HADIN ALLAH CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HADIN ALLAH CHAPTER A

HADIN ALLAH CHAPTER A

- - Post a Comment

 HADIN ALLAH CHAPTER A


          
Bismillahir rahmanirrahim
Sanye take da wata kodaddiyar atamfa koriya xanin ta kasa arage yake an dinke da zare da allura,ga tiren tallar gyada akai tana ta faman taunar cingam, a haka har ta karasa dai dai wasu yammata saan nun ta, ajiye tiran gyadar tayi gefe tare da janyo takalminta Dan ta kara daure shi da leda, Dan taga ledar ta fara kwancewa, ba Wanda ta kula a cikin  wanda ta tadda a wajan ba ta fi minti biyarba gyadar ta tafara karewa sosai mutane suke san gyadar ta, duk da kasancewar ta bata da tsafta hakan baya hana mutane siyan kayanta, musamman gyada da suka san ba ita take soyawa ba kuma a bawo take sannan a leda
       A hankali take magana wanda in ba kana kusa da ita ba baza ka taba jin me take cewa, mutum sai bakin jini tinda kika zo naga alama ko Biyar baki ba wlh in nice mai gyadar bazan kara samiki ba, a fusace yarinyar da take kusa da ita  wuyan ta ta shakuma suka fara dambe, mutanan wajan ne suka taso da gudu dan su rabasu,
" ke asabe me ta miki kawai dan neman masifa ki shakumi wuyan ta, wani dattijo ta ya rike hannun ta ke tambayqr ta,
Wlh tsokanata take yi"


Babu wani nan tin da *NUR* tazo wajan nan babu wanda ta kula taya zakice ta tsokaneki, wata yarinya dake talla a gefe ta fda, duk yadda asabe taso su fahimta suka ki fahimta amma suka ki fahimta saima rashin gaskiya da suke bata, suna hada ido da Nur tai mata gwalo, sannan ta cigaba da matsar kwallah,
Cikin fushi asabe ta dau farantin gyadar ta tai gaba, bayan ta saida gyadar ta dau farantin ta tai hanyar gida
Garin panisau gari ne mai rahama, ga kuma gonaki, sosai jamaar garin ke da sannar su Allah kuma ya azurta garin da mahauta, duk inda kika zaga zakiga ana saana, musamman wajan kofa sannan kuma da fada duk wuraran sanaa ne, kuma a wajan yammata garin ke zama dan saida abinci ko kuma wata sanaa tasu ta hannu,
Mutanan panisau akwai zuciyar neman na kansu ko yaro karami ne zaka gansa da  sanaarsa, sosai garin yake da niima
Tana tafe tana waka har ta karasa gdan su, ko sallama Nur ba tayi ba ta shigo gda direct kitchen ta nufa wata roba ta dakko zama tayi a kasa ta fara cin abinci a nutse kadan taci abinci ta maida kwanon kitchen ta goge hannun da taci abinci dashi akanta, sannan ta shiga cikin dakin su
.
    Umma Umma Umma kina Ina ne, Nur ta fda tana daga labulan dakinsu,
" ban sani ba ke wai baza kiyi hankali ba ne , kullum girma fa kike karayi, dan iskanci uban me ya hana ki yi sallama kawai zaki hau kwallan kira kamar baki san inda nake ba, wlh Nur ki fita idona na rufe duk sanda na danke ki baza ki ji da dadi ba, turo baki Nur tayi ta dauke kanta kamar ba ita akewawa maganaba, au dan wulakanci ina miki magana kina turan baki sbda kin raina mutane koh, umma ta fada tana janyo ta
" wayyo umma kiyi hakuri bazan kara ba dan Allah kar ki dake ni, tureta umma tayi ta mike dan fita
" haka kawai dan an tsani mutum sai ana dukanshi, wlh ba dan nasan umma ce ta haifqn ba Allah sai nace kishiyar uwa ce, dan dai kawai muna kamane, dariya ta kusa subucewa umma amma ta dake ta juyo,
Nur me kikace, hanjin cikin nur ne suka mada ummana ba magana fa nayiba haka nace ki soya gyada da yawa gobe dan yau ana ta nema sosai,
Kuma ki kace baki magana ba, mantawa nai ummana
Dariya kawai umma tai tayi waje tana rokon Allah ya shirya mata yarta
   Malam habu ne ya turo kekensa har cikin gda da sallama ya shigo gdan, umma sake zaune akan tabarma ta amsa masa sallamarsa, bayan ya jingine keken ya zauna kusa da umma, " sannu da zuwa malam" yauwa dije, ina nur ne, na aiketa gdan atine ta karbo mun kudi tin kan ai kiran mangariba kaga yanxu har kusan 8:30 amma bata dawo ba, umma ta fda tana daga labule dan ganin ko karfe nawa,
" Allah dawo da ita lpya" Amin malam, umma ta fda tana mikewa dan dakkowa malam habu abincin sa
   Idan na zagayo idan na zagayo idan na zagayo ace tafi kanwar maza ni kanwar maza bazan ki maza ba ko yanxu ma daga gun mazan na........ Dukan da umma tai wa nur a bayane yasa kin karasa wakar, nur sau nawa zance ki daina shigo min gda da waka gashinan ko kallon gabanki ba kyayi kin zubar min da miya,
Ganin abba a zaune yasa ta karasa da gudu ta fda kansa tana kuka, rarashinta dady ya fara yi hkri nur amma daga yau kar na kara ganin kin shigo gda bbu sallama, toh Abba, Yauwa yar gdan Abba tashi ki wanko hannun ki muci abinci, ba musu ta wanko hannunta suka fara cin abinci,  baifi loma hudu nur tayi ba ta dauke hannunta daga abinci, " me zan gani yar gdan abba naga kin dauke hannunki" eh abba na koshi ne" dije ya kamata a nemowa nur maganin cin abinci bnsan meye masalar yarinyar nan ba kwata kwata bata san cin abinci, zan tqmbayi atine ko tasan India zaa samu maganin dan nima rashin cin abincin yarinyar nan na damuna,
.
Honey pls ka hakura da tafiyar nan kaga fa yanxu kusan karfe uku gwanda ka bari sai gobe, sweat heart kiyi hakuri nan da panisau ai ba nisa bane dashi, kawai yau zuwa zanyi na ga kaka, insha Allahu gobe zan dawo da wuri, cikin shagwaba ta kara shigewa jikinsa, toh honey ka kula da kanka bnda kallon mata a hanya, kar ki damu sweat heart ai ke kadaice a raina bbu na biyun ki, dariyar jin dadi  tayi ta rakoshi har mota tana daga masa hannu har ya tafi
.
'Cikin mintuna da basufi arba'in ba ya isa garin panisau, daidai bakin tasha yaxo zai wuce kenan wata yarinya ta taho aguje tabi gabansa ba shiri yaja burki ya tsaya, ita kuwa batama san tayi ba, tasha damara da wani dukukkunannan hijab, cikin zafin rai Nura ya fito ya bi yarinyar nan, shakota yayi ya riko gashin kanta, ta waigo ta sauri zata mai rashin kunya, ya dau hanu zai kwada mata mari ina yaji sam bazai iyaba yarinyar tamai kwarjini dayawa.
      Sakinta yayi tayi gefe tana huci, budar bakinta tace Allah ya isa mugu kawai, cak Nura ya tsaya yakasa aiwatar da komai, haka yayi ta binta da kallo har taje gidin wata bishiya ta dauki tiren gyadarta tayi gaba, sai da ta bace masa sannan ya shiga mota ya karasa gida.
                 Salama alaikun kaka"a'a wanakeji kamar Nura badai kaine tafe da yamman nan ba, "Wlh nine kaka ta shimfida mai tabarma ya zauna, ruwa taje ta kawo mai mai sanyi cikin kwanon sha, ya karba yasha sannan suka gaisa, " ina kuma kishiyar tawa"tana lfy tace agaisheki"ina amsawa Aishatulle, kai kaka kidena batamun sunan mata, "toh mai mata sukayi dariya duka.
          Suna zaune sunata hira da kakartasa Nur tayi sallama ta shigo tasha damara a kugu, ga wata kwalliya data chaba adole wai tayi wanka kenan, ta gaishe da kaka, ta dinga hararar Nura dake zaune bai ma dago yaga ko wayeba yana ta danna wayarsa, kakata tace Nur me zaa baki?" kaka muka da daddawa da magi, sai lokacin ya dago suna hada ido ta gaa mai harara, kaka ta mike taje dakin ta daukowa Nur aikenta, Nur kuwa kaka na shiga daki tafara zagin Nura shi muma yarasa me yasa yakasa yiwa yarinyar komai kasancewarsa mutum ne wanda bayason raini, tace mugu kawai azzalumi Allah ya isana, dai dai nan kaka ta iso, "ke Nur menaji kina cewa, " a'a kaka waka nakeyi, ta amshi aikanta tayi waje.
         Sai jinjina sunan yake aransa Nur, tunda yani kaka ta fada shikenan ya ji sunan ya masa dadi kamar yadda yarinyar ta masa kwarnini, da tunani kalakala ya karasa hirarsa da kaka.
            Da magriba Alh Abubakar kakan Nura ya dawo daga kasuwa, sosai yaji dadiin ganin Nura saboda ya kwana biyu bai zoba, tare sukaci abincin dare sannan sukayi ta hira, karfe tara na dare Nura ya tafi dakinsa dake zaure ya kwanta don hutawa amma me tunanin Nur yaki barin zuciyarsa, dakyar bacci barawo ya sace shi.
            Misalin karfe sha biyu Nur ta fito sanye da wata bakar doguwar riga duk tasha faci, tana dauke da tiren gyadarta, dai dai kan dakalin gidan Kaka ta hango wannan bakon birnin aikuwa da hanzari ta karasa ta sake yimai tsiwa kamar yadda tamai jiya sannan ta fara tafiya, sai yace Nur taja ta tsaya amma bata juyo ba, cike da mamaki tace to ina yaji sunana"can sai ta tuna niya datane gun kaka, yace bani gyadar ta dari biyu, ta juyo ta aniye tiran tace mai ya diba goma goma ce, ya kwasshi kulli ashirin yabata mudinta ta dau tiranta tayi gaba.
    Misalin karfe biyar ya shirya sukayi sallama da kaka ya tafi, kafin ya wuce sai dayabi ta tasha ya sayi gyada gun Nur har yace tabar canjin dubu dayace dama, ta dari biyu kuma yasaya.
      Wlh sai naci ubanki uban waye ya baki kudi, nan ummanta tafara dukanta sai ga abbanta ya shigo, nan Nur ta nufi gunshi tana kuka, lfy dai ko, ina fa lfy malam yarinyar nan ta fara juyen gyada, nan abban ya tambayeta yadda akayi ta fada mai dake ita duk rashin kunyarta da rashin tsabtar ta bata karya.
        .
       A gajiye ya shiga gida, tun yana parking mota, Aisha ta fito tasha kwalliya sanye da wani less pink da stoch baki, yayi mata kyau sosai, da hanzari ta karasa gunsa"sannu da zuwa honey, ya dago habarta ya sumbaci goshinta sannu swt heart, nasameki lfy, "lfy lau sweet heart, yasu kaka?" Suna lfy sunce ma agaishe ki"ina amsawa, yana rungume da ita suka karasa falo, dakinsa ya nufa direct toilet ya shiga ya sakarwa kansa shower, tana hada mai abinci akan dinning.
         Daure da towel ya fito, daya kuma yana goge sumarsa ya zauna ya shafe jikinsa da mai, wadrobe ya bude zai dauki kayan sawa Aisha ta rungumesa ta baya, ya juyo da ita, suna kallon juna, sakarwa junansu murmushi sukayi, ya dauko kayan ta taimaka mai yasa kayan suka nufi dinning, ta zuba mai yadda zai ishe sa.
          Suna zaune a falo suna hira, Nura na zaune akan capet, inda Aisha take kan kujera, ya juyo yace af na manta, ashe nazo da gyada, da hanzari ya mike ya dauko key motarsa ya nufi waje, jim kadan sai gashi yadawo dauke da daurin gyada, da sauri Aisha ta karba, la!, tasoyu ce ashe sweetheart, kai kawai ya daga mata alamar eh, nan suka fara cin gyadar.
       Honey a ina kasamo gyada haka mai dadi?, "hmm kodai kaka ce ta baka, " a'a saya nayi gun wata yarinya NUR, Aisha najin sunan taji gabanta ya fadi, amma ta rasa dalili duk da tasan Nura bazai taba son yar kauye ba bare yar talla.
         Yanaji kinyi shiru?"a'a babu gyadar ce akwai dadi, nan yaji dadi anyaba gyadar Nur, anan ta tashi ta yi daki don tafara hamma.ai kuwa tana tafiya Nura ya fara tuna haduwarsu da Nur, kusan sai karfe sha biyu ya shiga daki, lokacin har tayi bacccinta.
          Nur kizo maza kije ki kaiwa kaka aikan nan sannan ki siyo mun kubewa, kai dan Allah badama mutun ya huta, dawa kikeyi Nur inace nikike zagi?, nifa badake nake ba tana tura baki ta amshi aikan.
           Nura ne ya fito sanye cikin kananan kaya, Aisha na zaune afalo misalin karfe tara na safe, da hanxari ta mike don taga alamar fita zaiyi, "Honey sai ina kuma?, ta tambaya atakaice, ba kalli inda take ba yace" panisau zani amma da yamma xan dawo, cikin rashin kuzari tace to baka karya ba, "hanu ya daga mata alamar baya bukata, shan gabansa tayi lfy kuwa honey?ba yadda nasa ba ganinka bane kodai na maka laifine, yayi murmushi ya rungumeta jikinsa, no sweet heart ba abinda kika mun yau koko da kosai nake shaawar sha shiyasa sainaje panisau xan karya, ta gamsu  da jawabinsa tare sukaje parking space har ya tada mota tana daga mai hanu.

       Isar sa keda wuya ya samu kaka ta sauke kokon kuwa, dama yasan daidai lokacin da take karyawa, bayan sun gaigaisa da kakannin nasa ne, ya dubi kaka, " nikam akwai wata yarinya dana sayi gyada gunta ranar ko kin santa, gyadar me dadi, "kodai  gyadar Nur ce domin duk garin nan gyadarsu tafi ta kowa dadi, inaga itace domin gyadar tana da dadi, kana sone?, " eh asayaomun ta dubu daya saboda Aisha ma tanaso.

   .
     Cikin mota nura ya Shiga ya dakko mata chocolate kwali uku, da murmushi ya karaso inda take
     " kanwata ga tsarabarko,  zaro ido nur tayi kai yaya nura so kake ummana ta Zane ni tace waya bani, murmushi yayi kanwata Umman mu baza ta dake ki ba kinji, naki wayyan, sanda zaa dakeni ai baka sani ba, nur ta fda tana turo baki, sosai nur ta burge nura, zuwa yanxu dai ya tabbatarwa da zuciyarsa yana san nur san da bai taba yiwa wata mace ba
     " yaya kana ji ina ma magana kai shiru, jin shirun yayi yawa nur ta tabashi yaya magana nake,
      Sai da nur ta tabashi ya dawo daga duniyar tina nin da ya tafi, yi hakuri kanwata wani tina nin na tafi da ban,
      " ni dai na tafi kar ummana taga na dade,  toh kanwata ki dauki chocolate din ko daya ce, ba musu ta dauka tai gaba ba tare da tajira taji me zai ce ba , tana tafiya ya Shiva gidan kaka
    " kaka akwai maganar da zamuyi da ke dan Allah" toh miji na ina jinka cikin nutsuwa nura ya fara magana ,
       " kaka wata yarinya nake so a garin kuma wallahi da gaske auranta zanyi, kuma bansan abin ya dau lokaci sbda makaranta zan sata,
      Toh wace yarinya ce mai saa a garin nan da har ta rikita tina nin mijina, ta sashi zuwa garin nan duk sati" murmushi nura yayi ya fara magana
       " Nur nake so tin lokacin dana sata a idona naji ta shiga raina da farko na zaci tausayi take bani sai naga kuma ashe harda kaunarta,
   Sosai kaka taji dadin zancen nura, farin ciki ta nuna sosai, domin tana san nur sosai kuma zata so su hada zuria da gidan su malam habu sbda mutuncin su
     Nura da namiji tilo wajan mahaifansa Alhaji Abdullahi, da kuma mahaifiyarsa hajiya memunatu, yana da yaya mace guda daya Ummul kairi sai kuma kannansa biyu mata Fiddausi sai kanwarsu karama fatima itace wadda shekarunta basu wuce  goma ba, asalin Alhaji Abdullahi haifafan panisau ne su Biyar ne wajan babarsu da babansu, Alhaji Abdullahi Dan kasuwa ne ya fara daga dako a kurmi had Allah ya daukakashi, har uban gidanshi ya bashi auran yarsa memuna sbda yadda yake da amana, ba yadda Alhaji Abdullahi baiyi da mahaifansa su dawo hotoro inda yake amma suka ki
    Malam habu asalin Dan garin panisau ne yana da mata data khadija amma dije ake ce mata, tin da sukai aure basu haihuba, har sun shire rai da haihuwa, Allah ya basu ya mace suka sa mata suna Nur sosai suke santa amma kuma hakan bai hana sun bata tarbiyya ba sai dai bata makarantar boko tana zuwa islamiyya har yanxu da take da shekara tara da haihuwa
    *cigaban labari*
Nura bai ba ranar sai da ta tabbatar masa  da cewa insha Allahu Zara shawo kan iyqyan Nur su yadda, sosai nura yaji dadi,
   Karfe tara na dare nura ya dawo gidansa da sallama ya shiga falon, Aisha sake zaune a kujera tana kallo ta amsa masa sallamarsa ciki ciki, kusa da ita ya zauna tare da janyota jikinsa, ture hannayansa tai ta canxa kujera, kusa da ita ya kara zama, zata tashi ya janyota ya matseta a jikinsa tare da tura bakinsa cikin NATA, saida sukai kusan minti goma a haka sannan ya dagota, sweat heart kiyi hakuri wallahi aiki ne yake min yawa yanxu vai kamata kina fushi Dani ba sbda kefa nake aikin nan, nura bai kyale Aisha va sai da ya tsarata sosai, ranar baccin farin ciki sukai sosai
Jikin Nur yayi zafi sosai, kaka ta jika maganin data karbo tabawa nur maganin sai shegen daci, dakyar ta iya hadiyewa.
        Nura yana fitowa yaga wani dan matashin yaro, "zo dan Allah in tambayeka, cikin ladabi yaron ya karaso kusa da Nura ya gaidasa, Nura ya amsa ya kuma ji dadin hakan, dan Allah ina ne gidansu Nur?ya tambaya yana kallon yaron, yaron yace bayan layine muje in kaika, godiya Nura ya dinga yiwa yaron, tare suka nufi bayan layi, adaidai kofar gidansu Nur yaron yace " ga gidan nan, Hanu Nura yasa a aljihu ya cire kudi ya mikawa yaron yace gashi ko nagode, yaron ya girgiza kai alamar bazai karba ba, dakyar Nura yasa yaron nan ya karbi kudin nan, yace dan Allah ka shiga kacewa kaka Nura ne yazo.
            Da sallama yaron ya shiga gidansu Nur bayan sun gaisa da ummanta, yace an aiko sane gun kaka, kaka dake daki tace zo gani nan, yace wai Nura yaxo, tace to kace ina zuwa yaron ya fita.
          Nura yana tsaye sai ga mahaifin Nur ya dawo, ganin bakuwar fuska yasa shi yayi turus, cikin ladabi Nura ya gaida abban Nur sannan, yace lfy dai malam dai dai lokacin kaka ta fito, a'a sannu da dawowa malam, a'a kece agidan namu h nazo duba jikin Nur ne, toh, wannan Nura sunansa jikana ne, abban Nur ya fadada murmushinsa yace a"a bismilla shigo.
    Tare suka shiga gidan, tabarma umman Nur t shimfida mai, ya xauna ya gaida iyayen Nur cikin girmamawa sannan kaka ta shiga ta taso Nur wacce jikin yanxu da dan dama dama, tana ganin Yayan nata ta sake mai murmushi, wanda hakan shi kadai yasan abinda yaji.
      Kusa dashi ta zauna, tace ina wuni yayana, lfy lau kanwata ya jikin ki?, jiki da sauki yayana ina Aunty Aisha, tana lfy tace na gaida kanwata, ina amsawa, yaya ina alawa ta, yace tana nan dayawa ma nakawo miki, yanxu nazo ne in kaiki asibiti, iyayen Nur kuwa ttsayawa sukayi suna kallon ikon Allah, kaka kuwa hakan ya mata dadi, Abbab Nur yace dama Nur kin san shi ne?,  kai ta daga alamar eh, shine yaban kudi ranar har umma ta dakeni, kuma shiyake sayan gyada sannan yake kawomun alewar birni, sosai ta burge Nura ya sunkuyar dakai, abba ya shiga godiya, kaka tace ba komai malam ai wannan ba komai bane.
         Da kaka da Nurane suka kai Nur asibiti, nan aka mata allurai aka bata magunguna, ya shiga da ita shoprite ya mata sayayya sosai harda kayan sawa sannan sukaje parks tadanyi wasa kadan kasancewar jikin da dan sauki.
    Sai magriba suka koma panisau, sosai iyayen Nur sun yaba da hankalin Nura kuma sun samai albark, Nura bai bar gidansu Nur ba sai kusan karfe goma na dare, haka dayazo da safe sai azahar ya tafi, yanxu kusan kullum gidan yake wuni, har sun saba da umma.
.
Fuskar nan ta ta a daure ta fito kamar wadda bata taba dariya ba, kusa da umma ta zauna, " umma gani ta fda tana turo baki, ni nace ina kiranki, kuma bakiga yayanki ba ne baki gaidashi ba,
" ina wuni" nur ta fda tana murguda baki,
" lpya lau" nura ya fda fuskarshi dauke da murmushi,
Umma ta mike ta shiga daki, kusa da ita nura ya dawo, nur me ya faru kike fushi dani, idan laifi nayi kiyi hakuri, " au bakasan ma kayi laifin ba bayan ka gani a fada har Zan taho shine ka juya ka canxa hanya, sai a lokacin nura ya gane nur ta ganshi, rausayar da kansa yayi, kiyi hakuri kanwata, kinga da auntyn ki muke tare kuma tana da fda sosai in taga ina miki magana zata fara miki masifa, ni kuma ban san bacin ranki, turo baki nur tayi ba tare da tace komai ba,
Baki hakura ba, ba dole na hakura ba, da kyar nur ta sakko suka fara hira sosai, ya dade a gidan sannan sukai sallama ya tafi,
Kullum sai nura ya zo gaidasu su danyi hira ba sosai ba sannan ya taxi sbda gudun kar Aisha ta masa korafi
Yau ta kama lahadi kuma yaune zasu koma gida Aisha ta azzazaleshi su tafi ita ta gaji ba yadda ya iya dole ya tafi ba dan ransa ya so ba ko sallama baima nur ba ya tafi, tinda nur ya tafi bai kara waiwaiyar panisau ba sbda ba yaso Aisha ta zargeshi ya fiso sai an tambayar masa auran ta sannan kowa ya sani,
Yau satin nura biyu baizo panisau ba tin nur na damuwa har ta shire shi aranta,
"Nur wai bazaki zo ki dau tallarba sai ranki ya baci koh, " umma yanxu zanxo so nake na dauraye jikina, au baki wanka ba, " umma ana wannan sanyi na yamma zanyi wanka, sbda kwaliyar jumaar ma da zanyi ne kawai yasa zan wanke jiki na, cikin bacin rai umma ta fito daman ta dora tukunyar sanwa, kwashe ruwan tayi sanan ta sirka, nur na kuka umma ta janyo ta yi mata wanka, sosai nur ta shiga rera kuka kamar wadda ake mata azaba, sanda aka gama mata wanka ta shige daki rai a bace,
Jin kukan nur ya sashi saurin karasowa cikin gidan, cikin girmamawa ya gaidata ta amsa, " umma me ya sami nur nake jiyo kukan tin a waje" bari kawai nura yarinya sai shegiyar kazanta kullum a na nuna mata bata ganewa, Allah sa umma baki dakar min kanwa ba, a'a ban dake taba wanka kawai na mata shine take ta rero kukan nan,
Bari na shiryata kar tamin ba dai dai ba toh umma bari naje na dawo,
Ya fda yana mikewa, sosai umma ta gyara yarta ta tamata kwaliya, sannan ta dora mata talla tai waje
Bayan sallar isha'i nura da kaka suka zo gidan su nur sun kwa ci saa Abba na nan tabarma umma ta shimfida musu suka zauna
Daman malam habu jika nane yaga nur yace yana so shine yake so a tambayar masa izini idan ba wanda ya rigashi, yana santa kuma baya so abu yay tsayi sbda yana san sata makatanta, da kyar Abba da umma suka yarda sai da nura yay musu kuka sosai ba karamin tausayi ya basu ba hakan yasa suka yarda akan ya turo mahaifinsa ai zancen auran, washe gari tin safe ya tafi gida wannan karan ko haduwa basuyi ba
" mlm kaga *hadin Allah* koh jibi yadda yaron nan yake san nur fatan mu dai Allah yasa tayi alfahari da auran da za a mata
" da daddare nura yaje ya sami mahaifinsa a daki, cikin girmama ya gaidashi, bayan ya gaida shi, sai yace ahm baba daman sai yafara Sosa k'eya, daman  me mahaifin yace, "um daman baba wata yarinya ce nagani danaje gidan kaka shine... Sai mahaifin nasa yayi murmushi yace, nura daman na dade ina jiran wannan ranar sai gashi allah yakawo ta, Allah yasa yar gidan mutunci ka samo, akwai wani abokina ma da naso ka auri yarsa amma tinda ka samo da kanka ba matsala fatana dai Allah yasa ka iya adalci tsakanin matan naka,
Cikin jin dadi yace insha Allahu dady zan iya
Allah yasa dady ya fda yana fadada dariyarsa
" yanxu ya kukayi da iyayen yarinyar, dady ya fda yana kallon Dan nasa, dady munje ni da kaka neman ixini mahaifin nata yace na turo manya na, kuma dady ban san abin da tsayi sbda yarinya ce ina so ta fara makaranta sbda bata yi, " kar ka damu nura insha Allahu zuwa ranar lahadi tinda bani da aiki sai naje, idan naje zan nemi amini na a garin muje ya rakani neman auran nata,
" toh dady na gode Allah ya kara girma, nura ya fda yana ficewa daga dakin
" nura meke damunka ne naganka fuskarka cikin farin ciki kamar anma bushara da aljannah, wata mata datijuwa ta fda wadda ga dukkan alamu mahaifiyarsa ce
" mumy bbu komai kawai dai aure nakesan karawa ne,
" kai Alhamdulilah amma nura kayi tinani mai kyau, ai gwanda ka kara auran yau shekarar ku kusan biyar da Aisha ko watan bata bata tabayi ba bare musa ran jika,
" mumy ni ba sbda haka zan kara aure ba kawai dan dai ina san yarinyar ne, kuma na fdawa dady yace lahadi zaije neman auren ta
" kai amma naji dady, ai bnyi tinani dady zai yarda ba haka, a ina ka samo mana yarinyar yar gidan wace, mumy ta fda cikin jin dadi
" mumy ba yar kowa bace hasalima yar kauye ce kuma karamace sanda naje panisau na ganta da fari na zaci tausayi take bani sai daga baya na gane ashe santa nake kuma..... Maganar da  mahaifiyarsa ta fara ne yasa shi saurin dago kansa,
Wallahi Allah nura baka isa ba dan wulakanci duk matan garin nan karasa wadda zaka so sai wata yar kauye jahila kaskantacjya, wadda da ita da kare basu da maraba a wajena,
" haba  mumy dan Allah mutum ce fah bai kamata kina mata haka ba, kar ki manta itama mutumce kamar kowa haba mumy, nura ya fda cikin Bacon rai,
" inalilahi wainailaihir rajiuna na shiga uku ni Hindatu, nura tin kafin kayi auran har ka fara min rashin kunya mumy ta karashe maganar cikin kuka,
Gaba daya jikin nura yay sanyi, ruko hanunta yay ya zaunar da ita a kujera, " haba mumy dan Allah ya kike so nayi so kike azabar Allah ta hauni, yaza ki dinga zubda hawaye sbda ni,
Dan Allah ki duba girman Allah ki daina kuka"
" nura tashi ka tafi gida dare yayi" dady ya fda ransa a bace, " dady mumy fa fushi takeyi dani, nura ya fda kamar zai yi kuka,
" nace ka tashi ka tafi kafin ranka ya baci koh'
Ba yadda nura ya iya dole ya tashi ya tafi
" wallahi wallahi wallahi kinji na rantse sau uku ko hindatu mudum kika ziga yaron nan ya fasa auranta wallahi kema sai na sakeki, kuma ko nura baiyi tina nin auro yar asalinsa ba, ni zan aura masa" dady ya fda ransa a bace, mumy zatai magana ya daga mata hannu, bnsan jayayya, ya fda yana shigewa ciki, ba yadda ta iya dole ta hakura amma a ranta ita kadai tasan muguntar da ta shiryawa yarinyar
Kamar yadda dady yayi alkawari haka kuwa ya cika, tin safe nura da dady suka kama hanyar panisau karfe tara suka isa garin panisau,
Da sallama suka shiga gidan kaka, suka kwa ci saa kaka na tsakar gida, cikin girmama suka gaidata bayan tayi musu shimfida
" baba gidan malam habu zani ko yana nan sai ya rakani nemowa nura auran yarinyar da ya gani, cikin mamaki kaka ta kallesa wane malam habu din bayan wajansa zaka neman auran , zaro ido dady yayi,  baba kina nufin aminina malam habu yarsa nura yake so, eh,
"Alhamdulilah amma naji dadi  sosai nura dama ita ce yarinyar da nake fda ma zan aura maka, sosai yaji dadin lalai wannan shi ake kira *hadin Allah*
Kuyi hakuri naso page din yafi haka amma kasancewar ina busy shiyasa banyi da yawa ba amma insha Allahu za muyi muku wanda yafi wannan insha Allah
.
       Malam habu na zaune tsakar gida kan tabarma Nura yayi sallam, Nur dake wanke wanke ta amsa sallamar itama, guri yasamu kusa da baban ya zauna cike da girmamawa ya gaida abban Nur, Nura yace"abba dama da daddyna muke tafe yana waje ma, Malam habu yace a'a jeka ce su shigo mana.
   Mikewa Nura yayi daidai lokacin umma ta fito ya gaisheta sannan yayi waje, tare suka shigo da daddynsa gefe dasu ya zauna, cikin mamaki Malam habu ya kasa magana, daddyn Nura shiya katse mai mamakinsa yace"kaga hadin Allah ko?, daga kai malam habu yayi alamar eh sai lokacin ya bude baki" badai ince Nura shine yaronka ba"kwarai shine kuma dama ya mun bayanin komai game da Nur shine yasa ma nacewa kaka xanxo gurinka muje gun uban yarinya, toh shine kaka take shaidamun ai yarka ce ma, naji dadin hakan sosai saboda dama niyyata na umarcesa akan yaxo ya nemi yarka, dayaxo mun da bayanin yasamu wata sai ban matsa ba ashe Allah ya riga ya hadasu wannan shine HADIN ALLAH.
  sun sha hira sosai ta yaushe gamo sannan daga karshe suka tsaida lokacin bikin nan da wata biyu, Daddyn Nura ya dubi aminin nasa yace "bana bukatar komai daga gareka domin Nur ya'tace, sosai malam habu yaji dadi haka ma umma tayi godiya sosai.
      Nura ne xaune kan dakalin kofar gidansu Nur yana jujjuya mukulin motarsa, Nur ta isa gurin fuskarnan tasha adon su na yan kauye wai ita adole tayi ado gyalen tasha damara dashi, da sallama ta isa gurinsa, ya dago yana mata murmushi ya amsa sallamar, guri tasamu ta zauna, ta dubeshi sosai sama zuwa kasa tace" yayana kayi kyau sosai, da mai hoto ya fito da munje an dauke ka, yayi murmushi sosai har kumatunsa ya loba yace "kanwata nagode kema ai kinyi kyau har kin fini, ya ciro wayarsa yace" zo ki gani ta matso ya nuna mata yadda zatayi ta daukeshi a hoto, hakan kuwa akayi ta daukesa sannan itama ya dauketa.
   Nura bai bar gidan ba sai da yaci turon umma na dare, washegari suka koma kano, Da sallama Nura ya shiga gidansa amma Aisha na zaune a falon bata ko san ya nayi ba bare ta amsa mai, ransa yayi masifar baci ya wuce dakinsa, wanka ya fada bayan ya fitone ya shirya cikin kananan kaya ya sake fitowa tana zaune inda ya barta, yaxo zai fita nan ne tasha gabansa, sannan taci kwalarsa wlh baka isa ba munafiki, duk abinda kake shiryawa ina sane toh wlh sai dai kasan insa xata xauna don wlh baxan xauna da kishiya ba, kai bari ma kaji baka isa ayi auren nan ba, cikin zafin rai da irin kalaman Aisha bai san lokacin daya dauketa da wani wawan mari ba, sai da taga taurari cikin hanxari ta sake shi ya juya ya fice abinsa.
      Durkushewa tayi agurin tana ta rusgar kuka, shikuwa tunda ya fice sai karfe sha daya ya dawo lokacin har ta gaji da kukan tayi bacci, afalo ya sameta tana bacci akan kafet kallon ya kashe ya dauketa ya kaita daki, ya kashe mata wuta ya rufe dakin ya nufi nasa.
Ku kasance damu anjima zamu cigaba amma sai ankawo wuta.
.
Washegari, Nura na fitowa daga dakin, dakin Aisha ya nufa ganin kofar a kulle yasa yayi turus ya murda amma a kulle, hakan ya tabbatar mai bata gidan, kitchen ya nufa ya hada tea yazo yasha, ya kishigide akan doguwar kujera.
   Misalin karfe tara na safe wayarsa dake gefensa tayi ringing jawo wayar yayi ganin sunan hajiyar Aisha yasa yayi saurin daga wayar tare da karawa a kunnen sa, ko sallama batai ba ta fara masifa
" wallahi nura ba isa ba dan wulakanci karasa wadda zakaima kishiya sai yar tawa kuma duk matan garin nan ba ka auri kowa ba sai ka tafi kauye ka dakko mata bagidajiya, jahila kaskantaciya, tin da mumyn Aisha ta fara zagin nur ya rintse idonsa dan har cikin ransa yake jin zafin abin ba yadda zaiyi da mumyn ne kawai,
" nura kanaji ina magana kamin shiru wato ka maidani yar iska ko, maganar da ta katsemasa tunanin da yake, " mumy wlh ba haka bane kawai dai ina san yarinyar ne kuma bata da aibu" ka ga dalla malam ba ca nai ka min wannan shashancin ba sai dai ka zaba ko Aisha ko yar kauyan da zaka dakko, bata jira cewar sa ba ta kashe wayarta
Dafe kasa yayi yana ta karanto adduo'i ya rasa yadda zaiyi mutane su fahimci san da yake ma yarinyar, yasan yana san Aisha amma san da yake ma nur bai taba jin yanayi ma Aisha shi ba da wannan tinanin bacci mai nauyi ya dauke sa
*Bayan kwana uku*
Mumy dan Allah kiyi hakuri ki bani matata wallahi ina santa, kuma ina san nur gaba dayan su bbu wadda zan iya rabuwa da ita, ki min addua Allah ya bani ikon rike su da amana, nura dake durkushe gaban mumyn Aisha yake fda cikin girmamawa
" wai nura sau nawa zan fda maka kar ka kara zuwa gidan nan da nufin tafiya da Aisha har sai ka janye batun auran wannan dabbar da kake ikirarun aura" rintse idon sa nura yayi jin zagin da mumyn Aisha ke wa nura ya sashi mikewa a fusace ya kalli mumy " indai yarki ce ki riketa ba zan kara zuwa neman dawo da ita ba kuma duk duniyar nan bbu mahalukin da ya isa ya hanani auran nur tin da mahaifina ya yarje min
" iyeeee nura ni zaka zaga sbda waccan jakar yarinyar wlh ba ka isa ka aure ta ba" ganin yana batawa kansa lokaci yay ficewar sa
Yana fita  ya ja motarsa yay  panisau cikin mintinan da ba su wuce arba'in nura yaje garin Gidan kaka ya fara zuwa bayan sun gaisa ya tafi gidan su nur akan dakalin gidan su ya hangota suna ta zuba tar carafke ita da kawayanta, sanda ta ganshi ta dauke kanta kamar bata gansa ba ta cigaba da yin yar carafeken, ganin bata taso ya sa yay tinanin wasa ya dauke mata hankali bata lura dashi ba cikin nutsuwa ya fito daga motar ya nufi inda suke
" sannun ku wasa ake yi, nura ya fda fuskarsa dauke da murmushi sanda ya karasa kusa dasu,
" eh wasa muke yaran suka fda suma suna dariya, nur ba magana, nura ya fda yana maida kallonsa gare ta, turo baki tayi ta ki ko kallon inda yake ganin bata da niyyar kulasa ya sashi dole ya kyaleta ya nufi  cikin gidan,
Da sallama ya Shiga lokacin Umma na tsakar gida tana bare gyada zatayi dambu, fuskarta dauke da murmushi ta amsa masa, kusa da ita ya zauna a gefen tabarma bacin ya gaidata cikin girmamawa
Hannu yasa ya dibi gyadar ya fara barewa
" umma daman karatu nake san fara koyawa nur kafin ayi auran mu koma can, kinga in ta fara makarantar karatun zai zo mata da sauki, " ba komai nura kullum adduata Allah ya biyaka domin mu kan bamu da abinda zamu biyaka, hayaniyar da suka jiyo a waje ne ana kuka yasa nura kin magana, umma kamar fda yaran nan suke kan tai magana wata yarinya ta shigo da gudu " umma nur ta fasawa ladidi kanta da dutse, kafin yarinyar ta karasa nura yay saurin fita, ganin yadda jini ke fita akan yarinyar ya sashi saurin sata a mota ya nufi karamin asibitin dake cikin ungwago, cikin sauri suka karbeta suka mata taimakon gagawa sannan suka hada masa magun guna suka bashi ya kamo hanyar panisau
" ladidi me ya hada ku da nur,nura ya fda yana kallon ladidi, wai dan ina cinyeta a yar charafke yau, kuma kullum in anayi itace ke cinyewa yau ne kawai na cinyeta fa, " kiyi hakuri kinji ladidi zan zane ta, toh ladidi ta ce
Har gida ya kaita aka masa iso ya shiga ciki ya basu hakuri tare da mika musu kudi
Umma ba karamin duka tayima nur ba wanda yasata ficewa daga gidan ita a dole tayi fishi, bayan nura ya dawo yaje ya dakko umma da kaka suka je suka duba jikkn ladidi
Muna barar addua son bashi da lpya
Allah ya baka lpya my abul kair
Nur bata dawo gida ba sai bayan sallar isha'i har lokacin nura na gidan umma, sanda ta shigo gidan umma ta zubawa nura abinci ta shiga daki dan tayi sallah
Cikin sanda take tafiya har ta shigo tsakiyar gidan kwata kwata bata ma lura da nura dake tsakar gida ba,
" gwanda ma kiyi tafiyar ki yadda kowa zai san kin shigo kuma sandarki bazai hana a dake ki ba ko" umma ta fda tana karasowa wajan ta,
" umma dan girman Allah kiyi hakuri wallahi vazan kara ba ki yqfe mun,
Janyota umma tai kin iya munafurci mana da siffar salahai in kinyi laifi amma wallahi sai na dake ki, umma ta fda lkcn da ta fara dukan nur,
" umma kiyi hakuri tin da tace bazata kara ba, nura ya fda yana riko hannun nur sosai ta makale a jikin sa sbda kar umma ta daketa, da kyar nura ya lalashi umma ta kyale nur sannan ya tafi
Kwanci tashi ba wuya wajan Allah bikin nur da nura ya rage saura sati biyu, nur an fara iya turanci, dan sosai nura yake mamakin yadda nur take da saurin daukar duk abinda akayi mata
Aisha kuwa tin tana sa ran zuwan nura har ta fara cire ransa, tin bata damuwa har ta fara damuwa duk ta rame sbda ko waya baya yi mata, suna zaune a falo ita da mumy ta kalli mumyn ta tace, mumy kinga nura sbda baya sona yaki dawo wa kuma gashi har ya kusa auro yarinyar da na tsana,
" kar ki damu Aisha zanje na sami mumyn nashi muyi magana, toh mumy na
Da daddare dady da nura suna daki suna tsara yadda za a yi bikin, " yauwa nura ina Aisha ne ka siya mata nata kayan nata, " dady ai ta dade bata gida ta kusa sati shida da komawa gida sosai dady yayi masa fda kuma yace yaje ya dawo da ita a yau, ba dan ya so ba dole yana barin gidan  ya wuce gidan mumyn Aisha
Da sallama ya shigo falon sosai Aisha taji dadin ganin sa amma ta dake, mumy ce ta amsa masa sallamar ciki ciki,
" mumy ina wuni, lpya lau ta fda a takaice, "ai na zaci nura baza ka dawo ba, " ayi hakuri mumy yanxuma zuwa nayi mu tafi, bari nai sai kun huce tukunna, sai da suka gama ja mashi rai sannan Aisha ta shirya suka tafi, da kansa ya bude mata gaban motar ta shiga ya ja suka tafi
" sweat heart ya kamta ki ajiye fishin nan nasan na miki laifi amma ki yafe mun kinji, nura ya fda yana dora hannunsa akan hannunta, dauke hannunta tayi tana turo baki, haba sweat heart kila ma ko missing dina bakiyi ba, ganin bata da niyyar tanka masa yasa a dole yay shiru har suka karasa gida, dakinta ta wuce tai wanka, shima haka, nura dai sai da ya tabbatar matarsa ta hakura a ranar dan saida suka lula duniyar masoya a ranar
Sosai nura yake gyaran gidan dady ne yayima nur kayan daki na gani na fda komai sai da yayi mata guda biyu, ganin yadda bangaran nur ya tsaru, yasa nura gyarawa Aisha bangaranta ko zata ji dadi, dan sosai yake san Aishar tasa dan ko a mafarki baiyi tinanin yi mata kishiya ba,
Ana saura sati daya biki yan uwan dady suka kawo lefe gidan su nur akwati goma sha biyu ko wanne cike yake da kaya, sosai muta nan garin ke zuwa ganin kayan nur kowa da abinda yqke fada, nur kuwa sai murna take ganin lodin kayan da aka kawo wai kuma duk nata ne a haka aka shiga hidin dumun biki
Sosai bikin yayi dadi yadda ake tsara bikin kauye haka akayi shi anyi kamu da sauran aladun gagarin an raba kaya na gani na fda duk Wanda ke garin panisau ya san da bikin nur haka ma yan gefen garin su *Jaba* *Rimaye* da dai sauran gefen garin
Allah ya baka lpya my cwt abul    Malam habu na zaune tsakar gida kan tabarma Nura yayi sallam, Nur dake wanke wanke ta amsa sallamar itama, guri yasamu kusa da baban ya zauna cike da girmamawa ya gaida abban Nur, Nura yace"abba dama da daddyna muke tafe yana waje ma, Malam habu yace a'a jeka ce su shigo mana.

   Mikewa Nura yayi daidai lokacin umma ta fito ya gaisheta sannan yayi waje, tare suka shigo da daddynsa gefe dasu ya zauna, cikin mamaki Malam habu ya kasa magana, daddyn Nura shiya katse mai mamakinsa yace"kaga hadin Allah ko?, daga kai malam habu yayi alamar eh sai lokacin ya bude baki" badai ince Nura shine yaronka ba"kwarai shine kuma dama ya mun bayanin komai game da Nur shine yasa ma nacewa kaka xanxo gurinka muje gun uban yarinya, toh shine kaka take shaidamun ai yarka ce ma, naji dadin hakan sosai saboda dama niyyata na umarcesa akan yaxo ya nemi yarka, dayaxo mun da bayanin yasamu wata sai ban matsa ba ashe Allah ya riga ya hadasu wannan shine HADIN ALLAH.

.

  sun sha hira sosai ta yaushe gamo sannan daga karshe suka tsaida lokacin bikin nan da wata biyu, Daddyn Nura ya dubi aminin nasa yace "bana bukatar komai daga gareka domin Nur ya'tace, sosai malam habu yaji dadi haka ma umma tayi godiya sosai.

      Nura ne xaune kan dakalin kofar gidansu Nur yana jujjuya mukulin motarsa, Nur ta isa gurin fuskarnan tasha adon su na yan kauye wai ita adole tayi ado gyalen tasha damara dashi, da sallama ta isa gurinsa, ya dago yana mata murmushi ya amsa sallamar, guri tasamu ta zauna, ta dubeshi sosai sama zuwa kasa tace" yayana kayi kyau sosai, da mai hoto ya fito da munje an dauke ka, yayi murmushi sosai har kumatunsa ya loba yace "kanwata nagode kema ai kinyi kyau har kin fini, ya ciro wayarsa yace" zo ki gani ta matso ya nuna mata yadda zatayi ta daukeshi a hoto, hakan kuwa akayi ta daukesa sannan itama ya dauketa.

   Nura bai bar gidan ba sai da yaci turon umma na dare, washegari suka koma kano, Da sallama Nura ya shiga gidansa amma Aisha na zaune a falon bata ko san ya nayi ba bare ta amsa mai, ransa yayi masifar baci ya wuce dakinsa, wanka ya fada bayan ya fitone ya shirya cikin kananan kaya ya sake fitowa tana zaune inda ya barta, yaxo zai fita nan ne tasha gabansa, sannan taci kwalarsa wlh baka isa ba munafiki, duk abinda kake shiryawa ina sane toh wlh sai dai kasan insa xata xauna don wlh baxan xauna da kishiya ba, kai bari ma kaji baka isa ayi auren nan ba, cikin zafin rai da irin kalaman Aisha bai san lokacin daya dauketa da wani wawan mari ba, sai da taga taurari cikin hanxari ta sake shi ya juya ya fice abinsa.

      Durkushewa tayi agurin tana ta rusgar kuka, shikuwa tunda ya fice sai karfe sha daya ya dawo lokacin har ta gaji da kukan tayi bacci, afalo ya sameta tana bacci akan kafet kallon ya kashe ya dauketa ya kaita daki, ya kashe mata wuta ya rufe dakin ya nufi nasa.

.

Washegari, Nura na fitowa daga dakin, dakin Aisha ya nufa ganin kofar a kulle yasa yayi turus ya murda amma a kulle, hakan ya tabbatar mai bata gidan, kitchen ya nufa ya hada tea yazo yasha, ya kishigide akan doguwar kujera.

   Misalin karfe tara na safe wayarsa dake gefensa tayi ringing jawo wayar yayi ganin sunan hajiyar Aisha yasa yayi saurin daga wayar tare da karawa a kunnen sa, ko sallama batai ba ta fara masifa

" wallahi nura ba isa ba dan wulakanci karasa wadda zakaima kishiya sai yar tawa kuma duk matan garin nan ba ka auri kowa ba sai ka tafi kauye ka dakko mata bagidajiya, jahila kaskantaciya, tin da mumyn Aisha ta fara zagin nur ya rintse idonsa dan har cikin ransa yake jin zafin abin ba yadda zaiyi da mumyn ne kawai,

" nura kanaji ina magana kamin shiru wato ka maidani yar iska ko, maganar da ta katsemasa tunanin da yake, " mumy wlh ba haka bane kawai dai ina san yarinyar ne kuma bata da aibu" ka ga dalla malam ba ca nai ka min wannan shashancin ba sai dai ka zaba ko Aisha ko yar kauyan da zaka dakko, bata jira cewar sa ba ta kashe wayarta

Dafe kasa yayi yana ta karanto adduo'i ya rasa yadda zaiyi mutane su fahimci san da yake ma yarinyar, yasan yana san Aisha amma san da yake ma nur bai taba jin yanayi ma Aisha shi ba da wannan tinanin bacci mai nauyi ya dauke sa

*Bayan kwana uku*

Mumy dan Allah kiyi hakuri ki bani matata wallahi ina santa, kuma ina san nur gaba dayan su bbu wadda zan iya rabuwa da ita, ki min addua Allah ya bani ikon rike su da amana, nura dake durkushe gaban mumyn Aisha yake fda cikin girmamawa

.

" wai nura sau nawa zan fda maka kar ka kara zuwa gidan nan da nufin tafiya da Aisha har sai ka janye batun auran wannan dabbar da kake ikirarun aura" rintse idon sa nura yayi jin zagin da mumyn Aisha ke wa nura ya sashi mikewa a fusace ya kalli mumy " indai yarki ce ki riketa ba zan kara zuwa neman dawo da ita ba kuma duk duniyar nan bbu mahalukin da ya isa ya hanani auran nur tin da mahaifina ya yarje min

" iyeeee nura ni zaka zaga sbda waccan jakar yarinyar wlh ba ka isa ka aure ta ba" ganin yana batawa kansa lokaci yay ficewar sa

Yana fita  ya ja motarsa yay  panisau cikin mintinan da ba su wuce arba'in nura yaje garin Gidan kaka ya fara zuwa bayan sun gaisa ya tafi gidan su nur akan dakalin gidan su ya hangota suna ta zuba tar carafke ita da kawayanta, sanda ta ganshi ta dauke kanta kamar bata gansa ba ta cigaba da yin yar carafeken, ganin bata taso ya sa yay tinanin wasa ya dauke mata hankali bata lura dashi ba cikin nutsuwa ya fito daga motar ya nufi inda suke

" sannun ku wasa ake yi, nura ya fda fuskarsa dauke da murmushi sanda ya karasa kusa dasu,

" eh wasa muke yaran suka fda suma suna dariya, nur ba magana, nura ya fda yana maida kallonsa gare ta, turo baki tayi ta ki ko kallon inda yake ganin bata da niyyar kulasa ya sashi dole ya kyaleta ya nufi  cikin gidan,

Da sallama ya Shiga lokacin Umma na tsakar gida tana bare gyada zatayi dambu, fuskarta dauke da murmushi ta amsa masa, kusa da ita ya zauna a gefen tabarma bacin ya gaidata cikin girmamawa

Hannu yasa ya dibi gyadar ya fara barewa

" umma daman karatu nake san fara koyawa nur kafin ayi auran mu koma can, kinga in ta fara makarantar karatun zai zo mata da sauki, " ba komai nura kullum adduata Allah ya biyaka domin mu kan bamu da abinda zamu biyaka, hayaniyar da suka jiyo a waje ne ana kuka yasa nura kin magana, umma kamar fda yaran nan suke kan tai magana wata yarinya ta shigo da gudu " umma nur ta fasawa ladidi kanta da dutse, kafin yarinyar ta karasa nura yay saurin fita, ganin yadda jini ke fita akan yarinyar ya sashi saurin sata a mota ya nufi karamin asibitin dake cikin ungwago, cikin sauri suka karbeta suka mata taimakon gagawa sannan suka hada masa magun guna suka bashi ya kamo hanyar panisau

" ladidi me ya hada ku da nur,nura ya fda yana kallon ladidi, wai dan ina cinyeta a yar charafke yau, kuma kullum in anayi itace ke cinyewa yau ne kawai na cinyeta fa, " kiyi hakuri kinji ladidi zan zane ta, toh ladidi ta ce

Har gida ya kaita aka masa iso ya shiga ciki ya basu hakuri tare da mika musu kudi

Umma ba karamin duka tayima nur ba wanda yasata ficewa daga gidan ita a dole tayi fishi, bayan nura ya dawo yaje ya dakko umma da kaka suka je suka duba jikkn ladidi

Muna barar addua son bashi da lpya

Allah ya baka lpya my abul kair

.

Nur bata dawo gida ba sai bayan sallar isha'i har lokacin nura na gidan umma, sanda ta shigo gidan umma ta zubawa nura abinci ta shiga daki dan tayi sallah

Cikin sanda take tafiya har ta shigo tsakiyar gidan kwata kwata bata ma lura da nura dake tsakar gida ba,

" gwanda ma kiyi tafiyar ki yadda kowa zai san kin shigo kuma sandarki bazai hana a dake ki ba ko" umma ta fda tana karasowa wajan ta,

" umma dan girman Allah kiyi hakuri wallahi vazan kara ba ki yqfe mun,

Janyota umma tai kin iya munafurci mana da siffar salahai in kinyi laifi amma wallahi sai na dake ki, umma ta fda lkcn da ta fara dukan nur,

" umma kiyi hakuri tin da tace bazata kara ba, nura ya fda yana riko hannun nur sosai ta makale a jikin sa sbda kar umma ta daketa, da kyar nura ya lalashi umma ta kyale nur sannan ya tafi

Kwanci tashi ba wuya wajan Allah bikin nur da nura ya rage saura sati biyu, nur an fara iya turanci, dan sosai nura yake mamakin yadda nur take da saurin daukar duk abinda akayi mata

.

Aisha kuwa tin tana sa ran zuwan nura har ta fara cire ransa, tin bata damuwa har ta fara damuwa duk ta rame sbda ko waya baya yi mata, suna zaune a falo ita da mumy ta kalli mumyn ta tace, mumy kinga nura sbda baya sona yaki dawo wa kuma gashi har ya kusa auro yarinyar da na tsana,

" kar ki damu Aisha zanje na sami mumyn nashi muyi magana, toh mumy na

Da daddare dady da nura suna daki suna tsara yadda za a yi bikin, " yauwa nura ina Aisha ne ka siya mata nata kayan nata, " dady ai ta dade bata gida ta kusa sati shida da komawa gida sosai dady yayi masa fda kuma yace yaje ya dawo da ita a yau, ba dan ya so ba dole yana barin gidan  ya wuce gidan mumyn Aisha

Da sallama ya shigo falon sosai Aisha taji dadin ganin sa amma ta dake, mumy ce ta amsa masa sallamar ciki ciki,

" mumy ina wuni, lpya lau ta fda a takaice, "ai na zaci nura baza ka dawo ba, " ayi hakuri mumy yanxuma zuwa nayi mu tafi, bari nai sai kun huce tukunna, sai da suka gama ja mashi rai sannan Aisha ta shirya suka tafi, da kansa ya bude mata gaban motar ta shiga ya ja suka tafi

" sweat heart ya kamta ki ajiye fishin nan nasan na miki laifi amma ki yafe mun kinji, nura ya fda yana dora hannunsa akan hannunta, dauke hannunta tayi tana turo baki, haba sweat heart kila ma ko missing dina bakiyi ba, ganin bata da niyyar tanka masa yasa a dole yay shiru har suka karasa gida, dakinta ta wuce tai wanka, shima haka, nura dai sai da ya tabbatar matarsa ta hakura a ranar dan saida suka lula duniyar masoya a ranar

.

Sosai nura yake gyaran gidan dady ne yayima nur kayan daki na gani na fda komai sai da yayi mata guda biyu, ganin yadda bangaran nur ya tsaru, yasa nura gyarawa Aisha bangaranta ko zata ji dadi, dan sosai yake san Aishar tasa dan ko a mafarki baiyi tinanin yi mata kishiya ba,

Ana saura sati daya biki yan uwan dady suka kawo lefe gidan su nur akwati goma sha biyu ko wanne cike yake da kaya, sosai muta nan garin ke zuwa ganin kayan nur kowa da abinda yqke fada, nur kuwa sai murna take ganin lodin kayan da aka kawo wai kuma duk nata ne a haka aka shiga hidin dumun biki

Sosai bikin yayi dadi yadda ake tsara bikin kauye haka akayi shi anyi kamu da sauran aladun gagarin an raba kaya na gani na fda duk Wanda ke garin panisau ya san da bikin nur haka ma yan gefen garin su *Jaba* *Rimaye* da dai sauran gefen garin

Allah ya baka lpya my cwt abul

.

Yau takama jumaa yaune dubban jamaa suka shaida daurin auran Nura da amaryarsa Nur Alan sadaki dubu Dari a babban masalacin sarki na fada aka daura auren, wayyo zo kuga yadda mutane suka dinga mamakin sadakin nur, kasancewar garin akanta ne aka fara sadaki dubu dari a can na hango cikin wata dakakiyar shada sai faman sheki takeyi, hakoransa kwa duk ya washe su kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki wanda bazai misaltu ba,

Amarya kuwa umma ce ta mata wanka da kanta sannan ta shafa mata mai da hoda jambaki kadan umma ta shafa mata sannan ta dakko mata atamfa sharaton green abinka da farar fata nan da nan fuskarta ta fara haskawa, tsayawa fadar yadda nur tayi kyau, bayan an daura aure angwaye suka zo gaida iyayen amarya, sosai nura yay mamakin yadda nur tayi kyau, ansha hotuna sannan angwaye suka tafi

.

Washe gari ta kama asabar ranar akayi yini anci an sha Alhamdulilah, bikin nur sosai ya kafa tarihi a garin panisau, wasu na murna wasu kuma na bakin ciki kasan cewar ba yayansu aka aura ba,

Karfe biyar motoci suka fara layi a unguwar su nur sai da aka kawo motoci guda goma sha biyu ko wacce mota sadadiyar gaske ce,

Anya hasantu dije ba sai da yarsu sukayi ba jibi yadda ake ta faman bidiri da kudi kamar baa san yau ba, haba fatsima ai wannan hassada ce da dai ba a san asalin sa bane sai ace an saida ta amma ba wanda bai san mahaifin yaron nan ba hasali ma kakar sa da ta haifj mahaifinshi har yanzu tana cikin garin nan ki daina wa mutum bakin ciki bbu inda zai kaiki, insha Allah hasantj na daina kuma na gode da waazinki gare ni,

Bayan sallar mangariba Abba ya kira nur ya mata fda akan ta nutsu ta daina kazanta dan a shekarunta bazai mata fdan aure ba kuma yasan nura ma bazai bari wani abu ya shiga tsakaninsu sai tayi ilimi, umma na kuka nur na kuka aka sata a mota suka kama hanyar hotoro, gaba daya sauran amaran gidan amarya aka wuce dasu a tarauni, motar amarya da iyayenta ke ciki a ka wuce hotoro dan gaida iyayen ango

.

Yan panisau ba karamin rudewa sukai ba sanda suka ga irin saruwar gidan ni kaina da nake gefe saida biro na ya fdi dan bn taba tsayawa nayiwa gidan kallon kullura irin na yauba,sister haima ce ta dunguran kai bayan ta mikon bison maza bisu ki gano mana falon,

Da Sauri nai bi bayansu

Masha Allah abinda duk mutanan dakin ke fda kenan, nima abinda na fara fada kenan sbda tsayawa fadar yadda falon ya hadu bata lokaci ne

.

Sanda aka kai nur gaida mumy fuskarta ba yabo ba fallasa ta karbe su jiki bbu kwari suka dau yarsu suka nufi gidanta

Karfe tara gida ya watse aka tafi mai dash panisau yan kai amarya na watsewa Aisha da kawayanta suka nufi part din nur Cikin tswa Aysher ta kalli nur da take zaune tana ta faman wasa da remote a gaban tv ta taba wancan ta taba wancan

" ke ina wadda kuka kawo gidan nan take yayar ki, nur ta kalleta cikin rashin fahimta, Aysher ta zaro mata ido nace miki ina Nur din da kuka kawo, nur ta mata bnza kamar ba da ita take ba dan uwarki ba magana nake miki ba, Aysher ta fda cikin tsawa, rai a bace nur ta mike ba dai uwata ba wallahi sai dai uwarki kuma nice nur din da kike nemar uwar me zan miki da kike nemana, nur ta fda tana rike da kugu, zaro ido Aisha tayi kadai nura wannan mara kunyar mara tarbiyar ya auro aiko ya kawowa kansh jaraba, Aisha taja hannun kawayenta suka yafi, nur kuwa komawa tai ta cigaba da wasanta,

.

Aisha tin da ta shiga daki take zagaye zagayen dan kawayenta ma kin shigowa sukai suka tafi wai ta basu kunya yarinya yar cikinta na mata rashin kunya amma taki tabuka komai,

Nura ne yay sallama tare da shigowa dakin cikin bacin rai Aisha ta juyo ta kalleshi,wallahi nura kaji kunya ka rasa wadda zaka aura sai wadda a haihuwar kaji kayi jika da ita, haba sweat heart bai kamata kina fdan haka ba nifa mijin ki ne yanxu dai ki kintsa zan kawo ta ku sasanta Allah ya min tsari tsatsan tawa da yar ciki na kai dai da ka zubar da girmanka da kimarka sai kaje wajenta, mtswww Aisha ta gallama nura harara ta shige dakinta tare da saka key ta rufe girgiza kansa kawai nura yayi ya nufi part din nur

.

Murda kofar dakin yayi ya shiga side din nur, a zaune ya sameta tana wasa yadda ya barta karasawa yayi ya durkusa gaban Nur ya riko hannunta, ta dago tana harararsa ya yi dariya domin dariyar ta bashi, kanwata lfy kike hararata?, ya tambaya ta turo baki ya mike tsaye itama ta tashi ya na rike da hanunta suka shiga bedroom dinta, wanka yaje yayi sannan ya fito ya umarceta da taje tayi wankan itama, amma fir taki sanin halinta ne tana iya taramai jama'a yasa ya rabu da ita ya hau gado ya kwanta, ta xo ta tsaya mai akai kerere tace yayana ni a ina zan kwanta?, ya yi kamar baiji ta ba, ta sake tambayarsa nan ne yaga zata dameshi yace ki hau gadon mana, tace tab ya zaayi mu kwana gado daya aradu baxai yiwu ba ta rike kugu kamar wacce zata yi dambe dashi, ya ce toh shikenan tunda bazaki hau ba ki kyaleni kinga bacci nakeji, ya juya mata baya ya kashe wutar dakin, ihu tasa tayiwo gadon da gudu, yayana dan Allah ka kunna wutar dakin, yayi banxa da ita ta saka mai kuka tana kiran ummanta.

.

        Ganin taki saurarawa da kukan yasa ya kunna wutar dakin, ya hango ta can kuryar gado ta rakube tana ta kuka, ya matsa kusa da ita yana bata hakuri, riko hanunta yayi aikuwa kamar jira take sai ta bige hannun ta runkura zata bar gadon yayi saurin riko ta.

     Ina zakije tace bansani ba cike da tsiwa, ta bashi dariya amma ya gimtse dariyarsa, ya fara lallashi dakyar yasamu ta hakura amma tace sai dai yabar mata dakin ta, mikewa yayi ya nufi kofa tana zaune tsakiyar   dagon yace sai da safe ya bude kofa zai fita kamar an korota ta taho da gudu tace yayana wlh tsoro nakeji, yace ba kince na bar miki dakin ki ba, tace toh dawa xan kwana wlb inajin tsoro, juyawa yayi ya fara tafiya, ai maza ta biyo sa, dakinsa ya nufa tana biye dashi.

        Kan gadon taje ta rakube, nan dai har bacci barawo ya sace ta, ya lullube ta da bargo ya kwanta agefenta.

Washegari shiya hada musu breakfast don yasan Aisha ba girki take ba bare tana jin haushin aurensa ya gama hadawa kenan driver gidan mumny ya kawo musu kayan kari, sai da ya tabbata ya hada komai sannan yaje ya tashi Nur dake bacci tun bayan tayi salla yasa tayi wanka dakyar hakan ma don yace xai mata ne, kaya ya bata riga da wando, rigar yello da bakin wando sai hula itama yello, ya tayata sukayi kwalliya tare sannan suka fito, har kan dinnig ya ajiyeta sannan ya nufi sashen Aisha.

    Tana zaune ta zuba uban tagumi ya zare hanun, cikin bacin rai tace lfy malam?"lfyr kenan ya fada ataikaice sannan yace swt hrt bako gaisuwa ne?ta galla mai harara ta juya mai baya, yayi lallashi amma taki kulasa haka ya mike ya tafi.

       Zama yayi yana zubawa Nur abinci sai ta kallesa tace"yayana naga kamar kana fushi dani don Allah kayi hakuri ka yafe mun, dagowa yayi ya kalleta ta sake mai murmushi ya mayar mata yace"ba abinda kika mun kanwata auntynku ce ta bata mun rai, nan take sai Nur ta hade fuska "yace lfy kanwata me kuma ta faru tace wlh wannan auntyn akwaita da masifa da jaraba ai na dauka kai babbane baza ta maka ba sai yara, tab halinta bayi da kyau, hanu yasa ya rufewa Nur baki yace tanada kirki fa Nur kuma tana sinki jiyan ma ranta abace yake, Nur ta jinjina kai aranta tace shegiya taji dashi azarihi kuma cewa tayi Allah yasa, " amin kanwata.

.

" kanwata ranar monday zaki fara zuwa makaranta hpe dai zaki maida hankali kiyi karatu, insha Allahu zanyi yayana, " yauwa my yar kanwa, dariya sukayi gaba daya, ganin mutum akan su yasa su tsagaita dariyar,

Wallahi nura kaji kunya anyi asara ka zauna kana shashanci kai da yar cikin ka wai kai baka yadda soyayya kake ba, mtswww Aisha ta karashe maganar tana tsaki,

"Haba swt hrt bai kamata kina min irin haka ba, wannan in kikai hakuri zaku zauna lpya yar kanwar tawa bata da matsala ai ya fda yana ruko hannunta, " mtswww dalla malam ni ka sakeni wallahi anyi asara ta fda tana fuzge hanunta tayi waje

" Allah ya kyauta abinda nur ta fda kenan tai waje,

.

*Bayan kwana3*

.

Nur ce kwance tana sharar baccin ta hankali kwance, nura na gefenta yana ta tashinta amma taki tashi ganin taki tashi kuma bata da niyyar tashi yasa nura daukarta cak ya dire ta a bandaki, kuka ta saki tana bubuga kafa ni wallahi kadaina tashi na in ina bacci, Allah sai na fdawa umma, duk abinda take idonta a rufe yake taki budewa, sosai ta burgeshi, ruwa ya diba ya watsa mata a fuska, ihu ta Saki tare da kankamesa, " sorry my kanwa , kuka ta dinga masa da kyar ya lalabata yayi mata wanka sannan suka fito, cikin wata doguwar riga milk ya shirya ta sosai ta yi kyau duk da ba abinda ta shafa a fuskarta, bnda mai da farar hoda sannan suka fito sukai break fast har lokacin Nur bata rai take batayi dariyaba, a haka suka nufi makaranta,

" kanwata har yanxu fishi akeyi dani ne dan Allah ki danyi min dariya mana kinga makaranta fa zan kaiki ko ba kyaso ki iya turanci da karatu ki zama babar likita,ya fda yana ruko hannunta,

Fuskarta dauke da murmushi ta juyo ta kalleshi, yaya da gaske zan iya turanci, "sosai ma kanwata ni dai fatana ki dage da karatu kinji" toh yaya zanyi, a haka suka karasa makaranta bayan an gwada ta aka sata a pri 1 nura ya tafi ya barta a makaranta,

Sanda auntyn su ta shigo tqji yaran suna turanci sosai suka burgeta, ranar dai Nur anyi abin arziki dan har aka tashi bbu wanda ta tsokana,

Karfe biyu dai dai nura ya zo daukarta, kasancewar bai tashi daga office ba ya sa ya wuce da ita office dinsa

"Yayana gaskiya makarantar da dadi sosai, kaji yadda suke turanci, nur ta fda fuskarta dauke da murmushi, toh kema ki dage ki iya turanci kinji kanwata, toh yayana amma zaka koyan koh, daga mata kai yayi sanda ya isa office dinsa kamal abokinsa ya tadda a bakin kofa,

"Nura ina kaje ne tin dazu nazo fa"

" Ayya am sorry naje dakko kanwata ne yaushe kazo kano din, wlh jiya nazo shine nace bari nazo mu gaisa,

Wow gaskiya kanwar nan taka tayi kyau sosai ina kamu" harara nura ya wulla masa, kaga bansan iskanci kamal, wlh da gaske nake indai zaka bani ita, ya fda yana kallon nur, baby ya sunanki, Nur sunana, ta fda tana washe bakinta, " kina da kyau, kaima kana da kyau ina m....... Tsawar da nura ya daka mata ne yasata kin karasawa, sosai nur take hargitsewa duk sanda aka mata tsawa, hannun kamal yaja suka bar wajan, " kaga malam ban san iskanci malam mata tace fah, itace amaryar danj" Ayya yi hakuri nura wallahi ban sani ba amma fa kayi saa, dariya nura yayi ya koma office dinsa inda ya bar Nur nan ya tadda

Hannunta ya rike suka Shiga office, kan kujera ya zaunar da ita ya cigaba da aikin sa,

" yaya kayi hakuri Dan Allah kaji" harara ya wulla mata haka nace kin mun laifi da zaki bn hakuri

Ranar sai shida suka koma gida

Suna zuwa gida part din nur suka nufa yayi mata wanka shima yayi wanka sannan ya nufi part din Aisha

.

Tana zaune akan kujera tana chrtn da alama kuma tana jin dadin chrtn din sallama yayi tare da shigowa dakin, ciki ciki ta amsa masa, kusa da ita ya zauna tare da dora kansa a kafadarta swt hrt ya gida, " gashi muna ciki" nayi missing dinki alot, tin da na fita ko ki kirani kiji yadda naje office koh, cikin bacin rai ya ta kalleshi tace wadda ka fita da ita din bata debe maka kewar ba, sbda tsabar rashin adalci tin da nake da kai ko sau daya ba ka taba zuwa dani office ba shine yau har da daukar yar cikinka kuma dan abin kunya a tambayeka wace kace matarka Allah kaji kunya Nura, murmushi kawai yayi mata yay waje ya tabbata kishi ke damun matar tasa

.

Kwanci tashi ba wuya wajan Allah su Nur an shiga wata daya da aure sosai ta dage da karatunta bata wasa hakan yasa aka maidata pr 2 tinda aka maida ta pri 2 takara dagewa da karatu ba laifi yanxu ta fara iya turanci duk da ba kwarewa tayi ba rashin kunyarta kwa na nan bbu inda taje kazanta ce dai aka rageta kadan kamar kullum tana zaune a daki tana yin assihnment din da aka bata

Akayi sallama tare da turo kofar dakin, ba tare da ta dago kai ba ta amsa sallamar

" ke dan uwarki kina jin mutane shine zaki musu shiru kamar wata saarki,

Fuskarta a hade ta dago tana kallon Aisha tace, " toh aunty me kike so na miki sallama ki kai kuma na amsa ta fda tana murguda baki,

" kut lalai yarinyar nan ni kike murgudawa baki, " eh din an murguda ina ruwanki dani kawai dan kinga ina kyale ki koh an fda miki tsoron ki nake ji da zaki dinga zuwa kullum kina zagina,

Cikin bacin rai Aisha ta kai mata mari, " Allah ya isa muguwa azzaluma kuma wallahi sai na rama shegiya kawai dai dai lokacin da nura ya turo kofar da zai shigo yaji nur na zagin Aisha ita kuwa Aisha najin alamun nura yasa tayi shiru sbda ta kullamata sharri ita kuwa nur ido ya rufe ta dage sai zagin Aisha take, nur ni kike zagi " eh din an zageki kuma wallahi...... Marin da nura yay ma nur ne ya sata kin karasa maganar, nan ta durkushe tana kuka

Nura kuwa hannun Aisha ya ja suka bar dakin, wallahi nura sai na koyawa yarinyar nan hankali jibi yadda kasa ta raina ni tana ta faman zagina, ta zage ki din da kin rike girmanki ai bazata zage ki ba kuma ai ke kikaje inda take, wallahi Aisha kar na kara ganin kinje dakinta kina jina ya fda yana tafiya ba tare da ya jira me zata ce ba yay waje dakin nur ya nufa har lokacin tana durkushe Inda ya barta, jikinsa a sanyaye ya karasa inda take, dagota yqyi ta kwace ni ka sakeni, haba kanwata kiyi hakuri bazan hakura ba din ni ka maida ni inda ka dakko ni jibi yadda fuskata ta kumbura ita ta maran anan nai mata Allah ya isa, sbda na zageta kaima kara mari na jibi fa yadda fuskata tayi, nur ta karashe maganar tana kuka,

Sai a lokacin ya lura da inda Aisha ta mareta, duk sai yqji ba dadi, am sorry kanwata bazan karaba kinji, da kyar nur ta hakura sai da yace zai kaita wajan wasan yara sannan ta hakura,

Washe gari ya kama asabar tin safe ya shirya nur tsaf cikin wata atamfa riga da skrt sosai nur tayi kyau cikin kayan, yana rike da hanunta har suka isa gaban mota,

" iyeeeee nura kana san gamawa da duniya lpya kuwa kasan hukuncin wanda basa a ladalci kuwa tsakanin matansu, me yasa zaka dau matarka daya ka bar daya, mumyn Aisha ta fda tana karasawa wajan su

Cikin girmamawa nura ya gaidata, mumy yanxu xamu dawo ai, kuma ai ba rashin adalci bane wannan dan na fita da Ita, sbda itama Aysher ai na fita da ita tana amarya

" yayana wace wannan din, kan nura yay magana mumy tayi magana cikin bacin rai

" uwarki ce dan ubanki shegiyar yarinya yar karama dake kin iya kisisina ai dole Aisha ta samo mafita kan ki girma munafuka kawai,

" wallahi ni ba munafuka bace sai dai in ke....... Kallon da nura yayi mata ne yasa ba shiri tai shiru,

Nura yanxu wannan tsinaniyar yarinyar ka auro wadda bata da tarbiyya batasan girman manya ba,

Mumy kiyi hakuri in Allah ya yarda zan mata fda, bai jira cewar mumy ba yasa nur a mota suka fice

Mumy kuwa masifa ta dingayi da kyar Aisha ta rarasheta tai shiru

" kanwata bbu kyau yiwa babba rashin kunya ki daina kinji, " toh yaya bazan karaba amma wacece ita, mumyn Aisha ce,

Ashe gadar masifar tayi, abinda nur ta fda a zuciyarta kenan, a fili kuma tace ai bn sani ba bazan karaba a haka suka karasa wajan wasan yara suna hirarsu

nura da nur sukaje wajan shakatawa da dama daga nan ya kaita shpn basu baro wajan ba sai kusan laasar direct gidan mumynsa ya wuce lokaci na farko da zai kaita gidan mumynsa tin bayan auransu, da sallama suka shiga falon lokacin ba kowa a falon hakan yasa nura yay mata izini da ta zauna a daya daga cikin kujerun falon yaje ya dawo, yana wata kofa ya shiga da zata sadashi da dakin mumy ya bi, tana zaune a daki ta idar da sallar laasar da sallama ya shiga ta amsa masa fuskarta ba yabo ba fallasa, bayan ya gaidata ta amsa yace mumy daban nur na kawo miki ku gaisa,
Hararsa tayi, " uban me zan mata da kakawo min ita, kuma kana tinanin wannan karamar yarinyar zanje na samu a falo ba ita zata zo ta sameni ba, mumy kiyi hakuri bari na kurawo ta, bai jira amsarta ba ya fice tana zaune inda ya barta, kusa da ita ya zauna " kanwata kinga mumy na yanxu zaki gaida dan Allah ki nutsu bnda rashin kunya kinji kin ga bna wa umma rashin kunya koh, " Allah yayana na daina rashin kunya kuma ko zaa dakeni bazan rama, " yauwa kanwata ta kaina taso muje, nura ya fda yana rike hanunta, " ga dakib mumyn nan ki shiga ku gaisa ni kuma zan tafi wajan aiki ana jirana da daddare zan xo na dauke ki, toh yaya Allah ya tsare, sosai nura ya ji dadin adduar da ta masa, yay mata murmushi ya tafi
.
Cikin nutsuwa nur ta tura kofar dakin mumy da sallama ta shiga mumy na zaune a gefen gadonta, ta amsa mata sallamar fuskarta ba yabo ba fallasa,
Har kasa nur ta tsugunna ta gaida mumy sosai mumy ta yaba da hankalinta domin tin da take da Aisha bata taba gaidata cikin girmamawa ba,
Duk tsanar da mumy ta mata a kaso dari yanxu bbu kaso sabain,
" nur ya gida lpya lau mumy, mumy yau yaya ya kaini wajan wasan yara sannan mukaje shpn munga mutane sa yawa ,
Hankali kwance nur ta fara bawd mumy lavarai masu bn dariya tin mumy na sharewa har ta fara darawa a take mumy taji son nur ya shiga zuciyarta dan jinta take kamar yar autar ta saar nur ce
" Nur labarin nan ya isheni haka kije kiyi wanka kizo ki ci abinci yanxu auta zata dawo daga makaranta sai ku cigaba da bata labari toh mumy na,
Karfe shida auta ta dawo daga makarantar islamiyya, sosai auta da nur suka saba suka zauna suna hirar su
Da daddare bayan sallar isha'i mumy nur da auta suna zaune sun cika mumy da hira suna bata labarai sun sata a tsakiya suna ta shewa ko wannen su ya dora kansa akan cinyar mumy
Dady da nura ne suka turo kofar tare da sallama sosai nura yaji dadin ganin nur da mumy suna hira,
A'A mumy hira ake da yayan naki dady ya fda yana zama a kujera cikin girmamawa nur ta gaida dady ya amsa fuskar sa dauke da murmushi,
Murmushi mumy tayi, nura ya kakeyi da surutun nur, dariya yayi mumy kema ta dame ki ke nan,
Sun dade suna hira,
"Nur Dan Allah ki tashi mu tafi dare fa yayi, ni wallahi anan zan kwana, abinda a gidan naka kullum auntyn nan tai ta zagina, nan kuma mumy ko hararata ba tayi,
Ba yarda nura baiyi ba akan nur su tafi amma taki, mumy ce tace a kyaleta ta kwana ba dan ya so ba haka nura ya tafi rai a bace
Washe gari nura bai zo gidan mumy ba sai kusan mangariba, lokacin su nur na falo suna hira ita da mumy da sallama ya shigo falon, nur na ganinsa ta tashi ta rungumeshi,
Sannu da zuwa yaya yauwa, ya fda fuskarsa a hade,
Mumy ina wuni, lpya lau, ina Aisha tana gaidaki nura ya fda yana hararar nur
Sanda nura yacewa nur su tafi ba musu ta tashi domin mumy tace kar tayi masa musu
Karfe tara na dare suka isa gida lokacin nur tayi bacci a mota a dakin ta ya kwantar da ita ya rufe mata ya nufi dakin Aisha
.
       Nur wai bazaki fito mu tafi bane?"yi hakuri yayana ganinan zuwa daidai lokacin Aisha ta fito tana wani rangwada tana shishshigewa nura, Nur ta fito rataye da jakarta tace mutafi yi hakuri, lokacin Aisha ta sumbaci goshin Nura Nur ta kau da kai a xuciyarta tace yan iska kawai tayi gaba abunta.
       Bari kiga na tafi kar nayi latti, ya saketa yayi gaba, Aisha ta kwashe da dariyar mugunta shegiyawa  wai adole kishi take ai yanxu xaki gane kuranki.
Amota nur taki kula nura yayi juyin duniya amma fir taki kulasa, hakan yasa ya nemi guri gefen titi ya tsaya, sai lokacin ta dago kai ta kalleshi shima ita yake kallo tace"yayana lfy?"na tsaya ne in kin gama fushin sai mu tafi, murmushi nur tayi tace  na dena d only bro, sosai yaji dadi sannan yaja suka tafi.
.
      Karfe biyu ya tafi skul dinsu, yana isa suna fitowa daga aji, ya dauketa suka tafi gida, kasancewar yau bayi da wani aiki yasa yana xuwa yaje ya watsa ruwa ya kwanta adakin nur.
     Karfe hudu ya farka yaga nur xaune gefensa tana assignment, ya mike ya shiga bandaki ya dauro alwala sannan ya yi sallar laasar.
   Yayana har ka tashi, "na tashi kanwata, dama inaso muyi magana dake, ta ajiye litattafan tace inajinka yayana, dama kanwata na samo miki malami dazai dinga koya miki karatun addini, agida sannan zan kaiki wata makaranta ta koyan girki, kwalliya da sauransu, cike da jin dadi tace" thankyou yayana Allah ya biyaka"amin yace shikam nur tana burgeshi saboda gata yarinya amma tasan abun daya dace .
    *bayan kwana biyu*
Malam sadi shine xaiyiwa nur karatun addini agida misalin karfe hudu da rabi xai dinga zuwa yana koyar da ita na awa daya da rabi, sun fara da tauhida yadda zata san waye ubangijinta.
     Sosai nur take gane karatu domin daya gama mata ya mata tambayoyi ta amsa, yaji dadi sosai shima, haka kuwa yake xuwa kyllum biya mata karatun.
      Yayana sannu da dawowa"yawwa kanwata ta karbi jakarsa ta ajiye mai, taje ta hada mai ruwan wanka, baki kawai yasake yana kallon ikon Allah, ta fito ta sameshi xaune bakin gado, ta xauna ita ma, tace yayana na hadama ruwa kaje kayi wanka, toh yace ya mike ya nufi bandakin sai dayaje kofar bandakin sannan ya juyo yace ko zaki tayani ne?"ta girgiza kai alamar a'a, ya shifa yayi wankansa.
        Yau amfara koyawa nur girki bayan ankoyar da ita yadda xata kula da mijinnta, tana ta doki ta dawo dama yau girkin ta ne ta hadawa yayanta abinci.
.
      Driver na direta ta shiga gida da mugun gudu, bankada kofar falon tayi ta shiga bako sallama tsananin doki ta manta ma ana sallama, Jitayi an dauketa da mari, ke wai wace irin jakace kuma yaushe xakiyi hankali dabba kawai, ta juyo afusace tace ke!malama karki kara marina kuma karki kara cemun jaka if not i will deal wit u useless kawai tayi gaba abinta, baki Aisha ta bude tana kallon Nur harta isa dakinta, kaya ta canja tasa simple kaya sannan ta nufi kitchen.
          Jallof rice tayi gidan ya dume da kamshi, Aisha na daki ta dinga jiyo kamshi cike da mamaki ta fito kichen din ta nufa kai tsaye ganin Nur na hada juice yasa ta tabbatar ita tayi wannan girkin, Aisha tace ke uban waye yasaki girki budan bakin Nur tace ubanki, ta dauko hanu xata sake kai mata mari taji anrike hanun ta baya, taji ance in kika kurkura kika dakamun mata kin daki aurenki, ya saketa, oyoyo yayana nur ta fada tayi gunshi rumgumeshi tayi sannan ta riko hanunsa ta sumbata tacw"welcm cwt bro thankyou my sis, ta amshi jakar sukayi daki, suka bar Aisha tsaye ta xubawa sarautar Allah ido.
       Nura ya tafi masallaci sallar isha kafin ya dawo Nur tayi wanka ta feshe jikinta da turarw ta sanya riga da wando masu shegen kyau pink colour, ta warware gashinta ya watso abayanta ta fito falon lokacin Nura ya shigo da saama, ta karasa gunshi ta ce wlcm yayana, ya rikota suka nufi dinning yana bude flask din wani kamshine ya bigi hancinsa, ya dago yana mata kallon tuhuma, gira ta daga mai tace daga yau ka dena cin abincin restuarant, yace toh oya go nd call ur aunty, ta mike ta nufi dakin Aisha, bankada kofar tayi tace inkin ga dama kixo muci abinci, Aisha ta biyota amma ina ta tsere, aisha na xuwa tace Allah ya kiyaye naci abincin wannan jakar, yar kauye, lokacin Nur ta mike tace ke saurara maratarbiya na miki warning baki jiba ki daina cemun jaka, aisha tayi kan Nur tuni nura ya dakatar da ita.
      Sosai nura ya yaba girki kuma yayi hamdala da Allah yasa xamansa da Nur hadin Allah ne
.
Kwanci tashi ba wuya wajan Allah su Nur an gama pri sch ana shirin shiga jss 1 ba laifi ta fara girma amma har lokacin bataje panisau ba sbda ya fi so Nur taje a yadda ba iyayenta ba kowa sai yasan tayi hankali ta nutsu,
Sai dai shi baya wata biyu bai je ba,
"Yaya kaga saura izu goma na hade qurani na hadda ta kuma kaga nayi izu ashirin da biyar so nake ka hadan walima sosai idan na hade sittin dina na kuma haddace talatin, insha Allahu kanwata amma ba yanxu ba nafiso sai kin gama ss3 kije ma su umma amma in akai walima kinga dole sai an fdawa su, ni dai yaya ina so amin ko ba a fdawa su umma ba, kar ki damu kanwata yadda kikace haka zaayi ya fda yana jan kumatun ta,
.
Cikin ikon Allah Nur aka shiga jss 1 sosai take maida hankali wajan karatun ta
Mlm sadi ne ya bawa nura shawara akan ya sata islamiyyar da yake koyarwa sbda zata samu littatafai da yawa, nura ya gamsu da batun mlm sadi kuma yace zata fara zuwa ranar asabar amma da sharadin zai na mata a gida ma, mlm sadi ya yarda
Nur ce cikin uniform dinta tana bakin gate tana jiran yayanta dan yau ya kara lokaci da yawa baixo ya dauketa ba, fuskarta a hade kamar bata taba dariya zama tayi ta dora kanta a kan kafarta sbda gajiyar da tayi,
   "Yan mata ya akayi ne naga kinyi shiru ke kadai ba azo daukan ki  bane, wani matashin saurayi da bai wuce shekara 15 jikinsa sanye da uniform ya fda yana zama kusa da ita, dago kanta tayi cikin kotsawa wlh baa zo daukana bane shiyasa, duk maganar da suke cikin turanci suke yinta, kafin yay maga motar Nura tai parkn ganin Nur da wani zaune kuma yaga alama hira suke ransa yay mugun baci, ga kuma kishi da ya tokaresa,
Ganin motar yayan nata yasa tayima saurayin sallama ta nufi motar
.
" yaya barka da zuwa ya rana, yau bakazo da wuri ba, nur ta fda tana rufe murfin motar bayan ta zauna,
Ko ta kanta baibi ba ya ja motar suka bar wajan
Ganin yanayin yayan nata yasa ta kalleshi jiki a sanyaye
  " yaya laifi na maka kaki kulani, cikin bacin rai ya taka burki ya tsaya,
" au sbda tsabagen rashin mutunci ma tambayata kike me kika mun bacin nazo na tadda ki da wani katan kuna hira, nura ya fda yana kallonta,
Ba karamin razana nur tayi ba da ganin yanayin yayan nata dan tin da take dashi bata taba ganin sa a haka ba
" yayana wallahi ban taba hira da shi........ Tsawar da ya daka mata ne ya sata hadiye zancenta,
  " wlh nur in baki min shiru ba sai na kwada miki mari bokon kin gamata daga yau tin da baza ki kare kanki ba,
Kuka sosai nur takeyi a motar har suka je gda, tinda nur ta fara kuka yake jin kukan a ransa amma ya dake yay banza da ita kamar bai san tanayi ba,
Nur na fita daga mota part dinta ta nufa ko jakarta bata dauka ba ta tafi tana kuka, lokaci Aisha na zaune a harabar gida tana waya kasa kasa ganin yanayin da taga nur yasata jin dadi, cikin faraa ta taso ta nufoshi,
" honey sannu da zuwa, yauwa swt hrt ya gda,nura ya fda yana kakalo murmushi shi a dole bayaso ya gane Aisha ta gane sunyi fda,
.
   "Honey wallahi daman tin dazu nake jiranka gaba daya missing dinka nake, gidan yau naji ba dadi, Aisha ta fda tana shigewa jikinsa,
" nima kan nayi msn naki da yawa swt hrt ya fda yana ruko hannunta suka shiga ciki, Aisha ce ta temaka masa yayi wanka, nan ta shiga janyo hankalin mijinta, cikin mintunan da basu fi ashirinba suka lula duniyar masoya,
Gaba daya Aisha ta mantar dashi komai dan tn da ya auri Nur Aisha bata mallaka masa kanta gaba daya in kwa taga a matse yake toh sai ta gama ja masa rai ranar haka suka kasancr har goman dare suna farantawa junansu, a haka bacci yay gaba dashi
Nur kuwa na shiga daki akan kujera ta kwanta tana rero kuka bayan anyi kiran sallar laasar tayi sallah ta juya ta shiga ba da sharar kuka a haka bacci yay gaba da ita
.
    Washegari da asuba Nura ya farka ganinshi dakin Aisha baiji dadin hakan ba duk da ranar girkinta ne, ficewa yayi ta kwashe da dariyar mugunta, dakin Nur ya nufa tana xaune kan sallaya ya shigo da sallama, amma fuskarsa bako alamar annuri, ta dago suka hada ido ganin yanayinsa yasa ta saukar dakai, ina kwana yayana, lfy yace atakaice ya juya xai fita da sauri ta riko mai jallabiya pls im really sorry yayana i dont mean to hurt ur feelngs pls forgive me.
      Durkusawa yayi yana kallonta ta ce pks, ya dago habarta is ok kanwata komai ya wuce amma kinsan ke matar aure ce kuma bai dace ki dinga kula wasu mazan ba, ni ne mijinki ni kadaine xakiyi hira dani sai abba da daddy, kai ta daga mai alamar taji tace insha Allahu bazan sake ba, murmushi yayi yace toh maza tashi ki shirya da wuri kar mu makara.
   Dakinsa ya nufa acan yayi wanka ya shirya, yana fitowa yaga Aisha xaune afalo tana ta danna dannen waya, honey ina breakfast dina"swt hrt kasan dai ba girki nake ba don haka ban daura ba, juyawa yayi ba tare dayace komai ba ransa yana suya dakin Nur ya shiga, tana shafa mai yayi sallama, hijab dinta ta dauko tasa, sannan tace yayana har ka shirya gashi ban gama ba, "no kixo ki hadamun breakfast, " a'a auntyn fah?, kawai kije ki hadamun breakfast xatayi magana yasa hanu abakinsa alamar tayi shiru.
.
    Cikin mintuna da basufi arbain ba ta hada mai tea ta soya mai dankali da kwai, ta dauko tazo wucewa Aisha ta mike ta jawo mata gashin kanta ke! Ubanwa kikayiwa wannan abun, budan bakin Nur tace wa uwarki, taja tsaki tayi gaba abunta.
    Aisha tana zaune ranta ya gama baci, Nurane ya fito yana rike da jakar Nur, da hanxari ta mike ta isa gabansa ta fara zazzaga masa ruwan bala'i, ai ya kawo yarinya ta raina ta, Nur kam ta watsa mata harara, ta kamo hanun yayan nata tace my Dear lets go tym is going, cikin mamaki suka kalli nur ta daga ma yayan nata gira tace haba my Dear kaxo mu tafi mana ko so kake adakeni? Ashagwabe tayi maganar sosai yaji dadin hakan, nan ya manta da Aisha tsaye ya sumbaci goshin Nur yace muje ta juyo ta kalli Aisha kallin wulakanci sannan tace"thankyou my dear.
          Yanayin da nur ta fara nunawa mijinta ya fara dagawa Aisha hankali, ga uwa uba yarinyar ta fara gogewa sosai akan zaman aure sannan taga alamar yarinyar nan komai na jikinta sun bayyana, domin kirjinta ya ciko, komai dai masha Allah.
.
         Kwanci tashi asarar mai rai Kokarin Nur yasa ta tafi ss1 nan ne ta hadu da gogaggun kawaye wadanda suke yayan mutunci nan fa suka dinga sata a hanya yadda zata kula da mininta, kuma tana daukar abunda suke fada mata don ta kuduri niyyar cusawa Aisha bakin ciki.
     Yau girkin tane tun data dawo take ta faman aiki, hadaddan abinci ta shiryawa yayan nata da juice kalakala, sannan taje tayi wanka, ta turara dakinta da turaren wuta.
.
        Tana zaune bakin madubi tana kwalliya Nura ya shigo da sallama, ta mike tana taku dai dai ta isa gu sa, "wlcm my dear ta rumgumeshi, nan yaji wani abu ya tsirga mai har tsakiyar kansa, ta sakeshi taje ta karasa adonta, yana xaune ya xuba mata ido har ta kammala, ya fito mata da kayan da zata sa wani dankarararan leshine dan ubansu tana dariya tace thanks dear ya tayata sawa sannan taje ta hada mai ruwan wanka.
Tare suka jero xuwa dinning lokacin Aisha tana zaune shaf yama manta da ita suka zauna suna shewa ya zuba musu abinci.nan Aisha ta taso tana huci.
.
   Toh ku biyoni don jin yadda xaa kaya nidai naja sis shamsiya da Abul.wuyan nur Aisha ta danka " wlh baki isa ba uban me kike takama dashi da zaki dinga min iskanci a cikin gidana, banza jahila yar kauye,
Duka nur ta kaima Aisha lokacin da ta kwaci kanta, da ubanki nake takama, bnza tabba kawai, wlh baki isa kin min na kyale ki, ganin fada suke iya karfinsu ya sa yaja hannun nur ya kaita gefe, ku me yasa baku da hankali kwata kwata baza ku rike mutuncin ku ba ko so kuke ku doran hawan jini, nura ya fda ransa a bace,
Ai tin da ka auro jahilar nan ka gama samun kwanciyar hankali a gidan ka, Aisha bn isa nace kiyi shiru kiyi ba, ai wallahi nura ba ka isa ka sa wannan kucakar yarinyar kuma jahila dabba wadda ita da kare basu da maraba a wajena, wlh ni ba jahila bace kuma  jahilar da ki ke kira tana gda tsohuwar bnza mai zuwa gidan yarta tana lalata tarbiyar yarta, kuma.... Dukan da nura ya kaimata a baki ya sata yin shiru,
" nur Aishan saarki ce ko mumyn saar kkce da zaki na zaginta, " ita baka ga abinda ta min ba sbda ita kana santa shine ita bazaka daketa ba sai ni ka daken, Nur ni zaki ma rashin kunya, Aishan ai ba saarki bace,
Toh dan ta girmeni shine akace ta zagen ko ta dake ni, ai bbu adalci a cikin a..... Duka ya kara kaimata a baki cikin fushi nur tai bngaranta,
"Aisha kinji kunya wlh banza a duniya ma akwai jahila kamar ke ki zauna kina fda da yar cikin ki wlh girma ya fdi, nura ya fda rai a bace,
" dariya Aisha tayi shi yasa naga kai da kaja girman ka bata ma rashkn kunya, cikin bacin rai nura yay bangaran nur,
Lkcn tana kwance akan gadon ta tana rera kuka, jikinsa a sanyaye ya karasa inda take dagota yayi ta kwace,
  
   " kanwata kiyi hakuri wallahi ba da niyya na miki ba, batan rai kikayi, yanxu nur ita bata barni na zauna lpya ba sannan kema bazaki barni na zauna lpya ba, gashi nan kinsa tana min gorin bakya min biyayya, ita bata ji magana ba kuma kema haka, kiyi hakuri idan na bata miki,
Ya fda yana mikewa har yaje bakin kofa Aisha ta fara magana cikin dasashiyar murya, " yayana" a inda yake ya tsaya bai juyoba kuma bai tafi ba,
" jiki a sanyaye ta taso tazo inda yake, " yayana kayi hakuri bazan karaba, ka yafemun bata maka da  nayi, fuskarsa dauke da murmushi yace na yafe miki, muje my ci abinci, ba musu ta biyoshi suka ci abinci sannan suka kwanta
.
Kwanci tashi ba wuya wajan Allah su Nur an  shirin fara waec nan da wata data, sosai nur ta maida hankalinta wajan karatu,
Har lokacin nura bai taba kusantar ta ba duk da fama da shawarta da yake, dan Nur Allah ya bata diri dan duk wani abu na cikar mace Nur na dashi,
Yayi ma kansa alkawarin bazai taba kusantar ta ba har sai tayi candy abu daya da yake damunsa rashin fara aladar da batayi bane har yanxu,
Kukan Nur ta nura ya jiyo ne ya katse masa tinani, cikin sauri ya nufi inda take, tqna durkushe a kasa tana murkutsutsu
" nur mai ya sameki, baki da lpya, daga masa kai tayi alamar eh dagata yayi dan ya kaita asibiti, turus yayi ganin jini a kasa inda take, daukarta yayi ya kaita bandaki yace tai wanka, dakinsa ya nufa ya dakko pad, daman ya dade da siya sbda jiran zuwansa, da kansa ya sa mata pad din a pant dinta, sannan ya nufi toilet din ya kai mata lakacin ta gama wanka kan ta fito ya gyara wajan,
Sanda ta fito ya sa mata doguwar riga mara nauyi ya rike hanunta suka nufi asibiti, magun guna aka hada mata sannan aka mata allura suka dawo gida
Cikin dare ciwo ya kara addabar nur kwata kwata ta kasa sukuni ko kadan Nura na gefenta haka suka raba dare sai kusan asuba bacci mai nauyi ya dauke su
Kwanci tashi ba wuya wajan Allah yaune su Nur suke zana jarabawarsu ta karshe a neco, daman sunyi jamb Alhamdulilah sakamakonsu ya fito da kyau har ya zarce yadda ake so
Karfe 12:00 dai dai suka fito daga exam hall dinsu sosai suka rikita makarantar da hayaniya suna ta faman rubuce rubuce ana ta exchangn number, ita dai nur saidai ta rubuta a takadda sbda har lokacin nura bai sai mata waya ba,
Wani kyakywan saurayi ya nufo inda ya tadda su tsaye,
Yan mata sannunku,
Hafsat kawar Nur tace yauwa sannu, nasan baku sanni ba sbda ni ba dan makarantar ku bane amma tare mukai neco daku, tin ran da na fara zuwa da naganki naji ina san kawarki ya fda yana nuna Nur, harara ta watsa masa, kaga dalla malam ni matar aure ce kayi hakuri ta fda tana mikewa hijab dinta ya janyo wanda yay dai dai ta tsayuwar motar nura a wajan
.
Wawan mari Nur tayi ma saurayin da ya ruko mata hijab dinta
" kai wani irin dan iskane mara mutunci wanda bai san darajar mace ba, na fda ma ina da aure shine zaka rukon hijab, Nur ta fda ranta a bace,
Sosai nura yaji dadin yadda nur tayima saurayin ya tabbata duk inda nur take zata rike masa mutuncinsa, a hankali ya karaso inda take
"Kut ni kika mara kinsan ko ni waye wallahi sai kinyi da kinsanin marina saurayin ya fda cikin borin kunya
   " dana sani uwarka zanyi shege mara mutunci, kuma sanin ko kai waye ba matsalata bace, domin baka da daraja da kima kamar ta miji na kuma insha Allahu kaima sai an ma matarka, banza jahili kawai, ta fda tana juyawa, ganin Nura a tsaye yasa hankalintq ya tashi dan bata san dame zai zo mata yau ba,
" yayana ta fda cikin tashin hankali, har ta nufeshi sai kuma ta juya ta ruko hannun kawarta,
" plsss hafsa ki fda masa yadda akayi wallahi yayana ban kulashi ba, shine yazo waje na dana ce masa ina da aure na tashi shine ya ruko min....
Hanunsa nura ya dora a baki alamar tai shiru,
" naga komai kanwata kar ki damu ai na yarda dake, cikin jin dadi ta rungumeshi " na gode yayana
" kar ki damu kanwata ya fda yana dagota daga jikin sa a mota ya sata sannan ya koma wajan saurayin,
" zan maka uziri a yau sbda hukuncin da matata ta dauka akanka ya burgeni ko ba komai ta disgaka a gaban mutane, wannan kadai ya isheka tashin hankali, kuma kamar yadda tace insha Allahu sai an maatarka fiye da abinda ka mata, nura yay tsaki ya bar wajan
Yau sati guda da gama makarantar Nur tana zaune a falonta tana kallo nura ya turo kofar tare da yin sallama, cikin faraa ta tashi taje ta tarosa tare da rungumeshi, sannu da zuwa yayana, " yauwa kanwata ya gida, wlh gashi Alhamdulilah, muje kayi wanka ta fda tana ruko hqnunsa, da kanta ta temakamashi yayi wanka sanda ya fito ya taddata kan gado tana jiransa, kusa da ita ya zauna tare da rungumota, Nur ina sanki sosai, nima haka yayana, kiss masu zafi ya shiga yi mata wanda nan take ya fara manta duniyar da yake ciki, ganin Nura na neman wuce gona da iri yasa nai sauri janyo hannun sister haima muka bar musu dakin,
.
Kukan da naji Nur nayi ne kuma ana rarashinta yasa nai saurin karbar biron wajan sister haima na nufi inda nake jiyo kukan
Nur ce kwance jikin nura tqna rero kuka kamar karamar yarinya, kiyi hakuri kanwata baxan karaba kinji ina sanki sosai na gode da yadda kika tsare mun budurcin ki, fatana Allah ya barmu tare,
Washe gari da safe nur kwance kan doguwar kujera tana kallon hotuna a wayar nura ya fito daga daki
.
   " kanwata zan wuce wajan aiki ki shirya da laasar zan dawo na kaiki ku gaisa da mumy daga nan sai mu wuce muyi wa umma Abba da kakq siyayya jibi zamu tafi panisau
Ihu nur ta Saki nagode yayana amma dan Allah bari na shirya ka saukeni yanxu gidan mumyn mafi shan hira da ita,
" haba nur yanxu sai da na gama shirina kuma fa da auntyn ki zamu fita tin dazu ta shirya,
" yayana kaya fa kawai zan canxa, toh sa kayanki ai akwai bata lokaci,
Wayarsa ta mika masa fuakarta a hade ta koma ta kwanta a kujera
Girgiza kansa yayi ya karaso inda take
    " sorry my dear tashi kije ki shirya amma karki bata lokaci kinji,
  Cikin murna tace
" thank yuh ta fda tana shigewa daki,
Aisha sosai ranta ya baci ganin tin dazu take jiransa yaki fitowa
Ganin nur zata bata masa lokaci ya sa ya leka
" kanwata ki sameni a wajan mota"
"Toh yayana"
"Swt hrt kiyi hakuri ki daina bata rai haka nan, " haba honey tin dazu fa nake jiranka, yi hakuri taso muta tafi ha fda yana ruko hanunta
Tus yayi sbda abinda ya gani cikin mamaki ya karasa inda take
"Kanwata me zan gani ba fa yau za mu tafi panisau din ba na ganki da akwati" eh na sani yaya amma ai zan canza kaya kaga kan laasar, sannan kuma in za mu fita da mangariba zan canxa dariya yayi ya karbi jakar yasa a baya
Aisha kuwa ranta ba karamin baci yayi ba da taga da nur zasu tafi dariyar tayi sanda ta tuna zatai an fani da damar nan ta kunsawa nur bakin ciki fuskarta dauke da murmushi ta bude gidan gaba ta zauna, nur kuma ta zauna a baya ya ja motar yay waje
.
   A gate din gidansu yaja ya tsaya , Nur ta bude kofa tayi waje, fitowa yayi ya dauka mata akwatin har ciki ya mikawa mai gadi, Aisha kuwa ta cika ta batse, Nur tana satar kallon Aisha sai da ta tabbatar su take kallo ta marairaice fuska"yayana wlh bana so ka tafi ka barni, nafiso ko yaushe na ganka kusa dani, nima haka kanwata amma kiyi hakuri zanje na kai Aisha gidansu xan dawo yau tare zamu wuni dake agidan mummy, sosai tani dadi ta rumgumeshi tace i luv u so much, "luv u too my dear ta silale tayi cikin gida, yana shiga mota Aisha taja wani tsaki har cikin ransa yaji tsakin amma bai tanka ta ba yaja suka tafi, itama akofar gida ya sauketa yayi gaba.
       Nur da sallama ta shiga falon ganin ba kowa yasa ta nufi dakin mummy, da sallama ta shiga aka amsa mata da gudu tayi kan mummy tana murna, mummy tace ke! Ni dallah karki karyani mana, mummy tana murmyshi tace sannu da zuwa ya'ta, lokacin daddy ya shigo, durkusawa  nur tayi ta gaida shi cikin ladabi, ya amsa yana murmushi yace ina mijin naki?, sunkuyar dakai tayi tace ya kai Aunty Aisha gida xai dawo, toh ita shine bata shigo ta gaida mu ba, Ita dai nur bata ce komai ba ya mike yayi waje.
      Nur da mummy sun taba hira, sannan Nur ta nufi kitchen, nan ta fara shirin girkin abincin rana, mummy ta rasa ina Nur take, kamshin abincin dataji ne ya bata amsar inda take, kitchen din ta nufa a kofa suka hadu Nur dauke da kololin abinci biyu, murmushi mummy tayi tace sannu da aiki, a kunyace Nur ta ce kai umma meye abun sannu don na dafawa iyayena abinci, sosai umma taji dadin jin kalaman Nur yanxu ne tasan tayi dacen sirika, aranta ta ce har da ina kokarin korre wannan baiwar da Allah yamun, Nur ta wuceta taje ta jera komai a dinning.
.
     Ta gama Hada komai ta shiga wanka bayan ta fito dama azahar tayi ta dauro alwala tayi salla, tana idarwa ta shirya cikin wata atamfa, sosai dinkin ya amshi jikinta, ta feshe jikinta da turare sannan ta mike xata fito falo, taji an murda kofa, Nura tagani tsaye ya harde hanu yana kallonta sai murmushi yakeyi, yayi balain mata kyau, ta karasa tana mai sannu da dawowa,  bude hanunshi yayi alamar taxo, noke kafada tayi tace yaya mummy da daddy fa suna nan, "toh meye ke ba matata bace, taki aikuwa ya karasa cikin dakin har inda take ya rumgumeta, badan taso ba, suna cikin wannan yanayin mummy ta iso ganin su yasa taja da baya ta koma, su kam sun lula don basu san ma ta xo ba.
     Karar wayar daddyce ta katse musu jin dadi, ganin sunan daddy yasa shi daga wayar da sauri, kuzo muci abinci, toh kawai yacw ya katse wayar, yaja hanun Nur suka nufi dinning.
      Nur ce tayi serving kowa, kamshi ya bude falon, daddy ya kalli mummy yace yau kam saboda sirikarki taxo shiyasa kika mana abinci mai dadi ko,?, ya fada yana kallonta, itama shi take kallo, " lailai sai dai muyi godiya wa Allah domin munyi dacen sirika tagari, a kunyace Nur ta sunkuyar dakai, sukayi adduar fara cin abinci sannan kowa ya fara ci, Nur takai loma uku xata kai na hudun kenan sai Amai, tuni Nura yayi toilet da ita, haka ta jigata dan sai data amayar da komai dataci, cikin rudani Daddy ya umarci Nura akan suje asibiti.
    Suna isa likita yasa ta kawo fitsari ya dau jininta gwajin farko sai ga ciki barovaro, sosai Nura yayi murna dajin wannan albisbir, kyautar dubu dari yabawa doctor, gidan su mummy suka wuce, kowa yaji dadi sosai, mummy tace lailai sai dai Nur ta dawo gidanta da zama ta reni jikanta, ta budawa idonta toka taki yarda haka dole suka yarda amma sai sunje panisau sun dawo.
.
Nura bai bar gidan ba sai kusan sha daya sai da mumy ta takura masa, da Aisha ta masa waya yqce ta tafi yana da uxiri, sanda ya dawo gida har tayi bacci, dakinsa ya nufa yayi wanka sannan yay alwala yay sallah ya godewa Allah da Allah ya bawa nur dinsa ciki fatansa Allah ya sauketa Lpya
Washe gari nura bai tashi ba sai kusan sha biyu na rana, yana tashi yay wanka ya nufi dakin Aisha tana zaune a falo tana chrtn,
Kusa da ita ya zauna swt hrt kin tashi lpya, lpya lau honey naga yau kasha bacci, bari kawai, jiya banyi bacci da wuriba ina aiki,
Ina break fast dina, amaryar taka bata yi ma ba, amarya ai a gidan mumy ta kwana, ai sai ka bita can ka ci,
" haba swt hrt me yasa kike haka, bai kamata ba fa ni mijinki ne, yanxu yaushe rabon da ki min girki,
Ai ba kana da wayayiyar kauye ba sai kaje ta maka, swt hrt ki fita harka ta wallahi zan mareki ni bnsan iskanci,
Ya fda rai a bace yay waje
Nur na zaune a falo tin tara take jiran zuwansa amma shiru mumy na kule da ita amma ta kyaleta,
Nura ne yay sallama tare da shigowa falon, mumy ce ta amsa masa sallamar kusa da nur ya zauna bayan ya gaida mumy
" ina kwana, nur ta fda ciki ciki, " lpya lau, mumy me akama nur ne naga ranta a bace, nima ban sani ba ai kunfi kusa sai ka tambayeta,
" mumy da abinci yinwa nake ji, wani irin yinwa ba daga gida kake ba, wlh mumy daga gida nake amma bata girka ba ya fda yana sosa keya, toh ai sai kaje kaci gashi can a dining, ba musu ya mike ya nufi dining mumy kuma tai daki,
A hankali yake cin abincin yana satar kallonta amma kwata kwata bata kallonsa ta mai da kanta ga tv tana kallo,
" nura ai ba inda zaka koh ga nur nan ka kula da ita zani anguwa yanxu amma da wuri Zan dawo, toh mumy Allah ya tsare
Mumy na fita nura ya taso daga dining ya taho inda take haba zabina, me ya faru fishin me kike yi Aisha ta bato min rai nazo inda zan samu sauki, sai na tadda azabar da tafi wancan na gwanda Aisha tamin rashin kunya da ke ki fushi da ni,
"Kanwata ki ce wani abu mana sai magana nake kin shareni, hararsa nur tayi tare da turo bakinta gaba
" kanwata ni kike hara nura ya fda yana zaro ido
" eh din an harara Dana San bakai break fast ba wallahi da bayar da abincin zanyi shikenan tinda kin tsaneni, nura ya fda cikin shagwaba, sosai ya burge nur hakan yasata fara kyakyatwa,
Gaskiya yayana kayi girma da shagwaba amma fa kayi kyau sosai, dariya yayi na gode kanwata,
"Amma yayana kasan zanyi missing dinka shine ka ki zuwa da wuri, bari kawai kanwata kinsan Allah ina tashi wanka kawai nayi na taho,
Har shabiyu fa bn tashi ba
" ayya kasha bacci, daman kayana zanje na debo Wanda Zan tafi dasu,
"Toh bari mumy ta dawo sai muje
" ina zaku mumy ta fda tana shigowa ciki
" yauwa mumy kayana zan debo, kwana nawa zata yi in ta je, mumy kwa Biyar nura ya fda yana kallonta
" wallahi aa mumy sati hudu zanyi,
zaro ido nura yayi
" gaskiya nur baki da hankali wlh,kawai sai na barki ki tafi kiyi wata guda a can
" toh ai baiyi yawa ba shekarata nawa rabona da garin tinda ka dakko ni daga garin baka taba kaini ba sai dan nace zani yanzu kace baka san zance ba,
" wlh nur kika batan rai sai na hanaki gaba daya naga in kina da ikon barin kanki, " bnda iko amma dai.... Mumy ce ta katseta ganin suna sanyin fda,
" nura ban san musu kawai ka barta tayi wata dayan tinda sanda ka hana ta zuwa ta maka biyayya bai kamata yanxu ka hanata zuwa ba,
Idan kinje ma kiyi shekara ki ga in zan damu, kisa driver ya kaita dakko kayanta, gobe in na sauke ki nur a panisau dan Allah kiyi zamanki kiga in zan nemeki, nura ya fda cikin bacin rai
" wannan kuma matsalar kace ba tawa ba
Ta fda tana shigewa daki,
Sai da akai laasar mumy tasa driver ya kaita gidan ta, lkcn Aisha na zaune ita da kawayenta suna shewa,
Hararsu tayi tai gaba,
" Aisha wannan kuma wace, kar ki ce mana kishiyar ki ce, " ita ce mana, kai amma fa tana da kyau, mtswwww kinga bansan iskanci
Nur na shiga daki ta fara hada kayanta sai da ta cika akwati biyu da kaya sannan ta kira driver yazo ya daukar mata
Sosai Aisha da kawayenta suke mamakin ganin yadda nur ta lodi kaya,
" Allah na godema da ka nunan wannan rana shegiya mayya ai daman mijina nawa ni kadai gasshi nan kin gama yayin ki an sallameki, Aisha ta fda lkcn da nur tazo kusa dasu
Mtswww tsaki kawai nur tayi ta nufi mota
.
Ku kasance damu danjn yadda zata kaya tsakanin nur da nura

Post a Comment for "HADIN ALLAH CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...