Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HANYAR BAUCHI CHAPTER B KARSHE

HANYAR BAUCHI CHAPTER B KARSHE

- - Post a Comment

 HANYAR BAUCHI CHAPTER B KARSHEHANYAR BAUCHI 🚎


Wattpad @UmNass


Page 5


Shuru ne ya biyo baya atsakanin su, sai kuma tarin fargaba da tsoron da yake sauƙa azukatan su.


"Kaddai ace Ƴan fashi ne suka kashe hanyar? Idan haka ne gara tun wuri mu juya salin alin mu nemi wata hanyar." Dattijo Habu ya faɗa cikin fargaba da rawar murya.


Wanda ya janyo sauran mutanen cikin motar suka fara cece-ku-ce.

"Inna lillahi wa inna ilaihirrji'u. Nikam na shiga uku nah!" Mubarakatu ta faɗa tana ɗora hannunta abisa kanta.


Juyowa Mutanen sukayi suna kallon ta, duk da kasancewar su cikin tsoro da ruɗani, amma ko kaɗan bai kai koda kwatar nata tsoron ba.


"Ba ke kaɗai kika shiga uku ba yarinya harda mu, dan yanzu bamu san mi kuma zamu tadda ba." Dattijo Habu ya faɗa yana sharce gumi akan fuskar sa, duk da uban ruwan da ake tsugawa, amma saboda tsoro da fargaba ya sashi jiƙewa.


Hakan ba ɗan ƙaramin tashin hankali ya ƙara jefa Mubarakatu ba. Hawaye kuma sai fama silala yake akan fuskarta, zuwa yanzu bata damu da kowa yaga damuwa da hawayen da yake zuba a idonta ba.+


Kai Direba ya girgiza cikin sanyin Murya ya fara magana "Bana jin cewar ɓarayi ne ahanyar gaskiya, domin da ace ɓarayi ne ahanyar da babu wanda za'aga haka atsattsaye. Nafi tunanin wata matsala ce ta faru ahanyar."


Kai Sarkin Kinibibi ya jinjina "Ƙwarai nima haka nake Hasashe. Amma kuma da wanan muhawarar tamu ai gara muje muji abin da yake faruwa inaga zai fi, tunda ruwan ya ɗan tsagaita zuba, idan mukaci gaba da zama ba tare da motsiba muna ƙara ɓatawa kanmu lokaci ne, duk da yanzu ma almuru ta shigo."


"Gaskiya kam da yafi dai." sauran fasinjojin motar suka faɗa.

Anan direban ya buɗe motar ya fita, suma suka bi bayansa ɗuuu kamar haɗuwar baki.


Yayyafin ruwa na sauƙa ajikin su, amma basu damu da haka ba, haka aɓangaran Mubarakatu hawaye ne ke faman zuba a idonta, dana sani kam tayi ta yafi aƙirga awanan lokacin.


Wajan wasu mutane suka ƙarasa wanda suke ta magana akan matsalar da ta kawo cunkushewar mutane awajen.


"Assalama alaikum."

Suka aika kusu da Sallama, wanda suma suka amsa musu gami da ɗan sakin Fuska agaresu.


"Lafiya kuwa muka ganku duk atsaye awaje ɗaya?"

Tambayar da direban su Mubarakatu yayi musu cikin fargabar amsar da zasu basu.


"Lafiya kam da sauƙi, dan gadar da zamu bi mu ci gaba da tafiya ita ta karye, sanadin ruwan daya ɓalle daga sauran hanyoyi da kuma wanda akayi yanzu."


"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" suka faɗa atare.

Sai mubarakatu data ɗora hannu bibbiyu akai, tana razkar kuka.2


"To amma ai akwai wata hanyar daga baya, sai dai ita zagaye ce akan wanan." Direban su Mubarakatu ya faɗa, cike da nema musu mafita.


"Ita ɗinma ta karye, dan muma da fari ita muka fara bi, ƙarshe sai dawowa mukayi ta nan, saboda wanan har tafi dama-dama tunda mota zata iya wucewa ta jikin ta ba tare da mutane da kaya ban."


"Kamar yaya kenan ?" Suka sake aika musu da tambaya cikin ƙaguwa da son jin zaren labarin.


"Eh ita gadar zaka iya wucewa ta kanta, amma fa kai ɗaya tal acikin ta, dan sauran fasinjojin ciki sai sun sauƙa su da kayansu, akwai masu iyo da fidda mutum sai su tsallakar da su. Amma idan ba haka ba kuna hawa to zata ƙarasa tsinkewa ku faɗo gaba ɗaya. Ko kai ɗinma hasashe ake akan wucewar ta ka, ba wai tabbaci garemu ba."


Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin mutanen da kuma direban motar, idan aka ɗauke Mubarakatu da ta ɗora hannunta aka, tana runtuma kuka da hawaye.


STORY CONTINUES BELOW

"Wanan ai mai sauƙi ne, ni na iya iyo zan tsallakar da ku gaba ɗaya, shi kuma direban sai ya fara gwada tuƙa motar ahankali." Matashin saurayi sarkin shisshigi ya faɗa yana jinjina kansa da kuma basu tabbacin maganar da yayi.


"To amma kuma kayanmu ya zamuyi da su?" Dattijo Habu ya faɗa cike da alhini.


"Kowa sai ya ɗauka akansa mana." ya basu Amsa cikin nuna halin ko oho.


Saurin katsesu mutumin da ya basu amsa yayi "To ai wata sabuwa yanzu sai kun bi layi, dan duk waɗan nan motocin da kukaga sunyi jerin gwano anan suna jira ana wucewa da ɗai-ɗai ne, dan gadar bazata iya ɗaukan nauyin fiye da mota ɗaya ba."


"Wayyo Allah nah! Yanzu duk yawan waɗan nan motocin sai mun jirasu kafin ace mun samu wucewa?" Mubarakatu ta faɗa tana ƙara kallon duhun daren daya fara ratsowa, dan magrib kam ta wuce sai dai ayi batun Issha'i.


"Ƙwarai kuwa Hajiya, sai kun jira, dan muma da kuke ganinmu anan muna jira layi yazo ta kanmu ne."


"To ni dai kam yau ban hararo shigata Bauchi ba." ta faɗa cikin rawar murya, gefe guda kuma tana ƙara Allah wadai da taurin kanta da ya janyo mata wahala da garari na rayuwa atafiya.


"In sha Allah zaku shiga bauchi Hajiya, dan yanzu ana samun raguwar motocin ai, dafa ko hangosu ba ayi."


Kai ta jinjina ba tare data ƙara magana ba saboda yanda zuciyar ta ta gama karaya da sarewa da shiga bauchi.


Wayarta ce ta yi ƙara ta ɗauka da sauri ganin Abdul ne, yafiyarsa zata nema wata ƙila ta samu sassaucin da zata shiga bauchi ba tare da wata matsalar ta ƙara faruwa ba.


"Kun isa lafiya dai? Naji shiru babu cikiya an samu Innah da su Addah Fatima (Fatima Alhassan) ko?" ya faɗa yana faɗaɗa sautin muryar sa, dan tunda yaji har ana kiran Issha'i yasan komi akayi tana gida ta manta da shi.


Agefenta kuma ji take kamar ya caka mata mashi azuciya, kamar kuma da saninsa yake aika mata da tsaƙon gatse.


"Abdul dan Allah ko ka min wata Addu'ar ne? Dan ban taɓa jin tashin hankali acikin tafiya ba kamar ta yau, na gaji da cin karo da ƙalubalen cikin ta, matsala taƙi barina daga wanan sai wanan." Ta ƙarasa maganar cikin sautin kuka.

Wanda yasa Abdul miƙewa daga kwance da yayi akan kujera "Mi kuma ya sake faruwa? Kaddai kice min har yanzu baki isah Bauchi ba?" ya faɗa cikin yanayin damuwa da fargaba.

Hawayen fuskar ta ta share, sanan taja hancinta "Ban hararo wa kaina shiga Bauchi ayau ba, duka hanzari da ƙaguwa da azal-zala irin tawa, bata yanke min nisa da sarƙaƙiyar dake cikin tafiyar nan ba, gaggawa da ci-da-zucin da nayi tayi agida har yanzu basu kawo ni Bauchi ba. Nayi dana sani yafi aƙirga ayau akan dama ban tsauwalawa kaina wajan yin tafiyar ba." wani abu ne ya tokare mata awuyanta mai ɗacin gaske adai-dai lokacin data zo nan.


Tuni jikin Abdul yayi sanyi jin Mubarakatun sa na magana da karaya, yau mubarakatu ce ke dana sani acikin tafiya, lallai wahalar data sha ta kai maƙura, ta kuma tsaya mata aƙoƙon rai "Mi ya sake faruwa acikin tafiyar taku?"


Gwauruwar ajiyar zuciya taja kana ta fuzgar da Iska mai zafi "Sai yanzu muka zo NINGI Abdul, gada har biyu ta karye babu wadda mota zata iya ɗauka ta tsallakar da mu, aƙarshe sai dai amana iyo da kayanmu aka."


"Ya Rabb!" ya faɗa cikin alhini kafin kuma ya tuntsure da dariya "Ga jakarki da Uban kaya kuwa acikin ta." sanan ya ƙara kwashewa da dariya sosai harda ƙyaƙƙyatawa.


"Abdul mana!" ta faɗa cikin sanyin murya.

Ɗan shuru yayi da dariyar tasa "Ina jinki. Amma garin yaya gada har biyu ta ɓalle?"


"Ruwa fa akayi kamar da bakin ƙwarya, ga magudanan ruwan da aka saki, maganar da nake maka har yanzu ana yayyafi."


"Taɓɗijam! Kice kinaga rayuwa yau, mu kam nan sai sanyi da ƙamshin ƙasa, yanzu haka ruwan shayi nake sha mai kauri, da indomie da ƙwai dana soya, suma da zafi-zafin su nake ci, dan naji ɗumi acikina."


Yawun bakinta ne ya tsinke, kafin ta ankare ya zuraro abakin ta "Abdul kai kam ai sallahr ka, dan na lura ko tunani na bakayi, da damuwa da halin da nake ciki? Ko wata waya mukayi bakinka na tauna kamar sarkin mataunan duniya, ni yau bazan iya tuna ruwan dana sha na ƙarshe ba balle kuma aje ga batun cin abinci." cikin jin haushi take maganar dan haushi sosai yake bata.


Dariya yasa ahankali cikin muryar lallashi ya fara magana "To ya kike so nayi? So kike dukan ya min yawa, ga na rashinki ga kuma na yunwa?"


Harara ta aikama wayar kamar yana kallon ta "Oho dai, kaje kayi ta ci rayuwa ce ai, amma idan da Addu'ar da ka min dan Allah ka gogeta na isah Bauchi lafiya, wallahi na gaji da garari."


Yanayin yanda take magana faɗa-faɗa da kuma kalar tausasawa ya bashi dariya sosai "Nikam ba Addu'ar dana miki, idanma akwai bai wuce ta Allah ya hankaltar da ke, rayuwa da abin da dumiya ke ciki."


Ido ta fiddo waje "Abdul kana so kace bani da hankali ne ahungunce?"

Bakinsa ya rufe da hannunsa "A'a ni na isa, ba haka nake nufi ba. Ammm an shiga masallaci idan na fito zan kiraki."

Saurin datse kiran yana dariyar katoɓarar da yayi, dan tsaf idan ya tsaya rigima ce zata ɓalle.

Agefenta kuma tabi wayar da kallo da aika mata harara, oh itama fa akwai tarin salloli akanta, ƙila harda tarkus salat ɗin data haɗa ta ƙara taimakawa wajan buɗe wahalarta.


🥀🥀🥀🥀🥀🥀


Hhhhhhh kada kuyi dariya da yawa, ku dai ku ƙara tattara kimarku da mutuntakar da kuke da ita, sai ku magantu akan abin dake malale aruhinku.


#TKMW

#NWA

#Cmnts, like share

#Giramamawa


©UmNassHANYAR BAUCHI 🚎


Wattpad @UmNasss


Page 6


Saƙar zuci ta shiga yi, ta kamo nan ta ɓalle nan, ganin duk abubuwan da take saƙawa ba kaita zasuyi ba yasa ta fara jero Istigfari acikin zuciyar ta.

Wata ƙila zata dace ta rabauta da samun sauƙin wahalar da ke gabanta.

Ita bama wanan ba, tunanin yanda zata bari wani tulelen gardi ya tsallakar da ita ruwa da sunan iyo shine yafi tsaye mata arai.


Sun ɗauki fiye da awanni huɗu awajan, tuni duhun dare ya shiga, ƙarfe kusan goma na dare tayi alokacin, ruwan da ake ma ya ɗauke cak.

Daga nan layi yazo kan motar su aka sauƙe musu kayan su. Kowa ya ɗauki ƙunshin kayan da ya zo da shi.


Aciki kuwa jakar Mubarakatu tafi ta kowa girma da nauyi, kai kace ƙunshin barin garin ne gaba ɗaya.


Kayan ta ɗaura da ƙyar tana nishi ta azasu akanta, wanda saida ta ji bayan ta da ƙirjinta sun amsa saboda tsananin nauyin da ta mata akai, ga kuma wata jakar arataye akafaɗar ta, wanda abaya ita ce kamar ta gayu, amma yanzu ta zame mata ƙarin wahala.


Ko wata ɗaga ƙafa da zatayi tanayin sa ne da fita da sauƙar nishi, wanda yake nuna tsan-tsar gajiya da nauyin kayan nata.+


Lokacin da tazo ta tadda sarkin shisshigi na ta tsallakar da mutane, hakan yasa yana hangota da saurinsa ya tare ta "Hajiya kawo kayan naki na tayaki ɗauka, sai kizo na tsallakar da ke."


Wata uwar harara ta aika masa, duk da duhun daya karaɗe wajan, taja dogon tsaki "Allah ya tsare ni ƙato ya taɓa ni har ya tsallakar dani, an faɗa maka agajiye nake da zaka wani ɗebo jeki zaka ɗaukar min jaka ta?" dama cike da jin haushin sa take na kiranta da yayi marar haƙuri abaya.


Mamaki ne ya kama shi, shi zuciyar sa ɗaya yazo dan ya taimaka mata ganin yanda take faman nishi da haki na ɗaukan kayan. Amma kuma sai gashi daga shirin taimako tana so ta masa bahaguwar fahimta.


"Allah ya baki haƙuri Hajiya. Ni da zuciya ɗaya nazo taimakon ki, haka kuma ina miki kallon yayata ne acikin tafiyar nan, shi yasa nazo da zummar taimakon ki, amma tunda kin gaza fahimta ta jeki Allah fissheki hanya."


"Ameen idan da gaske kake, sarkin shisshigin duniya."


Tana gama faɗar haka ta raɓe ta jikin sa ta wuce, baki ya riƙe yana ƙara jinjina girman fitina da rigima irin na wanan matar, duk ƙalubalen da suka sha ahanya, bakinta bai mutu ba asalima kamar ana ƙara buɗe mata wata sabuwar rigimar ne.


"Allah ya kyauta." ya faɗa yana bin bayan ta, dan ya samu ya wutar da sauran mutanen da suka rage.


Lokacin da Mubarakatu ta kawo bakin ruwan ta ɗauki lokaci tana nazari da tunanin shiga ruwan, gefe guda kuma tana hasaso tarin fargaba wajan shigar ta cikin sa.


Da ƙyar ta aro dauriya da dukkanin juriyar da ke jikinta ta tattare zaninta sama. Hannu bibbiyu ta ɗora ta riƙe jakarta gam, wadda zuwa yanzu nauyin ta ya ƙara daƙusar da ita.


Tana jefa ƙafarta wani sanyi ya mata dirar mikiya tun daga ƙafar ta har zuwa tsakiyar kanta, sai da ta runtse idon ta da ƙarfi, kana ta iya jarumtar zura ɗaya ƙafar tata, jin ruwan bashi da zurfi yasa ta taɓe baki "Ashe ma ruwan ba wani zurfi gare shi ba, tsabar kukutu da kuranta abu ne irin na mutane."


Cike da gadara take yawata ƙafarta tana jefata ako ina, sai da tayi nisa da tafiyar ta zo tsakiyar ruwan gaba ɗaya ta lume kwaaacammmm, sautin lumewa da nitsewar ta bada wanda sai da ruwa ya shiga ta baki da hancin ta, ga ƙarin nauyin uwar jakarta daya taimaka wajan buguwar kanta acikin ruwan "Wayyo Allah nah!" Ta faɗa cikin wata wahalalliyar murya da sautinta yake futa da bugawar zuciyar ta, saboda tsananin tsoron daya sauƙar mata alokaci ɗaya.


Rasa inda zatayi da ranta tayi, dan ko ina ajikin ta ya lume, saifa iya kanta da yake ɗauke da jaka sune kawai basu nitse aruwan ba.


Tafiya ta farayi cikin karaya da sarewa da rayuwa, hakan ya dirar mata da tsoro a zuciya, musamman na rashin wata masifa ce kuma zata samu kafin ta shiga ruwan.


Da ƙyar take iya ɗaga ƙafarta, tana ci gaba da tafiya bakin ta kuwa Addu'a take tana ƙarawa da kalmar Shahada, saboda ayanzu kuma ta fara fidda rai da rayuwa, gara taci gaba da yin Kalmar shahada wata ƙila idan mutuwar tazo mata ta samu sassaucin wani abun, ko ba komi ta tsira da mutuwa acikin musulunci.


Saida tayi tafiyar mintuna ashirin sannan ta samu ta fita acikin ruwan jikin ta tuni ya fara karkarwar sanyi.

Kowa na motarsu ya Hallara ita kaɗai ake jira, hatta motar su direban ya wuce da ita shima.


Kallon ta suke babu wanda yayi mata magana, dan zuwa yanzu kowa ya gama sanin halayyar ta, badan tausayi da zuciyar Musulunci ba to da tafiya zasuyi su barta.

Amma sanin hakkin ta da zai iya binsu yasa suka tsaya suka jira ta. Duk abin da ya faru tsakanin ta da Matashin saurayin, sun ji sun kuma gani da idon su.


Ƙara wayar ta tayi ta ɗauka cikin jakar hannun ta da ta jiƙe jagaf, dan ma Allah yasa akwai santsin leda da tuni kayan jakar ma sun jiƙe.


Suge jakar tayi ta ɗauki wayar cikin wahalalliyar murya ta fara magana "Abdul bana jin magana yanzu, kayi haƙuri anjima mayi wayar." ta faɗa cikin muryarta mai rauni da kuma sanyi.


"Kun Isa gida kenan? Tunda har kina cewa baki jin magana." ya faɗa yana murmushi wanda take jin sautin sa akunnen ta.


"A'a bamu isa ba, ƙila ina tunanin ajalina ke ɗaukana cikin tsinaki, wasu wahal-hallun da gajiyawar da ke tare da ni ba zasu faɗu ba. Amma koma miye ya faru idan kaji labarin mutuwa ta dan Allah ka yafe min kaji."


Jikin sa ne yayi sanyi sosai da jin maganar ta, zuciyar sa ce ta tsinke da fargaba alokaci ɗaya, muryar sa na rawa ya fara magana "Wani abun ne ya sake faruwa da ke kuma?"

Ido ta lumshe tana ƙara dai-daita tsayuwarta wanda sanyi ya fara kaɗa ta, muryarta ce ta fara rawa alamun sanyin da yake busawa yana taɓa ta sosai "Wasu abubuwan basu faɗuwa afatar baki Abdul, amma hasashe da ƙiyasi yakan hasko mana halin da wanda muka damu dasu suke ciki, idan kuma har zan faɗaɗa na buɗe zuciya ta wajan faɗa maka, nasan ƙunci ne zai maye wajan nishaɗin da kake ciki."


"Muubarakah! Ki sanar dani halin da kike ciki dan Allah?" shima ya faɗa cikin sanyin muryar sa, sosai tausayin ta ya kama shi, yana kuma jin tsoron abin dake faruwa atare da ita, ji yake kamar yayi tsuntsuwa dan ya risketa a inda ta ke, wata ƙila ya bata kariya da kulawa.


"Karka damu, babu abin daya faru mai tsanani. Ana jirana anjima zamuyi waya." tana gama faɗar haka ta datse kiran wayar Abdul ɗin.

Da kallo yabi wayar cikin sanyin jiki da kuma fargaba ta rashin sanin abin yi. Komi akayi matsalar dake tare da Mubarakatun sa ta zarta yanda yayi tunani, haka kuma ta shallake ko wani tsammanin sa. Azuciyar sa ya mata fatan alkhairi na sauƙa lafiya da kuma isah gida lafiya. Yana kuma fatan Allah ya tsayar mata koma wata wahala ce iya nan.


Gefen Mubarakatu kuma lokacin da ta gama waya ta ɗingisa da ƙyar ta ƙarasa kusa da su, saboda sanyi da iskar da ake ta taimaka wajan ratsa jikin ta, musamman kasan cewar kayan ta da suke jiƙe sharkaf da ruwa.


Tuni suka hau suka ci gaba da tafiya, babu laifi yanzu direban ya bama motar sa wuta, suna ɗan sauri da gudu. Suma kuma sauran fasinjojin jifa-jifa suke hirar, kowa jikin sa kuma yayi la'asar na rashin sanin makamar tafiyar su, ga duhun daren da kan ratsa ya taimaka musu wajan shiga tai-tayin su. Sai dai basu ƙara bi ta kan Mubarakatu da ke rakuɓe agefe ba, wanda zazzaɓi ya rufeta jirgif, ga wani Azababban ciwon kai da ƙirjin da ya haɗar mata alokaci guda.....


🥀🥀🥀🥀🥀


Saura ƙiris dai akai ga gaci, ko ban faɗa ba nasan kuna adana kimar nan taku agefe.

Ina kuma jin daɗi da martaba hakan.


#TKMW

#UmNass

#NWA

#CMNTS, LIKE, SHARE

#GIRMAMAWAHANYAR BAUCHI 🚎


Wattpad @UmNass


  Page 7/8


Sai da suka sake tafiyar awa guda sanan suka shigo cikin garin bauchi, wanda kowa acikin su sai da ya sauƙe ajiyar zuciya.

Da ji kasan dama sun riga da sun ƙosa, kana hankulansu gaba ɗaya ya kwanta. Sai Mubarakatu da take duƙuƙuna bakinta na karkawa da haɗuwar haƙoranta awaje guda, saboda zazzaɓin da ya fara galabaita ta.


  11:30 na dare suka tsaya atashayar Bauchi, garin tsit babu ya waitar mutane, sai fa ƴan tsirarun motocin da suke giftawa.


  Motar tana tsayawa kowa y Sauƙo yana hamdala abakin sa, babu kuma wanda ya ƙara ɓata lokaci acikin su ya kama gaban sa, bayan ƴar taƙaitacciyar sallamar da sukayi wa junansu.


Da ƙyar Mubarakatu ta iya fitowa, idanuwan ta duk sun ƙanƙance saboda kuka da zazzaɓin daya gama ratsata, sai faman tattara jikin ta take tana tsukewa waje ɗaya, hakan yasa ta fito ta fara jan jakarta wadda har an fito mata da ita.


  Da ƙyar take iya janta, haka kuma ƙafafuwan ta duk sun mata nauyi, saboda azaba. Bakin titi taja ta tsaya tana kuma jin darurawa da kuma alhinin inda zata samu abin hawan da zai kaita unguwar su. Dan titin tayau yake kamar anyi shara, asalima babu giftawar ko wani abun hawa.+


Wani tsoro ne ya ƙara kamata jin haushin karnuka na kusantowa gareta, waiwaye ta farayi tana lalimen inda sauti da haushin yake fitowa, amma bata ganshi ba, bata kuma ji daga inda yake fitowar ba.


  "Ya Allah ka dube ni, ka sassauta min, kada ka barni da iyawata ka kawo min ɗauki daga wanan matsin da nake ciki." ta ƙarasa faɗa hawaye na zuba daga idonta. Ga wata iska da ta kaɗa mai  ratsa jiki.

  Tafiya ta farayi tana nufar hanyar da take ganin zata ɓullu da ita, wata mota ce ƙarama mai launin ruwan ƙasa ta tsaya agaban ta.

  Tsayawa tayi tana tasbihi aranta da duk wata Addu'ar da tazo daga bakin ta gudun kada ace masu satar mutane ne suka tsaya agaban ta.


  Glass ɗin motar aka zuge cikin mamaki sai taga matashi sarkin shisshigin motarsu agefen direba yana leƙowa da mata magana "Hajiya shigo muje mu ƙarasar da ke gida, dan na tabbata yanzu ba zaki samu abin hawa ba."


Ajiyar zuciya ta sauƙe ahankali, ba tare da musu ko fargaba ba ta buɗe gidan baya na motar ta shiga. Aranta kuma tana girmama mutunci da kawaicin Matashin duk da wulaƙanci da gwaliyar data sha yi masa amma bai ƙyale taba ya sake taimaka mata akaro na biyu. Wanan ya zame mata wani sabon karatu, ta kuma ƙara shiga taitayinta acikin rayuwarta ta gaba.


Tana shiga suka Jaa motar suka fara tafiya, sai anan ta kula ashe karnuka ne har guda huɗu aɗan gaba da ita suke haushi 'Lallai Allah ya auna mata arziƙi, da ace ta ƙara ɓata lokaci to ko shakka babu da karnukan nan sunyi fata-fata da naman jikin ta.' maganar da Mubarakatu tayi azuciyar ta tana kuma sauƙe ajiyar zuciya.


"Hajiya wata unguwar zamu kai ki?" Matashin saurayin ya tambaye ta ba tare daya juyo ya kalleta ba.


  "Unguwar Zango"  ta faɗa cikin sanyin murya, wanda ya sashi juyowa ya kalleta, dan bai ɗauka ta iya magana ahankali ba, shi yasa yake tunanin ko ba ita ta faɗi unguwar ba.


  "Ina kika ce?"


"Unguwar Zango nace maka." ta sake mai-maitawa tana tattarawa waje ɗaya.

Kai ya jinjina sanan yace "Ashe ma bamu da tazara sosai."


"Allah sarki." ta faɗa tana ƙara takurewa waje ɗaya.


Daga nan ya juya suka ci gaba da hira shi da abokin sa sai alokacin taji sunansa Abbakar saddiƙ.


  Har ƙofar gida suka kawota, da sauri ya fito ya buɗe mata ƙofa ya kawo mata sauran kayan nata, kana ya tsaya ya bubbuga ƙofar gidan, sai da yaji alamun kamar magana sanan ya shige mota.

  "Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi." Mubarakatu ta masa godiya cikin sanyin muryar ta.


  "Ameen, Allah huta gajiya." ya faɗa gami da mata fatan samin sauƙin wahalar hanyar da suka shawo.


  Saida suka tafi sanan taci gaba da ƙwan-ƙwasa ƙofar gidan.


  "Wai waye ne cikin daren nan?" ta tsinkayi sautin muryar Yaya Surajo ta daki kunnenta.


Cikin rawar murya ta fara magana "Nice Mubarakatu daga kano yaya Surajo."


  "Mubarakatu kuma?" Yaya surajo ya faɗa cikin mamaki, sanan da rawar jikin sa ya buɗe ƙofar gidan.


  Tabbass Mubarakatun Inna ce, dube-dube ya fara yi can kuma ya sake kallon ta "Mubarakatu lafiya da tsohon daren nan? Ina mijin naki yake?"


"Ni kaɗai na taho Yaya." ta faɗa tana son rakuɓewa ta jikin sa ta wuce.


"Ke kaɗai kuma? Wata matsala ce ta haɗoki ke da mijin naki?" ya sake aika mata da tambaya saitin ta, dan tun bayan auren ta bata taɓa yin bulaguro ba tare da shi ba.


Gefen Mubarakatu kuma ayanzu ta fara jin jiri, da ganin duhu-duhu, sosai take ƙoƙarin aro dauriya da juriya dan ganin ta iya tsayawa da ƙafafuwan ta. Amma ina jikin ta ya ɗauki rawa na sosai.

  Kallon ta Yaya Surajo ya sake yi, tabbas bata cikin yanayin jin daɗi, amma kuma banda abin Abdul komi zai haɗasu ai bai kamata ya koro musu ita da wanan daren ba.


Ran sa ne ya kai ƙololuwa wajen ɓaci ya bata hanya ta shige gidan, sai da ta shiga tsakar gida ta yanke jiki ta faɗi.


Da sauri saurin mutanen da ke gidan suka iyo kanta, dan tunda suka ji ana bugun ƙofa suka san ba bugun lafiya bane, jin kuma an ambaci Mubarakatu daga kano ya sake jefasu cikin firgici da tsoron abin da ke tafe da ita.


Arikice suka ɗauke ta suka sakata amotar Yaya Surajo suka nufi asibiti da ita, tuni likitoci sunyi kanta kasancewar Asibitin kuɗi suka kaita.

  Ruwa da allurai aka mata barci ya ɗauketa.

Sai kaiwa da kawowa yaya Suraj yake, azuciyar sa kuma yana hararo girman rashin adalcin da Abdul yayima ƙanwar su, na barinta ta taho acikin tsohon daren nan.

Abban su kuma yana gefe azaune ya rafka tagumi, shi bai ma san ta ina zai fara bayyana damuwar sa ba.

So yake yaga Mubarakatun sa ta farfaɗo ya tambayeta abin da yayi silar barin ta gidan mijinta, da kuma ƙuncin data ƙunsa aranar yau.


Likitan ne ya musu alamu da su shigo office ɗinsa, cikin sauri suka bishi atare sun tadda yana ƴan rubuce-rubuce kana ya ɗago da kallonsa ga Abban.


  "Ya akayi kuka barta ta zauna da yunwa har taci jikin ta? Ga jikin ta baya son ruwa amma da alamu ruwan yau ya daketa sosai, wanda shi ya haddasar mata da zazzaɓin da ke jikin ta."


Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Abba da Yaya Surajo da kuma su Inna da suka kasa fahimtar bayanin likitan.


"Yau ɗin nan tazo daga Kano likita, bamu da masaniyar abin da ke damunta."


Kai likitan ya jinjina sanan ya zare gilashin dake idon sa "To gaskiya nayi mamakin ciwon daya kamata atsakanin wanan lokacin, Ulcer ta mata kyakkyawan kamu, kana zazzaɓi ya rufeta da ciwon kai mai tsanani, abu na gaba wanda yafi ɗaga mana hankali shine Zuciyar ta data tsinke alokaci ɗaya, sakamakon ganin wani abu daya tsorata ta ko kuma ya firgita ta. Lallai akula da hakan, idan irin hakan ta sake faruwa to zuciyarta ba zata iya ɗauka ba."


  "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un." kalmar da suka shiga mai-maita wa kenan cikin haɗuwar baki.


Gumi tuni ya jiƙe jikin Abba da Inna, yaya surajo kuma sai faman fifita rigarsa yake a jikinsa.

Wanan wani irin tashin hankali ne yarinya ƙarama tayi karo da shi? Tambayar da sukewa Mubarakatu da kuma tausayawa halin da suke cikin.


  "Karku damu, abin yazo da sauƙi ma da kuka kawota akan lokaci, yanzu ruwan da aka sa mata yana ƙarewa zaku iya tafiya." daga nan ya miƙo musu takarda magani da musu kwatancan inda pharmacy ɗin su yake da zasu siya mata.


Jikin su asanyaye suka tashi suka nufi ɗakin Mubarakatu bayan likitan ya basu tabbacin zasu iya ganin ta.


  Inna harda hawayen tausayin Mubarakatu sai da ya zuba akan fuskarta, ganin lokaci ɗaya fuskar ta tayi wasai.


"Abdul bai kyauta mana ba, wani irin zama suke shi da Yarinyar nan da ya koro mana ita da dare?" Inna ta faɗa tana matsar ƙwalla acikin idonta.


  Numfasawa Abba yayi "Yanzu dole sai dai mun jira ta tashi, sanan zamu san abin da ke faruwa tsakani ta

da shi mijin nata."


  Ahaka suka shafe fiye da awanni Uku har ruwan ya ƙare ta huta sanan suka nufi gida....


🥀🥀🥀🥀🥀


#TKMW

#NWA

#Cmnts, like and share

#GIRMAMAWAHANYAR BAUCHI 🚎


WATTPAD @UmNass


Last page 9/10


Koda suka je gida abinci inna ta kawo mata cikin faranti sai nono kindirmo da aka dama mata shi da zuma, ta ajiye mata agabanta.


Ai ganin abincin da Mubarakatu tayi ya taso mata da yunwar da ke maƙale acikin ta, nan ta shiga ci hannu baka hannu ƙwarya. Kafin wani lokacin ta cinye abincin tass, sanan ta janyo kwanon da aka dama mata furar itama ta shanyeta.


Tsoro da Al'ajabi ya kusan kashe su anan, mamaki na sosai ya kamasu ganin yanda Mubarakatu ta cinye abincin da ƙartai uku zasu ci su ƙoshi.


Kowa kallonta yake sai alokacin ta kula da aikin da tayi, sai kuma ta sunkuyar da kanta tana goge bakin ta da hannu.


"Sannu Mubarakatu, lallai Abdul ya cuceki, ya rasa horon da zai miki sai na Yunwa." Inna ta faɗa tana matsar ƙwalla a idon ta.


Da mamaki Mubarakatu ta kalli Inna "Abdul kuma? Wa ya faɗa muku horon yunwa yake min?" ta aika mata da tambayar cikin mamaki.


"Haba kowa ya ganki ai ya san kina cikin wani hali, kinga yanda idonki yayi zuru-zuru, ga kuma likita ya tabbatar mana da ulcer data miki mugun kamu, sanan abu mafi tsoratarwa zuciyarki data tsinke. Mubarakatu magana tazo ƙarshe ki sanar mana da abin da Abdul ya ke miki, mukuma zamu nemar miki hakkin ki." Surajo ya faɗa yana huci kamar kumurcin zaki.+


"Tabɗijam!" Mubarakatu ta faɗa tana kallon su ɗaya bayan ɗaya. 'Kenan su Abdul ma suke Zargi da zaman sa sila acikin wahalar ta, Allah sarki bawan Allah da sun san ƙoƙarin sa akanta da basu fara wanan tunanin ba.


"Ko kaɗan Abdul bashi da hannu acikin lalurata ta yau, asalima da ace zai san hakan zata faru dani to da ya bani kariyar da zata sa hakan bata faru da ni ba."


Harara Adda Fatima ta aika mata "Karki raina mana hankali, idan ba namiji ba babu wanda zaiyi silar haɗaki da tsinkewar zuciya, har kuma ya koreki atsakiyar daren nan."


Baki ta riƙe sanan ta girgiza kai "A'a wallahi kadama ku sa Abdul acikin maganar nan, dan koma miye ni na janyowa kaina shi... Daga nan ta basu labarin abin da ya faru tun farkon fitowar ta gida da hanata zuwan da Abdul yasha yi, har kawo tasku wahala da shiga ruwan da tayi kawo zuwanta duk saida ta faɗa.


Salati suka shiga rafkawa hannu bibbiyu suke tafawa, takaici ya hana Abba magana sai Yaya Surajo ne ya fara magana kamar ya kwaɗeta da mari "Amma da nasan abin da kikayi da kanki shi ya janyo miki rashin lafiya wallahi da ban ɓata lokacina na hana idanuwa barci saboda ke ba. Har yanzu kina nan da tsinanan taurin kanki da kafiyar tsiya wadda babu komi acikinta sai zunzurutun wahala. Allah sarki ni mai ƴar uwa na fara zargin bawan Allah Abdul akan shi ya kore ki ashe ke kika siyima kanki wahala da kuɗin ki. Wanan kaɗan ma kika gani mutuƙar zaki ci gaba da Taurin kai wata rana sai dai awuce da ke maƙabarta." yana gama faɗar haka ya wuce fuuu kamar kububuwa ya shige ɓangaran sa.


Kallonta Abba yayi anutse kafin nan yayi gyaran murya "Mubarakatu!" ya faɗa cikin tausasawa wanda ya sata saurin ɗagowa ta kalleshi, idonsa yayi ja ainin wanda da gani na ɓacin rai ne tsantsa, saurin sauƙe kanta tayi ƙasa dan ba zata iya jure kallon da Abban ta yake mata ba.


"Na ɗauka zuwa yanzu kinyi hankali kin sauya, na ɗauka duk abin da na faɗa miki abaya kin musu kyakkyawan ruƙo da hannu bibiyu, ashe ni nake nawa kiɗan da rawa, duk kuma sanda na faɗa miki magana yana shiga kina fiddashi ta ɗaya kunnun naki ne. Amma bazan ƙara ce miki komi ba, ba kuma zan ƙara tausasa muryata dan na lallasheki akan abun da ya zama halayya da ɗabi'un da kika ara kika yafama rayuwar ki ba. Idan kina da hankali abin da ya sameki yau ya zama Iznah agareki anan gaba. Gashi dai saurinki ya zame miki nawa, babu kuma abin da kika tadda wanda akace sai an jirayi zuwanki kafin ayi shi. Haka lokaci yake zuwa ya ruga da gudu ko ka amfane shi ko kuma ka barshi ya tafi."


STORY CONTINUES BELOW

Yana gama faɗar haka ya tashi shima ya shige nasa ɗakin ya bar su.

Hawaye kam a idon Mubarakatu yaƙi tsayawa, gashi dai ba da zafi Abba ya mata magana ba, amma maganar sa ta shigeta ta kuma ƙara ratsa dukkanin jikin ta.

"Ai baki fara kuka ba, kamar yanda zance baki ga komi ba, muddun kika ci gaba da biyantama zuciyarki hidimar abin da take so kiyi mata. Allah ya shirye ki." Inna ta faɗa itama tana tashi tana shigewa ɗaki, takaici da asarar kukan da tayi cikin rashin sani duk yabi ya isheta.

Ɗagowa tayi taga sai Adda Fatima ce ta rage awajen itama aika mata da harara "Kin zo kin haramtawa mutane barci, kin kuma faɗar mana gaba saboda shirmenki. Mtsss" ta ƙarasa maganar da dogon tsaki ta fice ta barta.

Tagumi ta rafka tana nanata tarin maganar da kowanne ya mata "Ya Allaha ka yafe min." abin data faɗa tana share hawayen fuskar ta.

Sanan taja jiki ta shige ɗakin Inna, kwanciya tayi sai alokacin ta ɗauko wayar ta, kusan Miss call ashirin ta gani na Abdul, tausayin sa da soyayyar sa suka shiga zuciyar ta "Bawan Allah, mai yi dan Allah." ta faɗa tana murmushi sanan ta danna kiran nasa.

Ringin ɗaya biyu wayar tayi ya ɗauka "Mubarakatu kun isa dai inji yanzu? Ina ta kiran wayarki ba amsa ko wani abun ya sake faruwa da ke? Kina jina Kuwa?"

Ajiyar zuciya ta sauƙe mai nauyi "Abdul mana ! Wacce zan amsa maka aciki?" ta faɗa tana gyara kwanciyarta akan gadon Inna.

Dariya yayi shima dan ayanda yaji muryarta yanzu ya tabbata hankalin ta ya dawo jikin ta "Duka nake son ji."

"To na isa gida, gani akan gadon Inna ta akwance."

Ajiyar zuciya ya sauƙe "Barka nah da arziƙi. To ya hanya ya gajiya."

Fuska ta yamutsa "Hanya babu daɗi mun barta da ƙyar, gajiya kuma akwaita dan sai da na dangana da ganin likita."

Tashi yayi zaune daga kwanciyar da yayi "Kamar yaya kika ga likita?"

Baki ta riƙe kamar yana ganin ta "Ai yau mutuwa ne banyi ba Abdul, yau kam naga cittar wahala mai tafe da attaruhun ƙuntatawa ahanya....... Tass ta bashi labarin hanyar na linƙayar da tayi aruwa, har diramarsu ta ƙarshe da iyayen ta da kuma abin da likita ya faɗa akan ta.

Haba Abdul mi zaiyi inba dariya ba, dariya yake yana ƙara haskota da jakarta aka acikin ruwa "Taɓɗijam! Ai ko ni namiji na ɗauki jakar nan nayi tafiyar mintu goma zanji ajiki na, balle ke mace acikin ruwa iya wuya. Lallai kinga iya-wuya." ya ƙarasa maganar yana ƙara kwashewa da dariya.

Haushi ne ya kamata ta fara magana "Kai ai dama ba'a taɓa maganar kirki da kai, kayi ta yima mutum dariya kenan. Sai da safe ma zan je na rama sallolin da suke kaina." ƙitt ta datse kiran ba tare da taji ta bakinsa ba. Shima ba magana zai iyayi ba dariya ce taci ƙarfin sa yayi ta yinta har ya gaji.

Sallolin da suke kanta ta rama kaff zuwa lokacin aka fara kiran Assalatu, tashi tayi ta gabatar da raka'atanil fijir kana ta ɗora da sallahr Asuba, ko Addu'a bata gama ba ta ɓungure sai barci.

*******

Kowa yazo yaga mubarakatu ya tambaya yaushe tazo Inna ke bada labarin irin tafiyar da tayi da kuma abin data tadda ahanya, kafin wani lokaci ƴan uwa sun koma tsokanar ta, dan ita kanta Inna abin dariya yake bata musamman da Adda Fatima ta hasko mata nauyin jakar Mubarakatu da kuma iyon da tayi aruwa. Tun tana damuwa har ta maida abin shiririta.

Ranar da Abdul yazo kuwa Mubarakatu tace ai ƙafarta ƙafarsa, abinma dariya ya ƙara bawa mutane.

Washe garin ranar da akayi bakwai suka ɗauki hanyar KANO ita da Abdul, har ƙofar gida suka rakota su Inna suna mata fatan sauƙa lafiya. Dan kayanta kam cewa tayi bazata koma da shi kano ba, wahalar da suka bata ahanya ma ya isheta, dan haka ta bama Inna ta rabar su. Tafiyar awa Uku dai-dai ta kawosu garin kano, Hamdala tayi ta sauƙe ajiyar zuciya ko ba'a faɗama Abdul ba yasan dalilin sauƙe ajiyar zuciyar ta.

Dariya kawai yayi ya jinjika kai, lallai wuya ko da magani babu kyau.

******

Bayan wata ɗaya

Zaune suke suna shan kayan fruit jifa-jifa suke hira, tsayawa Abdul yayi daga shan nasa ya kalli Mubarakatu da take sha bata ko ɗagowa kai "Mubarakatu gobe fa za'a yi bikin sauƙar ƴar gidan Anty Sadiya a Jega, kinga ni ba zan samu zuwa da wuri ba, ko zakiyi sammako idan yaso sai na sameki daga baya."

Kankanar da take sha ce ta ƙwareta kafin wani lokaci tari ya sarƙe ta, da sauri ya miƙa mata ruwa ta kwankwaɗa babu ko ɗagowa, kana ta ɗago da kallon ta ta kalleshi "Kace mi Abdul?"

"Zuwa Jega gobe nace zaki ci gaba na sameki acan."

"Allah ya tsare ni da tafiya amotar haya ni ɗaya tal, har Abadan abadina Abdul, ai ko baka da lokaci gara na haƙura gaba ɗaya wani lokacin naje ni. Dan ko amafarkina bana fatan Allah ya sake haskon tafiyar wahala acikin mota."

Fuska ya ɗan tsuke duk da dariyar dake cin sa "Amma ai ba ko yaushe ake samun matsala ba, kuma yanzu ni nace kici gaba ba wai ƙirƙirar ta kikayi ba."

"Abdul! Ai gara kace Mubarakatu na tsaneki na gaji da ke, da kace min naje na shiga motar haya nayi tafiya. Na taƙaita maka magana ko nan da Bichi bazan je ni ɗaya ba balle har Jega. Allah ya arama lokaci idan kayi free maje tare." ta ƙarasa maganar tana mai bashi tabbacin maganar ta.

Dariyar da yake riƙewa ce ta fito nan ya farayin ta babu ƙaƙƙautawa "Lallai kinji wuya."

Itama dariyar tayi "Ai idan kaji ance wahala ɗaya ma kenan. Naga wuya iya wuya tsirararta."

"Kai ki ɗan sakaya mata kaya mana." ya faɗa yana ƙara yin dariya.

"Ba wanan zancan, babu kuma kayan da suka samu mahallin zama ajikin ta."

Atare suka saka dariya gaba ɗaya suna kuma tuno kalar wuyar data sha ahanya, suna ƙara yin dariya.

🥀🥀🥀🥀🥀

Alhmdulillahi! Anan na kawo ƙarshen labarin HANYAR BAUCHI ina fatan kun ƙaru daga darrusan da suke cikin sa, ba wai nishaɗin abin da ya faru acikin tafiyar fa, ku kalli kyawawan faya-fayan darrusan da suke shimfiɗe acikin sa. Sai ku ɗauki mafi kyau ku watsar da wanda bashi da kyau ɗin cikinsa.

Post a Comment for "HANYAR BAUCHI CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...