukarkine”. Kaina na ɗaga kamar banason tafiyar jikina a sanyaye, ta nufi sashenta ni kuma na nufi ɗakin da aka saukeni na ƴan aiki, ƴar bakko ɗin kayana na ɗakko na fito bayan nama sauran sallama, kaina ne kemin ciwo sosai, dauriya kawai nakeyi.

     Dubu biyar hajiya ta bani, nai mata godiya da cewar ai zan dawo na sake mata kwana biyu kafin na tafi, da haka mukai sallama. Muna fitowa daga cikin gidan ana yin horn a ƙofar gate. Wani irin Masifaffen  faɗuwa gabana yay, shi kansa baba mai gadi a take ya diririce, saurin nunamin ɗakinsa yay yace na shiga ciki, shi kuma yaje ya buɗe gate ɗin.

     Drivern Alhaji kokino ya danno kan motar da sauri, kamar yanda baba ya saba duk sanda ya shigo gidan zaije su gaisa kafin ya shige, yanzunma hakan yayi, sai dai sama-sama Alhaji kokino ya amsama baba maigadi, yay ciki da masifar sauri tamkar zai tashi sama. Drivern ya kalli Alhajin ya kalli baba maigadi yana faɗin, “Anya kuwa lafiya gidan nan yake yau? Tunfa a filin jirgi yake azalzalata kamar wanda akace gidansa naci da wuta”. Baba maigadi yace “kadai bisa da jikkar ka dawo”. Yana ganin drivern shima ya shige yay saurin nufar ɗakinsa, jikkarsa  daya gama haɗawa Bilkisu ta haɗo da tata ta fiddo, ƙofa ya buɗe mata ta fice da sauri shima ya rufa mata baya, suna fitowa Jay na isowa wajen, da sauri bily ta buɗe gaba ta shiga baba kuma ya shiga baya, jan motar yay da gudu yabar anguwar.

          Da gani har baba muka sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma naji hawaye na gangaromin a fuska a hankali, kife kaina nayi saman jakunkunanmu dana shigo dasu kawai na cigaba da kukana, babu wanda yay magana a cikin motar har muka iso, sai sheshshekar kukana kawai.

         1

___________________________________


           Ɓangaren Alhaji kokino kam koda ya shigo falon sama yay cikin sassarfa, sam bayama jin sannu da zuwan da ƴaƴansa suke masa harda ma matar tasa. Kaɗan ya rage babbar rigarsa ta taɗesa ya faɗi a step na bakwai, yay azamar riƙe ƙarfen ALLAH ya soshi bai faɗinba.

     Matarsa da abin ya girmi kanta tuni ta take masa baya da hanzarinta, sai dai tana zuwa ƙofar ɗakin sai ta jita a datse alamar ya kulle kansa. Duk da bayau ya fara mata hakanba sai taji na yau yay mata zafi, ta shiga buga ƙofar tana ambatar sunansa amma ko tari bataji yayi ba. Tana nan tsaye hankalinta a matuƙar tashe ya buɗe ƙofar da ƙarfi ya fito, jikinsa sai ɓari yakeyi.

       “Alhaji lafiya wai?”. Maimakon ya bata amsar tambayarta sai cayay, “Wanene ya shigarmin ɗaki?”. “Alhaji ban gane wannan tambayarba, wanene zai shigar maka ɗakin bayan ni?......” “K!! Bansan iskanci, uban wanene ya shigarmin ɗaki?!!”. Yanda yay maganar tamkar zai haɗiyeta da mugun hargagi kuma sai duk ta firgice, jikinta na rawa ta shiga girgiza masa kai, “Alhaji babu wanda ya shiga wlhy sai ni, sai ko jikar baba maigadi da nasa ta gyara maka saboda aiki yamin yaw.....” wani irin wawan mari ya ɗauke fuskarta dashi jikinsa na rawa. “Sau nawa zanmiki gargaɗi akan saka wani yaymin gyaran ɗaki a gidan nan?!!”. Yanda jikinsa ke karkarwa dolene ya bama mai kallo tsoro, tunda take da shi ko sanda yay auren amaryarsa yana mata wulaƙanci saboda asirin waccan bai taɓa ɗaga hannu a kantaba ko murya irin haka, gashi gaba ɗaya tama lura baya a cikin hayyacinsa, mike damun mijinta haka ne? Mi Larai ta aikata masa a ɗakin da ita bata ganiba? dan yanzu ta shiga ta gama haɗa masa ruwan wanka ta kuma ƙara Air Fresheners a ciki bayan ta shirya masa abinci a dining....

      Cikin wata gigitacciyar tsawar ya kuma cewa, “Ina yarinyar take?!!!”. Share hawayenta tayi ta nufo ƙasa tana kiran larai, shima biye yake da ita yana baza idanu da babbar riga yaga ta ina larai zata ɓillo?. Sai dai tun kafin su sakko ƙasan ma ƴaƴansa da ma'aikatan gidan harsun bazu nemanta suma.

        “Momy wlhy fa Larai bata gidan nan”. A rikice hajiya tace, “Ban gane bata gidan nanba, yo ina zataje?”. Kafin wani cikinsu ya bata amsa Alhaji kokino yace, “Wai ita laran ƴar gidan uban wacece? Da ga ina kuka samota?!!”. “Dady jikar baba maigadi ce” laila ta bashi amsa a tsorace.

     “Maigadi?!!” ya faɗa a wani irin zazzaro idanu, kafinma wani yace wani abu tuni ya fice daga falon zuwa gate, driver kawai ya iske akan bench a zaune yana ƙoƙarin zuba abincin da aka kawo musu daga cikin gidan. “Kai Mati ina maigadi?!”. Yanda Alhaji yay maganar ne ya saka driver sakin plate ɗin abincin ƙasa a tsorace, “Alhaji lafiya kuwa?”. “Ina tambayarka maigadi kana tambayata kafiya?!”. “Ayi haƙuri Alhaji, yana bayi inaga, nima dana fito ban gansaba, nasan dai bazai wuce banɗaki ya zagaya ba”. “Ƙwanƙwasa masa maza ya fito” tashi driver yay ya nufi cikin ɗakin maigadi, sai dai yana taɓa ƙofar toilet ɗin da nufin bugawa sai kawai yaga tama buɗe da kanta, ya leƙa babu alamar mutum, kai da ganima ba'ayi amfani da ruwaba yanzun dan bayin a bushe yake ƙamas. fitowa yay da sauru yana faɗin, “Wlhy bayanan ashe”. Shaƙosa Alhaji kokino yayi yana faɗin, “Idan baya nan dan ubanka ina yaje?!” sosai hankalin kowa ya ƙara tashi, dan ya koma musu tamkar wani zararre. Jikin driver sai rawa yake dan yaji shaƙa, Alhaji kokino ya wullar dashi gefe ya shiga ɗakin da kansa. Hakan yasa Hajiya ta sake take masa baya duk da a tsorace take. Abun mamaki duk kayan baba maigadi babu su, sai abinda ba'a rasaba waɗanda sam basu da wani muhimmanci ga mai su. A yanzune hajiya ta fahimci lallai akwai abu a ƙasa kenan. A fili tace “Mi hakan ke nufi to?”. Cikin tsananin tashin hankali Alhaji kokino yace, “kezan tambaya Nafisa, shikenan kin kasheni Nafisa, taya za'ai har wani ya kawo baƙon ido gidan nan kai tsaye ki yarda da shi harki bashi damar shigarmin ɗaki?!!”. “Wlhy Alhaji ni....” hankaɗeta yay gefe batare da ya jira ta ƙarasa faɗaba, ya fice da saurinsa yabar mata ɗakin, kuka mai tsuma rai ta fashe da shi a ranta tana mamakin miyasa baba maigadi zaiyi haka? Shekaru nawa suka ɗauka tare bai taɓa cutar da suba sai a yanzun? shin minene maigadi yasa Larai ta aikata ne? Ta tuno fitarta ɗazun lokacin da take mata tambaya akan ina taje ita da aka saka aiki? Tabbas ba cikin nutsuwa larai ta bata amsa da cewar yana ta fita sharewa ba, amma da yake bata kawo komai a ranta ba sai bata zargeta ba.


STORY CONTINUES BELOW

SAUDIA


           Hankali tashe Anum ta ƙwala kiran sunan Abbu da Anuwar dake falo suna jiran shayi, har rige-rige. isowa suke cikin kicin ɗin, ganin Umm-Anun yashe a ƙasa yay masifar ɗaga hankalinsu, Anuwar ya tallafo kanta ya aza bisa cinyarsa yana mai fashewa da kuka, Abbu ne yay ƙarfin halin komawa ya ɗakko goran ruwan zam-zam ya dawo, a hannu ya zuba ya shafa mata a fuska. Ta kawo wani irin nannauyan numfashi da gurnani, ƙara ɗiba yay ya zuba mata a fuskar, nanma tagwayen ajiyar zuciya ta sauke a jajjere. Matsawa yay sosai yana ambatar ainahin sunanta, BILKEESU! BILKEESU!!, BILK...... Da sauri ta buɗe idanunta tana amsawa da “Na'am BAB......” sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa ta kafe Abbu da ido, saurin janyewa tai ta maida kan Anum, sai kuma ta kalli Anuwar da take a jikinsa. Cikin ɗan rawar baki tace, “Jawaad!”. Abbu da Anuwar suka kalli juna, sai kuma suka kalleta, zaune ta tashi tana raba idanu a kansu, sai kuma tai saurin dafe kanta tana faɗin, “Ya ALLAH”. Riƙe mata kan Abbu yayi yana faɗin, “Sannu, kinga tashi muje ɗaki”. Bata musaba ta yarda ya taimaka mata suka fita, sai faman lumshe idanu take saboda jiri.

     Kwantar da ita yay a saman gado ya ɗaura kanta bisa cinyarsa, umarni ya bama Anuwar ya ɗakko masa wani magani a ɗakinsa, babu jimawa Anuwar ya dawo, cayay ya zubashi a abin turare, nan danan hayaƙi mai ƙamshi ya fara tashi a ɗakin, shi kuma ya shiga karato addu'oi yana tofa mata. Cikin mintunan da basu gaza biyarba barci yay awan gaba da ita. Duk ajiyar zuciya suka sauke, kafin Abbu ya gyara mata kwanciya suka fito falo suka barta.

     Cikin ɗaurewar kai Anuwar yace, “Abbu Yah Jawaad fa ta kira”. “Naji Anuwar, amma lallai akwai wani abinda ya faru inaga, dan yanayinta yayi kama dana wadda ta dawo hayyacinta gaba ɗaya, dan a farko sunan baba zata kira ganin nine yasa tai shiru”. “Abbu to kona kira Yah Jawaad ɗin muji?” kansa ya ɗaga masa alamar eh.


★★★★★★★


         Su Jawaad na zaune a falon Alhaji babba sun rufu kan bilkisu da keta juye-juye a ƙasa da kukan kanta suna mata addu'a kira ya shigo wayarsa da Numbers ɗin ƴan saudiyyane kawai a ciki, ɗagawa yay yana miƙewa, daga can Anuwar ya gaishesa, sama-sama ya amsa masa da tambayar “ina Ummuna?”.

      “Gata a kwance barci ya ɗauketa, dan tana kitchen zata haɗa mana shayi kawai sai ta faɗi, ALLAH yasa Anum na tare da ita, sai dai abin mamaki ana saka mata ruwa ta kawo numfashi saita fara ambatar Baba saboda Abbu da ya kira sunanta, ni kuma tana kallona saita kirani da sunanka”. Lumshe idanu Jawaad yayi hawaye masu zafi suka ziraro masa saman fuskarsa, kafin yace wani abu yaji maganar Alhaji babba a bayansa. “Mi kuke ɓoyemani?”.

     Duk da gabansa ya ɗan faɗi sai ya matsa ya rungume Alhaji babba ya saki wani irin kuka mai tsuma zuciya wanda bai taɓa sanin ya iya irinsaba. Cikin matuƙar tsorata Alhaji babba shima ya riƙesa hannu bibbiyu, “Muhammad karka rikitar dani, minene ya faru dan ALLAH? Kai ne da kuka kuma?”. “Abubuwa da yawane suka faru baba, sai dai dan ALLAH kaimin alfarmar yimaka bazata a kansu daga nan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”. “Namaka Jawaad, ALLAH yay maka albarka”. Ɗagowa Jay yayi yana jinjina kai, Alhaji babba ya share masa hawayen, da ƴar tsokana yace, “Yau maza sun koma mata kenan?”. Murmushin ƙarfin hali kawai Jay yay masa, amma bai iya cewa komaiba.

      Ciki suka koma inda suka samu Bilkisu taɗan samu barci, tana jikin Batool da bata wuce gida ba. Kallonsu yay sannan ya kalli Bilkisun, “Baba bara mu wuce gida, shi baba zai kwana nan gidan kafin zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu, kema Batool ki tashi kije gida dare nayi, amma dan ALLAH karki gayama su Ummah komai sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zakuji koma mike faruwa”. Kanta ta jinjina masa, tace “To ya ya za'ai da mai sunan hajiya, bai kamata a tada taba tunda yanzu ta samu barcin”. “Karki damu bara na ɗauketa kawai”.

         Cak ya ɗauki bilkisu duk da yana jin nauyin su Alhaji babba, sai dai babu yanda zaiyi idan ba haka ɗinba. Sallama yay musu ya fito, Batool dake biye da shi ta buɗe masa baya ya kwantar da ita, sannan ya koma mazaunin driver ya zauna, ita kuma ta nufi inda driver ke jiranta. Kusan tare suka bar anguwar. Sai da ya isa gidane yama tuna da Sadiq da ya baro a office, hankalinsa a tashe ya ɗauka waya yay kiransa, bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, “Sadiq badai kana nan kana jiranaba har yanzun a station?”. “Ina nan wlhy Oga, harma dasu oga Aliyu”. “Ya salam, kayi haƙuri kaji, ka tafi gida kawai dare yayi, suma kace musu ina gida karsu damu”. Daga can Sadiq yace, “To oga”.

     Bayan ya ajiye wayar ya buɗe ya fito, sake ɗaukar Bilkisu yayi zuwa cikin gidan, ya shinfiɗeta a gadon ɗakinsa sannan ya koma motar ya ɗauka wayoyinsa. Kiran Anuwar ya sakeyi, ya tabbatar masa har yanzu Umm-Anum barci take, Abbu ya bama wayar sukaɗan yi magana sannan ya kashe, ya zauna a bakin gadonsa ya tsirama Bilkisu dake barci ido, gani yay harma taɗan rame masa a kwana biyun nan, wani tausayinta ya kamashi, matarsa ta isa a kirata jaruma a ko ina, shi harma baisan yanda zai musalta yaya ya keji a kanta ba, gadon ya hau ya rungumeta a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya a jajjere kamar wanda ya haɗiyi wuta.1

STORY CONTINUES BELOW

          DAREN ALKAIRI KO RUƊANI?.


     Dolene mu ambaci wannan dare da sunaye masuma yawan da sukafi haka a ɓangarorin mutane masu yawa. Jawaad, Alhaji babba, baba maigadi, Maman Amina, Yaya sule, Abbu, Abu-Siddiq, Anuwar, Anum, aunty Mahfuzah, da wasu gungun mutane sun ƙare wannan dare daga farkonshi har ƙarshensa wajen miƙama UBANGIJI godiyarsu da kukansu, a tsakkiyarsa ALLAH ya bama bilkisu da Umm-Anum damar farkawa suma sukabi ayarin masu bautar ALLAH da raya wannan dare da ƙiyamul laili.

          A ɓangaren Alhaji kokino kuwa da duk mai alaƙa da wannan tunkuya wannan dare ya kasance daren tashin hankali da ruɗani a garesu. Babban tashin hankalinma shine kowa ya gaza fasalta kamannin bilkisu a gidan balle ai maganar samun hotonta, sannan baba maigadi tunda suke dashi basu taɓa tambayarsa garinsu ba, abinda kawai suka sani daga ƙauye yake, wane ƙauye? Shine basu saniba, bayan kuma ya kai kusan shekara ashirin yana musu aiki, tsabar bashi bane a gabansu ba basu taɓa bibiyar komai nashi ba a rayuwa, dan shi Alhaji kokino wani irin mutum ne da abinda ke damuwarsa shine kawai mai muhimmanci  a garesa. Bai taɓa takaicin wannan baƙar halayyar tasaba sai a yau ɗin nan.

            Tun a daren aka baza jami'an tsaro neman baba maigadi, sai dai shiru kakeji, sudai sunce suna kan aikinsu. Daga can kuma tushen tsafinsu sam an kasa ganin inda su Bilkisu suke, abinda kawai suka gani shine an fasa tukunya.

      A daren duk wani mai alaƙa da wannan ƙungiya aka sanar masa gobe akwai mitin, duk inda kake dolene ka dawo dan gagarumin mitin ne mai muhimmancin gaske.

SAUDIA


          Tunda aka idar da sallar asubahi a ƙasar Abbu ya zaunar da Umm-Anum ya zayyane mata komai da ya sani game da ita dan su gwada suga ko hankalinta ya dawo jikinta sosai. Aiko a take ta shiga rairai masa kuka da roƙon Abbu akan ya kaita wajen ƴan uwanta, tanason tagasu, ita ba zata sake kwana a saudia ba sai ta dangana da ƙasar haihuwarta.

     Da ƙyar suka lallasheta shi da Su Abu-Siddiq da su Anuwar. saboda gudun zuwan irin wannan ranar a bazata yasa Abbu bai taɓa sakaci da duk wani abinda zai taimakesa akan fita ƙasar ba idan Umm-Anum ta dawo hayyacinta, dan haka ya bata haƙuri akan ta kwantar da hankalinta zasu tafi a yau ɗin nan komai dare insha ALLAH.

           Gari na ƙarasa wayewa suka fita shi da ɗan uwansa Abu-Siddiq, abinka da manyan mutane cikin amincin ALLAH sai gashi cikin awa uku sun kammala dukkan wani abinda ya dace, jirginsu zai tashi ƙarfe sha ɗaya na agogon ƙasar. cike da farin ciki suka kirasu a waya tunkan su ƙarasa akan su fara shirin tafiya. Ai Umm-Anum da Anum sunfi kowa ɗoki, Anuwar kam ai ba'a cewa komai, kayansa ya loda na fitar hankali, a cewarsa saiya more ƙasarsa da ƙyau, ya kuma more ƴan uwansa da bai sani ba. Sudai dariya sukaita masa kawai.9


__________________________________


         Da safe na tashi Alhmdllh, dan babu ciwon kan sam sai rashin jin ƙwarin jiki, ganin gidan yay ƙura naɗan tashi na fara gyarawa, amma yana shigowa sai ya hanani yace na barsa anjima Nabeelah zatazo ta gyara, yanzu muɗan sake kwanciya zuwa goma saimu fita zuwa gidan Dad zan ɗakko ɗayan wuri ɗin nan da nace na taɓa tsinta.

    Haka kawai sai na samu kaina da faɗuwar gaba mai tsananin gaske, dan kuzarin dana tashi da shi ya ida kakkaɓewa gaba ɗaya. Barcin da yaso muyi sai ya ƙauracema idanuna, harma shi yayi nasa ni idona biyu inata saƙawa da kwancewa, ga mafarkin danayi a daren jiya kafin na tashi naga yana salla nima nayo alwala sai dawomin yake a cikin rai. Da tunane-tunane na cinye nawa lokacin barcin, harma goman tayi ya farka. Kallon tuhuma yayta bina da shi akan banyi barciba, na dai fuske abina bance da shi komaiba. Tare mukai wanka, hakama shiri da taimakonsa na shirya dan duk bani da wani ƙarfin zuciya balle akai gana jiki kansa. Muna gama kimtsawa mun fito sai ga Nabeelah da breakfast.

         Zama mukai mukaci, koma nace yaymin ɗura, dan ko lauma ɗaya ban iya kaiwa bakina ba, sai da taimakonsa, daga ƙarshema sai na ringayin yunƙurin amai, dole ya ƙyaleni da iya abinda naɗanci muka fita muka bar Nabeelah a gidan akan bazamu jimaba zamu dawo, dan dama ai yau juma'a ce..


         Tunda muka bar gidan babu mai iya ƙwaƙwƙwaran motsi, nai shiru inata kallon hanya da sauke ajiyar zuciya, shima haka yay shiru idanunsa a rufe.

         Kai tsaye ya bama Sadiq umarnu akan yay horn a ƙofar gate ɗin, haka kuwa akayi, Sadiq yayi horn, sai da baba maigadi ya leƙo, ganin mune sannan ya buɗe gate ɗin.

    Kasa fitowa nai sai da ya fita sannan ya zagayo ya fiddoni, jikina ya ƙarayin sanyi, ga hawaye sun cikamin ido, narasa dalilin shiga irin wannan yanayin haka?. Yah Salman da ya fito daga sashensu daga shi sai wando da singlet yay turus yana kallonmu, boss yi yay tamkar baima gansa ba, sai nice nace, “Yah Salman!”. Da ɗan rawar baki ya amsa saboda wata muguwar harara da boss ya zuba masa, kafin ya ƙara da faɗin wani abu yaja hannuna muka shige falon da sallama.

      Mom na zaune tayi wujiga-wujiga da waya a hannunta, da alama magana ta gamayi a ciki, sai Aamilah a gefenta ta zabga tagumi. A tare duk suka kallemu da waro idanu na maɗaukakin mamaki da al'ajabi. Bayan boss na koma na laɓe, shiko ko'a kwalar rigarsa murmushi ma yaketa zubawa. Zama yayi ya kamo hannuna ya zaunar a gefensa.

       “Mom kun tashi lafiya?”. “Kuka ta fashe da shi kawai tana nunamu da hannu, sai dai tama kasa magana gaba ɗaya. “Kinga kwantar da hankalinki Mom, ba wani abune ya kawomu ba na tashin hankali, abu matata zata ɗauka mu tafi, “Miemaa tashi muje”. Kasa tashi nai dan nima jikin nawa rawar yakeyi hawaye na gudu akan fuskata, ya finciki hannuna yay ciki dani batare da ya saurari Mom ba, Aamilah dama bata iya furta komaiba dan tsorata.

    

    Tsaye Jawaad yay yana kallon ɗakin, dan an bala'in hargitsashi tamkar ɗan adam bai rayu a cikinsa ba. Lallai maganar baba ƙaura ta tabbata. juyawa yay ya kalli Bilkisu da itama tai kasare tana kallon ɗakin da mamaki na gaske. “Ina kika ajiye?”. Hannu ta ɗaga da ƙyar ta nuna masa jakar islamiyyarta da ita kaɗaice zaune a inada ta barta ba'ako motsata ba. Yana ɗora hannunsa akan jikkar Dad da basusan yana garinba ya shigo ɗakin tamkar an jehosa..............🤔😱✍55


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻40Page 56


................A yanda Dad ya faɗo mana ya sakani zabura nai baya zan faɗi, Cikin sa'a boss ya taroni jikinsa, nannauyan ajiyar zuciya na sauke wadda tai dai-dai da wadda shima Dad ɗin ya sauke yana dafe kansa. Sai kuma ya juya ya kalli bayansa da faɗin, “Kai Humaira kedai lamarinki sai ke, wlhy na zata wani abunne ya faru da yaran nan kikaimin wannan irin kira na ujila haka”.

         Cikin tsananin ɓacin tai Mom dake kallon Dad tace, “Hakama zakace Alhaji? Yanzu tsabar wulaƙanci yaran su shigo babu neman izini cikin gidannan har su wuto nan kai tsaye tsabar raini amma kace hakan ba zama wani abuba?”.

         “Haba Humaira, yanzu nan wanene baƙonki a cikinsu? Jawaad dai ɗanki ne, tun bai kai hakaba yake shiga har ɗakin barcinki ma balle cikin gidanki, hakama itama Bilkisun ɗiyarki ce, dan aure ya ɗauketa daga gidan sai kuma ya zama laifi dan ta shigo, mtsoww, dan ALLAH kisan kin girma”. Dad ya ƙare maganar da raɓata ya fice cikin ɓacin rai. Da kallo Mom ta bisa ranta na matuƙar suya, sai da ya ɓacema idonta sannan ta juyo garemu. “K yanzu bakiji kunyar zuwa gidan nan ba butulu? Wlhy nayi nadamar saninki a rayuwata, da nasan zaki zamarwa rayuwar zuri'ata tauraruwa mai wutsiya da namiki addu'ar ƙare rayuwarki cikin masifa har abada, dan da bazan taɓa amincewa kin raɓemu ba, amma ni da kaina zanyi maganinki. Kai kuma lusari shasha, yarinya ƙarama ta gama tawaiwaye rayuwarka da tsafi ka kasa ganin kowa da gashin arziƙi, inda Abdul-aziz ne ke raye ai da bakai masa hakanba, kaje ai duniyace, wanda bai zoba ma jiransa take wlh Jawaad”. Tana gama faɗa ta fice abinta tana huci tamkar wata kumurcin maciji.

         Juyawa nai na kalli boss hawaye na zirara bisa kumatuna. Fuskarsa babu wani alamar damuwa. Yama fiske abinsa tamkar ba'ai komai ba, ƙasa na sulale zan durƙushe ya taroni jikinsa, rungumeni yay cikin ƙirjinsa yana ɗan bubbuga bayana, kusan mintuna uku muna a haka, baice komaiba ni kuma inata zubar da hawaye masu zafi da ƙunar zuciya saboda kalaman Mom. “Boss dan ALLAH ka faɗamin yanda akai aurenmu ko nima zan daina tuhumar kaina da cin amana, ta yaya za'ai mijin yayata ya koma mijina rana tsaka? Bana ganin laifin Mom dan kalamanta gaskiyane a gareni, ni.......” Shiiiiii!!!!” ya faɗa yana ɗagoni da ɗan ranƙwafowa dan ya fini tsaho, ya ɗaura hannunsa saman bakinsa. Ruf kuwa na rufe bakin nawa ina cigaba da kallonsa tamkar idanuna zasu zubo ƙasa dan tashin hankali. Sassanyan Murmushi yay min da kanne min ido ɗaya, yay zipping bakinsa alamar karna sake magana. Kaina na girgiza masa hawaye na sake gangaro min saman kumatu, baki na buɗe zanyi magana ruf ya rufemin shi da nashi batare da ya bari na ƙarasa faɗaba, wata irin sumbata mai cike da sirrika masu wahalar fassara yake aikamin, tun muna tsaye bisa ƙafafunmu har hakan ya nema gagararmu mukai baya zamu faɗi, saurin riƙe bango yay muka jingina jikinsa. Ganin yana neman wuce gona da iri nai ƙoƙarin ƙwatar kaina dan na fahimci yama manta nanɗin ba gidanmu bane. Da ƙyar na samu ya barni, muka ƙurama juna idanu, tunda nake ban taɓa juriyar kallon tsakkiyar idanunsa a tsahon lokaci kamar haka ba. Ya matso da fuskarsa dab da tawa har muna shaƙar numfashin juna, wani munafukin murmushi da bai wuce laɓɓansa ba ya sakarmin, sai dai hakan bai hana dimples ɗinsa da nake tsananin burgeni loɓawa ba, ya lumshe idanu a hankali sannan ya buɗe yana ɗaura ɗan yatsansa saman laɓɓana da suka gama shan wajala a hannunsa yanzu. Cikin magana raɗa-raɗa yace, “A wasu lokutan baki yana ƙarya, yana yaudara, yana ha'inci. itako ZUCIYA abinda ke cikinta kawai take kuwwa a kansa, agaban kowa, a kuma ko ina. k wacece a gareni bakina yayi ƙanƙantar lissafa miki, wani jinin sai an tsaga ake ganesa a jini, karki zama mai gaggawa, karki zama mai wasiwasi, karki zama mai sakaci, dan bakowa bane mai ZINARIYAR ZUCIYA irin taki”. Ya ƙare maganar da ɗaura ɗan yatsansa saitin zuciyata. Kallon inda ya nuna ɗin nayi kafin na ɗago shima na kallesa, ya ɗagamin gira ɗaya da ɗan ƙyaƙyƙyafta idanunsa da suka koma sirkin jaa, “Ke ɗin ta dabance, idan nace tadaban ina nufin tadaban a kowanne daƙiƙa na bugun zuciya da numfashina Bilkisu”.

      Kamar wata sakarai haka na bisa da kallo harya fice a ɗakin. Gaba ɗaya ya birkicemin tunanina, kalamansa suna dai-dai da tambayoyin jarabawa masu wahalar gaske da ruɗani ga ɗaliban dake zana jarabawar ƙarshe ta barin makaranta. ‘Mike nan?’ na faɗa a fili batare da tunanin mai bani amsarba........

      Sanin hakan da nai ya sakani bin ɗakin da kallo tamkar baƙona, sai kuma na juya jiki a sanyaye na fice daga cikinsa. Idanuna akan boss da ke zaune bisa kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya suka fara sauka, sai Dad da Mom dake zaune suma kusa da juna, Yah Salman na daga can Dining zaune da waya a hannu, sai Aunty Aamilah dake jikin ƙarfen bene ita kuma a tsaye. Takawa nai a hankali gaban Dad na durƙusa, hawayene ke zarya a kumatuna masu zafi da saka ƙunar zuciya, “Dad ina kwana” ta faɗa muryarta a ɗarare. Murmushi yayi yana gyara zamansa, “Ɗiyata yau da kanki a gidan nan? Ko dai ɓatan kai kikayi?”. Hawayen da suka cikamin ido suka gangaro akan kumatunna, na ɗago kaina ina kallon Mom da girgiza ma Dad kaina. “Kayi haƙuri Dad, nasan ni ɗin mai tarin laifukace a gareku waɗanda a kullum nike cike da damuwa da kunya a kansu, Dad wlhy banci amanarku ba, har yanzu bansan dalilin da yasa kuka auramin shi ba a maimakon Yah Qaseem, Dad  inajinka a rainane tamkar mahaifina, banason nazama silar ɓacin ranka kona minti guda kai da Mom, banason ka ringa kallona matsayin tauraruwa mai wutsiya, dan ALLAH kace ka yafemin, ka samin albarka kuma, ka roƙamin gafara wajen Momy da ƴan uwana suma, ALLAH ne ya ƙaddara komai a nasarata, sai dai ya sanyaka ka zama sila, ka nunamin hanya a lokacin da mafi yawan al'umma suka rufemin tasu, ka haskamin rayuwa a lokacin da duhu ya lulluɓeta, ka zamemin gata, a lokacin da nake ƙasƙantacciya, duk wanda zaiga bilkisu a yanzu harta birgeshi kaine silar komai..........”

        Dad da yaji ƙwalla sun cika masa ido yasa hannu ya ɗaukesu yana ɗan murmushi da saurin dakatar da bilkisu, kafaɗarta ya kai hannu zai kamo sai kuma ya fasa, murya a sanyaye yace, “Haba ɗiyata ni bakimin komaiba wlhy, duk abinda kikaga ya faru a rayuwar ɗan Adam rubutaccene a littafinsa, ke yarinyar kirkice abin alfaharin kowanne uba, inajinki har cikin raina nima Bilkisu, duk kuma abinda ya faru kema ba laifinki bane namune, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci rayuwar aurenku ya baku zaman lafiya kinji, aje aita haƙuri, karki sake yin kuka domin hakan, ina fatan dai babu wata damuwa ko?”. Bilkisu tasa bakin gyalenta ta share hawayen tana gyaɗama Dad kanta, “Ba komai Dad, shiɗin mutumin kirkine, kullum ƙoƙarinsa yaga ya ƙyautatamin, zaɓin da kukaimin ƙyaƙyƙyawan zaɓine da nake alfahari da shi, na kuma tabbata har ƙarshen rayuwata insha ALLAH bazanyi nadama ba, nagode sosai da kulawarku a gareni”.

        Kallon inda Jawaad ke zaune tamkar baya a falon Dad yayi, cikin ƙara sanyaya murya yace, “Nagode sosai Jawaad, dama bana tsamanin saɓanin hakan daga gareka, ALLAH ya ƙara muku zaman lafiya.

         Jay ya ɗan ɗago idanunsa tare da tura wayarsa cikin aljihu. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Dad, irin kallon da kowa shi yasan ma'anar nasa. Jawaad ya janye idanunsa yana wani shegen murmushi da sake ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kafin yace wani abu Mom taja wani wawan tsaki tana miƙewa tabar falon.

          Duk muka bita da kallo banda boss da ya basa abinsa hankali kwance. sai da ta gama hayewa benen Dad ya sauke nannauyan numfashi yana sake kallon Jay, “Tana cikin fushine sosai akan damuwar ɓatan Mamana, duk inda muke tunanin samun yaron nan an gaza samunsa Jawaad, dama koda bakuzo nanba ni da kaina zanje gidanku akan maganar. Ka taimakemu dan ALLAH ”.

      Kafin Jawaad yay magana Bilkisu dake share hawaye tace, “Dad wani abunne ya faru da aunty Shahudah'n?”. Kansa ya jinjina mata cike da matsananciyar damuwa ya labarta musu komai, shi dai Jay baice ko uffanba, sai Bilkisu da keta sharar ƙwalla ita da Aamilah. Daga ƙarshe ma sai ya miƙe abinsa yana kallon bilyn, “Tashi mu wuce” ya faɗa a daƙile. Kamar bily zata fasa kuka dan takaicinsa, ta buɗe baki zatai magana ya zuba mata wata uwar harara..... Tsam ta miƙe tana haɗiye sabon kukan dake neman taho mata, “Dad zamu wuce”. Kallon Jay Dad yayi, “Jawaad bazaka bar mana ita ta yini ananba?”. Shiru yay kamar bazaice komaiba, sai kuma ya kalli agogon hannunsa ba tare da ya kalli Dad ɗinba yace, “Zamuje office ne”. “Shike nan to, kuɗan jirani”. Dad ya faɗa yana miƙewa.

       Jakar islamiyyar ya ɗauka yay ficewarsa batare da yacema bily komaiba.

        Da kallo kawai na iya binsa harya gama ficewa, naja numfashi ina danne zafin da zuciyata kemin, bansan miyasa boss yake hakan gasu Dad ba? Yana ƙara sakamin ruɗani da wasiwasine akan abinda naketa ƙoƙarin ƙaryatashi a zuciyata tun randa nai gamo da wallet ɗin nan...... Dawowar Dad ta katsemin tunani na, ya miƙamin leda babba mai ƙyau yana murmushi, “To ɗiyata ga tsarabarki nan, akwai kuɗinki na kayan ɗaki danai niyya sai dai hakan bata faruba, insha ALLAHU kafin kije gida zakiji alert, ALLAH ya ƙara zaman lafiya”. Hawayen da suka ziraromin na share, na durƙusa har ƙasa ina masa godiya da addu'oin fatan alkairi. “Babu komai Bilkisu. karki damu tashi kuje yana jiranki”. Jinjina masa kai nayi na miƙe, na kalli inda Aunty Aamilah take zanyi magana, wata muguwar harara ta watsomin tana jan tsaki da ɗauke kanta ta nufi ɗakinta. Duk da naji babu daɗi sai nai ɗan murmushi kawai najuya ga Yah Salman. Shima koda nai masa magana bai amsamin ba, haka na baro inda yake jiki a sanyaye naima Dad da duk abinda ke faruwa yana kallonmu sallama na fice.

            Fa kallo Dad yabi Bilkisu harta fice daga falon, ya sauke nannauyan numfashi yana gyara babbar rigarsa, kallon Aamilah da keta cika da batsewa yay ya ɗauke kansa, batare da yace mata komaiba ya haye sama abinsa. Ɗakinsa ya wuce, sai da ya rufe ƙofar sannan ya ciro wayarsa daga aljihu yay kiran Qaseem. Bugu biyu Qaseem ya ɗaga kuwa. Dad ya sauke numfashi yana cire hularsa ya zauna a bakin gadonsa, “Qaseem gasu nan sun fito, dan ALLAH ka danne ranka karka bari rigimar da kuka saba da yaron nan ta shiga tsakaninku, mu lallaɓasa musan inda Mamana take dan nasan wlhy shi kaɗaine keda masaniyar hakan”. “Karka damu Dad, namaka alƙawarin a daren yau sau Shahudah ta kwana gida, yanzun nan zan kirashi a waya nace masa yazo ya sameni muyu magana”. Qaseem ya faɗa yana danne ɓacin ransa da mugun tsanar Jay dake cimasa zuciya. Sallama sukai, Dad ya ajiye wayar yana sauke numfashi da haɗiye tsantsar damuwarsa akan rashin abar ƙaunarsa mafi soyuwa acikin ƴaƴansa. Qaseem kuwa daga can kiran Jay yayi duk da yana tunani da wahala ya ɗauka tunda bayin wayar sukeba, a yanzunma sai da Dad ya turo masa number Jay ɗin dan bashi da ita da.2


STORY CONTINUES BELOW

         A cikin mota na iske boss yana waya, bayan na shiga Sadiq ya rufe ƙofar kamar yanda ya buɗemin na shiga. Har muka kusa isa gida yana waya, koda kuma ya kammala bai kulani ba har muka ƙarasa gidan, a ƙofar gida yace Sadiq yay parking. Batare da ya kalleni ba yace, “Kije ciki”. Kallonsa nai zanyi magana ya sake ɗaure fuska. Haɗiye maganar nai kawai na ɗauki ledar da Dad ya bani zan fita ya riƙe ledan. Sake kallonsa nai, sai kuma na sakar masa ledar batare da nace komaiba na ƙarasa ficewa dan tsagwaron masifa na hango cikin ƙwayoyin idanunsa.

           Duk yanda naso riƙe hawayena a yanzu kasawa nayi, haka na shiga cikin gidan inayinsu duk da nasan Nabeelah tana a gidan kuwa. Kwance na isketa a babban falo tana barci, dan haka na wuce bedroom ɗina kawai na faɗa saman gado ina fashewa da wani kukan. Kusan mintuna biyar ina kukana kafin ƙarar shigowar saƙo ta sakani dakatawa, ɗaukar wayar nayi ina share hawayen dan zatona ko boss ne, zumbur na miƙe cike da firgicin ganin yawan kuɗin da Dad ya turo min. A fili nace, ‘Tashin hankali, kodai Dad bai lura baneba?’. Bani da mai bani amsa dan haka nai saurin yin dialing Number sa. Bugu biyu kuwa ya ɗaga, cikin rawar murya nace, “Dad a......” “Banason kice komai ɗiyata, kin cancanci fiyema da haka daga gareni kinji, ke dai ALLAH yay miki albarka”. “Nagode Dad, ALLAH ya ƙara buɗi na alkairi mai albarka”. Na faɗa cikin kuka. Ina jiyo sautin murmushinsa daga can, ya sake kwantar da murya yana lallashina cike da kulawa har sai da nayi shiru sannan mukai sallama.

          Jikina duk babu ƙwari na tashi na shiga bayi nai wanka da alwala, na idar da salla ina ƙoƙarin tashi dan naje na tado Nabeelah sai gata tama shigo da sallama. “Ai bansan kin shigoba, Sadiq ne da kulolin abinci inji Yayanmu”. “Abinci kuma?”. Na faɗa ina ajiye sallayar. Tare muka fita, da mamaki nakebin manyan kulolin da kallo, dan abincine na kusan mutane goma sha biyar ma. “Sadiq wannan fa?”. “Oga ne yace na kawosu, amma inagafa baƙi za'ayi dan naji yana waya akan nanda awa biyu da wasu mintuna ma zasu iso”. Bilkisu dake kallonsa kawai tace, “Yana ina shi?”. “Da muka saukeki Barrack mukaje, bayan mun baro can kuma na saukesa a General hospital sannan naje na amso wannan abincin, yanzu can zan koma na ɗakkosa dan yace dubiya zaiyi”. 

          Sallama yay mana ya fita, ni da Nabeelah kuma muka kwashe kulolin muka kaisu kicin inata tunanin baƙi kuma daga ina zasuzo haka to?. Bani da mai bani amsa, dan haka na koma ɗaki danna gyara jikina, Nabeelah kuma tai alwala itama.


JAWAAD

      

         Wayar da bily ta samu Jay nayi a mota wayace daga Qaseem dake a General hospital a killace, ya buƙaci ganin Jay ɗin da gaggawa, duk da hakan ya bama Jay mamaki baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen amsawa, shiyyasa suka ajiye Bilkisu a gida ita. Barrack suka fara zuwa wajen baba ƙaura da shima tun a safiyar yau ya saka aka kirashi a waya akan yana buƙatar ganinsa. yaso suje tare da bily ne dama, to sai kuma kiran da Qaseem yay masa ya shafe hakan. Kusan mintuna talatin ya ɗauka anan sannan suka fito.

         Likitoci basu bari Jawaad ya shiga wajen Qaseem ba kai tsaye sai da matakan tsaro na kare kai, ko ina na jikinsa sai da ya kasance a rufe ruf sannan aka kaisa inda Qaseem ya ke. Wajene na musamman.......


          Babu wanda yasan mi suka tattauna har na tsahon mintuna hamsin da uku sannan Jay ya fito, baka isa fahintar yanayinsa ba, dan kamilar fuskarsa ta shanye komai, sai dai kumafa jijiyar kansa tai masifar miƙewa ruɗu-ruɗu, hakama idanunsa jazur suke. Sadiq da tun da ya dawo yana zaune yana jiransa ya miƙe da sauri ya buɗe masa mota ya shiga, yana zama wayarsa nayin ring, daba dan yasan kirane mai muhimmanci ba bazai ɗaga ba, yay ƙoƙarin saisaita muryarsa suka gaisa da gambiya Munaya. Bansan mi tace masa daga canba, ya ɗan dai murmusa yana gyara zamansa da ƙyau. “Ina sake roƙon alfarma dai Ummu, Please a bani ƴar damarnan nima koda sau ɗaya ne”. Idanu ya lumshe a hankali yana cigaba da saurarenta, ya sauke ajiyar zuciya yana jinjina kansa kamar yana a gabanta, saida yay mata godiya sannan ya sauke wayar daga kunnensa yana cika bakinsa da iska ya fesar.


             Muna zaune a falo ni da Nabeelah ya shigo, sannu Nabeelah ta shiga jera masa, bai amsa mataba, sai dai ya ɗaga mata hannu kawai ya wuce abinsa. Da kallo muka bisa da gani har ita, na lumshe idanu da kwanciya jikin kujera ina sauke numfashi. “Shi dai Yayanmu kamar mai jinnu haka yake, yanzu zaki gansa a mutum anjima kaɗan ya koma dodo”. Nabeelah ce da wannan maganar cikin shagwaɓa, Bance da ita komaiba na miƙe, ruwa na ɗauka da kofi nabi bayansa.

          Ban samesa a faloba, hakan ya sakani binsa bedroom. A gaban mirror na iskesa yana waya da cire boturan shirt ɗinsa, ido muka haɗa ta cikin mirror'n kasancewar a bayansa na tsaya daf. Ni na fara janyewa, dan nikam banason ganinsa a cikin yanayin nan tsoro nakeji, cigaba yay da yin wayarsa tamkarma bai ganni ba. duk da hakan ya sosamin rai sai na nutsu ina saurarensa, mamaki ya kamani sosai dan fahimtar wayar yana yinta ne akan Aunty Shahudah, cikin tsoro-tsoro nake kallonsa lokacin daya ajiye wayar. “Boss wai kana nufin kasan inda aunty Shahudah take dama kenan?”. Rigarsa da ya gama cirewa ya jefa saman sofa, ya fara ƙoƙarin zare belt ɗin wandonsa batare da ya kalli sashenma da nakeba balle nai tunanin samun amsa. Sai da ya gama zame komai daga shi sai boxer sannan ya raɓani ya wuce abinsa. A take jikina ya fara rawa, na shiga ambaton innalillahi..... Ina kafe ƙofar bayin da kallo kamar zai fitone ya bani amsar da nake buƙata. Bansan sanda na zube a bakin gadonba na dafe kai, tsahon mintuna ina a haka wayarsa kuma nata faman ring a gefena amma banko kalleta ba. A haka ya fito ya sameni, yanzun ma dai ban ishesa kalloba, ya shirya a gaggauce cikin ƙananun kaya farin wando da farar riga, sai ya ɗaura baƙar jacket a sama mara hannu. Koba'a faɗaba yayi ƙyau sosai, dan shi mutum ne da koyaya ya saka sutura sai kaga ta zauna masa a jiki tsaf tamjar danshi akai. Tsabar wulaƙanci a gabana ya sake ficewa a ɗakin bayan ya zauna ya saka takalma a ƙafarsa, bansan sanda na fashe da kuka ba nai baya a saman gadon.


STORY CONTINUES BELOW

                 Gudu sosai Jawaad ya saka Sadiq shararawa dan jirgin su Umm-Anum harya sauka bisa ƙasa, duk da gimbiya ta sanar masa Takawa ya aika motocin da zasu tarosu hakan bai hanashi jin ɗokin son zuwa ya tarbo mahaifiyarsa da kansa ba, shi kaɗai yasan a yanayin da wannan ranar tazo masa, tazo masa da abubuwa kashi-kashi masu yawa, ruɗani daban al'ajabi da matsanancin farincikin dawowar mahaifiyarsa duniyarsa cikin ƙasar haihuwarta.

       Suna isowa su Umm-Anum na fitowa a jirgi Anuwar riƙe da hannunta. Da gudu Anum ta ƙaraso gaban Jay da tun tana sakkowa ta hangosa, jikinsa ta faɗa ta rungumesa. Duk da damuwar da yake ciki da yanayinsa na rashin son shiga harkar yara bai gaza karɓar ƴar ƙanwar tasaba kamar yanda taso, ya shafa kanta yana ɗan murmushi kafin ya janyeta a jikinsa ya nufi Umm-Anum. Haɗata yay ita da Anuwar ɗin ya rungumesu gaba ɗa yana maijin a yau babu tamkarsa duk faɗin duniyar nan. Kasan cewar yasan umm-Anum na fama da matsalar kafa bai tsaya ɓata lokaciba suka nufi inda Sadiq ya faka motarsa kusa da motocin masarauta guda uku da sukazo tarbarsu. “Ummuna Abbu fa?”. “Sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho suma insha ALLAHU, nima dan bazan iya haƙurin kaiwa goben bane shiyyasa”. Murmushi ya saki mai sanyi yana taimaka mata ta shiga motarsa da Sadig ya buɗe. Anuwar da Anum kuma suka shiga motar masarauta ɗaya badan sun so hakanba.

           Sai da ya tabbatar komai yayi dai-dai sannan ya zagaya inda Sadiq ya buɗe masa kusa da Umm-Anum shima ya shiga, ya riƙo hannunta ya sumbata, “Amsiyatul sa'iidah. Marhaban biki Ummuna”. Fuskarta ɗauke da murmushi da hawaye tace, “N: Kaifa anta Jay-p na”. Idanu ya lumshe a hankali yana haɗiye nauyin da ƙirjinsa yay masa da sake damƙe hannunta cikin nashi kamar mai gudun a ƙwace masa ita yace, “Ana bikhairin Ummuna”. Ta shafa kansa tana murmushi da faɗin, “Alhamdulillahi ala kulli halin Noorul Ayn”. Ɗagowa yay idanu jazur ya kalleta da sake sumbar hannunta ya ɗaura kansa saman kafadanrta yana sake lumshe idanu. “Ummuna nayi kewarki”. “Nima haka Muhammad Jawaad”. Ta faɗa tana sumbatar goshinsa.


           Cikin nutsuwa motocin suka fice daga airport ɗin, ta Jay ce gaba shi da Umm-Anum, sai kuma wadda su Anuwar ke ciki shi da Anum, sai ɗaya da babu kowa a ciki, ta ƙarshe kuma dogaraine.

   

_______________________


            Daga kukan da ya barni inayi sai barci ya kwasheni, cikin barci naji ana knocking ƙofar, na buɗe ido a hankali da tashi zaune dan nasan bazai wuci Nabeelah bace, bayi na fara shiga na wanko fuskata da hawaye suka bushe, sannan na fita. Nabeelah tai saurin riƙo hannuna tana faɗin, “Baƙinfa sun iso inaga, dan naji ƙarar buɗe gate”. Bata jira amsata ba taja hannuna muka fito babban falo. Kiciɓis mukai da Anum data fara shigowa. Ta daka wani uban tsalle ta ɗareni, tuni naji duk wani ɓacin ran da Boss ya barni da shi ya gudu, na rungumeta nima cike da tsantsar farin ciki.

         Anuwar ne na biyun shigowa, ya fara sauke idanunsa akan Nabeelah da ke tsaye tana kallon su bily da dariya, kafin ya maida ga su Bilkisun yana ɗan ɓata fuska. “Lallaima Aunty, ni baki ganniba sai wannan yarinyar”.  “Tuba nake Yah Anuwar ” na faɗa ina sakin Anum.

         

          A waje kam Jay ya taimakama Umm-Anum ta fito daga motar, ƙafafunta duk sunyi fushi saboda zaman jirgi, ga kuma dama ƙafarta na mata ciwo. Wani irin kallo take bin gidan da shi dan bazata taɓa mantawa da shi ba koda a magagin mutuwa take, gidan da yazama tushen komai na maida mijinta wane, gidan da yazama harsashin ginin ɗaukaka ga abin sonta, gidan da zata iya ambatonsa da komai a ɓangaren farin cikin rayuwar aurensu da akasinsa, gidan data haifi gudan jininta bayan shafe shekaru tana kuka da fatan samu. kallon Jay tayi hawaye cike da idanunta. A hankali ya kaɗa mata nasa kan yana ɗan murmushi. Ta sake damƙe hannunsa cikin nashi tana haɗiye abubuwa masu yawan gaske dake yunƙuro mata tun daga ƙasan zuciya har saman harshe. A hankali ya fara takawa da ita suka nufi ƙofar da zata sadasu da cikin gidan, suna gab da isa ƙofar falon Bilkisu ta fito cikin matsanancin hanzari.

         Nai saurin ƙarasawa garesu batare dana tuna da wani matsayinta na surukata ba, ni kallon uwa nake mata, uwa ɗinma mai muhimmancin gaske ga ɗa. sakin Jawaad Umm-Anum tai itama da sauri ta buɗema bily hannayenta, aiko tazo ta shige jikinta. A take hawayen da Umm-Anum ke maƙalewa suka gangaro mata saman kumatu. Kauda kai Jay yayi daga kallonsu saboda ƙwallan da suka cika masa idanu, sai ya tura duka hannayensa cikin aljihun farin wandonsa ya ɗaga kansa sama ya maida hawayen. Sai da ya tabbatar hawayen sun koma sannan ya sauke fuskarsa a kansu. Yanzu kam Bilkisu ta ɗago daga jikin Umm-Anum, sai dai su duka hawaye suke tana jeramata sannu da zuwa. Umm-Anum ta shafa fuskar bilyn tana ƙare mata kallo sosai, wani sassanyan murmushi ta sake saki da jawota jikinta ta sake rungumeta, dan ita kaɗai tasan mita gano.

           “Ummuna kumuje ciki, sai ku cigaba da murnan”. Jay ya faɗa a hankali kamar bashine yay maganarba. Kallonsa tai shima ta riƙo hannunsa suka sakata tsakkiya shi da Bilkisu, a haka suka shiga falon inda Nabeelah da Anum ke zaune surutu ya kaure tsakaninsu, Anuwar kuma ya tasasu a gaba yana kallon Nabeelah kamar ya samu wani majigi.

        Cak Umm-Anum ta tsaya tana kallon Nabeelah da itama tai mutuwar tsaye tana kallon mai tsananin kama da Ummahn ta. Kallon Jawaad Umm-Anum tayi cikin wani yanayi na alamar tambaya. Hannunta ya kama ya zaunar da ita yana ɗan murmushi, sai da ya tabbar ta zauna sannan ya kalli Nabeelah da ke ƙoƙarin gaisheta. Hannun Nabeelah ta kamo ta matso da ita jikinta, da ƴar rawar murya Umm-Anum tace, “Da ace mutum baya ƙara shekaru da girma ni dai da nace wannan Mariya ta ce Jawaad, kamar yanda nake kallon takwarata da kamannin Rahma”. duk da ba yaune karan farko da akace Bilkisu na kama da aunty Mah-mah ba a gabansa sai da ya kalli Bilkisun da tasha jinin jikinta, sai kuma ya ɗauke kansa yana zama kusa da Umm-Anum. “Ummuna ki kwantar da hankalinki kinji, dukkan abinda kike buƙatar ji zaki samu fiyema da hakan har sai kin gaji, yanzu dai kitashi a kaiki inda zakiyi wanka, kuci abinci ki kwanta ki huta, sai komai ya biyo bayan hakan kinji”.

      Kansa ta shafa da ja masa hanci tana faɗin, “Rigimammen Mama har yanzu dai ana taɓawa kenan”. Dariya duk su Anuwar sukayi, shi kuma ya zuba musu harara da kama hannun Umm-Anum ɗin ya miƙar da ita. Da kansa yay mata rakkiya har ɗakin bily, itama da tabi bayansu tai saurin shiga bayi domin haɗa mata ruwan wanka.


STORY CONTINUES BELOW

         Nabeelah na ganin Jay da bily sun shige da Umm-Anum tai saurin ɗaukar wayarta ta turama Ummah babba saƙo.

      Sai da suka tabbatar Umm-Anum ta shiga wanka sannan Jawaad ya fito, kayansu da Sadiq tuni ya gama shigo musu da su ya saka Anum ta ɗauka na Umm-Anum ta kai mata ɗakin Bilkisu, shi kuma ya kai Anuwar ɗakin baƙi inda zai zauna, Anum ma ɗakin baƙin dake cikin falon bily zata zauna. Bilkisu da Nabeelah da keta ALLAH, ALLAH su Ummah su iso sukai hidimar shirya abinci su kuma a tsakkiyar falon, dan yanda Umm-Anum ta gaji bai kamata a sakata zaman Dining ba.

       Tana son tabi Jay ɗakinsa dan ta nuna masa farin cikin data shiga na bazatar da yay mata akan zuwan su Umm-Anum amma haushinsa da takeji ya hanata aikata hakan, sai kawai ta sharesa ta cigaba da harkokin gabanta, dan farin cikin ganin su Umm-Anum ya shafe mata duk wani damuwarta kuma.  

           A ɓangaren Jawaad shima tun shigowarsa ɗakin ya ke zuba idanu ya ga bilkisu ta biyosa amma sai yaji tsit, duk da farin cikin ganin mahaifiyarsa da ƙannensa ya shafe masa duk wani ɓacin ran da ya samo daga Qaseem da gidan Dad hakan bai hana ransa sosuwa ba da ƙin shigowar Bilkisun, sai huci yake da jera tsagwayen ƙwafa, ayyanawa yake a ransa sai yayi maganin miskilancin yarinyarnan a yau ɗin nan basai gobe ba, dan ya gama lura gadon barcinsa da ta gama ganine yasa take neman fara kawoma rayuwarsa raini (Ka manta wulaƙancin da kai mata kai ɗazun saraki🙄😜).

          Tashi yay da ga kwancen da yake saboda jin an fara kiraye-kirayen sallar Magriba. Alwala yayi sannan ya fito, a babban balo suka haɗu da Anuwar da shima ya fito daga sashen baƙi da alamar shirin tafiya masallacin. Yayma abincin da aka shirya a tsakkiyar falon kallo ɗaya ya ɗauke kansa batare da yace komaiba suka fice shi da Anuwar dan falon babu kowa cikinsa.

             Da taimakon Bilkisu Umm-Anum ta dawo falon bayan an idar da sallar Magriba, suna zama Ummah babba da Ummah ƙarama da Batool nayin sallama, cikin matsananciyar faɗuwar gaba Umm-Anum ta juya tana kallon ƙofar dan ko'a cikin magagin barci waɗannan muryoyin sunfi gaban mantuwa a gareta balle ma a zahiri.

        Kasancewar akwai hasken Genretor da aka kunna tas suke ganin junansu, da ga Ummah ƙarama har Ummah babba jikinsu rawa yake da tsuma sosai, sun ƙurama Umm-Anum idanu tamkar yanda itama ɗin kallonsu take bata ko ƙyaftawa. Su dai su Bilkisu kallonsu kawai suke da son ganin yaya za'a kwashe. A haka Jawaad da Anuwar suka shigo suka samosu. Jay ya kalli su Ummah da mamaki sai kuma ya kalli Nabeelah da ya tabbatar itace da wannan aikin. Aiko sai tai ƙasa da kai gabanta na faɗuwa dan tsoro ta koma bayan bily ta maƙale.

      Ɗauke kansa yay daga gareta, ya ƙarasa gaban su Ummah ya tsaya a tsakkiyarsu, hannayensu duka ya kama a cikin nasa, a take duk suka ɗago suna kallonsa hawaye na gangaro musu saman fuskokinsu. Yanda laɓɓansu ke rawa zai baka tabbacin magana suke son yi amma sun kasa saboda ruɗani. Jay yaɗan murmusa yana mai lumshe idanunsa ya buɗe alamar tabbatar musu da wadda suke hasashen ce ba mafarki bane ko gizago. Cikin ƙarfin hali Ummah Babba tace, “Yarona da gaske kake Yaya Bilkisu ce a gabanmu ba mafarkin da muka sabayi bane?”. Yanzunma kansa ya jinjina musu, ya kuma ja hannayensu har gaban Umm-Anum da alamu ya nuna suman zaune tayi. Hannayensu ya saka a cikin nata yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushi yaja jikinsa baya.

           A gaban Umm-Anum Ummah ƙarama da Ummah babba suka zube suna fashewa da kuka mai tsuma rai da cin zukata. Umm-Anum ta kawo nannauyan numfashi lokacin da suka rungumeta su duka biyun a jikinsu.

       Su Bilkisu dake kallonsu suma hawayen sukeyi, Jawaad kansa sai da ƙwalla ta cika masa idanu, amma jarumta ta saka shi haɗiye kayansa ya koma cikin kujera ya zauna yana jin wani irin matsanancin farin cikin da ƙirjinsa ma ke neman gaza ɗauka. Su Ummah sunkai kusan mintuna huɗu zuwa biyar a jikin Umm-Anum suna raira kuka kafin su saki juna, hannayenta ta ɗaura saman kumatunsu tana shafawa da murmushi saman fuskarta ga kuma hawaye, suma dai murmushin sukeyi hannayensu duka akan nata kumatun suna share mata nata hawayen. “Ashe Mariya ta da Wasila basu girmaba har yanzun? Ashe shagwaɓar nan da akema Yaya tana nan ba'a fasaba”. Dariya ta kwacema su Ummah lokaci guda da kuka, jikinta suka sake faɗawa ta rungumesu tana dariya. Su ma ƴaƴansu dariyar sukeyi da hawaye banda Jay da murmushi ne kawai a saman fuskar tasa.

       Da sauri Umm-Anum ta sake ɗagosu tana faɗin, “Ina Rahmah take ita kuma? Ko ba'a nan take aure ba?”. Duk ƙasa sukai da kawunansu hawaye masu zafi sosai na sake rige-rigen fitowa daga idanunsu, Umm-Anum ta shiga girgiza kanta a hankali tana kallonsu a tsorace, “Karku cemin na rasa Rahmah Mariya, kar kucemin rabuwa ta har abada nayi da Rahmah dan ALLAH” “Sai dai haƙuri Yayah, Rahma ta jima da barinmu gaba ɗaya, ta tafi tafiya mai nisan zango da babu iyakar sake ganin juna sai idan ALLAH ya ƙaddara hakan a can wata rana”. Ummah babba ta faɗa zuciyarta na mata zogi tamkar a yaune Rahmah tabar duniya. Yanzun kam Umm-Anum ce ta fashe da kuka mai tsuma rai da cin zuciya, tana son Rahmah, tana ƙaunar Rahma sosai, dan tafi shaƙuwa da ita a kaf cikin ƴan uwanta.

       Ganin kukan nasu yana neman yin yawa gashi har ana kiran sallar isha'i sai Jay yay gyaran murya. ɗagowa sukai duk suka kallesa. Ya sakar musu murmushi da waro idanunsa waje kaɗan ya miƙa musu kwalin tissue da ya ɗauka saman centre table. Babu musu suka amsa. “Yauwa Momys ɗina ababen alfaharina, kukan ya isa haka nan kar ku ƙarar mana da hawayenku, lokacin kuka ya wuce yanzu farin ciki ake buƙata da godiyar ALLAH da ya kawo ranar da ba'a taɓa tunani ko tsamanin zuwanta ba, idan kuna kuka mu kuma mi zamuyi to?”. Cikin kaɗa kai Ummah babba tace, “Hakane Jawaad, ALLAH yay maka albarka kaida sauran ƴan uwanka kaji, a ina ka gano mana Zuciyarmu ne yaron albarka?”. “Ihhhmmm karku damu zan faɗa muku komai sweet Ummahs ɗina, amma ba yanzu ba sai tsohon can shima yana gefena”. Daƙƙuwa Ummah ƙarama tai masa tana faɗin, “Sai dai idan iyayenka ne tsoffi”. Dariya ce ta nema kufcema su Bilkisu, suka saka hannaye duk suka kare bakunansu banda Aunty Batool da tayi abunta sosai. Miƙewa yay ya dungurema Aunty Batool kai yay ficewarsa domin yin sallar isha'i.

          Bayan sallar isha'i natsuwa da ga UBANGIJI ta kuma saukar musu a zukata, duk da su Ummah suna ƙage da sonjin wani abu daga yayar tasu, kamar yanda itama a ƙagen take sai Jay ya hana, a cewarsa sai sunci sun ƙoshi sannan hakan zata kasance. Babu yanda suka iya suka yarda da batunsa, dan suma sunsan ya cancanci Umm-Anum taci abin ma ta kwanta ta huta, sai dai zukatansu bazasu iya jure hakanba.

      Ummah babba da kanta ta bama Anuwar da Anum abinci a baki cike da so da ƙauna, hakama Umm-Anum ta bama Aunty Batool da Nabeelah da Bilkisu, Jay kuma Ummah ƙarama ta bashi. Cikin wani irin farin ciki mai wahalar misaltuwa sukaci abincin suka ƙoshi, dan Umm-Anum har su Ummah ma sai da ta dinga basu a baki da kanta. Abin dolene ya sakaka kuka ya kuma birgeka. Sai da sukai nak da girki suka godema UBANGIJIN daya basu badan ƙarfinsu ba ba kuma dan sunfi kowa ba sannan su bily suka tattare wajen tas. Da taimakon aunty Batool da Nabeelah da Anum suka wanke komai tsaf. Yayinda a falo kuma Jawaad ke ta bama su Ummah labarin yanda komai ya kasance game da ganin Umm-Anum ɗin duk da dama tun a wancan lokacin ya labarta musu a sanadin Bilkisu ne. Wata iriyar ƙauna da soyayyar Bilkisu sai ta ƙara faɗaɗa da daɗuwa a cikin zukatansu. Duk yanda mai hasashe zaiyi tunaninta a zukatansu tafi gaban hakan ta wuce.

        Sabon babin fira aka buɗe a cikin falon ba tare da sunma tuna darene ba ranaba, babu mai kallon lokaci babu mai tunawa ma da shi. Ba suba ko Jay da baisan yawan surutu yau sai yaji hakan bai gunduresa ba, wani wajen ayi kuka wani wajen ayi dariya, wani wajen ayi tausayi da al'ajabi. Haka kawai bilkisu ta tsinci kanta da yin matsanancin kuka akan labarin Aunty Mah-mah (Rahmah), haka kawai taji tana ƙwaɗayin ganinta koda kuwa a hotone. Hakama Umm-Anum ta shiga matsanancin mamaki da jin wai Bilkisu ba ɗiyar Rahmah bace ba. Yayinda shi kuma Jawaad al'amarin yay masa tsaye cak a zuciya baisan dalili ba, kawai yanaji a ransa kamar akwai wani abu dake a binne game da rayuwar bilkisun, musamman idan ya tuna da maganar baba ƙaura akan duhun dake biye da Bilkisun, da kuma furucin baba ƙauran a jiya da yaje wajensa saboda kiran da yay masa. ‘Kai anya kuwa babu wani abu........?’ ya faɗa a cikin ransa yana kafe Bilkisu da idanu harta tsargu ta ɗan ɗago suka haɗa ido.

            Barci ma da kansa yasan inda yake zuwa yay sata, dan kuwa idanun waɗanan bayin ALLAH ko gyangyaɗi basaji balle ai maganar barci, suna zaune dingangan har agogo ya nuna ƙarfe uku saura na dare. Jay ne ya katse firar tasu da roƙonsu akan suje su kwanta haka da safe idan ALLAH ya kaimu saisu ɗora. Badan sunso hakan ba suka miƙe dan suma susan Umm-Anum na buƙatar ace ta huta kodan doguwar tafiyar da tayo wadda bata saba ba. Su mamaki ma abin ya basu dan basusan lokaci yaja haka ba, jima suke tamkar daren bai wuce ƙarfe goma ba. Dole dai yau su kwana gidan ɗansu.

       Ummah babba Umm-Anum da Ummah ƙarama ɗakin bily aka kaisu su kwanta tare da ƴar uwarsu, duk da dai ba kwanciyar sukaiba wani babin sabuwar hirar suka sake buɗewa ma su. Batool da Anum da Nabeelah kuma ɗakin dake kusa dana Bilkisu, Anuwar yana a ɗakin baƙi. Jay ya nufi nasa ɗakin, Bilkisu na shirin shigewa wajensu Nabeelah Ummah ƙarama ta korata ɗakin Jawaad.2

        Sosai kunya ta lulluɓeni har inaji kamar ƙasa ta tsage na shige, to amma yaya na iya suɗin ba abin wasana bane balle nai tunanin musu gardama ma, haka na nufi sashen nasa kamar na nutse dan kunya. Ina jiyo su Nabeelah namin dariya harda Yah Anuwar. Sam banso hakanba, dan naso ace mun samu nisa da juna ni da shi koda na kwanaki biyu ne dan ya fahimci inajin zafin abinda ke faruwa tsakaninsa da ƴan uwana, ƙila ta hakan zan samu ya faɗamin abinda ke faruwar. Badan a ciwon kan da nake ji ba da falo zanyi zamana na ƙarasa daren, haka dai na daure fuska a ciskule na nufi bedroom ɗinsa, ciki ciki nai sallama na shiga, yana kwance a saman gado da ga shi sai noxer kawai, idanunsa a rufe suke amma na tabbata ba barci yake ba, na ɗauke kaina daga garesa na nufi bayi. Ban wani jimaba na fito dan fitsari kawai nayi da abinda baza'a rasaba. Yanda na barsa haka na fito na samesa, bani da kaya a ɗakin, sai naita tunanin mizan saka na kwanta dan bazan iya barci da kayan jikina ba. Ganin lokaci na sake ja ga zazzaɓi nama neman saukarmin yasa na nufi Wadrobe ɗinsa, cikin sa'a kuwa idanuna saka sauka akan t-shirt ɗinsa mara nauyi ruwan toka, nasan indai na saka zata sakkomin dan babbace kuma girman ba ɗaya ba.

        Zagayawa nai ta ɗayan gefen na kwanta can ƙarshen gado na juya masa baya.....

       “K har kin isa mu kwanta a gado ɗaya ki juyamin baya!”. Na tsinkayi saukar muryarsa da furucinsa a fusace cikin kunnuwana. Ɗan rintse idanu nayi ina haɗiyar yawu da ƙyar, zuciyata sai harbawa take da sauri-sauri na tsoro. A hankali na juyo ina tura baki da sake ɓata fuska sosai, abin mamaki har yanzu yana a yanda yake. A ƙasan ido naɗan hararesa naja bargo na rufe har fuskata ma.

         Wani haushi ya sake kume zuciyar Jay, jiyake kamar yay mata filla-filla ɗin da saita ƙarasa daren da kuka, sai dai yanata ƙoƙarin danne fushinsa kawai.

        Ba ƙaramar razana naiba jin an fincike bargon, na waro idanuna dake cika da ƙwalla a kansa, fisgoni yay na faɗa jikinsa ya matseni tsam-tsam, wani marayan kuka na buɗe baki zan sakar masa sai dai kuma ya hana hakan ta hanyar baƙar muguntarsa da ya ƙware a iyawa, nasan bani da wani ƙarfin ƙwatar kaina daga garesa musamman ma a irin wannan lokacin da sam banajina ma garas. Ɓacin ransa baisa shi kasa bidani cikin salon natsuwa da salo mai tsayawa a zuciya ba.............

..............✍


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Page 57

          

___________________________________

SHAHUDAH

___________________


                 Saukar su Umm-Anum ƙasar haihuwarta tayi dai-dai da komawar Shahudah gida. Mom da Aamilah ne kawai a gidan, Dad ya fita tun bayan barin su Jay gidan. Waya Mom keyi da Mama Atika. A take ta saki wayar ƙasa ta tarwashe bisa tiles jikinta na tsananin tsuma.

         Shahudah da ke cikin wani yanayi kamar ba'a hayyacintaba ta ƙaraso cikin falon tana tangaɗi ta zube saman carpet. Da ga Mom har Aamilah zubewa sukai a gabanta jikinsu na rawa, sai kuma Aamilah ta miƙe da sauri taje ta leƙa waje. Babu kowa sai maigadi daya taimakama Shahudah ta shigo ya juya zai koma wajen gate. Komawa falon Aamilah tayi bayan ta rufe ƙofar ruf ta garƙama mata key. Ta koma wajen su Mom da gudu tana faɗin “Mom ita kaɗaice fa wlhy babu ɗan iskan”.

     Mom tace, “Nashiga Uku ni Aysha, Shahudah daga ina kike haka? Miyayi miki ne?”. Bata da mai amsa mata waɗanan tambayoyin dan Shahudah sai faman lumshe idanu kawai take. Mom ta ƙanƙameta a jikinta ta fashe da kuka tana jama ɗan-fir'auna mugayen addu'oi. Suna cikin haka akai knocking ƙofar, duk ɗagowa sukai suka zubama ƙofar falon ido kawai, sai dai daga Mom ɗin har Aamilah babu wanda ya iya motsawa. Shiru ba'a sake bugawar ba, hakan yasa suka share suka maida hankalinsu ga Shahudah.

        Salman dake buga ƙofa ganin ba'a buɗeba sai ya zagayo ta kitchen, shikansa ba ƙaramin mamakin ganin Shahudah yay ba, jikinsa har rawa yake wajen ƙoƙarin kiran Dad ya sanar masa Shahudah ta dawo.+


        Cikin mintuna ƙalilan sai ga Dad a hargitse kamar zai tashi sama, yanda yake buga ƙofar kawai kasan babu lafiya, Aamilah ta buɗe masa tana matsawa ta bashi hanya, da sauri ya shigo. A gaban Shahudah ya durƙushe tare da maido kanta jikinsa idanunsa na kaɗawa lokaci guda dan ɓacin rai. “Shine ya kawota?”. Yay tambayar yana kallon Mom. “Nima ban saniba Dadynsu, shigowarta kawai muka gani ita kaɗai. Leɓe Dad ya taune da ƙarfi, ya kalli Salman dake tsaye cikin damuwa shima, “Kai Salman kiramin Dr Tayyib, ke kuma Aamilah kiramin maigadi, ai bazai rasa sanin wanda ya ajiyeta ba”.

         Babu jimawa maigadi da Aamilah suka dawo falon, cikin girmamawa Maigadi ya rusina yana gaida Mom. Bata amsa masaba, sai Dad ne ya jefa masa tambaya, “Yaya akai Mamana ta dawo gidan nan?”. “Wlhy Alhaji ban saniba, kawai naji nishin mutumne a jikin gate, shine na leƙa nama zata ko yaran nanne masu addabama mutane, sai naci arba da ita kwance jikin gate ɗin, sai kuma ƙurar mota da nake zargin a ita aka ajiyeta”. Ran Dad ya ƙara digunzuma sosai, yay ma maigadi nuni da hannu alamar ya tafi kawai.

     Maigadi na fita Dr Tayyeb na isowa gidan, bai zaman ɓata lokaciba ya shiga bama Shahudah taimakon gaggawa bayan an kaita ɗakin Mom an kwantar a gado. Duk wani taimakon da ake buƙata Dr Tayyeb ya bata, ya kuma tabbatar musu da cewar babu wata matsala normal zata farka insha ALLAH, ruɗanine ya sakata shiga wannan halin kawai. Hakanne ya basu ƴar nutsuwa, har suka kira su Mama Atika suka sanar musu dawowar Shahudah ɗin.


          Normal Shahudah ta farka a safiyar yau kamar yanda Dr Tayyeb ya sanar musu, kasancewar ɗaki ɗaya, gado ɗaya ta kwana da Dad da Mom sai suka baibayeta da tambayoyi akan abinda ya faru da ita?. Tsaf ta kwashe yanda akai ta sanar musu.

         “Dad ashe shiɗin ba mijina bane, tunda ya tafi dani wani gida ya kaini kawai ya ajiye bamma sake ganinsaba sai bayan kwana huɗu, ya sanarmin a randa aka ɗaura mana aure a ranar Bb ya saka shi ya sakeni, yace dan kawai yana ganin mutuncinsa yay hakan, amma badan Bb bane wlhy ko za'a kashesa bazai sakeni ba, kuma koda ya sakeni badan na taɓa zama matar Bb ba da bazai ƙyaleniba sai ya ketamin mutunci, wai Bb yana da kimar da bazai iya mu'amulantar abu shima yayi hakanba, Mom wlhy Bb mutumin kirkine, dan ALLAH ku bashi haƙuri mu koma aurenmu kamar da, ALLAH yanzu na amince zan haihu ko nawa yake so”.

     Mom da Dad da mamaki ya cika suka kama hannayenta cikin nasu, cikin zafin rai Mom tace, “Zaki koma gidan Jawaad kuwa Shahudah, zaki koma kodan shegiyar yarinyar can tasan asirinta aikin banzane, namiki alƙawarin a yau ɗin nan basai gobe ba za'a maida aurenku da Jawaad”. “Mom da gaske? Dad kaima kuma ka yarda da hakan?”. “Ɗari bisa ɗarima kuwa mamana, duk abinda kikeso a duniyarnan saikin samesa ko minene shi, duk abinda Momynku ta faɗa kisa a ranki ya gama tabbata”. Rungume Dad tayi tana fashewa da kukan jin daɗi, suma suka rungumeta cike da so da ƙauna harma da tausayinta.

          Gari na ƙarasa wayewa Mom ta ɗauki Shahudah suka tafi family house ɗinsu.1


STORY CONTINUES BELOW

__________________________________

      BEEJAY

__________________


           Da ƙyar muka iya tashi sallar asuba, musamman ma ni da jikina ke ciwo ta ko ina, idanuna sunmin nauyi sosai na rashin barci da kukan da na sha. To nidai bansan randa zan zama jarumar ba, duk yanda zan fasaltama mai saurarona zai ga kawai nacika rakine da ragwanta, amma ni kaɗai nasan sirrin al'amarin kawai.

     Da taimakonsa mukaje bayi badan bazan iya tafiya da kaina bane, hakan kawai shi yaso shiyyasa ya kamani muka shiga tare. Tare mukai wankan da bamu samu damar yi ba saboda tsabar barcin da yaci ƙarfin idanunmu, muna fitowa ya fice daga ɗakin.

      Tsaye nai ina tunanin ta'ina zan fara ne? Bani da wani kayan sakawa a ɗakinsa sai abinda baza'a rasaba, tunanina ne ya katse jin motsin mutum da sallama ciki-ciki, ya ajiye kayan dake hannunsa kusan kala bakwai, sai leda da alamu ya nuna kayan barci dana cikine a ciki, ajiyar zuciya naɗan sauke, bai jira cewataba ya sake ficewa.


           Ana idar da sallar asuba ban zaunaba, ina ƙoƙarin tashi ya shigo ɗakin da sallama, da alama ko azkar bai zauna yiba balle ai maganar motsa jiki, jallabiyar jikinsa kawai ya zare ya ajiye ya haye gado, matsawa nai na gaishesa, batare da ya amsa minba ya jawo hannuna na faɗo kansa, “Ouch” ya faɗa a hankali alamar yaji zafi, ɗan kallonsa nai sai kuma na kumbura baki. Hancina yaja yana wani lullumshe idanu, ya birkiceni na koma ƙasa fuskokinmu daf da juna muna shaƙar iskar numfashin junanmu. Cikin yin mar-mar da idanu na tsoro nace, “Ina kwana?”. Shiru yay kamar bazai amsaba yanzunma, yanata ƙarema fuskata kallo, ya sumbaci goshina yana sake ɗagowa da ƙoƙarin saka idanunsa cikin nawa amma naƙi yarda da hakan. Saima ɓata fuska nai ina faɗin, “Abinci zan ɗora fa”. “Da wane ƙarfin?”. Ya faɗa a ƙasan maƙoshi, dan koni dake daf dashi badan ina kallon lips ɗinsa ba ba lallaine na fahimtaba. “Da nawa mana” na bashi amsa nima ciki-ciki. Nauyinsa ya ɗan sake sakemin yana faɗin, “Oh ni kika raina kikema raki dama kenan?”. Tuni idanuna sun fara tara ƙwalla, “ALLAH zaka kasheni”. Nai maganar a rarrabe dan na fara sauke numfashi da ƙyar. Yi yay kamar zai ƙarasa sakarmin nauyin sai kuma ya ɗagani yana dunguremin kai. Nannauyan numfashi na sauke ina lumshe ido irin na ALLAH na gode makan nan. Na yunƙura zan tashi ya maidani ya sake kwantarwa. “Barci” ya faɗa a cikin kunnena. “Idan nayi barci sukuma mi zamu basu suci?”. “Shiiii!!” ya faɗa batare da ya bani amsata ba. Shirun kuwa nayi ina masa kallon mamaki, yaja bargo ya lulluɓemu da shi tare da sakani a cikin jikinsa, a hankali ya furta, “Thanks you Miemaa”. Bansan dalilin godiyarba, dan haka na sake lafewa a jikinsa nace, “For What?”. “For Everything Zinaran” Ya bani amsa da wani irin salon da yasa tsigar jikina tashi. Sake lafe masa nai a jiki ina shaƙar mayataccen ƙamshin turarensa da akwanakin nan yakemin daɗi fiye da komai. barcin mukeji, dan haka kafin wani dogon lokaci yayi gaba da mu.


            Barcin da su Umm-Anum suka gagara yinsa a daren jiya yau suna idar da salla suka nema yinsa, koda Jay da Anuwar suka shiga gaishesu sama-sama suka amsa musu, Jawaad da yasan za'a rina yaja hannun Anuwar suka fito. Dama yasan ai wannan barcin sai sunyisa dan shi ba'a cin bashinsa daman.


        Kasancewar na kwanta da maganar abincin a raina sai barcina baiyi tsahoba na tashi, a hankali na zare jikina daga nasa na sauka a gadon, badan barcin ya isheniba na tashi, zuciyatace kawai bata aminta dana kwantaba bayan gida cike da baƙi. Ina fitowa babban falo naci karo da kulolin abinci, da mamaki na isa garesu na bubbuɗe, lafiyayyen breakfast ne a ciki wanda ya fito shar kamar ka zauna ka cinye kai ɗaya. Mamaki ya kamani na inda ake kawo wannan abincin? Sanin bani da mai bani amsa sai kawai na shiga kwashesu zuwa kitchen, na dawo nahau gyaran falon zuwa falonsa da nawa da duk inda dai bazan takurama masu barciba. Kafin su tashi na shirya abincin a falona na koma nayi wanka na na shirya tsaf cikin zani da riga na atanfa da sukaimin ƙyau.

      Jinai kamar ana kallona, na juyo da sauri na kalli gadon batare dana ƙarasa ɗaurin ɗan kwalin ba. Boss dake kwance idanunsa a kaina ƙyam ya ɗan lumshesu ya sake buɗewa a kaina cike da salo. “Dama ka tashi?”. Kansa ya jinjinamin kaɗan batare da yace komaiba. Ɗan kwalinma sai naji na kasa cigaba da ɗaurasa saboda idanunsa duk sun takurani, haka dai na daure na ƙarasa na miƙe har lokacin idanunsa a kaina. Toilet naje na haɗa masa ruwa na fito, yanzu kam zaune na iskesa a bakin gado da waya a hannu. “Ga ruwan wanka can”. Kansa kawai ya girgiza min, batare da yace komaiba. “ba yanzu zakayi ba?”. ajiye wayar yay ya ɗago yana kallona, “Barshi idan naci abinci zanyi, bara na duba saƙon nan da Jabeer ya turo min” yay maganar yana miƙewa ya nufi Computer ɗin dake a ɗakin inda ya gyara a can gefe tamkar wani ɗan office. Da kallo kawai na iya binsa, danni mamaki yake bani yanda sam bai gajiya da aiki. Komai banceba na gyara gadon kawai na fice daga ɗakin.

            A falo na iske Aunty Batool ta fito cikin shirin fita, na bita da kallon mamaki da alamar tambaya. Murmushi tamin kaɗan tana gyara mayafinta, “Zanje gida saboda abincin Alhaji babba, naga Ummah ganin ƴar uwarta yama mantar da ita”. Murmushi nayi, “Ah haba aunty Batool itama nasan ba mantawa tayi ba, kawai dai tana cikin yanayine mai wahalar fassara, to mizai hana ki ɗiba masa na nan? Idan kuma wani ya keso daban ai saina girka masa yanzun nan insha ALLAH”. “A haba, wahalan ai sai yayi yawa, bara kawai naje can ai zan dawo, koda yake nama san acan kuma yau za'a yini ma”. “A'a dan ALLAH, muje kiga na nan ɗin dai aunty Batool, shima idan yaji kin tafi can dan kawai dafa abincin baba ai bazaji daɗiba”. Nai maganar ina marairaice mata.

       Da ƙyar na samu ta amince mukaje kitchen ɗin, duk abinda tasan zai iya ci shi ta ɗiba masa, ta zuba a kwando ta fice riƙe da key ɗin motar da sukazo a ciki.


STORY CONTINUES BELOW

        Coffee na haɗa na koma kaima Boss, yanata aikinsa hankali kwance, na ajiye ɗan tray ɗin dana ɗora ƙaramar butar shayi da kofinta sai cokali a gabansa, tsiyayawa nai na miƙa masa, batare da ya kalleni ba ya amsa yana faɗin, “Waye ya fita da mota?”. “Aunty Batool ce” na bashi amsa a taƙaice. Baice komaiba yakai kofin bakinsa, ɗayan hannunsa kuma yana amfani da mouse.


★★★★★★


          Zuwa goma da rabi duk mun hallara gaban abinci, bayan gaishe-gaishe da tambayar lafiyar juna mukai zaman karyawa, kowa nacin abinci cikin salama bandani da naketa tsakurarsa, badan rashin daɗiba kuma, haka kawai dai nakeji bana sonci kuma yunwa nakeji.

       Jay ya lura bily batacin abincin sam, sai dai kunyar iyayensa ta hanashi cewa komai. Ummah babba ce ta lura da hakan, saita kira Bilkisu. Tashi nai na nufeta dan nazata wani abun zata sakani, sai dai ina zuwa ta jani ta zaunar kusa da ita, da kanta ta shiga ɗuramin abincin duk da nace mata na ƙoshine, ina kallon sanda boss ya sauke ajiyar zuciya. Daurewa kawai nake ina amsar abincin.

          Boss ne ya fara miƙewa alamar ya ƙoshi, yaɗan kalli iyayen nasa yana faɗin, “Bara naje na watsa ruwa kafin time ya ƙure, jirgin su Abbu ƙarfe sha biyu zai sauka”. Cikin kulawa Ummah babba da ƙarama suka amsa masa.

      Shigewarsa babu jimawa muma duk muka kammala, da taimakon su Anum na gyara wajen, gudun kar kwanikan su bushe sai mukai zaman wankesu, muna wanke-wanken ina tunanin abinda ya kamata na dafa mana da rana, dan koma daga ina ake kawo wannan abincin bana buƙatar a cigaba da kawosa, ya kamata nima in-lows ɗina suci girkina ai....


★★★


         Jay na fitowa daga wanka ya samu wayarsa na haske kasancewar a silent take, matsawa yay gaban mirror ya shiga shafa mai batare da ya duba mai kiranba ma, bayan ya kammala yana gaban Wadrobe zai ɗauka kayan da zai saka ya kuma hangar wayar tana haske, guntun tsaki yaja, ya ɗauka kayan da yake bukata ya fara sakawa, sai da ya shirya tsaf sannan ya nufi wayar yana idasa saka maɓallan rigarsa. Gabansa ne ya ɗan faɗi ganin Batool ce ta jera masa har missed calls kusan talatin, sai kuma number sojan da sukanyi magana da baba ƙaura idan hakan ta taso. tabbas wannan kiran bana lafiya bane, dan kaf cikin ƴan uwansa babu wanda ya kai Batool iya zama da shi da halinsa, inhar tai masa kira ɗaya tai na biyu taga bai ɗaukaba bazata sake kiransaba sai idan shine ya kirata. Yana ƙoƙarin kiranta sai gashi ta sake kira, ɗagawa yay da sauri....

         Daga can Batool ta sake fashewa da kuka jin an ɗaga, a cikin tsananin ruɗani tace, “Yayanmu akwai matsala, wasu mutane sunzo har gida sun tafi da Alhaji Babba da baƙon mutumin nan”.

         Wani irin yankewa ƙirjin Jawaad yay ya faɗi, furicin Batool ya jisane cikin kunnensa tamkar saukar guduma, cikin rawar baki yace, “Su su.. Su wanene?”. “Ban sansuba Yayanmu, ina ɗakin Alhaji babba ina gyarawa suka shigo. fuskokinsu duk a rufe suke da facemask, nima nasan da sun ganni bazasu barniba, tun shigowarsu nake kiran wayarka amma baka ɗaukaba, ina tsoron na kira su Ummah su ruɗar da kansu shiyyasa ban kiraba.....” Bai bata amsaba ya katse kiran, ƙirjinsa na wani irin lugude tamkar ana gasar dakan fura a kansa. Da sauri ya fice daga ɗakin, harya nufi sashen Bilkisu sai kuma ya jiyo dariyarsu a kitchen ita dasu Nabeelah, can ya juya ya nufa......

          Muna tsaka da yima Anum dariya boss ya faɗo kitchen ɗin, yanayinsa kawai ya sakani faɗuwar gaba, Anum da Nabeelah kam duk ɗauke numfashi sukai dan tsoro, baice komaiba yaja hannuna muka fice, har munje ƙofa ya juna yana watsama Nabeelah kallon gargaɗi, “Kucigaba da aikinku, idan kuma ƙafar wani ta fita a kitchen ɗin nan saina ɓallata”. Kai kawai suka jinjina masa, ya ja hannuna muka ƙarasa ficewa zuwa bedroom ɗinsa.

       “Boss lafiya kuwa?”. “Babu lafiya Miemaa, yanzu Batool ta kirani........ Akwai matsala ace su Ummuna susan wannan maganar, musamman ma ita da nasan yanzu babu wanda ta ƙagu ta gani kamarsa, dan haka kiyi shiru da bakinki yanzu zan tafi can, kosun tambaya kice nafita amma zan dawo yanzun k.......”. Da sauri na katsesa da faɗin, “Boss tare zamu tafi, nima bazan zaunaba”. “Bazai yuwuba Miemaa, idan muka fita mu duka zasu iya tunanin wani abu”. “Dan ALLAH kayi haƙuri mutafi tare, koba komai nima zanyi wani amfanin ai, zamana anan zaisa na kasa jurewa na tona asirin komai”. “Miemaa!....” “Please boss”. Nai azamar katsesa. Bakinsa ya cika da isaka ya furzar da ƙarfi yana ɗaga wayarsa dake haske. Ban saurari amsarsa ba nashiga ƙoƙarin canja kayana.


STORY CONTINUES BELOW

        Ta kitchen muka fita, bayan boss ya jama Nabeelah dogon gargaɗi akan ta kama bakinta wlhy, idan har sukace mun fita sai yay gutsi-gutsi da ƙasusuwanta yanda babu mai iya shaida itace harma Anum ɗin kanta. Daga haka muka fice, Sadiq baizoba, saboda weekend ce, dan haka boss da kansa zaiyi driving ɗin.

         Mahaukacin gudu ya ke zubawa tamkar shi kaɗaine da titin, to dama yaya lafiyar giwa balle....., dama can shi ɗin ɗan babu sauƙine wajen gudu da mota, balle yanzu data zamto na ƙare numfashi. Ko gezau banyi da gudun nasaba yau, gani nakema tamkar baya gudun, sai faman kaɗa yatsun hannuna nake jikinna na wani irin tsuma. Yayinda boss kuma yana tuƙi yana waya da su Oga Hafiz.

    Cikin mintuna ƙalilan muka iso gidan, mun iske tawagar su Jabeer a gidan harma da ƴan sandan zahiri, sai wasu daga cikin ƴan anguwa da abin ya faru akan idanunsu su Hafiz nata musu tambayoyi.

      Aunty Batool ta iso garemu da gudu tana kuka, riƙo hannunta boss yayi idanunsa na sake kaɗawa suna sake komawa jajur fiye da yanda muka fito gida. Bayanin duk yanda yanda al'amarin ya faru ta shiga yimasa kamar yanda tayima su Sir Ahmad ma. Kasa cewa komai yay, sai jikinsa dake wani irin rawar bala'i, ƙwanjinsa da jijiyoyin kansa na sake buɗewa, yanda ƙirjinsa ke sama da ƙasa kawai zai tabbatar maka zuciyarsa na gudu maiban tsoro dake neman fin ƙarfin gangangar jikin nasa. ya saki hannunta ya nufi inda su oga Aliyu suke. Matsawa nai na rungumeta muna hawayen tare, sai dai ni saɓanin ita ina ƙarfafa zuciyata yau ina lallashinta, sai da naga ta tsagaita da kukan sannan na ɗagota na share mata hawayen. “Ki kwantar da hankalinki aunty Batool, insha ALLAHU zasu dawo, kosu wanene ALLAH bazai basu dama akan ƙudirinsu ba”. “ALLAH yasa haka mami” ta faɗa wasu hawayen na sake jiraro mata. kiran da oga Jabeer yaymin ne yasa na taimaka mata ta zauna a cikin motar.


        Tun a yanda Jawaad ɗin ya taka birki sanda suka iso gidan su Sir Ahmad sukasan ransa a matuƙar ɓace yake fiyema da yanda sukai hasashen ganinsa. ganin Batool ta nufesa sai duk suka dakata daga yunƙurin zuwa inda yaken, bayan yabar wajen ya nufesu ne, Sir Ahmad yay saurin tararsa cikin zafin nama yana riƙe hannunsa “Jay! Ka kwantar da hankalinka, insha ALLAHU zamu gano inda suke, koma su wanene suka aikata hakan basuyi nisa damuba a halin yanzu tabbas, yanzu haka har su Jabeer sun fara ƙoƙarin gano inda suke. Ka nutsu banason ka fusata kanka da yawa, domin nutsuwarka ce abar buƙatarmu fiye da komai a yanzu. shin akwai wani da kake zargi ne?”.

          Jawaad dake tsaye kawai yana kallon yanda su Aliyu da sauran ƴan sandan keta kai kawo akan al'amarin ya lumshe idanunsa yana busar da zazzafan numfashi, “Sir! Kowama zan iya zarga a halin yanzun, sai dai hakan bazai saka na kasa fidda ɗaya a cikin dubu ba”. “Nasani gwarzona”. Sir Ahmad ya faɗa yana ɗan bubbuga kafaɗar Jay ɗin cike dajin ƙarin alfahari da ƙwazon yaron.

          Jabeer ne ya ƙaraso wajen riƙe da tab.. A hannu, yay salute ɗin Sir Ahmad sannan ya kalli Jay dake kallonsa shima. “Boss ƴan iskan mutanen nan basu bar wani alama ko kaɗan da za'a iya bibiyarsu ba, bayanan dake hannunmu ma a yanzu haka ko motar da sukazo a cikinta babu Number ma, abinda bayanan mutanen anguwa suke faɗa mana kawai motar baƙa ce, suma mutanen kuma baƙaƙen kayane a jikinsu, fuskokinsu a rufe”. Shiru yay yana kallon Jabeer cike da nazarin maganganunsa, kafin kuma ya kallesa yana ɗan cije lip ɗinsa na ƙasa, “Dama bana tunanin zasu bar wata alama ta zahiri, sai dai dolene za'a samu ta baɗini Jabeer. Zamanmu anan gidan baida wani amfani, inaga mu wuce office kawai”.

      Jabeer yace,  “Okay nima nayi wannan tunanin, dama isowarka muke jira muji ta bakinka, dan yanzu haka dai Number shi Alhaji Babba muketa ƙoƙarin bibiya saboda Batool tace tana zaton da ita ya tafi a jikinsa batare da suma maharan sun sani ba. a yanzu haka dai wayar na nuna tana titin gambari gab da babban titin ƴan robobi na gabashiya. Jami'anmu suma suna gab da isa wajen harda Aliyu”. Amsar Tab ɗin Jay yayi daga hannun Jabeer da sauri....

       Hakan yay dai-dai da isowar Bilkisu da wani tunani yazo mata a zuciya inda suke. Sai da tai Salute ɗin Sir Ahmad itama sannan taɗan matsa kusa da Jay da hankalinsa kega Tab... ɗin da ya amsa a hannun Jabeer, amma yasan da zuwanta, dan ƙamshin turarenta ma ya ishesa shaidar tana wajen. “Sir anya kuwa wannan aiken ba daga gidancan bane?”. Da sauri Jay ya ɗago yana kallonta, “Wanne a ciki?” ya faɗa cike da ƙaguwa. “Inda na dawo daga farauta shekaran jiya”. Kafeta yay da ido dan maganarta na tafiya bisa ƙamshin gaskiya. Ta ƙara risinar da kanta cikin girmamawa a garesu, cigaba tai da faɗin, “Bazai yuwu ace dama ya barmu ba, dolene zai bibiyemu kodan maigadinsa, sai dai bamu da tabbas, hasashene kawai nayi Sir”. Jawaad yay wani ɗan murmushi yana maida duka hannayensa biyu ya goya a bayansa, taku ɗaya biyu yay sai kuma ya sake juyowa, hannunsa ɗaya ya sauke daga bayan ya tura cikin aljihu, ɗayan dake riƙe da tab... Kuma ya ɗagosa yana goga tab... Ɗin akan hancinsa. Daga Jabeer har Sir Ahmad da bilyn duk kallonsa sukeyi. Wani murmushin ya sakeyi da tsayawa cak, bily ya nuna da tab... ɗin hannunsa yana faɗin, “Maganarki akwai ƙamshin gaskiya, dolene a cikin biyu a samu ɗaya, idan kuma nai wani nazari zan iya ɗaurasu a mizani guda ya zama aikin haɗaka ne”. Ya ƙare maganar yana maida dubansa ga sir Ahmad da ke binsu da kallo kawai. Kafin yace wani abu Hafiz ma ya iso riƙe da waya alamar magana ya gamayi. “Mutanen nanfa inaga sun farga da wayar jikin Alhaji babba, sam yanzu bama ganinsu alamar an kashe wayar”. Kallonsa duk sukayi, Sir Ahmad yace, “Dai-dai ina kuka daina samunsu?”. “Sir a Roundabout ɗin titin General hospital”. “General hospital?”. Jay ya faɗa cikin sigar tambaya. “Ƙwarai kuwa boss, ka duba ma zaka gani anan”. Tab... Ɗin Jay ya sake buɗewa, dai-dai inda Hafiz ya faɗa shima nan ya nuna masa, ya miƙama Jabeer tab... ɗin yana faɗin, “Yanzunan inason a bincikamin inda Alhaji Kokino yake, a kuma bincikamin inda Alhaji Ali da Qaseem suke, sai Mr Gebrail shima”. Yana maganarne yana daddana wayarsa daya ciro a aljihun wandonsa. Da mamaki na kallesa jin ya sako Dad da Yah Qaseem ciki, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska yasa na gaza cewa komai, sannan ma bani da wannan damar dan a fagen aiki muke matsayinsa na ogana ba miji ba. Da to muka amsa masa kawai, muna barin wajen.

       Sir Ahmad dake kallon Jay yace, “Miyasa ka lissafo waɗanan mutanen? Kana zarginsu da aikata hakanne?”. “Sosaima kuwa Sir”. Jay ya faɗa yana ɗaura wayar a kunnensa jin an ɗaga. “Munkaila kana ina?”. Bansan amsar da aka bashiba daga can, ya gyara tsaiwarsa idonsa a sashen da su Bilkisu ke magana ita dasu Jabeer yace, “Ka ajiye wannan aikin, yanzun nan kaje gidan Alhaji Ali a ɗakkomin maigadin gidansa da kuku”. Kansa ya gyaɗa da sauke wayar.

       “Jay ka sake sakani a duhu, wai ba kana magana bane akan Alhaji Ali dana sani baban Qaseem? Da shi Qassem ɗin kansa?”. Fuskar Jay cike da murmushin takaici ya jinjina ma Sir Ahmad kai, “Shi nake nufi Sir”. “To amma miya haɗashi da Alhaji kokino da har kake tunanin zasuyi aiki tare?”. “Hasashene kawai Sir”. Ya bama sir Ahmad ɗin amsa a taƙaice. Badan bai yarda da shi bane, yanason tabbatarwa kasafin ya buɗe aikin kowa ya sani........


STORY CONTINUES BELOW

______________________

      BABA ƘAURA

__________________


             Tun a safiyar yau baba ƙaura ya sa ake nemar masa Number Jay sai dai ba'a samu ba, iya ƙoƙari sojan dake taimakama baba ƙaura idan zaiyi waya da Jay yayi amma wayoyin Jawaad ɗin duk sun ƙi shiga, sai kusan goma na safe da ƙyar ɗaya ta shiga, sai dai kuma anƙi ɗagawa kusan kira goma.

        Ganin lokaci na sake ƙwacewa baba ƙaura yace sojan idan yasan inda gidan Jay yake ya kwatanta masa. Sojan shima bai saniba, dan haka yacema baba ƙaura bara yaje ya bincika ko za'a dace. Tunda sojan ya fita baba ƙaura ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba komai ya kawo hakanba sai abinda ya jiyo a daren jiya, ga lokaci yanata sake tafiya kuma.

       A jiya gaba ɗaya zaman ya gunduresa, jiyay yana sha'awar zagaya jeji, dan haka tun bayan sallar la'asar ya sulale yabar Barrack batare da sanin kowaba sai sojan nan da General ya ɗaura alhakin kula da shi akansa, yanda yaron ke masane ya sakashi ƙaunarsa harma yake masa wasu abubuwa na taimako, sannan baya ɓoye masa wasu abubuwan da suka shafesa, hakan yasa a fitarsa ta jiya ma ya sanar masa. Yayi ninƙaya cikin jejin sosai jiya bisa al'adarsa ta farauta da sanin sirrin jajejin da ALLAH ya bashi badan zaiyi farautar ba, dan ko karnuka babuma a tare da shi. Tun daga farkon dare har kusan ƙarshensa bai fitoba yana a dajin. sai da ya gama jin sirri mai girma daga shaiɗanun da suka maida wani yankin jejin nasu sannan ya fito, gab da asubahi ya shigo cikin gari, ana shiga salla masallaci yana isowa Barrack. A gaggauce yay alwala ya shiga masallacin shima. bayan an idar da salla ya saka sojan nan ya nemo masa Number Jawaad zaiyi magana da shi, sai dai sam an gaza samunsa, da aka samesan kuma ma sai bai ɗaukaba.....

     Dawowar sojan tasakashi tsayawa cak daga kai kawon da yake faman yi da tunanin daren jiya, cikin ɗoki ya sanar masa an gano family house ɗin su Jawaad ɗin, kuma yana ƙyautata zaton a ciki jay yake zaune da iyalinsa. Baba ƙaura yayi murna, sojan nan yay masa rakkiya har bakin hanya ya sakashi a napep da faɗama mai napep ɗin inda zai kai baba ƙaura. Kasancewar gidan su Jay sanan nan gidane sai akaci sa'a mai napep ya sani.

       Da ƙyar suka samu maigadin ya sauraresu, danshi tsoron baba ƙaura ne ya kamashi ganinsa sanye cikin fatun namin jeji, gashi babu hannu guda. Sai da baba ƙaura yayta masa magiya sannan ya sanar masa cewar Jawaad ba nan yake zauneba yanzu, yana gidansa da ke a A.Y street. Nanma sunsha daga kafin ya basu address ɗin, mai napep ɗin da yake yanada kirki shine ya sake ɗaukar baba ƙaura zuwa A.Y. sai dai suna shiga layin, motar Jay na fita. A gidan Jay ɗinma sunsha daga da maigadi kafin ya sanar musu Jawaad ɗin baya gida ya fita babu jimawa, suka roƙesa koya san inda ya nufa yace shi bai saniba. Sosai hankalin baba ƙaura ya sake tashi, burinsa kawai yaga Jawaad, harsun baro gidan ya roƙi mai napep ɗin suka sake komawa. Tambayar maigadi yayi ko ina drivern Jawaad ɗin?. Maigadi ya amsawa baba ƙaura a daƙile cewar yau Sadiq baizai zo aikiba yana gidansa. “Dan ALLAH ka faɗa mana inda gidan nashi yake zamuje mu samesa?”. baba ƙaura ya faɗa yana kallon mai gadin. A fusace mai gadi yace, “Kai malam kafa isheni, taya zan faɗa maka bayan bansan kaiɗin wanene ba? Nama sani ko cutar da waninsu zakayi, indai ma ogane yafi ƙarfinka dan shima wlhy aljanin kansane da kake ganinsa nan”. Murmushi baba ƙaura yayi, yace, “Yaro nafika sanin hakan ai, ka daure dai ka faɗa mana kokuma ka kira mana shi direban a waya idan ya gammu shi yasan manufarmu”. Kamar maigadi bazaiyi ba, sai kuma miya tuna oho masa ya ɗauka waya yay kiran Sadiq.

           Babu jimawa saiga Sadiq mai napep shima ya kasowa, yana ganin baba ƙaura ya rikice, dan baiyi zaton shiɗin bane da gaske. Haƙuri yayta bashi akan abinda maigadi yay masa, baba ƙaura yace babu damuwa, so yake yanzunan ya kaisa inda Jawaad yake shidai. Maigadi dai jikinsa yayi sanyi ganin yanda Sadiq ya bama baba ƙaura muhimmanci, a take ya shiga bashi haƙuri. Baba ƙaura yay murmushi kawai yace karya damu........


_______________________________


                Anbar ƴan sanda zagaye da gidan Alhaji babba, su Jay kuma suka kwasa zuwa station dan aikin zaifi yuwuwa acan cikin sauri.

      Bilkisu dai duk ta kasa sukuni akan sako Qaseem da Dad da Jay yayi a waɗanda yake zargi, zuwa yanzun kam tafara yarda da saƙe-saƙen zuciyaryarta, anya kuwa babu wani abu a rufe da bata saniba? Haka kawai mijinta da Dad bazasu ringa takun saƙa na kamar wasu maƙiya ba, a dafa surukinsa ne, sannan mijin yayar mahaifinsa ne. Ta tuna kallon kallo da suka dinga yima juna jiya duk da shi Dad yanata nuna babu komai.....

     Da wannan tunanin a ranta suka isa station, babu mutane da yawa saboda weekend ne. Ni da su oga hafiz muka nufi office ɗin boss, shi kuma suka nufi na sir Ahmad..

          

             Bamufi mintuna goma ba shima sai gashi ya shigo office ɗin ɗauke da takardu a hannu.

      Kujerar zamansa ya nufa yana faɗin, “Miemaa taso kiyi wannan aikin”. Miƙewa nai daga inda nake zaune ni kaɗai na nufesa. Kujerar zamansa ya nunamin, babu musu na zauna shi kuma ya shiga ƙoƙarin dai-daita Computer ɗin.

      Oga Jabeer da Hafiz dake can gaban Computers ɗin dake gefe guda biyu suka juyo suna kallonmu, Hafiz ne yace, “Boss babu watafa alamar waya data shiga tsakanin Alhaji kokino da Dadyn su Shahudah gaskiya, amma Dad yayi waya da Qaseem awa ɗaya da mintuna hamsin da uku da suka wuce. Barin inda nake yay ya nufesu, “Zamu iya samun maganar da sukayi?”. Jabeer da hankalinsa ke ga Computer gaba ɗaya yace, “Bazai yuwuba gaskiya, dan inhar mukai hakan zai gane, kasan wayar Qaseem tana da tsaro kamar yanda namu suke”. Jay yayi ɗan jimm na tunani. Numfashi ya furzar mai zafi yana dafe kansa dake sara masa, sai kuma ya zabura kamar wanda ya tuno wani abu. “Jabeer ina zuwa, bara na turo muku Numbers ɗin nan, dukansu inason mu tabbatar idan suna aiki a halin yanzun”. Yay maganar yana sake nufo inda nake, drawer ɗin jikin table ɗin ya jawo, flash ne da yawa a ciki, ya shiga ɗakkosu ɗaya bayan ɗaya yana duba rubutun da yay a jiki, cikin sa'a ya samo wanda yake nema, miƙamin yay yana faɗin, “Saka shi”. Yanda yake min magana babu wasa tattare da shi yasaka jikina har tsuma yake, sai da na gama dai-daita komai abubuwan dake cikin flash ɗin suka bayyana sannan ya ranƙwafo kaina, hannunsa ya ɗora bisa nawa dake a dafe da mouse muka ringa control ɗin Computer tare.

        A haka Sir Ahmad da wasu jami'anmu manya biyu suka shigo suka samemu. Nan take aikin ya sake ɗaukar zafi, ni dai ta ɓangarena da taimakon boss nakeyi. Kusan minti goma sha biyar mun duƙufa, hankalin kowa nakan abinda ke gabansa akai knocking ƙofar office ɗin, batare da jiran izini ba oga Aliyu ya shigo da sallama. Inda muke ya nufo bayan yayi salute ɗin su Sir Ahmad. Bansan miya gwargwaɗa ma Boss a kunne ba, na gadai shima boss ɗin ya miƙe ya nufi Sir Ahmad cikin zafin nama. Sai kuma suka fice shi da Sir Ahmad ɗin daga office ɗin.........


STORY CONTINUES BELOW

_____________________

      BABA ƘAURA

___________________


         Cikin mintuna ƙalilan suka iso station ɗin bisa taimakon Sadiq, sai dai kuma securitys sun hanasu shigowa musamman ganin yanayin baba ƙauran, sun musu roƙon duniya amma sun hanasu, Sadiq ya kira wayar Jay amma bai ɗagaba, hakan yasa suka koma gefe cike da damuwa, musamman ma baba ƙaura dake matuƙar matse da son ganin Jay.

      Suna a wajen tsaye su biyu Sadiq na cigaba da kiran Number Jay sai ga motar su Aliyu, harma an buɗe musu gate zasu shige Aliyun ya hango baba ƙaura ta mirror. Sauke gilashin motar yay ya saka ɗaya daga cikin securitys ɗin yay masa magana da baba ƙaura. Ganin shi ɗinne dai kamar yanda yay hasashe sai ya bada umarnin barinsu su shigo. Bayan ya shige da motar ya samu waje yay fakin ya fito shi da waɗanda sukabi masu ƙwamushe Alhaji babba, gaisuwa kawai yay da baba ƙauran ya shiga ya sanarma Jay.


          Duk da Aliyu ya sanar masa baba ƙaura ne hakan nbai hanashi yin mamakin ganinsa har station ɗinsu ba, ya ƙarasa fuskarsa babu walwala, dan duk yanda yaso aro fara'a ya azama fuskar tasa kamar yanda ya saba idan yaje wajen baba ƙaura hakan ya gagara. Cike da girmamawa suka gaishesa har Sir Ahmad.

          Kallonsu baba ƙaura yay ya ɗauke kansa yana faɗin, “Kagani har a wajen aikinka ko?”.

         Ɗan murmushi Jay yayi da cewa, “Babu komai baba, ai nasan zuwan naka mai muhimmanci ne”. “Hakane” baban ya faɗa yana sake maido hankalinsa garesu sosai. Yace, “Tun da safe na saka a nemomin kai amma hakan ya gagara, ba'a samunka da farko, daga baya kuma ta shiga ba'a ɗagawa”. Kai Jawaad ya dafe, “Dan ALLAH kayi haƙuri baba, wlhy na tsinci kainane a yanayin da komaima bazan iyaba”. “Gudun faruwar hakanne ya sakani yimaka neman gaggawa ai daman,  tun bayan wucewarka na tafi jeji ne, acan ma na kwana, dan sai gabannin asubahi na shigo gari, sanda na iso nan har an shiga salla. Na saka a nema min kaine domin isar maka da saƙon abinda idona ya ganomin jiya a cikin jajin nan. Muhammad Jawaad lallai akwai matsala babba dake tunkaroku, da idona na gani, na kumaji da kunnena, gashi rashin samunka akan lokaci ya nunamin alamomin fara faruwar matsalar dana guda ma a yanzun”.

         Hankalin Jawaad a tashe yace, “Baba hasashenka duk haka yake, yanzu haka zancen da nake maka anje har gida an ɗauke kakana, akan binciken inda zamu samesa muke”.

             “Wannan shine shirinsu na farko dama. Na zauna nayi ƙyaƙyƙyawan nazari mutanen nan ba haka nan suke bibiyarka ba, akwai wani abu aƙasa wanda akwai jininka a ciki, ina nufin cikin zuri'arku akwai wanda ke tare da mutanen nan.....” cike da mamaki Sir Ahmad da Jay suke kallon baba ƙaura. Ya jinjina kansa yana cigaba da faɗin, “Kar kuyi mamaki, neman duniya babu wanda baya ɓatarwa, lallai kamar yanda na faɗa akwai wani abu a ƙasa, dan babu rami miya kawo rami? Bayan abubuwan dana sani ke a hannunku akwai wani abu da kuka ɗakko a wani gida ne?”. Sir Ahmad ya kalli Jay, shima ya kalleshi, sai kuma ya maida dubansa ga baban yana jinjina masa kai. “Akwai wani tukunya baba, wanda.........” ya labartama baba ƙaura da Sir Ahmad komai.

        Baba ƙaura da keta faman jinjina kai cike da nazarin maganganun Jawaad ya sauke nannauyan numfashi. “UBANGIJI ya baku kariya sosai to akan wannan aikin, dan suna cikin ruɗani mai girma akan son gano wanda ya ɗauki tukunyarnan, amma sun gaza gano komai, inuwar wadda ta ɗauka ɗin kawai suke iya gani, sannan har yanzu tsafin nasu kuma bai iya nuna musu mahaifiyarka ta shigo ƙasarnan ba. Wannan hikima ce da rahama daga UBANGIJI, inaga iyakar suce tazo shiyyasa komai ya keta ƙwace musu. A taron da sukai daren jiya sun tattauna abubuwa da dama wanda zarge-zarge da yawa sun sami rinjaye a kai kanka, sai dai a yanda na fahimta na yau sai sun fisu muhimmanci. Dan haka nakeso ku kasance a wajen kai da matarka idan zai yuwu, sannan lallai matsayinku na jami'an tsaro wannan shaiɗancin ya kamata ma ace ku kawo iyakarsa ma baki ɗaya. Dan tabbas kakanka yana tare da su, acanne kawai zaku iya samosa a halin yanzun dama wasu mutanen da aka kai a wajen bisa zalunci da son zuciya”.

        Boss ya cika bakinsa da iska ya furzar yana taunar lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi. Kallon Sir Ahmad dake fahimtar dukan maganganun nasu a baibai yayi. sai kuma ya maida ga baba ƙaura yana faɗin “Babu damuwa baba, amma kana ganin ita zuwa da ita bazai zama haɗari ba?”. Ƴar dariya baba ƙaura yay yana kallon Bilkisu data fito da waya a hannu ta doso su, “Babu wani haɗari insha ALLAHU, matar nan taka akwai sirrika tattare da ita waɗanda ALLAH kaɗai yasan tushensu, amma haka kawai nakeji a raina kamar sunada nasaba da taka ƙaddarar. Amma ita ɗin ba jami'ar tsaro bace?”. “Eh jami'ar tsaroce, irin aikinsu ɗaya”. Sir Ahmad ya bama Baba ƙaura amsarsa. Baba ƙaura ya sake faɗaɗa murmushinsa “Ka barta itama ta nuna bajintarta a aikinta da ƙwazon da ALLAH ya bata, ALLAH yana tare daku a dukkan al'amuranku insha ALLAHU. kudai kuci gaba da gayama ALLAH”. A tare suka jinjina masa kawunansu da faɗin insha ALLAHU baba. “Karkuji komai, wannan tafiyar tafi ta farko sauƙi insha ALLAHU, ta wani ɓangaren kuma tafi waccan haɗari, dan haka runduna zaku haɗa mata da tafi ta farko indai aikin zakuyi da gaske” ya ƙare maganar dai-dai da isowar Bilkisu wajen.

       Rissinawa nai na gaida baba ƙaura da banyi tunanin ganiba anan, ya amsamin cike da fara'a da kulawa. Cikin girmamawa na miƙama Sir Ahmad takardar hannuna da aka aikoni na kawo masa. Amsa yay yana dubawa, ni kuma na maida dubana ga boss da yanayinsa ya bani tsoro. Da ido nai masa alamar ‘Lafiya?’. Kansa yaɗan girgizamin kaɗan yana lumshe idanunsa dake jajur.......

     Sir Ahmad ne ya katse mu da faɗin, “Jay inaga yanzu haɗa rundunar da zamu tunkaru jejin ne ya dace, bara na nema mana jirage masu saukar angulu yanzun nan, sai ku haɗa kayan operation ko”. “Okay Sir” Jay ya faɗa cike da karsashi na jami'i mai cikakkiyar lafiya da zafin nama..

     Tare muka koma da baba ƙaura office ɗinsa inda su Jabeer keta aiki cike da zafin nama da ƙwarewa. Boss ya ɗan bigi tebir da zafi-zafi yana faɗin, “Ayi shirin fita operation mun gano inda suke insha ALLAHU”. Duk juyowa sukai suna kallonsa da mamaki, harni kaina kallon nasa nake, amma sai ya ɗauke kai yana nufar telephone ɗin dake saman table ɗinsa yana jero sunayen waɗanda za'a kira yanzun nan”.

        Cike da bin umarni Aliyu ya fice zuwa office ɗinsa domin aiwatar da komai, shima bayan yayi waya da wani da bansan ko wanene ba ya ajiye yana kallona da nufar ƙofa yace na biyosa ni da Dawood da suka dawo da Oga Aliyu yanzun.

        Store ɗin station ɗin muka nufa, inda acan muka iske Sir Ahmad da wani ogan mu shima suna haɗa bindugu. Muma aikin haɗa wasu makaman aka sakamuyi. Mamaki ya kuma cika zuciyata, duk yanda nake hasashen al'amarin da alama ya wuce nan, nasan Boss mutum ne mai muhimmanci a hukumarnan tamu, ya cancanci a nuna masa kowanne irin halacci akan taɓa ahalinsa, amma yanda ake shirin fita operation ɗin sai nakeji a raina kamar ya zarce na maido kakansa kawai. Cikin mintunan da bazasu gaza talatin ba duk wani shiri an kammalashi, duk jami'in da aka buƙaci gani ya amsa kira, a mamakina harda su Ummie su dukansu, Rose harma dasu Ada, sai sauran jami'ai na departments ɗin da ba namuba ma. Dukanmu mun kasance cikin Uniform ɗin aiki, dan boss ma da yake sanye da kayan gida a da sai gashi ya fito cikin Uniform harsu oga Jabeer da Sir Ahmad ɗin kansa. An bamu bullet proof jacket duk mun sassaka, kafin oga Hafiz ya rarraba mana bindugu harda kibiya ga waɗanda suka samu horo na musamman a kanta, wasu kuma wuƙaƙe naga an basu manyan takubba, sosai mamaki abin yayta bamu mu baƙin shigowa hukumar, dan zan iya cewa wannan shine operation na farko gagarumi da za'a fita damu..............✍2


Da ace zan iya sai nabi wasunku da bulala goma-goma a ɗuwawu aradu🙄, wlhy nafiku son naga na kammala buk ɗin nan🤦🏻. Uzirin daya riskeni ya wuce dukan tunanin mai hasashe, yanzunma dauriyace kawai dason ganin na faranta muku, saɓanin wasunku da bakunansu ke furta abinda bai daceba a gareni😢🚶🏻.

16

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭8

*_FARIN WATA SHA KALLO🤓🤗_*

ZAFAFANKU SUN DAWO GAREKU A 2021😋😋😋😋🚴🏼🚴🏼
*_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥🔥🔥
*_SABUWAR SHEKARA_*
*_TAREDA SABON SALO_*👍

✔️ *_A DUNIYAR RUBUTUN HAUSA SU NA DABAN NE,_*
✔️ *_A DUNIYAR NISHADANTUWA DA KARATUN HAUSA SU DIN NA MUSAMMAN NE,_*
✔️ *_A DUNIYAR FADAKARWA DA QAYATARWA NA KARATU SU DIN NA FARKO NE,_*
✔️ *_A 'BANGAREN NISHADANTUWA DA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA MAI SHIGA RAI DA SANYA SHAUQI DA NUTSUWA TO SU DIN ZA'BABBINE,_*
✔️ *_A 'BANGAREN SANYA NISHADI DA BARKWANCI TO SU DIN QWARARRINE,_*

*_Shin ko kunsan su ake kira da zafafa biyar masu tashe?_*
_*Idan kin/ka san kai maabocin karatun littafan HAUSA ne to tabbas karku Bari ayi Babu ku*_
*_domin kuwa wannan karon sun dawo muku da wani sabon salon Wanda babusa a DUNIYAR karatu,_*
*_cikinsu Babu wadda bataga jiyaba bataga yauba a fagen nishadantarwa._*

*_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥

_*SUKAR BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )9

*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )

💙

_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )

*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )

*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,2

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*09044191709*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO1

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
Page 58

.................Muna tsaitsaye a inda aka bamu iznin tsayawa, Rose na mana bayani akan abinda zamu tunkara. Cikin takunsa na zaratan jami'ai da sukasan aikinsu ya fito Hafiz biye da shi da bullet proof jacket a hannunsa da alama ta boss ɗince, A boss ɗinsa dana fara sani yake yau, kura ga tsoro gaban tsoro, zakin da babu abinda ya sani face farauta a lokacin da yunwa ta ciyo cikinsa, gwarzon da baya alfarma ga dukkan wanda baima kansa alfarmarba, ɗaya tamkar da dubu abin buƙatar kowacce ƙasa, kowanne yanki, ko wacce zuri'a. Cike da izzarsa mai cike da tsantsar damuwa da ɓacin rai yazo gabanmu ya tsaya yana ƙare mana kallo ɗaya bayan ɗaya. Ya furzar da wani zazzafan huci daga bakinsa yana nunamu da yatsansa manuniya. “Kusa a ranku aiki zaku fita bakin rai bakin fama, sakacinku na nufin sakaci da ƙasarku, sakaci da yankinku, sakaci da garinku, sakaci da familys naku, idan kuka zama jajirtattu kun fido da martabar ƙasarku ne, yankunan ku, garinku da familys naku dama rayukanmu baki ɗaya da hukumarmu. Aikine mai cike da haɗari, ka kashe ko a kasheka wannan duk hukuncin ALLAH ne, shawarar kawai itace addu'a, ina fatan kuna faimta ta”.
       “Yes Sir!!!” muka faɗa cikin haɗa bakuna tare da buga ƙafa ƙasa mukai salute nashi. Juyawa yay ga Rose yay mata maganar da bamaji kafin ya kalli oga Hafiz shima. Shima maganar sukai suka bar wajen kuma zuwa inda su Sir Ahmad ke tsaitsaye tare da manyan jami'anmu da sojoji kusan goma sha biyar.
      Mudai muna nan tsaitsaye muna jiran umarni, a haka oga Jabeer ya zo wajen ya bamu damar zuwa mu shiga jirage masu saukar angulu (Helicopters) da za'ai tafiyar dasu. Mu matan an haɗamu ne a guda ɗaya, drivern mu ma ta kasance mace ce yarinya ƙarama da bazamu gaza sa'anni gudaba, sai baba ƙaura kaɗai daya kasance namiji a cikinmu wanda ya wuce muce masa uba kawai sai dai kakanmu. A yau babu zancen fira mu dasu Ummie, kowa addu'a ce ɗauke da bakinsa da fatan nasara, a can ƙarƙashin zuciya kuma tsorone da kowa ke ƙoƙarin dannewa. Sai da muka hangi tashin wasu jiragen kafin namu ya tashi, kusan duk sai da muka lumshe idanu kowa shi kaɗai yasan abinda ke a cikin ransa.1

STORY CONTINUES BELOW

             Kamar a wancan karon tafiyace mukai da hasashe bazai iya ƙididdigar iyakartaba, sai dai kawai muka tsinkayi saukar jirginmu a tsakkiyar jeji mai cike da surƙuƙi da haɗarin gaske. Mun firfito kowa na ƙoƙarin kare ƙurar da fankokin jirgin suka tayar da hannunsa domin samun damar ganin hanya da ƙyau, wasunmu da basa son ƙura har ƴan ƙananun tari sukeyi da atishawa. Su boss suma duk sun firfito a nasu. Sir Ahmad na ƙoƙarin buɗe taswurar jajenin da ya amsa a hannun oga Aliyu baba ƙaura ya dakatar dashi. “Ranka ya daɗe bama buƙatar wata taswura, insha ALLAHU komai zai kasance yanda muke fatansa, babu wani lungu ko kogo da zai layancemin a wannan jajenin kaf ɗinsa, inda muke buƙatar zuwan zamu dosa kai tsaye babu ko gargada a ciki”.
         Sosai naga al'ajabi a saman fuskokin jami'anmu, muko da muka san wanene baba ƙaura hakan bai zame mana sabon abuba, fatanmu kawai samun kariyar UBANGIJI da nasara.
       Tafiya muka farayi a cikin jejin, su oga Aliyu da boss da wasu a cikin sojojin da baba ƙaura ne a gaba, sai su Sir Ahmad a bayanmu. Munyi tafiya mai nisa kafin mu isa wani ƙyaƙyƙyawan tsuburi dake da ƙaramar ƙorama a gefensa, sai tsuntsaye jefi-jefi dake shan ruwa. Da hannu boss ya tsayar damu kafin mu ƙarasa ga ƙoramar, Oga Jabeer ya matsa kusa da boss, bullet proof jacket ɗin dake a hannunsa ya shiga ƙoƙarin saka masa suna magana, nidai ina satar kallonsune da faɗin ‘Ɗan gata rigarma sai an saka masa’. Ya juyo saitin da muke yana bama Jabeer bayansa danya gyara masa can, ido muka haɗa nai azamar janye nawa, a bazata naji yace, “Miemaa!”. Abinda ya tsargamin nai saurin haɗiyewa, yayi masifar iya ambatar sunannan fiye da zaton mai tunani, kallonsa nayi na amsa da “Na'am”. Ya ɗauke idanunsa daga kaina yana faɗin, “Ki gyara wannan jacket ɗin taki bata zauna da ƙyauba”. Gaba ɗayansu suka zubamin ido banda su Sir Ahmad da hankalinsu ba wajanmu yakeba. Kaina na jinjina masa ina haɗiye yawu da ƙyar dan yanda duk suka zubomin ido sai naji na takura. Nazifa dake bayanace ta taimakamin na gyara, idonsa har yanzu a kaina yace, “Matan nan ku kasance kusa da wani komai rintsi, sannan banda harbi a kai, ciki, ƙirji, duk harbin da zakuyi karya wuce ƙafa ko hannu da inda baza'a mutuba”. Kai muka jinjina masa da faɗin, “Okey Sir!!”.
        Rose ta taɓe baki tana harar Bilkisu ta gefen ido, duk da tasan abinda Jawaad ya faɗa musu dokace kasancewar a harbin da duk su bilkisu zasuyi babu kisa sai ankai maƙurar da babu mafita   taji zafi a ranta, dan a ganinta Jay ya faɗama bilkisu ne ita kaɗai kawai cikin tsantsar nuna kulawa, tunda harda cewa ta gyara jacket ɗinta. ‘Mtsossw’ taja ƙaramin tsaki a ƙasan maƙoshi da matsawa gaba.
        Da ga inda muke tsaye muna hango gini maiban mamaki da tu'ajibi, dajine sosai fa. amma sai ga gida a tsakkiyarsa, gida ginanne daya amsa sunansa gida da ko a cikin gari ya cancanci kallo bawai sakaran gini ba ne. Babu wanda al'ajabi bai sakashi kallon baba kaura ba. Cikin dattakonsa yay murmushi shima batare da ya kalli kowa a cikinmuba. “Wannan gini ginine da ya ɗauki kusan shekaru ashirin da bakwai a cikin jejin nan, magina aka kawo suka ginashi kamar yanda ake gina kowanne irin gida, duk shekarar duniya kuma sai an sabunta masa fenti da abubuwan ƙawa. Mabanbanta mutanene ke zuwa cikinsa ziyara, abinda suke aikatawa a cikinsa kuma, sai munje idanunku zasu gane muku komai a yanzun, domin yau ranace da suka ware ta musamman domin shaiɗancinsu, shiyyasama muke anan tsaye bisa ƙafafunmu batare da sun farga da zuwan namu ba”. Kawuna kawai muke iya jijjigawa kamar wasu ƙadangaru, shine yay mana nuni damu ƙarasa.
         Ararrabe muka fara dosar ginin muna zagayesa kamar yanda commander'n (boss) tafiyar ya bada umarni, ɗai-ɗai muka ringa shiga cikin dabara na salon aiki, ina niyyar bin bayansu nima aka riƙo hannuna, waigowa nai da sauri dan bansan waye da aikinba. Ya harareni damin alamar na dawo bayansa da idanu. Bani da zaɓin da ya wuce bin umarninsa, na dawo ta bayansa yana gaba, duk da gani a baya sai ya raba hankalinsa wajen kallon bayansa da gabansa, da haka muka shiga ciki muma kamar yanda oga hafiz da Aliyu, Jabeer sukayi, sauran kuma suna daga waje su da su sir Ahmad. Tafiya muke a sannu-sannu, babu wanda yay harbi dai a cikinmu kamar yanda har yanzu nidai banji motsi na alamar akwai mutum a gidanba.
       Cikin matuƙar zafin nama da ALLAH ya bama boss ya fisgoni tare da duƙar da ni saboda tahowar wuƙa da aka wulwulo a bazata wadda sam hankalina baya wajen, bakuma musan dga inda take ba, jikinsa na faɗa, shi kuma ya cafe wuƙar a hannunsa. ɗagowa nai ƙoƙarin yi idanuna suka sauka akan ƙafa dake ta wani ɗan lingu, komawa nai na duƙe har yanzun hannun hagguna na cikin na boss. Handkherchief ɗin aljihunsa nasa hannu na ɗauka, tsayawa yay yana kallona yaga mizanyi, na zare hannuna daga nasa na ƙarasa takawa inda ƙafar take cikin sanɗa, sai da naje gab sannan na miƙe sosai cikin zafin nama na ratayo handkherchief ɗin a wuyan wanda ke tsayen, kafin yay wani yunkuri na ɗaure masa wuya da ƙarfi yanda ko ƙara zaiyi babu maiji. Sukur-sukur ɗin da mutumin keyine na neman ƙwatar kai ya saka boss kallona, fuskarsa ɗauke da murmushin dana jima ban ganiba yaymin jinjina👍🏻. Nima sai nayi murmushin dan ya bani dariya a salon da yay da idanu da murmushin harma da jinjinar. Zagayawa yay ta ƴar ƙofar daya gani wajen wanda har yanzu nake ɗaure da wuyansa harya suma, yaymin nuni dana cire handky ɗin, ya kamasa ya kwantar ƙasa nima na zagaya.
        Jinjina ya sake min, cikin magana raɗa-raɗa yace, “Aikinki yayi ƙyau Babie”. Ɗan murmushi nai masa sannan muka shige ta ƙofar da muka gani cikin sanɗa. Saurin dakatawa yay yaɗan ja baya kaɗan muka koma jikin bango da ɗauke numfashi. Baƙin mutumin da sam babu imani tattare da shi yazo ya wuce ta kusa da mu sai dai bai kawo inda muke ba, har yay ɗan nisa sai kuma ya dawo baya yana waige-waige. Yana zuwa gab damu boss ya jawo masa riga ta baya, cikin wani irin zafin nama ya juyo sai kawai ya buga masa kansa yay baya,  oga Hafiz daya ƙaraso wajen ya taresa da saurin ɗora masa handkherchief ɗin hannunsa a hanci, da alama wani abun ya shaƙa masa, dan a take jikinsa ya saki. Ƙasa ya kwantar da shi yana ɗagowa, ya matso kusa damu sosai cikin magana raɗa yace, “Boss kuzo gasu tanan”. Binsa mukai cikin sanɗa ta hanyar daya biyo boss nata faman murza goshinsa da yayma mutum can gware alamar yana masa zafi wajen har yanzun.
      Tsaye muka tadda su Jabeer cikin matsanancin ruɗani, ni da boss muka ƙarasa jikin glass ɗin wajen da akayisa domin kwalliya kawai muka leƙa. A take tsigar jikina ta tashi, ƙirjina yay wata irin dokawa nai saurin yo baya ina ambaton ‘Wa'iyazubillah’. Boss kam tsaye yake kyam akan ƙafafunsa ya dasama wajen ido baya ko ƙyaftawa, sai dai jikinsa shi kansa tsuma yake, gashin duk sun mimmiƙe alamar shima tsigar jikinsa tashi take. Duk mai imani dolene ganin wannan shaiɗancin ya tada hankalinsa.
            Shirka ƙuru-ƙuru ga waɗanan shaiɗanun mutane da a zahiri suke ambaton kayinsu musulmai harsu shiga masallaci suyi salla cikin jam'i ma. Gaba ɗayansu zindir suke sai wani ƙyale ja da suka ɗaura a ƙugu ɗan guntu da iya al'aurarsu kawai ya rufe, sai wani ɗaure a kansu, durƙushe suke gaba ɗayansu sunyi Sujuda, tsakkiyarsu ƙaton kaskon tukunyar ƙasa ne da aka kunna wuta a ciki tana ci, sai babban shiɗaniyar tasu da kasancewarta tsirara yasa muka gane mace ce zaune bisa kujera kanta a duƙe itama riƙe da sandar da maybe itama ta tsafin nasu ce. Hawaye na gani suna sakkowa a kumatun boss, jin damshi a tawa fuskar ya tabbatar da nima hawayen nakeyi ashe. Ganin zasu miƙe boss yay saurin maidoni baya muka koma jikin bango, muna kallonsu ta haka. duk suka miƙe tsaye suna wani yare da su kaɗai sukasan mi suke faɗa, da fuskar Alhajin da naje gidansa na ɗakko tukunyar nan na fara cin karo, ganinsa da nai a hoto a gidansa yasa ananma na shaidashi, sai wanda ke a kusa da shi daya kasance shima mutum mai tarin faɗa aji a ƙasar nan, zuciyata wani irin luguden daka take kamar zata faso ƙirjina ta fito nakai dubana gana uku, shidai ban sanshiba kam, sai na huɗu shima ban sanshi ba, a na biyarne kam ƙafafuna suka nemi gaza ɗaukata, dan kuwa ba kowa bane face Uncle Nasir, bankai ga fita a ruɗanin dana shigaba na ganin Uncle Nasir idanuna suka sake sauka akan Dadyn Zuhrah, sai yayan Dadyn su Ummie dana taɓa gani a ranar bikin yayemu daga Jami'a. A haka na cigaba da binsu da kallo, wasu na riga da na sansu a tv, wasu kuma ɗai-ɗaiku a zahiri, wasu ko ban taɓa ganinsuba sai anan, nabi wanda ya juya mana baya riƙe da ƙoƙo da kallon sani, sai dai bana ganin fuskarsa, amma hakan bai hanani jin zuciyata raunana ba matuƙa akansa, so nake naga wanene amma ya juya baya.
     Durƙusawa yay yayi sujuda (Wa'iyazubillah😭) ga wannan la'ananniyar tsohuwar mata dake a kan kujera kamar basarakiya, sai kuma ya miƙe da ƙoƙon hannunsa yaje gabanta kansa a rissine ya miƙa ƙoƙon. Ƙyalƙyalewa tai da wata irin mummunar dariya da sam muryar tata bata kama data mata, sai kuma ta haɗe fuska tana faɗin, “Jariri!! Kai mutum ne mai daraja a wannan Bakandamiyar tamu, kaine farkon fara nasara ga dukkan matakai da tsare-tsarenmu da ƙa'idoji, kowane aikinka ka gudanar da shi babu kuskure ko sau ɗaya, sai a na ƙarshe da ya zama cikamakin ayyukanka ya gagareka?, ta dalilin yarinya ƙarama a cikamakin ayyukanka mun fuskanci asarori masu yawa. Hhhhhhhh Mun baka dama tun a watan jiya Jariri amma ka kasa damawa, munce ka nemo mana asalin yarinyar kace asalinta na farko daka kawo shine asalinta, sai dai mu bamu amince da hakanba. Lallai Jariri wannan yarinya bincikenmu ya gano mana akwai sirri mai nasaba da mafarkin mu na watan jiya dangane da ita. Jariri wannan itace dama ta ƙarshe da zamu baka akan wannan yarinya, Bakandamiyar mu na buƙatar jininta tunda budurcinta ya gagara, Jariri, idan ka gaza hakan daga nan zuwa kwanaki biyu zaka fuskanci mummunan hukunci daga Bakandamiya, zakuma mu saukeka daga shugabancin da kake kai. Sannan Jariri a yau ɗinnan ka tabbatar an sake ɗaura igiyar aure tsakanin gudalliyarka da yaron nan, inba hakaba bazamu yafe makaba a wannan karon dolene ka bamu jinin gudalliyarka........”
       “Tuba nake uwargijiyarmu, tuba nake uwa maba da mama, tuba nake mai share kukanmu, ina sake roƙon alfarmar a barni da gudalliyata dan itace zuciya ta, zan iya yarda na rasa abubuwa da yawa amma banda gudalliyata ya shugata, nayi rantsuwa da shugaban shaiɗanu a yau sai igiyar aure ta ƙullu tsakanin gudalliyata da halattaccen jinin Bakandamiya. Ina mai sake rantsuwa da a gobe saina kawo jinin wannan yarinya wa Bakandamiya shine zai zama abin kalacin mabiya Bakandamiya yake abar bautarmu”. (wa'iyazubillah😭🙏🏻)
           “Bakandamiya ta amsa maka, ta kuma baka damar ƙarshe ta dawowa da martabarka tare da dukkan muhimman abubuwan ƙungiya dake a hannun yarancan da jininsu ya halatta ga Bakandamiya. Kurakuranka zasu goge a dutsen rubuta laifuka bayan ka cika alƙawuranka da jinin babban ɗanka Jariri kamar yanda yake a rubuce a sharuɗan Bakandamiya”.
        “Naji na karɓa yake mai biya mana dukan buƙatunmu”.
      “Hhhhhhhhhhhhhhhhh!!!!!!!!!!!!!!” ta kece da wata mahaukaciyar dariyar da ta saka duk saida muka toshe kunnuwanmu saboda yanda dajin gaba ɗaya yake amsawa bama gidan kawai ba, tanayi tana tsiyaya masa wani abu mai kama da jini a cikin ƙoƙon hannunsa. Da baya baya ya baro gabanta yana wasu surkulle da shi kaɗai yasan abinda yake faɗi, sauran na amsa masa. 
        Mamaki, tsoro, al'ajab da ruɗani duk suka saukarmin lokaci guda ganin Dad a inda tunanina ko tsammani bai taɓa raya minba, saurin ɗaura hannuna nai na rufe bakinna jin kuka na neman kufce min. “D... Da...Daddy!!”. na faɗa cikin rawar murya dana jiki ina mai matsawa jikin boss dake tsaye abinsa yana kallonsu Dad ɗin shi da su Oga Hafiz.
        Cikin matsanancin furgici Dad ya saki ƙoƙon hannunsa da kai dubansa inda yaji muryar da bai zatoba ta ambaci sunansa. Ido huɗu sukai da bilkisu da jikinta ke wani irin matsanancin tsuma.
     A take Dad ya zazzaro idanu waje cikin tsananin firgici da ruɗani, jikinsa sai wata iriyar tsuma ya keyi domin ganin wadda bai taɓa zato ko tsammani ba. duk da glashi ya raba tsakaninsu, bai gaza gane bilkisu da Jawaad ba harma da jin furucinta raɗam a kunnuwansa, dan basu da wani shamaki wajen iya jiyo maganar juna duk da akwai hilashin daya rabasu.
      Bansan sanda wani ƙarfi da zafin nama yazomin cikin jini da jiki ba na bigi gilashin wajen da ƙafa jikina karkarwa saboda wata irin mummunar tsanar sa ce ta saukarmin lokaci guda da ƙyamarsa.
       Sauran abokan shaiɗancin nasa da tuni suma sun mike suna kallonmu a cikin matsanancin firgici na alamun bazata a fuskokinsu suka shiga ƙoƙarin motsawa cikin rawar jiki dan neman kariya.
        Kafin suyi wani yunƙuri su Jabeer sun afko suma tare da su Ummie dake jiran umarni a waje. Zagayesu akai da bindugu, hakan ya tabbatar musu basu da wata dama kuma saina miƙa wuya........
      “Ƙassaaa!!!!” Boss ya faɗa a iya ƙololuwar hasala jijiyoyin jikinsa na sake mimmiƙewa. Durƙushewa sukai bisa gwiwoyinsu suna aza hannayensu bisa kawunansu alamar yin surrender.
      Ban samu dawowa hayyacina ba daga kallon al'ajabi da ruɗanin da nakema Dad sai da Wani irin ihu shaiɗaniyar matarnan da tayi ya shiga dodon kunnena. miƙewa tsaye tai da buga sandar hannunta ƙasa, a take ɗakin ya fara turniƙewa da hayaƙi, sake bugawa tayi, sai jikinta ya fara canja launi harda su Dad ɗin suma. ta ɗaga zata buga na uku nai wani wawan tsale na dire a gabanta na riƙe sandar. Bazan iya fassara muku mawuyacin halin dana shiga ba a wannan lokacin, domin tsafi gaskiyar maishi ne, abinda kawai nake iya jiyowa harmutsewar wajen da ƙarar harbe-harbe ta waje alamar musayar wuta ta ɓarke tsakanin wasu a cikin  jami'anmu da suke a waje da yaransu masu tsaron gidan.......2

STORY CONTINUES BELOW

       Jawaad yay azamar nufar inda Bilkisu da matar nan ke riƙe da sandarnan, jikin bilkisu wani irin rawa yake da karkarwa ga zufa, amma dan taurin zuciya taƙi yarda ta sakar matar sandar.  ta gama fuskantar buga sandar nan da take sonyi zai iya zama kuskure ko halaka a garesu wajen baki ɗaya, kokuma wani siddabarun nasu zasuyi don son ƙuɓuta.
       Cikin tsawa Baba ƙaura ya dakatar da Jay da ya kai hannu domin bama bilkisu taimakon. “Karka taɓata, barta da ita!!”. Ya faɗa a kausashe yana nufosu, Hankalin Jay a tashe ya juyo yana kallon Baba ƙaura da girgiza kai, “Bazan iyaba bab....” kafin ya gama rufe baki baba ƙaura ya riƙo hannunsa, hakan yayi dai-dai da hankaɗa bilkisu baya da matar tayi, ta ɗaga sandar zata buga a ƙirjin bilkisun.

     Da sauri nai wani irin juyi sandar ta caki ƙasa, nasa ƙafa na taɗo tata ƙafar itama, baya tai, na bigi sandar da ƙafa itama tai sama na cafe cikin hannuna daga kwancen da nake.
         Wani irin mummunar amsa kuwwa ce ta karaɗe jejin lokaci guda, hakan ne ya saka ruɗani gasu Jay kowa ya shiga ƙoƙarin toshe kunnensa banda baba ƙaura da yasa ƙafa ya hankaɗa tukunyar kaskon wutar nan dake ci har yanzu ya kife a kujerar da matarnan take zaune ɗazun. Tamkar an tsaida ihun sai dajin yay cak lokaci guda kuma. Waige-waige su Jabeer suka fara dan su Dad gaba ɗaya basu a wajen sai matar kawai dake a kwance ƙasa inda bilkisu ta zubar da ita, saboda take mata ƙafa da Baba ƙaura yayi.
       Hankalinsu duk tashi yayi suka shiga leƙe-leƙen lungu da saƙo na cikin gidan hankulansu a tashe, sai dai abin mamaki babu ko ɗaya a cikinsu sai mutane da aka ringa zaƙulowa a cikin ɗakunan cikin hardasu Alhaji Babba da ke a cikin mawuyacin hali.
      Baba ƙaura ya cire jikkarsa ta fatar damisa ya ajiye ƙasa, da hannunsa ɗaya ya buɗeta ya ɗakko wani wani irin kibiya ta ƙarfe sai sheƙi take da walwali ya shaƙo wuyan matarnan ya miƙar da ita tsaye, watsa mata wani mugun kallo yay yana huci, a take ta ƙwalla kururuwa jikinta na rawa. “Barde kaga zan dawo dasu kaimin rai karka kassarani mai babban suna, na tuba nabika”. “Bana buƙatar tubanki shaiɗaniya, ai dama na faɗa miki nine ajalinki kokin manta na tuna mikii!!!!”. “Cikin rawar jiki take girgiza masa kanta, ya fincike manyan layun dake a wuyanta ya watsar ƙasa, a take ta zube a wajen tana fashewa da kuka. Cikin ƙwarewa da sararafa hannunsa guda ɗaya da dungulmin ɗayan ya ɗana kibiyar nan ta ƙarfe a kanta. Da sauri ta buga ƙasa da hannunta har sau uku sai gasu Dad dake can gefe rufe da wani jan ƙyalle sun bayyana.
       ‘Innalillahi wa'ina ilaihirraji'un yau muna ganin tsantsar tashin hankali da shaiɗanci, da a labaran tatsuniyoyi da fina-finai kawai muke jinsu. Koda ake cewa akwai matsafa a duniya da yankunanmu ban taɓa yardaba, a nawa zaton labarine kawai na ƴan shafawa labari shuni, ashe gaskene, ashe zan gani da idanuna, ashema harda jinina a cikinsu wanda na ɗauka uwa uba ma. Hawaye nake masu zafi da ƙunar zuciya, kaina juyamin yake gaba ɗaya dama duniyar kanta, tun ina fahimtar abinda ke faruwa har jina da ganina suka ɓace ɓat daga duniyar mutane, daga haka ban sake sanin abinda ke faruwaba kuma.

           Cikin zafin nama Ada ta tare Bilkisu da juwa ta ɗiba, a tsorace take kiran sunanta tana girgizata ganin batama numfashi gaba ɗaya. Aliyu ne yayo kansu yana tambayar lafiya, dan Jay tunda aka fiddo su Alhaji Babba yabar nan zuwa garesu.
       Ba Bilkisu ce kaɗai ta sumaba, Zuhrah tun cin karo da idanunta sukai da Abbanta ta sume, hakama Ummie ganin yayan mahaifinta tuni ta suma, sai cikin mutanen da aka iske a wajen da yawansu basa cikin hayyacinsu harda su Alhaji babba da basu wuci awanni da kawosu wajenba, dama ga tsufa kuma. Wasu daga cikin yaran su Dad an harbesu, harma da waɗanda aka kashe.
        Jejin ya hargitse sosai, bakajin komai sai ƙarar helicopters na sojoji dake shigowa cikin jejin saboda wayoyi da su Sir Ahmad suketa faman yi da amsawa. Dandanan sojoji da masu bada taimakon gaggawa harma da ƴan jarida dake cikin jami'an tsaron da su Qaseem duk suma suka iso. Cikin ƙanƙanin lokaci jejin ya sake harmutsewa da motsin mutane dana ababen hawa.
       Su Dad na durƙushe cikin ƙasƙanci daga su sai jajayen ƙyallayen kawunansu dana ƙugu da sukaɗan rufe jikinsu kaɗan, sai da jami'an tsaron da suka iso suka sauka sannan bisa alfarmar da General ya buƙata aka basu mayafai suka rufa, amma da Jawaad yace a haka za a fita jejin dasu har cikin gari domin sauran al'umma su gansu.
STORY CONTINUES BELOW

          Dajin fa kamar wasa sai gashi ya tara jama'a masu yawa kama daga manya-manyan jami'an tsaro, zuwa shugabannin ƴan siyasa da ƴan jaridu, dan babu abinda ke kai kawo sai helicopters da ƙananun jirage na yaƙi. Mutanen dake a cikin gari kansu sun fahimci ƙasar babu lafiya yau, dan kai kawon da helicopters keyi kawai ya isa amsa. yayinda kuma ƴan Jaridu suka fara nuna komai ta gidajen tv'n su live. Duk ta yanda manyan ƙasar sukaso kar hakan ta kasance basuci nasaraba, dan kuwa ƴan jarida sunada ƙarfin iko da ƴancinsu suma, balle kuma akan wannan al'amari mai tsananin saka ruɗani da al'ajabi ga duk mai sauraro bama kallo kawai ba.
       An shiga kwasar su bilkisu da suke a halin suma aka fara barin jejin dasu domin miƙasu ga likitoci su samu taimakon gaggawa, sai waɗanda suka sami harbi da gawawwaki da mutanen da aka samu an kawo harma da gawarwakin mutane da aka iske a wani ɗaki cikin freezer irin wadda ake saka gawarwaki a asibiti, dan gidan suna amfani da babban janareto dake basu wuta 24hours, duk wani abun more rayuwa kuma akwaisa a gidan hatta da ruwa.
        Su Jay ne keta kai kawo haɗa rahotanni har aka kammala kwashe mutane da gawarwaki da wasu kayan sirrika da ke a cikin gidan tas, basu baro jejinba sai bayan sallar la'asar, zuwa lokacin labari ya gama karaɗe lungu da saƙo na ƙasar harma da ƙasashen ƙetare, to abinka da manyan mutane da ake ganin mutuncinsu acikin manyan riguna da kuɗi suka saya musu.
     
__________________________

           
              Su Ummah basu farga da rashin su Jawaad a gidanba sai da su Nabeelah sukai kusan mintuna talatin da baro kitchen. Cikin ƙaguwa Umm-Anum ta kalli ƙannen nata cikin hausarta da bata fita da ƙyau yanzun tana faɗin, “Mariya wai ina ɗanku ya shige da matarsa ne? Nifa na ƙagu naga ubana, gara yazo ya kaimu ala bashshi sai su ɗakko su Abbun Anuwar ɗin daga can idan sun iso”. Murmushi Ummah babba tayi, ta kalli Nabeelah da suke kallon hotuna a wayarta da Anum. “K Nabeelah kiramin yayanku”. Cikin ƴar ruɗewa Nabeelah tace, “N...n.....na'am Ummah mi kika ce?”. “Ƙaniyarki nace dan gidanku” ta faɗa tana mata daƙƙuwa. “Kai Ummah ALLAH nifa banji bane ba”. “ALLAH ya shiryeki to, canai kije ki kiramin yayanku”. Jimmm tai na tunanin abinda zata faɗa, sai kuma dai ta miƙe ta fita, a babban falo ta tsaya tanata kaikawo, tarasa wacce amsa zata koma ta bama Ummah ne, tsoro faɗar gaskiya take kodan gargaɗin da Jay yay mata akan hakan”. Anuwar da ya shigo falon ya lallaɓo ta bayanta yaja jelar gashinta. A firgice ta juya zata ƙwalla ƙara na tsorata yay azamar rufe mata baki yana kallon sashen Bilkisu cikin ɗan zaro idanu. Sai da ya tabbatar ta nutsu sannan ya saketa yana sauke ajiyar zuciya da murmushi kan fuskarsa, “beauty ke matsoraciya ce gaskiya”. Cike da shagwaɓar data saba ta tura masa baki, “Yoni tsoro naji ALLAH, nazata Yayanmu ne”. Murmushi Anuwar yayi dake sake bayyana kamaninsa da Jawaad sosai yana ƙara narkar da idanunsa a kanta, “Kiyi haƙuri tam, halan laifi kikaima Yayan kike tsoron ku haɗu?”. “A'a ba laifi namasa ba, sai dai Ummah nason tajamin nayi masa yanzu”. ta ɗan wawwaiga kamar mai tsoron Jay ɗin ya ganta sannan ta juyo ga Anuwar da shima ke tayata waigen, ƙasa tai da murya cikin raɗa ta faɗa masa gargaɗin Jawaad. Sosai abin yaso bashi dariya, shifa tun a bikin su Jay ya fahimci Nabeelah akwai wautan autanci tattare da ita, “To ai kin kuma faɗamin yanzu, kenan bakiji gargaɗin nashi ba?”. Idanu ta waro waje sosai tana ɗaura hannunta biyu aka zata fashe da kuka”. “Kinga wasa nake miki” Anuwar ya faɗa da sauri ganin zata saka masa kuka. “To faɗamin mi zan cema su Ummah?”. Kafin ya bata amsa Aunty Batool ta shigo, ganin ta wucesu tana kuka sukai saurin bin bayanta.

      Hankalin su Umm-Anum a matuƙar tashe suka tari Batool, kowa tambaya yake jeho mata akan miya sameta?. Yanda duk suka rikice sai suka bata matuƙar tausayi, bata ɓoye musu komaiba ta labarta musu halin da ake ciki har zuwan su Jawaad da tafiyarsu office akan case ɗin.
        Faɗuwar Umm-Anum kawai sukaji batare da kowa yaga sanda tai yunƙurin faɗuwarba, hankalinsu a take ya sake tashi, basu wani tsaya maida yanda akayiba suka kwasheta zuwa asibiti, dole Batool ce tai driving ɗin, dan Anuwar baisan hanyaba.
      Anum da Nabeelah nata kuka su Ummah na rarrashinsu. Saboda ta samu kulawar gaggawa sai Batool ta nufi asibitin Dr Tayyeb da su, ai ko babu ɓata lokaci aka karɓesu da bama Umm-Anum taimako akan lokaci..........

__________________________

                A ɓangaren su Mom kuwa sun gama yanke hukuncin sake ƙulla auren Jawaad da Shahudah batare da neman yardarsa ba, dan haka babu wani ɓata lokaci mama Atika ta saka aka tattara mata su Uncle Sulaiman, sai dai kuma babu Uncle Nasir, acewar matarsa yayi tafiya tun daren jiya.
        Mom ta kira wayar Dad shima a kashe, hakan bai dameta ba, dan tasan shima burinsa kenan ai, dan haka sukace Uncle Uwaisu ya wakilci Dad ɗin, Uncle Sulaiman kuma Jawaad.
        Duk yanda Uncle Sulaiman yaso fahimtar dasu kuskuren yin hakan sam Mama Atika taƙi fahimta, saima rufesa da tayi da masifa tamkar zata cinyesa ɗanye. Haƙuri ya bata, a take aka tattara samarin gidan da maƙwafta kasancewar weekend ne aka sake ƙulla auren Jawaad Abdul-Aziz yusif da Sabeera Aliyu Fillo akan sadaki naira dubu ɗari da Uncle Sulaiman ya biya.
         Zo kuga farin ciki wajen Shahudah amarya dasu Mom da Mama Atika, dan a wannan karon sun ɗauki alwashin babu abinda zai dakatar dasu daga cika burinsu akan abinda suka jima sunama ƙwaɗayi. Ana cikin wannan murnarne ɗiyar Uncle Sulaiman tazo sashen mama Atika da gudu tana kuka da faɗa musu cewar suzo mama Badiyya na wani abu mara daɗin gani.
     Gaba ɗayansu suka kwasa Uncle Sulaiman har gudu yake da tuntuɓe dan mahaifiya tafi gaban wasa. Sosai hankalinsu ya tashi, murnar ɗaurin auren da sukeyi ta gushe tabar fuskokinsu baki ɗaya. Cikin gaggawa aka ɗauki Mama Badiyya zuwa asibiti, kasancewar kowa yasan matsalolin asibiticinmu na gwamnati sai Mom ta bada shawarar a nufi asibitin Dr Tayyeb zatafi samun kulawar gaggawa. Da wannan shawarar sukai amfani suka nufi can, sauranma suka shiga motoci suka dafa musu baya.
        Da gaggawa aka amsheta, itama sauran likitoci suka rufu kanta dan Dr Tayyeb yana wajen Umm-Anum a lokacin, sai da yaga numfashinta ya dawo jikinta, ma'ana ta farfaɗo sannan ya saka mata ruwa ya fito dan amsa kiran da Mom keta masa a waya. Sai a lokacinne shi yakejin cewar mama Badiyya suka kawo, bai tsaya bama su Ummah gamsashshiyar amsar da suke buƙatar jiba ya basu haƙuri akan su jirashi ya nufi ɗakin da aka kai Mama Badiyya..............✍21

Hummmm koya zata kaya a asibiti kuma tsakanin waɗan nan familys guda biyu? Ga tashin hankalin dake faruwa daga su Jawaad wanda duk ya shafi waɗanan ahali, kumuje zuwa dan jin yanda zata kaya masoya, dan aski yazo gaban goshi insha ALLAHU, kuma da gaske bily ta DAWO GARE KU🤗😍😍😘.6

ALLAH Ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻15

_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR... 🙋🏿‍♀️🙋🏿‍♀️INA KUKE NE? 🔊🔊KU MARMATSO, DOMIN ZAMAN JIRA YA KARE, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKA HADA HAZAKA DA KAIFIN TUNANI SUN SAKE ZAGE DAMTSE SUN ZO MU DA WASU SABBIN SALON RUBUTUN SU, WADANDA ZASUWA’AZANTAR, SU NISHADANTAR, KANA SY DILMIYA KU A KOGIN KAUNA, BASU TSAYA ANAN BA SALON RUBUTUN SU YA SAKE ZUWA DA SABBIN TSARE TSARE NA DARUSSA DABAN DABAN, DA KUMA HANYOYIN GYARIN JIKI DA WAJE._

_KADA KU MANTA MARUBUTAN ZAFAFAN DAI SUNE WADANDA SUKA YO MUKU HAR KASHI BIYU A SHEKARAR 2020 DATA GABATA,: WUTSIYAR RAKUMI DA GUDU DA WAIWAYE NA BILYN ABDULL. 2-DAURIN BOYE DA ALKAWARIN ALLAH NA SAFIYYAH HUGUMA.3-BURI DAYA DA QAUNAR MU NA MAMUH GEE-4- SAUYIN KADDARA DA DAURIN GORO NA HAFSAT RANO. SAI 5-KAI MIN HALACCI DA IGIYAR ZATO NA MISS XOXO.._

_A WANNAN SABUWAR SHEKARAR TA 2021 MA HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE DAWOWA DA WASU SABBIN DA’DADAN LITTATTAFAN NASU:_

                       _1_

_* SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA DA ABADAN TAZO MUKU DA SABON LITTAFIN TA MAI SUNA: *(SIRADIN RAYUWA)💜*_

                      _2_

_*HAFSAT RANO* MARUBUCIYAR  GUGUWAR SO DA RUHI DAYA, TA ZO DA SALON NATA LITTAFIN MAI SUNA: *(ABINDA  KE CIKIN ZUCIYA..*)💘_+

                        _3_

_* MAMUH GEE* MARUBUCIYAR TARAYYAH DA EZNAH, TAZO DA SABON ZUWA MAI SUNA: *(MIN QALB)❤️.*_

                           _4_

_*MISS XOXO* MARUBUCIYAR NAUFAL DA SAIFUL-ISLAM, TA YUNKURO DA WANI MAI SUNA: *(KIBIYAR AJALI)*💜_

                    _5_

_SAI MARUBUCIYA *BILLYN ABDUL* WADDA TAYO MUKU KWAI CIKIN KAYA, DA CIKI DA GASKIYA TA YINKURO DA WANI MAI TAKEN: *(YANKAN BAYA)*💝_

_RIGIJI GABJI DUKKAN WADANNAN LAGWADAR DADADAN LITTAFAN BIYAR ZASU ZO MUKU NE INSHA ALLAHU AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA;_

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Page 59

..................Motoci na alfarma aka aika daga masarauta domin tarbo su Abbu a airport kamar yanda aka aika tarbar su Umm-Anum, sai dai su masarauta aka wuce dasu, inda acan ɗinma suka sami tarba ta musamman da mutuntawa ga mai martaba sarki Sameer Saifudden da iyalansa, harma da ƴan majalissar sarki baki ɗaya. A yanda masarautar take yau ko ba'a faɗa makaba kasan anyi manyan baƙi a cikinta, waɗanda suka isa suka bunƙasa. An baje musu abinci na alfarma na ƙasarmu masu daɗi da daɗaɗa zuciya.

STORY CONTINUES BELOW

         Tun kafin tafiya ɗakko su Abbu Gimbiya Munaya tasa Amaturrahman ta nema Number Jawaad, amma taƙi shiga sam, ta kira ta Bilkisu kuma ba'a ɗagaba. Hakan ya bata mamaki matuƙa, dan tasan dai ai su Jay ɗin sunsan da zuwansu Abbu, a yanda suka tsara al'amarin kuma daga tarbo su Abbu a airport zasu wuce masarauta ne harsu Umm-Anum ɗin, bayan su Abbu sunci abinci sun huta sai su ɗunguma baki ɗayansu gidan Alhaji Babba, daga can idan dare bai rufaba zasu ƙarasa family house ɗin su Jay. To amma gashi har lokaci ya shige babu Jawaad ɗin babu dalilinsa.
        
          Basu ji halin da ƙasar take ciki ba sai sai kusan isowar su Abbu da awa ɗaya da rabi sannan takawa ya samu kiran waya daga gwamna akan ya buɗe television yaga tashin hankalin da a yanzu shima aka faɗa masa game da manyan mutane da ake ganin mutuncinsu a ƙasar, babban abinda ya razana gwamna kuwa harda wasu a abokansa masu manyan muƙamai kuma a gwamnatin tasa.
             Al'ajabi daya kume sarki lokacin daya buɗe tv kasa ƙwaƙwaran motsi yayi, dan shima ɗin ai akwai waɗanda suke matuƙar gaisawar zuminci a cikinsu sosai..........

_________________
ASIBITI
____________

                  Hankalin su Mom a tashe suna jiran fitowar Dr Tayyeb daga ɗakin da aka saka Mama Badiyya kira ya shigo wayarta daga mai aikinsu. Kamar bazata ɗagaba sai kuma mita tuna oho mata ta ɗaga wayar.
         A matuƙar ruɗe Talatuwa dake kuka ta zayyane mata abinda ya faru game da zuwan wasu mutane da sukace su ƴan sandane har gida suka tafi da kuku da maigadi.
    A tsawace Mom tace, “What!! K bansan shirme da hauka kinji, ubanmi suda suke gida kullum zasu aikatama ƴan sanda harsuzo gida su kamasu?”. cikin kuka talatuwa tace, “Wlhy hajiya da gaske nakeyi, yawwa gama wannan da kikacemin shine babban yaronku nan yazo gidan”. Da mamaki Mom tace, “Waye? Kina nufin Qaseem?”.
       “E...e...eh shi hajiya, wanda hotonsa ke a falo sanye da baƙaƙen kaya tare da Alhaji”. Jikin Momy har rawa yake wajen ambaton, “Da gaske Qaseem, yaushe suka barshi ya fito to? Kinga bashi wayar muyi magana nima gani nan zuwa gidan yanzun nan”. “T..t...to hajiya, bara nakai masa”. Talatuwa ta faɗa tana ɗan gudu wajen bin bayan Qaseem dako kallon inda take baiyiba ya haye sama ɗakin Dad direct. Yana kama handle ɗin ƙofar tana ƙarasawa garesa, da rawar jikin tsoro ta miƙa masa wayar tana faɗin, “Alhaji ƙarami sannu da zuwa, gashi inji hajiya zakuyi magana”. Wani mummunan kallo daya kaɗa hanjin cikinta ya zuba mata, cikin daka tsawa yace, “Ɓacemin da gani kona halakaki wlhy”. Zabura Talatuwa tayi da gudu tabar saman, yayinda Momy kuma taji komai ta cikin wayar, ita kanta tsawar Qaseem sai da ta sakata cire wayar daga kunnenta ma.

        Bata iya cewa sauran ƴan uwanta komaiba ta nufi hanyar fita daga asibitin da hanzari, duk faman tambayarta lafiya? da sukeyi bata juyoba balle ta amsa musu harta fice. Da kanta taja motar tabar asibitin zuwa gida.
       Akan hanyar momy na nufar gida ta fahimci garin babu lafiya, dan kuwa babu abinda take gamo da shi a tituna sai matsanancin holdup. Mafi yawancin inda traffic light suke an haɗa cinkoso a wajen sosai, ga jirage masu saukar angulu da keta yawo na kaikawo a sararin samaniya, wasu ma daf da mutane suke. Ratse ta ringayi ta cikin anguwanni tamkar yanda wasu motocin taga sunayi. Da ƙyar ta samu kanta a anguwarsu, tai fakin motar a ƙofar gida batare data kasheba saboda wani bahagon ruɗani da ta sake karo da shi kuma, ƙofar gate ɗinsu a buɗe take, ga jami'an tsaro sun zagaye gidan, cikin sake shiga ruɗani ta afka cikin gidan da sassarfa tamkar zaga kifa, ananma wasu jami'an tsaron ta sake cin karo dasu a cikin gidan, talatuwa na durƙushe gefe tana kuka ita da mai bayin fulawa.
         “Kai lafiya?”. Mom ta faɗa hajijiya na neman ƙwasarta zuwa ƙasa. Wani cikin ƴan sandanne ya bata amsa da faɗin, “Hajjaju wannan gidan yana a hannun hukumane a yanzun, akwai bincike da za'azo ayi a cikinsa daga yanzu zuwa kowanne irin lokaci”. Cikin tsawa da hucin ɓacin rai, “Mom tace kuɗin ubanwa muka sata to? Muba ƴan siyasaba ba ma'aikatan gwamnati ba, amma za'a turo mana jami'an tsaron binciken almun dahana da dukiyar ƙasa?”.
        “A'a hajiya, mu ba jami'an tsaron almun dahana bane ba, jami'an tsarone na farin kaya, da kuma amincewar Sir Qaseem Ali muke anan  bisa Umarnin Sir Jawaad Abdul-aziz Yusuf”. “Qaseem! Da Jawaad kuma?”. “Hakane hajjaju” ya sake bata amsa kansa tsaye.
       Wata ashariya da momy ta manta tama iyata ta kwaso ta dire bisa ƙasa tanayin wurgi da jikkar hannunta, ta shaƙo wuyan police ɗin tana huci, a take sauran suka zagayeta da bindiga. Murmushi Munkaila yayi yana ɗaga musu hannu alamar su barta, ya kalleta fuska babu wasa zaiyi magana ta tare numfashinsa. “Kai shashasha kasan mi kake faɗa kuwa? Ina Jawaad da Qaseem ɗin suke?”. Ɗan murmushi yay mata yana zame hannunta a wuyansa ya gyara rigarsa, “Sir Qaseem yanzu ya fita, Sir Jawaad kam yana filin daga”. Sake rikicewa kanta ya nemayi, batare data nutsu wajen fahimtar inda batunsa ya dosaba ta fice a gidan tamkar wata mahaukaciya.
      Mota ta sake shiga tabar anguwar batare da tamasan kalar tunanin daya dace ace tayiba, kanta tsaye station ɗin su Jawaad ta nufa, sai dai ɗan karen holdup ɗin da take fuskanta a yanzun ya zarece na ɗazu data riska tsakanin asibiti zuwa gida............

STORY CONTINUES BELOW

___________________
        JAY-QAS
________________

                Koda tawagar su Jawaad suka iso cikin gari cike suka iske station ɗinsu da manyansu da ƴan jaridu, abu na farko da suka farayi shine gabatar da sallolin azhar data riskesu a can da kuma la'asar da a yanzu aketa yinta.
     Suna idar da sallar ƴan Jarida sukai musu caa aka, Jay dai bai saurari kowaba daga shi har Sir Ahmad da sauran manyansu.
        Cikin son ƙure mutane irin na ƴan jarida ɗaya a cikinsu ya juya ga masu ɗaukar rahoton gidan tvn su yana magana a harzuƙe. “To jama'a kamar yanda kukai hasashe dai hakanne ta kasance, dan kuwa munga alamar rufa-rufar da muka saba gani ga jami'an tsaronmu idan laifi ya shafi manyan ƙasa yau gashi ta tabbata, to ta yayama zasu yarda su buɗe komai wa duniya bayan daga kawunansu sai surukansu da abokan iyayensu dama iyayen nasu. Haka za'a kifemu bayan kwana biyu muji shiru, bayan kuma tarin gawarwaki da mutanen dake a cikin mawuyacin hali da aka amso a hannun waɗan nan miyagu ƙuru-ƙuru duk mun gansu. ALLAH dai ya ƙyauta, dama ba sabon abu bane irin wannan a ƙasarmu ta gado. idan kaga ana yayata mai laifi da cecekuce da tada jijiyar wuya ga jami'an tsaro to talakane ya aikatashi, amma idan su masu faɗa ajinne suka aikata sai a rufe komai ruf da sunan kare mutuncinsu ko maganar shiga kotunsu bakaji balle musan an yanke musu hukunci. To kenan mu talakawa bamu da suturar mutunci ne? shiyyasa ake ƙwance mana zannuwa a kasuwa?”.
        A take wajen ya ɗauki ƙananun maganganun sauran ƴan jaridar, kowa na ƙoƙarin ɗaukar zancen ɗan jaridar nan ya zama sinadarin zazzage tasa maganar dake cin ransa.
         Ganin abun na neman kawo hatsaniya har wasu cikin ƴan jaridar na fassara abun da rufa-rufa Jay ya dawo garesu rai a ɓace. Ɗan jaridar da yay maganar Jawaad ya kafe da kallo idanunsa na sake rinewa zuwa jajur, duk da azabar ciwo da kansa ke masa haka bai hana maida masa murtaniba cikin tsananin ɗacin murya, “Kar kai azarɓaɓi akan garin daka shigo cikinsa baƙo. Karka yankema littafi hukunci abisa bangonsa, duk sharhin da zakayi batare daka buɗe rubutun cikinsaba kuskurene kawai da son zuciya zai biyo baya. Alokacin da jami'in tsaro yake filin daga shi kaɗai yasan wane irin kwazazzabo da ƙalubalene rayuwarsa ke fuskanta, da ace yanda ku ƴan media kuka iya yayata al'amari haka kuke bama jami'an tsaro gudunmawa wajen kare fituntunun da ƙasa ke a ciki da kowama ya zauna lafiya a duniya. Idan ƙoƙarinmu na aiki da jajircewa wajen tsayawa mu tantance ke hantarar ra'ayinka akanmu, to kasani sauyi ba namu bane, kai da irinkane zaku sauya. Duk lokacin da mukejin matsayinmu ya girmama a duniya wajen jama'ar cikinta, tomu samu gazawa akan ƙoƙarinmu ta ɓangaren aikinmu ko kasantuwar ɗaukakar tamu. Daga hakanne zamuga muɗin ba komai bane wajen waɗan nan al'ummar dake ɗaga darajojinmu da girmanmu a bakunansu da muryoyinsu. Daka zama mai ƙoƙarin ruruta wutar da bakasan tushentaba, mizai hana ka ajiye aikinka ka koma gidanka ka ɗaura zani kawai, koba komai ƴaƴanka zasu samu magirkan abinci biyu, shashasha kawai”.
      Tsitt wajen. yayi tamkar ruwa yaci kowa, sai su Sir Ahmad kawai dake murmushi da bin Jay ɗin da kallo tamkar yanda suma ƴan jaridar da sauran jami'an suka rakashi da idanu harya shige.
      Jabeer ne ya matsa garesu cikin ɓacin rai shima, ya sake kallon ɗan jaridar nan da maganar Jawaad ta sakashi duƙar dakai dan yaji kunya sosai da ganin kuskurensa akan kalamansa. “Aikin jarida ba neman kuɗi bane ko shiga rigar siyasa, aikine mai daraja abin girmamawa ga maiyinsa, ita daraja da gaskiya ake samota bada son a sani ba, kai da kayi waɗan nan kalaman kayisune bisa raɗin kanka kawai ko an sakaka badan aikin jarida ya baka damar yin hakanba, kai tsaye kake anan domin neman abinci wa iyalanka dake gida cikin kwanciyar hankali, shiko wannan da kakema gugar zanar cewar akwai kawunsa da surukinsa shiyasa ake rufa-rufa, tare da nasa iyalan ya shiga cikin jejin da baida tabbacin fitowa a raye. Atunaninka akwai sadaukarwar data kai wannan girma kuwa? Ku daina zubarma aikin jarida mutunci dan aikine na masu mutunci a kowanne lungu da saƙo na duniya, sai dai kaicon irinku masu girmama fitina da riritata tai faɗin da zata buwayi wanda kuke tunanin kun tozartar harta dawo ga iyalanku kuma cikin aikin jarida, baka dace da wannan aikinba sam, ya kamata ka ajiyesa ka koma ka saka rigar siyasa, inaga kalamanka da nuna iyawarka zatafi dacewa dacan ɗin”. Yay maganar da watsa musu harara shima yabar wajen.
      Sosai jikin duk ƴan jaridar ya sake yin sanyi, masu ƙara gishiri da magi akan batun sai suka koma gyara harsunansu suna miƙa rahoto mai inganci dan an tunatar dasu abinda suka manta domin kawai neman ɗaukaka da birgewa.1

STORY CONTINUES BELOW

          Duk jarumtar da Qaseem ke arowa yana ƙara ƙarfafa kansa da ita sai hakan ya nema gagara, kalaman Jawaad dana ɗan jaridar nan sun bala'in taɓa ruhinsa da zuciya, yabi bayan Jay hawaye na zurara saman fuskarsa batare da yayi tunanin gogewaba. A jikin ƙarfen lifter Qaseem ya iske Jawaad ya kife kansa dake tsananin sara masa, bai iya cewa dashi komaiba ya wuce zuwa office.
           Ƙamshin turaren Qaseem ɗinne ya fargar da Jay zuwansa, ya ɗago a hankali yabi bayan Qaseem dake kan lifter ɗin da kallo harya gama hayewa, harya maida kansa zai sake duƙarwa sai kuma ya zabura cikin faɗuwar gaba, haka kawai zuciyarsa ta ɗarsa masa wani abu dangane da Qaseem, yariga yasan yanda yake da zafin zuciya. Cikin zafin nama ya haye lift... ɗin shima, ganima yake bata sauri gaba ɗaya, sai faman kallon agogo yake dukda kuwa a mintuna biyu kacal take kaisu.
      Da gudu ya ƙarasa office ɗin Qaseem ɗin, yana taɓa ƙofar ya jita a rufe, hasashensa ya zama gaskiya kenan?, Qaseem ya shiga office domin aikata duk abinda ransa ya raya masa, baya yay ya daki ƙofar office ɗin da masifar ƙarfi, sai dai bata buɗeba amma ta girgiza. “Innalillahi...” ya faɗa yana bubbuga ƙofar da ƙwala kiran sunan Qaseem, sai dai ko sau ɗaya Qaseem ɗin bai amsa masaba, rikicewa Jawaad ya sakeyi, yabar wajen da gudu zuwa office ɗinsa dan ya tuna akwai key ɗin office ɗin Qaseem ɗin a wajensa wanda Sir Ahmad ya bashi ranar domin ɗaukar wasu files a ciki, da ƙyar ya iya gano keys ɗin saboda a rikice yake, yana ɗauka ya dawo da gudu.

      Jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar Qaseem daya samo bullets da ƙyar cikin office ɗin nasa ya ƙara azama wajen ɗurasu cikin bindigar yana kuka shaɓe-shaɓe  da hawaye. yana gama zuba bullets ɗin cikin bindigar  Jay na buɗe ƙofar ya shigo da gudu, saurin ɗaurawa a kansa yay da rawar jiki yana ƙoƙarin saka ɗan yatsansa saman kunamar bindigar jikinsa sai tsuma yake.
     Da matsanancin ƙaraji Jay yace, “Qaseem!!! Karkayiii!!!!!” yay maganar cikin wani irin doka mahaukacin tsalle ya dire gaban Qaseem ɗin da wawurar hannunsa  yay sama da shi harsashin da Qaseem ɗin ya harba ya samu p.o.p ɗin dake office ɗin. Yanda Jay ya riƙe haka Qaseem ma yaƙi saki, sai da suka ƙarar da harsasan duk biyar sannan Jawaad ya ɗauke fuskar Qaseem da mahaukacin mari cikin gushewar hankali.
       Wannan harbi shine ya maido hankalin su Sir Ahmad wajen, yayinda ƴan jarida da sauran mutane suka fara gudu sun zata hari aka kawo.
                “Baka da hankali ne!!!? Wace riba kake tunanin samu a kashe kanka da zakayi Qaseem? Kaifa musulmine! Taya zaka bari tunanin aƙidar yahudu da nasara har takai mizanin tasirin zama a zuciyarka irin haka? kai ƙoƙarin salwantar da rayuwarka da kanka!!! Kasan kuwa hukuncin wanda ya kashe kansa a addinin musulunci?. To sunansa KAFURI!!! kuma wlhy WUTACE zata zama sakamakonsa!!!”. Jay ya faɗa yana huci da nuna Qaseem ɗin da hannu.
        A zabure Qaseem ya hankaɗa Jawaad yay baya yana faɗin, “Bani da hankali Jawaad, wlhy da gaske na haukace, tabbas na haukace, minene amfanina idan na zauna a raye a wannan duniyar da babu komai a cikinta sai ruɗani?!!” ya finciko rigar Jay jikinsa na rawa, hawaye na zuba masa babu ƙaƙƙautawa, “Idan ka hanani kashe kaina mi kakeso nayi Jawaad? Wacce irin amsace dani da zan bama duniya akan mahaifin da nake kallo babu kamarsa a da? Matsayin suruki kawai ya taɓa amsawa a gareka amma akai maka gugar zana da halayyarsa yanzun, to inaga ni da yake mahaifina!!, da wane idanun kakeson na sake kallonsa Jawaad?! Dan ALLAH na roƙeka ka barni na kashe kaina na huta!!”....  Ya ƙare maganar da wani irin kuka mai tsuma zuciya da ya saka jijiyoyin kan Jawaad sake mimmiƙewa shima hawayen na taruwar masa a idanu. Jawo Qaseem yay ya rungume a jikinsa suka fashe da kuka a tare.....😭5

(Kai jama'a, wlhy zuminci ya wuce gaban wasa komai lalacewarsa😭😭)4

       
            Dalilin go-slow da Mom ta riska a hanya yasa ta iso station ɗin a wahale cikin dogon jinkiri, da kutsa-kutsar shiga cikin ƴan jarida ta samu shiga ciki da ƙyar, inda shigar tata tai dai-dai da harbin harsasai biyar da Qaseem da Jawaad sukayi. Da wannan ruɗanin da jama'a suka shiga ta samu damar bin ayarin su Sir Ahmad zuwa office ɗin Qaseem dan ta sani, bata fahimci can su Sir Ahmad ɗin ke yunƙurin zuwaba saida taga sun isa tare da su inda itama ta dosa.
     Itace farkon shiga office ɗin, sai tai tsaye turus tana kallon Qaseem da Jawaad dake rungume da juna da dauraren kalamansu.
         “Qaseem hakan ba mafita bane ɓata ne, ba'a samun hutu da saɓon UBANGIJI bisa ganganci, ka daina irin wannan tunanin”. “Dolene nayi Jawaad, ƙo Bilkisu da tazo a ƙarshen ƙaddarar kunyarta nakeji balle kai da sauran mutane, nayi nadamar kasancewata jininsa wlhy Jawaad”.

STORY CONTINUES BELOW

        Da sauri Momy tazo ta fincike kafaɗar Qaseem ta matsar da shi baya daga jikin Jawaad, batare da ta tsaya ta gama fahimtar matsalarba, jin sunan bilkisu kawai da tai a bakin Qaseem ya sakata harzuƙa da fassara matsalar akan bilkisun ne komai ke faruwa ma kawai, hawaye na zirar a kumatunta tace, “Qaseem wai mi kakeyi hakane? akan tsintacciyar mage, kake wannan hanƙoron da tura mana ƴan sanda gida saboda cin zarafinmu? Akan butulu da ya wulaƙanta ƴar uwarka har kake iƙirarin mahaifinka ya shirya tarwatsaka? TSINTACCIYAR MAGE! YARINYAR DA MUKA ƊAKKO A TSAKKIYAR RANA! YARIYAR DA......”
       
            “Da haɗin bakinki kenan mijinki ke aikata komai!!” Qaseem ya faɗa cikin matsanancin fushi tamkar zai haɗiye Mom, baya tai da sauri jikinta na rawa, cikin rawar murya tace, “Qaseem anya kana cikin hankalinka kuwa? Miya samu kanka? Ko an sauya mana kai ne?”.
       “Komai ma ya sameni fiye da yanda tunaninki ke baki ke da shi. Tun bansan kaina ba ke da shi kuketa nunamin banida wani maƙiyi a duniya sama da Jawaad, Why?. Mom! Nace Why? Shiɗin baɗan ɗan uwanki bane?, shi ɗin ba mijin ƴarku bane? Miya aikata mai zafine wai a gareku da har yau ban taɓa saninsa ba ni?......”
      “Qaseem!!” Mom ta faɗa cikin tsawa tana fashewa da kuka.
        Cikin ficewar hayyaci Qaseem yace, “Eh ki kira sunana koma sau dubune, gaskiyace bazan taɓa fasa faɗaba, to idanma baki saniba yanzu zan sanar miki, idan kuma kin sani bara na maimaita miki. Ita wannan tsintsiyar magen da kike magana MIJIN naki ya tsintota daga ranar ne dan ya jefata cikin abinda yafi ranar zafi, cikin wuta yay niyyar jefa mata rayuwa saboda cimma burinsa, mahaifinane shi amma nasha zarginsa da aikata abubuwa marasa ƙyau a cikin gidan nan, amma da naso ɗaukar mataki saina gaza hakan, na tabbata dukkan ƴan aikin da akai raping a gidannan shine yay musu.....”
      Tsawa Mom ta daka ma Qaseem jikinta na matuƙar rawa, “Qaseem!! Mahaifinka zaka ƙullana sharri irin wannan saboda Jawaad da Bilkisu?”.
        Da ƙarfi Qaseem ya daki tebir ɗinsa, kayan sama suka tarwatse, ya matsa gab da Mom yana nunata da ɗan yatsa ƙirjinsa na sama da ƙasa na kumburar zuciya. Ya cigaba da faɗin, “Tun kin nuna bakisan komaiba bara na faɗa miki to, tun lokacin da akaima ƴar matarnan Amina fyaɗe a cikin gidanmu na gaskata hakan a cikin raina, domin kuwa lemon da aka ajiye ta sha lemo ne da kaf gidan nan shi kaɗaine ke shansa, hakanma yasa ba'a ajiyesa a fridge ɗin kitchen sai na falonsa kawai, ko a falon ƙasa inhar baya ƙasar kwashewa kike ki maida masa sama, to tayaya akai ranar yaje kitchen har yarinyar ta gani ta ɗauka ta sha bayan shi mai shan ma baya nan? Abu na biyu sai da na ɗauki kwalin lemon a bola naje nai bincike akan ɗan sauran cikinsa na gane magani ne mai ƙarfi aka saka a ciki kuma a ƙalla ya kai kwanaki biyar da zubawa, abu na uku na zauna nayi dogon nazari da tunani harna gano ainahin maganain da akai amfani da shi, sai kuma kwatsam na tunano na taɓa ganin maganin a wajen Dad amma a wancan lokacin sai ya gayamin na ciwon bayane dan na gansa da shine a bazata, da yake kuma ban kawo komai a rainaba sai ban amsa na karanta ba a lokacin. Tun daga wannan ranar na fara bibiyar al'amuransa, sai dai abin mamaki bana iya cewa komai akan dukan abinda zan gani. to bara nama faɗa miki abinda baki saniba, a dukkan tafiye-tafiyensa cikin kashi uku biyu bayinsu yake ba, idan yace yabar ƙasarnan tafiyar sati biyu to kwana huɗu ko sati guda ya keyi ya dawo, da wannan makircin nasa yake amfani wajen aikata laifi a rasa wanene keyi a gidan, Mom ya kamata kiyi tunani da hankalinki, a dukka masu aikinmu uku da akai Raping a gidanmu duk sai baƙya nan ake aikatawa, kuma da anyi washe gari ko kwana biyu dayi Dad yake dawowa.......”
       Ƙasa Mom ta zube tana kallon Jawaad dake tsaye kawai yana kallon tamkar wani gunki, tun fara maganarsu baice komaiba bai kuma motsa ba. hawayene ke kwarara a idanun Mom tamkar an buɗe fanfo.
       Qaseem ya nuna Jay da faɗin, “Kayi haƙuri Jay ka gafarceni, zan faɗi wani abu a kan matarka duk da bata a wajen nan, tunda Bilkisu tazo gidanmu ban taɓa jinta a zuciyata da sunan soyayya ba, sai dai ina sonta matsayin ƴar uwata kawai. Amma tun randa na farka a barci naga Dad tsaye kaina a cikin ɗakina naji duk duniya babu wadda nakeso sama da yarinyar nan, ga wata sha'awarta mai tsanani inaji wadda inhar zata kasance kusa dani sai naji inason taɓa mata jiki, abin mamaki duk wannan sha'awar tata da nakeji ban taɓa jin zan iya lalata mata rayuwaba, ni dai kawai burina na taɓa jikinta ko nayi kissing ɗinta na rungumeta shike nan. Da ya ke kuma yarinyace mai tarbiya ko hannunta bata yarda na taɓa sai ta nunamin ɓacin ranta. Kuma saifa ina a kusa da itane nakejin hakan, amma da zarar bama tare da juna ni mantawama nake da ita gaba ɗaya. A daren da Dad ya fara shigo mata ɗaki har aka tsoratamu da ƙara a gidannan nine na fara fitowa, ni duk zatona mai gadine wani abu ya sama, shiyyasa nai gate kai tsaye, ina isowa maigadi na buɗema Dad ƙofa ya fita a gidan....”
          Dafe kai Jawaad yayi da sauri zuciyarsa na wani irin matsanancin harbawa da sauri-sauri, duk da Dad yake zargi dama hakan bai hanashi jin maganar tai masa nauyiba a ƙwaƙwalwa da zuciya....
         “Ƙwarai kuwa Dad” Qaseem ya bama ya sake maimaitawa yana kallon Mom cikin ido, “A tunaninki mai aƙidar kar ƴan uwansa su raɓesa ne zai ɗakko budurwa kamar bilkisu ya ajeta gidansa dan ya ƙyautata mata rayuwa kawai? Aini tun washe garin da aka kawota gidannan na ganta kuma akai min bayanin zuwanta nasan akwai manufa a zuciyarsa game da ita, sai dai narasa ta wace hanya zan kuɓutar da ita? Wannan mijin naki da kike ji da gani ramin bushiyane daga shi sai ƴaƴansa, ke kuma matarsa kura ce kema daga ke sai ƴaƴanki. Bara na sake maimaita miki shine keta bibiyar rayuwar marainiyar ALLAH akan fyaɗe har cikin gidan aurenta, da yaga bazai cimma burinsa cikin sauƙiba shine ya tafka mana asirin da har nai maganar shirya aurenta duk da a zuciyata sam ba haka bane ba. A gaban duniya ya nuna cewa ya ƙyautata mata rayuwa, zai kuma aurama ɗansa jininsa ita, amma sai ya zagaye ta bayan fage shi da ɗan uwanki Uncle Nasir suka zurmaki a ciki da ɗauraki a dukkan hanyoyin da suka gama tsarawa, ke kuma kika hau saboda baƙya son aurenmu bisa naki gurɓataccen tunanin na jahilci da son zuciya. Kuka ɗakko hayar ɗan fir'auna akan ranar ɗaurin aure za'a aura mishi ita, ni kuma zaɓinku, daga baya sai ace mistake aka samu, shi kuma dama kunbiyasa akan karya sake ya saketa duk bala'in da za'ayi har sai ƙura ta lafa an kaita gidansa. sai shi Dad yaje ya cika burinsa a kanta kawai batare da kowa yasan hakanba har ke kanki. Sai dai UBANGIJI ba azzalumin sarki bane, sannan shi yana dubi da ƙyawawan zuciyoyi masu tsoronsa da biyayya a garesa, ashe Jay ya saka ana bibiyar dukkan al'amarinsu basu sani ba..........”
         Zubewa Mom tai ƙasa kawai tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai tare da riƙe kanta da ke juya mata. Jawaad yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa da mai dawa kan Qassem. Murmushi mai ciwo da ƙunar zuciya Jay yay yana tura ɗayan hannunsa cikin aljihu, ɗayan kuma ya dafa kafaɗar Qaseem sukaima juna murmushi. Takawa ya sakeyi gaban Mom ya tsaya har lokacin fuskar tasa da murmushin, ya durƙusa a gabanta yana haɗiye ɗacin daya tokare masa maƙoshi, “Har yanzu ke uwace a gareni Mom, yayar mahaifina, duk da ina zargin kina cikin waɗanda suka tarwatsa masa ahali”.
      Da sauri Mom ta ɗago tana kallon Jay, ta shiga girgiza kanta tana hawaye, “Jawaad dan ALLAH kar kaimin wannan mummunar zargin, mi Abdul-aziz zaimin niko a duniyarnan da har zan tarwatsa masa a hali?......”
     Miƙewa Jawaad yayi yana ɗage kafaɗa da taɓe baki, “Wannan amsar a gaban alƙali zaki badata Mom ba ananba”.
         “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni Aysha wannan wace irin ranace”. Mom ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka.
       Qaseem da yakejin kamar ace yau ɗin ranar barinsa duniya ce yace, “Momy wannan ranace ta tonon silili, ranace mafi muni da a garemu bisa ga son zuciyar mijinki, rana ce da duniya suka san wanene shi? Mom Dad ya cutar da rayuwarmu, kaicon dukiyar da zata kasance haramtacciya ga mai ita, ki kalla yanda ake nunasu cikin ƙasƙanci dan ALLAH, wace riba sukaci? Wane alfahari suka barmana muyi? Wane tunƙaho da taƙama ya rage mana kuma?”.
        Mom da batasanma wainar da ake toyawaba game dasu Dad sai yanzu da Qaseem ya nuna mata a tvn office ɗinsa a take ta ƙwalla ƙara ta zube yaraf a sume.
     Jay daya fice ƙofar office ɗin ya tsaya dansu Sir Ahmad tuni suka bar wajen ganin maganace data shafi family ya dafe kansa da rumtse idanunsa da masifar ƙarfi, dan yaji dukkan abinda Qaseem ɗin ke faɗama Mom, ya kuma tabbatar ƙarar tata nada nasaba da ganin abinda ya farun.
STORY CONTINUES BELOW
___________________________
    Dr Tayyeb hospital   
_______________________

                  Kamar yanda ƙarar kai kawon jirage ta ɗauki mafi yawan mutanen dake cikin asibitin haka ta ɗauki tasu Anuwar dake zaune jigum-jigum suna jiran farkawar Umm-Anum, dan Dr Tayyeb ya sake shiga ya dubata, ya kuma musu bayani akan su kwantar da hankalinsu da ruwan da aka saka mata ya ƙare zata farka normal insha ALLAH.
         Aunty Batool ce ta fara miƙewa ta leƙa ta Window'n da suke a kusa da shi, da ɗan mamaki ta juyi tana kallonsu Ummah da faɗin, “Anya kuwa yau garin nan lafiya yake? Helicopters nefa na sojoji keta yawo wannan ƙarar da mukeji”.
      “Helicopters kuma? To miya faru kuma?”. Ummah ƙarama ta faɗa tana miƙewa itama ta leƙa. Tabbas kuwa zancen Batool gaskiyane, dan har wasuma dake cikin asibitin sun fara fita waje. “Gaskiya garin nan babu lafiya kam”. Ummah ƙarama ta sake faɗa tana nufar ƙofa.
    Da sauri su Anum sukabi bayanta harda Batoul da Anuwar ma daya bisu a ƙarshe shi da Ummah babba, sai dai Ummah babba na gabansa.
       “Ya salam”. Anuwar ya faɗa da sauri saboda karo da sukaci da wani bawan ALLAH dake ƙoƙarin shigowa shi kuma Anuwar ɗin yana yunƙurin fita. A kusan tare suka buɗe baku zasu bama juna haƙuri sai hakan ya gagara kowa ya cak a tsaye baki buɗe jiki na tsuma. Idanun Uncle Sulaiman tamkar zasu faɗo ƙasa dan ruɗani da al'ajabi, cikin sarƙewar harshe yace, “Ja...waa...” sai kuma ya gaza ƙarasawa ya girgiza kansa yana haɗiye yawu da ƙyar.
      Shiko Anuwar wani irin yamutsawa jininsa keyi da kansa, ya kafe Uncle Sulaiman da kallo tamkar ya samu television ɗin kallo. A haka Shahudah da sauran ƴammatan family ɗin sa'anninta suka iso wajen suma zasu koma ciki. A take duk sukaja wani wawan birki suna kallon Anuwar.
       “Kai!!”
Shahudah ta faɗa daɗan ƙarfi tana matsawa gab da Anuwar da binsa da kallo daga sama har ƙasa tana zagayashi. Nannauyan numfashi Anuwar ya sauke da ɗan lumshe idanu ya kalato busashen yawun daya rage masa ya hadiye da ƙyar da raɓawa ta gefen Uncle Sulaiman zai wuce. Caraf Shahudah ta riƙo hannunsa jikinta na rawa. “Kai dan ALLAH wanene kai?”.
        “Muhammad Anuwar Abdul-aziz yusif tafida”. Wata murya dake a bayansu ta basu amsa saɓanin shi Anuwar ɗin da sukaima tambayar. Juyawa sukai da azabar sauri har Uncle Yusif na neman zubewa ƙasa wajen rawar jiki.
        “Hajiya Mariya, kinsan mi kika faɗa kuwa?”. Uncle Sulaiman ya faɗa yana ware idanunsa akan Ummah babba data basu amsar.
       Murmushi mai ciwo Ummah babba tayi tana kamo hannun Anuwar ɗin cikin nata, “Alhaji Sulaiman ai ko baku sami wannan amsarba ya kamata kuyi tunanin hakan direct tunda wanda ya mutu baya dawowa ai ko? Kuma koda ace yaya nada rai ai bazai zauna a wannan ƙuruciyarba tunda har Jawaad daya bari matsayin ɗa ya wuceta”.
        “Haj....h...ha..hajiya mariya kin sake sakani a ruɗani wlhy, a ina Abdul-aziz ya samu ɗa bayan Jawaad kuma?”.
         “Biyoni da zakayi shine kaɗai zai baka amsar dukkanin tambayoyinka”. Ummah ta faɗa tana murmushi da kama hannun Anuwar suka nufi corridor ɗin da ɗakin da aka kwantar da Umm-Anum yake.
     Ba Uncle Sulaiman kawai ba, hatta su Shahudah bin bayansu sukai, yayinda wasu a cikinsu kuma suka nufu kaima iyayensu rahoto.

            Dr Tayyeb na ƙoƙarin fitowa daga ɗakin da Umm-Anum take dan ya sanarma su Ummah su shiga an cire mata drip yaci karo da Ummahn dake riƙe da Anuwar. Murmushi ya ɗanyi yana ja baya ya koma cikin ɗakin da juyawa ya kalli Umm-Anum dake kallonsu da murmushi yace, “Yauwa hajiya, dama zan sanar muku ku shigo ta tashi normal Alhmdllh, dan zama mu iya sallamarku kamar”.
    Kafin Ummah tace wani abu Uncle Sulaiman dake a bayansu cikin tsananin kiɗima yace, “Bilkisu!”. Da sauri Umm-Anum ta maida dubanta gareshi, sai kuma taɗan waro idanu waje itama tace, “Yayah Sulaiman!”. Cikin matuƙar rawar jiki ya afka cikin ɗakin, babbar rigarsa har tana neman taɗesa Dr Tayyeb yay azamar tarosa yana faɗin, “Subahanalillhi, Alhaji yi a hankali”.
     Duk da Umm-Anum batajin ƙwarin jikinta hakan bai hanata sakkowa daga saman gadon ba. Sakkowar tata kuma tayi dai-dai da faɗowar Uncle Uwaisu da sauran ƴan gidan su Jawaad ɗakin.
       “Wlhy itace da gaske!!” Uncle Uwaisu ya faɗa yana jan birki da ɗaga hannaye sama tamkar wani zararre.... Kafin wani a cikinsu ya samu damar sake tofa tashi Nabeelah ta kutso tsakkiyarsu jikinta na rawa, “Ummah! Ummah!! Ummah!! Ku kalla television, ku kalli abinda ya faru dasu Yayanmu a wajen ƙwato Alhaji babba, m....m..matsafa Ummah, wlhy matsafa suka gano acan.....”
       Uncle Sadiq ne yay azamar rarumar remote ɗin television ɗin ɗakin ya kulla, anko haske dai-dai inada ake fiddo su Uncle Nasir daga cikin gidan daga su sai jajayen ƙyallaye, Jawaad na rungume da Alhaji babba yana shafa masa ruwa a fuska za'a sakashi cikin helicopter shi da wasu a cikin waɗanda aka ceto.
        A take ɗakin ya ruguntsume da tsananin tashin hankali da ruɗani,
      Umm-Anum ta fashewa da kuka tana dariya kuma, cikin wani ƙarfin zuciya ta ɗaga murya wajen faɗin, “Rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya”.
        A take ɗakin yay tsit, suka juya gaba ɗaya suna kallonta a wani irin yanayi mai wahalar fassara a fuskokinsu................✍
10
Nima dai kam na tsinci kaina a yanayin har takai alƙalamina da faɗuwa a ƙasa batare da na shirya hakanba😳🚶.
1
Kuyi manegi babu editing yau🤒🚴🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
    9

_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR... 🙋🏿‍♀️🙋🏿‍♀️INA KUKE NE? 🔊🔊KU MARMATSO, DOMIN ZAMAN JIRA YA KARE, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKA HADA HAZAKA DA KAIFIN TUNANI SUN SAKE ZAGE DAMTSE SUN ZO MU DA WASU SABBIN SALON RUBUTUN SU, WADANDA ZASUWA’AZANTAR, SU NISHADANTAR, KANA SY DILMIYA KU A KOGIN KAUNA, BASU TSAYA ANAN BA SALON RUBUTUN SU YA SAKE ZUWA DA SABBIN TSARE TSARE NA DARUSSA DABAN DABAN, DA KUMA HANYOYIN GYARIN JIKI DA WAJE._1

_KADA KU MANTA MARUBUTAN ZAFAFAN DAI SUNE WADANDA SUKA YO MUKU HAR KASHI BIYU A SHEKARAR 2020 DATA GABATA,: WUTSIYAR RAKUMI DA GUDU DA WAIWAYE NA BILYN ABDULL. 2-DAURIN BOYE DA ALKAWARIN ALLAH NA SAFIYYAH HUGUMA.3-BURI DAYA DA QAUNAR MU NA MAMUH GEE-4- SAUYIN KADDARA DA DAURIN GORO NA HAFSAT RANO. SAI 5-KAI MIN HALACCI DA IGIYAR ZATO NA MISS XOXO.._

_A WANNAN SABUWAR SHEKARAR TA 2021 MA HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE DAWOWA DA WASU SABBIN DA’DADAN LITTATTAFAN NASU:_

                       _1_

_* SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA DA ABADAN TAZO MUKU DA SABON LITTAFIN TA MAI SUNA: *(SIRADIN RAYUWA)💜*_

                      _2_

_*HAFSAT RANO* MARUBUCIYAR  GUGUWAR SO DA RUHI DAYA, TA ZO DA SALON NATA LITTAFIN MAI SUNA: *(ABINDA  KE CIKIN ZUCIYA..*)💘_+

                        _3_

_* MAMUH GEE* MARUBUCIYAR TARAYYAH DA EZNAH, TAZO DA SABON ZUWA MAI SUNA: *(MIN QALB)❤️.*_

                           _4_

_*MISS XOXO* MARUBUCIYAR NAUFAL DA SAIFUL-ISLAM, TA YUNKURO DA WANI MAI SUNA: *(KIBIYAR AJALI)*💜_

                    _5_

_SAI MARUBUCIYA *BILLYN ABDUL* WADDA TAYO MUKU KWAI CIKIN KAYA, DA CIKI DA GASKIYA TA YINKURO DA WANI MAI TAKEN: *(YANKAN BAYA)*💝_

_RIGIJI GABJI DUKKAN WADANNAN LAGWADAR DADADAN LITTAFAN BIYAR ZASU ZO MUKU NE INSHA ALLAHU AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA;_

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO2

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
Page 60
...............Umm-Anum na kuka tana dariya duk a lokaci ɗaya ta nuna tv'n da yatsanta manuniya, cikin wani ƙarfin zuciya ta ɗaga murya wajen faɗin, “Rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya”.
        A take ɗakin yay tsit, suka juya gaba ɗaya suna kallonta a wani irin yanayi mai wahalar fassara a fuskokinsu. Kowa ya gagara cewa komai sai kallonta kawai da suke. Ta share hawayen da suka gama wanke mata fuska tana kallon Ummah babba. “Mariya a kaini wajen baba”. Da ƙyar Ummah babba ta iya gyaɗa mata kai a hankali. Bata ƙara cewa komaiba ta gyara mayafin jallabiyar ta data naɗa tamkar yanda larabawan Saudia keyi, Batool ta ɗakko mata takalmanta zuwa gabanta, dafa Batool ɗin tayi ta saka dan ƙafarta ciwo take mata kaɗan-kaɗan, tun jiya bata gama saki ba har yanzun.
        ta maida dubanta ga su Uncle Sulaiman dake tsaye tamkar sojoji, har yanzu babu wanda ya iya gaskata ruɗani da al'ajabin da idanunsu ke gani a zahiri da magiji. Hannayenta🙏🏻 ta haɗe waje guda tana ɗan murmushi, “Ku gafarceni, ganin Mahaifina a yanzu gareni yanada matuƙar muhimmanci”. Bata jira amsarsu ba ta raɓasu ta wuce abinta Batool da Anum da Nabeelah sukabi bayanta.

              Da kallo suka bita tamkar wasu wawaye harta fice ita da zugarta. Ummah ƙarama da babba suma sukai yunƙurin bin bayansu. Uncle Sulaiman ne ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin jiki da rawar murya yace, “Hajiya Mariya a ina kuka samu Bilkisu? Tun tsahon wane lokaci kuma?”. Kanta ta girgiza masa tana share guntun hawayenta itama, “Bani da ikon amsa waɗan nan tambayoyin Alhaji Sulaiman, inaga mu bari har sai lokacin da Yayah taso hakan da kanta, na tabbata zatazo ta sameku har gida insha ALLAHU. Mun barku lafiya”. Ta ƙare maganar da kama hannun Ummah ƙarama suka fice suma.
             “Uncle wacece ita ɗin wai?”. Shahudah da idanunta ke lullumshewa saboda hajijiyar da take gani ta tsananin tashin hankali ta faɗa tana dafe bango. Saurin ruƙota matar Uncle Sadiq tayi jikinta na rawa itama. “Shahudah!!” ta faɗa daɗan ƙarfi ganin jikin Shahudah ya fara saki alamar neman suma takeyi itama. Ruɗewa ɗakin ya ƙarayi, masu share hawaye suka ƙara ƙarfafa kukansu da sauti, yayinda wasu suke zubewa ƙasa daɓar tsabar shiga ruɗani da abinda ake nunawa har yanzu daga gidan tv.2

STORY CONTINUES BELOW

__________________
  STATION
_____________

                Da taimakon Jawaad da Qaseem aka fita da Mom zuwa mota, Qaseem ya shiga baya ya riƙeta yana kuka da kiran sunanta da roƙon karta tafi ta barsu, “Mom Please ki tashi, dan ALLAH karki tafi ki barmu muna sonki, idan kika tafi abin zai mana yawa Mom, idan kika tafi wa zamu kalla muji daɗi”. Ya ƙare maganar da kife kansa bisa fuskarta yana cigaba da kuka, shi kansa bai taɓa sanin shi rago bane mai rauni irin haka ba sai a yau, gani yake kaf duniya babu wanda ya kaisa shiga ruɗani da tsananin tashin hankali.
     Har Jawaad daya ja motar ya fice daga station ɗin Qaseem nata kuka rungume da Mom. A haka suka isa General hospital, inda suka tadda ƴan jarida da jama'ar gari cike anan ma, har takai da ƙyar ƴan sandan da aka zuba ke control ɗinsu. Burin kowa yaga gawarwaki da mutanen da aka ƙwato wajen su Dad. A haka dai aka samu shiga da Mom ciki da ƙyar. Darajar waɗanda suka kawotan yasa akai mata amsar gaggawa da miƙata wani ɗaki.
        
         Motar su Umm-Anum na shigowa asibitin ana shiga da Mom ciki, gurin a cinkushe yake da mutane, hakan yasa suka rasa hanyar da zasubi su shiga balle susan ta inda zasu fara. Aunty Batool ce tai tunanin kiran Jawaad, dan haka ta ciro wayarta daga bag ta fara nemansa, harta tsinke bai ɗaga ba, bata gajiba ta sake kira, nan ɗinma dai harta tsinken bai ɗagan ba. Kanta taɗan dafe zatai magana sai idanunta suka sauka akan Jawaad dake magana da wasu police su uku da alama suna masa bayani ne akan yanayin da asibitin yake ciki na cikar mutane da ƴan jarida.
     “Alhmdllhi ga yayanmu ɗin canma ai”. Dukansu inda take kallo suka kalla, kafin wani ya samu yin magana Anum da Nabeelah suka nufi inda yake, sai dai kafin su ƙarasa aka dakatar dasu a tsawace. Bayani Nabeelah keson ma police ɗin daya tsaidasun amma yaƙi saurarenta, hakan yasa ta fara masa magana da tsiwa dan sun roƙesa amma yana neman cin zarafinsu ma. Hayaniyarsu ta jawo hankalin Jay ya juyo. A bazata yaga ƙannensa, ya ɗan ɗaura hannunsa na dama saman goshinsa da keyi tamkar zai tsage saboda azabar ciwon kai. Da sauri ya kalli police ɗin da suke tare yana nunasu Anum ganin wancan ɗan sandan da suke tare ya ɗaga hannu zai mari Nabeelah amma ta duƙe. “Kaga, cemasa ya barsu suzo”. Amsa masa yay da to, yana nufar inda su Nabeelah suke, yay saurin riƙe hanun ɗan sandan daya sake ɗaga hannu zai mari Nabeelah dan bakinta yaƙi mutuwa saboda haushin baƙar maganar daya faɗa musu dan sunce su ƙannen Jay ne wajensa zasuje. A harzuƙe ɗan sandan ya juya zaiyi magana sai yaga ogansu, saurin gyara yanayinsa yay zai masa bayanin abinda ya faru tsakaninsa da yaran sai yaji ogan nasa yacema su Nabeelah suje wajen Jay ɗin. “Oga kasan mi sukayimin kuwa?”. Murmushi yay masa da ɗan buga kafaɗarsa, “Komi sukai maka kayi haƙuri. ƙanen yallaɓai Jay ne”.

          Da kaushin murya Jawaad daya tsare su Nabeelah da rikitattun idanunsa yace, “Miya kawoku nan?”. “Uh...Uhm Yayanmu bamu kaɗai bane, Ummu ce tace a kawota wajen Alhaji babba”. Nabeelah ta bashi amsa tana laɓewa bayan Anum idanunta cike da tsoro.
        Da sauri Jay ya hau waige-waige, saiko idanunsa suka sauka akan Batool da su Ummah da suma kallonsu sukeyi. Batare da ya sake cewa komaiba yabar wajen zuwa inda su Batool ɗin suke.

          Umm-Anum data rage a mota bata fitoba hango Jay ya nufosu ta fito da ƙyar dan jikinta duk babu daɗi, kallo ɗaya zakaima idanunta kuma kasan tayi kuka sosai, dan sun kumburi sun kumayi jaa.
       Sauri riƙeta Jawaad daya ƙaraso yayi, ya taimaka mata ta tsaya akan ƙafafunta sosai tana sauke ajiyar zuciya, “Ummuna miyasa kuka fito? Kallafa ƙafarki ta kumbura?”. Maimakon ta bashi amsa sai tambaya ta jefa masa, “Ina Bilkisu?”. “Amma Umm......” “Ni dai ina yarinyata nace maka?”. Numfashi ya sauke da ɗan ƙarfi yana lumshe idanu sai kuma ya buɗe lokaci ɗaya, “Tana ciki Ummuna, sun saka mata drip ne saboda ta suma acan, amma inama ganin ƙila ta farka yanzun dan tun ɗazun Dr Bello ya sanarmin ta farfaɗo”. “Alhmdllh, babana fa”. Yanzu kam ɗan murmushi ya mata da sumbatar hannunta, “Shiyyasa naga idanunki sun kumbura ko Ummuna, kinyi kuka?”. Kansa ta dungure tana ƴar hararsa, yay murmushi da kama kunnuwansa alamar na tuba.

STORY CONTINUES BELOW

★★★★

         Sun fara shiga ɗakin da aka kwantar da Bilkisu, kamar yanda Jawaad yay hasashe sun iske ta farka, tana zaune jingine da filo wata Nurse na bata abinci da takeci da ƙyar dan warin asibitin yay masifar addabarta, farkawarta amanta biyu saboda warin asibitin, yanzu ma Dr Bello ne da kansa yasa aka kawo mata abincin dan taci tasha magani kafin Jay yazo ya ɗauketa kamar yanda ya sanar masa.
         Gaba ɗaya tayi wani zuru-zuru, idanunta sunyi masifar kumbura da ƙanƙancewa, sannan sunyi jajur a ciki. shigowar su Jay yayi dai-dai da zaburarta ta sakko a gadon saboda tahowar amai, Nurse ɗin ta ajiye tray'n abincin da sauri tana ƙoƙarin kamota amma tuni takai toilet. Duk rufa mata baya sukai cikin tashin hankali, sai dai duk a ƙofar bayin sukaja birki, Jay da Nurse ɗin ce kawai suka sami damar shiga. Sosai hankalin Jay ya tashi ganin yanda bily ke yunƙurin amai tamkar zata amayo hanjin cikinta, Nurse ɗin na riƙe da ita tana jera mata sannu da shafa bayanta. Matsowa yay kusa da ita shima ya ruƙo hannunta. Da ƙyar aman ya tsagaita, ya taimaka mata da kansa ta wanke bakinta, sai numfashi take saukewa a wahale, kwantar da ita yay a ƙirjinsa tausayinta mai tsanani yana ratsashi, a ƙasan ransa kuma tunani yake ‘mi taci haka?’.
        “Ka kaini gida, banason warin asibitin nan”. Ta faɗa murya can ƙasan maƙoshi tana sake lafewa a jikinsa da shaƙar ƙamshin turarensa da yake ɗan dawo mata da nutsuwarta. Ɗago kanta yay ya saka fuskarta cikin tafukan hannunsa suna kallon juna, “Mi kikaci haka?”. Ya faɗa cikin tashi daskararriyar muryar yana raba idanu akan fuskarta tamkar zai gano abinda ke damunta anan ɗin. Matsawa tai zata sake kwanciya a jikinta tana faɗin, “Banci komaiba, warin asibitinne banaso nidai”.
            “Jawaad yaya dai?”. Ummah ƙarama ta faɗa kafin ya samu damar sake tambayar bily.6

         Da sauri naja baya daga jikinsa dan na manta bafa mu kaɗai bane, bango na dafe saboda jikina babu ƙarfi. Ban iya fahimtar amsar daya bataba dan hankalina baya a garesu, tadai riƙe hannuna ta kamani muka fita sunata jeramin sannu.
       Jay da duk damuwa ta sake lulluɓesa ya fita domin son ganin Doctor dan yazo ya duba Bilkisun ko akwai wata matsala data sakata aman ne.
      A ƙofar ɗakin sukaci karo da Dr Bello da Nurse ɗin dake tare da bilyn, da alama itace taje tai kiransa. Fuskar Dr Bello washe da murmushi ya miƙama Jay hannu, “Dadyn baby ai bansan ka shigoba ma”. Duk da Jay bai fahimci sunan da yay kiransa da shiba sai yaɗan saki fuska kaɗan amma ba murmushi yayi ba, yadai sassauta ta daga cinkushen da take. Doctor bai gajiyaba ya sake faɗin, “Dama sister ce ke sanarmin madam na amai, wannan babyn da alama soja ne, dan nakula zai wajiga madam da yawa tun yana ɗan ficit”. Yanzunkam dai sosai Jay ya kallesa da alamar tambaya, sai dai ya gaza cemasa komai. Lura da hakan da Dr Bello yayne ya sakashi yin murmushi suka ƙarasa shiga ɗakin da Bily take, inda su Umm-Anum suka zagayeta sunata jera mata sannu, kanta na'akan cinyar Ummah babba.
      Sai da ya gaisa da su sannan yayma bilyn sannu, kanta taɗan ɗaga masa kawai alamar amsawa, ya sake kallonta da murmushi ganin tanata faman rufe hannci, juyawa yay ya sake kallon Jay dake tsaye hannayensa duka a aljihu shima yana kallon bilyn. “Congratulations dear Friend, madam na ɗauke da babien mu ɗan sati shida. Ma'ana tana ɗauke da ciki ɗan wata ɗaya da sati biyu”.
          Babu shiri Bily ta janye hannunta daga saman hanci tana waro idanu waje, ganin duk yanda suka zuba mata ido suna murmushi yasa taji kunya, saurin juya baya tayi taja gyalen Ummah babba ta rufe fuskarta ƙirjinta na wata irin bugawa da sauri-sauri.
        Su Ummah kam fuskokinsu washe da murmushi sunata jerama UBANGIJI godiya da kirari, gaba ɗaya sai damuwar da suka yini da ita ta ɓace ɓat. Ubangayya da tunda aka fara cakwakiyar nan babu mai cewa yaga haƙorinsa a waje a take ya saki wani lallausan murmushi yana mai lumshe idanu, duk wata damuwarsa sai yaji ta gudu, farin ciki ya mamaye gurbinta. Dariyar su Ummah ce ta sakashi buɗe lumsassun idanunsa dake jajur, yay murmushi a karo na biyu yana girgiza kansa ganin iya shegen da Anuwar keyi shi da Anum da Nabeelah. Ya dage sai rawa yake yana waƙar larabawa shi a dole yayi ɗa ko ƴa, yayinda Anum da Nabeelah ke tayashi.
     Cikin dariya Ummah ƙarama tace, “Yarona dama haka kake da iya shege ina ganinka wani ustazu?”. Umm-Anum dake murmushi tana kallon Bily da duk abin nan da ake taƙi kallon kowa tace, “Kaɗanma kika gani indai Anuwar ne, dama can Ustaz ɗin da babu Ustazai ne”. Dariya su Ummah da Batool da Dr Bello suka sanya, Jay dai murmushine har yanzu a saman fuskarsa, kunyar iyayensa ta sakashi dakewa abinsa yanata dai kallon bilyn ta ƙasan ido.
     Aunty Batool tace, “Lallai ta maganar Doctor babyn nan namu soja ne, inba soja ba wannan gumurzu da akashawo amma ko gezau baiyiba saima nuna kansa da yayi wa duniya”. Sosai nanma suka sanya dariya, Dr Bello yace, “Gaskiyarki Sister kam, ALLAH dai ya inganta, kema saiki daure kiyi aure ki samo mana namu”. Duk kallon Doctor sukai banda Jay da Bilkisu dake ɓoye, Batool ta zuba masa harara. Shiko murmushi yayi abinsa yana sosa ƙeya waishi yaji kunyar su Ummah. Cike da tsokana Anuwar yace, “Su Aunty Batool kodai-kodai gidan Doctor zamu ɓulla ne?”. Duka takai masa ya kauce yana dariya, Doctor Bello ya kama hannun Anuwar yana faɗin, “Yauwa ɗan ƙanina tayani yaɗa manufa”. Yay maganar suna ficewa daga ɗakin.
          “A to mukam wannan indai na ƙwaraine ai bashi zamuyi Batool”. Umm-Anum ta faɗa tana kallon Batool ɗin. Ƙasa tai da kanta batace komaiba. Ummah ƙarama tace, “Yayah wlhy bansan ko Dr Bello da wata matsalaba, mutum kirkine ɗan manyan mutane, sai dai babansane ɗan rigima, amma shima bawai ta ashsha ba”. “Ato Alhmdllh, bara nazo na fara shirin aurar da ɗiya kenan”. Murna Nabeelah da Anum suka fara, ita dai Ummah babba batace komaiba, hakama Jay uffan baice ba, yayi kamarma baya a ɗakinne, idonsa gaba ɗaya yana akan motsin matarsa.3

STORY CONTINUES BELOW

★★★★★★★

              Koda suka baro ɗakin da bily take da sallama daga Doctor gaba ɗaya sai suka nufi ɗakin da aka kai Alhaji babba, daga shi sai baba maigadi a ɗakin, jikin Umm-Anum har rawa yake, sai da Batool ta riƙeta, cike da sassarfa ta ƙarasa gaban gadon da Alhaji babba ke a ƙwance an saka masa na'urar taimakon numfashi, sosai jikinta ke ɓari, ta durƙushe ƙasa tana kamo hannunta cikin nasa da fashewa da kuka tana kiran sunansa. “Baba kaine haka? ka tashi baba kaga BILKEESUN ka, nadawo gareku baba, baba ka buɗe idanunka ka kalleni dan ALLAH kozanji sassauci babana farin cikina” ta ƙare maganar da ɗaura kanta a gefen hannunsa tana kuka mai tsuma rai. Suma su Ummah hawayen sukeyi har Bily, Batool da Nabeelah da Anum. Anuwar ma hannu ya saka ya ɗauke nasa ƙananun hawayen tare da ƙarasawa ya durƙusa ta ɗayen gefen kakan nasa daya fara gani a yau karan farko na rayuwarsa, Anum tazo kusa dashi ta tsugunna itama tana ɗaura hannunta akan na Anuwar dake riƙe dana Alhaji babba. Jawaad dai yana kallonsu, sai dai bazaka taɓa fahimtar yanayinsa ba, kamilar fuskarsa ta shanye komai.
      A hakanli Alhaji babba yaɗan motsa hannunsa dake riƙe a cikin na Umm-Anum, saurin ɗagowa tai tana kallon hannun, ya sake motsashi a karo na biyu tare da kansa. tsitt ɗakin yay duk suka zuba masa ido. Sake motsawa yay fiye dana farko, sai kuma ya buɗe idanunsa a hankali ya sake maidawa ya rufe saboda nauyin da sukai masa, sake buɗewar yayi a karo na biyu, dishi-dishi ya fara hango Jawaad dake tsaye daga can ƙofar ɗakin yana facing nashi, ya ɗan kafesa da kallo tamkar dai yanason gano wanene?. takowa Jay yay a hankali zuwa gaban gadon, ya tsaya kusa da Umm-Anum tare da ɗan ranƙwafawa yanama Alhaji babba murmushi, hannu ya saka da kansa ya cire masa na'urar da aka saka masa. cikin magana a hankali yace, “Tsoho mairan ƙarfe!”.
     Karan farko Alhaji babba yay wani ɗan murmushi kaɗan da sake motsa hannunsa sai ya jisu duka biyu an riƙe. “Babah!” Umm-Anum ta kira sunansa cikin sanyin murya. Cikin wata irin faɗuwar gaba Alhaji babba ya juya saitin inda yaji muryar da bazai taɓa mantawaba a rayuwarsa, to kodai mafarki yakeyine har yanzun? Ya ayyana a ransa yana ware idanu akan Umm-Anum dake kallonsa tana murmushi da hawaye.
       Ya mata kallon kusan minti ɗaya kafin ya sake juyowa ya kalli Jay, sai kuma ya kalli Anuwar da Anum, ya sake maidawa ya kalli Ummah ƙarama da babba da Batool, Bilkisu da Nabeelah, cike da ƙarfin hali ya yunƙura zai tashi zaune dan ba'a ƙaramin ruɗani ya tsinci kansaba. Saurin riƙesa Jay yayi yana girgiza masa kai. Alhaji babba ya kalesa cikin muryar dake nuna bashi da lafiya yace, “Jawaad mafarkin dana sabane ko? Yo inba mafarkiba a ina nikam zanga mahaifiyarka ido da ido irin haka? Dan ALLAH kaga karka tadani a barcin nan barni nayi tayi ko ALLAH zaisa itama Rahmah da Maryam da Amina da Adamu zasuzo gareni duk mu haɗu anan”.
          “Baba ba mafarki ka ke ba, Bilkisun ka ce a gaske gabanka, nice na dawo gareku, ni ce ban mutuba baba”. Umm-Anum ta faɗa tana rushewa da kuka. Ai yanzunkam babuma wanda yaga sanda Alhaji babba ya tashi dingangan zaune yana riƙo hannun Umm-Anum cikin nasa duka, jikinsa sai rawa yakeyi, hannunsa ya ɗaura saman idonsa ya murza, ya kai kuma kan fuskarta ya shafa. Tabbas ba mafarki yakeba Bilkisun sa ce a gabansa, bilkisun daya rasa kusan shekaru ashirin dashida, bilkisun daya fidda rai da gani a wannan duniyar dukda yana tsananin ƙwaɗayin hakan. “Bilkisu dama kina raye?”. ya faɗa da tsananin rawar murya.
         “Ina raye baba, ganima ALLAH ya ƙaddara sake haɗuwarmu, na godema UBANGIJINA daya saka ka kasance mai tsahon ran da zan dawo na tadda, da ace na dawo baka raye bazan taɓa daina yima mutanen nan munanan addu'oi ba har randa numfashina zai yanke”. Fashewa Alhaji babba yay da kuka, ya kamo kan Umm-Anum ya ɗaura saman cinyarsa ya rungume yana sake fashewa da kuka mai ban tausayi da tsuma rai.

             Da ƙyar Jay da Doctor suka samu damar lallashin Umm-Anum da Alhaji babba, harma dasu Ummah dasu Bilkisu, sai dai fa Alhaji babba ya tubure akan ya warke a sallamesa ya tafi gida, anyi lallashin duniya yace sam baisan wannanba wlhy shifa bazai kwana a asibitin nanba koma mi za'ayi.
     Ganin ya rikice musu harda hawaye Jay yace Doctor ya basu sallama kawai, sai su sami likitan dazai dinga zuwa gida yana dubashi babu damuwa. badan Doctor yasoba ya basu sallama.
       Jay da Anuwar ne suka kama Alhaji babba aka kaisa har mota, yayinda itama Ummah ƙarama ke riƙe da Bilkisu da keta dauriya da ƙarfafa jikinta dukda batajin daɗinsa sam, sai dai ƙasan ranta wani irin farin ciki takeyi da barin asibitin da zasuyi. Motar ta musu kaɗan, dan haka suka shiga ta Aliyu da suka iso asibitin babu jimawa suma dan an ƙaro jami'an tsaro cikin asibitin saboda mutane dake neman kawo ruɗani, acewarsu sunason suga gawawwakin da waɗanda aka samo da rai ko akwai ƴan uwansu a cikinsu.
     Jay bai bisuba, cikin asibitin ya sake komawa inda Qaseem da Salman ke tare da Mom wadda ta farfaɗo amma sun mata allurar barci mai ƙarfi dan jininta ya hau sosai, Doctor ma yace badan ALLAH ya taƙaita mata wahalaba irin wannan faɗuwar da tayi zai iya sakawa ta kamu da paralysis. Sai da suka ɗanyi magana da Qaseem da shi kansa idan da za'a bashi gadon an taimakesa sannan Jay ya fito. Daya fito ɗinma wajen su Jabeer ya tsaya sukai magana sannan ya amshi key ɗin mashin ɗin ɗaya daga cikin jami'insu yabi bayan su Alhaji Babba.

STORY CONTINUES BELOW

_____________________
Dr Tayyeb Hospital
_________________________

                Shahudah dai suma tai a wajen, sai da cikin ƴan matan family ɗin wata tai ƙarfin halin shafa mata ruwa sannan ta kawo numfashi, hakama matar Uncle Nasir ita sai dama aka bata gado, ƴaƴansa nata kuka maiban tausayi da saka zukatan mai kallonsu rauni. Kosu Uncle Sulaiman sai da suka share hawaye dan tsananin tashin hankali. A yanzun kam sun fahimci zaman asibitin sam bazai yuwu a garesuba, dan haka suka tattara inasu-inasu suka nufi gida, dan anma hana kowa shiga wajen Mama Badiyya dama, ba'ason ai mata wata hayaniya ko kaɗan.
          Sun iso gida suka iske waɗanda suka bari anan cikin matsanancin tashin hankali suma, ciki harda Mama Atika da tafi kowa shiga ruɗani ganin halin da babba ɗanta yake a ciki da surukinta, tayi bala'in yin wujiga-wujiga da ita tamkar wata taɓaɓɓiya, dan sai surutai take, fitsari kuwa ba'a magana, tayisa a zane sau babu adadadi batare da tasan yanama zuba ba. Sai da ƴan asibiti suka isone suka fargar da ita halin da take ciki.
       Tabbas bayyana irin kalar ruɗanin da wannan ahali suke ciki ɓata lokacine, sai dai na bama kowa gari ya ƙiyasta a ransa. Gashi an turo jami'an tsaro sun zagaye sashen Uncle Nasir ɗin babu mai shiga kamar yanda akaima gidan Dad shima.
  
_______________________

             Ba ahalinsu Jawaad ne kawai a cikin ruɗaniba, duk ahalin dake da nasaba da waɗanan mutane yau hankalinsu baya tare da tunaninsu, anje kuma duk an zagaye gidajensu da jami'an tsaron sintiri, babu mai shiga babu mai fita. Waɗanda suka tsinci kansu a wani hali kuwa sai dai likitoci ake tura musu cikin gidajen suna dubasu.
     Sosai ƙasarma gaba ɗaya take a hargitse bawai jihar da abin ya faru kawaiba, idan ka buɗe tv da redio babu wani magana saita wannan tashin hankali daya faru. Masu jaje nayi masu ALLAH wadai nayi, waɗanda suka jima suna zarginsu kuwa suka shiga maimaita ai dama a rina. Ƴan uwansu masu mu'amula dasu da suka rasa wasu mutanensu da suka rasu ta wasu hanyoyin tuni suka fara yayibo hujjoji da zarge-zarge suna ɗora musu (Kusan ɗan Adam kamar jira yake🤦🏻, abinda ma ba haka yakeba sai ya maidasa hakan🙄🚶🏻😏).
             Masu ƙara gishi da magi a teburan masu shayi da gidajen suna da biki kuwa harda faɗin wai tukunya tukunya aka ringa fiddowa na farfesun mutane da gasashshen nama daga gidan😂, jini kuwa drom-drom sai kace wani mangyaɗa🤣. Aifa nayi ya samu a bakunan ƴan bani na iya, kowa burinsa ace shine ya fara kawo labarin🤒.1

___________________________________
ƘARAMAR HUKUMAR GWANSU
_________________________________

                Gidane madaidaici mai ƙyau, dan kuwa ko'ina na cikinsa mulmule yake da suminti, sannan an shafesa da fenti ruwan madara da ganye mai haske, ƙal yake da shara sai ƙyalli fasassun tiles ɗin da aka saka a tsakar gidan yake da ɗaukar ido. Yarone da zai iya kaiwa shekara uku ke barci kwance a ƙaramar katifa ta yara a tsakar gidan babu riga jikinsa saboda yanayin zafi, sai wani da bazai wuce shekara shida ba tsaye jikin ƙofar fita daga soron gidan yanata kumburi alamar wani abun akai masa.
      Matashiyar mace da bazata gaza shekaru ashirin da huku ba ta fito daga matsakaicin kicin ɗin dake tsakar gidan ɗauke da tukunya alamar abinci ta kwashe, bayanta goye da jaririya ƙyaƙyƙyawa tanata barcinta hankali kwance. Tunkuyar ta ajiye inda alamu suka nuna wajen wanke-wanke ne tana mai harar yaron dake laɓe jikin ƙofar. “Wlhy kabari na kamaka a gidannan Fharhan sai na maka dukan da ko ubanka ba ganeka zaiyiba, karkazo ka ɗauki abincin su Innata ka kakai musu tunda ni na aikeka gidan su Musbahun har aka dakeka”.
     Sake tura baki yayi gaba yana share ƴar ƙwallarsa, “To Umma ni kije ki amsomin ball ɗina, inaba hakaba ni bazankai abincinba kuma”. “Karka kai dan ALLAH kaga yanda zan kirɓa namanka a gidan nan mara mutunci..........”
          “Yaya?! yaya?! dai”. Da gudu yaron da aka kira da Fharhan ya nufi mai maganar daya shigo yana faɗin, “Oyoyo Abbanmu”. Buɗe masa hannayensa yay ya shige jikinsa, ya ɗagashi sama yana dariya da faɗin, “Babana duk faɗan da nai maka akan yima Umma laifi bakajiba ko?”. Yaron ya ɓata fuska yana kallon Umman tasa dake tsaye tanama mijin nata kallon mamaki, yace mata wannan satin bazaizo weekend ba, amma kuma sai gashi a bazata da yamma liƙis. “Abbamu buguna zatai fa”. “Laifi kamata ai ko?”. Girgiza kai yaron yayi, kafin yayi magana ta matso inda suke ta ɗauka leda viva daya ajiye ƙasa lokacin da zai ɗauki Fharhan. “Sannu da zuwa”. Tafaɗa har yau da mamaki tattare da ita. Murmushi yay mata, yasa ɗayan hannunsa ya shafa kan yarinyar dake goye a bayanta. “Mai gadon zinarina barci akeyi?”. “Ai tunda naimata wanka ta ɓingire, irin wannan zuwan bazata haka”. Murmushi yayi batare da ya bata amsaba ya ida shiga gidan yana faɗin, “Banga na hannun damar Inna ba?”. “Gashi can yana barci”. Ta bashi amsa da nuna masa inda ɗayan yaron ke barci. Sauke Fharhan yay ya kama hannunsa suka nufesa, saida ya shafa kan yaronsa sannan ya zauna gefen tabarmar da aka ɗaura katifar. Itama ledar ta ajiye taje ta kawo masa ruwan sha. Sai da ta ajiye sannan ta sake kallon Fharhan, “Kazo ka kaima su Inna abinci karka bari na sake maimaita maka wlhy Fharhan ”. Baki ya tura zaiyi magana Abbansa ya hararesa, “Kanason na ɓata maka rai ko?” da sauri yaron ya girgiza masa kai, “Ɗauka abincin ka wuce, ka faɗama Inna muma muna nan zuwa gidan”. Da mamaki ta kallesa, sai dai bata iya cewa komaiba har Fharhan ya ɗauka kular abincin su inna ya fice daga gidan.
        “Amma daga dawowarka kake.....” katseta yay da faɗin, “Firdausi babban al'amarine ya kawoni gida, zo kiga abinda na gano”. Babu musu ta nufesa, ya ɗago daga danna wayar da ya keyi ya miƙa mata wayar yana faɗin, “Ko zaki iya gane wannan?”. Da saurinta ta amshi wayar, hoton da taci karo da shi ta tsatstsare da idanu, kusan mintuna uku tana kallonsa cike da nazari ko ƙyaftawa batayi, da sauri ta zabura tana zaro idanu waje da ɗora hannunta saman baki, “Abban Fharhan wlhy kamar Bilkisu fa”. “Kama ko itace?” “Wlhy bana ko tantama Bilkisu ce wannan, ko wane irin canjawa zatayi a rayuwa bazan gaza ganeta ba, dan ALLAH ina ka samo mana Bilkisu? Bayan shekarun da muka ɗauka cikin nemanta babu ko labarinta”. Tai maganar tana zama kusa da shi cike da zumuɗi. “Nima yau na ganta Firdausi, a media naci karo da hoton yana yawo a dalilin abinda ya faru, tana cikin tawagar jami'an tsaron da suka nuna bajinta wajen kamo miyagun mutanen nan yan cultism, kinganta anan tare da mijinta ranar aurensu, shima jami'in tsarone”. “A...ab... Abban Fharhan wai kana nufin Bilkisun ce ta zama jami'ar tsaro kuma tai aure?”. “Wlhy kuwa haka na gani, auren nasu bai wuce wata huɗu ba akace, amma watanta kusan biyu kenan da tarewa, shiyyasa nake faɗa miki ki ringa ɗan shiga yanar gizon nan amma kinƙi, koba komai zaki san abubuwa da yawa da duniya ke ciki, yanzu hakama bakisan abinda ke faruwa a ƙasarba yau ɗin?”. “A'a na sani, dan ɗazun su Luba sunzomin barka kasan sanda na haihu tana Niger, to shine suke labarin, hakan yasa na buɗe redio anan naji komai”. Murmushi yayi ya sake miƙa mata wayarsa dake ɗauke da hoton Bilkisu da Jawaad a ranar dinner ɗinsu lokacin da suke wasan bindiga. Sosai Firdausi ta saku wani ihun farin ciki, ta rungume mijinta tana mai fashewa da kuka, “Wlhy itace Abban Fharhan, ashe zan sake ganin bily a duniyarnan. Abban Fharhan dan ALLAH muje gidan baba, wlhy nasan zaifi kowa farin ciki a yau, bashi da wani buri daya wuce gamo da Bilkisu, wannan shine burinsa, da fatansa a kullum”.
       Babu musu ya amince, ta ɗakko mayafi da kayan da za'a sakama Abbas dake barci, shibe ya amsa ya saka masa, ita kuma ta shiga da kayansa ɗaki ta kulle ƙofar, ta kullo kicin da ɗakin da suke saka kayan abinci da tarkace, ɗaukar Abbas daketa barcinsa yay a kafaɗa suka fice a gidan, saida ta kulle sannan suka ɗauki hanyar gidan Baba a ƙafa da yake babu nisa sosai.2

STORY CONTINUES BELOW

                Sun iske Fharhan nata bama inna labarin abinda akai masa a gidan su musbahu abokinsa kuma maƙwaftansu, tanata lallashinsa ita kuma. Sai dai shigowar su firdausi yasata maida hankali a kansu, Abban Fharhan ya kwantar da Abbas a gefen tabarmar da suke sannan suka zauna suna gaisheta.
       “Wai dama kazo garin Muktar?”. “A'a inna, zuwana kenan”. “To, shine kuma kuka taho nan? Lafiya dai ko?”. “Alhmdllh inna sai alkairi”. “To masha ALLAH, ai haka akeson ji”.
       Kamar yanda ya nunama firdausi hoto haka ya nunama Inna itama, kwatankwacin ruɗanin da Firdausi ta shiga innama haka ta tsinci kanta a ciki, da sauri ta shiga ƙwalama Baba dake ɗakinsa kira. Fitowa yay da ɗan hanzari dan dama bai jima da shigaba wanka ya fito yake kimtsawa dan dawowarsa kenan daga kasuwar ƙauye da yake zuwa yanzun yana sana'ar kayan miyarsa.
        Shikam ai ganin Bilkisu sai ya rikice fiye da zatoma, musamman dayaga hotunan waɗanda su Bilkisun suka kama, ya share ƙwallar data taru masa a cikin ido yana faɗin, “ALLAH mai iko, ALLAH mai hikima buwayi gagara misali. Muktar kayi haƙuri, dolene zuwa gobe mu koma birni tare da kai kuwa”.
       “Baba har dani dan ALLAH”. Firdausi ta faɗa tana share ƙwalla. Inna tace, “Wlhy nima kam ba'a barina baya, dolene naje ganin ɗiyata”. Itama muryarta da rauni a ciki tai maganar.
     A take babu wani ɓata lokaci suka yanke hukuncin tafiya birni gobe idan ALLAH ya kaimu koda kuwa idan sunje Alhaji lado da Jazuga zasu salwantar da rayuwar tasu kamar yanda suka faɗa musu a baya.4

____________________________

               Tunda muka baro asibitin saina samu ƴar nutsuwa, dan yanzu banajin aman sam, sai dai kawai rashin ƙwarin jiki da damuwar dake cike taf da ƙirjina harma da ruɗani, ganin duk abinda ya faru nake tamkar a mafarki zan farka zuwa anjima naji ba hakaba.
         Mun yada zango a gidan Alhaji babba, inda muka iskesa zagaye da jami'an tsaro har yanzun, dan ba'a basu izinin barin gidanba. Aliyu na ajiyemu ya juya da cewar zaije ya nemo mana abincin da zamuci.
          Kasancewar magriba tayi ba zama mukayiba, da yake bayan ɗakin Alhaji babba akwai isasun ɗakuna a gidan sai kowa ya samu wajen shiga a wadace, ni dai sakani Ummah ƙarama tayi nai wanka da ruwa mai ɗumi, kamar yanda Anuwar ya taimakama Alhaji babba shima yay wanka dan ya ƙara samun ƙwarin jikinsa.
        Bani da wasu kaya a gidan dan haka na rasa yaya zanyi, saina maida na jikina na fito, salloli ake bina tun daga zuhur har mgriba da akeyi yanzun, gashi kayan jikina bana tunaninma zasuyi salla.
    Ina cikin wannan hasashen Anum ta shigo ɗauke da leda, ajiyewa tai a saman gadon tana murmushi, “Ga kaya yayanmu ya kawo miki”. Kallonta nai da sauri, mamaki sosai a fuskata, “Yazo gidan ne?”. Kanta ta jinjina min, “Yazo yanzun nan shi da abokan nan nasa na wajen bikinku, amma sun fita massallaci, Ummah tace ki saka kiyi salla kizo kici abinci”. Kai kawai na iya jinjina mata, na miƙe nayi duk yanda tace, ina saka kaya ina kallon cikina dake a shafe tamkar babu kayan ciki ma, amma a haka ake maganar akwai ɗan mutum a ciki. Bansan murmushi ya suɓuce minba, na ɗaura hannuna akan cikin naɗan shafa.

              Lokacin dana kammala rama sallolin dake kaina anata kiran sallar isha'i, dan haka na gabatar itama. ban fitaba, na kwanta a saman gadon ƙafafuna a ƙasa fuskata na kallon silin ɗin ɗakin, idanuna a lumshe suke, yayinda hannayena duka buyu ke cikin rigata ina shafa cikina, ni kaɗai nasan mi nakeji a lokacin, ina farin cikin samun ƙaruwar da ALLAH kaɗai ke wadata bayinsa da ita, gefe kuma inajin ɗacin tsintar wanda zuciyata take girmama da daratawa bayan iyayen firdausi fiye da kowa a duniya cikin mummunan hali. Tabbas da ace wanine yazomin da wannan labarin akan Dad bazan taɓa gaskatashiba koda kuwa ace Mijina ne, sai dai kash, nice da idanuna na gansa, da kunnuwana na jisa, ba'a cikin mafarkiba ko magagin barci, ba'a labari daga bakin wani ba. Haɗiye ɗacin daya tokare maƙoshina nayi daƙyar ina buɗe lumsassun idanuna jin ƙamshin turaren dana fi ƙauna fiye da kowanne a duniya a yanzun.
        Jay daya jima da shigowa yana ƙare mata kallo harya gaji ya ƙaraso inda take ya durƙusa a bakin gadon. A hankali ya kwantar da kansa saman cikinta bayan ya janye hanayenta, ya lumshe idanunsa dake cike da nauyin damuwa dana gajiya.
           “Kin bayyana a ranar da tarihi bazai taɓa mantawa da itaba Little Beejay, rana mai cike da ruɗani kala-kala da ban al'ajab, ina roƙon ALLAH ya raya mana ke cikin aminci, ALLAH yasa ki zama hasken idaniyarmu da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W) baki ɗaya, kizama madubi mai haska addinin musulinci a kowace irin nahiya, kizama jaruma irin Mamanki.....”
          Murmushi ya suɓucemin babu shiri saboda jin sambatun da yakeyi, hannuna nakai saman kansa na fara shafawa a hankali ina sake faɗaɗa murmushi na, shi kaɗai ya ragemin yanzu a duniya sai gudan jininmu dake a cikin ciki, muryata da ɗan rawa nace, “Nidai insha ALLAH Little Jay ne”.
       “Tab, yarinya ban yardaba”. Ya faɗa yana ɗaga kansa da sauri da hawowa saman gadon ya zauna, yunƙurawa nai zan tashi ya riƙeni, maidoni yay jikinsa ya kwantar dani saman ƙirjinsa. Sai da na shaƙi ƙamshinsa na lumshe idanu sannan na buɗesu a kan fuskarsa ma'abociya kamala da kamewa ina murmushi. Shima murmushi yay min kaɗan yana kafeni da jajayen idanunsa, ya duƙo da fuskarsa dai-dai tawa ya sumbaci goshina da laɓɓana. Sake lumshe idanu nayi da kai hannuna saman kumatunsa ina shafawa a hankali har zuwa bayan kunnensa. “Thanks you Sweet Love” na faɗa a can ƙasan maƙoshi batare dana san shauƙi ya kwasheniba nai suɓutar bakin. Idanu ya ɗan waro alamar mamaki, cikin sarƙewar halshe yace, “Mi ki ka ce?!”. Cusa kaina nai a ƙirjinsa wani masifan kunya na lulluɓeni, ya ɗago fuskata da sauri yana faɗin, “Please Miemaa sake faɗa naji”. Ƙara ɓoye fuskar nayi da ƙyau. “Pleaseeeeeeee”. Ya faɗa a wani irin yanayin daya saka tsigar jikina tashi na sake ƙanƙamesa. “Sweet Love” na sake faɗa a hankali. “Oh my God, wannan rana ta musamman ce a gareni” ya faɗa da sake ƙanƙameni yay baya muka faɗa saman gadon ina jikinsa. “Lilly kinzo da tarin sauyi” ya sake faɗa yana shafa cikina da lalubar bakina ya haɗe da nasa.
       Karan farko a rayuwata dana fara maida masa murtanin abinda ya kemin kaina tsaye babu wani kunya kojin ɗar, a take ya haukacemin jikinsa sai tsuma yakeyi, munyi nisan kiwo sosai dan da gaske neman kaiwa inda yafi ƙauna yake nemanyi, ALLAH ya ceceni a bazata akai knocking ƙofar ɗakin.
        Nice na fara ƙoƙarin zare jikina daga garesa a wale, amma duk da haka ƙoƙarin maidoni ya keyi, na sake ja baya sosai ina sauke tagwayen numfashi da sauri-sauri da gyara rigata, sake knocking ɗin akayi, sai dai narasa ta yanda zan amsa, dan inhar nayi magana sai angane halin da nake a ciki, gashi kuma bansan wanene ba. Juyawa nai na kallesa, yana kwance a yanda na barsa idanunsa a rumtse yana sauke nasa numfashin shima, nasan tabbas yanajin buga ƙofar da akeyi, amma ya share abinsa hankali kwance. Yunƙurawa nai zan miƙe naje na buɗe yay saurin riƙo hannuna, sake juyawa nai na kallesa, yanzu kam ya tashi zaune, ya zaunar dani saman cinyarsa sannan yay gyaran murya batare da ya kalleniba. Daga wajen Nabeelah tace, “Yayanmu ance kufito aci abinci”. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, shikuma yace, “Uhhum”. Daga haka bai sake maganaba, Nabeelah ma haka saita bar wajen kasancewar tasan halin kayanta.
     Kallon juna mukayi, yaɗan kaɗamin idanunsa da suka ƙanƙance yana cika bakinsa da iska ya furzar. Bance komaiba na maida kaina na duƙar. Shima bai sake cewarba ya ɗagani daga cinyar tasa bayan ya shafa cikina. Matsawa nayi gefe ganin na samu ya sakeni, batare da yace dani komaiba ya nufi bayi.
     Ƙarar ruwa kawai na jiyo alamar wankama ya keyi kenan, na ɗan dafe kaina ina jinjina kaina, tunanin kar aga bamu fitoba ai zaton wani abunne ya sakani saka hijjab ɗina na fita ni, idan ya fito ya iskeni a can.

STORY CONTINUES BELOW

         Tunda na fito suketa jeramin sannu, Umm-Anum ta kamo hannuna ta zaunar a kusa da ita. Ɗan kallon Alhaji babba dake gefenta nayi na gaishesa, ya amsamin da kulawa tare da sakamin albarka da doguwar addu'a akan namijin ƙoƙarin da muka nuna a jejin can dan a cewarsa yanzu ya ga komai a labaran dare da suke sake maimaitawa. Kasa cewa komai nayi nidai, na juya na gaida Umm-Anum itama dasu Ummah babba, sai Yaya Anuwar da Aunty Batool da Aunty Haneefa, Aunty Saudah da sukazo suma babu jimawa, Anum da Nabeelah kuma na basu hannu mukai musabaha.
      Babu wanda ya tambayeni boss har aka fara zuba abinci a babban faranti kamar yanda Alhaji babba ya buƙata, muna shirin fara ci sai gashi ya fito sanye da kayan daya haɗo cikin nawa da Anum ta kaimin ɗazun. Ɗan kallonsa nayi ya zubamin harara, na ɗauke kaina ina haɗiye murmushin dake neman suɓucemin. Zama yay tsakkiyar Anuwar da Ummah ƙarama, shima yay bismilla kamar kowa ya saka hannu.

              Muna gab da kammala cin abincin wayarsa ta shiga vibration, da farko kalla yay zai ɗauke kansa, sai kuma ya ɗauka wayar da ɗan zafin nama yana ja baya daga gaban abincin, babu wanda yasan mi aka faɗa masa ya mike da ɗan hanzarinsa yana faɗin, “Zanje office, na manta shaf munada meeting wlhy”.
       “Meeting a daren nan Muhammad?”. Alhaji babba ya faɗa yana kallonsa.
          “To ya zamuyi baba? Akan case ɗin mutanen nanne, kasan manyan ƙasar sunyi caa akan batun, gefe kuma al'ummar ƙasar suma da zafi-zafi suke buƙatar suga hukuncin da za'a yanke, gashi a kuma a dalilin faruwar al'amarin allura na neman tono garma”.
       Murmushi Alhaji babba yayi yana faɗin, “Garmuna ma, dan ta wuce guda ɗaya. ALLAH ya bada nasarar ƙulla alkairi to, amma shiga ɗaki ka ɗakko magani kasha, wannan kan naka daga gani ciwo yakeyi”.
      Baiyi musu ba ya nufi ɗakin Alhaji babban ya ɗakko maganin, ruwa ya ɗauka a inda muke yasha sannan yay mana sallama ya fice. Muka rakashi da addu'a mukuma.

          Bayan kammala cin abincin zaman hira akai duk da gajiyar dake tattare da kowa, Umm-Anum ta fara bamu labarin rayuwar da ta tsinci kanta bayan barinta gida. Ma'ana sanda hankalinta ya dawo jikinta ta ganta a ƙasa mai tsarki, sai dai kuma ta gagara tuna komai daya danganci rayuwarta ta baya, da inda ta fito, da ahalinta.
     Kuka kowa ya keyi hawaye shaɓe-shaɓe, duk da nariga nasan duk wannan tunda mu an faɗa mana sanda mukaje saudia nima saida nai kukan. Ummah babba ma ta labarta mata yanda abubuwa suka faru bayan barinta gida. irin neman da akaita mata da tashin hankalin da Mama maryam da Alhaji babba da Rahmah dasu kansu suka shiga, harma da ƴan uwan mahaifin boss. Rasuwar Mama Maryam da Auran Rahma.
           Sai dai bayan wasu shekaru kuma sai kowa ya haƙura aka cigaba da binta da addu'a dansu tunaninsu koma ta rasune. Itama taci kuka, muma muka tayata.
       Har kusan ƙarfe biyu na dare bamu kwanta ba. dan da ƙyar Anuwar dasu Aunty Haneefa suka lallaɓa Alhaji babba ya yarda zai kwanta ya huta daboda jikinsa, gashi Doctor yace ya samu isashen barci.
     Muma duk tashi mukai mukaje muka kwanta kowa zuciya babu daɗi. cikin amincin ALLAH ni dai inama kwanciya barci mai nauyi yay awan gaba dani.

___________________________
Tafida family house
______________________

               Lokacin da labari ya isa kunnen mama Atika akan ganin Umm-Anum sai tahau surutai tamkar wadda ta zare, tun su Uncle Uwaisu na ɗaukal al'amarin matsayin ruɗani harya koma basu tsoro. Dan sosai neman fita take daga hayyacinta.
       Sake ruguntsumewa gidan yayi da tashin hankali, babu mai iya fahimtar yaren wani. Batun yunwa kuwa ai an manta da sunanta a wannan gida yau, dolefa aka danƙarama Mama Atika allurar barci ta ɓingire, har dare basa tare da nutsuwarsu, barema da Qaseem suka iso gidan Mom da itama take a jangwaɓe, ta tada hankalintane akan a maidata gida batason kwanan asibitin shiyyasa Qaseem ya kawota nan dan can gidan zamansa tashin hankali kawai zai ƙara mata.
        Itama dai Mom maganar dawowar Umm-Anum ta nema maidata ruwa, dan ruɗani ta sake komawa ciki fiye da tunani, al'amarin sai ya sake bama su Uncle Sulaiman da basu san komaiba mamaki, a ganinsu dawowar Bilkisu cikin ƙoshin lafiya abin ayi murnane bawai tashin hankaliba, amma yarasa miyasa abin ke neman zama wani iri ga wasu daga cikin ahalin nasu?. Bashi da mai bashi amsa, dan haka yay gum da bakinsa kawai.

STORY CONTINUES BELOW

       Saboda meeting ɗin da za'ayi shima dai Qaseem baro musu gidan yayi, sai da ya fara zuwa gidansa ya watsa ruwa yay sallar isha'i sannan ya nufi station batare da yay tunanin neman abinciba ma, dan shi sam a yinin yau bama abinciba ko ruwa sai ƙishirwa ta kaisa maƙura yake nemansa yasha.

______________
STATION
____________

                  Ɗakin meeting ɗin yay tsitt, tsumayen shigiwar oga kwata-kwata (Director General) daya iso garin a yammacin yau kawai sukeyi, kusan mintuna goma sai gashi ya fito tare da wasu manyansu. Duk miƙewa sukai tsaye domin girmamawa a garesu, suka ƙame tare da sara musu.
      Shima murtani ya maida musu sannan ya zauna da nuna musu alamar suma su zauna. Zama duk su Jay sukayi, bawai matsayin rank ɗin Jawaad ya kai ai zaman wannan meeting ɗin da shi bane, kawai ƙwazo da suka nuna akan aikin ya kai shi ga shiga wannan tawagar, dan gaba ɗaya gurin manyansune nacan ƙololuwa, sai su Sir Ahmad dasu Qaseem, sai dai shi Qaseem ma gaba ɗaya yama kasa shigowa ɗakin meeting ɗin, koda yazo sai ya maƙale a office ɗinsa ransa duk a dagule.
           An buɗe taron da addu'a a ɓangarorin addinan biyu, kafin D.G ya nuna kujerar data rage babu kowa cikin alamar son sanin wanda ya kamata ya zaunata. Sir Ahmad ne yay masa bayanin Qaseem, an ɗaga waya za'a kirasa Jawaad ya miƙe tsaye yana ɗaga hannu, damar magana Oga kwata-kwata ya bashi. “Sir ina neman alfarma”. “Muna saurarrnka”. “Sir Qaseem yana cikin tsananin ruɗani, inaga zamansa tare damu a wajen nan kamar zai ƙara tunzura tunaninsane ga wani abu daban, a ɗazun har mummunan hukunci yaso yankema kansa. mizai hana ai masa alfarmar barinsa kawai”.
     Tsit ɗakin yay alamar jiran amsa daga bakin Oga. Sai da yaja kusan mintuna biyu kafin ya jinjina kansa yana gyara abin maganar gabansa. “Maganar Cpt gaskiyane, kasancewar abinda zamu tattauna ɗin yanada nasaba da mahaifinsa akwai damuwa, kuma shi jami'inmu ne daya taka rawar gani a wannan hukumar, ya cancanci koda sau ɗayane a nuna masa hallacin hakan”. Duk kawuna suka jinjina, inda wasu kuma a cikinsu hakan bai musu daɗi ba, dan su kam basuƙi ama kori Qaseem ɗinba daga hukumar gaba ɗaya.

         Jawaad ne ya fara bayani akan matakan da sukabi dangane da kamasu akan dukanin bayanan sirri da suka samu, sai abubuwan da suka samo a gidan kama daga mutane zuwa wasu abubuwan daban, sai kuma adadin su Dad da suka kasance su 22 idan aka haɗa da shugabarsu data kasance mace. Sai ayyukansu da muƙaman wasunsu a cikin siyasa da kasuwancin wasunsu.
    Bayan ya kammala ya miƙa takardar da dukkan bayanan suke ciki ga Sir Ahmad, wanda shi kuma ya miƙama D.G.
         Amsa yay ya duba na tsahon wasu mintuna kafin ya ɗago yana kallonsu. “To duk kunji bayanai ga jami'inmu, mi zaku iya cewa ku?”. Hannu wani ya ɗaga aka bashi iznin magana.
      “Sir ina ganin kawai mu miƙasu kotu mana, dan dukkanin bayanan da Jay ya bayar an samu mutanen nan dasu a zahiri kuma duniya duk ta gani, a ganina bama buƙatar wasu hujjoji kuma”.
      Jin jina kai D.G ya shigayi, amma baice komaiba. Wani ya sake ɗaga hannu shima aka bashi izini.
       “Ni kuma Sir a ganina kamar kaisu kotu ba mafita bace, dan za'a iya amfani da siyasa wajen kuɓutar dasu, ƴan ƙasa kuma su cigaba da kallonmu da laifin daba namuba, kawai mu riƙesu a wajenmu har iyakar rayuwarsu”. Nanma dai kawuna kawai suketa jinjinawa, wanima ya sake miƙewa shima ya faɗi ra'ayinsa. Haka sukaita faɗar ra'ayinsu ta kowanne fanni, inda maganganun su duk suna akan turbar gaskiya da kuma muhimmanci mai ƙarfi, shi dai Jay baice komaiba ganin duk manyansane keta magana, saida kowa ya lafa sannan D.G ya kallesa da kulawa. “Bakace komaiba Jawaad, bayan kuma kaine jami'in dayasan sirrin case ɗin nan fiye da kowa a cikinmu”.
    Iska Jay ya zuƙa ya fesar, kansa a ƙasa yace, “Sir ai kune iyayenmu, zaku hango abinda mu sam bamu iya hangosa ba, duk hukuncin da kuka yanke muma zai zama dai-dai a garemu”.
      “Hakane Jawaad, amma kuma da kuke ƙasanmu zaku iya bada shawara mai amfani da zatafi wadda mu zamu kawo, domin ku a yanzu kuke ganiyar ƙuruciyarku da kaifin tunani, sannan kuke shiga lungu da saƙo akan kowacce matsala, kune kuke ganin komai dangane da al'umma, kune kuke fita farautar masu laifi cikin kowanne irin runtsi da ƙalubale, mu muna office zaune, idan kun bada shawara ai bazai zama kuskureba”.
       “Hakane Sir. To nidai idan har shawarata bata sauka a layiba ina ganin kaisu kotun shine babbar mafita, amma kafin hakan ya dace a faɗaɗa bincike dangane da masana'antunsu, da wajejen ayyukansu, akwai business da wasu a cikinsu ke gudanarwa a cikin ƙasa da wajen ƙasa, mizai hana musan mi suke fitarwa da shigowa ne? Masu ayyuka a gwamnati musan wane irin aiki suke gudanarwa a ofisoshinsu suma, daga haka mu basu damar neman lauyoyi muma mu samu namu ƙwararren lauyan. Hujjata anan itace dukansu waɗanan mutanen akwai zargin fyaɗe akansu wanda sam bama asan adadinsaba, sun lalata yara da yawa da mummunan aikinsu, ciki harda ƴaƴan ƴan uwansu. Duk yanda muke tunanin kare kanmu ga al'umma bazamu fitaba sai anyi komai akan idanunsu.........”
      “Tayaya za'ai komai akan idanunsu?, fili kakeso a ɗiba a tara duka talakawa ai zaman kotun a gabansu komi?”. Wani ya faɗa aɗan fusace yana kallon Jay ɗin.
     Murmushi Jawaad yay yana mai girgiza kansa, “Ba haka nake nufiba yallaɓai, abinda yasa na kawo wannan maganar ta al'ummah saboda idanma muna gudun manyan ƙasar zasubi ta ƙarƙashin ƙasa wajen saye alƙalan da zasu gudanar da wannan shari'a muryoyin ƴan ƙasa zai daƙile hakan, sannan suma manyan zasu tsorata domin inba waɗan nan jama'ar ai babu su, musaman idan mukai dubi da mafi rinjaye a cikinsu wannan shine hawa na farko da sukayi. sunason komawa na biyu, bazasu so sunansu ya ɓaci ba ai kodan mulkin da suka ɗanɗana suke kuma ƙulafuci da ƙwaɗayin komawa”.
      Sir Ahmad dake murmushi ya kalli D.G, “Sir Jay yazo da maganar hankali, dominfa wannan faɗan sam ba namu baneba, faɗane tsakanin al'ummar ƙasa da waɗanan mutane, idan kuma har mukai tunanin shiga ciki wajen kare mutuncinsu to lallai zamu fuskanci ƙalubale harma a ringa zargin muma da namu dalilin mara ƙyau a ƙasa, amma idan min fidda komai ga al'umma muka kuma nuna musu suma sunada ƙarfin iko akai su kansu alƙalan zasu shiga hankalinsu sosai, sannan ƴan siyasa bazasuyi wani tasiriba wajen yaɗa farfagandar da suka saba. Kaga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, mun kuma ƙarama hukumarmu kima da daraja a duniya baki ɗayama ba wanan ƙasar kawai ba”.
      “Wannan gaskiyane wlhy” wani ya faɗa cike da goyon baya akan zancen su Jawaad da Sir Ahmad.

         D.G yace, “Okay, inaga to zamu tsaya a wannan matsayar, zuwa gobe sai mu yanke hukuncin daya dace ko ya kukace?”.
      Duk kawuna suka jinjina masa cike da gamsuwa. Daga haka taron ya tashi. lokacin ƙarfe kusan uku na dare.
            Jay baibar station ɗinba saida yaje office ɗin Qaseem ya fiddosa, shine da kansa ya kaisa har gida sannan ya wuce gidan Alhaji babba, ya iske duk sunyi barci, dan haka ya wuce ɗakin da yake tunanin Bilkisu na a ciki. Kwance ya sameta ita kaɗai a saman gado ta cure waje ɗaya kamar maijin sanyi, yay ɗan murmushi da cire kayansa sannan ya raɓa ta gefenta ya kwanta tare da turata cikin jikinsa. A take ta shaƙi ƙamshinsa, sai ta gyara kwanciya kawai ta lafe tana mai sauke tagwayen ajiyar zuciya kamar wata mage.
      Murmushi ya sake saki mai sanyi, ya sumbaci kanta yana sauke tasa ajiyar zuciyar a jere.

________________
WASHE GARI
____________________

               Washe gari ta kama Lahadi, tunda safe Jay ya samu kira daga Gimbiya Munaya akan takawa da kansa zai yoma su Abbu rakkiya gidan Alhaji babba.
    Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama Jawaad ba, dan haka ya sanarma dasu Alhaji babba halin da ake ciki, su kansu sunyi mamaki, to amma idan akai dubi da matsayin su Abbun a wajen Takawa hakan ba komai bane face girmamawa.

★★★★★

         A family house ɗin su Jawaad ma sun wayi gari da shirin zuwa gidan Alhaji babba wajen Umm-Anum kamar yanda Uncle Sulaiman ya bada shawara shi da wasu a cikin sauran ƴan uwa.

★★★★★

          Ɓangaren su Firdausi ma tun da farar safiya suka kammala nasu shirin na nufowa birni, sai dai su saɓanin ƴan masaurata da familyn Jay ne, su gidan Jawaad sukai shirin zuwa tamkar yanda Muktar mijin Firdausi yay ƙoƙarin sama musu adireshi a daran jiya ta dalilin wani abokinsa ɗan sanda.

★★★★★★

           Maman Amina ma sun tashi ne da shirin nufar gidan Alhaji Babba kamar yanda Jay ya kirasu ya sanar musu suje dan Mama Safara'u ta gana da Umm-Anum.............✍

“Hummmmmmm!!!!! Wannan shine ake kira da ga wuri ga waina, to masu karatu, idanfa bakusan gariba to ku saurari daka, dan yanzu zamusan ma'anar ƘWAI CIKIN ƘAYA. su wanen ƘAYOYIN? su wanene ƘWAYAYEN?. Amsoshinku na'a page 61, saiku shirya kuma domin yin gangamin tafiya gidan ALHAJI BABBA mu gani wace wainar za'a toya shinnnnnnn?🚴🏼🚶🏻😢.
4
Masoya ZAFAFA 2021 fa sunata gagarumin shiri da yafi rukunin farko dana biyu da suka kawo muku a baya, mun shirya shiri na musamman domin ƙayatar daku da nishaɗantar daku da daɗaɗan labaranmu a wannan karonma, naga baƙwa motsawa😪, bayan kuma gagarumin shirin da muketa shiri dominku🤗.
ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭.3

Page 611

...............Cike da mamaki matuƙa Aamilah ke kallon Shahudah dake zaune gaban mirror'n ɗakin Mama Atika tana tsara kwalliya, taci jan wando da farar top ƙal mai ƙyau da akaima hoton zuciya a gaba, gefe kuma madaidaiciyar jikka ce mai azabar ƙyau da aka ƙawata da zanen furrani na zuciya.....
       “Sister! Wai mi kikeyi hakane?”.
Ɗago manyan idanunta tai da sukasha kwalli ta kalli Aamilah, sake maida fuskarta tai ga mirror tana dai-daita janbakinta da yay mata ɗas a baki. “Harma tambayata kike Aamilah? Kin manta yau Valentine day?. A duk irin wannan ranar kema shaidace ai ina shiryama BB wani abu, sannan muɗan fita yawo koda dakene idan shi yace bai zuwa. Tunda matsalolin nan suka fara kema kinsan hakan bata kasanceba, to amma yanda aka maida auren nan namu ai wannan ranar ni tazomin a dai-dai, koba komai zan sake tabbatar masa yana nan daram a raina, a shirye nake kuma nai waje da waccan jakar baƙauya daga garesa da baƙin asirinta”. Cike da takaici ƙarara a saman fuskar Aamilah ta girgiza kai ƙwalla na cika mata idanu, “Sister yanzu nan duk tashin hankalin da muke a ciki keta soyayya ma kikeyi? Wlhy bantaɓa sanin akwai kunyaba a duniya irin jiya, hatta da ƴan gidannan kunyar haɗa ido nake da wasu dalilin halin da su Dad suka jefa kansu da mu, amma ke tun a daren jiya nagama kin ware kamar komai bai faru ba, ga Mom can kwance yanzu haka zazzaɓi ne ma a jikinta, wlhy badan su Uncle Sulaiman sun matsa fitar nanba nasan babu inda zataje. Duk shirmen Salman jikinsa a sanyaye yake tun jiya ya kasa fita ko ina yana tare da Mom, amma ke........”
         Shahudah da kema Aamilah wani banzan kallo tunda ta fara maganar taja gajeren tsaki tana ɗaukar sosan hoda da ƙara gyara fuskarta. “Aamilah kenan, harma kece kike da bakin faɗamin ban damu ba? A kaf ɗinku nafi kowa shan kunya a al'amarinnan, dannice kullum mai posting pictures ɗin Dad a kowanne shafina, kinsan kuma yanda nake da ɗunbin fans. sannan a dukanin shafukansa hotunana yafi na kowa yawa a cikinku, wlhy tsabar baƙinciki gaba ɗaya shafukana na rufesu, ke a jiya saida na karya duka layikan na fasa wayar sannan na samu nutsuwa. Bayan wannan mikikeso nayi? Na rasa Dad, nakuma rasa BB a karo na biyu? Impossible dear, dolene na tsira da ɗaya, domin ina ƙaunar mijina. Nasan duk bayanin dazan miki ba fahinta zakiyiba tunda ba auren kikayi ba, dan haka karki bari a jimu a gidan mutane”.
     Baki a matuƙar hangame Aamilah da Mama Atika dake a kwance tana duk saurarensu suke kallon Shahudah data jefa Cingam a baki tana ƙara gyara zaman gashin dokin dake a kanta da siririn mayafin data yafa. Juyawa tai tana kallonsu kanta tsaye, “Kumuje. dan nifa namafi son mu fara isa dan naga Maman BB sosai naga kuma kalar tarbar da zatamin. Sannan naɗan faracin uban yarinyarcan kafin zuwa dare na tare”.
    Uffan babu wanda yace mata a cikinsu, Aamilah ta taimakama mama Atika ta tashi zaune dan dama tuni ta shirya, badan tasoba zata bisu, sai dai kawai waɗanda suka bada shawarar zuwa gidan Alhaji babba a yau sunfi su da basa son zuwa rinjaye, batason kuma tace bazataje ba a fassara al'amarin da wani abu daban, ko aga kamar tana baƙin ciki da dawowar Bilkisu ne.
      Sun iske mafi yawan jama'ar gidan suma duk sun fito harabar gidan, fitowarsu ta saka kowa ya zubama Shahudah idanu, dan taci wani uban dogon takalmine bayan ɗamewa datai cikin wando da riga. Uncle Sulaiman ya kalleta cikin ɓacin rai zaiyi magana Uncle Sadiq yay saurin riƙe masa hannu yana girgiza masa kai alamar karya ce mata komai, dan yasan yin maganar kan iya janyo wata fitina daban musamman ga mama Atika da tun jiya taketa datsama mutane magana a gidan tamkar ba uwace a garesu ba.
     Haɗiye maganarsa Uncle Sulaiman yayi, badan yaso hakanba. A sauranma babu wanda yay yunƙurin cewa komai, sai dai sunata kallon Shahudah data toshe da baƙin eyeglasess ga cingam a baki tanata tauna hankalinta a kwance.+

__________________
ZAFAFA 2021
_______________

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
 
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

STORY CONTINUES BELOW

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

______________________
  Gidan Alhaji Babba
_________________________

               Kasancewar mai martaba ya sanar da wuri zasuzo saboda yanada zaman meeting da su manyan jihar zasuyi game da abinda ya faru akan su Dad, tun daga sallar asuba bamu koma barci ba, aunty Batool da Boss suka fita suka haɗo kayayyakin da za'a buƙata na haɗa abinci, kasancewar munada yawa dandanan muka shiga hada-hadar haɗa breakfast. Koma nace dai sunayi, dan nikam bama wani aikin kirki nakeba dan sam banajin daɗin jikina. Wasu na gyaran gida wasu na haɗa abinci haka akai aikin, zuwa takwas na safe komai yayi tsaf kowa nata ƙoƙarin yin wanka. Da yake boss ya ɗakko mana kaya ni da shi tun fitar da sukai da aunty Batool sai banji damuwa da tunanin mizan sakaba, nai shirina tsaf cikin doguwar rigar lass ɗin daya ɗakko mini, sai dai bayan fauda babu abinda na ƙara, turarema kaɗan na saka na yafa mayafi na fito falo inda nake ɗanjin maganganun su Anum.
       Zamana baifi da mintuna uku ba mukaji ƙarar buɗe gate, miƙewa duk mukayi, Boss da Anuwar ma suka fito tare da Alhaji babba da suka sakko a tsakkiya, yasha gayu cikin farar shadda ƙal harda babbar riga, fuskarsa fayau alamar gyaran fuska yasha a ciki, sai baza ƙamshi suke su duka ukun. Ido muka haɗa da boss mukaima juna murmushi.
      Sune suka fara fita, mu kuma muna biye da su. Lokacin har motocin  guda uku zuƙa-zuƙa sun gama shigowa, sauran kuma duk sun tsaya a waje alamar bazasu samu waje ba dan habar gidan batacin mota fiye da bakwai. Akwai kuma ta Batool, boss sai na Alhaji babba guda biyu.
      Abu-Siddiq ne ya fara fitowa, sai Abbu. Da gudu Anum ta nufi Abbu ta maƙalƙalesa, shima ya tarba ɗiyarsa cike da ɗoki da kewa duk da shekaranjiya suka rabu. Mota ta biyu, Gombiya munaya sai mai martaba Sarki Sameer Saifudden cike da izzarnan tasa da kwarjinin girma da mulki, a take dogarai suka fara jera masa kirari tare da lulluɓe gaban motar har saida ya fito. (ALLAH ya taimaki ɗan autan jimina gagara ɗaukar shaho. Ɗawisu sarkin ado, hadari sa gabanka inda kakeso, kaga dutsen cikin ruwa bakasan ana rana ba, kainuwa dashen ALLAH. Ɗan sarki, jikan sarki, baban sarki kuma insha ALLAHU). Duk da sarauta da mulki na wannan sarki yana girmama duk abinda ya kasance a gabansa, ma'ana wanda yasan ya girmesa a shekaru, dan haka koda Alhaji babba da su jay suka ƙarasa gabansa ƙasa ya rissinar da kai alamar girmama ga Alhaji babba. Dan ya tabbata a haife zai haifesa.
     Sosai Alhaji babba yaji daɗin wannan girmamawa har fuskarsa ta bayyana.
       Ba'a ɓata lokaci ba akai musu jagora zuwa babban falon baƙi na Alhaji babba da yasha gyara da ƙamshi,  an kuma shirya musu abincin karin kumallo.
      Gambiya na riƙe dani sai faman taɓa jikina take da tambayata mike damuna. Nidai kaina a ƙasa nake faɗa mata babu komai, kawai gajiyace, da yake ita bata bi su takawaba muna tare da itane sai Ummah ƙarama ke faɗa mata ai ta samu jikane. A take Ummu ta rikice da murna ta rungumeni a jikinta kai kace niɗin jininta ce da gaske. Hakan ya ƙara saka kimarta da mutuncinta gasu Umm-Anum dama duk wanda yake a wajen.

STORY CONTINUES BELOW

       Daga haka mukai zaman yin breakfast, inda Ummu ta saki jikinta sosai kodan dama can ta riga ta saba da Umm-Anum ne oho. Sai dai kowa yaci ya ƙoshi Alhmdllh sannan su Nabeelah suka gyara wajen, bandani da Umm-Anum ta hanani tashi, a cewarta na zauna na huta haka nan.

   ★★★★

          Acan falon baƙi kam Abbu kasa sakewa yay yaci abinci saboda nauyin Alhaji babba da yakeji, hakama takawa da ƙyar yasha haɗaɗɗen shayin da Umm-Anum taima dahu na musamman saboda tasan shi da Abbu suna matuƙar son shayin, dan idan takawa yaje can sosai yake shansa, sai farfesun kan rago da shima yana matuƙar sonsa.
     Alhaji babba babu ruwansa, mutum ne mai sakewa da jama'a dajan na ƙasa da shi a jiki, dan haka yayta jansu da hira hardai suka saki jiki da shi, musamman Abbu daya fahimci shine surukin nashi kodan nannoƙewar da yaketa famanyi.

   ______________

        Bayan kammala cin abinci dukanmu muka ɗunguma falon baƙi inda su takawa suke kamar yanda Alhaji babba ya bada umarni, muna gama zama sai ga kira ya shigo wayar boss, tashi yay ya fita, mintuna baifi uku ba ya dawo ya sanar da cewar su Uncle Sulaiman ne. damar shigo da su Alhaji babba ya bada.
        Tunda suka shigo falon idona ya sauka akan aunty Shahudah sai kaina ya ɗaure, bawai alamunta na nuna bata tatare da damuwa bane, bakuma shigartace ta bani mamaki ba dan dama nasaba ganin abinda ma yafi hakan, yanda take ta faman shigewa jikin Boss da shi hankalinsama baya kantane ya bani mamaki, inajin lokacin da take faɗa masa wai tanason magana da shi. Banji ya bata amsaba, baima kalleta ba naga yabar inda take ya nufi kusa da Alhaji babba ya zauna.
         Harara ta watsomin tare da jan tsaki ta koma kusa da kakarsu ta zauna dan tsallakawa inda boss yake dai babu dama na sani. ɗauke kaina nayi tamkarma ban gantaba, dan ni bata gabana wlhy.
      Sai da aka fara buɗe taro da addu'a kamar yanda addini ya koyar, kafin kowa ya fara magana Umm-Anum ta kalli Alhaji babba, cikin girmamawa ta roƙesa dan ALLAH tanason idan da hali a kawo Dad da Uncle Nasir da Alhaji kokino gidan kafin ita dai tace komai, dan tanason ta maimaita dukkan abinda ta sani a gabansu gudun karma ace ta musu ƙazafi.
    Kowa kallon Boss yayi, dan ansan dai wannan aikinsane. Kansa ya girgiza yana gyara zamasa, “Bani da wannan damar, domin case ɗinsu babbane, sai dai........” sai kuma yay shiru yana ɗan kallon sashin da Takawa yake. Murmushi sarki Sameer daya fahimci inda ya nufa yayi, baice komaiba ya ɗauka wayarsa ɗaya a cikin wayoyinsa, ɗan danne-danne yay kafin ya ajiye, da alama dai text message ya tura. Babu jimawa kuwa wayarsa tai ƴar ƙara alamun shigowar saƙo. ɗauka yay ya duba, sai kuma ya ajiye yana kallon Boss, shima kallonsa ya keyi, Takawa ya jinjina kai alamar an gama. Murmushi Boss yay yana rissinar da kansa akamar girmamawa da jinjina.
       Da ɗan lokacin jira ne Gimbiya tai amfani wajen basu labarin yanda akai su Takawa suka tsinci Umm-Anum, har kaita asibiti da maidata saudia, da maganin da aka nema mata, bata kai ƙarsheba aka iso dasu Dad kowanne a cikin ankwa. Gaba ɗayansu kansu a duƙe sun kasa kallon kowa dake falon saboda kunya, jami'an tsaronma dake a tare dasu basu bada damar kowa ya raɓi inda suke ba, dan cikin kuka Aamilah ta nufi Dad amma sai suka daga mata tsawa, hakama yaron Uncle Nasir autansa hanashi taɓa Abbansa akai, dole ya koma jikin mamansa yana kuka itama tanayi.
     Gyaran murya takawa yay, a take falon yay tsitt, sai ƙarar ac kawai data taimakawa cinkushewar falon kakeji, dan falon yay matuƙar cika sosai. Hakan ya saka Jay miƙewa ya tada yaran da ƴammatan yace su koma falon cikin gida. badan sunso ba duk suka miƙe har bily. sai dai kuma Alhaji babba ya buƙaci Bilkisu ta dawo. a cewarsa zaman yanada nasaba da ita ita da Anum.
      Dawo mukai muka zauna, dama a raina naji haushi ganin banda Shahudah aka kora sai mu, dan ƙin tashi tayi ita, duk da kuma harda ita ya nuna ɗin.
        “Inaga kuka bashi bane ya dace ace munyi a wannan lokacin, haƙuri dayin amfani da lokacin zamuyi domin warware matsalolin dake a tsakkiya”. Takawa ya faɗa a hankali yana kallon kowa dake falon. Hakan yasa kowa ya sake nutsuwa aka sake maida hankali ga Gimbiya data cigaba da bada labarin Umm-Anum, bayyanar cikinta da kuma aurenta da Abbu da haihuwar Anum. Sai a yanzu Dad, Uncle Nasir, Alhaji Kokino sukama fahimci halin da ake ciki. Gaba ɗaya ganin Umm-Anum dajin ƙarin bayani game da ita daga bakin Matar sarki ya sakasu diriricewa, sai kallonta suke hawaye na kwarara bisa fuskokinsu. Uncle Nasir ne cikin kuka yace tabbas BA FARKON BA ƘARSHEN, da ace nasan da zuwan wannan rana da ban biyema yaudara ta azzalumai irinku ba Alhaji Sadi, yau gashi babu Abdul-aziz a duniya amma ina cikin tsananin kunya mai muni dako ƙaramin ɗana banason duba, mama kin bada gudunmawa, kema....” yay maganar yana kallon Mama Atika data duƙar da kai ƙasa tana hawaye. “Da baki zama mai hassada da ƙyashi ba da ban tsinta kaina a wannan halinba, da baki zama maison tafi kowaba da ban tsinci kaina a hakaba, tabbas ke uwace mahaifiya a gareni, amma tun daga jiya na farajin nadamar hakan, kaicon rayuwar da take ƙarewa da dana sani da ruɗani. kaicon jin daɗi da arziƙin da sakamakonsa yake zama wuta, inama nine Abdul-aziz...........”
         “Bashi bane kai, bakuma zaka taɓa zama shiba azzalumi, mai maida hallaci da butulci”. Umm-Anum ta faɗa a harzuƙe idanunta sun kaɗa sunyi jazur da ɓacin rai.
        Numfashi takawa ya sauke yana gyara alƙyabbarsa, yace, “Inaga mai makon wannan kace nace ɗin, mizai hana mutafi kai tsaye akan abinda ya taramu nan. Umm-Anum, mike faruwa?”.
         Cikin soyewar zuciya Umm-Anum ta kalli Takawa da yay mata maganar tana haɗiye zafin da takeji a ƙirjinta, kafin ta maida dubanta ga jama'ar falon baki ɗaya. “Basai na maimaita ba kowa yasan wacece ni, ɗiyar wacece, sannan wanene ya kasance mijina a shekarun baya, gwagwarmayar da akasha kafin zamansa wani abu harma ya zama wani abun. Abdul-aziz mutum ne mai matuƙar son ƴan uwansa, bai haɗa sonsu da kowaba hatta ɗan da ya haifa, yanda yake ƙaunarsu al'amarin har tsoro yake bani, dan nidai nasan suɗin da wahala ace suna sonsa kamar haka. Sai dai kuma ban taɓa magana ba, dan hakan ba hurumina baneba. Halayyarsa ta samo asaline kuma da yanda mahaifiyarsa tai masa tarbiyya akan ƙyaunar ƴan uwansa da zuciya ɗaya. Abdul-aziz yanada abokai tunkan yazama wani abu, sai dai babu wanda yafi shaƙuwa da shi kamar Sadi Kokino duk da kuwa ya girmesa da shekaru masu ɗan tazara. tare sukai karatu tamkar yanda ya faɗa min, sannan kuma aminine a garesa bawai aboki kawai ba. Sadi ya taka matuƙar rawa a bikinmu dan a lokacin yafi Abdul-aziz abin hannu, saboda shi yana juya dukiyar da mahaifinsa ya rasu ya bar masane shi da ƙaninsa. Bayan aurenmu nasha zuwa gidansa wajen matarsa, hakama matarsa tana zuwa wajena sosai, a haka muka zama aminai sosai har ALLAH ya ɗaga darajar Abdul-aziz ya zama gwamna, wanda Sadi yana ɗaya daga cikin waɗanda suka tsaya tsayin daka akan hakan har Abdul-aziz ya amince duk da baya buƙata. Harga ALLAH siyasar da Abdul-aziz ya shiga bata taɓa kwantamin a rai ba, sai dai nayi shiru ne saboda su Mama maryam da Baba duk sun amince masa, kuma shima naga ya karɓa, Alhaji kokino yana ɗaya daga cikin waɗanda sukaita nunamin muhimmancin mutane irin Abdul-aziz a cikin masu mulkin ƙasarnan, tun ina ganin suna tunzurashine kawai harna yarda dasu na shiga jerin masu masa addu'a. A haka ya kammala shekara huɗun farko a gwamna aka tsaidashi takarar shugaban ƙasa a bazata. Yaso ya bijire a lokacin kam, amma muka tsaya kai da fata ni da Sadi da Nasir da wasu a ƴan uwansu wajen roƙonsa ya tsaya tunda jama'ane suke buƙatar hakan. Haka ya haƙura dan darajar roƙon da mukai masa. An shiga hidimar kamfen da sauransu har dai gwamnati ta tsaya, Abdul-aziz ya zama shugaban ƙasa. Harkokin mulki sun fara zama da ƙafafunsu yanada watani huɗu, dan anyi naɗe-naɗe ga waɗanda ya dace, ciki harda Sadi wanda ya samu muƙami mai tsokar gaske, hakama Alhaji Ali. cikin amincin ALLAH suka fara fiddo ayyuka na cigaban ƙasa wanda ina ɗaya daga mashawartan na cikin gida. Ƴan ƙasa nata murna da nuna jin daɗinsu, sai dai kuma ga Abdul-aziz abubuwa sun fara canjawa, walwalarsa da kuzari duk sun fara raguwa, idan ya zauna sai kagansa zugum tamkar wani wanda abin duniya ya addaba. Abotarsa da Sadi kokino kamar ta fara ja baya, dan yawan zuwa da ya keyi gidan sai naga ya rage daga shi har Ali. A koda yaushe ya dawo gida yana manne da Jawaad kamar wani wanda za'a ƙwace masa shi. Idan na tambayesa mike damunsa kuma sai yace dani babu komai, ko yace, “Harka mulkin ƙasarnan sai addu'a Bilkisu, babu komai cikinsa sai baƙin tashin hankali, a zahiri kawai shugaban ƙasa yake amsa sunansa, amma a baɗini ɗaure yake tamau agun waɗanda ke zagaye da shi”. Nakan nema fashin baƙi akan wannan magana a duk sanda ya yita, amma sai dai yay murmushi kawai baya cewa komai. Tun ina ƙoƙarin tambayarsa ma harna daina, sai dai inata masa addu'a. Yana wata na goma da hawa mulki nakasa haƙuri nai masa tambaya akan Sadi da Ali, amsar daya bani itace kawai babu komai. Hakan yasa naji babu daɗi gaskiya. dan harna nuna masa. Mutum ne shi mai matuƙar sauƙin kai ga iyalansa. sai ya zauna ya dinga bani haƙuri damin nasiha akan wani abun barinsa a yanda yake yafi muhimmanci fiye da tonasa. Nanma dai haƙura nai na barsa badan naso hakanba, sai daga bayane na samu Mama maryam da maganar dan abin ya kasa barin zuciyata. A ranar yazo nan gidan, sai dai bansan mi suka tattauna ba, da ya koma gida kuma ban tambayesa komaiba”. Umm-Anum ta sauke numfashi da share hawayen dake gangaro mata, wanda su Bilkisu ma kukan suke a hankali. Ƙafarta mai ciwo taɗan miƙe da cigaba da faɗin,
  
            “A daren wata juma'a dake dai-dai da cikar Abdul-aziz shekara ɗaya da wata ɗaya akan kujerar mulki sai yay baƙi bayan sallar isha'i, tunda naga har ya yarda zaiga baƙin na tabbata masu muhimmanci ne, dan a ƙa'ida shugaban ƙasa baya irin wannan zaman musamman ma da daddare, kuma a cikin gida, gidanma a falonsa. Inason tashi na bisa naga wanene Jawaad dake fama da zazzaɓi ya hanani tashi dan yanata faman kuka, haka na haƙura nai amfani da telephone nai kiran su Wasila dake ɗakinsu, dan suna a tare damune kowa ya sani. Rahma ce ta ɗaga wayan, a cewarta Wasila tayi barci. Umarni na bata akan tasaka akaima baƙin Abdul-aziz abin sha, idan kuma suna buƙatar wani abu sai a haɗa da shi. Ta amsamin da to na katse kiran. Kusan mintuna arba'in da yin haka harma na manta ina jiran shigowarsa ne kawai sai ga Rahma ta shigomin a wani iri. Faɗa na fara mata, dan basa shigowa ɗakinsa inba da wani babban daliliba. Cikin rudin da take ciki tace, Kiyi haƙuri Yayah, wlhy wani abune ya sakani a ruɗani, zomuje ɗakinki kiji dan ALLAH kada Yah Abdul ya shigo. Ban musa mataba nabi bayanta muka fita, ina goye da Jawaad da yay barci a bayana”.
       (Yayah wai dan ALLAH mi su Alhaji Sadi keson Yah Abdull yayi ne yaƙi?). Ban ganemba Rahmah miya faru?. (Ruwan da kikace na saka a kaimusu saina iske ma'aikatan sunata faman aiki, kinsan kuma Yaya bason kowa yay masa aiki yake ba wani lokacin, shinefa na ɗauka da kaina nakai ruwan, to saina iske Yaya Nasir, Alhaji Ali da Alhaji Kokino tare da shi, sai dai kafin nai sallama naji wani furuci na Yaya Nasir daya saka bayan na gaishesu na ajiye ruwan na sake laɓewa, dan tundafa na shiga falon kan Yah Abdull a ƙasa alamun ransa a ɓace yake. Kinsan minaji kuwa?) kaina na jinjina mata a lokacin. (Ta cigaba da faɗin Yaya Nasir naji yana faɗin, “Amma dai Abdul-aziz kasan baka isa sanin sirrinmu ba sannan ka bijire mana, bafa wai dan bama sonka bane muke jawoka jikinmu, duk yanda kake tunanin mulkin ƙasarnan yafi ƙarfinka saika ɗaura ɗammarar da muke nuna maka, dan mulkin ƙasarnar baya buƙatar GASKIYARKA ko ƘWAZONKA balle son TALAKAWANKA”.  Murmushi Yaya Abdull yayi yana girgiza kansa, cike da ladabi yace, “Yaya dan ALLAH mu ajiye maganarnan, indai nine kusa a ranku abinda naji na gani a can wajen na barsa wlhy, kuma har abada bazan taɓa furtashi ga waniba koda kuwa ace Bilkisu ce ko Mama ko Jawaad. Amma hakan bawai yana nufin zan barku kucigaba da zama akan wannan hakalarba, kuji tsoron ALLAH, karku.........” da sauri Yaya Nasir ya ɗaga masa hannu, “Bama buƙatar ji”. Murmushi Yaya Abdull yay kawai yaɗan girgiza kansa, “Shikenan Yaya na bari, ALLAH ya ganar daku gaskiya idan kunada rabonta. Sai dai gaskiya koda zan haɗe wannan maganar a cikina bazan iya barin Sadi ya cigaba da sarrafa mugan ƙwayoyi ana cutar talakawa naba, dolene kodai ka rufe kamfaninka na sararafa magunguna, kokuma ni nasaka kwamitin bincike a kansa ƙarƙashin hukumar lafiya.......” a fusace Alhaji Ali (Dad) yace, “Mi kake nufi Abdul!? Kenan zaka iya mana SARAN ƁOYE (littafina na zafafa 2021🤗😋) kenan bayan kasan mu duka nan munada hannun jari a wannan kamfanin hatta da kai kanka ka sakama ɗanka hannun jari zaka aikata hakan kuma?”. “Babu wani maganar Saran Ɓoye Alhaji Ali, inda Saran Ɓoye zan muku da bazan fito na faɗa muku ba ai, sannan da kake maganar na sakama Jay hanun Jari a ciki ALLAH shine shaidata bansan abinda kukeyi a ɓoyeba kenan ai, nidai ABINDA KE CIKIN ZUCIYA ta (Littafin Rano a Zafafa 2021🤗😋) na fito na faɗa muku, dan ALLAH ya kukeson nayi? Ku kune garkuwata, a wannan tafiyar, amma kundawo kuna meman sakani cikin SIRAƊIN RAYUWA (Littafin Huguma a zafafa 2021🤗😋) kuma? Dama kun dafamin bayane domin kuyi amfani dani wajen cimma burinku ko mi? To wlhy! Wlhy! Wlhy!! Kunji sau uku, bazan taɓa cutar da talakawana danna faranta mukuba, bakuma zan taɓa nisanta kaina da UBANGIJINA saboda ku ba, sirrinku kuwa zan riƙe, domin wanda ya halicceku na kallonku, nayi imani da KIBIYAR AJALI.....(Littafin Miss Xoxo na zafafa 2021🤗😋)  sulke baya tareta saita gitta wataran, duk abinda yay farko zaiyi ƙarshe. Karku sake zuwamin gida akan wanan maganar daga yau na rufeta, kuma har gaban abada bazata sake tashiba insha ALLAH”. Kallon tsoro suke masa sosai, Alhaji Kokino zaiyi magana Alhaji Ali ya hanashi, shinefa na taho ganin Yaya zai fito). Ajiyar zuciya na sauke da cigaba da kallon Rahmah tamkar a jikinta zan samu amsoshina, fassara maganganunta nake amma babu wadda na iya samawa fassarar data dace, haka na haƙura na barta ta tafi ɗakinsu saboda farkawar da Jawaad yayi baban yaji kukansa ya shigo. Ban tambayesaba a ranar sai bayan sati kusan ɗaya, sai dai ko uffan baice daniba balle na samu amsa, haka na cigaba da masa naci daga ƙarshe yace karna sake damunsa akan abinda bai shafeniba. Ranar haka muka yini ran kowa a ɓace ni da shi”.
      Ta sake share hawayenta tana shaƙar numfashi da ƙyar, saida Gambiya ta bata ruwa tasha sannan ta cigaba.
        Tun daga wannan lokacin na fahinci abubuwa sun ɗauki zafi tsakanin Abdul-aziz da su Sadi, sai dai yaƙi faɗa min komai duk yanda naso ji, kamar yanda yay alƙawari ya saka kwamitin bincike akan kamfanin magunguna na Sadi, wanda abin bai nisaba aka ƙwace kamfanin batare da am bayyanama duniya mi aka gano a cikiba, sai dai abin mamaki ko sati biyu ba'ai da amsarba aka maida masa abinsa. daga wannan lokacin kuma yanayin yanda Abdul-aziz ke gudanar da mulki ya fara canja taku, baya iyayin komai sai abinda su Sadi sukace, ikon ALLAH dai talakawan ƙasa basu fahimci hakanba sai mu dake a kusa da shi sosai. Hankalina ya tashi sosai, dan ko shawara na bashi akan abu ko Baba da Mama maryam suka bashi sai yace ba hakaba, ga abinda Sadi da Ali sukace, ma'ana dai yafi yarda da nasu. Cikin wata guda duk ya susuce komansa ya koma ƙarƙashin ikonsu, mulkinma dai tamkar sune suke yinsa bashi ba, dan komai akan ikonsu yake gudana, sai sunce yayi yakeyi, wanda kuma sukace kar yayi komai muhimmancin abun bazai yisaba. Tun yana ciwo a tsaitsaye harta kaisa ga kwanciya, da ƙyar ya amince Doctor yazo ya dubashi a wata ranar laraba, a gwajin farko aka gano ciwon hawan jini tattare da shi, sannan zuciyarsa na barazanar kamuwa da ciwo kuma. Hankalina ya tashi, na dinga masa kuka da roƙon ya sanarmin abinda ke damunsa ko shawara na bashi, amma yaƙi. Bayan kwana biyu ya cigaba da ƴan harkokinsa yana nunamin ya warke, amma ni nasan akwai wata a ƙasa tunda nasha ritsashi yana hawaye, sannan idan ya zauna shi kaɗai zaka samesa yayi jigum yana tunani. Sai kuma rama da ya ketayi a tsaye wadda Baba da Mama maryam suka kasa haƙuri suma sai da suka tambayeni ko lafiya?. gudun karsu tashi hankalinsu nace babu komai kai kawone kawai irin na shugabanci da kuma ɗan zazzaɓi da yay na kwana biyu. Sun masa addu'a daga haka muka bar maganar.
         Bayan kamar sati shida da tashinsa daga wannan ciwo sai ya ƙara kwanciya, wannan itace kwanciyar data zama ajalinsa, a ranar bai fita office ba duk da kasancewar ranar aikice, yanama da meeting da gwamnoni, amma hakan ya gagara. Wajen yamma sai ga Sadi Kokino da Ali sunzo sun dubashi, ban kawo komai a rainaba na barsu daga su sai shi, ina ɗakina inama Jawaad shirin islamiyya sai ga Rahma da gudunta, sai dai tama kasa magana, hannuna kawai taja muka fito zuwa ɗakin da Abdul-aziz yake kwance. Sai dai muna kawo ƙofar ɗakin su Sadi na fitowa. Kallon Rahmah suka dingayi cikin wani yanayi daya sakani faɗin, “Lafiya kuwa? Miya faru?”. Cikin shashantar da zancen suka shiga gaisheni da tambayar jikinsa, tare da ɗorawa da faɗin ya kamata a sanar dan a fita dashi ƙasar U.S yaga likitan daya san aikinsa. Ban musa musu hakanba, dan nima ina buƙatar lafiyar mijina, na raɓasu na shige ɗakin sai na tadda Abdul-aziz a lulluɓe har fuskarsa, nai saurin matsawa na janye bargon. Ajiyar zuciya na sauke ganin idanunsa biyu, sai dai da alama hawaye yakeyi, amma jin motsina yay saurin sharewa ya maye fuskarsa da murmushi. Zama nai kusa dashi ina jera masa sannu, na shiga karanto addu'a kuma ina tofa masa kamar yanda ya buƙata, dan ya faɗamin jikinsa na masa zafi kamar ana hura wuta.
         Indai taƙaice muku a wanan dare  bamuyi barciba sam, washe gari muka wayi gari jikinsa ya rikice, da yayi tari sai jini, tun yanayi a ɓoye harna farga da hakan, sai dai ya hanani na faɗama kowa, a cewarsa zasu tafi asibiti gobe idan ALLAH ya kaimu zai samu sauƙi insha ALLAH. Badan hankalina ya kwantaba na yarda.
      Zuwa bayan sallar la'asar baba yaje gida ƴaɗan watsa ruwa dan tare damu ya yini sai ga Alhaji Ali (Dad) Alhaji Sadi Kokino, Alhaji Nasir (Uncle Nasir) da wasu mutane biyu daban saniba sunzo dubashi wai. Da yake muna falon ɗakin da yake kwance sai nace su shiga yana ciki, caraf Rahma ta riƙemin hannu tan girgizamin kai hawaye cike da idanunta amma ban fahimtaba, duk zatona damuwar ciwon nasane kawai, dan ita da Wasila tunda gari ya waye suke kuka, amma da yake Rahma tafi Wasila wayo a lokacin sai nata yafi yawa. Suna shigewa ta miƙe zaram ta kama hannuna tana nunamin ɗakin, mamaki abin ya bani na hau mata faɗa akan bata da bakine?. Har sannan bata tankaminba, kanta dai taketa faman jujjuyamin da fusgar hannuna muka zagaya ta Window.
        Ban taɓa ganin tashin hankali mai muni irin na wannan ranaba, dan kuwa zagaye muka hangi su Alhaji Kokino akan Abdul-aziz, sun lulluɓa masa wani jan ƙyalle suna wani kalar yare da su kaɗai suka san mi suke faɗa, duk yanda naso ɗaga ƙafa naje cikin ɗakin dagani har Rahma mun gagara hakan, a gaban idanunmu Nasir ya shiga zubama Abdul-aziz wani ruwa yana surkulle, sannan ya hau kansa yay....ya ya...yay fasiƙanci mafi muni da shi”. Umm-Anum ta ƙare maganar da fashewa da wani irin matsanancin kuka mai cin rai da zuciya, numfashin ta sai sama da ƙasa yake tamkar zata shiɗe.
      Tsitt falon yayi babu maiyin koda ƙwaƙwaran motsi, da alama dukansu sunyi suman zaune ne.
     Umm-Anum dake kuka tamkar ranta zai fita ta cigaba da faɗin, “Yana kuka da roƙonsa karya aikata masa wannan aiki maimuni, ga aman jini yanayi amma sam Nasir bai sauraresaba, sai da ya biya buƙatar zuciyarsa Ali ma yayi, Kokino ma Yayi. Duk muna kallonsu ni da Rahma, sai dai ko motsin kirki mun gazayi balle wani yunƙuri har suka fito suna kuka. Fitowarsu tayi dai-dai da dawowar baba tare da Mama Maryam. Sai ji kawai mukai suna faɗin Abdul-aziz ya rasu. Iya abinda naji kenan ban sake sanin mi nake cikiba sai a Saudia, shima ban tuna komaiba makamancin hakan sai shekaran jiya dana farka tamkar mai barci naga Anuwar da Abbunsu tare dani............✍
     10
__________________
ZAFAFA 2021
_______________

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
 
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Kwace wannan kodai itama su Dad sun ƙwamusheta ne🤣, na barku a gidan Alhaji babba kunata jira, yo sakawa sukai nimafa akai kidnapping ɗina, da ƙyar na fito a inda suka ɓoyeni😪🚶🏻🚴🏼.

Ku fara da waɗanan kafin na ƙara editing sauran na turo muku da safe idan ALLAH ya kaimu💃🏻. Yanzu kam mankaina ya tsiyaye sai an ɗura wani😣😪😫🚶🏻🚶🏻.

__________________
ZAFAFA 2021
_______________

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
 
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇+

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Page 62

....................Wani irin tsuma jikin Jay ya keyi irin wanda kowama bai taɓa ganiba, idanunsa sunyi masifar rinewa abun tsoro, duk wata gaɓa ta jikinsa ta sake buɗewa, ƙwanjinsa ya kumbura hakama jijiyoyin kansa dana dukkan sassan jikin nasa. Da sauri Alhaji babba daya fahimci komai zai iya faruwa a wajen dan yasan wanene jikansa da zafin zuciyarsa. yay azamar riƙo Jay ya rungume a jikinsa, duk da neman ƙwacewa da ya keyi bai sakesaba. sai ma taimaka ma Alhaji babba da Uncle Sulaiman yay suka danne Jawaad ɗin yanda bazai iya tashiba duk yanda yaso hakan. Kuka kawai ya fashe dashi dan zuciyarsa tai masifar kaiwa maƙura, Alhaji babba ma kuka ya keyi. ya kalli su Dad yana faɗin, “Amma Ali ka cuceni, yanzu kunsan da wannan zaluncin da kuka aikata amma harka iya zuwa neman auren Rahmah a wajena?”.
        Cike da tashin hankali da tsoron Jawaad dake a cikin idanunsu ƙarara Dad yace, “Munyi hakane domin rufe sirrinmu, dan bayan mun gama aikata abinda bokanyarmu tace ga Abdul-aziz sai kawai mukaci karo da Rahama da Bilkisu a bazata duk suna kallonmu ashe, duk da munsan asirin dake tattare damu bazai bari su iya komaiba a kanmu hakan bai hana  hankalinmu mummunan tashi ba, a take muka aika ɗan aike wajen bokanya, mukuma mukabi ayarin masu kukan mutuwa da jimami. Kafin a gama kammala haɗa gawar Abdul-aziz muka sake samun ɗan saƙo daga bokanya akan bilkisu da Rahmah. andai rufe bakin Rahmah kamar yanda bokanya ta faɗa har abada bazata sake tuna abindama ta ganiba balle wani ma yaji daga gareta, Bilkisu kuwa babu yanda za'ai bakinta ya rufu sai dai ta haukace, hakan kuma bazai tabbata ba sai idan data farka za'a bata ruwan tsafin da bokanya ta aiko dashi. Musan mu bazai yuwu muyi hakaba, dan haka Nasir ya kawo dabarar zuwa ga Humaira (Mom) da Mama (Mama Atika) dan ya sakasu suyi mana wannan aikin ta hanyar daya dace tunda suma akwai nasu burin akan dukiyar Abdul-aziz........”
      Kuka mama atika da Mom suka fashe dashi. mama Atika tace, “Wlhy ALLAH ne shaidarmu baku sanar mana akan hakan zakuyima Bilkisu asiri ba, Nasir ya samemu lokacin da aketa shirin fita da gawar Abdul-aziz, mukuma isowarmu kenanma babu jimawa. Yace muyi ƙoƙarin bama bilkisu ruwan maganin, ta hakane kawai zamu sami damar mallake duka dukiyar da Abdul-aziz ya tar.......” sai kuma ta kasa ƙarasawa ta fashe da matsanancin kuka. Uncle Nasir ya kalleta shima yana kukan,
         “Ki ƙarasa mana mama, ai duk kece silar komai, kece kike mana huɗuba akan karmu yarda kowa ya fimu a ƴaƴan baba, kece kika saka ƙiyayyar Abdul-aziz a ranmu, a cewarki an auro uwarsa a bayan baya amma ɗanta yazo yafi kowa arziƙi a gidan harda ƴaƴanki, bayan kuma mune ya dace muyi wannan arziƙin saboda kece matar baba ta farko, mukuma mune ƴaƴan farko a gidan. A dalilin wannan huɗubar taki na jefa kaina a halaka, tun bana ɗaukar huɗubar Alhaji Ali da Alhaji Sadi har suka fara tasiri a raina, nidai burina kullum na wuce Abdul-aziz arziƙi dan na faranta miki rai. hakan yasa duk muguntar dasu Alhaji Sadi suka kawo shawarar a aikatama Abdul-aziz na dinga biye musu, har takai sunyi ƙokarin jawo Abdul-aziz cikin tafiyarmu, dan har wajen bokanya an kaisa da yaudarar zata bashi maganin sammune saboda magautan siyasa. Ko'a hakanma saida ya tirje, nine naita lallaɓarsa harya amince ya bimu, koda yaje yaga abinda muke nufin ɗorasa a take ya bijire mana ya kuma nuna ɓacin ransa mai tsanani akan hakan. Sai dai zukatanmu sun rigada sun bushe a lokacin. gani muke kamar zai tona mana asirine. dan haka muka gaza ƙyale rayuwarsa ta huta, duk wani burinsa na aikata alkairi ga talakawansa mun daƙilesa ta hanyar asiri da muzgunama rayuwarsa, kowane aiki munyi bake-bake a kansa tare da handame dukiyar da aka keɓe danyin ayyukan, daga ƙarshema bokanya ta bamu tabbacin jinin Abdul-aziz zai taimaki tafiyarmu, dan haka muyi amfani dashi, kafin hakan kuma dolene muyi fasiƙanci dashi. Jinin Abdul-aziz shine jini na farko da muka fara salwantarwa, dan da duk abinda zamuyi na tsafi da jinin dabbobi mukeyi. Amma nasarar da muka samu da jinin Abdul-aziz yasa burikanmu sake faɗaɗa, muka fara sadaukar da makusantanmu. Mama da humaira sune suka ɗurama Bilkisu maganin da bokanya ta bamu bisa taimakon Uwaisu, mukuma lokacin mun tafi bizne gawar Abdul-aziz.
          Sanda muka dawo mun iske bilkisu cikin hauka tuburan, hakan ba ƙaramin daɗi yay manaba kuwa, dan asirinmu kam dai munsan ya rufu kenan. Ni na bada babbar ƴata kamar yanda bokanya ta sharɗanta mana, na kuma bada na Mama (Mama Atika) sai dai bokanya tace ba'a lokacin take buƙatar Mama ba, dan tana hango zatai mana amfani sosai a tafiyarmu, haka na musanya jinin Mama dana Mama Suwaiba da Mama Maryam, na kuma haɗa da matata ta farko. Shima Alhaji Ali aka buƙaci ya kawo, shi a take ya bada na Mamansa da ƙanwarsa, da ɗansa na biyu, sai dai kuma nace bai isa ya bada na ƴar uwataba (Mom), wannan dalilin yasa ƙungiya tai masa lamuni akace ya bada na wata matar idan yanada ita, kokuma ya ƙara aure, sai kuma jinin ƴarsa babba mace shima. Hankalinsa ya tashi dan yana tsananin son Shahudah, a lokacinma batafi shekara huɗu da wata bakwai da haihuwaba, yayta roƙo da neman alfarma akan zai canja da wani. Da farko Bokanya bata amince ba, sai bayan kusan kwana biyu dayin hakan ta bashi umarni akan ya auri Rahmah, hakan shine kawai zai kawo sake rufuwar asirinmu, sannan idan Shahudah ta girma yay ƙoƙarin haɗata aure da Jawaad, nanma zamuci moriyar hakan, indai ya aikata haka ƴarsa zata tsira da matarsa, idan Rahmah da ta haihu sai ya bada duk abinda ta haifa madadin Shahudah. Da wannan shawara da umarni yay amfani, na shige masa gaba ya samu auren Rahma ta wajen mahaifinta, dan lokacin Mama Maryam ta rasu. Tabbas badan baƙin asirin da mukaima Rahma ba bazata taba yarda ta auri Ali ba, duk da kuwa abinda ya faru kusan shekara bakwai a lokacin, amma  bata da wani zaɓi, dan ta ko'ina mun gama ƙulleta.
     Kafin auren Rahma da Ali ya tattara su Humaira ya bar ƙasar dasu, wannan duk yana cikin dabarun karta tada hankalintane akan za'ai mata kishiya, shi kuma Ali yana matuƙar sonta bayason tashin hankalinta. Sai da ya maidasu da kusan wata biyar sannan akai bikin, lokacin Bilkisu ta gudu daga gida saboda asirin da muka kuma tafka mata aka kai gidan Alhaji Kokino, burinmu haukanta ya nisan tata da gida har abada koda ƙasar waje ne ma taje. Badan Ali nason Rahma ya aura ba. bayan bikinsa da Rahmah itama ya ɗauketa daga ƙasar ya maidata Ghana da zama duk a cikin shirinmu, sai dai kuma acan ɗin saita gamu da wata ƙawa data tsaya tsayin daka wajen taimakonta da addu'oi ganin kamar batama cikin hayyacinta a rayuwar aurenta da Ali. ba komai yaja hakanba sai ganin yanda Ali ke gallaza mata, bata taɓa yunƙurin barinsa ba ko faɗama ƴan uwanta, sai dai tai kukanta ta share hawaye. gashi tana zuwa ta samu ciki kuma. Ganin matarnan zata buɗe mana aiki ya sake ɗakkota ya maido ta nan ƙasar, inda mukai zaman dakon haihuwarta....” Kuka ya sarƙe Uncle Nasir ya kasa cigaba, sai Dad da shima ke kukanne ya cigaba da faɗin,2

STORY CONTINUES BELOW

__________________
ZAFAFA 2021
_______________

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
 
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

________________

            “Tabbas na zalinci Rahama, dan a zamana da ita bata taɓa jin daɗiba koda na awa ɗaya, daga hantara sai ƙyara da gallazawa a tsakanina da ita. Bantaɓa bata ƴanci na matar aure ba. Abincima nakan batane tamkar wata dabbar da nake turka, kullum cikin roƙona take daban haƙuri amma ban taɓa saurarentaba, tunda cikinta ya cika watanni bakwai ta fahimci manufata a kansa sai hankalinta ya sake tashi, zuciyarta ta bushe, ta daina kuka akan dukkan gallazawar da nake mata, ta maida hankalinta wajen addu'oi akan ALLAH yakare mata cikinta, ƴan uwanta duk wanda yazo wajenta ko ƴan uwana roƙonta shine su tayata addu'a ta haihu lafiya. Daga randa na fahimci haka saina hana kowa shigowa gidan har ƴan uwana, na saka maigadin da babu wanda yake bari ya shiga saida izini na. Hakan ya ƙara saka Rahma a ƙunci da damuwa, nikam ko'a jikina ban taɓa jin tausayintaba, burina kawai ta haihu na samu cikar burina. A wannan halin cikinta ya cika watanni tara da wasu kwanaki, haihuwa kawai muke saurare, bana yarda nai tafiya mai nisa dan karta haihu bana nan, dama gashi na hana kowa shigowa gidan, na kuma ƙulle bakunansu da asiri har mahaifinta da ƴan uwanta. A wani dare ta farka da naƙuda, babu ko tausayi nazo kanta na tsaya, duk taimakon data buƙata naƙi yimata shi, haka taita wahala har wayewar gari bata haihunba, tunanin kar abinda zata haifamin ya mutu nayi asara ya sani shiryawa na nufi wajen bokanya ni da Nasiru, ko zamu samo wani taimakon da zamu bata ta haihu. Lokacin da muka dawo sai muka isketa ta haihu, sai dai babu ɗan sai ita kaɗai. Hankalinmu ya tashi, muka shiga mata tambaya sai tahau dariya da faɗin, “UBANGIJI baya zalinci ga kowa sai dai bawa ya zalunci kansa, jinin jinina yafi ƙarfinku azzalumai, ALLAH ya cire ƙwai a cikin ƙaya sai dai ku mutu, a yau kuma ALLAH ya tunatar dani duk abinda kuka binne akan yah Abdull, babu shakka kuma saina tona muku asiri, sai duniya tasan kuɗin su wanen........”
       Wani wawan mari na ɗauke fuskarta da shi tare da buga kanta a bango har saida ta suma, kafin na shureta da ƙafa ta farfaɗo, a hakanma bakinta bai mutuba, gaya mana duk maganar da tazo bakinta takeyi, hakanne ya harzuƙamu muka kwasheta zuwa wajen bokanya. A can ɗinma bakinta bai mutunba, ta dinga faɗa mana jininta shine jini mafi tashin hankali da zamu salwantar, “Daga wannan ranar bazaku sake samun kwanciyar hankaliba azzalumai, insha ALLAHU wataran sai Ƙaddara ta haɗa Jini da jini sun addabi jininku, Jawaad da ɗiyar dana haifa da izinin UBANGIJIN al'arshi sune zasu zamewa rayuwarku barazana da tashin hankali tun anan duniya, kuma in ALLAH ya yarda sune sanadin tonuwar asirinku a duniya, waɗanan kwayayen guda biyu sai sun kunna wuta bisa kanku ku ƙayoyi kun ƙone ƙurmus kafin kuje ga UBANGIJI shima yay muku nasa hukuncin. Sai kun tuna wannan ranar da wannan furucin da izinin ALLAH. Daga yanzu ku zauna zaman saurare da cikar lokacin da ƘWAI zai fita a cikin ƘAYA ta inda bakuyi zato ko tsammani ba. Domin biyune zasu ɗau fansa tare da ɗunbin al'ummah”.
      Wannan shine furucin Rahma na ƙarshe a garemu, muka aikata mata mummunan aiki tamkar yanda mukaima duk wanda muka salwantar. Duk da kuwa maganganunta sun shigemu, kuma tabbas sunyi tasiri a zukatanmu. Iya bincike bokanya tayi ko zata samo inda abinda Rahama ta haifa yake amma hakan ya gagara, abindama take gani jaririyar ta mutu, tun zukatanmu na rawa akan hakan har muka cire abin a ranmu muka cigaba da harkokin gabanmu, ciki harda aƙidar fyaɗe wa ƙananan yara domin amsar budurcinsu kawai kamar yanda bokanya ta sharɗanta mana. Rayuwa ta shuɗa, duniya ta samu a garemu, dan kuwa dukiya ta zauna ga kowanmu, duk abinda bokanya ta sharɗanta mana bi mukeyi, musamman ma ni da bana tsallake komai duk dan gudun kar bokanya tace na bada jinin mamana (Shahudah), haka kawai ALLAH ya jarabceni da matsanancin sonta fiye da suran ƴaƴana. gashi kuma bokanya tace min akwai nasarata tattare da ita, dama ƙungiya baki ɗaya, amma hakan bazai tabbata ba sai anyi aurensu da Jawaad. Da wannan damar mukai amfani wajen jan Jawaad jikinmu, duk da ita Humaira dai batasan ai nahin manufar ba, hankalinmu bai kwantaba har saida akai aurensu, sai dai kuma baiyi nisaba komai ya lalace, a lokacin mu kaɗai mukasan a irin tashin hankalin da muka tsinta kanmu, duk da daga baya bokanya tace mubarsu zatai wani aiki a kansu, amma a aura masa wata matar cikin ƴaƴan family ɗinsu, hakanma zai taimaka mana, sai dai sam Jawaad yaƙi hakan, mun buga ta kowanne fanni babu nasara, tun daga wannan lokacin komai na ƙungiyarmu ya ringa samun tangarɗa da ruɗani, ciki harda shigowar wani maharbi rayuwarmu, sai dai daga baya shi munyi maganinsa ta hanyar salwantar da rayuwar duka iyalansa dashi kansa. Ƙwatsam muna a wannan ruɗanin kuma sai ga Bilkisu ta shigo rayuwata a bazata, inda naci karo da ita a gidan ƴar uwata. Banyi sakaciba na ɗakkota, a washe gari kuma nakai sunanta ga bokanya kamar yanda mukeyi akan budurwar da duk muke buƙatar budurcinta, sai dai kuma Bilkisu sai tazo da banbanci ga sauran, dan bokanya tamin alƙawarin inhar na mallaki budurcin Bilkisu na cika dukkan sharuɗan ƙungiya, dukiyata zata sake haɓaka, zan kuma samu nutsuwa akan komaina. Tamin alƙawura da dama game da yarinyar, sai dai kuma komai bai yuwuba, dan yarinyar tana tattare da wasu sirruka da muka gaza ganewa har zuwa yau, ta zama sanadin rushewar abubuwa masu yawa a garemu ciki harda aurenta da Jawaad, tashin hankalin da muka fahimci yana tunkaromu a dalilinta yasa muka sadaukar da jininta ita da Jawaad.........”
    
__________________
ZAFAFA 2021
_______________3

STORY CONTINUES BELOW

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
 
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

________________
   
       “Babban sirrin dake tattare da ita shine amincewar UBANGIJI game da furicin mahaifiyarta game daku”.
          Wata murya ta bada amsa ga Dad a bazata. Gaba ɗaya falon suka juya suna kallon mai maganar cike da mamaki da al'ajabi. A bazata Bilkisu ta miƙe zaram tana share hawayenta, jikinta na wani irin tsuma da rawa tace, “Inna! Baba! Firdausi da gaske kune? Kodai gizon da kuka saba yiminne?”.
    Fuskar Baba cike da murmushi yace, “Mune ƴata ba gizo muke miki ba, mune tsaye a gabanki bayan rabuwar ƙaddara ta tsahon shekaru, na godema UBANGIJI daya sake haɗamu Bilkisu, na godema ALLAH daya kawoni wannan ranar dazan sauke nauyin da ɗan uwana abokina ya ɗauramin tsahon shekaru”.
     Da gudu Bilkisu ta nufesu ta rungume Inna da firdausi tana mai fashewa da matsanancin kuka, suma kuka suka sanya harda Baba. Mai martaba ne yay gyaran muryar da ta sakasu yin tsuru lokaci guda, cikin nutsuwa yace, “Su wanene ku? Mi kuma ya kawoku nan?”. Kafin a cikinsu wani ya samu damar bada amsa Jabeer dake bayansu tsaye yace, “Ranka ya daɗe suna tare da magana mai muhimmanci, tun da sassafe suke a gidan Jay suna jira dan suga matarsa, duk korar da maigadi yaymusu basu tafiba. Kasan yanayin da ake ciki, shinefa drivern sa ya kirani ya sanarmin, da naje bayanin da sukaiminne yasa na gamsu na kawosu nan”.
    Umarnin ƙarasawa ciki aka basu, sai da suka zauna da mika gaisuwa Bilkisu na maƙale da inna sannan takawa ya bama baba damar yin bayani akan abinda ke tafe da su. Baba ya sauke nannauyan numfashi yana mai duban Bilkisu da Inna ke sharema hawaye, sai kuma ya duƙar da kansa ƙasa ya fara magana da rawar murya. “Sunana Abdullahi, babban amini ga malam Adamu makaho. Abotarmu ta farane tun lokacin daya kama haya a gidan da nake, tun muna iya gaisawa da mutunci sama-sama tsakanin iyalanmu har muka zama aminai, matanmu ma haka. Kamar yanda na daɗe ban samu haihuwa ba Adamu ma hakane, cikin hikimar ALLAH sai ga ciki a jikin matanmu kusan lokaci guda ni da shi. Matata itace ta fara haihuwar ɗiya mace, ga tanan (ya nuna Firdausi) dan dama ta riga matar Adamu samun ciki da kusan watanni biyu zuwa uku. Kamar yanda al'adarmu take matata ta tafi wankan jego ƙauye, bayan tafiyarta da kusan wata ɗaya matar Adamu ta wayi gari da naƙuda, hankalinmu ya tashi dan ba watan haihuwarta bane, a haka muka ɗauketa zuwa asibiti, ƴan kuɗin sana'arsa ya ƙundume ya miƙa akai mata duk abinda ya dace, sai dai daga ƙarshe likita yace sai an mata aiki, dan ɗan dake cikinta ya ruɓe, ma'ana yadai mutu ma, barinsa itama zai zamarwa tata rayuwar barazana. Hakan ba ƙaramin tada mana hankali ya sake yi ba, gashi ƴan kuɗaɗen hannunmu sun ƙare, kuma suna buƙatar kuɗi kafin su mata aiki. Adamu ya barni a asibiti ya hau acaɓa ya kaisa can anguwarsu gidan iyayensa dana sani, dukda dai ya sanarmin mahaifiyarsa aka haifa a gidan (Alokacin Adamu na gani da ido ɗaya fa) sai dai kuma bai wuce awa biyuba sai gashi ya dawo rai a ɓace alamar bai samo komaiba. A gabana ya labartama Asiya komai, dukda halin ciwo da take ciki saita kwantar masa da hankali, tace yaje wajen yayanta Alhaji Ali (Dad) tasan zai taimaka musu. Baiyi musubu ya jani muka tafi tare, gidane katafaren gaske mai ƙyau da gate, a lokacinma duk gidan da kaga gate to lallai maishi ya tara, munta ƙwanƙwasawa amma ba'a buɗe mana ba, Adamu ya tura ƙofar cikin haushi sai gata ta buɗe a bazata, sai da muka lalleƙa babu kowa sannan muka shige cikin gidan batare da tunanin komaiba. Munta sallama a ƙofa nanma dai bamuji motsin kowaba, sai wani irin nishi da gurnanin kuka. Babu tunanin komai Adamu ya nema cusa kansa, na riƙesa ina girgiza masa kai akan karya aikata haka, tunda ba gidanmu baneba, kuma akwai mace a ciki. Hankalinsa dake a tashe na halin da asiya ke a ciki yasa bai saurareniba, ya fisge hanunsa ya shige ciki babu ko sallama. Duk da a tsorace nake banida zaɓin daya wuce bin bayansa nima. Sanda muka shigo cikin falon sai mukaji kukan ya yawaita, gashi ana kukan ne da addu'ar fatan neman ɗauki daga ALLAH, Adamu ya kalleni na kallesa, sai kuma duk muka kalli ƙofar da muke jiyo kukan. Kukan jinjiri ya sakamu dawowa a hayyacinmu batare da mun shiryaba, Adamu ya matsa jikin ƙofar da sauri yana magana. Daga ciki aka amsa da faɗin “ko wanene ya shigo dan ALLAH” kamar bazai shigaba sai kuma ya afka kansa tsaye, duk kiransa da nake famanyi bai saurareniba. Haka nabisa na leƙa sai dai ban shigaba, daga ƙofa na hango mace durƙushe tana naɗe jariri dake cikin jinin hauhuwa a zane, ita kanta inda take durƙushen duk jinine. Adamu na tsaye hankalinsa a tashe yana kallonta. Ɗagowa tai ta miƙa masa jinjirar jikinta na rawa, sai kuma tai cak tana kallonsa, kallo irin na kamar na sanka kokuma ina nasanka? Da rawar baki tace, “Mai kama da Baba!”.  Sai kuma ta girgiza kai da sauri tana hawaye. “Wannan ba lokacin tunanin hakan baneba, bawan ALLAH koma miya kawoka gidannan nasan UBANGIJI ne ya aikomin kai danka taimaki wannan baiwa da batasan komai ba sai iskar duniya data shaƙa a yanzun. Dan ALLAH ka ɗauketa, ka nisantata da gidannan, itaɗin ɗiyatace, mijina ke neman kasheta saboda matsafine, kaimin alfarmar saka mata suna BILKEESU, karka taɓa faɗa mata bakai ka haifetaba dan girman ALLAH har sai takai shekaru ashirin a duniya, ka binciki ɗan gidan tsohon shugaban ƙasa daya rasu, JAWAAD ABDUL-AZIZ ka haɗata dashi, ka sanar masa suɗin ƴan uwan junane, ɗiyar Rahama ƙanwar mahaifiyarsa Bilkisu ce. Suyi ƙoƙari su haɗa hannu wajen binciken mai gidannan da duk abokan da yake mu'amula dasu, babu isashen lokacin dazan maka bayani aka kaina da abinda ya faru, amma nasan komin daren daɗewa lokaci zai fiddo komai dan sharri baya ɓoyuwa a duniya. Ka ɗauki wancan akwatin akwai kuɗi da kayanta a ciki na baka halak malak, dan ALLAH ka bata tarbiyya irin ta addini, karka bar rayuwarta ta tarwatse da ruɗanin duniya, ka faɗa mata ina tsananin ƙaunarta fiye da komai dana mallaka a duniyarnan. Kai maza ka fita, suna gab da dawowa, idan suka iskoka zasu halaka ka da ita da ni baki ɗaya, ni kuma bana fatan hakan”. Ta ƙare maganar da wani irin kuka mai cin rai da zuciya. Motsin buɗe gate da mukaji ya sakamu fita da gudu, kafin mukai ƙofa mukaji ana shirin buɗewa, wani ɗaki muka shige da gudu muka ɓuya muna leƙen masu shigowar ta taga, a gaban idanmu Wannan (Uncle Nasir) da wannan (Dad) suka shiga ɗakin da matarnan take, duk maganganun da sukai ita dasu muna saurarensu, har lokacin da suka fita da ita daga gidan. Da ga ni har Adamu kuka muke rurus, sai dai bamu da wani ƙarfin ikon sakawa ko hanawa, sannan muna son cika mata alƙawarin fita da ƴarta daga gidan cikin aminci. Sai da muka tabbatar motarsu ta fice a gidan sannan muka fito muma muka fice da gudu, cikin amincin ALLAH mai gadin gidan yanzunma bai ganmuba ya shige cikin ɗakinsa kamar ɗazun da muka shigo yana ciki.
     Da kuɗin da matarnan ta bama Adamu akaima Asiya aiki, aka cire ɗanta mara rai, bayan an kamala mata aiki aka kaita ɗakin hutu. Adamu yakai jaririya da ya roƙa wata nos ta gyara ya kwantar kusa da Asiya. Bayan ta farfaɗo cikin dare bai ɓoye mata komai game da bilkisu ba, ita kuma saita amsa da daraja ta rungume tana kuka, dan koba komai ai ɗiyar ɗan uwantane. Abinda kawai Adamu ya ɓoye ga Asiya shine ɗan uwanta matsafine, bai faɗa mata wannanba, ya kuma roƙeni na ɓoye wannan sirrin dan ALLAH har sai lokacin da jaririya Bilkisu takai mizanin shekarun da mahaifiyarta ta roƙa kafin mu bayyana komai ga kowa. Na masa alƙawari da karɓar amanarsa, na rufe wannan zance a raina tamkar yanda shima ya rufesa ga kowa nasa suka cigaba da rainon bilkisu, har ALLAH yasa takai shekarun girma, sai dai kafin lokacin da Adamu ya cika alƙawarin sanar mata ita wacece ALLAH yay masa rasuwa sakamakon bigesa da mota tayi, itama kuma Asiya ALLAH yay mata rasuwa kafin shi. Musan ƴan uwan Adamu bazasu ɗauki Bilkisu ba, dan sun saka wasiwasi a ransu game da ita tun tana jinjira. Na ɗauki Bilkisu na cigaba da kulawa da ita kamar yanda Adamu yayta roƙona gab da numfashinsa zaibar jikinsa. Sai dai kuma na gaza cika alƙawarin lokacin da taƙadin yaron mai gidanmu ya shigo rayuwar gidan............” ya ƙarashe labarinsa da zaman Jazuga a gidansu, har faruwar komai na abinda bilkisu tai musu, da maidasu ƙauyensu da Alhaji Lado yayi, tare da gargaɗi da baza abokan Jazuga a ƙauyen suyi gadinsu. Doguwar jiyyar Firdausi da sukasha wadda tai kamar bazata rayuba har tsahon shekara kusan guda kafin ta warke ayi bikinta da ɗan uwanta, gashi a yanzu sunada yara uku, Musa (Fharhan), Abbas, sai bilkisu da firdausi taima bily takwara saboda ƙauna da soyayya haɗe da ɗunbin bege a gareta.1

STORY CONTINUES BELOW

       Jin wannan labari daga bakin Baba ya saka falon sake ruɗewa da koke-koke, Bilkisu kuwa data gigice tamkar wadda ciwon hauka ya sama lokaci guda ta miƙe zaram tana nuna Dad jikinta na wani bala'in karkarwa. “Baba kana nufin shine Mahaifina?”.3

      “Tabbas Bilkisu shine mahaifinki?”. Ai ganin Bilkisu kawai akai ƙasa wanwar ta sume. Dad kuma ya fashe da wani irin gigitaccen kuka da ƙwalla ƙara, ya shiga buga kansa jikin bango yana ihu maiban tashin hankali da faɗin “Tabbas Rahmah maganar ki ta zama gaskiya, Alaƙar ƙaddarar jiji dake cikin jini ta tabbata.....”. Ƙoƙarin riƙesa ƴansanda sukeyi, yayinda can kuma aka rufu kan Bilkisu ciki harda Jawaad daya ƙwace daga riƙon da Alhaji Babba yay masa.2
         Bayyana muku tashin hankalin da waɗanan mutane ke a ciki a wannan lokaci zaici tsahon lokaci bamu gamaba, komai ya sake hargitsewa da ruɗewa, dole ƴan-sandan dake a waje suka shigo cikin gidan tare da dogarawan sarki wanda shi yama rasa abin faɗa tsabar mamaki, a da gani yake babu wata ruɗaɗɗiyar rayuwa irin tasa, sai a yau yaga wadda tafi tasa muni da tashin hankali.
            Da ƙyar aka iya fita dasu Dad daga gidan, suna kuka da roƙon a yafe musu amma babu wanda ya sauraresu, sai ma tsinuwa da sukesha daga bakin kowa harda ƴaƴansu kansu da matansu. An shiga ƙoƙarin yayyafama waɗanda suka suma ruwa harda Shahudah da Bilkisu, da Mama Atika. Wadda itakam da alama ma dai faɗuwar da tayi tazo da sakamakon paralysis, dan ta gaza motsa komai nata sai ido takebin mutane da shi kawai tana kuka.
______________

          Komai fa ya sake rikicewa, gari ya ɗauki magana da ba'asan tayaya ta fita daga gidan Alhaji babba ba, sai daga baya aka fahimci camera aka saka jikin su Dad da ba'asan wanene ya sakaba, ta naɗe komai daya faru a gidan Alhaji babba, lokacin da aka maidasu office kuma a take aka fidda komai ta kafafen yaɗa labarai.
        Lokacin da takawa ya baro gidan Alhaji babba zuwa inda ake jiransa zasuyi meeting da ƙyar suka kai saboda hargitsewar da garin yayi, matasa ta ko'ina sun fara fitowa zanga-zanga da makamai akan sufa sai an basu su Dad sun kashe. Kamar wasafa saiga zanga-zanga ta fara faɗaɗa, dan harda ƴammata da zawarawa a cewarsu suma sunabin kadin haƙƙin ƴan uwansu dasu Dad suka lalatama rayuwa ta hanyar fyaɗe. Idan ba'a basu su Uncle Nasir ba zasu bankama station ɗin da aka ajiyesu wuta.
        Sai kuma rukunin magidanta da tasu zanga-zangar ta ɗauki manufa akan kisan tsohon shugabanƙasa Abdul-aziz Yousif Tafida, a cewarsu sumafa sai sunbi kadin jinin adalin shugabansu. Tofa jama'a sun fusata ainun, kowane titi ka zagaya mutane ke tittiɗowa zuwa station ɗinsu Jawaad da aka ajiye su Alhaji Kokino, tun jami'an tsaro na ƙoƙarin kwantar da tarzomar dake nemans harfa al'amarin ya nema gagararsu sai da aka kawo wasu jami'an tsaron kala-kala. Amma duk da haka al'amarin ya gagara. daga ƙarshema sai suka zagaye hall ɗin dasu Takawa sukai zaman meeting, acewarsu su fito su bada damar a fiddo musu dasu Kokino kokuma su haɗa dasu. Dan bazasu taɓa yarda sai ankai su Dad Kotu ba, su duk duniya basuga alƙalin da zai iya yima su Dad shari'a ba sam. Gara kawai su kashesu a haɗu a kotun UBANGIJI kawai.1

★★★★★★★

         Har dare gari yaƙi lafiya, tamkarma ƙara ƴan zanga-zangar akeyi. Jawaad na gida tare da ƴan uwansa dake cike da ruɗani da tashin hankali wannan al'amari har yanzu kira ya samesa daga office.  Duk yanda yaso ƙin fitar Alhaji babba sai da ya takurashi, acewarsa babufa yanda zasuyi, wannan al'amarin su barma ALLAH kawai shine zaiyi maganin waɗannan mutanen bawai ƙarfinsuba ko dabararsu. Haka ya fita jikinsa duk babu wani daɗi, ya sumbaci goshin bilkisu daketa barci yana haɗiye hawayen da suka cika masa ido, tausayin kansu yakeji daga shi har ita, musamman ma ita da nata al'amarin yazo a yanda basuyi zato ko tsammaniba, kenan Shahudah da Bilkisu ubansu ɗaya fa kenan? Bilkisu jininsa ce, jini mafi kusanci da muhimmanci a garesu, jinin wadda take da daraja a garesa, wadda ta yarda ta rasa ranta da farin cikinta a dalilin salwantar da mahaifinsa.
         Bai iya jan motarba sai Hafiz ne yazo har gida ya ɗaukesa, shi kansa halin da yaga garin yake ciki ba ƙaramin sake tada masa da hankali al'amarin yayiba, dare harya rufa amma mutane basu da niyya komawa gidajensu. Da ƙyar motarsu ta samu hanyar shiga station ɗinsu.
              Sun sami su Sir Ahmad cikin tsananin tashin hankali da damuwa, sune sukaimasa bayanin yanda akai komai ya fita har jama'a sukayo wannan gangamin na farautar rayukan su Dad. Ajiyar zuciya kawai Jawaad keta saukewa, tausayin su Qaseem da sauran iyalan waɗanan mutane kawai yakeji, dan haka ya bada shawarar a fita dasu Dad ta ɓarauniyar hanya abar station ɗin dasu zuwa cikin prison dasu ko hakan zaisa a samu sassaucin da hankulan mutane.
       Da wannan shawara ta Jawaad akai amfani, sannan D.G da kansa ya fita yayma jama'a bayani daban haƙuri akan su bari suga idan ba'a yankema su Dad hukuncin daya daceba sai su ɗauki matakin da duk sukai niyya, amma dan ALLAH yanzu su kwantar da hankulansu kodan dare.
       Da ƙyar suka amince akan safiyar gobe su farka da batun shigar su Kokino kotu, kokuma su su ɗauki doka a hannunsu game dasu. Garin baiyi lafiyaba sai da aka sake baza jami'an tsaro, duk yanda su Jay sukaso kwana a gidajensu yau kam ta gagaresu, sunata kai kawo akan mutane har garin ALLAH ya waye.

     
_________________

           Tunda na farka kallon kowa kawai nake, jinake tamkar an kwashemin ƙwaƙwalwa da zuciya an jefar gefe, kukan zuci zanyi kona zahiri? Wane kalar tunani zanyi akan wannan juyayyen al'amari ruɗaɗɗe? Iyayen dana tashi na gani ƙaddara ta juyasu sun zama ba nawa ba, waɗanda ban taɓa kawowa a tunanin hankali da ƙwaƙwalwa ba sune suka zama iyaye na gaskiya. Dad fa? Jama'a kuji wani batu tamkar a tatsuniyiyi da hikayoyin marubuta. Ashe shiyyasa nakejinsa a raina tun lokacin dana fara tozali dashi matsayin yayan innata? Shin murna ya kamata nayi shin kokuwa kuka? Baƙinciki kokuwa takaicin kasancewarsa Ubana ni jininsa? Wane hukunci ya dace dashi game da mahaifiyata da sauran al'ummar da suka cutar suka zalinta saboda son zuciya da ƙwaɗayi da burin duniya da kayan cikinta? Anya badan kalmomin bakina sunyi nauyin da zasu iya zama tuntuɓen harshe wajen aikata zunubiba da ban zazzagesu ga azzalumin uba irin nawaba kodan duniya taji tasan na tsanesa. Inama gaskiya bata fitaba na ciga da kallonsa matsayin yayan inna ba Mahaifina ba, inama ace banga wannan ranarba Mamana ta bari yayi tsafin dani nima. Inama.... Inama..... Inama.....?
      Bilkisu ta faɗa a fili tana rushewa da matsanancin kuka mai cin zuciya. Rungumeta Umm-Anum tayi suka cigaba da rerawa a tare. Kowa ka gani a gidan idanunsa a kumbure babu ko ƙyan gani, su Uncle Sulaiman tun a daren jiya duk sun koma gidansu, anan su kaɗaine zuri'ar Alhaji babba sai su firdausi kuma da Maman Yara da tun jiya tana nan, ganinta ba ƙaramin daɗi yayma Umm-Anum ba, inda itama a wajen maida yanda akayi ta sake buɗe komai dangane da abinda ta sani game dasu Dad ɗin da zamanta gidan Alhaji Kokino na tsahon shekaru dan kawai ta samu damar ɗaukar tukunyar tsafin da akaima Umm-Anum. Ganota da Alhaji Kokino yayi gameda taimakon da suke bama Jawaad ita da ɗan ƴar uwarta Gimba, kashesa da sukayi da kamatan da sukayi sukaita azabartarwa, harma da wasu manya-manyan sirrikansu da taji.
      Nanma dai ansha kuka mai ban tausayi, tare da jera ɗunbin godiya a gareta da addu'oin fatan alkairi. Duk yanda sukaso ganin kwanciyar hankalin bilkisu hakan ya gagara, daga ƙarshema saita fara bleeding, a matuƙar tashin hankali aka kwasheta zuwa asibiti, inda ta samu taimakon gaggawa a wajen Dr Bello. Jawaad baisan mike faruwa ba saida Nabeelah ta kirasa ta sanar masa, hankali tashe kuwa ya iso asibitin.
        To cikin dai ikon ALLAH an samu damar tsaida jinin, inda Doctor yay musu albishir da cewar cikinta na nan bai zubeba, sai dai tana buƙatar samun hutu dan gaskiya ƙwaƙwalwarta da zuciyarta suna cikin tsagwaron ruɗani, har jininta yama hau, idan da bama suyi gaggawar kawota asibiti ba da ba cikin kawai za'a rasaba ita kanta zasu iyama rasatan. To amma Alhmdllh yanzu kam komai ya dai-daita, sai kawai a jira farkowarta kuma aga abinda ALLAH zaiyi..................✍4

Ku dakaceni da sauran zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu idan na kammala editing😊😍😍😘🚴🏼.
3
ALLAH ka gafartama iyayenmu4

Page 63

....................Su Jawaad basu san wainar da ake toyawaba a gari, sai iface-iface suka dingaji da tashin hayaniya, sai kuma hayaƙi daketa turnuƙe sararin samaniya a hankali. Sai sukaga kuma mutane nata fita daga asibitin.
    Gaban Jay ya faɗi, ya zaro waya daga aljihu yay kiran Jabeer dan yaji ko lafiya?. “Boss wlhy akwai matsala, an fito da mutanen nan daga prison za'a kaisu kotu jama'ar gari sun tare motar sun banka mata fetur sun saka wuta. Wlhy duk yanda jami'an tsaro sukaso tsaidawa al'amarin ya gagara, harma an raunata mana ɗan sanda guda daketa ƙoƙarin basu kariya da roƙon mutane su kwantar da hankalinsu kotu za'a kaisu, kuma a yau za'a yanke musu hukunci. Amma sam basu sauraresaba, saima suka nema haɗawa dashi shima, dan acewarua shima nasune”. Innalillahi Jawaad keta ambata zufa na keto masa a duka sassan jikinsa. Dole yabar asibitin ya nufi inda al'amarin ke faruwa..

        Wuta taci su Alhaji kokino sosai kafin ƴan kwana-kwana suzo da masu bada taimakon gaggawa na jami'an tsaro, da ƙyar aka iya samun hanyama motar ta ƙarasa, police kuma suka fara jefa barkonon tsohuwa, da wannan damar aka samu mutane suka fara darewa har aka ƙarasa gasu Dad aka basu taimakon, sai dai kuma ina komai ya gama ƙurewa, dan wutar ta cisu sosai, sunta ihu da neman taimako basu samuba. Waɗanda basu mutunba ma da wahala ace zasu rayu, dan su Dad ko iya gane fuskokinsuma ba'ayi sam. A haka dai aka kwasosu zuwa General hospital inda su Bilkisu suke.
           Faruwar hakan yasa aka baza jami'an tsaron sintiri a kowane titi, tare da kafa dokar hana shiga da fita gaba ɗaya, kasuwanni da kowacce ma'aikata an rufesu ruf an kora mutane gidajensu. Garin yayi tsit, sai gidajen redio dana tv kawai ke aiki, anan mutane kejin halin da ake ciki.
         Kafin a ƙarasa dasu Dad asibiti wasunsu suka sake mutuwa, ciki harda Uncle Nasir kuwa. Suma dai an shiga da sune kawai, amma likitoci sunma rasa ta ina ya kamata su fara basu taimakon daya dace, gaba ɗaya jikinsu ya sale tas, yay jazur tamkar naman dake kusa da wuta ana masa gashi😭.
      Ba ƙaramin tashin hankali su Umm-Anum suka sake shigaba da ganin su Dad, duk da zalincin da sukaima rayuwarsu har hawaye sukai musu. Bama suba duk mai hankali yaga wannan bahagon al'amari dolene ya shiga ruɗani mai tsanani, ya kumaji tsoron wannan mummunar rayuwa da waɗanan mutane suka ƙirƙirar ma kawunansu. Gadai duniyar an tara, kuɗi, mulki, zuri'a, da komai amma an ƙare da tafiya a barsu cikin tozarci da wulaƙanci. Basu karesu daga faruwar kowanne irin bala'iba ko masifa ba, abinda suka tara da wanda suka shuka bai hanasu mutuwaba, bai hana ƙarshensu muniba, wannan shinefa ake kira da BA FARKON BA ƘARSHEN, yakai ɗan uwa bari murna akan aikata mummunan aiki kuma babu abinda ya sameka, bari tinƙaho da taƙama akan kai haƙƙin wani bai sakaka komai sai ƙiba da kwanciyar hankali, bari farin ciki kaine sama dakowa saboda kasancewarka azzalumi, bari taƙama da tinƙahon ka tara kai babu yanda aka iya da kai. Rage buri da hangen haramun domin kawai burge duniya ko morarta dayin bishasha a cikinta. Daure ka nema halak komai wahalarta da ƙaracinta, nisanta kanka daga haramun komai sauƙinta da zaƙinta. Ji tsoron UBANGIJI koda ace baka ganinsa to shifa yana kallonka. Kiyaye ruɗin duniya dana abokan banza ka kama ALLAH da abokan ƙwarai masu nuna maka muhimmancin tsoronsa. Ya ALLAH ka gafarta mana, kasa muyi ƙyaƙyƙyawan ƙarshe. ya rabbi ka ɗauki rayukanmu muna masu cike da ɗunbin tsoronka da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W)🙏🏻😭.13

__________________________________

           Al'amura sun sake ƙwaɓewa, a gaba ɗaya kwanakin satin da suka biyo baya, babu wani farin ciki daga jama'ama balle su Jawaad da iyalan waɗanan mutane. An samo gawar Aunty Mah-Mah (Rahmah) a gidan Dad cikin wani akwatin tsafinsu, ashe lokacin da suka halakata wata gawar daban suka kawo a zuwan itace, shiyyasa Dad ya hana kowa yimata wanka shine yay mata a lokacin. To ashema ba gawarta baceba, gawarta na nan cikin ɗakin sirrinsa da ko Mom ta rantse bai taɓa barinta ta shigaba, ita kuma duk tunaninta bai taɓa kaiwa ga hakanba.
     Abin sha'awa da tsarkake sunan UBANGIJI gawar Rahma fes aka sameta dukda sheɗancin da Dad ya ɗauki tsahon shekaru yanayi da ita. Fuskarta fayau tamkar a yaune ALLAH ya ɗauki ranta. Bilkisu ta rungume gawar tana kuka abin tausayi. Da ƙyar Jawaad ya ɗagata akan gawar shima yana nasa hawayen da baisan suna zirarowaba. Alhaji babba kam yayi dauriya matuƙa, sai dai haɗiyar zuciya kawai yakeyi da kukan zuci. Umm-Anum tai mata wanka aka suturtata. Ɗunbin al'umma daga ɓangarori da dama suka sake sallatar gawar Rahama a karo na biyu, ta kuma samu rakkiyar ɗunbin jama'a zuwa makwancinta na gaskiya.
       An samo zunzurutun kuɗaɗe da kayan tsafi kala-kala da wasu abubuwan a gidan Dad, hakama Uncle Nasir da sauran abokan sheɗancinsu irinsu Kokino. Kamfanoninsu ma an samo abubuwa masu yawan gaske masu matuƙar tada hankali, ciki harda kayan shaye-shaye kala-kala da tabar wuwu buhu-buhu da adadinsa ya tasarma dubu goma. Sai wasu gurɓatattun abubuwan da bama zasu lissafuba gamai sauraro.
     Ƙasa tayi tsitt, manyan dake huɗar kasuwanci dasu data abokantaka sun fito sunata ALLAH wadai da nisanta kansu da ɓoyayyun ayyukan su Dad ɗin, komai dai ya fito fili, anyi walƙiya ijiya taga kowa da komai. Inda aka bar iyalansu da waɗanda aka zalunta irinsu Jay da jiyyar zukata.
     Idan kaga Bilkisu a irin wannan lokacin dole ka tausaya mata, ga laulayin ciki ga tashin hankali da damuwa, sauƙintama ƴan uwanta da mijinta kowa tattalinta yake da burin ganin farin cikinta. Takanyi kukan jin daɗi da ganin ƴan uwanta zagaye da ita, waɗanda ada ta rasa samu.

STORY CONTINUES BELOW

★★★★★★

         Ɓangaren Shahudah kam ba'a cewa komai, ita babban kukanta da tashin hankali bawai ya ta'allaƙa da halin da Dad yake ciki na halin rayuwa da mutuwa bane, babban tashin hankalinta shine ance babu aure tsakaninta da Jay sai dai idan sakin Bilkisu yayi kota mutu, amma bazai yuwu suyi zaman aure a ƙarƙashin miji guda ba ita da ƴar uwarta da suke Uban ɗaya.
      Hakan ba ƙaramin tada hankalinta yayiba, babu kunya babu tsoron ALLAH ta dinga tsinema Dad da jera masa ALLAH ya isa cikin hausarta da koma fitar kirki batayi. Ƙiri-ƙiri ta nema haukata kanta. Mom ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi itama, da abinda ya dameta zataji kokuwa da haukar Shahudah, ko ciwon mama atika, ko kuma nisantarsu da Qaseem yayi?. Dan tun bayan lafawar komai Qaseem ya ajiye aiki yabar ƙasar gaba ɗaya batare da kowa ya saniba sai daga baya sukeji ta hanyar saƙon daya bar musu.

       A yanzu kam kowa burinsa Jawaad da mahaifiyarsa da ɗan uwansa su yafe musu a wannan family, musamman ma waɗanda sukasan sun muzguna masa bisa jagorancin makircin mama Atika da ƴaƴanta.
             Dan samun lafiyar Mama Badiyya ta sake bayyana abinda ta gani Uncle Nasir nayi a wani dare bayan ɗakunansu shinefa ya banka mata baƙin asiri itama ya tauye rayuwarta ta koma ita ba'a duniyaba ba kuma a lahira ba😪.
      Jay dai bai samu zaman sauraren kowaba, dan shi a yanzu ta matarsa ma yakeyi da fatan samun nutsuwarta da abinda ke cikinta.

★★★★★

          A kwanakin da aka cika kwana goma da sakama su Dad wuta shima ya mutu da safe yana ihu da kururuwa kamar yanda su Uncle Nasir sukayi lokacin da suma zasu mutu, ga wani irin kakari maiban tashin hankali, jikinsa kuma ya koma fari fat tamkar babu jini a jiki, gashi dama wuta ta gama ɗaye fatar gaba ɗaya. Da yamma Alhaji Kokino yabi bayansa da Abban Zuhrah, kamar yanda aka binne su Uncle Nasir babu wanka saboda ƙunar jikinsu haka shima Dad dasu Abban Zuhrah aka haɗasu akai musu salla aka biznesu da halinsu. Wata shari'ar dai kam lallai tafi ƙarfin alƙalan duniya, sai dai a jiraceta daga sarkin alƙalai kuma😭🙏🏻.1

     Haka rayuwa take su Dad sun tafi tamkar ba'ayusuba a duniyar dagasu har ayyukan da suka shuka, a hankali hankulan jama'a sun fara dawowa jikinsu daga abinda ya faru, sai kuma labarai da maida yanda akayi da har yanzun sun gaza ƙarewa. Yayinda akebin gidajen da suka bari ɗaya bayan ɗaya ana rushewa, wanda suke ciki kuwa ana barinma iyalansu dan su sami matsugunnin rufama kansu asiri. Masu ƙarfin imani a cikinsu kuwa sun tsame kansu daga komai na dukiyar acewarsu basa buƙata, dan dukiyace ta tsafi, sun gwammaci su ƙare rayuwarsu a talauci da su zauna a ƙarƙashin ikon dukiyar jinin al'umma.

BAYAN WATANNI BIYAR.

        Abubuwa sun sake lafawa, harma wasu da yawa sun faffaru, ciki kuwa harda komawar Umm-Anum Saudia tare da ƴan uwanta suka sauke faralin miƙama ALLAH godiya daya kawo musu ƙarshen komai cikin rahamarsa da hikimarsa. Bayan kammala aikin hajji su suka dawo ita kuma aka barta a can tare da mijinta da Anum, Anuwar dai kam yayi uwa yayi maɗaukiya a ƙasarsa ta haihuwa, harma an ware masa ɗaki guda a gidan Jawaad yana zaune tare dasu.

         Ansha bikin Nazifa da Ummie, harma da Zuhrah da wani ɗan uwansu da yake bala'in sonta dama abbanta ya ƙi bashi, yanzu bayan lafawar komai ya dawo, acewarsa ai ita yakeso, kuma ba ita ta aikata abinda ya faruba babantane, a yanzukam bashi a duniya, dukiyar daya barima sun ajiyeta ita da mahaifiyarta da ƴan uwanta.

      An kumasha bikin Amina da Yah Qaseem wanda Jawaad yaje yayo biko har ƙasar da yake, tare da zaunar dashi yay masa nasiha mai ratsa jiki, tare da bashi shawarar ya tallafi ƴan uwansa a yanzu da mahaifiyarsu dan shine uba, ya kuma nema musu malamin addini su koma islamiyya musamman ma Shahudah da har yanzu hankalinta bai gama kwanciyaba dan tana masifar son Jay. Lokacin da taga cikin Bilkisu da yanda Jawaad ke riritata ita da cikin ba ƙaramin shiga ruɗani ta sakeyiba, tasha kuka ranar harda shiɗewa kuwa.1

STORY CONTINUES BELOW

     Batool ma ansha bikinta da Dr Bello daya dage akan shifa da gaske yanaso babu wasa. Ganin tsakani da ALLAH yake sonta ta bashi dama ya kawo kuɗi aka gwangwaje.

         Alhaji babba ma bisa takurawar Jay suka ɗaura masa aure da Maman su Amina, da da Maman yara za'a haɗa masa ita ta roƙa arziƙi akan a barta dan ba isashshiyar lafiyace da itaba har lokacin, tana dai lallaɓawane bisa taimakon da kulawar da Jawaad ke bata.

        Ƙungiyar su Bilkisu nata ƙara haɓaka da faɗaɗa akan daƙile fyaɗe da hukunta duk waɗanda aka samu akan laifin. hukunci kuma mai tsananin gaske. Inda manyan mutane da shugabanni suma suka ƙara basu goyon baya domin fata da samun damar daƙile matsalar kodan addabar da taima al'umma.

        Mama Atika bayan wahalar jinya da tasha na kusan wata huɗu itama ALLAH yay mata rasuwa, su Mom da su Shahudah ansha kuka. Komai nasu sai ya daɗa yin sanyi kuma, musamman ma ita da duk ƙwalisarnan yanzu babu ita, babu Dad babu dukiyar da ake taƙama da ita.

             A ɓangaren rose kam ta buga ta buga taga babu ci, mai shiga tsakanin soyayyar Jawaad da Bilkisu sai dai ALLAH. Babu kalar ƙulle-ƙulle da munafurcin da bataima bily ba a station ɗin sai dai babu tasiri, daga ƙarshema da Jawaad ya ganota sai yasa akai mata transfer waje mai nisa a tsakaninsu. Wannan abu ya sakata jin takaici harda kukanta kuwa, ballema randa taji anƙarama su bily girma da ƙyaututtuka susucewa tayi duk da itama harda ita, a ganinta bily batakai ta kamotaba, amma ya ta iya da abinda yafi ƙarfin wuta inji kishiyar ƙonanniya. tana kewar jawaad ainun. dan koba komai idan tana ganinsa kusa da ita tana ɗanjin sassauci.

__________________
ZAFAFA 2021
_______________

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
 
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

★★★★

     A gidan Iyayen gayya kuwa ai ba'a cewa komai, cikin Bilkisu da har yanzu gata nanneda ya fito sosai, dan yana cikin wata na bakwai. Tattali sosai take samu a wajan Jawaad da duk ahalinsuma baki ɗaya, inda aka maido mata Nabeelah gidan tana tayata zama, gefe kuma tana shan soyayyarta da masoyinta Anuwar.
          Faruwar wannan al'amari ya sake maida bily miskilar gaske, dan ko Jawaad ɗin idan bata gadamaba saita yini batai masa maganar data zarta gomaba. Ta ƙara ƙwazo akan aikinta fiye da zaton mai hasashe, musamman ma da bayan lafawar abubuwa suka samu ƙarin girma itada duk jami'an da sukaje wannan aiki a waccan rana. Saboda cikinta dai bata fita operation, sai dai tayi ayyukan cikin gida kawai daga office. A gefe kuma tana sake samun ƙwazo da horo a wajen mijinta, wanda a kullum cikin sake nuna mata ƙauna da soyayya mai tsanani yake. Sam baison yaga tashin hankalinta ko damuwarta balle fushinta. Shidai fatansa ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo masa little Beejay kamar yanda yake faɗa a kullum.

STORY CONTINUES BELOW

          Cikin Bilkisu nada watanni taƙwas Jawaad ya sakata ɗaukar hutun dole, acewarsa saita haihu ƴarsa tayi ƙwari sanan. Aranar da hakan ta faru harda kukanta, amma sai yaƙi kulatama yay kamar bai jitaba, sai Anuwar dake mata dariya shi da Nabeelah suka koma lallashinta da lallaɓata.
        Tana shiga watan haihuwa Ummah babba tace zata maidata can gidanta, dan bazai yuwu a barta ta zauna nan babu babba tare da ita ba. Babu kunya Jawaad ya murje idanu yace shifa bai yardaba, idan dan babbane ya amince asamo wata tsohuwar ta zauna da ita, amma shi bai yarda matarsa tai nesa da shiba gaskiya.
     Ranar Bily ta tasashi gaba ta dinga kwasar dariyar mugunta, dan kawai ta rama abinda yay mata na sakata ɗaukar hutu a office saita shiya kaya kusan akwai huɗu na tafiya gidan Ummah babba, aiko ya murje ido ya balbaleta da masifa kamar zai cinyeta ɗanya jagab🤣.
      Aifa ganin yanda ya harzuƙa dole Ummah babba ta janye ƙudirinta, aka samo wata dattijuwa zata zauna dasu, ga kuma Nabeelah da Anuwar tare dasu. Ummah ƙarama da babba kusan kullum saisunje ganinta. Hakama maman Amina, dan cikin na shiga wata tara sai ya ƙara girma kamar wadda zata haifa ƴan biyu.


       ★★★★★★

A wannan ɗan tsakanin akasha bikin su Amaturrahman suma, inda Bilkisu ko sau ɗaya bata samu leƙawaba saboda cikinta, Jay yace idan ta haihu taje taima Ummu ALLAH ya sanya alkairi.
        Bayan anyi biki an shashshare Umm-Anum da itama ta halarta da Aunty Mahfuzah sukazo nan dansu gaisa da Alhaji babba. Randa suka cika kwana uku gidan Alhaji babban sai sukazo nan gidan Jay duba bily, danshi kullum yana zuwa can ya gaidasu, itako saita waya tunda bata fita sam.
        Ta taresu da tsantsar farin ciki, inda sukuma suketajin tausayinta da mata fatan sauka lafiya. Su Anuwar ne dai ke amsawa, itako kanta na a ƙasa dan kunya.
     Anuwar ya kumbura fuska yana kallon Umm-Anum daketa mammatsa ma bily hannunta daya kumbura. “Umm-Anum gaskiya nimafa amin aure, so kuke sai little tazo duniya taga Abbanta tuzuru”.
       Dariya duk suka sanya ƴan falon, banda Jay dake zaune gefen Umm-Anum yana latsa waya, yadai ɗan ɗago ya kalli Anuwar ɗin ya zuba masa harara ya ɗauke kansa. Sai da suka gama dariyarsu sannan ya sake kallonsa fuska babu wasa. “Kai baka da kunya ko......?” “A'a yayanmu nifa wlhy gaskiya na faɗa, yanzu dan ALLAH little zataji daɗine idan aka haifota ta iskeni babu aure, ita dai ai nasan tanason iske kawunta a dattijonsa ko”. Kai kawai Jay ya girgiza ya sake ɗauke kansa, dan indai shaƙiyancine akazo wajen Anuwar kowa ya shafama kansa lafiya, duk masifarsa kuresa yake shima har yagaza cewa komai.
     Umm-Anum da itama ke dariya yanzun tace, “To ni miye nawa, aiga mai maka auren nan a gabanka” tai maganar tana nuna Jay. Tasowa yay ya tsuguna a gaban Jay ɗin yana wani marairaice fuska. “Yayanmu dan ALLAH ka aurar dani kar a haifi little ina a ƙasa” yay maganar cikin harshen nasara da haɗawa da ƴar hausar daya fara kowa wajen Nabeelah”. Kunnensa Jay ya kama ya murɗa da ƙarfi, aiko a take yahau roƙo daban haƙuri. su Bily kuma namasa dariya.
     Cak ta tsaya daga dariyar tata jin bayanta ya riƙe, ta shiga yamutsa fuska tanason fiskewa amma hakan ya gagara, kamar wasa saiga ƙaramar magana ta zama babba, dan kuwa kafin wani dogon lokaci naƙuda ta tashi gadan-gadan, dama a gaba ɗaya kwanakinan naƙudar tsaye takeyi.
       Cike da rikicewa Jay ya sugunmeta daga ita har cikin sai mota, Anuwar ya jasu sai asibiti.

BAYAN AWA BIYAR.

        Bayan gumurzu da wahalar da bily tasha a ɗakin haihuwa ta sunkuto ɗiyarta mai kama da ubanta sak, dan yarinyafa tun bata gama hucewaba kamanin Jawaad ɓaro-ɓaro a fuskarta, sai dai kalar fatarta tazo daɗan duhu saɓanin yanda ake haihuwar jarirai farare tas.
      Ai murna wajen wannan ahali ba'a magana, a take Jay ya tauna dabino ya zuba mata a baki tare da miƙama Anuwar yay mata huɗiba da suna BILKEESU MAI GADON ZINARI, Alƙawarin ALLAH ya cika, Jawaad Abdul-aziz yousif ya zama Ɗan BILKEESU, mijin BILKEESU, baban BILKEESU, saura kakan BILKEESU🙄😜🤣lol.2

          A ranar aka sallami mai jego da jinjirarta dan suna cikin ƙoshin lafiya, bakin Jay ya kasa rufuwa, ya murje idanu sai kulawa yakebama matarsa da ƴarsa a gaban kowa.
     Washe gari ƴan barka suka fara ɓarkowa ta ko ina, ciki kuwa harda Shahudah dataita kuka dan damuwa, yayinda takejin zafi da tsanar bily har cikin ranta. (Shiriyar wanifa sai ALLAH yaso, bashi yuwuwa lokacin damu mukaso😫).
      Yah Qaseem ma ya kawo ƴar Aminatunsa, hakama matan su Jabeer dasu Ummie da abokan aikinsu harma da ƙawayen makaranta. Bily kam tayi goshi, kaga ƴar gatan dangi. Baba ƙaura ma daya koma daji abinsa tuni sai gashi yazo, dan yace yafi son zaman can, alkairan da manyan ƙasa sukai masa dasu Jawaad duk tattarawa yay ya bada gidan marayu, acewarsa sun fishi buƙata, sai dai ya riƙe waya suna gaisawa da abokan arziki irinsu jay, tananma ya sanar masa da haihuwar anayinta.

STORY CONTINUES BELOW

         Su Umm-Anum basu komaba har saida akai suna, inda kowa dai yasan sunan jinjira BILKEESU. Su Firdausi duk sunzo sun taka rawar gani, hakama abokansa su Abbati na ƙauyensu, inda ɗunbin jama'a sukai masa alkairi da dama wanda shi wasuma bai sansuba.
        Amaryar jego tasha gayu harta gaji, koni dai ta gama burgeni aradu🤗, balle kuma ubangayya Jay. Ansha hotuna inda naita hango fans cikin ƴan taron suna🤗. (Kunyima Jay halacci gaskiya😘😘😍🤣, dan yau Ƴan Team Beejay da team Qaseem da team Shahudah duk sun dunƙule waje ɗaya😋☺😉💃🏻.

★★★★★

       Ansha hidimar suna kowa ya gaji, wasuma har sunyi barci. Da ƙyar na iya miƙewa na shiga bayi dan na samu na watsa ruwan da Anum ta haɗamin. ita kuma na barta tare da Little Bee. Ban wani jimaba, da dai na samu jikin ya saki na fito.
        Tsaye nai a ƙofar bayin ina kallon wanda banyi zaton ganiba, shima juyowa yay yana kallona fuskarsa ɗauke da murmushin nan nasa mai tsada dasai ya gadama yake yinsa. “Umm-Bee ƙaraso mana”. Murmushi nayi na cigaba da takawa a hankali zuwa garesu, hannuna dake da damshin ruwa ya kama ya zaunar dani gefensa. Na ɗan sauke ajiyar zuciya ina kwantar da kaina gefen kafaɗarsa. “Sweet Love bakayi barciba daman?”. Fuskata ya shafa yana sake rungumoni jikinsa sosai. “Nakasa barcin Miemaa”. Idanuna na ɗaga da sauri ina kallonsa, “Miyasa hakan Dear?”. “Saboda MIN QALB (Littafin Mamu gee na zafafa 2021) ɗina mana”. Na ɗan lumshe idanu na sake buɗewa a kansa, cikin sake sanyaya murya nace, “Minene shi?”. Nunani yay tare da ƴarsa yana murmushi. Nai ƴar dariya da komawa jikinsa na kwanta ina shafa kan baby bee daketa barcinta hankali kwance, dan tasha wankane wajen inna tsohuwa yanzu babu jimawa.
      “Wai kinsan miya faru?”. Kaina na girgiza masa ina cigaba da shafa mata kai. “Ummuna tafa dage tare zaku tafi, nifa gaskiya gaskiya.......” kallonsa na sakeyi da sauri cikin ɗan zaro ido, sai ya fasa faɗa ya ɓata fuska kuma. Ƙyalƙyalewa nai da dariya da sumbatar kumatunsa ina faɗin, “Boss na Miemaa”. Ya ranƙwashi kaina yana hararata, “Oh hakama zakice ko? To nama fasa babu inda zaki, gara ki zauna nanda wata biyun ki sake ɗaukar wani cikin”. Idanu na zaro ina buga ƙirji, “Dan ALLAH rufamin asiri sweet Luv daina min wannan fatar kaji”. Dariya sosai ya sanya, ya kwantar da Little Bee tare da jawoni jikinsa muka faɗa saman gadon yay min runfa da jikinsa. Kallon juna muke cike da shauƙi babu mai ko ƙiftawa, sai da naji bakinsa cikin nawa na dawo hayyacina da sauke nannauyar ajiyar zuciya, son tureaa nake amma yaƙi bada damar hakan, na rinƙa dukan bayansa amma bai barniba saida yayi san ransa sannan ya sakeni ya miƙe yana dariya damin gwalo. “Dama abinda ya kawoka kenan ai” na faɗa iana ɓata fuska kamar zanyi kuka. Gwalo yaymin dai-dai zai fita yace, “Eh naji ɗin”.
       Fariya sosai nayi ina girgiza kai, na jawo ɗiyata na rungume ina sumbatarta dajin kamar na haɗiyeta na huta dan ɗunbin son da nake mata.

BAYAN WASU SHEKARU.

              Yarane kusan uku keta wasan basket ball a madaidaicin filin wasa dake a cikin wani ƙaton gida mai ɓangarori kusan huɗu. ina tsaye a wajen kusan mintuna huɗu saiga mata da miji sun fito daga ɗayan ɓangare na gidan, ba kowa bane face Anuwar da Nabeelah, suma suna sanye ga j.c. ihu yaran suka fara, biyu na kiran Abbah! Abbah! Abbah. Biyu na kiran Mamma! Mamma! Mamma!! Cikin ɗaga hannu irin na jinjina da ɗokin isowar abokin wasa. Anuwar yaja ƴan team ɗinsa, Little Bee, da ƙaninta na biyu Abdul-aziz suna kiransa (Awwab). Nabeelah kuma taja nata ƴan team, ƙanwar Little bee mai bimata Maryam suna kiranta (Khairiyya) sai yaron su Anuwar ɗin mai sunan Jawaad, suna kiransa (Khalifa). Wasansu suka fara cike da nishaɗi, basufi mintuna talatin da farawarba sukaji horn. Maigadi dake kallonsu daga gate yay saurin zuwa ya buɗe. Farar mota tas ta shigo gidan wadda Bily ke mazaunin driver cikin kayan aiki, Jay na gefenta shima sanye da suit yanata faman danne-danne a laptop.
      Da gudu yaran suka nufi motar suna faɗin, Abie! Miemaa! oyoyo. Bily dake murmushi ta kalli Jay shima ya kalleta, kafin su maida idanunsu ga yaran nasu dake tunkarosu. Awwab da Khairiyya suka nufi sashen da bily take suka buɗe mata, Little Bee da Khalifa kuma Jay suka buɗemawa. A tare suka fito fuskarsu ɗauke da murmushi. Jay ya ɗaga khalifa tare da sumbatar kumatumsa, shima yaron ya sumbaci Jay ɗin yana dariya da faɗin, “Abie i love you”. “I love you too second Jawaad” ya faɗa yana lakace masa hanci, kafin ya duƙa ya sumbaci Little bee ƴar kimanin shekaru goma itama. “Little BeeJay ɗina”. Fuskarta washe da murmushi sak irin na Bily tace, “Sweet Abie na i love you” tai maganar da sumbatar hannunsa itama. Ta matsa jikinsa ya rungumeta ta gefen hannun damarsa, na haggun kuma yana ɗauke da khalifa.
     Acanma dai Awwab da khairiyya suna maƙale da Bily, saida suka gama ɗokin ganinta sannan suka dawo wajen Abie, ya sumbacesu suma a kumatu kamar yanda yayma su Khalifa. Kafin su Anuwar su ƙaraso suna musu barka da dawowa.
     Cikin tsokana bily tace, “Iyayen da basa girma da shiriritar ƴaƴansu”. Dariya Anuwar da Nabeelah sukayi, Jay dake murmushi shima yace, “Karki ja mana yanda muka dawo a gajiyanen yanzu su tara mana ciwon kai suda ƴaƴansu, zomu gudu muje mu hutama ranmu princess”. Cikin dariya Anuwar yace, “Idanma kun gudu binku zamuyi, dan yau a falonka aka haɗa dinner. Idanu Jay ya zaro sosai. sai kuma ya ɓata fuska yana kallon Bily cike da langaɓe kai. “Miemaa kinajifa, nidai ALLAH ban yardaba hutawa zanyi”. Kafin bily ta bada amsa yaran suka shiga ihu da tsalle suna faɗin suma basu yardaba a falon Abie zasuyi dinner yau”.
       Ƙwafa Jay yay yana kallon Nabeelah, “Auta kece kika haɗamin wannan aikin ko, maganar gaskiya ayi hutu na tarkataku ku tafi Saudia wajen Ummuna muma muɗan huce gajiya da matata a gidanga. A waje dambe da ɓarayi a gida dambe da iyayen yara da yaransu”.
    Sosai Nabeelah da Anuwar ke dariya, Nabeelah tace, “ALLAH babu ruwana, Abban Little ne”. “Kai ko?”. Jay ya faɗa yana kama kunnensa. “ALLAH da zafi Yayanmu” Anuwar ya faɗa cikin marairaicewa yana riƙe hannun Jay. Yaran suma duk sai suka marairaice suna faɗin, “Sorry Abie Abbanmu yanajin zafi sosai”.
     Dariya Bily takeyi. Jay dake murmushi ma ya saki kunnen Anuwar ya kama hannun matarsa suka shige dan anfara kiran sallar magrba. Kayansu yaran suka kwasa daga mota tare da tsarabar da aka yo musu sukabi bayansu. Anuwar da Nabeelah ma suka nufi ɓangarensu dansu watsa ruwa  tu fito.✍😭🙏🏻

ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN.6

Na godema UBANGIJIN al'arshi daya bani ikon kammala wannan littafi daya jani dogon zango, kuskure. dana tafka a cikinsa ALLAH ka yafeni, abinda nayi dai-dai ALLAH ya haɗamu a ladan daku masoya da mukai tafiyar tare.


Post a Comment for "KWAI CIKIN KAYA CHAPTER C KARSHE BOOK2"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...