HAUWA CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAUWA CHAPTER A

 HAUWA CHAPTER A


KANO+


Kallonta ya yi tare da girgiza kai cike da takaici ya ce "Haba Hauwa, ya za ki shigo Parlo haka ko Sallama babu? Cike da rashin kunya ta ce "ban iya ba".

Bai ce komai ba, ya maida idanuwansa ga TV.

Jim kaɗan, Uncle Ahmad ya shigo ɗakin, jiki na rawa na zaunen ya miƙe tsaye ya karɓo Jakar hannunshi tare da cewa. "Barka da fitowa" cike da murmushi ya ce "ZAID kenan".

Wanda aka kira da Zaid ya murmusa.

"Daddy Ina kwana?"

Uncle Ahmad ya kalli tilon ɗiyarshi ya ce "Hawwa, kin tashi lafiya?".

Murmushi ta yi a taƙaice ta ce "Eh".

"Makaranta fa?"

"Daddy ba zan je ba"

Ba tare da damuwa ba ya ce "kira mini Mummynki".

Da shagwaba irin na sangartattun 'Ya'ya ta miƙe ta shige cikin gida.

Jim kaɗan sai gashi sun dawo tare.

Matar ɗauke da murmushi tana mai kallon Maigidanta ta ce "har ka fito?".

Ya amsa mata da "Eh, mun fito".

Zaid ya ce "Ina kwana Aunty".

Ba tare da ta kalle shi ba ta amsa tare da maida hankalinta ga Maigidanta.

Uncle Ahmad ya ce "Ku yi buɗa baki yau da Zaid, shi ma yana Azumi."

Ɗan basarwa ta yi kafin ta ce "Za a yi".

Uncle Ahmad ya ce "To mun wuce"

Ta ce "Sai ka dawo Allah ya bada Sa'a".

Daddy "bye-bye".2


Haka suka jera suka fita garage wurin parking motocin gidan, Zaid ya buɗe ma Uncle ƙofar Mota mai ƙirar High Lander, kafin ya zagaya ya shiga kujerar Driver ya ja motar, Maigadi ya buɗe suka bar gidan.


NASSARAWA

21/03/2015


Dariyar ƙeta kawai take yi. Dariyar har ya soma ƙular da ita. Tsaki ta buga ta ce "Dagaske Aisha ba zan sake gaya miki abu ba".

Da ƙyar Aishar ta iya tsaida dariyarta ta ce "Yi haƙuri  WATTY, na bari, rainin wayau ɗinne ya ba ni dariya, don ya raina mutane, ina ake wa Namiji Auren dole?".

Watty ta ce "rabu da ɗan borin kunyan, Allah ni ba son shi nake ba, amma don ya rainani zai ce min Babanshi ya zaɓar mishi Mata, ɗiyar Abokinshi ce, shi ba ya sonta, waye-waye ɗin shi, yen-yen-yen, na ce to kana Namiji ya za a maka Auren Dole? Wai ai biyayya yake yi, can you Imagine? Mtsw, da Son shi nake da na kamu da hawan Jini."

Aisha ta gumtse dariya ta ce "to wai sai cewa kike ba son shi kike ba, meyasa kike ta nanata maganar tun ɗazun ? Hmm, ke dai kawai an kasa ki".

Watty ta wurga ma ta Harara ta ce "Za ki ga wanda zai sake baki labari" ta fincike hanunta.

Aisha ta guntse dariya ta ce "Ki yi haƙuri Sis".

Banza ta yi ta ƙyaleta.

Sake kamo hanunta ta yi ta ce  "Hauwati"

Kai ta rausayar ɗayan gefen.

"Haba Watty, meye abun fushi? Ko dai duk Kishi ne saurayi zai yi aure? Shi ne za ki huce kaina?".

Hararrata ta yi ta ce "ke dai kika sani, ni ce ma na biye miki".

Cike da zolaya Aisha ta ce "Dama mai za ki yi da wannan duna black ɗin? Ke da kike da saurayi Ready Made, son kowa ƙin wanda ya rasa?".

Ba ta san murmushi ya bayyana a fuskarta ba, amma ta ɗan basar ta ce "Wa?".

Aisha ta ce "Ya Bu mana".

Hauwaty ta ɗan lumshe ido kafin ta buɗe ta ce "wai so nawa zan gaya muku ba soyayya muke ba?"

Aisha ta miƙe tare da ɗaga kafaɗa ta ce "Oho, rana bata ƙarya, ke ni na tafi gidan Inna."

Watty ta ce "mu je tare".1

KANO


Shigowa ta yi ta gansu kan Table suna Buɗa Baki, wuce su ta yi.

Ya san ba za ta ba, amma ƙila ya ci sa'a taje saboda idon Babanta.

Murya can ƙasa ya ce "Hawwa don Allah ɗauko min ruwan da bai da sanyi."

Banza ta yi ta ƙyale shi, shiru ya yi daga inda yake yana kallonta.

Uncle Ahmad ya buɗe baki a kausashe ya ce "Hawwa!"

Baki ta turo ta ce "Daddy kallo fa nake yi".

Baban ya ce "Hauwa tashi ki ɗauko mai ruwa marar sanyi".

Tashi ta yi rai na ƙuna tana bubbuga ƙafa ta nufi kitchen tana ƙunƙuni.

"Shi mutum gurgu ne da ba zai iya zuwa da ƙafarshi ba? Ba dama a ga mutum zaune haka za a dinga takura mishi, gwara ma mutum ya zo ya tafi Gidansu."

Murmushi mai ciwo Zaid ya yi, da alama Baban bai yi mamakin kalamanta ba, suka ci gaba da buɗa bakinsu, ta kawo ruwan ta dankwafar mai a gabanshi.

Daddy ya ce "Good Girl".

Turo baki ta yi ta wuce cikin Parlo.

Daga Sallar Isha'i Zaid ya wuce gidansu bayan sunyi sallama da Uncle Ahmad da niyyar gobe zai fito da Safe.1


STORY CONTINUES BELOW

Da Sallama ya shiga Gidan, ba wuta, babu mai a Generator. A zaune ya iske 'yan gidan a tsakar gida kan Tabarma.

"Ya dai, Gen ɗin ya buga ne?".

Yayanshi Fahad ya ce "Petrol zan siyo Mama ta ce a bari sai gobe tunda Tara ta kusa".

Wuri ya samu kusa da ƙanwarshi Batool.

Mama ta ce "Barka da shan ruwa Zaidu, fatan ka cika cikinka Gidan Uncle Ahmad ɗin".

Kafin ya yi magana ya ji Batula na cewa "Barka da safiya, barka da yamma, Ina zan kai ka, barin share ma zufa Uncle".

Kallonta ya yi, ya ga a tsaye take tana durkusa kamar tana gaida Sarki.

Yaya Fahad ya tuntsire da dariya, Amina da Baffa suka taya shi.

Hakan ya sa Batul ƙara ƙaimi wurin abunda take yi.

"Uncle na maka Firfita?" Dariya suka fashe da har Mama sai da ta Dara.

Kwaikwayon wani takeyi, Shi take kwaikwayo, shi suke ma tsiya, ya saba jin irin tsiyar da 'Yan uwanshi ke mishi, ba su tashi mai irin haka sai randa ya yini tare da Uncle Ahmad.

Wai haka yake yi in ya ga Uncle Ahmad, a cewarsu in yana gaban Uncle Jikinshi rawa yake yi, wai harta Takalma in Uncle Ahmad  zai sa, sai Zaid ya gyara mai tsayuwarsu a ƙafar shi ya saka Handky ya goge, a cewarsu fa.

Zaid ya murmusa ya ce "ku dai kuka sani, ko zubewa na yi ƙasa ya bi ta kaina ban faɗi ba, ƙanin Babana ne".

Wani abu Batul tayi wanda ya saka su tuntsirewa da dariya.

Zaid ya girgiza kai ya tashi ya yi hanyar cikin Gida yana faɗin "ba zan biye muku ba".

N A S S A R A W A

Watty ta kalli Kakarta ta ce "Inna da gaske Ya Bu ba so na yake yi ba".

Inna ta ce "to ni me ya sa ya ce min kun ruga da kun haɗe kanku?".

Watty ta ce "Ni Inna Wallahi ban sani ba, ƙila don kar da ku matsa mi shi kan sai ya yi aure ne".

Inna ta ce "Ke Hauwaty ki fita Ido na, ko da ya ke, zai zo hutun ƙarshen mako, zan turke ku tare".

Watty ta yi dariya ta ce "na yarda Wallahi".

Saƙe-Saƙe zuciyarta ta fara. 'Amma idan na samu Ya Bu a matsayin Miji ai na warke.'

'Ya haɗu iya haɗuwa'

Da wannan tunanin ta isa ɗakin Mamarta. Zaune ta ganta tana cin Tuwo.

Zama ta yi kusa da ƙafarta.

"Sannu Mama".

"Yauwa Watty, wai na tambayeki mana?".

"Eh Mama".

Mamar ta haɗiye lomar Tuwon ta ce "Me ya sa kike ɓoye mini abu a matsayina na mahaifiyarki, me ya sa ba kya gaya mini gaskiyar lamarinki?".

Cike da rashin fahimta take kallon Mahaifiyarta.

"Mama ban gane ba?".

"Hmm, Watty ke nan, ba tun yau na ke ji a cikin gida wai soyayya kuke da Abu, har Inna ta ce za a yi bikin ku bayan Sallah, ban san soyayyar ta yi ƙamari har haka ba, har ake maganar aure, magana har ta karaɗe dangi".

Watty ta zaro ido cike da mamaki ta ce "Wallahi Allah Mama ban sani ba, ni ban taɓa tsayuwa da Ya Bu ba da sunan wai zance, Mama ki yarda da ni wallahi, ni ban san me ya sa yake ce ma mutane soyayya muke ba".

Mama ta taɓe baki, ba wai don ta yarda ba ta ce "shi ke nan".

Watty ta shige cikin ɗaki, haushi ya kamata, a kan me Ya Bu zai ta gaya ma dangi ƙarya? A kan me zai ce Soyayya suke alhalin ba ita suke ba, aurenta bayan sallah? To da izinin wa? Lallai, dole ta kira shi a waya, dole ta roƙe shi kan ya dai na cewa mutane soyayya suke, alhalin ba shi suke yi ba, gashi har mamarta mahaifiya ta yarda.

Can gindin window ta matsa, ta latso number Ya Bu.

Kira na biyu ya ɗauka.

"Hello".

Shiru tayi ta kasa magana.

Cikin wani murdadden murya yace "Little, kina jina?".

Ajiyar Zuciya ta sauke tace "Ya Bu ina wuni?".

"Lafiya kalau" ya amsata "ya 'yan Gidan?".

"Alhamdulilah".

Shiru ya biyo baya.

Yace "Yadai?"

Kwarjini ya mata kamar yana gabanta.

"Ehen, Ina jinki".

"Uhm, wai dama a nan Gida ne a ke cewa wai Soyayya mukeyi".

Yace "Toufa! Su 'yan Gidan suke cewa haka?".

Baki na rawa tace "eh haka suke cewa".

Yace "kuma ba haka bane ba ko?".

Tace "Eh mana".

Yace "to bari na zo Gidan on Friday sai mu hadu tare mu ce musu ba Soyyaya mukeyi ba, kin yarda?".

Tace "eh na yarda Wallahi".

Yace "to my little take care kinji?".

Lumshe Ido tayi ta bude tace "Bye-Bye".

Ta katse Wayar.

Ba ta san Dalilin da ke sa Kirjinta bugawa a duk lokacin da take magana da Ya Bu.

A fili tace "Ya Abu, Ya Bu".

Aisha ta ce "wallahi ba Dangi ba, ni ma ban yarda ba Soyayya kuke yi ba".
Watty ta ce "na gama rantsuwa, ku yarda da duk abun da kuke son yarda, zai zo ranar Juma'a, zai faɗa ma Inna, Idan ku ka ji daga bakin shi, za ku fi yarda".
Ta juya ma Aisha baya ta kwanta.
Ranta ya fara ɓaci ainun.
'Me ya sa ba sa yarda da Ita? Hmm, gwara ya zo a yi ta ta ƙare'.

J U M A ' A H

Misalin ƙarfe biyar (5:00) na rana Ya Bu ya yi sallama a Family House ɗin su.
Tuni yaran gidan suka fara sanar da zuwansa.
Tana ɗaki ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, leƙawa ta yi ta window taga ko za ta hango shi.
Kasa zama ta yi haka nan ta kasa tsaye.
Aisha ba ta nan da ta samu ƙwarin guiwar fita.
Bayan daƙiƙai 45 ta ji sallama a ƙofarsu.
Da ƙyar ta iya amsawa tare da fitowa daga ɗakin zuwa Parlorn.
Ya Bu na zaune sai ƙamshin Turaren Oud Zenab yake yi .
Kafeta ya yi da shanyanyun idanunshi.
Kasa jure kallon ta yi ta ɗauke kai tare da zama kan kujerar da ke dan nesa da shi.
"Ya Bu ina Wuni?"
Bai amsa ba ya tsura mata ido don ya san hakan na tasiri a zuciyarta.
Ganin ba amsa ya saks ta ɗago kai a hankali ta kallo shi.
Ita ɗin yake kallo,
ba ta iya ɗauke kanta a kallonshi ba.
Ita ma ta kafe shi da idon zuciyarta na kitsa mata wani abu mai kama da So ko Shauƙi.
"Watty" ya furta a hankali.
Da ƙyar ta iya amsa mai da _na'am_.
"Ki tashi muje mu gayawa su Inna ba soyayya muke yi ba".
Dauke wuta ta yi da jin abunda ya faɗa, sai ta ji ba ta ji daɗi ba, sai ta ji ba ta so a faɗa wa Innar, a barshi kawai a hakan, su je suyi ta cewa soyayyar suke, ƙila wata rana suyi, 'yar maganar nan da suka yi, ta ji duk ta kamu da son shi wanda yake nan tun kafin ta kai haka".
Ya san lagon Mace, ya tako har gabanta cikin wani irin salo da murya ya ce "Watty, in gaya musu ba Soyayya muke ba?".
Sadda kanta ƙasa tayi ta fara wasa da 'yan yatsunta.
"Ki na so mu fara Soyayyar?".
Zumbur ta ɗago kanta.
Tambayar ta ji a bazata.
Kai ya gyaɗa mata tare da kashe mata ido ɗaya.
"Answer me Watty, do you Love me?".
Hannayenta biyu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi mai sauti.
Ya san tarkon shi ya kama kurciya, ya miƙe ya koma kan Kujera.
Tambayar ta ya yi. "Ina su Aunty, na ga sashen Inna ba kowa sai Innar?"
Da ƙyar ta ɗago ta ce. "Sun je suna a Unguwar Dutse".
Ya ce "ke me ya sa ba ki bi su ba".
Ta ce "haka nan".
Ya ce "Ba wani, na san Watty ta ba ta son hayaniya".
Wani farinciki ya lulluɓeta.
Ta ce "Me ka cewa Inna?".
Ya murmusa ya ce "Na ce mata Soyayya muke, kuma ta ce zata gaya wa su Baba idan sun dawo".
Daɗi ne ke lulluɓe Watty, ai magana ta ƙare in dai su Baba suka ji.
Sun daɗe suna hira, jin dawowar su Aunty ya saka shi ɗan gyara zama, suka shigo ya gaishe su, Kafin ya fita.
Duk suka bi Watty da kallo, sum-sum ta miƙe zata fita.
Yaya Nini ta kirata, "zo nan munafuka, anjima sai ki ce ba soyayya kuke ba".
Duk suka mata caaa!
Aunty ta ce "kai ni ku kyale min Autata, Watty yi tafiyarki gidan Inna".
Kamar jira take ta fita da ɗan sauri.

I N N A

Inna na da zuri'a mai ɗan yawa ba laifi, Yaranta 7, jikoki za su kai kusan 50.
Alhaji Hamza shi ne ɗan Inna na Biyu, yana da yara 6.
Cikin yaran Inna harda Baban Watty wanda shi ne kusan Autan Inna.
Kamar yadda Yaran gidan ke kiran Alhaji Hamza Baba Babba.
Baba Babba yana da ɗan Kuɗi don Custom ne kafin ya yi retire. Babban ɗan shi mai Suna Abubakar, ƙannenshi na ce mishi Yaya Abu.
Aisha autarsu ita ta saka mishi Ya Bu, kowa ya ɗauka manya da Yara.
Shekarun Ya Bu 32, a nan Nassarawa ya yi Nursery zuwa matakin Secondary.
Baba Babba ya kai Ya Bu ƙasar Ghana don ya haɗo Degree tun yana da Shekara 20. Ya Bu ya haɗo Degree ta Farko da ta biyu duk a Ghana ba tare da ya zo gida ko sau ɗaya ba.
Mahaifanshi sun yi sun yi ya dawo kullum sai dai ya ce yana hanya In sha Allah.
Inna kan yi faɗa Sosai ta ce Baba Babba ne ya sa masa Ido, nan da Ghana ba ma wata ƙololon duniya ba ya ki ya zo, to su suje su dawo dashi tunda ba ƙasar Ubanshi ba ce.
Sai dai suyi ta tausarta suna ba ta haƙuri.
Mahaifiyar Ya Bu ta kan kira shi tayi ta kuka ta ce don Allah Abu ka dawo gida, ƙannenka duk sun girma, shekararka 10 a Ghana, duk sun mance ka, don Allah Abu ka dawo Gida.
Ya kance Mama don Allah ki yi hakuri, wallahi dole na zo gida, kawai na fara aiki ne a nan, kuma so ɗaya suke bada hutun ma'akaita a shekara shi ma gajere. Zan zo, ku ɗan yi haƙuri.
Haka ya shiga Shekara ta 11 a Ghana, kullum excuse ɗin yau daban na gobe daban. Sai Danginshi suka saka masa ido.
Inna ta ce a saka shi a Addua ƙila ma kurciya aka mishi.
Haka suka   duƙufa Addu'a har Allah ya karkato da hankalinshi gida.
A cikin Shekarar ya sanar da zuwansa don ya samu wurin da zai yi aiki a Abuja.
Nan suka fara shirin tarban Ya Bu.
Wata Laraba Ya Bu ya sauka a Airport ɗin Abuja, washegari Alhamis bayan Asuba ya taho Nassarawa, ƙarfe 9 ya iso Gidansu.
Murna gurin Mahaifanshi da 'yan uwanshi ba a magana, kowa sai da ya rungume shi.
Baba Babba ya ce ku mu tafi Gidan Inna, haka suka ɗunguma baki ɗaya sai Gidan Inna.
Gida ya kachame da Murna.
Inna ta riƙoshi, tayi ta shafa shi, harda 'yar ƙwallarta.
Dangi suka dinga shigowa mai barka.
Aisha ta jawo Watty har gaban Ya Bu.
"Ya Bu ga Wattyn"
Watty na murmushi tace "Ni sakeni, kin wani matseni kamar zan gudu"
Aisha tace "ba tun dazun nake cewa ki matso ku gaisa sosai ba?".
Ya Bu yace "Lallai Watty, kin girma, rabo na da ke tun kina yawo da Pant".
Fuska ta shagwabe tace "Kai Ya Bu".
Sukayi dariya gabaki daya.

Kwanan Ya Bu Uku, Kullum sai yazo Gidan Inna, kafin ya tafi sai ya lek'a Sashensu Watty ko da tana Makaranta.
Inna ta fara yi ma Abu maganar Aure, sai dai yayi dariya.
Tun maganar Inna bata damun shi har ya zo ya fara jan baya da Gidan Inna saboda Maganar Auren da take mishi.
Inna da ta lura Abu ya dauke k'afa daga Gidanta sai ta saka Alhaji Babba ya zo Gidan tare da shi, bayan Sallahr Juma'a suka iso Gidan Inna.
Baban Watty na nan kusa da k'afar Inna.
Bayan sun gagaisa Inna tace "Wato kai Habubakari don ka raina ni, yaushe rabonka da zuwa Gidan nan don na maka maganan Aure? To gaka ga Iyayenka sai ku mai Magana".
Alhaji Babba yace da Baban Watty "K'arami ga ka gashi".
Baban Watty yace "Abubakar, in dai Lissafi na daidai ne, Shekarunka 32, ba zai yiwu ka zauna hakan nan ba Abu".
Shiru yayi da ya tuna shi fa Aure be cikin kayanshi bai ma da lokacin Kan shi har za a fara matsa mishi kan Aure.
Alhaji Babba ya dora da cewa "ya zama dole kayi Aure Abu, ka duba cikin danginka ga su nan, su Hafsat, Fatiman Aliyu, Fatiman Mardiyya, duk sun gama Makaranta".
Nan da nan Ya Bu ya soma hararo Hafsat, da Fatin Baba Ali, da Fatin Aunty Mardiyya, duk ba sa kalar cikin Matayen da zai So, shi fa Auren kwata kwata bai kanshi, amma ya san in bai musu wata dabara ba, ya na ji yana gani zaa hadashi da wata Bagidajiya.
Wata dabara ta zo mai yace "Ai ni fa Baba mun riga da mun daidaita da Watty, dama sai ta gama Makaranta na so na gabatar muku da Maganar".
Baba K'arami ya fadadda Murmushinshi yace "to ai Wattyn WAEC suke, ina jin ko sati biyu ba za su k'ara ba za su gama, ka ga ko da sun gama sai ayi Auren".
Ido ya k'walalo yace "JSCE dai ko?".
Baba Babba yace "wani JSCE? WAEC aka ce maka fa, tare suke da Aisha fa".
Ya Bu da mamaki yace "Wattyn?".
Baba Babba yace "Ita fa, ba ta gaya maka bane? To da ka na nufin sai nan da Shekaru 3 zaka yi Aure? Anya Abu?".
Shiru yayi yana nadamar Maganar Watty ba ki daya, shi fa wai don ya sa su bar Maganar yace sun daidaita da Watty ashe gudun gara yayi ya fada gidan Zago, guntsun tsaki yayi, a ranshi yace "gwara Wattyn, ta fi sauran Wayewa, amma duk da haka akwai damuwa".2

Haka zance ya zagaye Dangi, wai Ya Bu da Watty sun daidaita kansu, kowa ya ji dadin wannan Abun, banda Watty da take ta mamakin yaushe suka ma taba kadaituwa da Ya Bu har Soyayya ta shiga, duk wanda tace ma ba Soyayya suke ba sai su dauketa mai k'arya, harta Mahaifiyarta bata yarda da ita, abun na ba Watty Haushi ba mai yarda da ita.
Tun ta na Rantsuwa har ta sa ma kowa Ido.
Ya Bu Namiji ne wacce ba Macen da zata k'i shi, amma rashin furta mata So da be yi ba yana damunta.
Tana mamakin inda maganar nan ta samo Asali, yanzu haka abun Inna ne, ita ta hada Zancen, k'ila ma ba Ya Bu din bane, haka dai tayi ta sak'e sak'e.
Wannan Zuwan ne ya wanke mata ranta tas tunda dai ya nuna mata yana Sonta.

K A N O

Ran Batul 6ace tace "Umma to wai meye abun damuwa kan halin Hawwa?"
Umma tayi murmushin takaici tace "Batul me nayi ma Hawwa? Hawwa fa da na rik'eta tun tana shekara 4, me na ma Hawwa haka da gaisuwa be hadani da ita? Naji haushi matuk'a Batul. Hawwa dauke ido tayi ta fara Wayar k'arya ta shige daki,  ta nuna kamar ba ta san ina gurin ba, har na bar Gidan Hauwa bata fito ba, Wallahi Zuciyata kamar ta fito, nidai Allah ya gani Rik'on gaskiya na ma Hawwa, ni dai ba za tace na Zalunceta ba, saboda so biyu na taba dukan Hauwa, na farko da ta daura Dish a kai nace ta sauke ta k'i ta ruga da gudu Dish ya fado ya fashe na sa zabori na tsauleta dashi, sai kuma da girmanta ta min fitsari a Parlo kan Carpet ba bacci ba ba komai ba, na duma mata dundu a baya shima sai da mukayi rigima da Abbanku kamar zai dakeni don na hukunta Hauwa nace ni ko inshaAllahu ko me zatayi ban sake dukanta, to me na ma Hauwa?".
"To Umma sai mene in Hauwa bata gaishe ki ba ko ba ta miki magana ba?"
Zaid su ka gani a bakin k'ofa da alamar ya gama jin maganganunsu.
Ya Cigaba "Umma meye abun damuwa? Ni fa ba na saka Hauwa cikin Mutane, Don Girman Allah ki bar Damuwa Umma, ba ta da hankali, bani so kina damuwa".
Umma tace "Zaid Ba damuwa nake ba, Mamaki ne kawai"
A takaice yace "To ki bari".
Ya daga labule ya fita ranshi na suya.
"Hauwa!! Hauwa!!"
Tsanarta ke ratsa zuciyarshi.Hajiyar Rijiyar Zaki, kamar yadda Jikokinta ke kiranta, na da yara guda biyu, Abdullahi da Ahmad.
Tsakanin Alhaji Abdullahi da Alhaji Ahmad akwai tazara sosai kusan Shekaru goma zuwa Sha Biyu, lokacin da Alhaji Abdullahi ya je SS1 a lokacin Alhaji Ahmad ya shiga Primary. Sun taso cikin so da ƙaunar junansu don Mahaifiyarsu ta musu tarbiya da hakan.
Har Lokacin da Alhaji Abdullahi ya auro Sa'adatu suna zaune a nan gidan Mahaifiyarsu.
Ahmad a nan ɗakin Amarya yake dudumar shi, kodayaushe yana dakin Amarya har ya ƙare samartakan shi, ya za mana bai da aminiya sama da Sa'adatu, sun shaƙu matuƙa.
Lokacin da ya je ƙaro Ilimi a Sokoto, lokacin ne Saadatu ta haifi ɗanta Namiji mai suna Fahad.
Ba a yi Shekara biyu ba ta sake haifar mai sunan Surikinta marigayi Bello, amma Bello ba rayayye bane ya rasu ne lokacin da yake ciwon Ela, ba a fi Shekara biyu ba ta sake haihuwar Fatima, itama Fati ba ta daɗe ba ta rasu, sai tsoro ya kamata, ko dai duk haihuwar da za ta yi yaran ba ma su zama ba ne, ta fara shakkun wani haihuwar, ta rungumi ɗanta Fahad da niyyar ɗan tsagaitawa da haihuwa sannan. Can kuma Allah ya azurta ta da wani cikin inda ta haifi yaro mai kama da ƙanin babanshi, hakan ya sa Ahmad ya ɗaura duk son shi kan Yaro, harta huɗuba shi yawa yaron da Zaid. Ya zamana in har Ahmad na Kano to baya rabuwa da Zaid, wankin kayanshi shi ke yi, harta goya shi yake a bayan shi, in ko ya koma Sokoto har ƙagara yake ya dawo Kano  don Zaid.
Tsakanin Sa'adatu da surikarta sai sambarka, don sa'adatu na da haƙuri matuƙa, zama da uwayen miji sai Allah, amma Sa'adatu zaune take lafiya da uwar mijinta, duk abunda take so tana mata, tana toshe duk wani hanyar da zai kawo rashin jituwa da Mamar Mijinta, kullum rana sai ta shiga ɗakinta ta share mata ta gyara mata, abinci kuwa duk da tana dafa nata amma sai Sa'adatu ta zuba ta kai mata.
Ahmad na kammala karatun shi a Sokoto ya ce aure zai yi, ashe soyayya yake yi da Iklima 'yar makwabciyarsu tun kafin ya tafi makaranta.
Mamarsu ta ce "ka bari ka fara ko da sana'a ce kafin ka ɗaɗɗago aure mana?".
Baki ya turo ya ce "ai ba za a rasa yadda za ayi ba"
Abdullahi na dariya ya ce "Mama ɗan ki fa ya so Aure, ki tattaro kuɗi kawai Hajiya a aurar da shi".
Hararsu ta yi ta ce "ku haɗe minip kai 'yan nema, kwa bari na tuntuɓi kawunku ko?".
Abdullahi ya ce "to shi kenan".
Sa'adatu tana ta tsokanan Ahmad wai ya yi rashin kunya ya ce "ke ƙyaleni na yi, in ba haka ba cutar kaina zan yi".
Ta ce "lallai yaran zamani, ashe zuwan da Ikilima ke yi gidan nan ba don Allah ba ne, gurinka take zuwa".
Ya yi dariya ya ce "ai duk ganewarki an daɗe da barin ki tasha, ni fa na fara shiri, kin san sunan da zan sama ɗiyata ta farko?".
Sa'adatu ta riƙe haɓa ta ce "a'a Allah ya baka haƙuri, tun yanzu? To wani suna zaka saka mata?".
Cikin Jin daɗi ya ce "Hauwa'u"
Ta ce "Lallai Ahmadi ba zaka ma Hajiya takwara ba?"
Ya fashe da dariya ya ce "zan manta wallahi, amma sai na yi Hauwa".
Ta ce "kana da iyayi, ji yadda kake kiran Hauwa ɗin kamar ba tamu ta gargajiya ba".
Ya ce "aa ni dai ɗiyata ba Hauwa ba ce ba, ki ce Hawwa, ki sa boko a ciki".
Ta yi dariya ta ce "Ahh, Allah ya baka hakuri, uban feleƙe daɗin abin ma Mijina ya fika bokan"
Ya miƙe ya ce "oho dai ba haka aka so ba, ƙanin Miji ya fi Miji kyau".
Ta ce "ka raina kanka in ka yi zaton ka fi Mijina kyau".
Ya miƙe tsaye ya kakkaɓe takalman shi ya ce ba dani za ki yi mahawarrar nan ba, na yi nan in Zaid ya tashi bacci zan zo na ɗauke shi".
Dariya ta yi a fili ta ce "Ahmadi ɗan Gidana."1

Ba da dadyewa ba aka yi Auren Ahmad da Iklima. Nan ɗakin kusa da na Sa'adatu Abdullahi ya gyara ma Ahmad don ya zauna da Amaryarsa.
Har Amarya tayi Sati biyu, Sa'adatu ke bata abincin Safe, Rana, Dare, har sai da Hajiya tace ma Sa'adatu "ki barta ta fara Sanwa" murmushi Sa'adatu tayi.
Da Iklima ta shigo yi ma Hajiya sai da safe Hajiya tace "Iklima, ya kamata ki fara Abinci ko?"
Iklima tace " to InshaAllah Hajiya"
Washegari kuwa ta yi Abincinta, kamar yanda ta ga Sa'adatu nayi haka tayi ta sa ma kowa a kwano.
Zaune suke Lafiya k'alau ga ba ki dayan su, suna jin dadin zamansu sosai, in dai Abdullahi zai yi cefane to k'ulli biyu zai yi, har da gidan Ahmad, breadi in zai sayo sai ya sayo har da na gidan Ahmad kasancewar Ahmad baya aiki sai dan buga-buga.
Abdullahi kan aiki Fahad da dari biyu yace kai ma Anty Ikilima, ta amsa ta lek'o godia kanta a k'asa don sosai ta ke kunyar Baban Fahad da shi take surukkuta.
Haka rayuwa ta cigaban musu, har Abdullahi ya samu ya kutsa Ahmad a wani Secondary School yana koyarwa. Iklima kuwa har yau ko barin wata bata taba yi ba, in ta nuna damuwa Sa'adatu ce ke tausarta.
Har yanzu dai Zaid dan Gidan Baba Ahmad ne da Aunty Iklima don wata rana har bacci yake a dakinsu.
Zaid na da Shekara 5 Sa'adatu ta sake haihuwar Fatima takwarar Hajia, sai ake ce mata Batul, Iklima k'arara yanzu take nuna damuwarta kan rashin haihuwarta, shi ko Ahmad ko a jikinshi, don Yaran danuwanshi sun isheshi.
Shekara bata zagayo ba Iklima ta fara Amai, ai ko ya tabbata ciki ne, murna gun su baki daya baa maganar har Hajiya.
Cikin dai ya zo mata da wahala, sosai cikin ke wahalar da ita, kullum Iklima cikin ciwo take, har ciki yafi wata 9 bata haihu ba, a ka sa ranar Aiki, kafin ranar Aikin ta haihu da kanta amma ta sha bak'ar wahala.
Kamar yanda ya dau Alk'awari ranar Suna diya ta ci sunanta Hauwau.
Hidima ba wacce Sa'adatu batayi da Iklima ba, kafin mai ma Iklima Wanka tazo ta daura ruwan Wanka Sa'adatu ta daura, da mai wanka tazo sai dai ta kwashe ruwa.
Ko da Iklima ta koma Gida, Sa'adatu bata daina mata Hidima ba, ta na lek'awa kasancewar su Makwabta.

STORY CONTINUES BELOW
Bayan 'Yan Watanni.

Transfer Abdullahi ya samu a wurin aiki zuwa Garin Kogi Lokoja,       a wurin Aiki suka bashi Gida 3 bedrooms za kuma su dauki nauyin karatun yaranshi guda 4.
Sosai danuwanshi ya tayashi Murna.
Abu daya Sa'adatu ta lura dashi, in an fara Maganar tafiyarsu Kogi, Iklima na chanza fuska, sai ta mata uzuri da k'ilan bata son su rabu ne don sun Shak'u.
Ashe ba haka bane, sai ta ji a cikin Anguwa wai Iklima na ta cewa "tun da aka ce Sa'adatu zata Kogi ta chanza, ta ke wani cin magani irin ita Allah ya daga likafarta zata bar gari, zata bar uwar MiJi" maganganu dai haka, ko kadan ba ta ji dadi ba, amma bata ce ma Iklima komai ba.
Lokacin tafiya, an yi shirin zasu tafi gaba ki daya har iklima da hajia kan suje su ga wuri, Iklima tace ba zata ba, wai zasuje kauye da mamarsu gaida kawuninta. Ahmad bai damu ba, lokacin tafiya sukai sallama da kowa suka wuce Kogi.

Gida yayi Gida, kwanan yan Kano 7 kafin suka koma garinsu, a hankali suka gyara Gida.
Fahad da Zaid suka shiga Makaranta a nan birnin Lokoja.
Sa'adatu ta shiga Islamiya nan k'asansu, har sun saba da zama su kadai, ta kanyi kewan Hajiya da  Iklima, in an danyi Sati biyu zuwa Uku, Abdullahi na hawa motan haya yaje Kano dubo Mahaifiyarshi, daidai da sau daya Iklima bata tambayan ya aka baro su Zaid ba, ko ta tambaya ya suke.
  Abdullahi ya ba k'aninshi shawara ko ya fara bussiness don ya ga kamar Teaching din nan ba zai rik'e shi da iyalinshi ba in nauyi ya k'aru mai yace ai akwai wani aptitude test da za a yi a Lagos zuwa k'arshen wata yayi applying, in Allah ya sa da rabo za su nemeshi, adduoin Fatan Alheri ya ma danuwanshi.
  Allah cikin ikon shi a ka nemi Ahmad, ya hau hadadar hada kudin Motar da zai je Kogi, Hajiya da Iklima suka mai fatan Alheri, ya tafi Kogi, dadi kashe Fahad da Zaid ga Baba Ahmad, a Dayan dakin aka saukeshi wanda Katifa kadai ce a ka yada Amma dakin share yake fes.
Rannan kusan kwanan zaune Ahmad da Abdullahi sukayi suna fira, randa Ahmad zai tafi Abuja don daga nan zai sami motar Lagos, Abdullahi ya dauko kudi dubu biyar ya bashi, ya dauko Kaftan riga da wando kala biyu da hula yace "ka saka, kasan in za a yi job interview sai ka shirya sosai".
Ahmad yayi dariya yace "nagode"
Abdullahi ya kai k'anenshi Tasha tare da mai fatan Alheri.
  Su Sa'adatu ba sa zuwa kano sai da dalili kamar Sallah, Rasuwa sai Biki, in sun zo bai fi suyi kwana 7 ba sai su koma, wannan abu na ma Iklima ciwo, Sa'adatu ta lura Iklima ta chanza kwata-kwata ba Iklimar da ta sani bane, don ko tsarabar da ta ma Hauwa Iklima ba ta wani nuna jin dadi ba sai 'Madallah' da tace, to Sa'adatu bata wani damu ba don ta san ba zata fi Sati a Kano ba.

*A GURGUJE*

Ahmad ya sa mu aiki a wannan Masanantar, kuma sosai yake samu, a nan branch din Kano a kayi Posting dinshi. Ahmad ya fara samu sosai har dangi sun fara shaidawa, domin shi dan fachaka ne, shi dai kawai a ji dadi, da ya kwashi Albashi sai ya shiga dangin Babansu da na Mamansu duk yayi ta musu Alheri, harta dangin Sa'adatu ya kan aika musu da buhun Shinkafa yace inji Abdullahi wanda be ma san yanayi ba.
Ahmad ya kan tura ma Abdullahi kudi ba wai don shi bai dashi ba, aa saboda Alheri dank'one.
Iklima tace "wai kai yanzu meye abun tura ma Baban Fahad kudi, ya fi ka Kudi fa".
Yace "Lallai Iklima, meye don na tura mai kudi?".
Tace "ba laifi, amma banga amfanin k'ara ma mai k'arfi k'arfi ba".
Yace "kin ban mamaki Iklima, ai banyi zaton ko Albashi na dungurudum na dauka na ba Abdullahi zakiyi magana ba, kar ki manta, kudin motar da naje Lagos interview Abdullahi ya bani su, ke harta kayan da na saka naje Interview kayan Abdullahi ne".
Ganin ya dau zafi ya sa tace "Allah ya baka Hak'uri".

Sa'adatu ta sake haihuwa, mace ta samu, da labari yazo Kano Iklima da wani daci tace ma Hajiya "ashe Sa'a ciki gareta?" Hajiya tace "da ba ciki da ta haihu?" Ta6e baki Iklima tayi.
Da akayi maganar 'yan zuwa Suna, Ahmad yace "Ni zan yi shatar golf biyu aje suna a dawo"
Hajiya tayi ta sa mai Albarka. Iklima dai duk taji ba dadi a ranta.
Haka a ka cika Motoci biyu da Mata suka je Suna Kogi suka dawo. Iklima sai k'ananun maganganu take tayi.
****

Duk Sallah sai ya ma Zaid da Fahad kaya irin nashi ko kala nawa zaiyi, Batul kuma irin 'yan katin da ya sayo ma Hauwa shi yake siyo mata.
Sa'adatu kuma ya bata 5k yace ta siya abunda ranta ke so.
Burin Ahmad ya Kyakyautata ma Yayanshi Abdullahi, be son me zai yi ba ya sa Yayanshi jin dadi, kawai ya yanke hukunci, ya yanke hukuncin mallaka mai Hauwa, da daddare ya samu Hajiya da maganar.
Hajiya ko ta ji dadi tace "amma ka yi tunani, Abdullahi kau zai ji dadi, kaga sai Sa'a ta hada ta rainesu tare da Batul".
K'warin guiwa ya samu sosai ya mata sai da safe ya shiga Daki.
Iklima na ba Hauwa Abinci ta na kuka.
Ya mik'a hannu ta bashi ita yace "Hauwa ya dai?".
Iklima tace "wai Abinci me ba ta so, ita ba ta da abokin fada irin Abinci?".
Yayi dariya yace "to sai a mata dure in bata ci?"
Tace "ba ta san abinci"
Yace "amma na ga da bikin Falmata suna ci da Batul harda wawa sukeyi".
Tace "hadama ne, in dai zata ci da yara 'yanuwanta to za ta dan ci da yawa, amma in ita kadaice to sai dai ta ba dadi za ta ci".
Yayi dariya yace "ki hada mata kayanta"
Tace "ina zamu?".
Yace "ina zata dai, Lokoja zan kaita".
Dan jim tayi kafin tace "hutu zata?".
Yace "aa, Abdullahi zan kai ma diyarshi".
Tace "ban gane ba?".
A takaice yace "Hauwa zata koma Gidan Babanta Abdullahi, diyarshi ce, tsakaninmu da ita in sun zo Sallah dai kamar yanda suka saba".
Hankalinta in yayi dubu ya tashi tace "Kai Ahmad bangane ba".
Yace "donAllah ki hada mata kayanta da wuri da Asuba zamu tafi".
Tsalle tayi ta dire tace "ba ka isa ba, ba inda zaka tafin man da diya".
Yace "zancen kike so, gobe war haka Hawwa na gidansu".
Tace "Wallahi Allah baka isa ka rabani da tilon diyata ba, ba ka isa ba Ahmad, wallahi Allah baka isa ba".
Mik'ewa yayi ya aje Hawwa yace "Za mu ga ni da ke wa ya fi Iko a kan Hauwa".
Nan ta dinga surfa ruwan Bala'i tace "Duk munafuncin da aka k'ullo ma ba zai yiwu ba, ba inda Hawwa zata tafi".
Yana jinta bai tanka ba a ranshi yace "zan ko nuna miki isa ta".1

#HIklima ta kasa zaune ta kasa tsaye duk ji tayi Duniyar na juya mata, ta na ji ya dawo ya hau gado ya kwanta amma sam bacci bai zo mata ba, bacci ya gaggareta.

4/6/2000

Asubar Fari taji tashin shi, ya fita Masallaci, ita dai mamaki kawai, kamar kullum bayan yayi Sallah ya nufa dakin Hajiyarsu.
Da k'yar Iklima ta tashi ta fito ta dauro alwala tayi Sallah.
Ta na kan darduma ya shigo, ido ta bishi dashi ta ga ya nufa Toilet.
Ba da dadewa ba ya fito yana tsane kanshi, ya shafa Mai ya fito da Kaftan ya ajiye a kan Gado.
Boxers da Singlet ya saka kafin ya nufa inda Hauwa ke kwanciya ya dagata chak ya sa ta kan Kafadarshi yana bubbuga bayanta a hankali.
"Hauwa, bude ido".
A hankali ta bude ido da alama bacci be isheta ba, tsoro ya mamaye Iklima ganin da tayi ya shiga Toilet da ita da alama Wanka da Brush zai mata.
Ta na zaune kamar wacce aka dasa a gurin har suka fito ya nadota a Towel ya daura kan Gado, ya dauko Man shafawa ya shafa mata kafin ya bude Drawern ta ya ciro mata riga da wando 'yar kanti, ya dauko Sweater ya saka mata da dan Himar.
Sai a Lokacin ya kalli Iklima yace "baki hada mata Kayan ba ko Iki?".
Kamar jira take ta fashe da Kuka ta gangaro har inda suke zaune ta na kuka tace "donAllah Ahmad kar ka rabani da ita, ita kadai gareni Ahmad donAllah ka min rai".
Tausayinta yaji sosai, ya sauko da Hauwa daga kan Gadon yace "je dakon Hajiya ki sha Tea".
Gari ya fara wayewa kuma akwai Wutan da ya haska Tsakar Gidan baki daya, Hauwa ta ruga dakin Kakarta don shan Tea.
Ahmad ya tattaro Iklima Jikinshi ya hau lallashi.
"Ki fahimceni Iki, ba wai san rabaki da Hauwa bane, ba wai zan yi haka bane ko don na nuna isa ko fin k'arfi, tabbas Hauwa ita kadai garemu, amma da wayon mu ko dabara? Aa babu, Allah da ya bamu ita, shi zai sake bamu wata, wasu da yawa ma InshaAllah"
Nan ta dubure ta hau Masifa tana wallahi ba zata bar Hauwa ta tafi ba.
Banza yayi ya k'yaleta kafin ya mik'e ya dauko dan Akwati zai hada kayan Hauwa ta yi tsalle ta dire tace wallahi ba zata bada kayan Hauwa ba.
Kafadu ya daga yace "kin manta yaron da Kudinshi?" Ya dau Wallet dinshi ya saka a Aljihu ya nufa dakin Hajiya.
Ta rufa mishi baya
Lokacin Hauwa har ta gama shan Tea and Bread.
Iklima tace "Hajiya wai Ahmad Lokoja zai kai Hauwa?".
Hajiya tace "Iklima ba gaisuwa?"
A hasale tace "wa ke ta gaisuwa yanzu?".
Ahmad ya girgiza kai yace "Kulll Iklima".
"Wani Kul? Kul na me? Cutata fa zakuyi? Kun hada baki, zaku zalunceni".
Jikin Hajiya yayi sanyi tace "Ahmad ko zaka bar tafiyan, Allah barshi in ta dan k'ara wayau sai a dinga kaita Hutu"
Cikin wani irin yanayi Ahmad yace "Aa Hajiya, donAllah aa Hajiya, mu mun tafi ki mana Addua donAllah"
Hajiya ta sauke ajiya zuciya tace "Allah ya tsare ya kaiku lafiya, ya tsareku daga sharrin K'arfe, Mutum ko Aljan"
Ameen ya amsa tareda daukan Hauwa ya fita, kamar Mahaukaciya ta rufa mai baya tana ta zabga Zagi.
Ko warming Mota be tsaya yi ba ya fice daga Gidan.
Suna fita ta zube k'asa tare da fashewa da wani irin Kuka.
Tsallaketa Hajiya tayi ta shige daki, Iklima ta mik'e a fusace ta fita daga gidan bak'in ciki kamar ya kasheta.
Gidansu ta fada, Babanta na kan Kujerar da ya saba Zama duk bayan Sallahr Asuba, yana ganin yanayinta ya san cewa ba Lafiya, rik'ota yayi ya tambayeta me ya samu Ahmad din?
Cikin Kuka tace "wai Baba saboda Zalunci, Ahmad ya dauki Hawwa wai zai kai ma Abubakar, wai ya bashi ita duka, kamar wani kaya".
Ido kawai Baban ya bi ta dashi kafin chan yace "to sai mene? Wai Iklima meke damunki? Yaushe zaki yi hankali?"
Cikin k'unan rai tace "Baba wai ta yaya zaiyi kyautar diyar da ita kadai garemu? Yaushe muka sameta ma balle ya bada ita?".
A tak'aice yace "fitar min daga Gida"
Zata sake magana ya daka mata tsawa ta fita a guje ko gun innarsu bata shiga ba.
Yinin Ranar Iklima duk ta susuce ta fita hayyacinta, ta dauke ma kowa wuta dif.

L O K O J A

Karf'e uku yara sun dawo daga Makaranta, Sa'adatu ta zubo musu Abinci suna ci sukaji Sallamar Uncle Ahmad, da gudu suka bar abincin suka nufeshi don mishi oyoyo.
Ganin ba shi kadai bane ya sa Fahad tarbo Hawwa, Batul ta rungume k'afafunwan Uncle Ahmad shi kuma Zaid ya chabeshi sama suna murna.
Sa'adatu ta lek'o tace "wai wai wa nakeji kamar Ankul Amadidi?" Dariya yayi yace "mune Matar Yaya".
Ta karbi Hawwa tace "Harda su Hauwa? Ina Iki din?" Uncle Ahmad yace " suna Kano da Hajiya duk suna ta gaishe ku" "muna ta amsawa, bismillah" ta yi gaba ya bita baya ta bude Parlon ya shiga ya zauna yaran duk suka yayyabeshi,l okaci kadan sai gashi ta gabatar mai da Abincin Mijin nata, tace "ku je ku ci Abinci mana kar ya huce" suka dan choge tace "Uncle Ahmad din ba tafiya zaiyi ba kwana zaiyi, ku je ku ci ku barshi ya huta sai ku mai firan ko?" Da k'yar ta samu suka fita, ta tura Hauwa wurin Batul tace kuje ku ci tare in kun cinye sai a k'ara muku, na san na sa miki naki ke kadai baci zakiyi ba".
Uncle Ahmad yace "to ke Madam haka akeyi? Abincin Maigidan zaki bani?" Tace "kai dai kaci ban son gulma, kafin ya dawo zan tuk'a mai wani" yace "oho ni dai ko yanzu ya dawo abuncin nan nawane zance dama bakiyi dashi ba" tayi dariya tace " k'annin Miji Ho" ta fita shima dariyar yayi ya sauko k'asa don kwasan tuwo.

STORY CONTINUES BELOW
Biyar ta wuce Baban Fahad ya dawo, da murna yaranshi suka gaya mai Uncle Ahmad yazo, ya dauki Hauwa yana tambayarta Hajiya da mamarta, bata bashi amsa ba, da faraa ya karasa parlo inda k'anenshi ke zaune, a mutunce suka gaisa yana tambayarshi mutanen Gidan.

Kwanan Uncle Ahmad Biyu a Lokoja yayi haramar tafiya, sai a ranar da zai tafi ya ke sanar dasu duka cewa ga Hawwa nan ta zama mallakinsu.
Sa'adatu ta kasa daurewa tace "wai Ahmad ina Iklima? Matsala kuka samu?" Ya girgiza kai yace "ko daya, raayi na ne na ba wa Yayana Abunda na fi so a rayuwata, kaunar da zan nuna mishi kenan, na san kuma ke zaki riketa kamar su Batula, shiyasa ban da fargaban komai Sa'adatu".
Sa'adatu tace "ni ba wai ba zan rik'eta bane, aa kawai dai na san duk yanda akayi ba k'aramin tashin hankali akayi da Iklima ba kan rabuwarta da Hauwa, gashi ba ta da kowa a gabanta".
Ahmad yace "kar ki damu da Iklima, ba matsala bace".
Zata sake magana Baban Fahad ya girgiza mata kai yace "mungode kwarai Ahmad, Allah ya bamu ikon bata tarbiya, Allah ya bar zumunci".
Ahmad yayi godiya sosai, ya ciro kudi mai tarin yawa yace "a ma Hauwa da Batul Siyayyan kaya don kayan Hauwa na Kano".
Sa'adatu tace "Allah amfana angode".
Hauwa Wurin tafiyar Babanta ta sha kuka sosai daga nan sai ta yi bacci, da kuma ta tashi ta manta.

A kwana a tashi ba wuya gurin Allah.
Baban Fahad ya saka Hauwa a makarantar su Batul, komai iri daya yake mata da Batul, babu bambanci.
Ba abunda ke kai su Kano, sai da dalili kamar Biki ko Sallah ko Taaziya, randa Hauwa ta fara Zuwa Kano bayan komawarta Lokoja k'in zuwa gurin Iklima tayi, Iklima taji haushi sosai don har kuka tayi, ta sami Sa'adatu a daki tace "Lallai Sa'adatu, kun shiga tsakanina da diyata, na zo zan dauketa kamar ta ga Dodo sai kuka? Amma Allah sai ya saka min".
Sa'adatu tace "Iklima ki gaya min meye laifina? Ki min adalci, ina zaune a ka kawo min Hauwa, Mijinki ya kawota da kanshi, sai ince ku koma? Yace ya ba Abbakar ita, ni meye nawa? Gidana ne? Sai ince ba zan rik'eta ba? Meye nawa tsakaninki da Allah?" Cike da bombotai tace "oho dai, abunda kuka min sai Allah ya saka min" Sa'adatu bata sake cewa komai ba har Iklima ta gama ta fita.
****

Sa'adatu sosai take kula da Hauwa tsakaninta da Allah, duk da Hauwa irin sakatattun yaran nan ne da shagwaba tayi mata yawa bata magana lafiya lau sai ta hada da kuka, da ko Baba ya ji tana kuka da ya fito jiki na rawa ya dauketa yana lallashi "wa ya saki kuka Hawwan Baba?" Cike da shagwaba tace "Jaid ne" Baba kuwa ya kama Zaid ya buga son rai, babu mai kwaban Hauwa saboda da an mata fada sai kuka, so da yawa zaayi abu da rana ba zatayi kuka ba sai ta jira yamma lokacin da Baba zai dawo aiki, da taji tsayuwar Motar shi zata nufi garage tana kuka tace "Batul ta bigeta, ko Mama ta mata fada" In Batul ne ya kamota ya shaudeta, in kuma Mamar ce sai yayi ta Tijara da fada don an bata ma Hauwa.
Kuma har gobe in Sa'adatu taje Kano sai Iklima ta yada mata magana kan Hauwa.
Sa'adatu tun tana hak'uri har dai rannan gaban Iklima ta ce ma Ahmad "Ahmad, DonAllah don Annabi ka ce ma Iklima ba da sanina ka kawo Hauwa Lokoja ba, ba ka yi shawara dani ko da Abbakar ba, wai ni kullum raina sai ya baci kan Hauwa?" Ahmad sai ya kalli Iklima yayi k'wafa yace "Sa'ar Mata donAllah abun nan ya daina damunki, Hauwa ta kuce, haihuwarta kawai Iklima tayi, amma ta kuce, ki daina kulata".
Iklima ta dinga cika tana batsewa.

Shekarun Hauwa 12 a Lokoja, har ta yi JSCE, Baban Fahad ya kira Uncle Ahmad yace "Ya kamata Hauwa ta zo hutu gurin Uwarta ko tunda sun samu long Vacation" Ahmad yace "saboda me Yaya?" Baban Fahad yace "Ahmad Mahaifiyarta na da rai ba wai ta mutu bane, kar ka manta tana da hak'k'i a kanta, ba zai yiwu ace wai sai munzo Kano biki ko Sallah zata ga Mahaifiyarta ba, kuma ma ba wurinta take zama ba, Ahmad akwai Hakki, hutune na kusan wata 3, a matsayina na Ubanta, zan kawota tayi hutu wurin Mahaifiyarta" Ahmad yayi dan Jim kafin yace "harda Batul ko?" Baban Fahad yace "ai Batul na Makaranta, SS2 take, su basuyi hutu ba, dama hutun na Js3 and SS3" kwatakwata beji dadi ba amma yace "Shikenan Allah ya kawo ku lafiya".
Dama Hauwa ta san Umma ba mamarta bace, saboda zuwa Kano dubu sai Iklima ta gaya mata cewa ita ce uwarta tun tana k'arama aka rabasu.
Tamfatsetsen Gida Uncle Ahmad yayi a wata Unguwar 'yan gayu, ba yanda beyi su koma chan da Hajiya ba, Hajiya tak'i, sai dai ya mata renovating Gidan ya rushe ya masu Ginin Zamani, Flat 2 yayi, sai BQ,Hajiya tace "ita BQ din zata zauna, a bar ma Abbakar da Iyalanshi Flats in sunzo, mai taya Hajiya zama Ahmad yaje ya dauko cikin dangin Hajiya, so ko kadan Hajiya bata da kadaici, shi ko Ahmad kudi zuwa mai yake ko ta wani lungu da sak'o, in ana kiran masu kudin Kano sai an sako Ahmad Danbatta a sahun farko.
Burin Iklima ya cika ta koma Unguwar Masu Kudi, ta fara mu'amala da matan Manya, nan  da nan tayi Clean.

STORY CONTINUES BELOW
Zuwan Hawwa Kano ba k'aramin farinciki yasa Iklima ba, ko da yaushe zaka ganta cikin kazar kazar, kullum cikin tambayarta "me Sa'adatu ke miki? Tana dukanki? Tace "aa" yaran fa?" Sai tace "ko harara na yayi Baba ya kamashi sai ya duke shi, ni ai Aunty duk wanda ya bugeni Baba sai ya mai Shegen duka" ba haka Iklima ta so ba, ta so a ce cuzguna ma diyarta akeyi, ta samu dalilin cewa ba zata koma Lokoja ba amma bata da wata hujja.
Sai da Hawwa tayi wata 2 a Kano kafin ta koma Lokoja sai dai wannan karon Hawwa ta chanza sosai, rashin kunya da shegiyar k'arya da makirci, ko yaya ne ka dan bata mata rai zata fashe da kuka tayi ta ihu wai ka bigeta Baba ya sameku ya shaudeku, ba wanda bata kunsa ma bakinciki sai Ya Fahad, shima don tana tsoronshi ba ya mata da kyau, don duk randa Baba ya bigeshi ta kan ita, samunta yake ya rama shiyasa bata shiga sbagarshi.
Akwai ranar da Batul sukayi dambe da Hauwa ta kan Socks din Makaranta, Batul tace na ta ne, Hauwa kuma tace ita ta wankeshi sai ta saka yayi datti kamar yanda ta daukeshi,Batul ta buk'aci ta bata abunta Hauwa ta k'i bata, Umma tace "Batul ki bar mata" Batul cikin zafin rai tace "Mama na bar mata fa kikace, to wanne zan saka? Wallahi sai ta bani" ta hau kiciniyar kwacewa har dai ta ture Hauwa k'asa.
Da Hawwa ta fasa wani irin Ihu sai da Baba da ke bacci a dakinshi ya fito a gigice, yana shigowa yaga Hawwa na birgima be tsaya jin baasi ba ya rufe Batul da duka, saboda zuciya da ya dauketa ya jefar sai da ta bugi madubin dakin da ya dan yanketa tuni Jini ya wanke mata hannu, ya sake nufarta da niyyar cigaba da dukanta, Sa'adatu bata san Lokacin da ta sha gabanshi ba, ta na mai girgiza kai, ta na Kuka, kasheta kake son yi Baban Fahad? Dubeta ba ka ganta cikin Jini ba? Turus ya tsaya, sai a lokacin ya gane ta'asar da yayi, Idon Saadatu yayi jazur, har Hawwa ta tsorata da ganin Umma haka don kukan da takeyi ma dainawa tayi ta lab'e bakin Gado.
"Abubakar kaji tsoron Allah, ace kullum kai saboda Hawwa kake yanke danyan hukunci? Ji abunda ka ma Batul, ba ka san me ya faru ba amma aa don Hawwa na kuka kake neman nakasa min ita, ba'ayi sati daya ba da kama Zaid dukan tsiya ta kan Hauwa, Zaid dai da yake k'okarin Shiga Jami'a be wuce duka a gunka ba in dai ya bata ma Hauwa to ko shi ke da gaskia haka kake kama shi kana laftarshi, kai harta ni sai dai in ban ma Hauwa Fada ba, ka dinga tijara cikin gidan nan kana bata mata kowa rai, k'ila da da hali nima da ka dakeni ta kan Hawwa, haka ne soyayyarka ga Hauwa? Hakan da kakeyi shi zai sa mutane suce ka mata gata? Ko kuma bata wahala gidanka ba? A ce bacin raina da na yarana ta kan Hauwa ne? Kulluk uwata na zagina ta kan Hauwa? Me mukayi ba daidai ba donAllah don Annabi, Abbakar kaga baya ga so biyu ban sake dukan Hawwa ba, Abbakar kar ka k'ara dukan yarana ta kan Hauwa, su ma ai 'ya'yane"
Duk jikin shi yayi sanyi, yaji garin ya mai Zafi ganin Batul kwance sheme kamar ta suma ya sa shi cewa "Sa'adatu ki dan duba Batul" ko kallon inda Batul take Umma batayi ba tace "ba zan dubata ba" ya dai k'arasa gunta a tsorace ya taba jikinta tuni massasara ya rufeta cike da damuwa yace "donAllah gyarata muje Asibiti" ko kallon wurin ba ta yi ba tace "ba zanje ba" Baba ya tsorata da lamarin Umma amma sai ya yarda da cewar Hausawa na mai hak'uri bai iya fushi ba, k'wala ma Fahad kira yayi ya shigo jiki a sanyayye yace "je ka ta da Mota".
Haka Baba ya sabi Batul ya fita da ita, Hawwa ko duk ta sha jinin Jikinta ta tsorata sosaim, bata taba ganin Ummansu haka ba.
Makarantar da baaje ba kenan.5

Wani Iftila'in da ya faru a k'arshen Shekara shine Gwamanati ta rufe Maaikatar da Baba ke aiki, wai Chinese Company sun siya Maaikatar tasu, tashin hankali Baba ya shiga, da ya gaya ma Uncle Ahmad sai ya tausheshi da cewa Alheri ne inshaAllah, ya dawo Gida Kano kawai ya samu wani aikin don lokacin retire din nashi beyi ba, Hajiya ma cewa tayi ina laifi Zaman Bariki har Shekara 15? Su dawo Gida haka nan, Allah ya sanya ma zaman da sukayi Albarka".
Duk sun damu amma Baba ya nuna musu ba wani abu inshaAllah.1

Baayi wata uku ba suka tattaro suka dawo Gida Kano, dama Gidan na Maaikatar ne bana Baba ba.
Duk Uncle Ahmad ya chanza musu furnitures, dakin samari da dakin 'yanmata, dangi na ta zuwa musu sannu da zuwa suna musu fatan Alheri, Iklima tazo yin musu Allah sa Alheri, da zata tafi tace "yau yanmatan Umma muje ku min kwana mana?".
Hauwa ta kalli Batul Umma tace "ku dauki kala biyu ku je" da murna suka nufa dakinsu don ciro kayansu suka bi Anty Iklima harda auta Husna.
Baa dade ba Uncle Ahmad ya kawo form din best school a Kano ma Batul da zatayi SSCE, Hauwa da take SS1 sai Husna da zataje Js1, Zaid dama bai samu JAMB ba yana jiran wata shekara ya sake zanawa, Ya Fahad kuwa ya gama Polytechnic a Chan Lokoja ya samu Diploma.
Allahu Aaalam Allah kadai ya san me Iklima tace ma Hauwa, rana daya Hauwa aka nemi Hauwa aka rasa ashe ta kwashi kayanta ta koma wurin Mahaifiyarta, Uncle Ahmed ya ga ta shigo da Akwati yace "Hawwa yadai? Tace Baba nidai ma dawo wurin Mamana" wani tsawa ya daka mata yace ta koma gida, ta k'i kamata yayi ta gashi ya jata ya maidata Gidan Baba Abbakar, Hauwa ta dinga tijara kamar yarinya tana kuka harda birgima a k'asa wai ita a maidata wurin Mamarta.
Haka Hawwa ta tara mutane tana kuka, Uncle Ahmad yazo zai daketa Baba ya hanashi, kusan so 3 tana guduwa yana maidota, karshe dai har Uncle Ahmad ya kamata ya mata dukkan tsiya.
Hawwa ta tsane kowa, gidan nan ta hana kowa kwanciyar hankali.
Rannan aka taru meeting, kowa ya hallara, Uncle Ahmed hankalinshi tace saboda sabon dabi'ar Hawwa, Iklima ko tana zaune tana karkada k'afa, duk a kan dai an hana Hawwa ta dawi gunta.
Baba ya kalli Hauwa yace "Hauwa me muke miki ne da ba kya so? Hauwa me ya sa kike gudunmu? Tun kina 4years meyasa sai yanzu zaki guje mu? Hauwa kin min adalci? Irin son da nake miki Hauwa ni yanzu kike gudu? Cike da rashin kunya tace "ni baka min komai ba, ba wanda ya min wani abu, ni dai kawai a maidani wurin Mahaifiyata tun da dai da ranta, ba mutuwa tayi ba".
Cike da zafin nama Uncle Ahmed ya tashi Hajiaya ta dakatar da shi ta hanya kiran sunanshi.
"Ahmed, kar ka sake dukan Hawwa, ka barta, Hawwa ki kwashi kayanki ki bi Mahaifiyarki, ba ta mutu ba da ranta".
Cike da tashin hankali Uncle Ahmed yace "Hajiyaa!!"
Hajiya tace "Babu dalili Ahmed, me suka mata? Me suke mata haka da yarinya tun tana shekara 4 take gunsu rana daya ta guje su, kai kasan akwai abunda uwarta ta ke kitsa mata"
Iklima tace "yo ni me na je kitsa mata? Ai babu yanda zaayi a raba uwa da yarinyarta ayi tunanin zaa kwana Lafiya, ai abunda Sa'adatu da Yaranta suka ma Hawwa sai Allah ya saka mata".
Cike da zafin rai Saadatu tace "Ni da Yarana? Me muka mata Iklima? Me muka mata?" Baba yace "Saade ki shiru" tace "uhm uhm Baban Fahad bari ta gaya mana, Hawwa me muka miki? Bana baki abinci? Ko aikin gida na duka ke kikeyin shi? Me muka miki Hawwa? Wallahi Tallahi Ahmed, Shekarun Hawwa 13 a Lokoja so biyu kachal na taba dukanta, Abbakar kuwa so daya be taba dungurinta ba, sai yawan fadan da sukeyi da Batul sai Zaid, wanda da ta kai su kara Yayanka sai ya mana wulakanci duka, Ku Kalla tabon da ke jikin fuskar Batul da shi zata koma ga Mahaliccinta, Babansu ya ji mata ciwo ta kan Hawwa, ku dubi jikin Zaid dul ya fashe saboda mugun bugun da Abbakar yake musu in dai ta kan Hawwa ne, Gidan nan wallahi ba wanda bai tsoron sa6a ma Hawwa, saboda matukar Hawwa tayi kuka hankalin kowa a gidan nan ba kwance yake ba, ki gaya min mai muke yi ma Hawwa?".
Iklima tace "humm a dai bar maganar, amma cuta ai kun cuce mu, wata shariar sai a Lahira".
Saadatu ta mik'e zuciyarta har k'una takeyi tana magana tana sarkewa tace "Iklima, idan ni ko yarana mun zalunci Hawwa Allah ya saka mata tun a duniyar nan".
Ahmed ya girgiza kai cike da takaicin Hawwa da uwarta kamar yayi kuka yace "Don Girman Allah kiyi hakuri Saadatu, Hawwa diyarki ce, ko yankar namanta kikeyi ba mai ce miki don me, ba wacce ta isa ta rabaki da Hawwa".
Saadatu tace "aa Ahmed nagaji, nagaji wallahi, ace ni da yarana bamu da wani bak'inciki sai na Hauwa da Iklima? Nagaji".
Baban Fahad yace "Sa'a nace ya isa" ya ja numfashi  yace "Ahmad, ka barta ta tafi, Hawwa ta koma gun Mahaifiyarta, duk randa Hawwa tayi kewarmu, ta san inda zata samemu".
Uncle Ahmed yace "Yaya kayi Fushi ne?".
Abbakar yace "Aa haba dai, hakan dai ina ganin shine mafi a ala, kuma zai fi ma kowa kwanciyar Hankali".
Hajiya ma ta nuna goyon bayanta ta sake tofawa, nan dai aka yanke hukuncin Hawwa ta koma gun Iklima.
Uncle Ahmed dai be ce ma kowa komai ba ya fita.
Kamar jira Iklima da Hauwa suke suka rufa mai baya.
Zaid dai zuciyarshi zafi kawai takeyi.
Haka dai taro ya tashi.
***
Da k'yar aka samu Ahmed ya fara sake ma Hawwa da Mamarta da duk ya kullesu, haka dai a ka cigaba da rayuwa.
Uncle Ahmed ke biya ma su Batul da Husnah Makaranta, duk abunda ya siyo ma Hawwa sai ya siyo ma su Batul.
Driver ke daukan Hawwa ya biyo ya dauko su Batul kafin ya wuce ya kaisu makaranta.
Iklima taje Makarantarsu ta chanza ma Hawwa Suna daga Hauwa Abubakar zuwa Hauwa Ahmad, randa Uncle Ahmed ya gane sai da ya ma Anty Iklima saki daya, Aikuwa Hajiya da Baba suka saka ya maidata amma bata mak'iya kamar su.

A kwana a tashi.
Rayuwarsu ta chanza gabaki daya, zumuncinsu yayi rauni amma banda na Iyayensu, Hawwa bata zuwa gaidasu Umma, sau da yawa sai tazo unguwar gidan kakaninta mahaifan Iklima ta bi ta k'ofar Gidan Hajia amma bata shiga, ba ruwanta da Husnah da Batul ko sun hadu a School, bata masu magana, har Batul ta gama Makarantar, Kamar ba Hawwan da suka sani ba, duk ta chanza, to suma dai sai suka ja baya, kullum korafin Uncle Ahmed bai wuce kan su Batul ba sa son zuwa Gidanshi, to gidan ne ya fi karfinsu, su je ko tayin ruwa ba a musu, a ma bar su a parlo har sai sun gaji su tahowarsu. Zaid ko kullum yana Gidan don binibini Uncle Ahmed zai kirashi yaje. Uncle Ahmed ya samo ma Zaid Admission a Northwest University, Fahad kuma yayi joining BUK sun bashi DE level 2.
Shariyan Iklima ko Hawwa baya damun Zaid don dukansu biyun ya musu wuri ya aje, in yaje Gidan abunda ya kaishi kawai yakeyi ya dawo ba ruwanshi da su.
Uncle Ahmed ba ya jin dadin abubuwan da ke faruwa tsakanin Matarshi da Matar Yayanshi duk da ya san Sa'adatu bata da matsala kwatakwata.
**
Wata rana Ana Bikin diyar k'anwar Hajiya a Jambulo, dangi duk an hadu ana cin yinin biki, Sa'adatu na zaune kan tabarma da wasu kawayenta, ta ji Iklima na ba Matar dan k'anwar Hajiya labari "Ai in gaya miki Hawwa duk bata da kunya, matsayina na Mahaifiyar Hawwa ban isa in sakata aiki tayi ba, Hawwa k'uiwa, Hawwa kazanta, Hawwa Mita, kin ga Hawwa shekarunta 16 amma bata iya abinci ba, ke tsintsiya Hawwa ba ta iya rikewa ba, ba ta iya komai ba a matsayinta na diya mace, hmm ai ni tsakanina da Saadatu sai Allah ya isa, ta lalata min yarinya bata da wani mamora".
Zuciya taci Saadatu ta nufo su tace "Iklima, ni kike yi ma Allah ya isa? To Alhamdulilah ni dai ban ma Hawwa tarbiyan banza ba, baace Hawwa na sata ko bin maza ba, kuma nagode Allah baa ce na maida Hawwa Baiwa ba, ko ace duk wahalar gidana ita ke yinshi, to Iklima Hawwa dai ta dawo gabanki ko? To duk wadannan abubuwan sai ki koya mata, ki mata tarbiyar da kike so".
Iklima tace "yo ai Icce tun yana karami ake tankwarashi, ta riga ta rik'a yanzu, ai kun gama cutata"
Zata tanka  wata cousin dinsu Baban Fahad ta hanata tace "Haba Saadatu, bamu sanki da haka ba, ya zaku tsaya kuna chachan baki a gidan biki?"
Saadatu ta fashe da kukan bakinciki tace "Ya zanyi Yaya Zulai? Da da muke tare da Hauwa ban huta da maganarta ba yanzu ma da bama tare ba zan huta ba? Kullum Iklima mula hadu sau tace na lalata Hauwa?Me Iklima take so nayi ne?".
Jan Saadatu akayi aka kai ta dakin Uwar biki ana lallashinta, yan fadar Iklima kuma suna gabanta suna neman suna ko zata basu wani abun.
Haka dai rayuwar ta cigabar musu har zuwa yau
Wannan Kenan.

7/

NASSARAWA

Nan dakin Inna Aka saka bikin Watty da Ya Bu, Sati biyu cur, ba ai wani dogon shiri ba, aka daura Auren Hauwa da Abubakar a nan Baban Gida, aka dauko Amarya a ka kai Flat din da Ya Bu ya kama a Hayin Gada, Babanta ya mata kaya daidai iyawanshi.
Ranar da aka kaita ranar Ango ya shigo dakin Amarya.Watty ta buɗe idonta da ƙyar, 5:20am, da sauri ta gungura toilet tayi wanka kafin tayi Alwala ta fito ta nufi akwatinta ta ciro wata Jallabiya ta saka Hijab ta tada kabbarar Sallah, kamar kullum sai da tayi Raka'atainil Fajr duk da ta makara kafin tayi Sallahr Asuba, bayan ta gama ta yi Zikr, ta kalli Agogo taga ƙarfe 6 ta tashi ta linke hijabinta da Jallabiya, ta hau Gado tana mai kallon Ya Bu da ke ta bacci cikin kwanciyar hankali, murmushi ta yi tana jin Son shi na shigarta, ta koma bacci don a zatonta har masallaci yaje ya dawo ya kwanta, don ya barta ta huta shi ya sa bai tadata Sallah ba, komawa ta yi ta kwanta wani baccin.

Ba su suka farka ba sai ƙarfe 10:40am, miƙewa ta fara yi ta shiga toilet ta sallo wankanta tare da yin brush, ta fito ta nufi mirror ba tare da ta kalle shi ba, shi ma ba tare da ya kalleta ba ya shige toilet.
Ta shirya tsaf cikin riga da skirt ɗinta na atamfa, ta feshe jikinta da turare, ya fito ɗaure da ɗan tawul, kallo ɗaya ta mai ta ɗauke kai, murmushi ya yi ya zura kayan shi, kafin ya ɗauki darduma don yin Sallah, ji tayi ya burgeta don tabbas Sallahr Walha zai yi, Allah sarki Ya Buu akwai Ibada.

Breakfast ya fita ya samo musu, tana zaune ya dawo, ya shiga kitchen ya wanko plate da spoon ya haɗo musu da tray, cike da ƙauna suka yi  kalaci. A zuciyar Watty tana ji tafi ko wacce mace sa'a a duniya, haka ta dinga biye ma Ya Bu suka sha Soyayya.
Suna zaune a Parlo har Azahar ta yi, sallamar Aisha da wasu 'yan'uwansu ya sa Ya Bu Shigewa ɗaki, abinci da ragowan kayanta suka kawo mata, Aisha ta dinga zolayan Watty wai har ta yi ƙiba, ko dai har ta ɗauki cikin ne? Dariya kawai Watty take yi, suna gidan har bayan Sallahr Laasar kafin suka tafi.
Watty ta idar da Sallahr La'asar ta ce bari taje ɗaki gurin Ya Bu, ya zo su ci Abinci, tana shiga ɗakin ta hango shi kwance kan gado, da za ta juya sai kuma taga La'asar na neman wucewa, bata tunanin ya yi Sallah, zuciyarta ta ce "ko azahar ɗin ma ya yi? Ai muna zaune su Aisha suka shigo tun kafin a kira sallah, kuma tunda ya shiga bai fito ba, ƙila kuma ya yi a ɗaki" saƙe- saƙen da zuciyar ke yi kenan har ta yanke hukucin bari dai ta tada shi.

Tun tana kiran sunansa bai amsa ba har ta matsa kusa dashi tana ɗan bubbugashi a hankali gami da kiransa "Ya Bu, La'asar ta yi fa, ta shi kayi Sallah" haka tayi ta fama amma ko motsa yatsa bai yi ba, har ta gaji ta kyale shi, to ita ya zata yi kuma? Haka ta koma Parlo amma duk taji bata da wani sukuni, bayan mintuna talatin ta sake komawa ɗakinta ci gaba da tada shi amma bai motsa ba, kamar tayi kuka ta haƙura, can gab da Maghrib ta koma, yanzu kuma tsoro ya mamayeta, da ba dan yana minshari ba to da ta ce ya mutu, bacci yake kamar gawa, duk wannan kiran da ta mishi, da bubbuga shi da take yi bai sa ya farka ba, ko itace bata buge shi da karfin da zai tashi ba? Dan tsaki ta ja.

Ya Bu bai tashi ba sai da aka yi Sallahr Maghrib gab da Isha'i, straight  toilet ya faɗa ya yi wanka, motsin shi taji ta isa ɗakin da sauri yana toilet, can sai gashi ya fito, kallonta ya yi ya kashe mata ido, lumshe ido tayi a hankali ta ce "Ya Bu, ka bani tsoro" dan damuwa ya ce "Me ya faru Wattyta?" Ta ce "haka kake da nauyin bacci? Ina ta tadaka kayi Sallah tun ɗazun, har na tsorata wallahi" murmushi ya yi ya ce "barin yi Sallah" zama tayi bakin Gado, shi kuma ya haɗe Sallahr  Azahar, Laasar, Maghrib da kuma Isha'i.7

Sai da ya gama ya miƙa mata hannu ta ƙaraso cike da kunya, ya ce "Baby, Yunwa nake ji, kin ci Abinci?" Wani abu take ji yana tsirgarta, a hankali ta girgiza kai ta ce "a'a banci komai ba".
Miƙar da ita ya yi ya ce "shirya muje mu ci Abincin a waje".
Wardrobe ta nufa ta ciro babban mayafi ta ce "na shirya".
Hannunta ya kama suka fita bayan sun rufe Gidan.

K A N O1

Babu abinda ya canza na daga halin Hawwa ko zumuncinta da na yanuwanta, ya zamana Iyayensu Maza kaɗai ke zumuncinsu, ko Sabga ake yi idan Umma ta san za ta haɗu da Aunty Iklima ko Hawwa ta gwammace taje bikin da safe ko da daddare ko kafin ranar bikin don dai kar ma su haɗu balle ranta ya ɓaci, tana guje musu kam don dai a zauna Lafiya.
Hawwa har ta shiga Jami'a, ajinsu ɗaya da Batul kasancewar ta 6ata shekara ɗaya don bata samu Jamb da wuri ba, duk da ba department ɗinsu ɗaya ba amma suna yawan haɗuwa, ba su iske Zaid a makarantar ba saboda lokacin da ta shiga Level 1, Zaid ya gama Jami'ar yana shirin tafiya bautar ƙasa garin Bauchi.
Yaya Fahad kuwa ya yi aurensa a nan gidansu ya ajiye Matarshi, yana aiki  a wata Ma'aikata da Uncle Ahmad ya samo mishi.
Wannan Ke nan.

STORY CONTINUES BELOW
N A S S A R A W A

Abuja yake zuwa aiki, yana zuwa gidan duk hutun ƙarshen mako yayi weekend ya koma Sunday, in har ya koma Aisha ƙanwarshi ke zuwa taya Watty kwana.
Zaman Lafiya suke yi, yana bata duk wani cikakkiyar kulawa, da so da ƙauna, matsalar ta dashi ɗaya ne, Tarik'k'u Salat, zai yi Sallah amma fa ba kan lokaci ba, so da yawa a lokacin da zata yi Sallahr Walha wallahi a lokacin yake Asuba, Ya Bu sai ya haɗe Sallah uko ko hudu ya yi lokaci guda, duk da yawancin lokuttan Sallahr yana bacci ne, so da yawa tana mamakin wani irin nauyin bacci ne dashi da duk yadda ta tashe shi baya tashi, wasu lokutta har ruwa take yayyafa mai, sai ya yi kamar zai tashi sai ya koma, tana takaicin haka sosai,ta taɓa mishi magana kan yawan baccin shi da jinkirta Sallah ya ce "Ido na biyu lokacin da ake Sallahr kinga ban yi ba?" ta girgiza kai ya ce "to shi mai bacci ana mishi uzuri kin gane?" Yadda ya cika mata ido ne ya sa ta yi saurin gyaɗa kai.7

Haka suka ci gaba da rayuwarsu ba su da wata matsala amma dai jinkirta Sallahn da yake yi na matuƙar damunta, tana son shi sosai ba ta son ɓacin ranshi, shi ya sa da ta lura ranshi na ɓaci idan ta masa maganar barin Sallah sai ta daina kawai don a zauna lafiya amma kullum tana taya shi da addu'a Allah ya shirye shi.

Watty tayi nauyi sosai don watan haihuwarta ya tsaya, Inna ta ce "Ya Bu ya maidota gida har sai ta haihu" hakan kuwa aka yi.

Wata Laraba, da misalin k'arfe 9 na safe, Watty  ta fara nak'uda a hankali, zurfin cikinta bai barta gaya ma Mamarta ba, ta dai dinga nurk'ususu, abun Allah sai ga Inna da kanta ta dogaro Sandarta, yanayin da ta ganta ya sa ta rafka Salati tare da aika matar da suke tare tace "maza je kira min Binta, kice ta yi ma K'arami Magana" matar ta kwasa da gudu inda ta ga Binta a tsakar Gida.
Jim kadan sai ga su nan sun shigo a sukane, ba wata wata a ka tallafo Watty akayi Asibiti da ita inda take awo, lokacin nak'udar ta taso gadan-gadan, amma cm din ya hau ya sauka.
Tun k'arfe 10 na safe ake abu daya sai gab da Maghrib ta sauka, duk ta jigata ta fita hayyacinta.
Namiji ta haifa Lafiyayye, murna wurin dangi ba a magana, Asibiti cike yake dam da dangi don har Mamar Ya Bu na gurin, Aisha ce ta fara yi ma Ya Bu Albishir kafin  sauran dangi suka dinga kiranshi suna mai barka, alkawarin zuwa yayi gobe da sassafe.
Washegari kuwa sai gashi wurin k'arfe 11, har Aisha na mai tsiya tace "Ya Bu nayi zaton asuba a nan zata yi maka" harararta yayi yace "Ina Boy dina?" "Yana dakin Inna" tare sukaje dakin Inna inda suke, Ya Bu ya dauki yaronshi ya rungume yana zabga ma Watty murmushi ita kam tana ta nok'e kai.
Ranar Suna yaro yaci sunanshi Zaid, Ya Bu bai ma kowa karan yi musu takwara ba ya ba danshi Sunan da ke mishi dadi a rayuwa.
Sai da Watty tayi kwana arba'in da shidda kafin aka maidata dakinta.1

Watty ta cigaba da rainon D'anta Zaid da ya ke ta saurin girma, yau da niyyar gyaran dakin Ya Bu ta tashi don yau Juma'a yau zai dawo weekend, goya Zaid tayi a bayanta ta hau kaka6e-kaka6e zanin Gadon yayi datti da k'ura da alamun tun da ta tafi Gida shi ne a kan Gado, ko da akayi sharan Gida ba a yi na dakin MaiGida ba, wardrobe ta bude don dauko wani Zanin Gadon, kwalebari ne suka biyo bayan bude k'ofar da tayi, kwalebari masu yawa, har ta dan tsorata ta dan ja baya don wasu sun fado mata a k'afa, da mamaki ta bi kwalaban da ido sun kusa dari biyar ko sun ma fi, ashe a buhu ne ma ake sakasu cikarsu ne ya sa su zubewa, durk'usawa tayi ta dauko kwalba daya ta juyashi a hannunta ta neman turancin da zata karanta, sai dai Kash rubutun na Chanisanci ne ba Turanci ba, shakka babu maganin made in China ne.
Nazarin kwalbar tayi tabbas Syrup ne amma maganin meye? Ya Bu be da lafiya ne? Ko dai yana da wani ciwon da ba ta sani ba? Tambayoyin da ba amsa take ta ma kanta kafin daga bisani ta tashi ta tattara empty bottles din ta hadesu a buhun ta cirosu daga wardrobe din don ya fara warin maganin kamar dai Chemist.
Ta kusa Awa daya tana gyaran Dakin kafin ta shiga kitchen ta shirya abinci fried rice da zobonta na taran Miji.3

K'arfe 4 ya shigo gidan, ta tarbeshi da Zaid a hannunta, hadesu yayi gabaki daya ya rungumesu, suka dawo Parlo, bayan ya ci Abinci ya shiga don yin wanka ya dawo sanye da Jallabiya, suna nan tare har gab da Maghrib yace mata bari yaje Gida ya gaishe su.
Tace "Honey in shirya?"
Yace "No duka yaushe kika dawo daga Inna? Ku zauna ba zan dade ba zan dawo"
Murmushi tayi tace "To Allah ya kiyyaye Honey, ina gaida su".
Murmushin ya mayar mata a ranshi yace "Watty kenan, ba dai tayi fushi ba ko so daya".1

Sai wurin k'arfe 9 ya shigo Gidan, lokacin Watty ta shirya cikin wata riga da wando night gown, Zaid yayi bacci yana kwance kan Gado.
Manne suke da juna suna kallon NTA news, ta dan muskata gami da gyaran murya ya kallota yace "Yadai?" Tashi tayi zaune tace "Honey, danAllah baka da lafiya ne?" Hankalinshi ya tattaro gabaki daya yace  "aa, me kika gani?"
Tace "ina maka gyara a daki naga Empty bottles, da yawa fa, kamar dai you've been taking them all your life".
Fuskarshi ta gani ya chanza yace "Lafiya ta Lau"
Tace "to magungunan na meye?"
Kusan tsawa ya mata yace "ina ruwanki? Ban son bin diddigi"
Tsorata tayi sosai da sauri tace "Kayi Hakuri don Allah, ba ni son bacin ranka donAllah".
Tsaki yayi ya mik'e ya shiga daki, haka kurum Watty taji jikinta duk yayi sanyi, duk ta rasa sukuni.

SATURDAY

Sunnah TV take kallo, Mallam Aminu Daurawa ne ke magana a kan Barin Sallah da Hukuncin mai Tarik'ku Salat a musulunce, ta san Hukuncin amma sai taji wannan ya tsoratata, tunawa tayi da Ya Bu na can na bacci, ba Azahar bare Laasar ga Maghrib ya k'arato, ji tayi k'irjinta ya mata nauyi, da sauri ta shiga Daki, taga ashe har ya tashi yayi wanka yazo yana hada Sallah.
Sai da ya gama ya dago ya kalleta? Ta na son magana amma ta kasa
"Ya dai?"
Baki na rawa tace "Honey magana ne dani"
Ya tattara natsuwarshi gabaki daya ya bata yace "go on"
Kwarjini ya mata ainun, ta rasa ta yanda zata fara dabara ta zo mata na runtse ido ta fara magana.
"Sunnah TV nake Kallo, Mallam ke magana a kan mai Barin Sallah"
Ba ta bude ido ba bata ga kallon da yake mata ba, amma bayan ta nisa taji yace "Ehen Ina Jinki" alamun ta cigaba
Ba tare da ta bude ido ba ta fara
"Ubangiji mai girma da daukaka yana cewa cikin Littafi mai girma, a cikin Suratul Maryam aya ta Hamsin da tara zuwa sittin (59- 60)
"SAI WADANSU YAN BAYA SUKA MAYE A BAYANSU SUKA TOZARTA SALLAH, KUMA SUKA BI SHA'AWOWINSU, TO DA SANNU ZASU HADU DA AZABA, FACE WANDA YA TUBA, KUMA YA YI IMANI, KUMA YA AIKATA AIKI NA KWARAI TO WADANNAN ZA SU SHIGA ALJANNA KUMA BA ZA A ZALUNCESU DA KOMAI BA"1

MENENE TOZARTAR SALLAH"
Ibn Abbas (RTA) ya ce, ba ana nufin tozarta Sallah shi ne barin Sallah baki daya ba, a'a ana nufin jinkirtata daga lokacinta.
Sa'id Ibn Musayyib Allah ya kara yarda a gareshi, shugaban tabi'ai ya ce, tozartar Sallah shi ne kin Sallahr Azahar har lokacin Sallahr La'asar ya shiga, ko kin Sallahr La'asar har lokcin Sallahr Magariba ya shiga, ko kin Sallahr Magariba har lokacin Sallahr Isha'i ya shiga, ko kin Sallahr Isha'i har ketowar  alfijir"
Da wata irin muryar taji ya ambaci sunanta cikin Firgitarwa "Ke Hauwattty"
Da sauri ta bude Ido cikinta tuni ya duri ruwa bakinta har ya fara karo.
Yace "me kike so kice?"
Baki na rawa tace "Ya Bu...dama na ga kana bacci ne lokacin Sallah, kuma baka yi da wuri"
"Don Ubanki Kafiri kike so kice ne ni?"
Dam ta ji gabanta ya fadi "Ubanta? Me ya kawo Zagi kuma?"
Tace "kayi hakuri, kar ka Jahilci Maganata"
Kamar Jira yake ya rufeta da duka "Dan Ubanki Ni ne Jahili? Hauwatty ni kike ce ma Jahili?"
Dukanta yake ko ta ina ihu take ta na neman taimakon agaji, da ya gwara kanta da bedside drawer dif kakeji.5

Ghen Ghen Wasa Farin GirkiSuma ta yi? Allah Aalam, nan take k'asa sheme ba ta ko motsi, shi ko ba abunda ya dameshi ya hankada Gado ya dauko 'yar kwalbarshi ya bude ya titiki 'yan kayanshi ya fadi ya dora wani sabon baccin kan Gadon.
Ba ta san tsawon mintuna nawa ta dauka a haka ba'a cikin hayyacinta ba, kamar daga sama taji kukan Zaid, firgigi ta tashi sai kuma tayi sauri ta koma dalilin tsamin da jikinta yayi, kukan Zaid ta cigaba da ji wanda yake yin shi da k'arfin shi, a hankali ta dinga jan jiki har ta bar dakin Ya Bu ta nufi Zaid cikin zafin nama ta rungumeshi ta na kuka kafin tayi k'arfin halin fiddo mama ta bashi ya sha.

Har Ya Bu ya koma aiki babu wani sakin fuska da Watty ta samu daga gareshi, tun kafin ya isa Abujan ta mishi dogon Text na ban Hak'uri da neman yafiya, amma baiyi reply ba, har Sati ya zagayo Ya Bu be kira Watty ba, sai gashi ko ran Friday, ko da ta nufeshi don amsar jakkarshi tureta yayi, babu dama ta mai maganar Arzikki sai ya zageta ko ya hantareta, da abun duka da ba na duka ba dukkanta yakeyi, ya maidata wata punching bag dinshi, sosai Watty ta shiga damuwa ta zabge lokaci daya tayi wata irin rama, babu wanda ta kai ma kukanta, ko Aisha da ta lura da chanzawar Aminiyarta kuma 'yar uwarta ta sha tambayarta amma sai tace wallahi bakomai.
Sosai Watty take son Ya Bu shiyasa har yau take mashi uzuri da bacin rai ne nhar yake sashi dukanta, k'ila a wurin aiki ne ake bata mai rai, uzuri take bullo ma kanta don bata ma so ta sa ma ranta Ya Bu ya tsaneta.1

Watty kam ta saba ko ruwa ta aje mishi sai ya rankwasheta, so da yawa tana mamakin meye jawo wannan tsanar? Me ya faru da soyayyar da ya nuna mata a baya? Meye laifinta don ta so shi? In taje Gida kowa sai ya tambayeta dalilin ramarta harta Inna sai da ta tambayeta damuwarta, sai tace bakomai, in kuma a ka matsa mata da tambaya sai tace "Kun manta wai shayarwa nake? Tsotso ne ke k'arar dani, In ba yayeshi nayi ba ai ba zan bar ramar nan ba" jinta kawai sukeyi amma sun san ba haka bane.
Inna ta sha tambayar Ya Bu sai yace "Damuwar me kuma Inna? Ki tambayeta in ta na da wani damuwa" Inna tace "wallahi tace bata da damuwa, wai tsotso ne" yace " to kuma, ko fata kuke ta samu damuwan? Tunda tace muku ba ta da damuwar komai ku k'yaleta mana" Inna tace "to Shikenan".

Watty duk ta yank'wane, babu wani abu mai dadi da ke hadata da Ya Bu, sai ta lura yanzu ya bar zuwa Aiki, tayi zaton hutu ya dauka, ashe korarshi akayi a gurin aikin sakamakon baccin da ya ke yi a office mara amfani, yanzu kullum yana gida baya da aikin fari bare na bak'i, banda bacci ba abunda yakeyi, sai dare ya yi ya fita yaje Family House da ya dawo ya sake wani baccin sai wani Maghrib din, sosai Watty ke shiga damuwa, ta kan shiga Internet ta binciki dalilin da ke sa mutum yayi baccin sama da Awa 16 a rana, ko dai Gida zasu nemi magani, duk da tsoronshi da takeyi, ta yanke hukuncin taranshi da maganar neman taimako Gida in ya tashi bacci, Zaid na bacci ba wuta har wayarta ta mutu, fita tayi waje wurin baranda ta sha iska tana kallon dayan Flat din da ke ciki Gidan, idonta ya kai kan Windown Parlon Gidan, Mata daMiji ta hango suna Gudu suna dariya, yaransu biyu na biye da su suna zagaya kujera suna k'yak'yata dariya, murmushi tayi taji sun burgeta, chan sai ta ji k'irjinta ya mata nauyi, sun bata sha'awa sosai, Mamar Amir da Amira ta girme mata da shekaru don har tayi degree dinta na biyu, atleast tayi shekara 12 da aure, amma ji su kamar Yara suna zabga Soyayyarsu, ita da ko shekara daya bata yi da aure ba duk ta zama abun tausayi, babu wani abu tsakaninta da Miji sai Zagi da hantara da ma duka, gani tayi zuciyarta zata fashe tayi saurin shigewa Gida ba tare da ta kulle kofar parlorn ba.

Kan idonta ya tashi ya yi wanka ya hade Salolinshi, ya hau kan Dining Table ya ci Abinci.
A daddare ta isa gareshi ta ja kujera ta zauna, murya na rawa ta fara magana.
"Ya Bu, donAllah ka ma maganata kyakyawan Fahimta" be motsa ba balle ya tanka ta cigaba da cewa "Ya Bu, kullum na tambayeka me na maka ka tsaneni baka bani amsa, kar ka manta kana da hak'ik'i a kai na kamar yanda na ke da shi a kan ka, ina tsoron rayuwa, ina tsoron Allah, Ya Bu hak'i na ne na gaya maka gaskiya ko min dacinta, matarka ce ni ta sunna, ina so da ni da kai mu samu rabauta ranar gobe k'iyama, ina so yaronmu ya tashi da Ibada wanda ya ratsa duk wani bargo na jikinshi, ina so su kasance a sahu na gaba a Masallaci shi da Mahaifinshi, ina so Zaid yayi Alfahari da Mahaifinshi, Ya Bu donAllah muje gidan Inna, ka ga ya musu matsalarka, su taya mu neman magani, ni nasan baccin da kakeyi ba na lafiya bane, amma in suka taimaka mana, na san komai zai tafi daidai, inshaAllah Ya Bu..."
Lafiyayyen Marin da ta ji a fuskarta ne ya sata yin shiru, chan kuma sai taji an shak'o wuyarta an dagata daga kan kujerarta, hannu bibbiyu ta sa ta rufe bakinta don kar k'ak'arin da takeyi ya tada Zaid din da ke bacci, kifa mata mari yake tayi ta hagu ta dama, ita ko bata bude baki ba balle tayi kuka mai sauti amma hawaye ba su bar tsere a kumatunta ba.
Be sake mata wuya ba, bai bar marinta ba ya ke fadin "Hauwatty kin raina ni, ni zaki ta sa gaba kina min maganganun Banza? Ni saanki ne Hauwatty? Ko Aisharmu ba ta girmeki ba, har kin yi girman yi min waazi? Har kina min hannunka mai Sanda kar Zaid ya tashi Ubanshi bai zuwa masallaci? Jahili kike ta son ce min ko?".

STORY CONTINUES BELOW
"Ya Abu!"
A firgice ya ji muryan Aisha, da sauri ya juyo tare da sake wuyan Hauwaty ta zube k'asa tana kuka mara sauti, itama Aishar Kukan takeyi, ta k'arasa gun Wattyn da ke zube a k'asa.
Da k'yar Watty ta dago kai ta kalli Aisha tace "Sis baki ce min kina Hanya ba?"
Aisha ta sharce hawayenta cikin Zafi tace "tashi mu tafi Gidan Inna"
Hankalin Ya Bu ya tashi yace "Aisha, listen, i can Explain"
Cike da rashin kunya Aisha tace "ka adana duk wani bayani, ka bari sai munje wurin Inna"
Watty da k'yar tace "Aisha, laifi na mishi fa"
Cikin Zafi Aisha tace "Laifin da kika chanchanci mari fiye da 30, ga hannunshi a wuyanki kamar zai shek'e ki? In munje gaban Inna sai ki mata bayanin Laifin".
Ya Bu zai yi magana Watty ta tarbeshi da cewa "Ka bar ni na mata magana, ba zata gaya ma Inna ba, ba zata gaya ma kowa ba".
Cikin rashin sanin abun yi Ya Bu ya wafci mukullin motarshi ya fita a guje cike da fargaban mai zaije ya dawo.

Aisha ta ja kujerar dining ta zuba ma Watty Ido tace "Start Talking, and dont dare lie to me"
Tare suka taso da Aisha tun suna a zanin goyo, Aisha 'Yar uwarta ce, K'awarta ce, kuma Aminiyarta ce, duk da Uwarsu daya Ubansu daya da Ya Bu, zata rantsev Aisha ta fi sonta a kan Ya Bu, boye mata gaskiya ba zai chanza komai ba.

"Aisha zan gaya miki komai, ba zan boye miki komai ba, amma sai kin daukar min Alkawari, Alkawarin ba za ki ta ba gaya ma kowa abunda kika gani yau ba, ko kuma abunda zakiji yanzu ba" ba tare da wani tunani ba Aisha tace " na miki Alk'awari"
Watty ta fara "Mata da yawa matsalarsu da Mijinsu ba ya wuce suce Mazajensu na neman Mata, ko sun kama Mazajensu na cin amanarsu, nikam ko so daya wannan bai taba zama matsalata ba don ba ya yi, Aisha tunda mukayi aure da Ya Bu, kusan shekara daya kenan, wallahi wallahi Aisha ban taba ganin Ya Bu yayi alwala yace bari yaje masallaci ba, ban taba ganin ya Bu ya fita lokacin Sallah yaje masallaci ba, wallahi tallahi, in na mishi k'arya Allah ya saka mishi"..
Da tsananin mamaki Aisha tace "Inalillahi, ba ya Sallahr ne?" Watty ta murmusa tace "yanayi amma ba kan lokaci ba, hade miki Sallah zaiyi Asuba Azahar Laasar Maghrib, wata rana Isha'i sai washegari zai yita......kinji kinji" Watty ta kwashe labarin komai ta ba Aisha, ba ta boye mata komai ba, tun kafin Watty ta gama bada labarin Aisha take hawaye, tausayin Watty take yi da kyar Watty ta lallasheta tayi shiru.

Aisha tace "Hauwatty, ta ya ya ki ka jure wannan abun tsawon watannin nan? Watty meyasa ba ki gaya ma Iyayenmu ba, ko ma Inna?" Da sauri ta girgiza kai "ina Sonshi, bani so yayi bak'i a wurin Iyayenmu, ke ma Amana ban yarda ki gaya ma kowa ba"
Cike da Takaici Aisha tace "So ko Hauka dai? Watty ki dai na tsayuwa yana dukanki, da ya dake ki ki rama" Watty ta dan yi dariya tace "to Mama Aisha" Aisha ta sha mur tace "i am serious, wai Domestic Violence din da muke karantawa a Instagram shine a gabanmu? Ya Allah" shiru suka dan yi kafin Aisha tayi zumbur ta tashi tace "Shaye-Shaye yake, zo muje mu bincika Dakin" kamar Sakara Watty ta bi Aisha, suka hau neme neme amma ba su ga komai ba, buhun empty kwalban ma ya fita dasu, Aisha ta bata shawarar ta sanya mai ido.

Ko da Aisha ta koma Gida, kasa hak'uri tayi sai da ta gaya ma Mahaifiyarsu, Mama ta sha Kuka, ta kira Watty tana bata hakuri tare da rokonta Alfarman ta rufawa Mijinta Asiri, kar ta gaya ma kowa, duk da ta san hakan Son Kai ne, ba zata so Iyayenshi Maza su dauki Hukunci kanshi har su hayak'ashi ya bar k'asan ta samu ya dawo da k'yar, Watty tace "Mama kar ki damu, babu wanda zan gaya ma wa, Aisha ma don gabanta akayi da bata sani ba" Mamar Ya Bu tayi ta ma Watty Godiya tare da yi mata adduo'i kala-kala.1

Ranar da Ya Bu yaje Gidansu Mamarshi ta dinga mishi fada kamar zata ari baki, sosai ya bata hakuri yace ya daina, ko da ya dawo Gida bai ma Watty maganar ba, ya dai ci Abinci, ya dirka maganinshi ya hau Gado, bai fasa halayenshi ba amma ya bar dukanta, sai da sukayi kwana biyar ba wata matsala, kadaran kadahan.

ZAID;
Daurin Aure gareshi a Nassarawa, Abokananshi kusan su 6 ke Nassarawa State, duk a Jami'a suka hadu, daurin auren Ali Ali za'ayi nan da kwana 5, amma Abokanshi sun matsa mai kan sai yazo kwana uku zuwa daurin Auren saboda akwai shagalin bikin da za'ayi, ranar Laraba Zaid ya dira garin Nassarawa, Abokinshi kuma Amininshi Hashim Umar ya dauke shi a Tasha ya nufa Gidansu da shi, Straight sashen kakarsu ya nufa dashi, inda Inna kakarsu ta mishi tarban karamci.
Hashim yace "kinga Inna, wai sai dai na kaishi hotel yayi masauki, ba zai sauka a nan ba"
Inna tace "kai dan Kano, ka raina Gidan namu ne da ba zaka sauka a nan ba? Ko kudin ka zuba yake kana son ka kashe su?"
Da sauri Zaid ya girgiza kai yace "aa wallahi Inna, ban son na takuraku ne"
Tace "baka ga Girman Gidan nan ba? Ai ban tunanin ko fadar Sarki ta kaishi Girma, Sassa ya fi 15ciki, ba wanda zaka takuramawa, indai ba rainin arziki ba, to ka zauna a nan ko shekara kayi bame ce maka don me" Hashim yace "balle kwana 3 zaiyi, Lahadi zai koma"
Inna tace "to kaji"
Godia Zaid ya tayi Inna tace "je ka huta".
Hashim yayi Gaba Zaid ya bishi a baya suka nufa Sashen Samarin Gidan.

STORY CONTINUES BELOW
WATTY;
Tayi mamakin yau ganin idonshi biyu da safe haka don 12 ba tayi ba, da alama fita zaiyi, wanka yayi sannan ya fita warming mota ya dawo yace "zan fita, ba dadewa zanyi ba kar kiyi abinci yau, Gidan abokin aikina na da aka gayyacemu Lunch, mu ma in an dan kwana biyu sai nayi inviting dinsu, but shi sai weekend tunda yana zuwa aiki".
Da dan tsoro tace "Ya Bu korarka akayi a wurin aikin naku? Na ji jiya ma kana waya".
Ba ta san meye abun tunzura daga tambaya ba, ji dai tayi ya mak'ure mata wuya yana cewa "Labe kike min dan ubanki?" Ya dinga kifa mata mari" nan da nan ta daburce tana kuka tana bashi hakuri amma kamar ingiza shi ake, ya cigaba da nausar mata ciki yana kifa mata mari kala kala.

Jin muryar Aunty Binta su kayi "kam bura uba"
A daburce ya sake Watty ta durk'usa nan tana kuka, kukan takaici, shikenan kowa ya gama sanin zaman da takeyi da Ya Bu tunda Aunty Binta da kanta ta ga yana dukanta, Aunty Binta itace First born a dakinsu, bata da hak'uri ko kadan, zafi gareta sosai, Asibiti tazo kusa da Gidan Watty shine ta biyo, ashe da rabon ta gane ma idonta haka.
K'arasa gun Watty tayi ta dirka mata wani uban Dundu tace "danubanki Mijinki kika tsaya yana kilarki kamar Jakka? Ki gaya min randa Babanki ya taba daga hannunshi ya dungureki bare ya mareki, ki gaya min" kafin Watty tayi magana Aunty Binta ta wurga ma Ya Bu wata Uwar Harara tace "ka daki Aurenka wallahi" Aunty Binta ba tsararshi bace ta girme mishi, sai cewa yayi "kiyi hakuri Anty, wallahi sharrin Shaidan ne" bata tanka shi ba tace "ki je ki dauko mayafinki" zatayi magana ta rufeta da duka cike da takaici da sauri Watty ta ya fito Hijabi a daki Aunty Binta ta figi Zaid ta tasa k'eyar Watty suka bar Gidan, Ya Bu ya bi bayansu yana ma Aunty Binta Magiya amma bata kulashi ba Illa tsaida Keke Napep din da tayi suka shige.
Tsoro da fargaba ya cikashi da ya tuna Inna ta san labarin nan ya Mutu.

Straight Dakinsu suka nufa, Watty na ta kuka, Mamar Watty na ganinta ta taso da gudu ta rik'ota, Me ya faru da ke ni Dije? Binta me ya sameta?" Cikin zafi da k'unan rai Anty Binta tace "Mama ba na ce miki yau zan je ganin Likita ba? Wai da na gama Mama sai nace barin shiga mu gaisa da Watty kar ace nazo har anguwar ban shiga ba, Mama ko da naje sai naji ihu, na ko ci saa kofar a bude, ina shiga kawai sai naga Abu ya kama Watty yana ta marinta har da nushi Mama dukanta yake ko ta ina, Mama Watty Sakara ce, dama ni nasan yarinyar nan ta na da damuwa kuma wallahi ba yau ya fara ba, don Ubanta sai ance me ya sata rama sai tace shayarwa ne"
Tuni idon Mama ya chanza da k'yar tace "ku muje gun Inna"
Watty ta fashe da kuka "donAllah Mama.."
Bata k'arasa ba Aunty Binta tace "Zan ci Ubanki Hauwatty, kinsan ban wasa dake" jiki ba laka suka k'arasa gun Innar.
Aisha na Dakin Inna don jiya a Gidan ta kwana, tana ganin Watty ta k'araso da gudu ta tallabota rai bace tace "dukkanki ya k'ara yi ko?"
Aunty Binta tace "Oh kema kin san yana dukanta ko? Munafuka baki fada ba"
Inma tace "wake dukkan wani?"
Aunty Binta ta fetse mata abunda idonta ya gane mata, Aisha bata damu da Dangantakarta da Ya Bu ba na Uwa daya Uba daya, Anty Binta ma direwa itama ta gaya musu abunda ta gani ranar da taje Gidan.
Inna banda tafa hannu da sallallami babu abunda takeyi hannu take karkadawa "Aa Ban yarda da Duka ba"
Aisha tace "Inna ai ba shikenan ba, Watty gaya musu halayenshi na k'in Sallah".
Cike da haushin kowa Watty tace "yana fa Sallah"
Aisha tace "ki gaya musu ko na gaya musu".
Inna da mamaki ya gama cikata tace "Hauwatty matso kusa dani, ki gaya min irin zaman da kukeyi da Abubakar".
Watty kuka kawai takeyi, wato duk yanda take boye sirrin mijinta rana daya ya tona ma kanshi asiri, bata da wani Zabi da ya wuce basu labarin komai.
Mamarta kuka takeyi sosai, Inna kuwa kamar ruwa ya cinyeta, Aunty Binta ji take kamar ta sa ma Watty Belt ta mata dan banzan duka.
Shi dama Auren Zumunci ko ya k'ara Zumunci ko kuma ya wargazashi, bata tunanin zata sake ganin Abubakar da mutunci.

Inna chan dai tace "Shikenan, ke Watty, shiga kewaye ki watsa ruwa, Aisha kira man Iyayenku gabaki dayansu ina son ganinsu duka, Bayan Laasar, a kira taro gabaki daya 'ya'ya da jikoki, harda Abubakarin".
Mama ta ja jikinta ta koma bangarenta, Aunty Binta ta zauna a dakin Inna, Watty da sauri ta fada Toilet ta na kuka sosai, burinta daya kar a rabata da Ya Bu dinta, don ta ga terere Inna ke niyyanyi da Shi.4

STORY CONTINUES BELOW
Tun kafin ayi Laasar 'yan Meeting suka fara zuwa, Iyaye da Jikoki, nan farfajiyar Gidan aka sa Canopy da kujeru kamar zaayi biki, in dai irin Meeting dinnan akeyi a waje ake yu sabida daki ba zai dauke su ba.
Bayan sun shigo daga Sallahr Laasar Hashim ya kalli Zaid yace "ka k'arasa ciki, za muyi Family Meeting ne, it wont take Long, in mun gama sai mu je wurinsu Ali Ali, Zaid kai ya daga mai alamun ya gane amma yana mamakin wani irin Meeting ne kamar Biki, da Canopy da Kuneru, kai harma da k'armar Loudspeaker irinta Masallacin nan, amma dai bari ya bar mamaki din ya ga Gidan Babba ne tabbas Inna na da Zuria.

Dai dai aka fara zuwa Filin Meeting din, daga bisani kowa ya hallar har shi Ya Bu din, Inna ta fara magana a Lasfika, Gidan baa jin komai sai muryar Inna da ta karade Gidan, ba ta damu ko Makwafta zasu ji ba don ita bata shiga harkan Gidan Kowa ba, ba ta tsammanin zaa shiga nata.
Ba tare da 6ata lokaci ba ta sanar dasu sababin Taron kan Abubakari ne da Hauwatty.
Nan da nan ta basu labarin irin zaman da Hauwatty takeyi da Abubakar,Babanshi ya zaburo zai bugeshi Inna ta haneshi ta hanyar cewa "kul, kar ka dakeshi, bar shi, fiye da shekaru 10 ba ka tare damu Habu, bamu san halinka ba muka dauki diya mai hakuri, mai natsuwa, mai sonka muka baka, ashe banda zaluntarta ba abunda kakeyi, to ta k'are, ba Jakka bace ba, ina so ka gaugauta bata takarda gaban kowa"
Tuni Ya Bu ya zube gabanta "Inna kiyi Hakuri, wallahi ba zan iya rabuwa da Hauwaty ba, dama sharrin Shaidan ne, amma wallahi ma bari Inna, ba zan sake ba" kuka yake sosai yana magiya amma Inna tace bata san zancen ba.
Watty tuni idonta ya fara zubar ruwa ta durk'usa gaban Inna tana cewa "Innarmu kiyi hakuri donAllah, wallahi sharrin Shaidan ne, karki rabamu ba zai sake ba" duk wani mai son gaskiya ji yayi kamar ya rufe Watty da duka, wasu kuma tausayinta suke suna Allah Sarki So hana ganin Laifi.
Mamarta kuwa da Yayyinta Mata kamar su fincikota suyi mata mugun duka.
Ganin suna neman saka ma Inna ciwon kai ya sa Inna ta sallami kowa tare da cewa Abubakar ya fitar mata daga Gidanta kuma kar ya sake ya dawo sai da takardan Watty.
Inna ta shige Sashenta, Watty tayi saurin bin bayanta don yau ta kuskura ta shiga wurin Mamarta yayyinta dafata zasuyi.

Hashim ya shiga gurin Abokinshi rai bace, Zaid ya tambayeshi yadai Maza? Tsaki ya buga da k'arfi, yace "kai dai bari, akwai wata Cousin dita da ta auri wani Cousin din mu less than a year fa, kullum sai ya daketa, duka fa ba na wasa ba, gashi baya son Sallah, ina tunanindan kwalba ne, duk yasa Hauwatty ta rame ta fita hayyacinta, amma donubanta don inna tace raba auren zatayi harda birgima tana rokon a yafe mishi tana son mijinta can you imagine?"
"Hawwa" Zaid ya raya a ranshi, kafin chan yace "kuma cousin din naku, kun san halinshi me ya sa kuka aura ma Innocent kamarta?".
Hashim yace "wallahi he manipulated her, ba wanda ya san halinshi, fiye da 15 years fa yayi a Ghana be dawo Gida ba, yana dawowa Inna ta aura mishi ita fa shine yake kilarta kamar Donkey".
Zaid ya tausaya ma Watty matuk'a addua kawai ya mata.1

Ana Sallahr Maghrib ta san yanzu za'afara shigowa yi ma Inna bankwana, ba ta son ganin Sisters dinta don zaginta zasuyi kila ma Anty Binta ta daketa, ba tare da ta sanar da kowa ba ta fita daga Sashen Inna, dama babu wuta Gidan, babu Gen din duka Gidan, sai ko wane sashe da nashi Gen din, ina zata inda ba zaa nemeta ba? Sassan Samari ta nufa ta je ta zauna a kan dakalin dakin Yaya Kabir don baya gari, hada kai tayi da guiwa tana hawaye a hankali.

Bayan zamanta da kusan Minti 40 Hancinta ya jiyo mata wani daddadan k'amshi.
Fitowa yayi sanye da wani Sky Blue Shadda Kaftan da Hula, sai zabga k'amshi yakeyi, yayi shirin tafiya Dinner, sashen Inna zai je inda Hashim yace ya sameshi, kofar dakin ya ke kullewa da makulli.
A firgice ta mik'e don ta ga wani dogon mutumin da ba danuwanta ba, shi kuma ya juyo da sauri yayi baya yana haskata da torchlight din wayarshi.
Sai ga wuta, Hasken Lantarki ya haskaka wurin gabaki daya, a hankali Zaid ya sauke hannunshi da yake haskata, wutan da aka dawo dashi ya isheshi baya bukatar k'ari.
Kallonta yakeyi sosai kamar yanda take kallonshi sosai, kusan mintuna 2, kafin daga bisani ya fara taku ya wuceta ba tare da sun tanka ma juna ba.

Dakin Inna ya nufa, tun kafin ya shiga ya ke jiyo kukan yaro, kasa shiga yayi don yaji muryoyi da yawa.
Inna tace "don nace ba zata koma gidan Habu ba shine ta diremin Zaid a tsakiyar parlo, yaro sai kuka yakeyi".
Anty salima ta dinga rirrriga shi tana "yi shiru Zaid Zaid Zaid"
Zaid da ke waje ya shigo tare da cewa "Naam"
Hashim yace "kai ba kai ba hahaah"
Inna ta dan murmusa tace "da takwaranka ake".
Yana jin Hashim na ma yanuwanshi bayanin cewa shi abokinshi ne yazo daurin aure.
Zaid ya k'arasa gurin Aunty Salima ya mik'a mata hannu alamun ta bashi Zaid ba gardama ta bashi.
A kan kafada ya sashi yana ririgashi bakinshi na kan kunnenshi yana dan hurawa kadan kadan.
"Ashe akwai mai irin Sunana?"
Inna tace "aiko gashi kam"
Zaid yace "nidai da wayau na ban taba haduwa da mai irin Sunana ba"
Wani irin Kuka da Zaid karami ya saka ya sasu yin shiru.
Anty Salima tace "wallahi Inna sai na mari Hauwatty na ganta, yaro tun dazun yake ta kuka? Ba za ta zo ta bashi ya sha ba, ba inda ba a nemeta ba a Gidan nan, tana daukan alhakinshi fa".
Wani dan nazari Zaid yayi, da azama da sauri ya mik'a ma Aunty Salima Zaid, ya fita dadan sauri yace "Ina zuwa".
Sauri sauri Gudu gudu ya koma Sashen baya.
Tana nan a durk'ushe inda ya barta, jin takun mutum, da k'amshin shi ya sa ta mik'ewa da sauri.
Kallonsa ta keyi tana mamakin waye wannan.
A hankali cikin wata irin murya mai kama da rada yace "Hawwaa"...

Post a Comment for "HAUWA CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...