Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KINA RAINA CHAPTER 1

KINA RAINA CHAPTER 1

- - Post a Comment

 KINA RAINA CHAPTER 1
💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Page 1.Matashiyar budurwa ce wacce ba zata wuce shekaru 17 zuwa 18 ba a duniya ta fito daga wani corridor da zai sadaka da  palourn gidan.


Sanye take da arabian gown sky blue tare da dan karamin hijabi dai dai shoulder d'inta pink colour,kafadanta na rataye da handbag wanda yake dauke da dan books dinta tare da sauran tarkacenta.1


Dining site ta nufa direct,inda mahaifinta da matarsa ke zauna yana breakfast.

Da dan fargaba ta karasa inda suke, muryanta na d'an rawa tace "daddy barka da safiya, an tashi lafiya?"  Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa da "lafiya" take jikinta yayi sanyi har kullum tana fatan ace zata ga sauyin hali daga mahaifinta amma inaa abin dai ba a cewa komi.1


Mai da dubanta tayi kan momy dake ta doka murmushi tace "barka da safiya mom." Cike da fara'a tace "barka da tashi princess." Hmm shine abinda tace a zuciyarta.1


Karamin cup taja ta hada tea sannan ta zauna tana kurb'a kad'an kad'an yayin da mahaifan nata ke d'an zantawa kad'an kad'an.

Sipping last drop na tea dinta tayi ta mik'e tare da fad'in "zan wuce sai na dawo."


D'ago da kanshi babanta yayi fuskarsa a tamke yace "keh! Ina zaki?" Cike da mamaki ta kalleshi sannan tace "daddy school ba." Mai da dubansa kan momy yayi yace "ke baki fad'a mata bane?" D'an sunkuyar da kai momyn tayi cike da kissa tace "haba daddy ai ni ban dauka da gaske kake yi ba."1


Tsaki ya ja cikin daga murya yace "wani irin baki dauka da gaske nake yi ba kinga na taba wasa irin haka ne?"

Hannunshi dake kan table din ta dafa tace "daddy Allah ya huci zuciyarka ni dai ba za a ji mutuwar sarki a bakina ba balle inyi bakin jini..."

Kafin wani a cikinsu yayi magana tayi saurin cewa "wai me yake faruwa ne? Meye ne za a gaya min da ya shafi zuwana makaranta na?" Bata iddasa rufe baki ba daddy yace "na soke zuwanki makarantan ne!"

Take hawaye suka fara suntiri kan fuskarta bata iya cewa komi ba sai zubawa momy ido da tayi.1


"Ki daina kallona haka tunda bani na hanaki zuwa makarantan ba." Cewar momy girgiza kai tayi ta mayar da dubanta kan mahaifinta duk wani tsoro ya kau daga zuciyarta "daddy why? Me nayi da za a soke min karatu,me yasa baka sona yanzu daddy?"

Kau da kai yayi gefe yace "tunda kince ke ba kya ji ai kin ta jawowa kanki kenan,tunda kin san baki gane karatu gwara na daina asarar kudina ina biya miki kudin makaranta,ko da yake ba ganewa ne baki yi ba ko soyayya ce kika soma."


Zaro ido tayi tace "daddy ni kuma? Soyayya? Haba daddy wallahi kaje ka bincika ka ji babu wanda nake kulawa da sunan soyayya cikin makarantan nan."


"Baki soyayya cikin makaranta amma ai kina yi cikin anguwa in ba haka ba uban me kike zuwa yi kullum wajen wancan shashashan yaron can me shago kullum?"  Daddyn ya jefo mata tambaya


Kafin ta bashi amsa momy tayi carab ta ce "kash daddy karatu yake koya mata fa." Ta fadi hakan da murmushin da maimunatu ce kadai ta san ma'anarsa1

Karatun kaniya yaron da ko secondary bana jin ya kammala in yana da ilimin karatun da take yi me yake ci da shagon provision me ya sa karatun bai tsinana masa komi ba?"


Ita dai memunatu bata iya cewa komi ba banda hawayen da take yi tana shirin bud'e baki tayi magana daddy ya katseta ta hanyar cewa "maza ki b'ace ki bani waje ki kuma fara shiri dan ba zan ajiyeki a gabana ki sa min ciwo ba nayiwa Sa'idu magana zai sama miki makaranta a nan cyprus kuma ba zaki je kiyi wani engineering course ba business zaki je ki karanta i cant waste my money on you."2


Tana shirin protesting kaman ance ta kalli momy sai taga tashin hankali a fuskarta da alama bata san da maganan zuwa cyprus din ba murmushi ta sakar mata da ta lura daddy bai kallonta.1


STORY CONTINUES BELOW

Mai da dubanta kan daddy tayi tace "daddy dan Allah daddy na tuba ba zan sake zuwa wajenshi ya koya min karatu ba wallahi Khalid yana da sani ba soyayya muke yi ba daddy plssss." Wani tsawa ya daka mata da ya sakata tashi ta bar wajen tana kuka...1


Kwance take idonta a lumshe zuciyarta fal yake da jimantawa kan,she cant believe tayi asarar karatunta duk gwargwarmayar nan da tasha na shekara d'aya tana shiga shekararta ta biyu a datse mata karatun a dawo da ita baya?1


Ba zata tab'a yafewa momy ba da take yi mata katsalandanna cikin rayuwarta,take cutar da ita a sid'ade.

Wayar ta ce ta d'au ringing a hankali ta bud'e k'wayar idonta tare da karkata kanta zuwa ga inda wayar take ko kafin ta mik'a hannunta ta d'auko kiran ya katse da alama flashing ne.1


Murmushi ta sauke tun kafin ta duba ta san waye dan ta san mutum d'aya ke yi mata flashing.

'Ya Khalid' gyara kwanciya tayi tare da danna kiransa.


Murya can k'asa tace "yayana!" Cike da damuwa yace "kanwata ina kika shiga kwana biyu ne duk kin b'ata bana ganinki ko makaranta bana ganin kina zuwa?"


Idonta ne ya ciko da k'walla cikin rawar murya tace "daddy ne ya hanani fita wai ya soke makarantan."

"Subhanallahi maimunatu me kika aikata haka da ya fusata daddynki har ya yanke wannan d'anyan hukuncin?"

Kuka ta fashe dashi kafin tace "yah khalid kaima ka na ganin akwai laifin da ni maimunatu zan iya aikatawa da har daddy zai hanani school? Haba yayana kaman baka san halina ba...." Ta karasa maganar cikin sheshekar kuka1

Cikin d'imaucewa yace "no no tsaya kiji yi shiru ba nufina ba kenan,sorry ko dear sister,now tell me,me ya faru? Me yasa daddy hanaki zuwa school?"1


Jan hanci tayi sannan ta fad'a mishi dukka dalilan da yasa daddynta soke karatunta a Nigeria yake shirin mayar da ita wata kasar.

Numfashi ya ja ya fitar sam bai ji dadi ba da ya zama silar rugujewar burinta cikin jimami yace "maimunatu me yasa baki gaya mishi ba soyayya muke ba?" Cikin karyar da murya tace "nayi kokarin fahimtar dashi hakan yaki ganewa bai yarda cewan taimaka min kawai kake ta fanni karatu amma sam yaki ya gane shi gani yake in kana da wannan ilimin me zai sa kayi zaman shago?"1


Murmushi Khalid yayi me sauti sannan yace "daddy ya manta ba kowa ke samun cin gajiyar karatunsa ba,tunda shekara nawa da gama karatun ba aiki ba sai mutum ya kama sana'a ba?"1


Cike da karaya tace "toh" tare da juya hannunta irin ban san ya zanyi din ba tace "yaki tsayawa ya fahimce ni balle ya gane hakan."

Cikin sanyin muryan shi da yake karyar mata da gab'ob'i yace "ko inyi mishi magana ne maimunatu wala Allah ya fahimceni." Da sauri ta girgiza kai kaman tana gabanshi tace "ah ah,yin hakan zai iya tado da wata matsalar ka rabu dashi kawai mu cigaba da yi masa addua Allah ya ganar da shi da wuri.2


Sauke ajiyan zuciya yayi yace "toh shikenan tunda kin ce haka beside kina buqatan change of enviroment"

Langwabe fuska tayi kaman tana gabansa tare da tabe baki tace "ahh ahh..." Dariya yayi yace "oh zaki fara shagwab'ar taki ta fama ko.

Zolayan ta ya cigaba da yi ita kuma tana zuba mishi shagwaba,she enjoy this cours Allah knows she is falling for him saboda kyautatawarsa a gareta amma ita ta lura babu wannan a ranshi.2


Juyi tayi a kan gadonta lokacin da ta ajiye wayar a gefenta,me yasa ba zai noticing dinta ba? Ko dan yaga standered na rayuwarsu ba d'aya bane? Ai arziki na Allah ne beside yayi karatunsa yana samun aiki komi will be alright.1


Lumshe idanuwa tayi tana tuno kyakyawar fuskarsa dan siriri dashi farin bafulatani murmushi ta saki,lokaci guda kuma idonta dake lumshe ya fara tsiyayar da hawaye tunowa da tayi da tafiyarta kila bayan tafiyarta ya manta da ita ya fara soyayya da wata.2


Haka dai ta kwanta tana tunane tunanen wanda bai san tana yi ba har bacci yayi awon gaba da ita.


Few days later Maimunatu na zaune momy ta shigo cikin gayu tana tauna chewing gum,she is so young ba zata fi irin 32 zuwa 33 din  nan ba daddynta ya aurota 10 years back bayan rasuwar asalin momynta da shekara biyu,she was five when she lost her momy. Daddynta ya shiga tashin hankali sosai na rashin mom dinta sannan duk yawan family dinshi da na mom dinta ya hana kowa daukanta shi yake kula da ita ko yan aiki baya bari suyi hidimarta.

Shi zai yi mata wanka ya shiryata ya kaita sch sannan ya wuce office closing hours dinta na yi zai je ya daukota su koma office dinshi tare inda zasu ci abinci ya barta tayi ta wasanta shi kuma yana aiki kafin lokacin islamiya dama unifoam dinta na jakanshi haka zai kuma shiryata ya kaita.1


STORY CONTINUES BELOW

Closing hours dinta na islamiya dai dai yake da closing hours dinshi na office in yabi ya dauketa sai su wuce gida inda zasu yi wanka su shiga kitchen tare haka zai ta biye mata suna shiririta yana girki ita kuma tana barna.


They lived like that har na tsawon shekaru biyu shakuwa me tsanani ne ke tsakaninsu he was her best friend. Ana cikin wannan yanayin abokanshi suka yi ta bashi shawara ya kara aure been a single dad was not easy ya hana kansa jin dadin rayuwa ta fanni da yawa shi ma'abocin kallon ball ne da yin kwallo amma saboda hidimar diyarsa ya watsar da komi hatta abokansa in suna son ganinshi sai dai suje office ko gidansa saboda ya dedicating lokacinsa wa diyarsa few of abokansa ne ke inviting dinshi cin abinci gidansu saboda diyar ta mingling da yaransa uncle sufyan was one of them yana sonta sosai every weekend zai ta rokon daddynta ya kaita gidanshi ta kwana da kyar wani lokacin ya yarda wani lokacin yaki.


Uncle sufyan na cikin mutanen da suka dinga rarrashinsa da yayi aure shi ya had'asa da kanwar matarsa Rahina wacce take gab da gama NCE dinta (abdul) daddy ya amince da auran Rahina saboda ya san matar sufyan bata da matsala tana da kirki sosai ko da yanda in maimunatubta shiga cikin yaranta take sajewa dasu ba a nuna mata wani bambanci.1


Sunyi dating for few months inda ya dad'a sakankancewa da kyawun halinta musamman ta yanda take jan diyarsa a jiki wani sa'in har kwana take a wajenta tun a lokacin ya hori maimuntu da ta dinga kiranta da momy tun basu yi aure ba.


Ana cikin wannan tafiyar suka yi aure sosai Rahina ke kula da maimunatu kullum cikin dawainiyarta yake hakan na yiwa Abdul dadi sosai hakan na kuma kara mata kima a idonsa.


Yau da gobe sai Allah tsananin soyayyar da abdul ke yiwa diyarsa ya fara tab'a zuciyar Rahina taji tana son ta haihu ko dan itama ya nunawa nata jini kauna irin haka gashi sun kwashi shekaru biyu da aure babu ko labarin ciki duk sai tabi ta damu kanta ko da ta nufeshi da maganar assuring dinta yayi da shi bashi da damuwa haihuwa ta Allah ne so ta kwantar da hankalinta kawai.1


Bata kara shiga tashin hankali ba sai da suka haura shekaru biyar da aure babu ko bari kuma ta lura ko a jikin abdul ko dan yaga shi yana da diya ne da tunkare sa da maganan sosai ranshi ya b'aci yana tambayanta dama bata dauki maimunatu a matsayin diyarta ba wato diyar miji ta dauketa hakuri ta bashi sosai ta nuna mishi ba nufinta ba kenan ai itama maimunatun zata ji dadi in ta ganta da siblings sosai ya gamsu da maganarta suka je hospital inda suka yi tests duk da dai shi dama ya san lafiyarsa kalau tunda ga kwan shi a duniya.1


Ilai ko Rahina aka samu da matsala ranan kam ta wuni ta  kwana kuka tun yana lallashinta har ya hakura ya kyaleta da kanta ta lallashi kanta bayan wasu kwanaki.

A1


Ai kuwa shareta da yayi ya masifar bata mata rai wato dan yaga yana da wannan shegiyar yarinyan ko haka nan ta dau tsana ta dora mata zagon kasa take yi mata sosai ninka kulawarta da tarairayar da take yi mata tayi a gaban idon mahaifinta da sauran jama'a in suna su biyu kuma tayi ta yaba mata magana tana sata aiki.1


Maimunatu bata fi 13 years ba ta fara girka abinda zata ci duk lokacin da daddynta bai gari,tana shan wahala sosai da yunwa in daddyn bai gari hakan yasa ta fara shiga cikin masu aiki tana koya in yana nan ko da ya tambayi dalilin da yasa yake ganinta a kitchen sai momyn tayi carab tace cikin kisisina ai gwara ta koya tun yanzu macece fa zamu aurar da ita a zo ana mana complain din bata iya girki bane?"1


Gyada kai yayi kawai yana danna waya a zuciyarsa fadi yake gwara kam ta koya tunda ni gashi na buge da cin na masu aiki tunda ke din ba iyawa kika yi ba lumshe ido yayi tuno da tsohuwar matarsa still a cikin zuciyarsa yayi mata addua,ya missing dinta in every aspect abinci, on bed, kai a rayuwarsa gaba daya.

Haka rayuwarsu ta cigaba cikin kissa da kisisina momy ke azabtar da maimunatu in har ta lura maimunatu na son abu cikin hikima da nuna ilar abin ta cusawa daddy kin abun a hana maimunatu,ta bi ta toshe mata duk wani jin dadin rayuwa ba tare da sanin kowa ba duk sai mutum ya dauka salon nata bayar da tarbiyan kenan tunda ita bata dashi balle aga ta nuna banbanci tsakanin maimunatu da nata yaran.

Sannan kusan ko da yaushe cikin karban kudi take da sunan yiwa maimunatun shopping sai dai ta siya mata one or two things ta soke sauran kudin tun maimunatu bata fahimci mugunta take yi mata ba har itama ta gane kuma ta san ko wa zata fadawa ba yarda zai yi ba saboda yanda take nuna mata soyayya a idon mutane.1


Bata kawa ko daya ko da kuwa a cikin familyn su ne tsakaninta da cousins dinta sai dai gaisuwa da murmushi she is a very reserved girl dan bata da hayaniya sannan kunyanta shi ya kara mata rashin son shiga cikin mutane.1


Back to story

A cikin kwanaki kad'an aka gama shirye shiryen tafiyanta cyprus abu daya da ta lura dashi shine wannan maganar tafiyan ba na kwanan nan bane dama can daddy na da plans dinshi na tsigeta a karatunta na Nigeria kenan.

Ba ita kadai take jimamin tafiyatan ba hankalin momy a mugun tashe yake dan har ta hango daddy ya damkawa maimunatu company dinsa in ta dawo daga karatu dan tabbas ta san hikimarsa ta turata karanto kasuwanci kenan har kullum tana bakin cikin rashin haihuwarta dan ta san kila da ta haifi namiji yanzu amma saboda bata haihu ba ko mutuwa yayi yau sai dai a bata tumminin takaba (ku jifa? Sai kace wani ya san gawar fari) da wannan tunanin ta kuduri niyyar tarwatsa karatun maimunatu.2


Duk yanda maimunatu bata son tafiyarta wani kasan Allah cikin ikonsa sai taji wani relief da ta bar gidansu bakin cikinta d'aya ta baro khalid ba tare da samun yanda take so ba.1


Karatu ta fara ka'in da na'in bata kula kowa harkan gabanta kawai take hatta roommate dinta basa wani hurda abinda ya kawota shi take yi ga wani tsoro da kunya da take dashi hakan ya sa takadarun turawan ajinsu suyi ta takalanta musamman da suka lura bata son a rabi jikinta.3


The fun is about to start......😁4


Zaune take a kan grass carpet dake cikin makarantansu littafai ne baje a gabanta tana programmes biyu take yi daddy ya saman mata Bsc akan business yayinda ita kuma ta applying wani program kan economics,so she is pretty occupied bata ma samun time din kanta kullum cikin karatu take.


Leggings ne a jikinta sai wata katuwar sweater na saka wanda yazo mata har kusa da guiwa kafanta sanye yake da snikers masu kyau tayi rolling gyale a kanta baka ganin komi sai dan karamin fuskanta kaman na mage sai zara zaran yatsunta dake ta faman rubutu zata kalli abu a system dinta sannan ta duka ta yi rubutu a littafinta sannan occasionally ta bude texts books din gabanta.1


Yafi 20 minutes a tsaye yana kallonta babu abinda yake kallo illa cute bakinta dake motsi shi kadai alamun she is reading out sannan wani sa'in ta d'an turoshi ko ta ciji gefen lips dinta haka dai take ta faman twisting bakinta ita kadai bata ma san tana yi ba saboda she is so engross in what she is doing.

She is so cute and he want to have a taste of that lips amma ya sani daga ganinta karamar yarinya ce sosai and she look innocent daga yanayin fatarta ya san she is black ko da take da haske black din ma muslim saboda yanayin yanda ta suturta jikinta da kuma bakin da ya hango a saman goshinta so musulman ma religious one (tabon sallah bashi ne ke nuna mutum is religious ba though) ajiyan zuciya yayi ya kara hard'e kafafunsa tare da zura hannunsa cikin aljuhun jeans dinsa yana dad'a kare mata kallo,kallon da musulunci ya hana wato kallon kurullah.

Saukar da idanunsa yayi daga bakinta zuwa kirjinta da ya taso kaman ba na teenager ba its so full and round ba siririya bace amma akwai kaya a wajen lashe lips dinsa yayi yana shafa very short beard d'insa wayarsa ce tayi beeping a hankali cikin nutsuwa ya zarota message ne daga mr Hilton supervisor dinsa da ya zo gani sanar dashi yake shi zai shiga meeting tunda ya jirasa bai zo ba.2


Tab'e baki yayi tare da d'aga kafada ya cigaba da kallonta.

Ji tayi a jikinta ana kallonta  a hankali ta d'aga kai ta tana waige waige can gabanta kad'an ta hango mutum jikin oak tree ya zuba mata ido ba ko kyaftawa.


Da sauri ta sauke ido yayin da zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri  sakamakon abu biyu na farko kaifin idanunsa na biyu kwarjininsa.

Tsinatar kanta da kasa cigaba da abinda take yi tayi lokaci guda brain dinta ya toshe ta kasa fahimtan komi.

Inuwarsa ta gani a kanta ta kwalalo ido wajeKomi nata ya tsaya hatta rubutun da take yi ta kafe system dinta da ido amma babu abinda take fahimta ya gane hakan ne saboda yanda ya ga bakinta ya daina motsi kuma ta tsirawa screen ido.

Murmushin gefen baki yayi knowing he have that effect on her dan dukawa yayi ya tsuguna akan kafarsa index finger dinsa ya saka ya d'ago fuskarta "hello beautiful" ya fada cikin soft voice,blinking idanunta tayi kaman wacce haske yayi mata yawa duk dan ta avoiding eye contact dashi motsi bakinta yake yi alamun tana so tayi mishi tsaki amma ta gagara saboda kwarjinin da yayi mata.1


Karkatar da kanshi gefe yayi yana kallan yanda take pouting bakinta tana mayarwa.

Tattaro dukka kuzarinta tayi ta ture hannunsa dake rike da habbanta cikin sassarfa ta fara tattara kayanta tana cusawa cikin jakarta tsaya yamike tare da mayar da hannunsa cikin aljuhu yana kallon yanda jikinta ke bari dan dukawa yayi ya dauki textbook dinta daya business strategy.1


Ba tare da furta komi ba ta mike  bar wajen bai yi yunkurin dakatar da ita ba duk da littafinta dake rike a hannunshi kara kallon cover din littafin yayi tare da flipping page din farko Maimunatou Abdullah ya furta a fili such a nice name but too long bayanta yabi da kallo daidai lokacin da ta kule "such a cute kitten"  dan dariya yayi nemanta ba zai yi wuya ba ya san me take karantawa ya kuma san sunanta he will hunt her and he will find her.1


STORY CONTINUES BELOW

Tana shiga dorm dinta ta fara cire kayan jikinta sai da ya rage daga ita sai pant da bra tabi kan gadonta ta mike stretching tayi kaman wata mage akan gadon tare da lumshe ido handaome face dinshi ta ci karo dashi da madaidaitan idanunsa masu kaifi da sauri ta bude idonta  he means trouble ba abinda ya kawota cyprus kenan ba she is not gonna be one of those children da za a turo su karatu su bige da shiririta.

A hankalinta mike ta janyo jakanta dan dauko wayarta ba kowa bane ya fado mata a rai ba sai yah Khalid dinta tunda tazo garin nan fiye da watanni uku bata kara jin duriyarsa ba ta rasa waye ya samu daman goge mata contact dinta dukka kafin ta taho.

Tsaki taja tare da mikewa zauna sai yanzu tayi da na sanin rashin hulda da kowa a anguwarsu da yau ta sa an bincika mata halin da yake ciki gashi daddy yace ba zata dawo ba har sai ta gama karatunta.

Tashi tayi ta je ta dauko bathrobe ta saka a jikinta tare da bin inda kitchen dinta yake coffe ta dafa sannan ta dawo ta zauna coach tana sipping ta missing daddy he was her only best frnd yanzu ta rasa wannan shakuwar da soyayyar tasa duk a ta dalilin momy dole ne tayi abinda daddy yake so dole ne tayi abinda zai yi alfahari da ita.1


Searching dinta yayi a dukkan social media da ya san zai iya samun matshiya kamarta yayi amma bai sameta a ko daya ba sai facebook babu komi kuma a acct din sai hotunan flowers and mostly dahlia and she dont have much frnds could she be a loner d'aga kafadu yayi irin ba damuwarsa bane he will change that in a bit.


An yi sati daya da haduwarsu  a cikin sati dayan nan ya samo duk abinda yake son sani game ga ita yayin da ita ta manta ma ta hadu dashi kwanakin farko na cikin satin da suka hadu dai ya tsaya a ranta daga baya kuma ta watsar dashi ta fuskanci karatunta.


Wata rana ta fito tana zaune a cateen tana shan orange juice lokaci guda kuma tana searching abu a internet game ga karatunta taji ance "ke ba kya gajiya da karatu ne har a wajen cin abinci ma karatu kike?" Kafin ta daga kai ta san ko waye da kuma irin amsan da zata bayar ya zauna kujeran dake kallon nata.


Is the same guy from the other week wanda ya dauke mata littafi ashe bahaushe ne he doesnt look like one,yafi mata kama da irin Ethiopian din nan kallonshi tayi ta gefen ido ta watsar murmushin gefen baki yayi ya mika mata hannu "i am Marwan Mahmud" kallon hannunsa tayi ta kau da kai gefe a hankali ya dauke hannun tare da sosa gefen wuyansa ya lura miskilan gaske ce amma bayan miskilanci ya lura akwai mugun tsoro a tattare da ita bai ma san ta inda zai fara b'ullo mata ba he really like her at first da ya ganta kawai burgeshi tayi but yanzu da ya bincika yaga yanda take rayuwanta he feels interested he want to be part of her life ya canza rayuwarta daga mara armashi zuwa me armashi she is all alone bata da kawa bata da aboki ita kadai take rayuwarta,rayuwa haka ko ba zai taba yuwuwa akwai cutarwa zai cire mata duk wani tsoro zai koya mata fuskanta rayuwa bai san me yasa take killace rayuwarta ba and he doesnt care all he knows shine zai kawo canji a rayuwarta she is too young ace kamar ita tana da wata matsalar rayuwa.

Kallon yanayin dressing dinta yayi yau doguwar riga ta saka baka mai fadi sosai ta nade fuakarta da blue din gyale kamar dai wata balarabiya dabara ce ta fado mishi dai dai lokacin da take shirin mikewa yayi mata sallama dan jim tayi kafin ta amsa sallamar tasa da muryarta dake dashe naturally murmushi yayi me fadi irin nayi nasaran nan ba haka ya zaci muryarta ba yayi zaton zai ji er siririyar muryar yanayin suffarta sai yaji sabanin haka muryarta ta dan disashe muryar tayiwa jikinta girma.1


Bag pack din shi ya ciro ya zuge zip dinta a hankali cikin nutsuwa ya saka hannunsa ciki ya zaro textbook dinta dan boyayyan ajiyar zuciya ta saki dan sosai take buqatar wannan littafin ajiyeshi kan table din da ya rabasu yayi yace "here u left this the other day miss maimunatouuuu." Ya dan jaa sunan saboda shi kam yanzu ya kasa tantance ita din er ina ce duba ga ya mata hausa bata amsa amma abin mamaki sai yaji ta amsa da "nagode" bayan ta sungumi littafinta bata yi mamakin da ya san sunanta ba tunda littafinta ya shafe tsawon sati a hannunsa kuma sunanta na zane a jiki.


Ajiyar zuciya ya sauke yace "wow! Ashe ke din dai bahaushiya ce i thought ai na kuskure da nayi miki kallon bahausa." Murmushi ta dan saki amma bata ce komi ba dariya ya bata in bai mata kallon hausawa ba toh dame tayi kama.


Haka dai yayi ta yi mata surutu amma ita bata cewa komi sai dai tayi murmushi ko ta gyada kai sai da yace yana so ya zama frnd dinta ne ta dan yi jim tare da yin shiru ganin expression din fuskarta yasa yayi saurin gyara zancen ta hanyan cewa ba dan komi ba sai dan ya dinga taimakonta akan harkar karatu tunda course dinsu daya though shi phd yake yi akan business da mamaki sosai take kallonshi.

Dan daga kafadu yayi yace "toh ya bawa zai yi in an sashi dole yayi karatun dai bai so." Dariya ta dan yi da ya bayyanar da jerin fararen hakoranta da siririn wushiryarta cikin dariyar ta saka zara zaran yatsunta ta rufe bakinta dan mirmushi yayi ya kureta da ido she look so cute laughing.


Lura da yanda yake kallonta ya sa ta tsai da dariyarta tare da sauke kwayar idonta gyara zaman veil dinta tayi tare da gyaran murya na rashin sanin abin yi dan kallon ya takurata.


A can tsakiyar kanta ta tsinci muryarsa yace "me ya baki dariya haka?" Dan murmushin da bata yi niyyan yi bane ya kubce mata ta dan pointing dinshi tace "kaine mana." Gira daya ya daga yace "ni kuma? Me nayi i just stated the truth." Murmushi mw fadi tayi tace "how on earth mutum babba kaman kai za a mishi dole ina ce sai mu ai en yara." Dan hada gira yayi yace "now wait! Nine babba? I am just 27 years kuma ba gashi ba an min dole field dina dabban an sani nazo yin karatun da bashi ne ba." Cikin dan tausayawa tace "ayya menene field din naka." Dan ta san zafin karanta abinda ba shi kake ra'ayi ba (iyaye a bar yara suyi zabin su pls sa kai yafi bauta in mutum ya choosing ra'ayinsa bai bashi wahala amma in ba abinda yaro yake so bane sai anyi da gasken gaske.) Daga kafadu yayi alaman hakan nature dinshi ne yace "i am a doctor circumstances ne ya saka ni zuwa karatu on business a dai dai lokacin da ya kamata ace na fara aiki." Zaro ido tayi cike da mamaki tace "oh wow! Kai doctor ne? This is amazing kai kam ai kaji dadi at least ka zama abinda kake son zama nifa i always wanted to be an engineer amma this is where i landed, is a shame gaskiya i envy you,you become what you want to become and at the same time u please ur dady i wish nima na samu wannan daman...." Shiru tayi ganin yanda ya kure bakinta da kallo tana dogon sharhi mamaki a shimfide a fuskarsa dama tana magana me tsawo haka itama mamakin kanta ne ya kamata yanda ta zauna ta saki baki ta na zuba surutu a gaban total stranger kaman wacce aka tambayeta wani kunya ne ya rufeta da sauri ta mike wannan karon ba tare da ta manta ba ta sunkuci komi na at once zata bar wajen shima mikewa yayi tsaye tare da rike elbow dinta........2Kallon shi tayi sannan ta kalli hannunshi dake rike da ita, da sauri ya saketa. Fara tafiya tayi hakan yasa ya fara binta sai da suka fita daga cateen basu cewa juna komi sai da yaga sauri kawai take yi kuma taki kulashi yasa yayi saurin shan gabanta cak ta tsaya, kyafkyafta ido ta fara wanda ya sashi fahimtan tana hakan ne whenever she us nervous .

Yace "pls maimunatou listen wallahi ba zan cutar dake ba da alheri nake nufinki dan Allah ki ban dama  you will never regret it"  sunkuyar da kai tayi bata ce komi. Jin tayi shiru kuma bata yi yunkurin wucewa ba yasa yace mata "kinji?" Sai da ya kuma maimaita mata sannan ta gyad'a kai a hankali. Murmushi ya saki cike da farin ciki yace "thank you so much, frnds are we? " murmushi tayi tare da kara gyada mishi kai shi kam dama tunda ta amsa shi yake sakin murmushi.

Dan fara tafiya suka yi,shiru basa cewa komi shi kam mamakin kanshi yake yi yanda ya rasa abinda zai ce mata karamar yarinya na neman dagula mishi lissafi.

"Shekarunki nawa?" Shine tambayar da ya jeho mata. Dan juya ido tayi tace " i will turn 18 in two months kaga ka bani 9 years" ta fadi hakan tana kokarin nunawa da fingars dinta,amma saboda abubuwanta da ta rungumo yasa ta kasa yi dariya suka yi dukka ganin struggling din da take yi.

Waje suka samu suka zauna har lokacin suna dariya ajiye kayan tayi a gefe fuskanta dauke da murmushi ta d'aga yatsunta tara tace "shekaru haka ka fini dashi."

Karkatar da kai yayi yace "no its a decade" dan harararsa tayi tace "in 2 months fa zan cika 18 and you said u re 27." Gira d'aya ya daga yace "toh ai baki cika ba zaki cika kika ce."

Shagwabe fuska tayi tace "ah ah ni dai ban yarda ba wannan wayo ne."

Murmushi yayi tare da zuba mata ido he just like the girl she have a free spirit locked inside.3


Dan sadar da kai tayi tana wasa da yatsunta few minutes da haduwanta da wannan mutumin amma har ta sake mishi ba tare da ta shirya hakan ba,yanayin yanda yake nuna kulawa da damuwa a kanta yasa take jinsa kama yah khaleed d'inta."3


Dan kallon agogon hannunta tayi tace "uhmm i need to go ina da class in few minutes nagode sosai." Ta mike tana gyara rolling dinta tare da sab'a bag park dinta bayan ta adana abubuwanta.

Shima mikewa yayi tare da cusa hannunsa cikin aljuhu yace "Ok ba laifi nima lemme get going but before that...." Ba tare da ya karasa ba ya dan duko kanta saboda ya fita tsayi, dan kame jikinta tayi tare da runtse idanu. Murmushi ya saki yasa hannunsa ya zare wayarta dake cikin hannunta a hankali ta bud'e idonta daya sannan ta kuma bude dayan jin ba tab'ata yayi ba.

Mika mata wayan yayi bayan ya zuba numbers dinshi cikin wayan tara da tura nata zuwa nashi.1


Ansa tayi yace "will give you a call sai mu san yanda zamu arranging abubuwa a tsakaninmu."

Gyad'a mishi kai tayi ta fara tafiya shi kam kara gyara tsayuwa yayi yabi bayanta da ido kafafunta har hardewa suke saboda yanda take ji a jikinta yana kallonta.1

Haka ta gama wunin ranan tana tuno haduwarta da marwan,tunani take shin ta bashi dama ne ko kuwa? Shin tana iya yarda dashi ko kuwa? Ta yaya za a yi ta gane cewan ba cutar da ita zai yi ba,bai yi kama da azzalumi ba amma azzaluman ba kama suke dashi ba in kayi la'akari da yanda momy take an angel on the outside a devil inside.

Marwan kam bayan rabuwarsu wani volunteering work ya tafi ta haka kad'ai yake samu yayi amfani da skills dinsa na doctor bayan ya gama very late ya tafi gidansa ya freshen up sannan ya zauna tunanin maimunatou"tsk ahhh her name is too long." Hannunsa biyu yasa ya shafi fuskarsa yana tuno nata cute face,yanda idanunta ke yi whenever she is nervous wani murmushi ne ya kubce mishi tuno da hirar su na yau ashe tana magana sosai ba yanda ya zata ba which means rayuwa ne ya mayar da ita miskilan karfi da yaji.

Dan hura hanci yayi feeling her pain all over him ko da wasa bai son sanin abinda ke sata zama reverse he dont wanna pry cikin abinda bai shafeshi abu daya zai yi he will take care of her and bring her out of her shell saboda yana jinta a ranshi sosai ba zai iya fada mata hakan ba dan zata iya tsorata dashi saboda haka zai bita a hankali har sai ta sake dashi which yanda ya lura is not going to be hard.4


STORY CONTINUES BELOW

Sai da aka yi kwana biyu marwan bai kirata bai mata text tun tana sa rai tana duba wayarta har tayiwa kanta fada ta share but deep down tana so taji daga gare shi and she dont why she tried to keep herself busy dan ita karta kirashi ko tayi masa text.

A kwana na uku tana zaune gaban system dinta tana karatu a ranta so take ta round up taje shopping abubuwanta sun kare wayarta da take gefene ta fara haske kasancewan tana silent a hanzarce ta kai hannunta kai dan is hardly wayarta tayi ringing dan babu me kiranta sai daddy wasu lokutan ko kuma momy in tana so ta impressing daddy.

Ganin me kiranta ya sa gabanta faduwa bata san me yasa take jin haka ba tsoro yake bata komi? (heheh wai tsoro ne?) Wayar na gab da tsinkewa ta picking shiru tayi bata ce komi ba.2


"Hello miemie are you there?" Dan tattara giranta tayi ta cire wayar daga kunnanta ta kara duba me kiran shi din ne dai amma me yasa yake kiranta da wani suna ko dai wata zai kira ya kira ta? Nan da nan taji ranta ya baci tana shirin ending call din taji yace "maimunatou! Baki ji na ne?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da jin wani wasai cikin rawar murya tace "uhm uhm ina ji,i thought bani zaka kira ba." Murmushi yayi yace "me yasa kika yi tunanin haka?" Dan kyafkyafta ido tayi tace "uhmm u called me miemie." Dariya me sauti ya saki cikin dariya yace "saboda nace miemie ne kika yi tunanin ba ke zan kira ba wato?" Bai jira ansanta ba yace "well maimunatou yayi min tsayi da yawa shi yasa na cutting sunan and i decided to call miemie daga yau ok?" Dan zaro ido tayi kwana nawa da haduwarsu amma har ya canza mata suna abin mamaki and she like the name.

Hira suka dan tab'a duk da surutun shi yake tayi ita tana sauraronsa sai lokaci lokaci take bashi amsa kafin ta farga har lokaci yayi and tana so taje store sallama tayi mishi ba don ta so ba dan sosai ya debe mata kewa.

Shirita tayi tsab na zuwa store yau garin ba sanyi hakan ya sa ta saka dogon wondon jeans da wata sleeveless riga sosai portable shape dinta ya fito kamar dai wata model sai ta yafa gyale a kanta ta fita.2


Tana tsaka da shopping kawai taji tayi karo da kirjin na miji tuni jikinta ya fara rawa tana kokarin bashi hakuri magnan ya makale a bakinta ganin Marwan shima da mamaki yake kallonta,kallon suturar jikinta yayi bai taba zaton tana fita haka ba,boobs dinta ya zubawa ido yanda suka taso suka cika gaban kirjinta gyara murya yayi tare da kau da kai gefe cikin wan irin calmness da bata san yana dashi ba duk dai shi din ba wai hayaniyar hawa kai gareshi ba yace "baki ce min zaki fito shopping ba." Sunkuyar da kai tayi kaman wacce tayi laifi ko dan salon yanda yayi maganan ne yasa taji ta kara takura oho1


Tattausan hannunta ya riko yace "shikenan lets shop together." Boyayyan murmushi ta saki amma har lokacin bata dago kanta ba sannan gaba daya ji take kaman an jona mata electricity a hannunta haka suka yi ta zagaya store din tare suna picking abinda suke so tun bata sake ba har ta sake bayan sun gama suka je kafin ta fito da card dinta har ya bayar da nashi kuma ya kobe ta da ya mishi godia.

Marwan ya ja maimunatou a jiki sosai tun tana jan jikinta har ta sake dashi sannan ta sani deep down ta kamu da sonshi amma shi ta rasa ina ya dosa he thought her so many things yana sata tayi dariya har cikinta kulle  a very small gesture yana sata kamuwa da son mutum saboda abinda ta rasa kenan so daya ta taba inviting dinshi zuwa gidanta shima sai da yayi mata gwari dan ko karatu zai koya mata sai dai suyi shi a park ko library, tsayuwa yayi sosai ya karewa dakinta kallo its not so cozy dakin da gashi nan so plain kaman ba dakin mace ba ya lira shi doesnt pay attention to girly things kawai harkan gabanta take yi dakin ba wani deco ba komi.

The following day buckets na paint ya siyo kusan kala hudu da yake weekend ne tana cikin bacci taji knocking idonta cike da bacci ta mile ta dauke robe dinta ta saka mamaki fal ranta who could it be dan lekawa tayi ta hangoshi tsaye hannayensa cikin aljuhun wandonsa,dan zaro ido tayi da mugun sauri ta dauki hijabin da tayi sallah dashi ta saka ta saka tafukan hannunta ta goge fuskanta sannan ta bude mishi murmushi yayi yace "awwww so cute with the sleepy face a cikin hijab." Sunkuyar da kai tayi tana smiling ciki ciki ta furta kalman "thanks!" Murmushi yayi yasa yatsansa ya dago da kanta yace "you should always wear hijab bata ce komi ba shima dukawa yayi ya dauki paints din ya umurceta da ta shigo da sauran cike da mamaki ta bi bayanshi fada mata yayi dakinta bai yi kala da na mata ba. Dan tattara gira tayi yace "yes ko gidana yafi naki zama cozy,now help me move things mu fara aiki." Haka suka fara matsar da kaya tea suka sha kafin suka fara painting yana nuna mata yanda za tayi har lokacin hijab ne a jikinta.

Kafin ace me ta fara jin dadin painting din bata taba yi ba but it was fun bata ankara ba taji an shafa mata abu me sanyi a fuska zaro ido tayi lokacin da ta shafo taga paint ne kara waro idanunta tayi tana kallonsa yana kyalkyale mata da dariya bata san me ma ya kamata tayi ta san wasa yake mata but she dont know how to respond shafa mishi itama ya kamata tayi ko me katse mata tunaninta yayi ta hanyar shafa mata karamin paint brush din hannunsa a kan hanci zuwa baki kara kwalalo ido tayi zuwa lokacin da idanunta na iya barin socket dinsu saboda yanda take fitar dasu da sun tunbuke itama debo paint din tayi ta shafa mishi a wuya cos he is way taller shikenan kuma sai wasan paint ya tashi suka yi kaca kaca da jikinsu da paint har zuwa lokacin bata samu daman shafa mishi a face and target dinta kenan

Tura shi kasa ta yi sai aka yi sa'a ya loosing balance dinsa ya fadi bata yi wata wata ba ta bishi ta shafe mishi fuska da painta din hannunta kasancewar daga ita sai pant da bathrobe ya sa bare laps dinta fito am hijab dinta ma ya haura cikinta a waje kadan zata daga yaga bare boobs dinta tuni ya shagala da kallon smooth skin dinta without thinking ya dora hannunsa kan lap dinta a zabure ta mike kaman wacce aka jonawa electricity.

Kara jan rigar tayi ta daure tare da gyara himar dinta shima zaune ya mike tare da lankwasa kafarsa daya ya daura hannunsa akan guiwansa he is trying to calm his hormones just seeing her like that turns the devil in him on.

Tun daga ranan duk su biyun suka fara samun sleepless nights kowa na tunanin dan uwansa in a naughty way ita ta gama yarda da tana sonshi but bata san daga wajenshi ba she believe shima yana sonta in bai sonta he will not be with her from the first place(yarinta you believe what you want to believe) on his side ya sani at first is lust yazo ya zama tausayi not that ta rasa komi na rayuwa but she lacked love and attention.  gradually he started liking her but now.... Mehnn he doesnt know what he feels anymore.7


Since then it has been very ackward tsakaninsu yaci alwashin sai ya gyara hakan

wata rana sunje wani park suna zaune kan grass carpet hankalinta yayi nisa tana kallon wasu yaran turawa suna wasa bata ankara ba taji an tickling dinta kafin tayi wani yunkuri ya sake sakar mata wani cakulkulin dariya ta fashe dashi tana kokarin kwatar kanta amma ina cakulkuli kawai yake mata yaki releasing dinta garin dariya tare da kokarin kwatar kanta suka bige da kwanciya kasa suna rolling dariya take yi har hawaye na fita a idonta.

Tsayawa yayi da cakulkulin yana kallon fuskanta how she was laughing so hard bai taba ganinta this free duk da yana sa ta dariya but na yau is different he cant hold back anymore.

A hankali ya motso da fuskarshi dai dai nata bata ankara ba taji numfashinsu na gaurayiwa cikin rabin second ta bud'e idanunta wanda hakan yayi sandiyar sarkewan idanunsu waje daya sun kai 40 seconds suna kallon cikin idanun juna sannan zuciyarsu na wani irin bugawa da souri sauri kara matso da fuskarshi yayi dab da nata kasancewar tana kwance a kasanshi ne. Wani tsoro ne da fargaba ya kamata saboda motsi kadan zata yi lips dinsu ya gogu sai faman kyafkyafta ido kawai take yi a hankali ya furta "I love you!" Kafin tayi reacting kuma ya rufe distance din dake tsakanin lips dinsu soft lips against soft lips a hankali ya tsotsi lower lip dinta sannan ya koma ya tsotsi upper lip din wani irin juyawa kanta ke yi idanunta sun tsaya cak da kyaftawar da take yi.2Briefly ya kissing dinta sannan ya releasing lips dinta yana kallon fuskanta. Gaba daya bata cikin hayyacinta a tsorace take ta shiga shock ganin haka yasa ya dan jijjigata yana kiran sunanta.

Numfashin da ita kanta bata san ta rike ba ta saki me karfi tare da shesheka,lumshe idanu yayi yana hamdala hakan ya bata daman tureshi ta mike tsaye duk jikinta gaba daya zikiri yake sai waige waige take yi dan ta tabbatar babu wanda ya gansu,ta manta a kasar turawa take da sauri ta fara tafiya riko hannunta yayi yana fadin "maimunatou relax" yau ko miemie din ma bai samu daman fadi ba dan shima a kidime yake musamman yanda yaga ta koma kaman wata zararriya sai kokarin kwace hannunta take yi tana gunjin kuka amma kuma Allah cikin ikonsa ba kukan take ba kawai tana cikin firgita ne ganin haka yasa ya janyota ya rungumeta tsam a jikinshi yana jijjigata a hankali jikin nata ya bar bari kwakwalwanta ya fara tariyo abinda ya faru numfashi taja a zabure kaman irin wanda aka tsikara din nan.

Kokarin raba jikinta da nashi take yi ya kara rikonta da kyau yana mata shuuu a kunne daina kiciniyar tayi tare da lafewa a kirjinshi hannunta take dagawa a hankali kaman wacce zata zagaye a jikinshi sai ta fasa ta sakesu a gefenta sai da ya tabbatar she is calm sannan ya saketa saukar da kwayan idonta kasa tayi saboda wani kunya da ya rufeta innalillahi he just kissed her kuma yace mata I love you,is he for real? Tana cikin tunani har yaje ya dauko jakankunan su ya dawo ya rike hannunta har lokacin bata dago da kanta ba suka fara tafiya zuwa inda motarsa yake.3


Passenger side ya bude mata ta shiga  sannan ya zaga ya shiga side dinshi key yayiwa motar suka fara tafiya zuwa block din da apartment dinta yake.

Babu wanda yace komi a cikinsu har suka isa apartment dinta tare suka fita yana rike da jakanta har kofan dakinta sannan ya mika mata sai a wannan lokacin yayi magana shima ba wani abu yace ba sai da safe yayi mata ya juya ya tafi bayan ya tabbata ta shiga ciki.1


Jingina tayi da jikin kofan tare da lumshe ido hannunta daya a kirji what just happened? Ya declaring mata soyayyarsa sannan ya kissing dinta. Yanzu me zai faru? Da gaske ma sontan yake ko kuwa in yana sonta why is he silent after everything? Sulalewa kasa tayi ta zauna a jikin kofar har lokacin idonta a kulle kunya take ji sosai ita ko rike mata hannu da yake yi ko y rungumeta kunya yake bata yau kam abin yayi gaba har da kiss a public.

Palms dinta ta saka ta rufe fuskanta kaman tana gabanshi.

Murmushi tayinta mike tare da daura yatsunta a kan lips dinta kan coach ta kwanta tare da rungume throw pillow  recalling komi take yi the look on his face,i love you da ya furta and oh the kiss. In ta tuno da kiss din sai ta boye fuskanta haka dai tayi ta shiririta ko kadan zuciyanta bai kawo mata haramci ko rashin kyan abinda suka yi ba because she was in love sannan ta saba ganin ana haka a gabanta (one of the illan zama cikin turawa kenan)3


Marwan na shiga cikin motarsa ya fara buga stirring wheel yana fadin "fuck! Fuck! Fuck!" Garin ya aka yi ya bari ya rushing dinta damn! Seeing her laugh makes his heart flutted bai san lokacin da ya aiwatar da komi his feelings get the best of him yanzu bai san me ke tafiya a brain dinta duk ya firgita musu yarinyan mutane dole he will have to make things right dole ya canza mata tunanin he mean it when he said he loved her amma ba ta haka ya so ya fada mata and that kiss? Hell it was his best even though she wasnt responding but he love it her lips were so soft and full she taste like dahlia which means tana amfadi da lip balm me kamshin flowern.2


Yes! Ya samu mafita ta yanda zai gyara kuskurensa he will woo her sai ya tabbatar ya siye zuciyanta before her birthday nan da kwanaki takwas kenan da wannan tunanin ya ja motarsa ya bar wajen.1


Daren ranan da kyar bacci ya iya sace maimunatoo saboda tunanin marwan gashi tunda suka rabu bai kirata ba bai kuma texting dinta ba.

Da asuba tana tashi ta duba wayarta message ta gani kwaya daya cikin rawar jiki ta bude dan tsaki ta saki ganin alert ne na kudi da daddy ya turo mata.3


STORY CONTINUES BELOW

Ajiye wayar tayi ta shiga bathroom dan yin alawla kan in ta fito sai ta kira daddyn ko ta yi mishi text. These days har mantawa take yi da en gida Marwan kept her occupied abin mamaki daga ita har shi babu wanda ya taba hiran family din shi kawai abinda yake gabansu su ke yi but things will have to change yanzun tunda she is officially his girlfriend murmushi mai fadi tayi tare da tsallen murna a hankali murmushin ya koma frown tunowa da tayi tun da suka rabu be kirata ba ko ya dai ya regreting moment dinsu ne haka tayi ta sake sake har tayi shirin classes.3


Tana bude kofarta saura kadan tayi kwallo da bouquet na Dahlia dan tattare giranta tayi tare da dukawa ta kalli sunan dake attach da flowern da sauri ta dauka ta koma cikin dakinta ganin good morning miemie a rubuce rungume flower din tayi tana juyi tare da kyalkyale dariya she cant believe it ashe yana sonta da gaske.

Sai da ta gama rawarta sannan ta addana flower din da gudu ta fita ganin ta kusan latti.1


Yana tsaye a ta gefen block dinsu hannunsu soke cikin aljuhun wandonsa yana so  yaga fitanta aiko da gudu yaga ta wuce tana tsare taxi murmushi yayi tare da girgiza kai he can see that she is happy this morning yana fatan ace shi ya sata wannan farin cikin.1


Yinin ranan maimunatu tayi shi ne cikin farin ciki kowa ta gani sai ta sakar mishi murmushi mutane nata mamakin what the changes is all about.

She even say hi to few people wadanda suka so su kusanceta taki,ko a cateen bata zauna ita kadai ba tare da wata balarabiya suka zauna. Allah Allah take ta gama classes taje gida ta kallo flower dinta wayanta kam ta duba yafi so a kirga babu text ko call din marwan ko daya tun bayan reply da yayi mata da ta tura mishi da thanks for the flower.2


Marwan was a bit busy ranan saboda ranan yayi defence dinsa amma hakan bai manta ya aika mata wani set of dahlia din ba. Tana zuwa gida ta ganshi a door step dinta tsalle ta daka tare da ihun yes! Kafin ta dauka.

Inhaling kamshin flower din tayi tare da lumshe ido she cant believe he is been romantic,this is her fairytale she is cindarella and he is her prince charming.

Unlucking kofar ta tayi tana kara tabbatarwa kanta ita cindarella ne gashi kuwa tana da wicked step mom.

Cikin bed room dinta ta kai flower din ta ajiye shi a gefen bedside dinta zama tayi a kan gadon sannan ta rubuta mishi short message na godia still kaman safiya reply iri daya yayi mata "its my pleasure" dan bata rai tayi tare da bubbuga kafarta a kasa "ya baya cewa komi?" Tayiwa kanta tambaya dora yatsanta daya tayi a kan lips dinta kaman me tunanin a hankali tace "toh ko in kirashi ne? Hmmm ina na kirashi sai ince mishi mene?" Rufe fuskanta tayi da tafukan hannunta alamun taji kunya "wayyooooo ni! Marwan mana." Tashi tayi tsaye ta fara  stripping kayanta tattarasu tayi ta rungume kayanta daga ita sai pant ta wuce bath room cikin loundry ta zubasu sannan ta bude shower.2


An kwashe sati guda Marwan yaki nunawa maimunatu kanshi sai dai kullum zai aika mata da gift so biyu safe da yamma chocolate,candy,designers perfunes,teddy bear and all sort of girly things tun tana matsuwa da son ganinshi har ta hakura gashi ko kiranta yaki yi she wonder  what game he is playing gashi itama ta kasa kiranshi sannan ta kasa mishi text ta tambayeshi me yasa yaki zuwa wajenta ko yaki kiranta.1


Tafi alkanta hakan da kiss din da yayi mata kiss din da yaki barin kwanyanta kiss din da in ta tuno sai ta rufe fuskarta dan kunya. Kiss din da shine abu na karshe da take tunawa kafin tayi bacci.1


A cikin satin nan rayuwar maimunatu ya canza sosai ta fara shiga cikin mutane suyi karatu tunda wanda yake koya matan ya kaurace mata1

Daren ranan da zata cika shekaru sha takwas a duniya bayan ta gama assignment dinta ta kwanta tana ta tunane tunane her life is so lime babu komi a ciki is so tastless zata samu lokaci ta siyo set na television ita babu wani abu na fun da take yi she doent play game bata kallo bata karance karance she doesnt have a hobby she only reads her notes books and textbooks.1


Yanzu da take interracting da coursemates dinta har tayi dariya ita fa da bayan yah khalid babu wanda yake ganin dariyarta sai dai ko murmushi oh Allah sarki yah khalid! Ta furta a hankali ta san shi kadai zai missing dinta duk Nigeria dan ko en makarantansu ma bata da kawar da zata ce Allah sarki ko maimunatu tana ina she doubt in akwai wanda zai noticing ma bata zuwa

So yah khalid ne kadai zai missing dinta and maybe daddy dan tabe baki tayi tuno da daddy kam ma ba sai ya tuna da ita ba yanzu rabon da su yi waya kusan sati biyu tunaninta ne ya tsaya cak tunowa da tayi  ya kamata ta kira daddy tace mishi taga sakonsa tashi tayi ta nufi kan desk dinta dan daukan wayanta.1


Dai dai lokacin 12 biyu ta doka wanda yayi dai dai da door bell dinta ya ringing Waro idanu tayi tare da freezing kara kallon time din wayanta tayi dan tabbatar da time din, kara buga kararawar kofar ya sata antayawa dakinta da gudu tare da rufe kofa.

Tsaki marwan ya ja na rashin samun cikar burin sa yarinyan ta ruining mishi plan da taki bude kofar lift ya shiga ya sauka kasa tare da yiwa mutanen da ya hiring alamun su dakata .1


Iska yaja ya fesar yana tunanin mafita murmushin gefen baki yayi ganin ya samu wata hanyar a hankali ya saka hannu cikin aljuhun jacket din sa ya fito da wayarsa1

Text ko kiranta zai yi? Shine ya kasa tantancewa tsaki ya kuma ja ganin har 5 minutes pass 12 ba tare da tsaywa bata wani lokaci ba ya danna kiran layinta.1


Maimunatu kuwa tunda ta kudundune a cikin bargonta a rintse ido tana addua ko kwakwaran motsi bata iya yi,vibrating din wayarta ne ya kuma firgitata ta kara kankame jikinta a hankali ta dago wayar dake hannunta taga caller id din ai bata san lokacin da ta flinging duvet din da ta ruhu dashi ba ta nemi tsoron ta rasa cikin rawar jiki ta picking wayar tana dauke numfashi abinda tayi ta jira fiye da sati1

Murmushi ya saki mara sauti kafin muryarsa cike da authority yace "look out of you window lumshe idanu tayi muryarsa na ratsa ko wata gaba ta jikinta sai taji kaman ta dauki lokaci me tsawo bata ji daga gare shi ba this is pure torture ko kadan bata fahimci me yace ba ta shagala da jin dadin muryarsa.1


Jin tayi shiru yasa yace "miemie are you there? Nace ki kalli window dinki i have a suprise for you nazo kofarki baki bude ba." Dafe kanta tayi tana scolding kanta for not opening the door a hankali tace "ok"1

Karasawa tayi jikin window din tare da zugewa har lokacin wayar na kunnenta rintse ido  tayi lokacin da sanyin iskan waje ya doketa cikin rawar sanyi tace "ina window din." Bai ce mata komi ba ya umurci hired people din shi dasu aiwatar da abinda zasu aiwatar.1


Boooomm taji abu a kanta  Jan numfashin tsorata tayi ta kalli waje wani numfashin ta kuma ja wannan karon na mamaki wanda ya saka shi sakin murmushi.

Wai abin takaici tun yaushe na gama last part din nan amma bai appear naji haushi sosai ban ma san ya na kara rubutawa ba.Murmushi yayi tare da furta abinda take kallo "happy birthday love"

Maimunatu bata iya cewa komi ba sai kallon sama da take yi inda happy birthday love ke ta fashewa cikin shape din heart a sama how on earth is that even possible tana ce a film ne kawai ake haka lallai marwan is something else.1


Marwan! Yes Marwan har yanzu fa yana kan waya cikin rawar murya domin idanunta tab yake da hawaye tace "Marwan thank you! Thank you so much this means al lot for me." Shushsh shine abinda yace mata a hankali tace "amma me yasa marwan? Why?" Cikin sanyin murya yace because i love you miemie." Jan hanci tayi na kokarin hana kanta kuka tace "why me? I dont think i am upto ur standered why me ga mata nan kala kala a gari classy babes why me? I have nothing to offer Marwan."2

Murmushi yayi yace "ni duk ban gansu ba ke na gani miemie and stop saying you dont have anything to offer you have a lots to offer you are unique in ur own way sannan ni ban son komi a wajenki just you."1


Cikin sanyin jiki tace "but...." Katseta yayi da fadin "shuhsh dont day anything,no buts jeki samu ki kwanta ki huta tomorrow is gonna be a long day and i want you to enjoy every bit of it and zamu cigaba da maganan mu when the time is right just know that you are mine maymunatu mine alone!  Now go to sleep will see tomorrow"  daga haka ya katse kiran ya barta da waya a kunne tana mamakin tune din da ya using kaman wani yace zai kwace mishi ita murmushi tayi tare da kara kallon sama duk da abin ya watsa kulle window dinta tayi tare da yin tsalle tana juyi dan dama ita abu kadan zaka yi mata na kulawa ka siye zuciyarta bata raina kyautatawa time ta duba taga 1 saura da sauri ta hau gado tare da yin addua.4


Rintse ido tayi amma bacci yaki zuwa sai ta rufe ido sai ta fara tuno kalamansa sai juyi take tana murmushi she cant believe ita ta manta yau za cika 18 years amma shi bai manta ba he is sooooo romantic she cant ask for more Allah yasa kar momy ta zuga daddy a kan marwan Allah yasa su barta ta aure shi.2


Kunya taji ganin karama da ita amma ta fara tunanin aure kife kanta tayi a kan pillow kaman wani na kallonta da haka bacci barawo yayi awon gaba da ita.1


Washegari da kyar ta tashi tayi sallah ta koma wajen ten door bell dinta ya tasheta bacci cike da idonta ta bude kofar ba ma tare da ta duba ko ta tambaye wanene ba.1


Kyafkyafta ido yayi tayi tare da murzawa Marwan ne dai tsaye gabanta tabe baki tayi tare da turo shi,lakace mata kumatu yayi ya raba ta gefenta ya shiga dakin.1


Dan juya idanu tayi ta shiga tare da rufe kofar haka kawai sai ta tsinci kanta da jin matsanancin kunyanshi ta kasa juyowa shi kam murmushi yayi ya shige kitchen dinta sai da taji burutunsa a kitchen tayi saurin shiga bathroom din zaro idanu tayi ganin yanayinta a mirror dogon wando ne a jikinta da ta saka saboda sallahriga ce mara nauyi a jikinta fara sannan kana iya ganin shatin nipples dinta saboda rashin nauyinta dafe kai tayi kaman tayi kuka tana kara karewa kanta kallo yanda gashinta yayi buya buya duk ya tashi sama tsaki taja kafin ta dau brush dinta ta bude tab ta wanke kafin ta matsa toothpaste ta fara brush bayan ta gama ne ta bude hakoranta tana kallon haskensu kara kallon kanta tayi tsaki wanka ta deciding tayi kofar bathroom din ta sakawa key kafin ta fara stripping kayan jikinta.3


Wanka tayi cikin nutsuwa sannan ta goge jikinta cikin bathroom din ta mayar da kayan da ta cire a jikinta saboda dashin ruwan jikinta sai rigar ta kara lafewa a jikinta tsaki ta ja ta dakko bathrobe ta dora a kai.

Luckly tana da comb a bathroom din sai kawai ta combing kan nata tana shirin ajiye comb din taji knocking sai da ta firgita dan tsoro ta yar da comb din hannunta.2


Gyaran murya tayi tace "ina zuwa" ko maganan ma sai da muryarta tayi rawa kara dan kimtsawa tayi sannan ta fito kanta a kasa ba tare da kalleshi ba tace ina zuwa tare da nufan bedroom dinta.1


STORY CONTINUES BELOW

Gyada kai yayi yana cusa hannunsa cikin aljuhun wandonsa kallon aikin da yayi ya kuma yi yaga he is satisfy.

Pacing ya fara yi yana jiran fitowanta haka nan ya tsinci kansa da jin nervouseness shi wallahi bai son jira he hates waiting sai yaji duk ya kagu.1


Sai da ta kwashi 10 minutes ta fito cikin straight skirt da riga dai dai guiwa kasancewar kayan ya matseta sai shape dinta ya fito sosai cikin nan a tsuke kaman Allah bai ajiye komi a ciki ba kanta daure da vail.

Bata shafa komi a fuskanta ba bayan face cream amma haka nan tayi mishi wani irin kyau duk da dama ba wai ya taba ganinta da kwalliya bane but she look more cute today her beauty is natural.1


Ganin bata dago kai ba balle taga aikin da yayi ba yasa shi zagayawa ta bayanta yasa hannunsa ya zagaye kugunta sai da ta ja numfashi lokacin da hannunsa ya taba jikinta dan ji tayi kaman an saka mata electical shocking dan dukawa yayi ya saka kansa a kafadanta. Dan juyo da ita yayi dan su fuskanci gaban couch dinta yace"look." A hankali ta daga kanta wani numfashin ta kuma ja alaman tayi mamaki murmushi yayi yana son yanda take jan numfashi in ta tsorata ko ta yi mamakin abu.1


Abinci ne na breakfast kala kala a jere a kasa ga wasa flowers da ya decorating wajen ita duk bata san da yaushe ya shigo da wadannan kayan ba a hankali ya sake ta tare da riko hannunta suka nufi inda abincin yake ga wasu en kananan cake na alphabet da aka rubuta happg birthday babe.

Zaunar da ita yayi,nan da nan idonta ya kawo kwalla lura da hakan da yayi ne ya saka ya dan dukawa gabanta a hankali yace "miemie me ya faru me yasa ki kuka? Did i do anything wrong?"2


Girgiza kai tayi tana kokarin dauke hawayen idonta,rike hannunta yayi ya saka nashi yatsan ya dauke mata hawayen daya bayan daya.


Murmushi ta kakalo cikin dasashen murya tace "ba komi i am just happy." Shima tayata murmushin yayi yace "haba dai,babe baki ga komi ba this is just the begining am gonna shower you with love." Sadar da kai tayi xuciyarta kal bata taba sanin akwai lokacin da zai zo ta riski kanta cikin farin ciki ba.1


Haka suka yi breakfast yana kara jaddada mata yana yake sonta ita dai bata cewa komi sai dai tayi murmushi ta sadar da kanta shi kuma duk kokarinsa na yaga ta sake dashi ne.


Sun kai one hour suna breakfast saboda yanda take cin abincin cike da yanga wanda ba aai yangar take yi ba tsabar rashun sakewa ne sai da suka gama yace mata taje ta canza kaya zasu fita sannan ta saka dogon wando dan fitarsu na buqatan wando. Cike da mamaki taje tayi yanda yace shi kuma ya fara tattara wajen da suka bata yana packaging mata abun da basu ci ba yana sawa a cikin fridge.1


Fitowa tayi cikin blue jeans da karamar jan riga kallonta yayi yana jan numfashi tare da saukewa a kai kai yace "please change into something else rigar tayi kankanta da yawa dan tabe baki tayi ta koma ta saka wani rigan da ya dan sauka kallonta yayi haka kuma sai yaji shima bai mishi ba amma sai ya daure suka fita.1


Tafiya suka yi me nisa kaman zasu bar gari yana ta janta da tadi tana amsashi sama sama saboda kunya sai da suka bar cikin gari suka dauke hanya suka yi wata kwana shima wani tafiyar suka yi a kan kasa kafin suka isa wani range baki bude take kallon kyaun wajen

Wani bature ne ya fito cikin shigar cowboy amma ya dan manyanta rungume marwan yayi suna dariya basu gama farin cikin ganin juna ba wata budurwa ta taho a doki tana gani marwan tayi wani irin dirkowa wanda ya saka maimunatu dafe kirji dan tsorata da gudu taje inda marwan yake ta dalle jikinshi tare da zagaye kafafuwarta a kugunsa riketa yayi yana dariya haka shima baturen sauka tayi daga jiknshi tare da dankara mishi wata kiss me kara a lips dan yamutsa fuska maimunatu tayi cike da kyama da takaici tare sa kawar da kai. Dan satan kallonta marwan yayi yana yake yace "careful ann" dariya tayi tace i just so much missed you,where have you been all this while?" Sosa kansa yayi yace cikin harshen turanci ina nan,abubuwa ne kawai. Here ga budurwata nan na kawo muku."ya gesturing musu inda maimunatu ke tsaye a gefe sai faman blushing take yi tare da karasawa gefenta ya dora hnnunsa kan kafadarta.1


Zaro ido ann tayi ta kalleshi tare da

Kallon dayan baturen tana tambayansa is he for real? Daga kafa yayi alamun gaki gashi karasawa tayi kusa dasu tana karewa maimunatu kallo takaici ne ya cika maimunatu ganin yanda ta sata a gaba tana inspecting dinta a hankali tace "wow she is so cute but young." Dariya marwan ya saki yace "i know you will like her." Maimunato bata ankara ba taji ta finciketa tare da rungumanta tana kokarin maka mata irin kiss din da tayiwa marwan da sauri marwan ya janyeta tare da ce mata "she will not like it." Murmushi tayi tare da daddaga giranta inviting dinsu ciki suka yi girgiza kai marwan yayi sannan ya fada musu abinda ya kawosu.1


Ann ce ta jasu zuwa stable din inda maimunatu taga kosassun dokuna umurtatan ta tayi da ta zo ta hau da sauri ta girgiza kai dan bata fuska tayi tare da kallon marwan dariya yayi yace mata "ai bata taba hawa ba wani light brown ta nuna tace "toh ta trying genty ba zata zaburar da ita ba. Kada mata kai yayi yace ba damuwa taje zai kula da komi fita tayi ta barsu juyo da ita yayi yace " do you trust me? Gyada kai tayi cike da tsoro, limshe ido yayi yace "then trust me." Daukanta yayi ya dorata kan genty ya ganin yanda jikinta ke rawa ya sa shima yawa kan dokin dan numfashi taja da ya sashi sakin murmushi a hankali suka fara tafiya yana mata magana a kunne a hankali wanda yake sata sakin mirmushi.1


Tafiya suka dinga yi a hankali suna zaga field din maimunatu kam cinyoyinta suna fara zafi tace mishi ta gaji maimakon ya mayar dasu sai taga sun dau wani hanya inda suka fara shiga wani waje me koren ganye bude baki tayi ita kam abu kadan ke burgeta wani darduma aka shimfida tare da jera abubuwan ci ashe ya gayawa ann abinda yake so tayi mishi.1


Sauka yayi ya sauketa, d'an picnic suka yi a nan ne yake gaya mata wacece ann kawarsa ce a med school roger kuma mijinta ne sosai maimunatu tayi mamakin yarinya da ita ta auri tsoho sai da suka gama  sannan suka tattara suka koma cikin gidan inda suka yi musu sallama suka tafi.1


A tunanin maimunatu gida zasu ganin dare ya fara yi sai taga sun daukin wata hanyan inda ake skating ya kai ta da wayo da komi ya shigar da ita wajen kankameshi tayi dan tana tsoron faduwa sabida tsantsin kankarar sai dariya suke yi a haka yayi ta janta yake yi a haka suka  dau lokaci maimunatu laugh so hard ta manta ma da duk wata kunya a haka suka fito suna dariya yana like da ita  wayarta ce tayi ringing hakan ya sata fito da wayar da ga cikin jakanta dariyarta ne ya tsaya ganin sunan MOMY....

Post a Comment for "KINA RAINA CHAPTER 1"