KINA RAINA CHAPTER 10 KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KINA RAINA CHAPTER 10 KARSHE

 KINA RAINA CHAPTER 10 KARSHE


D'an jim maimunatu tayi cike da tausayinsa itama kukan take yi she wish she can ease the pain amma babu abinda zata iya mishi she wish zata iya sa shi a jikinta ya rarrashe shi but thats not the way foward for both of them.

Rayuwarsu is almost iri daya ta wani gefen kuma a very different story1

Numfashi ta sauke tana goge hawayen fuskanta sannan cikin taushin murya tace "Allah ya jikansu da rahama ya kara haskaka makoncinsu,what can we do da ya wuce muyi musu addu'a we have cried enough for their lost."1


Gyada kai yayi yana kara goge fuskansa da tafukan hannunsa sannan yace "ban yi maraicin uwa ba dan ban san maraici ba mami was there ta soni tana kuma kan sona kaman ita ta dau cikina ta haifeni i lack nothing ta bangaren kulawar uwa tayi min abubuwan da ko uwar da ta haifeni ba lallai tayi min ba, ita na budi ido na sani a matsayin uwa da dumin jikinta na saba nononta shine abinci na i gave her sleepless nights saboda kuka ko ciwo toh me kuma ya rage mami zata min haihuwata ce kawai bata yi ba amma tun daga ranan da aka haifeni take dawainiya dani har yau din nan miemie in mami ta ganni cikin bacin rai hankalinta tashi yake, har yau din nan in mami ta ga ban ci abinci ba bata da nutsuwa, miemie mami na sonki duk da ko hotonki ban taba gwada mata ba but tana sonki saboda ina sonki."1


Wasu hawaye ne suka barke mata sosai ta kasa gane kukan tausayinshi take yi ko nasu dukka a hankali tace "how lucky of you!" Cikin sauri ya gyada kai yace "i know i know."1


"At first grandparent dina sun so suyi borin sai dai lallai a basu ni daddy ne ya saka su a gaba da kukan da wanne suke so yaji da rashin matarsa ko da rashin dan da ya kwashe shekaru yana jiran zuwansa duniya ya kara tabbatar musu da in dan sun gansa hannun nafisa ne hankalinsu ya tashi ta hankalinsu ya kwanta nan gaba kadan sai sun gode mishi sun godewa nafisa saboda irin rikon da zata yi wa dansa shi ya san matarsa ya san kalanta  da wannan ya samu ya shawo kansu su ka hakura suka tattara suka koma ukraine bayan anyi bakwai.


1

Ranan da aka yi bakwai daddy ya shiga wajen mami dan yaji sunan da take so a saka ranan ma sai da tayi kukan dadi tana shafa kaina cikin crib dina tace "dear Marwan nake so ina son sunan nan dear zaka saka mishi?" Juyo da ita yayi tana fuskantarsa ya rike fuskanta a hannusa biyu yace "anything for my dear,Nafisa ke d'in wata baiwa Allah yayi min da ba ko wani namiji yake yiwa wato ke din wata kyauta ce da Allah ya bani har yau din nan banga ta biyunki ban ji labarin me irin halinki ba, sometimes i do wonder ko kina sona ko kina kishina kuwa? Wasu lokutan kuma da kaina nake bawa kaina ansa son da kike min ha sa kike son duk abinda nake so and son da kike min ya saka baki nuna kishinki karara duk da abin yana cinki a rai. Dear kiyi hakuri na gaza miki a ta wani fannin duk tarin son nan da kike min bai hana in karo miki abokiyar zama ba ki yafe min dear i am so sorry." Ya fada yana hawaye yatsunta ta dora bisa lips dinta itama nata idon na kwaranya da hawaye tace "karka ce haka dear kar kace,in kace haka baka yi wa zainab adalci ba kar ka taba kiran shigowar zainab rayuwar mu a bisa kuskura she was never a mistake you loved her genuinely me yasa dan yau bata nan zaka kira auranta a bisa gazawa? Kar kayiwa soyayyan ku wannan kushen na sani kana sona auran zainab da son da kayiwa zainab suna cikin kyakyawan kaddararka take a look at what zainab left for us ta shigo rayuwar mu cikin dan kankanin lokaci dan ta sada mu da farin cikin ta tafi ta bar mu da kewarta." Ta fada tana shigewa jikinsa tare da fashewa da wani kukan.

1

Wani abin al'ajabi ina da shekaru uku a duniya mami ta fara laulayi murnan da suka tsinci kansu a ciki ba a magana saboda samun abinda suka fidda rai daga samu ko da yake ance mumini baya cire rai daga rahaman ubangiji.1


STORY CONTINUES BELOW

Maganar cikin na bazuwa cikin dangi sai ga yan bani na iya kuma suna labarin ai bari ta haifi nata zata daina kula da marwan.1


Aikam mami ta basu mamaki dan ko da cikinta ya kai lokacin haihuwa cike take da tsoro saboda tana iya tuno wahalar da zainab tasha wajen haihu amma Allah cikin ikonsa sai haihuwar ta zo mata da sauki ta haihu cikin kankanin lokaci ta haifi baby girl.1


Wanann karon ma daddy ya bata zabin sunan tace Zainab sai ayi mata inkiya da mufliha ma'ana(kyauta daga Allah) take so domin ita din kyauta ce daga Allah yarinya taci sunan mufliha.1


Mufliha da take jaririya bata samun kulawan da marwan dan kusan 4 years yake samu wannan ya sa daddy samo musu nanny dan Alhamdulillah lokacin arzikinsa na ta habbaka.1


Mufliha na da shekaru 5 mami ta fara jin alamun tana dauke da wani cikin sam bata taba kawowa ranta samun wani ciki ba lokacin da aka tabbatar da cikin ko kuka suka saka duk su biyun na tsananin murna wannan cikin shine silar samun zaman lafiyar mami a cikin family.1


A haihuwar mubeena ne grandparent dina suka zo dubani tare da new born baby daddy ya farin ciki sosai da zuwan na su kyauta me tsoka grandpa yayiwa baby a nan ne kuma yake shaida musu an gama ginin company dina da aka gina da sunan mamana karamin company ne amma ana fatan wata rana ya habbaka.1


Sunan company din ne dai aka rasa me za a saka daddy yace a saka sunan zainab baban sadiq yace hakan ma yayi amma da yake ina zaune a wajen ake shawaran kuma naji na wa ne nace "ah ah sai dai a saka Nafisa." Duk kallona suka yi da mamaki.

Daddy yace "ah ah marwan ba za a yi haka ba,wa ma ya saka bakinka a ciki?"1


Dan jim kakana yayi kafin yace "mohammad barshi ya zabi sunan company din da yake so tunda nashi ne,now tell me wani suna kake so." Shiru nayi ina tunanin tunda daddy bai son a sa sunan mami ni kuma ita nake so a saka sunan ta toh ko ince mah ne abinka da yarinta ni a dole mah din na nufin mami sai naga toh ai za a gane sunan ta ne in nace moh bba za a gane ba tunda ba momy nake ce mata ba da wannan shawaran ta yarinta nace "moh company" dariya duk suka yi har daddyn suka ce moh kuma a ina ka samo moh? Sai gani ina wuri wuri baban sadiq ne yace "tunda an hanashi sa sunan uwarsa ya saka na uban ai moh mohammad kenan yanzu ai sai ka hanashi ."

1

Girgiza kai daddy yayi yacewa grandpa dina daddy ba za a biye ta yaron nan ba a saka sunan margayiya kawai grandpa yace ah ah zabina za a using mafarin moh enterprises kenan wanda tun daga wannan lokacin ban ma kara waiwayan maganan company din ba dan ni babban burina shine zama likita yayin da burin sadiq 2nd cousin dina zama soja yake a cikin burinsa.1


Bayan na gama secondary sch na cewa daddy medicine nake so yace sam kasuwanci zan karanta ni kuma na dage kai da fata ga abinda nake so da kyar mami tayi mana sulhu ta lallaba daddy ya barni in karanci medicine amma da sharadin daga baya zan karanci business dan a cewar sa babu me cigaba da mun wahala shi da baban sadiq have done enough nace eh na yarda.1


Lokacin moh enterprises ta fara habbaka sosai har ma anyi branch dinta a katsina.


Shigana medicine sch idona ya bude da yammata bakaken fata da turawa tun ina biye musu da sunan friendship har shedan yayi min ganga na taka rawarsa tun daga lokacin da na san dadin abin kuma shikenan.

Tabe baki maimunatu tayi ta kawar da kai murmushi yayi ya cigaba da magana.2


Ina gama makaranta daddy ko barina in numfasa bai yi ba ya cilla ni cyprus ashe a nan zan hadu da mahadin rayuwata1


Hmmm shine abinda maimunatu tace kawai

Zuwan ki rayuwata change everything though ko da nazo cyprus bani da sukuni bani da lokacin kaina har sai da na kusan gama phd dina lokacin ina project na ganki numfashi ya ja tare da yin shiru a hankali ya fitar da numfashin kafin cikin magana wanda ya fi kama da rada yace "at first i just wanted to play around." Dago kanta tayi da sauri tana kallonsa gyada mata kai yayi yace "yes sai dai kuma na lura rayuwarki ba a nitse take ba tausayinki ya shigeni a hankali wannan tausayin ya rikide ya koma so miemie ban furta miki kalman so ba har sai da na tabbatar lallai din ina sonki althou the first time it just slipped after i kissed you na janye jikina na kaurace miki dan in tabbatarwa da kaina sonki nake da gaske ko karfin sha'awarki da nake yi ne dan tabbas i dont get myself around you sai da na tabbatar sa gaske nake sonki na kara furta miki ranan da kika cika shekara 18.

1

The moments we spends were the best of my life i cherish every second we spend its what keep me going na kasa barin cyprus saboda ke daddy ne yace zai saba min matsawar ban dawo gida ba wannan shine dalilin tafiyana in barki.

1

"Bayan mun rabu na shiga jirgi tunanin barinki ya taba min zuciya ba kadan ba har naji da zan iya bijirewa kiran daddy da na bijire masa na zo nayi zamana dake toh amma nafi kowa sanin hakan ba mai yuwuwa bane dan tsab daddy zai zo har cyprus ya tisa keyata a gaba tunda na kusan shekara da gama karatuna kece dai kike zaunar dani a cyprus. Daf da jirginmu zai tashi ana sanarwa na kira layinki baki dauka ba na damu kwarai dan na san kina can kina kuka shi yasa har baki ji kirana ba abin haushi ina sa ran in mun tashi zasu connecting mana wi fi sai suka sanar da mu tare da bamu hakuri cewan wi fi din is not available, Na tafi da kudurin ina zuwa gida zamu yi magana dake dan zan gabatarwa da daddy maganan ki domin a samu mahaifinki dan ni karan kaina na san ba zan jure rashinki a tare dani.1


Ina sauka Nigeria na tarar da mutuwar kakar sadiq wato yayar kakana abinci kawai naci muka nausa daura a daren ranan ne nake fadawa grandma labarinki tace min tana son tayi magana dake sai dai me sama da kasa na nemi wayata ban gani ba ba zance ga inda na yarda ita ba amma na nemeta na rasa gashi banzo da system dina ba hakuri na bata nace kafin su wuce zan hadaku yanzu ban ga wayata ba.1


After 3 days muka dawo Abuja na duba dakina still ba wayata na dauko system dina in nemeki ta email abin mamaki i never had ur email cos ko da wani lokaci muna tare luckly ur number was saved a kan email dina da sauri na dauka na kiraki amma baki dauka ba na kiraki yafi so ba adadi amma ba respond hankalina ya tashi na kira wani frnd dina a cyprus yaje ya duba min halin da kike ciki yaje har so biyu yace ya buga gidanki ba a bude ba. Na roki daddy ya barni inje cyprus in dawo yace "matsawar na bar kasan nan ba da yardansa ba Allah ya isa tunda ni neman matana ya sa na kasa rike responsibility na dan dama an gaya mishi tare da wata nake zama shi yasa naki dawowa2


A cikin wannan halin sadiq ya dawo daga wani course bala'in kyau yayi min cikin unifoam na ko gaya masa yace "ai ba wani damuwa bane yanzu ma haka ana  shirin shiga short service in ina so akwai shige shigen da zai min a shiga dani ba tare da wani tunani ko shawara da kowa ba na amince.1


Ko sati ba ayi ba sadiq yace inzo in sameshi a kaduna ina zuwa ya ce min yau fa ake shiga training zan shigan nace eh zan shiga na shiga tare da bad mishi sallahun yaje ya dubo min ke a cyprus daga nan na shiga gidan soja dake a raina duk motsi duk wani wahala da zanyi maimunatu KINA RAINA duk wani numfashi da zan shaka ko in fitar KINA RAINA haka na kwashe wata 9 a gidan soja ina fitowa abinda na fara tambayan sadiq kece yace min wallahi ya kiraki baki dauka har can yje amma bai tarar dake ba hankalina yayi mugun tashi sanann na san zan je in tarar da wani tashin hankalin a gida.

3

Sosai daddy yayi fushi dani har da mami ma na rasa sukunina miemie a wannan lokacin ga rashinki ga fushin iyayena daddy yace inje inyi yanda nake so tunda ni babu wanda ya isa dani da kyar da sudin goshi tare da tattaro mishi abokansa ya sauko mami kam sai da taga ina shirin cire musu khakinsu ta hakura.1


Abu na farko da nayi bayan saukowar iyayena shine zuwa cyprus inda na sami labari a inda kika karbi haya na cewan tun bayan tafiyata kema kika tafi naje school amma suka ki disclosing min komi naki da sanyi jiki na baro cyprus ban san inda zan sameki ba ban san family name dinki ba ban san a wani gari ma kike ba banda wata rana da kika ce min a abuja kuke.1


Nayi tir da irin zaman da muka yi kaman wasu wawaye nama fi daukan kaina wawa da bamu san komi akan juna ba i had sleepless nights saboda rashin sanin inda zan sameki bana iya kallon ko wacce mace da sunan mace na san kin yi min illa a rayuwa iyayena suna so inyi aure na kasa samun wacce zan so har in aura matan banzan ma bani sha'awarsu duk wacce ta kawo min kanta sai dai ta koma da haushinta ni bana sha'awa ko son kowa in ba ke ab kin tafi da wani bangare na rayuwana.1


Sai gashi kwatsam na ganki cikin moh enterprises a lokacin da na fidda rai dake sai dai zuwan naki ya zo min da kalubale kala kala.2


Maimunatu yau kin san wanene ni kin san waye marwan kin san dalilina na tafiya da kuma rashin ji daga gareni shin zaki amsheni a yanda nake with my flaws ko kina kan bakanki?"

Shiru yayi ya tsareta da manyan idanunsan nan baka jin motsin komi sai hannun agogon dake girke a bangon dakin duk second daya da zai wuce sai bugun zuciyar marwan ta sauya yana tsoron jin kalmomin da zasu fito daga bakin maimunatu he mean everything he just said matsawar bata sonshi zai rabu da ita amma ya sani rayuwarsa zai shiga taraddadi amma na dan wani lokaci ne domin komi na duniyan nan me wucewa ne rayuwarsa da maimunatu zai wuce kamar ba a yi ba shi mai juriya ne zai jure rashinta kaman yanda ya jure a wancan lokacin, abu daya ya sani shine har ya koma ga mahallicinsa maimunatu zata kasance cikin zuciyarsa dan ita din tana ransa a ko wani wucewar dakika sonta wata halitta ce a cikin zuciyarsa da bashida ikon kankaresa da kansa har sai wanda ya kirkiri son ya raba shi da shi.

3

Kaman daga sama ya jiyo muryarta cikin natural sanyin ta da ya santa da shi tun fil azal, ba muryar masifarta da ta kirkira dare daya ba tace "ka sani kaine mutum na farko da zuciyata ta fara so a ko wani fitowar rana da faduwarka KANA RAINA ina so bani so tunaninka na makale a cikin raina i hated myself for loving you ban daukeka komi ba face fasiki mayaudari!" Rintse idanu marwan yayi domin sosai kalmominta na karshe ya bi duk wata jijiya da ke makale jikinsa ya haura zuwa brain dinsa.4


Numfashi ta sauke ta cigaba da cewa"but then what can i do da abinda ba ni na daurawa kaina ba na dade da ganewa ba sonka ne ba nayi ba bakin cikin halayanka nake yi marwan,kyamar halin da ka sakani a zamanin zaman mu a cyprus nake ko ka san cewa babu namijin da ya taba rike hannuna wanda ba muharramina ba sai kai,ko ka san kaine ka taba kusanto ni da zina ko ka san abubuwan da muka aikata ni da kai wata nau'i ne na zina? Ba lallai sai da penetration bane zina ke aukuwa ta yaya kake so in kalleka in kalli future da kai marwan?5


Ka duba halin da ka saka mubeena a ciki nayi imani hakkin matan da kayi mu'amala da su ne ya sauka kan mubeena ba zance bata da laifi ba akan abinda abinda ya sameta ko in daura laifin kocankwan kanka ba but kaine jagaba akan abinda ya faru da ita.2


Kaman yanda aka ce ku nemawa diyoyin ku uwa ta gari haka muma yake a gare mu,wacce uwa ce kake tsammanin zata so yau ace ga abinda uban yayanta ya aikata? Ban kasance mazinaciya ba ban taba kasancewa da wani namiji ba in ba kai ba yaya tsoro ba zai kamani ba?"1


Cikin murya kaman me rada yace "but i repent kuma zamu yi musu addu'a nothing will happe in sha Allah have trust on him."1


Gyada kai tayi tace "i will accept you but with one condition." Cikin sauri yace "name it!" Hannunta ta dan daga tace "chill we are not in a business field  trying to seal a deal aure kake nema." Ta karashe magana tare da daga gira daya.2


Murmushi yayi tare da gyaran murya har ma da gyara zama yace "tohm naji na gyara,now whats your condition?"

Daga idonta sama tayibtare da tsuke baki ta dan dafe gefen kumatunta da yatsanta daya kaman me tunani shi kuma ya shagala da kallon zanan lallin da aka yi mata wanda ya zauna yayi das akan fatanta kaman a manna mata shi ji yayi kaman ya kamo hannun yayi ta manna mishi kisses kawai.3


Sauke idanunta tayi akan shi tace "its conditions not condition gaskiya." Waro idanunsa yayi yace "woah now am scared,ya nake ji kaman wannan conditions din naki is not something good?" Dan tabe baki tayo tare da daga kafadu tace "ai in zaka iya ne ko?" Gyada kai kawai dan ya san koma meye zai iya matsawar bai sabawa addininsa ba wanda ya san maimunatu wont ask for something like that.2


"NO more brotherly hug to any of your cousins." Daga kai yayi ya cire yatsansa daya yace "one" tace "ba zaka kara tab'ani ba har sai shari'a ta mallaka maka ni." Ya kara fitar da wani yatsa na biyu yace "tw....wait! What?" Gyada kai tayi tace "yeah,you heard me hakan ne zai tabbatar min da kana sona ko kuma jikina kawai kake so ba zan boye maka ba kokontan ingancin son da kake min yana daya daga cikin abinda yasa nake doubting soyayyar ka gani nake jikina kawai kake so tun wancan lokacin da baka samu ba ka kuma sai baka kara waiwayata ba yanzu kuma da ka ganni kake kokarin samu."4


Wani yawu mai kauri ya hadiye yace "dan Allah ki daina doubting son da nake mikj kice komi amma ki daina karyata son da nake miki miemie ina sonki wallahi pls ki yarda dani ko da baki yarda da kalma bakina ko daya toh ki taimakeni ki yarda da wannan dai daya."1


Kallonsa tayi cikin ido tace "toh ka tabbatar min da wannan soyayyar da kake min ka sa min yardanka a cikin zuciyata da raina."1


"Saboda already ina cikin ranki ko? Yarda dani babu a tattare da ke."1


Wani irin murmushi tayi mishi me narkar da zuciya tace "eh kana raina a ko da yaushe."1


Wani irin juya idanu yayi tare da dafe kirjinsa dan wallahi sai da zuciyarsa ta skipping beat a hankali yace "nima tun ranan da na fara ganinki KINA RAINA i thought its just love uhm uhm ashe soyayyar karamar yarinya ne ya kamani da zan kwana but yau zan koma in cewa daddy mun gama fahimtan juna pls a bani matata" dukka giranta ta daga tace "oh really? I dont recall hearing you say ka aminta da conditions dina." Rolling idanuwa yayi yace "na aminta da duk wata condition dinki da wanda kika fada da wanda ma baki fada because i love you and i want to make you mrs moh."3


Wani murmushin tayi mishi tana jin wani fresh air na ratsa duk wata kofa ta gashi dake jikinta mik'ewa tsaye tayi ta kama hanyan kofa tace "kaci abinci la'asar tayi." Sai da ta kai kofan ta juyo tare da cewa "hey you really look good in kaftan zan siya maka hula irin naku na yan Borno......" Da sauri ta fice daga dakin yana kiranta amma tayi nisa.

Girgiza kai yayi kawai tare da mikewa dan yaji masallacin anguwan suna tayar da sallah,da hanzari ya fice.1


Maimunatu kam ta sami mama da aunty khadija na sallah a palon mama sai kawai ta shige cikin kuryar dakin itama ta gabatar da nata alawlan.

Tana cikin addu'a tana murmushi aunty khadija ta shigo dakin itama murmushin tayi har tana shirin tsokananta sai ta fasa ta mayar da hankalinta kan sadiq da yake bacci kan gadon mama.1


Ninke sallayarta tayi ta karasa jikin mirro tana kara gyara fuskarta ita dai aunty khadija da kallo kawai take binta. Tana cikin sa lip gloss aunty khadija tace "kin gama dashi din ko in fadawa daddynki maganar?" Juya idanunta tayi tace "aunty khadija mun shirya ba sai kin gayawa daddy ba." Kama haba aunty khadija tayi tace "wai daman fada kuka yi ne?" Gyada kai tayi amma bata ce komi ba ganib haka yasa aunty khadija tabe baki ta san ba gaya mata zata yi ba.1


Zama tayi bakin gadon dakin tana kada kafa aunty khadija tace "naji kaman ya shigo fa ba zaki koma wajensa ba?" Dan girgiza kai tayi tace "bari a dan yi kaman 5 minutes haka." Dan dariya aunty khadija tayi tace "su aji manya." Itama murmushi tayi dan ta san tabbas in bata yiwa kanta burki ba a kan marwan ba wani aji ne da ita ba gwara ta koya controlling kanta a kanshi in ba haka ba tsaba wahala zata sha a hannunsa da wannan shegen ikon nasa gwara ta koyi kwatarwa kanta yanci. Babu gardama a tsakaninsu amma kam babu tursasawa tsakaninsu wannan karon.2


Kallon agogon wayanta tayi sannan ta mike ta nufi kan mirror har ta dau turare zaata kara a jikinta sai ta fasa ta juya ta kama hanyan  palon alhaji inda marwan ke zaman jiran dawowarta.

Turus tayi ganin bai taba komi na daga abincin da ta ajiye mishi ba.1


Tana daga tsaye a bakin kofar ta rike kugu hade da karyar da wuya tace "baka ci abincin ba?"  Baya iya ganin fuskarta saboda ranan la'asar da ya kallo kofar da take tsayan sai ya zama ta bawa ranan baya.


Yace "baki bani ba zanci miemie?" Girgiza kai tayi ta karaso gabansa ta duka tare da bubbude warmers din serving dinsa shinkafa da wake da miyar tayi sannan ta tsiyaya masa zobo ta koma gefe ta zauna sakkowa kasa yayi ya zauna dan kallonta yayi yace "miemie pls sakkowa min dasu kasa." Kasake tayi tana kallonsa amma yana kallo ta gama arranging mishi komi kan center table din ba tun yau ba ta san marwan da son mulki da ba da order a fili tace "somethings never change." Ta fara sauke abincin.2


Shima murmushin yayi dan tuno wannan kalaman su ya using ranan meeting dinsu ranan da ya fara ganin ta a Moh.

A nutse yake cin abincin yana jin dadinsa na ratsa mishi kwanya kunnensa har motsi yake yi sosai ya missing irin cimar nan shi bai san me yasa gida basu son yin irin abincikan nan ba da wuya a mixing shikafar da wake sai dai tsuranta ko kuma a saka mata su carrots dama dama zobo wasu lokutan ana yi,haka dai yayi ta sake sakensa yana cin abinci dan dama haka ya taso komi babu a cikinsa ko breakfast bai yi ba.

1

Maimunatu kam tsura mishi ido tayi tana mamakin abincin da yake ci ta san shi ba ma'abocin cin abinci me yawa bane amma ta lura ya kusan cinye tulin abincin da ta saka mishi banda yankan nama kusan hudu da ya cinye Allah ya sa ta saka mishi abincin da yawa duk sa ta san shi ba abinda ya dame shi in bai koshi ba cewa zai yi ta kara mishi.1


Kau da kanta gefe tayi tana wasu tunane tunane kaman ance umya dago yaga ta kurawa waje daya idanu da alama tayi zurfi cikin tunanin da take yi kara tsiyaya zobon yayi ya sha sannan ya tsiyayya ruwa ya sha ya sa tissue ya goge bakinsa shi kanshi yayi mamakin abincin da ya ci ko da yake rabon da ya zauna ya ci abinci haka an dade.1


STORY CONTINUES BELOW

Kara mayar da kallonsa kanta yayi yace "tunanin me kike yi haka?" Limshe idanu tayi tace "tunanin abinda ya hanaka tambayata dalilin barina cyprus?" Daga gira yayi yace "is it really important?" A zafafe ta fuskance shi tace "dalilin rabuwar mu shine bashi da mahimmanci?" Da sauri ya daga hannayensa sama yace "ba haka nake nufi ba ke kin sani a times i dont like asking questions cos i sometimes feel in mutum na son in san abu zai fada min bana son takurawa mutum." A kule tace "this same atittude ya janyo bamu san komi a kan juna ba,you dont like asking and you dont like telling kai sai an tambayrka me ye amfanin hakan in baka canza hali ba abubuwa zasu ringa faruwa wanda zai taba rayuwar mu."2

Gyada kai yayi yace haka ne but kiyi hakuri zan gyara,what happened why did you left??" Harara ta galla mishi kafin ta fara bashi labari, aikam kafin ta gama jikinshi har rawa yake yi dan bacin rai kuma shi kam deep down ya san waye da aikin nan but why? Sai faman hadiye yawun bacin rai yake yawun nasa ma ya kafe hakan ya sa makogoransa bushewa ruwa ya tsiyayay ya sha yana fitar da numfashu kaman wanda yayi tsere yace "me yasa ake bin rayuwarki a cyprus kin tuna time din da na taba bin wani da gudu na anshi wani camera a hannunsa?" Gyada kai tayi da sauri cos she could vividly remember ranan.1


Yace "hotunanmu aka dauka ina rungume dake baki ta bude tare da idanu cike da mamaki ya cigaba da magana "ba tun yau ba tuntuni ake so a bata ki a idon mahaifinki amma Allah yana kareki sai wancan lokacin i am so sorry bana tare dake a lokacin hardship dinki." Gyada kai tayi tace ba komi.

1

Zaro wayarta yayi daga aljuhunsa yace "ga phone dinki daddy yace in baki ni zan koma yau,da na so sai gobe ko jibi but i cant wait to make you mine zanje in samu dadyna ince mishi mun daidaita suje a tsayar da magana ko." Da rawar hannu ta ansa wayar tace "tun yaushe dady ya baka wayata?" Hararanta yayi yace "ina miki maganan auranmu ke kina min maganan wayarki ko kina tsoro ko na korar miki samari ne?"2


Itama hararan nasa tayi sai kuma suka fashe da dariya tace "da wannan yamman zaka yi tafiya biyar fa ta wuce." Gyada mata kai yayi yana limshe ido yace "kar ki damu, ni da kin shirya da mun wuce tare kin tafi kin bar aiki."2


Make kafada tayi tace ni ba zan koma ba fa sai ranan clearance din karshe." Dan kankance idanuwa yayi yace "baki isa ba fa wallahi gwara ma ki shirya ki koma mubeena ba zama take yi ba,wai tsaya ma ba zaki je bikinta bane?" Tabe baki tayi tare da watsa hannayrnta ta ce "gani nan dai am not sure ko zani." Tabe baki shima yayi yace "tsakaninku, but ki dawo aiki malama in yaso in kin gama sai ki zabi bari ko zama which zama ne zai zama na sani."1


Ita dai bata ce mishi komi ba kan komawarta aiki haka suka yi sallama cike da kewar juna hade da shaukin juna.1


Ranan kowa yaga fara'arta a gidan sai wani shige da fice take ana kawo wuta ta saka charging wayarta ta kunna ko gama booting wayar bata yi ba kiran mubeena ya shigo dafe kirji tayi tace "na shigesu." Da sallama ta dau kiran1


"Matan yaya ai wallahi zaki sani tafiya ba neman permission? Ajiye matsayinki zanyi in hukuntaki sannan ki koma matar yayan nawa." Rolling idanuwa maimunatu tayi "kafin komi cire min wannan sunan na matan yaya,wani yayan naki? Dan Allah bari karki wani bata min suna."1


Shewa mubeena tayi tace "casss ni zaki yiwa bariki? Toh yayana da ya kaeo miki wayarki shi nake nufi ai ya gaya min ya kawo miki har ma kun daidaita kin yafe mishi barinki da yayi a cyprus." Kwal kwal tayi da idanu tsoronta Allah marwan bai tona mata asiri ba.

Dan tsaki taja tace "zaku ji dashi ai." Daga nan kuma suka fada hiran bikin mubeenan ds za ayi tana rokonta ta dawo ayi da ita.1


Ita dai jinsu kawai take amma ina ita ina zuwa biki gidan surukai haka kawai yawon zuwa nuna kai (inji goggona 😂) 

2

Marwan kam 9 saura ya isa abuja palon daddy ya wuce direcr inda ya tarar dashi da mamy har ma da mubeena a zaune ana kallon news ba tare da wani bata lokaci ba ya gabatarwa da daddy buqatarsa kallonsa mami tayi cike da farin cike tace "surukar tawa ta sakko kenan?" Rungume mamin yayi yace "mami ba ma ki yarda da dan naki ba kenan?"  Murmushi tayi tace "marwan tuni na yarda da nacinka da rigimarka." Duk dariya suka saka mubeena tace "ai ni yayana kayi min kwabsi da ka sani baka shawo kanta ba sai bayan bikina gashi yanzu da kyar ta zo bikina duk yanda nake da ita,miemien ma dai yar kauye ce." Yana shirin ci mata uwa mami ta rigashi tace "kinci gidan ku ja'irar yarinya ance muku kowa ne irinku kannen turawa kunya ai adon mace ni wallahi kullum naji labaringa kara burgeni take." Washe baki mubeena tayi ta ce "mami sai ma kin ganta ba ruwanta da magana." Daddy yace "gashi Allah ya hadata da magananne ni ban san inda ka dauko magana ba ni dai ba ma'abocin surutu bane haka ma zainab sai dai mamin taku hala." Carab mami tace "eh munji din mu dai zamu yi magana ai bai dakko magananka ba amma ya dakko rawar kai da wutar ciki in ana son abu ga rashin hakuri." Girgiza kai daddy yayi yana murmushi ya mayar da hankalinsa kan tv suma yaran nasu dariya suke musu dan kullum dramar su kenan shi yace mata me surutu ita kuma tace mishi mara hakuri ko me wutar ciki wani sa'in yaran ke raba gardama in suka fara2

Majmunatu nayiwa aunty khadija kitso kiran daddynta ya shigo wayar aunty khadijan bata san me yake cewa ba sai ansa eh da to da ah ah da aunty khadija ke bashi amma ta tabbata akan ta ake maganan musamman da taji aunty khadijan tace "zan kara confirming sai in kiraka yanzu." Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar.1


Kaman daga sama taji aunty khadija ta jeho mata magana "iyayen marwan sun kira suna so su kai kudin auranki shine yah abdul yace in kara tambayanki kin tabbata kin aminta da marwan a matsayin abokin rayuwarki?" Ai duk sai ta duburburce ta rasa me zata ce sai eye da na'am da take fad'a  daure kanta auntt khadija tayi dan dama sun gama tace "ki nutsu ki ban amsa this is a lifetime decision duk da na san kun daidaita but dole mu kara ji daga bakinki so yi maza ki gaya min mu ake jira dan a basu amsa.1


A hankali ta gyada kai tace "na amince aunty khadija.!" Gyada kai tayi tace"Allah ya tabbatar mana da khair yanzu zan kira in gaya mishi amma bari in samu mama in gaya mata tukun." Daga haka ta fita a dakin maimunatu ji tayi gwara ta tashi ta tafi gidan uncle sadam inda ba a san maganan ba,shikenan ta tabbata marwan zai mallaketa murmushi tayi tana kiyasta halin da zasu riski kansu ranan da aka ce sun mallaki juna, tana shirin mikewa wayarta ta hau ruri murmushi tayi dan ta san ba zai wuce marwan din ba amma me tana duba fuskar wayar ta ci karo da harafi daya da ta serving mamallakin number din da shi ba ko wani harafi vane sai harafin da sunansa ya fara dashi wato capital later Dan jim tayi tana kallon kiran,kaman kar ta picking sai zuciyarta tace mata meye amfanin avoiding calls dinsa? Picking tayi tare da yin shiru tana jiyo sanda ya sauke ajiyan zuciya sannan cikin muryar shagwaba yace "haba maimoon,mai na aikata haka me girma da zaki shareni kwana biyu sannan ni in na kira baki picking,kin san a halin da kika sakani kwana biyun nan kuwa? Gashi kinki ganina in naje gidanku sai ace min baki nan,why maimunatu?" Ya karashe magana yana wani sakin kukan shagwaba.4


Tabe baki maimunatu tayi tana ji kaman ta kurma ihu ko ta kudunduma mishi ashar dan takaicin shagwabar na sa sabanin da, da abin yake bata dariya.1


Juya idanu tayi tace "uhm" kawai dan ta ma rasa me zata ce mishi tana sake saken abinda zata ce mishi ta sake jiyo muryar tasa yana mata tabara "uhum mimi? Talk to me mana mimina." Bata san lokacin da magana ya fito bakinta ba "dont! Dont ever call me that again,baka da wannan daman na kirana da sunan nan." Ta sauke numfashi tana limshe ido dan cikin tsawa tayi maganan shima shiru yayi kafin cikin sanyin murya yace "am sorry,amma me nayi miki haka? Menene laifina? Pls ki gaya min domin na baki hakuri ina tsananin sonki maimunatu pls kar ki guje min kar ki bari wani ya shiga tsakanin mu." 4

"Babu abinda kayi min babu kuma wanda yake shirin shiga tsakanina da kai but i am sorry for wasting your time aure zan yi Tahir nan ba da jimawa ba."1

Wani irin zabura yayi yana cewa "no no no no pls kar kiyi min haka,kin san a halin da zaki sani kuwa matsaear kika yi min haka dan Allah kiyi hakuri ki saurareni wallahi i will explain everything to you amma kar ki barni yaya zaki yi min haka,yaya zaki kubce min a daidai wannan lokacin da nake jina me sa'a maimunatu pls ki saurare ni wallahi ba laifina bane sharrin shaidan ne har ga Allah na sota pls dont believe duk wasu abubuwa da ta ce miki kar ki badi mubeena ta raba mu ita ba gashi auranta zata yi ba." Gaba daya ma a rude yake bai san me yake fadi ba shi dai burinsa maimunatu ta saurareshi dan da gaske yake yana tsananin sonta.2


Maimunatu bata ji tausayinsa ko na kobo daya ba tace "ban gane me kake fada ba fa Tahir,me ya faru? Me yasa Mubeena zata rabamu kayi mata laifi ne?" Shiru yayi yana kokarin tariyo magnganun da ya gama fada cikin rudani. Kar dai mubeena bata gaya mata ko mi ba ya so ya tona ma kansa asiri? Bai gama tunanin ba ya jiyo sautin murmushinta.1


"Hmmm the cat got ur tongue? Tahir kenan you think zaka escaping sakamakon abinda ka aikatawa mubeena ko? Wrong! Allah ba azzalumi bane Tahir sai dai wanda ya zalinci kansa kai da karan kanka ka zalinci kanka anyway bani da hurumin gaya maka ko wani irin magana saboda duk wanda yayi mai kyau kansa yayiwa kuma maganan aure babu ruwan mubeena ina tunanin ko da maganan mubeena ko babu ba zan aureka ba kayi hakuri saboda i found my lost love ina maka fatan Allah ya hadaka kai ma da wacce zata soka tsakani da Allah kaima kuma ka sota haka." Ba ta jira komi ba ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya.

1

Tahir kam saroro yayi yana kallon fuskar wayarsa dake dauke da hoton fuskan maimunatu tana murmushi bai san yanda aka yi ya yi saken da soyayyarta ta yamutsa mishi zuciya ba.

A zabure ya mike kaman wanda aka tsikareshi keys dinsa ya kwashe ya fita daga gidan a guje yake tuki motoci sai kauce mishi suke Allah ne kadai ya kai shi inda zashi lafiya.1


Cikin sa'a yana shiga ita kuma tana shirin shiga motarta ita da kawarta da kuma cousin dinta suka tsaya suga waye ya shigo gidan haka, fitowan Tahir ya sata jan tsaki tayi kokarin bude motar ta kasa saboda yanda jikinta ke rawa.1


Bata ankara ba taji ya damko dantsenta ya fara janta keeee kallon kallo sauran yammata biyun suka tsaya yi dan dai sun san wannan ba muhammad bane gwara ma cousin dinta ta so ta gane face dinshi.1


STORY CONTINUES BELOW

Bai sadata da ko ina ba sai guest sitting room duk a idanun marwan dake tsaye kan balcony dinsa yana shan black tea murmushi ya saki sannan ya koma cikin sitting room dinsa.1


Wurgi yayi da ita cikin palon yace "Mubeena ko ma meye ya faru tsakanin mu i think is in sthe past ko? Toh amma wani munafurcin ne zai sa kije ki hadani da maimunatu? Shikenan dan wani abu ya taba shiga tsakaninmu sai ba zan yi aure ba? Toh naga ko ke da kike da tabon abin gashi nan zaki yi aure sai kice ni ba zan yi ba." Hancinta ta ja ba dan tana kuka ba sai dan masifa na cinta tace "zaka yi aure Tahir amma ba zaka taba auran wacce na sani someone i care for ba,ba zan taba bari macuci azzalumi mayaudari irinka ya auri someone innocent da na sani ba,maimunatu is beyond ur reach ba sa'ar auranka bane tafi karfinka kaje can wata duniyar ka nemi matar auranka amma ba maimunatu ba."

3

Sassauta murya yayi yace "dan Allah mubeena kar kiyi min haka kije ki ce mata da wasa kike yi wallahi mubeena ina tsananin son maimhnatu i can do anything to have her na tuba mubeena ki yafe min but kar ki shiga tsakanina da maimuna kuma ni ban yaudareki ba mubeena i loved you amma ban san me ya shiga kaina bane a wancan lokacin pls ki yafe min." Wani dariyar rainin hankali tayi tace "wato baka san me ya shiga kanka ba? Ni duk ba wannan ba i can do nothing for you dan in maimunatu na sonka babu wanda ya isa rabaku beside maimunatu na da wanda take so bata da lokacin karamin mutum irinka AURE zata yi."

1

Kalmar auren ita ta tunzura shi ya daga hannun zai kwada mata mari carab yaji an rike hannun yana juyawa suka yi ido biyu da marwan wani yawun wahala ya hadiye dan ya san marwan kaman yunwan cikinsa tsoronsa daya Allah yasa bai san tsakaninsa da mubeena ba.1


Cikin ina ina yace "yah uhn yah marwan ka ganta tana min rashin kunya dan nace ina son kawarta..aahhhhh." Ya sa ihu saboda yanda marwan ya juya hannunsa bai saki ba sai da yaji hannun yace k'as  sannan ya sake hannun yana lilo kallon inda mubeena take tsaye yayi idanun nan nata duk a waje yayi mata alamun ta fita daga dakin ai da gudu ta fice jikinta na rawa yayanta ya iya mugunta.1


"Babu abinda zan iya yi maka in huce Tahir saboda ka riga kayi min barna in nace zan sa hannuna a jikinka ko in sa a dake wallahi sai na kai ka har lahira shi ya sa ba zan kulaka ba zan barka da rayuwa ta koya ma hankali shawara daya kawai zan baka ka canza rayuwar nan dan bata da riba ka san waye ni ka san abinda zan iya aikatawa sai dai ni ka san bana abina da yaudara tunda na gaya maka ba riba toh ba riba Tahir you better repent ka koma ga Allah,one more thing ka fita batun maimuna dan maganan da nake maka yanzu akwai sadakina kanta bana ji ma su alhajinku sun baro gidansu a yanzu haka.

2

A mutukar firgice tahir da tunda marwan ya fara magana kansa yake a sunkuye ya dago yana kallon marwan lumshe manyan idanunsa yayi tare da daga mishi kai "stay away from her in kana son kanka da lafiya,zan iya yafe komi amma banda abinda ya shafi miemie."1


Daga haka ya juya ya bar Tahir a tsaye kaman statue kokarin daga hannunsa yayi dan ya shafa fuskarsa ya tabbata ba mafarki yake ba,amma sai me hannun yayi masa nauyi sai lokacin ya ji wani zugi ya ziyarci hannunsa.2


A hankali ya fara jan kafansa har inda motarsa take baya ganin kowa sbd yanda idonsa ya rufe hannunsa daya ya saka ya bude motarsa ya shiga.1


Shikenan yanzu ya rasa maimunatu? Ya san bai isa yayi takara da marwan ba, toh wani takara ma bayan manya sun shiga cikin magana bai san lokacin da ya fashe da wani irin kuka ba, sai da yayi me isarsa ya tayar da motan ya fice a gidan a guje yana tafe yana kuka ko gabansa bai kallo hakan ya janyo masa mummunan hatsari.1


Ko da aka kaishi asibiti ya goce a cinya bayan karayar da marwan ya riga ya jaza masa a hannu sai dai muce Allah ya ba Tahir lafiya.

1

Kwanci Tashi asarar me rai lokaci ya ja anyi auran mubeena,haka su maimunatu an gama service sai shirye shiryen auransu ake yi.

Tsabtattacen soyayya suke gudanarwa tsakaninta da marwan sosai yayi kokarin ganin ya kiyaye dokokinta dai dai da hannunta baya rikowa hakan ba karamin dadi yayi mata abu daya ta sani duk randa ta shiga gidan marwan mai kwatanta a hanunsa sai ya shirya.1


Ana sauran kwanaki auransu shi da Sadiq suka kawo mata ziyara wanann shine karo na farko da ta ga sadiq sai labarin juna da suke sha a wajen marwan sai da ya gama zolayanta sannan ya tafi ya barta da marwan din a palon saukar baki na gidansu maimunatun.1


"Miemie wai ina saurayinki ne dictective dan fulani?" Harara ta doka mishi tace "wani saurayin da duk ka gama korasu wai ma tun kafin ka tabbatar zan aureka ka wani korar min saurayi" murmushi yayi yana relaxing akan kujera yace "wa ya ce miki ban tabbatar zan aureki ba? Bari kiji tun ranan da na fara ganinki for the second time na san na mallakeki na gama dan ji nayi ko aure kike dashi sai mijin ya sakar min mata na atoh ba zan gama training dinki wani yazo yayi min awon gaba dake ba."2

Girgiza kai tayi tace "sannu mr pride,kai dai kawai kace kayi sa'a amma in fara so ne ai khalid ya ri..."1

"Naji naji ya rigani fara ganinki ko fara sonki whatever it is ni nafi kowa sonki ke in banda abinki me zaki yi da mijin wata bayan gani nan ina mutuwa ina tashi akanki." Dariya tayi tana rife ido tace "kwantar da hankalinka maimunatu ai taka ce jiya Habibarsa ta kirani wai tana so in tura mata acct details dina zata turo da kudin anko ni duk sai kunya ma ya kamani."1


"Kya ji kunya mana tunda da zaki aure mata miji yanzu gashi dan murna har asobe din bikinki zata yi kin rabu mata da miji ta huta,anyway na manta nace zan forwarding ma aunty khadija kudin 20 people kinga sai ki bata a ciki ba sai ta siya ba ki turo min da acct details din aunty khadijan."1


"Toh an gode Allah ya kara budi,but wanne zaka siya musu?" Ba tare da ya kalleta ba yana replying measage din sadiq dake jiransa yace "na dukka events din mana." Bata yi mamaki ba dan ta sna zai yi abinda yafi haka in dai akan wannan bikin ne.1


Mikewa tsaye yayi ganin haka yasa itama ta mike dan matsowa yayi kaman wanda zai shige jikinta har suna jiyo numfashin juna amma jikinsu bai taba ma juna ba cikin wani irin murya yace "i cant wait to have you mi amor." Limshe idanu tayi ta bude tare da hadiye yawu ta fito da halshenta dan wetting dry lips dinta dan lokaci daya taji bakinta da makogoranta sun bushe.1


Baya ya dan ja yana dariya ya fita ba tare da ya ce mata komi ba dan tsab ba tun yau ba ya san irin maimunatu.1


Ita kam kunya ne ya rufeta taji kaman kar ta fita  amma dole ta  fita ko dan ta yiwa sadiq sallama hada rai tayi ta fice.

1

Komi aka sa mata rana in da rai.....

Yau ne aka daura auran marwan da maimunatu, fadin irin taro da shagalgulan da aka yi bata lokaci ne amma garin abuja da kewaye sun shaida ana auran manya haka social media duk inda ka juya duk shafin da ka shiga shagalgulan auran ake yadawa da wanda suka sansu da wanda basu sansu ba.1


Haka dai aka yi taro aka watse lafiya aka sada amarya da gidan angonta.

Ina labarin ango marwan? Sai shiri ake za aje ga amarya ji yake yi kaman ya hutar da duk wani me rakasa zuwa gidan nasa amma ya san bai isa ba tunda ba kowa ne zai raka shi ba illa daddyn sa dan a cewarsa shine babban abokin dan nasa.1


Kasancewan kawayen nata duk sun tafi sai mubeena dake zaman jiran muhammad in sun rako marwan su tafi yasa marwan kutsa kai cikin dakin da suke zaune yace mubeena ta fita muhammad na waje ita kuma maimunatu tazo suje babban palon gidan.1


Nasiha sosai daddy yayi musu sannan ya sallame su ya tafi har jikin motarsa marwan ya rakasa sannan ya bawa sojan dake gate umarnin rufe gidan shima ya shiga ya rufe ko ina. Bai samu maimunatu a inda ya barta ba da alamun ta shiga ciki murmushi yayi ya shiga kitchen ya fito da plates sannan ya dauki ledarsa ta kajin amarci lol.1


Maimunatu a mugun tsorace take dan ta san marwan kaman yunwan cikinta alawla suka yi suka gabatar da nafilar sunna da annabi (SAW) ya umurta da ayi a daren aure ya dade yana musu addua sannan suka shafa.1


Wani kamshin dadi ne ya bugi hancinta wanda ya sa yawunta tsinkewa da ya bude naman juyewa yayi a plate kaman ba maimunatu da ta saba cin abinci a gaban marwan ba sai gashi ta kasa cin naman da kyar taci ukun da ya saka mata a baki sai fresh milk da tayi ta sha ita mamakin marwan ma take yanda yake abu kaman ba shi ba. Sai da suka gama ci ya tattara tarkacen ya fice dasu ita kuma ta dau riga da wando na bacci ta shiga bathroom tayi brush sannan ta canza kaya.

3

Ko da ya dawo bathroom din ya shiga yayi wanka ya fito cikin boxers ita dai tana kwance a takure a kan gado ya gana abinda zai yi sannan ya hawo gadon.

Rintse idanu tayi gabanta na faduwa tana ji kaman wannan shine karo na farko da ta hada shimfida da marwan ko dan tana ji a ranta wannan karon akwai abinda zai biyo baya bayan foreplay din da suka saba gabatarwa ne ko me yasa take feeling nervousness oho dan jin marwan din take a yau din kaman wani bakomta shiru tayi tana anticipating next move din shi. Ta kai 10 minutes a haka amma sai taji shiru dan gyara kwanciya tayi tare da juyowa zuwa ga gefen da yake kwance dan kyallara ido daya tayi dan taga me yake aiwatarwa yana kwance idanunsa na kallon ceiling yayi pillo da hannunsa daya yayin da dayan yake a kan cikinsa movement dinta ne ya sashi dan juyowa ya kalleta ganin idanunta a rufe ya sa shi mayar da kansa yanda yake.1

Mamaki ne fal ran maimunatun tun tana expecting jin saukan hannun marwan a jikinta har bacci barawo ya saceta dama ga gajiyar da ta kwasa ta shirye shiryen biki da hidimar bikin gaba daya.1

Yanayin saukar numfashinta ya sa shi sanin bacci ya dauketa juyo da fuskarsa yayi yana kallon cute face dinta ta cikin dim light din dakin cute small lips dinta ya tsurawa ido wanda are slightly open lashe na sa labban yayi dan jin su a bushe lokaci daya he want nothing more than to kiss them right now a hankali ya kai hannunsa kaman zai taba lips din da dan yatsansa limshe manyan idanunsa yayi tare da janye hannunsa ya dade yana sake sake a ransa har shima bacci ya daukeshi.
1
Washegari da safe da mamaki maimunatu take kallonsa anya marwan dinta ne wannan shi kam ko a jikinsa sai tsokananta yake yi amarya amarya ko da suka zauna breakfast ma shi ya feeding dinta amma har zuwa lokaci bai tabata ba abim ba karamin daure mata kai yayi ba cos the marwan she knows ba ta zama halaliyarsa ba ma couldnt take his hands off her amma yau gata ga marwan da igiyoyin auransa uku sarke da ita amma bai mata komi ba who will ever thought zata sha a daren jiya.1

Wayarta ce tayi ringing marwab da yafi kusa da wayar ya mika mata mikewa yayi ya shiga dakinsa  yana murmushi ganin mubeena ce ta kirata ya san ta kira taji kanun labarai ne wani murmushin ya kuma yi me fad'i a fili yace "irin ga maye"2

Da shakiyancin mubeena ta soma cin karo maimakon sallama rolling idanunta tayi tace "ke dai kina da matsala wallahi." Shewa mubeenan ta saki wanda ya sa maimunatu kawar da wayar daga kunnanta tace "wai ya naji muryarki garau ne unlike ni a washegarin ranan da aka kawo ni Allah i never expect zanji wahalar da naji ashe ba karamin gyara na sha ba kema kuma na san kin sh..."
"Wayyo Allahna mubeena naji labarin nan like a thousand time and yes muryana garau saboda ba yaki muka yi ba we just made love kuma ba kowa bane rago irinki." Wani irin ihun shewa mubeena tayi marwan ma da yake fitowa daga dakinsa cikin shirin fita da sauri ya koma saboda dariyar da ta ke shirin kubce masa.2

"Na shiga uku dare daya yayana ya bude bakin mems i cant imagine bakinki in a month mutum sai yayi da gaske naga uwar mijinki ta tashi da asuba ta mike pepper soup da kanta sai a zage a sha." Kallon warmer din da pepper soup din yake tayi tace "ai kuwa ban sha ba yanzu zan zo in sha ban iya cin wani abin kirki....."2

"Kinji bakinki ba appetite ko? Kisha zaki ji bakinki yayi dadi nima haka na tashi washegari." Mubeena ta katse ta dafe kai maimunatu tayi tace"auta sai da anjima wallah da akanki aka fara first night da mun shiga tara ba uku ba."1

Tana ajiye wayar marwan ya fito cikin shirin fita sai da gabanta ya fadi cos tama manta yana iya jin hiransu kame kame ta fara yi ganin haka ya saka shi basarwa yana karasa daura link din hannun rigarsa yace mata "babe bari in je in sallami su sadiq they wanted to come nace musu kina hutawa." Hadiye yawu tayi tace "ayya da ka barsu sunzo ai yanzu ma na san gidan za a fara shigowa "1
STORY CONTINUES BELOW
"Nah bana so su zo suna gane min amarya ne shi yasa nace musu haka." Ya karashe maganan yana kashe mata ido  sauke idanunta tayi tana wasa da yatsunta bata ankara ba taji saukan lips dinsa kan goshinta "ki kula da kanki." Daga haka ya saka kai ya fice ya barta a daskare a wajen.
Tunda ta shigo gidan wannan shine firat affection da ya nuna mata shafa goshinta tayi tana murmushi.1

Da wannan farin cikim ta mike ta gyara inda suka karya.
Wunin ranan yan uwanta da nashi da zasu koma a ranan ne suka yi ta zuwar mata, ta kwashe kwanaki uku tana dawainiya da da baki yan uwa da yan anguwa kullum a gajiye take kwanciya ko jiran marwan bata yi shima da baya wuni a gida sabida matan dake shigowa a kwanaki ukun nan har zuwa lokacij babu abinda ya wanzu a tsakaninsu.1

Tun maimunatu na mamaki har abin ya fara bata tsoro ko dai wani abu ya sameshi ne sai taga toh ai ba wai auratayya kawai bane basu yi sam bai shiga harkanta sosai baya wani zama suyi hira ko suyi wasanninsu yanda suka saba toh ko tayi mishi wani laifin ne? Tunda ko kafin bikin ba karamin namijin kokari yayi ba na ganin ya kiyaye sharudanta waro idanu tayi tace to ko dai har yanzu yana considering sharuddan ne gaba daya maimunatu ta zama confuse ta rasa tunanin da zata yi karshe kawai sai ta fashe da kuka.1

Kuka take yi sosai har aka kira magrib ta tashi tayi sallah ta roki Allah ya daidaita tsakaninta da mijinta ita ba love making din take bi ba ita she just want her marwan back wannan sarkin nacin da iko.1

Sai da aka yi sallan isha ta tashi ta canza kaya zuwa doguwar rigar bacci har kasa pant kawai ta saka a ciki ga rigar silk sai ta bi jikinta ta lafe dining ta nufa dan ta setting masa table taje ta kwanta da tayi niyyan tarar sa ta tambayesa ko tayi masa wani laifine sai taga rashin dacewar haka.1

Tana kokarin shiga yana shigowa duk sai suka tsaya cirko cirko shi bai shigo ba ita bata shiga ciki ba ya kurawa surarta ido nipples dinta that are visible yake kallo kaman ya kai musu cabka gyaran murya tayi tace "sannu da shigowa tana gyara hular kanta.
Da sauri ya karasa shigowa cikin palon jin muryarta a dashe ya karasa gabanta yana bin fuskarta da kallo dan yatsansa ya sa ya dago da habarta cikin sanyin murya yace "miemie kukan me kika yi?" Maimakon tayi magana sai bakinta da habanta suka fara rawa alamun wani kukan ya taho mata.1

Janyota jikinsa yayi ya rungume aikuwa ta fashe da kukam sosai rintse idanu yayi yana jijjigata sai da tayi me isarta sannan ta fara kokarin janye jikinta sassauta rikon da yayi mata yayi amma bai saketa gaba daya ba sai ya zagaye hannunsa a kugunta yana kallon fuskarta ita kuma sai kokarin boye fuskan take.1

Yace "toh yanzu gaya min kukan me kike yi a gidana? And dont u dare drop a single tear again." Jan hancinta tayi tace "ba komi." Hararanta yayi yace "ban gane ba komi ba kinyi kuka bana nan na tambayeki kin kara wani kukan and kina ganin i will believe ba komi kike kuka?" Tabe baki tayi tana kokarin mayar da hawayen da suka cika mata ido tace "uhm uhm ba kai bane?" Waro mata manyan idanunsa yayi yace "ni kuma? Me nayi? Yaushe ma na zauna a gidan balle in miki wani abun?" Dunkula hannunta tayi tana dukan kirjinsa tace "toh shine ai,baka zama dani,baka hira dani and u dont touch me." Ta karasa maganan a hankali yi yayi kaman bai ki ba yace "na'am" wani kukan ta kara fashewa da shi tana kokarin fizge jikinta bata ankara ba kawai taji ya hade bakinsu waje daya.
Wani irin deep hot kiss ya bata wanda ya sa notikan kanta kuncewa ko da ya sake mata bakin ta kasa tantance a inda take gidan daddy take ko gidanta na cyprus ko kuwa gidan marwan din na cyprus kafin ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi ya sunkuce ta in a bridal style zuwa dakinsa.1

Bata ji takunsa ba balle ta san sun isa saboda ji kawai take tana floating a sararin samaniya har sai da ya sadata da kan gadonsa maimakon ya mayar da bakinsa kan nata ah ah sai yayiwa lips dinsa masauki a gefen wuyanta hannunsa dukka biyu ya saka ya tattaro rigar zuwa hips dinta ya sada tafukan hannunsa da bare skin dinta da ya sha gyara daga nan kuma marwan da maimunatu basu san duniyar da suka fad'a ba amma hakan bai hana shi biyar da ita yanda ya kamata ba he took her so slowly and gentle indeed marwan made love to her in an unforgettable and romantic way.
2
STORY CONTINUES BELOW
Daga nan kuma fa amarci assalamu alaikum karshe ma visa yayi musu suka tafi cyprus where it all began sai daga baya yake gaya mata dalilin da ya saka bai nemeta saboda yana so ya tabbatar mata ita yake so ba wai jikinta kadai yes he is very much in love da jikinta amma maimunatu yake in a whole.1

Murmushi tayi ta kara shigewa jikinsa  a lokacin suna bakin pool din gidansu na cyprus tace "i doubted ur love i mistook it with lust but ban yarda zan aureka ba sai da na tabbatar da zuciyar marwan tawa ce ba wai gangan jikina kadai yake so ba ina sonka muddin raina sannan kana raina a ko wani lokaci" dan hancinta ya ja yace "nima kina raina ina tare dake bana tare da ke a ko wani yanayi *kina raina* miemien marwan." Kafin ta bashi amsa ya fara yi mata salon dake mayar da ita mute na karfi da yaji."1

Watan su daya a cyprus suna shirin dawowa kiran momy ya shigo wayarta da mamaki ta kalli marwan ta nuna mishi daga kafadarsa yayi ya cigaba da shan coffee dinsa dan har cikin ransa yake kin matar dan ya san abubuwa da yawa da suka faru da maimunatu akwai saka hannunta a ciki he just choose to keep quite dan ba huruminsa bane kuma duk inda aka je aka dawo uwa take a wajen maimunatu ita ta raineta ta bata tarbiya duk da a cikin ranta mugunta tayi mata amma taimakonta tayi ta wani gefen.1

"Maimunatu kinji wai daddy aure yayi bai gaya min ba?" Zaro idanu maimunatu tayi tace na shiga uku wani daddyn? Yaushe?" Cikin kuka tace "dazu yake gaya min fisabilillah ta ina na kasawa bawan Allahn nan maimuna ke shaida ce  irin kyautatawa mahaifinki da nake yi amma ki duba da me zai saka min na rasa wanda zan kira in ji dadi auntyna (matar uncle sufyan) ita da mijinta suna bayanshi maimuna ya zanyi wallahi ina son abdullahi duk wani abu na rayuwa na da nake yi saboda shi ne maimunatu ki taimakeni..." Gaba daya maimunatu sai ta gigice jin yanda momy ke kuka ta san momy iron lady ce kuma tana tsananin son daddy shi yasa ma take kishi da ita maimunatun.
2
"Momy ki nutsu dan Allah kiyi hakuri zan kira daddyn inji gobe muma muna hanya amma bamu da abinda za mu iya yi tunda kince an riga da an daura ko? Dama dai ba a daura bane ko ma dai yaya ne zamu yi magana da daddyn."1
"Ai shi yasa bai gaya min ba sai da aka daura dan Allah kisa shi ya saketa mainunatu." Saroro maimunatu tayi a ranta tace toooh kan momy daya kuwa ko duk kishin ne ya rufe mata ido ta manta daddy ne ya haifeta ba ita ta haife shi ba. Can kuma momyn tace "tsakaninki da Allah baki san yayi aure ba?"
Da sauri tace "wallahi ban sani ba." Ganin kaman momyn bata cikin hayyacinta yasa tace "momy kisha ruwan sanyi kiyi alawla kiyi karatun qur'ani ki samu ki nutsu ki cire duk wata damuwa a ranki insha Allahu muna bisa hanya."
1
Daga haka suka yi sallama mayar da dubanta kan marwan tayi da yake sauraronsu amma bai basu hankalinsa ba tace "baby kaji wai daddy yayi aure?" Murmushi yayi yace "ma sha Allah naji dadi kai Allah ya sanya alkhairi." Kankantar da idanu tayi tace "momy fa aka yiwa kishiya." Wani kallo yayi mata yace "you are not serious." Ya cigaba da abinda yake yi kunkuni ta kama yi tace "ai bari in kira daddyn ana zaman lafiya ya kama yin wani aure duk yanda momy take kyautata mishi." Shi dai marwan bai ce mata komi ba sai ma murmushi da yayi yana danna wayarsa.1

"Hello daddy wai da gaske kayi aure?"
Ta fada cikim takaici
"Waoh maimunatu babu ko gaisuwa? Daukan zafin na miye?"
Cikin marairaicewa tace "haba daddy ana cikin zaman lafiya ka karo wani aure? Yanzu fa momy ta kirani hankalinta a tashe wai kayi aure sai sambatu take yi."
Murmushi yayi me sauti yace "ita momyn taki ta kiraki tace miki nayi aure?" Gyada kai tayi kaman tana gabansa tace "eh kuma sai kuka take yi." Yace "amma ta fada miki wacece amaryar?"1
Cikn sanyin jiki tace "ah ah daddy,wacece?"
Yar dariya daddy yayi yace "toh auntynki khadija ce kanwar mahaifiyarki."  Wani irin ihun murna maimaunatu ta saka wanda ya sa daddy kashe wayar yana murmushi.1

Jikin marwan taje ta fada tana murna "baby daddy ya auri aunty khadijata wayyo Alhamdulillah wai baby i cant keep calm." Murmushi yayi yana jan kunnenta yace "kar ki kara yin irin wannan tsallen i dont like it sam is not healthy for you."1
STORY CONTINUES BELOW
"Kash! Babe ce maka fa nake dady ya auri aunty khadija." Dukka giransa ya daga mata yace "na sani ai dazu su daddyn mubeena suka tafi daurin auran."1

Waro idanu tayi tace "and you dont think ya kamata ka gaya min?" Daga kafadu yayi yace "ba gashi mamanki ta gaya miki ba?"  Kara kwalo idanu tayi tace "wayyo Allahna ya zanyi da momy?"
1
Washegari saukar yamma suka yiwa Nigeria a gidan su marwan suka sauka mami sai nan nan da ita take yi musamman ma da yake da zazzabi ta sauka kaman wacce ta hau jirgi a karo na farko.

Hakan ya sa suka kwana a side dinsa na gidan duk yanda maimunatu ta so suje gidan daddynta a ranan marwan bakam yayi mata.

Washegari da kyar ta kai tara mami sai dariya suke mata tare da mamin duk suka dunguma suka je sunje sun tarar da gidan shake da yan zariya tuni maimunatu ta shige cikin yan uwanta ana raha nan momy ta kara tabbatarwa blood is thicker than water dan sai can rana maimunatu ta shiga wajenta tana bata hakuri ita maimunatu kunya take ji ta fuskanci momyn.1

Maimunatu sai nan nan ake da suruka gaba daya ta cike mata gaba da abincika kala kala yan uwanta sai tsiya suke mata itama mamin idonta na kan maimunatun da taga zata fara wani aikin wahala zata ce kai ku kira min maimuna ba dadi take ji ba maza mufliha nemo min ita (da yake itama tazo ta samesu a gidan) gaba daya kowa a wajen sha'awar mu'amalansu ake sai la'asar driver ya mayar da mami ita kuma sai da aka yi magrib marwan ya zo ya dauketa.
1
Satinsu daya da dawowa kowa ya koma bakin aiki inda maimunatu take kan kujeran mubeena dake dauke da tsohon ciki itama da nata karamin cikin.1

Tsakaninta da ma'aikatan wajen sai girmamawa kowacce yarinya ta kama kanta dan a gaban uban kowa marwan ke nuna son matarsa in ya ga dama a tsakiyar meeting zai janyo hannun abarsa ya kissing babu kuma wajen da ya zaman masa shamaki a ma'aikatar  a ko ina zai rungumeta a ko ina zai kissing dinta kowa ya san irin soyayyar da moh yake yiwa matarsa haka nan sun sha su ci karo da hotunansu a social media an dauke su basu sani ba cikinta na fara fitowa kuma habawa kulawa da soyayya babu kama hanun yaro.1

Bayan dogon jinya tahir ya dawo aiki amma yana dingishim da sai ka lura ka san yana yi sosai yayi nadama har cikin ransa yake son maimunatu amma bashi da yanda zai yi.1

Tsakanin habiba matar khalid da maimunatu zumunci suke yi ba laifi tun maimunatu na jan jiki har ta hakura suke zumuncinsu marwan duk yanda khid ya shige masa yaki dan sosai yake kishinsa.1

_few years later_
Yarinya ce yar kimani shekaru uku a duniya  sai guje guje take yi ta hau wannan kujeran ta dira a wancan maimunatu dake zaune da cereal a hannunta ga katoton cikimta ta saka shi a gaba sai fama take da yarinyan "meena wallahi kar ki bari in mike ba zaki zo ki ansa abincinki ba ?" Yarinyan kamar ba da ita ake yi ba ta cigaba da tsalle tsallanta yunkurawa maimunatu tayi ta mike Allah ya bata sa'a ta cabko meenan dungure mata kai tayi sannan ta zaunar da ita ta fara bata abincin sam taki nutsuwa ta karba karshe ma sai da tayi sanadin da ya zube  a jikin uwar ai ko rankwashi ta sakar mata da ya sakata kwanciya a kasa tana birgima hannunta dafe da kanta.1

Cike da takaici take kallonta sai ihu take yi kaman wacce ta zane "yi min shiru ko in tashi in babbalaki a nan wajen sakaran yarinya kawai."1
Da sauri marwan ya shigo wurgi yayi da brief case dinsa ya isa ga babynsa cak ya dagata ya dora a kafadarsa yana jijjigata tsaki maimunatu taja wani irin mugun kallo ya aika mata da shi itama ta harareshi har da murguda baki bai ce mata komi ba ya wuce da yarinyan a hannunsa
"Aikin banza sannu me ya da yake kai ka dau cikinta ka haife ko kai take bawa ciwon kai hararanka ba shi zai hanani kilanta ba in ta min." Tana mita tana tattara wajen karshe dai dole ta kira a zo a gyara ta wuce dakinta dan gyara jikinta.1

Tana fitowa wanka ya shigo dakin hararansa tayi shi kuma ya sakr mata murmushi ta baya yaje ya rungumeta dan yanzu rungumeta ta gaba ya dawo aiki "yi hakuri mana babyna kin san sam ban so kina dukan meenah amma ke saurin hannu gareki." Ta cikin mirror ta kara banka masa harara tace "ga babynka can meena bari in haihu kuga in akwai wamda zan kula a cikinku ni yanzu ai na san ka daina yina."1

"Wa ya gaya miki? Kema kin san *KINA RAINA* Duk son da zan wa yarana dabban ne da wanda nake miki." Yana maganan yana cusa kansa tsakanin  wuyanta cikin sarkewan murya tace "ina meenan?" A takaice yace "tayi bacci." Yana warware towel din jikinta a hankali ya jata zuwa bed dinta ya kwantar yana sarrafa boobs dinta that are full and firm saboda ciki.

Cikin shagwababbiyar murya yaji ance "*Papah*"4
Alhamdulillah Allah yayi yau mun kawo karshen wannan littafin by Allah ni karan kaina ina jin kaman kar ya kare ba wai dan yayi min dadi ba sai dan yanda kuke bina ba tare da gajiyawa ba ina mika godiyana

Post a Comment for "KINA RAINA CHAPTER 10 KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...