Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KINA RAINA CHAPTER 6

KINA RAINA CHAPTER 6

- - Post a Comment

 KINA RAINA CHAPTER 6


Wani yawu me daci ta hadiye tare da jan hanci sai ta kakalo murmushi ta dafa hannun mubeena dake kan nata tace "its ok,abu ne da ya riga ya wuce bana son tunowa." Gyada mata kai mubeena tayi tare da squeezing hannunta ba ta pressing ba duk da yanda ta so taji wanene wannan da yayi wa maimunatu illa,sosai take sha'awan rayuwar maimunatu bata da hayaniya da ace yau yayanta is single babu abinda zai hana bata yi ruwa tayi tsaki ba ya so maimunatu toh ina shi din idanunsa ya rufe akan soyayyar babe dinshi and there is nothing anyone can do yanda ya likewa yarinyan nan.2


Gyaran murya maimunatu tayi ganin mubeena tayi nisa cikin tunani a hankali ta dawo da dubanta kan maimunatu itama ta kakalo murmushi tana shirin yin magana wayarta dake kan table ta fara ringing da sauri taje ta picking ba kowa bace adda muflee ce "sorry yanzu zata kawo miki." Ta dan yi jim kafin ta ansa da "toh shikenan,right away." Daga haka ta katse kiran file din da maimunatu ta shigo dashi ta fara dubawa tana signing maimunatu na zaune tana kallonta har ta gama sannan ta taso ba tare da ta jira mubeenan ta kirata ba

Mika mata file din tayi fuskanta dauke da murmushi tace "pls ki kaiwa adda muflee tana jiranki yanzu,we will continue our discussion whenever you are ready." Murmushi ta saki tare da gyada kanta amma ta sani ba zata taba cigaba da wannan discussion din da kowa ba an gama shi  kenan har illa mashaaAllah.1


Office din madam mufleeha tayi da ikram karaman baby dinta ta fara cin karo yarinyan na ganinta ta taso da gudu ta rike kafafunta anwar ma dake zaune kasan carpet din office din ya taso da gudu yana mika mata hannu.6


Murmushi tayi ta tsuguna duk ta rikesu a jikinta tace "ina zuwa bari in ba momy aika in zo ko?" Da haka ta karasa cikin makeken office din zuwa table din mufleeha yaran na binta a baya kaman jela.


Murmushi ta sakar mata lokacin da take gaisheta ta sa hannu ta ansa file din tana tsokananta maman yara dan dama haka take matsawar suka hadu da yaran zasu like mata sai sun bita har office dinta.1


Yau ma haka suna shirin binta wani matashin saurayi ya bude kofar office din saura kadan ci karo maimunatu taja baya kallo yake kare mata ita kuma ta mayar da kanta gefe dan ta tsani kallo.


Ihun yaran ne suna mishi oyoyo uncle ya dawo dashi daga kallonta da yake yi mamansu ta dafe kai tace "yauwa gwara da kazo ka debi yaranku ku bar min office yara sun mayar min da office kaman nursery da sauri maimunatu ta fita ba tare da ta tsaya taji amsan da zai bata ba.1


"Hamma Khalid me yasa kake hora ni haka,nace maka ban san cewan zata baza hotunan ba me yasa ba zaka fahimce ni ba?"1


Rintse idanu yayi yana massaging goshinsa da hannu daya yayin da dayan hannun yake rike da wayarsa yace "biba ba horaki nake yi ba sam,kawai ina nuna miki mahimmancin jin maganana ne,nifa mijin da zan aureki ne in baki fara kwatanta jin maganana tun yanzu ba when zaki fara?"1


Kara gyada kwamciyarta tayi hade da turo baki kaman tana gabanshi tace "ni ban ki jin magananka ba,ni wallahi yanda kake complain kan fitan hotunan sai ya dinga ban mamaki kaman wanda suka aikata wani mugun abu,hamma ko dai baka so a ganno da kai ne ko ban kai in zama matar shahararren dan binciken da kasa tasan da shi bane,ko kuma akwai wacce kake boyewa ni?" Ta karasa maganan tare da kankantar da ido kaman tana gabanshi.1


Da sauri ya girgiza kai yace "ko kadan, kina magana kaman bani na ganki nace ina so ba,why wouli i be ashame of showing you to the world?"

Limshe idanu tayi a hankali tace "i thought as much,hamma yaushe zamu je yola ne time na ta karatowa ammi tace in tambayeka."1


Numfashi ya sauke yace "me yasa wai ba za a bar maganan zuwa yolan nan ba sai bayan biki wani zuwa gaisuwa da bankwana sai kace wanda zasu auri bare." Tabe baki tayi tace "al'ada ce dole muyi hamma."1


Murmushi yayi yace"biba yaushe zaki daina ce min hamma ne?" Rufe ido tayi kaman tana gabanshi a hankali tace "soon,hamma ai lokaci ne kuma ya kusa." Dariya yayi yace "Allah ya kaimu lokaci zamu ga karshen cika baki. "

Dariya kawai tayi suka yi sallama fuskansa dauke da murmushi habiba akwai kunya bai san ita da maimunatu wa yafi wani kunya ba he will be one of the lukiest person in thw world in ya samesu su biyu dan duk basu da problem,banbancinsu kadan ne habiba na da surutu whole maimunatu ke da zurfin ciki.1

Dailing number din maimunatu yayi ya sa wayar a kunnan sa,yanda kiran ke dokawa haka zuciyarsa ke dokawa yana adduar Allah yasa ta picking sai da wayan ta kusan tsinkewa ta picking.1


Tana iya jiyo saukar ajiyan zuciyarsa "munah." Ya furta can kasan makoshinsa sosai muryar da yayi amfani da ita ta tsirga cikin jikinta,jin bata amsa ba ya sashi mainata kiran sunanta.1


Gyaran murya tayi kafin ta amsa sannan ta zarce da gaisheshi. Wani dadi ne ya ziyarci zuciyarsa jin muryarta normal sabanin kwanakin baya da tsinci labarin auransa.1


"Munah ya kike?"

A gajarce ta amsa da"lafiya lau."

"Ya soyayyata kuma?"

Ya kara jefo mata wata gaisuwar

Dan murmushi tayi tana nanata kalman soyayyah

"Yes soyayyah ta munah,pls maimunatu kar ki rejecting dina."

Shiru tayi tana sauraronsa.

Bai damu ba ya dinga nuna mata yanda yake sonta sannan abinda yake shirin yi ba haramun bane.1


A hankali tace "khalid!ka sanarwa da amaryarka kana neman wata bayan ita?" Shiru yayi murmushi tayi tace "look here,i dont want to be the side chick,khalid in iyayenka da matar da zaka aura sun san da maganata,sun san cewan kana son aurena bayan habiba kuma suka amince khalid sai ka dawo muyi magana amma in ba haka ba,naki in yarda da zama side chick an dade ana yi amma sam ba zai faru a kaina,in kaje ka nemi yardan iyayenka da matarka sai ka dawo muyi magana wala Allah in yarda.....Yana shirin magana ta dakatar dashi ta hanya katse kiran,fadawa tayi kan gadonta tana mai da numfashi a hankali ta tashi zaune tana kiciniyar cire hijab dinta dan dama ta idar da sallah ne.1


Har ga Allah tayi fatan ace babu maganan auran wata a tattare da khalid da tafi kowa farin ciki,khalid shine mijin da zata aura kawai ta samu kwanciyar hankali ba tare da tuno da wani marwan. Tun ba yau ba ta san khalid yana da hikima da tsari na lallaba diya mace ya iya tarairaya,iya bi da macensa ya sa ta fara sonshi kafin tafiyarta cyprus kafin marwan ya shigo rayuwarta.5


Marwan ba kowa bane face fasiki dan da ta biyewa marwan kilan da tare da dansa ko diyarsa yanzu, gaba daya in ta duba kudu,gabas,da arewa sai ta ga sam marwan bai dace da rayuwarta ba,marwan ba mutumin kirki bane duk namijin da zai so ya kebe da macen da ba muharramarsa ba lallai dan iska ne. Ita ko me ya rufe mata ido har ta fada soyayyarsa? Ko da yake kadan daga aikin samarin shaho sun san duk ta yanda zasu bi su cusawa mace soyayyansu daga baya su zame su barta da ciwo a zuciya.2


In ta zauna tana tariyo rayuwarsu sai ta ga ba komi bane face iko da gadara marwan ya nuna mata a zamantakewarsu,ya koya mata karban yancinta a wajen wasu amma sam bai koya mata karban yancinta awajensa baya mayar da ita kaman baiwarsa yana ordering dinta around,she cant believe she even let him chose her clothes.2


Tafukan hannunta ta saka ta rufe fuskanta dashi wannan abin kunyar har ina? Saurayi ba miji ba ita kuwa wata irin sakara ce? God! She was so neive amma dai wallahi marwan ya rainata chai! Allah ya hadashi da mace dai dai dashi.1


Murmushi tayi tana picturing marwan da mace iron lady a fili tace "tab ashe ko za a kona gidan,wannan iyayen son girman." How she wish yanzu zai zo yaga yanda rayuwarta ya canza lallai zai sha mamaki she is not more that nieve miemie.1


Wow! Miemie! It has been so long that someone called her with that name sam bata yarda da taga wani ya dau hanyan kiranta miemie zata dakatar dashi1


Akwai wani lokaci da ta shiga sahad tana wajen kayan shafe shafe wata cute yarinya da bata fi 2 years ba tazo tana ja mata riga tsugunawa tayi tana kallon fuskar cute yarinyan fuskanta dauke da murmushi ta ja kumatun yarinyan tare da tambayanta ya akayi

Hannu yarinyan ta bude mata alamun ta dauke ta tana shirin yin magana taji wani murya mai kaman na marwan yana kwala kiran miemie bata sani ba ko yanayin yanda marwan ke kwala kiranta ne mutumin yayi amfani dashi ya sa taji muryar yayi mata kaman na marwan ko muryan marwan din ne dan juye juye ta fara tana neman ta inda muryan yake fitowa.1


Da gudu taga wannan yarinyan ta nufi inda muryan yake maimunatu bata lura ba tana kokarin ganin mamallakin yarinyan nan ta bugewa wata hajiya basket dinta da sauri ta bata hakuri tare da kwashe mata ko da ta gama babu su babu alamunsu haka taje ta biya kudin kayanta ta fita a cikin mota wajen zaman passenger ta hango yarinyan hannun wata farar mata suna zaune amma babu kowa a mazaunin driver.1


Kwarai maimunatu ta so ta tsaya taga mahaifin yarinya sai taga rashin amfanin yin hakan.


Numfashi ta sauke tuno inccident din kila ma marwan ne,kila yayi aure har ya haihu dariya tayi tana tunanin ta yaya ma marwan zai sawa diyarsa sunanta ai wanda yake da muhimmanci a rayuwarka shi kake yiwa takwara ta ayyana a ranta.1


Karan da wayarta yayi ne ya firgitar da ita da sauri ta janyo wayar tana mamakin dalilin da zai sa mufliha ta kirata da daren nan dama dai mubeena ce wannan sarkin surutun.


Cikin nutsuwa ta amsa kiran da dariya mufliha take magana tace "yi hakuri maimuna na kiraki da dare." Murmushi maimunatu tayi tace "no ba komi ya su ikram?"

"Lafiyansu kalau,yauwa maimunatu zaki iya tuna uncle dinsu ikram da kika gani ranan a office dina?"

Dan jim maimuna tayi tana so ta tuno ranan "wanda ya zo kina shirin fita ranan da su ikram suka yi mid term break?"


STORY CONTINUES BELOW

A hankali memorynta ya tuno da ranan da sauri tace "yeah yeah na tuno shi amma gaskiya ba zan gane shi ba." Dariya tayi tana ji muflihan tace "toh kai kaji" duk sai kunya ya rufe maimuna dan tana da tabbacin wanda ake magana akai yana kusa kuma yana jin abinda tace.1


Cikin ina ina tace "kin san uhm zan fita ya shigo toh kuma ban kalli fuskanshi ba." Dariya mufliha ta kuma yi abinda da bata cika yi ba kenan tace "karki damu ai na san ba zaki kalle shi ba,toh dai ni tun ranan ya sani a gaba wai sai na bashi number dinki ku dinga gaisawa ina ta mishi wala wala toh shine fa yau ya zo ya ritsani wai sai na bashi number din shine nace bari in kiraki in tambayeki tukunna."


Shiru duk su biyun suka yi,mufliha tana sauraron taji amsan maimunatu ya yin da ita kuma take kokarin tuno fuskan saurayin ta kasa and ita ba wani shirib welcoming issue din wani saurayi take yi ba she already have enough on her plate...1


"Kanina ne maimuna,uncle dinsu ikram ina mai tabbatar miki ba zaki samu matsala dashi ba he is an easy going person."mufliha ta katse mata tunani ganin shirun nata yayi yawa.


A hankali maimunatu cikin rausayar da kai tace "toh shikenan maman ikram tunda kin ga ba damuwa ki bashi number din nagode."

Cikin murna mufliha tace "ah ah wallahi nice da godia for doing me such favour kina da kirki da hankali maimuna and i want the best for you." Murmushi maimuna tayi cike da kunya tace na gode daga haka suka yi sallama.

Tana ajiye wayan wani kiran ya shigo unknown number ne har ba zata picking ba sai ta picking.


Ajiyar zuciya ya sauke daga daya bangaren yace "i thought ba zaki dauka ba."

Dan yamutsa fuska tayi tace "wake magana pls?"


"Oops sorry! Taheer ne,taheer ke magana." Kara yamutsa fuska tayi dan still bata gane ba tana shirin cewa wani Tahir? Yayi carab yace "pls forgive my manners,sunana Tahir kanin aunty mufliha uncle din su ikram."

"Oh! Barka da dare." Ta fada a sanyaye.

Murmushi yayi me sauti yace "barkanki dai gimbiya,ya kike ya shirin shiga weekend?" Dan tabe baki tayi tace lafiya alhamdulillah.1


Daga nan kuma suka yi shiru dan sam Tahir bai ga fuskan da zai cigaba da yi mata surutu ba.


A hankali yace "i hope ba zan zama takura ba a gareki?" Sai a lokacin ta dan saki murmushi tace "no haba kar ka damu." Ajiyan zuciya ya sauke yace "toh nagode i promise you wont regret knowing me." Mai da kanta kan pillow tayi tana murmushi tace "toh Allah yasa ameen."

"Toh maimunatu tell me about you,who is maimunatu and how many hearts did maimunatu break?"

Dariya tayi wanda ya ji shi har cikin kwanyan shi tace "ni maimunatu! I have never broken anybody's heart." A zuciyarta kuma tace sai dai ni da aka breaking min nawa ya kasa warkewa.1


"Toh ni dai ki ban labarinki." Ya fada a shagwabe murmushi tayi da alama wannan mutumin dan daru ne tana shirin magana call ya shigo wayanta dan cire wayan tayi daga kunnanta ta duba caller id din.

"Hello kina jina?" Ya tambayeta jin tayi shiru da sauri tace "eh ina jinka,dan Allah bara in dau wayan boss dina." Dan jim yayi yace "that will be mubeena ko?" Zuwa lokacin wayar ta katse tace "eh ita ce." A hankali yace "pls do me a favour kar ki fada mata about me yet sai komi ya kankama." Tattara giranta tayi tace "why will i tell her about you? She is my boss fa,hold on gata ta kara kira." Bata jira amsansa ba ta picking call din dan bata so wayar ta kuma yankewa.

Wayyo sorry maimunatu na kira ki late na katse miki tadi." Rolling idanunta maimunatu tayi mutanen nan da iya cewa sorry tace "ba komi,i hope dai lafiya?" Gyada kai mubeena tayi tace "lafiya ba lafiya ba,yayana zai sauka a Nigerai 2am na yau,saboda akwai board meeting da za ayi sannan ya gama abinda yaje yi rannan monday din nan za ayi board meeting din karfe 10am." Ta karasa maganan tana nishi kaman wacce ta yi tsere gira daya maimunatu ta d'aga tace "okey?"

"We have new investors and i need you to be there." Da sauri ta tashi zaune tace "ban gane ba,mubeena kin manta ni serving nake yi why should i attend the meeting?"

Numfashi ta ja ta saki kafun tace "saboda ina so ki zauna a kujerana in nayi aure so i want you to impress my brother bana so in bashi labarinki ya ga kaman ina tura ki ne i want him to see what you are capable of shi da kanshi ba sai an gaya mishi."3


Zaro idanu tayi tace "toh ni me zanyi a board meeting? Mubeena zaki saka ni a tsaka me wuya."

Juya idanu mubeena tayi tace "keh! I am the boss here and u will do as i say babu abinda zaki yi a wajen meeting din banda abinda kika saba yi a ko wani meeting."

Ajiyar numfashi ta sauke tace "toh i will do just as u say."

"Good ranan monday zaki yi elegant shiga be in your best and come early zamu tattauna akan abinda zamu yi."1


Tace "toh inshaaAllah,nagode Mubeena nagode da soyayyar a gareni."

"Tsk ke kika sani,ni sai da safe joor." Daga haka ta kashe kiran

Dariya maimunatu tayi tana girgiza kai sosai take mamakin son da mubeena take mata tana so ta sake da ita su zama kawaye sam ta kasa ba a jininta bane yin kawa ko jalila kullum cikin yi mata complain na rashin kirki take tana son jalila tana respecting dinta na tsaya mata da tayi a rayuwa.1


Sms ne suka shigo wayarta daga wajen suitors din nata uku,ko wannensu na mata fatan tayi bacci lafiya murmushi tayi a fili tace maimunatu mai mutane.1

Monday da sassafe maimunatu ta fita bayan ta jera adduoin samun nasara da abinda yafi alkhairi a gareta saboda haka nan tunda suka yi magana da mubeena kan meeting din zuciyarta ke bugawa lokaci lokaci sai taji gabanta ya fadi.1


Daren lahadi da kyar ta samu ta rintsa saboda fargaban da ita kanta bata san na menene ba.


Da safe ta tashi ta shirya cikin dogon wandon suite peach colour sai yar karamar riga milk colour da ta saka ta tuck in dinshi cikin wandon da yake har rabin cikinta. Jacket din suit din ta saka wanda ya rufe saman ass dinta kadan babu maballi a gaban rigar so a bude yake kana iya hango rigar ciki milk kala,cover shoe ta saka milk kala ta yane gyale peach a saman kanta sannan ta saka glass me haske,babu abinda ta shafa a fuskanta daga powder sai lip gloss me glowing.1


Sosai tayi kyau gwanin sha'awa jakanta ta dauka milk colour ta fita tana adduan Allah yasa daddy baya palo ta dauki karamar motarsa.


Allah cikin ikonsa babu kowa a palon da sauri ta dau key din ta fita tana addua.


Duk sammakonta ta iske motoci a cikin company din ciki har da motan mubeena kusa da ita wata farar jeep ce kirar benz tabe baki tayi dan ta san yau dole a ga manyan motoci a wajen.

Office dinsu ta wuce direct,kofar office din mubeena a bude yake har zata shiga sai ta fasa jin ba ita kadai bace.1


Da sauri aka shigo office din wani saurayi ne dauke da jakan suits a hannunshi me tsada yana sanye da khakin sojoji gira daya maimunatu ta daga a ranta tace tooooh masu abu da abinsu securities din ma nashi sojoji ne.1


Cikin rawar jiki sojan yace mata "is my oga inside? " tabe baki tayi tace mishi "i really dont know,nima yanzu na zo." Gyada mata kai yayi ba tare da ya nemi izininta ba ya kutsa kai cikin office din mubeena bata yi mishi magana ba ko ta hana shi dan wallahi bata shirya yin battle da soja ba.


Tana nan tsaye tana fito da aikinta taji tsawan da ya hargitsa mata hanjin cikinta.


"Will you get out of here? Does this look like my office to you? Useless fellow." Da sauri sojan ya fito ya wuce maimunatu dake tsaya a sandare tana kokarin tantance muryan da taji.1


Bayan sojan tabi da sauri amma kash elevator din ya sauka stairs ta bi dan ta cimma shi ta tambaye shi wanene oganshi bata so ta tabbatar da abinda kunnanta ya jiyo mata.


Tana bude kofan elevator din da suma suka biyo ya bude mubeena da mufliha a gefe da gefensa


Lokaci daya idanunsu ya sarke waro manyan idanunsa yayi yace "Ya furta yana kara waro manyan idanunsa,a lokaci daya mufliha da mubeena suka bi inda idanuwansa ke kallo da nasa idanun.1


Duk da tsananin firgicin da maimunatu ta ke ciki bai hana ta jin wani iri ba ganin idanu sunyi yawa a kanta.

A sukwane ta koma ta inda ta fito tare da janyo kofar ba tare da ta damu da takalmin dake kafanta ba ta dinga haura steps din da sauri sauri gudu gudu burinta ta tsince kanta a office dinta.1


Sauke ajiyan zuciya tayi lokacin da ta isa cikin office dinta tare da dafe kirjinta saboda yanda yake bugawa.1


Rintse ido tayi tana motsi da bakinta she cant believe she is seeing him again after such a long time. Me yake yi a nan?1

Cikin sassarfa ta karasa gaban table dinta tare da zama slightly a kai Marwan will not be the end of her,she is a full grown woman now, ba zata yaudaru ba this time around. Geez! why is she blabbing? Ganinshi ba wai yana nufin ya dawo cikin rayuwarta bane.1


5 years ago he used her,he took advantage of her love for him tashi daya ya bace b'at babu shi babu labarinsa not even a single text.2


Wasu hawaye ne suka nemi kubce mata,ta fara kyafkyafta idanu tana son mayar dasu.


Dafatan da taji anyi ne ya sa numfashinta daukewa na wucin gadi.1


Ganin ta koma ya sa mufliha da mubeena  mayar da dubansu kan yayansu duk sai suka ganshi a firgice kaman wani wanda ya ga abin tsoro har lokacin idanunsa na kan kofan mufliha ce ta dan dafa kafadarsa tace "hey are you ok?" Wani yawu me daci da kauri ya hadiye kafin ya bata amsa mubeena ta kara jefo masa wata tambayan

"Yayana ka santa ne?"

Girgiza kai yayi yace"i want to be alone." Ba tare da ya jira amsansu ba ya kama hanyan dayan wing din company din inda zai sada ka da office dinsa kallon juna suka yi tare da tabe baki mubeena tace "bari in duba maimunatu,ke kuma fill him up da abinda ya kamata ya sani amma dai duk rintsi he should be ready in an hour,we dont wanna keep our investors waiting."1

Harara mufliha ta galla mata tace "toh sannu uwar mu." Dariya tayi ta juya tare da danna number din floor din da office dinta yake a jikin elevator din.


Tun a hanya ya fara balle bottuns din jikin rigar camoa din dake jikinsa dan sam tunda ya diro nigeria bai samu sukuni ba ko zama bai samu ba da asuban fari office dinsu ya fara wucewa ya reporting sannan daga nan direct ya wuto company dinsa.1


Sai me? Idanunsa yayi masa ganin da bai tab'a tunani ba

Me take yi a nan? Is it really her? Mieminshi? Ashe zai sake ganinta she is back his baby is back,she was his from the begining, he tought her many things ya kasa mantata she was his muse barinta was never his intension and ya nemeta kaman zai halaka kanshi amma bai sameta ba, yanzu ta dawo gareshi she is back.1


Ya sani daga yanayin shigarta bata yi aure ba kai ko tayi aure koma waye mijin dole ya sakar masa ita because he owned her ita tashi ce shi kadai babu wani mahalukin da ya isa ya mallaketa bayanshi and she know better than to mess with him.3


Murmushi ne ya subuce mishi tuno da innocent face dinta whenever he kissed her how he missed those soft full lips against his.

He will have her back he will have her again!1


STORY CONTINUES BELOW

Limshe idanunsa yayi yana murmushi lokaci daya yana shakar kamshin da kayataccen office dinsa yake yi.


Tuno surarta da ya gani yanzu yake yi komi ya kara cika a hankali yace "miemie na." Da sauri ya bude mayan idanunsa tunowa da yayi da irin kallon da take jefansa dashi.

Me hakan ya ke nufi? Ba dai tuhumarsa take yi da laifin da ba nashi ba?2


Baya tunanin ta kai shi shiga tashin hankalin rashinta lokaci daya ta b'ace b'at a rayuwarsa kaman wacce bata tab'a existing ba and yau Allah cikin hikimarsa ya kawota har domain din shi.


Murmushi yayi yana shiga cikin suite dinsa dake manne da office din yana cire kayansa zai tuno mata da duk wasu darrusa da ya koyar da ita in ta manta mubeena da mufliha are the only two people da suka sa bai had'ata da kirjinsa ba time din da ya ganta ya san she can never resist his touch but no yana so family dinshi su respecting dinta nan ba cyprus bane he just hope and pray he can keep his hands to himself.


A fili yace "i will have to get over with this goddamn meeting in gana da baby na,i wonder what she is thinking of right now." Da wannan tunanin ya shiga bathroom.1


A nutse ta jiyo wani irin ajiyar zuciyane ya kwace mata ganin mubeena ce ba wanda ta ke tunani ba lumshe idanu tayi hawayen da take ta kokarin mayarwa suka zubo mata a kidime mubeena tace "subhanallahi! Maimunatu yaya haka? Kin san yayana ne? Wani abu mara kyau ya taba hadaku ne?"1

Kakalo murmushi tayi tare sa bud'e idanunta tasa yatsanta tana dauke hawayen da suka zubo mata cikin rawar murya tace "ko d'aya kawai kunya da tsoronsa ne suka dirar min a lokaci daya cos ban expexting ganinsa ba kuma for the whole weekend tunanin yanayin haduwarmu nake ina tsoro kar in messed up in disappointing dinki." Maimunatu ta fada cikin sauri ita kantabta sha mamakin yanda karyar ke flowing ba gargada amma abu daya ta sani matsawar aka ce ta maimaita abinda ta fada she cannot remember a single word."1


Murmushi mubeena tayi tace "ke dai fadi gaskiya ko dai yayana ya gigita tunanin yarinyan kin san yayana akwai firgita yammata."1

Dan hararar wasa ta sakar mata tana arranging abubuwan da zata needing a wajen meeting din.


A hankali mubeena tace "kin san wani abu?" Ba tare da ta kalli maimunatu ba ko ta ji ansanta ta cigaba da magana "yayana yana firgita yammata amma shi yammata basa firgitashi,zamanin tasowarsa yayi rigima he was a real player duk yarinyan da ta shiga tarkonsa ta shiga uku so da dama kawayen adda mufli sun sha cewa suna sonshi adda zata ce ba ruwanta ke ko shi yaga kawar adda yace yana so sai mun gaya mata ba ruwanmu in ya breaking mata heart dan kwararre ne ta wannan fannin zai koya miki sonshi ya zame jiki ya bar ki da jinyan zuciya da gangan jiki  kullun maganan hajiyarmu daya ya rufa mata ya rufa mana asiri ya daina bin yaran mutane kar aya ya sauka akanmu amma a banza tashi daya Allah ya jarabe shi da son wata tun daga kanta yayana bai kara kallon wata diya mace da sunan so ko sha'awa ba da alama tana da mugun kishi ko kuma son da yake yi mata yafi karfinshi da har baya iya kallon wata mace a matsayin mace."1


Tab'e baki maimunatu tayi dan sam bata jin armashin hirar da mubeena take yi mata wanda ta kasa gane gargadi take mata ko gugan zana akan yayan nata bane,bata san cewa abubuwan da take fada kadan ne a ciki bata sani itama she was once a victim sai dai Allah bai bashi nasara akanta ba duk da haka yayi mata gibi a rayuwa gashi shi he moved on har ma ya fada son wata ba ita ba.1


Kamar an fuxgo maganan a bakinta tace" toh ina ita budurwan ko matar da yake so din yanzu?"

Ajiyar numfashi mubeena ta sauke tace "tana nan any moment from now zasu yi aure,cikin yan shekarun nan kwata kwata bai samu zama bane amma inshaaAllah muna sa ran wannan lokacin zai settling down yace matar da zai aura me kunya ce bafillatana usul taki yarda mu santa wai sai lokacin da aka kawota cikinmu."1


Ta juyo da dubanta kan maimunatu fuskanta cike da annuri ta lura mubeena na matukar son yayantan nan itama murmushin yake tayi tace "lallai yah moh din nan naku sai shi." Ta fadi sunan ne dan ta kara tabbatarwa marwan din ne dai ko wani ne duba da wannan karkaffan namiji ne sannan kuma in ba wai ta rikice bane kaman khakin sojoji ta gani a jikinsa while ita marwan dinta ya fada mata shi doctor ne kuma ita ma ta tabbatar da hakan.


Kaman daga sama taji mubeena na cewa "ke sunansa Marwan,moh muhammad ne wato last name din mu tun yana high school ake kiransa da last name dinsa kuma kinga a wajen aiki capt moh ake ce mishi shi yasa da yawa suke ganin moh sunansa ne amma asalin sunansa marwan."1


Gyad'a kai tayi zuciyanta nayi mata d'aci marwan din ne dai ba wani ba another big lie marwan is a soldier. Kallon time tayi taga lokacin meeting din ya karato

"Amma kin san nayi mamakin ganin firgici a fuskan yayana ban taba ganin hakan ba sai Allah me yasa yayana ya firgita da ganinki."

D'aga kafada tayi tace "anya ba dai ganina ba maybe wani abin dai." A zuciyarta ko tace ya ba zai firgice ba ya ga past dinshi.2

"Maybe kuma kyaunki ne ya rud'ashi" cewar mubeena


Dan hararanta maimunatu tayi kasa kasa Dan kowa ma haushin shi take ji a yanzun nan tace" duk yammatan da kika ce min yayi sannan da rashin zamansa a kasan nan bana gani akwai kyaun wata mace da zai firgita shi sannan duk wanda yake soyayya wani opposite sex bai burgeshi in ba partner dinsa ba." Cike da tunanu mubina tace "kuma haka ne amma ai ni kinga dictective dan fulani na burgeni amma habibina nake so,kuma ke din ai wani sirratacn kyau ne dake da ba kowa zai gane ba sai irin si yayana da suka goge da sanin yammata." Ta fada tana kashe nata ido.

Rolling idanu memunatu tayi tace  "Ma'am i think ana buqatan mu a board room." Ta tsaya tana gyara zaman rigarta murmushi me fadi mubeena tayi mata dukkanin hakoranta a waje.1


"Ke dai wallahi ban son me yasa ba kya son ayi hiran soyayya dake ba" tab dinta ta dauka da abubuwan da mubeena zata buqata ta tsaya gaban mubeena tana kallon fuskanta dan pouting bakinta mubeena tayi sannan ta dan buga kafanta.....Duk taku daya da zasu zuwa board room din dai dai yake da bugun da zuciyarta yake yi fargaba biyu ne a tattare da ita zama cikin manyan masu kudi sannan kuma ga marwan.1


Duk inda suka zo wucewa gaishesu ake yi kasancewar mubeena babba a wajen.

Sannan securities ne kaca kaca a cikin companyn ko wani kusa ya zo da tasa tawagar1


Safina ce cousin dinsu ta ja tsaki ganin da maimunatu za a je meeting din she cant believe daga zuwan yarinyan har ta samu shiga haka ji yanda tayi classy dressing kai kace tana daya daga cikin family din alhaji moh bata san maimunatu ma iyayenta ba matsiyata bane.1


Mubeena na shirin bude kofar board room din maimunatu ta rike hannunta tare da rintse ido tana tsananta addua kallon bakinta da yake motsi mubeena tayi tana murmushi tare da dafe hannun maimunatu dake rike da nata tace "is going to be alright,just breath in and out." A hankali maimunatu ta ja numfashi ta saki cikin murmushi mubeena tace "good" sannan ta bude kofan.


Sau tari maimunatu na mamakin mubeena duk shiriritarta sarai ta san me take yi when it comes to work ba zaka gane mubeena ce ba wannan mashiriranciyar1

Dakin taron cike yake da maza da mata koma fiye da haka suna zaune sai tattaunawa suke cikin su har da mufliha da Tahir wanda maimunatu bata ganeshi ba duk da irin kallon da yake jifanta dashi tare da murmushi gaggaisawa mubeena ta fara yi dasu tana gabatar da maimunatu


Alhaji Nasir shetima daya daga cikin manya manyan yam kasuwan Nigeria ne wanda kuma yake da 10% share a moh enterprises kuma mai mafi yawan share a company din bayan mamallakin company din dan sauran daga mai 5% sai 6% sai 7% ne.


Fuskarsa na dauke da murmushi ya cewa mubeena "mashaaAllah da samun mataimakiya kyakyawa ne hazaka." Murmushi itama mubeena tayi dan tuni ta saba da halin alhaji shetima da yaga yar kyakyawar budurwa jikinsa zai hau zikiri tace "Nagode sosai yallabai tabbas maimunatu akwai hazaka kuma ina jin dadin aiki da ita sosai." Hannu ya mikawa PA dinsa ya karbi complementary card dinsa ya mik'awa maimunatu tare da cewa "hajiya maimunatu ga katina ki bani kiran in kin kammala bautar kasan ki kina neman wajen aiki inshaaAllah zaki samu." Maimunatu bata yi mamakin sanin da yayi tana serving ba kasancewar id card dinta na like gaban rigarta da murmushi ta ansa katin dai dai lokacin da zuciyarta ta ba da wani irin sauti sakamakon bude kofar gaba daya da akayi Marwan ya shigo cikin dark ash din suits.1


Nan da nan yawun bakin maimunatu ya kafe sai hadiye yawu take ba kakkautawa domin ta samu ta jika makoshinta da ya bushe lokaci guda ruwa mubeena ta mika mata a hankali yanda ba wanda zai ji tace mata "relax yaya baya cizo." Daga nan ta nemi waje ta zauna itama maimunatun ta zauna a gefenta ba tare da ta daga kai ta kalli kowa ba

Idanun marwan fes akanta murmushin gefen baki yayi ganin halin da ta shiga daga shigowarsa akan idanunsa wancan tsohon banza ke bata kati duk da bai san a wani dalili bane har ma tana sa hannun ta ansa fuskarta da murmushi.1


Cikin takunsa na isa ya karasa shiga cikin dakin babban kujerar sa ya nufa wanda yake girke a head na tabkeken table din da yake zagaye da kujeru masu yawa ya zauna.


Maimunatu ita kadai ce karamar ma'aikaciya a cikin dakin tarin babu wani secretary ko personal assistance a dakin taron sai ita wanda hakan ke yi mata nuni da itace CS1


Ba tare da wani bata lokaci ba suka fara gudanar da abinda ya tarasu a wajen sam hankalin marwan bai kan kowa sai maimunatu dake zaune kanta a duke tana rubutu a tab dinta da alama tana rubuta minutes ne sam taki dagowa ta kalli kowa shi kuma so yake ta kalle shi dan bakinta kawai yake kallo tana motsa shi kaman yanda ta saba "somethings never change." Ya fada a hankali amma kowa yaji ka sancewar akwai mouth piece a jikin suits dinsa shirun da wajen ya dauka ne ya dawo dashi kallon kowa yayi da idanunsu ke kanshi sai a lokacin ya farga da abinda yayi dan gyaran murya yayi tare da kara musgutawa a hankali cike da kasaita yace "go on" duk da bai san wanda ke magana ba ko akan me ake maganan.6


A haka aka round up din meeting din ba tare da ya tabuka komi ba ta kasan lashes dinsa yake kare mata kallo babu wanda ya iya karantar halin da yake ciki sai ita da ta san yana kallonta dan jikinta ya bata yana kallonta ko daman can shi mayen kallonta ne kuma tana yawan gaya mishi ba taso.1


Duk da ta lura a cikin dakin ba shi kadai yake kallonta ba,wanda ke zaune kusa da mufliha wanda tafi tunanin Tahir ne da kuma Alhaji Nasir duk yawancin lokuta idanunsu na kanta amma me? Idanun marwan sunfi ko wani idanu kaifi a tattare da ita bata da wani buri da ya wuce a kammala meeting din nan ta tashi ba tare da wani abu ya hadata da marwan ba which she doubt.1


A haka tayi zaman awa hudu da meeting din ya dauka a takura. Ana cewa an gama ta fara kokarin tashi bayan sauran manyan bakin sun fara fita har lokacin marwan na zaune bai mike ba balle ya sallami bakinsa.1


Cike da girmamawa wasu daga cikinsu suke karasawa inda yake su yi sallama tare da nuna mishi son ganinsu da yake sai dai yayi murmushi yace zai duba yayin da wasu suka fita ba tare da sun waiwayeshi ba suna ganin karamin yaro dashi zai nuna musu iko ko dan yaga shine mamallakin company din ai dai ya san su ba matsiyata bane.1


Mufliha da mubeena ke kokarin takawa bakin nasu maimunatu na mara musu baya ganin haka dan dama tun tuni idanunsa na kanta da sauri ya dan d'aga murya wacce take cike da kasala yace "auta ur secretary should stay."1

Dam gaban maimunatu ya fadi murmushi mubeena ta mata tare da gyada mata kai ita kuma ta girgiza kai hawaye na dan taruwa a idonta dan bata rai mubeena tayi ta ja ta gefe tace "wai meye haka ne? Be strong mana sai kace kinga me yanka mutane." Ta fada cike da haushin yanda maimunatun ke nuna karara bata son abinda zai hadata da yayanta mafi soyuwa.1


Cikin haushi tace "na tabbata ba criticising dinki zai yi ba zai so dai yaga kuma yaji abinda aka tattauna a taron dan na lura sam hankalinsa baya kan taron just be brave kar ki ban kunya."1


Daga haka ta sa kai ya fice numfashi taja ta fitar ta nufi inda yake zaune wata mata da ake kira hajiya baraka na zaune kusa da shi suna dan magana isowarta wajen yayi daidai da lokacin da hakiya baraka ke cewa "gaskiya dai ya kamata ka shigo tunda kana kasar na san baby zata yi matukar farin ciki da zuwanka dan kwanaki take min korafin rashin kirkinka." Murmushi yayi yayin da maimunatu dake tsaye a dayan barinsa duk da luguden da naman zuciyarta keyi bai hana ta dan tabe baki ba a hankali tace 'na mamajo."

Karab a kunnensa4


Murmushi yayi me sauti yace "hajiya inshaaAllahu zan zo a mika min sakon gaisuwana gun baby ta kwantar da hankalinta zata ganni nima nayi kewarta ai." Yar dariya hajiyar tayi tace "atoh ai kun fi kusa ni ba zan wuce sai ka shigo." Da haka ta mike ta nufi kofar duk suka bita da kallo har ta fice a tare suke jin sautin zuciyoyinsu na canzawa.1


Ko da fitan hajiya da Taheer ta ci karo yana dakon jiran fitowar maimunatu dan dazu ganin mubeena ne ya sa ya kasa tunkararsa dan sam baya son mubeena ta san da zancen yana son maimunatu har sai ya kama zuciyan maimunatun ta yanda ko da mubeena ta sani ba za tayi nasara tarwatsa mishi farin ciki ba ta kan abinda ya riga ya wuce kuma kaman yanda take da na sani shima haka yake da na sani.1


Maimunatu bata ankara ba dan hankalinta na kan kofa saboda sam bata son kallonsa balle su hada ido sai ji tayi kawai ya janyota ta fada kanncinyarsaA'uzubillahi" shine kalmar da maimunatu ta furta cike da tsoro ta kalli kofa sannan ta fara kiciniyar mikewa amma tam ya matseta a jikinsa har tana jiyo saukan numfashimsa a wuyanta nan da nan jikinta ya fara b'ari sai kokari take ta kwace jikinta.1


Cikin rawar murya tace "yallabai dan Allah ka sakeni ni ba yar iska bace." Cusa hancinsa yayi tsakankanin  wuyanta tare da furta "how i missed this." A can kasan makoshinta duk da gyalen da yayi musu katanga bai hanata jin wani familliar feelings na taso mata kara yunkurin tashi tayi taji ya kara matseta zuwa lokacin ranta ya kai kololuwa wajen baci adduanta daya kar wani ya shigo ya samesu a haka.1


Cikin tsawa tace "dallah malam na gaya maka ni ba yar iska bane ka rabu dani ko,in ka saba iskancinka toh ni ba sababbiya bane ka sakeni tun kafin in tara maka jama'a."1

Cak ya tsaya da abinda yake yi ya sassauta rikon da yayi mata ba shiri ta mike tana gyara kayanta a hankali yace "miemie ni kike d'agawa murya haka?" Wata uwar harara ta banka mishi tana kara gyara rolling din gyalenta dan kar ta fita a zargesu shi kam sai kallonta yake yi.1


Tana gamawa ba tare da ta ce mishi komi ba ta fara tattara yan komatsanta zata fito ya riko dantsanta  cike da mamaki cikin fusata yace "miemie wai ba dake nakw magana bane kin mayar dani dan iska?" Kwace jikinta tace "da kai me ye ba dan iskan bane? Kuma bari kaji ni ba sunana miemie ba da ubana ya rada min suna ba miemie yace sunana ba sunana maimuna in zaka iya kira fine in baka iyawa tafi nono fari,on a second thought ban ma son kara jin sunana a bakinka dan ban sanka ba kuma bani buqatan sanin dan iska irin wanda da ganin mutum zai cakume sannan kuma murya kuma da na daga maka kai ka siya tunda ka tabani ba da izinina ba in kai baka girmama mahallicinmu kan abinda ya haramta ba banga abinda zai sani in girmamaka a matsayin uban gidana ba mtsseww." Ta sa kai ta fita kar ku so kuga yanda zuciyanta ke rawa zuciyanta cike yake da tsoro dan tafi kowa sanin munin fushin marwan wallahi yana iya tara mata jama'a yanzun nan da hargaginsa na banza.2


Tana fita taci karo da Tahir yana pacing kofar dakin taron tana fitowa ya taho inda take da hanzari har zai riko hannunta ya fasa fuskarsa dauke da murmushi yace "hope all is well?" Da mamaki ta kalleshi sannan ta kalli dakin taron ajiyar zuciya ta sauke sanin da tayi dakin sound proof ne na waje ba zai ji na ciki ba murmushi ta dan saki na yake tace "yeah am good,me ka gani?"1

Marwan kasa kwakwaran motsi yayi dan ya cika da mamaki ko dai da gaske wannan ba maimunatunsa ba ce? Maimunatu da ya sani bata da hayaniya she is as frigile as a morning flower amma yau she stood up to him ya san ko zata yi wa kowa tijara but not him toh me ya faru me ya canza maimunatunsa yayi zaton tana ganinshi she will rush to him in tears tana tambayan inda ya shiga me ya faru basu kara jin duriyar juna ba amma me sai ya ga sabanin haka.4


Dan murmushi yayi ya sani fushi take da shi,fushi take bata kara jin labarinsa ba shima ai yana fushi amma zai ajiye fushinsa ya lalasota ya shawo kanta ya san ya zai yi.1


Da wannan tunanin ya mike dan ya fita yana fita idanunsa ya masa mugun gani.1


"Ba komi! Tahir yace tare da cusa hannunsa cikin wandon suits dinsa dan karkata kai tayi tana kallonsa yayi kyau abinshi shima cikin suits she wonder me yasa suits ke yiwa dogayen maza kyau,marwan ya san wannan kallon ya san tana appreciating Tahir ne nan da nan ranshi ya b'aci sai hadiyen yawu yake.1


A tare suka yi magana ita da tahir

"Kin ci abinci?"

"Kayi sallah ma kuwa?"

Dariya suka saki a tare maimunatu na dafe bakinta tare da saukw kanta.

Gyaran muryan marwan shi ya dauke dariyar maimunatu d'ip.1


"Taheer me kuke yi a nan har yanzu?" Cikin murmushi yana kallon maimunatu yace "zamu je cin abinci ne da miss maimoon." Dan tabe baki marwan yayi ya ciro hannunsa daya cikin aljuhu yana duba time a jikin rolex wrist watch d'insa yace "wuce muje muyi sallah first." Dan shagwabe fuska tahir yayi yace "yah marwan ci na gaba da sallah fa."

Marwan bai kalleshi ba yace "miemie wuce ki cewa mubeena ina son minutes din meeting din nan a email dina in an hour."

A kufale tace "maimunatu sir. " daga kafadu yayi yace "whatever" tabe baki tayi kaman tayi tsaki sai taga rashin dacewar hakan tunda ga taheer a wajen zai mata kallon rashin da'a har ta shiga elevator dan ta tura mishi haushi tace "T sai naji kiranka." Kafin Tahir ya bata ansa kofar ya rufe sunkuyar da kai marwan yayi yana kallon takalminsa dagowan da zai yi sai da Taheer ya tsorata saboda yanda lokaci daya farin ya koma ja kowa ya san irin temper din marwan shi yasa kowa ke kiyaye masa yana da saukin sha'ani amma fushinsa ba kyau.1


"Yah Marwan muje sallahn ko?" Ya fada dan yana tunanin sabosa yayi masa musu a gaban employee din shi ne dan girgiza kai yayi yace "jeka kawai,ya juya ya nufi private elevator dinshi har ya kai ya juyo yace wa Tahir "bana son shashanci in zaka wooing mace not in my building." Gyada kai Tahir yayi sannan ya juya ya bar taheer a tsaye, shi ba wawa bane marwan is indirectly telling him kar ya bi bayan maimunatu sai in sun bar cikin company dinshi.

Dan daga kafada yayi ya nufi elevator.1


Maimunatu na shiga office dinta kiran Khalid na shigowa dan tsaki ta ja tare da fad'in "not again." A nutse ta dauka tare da sallama cikin taushin murya yace "munah are you ignoring my calls again?" Jikinta ne yayi sanyi tace "khalid ba haka bane na riga na gaya maka in har kaje ka aiwatar da abinda nace maka wallahi zan aureka." Numfashi ya sauke yace "zan shigo in mayar da ke gida in an tashi aiki." Lumshe idanu tayi tace "da mota na zo."

Bai ji dadi ba sam amma sai yace "toh in sameki a office ko gida dan ina so muyi magana." Daga kafada tayi tace "duk wanda yayi maka."

"Alright zan kiraki,ki kulan min da kanki. " tana ji ya blowing mata kiss shiru tayi ba tace komi ba ta limshe idanu tana jin sound din kiss din har tsakan kanta.

"Me kike nufi DA zaki aure shi in ya aiwatar da abinda kika ce........?

Post a Comment for "KINA RAINA CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...