KAMAI NISAN JIFA CHAPTER 3 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KAMAI NISAN JIFA CHAPTER 3
KAMAI NISAN JIFA CHAPTER 3

Wani irin kishine ya tokari Atif a k'irjinsa amma seya nuna kamar baiganiba ya k'araso gun Farhan suka gaisa tare da tab'a hira sannan suka wuce.
Mubinat tana k'ok'arin shigewa d'akinta setaji an janyota ta fad'a jikin mutum. Fiskarsa ya manna da nata yayinda sajen fiskarsa yake gogan  gefen fiskanta yace "Where are you coming from?"
Nanne ta gane cewa Ya Atif ne "Nakaiwa Ya Farhan key ne,harka dawo?"
"Yeah na dawo,i'm just missing you shiyasa nadawo dan inganki"
"Hhhh,kasan dai nan bamukad'ai bane ko?"
"Eh ai babu wanda zaizo"
"Umma tana cikifa,kuma at any time zata iya fitowa"
Jin hakan yasa ya saketa,juyowa tayi tare da d'aura hannayenta akan kafad'arsa tace "Yana ganka hakane,kodai yunwa kakeji?"
Cikin shagwab'a yayi maganan "kawai inaso injiki kusa danine"
Ganin yanayinsa yasa ta rungumesa tsam sannan tayi magana cikin raha "i'm here my luv,dan haka ka dena damuwa"
Dad'i yaji mara misaltuwa ya sake matseta sosai shima yana shak'ar k'amshin jikinta mai dad'i. Sallamar su Farhan ne yasa yayi saurin saketa tare da shafan kansa yace "Bismillah"
Ita kuwa Mubinat d'aki ta wuce cikin hanzari dan taji kunya sosai.
Tunda Farhan yagansu ahakan seya fara tunanin wato har habibty ta manceni cikin sauk'i haka,ga dukkan alamu yanzu naga sun shak'u sosai, Allah ya basu zaman lafiya nikuma ya Allah ka ciremin k'aunar matar wani azuciyata.
Tunda mubinat ta shige d'akinta take zaune ta kasa fitowa dan kunya datakeji. Muryan Umma taji tana kiranta,hijabin jikinta ta cire sannan ta rufe jikinta da gyalenta ta fito,duk suna zaune akan daining harda Atif d'in. Cikin sanyi jiki ta wuce kichine "Gani Umma"
"Mekikeyi a d'akinne,kije ki zuba musu abincin"
"To" sannan ta wuce.
Plate hud'u ta zuba abincin,sannan tasa miya a uku ta mik'awa Shureim sannan Atif se kuma Ahmad.
Shureim ne yace "Sis Mubi yabaki fara bawa Ya Farhanba,ai shine bak'o"
Farhan ya katseshi da "To saurin me kakeyi,kamata yayi ta farabawa Atif kafin ta bamu"
Jikin Mubinat yayi sanyi dajin kalaman Farhan,dan wani irin fassara tayiwa kalaman nasa.
Tasan miyan da yaji,shi kuwa Ya Farhan bayacin yaji,dan haka ta bud'e wani kula ta zumo mishi sorce d'in hanta wanda ita da kanta tayi danshi kad'ai.
Bayan ta zubane tanada niyan mik'a mishi,amma seyace "Kibarshi kawai zan d'auka"
Sam bataji dad'in hakanba,shikuwa bada wata manufa ya fad'aba.
Kallon Atif tayi tace "Ya Atif zanje gun Amal"
"Amma dai kinsan bakici abinciba ko?"
"Eh idan na dawo zanci"
"No Sis Mubi kici kafin ki tafi"
Marairaicewa tayi "Dan Allah Ya Atif yanzufa zanje in dawo"
Yadda tayi maganan yasa Farhan da Ahmad suka kalleta. Dukda tasan cewa sun kalleta,seta sake cewa "Kaji please?"
"Shikenan kije,but karki dad'e"
Murmushi tayi tare da cewa "Done" sannan ta fice.
Kowanne acikinsu da abinda yake tunawa aransa.
Bayan sun gama cin abincinne kuma Shureim yashiga da kwanukan kichine. Sallamar Amal da Mubinat ne ya katsesu da hiran da sukeyi.
"Ina wuni Ya Farhan?"
"Lafiya Amal yakuke?"
"Lafiya lau,kadawo lafiya,yasu Ummi?"
"Lafiyansu lau duk sun gaisheku"
"To muna amsawa,sannan ta kalli Ya Atif suka gaisa se kuma Ahmad.
"Wato shine kikak'i fitowa seda k'awarki taje ko?" Cewar Ahmad.
Shuru Amal tayi batace komaiba,inda Mubinat take murmushi tace "Ashedai haka abin yake,hmmm to Allah ya tabbatar da alkhairi tunda kin b'oyemin aigashi ya fito fili."
Kunya sosai Amal taji,musamman ma da Ya Farhan yake zaune agun.
Ahmad ya mik'e tare da cewa "Mu muna daga waje kafin ku fito" murmushi sukayi sannan Amal tabishi cikin jin kunya.
Shureim ne ya k'yalk'yale da dariya yace "Abun yayi" kowa dake parlour seda yayi dariya,Sis Mubinat ce tazo taja kunne shi tana cewa "Ka fara koyon iyayi ko?"
Ihu Shureim yayi "Wayyo Ya Farhan kaga tana jamin kunne ko,kace ta rabu dani"
"Baza'a rabu dakai d'inba seka gayamin dalilin dayasa kasa bakinka acikin maganan"
"Wayyo Ya Farhan... "Yihak'uri Sis Mubi bazai sakeba"
"Ya farhan wlh seya furta da bakinsa"
"Tokaji"
"Wlh bazan sakeba" ya fad'a.
Dariya sukayi harda Atif sannan ta wuce d'aki. Muryan Atif taji yana kiranta dan haka ta dawo "Gani"
"Mik'ewa yayi "zanje ana nemana,amma bazan dad'eba zan dawo zauna kuyi hira mana kafin Ahmad yadawo"
"To seka dawo,please d'inkina Ya Atif,dan yanzu ya kirani agidansu Amal waiya gama"
"Ok badamuwa" ya furta tare da bata peak agoshinta sannan ya fita.
Tunda ya fita taketa binshi da kallo har sedaya bar gidan. Ajiyar zuciya ta sauke sanan ta zauna tana kallon Farhan inda suketa hira da Shureim.
"Ya Farhan" ta kira sunanshi.
"Na'am" ya amsa yana mai kallonta
"Wai har yanzu baka tuna daniba?"
"Sis mubinat ce mana"
"Shureim tashi ka bamu guri" cewar Mubinat
"To" Shureim yace sannan yabar parlour'n.
Kallon juna suka tsayayi sannan tace "please Ya Farhan ka'ajiye wasa agefe ka gayamin gaskiya dan Allah"
"Sis Mubi nasanki a matsayin k'anwata mana kamar dai yadda na d'auki Shureim"
"Haba Ya Farhan,nifa masoyiyar kace abin begenka,kaunace mai k'arfin gaske a tsakaninmu meya zaka mance duk wannan ne wai? Abin yana min ciwo sosai azuciyata wlh"
"Kiyi hak'uri habibty,amma bazan tab'a sanar dake cewa nasan alak'ata dakeba hakan shine zaifi zama alkhairi agemu dukka... katse mishi zancen zucinsa tayi da cewa "meyasa kayi shuru kake kallona Ya Farhan?"
"Sis Mubi idan kina fad'an hakan kunya nakeji wlh,danni sam bansan duk wad'annan kalaman nakiba."
"Shikenan Ya Farhan,naji kuma nagode insha Allah bazan sake maka magana akan hakanba,katayani da addu'a Allah ya ciremin k'aunarka acikin zuciyata Ya Farhan,dan babu amfanin ajiyarta ayanzu, danta hakanne zan samu damar dasa soyayyar Ya Atif acikinta in kuma iya mallakamasa kaina amatsayina na matarsa...!
   Tana kaiwa nan ta fashe da kuka tareda wucewa d'aki dagudu.
Rufe idanunsa yayi tare da furta "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,nanemi da indawo nigeria ne dan indinga kallonki habibty,ashe kuma haka zanzo in tarar,i'm sorry for hurting you habibty,i'm really sorry" sannan ya fice daga parlour ciki damuwa.
Duk abinda yake faruwa akunne Umma,damuwane cike azuciyarta,wato dama babu wani abu daya shiga tsakanin Atif da Mubinat?
Lallai Atif yayi k'ok'ari aure kusan wata uku, zata gamu dani wlh dannasan daga gurintane.
Wayanta ta d'auka ta kira Atif,cikin hanzari ya d'auka yayinda take goge k'wallanta yace "Hello Sis Mubi yane?"
"I miss you Ya Atif,dan Allah ka dawo mufita tare"
"Alright i'm on my way" yafurta yana maijin dad'i sosai har cikin ransa tare da tunanin yanzu kam Sis Mubinat tafara sonshi.
Jin horn awajene ya tabbatarwa Mubinat cewa Atif ne. Dama ta gyara fiskanta harda powder dan haka kai tsaye ta wuce tare dacewa Amal "Mun tafi unguwa semun dawo"
"To Allah ya kiyaye hanya" cewar Amal
"Ameen" sannan ta fice.
Tana shiga motar ta rungumeshi,murmushi yayi sannan yace "Ashe dai dagaske kikeyi"
"Au daka d'auka dawasa nakeyine,i'm serious and i love you so much"
"You love me as your broth...shhhhhhh "No, as my husband Ya Atif,i love you so much."
"Are you kidding me Sis Mubi?"
"Hmm,meyasa ka kasa yadda da abinda kaji na furtashi da bakina? Ya Atif daga yau na mallaka maka kaina daduk wani abu dana mallaka,kayi duk abinda kaga dama dani bazan sake dakatar dakaiba Yamijina."
"Alhamdulillah" cewar Atif, farincikine tun daga cikin  zuciyarsa harta bayyana akan fiskarsa,wanda ya kasa dakatar da hakan..."Alhamdulillah Allah nagode maka daka amsamin addu'ata cijin sauri" cewar Atif.
Murmushi tayi tace "Dama haka rayuwa take Ya Atif,ban tab'a tunanin cewa bazamuyi aure da Ya Farhan ba,dama kana naka Allah yana nashi,na hak'ura da Ya Farhan sedai har yanzu akwai k'aunarsa acikin zuciyata wanda nasan se'a hankali zaifita... shuru tayi tana hawaye tare da kallon fuskar Atif,sake rungumeta yayi yana rarrashinta. Cikin zuciyarsa kuwa cewa yake "I'm sorry Sis Mubinat,i'm so sorry for hurting you,i hope you will forgive me one day."
Bayan ya share mata k'wallan fuskantane sannan suka kama hanya,juyowa tayi ta tambayeshi "Ya Atif ka karb'amin d'inkin nawa?"
Juyawa yayi yana kallon seat d'in baya,wanda itama ta juyo da ido tana kallo. D'inkintane acikin leda ta hango,murmushi tayi tare da cewa "Thankyou love"
Peak ya manna mata akumatunta dan yaji dad'in sunan data kirashi dashi "Love."
Suna tafiya suna hirarsu mai dad'i yayinda take bud'e d'inkunanta tana yaba irin kyan da sukayi.

Tun daga nesa suke hango wani mutum yana zane wata da bulala babba ahannunsa yayinda mutane suketa taresa amma ina!
"Subhanalillah" Atif ya furta tare da saurin tsayar da motarsa agun ya nufi gun mutumin yayi saurin  rik'e bulalan tare da tambayansa "Malam lafiya haka kake dukan mace akan titi hala 'yarkace?"
Ganin yadda yarinyar take birgima da ihu saboda dukan datasha yasa Mubinat ta kashe motar  tare da zaro key ta fito tazo inda suke.
"Ai wlh koda kasheta ma nayi baza'a tuhumeniba,shegiya asararriya wlh Allah ya isa tsakanina dake! Cewar wannan mutumin.
"Subhanalillahi,dan Allah Malam kadena mata irin wannan mummunan furuci baikamataba" cewar mutanen dake tsaye agun.
Mubinat da sauran matan dake gurin suka d'agata tare da kakkab'e mata jiki suna bata hak'uri tare da tambayarta "Mahaifinkine?"
Cikin muryar kuka tace "Miji nane"
Mamaki ya kama duk wanda yake gurin harda su Atif dayake sunji abinda tace.
"Mijinki?me kika aikata masa haka yake miki wad'annan mummunan kalamai kuma yana matsayin mijinki baiwar Allah?"
"Sam banga laifinsaba wlh,kubarshi ya hukuntani yadda ya kamata,imma yakaiga kisa tofa karku tuhumesa."
"Kidena fad'an haka 'yar'uwa,wa kika kashe mishi dazakice haka?" Cewar Mubinat.
"Ai gwanda ta kasheni wlh,wlh gara ta kasheni insan bana raye gabad'aya da wannan abu data jajib'o mana" cewar mijin.
Hankalin kowa seya tashi agurin.
Mubinat tace "Kinga baiwar Allah, karkice na miki shishshigi amma dazanso insan abinda kika aikata haka dahar zaisa mijinki ya baro cikin gida yazo har kan titi yana dukanki a idon duniya tare da kalamai mara dad'inji haka."
Yarinyar ta kama hannun Mubinat "Yar'uwata ke matar aurece?"
Mubinat tace "Eh nimatar aurece"
Yarinyar ta sake cewa ku nawane agun mijinki?"
Mubinat ta kalli Atif sannan tace "Nikad'ai ce."
Yarinyar tace "Shinkin kasance kina amfani da magungunan mata?"
Mubinat taji kunya sosai,amma seta daure tace "koso d'aya ban tab'a amfani dashiba."
Yarinyar seta saki hannun Mubinat tare da juya musu baya ta fara magana kamar haka...

Nida mijina soyayya mai tsafta mukayi kafin mukayi aure,matansa uku nice ta hud'u.
Kowacce gidanta dabanne,yana da yara tawkas aduniya. Bayan aurenmu da wata biyu k'awayena suka fara zugani akan infara amfani da maganin mata saboda wai bani kad'ai bace agun mijina.
Da fari dai sam band'auki shawarar suba,amma daga baya sena fara tunani akan maganganunsu,wanda hakan yasa nabi d'aya daga cikin k'awayena muka fara zuwa gun wata mata da ake kira da Hajiyan Juyi.
Hajiyan juyi ta shahara sosai ta fanni saida maganin mata,muddin kika sayi magani agunta to lallai zakiga aiki babu kokonto.
Ita dai Hajiyan juyi tayi aure,amma seta raba Uwa da D'anta ko kuma ta raba mata da miji saboda aiki da takeyi da maganin mata. Gabad'aya d'auke hanali miji take sedai abinda tace dashi,hakan yasa iyayen mijinta suke raba aurensu. Hakan yasa bata zaman aure,duk gidan da aka aureta tofa seta raba mijin da iyayensa,matansa,harma da 'ya'yansa. Kuma koda namiji ya rabu da ita to wlh seyayita bibiyarta kodan samun biyar buk'atarsa sannan ya zuba mata kud'i mai yawa.
Ganin yadda take samun kud'ine seta mayar da abun kamar sana'a. Sannan bata sauraron k'anana da manyan mutane take harka wanda a rana d'aya zai bata dubu hamsin.
Wata rana wani d'an isa d'an duniya irinta yaje suka gama abinda zasuyi sannan ya sallameta.
Hajiyan juyi bata fasa had'a magungunan mataba na sayarwa kuma masu tsada sosai. Dan d'an k'ulli garin magani da zaki shanye atake kawai to dubu gomane,amma fa idan kikayi amfani dashi tofa lallai sekin sami fiye da haka agun mijinki. Intak'aice muku seda mijina ya rabu da gabad'ayan matayensa saboda yadda Hajiyan juyi ta fito dani. Magunguna kala kala take had'amin kuma sam bana ganin tsadansu.
Ninasa mijina ya dawo da sauran matayansa daya saka, saboda na zama tamkar gimbiya 'yar gidan sarki,duk abinda na tsara dashi yake aiki kuma ya d'aura sauran matansa akai.
Wata rana Hajiyan juyi ta had'a wani tsimi mai suna "Yankan wuka" wannan tsumin a wani k'aramin roba take zubashi wanda roban bai wuce k'ananan roban youghot ba. Cikin wannan roban dubu sha biyar take sayarwa,sannan ta zubasu a wannan robobin sunfi guda d'ari saboda daga wani states ma zuwa ake ana saye ko kuma aturo mata da kud'in ta account sannan tasa kayan a tasha akai maka duk inda kake so.
Bayan na sayi tsumin nida k'awatane muka koma gida,chokali uku kawai zaki sha arana atake zaki fara jin aikinsa kekanki bare kuma wanda akayi dominshi. Wallahi 'yan'uwana washe garin da safe mijina ya sayo min mota E O D sabuwa dal,ya canja min komai na kayan d'akina,ya sayomin iphone 7 sannan tare muka tafi aikin hajji dashi dayake dama duk sauran matansa sunje. A hajjinma seya d'aukeni munje hotel nabiya masa buk'atarsa sannan mudawo masaukinmu. Nikaina mamakin kaina nakeyi wallahi,bazan iya tuna irin kud'ad'en dana samu agunsaba,dan nakai iyayena hajji,ya sayawa babana mota 4O6,sannan ya gyara mana gidanmu ya kuma baiwa mahaifiyata jarin dubu d'ari biyu. Kai duk wani na gidanmu sedaya taimakawa,lokacin aurenmu wata takwas.
Wata rana natashi da rashin lafiya sosai,mukaje asibiti,bayan gwaje-gwaje da akamunne result ya fito wai ina d'auke da HIV AID'S... "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" su Mubinat da sauran mutanen dake tsaye agun suke furtawa yayinda ita kuwa yarinyar take kuka sannan taci gaba da cewa
Mijina yayi mamaki sosai,dan yasan bana tarayya da wani,hakama kuma shi sam baya neman matan waje. Kuka naketayi ina cewa wlh banyardaba ta ina zan samu HIV? Doctor ya tabbatar da cewa lallai ina d'auke da ita wlh,hakan yasa mijina shima yace amishi test d'in,koda result d'insa ya fito duk iri d'ayane da nawa. Hankalinmu ya tashi matuk'a,wayansa yaciro ya kira wani kan cewa aje a d'auko sauran matansa ukun domin ayi musu gwajin suma,ai kuwa mata biyun duk suma suna d'auke da cutar,Uwargidansane  kawai batadashi. Doctor yace "Yaushe rabonka da Uwargidanka?"
"Tsawon wata uku kenan,tun kafin ta haihu kuma har yanzu jego takeyi." Cewar mijinmu.
Doctor ya sake cewa "Kana nufin da wad'annan ukun kawai kake tarayya baka neman matan waje?"
Mijinmu ya bashi amsa da "Eh"
Haka dai akayita tambayarmu muna bada masa dukkanmu, daga k'arshema mijinnu ya tabbatarwa doctor cewa ya aminta damu sosai babu wacce take bin maza acikinmu.
Haka muka dawo gida da sanyin jiki kowa hankali atashe. Wayar k'awatace nagani kamar bazan d'aukaba se kuma na d'auka. Kuka takeyi tare da sanar dani damuwarta irin nawa sak,mamaki ya dad'a kamani,nan dai nima na gayamata nawa,sannan harda wasu k'awayenmu su biyu take sanar dani. Intak'aice muku yazamto mutane sama da talatin kowa damuwarta irin tamuce.
Ana cikin hakanne sega sanarwa agidan radio daga bakin Hajiyan juyi..

Assalamu alaikum 'yan'uwana mata,nice wadda kukafi sani da Hajiyan juyi. Nazo gidan radio ne badan komaiba sedan innemi gafarar ku daku da mazajen ku akan zalincin ku danayi.
Kamar yadda kowa yasan wacece ni ya kuma san sana'ata,tun bayan da wani d'an iska yayi tarayya dani na kamu da ciwo mai zafin gaske,ko danaje gun doctor se aka tabbatar min da cewa ina d'auke da cuta mai karya garkuwar jiki.
Hakan yasa na dakata da wannan sana'ar tawa,amma masu cuta irin tawa sukanzo muyi abinda muka saba.
Bayan nan nayi tafiya domin inje sayo kayayyakin da nake had'a maganin mata dashi,na kashe kud'i sama da dubu d'ari biyu da hamsin akan magun gunan. Bayan na dawone daga tafiyan sena zauna domin had'a tsimina mai suna "yankan wuk'a".
Na gama had'a komai da komai a cikinta,sena manta ban yanka d'aya daga cikin had'in ba. Na d'auko wuk'a ina yankawa,sakamakon kaifin wuk'anne sena yanke tafin hannuna yanka sosai. Kan in mik'e daga inda nake jini yayi ta zuba acikin wannan had'in tsimin dake gabana,ni kuma gaskiya bana jin zan iya zubar da wannan stimin dan kud'i mai yawa na zuba a kanshi gashi kuma gaba d'aya na had'ashi babu ragowa. Sam banyi tunanin wannan d'an jinin nawa daya zuba a cikin tsimin zai haifar da matsala ba,se dana je na tsaftace hannuna dana yanken kafin nazo na k'arasa had'a tsumin. Shikanshi tsimin dama bak'i-bak'i yake kuma jaja-jaja,dan haka na zuba acikin robobi na ajiye akazo aka sayesu tas harma ana neman wasu saboda tsabar k'warewa ta a wannan harkan.
Bayan na koma ganin doctor ne nake masa tambaya cikin dabara akan abinda ya faru da tsimina,doctor ya tabbatar min da cewa lallai mutane zasu iya kamuwa da cutar danake d'auke da ita.
Tun daga wannan lokacin se hankalina ya tashi sosai nashiga damuwa fiye da tunanin mai sauraro,saboda mutane sama da dubu d'aya suke sayan kayan mata a gurina,idan akace duk sun kamu da wannan cuta aina shiga uku,musamman ma masu kishiyoyi. Kullum cikin kuka da damuwa nake, na zauna zaman jiran abinda zaije ya dawo,wata uku na farajin k'ishin-k'ishin,kan in ankara naji anata zance mace ta kamu da cuta kuma bata bin namiji, lokacin danaji aminaina suna wannan hiran, shikenan nasan lallai maganar doctor ya tabbata hakan yasa nazo gidan radio domin neman gafarar ku dan Allah kuyafe min ni Hajiyan juyi yau duniya ta juyoni gareku...
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" mutanen dake tsaye suna sauraran bayanin wannan yarin yar suketa maimai tawa.
Taci gaba da cewa "wannan shine abinda nama mijina,na halaka shi na halaka kaina harma da sauran abokan zama na. Tir da mai hali irin nawa...
"Tabd'i" cewar Mubinat, amma gaskya baiwar Allah na tausaya miki, domin kin d'auki alhakin 'yan uwanki da mijin ki. Ta dubi tarin matan dake tsaye agun duk jikinsu yayi sanyi dajin labarin.
Su kuwa mazajen cewa suke "Allah dai yasa matata bata d'aya daga cikinsu" suka yiwa mutumin jaje sannan suka wuce gida cikin sauri dan suje su d'ibi matan su zuwa asibiti. Atif ya dubi Mubinat wanda taketa bayani mamaki ne ya kamashi sosai, ganin ita dai yarinya ce 'yar kimani shekara ashirin aduniya amma gata gaban manyan mata wasuma iyayen tane tana musu bayani kamar wata malamar su tana cewa...

"Haba 'yan uwana dan Allah mu dena yaudarar kanmu."
"Ina da wata k'awata mai suna Aisha Kabir, k'ila wasu daga cikinku sun santa,dan mahaifinta babban mutum ne agarin nan."
"Tare muke koda yaushe dani da ita da kuma Amal, Aisha ta aminta da maganin mata sosai tun muna 'yan mata komai aka bata sha takeyi. Munyi-munyi da Aisha tadena sha amma tak'i, ana aurenta saura wata uku Aisha tazo mana da wasu magun guna wai ance yana had'a mace ta matse sosai, mudai munk'i amin cewa dashi kuma mun hana ta amma tak'iji seda tayi amfani dashi. Dana matsi dana sha da kuma na tsarki duk tayi amfani dasu.
Kuma saya takeyi sosai sedai idan bataji ance ga sabon fitowa ba.
Bayan bikin Aisha da wata biyu ta fara rashin lafiya, kowa tunaninsa ciki Aisha take d'auke dashi, amma da akaje gun doctor se yace ba ciki bane kawai dai zazzab'i ne, akayita jinya zazzab'i yak'i tafiya se aka koma gun doctor. Bayan an gama dukkan bincike ne se aka gano cewa kansa ne da ita, kuma kansan a gabanta yake. Ita kanta tayi mamakin abinda doctor yace,wlh tun daga lokacin Aisha tasa damuwa a ranta ciwo yak'i warkewa, kuma ta sanar da doctor cewa maganin mata ne take amfani dashi tun tana budurwa wanda muma shaidane akan hakan.
Intak'ai ce muku watan Aisha hud'u a d'akin mijin ta Allah yayi mata rasuwa."
Mubinat ta tsaya da labarinta anan tana share k'walla tare da fad'in "Allah ya jik'anki Aisha" mutanen dake gurin suka amsa da "Ameen"
Mubinat taci gaba da cewa "Me yasa muke yaudaran kanmu ne mata? Inba yaudaran kaiba kina budurwa meya kaiki amfani da maganin mata wai kina matsi dashi? Kuna tunanin akwai wani maganin mata da budurwa zata sha harya sake had'e ta fiye da yadda Allah yayi mata halittan ta? Haba 'yan uwana! Wlh duk wanda ya gaya miki wannan to babban mak'aryaci ne kuma mayaudari, dan duk mai ilimi da tunani wlh baza a yaudare sa da ire-iren wad'an nan abubuwa ba. Gaba d'ayan mata yanzu akan maganin mata suke cinye duk arzikin su, basa iya yiwa kansu komai bare suma 'ya'yan su ko iyayen su da suka haife su. Kuma wlh maganin mata yanzu zanba ne, wata ma kuka zata daka tasa citta da kanumfari indai yana kamshi shike nan a baki k'ullin sa naira d'ari ace kisha da madara zakiga aiki. Wata ma bata san me dame aka had'a ba, amma duk se a yita saya daga baya ya zama miki illa a rasa gane me yake damun ki.
Dan Allah 'yan'uwa na mata mufarka, mudena yadda ana cutar damu bayan muma muna da damar gyara kammu da kammu base munje gun wata ko wani ya mana k'arya ya cucemu ba. Duk duniya babu abinda yake kawo wa mace ni'ima irin kwanciyan hankali, kai ba mace kad'ai ba hatta na miji, duk wacce bata yadda ba to dan Allah ki zaunar da mijin ki ki tambaye shi na tabbata zaki yarda da magana ta. Duk macen kona mijin da bashi da kwanciyan hankali to dole ki samesu da k'aran cin ni'ima wlh.
Bawai nace ku dena amfani da maganin mata bane, ina nufin ki had'a shi da hannun ki wanda ke kin san abin da kika harhad'a acikin sa bawai kije ki sayi fitina da kud'in kiba kizo kina ciza yatsa daga baya. Inda zakuci gaba da biyo ni, to  zakuji irin abu buwan dake k'arawa mace ni'ima da kuma d'an d'ano...
Atif ne yayi saurin shigowa gefen matan, dan gaba d'aya an zaga ye Mubinat ana jin bayanin ta mai d'auke da darusa iri-iri ya kamo hannun ta tare da cewa "Kuyi hak'uri, lokacin tafiyar mu yayi"
Muryan mata kake jiyowa ana cewa "Dan Allah kad'an k'ara mana minti goma bawan Allah"
Amma ina, bai ma tsaya sauraran suba, ya janyeta  daga k'arshe ma d'aukan ta yayi cak har cikin mota. Mutane se binsu da ido akeyi yayin da wasu suke cewa "Ai dole ya d'aga ta, irin wan nan bayani nata aima yaci ace ya goya ta wlh, k'aramar yarin ya da basira haka."
Suna tayi dai wasu samarai kuwa cewa suke ai itace matar Atif Muhammad Bakari d'an wasan k'wallon nan ai d'an uwanta ne, da bashi zata aura ba wani balarabe ne mai suna Farhan, sakama kon accident dayayi ne yayi losing memory d'in shi shine aka had'a ta da Atif d'in.
Wani daga gefe yace "short up duk bakusan komaiba, accident d'in Farhan d'in ai abune shiryay ye, kuma se Allah ya kaddara hakan zai faru dashi, mubar wannan zancen tunda bai shafemu ba danni wlh Atif d'in burgeni yake yi Allah, akwai iya short d'in ball."
Eh wlh gaskiya nima gayen yana kai min, infa ball ya shiga hannun sa tose ya cinyesu kamar maye wlh. Haka dai sukai ta hiran su sannan suka wuce...

"Me yasa ka janyoni ban gama magana ba Ya Atif?"
"Sabo da maza sunyi yawa kuma duk sun tsaya saura ran baya nanki ne kuma suna kalle min ke wanda hakan yasa naji kishi sosai a cikin raina."
"Hhhh kai Ya Atif har wani kishi kake yi a kaina?"
"Hmm bazaki tab'a ganewa bane Sis Mubi,i love you more than you'r thinking" ya fad'a tare da mai da kansa kan driving kamar mai yin tunanin wani abu.
Kallon shi take tayi tare da shafar sajen fiskar sa da hannun ta tace "Are you thinking of something?"
"Yes" yace da ita
"Tell me, mene ne?"
"Matso da kunnen ki kiji"
Ba musu ta matso dashi tana sauraron sa.
"Ina tunanin irin kukan da zakiyi yaune" ya rad'a mata tare da cizan kunnen nata a hankali yana mata dariya mai had'e da zolaya...
"Kuka kuma Ya Afit,me zai sani kuka ni kuma?"
Murmushi yayi tare da cewa "Im just kidding"
Se daga baya ta gano abinda yake nufi,tace "Hmm hakama zaka ce ko,bayan kasan ina tsoro?"
"Sis Mubi ai mun saba,bai kamata ace har yanzu kina tsoro naba."
"To mubar maganan ina zaka kaimu?"
"Sai dake zanje inyi"
"Hhhhh to shikenan muje"
"Haka kika ce ko?"
"Eh,indai ta wannan b'angaren ne ai bani da tsoro"
"Hhhh Sis Mubi nawa"
Wayar sace take ringing,number ce babu suna,amma sam seyak'i d'auka. Mubinat tace "Me yasa kak'i d'auka?"
"Ba komai rabu dasu"
"Su waye ne?"
"Wasu ne nayi musu alk'awarin zan basu kud'i shine suketa damuwa wlh."
"To Ya Atif kasan uzurin sune,wata k'ila suna da buk'atan kud'in ne a yanzu pls ka d'aga wayan."
Badan ya soba ya d'auka "Hello wai dan Allah me yasa kuke haka ne,ni nace zan bada kud'in nan kuma shikenan se kuyi ta damuna da waya,haba dan Allah ku d'aga min k'afa mana." Kyat ya kashe ba tare da yaji abinda zasu ceba.
Mubinat ta kalleshi taga alaman ransa ya b'aci,dan haka ta rik'o hannun sa  sannan ta kira sunan shi  "Ya Atif"
Juyowa yayi yana kallonta "Na'am,karki damu ba komai"
"Akwai mana,meya b'ata maka rai haka cikin k'ank'anin lokaci?"
Murmushi ya k'irk'iro yace "Komai ya wuce manta dasu,zan nemesu anjuma in basu."
Mubinat bata sake cewa komaiba shima kuma haka har suka isa gurin sayan ice cream. Tana zaune a cikin mota har yaje ya dawo sannan suka koma gida...

Suna isa ta wuce d'akin Umma tayi alwala tare dayin sallan la'asar.
Bayan ta idar ne ta nufi parlour'n Abba dan duk suna can ana ta hira harda Mahaifin Farhan.
Sallama tayi tare da gaida Mahaifin Farhan da kuma Abbanta. Nan hira yaci gaba da gudana a tsakanin su ana ta raha,yayin da Farhan yake ta kallon Mubinat cikin dabara ba tare da angane ba. Ita kuwa sam tak'i kallon inda yake tana ta Game a wayan ta.
Haka kawai taji ta tsargu seta d'ago da kanta ai kuwa se sukayi 4 eyes,murmushi ya sakar mata,ita kuwa seta bushe tana kallonsa ko k'yafta ido batayi. Ganin hakan yasa Farhan huro da iska daga bakin sa zuwa gareta tare da lumshe idanunsa.
Kunya taji sosai daya ganota tana kallonsa. Mik'ewa yayi yare da cewa Abba zamu shiga gari da Ahmad zuwa anjuma zamu dawo. "To Allah ya kare Farhan sekun dawo" cewar Abban Mubinat
"Ameen" suka amsa sannan suka yiwa Mahaifin Farhan sallama suka fita tare da shureim.
  Su kuwa sukai ta hira har kusan magrib kafin Abba da Mahaifin Farhan suka wuce masallaci.
Bayan anyi sallan ne Atif yazo ya sami Mubinat a d'akin Umma tana kwance yace ta tashi su tafi.
Cikin hanzari ta shirya dan bata so su sake had'uwa da Ya Farhan.
Sunyi sallama suna gun mota sega Farhan da Shureim sun fito daga waje. Atif yace "To mu zamu wuce"
"To bari in kawowa Sis Mubi tsarabar ta inji Ummi."
"Ok" cewar Atif,sannan Farhan ya wuce.
Leda ce mai kyan gaske 'yar dai-dai, acike yake dam ya mik'a wa Atif.
"Mun gode" cewar Atif. Ita ma Sis Mubi tace "Mun gode" tana kallon shi. "Ba komai Allah ya kiyaye hanya" cewar Farhan.
"Ameen" suka amsa a tare sannan suka tafi inda Farhan yake ta bin motar da kallo har suka bar gidan sannan ya kamo hannun Shureim suka tafi.

Bayan sun koma gida ne ta bud'e ledan da Mahaifiyar farhan ta aiko mata,kaya ne kala biyu masu kyau,se kuma turare masu k'amshi guda hud'u,da turaren d'aki da kuma jallabiya guda biyu na Atif se sark'a da 'yan kune.
Dad'i sosai Mubinat taji,haka ma kuma Atif d'in. A wayar Mubinat suka kira ta sukayi mata  godiya.
Mubinat ta shiga toilet da niyan yin alwala tayi sallan isha kenan se taga period nata yazo. Shuru tayi ta kasa fitowa dan irin zumud'in da taga Atif yanayi a yau,cikin sanyi jiki ta fito tare da cewa "Ya Atif" se kuma tayi shuru.
Har inda take tsaye yaje ya rik'eta yace "Lafiya?"
"Period d'ina na gani yanzu"
"Wasa kike min ko?"
Sun kuyar da kai tayi tace "Wlh da gaske nake maka"
Ganin yadda tayi ne yasa ya rungume ta "Karki damu ba komai ina ce 2days kawai kike yi?"
Kai ta d'aga mishi alaman "Eh"
"It's okay with me ki dena damuwa zan jira kinji?"
Murmushi tayi tare da shigewa jikinsa shi kuwa ya rungume abarsa...

Haka suka kasance cikin so da k'auna a wannan kwana biyun.
Ranan da Mubinat zatayi wankan tsark'i tun safe ake kiran number'n Atif da wata number amma yak'i d'auka.
Haka yasa ranan ya fita da sassafe dan zasuje wani gari dukkanin su 'yan k'wallon,kuma zasu d'an jima na awanni bakwai zuwa takwas kafin su dawo.
Kamar bazasu rabuba amma haka ya tafi ya barta.
Fitarsa da awa biyu sega wasu mutane suna nocking na gate d'in gidan. Mai gadi yana bud'ewa se aka kamoshi aka d'aure shi sannan aka shiga cikin gidan aka fara nocking. Mubinat tana kwance a d'aki ta mik'e zuwa k'ofa ba tare da tunanin komai ba ta bud'e. Ba k'in fiska ta gani maza su uku suna tsaye kaman sojoji,k'irjin Mubinat ya buga sosai danta d'auka ko wani abu ne ya sami Atif.
"Lafiya kuwa,meya kawo ku?" Ta tambaye su
"Lafiya k'alau hajiya munzo ne danmu tafi dake"
"Ku tafi dani? Zuwa ina kenan?"
Kallon junansu sukayi sannan suka sa dariya "hahahaha" tare da kamo Mubinat suka d'agata cak,ganin zata tona musu asiri da ihunta ne yasa suka shafe fiskarta da wani powder. Shikenan ta dena motsi kwata-kwata,ahaka suka fita da ita zuwa motarsu.
  Mai gadi yayi iya bakin k'ok'arin sa yaga ya sanar da Atif amma hakan bai yuba sema duka daya sha a gunsu sannan suka d'aure shi suka barshi agun sukai tafiyarsu da Mubinat acikin motar su...
Gudu suke sosai da motar kaman zasu tashi sama. Sunyi tafiya na tsawon minti goma kenan sai ga wani yaro akan keke saura kad'an su bugesa amma Allah ya kare. Jin yadda motar ta taka birki ne yasa Mubinat ta farka tare da binsu da kallo.
Salatep d'in bakinta suka cire tace "Dan Allah mena muku,kuyi hak'uri ku mai dani gida dan Allah?"
"Hmm ki dena b'ata bakinki zamu rabu dake inhar mun sami abinda muke so."
Gefen glass take kallo ko zata gane ta inda suke tafiyan amma sam bata gane ko inaba.
Hakan yasa ta fara yin kuka tanata kalle-kalle,ai kuwa seta ga Almajirinsu Musa akan keke. Dabara ne yazo mata dan duk glass d'in motan arufe yake kota kirashi bazai jita ba. Rufe baki tayi kaman maijin amai tana cewa "Um um" tare da nuna musu bakinta da hannunta. Hakan yasa suka gane tare da sauke glass d'in motan na gefen baya.
Tana d'an fitar da kanta tayi saurin yin magana da k'arfi tace "Musa Mubinat ce dan Allah ka taimakeni d'aukeni suka...!
Rufe mata baki sukayi tare da shigo da ita suka manna mata salatep d'in suna cewa "Wato mu zaki mannawa hauka ko,zaki gane kurenki kuwa.
Tabbas Musa yaji muryan Mubinat kuma yaji wasu kalamanta wasu kuma baiji ba. Ko daya kalli motan seya hango ta tana ta faman d'aga mishi hannu bakinta arufe. Su kuwa sun kasa gane wanene Musan,dan lokacin data kirashi mutane sunkai biyar agun manya uku k'anana biyu ne,sannan basuyi tunanin yaro bane wanda Mubinat ta kira. Shiyasa sam basuyi zaton keken Musa su yake biba dan sun ganshi k'aramin yaro ne.
  Shi kuwa Musa seyama dena kallon motarsu dan karsu zarge shi, yabi ta wata hanya daba kan titi bane amma yana kallon duk inda motarsu take bi.
Ita kuwa Mubinat sun kwantar da ita yayinda wani daga cikinsu yake shafe kan k'irjinta yace "Muma bari mud'an more kafin muje Oga ya tab'aki, d'ayan yace gaskiyane fa" sannan shima ya fara shafar d'aya b'angaren k'irjin nata suna dariya suna cewa "kaji laushi kaman auduga."
Haka sukayita matse bubs d'inta harda sa hannu acikin rigarta sukayi suna matsewa.
Kuka sosai Mubinat takeyi tare da fad'in "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" acikin ranta dan bakinta a manne yake, sannan sun d'aure hannayen ta da kafafuwa ta yadda bazata iya yin komai ba sedai ta juya dama da hagu shima kuma babu hali dan sun takurata sosai. Hakan yasa taketa hawaye masu zafi tana kiran Allah a ranta. Cak kuwa taji sun d'auke hannayen su daga kan k'irjinta sakamakon isowa inda zasu tsaya.
Musa yana lab'e daga cikin ciyawi yaga sun fito da ita tana bisa kafad'an d'aya daga cikinsu sukayi ciki da ita.
  Aguje Musa ya d'auki kekensa yayi bakin titi,isarsa kenan ya samu keke nape,daga shi har kekensa suka shige ciki.
Atif ne ke dawowa motar sa cike take da tsaraba kala daban-daban wa Sis Mubinat,dan sun gama meeting d'in da wuri sosai.
Isar shi gate kenan maigadi ya bud'e k'aramin k'ofa cikin tashin hankali da tsoro yana cewa "Yallab'ai,wasu sunzo sun d'auke matar gidan sun tafi da ita"
  "What!" Ya fad'a cikin tsawa yana k'arewa maigadi kallo. Da ganinsa kasan an dakeshi ne har rigan sa ta yage.
  Yaci gaba da cewa "Wlh nayi iya k'ok'arina amma ina,sunfi karfina kayi sauri ka bisu sunkai minti sha biyar da fita babu waya a hannuna domin sun kwace alokacin dana so in sanar dakai."
"Oh my God"
"Waye su?"
"Kuma su nawa ne?"
"Sannan wace irin mota  and what is d colour gaya min!"
Cikin tashin hankali yake jero wad'an nan tambayoyin wa maigadi.
"Farar mota ce bus haka babba Yallab'ai."
A 360 Atif ya d'ibi mota batare daya san inda zaije ba. Tunani yake aransa "To waye zai min haka,babu wadda nama laifin da zaimin haka ai,koma wanene shi he will pay for it wlh."
"He will pay for it!" Ya fad'a a tsawace.
"Nasan zaku kirani tunda kuka d'auke min mata,toku kirani manaa! Me kuke mata haka tsawon 15 minits da d'au kanta amma baku kirani ba har yanzu?
"Oh Sis Mubi,Allah ya kare min ke aduk inda kike,ya Allah ina zan samu Sis Mubi nah?" Ya fad'a yana hawayen da baisan sun fito ba...

"Ya Farhan ka tsaya ga can Musa almajirin mu yana biyomu aguje da keke kuma mu yake biyowa" cewar Shureim.
Take Farhan ya tsaya suna jiran isowar sa. Tun keken nashi bata gama tsayawa ba ya yarda ita tare da k'arasowa da gudu yana haki yace "Ya farhan, Sister Mubi nagani cikin wata mota  tana cikin had'ari domin naga bakinta a d'aure tanata d'aga min hannu shine nayita bin motarsu har naga inda motar ta tsaya."
  Yaci gaba da cewa "Maza ne kusan su hud'u suke d'auke da ita se wutsil-wutsil take da k'afafun ta, lallai tana cikin had'ari Ya Farhan..."Musa ka tabbatar da abinda kake fad'a kuwa? Ka tabbata ita ka gani?"
"Eh wlh ita ce,kanta ko d'anwali babu,kuma harta kira sunana ma Ya Farhan muje inkaika gun."
Farhan ya kalli Shureim, take Shureim ya fara kuka yana cewa "Koma ba ita bace muje Ya Farhan banaso wani abu ya sami Sister Mubi dan Allah muje."
Waya Farhan ya ciro ya kira Atif,amma ba'a d'auka ba,seya tuna da cewa yau su Atif suna meeting. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, hakan yana nufin bayan fitan Atif ne aka d'auke ta?"
Gudu sosai Farhan yakeyi tare dabin kwatan cen da  Musa yake mishi. Cikin zuciyarsa kuwa addu'oi yake tayi na nema mata kariya aduk inda take.

Koda suka iso gurin,se Farhan yace su zauna acikin mota, sannan ya kira Ahmad ya sanar dashi komai da kuma inda zasu same su sannan ya shiga cikin ginin.
  Sanye yake da suite bak'i ajikinsa da kuma bak'in eye glss a fiskarsa da wani k'aramin kwalba a hannun sa wanda bansan kona menene ba.
Shigar Farhan baiga komai ba, a hankali yake taku tare da k'arewa gurin kallo, babban gini ne sosai wanda babu rufin kwano a saman.
Shi kansa ya tsorata da yadda gurin yake da girma sosai, bai san ta inda zai fara dubata ba, dan haka seya fara kiran sunan ta
"Sis mubi!"
"Sis mubi!!"
"Sis mubi!!!"
Ita kuwa tana kwance a k'asa haihuwar uwarta babu komai a jikinta duk sun rabata da kayan dake jikinta sun d'aure mata k'afafu da hannaye  sannan an manne bakin da salatep babu halin yin magana.
Tabbas taji muryan Ya Farhan kuma ta tabbatar da cewa lallai shi d'inne.
Hakan yasa taji d'an sanyi a ranta, amma kuma data tuna da cewa  babu komai a jikinta se taci gaba da kukan data dad'e tana yin shi.
D'aya daga cikinsu yace "Muryan wani nake jifa."
Ogan nasu yayi magana "Kuje ku duba, kafin nan na more da wannan sura da yake neman haukata ni"
Cikin sauri suka fito...ido hud'u sukayi da Farhan,nan suka nufo kansa da niyan fad'a amma seya zille musu yayi saurin bin hanyar da yaga sun fito. Me zai gani, Sis Mubi ce kwance ba komai a jikinta yayin da wani saurayi yake k'ok'arin yimata fyad'e.
Cikin tafasan zuci ya jefesa da kwalban dake hannun sa a dai-dai k'eyar kansa.
Su kuwa na bayan Farhan d'in suka masa taron dangi kowa da inda yake kai masa duka, d'ayan kuwa wani ice ya d'auka ya bugawa Farhan akai, Mubinat kuwa tana ganin haka seta fara cewa "umm-umm" tana ta girgiza kai tana kuka wanda baya fita...

Post a Comment for "KAMAI NISAN JIFA CHAPTER 3"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...