KINA RAINA CHAPTER 9 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KINA RAINA CHAPTER 9

 KINA RAINA CHAPTER 9


Kallon kallo suka tsaya yi jijiyoyin kansa kaman zasu ballo su rabu da kan tsaban yanda suka tashi,idanunsa sunyi jazir alaman tashin hankali ko b'acin rai hakoransa kam ba dan Allah yayi su da karfi ba da tuni sun tarwatse saboda irin yadda ya datse su hannunsa na dunkule a gefensa.

Hadiyar yawu maimunatu tayi ta kau da kai tana kame kame ta sani a halin da yake cikin nan babu abinda ba zai iya yi ba.3


Abu d'aya ta sani ba zai tab'a bugunta ba marwan na da zuciya da fushi amma ba mai bugun mace  bane, ganin tsayuwar tasu tayi yawa bai iya kuma furta mata kanzil sannan ita ta amayar da nata ya sa ta juya dan ta bar shi ya digesting abubuwan

Har ta kai kofa ta juyo tace "and kar ka yi gigin zuwa ga Tahir a wannan halin and course a scene, kanka zaka tonawa asiri ba shi ba dan tonuwar asirin mubeena naka ne." Daga haka ta saka kai ta fice ta barshi a tsaye yana shirin fashewa.2


A hankali a hankali ya dinga jan numfashi yana sakewa tare da kama addu'a a bakinsa a hankali ya saki dunkule hannunsa da yayi tare da jan numfashi me tsaawo ya saki. Wuri ya samu a inda yake tsaye ya zauna ya tankwashe kafarsa tare da tallafo kansa cikin hannayensa kuka yake so yayi ko zai ji dadi amma sam babu alamun kukan sai wani yaji da radadi da yaji idanunsa na yi zuciyarsa na kuna.2


A hankali yake taryo maganganun maimunatu kap ya sani babu karya a cikin abinda tace shine shine silar abinda ya samu mubeena shi ya janyo komi shi ya bata komi mami ta sha gaya mishi "marwan kar abinda kake yiwa diyoyin wasu ya fada akan kannenka ka sani kanne mata gareka kar ayoyin Allah ya tabbata akansu. Ko dan su ba zaka tuba ka daina wannan mummunar d'abi'ar?"  Bude tafukan hannunsa yayi ya saka fuskarsa a ciki a wancan lokacin yana kafa hujja da shi baya bin mace sai dai ta bishi shi babu wacce ya taba yiwa dole. Cikin wata iriyar murya yace "autar mu,auta i am sorry na zalunceki na dade rabon da in kwanta da wata diya mace amma laifina na baya ya fada akanki auta dole miemie ta kyamaceni,ni din abin kyama ne ni din kazanta ne Allah na tuba Allah na tuba kar ka saukar da wannan masifan kan zuriyata da ban haifa ba kar halina ya shafi diyoyin da basu ji ba basu gani ba."2


Ganin zaman da surutan ba zai mishi ba ya sa ya mike ya shiga suite dinsa na office din tare da kullowa bathroom ya fada ya dora alawla sam tunkarar Tahir a halin yanzu baya cikin lissafinsa dan ya san ana iya dauresa dan kam sai ya kaishi har lahira.


4

Maimunatu kam tafiya kawai take yi tana hada hanya ranan yau ta zo mata a dabaibaye tana isa office dinta ta tattara duk wani abu da ya shafeta ta kwasheshi tas dan ta kudurta a ranta ita kam daga yau ta gama service dinta dan dama ai saura kadan,tana aikinta cikin jin dadi da kwanciyar hankali har tana considering aiki a Moh enterprises amma zuwan marwan ya ruguza komi tunda ya zo take cikin tashin hankali matsalan yau daban na gobe daban.1


Da wannan tunanin ta kwashe duk wani abu nata ta bar companyn kirar Tahir ne ya shigo wayarta tsaki taja tana mamakin mask din da ya sawa fuskarsa da ya iso gareta ko da wasa bai taba gigin ko taba mata hannu ba ashe kura ce da rigar akuya fuska biyu gareshi shi yasa yake bin duk wata hanya da mubeena ba zata sani ba dan gudun tonuwar asirinsa taji tsoron maza har gwara marwan bai boye mata shi wanene ba ya fito mata da halinsa Tahir kam kungurmin munafuki ne wato maza dai duk haka suke ita kam yanzu bata san wa zata trusting ba har khalid sai lokacin ma ta tunoshi dan tun ana gobe daurin auransa rabon da ya kirata dan dama ita tun da maganar auransa ya bayyana ta daina kiransa ranan auransa ma text ta mishi na tayashi murna ya aiko mata da kalmar godiya.3


Duk da halin da take ciki na dacin rai bai hanata murmusawa ba ina kuwa zata ga kiran khalid yana da sabuwar amarya ai kuma sai mai ya bar kan kaza kafin ya waiwayeta.1

STORY CONTINUES BELOW

Tana shiga gida wacce ta samu zaune a palo suna kallon kallo da momy ya sa gabanta mummunan faduwa dan babu tantama wannan tana da alaka da mahaifiyarta saboda tsantsar kamansu cak ta tsaya tana kare mata kallo da yaron dake zaune a gefenta murmushi tayi mata hade da hararar wasa tace "ba zaki karaso ki gaishe da mutane ba kin wani coge a can?" Ai da gudu maimunatu ta watsar da abin hannunta taje ta rungumeta dan ta sani wannan itace aunty khadija itama rungumeta tayi cikin tsantsan farin cikin ganin diyar yar uwarta yanda ta zama wata classy babe me aji aka bar momy da kau da kai har da jan dan guntun tsaki sadiq ne ya fara ture maimunatu daga jikin mamansa irin shi yana kishi dariya suka yi suna kallonshi dai dai lokacin da daddy ya shigo dan shima wayr kawai suka yi da aunty khadija yace yana karasowa

3

Kaman maimunatu shima sandarewa yayi da ganin aunty Khadija dan sai yake ganinta kaman hajararsa ke doka mishi murmushi.

Ta san me yake yiwa wanann sandarewar ta sani tun kafin tayi aure ana fadar kamansu da yayarta amma sunfi alkanta kamar da ta jini ce kawai dan ita hajara a murje take gata da kumatu masu kyau da taushi yayin da khadija ta taso da wani irin siranta kaman zata karya fuskar nan babu nama Allah cikin ikonsa tana aure ta murje lokaci guda ta koma Hajara dawowantan nan babu wanda bai yi maganar kamanninta da margayiyan ba.3


"Yah Abdul ba ita bace wannan khadija ce ba fatalwa take maka ba." Ta fada tana dariya murmushi yayi yace "gidanku khadija,wane ke da kamo kafar matata,ta dan dai sam miki kyan kadan amma kema kin san ta fiki." Ya fada da wani irin kewa a muryarsa momy kam ta cika fam kiris take jira ta fashe mikewa tayi ta shige ciki ba tare da ta cewa kowa komi ba dan yanzu hakan ta tsira bata cika magana kasafai da duk wani me son maimunatu ba ko da kuwa matan abokan daddy ne yanzu ko pretense din tace ta yafe ba zata dinga asara akan shegiya ba.2


Kallo aunty khadija ta bita da shi sannan ta mayar da kallonta kan daddy da maimunatu da suma ita suka bi da kallo tace"haka ita kuma matar gidan take?" Kaman hadin baki uba da yar duk murmushi kawai suka mata da alama sun saba da hakan.1


Mikawa sadiq hannu daddy yayi yace "kai big boy zo nan.." A hankali yaron ya taka ya isa gare shi tambayarsa yayi ina babansa? Shiru shi dai yayi yana kallonsa cikin american english khadija tayi yaron magana na yayi gaisuwa nan da nan ya fara gaisar da daddyn cikin irin turancin da mamansa tayi masa rungumeshi daddy yayi yace "khadija kece dan namu bature ne ina babansa?" Murmushi tayi amma bata amsa mishi tambayarsa ba sai ma tambayar izininsa da tayi na son tafiya da maimunatu zaria tayi ko da kwana biyu ne.2


Kallon maimunatun yayi yace "toh ke kinji za a barki a can wajen aikin naki?" Cike da murna tace "eh bari inje in shirya." Da gudu ta tattara abubuwan da ta shigo da su ta haura sama taji dadin tafiyan nan domin she need a break from all this drama.

3

Da dare mubeena na zaune a dakinta ta zabga uban tagumi taji an kwankwasa kofarta kafin a turo duk girman gidansu mutum biyu ke da wannan dabi'ar daddy da marwan

Daddy ba kasafai yake shigo mata ba sai dai in bata da lafiya.1


A dan firgice ta kalli yayan nata kana iya hango tsoro tsamo tsamo a cikin idanunta sabye yake da 3quarter na kamo da karamar riga mai round neck shima na camou.

Jiki a sanya ya karaso cikin dakin tare da zama a gefenta sunkuyar da kanta tayi tana wasa da hannunta a hankali ya kamo hannunta daya yace "auta!"  Dago da fuskarta tayi bakinta na rawa alaman zata fashe da kuka any moment.2


Girgiza mata kai yayi yace "kar kiyi kuka auta,kiyi hakuri kinji na san ba haalinki bane na ji komi amma idona ya rufe a lokacin shi yasa har na dokeki alhalin nine me laifi ni na janyo miki wannan mummunan kaddaran kullum mami na fad...."muryarsa ce ta fara rawa sai yayi shiru cikin kuka mubeena tace "yayanah kayi hakuri duk  wannan ba hujja bace na aikata laifi babba nima din Allah kuma ba ruwansa da wai wani ya jawo ko ba wani ya jawo ba yayana ka sani na tuba ina kan istigfari shekara uku kenan kuma tun lokacin makamancin haka bai kara faruwa ba ko muhammad da zan aura baya taba ko hannuna balle a kai ga wani abu dan tun farko mu muke jawowa kanmu da muka ari halayyan turawa muka yafa dan Allah ma ya fadi mana _la taqrabu zina_ amma mu kullum cikin kusantarta muke rike hannun juna ko rungumar juna da wanda ba muharamman mu ba, ba komi bane a wajen mu ta yaya masifa ba zai fada mana ba ya kai mu da aika zina?" Gyada kai marwan yayi cikin jin kunyar kanwar tasa ya san iyakar gakjiyanta take fada amma sai yake jin kaman tana mishi gugan zana."2


Yace "auta kinyi gaskiya tun haduwata da miemie shekaru 5 da suka wuce ban kara sha'awar wata ba tun daga kanta ban kara waiwayan zina ba amma ta bakinki ban daina kusantar zinar ba tunda ina rungume macen da muharramata ba amma in shaa Allah auta daga yau na dau gyara akanki Allah ubangiji ya yafe mana gaba ki daya."2


A hankaali ta amsa da ameen yayana. Shiru suka yi na dan wani dakikai marwan na lura da yanda mubeena ke motsi da baki yace "auta da magana a bakinki me kike son fada?" Dan murmushi tayi tana sosa gefen wuyanta tace "uhmm uhmm yayana ba fa komi bane dama dama tambayanka zan yi dan Allah wacece wannan miemien?" Murmushi yayi tare da daga kai yana limshe ido yace "kina so ki san miemie dina?" Ta gyada kai yace "auta miemie tace bata sona ba zata aureni ba saboda kaddarar da ya fada mana ni da ke tana tsoron kar irin kaddarar ta fada kan zuriyarta." Cike da mamaki tace "yaya ban gane ba? Ya akayi ta sani kai ka fada mata? Yaya me yasa zaka fada mata?" Ta jero masa tambayan a kidime.2


Cikin murya me cike da rauni yace "auta i dont have to tell her anything ta san komi tunda a gabanta komi ya faru,miemie dina itace maimunatu secretary dinki....Waro idonu tayi ta saki baki tana kallonshi na sure ko ta ji abinda ya fad'a gyada kai yayi yana murmushi ya saka dan yatsansa a kasan habanta tare da rufe mata baki da kyar ta tattaro tunaninta tace"yayana ban fahimceka ba,ban fahimci ta inda maimunatu ta zama miemie dinka maimunatu ta zo moh enterprises just 8 to 9 months ago kai kam ma gaba daya da dawowanka bai kai 2 months to how?,when duk hakan ya faru? Right now i am really confuse ."2


Murmushi yayi tare da gyara zamansa yana fuskantarta ya riko hannunta kafin yace "ni ban san maimunatu a moh enterprises ba na santa shekaru kusan shida zuwa bakwai da suka wuce rabona da in ganta kuma ya kusan shekara biyar." Ai kam zuwa lokacin da idanu na barin socket dinau saboda gwaluwa da na mubeena ya bar nata cikin inda inda tace "yayana how?... I mean when.... Ya salam" ta dafe kanta dariya yayi yace "calm down zaki ji yanda muka hadu a cyprus ne time din da naje phd dina........" Nan dai marwan ya kwashe haduwarsu da miemie da soyayyarsu da shakuwarsu ya gayawa mubeena har da zuwa rabuwansu.

2

Cikin tsananin farin ciki mubeena take kallonsa ta wani gefen kuma tausayinsu taji sun rabu Allah ya kara hadasu bayan shekaru biyar shi yasa maimunatu take wasu abubuwa in ta ganshi amma kuma? Cikin confusion tace "toh yayana me yasa kuke nunawa kaman baku san juna ba?" Fuskarsa cike da damuwa yace "in ta nine i will show the world my woman amma hakan zai yuwu ne in tana sona ko tana son a san ita din tawa ce,miemie ita ta fara nunawa bata sanni ba da na confronting dinta sai ta nuna she dont want anything to do with me? Abu daya na sani tana tsananin fushi dani fushin da na kasa gane mafarinsa she thinks i wanted to take advantage of her which i never did,yes we did some stuffs but i never sleot with her." Ya fada yana lowering kwayan idonsa

1

Mubeena tace "tana tunanin kayi amfani da soyayyarta da yarintarta ne kuka yi wasu abubuwan saboda ta gane kayi haka da wasu kafin ita?" Ya gyada mata kai a hankali tace "i am sorry yayana i think i contributed wajen bataka a wajen munah amma banyi hakan da wani manufa i told her da kai din player ne amma yanzu son mace daya ya canza ka wanda yanzu na gane ita din ce macen da nake magana." Murza hannunsa tayi tace "wallahi yayana maimunatu na sonka kar ka karaya har yau banga namijin da yau ta nuna mishi soyayya mutum daya shine mai daraja da na sani a wajenta dict danfulani shima ta tabbatar min babu soyayyarsa a tare da ita soyayyanta na ga wani ammma bata gaya min waye ba yau dai ina ganin na samu amsata." Murmushi yayi mata yace "i hope so domin miemie itace farin cikina." 2

Kame baki mubeena tayi tare da fadin"wow! Ga yayana in love." Zungure mata kai yayi yace "na fara wasa dake ai, yanzu kin san matsayin mimi sai ki tayani yakin samunta already daddy ya nema min izini a gidansu and mahaifinta yace in nemi miemie kuma sam taki saurarata."1


Cikin tausayawa tace"yaya are you sure iyakacin laifinka kenan? Me ma ya raba ku and why didnt u guys get in touch?"

A hankali ya warware mata komi kuma ta fahimta tace "toh ga laifinka na farko dole sai ka warware wannan laifin sannan komi ya zo maka da sauki yanzu kallon mayaudari kawai take maka gani take dan kawai Allah ya kawota gareka ne amma baka yi yunkurin nemanta ba."2

Shiru yayi yana tunanin tabbas mubeena tayi gaskiya me yasa bai taba kawo wannan a matsayin matsalarsu ta farko ba? Tsam ya mike yace "thanks auta,kiyi bacci me dadi." Dariya tayi tace "Allah ya tashe mu." Yana amsa mata ya sai kai ya fice.1


Wani irin tsallan dadi mubeena tayi yayanta maimunatu yake so har yanzu ta kasa yarda,ita bata san irin zurfin cikin muna ba kai! Murna take yi har da rawa gaba daya ta manta da duk wani matsalarta.

Da sauri ta janyo wayarta ta kira sai dai ta taki rashin sa'a wayar a kashe.

Kwanciya tayi tare da kudurtawa zuciyarta gobe da sassafe ta gidansu zata bi ta dauketa suje office tare.2


Marwan time ya duba ya ga har goma ta wuce wannan dalilin kadai ya hana mishi zuwa gidansu maimunatu a wannan daren ya kira wayarta bila adadin amma a kashe da zai iya sammakon zuwa gidansu da gobe a nan zata tsince shi amma zai jira zuwanta a office dinta ai b'oye b'oye ya kare tunda ya fara bayyanawa yan uwansa yanzu mufl ce kawai bata sani ba.

2

Maimunatu kam a ranan suka wuce Zaria zuciyarta fal farin ciki bata taba tunanin zata tsinci kanta a cikin farin cikin da ta riski kanta ba dan zata ga dangin mahaifiyarta this is not her first toh ita ko ta je ma bata iya sakewa dasu amma ganin aunty khadija duk sai taji kaman taga mahaifiyarta duk da kasancewar aunty khadija ko kusa da haifanta bata yi ba dan duka duka bata fi 30 years ba.1


Murmushi tayi ta mayar da kanta ta kwantar jikin seat tana tuna wayarsu da uncle sufyan kafin ta sakko da kayanta kasa.


"Munari kin koreni karfi da yaji,kin daureni da jijiyoyina i never know u are this smart."2

Murmushi tayi dan ta san me yake wa hakan amma sai  tace "ni kuma yau me nayi uncle?"1


"Meye ma baki yi ba maimuna? Kin cewa mahaifinki na san da zuwan manema auranki shi yasa nace ya tambayeki,haba munari wannan ba cin fuska bane?"

Dan turo baki tayi tace "ah ah uncle sam ni ba zan taba iya ci maka fuska ba kawai na rasa madafan da zan dafa ne da daddyna ya tambayeni sakon da kace zan bashi,uncle sosai ka saka ni a tsaka mai wuya wannan hanyar ita kadai ce mafitana dan ba zan taba iya kallon idon mahaifina ince mishi amininka wai yana sona da aure ba. Uncle ka auna ka gani pls."2


Goron nunfashi ya sauke yace "toh ai shikenan maimunatu Alllah ya sa hakan shi yafi alkhairi yanzun kam ai dole in janye ina ni ina takara da cptn moh yaro matashi me ji da kuruciya sannan ga yan kobonsa a aljuhu wannan ai mijin manyan mata ne irin maimunatu."1


Murmushi tayi tace "hmm uncle kenan." Yace "ahan zata fara ba,na barki lafiya mrs moh." Daga haka ya kashe wayar itama tsaki ta ja da ta tuno da marwan da matsalarsa wannan ya sa ta kashe wayrta gaba daya ta wurga ta kan gado ta cigaba da shirin wanda yayi sandiyar manta wayar tata gaba daya.2


Tsaki tayi a fili aunty khadija tace "ya dai? Ko duk haushin manta wayr ne ko ana fargaban haduwa da dangi?" Dan murmushi tayi tace "wayar dai aunty." Murmushi tayi mata tace "karki damu gobe sai mu sa daddynki ko a motane ya turo mana dashi kar surukin mu ya kira bai ji ba hankula su tashi " dariya tayi tana boye fuska tace "ni Allah ba wani suruki kawia dai ban samu na gayawa boss dina bana za ayi expecting ganina a aiki gobe ." Duk da ta san ko bata yi tafiya ba bata da niyyan zuwa office ba ita da office sai ranan clearance dinta na karshe .1


Aunty khadija ta katseta ta hanyar cewa "uhn uhn ke dai abinda naji ance ma boss din naki gaba daya shine surukin namu."

Waro idanu tayi tana mamaki a hankali tace "daddy ya koyi surutu..."1Mubeena da tsananin farin ciki ta tashi ba zaka ce ita can take cikin tashin hankali ba jiya, Allah Allah take yi  ta ganta a gaban maimuna da izzarta ta kama hanyan gidan su maimuantun Kuma har lokacin Bata bar Kiran wayarta ba duk da har zuwa lokacin ba ya shiga.

3

Tana Isa bakin gate din motar daddy na sawo Kai sai ta gyara parking kawai ta fito Shima ganin haka sai daddyn ya fito, Dan rissinawa tayi ta gaisheshi hade da gabatar da kanta as kanwar Marwan Kuma abokiyar aikin maimunatun kara fadada murmushinshi daddy yayi yace"madallah, ya baban naku da shi Dan uwan naki?" Dan har cikin zuciyan shi daddy yake son maimunatu da mutanen Nan masu nagarta (saura kuce dan yaga suna da kudi ne😏) murmushi tayi Tana sadar da kai da Kai tace "kowa lafiyq, amm Daman na biyowa maimun ne muje wajen aiki. "3


" Ashha ai kuwa kinga anyi rashin sa'a yanzun nan da na fito dama zan bi Tasha ne in sa mata wayarta a mota Dan jiya da yamma tabi kanwar mahaifiyarta Zaria manta wayar da tayi ne ma ya sa bata sanar daku ba. " Dan murmushin yake mubeena tayi tace " wayyo! In ba damuwa daddy ka bani in sa mata wayar a mota tunda munfi kusa da tasha Kuma ba mamaki yayana kaga ya kama hanyan zarian yau ko gobe."2


Dan dariyar jin Dadi daddy yayi yace " toh shikenan. " Ya koma cikin motar ya fiddo mata da wayan.


Godiya tayi mishi sannan suka yi sallama sannan kowa ya kama hanyan wajen aikinsa.


Mubeena ji tayi ta fashe da kuka ga maimunatu tayi Nisa ga wayarta a hannunta  tsaki ta ja Dan haushi ta san sai yayanta yafi ta bakin cikin wannan tafiyan da maimunatu ta tsira dare daya ba tare da sanar mata kafin ta tafi ba.

1

Marwan bai Sami kansa ba ranan saboda da sassafe ya Sami Kiran ogansa daga abacha barracks suna wani aiki ne ya rike su har yamma mubeena Kam ta bar mishi missed calls ba adadi Dan wayarsa ma a silent ya sata.

1

Sai bayan magrib ya bar cikin barracks din maimunatu kawai yake muradin gani ko gida bai nufa ba balle ya cire uniform dinsa  ba ya wuce gidansu for the first time.1


Yana tunanin ko ya haduwarsu zata kasance oho


Yana tsaye cikin compound din hannun rigarsa a nannade tun alawlan magrib da yayi hannunsa daya cikin aljuhu dayan rike da wayarsa Yana kara Kiran layinta for the 100th time  Amma the same story hango daddy yayi yana shigowa da sauri ya karasa gareshi tare da dan rissinawa yana gaidashi shiru suka yi kafin cikin tsoro daddy yace "kanwarka bata gaya maka maimuna ta tafi Zaria ba?" Ya tambayeshi dan sai yanzu ya ga wautarsa na bayar da wayan maimunatun ga stranger.1


Girgiza kansa yayi yace"wai mubeena?" Da sauri daddy yace "eh ita." Ajiyan zuciya ya sauke yace"duk ya bamu hadu ba amma naga missed calls dinta."1

Sai lokacin hankalin daddyn ya kwanta inviting Marwan cikin gidan yayi yaci dinner yace ah ah zai wuce gida.


1

Mubeena na kwance Tana aikin nata na fama waya Marwan ya banko kofar yau ko knocking din ma bai yi ba a firgiceta mike hade da dafe kirjinta tace "Kai yayana ka tsoratani"  Dan dafe kansa yayi yace"sorry daga gidansu miemie nake." Kashe wayarta tayi tace"to ba Ina ta kiranka baka picking ba."  Ta mike hade da dakko wayarta a kan mirror dinta tace "ga Nan wayarta daddynta zai Kai park nace zan Kai." Da sauri ya Mika hannu yace" bani nan gobe zani zarian. " Murmushi tayi tace I thought as much. " Tare da mika masa wayar " yayana zani. " Girgiza Kai yayi yace" ba yau ba. " Ya fada tare da fita a dakin.3


Tun a hanyar shiga side dinsa ya kunna wayar ko gama booting bata yi ba kira ya shigo wayar murmushi yayi da yaga me kiran......

1

Cikin isa da izza ya ansa wayar yayi magana minti daya zuwa biyu yayi sannan ya kashe wayar cike da satisfaction wanka yayi yana jinsa cikin nishadi sannan ya janyo wayar yana dubawa.1


Ba karamin dauriya yayi ba wajen kin duba messages dinta gallary dinta kawai ya shiga yana kallon  hotunanta gwanin kyau babu komi a fuskarsa sai fadaddan murmushi1


Zaune ya tashi yana kara bude hakoransa da ganin abinda yake cikin wayar hotunta rungume da teddy din da ya cire makudan kudi ya siya mata on her 18th birthday hakan yana nufin har yau tana yinshi.

2

Bai kara shagala ba har sai da ya ci karo da hotunan su na cyprus tashi yayi yana juyi gaba daya murna ta cika shi kisses ya dinga mannawa wayar kamar wayar gaba daya ce maimunatu.1


Daren ranan dai marwan bacci farin ciki yayi da safe kuma da kyar ya bari goma tayi kafin ya je office din daddy dan samun address din inda take a zaria minti goma bai kara yi a garin abuja ba ya dauki hanyan zaria.1


Tafiyar awa biyu yayi saboda tsananin gudun da yake yi bai tsaya ko ina ba sai anguwar da daddy ya gaya masa.

Fitowa yayi daga motarsa  a wannan lokacin maimunatu ta fito ita da Badamasi second  cousin dinta zai kaita gidan su ta gai da mamansa ta sha kyau cikin riga da skirt na atampha ya tsaya sai kashe mata hotuna take wai tayi kyau ita kuma tana kyalkyala daria.1


Cak numfashin marwan ya tsaya kunnuwarsa har wani tiririn hayaki yake fitarwa dan masifa idanun nan har sun canza kala run rine ta juya tana yi wa badamasi magana ne idanunsu suka sark'e take maganan ta kwarar da ita ta fara tari ba kakkautawa.1

Hannu badamasi ya sa yana dan bubbuga mata baya bai ankara ba sai ji yayi an cabke hannunsa tare da murdewa...Ahhhh malam meye haka ka sakeni man, me nayi maka?  Badamasi ya fada cikin tsananin jin zafi amma bai yi kokarin kwatan kansa ba dan ya san motsi kadan zai yi yaji masa rauni.

Maimunatu ma cikin kidima da takaici ta kara matsawa kusa dasu tace "marwan meye haka? Sakar mishi hannu mana,me yayi maka ni ban son tsaban salon mugunta ka sakar mishi hannu."2


Hayaniyarsa ne ya saka mama da aunty khadija fitowa ganinsu ya sa marwan sake badamasi sunkuyar da aki aka bar badamsi da yarfe hannu yana aikawa da marawan wasu uba uban harara amma ba daman karasawa kusa dashi saboda yanda yayi masa kwarjini duk wannan hararar ma bai iya kallon idanunsa.

1

"Me ke faruwa haka nake jin hayaniyarku,bawan Allah lafiya?" Mama ta wurgawa marwan tambayan da ya sashi rasa nutsuwarsa mai da kallonsa kan maimunatu yayi tare ds dan marairaice mata harara ta banka masa ta kawar da kai yayin da badamaai ya ke kora musu bayani "kawai fa muna tsaye da maimuna ta fara tari shine nake buga mata baya ban ankare ba kawai naji wannan mutumin yana kokarin raba min hannu biyu ban ma san daga inda ya fito ba. Maimuna ko ke kin sanshi dan naji kaman kin kira sunanshi?"4


Duk suka zubo mata idanu,diri diri ta fara tana daga hannu bakinta na motsi amma ta ma rasa me zata ce,toh me ma zata ce din ta san shi ko me? Shine wanda yake sonta ko wanda suke son juna? Ita bata san irin marwan ba bakar zuciyarsa sometimes makes behave like a lunatic haba ayi mutum ba hakuri.4


Dan kankantar da idanu aunty khadija tayi tace "ko kaina marwan?" Da sauri ya daga kai tare da sauke wani irin ajiyar zuciya dan shi kam kunya duk ta rufe shi gaba daya al amarin yarinyan na sashi rasa hankalinsa da nutsuwarsa bai iya controlling kansa a duk wani abu da ya shafeta ta ko wani fanni.2

"Haba ko da naji wannan aikin masu kishi ne,kai kam badamasi barkanka da ba a raba ka da hannunka ba ina kai ina taba budurwar soja, malam marwan bismillah duk munyi tsaye a waje ai tun jiya yah Abdul yace min kana hanya.1


Zunguro baki maimunatu tayi tsaban takaici ta koma cikin gidan kafin kowa ma ya shiga ta shige dakin mama.1


Sum sum marwan yabi bayansu yana kan scolding kanshi for his behaviour sai da aka sadashi da palon alhaji sannan aka gaisa mama tace "kai kuma daga zuwa zaka balla min hannun megida tunda kai ka riga ka zabi wancan uwar kuncin ko?" Sunkuyar da kai yayi yana murmushi cike da kunya yace "ayi hakuri hajiya akasi aka samu inshaa allah hakan ba zai kuma faruwa ba,ale Badamasi dan Allah kayi hakuri." Murmushin yake Badamasi yayi yace "ba komi" amma a kasar zuciyarsa yana yiwa kanshi da sauran samarin dangin jajen rashin maimuna duk wannan hadewar tata da ilimin ashe a wani wajen ake neman auranta su basu da rabo akanta tun ranan da suka iso ya riga kowa zuwa wajenta duk da miskilancinta sai da ya san yanda ya cusa kanshi a wajenta har suka dan saba a cikin kwanki biyu rak amma ashe wani ya riga ya musu shigan sauri.6


Aunty khadija ne tace "kishi kan abinda kake so yana da kyau amma dai ayi me hankali shine dai dai."1


Gyada kai yayi yace "haka ne nagode sosai." A ranshi kuma yana fadin wannan dince kanwar mahaifiyarta kenan tunda mama dai da alama ita ce kakar yayi mamaki dan sai yaga gaba daya ba zata fice sa'ar mufliha ba shiru suka dan yi kafin wani yayi magana ladan ya kwada kiran sallan zuhr dole Badamasi da Marwan suka mike dan zuwa masjid.2


Mama kuma tayi tsakar gidan dan inda rana ne tafi jin dadin ta'amalinta a tsakar gidan yayin da aunty khadija ta shiga uwar dakan maman inda ta tarar da maimunatu ta fito daga bathroom din cikin dakin dauke da alaula bakin nan yayi gabas saboda yanda aka turo shi ga abu dan tsut sai ya kara tsukewa.1


STORY CONTINUES BELOW

"Zo nan." Aunty khadija ta kirata suka zauna a bakin gadon mama "kuncin me kike yi?" Girgiza kai tayi tace "babu komi." Dan hararar ta tayi tace "ban gane babu komi ba,tunda saurayinki yaxo kike wani hada rai bana jin ko gaisawar arziki kunyi kin shigo daki kina dacin rai,ko sonshi ne baki yi?" Ga mamakin aunty khadija maimunatu sai ta d'aga kai rike haba tayi tace "au Allah? Toh ni kuma naji labarin shi yake neman auranki yanzu kuma kince min ba kya sonshi." Kara tura baki tayi tace "nifa ba neman aurena yayi ba fa izini kawai ya nema ai kuka izini bashi bane aura."2


"Hmm haqqun,toh yanzu dqi tunda baki sonshi gwara an sanar da mahaifinki ya dakatar dashi dan naga saurayin naki dan zafin rai ne kar azo ayi abinda za ayi dana sani gwara ya rabu dake ya bawa wasu daman  nemanki dan tabbas in wannan yana rayuwarki babu wani da namijin da ya isa ya tunkareki baki yanda ya kusan karya badamsi ba bawan Allah."2


Maimunatu tace "atohhh kema kin gani ai shi zafin ransa yafi karfinsa in ya fara fushin kishinshi sam baya ji baya gani duk ya bi ya dagawa mutum hankali ya hana mutum sukuni da kyar fa yake sakkowa yau ma dan ya ganku ne aka samu sauki,tun da ma da baya aikin soja ya aka kare ballantana yanzu."1


Baki da hanci aunty khadija ta bude tana kallon maimunatu me cewa bata son marwan amma tana ba da sharhi akan kishinsa da yake daga mata hankali wanda a bayaninta ya na nuna ya nuna tashin hankalin da take shiga in yana fushin kishin.1


"Baby miko min wayata in kira yah abdul kawai gaskiya a dakatar dashi."

Maimunatu dake halfway na bata wayar ta janye ganin wankin hula zai kai ta dare tace "ah ah aunty ki barni dashi kawai."1


"Ah ah bani kawai baby tunda baki sonshi ban ga amfanin batawa juna lokaci ba kuma ai ta inda aka hau ta nan ake sauka kafin ya nufeki sai da ya nemi yah abdul ko ba haka ba."1


"Aunty ki bari dan Allah nace miki ni na san me zan mishi ba sai an kira daddy ba."1


"Yau naga ikon Allah ba ke kika ce baki sonshi ba?"1


Turo baki tayi ta kawar da kai gefe tace "ni fa da bakina ban ce bana sonshi ba."2


"La'ila ha'illallahu! Maimunatu yanzu ba dazu ba na tambayeki kina sonshi kika ce ah ah amma yanzu zaki mayar dani makaryaciya to in kina sonshi tun zuwansa kuncin me kike yi?"1


"Toh ai ni aunty eh kawai nace miki kuma bashi bane ya tashi yazo ina shirin fita shikenan yanzu ya rushe min fitata." Ta fada taba kawar da kai tana neman hijab leka fuskanta aunty khadija tayi tace "eh ai kya kawar da kai tunda kin mayar dani mama kakarki ba,zaki ji da guntun gulmanki munafuka ki tsaya kumbiya kumbiya yanda mata yanzu suke jin kaman su fara kidnapping maza suna adanawa a gaban idonki wata zata yi wuff dashi kuma baki da abinda zaki iya yi yarinya.3


Kunkuni ta fara tare da kokarin tayar da kabbara aunty khadija tace "hattara dai yarinya gaban Allah zaki je tafi da nutsuwarki ki nemi zabin Allah ko zaki dace." Daga haka ta shiga bathroom itama.1


Lokacin da suka idar da sallah har su marwan sun dawo aunty khadija ta saka maimuna a gaba ta hada mishi abinci dan dama sai da maimunan ta gama girka musu lunch tayi shirin fita.1


Sallama tayi bakin kofan har lokacin tana sanye da hijabinta da tayi sallah baka ganin komi sai dan fuskanta a cikin hijab din yayi mata kyau sosai.1


Waya yake amsawa amma ya shagala da kallonta har ta ajiye tray din abincin da take dauke dashi ta juya taje ta dauko na ruwa da drinks da cups suma ta dire su sannan taje gefe ta coge bakin nan a dane kaman karin kunama.1


Rasa abinda zai ce mata yayi wannan tokan da tasha a hankali yace "miemie hijab din nan yayi miki kyau zan sa miki su sosai a lefe." Hararansa tayi tace "wa zai aureka? Ni ba zan aureka ba,bar ganin ka bi ta wajen iyaye babu me min auran dole so ka bar mafarkin aurena dan ni ba zan auri me bugun mutane ba wata rana ka kamani kayi min duka."4


Waro manyan idanunsa yayi yace "miemie kuma? Yau kuma da hujjan dukane ba zaki aureni ba haba maimunatu komin girman laifina a wajenki yaci ki yafe min haka na tuba,daga yau ki lika min wannan laifin sai gobe ki lika min wancan its not fair maimunatu wa kika taba ganin na doka?"1

"Oh really? Not fair ko? Har ma kana tambayata wanda ka taba duka a gabana nan shekaran jiya ka yiwa mubeena dan banzan duka a gabana still yau ka biyoni har garin mu zaka balla min dan uwa ta yaya zan tabbatar da cikakken hankalinka ta yaya zan tabbatar da safety na a gidanka?"3


Shiru yayi ya zuba mata idanunsa da suka chanza kala ji yake yi kawai ya gwada tursasa zuciyansa ya rabu da yarinyan ko zai huta da rashin mutuncinta a hankali yace "maimunatu for the last time zan tambayeki fada min me kike so inyi in tabbatar miki da son da nake miki in tabbatar miki da cewan ni muhd marwan in ina da hali ko kuda ba zai sauka a jikinki balle wani abin cutarwa ko ni da karan kaina in cutar dake,ni kuma insha Allahu zanyi shi in har hakan zai sa ki yafe min ki sake bani dama a rayuwarki in kuma nayi baki ga zaki iya rayuwa dani ba na rantse da sarkin mulki wanda numfashi na ke hannunsa zan tafi zan bar rayuwarki without a second glance ba dan bana son ki ba sai dan in miki abinda kike so."3


Wani irin yawu maimunatu ta fara hadiyewa akai akai bata tsammaci hakan a wajensa ba gashi yayi mata kuri da idanu duk sai ta rasa nutsuwarta dan gani tayi idanun nasa sun kara dakwala dakwala dan girma in idanunta basu yi mata gizo ba kaman hawaye ta hango kwance cikin idonsa.3


A hankali kaman me koyon magana tace "me ya faru bayan tafiyarka da ya hana ka waiwayeni?"Still yayi idanunsa na kanta a hankali ta gyada mishi kai tace "yes ina son sanin dalilin da ya saka ka wofintar dani,ba tare da ka waiwayeni ba in banda yanzu da Allah ya sa ka gan ni a bagas har cikin companyn ka. Ban san kowa naka ba ban san wa zan tambaya kai ba wayarka bata zuwa me kake tsammanin zan yi zato marwan tunda kai ka san inda nake kai kana da number din sa zaka sameni. Shi wannan bai isa kadai ya sani in kasa yarda da kai ba a karo na biyu? Bayan wannan ga mummunan halinka da nazo naji labari a wautana nayi zaton da ni kadai kake wannan abin saboda ni din kana sona yasa kake sha'awana sai naji ashe marwan dai is a big player i thought i know you ashe ban sanka ba you are a total stranger.1


Numfashi ya ja ya fesar sannan yace "i never left you intentionally." Gyada kai tayi bakinta a tabe tace "shi yasa nake son jin uzurinka." Mai da jikinsa yayi cikin kujeran da yake zaune tare da lumshe idanu kaman wani basarake sannan ya fara magana

2

Marwan muhammad sunana ni ne d'a na farko a wajen mahaifina duk da kasancewar ba mahaifiyata bace matar mahaifina na fari ba mahaifina cikakken dan Borno ne a nan barnon kuma ya auri matarsa ta fari Nafisa. Alhaji muhammad da Hajiya Nafisa sun yi aure tun na saurayi da budurwa amma Allah bai basu haihuwa ba har Allah yasa alhaji muhd ya sami aiki a Abuja suka dawo birnin tarayya da zama.7


Sai da suka yi shekara biyar Allah bai basu haihuwa ba sunje manya manya hospital amma an tabbatar musu da lafiyar su kalau lokacine bai yi ba.

Amma a can Borno sun damu da rashin haihuwar nafisa har ake mishi tayin ya dawo gida ya kara aure yaki duk sai yan uwansa suka tsangwami Nafisa akan ita bata haihuwa sannan ta hana shi ya kara aure.2


Tasha taje ta sameshi tana kuka ta rokeshi ya kara aure ko zata huta da maganganun da danginsa suke yi amma fafur yaki.1


Kwatsam wata rana ya fito daga gidansa zashi sallan magrib yaga wata budurwa ta shiga makotansa da alama daga jami'a take kallo daya yayi mata ya san ta riga da ta kama zuciyarsa ana idar da sallah ya dawo gida sabanin da, da sai ya yi isha yake dawowa da mamaki Nafisa ta tareshi ko lafiya bai boye mata ba ya gaya mata bayan fitarsa yaga wata yarinya ta shiga gidan makotansu yaji yana sonta.1


Duk da maganar ta daki Nafisa amma sai ta daure kasancewar mu'amularsu abin sha'awa ce itace kawarsa itace abokiyar shawararsa itace aminiyarsa.

Sai tayi yake tare da cewan "toh amma kai ka mata magana?" Girgiza kai yayi yace" ah ah shiganta fa kawai na gani babu daman da zan yi mata magana ni yanzu tsorona daya kar ba yar gidan bace in zo in kasa samota."1


Dan jim tayi tana kallonsa yanda duk ya rikkce kan maganar yarinyan da bai ko san sunanta ba ta sani mijinta na sonta amma hango soyayyar yarinya a idanunsa ba karamin kidimata yayi ba.1


Ganin kallon da take mishi yasa ya sha jinin jikinsa tare da fara kame kame murmushi tayi tace "ka kwantar da hankalinka na tabbata yarinyan a gidan take dan na tuna mamann sadiq tace min kanwar baban sadiq din zata fara karatu a nan garin ko ba gidan bane?" Da sauri ya gyada kai yace "eh nan ne."

"Toh shikenan da safe zanje in confirming " gyada kai yayi amma a zuciyansa yana ji kaman yace mata taje yanzu amma ya san in yayi haka bai kyauta ba.2


Daren ranan da kyar duk su biyun suka rintsa duk da ko wannensu na kokarin yayi yanda dayansu ba zai gane idon dayan biyu ba.1


Washegari bayan ta rakashi zai tafi aiki ya juyo yace "dear kar ki manta da shiga wajen maman sadiq din." Murmushi tayi tace "oh dear!" Sai kuma kunya ta kamashi yaja motarsa ya fita, kwalla ta dauke a idanunta kafin ta shiga ta kimtsa kafin ta shiga gidan maman sadiq.1


STORY CONTINUES BELOW

A zaune ta sameta tana bawa sadiq dan wata hudu nono suka gaisa ta ansheshi tana mishi wasa maman sadiq tace "oh aunty Nafisa sai yau kaman bama anguwa daya." Hararar wasa tayi mata tace "ai ke naga shigowa kike ko sadiq ba kya kawo min." Dariya tayi tace "afuwan ai dan na samu me tayi ne." bata dade da zama ba wata yar budurwa ta fito cikin shirin fita a ladapce ta gaisheta sannan tayiwa auntynta sallama ta fita cikin sakin fuska Nafisa tace "maman sadiq kinyi bakuwa ce."

"Eh kanwar abban sadiq da na gaya miki zata zo karatu ce ta zo daga ukraine kin san iyayenta sun dage a Nigeria zata yi karatu."1

Fadada murmushinta tayi tace "ayya gata da alamun ba zata yi fitina ba na ganta me kunya da ita kaman ba girman turai ba." Dariya maman sadiq tayi tace "ai zainab kenan haka take to ko ni da nake gidan nan sai nayi da gaske in ganta sai dai ta dauki sadiq su kule daki."2


"Allah sarki amma ya kuke da ita?"  Nafisa ta tambaya

Maman sadiq tace "da babanta da kakar sadiq uwa daya uba daya suke cousins ne su ita kadai ce diyar mahaifanta sun dau son duniya sun daura mata ba a nan aka haifeta ba amma iyayenta suna mata sha'awar zaman nan saboda halayyanta da kawaicinta da daura zata zauna baban sadiq yace za a shiga hakkinta ta zo nan sai ta shiga makaranta."


Da wannan information din Nafisa ta koma gida tana Allah Allah mijinta ya dawo ta sanar dashi ko da yaji wacece ita sai jikinsa yayi sanyi ita tayi ta karfafa mishi guiwa kan ya samu baban sadiq da maganan.1


Haka ko aka yi baban sadiq yayi murna dan dama iyayenta sun fi so ta auri dan kasansu inda za a samu matsalar yana da mata amma in sha Allah ba zai zama da damuwa ba ya cusa kansa wajen yarinyan dan iyayenta na son farin cikinta.1


Muhammad ya samu soyayyar zainab dari bisa dari ranan da maman sadiq taji labarin bori tayi wa da kanwar akan su mayar da ita maciya amana sai da nafisa ta nuna mata babu komi da yardanta mijinta ya faea neman zainab sannan ta hakura.2


Zainab kam ba karamin kunyan nafisa take ji ba bata yarda su hadu sam ko kofar gidan zata wuce da sauri take wucewa dan ma kar wata rana su hadu haka in ta shigo gidan maman sadiq juyin duniyan nan za ayi da ita ta fita amma fafur taki har ma ta rufe kofa sai dai Nafisa tace mata "ki gama boyonki ni da zamu zauna tare."1


Ba a dau wani lokaci ba aka yi auransu inda ta tare cikin gidan a sashin muhammad din inda iyayrnta suka yi bajinta wajen zuba mata dukiya a ranan ne kuma aka damka maga takardun filin company dinta da za a gina nan ba da jimawa ba.1


Zaman lafiya da lumana ake yi a cikin gidan muhammad sam nafisa ba mai fitina bace balle zainab da magana ma ba yinta take yi sosai ba kasancewar hausan nata ma ba wani fita yake yi ba.1


Ko wata biyu bata yi ba ta fara laulayin ciki nan da nan labari ya bazu a ko ina a dangi cewar amaryar muhammad ta samu ciki daman nafisa ce bata haihuwa takanas ake zuwa daga borno a dubata dan duk sun tare wajenta dama gata yar masu maiko ba irin zugin da ba a mata akan nafisa amma nata ido dan ta san nafisa me sonta ce tsakani da Allah.2


Watanta tara cif da aure ta tashi da nakuda me zafi ba wani bata lokaci aka kaita hospital ba karamin azaba yake sha ba ta kwashe awa takwas tama abu daya muhammad da nafisa hankalinsu ya tashi.1


Nurse ce ta fito ta shaida musu tana son ganin nafisa da sauri nafisan ta shiga ta tsorata kwarai da halin da ta sameta murmushin karfin hali tayi tace "aunty ina tayi miki addu'a Allah ya baki ciki kema tunda na fara nakuda." Murmushi Nafisa tayi tana goge hawayenta tace "anya anya zainab zan iya wannan wahalar?" Gyada mata kai tayi tana murmushi tace "zaki iya mana aunty nima gani karama ina tayi amma fa da wuya." Ta fada hawaye na zubo mata dan hutawa tayi tace "yanzu ba ciwon sosai shine uncle muhammad bai shigo ba (dan dama haka take ce masa yanda yaran anguwa ke ce masa.) Da sauri ya shigo dan dama yana jingine jikin kofa kama dayan hannunta yayi yace "zaina ba gani i am so sorry." Murmushi tayi ta zare hannunta ta dora akan fuskanshi tace "sorry for what? Ka bani farin ciki da ka bani babyn nan i just hope and pray babyna yayi kama da kai ya dauko kyakyawan idanunkan nan. " ta shafa manyan idanunsa tace"da dark skin dinka me kyau mmm." Ta lumshe idanu tana hura hancinta da alama zafin ciwon ya dawo mata saboda yanda zufa ya rufeta lokaci daya bude idanun tayi tace "aunty ke kadai na yarda ki rike min babyna this is my last wish ki bawa babyna tarbiya nagartacciya da ke kadai na yarda dan na san ke din mutum ce me kyakyawan zuciya ko ina da rai ko bana sa rai kene mai yiwa babyna tarbiya balle ma i know i cant make it."  Duk su biyun kuka suke amma ita ba ko hawaye sai wani irin nishi da ta fara me gurnani da sauri doctor ta daeo kanta tare da nurses ana ta push ta push din kam amma iskan farko da danta ya shaka na duniya shine nata na karshe ta haifo danta namiji wanda ke tsananin kama da mahaifinsa ko da yake jariri dakwal dakwal din idanunsa sun nuna amma zainab bata da rabon ganin wannan tsananin kaman da uba da da suka yi.2


Rasuwar zainab ta jijjiga mutane da yawa babu kaman iyayenta,muhammad da nafisa dan tunda ta rungume jaririn bata sake ba ita take mishi komi ita ta nemo yanda zata samu ruwan nononta fara bawa babyn babu wanda ya sani ana tsaka da zaman makokine yayar muhammad ta shiga daki ta ganta tana shayar dashi nan da nan kuwa ta tara mata jama'a abinda yayi silar janyo hankalin yan waje har muhammad ya shigo inda ya tarar an sa nafisa agaba ana mata tijara baby na hannun kakarsa yayin da maman sadiq da nafisan suna rungume suna kuka tambaya yayi ko me yake faruwa  tsalab yagana tace "wannan juyar matar taka mana da kinibibi ta dauki diyar margayiya tana shayrwa tsabar makirci salon yaje umya tsotso mugun abu."2


Sosai ransa ya baci ya sa hannu ya karbi dan sa a hannun kakarsa ya ma manta wai surukarsa ce ya dankawa Nafisa yace "ku shaida ni muhammd in nine mahaifin wannan jaririn wanda yayi sanadin zuwansa duniya na dankawa matata Nafisa shi a matsayin danta ko bayan raina ban yarda wani ya karbesa ba wannan shine burin mahaifiyar yaron kuma burina bana so ko da wasa a kara tayar da maganan nan ko nan gaba yaro abin ikona ne kuma na zabi Nafisa ta zama uwa ga d'ana duk wanda hakan bai masa ba hana iya fita ya bar min gidana ke kuma Nafisa ga yaro nan naki ne amana uwarsa ta baki nima yau na kara miki ga amanarsa nan ki tarbiyantar da shi kaman yanda uwarsa take so."1


Shiru marwan yayi ya rintse idanunsa hawaye suka zubo tunowa da maganar mami kullum in ya aikata ba dai dai ba "Marwan naci amana kana sani ina ji kaman naci amanan zainab amma Allah ya sani ba tarbiyar da na baka ba kenan." Wasu lokutan tana fadan hakan tana hawaye kaman yanda shima yau din yake hawayen da na sani.

Post a Comment for "KINA RAINA CHAPTER 9"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...