KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 1 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 1

KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 1Kuka sosai takeyi kamar wacce akayiwa rasuwa ta zamto abin tausayi gaduk wanda yaganta.

Amal ce zaune agefenta itama kukan takeyi tana rarrashinta,dukda tasan cewa sam *mubinat* bata sauraronta amma taci gaba da rarrashi tana cewa "Dan Allah mubinat kidena kukan kanki zaiyi ciwo kibarwa Allah komai kinji?"

"Dago da kanta tayi fiskanta cike da kwalla da majina tace "amal kibarni inyi kuka kozanji sanyi araina,amal ina son Ya atif sosai amma son yaya da k'anwa bawai so na masoyi da masoyiyaba bazan taba iya mallakamishi kainaba dan haka nibanga anfanin aurenmuba wlh zaku nemini ku sara muddin aka d'aura wannan auren wlh bana k'aunarsa a matsayin uban 'ya'yana kije ki fahimtar dasu ABBA kozasu fasa auren pls amal...

  "Kuka sosai amal takeyi tare da k'ara rungume aminiyarta tana cewa bakin alk'alami ya riga daya bushe an gama raba katin aurenku nan da 2hrs za'a d'aura muku aure dole kid'au wannan kaddaran mubinat kibarwa Allah. Shuru amal tayi saboda ta kasa karashe maganan sakamakon kuka dayaci karfinta tana goge kwalla.

  Mubinata ta tsaya da kukanta dan ganin yadda amal tashiga damuwa,kamota tayi tana goge kwallan tace shikenan amal nahakura kidena kuka,da sauri amal ta d'ago kai tana kallon mubinat amma daga ganin fiskanta tasan akwai wani abu aran mubinat bawai ta hakuran bane.

"Yauwa mubinat pls karki sakeyin kuka bari inje gida in d'ibo kayana dan mushirya akan lokaci kinji?" To tace da ita sannan amal ta tafi.

Mubinat ta fito tsakar gida ko d'ankwali babu akanta gun abba ta wuce,amma bayanan umma kawai ta samu da mutane anata hidima. Kusa da umma taje ta rik'ota tace umma kina sona kuwa kamar yadda mahaifiyata take sona? Umma ta kamota zuwa jikinta tace haba mubinat ina k'aunarki fiye da hakama meyasa kike fad'in haka,kidena kinji?

Janye jikinta tayi daga gun umman tana komawa da baya tare da kwalla tace sam banga alama umma,da kina sona dakin dakatar da wannan auren tunda kowa shaidane cewa banzab'i ya atif a matsayin mijiba wlh Allah bana kaunarsa idan kuma akayi auren wlh bazaku sake ganinaba wannan alk'awari na d'aukawa kaina. Tana kaiwa nan ta fice aguje taa kuka mai karfi,kowa a palon jikinsa yayi sanyi, umma kuwa hawayene yaketa zuba daga idanunta tanajin irin k'unar da mubinat 'yarta keji,amma babu abinda zata iyayi akai domin lokaci ya k'ure.


  Atif ango kuwa yana can shida friends nashi sunata shirye shirye,amma sam hankalinsa nakan *sis mubinat*,shikanshi tausayinta yakeji amma kuma bazai iya hak'uraba dan yana matuk'ar k'aunarta fiye da tunanin masu karatu.

"Guys zanje gida idan kun gama zamu had'u,ok sukace dashi sannan ya d'auki motarsa se hanyan gida. Wayar amal ya kira ,bugu d'aya ta d'aga tare da sallama,amal kuna tare da sis mubee ne? A'a yanzu na barta a gida amma zan koma yanzu. Ok amma ya take? Well gaskya babu wani canji akan yadda ka sani,tana nan akan bakanta. Hankalinsa atashe yace "oh my God" pls amal kishawomin kan sis mubee,amal i luv her nd i promise to take care of her pls amal do mosething bazan iya rayuwa ba sis mubee ba plss. Dukda cewa itama amal bata son mubinat da ya atif amma yana bata tausayi sosai har cikin zuciyarta,kuma tasan cewa ya atif zai rik'eta rik'o na hak'ik'a zai kula da ita sosai amma kuma kash sam mubinat bata k'aunarshi. Atif yaji shuru daga b'angaren amal dan haka ya sake cewa amal ar u there? "Tace yes bakomai ya atif amma pls ina neman wata alfarma agare dukda dai nasan baishafeniba pls karkayi k'ok'arin tarayya da mubee harse ta fara sonka pls?"

"Shuru atif yayi,azuciyarsa kuwa cewa yake damuwar sis mubee kenan,tabbas yasan sis mubee ne ta gayamata hakan. Murmushi yayi tare da cewa indai wannane matsalar takwantar da hankalinta,amal zan zauna da sis mubee koda babu komai tsaanina da ita i promiss. Shikenan ya atif bari inje gurinta dan ita kad'ai na bari.


  Muryan shureim takeji tundaga waje yana dariya. Wuf ta tashi kamar ba itaba ta fito tsakar gida da gudu ta k'arasa gun motarsu. Da sauri shureim yazo ya rungumeta yana kwalla,kwallan data gani a fiskar shureim ne yatabbatar mata da cewa yauma babu wani nasara da'akayi.

Mik'ewa tayi ta nufi hanyan zuwa shashinsu tana zubar da kwalla masu zafin gaske,shikuwa baida niyan tsayawa sam,dan haka tasha gabansa ta tsaya suna kallon juna cikin ido.

"Meyasa kake son ka haukatanine,meyake faruwane nakasa fahimtar komai *ya farhan* dan Allah ka fahimtar dani,nan da 1hr za'a d'aura min aure fa da ya atif shikenan bani bakai fa ya faran mun rasa junanmu fa kenan baka ganewane wai? Dan Allah ka dawo hayyacinka ya farhan dakai kad'ai zan iya rayuwa pls ya farhan ka farka daga baccin da kakeyi plsss idan na rasaka rayuwata batada amfani habibina pls...

Motar atif ne ya shigo haraban gidan,tun daga nesa yake hango sis mubee durkushe agan farhan tana kuka sosai. Farhan yace sister mubinat pls kidena kuka ki tashi kinji? Shureim yace dole tayi kuka ya farhan yaza'ayi ace ka kasa ganeta aurentafa za'ayi yah farhan ina tausaya maka idan har kazo ka gane wacece sis mubee agurinka dan wlh nasan halinda zaka shiga seyafi wanda ita take ciki ayanzu dan nikad'ai nasan irin k'aunar da kakeyiwa sis mubee dan Allah kadowo hayyacinka yah farhan.

"Sam farhan bayason ganin shureim cikin damuwa dan haka ya rik'o shureim yana share mishi hawaye yace "shureim naganeta mana sis mubee ce kacemin koh aiban manceba kacemata tadena kuka. Kamance mana, kaizaka rarrasheta baniba domin rarrashinka take bukata a yanzu.

  Kallonta yayi cike da murmushi afiskarsa yace "tashi sis mubee nd pls stop craying okay?" Koba komai taji sanyi a ranta,atare suka d'ago zuwa sama yana mata murmushi itama haka.

  "Atif ya dad'e atsaye yana kallonsu,matsowa yayi kusa da farhan suka gaisa,ai kuwa seyace toga sis mubee kasake rarrashinta koza dena kuka,atif yayi murmushi yace ai duk gidannan kai kad'aine zaka rarrasheta tayi shuru kainedai ka kasa gane hakan. Mubinat ta maida kallonta gun ya atif,hannunsa ta janyo da sauri shikuwa yana biye da ita kamar k'aramin yaro har palo,sannan ta durk'usa agabansa tana cewa "tunda kasan da hakan pls ya atif kadakatar da aurenmu kace baka sona dan Allah ya atif kataimakeni?"

  Shima duk'usawa yayi cikin fiskan tausayi da damuwa gabad'aya ya canja kamar ba atif d'an gaye da aka saniba yana kallonta har cikin ido yace dazan iya danayi tuntuni sis mubee amma wlh bazan iyaba kiyi hak'uri sis mubee.

Kuka tafarayi tana dukansa ak'irjinsa tanacewa wlh zaka iya furtawa fa kawai zakayi dan Allah kaje ka gayawa abba cewa kapasa dan Allah ya atif? Sis mubee kekike ganinsa kawai amma bakina bazai iya furtawaba,ki amince dani zan rik'eki fiye da farhan zan k'aunaceki da nuna kulawa fiye dashi pls kibani dama my luv? Hannunta ya rik'o wanda take dukansa dasu d'in yana kissing nasu.

  Janye hannun tayi ta mik'e dagudu zuwa d'aki tana kuka,da sauri yabi bayanta amma tasa key sautin kukanta kawai akeji,koda ya duba agogon hannunsa saura 30minits d'aurin aurensu dan haka yafito yabarta...


K'ofar gidan alhaji abdullahi bakari acike yake da jama'a,sakamakon d'aurin aure da za'ayi na atif muhammad bakari da kuma mubinat abdullahi bakari.

Guri yayi kyau sosai inda ango yasha farin voyel mai kyau tasha aiki bansan wani kyau zance muku atif yayi tunda mada shid'in maikyaune. Fararen hakwaransa kawai ake gani a waje,wanda yake k'ara masa kyau.

   Abokansa kuwa ankon shadda milk sukayi duk aikinsu kusan iri d'ayane. Hmm kusan 'yan kwallo da farin jini karkuga yadda suka had'u abundai se wanda ya gani.

Mubinat kuwa tundata shiga d'aki ta kulle kanta sam tak'i bud'ewa ko wanka tak'iyi,babu yadda ba'ayi da itaba amma sam tak'i bata sauraron kowa. Jitake kamar ta gudu amma babu halin yin hakan,ahankali ta bud'e kofar lokacin datajiyo an fara shirin d'aura aurenta.

Yana shirin fita zuwa gun d'aurin auren sakamakon lattin da shureim yasa sukayi,kawai seyaji an damk'i garensa tabaya ance "ya farhan dan Allah karkaje wannan auren ka d'aukeni mugudu dan Allah."

"Me hakane kikeyi sis mubee,dumekifa ko d'ankwali babu kuma ga mutane pls kikoma ciki kinji?" "No ya farhan wlh bazakajeba bakuma zanje ko ina sedai mutafi tare,wlh bana son wannan auren pls kadakar domin kai kad'ai zaka iya dakatar da auren pls ya farhan." Kuka sosai takeyi,inda 'yan'uwa suka janyeta amma setayi saurin rungume ya farhan tare da damk'eshi gam ajikinta tana kuka.

"Wlh bana sonshi kainakeso ya farhan kaine farincikina dan Allah kusakeni bana son wannan auren ya farhan nakeso dan Allah abba kar'ayimin auren dole kutausayamin dan Allah.

Amal da shureim dai se kuka sukeyi tare da k'anwar atif d'in mai suna aisha.

Mutanen wajema suna iya jiyo kukan mubinat,kuma sam an kasa b'anb'areta daga jikin farhan.

Shikanshi farhan tausayinta ya kamashi,kuma sam yakasa janye jikinshi daga nata kome yakeji aranshi oho. "Stop it sis mubee kinsan me kikeyi kuwa,yakamata ki amince da wannan auren dan Allah kibarni in tafi...katafi? Zuwa ina kena,sedai mutafi tare wlh Allah bazan tab'a sakekaba sedai inna dena numfashi,baka ganewane wai? You are the one that i love ya farhan kaine abun k'aunata soyayyarka na fara ginawa azuciyata ya farhan ina duba halin da zaka shigane bayan kadawo hayyacinka yama za'ace babu wacce zata b'ace a kwakwalwarka seni,meyake faruwa dakaine ya farhan? Nice fa habibtinka kamance wannan sunan "habibti?" Kaine kasamin shi kaine malaminafa...atif ne yajanyeta da kyar ajikin farhan,se ihu takeyi tana banaso karku rabani da habibina dan Allah karka je gun auren ya farhan i love you pls karka fita. Umma ce ta wanketa da mari tace "wai me hakane mubinat,kishiga hankalinki fa,haba umma kemafa kinsan komai dan Allah karku rabani da zuciya domin ya farhan shine zuciya inbashi bani umma.

Hawaye umma takeyi tana cewa nasan haka,amma Allah yayi atif shine mijinki ba farhan ba kisa hakan aranki. Ganin farhan yakai har gate din gidanne yasa ta k'ara kuka tana cewa "habibi" take ya juyo yana kallonta, "iwaly habibi" tana hawaye ta sake furta "yon habibi" ya farhan ina fatan bazaka mance wad'annan kalmominba guda biyu,idan kamance komai tofa inaso ka tuna da wad'annan kalmomin,ka tuna da "innoby habibtee?"

  "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" farhan ya juya ya kalli shureim sannan ya maida kyawawan idanunsa kan mubinat,take kwalla ya cika masa ido domin tabbas ya dawo hayyacinsa daga jin wad'annan kalmomin da habibtinsa ta furta.

Amma ina bazai iya b'ata wannan aurenba adaidai wannan lokacin,hannun shureim ya kamo suka fita gun d'aurin auren.

Mubinat kam seta rungume ummanta tacigaba da kuka yayinda atif ya koma gun d'aurin aurensa cike da damuwa a ransa.

  Tunda farhan ya fita yaji kamar zazzab'ine takeson kamshi,domin ya tuna komai. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yaketa maimaitawa azuciyarsa. Ahmad abokinsa ya lura dashi dan haka yazo kusa dashi yake tambayarsa farhan are you okey? "No i'm not ahmad,tell me something auren habibti akeyi da atif dagaske?" Zaro ido ahmad yayi yace habibti fa kace, kana nufin kadawo hayyacinka ka tuna da komai? Kai kawai ya d'agawa ahmad,Alhamdulillah ahmad ya furta tare da niyan mik'ewa yace za'a d'aura aurennan dakai barina sanar da abba...no ahmad karka b'ata wannan auren duk d'ayane ai,nida atif duk abu d'aya dan haka kamance cewa nadawo hayyacina kabarshi aranka batare da kowa ya saniba hakan shizaisa habibti tazauna agidan atif. Ahmad yace naji mai sadaukarwa,amma kai kuma fa zaka iya hak'urin rashintane? Farhan yasa hannunsa abaki tare da fitar da iska yasake shafar hular kansa yace i don know...


Hmmm an d'aura aure an gama komai,amma sam farhan baima sam meyakeyiba. Mahaifinsa ya janyo daga gun d'aurin aure bayan ya gama gaisawa da mutane,mota ya sanya mahaifinsa ciki shida abokinsa ahmad sannan yacewa shureim yaje gida yanzu zai dawo,sam shureim yak'i,seyace to kaje ka rarrashi sis mubee zan dawo yanzu mufita dakai kaji? To yace sannan ya tafi da gudu.

  Farhan bai b'oyewa mahaifinsa kan cewa yatuna da komai yadawo hayyacinsa,ya gayamasa komai harda kwalla akan rasa mubinat masoyiyarsa dayayi. Mahaifinsa ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi,bak'in ciki zaiyi koko farin ciki? Farhan yacigaba da cewa abbi bazan iya cigaba da zamaba ahalin yanzu,dan haka zan koma gun ummi dama viza na yana nan,zanje ind'an huta abbi. Rungume mahaifinsa yayi yana mai zubda hawaye masu zafi,ahmad kuwa se shafar kafad'arsa yake shima yanajin abin aransa.

Mahaifinsa ya aminta da dukkan shawaransu,yasan acan madinan gun mahaifiyarsa da kuma sauran 'yan'uwansa zaifi samu sauk'i akan  zamansa anan nigeria.

  Da wannan shawaran suka rabu,kuma sunyi alk'awarin bazasu sanar da kowaba...


Bayan sallan isha aketa shirin d'aukan amarya mubinat wanda har wannan lokacin tak'i tayi wanka,babu yadda ba'ayi da itaba amma sam tak'i,dan haka aka kyaleta akace zakije kiyita mishi wari ai,ko kulasu batayiba tama bar musu d'akin rik'e da waya a hannunta.

  Wayar atif ta kira sekuwa aka d'auka da sauri tare da cewa "hello sis mubee" inaso inje gun ya farhan muyi magana,dad'i atif yaji wato harta farayin biyayya,bakomai yace da ita na amince miki. "Kasanfa dolene idan naje sena rik'eshi naji d'uminsa akusa dani,bakomai sis mubee na amince indai hakan zaisaki farinciki tobakomai kije fatana shine kidena sa damuwa a ranki pls my luv. Ya k'arasa maganar kamar mai shirin yin kuka,katse wayar tayi batare datace komaiba ta nufi d'akin ya farhan da sallama ta shiga.

Farhan yana had'a kayansa shikuwa ahmad yana zaune yayi tagumi.

Idanun farhan take gani wanda yake d'auke da tambaya,mik'ewa yayi yanufo inda take tsaye shima idanunta yakebi da kallo duksun dishe kamarba idanun habibtinshiba masu kyan kallo.

"Ya farhan ina zakaje kake had'a kayanka?"

Idanunsa ya k'aik'aya yace zanje gun ummi nane. "Umminka,kana nufin can saudi?"

Kai ya d'aga mata alamun eh. "Tomeyasa yanzu,meyasa zaka tafi kabarni ya farhan dan Allah karka tafi kabarni kayi hak'uri."

  Murmushin k'arfin hali yayi yace "sis mubee ummi bata jin dad'ine kuma tana buk'atana kusa da ita kinga dolene in tafi ko?" Kaita d'aga tare da share kwallan idanuta tace"Allah yabata lfy,yace ameen.

"Yaushe zaka tafi kuma yaushe zakadawo?"

"Gobe zan wuce abuja,jibi kuma zamu tashi." Shuru tayi nad'an wani lokaci sannan ta matso dab dashi ta rungumeshi tanana kuka mai shiga zuciya,wani iri yaji,seya fara k'ok'arin janyeta daga jikinshi "kibari mana sis mubee,kefa matar wanine yanzu."

  "Dan Allah ka kyaleni kozanji sanyi araina,kumama aina nemi izinin yin hakan kafin nazo nand'in."

"Kina nufin...dan Allah kayi shuru ya farhan,kabarni inji da abinda yake damuna acikin zuciyata pls."

Farhan yasan hakan baidaceba,amma shima yana cikin wani hali wanda awannan lokacin jin mubinat kusa dashi shine kawai mafita agareshi,dan haka shima yasa hannunsa biyu ya rungumeta tsam ajikinsa yana hawaye.

Sallamar atif ne yasa farhan yayi saurin saketa tare da goge kwallan fiskarshi yamaida kallonsa gun atif,ita kuwa mubinat ko'a jikinta batama san yashigoba tana rungume da farhan tana kuka ahankali...


Dukda cewa Farhan ya janye jikinsa,amma sam mubinat tak'i sakeshi. "Sis mubee ga mijinki yazo,kije ku tafi."

"Bazan jeba,dan Allah ka kyaleni Ya farhan kadena tayar min da ciwon zuciyata kabarni in kasance tare dakai koda na wannan lokacinne,inama da Allah zai d'auki rayuwata ayanzu,danafi kowa farinciki domin ina tare dakai habibina."

  Murmushi yayi tare da janyeta daga jikinsa yace "kinsan me kike cewa kuwa,matar aurece ke ayanzu kuma kina rungume da wani taya zakiso Allah ya d'auki ranki sis mubee,haka babu kyau karki sake fad'an hakan kinji?" Tundaya fara maganar take kallonsa tana hawaye,sedaya gama tace ai duk nasan wannan Ya farhan,koka mance ka koyar dani a islamiyya,kawai dai ahalin da nake cikine yanzu babu wani abu danyi inji dad'i hakan."

Ajiyar zuciya yayi yace "nafahimceki,amma fa shi bawa ana sonshi da tawakali da kuma imani aduk lokacin da Allah ya jarabcesa,dan haka kiyi k'ok'ari kicinye wannan jarabawan kamar yadda kike cinye jarabawan makaranta kinji?"

  Ido ta k'ura mishi tareda cewa cin jarabawan makaranta,ya akayi kasan hakan bayan baka iya gane koni wacece agurinka? K'irjin Ya farhan ya buga sosai danya so ya kwapsa,seyai saurin wayancewa yace "em ai shureim yana gayamin koma akanki shiyasa,ya k'are maganar yana murmushi,ita kuwa kallonsa kawai takeyi bata ko kyafta ido.

"Hannunta ya kamo batare dayace komai yakaita hargun da atif yake tsaye,sannan ya kamo hannun atif yayahad'a danata tace ga sis mubee a damk'amaka ita atif,dan Allah ka rik'eta da amana,sannan kayi hak'uri daduk wani abu dazata maka,ka d'aukeshi amatsayin yaranta nasan watara zata dena."

  "Ke kuma sis mubee kisani aljannarki tana gareshi tun lokacin da aka d'aura muku aure,dan haka zab'i yana gareki, kisani miji ya wuce iyayenki a yanzu,dan shiyake da iko dake ba iyayenki su sunriga dasun gama nasu,dan haka kiyiwa mijinki biyayya kicire komai aranki hakan shizaisa kusami zaman lfy kinji k'anwata"

  Duda dai mubinat tana cikin wani hali,amma kalaman farhan sun ciga jikinta sosai wanda yake k'ara fito da kwalla daga idanunta,nagode tace dashi cikin muryan kuka sannan ta janye hannunta daga nasu ta fita da sauri tana kuka.


Ahmad yasan kawai farhan daurewa yayi amma akwai ciwo babba azuciyarsa. Shi kuwa atif godiya sosai yayi sannan yabi bayan mubinat.

Fad'awa kan gado farhan yayi yana zubar da kwalla tare da fad'in "innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ahmad ne yayita dannansa harya d'an samu sa'ida sannan sukaci gaba da shirya kaya.


Tunda mubinat ta koma cikingida aikin kuka kawai takeyi,dan tabbas maganar Ya farhan gaskyace,sannan tasan koda wasa Ya atif bazai tab'a rabuwa da itaba,dan haka taci kukanta harta godewa Allah. Nasiha sosai abbanta yayi mata hakama umma,shi kuwa shureim tayata kuka yakeyi yana cewa "sis mubee dan Allah karki tafi kibarni,rungumesa tayi sunata kuka dan tana mugun son k'aninta kuma autansu fiye da kowa aranta,da kyar aka rabasu sanan aka wuce da amarya gun motocin da suke jere acikin gidansu.

  Motoci ba'a magana,duk dadai masu karatu basusan waye atif ba,amma kuci gaba da biyoni zan warware muku komai.

  Motar da akasa amarya sabuwce dal,dama musamman yasayeta dan d'aukan sis mubee nashi kuma amaryansa. Abokinsa mansur ne kejan mota amal tana gaba se kuma mubinata da yapendoninta biyu abaya.

  Hmmm gidan amarya sedai muce masha Allah base nayi bayaniba,koma dakomai ansa,bayan sun shiga yapendoni suka sake mata fad'a dama ance babu wanda zai kwana agidan se k'awayenta guda biyu kamar yadda abba ya tsara wato amal babbar k'awarta kuma aminiyarta se kuma k'anwar atif wato aisha.


  Bayan an maida kowane se ango da abokansa 'yan rigima sunata k'orafi wai ba'ayi event ba ko guda d'aya ai biki baiyiba kenan. Ati ya fusa yace "wai meyasa kukemin hakane,kunfi kowa sanin yadda akayi auren amma kuma kuke k'orafi i hate this wlh." Mansur yace sorry man bai kamata ango yana fushiba come down tsokanarka muke,but idan komai ya daidaita atsakaninku dolene mu had'a party. Wani wawan kallon ya watsawa nabil tare da wucewa ciki suka bishi a baya.

   Nanma bawani dad'ewa sukayiba baya sun ajiye musu abin ciye ciye sannan sukayi sallama suka tafi.

Gida ya rage ango da amarya se kuma amal da aisha,duk cikinsu babu wanda yace komai kowa yayi shuru,amal tace aisha ina zamu kwanta ne dan gaskya nina gaji bacci nakeji. To nan dai d'akintane cewar aish,sedai muje d'aya d'akin. Babu inda zakuje,duk anan zamu kwana.

Amal tasan halin mubinat,dan haka bata tsaya jayayyaba kawai ta gyra kwanciyarta se bacci. Aisha kuwa cewa tayi "mubinat kinsan dai ni k'anwar Ya atif ce uwa d'aya uba d'aya,kuma kinsan naso aurenki da Ya farhan 100% amma Allah baisa shine mijinkiba,dan haka dan Allah kimance da baya kirik'eshi da amana pls mubinat,Ya atif yana miki k'aunar da komai kikace kina so zaiyi amma fa bazai iya sadaukar dake ga waniba.

Mubinat tayi kuka harta gaji dayin kukan dan haka tayi shuru tare da cewa aisha to.

Tabbas tasan aisha tana sonta sosai,dan haka ta mik'e tare da cewa aisha "kuci abinci mana, dan kuma bakuci komaba,bari naje na watsa ruwa."

  Aisha taci ta k'oshi sannan ta kwanta. Bayan mubinat ta fito ne ta goge jikinta kawai sannan tasa doguwar riga itama ta kwanta,kuma yunwa takeji sosai danko karyawa batayiba.


Shikuwa atif yana can shi kad'ai yanata kiran number'n sis mubi amma ba'a d'auka dantabar wayan acan gida cikin walldrop nata. Number'n amal ya kira akashe,dan haka ya fito daga d'akinsa zuwa nata,abakin k'ofa ya tsaya yana nocking tare da kiran sunanta "sis mubi" ahankali yake kiran sunan. "Na'am ta amsa tare da tunanin mekuma yazoyi?"

Komawa yayi hanyar zuwa d'akinsa,koda ta bud'e bata ganshiba seta hangoshin nesa da ita. Bayan ta rufo k'ofarne tanufi inda yake tsaye tace "gani." Hannunta ya rik'o tare da janta a hankali seta janye hannunta ta tsaya cak tare da b'ata rai.

  Matsowa yayi inda take ya sake rik'o hannunta yace "kiyi hakuri magana zamuyi yanzu zaki koma" hakan yasa tabishi a baya har suka shiga d'akinsa.

   "Kiyi hak'uri ki zauna pls"

"Ni bazan zaunaba"

"Y?"

"Bakomai"

"To shikenan ni bari in mik'e,hakan yamiki?"

"Silent"

Hannunta ya rik'o "sis mubi yunwa nakeji,nasan kema bakici komaiba pls kizauna ga yogot na kawomiki dan nasan kina so."

Bamusu ta zauna ahankali dan gaskiya tana jin yunwa sosai. Dad'i yaji,dan haka ya d'auko tare da cips da sauransu ya ajiye agabanta yace"indinga baki?" Kai ta girgiza masa alaman a'a,"to bisimillah kifar ci."

Hannu takai kan yogot d'in,seyace barina bud'e miki,mik'amata yayi tasha sata ajiye ta fara cin cips d'in shima haka.


Bayan tajci ta k'oshine setace "nizanje in kwanta"

"Ok kijira ingama se'in rakaki."

Shuru tayi tana kallon gefe harya gama sannan ya mik'e tare da kamo hannunta yace "tomuje."

  Yana rik'e da hannunta har suka isa k'ofan d'akinta sannan ya sake rik'o d'ayan hannunta ya janyota jikinshi ahankali tafad'o a jikinsa,seya rungumeta da hannayensa biyu.

Karon farko kenan da hakan yafaru da yardanta,dan haka setaji wani iri. Magana taji yayi cikin wata irin murya mai kashe jiki yace "I love you sis mubinat,i luv u so much tare da sake matseta a jikinshi." Ita kuwa seta fara kwalla tana tuna Ya farhan. Ahankali ta janye jikinta daga nashi tace "seda safe" sam yak'i sakin hannunta duka biyu yana rik'e dasu,ita kuwa seta sunkuyar da kanta tak'i kallonsa,sake matsowa yayi dab da ita ya rik'o fiskarta tare da manna mata kiss a lips nata yace "Allah ya tashemu lfy" da sauri ta shige d'aki sannan shima ya tafi zuciyarsa cike da farinciki...Lips d'in nata taketa tab'awa da yatsun hannunta tare da juyawa ta kalli su aisha wanda sun dad'e dayin bacci,ahankali ta kwanta amma sam bacci yakasa d'aukanta farhan kawai take tunawa.


Da asuba bayan anfito daga masallacine farhan ya wuce gun abba bayan sun gaisa da umm ne yake sanar musu da tfyansa madina gun mahaifiyarsa. Abba yasan da zance tunda mahaifin farhan ya gaya mishi tun a dare jiya,dan haka suka mishi addu'oi tare da fatan Allah ya kaishi lfy.

"Idan ka tafi yaushe zaka dawo ya farhan?"cewar shureim. "Karka damu bazan dad'e sosai wannan karon 2month zanyi indawo"

"Har wata biyu ya farhan,toni dawa zaka barni kenan babu sis mubi kuma babu ya atif"

"Ai zan dinga kiranka a waya muna hira,kaga zan d'ebe maka kewa koh?" Ya shafi kansa tare da cewa muje ka tayani shirya kayana,bamusu ya mik'e suka fita atare yayin da iyayen mubinat suke binsu da kallo.

"Hmmm rayuwa kenan" kewar umma,yanzu abban mubinat shikenan farhan ya rabu da mubinat? "Haba hajiya meyasa kike son dawo da hannun agogo bayane,kinsan dai yanzu mubinat ta zama matar atif,kuma ai da atif da farhan duk d'ayane.

  "Hakane alhaji amma ai ita mubinat takasa gane hakan,wlh ni tausayinta nakeji acikin 'yan kwanakinnan ta dena cin abinci kar wani cutar ta kamata alhaji,kuma mubinat bazata tab'a sakewa da atif ba musamman ma idan farhan yana raye."

   "To hajiya yanzu dai abinda ya dace damuyimata shine addu'a,Allah ya daidaitasu yabasu zaman lafiya" amenn cewar umma.


8:00am ahamad yazo kai farhan airport,harda shureim akayi rakiyan dan rigima dayaketa musu.

Suna isa farhan yayi musu sallama sukuwa suka dawo gida.


Can gidan amare kuwa,bayan sunyi sallan asuba suka sake komawa bacci abinsu.

Shikuwa atif wanka yayi ya shirya cikin galila ash wanda tasha aikin yayi masa kyau sosai seya kira number'n amal. Tunda tayi sallah ta bud'e wayan yanata ringing,da sauri ta farka tare da dubawa taga atif ne. "Hello ya atif ina kwana"

"Lfy amal kun tashi lfy?"

"Lfy lau wlh"

"Em sis mubinat fa?"

"Tana bacci"

"Ok toshikenan dama zan fitane ko akwai abunda kuke buk'ata?"

"Eh zanso akawo mana indomie da kuma kayan miya na tabbata sis mubi zataci idan na girka dan tana son indomie musamman idan yaji attarugu."

"Ok badamu,akwai komai a kichine kayan miyanne dai babu bari inje inkawo muku dame dame kenan?"

"Tattasai albasa attarugu da carrot"

"Done,idan ta tashi kisanar da ita cewa nafita pls"

"Insha Allah zataji."

"Em amal nace ba,wayanta baya kusa da ita ne?"

"Yeah mun mantashi a gida cikin walldrop nata ne"

"Ok thanks"


Amal ta ajiye wayan tare da juyawa ta kalli inda sis mubinat take,baccinta kawai takeyi,hannunta takai kan mubinat aisetaji jikinta da zafi sosai.

"Subhanalillah,mubinat zazzab'i kikeji koh?" Hakan yasa mubinat da aisha farkawa suna mik'a.

"Dan Allah kubarni bacci nakeji"

"Mubinat ba bacci kikejiba zazzab'ine yake damunji kinji jikinta kuwa cewa amal."

Aisha tasa hannu a yuwanta aikuwa seta cire da sauri tace "to ai dole a sanar da ya atif"

Wayarta ta d'auka ta kirashi,kamar yana jira kuwa ya d'auka hello aisha yadai?

"Ya atif sis mubinat ce jikinta zafi kamar wuta alamun dai zazzab'ine yake son kamata"

"Subhanallah,toshikenan ina dawowa yanzu"

"To"

  Hankalinsa atashe ya gama yimusu sayayya sannan ya dawo cikin sauri.

D'akin ya nufa da sallama,suka amsa tare da mik'ewa bayan sun gaisheshine se suka fita zuwa kichine.

  Ahankali ya zauna gefen gadon kusa da ita tare da d'aura hannunsa akan wuyanta. Motsa jikinta tayi ahankali tare da bud'e idanunta saboda k'amshin turarensa dataji,ido hud'u sukayi dashi yace "sis mubi tashi muje inkaiki muga doctor"

"Uhm uhm babu abinda yake damuna bacci kawai nakeji fa"

"Yazakice haka bayan gashi jikinki yayi zafi,sannan kalli yadda kike mik'an zazzab'i pls tashi muje kinji?"

"Ya atif bazanje ko inaba zansha magani kawai anan"

"Ina aka tab'a yin haka sweetheart,kiyi hak'uri muje yanzu zamu dawo sekiyi baccinki kinji?"

"Nifa bazanjeba"

   Hulan kansa ya cire tare da d'agota ya ajiye akan cinyoyinsa kamar wata k'aramar yarinya "wlh dolene muje kiga doctor dan gaskya bakida lfy tashi muje"

Kanta ta kwantar ajikinsa tayi magana ahankali "ya atif dan Allah ka barni in kwanta wlh bacci nakeji"

Kanta ya shafa ahankali tare da mata kiss yace "kekike ganin kamar baccine sis mubi amma wlh baki da lfyne,kuma kinsan dole semunje kinga doctor ina gyalen doguwar rigan naki?

"Nifa bazanje ko inaba karabu dani"

Ajiyeta yayi ta koma ta kwanta,shikuwa ya dubo gyalen da himar nata,tunkan ya k'araso ta mik'e da sauri zuwa toilet ta dinga kwaro amai sosai wanda kusan ruwane kawai take amarwan,se kuma wani green yawu haka.

Atif ya rikice sosai ya nufi inda take sunkuye rik'e da cikinta tana juyi. "Sorry sis mubi" yafirta cikin murya mai ban tausayi yana rik'e da ita.

Shiya kurkure mata baki tare da wanke mata fiska sannan suka dawo,d'ankwalin ya d'aura mata sannan yasa mata himar fari ya d'auki hulansa ya rik'ota "muje"

"Kin tafiya tayi tana tsaye"

"Sis mubi karmu fara haka dake fa,idan kink'ifa zan d'aukeki wlh" tasan zai rina,dan haka ta fara takawa a hankali yana rik'e da ita.

"Amal"

"Na'am ya atif"

"Zankai mubina hospital semun dawo"

"To,itace mukajiyo tana amai?"

"Eh semun dawo"

"To Allah ya sauwak'a,suka furta atare"

"Ameen."


Tunda suke tfy yaketa mata magana amma batace dashi komaiba yana rik'e da hannunta yana kuma driving.

Suna isa aka mishi komai shap shap suka wuce gun doctor. Atif ne yayiwa doctor bayanin komai,inda yace kusan sati kenan batacin wani abinci.

Bayan doctor ya gama dubatane yace lallai za'a bata gado, dan za'a samata drip ga kuma allurai da za'a mata suna dewa.

Daga atif har mubinat seda sukai mamaki akan hakan,doctor ya sake cewa "when last kikayi period naki?"

Kai ta d'aga ta kalli atif,murmushi ya mata sannan ya dubi doctor yace "em babu abunda kake tunani doctor,dan jiya aka d'aura mana aure"

Hahah atif kenan,ai ciki yana iya shiga cikin dare d'ayama.

"Nasan haka doctor,amma babu abinda ya faru tukunna."

"Ok,tomuje in nuna muku d'akinku cewar doctor."


Atif ya kira abban mubinat da kuma iyayensa ya sanar dasu cewa anba mubinat gado,dukkansu seda hankalinsu ya tashi sosai. Cikin hanzari umma ta shirya tare da abincinsu suka tafi.


Da misalin 10:12am farhan ya kira ahmad yace ina abuja. Ananne ahmad yake sanar dashi cewa ankai sister mubinat hospital harma an bata gado.

"What! Mekake cewa ahmad?"

"Tana hospital,nima can zan tafi kenan yanzu haka."

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" ooh noo habibti, i'm so sorry habibti cewar farhan...


Atif ne ya dawo gida domin d'aukawa mubina indomie. Duk wani abincin dasu umma sukakai mata sam tak'ici tace aje a kawo mata indomi,hakan yasa atif ya tafi gida cikin hanzari.

Sun gama komai dan haka suka shirya kayansu da komai suka biyo ati zuwa hospital.

Kwance take ansa mata drip na ruwa,su abba harsun koma anbar iyaye mata su umma da kuma iyayen atif.

Tana kwance su atif suka shigo dasu amal. Atif ya kasa sakewa agunsu umma dan haka ya ajiye malt peak milk da su fruit daya sayo sannan ya fita. Amal ce ta zuba mata indomie tace sannu mubinat taso kici,da taimakon amal ta tashi zaune,sannan ta ajiye mata plate d'in.

"Inbanda ke mubinat yanzumafa doctor yace ulcer ce ke damunki,kuma shine zakice kese abu mai yaji?"

"Umma tunda an samu zataci ai gara abarta taci koda kad'anne inyaso se'a had'a mata maltina da peak tasha,cewar amal"

Haka kuwa akayi,taci ba laifi sannan tasha ta kwanta se bacci dama tana jin baccin sosai.


12:00 su umma suka tafi dan har wannan lokacin bacci mubinat takeyi. Amal tace zata zauna da ita,aisha kuwa tabi 'yan gidansu suka tafi.

Bayan anyi sallan azahar atif ya dawo lokacin amal tana sallah. Kusa da mubinat ya zauna akan gadon tare da tab'a jikinta yaji yayi sanyi.

Nanma k'amshin turarensane ya tasheta daga bacci. Ahankali ta bud'e ido ta kalleshi,gabad'aya shima ya rame sosai dan shima babu kwanciyan hankali atare dashi tunda aka fara zancen bikinsu. Murmushi yamata tare da rik'e hannunta,se tausayinshi ya kamata,koma komai Atif yayantane kuma duk cikin yayyunta yafiji da ita hakama kuma ita d'in,tana k'aunarshi sosai fiye da sauran yayyunta.

"Murmushin itama ta mayar mishi tare da cewa Ya atif ina Ya farhan?"

"Farhan ya wuce abuja d'azu da safe harma ya sauka lfy,ya kumace ingaisheki da jiki."

Sam bataji dad'iba,amma seta nuna kamar bakomai tace "nagode."

"Ya jikin naki,meyake miki ciwo yanzu?"

"Bakomai,k'irjinane kawai"

"Sorry,amma yakamata kidena cin yaji tunda k'irjinki na ciwo,cin yaji zai k'arasa miki ciwonne kinji?"

Gyara kwanciyarta tayi tace "to"

Hannunta ya kalla ashe ruwan ya k'are harya far jan jininta,aida sauri ya cire mata ya goge mata hannu.

"Thankyou" tace dashi

"Bana buk'atar godiya daga gareki"

Hmm Ya atif ashe dai kaima doctor ne,cewar amal.

"Eh to nima dai yaune na fara koyo akan sis mubi"

Dariya sukayi,ita kuwa sis mubi tayi d'an murmushi.

"Inaso inje inyi alwala"

"Ok muje inkaiki toilet d'in"

"Aizan iya zuwa dakaina kazauna kaci abinci."


Amal ta zuba mishi abincin dasu umma suka kawo. Atif yaci sosai sannan yasha maltina da ruwa seya jingina ajikin gadon har mubinat ta idar da sallah sannan ya bata guri ta kwanta.


Mubinat tasamu sauk'i ba laifi,ruwa leda uku tasha,Atif yaso a sallamesu amma doctor yace sedai zuwa gobe da safe dan se'an k'arasa mata drip nata da allurai.

Abba sun tafi da amal bayan isha,inda akabar Atif da matarsa kad'ai.

Nanma ba laifi taci abincin kad'an sannan tasha kunun gyad'a da umma tayi mata. Bayan ya tabbatar data k'oshine shima seyaci,yanaci friends nashi sukazo su 7.

Sun dad'e suna hira ita dai mubinat bata cewa komai se kusa 10 suka tafi.

Wayar atif ne tayi k'ara ya d'auka tare da cewa "Farhan"dad'i mubinat taji dajin sunan,dan haka ta kasa kunne dan taji mezaice. Alhamdulillah da sauk'i sosai wlh gobema za'a sallamemu insha Allah. Ok gatanan,sannan ya mik'awa mubinat.

"Hello"

"Sis mubinat"

"Ina wuni,ka isa lfy"

"Alhamdulillah ya jikin naki?"

"Dasauk'i"

"To Allah yabaki lfy"

"Ameen nagode"

"Bakomai seda safe zan sake kira"

"To" sannan ta mik'awa Atif ya karb'a suka gama magana sannan sukayi sallama.

Atif yace kiyi baccinki idan ruwan ya k'are zan kirasu kinji?

"Kanta ta d'aga alaman to" sannan ta fara bacci shikuwa se kallonta yakeyi...

Damisalin 1:7 ruwan ya k'are,dan haka ya cire mata dama seda asuba za'a sa na k'arshen. Dan haka yahau kan gadon kusa da ita ya kwanta tare da rufesu da bargo daya kawo musu yana manne da ita ajikinsa.

Atif ya gaji ga bacci dayake damunsa,dan haka yake baccinsa hankali kwance. Koda mubinat ta farka tajita manne da mutum seta tsorata,arazane ta tashi tana cewa waye kai?

Hakan yasa atif ya farka ido duk bacci yace "it's me Atif sis mubi,kwanta kiyi bacci bakomai" bamusu ta koma ta kwanta shuru,shikuwa sake kamota yayi ya manna da jikinsa suka koma bacci.

Da asuba doctor yayi nocking,Mubinat ce ta fara farkawa sannan ta tab'a Atif,kashi doctor yazo. Da salati ya farka tare da shafar kanta yace "ya jikin?"

"Da sauk'i"

"Kiyi hak'uri natakuraki ko"

"Bakomai doctor yana nocking"

"Ok bari inje in bud'e mishi k'ofan danna rufe."

Bayan ya bud'e ne Doctor yace "yamai jikin?"

"Da sauk'i sosai"inji Atif

"Ok kuyi salla senazo nasa mata ruwan daya ragen"

"Ok toh"


   Bayan sunyi sallah ne Doctor yazo yasa mata ruwan. Ta lura da cewa bacci bai isheshiba,dan haa tace "nifa zama zanyi kazo ka kwanta anan"

"Karki damu zuwa anjuma za'a sallamemu idan muka koma gida zanyi baccin"

Kallonsa kawai tayi bata sake cewa komaiba.


Sallamar su ummane ya katse mishi kallonta dayakeyi. Bayan an gaisane amal ta zubawa mubinat abinci,sannan ta zubawa Ya Atif shureim yakai mishi can waje cikin motarsa,yana ci suna hira.

k'arfe goma aka sallamesu,tare da magunguna da kuma shawarwari da Doctor yabasu. Nan sukayi sallama,mubinat wai sam sedai su koma da amal amma umma tak'i tace "kema kinsan bazaiyuba mubinat,itama ita kad'aice agidansu kin kuma san komai basena sake gayamikiba. Haka sukayi sallama suka tafi,shima Atif ya d'auketa suka tafi gidansu.

Suna isa ta wuce d'akinta agyare tas,tasan aikinsu amal ne,dan haka ta wuce toilet tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga pink seta kwanta.

Shima Atif wankan yayi yasa kayan ball nashi ya fesa turare sannan yazo gunta tana kwance yasameta.

"Bacci zakiyi?"

"Eh"

"To bari inzo intayi zaifi dad'i koh?"

"Silent"

"Bakice komaiba"

Daidai nan ya kunna a/c tare da jan bargon dake shinfid'e akan gado yarufesu. Shuru tayi kamar ba mutum agun,ganinshi tayi ya matso kusa da ita yana kallonta.

Mezai faru taji yana kissing na lips nata cikin wani irin yanayi,kaucar da kanta tayi zuwa gefe tace

"Nifa bana so"

Murmushi yayi yace

"To aini ina so"

"Da gaske nake fa wlh bana so"

"Tonaji,but pls kibarni for d second time"

"Silent"

Hakan yasa ya k'arayi kusan 2mint sannan ta janye jikinta tare da juya masa baya.

Ajiyar zuciya ya sauke,sanan ya matso inda take ya rungumeta ta baya tare da cewa "Ok let's sleep"

But bazaki dinga hanani lips nakiba sis mubinat,kin amince?

"Eh" na amince indai bazaka nemi wani abunba bayanshi.

  Shuru yayi kamar mai d'an nazari sannan yace "yeah,na amince tunda hakan kike so"

Dad'i taji aranta tace "thankyou"

"Anything for you sis mubinat, i will do anything just to make you happy, koda kuwa nizai zamemin damuwa.

Shuru tayi tana nazarin kalamansa,shikuwa ya matseta ajikinsa yana shak'an k'amshin dake jikinta yace "i love you."

Ahaka dai sukayi bacci basu suka tashiba se  4:10pm


Post a Comment for "KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 1"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...