KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 9 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 9

KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 9

- - Post a Comment

 KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 9


Taro ne na manyan mutane dan haka gurin ya k'ayatu sosai,gashi cike yake da sojoji da police sakamakon manyan mutane da suka halarci taron.

Farhan shine wanda ya bud'e wannan taro da addu'a sannan aka fara gabatar da program cikin harcen turanci inda kowa yake sanya albarkacin bakinsa d'aya bayan d'aya.

Harda yaya Atif se dayayi jawabi dan bai samu tafiya wasan k'wallon da zasu jeba.

Anci ansha aka raba sadaka sosai wa mutane bayin Allah,tare da tabbatar wa jama'a cewa duk wasu masu neman aiki daga wanda suka gama degree harda 'yan secondary da basu samun daman cigaba da karatun suba da suzo wannan company zai taimaka musu su samu abinyi.

Nan fa iyayen yara sukaita murna ana sake sanya albarka a wannan company.

Mubeenat ce ta kira Ya Atif tace "Please Ya Atif ka gayawa Ya Farhan ayi neman taimakon addu'oi agun jama'a kan Umman Amal asata a addu'a."

"Ok Sis Mubee"

Tana ganinshi ya sanar da Ya Farhan lokacin Abban Mubeenat ne ke magana kawai se sukaji yana magana akan b'atar Umman Amal tare da neman taimakon addu'a agun 'yan'uwa.

Nan take Amal ta fara k'walla Mubeenat dake zaune kusa da ita ne take rarrashinta daga nan aka rufe taro da addu'a aka fara watsewa.

Mubeenat Amal da Aisha ne kad'ai a motar Ya Atif shi kuwa Shureim yabi su Farhan,su Umma kuwa suna can motar su Abba.+


  Bayan an dawo gidane aka sake zama inda Abbi yake sanar da Abba cewa zuwa wani sati zasu koma,amma Farhan ya dawo nan da zama kenan sannan zaici gaba da zamane anan gidan tunda can shi kad'ai ne idan sun tafi.

Dad'in hakan sosai Abba yaji tare da nuna farin cikinsa akan hakan.

Da gudu Shureim ya mik'e yaje inda Farhan yake zaune yace "Ya Farhan shikenan ka zama d'an gidanmu zamu dinga zuwa yawo ko?"

Hhhh akasa dariya yayinda shi Farhan kuwa yayi mishi murmushi tare da shafar kansa yace "Yeah"

Ummin shi kuwa cewa tayi "Habibty kin samu Yayyu biyu kenan"

Cikin jin kunya Mubeenat ta kai idonta gun Farhan wanda shima ita yake kallo har cikin ido gashi ko k'yafta idon bayayi. Hakan yasa taji kunya tare da saurin maida idanunta kan Ya Atif wanda ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa.

Dad d'in Atif ne yayi musu godiya tare da sallama sannan suka wuce da Ya Musty da kuma Hajiyansu se mom d'in Atif.

Dama Aisha kam tace se dare Ya Atif zai maidata gida.

Amal kam tunda suka dawo ta kwanta a d'akin Mubeenat baccinta kawai take sha.


Mahaifiyarta kuwa bata tsaya ko inaba se'a zanfara,inda ta fad'a hannun wani mutumin kirki mai suna Buba. Mutum ne mai kirki sosai,koda suka had'u yana ganinta yasan dai akwai wani abu tattare da ita,gashi duk abinda aka tambayeta se tace bata sani ba,sunanta ne kawai idan aka tambayeta se tace Samira.

  Bayan sallan isha Aisha da Mubeenat suka raka Amal har gida inda suka sami Samira da Sagir zaune a parlour suna hiransu cikin raha da kwanciyar hankali.

Cikin b'acin rai Aisha tace "Hmmm d'an adam butulu,kowa yayi mai kyau dai kansa yayiwa mutane babu tsoron Allah ko kad'an azuciyarsu?"

"Kedai yi shurunki Aisha,bakiji hausa sunce *komai nisan jifa k'asa zata dawo ba*,muna nan muna addu'a Allah ya toni asirin duk wani mai hannu akan b'atan Umman Amal ameen" cewar Mubeenat.

Cikin fushi Sagir ya nufosu "Ku kuma wani mahaukacin karene ya cijeku kukazo nan kuna mana haushi?"

Cikin gatse Aisha ta bashi amsa "Mahaukaciyar Uwarka ce ta cijemu kaga ko dolene muyi haushi dan a cikin karnukanma ita rik'ak'k'iyace sosai."

Dosota yayi da niyan zai mareta se Amal ta shiga tsakaninsu yayinda itama Samiran ta kamo hannunsa tana cewa "Bana son neman magana Sagir ka k'yalesu"

"Idan bai k'yalemuba ma ya zaiyi damu,nan gani nan bari" cewar Aisha.

"Wlh koda wasa Sagir karka kuskura kace zaka tab'a d'aya daga cikinsu dan wlh wahala zaka sha" cewar Amal.

"Kubar ganin iyayenku masu kud'i ni babu abinda ya dameni wlh maganinku zanyi marasa kunya"

"Kaga nan babban mara kunya golai-golai daku kunzo zama a gidan matar aure daga kai har sakariyar 'yar taka kunzo kunyi butulci to munsan komai wlh ku jira kamuwar Allah butulai kawai."

"Ke Aisha kike ko wa wlh ki kame kanki kina jina ko?" Cewar Samira.

"Idan nak'i kuma fa? Zaki tayani kamewane munafukai kawai duk cikinku babu wanda ya isa ya dakatar dani daga abinda nayi niyan fad'a sedai in gaji inyi shuru shashashai kawai."

Jiki sanyaye suka tsaya suna kallonta yayinda Mubeenat tayi dariya tace "Amma kinmin dai-dai Aisha,barsu da wannan ma kin basu na bacci wuce muje Amal" nan suka wuce suka kaita har d'akinta sannan suka fito suna musu kallon banza tare da cewa "Wlh ta Allah ba takuba,koma menene kukayi zamu gano komai cikin sauk'i makirai kawai" sannan suka fice daga gidan suka barsu a tsaye.

Cikin sanyin jiki Samira tace "Kai Sagiru anya kuwa ba zarginmu jama'a suka farayi ba?"

"To kema dai seme idan sun zargemu,ai babu wani bai shaida a kanmu dan haka yau kiyita kuka kice mishi zamu bar gidan tunda gashi abinda yarama suke fad'a" nan dai ya kitsa mata komai sannan ya fice.

Atif ne ke driving zai mayar da Aisha gida shida Mubeenat.

Magana suketayi akan b'atan Umman Amal inda suke cewa "Wlh Ya Atif duk yadda akayi suna da hannu akai"

"Shhhh bana ce muku karna sakejin hakan daga gareku ba,zato kuke yifa kuma zato zunubine koda kuwa gaskiya ce dan haka karna sake ji kudai kucigaba dayin addu'a Allah ya bayyanata."

"Ameeen" suka furta sannan suka kama yin wani hiran har suka isa gida.

Gum Mom Atif ya wuce,Aisha da Mubeenat kuwa d'aki suka wuce inda Aisha ta fito mata da kayayyakin da angonta Fahad ya kawo mata.

Nandai suka tab'a hiransu sannan ta d'ibawa Mubeenat nata kason harda bra guda uku masu kyau.

Gun Mom ta wuce da Hajiyan su Ya Musty ta musu sallama sannan suka tafi.

Suna shiga cikin gida ta hango motar su Ya Farhan.

"Ya Atif naga kamar motar su Ya Farhan,me kuma ya dawo dasu oho"

"Ko sunyi mantuwa ne may be."

Atif yana gaba tana binshi a baya har suka k'arasa parlour'n Abba.

"Yawwa to gasu nanma sun dawo,Mamana dama Ummin Farhan ne tace lallai se'a d'aukoki wai zakici gaba da zama a gidansu harse bayan sun tafi kafin ki dawo gida."

Cikin jin kunya ta kalli Atif dake zaune ta gefenta yayi mata murmushi itama haka sannan ta kalli Farhan da Abdullahi tace "To Abba duk yadda kace"

"Kije ki had'a kayanki kizo ku tafi kar dare yayi ko?" Cewar Umma.

"To" sannan ta wuce ta had'o kayanta a k'aramin kit ta fito da ledan da Aisha ta bata a hannu.

Atif da Shureim ne suka rakosu hargun mota sannan suka koma, Farhan yaja mota se gida batare da sunce da ita komaiba hiransu suke su biyu tana sauraronsu amma baji takeyiba dayake larabci ne.

Suna isa ta d'auki kit nata da leda batare data lura cewa bra nata guda d'aya ya fita daga ledan ba,zata wuce se Farhan yace da ita "Let me help you" tare da mik'o mata hannun shi. Ba musu ta mik'a mishi kit d'in sannan ta wuce da ledan tare dayin sallama ba kowa a parlour duk suna ciki dan haka ta wuce d'akin Ummi inda ta saba zama.

Ledan ta ajiye a walldrop sannan ta zauna daga gefen gado tana jiran isowar kit nata.

"Slm"

"Wslm tasa hannu ta karb'a tare da cewa thanks"

Murmushi kawai yayi mata sannan ya tafi ta wuce ta ajiye kit d'in tare da bud'ewa ta d'auki rigar baccinta sannan ta rufe ta mayar.

Seda ta wasta ruwa ajikinta sannan tasa kayan bacci ta haye gado.

Ummin Farhan ce ta shigo da sallama ita da Farhan,amsa sallamar tayi tare da tashi ta zauna. Kusa da ita ta zauna "Habibty kin gaji da zama damu ne yasa kika gudu?"

Murmushi tayi tare da cewa "A'a"

"To meyasa kika tafi da kit naki,kodai dan bakya tare da Atif ne anan naga idan kina kusa dashi kinfi sakewa"

"Ba haka bane Ummi kawai dai danmun saba ne dashi sosai,Ya Farhan bai fiye son magana ba shiyasa."

Murmushi yayi tare da kallon wayar hannunsa yace "A hakan shine bana magana?"

"Eh ba kaman Ya Atif ba gaskiya"

"Karki damu Habibty a hankali zai sake dake asalinsa haka yake inba dani da Abbi nashiba se kuma Abdullahi,amma ko 'yan'uwanshi nacan Madina haka yake dasu."

Kallonsa tayi shima kuma ita yake kallo yayi murmushi. "Kin gani ko Ummi shifa sedai yayi murmushi ya danna wayarsa amma baya magana dake da Abbi kawai muke hira shiyasa naji ina kewan su Ya Atif da Shureim"

"Habibi"

"Yes Ummi"

"Kaji abinda tace ko,dan haka ka sake kana mata hira kamar yadda kakeyi da Abdullahi"

"Ok Ummi" ya fad'a sannan ya wuce walldrop nata ya bud'e ya ciro bra nata daya gani a mota ya b'oye acikin suite nashi shine yanzu ya ajiye mata akan kit nata.

"Habibi me kakeyi agun?"

Juyowa yayi yace "Na d'auki ajiya nane dana mance aciki" sannan ya fice yabar d'akin.

Hira sosai sukayi sannan Ummi ta fita,cikin sauri Mubeenat ta mik'e taje inda Farhan ya bud'e cikin mamaki taga bra nata akan kit d'in kuma tasan babu komai akan kit nata dukta kimtsasu acikin kit.

Hannu tasa ta rufe bakinta "Kardai a motarsu na mance shine ya gani ya kawo min,ohh wannan abun kunya har yaushe ni Mubeenat?" Ta fad'a kan gado tana mai jin kunya..Tana kwance taji wayarta ya fara k'ara,koda ta duba bak'uwar number ta gani,ta d'auka tare da cewa "Hello"

Wani daddad'ar murya taji yayi magana a hankali "Habibty"

Cikin mamaki taji muryan Farhan,to a ina ya samu number na kuma? Katse mata tunanin yayi da cewa "Kince bana miki hira kamar Atif?"

"Eh mana Ya Farhan"

"Uhum me kike so ince miki to?"

"Babu kawai dai ka saki jiki dani tunda nima k'anwarka ce"

"Ok zanyi k'ok'arin hakan"

"Gaskiya ya kamata kagafa tare zamu zauna yanzu idan su Ummi suka tafi"

"You know what Habibty?"

Cikin sonji me zai fad'a tace "Seka fad'a"

"I will gonna miss them Habibty,i love my parent so much and i don't wanna miss them serioursly."

"Eyyah dama haka rayuwa take Ya Farhan,yau ina Umman Amal? Koda wasa bamu tab'a kawo hakan zai faruba,amma dayake rayuwace kowa da yadda Allah ya tsara mishi yau an nemeta an sara..."

Jin shuru da Mubeenat tayi ta kasa k'arasa maganar saboda k'walla daya zo mata yasa Farhan yayi saurin gane cewa kuka takeyi,hankalinsa a tashe yayi magana cikin rarrashi "Habibty are you craying? Pls stop it i don wanna see you craying and i don't know why"

"Habibty,please ans me okay?"

Cikin jin dad'in yadda ya nuna kulawarsa a gareta ta share k'wallan tare da cewa "It's okay i'm fine now"

"Are you sure?"

"Umhum" ta bashi ansa.

"You know what Habibty? When ever i'm talking to you i'm just so happy and kuma bansan dalili ba?"

Murmushi tayi mai d'an sauti "Yaya Farhan kenan,wato dai kana so in dena kuka shiyasa ka gayamin haka ko?"

"Uhum,is not like that Habibty i'm serious"

Bata san me zatace dashi ba dan haka tayi shuru tana murmushi a b'oye.

"Habibty are you there?"

"Yeah"

"Then meyasa kikayi shuru,kodai kin fara jin bacci ne?"

"A'a kawai dai bansan me zance maka bane"

"To shikenan,kince bana magana sosai shiyasa na kiraki dan in miki hira,ina fatan kinji dad'in hiran namu duk dadai nasan ban iya kamar Atif ba but i try ai ko?"

"Hhhhh sosai ma kuwa ai gara hakan"

Murmushi yayi mai sauti sannan yace "Alright Habibty,na miki hira nizan kwanta ma'assalam"

"To nagode sosai bissalam"

"Kinji Abdullahi ko? Wai dawa nake hira haka?"

"Hhh ina jinshi"

"Bari in bashi seki bashi amsa"

"Ok" ta fad'a tana dariya.

"Habibty?" Dariya Mubeenat tasa tare dayin magana cikin harcen turanci "Ya Abdullahi harda kai?"

"Ok kina nufin shi kad'ai ne zai kiraki da Habibty?"

"Rufa min asiri ba haka nake nufiba,shima ai a bakin Ummi yaji"

"To indai hakane shi meyasa baki mishi tambayar da kika min ba?"

"Hahhh haba Ya Abdullahi karka min wata fassara daban please" tana dariya.

"Ai nama yi miki..." karb'an wayar Farhan yayi yasa a kunne a lokacin Mubeenat tanata dariya tare da cewa "A'a kayi hak'uri kaima ka kirani da Habibty'n shikenan?"

Murmushi Farhan yayi tare da cewa "Nidai ban amince maka da hakanba ka kirata da sunanta koba haka bane Habibty?"

Dariya Mubeenat tasakeyi "Ya Farhan karka had'ani da shi fa nidai ba ruwana"

Shima dariyan yayi tare da cewa "Ok Habibty good night"

"Good night" sannan ta ajiye wayar tana dariya.+


Washe gari da safe kuwa ana zaune ana breakfast gabad'aya hankalin Farhan akan Mubeenat yake,ita kuwa abincinta kawai takeci.

"Habibi yaya dai,bangane makaba kwana biyunnan fa" Cewar Abbi.

Dukkanninsu suka maida dubansu kan Farhan,murmushi kawai tayi tare da cewa "I'm fine Abbi"

Kallonsa kawai Mubeenat tayi sannan tace "Abbi duk damuwarsa shine zaku tafi ku barshi anan shi kad'ai right Ya Farhan?"

Kallonta yayi tare da cewa "Yeah it's true" yana mata murmushi itama haka. Kallonta ta mayar dashi gun Ummi tare da cewa "Amma ai Abbana ma a matsayin Abban shi yake hakama kuma Ummana ko Ummi?"

"Kinyi gaskiya Habibty,sannan gashi da aboki Atif ga kuma k'anne har biyu Ke da Shureim"

"Ehen Ummi gaya mishi dai,harma da Amal kinga mu ukku ma kenan" ta k'arashe maganar cikin zolaya.

"Keba K'anwarsa bace kawai Mubeenat,burina shine in had'a zuriya da Aminina wato Mahaifinki"

Kunya sosai mubeenat taji da maganar Abbi dan haka d'aki ta nufa cikin jin kunyarsu.

Farhan ya kalli Abbi nashi sannan ya kalli Ummi se yayi murmushi.

Kakansu kuwa magana yayi cikin zolaya "Idan kuma Farhan d'in baya so se'a bawa Abdullahi kafin mu koma se'a tsayar da maganan aure kawai."

Cikin zolaya Abdullahi yace shikenan kuwa Abbi dama yace min baya sonta."

Da sauri Farhan ya juyo yana kallon Abdullahi,su Ummi kuwa se dariya suke mishi.

Mik'ewa yayi tare da jan kunne Abdullahi yace "I lost my apatite" sannan ya koma parlour ya zauna sunata dariyan shi.


Abbin Farhan da Abban Mubeenat ne zaune suna hira inda Abbin Farhan yake gaya mishi burinsa shine ya had'a Farhan da Mubeenat aure inhar hakan zai yuwu.

"Nayiwa Farhan magana akan hakan,amma dai baice komaiba tukunna inaga mud'an bashi lokaci kafinnan sun sake shak'uwa da ita Mubeenat d'in nasan wata rana da kanshi zaizo min da zancen."

"Ba komai Aminina Allah ya tabbatar da alkhairi ya kuma had'a kawunansu" cewar Abban Mubeenat.

"Ameen" sannan sukaci gaba dayin hirarsu.


Gidansu Amal kuwa bayan Samira ta d'aga hankalinta ne ta nuna lallai da gaske zasu tafi shine Abban Amal yace da ita ta zauna zai aureta domin ya maye gurbin Umman Amal da ita.

Murna agun Samira ba'a cewa komai,nan Abban Amal yajewa Abban Mubeenat da zancen aurensa da Samira.

Abban Mubeenat baiyi mamakiba saboda maganganu da suke yawo a gari kan cewa da hannunsu Samira akan b'atan Umman Amal,sannan ga maganar da Amininsa wato Abbin Farhan ya sanar dashi kamar dai yadda Kakan Farhan ya gaya mishi cewa akwai asiri a tattare da Abban Amal dan haka a dage mishi da addu'oi.

Tun daga lokacin Abban Amal yana iyakan k'ok'arinsa na mishi addu'oi da kuma karya sihiri na ganyen magarya da akeyi,wanda ko an mishi aka bashi ruwan a gora indai yakai gida tozai gayawa Samira komai da aka gaya mishi a waje,ita kuwa seta ce to Abban Amal aise a gwada.

Amma yana barin gurin zata zubar da wannan maganin da aka bashi setayi dabara ta d'ura wani ruwan maganin da Malam na gura ya basu.

Shiyasa abun nashi yaketa gaba2 har'i zuwa yanzu dayazo musu da maganar auren Samira.

Babu yadda suka iya dashi tunda baya d'aukan shawaran kowa sena Samiran,dan haka aka zuba mishi ido ana tayashi da addu'a.


Yaune su Ummi suka koma k'asar Madina,inda suka bar Farhan cikin kewa sosai.

Kafin su tafi sunje Company sau biyu suna ganin yadda ayyuka suke gudana.

Abbi nashi yace lallai yaba Mubeenat babban matsayi ata gunshi dukda dai secondary skul kawai ta gama a yanzu. Haka kuwa akayi yace ba damuwa amma har yau bata fara zuwaba kuma ta nemi alfarma agun Abbanta daya nemawa Amal ma sesu dinga tafiya tare kota d'an samu sauk'in b'acin rai da take fama dashi a gida.

Yau ne Farhan ya dawo gidansu Mubeenat da zama gaba d'aya,dan seda yayi kwana biyu acan kafin yau ya dawo.

Mubeenat da Shureim ne suka k'arasa gun motar da murnansu "Ya Farhan sannu da dawowa"

"Thankyou Habibty" sannan ya kalli Shureim tare da d'aukan shi sama "Atif ya tafi ko?"

"Eh sun tafi tunda sassafe" cewar Shureim.

"To Allah ya kaisu lafiya"

"Ameen" suka amsa dukkansu sannan Mubeenat ta kamo kit nashi tana ja.

"Habibty stop please" cak ta tsaya tana jiran mezai ce. Sauk'e Shureim yayi yaje ya karb'i kit d'in a hannunta "Is too heavy Habibty take this" ya bata k'aramin kit d'in sannan Shureim ma ya d'auki wani kayan suna tafiya can side d'in su Ya Atif d'in.

Dama Mubeenat ta gyara komai a d'akin yayi tas gashi se k'amshine kawai yake tashi. Shiya karb'i kayan ya kai har zuwa ma'ajiyarsa wato walldrop dake d'akin babbane sosai gashi fari tas.

Mik'ewa tayi tare da cewa "Bari naje na kawo maka abinci"

"No Habibty i'm okay"

"A ina kaci abincin kenan?"

"Mun fita da Ahmad d'azu munci abinci"

"Waye kuma Ahmad Ya Farhan,har kayi abokai kenan?"

"Hhhh Habibty wanda kikace muje mu sayi mota agunsu ne,mun d'an saba dashi Ahmad d'in shine dai abokina a yanzu"

Murmushi tayi tare da cewa "A hankali zaka zama d'an gari,toni zan koma ciki me za'a dafa maka zuwa anjuma?"

"Anything Habibty" ya fad'a yana mata murmushi.

"Ok kad'an huta yanzu to,Shureim muje ko?"

"Kibarmun shi mana yamin hira"

"To shikenan,se anjuma" sannan ta fice yana binta da kallo dan kayan da Ummin shi ta kawo mata ne a jikinta yayi mata kyau sosai doguwar rigar...


Bayan sallan isha dukkansu suna zaune a parlour'n Abba suna hira inda Abba yake yiwa Farhan magana akan ma'aikatan da aka d'auka aiki a company da kuma store.
Murmushi Farhan yayi "Uncle ba komai insha Allah,fatanmu shine Allah ya mana jagora akai"
Aka amsa da "Ameen" sannan Shureim dake zaune akan ciyar Farhan yace "Ya Farhan ka dinga kiranshi da Abba mana?"
Kanshi ya shafa tare da cewa "Abban wa kenan zance? Abban Sis Mubeenat ko Abban Shureim?"
Cikin sauri yace "Abban Shureim dai,dan kasan nine d'an auta"
Dariya sukasa dukkansu sannan Farhan yace "To shikenan Abban Shureim hakan yayi maka?"
"Sosaima"
Wayar Mubeenat ce tayi k'ara cikin sauri da murna ta d'auka domin ganin Number'n waje ke kiranta tasan kawai Ya Atif ne.
"Hello Ya Atif"
"Ooh my sweet sis i miss you"
"Me too Ya Atif ka isa lfy,ya kake?"
Hankalin Farhan gaba d'aya seya koma gurinta yana sauraron me take cewa.
Abba kuwa cewa yayi "Kinga Atif ko,wato Mamana ya fara kira dankoni bai kirani ba"
"Ato kasan yadda yakeji da ita ai shiyasa" cewar Umma.
Shureim ne yazo gun Mubeenat da take ta murna suna hira "Sis Mubee kibani mu gaisa kinji?"
"Ya Atif ga Shureim zaku gaisa"
"Ok bashi" sannan ta bashi suka gaisa sannan yace taba Umma nanma suka gaisa tana mishi tsiya "Wato k'anwarka ka fara kira ko?"
"Umma amin afuwa nayi kewarta sosai ne wlh"
"To ai shikenan ga Abbanta yana maka magana"
Cikin jin kunya yace "To"
"Atif kun isa lafiya?"
K'yeyansa ya sosa "Lafiya lau Abba,ya na barku?"
"Alhamdulillah to ahuta gajiya"
"To Abba seda safe" sannan Mubeenat ta karb'a ya tambayeta ina Farhan nan ta mik'e takai mishi ya karb'a suka gaisa sannan yayiwa Mubeenat sallama.
Missed call na Amal ta gani,dan haka tace "Abba zan shiga gidansu Amal"
"Mamana kinsa bana son fitarki da dare fa musamman yadda gidan nasu yake a yanzu ranan ma Hamaifin Amal d'in ya gayamin abinda kukayiwa Sagir da 'Yarsa bana so kina shiga hidimar su,kiyi abinda ya kaiki kawai ki fito"
Cikin girmamawa tace "Kayi hak'uri Abba zan kiyaye insha Allah,yanzu ma missed call nata na gani shiyasa"
"To kuma zaki fita kibar Yayan naku?" Cewar Umma.
Mik'ewa Farhan yayi "Bakomai Umma aiga Shureim yana min hira sosai zamu shiga"
"Farhan zaka wuce?" Abba ya tambaye shi
"Eh seda safe Umma"
"To Allah ya bamu alkhairi"
"Ameen" sannan ya wuce rik'e da hannun Shureim.
"Abba inje? Yanzu zan dawo"
"Jeki Mamana banda neman fad'a"
To Abba sannan ta fice inda ta hango Farhan da Shureim can zasu shige side nasu.
"Ya Farhan?" Ta kira sunanshi tare da k'arasawa inda yake tsaye yana jiran me zata ce.
Har inda suke tsaye ta k'arasa "Ya Farhan kardai ace bacci zakayi?"
Murmushi yayi "Haka ya kamata ai ko?"
Marairaicewa tayi "Please Ya Farhan ka rakani?"
"Habibty...?"
"Please Ya Farhan? Bazan dad'eba a bakin gate fa zaka tsaya please...?"
"Kink'i kimin hira zakije kima Amal sannan kice in rakaki kin kyauta min kenan Habibty?"
Kunya sosai taji dajin kalamansa,cikin wata irin murya wanda itama batasan ta yishiba tace "I'm sorry"
Murmushi yayi tare da cewa "Muje" amma badan ya soba.
Dad'i taji suka tafi amma shi dai da Shureim yake hira suna tafe har bakin gate d'in su Amal sannan yace "Habibty please don't keep me waiting"
"Alright" sannan ta wuce ta barsu a tsaye.
Rungume Mubeenat tayi tana k'walla "Mubee yanzu Abba yake sanar dani wai gobe sartuday ne d'aurin aurensa da Samira fisabilillahi hakan ya dace kenan?"
Jikin Mubeenat yayi sanyi tama rasa me zata cewa Amal. "Kiyi shuru ki dena kukan please Amal muje waje nabar Ya Farhan a tsaye shida Shureim suna jirana"
Cikin mamaki Amal tace Farhan kuma?"
"Eh ya dawo gida yau ai,Amal please kidena sa damuwa sosai a ranki karya janyo miki wani abun" sannan ta janyo hannunta suka fito waje.
Farhan ne tsaye shida Shureim yana danna wayarsa.
Cikin dauriya Amal ta gaishe dashi ya amsa batare daya kallesu ba.
"Ya Farhan zan iya ganinka a gefe?" Cewar Mubeenat.
Cikin mamaki yace da ita "Sure" sannan ya saki hannun Shureim ya koma gefe tana biye dashi.
"Ina sauraronki"
"Ya Farhan dama akan Amal ne please kayi mata magana akan ta ragesa damuwa aranta yanzu haka kuka na sameta tanayi wai gobe ne auren Abbanta da Samira."
Wayarsa ya mayar aljihu tare da sake matsowa kusa da ita yayi magana ahankali "Please Habibty karki sani a cikin wannan maganar dan bansan me zance mata ba."
Cikin sanyin jiki ta kalleshi shima ita yake kallo,wato dai shi Ya Farhan ba kaman Ya Atif yake ba,ni a nawa tunanin na d'aukeshi kamar Ya Atif ne shima kuma ya d'aukeni a hakan,amma inaga shiba haka yakeba.

Cikin sanyin murya tace dashi "Kayi hak'uri Ya Farhan,bazan sakeba" sannan ta juya ta nufi gun Amal tare da rungumeta shi kuwa yana kallonta kuma yaga kamar bata ji dad'in abinda yayi mata ba.
"Amal kiyi hak'uri,wlh bansan me zance mikiba,karmu gaji gurin kaiwa Allah kukanmu watarana se labari,kije ciki nizan tafi gida."
"Nagode Mubeenat,Allah yabar zumunci"
Murmushi tayi tare da cewa "Ameen" sannan ta sake rakata ciki ta fito ta sami Farhan da Shureim a tsaye.
Batare data kalle shiba tace "Ya Farhan muje" sannan tayi gaba suna biye da ita a baya har suka shigo cikin gida sannan ta sake juyowa tace "Thankyou"
Murmushi kawai yayi mata sannan ta wuce gefen Ummanta yana binta da kallo.
Ko daya koma d'akinsa seya kira wayarta amma yayita ringing bata d'agaba.
Tana zaune akan gadonta tana ganin call nashi amma sam tak'i d'auka tana maganar zuci "Insha Allah na fita harkarka kenan Ya Farhan,dan naga kamar ina shige maka dewa wanda kai kuma bason hakan kake yiba."
Texs ne taji ya shigo mata da sauri ta duba dan taga waye ne,cikin mamaki taga Farhan ne.+

  Habibty please pick my call i just wanna talk to you please?"

Tana gama karantawa se ta tsinci kanta dason jin me zai gaya mata,amma seta share yanata kira tak'i d'auka har bacci ya d'auketa.
Washe gari da safe tunda suka had'u a parlour'n Abba aka gaisa gaba d'aya shikenan ta tashi ta koma d'akinta,tana duba wayarta taga texs kamar haka

_Please Habibty don't get mad at me i'm sorry for what happen you know that you're my Ummi's Habibty right? That's why i don't wanna hurt you please i'm sorry Habibty_

Bayan ta gama karantawa ne se tayi murmushi tare da sake karanta texs d'in tana jin dad'i har cikin ranta wanda bata san dalilin hakan ba.
10:00am aka d'aura auren Samira da Abban Amal akan sadaki naira dubu hamsin. Amal tana gun Mubeenat se kuka takeyi Umma tana bata hak'uri.
Ita kuwa mubeenat tun daga wannan lokacin taja baya da Ya Farhan gaisuwan safe ne kawai yake had'asu a parlour'n Abba,koda wasa bata barima su sake had'uwa kullum tana cikin d'akinta ko kuma tayi gun Amal.
Tun Farhan baya damuwa sosai harya fara damuwa yana so yaga sun zauna suna d'an hira amma sam baya samun wannan daman,kuma koya kira wayarta bata d'auka dan haka ya dena mata texs d'inma.

Farhan ya cewa Abba idan akwai Islamiyya tagunsu zaiso ya dinga karantarwa koda week ends haka.
Abba yaji dad'i sosai yace dashi akwai Islamiyya kusa kuwa wanda su Mubeenat suke zuwa sedai yanzu ana hutu ne idan aka koma zai mishi hanya.
Godiya sosai Farhan yayiwa Abba sannan ya sanar da Ahmad sunata hiransu dan sun shak'u cikin 'yan k'ank'anin lokaci dayake halinsu yazo kusan d'aya Ahmad bayi dason magana sosai.

Yau kusan kwana hud'u kenan rabon Mubeenat da Farhan suyi wani magana mai tsayi a tsakaninsu.
Umma ta kirata tace da ita taje ta gyarawa Farhan d'aki tunda ya tafi can gurin aikinsa.
Key d'in d'akin ta karb'a agun Umma sannan ta nufi d'akin ta fara gyarawa cikin sauri dan bata so ya dawo su had'u.
A waje ya ajiye motar bai shigo da itaba dan mantuwa dayayi zai d'auka sannan ya juya.
Gefen Umma ya nufa acikin zuciyarsa kuwa cewa yake "Allah yasa kina parlour Habibty" da sallama ya shiga Umma ta amsa tare da fitowa "A'a Farhan kaine?"
"Eh Umma mantuwa nayi"
"Allah sarki,yanzu kuwa naba Mubeenat key d'in nace taje ta gyara maka gurin"
"Ok Umma" sannan ya fice yana farin ciki aranshi seya ji wayarsa na ringing,ko daya duba Ummin sace ya gani dan haka ya d'auka suna magana.
Tun daga ciki Mubeenat ta jiyo muryar shi yana magana,aise ta rikice gashi bata gama gyaranba. Kanta ankara taji yayi sallama tare da bud'e k'ofar sukayi ido hud'u yana magana a waya amma duk hankalinsa agunta yake.
A zuciyarta kuwa so take idan ya shigo ta fice,ai kuwa kamar ya ganota seya tsaya a jikin k'ofan tare dasa wayarsa a hands free yace "Ma'am Ummi me kika ce?"
"Nace ina Habibty Mubeebat?"
Kallonta yakeyi itama kuma jin Ummi na tambayarta yasata kallon shi.
"She's fine Ummi"
"Let me talk to her Habibi"
Kallonta yake har yanzu itama kuma haka sannan yace "Ok" tare da mik'a mata wayar.
Kunya taji sosai dan haka tasa hannu ta karb'a tare da juya mishi baya tace "Ummi?"
"Ohh Habibty how are you?"
Cikin murna ta amsa "I'm fine Ummi ina wuni,ya Abbi?"
"Lafiya Habibty,kina kulamin da Habibina kuwa?"
Da sauri Farhan ya matso bayanta ya tsaya daga gefenta dan yaji me zata cewa Ummin shi.
Juyowa tayi suna kallon juna sannan ta d'an sake matsawa gefe tace "No Ummi" ahankali.
"Why Habibty?"
Gabanta Farhan ya dawo ya tsaya suna fuskantar juna tace "Saboda baya so ina takura mishi shiyasa nad'an bashi iska Ummi amma ba laifina bane hakan" ta k'arasa maganar cikin girmamawa kamar Ummi tana ganinta.
Shi kuwa Farhan mamaki ta bashi dan tana ganin cikin idanunsa ta fad'i hakan ko k'yaftasu bata yiba seyaji ta burgeshi sosai dan batama Ummi k'arya ba.
"Shi Habibin nawa ne yayi miki haka?"
Kallonsa ta sakeyi tare da sake juya mishi baya sannan tace "yes Ummi"
"Amadadinsa ina baki hak'ur..."
"Shihhhh" ta katse Ummi. "Please don't say it Ummi aiba komai ya wuce,nice zan baki hak'uri akan k'in kulashi i'm sorry Ummi?"
"Habibty shiyasa na zab'eki a matsayin surukata,Allah ya muku albarka Habibty."
Kunya sosai Mubeenat taji da kalaman Ummi tace "Ameen" sannan ta mik'awa Farhan wayan batare data bari sun had'a ido ba tayi niyan fita daga d'akin,cikin sauri ya rigata k'arasawa bakin k'ofan ya jingina ajiki yana magana da Umminsa yana kallonta tare da mata wani irin kallo.
Tsaye take kamar wanda ruwa ya daka dan kunya daya kamata.
Bayan Farhan ya gama wayan ne ya tako a hankali har inda take tsaye kanta a sunkuye ya d'an sunkuyo kad'an ta yadda zaiga fuskarta itama haka,cikin jin nauyinshi tasa hannayenta biyu ta rufe fuskarta dashi tana murmushi.
Mik'ewa tsaye yayi tare dayin murmushin shima sannan yayi magana ahankali kamar baya so wani yaji abinda zai fad'a mata cikin daddad'ar muryarsa.
"Habibty?"
Wani irin shock taji a jikinta ga daddad'ar turarensa da yake shiga hancinta ahankali tak'i cewa komai dan haka yaci gaba dayin magana kamar haka.
"Habibty i'm sorry for what happen,and please ki cireshi aranki banyi hakan da wata manufaba sedan bana son shiga harkar da bata shafeniba ne a matsayina na bak'o."
"Sannan meyasa bazaki gaya min cewa bakiji dad'in hakanba se kawai ki d'auke min wuta bayan kinsan Ummi ta baki amana ta?"
"Habibty kinsan bani da wani abokin hira anan se Ke,amma shine kika pornishing d'ina kin kyauta min kenan a matsayina na bak'o a gidanku?"
"And kuma nayita kiranki kika k'i d'aukan wayata,haka kuma nayi miki texs amma babu reply Habibty...?"
  Cikin wata irin murya mai kwantar da hankali tace "Kayi hak'uri bazan sake ba" tana rufe da fuskarta har yanzu.
Dad'i yaji har cikin ranshi yace "Bakomai ya wuce,na kuma gode da gyaran d'aki,mantuwa nayi shine na dawo d'auka bari na d'auka sena baki guri tunda kunyata kikeji."
Bayan ya d'auki abinda yazo d'auka ne seya zo dai-dai kunnenta na gefen dama ya rad'a mata "Thankyou Habibty"
"Na barki lafiya" sannan ya fita da farin cikin fal akan fuskar shi...
V & CTun daga wannan ranan Mubeenat take jin kunyar Ya Farhan,musamman ma dataga alamunsa akanta.
Yaune Abba da Farhan sukaje ismaliyya aka gama komai an d'auki Farhan Malami a wannan islamiyya dan wani sati za'a koma,Shureim se murna yakeyi zai dinga bin Farhan a mota.
Atif kuwa satinsu biyu sannan suka dawo,daga shi har Mubeenat sunyi kewar junansu sosai dukda dai kusan kullum suna manne a waya kamar saurayi da budurwa,shiyasama daya dawo har Farhan ya fara tunanin kodai akwai soyayya a tsakaninsu ne amma se daga baya ya fahimci cewa shak'uwace kawai wanda hakan ya burgeshi sosai.
Tunda Atif ya dawo mubeenat bata samun baiwa Farhan lokacinta kamar daba,dan kusan kullum suna fita yawo koma gidan friends nata lokacin da Atif baya nan Farhan shine mai kaita ko ina amma banda yanzu da Atif ya dawo komai ya sauya.
Haka dai rayuwarsu taci gaba har tsawon shekara d'aya.+

*~~~~~~*
Alokacin Farhan ya zama cikakken d'an k'asa dan kusan ko ina ya sani gashi shak'uwarsu da Mubeenat ya k'aru sosai wanda shi sam baya so tayi nesa dashi.
Ko a office ne minti d'aya biyu zai kirata dayake ita da Amal acan suke aiki tare dashi,duk wata suna da albashinsu 30k ta hakanne suke hidimarsu sosai basu rasa komaiba dama kuma Abban Mubeenat komai zaiyiwa Mubeenat to ita da Amal yake had'awa duk dan ta kwantar da hankalinta na rashin Mahaifiyarta da har yanzu ba'a san inda take ba.

Shureim yana zaune yana tuna tambayoyin da Farhan yayi mishi akan Mubeenat na tana da saurayin da take so ne?
"Meyasa Ya Farhan yamin wannan tambayar kodai son Sis Mubee yakeyi ne kuma yana kunyar sanar da ita? Indai hakane nasan abinda zanyi dan wlh bazan bari Ya Farhan ya saurari wannan 'yan matan islamiyyan namuba wanda suke had'oni da wasik'a gurin Ya Farhan."
Parlour'n Umma ya nufa yaga Sis Mubee kwance tana bacci dan haka ya koma d'akin Ya Farhan ya d'auko hotonsa guda d'aya yazo ya d'aga hannun Mubeenat a hankali yasa hoton akan cikinta sannan ya mayar da hannun nata ya koma d'akin Farhan da sauri ya kwanta yana game a laptop nashi.
Bayan minti talatin sega Farhan ya dawo gida,kai tsaye parlour'n Umma ya nufa da niyan ya gaisheta da gida sannan ya wuce.
Mubeenat ya gani kwance tana bacci tare da farin abu akan cikinta,haka kawai yaji yana son ganin menene wannan abun. Na baku labarin gurinnan a baya dan haka zanci gaba daga inda ya koma d'aki rik'e da hoton a hannunsa yana tambayar Shureim ya akayi Sis Mubeenat ta samu hotona?
"Ya Farhan kasan tana zuwa gyara maka d'aki watak'ila anan tagani ta d'auka."
Murmushi Farhan yayi tare da rage kayan jikinsa ya wuce toilet yana tunanin "Kodai itama Sis Mubeenat ta kamu da soyayyata ne?"

Dama Farhan ya gayawa Abbi da Umminsa cewa yana son Habibty kamar yadda suke sonshi da ita tun a baya,amma ya sanar da Abbi nashi cewar karya gayawa Abba shi da kanshi zai nemi izini agun Abba kafinma ya sanar da ita Mubeenat d'in.
Murna sosai sukayi da har Farhan ya aminta da Mubeenat dan kanshi,dan haka sukaci gaba dayi musu addu'an alkhairi.
  Bayan sallan isha Farhan yaje gun Abba a parlour sund'an tab'a hirane sannan yace "Abba dama nazo ne da wata buk'ata nawa"
"To Farhan ina jinka"
Cikin girmamawa ya sunkuyar da kansa ya fara magana cikin jin kunya "Abba dama ina so in nemi izini agunka ne akan Sis Mubeenat,indai ba'a riga da an amsawa waniba ina so inje mata da buk'atata inhar ka amince min?"
"Alhamdulillah" Abba ya fad'a acikin zuciyarsa,a fili kuma yayi murmushi irin nasu na manya sannan yace "Toba komai Farhan na maka izini idan kun dai-daita shikenan, fatanmu shine Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
"Ameen Abba nagode,sannan inaso asani acikin addu'a."
"Insha Allah Farhan,Allah ya had'a kawunanku"
Ameen Abba nagode sosai" sannan ya fice duk kunya ya kama shi.
Fitar Farhan ne Abba yaketa addu'oi acikin ransa,dan Farhan mutum ne wanda ko wani uba zaiso ace 'yarsa ta samu miji kamarsa,ga Addini ga nutsuwa da sanin darajan mutane.
Nan take ya kira Umman Mubeenat ya sanar da ita wannan abin farin ciki daya samesu yau,itama murna sosai tayi tare da yin addu'a "Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
Abba ya amsa da "Ameen"

Washe gari da safe bayan sun gama shirin zuwa gurin aiki,Farhan ne ya fita dasu ita da Amal. Mubeenat ce a gaba se ita Amal d'in a baya.
"Ya Farhan amma dai yau bazamu dad'e sosaiba nida Amal don yau za'a fara program na auren Aisha Kabir"
"Ok Habibty,bakomai"
Murmushi tayi tare da juyowa ta kalli Amal sukayiwa junansu murmushi.
Isarsu k'awayensu ko kuma ince abokan aikinsu suka taho ana gaida Farhan "Good morning Sir"
"Morning dukkanku kuzo nan"
Duk aka taru har dasu Amal ana sauraron abinda zaice.
Fuskarsa cike da fara'a ya fara magana cikin nutsuwa "Bakomai ne yasa na tara kuba sedan wata alfarma da nake nema agurinku"
Kowa yayi shuru yana son jin menene kuma yau Sir zai nema agurinmu,harda su Mubeenat a wannan tunanin.
Yaci gaba da cewa "Ina buk'atar addu'oinku akan wani abu da nake nema Allah ya tabbatar min da alkhairi akan sa"
Nan aka amsa da "Ameen"
Sannan wani yace Sir akan company namu ne?"
"No! Neman aure nakeyi,dan haka ku tayani da addu'a please?"
"Masha Allah Sir Allah ya tabbatar da alkhairi Allah yasa rabon kace"
Cikin jin mamaki Mubeenat da Amal suka kalli junansu "Neman aure kuma? A ina kenan Ya Farhan yake neman aure?" Suke tambayar zuciyarsu wanda duk hankalinsa agunsu yake.
"Ameen" ya furta tare da cewa "Nagode zaku iya tafiya"
Nan guri ya watse kowa ya koma gun aikinsa suna mamakin wace mai rabo ce haka Sir Farhan yake nema?

Mubeenat da Amal dai abun ya damesu sosai,dan har Amal tana cewa Mubeenat nifa gani nake kamar Ya Farhan yana sonki? Hmm kema dai to idan ma yana sona ai bai tab'a gaya minba dukda dai nima nakanyi wannan tunani wani lokacin.
Bayan Mubeenat ta gama tunaninne ta kalli Amal tace "Amma kuma fa banji zancen Ya Farhan yana neman aureba,kinga aiko Ya Atif ma zai gaya min ko kuma su Umma ko?"
"To nima dai mamakin da nake tayi kenan tun d'azu wlh,gaba d'aya jikina yayi sanyi Mubeenat."
"To koma dai wacece Alah ya tabbatar mishi da alkhairi."
Cikin sanyin jiki Amal ta amsa da "Ameen."

Bayan awa biyu Farhan ya kira Mubeenat a waya,batare da b'ata lokaciba ta d'auka tare da cewa "Hello Sir"
Cikin murya mai dad'i yace "Bana gaya miki indai nida ke bane ki dena kirana da Sir?"
Murmushi tayi "I'm sorry Ya Farhan"
"It's okay,zan iya samun coffee?"
"Sure" sannan ta katse wayar taje ta had'o kamar yadda ta saba tayi sallama sannan ta shiga yana zaune yana shan sanyi AC.
Ahankali ta ajiye akan table dake gabansa tace "Bisimillah Ya Farhan" fuskarta d'auke da murushi.
Kallonta yayi tare da cewa "Thanks" sannan ta juya zata koma yayi saurin kiran sunanta "Habibty?"
Cak ta tsaya tare da juyowa "Na'am"
"Baza kimin murna bane kodai bakiji abinda na fad'a bane d'azu?"
Murmushi tayi tare da k'aik'aya kanta a hankali "I'm sorry,na tayaka murna Ya Farhan Allah ya tabbatar da alkhairi."
"Ameen,amma har cikin zuciyarki kika fad'i hakan?"
Kallonsa tayi cike da mamaki "Eh mana ai abun farin cikine sosai dukda dai baka sanar daniba tun a gida seda muka zo nan"
Coffee d'in ya ajiye tare da mik'ewa yazo har inda take tsaya yana kallon kyakkyawar fuskarta tare dayin k'asa da muryarsa "Kina nufin bakya kishi?"
Kallon juna suka tsayayi tace "Kishi kuma? Akan me zanyi kishi ya Farhan,ai sedai intayaka murna"
Lips nashi ya tsotsa tare da sake kallonta "Are you sure Habibty?" Yana mai kallon cikin idanunta.
Wani irin nauyinsa taji dan kallon dataga yana mata,dan haka tayi saurin sunkuyar da kanta tace "Yes,zan iya tafiya?"
"Yeah,k'arfe nawa zaku tashi yau?"
"12:00 dai ko kuma idan munyi sallan azahar"
"Ok wazai maidaku?"
"Ya Atif zaizo ya d'aukemu"
"Badamuwa idan kun shirya ki gaya min"
"Ok" sannan ta wuce yana binta da murmushi...

Bayan ta dawo ne take sanar da Amal yadda sukayi da Ya Farhan.
"Mubeenat kodai kece yarinyar da yake fad'a to?"
"Ni kuma? Meyasa kikace haka?"
"Kiyi tunani mana,babu wanda yasan da zancen a gida,dan dole ace wani ya sani,sannan duk yadda kuke dashi bai gaya mikiba kuma sannan yanzu yana gaya miki wai bakya kishi ne? Wlh nidai gani nake kamar kece kawai dai dan bai gaya miki bane,ki duba irin salo kala-kala da yake gwada miki fa."
Ajiyar zuciya Mubeenat tayi sannan tace "Hmmm nidai mubar wannan zancen please,koma wacece dole dai zamu santa."
Nan suka bar zance sukaci gaba da ayyukansu har akayi azahar sannan ta koma office nashi yana rubutu ta sameshi.
"Ya Farhan zamu wuce"
"Ok Atif d'in yazo ne?"
"Eh yana waje"
Pen d'in hannunsa ya ajiye tare da mik'ewa ya bud'e wani guri da yake ajiyan kud'insa ya fito da rapan 200 sabbi dal-dal yazo inda take tare da kamo bag nata yasa mata a ciki tana tsaye tana kallonshi.
"Ya Farhan wannan kuma fa?"
"Kyautace na miki,kiyi hidimar bikin Aisha da shi."
"Amma Ya Farhan ai Abba ya riga daya bamu duk wani abu da muke buk'ata a wannan bikin"
"Na sani,aina Abba daban nawa kuma daban,bana so muyita jayayya Habibty please?"
Badan tasoba tace "Thanks,amma kai bazakaje bikin bane? Tafa ce mun in gaiyaceka bikin?"
Murmushi yayi "Kina so inje ne?"
"Eh aiya kamata tunda an gayyaceka ko?"
"Hakane amma tunda kinje ai kin fansheni"
"A'a Ya Farhan kai dani ai abu biyu ne,gaskiya ya kamata ace kaje koda d'aurin aurene."
"Habibty ni dake abu guda d'ayane ki dena maidashi biyu please,sannan zanyi k'ok'ari inje d'aurin auren shikenan?"
Murmushi tayi tare da cewa "To ai hakan yafi,zamu wuce seka dawo mun kuma gode."
Murmushi yayi mata "You take care Habibty"
Kallonsa ta tsaya yi dajin kalamansa,murmushi tayi mishi tare da cewa "I will byee" sannan ta wuce yana tsaye zuciyarsa cike da sonta.
Har seday yaga sun fice sannan yabi bayansu yana ganinsu har suka k'arasa gun motar Atif,su biyune shida abokinshi wanda Mubeenat ta tsana.
Fitowa sukayi shida abokin suna kallonsu,take Mubeenat ta had'e rai ta juya musu baya tace "Amal karki shiga barsu su tafi kawai mahau nape."
Duk Farhan yana hangosu daga nesa. Atif ne yazo gabanta cikin rarrashi yake mata magana "Sis Mubee i'm sorry wlh a hanya muka had'u kuma kinga babu yadda za'ayi in barshi motar sace ta samu matsala."
Rai b'ace tace "Nidai bazan shigaba ai kasan bana son maganarsa amma ka taho dashi,nidai ka taro mana nape zamu shiga mu tafi."
Marairaicewa yayi tare da had'a hannayensa biyu yana bata hak'uri "Haba sweet sis haka zaki min agaban mutane,so kike a mana dariya kuma yau? Please kiyi hak'uri kinsan fa bana so inga kinyi fushi."
"Nifa bazamu shigaba indai tare dashi zamu tafi,gabad'aya na tsaneshi wlh sam baya burgeni."
Atif yaga dai da gaske takeyi dan haka yad'an b'ata rai tare dayin magana cikin wani irin murya "Yanzu duk abinda na gaya miki baki jiba kenan ko?"
"Kayi hak'uri Ya Atif gaskiya bazamu bika ba."
"Haka kika cemin ko? Meyasa kikace nazo na d'aukeku to?"
"Amma ai banyi tunanin  dashi zaka zoba"
"Nagode Sis Mubee,zanje in ajiyeshi sena dawo na d'aukeku dan gaskiya bazan iya cemishi ya sauka ba." Yana kaiwa nan ya barta tsaye ya wuce da alaman baiji dad'in hakan ba.
Cikin sauri tabi bayanshi tare da rik'o hannunsa ya juyo yana kallonta "I'm sorry" ta fad'a tare da bud'e motar ta shige badan tasoba Amal ma ta shige sannan shima ya shiga yaja motar.
Komai akan idon Farhan akayi. Tunda suka fara tafiya babu wanda yayi magana in banda Amal data gaishesu.
Atif yasan Mubeenat fushi takeyi dan haka yace da ita "Sis Mubee bazaki gaidashi bane?"
Cikin b'acin rai tace "Ina wuni"
"Lafiya k'alau" bayan wannan bai k'araba dan yasan koya k'ara ba amsawa zata sake yiba.
Ta mirrow Atif yake kallon fuskarta a had'e kamar wadda akayiwa duka.
Bayan isarsu gidane tayi saurin bud'e k'ofa ta fice batare datace komai ba.+

Sun shirya sunyi kyau sosai har sun fito sega Atif ya shigo gida. Had'e rai ta sakeyi ta kamo hannun Amal suka wuce.
Fitowa Atif ya sakeyi da motarsa ya biyosu waje tare da cewa "Sis Mubee i'm sorry muje in kaiku?"
"Bakomai zamu hau nape ne"
"Karki yadda danifa kizo nan." Ba musu taje ta tsaya daga gefensa ita a dole tayi fushi.
"Hhhhh oh my Sis Mubeenat Abdullahi,fushi baya miki kyau sam wlh"
Badan tasoba dariya ya kubce a fuskarta "Wlh Ya Atif niba ruwana da kai mun b'ata"
"Ta ina kika tab'a jin hanta da jini sun b'ata? Hakan zaiyu kuwa Amal?"
"A'a bazai yuba Ya Atif"
"Ato kinji abinda Amal tace ko? Come on kushigo muje karna saku yin late."
Tana gaba Amal na baya suka tafi yanata zolayarta wani lokaci tayi dariya wani lokacin kuma ta makze.
"Nidai wlh mun b'ata Ya Atif ka rabu dani kawai"
"To shikenan bari muyi hiranmu da Amal tunda kince haka" haka kuwa sukaita hira da Amal amma yana kan zolayar Mubeenat har suka isa gun bikin acan suka sami Aisha k'anwar Atif danta rigasu zuwa,nanma dai Aisha tazo sukaita hira suna zolayar Mubeenat wanda ta gaji ta shige ciki ta barsu a waje.

Bayan an gama komai ne sukaita watsa pictures daga nan Atif yazo ya d'aukesu tak'i zama a gaba har seda suka je suka sauke Aisha a gida sannan Mubeenat ta dawo gaba suka wuce gida.
Kusan 8:35pm Farhan ya aika Shureim daya kira mishi Sis Mubeenat.
Tana kwance a d'akinta tana kallo ya shigo "Sis Mubee Ya Farhan yana kiranki"
"Ya Farhan kuma? Ina yake?"
"Gashi can a zaune a parlour'n Umma"
"Ok kace mishi ina zuwa" sannan ta mik'e dama rigar bacci ne a jikinta dogo dan haka ta d'auki himar nata tasa sannan ta fito.
A tsaye ta sameshi yana sanye da blue shets yana kallon fitowarta fuskarsa d'auke da fara'a. Kallonshi ta tsaya yi "Ya Farhan gani"
"Habibty nazone domin muyi wata magana dake inhar babu matsala"
"To bismillah ka zauna" sannan itama ta zauna tana kallon shi.
"Habibty na nemi izinin yin magana dake agun Abba,a gaskiya Habibty na dad'e dasa k'aunarki a cikin raina furtawa ne kawai banyiba se yau."
Kunya sosai Mubeenat taji dan haka ta sunkuyar da kanta k'asa tana mai jin dad'i har cikin ranta.
"Habibty ina neman izini agunki daki bani damar shigowa cikin rayuwarki,ina so in zamanto miji a gareki inhar zuciyarki ta amince dani."
Shuru Mubeenat tayi dan wani irin kunya dataji ya kamata.
"Habibty bazan takuraki na cewa sekin bani amsa a yanzu ba,kije kiyi tunani ina jiran amsarki."
Nanma shuru tayi bata ce komaiba se b'oye fuskarta da takeyi acikin himar nata.
Murmushi yayi tare da cewa "Shureim zomu tafi,naga kunyata takeji yau."
"To Ya Farhan" sannan suka mik'e a tare suka fice.
Ajiyar zuciya Mubeenat ta sauke tare da mik'ewa cikin sauri ta wuce d'akinta tana mamakin abinda taji daga gareshi.  
  No Amal ta kira ta sanar da ita duk yadda sukayi da Farhan a yanzu.
Murna sosai Amal tayi tare da cewa "Bana gaya miki ba,kai Mubeenat na tayaki murna wlh me kike jira da bazaki ce mishi yes kema kin amince ba?"
"Hhhh kai Amal,aidai kinsan da kunya in iya amsa mishi nan take yana zaune yana kallona ai dole sena d'an ja mishi class ko?"
"Hhhhh su Sis Mubeenat masu jan class,to nidai ki gama jan class naki ki amsa mishi musha biki,dan zanso inganki a gidan Ya Farhan wlh abun zaiyi kyau sosai"😜
"Bakida dama fa,nidai seda safe zan kwanta"
"To Amaryan Ya Farhan barima in had'a muku nickname tun yanzu kuma haka zan mayar akan wayatama" shuru tayi kamar maiyin wani nazari sannan tace "Yawwa FARBEEN KO FARBEENAT seki zab'i d'aya?"
"Hhhh Allah ya shiryeki Amal seda safe zan gaya miki wanda na zab'a"
"To Allah ya bamu alkhairi" sannan ta ajiye wayar suna dariyan junansu...

Post a Comment for "KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 9"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...