HANYAR BAUCHI CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HANYAR BAUCHI CHAPTER A

HANYAR BAUCHI CHAPTER A

- - Post a Comment

 HANYAR BAUCHI CHAPTER A*HANYAR BAUCHI* 🚎


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


® *NAGARTA WRI. ASSOCIATION*


Page 1


Bissmillahir rahmanir rahim


Godiya ta tabbata ga Allah s.w.a wanda ya bani ikon rubuta wanan labarin, ina kuma roƙonsa da ya kare ni da dukkanin wani mummunan abu.


Wanan labarin ba ƙirƙira bane da gaske ne ya faru, sai dai ɗan ƙari da ba'a rasa ba dan bama labarin armashi.


__________


Ɗebo kaya take tana ƙara danna su acikin jaka, ko ina aɗakin ahargitse yake da kayayyakin da take zubowa daga cikin wadrof nata.

Danna jakar tayi saboda kayan da ta cika, sanan ta rufe ta da ƙyar, duk ta haɗa uban gumi, kamar da tayi gagarumin aiki.


Shigowa ɗakin yayi da sallama abakin sa, turus ya ja ya tsaya ganin tulun kayan da ta barbaza akan gadon, ga kuma lokar kayanta awangale duk an hargitsa su.+


Kallonta yayi yaga tana dai-daita zaman mayafinta ajikin ta "Wai ina zaki je ne haka?" ya tambaye ta cike da mamaki.


Ɗagowa tayi ta aika masa da wani kallo mai kama da na ban haushi "Ban gane ina zani ba? Bayan kuma kana sane da yau ne ake sadakar ukun Baffa nah."


Sassauta muryar sa yayi cikin lallashi ya fara magana "Amma ai nace kiyi haƙuri mu tafi tare nan da kwana uku, saboda aiki na da bazai barni na tafi ayau ɗin ba, kinga Allah basshi sai mu samu sadakar bakwai."


Afusace ta fara magana kamar da yake mata magana da zafi "Tabɗi jam! Lallai ma Abdul ɗin nan, har na tsaya sai anyi kwanaki shida sanan xanje gaisuwar Baffa nah. Ko dan ba naka kawun bane ya rasu shi yasa kake so na tsaya jinkiri anan bayan ga duka ƴan uwa da abokan arziƙi na can suna zuba idon ganina."


Kai ya dafe har yanzu muryarsa akwai rauni da nuna lallashi atare da ita "Ko kaɗan Mubarakatu, sanin kanki ne kin san badan tarin aiyukan da ke gabana ba da tuni mun tafi tare, amma duk da haka kiyi haƙuri ai gaisuwa ɗaya ce, ko nan da shekara ce bata tsufa, balle kuma acikin kwanaki shida dayin mutuwar, Addu'a kaɗai yake buƙata, kuma aduk inda kike zata isa gareshi."


Baki ta saki cikin mamaki da alhinin maganar Abdul ɗin "Shekara fa kace Abdul? Magana nake maka akan Baffa na ne daya rasu har Alhajin mu ya kiraka ya sanar da kai."

Baki ta ciza sanan taja jakar data shirya kayanta ta fara tafiya, har sai da ta ƙaraso kusa da shi tana kallon sa "Kai ne kake buƙatar ɓata lokaci dan zuwa yin gaisuwar, kake kuma da zaɓi akan kaje ko kuma ka tsaya, ni dai kam bazan ƙara koda mintuna goma anan gidan nan ba."


Tana ƙarasa faɗar haka taja jakarta ta wuce shi, da sauri ya bita yana kiran sunan ta, gabanta ya sha "Shikenan naji kiyi haƙuri ki zo na kaiki tasha ki hau mota, nima ba na faɗa da wata manufa ba, kiyi haƙuri."


kai ta girgiza ba tare da tayi magana ba, haka ya kinkimi jakar kayan duk da uban nauyin da take da shi, shi dai mamaki ne ya ƙi barin sa yayi shuru, bayan ya ajiye jakar a bot ɗin motar ya juyo da kallonsa gareta "Nikam wanan uban kayan da kika loda kamar mai barin gari gaba ɗaya, kuma duk wai axuwa gaisuwar mutuwa ne hakan?"


Bata ce masa komiba saboda har yanzu acike take, tafiyar da ya kamata ace tun ƙarfe shida tayi ta gashi yanzu bakwai na safiya har ta gota, amma kuma yana ƙara so ya ɓata mata wasu lokutan da surutun sa.

Motar ta shiga tana ƙara kallon agogon da yake maƙale ahannunta.


"Abdul mana! Kamar na takura ka ne akan kaini tashar nan, gashi kuma kai ka roƙi alfarmar zaka kai nin, ba wai tilastaka nayi dole ba."


Bakin sa ya rufe da hannunsa sanan ya tada motar "Yi haƙuri Madam Mubarakatu, bana so nayi kewarki ne."


Daga haka suka fice agidan bayan mai gadi ya wangale musu get haɗe da musu Addu'ar sauqa lafiya.


Tafiya suke babu mai cema kowa komi, jefi-jefi tana ƙara kallon agogon da yake saƙale ahannun ta tana buga tsaki musamman da ake samun yawaitar go slow ahanyar.


ƙarfe 7:30 suka shigo tasha, wata ajiyar zuciya ta sauƙe mai nauyin gaske, cikin jin daɗin dan wani nauyi take ji kamar an sauƙe mata.

Kallon tashar yayi ya fara yamutsa fuska, dan ko kaɗan baya sha'awar shiga motar haya akaran kansa balle kuma ga matar sa.


Kuɗi ya zaro acikin aljihun sa ƴan dubu duba, ya ƙirga dubu Ashirin ya miƙa mata "Gashi wanan ko zakiyi wata hidimar da su, duk da nasan nima zaki ganni acikin kwanaki uku in sha Allah."


murmushi ta ɗanyi wanda iyakarsa laɓɓan ta "Na gode sosai, Allah ya ƙara arziƙi."

"Ameen"

Sanan ya fito acikin motar, kai tsaye motar da yaji ana kiran Bauchi yayi anan ya biya kuɗin motar, sanan ya ɗauko jakarta aka saka abut ɗin motar, duka motar babu mata maza ne, abin da ya tsana kenan.


"Kinyi sa'a mutum ɗaya ya rage motar ta cika." ya faɗa cikin ƙarfin hali, amma azuciyar sa haushi ne cacir.

Fitowa tayi ta shiga motar tana faman rakuɓewa agefe, wanan shine karo na farko da ta taɓa shiga motar haya, gashi kuma duk maza ne babu mace ko ɗaya.

Leƙowa yayi ta jikin window ya fara mata magana "Hankali na bai kwanta akan wanan tafiyar taku ba, amma ganin kin dage yasa bani da zaɓin da ya wuce na biki da Addu'ar sauƙa lafiya, ki kular min da kanki."


Ɗagowa tayi tana kallon sa, karo na farko arayuwar ta da zata yi tafiya mai nisa ba tare da shi ba, tun bayan auren su, so take tace ta fasa, amma kuma tayi yaya da dubbanin mutanen da suke jiran gaisuwar ta.


"In sha Allah." ta faɗa tana murmushi, dai-dai lokacin da motar su ta fara tafiya, hannu yake ɗaga mata har sai da yaga fitar su acikin tashar, sanan ya sauƙe wata nannauyar ajiyar xuciya.


Cikin sanyin jiki ya shiga motar sa ya nufi wajan aikin sa..

🥀🥀🥀🥀🥀🥀


Tafiya maganin gari mai nisa, ban sani ba ko kun hasaso sauqin da ke cikin tafiyar Mubarakatu.

#TAURIN KAI MAFARIN WUYA

#NWA

#CMNTS, LIKE AND SHARE

#GIRMAMAWA


©Um NassHANYAR BAUCHI 🚎©BY Um_Nass 🏇


Page 2


Gudu sosai direban motar yake wanda har suka fita acikin garin kano, ya kuma ƙure waƙa na tashi amotar.

Shuru mubarakatu tayi tana kallon gefen window ga kuma abin haushi duk sun cikata da surutu, baka jin sautin komi saina muryoyin gardawan dake motar, da kuma sautin waƙar da ba'a fahimtarta.


Har tsakiyar kanta take jin sautin hirar tasu, wanda take fita kamar an buɗe bututun radio marar yi 'Nikam wata ƙaddara ce ta kawo ni shigowa motar haya?' tambayar da tayima kanta kafin kuma ta ɗora da ɗan ƙaramin tsaki. Wanda ya janyo hankalin wanda ke kusa da ita.


"Hajiya lafiya dai kike ta faman tsaki ke ɗaya?"

Harara ta aika masa da shi kafin ta juyar da kanta ba tare da ta tanka masa ba.


Gyaɗar dake hannunsa ya miƙa mata "Bissmillah gyaɗa amaro hajiya, tafiya ana ɗan motsa baki tafi armashi."+


Kallonsa tayi aƙalla bazai wuce sa'anta ba amma yanda yake magana kamar wanda ya yankema ƙasa cibiya, kai ta kawar tana mai gwaɓe baki "Nagode"


Kai ya jinjina, sanan ya maida hankalin sa ga sauran abokan tafiyar, nan suka ci gaba da hirarsu kamar dama can sun san juna.

"Ya Allah!" Mubarakatu ta faɗa tana dafe da kanta da ya fara juya mata.

Sanan ta kai kallonta ga mutanen da basu damu da shiga lamarin ta ba "Haba bayin Allah, ku ko gajiya bakwayi da surutu kamar da kuka samu wajan cin kasuwa."

Kallonta sukayi sanan suka kwashe da dariya, kafin wani ɗan dattijo yayi magana "Haba yarinya, ya Allah zai tsaga mana bakin magana kuma ace muyi shiru, duk nan da kike ganinmu yau muka taɓa haɗuwa, amma kasancewar mu musulmi da kuma zama amota guda yasa mun san juna."

Tsaki tayi ahankali "Amma kuma ai kwayi fatan mu sauƙa lafiya dai, akan wanan surutun naku da ba amfanar damu zaiyi ba."


"Yo fata na nawa kuma, tun fitowarmu gida muke Addu'a har kawo tashin motar, bakinmu baiyi shuru ba." ɗaya daga cikin mutanen mota ya bata amsa.


"Sanan batun rashin amfanin hirarmu ke ce dai bakiga amfaninta ba, amma mu da mukeyi mu zamu bada labarin amfaninta." Dattijon ya faɗa yana jefa goro abakin sa.


Shiru tayi bata ƙara magana ba, sanin cewar ko tayi ba fahimtar abin da take nufi zasuyi ba.


Ci gaba sukayi da tafiya yayin da aka zo tsakiyar hanya, ga gargada da kuma hawa da sauƙa, gefe guda kuma direban sai raraka gudu yake abinsa.

Ƙuuuuuuuu kakeji motar ta bada wani sautin ƙara, nan kan Mubarakatu ya haɗu da jikin Windon motar ya bada sautin Ƙuuummmm.

"Wayyo Allah kaina!" ta faɗa tana dafe da saitin kanta, wanda azaba ta sata furta hakan ba tare da ta sani ba.

Haba mi mutanen motar za suyi inba dariya ba, yanda tayi maganar da kuma salon yanda take buƙatar agaji kaɗai ya isa ya sheda zun-zurutun azabar da taji ajikinta.

"Sannu kinji Hajiya." na kusa da ita ya faɗa yana ƙoƙarin ƙunshe dariyarsa.

Ko ta kansa bata biba saboda azabar da ke saitin kanta ta ishe ta. Kafin wani lokacin kuma goshinta ya ɗan cure saboda tanan ta samu buguwar.


Basu ƙara wata tafiya mai nisa ba motar su ta tsaya cak, bayan ta bada wani sauti mai ƙaran gaske.

Ido Mubarakatu ta fiddo waje cikin firgici da tsoro "Mi kuma ya faru Direba?"

Juyowa yayi ya kallesu "Wallahi nima ban saniba hajiya, sai dai naje na duba."

Fita yayi ba tare da ya jira abin da zasu ƙara faɗaba ya buɗe gaban motar.

Wani hayaƙi ne ya masa Sallama wanda saida ya matsar da kansa ya gama ficewa.


"Turƙashi!" ya faɗa yana sharce gumin da ke zubo masa, kasancewar yanayin damina da ake ciki, idan ba'ayi ruwa ba to akwai zafin rana mai ratsa mutane.

Ɗan taɓe-taɓen sa yayi ya rufe motar, sanan ya koma ya tada motar, amma firr taƙi tashi, yayi hakan kusan sau goma amma babu abin daya sauya.

Ƙarshe ya ƙara fita ya duba injin da kuma ƙasanta, ba abin da ya iya sai tsayawar da yayi yana aika kallonsa ga motar da mutanen cikinta.


Leƙa motar yayi ya kallesu "Akwai matsalafa sosai, dan motar nan ta ɗauki zafi da yawa. Sai mun jira ta huta."

Fitowa sauran mutanen sukayi suna miƙa da wara hannunsu. Sukam ko ajikinsu saima cewa da suke "Mun samu rarar lokacin da zamuyi taɗi awaje."


Afusace Mubarakatu ta fito ta kalli Direban motar "Wata irin mota gareka da har take buƙatar hutu acikin tafiyar da ko awa guda bamuyi ba?"


Kallonta yayi sanan ya karyar da kai "Wallahi bata taɓa yin hakan ba Hajiya sai wanan lokacin, amma kuma nafi kyautata zaton rashin service ɗin da ba'a mata bane ya kawo haka, sai kuma rashin juyen mai da aka samu tsaikon yinsa shima."


Ido ta fiddo waje cikin firgici kafin ta ɗora da salati "Bakwa yima motarku service kuke doguwar tafiya da ita? Ya Allah!" ta faɗa tana shafa fuskarta, idanuwanta tuni sun sauya kala zuwa jajaye.


"A'a munayi Hajiya, dan duk bayan wata biyu muke yiwa mota service, shi kansa juyen bayan wata ɗaya muke yinsa, kinga yau ne ya kamata ayi, amma kuma sai ga tafiya ta taso, babu ta yanda zan iya yin sa."


"Hasbunallahu wani imal wakil!" ta faɗa tana tafa hannayenta.


Sanan ta kalli direban sosai "Amma kuwa kuna zalintar mutane da ita kanta motar, ace sai wata ake mata juyen mai, bayan duk mako ɗaya biyu ya kamaata ace ta samu hakan, gashi kuma service ɗin da shima ya kamata ace anayinsa asati ɗaya shine sai bayan wata biyu shima kukeyin sa. Wata irin rayuwa ce wanan ta cutar kai-da-kai?"


"A'a hajiya muna yi mata dai-dai ƙarfinmu, karki manta mu kasuwanci muke da ita, idan muka tsauwala da zafafa hidimar yi mata juye da service tofa zamu rasa har uwar kuɗi balle kuma riba."


"Ba shakka." ta faɗa tana jinjina kanta da rintse idonta.

Dan wani takaici ne yake kamata, ga ɗacin da ya riƙe maƙoshinta, tsab zata zagi direban motar idan taci gaba da tsayawa akusa dashi.


"To ki ɗanyi haƙuri ki koma gefe kema ki zauna. Nan da muntuna talatin sai mu hau mu tafi."


Ɗagowa tayi da niyar aika masa baƙar magana, amma kuma sai ƙaran wayarta ya katsar da ita, tayi saurin zaro wayar ta duba.

Sunan Abdul ne wanda ta sakayashi da Zumar Ƙauna ajiki, ɗagawa tayi kafin yayi magana ta fara masa magana hawaye na sauƙa akan idonta "Abdul ni kam yau naga gararin motar haya, da nasani nayi haƙuri min tafi tare, gamu atsakiyar jejin Allah sai mun jira mota ta huta kamar basarakiya. Sanan muci gaba da tafiya."


Dariya yasa daga ɗaya ɓamgaran saboda yanda yaji muryarta ko ba'a faɗa masa ba yasan kuka take "Ai abin da nake ƙoƙarin nuna miki kenan. Amma wata mota ce haka?"


Baki ta taɓe sanan ta masa bayanin da direban motar ya mata, habawa nan ya fara dariya harda riƙe ciki.

Haushi, takaici suka sata kashe wayar sanan ta samu waje ta zauna tana rafka uban tagumi.


🥀🥀🥀🥀


Ɗit-ɗitt maza ku matso ku kimanta kimantawarku, dan hanyar Bauchi ta ɗauko zafi da gargadar dakan sauƙa ahanya.

#HanyarBauchi

#NWA

#CMNTS, LIKE, VOTE

#GIRMAMAWAHANYAR BAUCHI 🚎


WATTPAD @UmNass


Page 3


Tagumi tayi hannu bibiyu tana kallon inda suke, jeji ne na sosai, su kaɗai ne awajan sai ƴan tsirarun motocin da suke wucewa jifa-jifa, acikin su da sun gansu sukan tsaya su tambaya ko lafiya?

Amsa ɗaya Direban ke basu "Zafi ta ɗauka suka jiran ta huce ne."

Daga haka sai su su wuce su barsu ba tare da sun sake wata maganar ba, sai ta fatan hucewarta lafiya.


Gefe guda kuma sauran mutanen motar ne suka baje suna rattaba hirarsu kamar sun samu gida. Takaicin su sosai ke kama Mubarakatu, haka kuma akai-akai takan duba agogon da ke saƙale ahannunta.

12:30 har yanzu basu Isah bauchi ba, gashi tun 8:30 motarsu ta fito daga Kano, shima dan sun samu tsaikon go slow ɗin da ke garin.

Tashi tayi ta nufi wajan direban daya saje da sauran ƴan tafiyar suna Rattaba Hirarsu "Umm Nace ba, har yanzu Mintuna talatin ɗin basuyi ba ne?"

Da sauri Direban ya duba Agogon yaga lokaci ya ja, cikin sauri ya miƙe "Yi haƙuri Hajiya, shaf hira ta mantar dani."+


"Ai naga alamun hakan, duka acikinku babu wanda ya matsu da ya isah Bauchi."


Kallonta sukayi sanin dasu take, amma babu wanda ya tanka mata, sai shiga motar da sukayi. Ganin hakan yasa itama taje ta ƙume amazaunin ta tana dudduba wayar ta.


Bayan shigar su motar Direban yayi ta ƙoƙarin tada motar, amma furr motar taƙi taduwa, yayi hakan yafi sau goma har ya haɗa uban gumi.


"Ya dai?" Suka tambaya cikin haɗuwar baki.


Gumin Fuskarsa ya sharce saboda zafin da motar ta haɗa masa "Wallahi taƙi tashi duk ƙoƙarina akan hakan."


"Kamar ya taƙi tashi direba?" Mubarakatu ta faɗa tana wara manyan idanuwanta, zuciyar ta kamar ta faso saboda takaici da zafi.


Fita Direban yake ƙoƙarin yi yana bata amsa "Matsalar ba daga zafin data ɗauka bane, dole akwai abin da yake buƙatar dai-daituwa acikin ta, gashi ni ba wai na san komi dake da alaƙa da motar bane." yana ƙarasa maganar ya fita waje, suma sauran mutanen suka fice.


Zufa ke fitowa daga ko ina na jikin Mubarakatu, ga wani takaicin daya gama Lulluɓai ko wani sashi na zuciyar ta. Hawayen da bata san da wanzuwarsu ba suka farar ankarar da ita sauƙarsu.


Gogewa tayi ta fito cikin jin haushi ta kalli Direban "Amma kasan ka cuce mu ko? Tunda kasan motar ka bata da lafiya Fisabilillahi ai bazaka ɗauki fasinjan nesa ba. Yanzu gashi ka katsema kowa hanzarin sa da uzurin sa, abin da nake ta fatan sauri naje na samu gashi da alama bazan same shiba. Wai ma waya baka shawarar fara tuƙin mota bayan babu abin da ka sani akanta? Acikin wanan ƙungurumin jeji taya yane zamu jure zafin rana da kuma muggan abubuwan da bamu san ta ina zasu ɓillo mana ba?"


Duka kallon ta mutanen suke baki sake, musamman yanda ta tasa direba agaba da faɗa kamar ta kwaɗeshi.

Shikam yasan yau komi za'ace masa shi ya siya, Addu'a yake akan kada suma sauran fasinjojin su masa tijara kamar ta Jarabatun macen nan, daya lura ko kaɗan bata da haƙuri.

Kai ya risinar ƙasa yana sassauta murayar sa "Kiyi haƙuri ƙanwata, ni kaina da nasan motar bata da lafiya da ko kaɗan bazan fara ganganci ɗaukan fasinja ba. Haka kuma acikin ko wani abu na rayuwa kin san mutum baya rasa inda Allah baya jarrabarsa, to wanan itace ƙaddarar mu, amma in sha Allah zamu samu mai taimaka mana ko acikin masu wucewa ne."


Kai ta jinjina tana ƙara aika masa da harara "Haka ko wani mutum yake faɗa ai, da abu ya samu sai yace Jarrabawa ko kuma ya liƙawa ƙaddara, bayan shi ya janyo hakan da kansa, yanzu da ace kana ma motarka service da juyen Mai da hakan bata faru ba ai."


"Ke kam yarinya baki da haƙuri ko kaɗan, kinaga dai agirme ya girme miki amma kinzo kina ta masa magana marar daɗi, ai ko ba komi tunda yace kiyi haƙuri ki barma Allah komi kya haƙura ai. Haka kuma ki kyautata zato da tsammani na alkhairi aduk inda kike, amma kinzo nan kina mana fatan mungwayen abubuwa." Dattijon cikin motar wanda zuwa yanzu kowa yasan sunansa Baba Habu ya mata magana.


"Haba Baba! kaima nasan ranka ya ɓaci akan rufa-rufar da yayi mana, haka nan sai an gama cutar mutum ake tsirar bashi haƙuri, yanzu ina ranar hakan?" ta faɗa cikin ƙara jin haushin sa, da ya shiga kare direban akan maganar da ta shefesu duka.


"Eh koma naji haushi na masa uzuri, amatsayinsa na ɗan Adam wanda yake da ajizanci arayuwa, to kema kiyi haƙuri ki ƙara jira zuwa anjima muga abin da Allah zaiyi."


Kai ta gyaɗa ta koma gefe ta zauna 'Wanan kalmar! Wanan tausasawar! Wanan musayan kalmar da take ta kai kawo tsakanin tafiyarta zuwa mafarin ƙunsar takaicina da ban haƙurin data gagara yi su suka zama sila na janyo mata rashin madafa acikin tafiyar da ta fara yinta, cikin taurin kan da ya zame mata sila na ƙin haƙura da tausasawar da Abdul keyi mata, da yanzu tana gidanta. Gashi ita ba'a Bauchi ba ita ba a Kano ba. Abanza kuma tazo tana haƙuri da shanyuwa atsakiyar ranar da babu girgije ko kuma gajimaren da zai tare mata sauƙaƙa jin sauƙar zafinta atsakiyar kanta.' tarin ƙiyasin maganar da take yi kenan azuciyar ta, tana kuma nadama akan tafiyar data farayi, wanda aciki bata san kuma mi zata tadda agaba ba.

Wanan zai iya zama mabuɗi ko mafari na buɗe shimfiɗaɗɗiyar wahalar da take cikin tafiyar da Taurin kanta ya zame mata sila da kuma tsani na shan wuya acikinta.


Wayarta ce tayi ƙara alamun shigowa kira, ɗauka tayi ba tare data ce komi ba ganin sunan Abdul ajiki "Motar taku ta tashi kuwa?"

Tambayar da ya aika mata asaitin ta cikin muryar tausasawa agareta.


Ajiyar zuciya ta sauƙe wanda har saida yaji "Har yanzu bata tashiba Abdul, asalima ba daga zafin data ɗauka matsalar take ba?"


"Kamar ya kenan?"


"Nikam ina zan sani Abdul, bayan shima kansa direban janta yake ba tare da ya san asalin rayuwar ta da kuma abin da take so ko kuma bata soba." ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka.


Hakan yasa Abdul kwashewa da dariya sosai "Sai kace wani mutum har zai san komi na rayuwarta, wai ko tun yanzu kin fara gajiya?" dariya yaci gaba da yi, dan bai wani maida maganar ta gasken gaske ba.


"Abdul mana! Kabar batun dariya da gaske bai iya gyara motar ba."


Yana dariyar ya bata amsa "Ai dama ba duka direbobi ne suka iya gyara mota ba, idan da gari akusa ya ɗauko muku mai gyara, ko kuma ku jira wani yazo zai taimaka muku."


Ajiyar zuciya ta sauƙe tana fuzgar da iskar dake bakinta, wanda ayanzu tana cike da jin ƙishi na ruwa "Abar wanan batun, yanzu kana shan A.c abinka da shan ruwa mai raɓar ƙanƙara hankalinka kwance, ni kuma gani atsakiyar raɓawar zafi da kaɗawar iskar dake tafiya da hucin gashin rana."


Wata dariya ce ta zoma Abdul sosai "Ki bari Hajiya, saima kin ganni, yanzu na gama cin dambun naman da kika min na kora da ruwan lemo."


Muƙuttt ta haɗiyi yawu wanda yasa Abdul ƙara sakin dariya "Minene wanan kamar faɗuwar abu?"


"Yau baka aikin komi kenan sai na ci da sha?" ta katse masa maganar cikin jin haushin abin daya faɗa mata, shi yasafa akace wani lokacin maza basu da adalci, yanzu da shi wani ne ai yasa mata lemo aƙunshin kayanta, sai ya haɗata da kuɗin da basu da amfani awanan lokacin.


"Aiki kai! Yanzuma na dakata naji yanda kike ne, ina kewarki sosai."

Baki ta taɓe "Banga alama ba tunda kana ci kasha mai sanyi abinka."


Dariya ya kwashe da ita sosai "Kefa kika tanadar min hakan kafin ki tafi, kuma miye laifina dan naci."


"Babu" ta faɗa kafin ta datse kiran wayar.

Da kallo yabi wayar yana ƙara sakin dariya abinsa, "Mubarakatu tawa" idan da abin da zaiyi kewa bai wuce shirme da fushin da take da shiba. Daga haka yaci gaba da duba takaddun da suke gabansa, akai- akai yake murmushi idan ya tuna magaran da sukayi da ita.


🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


👏👏👏Rap rap Wow naga Mubah ta samu zunzurutun matayata alhinin tafiya da kuma tarin masu taya Abdul warwara haƙora dan yin dariya wa tafiya Mubah.

Naji daɗin cmnts da fatan alkhairin da kuka min, hakan ya ankarar dani da cewa har yanzu akwai wanan Kimar akwai kuma tarin dafifin da ke ɗauke da GIRAMAMAWAR da ko wani shafi ke ɗauka. Na gode muku sosai. Ina kuma ƙara aranta ko wata martabawa da mutuntakar data zarta ko wacce acikin tafiyar da aka farata.


#TaurinKai MafarinWuya😥

#NWA

#CMNTS,LIKE SHARE

#GIRMAMAWA


©BY UmNassHANYAR BAUCHI 🚎


  WATTPAD @UmNass


Page 4


  Sun shafe fiye da awa guda suna tsaida duk wani mai motar da ya zo wucewa, amma cikin rashin sa'a duk wanda zai wuce baya tsayawa iyaka su ɗaga musu hannu su wuce da gudu.


  Takaici da dana sani Mubarakatu ta yi shi yafi aƙirga, ga wata azababbiyar yunwa da ƙishir ruwar da take ɗawainiya da ita. Sallah kam ba'a ma batun ta dan babu alamun samun ruwa awajan, su kansu wanda suke tafiya tare babu wanda yake batun sallah.

Ga kuma kasuwar hirar da suka ci gaba da buɗewa hankalin su kwance.

  Kai ta dafe tana auna tazarar tafiyar da take gaban su ayanzu, gashi har kusan ƙarfe 2 rana na shirin yi.


  Tashi tayi da zumar sake yima direban motar magana, sai ga wani direban yazo wuce, tsayar dashi sukayi gaba ɗaya, duk da motar sa acike take, haka ya ja ya tsaya.

"Lafiya kuwa?" ya aika musu da tambayar yana leƙo da kansa ta jikin motar.


"Wallahi mota ce muna tafiya ta tsaya, da fari ma nayi tsammanin ko gajiya tayi muka tsaya ta huta, amma da nazo kunna ta taƙi tashi."


Kai direban ya jinjina sanan ya juyo da kallon sa ga fasinjojin dake motar sa "Dan Allah kuyi haƙuri na duba musu."+


"To ba komi, Allah ya sa ta tashi." suka faɗa cikin haɗuwar baki.


Fita yayi ya fara duba motar, bayan ya ɗauki kayan aikin sa dake motar sa.


Sai da ya shafe mintuna goma sanan ya kunna motar, cikin sa'a motar ta tashi.

  Nan Mubarakatu ta sauƙe wata wawiyar ajiyar zuciya, tana washe bakinta wanda kana gani na tsan-tsar farin ciki ne "Alhamdulillah. Wahalar mu tazo ƙarshe."

Ƙarasawa sukayi kusa da direban da ya gyara musu motar, cikin jeruwar baki suke masa godiya.

Murmushi yayi "Ba komi ai duk yiwa kai ne, sai dai kana kula wajan tuƙin motar, kana matseta sosai da shiga inda bai kamata ba, ba tare da ka rage sautin gudun naka ba."


Kai Direban ya jinjina "Gaskiya nagode sosai, in sha Allah zan kula."


  Fatan alkhairi da sauƙa lafiya ya musu, sanan ya shige motar sa yana ɗaga musu hannu,  suma suna ɗaga musu.


Daga nan suma suka shiga cikin motar suka fara tafiya, tuƙi ya fara yi cikin sinɗa da lallama gudun kada ya sake afkawa irin matsalar farko.


  Gefe ɗaya su kuma sauran fasinjojin sun ci gaba da cakaniyar su, da hirar da baka fahimtar abin da ake faɗa acikin ta.


   Kallon gefen windo Mubarakatu take, tana kuma kallon yanda Direban nasu yake faman tuƙa motar, da yi musu tafiyar hawainiya kamar da baya son su isa inda suke.

Gaza haƙuri tayi ta buɗe bakinta ta fara magana "Nikam wata irin tafiya muke haka Direba? Idan ba har so kake mu kwana ahanya ba ya kamata ka ƙara saurin motar ka."


  Juyowa yayi ya kalleta sanan ya mayar da kallonsa ga tuƙin sa "Bakiji maganar da Direban da yayi akan cewar matse motar, da gudun da nake shi ya kawo matsala agaremu ba? Shi yasa yanzu nake lallaɓa tafiyar, sanin idan naci gaba da tuƙi irin na baya zamu sake fuskantar matsala."


Dafe kai tayi cikin jimami da takaici na bahaguwar fahimtar da Direban nasu yayi "Ni kuwa na fahimci jawabin Direba mai lasisi. Kai ne dai ka gaza fahimtar inda bayanansa suka sa gabA, yayi maka magana akan taƙaita shiga ko ina da gudu da motar, amma ba wai magana yayi maka akan ka mana tafiyar hawainiya acikin kwalta mai kyau ba."


  Kai ya gir-girza "Ki dai barni kawai na tafi ko ina ahankali, saboda idan nace zan ƙara malejin gudun to kamar na ƙara ƙure mata hanyar da zata sake gajiya."


  Tsaki tayi mai sauti, wani ƙunci na ƙara sauƙar mata, ba zata iya ƙiyasin daɗin da taji acikin wanan tafiyar ba, idan kuma har tace akwaishi to kai tsaye zai iya komawa sifili ne, Ma'ana babu alamu da wanzuwar sa.

Amma idan akace kuma ta faɗi wuyar da ke cikin ta, to da gudu zata ce akwai Zunzurutun ta, mafi yawa da tsanani.


   "Uhmm Hajiya kema fa kina da gajan haƙuri na lura, acikin tafiyar nan kowa haƙuri yake saboda sanin halin rayuwa, amma ke abu kaɗan kinyi magana da mita akansa. Ya kamata ki sassauta ma zuciyar ki, kiyi kamar yanda kowa yakeyi." Matashin dake kusa da ita ya faɗa. Wanda ta masa laƙabi da sarkin shisshigi da manyance.


Harara ta aika masa kana ta juyar da kallonta ga sauran mutane "Ku ai damuwar ku da dalilinku ƙila kaɗan ne akan nawa, ba zaku fahimci raɗaɗin da nake ji ba. Wata ƙila saboda duk ku maza ne shi yasa kuke ga rashin haƙuri na." muryarta da ɗan zafi-zafi take fita, saboda yanda suke mata kallon Fitinanniya marar haƙuri acikin tafiyar.


  "Mu kuwa muka fahimci ci-da-zuci irin naki, da kuma ƙaguwa da azalzalar da kike da shi acikin tafiya." Dattijo Habu ya faɗa yana tauna goron bakinsa.


Dariya suka saka gaba ɗaya, wanda hakan ya ƙara ƙular da mubarakatu, wani maƙoƙon baƙin ciki ya dirara mata, da kuma karaya.

  Kanta ta kawar daga kallon su tana ci gaba da kallon windo, idonta tuni ya tasamma zubar ƙwalla.

 

  'Yau komi akayi bata tashi da sa'a ba. Ranar yau ta zo mata cikin duhu da baƙin da ke baƙanta zuciya da ruhi.' goge hawayen Fuskarta tayi.

  Wanda duk acikin motar babu wanda ya ƙara kula da ita da kuma abin da take.


Cikin tafiyar sinɗar da suke kuma aka fara iska mai ƙarfi da alamun sun shiga yankin da ake ruwa, kafin su ankara kuma an ɓalle da ruwa da iska mai ƙarfin gaske.

Nan suka fara salati kowa na ɗaukan Addu'a abakin sa.

Mubarakatu kuma gabanta ya hau faɗuwa, ga wani tsoro daya dirar mata. Allah ya sani tana mutuƙar tsoron ruwan sama ko agida, balle kuma atsakiyar dokar jeji.


   Nan gudun motar ya ƙara raguwa saboda ƙarfin ruwan, suna tafiya ahankali har suka ƙaraso hanyar NINGI, anan kuma suka hango motoci burjuk atsaye. Ga kuma wasu sun fiffito hannayensu riƙe da lema.

 

"Mi kuma yake faruwa anan?" tambayar da suke aikawa kansu kenan, ba tare da sun samu koda amsa ƙwaya ɗaya ba.


   "Wata sabuwa."


 

🥀🥀🥀🥀🥀🥀


#TKMW

#NWA

#Cmnts, like, share

#GIAMAWA


  ©UmNass

Post a Comment for "HANYAR BAUCHI CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...