HAUWA CHAPTER B KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAUWA CHAPTER B KARSHE

 HAUWA CHAPTER B KARSHE


Zata rantse in da akwai wasu a wurin ba zasuji abunda ya fito daga bakinshi ba, k'afafuwanta ke neman zubar da ita k'asa, da k'yar ta samu ta daidaita natsuwarta.

"Hawwa" ya sake kira a karo na biyu, sunanta ne, amma ba za ta iya tuna when last wani ya kirata da suna Hawwa ba, ko da Hauwa'u ne, ba manya ba yara ba, sunantah baya wuce Hauwatty ko Watty, amma sai gashi wani na kiranta da Hawwa, ba ma Hauwa ba kamar yanda ake fada, aa Hawwa, Hawwa fa? Kamar 'yar karamar yarinya? Bata gama kitse kitse a ranta ba taji muryarshi cike da sanyi da kula yace "Yaronki na ta Kuka, meyasa kika barshi?"

Sai yanzu ta tuno dashi a hankali tace "Zaidd"

Cikin rashin sani yace "Naam?"

Da mamaki ta kalleshi kafin tace "sunan Yarona kenan"

Murmushi ya subuce mishi yace "Sunana kenan".

Duk wani minti da ta k'ara a wurin bata lokacine, Zaidunta na chan na kuka, da sauri ta bar wurin, Zaid ya bi bayanta da kallo, kafin yayi saurin yi Istighfari da ya tuna Matar Aure ce.4


Tun kafin ta shiga Sassan Inna taji ana cigiyarta, ta san kowa ya tsaneta, to ita meye laifinta? Tana shiga dakin kuwa a ka yi mata caaaa kamar zasu ari baki, ba ta kula kowa ba dai ta karbi Zaid domin shayar dashi, takaici ta ya sa danginta yi ma Inna sai da Safe suka fara zamewa, Hashim ma fita yayi ya iske abokinshi Zaid suka nufi gurin Abokansu daga nan zasu wuce gun Dinner.2


Cikin kwanciyar Hankali Watty ta ke shayar da Zaid har ya koma bacci, ta kai shi chan k'uryar Inna don ta san yanzu lokacin shigowan Iyayenta maza ne.

Ta na jin Shigowar Ya Bu Inna ta mishi wulakanci ta fatattakeshi ya fitar mata a daki, Watty ta fito da sauri tana bata hakuri Inna ta korata daki itama, ran Watty kuwa yayi k'ololo gun baci.5


Wurin k'arfe 10 ta ji shigowar Inna dakin, ba ta ce mata komai ba, ta hau dayan Gadon k'arfenta tayi adduointa ta kwanta.

Washegari bayan sunyi Sallahr Asuba

Inna tace "sauko nan Watty"

Ba gardama ta sauko daidai carpet din Sallahr Inna, Inna tace "Watty, kina son Abubakar?" Kamar jira take tace "Inna wallahi Ya Bu chanzawa yayi, shima ai yana sona, ki mishi hakuri, wallahi zai chanza, in kikace zaki rabamu Inna Zaid fa? Haba Inna?".

Mamaki ya sa Inna wangale baki, lallai Watty ta fi k'arfinta tace "Watty, dukanku jikokina ne, ina sonku, ba zan so daya ya tauye ma daya hakki ba, ko kuma daya ya zalunci daya, mutunci nake so na siya miki".

"Inna ai wallahi na san ya gane kuskurenshi, ai da kikace zaki rabamu baki ga tashi hankali a tattare dashi ba? Wallahi ba zai kara ba"

Inna tace "So ya rufe miki Ido Watty, duk randa na san cewa bai bar dukanki ba to Wallahi kiyi kuka da kanki, don ba ruwana" da sauri Watty tace "na yarda" girgiza kai Inna kawai tayi tace "je ki gaida Iyayenki".7


Cike da Jin dadi ta fita, don ta san yau zata koma dakinta.

Da Sallama ta isa gurin Mamarta, tana kan Carpet tana Lazimi, jiranta tayi har ta gama, ta gaidata.

Mamarta ta amsa, tace "kin gama gudunmu?"

Watty ta rik'o hannun Mamarta tace "Mama ba fa gudunku nakeyi ba, naga Anty Binta tayi fushi ne, na san in tana gani haushi zata yi ta ji, shiyasa nace bari na kyalesu sai yau"

Mama tace "Watty kina gannin kamar an matsa miki? An shiga rayuwarki an takuraki ana so a rabaki da Mijinki? Ba haka bane, Mata ce ke ba Jaka ba, manzon Allah yayi hani ga Miji ya daki matarshi, yace in har ya zama dole to ya wafdeta da gefen rigarshi, rashin Ibadarshi tsakaninshi da Ubangijinshi ne, amma Watty ba zan taba so ki tsaya yana dukanki ba, wata rana ba a san inda dukan zai tsaya ba, ba a san inda zai bigeki ba, kar ya nakasa min ke Hauwatty ta, kinga Shekarun Binta 32 ko? To shekaruna 33 da aure, Babanku bai taba dunguri na ba, yayyinki su 4 ban taba jin wata na korafin Mijinsu ya hararesu balle ya dake su, sai ke Watty ta? Autata? Autan Mamarta? Har ni kike ma zurfin ciki? Ni mahaifiyarki da na kawoki duniya ni zaki dinga boye ma irin haka?"

Kuka mamar ta fashe dashi, hankalin Watty ya tashi, saboda So, mamarta yau take zubar mata da hawaye da sauri ta shiga goge mata fuska.

"DonAllah Mama kiyi hakuri, ki bar kuka, ki kayi Kuka, ba zan taba jin dadin gidana ba, aurena ba zai taba albarka ba, mama ki bar kuka don Allah, Ya Bu ya bari, daman sharrin shaidan ne, Inna ta tsorata shi, ba zai k'ara ba Allah".

Mamarta ta tausaya mata matuk'a ta san So ne "in har kina son ki bar ganin Kukana Watty, kar ki sake boye min komai, kar ki sake tsayawa ya dakeki, ki min alk'awari Watty" hawaye kawai takeyi tace "na miki Alk'awari Mamana, ba zan sake boye miki komai ba, kuma ba zan sake tsayawa ya dakeni ba, da yazo dukana zan gudu".

Mamarta ta girgiza kai don tana ganin har gobe Watty k'uruciya ke damunta.9


STORY CONTINUES BELOW

Sun dade suna magana da Mamarta inda take bata shawarwari kan yanda zasu zauna lafiya da mijinta, a karshe tace ta kira duka yayyinta hudu su bata shawara, tace InshaAllah,bari ta gaida Baba ta koma gun Inna kar Zaid ya tashi.

Sai da ta shiga ta gaida Babanta kafin ta koma sassan Inna.


Yaya Hashim da wannan na jiya ta iske a gaban Inna, gaidasu tayi zata shige daki Yaya Hashim yace "yanzu ke Watty komawa zakiyi gidan Bak'in mugun nan?" Zumburo baki tayi ba ta tanka ba "kar dai ki sake tsayawa ya dakeki, da ya yunkuro ki gudu ki dawo gida" da sauri ta nufa daki gami da cewa "ba ma zai k'ara ba" Hashim baki bude yace "danubanki Soyayya ya sa kin zama mara kunya ko?"

Inna tayi dariya tace "So hana ganin Laifi"

Hashim yace "So ko Yarintar Hauka?"

Inna tace "ina ruwan Watty? Kai Zaid yanzu yau din zaka wuce? Baka sake mana kwana?"

Zaid da tun shigowan Watty ya kasa motsa ko da yatsarshi yace "uhm Inna, kawuna ke jirana a Abuja, a na daurin aure 11 zan wuce"

Inna tace "Allah sarki, donAllah ka dinga zuwa kaji Mai sunan Jikana"

Zaid ya murmusa yace "InshaAllah, a gaida takwarana in ya tashi"

Inna tace "zai ji inshaAllah"

Hashim ya fara mikewa yace Inna bari mune daki, Inna tace "to nagode".

Suka fita tare.5


Da gari ya waye Sisters dinga duka sunzo, suka sakata a dako,wannan na fada wannan na fada, sai da suka mata kacakaca kafin suka koma lallashi, suna koya mata abubuwan da zata yi incase bai shiryu ba, sun dai jajjada mata kar dai ta sake tsayawa ya daketa, Anty Binta tace "da ya dakeki ki rama, kam bala'i, da ni ce ke cikin bacci zan samu shege na ladaka mishi na jakki, kuma ni da gidan naka har abada" Anty Rally tace "uhm uhm Ya Binta, kar ma dai ta tsaya har ya daketa, Watty mace mara 'yanci banza ce, yanda kika nuna kina sonshi haka a fili, to fa ko wani shara ya dauko kanki zai zubar, ba muce ki koyi rashin kunya ba, amma ke kadai zaki k'watar ma kanki 'yanci, ke kadai zaki sai ma kanki mutunci"

Anty Sady tace "kuma koma me yake sha ya bar kawo miki shi gidanki, ya sha duk uwar da zai sha chan waje" cikin sanyi tace "wallahi ban taba gani ba, sai dai na ga kwalebari, rannan da Aisha mun duba dakin kaf ba mu ga komai ba" nan dai suka cigaba da bata shawarwari, sosai nasihun da yayyinta suka mata suka shigeta, Alk'awari daya ta daukar ma kanta, duk runtsi, ba zata sake tsayawa ya daketa ba.

Haka dai Ya Bu ya zo ya dauketa bayan ya sha gargadi masu k'arfi wurin kakarsu da kuma iyayenshi.4


B A Y A N W A T A 1


Zamansu yanzu ba laifi yayi kyau, ko da yaushe suna tare, yana wasa da 'danshi, ba inda yake zuwa don yanzu baya aiki, amma dai hali zanen dutse, bai bar baccin asarar nan ba, kuma ita bata taba ganin ya sha komai gabanta ba, haka dai ta sanya mishi ido ta cigaba da bautar Ubangijinta da kula da danta.

In bata da aikin yi sai ta kunna data ta shiga Instagram don ganin abunda duniya take ciki, page din Northern Hibiscus ta fiso saboda ko ba komai ta naganin labarai kala kala, tana kuma ganin shawarari daga wurin mutane daban daban, tana son karanta comment sections, ta ga cases da yawa kan Domestic Violence, wanda mazajensu ke dukansu, yanda wasu matan ke chaka ma mazajensu wuk'a, sai dai tayi tir da lamarin, don ko me ya Bu zai mata, zuciya ba zai sakata ramawa ba balle ta dauko makami ta chaka mai, a Instagram ta waye da irin abubuwan nan, da yanda zata tafiyar da Miji.

****8


Mahaifin Angon da Zaid yazo bikinshi watan morning da ya wuce ne Ya rasu, Zaid yayi shirin zuwa Nassarawa gaisuwa daga Kano.

Motar haya ya hau tun asuba , wurin k'arfe biyu ya isa Nassarawa, yana isa garin Nassarawa okada kawai ya hau ya nufi Family house dinsu Ali Ali inda ake zaman gaisuwa.

Nan Zaid ya ga Abokanshi na jamia daga gari dabandaban sunzo gaisuwa, lallai an yi ma Ali Ali Kara.

**1


Da sauri ya shige Daki rik'e da wani dan karamin box, tun da yamma ya fita be dawo ba sai 9 na dare, sai da ya faka idonta ya shige daki da sauri tare da sa key.

Dakin ta biyoshi ta kwankwasa mai, da sauri ya rufe kwalban ya maida cikin kwalin ya tura k'arkashi gado ya bude mata k'ofa, tace "Ya Bu, afuwan pampers din Zaid ya k'are" dan tsaki yayi yace "meyasa tun dazun ba ki fada ba, sai yanzu da na dawo gida baki daya?" Kallonshi tayi tace "Sorry, wallahi banyi zaton duka ne ya kare ba, na yi tunanin akwai ragowa ko guda daya ne" duk bai ji dadi ba, bai da zabin da ya wuce fita yaje ya siyo bakin titi, jan k'ofar yayi, ya fita daga Gidan, haka kurum taji tana son ganin abunda ya shigo dashi, kai tsaye ta koma dakin, ta duba ta duba bata gani ba, idonta ne ya kai kan K'arkashin gado, da sauri ta janyo dan k'aramin kwalin da ya sha nadin celotape duk da an farka, a hankali ta bude box din, ganin dan kwalbar magani wanda tabbas ta shaidasu sune yake tara kwalebarin da ya shanye a wardrobe, wata 'yar takardar receipts ta gani jikin kwalin guda biyu, da mamaki ta bude ido don ganin shipping akayi daga china, dayan kuma kudin maganin ne $150 kenan duk daya $50, ba ta san nawa ne dollar 50 a naira ba amma ta yi amanna ko be naira dubu ashirin ba to ya kusa, daya ta lura an fasa an dan sha abunda bai wuce marfin kwalbar ba, to wannan mai aji ne ba duka ake kwankwadewa ba kenan? kila overdose yakeyi shiyasa baccinshi ya shara, kitse kitse take ta yi a zuciyarta kafin daga bisani zuciyarta ta raya mata wani abu da sauri ta bude toilet din da ke jikin dakin ta shiga .

Kwalebarin da bude duk ta juye maganin cikin WC, sai da ta tittilar dasu duk kafin tayi flushing, ta bude wardrobe inda yake aje empty bottles dinshi ta saka ciki har kwalin.

Ta koma parlo ta zauna tana kallon Arewa 24.6


STORY CONTINUES BELOW

Ba da dadewa Ya Bu ya dawo, ta tarbeshi tare da mai Sannu da zuwa da kuma godiya ta karbi Pampers din daga hannunshi ta dauki Zaid da ke kwance ta yi dayan dakin dashi.

Ya Bu ya koma dayan dakinshi ya nufa k'arkashin Gado Straight ya ga wayam, babu ajiyarshi, da mamaki ya jawo drawern madubi ko nan ya aje amma be ga kwalinshi ba, da dukkan karfinshi ya hankada Katifar kan Gadon amma ba alamar kwalinshi, da sauri ya fita duk da ba da mota ya fita ba yanzu ya bude har boot amma bai gani ba, kamar wani zaucacce ya shiga dube dube ko wani lungu da sak'on gidan, shi dai ya san ya shigo dashi, har ya sha murfi daya, tabbas ya shigo dashi dakin, komawa yayi yana ta duba kamar wani mahaukaci.

Watty na lura da duk abunda yakeyi, amma bata ma fito ba.

Da k'arfi ya kwala mata kira, gabanta ya fadi, sai da sa ma kanta natsuwa kafin ta nufa dakin da kuddirin ko mai ta fanjama fanjam, ba dai zata tsaya ya daketa ba.

Ta isa tace "gani" fuska daure yace "ina abunda na shigo dashi?" "Pampers?" Ya ja dan tsaki yace "ba Pampers ba, kafin pampers ai na shigo da wani kwali" kai tsaye tace "nidai banga ka shigo da komai ba" abunka da wanda bai cikin cikeken hankalinshi yace "ko?" Tace "gaskiya" tunani ya fara yi anya ya shigo dashi? Yana tsaye, tana tsaye.

Kamar ance ya bude wardrobe ya bude, kwalinshi ya hango, da sauri ya sa hannu yana gode Allah har da guntun murmushin shi, wai irin ashe nan na barsu.

Sai dai ya lura marafan duk a bude suke, kuma ba komai cikinsu, da tsananin mamaki ya shiga neman sabbin bottles dinshi cikin tsoffin.

Bai gani ba, zama yayi kamar wani zautace.4


Cikin fushi ya sha gaban Watty da ke niyyr barin dakin gabanta na tsananin faduwa.

"Ina ruwanki da abuna?"

Baki na rawa tace "ban san me kake cewa ba"

Ta nemi hanyar wucewa ya maidota baya "kar ki mai dani sakarai mana Watty, da hankalina, ni zaki rainawa wayau? Kinsan nawa na kashe? Kinsan nawa na kashe na siyo? Zaki zubar min?" Jikinta rawa ya fara ganin ya chanza lokaci guda, ta san me sai biyo baya, gwara ta nemi hanyar tsira, da sauri ta biyo ta gefenshi zata gudu, ya yi nasaran chapko ta da hannun shi tare da jefata kan Gado, hawa kan gadon yayi ya falla mata mari, budar bakin Watty tace "Allah ya isa mugu Azzalumi" abunda ba ta ba yi ba, shima da kanshi ya sha mamaki, yunk'urowa tayi zata tashi ya sa sa guiwan hannunshi ya bugeta, ba a ko ina ya sameta ba illa idonta, za ta rantse da Allah ta ga wani farin haske ya gifta mata a idon, daga bisani ta ga duhu na mamaye idon a hankali, ita ta san ba kuka takeyi ba, amma hawaye ke fita daga idonta na hagu inda ya bugeta dashi, hawayen me yawa, hannu daya ta sa ta rufe idon saboda wani irin radadin azaban da takeji.

Shi ko Ya Bu tsoron kar ta fada gida ne ya sa shi k'yaleta ya fada toilet.

Watty da sauri ta koma dakinta hannunta a kan idonta na hagu, wani radadi takeji a cikin idonta na hagu, ji tayi hannunta ya cika da ruwa, a firgice ta cire hannun da ta rufe idonta dashi, ruwan hawaye ta gani cike da hannun kamar ta kwalfo ruwa, tsorata tayi, tabbas ta san idonta ba lafiya.

Da sauri ta wawuro Wayarta, ta latso Mamarta, ringing daya kuwa ta dauka, Maman ta dauka da Sallama "Watty?" Wani kuka mai sa idonta ciwo takeyi tace "Mama, donAllah azo a daukeni, Mama kuzo ku daukeni"

Hankali tashe Mamar tace "mai ya faru Watty? Dukkanki yake?" Watty tace "Mama nidai a zo a daukeni" da sauri Mamar ta mik'e tace "Babanku na gurin Inna, bari naje na gaya mishi, za ya zo yanzu".

Watty ta kashe wayar ta dauko dankwalinta ta rufe Idonta da shi don har yanzu Hawayen bai bar zuba ba.

**9


A dakin Inna ta iske Mijinta da Hashim da wani wanda ba ta sani ba, Baba yace "Lafiya Maman Watty?" Cikin kuka tace "Watty ce ta kira, wai aje a dauketa" "saboda mene ?" Ya wuce Abun dukanta yake? Nidai ka dauko min ita, kar ya nakasa min ita" Inna ta kalli Baban Watty tace "je ka daukota" Hashim yace "Baba bari na daukota" Inna tace "in ba Baban ya gani ba ba zai bari ta biyoku ba" Baba yace "muje baki daya".

Zaid ya san ba huruminshi bane, amma zuciyarshi ya damu da ya ga halin da Watty take ciki, ya tashi ya bi bayan Hashim din.

Su 3 a mota ba me cewa uhm ko uhm uhm,har k'ofar gidansu Watty, inda baba ya ga rashin dacewar shigarshi yace "Hashim, kuje ku taho da ita" Zaid ya riga bude k'ofa, suka shiga Gidan, har flat din su Watty, k'wank'wasawa sukayi, da sauri Watty ta fito daga daki ta bude musu k'ofa dama shirye take, shima Ya Bu din yaji knocking din, da mamaki ya fito don ganin waye da daddaren nan, ganin Hashim da wani dogo ya sashi sakin baki, Watty ya gani sanye da Hijab zata ra6a ta gefensu ta wuce, maganin da ya sha ya fara aiki, ya dan fara wujijigashi ya nufesu ya tangadi yana "Ina zaki Watty?" Hashim ya sha gabanshi, "Umurni ne daga wurin Inna, tace mu daukar mata Jikarta mu kai mata ita Gida" "ba inda zata, ba inda zaku tafin min da mata" Hashim cike da rashin kunya yace "to in ka isa ka hana mu gani, wanda bai san darajar Mace ba" cikin bulayi yace "Hashim, ni kake gaya ma wannan Zancen, ni ba yayanka bane?" Guntun Dariya yayi yace "Idan ka kuskura ka kawo mana matsala, zan maka dukan tsiya na barka kwance a yanayin da na ganka kamar ka hau network Big Bro" Watty ta juyo da hannu a fuska tace "Yaya, Zaid a wanchan dakin" Hashim ya kalli Zaid yace "Get him please" Ya Bu yayi wani tsalle ya damk'o wuyan Zaid "kai bare, ina zaka? Waye kai da zaka shigo min gida har ka nemi shigar min daki" kafin Hashim ya taimaki abokinshi, a hankali ya sausauta rik'on ya koma kan kujera ya zauna kamar wanda aka ma dukkan tsiya, cike da mamakin sauyin yanayinshi, Watty tace "kar ku damu, ai ya dan sha, bacci ne zaiyi, sai kuma La'asar di gobe" Hashim ya girgiza kai yace "Allah shi kyauta" ya nufa dakin don dauko Zaid.2


STORY CONTINUES BELOW

Zaid ya dan matso kusa da ita yace "Free Yourself" sai ga Hashim ya fito da Zaid a hannu, Watty ta jawo mai Gidan ta datse, da ta cire hannu sai ki ga hawaye cike da hannun kamar ta tara hannu a pampo.

Babanta ta gaisar ta shiga inda yake zaune, amsawa yayi ba tare da yace da ita komai ba,

Gida suka koma Straight, Sashen Inna sukayi baki daya, Inna da Mamarta suna nan zaune Jigum Jigum.

Tana Shigowa duk suka mik'e, Inna ta riko Watty da take mata murmushi, "Dukkanki ya sakeyi ko?" Murmushi tayi tace "Kayan Mayen da yake sha ne na gani na zubar a Masai, shine da ya dawo ya tuhumeni na k'aryata, shine ya Mareni" Inna tace "bar shi zai zo ya sameni" cike da lura da ita tsaf Mama tace "Me ya sami Idon ne kika rufe shi" tace "hawaye yakeyi" "cire hannun" ta na cirewa kuwa sai ga ruwa Shaaaaaa kamar an bude pampo, da sauri ta maida hannun ta rufe, tsoro ya ba su Mama tace "Wannan hawaye da yawa haka" Watty tace "wanda ya zuba a gida ai zai cika Jug" ido duk suka zaro sukace "Iye?" Hashim yace "ko ya dakeki a Ido ne?" Watty tace "da Idon hannu kuwa" da Sauri Inna tace "ai maza a kaita Asibti" Hashim yace "Muje Watty" Mama ta kalli Baban Watty tace "zan bisu" ya gyada mata kai, Inna ta ce "zo Hashim ka karbi wani abu ku tafi da shi" Hashim ya tsaya Inna ta irgo kudi ta bashi.

Har da Zaid suka dunguma Wani Private Eye Center na garin mai Asibitin Dr Hashim yana aikin gwamnati, da Safe, da daddare sai yazo Asibitinshi, suna isa suka nufi Emergency,

Mama ta siyo Kati nan da nan.

Doctor ya k'araso gurin cikin kayanshi na Likitoci, aka zaunar da Watty kan kujera, Mama a gefen kujerar, Hashim da Zaid a tsaye,

Dr din dan gayu ne, ya burgesu duk, har Watty da take fama da Ido daya ta yaba gayunshi a ranta, da murmushi yace "Mama mai ya samu idonta?" Tare da bude idon Watty da hannun hagu hannun dama kuma yana goge mata hawayen da me zuba a idon da cotton wool, a lokaci daya kuma yana sauraron Mamar da take cewa "bigeta akayi da guiwan hannu" yace "yaushe?" Tace "yanzu da daddare" abunda ya gani a idon ne ya sa shi dauko dan k'aramin torchlight irin nasu na likitoci da sauri ya haska idon da kyau don ya tabbatar da abunda yake gani, gami da cewa "Ya Salam! Idonta ne ya tsage, an tsaga mata Ido, nan wurin farin, da ba kuyi gaggauwan kawota Asibiti ba da Ruwan idonta ya tsiyaye, kuma ganinta zai zama sai a hankali maybe ma ba za ta sake gani da idon ba,amma Alhamdulilah, yanzu za'a shiga da ita theater room a dinke Idon"

Mutuwar Zaune Watty tayi, Mama kuwa hannu biyu ta saka ta toshe bakinta saboda kukan da ke niyyan kufce mata, Doctor ya latso wayar intercomm din Asibiti, yace Prepare for a Surgery in 10" ya dan yi rubutu a takarda ya mik'a ma Hashin yace "kaje wurin cashier kayi making payment, suna Transfer da kuma POS" Hashim ya amsa yace "ina zan bi?" Doctor din yace muje na nuna maka nima i need to change for the Surgery" suka fita tare.8


Mama ta na kuka ta ke cewa "Ya nakasa min ke Hauwatty, ya nakasa min ke".

Watty bata son yin Kuka, in tayi kuka zata karaya bata so ta karaya, hannun mama kawai ta rik'e ana ta tana summoning courage da strength a hannun Mama.

Kafin su k'arasa gun Cashier, Dr yace da Zaid k'anwarka ce? Zaid da duk jikinshi yayi sanyi ya kasa amsawa, Hashim yace "k'anwata ce" Dr yace "me ya faru ne? Gaarin yaya aka buge mata ido, accidentally? Or Intentionally?" Hashim ne yace "Might be intentional" Dr yace "who did this?" A takaice Hashim yace "Mijinta" tsayawa Dr din yayi yace "Mijinta? Wannan yarinyar na da aure? She? A victim of domestic violence ? And what are your parents going to do about it?" Murmushin takaici Hashim yayi yace "Nothing, because he is Family too, amma hopefully a raba auren saboda ba wannan bane karo na farko" Doctor yaji tausayin Watty sosai, yace "ga inda zaka biya kudi chan, ka kai receipt chan, su zasu shiryata su kawo ta theatre room" Hashim da Zaid suka nufa gurin, shi kuma Dr ya bi wani hanya.


Cikin Mintunan da ba su wuce 20 ba aka gama process din da zaayi aikin, Wasu nurses ne suka nufi Inda su Watty suke don tafiya da ita, Mama tace "Ki ta addua Watty, InshaAllah zaa dace" gyada kai kawai tayi ta bi nurses din" Mama tace "Hashim kira min Kawunka donAllah" ko bata fada ba ya san ta na nufin Mijinta ne, ya kira Baba k'arami ya bashi Mama, chan gefe Mama ta tsaya tana bashi labari tana kuka.

Zaid duk yaji zuciyarshi ta karaya, Hashim yace "kaga Coincidence, duk randa kazo muke jin labarin matsalar Watty da Mijinta, this is the 2nd time ko?" Zaid dai zama yayi duk ya ji jikinshi ba lakka, agogon hannunshi ya kalla ya ga 11 saura minti 10 an shiga theater da ita sai fatan Allah ya sa a dace.


STORY CONTINUES BELOW

D A K I N A I K I


Watty sanye da kayan Patient zaune kan wata kujera mai hade da na'ura mai dauke da k'atuwar fitila a Ido, ba ta son hasken don Idon na zafi, Nurses uku ne sai Dr din, Nurse ta maso gabanta ta aje kwanon silver da yake dauke da allura da syringe, sai auduga.

Tace "gyara Allura za'ayi" Watty ta nanannade Hannun rigarta ta mik'a Hannu don a mata Alluran, nurse tace "ai ba a nan zaayi ba" Watty ta danyi tsaki bata son Allura a mazaunai, amma bata da wani zabi da ya wuce ta juya a mata, ganin ta na neman juyawa nurse tace "ba fa anan zaayi ba, anaesthesia ce" Watty ta muskuta tace "a Ina za'ayi?" Kai tsaye nurse tace "a Ido" cike da firgici ta zabura tace "Iye? I me? Ido? Ba na so, wallahi bana so, ko tsokale ido mutum yayi da hannu ya ya kare? Balle allura a ido bani so ayi aikin, kar ayi aikin in har sai an tsira min allura a ido" ta na neman tashi, nurse ta juya ta kalli Dr alamun ita fa ta gaji Dr ya mata magana da hannu, ta matsa shi kuma ya matso kusa da ita.

Cike da sanyinshi yace "Hauwatty, na fadi sunan daidai?" Bata amsashi ba amma ido daya a kanshi yake, ya fara mata bayani cike da lallashi da kula yace "I believe kina so ki dawo kamar kowa, in ba a miki aikin nan ba zaki rasa ganinki, Alluran Anaesthesia ana yinta ne don kashe zafi a wurin da zaayi aiki, in aka miki alluran nan, to ba zaki ji zafi ba ko kadan, ki yarda dani" kwantar mata da hankali ya cigaba dayi har ya lura tayi lak'was, hanni ya mik'a ma nurse alamun ta bashi Allurar, ta mik'o mishi.3


Wani irin dakewa tayi, tare da jin duk wani gaba na jikinta na bata hadin kai, ji tayi kamar ba ita ba, zuciyarta tayi sanyi ta k'ek'eshe, tana jin bismillahn da Dr yayi, tana jin sanda ya mata Allura cikin Ido, ko k'wakwaron motsi kuwa Allah ya hana tayi, da taimakon Nurses din Dr ya dinke wurin da ya tsage a idon, yanda aka dinke k'warya haka aka dinke idon Watty, kamar ko wani Surgery da yakeyi, da ya gama zai kalli wanda suka tayashi aiki yace "Alhamdulilah it's Successful" Nurses suka hada baki wurin cewa "Congratulations Doc" murmushi yayi yace "ku maidata ICU, ku samata drip, ku cire mata bandage after 48 hours, ku diga mata Evril after every 30mins" ya musu bayanin magungunan da zasu dinga diga mata, Yayi rubutu a file dinta ya fita.


A reception ya iske su sunyi jigum jigum, suna ganinshi suka mike tsaye cike da tsammani, yace "Alhamdulilah an dinke wurin, amma an rufe mata idon da bandage saboda haske, zaa kwance bayan kwana biyu, akwai magunguna kuma da zata dinga sha sai na digawa, ko da yake bari sai an kwance bandage din sai a muku bayani,yanzu dai tana bacci Alluran zai saketa inshaAllah zuwa gobe, in ta farfado zaa cireta daga ICU a maidota Ward " yayi musabaha da Hashim da Zaid yace "Mama Allah ya kara sauki sai da safe".

Mama ta zuba mai Godia, ta umurci su Hashim da su koma Gida su kwanta, Hashim yace "Aunty kema ki zo mu tafi, kinga yace tana ICU, kuma wai baa jinya, mu tafi gobe sai na maidoki da Sassafe" Maman Watty tace "uhm uhm Hashim, kuje kawai, ni ina nan" Hashim yace "to ina zaki kwanta Aunty, bari muje mu kawo miki Bargo da Pillow?" Agogon da ke mak'ale a bangon reception ta kalla tace "Sha biyu da minti arbain, yaushe kaje ka dauko ka dawo? Kar ka damu Hashim? Nagode Allah ya bar zumunci, Jikana na gode Allah ya saka da Alheri" da nauyin baki Zaid yace "Ameen Allah ya sauwake".

Haka suka tafi duk zuciyoyinsu babu dadi, Mamar Watty kuwa ta samu wani wuri ta rakube.

Wurin k'are daya Dr ya fito zai tafi gida ya ganta ya umurci masu aikin Asibiti da su kaita Amenity akwai empty gadaje ta kwanta a chan ya fiye mata nan hakan kuwa akayi.4


Kafin gari ya waye labari ya zagaye dangi Ya Bu ya fasa ma Watty Ido har an yi ma aiki Ido.

Zaid kuwa na gurin Inna da ya farka tsakar dare don shan Mama ba wacce zata bashi, ya ci kukanshi bawan Allah, sai dai Inna ta bashi zamzam, wurin karfe uku da kukan ya kara yawa Inna da kanta ta shiga kitchen domin hada mishi wani kunu da take ma kanta tana sha, kunun Alkama da waken soya, ta yi shi da ruwa kuwa ta saka dan sugar kadan, ya huce ta dura mai a ciki, duk da ya sha sosai saboda yunwar da yakeji amma bai bar kuka ba har gari ya waye basu runtsa ba saboda kuka.


Kafin k'arfe takwas na Safe Inna ta sa an gama hada ma su Watty Kalaci, Soyayyen Dankali da kwai sa ruwan Tea, Hashim yace Inna bari na kai musu yanzu dama zan je kai Zaid tasha yau zai koma" Inna tace "Zaid, ka gaida min Danginka mun gode, kar ka manta ka zo ka ziyarce mu duk lokacin da kake da lokaci kaji?" Ya murmusa yace "InshaAllah Inna, nagode Allah kara lafiya".

Daukan Basket din Hashim yayi suka shiga Mota.

Hashim yace "bari na fara saukeka a Tasha"

Zaid yace "aa wallahi, muje a kai musu Breakfast din, sai ka kaini"

Asibitin suka nufa, a reception ya nemi Mamar Watty be ganta ba, wata maaikaciya ya tambaya tace "ita wacce aka ma aikin tana chan ICU ita kuma matar tana Amenity" Hashim yace "Zaid barin nemota" yayi gaba, Zaid yayi tsaye tare da tsurawa K'ofar ICU ido, yana son ganinta kafin ya tafi, ba tare da wani tunani ba ya k'arasa Cikin inda take kwance, tana kwance tana baccinta, numfashinta na sauka a hankali, bakin gadon ya tsaya, chan ya samu kanshi da magana inda yake cewa "Hawwa, ki warke ki cigaba da gani kinji? 'Yancinki a hannunki yake, ke kadai zaki nemar ma kanki, kin chanchanci jin dadi, kin chanchanci farinciki, kin chanchanci duk wani jin dadi na rayuwa, kin chanchaci Miji mai sonki wanda yasan darajarki, ki neman ma kanki mutunci kiji dadin rayuwa kinji Yarinyar Kirki?" Chan kuma zuciyarshi ta tambayeshi Zaid me kakeyi? Da sauri ya fito daga dakin Zuciyarshi na k'una for no reason, tausayinta ne kawai fal cikin zuciyarshi, ya za'ayi yarinya kamarta ta dinga shan wahala haka? Wannan fa Batul dinsu ta girmeta.

Sai ga su Mama da Hashim sun bullo, gaishe da ita yayi, ya mata Sallama suka mishi fatan isa lafiya, Hashim ya kaishi tasha.7


Wurin 10 na Safe Watty ta farfado, nan nurses suka maidota Ward cikin sauran Mutanen da akayi ma aiki wanda ba a kai ga Sallama ba, dangi ko sai zuwa sukeyi wasu na zuwa wasu na fita, tuni aka kawo mata Zaid don ta shayar dashi, ba a cire bandage din ba, sai gobe, wata Nurse ta samu Inna tace "Baba, don Allah ku koma Gida, kun cika Asibitin, kun ga ba ku kadai bane, ana shiga hakkin yan Ward, kuma in Doctor ya zo zai mana fada, please Baba ku tafi Gida, ba zata wuce kwana 3 ba zaa sallameta" Inna tace "Afuwan kuyi hakuri, Auta ce shiyasa kuke ganin wasu na shiga wasu na fita, zamu koma zamu jirata a Gida" Inna ta takarkata Ahalinta suka koma gida, a bar ma Watty Zaid, Mama ma ta tafi Gida don ta huta Aunty Binta ce ke zaune da Watty a Asibitin, Watty na kan Gadon Asibiti amma Aunty Binta bata bar zaginta ba, "danUbanki ba ke dadi miji ba? To gashi ya nakasa ki, ba wanda zai ce miki kar ki koma, ki koma Watty" ita ba ta san wa ya bada shawaran a bar mata Aunty Binta ba, tana fama da kanta, tana k'ara mata zafi.


Wurin k'arfe 6 na yamma Ya Bu ya shigo Gidan cike da tsoro da fargaban abun da zai tarar, duk zatonshi Watty na gida, Sallama yayi dakin Inna ya gaidata tace "Mallam Habu, Allah yayi ka tashi?" Kai ya saddar, ya kasa magana, itama bata ce mai komsi ba, bai ga Watty ba bai ga alamunta ba, ba fuskan tambaya haka ya fita daga Sassan Inna, ba zai iya zuwa Sassan Baba k'arami ba, kunya, haka ya tarkata ya tafi Gidansu, nan ma babu wanda yayi mai maganar bisa ga Umurnin Inna, da ya tambayi Aisha ko tana da masaniyar inda Watty take tace "Ya Bu fita tayi? Ai tana Gidanka bansan ko ta je anguwa ba" haushi kamar ya sa mata hannu, ya zaiyi? Rana zafi inuwa k'una.5


Washegari

Watty Gaban Likita zaune yana kwance mata Bandage, sai da ya warware idon gabaki daya, ya umurceta da ta bude Ido, budewa tayi a hankali, Doctor ya dinga nazarinta, kafin ya umurceta da ta rufe idon dama da hannunta, tayi yanda yace, da yatsunshi ya jarabata ya ga dai tana iya fada mashi duk alamar da ya mata amma ya lura da wani abu game da ita.

Ya Lura Idonta ya jirkice, ma'ana kwayar Idon ya koma wani bangare na idon, ta zama mai kallon ruruwa, wanda ake cema kallon harara garke, sannan kuma bata ganin abunda yake nesa a takaice Mijinta ya Nakasata....Wani abu taji yana mata yawo, hawaye kawai ta fara yi, da sauri Dr Nazifi ya girgiza mata kai, kujera ya jawo ya zauna kusa da ita. Hauwatty ya kira sunanta, kin san akwai Masu kare mutuncin Mata da kuma yara k'anannu? A hankali ta gyada kai, yace "kin san zaki iya kai Mijinki k'ara gurin kan Domestic Violence?" Kai ta sake gyada mai ya cigaba "amma in ba ki son kaishi k'ara, kin san kina iya raba kanki daga shi? Kin san kina iya freeing kanki? Duk yanda wani ke son rabaku, in kika turje kina so, ba wanda zai hanaki amma ki sani, mai dukan mace daban ne, tunda ya fara, ba zai bari ba, its like an addiction, it will be hard for him to stop, ban san labarinku sosai ba, amma from the little i picked, this wasnt the first, kuma it definitely wont be the last, saurin hannun maza masu dukan matayensu kamar namiji ne mai shan sigari, ko yaya ne sai ya sha, haka ma wannan ko yayane sai ya mangareki, nan gaba ko gaban waye ba zai ji kunya ba, balle kum fara aje zuria".

Murmushin yak'e Watty tayi, ba ta son yawan magana ba ta kuma so a yi ta magana daya.

Dr Nazifi yace "na dameki ko? Kiyi hakuri, haka nake fa da naci, kiyi hakuri, we all want the best for you" Watty tace "wannan maganin shine kace bayan ko wani awa 6 zaa saka ko?" Murmushi ya mata, ya lura bata son maganar, ya gyada kai yace "ki kula da kanki, bayan 2weeks ki dawo a sake duba idon, ga wannan Glass din ki dinga sawa a ido, kar ki bar idon gurin haske musamman na waya, Allah ya kara sauk'i" a k'agare take dama, ta mik'e wuf tare da karban Gilashin da ya miko mata tace "Amin, nagode" ta fita waje inda Mamarta take ta gaya mata ya sallameta yace ta dawo bayan Sati biyu.

Mamarta ta rik'o hannunta tace "muje Gida, Watty ance Mijinki tun jiya bai bar k'ofar dakin Inna ba duk da ta koreshi, wai sai an gaya mishi inda matarshi take, nace ba zan koma da ke ba Inna tace aa mu koma gida, Watty, kinga dai abunda ya faru da idonki, duk da tsautsayi bai wuce rana, Watty.." ba ta bari Mamar tayi magana ba ta ambaci sunanta alamun ya isa tace "Mama, muje gida" Gaban Mamarta ya fadi, tana tsoron kar Watty ta koma gidan Jiya, don da alama har yanzu diyar ta ta na son Ya Bu.2


Sun isa gida Straight Sashensu suka nufa, parlorn cike yake da yayyinta, daya bayan daya ta kallesu ta gaidasu cikin gilashi, suka amsa tare da mata Ya Ido? A hankali ta zare madubin idonta, sosai suka tsorata ganin Idon watty ya juye ya koma mai harara garke, inda take kallo daban, inda abu yake daban, daya daga cikin yayyinta ta fashe da kuka tace "haba Aunty Binta, don banzanci ya kare a gurin Watty sai tace zata koma? Ido fa? Duba yanda ya mayar mata da ido" Anty Binta tace "wallahi Laura kar kiyi mamaki, Watty kuma da wauta, son Abu take kamar ranta, ai bata iya rabuwa dashi" dayar tace "aiko Watty ta koma ma Abu wallahi wallahi mama ba ruwana da ita" Idon Watty ya ciko da hawayen jin zafin maganganun yayyinta, Mama tace "ku bari donAllah, likita yace ta guji kuka" cikin muryar kuka tace "wai Yaya, mai kuka daukeni ne?" Ta juya da sauri ta fita, Mamarta ta rufe bayanta tana cewa "Kun ga ko, zata komama Abu" yayyinta 3 suka bi bayanta, Aunty Binta cikin zafi tace "ku kyaleta don Ubanta, jiki magayi, dayan idon zai bugo nan gaba, sai ta makance da hujja".


A Sashen Inna.

Ya Bu na gannin Watty ya mik'e tsaye, yana neman rik'ota, kallo daya ta mishi ta gane muguwar ramar da yayi, tsaye sukayi suna kallo da karantar junansu, Inna ce ta lek'o tace sai ku shigo ciki ko? Gabaki daya yan waje suka shiga Parlon Innan, wasu na zaune wasu na tsaye.

Ya Bu ya durk'usa gaban Watty tare da rik'o kafaffunta, magiya ya fara yi mata "ki yafemin Watty ta, donAllah ki yafe min, wallahi na bari ba zan k'ara ba" durk'usawa tayi gabanshi tare da tallafo fuskarahi ba tare da ta damu da Idanun da ke kallonta ba "Ya Bu donAllah ka bar kukan nan, na yafe maka, wallahi na yafe ma duk abunda ka min duniya da Lahira" haushi ya turnike sisters dinta da sukeji ba kamar Anty Binta da ta leko yanzu, ji take kamar ta rufe Watty da duka, Lallai Watty banza ce sakara, ba wanda ya iya ce musu komai, har Inna da ke zaune tana kallon Watty, mamakinta takeyi, wani irin So ne take ma Abu haka da ya sa ta shure komai ta yafe mishi?.6


Cikin murna Ya Bu ya kalli Inna yace "kin gani Inna, dama nace miki Watty bata iya rayuwa ba tare dani ba, rabamu babban kuskurene, Watty ta shi mu tafi Gida kinji?" Wurin kamar ruwa ya cinye kowa, ba wanda ya iya cewa k'ala, Ya mik'e tare da jan hannunta, tokarewa tayi ta cije, a hankali ya juye gareta, ido cikin ido suke kallon juna, gabanshi ne ya fadi, sai yanzu ya lura da Idonta, sai yanzu ya lura Idonta ya chanza, halittar fuskarta ya chanza, duk da bakinshi ya mai nauyi sai da yayi k'arfin halin cewa

"Mu tafi Gida Watty"

Jan ta ya sakeyi, ta tokare ta k'i motsi, wani murmushin da bai taba ganin ta yi irinshi ba ya ga tayi cikin yanayinta tace "ba zan bika ba Ya Bu, ba zan iya zama da kai ba kuma, nagaji Ya Bu, nagaji" tsoro da firgici suka diran mai lokaci guda yace "kince kin yafe min"

"Eh, na yafe maka a nan duniya, Allah kar ya jarabceka da hak'k'ina a nan rayuwar, na yafe maka a chan Lahira, Allah kar ya mana Hisabi ranar gobe k'iyama"

Karkarwa bakinshi yakeyi "to mu koma Gida tunda kin yafe min"

Kai ta girgiza mai "ba zan iya ba, zamanmu ya k'are"

Tallafo fuskarta yayi da hannuwanshi biyu yace "Watty nace na bari, ba zan sake ba, na miki Alk'awari"

"Haka kace wancan karon, alkawarin ka min, amma ka sake"

"Dagaske nake wannan karon, i am going to make everything right(zan daidaita komai)"

Murmushin takaici tayi tace "harda Idona? Zai dawo daidai?"

Dif yayi ya kasa ansa mata kusan seconds 15, kafin a hankali yace "Zaid..Zaid fa? Ki dube shi, kar ki mana haka, ya rayuwarshi zata kasance in muka rabu?"

Katseshi tayi tace "Shi ko na duba, ya zai tashi ya ga Mahaifinshi na dukan mahaifiyarshi? In ya koya fa ya yi ma yaran wasu? Ki kuma ya sa tsanar Mahaifinshi a ranshi kan abun da yake ma mahaifiyarshi, kana tunanin zanji dadi ko nagode mishi in ya tsaneka ta kan abunda kake min? Kar ka damu rayuwarshi zata kasance ingantacciya bayan rabuwarmu"2


STORY CONTINUES BELOW

Sosai yake kallonta, ya lura tunda ta fara magana ko gezau batayi ba, idonta kuma a bushe ba k'walla ko kadan, wannan wata ce tazo mai a sigar Wattynshi, wannan ba Wattynshi bace, wannan zuciyarta ta k'ek'eshe, Wattynshi kuma mai tausayinshi ce.


Baban Ya Bu ne ya shigo parlorn a harzuk'e ya nufo Ya Bu gadan-gadan "mutumin banza mutumin wofi, kaii Abubakar baka da mutunci ba kuma ka da kunya, har nema kake Hauwatty ta koma dakinka? Gaban Uwarta da danginta kake kuka bayan abunda kayi mata don tsabagen rashin kunya, to ai ko Wattyn ta amince zata koma ni ban yarda ba, dole yanzu ba anjima ba ka saketa, mutumin banza, na yi danasanin neman maka aurenta, kuma harda laifinmu, da muka aura mata mara tarbiya irinka, Allah ya san ban taba dungurin mahaifiyarka ba, amma kai gashi kayi sanadin idonta, to wallahi baka isa ka hadani da danuwana ba, baka isa zumuncinmu ya wargaje ta kanka ba, ba ka isa ka lalata mana zumuncinmu ba, ni dama ba ka dawo ba, dama ba mu matsa ka dawo ba, dama ba mu maka addua ka dawo ba, da ka shiga tsakanina da zumuncin 'yanuwana gwara na yafe ma duniya kai, dama chan ka manta da mu, Abubakar, ko baka saki Watty ba, wallahi wallahi kaji na rantse sai na raba auren, auren ku da zamanku ya k'are".


Ya Bu kuka yakeyi bilhakki, kan Watty a kasa bata bari sun hada ido da kowa ba, Ya Bu ya bude murya yace "Inna, ki taimakeni"

Inna da jikinta ya gama yin sanyi da duk wani abunda ya faru yanzu tace "Abubakar, wallahi da Watty ta amince zata koma dakinka, ba wanda ya isa ya hana, amma da kanta ta ce ba zata koma ba, kayi hakuri".


Babanshi ya chafe "zaka Saketa ko kuwa? Ka saketa Abubakar tun ban maka baki ba"

Dabas ya zauna k'asa, shikenan katangar k'arfe ya shiga tsakaninshi da Watty, ko bai saketa ba, zasu raba auren, a hankali yace "na saketa Baba, kar ka min baki donAllah, na sakeki Watty Saki daya".

Lumshe Ido Watty tayi, babu wanda ya iya karantar yanayin da take ciki, tafiya ta fara yi tayi hanyar fita Parlorn, inda su Aunty Binta suke tsaye, daidai yanda zasu iya ji tace "Na san ciwon kaina, ni ba sakarar da kuke tunani bace" ta wuce su suka bita da kallon tausayi, tana shiga sashensu ta shige chan cikin k'urya ta fada kan Gado ta cizga kukanta...6


K A N O


Kullum Zaid sai ya kira Hisham don jin yaya jikin Watty, Hisham ya sanar dashi an sallameta jiya, yanzu haka ta na gida.

Zaid ya rasa gane wani gidan yake nufi, Family house dinsu? Ko kuma Gidanta? Zumbur ya mik'e ranshi duk a jagule, yanzu yarinyar nan komawa tayi gidan mugun chan? ranshi ya baci, contact list dinshi ya shiga ya dubo numbernta da ya ma saving da "Hauwa"

Number ya dinga juyawa a wayarshi, satar numbern yayi a wayar Hisham, Ya Allah, ya saci numbern matar aure, zuciyarshi zafi take mai, bai san me ke ingizashi ba, amma yana jin Watty kamar k'anwarshi Batul, ya damu da sanin halin da take ciki, ya damu da ya ga ta fita da k'angin da take ciki, baya so kuma ya cigaba da tambayar Hisham game da ita, ba ya so ya ga kamar yana bin didik'inta, daga kwancen da yake ya yanke hukuncin tura mata text, jiran kusan awa daya yayi don reply amma shiru, daga karshe ya boye number ya kira sai dai yaji wayar kashe. Kanshi ya dafe yana karanta adduoin sanyaya zuciya.

***


BAYAN SATI 2


Zurfin cikin Watty ba zai sa a karanci yanayin da take ciki ba, da ta gama Idda za ta koma makaranta, zamanta haka ba zai yiwu ba, wayarta kuwa ta kasheta ta k'uddirta sai ranar data gama Idda zata kunnata, danginta na k'okari a kanta wurin ganin batayi kadaici ba, Aisha kullum tana wurinta, zumuncinsu ko kadan bai lalace ba.1


Ya Bu, tunda yayi Sakin na ba wanda ya sake sakashi a ido, Mamarshi ta shiga damuwa sosai, ta kira wayarshi yafi so nawa amma a kashe, da kanta taje Gidan amma a kulle saboda Babanshi ya sa an kwashe kayan Watty tas an dawo dasu nan gida, fargabanta kar ya fada cikin wani mawuyancin hali, addua take mishi duk inda yake Allah ya kare mata shi.


Ranar Laraba Watty ta koma Asibiti kamar yanda Dr Nazifi ya umurceta don a sake duba idon, bayan 'yan gwaje gwaje Dr Nazifi yace "Dinkinki ya warke, babu kuma wani abu a idon, sai dai wannan kallon ruruwan" murmushi ta mai tace "na saba ai" yayi shiru chan sai yace "Ina Zaid?" murya a shak'e tace "yana wurin Inna" da tsoron amsarta ya tambayeta "Kin koma dakinki ne?" Kanta ta saukar k'asa tace "aa ya Sakeni" zata rantse ta ji yayi hamdala a hankali, tashi tayi tace "barin je" yace "zauna, ai ban sallameki ba, akwai magungunan da zan rubuta miki" zama tayi ta na wasa da yatsun hannuwanta, yana rubutu yana kallonta har ya gama, maimakon ya bata sai kiran wata nurse yayi a intercomm din asibitin, jim kadan sai gata, mik'a mata takarda yayi yace "get these for me"

Cike da biyayya tace "Okay Sir" ta fita.

Office din yayi shiru sai karan fanka da A.C kawai kikeji, ba fira sukeyi ba, amma duk sun natsu, sai ga nurse ta dawo da magunguna a leda, ta mik'a mishi, ya karba ya zazzage a kan table ya fara yi ma Watty bayanin yanda zata digasu.

Karba tayi ta shiga zabga godiya, ta mishi Sallama tare da mik'ewa ta fita, Dr Nazifi ya bi bayanta ba tare da saninta ba, har ta tsaida Keke Napep bata san yana bin ta ba, a baya ya dinga binsu har suka iso Gidan Inna, sai da ya tabbatar ta shige kafin ya murmusa yace "zan dawo".7


STORY CONTINUES BELOW

Dr Nazifi


Ophthalmologist ne wato Likitan Ido ne da yayi karatunshi a India shekarunshi sha biyar a India, yayi karatu kuma ya fara aiki a wani Asibiti Apollo Hospital ne a k'asar Indian har ya zama consultant, kafin daga baya ya yanke hukuncin dawowa Gida Nigeria don ya taimaka ma k'asarshi, yana aiki a babban Asibitin General Hospital din Nassarawa, sannan kuma yana da Asibitin kanshi wanda ya bude ya na ganin Patients da daddare da kuma Weekends, shekarunshi 49, in ba gaya maka shekarunshi akayi ba ba zaka gane ba saboda kama yake da irin matasan nan yan shekaru 28 zuwa talatin, matarshi guda daya Lauratu, shekararsu 17 da aure amma Allah bai basu haihuwa ba, duk wani Asibitin da ke India ba wanda ba su je ba don neman haihuwa amma shiru kuma an tabbatar musu dukkansu Lafiyarsu kalau, lokacine bai yi ba, Laura ta na damuwa da rashin haihuwar amma kullum Dr Nazifi na kwantar mata da hankali da tunasar da ita shi haihuwa na Allah ne, bata samu matsalar dangin Miji ba don bayan aurensu da shekara 2 suka koma India, bata ganinsu ba sa ganinta balle ayi tsegumin rashin haihuwar, tsakaninsu da Nigeria sai dai su zo hutu, da kuma an gama hutu sai su koma, Mamar Dr Nazifi ta so kunna wuta kan sai ya sake wani auren saboda rashin haihuwar Lauran ya shaida mata ai shine mara lafiyan, shine baya haihuwan, shiru kakeji ba ta sake magana ba har ta koma ga mahallicinta, Dr Nazifi na san matarshi sosai baya son bacin ranta, bayan dawowansu Nigeria ya samar mata wani aiki a wata maaikata tana samu sosai don masters dinta biyu, bata damuwan komai sai ta rashin haihuwa.

Wannan Kenan.2


KANO

Batul ta shigo parlo taga Umma ta zabga tagumi, har ta zauna Umma ba ta san cewa Batul ta shigo ba, sai da Batul ta zare mata hannun daga tagumin Umma tayi firgigi, daidai da shigowan Yaya Fahad, duk sun lura Mamar tasu na da damuwa boyayye.

Fahad ya kalli Batul yace "me ya faru? Me aka ma Umma?" Batul tace "ka ga Ya Fahad daga school nake na shigo na ganta haka" duk hankalinsu suka mayar wajenta Fahad yace "Umma yadai?" Naunauyar ajiyar zuciya ta sauke tace "Yanzu Aunty Sarah ta bar wannan kujerar da kake zaune, tazo min da wata magana, wai ashe Zaid da Hawwa sun daidaita kansu abu yayi kyau, da mamakina nace wani Zaid da Hawwan? Tayi dariya wai ina yi kamar bansani ba, nace wallahi bansani ba, ni ban ma gane maganar ba, nan take shaida min cewa Ahmad yace ma Saidu mijinta zai hada auren Zaid da Hawwa k'arshen Shekara tare da na Batul".

Gabaki dayansu suka zaburo, Batul tace "Umma bangane ba"

Umma tace "Uncle Ahmad dinku ke son ya hada Zaid da Hawwa aure, tare kuma yake so ayi da naki"

Batul tace "Shi Ya Zaid din yace yana son Hawwa?"

Ya Fahad yace "Umma, kinyi magana da Abba?"

Kamar daga sama Abbansu ya shigo, ganinsu cikin yanayin nan ya sa shi tambayar baasi, Fahad ya ma Batul alama da su shiga ciki, tashi sukayi suka basu wuri.

Suna shiga ciki kuwa Umma cikin k'una tace "yanzu Abban Fahad, a matsayina na Mahaifiyar Zaid, har ku yanke hukuncin aurar da Zaid, banda arzikin a gaya min sai dai naji a waje?"

Cikin rashin fahimta yace "Ade ban gane ba?"

Gani take ma rainin wayau zai mata tace "Zaid da Hawwan da kuke so hadawa aure mana"

Cike da mamaki yace "Zaid da Hawwa kuma, inji wa? Wannan labarin kuma daga ina?"

Sai yanzu tayi naam be san da zancen ba, don mijinta baya boyeboye, a hankali ta mishi bayani yace "Tooooo, to ni wallahi bakinki nakeji"

Kamar zatayi kuka tace "tace tunda ka auroni, sai dai ace Saade ga yanda zakiyi, ina so bana so zanyi, bani da wani zabi sai abinda kukace, banda ikon da zaa nemi shawarana sai dai na hau kai in an zautar, kuma dan da na haifa ace zaa min iko dashi? Har ayi maganar hadin aurenshi ban saniba?"

Abban Fahad yace "Wallahi Saade bakinki nakeji, kuma nayi Imani Hajiya bata sani ba da ta min zancen, Ahmad yake abunshi, bai min magana ba, in kuma hadin yake so ko ba dade dole ya mana maganar, tunda ba zai aurar dasu ba da sanin mu ba, yanzu haka maganar ma rumor ce, Ahmad ai baida abokin Shaawara da ya wuce ni, in ma hakan ne ni zai sama ba Sa'idu ba, ni ban ga wani abun tashin hankali ba" chan tace "nima dai ina mamaki, ace ko ba komai ai ya nemi shawararmu" haka dai suka bar maganar, ta raya a ranta k'ila Sarah bata ji da kyau ba, kila Ahmad cewa yayi yana so duk ya aurar dasu gabaki daya December.


STORY CONTINUES BELOW

Abun mamaki kuma sai magana ta fara fitowa daga bakin dangi, Zaid zai auri Hawwa, Hajiya bata mata maganar ba, da alamu itama bata sani ba, amma da ta hadu da mata biki ko suna sai an mata murna, ta sake taryan Abban Fahad da maganar, yace "wai ke meye kike tashin hankalinki? In ma hakan ne ni ban ga abun tashi hankali ba" fita tayi kawai, ita ta ga abun tashin hankali, ita ta ga mai ta gani, ita ta san mai ta hango, shiru kawai tayi ta k'uddirta a ranta duk randa Ahmad ya tareta da maganar nan, zaiji magana kuwa, Danta ya auri Hawwa? Yarinyar da ba ta san girman kowa ba? Ba zai yiwu ba.

Ta san Zaid da shiga damuwa, abu kadan ke tsaya mai ya dameshi ya hanashi sukuni, nan ta gargadi yanuwanshi kan kar su mai maganar tunda har yanzu Uncle Ahmad baiyi magana ba.

***

B A Y A N  W A T A  U K U4


A cikin Motarta take jin wak'okin zamani, sanye take da Bak'ar Jallabiya da tayi mata kyau matuk'a, shigar da Alamin dinta ke so kenan ta larabawa, shiyasa duk ranar da zasu hadu take yin shigar, tuk'i take yi cikin k'warewa, Zance zata, Saurayin da take so baya zuwa wurinta, a cewarshi tafi k'arfinshi, ba zai iya zuwa Gidansu ba da sunan zance, mai wankin gidansu ya fishi daraja, ranta baci yake a duk lokacin da Alamin dinta yace tafi karfinshi, randa ta matsa mishi sai yazo da yaje Hajiya Iklima ta mishi wulakanci sosai, kuma da ta gano asalin Alamin din, sai ta saka k'annenta su ci mishi mutunci suna mai warning kan ya rabu da diyar Hajiya Iklima, tun baya gaya ma Masoyiyarshi k'alubalen da yake samu sanadiyarta har ya fara gaya mata, a duk lokacin da ya gaya mata sai sunyu fada da mamarta, har gaba takeyi da Hajiya Iklima ta kan Alamin dinta, tana son ganinshi kullum, amma kamar kulluk gaya mata iyakar gaskiyarshi yake na ba zai iya zuwa gidandu ba, sai tace "shikenan, ba sai kazo ba, ni zan dinga zuwa ina ganinka" sai tazo Anguwar bata shiga gidajen kakkaninta ba ta uwa ta uba ba, da ta zo bakin shagon da yake zama, zatayi horn, ya shigo motar su zabga zancensu su ya fita ta kama hanyar Gida.2


Haka ma yau tayi Horn gaban Shagon Dinkin da yake zama, tayi horn, ta hangoshi ya hangota amma yak'i tasowa, gaban Hawwa ya fadi, da idan tazo tun kafin tayi Parking zai taso jiki na rawa, amma yau yayi mirsisi, horn ta cigaba dayi amma ba alamun zai taso, abokinshi yace "Amin ga fa Hawwa chan" tsaki yayi yace "kyaleta" Hawwa ta dinga kiranshi a waya yaki dauka, Abokin ta kira a waya jikinta duk yayi sanyi, tace "wai Alamin be ganina ne? Ka ce mishi yazo danAllah" tana jin muryarshi yace "ba zan zo ba, ba ni ba ita" gabanta taji ya fadi, tace "wallahi ko yazo ko ni nazo gaban shago" ya san zata aika, zata jawo mai magana, tashi yayi a fusace ya nufo motar gwara ayita ta k'are.


"Ka shigo muyi magana"

cike da bacin rai yace

"ba zan shigo ba"

"to bari ni na fito"

Ta na fitowa kuwa ta fashe da kuka "Alamin dina me na maka ka tsaneni lokaci guda? Meyasa kake min haka? Kana kona min zuciya, meye laifina?"

Baya son kukanta don ta bar kukan yace "ni ki gaya min meye laifina? Son ki shine laifi? Ashe don na so ki ake kirana da kwadayayye? Ake zagar min Mahaifa, Hawwa Ina sonki sosai, amma ba zan tsaya a zagar min Mahaifa ba saboda ke, haba kamar kina ciyar da mu ko tufatar damu ake ce mana kwadayayyu? Don na soki Hawwa? Sonki ne laifi?"

Hawayenta ya sharce da sauri tace "Mummy ta sake zuwa ne?"

Shiru yayi

Ta daka mai tsawa "nace Mummy ta sake zuwa ne?"

A hankali ya gyada kai yace "su Abba ne da Khalifa"

A tak'aice tace" good"

Ta fada motarta ta finciki motar da karfi ta bar unguwar a guje, ko shiga da motar batayi gida ba ta fito ta fada gidansu tana kwada ma Mahaifiyarta kira tun daga haraban Gidan.1


"Mummy!!" Hawwa ta k'wala mata kira kamar wata tsararta, da sauri Hajiya Iklima ta k'araso tana tunanin wani abu ya samu diyartata saboda yanayin da ta ji muryarta ta san cewa ba lafiya.

Rik'ota zatayi Hawwa ta matsa baya da sauri cikin zafi tace "Mummy wai meyasa kike min haka? Meyasa kuke min haka? Ina ruwanki da Alamin? Nace miki ki fita daga harkanshi, idan ba zaki amince dashi ba, ki kyaleshi, ni na amince dashi, amincewa ne dama ya kamata ba naki ba, nace shi nake so, shi zan aura, ba wanda ya isa ya rabani dashi, to kin san da wannan kuma meye zaki sa su Uncle KB tozartashi? Don me zaki sa a dinga wulakantashi, ana ci mai mutunci ana zagin Iyayenshi? Meye laifinshi?"3


Kamar tsoron diyartata take, ta fara bata hak'uri, "Hawwa, donAllah ki bar daga murya, yaron nan ba ajinki bane, Diploma fa gareshi, gidansu basu da komai, unguwarsu duk kwata, teaching yakeyi, primary ma for that matter, sai yayi buga buga ya ke ciyar da Mahaifiyarshi da k'annenshi, mai na sama yaci bare ya ba na k'asa? Mai zaku ci? Chalk? DonAllah ki manta da wani Alamin".1


Ran Hawwa ya baci matuka da jin kalaman Mahaifiyarta ga Masoyinta, idonta ya k'ank'ance saboda rashin kunya, "Mummy, ki gaya min lokacin da kika auri Daddy me yake dashi? Bai da komai kika aureshi, Abincin da zakuci safe rana da dare Daddy ke nemo muku? Ba Baba Abdullahi ke baku ba? Mummy dakin da kika zauna kina amarya Baba Abdullahi ya gyara muku, Daddy ya sha gaya min cewa ya sha aron kayan Baba Abdullahi ya zo gurinki zance, duka duka yaushe Daddy yayi kudin da za ki dinga k'yamar wani talaka? Unguwar kwatocin da kike magana, ba Anguwarku bane? Ba anguwar su Daddy bane? Ba anguwar kika zauna shekara da shekaru ba? Hajiyarsu Daddy har gobe tana Anguwar, To meye aibu dan nace dan Anguwar nakeso? Kika san arzikin da Allah zai mishi nan gaba? Dare daya Allah kanyi bature, ke kin sani ai, tunda haka ya faru da daddy, Alamin shine Farincikina, in kika cigaba da sawa ana bata ma Alamin wallahi zaki nemeni ki rasa".6


Fuu ta wuce sama ta bar Hajiya Iklima tsaye baki bude, Hawwa ta kasheta da mamaki, bata taba zaton Hawwa zata iya kallonta ta gaya mata magana haka a matsayinta na Uwarta Mahaifiya, hawaye ta ji kawai ya gangaro mata, ranta ya sosu, duk son da take ma Hawwa, haka zata mata? Diyarta ta ci mata mutunciDon ta so siyan mata mutunci kamar kullum ayanawa tayi a ranta "Sa'adatu ta gama cutarta, bata ba Hawwa tarbiya ba".1


N A S S A R A WA


Wayarta ta dauko ta jona charge 57% ta gani, barin wayar tayi don ta cika ta kunna, bayam awa daya da yan mintoci ta shigo dakin tare da cire charge din ta kunna wayar, messages sukayi ta shigowa, daga MTN wasu daga Ya Bu lokacin da take Asibiti kafin ya saketa, wani message ne ya ja hankalinta, ta karanta, wuri ta samu ta zauna sosai don sake karantawa;


Muturwa Aure ba dadi, haka ma yarda da cewan wanda kika so ba dukkan kauna, sadaukarwa da lokaci gareshi har karshen rayuwarki yana muzguna miki tare da zaluntarki, akwai abubuwan da ko ba ki fade su a bayyane ba chan k'asar zuciyarki kin san cewa ga fa abunda yakama ceki Saboda kina sonshi, saboda ke yarinyar kirki ce, kina fatan zai chanza, kina adduar ya chanza, ba ki cire rai zai chanza ba sai dai kash, bakin alkalami ya bushe. Amma baki so ki yarda da hakan, sai kika zabi ki kara hakuri, kika zabi tuna lokacin da kuke cikin farinciki, ki na bata lokaci wurin yarda da abin da ya kamaceki, ya kamata ki kalli gaba, ki duba rayuwarki, ki duba ta takwarana Zaid, ya kamata kiyi abunda ya kamaceki, ya kamata ki kasance cikin farinciki, ya kamata kuma kiyi abunda zai fisheki, babu wanda zai ce miki don me don kin zabi ki so kanki a karo na farko, so so ne amma son kai ya fi, ki rik'e Allah, ki ta addua, kice "Ya Allah, in cigabana da zama da mijina shine mafi alheri a gareni, Allah ka daidaita tsakaninmu ka bamu zaman lafiya, in ko rabuwa dashi shine mafi alfanu, Allah ka saukaka min komai, ka musayyamin shi da wanda ya fi shi Alheri, donAllah ki kasance cikin k'oshin lafiya.1


Ta karanta sak'on nan fiye da so 5, ranar da text din ya shigo ta duba, ranar da Ya Bu ya saketa ne, duk tunaninta ta kasa gane waye, yanke hukuncin kira tayi, missed calls har biyu baa dauka ba, chan ta tura text.


Z A I D


Wayarshi ce take ruri, gabanshi ya fadi da ya duba ya ga Hauwa, kasa dauka yayi har wayar ta tsinke, wayar ta sake shigowa, kamar dazun har ta katse bai dauka ba, gabanshi kawai dukan uku uku yake sai chan ya ji shigowar message da sauri ya bude.

"Nagama Idda kwana tara da suka wuce, nagode da kalaman k'arfin guiwar nan, Allah ya saka da alkhair"


Lumshe Ido yayi ya bude, wani dadi, farinciki da annashuwa suka dirar mai lokaci guda daya.

Kiranta yayi, dauka tayi, shiru duk sukayi kafin ya katse shirun da cewa

"Hello, Yarinyar Kirki"

Wani abu ta ji da ba zata iya kwatancenshi ba, Mixed feeling ne, shiru tayi, ta kasa amsashi.

"Yarinyar Kirki" ya sake cewa

Ba tare da tayi wani dogon tunani ba tace "naam Yaron Kirki"

"Allah ya miki Albarka Yarinyar Kirki"

"Ya Allah" ta furta a hankali.

"Kinji? nace Allah ya miki Albarka Yarinyar Kirki"

Lumshe ido tayi ta bude, ta na karban duk wani sakkon da yake isar mata "Allah ya maka Albarka Yaron Kirki"

"Amin Yarinyar Kirki"

"Ya Sunanka?"

Murmushi yayi yace "Sunana Yaron Kirki"

A hankali ta furta "Yaron Kirki"Daga waje yaji muryan Batul ta na cewa "Ya Zaid Umma na kira" yace "Ina zuwa Yarinyar Kirki, zan kiraki" murmushi ta sakeyi tace "sai ka kira Yaron Kirki" ya datse kiran ya fita amsa kiran Mahaifiyarshi.+


Ta na zaune kan tabarma a tsakar gida, inda kafarta yake ya samu guri ya zauna, Yayanshi Fahad a kan yar k'aramar kujera, Batul daga gefe, yanda ya ga sunyi jigum-jigul ya zargi ba lafiya, yace "ya akayi ne? Me ya faru?" Umma tace "Zaid, na sanka da damuwa da saka abu a rai, shiyasa tun farko banyi niyyan gaya maka ba, amma ganin yanda magana ke yawo cikin dangi na san ba da dadewa ba zai dawo kunnenka"

Cikin zak'uwa yace "Umma menene?"

Kai tsaye tace "Hawwa ake so ka aura"

Cikin wata irin murya mai cike da tashin hankali yace "Hawwa? Umma Hawwa? Su wa ke so na aureta? Ni nace aure zanyi yanzu ne?"

Ganin yana neman fita daga hayyacinshi ya sa ta cewa "saurara kaji, Uncle Ahmad dinku yake so yayi hadin nan, bai gaya ma Babanku ba, bai gaya min ba, kai ma bai gaya maka ba chan cikin dangi magana ke yawo, to mu sanya mishi ido muga iya gudun ruwanshi, ai dai ba zai maka aure ba tare da saninmu ba ko?" Gani tayi hak'oranshi na garuwa da juna, magana k'wak'wara ya kasa yi, abunda take gudu kenan tun farko, amma gwara da ta gaya mai.

Hannunshi ta dan rik'o tace "Zaid kar ka daga Hankalinka, Kai dai kawai ka zama cikin shiri, don zai iya taranka da maganar, na san Ahmad da kwarjini, kar ya cika maka ido ya maka kwarjini ka amince, ko da ya zo maka da zance ka gaya mishi kana da wacce kake so Hawwa kuma k'anwarkace kamar Batul".

Shi dai Zaid ya kasa magana, duk ya basu tausayi chan dai yace "Zanje daki Umma"

"Kaje daki Zaid"

Kamar jira yake yayi wuf ya shige cikin dakinshi.2


Ya na shiga dakin ya rik'e kanshi da ke barazanar tarwatsewa, gani yake kamar ya auri Hawwa ya gama, don matsayin Uncle Ahmed a gurinshi ya wuce ya bashi diyarshi yace bayaso, Uncle Ahmed ya mai hallaci ya nuna mai so, ba zai taba k'in jininshi ba, duk da auren Hawwa zai zame mishi kamar daukewan duk wani irin jin dadinshi da walwala.

Kafin Maghrib zazzabi mai zafi ya rufe Zaid, haka yake in ya sa abu a ranshi, duk ya takure, Ummanshi har tayi nadamar sanar dashi, jiran tsammani suke, suna jiran ranar da Uncle Ahmed zai fito da k'uddirinshi fili.

N A S S A R A W A


Ranar Watty ta yini da waya a hannu ta na jiran kira daga Yaron Kirki, shiru be kira ba, har dare, ko lafiya? wata zuciyarta ta so ta kirashi,dayar zuciyar kuma ta haneta ganin wayar da sukayi duka-duka daya, ba ta san komai game dashi ba, kuma basuyi sabon da zaa ce ta kirashi ta ji ko Lafiya ba.

Haka dai ta kwanta bacci tun tana tunanin Yaron Kirki, har dai bacci me nauyi ya dauketa.

****

Bai kirata ba har bayan kwana biyu, ita kuma har i yau bata daina tunaninshi ba, karatun ta natsu ta ma kanta.

"Ban sanka ba, naga sak'on ka, na kiraka, na yi waya da kai, kace zaka kirani, ba ka kirani ba, ka tsaya min a rai, me kake so nayi Yaron kirki? Na kiraka? Ina mace? Nayi ta bibiyarka? Wai ma meye ma zan damu da kaina da kai? Mtss, in ni kake jira na kiraka, zaka bushe".

Tun daga ranar ta yakice tunanin Yaron Kirki daga kanta, ta na matuk'ar k'okari wurin ganin bata tuna shi ko so daya ba.


Daga Sashen Inna aka kirata, dankwali ta daura ta nufa Sashen, ta shiga da Sallama, nadamar rashin saka mayafi tayi ganin ba Inna kadai bace.

Murmushi tayi tace "sannu da zuwa, ina zuwa" ta shige dakin Inna, wardrobe din Inna ta bude ta dauko Gyalen Inna ta dawo Parlorn.

Kan kujera ta zauna fuska dauke da murmushi tace "Doctor Ina Wuni"

Murmushi ya mata yace "Hawwatty, kina lafiya?"

"Lafiya lau ya aiki?"

"Aiki Alhamdulilah, Ya fuska?"

Tace "ahh na warke kwarai Alhamdulilah, dama ka san gidanmu ne?" Bai kai ga bata amsa ba

Inna tace "Wattynmu, wai Dapta yazo da wata magana ne, game da ke, nace ahh lallai kizo ya gaya miki da kanki don ba maganata bace"

Raurau tayi da ido tace "Idona zai sake samun matsala ko?"

Murmushi yayi yace "Aa Watty, Zuciyata ce dai zata samu matsala in har baki amince min ba" ware idanuwanta tayi tare dan lumshesu ta bude, inda take kallo daban da inda yake.

Inna tace "Kinga Watty, zuwa yayi guna wai yana neman aurenki, ya jira kin gama Idda shiyasa ya gabato don kar a mishi shigar sauri, ya nemi ya gana da Magabatanki nace mishi magana daya ce, yanzu ke bazawara ce, zabin aure na gareki wurin ke kadai, ba huruminmu bane zaba miki Miji, ko wurin Iyayenki maza yaje wurinki zasu turashi, don ke ba budurwa bace da zamu miki iko kan wanda zaki aura, ke kadai ke da damar zabar ma kanki mijin Aure, ba abu bane na sauri, ki dau lokacinki kiyi tunani"

Tunda Inna ta fara magana take wasa da yatsunta da Inna ta buk'aci tayi magana sai tace "nifa Inna yanzu tsakanina da Allah ba aurene ke gabana ba, Karatu nake so na koma"

Inna tace "'magana ta Allah kin san Iyayenku ba zasu yarda ba, kinsan ba aladar gidan nan bane Mace ta cigaba da karatu ba aure, duk sauran yayyanki da danginki mata daddayaku ne mazajensu suka amince musu da su cigaba da karatu, Kinsan dai Iyayenki ba zasu bari ki cigaba da Karatu kina karkashinsu ba, in kina da burin karasa karatu kya yi a dakinki, Allah barshi sai kuyi yarjejeniya da mijin da zaki aura".


STORY CONTINUES BELOW

Shiru Watty tayi sosai, Dr yace "Alkawari ne Watty, in Allah ya sanya ke rabo nace, zan nemar miki Makaranta ki cigaba da karatu, Ina da Mata banda yaro ko daya, zan rik'e Zaid kamar ni na haifeshi".

Shiru Watty tayi sosai, ganin bata da niyyar amsashi ya mik'o mata waya yace "ki sanya min numberki, zan dinga kiranki donAllah, ba zan yi rushing dinki ba".

Dan basarwa tayi kafin daga bisani ta sanya mishi numberta godiya ya mata, tare da godema Inna ya musu Sallama ya fita.

Nan Inna ta dinga bata baki, bata ce ta amince da Dr ba, amma ta na tunasar da ita ko shekara nawa zatayi a gida batayi aure ba, Iyayenta ba zasu yarda ta cigaba da karatu ba, rufin asirinta Aure.


K A N O

H A W W A


Kamar za ta yi kuka tace "Alamin dina dagaske babu mai rabani da kai, donAllah ka yi hakuri"

Cike da tausayinta yace "Hawwata bansan ya zanyi ba, ana ce min wai ba mu dace da juna ba, Hawwa ina tsoron gaskiya ne hakan, duk yanda banson fada Hawwata kin fi karfina, sahun Giwa ya zarce na Rak'umi"

Hannu ta sa ta rufe mai baki tana girgiza kai tace "kar ka sake fada, bana so na k'ara ji, ni Alamin dina nace ina sonka, kuma wallahi sai na aureka, ko da kowa zai juya min baya, nidai ka min Alkawarin Aure"

Gani yake kamar bata fahimtar abunda yake so ta gane yace "Hawwata, ba Auren ba, banda abunda zan rik'eki, Hawwa ban son ko zan baki farincikin da kika saba dashi ba, Hawwata bansan ko zan iya miki Hidimar da kika saba dashi ba, bana so na miki k'arya, ina sonki sosai, ba zan taba nadamar sonki ba, amma wallahi Hawwa banda abunda zan rik'e ki dashi"

Murmushi tayi cikin kukanta tace "Ka bani tabbacin da nake sonji Alamin dina, tunda kana So na, angama, zamuyi Aure kaji, ka ajiyeni a dakinka a gidan Goggo, zanci abunda duk ka kawo, in ba ka kawo komai ba, zan rungumeka na ci bakinka nayi bacci"

Wani murmushi mai sanyi ya sakar mata tare da fadin "Hawwata"

Itama murmushin tayi tace " Alamin dina".2


A G U R G U J E


ZAID


Zaid ya na cikin tsananin damuwa, ya rame duk ya jeme, har Uncle Ahmed ya tambayeshi damuwanshi yace mishi kawai bai lafiya ne, ya bukaci da yaje asibiti, Zaid bai jin dadin komai, bai da walwala, yana ta kanshi,ya ma manta da wata Yarinyar Kirki, ba ta ita yake ba, shi kawai burinshi ya ga ya kubuce ma auren Hawwa, duk da Uncle Ahmed din bai furta ba, amma ya san ya furta ba makawa sai anyi, haka dai ya koma wani sukuku da shi.


W A T T Y


Abu daya me ba Watty mamaki, ganin yanda Mazajen aure su kayi mata chaaa zuwa suke daga wuri nesa da kusa neman aurenta, sosai take mamaki wai ko dai hotonta aka kai Massallaci aka ce bajawara ce ita? Yau in Bajawarinta Suleiman yazo, gobe wani bajawarin zaizo, Babanta ya gaya mata ba zai yiwu ta dinga tara mai Maza haka ba, duk da bata kulasu, ta fiddo daya a tsaida magana zaif.


Zama tayi tana nazari, ita tasan dole mai Mata zata aura a matsayinta na bazawara mai da, wa zata fiddo cikinsu da ya wuce Dr Nazifi? Dr Nazifi ai ya cika ta so shi mutum ne mai cikar zati da kamala, ta hanya daya ya siye Watty, ta nuna mata kula da tsantsar Soyayyan da ta dade tana burin tayi irin shi da Ya Bu, ta dade tana mafarkin samun irin wannan Soyayyar.

Dr Nazifi ya dan Manyanta amma in ya mata wani abu kamar chewing gum boy dan shekara 24, shine Shagwaba, shine kiranta duk wani lokacin da bai da aiki yana tambayarta ta ci abinci, ya Zaid dinshi, tana kular mai da yaronahi ko? Shine kiranta Baby, shine kiranta Waffles, wai shi yanzu bai ce mata Hawwatty sai dai Hawwaffles, wai duk Soyayyar ce haka kamar ba dan shekara arbain da dori ba, dan boko ne tsantsa, shiyasa take sonshi, kuma ta amince dashi, batayi hanzari ba ta duk'ufa da adduoi da Sallahr Istikhara zuciyarta ta aminta dashi, ta gabatar ma Iyayenta dashi.

Ba boyayyen mutum bane, sananne ne, aka dukufa bincikenshi ciki da bai, bayan duk an amince da Juna, aka sanya Biki Wata 3.


Bayan Wata 3

Matar Mutum K'abarinshi, Watty ta zama Matar Dr Nazifi, kayan dakinta na gidan Ya Bu tas aka maida mata sabon gidan Aurenta don ba suyi komai ba, ba gida daya take da Kishiyarta ba, wani three bed room flat Dr ya kama mata take zaune.

Anty Binta sun tsaya mata wurin gyaran jiki da shawarwari kan zama da Miji da Kishiya duk da ba tare suke ba.

Kishiyarta tayi tashin hankali da zaayi aurenta ko ba tayi ba ita dai ba ta sani ba, Mijinsu ma bai ce mata komai ba, ta san ana hada Amarya da Uwargida a yi musu Nasiha bayan Aure su dai baa musu ba, ba ta taba ganin Uwargidanta ba, ta dai santa a hoto amma bata tunanin in ta ganta Zahiri zata ganeta, amarcinta taci na kwana bakwai kafin ya sanar da ita zai dinga zuwa wurinta bayan kwana bibbiyu, kuma Alkawari ya cika mata ya sakata a Computer School da niyyar in an fara Jamb zatayi ta wuce Jamia.1


STORY CONTINUES BELOW

K A N O

Waya ta ke da Farincikinta Alamin, ji tayi an daka mata tsawa, cikin kwanciyan hankali tace "Alamin dina, ina zuwa, zan kiraka" ta kashe wayar tare da kallon Mamarta.

"Yadai Mummy?"

Hajiya Iklima ta kalli diyarta cike da takaici tace "wai Hawwa ba za dai ki fita daga harkan Alamin din chan ba?"

Hawwa cikin dan daga murya tace "wai Mummy mai ya miki?"

Haj. Iklima tace "bai min komai ba, amma bata lokacinki kikeyi, don ba zaki aureshi ba, mai na sama yaci bare ya bawa na k'asa?"

Hawwa cikin daci rai tace "ni dai zan zauna dashi ko? To nace shi nake so shi zan aura, Mummy duk randa na zo nace ki taimaka min da ko naira50 ne Mommy ki tsinemin".

Da mamaki Haji Iklima tace "Eye? Kina da hankali? Anya yaron nan ya barki haka? Anya ba asiri ya miki ba? To wallahi ko asiri ya miki sai ya karye, don baki da Miji da ya wuce Zaid"

Shareta zatayi da, amma sai taji maganar k'arshen ya zo mata wani iri ta dakatar da Mummyn da ke niyyan wucewa

"Mai kikace Mommy? Wani Zaid?"

Mommy tace "Wani Zaid din kika sani? Na Saade mana"

Wani dariya Hawwa ta fashe da shi tace "Lol Mommy Lol"

Mamaki ya kama Haj. Iklima tace "Lol? Ban gane Lol ba"

"Mommy ai naji kina wani maganar banda Miji sai Ya Zaid"

Harda rike k'ugu Haj Iklima tace "Eh gwara ma ki kwantar da hankalinki, ki koya ma kanki Son shi don shi zaki aura".9


Hawwa tace "Ni Mummy ina mamaki, donAllah baki ji kunyar maganar nan ba? Bai miki nauyi a baki ba? Yaushe kika zama Fan din Umma ne? Balle Yaranta? Mummy tunda nayi wayau fa kike nema ki rabani dasu har sai da na bada kai bori ya hau, Yaushe kika fara sansu da har kike nema na aureshi?"

Hararta tayi tace "eh din ai bance ina son su ba, Zaid din ne Daddynki yake so ya hadaku, kuma ai Zaid daban ne Yaron Babanki ne, sai abinda yace yakeyi, kuma baida bakin halin Saade da wannan Fahad din mai zafin rai, kuma dai duk yanda banson hada iri da Saade Zaid din ya fiye min aurenki da wannan Fak'irin Alamin din, to ki ma sani tun yanzu, Zaid zaki aura".

Hawwa jin labarin tayi kamar na gizo da na k'oki wato tatsuniyya, earpiece dinta ta maida kunne tare da cewa "OK ooo" ba tare da damuwar komai ba ta daura kafa daya kan daya ta saka sautinta, don ta san ba zaa taba yi ba, ba zai taba yiwuwa bane.

*********5


Hawwa Ahmed miskila ce, baya ga Mahaifinta da Alamin dinta, da Sheela k'awarta ba ta sakewa da kowa, harta Mahaifiyarta, da wuya kaga sun zauna suna firan 'ya da uwa, ta fi zaman daki da wayarta a hannu da earpiece a kunnenta.

Kallon da mutane ke mata shine mai girman kai da mai raina arzikin dan adam, wanda daga kan masoyinta Alamin zaa san bata da rainin arziki tunda har take son shi kamar ta kai kanta gidanshi, rashin shiga harkar mutane ya sa ake mata lakabi da yar jiji da kai, fadar gaskiyarta ba tare da sakaya magana ba ya sa aka dauketa a wacce ba ta iya magana ba.

Hawwa Shagwababbiya ce sosai, Hawwa akwai ta da k'uiwa, Hawwa bata da saurin sabo, in tayi wani abu kamar mara wayau, ita dai ga rayuwarta nan dai.

Baya ga haka Hawwa ba ta da wani mummunan dabia, tabbas tarbiyar Saadatu ce, laifin Hawwa daya, ta yasar da Iyayen Goyonta wanda hudubar Uwarta da kuma dama rashin son mutanen ya sa ta watsar dasu.

***4


Lectures gareta 9, ta sauko daga sama ta nufi babban Parlo, Daddy da Mummy na kan Dining table suna breakfast har ta nufe su ta ji suna maganarta, birki ta ja ta koma baya.

"Nace miki ki bar mata maganar Iklima, ki zuba mata ido, zata daura ma kanta aure ne? Ko guduwa zatayi taje wani wuri a daura musu aure, in dai nine Mahaifinta ai nace bata da Miji sai Zaid ko?"

Hajiya Iklima tace "yanzu yaushe zaka fito fili da maganar ba ni so a samu matsala"

Uncle Ahmed ya kalleta sosai yace "matsala? wurin Zaid d'ana? Ko kuwa Yayana? Babu wata matsala fa"

Hajiya Iklima tace "Hawwa fa?"

"Ko ta bada matsala a farko, dole ta bada kai bori ya hau, so nawa akayi auren da ba na Soyayya ba bayan anyi tsiya da farko a zo ana Soyayya me zafi, kamar ba kece kike karence karence ba? Ba abinda marubatan hausan naku ke rubutawa ba? To itama hakan ne zai kasance da su, balle na san babu k'iyayya tsakaninsu, akwai wannan 'yanuwataka na jini wanda kika tsaga tsokarsu zaki ga jinin ko wannensu a jikin danwanshi"

Mummy ta numfasa tace "yanzu duk December zaa hada Auren ayi harda na Batul din?"

Dan shiru yayi na dan lokaci kafin yace "kin gane Iklima, akwai wani course da nake so na tura Zaid yayi a South Africa, 7-9months course ne, office na so yayi presenting certificate din zuwa May next year kin ga Shekara daya kenan, so i was thinking ko sai ya dawo sai a yi nasu auren".

Mummy cikin damuwa tace "uhm uhm, ni dai da anyi auren December din, sai ya dawo ya tafi da Hawwa chan, ina tsoron tafiyarshi da rashin auren a shekarar nan zai sa ta ki rabuwa da Alamin din nan"

Uncle Ahmed yace "Iki, course din na bukatar Concentration, Karatun baya son Distraction, kuma Hawwa zatayi Distracting dinshi don wallahi na santa akayi auren nan haka zata hana mishi kwanciyar hankali a wata ka'sar da babu mai kwabanta, gwara kawai a bari ya dawo, ina da Plans kan Zaid, ina so ya gajeni ko da nayi retire".

Mummy tace "to a daure Auren, in ya gama course din ya dawo Nigeria sai ta tare, ni ina tsoro".

"Wai Tsoron me kike? Kin manta waye Zaid ne? Zaid fa na aje kara nace kar ya ketara wallahi ba zai ketara ba, duk mai na sashi yanayi, kuma wallahi na san ba zai bijiremin kan auren Hawwa ba, amma duk da haka, ana iya daura Auren December, in ya dawo sai ta tare, but still zan gaya mishi k'udirina, kuma zan tambayeshi raayinshi kan a daura tare da na Batul, ko sai ya gama ya dawo, zan mishi duk yanda yake so don yana bina sau da k'afa ba zan tauyeshi ba"

Naam tayi cike da gamsuwa da maganarshi.


STORY CONTINUES BELOW

Sosai ta ji kanta na juyawa, ashe da gaskiyar Mummy? Ashe so dai ake a rabata da Alamin dinta a aura mata Ya Zaid, kuma tabbas ta san tunda taji maganar nan daga bakin Daddynta da kanshi, tasan tabbas ba zasu wanye da kyau ba, ba makawa sai anyi, sosai ta tsorata, ba zata taba son hasko rayuwarta ba Alamin dinta a ciki ba, dole ta sama musu mafita.

Gyara tsayuwarta tayi tare da jan naunauya numfashi, tas ta shanye maganganun da taji Iyayenta nayi, ta k'arasa gunsu kamar bata ji komai ba, sallama tayi tare da gaishesu, suma kama kansu sukayi gudun kar ace ta ji su, ganin dai bata nuna komai ba Daddynta yace "Hawwa School zaaje?" Ta murmusa "eh dadi, yau 9 gareni, bari na je"

"Breakfast fa?"

A takaice tace "its too early, zanci in na fito first lecture"

Adduar saa suka mata ta musu Sallama ta fita daga Parlorn tana k'okarin saita numfashinta don ba karamin namijin kokari tayi ba da ba tayi ihu ba ko ta yi kuka, direct motarta ta nufa, ta kunna tare da barin Gidan, maimakon tayi Makaranta, sai tayi hanyar Gidan Baba Abdullahi.


Shiga Gidan tayi da Sallamar da ta sa ba wanda yaji, ba za ta iya tuna when last ta tako Gidan nan ba, kai tsaye Parlorn Gidan ta nufa, Batul a Parlo tana breakfast shirye cikin kaya da alama Makaranta zataje.

Kallon Juna su kayi, Batul ya fara dauke kai, hakan bai damu Hawwa ba, tace "Bee ina Umma?" Sunan da take kiranta da shi kenan tun suna yara, Kamar ba zata amsata ba tace "ta na Kitchen" Straight Kitchen din ta nufa inda Umma ke soya Dankali.

"Salam Alaikum, Umma ina kwana?"

Gaban Umma ya fadi, da mamaki tace "Hawwa? Lafiya da safen nan?" Ba ta damu da rashin amsa gaisuwar ba tace "Eh Umma lafiya, Ya Zaid nake nema, ya na nan ko ya tafi Office?"

Umma da mamaki tace "Zaid kuma?"

Hawwa ta daga girarta tace "Eh"

Rausayar da kai tayi tace "yana dakinshi"

Ba ta sake magana ba ta fita daga Kitchen din.

Shiru Umma tayi ta na nazarin dalilin da ya saka Hawwa neman Zaid, ba zata iya tina lokacin da ta ga Zaid da Hawwa suna fira ba, ba ma za ta tuna ranar da Hawwa ta tako kafarta ta zo Gidan ba, ba ta yi kusanci da Zaid din da zata zo neman shi ba, ko dai itama taji labarin ana so a hada Aurensu ne? Ko itama ta na so? Umma ta tsame dankalin kan Gas ta sa a cooler ta rufe ta bi bayan Hawwa.

A Parlo Batul tace "wai Umma me Hawwa ke so ne?"

A takaice Umma tace "Zaid take nema"

Batul da mamaki tace "Ya Zaid kuma?"

Umma ta yi hanyar fita tace "Uhm"

Batul ta rufa mata baya.


Mamaki kamar ya kashe Zaid, tunanin mai Hawwa ta ke yi a Gidansu, a cikin Dakinshi yakeyi, kafin yayi magana tace

"Yaya Zaid"

Duk da gabanshi na faduwa kan be san me zata ce mai ba da bacin rai yace "menene?"


"Wai Daddy yake so ya hadamu Aure ni da kai"

Zaid cikin dacin rai yace "to sai mene? Sai muyi auren meye a ciki?"

Hawwa ta kallo shi sosai ta tabe baki tace "kamar dagaske"

Zaid yace "i mean it, in yana so ya hadamu aure sai muyi, ni da ke duk ikonshi ne sai yanda yayi damu"

Hawwa ta mike ta tako daf dashi tace "Kace mai baka son Auren, kana da wanda kake So"

Cikin tsawa yace "ba zan ce ba, haka mukayi da ke nace miki inda wacce nake so? in ke Uncle Ahmed yake so na aura, to ke zan aura, ke ki bijire mai ba, ni kam ba zan bijire mai ba"

Hawwa kamar tayi kuka tace "Yaya, kar mu yaudari kanmu, ka san na san ba ka so na, in short ka tsaneni, ta yaya zaka aureni just kawai don Daddy na so? Ka k'untata ma rayuwarka saboda faranta ran Daddy?"

Zaid ya katseta yace "eh don na faranta ranshi, kuma abunda zanyi kenan, na faranta ranshi"

Hawaye ta fara tace "Ina da wanda nake so Yaya, Alamin nake so, ni wallahi shi nake son Aura, Yaya ba zan iya zaman aure da kai ba wallahi, kai ka san akayi auren babu mai kwanciyar hankali cikinmu"

"Kin dade baki ta dama mana hankali ba"

"Uhm uhm Ya Zaid, Abunda ake gudu wata rana zai faru, Zumuncinsu Daddy zai ruguje, su Daddy ba su yarda matsalar Umma da Mummy ya shafe zumincinsu ba, to wallahi zan rantse maka mu 'ya'yansu zamu saka zumuncinsu rugujewa, ko ba su fito fili sunyi fada ba, zasuyi baya da junansu, kuma su dinga saka ma junansu wani tunani tsakaninsu"

Zaid yace "you see, ba su bari Matayensu sun shiga tsakaninsu ba, ta yaya zasu bari diyansu su shiga tsakanin zumunci da suka gina shekaru sama da talatin?"

Murmushi tayi tace "Ya Zaid, ba ka san yanzu kowa kanshi ya sani ba? Ba ka san cewa kowa nashi kawai yake so ba? Ba ka san cewa duk Son da Daddy ke maka ba kamar ni ba? Zan ta hada maka sharri ne, tun ba ya dauka zai fara dauka, zai fara jin ba dadi, kila ma ya tunkareka da maganar, kai kuma zaka ga rashin dacewar haka, abun zai dinga damunka, zaka dinga gaya ma Umma, tun ta na shiru, harta fara gaya ma Baba Abdullahi, tun baya jin komai, ka san zuciya, wata rana zai ji ba dadi, har ya k'ullaci Daddy, rayuwar nan, abunda ke faruwa kenan, to speak the truth".

Baki bude Zaid ke kallonta yana mamakinta yaushe ta iya zaro zance haka

Murmushi tayi tace "No, ba wai ina da tabbacin hakan zai faru bane, misali nake baka kan hakan na iya faruwa, lets be realistic, Yaya, as i told you ina da wanda nake so kamar raina, Mummy ce bata son shi saboda shi ba kowa bane, baya aiki, diploma gareshi, yana nan a Unguwarsu Hajiya, Alamin sunanshi, ni kuma wallahi zan iya mutuwa in ban aureshi ba Ya Zaid"

Hannunshi ta rik'o hawaye na zuba a idaniyarta  ta cigaba "ka taimakeni Yaya, na san baka sona, kawai Farincikinka kakeso kayi sacrificing saboda Daddy, donAllah lets not get married and regret it for the rest of our lives"

Hawwa bata taba bashi tausayi ba irin yau, ba kuma ta taba burgeshi ba irin yau

Baki na rawa yace "me kike so nayi yanzu?"

Da sauri fuskarta ya chanza zuwa murmushi ta share hawayenta tace "naji Daddy na cewa zai tura ka wani course a South Africa, mummy ta bashi shawara ayi auren mu tafi tare, yace aa zanyi distracting dinka, na hana maka kwanciyar hankali na zame maka Liability"

Daria sukayi su biyun

Yace "Wai haka?"

Murmushi tayi ta gyada kai tace "hakan ne"

Dariyar suka sake yi

Yace "ehen?"

Tace "wai tunda October zaka tafi, sai mummy tace to a daura auren rana daya da na Batul, sai ka tafi kai kadai, in ka dawo Bayan Azumi sai na tare, shine Daddy yace sai ya tambayeka mai ka gani don kar a shiga hakkinka"

Zaid yace "then what am I supposed to do?"

Hawwa tace "nasan baka son ce ma Daddy aa, its hard for you to reject him, i have a better plan"

Yace "What?"

"Kace mishi kana so ka tafi with fresh mind ba tare da tunanin wani responsibility ba, ka na so ya bari in ka dawo lafiya, bayan Azumi ko ranar Sallah ne sai a daure Aurenmu"

Zaid yace "to dabarar taki fa?"

Tace "dabarar itace zan tabbatar kafin ka dawo, na zama Matar Alamin".

Ya zaro ido yace "me kike shirin yi?"

Daria tayi tace "ba guduwa zanyi ba i promise,

Da kansu zasu aura min shi, kai dai do as i Say, mu taimaki juna".

Zaid yace "shikenan, zanyi hakan in Uncle Ahmed ya min maganar"

Ajiyar zuciya tayi tace "Okay then, i guess we are on the same page"

Shiru ya danyi kafin yace "Hawwa"

Ta kalleshi irin ina jinka din nan

Yace "I dont hate You, wani Yaya ke tsanar k'anwarshi? halaiyarki ce kawai bani so"

Murmushi tayi tace "I know"

"Ki chanza halinki"

Ita wai me takeyi da ake cewa halinta bai da kyau? Basarwa tayi tace "barin je"

Bai amsata ba ta juya, wai ashe Batul da Umma na dakin,duk abunda suka tattauna sun ji.

A tsayin shekarun nan Hawwa bata taba burgesu ba irin yau, wani abu da basu taba ji game da ita ba sukaji yau.


Hawwa ta kallesu ba tare da damuwar sun ji ta ba tace "Umma na tafi School"

Ingattaciyar Murmushi ta sakar mata tare da cewa "Allah ya bada saa Hawwar Baba"

Hawwa ta ji wani shaukin da ta dade bata ji irinshi ba Hawwar Baba, sunan da Baba Abdullahi ke kiranta dashi kenan.

Hawwa ta kalli Batul tace "kina son Lift?"

Duk da farinciki ya cika Batul amma sai da ta galla mata harara tace "Lift? I have a Car too"

Hawwa tace "Umma kice mata shiga Motar k'anwarta ba zai sa hanaki k'iba ba dai"

Dariya sukayi su duka banda Batul din da ta sha mur, ita wai a ganinta siririya ce sosai, Hawwa ta san lokacin da Batul ke cin Abinci sosai don kawai tayi k'iba.

Zaid yace "Bee, shiga Motar k'anwarki ba zai hanaki kiyi kiba ba, ki shiga, maybe ma ki ga kin fara kiba"

Batul na son daria amma ta fuske tace "kar nayi kibar, zanje da Motata"

Hawwa ta fita daga Dakin tana cewa "to ni bari na shigo da tawa motar gareji, zan biki a taki motar, just dont throw me out in munyi nisa".

Dariya sukayi baki daya, Farinciki suke baki dayansu, sosai su ke jin dadin sabon halin Hawwa, dama chan ba sa k'inta, halinta ne kawai ba sa so.

Umma ta kalli Batul da Zaid da kallo kadai zaka musu zaka san cewa suna cikin Annashuwa, sanadiyar Hawwa, Hawwa ta sanyasu Farinciki a rana daya, Hawwa ta maido ma Zaid walwalar da ya rasa watanni uku da suka wuce.


Daga chan waje sukaji Hawwa ta bude murya tace "Ya Bee zanyi latti fa"

Batul ta bude murya tace "Ban gayyaceki ba dama, ki yi tafiyarki"

Su ka karasa gabaki daya

Batul ta koma parlo ta dauko jakkarta.

Umma ta rakasu har Garage.

Hawwa na gaban motar Batul.

Motoci 3 ke garage din, Motar Zaid k'irar Elantra, Motar Batul da Hawwa k'irar Focus kala kawai ta banbanta motar tasu, wanda duk Uncle Ahmed ne ya siyo musu don zuwa makaranta.

Umma tace "Zaid yi tafiyarka Aiki, kar ka biye ma dramarsu sun saba latti dama, kamar su kawai mallamin zai tsaya jira"

Zaid yace "nima Umma ba Aikin zani yanzu ba akwai inda zan fara zuwa"

Umma tace "ina zaka? Kar kawunka fa ya ta jiranka"

Zaid yace "Unguwarsu Hajiya zani, akwai wani yaron da nake so a min bincikenshi"

Hawwa ta zuro wuya ta Window tace "Ya Zaid Alamin dina?"

Motarshi ya fada, tare da Hararta yace "Eh Shi, kuma wallahi ko sigari naji ance yana sha, ki manta da maganar aurenshi"

Dariya tayi tace "na yarda"

Batul tace "yarinya kin bonu, Har Cikin Hanjin Sadik Ya Zaid ya binciko da ake bincikenshi, Allah ya soni baida negativity".

Zaid ya galla mata harara yace "My friends ku wuce School"

Dariya sukayi gabaki daya

Horn yayi, Maigadi ya wangale Gate, Batul ta fara fita, kafin Zaid ya bi bayansu.

Umma ta murmusa tana musu fatan a dawo Lafiya, yau tayi mata kama da SallahAlamin ya murmusa yace "karambani ne irin na Dan Talaka, ni ai na san Hawwa tafi karfina".

Zaid yace "ba wannan na tambayeka ba, cewa nayi kana son Hawwa tsakaninka da Allah, kuma kana son Aurenta?"

Alamin ya ci serious "Hawwa ta min hallacin da ba zan iya yaudararta ba, tsakani ga Allah nake sonta, sosai nake k'aunarta, amma"

Dakatar da shi Zaid yayi ta hanyar daga mai hannu "Ya Isa, naji abunda nake son ji, zan kuma yi bincike a kanka, za kuma ka ji daga gareni"

Hannu ya mik'a mai sukayi musabaha.2


N A S S A R A W A


Tana daga Kishingide ta ji shigowarshi, kusa da ita ya zauna, suka sakar wa juna murmushi, kwantar da kai yayi yace "Waffles, Laura ta dawo Jiya, ina so na hadaku, bana so yau ya wuce ban hadaku ba, so ki shirya please, zamuje Gidanta" murmushinta ya so bacewa, amma ta amma tayi k'arfin halin barinshi a fuskarta tace "a shirye nake mayafi kawai zan dauka" Sajenta ya shafa tare da mikewa ya fita "ina cikin Mota" kai kawai ta iya daga mai.

Yana fita ta danne zuciyarta da hannunta, wani abu take ji, bata da tabbacin ko Kishi ne ko kuwa tsoron haduwa da Laura ne, ashe bata nan, ashe tafiya tayi, ta na cikin sake sake wayarta tayi k'ara, har ta dan firgita, Aunty Binta ce, ta dauka da Sallama.+


"Ke lafiya? Meye muryar ki ke rawa? Watty tace "Uhm Aunty, Gidan Matar Dr zamu"

"Oh ba ku taba haduwa ba dama?" "Eh, ashe ba ta nan, tafiya tayi" Aunty Binta tace "to meye na fargaba? Ke ki tafi kanki tsaye, ba surukarki bace, kishiyarki ce, kar kuma ki manta ke kanwar wacece, kanwar Binta ce ke, kuma Binta bata tsoron Kishiya"

Watty ta dafe kai "Aunty, barin je, ya na jirana a Mota"

"Ki kirani in kun dawo" k'it ta kashe wayar, ba tare da bata lokaci ba, Watty ta shiga Daki ta dauko Gyale, ta yafa kulle Gidan tayi kafin ta iske Dr a Mota, ya ga tsoro a tattare da ita, hannunta ya riko tare da mata murmushi, don ya kwantar da hankalinta yace "daga chan sai muje mu karbo Zaid Gidan Inna ko?" Nan da nan fuskarta ya washe ta gyada mai kai cikin Amincewa.

***3


Lek'ensu sukeyi ta window, yanda suka jero kamar a filin dinner zasu mazauninsu, ran Laura ya sosu matuk'a.

Laura tace "yanzu wanchan yar yarinyar ta taba aure har ta haihu?"

Shema tana haki cikin rada tace "Wallahi wallahi yarinyar nan ciki gareta, wani haihuwan zata sakeyi, ciki ne da ita"

Laura ta zaro ido tace "Cikin Lafiya Shema? Yau fa kwanansu 10 da aure, wani irin ciki? DonAllah bar fade" ta dafe kirjinta.

Kafin shema tayi magana Door Bell din Parlon yayi k'ara.

Shema ta kalli Laura tace "Compose yourself"

Dan gyarawa tayi ta nufi k'ofar duk da gabanta na dukan chalugude amma ta aro murmushi.

Ta bude Wattyn ke Gaba sai Dr a bayanta.

Suna hada Ido Laura ta hau tafa hanayenta ta na wani tsallen Murna ta na cewa "oyoyo ga ta ga ta, ga k'anwata" ta rungumeta.

"Lahh mai kirki" Watty ta fada a ranta tare da rungumota itama.

Dr kuwa bakinshi kamar ya yage don murna, shi ya san Lauransa ba za ta bashi kunya ba.

Hannun Watty ta ja har farfajiyar Parlon ta zaunar da ita.

Dr yace "Lee meye haka? Ni fa?"

Laura ta dan yi dariya tace "Dee Amaryata fa na gani"

Dr yace "sai ki manta Mijin?"

"Allah baka hakuri, ina zan manta Mijin? zo ka zauna"

Yayi dariya shima ya zauna.

Shema ta karaso tana cewa "sannunku da zuwa, Dr ina wuni?"

Dr Nazifi ya amsa da dan murmushi "Lafiya Shemau"

Shema tace "amma MashaAllah amaryarmu, kina da kyau"

Ta fada ta na shafa mata fuska ta gyalenta.

Ita dai Watty kanta durkushe a k'asa banda wasa da yatsu da murmushi da ke dauke a fuskarta bata komai.9


Kafin kace kobo an cika gaban Watty da kayan ciye da lemuka kala-kala, ita dai murmushi kawai takeyi,

Laura ta lura Watty bata taba komai ba tace "hana dear, ki ci snacks mana" murmushi Watty tayi tace "Aunty bana jin Yunwa" Laura ta dan sasauta murya tace "ki sha drink din to" Watty tace "daga Gida fa muke Aunty"

Dr yace "ni bari na ma kaina tayi" ya mike tare da nufo Tray din.


Laura da k'awarta shemau suka tareshi "Aa wallahi na amaryane"

Shema tace "wallahi in ba so kike muma in munzo Gidanki mu k'i shan ko ruwa ne ki sa wani abu bakinki"

Dariya tayi tace "afuwan Aunties, be kai nan ba"

Ta dauki Samosa ta saka a baki ta zuba juice a cup.

Dr yace "wannan Son kai ne"

Laura ta mai gwalo tace "Sorry Hubby"

Sun kusa 30mins Kafin suka dau niyyar tafiya.

Har bakin Mota suka rakasu.

Hannu sukai ta daga musu har suka bar farfajiyar Gidan.4


STORY CONTINUES BELOW

Hankalinta ta maida ga Shema'u "Yanzu na ke iya numfashi da kyau, me kike nufi da ciki gareta?"

Shema tace "kin san Allah Laura, Yarinyar chan is Pregnant"

Hak'oranta ta datse "ba ta isa ba, ai ba sai tana da Lafiya zata iya daukan Cikin ba? Indai Lafiya ne, to tuni ta yi sallama dashi, bazawarar banza"

Shema tace "naga ba ta ci Samosan guda biyu ba, bata taba kamar da springrolls ba, zai yi kuwa?"

Wani murmushi Laura tayi tace "ko gatsa daya tayi, zai yi, balle ta kora da ruwan Lemu"

Shema tace "yaushe zai fara aiki?"

Tafiya ta fara yi kafin tace "in less than 72hours"

Shema ta sa ihun murna tace "babu Wanda zai zargeki kuwa, Laura ina tsoronki"

Murmushi kawai Lauran tayi ta cigaba da tafiya zuwa Cikin Gida.5


A mota Dr yace "Yadai Waffles? Ya kika ga My Laursa?" Sosai Watty ta ji Aunty Laura ta burgeta, ita dai ta na son Wayayyu 'yan boko, indai haka ne wallahi zata bita sau da k'afa, don ta lura Aunty Lauran ba ta da Matsala.

Hararshi tayi tace "if she's your Laura and I am?"

Ya riko hanninta da hannu daya, dayan kuma na kan Sitiyari yace "you are my Waffles"

Murmushi tayi mai rikitashi.4


Gidan Inna suka wuce Straight, kowa ya ji Dadin ganin Watty, kwananta 10 amma har tayi wani irin Ja irin na masu kwanciyar hankali.

Nan ya barta yace bari yaje ya dawo.

Inna ta gaya ma zata tafi da Zaid.

Inna tace "ni fa na saba dashi"

Watty tayi rau da Ido tace "donAllah Inna, yau fa zai koma Chan Gidan Aunty Laura, ni kadai zan kwana, ya fi na dinga jin motsi ko yayane"

Inna tace "sai yau zai koma dayan Gidan?"

Watty tace "tayi tafiya ne lokacin Bikin wallahi baki ganta ba mai kirki"

Inna tace "Uhm, Allah ya kwabe fitina"

Watty ta mike tace "Ameen, barin je wurin Mama"

Watty tayi hanyar Sashensu sai ga Wayar Aunty Binta.1


K A N O

Hawwa ta k'i komawa Gida, ko da suka gama Lectures Batul ta bi suka dawo Gidan Babansu.

Da daddare bayan Sallahr Isha'i Uncle Ahmed da Zaid suka shigo Gidan, daidai da daukewar wutan lantarki.

Umma tace "da Zaid da Babanshi sun dauke mana wuta"

Uncle Ahmed yace "abu na Generator"

Zaid yace "Gen din ya buga"

Uncle Ahmed yace "kuma ba ka kai gyara ba, ba kuma ka kira mai gyaran ba"

Baba Abdullahi yace "dama ni k'arar gen ciwon kai yake sakani, Ina Batul ta dauko Tabarman nan a shimfida waje duk a sha iska"

Umma ta kwala wa Batul Kira "ki dauko k'atuwar Tabarmar nan, ku kuma fito waje kun k'unshe kanku a daki kamar wasu masu yinin jego"

Uncle Ahmed yace "ita da waye?"

Umma ta tabe baki tace "Hawwa mana"

Wani Dadi da mamaki suka dirar mai amma bai ce komai ba.


Sai ko gasu sun fito rik'e da Tabarmar.

Hawwa ta sakar ma Batul da ta ga Babanta tace "Daddy yaushe kazo?

Batul tace "Uncle Ahmed ina wuni?"

Ya amsa da cewa "Lafiya Batul, ke da baki gaisheni ba kizo ki matseni ba gaya miki yaushe nazo"

Ta dan bubbuga k'afa cike da shagwaba tace "mun fa gaisa fa dazu kafin na fita"

Uhm kawai yace tare da neman ma kanshi wuri a tabarman.1


Wayar Uncle Ahmed yayi Ringing Matarshi ce ya dauka, dag Jin muryarta hankalinta a tashe yake.

"Ka ga Hawwa bata dawo daga Makaranta ba har yanzu, wayarta kashe"

Saurin katseta yayi yace "ga ta nan"

"A ina?"

"Gidan Babanta mana"

Zaro ido tayi tace "tare zaku dawo ko?"

Yace "ba tare muka zo ba"

Ya kalli Hawwa yace "ki kira Mamanki ta damu"

Sai a lokacin Hawaa ta tuna da wayarta a kashe.

Ya Zaid ara mun hasken wayarka"

Bece komai ba ya bata wayar

Daddy kamar ya kashe Uncle Ahmed.

Duk suna zaune a Kan Tabarma ana fira.


Hawwa ta kira Mamarta

"Hawwa me kika je yi Gidan nan?"

"Haan, Mummy ni da gidanmu?"

Ganin ta na neman gaya mata magana tace "ki biyo Daddynki ok?"

Kai tsaye tace "aa kwana zanyi, gobe ma zanzo na kwashi kayana"

Hajiya Iklima tace "kar ki fara,wallahi ki biyo Babanki ki dawo Gida"

Hawwa tace "Mommy ai nan ne gidanmu kin manta?"

Alamin ke kiranta, ba ta jira komai ba ta dau wayarshi tare da barin Mommynta a Hold.

Bakinciki kamar ya kashe Hajiya Iklima.3


"Hello Alamin dina"

"Da wa Hawwata ke waya?"

Murmushi tayi tace "Mommy ce wallahi"

Da mamaki yace "ke kina ina kuke Waya da Mommyn?"

A takaice tace "Gidanmu na Tarauni"

Ya gane Gidan yace "na manta dazun muna tare da Yayanki"

Zama ta gyara "DonAllah? Me yace maka? Dama yace mun zai nemoka, ashe kun hadu, be ko gaya min ba, ya kukayi dashi Alamin dina?"

Dariya yayi ya fara labarta mata.

Kusan wayar minti sha biyar sukayi tace "bari ta koma waje, in ta dawo zata kirashi.

Sallama sukayi, ko da ta fito waje ta ji ana amsa Sallamar Mommynta, a ra ranta tace zuwa tayi kenan, ita fa ta kyaleta ba inda zata.


STORY CONTINUES BELOW

Nan da nan wani nazari ya zo mata, kowa na nan, Babanta Abdullahi na share mata kukanta yana bin bayanta a duk abunda tayi, zatayi amfani da damar nan ta kawar da k'udirin Mahaifinta.

"Aunty Iklima Ina wuni?"

Yaran suka gaidata

Ba yabo ba fallasa ta amsa, kan tabarmar kusa da k'afar mijinta ta zauna ta gaida Baban Fahad "Yaya Ina wuni?"

Baba Abdullahi ya amsa "Lafiya lau Hajiya, ya Gida?"

Ta amsa, ta kalli Maman Fahad tace "Saade Ya Yaran?"

Saadatu ta amsa da "duk lafiya"

Hajia Iklima tace "Hawwa naji shiru, shine fa na biyo sahu"

Hawwa tace "Yo ai Mommy nace miki nan zan kwana?"

Dariyar yak'e tayi tace "ki bari a yi hutu"

Hawwa tace "sai kace yarinya?"

Duk dai kowa yayi shiru suka zuba musu Ido Iklima na magana Hawwa na maida mata.

Hawwa ta tuno Plan dinta ta matsa gurin Zaid tace "Ya Zaid ashe ka ga Alamin"

Harararta yayi yace "shuttup"

Baba Abdullahi yace "waye kuma Alamin?"

Zaid yayi shiru, karaf Hawwa tace "Abba wai So na yake"

Zaid ya dafe goshinshi, Uncle Ahmed ya girgiza kai cike da takaici, Umma Wautanta kawai take gani.

Baba Abdullahi yace "Zaid yi min magana"

Zaid ya dan nisa kafin yace "Abba, wani yaro ne a nan Unguwarsu Hajiya yake Sonta, dama ina jira na gama bincikenshi ne kafin nayi maka Magana"

Abba yace "yaya nisan Bincikenka?"

Zaid ya dan kalli  Uncle Ahmed ta gefen Ido ya ga ko shi yake kallo, dauke kai yayi ya cigaba da magana kamar be san Uncle Ahmed din na shirin bashi Hawwa ba.


Zaid yace "Abba Yaron baya da wani muguwar dabi'ah, amma dai na saka a dan sa mai ido na wasu dan lokaci, in har an kamashi da wani nakasu, sai a sallameshi".

Abba yace "da kyau, Ahmed kaima zan wakiltaka binciken Asalin Yaron da kuma tarbiyya, Zaid ya maka bayanin Yaron da inda yake, sai ka dasa naka binciken, kasan ta yaro kyau take bata k'arko".


Shiru Uncle Ahmed yayi be ce komai ba, Baba Abdullahi ya lura da yanayin da danuwan shi ya shiga, da sauri yace "Yadai Ahmed?"

Uncle Ahmed ya dan nisa yace "Yaya, dama akwai wata magana da nake so na maka, ban maka bane saboda ina jira na gama shirin tafiyar Zaid Cuba Course dinnan da na gaya maka, amma tunda abun yazo da haka, bari na fada gaban kowa yaji".1


Gaban Umma ya fadi, gaban Zaid kamar ya fito, dukkansu sai da jikinsu yayi Sanyi, sun san Baba Abdullahi,  baya iya cema danuwanshi aa.

Uncle Ahmed yace "Yaya, dukkanku shaida ne irin So da K'aunar da nake ma Zaid tunda ya shigo Duniya, burina shine na hada Auren Zaid da Hawwa don kara karfaffa zumuncinmu"

Baba Abdullahi ya washe hak'ora yace "Alhamdulilah, wannan abu ya min dadi, tuwo na maina kenan".

Gaban Zaid da Hawwa ya fadi daga jin furucin Baba Abdullahi.

Uncle Ahmed yace "shi ne nake ganin Gida bai k'oshi ba ina zaa ba Waje?".

Baba Abdullahi yace "Sosai kuwa"

Uncle Ahmed yace "na so a hada Auren da na Batul, amma kuma hankalina zaifi kwanciya idan yaje ya dawo, 9months Course ne, da ya dawo sai a daura".

Baba yace "hakan ma yayi"

Wurin shiru kamar ruwa ya shanyesu, banda Muryar Abba da na Uncle Ahmed baa jin komai.

Baba Abdullahi ya kalli Hajiya Iklima yace "ya kukace Uwayensu?"

Aunty Iklima ta murmusa tace "ai kun gama magana, Allah ya kaimu kawai"

Uncle Ahmed yace "Saar Mata baki ce komai ba"

Shiru tayi kafin ta kalli Zaid da Hawwa ta ga duk sunyi fuskar tausayi, duk sai suka bata tausayi "uhm nace ai da an tambayi Yaran, aji daga bakinsu, don su zasuyi zaman auren, don kamar Hawwa tana da wanda take so, kar ganin neman gira a rasa ido, garin karfaffa zumunci a rusashi"

Uncle Ahmed yace "donAllah ki bar zancen wata Hawwa, shi Zaid bai nuna yana son Wata ba sai ita, bar zancen nan haba".

Baba Abdullahi yayi dan tunani yace "ka san, tun da yaran nan zasuyi zaman nan, mu ji ta bakin su, kasan Yaran Zamani, baa yi musu dole wallahi".


Abba ya kalli Hawwa yace "Diyata, ba zan tambayeki in kina da wanda kike so ba, tambayar da zan miki shine, shin zaki iya zaman Aure da Zaid? Zaki iya maida Son da kike ma wanninsa kansa?Zaki iya??"

Ba ta bari ya gama tambayar ba ta katseshi "Wallahi Abba ba zan iya ba, Abba Alamin dina na ke so" Uncle Ahmed ya taso gadangadan yayi kanta, Baba Abdullahi ya dakatar da shi.

Huci yake yi kamar Zaki, da Yayanshi ya barshi, da sai ya ma Hawwa Ha6o, sai ya mata dukan da tunda tazo duniya baa taba yi mata irin shi ba.3


STORY CONTINUES BELOW

Uncle Ahmed ya cigaba "DanUbanki Zaid din zaki ce ba kya so? Tunda ba kya son Zaid nima baki so na, ni ma ban sanki Hawwa"

Abba yace "SubhanaAllah Ahmad, ashe kai ma Yaron ne? Meye haka? So kake ta cuci kanta, ta yarda a aura mata shi, ta karashe rayuwanta cikin k'unci? Wallahi ta min daidai"

Uncle Ahmed cikin daga murya yace "haba Yaya, wallahi kai ke sa Hawwa na tabara yanda take so, Yaya baka taba tilasta ma Hawwa, wai tsoronta mukeyi ne? Ba ta isa ba wallahi, mu muka haifeki ba ke kika haifemu ba danubanki"

Ya juya ya kalli Yayanshi yace "ka san ina yin duk wani abun da ka sakani yi ko ina so ko baniso, wannan karon  zaka barni nayi wannan abu dayan Yaya"

Baba Abdullahi ba ya so k'aninshi yayi tunanin kamar baya son hada auren Zaid da Hawwa, ko kuma yana so ya nuna fin karfi a kan Zaid, yana son Kaninshi, zai bar mai komai.

Baba Abdullahi ya nisa yace "kayi abunda kake ganin daidai ne, zan goya maka baya InshaAllah"

Uncle Ahmed ya murmusa yace "nagode Yayana"

Lokaci daya ya sha mur ya kalli Hawwa yace "wallahi wallahi in Zaid ya amince sai dai ki mutu, ko gawanki sai an kai Gidan Zaid, kin daiji na rantse".

Wani Kukan Tashin Hankali ta fashe dashi mai kara mai sauti, Batul na son tashi ta lallasheta amma ta kasa.1


Uncle Ahmed ya kalli Zaid yace "Zaid, ka gaya min tsakaninka da Allah, kar ka dubi Alakata da kai, ka gaya min zaka iya zama da Hawwa a matsayi matar aure? Zaka iya Sonta?"

Kan Zaid a k'asa, kamar mace wasa yake da yatsun hannunshi, kasa motsi yayi kwakwara, sai dai Uncle Ahmed ya maimaita tambayar so kusan Uku, kafin ya amsa.


"Idan Umarni kuka bani, kuka ce Zaid ka auri Hawwa,  zan bi ku, zan yi abunda kuka umurceni, Don farincikinku, amma Father, in don ni ne, Hawwa k'anwata ce, yanda ba zan iya auran Batul ba, haka na dauka ba zan iya auran Hawwa ba, yanda nake son Batul, haka nake son Hawwa, da Batul da Hawwa daya suke a wurina, wanda suka zaba a matsayin abokanan zamansu, sai inda k'arfina ya k'are wurin ganin ba su auri wanda zai wulakantasu ba, ko ya k'i daukansu da muhimmanci, tuni na fara bincike kan Alamin din da take so, kuma na gaya mata dole tayi hak'uri dashi in na kamashi da wani laifi".4


Uncle Ahmed yace "ba ka son Hawwa? Ba za ka iya aurenta ba kenan"

Maganar tama Zaid nauyi a baki, ta ya zai dube Uncle Ahmed yace be son gudan jininshi?"

Shiru yayi.

UncleAhmed yace"ehen, kai nake sauraro"

Miyau Zaid ya hadiye yace "Hawwa Shak'ik'iyata ce, Muharammai ba sa auren junansu"

"Fak'at" inji Uncle Ahmed.

Hajiya Iklima tace "Wallahi Saade ce ta hure mishi Kunne, ita ta zugashi, yaushe Zaid ya fara k'etara maganarka"

Umma ta kalli Mommy baki bude tace "gabaki dayan mu a nan muke zaune a nan, yaushe kika ji bakina?"

Hajiya Iklima tace "rufa mana baki, bansan fuska biyu, na san baki son Hawwa, ba kuma zaki so danki ya aureta ba, shiyasa kika ce ya bijire maAuren"

Kafin Saade tayi magana Uncle Ahmed yace "kafin Wani yace be son Auren, wa ya fara cewa be son auren ? Diyarki, kafin wani ya bijire ai Diyar taki ta fara bijirewa, kar ki kawo mana wani tashin hankali a nan, nidai abunda na sani shine, wallahi da Zaid ya amince, yace yana so to wallahi sai anyi Auren ko da zata dinga mutuwa tana tashi ne, sai na kaita Gidanshi"6


Baba Abdullahi yace "haka nan da Hawwa ta ce tana son Zaid, ko yana so ko bai so sai ya aureta dole"

Uncle Ahmed yace "Wallahi in bai so kace zaka mai Dole ni da kaina zan kaishi Duniya nace ya shigeta na yafe mishi".

Baba Abdullahi yace "Oh Abun Son kai ne, to dadin abun dai mu muka riga rejection"

Uncle Ahemd ya murmusa, ran kowa yayi sanyi banda Hajia Iklima.

Baba yace "a ci gaba da Binciken Alamin, in ba wata matsala a hade bikin da na Batula"

Uncle Ahmed yace "ni ina ruwana? Ni da na so ku da arziki?"

Hajia Iklima tace "wai wani Alamin ? Yaron da ko sanaa bai dashi, ba cis ba as, sai zaman gaban shago1?"

Hawwa tayi karaf tace "wallahi tailor ne, yana aiki"

Baba Abdullahi yace "Hawwa kar na sake jin muryarki, kiyi magana kadai in an tambayeki, kin gane?

Kai ta gyada alamun ta gane.

Ya kalli Iklima yace "me ye matsalarki Hajiya?"

Ta dan matso tace "wallahi Yaya baka ga yaron ba, naira 50 ba zaka saye shi ba, yana fama da wata jampa, gidansu ba ma tsaka tsinke, faqirun ne, shi kuke so ku ba diyarku? Me na sama ya ci bare ya ba ma k'asa, a dai matsayin babanta ai Hawwa sai dan Gwamna ko Minista,  wannan ai abun kunya ne da tonan asiri, wai auren tela, Allah ya suttura wallahi, ko Zaid don dai Gida ne"

Kowa baki bude yake kallonta, karambani ya sa Umma cewa "haba Iklima, da Arziki da Talauci duk na Allah, kar kuma ki manta dare Allah kanyi bature"

Kamar ta mareta tace "ni na san baki son duk wani cigabana Ade, na sani, duk abunda zaa min dariya shi kike so, in haka ne, ki ba Batul mai dinkin mana, ki aura mata telan sai na san kin fi kowa tauhidi, kina so diyarki ta huta kin kaita gidan hutu, kina son diyata ta wahala kina so ki kaita gidan wahala, to wallahi ba dani ba"

Umma tace "ai Iklima da ace Batul ta dauko mai kwasan kashi tace shi take so wallahi sai an aura mata shi in bai da aibu, kuma Batul da Hawwa duk daya suke a gu na"

"Ahayye ko zaki shekara kina gaya min haka ba zan taba yarda ba Ade".3


Abba ya daka musu tsawa duk suka natsu zai yi magana Uncle Ahmed yace "ka barni nayi magana Yaya".

Dama ya bashi.

Uncle Ahmed ya kalli matarshi yace "Da ban bada goyona kan Alamin ba dan ina kyamarshi bane, aa don ina so na ba Dana ne na k'i Alamin, wannan haukan da kikeyi, shi ya kara min kwarin guiwa da jin ina son Auren Hawwa da yaron nan har raina Wallahi, Hawwa zata auri Telanta, in kin ga dama saboda anyi abun kunya kar ki sake taka kafar waje, zan tabbatar duk wani kafa na Gidan radio da talabijin sun sanar da auren diyarki da tailornta, har ke kinada ikon kyamar talaka? An fa san asalin angulu, ko ni da kike takamar ina da kudi wani kalar talaucin rayuwane ban gani ba?Iklima ki bi duniya da rayuwa a hankali, ina sake jadda miki Aurensu ba fashi, ki tashi ki koma Gida yanzu mara tunani kawai"

Tashi tayi tana k'unk'unai.

Be so mata haka gaban Yara ba, amma ya lura bata da hankali.

Kallon Zaid Uncle Ahmed yayi yace "Proceed with the BackGround Check"

Umma tace "lokacin cin Tuwo Yayi"

Duk akayi dariya, ran Hawwa ko wasai yau zatayi bacci harda minshari.3


Bayan kwana 2


N A S S A R A W A


Yau zai dawo dakinta da Laasar, duk ta gama shirin tarbanshi, wasa sukeyi da Zaid, sai taji bacci na neman dauketa, a hankali a hankali bacci ya saceta kan doguwar Kujerar da take kwance, ganin haka Zaid da ke zaune kan cikinta ya sauka ya kama gabanshi, ba ta san bacci minti nawa tayi ba ko na awa nawa, sai ga Mafarki, mafarki da rana, ba kasafai take mafarki da daddare ba balle da rana.

Zata iya shaida Namomin daji Uku, Zaki, Kura da Damisa, bin ta sukeyi da gudu, sai ko mage ta zo ta ceceta, Magen ta dinga gudu Watty na binta a baya, wani tsalle da Kuran tayi sai gata a gabansu duka, mage tsoro Watty tsoro, kafa kura ta daga ta take magen nan, sai da cikin magen ya fashe ji kake tus kamar fashewan Balanbalan, Jini duk ya bata kayan Watty, firgigi ta tashi daga baccin nan tana fadin "Inallilahi wa ina ilaihir rajiun" danshi taji kamar ruwa, yunkurin mik'ewa take  amma ta kasa saboda nauyin da jikinta ya mata chan sai taji mararta ya sake murdawa, da sauri ta dafe cikinta, chan sai taji kamar fa ta na kwance cikin ruwan ne, a hankali ta kalli kasanta don kar ace fitsarin kwance tayi, Jini ne malale.

"Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" jinin meye wannan? Tana da tabbaci daya, wannan Jinin bana Haila bane, Period dinta sai karshen wata. To wai Jinin meye wannan?Kukan Zaid ta fara ji sama sama, daga baya ta ji kukan ya tsananta, ko hannu ba za ta iya dagawa ba, kuka sosai yakeyi, ya rarrafo gabanta yana dukanta, hawaye kawai takeyi tana girgiza kai, kukan da Zaid keyi yana daga mata hankali sosai, zafin da mararta yakeyi yana sa ta na ganin mutuwa zatayi, addua ta fara yi a ranta, Allah ya jefo mata wani.


Bata san tsawon lokacin da ta ke a haka ba, Zaid ya gaji da kukan, shiru yayi yana sauke numfashi a kai a kai, daga nesa ta ji k'wank'wasawar k'ofa, ba za ta iya motsa ko yatsa ba, jin alamun akwai wani bakin kofan Zaid ya rarrafa ta wurin tare da sake wani kuka mai karfi, Watty ta runtse idonta, hawaye ya cigaba da kwaranyo mata, wannan kuka na Zaid, bata son shi, bugun k'ofan ya tsananta, ta na ji muryan Dr yana k'wala mata kira

"Waffles!! Ina kika shigene, zo ki bude k'ofa"

Ba ta iya motsawa, Zaid bai bar Kuka ba.

Wayarta ta soma k'ara, tayi amanna Dr ne, to me zata iya yi?"

Hawayenta ba su tsaya ba.

Dr ya lek'o ta Window, kan Kujera ya hangota cikin wani yanayi me wuyan fassaruwa, gabanshi ya yanke ya fadi, hantar cikinshi ta kada, kar dai ya bar diyar mutane ita kadai a gida ta mutu, jikinshi na rawa ya kira wani k'aninshi kan ya kira mai masu balle kofa.


Kusan rabi awa ya shude, kafin aka 6alla k'ofar, da gudu Dr ya k'arasa, tuntube yaci da Zaid da ya gama galabaita, daukar shi yayi ya mik'a ma k'anninshi da ke niyar shigowa Parlon, ya karasa gudun Watty hankali tashe, bata motsi, cincibarta yayi, ya ga Jini kwance malale kan Kujera, kan shi ya sara, ya fita da ita rungum a jikinshi, Mota ya sakata ya nufi Asibiti da ita, a emergency aka karbeta  a ka duk'ufa a kanta.


Ba jimawa ta dawo hayyacinta, amma jikinta a sake yake don ta galabaita da yawa, drip aka saka mata, bayan yan tambayoyi, Dr ya shaida ma Dr. Nazifi matarshi tayi barin ciki 'yan kwanaki, ko kadan bai ji dadi ba, yana gaban Gadonta har su Aunty Binta da Aisha suka shigo, dama a hanyarshi ta zuwa Asibitin ya sanar dasu halin da ya iske Wattyn.

Jajanta ma juna sukayi, ko zama basuyi ba sai ga Laura ta fado ko Salama batayi ba, kuka take  kamar an aika mata da sak'on mutuwa, galala yan Dakin suka bita da Kallo.


Dr Nazifi ya rikota tare da cewa "Calm Down Laura"

Cikin kissa ta ke kuka tana cewa "Oh ni Laura, yanzu Waffles dinmu miscarriage tayi?"

Cike da tausayinta Dr yace "kiyi hakuri lee, Allahn da ya bamu na farko, shi zai sake bamu"

Kuka takeyi sosai tace "Allah sarki Waffles dinmu, ta wahala na sani"

Su Aunty Binta sun sha mamakin kukan da Laura keyi, nan da nan suka gane Kissa ce da tsantsar munafurci.


Aunty Binta da ta lura da abun nata ba na k'arewa bane tace "Hajiya Laura muna Lafiya?"

Kallonsu tayi tare da goge hawaye "kuyi hakuri ban lura da ku ba, hankalina gabaki daya yana kan Waffles"

Aunty Binta tace "kar ki damu, ciki ne ko? Allah zai kawo wani, ai mai haihuwar ce"

Laura ta hadiye wani bakinikin da ya tokare zuciyarta, kamar wannana matar bakar magana ta gaya mata, dannewa tayi tace "burina Waffles ta ji sauki da wuri".

Murmushin bariki suka mayar mata kamar yanda take musu, ai bariki iyawa.


Bayan kwana biyu aka sallami Watty, Inna ta so ta dawo gida, amma Laura ta hure ma Dr kunne da cewa "haba Neenee, kwana 16 da aure, sai ka bari matarka ta koma Gida da sunan ta koma jinya? Mai amfanina? Haba wannan ai tonon asiri ne ma wallahi"

Nazari yayi hakan yasa yace ma Inna "da tayi hakuri ta bar Watty a dakinta, kula da ita ba zai  gagara ba"

Hakan kuwa akayi, amma an tafi da Zaid gidan Inna, don kar ya takura mata.

Kwance take kan Kujera, Dr ya shiga masallaci, ta ji wayarta na ringing, cirowa tayi daga charge, number ce, ba ta san mai ita ba, hakan ya sa ta amsa da Sallama".


K A N O


Driving yakeyi fikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kamar yanda kullum take fado mai, haka yanzu ta fado mai, ko so daya bai taba manceta ba, ganin baida sukuni a watannin bay da suka wuce ya sashi taku a sannu, ba yaso ya fara abunda yasan ba mai yiwuwa bane, ba ya so ya ci nasarar dasa mata sonshi bayan ba aurenta zaiyi ba, amma yanzu yana da tabbacin cewa ba auren Hawwa zaiyi ba, yana da ikon son ko wacece, wayarshi kawai ya zaro daga inda take charge a jikin motarshi, jinjina kai yake cikin Nishadi yana latsa wayar yana kallon Titi, numberta ya latso, kira yi, ya kara a kunne, cikin sakwan da bai wuce 10 ba ta dauka da Sallama, lumshe ido yayi.


STORY CONTINUES BELOW

"Assalam Alaikum" ta fada cikin muryarta.

Ya amsa mata "Waalaikum Salam"

Ji yayi ta danyi shiru, ko dama bata yi saving numbernshi ba, a ranshi yace to dama ka dau wata fiye da uku ba ka kira ba ko tayi ai ta goge.

Ya san tana neman k'arin bayani, shiyasa bata yi magana ba.

Cikin yanayinshi, da murmushi a fuskarshi, kamar yana gabanta yace "Kiyi hakuri, na dauki lokaci ban kiraki ba, baa son raina bane, wasu abubuwa ne suka sha min kai Yarinyar Kirki".

Zai rantse Gabanta ne ya fadi don jin yanda ta dauke lokaci guda.

Murmushi yayi yace "kinyi ta jirana ko? Kin ta tsammanin Kirana ko Yarinyar Kirki?"

Naunauyar Ajiyar Zuciya tayi, da k'yar ya hada kalmomin da ke fita a bakinta saboda rawar da muryata keyi.

"Na...nayi...nayi...Aure"

Cikin yankewar gaba tare da jirin da ke neman daukarshi ya gangara wurin wani Shago yayi Parking da kyar shima yace "mai kikace?"

Amsa ta bashi wannan karon kai tsaye "Aure nayi, yau kwanana 19 da aure"

Shiru sukayi gabaki daya kafin yace "Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya da zuria Dayyiba, Allah ya baki dauwamammen farinciki, Allah Allah yayi maki Albarka"

Bai jira ta amsa ba, ya kashe wayar tare da kifa kai a kan sitiyari.

*

Daga chan Nassarawa Watty ta fashe da wani irin kukan da bata san na meye ba.


Tun daga ranar Zaid ya nemi sukuninsa ya rasa, ba shi da wani  walwala, ya koma jiya iyau, Umma ta tambayeshi in yana da wata damuwa ya sanar masu yace "shi lafiyarsa lau" harta Uncle Ahmed ya san Zaid bai da wani walwala, Hawwa ma har daki ta bishi ta na tambayarshi matsalarshi yace babu, tace "Ya Zaid, ka gaya min, yanda ka share min kuka na inshaAllah zan share maka naka" kamar zaiyi magana amma da yake zurfin ciki gareshi, bai ce komai ba, da ya ga zata matsa mishi kan zance, koranta yayi daga dakin taje ta gaya ma Umma yanda sukayi,Umma tace "ku kyaleshi, zurfin cikinshi ya fi shi karfi, in tayi k'amari zamuji, ku sa mishi Ido" aikuwa na mujiyan suka saka mishi.


Wata Jumu'ah abokinshi Hashim ya kirashi su sada zumunci, sai da gabanshi ya fadi da ya ga kiran, yana ganin kamar Watty ce, haka dai ya daure ya dauka suka gaisa ya tambayeshi Nasarawa da Inna yace kowa Lafiya kalau, yace kaga last 3weeks ma Wattynmu tayi aure" kamar a lokacin ya fara jin labarin don sai da gabanshi ya fadi yawunshi ya kafe, da kyar ya iya lalubo "Allah basu zaman lafiy Ameen" Hashim bai jashi da fira ba don ya lura Abokin na da wani sabga gabanshi, sai ya kare zancen da dama ya ga sun kwana biyu basu gaisa ba shiyasa ya kira don su sada Zumunci, Zaid yace "nagode sosai, sai na kiraka" a haka suka ajiye wayar, Gaban Zaid bai daina fadiwa ba, Inallilahi wa ina ilaihir rajiun ya shig maimaitawa har ya samu saida.

(Bayan Wata Daya da Sati 2)

Ba Kano ba, Nigeria gabaki daya ta ishe Zaid, shi ya k'agara ya tafi Cuba, amma Uncle Ahmed ya sanar dashi an samu Delay kan tafiyar, yana iya yiwuwa ma sai bayan Bikinsu Hawwa, ko mkadan bai ji dadi ba, so yayi ya tafi ya nesanta

kanshi daga inda zaiji Kalmar 'Aure' amma ya ya iya? Tunda ba shi ke da tafiyar ba.


L A F I Y A


Watty kam tunda tayi bari take fama da jiki, yau zazzabi, gobe ciwon jiki, a haka dai a daddafe ta fara zuwa Nursing School din da Dr ya samo mata ba wai don ta na jin dadin jikinta ba.

Haka ta dage ta cigaba da karatun nursing dinta.

Mijinta mai Sonta ya na bata dukkan wani kulawa da kauna da take bukata, har Mota ya siya mata 206 don zuwa Makaranta, da kanshi ya koya mata tuk'in, ta kan gitta ta wurinsu Inna, Inna ta matsa mata kan ciwon da take yawan yi, Watty ta kwantar mata da hankali cewa tana shan magungunan Zazzabi, Inna tace "ko Ciki ne?" Watty ta zaro Ido, "Ciki dai Inna ? Yaushe nayi bari? Inna kawai zazzabi ne" Inna bata ja zance ba tace "Allah ya sauwake" ta amsa da "Amin" wurin Mamarta ta wuce, ta dauki Zaid kafin ta wuce Gida.

**

Duk da Watty na da dauriya, da ka kalleta ka san cewa lafiya ya mata karanci, ba kwance take ba, amma can cikinta bata da Lafiya, tana kokarin dauriya don kar ta ta da hankalin Mijinta don yana shiga damuwa a duk lokacin da take ko da ciwon Kaine.


Bayan barin da tayi, ba ta sake Period ba, tayi zaton ko ya rikice ne saboda Bari, amma da ta ga wata biyu shiru sai ta shiga damuwa, ta gaya ma Dr Nazifi tana san zuwa ganin Likita, yace "ki bari na kaiki Gobe, ban zuwa Asibiti" tace "inshaAllah bakomai, zanje yau din" haka dai ya amince ta tafi Asibitin, bayan yan gwajegwaje ya tabbata Ciki gareta na sati 11 wato Wata 2 da sati 3, hamdallah tayi dai.

Yau Gidan Laura zai kwana, da daddare bayan Ya dawo daga Asibiti wurin 10 ya kirata don jin ya gajiyar Asibiti, da ban hakuri na be lek'ota ba, yayi dare sosai ya ma wasu aiki ne, tace "haba ba komai" ya Likita tace? Ya tambayeta, murmushi tayi kamar yana kallonta tace "wai Ciki gareni, 11weeks" zata rantse tsalle yayi, "Allahu Akbar, Waffles Ya Allah, Allah nagode maka" tana ji ya bude k'ofa yana kiran "Lee, Laura, zokiji" ji tayi Anty Laura tace "ya dai wanan kira haka?" Yace "Guess What? Waffles dinmu is 11weeks Pregnant" ihun dadi Laura ta buga ta kwace wayar hannun Dr ta kara a kunne

"Waffles dinmu, are you Okay? Ba dai abunda ke miki ciwo ko?"

Cikin Kunya Hauwatty tace "Aa Aunty babu"

Laura tace "Good, ki kwanta yanzu, zan zo ganinki gobe kinji?"

Waffles tace "to Aunty nagode sai da safe"

Laura ta ba Dr waya, sai da suka kara 5 mins kafin ya barta ta kwanta.

Bayan Watty ta taso daga School, ta iske Laura a Gidanta, ba ta yi mamaki ba don Dr na da Key, kila shi ya kawota, Watty ta iske Tuwon semo miyan kubewa danye kan dining table maana Aunty Laura ta mata Abinci, ta ji dadi sosai don cikin nan da alama dan Tuwo ne, sosai ta ci tuwon nan, Laura na ta ririta ta kamar wata kwai, bayan kwana biyu da zuwan Laura Gida, Watty tayi Barin cikin nan.12


STORY CONTINUES BELOW

K A N O


Tunda Magabantanshi suka nema mishi Auren Hawwa bai huta ba, saboda hada lefe, duk da Hawwa tace "wallahi kar ya damu da wani lefe" amma dai dole yayi kokari ya fitar da ita kunya yanda ta rufe ido tace sai shi, sai ya taka rawar gani, ba karya zaiyi ba, amma inshaAllah sai yayi iya kokarinsa wurin ganin ya tabuka abun azziki.

Yana kan Keken dinkin shi yana hada dinkin da yanka, wani yaro ya shigo shagon, yace "wai ana sallama da Alamin"

Yaron  Alamin yace "wai inji wa?"

Yaron yace "wani ne a Mota"

Alamin ya tsaya tunanin ko waye ke nemanshi.

Ya sauka kan Keke, wani dan shagon yace "Oga in hade maka rigar?"

A takaice Alamin yace "aa"

Dariya yan shagon suka fashe da, dayan yace "ina Oga zai bari wani ya mai dinkin Amaryarsa?"

Suka sake sa dariya, be kulasu ba ya fita waje.

***


Hajiya Iklima tace "ai ni da Saaden daya ne, in taje kamar naje ne, ba sai anje dani ba, su je kawai"

Uncle Ahmed ya kalli Hajia Iklima cikin bacin rai yace "4 ta miki a gidan Yaya Abdullahi, tare zakuje siyayyar in na isa dake kenan"

Hajiya Iklima ta hayyayako "meye laifina? Don nace kar ayi asarar siyan ma Hawwa kayan Zamani bayan bamusan akurkin da zai kama mata ba? Yanzu in aka siya Royale Bed ko Italian Bed ko Turkey Bed ina kake tunanin zaa kafa Wardrobe din? Waje? Tsakar Gida? In naganin na damu da kar ayi asarar kudin shisa nace a bari in anje an ga gidan da zai kaita sai a mata siyayyan da zasu shige, ayi daidai ruwa daidai kurji, dan gadonta na dari da hamsin ya isheta".

Kallon da yake mata ya sa ta yin shiru yace "ba kudinki bane, ba kuma damuwarki bane, kiyi abunda nace Iklima" ya fita rai bace ya barta da gunguni.

****


Zaid ya hango tsaye wajen motar, da sauri Alamin ya karasa tare da mik'a mai Hannu, musabaha sukayi, Zaid da dan murmushi yace "mu shiga Mota mu zauna" ba musu Alamin ya nufi dayan kujerar, Zaid ma ya nufi na direba ya zauna, kunna motar yayi tare da kunna musu AC.

Sake gaisawa sukayi, Zaid yace "ya shirye shiryen biki?"

Alamin ya murmusa yace "Alhamdulilah, muna tayi"

Zaid yace "kar dai ka takura kanka, kayi iya abinda kawai kake iyawa"

Alamin ya sake murmusawa yace "babu takura inshaAllah".

Zaid ya mai addua da "to Allah ya rufa asiri"

Alamin cikin jin dadi yace "Ameen Yaya Zaid nagode kwarai dagaske"

A ranshi ya yi dan guntun murmushi shi ya san bai girmi Alamin ba, sai dai su zo tsara, amma saboda Hawwa ance mishi Yaya.

"Zan wuce"

Alamin ya mika mai hannu tare da cewa "Nagode kwarai dagaske, Allah bar zumunci"

Zaid ya amsa da "Amin"

Har Alamin ya bude k'ofa Zaid ya dakatar dashi ta hanyar cewa "ga wannan ko?"

Alamin ya dan kalloshi tare da kallon Envelop din ya fuskanci kudi ne, bandir kuwa, cikin mutuwar jiki yace "na menene?"

Zaid ya rasa me zai ce, chan yace "Gudummuwata ce"

"Ahhh ba zan karba ba, ai tunda ka bani kanwarka, ai ka gama min komai nagode wallahi"

Ya juya zai fita, Zaid yayi saurin riko hannunshi, "Meye laifi don Aboki ya ba Abokinshi gudumuwar biki? Nima in nawa yazo, zanzo har shago na karba, yanzu dai ka amsa, tsakanina da kai ne, wallahi ba wanda ya sani, gudummuwa ce kawai"

Jikin Alamin yayi sanyi sosai, yana tsoron karban kudin nan, amma yanda Zaid ya kanainayeshi ya sashi saka hannu ya karba, zaiyi magana Zaid yace "bari naje, donAllah kar wanda yaji maganar nan, kai min alkawari"

Shiru Alamin yayi, yace "InshaAllahu" envelop din ya tura cikin riga, ficewa yayi yana kallo Zaid na reverse, wayarshi ya ciro a gaban Aljihu ya kira Sani yaron shagonshi

A takaice yace "na tafi Gida".


Alamin bai tsaya ko ina ba sai Dakin Hajiyarsu, gabanta ya ajiye kudin ya gaya mata duk yanda yayi da Yayan Hawwa da ya irga kudin dubu dari biyar ne cif.

Hajiya tayi dan nazari kafin tace "to Allah ya saka mai da Alheri, Allah ya rufa asiri, kai yanzu kayi amfani da kudin ka gyara muku dakunan chan biyu, a bige dakinka a hade a yi ciki da Parlo da toilet, daga chan kuma a mata kitchen dinta, yanda dai ka tsara zakayi in Allah ya hore maka, to gashi Allah ya hore ma.

Kiran Hawwa ya shigo wayarsa, ganin ita ce Alamin yace "haka ne, gasu dai ki ajiye a wurinki, ina zuwa" ya fita tare da ansa wayar.

"Alamin dina"

Ya amsa da "Me Hawwata keyi?"

"Kasuwa zamuje"

"Da marece haka?"

"Muddassir Gallery zamuje"

"Oh ou, to sai kun dawo ko??"

"Korata kake Alamin dina?"

Da sauri yace "aa wallahi"

"Ya Zaid din da muke jira tun dazun be zo ba, kuma shi zai kaimu, Abba yace mu tafi dashi, Ya Fahad baya nan"

Kiran Zaid da akayi ya sashi tuna Alherinsa gareshi.

Yace "yanzu ya bar nan kuwa"

"Yazo gun Hajiyarsu Abba ka ganshi?"

"Aa wurina yazo wallahi"

Da mamaki tace "wurinka? Me yazo yi?"

Alkawarin da ya daukar ma Zaid ya tuna.

"Me ya faru Alamin dina, me ya kawo Ya Zaid wurinka?"

Ganin zata iya rikice mai ya sashi cewa "Alheri yazo ya min, Alherin da ba wanda ya taba min irinshi"

Wani murmushi ya subuce mata tace "Alherin mene? Wani irin Alheri?"

Dariya ya danyi yace "wani Alheri ya wuce kanwarshi da ya bani?"

"Uhm" kawai tace ta san dole akwai abunda Yayanta ya ba Alamin dinta, koma meye, zata ji.

Alamin dina ga Ya Zaid din ya dawo bari mu tafi, fatan a dawo lafiya ya mata, sukayi Sallama.


STORY CONTINUES BELOW

Da sauri ta karasa gun Zaid da ya fito daga Mota tambayarta yayi "Aunty Iklima tazo?"

Dariya tayi tace "tun kafin 4 mommy tazo, ta gaji da jira ina ji tana buga tsaki"

Zaid ya karasa ciki yana "afuwan i was caught up"

Bin bayanshi tayi sauri sauri tace "Ya Zaid ashe kaje gurin Alamin, wai yace" katseta yayi ta hanyar cewa "Shut Up" ya shiga ciki da sallama

Murmushi tayi, Ya Zaid ya ma Alamin Alheri, ko ma meye ta lura daga Ya Zaid din har Alamin din ba sa so ta sani, ko ma meye ya mai, taji dadi, za kuma ta cigaba da jin dadi, duk me Yayanta ya ma Alamin dinta, ta tabbata saboda ita ne.

****^^^****


Da zaa fita Hajiya Iklima tayi saurin shigewa Gaba, Umma ta zauna baya tare da Hawwa da Batul, Zaid ya tuk'a su suka tafi Muddasir Gallery.

Ya Zaid ne Bankin Uncle Ahmed kudin duk na hannunshi, kowa ya shiga zaban abunda yake so, ba dama Hawwa tace tana son kaza sai, yanzu ma wasu Coolers ta gani masu kyau tace "Umma ina son wannan" Mommy tayi dariya tace "a wani gidan zaa sa? Haha ki dauki ga set din Samiru chan masu kyau kinji ba irin Coolers dinnan ba, wannan ai sai Gidan Tiles, gidan Gate" Umma ta girgiza kai a ranta tace "diyarta ma kenan" a fili tace "Oya Hawwa dauka, Abbanku yace duk abunda kuke so ku dauka" Hawwa bata tanka Mom dinta ba ta cigaba da daukan duk abunda take so.

Ganin habaicin yayi yawa ne, ya sa ta daina ma

Daukan komai ta ciro wayarta ta fara latsa, da batul ta lura Sai ta dinga daukan komai bibbiyu, nata daya na Hawwa daya, Umma dai bata ce komai ba don ta san ba karamin aikin Iklima bane ta bada kanta tace zatayi fada A Kasuwa, kusan Maghrib Umma tace "a bari haka kuma sai gobe a cigaba, gobe sai a fito da safe.

Wurin biya suka nufa, aka musu packaging suka tafi Gida, duk da ana ta kiraye kirayen  sallahn maghrib Mommy bata tsaya sallah ba ta shiga Motarta ta wuce Gidanta.


B A Y A N   W A T A 2


N A S S A R A W A


Laura da K'awarta Shema suna fira, ran Laura bace "Don Uban yarinyar nan, ciki ciki kamar kaza? Kamar a ruwa takeDa wani ya bare sai ta dau wani? Ko tausayin kanta bata ji? Bakar wahalar da ta sha wurin last miscarriage har da wanki ciki aka mata bata dandara ba, amma da yake kaza ce ita, ciki be mata wuya har ta dauka, Shima Dr kamar Cingam ya dinga nane mata.

Karkarkada kafa takeyi, Shema tayi kwafa tace "Sai fa da nace miki kizo muje wurin bokan nan, kika ce ke ba ki son shirka, yo da tuninmun wuce da maganar wata Wattyn banza, shima Dr ba zai sake marmarin Aure ba har ma wata tazo da niyyar haihuwa ba"

Laura ta ja numfashi tace "ni ban son harka da bokaye, in Asirinsu yayi wata rana zai karye a koma Gidan Jiya, aikin Boka baya daurewa, da kissa da kissisina Wattyn nan zara bar gidan nan, cikin da ke jikinta shima zai zube, in ba zata gaji da ciki ba, nima ba zan taba gajiya da barar da shege ba".

Shema tace "yanzu kin ma Dr maganar ya hadeku?"

Laura tace "no bari sai cikin nan ya zube sai na samu hujjar da zan bashi ya hade mu"

Shema tace "haka, da kissa da kissisina zata bar gidan, kissan mummuk'e kawai alaji, kinta mata zagon k'asa"

Chafewa sukayi ran   Laura na suya.

****


KANO

BIKI SAURA SATI BIYU

A ka kawo lefen Hawwa Gidan Baba Abdullahi, sosai akayi mamakin Alamin don yayi kokari ba na wasa ba, don karfin hali harda atamfar super kala biyu, kuma yawancin kayan cikin ya dinke mata su cikin styles masu kyau na zamani, sosai aka yaba gwanintarshi, Batul ma an kawo mata nata lefen abun dai sai sambarka.

Jigawa Batul zata zauna a satin bikin su Aunty Iklima sukaje jere, ana jibi daurin Aure Umma da wasuu daga cikin dangin Aunty Iklima suka je gidan Hawwa don jere, sosai su ka sha mamaki, Two bed rooms ne daya ciki da Parlo da toilet sai extra room da kitchen a hade, Alamin yayi kokari matuka, komai ya shige, kayan kitchen ne dai ba su dauke kitchen din ba aka dura mata ragowan kayan cikin wardrobe din dayan dakin, Umma ta shiga dakin Hajiar Alamin tayi Sallah, Umma ta lura Sirikar Hawwa kamar ba zata yi matsala ba, har bakin kofa ta rakasu tana musu fatan Allah ya huta Gajiya.

Ranar Jumaa akayi Luncheon wanda har Baba Abdullahi sai da ya halarta, amare da angwayensu sunyi kyau sosai matuka,ranar Asabar aka daura auren bisa sadaki dubu 50 dukkansu, a ranar Uncle Ahmed da kanshi ya kai Batul Gidanta a Jigawa, Hawwa kuma Baba Abdullahi ya danganata da dakinta, Batul ta sha kuka kamar ranta zai fita Hawwa kuwa ko digon hawaye batayi ba, wasu na cewa zatayi ita ko a ranta tace "kukan me zanyi?

Allah ya Bada Zaman Lafiya Batul n Hawwa.

****

A Gurguje2


STORY CONTINUES BELOW

Bayan Wata 3 Zaid ya daga Zuwa K'asar Cuba, Hawwa na da Cikin wata biyu, Batul ma haka, Hawwa na zaune Lafiya da Alamin, son da take ma Alamin ya sa take son Hajiyarsa kamar Uwarta, sisters din Alamin ma tana ji dasu, kawai sai ta dauko jallabiya tace "Aisha gashi na baki" ko tace "kina son kaza?" binibini tana dakin Hajia, ita ko Hajiya gani take tunda Hawwa ta bar daula tazo ta zauna da danta da be da komai ai ta gama mata komai, ji take da Hawwa sosai, ina laifin me son naka? Alamin kam sosai yake hakuri da Hawwa saboda ko Abinci ba ta iya ba, amma da yake yana sonta, kuma kusan kullym yana gida, kuma dai shi dan halak ne baya manta Alheri da karamci Iyayen Hawwa da ita Hawwan gareshi, be taba damuwa ba, illa kasancewar da yake da ita a Kitchen yana koya mata girki don ko sosai ya iya Abinci, a cikin wata ukun nan Hawwa ta fara gogewa a harkar Abinci, zama suke Lafiya lau dinsu da dadi ba dadi. Alkawari tama kanta duk me ya faru duk rashin da zasuyi ba zata taba zuwa gida neman taimako ba balle mommynta ta samu abun goranta mata.

*******

Bayan Shekara daya1


NASSARAWA


Duk wanda ya san Watty ya san akwai damuwa tattare da ita, ta sirance ta yi bak'i, idonta ya sake jirkicewa kallon ruruwan ya karu sosai, zaman lafiya takeyi da Mijinta da kishiyarta da yanzu suna zaune gida sakamakon wani barin da ta tabayi, Laura ta roki Dr da ya hadesu saboda gudun kar wani abu ya sameta kuma ita kadai ce a gida, gwara in da mutane abun zaizo da sauki, gashi mai aikin Watty karama ce, Dr baida matsala ko kadan, ya dauka abunda Laura tace da zuciya daya, da ya je ma Watty da bukatar hadesu bata ja ba, don ta san bata da matsala da Aunty Laura, ya hadesu suka cigaba da zama lafiya.

Wani abu da Laura keyi shine, in Watty tayi baki, to inshaAllah nan zata zo ta tare a parlorn Watty, da ita zaa sha fira har bakin su tafi, ko su Aunty Binta ne, duk yanda Watty take so ta kebe da danginta in sunzo, Laura ke musu kabekabe, bata matsawa ko nan da nan, abun dai ya na damun Watty kadan, don ita in Lauran tayi baki da taje ta gaishesu take fitowa, to meyasa ita bata bata privacy dinta? Amma ta bar damuwa don a ganinta shaidan ne yake so ya hadata da Auntynta Laura bayan suna zaunensu lafiya, ai wanda ya damu da kai shi yake son naka, to ta bar damuwa duk da Aunty Binta na ma Watty gargadin yawan shige ma Laura da takeyi, Watty bata ji ba don gani take da Aunty Laura da wani bakin hali da tuni Halin ya fito.

Ganin kamar Watty na biye da ita, sai ya zamana ta fara zugata kan abubuwa, tana so ta hadata fada da Dr, tana so Wattyn ta fara ma Dr rashin kunya,to da yake tun asalinta Watty bata iya rashin kunya ba, bata daukan karatun Laura, haka ma randa Dr yayi tafiya zuwa Kasar China, akwai wasu laces da wata yar Nigeria ta amsa kudi a gurinshi ta siyo mishi iri  daya sai dai colors suka banbanta, shi mai mata ya kawo musu ya ba Laura yace ki dauka colorn da kike so ki kai ma Waffles nata, Sosai Laura ta nuna murnarta da ta ga laces din harda rawan bariki, ta kwasa duka tace barin kai ma kanwata ko.

Ta na shiga Part din Watty ta zauna ta tabe baki tace "Waffles kalli wasu laces da Dr ya siyi mana, wani oldfashioned, wallahi tun last Sallah akayi yayin wadannan munanan laces din, kuma nasan haka  yaje a ka bugar mishi baki ya bada kudi masu yawa aka bashi cheap laces dinnan, gaskiya in ya shigo kice mishi mudai ya dinga bamu kudinmu muna siya da kanmu"

Tunda ta fara magana bakin Watty yake a bude, mamaki kawai take da ta gama jin nata tace "haba Aunty, ai ina tunanin ko london wax yanzu Dr ya siyo ya bamu karba mukeyi muna rawan jin dadi balle wadannan dankareren laces din, ni wallahi ban taba ganin irinsu ba, sosai sukayi kyau, ai ki basuyi kyau ba ai rainuwa ba namu bane, ko ko Aunty?"

Wayancewa Laura tayi tace "ai shiyasa shawara da dadi, ka samu mai baka shawara ma wani abune"

Watty tace "gaskiya ne ai mu ko atamfa roba roba ya kawo wallahi mun gode, Allah ya kara girma da arziki mai amfani"

Da borin kunya Laura ta bar Parlon Watty ta na tsine mata a ranta.


K A N O


Hawwa da danta dan wattani 10 ana kiranshi Abbah don ya ci sunan Baba Abdullahi kuma Alamin ya ma Babanshi mahaifi takwara tunda shima sunanshi Abdullahi, Hajiyar Alamin ciwo takeyi sosai, Cancer ne amma bai fara wahalar da ita ba don sun fara magani da treatment da wuri, to treating Cancer sai in Allah ya dafa maka, Alamin yana iyakar kokarinshi don akwai lokacin da ciwon ya dan tasota gaba, sai da ya sallami yaran shagonshi ya saida shagon yayi hidimar asibiti da kuma ta gida, ga kannenshi uku da yake daukan nauyi, ga mata ga da, abun ya mishi yawa.

So daya Hawwa bata taba zuwa gida ta nemi taimako ba, Umma dai ba zata dinga zuwa gidan Diya ba, ba zuwa takeyi ba ma, Hajiya Iklima ma haka, sai dai ita Hawwan taje, Batul bata gari balle, dama chan Hawwa ba me shiga mutane bane ba me zuwa gidanta sai jifa jifa, a hankali ta fara saida Yan kunnenta da sarka, Alamin baida zabin da ya wuce amincewa da kudin don in bai karba ba baida inda zai samu kuma Mahaifiyarshi na cikin wani hali, shi ya san matarshi mai rufa mai asiri ce, madallah da Hawwarsa Ummu Abdallah.

*

Tunda Zaid ya tafi Cuba Shekara daya da Watanni bai taba dawowa ba, dama plan din sai ya gama Course din baki daya zai dawo.


STORY CONTINUES BELOW

N  A S S A R A W A


Tagumin ta buga, tana cikin matsanancin damuwa, ta lura wankin hula na neman kaita dare, da duk numfashin da take saukewa ta tsani bude ido ta ga Watty cikin gidan nan, ta lura zubar mata da duk wani cikin da takeyi ba shine mafita ba, so take ta ga an wayi gari Watty bata gidan, ace abu an kusa shekara biyu, dangin Wattynma kamar ba sa sonta sunki dauketa, zuciyarta baki shaidan na kada mata ganga, ta gaji da karyar tana son Watty alhalin bata taba sonta ba, ta gaji da mata murmushi wanda kuka take yi a zuciyarta a duk lokacin da ta murmusa mata, ta tsaneta, tsana mafi muni, ta ma yi kokari da ta yi sharing Dr da ita na shekara kusan biyu, to wallahi ta kare, dole ta fitar da Watty a rayuwan Dr baki daya, yanda Dr ke son Watty, bata tunanin ko ita da tayi shekara kusan ashirin da shi yana mata irin Son da yake ma Watty, Alkawari tayi, yau ba gobe ba, Watty sai ta shek'a barzahu.

Ba zata bar Watty da rai ba, in ta musu asiri Dr ya saketa, wata rana Asirin sai karye, ko kuma kaikayi koma kan mashekiya, ita Dr ya saketa, kuma ya cigaba da rayuwanshi da Watty kinga ko ta rasa, ta na san Mijinta sosai, yau dole komai yazo karshe, ta san Watty na makaranta, yau Dr a dakinga yake ta san Watty ba abinci zatayi ba tunda Miji ba dakinta yake ba, kitchen ta shiga da kanta ta girka mata best food dinta Tuwo miyan kubewa danya, ta san watty da son Ginger Juice ta mata shi, cikin miyar da kuma juice din ba tare da fargaba ko shakku ko tsoro ba,  ta zuba sniper a ciki.

*********


A galabaice ta fadi kan kujerar Aunty Binta tana maida numfashi, Aunty Binta ta kalleta cike da tausayawa, tace "Watty, anya ba zaki dawo Gida a nema miki maganin Hausa ba? Wannan karewar da kikeyi yana ban tsoro, sai fayau kike yi, dubeki donAllah"

Wahallalen murmushi tayi tace "Aunty Wallahi gajia ce kawai, kin san daga School nake, biyowa nayi mu gaisa naga kwana biyu, yanzu in na huta zan wuce gida na huta gobe weekend"

Aunty Binta ta tabe baki, don ta san Watty da kafiyya da zurfin ciki, ba tun yau ake cewa ya koma gida ta huta ba amma ta ki, ganin maganar ma bata lokaci ne yasa ta barin zancen "Ina Zaid?" tace "na san yau Goggo ta aiko dashi ya zo ya min weekend tunda dai ba makaranta" fira sukayi sama sama, Aunty binta na lura da ita, tana magana tana cije baki kamar wani abu na mata ciwo, ba dai tace komai ba don ta san zata musa mata, sai bayan laasar tayi haramar tafiya, a hanyar fita ta ci karo da wani mutum, tace  "oh sorry" be ce mata komai ba, suka dan kalli juna kafin ya rabeta ya shige cikin gidan Aunty Binta.


Da sallama ya shiga parlorn Aunty Binta

Ta na ganinshi ta dan zaro Ido, sosai ya chanza, amma ya zaa yi ta manta yaron da sukayi yarinta tare? "Abu?" Murmushi yayi yace "Binta" "daga ina kake? Shekara biyu ko ma uku ne rabonka da gida? Ka hadu da Watty a waje, Watty ta ganka?"

Bai amsa sauran tambayoyin ba yace "Watty ta na nan ne?"

"Yanzun nan ta bar Parlorn"

Tsaya ya mike "Aunty Watty ce na hadu da ita yanzu a tsakar gida, wata mai fararen kaya kamar na nurses?"

Da kai da baki ta amsa "eh itace"

Lokaci daya hankalinshi ya tashi yace "me ya sameta? Ya na ga ta koma haka?"

Aunty Binta bata san me zata ce mishi ba.

Cikin daga murya yace "Binta, bani Labarin Hauwatty".

******


Ta na Isa gida tayi Sallama a Part din Aunty Laura, Laura tace "sai yanzu?"

"Wallahi Aunty daga Gidan Aunty Binta nake, ta na ma gaisheki"

Laura ta san karya ne, ta san yanda bintar nan ta tsaneta ba zata taba cewa a gaisheta ba, tace "kije ga tuwo miyan kubewa da ginger juice chan kan dining dinki na aje miki"

- [ ] Murmushi Watty tayi tace "thank You Aunty, you are a life saver, bari na fara da wanka na rage wannan kayan jikin nawa" dama ke nake jira ki dawo, zanje na gaida mamar Shema ba lafiya" "ayyah a gaida Aunty Shema, da ban gaji ba da na biki" Laura tace "bakomai zan kaiki gobe"tayi gaba Laura ta bita da harara tace "yau sai lahira, zakiyi kwanar keso yau, gobe sai kwanan kabari" yarda ya sa take bar ma Laura Key din Part dinta, so batayi mamaki don Laura ta bude part dinta ta ajiye abu ba.

- [ ] Gudun zargi ya sa Laura barin gidan don ma kar ace tana gidan ta mutu.

***

   Wanka ta shiga ta fito ta shafa mai, ta zauna ta sa wata doguwar riga kenan taji message ya shigo mata waya, number ne ta bude "ta ga zo ki karba Zaid, sauri nakeyi ba zan shigo ba" mikewa tayi ta zuri Hijab dinta ta fita don dama tana tsammanin Zaid din daga Gidan Hajiyarsu Ya Bu.

Tana fita ta ga Aunty Binta da wani a Mota, da mamaki tace "Aunty, wa ya kawo miki Zaid? Ganin fuskar Aunty Binta ba walwala ya sa gaban Watty faduwa, ko dai, ba ta tankata ba, ta kalli mutumin da ya ki bari su hada ido, Aunty Binta tace "shigo Watty" tsoro ya kama Watty Mamarta ba lafiya ne? Ko inna ce? Ko dai mutuwa ce" ba ta tsaya tambayar baasi ba ta shige mota, shiko ya ja mota ya nufi family house dinsu Watty.


Watty tace "Aunty ki gaya min wa ya mutu?"

Binta tace "Watty ba ki gane Abu bane?"

Watty tace "wani Abu? Waye Abu, ni dai ki gaya min Waya mutu"

Aunty Binta tace "babu wanda ya mutu, Ya Bu ne ya dawo, wai don na gaya mishi baki cika lafiya ba ya damu sai na kawoshi gidanki, da na ki har kuka yayi wallahi, wai shi wallahi sai an daukoki daga wannan gidan an miki magani"

Tunani ya cika kwakwalwar Watty duk ya yamushe ya bushe ya tare kasumba da mamaki ta dinga maimaita "Ya Bu kuma" ta mirror ya dinga kallonta, chan yaji ta chanza murya ta ce "ka maidani Gida, ni ba abunda ke damuna, ka maidani gidana, na fito ba da izinin mijina ba"

Ya Bu yace "Watty, let me help you, donAllah"

Tsawa ta daka mishi tace "nace ka maidani gida ko?"

Kafin wani yayi wata magana wayarta ta dau ruri, Mustafa ta gani, kanin Dr ne, duk inda Dr yaje to Mustafa ke kaishi, tabbas yanzu ma ta san yana tare da Dr da sauri ta dauka "mustafa"

Ji tayi yana kuka wiwi "Aunty Hauwa kuna ina ne? Baki ba Aunty Laura?"

Da sauri tace "kuna Gida ne? Ina Dr? Me ya faru"

Fashewa da wani kuka yayi yace "muna Gida, Allah yayi wa Dr Cikawa".

Cikin wani irin karaji Watty tace "Inallilahi wa ina ilaihir rajiun"

Ya Bu ya taka wani wawan birki.

"Wani Dr din? Yanzu na bar Gidan ko minti 7 banyi da barin gidan ba, me kakeso ka ce min mustafa?"

Kukan da yaci karfin Mustafa ya kokarta yace "Dr ya rasu wallahi" kashe wayar yayi.An rasa me magana a cikinsu, ba abunda ke tashi a motar sai sheshek'ar Watty da take kuka mara sauti, har suka iso Gidan, bata bari motar ta tsaya ba ta bude murfin Motar dole Ya Bu ya ci burki, an wangale Gate din Gidan, don yan Unguwarsu suna ta  shiga gidan.

Kusan a guje Watty ta shiga Gidan, bata damu da binta da kallo da akeyi ba, ta k'arasa chan cikin Gidan.

Aunty Binta da Ya Bu suka rufa mata baya, kusan a tare su ka shigo Gidan tare da Laura, saboda Ihun Laura ne ya sa su juyawa suga yanda ta arto a guje tana yarfa hannu sama kamar tababbiya, yanda Mustafa ya kira Watty, haka ya kira Laura ya sanar da ita mutuwar Dr.

Watty ta iske durkushe a gabanshi, bata san Lokacin da ta bangajeta ba tare da daura kanshi kan cinyarta, "na shiga Uku na, Dr ka tashi donAllah, wallahi Allah ba zan iya rayuwa babu kai ba"

Wata mata da suke makwaftaka tace "haba Laura, ya kike kururuwa a gaban Gawa?"

"Ku barni nayi, Dr ya tafi ya barni"

Watty dai na daga gefe tana hawaye Imani da tsoron Allah na k'ara shigarta, yanzu yanzu sai Allah.

Wayar da Mustafa yayi ma danginsu ya sa su cika Gidan Cikin Minti 30.

Immediate Brother din Dr tace "Musty Me ya faru? Daga bari kuje ku dauko Files?"

Mutane suka sako kunnuwansu don har yanzu ba wanda ya san Dr Hatsari yayi, ko ciwo yayi? Ko kuma babu ko daya"

Musty da muryarshi a shake take yace "Yaya Umar,  bayan mun rabu da kai yace Files na dakin Aunty Hauwatty, mu kazo Gidan tare muka shiga gidan, yana gaba ina baya, da sallama muka shiga Gidan, muka iske mai aikin chan, har Dr ya nufi dakin Aunty Laura ta sanar dashi yanzu ta fita tace ba zata dade ba, sai yace "Files din na dakin Aunty Hawwatty, sai mu ka nufa ni dama da niyar mu gaisa da ita, Sallama mukayi kai tsaye ya shiga dakin yana kiran Waffles, ya kirata fiye da so uku, ba amsa, ya bubbude dakunan bata nan, Files din ya ciro ya dawo Parlo inda ya barni zaune kan kujera, ya kalleni yace "Musty yau matayen Gidan nan sun ci ganye, duk sun fice ba da izini na ba, nasan Dr da barkwanci sai kawai nayi murmushi, Dining naga ya nufa nima na bishi da ido, Jug din da ke suracin sanyi da ake ganin abunda ke ciki ya daga yana cewa "Waffles mayyar Ginger Juice, kai ya kafa yana shan ginger juice dinnan, nace Dr bari na dauko maka Cup yace aa mu tafi kawai, wallahi Allah ba mu bar Parlorn Aunty Hawwatty ba ya fara k'akari, kafin na rikoshi wallahi ya fadi, duk da ni ba likita bane, kallo daya na mai na san cewa ya cika".

Inallilahi wa ina ilaihir rajiun kawai mutanen gurin ke nanatawa.

Kanwar Dr ta nufi Hauwatty da gudu da chakumota wuyanta tace "Wallahi ke kika kasheshi"

Kafin ta fahimci me take cewa taji wata yayarshi ta rufeta da duka "uban me kika sa mishi a Juice? Wallahi ba zamu barki ba"

Wani kukan kura Ya bu yayi ya dira gabanta, ya mata kariya, kar wanda ya sake dukanta, ai ko nan akayi musu chaaa ana dukan Watty da Ya Bu, Aunty Binta kanta ya kulle ta kasa motsi, sai da wani Kawunsu ya tsawatar musu yace "haba me kukeyi haka? Meyasa kuke hargowa gaban gawa? Wannan wani irin abune? Ku bari a kaishi makwancinshi mana"

"Wallahi Kawu Ibrahim Yarinyar nan ta kashe Dr, ashe sululu kasau ce? Ba zamu yarda ba wallahi yanzu ba anjima ba sai ta gurfana gaban alkali"

Nan take wani ya kira Police Station, Kukan Watty ya tsaya chak, Kallonsu tayi yanda suka zagayeta, Aunty Binta na daga gefe ta kasa daga yatsa.

"Allah ya ji kanka Dr, Allah ya gafarta maka, Allah ya sa ka huta, Dr mijin kirki ne kuma Adali, donAllah don Annabi ku mishi suttura ku kaishi Gidanshi na gaskiya, ni ce dai ko? Ba zan gudu ba, ni dai a mishi Wanka donAllah"

"Rufa wa mutane baki, Musa a zucci Firauna a baki, ai ko da hakkin Yaya Laura aka barki kin kade"

Lauran da akace ne ya sa mutane juya kallo zuwa inda Gawar Dr take da Laura da ke kwance gefenshi, ashe Suma tayi, ba wanda ya san tun yaushe take a yanayin nan, ashe tunda taji silar mutuwar Dr ta sulale ta fadi kusa dashi.

Da gudu sukayi gurunta, kanwar Laura ta rufe Watty da duka, shikenan bakincikinki ya kashe mana Aunty Laura, wallahi ba zamu yarda ba, Aunty Laura na son mijinta kin yi sanadiyar mutuwarshi, Allah ya tsine miki" Aunty Binta ganin abun ba na karewa bane ta kira Gida, ana nan ana abu daya har su Inna da Baba suka zo, Inna ta dogara sandarta ta sha gaban Watty ta kallesu one by one tace "Me ya mata da zata kasheshi? Ko wannenku nan ya san tsantsar soyayyar da Dr ke ma Wattynmu, kun tsaya kuna ta ihu bayan duk abunda kukeyi Gawa na jinku, ku baku yarda da Kaddara ba, baku yarda da mutuwa gaskiya bace ba, ba ku yarda mutum haka kurum na iya mutuwa ba, to shi da ya mutu baiyi gaggawa ba, mu da ya bari, bamuyi Jinkiri ba, ku tuba ga Allah, kar Imaninku ya raunana"


STORY CONTINUES BELOW

Siren din motar Police sukaji, wanda yayi daidai da farfadowan Laura da aka shafa ma ruwa a fuska, Polisawa suka finciko Watty da ke bayan Inna, babu wanda ya iya hanasu har Ya Bu da kanshi yayi zafi yana tunanin yanda zai fiddo Wattynsa daga wannan k'angin, Laura ta fashe da wani irin Ihun da ya farga da kowa, sosai mutanen gurin suka tausaya ma Laura, a cewarsu Watty ta fi daukan Hakkinta.

Wani tsalle da Laura tayi ta shak'ure wuyan Watty kamar zata kasheta tana fadin maganganu da daga ji an san bata cikin hayyacinta "donubanki shi kika bari ya sha Juice din? Ba ke nace ki sha ba? Wallahi kema sai na kasheki, kinsan ba a dakinki yake ba meyasa kika bashi? Janaizar ki fa na so ayi ba na mijina ba, wallahi muje dakin sai kin ci tuwon kuma ki kora da juice din" jan Watty ta fara yi, Watty ba tayi kokarin kwace kanta ba, babu wanda ya kawo mata dauki kuma, babu ma wanda ya fahimci kalamen Laura, su dai sun san reaction takeyi a kan kissan gillar da Watty ta ma Dr.


Ya Bu ya fahimci wani abu, yan zargin wani abu, kusa da su ya taka ya riko hannun Laura, wanda na damanta na arm din Watty, cikin dabara yace"Kinga laifinki ne da baki ce mata nata kadai bane, ai da kin gaya ma Watty kar ta bari Dr ya sha"

Cikin hankalin da ke gushe tace "yo ina na san Dr zai ma dawo a lokacin nan, ai kuma ba dakinta yake ba, bansan me ya kaishi dakinta ba har ya sha abunda ba nashi ba, wallahi da na sani da sai na bari yayi tafiya"

Hankalin mutane ya fara yowa kan Laura, da dama ba su fahimci zancenta mai kama da soki burutsu ba.

Ya Bu yaji dadi sosai da hadin kai da gusasshen hankalinta ya bada, ya dan murmusa yace "laifin ki ne da bakiyi takatsantsan ba, gashi yanzu Dr ya tafi ya barki, amma kinsan yanzu haka bai mutu ba tunda ba su kaishi asibiti ba, kila dogon Suma ne"

Da sauri tace "dagaske ko? Muje ka kama minshi motana na waje mu kaishi Asibiti" yanda take magana kamar ba kowa a gurin, bata lura da mutanen da ke gurin ba, ko bata ganinsu ne oho.

Ya Bu yace "tsaya dai wai shin Poison ne? Ko maganin bera shine be da wuyan samu?"

Da sauri tace "Sniper ne"

Ya Bu ya daga Hanayenshi biyu sama maana Faqat!

Mustafa yace "Yanzu Aunty Laura Aunty Watty kika so ta sha Juice din Dr yasha?"

Cikin Masifa tace "ji min Musty, ta ya zan kokarin kashe rabin raina? wallahi yar matsiyatar chan na zuba mawa na so ta mutu, amma barni da ita kama min Dr mukaishi Asibiti please"

Kawun Dr yace "Ke kika kashe Dr kenan?"

Tace "Ai be mutu ba, Wattyn chan na so ta sha ta mutu don wallahi na tsaneta"

Tambayoyi suke mata, tana amsawa cikin zarewan hankali, yanuwanta suna ta tsungulinta amma cikin ikon Allah duk tambayar da aka mata sai ta amsa, har tana cewa "yo gani nayi wankin hula na neman kaini dare, yar kan uba tun da tazo take ciki kamar kaza, aiko duk cikin da tayi na barar da shegu, amma bata bar yin cikin ba, ina zan bari ta haihu shekarata kusan ashirin da Dr ban haihu ba, nace wallahi be yiwuwa, da naga dai zubar da cikin ba zai min amfani ba na yanke hukuncin shekata barzahu"

Watty da idanunta suka gama bushewa ta fincike hannunta daga rikon Police, takowa tayi har gaban Laura ta daga hannunta ta Mareta ji kake tasss ta ce "Allah ya Isa, Allah ya saka mana" ta juya ta kalli Kawu ta fashe da wani Kuka tace "donAllah ku mai Wanka ku mai sutura, ni ba zan iya ba da nayi"

Laura cikin hargowa tace "Ubanki zaa ma wanka, ce miki akayi ya mutu? Kece dai zaki mutu"

Polisawan nan suka nufo Laura tare da saka mata Ankwa.

Kawu yace "ku tafi da ita danAllah"


Aunty Binta ta rungume Watty, ta cigaba da kuka a kan kafadun Auntynta.

Aka yi Gate da Laura da ta fara Tirjetirje, ina zaku dani? Bakuji Dr na kirana ba, ku kyaleni, naje na bashi ruwa ya sha, Dr kace su sakeni, sambatu ta dinga yi har aka fitar da ita daga Gidan, daya bayan daya danginta suka fara samfewa, Watty da disasshiyar murya ta kalli Mustafa tace "Musty ka bude Side din Dr aje chan a mishi wanka" mukullin ya ciro a Aljihunshi ya nufa Side din Dr.

Watty bata ma kowa magana ba ta nufi Cikin Gida inda Side dinsu yake, chan sai ga ta ta fito da tabarma manya guda Biyu, dangin Dr suka nufeta da sauri tare da karbe Tabarman suna cewa "ai da kin bari mun dauko"

Shimfidawa sukayi, ta kalli Mazan da ke gurin tace "Bismillah ku zauna" wasu mazan suka zauna suna mamakin karfin halinta.

Matan kuma suka bita ciki, Inna ta tura Yaya Hashim Gida ya dauko tabarmai a Store, don wannan yayi kadan.

Kawu ya kalli Shakikkan Dr yace "ku mu shiga mu mishi wanka, an siyo Linkafanin?" Wani yace "Aminu ya tafi be dawo ba, kafin a gama wankan na san zai dawo"

Su 6 suka nufa yi ma Dr Wanka sai Mustafa da ya fito ya zauna a barandar don shi ba zai iya tsayawa ba, Dr Yayanshi ne kuma Ubanshi, Dr yafi yarda dashi fiye da kowa, shi kamar PA dinshi ne, shine drivernshi shine Maajinshi, shine komai dinshi, yanzu shikenan ya tafi, Allah ya isa Allah ka tsine ma Laura.

A cikin Gida kuwa Mata Zaman jigum jigum sukayi, Aunty Binta ta fito da Cooler Tuwo da Miyar kubewa da Juice din da Laura ta ma Aunty Binta tace "bari ta ba wannan Mustafa ya kai Police Station tun da dai Evidence ne".

Watty tace "Aunty ba dai Mustafa ba, ana bukatarshi a nan".

Yayar Dr tace "akwai Mota Hannuna, bari muje, na san Maza na gurin Wanka"

Aunty Binta tace "to muje"

Tare suka fita.


STORY CONTINUES BELOW

Kafin bayan Isha'i an ma Dr Sutura sai zuba kamshi gawar take, ganin dare yayi ya sa aka bar Kaishi sai gobe in Allah ya kaimu da karfe 8 na safe, Dr maraya ne amma yana da tarin Yanuwa da suke Uba daya da kuma wanda suke Uwa daya Uba daya, bai taba haihuwa ba, amma yana da yayan dangin da yake daukan nauyi, Labarin mutuwar likitan ciwon Ido Dr Nazifi ya zagaya duk wata kafa ta yada zumunci, sosai Alummar Jahar Nassarawa suka girgiza, musamman wanda suke kwance a halin yanzu a Asibitinshi suna jira 8 yayi ya zo dubasu.


Adduoi a ka dinga shiga ana ma Dr, Kawu ya bukaci Watty da ta shigo ta mai Addua, kyam ta tashi ta shiga Dakin, duk karfin halin da ta jima tanayi, sai ta karaya da ta ga Dr kwance cikin makara daure cikin Likafani, tsoron Allah da Imani suka samu wuri a zuciyarta, da kyar ta karasa gaban Gawar ta durkusa kan guiwowinta biyu.

Sallama ta mishi, kafin ta dinga mishi adduoi, ta na hawaye, kusan minti 40 kafin ta iya fitowa.

Haka sukayi kwanan Makoki

Washegari tun karfe 7 gidan ke cika da Maza da Mata yan janaiza, duk fadin Gidan nan sai da  yayi kadan, Fillin Kwallo aka bukaci da aje chan ayi Sallahr, haka kuwa akayi bayan Watty ta sake shiga ta mishi Adduar dacewa da shiga Kabari a Saa, tafiyanshi ya dawo musu da Mutuwa sabo, Mata sai kuka suke wiwi, haka aka dunguma aka ma Dr Sallah kafin aka kaishi Gidanshi na Gaskiya, Allah ya ji kan Dr Amin.


Sai da akayi Makokin Kwana 7, kafin mutane suka tsagaita da zuwa, Inna tace a bar Watty tayi Takaba a gidanta dama bata da niyyar komawa gidansu, nan Gidan Dr Watty ta cigaba da Takaba, Laura kuwa ta fita hayyacinta da alamun kwakwalwarta ya ta bu, daga Police Station aka gurfanar da ita gaban Alkali, duk tambayar da aka mata amsawa takeyi, Alkali ya yanke mata hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso, ko da labari yazo ma su Watty, ba wanda ya tausaya mata, banda Allah ya isa da suka dinga jefa mata don ta fara ganin sakkayya tun a Duniya.

Watty ta dinga ba mutane Labarin kalar Soyyayar da Dr yake nuna musu, ashe Files din da ya dawo dauka a dakinta ranar da ya rasu Fili ne zai siya musu ita da Laur Mustafa ke gaya musu haka, aikuwa suk dinga laantar Laura.

***

Laura ko tun kafin ayi sadakar bakwai ta gama figewa ta lallace, ba abunda takeyi a gurin sai tona ma kanta Asiri, kafin Dr yayi kwana Arbain da rasuwa Laura tayi mutuwar wulakanci a gidan kaso, kowa yayi Tir da halinta.


Dr na cika kwana 10 da rasuwa Watty ta tattara kayanta ta koma Gidansu, kowa burinshi ya kwantar ma Watty da hankali, da ta zauna ita kadai ba abunda takeyi illah kuka, Dr ya cika Masoyi nagari, roko take Allah ya sa in tana da rabo mijin da zata aura nan gaba ya so ta kamar yanda Dr ya so ta har ya koma ga mahallincinshi.

**


Tun lokacin rasuwar, sai da hankali ya dan natsa ta sa a ka kira mata Ya Bu, lokacin da ya shigo parlorn Inna cike yake da Iyaye da dangi, a kasa ya zauna kusa da kafan Inna ya kasa kallonta, tambayar shi tayi me ya faru dashi? Ina yaje tsawon shekarun nan?.

Shiru yayi ba amsa, sai da mahaifinshi ya daka mishi tsawa "ba zaka yi magana ba dan nema?"

Kowa ya kasa kunne yaji tun balle mamanshi da tunda ta ganshi a gidan Rasuwan take neman su kebe amma be bata dama ba.

Baban Watty yace "Abbakar, ya rayuwanka bayan rabuwa?"

Magana ya fara "Bayan na saki Watty, na san cewa ni dai ba zan iya zama a Gida ba, na tafi wurin abokina a Abuja, daga nan na wuce Ghana, da na je Ghana kuma na cigaba da kalar Rayuwar da nayi a baya, to nidai wallahi ba da dadewa ba na fara wasu irin mafarka da Watty, Mafarkan munana, tun ba sa damuna sai suka fara damuna, bayan nan, sai komai ya juya min baya, abincin da zanci yana neman gagarata siye a Ghana, dama ba aiki nake ba, sai kwatsam na ga Zaid na karatun Qurani a Instagram page din Aisha, Zaid dina ya na karatun Suratul Naba'i, wanda da nace zan bi karatun sai na fara cin baki, nan take hankalina ya tashi, mai na maida rayuwana? Yaron cikina ya iya karatun da ni na mance, nadama da da nasani suka lullubeni, nan take naji sha'awar zama Uban da D'ana zaiyi alfahari dashi, hankali kuma sai ya yo Gida, na dau Alkawarin zama mutumi nagari, ina so na gyara kuskurena na da, ina so na gina sabuwar rayuwa da Matata da Yarona, sai nafara shirin dawowa gida.

Sai wata Laraba nayi mugun mafarki da Watty tana bina tana na taimaketa, hankali na ya tashi sosai, na rantse yau a Nigeria zan kwana, ranar Alhamis gab da Sallahr Asuban Jumaa jirginmu ya tashi, mu ka iso Nigeria, ina lagos, daga Lagos na taho Abuja daga Abuja na biyo motar Nassarawa, ina Sallahr Jumaa na tafi Gidan Binta don na san ita kadai ce zata gaya mij komai game da Watty, har haduwa nayi da Watty gaban gidan amma duk bamu gane juna ba saboda chanzawan da tayi, naga tayi mugun baki da lalacewa, bayan Binta ta gama min Masifanta ta ke ce min ai Watty ce ta fita yanzu, ina jin haka na san cewa Watty na cikin Matsala, na tabbatar mafarkai na ba a banza ba, zuciyata ta dinga tafasa, burina na cirota daga halin da take ciki, shine na birkice ma Binta nace sai ta kaimi Gidan Watty na daukota munje gaban Inna, shine fa da akayi hakan ne aka kirata ake sanar da ita maganar Mutuwar Mijinta.


STORY CONTINUES BELOW

Parlon Inna shiru banda sheshekar mataye masu raunan zuciya baka jin komai, sosai Ya Bu ya basu tausayi, a hankali ya tashi ya taka har gaban Watty ya zube guiwa bibbiyu gabanta, kuka takeyi a hankali, "Watty ki yafe min" yafiyarta ya shiga nema da sauri tace "tun kafin ka bar Gida, gaban kowa na shaida maka na yafe maka duniya da Lahira"

Yace "ki sake cewa"

Tace "na yafe maka Ya Bu"

Murmushi yayi yace "nagode kwarai Hawwaty, na gode da kalar Tarbiyan da kika ba Zaid, nagode Allah miki Albarka"

Murmushi ta maida mai tace "bani na ma Zaid Tarbiya ba, Hajiya zaka ma Godia don tun tafiyanka yana gurinta, ni dai sai yazo min weekend"

Da sauri ya rarrafa gun Mahaifiyarshi yana rokonta gafara, rungumeshi tayi tana kuka tana cewa ta yafe mishi duniya wa lahira.

Ya roki gafarar su Inna da Baba kowa ya yafe mai, gabansu ya dau Alkawarin zama Uba nagari da Zaid zaiyi alfahari dashi.


Ya Mike ya kalli su Inna da suka zuba mai ido kamar suna kallon Film yace "a Ghana burin da naci shine, na zo na dauke Watty muyi aurenmu mu zauna lafiya da Zaid, amma yanzu ganin Watty a halin da ta ke ciki na san cewa tun farko ni na fara lalata mata rayuwa, na riga na mata Illa, sake neman aurenta kamar Son kai ne, Watty yanzu tafi karfina wallahi don ta wuceni nesa ba kusa ba, ina neman rokon alfarma Inna da ku kyaleta ta huta, kar ku sake mata maganar Aure, duk da yanzu ita ce ke da hakkin zabar ma kanta Mijin aure, kar ku matsa mata a kan sai ta fitar da wuri, aurenta Biyu a shekarunta da basu wuce 22 ba, tasha gallazar Miji a aurenta na farko, aurenta na biyu tayi wahalar Kishiya, kar ku bari tayi garaje gun aurenta na 3, yarinya ce, zata sake auren, ko bajima ko ba dade zatayi, donAllah ku kyaleta haka nan".

Inna ta jinjina kai cikin amincewa tace "InshaAllahu babu wanda zai takura mata kan maganar Aure, Allah ya maka Albarka Abbakar ya baka mata ta gari ya shiryaka kuma"

Ameen ya amsa da murmushi.

Girman Ya Bu ya karu a idon Watty sosai taji dadin maganganunshi.

***2


K A N O


Kallonta yakeyi cike da abubuwa uku, k'auna, girma da tausayi, kamar zai kuka ya kauda kai, kara matsowa tayi kusa dashi tana murmushi, tace "Ka karba Alamin dina, ka karba a mata Chemotherapy din Wednessday"

Kukan dai ya sake "Hawwata, wallahi ni ba kowa bane in babu ke, a duk lokacin da na mikar da hannuna da niyyar ansa kudi daga gareki wallahi ji nakeyi kamar kasa ta bude in shige saboda kunya, tunda na auroki gashi Abba ya kusa shekara, ban taba miki kyautan dubu 5 ba haka nan, ya zamana ke ke daukan nauyina, na mahaifiyata da kanena, kuma ba wai don kina da kudin ba, kema rigima ce, kina daukar kaddarorin kina saidawa, Hawwata na hanaki bakiji, bakiji, ya zanyi?" Ya rufe fuskanshi da dukkan hanayenshi kudin ta ajiye a gefe ta ciro hannunshi daga fuskarshi, ta share mai hawayenshi, light kiss ta mishi a lebe kafin tace "kalar Son da nake maka kenan, irin wanda zanyi komai don ganin Farincikinka, ka manta i am not anyway close to perfect? Amma

You made me feel loved, kayi tolerating dina through my worse times, ban iya magana ba, duk yanda na yabo maka bakar magana a duk lokacin da mukayi sabani baka bata ranka, Hajiya tun da nazo gidan tsakanina da ita sai Alheri, ta nuna min So, ta na sane da irin zaman da nakeyi da kai ina amarya na rashin iya girki, amma bata taba kusheni ba ko gwasuleni, illah koya min da takeyi da jana a jiki, kanenka tsakanina da su sai girmamawa, na san ban girme sadiya ba, amma Aunty Sama aunty kasa, to Alamin dina don nayi maka, nayi musu na fadi? Komai zan iya ma Hajiya don jin ta nake kamar ita ta haifeni, ina sonta sosai musamman da ta haifa min kai"

Dariya ta sashi ya ko fashe da dariyar, tare da kawo mata wata irin runguma mai dauke da sakkoni da dama.

Ganin lokaci yasa ta cewa "kaje ka yi booking din, in yaso in nagama Abinci sai na taho Asibitin"

Ya dan marairaice yace "ba me tayaki abinci yau, ko na turo miki su Sadiya"

Tace "aa wallahi ka barsu chan gun Hajiya"

Ya kalli Abbah da ke ta hidiman shi yace "wanchan baban naki ba zai bari kiyi aiki ba, barin tafi dashi Asibiti"

Tace "wallahi tabe tabe yake a Asibitin Alamin dina, ko ka kaima Ummashi, in mun dawo Asibitin muje mu daukoshi"

Yace "to hadashi da kayan bukatanshi"

Da sauri ta tashi sai gata da baby bag tana chusa Pampers a ranshi yace "pampers din ma yaushe rabon da na siya?".


STORY CONTINUES BELOW

Hawwa ta dade a kitchen kafin ta kammala hada abinci, a warmers ta zuba kafin ta shige toilet domin sake wani wanka, ta fito kenan taji kwankwasawa, da sauri ta zura doguwar rigarta ta nufi parlo, baki bude da mamaki take kallonta, ba zata iya tuna yaushe rabon da ta zo ba sai dai ita taje "Mummy? Kece? Bismillah"

Hararta Hajiya Iklima tayi tace "bangane nice ba"

Hawwa tayi murmushi tace "yo ai naga baa sati kike zuwa gidanku kuma sai kin wuce gidan nan amma baki tsayawa mu gaisa"

"Yo me zan zo yi dama? Yanzun ma naga mijinki ya fita ne nace barin zo inga ya Irin zamanku yake"

"Lafiya lau muke zamanmu"

"Naga ya fita da Abba ina zasu?"

A takaice tace "Gidan Umma"

"Eh ai da yake Saade ce Uwar Uwarshi chan kawai ake kaishi, bani gayya dama yayi ta zuwa chan"

Hawwa tace "ai bama zaa kawoshi ba"

Hararta tayi tace "ko ruwa ba zaa kawo min ba?"

Hawwa tace "Mommy bamu da bottle water"

"To ke me kike sha?"

A takaice tace "tafasawa mukeyi muna sawa a fridge"

Hajiya Iklima ta mik'e tsaye ta nufi hanyar daki tana cewa "Uhm, baringa ko ana tsafta"

Da sauri Hawwa ta sha gabanta tace "Mummy ina zaki?"

Ba tare da ta ji komai tace "inspection zanyi, in ga kina gyara"

Wani dariya Hawwa tayi tace "Mummy muje ki duba kitchen dai da wanchan dakin, tunda kin ga dai ga Parlo tsaf"

"Wannan dakin fa? Hala kazanta ke ciki ba ki gyara ba?" ta tambayeta.

Hawwa tace "sam gyare yake tsaf"

"Matsa na gani"

Hawwa tace "aa fa mommy"

Da mamaki Hajiya Iklima tace "saboda me?"

Kai tsaye Hawwa tace "saboda dakin Alamin ne"

Haushi ya kama Hajia Iklima tayi niyar banketa ta shige dakin amma Hawwa ta kasa ta tsare tace "ba zata shiga ba"

"Haba Mommy wai meye kika nace sai kin shigar min dakin miji? Nace miki na gyara"

"Matsa min na shiga Hawwa"

"Gaskia Mummy aa, kinga ko Hajiarsu wallah bata taba shigowa dakin nan ba ita da muke tare da ita, iyakarta parlo, sai ace mamata tazo ta shigar min dakin miji? Ko kema fa Hajiyarku bata taba shiga dakin Daddy ba"

Ran Hajiya Iklima yayi mugun baci, Saade ta gama da ita a rayuwar nan, Saade ta shiga tsakaninta da diyarta, Hawwa bata jin komai take datsa mata magana, ko da yake ita ta kawo kanta, cike da masifa tace "kar ki sake zuwan min Gida"

Hawwa ta murmusa tace "nima ina sonki Mommyna"

Ganin Hawwa na neman haukatata yasa ta fincikar jakka ta bar gurin.

Hawwa dai tayi daria a baiyane tace "Mommy Mommy".


N A S S A R A W A


Tun kafin Watty ta fita Takaba ta lura da taketaken Yayan Dr, ta lura so yake ya aureta, ta lura kuma dangin Dr na so, sai dai Wattyn yanzu ba ta da bace, Wattyn yanzu duniya ta koya mata hankali, kuskure so biyu darasi ne, Wattyn yanzu ta san rights dinta, kuma ta bar kawaici, ta bar kuntata ma kanta don farincikin wasu, Aure yanzu ba a gabanta yake ba, da ta gama Takaba zata maida hankalinta a kan Karatunta, idan Allah yayi zata sake wani auren nan gaba, tana da tabbacin abu biyu, ba zata kissa da kissisinar kishiya ba, ba kuma zata zauna da Miji azzalumi ba.


Watty ta gama Iddanta, har akayi rabon gado kamar yanda addinin musulunci ya tanada, kasancewa Dr baida D'a baida mahaifa sai mata da yanuwa, haka aka ba Watty Mafi yawa daga Kaddarorin da Dr ya Bari, Musty ta ba kyauta wani gida 3 bedrooms a layout tace "Dr yayi alkawarin in auren ka ya tashi shi zai baka muhalli, to na cika mishu burinshi" saboda murna sai da Musty yayi kuka, kowa yayi tashi ma Watty Albarka, abun hannunta sam bai rufe mata ido ba, kyauta sosai takeyi, kasancewar ta koma Gidansu da zama aka sa yan haya nan gidan don babu yanda zaayi ta zauna a wannan gidan ita kadai, barin gidan ba kowa kuwa gidan zai mutu.

Duk abunda Dr ke ma Goggonnishi da Kawunanshi, Watty na kokari kyautata musu, haka ta cigaba da Karatun Nursing dinta cikin kwanciyar hankali.


K A N O


Yau Juma'ah Hawwa Dadi kamar ya shideta, Abba da Umma ne zasuzo kamar yanda Ummansu ta sanar da ita jiya da daddare cewa Abbansu yace gobe zasu kawo mata Ziyara.

Ta riga ta gaya ma Alamin yau ba zata samu zuwa Asibiti ba, so in fa gama abinci zata kira Sadiya ta dauka.

Yace shima zai je ya dawo ya gaisa da su Abba.

Tun safe Hawwa ta dafa Sobonta ta hada ta sa a fridge dinta, tuwon semo tayi da miyan kubewa, sosai Hawwa ta iya abincin mutane da yawa yanzu, da ta gama ta zuba ma yan Asibiti ta kira sadiya amma wayar bata shiga, ta kira Alamin shima hakan, sai bata damu ba tasan zatazo ta dauko ko zuwa bayan Jumaa ne.

Bayan Jumaa kam sai ga Abba da Umma da alamu daga Massalacin Jumaa suke, Ina zaa saka dasu Hawaa take tayi, ta gabatar musu da abinci suka ci, Abba ya dauki Abba takwaranshi yana mai wasa, yace wai ina mutanen gidan naku?"

Hawwa ta dan shafa keya tace "suna biki ne"

Umma tace "ke bakije ba? Saboda Abbanku zai zo ko?"

Murmushi Hawwa tayi tace "naje Jiya ai, kuma zani gobe"

Abba yace "da kyau yar gidan Abbanta, dama ina zakije Abba zaizo?"

Kafin ta ce komai sai ganin Sadiya tayi ta shigo Parlorn tare sa rungumeta tana kuka da karfi

Hankalin Hawwa yayi dubu ya tashi ita ma kukan ta saka tace "mun rasa ta ko Sadiya?"

Da sauri Sadiya ta girgiza kai tace "ba mu rasata ba, amma gab muke da rasata in baa mata leukemia therapy ba, zamu rasata"

Umma tace "wacece ba lafia Hawwa"

Sai yanzu Sadiya ta lura da mutane.

Sai ta kanta tayi tare da gaidasu

Umma bata amsa ba tace "Hawwa wacece ba lafiya?"

Hawwa ta tuna karyar da ta sharara musu na cewa suna biki.

Ganin bata da niyyar amsawa ya sa Sadiya tace Hajiyarmu ce ba lafiya.

Umma tace "SubhanaAllah me ya sameta?"

Sadiya tace "dama bata da Lafiya"

Ummu tace "waiyo Allah, zazzabi ne ko na zamani?"

Ruwa ya cika a idon Sadiya tace "aa, Cancer ne, Cancer na Jini"

Umma ta doka Sallati

Abba yace "wacece? Cikin sanyi tace Uwar Mijin Hawwa"

Ta kalli Hawwa tace "kika ce suna gidan Biki"

Sadda kanta tayi kasa, hakan da tayi ne ya sa su ganewa Hawwa na boye musu wani abu.

Baba Abdullahi yace "Maman Fahad muje mu dubota" Umma ta mike tsaya tare da galla ma Hawwa harara da sauri Hawwa ta dauke ido.

Sadiya ta nufa kitchen dauko Food Basket, sauri sauri Hawwa ta sabi Abbah a hannu ta rufe Parlorn ta bisu waje inda Abba yayi Parking.


STORY CONTINUES BELOW

Hawwa da Sadiya suka shiga baya, cikin natsuwa Umma kema Sadiya tambayoyi, "tun yaushe take ciwo?" Sadiya tace "ta fi wata 6" Umma ta jinjina, tana son yi ma Hawwa kacha kacha amma bata son yi gaban Sadiya, daurewa tayi tace A asibiti?"Sadiya tace "in ciwon ya matsa mata ne muke kwana a Asibiti".

Shiru sukayi baki daya, har sukazo Asibitin Mallam Aminu Kano, Sadiya ce gaba su kuma suna binta a baya, Hawwa ko sai jan jiki take.


Alamin na ganin Abba ya mike tare da boye mamakinshi yana mai sannu da zuwa, Abba ya amsa yana mai ya mai jiki, Umma ma ta mishi ya mai Jiki, Hajiyar na kwance kamar mattata, ga Aisha nan bakin gadon duk sunyi jigum jigun.

Abba yace "Alamin ko so daya baku taba gaya mana Mahaifiyarku na ciwo ba, ba kai ba ba matarka ba" shiru Alamin yayi yana wasa da yan yatsun shi kamar mace.

Abba yace "me ake ciki yanzu?"

Shiru Alamin yayi kafin ya kalli Hawwa da ta gyada mai kai alamun yayi magana.

A hankali ya fara magana idanunshi tuni suka kawo ruwa "Abba dama ana mata Therapy ne, to wannan watan suka ce zasu fara mata Leukemia Therapy, idan baa fara ba zamu iya rasata, dama sun bata wata 3 amma sunce in baa fara ba zamu rasata cikin sattitika"

Abba yace "to sai a fara ko?"

Alamin yayi shiru.

Abba ya gane matsalar kudi ce, yace "ina zuwa"

Abba ya kira Kanenshi a waya Uncle Ahmed ya ansa cike da girmamawa "Sallam Alaikum Yaya"

"Waalaikum Salam Baban yara kana ina?"

"Banyi nisa ba Lafiya?"

"Eh muna Asibiti, sirikar Hawwa ce ba lafiya, tana ta jinya kusa wata 8"

"SubhanAllah Yaya wallahi bansani ba"

"Eh nasani muma duk bamu sani ba sai yau"

"A wani Asibiti ne?" Baba Abdullahi yace "Asibitin Mallam"

"Ok gani nan zuwa"

Baba Abdullahi yace "Ahmed suna bukatar kudi gaskiya"

Uncle Ahmed yace "babu matsala gani nan"

Baba Abdullahi ya kashe waya ya koma dakin.

Uncle Ahmed ya kira Hajiya Iklima yace "Ikee maza ki taho Asibitin Aminu Kano"

Hankali tashe tace "lafiya?"

"Surukar Hawwa ce ba lafiya"

Dan jim tayi tace "Allah ya sauwake"

"Ki sameni a chan"

"Laasar tayi fa, kasan da wuri ake kiran Maghrib yanzu, zanje gobe"

A zafaffe yace "Iklima, Yanzu!"ya kashe wayar, dama ya ma Driver umurnin zuwa Asibiti.


Ba da dadewa ba Uncle Ahmed ya iso, Alamin ya shigo dashi, hanyar shiga dakin ya kecewa "ashe ta dade tana ciwo, wallahi banji ba ko so daya, kayi hakuri donAllah, ai da na kira ko da ban zo ba" Alamin yace "ba komai Baba".

Kannen Alamin suka gaida Daddy, har Hawwa, nan Abba ya ma Daddy bayani, magana ce ta kudi, Daddy yace ina takardar? Alamin ya zaro ya bashi cike da girmamawa.

Kudin ya gani  a fili ya karanta yace "dubu Dari da Saba'in?" To bari a fara biyan na wata Biyu" ya zaro wayarshi ya dan fara latselatse, ya kalleshi yace

"Karanto Account number dinka"

Gumtse baki yayi kamar ana niyar bashi magani a baki, ya ki magana, a karo na biyu Uncle Ahmed ya sake tambayarshi, amma ba alamar zaiyi magana.

Abba yace "Ke Hawwa kina da Account din mijinki?"

Kai ta gyada tare da karanto ma Daddynta Acct numbern. Nan da nan ya mai transfer350k yace ka biya na wata biyu, saura sai ayi abunda ba'a rasa ba.

Hawaye ya gangaro ma Alamin ya dai kasa motsi.

Sadiya da Aisha suka zube gaban Daddy suna zuba mai godiya tare da adduoi masu tarin yawa.

Hawwa sosai taji dadi.

Alamin zaiyi magana Abba yace "je ka biya Alamin, the earlier the better"

Da sauri ya juya ya fita daga dakin, Aisha ta bi bayanshi.

Sadiya ta matsa kan GadonHajiyar.

Iklima ta iso da kwatance, bayan ta ma Sadiya ya mai jiki, fitowa sukayi baki daya zuwa wata 'yar baranda.

Umma ce ta fara mata fada kamar zata daketa "yanzu Hawwa uwar mijinki na kwance ciwo wata da wattani baki gaya mana ba ko so daya? Yanzu duk kallon da suke mana na rashin kirkine, har kina min karya sunje biki ko?"

Daddy yace "ashe baki bar wannan zurfin cikin naki ba ko?"

Abba yace "Mamana gaya min, meyasa baki fada mana ba? Meyasa baki ce suna neman taimako ba, meyasa baki gaya min Abbanki ba?" Murya na rawa tace "Abba bana so na daura ma nauyi" yace "ai ba ni ba Hawwa kin san Daddynku zai bayar, ni ai banda kudi, baki ga ma yanzu shi na kira ba?"

Mummynta ta kalla tace "Abba bana so Mummy ta goranta min ne, dama tuntuni na dauki alkawarin duk rashin da zamuyi ba zan taba zuwa gida nace a taimaka min ba don Mummy tayi Alkawarin yi min dariya duk randa nazo neman taimako"

Cikin fushi Uncle Ahmed yace "kudinta ne? Ko itace me taimakawan, meye amfanin kana dashi bakayi ma naka ba, duk abunda zanma Alamin ko nashi ai ke na mawa, mudai baki kyauta mana ba Hawwa, na san ana chan ana zaginmu a gari, ke kuma ki cigaba da wannan bakin halin naki"

Hájiya Iklima tace "ji yarinya zata min sharrii, to abunda akayi shekara ni na ma manta"

Daddy yace "ke dai kika sani mai mugun hali"

Turo baki Hajiya Iklima tayi.

Uncle Ahmed yace "in dai ba zan taimaka ma na kusa dani ba, banga amfanin kudin ba, to sauran treatment din ya sukayi? Eh?" Ya tsare Hawwa da ido.

Ba ta da zabi da ya wuce fadan gaskiya tace "Sarka da yan kunnena na saida, wallahi ba shi yace na saida ba, naga dai suna da bukata nikuma ina da yanda zanyi"

Ran Uncle Ahmed ya sake baci yace "yanzu da bamu sani ba Gadonki zaki sayar?"

Baba Abdullahi yace "ya isa Ahmed, Hawwa baki kyauta ba"

A hankali tace "kuyi hakuri donAllah"

Baba Abdullahi ya ma Hawwa nasiha, tare da jan kunne, ya kuma lura Hawwar tasu yanzu ta san ciwon kanta, ta na da cikin mataye masu rufa ma Mijinsu asiri, ya kuma sanar da ita duk ranar da suke da bukatar wani abu kai tsaye tayi magana, in bata iya ma Daddynta magana tayi mai shi zai karban mata gun Daddynta"

Hawwa taji dadi da kwanciyar hankali.


STORY CONTINUES BELOW

Suna nan jigum jigum Alamin da Sadiya suka dawo. Sunyi payment din, zaa fara treatment din da karfe 7 na dare.

Fatan sauki suka mata, kafin suka tafi.

Alamin sai yaji wani irin dadi, kulan da surukanshi suka nuna kan mahaifiyarshi ya mai dadi, ko ba komai ya san cewa suna son abunda Diyarsu takeso, harta Hajiya Iklima sai yaji duk rashin kaunar da take mai ba wani abu bane, tunda har zata iya zuwa dubiyar Mahaifiyarshi ai hakan ya fi mai komai.

Washegari

Sosai Hajiyar Alamin ta ji dadin Treatment din da aka mata, don har zama tayi da kanta, nan ta kalli Ahalinta tana mai tausaya musu tace "kuyi hakuri, na sani ni larura ce"

Sadiya tayi karaf tace haba Hajiya, wace irin Larura kuma, nidai kici Abinci bamu sonjin komai"

Murmushi Hajiyar tayi tace "Hawwa, ko ba a gaya min ba nasan kaddararki kika saida kika bada kudin magani na ko?" Da sauri Hawwa ta girgiza kai tace "babu abunda na saida Hajiya, ki bar tunanin komai sai warkewanki"

Ta kalli Alamin tace "in ba abunda ta saida hakan na nufin ka ciyo bashi?".

"Hajiya ban ci bashi ba wallahi, Mahaifan Hawwa sunzo jiya, su suka taimaka min"

Hajiya tayi shiru kafin tace "zuwa kikayi kika daura musu nauyina? Suma suna fama?"

Hawwa tace "donAllah Hajiya ki bar maganar nan, da kansu sukazo ba wanda ya gaya musu, kiyi hakuri kici abincin"

Murmushi tayi tace "Hawwa, ke Alheri Ce a garemu kinsani ko?"

Hawwa hawaye ta fara ba tare da ce komai ba, Hajiyar bata sake magana ba ta cigaba da breakfast.


Kasancewar yau din Saturday, karfe 12 na rana Hawwa tace "barin koma Gida, ko 'taliya ce nayi mana" Alamin ya murmusa.

Kafin ma ta tashi an turo kofar da Sallama.

Batul ce da sauri Hawwa ta mike tana oyoyo sis ta nufeta don ta rungumeta, Batul ta galla mata harara tace "ko kice min Hajiya ba Lafiya" kafin Hawwa ta yi magana ta ga Yaya Fahad dauke da basket, Matarshi itama dauke da nata basket din, da Abba da Umma da Mommy da Daddy securities biyu a bayansu dauke da Carton din Ruwa da Juices, dayan dauke da kayan Tea.

"Ah jiki yayi kyau sosai MashaAllah cewar Abba"

Gaigaisawa aka fara yi ana tambayar ya mai jiki da adduoi sosai a gareta.

Mai jiki da bakinta ta dinga amsasu kafin ta shiga zuba godiya kan taimakon da suka mata da dawainiya addua ta dinga musu tare da yabom Hawwa gabansu tana fada musu dumbin alheran Hawwa gareta da zuriarta.

Alamin ba zai misalta farincikin da yakeyi ba, a zuciyarsa rokon Allah yakeyi "Allah duk ranar da zan butulce ma Hawwa, Allah ka dauki raina kafin ranar"

Harta Zaid dake Wata kasar sai da ya kira ALamin ya jajanta mai kuma ya gaisa da Hajiyar ya mata fatan samun lafiya.

Mintinsu talatin, Abba yace "mu rage don ta samu ta huta"

Godia Hajiar tayi ta musu kamar lafiyarta kalau, su Umma suka mata sallama, su Yaya Fahad ma haka, Duk suka fita, Batul tace "Umma ku tafi da Khalil sai anjima zan" Umma tace "ai har Abban ma ya taho mu tafi, in ba haka ba zasu isheku a Asibitin nan"

"Gidana zakaje ko Khalil?" Khalil ya gyada kai Mommy ta sabeshi, haka Allah ya hada jininta da dan Batul, bata tunanin yanda takejin dan Batul a ranta tana jin dan Hawwa haka, ganin haka Umma ta sabi Abba tace "zo muje Mallam Audullahi" Alamin yace "Umma kin dai dauki mai gidanki" tace "dama me yakawo daukan maigidan wasu?" Duk sukayi dariya, Abba da Daddy dama sun riga fita, suma suka rufa nusu baya, Alamin da kannenshi suka rakasu har Mota.

Batul sosai taji haushin Hawwa don gaban Hajiyar take ta ma Hawwa fadan in bata sanar da kowa ba ai ita ta sanar da ita"

Hajiya ta dinga kare Hawwa tace "waiyo ni ce na hanata, kiyi hakuri"

Batul tace "Allah Hajiya diyarkin nan bata da wayau, jiya da Umma ta gaya min da kyar nayi bacci, yau da safe na taho daga Jigawa"

Hajiya tace "Allah sarki, ai da baki wahala ba, a daiyi mata hakuri"

Batul tace mata ga "Farfesun Hanta Umma ta miki, a zubo miki kisha har da romonko?"

Hahiya ta murmusa tace "Nayi kalaci, banjin yunwa" Batul tace "ai na karin jini ne Hajiya" tace "to bari su Sadiya su zubo min.

Batul ta mike ta zubo mata ta bata Hajiya tayi godia.

Alamin da kannenshi suka shigo, "wow wannan shagali Hajiya, kinji kamshi tundaga waje" cewar Aisha Hajiya ta kalli Hawwa tace "ki zubo kinji Hawwa ki sha"

"Hajiya mu fa?" Inji Sadiya.

Hajiya tace "sai diyata ta ci ta rage"

Suka sa dariya "Wallahi Hajia son kai, kin fi son Aunty Hawwa" shi dai Alamin murmushi kamar bakinshi zai yage.

Tun daga ranar, duk rana ta Allah sai an kawo Abinci daga Gidan Baba Abdullahi, suma sukan dan lek'ota.

Daddy ya sa ma Mummy dokar zuwa itama, kuma duk randa tazo sai ta taho da Basket din Abinci, Daddy yana kiran Alamin don yaji in akwai wani abu, to yana tabbatarwa yana sa ma Alamin kudi a account don sauran Medications din.


Haka suka cigaba dayi har Wata 2, lokacin Daddy yake ce ma Yayanshi anya ba zasu kai Hajiya India ba, Yayan ya amince don ya san kaninshi na da ikon yin hakan ba tare da takura ba yace "sosai, Allah ya bada lada"

A asibiti ya sanar musu, Hajiya ta nuna rashin amincewarta ta hanyar cewa "Alhaji donAllah kar kayi asarar kudinka, wallahi hidimar da kukayi a baya ya isa haka, bani da kamar ku duniya, kuka dauki diya kuka ba dana, diya kuma me sona me kaunata me son nawa, ai kun gama min komai" Daddy yace "bakomai Hajiya, komai sai da hali akeyi, akwai halin yin hakan kar ki damu" Alamin dai bai ce komai ba, yana dai ta mamaki irin dumbin Alheran mutanen nan"

Bayan tafiyarsu Hajiya tace "Babana, ko bayan raina ka Wulakanta Hawwa, ko ka ci amanarta, ba ka kyauta min ba"

Alamin yace "Allah kar ya nuna min ranar da zan yi mata daya daga cikin abubuwan nan"

Hajiya tace "Ameen".

Kafin Uncle Ahmed ya ma fara Processing tafiyar su India, ciwon Hajiya ya warke baki daya,Allah ya dauki ran Hajiya, Hawwa tayi kuka kamar Uwarta mahaifiya ta rasa, su Sadiya sun zama marayu gaba da baya.

Zaid daga chan Cuba yake kira dan yi musu taaziya.


Hajiya na da Sati biyu da rasuwa Uncle Ahmed ya kira Alamin Gidan Baba Abdullahi.

A parlorn Baba Abdullahi suke zaune su Uku, Suna kan kujera shi kuma yana zube kasa kamar mai neman gafara.

Baba Abdullahi ke magana yace "kaga Alamin Girma da nauyi ya sake hawanka, yanzu kacokam kaine gatan Kannenka da Matarka da Danka da masu zuwa, dole sai kayi tsayin daka zaka iya sauke masu hakkinsu duka, Hawwa tace kana da Diploma ko?"

"Eh ina dashi"

Baba Abdullahi yace "ya kamata ka koma Makaranta"

A ladabce yace "dama ina da niyyar hakan, na mayi Applying D.E a nan BUK admission kawai nake jira"

"Da kyau sai Sanaa, na san dai ka iya dinki, ka na yi har yanzu?"

Alamin ya shafe kai yace "eh to lokacin Hajiya bata lafiya na saida shagon dinki na, amma InshaAllah zan dawo dinkin"

Uncle Ahmed ya sa baki a karo na farko yace "kayi tunanin Bussiness Plan, ka min breakdown sai na baka jari" zaiyi magana Daddy yace "baka daukeni Uba ba?" Da sauri ya girgiza kai yace "kune Iyaye na yanzu"

Uncle Ahmed yace "to Babanka ya baka umurni yace ka nemo bussiness plan, in kuma kana da wani a zuciya kayi magana"

Alamin yace "Daddy, ko a lokacin da nake Dinki Allah ya sa na samu karbuwa, ina da yara wanda suke kasa na, kuma suke koya a guna, to duk tare dai mukeyi, zanso komawa aiki na na da"

"Me kake bukata?"

Alamin yace "Shago da kayan Aiki"

Daddy yace "kayi budget ka kawo" Alamin ya tashi yana godiya sosai kamar zai ari baki.


Cikin Wata daya Alamin ya dawo bakin Aikinshi, da shagonshi da yaranshi 3 wanda ya aminta dasu a da, Keken dinkinshi biyu daga kasar china ma yayi ordernsu, cikin Ikon Allah Allah ya dafa mai, customers dinshi na da suka dawo saboda dama chan yayi suna a dan layinsu,

Alaminco Tailoring Service sunan Shagon, a hankali ya zamana in dai kin waye kin kuma cika to a Alaminco Tailoring Service ake miki dinki, nan da nan sunan ATS ya zagaye Kano.

A hankali ya chanza Shagon da yafi wannan girma ya karo Ma'aikata da kayan Aiki, dama chan bai da ganda, yana aiki ne da karfinshi, ga amana, shiyasa ake son kawo mai Dinki.

Alamin kudin da ya tara dubu dari da kusan da ashirin, abu na farko da ya fara yi shine ya siyo ma Hawwa zoben zinari dashi ya kawo mata harda receipt din.

Ta rungumeshi tana jin dadin yanda rayuwa ke sauya musu yace "alkawari ne, a hankali zan siya miki Sark'a da yankunne yan ubansu"

Ta kanne ido tace "bashi ne kake biya?"

A hankali yace "aa, kyauta ne tsakanin miji da mata, ai tsakaninmu ba bashi"

Dariya sukayi baki daya.

Zaman su gwanin dadi da shaawa, Sadiya da Aisha suna matukar son Aunty Hawwarsu, yanzu basu da uwa da ta wuce ta, shiyasa suke matukar girmamata duk da Sadiya ko bata girmi Hawwa ba to zasuyi tsara, haka rayuwarsu ta cigaba cikin daukakar da Allah ke musu.

Ba a rufe Shekara da rasuwar Hajiya ba Alamin ya ma Sadiya Aure da wani dan Kasuwa, sosai yayi mata hidima a matsayinshi na ubanta, Hawwa ma har yinin biki tayi, Sadiya na zaune a Danbatta, ya rage saura Aisha.


B A Y A N  SHEKARA 3.Yaje k'asar Cuba da niyyar yin course din wata tara na wurin Aiki, be dawo Nigeria ba sai da ya hada da MSC, ya zama cikakken mutum da ya hada komai sai aure da beyi ba, har dangi sun fara mishi maganar aure, da yawa suna so su hadashi da 'ya'yanesu, Zaid be da raayin auren zumunci, don da zaiyi auren zumunci da kanwarshi Hawwa ya aura shekaru 5 da suka wuce, Zaid be rufe shekaru Talatin da uku ba amma hankalinshi da tunaninshi kaf na manya ne, sosai ya kawo cigaba a maaikatar Uncle Ahmed, shiyasa Uncle Ahmed ke alfahari dashi.

Akwai wata Yarinya Maimuna da Zaid yake zuwa gurinta, tun da ya dawo Nigeria, nan kasan Unguwansu take, Maimuna na da kyau, tana kuma da hankali daidai gwagwado, yayyinta 4 mata duk cikin yayyin ba wacce tayi aure, to ganin kanwarsu ta samu mai sonta da aure ya sa suke mata Pampo, irin ta tambayeshi kudi haka, ko ya siyo mata kaza ko kaza, duk abunda tace Zaid ya siya mata yana siyowa saboda yana dashi din, kuma shi bai ma dauki hakan wani abu ba, Zaid ya san yanda ake kula da mace da duk abunda mace take so, ko kiranshi tayi bai dauka ba, bai jin komai yayi ta bata hakuri har sai ta hakura, bai da girman kai ko kadan, shiyasa Maimuna kejin dadinshi.


Wata rana Zaid ya je Gidan Batul da yake sun dawo garin Kano da Zama, daga gidan Batul ya wuce Gidan Hawwa da ke GRA, Babban Gida ne wanda Alhaji Alamin Ya gina na zamani, suna kan dining suna cin Abinci har Alhaji Alamin din Wayar Zaid tayi ringing, sun saba sosai da Alhaji Alamin so be kunyar shi ko kadan, ya dauka kawai ya saka Handsfree.

"Hello, sai yanzu ka ga damar kuna wayar?"

Dan jim yayi kafin yac e "wayar kunne take fa baa kashe ba"

Cike da gadara tace "to na ma k'arya"

Kamar yana tsoronta yace "aa ba haka nake nufi ba"

Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Hawwa da Alamin da kuma Aisha, suna mamaki wacece wannan da ta ciri tutan yi ma Zaid haka kuma yana biye da ita.

"Uhm nace ba, bikin kawar yayana da na gaya maka, karshen wata ne fa"

Abincinshi ya cigaba da ci yace "munyi maganar biki kuwa?"

Suna jin magana a background din kamar ana gaya mata abunda zatace.

Sai chan tace "kana nufin ka manta?"

Cike da kwantar da kai yace "sorry dan tuna min"

Magana suka cigaba da ji kasa kasa, Hawwa dai ta rungume Hannunta kan Kirjinta tana jin ikon Allah kuma a lokaci daya ta cika tayi Pam.

"Eh, Best friend din Yaya Sady ce, kuma kaga dole mu taka rawa ko, zamuyi Anko, kuma Yaya Sady na son bata gudummuwa"

Kallon da Hawwa ke mishi ya sa shi sarkewa da sauri ya kurbi ruwa yace "Okay Muna zan zo Anjima bayan Maghrib InshaAllah"

"To sai kazo, donAllah zan maka texting maganin Mama ka taho dashi, dazun aka rubuta a Asibiti"

"To ba damuwa InshaAllah".1


Wayar ya katse, kafin ya sake kai lomar Abinci da ya dibo Hawwa cikin bacin rai tace "YaYa"

Kallonta ya tsayayi kafin yace "Ya akayi Hawwa?"

Cike da bacin rai tace "Yaya Wacece wannan?"

Lomar ya kai kafin yace "ita zan aura, Maimuna"

Hawwa ta katseshi tace "wallahi ba zaka aureta ba, kam bala'i har akwai wacce zata maida min Yaya Errand Boy?"

Alhaji Alamin yace "su Ummin Abba Dangin Miji"

Charaf Aisha tace "Allah Uncle Zaid wannan bata da hankali, ji fa abunda take cewa, Yaya bakaji ba?"

Yayanta ya harareta yace "Wa ya saka bakinki?"

Hawaa tace "Allah Daddyn Abba gaskia ta fada, bata da Hankali, kalli fa yanda take magana, kuma take rok'o kai tsaye, da alama kuma abinda take cewa gaya mata su ake, bakaji muryoyi a background ba?"

Cikin sanyin Jiki Zaid yace "Sisters dinta ne"

Hawwa tace "yanda ka sakata a Handsfree, haka ta sakaka, amma bambancin ita gaya mata abunda zata ce akeyi, Yaya wannan yarinyar ba ta kwarai bace"

Da sauri yace "Allah Hawwa bata da matsala, Sisters dinta ne"

"Oh ka sani kenan?"

"Ai ba su zan aura ba ita zan aura"

"Su Yayyin duk sunyi aure?"

A dan tsorace yace "ba wacce tayi aure cikinsu"

Hawwa tace "su nawa ne?"

Yace "Su 4 ne sai Maimuna ta 5"

Da sauri Aisha tace "Akwai Hafsy a gidan?"

Da sauri Zaid yace "eh daga Hafsy sai Maimuna"

Hawwa tace "kin sansu ne Aisha?"

Aisha tace "Aunty Hawwa, ina ranar da mukaje Saloon a Unguwarsu Umma? Ni ana min kitso kikace bari kije ki dawo?"

Da sauri Hawwa tace "eh" ta na neman karin bayani.

Da kika dawo daukata ba na nuna miki wasu na ce miki sisters bane su 5?"

Tace "ehen?"

"To Aunty sune fa na nake baki labari kika gwasuleni kikace ina ruwana, baki son gulma"

Tsaf ta tuna ranar da abinda Aisha take gaya mata Ido ta zaro tace "donAllah?"

Aisha tace "wallah"

Hawwa tayi murmushin takaici tace "gaya mai me ya faru a ranar"

Alamin da Zaid suka zuba ma Aisha ido ta shiga kwararo zance;

"Wai ita kanwar sukeyi ma fada, duk suka hade mata kai, wai sunce ta tambayi Sabon saurayinta da ya dawo daga Karatu Kudi, tace ita kunya takeji kuma bai dade da bata kudi ba, babbar yayar harda dungurinta tace waya ce miki ana tausayin Namiji? To shi wannan bai san yawan kudinshi ba, kuma in ba ki nuna kina so ba, ba lallai ya baki ba, kinsan masu kudi, sai mai Saloon tace haba ku kyale min Kanwana mana, Ita Hafsy tace Allah Aunty Bola bakisan Maimuna ba, daga sama Allah ya jefo mata tsuntsu gasasshe, ta cinye ne take jan aji, daga kasar Cuba ya dawo, last month, first zuwanshi gidanmu ya bata 30k, an fi kwana 10, amma yanzu ana koya mata ways of samun kudi tana yanga"

Mai Saloon tace "ahhh 30k daga zuwa? Ke Muna sakarya ce ke? To wallahi ki saki jiki ki ci kudi, kuyi aure ki zama gatan gidanku, kuma kar ki manta dai da Aunty Mai Saloon"

Dariya suka fashe Surry tace "ta tsaya ma Arziki yanga, ni wallahi in sanya zatayi ni sai na karkato da hankalinshi guna, ai ni da ita duk dayane"

Hafsat tace "kai Aunty Surry tsofaitsofai dake kice ke? Sai dai ni wallahi"

Maimuna tace "nidai ku bar min shi donAllah, kudi ne ko? Wallahi zai bani"

Aunty Mai Saloon tace "wai ba ku bar yi ma juna Snatching ba?"

Babbar yayarsu Sadiya tace "kyale yan burauban, inga wacce zata ma Muna Snatching, wallahi sai Auta ta aureshi, ku da baku da na aure kuma ku cigaba da holewarku, ita ko ta samu na aure"

Surry tace "Aunty Sady ya kike ware kanki? Kice duk mu ne ko?"

Hafsy tayi dariya, Sady tayi dariya ta kalli Maimunar tace "oya latso shi ki samo mana wani abu" Maimunar ta dauko waya ta kira Saurayin tace "donAllah tana bukatan kudi uzuri gareta" ba jimawa kuwa sai ga credit alert din 50k, nan suka hau shewa suna zugata mai Saloon ma na yabon saurayin fa, nidai ina zaune har aka gama min kitso, shine Aunty Hawwa kika shigo, shine fa na fara baki labari kika gwasuleni, ashe Uncle Zaid ne ma saurayin".


STORY CONTINUES BELOW

Kamar ruwa ya shanye Zaid haka ya dauke dif.

Ya san Maimuna na tambayarshi kudi, bai taba gajiyawa ba, amma ashe haka suka daukeshi? Sakarai Gara? Wato a wanke gara ko? Ranshi ya baci matuka sosai, ya dan kalli Hawwa ya kawar da kai.

Hawwa tayi dan dariya tace "Ni na san ba wai kana mata mugun son da idan baka aureta ba zaka shiga matsala, Yaya magana ta Allah baku dace ba, wallahi ka aureta kamar ka auresu ne, don sai abunda suka ce zatayi, kai da gidanka da matarka amma sai yanda Sisters dinta suka tsara maka".

Ya debo abinci yace "an wuce gurin kuma InshaAllah" kafin ya kai loma baki gabaki daya yaji Maimuna ta sire mishi.

Ta san iyakar gaskiyarshi kenan.

Alamin yace "Dangin Miji Ho"

Hawwa tace "naji din, ba wacce ta isa ta daga ma Yayana hankali, maganin kar a fara kar ayi".

Alhaji Alamin yace "Ga Mata a gari samun ta gari yanzu ba zai ma wuya ba, Nagartacce"

Murmushi Zaid yayi, Hawwa tace "sai dai ko in bece yana so ba, ba wacce zata ki Yayana son kowa kin wanda ya rasa"

Dariya kawai yayi ya cigaba da cin Abinci, tun daga ranar Zaid ya rabu da Maimuna, tayi kiran tayi message din ba amsa.


N A S S A R A W A


Shekara daya kenan da rasuwar Inna, Inna ta rasu a Azumin bara, fadan tashin hankalin da Ahalinta suka shiga bata baki ne.

Ya Bu yayi Aure tun kafin rasuwar Inna, yana da diya Me suna Hauwa wanda yace Inna ya ma Takwara, sosai ya kintsu, kamar ba Ya Bu din da ba, zaune yake da Iyalinshi lafiya, Zaid kanzo gidan Babanshi lokaci zuwa lokaci, kamar yanda yake zuwa gun Mamanshi, amma Zaid dan Gidan Hajiyar Ya Bu ne.

Aisha kanwar Ya Bu na aurenta a Abuja, Yaranta Biyu.

Yaya Hashim kuwa aurenshi saura kwanakin da ba su wuce 20 ba.


NATIONAL HOSPITAL NASSARAWA

Nurses on Training suke fira, takun tafiyarta ya sasu kallon inda take fitowa, gab da su ta musu Sallama duk suka amsata da "Sister Hauwatty ina wuni?" Ta amsa su tayi gaba cike da nutsuwa, kamar jira suke ta rufa baya suka fara firanta daya tace "Ni dai wallahi Sister Hauwatty na burgeni ba ta da matsala"

Daya tace "ni banson yanda take jin kai tana da tak'ama"

Daya tace "kai Rabi Kiji Tsoron Allah, kin dai fadi san ranki ne, amma ke kin san da tana jin kanta da tak'ama da bata zo tayi aiki a Asibitin nan ba, kinsan tarin kudinta da k'addararta da Marigayi Mijinta ya bar mata kuwa? Ke har Asibitin Ido gareta kuma har Indiyawa take gayyata Asibitin suna mata Surgery, da ta da dan girman kai wallahi da ba mu ma santa a Asibitin nan ba"

Duk suka amince da hakan Rabi dai ta tabe baki tace "nidai Allah tana da Girman Kai"

Salma tace "kedai Rabi kina dai daga cikin Mata masu jin zafin cigaban Mata, wannan Hassada ce"

Ganin abun zai zama fada daya tace "a dai bar maganar".

*


Duk da ba wani k'iba tayi ba, amma ta ciko sosai, ba fara bace amma fatar ta gwanin kyau, sune fa irin masu fatar da ake cewa Melanin Pops, to kudi da kwanciyar hankali sun zauna mata, cike da Aji take tafiya har ta kai Parking Lot inda ta ajiye a Motarta, ta shiga ta yi reverse ta bar Asibitin cikin Kwanciyar Hankali.

A hanya Alhaji Ibrahim ya kirata, ta dauka da Sallama.

"Sister Hauwatty Barka da tashi daga Aiki"

"Har idonka ya gane maka na tashi?"

"Eh to ai nasan cewa senior Nurses ba su wuce 3-4 a Asibiti, Nurses ne da basu kaiku ba masu Shift har dare"

"Haka dai kace"

"Hakan ma Yake, ya maganarmu?"

"Kayi hakuri ba zan iya ba"

"Ba zaki iya ba? Ko ba zakiyi ba?"

Tace "uhm um Alhaji, kagane, bana so a kaina kayi rashin Adalci, kace duka Matayenka guda biyu babu wacce ta wuce secondary,babu mai aiki, to ni kuma fa? In na zo ba zan yi aiki ba? Ya zanyi da aiki na?"

"Na gaya miki wannan ba matsala bane"

Tace "gaskia ka daiyi hakuri"

Yace "ki dai je ki huta, zan kira ki anjima"

To kadai tace ta kashe wayarta tare da girgiza kai.

Ta maida hankalinta kan Driving dinta.

****


Mamarta ta bita da Ido, duk inda tayi idon Mahaifiyarta a kanta.

Ta lura da hakan shiyasa ta zo ta zauna tana kallonta Mamar tace "Yadai Watty?"

Watty ta murmusa tace "Maaa Ke dai zan tambaya? Naga kina ta kallona, wani abu kike so muyi magana a kai?"

Mamarta ta rausayar da kai tace "ina Matukar Alfahari dake Hauwatty, abubuwan da kike ma Addini da Kudin gadonki, alheran da kike ma daginki da na tsohon mijinki ki Allah kadai zai miki sakayya, kin samu duniya Watty saura miki Lahira kuma tun a nan duniya zaki fara gyara Lahirarki ina miki Addua ko da yaushe"

Watty ta riko hannun Mahaifiyarta tace "Mama, baki gama magana ba, nasan akwai wani abu a bakinki"

A takaice tace "Aure!"

Watty ta murmusa irin dama na san abunda zaki ce kenan.

"Duk cikar Mace, bata kai ba in har bata da Aure, duk kudin Mace duk arzikinta tana da ragi in har ba ta da Miji, Watty tun Inna na da rai kowa ke sa ran zakiyi Aure, ganin ba auren farko bane ya sa aka hana kowa yi miki magana, ya sa aka sa miki ido a ga har yaushe zaki tsaya haka nan? Amma na lura ke babu aure gabanki, Kinsan ba zai yiwu ba. In ban gaya miki gaskia ba wa zai gaya miki? DonAllah ki nutsu cikin manemanki ki fitar da wanda hankalinki yafi kwanciya dashi, Kinji Hauwattynmu?"

Watty tace "Maa ki dinga min Addua, InshaAllah zan fitar, wallahi cikin maneman nawa ne har yanzu ban natsa da kowa ba"

Mama tace "saboda ba sa gabanki, ba kya kulasu, aikinki kawai kika saka a gaba"

"Maa ba haka bane"

"To nidai donAllah ki basu lokaci, har ki fitar da miji"

"InshaAllah Maama, InshaAllah zan gabatar muku da miji nan ba da dadewa ba"

Mama taji dadi ta sanya mata albarka.

Watty ta amsa ta mike, InshaAllah cikin manemanta zata zabi wanda hankalinta yafi kwanciya dashi su daidaita sannan ta gabatar musu dashi, abu daya ta sani shine ba zata auri wanda zata kuntata ma kanta ba don ana so tayi aure ba.

Wannan kenan.


STORY CONTINUES BELOW

K A N O


Tun randa Ango Hashim ya kira Zaid yaji yana tambayarshi yaushe zai taho gabanshi ke faduwa, binibini sai yaji faduwar gaba, an dade da yaje Nassarawa amma zuciyarshi na da rauni wurin mance muradinshi a Nassarawa, da ta fado mai ya ke istighfari don be son tunanin matar da take mammalakiyar wani, zai yi iya kokarinshi na ganin ya yak'i da zuciyarshi ko da sun hade don yasan dole su hadu.

Ana Gobe Daurin Auren Hashim, Zaid da wasu Abokansa biyu sukayi Mahada suka tafi garin Nassarawa,yau zaayi Dinner gobe daurin Aure, sai yamma Lis suka iso.


N A S S A R A W A


Abokai sun hadu ana ta shegantaka, ana irga gaurayen da basuyi aure ba, Hashim yace nidai kar a sakani ciki tunda dai gobe uwar haka sunana Mijin Amina, dariya sukayi. Wani yace "Zaid Abdullahi ne direban gwaraye, sai Salis Ashafa, sai Hamza Bala"

Salis yace "Ku tsaya nan, aurena sati daya zuwa Azumi kaga ko na kusa fita nima"

Shewa suka sa kamar Mata suka ce "Sheeeege, to matsala dai ake samu ana amarci da Azumi"

"Kai Lafiya lau ne, a daiji Alhaji Zaid yaushe zai kiramu?"

Zaid sai dariya yake tayi ya k'i magana

Wani yace "danubanka kazo ka nema cikin k'annanmu"

"Ai tun da kuka ga har Yaje Cuba ya dawo beyi aure ba, to tabbas yana jiran wata ne"

"Ka dai tsaya wasa, mu ta biyu zamu samu yau wurin Dinner"

Shi dai Zaid banda dariya ba abunda yake musu.

Haka suka dinga fira suna cin abinci, lokacin Sallah kadai ke fitar dasu, bayan Maghrib kuwa suka sauya kaya zuwa na Dinner, suna yin Ishai suka yi Convoy zuwa Gidansu Amarya don kwasan yan Dinner don zuwa gurin Event.


Bridal Train za'ayi, haka suka jera kansu a tsare suka shiga farfajiyan Hall din.

Hashim da Amaryarshi sunyi kyau duka har sun gaji, mazauninsu suka zauna, Zaid da Abokanshi suka sa mu wani table of 10 suka zauna, kawayen Amarya ma haka da yake sune gabagaba babu ma wanda ya zauna musu a guri.

Chan an fara gudanar da shagalin Biki, aka bukaci Amarya da Ango a Filin rawa su kadai.

Sun fito suka fara taka rawar i love you baby na Ali Jita.


Aisha tace "ta so muje muyi rawa"

Watty tace "to mazari uwar rawa, ni lik'i kawai zanyi"

"Naji din muje"

Hannun juna suka rike, su ka shiga ratsa mutane har suka isa gaban Amarya da Ango, 20 20 Watty ta shiga lika musu cike da Aji ta na murmushi, Hashim ya dinga zabga mata murmushi Amarya kuma tana dan rawa tana nok'e kai.


"Fa ta barakallahu ahsanal khaliqin"


"Wallahi na samu mata" cewar wani daga cikin Abokan Ango ya na nuna masu Watty.

"MashaAllah ta hadu, ko kaje ko ni inje"

"Donubanka da matarka, dazun kuka gama min gorin Aure, to na samu nidai"

Bari wallahi naje na mata lik'i yau kudina duk jikinta zai k'are"

"Muje wallahi mai rabo ka samu"

Dago kan da zaiyi ya ga wai wacece ta tafi da imanin Abokanshi ya sashi hooking.

Dakatawa Zuciyarsa tayi na wasu lokkuta kafin ta dawo Aiki.

Yarinyar Kirki. Meyasa suke maganar Matar aure har ana kasafata kamar wata haja? Har duk suna neman gardama a kanta? Lokaci guda ya ji ranshi ya baci.


Wani daga Cikin Abokan yace "Yan iska to Bajawara ce"

Masu niyyan zuwa mata lik'i suka koma suka zauna.

Dayan yace "ba fa wanchan ba, dayar mara tsawon"

"Itafa Watty, dukansu cousins din Hashim ne, Aisha itace kanwar Mijinta na farko"

Cikin sanyi jiki yace "Kana so ka ce mana auren waccan yar yarinyar biyu?"

"Ras kuwa"

Gaban Zaid ya dinga duka da sauri, ta sake fitowa kenan? Meyasa bata zaman gidan Miji, meyasa take auran wanda basu san darajarta ba, haka kurum yaji ranshi na baci.


Ganin an fara chunkoso a wurin rawa ne ya sa Watty zame jikinta don komawa Mazauninta, ta gabansu ta zo ta wuce duk suka bita da ido, tana rufa baya suka dasa chapternta.

"Waiyo ga yarinya har yarinya, Ashafa kaje mana?"

"Waaaa? Ina saurayi danye dani? Sai dai ku masu Mata"

Mikewa Zaid yayi zai nufi gurinta saboda yanda zuciyarsa yake zafi.

Rikoshi yaji anyi "Zaid gunta zaka? Bakaji ance Bazawara bace?"

Cike da takaici yace "donAllah sakeni"

Ba musu ya sakeshi ya nufi gunta.

Ta na zaune ita kadai don yan table dinsu duk sun yaye suna dancing Floor.

Kusa da ita ya zauna, ita ko sai ji tayi an zauna kusa da ita.

Dagowa tayi don ganin waye.

Bata manceshi ba, Abokin Yaya Hashim ne mai sunan Yaronta.

Zata gaisheshi kenan taji ya watso mata wata irin tambaya da ya sosa ranta.


STORY CONTINUES BELOW

"Meyasa Baki zaman Aure? Shin Mazan ne basu da Hali? Ko kuma kece mai matsalan? A shekarunki yanzu wai har kinyi Aure Biyu? Haka zaki sake wani Auren, jim kadan ki fito? Wace irin rayuwa ce wannan?"


Ba ta san dalilin da yasa taji maganganunshi sun mata zafi sosai ba, wasawasa taji hawaye na neman zubo mata, daidaita kanta tayi tace;


Cover by LubnaSufyan

"Kar ka dora ayar tambaya akan shafin da k'addara ta bude min, baka san me yake rubuce a naka me zuwa ba"

Mikewa tayi tsam ta bar wurin a fusace, da sauri ya bi bayanta shi bai san me yayi zafi haka ba, har ta fita daga hall din, wurin da ta aje motarta niyarta ta bar gurin baki daya, hannunta ya rik'o tayi saurin fizgewa ta juyo cike da tsiwa "menene? Meye?" bai iya fada ba sai yace "ki gafarceni, ba niyyata na bata miki ba, Allah ya baki hakuri yarinyar kirki"

Da sauri ta kalleshi tana tuna wani abu game da abokin Yayan nata.

Bakinta na rawa tace "Yaron Kirki? Kai ne dama?" Wani murmushin takaici tayi tace "saboda ka san yanda Aurena na farko ya kasance shine kake ganin ni wawiya ce da banyi dacen Miji ba? Kasan ya Aurena na biyu ya kasance ne? Dr mijina bai taba min kallon banza ba, da aka ce maka banda aure ka tambaya dalilin rashin Aurena?to Dr rasuwa yayi, na mishi takaba, ba raba aurenmu akayi ba, ba kuma sakina yayi ba"

Girgiza mata kai ya hau yi yace "ba haka nake nufi ba, kiyi hakuri, wallahi bansan rasuwa yayi ba, kuma ina tausayinki a shekarunki ace aurenki 2, shine raina yake tafasa na kejin bakincikin mazajen da basu san darajarki ba har suke kuntata miki, Allah ya ji kan Mijinki, amma ki fahimceni ba wai ina nufin rashin dacen auren da bakiyi ba laifinki bane, bana son tunanin kina wahala balle ma na ganki cikin wahalar, zuciyata kasa dauka takeyi" tsagaitawa yayi da magana, ya lura da Mazan wurin da ke neman kawo mata hari, bai san ko ta ba wa wani zuciyarta ba, amma ba zaiyi kasa a guiwa ba, ba zai bari ta subuce mai wannan karon ba, ba zaiyi sanya ba.

Ya cigaba "Saboda... Saboda Ina Sonki, Ina sonki Yarinyar Kirki".

Baki bude take kallonshi,

Kafin tayi wani magana yace "so daya baki fita a raina ba, kina mak'ale cikinta, har kuka sai da nayi ranar da kikace min kinyi aure, nayi dakon Soyayyarki, nayi kokarin na yakiceki a zuciyana don kin zama mamalakiyar wani, na san haramun ne tunaninki, amma na kasa, sai dai da kin fado min nake istighfari, wallahi Allah ina Sonki Yarinyar Kirki".


Wani miki ya famo mata a zuciyarta, kafin tayi wani magana ya katseta da cewa "kinga na kasa kwantar da hankalina na nemi wata yarinya, bansan meyasa babu macen da take burgeni, ashe Allah has reserved the best for me, Hawwa, donAllah dont turn me down, i've been in love with you through your first marriage, throughout your second marriage and now Allah ka yafe min amma Allah ya san yanda nayi kokarin daina tunaki"

Ya gama kashe mata jiki, za tayi karya in tace ta mantashi, ya kan fado mata ko da ta ke da auren Dr, sai dai tayi Istigfari ta kawar da tunaninsa don Shaidan ne yake so ya mata sake sake, tayi kewarshi sosai, sosai take jin nutsuwa a tare dashi, maganganunshi sunyi tasiri a zuciyarta, sai dai reality daya, ita da shi ba su dace ba, a hankali ta furta "Saurayi ne kai, ni ko na taba aure, aurena biyu,ina da yaro, kar ka bata future dinka, kar ka bata lokacinka kuma ni da kai bamu dace ba"

Katseta yayi yace "Inji Wa? Injiwa yace bamu dace ba? Ni ko da ke na dace, ki bani dama na nuna miki dacewar da mukayi"

Watty ta yi shiru yana neman birkita mata lissafi tace "Zan koma ciki, bye" ta shige cikin hall din ya bi bayanta jiki a mace.

Kusan tare suka shigo Hall din, kan idon Abokansa, "ta ma wulakanci ko? Zawarawan nan sun fi yanmata jan Aji"

Wani murmushi Zaid yayi yace "sai na kawo muku Invitation.

"Kai Ka zo ka nemi Danya Shakaf"

Itace "danya Shakaf dina"

"Aurenta Biyu"

Yace "ko dari ne"

Daidai nan aka kira Abokan Ango, Zaid ya fara mikewa ya je yana musu liko yana wani farinciki kamar yaga ya auri Wattyn.

*****

Washegari aka daure auren Hashim da Amaryarsa, Zaid yayi ta wulga ido inda zai ga Watty amma be ganta ba.

Akwai Haddar Numberta akanshi tun shekarun da suka wuce, ya saka a wayarshi ya kirata, kamar ba zata dauka ba sai chan ta dauka da sallama.

"Yarinyar Kirki ina son ganinki"

Numfashi ta sauke tace "atleast ka amsa sallamar ko?"

Da sauri yace "Waalaikum salam, ina zan ganki?"

"Yanzu dai i am not available, ina Gidan Ango"

"Gidan Ango? Gani nan zuwa"

Kafin tayi magana ya katse wayar.

Wayar ta bi da ido.

Aisha tace "Jawarin ne ko?"

Watty ta rausayar da kanta tace "wallahi Saurayi ne"

Aisharsu Ya Bu ta tsaya kallonta tana nazari tace "Kina Son Shi Watty"

Watty tace "it doesnt Matter, Saurayi ne, nikuma aurena biyu"

Aisha tace "Son da kike mishi fa?"

"Wannan ba matsala bane, cikin wanda suke zuwa guna zan zabi daya na so shi"

"You Deserve to be Happy Watty"

Murmushi tayi tace "I am Happy Sholi"

Aunty Binta ta lekosu tace "kus kus din me akaeyi?"

Aisha tace "Aunty Binta wani take so wai don saurayi ne ba zata aureshi ba, a ganinta kamar ta kwareshi"

"Ni nace miki haka?"

Aunty Binta tace "in shi be ki aurenki ba don me ke zaki ki aurenshi?"

Kafin ta cewani abu wayarta tayi ringing.

Shine!

Ba zata dauka ba, Aisha tayi wuf ta dauka ta sanya speaker.

"Hello Yarinyar Kirki Ina waje gidan Hashim"

"Mu fa tarban Amarya muka zo, ai nagaya maka i am busy"

"Please, ba zan ci miki Lokaci ba, kin ga Gobe zan koma Kano"

Aisha tayi wuf tace "gani nan fitowa"

Watty ta harari Aisha.

Aunty Binta tace "kije Watty, wa ya san Gobe?"

Cikin sanyin Jiki ta fita.

Daga chan gefe yayi Parking Benz dinshi,

Fitowa yayi ya karaso gunta.

Kwarjini ya mata ta kauda kanta.

"DonAllah muyi magana"

"Ina jinka"

"Mu shiga Mota"

Ba musu tayi gaba ya bi bayanta da sauri har ya cimmata ya bude mata kofa ta shiga, shima ya zagaya ya shiga, kunna motar yayi ya bar gurin, ba ta ce mishi komai ba.

Har suka zo wani wuri yayi Parking.


STORY CONTINUES BELOW

"Kiyi hakuri da abunda ya faru Jiya, baki fahimceni bane"

A hankali tace "ya wuce"

Shiru sukayi kafin chan yace "Ina so ki bani dama in shiga cikin manemanki"

Karkatowa tayi suka hada ido wani gabaki dayansu sai da sukaji wani yanayi.

Daurewa tayi tace "kagane, ba na so na bata maka lokaci ne"

Da sauri yace "kin fitar da miji ne?"

Kai ta gyada tace "aa, ko na baka dama lokacinka nake batawa, ba kai zaka ma kanka aure ba, kana da dangi, ba kuma zaka boye musu cewa na taba aure har ina da yaro dan shekara 6 ba, dole su san cewa aurena 2"

"Zaid yace wannan ba matsala bane, ni ban damu ba ko aurenki nawa, ni nagani, ni nace ina so, ni zan zauna dake"

Murya ta karya tace "ba kai ba, danginka"

Yace "ba su da matsala"

"Uhm uhm, ba kasani ba, in ka koma ka tuntubesu, zaka ga me nake son fahimtar dakai"

Wayarsa ya zaro yana neman number.

Kallo ta bishi dashi

Yace "Tsaya kiji daga garesu"

Da sauri tace "wa zaka kira?"

A takaice yace "My Beloved Sis"

A Handsfree ya saka ta dauka "Hello Yaya"

Yace "Hawwa na samu mata"

Da dan murna tace "Allah Yaya? A Nasarawar?"

Yace "eh, amma ta taba Aure harda Yaro daya, shes about Your Age"

Jim Hawwa tayi kafin tace "kana sonta ta na sonka?"

Yace "Ina Sonta kam, da alamu kuma itama tana so"

Ya bi Watty da Ido tana sauraren me Hawwa ke fada.

Tace "Then Yaya Its Fine, in har tana sonka kaima, its fine, Happiness inka is all that matters to us"

Cikin jin dadi yace "Nagode Hawwa".

Kit ya kashe waya, yana mai kallon Wattyn da ta shiga wani yanayi, tsigar jikinta na tashi.


Yace "kinji ko? Na gaya miki dangina ba haka suke ba"

Tace "Ba tayi judging dina ba, batayi criticizing ba"

Yace "ai in kowa yayi Judging dinki Hawwa ba zata taba Judging ba, musamman ita da ta yarda da Soyayya, babbar Yar Soyayya ce, tana yin So don Allah ne, she understands"

Watty tace "Your Mom?"

Yace "ai Hawwa taji, kafin naje Kano i am sure kowa zaiji, kar ki damu Allah, na san lokacina ne baki so ki bata, to ni nace ki bata min lokaci nine da godiya"

Murmushi tayi tace "i will only accept in ka samu approval daga Mama"

Murmushin yayi yace "Yarinyar Kirki, ina kaunarki"

Lumshe ido tayi, idan har ta sake minti 4 anan to tabbas zata fallasa duk wani sirrin da ke ranta, ka maidani Gidan Ango"

Bai amsata ba ya tada Mota.

Ko da daddare sai da ya dawo Family House wai ya zo mata Sallama gobe zai tafi, cikin lokaci kankani Soyayyar junasu ya dasu a cikin Zuciyoyinsu.

Washegari ya dauki hanyar Kano tare da Abokansa 2.


K A N O


Sai da Hawwa ta bari duk sun hadu a gidan Baba Abdullahi ta dauko maganar Zaid ya samu Mata, yana jin haka ya fara latsar waya.

"A ina?"

Cewar Batul

"Chan Nassarawa ya ganta"

Uncle Ahmed ya kalli Zaid yace "wai haka?"

Zaid ya kasa magana Hawwa tace "Allah Daddy dagaske ne"

Umma tace "kaima dai Uncle Ahmed har kaji maganar Zaid daga bakin Hussainarshi har ka tambaya in dagaske ne? Ka dai so ka ja zance, Muma duk yanzu mukeji"

Abba yace "to MashaAllah, ai dama zaman naka haka ba zaiyiwu ba, ai sai a zo a yi me yiwuwa Ahmad"

Uncle Ahmed yace "InshaAllah, sai muje mu nema mai aurenta a Nassarawar"

Zaid ya kalli Hawwa, ya mata alama da ido irin tayi dayar maganar Hawwa ta daga mai gira.


"Da yake kunsan Sunan danta Zaid fa"

A sama Maganar ta dokesu, Zaid ya dafe kai, ba haka yaso ta ce musu ba, Batul ce tace "har Da gareta?"

Hawwa tace "dan shekara 6"

Batul ta dan chanza fuska tace "Ta taba aure kenan?" Hawwa tace "Aurenta Biyu"

Abba yace "kai Mallam Zaidu Bazawara kake so kenan?"

Uncle Ahmed yace "amma na tabbata dama tun kafin tayi auren fari kake sonta ko?"

Zaid yayi shiru yana tsoron kar su hanashi ita, cewar Umma kadai yake sonji amma Umma taki magana, yana jin Batul samasama na wasu surutai sai chan yaji Hawwa na cewa "tsararmu ce fa, Aurenta na biyu Mijin rasuwa yayi, na farkon kuwa raba auren akayi mijin ke dukanta shiyasa aka raba"

Abba yace "to dama ina amfanin zama? Ai gwara da aka raba don wata rana sai ya kasheta"

Hawwa tace "kai dai bari Abba, ai ya fara nakasata tunda har ya jirkitar mata da Ido" yanda Hawwa ke bayanin Watty zaka rantse da Allah ta santa haka ta dinga basu labari suna tausaya mata.

Uncle Ahmed yace "ka tamabayesu yaushe zamuje?"

Zaid yaji wani sanyi a ranshi, Hawwa ce tace "ko me ke nan Daddy zan sanar da kai" yace "wai hala kin santa, yanda kike zaro labaranta sankasanka"

Abba yace "kai dai Uncle dinsu kana son jan Zance, aka ce maka tsakanin Zaid da Hawwa Sai Allah, Hassan da Hussaina fa kakeji, ai dole ta san komai game da matar da Hassan dinta zai aura, Allah dai ya kaimu"

Uncle Ahmed yayi dariya yace "Umman Yara baki ce komai ba"

Umma tace "Ubangiji Allah ya sanya Albarka ya tabbatar da Alheri"

Suka amsa da Ameen

Abba da Uncle Ahmed suka shige ciki.

Zaid ya rarrafo gaban Mahaifiyarshi yace "Umma kin yarda na aureta?" Umma tace

"tunda kana sonta Zaid meyasa ba zan yarda ba?"

Batul tace "Aurenta biyu"

Umma tace "ke da kikayi daya har zuwa yanzu dabarar kice?"

Da sauri Batul tace "Ahh Hajia Umma nidai ha haka nake nufi ba wallahi, Allah baki hakuri"

Umma tace "ko aurenta nawa, indai ka yaba da tarbiyarta da hankalinta da nasabarta, babu wata matsala InshaAllah"

Sosai Zaid yaji wani iri dadi a ranshi, waye yace ba shi ne yafi kowa dacen Uwa da Dangi ba? Alhamdulilah da Su.

Tashi yayi ya shige ciki, Hawwa na mai ikirarin Angon Watty.

Batul tace "wannan Zak'ewar da kikeyi Allah ya sa dai ta san da zamanki"

Hawwa tace kema kinsan wannan doka ne, ai da bata sanni ba, kuma da baku santa ba, sai da nayi clearing dinta kafin na kawo maganarta"

Batul ta harereta tace "to anji, mai danuwa".

Umma tace "to uwayen rashin jituwa, ku zo ku ci tuwo kafin mazajenku su zo daukanku"


STORY CONTINUES BELOW

Yana shiga daki ya fada kan katifa tare da janyo Pillow ys rungume a kirjinshi, wayarta ya kira tana dauka yace "Yaushe zan turo Magabata na?".


N A S S A R A W A


Gabanta ke ta faduwa tunda Zaid ya ce mata Hawwa zata gaya ma Iyayensu game da ita, son Zaid ya ratsata daga tafiarshi kano zuwa yau, kwana 5 kenan, ba ma ta so tayi tunanin rabuwa dashi, sosai ta kwallafa ranta a kanshi har take mamakin yaushe ya kanannaye zuciyarta haka, har nafila tayi tana rokon Allah Allah yasa kar danginshi su gujeta, gabanta ne yayi mummunan faduwa da ta ga kiran wayarshi hannu na rawa ta dauka.

Abunda taji ya sa ta lula sama ta diro kasa.

"Yaushe zan turo Magabata na?".

Ita dai yanzu ba yarinya bace, babu wani kunya, ba zata tsaya wani sanya ko wani jan aji ba, aurenta biyu, tunda ya tambayeta yaushe zai turo ta san cewa dole danginshi sun yarje mai, ba ma ta so taji dawa dawa ya bada goyon baya a takaice tace "Ranar Jumaa"

Yace "nan da kwana bakwai?"

Tace "eh ko yayi kusa?"

Da sauri yace "aa Reina"

Duk da bata san maanar abunda ya fada ba, ta ji wani irin shauki da ta ji fadarshi,

Lumshe ido tayi tace "Menene Reina?"

Cikin wata murya yace mata "yana nufin Queen in Spanish"

"Waya koya maka Spanish?"

"A Cuba"

"To idan zan kiraka da King in Spanishi fa?"

Wani juyi Zaid yayi kan gadonshi, cikin wata wahallaliyar murya yace "sai kice Rey"

Cike da jan hankali tace "Rey"

Zaid yace "Te amo Mi Reina"

Ko ba komai ta san wakar Rihanna Te amo, tayi ammana yanzun cewa yayi "Ina Sonki Sarauniyata"

Sosai take jin kanta a gajimare itama tace "Te amo Mi Rey"

Sosai Zaid yayi dariya, yana jin kanshi a Sama, Soyayya suke wa junansu mai cike da tsafta mai tsantsar kauna, dukkansu wannan ne karo na farko da suke jin haka game da kansu, Watty ta gane yanzun ne take So, tabbas wannan Shine Son So.


Tana gama Waya dashi ta daka wani tsallen murna ta kira Aunty Binta.

Tace mata Zaid zai turo magabatanshi nextweek Friday sosai taji dadi tace gobe zata zo Gidan ta fada ma su Baba don a fara shiri, Watty tace "aunty da dai kawai kin kirashi yanzu kin gaya mai, gobe kina zuwa shirin kawai zaa fara"

Aunty Binta "Shegia yaushe kika fede haka"

Watty tayi dariya tace "wallahi ba yin kaina bane"

Tace naga alama

A daren Aunty Binta ta Kira Babansu ta sanar mai dashi ta kira Mamarsu ma haka, sosai sukaji dadi dama kamar jira ake ta samu Miji.

Nan da nan magana ta zagaye Dangi.


Jumma kuwa mai zuwa Uncle Ahmed da wasu dangin Abba da na Umma su ka Nufi Nassarawa don nemana Aure, Zaid ya so yayi Jagoranci amma Uncle Ahmed ya hana, suna zuwa Hashim Ango ya musu iso Family house, suka samu tarba mai kyau, basu bar Gidan ba sai da Uncle Ahmed ya bada Sadaki naira dubu arbain, a ka kuma saka ranar Biki nan da wata 3 saboda Aikin Wattyn, Baban Ya Bu yace "Alhaji Ahmed sai ku fara neman mata Transfer ko Aminu Kano ne"

"Eh InshaAllah hakan ba zai gagara ba, don ba zaiyiwu ace ta dinga zuwa Nassarawa ta bar min Da a kano ba, ai sai inda karfina ya kare wurin ganin ta damu transfer"

Suka yi dariya sukace "wannan uba baya kawaici?"

Danuwan Umma yace "ai Ale Ahmed son yaronshi yake kamar me, ba ya da kawaici ko kadan kan Zaid"

Nan akayi ta raha suka rabu sun girmama juna.


Tun daren Jumaar Zaid ya matsa ma Watty sai ta kira Uncle Ahmed taji ya aka kare, nan yake gaya mata sun bada sadaki biki kuma nan da wata uku, sai ku hau hada lefe.

Dadi Hawwa taji sosai ta kira Zaid ta mishi Albishir, sosai yaji dadi, itama Wattyn Babanta da kanshi ya kawo mata Sadakinta, yana juyawa tayi sujudushukur.

Wannan Kenan.

BAYAN WATA BIYU


TALENT INTERNATIONAL SCHOOL


Ruler ta dauko ta kwala mai a bayan hannu so hudu, karaf kan Idon Proprietress da take zagaye makarantar tata tare da Makarabanta, da sauri da zagayo ta shigo Aji, Yaran suka mike suna gaidata, Abbah Kam tuni ya na ta kuka, Mai makarantar ta rungumeshi tana lallashi har yayi shiru.

Ta kalli Malamar Ajin tace "Teacher Hawwa, to my Office, Now" ta ja hannun Abba, Hawwa ta bi bayansu sum sum.


STORY CONTINUES BELOW

Ga Headmistress tsaye, ga Proprietress ga Teacher Hawwa ga kuma yaro na ta shesheka,

"I understand You are His Mother(na fahimci cewa kece Mahaifiyarsa?)"

Cike da ladabi Hawwa tace "Yes Ma"

"Teacher Hawwa if you want to keep your Job, you have to abide by our Rules(idan kina son aikin nan dole ne ki bi dokar mu"

Ta san laifinta ta yi sauri tace "Sorry Ma, it wont repeat itself again(kiyi hakuri, ba zaa sake ba"

"Good, remember you are his Mother at home, and his Teacher at School"

Cike da ladabi tace "Yes Ma"

Hawwa tayi godia ta fito rik'e da Abbah ranta bace "Wani irin abu ne haka? Ace ba zaa hukunta yaro in yayi laifi ba? Don ya na nursery2?"

Tun daga ranar da yaji an ma Umminshi fada ta kan dukanshi Abbah ya fara iyar shege a School, ya nemi tsokanan wannan ya daki wanchan, ya zubar ma wanchan da abinci, ya karya musu crayons da pencils, ba halin ta dake shi, ko in sun koma gida tayi Punishing dinshi washegari sai ya rama a makaranta ta hanyar rashin ji, abun ya fara isar Hawwa ta gaya ma Babanshi sai dai Alhaji Alamin yayi dariya yace kar ta damu k'uruciya ce.

Hawwa na san aikinta sosai don ba laifi mai makarantar na biya kuma tana son abunda takeyi wato teaching yan nursery, kudin Mijinta ko na Mahaifinta be sa taji tafi karfin koyar da yara yan aji biyu ba, in tana koya musu tana komawa kamarsu ne, dokar makarantar ce baa dukan dalibanta har sai sun wuce primary3query ake ba malamin da aka kama yana bugun yara, hakan yasa Abbah yake mata rashin ji a makaranta don bata dukanshi amma dole tayi maganinshi.


Kamar ko wani Saturday din karshen wata, sukan hadu a Gidan daya daga cikinsu suyi Lunch har mazajensu, to wannan Saturday din ya fada gidan Batul.

Wurin 10 Hajia Hawwa da Aisha da Abbah suka nufa gidan Batul don tayata Aiki kafin 2 Alhajia Alamin ya karaso, Abbah sai dadi yake ji zaije gun Anwaar

A hanya Zaid ya kirata yace tana ina zaizo ya bata Kudin takalmomin da jakkuna da zata siya na lefe, tace "ita gata a hanyar gidan Batul"

Yace "to gashi nan, su hade gidan Batul din.


Suna isa ba da dadewa ba Hawwa ta bi Batul Kitchen, ta dade tana aikin, suna aiki tare Hawwa ta zayyana ma Batul abunda Abba yake mata a makaranta, yanzu a gida ma ya rainata, Batul tayi daria tace "abunda kika ma Aunty ne ake miki" Hawwa ta harareta tace "ni me na ma Mommy? Allah this is serious, yanzu fa in na dake Abbah har gwalo yake min yace aidai banji zafi ba, ko ya cire wando ya turo min duwawunshi yana rawa" batul ta zaro ido tace "Abbah? Ahh lallai this is not funny" Hawwa tace "wallahi kam, na damu, ga Babanshi baya mai komai wallahi, Aisha kam ta dakeshi ramawa yakeyi"

Batul tace "aiko be isa ba" Bayan kofa ta dauko wata sharbebiyar tsintsiyar kwakwa ta zaro kwara uku, ta daga labule ta kwala mai kira sai ko gashi da gudu sunyi wasan ruwa duk sun jike kayansu.


Anwaar ya san halin Mommynshi bata da wasa akwaita da discipline yaki shigowa, Batul ta riko Abba da dukkan hannayenshi, ta cire mai kaya ta mishi zindir, ta kwalalo ido tana zare mai ido, nan da nan ya shiga taitayinshi yana ganinta dauko zaborin ya fara kokarin kwace kanshi sai dai rikon da ta mishi ba na wasa bane.

"Abbah Ina wasa da kai?"

Da sauri ya girgiza kai,

Ta nuna Hawwa tace "wannan wacece?"

Baki na rawa yace "Ummi ce"

"Tsarar kace kake mata rashin kunya a class? Har ta dakeka ka mata gwalo wai baka ji zafi ba?"

Yayi shiru.

Ta shaudeshi ya yi wani ihu tace "kaji zafin wannan?"

Da sauri ya gyada kai yana kuka yace "Mommy akwai zafi Allah"

Ta sake shauda mai tace "aa ba zafi"

Ta sake tsula mai, kuka yakeyi yana "Mummy sorry, mummy sorry Ummi Help, Ummi na bari Allah"

Batul bata daina tsaula mai zaborin nan ba ta dinga tsaular shi, har dai zuciyar Hawwa ta karaya daga irin hukuncin da Batul take ma Abbah, ba dai ta motsa ba, sai da Batul ta tsayleshi son ranta kafin tace "zaka shanye kukan nan ko sai na kara shaudarka?" da sauri ya gumtsa bakinshi yana tattaro nutsuwarshi don kar ya sake laifi, tace "danubanka mu muka haifeka ba kai ka haifemu ba, ba ka isa ba, wuce ka ba Ummin hakuri"

Hawaye be bar sunturi a idonshi ba, ba ya son buda baki don ya san kuka zaiyi da hannu ya mata alamar Sorry.

Batul ta wawuroshi tace "Allah ya sa na sake jin kayi rashin ji a Class, ko inji ana maka magana baka ji, ko Aunty Aisha ta dake ka ka rama, ko ka dinga cire wando kana rawa, sai na sake kaika an maka kachiya, comeon wuce a sake maka kaya" ta kalli Anwaar da ke ta lekowa tace saura kai, kai in na kamaka ka dai sanni"

Sum sum Anwaar ya shige dakinshi, Abbah ya bi bayanshi, zai kwashi kayanshi a kasa, Mommy Batul ta daka mai tsawa da sauri ya fada dakin, Batul ta kalli Aisha tace dan kira Habiba ta chanza musu kaya.


STORY CONTINUES BELOW

Kamar daga sama sai ga Zaid ya shigo, Abbah ya fito sanye da kayan Anwaar da yake kansu daya, oyoyo Anwaar ya mai, Abbah ya dan makale, Zaid ya daukeshi ganin yanda fuskarshi yayi ja da alama kuka yaci.

"Me aka maka babana?"

A hankali Anwaar yace "Mommy ce ta cire mai kaya ta zane shi da zabori"

Zaid yace "kayi rashin ji ko? Ka daina kaji"

Kai ya gyada yace kuje kuyi wasa.

Kitchen ya nufa Inda yake jin muryoyinsu "Lahh Yaya yaushe kazo?"

Idonshi ya sauka kan lafiyayyun Tsintsiya kwakwan dake kan Chestfreezer, ya dauka ya nufi Hawwa dashi, kamar ko ta sani tace "wallahi Batul ce"

"Ohhkece Katuwar banza" ya sauke mata a gefen hannu.

Batul tace "Lah Ya Zaid akwai Zafi fa"

"Oh kinsan da zafi kika zane Baba da shi"

"Ya Zaid wallahi Baban nan naka baya ji" nan ta zayyane mai abunda yakeyi da kuma abunda ta mai"

Aiko ya sake shauda mata tayi baya da sauri yace "sai kuma akace duka shi zai sa ya chanza?"

Itama Hawwar ya samu ya tsaula mata yace "kuji inda da dadi"

"Baki ta turo tana murza wurin da ya sameta tace "to ni me nayi?"

Yace "Allah sai na hadaku da Umma yanzu"

Wayarsa ya ciro ya gaya ma Umma abunda ya faru, Umma ta dinga fada tace "wai bana hanaki dukan yaro irin haka ba? kinga Batul ki rage wannan tsaurin naki, ke saurin hannu komai kice zaki daki yaro ko? Ba kisan yawan duka na kangarar da yaro ba? Ku wa ya dukeku? Wani rashin jine bakuyi ba, wallahi ya isheku, ku fita idona, ke Hawwa baki iya hukunta yaro sai kin dauko ruwa gora tun daga Tarauni zuwa Sharadda hukunci ko? Ke kuma uwar discipline kika tsaule yaro? To in sakeji duk saina bata ranku, uwayen banza kawai" Ta katse wayarta.


Kumburi sukayi da bakinsu, Zaid ya ciro ATM ya mikama Hawwa yace "tace Size 36-37" Hawwa ta dauke kai don taji haushi karar da ya kaisu yace "zaki karba ko sai na sake tsula maki"

Baki ta turo kamar yarinya tace "Ya Zaid da fa Mijina kake dukana"

Baki ya hangame yace "inyeeee, lallai Hawwa wuyanki ya isa yanka"

Karban Atm din yayi

Yace "meye ma pin din?"

Kauda kai tayi tace "2870"

"Good, sai anjimanku good for nothing Mothers"

Duk suka turo baki ya ficewarshi ya kyalesu suja kunkuni.

Suna jin alamar rufe kofa Batul tace "Mijin Bajawara kawai"

Hawwa ta harareta tace "ya baki fada gabanshi ba?"

Batul tace "na fada gabanki ai kamar na fada gabanshi ne, kiyi abunyi"

Hawwa ta galla mata harara tace "Bajawarar da tafi wata Budurwa ba, ke ai Watty ta hadu nikam tana burgeni"

Batul tace "kina magana kamar kinsanta kin taba ganinta"

"Oho abunda Yayana yace, ai hakan ne, he said she is good, so she is good"

Batul tace "ku dai kuka sani, ku kashe ku birme ku kadai"

Hawwa tace "eh din munji, yanzu ma dai in munyi Lunch din donAllah zuwa Laasar sai mu shiga Kasuwa tare"

Nan Hawwa ta dinga ba Batul Labari Hauwatty, Batul ta tausaya mata matuka.

*****


Hajiya Iklima na nan an gama hamshakincewa.

Har gobe bata daina cewa Saadatu ta rabata da diyarta ba, har gobe bata dai na jin haushi Saade ba, kyashi ciwo ne don kuwa Hajiya Iklima ta fi Hajiya Saade Kudi da komai amma bata daina kyashinta ba.

Mai hali baya fasa halinsa, bata shiga dangi kuma har gobe tana raina arziki mutane akwaita da kallon mutane a dage.

Yauwa ma kiran Zaid tayi yazo Gida ya zauna tace "kai Yanzu bazawara zaka aura kana saurayi?" Shiru ya mata tace "kazo ka duba yaran Friends dina"

Bece mata komi ba, wani hadadden ledar da ke gefenta ta mika mai tace "ai shikenan kai ka sani, gashi ka saka ma Bajawara a Lefe"

Ya kagara ya tafi ya amsa hannu biyu yace "nagode Allah ya saka da Alheri"

Gida ya wuce ya nuna ma Umma lokacin Yaya Fahad na gaban Umma yace "Aunty Iklima ta bani wai a saka a lefe"

Umma ta washe baki tace "ahh mai muka samu?" Ta karba ta bude akwatin farko

Zinari ne Yan kunne da Sarka da zobe, sai na biyu Awarwaro ne duk kyalli suke, da turaruka a manyan kwali kusa guda6 daga gani masu kamshi da tsada ne.

Ya Fahad yace "yanzu nan Umma wannan karfen sai ace Zinari ne ko?" Tace "daham kuwa" Fahad yace "yanzu wannan ya kai nawa?"

Tace "dari biyar ko fi"

Yaya Fahad ya zaro ido yace "wannan din?"

Umma tace "Yo Iklima ai bata siyan karamin abu"

Yaya Fahad yace "ai Aunty Ikeey akwai Harkar Girma"

Umma ta murmusa tace "Zaid kaje ka gwada ma Abbanku yana ciki, sai ka sami Uncle dinka ka nuna mai, daga nan sai ka kaima Uwar dakinka ta aje ko?"

Zaid yace "eh zan hada da kayan da aka turo daga lagos na kai mata"

Tace "miko min wayata ga ta nan kusa da kafarka na kira nayi Godia"

Zaid ya mika mata wayar ta latso number Hajiya Iklima, kamar ba zaa dauka ba, sai aka dauka cike da isa.

"Hello Auntyn Yara"

"Muna lafiya? Ya shiri?"

"Alhamdulilah haka aka cika Zaid da abun Arziki?"

Cike da isa tace "Ah haba bakomai, Zaid nawa ne ai"

"Angode Allah ya saka da Alheri"

"Ameen Ameen"


STORY CONTINUES BELOW

Zaid ya nufi Gidan Hawwa ya kai mata Gudumuwar Mommy sosai taji dadi tace barin kira nayi godia.

Tana kira tace "Mommy kin kankaro mana mutunci, mun gama kuma dasu dole mu bigi kirji, ta hadu sosai, sai santinta nake"

Hajia Iklima ta tabe baki tace "da dai Budurwa ce da haduwar tafi haka dai, Zaid ya dai ki ji ya nace"

"Mommy me yayi saura tunda rana kawai fa ake jira, kuyi hakuri kawai"

"Yo hakurin me zamuyi? Mu zamu zauna mai da ita, ai tunda yaga zai iya yayi ta fama ai"

"Yauwa abunda nake so ku gane kenan, shi yace yana so" ni ci ni

Katseta tayi tace "kin gama godiar? Mijina ya dawo"

Hawwa tayi dariya tace "Allah bar Mommyna, mungode Allah saka da Alheri Allah bar kauna da Daddy"

Murmushi Mommy tayi tace "Ameen Surikar Bazawara"

Hawwa tace "Kai Mommy"

Kit ta kashe wayar tana daria.

Nan Hawwa ke gaya ma Zaid yanda sukayi, yace "nima haka tace min"

Hawwa tace "ita dai Mommy ba ruwanta, zata fada maka ranta in ta maka dadi ruwanka in ma bata maka dadi ba ruwanka" murmushi kawai Zaid yayi.

*****


A daren Uncle Ahmed ya shigo da Akwatuna Set Biyu, ta bi Akwatunan da kallo, tace "Akwatunan Zaid din kenan?"

Yace "aa"

Da mamaki tace "na waye?"

Kai tsaye yace mata "ciki ki zaba ko wani set kikeso, abunda ke wannan akwatin shi ke dayan, Colors ne kawai suka banbanta"

Gabanta ya fadi, bakinta yayi nauyi

Yace "ki dauki lokaci ki zaba ki darje wanda kike so Uwargida"

Kirjinta ya halba, kar dai Aure zaiyi, kar dai Akwatunan fadan kishiya ne, amma Ahmed ya gama da ita, sai yanzu da suka fara ajiya Jikoki zai mata kishiya"

A hankali tace "Aure zakayi?"

Bai amsa ba sai dai ya dan yi murmushi yace "Kaii Ikee" yayi wata dariya ya wuce ciki.

Shikenan Maganar ta tabbata, Ahmed aure zaiyi, yau ta shiga uku.

Da sauri ta bishi daki, gabanta na faduwa, sai taji yana waya yana cewa "eh gobe zaa kawo miki Akwatunan, sai me kike so kuma?"

Da sauri ta shige dakin ta fincike wayar cike da dumbin Tashin Hankali.

Gani Hawwa ne ya sa ta Kafa kunne tace "Hello!"

Hawwa Daddynki Aure zaiyi, be min kishiya ba tuntuni sai yanzu"

Hawwa tace "kishiya kuma? Aa mommy"

Tuni ta fara kuka tace "Wallahi gashi ya shigo da Akwatuna seti biyu, wai na dauki daya, na fadar kishiya ne, bana so, ya hada duka ya kai mata"

Hawwa ta fashe da dariya tace "Mommy Akwatin Lefen Ya Zaid ne fa nace ya mana order yanzu yake ce min sun iso daga Dubai gobe zai aiko min dasu Gida"

Cike da rashin gamsuwa tace "Aa ba haka bane, aure zai sake"

Hawwa tace "donAllah mommy ki bar magana, Empty Boxes ne fa, ki bude ki duba donAllah"

Kamar zautatta ta fita daga Dakin Daddyn, yana dariya ya bi bayanta, haka ta bude akwatinan nan tas guda 10 taga bakomai ciki, harta kit sai da ta tabbatar, dagowa tayi ta ga Daddy na Dariya tace "Wallahi Allah ka shammaceni" da gudu ta bishi ya na gudu yana ashe ana sona, kice da an min laifi na siyo akwatuna na ajiye" Hawwa dai taji alaman sun manta da ita don soyayyarsu suke zabgawa son rai, ta murmusa ta kashe wayar tana musu Adduoi.1


N A S S A R A W A


Daga Bagaren Amare shiri sukeyi kamar auren farko. Aunty Binta ta nata gyaran Kanwartata.

Mai makon Mata Maza suka kawo lefe don takaita Bidi'ah.

Komai yayi sambarka, Watty ta yi Goshi.

Bayan Sati Biyu kuwa sai da Nassarawa ta shaida Kanawan Dabo sun shigota.

Aka daure Auren Watty da Zaid

Alkawari ya cika.

Bayan yan shagulgulan Biki, a ka yi Kano da amarya, washegari yan kai Amarya suka dawo Nassarawa taro ya tashi lafia kowa sai sambarka yakeyi.


A nade cikin lafayarta ya isketa zaune bakin Gado, da sauri ya karasa gunta, a hankali ta dago ta zuba mishi idanuwanta wanda suke a juye kamar ba shi take kallo ba, hannayenshi biyu duka ya mika mata, cike da yanga da jan aji ta daura nata a kan nashi, a hankali ya dagota ya danganata da jikinshi, rungume juna sukayi na tsawon lokaci, a kunnenta yace "haka nake son yi tun da dadewa Yarinyar Kirki, i wanted to do this for long wallahi"

Murmushi tayi tace "ni din taka ce"

Murmushin ya mayar mata yace "ke din tawa ce, Allah ya miki Albarka Yarinyar Kirki"

Yanda ya fada ya sa ta dariya tace "Ameen Yaron Kirki"

Cike da kauna yake kallonta ya kai bakinshi ga nata, yanda jikinshi yake rawa ne ya sa ta gane he is new to the system, sake tabbatar mata da hakan yayi da yace mata "You make my Dopamine levels go all silly, i love you T"

A kumatu ta mai kiss, yace "Allah ya bani ikon Kula da ke, Allah ya hanani zaluntarki"

Lumshe ido tayi ta bude tace "Amin yaron Kirki, Allah ya bani ikon yi maka biyayya, Allah ya hanani bijire maka"

Hannuta ya murza yace "Sallah, ya kamata muyi Sallah"

Gyada mishi kai tayi, ya ja hannunta ya tura Toilet.

Chogewa tayi tace "ina fa da Alwala na"

Dariya yayi yace "Afuwan, shimfida mana darduma"

A wannan daren suka zage suka nunawa junansu tsantsan kaunar da sukewa junansu.

Allah ya bada Zaman Lafiya ameen.

****


STORY CONTINUES BELOW

Jumaar Farko bayan tarewarta ya kaita Gidansu, bayan ta musu Abinci da Snack, tun Azahar take Gidan, ya tafi ya barta daga ita sai Umma, sai bayan Isha'i ya dawo daukanta, a gajiye. A bakin Kofa ya tsaya ya lek'o Parlo, Umma tace "daga bakin kofa?"

Yace "Umma Jigawa fa muka je da Uncle Ahmed, wallahi nagaji"

Tace "Ai sai kuyi ta tafiya, ka huta gobe weekend"

Ba tare da ya kalli Inda Watty take zaune ba yace "Hawwa, Muje, sai da Safe Umma"

Umma tace "Allah ya tashe mu lafiya, ka biya kitchen ka daukar mata Kulolinta, munci Abinci Allah yayi albarka"

"Ameen" yace ya nufa kitchen, be kalleta ba ya fita.

Murmushi Watty tayi a ranta tace "Mijina Sarkin Kunya, wai yau itace Hawwa, ko kallonta ya kasa yi"

Har kasa ta durkusa tace "Umma sai da safe, mungode Allah ya saka da Alheri"

Umma tace "mune da godia Hauwatty, Allah ya yi albarka"

Watty ta fito ta nufi mota.

Yana zaune tana shiga ya kalleta a shagwabe yace

"Baby nagaji"

Dariya ya bata tace "oh yanzu ka samu bakin magana harda idon kallona?"

Dariyar yayi ya san inda ta dosa tace "ashe haka kake da kunya? Abun ya maka kyau"

"Nine fa autan Maza, itama baki ga tana kunya na ba?"

Ta yi dariya tace "muje gida na maka tausa, duk gajiar nan zata tafi"

Ya tada Mota yace "shiyasa nake sonki Yarinyar Kirki"


Washe gari Gidan Uncle Ahmed suka nufa, kasnacewar Weekend ne yana Gida.

Watty ta zauna a kasa daidai kafar Hajiya Iklima tace "Mama Ina wuni?"

Hajiya Iklima tace "haba tashi zauna kan kujera mana"

"Aa mama nan yayi"

Waiyo dadi kashe Hajia Iklima, ita dai a rayuwarta tana so a bata girma, gashi an zauna kasa tana saman kujera, gashi ance mata Mama, hakan da Watty tayi ta saye zuciyar Hajiya Iklima, Uncle Ahmed ya fito suka gaisa da Watty, Hajia Iklima nan nan takeyi da Watty, ta bata mamaki bata yi zaton akwai jawarawa masu kunya ba, sosai Watty ta burgeta, da zata tafi ta cikata da kaya a jakka ta bata, Watty ta karba hannu bibbiyu tace "Nagode Mama, Allah ya saka da Alheri" abunda Hajiya Iklima batayi tayi yau, rakiya har kofar gate, tana daga ma Watty Hannu, Zaid yayi mamaki matuka.

Hajiya Iklima ta dawo tace ma Uncle Ahmed "ni ai surukata daya duk duniya" ya lura Watty ta samu karbuwa gun baudaddar matarshi, yace "wa kenan?"

"Matar Zaid mana, Hauwatty, ai da ita kadai zanyi surukkuta"

Uncle Ahmed yayi dariya yace "Matar Fahad fa? Mijin Batul da Hawwa fa?"

"Ai duk ba ruwana dasu, ai ni Hauwaty kadai ce Inlaw"

Yayi dai dariya, ba zai gane yanda abun ya mata dadi ba, saboda yanda taji dadi har Hajia Saade ta kira tace "Zaid ya kawo mata Surukarta"

Umma tace "Ahh Lallai Hauwatty ta ciri tuta"

***


A hankali A hankali Zaid ya ke zagaye Hauwatty da gidan Danginshi, yana kaita ana gaisawa, Watty wayyaya ce ta iya zama da mutane nan da nan ta samu karbuwa a cikin Family, ba da jimawa ba ta so ma zuwa Aiki a Asibitin Aminu Kano.


Bayan Shekara daya


Ciki baya zama a Mahaifar Watty kasancewar bari bari da tayi a baya.

India sukaje da Zaid don ganin Gynecologists, Mahaifar tata ta dan samu matsala saboda kwayoyin da Laura ta dinga bata na zubda ciki, Magunguna akai ta bata har aka daure mata Mahaifa don cikin ya zauna, cikin ikon Allah yanzu tana dauke da cikin Wata biyu.

So daya yaronta Zaid yazo mata hutu kasancewar ya shiga Makaranta, Gidajenta da ta bada haya sun biyata kamar ko wacce shekara, ta na samu Alheri da Asibitin Idonta, ta na daga Kano take managing komai da yake tana da Amintattu a Nassarawa, tunda tayi aure so biyu kawai taje Nassarawar, Alheri da take ma danginta  bata fasa ba, har dangin Dr ta cigaba da musu duk abunda Dr yake musu, nan Kano ma tana Jan Dangin Mijinta a jiki.

Ita fa sai da ta kusa shekara da aure kafin ta san cewa Hawwa diyar Uncle Ahmed ce, duk zatonta Diyarsu Umma ce, kusancin Hawwa da Mijinta ya fi karfin na Cousins, bata san asalin Labarinsu ba, bata taba tambaya ba, ba a bata labari ba.

******


A Gidan Zaid, a kan Dinning Table din Gidan Abinci ne kala kala, Watty da Hawwa da Batul da Aishar Hawwa ke kai kawo tsakanin Table da  kitchen, sauri suke su gama setting Table kafin Mazajensu su shigo, kusan rabin Awa sai ga Zaid yayi sallama, bayanshi Alamin din Hawwa ne da Faisal din Batul, jagoranci ya musu har bakin Table din suka zauna.

Matan sukayi serving din Mazajensu, suka fara cin Abinci ana fira ana raha.

Zaid yace "wai sai kuka tura ma Ummana Yara? Mai makon a zo dasu?"

Batul tace "ai Ya Zaid da su na nan da baa gama abinci ko daya ba balle kuzo yanzu kuci"

Zaid yace "to ita shikenan sai ita bakinta yayi tsawo? Ta sha wahalar iyayensu ta sha wahalarsu?"

Hawwa tace "wallahi kam Yaya barin ma Abbah da Anwaar dole su sakata ciwon kai balle sun maidata Kaka, dama Mommy aka kai ma su da sunyi Ladab, Mommy akwai zafi"

Batul tace "Ai Mommy is hotter than fire, ba wasa, ita ko irin wasan da da jika batayi"

Hawwa tayi dariya tace "yo ko mu iyayensu shakkar mommy muke baresu"

Watty tayi dariya tace "Nifa wallahi bana ganin Zafin Mama, Allah Mama bata da fada, ba ruwanta"

Hawwa ta kalli Batul suka chafe suna jinjina kai, sun san irin kyakyawar Alakar da ke tsakanin Hajiya Iklima da Watty, su kansu suna mamaki.

Hawwa tace "eh lallai su masu Mama".

Haka suka gama cin abinci Aisha ta tattara kayan ta kai Kitchen.

Fira sukeyi mai dadi suna jin dadinsu, Zaid yace "Yauwa na tuna, akwai wasu tsohuwan Ajiyar da na dauko gidan Umma, hotunan Hawwa da Batul suna yanmata"

Watty ta saka dariya tace "Nagani jiya ai nasha dariya, lokacin kuna yan shilla"

Ganewar hoton ya sa Batul da Hawwa dariya, Batul tace "su Hawwa har da majina"

Hawwa tace "ke kuma Abba ya dakeki kinci kuka hawaye duk ya bushe"

Zaid yace "barin dauko ma Mazajenku suga wasu suka aura" tashi yayi ya nufi TV Stand kasancewar har yanzu suna kan Dining Table ya sa za Zaid daga murya yace


"Hawwa dan zo"


A lokaci daya Watty da Hawwa suka mik'e, sai kuma su ka fashe da dariya.

Batul ta dan daga murya tace "Ya Zaid baka banbance wa kake kira ba"

Ita Watty ta san da ita yake, don Hawwa yake ce mata a duk lokacin da suke basu kadai ba, gaban mutane yake ce mata Hawwa.

Hawwa tace "ba Hauwa yace ba, Hawwa yace which means ni"

Batul tace "dadi na dake zak'ewa, meyasa zai ce kizo a gidanshi? Ga matarshi kuma kusa?"

Hawwa tace "Yaya wai wa kake kira? Ni ko Aunty Hauwatty?"

Zaid ya dawo wurinsu ya gansu tsaye sai ya murmusa yace "aww nayi causing, confusion"

Alhaji Alamin ya murmusa yace "gaskia a dinga differentiating, nidai Matata ce Hawwa, kowa ya sani, ka kira taka da Hauwa"

Zaid yace "Hauwa, sai kace wata kulu"

Mijin Batul yace "yo ba kulun bace?"

Zaid yace "aa wallahi Bar maidata tsohuwa"

Batul tace "to Yaya kace mata Hauwatty"

Watty tayi dariya tace "ai ba ya ce min Hauwatty ko watty, ban taba ji ba"

Zaid yace "kyalesu, wai ma ina ruwanku? ya kuka wani damu da abunda nake kiran Matata? Banson sa ido"

Mijin Batul yace "ahhh Alhaji Yaya Zaid ya kake wa Matata fada?"

Zaid yace "in kaji Haushi kaje ka auri me suna Hawwa kaima"

Batul ta zumburo baki tace "kai Ya Zaid"

Mijin yace "Batul ita ta isheni".


Karo na farko Zaid ya cire kunya ya tallafo Matarshi yace

"Nidai ga Hawwa ta nan"

Alamin ma ya tallabo Hawwarsa yace "nima ga Hawwata nan"

Mijin Batul yace "Ahhhh Allah ya baku Hakuri, nidai banda Hawwa amma ga Batul ita"

Duk suka fashe da dariya suna masu son Zumuncinsu.

Allah ya kara mana zumunci.


ALHAMDULILAH.


Ku Makaranta? Wacece Hawwarku?

Nidai Hawwar Alamin ce tawa

Watty kuwa ta Zaidu ce.

Post a Comment for "HAUWA CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...