KISHIYOYINA CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KISHIYOYINA CHAPTER A

 KISHIYOYINA CHAPTER A


       
Tana tsaye a gaban me kayan miya tana jira ya zuba mata a cikin Leda.+

Cikin daddadar murya taji an mata sallama,a hankali ta juya idonta ya sauka akan wanda ya yi mata sallamar.
Nan da nan ta d'an dabarbarce, tare da yin murmushi ta juyar da kai, tana  Mai d'anjin kunya a fuskar ta, a hankali ta d'an duk'a ta gaishe shi.

Salim ya amsa yana mai binta da Kalli. Salim matashin saurayi ne da ya mato a kan FAD'IMATU- AZZAHRA'U yarinya mai cike da kwarjini da kamala.

Cikin murmushi ya kalleta ya  ce "zahra kwana biyu kin buya? duk sanda na je gidanku cewa ake ba kya nan", cikin jin kunya ta ce "ba..na nan kwana biyu,na je

garin
kaduna ne"

Ya ce "anya! ai na bugo wayar ki amma ba ta shiga."

Sunkwi da kai tai ta kalleshi "wallahi na yi matsalar caji NE kwana biyu shiisa." Katse hirar me kayan miya ya yi  ya mik'o mata, da sauri ta karb'a tai gaba.

Salim ya yi murmushi ya bita a baya sai  zabga sauri take, ya ce "se ka ce wadda za ki tashi sama."

Ta 'danyi ya ke,"wallahi ina sauri ne" saboda goggo na jira na."

"To shi ke  nan ba matsala, da ma nima zan d'anje wata Unguwa ne,amma gobe zan lek'o"

"Allah ya kaimu" Ta fad'a tana  Ci gaba da tafiya. Tsayuwa ya yi ya bita da kallo, shi kam ya rasa me ya sa zahransa ke d'ari- d'ari da shi, in de suka had'u a hanya ta dinga sauri kenan,ina ga ko kunyar a ganta da saurayi ta ke ne!  nan ya yi murmushi Zahransa dabance yana son mace me
kunya ( kunya adoce a garemu mu mata, ya kamata mu Kara damketa)

ZAHRA kam ganin ta  yi mai  nisa sai  ta rage sauri ta Shiga tafiya kamar wadda k'wai ya fashe mata aciki tare da d'an sakin  murmushi a fuskarta, domin duk sanda ta d'ora ido akan SALIM ba ta iya tab'uka ko mi ga matsanan- ciyar kunyar sa da take ji a gefe d'aya kuma tana jin tsoron kar wani d'an gidansu
ya ganta, ta san nan da nan za su kai gulma,musamman in babansu na nan su sa a yi tai mata fad'a, shiisa take ta ka tsantsan,tana shiga soron gidansu tai karo da yaya Abbas, ta ke kuwa ya da ka mata tsawa "ke da ga ina kike?

Cikin ina tace "Goggoce ta aikeni siyo kayan miya"

"Au!" ya fad'a yana muzurai  irin na manyan yayye, yayi gaba  ya fice daga soron. Ita kuma ta shige ciki.

Goggo da ke bakin famfo ta d'ago kai ta killeta "Sannu agantalaye, da ga aiken ki kin zauna ko? to wa zai miki wanke -wanken nan
ne?

  "ki yi hakuri" ta  fad'a ta nA nufar Madafa dan  d'ora Sanwa( abinci)

ZAHRA'U 'ya ce ga malam mu'azu wanda asalinsa d'an kano ne wanda ke zaune a k'aramar hukumar dala cikin k'waryar kano acikin unguwar gwammaja, yakasance yana da rufin asiri daidai gwargwado, yana kasuwancinsa a k'ofar wambai, ya yi aure da mata biyu.Allah ya albarkace shi  da
da 'ya'ya goma.

Goggo ita ce matarsa ta farko wadda sukai Aure tun saurayi da budurwa , ya Abbas shine babba sai me bi masa ya Atiku, san nan ya Abubakar, se ya Mubarak san nan Mariya,Rukayya da Zainab.

In da ya Atiku da Abbas su ke kasuwanci, ya abbakar kuma yana aiki a ma'aikatar (water  resource) kuma kowanne ya yi aure a cikinsu in banda mubarak wanda be samu aiki ba, kuma yace ba zai kasuwanci ba. Matan kuma duk an musu Aure.Wad'an nan sune na wajen
Goggo.

Sai Amina wato mahaifiyar FADIMATUZ- ZAHRA'U, ita zahran ita ce babba, se Aminu da ke binta san nan kultum Auta duk sune k'anana a gidan.

A yanzu haka maman zahra ba ta gidan don tun
bayan haihuwar kultum suka rabu da malam mu'azu, a zamansu  kishin Mummuk'e goggo ke mata,sakamakon masifa da Allah ya d'orawa goggo , had'e da rashin kawaici,ba k'aramin hakuri amina tai da goggo ba, wanda kishin goggo da kisan mummuk'enta ya haifar da rashin jetuwa ga malam mu'azu da amina, da ya ke Allah ya yi sai sun rabu hakan ta bar gidan.

Bayan barin Amina gidan goggo taci gaba da rik'e su zahra ba tsangwama ba
takura, sai dai fa ta k'ark'ashin k'asa ta  kan had'a tuggun da malam zai zane su zahra'u. Tsoronta su  ke  ji sosai Sobida fad'an goggon abu kad'an mutum zai sai ta hau! Sama, barin ma ace ita zahrance tai  abun, tofa abin nema  ya samu haka za taita lugwigwita zancen, domin sam ba ta son zahra ko kad 'an,  dan a cewarta zahra gulmammiya ce irin Babarta. Shi kam saminu miskili ne. Auta kultum kuwa ita anayi da ita.

A yanzu haka zahra ta gama Secondry
School A wannan shekarar. Shekarunta sha-takwas (18) tana san cigaba da karatu,  amma malam mu'azu
ya ce ba za ta cigaba ba sai  in a d'akinta, idan had mijinta ya yarda don Aure zai mata,dama ita ba ta sa abun aranta ba tun da tasan  duk yayunta su Mariya ba wacce ta cigaba da karatu.
wan
nan kenan.

  SALIM Matashin saurayi meji da k'walisa da gayu sam bayason kazanta kullum zaka ganshi tsaf tsaf. Ɗ'ane agidan Alhaji D'alha  tsohon ma aikacin Gwabnati wanda yay ritaya, Inda a yanxu hakan sede rufun asirin ALLAH tare da matarsa Rukayya.

Salim

S


hine da na uku a gidansu maza biyu yayunsa da k'annensa mata, ya kammala Digiri ɗinsa ashekarar 2012 wanda a yanzu hakan aiki

yake nema, ya dad'e yana k'aunar zahra don tin tana 'yar 12yrs yake santa tun tana gudu inyayi mata magana har ta dena, sun

shaku sosai bayan ta gama Secondry ne yake zuwa gunta zance,inda malam mu'azu sam baya son alak'ar su kawai de yayi musu shiru ne dan yaga iya gudun ruwansu,bawai don Salim bashi da tarbiyaba, ba kawai hakan nan be maiba,su kansu su ya Atiku

ba sa son ganinta da wani saurayi duk da ba wani ta tsayarba.


Salim shine zabinta, suna zuwa unguwar duk ran juma'a suna shiga gun tsofin abokan su shiisa ta ce Salim ya dena zuwa ran

juma'a sai de idan ya samu lokaci duk ran Saturday ya zo su sha hirarsu, shi kam a ganinsa ba me raba shi da zahra2


  Aminu ne ya taso daga Schooll duk ya gaji,ya shiga kitchen ya tarar da zahra na ɗora girki ya kalleta "Anty zahra yanzu na gamu da Salim yace na gaisheki wai  anjima zai shigo"

Tace "to naji."


Sallama ta ji daga k'ofar gida tai saurin futa tana kiran Aminu kan ya je ya duba, daga cikin ɗaki

yace shi baza shi ba don ya gaji.


"Ai shi ke nan,kai dama haka kake" kamar mace se kace ba namiji ba kullum kana ɗaki."


Ganin yanda mutumin da ke waje yana ta ƙwala sallama ya sa, ta zari hijab ɗinta da ke akan igiya tai gaba,tana zuwa soro taji magana tad'an lek'a taga mota a k'ofar gidansu, ga mutumin a daidai bakin ƙofar, ta ɗan rusuna ta gaida  mutumin da alama abokin

Babanta ne, yace 'yan mata babanki na nan kuwa?  tace  "yana kasuwa be dawo ba"

"Kash!! idan ya dawo kice mai Alhaji umar ne na tudun wada" ta amsa da to ta tashi ya bita da kallo.


Ta koma taci gaba da aikinta ,tana gamawa ta zuba a fulas takaiwa goggo, tana Alwala ta kalleta "zahra me ya hanaki gama girki da wuri?" tace "goggo kayan miyan ne ba asamo dawuri ba"

"Kin tsaya de lak'ai- lak'ai ..1


Shi kam Alhaji umar bayan fitarsa se yayi hanyar kasuwar da Malam mu'azu yake, yana zuwa

kuwa ya sameshi, nan suka gaisa yaushe gari, domin sundad'e  ba su had'u ba, abokinsa ne tun suna yara, shi Allah ya wadata da arziƙi, dalilin da ya sa abotar ta su ta ja baya, kenan, bayan sun gaisa ya ke shaida mai ai daga ma Gidansa ya ke, da har ze tafi se ya Gwammace da ya zo kasuwar.


Malam mua'zu yace "Masha Allah" sun d'an tab'a hira Alhaji ya gyara tsayuwa yana mai son faɗin Abinda ya tsaya mai a rai.

Wato mu'azu "na ga

iri a gidan ka"

Malam mu'azu ya ce "wanne iri fa?" Murmushi ya yi tareds gyara hularsa.


"Wato na ga'ƴarmu

ta girmam


"Au ho, Fateema! ai kasan girman d'an mutum ba wuya."

     

"Hakane, nan Ya yi gyaran Murya "A gaskiya idan ba'ai mata miji ba ina so"


Malam mu'azu  ya kalleshi da mamaki, sai kuma ya yi dariya "kai da kanka Alhaji" ya ce "wallahi kasan abun Allah"


"Ai wan nan abun so ne, kaima me iya ba da ita ne , balle kuma,kaida kanka ke so,in dai nine mahaifinta  na ba ka ita" Alhaji umar ya sa dariya "masha Allah! ikon Allah! Nan fa ya shiga godiya sosai.1


Sun daɗe suna hira, Sannan su kai sallama ya ke shaida mai zai shigo wani satin.


Shi kam malam Mu'azu murna ce fal! a cikinsa don zumuncinsu ze dad'a

k'ulluwa, ya kuma ɗore, cikin farin ciki ya ji zaman kasuwar ma ya  isheshi,yana jin zumuɗin ya tafi gida ya sanar da mai ɗakinsa, nan ya kulle shagonsa ya tafi gida. . .


Salim ne zaune a k'ofar
Gidansu zahra kan dandamali ya karo uwar hula se karkad'e gefen
wandonsa yake, tare da goge saman takalminsa da wani yanki, ya k'osa ya ga sanyin idaniyarsa.Kamar ta san ya ƙagu kuwa, sai ga ta nan cikin takunta me sanyi tak'araso soron gidansu ta tsaya, ta d'an leka daga kanta ya waiwayo suka hada ido tai mai murmushi da sauri ta sunkuyar da kan sakamakon kunya da ta kamata tace
"ka taso ga kujera a soro"
Cikin murmushi ya ta shi ya shiga suka ya zauna ita ma ta zauna suka gaisa, nan hira ta tashi suna yi suna Aunawa juna Murmushin kauna. A zzuciyarsa ya shiga yaba kyawun zahra, shi kam ba ya gajiya da kallonta. ta kasa sakewa sakamakom idanuwansa da ke kashe mata jiki.+

Murmushi ya yu tare da sakin wani gwauron numfashi "Zahra Beauty"
Ba ta dago ba sai kuma sunne kai da ta yi, nan ya ci gaba "bansan wani irin so nake miki ba! A hankali ya karashe maganar da cewa "karki barni Zahrata" ya karashe da kiran Sunanta cikin wani tattausan sauti, inda taji shi har k'wak'walwarta.

"Kunyar nan ta yi yawa zahrata"

"Ai kai ke sani kunya da kalamanka"
"idan ina gabanki bansan ina yin su ba."
Ya fada yana kara kusantar da kansa gareta.

Sund'au tsawon lokaci suna hira,sai wajen shi
an kusa kiran Magriba Maalam mu'azu yazo ze wuce masallaci, da sauri Salim ya sauko daga kan kujera ya gaishe shi nan a dan fusace ya ce "hirar ta isa a tashi ayi sallah ya fice abinsa"
Salim ya kalli zahra "toni zan wuce se jibi ko?"

Tace "Aa, se next week" ya tsaya
ya kalleta "so kike na kwanta ciwo ko?"

Tai Murmushi tare da cewa "wayo ke nan" murmushi ya yi sukai sallama kowanne zuciyarsa fes. .

Tana shiga gida! Goggo ta balbaleta da fad'a "ke zahra ke kullum yaron nan yazo sekin barni da aiki ko? to maza -maza kizo ki k'arasa don k'afata ciwo take, ke kullum
Na gaya miki Magana ba kyaji duk munafircin Uwarki kin dauka ko maji ma gani" ta d'auko buta ta fara Alwala zahra kamar an da sa ta a wajen, abu d'aya ta tsana taji Goggo na fada irin tace ta dauko gulmar uwarta,cikin jin haushi tai kitchen tana
k'un-k'uni ita inde fad'anta ya tashi haka take ,tana cikin tunani taji goggo na magana "au ina aikin? zaunawa kikai kina tunani? wallah ki kiyayeni tom."

Ta juyo ta ce "kiyi hakur" ko kallonta ba taiba tai dakinta, nan zahra tai tsai! can ta kumbura kumatu ta shiga magana a hankali "ba dama a ganka cikin farin -ciki se an bata ma' nan kama aikin da sauri ta gama ta daura alwala ta shige daki.

Washegari wajen k'arfe goma Zahra na wanke- wanke. Da yake ba School duk su Auta na gida ,da gudu Auta tazo "Anty wai kizo inji baba." da sanyin jiki ta d'auraye hannunta ta tashi ta shiga tana adduar Allah ya sa ba kararta goggo takai ba.

Yana zaune Lokacin ya gama breakfast nan tace "baba gani!" ya d'ago ido tare da gyaran murya ya kalleta "zahra kin san ni ne ubanki ko? kuma idan kina son samun albarka arayuwarki dole
kibi ni inde bai sab'awa sharia ba"
tace "hakane baba" yace
"To kinsan uba shine ke da damar zab'awa 'yarsa Mijin Aure inde budurwace ko? Ta gyada kai, "to ni de A matsayina na babanki na zaba miki Miji."

Da sauri ta d'ago ido, take jikinta y fara rawa ga k'irjinta da ya hau bugawa da karfi,yana kula da ita, ya nisa ya ce "amma na ga wani yaro na zuwa wajenki,
na bashi nan da sati ya futo idan kuma be fito ba dama nai miki miji dande na fita hak'k'inki ne tun da zamani ya canja"

Sunkwi da kai ta yi dan kalamansa na karshe sun faranta ranta.Kamar wacce akaiwa albishir da zuwa makka ta hau kan zabin bazatar da ya bata.

"ALLAH YAY MIKI ALBARKA" Ya fada yana mai kishingida ya shiga tunanin in har dai yaron ya fito to zai bawa alhaji hakuri, yana fatan ace ya gaza.

Ita ko tashi tai ta fita daga dakin tana mai addua.

**
Malam mu'azu da kansa ya sa aka kirawo mai salim ya ke gayamai kan,cewa ya fito don shi Aure zewa 'yarsa.

Nan fa sslim ya amsa tare da zulumin yanda abin ya zo mai bagatatan! Bai ka sa a gwiwa ba, ya samu babansa da Maganar, Alokacin Babansa yana karanta Jaridar daily trust, ya ajeta gefe tare da zare gilas dake idonsa ya kalli Salim "yanzu kai Salim kana da ai kinyi da zaka tarko Aure?."

ya sosa k'eya "Alhaji zan nema ai" Alhajin ya kalleshi " ba zata sab'uba, ba yanzu zakai Aure ba, kana ganin yayunka ba wanda yayi maganar Aure se kai? suda suke da aikin yi ma, dudu shekarunka nawa? ka ga ni yanzu ba k'arfi gareni ba kayi hak'uri kabarsu su yiwa 'yarsu Aure".

Cikin tashin hankali Salim ya dago y ce Dady don Allah ka taimakamin"

"Salim, Alhaji ya fad'a, yq ce
ba ma sa'insa da ku kuma kasan ni ba na magana biyu, dan haka ya rage na ka, ka tashi ka fita.

Nan ya tashi da k'yar yake tafiya se layi yake ya tafi b'angaren Mamansa yana zuwa ya fashe da kuka cikin tashin hankali tace "Aa meye?" yace "kitaima kan Mami za'a rabani da Zahra, Dady yace banda sana'a
bazan Aure yanzu ba"

Ta dad'e bata ga kukan salim ba tun yana k'arami, ta ce "ai wannan abin da kai ya nuna har yanzu da sauranka akan mace ka zauna kana kuka" ganin kamar ba ya ma gane me take cewa ya sa ta sassauta, nan tai ta kwantar mai da hankali tace "matar mutum
kabarinsa, sai ka yi hakuri ka fawwalawa Allah" tace yayita maimaita INNNALILLH WA INNA ILAIHI RAJU'UN hakan ya tashi ya tafi d'a kinsa
se maimaita wa yake, take ya i zuciyarsa tai sanyi.

Tunanin ya zai yi in ba zahra ne ya sa shi a gaba.Wani tunani ne ya fado mai zumbur ya mik'e ya fara tunanin abinda ya
ayyana ne mafitarsa.

Assalamu alaikum ftan na same ku lafi

Shagon printing na sa ne ya fado mai shi ya ma manta lokacin da yayi mai budewar karshe tabbas da shi zai fake wajen nunawa babansa yana sana a kuma tana kawo mai kudi.+

Ranar juma a  da misalin karfe 6 Alhaji Umar na k'ofar gidan su zahra .Yana nan cikin mota yana jira ya ga tawowarta,nan da nan ya gyara  ya shiga washe baki.Tun daga can ne sa ta hango motar gabanta ya fadi jikinta ya hau rawa ta damke hannun auta dan ji take kamar ta fasa ihu,sun karaso daidai wajen cikin ladabi ta gaishe da shi, jikinsa na rawa ya amsa ,tare da jan auta da hira da yake uwar surutu ce se ta biyemai , ita kuwa ta shige gida,goggo na ta yankan yakuwa, harararta tai tace "yawwa da ma ke ake jira. Alhaji umar ne ke jiranki a waje.

"Jira na kuma goggo ?"
"eh!ko haramun ne?

Wani abune ta ji ya tokare mata wuya kamar ta fasa kuka.Ganin yanda goggo ta tsare ta da ido, ya sa a hankali ta juya ta fita ta karasa gaban motar tana mamakin kiran. Murmushi ya yi ya cire hularsa wadda gashin kansa harda furfura Bayan sun gaisa Auta ta shige gida ya ce "na san ba ki san komi ba ,ba ki san  dalilin zuwana ba ko? To na zo ne batun   Aurekin dan na ganki ina so."

  Dafe kirji tai,  sauri tai ta sunkuya kasa  "Baba! ni kuma? yace "tabbas na rok'i Alfarma an bani Izinin nemanki fatan zamu fahimci juna" nan da nan ta fara hawaye "dama baba kaine wanda ake cewa zan Aura!?
Bai amsa ba sai murmushi da ya yi, sai
ta sunkwi da kai "Baba don grman Allah ka yi hakur wlh inada wanda nake so yace "nima ina sonki duk da tsufana."

  Ta shi tai da gudu ta shige gida. Alhaji umar ya hau Motarsa ya tafi.

Alhaji umar asalinsu d'an  bauchi ne kasuwanci ya kawo iyayensa kano har aka sameshi, ayanxu hakan yana zaune a  unguwar yakasai da ke kano Allah ya hore mai yana da wadata,domin  duk yakasai ansan da zamansa ,yana da mutunci a idanun mutane.
yana da Matan Aure har guda uku. Hajia zainab,Hajiya Uwani, hajia magajia.Duk yawan wadatar da ya ke da shi Allah be hore masa
haihuwa ba. Abun ya dame shi sosai. Abota tsakaninsa da malam mu'azu ta samo asali ne tun a Secondry scl Allah ya hada Jininsu har yanzu kuma suna abotar shiisa da yaga zahra yana so malam mua'zu ya Amince babu gardama saboda aminci.

    
  Alhaji umar wajen takwas ya shiga gida ,domin a yau ya ke son sanar da Matansa batun

Aurensa, bayan ya gama cin abinci yayi hamdala yana zaune a falonsa hajia
Uwani ta shigo ya ce mata taje ta kirawo sauran matan
kowacce ta zo, ba tai kasa a gwiwa ba ta juya, sai ga su duk sun shigo daya bayan daya, bayan sun zazzauna yayi gyaran murya. "Ina son sanar muku ne cewa zan kara aure, kuma nan da sati biyu, shiisa na kirawoku don na shaida muku"
Da sauri suka kalli juna cike da mamaki hajia uwani ta tashi tsaye "haba Alhaji ya da
girmanmu gotai-gotai za kai mana haka? kai ba abun kunya bane a gareka ka ce wani za ka kara aure."

"To haramun ne?
Hajia magajia ce ta tashi fuu! tai waje  tana magana "wallahi Alhaji mu zuba mu da kai" ta karashe fada ta fice.

Hajia zainab tace "Allahji ko dan ka ga bama haihuwa ko?" yace "duk abinda za ku ce kuce, amma wallah ba zan fasa ba, kuma sai na Aurota"

Ya tashi fuu ya shiga uwar dakinsa hajia uwani da ke tsaye ki gam! Har lokacin ta ce cikin fusata "ina! ina!  ace ina raye Alhaji ya Auro wadda za ta haihu! Hajiya zainab ta ce ke ma kya fada.
Dariya uwani tai ta ce, sai ni Hajja jabba, wallahi sai na ga bayan Auren nan don ba zai  janyo mana abun kunya ba."

Ta shi sukai sukaje falo sukai cirko -cirko, suna ta shawarar yanda zasu yi hajiya  zainab tace shawara ku kawo kunnuwanku in fada,nan ko suka kawo ta kitsa musu, wani irin shewa sukai tare da tafawa....

    Washegari
Da sassafe hajiya zainab tai shiri ko alhaji be san fitarta ba, wani k'auye ta tasamma  gun wani malamin duba, dan a tarwatsa auren dan ba su dau lamarin da sauki ba, bayani tai mai ta sheda mai zancen Auren alhaji, da kuma yanda suke so a watsa abin, dariya yayi ya hau buge-bugen kasa ya gama bincikensa ya d'ago ya kalleta "hajiya idan za ki bi ta tawa ki bari ai auren nan domin ba makawa se anyi, akwai dumbin alheri da ke kewaye da auren.Cikin tashin hankali tace "malam ba wani taimako?" yace"+

Hajiya idan kina son kanki da arziki ki bar shi kawai"

"Ka taimaka malam ko nawa zan biya, ni da kishiyoyina muna cikin tashin hankali."

Sai da ya ja gemunsa sanan ya kalleta, "taimako daya zan miki,zan baki laya da hayaki kije kiyi,muddin kikai to sai wani ba amaryar alhaji ba", guda ta saki agabansa ta ce "Allah ya ja da ranka boka."
Nan yayi mata bayani yanda za ta yi da maganin.Haka ta ajje mai kudi ta tafi zuciyarta fes.

Da karfi ta koma gida, matan na zaune akan kushin suna hira ta shiga, nan fa suka maida hankali kanta, wata shewa suka sanya bayan ta gama shaida musu, hajiya uwani tace "da zafi-zafi akan bugi karfe bari kuga" nan ta karkace kai  ta kwala kiran  Nadiya, amsawa nadiya tai tana mai tawowa '(Nadiya 'yar ruk'o ce, da hajiya uwani ta d'auko ta a danginta, a k'allah kowacce a ciki  ta d'auko 'ya'yan ruk'o daga bangarenta, tinda ba sa haihuwa. Domin kowanne yaro ka gani agidan d'an ruko ne,kuma ta bangaren matan. Abangaren alhaji kuwa babu danginsa da ya isa ya zo yayi kwana ko biyu ne a gidan, hantarar su uwani ma ya ishi mutum ya koma inda ya fito, daga su sai su, babu yanda alhaji ya iya sai de kallo.

Nadiya ta kalli  hajiya  "ga ni hajiya" "aikenki zanyi ki samo mana gawayi makota.
Hajiya me zaki da gawayi kuma bayan bakwa san warin kalanzir."

"Kinga Nadiya in za ki je ki je bana son sanya ido."
zumbura baki tai gaba ta bar falon.
Nan suka ci gaba da zantawa hajiya zainab na yin breakfast.

****
Bayan nadiya ta samo gawayin hajiya uwani ta karba ta shiga kitchen ta hada garwashi ta dauko suka duru su ukun cikin wani daki,nan fa hajiya zainab ta bude jaka ta fito da laya ta saka a garwashin, take ta fara konewa, daga bisani su ka dauko hayaki suka zuba, nan da nan  hajiya uwani ta dauka suka kewaye kaskon suna yi suna kare hayakin saboda yanda yake budade idanuwansu, sunan zahra hajiya uwani ta fara kira da dan karfi s har wani amsa amo muryarta ke yi, har sai da ta kira sau uku.

Wanda adaidai lokacin zahra na daki, ta zubawa wani frame da ke sakale a bangon dakin ido, kamar an buga mata guduma  ta ji kanta na sarawa, nan da nan ta ta shi zumbur tana kallon gefenta, duk sai ta diririce tana neman fita hayyacinta, hanyar  fita daga dakin ta dosa ko gabanta bata gani

Taka kafafuwanta kawi take yi tana dosar titi, so take kawai ta kauce daga ma unguwar dan ji take kamar ana maka mata guduma aka,so take kawai tabar nahiyar ma  sai layi take harta karasa bakin titi,duk wanda ya ganta sai ya yi tunanin ba daya take ba, sabida ko takalmi babu a kafarta, ballantana mayafi.+

Tsakiyar titi ta karasa, dan kanta duk ya juye,  adaidai lokacin wani babur ne ya tawo a guje saura kad'an ya buge ta, da sauri aka jata baya ta fadi luuu a kasa gefen titi a sume.

Cike da tashin hankali salim ya sauko aguje daga kan babur, dan ya gane zahra ce da wani irin sauri ya karasa gabansu inda mutumin d ya taimaka mata ya tsaya dan ya rasa ma mai zai mata.

Ganin yanda salim ya gigice yasa mutumin yace kasanta ne? juyawa yayi yaga yanda mutane suka cika wajen ya ce "eh ni ....

Ana haka sai ga aminu nan aguje dan a idonsa komai ya faru shi ya taimakawa salim suka kaita gida, ko motsi ba tai halin da goggo ta ganta ita kanta ta firgita da taimakon salim aka kaita asibiti sun taimaka ta farfado amma sam bata cikin hanklinta sai fusge fusge take kwananta biyu, kuma duk wanitimako anbata amma sukam ba su ga wata cuta atare da it ba,  nan fa hamkalin su ya dada tashi likita, ya bada shawarar akaita gida ai mata na gargajiya.

Hakan ko akai aka komar da ita gida sai buge- buge takeyi duk tsanarta da gogge tai saida ta bata tausayi,kannenta su aminu kullum kuka da cewa suke ta haukace, salim ko kullum yana tafe, malaa har tausayinsa, tabbas ya gano tsananin kaunar da yakema yar sa amma aikin gama ya gama, duk da cewa ba suyi wata magana da shi ba tun lokacin da ya ce  y turo iyyensa, sai a asibutin yake sanarr mai yana nan yana so iyayensa su yarda da aurensa.Komai ya gayawa malam kan abinda iyayensa suka ce game da auren. Nan malam ya ja shi ya bashi hakuri ya nanuna mai muhimmancin hakuri da yanda da kaddara tare da bin maganar manya,Sannan ya kara da cemar daman kwanakin da ya bashi kan iyayensa zu so ya cika, dan haka yayi ma zahra miji.

STORY CONTINUES BELOW

A ranar salim zazzabine ya rufeshi ya koma gida  ya bar asibitin.Yana jin ba zai iya hakura ba zai dada tausar babansa watakil ya amince, yasan muddin mahaifin  na sa yaje gurin malam baban zahra da kansa zai iya ci alfarmarsa a fasa auren zahra da wancen.

Su ya atiku kowa dai hankali ya tashi  satinta daya a haka malam ya kirawo wani malamin addini wanda yakan bada taimako,malamin yana ganinta ya shaida cewar da sihiri a jikinta, cikin ikon Allah wata daya tai akwance ta fara dawowa hayyyacinta, abin ya zo musu da sauki duk wannan abun da ake alhaji bai sani ba, sukam su uwani ganin alhaji yayi shiru da maganar ya sa suka sakankance kan aikinsu na boka yaci.

Salim ne gaban mahaifinsa kamar yanda ya saba uban na zaune yana karanta jarida, cire glass yayi ya kalli salim yace "wato kai ba zaka hakura ba ko? Printing har wata sana'a ce? kana tunanin ita ce za ta iya rike maka gida? in dai nine na haifeka kabar maganar nan banson ji.Tunda ma iyayen yarinya sunyi mata miji ai kaga abu yama zo da sauki dole ka hakura ka fuskanci abinda nake san dora ka akai."

Hawaye ne yaji ya zubo mai yayi sauri ya juyar da kai dan kar uban ya gani,  tunota  da halinda ta ke ciki shi yasa ya dadajin rauni, ita macen  da yake so kamar me, zahra itace mabuduin zuciyarsa.

Da fargaba ya ce Dan Allah  daddy ka taimaka min bai," dady bai sak bi ta kansa ba ya wuce ya bar wajen, ganin hakan yasa a salube salim ya tashi ya bar wajen kansa har ciwo yake mar, yana tunanin ya zama dole ya taushi zuciyarta ya bata hakuri gameda lamarin tunda ya gano zahra ba rabonsa ba ce.

STORY CONTINUES BELOW

*BAYAN WATA DAYA*

Fes zahra ta warke sai ragowar rbutu da take sha,a wannan lokacin alhaji yake kokarin kai kudi da sa rana.

Sati da ya zagayo aka kai kudi da saka rana da lefe duk a hade, aranar zahra in banda kuka ba abunda take, ita sam! Ta dauka an manta ma ganin halin da ta shiga ma ta dauka alhajin zai ce ya fasa, ita gashi ba
kawaye gareta ba balle su taya ta jimami, ko bata shawara, domin bording school tai wato F.G.C KAZAURE duk suna nesa dan tunda taicandy ba wacce suka sake haduwa.

Sai su anty mariya ne suka zame mata kawayen suke lallasarta
kowacce da 'ya'yanta ta zo,da yake Jininsu yafi had'uwa da zainab,dan duk cikin yayan goggo itace ba ruwanta ita ke nuna mata so tun tana karama, shiisa jininsu ya fi haduwa kuma bata nuna mata yan ubanci, nan tai ta bata baki, tana nuna mata muhimmancin yarda da kaddara.

Zaune suke duk sun barbaje afalo Mariya takalli zainab taga yanda ta ta sa zahr agaba tana ta lallashi,  ta ce "kema zainab
da bata lokacik kike,yo karta yarda man Aurene dai ba fashi. Rukayya ta ce
" wallah kam karma tayarda man kanta farau?

Zanab ta dago ta kallesu "kai haba! mu fa yayunta ne manya, duk cikinku wa ce ta Auri babban mutum haka? haba balle ita d'anya sharaf yrinya, ni kam wallh banji dadin auren nan ba ,goggo can cikin daga daki
"to Abuwa kinfara ko? to meye naki a ciki? ba Ubanta ne yaso  hakan ba!"

Zainab tace "haba goggo k'anwarmu ce fa, ai dole mu lallashetq."

STORY CONTINUES BELOW

Ya atikune ya shigo gidan da matarsa yaji ana maganar yace "ku barta man, wallah in baki mana shiru ba sena farfasa miki jiki."

Da saurri ta shige daki dan tsabar tsoronsa take, nan da nan zazzabi ya rufeta gashi sun isheta da hargowar ganin kaya. .

*BAYAN KWANA 2*

Wajen la'asar tana wanke kayanta akai
Sallama. A hankali ta daga kai ta kalli kofa tare da amsa sallmar budurwar da ke dada shigowa tsakar gidan.

Taunar chewgum ta ke  fuskarta ta sha fenti na poundation ta yi  kwalliya dai sai kallon ko'ina take tana yatsinar fuska.

Sannu d zuwa zahra ta ce, sannan ta kwala kiran  sunan  goggo tana cewa ta zo ta yi bak'uwa, da sauri nadeeya ta dakatar da ita, "ke ba gunta nazo ba ,ina bukatar ganin Zahra ne"

Kallonta zahra ta yi, ta dago da d'an murmushi a fuskarta ta ce ai nice! tabe baki nadeeya tai tace ta kwana gidan sauki. Kalleni nan sunana Nadiya 'ya d'aya daga cikin 'ya'yan Alhaji Umar da zaki Aura, wato na zo yi miki kashedi ne da babbar murya. Muddin kika bari aka kawo ki cikin Manyan mata iyayena wallahi saikin raina kanki domin mu nan mun isheki, kalleni koni nan na girmeki don haka kishi da iyayena matsalane in,fatan kin gane."2

Saroro zahra tai ta kalleta tai murmushi ta "to na ji."

Jin hakan ya sa  ta sakai ta fita. Zahra dake tsaye kamar an dasa ta ta tab'e baki "banza kawai ta dauka son uban nata ma, ake wallahi sai kun Gwammace kid'a da karatu."

Wasu Hawayene suka fara zubo mata sharrr!domin Ubanta ne ya janyo mata amma ya ta iya da da hanyar da zata bi da ta bi, tabbas rashin uwa babban gib'i ne,duk rashin Mamanta
ne ya janyo mata. . . .

*****
BAYAN WATA DAYA
Satin biki ya kmq, gida ne  ya fara chika don gudanarda harkar biki duk su Mariya sunzo da iyalansu haka yan uwansu na nesa da kusa duk sun bayyana.  Zahra duk
ta fita hayyacinta,domin ko gyaran jiki tak'i bari ai mata.

Hayaniy ce ke tashi a tsakar gidan wani yaro  ya yi sallama, lokacin zahra na bakin famfo tana alwala,amsa sallamar tai yaron ya ce "Anty zahra wai gashi inji wani ya ce a baki" ya mika mata wasik'a ta karba shi kuma ya koma, a hankali ta bud'e wasikar cikin sauri, taga  sunan
salim b'aro- b'aro, kalaman rabuwa ne domin yana
shaida mata shi kam yayi gaba domin bazai iya ganin Aurenta ba, ya tafi sai wata rana.

Cikin kuka ta durk'ushe anan bakin famfo ta b'oye kanta ta shiga kuka ba wanda zai lallasheta ballan tana ya bata baki. Ji tai babu wanda take bukatar gani sai mamanta,nan ta wanke fuskarta ta silala daki ta dauko mayafi. Da sauri ta fita  ta tafi gidan Mamanta.

Ko da ta je kuka taita yi ma maman kamar za ta shide, ita kanta maman daurewa take dan ta san an kwari yarinyarta amma babu yanda za tai, zama gefen zahran maman ta yi . haka tai kwantar mata da hankali tare da
mata nasiha na ta yarda da d'aukan k'addara dayin biyayya da samun rabauta duniya da lahira. Sai wajen laasar tabar gidan mamanta cike da kewa.

Washegari aka fara biki aka sha shagalin  kamu da walima.

Ranar Asabar Aka d'aura Aurenta da Alhaji umar wanda takira Auren k'addara domin tunda safe zazzabi me zafi ya rufeta.

Allah sarki duk ta kod'e ta jeme abun tausayi haka aka gama biki lafiya aka kaita dakin mijinta,wanda ta kirawo kurkuku......to
Makaranta kubiyo ni donjin yanda zaman nata zai kasance da kishiyoyinta. .

Tunda aka kai zahra gidanta ta na kudundune akan gadonta in banda kuka ba abinda ta keyi, zuciyarta na kuna lalle sai ta danawa mitumin nan bak'in ciki, domin ya cuceta yayi sanadiyarr rabata da
farin -cikinta ,tana yar yarinyarta ace  ta auri kamar Mahaifinta
ya kusa jika da ita yaya za ta iya zaman aure da shi tana ganinsa kamar babanta. Abin bakin cikin  ya zatai da wad'annan matan nasa? runtse ido ta yi cikin matukar jigata da rauni hawaye na ci gaba da zubowa, ba ta tsagaita da kukan ba har saida tq ji kqnta na barazaar fashewa saboda ciwo.Bacci ne ta ji ya fara daukanta ta ji  an bud'e k'ofa nan da nan k'irjinta ya buga takun da ta ji ya tabbatar mata cewar. Alhaji Umar ne, Ahankali ya tako ya zauna kusa da ita, ya dade yana kallonta kana ya saki ajiyar zuciya  ya kira sunanta "zahra" ko motsi ba tai ba ballantana ta dago kai  ta amsa.

Hakuri ya shiga bata don ya san ba bqcci ta ke ba tana "zahra ki
yarda da k'addara walau me kyau da da mara kyai Allah ba ya dora bawa abinda yasan ba zai iya ba, duk da ni tsoho ne nai miki tsufa to ki godewa Allah tunda soyayyace ta gifta, na miki alk'awarin kula dake cikin dukkanin karfina, duk abinda ki keso shi zan miki, kai har fa Makarnta zan saka ki kici gaba, wallahi Allah ne ya hada jinina da naki, kinji zahrau baby ya fada tare da shafa tafin kafarta,kamar an dasa gunki bama ta dago kai takalleshi ba, duk da cewa shafa kafarta da yayi saida gabanta ya fadi tsoro ya sake shigarta amman haka ta dake taki ko motsawaa.Ya dade a zaune ganin a tunaninsa bacci ya yi mata nisa, ya tashi ya fita bayan ya  aje leda shak'e da kayan motsawa a marmari d'ayar kuma
Gasassun kajine se tururi suke d'ayar ledar kuma fresh milk ne aciki,  jiki a  sanyaye ya sa kai ya fice yana  fita ta tashi tad'au ledodin duk ta watsar da su a tsakiyar
d'akin,ta saka kuka hawaye sai zuba suke hakan ta dade zaune karshe ta daure ta shiga toilet tai alwala tai sallah tareda kaiwa Allah kukanta ya saukaka radadinda take ji aranta, wani bacci ne ya kwasheta akan darduma.

STORY CONTINUES BELOW

****
Cikin barcin taji ana dukan kafarta firgigit ta tashi zaune tana mutstsike idonta, mata
ta gani birjik ad'akinta. wajen su bakwai sai da ta gama k'are musu kallo,san nan ta tsayar dashi kan Nadiya dake taunar
cingam k'as -k'as atsaye, ta cokalo d'an kwali gaba(ture ka ga tsiya) tana jijjiga cikin zuciyarta tace yanzu da wan nan zanfara kenan daga
Zuwa gidan! Kanta gama tunanin jitai an daka mata tsawa d'aya daga cikin shirga- shirgan Matan ce tai magana wato Hajia uwani  tace "yanzu ke yarinya
dan rashin kunya  ki rasa inda zaki shigo sai gidan nan ko? ba kya ganin kamar ya fi karfinki? Ta fada tana zaro ma zahra ido.
"To kii sani kin sako kanki a wahala ,kin ganmu nan, Manyan mata ne, mu  manya ma ba sa
had'a kishi damu balle ke 'yar cikin mu. . ." Sunkuyar da kai ta yi jikinta na bari ta kasa ko motsawa.

Nadiya ce ta matsa gabanta ta d'au apple a kayan marmari da alhaji ya kawoma zahran ta gutsura ta fara taunawa  tace "ke ban gaya miki karki shigo gidanmu ba? Da alama ba ki jin magana ko? to wallahi kin
dauko romon dahuwar kanki mu zuba mu dake Dan halak ka fasa.Tsigai nan
nasa sai ta miki duka.
wata figaggiya ban k'ararriyar yarinya ta futo ta tsaya agabanta tana yatsina k'afafuwanta siri
-siri, ta kalli zahra ta ce "fatan kin fahimta" cikin takaici Zahra ta d'an sunkwi dakai.

Hajia Zainab ta taso takama kunnenta "kalleni nan ko Uwarki bata isa in kishi
da itaba ,kuma yarinya duk abinda ake A gidan nan sai
kin fito kinyi.

Cikin takaici Zahra ta d'ago ta kallesu "haba bayin Allah menai muku ya da zuwana gida za ku zo kuna mun hargagi ad'aki ta kalli tsigai datai mata tsegege aka "ke kuma ki matsa da ka kaina don bada ke zanyi ba data bayanki zanyi." Ta fad'a k'irjinta se dukan uku -uku yake saboda tsaro amma hakan ta dake Hajia uwani ce tai k'wafa .Nadiya tazo zata fuzgota Hajia zainab
tace k'yaleta "damu take zen-cen" nan suka sa kai suka
fice, takaici da hawaye suka xubo mata da tausayin kanta hakan ta zauna
ad'aki tak'i fita balle tasan ya gidan yake Muk'ulli ta d'auka ta kulle d'akin .Jitai cikin ta na k'ugi hakan yasa ta dau ledar k'azar da ta watsar ita  ta bude ta fara, ci jitai  ana bugu, gabanta ya fad'i sai ta ki tashi ta bude dan tasan Alhaji Umar ne ko matansa "wallahi tsohon nan sai ya gane
kurensa, ba shi me budurwar zucia ba! tai k'wafa, ta harari kofar, haka ya gaji ya koma.
Washegari!! Da sassafe Alhaji Umar ya shiga  dakinta ya ji abude, tana ganin shi ta matsa baya ta sunkwi da kai,  murmushi kawai yayi ya kalleta  "zahra wai mai ya sa sa kike Gudu na ne? Menai miki? haba kin san  ni fa mijinki ne"

Kuka ne ta ji ya zo mata c "Amma Baba ai kasan kai matsayin mahaifina kake, na gayama da wanda na keso mesa za kaimun haka?" ya ce "Allah  d'aya. Shi ya  san k'aunar ki, kinsan ance matar mutum kabarinsa, me kikeso na sayo miki ne?

Juyar da kai ta yi tace "ba na san komai"
"A kullm ina baki hakuri na san na kuntatta miki amman ki sa a ranki hakan mukaddarine."

Abun na bata mamaki tsoho kamar sa yaxauna yana irin hakan gabanta ita ka kome ze mata baxata so shiba hakan tai tsaki ta danno k'ofa .

Alhaji Umar ya dafekai ,haka yayi hanyar waje ,su Hajia Uwani ne atsaye wajen kitchen suna ganinsa suka hau dariya don seda
Hajia Zainab taxo ta lab'e taji komi. Hakan ya shirya yafita suna ganin yafita sai sukai hanyar d'akinta da yake ita d'a kinta na kusa dana Alhaji ,danna k'ofar sukai da k'arfi.Hajia uwani
tace ke tashi ki fito ki mana aiki don ba xaki xo Gidan Mijin mu ba dole ki futo ki girki dama azuciye take nan
ta kallesu d'aya bayan d'aya kar kuga nai muku Rashin kunya don naga baku da alamar jan girmanku."
"iyeee!!!yayi miki kyau" inji Hajia Marym ta tab'e baki "idan jika ne kun-kusa yi dani Amma don yada girma kunzo kuna mun shirme aka" kallon kallo suka
fara yi da sauri hajia Uwani ta janyo ta ta wanka mata
mari nan suka rufar mata da duka.Tsigai ce ta shigo aguje  ta ce" Hajia ga Alhaji
nan ya dawo" ai da sauri suka saketa kowacce tayi waje. .

Zamewa tai tana Kuka kamar ranta zai futa duk idanunta
yayi jaa "wanne irin jarabawa ce ta riskeni ya rabbi ka kawo min dauki."

Shi kuma Alhaji Umar dede lokacin ya karaso falon ya gansu, kowacce a zaune sun turb'une fuska ,ya tsaya ya kallesu "me ya sameku
na ga kowacce fuska ba Annuri"

Hajiya Zainab ta tab'e baki "yo ai baka Maidamu komai agidan nan ba Alhaji, tunda kayi Aure ai kamata  yayi ka d'auko Amaryar taka ka kawo mana Mu ganta. A zuciyarsa kwa Mamakin su ya ke yi, ya san ba sa jetuwa gaba d'ayannsu,amman tunda ya ce zai aure duk sun hade kai, nan ya numfasa to "kuyi hakuri" samun daya daga kujerun yayi ya zauna ya kalli hajiya, dake gefensa, ya ce taje ta kirawo Amarya da sauri ta tashi tai hanyar d'akin ta shiga tana tab'e baki "Alhaji yace kizo" . Zahra kam ba ma tasan tanayi ba ta daga kanta "Alhaji yace kizo." ta kalleta idan ta ce to"  jim tai azaune
Da kamar ba zata jeba, sai ta tashi ta d'aurayo fuskarta
ta fita da k'yar takai kanta falon don tunda aka kawota
bata tab'a fita ba, zama tai ak'asan kafet su Hajia Uwani an hakimce akan kujera suka nuna kamar ba su santa ba Hajia "yanzu Alhaji wan nan ka Auro sa'ar 'yar cikin mu" yace "haramun ne? ya kallesu daya bayan daya ''to gata nan amana na baku banda hatsaniya kuja Girmanki, ke kuma ki ja
kan k'ank'antarki ki musu biyayya."

Hajia Uwani tai farat "Alhaji kuma dole araba girki da ita duk ran girkinta ita zatai  mana,
haka muma."

STORY CONTINUES BELOW

  "Sai na ji ta bakinta,duk ba kuna da yan aiki ba,  ya kalleta "kin Amince da hakan?
    
Tace "eh" dariya yayi yace baby zahra kodai na samo miki kema taki mai aikin dan aiki zai miki yawa".
"Aa abarshi ta fada kawai, washe baki yayi yace "to!! to shi ke nan zahra baby"

Sakin baki sukai suna kallon alhaji da mamakin kwarkwasar da yake yi gaban karamar yarinya, nan ya sallamesu ta tashi ta shiga daki ta fada  wad'a wanka tafito fes da ita ta kwanta hacci mai nauyi ya kwasheta.

Hayaniya ce ke tashi a falon, cikin magagin bacci ta tashi da sauri ta mike ta  shige bandaki ganin ma har laasar ta yi ta wanko fuskarta ta fito har lokacin hayaniyar ba ta tsagaita ba,k'aramin mayafi ta yafa ta sanya takalmi ta fita ta karasa karamin falo,
ta bi wata kofa ta shiga babban falon gidan.

Nadiya ce da wata budurwa da bata ta tab'a ganinta a gidan ba, sai yau, sai fad'a suke har da su  gore-gore. Zama tai a daya daga cikin kujerun tana mamakinsu a zuciyarta.

Hajiya zainb ce ta fito daga kitchen "iyee! ke Nadiya wato baki da Mutunci ko, Amiran kike zagi har dai mata gorin ba gidan
ubanta ba ne? to ke din gidan ubanki ne ehe ? Yanda tazo cirani kema hakan kika  zo, haba yarinya duk kinbi kin zak'e."

Zumbura baki nadeeya tai ta ce "oho dai."

Daga bakin kofa hajiya Uwani  ce ta fito itama jin hayaniya ta ji maganar hajiy zainab, batai kasa agwiwa ba ta ce  "amma dai kin san duk gidan nan  nadeeya tafi fada gun Alhaji ko? har yaushe Amiran tazo gidan?"

Hajia Zainb tace "oho dai! duk d'aya
suke."

Zahra dake zaune daga can ta gefe tayi tsaki,cikin zuciyarta ta ce "banzaye ashe ma duk ywn cirani ne, ai kam nadaina raga musu. Ta shi tai tabar wajen jitai sun cigaba da cece kucensu da gori,
d'akinta da yake da tv aciki ta zauna tana ganin wani film da ake a Bollywood wato Sahrul Asmar ,tana son film din sosai.

STORY CONTINUES BELOW

Wayarta ce tahau ruri. Taga sunan Alhaji ta rasa yama akai yasa mata nomber dinsa harda wani seving da (alhajina)  ta kashe kiran  ta aje wayar agefe zuciyarta na faman dukan uku uku.

Cikintane ta ji ya faraa kugin yunwa gashi ba ta san kitchen ba, sai kawai ta  tashi ta fita............

Taku take kaamr mara gaskya domin bata san ina kitchen yake ba, se dube dube take ,dak'yr ta gano
shi ta shiga, ba laifi komi a kawwame yake,ta rasa me zatai ma, can daga nesa ta gano kwalin indomie ba shiri ta d'auko daya, ta kunna gas tare da d'ora
tukunya k'arama Jikinta har rawa ya ke yi sabida yunwa.Ta harhada komai na dahuwar  ta koma gefe.

"Iyeeeeeee!!!! Taji an ambata daga bayanta, juyawa tai taga Nadiya ta kama k'ugu tana kallonta tana yatsina, maido da kallonta tai kan tukunyar ta dauko filet ta kwashe indomie din dan ta dahu,  "Malama
bani" cewar nadiya na kallonta cikon ido  da mamaki ta ce "me zan baki?

"Indomien da kika dafa"

Tsaki tai ta juya ta dauko cokali ta,dau fiket din zata fita, "nadiya kike kowa? To na karfi ne"

Warce kwanonta yi ta,juya zata tafi,zahra
  Mird'e hannunta tayi ta kwace tare da turata baya.

Kara ta saki.Hajia Maryam dake falo ta jiyota ta shiga da sauri "me na ke gani?" cikin kisisina Nadiya tahau kuka "wai don na d'au indomie shine ta kwad'a min murfin tukunya."

Zahra kam tsayawa tai saroro, Hajia ta kalleta "ke wai bakisan me
kike bane ? mema ya kawoki nan? maza maza ki fito"

Tabe baki tai ko kallonta ba taiba tajuya zata bude firji za ta dau ruwa. Da sauri ta ji an fizgota , kan tai kwakwkwaran motsi ta ji hajiya maryam ta sauke mata mari a kunci.

Cikin k'unar rai ta dafe kuncin hawaye ya shiga zubo mata,  tace"Hajia wai me na tsare muku ne ? naga dai gidan miji nane,  ba wanda ya isaa ya hanani abinda na ga dama ." Da sauri nadeeya ta cakumi zahra " ki san wanne kalami za ki gayawa mamana dan yanzu sainai raga-raga dake,gani tai idan bata rama ba za a k'wareta dambe suka hau yi harda su cizo .Hajia Uwani ce da Hajia zainab suka lek'o "wai
meke faruwane? Tsigai da Amira ne suka shiga kitchen din, tuni Tsigai ta shiga  fad'an, suka tarar mata nan Zahra ta haukace musu tai kukan karfi ta wullar da
Tsigai gefe ta rarumo, Nadiya abun tsautsayi ruwan zafin da hajiya zainab ta ajje awani bokiti, ya kwarowa Nadiya a gefen cinya k'wala ihu tai tana murzawajen, ganin duk hankalinsu ya koma kan nadeeya ya sa,tai sauri  ta fito daga kitchen din duk gashinta ya barbazu, hajiya  uwani ce ta damk'ota "dan ubanki ina zaki ai kin shigo hannun
mu" mari ta kai mata zahra ta sanya kuka "dama ina cike da ke a gidan nan, kalleki nan ficiciciya da ke, har,kin iya kishi ko?  ho! ho!! ho!!! yaro baisan wutaba sai ya taka ta.

Finciike,jikinta tai ta bar wajen tana hawaye.

Biyota sukai tare da buga k'ofar "ki bud'e ko mu karya kofar"  daga ciki tace "ku
karya din wallh ba zan bud'e ba" hajia Uwani ta kalli hajia zainab ta ce, kinji  yar iskar yarinya me kama da Aljanu"

Nadiya ta karaso
Se balbalin fada take ta nayi tana firfita cinyarta. Amira dake
gefe a tsaye in banda dariya ba abunda ta keyi ,taji dadi domin har  a lokacin  basu shirya ba. haka suka gaji suka koma falo,kowacce ta
dafe  kai "amma idan muka bari yarinyar nan taga lagonmu wallah  mun kad'e 'yar cikin mu ace ta gagare mu, shawara suka yanke
akan k'untata mata ta yanda sai ta bar gidan da kanta, haka suka tsaida shawara kowacce tai d'akinta.

STORY CONTINUES BELOW

Tsigai ta kalli Nadiya "Allah Anty Nadeey yarinyar nan k'arfi gareta  nadey ta ce "barta za ta  gane kuranta, ne an gaya mata ana shigowa gidan manyan mata haka kuma da rashin kunya, Tsigai duk tsiwar ki ashe ba karfi ne da ke ba, naga aiba girmarki za tai ba sede ta fiki jiki"

Tsigai tace "kaji Nadiyar nan keda kike ma gabjejiya kika kasa in mata balle ni sillen kara."
Amira da kejinsu takunshe baki tana dariya,

Zahra kuwa  dake bakin kofa tasa kuka duk rigarta ayage ga yunwa na Addabarta, da sauri ta bud'e firgi din  dakinta wayam taga ba komi se youghut haka ta  dauka ta kwankade shi  tana gama sha Amai ya biyo baya sabod yunwa ta cita ga jikinta yayi laga -laga sabod dakuwar da sukai kuka taci gaba dayi da k'yr ta tashi ta shiga toilet tai  wanka tafito abakin gado ta kwanta baccine ya saceta.

Alhaj  ne ya dawo ya turo kyauren d'akinta jinshi yayi abud'e ya shiga ya ganta kan gado,ya taka a hankali ya zauna gefen gadon ya kura mata ido yana ayyna abubuwa da dama akanta,shafa fuskarta yayi zuwa wuyanta ya ji zafi zau!.

Kamar a mafarki taji ana shafa wuyanta sai ta bude ido da sauri, daga kwancen ta ja  baya da baya ya kalleta "ki dena rufe d'akinki meke damuunki? ta kauda kai, zuciyartq cike da rauni kuka na neman kubce mata musamman tuno da abinda ya wakana da matansa da zu, har zata gayamai sai kuma tq bar abin aranta.Ammqn wata zuciyar ta katseta da sauri kan ta gaya mai dan ya taka musu burki.

  "Sai da na ce bana son Aurenka ban dace da kaiba, ga shi Matanka kullum se
sun dake ni akan abinci, ta fashe da kuka janyo ta yayi
zai Rungume ta ja da baya yace "haba zahra ni fa mijinki ne ?" nan ta durk'usa don Allah ka sauwake mun wallahih kullm na ganka kamar
Mahaifina nake gani"

Sunkuyar da ka yayi "kiyi hkr zahra Allah ne ya doran k'aunarki ,don Allah kibani had'in kai",nan taja da baya "bazan iyaba"
"nifa mijinki ne ko dan tsoho ne ni" ya fada yana mai kokarin cire babbar rigarsa, da gudu
tai cikin toilet tana kuka dafe kai yayi  Allah ne ya
jarrabeshi ya zeyi,yasan tabbas za ta sauko daman ya riga da ta shiryama lokwcinne yasan dole sai yayi hakuri  ajiye mata ledar da ya shigo mata da shi yayi, ya fita yana share zufa dole ya d'au mataki don matansa ke dada rikita ta. D'akinsa ya shiga ya zauna, yana ayyana rashin kirkin matansa, ga rashin haihuwa na damunsa  nan  ya daga hannu yana rokan Allah ya bashi magaji.

  Yau satin zahra d'aya agidan Aurenta amma har yau taki bari Alhji umar ya rabeta ma, kullum cikin  rufe kofa take ,yau tachi Alwashin komi ta fanjama-fanjam dan ta gaji da zaman daki haka nan,tai wanka  taci uwar kwalliya da wata atampa super holland kalar green sai ta fito amarya sak! ,ta fito babban falo ganin su hajia tai duk dai 'yn gidan  a zaune a falo sunata hira tace "sannun ku Amira ce kad'ai ta amsa Nadiya tai tsaki tabi kayan jikinta da kallo.

Hanyar kitchen tayi, da sauri Amira ta tashi ta bita tad'an tsaya abakin kitchen   "Anty sannunki" ta kalleta da Murmushi a saman fuskarta "yawwa sannu."

"Mai za ki yi ne? ta tambayeta. Tace "zan danyi girki ne wallah yunwa nakeji"  "bari na ta yaki" cewar Amira, ta tsaya gefenta da yake duk kayan kitchen din sabbi ne alhaji ya zuba lokacin da za a kawo zahra ya zama kowa zai iya amfani da komai tunda na sa ne babu gadara da wani zai, sun fara aikin suna hira kad'an-kadan sai ga nadiya ta shiga tace "lalle Amira  ga munafuka! nan kuma kika komo!
Magulmaciya."

Amira dake yanka albasa ta ce"meye ina ruwanki to."
Tsaki tai ta juya ta fice, babu dadewa sai ga ta nan ita da Hajia zainab ta ce "sannu yar halak! wato bakya tayani
kishi ko? kin san don ta haihu da Alhaji iyayenta suka lakano mai ita dan tq ci gado ko? to wallh ban Lamunta ba! kuma ki
fito ki wuce" sum -sum Amira ta fito ta gallawa Nadiya harara "banza Magulmaciya" hajia zainab ce tai ciki ta cafko Zahra don gidanku fito  Aljana kawai" fuzgewa zatai Hajia ta kuma damketa ta jata har  falo ta dan gwarar da ita agabansu, duk suna kan kujera Hajia Uwani tai Gyaran murya."D'ago ki kallemu, kin san ko babarki ba zatai kishi da muba balle ke 'yar cikin mu k, to ki shiga hankalinki na ga kin fara Gagara kinga mun d'aga muki k'afa ko? to yanzu zamu tabbatar miki kin shigo Gidan Kishiyoyi kuma
manya, to mun kafa miki doka idan safiya tayi k'arfe tara kin san Alhaji yafita to kema za ki fito ki hau aikin gida, kuma duk yawan mu nan ke zaki girka ki bamu, mundena komi, kinga girkin rana dare duk ke zaki dunga yi Alhaji dai nn gani nan bari.

Zahra da sauri ta d'ago kai "ki kallemu da kyau!"
"hajia ni ba son Mijinku nake ba dan Allah ku k'yaleni ku duba yarintata ni ba zan iya ba, duk kansu dariya suka sa "ke yarinya wallah kishiya ko  Jaririya ce to kishiyace don haka kibi abinda muka ce ki samu lafiya.

Hajia Maryam da ba ta fiya magana ba "cikin daga Murya ta ce "Zahra!
  Zahra! zahra!! Kingan ni nan!!! wallahi zan iya turgud'eki." Zahra ta kalleta ta ganta
irin jibga- jibgan nan ne,nan take Jikinta yahau rawa, "koda wasa kika gayawa Alhaji kashinki ya bushe."

Hawayene ya zubo mata sharr! tasa hannunta ta share tace "naji ku kuma zanbi abinda kuka ce" nan ta tashi  Nadiya tace "da ya fi miki"
wani ban zan kallo ta watsa Nadiya wanda yake nufin
zamu had'u ne . . . .

Wajen 12 zahra na kwance akan gadonta, tunani yayi mata yawa tako ina bata jin dadin zaman gidan,ita kam wa nan aure bata san irin saba,Hajiya ce ta shigo da kanta "ke seki taso
ki dora girki don kar rana tayi" cikin sanyaya ta tashi suka shiga kitchen kamar
'Yar aiki haka ta sata gaba shinkafa ne wajen kwano d'aya da rabi ta dafa sannn tazo tai Jallof na taliya se wajen 2:30 ta gama duk
ta gaji ko gama kwashewa batai ba a flaks sai ga su nan kowacce da kwanuka, haka duk suka diba da kayar aka bar mata kad'an ta tashi  ta tafi tana mamakin irin cinsu da makircinsu dan duk sun canja,agaban alhaji sai suyi ta janta suna kanwarsu amma a bayan idonsa kisan mummuke sallah tai da yake ana zafi
ta sake wanka sbd duk ta gaji kishingid'a tayi sai bacci Amirace ta shiga dakin "wai kizo inji hajia" ta d'an tashi suke jera
Amira na bata hakuru  akan irin zaman da suke da ita, suna zuwa Hajia tace "ke banason wan nan girkin naki ,d'an wake na keso" tace gaskiya na gaji
nima fa matar gida ce" hajia tace "Au bakiji ba kenan!"

A toh ni dai na ce na gaji,
  Sauran matanne suka fito, ganin hajiya maryam yasa ta jiya tai hanyar kitcehn dan tasan ynzu intaki saita doketa kamar yarta. Tsaki tai tana jin gwanda ta gayawa alhaji takurar da sukai mata,  ya maida ita gidansu dan ta gaji, wajen awa daya ta yi ta gamata fito,ta kawo mata,
cikin murmishi ta kalleta "yawwa yan mata" hawaye ne taji ya zubo mata, kamar wadda kwai ya fashewa aciki.

Sai alokacin taci nata abincin  wajen 4:30 ta fito don dora sanwar dare, nan ta gansu birjik kamar kayan wanki akan kujeru, ta d'auke kai hakan ta shiga ta fara hada girkin dare haka tayii ta tuk'a tuwo tana yi tana tsaki fulas ne kaloli se zubawa aciki take, haka ta tayi ta gama, dan mugunta suna da 'yan aiki duk suka kore su,jin lokacin da alhaji ya ce zai dauko mata mai aikin shashenta tace Aa, hakan yasa suka kulla mugunta suka koru na su dandai su loda mata aiki, kuma wani ikon Allah har i wannan lokaci alhaji bai san me ake ciki ba, sai masu yi musu aike -aike kawai kawai suka bari,dib'ar nata tai ta tafi d'akinta jikinta har ciwo yake saboda tuk'in da ta yi, kamar kullum karfe 8 ta rufe dakinta......

Post a Comment for "KISHIYOYINA CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...