GORAN DUMA CHAPTER B KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GORAN DUMA CHAPTER B KARSHE

GORAN DUMA CHAPTER B KARSHE

- - Post a Comment

 GORAN DUMA CHAPTER B KARSHE


Yaga Namu
Hawaye Wani Na Bin Wani A Kuncin Yushau Bai Taba
Riskar Bakinci Irin Na Yau Ba,kuma Baita Ba Zaton Fushin
Da Alhji Keyidashi Yakai Haka Ba Donshi A Ganinsa
Laifinsa
Baitaka Kara Ya Karya Ba,amma Gashi Har Mahaifinsa
Naneman Yimasa Baki Dole Ya Maganu Yadinga Bashi
Hakuri Wanda Baiya Cin Galabar Alhjinba Ya Ce Hakuri
yazam Dole Yushau Allah Ne Ya Jarrabeni Da Zamowarka
Jinina Bayan Na Tsani Mutum Mara Uzuri Irinka,abinda
Kawai Zan Tunamaka Shine Mai Kyautatawa Za A


Sakamasa Da Kyautatawa Mai Munanawa Kuma Za A
Munana
Masa,
na Mayar Da Ruma Alhji Yushau Yafada Cikin Sheshekar
Kuka
Haba Alhji Yakara Tunzura Yamaka
Masa Harara Ya Ce Zan Kwantara Maka Zagi Wallai Ai
Yanzu Ba Matarka Ba Ce Bare Ka Mayar,kaiko
Matarka Ce Ka Mayardin Wallahi Saina Maka Ka A Kotu Da
Yushau Yakasa Magana Saiyamike Zai Bar
Falon Alhji Ya Ce Malam Bakaimin Maganar Sunan Yaran
Da Goronsu Ba Ya Tsaya Batare Da Ya Juyo Ba
Zanturo Da Goron Da Safe,sunan Kuma A Bawa Ruma
Zabi,alhji Ya Ce Bazata Zaba Ba,arasa Abin Arzikin Daza Ayi
Mata Sai Zabin Suna?
Na Yarda 'ya"yanta Ne Tunda Ita Da Haifo Dan Haka Idan
Rabonta Zataiya Haihuwar Goma A Bayansu To Ta Sanya
Sunan Datakeso A Inda Akasan Darajarta Saboda Haka
Idan Ba 'yan Nanaye Kakeson A Rada Musu Ba Ka Tsaya
Ka Zabarmusu
Wani Matsanancin Kishi Ya Tokaremasa Kirji Wai 'ya'yan
Dayakeji Dasu Kamar Tsoka Daya Amiya Su akema
Kishiyoyi Goma Yanzu?
Kuma Bama 'ya'yansa Ba, 'ya'yan Wani Gardin,fuskarta
Yanuna Bacin Rai Ya Ce Asanya Wa Macen
Hamida,namijin A Kirashi Auwal
Ba Bu Ubanda Zaisa Masa Auwal Wallahi A Gidan Uwar
Wa Ya Ciyo Auwal Din?In Ma Izgili Kake Za A Haifi Auwal
Din Ne Amma Bakai Zaka Haifa Ba,yushau Yakara Kulewa
Ya Ce To Asamasa Auwal
Yai Gaba Tunkafin Yatashi Motar Sa Yakira Wani Abokin
Cinikinsa Ya Bidi Bashin Dabbobin Yanka Sannan Ya Koma
Agadasawa Ya Siyo Goro Ya Tsaya Wani Kanti Ya Sai Alewa
Duk Ya Watsa Bayan Mota Yana Mita Allah Ya Rufamin
Wannan Asirin Idan Ma Anayi Ne Don A Tozartani,
******
Wannan Dalilin Ya Sanya Ya Dauke Kafa Daga Gidan Kuma
Ko A Waya Baya Gaida Kowa Bare Afadamasa Ba Bu Dadi
Ko A Tambayeshi Wani Abu Saidai Fa Rayuwa Na Kara
Kuntata Agareshi Dankuwa A
Inda Bai Hanawa Kansa Zuwa Bama Wato Gidan Nasa

Yanda Sumolinsa Wanda Ya Fahimci Tafi Kashi
Doyi Sumoli Raina Kama Kaga Gayya Ce,wadda Kuma
Yake Zargin Yafada Tarkonta Na Abindayaketa Yawanji A
Bakin Mutane Wato So,ba
Ya Iya Tsawatar mata
Ruma Da Yaranta Suka Ci Gaba Da Samun Lfya Cikin
Horewar Ubangiji Tare Da Kyakyawar Kulawa Da Suke
Samu Amma Badinin Zuciyar Ruma Na Mugun Ciwo
Dangane Da Banzantarwar Da Yushau Kemusu Ita Da
Yaranta,ayanzune Kuma Take Kara Tabbatar Wa Kanta A
Boye taSha Saka 'ya'yanta Taita Kukan Rashin Dacen Uba
Wanda Baisan Darajar Suba A Matsayinta Na Sikila Ta
Tabbatar Duk Sikila
Satinta Biyar Da Haihuwa Maimuna Yayar Hafsa Ta Haihu
Son Biki Irin Namata Sai Suka Kulla Ai Hadawa Zasuyi A Yi
Biyan Bashin Bikin Sunansu Hamida Rana Guda Inda
Maimuna Zata Baro Gidanta Lokacin Sunan Su Hadu Anan
Gida Ayi Taron Sunan Alhji Badan Yasoyima Yushau
Mugunta Ba Ba Bu
Abinda Zaisa Ya Laminta Amma Da Sauri Ya Yarda
Yakuma Aiki Jakada Mubarak Takanas Yakiramasa Yushau
Wanda Ya Amsa Cikin Kaduwar Hanta Da Cewa Gobe Da
Yamma Zaizo,ya Manta Dadare Bai
Gama kasa Kayan Karin Kumallo Ba, Wato Bai Siyo
Madara Ba Asafiyar Ranar Sumoli 'yar Kwaya Saita Tafasa
Masa Ruwan Bununsa Ba Bu Ko 'yar Citta Takawo Masa
Yaso Yashareta Saiyagama Rashin Hakadai Sukaita Jifan
Kawunansu Da Bakar Magana Daga Karshe Takare Ta Ce
Yaufa Sauran Kwana Uku Sunan Gidansu Hakane,yaushe
Zaka Gidan?
Ya Ce Yauma Dadare Zani,ta Ce Idankaje Inkasami Hafsat
Ko Asiya Katambayi Su Bayanin Ankon Dazamuyi,ok,
Kawai Ya Cemata Ta Ci Gaba Dayimasa Lissafi Ya Fara Bata
Amsa Ranshi Inyai Dubu Ya
Baci daga Nan Suka Daura Daga Inda Suka Tsaya Hajiya
Ta Ce Ashe Da Gaske Kazo Har Ina Karyatawa
Ya Gaidata Tare Da Ce Eh Naga Gidan Cike Da Mutane
Shiyasa Ban Karasoba,suka Dubi Juna Ita Da Alhji Yo
Waye Bakonka A Bakin Alhalin Duk 'yanuwankane, Haba
Ke Kuwa Ai Dole Da Kunya Mutum Ya Fita Zakka A Dangi
Idan Yana Da
Kunyarba Inji Hajiya Alhji Yakuma Cewa Haba Ko Baiji
Kunyarmu Kashin Duwawunsa Daya Wulakanta Ba,ai Zaiji
Kunyar Uwar Ruma Wadda Ta Wanke Diya Taba Shi
Yanemi Kashewa Don bayaso,,wallahi Kuwa Kaga Tun
Tanajin Wai
Wai Yanzu Taga Dahir Kwananta Biyu A Gidannan Bata
Keyar Ka Ba Kazo Ganin Ya'yanka Ko Da Kuwa
Kazo Yi Uwar Su Sannu Dashayar Dasu Ba Tab!Ai Sai
Mutum Yasan Mutunci Zaiyi Saida Alhji Yainisa Da Cin
Abincinsa Yadago Ya Cemasa Karkace Banyimaka Tayi Ba
Idanzaka Ci Bismillah Naga Kana Wani Kikkifta Idanu

Don Bukata Yushau Na Matukar Bukatar Abincin Amma
Yanayin Tayin Ne Yaimugun Kular Da Yushau Ya Girgiza
Kai Musamman Daya Tuno Dangantakar Sa Da Alhji A Can
Baya Farkon Aurensa Da Ruma Yadda Alhji Kenan Nan
Dashi Kamar Abokinsa Ya Bashi Kyautar Kudi Yafi Akirga
Yaimasa Wasa Suci
Daga Kwarya Daya Amma Ayanzu Alhji Ya Zama Kamar
Wani Mugun Ubangida Da Yaronsa,sanda Ya
Cinye Abincinsa Tsab Ya Ce Yadai Malam Nifa Zanshiga
Ciki Yamike Yakwaso Masa Rasitai Ya Zubemasa Ka Duba
Kwanan Wata Da Kyau Iyalanka Din Nan Ne Suka Kokoma
Asibiti Idan Yushau Garau Yake Dubasu Sunakara
Rikitamasa Lissafi Daya gaza Saiyaje Fasu A Aljihu Yadubi
Alhji Ya Ce Shikenan Za A Kawo Kudin Gobe BaBu Laifi
Dama Kudin Wancan Asibitin Ma Baka Gama Biyana Ba
Inji Alhji Ya Ce Baka Fa Sake Magana Akan Shawarar Nan
Ba Tun 'yan Kudin Daka Bayar Baka Kuma Bayarda Ko
Sisiba,
niyanzu Ba Kudine Dani Ba,
"to Waye mai Kudin"?
Cewar Alhajin........
.
Hehehe... Pls inda mai kudu a hanu ya taimaki Yushau
mana.?
Ko karokaro zamu masa ne mai biyar mai goma? Lol.z
Dan Aunty
GORAN DUMA (P 45)
.
.
Kaga Malam Wannanfa Umarnin Ubangijine Ba Bulus Na
Kwaso Maka Inci Ba,ruwankane Kayi Ko Ka Bari,kanka Ka
Zalunta Bawaniba mu Sai mubarka Da Allah,
hawaye Yafara Zarya Yushau Najin Mahaifinsa Na Neman
Yimasa Baki Akan Alamarin Da Zai Iya Daukemasa Nauyi
Shi Dayake Dancikinsa,wallahi Tallahi Dagaske Nake
Banida Kudine, Ba Bayarwa Bane Banasanyi,
aishine Na Ce Saimu Barka Da Allah Kokuma Wallahi Ka
Kwashi 'ya'yanka Kujeko Nonon Akuya Ne Ku Dunga
Tatsowa Kubasu
Allah Ya Baka Hakuri Ayanka Min Abinda Akeso Na Bayar
A Wata Zandinga Bayarwa,
Kasami Hajiya Ta Yankamaka,ya Ce To Godiyanake Allah
Yakara Girma Alhji Yakara Koro Wani Lissafin Ga Wata
Dawainiyar Ma Data Billo Kasan Mata Da Biki Yaimasa
Bayanin Sunan Daza Ayi Kashiga Hajiya Taimaka Lissafin
Nidai Ankarbarmin Dubu Ashirin dina Dazu Saika Bani
Abina Yanzu Saboda Takaici Ya Zira Hannu Ya Ciro Kudi
Yatarar Gabadaya Dubu Bakwaine Ya Zari Dubu Daya
Yamikama Alhji Shida Karike Wadannan Zanciko Maka
Ragowar
Gobe,a A Ka Mayarda Ita Kabani Har Ita Dubun daka Cire
Haka Alhji Yahada Duka Bakwaidin Ya Amshe Ya Ce

Dafatan Zaka Biyamu Bashinmu Zuwa Gobe Saboda Shi
Dai bashi Nauyine Dashi,idan An Sauke A Huta,
Yushau Yashiga Gurin Hajiya Taimasa Nata Lissafin Ya Fice
Yanazuwa Gida Da Tsohuwar Yunwar Sa Yaga Sumoli
Koruwa Bata Bashiba Takwaso Masa Kayan da taje
Kasuwa Tasiyo Ya Ce Wakika Tambaya Dazaki Fita?
Haba Darling Saika Ce Wata Matar
Kauye,aransa Ya Ce Wai Wannance Wadda Ya Zabo Dan
Yanason ko Soron Kofar Gidansa Saitanemi Izininsa Kuma
Inya Ce Karma Tataka Soron Zata Yarda Ya Isa,ba Abinda
Yafado Masa Sai Kalmar Kar She Na Mahahfinsa
Wato'WADDA NA HAKIKANCE FITINACE AGAREKA.
Saboda Bacin Rai Da Kyar Yake
Taunar Abincin Itako Ta Tuntsire Masa Da Dariya,.,kai
Honey,ci A Hankali Ba Guduwa Zaiyiba,
*******
Ance mai Hankali Baya Damuwa Da Lamarin Duniya
Domin Damuwa Da Bacin Rai Basa Gusar Da Masifa,ruma
Ta Gwada Wannan Falsafar Kodon Tsira Da Cikakkiyar
Lfya Amma Tagaza Iyawa,duk Yadda Taso Ta Fitar Amma
Ta Gaza Iyawa,duk Yadda Taso Tafitar Da Wulacinda
Yushau Kemata Aranta Ruma Kam Ita Tasan Halinda Take
Ciki Allah Ma Yasan Sun Sameta Kuma A Muhallinda Ya
Dace Wasu
Masu Sikilar Yaya suke Musamman Ma Idan Abin Yahadu
Da Rashin Gata Ita Tasan Abinda Suke
Bukata Idan Suka Galabaita Ita Tasan Da Cewar Akwai
Ciwansu A Duniya Ba Son jiki Bane Lallai Tunda Itasuka
Sama Mai Irin Ciwansu Allah
Yaimusu Babban Gata
BAYAN WATA TAKWAS
Allah Mai Yadda Yaso Watannin Su Hamida Tara Cif Da
Haihuwa Allah Ya Amshi Ahmad Bayan Jinyar Kwana Daya
Baisan Inda Yake Ba Bayan Zace Zacen Akadinga Yi Ruma
tashiga Cikin Wani Hali Na Kidimewa Tayi Kuka Sosai
Haryakai Ce Iyayan Sun fahimci Ba Kukan
Rashin Ahmad Ne Kawai Ruma Take Ba Harda Narashin
Auwal Tare Da Wani Abu Na Wulakancin Da Yushau
Yakemata Wanda Tunda Ya Daukesu Sau Daya Baikara
Daukansu Ba,har Bayan Rasuwar Bata Yarda Tagaisa Da
Yushau Ba Haka Dai Ruma Takasance Cikin Jimami Inda
Safiyar Watarana Taje
Gurin Hajiya Da Kukanta Ta Ce Hajiya Ki Rokarmin Alhji
Inason Komawa Abuja Dan Nikam Nasan
Kano Bata Karbeni Ba
Hajiya Ta Tausayamata Kwarai Alhji Dakansa Yazo Dakin
Ruma Inda Yaga Tana Gasa Mata Mukamukinta Ya Ce
Yanaga Kina
Gasata Ta Ce Masa Ta Dameni Da Kuka Kuma Nan Take Ta
Bawa Shiyasa Nake Gasamata Ya Ce Asha
Allah Yasauwake Yasa Kaffarane In Angama A Miko Min
Ita Tagama Ta Sauya Mata Kaya Tamika Masa Yakarba

Yana Zolayarta Bayan Yajima Adakin Har Hamida Tai Barci
Ruma Ta Amsheta Ta Kwantar Da Ita Alhji Ya Ce Kwana
Nawa Kikesa Ran Zaki A Abuja?
Azuciyarta Ta Ce Wai Daga Zuwa Karatu Sai A Kaga Wa
Mutum Zaman Dindindin?
Takasa Magana Ya Ce Sati Daya Ko Biyu?
Yai Gyaran Murya Banji Dadin Yadda Furucin Dakikai
Amfani Dashi A San Zuwa Abuja Ba,na Cewa Kano Bata
Karbekiba Ki Caje Maganar Nan Da Kyau Zaki Tarar Da
Kure A Cikinta, Domin Ubangiji Bai Hukunto Kaddarar
Mutum Rataye Da Gurin Zama Ba,jikinta Sanyaye Ta Ce
Astagfurullah,
yadago Ya Ce Yauma Zansake Zuwa Miki Da Kokon Barar
Alfarma Ina Mai Cike Da Yakinin Jincewa Alkhairinki Da
Tawakkalinki Bazai
Saki Gaza Yimin Ba Gabanta Yafadi Aranta Ta Ce Allah Yasa
Alhji Ba Komawa Gidan Yushau Zaice
Ya Ce Lallai Kinzo Kano Cikin Farinciki Da Wani Abu Na
Koshin Lfya Abubuwa Dayawa Sunfaru Wadanda Allah Ya
Tsarasu Danai Sila Kamar Auren Yushau Wandayake Cikin
Kaddarorinki Marasa Dadi Har Yanzu Ina Nadamar Da
Kasa Yafewa Kaina
Kuma Na Tabbatar Nadamata Bazata Gusheba Idan Ba
Ganinki Nai Cikin Farinciki Ba Amma Yanzu Ruma Saiki
Kinkimi Min Maganar Komawa Gida?
Kiyi Hakuri Kimin Alfarmar Ki Bani Lokaci Mui Addua
Mumika Wa Allah Kokenmu Mujira Hukuncinsa
Nayi Alhji Tafada Cikin Tawakkali Da Rarrauniyar Murya
Hakikatan Bataji Dadin Yadda Yake Dora Wa Kansa Laifi
Ba Acikin Abinda Yushau Kemata Dantana Da Yakinin In
Ana Bada Numfashi Alhji Zai Iya Bata Nasa Saboda
Damuwa Da Kulawa Ta Ce Masa Amma Inason Kai Ziyara
Wannan Ba Bu Laifi Kijekiyi Wata
Daya Ko Biyu Ki Dawo Allah Yaimiki Albarka Amin Kwana
Biyu Tsakani Ta Hada Kaya Ta Nufi Abuja,
******
Yushau Yadawo Kasuwa A Gajiye Karfe Shida Amma Har
Shida Darabi Ba Bu Alamar Sumayya Allah Kana Gani
Cikin Tausayin Kai Goshin Magaruba Ta Shigo Tare Da
Almajirai Uku Ta Ce Ma Almajiran Kai Sharemin Tsakar
Gidan Da
Kicin Kai Gyaramin Falo Ka Goge Tayil,kaikuma Yimin
Wanke Wanke Ka Feremin Doyannan Don Wancen
Hayatun Saiya nemi Dagamin Hankali Akan Abinci,wata
Bakar Zuciya Tataso Masa Amma Haka
Yashare Yai Alwala Yatafi Massallaci Dan Yatuna Lokacin
Ruma Ko Adama Bata Isa Ba Shi Abinci Ya Ci Ba Amma
Gashi Yanzu Ashe Har Girkin Almajirai Yakeci,
Bismillah Ga Abinci Yaduba Soyayyar Doya Ce Mai Fulawa
An Kawata Ta Da Farin Kwai Dajan Tumatir Tai Shar
Kamshi Maidadi Natashia Amma Saiyarufe Yana Toshe
Hanci Lfya Kake Wani Toshe

Hanci Hayyatar Tawa Batakainan Ba Dahar Zanci
Jagwalgwalon Almajirai Nandai Suka Hau Sama
Suka Fado Ita Tana Korafin Yaki Kawo Mata 'yar Aiki
Shikuma Ya Cemata Ke Wannan Dama Zamanki Kikai
Agidanku Kika Mutu Ba Bu Aure Da Gangan Ake Cutar
Mutane Ake Damfarar Musu Kudi Azuwan
Ba Aso Kui Zurfin Ilimi Ashe Rabuwa Da Ja'ib Ake,
tuni Sumoli Ta Barke Da Kuka Ayya Inza Ai Wasa Ayi
Darling Amma Banda Tsikarar Uwar Miji,
yanzu Dan Allah Audine Zaiwa Talle Gori?
Ai Wallahi Garani Iyayena Suna Sona Har Ma Zasu Inganta
Rayuwata Sun Damfara Wa Wani Amma Kaifa?
In Bandani A Duniyar Nan Kafadamin Wake Sonka,?
Kuma Wallahi Sweety Barikaji Ba Fa A Kauye Muke Ba
Dazan Zauna Kadinga Cin Zarafin Iyayena Shi Zaman
Duniya Susar Jakine Yimin In Maka Allah Inka Ci Gaba Da
Zagin Iyayena Zan Rama Don Iyaye Basufi Iyaye Ba,kaima
Danaka Iyayen,kewofintar Dakai Kaso Abinka Bareni Da
Nawa Ke Lelena,
ai Kuwa Zanfara Turamiki Ashar Daga Karamin Alhaki
Sweety Da Darling Dindakike Cemin
Tamike Tana Dariya Har Da Sunkuyawa Har Takai Dakin
Baccinsa Ta Ce To Honey Turamin Ashar Din Mana
Iyayenmu Daya
Haka Dai Rayuwa Tadinga Tfya Kwanaki Suka Dinga
Karewa Har Takai Watara Na Yushau Ya Zarce Gidansu
Wanda Rabonsa Da Zuwa Tun Rasuwar Ahmad Dakuma
Niyyar Gyara Dangantakar Sa Da
Iyayansa Kafin Tunanin Hukuncin Dazai Duka Akan
Sumoli,
Gaisuwar Sa Ma Da Kyar Hajiya Ta
Amsa,yajima Zaune Gabanta Kala Batasake Ce masa Ba
Yatuna Ba Buwani Abinda Zai faranta musu Rai Irin Ruma
Dan haka Yai Niyyar
Yaudarar Su Hajiya Ina Rumaisau Banji Motsinta Ba?
Hajiya Kamar Ta Kifa masa Mari Saboda Haushi Anan
Tahadiye A Takaice Ta Ce masa "Bansaniba".....
Ya dubo dayan gefen yace Dan Aunty ina Ruma?
Hehehe... Jama'a wace irin amsa zan ba Yushau?
.
Dan Aunty.GORAN DUMA (P 46)
.
.
Yai Dif Jiki A Mace Yanufi Kicin Wajen Talatu, Rumaisau
Sunje Unuwane?
Eh Suna Abuja,
da Mamakinsa Kwana Nawa?Watansu Hudu,yakarajin
Rudewa An Tafi masa Da 'ya Batare Da Saninsa Ba,ziyara
Ko Zaman Dindin?Daga Ziyarar Wata Biyu Gata Tana
Neman Haure Wata Hudu Saboda
Kaguwa Da Tambayar Atakaice Take Amsamasa,
Saidai Naji Hajiya Nafadin Kila Cikin Watan Nan Su Dawo

Yai Sallama Ya Bar Gidan Ya Wuce Gidan Maikudi
Abokinsa Yakaimasa Koken Sumoli Yaimasa Nasiha Da
Shawarwari Akan Haka,
hakadai Sumoli Taci Gaba Da Gara Yushau Yarame Ya
Lalace Hartakai Watarana Hatsaniyar Takai Ga Yushau Ya
Zageta Tarama Da Kaima Tir Dakai,kawai Kaita Tsinemin
Mugun Mutum Kawai Tunda Na shiGo Gidanka Nakasa
Gaba Na Kasa Baya Kullum Cikin Zulumin Bala'inka Na Ke
Ashe Duk Zakin Bakinka Damin Ina Waje Na Yaudarane
Aurenka Cike Yake
Da Rashin Kwanciyar Hankali
Kayan More Rayuwa Ba Bu Saita Fashe Da Kuka,
to Fita Fita Nasake Saki Daya Kitafi Gidanku Ta Ce Wallahi
Tallahi Baka Isa Ba,ba Bu Inda Zani Na Rantse Da Allah
To Ki Zauna Watarana Zanyi Ajalinki Don Bazan Jure
Wannan Rashin Tarbiyar Ba
*****
Innar Ruma Ta Kware Dasanin Hanyoyin Hilatar Mutum
Da Tattalinsa Ruma Kam Da Hamida Suna Samun Kulawa,
Duk Azaman Da Ruma Tai A Abujane Karance Karancenta
Yadawo Kuma Daidai Wannan Gabarne Tasami Damar
Zama Marubuciyar Tauraruwa Jaridarta Ta Aminiya Tun
Tana Abuja Bisa Sahalewar Mominta
Alhji Ya Gaji Da Kawaici Yatanka Mata Rumaisau Kin Saba
Alkawari Fa Tai Dariya Cikin Satin Nan Ko Na Sama
Zandawo,
Dazaki Hakuri Kidawo Danafi Kowa Farinciki,
Wallahi Zandawo Alhji Amma Ina Neman Alfarmar Barin
Hamida Wajen Momin Domin Ta Saba Da Ita Harma Tafi
Damuwa Daita Akaina BaBu Laifi Inkin Tsayar Da Ranar
Dawowa Kisanar Dani Nazo Na Daukeki Na Gaisa Da
Hamida Tunda Nan Za A Barota Sukai Sallama
Ranaku Suka Dan Wuce Inda Rayuwar Sumoli Da Yushau
Bata Canza Daga Yadda Take Ba Shidai Baikulata Itakuma
Tanasan Yamaidata Yushau Kam Baidawo Wa Gida Sai
Cikin Dare Itakuma Sumoli Data Lura Da Hakan Safiya
Nayi Yafita Itama Ta Dasa Kwalliyarta Ta Shiga Dakinsa
Tadauki Kudi Ta Shi Ga Gari Adalci Daya Yaimata Bai
Kullemata Sito Ba,kuma Yana Ajiye Kayan Abinci DaiDai
Bukata Sannan Yasan Tana Zarar Masa Kudi Dari Biyar Ko
Dubu Daya, Duk Yashare Danyaga Bata
Daukar Wanda Yafice Kima Sumoli Sunyi Wata Daya A
Haka Tafara Laushi Tare dayin Girki Dashi A Wani
Rana Ta Boyewata Kawarta Da Sukai Rikici Da Mijinta
Yakoreta Gidansu To Tana Tsoron Mahaifanta Kawai Sai
Sumoli Ta Bata Mafaka A Gidan Yushau Baisaniba, Inda
Bayan Mahaifinta Yagano Tana Gidan sukazo Tafiya Da Ita
Da Cewar Zasui Karar Sa Saboda Aje Matar Aure Da Yai A
Gidansa
Kaitsaye Falon Yushau Ya Dosa Tare Da Iyayan Samira Ya
Kwankwansa Kofa Yana Kwada Mata Kira Ta Fito A Firgice
Yadaka Mata Tsawa Ina Yarinyar Danagani A Gidan Nan Ta

Ce Ai Batanan Tunjiya Au Shekaranjiya Tatafi Yasheketa
Da Mari Yashige Falon Ya Tadda Mata Sama Da Goma
Sunata Cashewa
Duka Yakorasu Itakuma duk Aranar Yushau Yakara Ma
Sumoli Saki Daya Takara Daukan Alwashin Bazata Je Koina
Ba Ranar Kam Yushau Bai Runtsa Ba,kuma Yatabbatar
Alhakin
Rumane Yakamashi Ita Yakewa Kallon Masifa Ashe Ita
Rahamane In Aka Jerata Da Sumoli,haka Sukaci
Gaba Inda Sumoli Takara Canza Salon Karkato Da
Hankalin Yushau Gareta Amma Yagagara Haka Yushau
Yakara Komawa Ga Abokinsa Maikudi Wannan Karan
Gurin Mahaifiyar Ta Sukaje Amma Me Bata Wani Daraja
Koken Nasu Ba,tadai Ce Zatai Mata Fada
****
Maman Ta Cemata Dazu Da Safe Sai Ga Mijinki Yakawo
Kararki
Sumoli Ta Ce Ashenan Yayo Aima Haryasakeni Ummanta
Ta Ce Ashe Munafikine Inaganinsa Haka Ta Ce Karkidamu
Suka Zarce Can Wajen Wani Boka Sai daf Da Magariba
Tadawo Tagama Abinci Aka Bade Masa Abinci Da
Magunguna Haka Dai Zaman Nasu Ya Ciga Ba Har
Suka Sake Share wata Uku Batare Da Anji Kansu Ba Sai
Halin Sumoli Yafi Nada Tambaya Zuwa Anguwa Kullum In
Ma Bai Barta Ba Zatatafi ,
Kayan Abinci Taiyanda Taga Dama Dashi Hartakai Sumoli
Tanason Yushau Ya Biyamata Makaranta Tadora Daga
Indata Ta tsaya
To Ashe Dai Tana Jika Tunda Har Sumoli Ta Furta Maganar
Komawa Makaranta Hakan Dai Baisamu Ba Danko A
Mafarki Bazan Lamunta Ba, Na Lura Idan Na Biyemaki
Kwanan Nan Zanyi Mutuwar Tsaye,
Awata rana Sumoli Takaremasa Rashin Mutunci Da Gori
Kan Kayan Abinci Ya Ce Mata Tir Tir Dake Sumoli Kin
Munana Halinki Ni Allah Yayemin Jidalin Aurenki Idan
Dagaskeni Bana Rufamiki Asiri Ki
Sami Mai Rufamiki Idankuma Ni Ni'imane Atare Dake
Allah Na rokeKa Daka Janye Miki Ni Kozaki
Hankaltu,na Tabbata Matukar Inatare Dake Kece Ajalina
Ya Fice Yafada Motar Sa Yatuno Ruma Yadda Yake
Munana Mata Da Dukkan Gabbansa,ya Hantareta,ya
Bautar Da Ita,ko Bata Da Lfya,yaki Kula Da Lfyarta,yaki
Taimaka Mata Alokacin datake neman Taimakonsa,yaha
na Kudin Cefane Koda Bai Aje Kwayar Hatsiba Amma Ko A
Fuskarta Bazata Nuna Fushiba Balle Harshenta Ya
Furta,kuma Bata Kasa Kyautata Masa Ba Bare Ta
Kauracemasa, Unguwa Kamsaita Share Wata Biyu Bata
Leka Kofar Gidanba,kuma Dukda Tana Da Alaka Da Masu
Hannu Da Shuni Bata Taba Ganin Abu Ta Ce
Asaimata Ba Ahaka Take Binsa Saudakafa Har Lokacinda
Gangandinsa Takadamasa Kidan Watsar Da Ita Yazabi
Sumoli Ya Biyemata Yawatsar Daduk Dangi To Yau Ga

Kangin Rayuwar Dayashiga Ya Bata Dakowa Nasa Adalilin
Sumoli Waidamezaiji?
Da Fushin Mahaifinsa?
Ko Da Matsin Rayuwa?
Ko Kuma Masifa Da Balain Ta Na Cikin Gida?
Yaukam Da Tunanin Ruma Yawuni Musamman Dayake
Ganin Akwai Sauran Damarta Nakomawa Tunda Saki
Daya Yaimata Kuma Ba Maganar Aurenta Da Wani Allah
Yadubeshi Tadawo Rayuwar Sa Ko Farinciki Yadawo
Rayuwar Sa Har Yake Ganin Zai Cire Nauyi Da Kunya Da
Tsoro Ya Tunkari Alhji Da Hajiya Har Ita Ruma A Gobe
Yana Iya Yiwa Abuja Tsinkesu Yanke Masa Duk Irin
Hukuncin Dasukeso Indai Zasu Dawo
Masa Da Ruma
Yaje Gidansu Da jin Kumajin Zai Motsa Kwanji Amma Sai
yatarar Da Alhinin anyi Rashi A Rogo Saboda Haka
Yahadiye Abinda Ya kawoshi Da Safe Yanufi Rogo Ashe Da
Rabon Zai Tsinka Dami Akala Wato Tsinto Ruma...
<==KAN DUTSE!==>
Karasowar Yusha'u gare ta da 'karar shigowar sa'kon
murya karo na biyu a wayarta ya katse mata tunanin
JIYANTA wanda ba ta dire ba.
Ta kasa hankalinta biyu, kallon Yusha'u da damuwa da
sakon wayarta. Ta san sa'kon MAHAUKACIN MASOYI ne,
mahaukacin da wani lokaci zuciyarta ke hararo basajar
Yusha'u, amma yanzu yana son 'karfafa shakkar in shi din
ne, don ga shi a tsaye, ga kuma sakon ya shigo.
Yusha'u ya gyara tsayuwa lokacin da ya gaji da cika da
dokin abin da ke ranta game da shi ya zarce wannan
kallon 'kurullar da ta ke masa.
Kamar ta san abin da ransa ya raya masa, ta kawar da kai
a sannu tare da shan kunu, sai ya shiga taitayinsa, amma
da yake kamar bai gaji iya rarrashi da siyen soyayya ba,
iyakar maotsinsa sai ya 6uge da son kyautata murya ya
ce. "Ban san al'adar da ke tilasta miki zuwa kan dutsen
nan ba, kuma duk sanda kika zo sai an biyo
bayanki".
Ko kadan ba ta yi niyyar zata amsa ba, sai kawai ta 6uge
da zuge jakarta ta zura wayarta, sannan ta fara tafiya tana
cewa. "Dan ma ba a dare a gida".
Ya biyo ta cikin daga 'kafa saboda son su jera.
"Kin fada za ki kwana ne?"
Har zata amsa da fatar baki sai kuma ta ga asarar hakan,
ta girgiza kai tare da duba agogo..
.
Chakwakia..
Ga Yushau ga Mahaukacin masoyi ga kuma Dan Aunty?
Ko ya zata kare. Amma dai ni hankaki na akwan ce yake
tunda tace in ba niba sai rijiya, lol.
Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.
Dan AuntyGORAN DUMA (P 47 )
.

.
Karfe shida saura kadan za su kai wajen isha'i ke nan
kafin su je gida. Ba wannan ya fi yi mata ciwo
ba, sai yadda Yusha'u ya yi damarar dole sai sun tafi tare,
ba dan Hajiya ta yi mata kashedin kwana ba da babu abin
da zai hanata kwana, saboda kawai kar ta jera da shi.
Yana ta fuffurzo mata magana da 'karfin hali da na kwanji
har suka 'karaso gidan Goggo tana cika
tana batsewa suka yi sallama da Goggo mai yi mata
nasihar ta saurari Yusha'u a fakaice. Suna fitowa kofar
gida dan babur din da ta yiwa maganar ya dawo ya kaita
tasha ya karaso.
Cikin dakewa kuma ta doshe shi ya karkata mata mashin
din a gaban Yusha'u ta haye.
Duk yadda ya zo wuya sai ya rasa matakin da zai dauka
wanda ya wuce binsu a mota har tashar. Ta salllami mai
mashin shi kuma ta yi d'amarar share shi, sai da ya matsa
mata da hon sannan kamar dole ta zo ta shiga motar.
Sai da tafiya ta fara nisa sannan ya tsinka shirun
tsakaninsu.
"Na yi miki.....mtsw..... Abu dan gayya, abin da kika yi yau
nayi masa kallon gayya..."
Wannan karon yana sauke numfashi ta amsa.
"Ba gayya ba ce, kamar matsa min ka yi sai mun taho
tare, na yi kokarin in hana zuciyata nuna ba ta
son biyoka ta gaza, wannan shi ne abin da ka dauka
gayya".
"Shi ne kika za6i ki sa6i Allah?"
Ya fada yana nacin kallonta.
Ita ma ta dan yi masa zuru na rashin fahimta, ya mayar
da kallonsa ga titi.
"Kin ba ni haushin da kika yi niyyar ki ba ni na kuma
kar6a cutar da yadda kika so. Wai a gabana ki haye bayan
wani 'kato ya goya ki... 'kazantar ta wuce 'kazanta..."
Ta tare shi ba dan zuciyarta ta fara zafi ba, sai dan kar ta
ba shi sararin da zai ci gaba da nuna mata iko.
"Ka daina fadar wani a gabanka, dazu ma da babu kai shi
ya dauko ni, kawai ka kaddara rayuwa ce ta
'yanci da rashin mafadi...."
Mamaki ya ishe shi, ya juyo yana kallon ita kuma ta maza
ta shiga binciko wayarta a jaka saboda 'karar shigowar
kira, kafin ta gama fito da ita kiran ya katse. Da ta duba
lambar kiran sai ta tarar da 6oyayyar lamba (hidden
number).
Ta shiga juya wayar tana kallo, shi kuma Yusha'u ya sami
sararin magana.
"Ni kike fadawa haka Rumaisa'u?"
Ta yi saurin dagowa ta dube shi ba tare da fuskarta ta
sauya ba. Ta yi saurin dagowa ta dube shi ba tare da
fuskarta ta sauya ba.
"Ban dauki maganata wani cin fuska ba, na fada ne dan
ban ga abin 6oye-6oye ba...

In dai mutum ba ya iya hanzartar da wani akan wani abu
da zuciyarsa wanin ta 'kulla masa, to kai tsaye gara ya yi
abin da ya shiryawa kansa, ya kuma fito da shi
kowa ya gani, Allah basshi duk wanda yake jin an shiga
hakkinsa sai ya fito ya nema".
"Allah Ya ba ki hakuri".
Abin da ya ce mata ke nan, ita ma cikin ko'in kula ta ce.
"Amin".
Ta ciro bututun sauraren magana na kunne (earphone)
daga jakarta tana zurawa a wayarta dan ta ji sakon
muryar Mahaukacin masoyi, wanda ya shigo mata dai-dai
da zuwan Yusha'u kan dutse.
Ammma sai Yusha'un ya katse mata hanzari da tambayar.
"Ina Hamida?"
Ta kuma dagowa ta kalle shi fuskarta babu alamar wasa
ta ce.
"Wace ce haka?"
Cikin bayyana mamaki ya ce. "Hamida nawa kika sani?"
Ta dan d'aure gira ta yi 'kasa da ido.
"Wadda na sani ba mu ta6a lurarta da kai ba, ban san
akwai wata ala'a tsakaninu ba shi yasa na yi mamakin
yadda aka yi ka san da rayuwarta a doron 'kasa".
Ya yi kasa'ke lokacin da zuciyarsa ta fara bugawa,
Rumaisa'u ta sauya matu'ka ba kamar sanin baya
da ya yi mata na rashin kullaci da 'kankantar da laifi ba,
sannan yanzu harshenta ya yi kaifi, zuciyarta ta yi 'kwari
yadda ba ta shakkar fada masa duk wata
magana da ta zo bakinta. Hamida 'yata cikinsa Rumaisa'u
ke keta idonsa ta fada masa wai ba ta san da wata ala'ka a
tsakaninsu ba.
Sai dai dole ya share saboda ya fi kowa sanin dalilin da ya
sa ta fadar hakan.
Dalilin da ba ya son ya tuno bare ya fadi abin da zai sa ita
ta tunatar masa.
Sai ya watsar da wannan maganar ya kamo wata, duk da
a kan Hamidar. "Ya ya jikinta?"
Ta juyo masa da fushi, sai dai ya yi dai-dai da latsa
ma6allin sauraron muryar Mahaukacin Masoyi da ta yi.
-''Kamar kina cikin fushi yau, na dame ki ko?
In kin dauki abin da nake miki damu kar ki dauke shi
zalunci, ko zuciyarki ta raya miki zaluncin ne ki
tunatar da kanki fadin Manzon Allah (S.A.W). 'Kada ku bi
mutane ku ce in sun kyautata ni ma zan kyautata, in sun
yi zalunci ni ma zan yi zalunci...
ku tsaya da 'kafafunku in suka yi zalunci ku ku kyautata".
Ta yi tsuru idonta akan wayar Yusha'u da ke ajiye lokacin
da sa'kon ke maimaita kansa a kunnuwanta. Hakan kuma
ya yi tasirin sauke fushin da ta 'kunso a radadin da zata
yiwa Yusha'u, 'kari a kan sa'kar da zuciyarta ta yi mata na
ta binciki Yusha'u Mahaukacin Masoyi da sa'konninsa.
A 'kagauce ta amsa masa tambayarsa.

"Da sauki". Zai yi wata maganar ta riga shi cikin sar'kewar
murya.
"Me yasa kake damuna da yawan turo sa'konni?
Duk abin da kake son sanar da ni ai gara ka tunkare ni kai
tsaye ka fada min".
Wato ta yi masa basaja ke nan. Ya tare girar da ke
bayyyana mamaki tare da dafe kirji ya ce.
"Ni?
Ai kuwa kin san rubutu ba dabi'ata ba ce, layi biyu na
rubutu akan na yi shi gara na kashe dari biyar a waya
balle na dame ki da wanda zai gundure ki Rumaisa'u".
Ya kare da tausasa murya yana dan kallonta.
Ta yi saurin kawar da kai tana da na sani.
Ta gamsu da ma'anarsa, mawuyacin abu ne ka ganshi
yana rubutu, kai ko karanta sa'ko ba cika yi ba, in ka yi
masa sa'ko ma ka yi a wofi, koda yake ita kanta ma
basirarta ce ta toshe, sakonnin Mahaukacin Masoyi sun yi
kama da na dan leken asiri ko wani mai gani har hanji.
Ta ci gaba da raba hankulanta uku, kan kallon wayarta
sanan ta daga kai ta dubi Yusha'u tarwai, alhalin kuma
zuciyarta ta kwarzaheta da haske mata fuskoki kala-kala
wadanda ta ke zatawa Mahaukacin Masoyi tare da
zuciyoyi iri-iri wadanda ta ke hasaso niyyarsa da
manufarsa a kanta,
wannan ya yi dalilin da har suka 'karaso Kano ba ta
fahimci sabon kundin da Yusha'u ya bude ya fara karata
mata ba, kundin da yake son nuna shi ne wanda ta ke
'karkashin mulkin mallakarsa shekaru kusan uku da suka
gabata ba, ba shi ne wanda kamar a tsohuwar rayuwarsa
ta ke zaton lokacin da aka raba maganganu masu dadi da
taushn furuci an manta da shi ba.... Ba shine kaza ba
shine kaza ba!
Wannan da suke tafe yanzu kamar Yusha'u ne a fuska da
riga kawai, amma ayyuka wani ne daban...
.
Dan Aunty.GORAN DUMA (P 48)
.
.
Lokacin da ta fara barin kunnuwanta su saurare shi sai
zuciyarta ta cika da dokin ta san makasudin wannan
sauyawar, ga6a kawai ta ke jira ta nemi ba'asi, kuma ta
tabbatar masa ita fa ba a sauyata ba, ba a sauya
Rumasa'u daga kasancewarta sickler ba, kuma ba ta
daina laulaye-laulaye ba, sannan ba a kwashe mata zurfin
karatun da yake ganin shi ne tsanar da ya yi mata ba.
Ga6ar da zata nemi ba'asin ta zo dai-dai lokacin da suke
jiran danja a Gadon Kaya kan titin B.U.K zuwa Ibrahim
Taiwo Road, sai dai abubuwa biyu ne suka faru a dai-dai
lokacin, wato Yusha'u ya nuna mata Yahya Guasau Road
ya ce mata.
"Kin ga hanyar gidan da nake gina miki, na san ba zaki so
zama gida daya da kishiya ba..."

Ta ci gaba da raba hankulanta uku, kan kallon wayarta
sanan ta daga kai ta dubi Yusha'u tarwai, alhalin kuma
zuciyarta ta kwarzabe ta dahaske mata fuskoki kala-kala
wadanda ta kezatawa Mahaukacin Masoyi tare da
zuciyoyi iri-iri wadanda ta ke hasaso niyyarsa da
manufarsa akanta, wannan ya yi dalilin da har suka
'karaso Kano ba ta fahimci sabon kundin da Yusha'u
yabude ya fara karata mata ba, kundin da yake sonnuna
shi ne
wanda ta ke 'karkashin mulkin mallakarsa shekaru kusan
uku da suka gabata ba,ba shi ne wanda
kamar a tsohuwar rayuwarsa take zaton lokacin da aka
raba maganganu masu dadi da taushn furuci an manta
da shi ba.... Bashine kaza ba shine kaza ba!
Wannan da suke tafe yanzu kamar Yusha'u ne afuska da
riga kawai, amma ayyuka wanine daban.Lokacin da ta
fara barin kunnuwanta su saurareshi sai zuciyarta ta cika
da dokin ta
san makasudin wannan sauyawar, ga6a kawai ta kejira ta
nemi ba'asi, kuma ta tabbatar masa ita faba a sauyata ba,
ba a sauya Rumasa'u dagakasancewarta sickler ba, kuma
ba ta daina laulaye-laulaye ba, sannan ba a kwashe mata
zurfin karatun da yake ganin shi ne tsanar da
yayi mata ba.Ga6ar da zata nemi ba'asin ta zo dai- dai
lokacinda suke jiran danja a Gadon Kaya kan
titin B.U.Kzuwa Ibrahim Taiwo Road, sai dai abubuwa
biyune suka faru a dai-dai lokacin, wato Yusha'u yanuna
mata Yahya Guasau Road ya ce mata."Kin ga hanyar
gidan da nake gina miki, na san ba zaki so zama gida daya
da kishiya ba...
"Kunnuwanta ba su gama kwashe
maganganunsaba ta dago a fusace ta dube shi, amma sai
aka yirashin sa'a bai san tana yi ba, saboda yana cinikin
faifan C.D, duk da haka sai ta ta6e baki tajuyar da kai
zuwa kallon tagar mota, sai kuma idonta karaf kan wani
matsashi da ke cikin wata Toyota Parado da alamun ya
jima yana 'kuramata ido, kafin ta tantance kalolin
fuskarsa ko dalilin wannan kallon maitar da ya yi mata
Karan Farko A Tsawan Tarihin Rayuwata
Naji Yakamata Nai Shawara A Wasu Lamurana,saikawai
Naga Zuciyata Taza Beki Dan Ki Zama Abokiyar Shawarar
Yushau Yafada Cikin Wata Raunanniyar Murya Da Ruma
Bata Taba Mafarkinjinta Daga
Gareshi Ba Kodayake Ita Bata Cikin Hayyacinta Batamasan
Abinda Yakecewa Ba Ga Badaya Tadinga Waige Waigen
Bayanta Tamkar Zata Tsinke Wuyanta Motocin dasuke
Biyo Bayanta Sukadinga Yimata Gizo Tadinga Ganinsu Duk
Sun Zamemata Toyota Parado Da Alama Game Din Nata
Yanada Yawa Domin Lokacin datake Jin Yakamata Ta Zira
Kai A Tagar Motar Tadinga Gano Baya Sosai A Sannan
Wata Kalmar Yushau Tadaki Dodon
Kunnenta,so Nake Na Sallami Sumoli,amma Ina Tsoron

Alhji Dan Allah Kibani Shawara Ruma Tadubeshi Da Sauri
Tana Neman Tafarka Daga Wannan Rikitaccen Mafarkin
Ido Biyun Daya Fizgeta
Ba Bu Shiri Can Ga Mahaukacin Masoyi Nan Kuma Ga
Mahaukacin Tunani Da Zartar Da Hukunci Cikin
Haukansa,saboda Dokinsan Ruma Ta Amsa Masa
Tambayar Sa Ya Bita Da Kallo Ta Hana A Kunna A.C
Gashikuma Tana Zufa Waimeke Faruwane?
Da Yushau Ya CigaBa Da Kallanta Da Kyau Ma Saiya Ji
Wata Irin Shakkarta Ta Mamaye Shi Nantake
Bakinta Na Rawa Ta Ce Da Akame?Inatakira Kina Watsawa
Juji,,
tayi Mugun Zuwa Wuya Amma Hakurarriyar Muryarta Ta
Taka Rawa Wajen Boye Wa Duk Da Kuwa Katse Mutum
Inyana Magana Alama Ce Daga Alamomin Nuna
Fushi,wadannan Hirarrakin Naka Waikana Ganin Sunada
Amsa Agurina?
Ya Jahilce Ta Da Ido Amma Baice Komaiba Har Ita Ce
Datakejin In Anbar Maganar Ahaka An Cida
Guminta,takara Zunkudo Maganar Cikin Rauni Da Rawar
Harshe,kana Laakari Kuwa Da Maganganun Da Suke
Fitowa Bakinka Yau Da
Kunnen Wadda Suke Zuwa?Rumaisau Fa! Sikila Nan Mai
Ririta Ciwo Wadda Tai Zurfin Karatu Ba Pre Boko Ba,
Bazawararnan Mara Daraja Wadda Tumatirin Gwangwani
Yafita Kima
Fuskar Yushau Na Nuna Hakikanin Gaskiyar Sa Kidaina
Dawo Da Bara Bana Ruma Idankika Duba Tarin Manyan
Sahabbai Duk Zaki Tarar Da Manyan Kafuraine Suka Karbi
Hasken Muslunci Badaidaine Ba Don Mutum Yai Wata
Barna A Baya Kuma Yadawo Yagane Kuskurensa Ace Sai
An Dauwama Masa Waccen
Ta Rausayar Dakanta Alamar Mamaki Lallai Kayi Kwatance
Mai Kyau Yaya Saidai Kamanta Musulunci Gaskiya Ce
Kwaya Daya Tal Wadda Duk Juyinka Haka Zaka Tarar Da
Ita Amma Musulmi Kuma
Mutane Sun Mallaki Hali Da Halitta Wanda Suke Iya Sauya
Wani Su Bar Wani Har Suje Kabari dashi Kamar
Kai Kenan Daka Sauya Hali Dagayimin Kallan Wata Yar Ta
Adda Zuwa Mata Mai Daraja Wadda Sam Ma Bataimin
Kyau Ba,amma Niban Sauya Halitta Ta Kasancewata Sikila
Ba,kuma Ilimin Boko Danasamu Ya Sha Kwanyata Kenan
Har Mutuwata Lallaikenan Inkai Ansauyaka Da Alamar
Niba A Sauyani Ba,ko Ma Kila Baza Sauya Dinba,ya Bude
Baki Zaitareta Ta
Dakatarda Shi Jinan Yaya Yushau Ba A Sauya Ruma Sikila
Ba Saikuma Akasami Hamida Sikila Wakwafinta Kana Iya
Bude Kwanji Mu Ga Sauyinta kAkanta Kafin Nina Ga Ko
Dagasken Ka Sauya?
Ba Lallai Sai Zaka Amfanar Da Abu Zaka Jajirce Nuna
Akansa Ka Sauya Ba,
yanzu Kam Jikinshi Yai Sanyi Kalau,amma Wani Fushi Da

Makakin Kalmar Ji Nan,datake Tabbatar Masa Bai Sauya
Din Ba Da Gaske Hakan Ne Yasanya Yajima Bai Ce Komai
Ba Naga Na Tambayeki Hamida Kisa Tambayata A
Kwandan Shara Nikuma Na Dauka Idan Dai Ka Sauya Ba
Ka Bukatar Tambayata,
idan Fa Har Dagaske Matsayin Mu Dakai Dayane A Wajen
Hamidar Bazan Iya Kirga Sau Nawa Nake Neman Hamida
Naganiba,amma Ba Tambayar Kowa Ita Ba,taimasa
Maganarne A Kagauce Saboda Gajiya Da Tambayar Sa,
yushau Yanaganin Rayuwa Da Ita Ce
Farincikinsa Zai Kammala,ya Sheka Smoli Ya Tarar Ba Bu
Kwaya Sainake Ganin Baikamata Ba,ki
Katseni Akan Matsalar Cikingidana Danakeson Sanar Miki
Zan Warwaremiki Wacece Sumayya
Tana Bin Wata Toyota Tai Gidan Murtala Su Kuma Suka
Karkata Suka Shiga Titin Gandun Albasa Saitaji Zuciyarta
Ta Cika Da Mugun Fushi Ta Ce Ashe Lokacinda Zaka Auri
Sumoli Danikai Shawara?
Kodayake Bakai Shawara Dani Ba Kayi Aikin Dayafi
Shawarar Kasakeni Domin Ka Aureta,kabarnida Ciki
Batare Daka Taba Waiwayata Lfyata Da Ta Abinda
Kecikina Ba,dukda Dai An Matsa Maka Daukar Nauyi Na
Haifi Abin Cikina Irina Masu Matukar Rauni
Wadanda Bankira Hai Huwar Su Abin Burgewa
Ba,ammdai A Matsayinsu ammadai A Matsayinsu Na
Tsatso Kamarkoba A Godemin Haihuwar Su Bayakamata
A Godewa Allah Ta Hanyar Kuladasu Da Kuma Tausayinsu
Har Allah Yai Ikonsa Akan Ahmad Kuma Me?Hamida Ma
Tabi Sahuna Nazama Tumatirin Gwangwani,wane Irin
Sonkai Ne Wannan Daza A Ce Mu Wannan Iyalin Masu
Kama Da Abin Kyama Zaka Kawo Wani Abu Game Da
Matar Dakayi Man Wanna Tozarcine Dominta,ta Girgiza
Kai Cikin Tsananin Takaici,bazan Iya Zagi Bane Yaya
Yushau Amma Tabbas Yaudana Zageka,
idan Zaki Zageni Kiji Sanyi Ki Gwadamana Ruma
Ammadai ki Saurareni Dakinji Cewa Badan
Sumoli Nai Laifindakikejin Yai Girman Dazaki Kasa Yafewa
Ila Dai Kuskuren Fahimta Batasan Lokacindata Maka Masa
Harara Ba,taso Tai Tsaki Tashareshi Banida Bukatar Ji,ka
Bar Abinka Zaimaka Amfani Nima Ka Barni Dan Allah Inji
Da Abinda Yadameni,nasan Abindake Damunki Ai,da
Sauri Tajuyo Ta Dubeshi Kuma Daidai Lokacinne Yahau
Layin Gidansu Daga Gefensu Kuma Ga Toyotar Nan Data
Hargitsa Ruma Nafitowa Daga Titin Gidansu Yushau
Yanunamata Yana Dariya,wai Ba Wacen Motarbane Naga
Ta Gigitakiba ?...
.
Dan Aunty
GORAN DUMA (P 49)
,
,
Dakin Nemi Shawarata Akanta Kila Da Ina Da Abincewa

Rudani Da Tashin Hankali Take Kallan Yushau Tana Kuma
Waiwayen Motar Harta BaCe maganinta,,shikuma Yushau
Yaita Kyalkayata Mata Dariya Har Suka Karasa Giada
Bataimasa Magana Ba, Taiwanka Tai Sallah Da Cin Abinci
Duk Cikin Alhini Tanemi Guri Musamman Ta Zauna Dantai
Tunanikan Mahaukacin Masoyi Takasa Lamarin Nan
Mahaukacin Masoyi Yafara Ruda Ta Bayan Rashin Auwal
datai A Duniya Nan Ta Cire Rai Akwai Wani Abin Rudu A
Cikinta,amma Halittar Mahaukacin Masoyi Naneman Ta
Tsoratata Indai
Dan Ganine Todazu Taganshi Kumadaga Ganin Dataimasa
Ya Zuwa Yanzu Bata Taba Rudewa A
Lamuranta Irin Na Tsukun Lokacin Nan Ba,infa Har da
gaskene Ba Plan Din Yushau Bane,taga Motar Su A Layinsu
Meyazo Yi Gidansu?
Menene Manufar Sa Akanta?
Menene Alakar Sa Da Yushau? Kawai Saitafada Watsup
Dan Rage Kewa Da Tunani Tafara Rage Kewar Da Sakon
Friends Data Tadda Sun Turo Mata Kwatsam Sai
Hannunta Yafada Kansakon
Mahaukacin Masoyi Wanda Takejin Tagoge Lambar Sa
Dake Layinta Na M.T.N Ta Adana A Layinta Na Etisalat
Wanda Tahau Watsup Dashi Lambar Tasama Waddatake
Kaddarawa Cewa Matacciya Ce Agurinta Tunda Ko Ankira
Bata Shiga Duk Da Kuwa Akwai
Lokutan datake Leka Blacklis ta Ta Tarar An Zare
Lambar,kuma Wannan ke Kara Bata Tabbacin
Mahaukacin Masoyi Aljanine Ba Mutumba Tunda Dai Ita
Ke Rataye Lambar Amma Sai A Sauketa Duk
Jikinta Yadau Rawa Kasancewar Sakon Nasa Biyune
Akwaina Murya Akwai Na Hoto Tanadubawa Saita Tadda
Dandasheshiyar Fulawa
Da Wasu Kalolin Baloon Sun Zagaye Ta Daga Kasa Kuma
Cikin Wani Rubutu Mai Kyau An Rubuta HAPPY BIRTHDAY
MY LOVE WISHING U MANY MORE BLESSED RETURNS OF
THE DAY,gabanta Yai Mugun Yankewa Yafadi Cikin Rawar
Jiki Tafara Jera Yatsun
Hannunta Tana Kirgawa Kamar Sune Zasu Tabbatar Mata
Da Cewa Yaufa Sha Shida Ga Watan Febrairu Kuma
Ayaudin Ne Take Cika Shekaru Ashirin Da Takwas Cif A
Duniya Ita Bata Tuna Hakanba Saida
Mahaukacin Masoyi Ne Ya Tunamata TabbaCin Yasanta
Dayawa,kila Sanin Ma Da Bataima Kanta Ba Ta Matsa
Sakon Murya Taji Ance Rumaisau Ance Abinda Yawuce
Tarihine Abinda Baizo Ga Gaibune,amma Yau Tawa Ce
Kuma A Cikinta Nake Lallai Masu Wannan Hikimar Sunyi
Gaskiya Dan Shekara Ashirinda Takwas Dinki Na Baya
Basan Dasuba Sai Kwatsam Na Tsince Su Yau A Cikin
Tarihina Danaki Dayake Yaudin Tawa Ce Har
Gani Cikin Masu Farincikin Tarihinki,abin Mamaki Na Cika
Nawa Shekarun Ban Tuna Ba,amma Naki Tun Sha Biyun
Daren Jiya Suka Fado Min Duk Da Kuwa Bana Muhallina

Tabbas Ba Bu Karya Na Cancanci
Zama Mahaukaci A Soyayyarki Inafatan Shekarun
Gaibunki Duk Tsawansu Muyi Su Tare,dafatan Kinje Gida
Kalau?
Ta Saurari Sakon Yakai Sau Ashirin Mamaki Take Ko
Fargaba?
Itakanta Tarasa Daya Amma dayake Kamar Mahaukacin
Masoyi Natare Da Abinda Zuciyarta Ke Sakawa Kawai
Saigashi Ya
Zabar mata Fargaba Inda Wani Gajeran Sako Nasa Yafado
Mata KISHIRYA DAGA YANZU ZUWA KO WANE LOKACI
ZAKI IYA KARBAR SAKONA,
firgici Tafara Bin Dakin Da Kallo Cikin Mugun Dauke
Numfashi Babu
Abindake Motsi A Dakin Amma Saitadinga Jin Lallai Ba
Itakadaine Acikinsa Ba Tadinga Adduoi Saiga
Mubarak Yashigo Dauke Da Katuwar Leda Tai Sauri Ta
Gyara Fuskarta Suka dubi Juna Suna
Murmushi,yajiye Yana Bata Bayani Dazu Dabda Zaku
Shigo Kikai Bako Bako?
Mubarak Ya Bita Da Kallo Saboda Ganin Firgicewardatai
Anti Bako Mana Meyafaru?
Kokin sanshine?
Ta Girgizakai Dasauri Ga Sako Nan Ya Bayar A Baki
Waiyana Tayaki Murnar Zagayowar Haihuwarki Baki Bude
Take Kallan Mubarak Baki Na Rawa Tadubi Kayan
Tadubeshi bai Fadi Sunansa ba,kuma Daga Inayake?
Yafada Sunansa Ashir Kuma Tarauni Yake In aka fadamiki
Haka Zaki Gane Batagano Komaiba Face Mahaukacin
Masoyi Yazo Ya Bide Iyayanta Ta Wannan Sigar Kamar
Yadda Yake Gasa Nata Lissafin
Da Sauri Tadaga Ledarta Jirkice Shi A Gefe Saitatuna Ya Ce
Kishirya daga Yanzu Zuwa Kowani Lokaci Zaki Karbi Sako
na baBu Abinda Ledar Takunsa SaitarkaCen Kayan
Kwalliya Masu Tsada Tare Da Turarurruka haka Tadinga
Karanta Katutukan Happy Birthday Wanda Sunkai Kala
Ashirin Batare Da Kwakwalwarta Na Fassara Mata
Ma,anar Suba Ta Watsar Cikin Tsananin Rudani Kana Gida
Lokacinda Yazo?
Eh Ina Gida Kaganshi?
Kaga Motar Daya Hawo?
Mubarak Ma Yafara Rudewa Dan Baita Ba Ganinta
Cikinrudani Haka Ba Dawowata Kenan Ya Shigo A Motar
Sa Toyota Wankan Tarwada Ne Yana Ta Tsatsaman Jiki
Yana Da Fara A Yanasan Hakadai Yaita Wassafa Mata
Shi,tuni Ruma Takasa Magana Saidai Binsa Tai Da Ido
Saima Yabata Wani Mugun
Tausayi Saboda Yana Tunkahon Yai Hira Da Aljani
Kinganeshi?
Ka Kalli Yatsun Kafar Sa?
A,a Na Tabbatar Daka Kalla Saikaga Kofato
Kofato Aunty?

Ta Ce E,h Irin Na Doki Ba Dan Inada Yakini Ashir Ba
Mutum bane Tagama Hada Kayan Taware Katunan
Tamika Wa Mubarak Ledar Dan Girman Allah Fita Da
Kayan Nan Ka Sadakar Mubarak Yadubeta Ya Dubi Kayan
A Tsorace Waimeyasa Kika Ce Aljanine?
Ta Ajiye Ledar Ta Turamasa Wayoyinta, Ta Cemasa
Dazaka Shiga Wayata Duk Social Netwok Danake Yi Zaka
Tarar Da Manyan Alajabinsa Dake Nuni Kan Abotar
Kan Abotar Sa Da Zuciyata Waddayake Sanin Duk
Abindayake Raya Wani Lokacin Har Da Abinda
Gangar Jikin Ke Aiwatarwa Kamar Daiyanzu Taimasa
Bayanin Komai Adaddafe Yakaranta Yayarfar Da Wayar
Tamkar Wanda Yarfar Da Maciji Yamike Yana Goge Tafin
Hannunsa Da Riga Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun,anti
Tun Yaushe
Hakanke Faruwa?
Munshiga Uku Gashi Ya Ce Gobe Zaidawo Hakayace?
Ya Ce Eh Ammake Dawani Idan Zaki Ganshi?
Nima Da Tsautsayi Yahadamu Ina Danasani Ruma Ta
Tuntsire Da Dariya Kaifa Sokone Mubarak Saika Ce Ba
namiji Ba Tabbas Nikam Ko
Ifiritine Inasan Ganinsa,
Tunsanyin Safyar Mubarak Yadaka Sammako Ya Bar
Gidan Gashi Alhji Da Hajiya Basanan Suna Egypt Sai Gobe
Zasu Dawo Dan Tun Adaran Mubarak Baiyi Barcin Kirkiba
Babu Irin Shakkar Da Wasiwasin Da Ruma Bataiba A
Safiyar Yau Dawani Alajabin Nasa Tatashi Inda Tataradda
Makudan Kudi Yaimata Transfer Alayinta Na M.T.N Har
Naira Dubu Ishirin,sannan Ya Rubuta To Gashinan Agaisa
Da 'yanuwa Masu Taya Murna Aljanu Ma Sunsan Takan
Waya Da Internet Harma Da Yadda a Ke Kyautata
Soyayyarsa Ta Hanyar
Kyautar Kudi A Waya A Tsawan Ranar Ta Saurari Suratul
Bakara Yakai Sau Biyar Karfe Hudu Da Rabi
Daidai Neman Isonsa Yakaraso Mata Daka Ta Hanyar
Mairo Maimusu Wanke Wanke Nandanan Ta Tsorata Fiye
Da Mintuna Talatin Tana Safa Da Marwa Saiga Mairo Uwar
dakina Kin Manta Da Bakonne?
Haba Uwardakina Adinga Daurewa Ana Kara Wa Zuciya
Dangana,tajuya Idanta Cike Da Hawaye
Kingano Min Yatsun Kafar Sa?Yatsun Ne Kokuma Kofato?
Wanne Irin Kofato?
Yo Ni Inama Zanga Kafar Sa Akwai Safa Meyakawo
Wannan Maganar?
Nifa Dukma Kinfir Gitani Nidah Dazaki Iya Dakingano Min
Yatsun Komai A Jikin Mairo Rawa Yake Ni Bazan Iya Ba
Wallahi Har Gudawa Na Neman Tsinkemin, Duk Da
Halinda Ruma Keciki Na Rudewa Saida Dariya Yaso
Kwacemata Tadauki Hijabi Ta Doshi Kofa Tana Cewa Ni
Zaniya Bara Naje,
Haka Tadinga Kalimatush Shahada Gwamma Ma Tazarce
Inda Masoyinta Auwal Yaketake Fatan Sui Rayuwa A

Aljannah Maimakon Tai Sallama Kawai Sai Ta Rangada
Kalmar Shahada Tafada Dakin
Wanda Ke Zaune A Dakin Yadago A Firgice Yadubeta Cike
Damamaki,itama Ta Tsaya Cak Tana Kallansa Ba Bu
Kakkautawa Cike Da nata Mamakin Shiya kasa Magana
Itakuma Ta Bige Da Nuna Shida
Hannu Tana Kokarin Magana Amma Takasa Ranki Yadade
Fuskar Sa Cike Da Faraa Har Kumatunsa Suka Loba
Wanda Suke Nunawa Ruma Zallar Kuruciyar Sa,ta Isa
Kujera Ta Zauna Tana Kokarin dawo Wa Zuciyarta Doka
Da Oda Batasan Yaudarar Kanta Bare Ta Cutu Kota Cutar
Dawani Amma Wannan Tabbas Bashine Mahaukacin
Masoyiba Ta Cemasa Ashir Manyan Gari,ya Ce
Hakadai Kikecewa Ya za ai muzama Hakan Kiduba Fa
Shanyar Dakikaimin Har Na Tsawan Kusan Awa Daya....
.
Ayi hakuri na rashin ganin post jiya, en wasu abune suka
shige min gaba, da patan za ayi min uzuri.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 50)
.
.
Kamanta Dan Allah Ya faru ne Bisa Akasi Wai Da Gaske
Kaine Bakon Dayazo Jiya Har Ya Bar Sako Ya Ce Eh Wani
Abu Ne Yafaru?
Ta Ce A.Ah Da Akemin Kwatancenka An Ce Kazoda Toyota
Shine Nake Ga Aikamar Ma Mun Hadu A Gadon Kaya
Jiyan,
kai Banibane,ainafi Wata Banhau Wannan Titinba,anzo
Gurin Ruma Tafada A Zuciyarta Kaine Katuromin Sako?
Ni Ina Naga Lambar Wayarki Alhalin Kinhana,waimaduk
Meyakawo Wannan Tuhume Tuhumen Daga Zuwana?
To Inakasan Ranar Birthday di NA? Haka Dai Sukai Ta Hira
Har Saida Ruma Tagamsu Ba Ashir ne Mahaukin Masoyi
ba Abin Mamaki Suna Zaune Sai Ga Shi Gowar Sakon
Mahaukacin Masoyi,ya Cemata Kamar Daikina Cikin Wani
Uzuri
Ko Mudaga Tattaunawar Mu Sai Wani Lokaci Nazo
Datarin Burika Akanki Wanda Nake Wafatan Su Sami
Matsuguni A Zuciyarki Da Duniyarki
Ta Cemasa Banasan In Wahalar Da Zuciya Ko Gangan Jikin
datake Jin Kaunata Ashir Tun Ranarnan Danaga Baka
Gamsu Da Abinda Nagayamaka Ba Ba Waka Naso
Namaka Ba Dana Cemaka Banida Wata Daraja Da Kamar
Kai Zaka soni Kuma Nima Ban Shirya Son Kamarka Ba
Hakadai Ashir Yaita Kokarin Kwatanta Mata Irin San
Dayakemata Itakuma Ruma
Tadinga Gayamasa Illar Dake Tattare Da Aurenta Hardai
Sukai Sallama.
Wanene Ashir?
Kwanakin Bayadasuka Wuce Kafin Mahaukacin Masoyi
Yafara Nasa Almarar Ruma Tai Shirin Zuwa Abuja Da

Niyyar Jifan Tsuntsu Uku Da Dutse Daya Wato Ziyarar
Ofishin Jaridarta Aminiya,dakuma Gaida Iyayanta Da
Yayarta Balaraba Sai Kuma Uwa Uba Datake Boyewa
Aranta Kadai Wato Dora Sansanyar Kallo Kan Sanyin
Idaonta Wato Hamida Anahaka Sai Yayarta Takirata A
Waya Taroki Alfarmar Da Taje Gidankawarta Fatima
Matar
Abu Turab Wandake Tarauni Takarbo Mata Turarurruka
Datakawo Mata Daga Dubai,fatima Ba Bakuwarta Ba
Ce,dayamma Tadauki Mubarak Yarakata Amma Suna
Zuwa Ko Gidan Bai Shiga Ba Yahaumata Magiyar Taimasa
Uzuri Yana Da Kallon Kwallo Yadawo Bayan Sallar
Magariba Su Tafi,tana shiGa Fatima Tatare Da Murna Suka
Gaisa Suna Zaune Sai Ga Baby Hindatu Kyakyawa Kamar
Uwatta Ruma Takarbeta Tana Tunanin Tata Gudan Jinin
tare Datakaicin Yushau Wanda Ya Nesanta Su Da Juna
Lokacin Da Abu Turab Yazo Ruma Taga Ririta Hindatu
Gun Mahaifinta Saida Kwalla Yazubo Mata Ta Ce Zata Tafi
Fatima Taiwa Abdullahi Kallon Wutsiyar Ido Kinga Badan
Wannan Man Dinba Ma Kallon Ne Zai Dauke Masa Hankali
Ba Dakawai
Inkingama Saimu Kai Baikamata Muci Amanar Momiba
Nanda Magariba Saimu Kaita Har Gida Haka Tazauna
Dasu inda Ko Minti Goma Ba Ai Ba,sai Ga Bakonsu Ashir
Kanin Abu Turab Ubansu Daya,
Ashir Yaita Kallon Ruma Tasaci Zuciyar Sa Ya Ce Aunty
Hakadai Yafurta Zuciyar Sa Inda Ruma Ta Cewa Fati Da
Abu Turab Kundai sanni Datarin Matsaloli Hakadai Har
Sukai Sallama Ruma Bata Amince Da Bukatar Ashir Ba
Sukakaita Gida, Mairo Tashigo Falon Tasami Ta A Tsaye
Takurawa Kofar Fita Daga
Falon Ido,a Rikice Mairo Ta Ce,yaya Dai?7
da Sannan Ta tunada Yadda Sukai Da Mero,ruma Ta
Tuntsire Da Darya, Yatafi Ashe Mutumne Ba Wanda
Nazata Ba Kanin Mijin Anti Fatine Kawar Anti Balaraba
Anmmadai Kindau Hakki Uwardakina Tsuguno Na Uku Na
Rantse Mubarak Ma Sau Uku Yana Matsamin In Lekaki
Hankali Atashe Dakyar Nai Shahada Nataho Ruma Kam
Dariyatake Sai Bayanfitan Mairone Ta Tuna Dasakon
Mahaukacin Masoyi Saitatafi Kuryardaki Saida Ta
Tabbatar Taima Dakin Adduoin Tsari Daga Shaidanu
kuma Ta Ceyakamata In Nemi Naurar Satar Bayanai
Adakinta Ko Kuma A Zuciyarki Ba Zuciyarta Ta Rayamata
Haka Innalhllahi Wa Inna Ilai Hirajiun Tadinga Furtawa
INADA TSANANIN KISHI RUMA BAZAKIYIMIN GATANDA
ZA A CE DON NIKADAI A KA HALLICCEKIBA?
WANNAN Kashedine Ko Gargadi Tatambayi Kanta Sakon
Ya Isone Daidai Lokacinda Take Zance Da
Ashir Kenan Mahaukacin Masoyi Ya Ganta Da Kishiyarsa
Karon Farko Kenan Datun Bullowar Mahaukacin Masoyi
Rayuwarta Taji Kwalla Ta Cika Mata Ido Anjima Kadan Ma
Sai Ga Kuka Shabeshabe Lallai Ba Kowani Abu Kebata

Kuka Ba Musamman Wanda Takeson Nuna Jarumtar
Karbar Kaddara Amma Tabbas Mahaukacin Masoyi Yafara
Girman Da Jarumtakarta Zata Gaza Boye Sirrinsa Ita Kadai
Ko Kuma Kokarin Samowa Kai Mafita Ita
Kadai,doletazabi Daya Ciki Kodah Ta Runtse Zuciyarta
Mahaukacin Masoyi Yadaina Hango Ciki Ko Kuma Zuciyar
Tata Ta Runtse Idanuwanta Masu Mamakantar Da Ita
Lamarin Mahaukacin Masoyi Ko Girmama Su Yadda Suke
Firgita Zuciyar,kamar Na Biyu Ta Dauka Ta Goge
Hawayenta A Fili Kuma Ta Furta Cikin Sarkewar Murya Kai
Baka Dasuna?
Sai Almajanuni A Soyayya?
Lallai Kanada Kishin Abindakake Da Wanda Yafika
Kishinsa Kakeson
Abinda Yake Da Wanda Yafika Sonsa Wato Ni!
Shin Zaka Iya Son Gawa?
Ruhin Soyayyata Fankone Bazai
Amfaneka Da Komai Ba Gara Ka Adana Haukarka Kozai
Amfaneka Gaba
Tana Ta jira Taji Sako Sai Ga Wata Gajeriyar Sako BAYAN
HAUKA SO NA MAKAHONE,SHARAFINSA YAKE SHA
BATARE DA BUKATAR RADDI BA,INASONKI,KARKI MANTA
DA WANNAN
Nantake Kwakwalwarta Ta Tsaya Da Aiki Cak Komai A Tare
Da Ita Ya Koma Sifiri Kafin A Guje Su Harba Can Baya
Tuno Mata Da Kalmar Dako Daza A Ce Katondin Benelin
Ta Kwankwada Bazatakasa Tuna Daga
Wanda Ta Taba Fito Mata Ba Danko Sakon Mahaukacin
Masoyi Bashida Bambanci Da Kalmar Datashiga
Tsakaninta Ta Karshe Da Masoyinta
Auwal,to Ina Mahaukacin Masoyi Ya Samota?
Data Rasa Amsa Saitakara GiGicewa Cikin Rudu Tamike Ta
Garkama Wa Kofar Dakinta Mukulli Tanemi Guri Na
Musamman Ta Zauna Tafara Gurzar Kukan Rashin Auwal
A Madadin Kai Tsaye Tazaci Kukan Haukan Da
Mahaukacin Masoyi Keneman Zozamatane,tadade
Dasanin Tanason Auwal Kamar Yadda Tajima Da Sanin
Asarar Data Tafka Na Rashin Auwal Wanda Yatanada Mata
Ita Da Iyalanta Duk Wani Farinciki Da Hawayen Share
Kuka,kece Farincikina,don Ki Haifi 'ya'ya Irinki Zantanade
Su Da Hakurina Da Juriyata Dakuma Tattalin Aljihuna
Iyakar Iyawata Inada Wannan Burin A Raina Na Kuma
Niyyaceshi Wasudaga Cikin Alkawuran Auwal Kenan
Aranar Dazaibar Duniya
Ta Zabga Asarar Wannan Alwashi Da Alkawarinsa Ita Da
'ya'yanta Yauga Wani Ibtilainda Auwal
Baitaba Hasaso Mata Ba Ya fada mata Duk Wannan Gibine
Daga Cikin Manyan Gibinan Da Rashin Auwal Ya
Haifarmata Domin Idan Yana Duniya Ko Shaidani Sai Yaji
Kunyar Keta Idon Auwal Yazo Mata Da Rudu,mahaukacin
Masoyi Yasami Rayuwarta Cikin Rashin Gata shi Yasa Mi
Sararin Yimata Wasa Mai Saurin Tafiyar Da

Numfashi,amma Menene Hadinsa
Da Maganganu Irin Na Auwal? Tafikowa Sanin Auwal Ya
Mutu Itamusulma Ce Dake Da Imani Duk
Wanda Yamutu Yatafi Kenan Bare Ta Tafi Kan Kirkirar
Musu Tsammanin Akwai Fatalwa Haka Ta Ci Gaba Da Kuka
Da Tsora Ta Aranta Kuma Tanasan Sanin Shin Waye
Mahaukacin Masoyi?
3-2-2013
Takomawa Dabiarta Ta Baya Kauracewa Wayoyinta Tare
Da Kauracewa Sakonni Daga Nakan Layin Wayarta Har
Gaba Daga Jakar Sakkonninta Na Social Network
Inkadauke E-mail Dinta Wanda Batada Damarjuya Baya
Kodake Ma Satinta Biyu A Kwance Shikansa E-mail Din
Shigar Sauri Take Mai Idanta Yasha Gane Mata Na
Mahaukacin Masoyi Amma Saita Share Tawuce
Kaurardataiwa Social Netork Shine Gina Katanga
Tsakaninta Da Makaranta Shafinta Na Jarida Musamman
Dake Satin Daya Gabata Tai Rubutune Dan Gida Wato Kan
Mutane Irinta Sickler Amma Saboda GanaWa Kanta
Sukuni A Dukkan Kafar Da
Sakonsu Zai Risketa Saibata Sami Wasu Ra,ayoyin
Makaranta Sosai Ba,saboda Haka Yau Tadauki Kafa
Zuwa Gidan Waya Debo Wasiku Saidai Kash Guda Daya
Kawai Ta Tarar Ta Juyo Gida Tanashigowa
Gidanta Cikaro Da Motar Yushau Tashi Ga Gida A
Tsammaninta Zata Taradda Shi Gaban Hajiya A
Durkushe Kamar Yanda Ta Saba Ganinsa Idanyazo Gidan
Hajiyar kuma Nazaune Tana Gyaran Farce
Fuskarta Ba Bu Annuri Gakuna Sumoli Matar Yushau
Idanta A Talabijin Hajiya taimata Sannuda
Dawowa Da Fara'arta Sumoli Kuma Ta Tsurawa Ruma
Idon Danganin Tagano Muninta Itakuma Ruma Nata
Kallon Kan Sumoli Uwar Eye Shadow Allah Yaimata Sansa
Saika Ce Wadda Aljani Ya Aura.....
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 51)
.
.
Ta kuma iya baza Turare Tamkar Mai Shirin Shiga Turaka,
adan dogashe Ruma Tazauna Hannun
Kujera Aka Gaisa Sannan Tamike Zata wuce Ciki Yushau
Yayafito Da Zance Nizanfara Baki Albishir
Rumaisau Atika Ta Haihu Dazun Nan Da Sauri Hajiya Da
Sumoli Sukaimasa Wani Irin Kallo Sumoli Na Tsarguwa
Da Tuhuma Hajiya Na Ganin Kamar Abinda yayima
Baimasa Kyau Ba,itakanta Ruma
Saitarasa Da Bakinda zata Amsa Ikon Allah Ashe Abinyazo
Jiyannan Fa Muka Hadu Tana Tafiya Kafarta Na Hardewa
Take Maganar Hartakule Inda Ta Bar Yushau Da Bin Gurin
Da Ta Bace Da Kallo Tana Shiga Daki Ta Lalubo Wayarta
Cikin Watsar Da Fargaba Ta Ari Farinciki Ta Yabawa

Zuciyarta Tana Lalubar Atika Sai Ga Atika Taturo Mata
Sako
Bayantagaji Dakiran Wayarta Daidai lokacin da take
Kokarin Bude Sakon Atika Wani Sakon Yafado Cikin Akasi
Ta Bude Shi Batare Data Shirya Ba, Wato
Sakon Mahaukacin Masoyi,
INADA YAKININ ZAKIN BAKI YA RUDARKI AMMA
HAUSAWA SUNCE DUKA YAU,DUKA GOBE,SHIKESA
BAKIN BA'AUZINI TAWAYE,SABODA HAKA NAKASA
NATSUWA AKAN WANDA NAKIRA YANA FARAUTAR
ZUCIYARKI ALHALIN BAIFINI SONKI BA KIBI A HANKALI,
MAHAUKACIN MASOYI
karon Farko Da Sakon Mahaukacin Masoyi Ya Bata Dariya
Itama Bata Hakikance Dalilin Dariyarba.Kawaidai Tajita
Tanayine,afili Ta Ce Wannan Halittar Fa Bashida Matsala
Ga Dukkan Alamu ni yakeson Gadarwa Matsalar,ana Ga
Yaki Yana Ga Kura Tanata Faman dariya Ta kira Atika
Sukai Shewar Murnar Su Nasamun Karuwar Atika,
Taimata Tsegumin da Aka Saba Ke Mutanenkifa Sunkawo
Min Ziyara Suka Tarar Anyi Haihuwar,suwafa?Shagonki Da
Pre-bokonsa Mana
Yanzu Tagama Yimana Feleke Sukawuce Zuwanan Gidan
Ruma Tai Murmushin Yake,ai Har Sunzu Bangane
Wadanda Kikenufi Bane,ruma Kunyar Kanta Takeji Idanta
Shiga Aka Zagi Sumoli Da Ita
Duk Yadda Sumoli Takai Ga Mugun Hali Daitafita Domin
Ita Yushau Yaso Harya saketa Akanta Kuma
Garunan Shekaru Kusan Uku Suna Zaune Ba Ajikansu
Sabanin Ita Da Shekara Dayama Suka Kasa
Hadawa Tare,atika Ta Ce Tasami Su Hafsat Anan Sabodata
Kawomin Lesunan Nanda Muke Maganar Mui Ankonsu
Ranar Suna Ai In Fadamiki Sumoli Nazuwa Takwashi Uku
Wai Itama Zatai, hafsat Suna Tafya Ta Zube nata Nan Ta
barminsu Wai Indai Sumoli Zatai Ankon Ita Wallahi
Tafasa,suka Fashe Da Dariya Ruma Ta Ce Dandai Hafsat
Taki Karbar Shawaratane Amma Tuni Nafadamata
Tadaina
Ganin Bakin Wannan Iyalin Ita Take Dauka Ta Wata Tsiyar
Shi Yasa Da Yaya Yushau Yaki Rayuwa dani
Take Ganin Bakinsa Amma Har Ga Allah Nasan Tuni Ni Ba
Wata Tsiya Ba Ce Dukwanda Ma Zai Aureni
Alfarma Yamin Wanda Kuwa Yaga Bazai Iya Hakurin Yimin
Alfarmar Ba Wallahi Baikamata Aga Laifinsa
Ba Atika Ta Ce Aike Matsalarki Kenan Daga Anfara Magana
Saiki Kwaso Wa Mutane Kayan Haushi,kinga Ni Sai Anjima
Ni Da Baby Muna Zuba Idan Ganinki Daga Nan Zuwa
Gobe Nasankemai Hajiya Idankin Zakifito Yanzu Sai
Anyimiki Zancen Zama Ki Huta,
"Dan Bani Da miji ne Ma kike Sa Ran Zanfito Yanzu In
Taho Gidanki Itama Ruma Ta tareta Da Zolaya Atika Ta Ce
Ina kika Kai Mahaukacin Masoyi?
Ruma Na Sauke Wayar Ta Zauna Kan Kujera Kuncinta Har

Yanzu Murmushi,tarasa Dalilin Jin Farin cikinta Da Yawa
Irin Na Daidai Wannan Lokaci Dajin ba Abu Daya Ne
Kawai Ya Faranta Mata Raiba,wato Haihuwar Atika Sakon
Mahaukacin Masoyi Ma daya sanyata Dariya Farinciki Ba
Tashiga
Laluben Zuciyarta Don Nemo Dalilin Farinciki Sakon Nasa
Tajima Suna Tirzawa Ita Da Zuciyar Tata
Sannan Suka Yanke Hukuncin Cewa Sakon Masoyi Yana
Nuna Tsantsar Kauna Gareta A Kowanne Lokaci A
Matsayinta Na Ba Kowan Kowa Ba Lallai Kowace Irin
Halitta Ce Mahaukacin Masoyi Tabbas Masoyine Bata
Shakkar Cewa Inbata Fara Shakuwa Da Sakonninsa Ba
Sannan Inta Ci Gaba Da Nesanta Kanta Da Sakonninsa
Dole Taikewa Kamar Yadda Ita Da Zuciyarta Suka Yarda
Sunyi Kewa A Kwanakin Da Suka Gabata Tazauna Tajanyo
Wasikar Datakarbo Daga Gidan Waya Adireshin ANNUR
MIKYWAY CAFE DAGA ABUJA?
CAFE DIN DAKE ABUJA INDA KUMA TASAI WAYOYIN
HANNUNTA BIYU TASAI MODERN DINTA INDA TA
SAI KYAMARARTA INDA TASAI......... KAI BAZATA IYA
KIRGAWA BA.
Inhar Taje Hankalinta Baya Kwanciya Tanaji Ajikinta
Kamar Tana Da Nasaba Da Gurin, Tanata Tunani Ta Bude
Wasikar Ko Kuma Kawai Ta Share Taikarfin Hali Ta Bude
Taga An Rubuta ""RAYUWATA ZAN BAYYANA MIKI KAINA,
NAKI MAHAUKACIN MASOYI"" TARE DA SA HANNUNSA,ta
Ce Wato Mahaukacin Masoyi Daga Annur Mikyway
Yake,ya Abinyake?
Innalillahi Wa Inna Ilaihirajiun
Tanamamakin Yaya Haka Tafaru,,dago Kan Nan Dazatayi
Saitaga Alamun Mutum A Inuwar Labule Ta
Taga ,yanaganin Ta Dago Da Sauri Ya Bar Wajen,takori
Dukan Da Zuciyarta Take Cikin Zafin Nama Ta Isa Tagar Ta
Yaye Labulen Tahau Leke Leke Amma Bataga Komai Ba
Sai Motocinsu Dake Gurin Kwanyarta Tafara Dawo Mata
Da Abindata Karanta A Takardar Mahaukacin Masoyi
Zanbayyana Miki Kaina Shine Wato Yanzu Ya Bayyana A
Labule Taja Baya Tana Raya Abubuwa Masu Wahalar
Fassara Wanda Tagama Hakikancewa Mahaukacin Masoyi
Ba Aljanibane Amma Abinda Mahaukacin Masoyi Keyi
Yawuce
Azaceshi Cikin Mutane,to Waye?
Ta Fizgo Hijabi Ta Zira Ta Ce Zan Binciko Waye
Kai,abindayakama Naikenan A Farko, kasha Zamanka Zan
Nemoka,
a Falo Ba Yushau Ba Hajiya Sai Sumoli Tafice Itakuma
Sumoli Ta Tsargu Don Haka Ta Mike Ta Hau Lekenta Ta
Taga Ruma Nafita Ta Hango Yushau Yafito Ta Tsakanin
Motoci Kaitsaye Ya Nufota Take Ta Tsargu Da Ganinsa
Kuma Ta Alakanta Hakan Da Mahaukacin Masoyi Fuskarta
Daure Ta Tsaya Ina
Zaki Haka?

Ta daga Takardar Tsakaninka Da Allah Yaya Yushau
Bakada Masaniya Akan Wannan Takardar?
Yanamata Kallan Rashin Fahimta Ya Karba Yana Nazarinta
Cikin Yamutsa Fuska Kirjinsa Na Dukan Uku Uku Basaikin
Hadani Da Allah Ba Ruma Wallahi Bansan Komai Akanta
Mene yafaru?
Ta Amsa Takardar Tana Nazarinta Yanzu Ina Daki Naga
Inuwar Mutum Naleke Nata Labule Ko Kaganshi
Tunda Tanan Ka Bullo, Kallon Juna Sukai Ido Cikin Ido
Wanda Yushau Yake Da Yakinin Hakan Baitaba
Faruwa Tsakaninsa Hakanyasanya Masa Muguwar Kasala
Kirjinsa Nata Bugawa Da Sauri Taja Baya Ayanzu Kam
Tasan Yushau Ya Wanke Hannu Nezai Danna Maballin
Kunno Mata Danjar Bakin ciki Wahala Da Kunan Zuciya,
Tsoronta Daya Kada
Hakan Yafaru Gaban Abbah Dan Zata Iya Keta Idan Alhji
Ta Ce Batasansa Tajuya Zata Bar Gurin Ga Mamakinta
Saitaji Yushau Ya Ruko Hannunta Yaja Ta Baya Dasauri
Suka Shiga Tskanin Motoci Tsoro Da Shakku Tuni
Sungama Mamaye Ta
Yaya Yushau Menene Haka?
Sai Ga Hawaye Daga Idansa So Nake Na Baki Kalmar Da
Ban Taba Baki Ba Duk Tazo Kunnenki A Makare Saidai
Niyanzu Take Shan Sharafinta A Kirjina Alhalin Ina Cike
Da Jin Haushin Ciwan Rashin Zuwanta INASONKI
RUMAISAU WALLAHI INASONKI
Dasauri Ruma Ta Ce Kadaina Rantsewa Meyasa?
Indaza A Laluba Zuciyarka Da Kyau Sai Antarar Da Kaffara
Takamaka
Bajinsona Kake Ba Illah,,,
yatareta Ruma Duk Abinan Danakeji A Kirjina Game Dake
Kicemin Baso Bane?
Taja Baya Hawaye Suka Fara Zuba Daidai Lokacin Idanta
Yakai Kan Sumoli Ta Ce SO DAYANE TAK TUNI NA
SADAUKAR DA NAWA GA WANDA YA CANCANCESHI DUK
DA UBANGIJI BAI NUFA ZAMUCI GAJIYAR SA NIDA
WANDA NASO DINBA,ILLA JIN KUMAJIN RADADIN
DANAKE JI YAZAMA
KAFFARA,AMMA NAKA SON KAGA INDA KA SARAYAR
DASHI,TA NUNA MASA SUMOLI
Yakalli Sumoli Baiji Zuciyar Sa Ta Sauya Ba......
Yaitsaki Yamaida Kallansa Ga Ruma, Ruma Ta Ce "Nikuma
TAWA RAYUWAR BA A KIRKIRETA DAN TAZAMA FANSAR
FARINCIKINKA BA YAYA YUSHAU MURUFE WANNAN
CAFTAR AUREN JUNA DA MUKAI A
BAYA KUSKURENE DA CIN AMANAR ZUCIYOYINMU
WADANDA DUK BA HAKA SUKESO BA HAKA ZALIKA
IYALAN DAMUKA SAMAR BA HAKAMUKASO BA NI NAI
DANASANIN HAIHUWAR SU DOMIN TAUSAYIN
RAYUWARSU KAI KANA BAKINCIKIN HAIHUWARSU
DOMIN TAUSAYIN RAYUWAR SU KAIKANA BAKINCIKIN
HAIHUWAR SU SABODA BASU FITO DAGA MACEN DATA

CANCANCI HAIHUWAR 'YA'YANKA BA,
KI Bar Maganar Nan Dan Allah Tafara Tafiya
Ya Ce Zansa Karfi Da Lallashi Kidawo Rayuwata Zanbaki
Abinda Ban Baki A Baya Ba Wato So Da Kulawa,
Takada Kai Ta Ce ToGA HANYA NAN AMMA KAMAR AKWAI
WANDA YAFIKA KARFI DA IYA LALLASHI AKAN HANYA
WATO DAN AUNTY.
.
To en gidan nan ku zama shaida Ruma ni take so , kunji
dai da bakinta..lol.
.
Sai jibi ma dora.
.
Dan Aunty
GORAN DUMA (p 52)
.
.
Takada Kai TaCe To GA HANYA NAN AMMA KAMAR AKWAI
WANDA YAFIKA KARFI DA IYA LALLASHI AKAN HANYA
WATO MAHAUKACIN MASOYI IN ALAMUN KARFI YANAGA
MAI KIBA SAI INGA KAMAR ZAI IYA KAYARDAKAI
Tunda tai maganar Tai Taga Yanayin Sa Ya Sau Dan taga
Ko suna Da Alaka Da Mahaukacin Masoyi,ransa A Bace Ya
Ce wanene Mahaukacin Masoyi?
Wannan kuwa Ba cin Fuska Bane?Zakijerani Dawani
waima Mahaukaci Asan Dan kinga Nafada Sonki Ruma?
Saitasami Kanta Dayimasa Murmushin Mamaki Sannan
Takauda Kai Batare Data Amsamasa Ba Tawuce Cikingida
Ta
Barshi Agurin Motocin Sumoli Naleke Ta
Window,gabadaya Zuciyar Ruma Ta Zaku Da Sanin
Mahaukacin Masoyi,tanazama Adaki Sai Ga Sakonsa Ta
Waya Wanda Ke Nuna Shaidar Yagama Kallon Diramarta
Da Yushau HANKALINA SOYAKE YA KWANTA ASHE BANI
NAKE YAUDARAR ZUCIYATA
BA?
TAJIMA TANA RADAMIN ZAKI SOMU, Cikin Karkarwar
Hannu Tasami Kanta Da tafa Gajeren Sako Taimasa Amsa
A Karo Na Farko,WAYE KAI?
INA SON IN SANKA,
Taitajiran Amsa Har Karfe Goma Na Dare Tadinga Kiran
Wasu Layiyyinkansa Bata samuba Taji Afuwar Son Tasan
Mahaukacin
Masoyi A Yau Tamkar Dandayaso Fitowa Cikin Mahaifiyar
Sa Dan Haka Tanemi Abinda Yake Mata
Dadi A Duniya Tarasa,sai Ta Hau Social Network Ta Tura
masa KALAMANKA NA NUNA JARUMTA A
SOYAYYA DA RAYUWA,AMMA AYYUKANKA SUN KASA
TABBATAR DA HAKAN,YAKIN BOYE DAGA MUTUM
BOYAYYE?
LALLAI BUYA YAYIN CIMMA BURI ALAMACE TA
RAGONTAKA,IDAN BA A CIKIN RAGWAYE KAKE BA

INASON INSANKA,
Tafi Awa Biyu Sannan Tasami Gajeriyar Amsa Ta Inbox
Dinta A Facebook,LOl!
BANSAN NI RAGONE KO JARUMI BA,ABINDA KAWAI
NASANI NI MAHAUKACINE A SOYAYYARKI
MAHAUKACINDA IN BAI SHIGA SAHUN DAKARU A
KWANJI BA DA ADALCI ZA AKIRA SHI BARDE A
SOYAYYA,KINA SON GANINA?
NAZACI KINCI ALWASHIN GANONI DA KANKI,
TANAKARANTA Wanna Sakon Nasa Tamike Zumbur Kawai
Saitasami Kanta Da Kwankwasa
Kofar Dakin Baccin Hajiya Tsawon Mintuna Biyar,sai Ga
Hajiya Tafito Daga Sashen Alhji Cikin Magagin
Bacci Fuska Cike Da Tsoro Tana Duban Agogo Wanda
Yanuna Sha Biyu Da Rabi Lfya Jikin Ne Ruma?
Arikice Take Idanta Fal Da Kwalla Takama Hannun Hajiya
Inason Zuwa Abuja Gobe Indawo Jibi,kinemarmin
Wannan Damar Wajen Alhji Dan Allah Meyafaru?
Wani Abu Kike Da Bukata Kikejin Mu Bazamu Iya Yimiki
Ba Sai A Abuja?
Kina Girgiza Kai Kina Kuka?
Amsarki Na Nufin E,h Da A,a Kenan,ba Abin Kuka Bane
Hajiya,raunina Ne Kawai Yakawo Kukan,a Barni Inje
Abuja Nai Alkawarin Da Nadawo Zansanar Dake Komai
kuma Na Rantse miki Da Allah Sai Kaddarar Ubangiji
Inzan Dara Jib
Ruma Na Sauka A Tashar Utako Maimakon Ta Dauki
Shatar Mota Zuwa Gidantake Wuse,kawai Saita
Umarci Dan Tasi Dayakaita Milkway Cafe Bata Da Yakinin
Zatajima A Ciki Ko Bazata Jimaba Dan Haka Tasallami Dan
Tasi Tataka Cikin Barin Jiki Dana Zuciya Ta Shiga
Kantin,babu Abinda Ke Yawo Aranta Irin Sakon
Mahaukacin Masoyi Na Safiyar Yau INAJI A JIKINA A YAU
ZANGA MASOYIYATA,
Kamar Kullum A Milkway Na Baya BaBu Abinda Ya Ragu A
Kallon Mayatar Da Ma,aikatan Gurin Kemata Saima
Karuwa Datake Tsammanin Yi,itama Ta Dake Ta Janyo
Daddatan Magani Ta Ci Kuma Tadinga Tafiyar Kasaita Har
Taisa Bangaren Datafi Wayo Wato
Yanar Gizo,ina Son Ganin Manajan Gidannan Malam
Bayan Sallamar Ko Gaisuwa Bataimasa Ba To Madam Kira
Shi Za Ayi Ko Kuma Kai Ki Gurinsa Za Ayi Akaini, Kaitsaye
Tafada Cikin Cin Magani Tamike Tana Rataya Jaka,zo
Muje,bayan Yagama Jimaminsa,har Ofishin Manaja Tai
Arba Dashi Gajeren Mutumin Nane Wanda Ya Ce Kallanta
Yafi Kallon Talabijin,suna shiGa Taga Fuskar Rashin
Gaskiya Atare Dashi Lfya Garba?
Yatambaya Arikice Bayan Tafiyar Garba Office Din Yai
Shuru Shiyasakata A Kwandan Shara Yanata Tafa Sako A
Wayar Sa Itakuma Tanata Nazarin Ofishin To Hajiya
Inajinki, Nazo Ne Inji Dalilinda Yasa In Nazo Gidan Nan
Nake Zama Muku Magiji In Ban Manta Ba Kaida Kanka Ka

Taba Fadamin Nafi Majigin Dadin Kallo
Mudin?
Kalmar Dayafada Cikin Alamar Shakansa Ma Baiyarda Da
Kansa Ba, Kudinfa Ta Amsa Rai A Bace,yai Kasake
Hankalinsa Nakan Waya, Shikenan Abinda Kikeson Sani?
A Amsa Min Wannan Tambayar Mana Sai Aji Idan Akwai
Wata, Karon Farko Dayai Murmushi, Kin Tsargu Ne Kawai
Amma Ni Ban San Munakallanki Kamar Majigi Ba,nidai
Kawai Nasan Bama Iya Ganinki Bamu ShiGa Rudani Ba
Amma Har Yau Bamu Gano Dalili Ba,duk Da Haka Kiyi
Hakuri,
ruma Taji Kamar Ta Kwarfa Masa Mari Saboda Haushi
Amma Ta Hadiye Ta Balle Jaka Ta Fito Da Takardar
Mahaukacin Masoyi Wadda Ya Aiko Ta Gidan Waya Kuma
Daidai Wannan Lokacin Sakon Mahaukacin Masoyin
Yashigo Wayarta,
ASHE DA GASKE KINA SON GANINA DAN ALLAH MEYA KAI
HAKA DADI A DUNIYATA TA YANZU?
TA Hada Da Wayar Da Wasikar Duba Wasikar Nan Waya
Rubuta
Ta Agidannan Kuma Sa Hannun Watake Dauke Dashi Duk
Taimasa Tambayoyine Cikin Hanzari Da Hadiye Rikitarta
Manaja Yafi Minti Biyar Yana Juya Waya Da Wasika
Sannan Yadago Muryar Sa Na
Rawa Ya Ce,lambar Da Sanya Hannu Duk Na NAZIFI
MUHAMMAD NE
Nazifi Muhammad?
NAZIFI MUHAMMAD?
Tasake Maimaitawa A Rude Ganin Yakasa Amsa Mata
Kuma Yana Bintada Wani Rudadden Kallo,amma Bakinsa
Yakasa Furta Kalma Ko Guda,taja Kujera Datun Tuni Take
Tsaye Rike Da Majin gininta Ta Zauna Inatambaya Kayi
Shuru?
Madam Tambaya Kikayi Kenan?Nazaci Maimaita Sunan
kike Domin Yanamiki Dadin Fada?
Ta Hadiye Doki Da Mamakinsa Kuma Datakara Saitajanye
Dukkan Rudanin Da Fuskarta Ke Nunawa Ta Barwa
Zuciyarta Tanaji Dasu,to Ba Bu Laifi Inason Ganinsa,baya
Gari Takara Zuramasa Ido Kuri Tsawon Lokaci Ta Ce
Menene Matsayinsa A Gidan Nan?
Shine Mamallakin Wajen,da Sauri Tajuyo Amma Naji
Kakira Sunanshi Kaitsaye?
Yadan Fara Dariya Aikamawa Take A Daure Mai
Daurewa,hakane Ina Son In Sani Mutum Ne Ko Aljan?
Mamaki Ya Bayyana Karara A Fuskar Sa Bakinsa Na Rawa
Ya Ce Wanne Irin Aljani Kuma?
Dama Aljannu Abokan Huldarmu Ne Dahaar Zan Shaida
miki Shi A Mamallakin Gidan Nan,
tatareshi Cikin Ci Da Zuci Kukusani Ni Ba Matsayinsa Nazo
A Sanar Dani Ba,shinakeso In Sani Dan Haka Karmu Ja
Maganar Kasanar Dani Ranar Dazai Dawo,
To Kahadani Dashi A Waya Cikin Jimami Ya Ce To Bara

Nanemi Izini Agurinsa Yatafa Sako Yaturamasa
Sannan Ya Tsaya Dako,can Sai Ga Amsar Amincewa
Sannan Ubangida Nasa Yakirashi A Waya,kaitsaye
Shikuma Bai Daga Ba Saiyamika Wa Ruma Tare Da
Mikewa Yabar Falon Tadaga Wayar Dajin Karfin
Gwiwar Juya Harshe Yadda Taso,amma Daga Sallamar Sa
Ya Warware Mata Duk Notikan Laka Da
Karfin Hali Baki Yahau Karkarwa Jiki Yadauki Bari,duk Da
Haka Bata Iya Amsa Sallamar Ba,ranki Yadade Ance Kina
Son Magana Dani,?Tattausar Muryar Tasa Takara Dukan
Dukan Kunnenta Da Zuciyarta Kawai Saitaji Wani Irin
Rauni Ya Mamayeta Dan Haka Batun Tai Maganarma Bata
Tasoba
Rumaisau Kinajina Kuwa?
Cikin Mamaki Tadanyi Wani Nishi, Waye Wa,,,,wa Takasa
Direwa Kawai Saita Hakura Rumaisau Yaya Jikin?
Kawai Saitasami Kanta Da Sheshekar Kuka Itakanta Takasa
Tantance Abinda Yasata Kuka baitankamata Ba Tsawon
Lokacin dataji Kamar Bawa Kanta Hakuri
Amma Kafin Tafadi Abindata Sak'a Fada Ya Rigata Cikin
Wata Irin Murya Mai Rauni, "kin Dauki Hakki. .
.
Dan Aunty
GORAN DUMA (P 53)
.
.
Kin Nemi Tarwatsa Zuciyata Mai Sauraronki Kina
Kuka,,dakin San Hakane Da Ba Kice A Hadaki Daniba Gara
Yin Umarnin Duk Inda Nake Nazo Nasameki Zanyi
Biyayya Nazo Kuma Ina Da Yakinin Inkinga Kaunarki Dake
Kwance A Kwayar Idona Zaki Tabbatar Inkinyi Kuka
Agabana Zaki Cutar Dani,maganganunsa Sunkara Rudata
Ainun,data Lalubi Ilahirinta Sai Ta Tarar Ita Kanta Neman
Manta Kanta Take,bare Ta Tuna Maganar Dazata Fadawa
Wannan Majanunin Magana Wadda Ta Shafi Jiya Dayau
Dinta Shida Ba A Toshe Masa Basirar Ba Saiyaja Sunanta A
Hankali Tamkar Yaimata Allura
Saigata A Farke,bakinta Yagaji Da Bari Ya Furta Abinda
Kwakwalwartata Ta Kera Watakila Ina Kuka Ne Saboda
Bansan Da Irin Mutumin Danake Tare Ba,,ina Kuka Bisa
Yadda Kake Wahalar Da Zuciyata Tare Da Gangar Jikina
Yakatse Ta Cikin Muryar Lallashi Kinga Yi Hakuri Ki Koma
Gida Zanzo
Nasameki Har Gidan Ya Katse Wayar, Ruma Tai Tsuru Da
Wayar A Kunne Batare Data Iya Saukewa
Zuciyarta Na Bugawa Fat Fat Hajijiya Na Dibanta Saidai
Takasa Motsawa Nanda Can Sai A Manaja Ya Ya Ce Mata
Kano Kika Nufa Ko Wuse?
Ta Juyo Tana Binsa Da Kallo Da Alamar Tai Mamakin Jin
Kanonta A Bakinsa Da Wuse Wannan Ya Tabbatar Mata
Duk Shakiyancin Da Ake Mata Yana Da Masaniya Saitaji
Ranta Yai Mugun Baci Ta Ajiye Masa Wayar Sa Takarasa

Goge Hawayenta Kunnuwanta Kuma Na Sauraronsa Yace
Yayi Umarnin Duk Inda Kika Nufa Idan Kina Da Bukata A
Bayar Da Mota Akaiki Bata Tsinka Ba Kallan Dataimasa
Yana Tattare Da Amsar Banida Bukata Ta Wuce Kai Tsaye
Batare Data masa Sallama Ba Ta Bar Office Din, Shikuma
Baidamu Da Basarwarta Ba Yatake Mata Baya Ya Rakota
Har Bakin Titi Ya Tayata Jiran Tasi,bai Mata Magana Ba
Itama Hakan Bayan Sun Tsayar Da Motar Shiya
Sallami Mai Tasi Yaimata Bankwana Ita Ko Tankasa
Bataiba, Tana Mota Tanata Lissafe Lissafen Yadda Nazifi
Yake Da Yadda Har Ya Wuce Makadi Da Rawa A
Sha'anoninta Har Dana Tsakaninta Da Zuciyarta Wadanda
Suka Yi Kama Da 'ya'yan Cikin GORAN DUMA Wanda Sai
Anfasa Za A Iya Lissafawa Tai Shige Da Fice A Duk
Lungunan Zuciyarta Dakuma Magabatan Alamuranta
Musamman Cikin Rayuwarta A Abuja Dakuma Milkway
Danta Gano Ko Ta Taba Cin Karo Da Wannan Mai Kiran
Kansa Mahaukacin Masoyi,amma A Sunan Manajansa Ya
Shata Masa Wai Nazifi?
Ta Shafa Sosai Ba Ta Tuna Shi Dinba Sai Can Ta Dan So Ta
Tunano Shi Bayanta Tariyo Sha Biyar Ga Watan
Nuwamba Na Shekarar Dubu Biyu Da Sha Biyu A
Kwakwalwarta Shugaban Milkway Ya Fado Mata,amma
Acikin Basaja Yadda Yanzu Zata Kasance Cikin
Shakkunshine Nazifi Kokuma Wani Daban 15 Nov 2012
Sunyi Da Nusaiba Kanwar Mijin Yayarta Balaraba Zatazo
Raka Ta Milkyway Dan Ta Siyo Ipad Satika Kadan Da Fara
Rubutunta A Jaridar Aminiya Don Saukaka Mata Aiki,sai
Nusaiba Taimata Waya Cewa Suhadu A Milkyway Ta
Tsayar Da Motar Innarta Honda A Harabar Milkyway
Tanemi Kiran Nusaiba A Waya Amma Saita Tarar Wayarta
Ba Bu Ko Kobo Haka Tajima Zaune Cikin Motar Tana
Waige Waigen Shigowar Nusaiba Dazama Yafara
Gundurarta Saita Fito Ta Rumgume Hannu Ta Jingina Da
Motar Tana Ta Faman Baza Idon Kan Motoci Da Mutanen
Dake Shige Da Fice A Wajen,cikin Haka Wata Shudiyar
Jeep Ta Shigo Harabar Milkyway Hade Da Tagumi Ta Tsura
Mata Ido Har Tazo Ta Gifta Ta Kadan Tatsaya Kafin Kuma
Ta Gifta Ta Din Ne Suka Hada Ido Da Matukin Motar,wani
Matashi Baki Mai Dogon Hanci Da Fararen Idanuwa Yana
Sanye da Bakin Wando Da Shudiyar Tshirt Da tambarin
Mikyway Cafe Ta Kawar Da Kai Saidai Jikinta Ya Ci Gaba Da
Batashi Baidauke Idanuwansa
Daga Kanta Ba Harya Wuceta Kamar Mintuna Goma Bai
Bude Motar Sa Yafito Ba Tana Tsaye Tana Ci Gaba Da
Waige Waigenta Har Idonta Yazo Zagaye Kan Motar Sa
Adaidai Lokacin da taGa Yana Gyaran Madubi Da Alama
Ita Yake Karewa Kallo,ranta Yai Mugun Baci Har Ta Zabga
Masa Harara A Duhu Tayi Tsaki Tare Da Duban Agogo
Cikin Takaicin Nusaiba Asannanne Tasami Azancin Shiga
Ciki Tasanya Kati A Wayarta Dan Kiran Nusaiba Ta Rufe
Motarta Tanufi Ciki Agurguje Ya Rufe Mota Ya Biyo

Bayanta Don Haka Takara Daga Kafa Dab Da Isarta Ta
Waiga Saitaga Manaja Nadan Rusunawa Matashin Nan
Yana Masa Barka Da Zuwa Tasake Hada Ido Da Shi Tadan
Motsa Baki Alamar Bataji Dadi Ba
Ka Share Yallaban Nan Yau Malam Kakira Ni Da
Muhammd Kawai Domin Acikin Tarko Nake Neman
Maitayani Yakin Kubuta Nake Batare Da Daddawar Da Na
Kamo Ta Subuce Ba,bata Damu Da Zantikanta Da Suka
Biyo Baya A Tsakanin Matashin Da Manaja Ba Domin
Zaurance Suke Harma Da Sauya Harshe Zuwa French
Wanda Gaisuwa Kawai Ta Iya Dashi A
Cikin Zafin Nama Kuma Sai Gasu Gaban Kantar Lokacin
da take Mika Dubu Dayan Katin Sun Dauke Hankalin Mai
Bata Katin Dayimasa Zance Shima Cikin Harshen Da Bata
Lakanta Ba Dan Haka Yakasa Dauko Mata Katin,ranki
Yadade Barka Da Yau,inji Matashin Nan Wanda Yadamu
Da Kallonta Bayan Yazo Dab Da Ita Ya Tsaya,,yauwa Barka
Dai Kamar Nasan Fuskar Nanfa Afuwa Cankowa Nakeson
Nayi
Yasa Nadamu Da Kallanki, Ta Gyara Tsayuwa Da Kyar Ta
Ce Hmm,,kamar Munyi Karatu Da Kyar Ta
Ce,,hmm,,kamar Munyi Karatu Tare?Bata Tankamasa
Ba,hm,,,bani Katin Mana,,,
yadan Yi Turus Cikin Kallanta Sannan Ya Ce Ranki Yadade
Kozaki Miko Min Wayar Na Kwashe Miki Lambobin
Ansami Matsala A Katin munan Idan Ba Ai Taka
Tsantsanba Batai nazarin Komai Ba Tamika Masa Wayar
Karaf Manaja Ya Amshe Wai Shizai Samata Da Alama Na
Takuramiki Ko?
Ba Haka Bane Wai A Ina Mukai Karatun Tare?
Alamar An Kureshi Ya Ce A Bayero Univer Sity Mun
Karanci Aikin Jarida Wannan Yasa Tadan Sauko Harda
Murmushi Hakane Yaya Bayan Rabu Sai Alkhairi Tuna Min
Suna Ta Ce Cikin Kwanciyar Hankali Rumaisau Aliyu
Ahmad Haka Kuwa Na Tuna Takara Dubansa Da Kyau Da
Alama
Tanada Shakku Saidai Yadda Yayi Fuska Saitaji BaBu
Bukatar Ta Tambaye Shi Kokuma Tayi Ja Inja
Dashi To Hausawa Sunce Bata Karya Wuya To Kuwa Ta
Yafo Ta Harzuwa Lokacinda Za A RaBu Saura
Dame?
Sai In An Kuma Haduwa Haka,nikuma Sunana Nazifi
Muhammad To Madallah Ta Tattara Dukan Hankalinta Ga
Abokinsa Gajere Wanda Take Tsammanin Abinda Yake Da
Wayarta Ya Wuce Loda
Kati Ta Tsuke Fuska Ta Ce Masa Malam Yayadai?
Kar Ka Wuce Gona Da Irifa!Yaki Dagowa Ya Dubeta Yana
Bata Amsa Habadai Aimu Bamu Da Irin Ma Shimuke
Nema Madam Yana Rufe Baki Yamika Mata Wayar Ta
Karba Tana Tura Baki Bata Tanka Wa Kowa Ba Ta Bar
Gurin Kwaji Dashi Tafada A Fili Ta Fice Daga Farfajiyar
Tana Neman Nusaiba ,nusaiba Takaraso Suka Shiga Sayen

Wayar Inda Batasamu Siyen Ipad Din Datai
Niyya Bama Sakamakon Garabasar Waya Mai Tsada Da
Suka Yi A Kananun Kudi Abinda Ta Iya Tunowa
Kenan A 15 Nov 2013
Amma Tayi Ta Tuno Fuskar Sa Takasa Ballantana Ta Iya
Tuno Ko Ta Kalli Kafarsta Taga Kofato Shiyasa Data Tuno
Hakan Baiwani Sanyaya Mata Raiba Yadda Ranta Ke Jagule
Saitaji Inama Ace Ta Wuce Kano Yau?
Duk Tsiya A Yanzu Kano Tafi Abuja Kwanciyar Hankali
Domin Basajar Kano Ta Waya Da Social Network Kawai
Ake Mata Amma Ta Abuja Bayan Rainin Hankali Tattare
Dake Databa Rai, Ta Karkare Ta Hadiye Damuwarta Bayan
Ta Tarad Da Gudan Jininta Hamida Ba Bu Lfya
Wani Kurji Ya Fito Mata A Kirji Tanata Faman Jinya Saita
Fake Da Tausayin Hamida Ta Hada Kukan
Tausayin Da Basajar Mahaukacin Masoyi Ta Ci Kuka Ta
Koshi A Zuwan Ciwon Hamida Ki Gode Allah Kawai Da Ba
Kauye Kika Bayar Da !Yar Riko
Ba,munyi Tunanin Huda Mata Kirjin Nana A Gida Amma
Muka Nufi Asibiti ashe Damunyi Hakan Da Danyen
Hukunci Muka Yanke,inji Momin Ruma Ruma Ta Tsayar
Da Kuka Tazaro Ido Cikin Mugun Kaduwa Lallai Allah Ya
Tseratar Da Hamida Domin Da Anyi Hakan Akwai Matsala
Saita Biyewa Momi Wajen Hamdala Ga Allah Har
Washegarin Momi Najiran Jin Wani Abu Daga Ruma Akan
Zuwanta Abuja Domin Hajiya Tasanar
Mata Komai Amma Ruma Taki Tankawa Duk Da Cewa Ko
Gabadaya Aka Duba A Jikinta Tana Nuna Damuwa Da
Kasala Amma Iyakarta Haka Cikinta Mai Hadama Ya
Hadiye Shi Kadai ya Hana Bakinta Furtawa Sai Ga Tama
Tana Shirin Komawa Kano Momi Takasa Daurewa Saita
Tareta Da Zancen
Tunjiya Nake Kawaici Inajiran Jin Kin Furta Abinda Ke
Damun Zuciyarki Da Rayuwarki Amma Ga Alama Kina
Son Na Karya Billena Na Tambaya,
Ruma Tayi Walai Da Ido Tana Murmushin Yake Lah!
Mekika Gani Momi?
.
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 54)
.
.
Ni Ba Bu Abindayake Damuna,kinganki Kuwa?
Komai Naki Yana Nuna Damuwa Inana Ture Wayar
Damukai Da Hajiya Kenan,ruma Tayi Kasake Bata Da Ta
Cewa Tunda Hajiya Ta Burma Mata Ciki,momi Ma tadan
Ja Fasali Fadamin Ruma Meke Faruwa?
Naso Ace Saida Kikazo Gidan Nan Sannankika Nufi Sabgar
Taka Kawoki Abuja Nayi Niyyar Sanyawa
Abiki A Boye Aga Abinda zakiyi,amma Saikika Shammaci
Niyyata Har Yanzu Ruma Bata Da Niyyar

Tankawa So Ma Take Ta Fashe Da Kuka Saboda Tunano
Yadda Tayi Kwanar Jinya Da Zuciyarta Kowa A
Kuntace,kame Kamen Tashoshin Ainihin Mahaukacin
Masoyi Ya Cunkushe Wa Kwakwalwar Amma Har Cajinta
Yakare Bata Canko Wadda Zata famata Shi Tar Tar Ba
Anya Wannan Rayuwar Zata Dore Ciki?
Ta Ina Zata Bi Ta Kubuta?
Kawai Sai ta sami Kanta Cikin Hawayen Momi Kam
Tausayin Da Rauninta Akan Ruma Tana Hadiyewa Har Taci
Nasarar Data Bata Kwarin Gwiwar Yimata Nasiha
Zanyi Murna Idan Ba Tarkon Soyayya Kika Fada Ba Ruma
Dan Banasan Kifada Tarkon Son Mutumin Da Bai
Cancanta Ba Dan Baisan Muhimman cin ki Ba
Haryaja Ragamar Rayuwarki Cikin Son Zuciyar Sa
Kawai,mace Irinki Datafi Sauran Mata Rauni Tana
Bukatar Taka Tsantsan Acikin Soyayya Kinfi Kowa
Sani,aranta Ta Ce Kamar Momi Nasan Cinka Abinda
Ke Wakana A Tsakaninta Da Mahaukacin Masoyi Saidai
Kurkuren Lis Cewa Ita Tafada Tarkon So Ba Wata Hallitar
Ce Tafada Tarkon Son Nata Ba Kila Momi Bata Taba
Hasaso Ko Tarkon Sonka Aka Fada Kana Iya Shiga
Hadariba Ta shiGa Goge Hawayenta Batare Data Kammala
Tunaninba Inafatan Dazara Kinkoma Zaki
Cikawa Hajiya Alkawarin da kika Daukar mata?
Da Sauri Ruma Tadago Tayi Ma Momi Duban Rashin
Fahimta Momi Tamike Tana Shirin Barin Wajen Tana
Amsa Mata Tafadamin Kin Mata Alkawarin Kina Komawa
Zaki Sanar Da Ita Dukkan Abinda Ke
Akwai Ruma Tashi Ga Gyada Kai Batare Da Hayyaci Ba To
To,,,,dama Bazan Karya Alkawari Ba,
************
tana Isa Kano Daidai Lokacindatake Shiga Harabar
Gidansu Sakon Mahaukacin Masoyi Nafado Kasancewar
Wayar Na Hannuta Cikin Dukan Zuciya Ta Kashe Ido Ta
Hau Dubawa BARKA DA ISOWA RANKI YADADE,IDANKIN
HUTA KILA ANJIMA NA SHIGO MUGA JUNA
MAHAUKACIN MASOYI
Bataji Bakinciki Kofargaba Game Da Sakonsa Ba Tadai
Samikanta Cikin Saurin Shigewa Cikingida Wanda
Batafara Mamakin Neman Dalilinsa Ba Sai Gata Tashiga
Gidan
Mutangida Nata Hidimar Murnar Yimata Maraba Rashinki
Ko Na Awa Dayane Agidan Nan Kufai yake
Mayaimin Da Gidan,inji Mubarak Koyai Dariya Amma
Ruma Murmushin Yake
Hajiya Tun Daga Shigowar Ruma Tadora Mata Ido Ta
Cemasa Idan Tai Aure sai Muga Yadda Zakai Mubarak
Zaiyi Magana Tatare Shi
Kajira Nai Sallar Magariba Bar Tadin Ka Wuce Alwala
Yawuce Yana Dariya Aima Zan Barta Ta Huta Sai Gobe
Zamu Fanshe Hirar Kiyi Sallah Kici Abinci Muzauna Ko?
Fuskarta Ba Bu Alamar Wasa Kilatayi Hakan Ne Dan Kar

Ruma Takawo Mata Wargi Hakanyasa Ruma Tadinga
Komai Cikin Fargaba
Tana Saka Yadda Zata Sanar Da Hajiya Murdadden
Labarinta Da Mahaukacin Masoyi A Kar She Tatarar Da
Bata Da Zabi Illai Tasanar Mata Komai Tinda Tai Alkawari
Da Wayarta Akai Tattaunawar Tadinga Nunawa Hajiya
Komai Na Sakonninsa Duk Da Hajiya Takidime Amma Bai
Hanata Magana Anutse Ba Meyasakika Ci Gaba Da Rike
Wannan Abin A Zuciyarki Kekadai?
Kuma Mekikaje Yi Abuja?
Hajiya Taimata Karin Bayani Ikon Allah HajiYa Tafadi Cikin
Jinjinawa Tare Da Nanata Kalmar Duk sunyi Shuru
Zuciyar Kowanne Tai Nisa A Saka Wani Aikinda
Zuciyartata Ta Hada Cikin Lissafin Shine,fargabar Allah
Yasa Anjima Din Nasa Karta
Zamo Tsakar Dare Dan Karya Bayyanar Mata Abinda Tafi
Zatonsa,wato Aljani Ko Kadan Batason Ya Bayyana A Haka
Batare Da Dalilin Tsoronsa A Aljani Ba Saitare Da Dalilin In
Aljanin Ne Sun Rabu
Kenan,inkin Amince In Sanar da Alhji Wanna Katon
Labari In Ganin Dole Maza Su Shigo Ciki Hajiya Ta
Katsewa Ruma Tunani Duk Da Ita Ma Bata Hattama Nata
Tunanin Ba,amma Tasanya Masa Karfi,mujira Yau Da
Gobe Da Jibi Dan Ganin Abinda Zai Biyo Baya,karmu Tashi
Hankalin Kowa Hajiya Kila
Lamarin Baikai Natashin Hankali Ba,yaya Zanyi Da
Mominki Mai Jiran Nakai Mata Kanun Matsalarki?
Hankalin Momi Atashe,,,rumaisau Rumaisau Tamike Cikin
Alamun Son Ficewa Daga Falon Fuskarta Na Nuna Gajiyar
Jiki Data Zuciya Ki Kyale Ta Kawai Hajiya Yadda Momi
Take Damuwa Cikin Matsalolina
Inason Duk Abinda Zataji Akaina Indai Zan Iya To Taji Mai
Dadi,,shikenan hajiya Ta Fada Badan Taso
Ba Ta Bi Ruma Da Kallo Har Ta Kule Tanadan Dingisa
Kafarta Wadda Kem Bayan Kwanar Fargaba Tare Da
Tsammanin Bango Zai tsage Mahaukacin Masoyi Ya Bullo
Ruma
Batasami Bacci Ba Saikarfe Hudu Saura Hakan Ya Janyo
Da Kyar Ta Iya Katse Bacci Ta Gabatar Da
Sallar Asuba Akan Lokaci Sannan Ta Koma Ta Ci Gaba Da
Ramuwar Bacci,karfe Tara Daidai Wayarta Ta Farkar Da
Ita Da Shigowar Kira Saidata Koshi Da Kallon Agogo Har
Kiranya Katse Sannan Tasami
Taba Wayar Daidai Lokacin Wani Kiran Yasake Shigowa Ta
Daure Ta Hadiye Kasalarta Ta Daga Tare
Da Sallama Yushau Ya Amsa Cikin Kuzari Nayi Ta Baza Ido
Inganki Gidan Atika Jiya Har Dare Bangankiba Kuma Naji
Atika Ma Na Mitar Baki Zo Dubata Ba,ta Basar Ta Ce Yau
Zanje,yushau Yadan Jinkirta Sannan Ya Ce Karfe Nawa?
Ina Son Mu Hadu Ne Akwai Muhimmiyar Maganar
Danake Son Mu Tattauna,bansan Lokacin Dazan Shiga Ba
Tafada A Raunane,amma Ta Raunana Muryar Tatane Dan

Ta Basar Da Zuciyarta Wadda Ta Dauki Zafi Inta Bar
Muryarta Dazafi Kila Ya Rage Mata Kima Shikuma Saiya
Marairaice Kidaure Ki Tsara Lokaci Shigar Taki Ko Saboda
Ni,
Ba Lokaci Zanzo In Batamiki Ba Ruma Ragowar
Rayuwarmu Nakeson Muyi Wa Garambawul,
tayi Iyakar Bakin Kokarinta Tai Magana Amma Takasa Don
Kar Ta Cika Rashin Mutunci Da Kyar Ta Ce Ok
Yushau Baidamuba Yasake Zagewa Da Rarrashi Ko Wuni
Zakiyi?
E,h Wuni Zanyi Toki Saka Idan Ganina Bayan Laasar Yayi
Kyau Ta Amsa Masa Ta Kashe Wayar
*******
A Gaggauce Yushau Yahau Shirin Fita Alhali Ya Shaidawa
Sumoli Yaukansa Ciwo Yake Kodake Da Biyu Ya Ce Haka
Dankartadameshi
Yasamu Damar Yin Tunani Hanyar Dazasu Samo Masa
Ruma Na Biyu Kuma Mugun Haushinta Yakeji,jiya Ya
Dauketa Yakaita Gidan Atika Da
Kwadayin Haduwa Da Ruma Yadinga Zarya A Gidan
Tsammanin Ganinta Amma Har Dare Ba Bu Labarinta Ta
Ce Masa Kaikuwa Dan Allah Ko Bazaka Sauya Motar Nan
Ka Daure Kakai Ta Gareji Adan
Kwaskware Injinta Ayimata Sabon Fenti Fisabilillahi Kai
Ko Kunya Bakaji Kowa A Danginka Shar Shar Da Motocin
Nunawa Sa,a Amma Kaikana Fama Da Karfen Shekaru
Aru Aru Haka Zuciyar Yushau Ke Tafarfasa Daidai Yadda
Sumoli Take Masa Magana Tunda Uban Wani Bai Sayi
Shar Ya Baniba Sai A
Kalleni Da Wanda Allah Ya Bani Sai Dai Idan Anga Ban
Cancanci Zama A Irin Wannan Duniyar Da Wannan Motar
Ba To A Iya Kokarin Rufe Ido A Bude Kar Aganni,
ai Bakafadi Ba Yushau Idan Ka Saka Wa Ubana Da Zagi Da
Cin Fuska Tunda Yadauki Aure Yabaka Da Wuya Ba Bu
Dadi Ina Zaune Ina
Rufa Maka Asiri Yakada Kai Cikin Fushi Sumoli Takara Da
Cewa In Ma Sake Zagina Zakai Yushau Zageni Mana,,,,
insauran Gashin Kumarka Bai sanyani Kuka Zaginka Ai
Bazai saniba Karamin Misali Auranmu Kusan Shekaru Uku
Banta Ba Batan Wata Ba Amma Dan Masifar Mammako
Sha Katafi Kakasa Kai Ni A Nemo Dalilin Rashin
Haihuwata,,.,,ta Dawo Cikin Kwalliya Malam Inakake
Shirin Zuwa Bayan Kace Bakajin Dadi Ya Cemata Yasamu
Kiran Gaggawa Daga Office Ta Ce Bara Nadauko Mayafi
Mufita Tare Inba Gidanku Zakaje Ba,gidan Dakana Rabe
Rabe Kana Komai Amma Baka Kasa Motsa Kwanjin Son
Zawarci Ba,yafice Bai Tanka Ba
Tadawo Da Mayafi Ya Ce Wai Malama Ina Zakibine?
Muje Kasaukeni Gidan Atika mana Kashiga Ka Biya Kudin
Lesunan Ankon Suna....
,
dan kari, ni ma dole naje gidan Atikar nan nasha kallon

yadda zata kaya,
ko da akwai pasinja anan gidan??
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P .55)
.
.
Dubu Nawa?
Dubu Arbain Da Takwas Mana Ta
Amsa Masa Kai Tsaye Tana Taunar Cingam Kas Kas,cikin
Tsawa Ya Ce Daga Dubu Goma Bazan Karamiki Ko Ficika
Ba In Baki Da Kudi Ki Mayar Musu Kayansu Ba Bu Jimawa
Sai Gata Tadawo Dauke Da Lesunan Ta Zube Masa Kan
Gado Cikin Fusata
Gasunan Katafi Dasu Ka Mayar Bani Dubu Goman Zanbi
Wata Hanyar In Samo,ai In Na Ce Dakai Zan Dogara Har
Abada Araba Danni Zan Tabbata
Bai tanka Ba Ya Kirga Dubu Goman Ya Zubemata Kan
Durowa Ya Kwashi Lesunan Yafice Sannan Ta Kwashi
Kudin Tajefa Ajaka Ta Kulle Gidan Ta Fice Sai Gidan Wata
Kawar Mominta Hajiyar Dubai Da China
Ta Kwaso Lesunan Bashi Ta Wuce Gurin Dinki Ta Bayar Da
Dubu Goman Yushau A Kudin Dinkin,
gidan Abokinsa Mai Kudi Ya Nufa Inda Matar Sa Tasha
Fada Masa Matsalar Sikila Da Bukatar Su Ayanzu Kam
Yanade Hannu Zaitafi Neman Iliminsa
Kaga Na Jaruma Sumayya Mai Zizar Sunan Sumoli,kaga
Mutum Na Musamman Wanda Kiyayyar Ruwa Kesashi
Kiba Soyayyar Sumoli Ke Sanyashi Rama,,
irin Wannan Kirarin Maikudi Abokinsa Kemasa Yushau
Kam Kasa Magana yayi.
Haka Dai Tazage Tana Bashi Bayanin Masu Ciwan Sikila
Saboda Sunadasu A Danginsu Inda Duk Wata Alama
Yushau Yaji Tafada Yanaganinsa Ga Ruma Hartagama
Yatafi Abinsa Tare Da Yunkurin Komai Zai Daidaita Tunda
Yagano Bakin Zaren,
*********
garin Rana Sosai Ruma Damai Adaidaita Sahunta Keke
Napep Suka Hau Titin Layin Gidan Atika A Unguwar
Hotoro Ruma Na Cike Da Dokin Akarasa Gidan taga Dangi
Taga Kuma Sabuwar Bakuwar
Dasuka Samu,dahaka Tadinga Binne Mahaukacin Masoyi
Da Matsalar Sa Koda Na Wuni Dayane Tall,wato Taje
Tadawo,basui Nisa Da Hawa Titinba Sai Ga Adaidaita
Sahun Ya Mutu A Titin,subhan Allahi
Kabiru Meyafaru??
Karfen Nan Yagaji Dani Hajiya Shekaran Jiya Fa na
Karboshi Daga Gurin Mai Gyara Inda Yacimin Naira Dubu
Ashirin Da Takwas Amma
Tunjiya Yafara Yimin Mahangurba,ruma Tadan Yi Dariya
Kalmarsata Karshe,ta Duba Agogo Taleko Kai Tana
Kokarin Hango Kabiru Wanda Yadawo Ya Shi Ga Turata

Gefen Hanya Inda Ya Tsayar Da Shi Gefen Wani Mota
B,M,W, Series 5 Wadda Ke Kafe Gurin Tun Kafin Keke
Napep Dinsu Takaraso Nan Dukda Akwai Dan Duhu
Gilashin Motar Ana Iya Gane Matashin Direban Dake
Kwance,mazauninsa Yana Sauraren Wakar The Power
Love,maitashi Kasa Kasa Daga Bakin Celine Dion,sama Da
Mintuna
Goma Ruma Na Cikin Adaidita Sahu Zafi Da Ciwon Jira Na
Dimarta Har Ta Kosa Tafito Ta Tsaya Akan
Kabiru Wanda Yake Tabe Tabe A Injin BaBurdin,haryanzu
Dai Kabiru?Wallahi Kuwa Tundazu Nake Faman Taremaki
Adaidaita Din Dazai Karasa Dake Amma Kinga Duk A Cike
Suke Zuwa,ikon Allah Tabi Titin Da Kallo Tana Rayawa
Aranta Inama
Zata Iya Data Karasa A Kafa Ta Huta Da Tsayuwar Ta Dora
Da Zolayar Sa To In Hakane Kuwa Zanbaka Hutu Tunda Ga
Ya Shirya Hadamu Yayimana Mahangurbar Tare Yau
Wannan Zafinda Ake Kwadawa Idan Ya Rikide Yazama
Hadari Yazubda Ruwa Fa?
Kabir Yafara Yunkurin Tare Wani
Adaidaita Dayashigo Layin Yana Amsamata Nima Haka
Nafara Tunani Ai Karshen Watan Nan Ma In Allah Yaso
Zan Sauya Yana karasowa Sukaga Ai Cike Yake Da Mutane
Ruma Ta Rungume Hannu Ta Ce Bar tarewa Ka Koma Ka
Lallaba Ko Zai Hakura Ya Bari Ka Karasa Dani,
Dukansu Sukai Dariya YakoMa Yana Tabata Mintuna Biyar
Tsakani Matashin Nan Ya Bude Motar Sa Yafito Ya Riski
Kabiru Baidamu Da Kallon Rumasau Ba Sam,kamar Yadda
Itama Bata Mayar Da Hankali Akansa,saida Maganar Sa
Taja Hankalinta
Ranka Yadade Meyasami Keken Naka Dazaka Shanyata
Arana Haka?
Abinda Kabiru Ya Kaddara Shine Ruma Tasan Matashin
Danhaka Ya Amsa Da Kar Sashi,tsautsayine Yallabai Kuma
Muna Ta Kokarin Tare Wanda Zaikarasa Da Ita Bamu
samuba,ya Dago Suka Gaisa Yacigaba Da Duba Injin
Din,sai Ya Bar Ruma Da Tunanin Ina Tasan Matashin
Saurayin Baki Mai Dogon Hanci Da Fararen Idanu,?
Bata Canka Ba,takuma Kasa Kojin Kunyar Kallon da take
Masa Bare Ta Hakura Cikin Faduwar Gaba Da Raunin
Zuciya Iri Iri,can Yajuyo
Yadubeta Duban Da Bai Nuna Mamaki Ko Tuhumar Kallan
Datake Masa Ba Yadago Ya Dubeta Aransa
Yana Mamakin Kota san shine Takemasa Kallo Haka
Yanuna Motar Sa Kinga Muje Inkarasa Dake, Tajima
Mamaki Yadda Yake Kokarin Bata Umarni Irin Na Yaya Da
Kanwa Amma Hakan Bai Hana Ta Daure
Gira Ta Cemasa Bisa Wace Hujjar,,?
Ragowar Maganar Tamakale A Makoshinta Bayan Tagane
Motar Data Dan Gifta Su Kadan Yanzu Ta Yushau Ce Kuma
Da Alamu Ya Ganta Dan Gashi Can Yana Kokarin Samun
Guri Ya Tsaya Nantake Taji Haushi

Da Kyashin Ya Ce Tazo Yakaita Kuma Itama Ta Bishi Suje
Gidan Mutane Da Kowa Yagansu Tare Zai Ga Bakinta
Arashin Zuciya Kawai Saita Zabi Bin Matashin Nan Wanda
Zuciyarta Ta Darsa Mata Kila Irin Kannen Mijin Anti
Atikane,tunda Gashi Yasan Ta Ita Kuma Tanai Masa Kallon
Sani,to Nagode Tasami Kanta Da Fada Tare Da Kada Kai
Alamar Amincewa Ta Dubi Kabiru Ka Kyale Shi Kaje Ka
Nemo Mai Gyara Idan Na Dawo Da Yamma Kazo
Kasameni Da Sauri Ta Bi Bayan Saurin A Zuwan Bataga
Yushau Wanda Ya Bude Mota Ba,da Alama Shima
Matashin Kamar Yagane Abinda take Gudu Cikin Zafin
Nama Yadaga Motar Suka Bude Yushau Da Kura,daidai
Lokacin
Dayake Daga Musu Hannu,
matashin Ya Figi Motar Kamar Mai Shirin Tashi Sama
Fuska Ba Yabo Ba
Fallasa Idansa Ga Titi,hakan Kuwa Ya Kada Hantar Ruma
Tafara Zargin Kanta Da Gangancin Kaikanta Makasa,
Har Suka Kusa Gidan Anti Atika Ba Wanda Yai Motsin
Ha,inci Atare Dashi Bai Dubeta, Ba Illa Yanata
Hidimar Tukin Motar Sa Yanabin Wakar Sa,can Yajuyo
Yana Rage Karar Sautin Au Namanta,ruma
Yayajiki,nauyin Da Zuciyarta Tai Wajen Kokarin Ta Gano
Inda Tasanshi Kokuma Tasan Muryarsa Ya Sanya Ta
jinkirin Amsa Masa,da Sauki,dafatan Iyali Da Kowa Lfya,ta
Kara Da Cewa Muryarta Na Rawa,akwai Alamun Ya
Shanye Mamaki Lokacin Dayake Amsamata Kowa Lfyar
Su Lau,kayi Hakuri Banfa Ganeka Ba Wallahi,,
murmushi Kawai Yai Ya Basar Har Suka Karaso Batare
Datamasa Iziniba Yanemi Guri Ya Tsaya Da Mota,adan
Zuciye Zatafita Bakiji ba?
Da Sauri Ta Tsaya Bayan Tafitarda Kafarta Na
Farko,yanawasa Da Key Holder Inkinshiga Dan Allah Ki
Gaidamin Mai Jegon,takarasa Ficewa Cikin Fusatarta
Wadda Kuzarin Gangar Jikinta Ce Kawai Kenunawa Ta
Rufemasa Motar Nagode Wazance Yanamata Barkar?
Idanta Akan Makullin Motar Dayake Kadawa Cikin Sakanni
Kadan Hantar
Cikinta Yai Mugun Kadawa Sukadinga Lugude Abubuwa
Biyune,wani Irin Kallo Dayake Mata,sannan Da Da
Tambarin Milkyway Datagani Manne A Key Holder
Sa,batagama Rudewa Ba Bare Tanemi Mafita
Ya Tashi Motar Yafara Ja Sannu Yana Amsamata Cikin
Murmushi MAHAUKACIN MASOYI Da Sauri ta
Janye Jiki Tare Da Kokarin Tantance Shi Duk Da yaja
Motar Aguje Haryana Neman Bugeta Ita Ma Kamar Zubin
Haukar Bana Ta Diba A Guje Cikin Gida Daidai Lokacinda
Yushau Ya Tsayar Da Motar Sa Inda
Mahaukacin Masoyi Yadaga A Kidime Tafada Falon Atika
Wanda Ke Cike Da Dangi,asiya MAIMUNA
HAFSAT,DA YA'YAN KANWAR HAJIYAR SU HASANA DA
HUSAINA,jiyo Sallamar Ta Kafinta Shigo Falon Ya Sanya

Kowa Yadau Murna musamman Hafsat Wadda Tatashi
Yiwa Ruma Oyoyo,amma Ina Ruma
A Birkicetake,tana Zuwa Ta Suri Wayar Asiya Komai nata
Rawa Sai Gashi Takarde Dakin Da Muryar
Abdullahi Madarut Acikin Suratul Bakara Ta Ajiye Akan
Kujera Taja Jiki Gefe A Hankali Ta Zauna,,falon Yai Tsit
Cikin Alamar Tambaya Kuma Danta Gajarta Musu Aiki
Saita Hada Tambayoyin duk Ta Amsa A Kalmomi
Kadan,motar Aljani Na Hau Shiyakowani Har Kofar Gida
Suka Dinga Duban Juna Anrasa Wanda zai yi magana.....
.
Dan Aunty
GORAN DUMA (P.56)
.
.
Hafsat Ta Ce Shine Wannan Ya Shigo Ta Girgiza Kai Toyaya
Akai?Kowa Saitambayarta Yake Sai Ga Yushau Da Kyar
Suka Kori Rudu Aka Gaisa Idan Aka Cire Ruma Wadda
Take Takure Tana Karkarwa Yushau Yakore Kunya Da
Nauyi Cikin Kishi Da Fargaba Da So,cikin Rada Hafsat Ta
Matsa Kusa Da Ruma Ko Yaya Yushau Ne Aljanin?
Ruma Ta Girgiza Kai ,to Ku Kashe Karatun Mana Kunata
Faman Sheka Surutu Kuma Kun Ware Kuna Sheka Kuka
Suka Kashe,,,kekuma Kalau?Yanzufa Naganki Lfya Harkina
Shuka Min Wulakanci Ki Barni Tsaye
Yanzu kuma Gaki A Burkice,duk datana Cikin Rikita Bata
fasa Jin Haushin Son Nuna Mata Iko Da Yushau Yakeba
Waita Wulakan tashi?
Dan kawai Ta Guji Hawa Motar Sa Ta Ce Kai Yaya Yushau
Kadaina
Mayar Da Allura Garma Wulakancin Mena Shuka Maka?
Amma Nasanar Dake Takanas Yau Zan Zo Gidan Nan
Donke Daidaine Acce Kin Ganni Kin Shareni?
Saima Budeni Da Kurar Dakikayi?Bisa Wani Dalili Zakazo
Gidan Nan Domin Ni?
Cikin Dacin Murya,kowa Kallansa Kawai Yake Yakore
Kunya Kan Tsinkawar Da Ruma Taimasa Gaban Kannansa
Inkin Kwantar Hankali Tunda Nazo Ai zan Fadamaki
Dalili,,
cikin Ci Da Zuci Ta Ce Saidai Wani Lokaci,ni Wallahi Yanzu
Banda Sukuni,
ran Yushau Ya Baci Sosai,amma Dole Yashanye Yana
Nazarin Ruma Saikawai Ya Kaddara Aljanarta Ce Ta Bijiro
Take Masa Rashin Kunya A Fahimtar Dayaima Matar
Maikudi Amininsa Kenan Amma Tuniya Kwana Da Sanin
Ruma Ba Halinta Ba,amma Dai Makakin Kishin
Saurayin Ruma Ta Hawo Motar Sa Ya Gallabi Zuciyar Sa Ya
Ce Wanne Shegen Ne kika Hawo Motar Sa Ya
Badamin Kura?
Ta Dauki Lokaci Bata Amsa Ba Kowa
Yai Tsit Inka Cire Hafsa Wanda Dukkan Alamunta Kenuna
Ita Idan An Bar Ta Zata Iya Bada Amsar,

Kamar Aiken Amsar Daga Mahaukacin Masoyi Sai Ga
Sakon Tex Dinsa Yafado Wayar Zuciyarta Tadinga
Azalzalawa Ta Karanta Kozata Ga Abinda Zai Bata
Tabbacin Kasantuwar Sa Jinsin Aljanu,INA
MAIYIMIKI RANTSUWA DA ALLAH NI NAFI KOWA
CANCANTAR ZAMOWA JAGORANKI,BA A SO KAWAI BA
HAR DA BARAZANAR KAMUWA DA CIWAN
ZUCIYA IDAN AN SOKEKI KO A TUKUICINE KAWAI BATARE
DA SO BA,KI TAIMAKA AKARE NAWA MUTUNCIN KAR KI
BARI A AIBATA MIKI NI.
NAKI MAHAUKACIN MASOYI BA SHEGE BANE DAN HALAK
NE!
Tasami Kanta Da Kallon Tsakiyar Idansa Cikin Kuka Ta
Ambata,a Maimakon Tasanar Dashi Cewa Aljani Ya Dauko
Ta Bayan Ta Ga Tabbacin Aljanancinsa A Sakonsa,amma
Aljanin Baiyi Tasirin Komai A
Zuciyarta Da Fargabarta Ba,illa Zuciyarta Data Yi Mugun
Raunin An Ce Masa Shege Bata Hana Ba,wani Mugun Kishi
Ya Turnuke Yushau Yanata Kallanta Kallan Dake Son Dawo
Da Ita Hayyacinta Tagane Cewa Ta,addanci Fatakewa
Zuciyar Sa A Kokarinta Nafifita Wani A Kansa,amma
Maimakon Haka Sai Ruma Takara Wani Taddancin Cikin
Kuka Ta Maimaita Kalma Daya WALLAHI BA SHEGE BANE,
yushau Dayaji Ashar Naneman Kwace Masa Saiya Fice
Daga Falon ,falon Yai Tsit Illah Sheshekar Kukar Ruma Sai
Can Hassana Tafasa Shirun Cikin Yanayi Na Zolaya Da
Nuna Tausayi, ABIN TAUSAYI
WALLAHI,YAYA YUSHAU YA FARKA DAHDAI LOKACIN
YAKUSA MAKARA YASAMI WANI MAI KWANJI YAYI FASHIN
ZUCIYAR, Hakan Yasa Kowa A
Falon Yah Dariya Ruma Kuma Ta Tsagaita Da Kuka
Takoma Hidimar Goge Hawaye,dan Allah Wai Yaya
Akaine?
Kin Barmu Cikin Duhu.Da Gaske Aljanine Yakawoki Kuma
Shi Kika Zaba Kikabar Yaya Yushau?
Maimuna Ta Cehaka ,hafsat Ta Zabga Mata Harara,a
Kayan Miya Meyeshi Yaya Yushau Da Baza A Barshi Azabi
Waniba?
Zuciyar Ruma Kam Arude Take, Tamike Ta Isa Ga Usaina
Ta Amsa Jaririn Tana Amsa Tambayar Maimuna A SURA
KYAWAWAN
DABIU DA SHIRYA KALAMAI MUTUM NE BA
ALJANBA,AMMA A WASU AYYUKA YANAKAMA DANA
ALJAN,NASHIGA WANI HALI,WANDA YASANYA NIKAINA
NAKE MAMAKIN ZUCIYATADA IDAN BANYI KARYA BA ZAN
FADI TA FADA TARKON SON ABINDA BATASANI BA,KO
ALJANINE WALLAHI NAFADA TARKON SONSA,CIKIN
TSANANIN RAUNI TAKARASA MAGANAR Duk Suka
Tsagaita Da Alama Bada Wasa take Ba Hafsa Ta Ce
Waiwanene?
Mahaukacin Masoyi,lahaula Wala Kuwata Illah
Billah,kinganshi

Da Idanki?
Shiya Daukoni Yakawoni Nan, Bayan Ta Zayyanamasu
Yadda Haduwar Su Takaya Tare Kuma Da Cewa Tariski
Sakonsa Akancewa Na Yana Dab Da Bayyana Mata
Kansa,kun Barmu A Duhu Ku Warware mana?
Inji Asiya,
hafsat Takalli Ruma Kallan Neman Izini,ruma Tamike
Tadauki Jariri Tana Ce Kisanar Dasu,
Ta Wuce Kaitsaye Dakin Barcin Atika Kozata Samu Damar
Wassafo Surar Mahaukacin Masoyi, Amma Tana Sauraran
Hafsa Datake Basu Labarin Mahaukacin Masoyi Da Nuna
Musu Tex Din Sa A Wayarta Bayan ta gama Kowa Ya
Jinjina,wasu Suka Shiga Rudu,amma Abu Daya Ya
Karfafamata Guiwa
Maganganun Da Hafsa Take Kuma Cikin Yakini Da Gasgata
Kai,na Bawa Kaina Sati Biyu Da Izinin Allah Sainabinciko
Mutuminnan Haka,kawai Bazai Zautamin Yaruwa Ba
Wallahi,ta Wace Hanyar?
Atika Ta Tambaya Kin Manta Mijina Dan sandan Cikine?
Lambobin Wayar Sa Nadauka Sun Isa Nagano Indayake,
**********
Bayan Wuni Cikin Sake Sake Yushau Ya Yanke Shawarar
Daukan Kwaryar Ban Hakuri Zuwa Ga Alhajinsa Bisa
Abinda Yafaru A Baya Da Kokon Barar A Mayar Masa Da
Ruma Yagyara Aurensa,yagama Shakulacin Bangaransa
Wajen Hajiya,haryakai Ga Isa Ga Alhji Wanda Yasanyashi
A Kwandan Shara,yajuyo Ya Fuskantanceshi,NASO NA
TUNA WANNAN FUSKARKUWA?
YALLABAI DAGA INA?
Duk Dakuwa Wutar Dake Zuciyar Sa Tana Raya masa Kuka
Yakamata Yayi Danhakan Kadai Ya Isa Nuna masa Saiya
Wahala
Malam Banfa Ganeka Ba Daga Ina?Kawai Sai Yushau
Yasami Kansa Da Fashewa Da Dariya Yana Kallon Alhji
Wanda Ko Kadan Dariyar Batasa Shi Ya Sassauta Damarar
Dayai Wa Fuskarsa Ba,saima
Yakawar Dakai Yaitsaki,hakan Ne Yasanya Yushau Yadan
Shiga Taitayinsa,yadinga Kokawar Gyara
Zama Yafara Bada Hakuri Na Tsawan Minti Gowa Sha
Biyar,alhji Na Saurarensa Har Saida Takaici Ya Sanya Shi
Tare Yushau Cikin Sarkewar Murya Dan Allah Malam Bari
Batawa Kanka Lokaci,wai Hakuri Kadaine Kawai Yakamata
A Rayuwa?
Bashi Kadai Nara Sa Ba,abubuwa Da Yawa Wadanda Na
Sasa A Bangarenka Wadanda Sukafi Su Muhimmanci
Suna Fi Bukata,,,cikin Zumudi Yushau Yatare Shi Saboda
Yana Zaton Alhji Zaice Ya Mayarda Auren Ruma Amma
Sabanin Haka Kaitsaye Cikin Muryar Tura
Haushi Alhji Ya Amsa,biya Na Kudaden Dasuke Wuyanka
Mana,wadanda Nadinga Hidimar Iyalinka
Dasu Tun Bayanda Ka Saki Uwar Su ,saima Ka Daukemin
Kafa Da Aljihu Ka Barni Da Nauyi Danka Tabbatar Lallai

Bazan Iya Kaisu Bola Na Zubarba!
Ka Yi Ta Banzar Yushau Domin Komai Na Nan Arubuce
Na Na Adana Ko Mutuwa Nai Na Sanar Da Magada
Sunemi Hakkinsu A Wajenka,,,
cike Da Rauni Yushau Yatare Shi,,kayi Hakuri Zan Biya
Alhji,a Bani Adadi Sainafara Biya Daga Wannan Watan,
daka Kyauta Wa Kanka,cikin Ko Inkula Alhji Yafada,falon
Yai Tsit Inbanda Bugawar Zuciyar Yushau Wadda Ke
Tattara Dukan Kafofin Da Zata Sauke Karfin Halin Data
Wanko,akarshe Dai Da Ya Hattama Sai Bakinsa Ya Karbi
Karfin Halin Yafurta Cikin Sarkewar Harshe,idan Rabuwa
Da Ruma Ne Ya Nisanta Ni
Daku?
Kuma Har Shine Yaisa Abin Sanyawa Ka Manta
Kamannina Alhji Ina Neman Alfarma Kadawo Dani Kusa
Daku,,ku Mayar Da Diyancina Dan Haka Inaso Ka Sanya
Albarkarka Ka Bani Dama Na Mayar
Da Aurena Da Ruma...
tunkafin Ya Dire Akwatin Tara Fushin Alhji Ta Cika,ya
Yunkuro Da Fushi Yatareshi,,,wallahi Tallahi Danasan
Maganar Dazakai Minkenan Na Rantse Da Allah Da
Samsam Ban Saurareka Ka Sarayar Min Da Lokaci
Ba,saboda Haka Idan Ba Son In Sassaba Maka Kamannin
Ka Ba,to Ka Digawa Wannan Maganar Aya,
yushau Yai Tsita Cike Da Fargabar Ta Inda Zai Billowa
Alhjin..
Dan Girman Allah Alhji Ka Bani Dama Na Fahimtar Dakai
Akasin Da Aka Samu Cike Da Takaici Alhji Yake Kallon
Yushau Cikin Yanayi Nata Gina-ba-ta-shiga Ba Ya Cemasa
Ahau!Inajinka Yushau Ya Gyara
Zama Jiki Na Bari Ina Son Ruma Alhji Duk Wata Mace a
Duniya Bayanta Zata Bi A Zuciyata,ban Fahimci Hakan Ba
Sai Bayan Rabuwarmu Amma Fushin Da
Kuke Ciki Ya Dinga Tsoratani Yana Hanani Kawo Kaina.....
.
Dan Anti.
.
.
Sannan Sai Gurguwar Fahimtar Dana Yiwa Ciwonta
Wanda Shine Kashi Casa'in Na Rashin Jituwarmu,ayanzu
Kuwa na Nemo Iliminsa Na
Tabbatar Matsala A Dalilinsa Takare Kuma Idan An Bani
Dama Na Ci Alwashin Sai Ruma Ta Rabu Da Ciwon Nan
Haihata Haihata Cikin Izinin Allah,
oh Kana Da Kudin Daza a Canza ,mata Bargo Ko?
Alhji Yakatse Shi A Shashance Cike Da Ladabi Yushau Ya
Amsa A Iyakar Gaskiyarsa,a Binciken Danayi Nagano
Shafar Jinnu Ce Naci Alwashin Daganan Har Saudiya
Zandauki Nauyinsa Ayimata Rukiya,
alhji Yafara Yiwa Yushau Duban Mahaukaci,da Kyar Ya
Hadiye Wani Yawu Daya Cikamasa Makogwaro,yanunawa
Yushau Kofa,tashi Ka Barmin Gida,,,,,,,,!,,

Nima Ina Da Malaminda Zan Nemo Yaimaka Rukiyar
Dankafi Ta Bukatar Rukiya,,,
yushau Yai Funfurus Yakitashi Sai Shi Alhjin Yamike To Ni
Barina Barmaka Dakin
Kafin Yushau Yai Magana Tuni Ya Fice Danshima Ya Mike
Jiki A Sanyaye Yana Kokarin Ficewa Zuciyar Sa Na
Karkatar Dashi Cewa Kawai Yadage Ya Nemo Kan Ruma
Dakanta Inta Kawo Wa Alhji Maganar Komen Ai Bazai
kiba,
***********
Kwanaki Uku Da Suka Biyo Baya Mahaukacin Masoyi Ya
Bace A Rayuwar Ruma Ta Zahiri,wato Ba
Bushi A Sakonninsa Kuma Ba Bu Shi A Zahiri Kamar Yadda
Ya Billo A Matsayin Direban,dayakai Ta Gidan
Atika Amma A Badininta Yananan Yana Ninkaya,wuni Da
Kwana Yana Shige Da Fice A Zuciyarta Mai Wassafa
Kamaninsa Tanakara Kawata Wa kanta Shi,abuna Biyu
Kuma Tana Canke,canken Mutum Ne Shiko Aljan Sai Abu
Na Uku Tana
Tunanin Koma Waneneshi Wato Mutum Din Dai Ko Aljan
Dinshine Wannan Nazifi Muhammad Daga
Milkyway,sai Abu Na Karshe Shine,tanason Ganinsa A Fili
Rayuwarta Ba Irin Yanzu Daya Ke Kan Katangarta
Ba,kowace Irin Rawa Zaitaka A Fili Saita Cika Kanta
Tsakar Dare Ana Gobe Sunan Jaririn Atika,bacci Ya
Kaurace Mata Fau-fau Bayan ta gama Laluben
Mahaukacin Masoyi A Dukkan Kafar Daya Taba Lalubota
Bata riskeshi Ba,kama Daga Kiran Waya Akwatin Tura
Sako,social Network Da Sauransu Amma Shiru Ba Bu
Alamar Shi,da Bacci Ya Kaura
Cewa Idanta Sai Gata A Zaune Tanakaranta Wasikar
Jaki,kamar Daga Sama Wayarta Tayi Tsuwwa Cikin Razana
Da Barin Jiki Ta Wawurota Amma Sai Taga Hafsat
Damamaki Ta Daga Da Sauri Ko Sallama Batai Ba Hafsat
Lfya?
Cikin Doki Ta Ce Lfya Kalau Nakasa
Jiran Wayewar Gari Da Tsegumina Meyafaru?
Ruma Tatare Ta Cikin Doki Hafsat Ta Ce Sani Munafikine
Yasan Abubuwa Dayawa Dangane Da Mutuminnan,
Wanne Mutumin?
Hafsat Ta Ce Harkin Manta?
Mahaukacin Masoyi Mana Sai Ga Ruma A Tsaye Cikin
Tsananin Rudani Ta Ambata Da Gaske?
Yanzu Dama Canda Sa Hannun Sani Abinda Mutumin Nan
Kemin?
Hafsa Tatare Ta Cikin Sauri Ko Daya Satin daya Gabata
Shima Yasani Ruma Ta Sauke Kakkarfar
Ajhyar Zuciya Innalillahi Wa Inna Ilai Hirajiun To Mutum
Ne Ko Aljani?Kuma Meye Takamar Sa?
Hafsat Na Shirin Amsamata Sani Ya Karbe Wayar Ya Ce
Haba Shekara Uku Ba Bu Aure Wasane?
Kin Manta Cewa Katon A Addancin Ne Ka Bugowa Amare

Waya Tsakar Dare Irin Haka Ko Baki Duba Agogo bane?
Su Waye Amaren Waiku?
Tafada Cikin Zolaya Tare Da Jin Ciwom Yayankemata
Samun Haske Akan Majanuninta Sani Ya Ce Mu Mana!
Saida Safe Kafin Ka Ajiye Saika Amsamin Tambayar
Danaimata Sarkin Kulle Kullue Kanaganin Ana Neman
Kasheni Da Raina Amma Ashe Kaine Mai Bada
Gudumawa,saiki Hau Duro Ki Fada Ya Ce Cikin
Zolaya Yakashe Wayar Gabadaya,tafada Gado Tana
Ambatan Allah Wato Mahaukacin Masoyh Mutum Ne Ba
Aljani Kamar Yadda Tayi Tsammani Ba Indai Sani Yasanshi
To Ta Tabbata A Duniyar Su Ta Mutane Yake To Amma
Tayaya Yakemata Sidda Baru?
Tajima Tanakokarin Amsa Tambayar Amma Takasa Saita
Hakura Ta Kamo Tashar Wadda Ta Tarar Da Shiryayyun
Wasu Tambayoyin Ba Bu Amsa Wato Mene Ne ManuFar
Sa Akanta?
Yana Da Masaniyar Cewa Ita Sikila Ce?
Kamar Amsa Ga Tambayoyinta Sai Ga Wani Kira Daga
Hafsa Da Sauri Ta Amsa Ta Ce Yi Saurin Amsamin Kafin
Kafin Sani Yadawo,cike Da Zolaya Hafsa Ta Ce Aiyana Kusa
Kwalar Rigarsa Naci Ya Sallama Na fada miki Wani Abu
Daya Da Zai Kwantar Miki Da Hankali
Inajinki,
hafsa Tai Kasakasa Da Murya Ta Ce
Mahaukacin Masoyi Wato Nazifi Muhammad Mutum Ne
Kuma Da Gaske Mahaukacikine A So,yayi Nisa
Fiye Da Yadda Kike Tsammani,kuma A Nawa Tsammanin
Ba A Ta Ba Sonki Kamarki Haka Ba Rumaisa"u
Karyakike Hafsa,ruma Tafada A Fusace Cikin Sauri Maitafe
Da Kuka Mai Tuna Baya Ni Ban Taba Wani Kamar Auwal
Ba,kuma Ban Yarda Za A Sami Wanda Zaiso Ni Fiye Da Shi
Ba Tanason Zarcewa Da Kuka Hafsa Ta Tareta Cikin
Rudani Rage Kukan Karki Janyo Hankalin Iyayenki Gobe
na Sha Luguden Fada,duk Da Tuntuni Maganar Taje
Kunnen Alhji,rumaisa Tanemi Dauke Numfashi Cikin
Rudani Amma Kafin Ta Tanka Hafsata Ta Rigata Indai Za A
Sami Mai Son Naki Zuciyarki Ta Yarda Da Haka,ba Wai
Angama Samun Mai Sonkine Kwata Kwata Ba,kidan Bude
Wa Wannan Dan Tahalikin Zuciyarki Kadan Yasami Guri
Ina Mai Tabbatarmiki
Lokaci Kadan Zai Gawurta Harki Gane Nisan Fifikonsa Da
Au...
Ke Tafi Can Ruma Tafada A Fusace Ta Kashe Wayar Cikin
Zafin Zuciya,kwana Tai Safa Da Marwa Da Rashin
Barci,saboda Damuwa Da Rikita Yajanyo Mata Wani
Matsananchn Ciwon Kafa Da Misalin Karfe Takwas Na
Safiyar Ranar Inda Ciwon Kafa Da Misalin Karfe Takwas
Na Safiyar Ranar Inda Ciwan Yadinga Shan Sharafinsa Har
Fiye Da Awa Daya Saida Kowa A Gidan Hankalinsa Yatashi
Ita Ruma Mai Ciwon Kuka,mairo Mai Tausayi Kuka Hajiya
Da Alhji Da Mubarak Ba Bu Wanda Hankalinsa Ke Kwance

Har Saida Ciwan Ya Lafa Alhji Yatafi Da Ita Asibiti,daga
Asibitin Ne Kuma Taki Yadda Amayarda Ita Gida Saidai
Mubarak Yakaita Gidan Suna Kawah Duk Da Kuwa Bata
gama Wartsakewa Ba Ana Dai Abinda Yafi Ciwo Ajikinta
Shine Zuciyarta Dake neman Gazawa Da Lissafin
Mahaukacin Masoyi,hayaniya Bata Barta Ba Dole Atika Ta
Waremata Falon Mijinta Ta Kwanta Jefi Jefi Wasu Kanshi
Go Su Dubata Balaraba Yayarta Ta Shigo Ta Cemata Wai
Wanene Wancen Da Sani Keta Faman Nunawa Mutane A
Matsayin Mijinki?
Abin 'yar Hakane Ruma Kinyi Miji Ko Albishir Ba Bu?
Cikin Rudani Ruma Tatashi Zaune Ban Sanshi Ba
nima,balaraba
Takalleta Sororo Har Nawasu Lokuta Ta Ce Dagaske?
Ruma Takoma A Kasalce Ta Kwanta Balaraba Tamike Cikin
Sanyin Jiki Ban So Haka Ba Gaskiya Naso Ace Kinsan
Shi,kuma Kece Kika Bashi
Damar Yazama Mijinkh Saboda Nutsuwar Sa Da Kalamar
Sa Dakuma Abinda Bani Kadai Na Hango Ba Wato Tarin
Kaunarki Atare Da Shi,duk Kwakwar Balaraba Takasa
Fahimta Abinda Ruma Ke Rayawa Aranta Balaraba Tafara
Tfya Tana Cewa Nadanyi Hira Dashi Har Na Fahimce Shi
Dan Hadejane,kuma Mazaunin Abuja,yaushe Kakayi Hirar
Dashi?
Cikin Hanzari Ruma Tafada Tana Dagowa Balaraba Hannu
Alamar Dakatar Da Ita Barin Falon,saboda
Kasalar Gangar Jikinta Yanzunnan Balaraba Ta Amsa ,au
Ance Ma Nasanarmiki Zai Shigo Ya Dubaki,cikin Kuluwa
Ruma Ta Amsa Ba Bu Laifi Ta Koma Ta Kwanta,balaraba
Ta Fice Daga Falon Batare Da Ta Canka Dalilin Kuluwar
Ruma Ba Duk Da Tana Tunanin Ce Wa Marigayi Auwal Ta
Tuna Ruma Takasa Cankar Inda Zuciyarta Fada Dokin
Gani,fargaba Kojin Kallan Mahaukacin Masoyi?
Yau Kuma Yanzu?
A Haka Tajiyo Takun Sawaye Tare Da Muryar Sani Yana
Karadin Hirar Sa Ta Dora Idanta Kir Akan Kofa
Cike Da Dokin Ganin Inta Ga Nazifi Muhammad Kar To
Taga Kafar Sa Da Kofato Dan Kuwa Idanta Na Kan Inda
Kafafunsa Zasu Duro,sani Ne Yafara Shigowa Cikin
Yanayinsa Na Faraa Da Kuzari Kamar Koda Yaushe Nazifi
Biye Da Shi Cikin Matsananciyar Kasala Mai Alamun
Tasowa Daga Zuciya,ba Kamar
Ko Yaushe A Ganin Dataimasa Cikin Kananun Kaya Ba,yau
shiGar Manyar Kaya Yayi Na Shadda Ruwan Toka Yar Ciki
Da Babbar Riga Bata Damu Da Zolayar Sani Ba Ahankali Ta
Dauke Idonta Daga Kallansa Zuwa Wani Wajen ...
.
Dan Aunty
Al-Hada Hada Hausa Book stories
GORAN DUMA (P 58)
.
.

Sani Yadubi Ruma Wannan Wace Irin Tarba Ce?
Karkuma Ki Kalawa Ciwo Dan Fuskarki Tanuna Da
Sauki,takalli Sani Garau Ta Shiga Gyara Mayafi
Wanda Ta Lullube Kafafuwanta Dashi Tun Lokacin Dataji
Takun Shigowar Su Dahaka Ta Bar Tambayar Sani Tabi
Ruwa,hakan Yasa Sani Da Nazif Sukai Murmushi Nazifi Ya
Ce Ankuma Ce Tun Tuni Kina Dokin Ganina Ni Ma Ban
Zaci Wannan Tarbar Zansamu Daga Gareki Ba Sai Yanzu
Ta Fahimci
Kwakwalwarta Ta Tsaya, sani yatafi yabar Ruma da nazifi
alamu yanuna a tsorace take tundaga fitar sani daga falon
nazifi ya mike
cikin kwarin guiwa a tsorace cikin zafin nama sai gata a
zaune tana
kallon kofar cikin Gyara wuyar Riga yakaraso tsakiyar
falon ya zauna kan teburin dake girke a tsakiyar dakin
Wanda ya basu Damar kallon juna ruma cikin tsananin so
da farin cikin ganin masoyin Ruma tafara kauda kai cikin
cin magani yace najima INA kaucewa haduwa dake idan
kina cikin rudu ALLAH bai nufa ba amma dai nayi nasara
ba wani na ya rudaki ba nida kaina na rudaki yatsayar da
maganar saboda yaga bakinta na motsi alamar zatai
magana amma yana rufe baki sai yaga ta hadiye yaya jiki?
Nanma kallonsa kawai tayi ta kauda kai yace nasan
abinda yajanyo fushinnan lokacin da kika so ganina naki
ki ganni ba fushi ya dace kiyi ba Ruma kamata yai kinemi
ba'asi cikin karkarwar murya tace wa yace maka inason
ganinka?
kaitsaye ya amsa cikin daga gira kintashi daga kano
takanas zuwa abuja din kiganni cikin tilastawa kai
wani fushin face duk yafarune cikin kuskure Yanzu
najanye saboda haka kana iya tafiyarka idan kazone
domin na ganka takaj
da raunanniyar murya yace badon kiganni nazoba nine
nazo don na ganki domin nikadai kesonki nakuma cika
son kai Dan banbaki damar kisoni ba a tsammanina nawa
son ya wadatar tace masa
wannan bayanin naka sunyi hanzari domin kai yakamata
nafara sani ba kalaman soyayyarka
ba amma idan kagama boye boyen kenan
nagama yafada da sauri shiyasa nacemiki nafiye son kai
na boye mini kaina yayinda na zurfafa a sonki har nakai
bigiren da raina kejin in an raba shi da sonki bazai iya
cigaba da nunfasawa ba nantake kwalla tacika mata ido
domin maganarsa tatuno mata da
auwal babu alamun shakku ta amsa masa rashin masoyi
baya kisa dayanayi dabaka ganni a Raye ba har ka soni.
nazifi ya dauke wuta dad fuskarsa da gangar jikinsa sun
nuna damuwa kishi yajima cikin kallon shimfidar falon
kamar yadda taciga ba da kallon talabijin zuciyarta a
auwal batare da nadamar maganar dataiba said a ta
hangi inuwar nazifi a tsaye tajuyo ta dubeshi lokacin

yakusa kofar fita falon tagama yanke kaunar sai fice baice
komaiba amma sai ya jiyo a sanyaye yace nasan ba zafafa
cimma burina ne yasanya nijin cewa ALLAH ya
karbi ran Auwal ya barmin me ba don nafishi
cancantane.na fishi sonki na kuma fishi cancantar zama
mijinki RUMAISA'U sikila..,.
watakila sai lokaci yayi zaki fahimci hakan tai shuru tana
kallonsa da alama kamar laluben ta inda yafi Auwal
cancanta take
zanwuce masaukina yanzu badon zantakura mikaba
danazo gidan yau da dare gobe don inanan kano har
safiyar jibi itadai kam hawaye take face masa jimana
tareda karfin halin mikewa tsaye yajuyo ya kalleta tadanyi
kamar xatafadi a
kokarinta na gyara tsayuwa da sauri yadaga mata hannu ,
a, ah koma ki zauna ta koma ta xauna tace maasa kafin
goben inasan sanin kai waye I na tsammanin a duniya
babu abinda ya shige min gaba kamar son sanin amsar
wannan tambayar akwai wani suna dazan sake amsawa
ne banda
MAHAUKACIN MASOYI?
wannan sanin yakamata ki rike ba na tsammanin
zakisami Wanda yafishi da gaske ne ni MAHAUKACIN
sonkine ba wannan nake tambayaba ai tundazu akan
haka muke magana tambayata anan itace ta wace hanyar
kake shiga zuciyata?
tawace idon kake kaina hatta a lokutan da nakasance
nesa da idon kowa yakada kai yana dariya au hakanefa
duk naji zarge zargen
dakikemin wajen sani zargi ne wato ba gaskiya bane?
ta tambaya cike da mamaki kwarai da gaske ya amsamata
shikenan saika tabbatarmin da gaskiyar yanzu.
ya CE a irin wannan lokaci n dakika cakuda min zuciyata
da takaici ?
INA girmama Auwal don darajar zuciyarki tasoshi ni
kuma masoyin kine ke da komanki amma girmamawar
taki shafe kishina ya fice ya var falon tunbayan fitar
MAHAUKACIN MASOYI Gidan sunan yaimata zafi tatashi
tashiga cikin jamaa inda ake ta kayakaya murna da
daukan hotuna kozata manta amma hotunan
MAHAUKACIN MASOYI a cikin zuciyarta musamman
daidai lokacin da yake cewa NASAN BA ZAFAFA CIMMA
BURINE YA SANYA NAJI CEWA ALLAH YA KARBI RAN
Auwal YABAR MINKE BA DON NAFISHI CANCANTANE
NAFISHI sonki KUMA NAFISHI CANCANTAR ZAMOWA
MIJINKI RUMAISAU sickle INA GIRMAMA Auwal DON
DARAJAR ZUCIYARKI TASOSHI NI KUMA MASOYINKINE KE
DA KOMANKI AMMA GIRMAMAWARKI TAKI SHAFE
KISHINA
wadannan zantukannasa sunki bacewa daga zuciyarta da
alama duminsu ne yake ta faman kyankya sar son
ubangidansu wato MAHAUKACIN MASOYI a kirjinta

ta yarda ya iya so tunda ya iya sonta ita da son dataiwa
waninsa AUWAL kuma kishinsa ya na nan daram amma
baya runtse masa I do ya ya mayar masa da sonta
kiyayya ,tabbas ko yayane zai iya
zama waziri a fadar so da kaunarta yayinda auwal yake
sarkin sarakuna ,
##****************
Dan rumaisau yushau ya isa gidan sunan da gamma da
sunan wai yaje daukar sumoli wadda ta mayar da kanta
amarar biki da karfi da yaji yayi katari an kwakolo
rumaisau da kyar zuwa wajen daukar hotuna a harabar
gidan sai gashi dayin abinda babu shi a cikin tsarinsa
wato shiga sabgar bikin
mata ya rungume hannu ya tsaya kusa da kanin mijin
atika yana satar karewa Ruma kallo Wanda kaf Cikim
matan dasukazo sunan sinfita daukan ado amma a haka
it'a kadai kallon ta ke buga masa
zuciya musamman daya hangota da sumoli fara tas kuma
ko aljana ta shafa mata lfya wajen caba
kwalliya NASA wasane baidau kallon Ruma kadai buga
masa zuciya ba komai daya shafeta ma buga masa
zucuyar yake ba said a kunnensa ya kwaso masa muryar
Hassana NA cewa rumaisau amma dai baki da kirki tun
safe kin kulle a daki har mijin naki yazo ya tafi ai kamata
yai Ku kafa tarihin kwasar
hotuna a ranarnan,,,,
acikin rudu YUSHAU yake amma kunnuwansa sunjiyo
amsar ruma tace fadar miji a baki baya muku wuya babu
Wanda ya danka min sadaki amma Ku daga ganin sarkin
fawa sai miya tai zaki hassana tabar gurin tana amsamata
nasan yayi nasara ya gama din mai irin fuskarsa da
zuciyarsa sun cika saurin nasara,
fiye da awa daga YUSHAU na jinyar zuciyarsa da Neman
mafita har SUMOLI tagama sallamarta tasameshi a mota
babu magana kawai yatashi motar ya fice sumoli TAGaji
da shan kamshi Dan haka ita ta tankashi tana taunar
cingam ranka ya Dade lfya kuwa ?
lfya mekika gani?
saida ta jero kwa say uku cikin gwaninta tace naganka a
firgice ne sannan yinin yau kadai naga kakara
ramewa,badon kaidin kai bane aidanakaika asibiti ko
ruwa adan samu daura maka Leda guda inka yarda
nakaika gurin kawata
FAUZIYA D SULEMAN takara mka nasan kyauta zataimaka
in kudin kakeji
yushau Yasan Iskancin tane Ya Motsa Amma Tunda Bai
Shirya Masa Ba Sai Ya So Basar Da Maganar Da Cewa
Inatare Da Hayaniyarki Aina Bar Kiba Sumayya Ke Ai
Gashi Nan Kina Shirga Kiba, Wallahh Tallahi Ba Bu
Ruwana Tsabar Ma makon kane Yake
Ramar Da Kai Ni Din Ma Kibar Godiyar Allah Ce Ba Dan
Haka Ba Nasan Sai An Kirga Kashi A Kirjina Inya Ci Gaba

Da Takaici Yasan Sai Ya Haifar Masa Da Ciwan Zuciya
Sumoli Bata Damu Ba Dan Haka Yaja Bakinsa Yai Shuru
Daganan Ta Ci Gaba Da Zuba Har Ta Cemasa Yau Kusan
Sati Biyu Kenan Bata Ga
Aladarta Kuma Tana Jin Kasala Da Tashe Tashen Zuciya
Kila Cikine Tare Da Cin Alwashi Na Rantse Da Allah Nima
Ina Haihu Saina Yi Wadannan Bidioin Andaina Barina A
Baya Tayi Jiran Amsa Harta Kule
Ta Cemasa Haba Malam Kokana Da Yakinin Cikinannan In
Natashi Kwado Zan Haifa Aikataya Ni Murna Ko Na Ganin
Idoce Maimakon Haka Sai Cin Magani Kake Yayi
Murmushi Ya Ce Kece Da Wauta Wallah Tun Kafinki
Tabbatar Da Cikin Harkin Fara Lissafin,,
tatareshi Tana Dariya To Meza A Fasa?
Ya Ce To Allah Ya Inganta Amma Dai Kidaure Ki Haifo
Nimiji Mai Kama dani....
.
Dan Aunty
GORAN DUMA (P. 59)
.
.
summaya Tazaci Yabo ne Cikin Tuntsira Dariya Ta
Ce,insha Allah Namiji Zan Haifo Lafiyayye Ammame
Kama Dani Don Nafika Kyau Ya Kada Kai Kawah Da Alama
Hankalin Nacan Ga Ruma Sumoli Ta Ce To Waimeyasa Ka
kE son Namiji?Bawai Namijin Nafiso Ba A A Kece Kawai
Har Abada Banaso Ki Haifo Mace Dan Me?
Cikin Doki Da Tashin Hankali Ya Ce Dan Banason Ki Haifi
Mace Ta Gado Halinki Na Zamo Kullum Cikin Kiran
Mubarak Ya Daura Mata Aure In
Kuma Ba A Yi Sa'ar Maikai Zuciya Nesa Dazai Saketa Cikin
Sauki Ba Saiya Nadamata Na Jaki Kafin Ya
Sakota Kai Dan Giya Ne Ma Nasan Saita Janyo Abinda
Kullum Zai Sa Ya Yanke Tada Muka,...
sumayya Tai Mugun Zuwa Wuya Danhaka Takasa Maida
Martani Har Saida Tagansu A Tsakiyar Gidansu To Allah
Yasa Namijin Kar Ya Biyo Halinka Wallahi Har Nafara
Tausayama Matan Dazasu Aure Shi A Waje Acan Amma
Dasun Shigo Ko Gizago Da Mammako Ya Ishesu Oho Dai
Yafada Cikin Dariya Sannan Yajuya Yafice Daga Gidan A
Guje Yana Dariya Yanufi Masallaci....
Yushau Kaitsaye Bayan Dawowar Sa Daga Sallar Ishai
Kaitsaye Yakoma Gidan Suna,ba Bu Yadda Atika Batai Da
Ruma Ta Zauna Ta Kwana Ba Amma Taki Yarda Haba
Aunty Atika Menene Bambamcina
Da Hafsat Ita Bakice Ta Zauna Ta Kwana Ba?
Cikin Raha Ta Cema Atika Kowa Na Dariya Atika Ta Kada
Kai Babu Bambamci Sadakine Kawai Ba Miko Waliyyai
Sun Daura Auren Ba,wato Yadda Take Da Kifinta A Gora
Haka Kike Danaki,
oho Kuma!Ruma Tafada Cikin Dariya Ana Haka Sai Ga
Mubarak Ya

Shigo Yana Wata Dariya Wadda Tasha Bambam Da
tasu,ruma Ta Nuna Masa Kofa Karka Zauna Muje
Ka Kaini Gida Naga Aunty Atika Ta Dage Sai Ta Mayar Dani
Arha,,,
mubarak Yatareta Yana Dariya Ya Ce Ai Bata Kai Yaya
Yushau Ba,shi Da Duk Ma Yakeson Siyenki Baki Ga
Fa,kamar Zai Rushemin Da Kuka Yake Rokona Na Rokeki
Da Girman Allah Kifito Ki Saurareshi,ruma Na Takaici Su
Asiya Na Shewa Asiya Ta Ce GORAN Ruma Fa Manyan
Kamu Ya Yo Guda Biyu Dazu Ya Kamo TIGER SHARK
YANZU KUMA YA KAMO KAWARA Dakin Yafara Gaurayewa
Da Dariya Hafsat Ta Ci Magani Dazu Harda Kwanciya
Akasa Amma Dai Aunty Asiya Kin Iya Yanka Lasa Nawa
Tiger Shark Zai Wa Kawara?Yaya Yushau Ne Ya Zama Haka
A Wajenki?
Suna Ta Dariya Kamar Abin Arziki Maimuna Tarike Hannu
Ruma Kamar Abin Kirki Tanajan Ta Zuwa Kofar Daki Allah
Sarki Wallahi
Kawaran Can Ya Fara Bani Tausayi Jeki Ganshi Ko Na 'yan
Mintunane, Itakanta Ruma Sai Suka Bata
Dariya Ta Yafito Mubarak Tana Cewa Zo Mu Wuce Daga
Nan Mubarak Mubarak Yai Dariya Ya Ce A,a Ki Daije Anti
Kawararnan Mu Karfasa Ta Ke Zame Mana Ba Muya Ta
Bude Kayar Baya,ruma Ta Fice Ta Bar Su Cikin Rashin
Kwarin Guiwa Dajin Takaicin Shi Ga Hanci Da Kudundune
Da Yushau Kemata Tasameshi Tsaye Jikin Motar Sa
Mubarak Yasanar Dani Kana Nemana Baiji Dadin Yadda
Ta Daure Fuska Ba Dan Haka Yajima Baice Komai Ba
Yanumfasa Ya Ce Yaya Gajiyar Taro?
Alhmdlah Ta Amsa Masa Cikin Kokarin Tilastawa Kai
Dazun Har Natafi Bamu Gaisa Ba Duk Da Cewa Takanas
Domin Na Ganki Nazo,ta Dauki Maganar Nasa Rainin
Hankali Amma Cikakken Nata Hankalin Ya Shanye Nuna
Bacin Rai Saita Ce Hakane Tokasan Komai Sai Allah
Tabbas Yafada Yana Kokarin Dorawa Amma Saita Rigasa
Zarcewa Yanzu Kuma Dare Yayi Sai Wani Jikon Kenan?
Muzamu Wuce Gida Kedawa?
Cikin Rashin Jindadi Nida Mubarak ne,in Ba Bu Damuwa
Me Zai Hanaki Zona Kaiki Gidan?
Akwai Wasu Muhimman Batutuwa Danakeso Mu Tattauna
Dake A Hanya Tadanjima Alamar Ranta Baisoba,kome
Kika Gani?
Kaje Kawai Ma Hadu Wani Jikon Har Waya Nayi Wa
Mubarak Yazo Daukana Bazaiji Dadi Ba Idan Na Bar Shi
Yakoma Shi Kadai Indan Shine Barina Nemi Afuwa Kafinta
Tare Shi Har Yafara Magana Da Mubarak A Waya Afuwa
Mubarak Zan Wuce Da Ruma Zuwa Gida Kataho Kai Kadai
Ya Budemata Kofa Ya Zagaya Bata Da Zabi Dole Ta Shi Ga
Motar Zuciyarta A Kuntace Yushau Yaita Kalatarta Da Hira
Dazata Budemasa Damar Gabatarmata Da Kudurinsa A
Saukake,amma Ruma Tai Fuska Kalmominta Tamkar Sai
Ya Siya Kamar Yadda Dariya Da Murmushinta Sukenuna

Karara Sunfi Karfinsa Saida Yaga Haza Sannan Yai Wa
Shirin Nasa Kutse
Ruma Ina Muka Kwana?
Dame Fa?
Yajima Yana Tunani Wajen Kirkirar Kalamai Masu Dadi
Wanda Baima San Ya Iyasu Ba Bansan Komai Ba A Yanzu
Sai Sonki RUMA KOMAI NAWA RARRAUNA NE SABODA SO
KARFIN GUIWATA KADAN NE SHINE GANIN ALLAH YA
JINKIRTA MIKI AURE DOMIN NA DAWO MIKI A MATSAYIN
MASOYI
MAI SHAFE KOWANNE IRIN AIBU NAKI,
ya Tsagaita Amma Shiru Kakeji Saidai Kawaicintane Kawai
Ya Boye Mugun Takaicin Da maganganunsa Suka Kunsa
Mata,musamman Daya Tuno Wani Kurarin Zawarci
Dayaimata A Can Baya Kafin Ya Saketa Wanda Ya Tabbatar
mata In An Sake Bazata Auru Ba Sai Shi Daya Saba yimata
Alfarma Yadawo Zai Sake Yimata Wani Alfarma Ta Kada
Kai ta Sake Amma Ta
Hadiye Komai Saidai Ta Bar Hawaye Nashan Sharafinsa A
Fuskarta Dayake Fitilar Motar Bata Cika Haske Ba Kuma
Wani Kaso Na Hankalinsa Nakan Tuki Bai Lurada
Hawayenta Shurunta Kuma Yakara
Masa Karfin Guiwa Ci Gaba Da Magana Dan Ki Tabbatar
Da Cewa Da Gaske Nake Duk Surukutar Dake Tsakanina
Da Alhji Kwanakin Uku Da Suka Gabata Na Nade Kunyata
Najemasa Da Maganar Yayi Farin Ciki Kwarai Saidai Ya
Bani Damar Na Nemi Hadin Kanki A Ganinsa Wannan Ne
Horo Gareni Bisa Kurarkuren Dasu ka faru, Mu Dauko
Hamida Mu Rike Abarmu Zan Sake Rantse miki Da Allah
Na Shiryawa Dukkan Lalurarki Ke In Takaita Miki Ma Har
Na Fara Nemar Miki Magani,
tun Lokacin Daya Ambaci Zuwansa Wajen Alhji Ta Watsar
Da Kallon Windon Motar Ta Koma Kansa Cikin Dauke
Numfashi Bata Kuma Kara Fahimtar Maganganunsa Ba
Tun Bayanda Ya Fadi Sharadin Alhji,tayi Shakkun
Sharadin Wanda Ke Cike Da Danne Hakki,wanda Tana
Kara Jaddada Shakkar In Zai Fito Daga Alhji,a Hankali Ta
Dauke Kai Daga Kallonsa Ta Cemasa Nayi Farinciki Tunda
Alhji Ya Bayarda Damar Yarda Tana Hannuna Dan Haka
Ina Mai Baka Hakuri Tare Da Tunatar Dakai Ni Da
Ayyukana Bamu Sauya Ba Ciki Har Da Zuciyata Mai Bijiro
Da Kudirori Ta Sanya Gangar Jiki Aiwatarwa Lallai Kafin In
Aureka Na Zaci Banida Zabinko Mawazan Aura Tunda Na
Rasa Wanda Zuciyata Keso Amma A Yanzu Na Fahimci
Aure Ba Hakkin Kaina Ni Kadai Bane,lallai Ko Na Sarayar
Da So A Cikinsa Dole In Nemo Wa 'ya'yana Da Zan Haifa
Lafya Da Farinciki
Bangane Abinda Kike Nufiba?
Tawa Rayuwar Baata Da Sauran
Tanada Na Zuci Ko Na Gangar Jiki Amma Dolene Inyi Aiki
Tukuru Dan 'ya'yan Dazan Haifa Su Zamo
Masu Lfya Ba Irina Ba Cikin Matakin Kuwa Harda Hakura

Da Aure Idan Ban Sami Mai Nau'in Jinin Dazan Haifi Masu
Lfya Ba,
sun Isa Harabar Gida Yajanyo Wata Leda Dama An
Fadamin Kune Kuke Daurewa Aljanu Gindi Ta Hanyar
Manta Kaidinsu Kuyi Tamika Wuya Ga Asibiti, Cike Da
Mamaki Wato
Mai Hali Duk Inda Ya Juya Baya Sauya Halinsa Ko Ta Ina
Yushau Ya Bullo Saiya Nuna Shi A Baude Yake,fitsarin
Rakumi Ne Ance Maganin Sikilane Karafiyan Idankin
Gama Shansa Zanzo Muje Amiki Rukiya Ba Gaggawa Nake
Ba Ruma Inkin So Saikin Warke Garau Zaki Koma Dakinki
Koda An Daura Auren
Tuni Ruma Taiwa Kwalbar Rikon Tsantsani Shidai Kallan
Mahaukaci Karafiyan Takemasa Kamar Magani Karfiyan
Din Daya Kawo Mata
Kinyi Shuru?
To Nagode Da Kokari Allah Ya Bar Zumunci,tatashi
Zatafice Daga Motar Ya Ce Baki Ce Komai Ba Ai?
A Lalace Ta Ce Da Me?
Game Da Hujjojin Dana Kawowa
Hanzarinki Na Nema Wa 'ya'yanmu Makoma Mai Kyau
Takarasa Ficewa Mujinkirta Tattaunawar Har Saina Gama
Maganin Munga Abinda Haliyai,to Ba Bu Laifi Yafada Cikin
Karsashi Dajin Farincikin Ruma
Tadawo Rayuwar Sa Tagama Indai Wuyar Ciwo Shine
Kasa Gano Maganinsa Sukai Sallama Yafice
Tashi Ge Gida Kulallen Kanta Dauke Da Yushau Tsohon
Miji,tare Da Mahaukacin Masoyi Sabon Miji,
Daidai Lokacine Alhji Ya Saki Labulen Falonsa Shima Nasa
Kan A Rude,shine Yake Kishin Ruma Da
Rayuwarta Ita Bata Kishin Kanta Harda Bazata Iya Gane
Yushau Dan Ta Adda Bane A Rayuwarta,
bayan Share Dare Cikin Raba Daidai Tsakanin Bacci Da
Ido Biyu Bayan Sallar Asuba Tasamu Ta Runtsa Karfe
Takwas Da Rabi Mairo Ta Farkar Da Ita Da Zummar Ta
Amsa Kiran Alhji..
.
Hhhh.. Wai dan ta adda?
Lallai kuwa Yushau dan ta adda ne Naziri kuma dan
Kidnapin.
Dan Aunty kuma Masoyin Ruma...
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 60)
.
.
Tun Data karasa Farkowa Ta Shiga Rudani Da Fargaba Dan
Tana Da Yakinin Banza Batakai Zomo Kasuwa A Gurguje
Takarasa Shiryawa Ta Iske Shi Afalonsa Yadda taga Fuskar
Alhji Kuma Ya Kara Bata Tabbacin Da Sauki Lfya Suna
Gaisawa Bai Tsaya Bata Lokaci Ba Yace Jiya Naga Yushau
Yakawo Ki meke Tsakaninku?

Kayan Cikinta Suka Kada Ba Komai Alhji Ko Dai Bakyaso
In sani?
Rauninta Yasanya Alhji Ya Rage Gizagon Fuskar
Sa,kwanaki Yazo Yasameni Da Maganar Yanaso Ya
Mayar Da Aurenki Atakaice Bamu Rabu Ta Dadi Da Shiba
Sai kuma Abin Mamaki Da Takaich Jiya Sai Na
Ganku Tare Kila Kin Karbi Tayinsa Kenan Gaskiyar Magana
Abin Baiyin Dadi Ba Sam!
Ruma Taji Wani Irin Tausayin Alhji Ya Rufeta Ashe Sharri
Yushau Ke masa Daya Ce Wai Ya Amince Ta Natsu Kafin ta
Amsa Dan Bata Manta Tsakanin Da Da Mahaifi Sai Allah
Duk Abinda Za Ai Lallai Baikamata Ta Wuce Gona Da Iriba
Muna Shirin Tahowa Gida Da Mubarak Ajiya Yazo Yanemi
Alfarmar Dan Allah Inzo Yakaini
To A Hanya Dai Ya Nuna Min Manufar Sa Kamar Yadda Ya
Sanar Dakai Amma Ban Amsa masa Da
Komai Ba Cike Da Doki Alhji Ya Ce Yauwa Kinyi Kyan Kai
Dan Ni A Wajen Batun Komawa Auren Yushau Ma Sam
Bata Tasoba Wanda Hakan Yasa Har Nadanyi Miki
Karambani Ban Sani Ba Ko Dadi
Zaiyi miki Kokuma Daci Ta Dago Cikin Muguwar Fargaba
Meta Zata?
Wani Yaro Mai Hankali Da Mutunci Kuma Dan Babban
Gida Shekaran Jiya Nan Yazo Min Da Kokon Barar Aurenki
Ni Kuma Nai Masa, Har Yanzu Ta Kasa Dauke Ido Alamar
Dukkan Furucinsa Suna Sauka Inda Yakama A
Kwanyarta,anyi Masa Amanna An Bashi Auranta
Kenan,wanene Wannan Ya Dace Da Ita Zallarta Mai Amsa
Sunar Ruma Kuma Mai Dogon Numfashi A Matsayinta Na
Sikila?
Tambayoyinda Sukemata Yawo A Makogoranta Kenan
Amma Ta Tabbatar Bata Da Muhallin Furtasu Nayi Masa
Amanna Ai Ba Sadakinsa Na Karba Nakira Shaidu Ba
Ruma Kamar Yadda Na Fada Miki Hankalinsa Na Yaba
Dakuma Gidan Da Yafito Saikuma Tarihin Son da Yake
Miki Wanda Naji A Bakin Sani,,
Waye Shine?
Kaitsaye Ya Ce NAZIFI MUHAMMAD Aiya Cemin Kinsan Shi
Kamar Ta Girgiza Kai Cikin Rudewar Kwakwalwa Amma
Saita Cije Rudunta Yasha Sharafi A Kwanyarta Kadai
Muryarta Na Rawa Ta Ce, Nasanshi Daga Nesa,
shima Hakan Ya Cemin Inji Alhji Yafito Daga Hadeja Ta
Jihar Jigawa Daga Shahararren Dan Kasuwar Nan Alhji
Muhammad Hadi Da Mahaifiyar Sa Hassana Haifaffiyar
Kano Da Rano,yayi Digirinsa Na Daya Sanin Halayyar Dan
Adam Na Biyu Ya Karanci Kasuwanci Amma Daya
Bangaren Yanada Nasibi Sosai A Bangaren Na,ura Mai
Kwakwalwa Saiya Hada Taura Biyu A Baki Ya Ke Taunawa
Ji Da Harkokin Kasuwancin Mahaifinsa Da Kuma Nasa
Harkokin Na Aiki Karkashin Kamfanin Layin Waya A,T,S
Dakuma Shagunan Sayar Da Kayayyakin Da Suka
Danganci Sadarwa Daya Daga Ciki Shine Milky Way Cafe

Dake Abuja Ya Samarmin Ma Anan Ya Ganki Bayan
Wannan Yana Da Kamfanin Ginin Website Tare Da
Ma,aikata Shekarunsa Talatin Da Biyar Yataba Neman
Aure Sau Biyu Allah Bai Nufa Ba Dan Haka Ya Jingine
Maganar Auren Wadda Bata Tashiba Sai Akanki
Atakaice
Ta Ture Duk Wani Shi Ga Ukun Data Shi Ga Farinsani A
TariHi Amma Baimasa A Shige Da Fice Ba Wanda
Yake Bashi Damar Kama Da Aljanu A Ayyuka,kila Dukkan
Aiyukansa Ko Na Neman Aurensa Kawai Kila Matahaka
Matan Kan Kubuce Ciki Har Da Ita
Alhji Ya Ce Nayiwa Mahaifinsa Farin sani Haka Dai Yaita
Bata Tarihin Nazifi Ciki Harda Wahalar Da Mahaifiyar Sa
Ta Sha Wajen Haihuwar Sa Inda Dole Likitoci Sukaiwa
Mahaifiyar Sa Tiyata Aka Ciro Nazifi Wanda Daganan Aka
Ciremata Mahaifa Saboda Haka Nazifi Shine Danta Na Fari
Kuma Autanta Saida Mahaifinsa Yataya Ta Karajin
Alkunyar In Ya Kara Aure Zatai Tsammanin Haihuwa Yake
nema Har Zuwa Yau Bai Zubar Da Makaman Karar Nan
Tasa Ba
Ruma Wannan Halaccin Nasa Ma Yana Daya Daga Cikin
Abinda Nake Fata Nazifi Ya Gada Kisami Danshi Ruma,
ruma Tayi Nisa Zuciyarta Na Rage
Nauyi Tana Kara Mata Damun Fuskokin Nazifi Da Kallo Ba
A Mai Suddabaru A Waya Da Sakonnin Test Ba,a Fuskar
Da Alhji Kawai Yasanshi Dakuma Cuda Jiyanta Da Yau Mai
Auwal Da Yushau Sannan Goben Ta Wadda Nazifi Keson
Shiga.
Kije Kiyi Nazari Zaizo Yau Ku Tattauna Kuma Ba Bu Dole A
Ciki In Baimiki Ba Ko Ke Banason Ki Cuci Kanki Ki Karbe
Shi Bare Ni Nayi Miki Kuka,
TaCe masa Yasan Ni Sikila Ce?
Yasan Ni Bazawara Ce?
Yasanki Ciki Da Bai Kafin Yazo Neman Aurenki Alhji A
Yanzu Nasan Ba Kyan Hali Ko Na Asali Kawai Nake Nema
A Miji Ba Ina Neman
Nagartar Lafyata Ko Ta 'ya'yan Dazan Haifa,,tuni Na
Sakawa Raina Zuwan Mijin Da Zan Haifa 'ya'ya Masu Lfya
Ko Da Kuwa Cikin Jiran Mutuwata Zata Riskeni,
ban Fahimcekiba Tajima Cikin Girgiza Kai Da Rausayawa
Idonta Cike Da Hawaye Ta Ce Ina Nufin Ka Bani Sati Biyu
Na Tattauna Da Nazifi Tattaunawa Dangane Da Ciwona
Sannan Muje Asibiti Nasan
Matsayinsa In An Sami Akasin Da Lfyar 'ya'yan Dazamu
Haifa Zata Shiga Gararin Jihadi Ne Mucetosu
Ta Hanyar Hakura Da Auren juna In Kuma An Dace Nayi
maka Alkawari Sakeyi Maka Biyayya Akaro Na Biyu
Alhji Ma Yaji Hawaye Naneman Kwacemasa Na Gamsu
Insha Allah Ba Za Akara Samun Akasin Da Aka Samu A
Baya Ba,tamike Ta Bar Falon Daidai Lokacinda Wayar
Hannunta Ta Kad'a, Hello Akayi Shuru Da Alama Anajinta
Saita Sake Maimaitawa Rumaisau Nazifi Yakira Sunanta

Cikin Yanayin
Nutsuwa Da Kuma Damuwar Yadda Yaji Muryarta Tai
maza Tajanyo Natsuwa Na Am Barka Da Safiya
Barkanki Dai Yaya Naji Muryarki Kamar Kina Cikin
Damuwa Yadan Gitse Murya Ko?
Zuwa Yanzu Nasan Kinsan Waye Mahaukacin Masoyi
Kuma Waye Nazifi Muhammad To Don Allah Mu Ajiye
Game A Gefe Guda Muyi Abin daya Kamatarmu Ina Cikn
Rudun so Ruma Ba Bu Abinda Zai Warware Ni Sai Shiga
Zuciyar Wadda Nakeso Nasamo Aminci Kuma Naji
Matasayi Na Ina Sonki Ruma Karkiya Wasa Da Alamarina
Bokanci Ko Aljananci Datake Zata Masa Ya Dawo Sabo Ta
Ina Yasan Alhji Yasanar Da Ita Kansa?
Wannan Yasa Ta Tare Shi San Dataji Zaizarce Da Maganar
Abinda Ya Riga Yafara Samun Gurbi A Yuciyarta Wato
Sonsa Gyara zancenka Dai Nasan Nazifi Muhammad
Amma Har Yanzu Bansan Mahaukacin Masoyi Ba Yai
Karamar Dariya Ai Bakiso Ki Gani Bane,,to Ina So Insanni
Yaushe?
Duk Lokacin Daka Shirya,
Nasanar Dake Yau Kawai Nake Da Ita A Kano Kin Lashi
Lokatai Da Yawa A Hutu Cikin Rashin Kulawa Ta Ce Ba Bu
Matsala Muna Iya Daga Sanin Har Zuwa Lokacin Dazaka
Samu Lokaci Kai Tsaye Ya Amsa Ko?To Dama Nakira Kine
Inji Karfe Nawa Kika Shirya Zuwana?
Dazaka Zo Din Kakemin Lissafin Na Lashi Lokuta Saboda
Haka Zaka Buga Sammako Gobe E,h Ai Maganar Aurena
Zata Kawo Ni Ba Maganar Mahaukacin Masoyi Ba Ruma
Tadan Rausaya Kai Na Gajiya Da Yawo Da Hankali Inkaji
Wani Abu A Bakina Dangane Da Aurenka Malam Ai Ka
Kaddara Kawai Ba Daga Zuciyata Yataso Ba Ta Yaya Zan
Auri Mutumin Da Ban sani ba?
Au Yanzu Baki San Nazifi Muhammad Ba Alhalin Nasan
Alhji Bazaimiki Kwange A Tarihina Ba Ta Cemasa Nida
Mahaukacin Masoyi Nake Magana Yanzu Shine Kuma
Bansaniba,yaCe mata Shikenan
Kishare Mahaukacin Masoyi Ki Saurari Nazifi Muhammad
Kawai Ki Sanar Da Ni Lokacin Da Zanzo Don Allah
Karo Nafarko Datayi 'yar Dariya Shikenan Kazo Bayan
La,asar Ka Saurari Maganganun Fatar Bakina Wadanda
Suka Sha Bambam Dana Zuciyata Zaka Fara Sanin
Gaskiyar Zuciyatane Daga Ranar Dana Sanka A Hakikanin
Sunayenka Biyu Nazifi
Muhamma Da na Mahaukacin Masoyi
Nidai Bukata A Saurareni Yafada Yana Ci Gaba Da Dariya
Har Ta Kashe Waya Bai Ankara ba,
.
Pls. Amin uzuri rashin jina kwana biyu. Kauyen namu ne
wutar ta baci, babu caji...
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 61)

.
.
Katin Zamowarta Sikila Tagani A Hannunsa Wanda Da
Alama Tayi Murna Da Ganin Haka Ya Zauna A Kujerar
Kusa Da Ita Ya Ce Kinama Gamsuwa Da Sanin Dakika Yiwa
Nazifi Ko Kina Bukatar Kari?
Ruma Tadubi Shi A Takaice Cikin Yanayin Kasala Da
Sanyin Jiki Amma Rudu Ya Hanata Tankawa Dole Ta
Kawar Dakai Tana Dan Kebe Baki Na Rashin Madafa
Nazipi Ya Mike Ina Zuwa Ya Ajiye Card Din Itakuma Tana
Tunanin Miyaja Raayinsa Haka Bata Canki Adadin Lokaci
Ba Yadawo Falon Hannunsa Dauke Da Wasu Takardu Kai
Tsaye Ya Karaso Gareta Yamika Mata,hannunta Na
Karkarwa Ta Karbi Takardun Tafara Kirgasu Da Ido Guda
Uku,sannan Cikin Sa Wa Azarbabi Karfi Ta Fara Nazarin Ta
Farkon A Natse Dukkan Takardun Sunfito Daga Asibitin
Koyarwa Na Aminu Kano Takardar Farko
Ta Sakamakon Gwajin H,I,V NE Kanjamau Wanda Yanuna
Ba Bu Cutar, Batasan Abinda Ya Rudata Ba Da Sauri Cikin
Bugun Zuciya Tajanyo Takarda Ta Biyu Itakuma
Sakamakon Gwajin Ajin Jini Ce Blood Group Wanda
Sakamakon Yanuna Rukunin Jinin Nazifi B Ne Ganin
Hakan Yakara Mata Dokin Na
Ukun Wanda Takesa Ran Nan Makomar Aurenta Yake A
Takarda Na Ukun Indai Dagaske Nazifi Yasan Ita Sikila Ce
Da Gaske Ita Ce!Taji Gabanta Yasake Tarwatsewa Cike Da
Tsoro Tabi Takardar Da Nazari
Sakamakon Gwajin Gynotype Ne Kamar Yadda Tazata
Tako Yi Dokin Ta Tarar Duk Wani Nauin Da Ake Wa Duba
Da Nazari Tayiwa Takardar Nan Tayi Na Fargaba Tayi Na
Doki Tayina Shakka Tayi Na
Tabbatarwa Tayi Na Murna Sakamakon Gwajin Nazifi
Yanuna 'ya'yan Jininsa AA NE Akar She Ta Daga Ta Dube
Shi Cikin Zubar Da Hawaye,zuciyarta Da Kwakwalwarta
Basu Tattauna Bataji Sun Aiki Bakinta Na Yanke Hukunci
Mekake Nufi?
Tafada Cikin Rauni Wanda Hawaye Ya Taimakawa Nuna
Kai Nazifi Ya Zube Gabanta Cikin Kuzari Ya Dafa Hannun
Kujerar Datake Zaune Maimakon Hannayenta Da Inda
Halacci Su Suka Kamata Yadafa Shima Idansa Suncika Da
Kwalla Amma Ya Kyalesu Ya Bayyana Daga Makyankyasar
Soyayya Suka Taso Bana Rauni Ko Farin ciki Irin Nata Ba
Yazura Idonsa Cikin Nata Ya Ce Ina Nufin Nazifi Ya
Cancanta,,,na
Cancanta Ruma Kizo Mu Rayu Tare Tayi Baya Cikin
Tarairayarmu A Matsayin Ma Aurata Taimakon
Junane Ruma Ko Wannan Yakamata Kituna Inasonki
Ruma Idan Kin Aureni Kin Yi Taimako Kuma Kin Ceto Dan
In Ba Haka Ba Kila Son Naki Ya Iya Kisa In Narasa In Na
Aureki Na Taimakeki Dan
Rauninki Na Bukatar Mai Sonki Irina Lfyarki Tana Bukatar
Mai Sadaukar miki Da Komai Irina Ya'yanki Suna Bukatar

Sirkin Jinina Wanda Zai Cetosu Daga Zama Gundarin Sikila
Taji Tana Neman Barkewa Da Kuka Sai Rausaya Kaikawai
Take Ta Ce To Idan Hakane Kaine Kawai Zaka Iya Taimako
Bandani Domin So A Aure Yakamata Ne Ba Wajibi Ba
Zaman
Lfya Da Kwanciyar Hankali Kan Riskar Da Kyakyawar
Manufa Kammaluwar Iyali Masu Koshin Lfya Da
Kyakyawar Zuciya Sune Manufar Iyali So Ne Zai Jagoranci
Haka Ko Hakuri Da Sadaukarwa
Yanzu Hankalin Nazifi Yafara Kwanciya Yanzu Zuciyar Sa
Ta Canja Bugu Daga Fargabar Yada Manufa Saboda Ta
Shinshino Nasara Yanzu Bugunta Na Cin Nasarane
Dakuma Wanzuwarta A Fagen Da Masoya Ke Taka Rawa
Sabanin Da Can Ba Da Take A Matsayin Masoyiya Ita Kadai
Kuma Take Taka Rawarta, Yamike Tsaye Yana Nazari Ya Ce
Sam
Bazan Yarda Da Raayinki Ba Abubuwa Da Dama Nacin
Albarkacin So Ni Shaidane Zuciyata Babban Masaki Takai
Aka Cika Mata Da Sonki Ba Shine Dalilin Dazan Iya
Sadaukarmiki Da Komai Ba?
Tun Da Dadewa Nasan Type Din Jinina B Ne Amma Banta
Ba Daukar Sa Wata Tsiya Ko Ya Sanya Ni Murna Ba Saida
Na Tarar Danaki Type Din AB Wanda Da Aceni
AB Ke B Kila In Dauwama Cikin Rauni Da Kukan Bazan Iya
Biyan Hakkin Soyayya Ba Alokacin Dakike Bukatar jini
Tanadin Zaman Lfya Da
Kammaluwar Iyali Ne Ko Kuma Tanadin Sadaukarwa So?
Ruma Kamrauninta Yasa Ta Sheshekar Kuka
Kwakwalwarta Ta Gaza Nazifi Ya Durkushe A Gabanta Ni
Inkin Danganta Son danake
Miki A Tanadin Aure Kawai Kin Yiwa Son Kwange Ina
Sonki Da Kyau Zan Iya Sadaukar Da Komai Dominki,in
Ban Aureki Ba Ma Ba Fasa Sonki
Zanyiba,dan Haka Nasan Sonki Ba Shiga Zuciyata Dan
Bukatar Aure Kawai Ba Yadda Nake Jin Sonki
Ba Haka Na Saba Ganin Maza Nason Matayensu Ba,takasa
Magana A Cikin Tunaninta Abu Uku Kacal Ne Aranta
Amma Masu Fadi A Tarihinta, "Auwal Yadawo,tafada
Acikin Ranta Yayinda Kamar Nazifi
Yasan Tunaninta Ya Ce Nafi Auwal Sonki Ruma
Ina kasan Auwal?
Kai Tsaye Nazifi Ya Amsa Komai
Ake Nasani Ruma Wannan Zai Baki Shaidar Ban Fara
Sonki Da Wasa Ba Ta Cemasa Duk Lokacinda Ka Shirya
Nasan Sirrin Mahaukacin Masoyi
Saikadawo Ka Karbi Amsata
Cikin Dariya Ya Mike Tunda Kince Duk Abinda Zanji Daga
Gareki Yau Na Fatar Bakine Na Yarda Da Maganarki Ta
Yanzu A Fatar Baki Acan Cikin Zuciyarki Nasan Kin Binne
Amincewa Dani Duk Ranar Dakika San Mahaukacin
Masoyi Saikin Baniko?
Nayarda Zantafi A Hakan Wato Da Gaske Har Yanzu Zakaci

Gaba Da Wasa Da Hankalina!Haka!Bazaka Tausayaminba?
Da Gaske Ruma Bansan Mahaukacin Masoyin Dakikeson
Saniba Baya Gani Da Nake Tsaye Gabanki Ba,har
Yanzu Nakasa Gano Abinda Ya Baki Mamaki Ko Yake
Rudaki A Mahaukacin Masoyi Ko Sunan Ne?
Wato Mahaukacin Masoyi?
In Shine Abokina Mas!Ud Ya Rada Min Tun Bayan Ganin
Haukan Son
Danakemiki Daga Gani Daya Kacal Sannan A Lokacin
banda Sunanki Da Lambar Wayarki Daya Ban San Komai
Akan kiba, Kaine Bakasan Ni Ba Anya?
Ta Ina Ka Bi To Kasanni Da Har Kake Iya Sani Nani Da
Abinda Zuciyata Take Rayawa Taina Kake Kallon Halinda
Nake Ciki Har Kayi Tsokaci Akai?
Ban Manta Ba Kayimin Ganin Farko Ne Ranar 15th Nov
Kuma Ina Tsammanin Tun Wajen 18th Nov Nafara
Samun Sakonninka Wadanda Suke Nuni Kana Ganin Duk
Motsina Da Gaske?
Cikin Bayyana Mamaki Kinsan Da Haka Kika Kasa Sanar
Dani Saida Lokaci Ya Kure?
Kinga Yanzu Za Akira Sallar Magariba To Naji Kwantar Da
Hankalinki Kibani Sati Biyu Inje
Gida In Rago Ayyukan Gabana Indawo Takanar Inzo
Muwuni Kina Nuna Kwarewar Aikinki Akaina Wato
Jaridanci Na Ci Alwashin Ba Bu Amsar Da Ba Zan Bayar
Bisa Zahirin Gaskiya Ba,,,,
kayi Alkawari?
Nakusa Ta Ce Ba Bu Laifi Allah Yakaimu Ina Rokon
Alfarmar Kafin Satin Biyun Kibani Damar Turo Manya Su
Share Fagen Neman Aurena,,na Karanceki,,kuma Bakinki
Ma Bai Furta Sharadin Aurena Jigine Yake Da Sanin
Mahaukacin Masoyi Ba,,
to Yanzu Na Furta Tafada A Hanzarce Da Alamun Matsawa
Kanta Da Dakewa Shikenan Ma Na Samo Amsar, Ita Ce Ba
Haka Bane Tundakin Tabbatarmin Furucin Bakinki
Dabanda Kudurin Zuciya Dole Tasami Kanta Cikin Dariya
Tana Kada Kai Kawai Shima Yana Tayata Sai Sannan
Hankalinta Yadawo Kan Abincin Saukar Babban Bakon Da
Aka Jeremasa Bakaci Komai Ba?
Wayafada Miki?
Tarakashi Har Wajen Motar Sa Dan Tafiya Suka Tsaya
Suna Dan Hira Yana Bugun Cikinta Danjin Kalmar
Amincewa Daga Fatar Bakinta Kamar Daga Sama Yushau
Ya Jefo Tambaya Daga Bayanta Rumaisau Wanene
Wannan?
Ta Shanye Cikin Firgici Sannan Tajuya Ta Dubi Nazifi
Wanda Ke wasa Da Makullin Mota Yana Cillawa Sama
Yana Cabewa Yanayinsa Yana Nuna Banza Ya Baiwa Ajiyar
Yushau Tun Datana Dayakinin A Sanin Da Yaimata Bazai
Kasa Sanin Yushau Cikin Rayuwarta Ba Sau Uku Tana
Kallon Mutanen Biyu Dake Gabanta Daya
Bayan Daya Tamkar Mai Canki Cankin Wanda Zata Fifita

Ko Wanda Zata Kaskantar Yushau Yazo Wuya
Kamar Sunaso Su Yarfashine,kai Bakasan An Mata Miji
Bane?
Ruma A Firgice Tajuya Tare Da Dora Hannu Aka Kuma Da
Shirin Kurma Ihu Musamman Data Ga Nazifi Na Dunkula
Hannu Murya A Tausashe
Nazifi Ya Amsa Aini Ne Mijin Ranka Yadade Sannan
Yashiga Motar Sa Yanadaga Ma Ruma Hannu Zamuyi
Magana A Waya Daga Yushau Har Ruma Sunyi Mutuwar
Tsaye Kowa Danasa Dalilin Mutuwar,nazifi Na Bacewa
Yushau Ya Farko Ta Hanyar WaiGowa A Fusace Ga Ruma
Dan Ya Sauke Mata Fishinda Ya Tattara Amma Yana
Waigowa Yagawayam Tuni Ta Bace Cikin Rashin Hayyaci
Shima Ya Ruga Tasa Motar Ya Figa A Guje..
.
Dan Aunty
GORAN DUMA P( 62)
.
.
Masud Na Kwance Rigingine Kan Gado Da Laptop
Gabansa Yana Shawagi A Shafin Zumunci Na Facebook
Nazifi Nata Faman Kai Komo A Tsakiyar Falo YazaBuro A
Fusace Ya Fusge Laptop Kamar Zai Bugata Kasa Saikuma
Yafasa Ya Dangwarar Da Ita Kan Sofa Yajuya Cikin
Hargagi, Wallahi Zan Kashe
Kada Mari Malam Nazo Da Matsaloli Amma Ka Hana
Kwakwalwarka Ta Tayani Neman Waraka Da Wannan
Latsetsen Takaici Ya Ishi Masud Yayi Zugui Yana Kallon
Nazifi Sai Can Ya Basar Cikin Ko Inkula Ya Ce Aume Ma Ka
Ce Menene Matsalar Ya Ce Da Alama Tarkona Yagama
Kama Ruma Harma Nayi Azarbabin Sanar Da Ita Kafin
Sati Biyu Zanturo.
Munfito Zataimin Rakiya Muka Ci Karo Da Wannan
Banzan Mutumin Yushau Alamunsa Sun Nuna Lallai
Yanzu Tauraron Ruma Haske Yake A Idonsa,,ina Tsoron
'yan Ubanci Da 'yan Uwanci Masud Za A Iya Yankan
Bayana Bayana Idan Nayi Wasa,,kasamo Wata Dabarar?
Da Sauran Aiki Masud In Nayi Nasarar Samun Fage A
Damar Auren Ruma Yaya Zanyi Da Kwanjin Yan
Uwantakarta Da Wancen Karen Yushau?
Ummanan Da Tata Rigimar Wanda Zata Hanani Na Ci Da
Zafi Kar Rabon Wani Ya Shiga
Masud Yayi Kasake Yana Sauraron Nazifi Tamkar Tausaya
Masa Yake Amma Yana Direwa Sai Ya Saki
Tsaki Ya Janyo Computer Sa Zo kagani Abinda Nagano
Maka Shegen Ci Da Zucinka Yahana Ka Gani Jikin Nazifi Na
Bari Yatafi Da Sauri Yakurawa Allon Computer Ido Masud
Ya Budo Status Din Ruma Wandatai Mintina Talatin Da
Biyar Da Suka Wuce Gajeren Sako Ne Amma Mai Dauke
Muhimmanci
KOKARI SHI KE BUDE KOFAR DAKE KULLE SANNAN BABU
ABINDA KE MIKAR DA SANDARKA SAI NACIN

DADDANNAWA
Shine Sakon Na Ruma Wanda Nazifi Yadinga Karantawa
Yana Maimaitawa Tundaga Kan Rubutun Wanda Idonsa
Yakema Ganin Tamkar An Zana Da Ruwan Goal Ya
Ce Kai Abokina Narage Maka Labari Kasan Ruma Kallan
Aljani Ko Mutumin Boye Takemin Duk A
Dalilin Basajar Daka Bayar Da Shawarar Ayimata Dagaske
To Meyafaru Nan dai Suka Gama Hirar Su A KarShe suka
Ce Mu Kulla Shawarar Yadda Umma Zata Amince Akan
Kari Yadda Bazaka Saba Alwashin Daka Ci Na Tura Manya
Kafin Sati Biyu Ya Cemasa Tunfarko Kayi Raguwar
Dabarar Sanar Da Umma Cewa Ruma Bazawara Ce Kuma
Ka Zabeta A Wadda Zaka Juyewa Dukkan Cikinka Akan
Ruma Ya Ce Kaima Dai Masud Kai Ka Dauki Zawarci Kuren
Daza A Dinga Faman Boyewa Allah Na Tuba Ni Zawarci
Bashi Yaimin Riga Wando Inba Donshi Ba Na Isa Inga
Ruma Ballena So?
Mahaukacin Masoyi Inji Masud Cikin Dariya Lokacin daya
ga Nazifi Ya Fitittike Yana Wanke Zawarci Kawai Ta Inda
Zamu Bulluwa Umma Ta Gane Hatsarinda Nake ciki?
Masud Yasake Lulawa Tunani Nazifi Ma Haka Amma Sai
Yari Ga Farkowa Oh Na Tuno Wata Hikimar Zan Gwada.
,
BAYAN WATA UKU
Nazo Ne Karakani Gidan Wani Shahararren Boka
Dakasani Maikudi Kai Ko Matsafine Ni Dai Bukata Kayimin
Rakiya Gurinsa Yushau Ke Fadawa Abokinsa Maikudi Cikin
Tsanani Tashin Hankali Maikudi Cike Da Mamaki Harda
Tsoro Ya Ke Kallon Yushau A Lfyarka Kake Kuwa Yushau
Badan Nafi Kowa Sanin Tsantseninka Bana Ranste Da
Allah Ba Abinda Zai Hanani Rantsewa Sholisho Ka Shaka
Yushau Ya Furzar Da Numfashi Bayyana Takaici Da
Tsananin Damuwa Banta Ba Zata Ba,banta Ba
Ganiba,banta Ba Jin Labariba,na Rantse Da Allah Kuma Ko
Za A Mutu Bazan Laminta Ba
Maikudi Yakara Duban Yushau Yafara Zargin Hauka
Yushau Ya Ci Kuka Yakoshh Yafara Share Hawaye Iyakar
Cin Mutunci Da Wulakanci Anyimin Maikudi Wai Inje
Gidan Mujiya Sai Na Tarar Da Taron Biki Har Andaura
Aure Shekaranjiya,,maikudi Yatare Cikin Zumudi Da
Fargaba Daurin Aurenwa?
A Zafafe Yushau Ya Amsa Daurin Auren Ruma Dana Niki
Gari Har Niger Kwana Goma Sha Biyu Dan Nemo Mata
Magani Sikila Nayi Asarar Kudi Nayi Asarar Lokaci
Na Har Kasar Haihuwa Duk Dan In Nunawa Ruma Zan Iya
Rasa Rai Dominta, Amma An min Adalci
Idan Na Dawo Na Tarar Ta Auri Wani?
Banta Ba Ganin Iyayen Dakekin Jininsu Da Gaske Irin
Nawa Ba Sun Sallame Ni Kuma Nima Yanzu Zan Nade
Kafar Wando In Sallama Su Maikudi Ya Kadakai Cikin
Jimami Babu Dadi Amma Da Yardar Ruma Katafi Niger
Kuma Tasan Maganinta Zaka Karbo?

Cikin Tsawa Ya Amsa Tasani Tasan Komai Jinake Kaika
Sanar Da Ni Inda Zan Samo Fitsarin Rakumi Bada
Kaimuka Jeyawo Neman Kunkurunba?
Dawa Mukaje Gidan Sarkin Baka Karbo Magani Nine
Sikilan Nina Kesha?
Ba Ita Nake Kaiwa Tana Sha Ba?Kuma Tasan Dalilin Hakan
Harma Da Shirinta Na Cewa Intaga Ta Fara Samun Sauki
Zata Sanar Dani Ranar Da Zanje Niger Din Ma Ai Na
Jemata Sallama Tasan Kuma Ko Kuda Bani Da Shi A Niger
In Ba Maganinta Ba Uban Me Zanjeyi?
Yasake Fashewa Dakuka Ba A KyauTa Maka Ba Maikudi
Yafada Yake Maimaitawa Amma A Fatar Baki Amma Cikin
Zuciyarsa Yanajin Hakkike Dawainiya Da Yushau Allah
Yaimasa Niima Amma Sai Yajefa Hankalinsa Dawa Bai
Ankara Ba Sai Da Niimar Ta Subuce Yayiwa Kansa
Tsirara,shine Yanzu Zaizo Yayiwa Mutane surutu.
Ina Kace In Rakaka?
Yushau Ya Tsayar Da Fyace Hanci Yakara Daure Gira Gurin
Rikakken Boka Ko Matsafi Zaka Kaini Ya Farraka Tsinannu
Abin Haryakai Haka Yurhau?
Maikudi Yafada A Raunane Yushau Ya Ce Banga Mafitar
Datafi Wannanba Idan Na Kyalesu Kashe Nizasu Yi
Allah Sarki Inji Maikudi Ya Ce Bangane Ba Yushau Kana
Tsoron Mutuwane Wadda Tazame Maka Dole Dankanajin
Dadin Wannan Duniyar Kokuma Domin Son Dakakewa
Ruma?
Ban Banbanta Da Kowa Ba Maikudi Rayuwar Duniya
Wahala Ba Kuma A Kaunar Mutuwa Yo Kowa Ma Baiji
Dadi Ba A Duniyarnan Bare Ni Mai Somoli
Dariya Taso Kubcewa Maikudi Amma Ya Hadiye Amma
Kasan Dahaka Kake Kokarin Jefa Kanka Wata Musibar Ta
Fishin Allah Wajen Bin Bokaye Alhalin Inzaka Tuna Fishin
Iyayenka A Hakkin Ruma Ne Yarataya Maka Sumoli Yatari
Shi A Fusace Wanne Hakkin Ruma Na
Danne?
Karka Fadamin Maganar Banza Mana In Baka Da Abin
Cemin Ni Ina Dashi A Fusace Yakarkade Rigar Sa Yatafi
Maikudi Nata Kira Yaki
Dawowa Bai Zame Koina Ba Sai Falon Gidansu Bayan
Yasami Tabbacin Dukkan Baki Sun Darare.
Kaiko Hajiyata Cika Da Mamakin Yadda Yau Dinnan
Yushau Ke Gaisheta A Tsaye Dan Haka Ma Tasaki Baki Tana
Kallansa Kaitsaye Ransa Abace Sai Faman Huci Yake
Murya Ya Daure Hajiya Ta Ce Kaiwai Lfya?
So Nake Aje Abuja A Daukomin Hamida Na Fasa Kyautar
Dama Ai Bada Izinina Aka Kyautar Da Ita Ba Hajiya
Tafahimci Ba Cikin Hayyacinsa Yakeba Tsabar Kishine
Kawai Ke Wajigashi Dan Haka Ta Sanya Masa Ido Yadinga
Sakin Maganganu Son Rasa Saida Ta Lura Yana Neman
Wuce Gona Da Iri Sannan Tata ka masa Burki Malam Kar
Kasake Ka Zageni Yai Tirjiya Kamar Mai Shirin Barkewa Da
Kuka Ba Zaginki Zanyi Ba Hajiya Kawai Ni A Karbo Min

'yata Da Sauki Ai Indai Ba Ruma Za A Dauko Maka Ba
'yarka Za A Dauko Maka Gaskiya Da Sauki Inji Hajiya
Hawayen Dayake Ta Rikewa Ya Subuce Masa Yana Murza
Ido Yana Tafiya Da Baya Zuwa Zanyi Na Dauko 'yata Ku
Hadamu Ku Kimu Tare Yana Maimaita Kalma Daya Ya Fice
Daga Falon Cikin Rudu,
********
Yashafe Sama Da Sati Hudu Yana Jinyar Zuciya Wanda Jiki
Yataya Ta Da Zazzabi A Wannan Dan Tsukin Ne Kuma
Yakara Tabbatar Duniyar
Tajuyamasa Baya Da Kyau Ba Bu Dangi Ba Bu Ruma
Sumoli Da Yazaba Kuma Takara Nisa Dashi A Zatonsa
Yanajinyar Nan Zata Rage Gantali Ta Zauna Takula Dashi
Amma Ba Bu Abinda Yaragu Sannuma Saitagadama
Takemasa Intsiyartama Yatashi Har Tsiyatakemasa Tawon
Wata Daya Ya Warware Yafi Sabgoginsa Cikin Ikon Allah
Kuma Sai Ga Sumoli Ta Kwanta Tanata Jinyar Alaye Iri Iri
Na Ciki Ita Bai Risketa Ba Saida Cikin Yafara Girma To Mai
Waina
Ruwa Bare Yasami Mai Ai Nan Sumoli Taga Bakin Halin
Juya Baya Domin Shiko Samun Na Rainawar
Ma Baya Yimata Tun Tana Daukar Lamarin Wasa Harta
Fara Tuna Masa Kanta Da Mawuyacin Halinda Zata Iya Shi
Ga Wata Rana Mominta Ta Yasar Da Zuciyar Datai Na
Dauke Kafa Daga Gidansu Tun Da Sumayyan Ta Bata
Labarin Yushau Yai Tawayen Adaina Zuwa Masa Gida
Tundaga Tsakar Gida Tafara Cin Karo Da Bola Har Tsakiyar
Gado Inda Sumoli Ke Kwance Kangayau A Kasalce
Mominta Yar Da Mayafi Ta Dago Tana Salati Tamkar Zata
Fasa Kuka Na Shiga Uku Ummi Haka Aka Wulakanta
Minke?
Ina Yushau?
Yatafi Kasuwa" cewar Ummi.....
.
Yo ai gwanda Yushau yasan makomar sa, ko da yake ni
sadaukarwa nayiwa Nazifi na daga masa kafa,
.
Abbas Abdulkadir Hada Hada ( Dan Aunty )
GORAN DUMA ( P 63)
.
.
Tsawan Lokaci Suka Dauka Suna Kwashewa Wa Yushau
Albarka Sannan Takira Wani Dan Makwabtansu Yakai
Sumoli Asibiti Tagama Yimata Hudubar Tsiya Tare Da
Jaddada Mata Lallai Inyadawo Ta Cemasa Tana Nemansa
Tundaga
Kofar Gida Yushau Yasan Ansami Canji Saidai Ko Ajikinsa
Wai Antsikari Kakkausa Ya Ratsa Kamshin Daya Turare
gidan Ya Wuce Dakinsa Baijima Dazama
Sumoli Ta Riskeshi Cikin Karfin Hali ta Zauna Hannun
Kujera A Dogashe Baiko Dubeta Ba Ya Ce Sannu Dajiki Ta
Tabe Baki Jiki Aiya Kusa Warkewa Maganar Data Kawo Ni

Gurinka Kenan Inajinki
Ta Dauke Kai Nayanke Shawarar Kawai A Zubar Da Cikin
Nan Ina Tsammanin Kwayoyin Maganin Da
Kike Banka Sunfara Zamemiki Kwayoyin Maye
Naji Idan Ma Daga Turu Aka Kunto Ni Cikin Dai Ajikina
Yake Da Ko Ya Koma Ko Na Haifa Da Alama Kaina Zan
Haifawa Ba Wani Shegen Ba Batadireba Yakifa Mata Mari
Kena Dai Na Raga Maki Sumayya Idan
Maguzawane Suka Haifeki Dan Allah Kullum Kidinga
Gaisheni Da Ashar Nikuma Nayi Alkawarin Amsa
Miki Da Mahangurba Ba 'yan Dambe Suka Haifeni Ba
Amma Sabodake Zan ara in yafa,
"Duka? Ta katseashi, In Na Zage Ka Hukuncina Duka Da
Fasa Baki?
To Ina Na Zubar Da Cikin Mene Hukuncina?
Dan Wallahi Ba Bu Tsinanne Da Zai Sanya Ni In Haifeshi
Yayi kokarin Kawo Mata Wani Bahagon Marin Amma Ta
Goce A Guje Tayi Kofar Daki A Tsaya Daga Bakin Kofa
Tana Harararsa
Kika Zubarmin Da Ciki Sumoli Na Rantsemiki Da Allah
Saina Daure
Ubanki Wanda Bai Baki Ilimi Da Tarbiya Ba
Allah Sarki Aini Da Sauki Tarbiya Ce Ma Gaba Daya Ba A
Baniba Wani Shegen Bashi Aka Yiya Tankwabe Kuma
Wallahi Kasake Zagin Ubana Saina Rama Dan Uba Bai Fi
Uba
Yadda Yushau Yatunzura Yasan Idan
Ya Biyemata Saidai Adau Gawarta Kificemin Daga Daki Ta
Cemasa Kuma Momi Ta Ce Kaje Tana Son
Ganinka A Tunzure Ya Ce Ba Bu Inda Zanje Wallah Idan
Kuma Za A Daukeni Akai Sai A Gwada
karfe Goma Na safiya Ruma Tafarka Cikin Kasala Ta
Waiwayi Makwancin Nazifi Ta Tarar Ba Bushi Da Sauri
Tayi Kokarin Korar Kasalar Ta Hau Lalubensa A
Bandakuna Kafin Takoma Sauran Dakuna Da Falo Ba
Bushi A can Teburin Cin Abinci Ta Tsaya Fakare Tana Bin
Kayan Abincin da kallo, Alamu Sun Nuna Yaci Nasa Yafice
Kwakwalwarta Ta Karade Da Tunanuwa Barkatai Har Daga
Karshe Daya Daga Ciki Ya Bata Kwallah Shine Yushau Ya
Sha Muzanta Mata Da Dogaronsa Akan Kasalarta Tayi
Yawa Bata Kula Dashi Yadda Yakamata Duk Da Cewa Tana
Iyakar Kokarin Tashi Taji Da Shi Kafin Yatafi Harkokinsa
To Nazifi A Tsawon Zamanta Dashi Na Watanni Kusan
Biyu Bata Taba Farkawa Ranar Aiki Ta Tarar Ya Fice Batare
Daya Bar Mata Duk Wani
Gibin Aikin Dazata Sami Lada Ba Wato Ya Cikamata Gida
Da Masu Aiki Mata Har Kala Uku Mai Share
Share Da Wanke Wanke Ga Kuma Mai Girki Daban Banda
Maza Masu Aiyukan Karfi Irinsu Wanki Da Kula Da
Farfajiyar Gida Yanuna Rashin Amincewar Shigar Masu
Aikin Dakunan Baccinsu Amma Bata Ta
Ba Farkawa Ba Tatarar Da Dakunan A Gyare Ba Ma'ana

Shiyake Gyarawa Kenan Kasala Da Cututuka
Sun Taka Rawa A Tsinke Aurenta Na Baya Idan Antafi
Ahaka Kuwa Nazifi Bazai Dayo Yatsaneta Ba Duk Da
Dumbin Sondayake Mata?Kwanakin Can Ta Taba Yanke
Shawarar Hana Idonta Baccin Safe
Bayan Azkar Din Safiya Kasancewar Kullum Nazifi Kan
Dawo Masallaci Yasamu Ta Koma Bacci Ranar
Saiyasameta Farke Cikin Kulawa Yafara Nazarin Ta Har Da
Bincikarta Hannu Da Kafafu Ina Fatan Lfya Ruma?
Banjin Dadin Yadda Kullum Nake Farkawa Ban Tarar Da
Kai Ba Ban Sami Ladanka A Komai Bako Da Karamine In
Fesa Maka Turare Yayin Shirin Fitarka Tafada Cikin
Tausasa Murya Tadan Kishingida A Kirjinsa Hakandatai
Nekuma Ya
Tabbatar Masa A Kasalcenta Take Ta Sadaukarne Kawai
Danta Faranta Masa Rai Ya Kwantar
Dakanta A Kafadar Sa Yana Shafar Gashin Ta A Hankali
Shine Yanzu Kike Hana Idanki Bacci Dankiyi Me?
Mu Gaisa Kuma Intayaka Shirin Fita Ai Nafasa Yau Ba Bu
Inda Zani Yafara Matsamata Gabobi Cikin Shakku Ta Ce
Habadai Ammafa Jiya Harkarfe Biyu Kana Fama Da Aiki
Kuma Ka Ce Min Sammako Zakayi Ka Fita Dashi
Nafasa Ya Cemata Yana Gyara Bargo Ya Kwanta Ruma
Tayi Sakare Tana Binsa Da Kallo Kamar Yadda Nasa Idon
Ke Kallonta Yamiko Mata Hannu Bacci Nakeji Sosai Zoki
Tayani Ba Musu Domin Abinda Take Bukata Kenan Tajeta
Kwanta Ba Bu Jimawa Bacci Ya dauketa Bata Farka Ba Sai
Goma Da Rabi Nankuma Ta Shafa Ba Bu Nazifi Data
Bincika Sai Ta Tarar Tun Bakwai Yafita Batafi Rabin awa Da
Komawa Bacci Ba Kenan Wannan
Yasanya Tafara Shakkun In Gaskiya Yafadamata Daya
Baya Saita Canja Dabarar Inda Saita Alarm A Wayarta Dan
Tadinga Tayar Da Ita Karfe Shidda Da Rabi A Ranar Nazifi
Na Dawowa Gida Abinda Yafara
Tambayarta Kenan Mizaki Dinga Yi Karfe Shidda Da Rabi
Na Safiya Dakika Sanya Kararrawa Tadinga
Tashinki?
Tadubeshi Cike Da Tsoro Da Zargi Baki Bude Da Kyar
Tasamu Amsa Masa Waya Fadamaka?
Yai Gaba Alamar Nadamar Furucinsa Amma Sai Yai Fuska
Ruma Saikin Nuna Min Dole Ke 'yar Kano Ce?
Amsa Nake Bukata Ba Tambaya Ba Tawuce Kichen Ta
Shiryamasa Kayan Jika Makoshi Takawo Masa To
Sannu Allah Yaimiki Albarka Yafada Bayan Yadire
Tambulan Ya Lura Da Ita Cikin Tsarguwa Ta Zauna Kan
Coffe Table Daga Gefensa Na Hagu Tanajan Yatsunta Cikin
Fuska Ba Yabo Ba Fallasa Mahaukacin Masoyi Mamaki Ya
Shige Shi Dakyau
Amma Ya Daure Ya Basar Yana Binta Da Ido Tsawon
lokaCi Na fada maka Matsala Ita Ce Banajin Dadin Yadda
Muke Sallama Da Juna Da Dare Ko Da Asuba Shi Ne Dalilin
Saita Kararrawar Yadan Yi Jim Sannan Yakawar Dakai

Daga Kallonta A Tausashe Ya Ce Shikenan Ki Bar Abarki
Kar Kicire To Amsa Min
Tawa Tambayar Inakasan Na Sanya Alarm?
Dazu Na shiGo Kina Wanka Ankira Wayar Na Zo Amsawa
Nagani Tasan Karya Yaimata Hakkum Amma Yanada
Kwarjini Da Bata Iya Musu Dashi Dan Haka Tai Murmushi
Ta Rausayar Dakai TaCe Ok Tana Ci
Gaba Dajan Yatsun Hannunta Suna Kara Yakamo
Hannunta Yana Dubawa Cikin Kulawa Meya Sami
Yatsun?
Ba Komai Tafada Cikin Kasa Hankali Tana Sane Wane Ne
Mahaukacin Masoyi Ta Aura Amma Bata Taba Tsammanin
Lullubin Birin Zai Zarce Har A Cikin Zaman Aurensu Ba
Gashi Dai A Yanzu Tana Da Kusanci Dashi Yadda Take Caje
Shi Ciki Da Bai Bata
Tarar Da Alamun Zamowar Sa Jinnuba To Ta Ina Yake
Samin Boyayyun Al'amuranta?
Tayi masa Wannan Tambayar Tafi Sau Ashirin Yana
Wawantar Da Ita Kin Tabbata BBu Komai?
Ya Katse Mata Tunani Lokacinda Yafara Taya ta Jan Yatsun
Ta Bi
Yatsun da Kallo, Inafata Kinsha Magungunanki?
Na sha Ta Amsa Atakaice Ya Bita Da Nazari Sannan Yajata
Jikinsa Fadamin Meya Bata miki Rai Ina
Tambayar Sanya Alarm Ceki Yafemin Naimiki Alkawarin
Bazan Sake Ba Kinji?
Da Sauri Takada Kai Duk Da Bai Bata Wannan Damar Ba
Saita Sami Kanta Cikin Kwalla Baka Da Abinda Zai Batan
Rai Kwata Kwata Nazifi Amma Ina Bukatar Ka Yarda Dani
Dari Bisa Dari Ban Fada Tarkon So Irin Naka Ba Amma Ni
tun Asali Rayuwata Tagaji Rashin Manta Alkhairi Halittar
So A Cikin Zuciyata Mai Saurin Mika Wuya Ce Ga
Kyautatawa Kawai Dan Haka Ka Zaci Kirjina Cike Yake Da
Kaunarka Da Zata Yi Haihuwa Ka Kyautatamin Ko Baka
Kyautata Ba Ya Rungumeta Da Kyau Bukatarki Kenan?
Aina Yarda Dake Dari Bisa Dari Ruma Kyautatawata Ba
Dalilinta Kenan Ba Watoki Soni Dalilinta Yasamu Ne
Karkashin Tausayi Da Soyayyar Dani Nake Miki Ko Yaya
Kike Haka Nake So Ko Yaya Zanyi Dawainiya Haka Nakeso
Kin Fahimceni?
Ya Dago Fuskarta Yana Duba Wani Irin Shaukin Sonsa
Yakara Mamaye Mata Kirji Har Yai Tasirin Hana Ta Cigaba
Da Neman Sanin Mahaukacin MASOYI
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 64)
.
.
Ina Tune Hafsat Kasalata Da Ciwona Sun Taka Rawa
Wajen Jawo Min Tsana A Gurin Yaya Yushau Kila Har Yake
Ganin Ba Bu Asara Inya Rabu Dani In Nazifi Ya Dauki
Wannan Matakin Akaina Bana Tsammanin Zan Iya Jurewa

Da Kyar Zan Iya Rayuwar Da Babu Shi,,
hafsat Ta Ce Cikin Tausasawa Karka Cika Wa Kwakwalwark
Tunani Da Zargi Mara Tushe Ruma Bai Kamata Ki Sanya
Kuka So Yasa Ki Ba
Ruma Ta Ce Nafadamiki Hujjata, Hafsat Ta Ce Aina
Fahimceki Abinda Kika Kasa Tunawa Shine In Yaya Yushau
Bai Yarda Da Sikila Ba Yana Mata Kallon Gaibu Ko Shafar
Jinnu A Wajensa Daidai Ne Ya Tsani Kasalarki Amma
Nazifi Yasan Sikila Ciki Da Bai A Dalilinki Ta Yaya Zai
Karyata Yadda Rayuwarki Take?
A Ganina Zaton Hakan Dakike Masa Ma Kaskantar Da Son
Dayakemikine?
Ruma Ta Sauke Wata Doguwar Ajiyar Zuciya Karfafa Mini
Gwaiwa Daikike TaCe mata Sonda Yakemiki Baikai Haka
Ba Baya Sona Kawai Nake Bukata Ba Yaita Sona Har Abada
Nake Nema Hafsat Dan Son Dayakemin Yana Da Tarin
Alfarma Da Aminci A Kulliyar Rayuwata Wanna Yana Cikin
Jerin Adduoina Danake Miki Ruma Wata Kwallar Farinciki
Ta sauko daga idonta.
Daga Hirar Da Ruma Tayi Da Hafsa Sai Ga Kiran Nazifi Ya
Shigo Ta Daga Ta Cemasa Ranka Ya Dade Zanyi
Fushifa Muryar Sa Da Alamun Damuwa Ya Ce Oh Kezaki
Fara Yin Fushi Konizan Fara?
A Rikice Ta Ce Da Akayime?
Nazifi Inkayi Fushi Ba Bu Rumaisau Menayi Ya Amsa Kina
Raina Son Danake Miki Har Kike Danganta Rawarsa Da
Kasalarki In Yushau Ya
Tsane Ki Dalilin Kasala Har Takai Ga Yasake Ki Kila Ya
Aureki Ne Donkiyi Masa Hidima Nikuwa Na Aureki
Ne Don Ina Sonki Tunkafin Haka Na Shiryamiki Hidima
Kaico Har Zuwa Yau Ruma Baki Ga Na Cancanci Kar A
Hada Kafadata Data Yushau Ba?
Zuciyarta Ta Nemi Dakatar Da Aiki Amma Wasi Wasi Ya
Hana Hakan Tafara Waige Waige Ko Nazifi Ya
Boye A Wata Kafar Ne Har Yasan Tayi Hirar Sa Da Hafsat
Amma Takasa Gano Amsar Ta Cemasa Nazifi Ina Sonka
Tasake Maimaitawa Kaji Alfaharin Ban Taba Furtawa
Yushau Wannan Kalmar Ba Kai Kuwa Na Sha Furta Maka
Bin Hakki Da Gaskiya Nan Ma Taji Jiran Amsa Cike Da
Fargaba Ta Cemasa Kadaure Karkai Fushi Yace Bazanyi Ba
Amma Ina Sonki Sani
Indai Ruma Ce Ina Sonta Badai Ruma Dai Ruma Sikila Ba?
Ko Mai Amsa Zallar Sunan Ruma Da Mai Amsa Zallar
Sunan Sikila Bazanta Ba Tsana Ba Bareke Ki Dinga Tuna
Haka Ta Ce Na Rike Ya Katse Wayar To Muwuni Lfya A
Wani Bangaren Kuma Farin ciki Yanata Faman Kwatarta
Aminci Da Alfarma A Mahaukacin Masoyi Yaugata Da
Tankasaheshen Gida A Unguwa Mai Daraja Har A Garki
Area I11
**** *******
Lokacinda Cikin Sumoli Yai Wata Takwas Saida Yushau Ya
Gwammace Daya Barta Ta Zubar Saboda Azabar Lissafe

Lissafe Ga Matsaloli Sunyi Masa Yawa Ga Basussuka Sun
Masa Yawa A Wata Juma,a Yana Kasuwa Wajen
Kasuwancinsa Aka Doko Masa Waya Daga Ofishin 'yan
Sanda Na Unguwarsu Wai Ana Son Ganinsa Hankali A
Tashe Ya Tafi Sai Ga Sumayya Tafito Tana Tura Ciki Tun
Kafin A Sanar Dashi Dalilin Kawota Yafara Hargagin Nade
Tabarmar Kunyarsa Da Hauka Meyasa Aka
Kawo Masa Mata Ba Tare Da Saninsa Ba?
Ta Inda Yake Fita Bata Nan Yake Shiga Ba Sam Yaki Yarda
Da Saurari Bayaninda 'yan Sandan Suke Masa Sai Ma Ya
Fice Ya Bar Ofishin Yan Sanda Hargagi Kuje Ku Hadiyeta
Babu Abinda Zanyi Kai Karama Zankai Ku Yawuce Yai
Tafiyar Sa Kwananta Uku A Rufe Wata Daga
Kawayenta Tayi Belinta Ba Dai Wani Abu Ya Kaita Hannun
Hukuma Ba Sai Kudin Matar Nan Data Ci Na
Ankon Sunan Atika Wanda Ta Kasa Biya A Kofar Gida Taga
Motar Yushau Taita Buga Kofar Yaki
Budewa Dole Taja Jiki Taje Gidansu Ta Kwashe Komai
Tasanar Ma Ummanta Haka Taita Mata Hudubar Banza Da
Zagin Yushau Bayan Sallar Magariba Suka Yi Kofa Gidan
Tsinke Yana Masallaci Suka Zauna Zaman Jiransa
Canwajen Karfe Tara Sai Gashi Yadawo Da Take Away
Dinsa A Hannu Yana
Ganinsu Yai Turus Kamar Ya Juya Amma Idan Momi Yai
Masa Katanga Yashiga Yimata Maraba A
Cunkushe Ya Shige Ciki Sunjima A Dakin Sumoli Suna
Jiran Yazo Gaishe Da Suruka Amma Babu Shi BaBu
Alamunsa Momi Ta Ce Lallai Wannan Takadarin Kansane
Tasameshi A Dakinsa Momi Najiranka Fa Tana So Tatafi
Waike Don Allah Zaki Barni Kuwa Na
Karasa Shekarun danazo Yi Duniya Da Sauran Lfya?
Wane Irin Bala'i Ne Tunda Kika Shigo Rayuwata Kin
Dagula Ta Gaba Daya Har Nafara Manta wani Abu Waishi
Farinciki To Yanzu Dai Kayi Hakuri Kazo Ka Fara Gamawa
Da Mominka Ga Dare Yafarayi Kaji
Yushau Ya Hayayyako Da Bala'i Toko Abincin Ma Bazanci
Bane?
Allah Ya Baka Hakuri Bayan Yakammala Ya Karasa Ya
Zauna Dab Da Kofa Ko Gaisuwa Ba Bu Ya Ce Gani Ita
Kanta Baki Na Rawa Ta Ce Masa Saikuma Kasamu
Wanman Mummunan Labari Yai Banza Da Ita Ta Bige Da
Bashi Hakuri Saboda Ta Lura Baida Niyyar Amsawa
Tagama
Surutanta Ta Wuce Tana Fita Yadubi Sumoli Ya Ce Kinsan
Allah Sisi Bazan Biya Ba Idan Sungadama Suzo Su Kara
Damkeki Ai Bani Na Aikeki Ba Yafice Haka Suka Ci Gaba Da
Zaman Doya Da Manja Yushau
Fishi Sumoli Kuma Tana Dannewa Tana Ladabi Har Yafara
Saukowa Kwatsam Ranannan Yasami Kiran
Gaggawa Daga Mahaifinsa Ta Hannun Mubarak Wanda
Yazo Har Gida Ya Ce Yatafi Dashi Tunda Yaje Mahaifinnasa
Kemasa Wani Irin Kallo Me Alaka Da Tausayi Har Dai

Yakare Da Cewa Wai Kai Baka Da
Lfyane?
Ramarka Fa Tai Yawa Saika Ce Maifama Da Cutar Cida
Lfya Lau Alhji Yanayin Rayuwane Kawai To Allah Ya Gyara
Dama Nakiraka Ne Naji Inda Aka Haihu A Ragaya Harka
Lalace Wajen Cinyewa Mutane Kudadensu Ni Danazaci
Nawa Kawai Kakeci Amma Kusan Mutane
Biyar Nakawo Min Kararka Akanka Hakadai Yushau
Yadinga Kamekame Tsakani Da Allah Yushau Ka Fada Min
Gaskiyar Abinda Ke Faruwa Da Rayuwarka Dan Da Dai Ba
Haka Kakeba Kokafara Shaye Shayene?
Ku Yafemin Alhji Nasan Tabbas Fishinku Na Tasiri A
Rayuwata Kuma Sakayyar Abinda Nayi Muku Ne Yasanya
Aka Jarrabeni A
Cikin Abinda Na Zaba Na Barku Wai Matarka?
Alhji Ya Ce Cikin Mamaki To Meye Nata A Kudin Da
Mutane Ke Binka?
Nandai Ya Kwashe Halin Zamansu Da Ita Yafada Masu
Alhji Ya Ce Har Yanzu Banji Hannunta A Kudin Mutane Ba
Yushau Inbaka
Dauka Ka Bata Ba Aiba Daureka Zata Yi Ta Ce Saika Bayar
Zata Sakeka Ba Nandai Yushau Yaimasa Karin Bayani
Akanka Alhji Ya Cemasa Yanzu Kenan Kaga Shaidar Cewa
Ba Zurfin Ilimi Ne Ke Hana Tarbiyaba?
Na Tabbatar Idan Na Rantse Bazanyi Kaffara Ba Duk Cikin
'ya'yan Gidan Nan Ba Bu Wace Zata Iya Haka Agidan
Mijinta Sannan Duk Wahalar Dawainiyar Da
Zata Duk Dawainiyar Da Zaka Yida Ruma Sikila Ina Da
Tabbacin Bazata Wahalar Dakai Kamar Wannan Matar Ba
Tun Daga Kunan Zuciya Zuwa Aljihu
Duk Na Fahimci Kurena Ina Mai Neman Gafararka Kaida
Hajiya Ba Bu Komai Ya Wuce Abu Biyu Ya Burgeni A
Alamarinka Hakurinda Kayi Na Kaucewa Yimata Saki Uku
Bare Inkayi Sakin Taki Tafiya Ku Fada Halaka Dakuma
Yadda Ka Iya Rike Babunka Ba Tare Da Ka Zubarda
Kimarka Wajen Roke Roke Ba Yushau Kam Yakara
Natsuwa Kuma Kaima Ka Tsarkake Zuciyarka Kayimata
Rikon Gaskiya Sannan In Allah Ya Sauketa Lfya Karkai Wa
Danta Ko Diyarta Rikon Dakaiwa Hamida Bana
Tsammanin Zuciyar Yushau Na Dukan Uku Uku Wallahi
Duk Zan Gyara In Allah Yaso Cikin Satinnan Zanje Abuja
To yayi Kyau Alhji Yafada A Gajarce Kuma Yatashi
Yadauko Cek Ya Hau Signing Yushau Na Kallo Yana Hadiye
Yawu Ga Wannan Kadan Toshe Wata Kofar Sauran
Basussukan Kuma Ka Barni Zanji Dasu Inji Alhji Farat
Daya Yushau Ya Kirga Kudin Dake Cek Din Naira Dubu
Dari Biyar Ne Nanfa Yafara Godiya Kuma Na Yafemaka
Kanemi Gafara Wajen Mahaifiyarka.
.
Iyaye kenan, duk wanda ya sabawa umurnin su bazai ga
da kyau ba, dunia ma kadai ta isheshi.
Allah Ya sa mu gama da iyayen mu lafiya Ya sa albarka a

rayuwar mu baki daya.
Aamiin,
Dan Aunty...
GORAN DUMA (P 65)
.
.
Dubu Dari Uku Ya Zaunar A Asusunsa Ya Kwashe Dubu
Dari Biyu Ya Doshi Gida Dasu Cike Da Cin
Alwashin Indai Kudi Na Siyo Soyayya Da Zaman Lfyar
Sumoli Abin Takaici Bai Sameta A Gida Ba Yadinga Tsaki
Ya Bude Drwer Ya Watsa Kudi Yafice Ya Bar Gidan
Hartadawo Tamai Sannu Da Zuwa
Kwana Hudu Suna 'yar Gaba Da Ita Sumoli Tai Halinnata
Na Rashin Riko Dake Shima Yaso Hakan Sai Ya Bada Kai
Bori Ya Hau Cikin Wannan Satin Sukaje Asibiti Awo Likita
Ya Tabbatar Musu Sufara Shirin Amsar Bako A Hanyar Su
Ta Dawowa Yayi Mamakin Da Batafara Yimasa Lissafin
Abinda Za A Kashe Ba Yafara Hamdala Shiriya Tazo Mata
Kamar Yanda Shima Yazo Mata Kwamfa! Cike Da Tsananin
Mamaki Da Sanyin Jiki Yagama Hargitse Dukkan Maajiyar
Kudinsa Bai Tarar Da Dubu Dari Biyun Daya Ajiye Ba
Yanemi Guri Dirshan A Falo Ya Zauna Yana Faman Hada
Gumi Yana Tunanin Yadda Kudinnan Suka Yi Tsuntsuwa
Suka Tashi Dole ya Kira Sumoli Ya Tambayeta Kudindana
Ajiye A Drawer Dakina Nake Nema Sumoli Ta Yatsina
Fuska Wanne Irin Kudi Ya Cemata Banason Tambayar
Raini, Naira Dubu Dari Biyu Ne Kudin Eye!Amma Dai Da
Mamaki Yushau Ko Mafarki Kake?
A,a A Sume Nake Haka Sukadinga
Casa Bala'i Har Na Kwana Biyar Cur Kamar Su Kashe
Kansu Ranar Kwana Na Biyar Dinne Yana Shirin Fita Sallar
Azahar Aka Dinga Murza Kararrawar Gidan Can Sai Ga
Sumoli Tana Takawa Da Kyar Fuskarta Akumbure Saboda
Kuka Ta Cemasa Don Allah Ka Bude Momina Ceta Zo Meta
zoyi?
Ni Nai Mata Waya Na Sanar Da Ita Komai In Ma Biyan
Kudin Ne Nasan
Zata Biyaka Tunda Kace Ni Na Dauka Tsinanniya Kawai A
Firgice Sumoli Ta Ce Wa!
Niko Ita?
Yakawar Dakai Rai A Bace Oho Miki Yamike Yazari Key
Yana Budewa Momi Kofar Ko Kallonta Baiyi Ba Yajuya Ciki
Abinsa Can Sumoli Tazo Waikazo Inji Momi,babu
Indazani Ku Gama Kintsa Gulmarku In Ma Miko Min
Kudina Zatayi Sannan Tatafi Dake Inajira Har Sumoli
Zata Tanka Da Tsiwa Tana Tuna Marin daya Zabga Mata
Shekaran Jiya Saita Hadiye Can jimawa Yai Alwala Kamar
Mai Zuwa Masallaci Yafita Amma Saiyadawo Ya Labe
Musu Muryar Momi Yafara Jiyowa Ai Duk Laifinkine
Ummi Tunda Kin San Wutar Cikin Mijinki.
Ni Dakinyi Shawara Dani Tun Lokacinda Kika Dau Kudin
Dakinzo Munje Wajen Malam Ya Kulle Bakin Ja"iri

Naje Fa Tun Kwana Daya Da Daukar Kudin Malam Ya
Cemin Indai Yushau Zai Iya Tunawa Da Kudin Nan Tozai
Tuna Ranar Da Aka Haifeshi Kema Momi Kin Manta Taurin
Kan Mugun
Mutumin Nan Ne Kawai Asirin Muke Kamar A Bayan
Farcensa Yake Makalewa Mts!
Aikin Banza Yo Dole Saita Hanyar Asiri Za Aci Kudinsa?
Banda Ma Dai Ke Sokuwace Doluwa Kawai In Nice Ina
Ganin Wura Wura Zai Gane Na Taba Kudin Ba Sai In
Kunna Masa Gobara Ba Ya Isa Ya Ce Kudin Wutar Bazata
Kone Suba,wallahi Danasani Hakan Nai Masa Akalla Da
Baitashi Hankalina Yanzuba Yushau Yadinga Hirji A Zuci
Ciki Tashin Hankali A Iyakar Zace Zacensa Baita Ba Zaton
Taurin Kan Sumoli Yakai Haka Ba
**** *****
Doctor Aiki Yasha Kaina Ban Sami Rako Matata Ganinka
Ba Nazifi Ke Fadawa Likita A Waya Hakane Batafi Minti
Goma Sha Biyar Da Barin Asibitinnanba Ya Cemasa
Ammafa Kusan Sati Biyar Kenan Tanafama Da Yawan
Laulayi Ai Satindaya Wuce Da Mukazo Ma Na Sanar Daka,
To Gaskiya Har Yanzu Ba Bu Sauki Jiya Cikin Darema Saida
Ta Kwara Amai Shima Likitan Cike Da Doki Ya Amsa Waida
Bari Nayi Tafara Baka Albishir Naga Kamar
Taso Haka Wane Albishir?
Tana Dauke Da Juna Biyu Na Sama Da Sati Shidda A
Firgice Nazifi Ya Ce Kace Me?
Da Gaske?
Dariya Kawai Likita Yake Yana Jin
Nazifi Na Sumbatu Har Daga Karshe Wayar Ta Katse
Kwana Biyu Nazifi Na Hadiye Murna Da Farin cikinsa
Yanajiran Ruma Ta Bashi Albishir Dinda Kanta Kamar
Yadda Likita Ya Gayamasa Amma Ta Share A Kwana Na
Uku Yakasa Daurewa Yadawo Da Wuri Ya Ce Mata Na Fiye
Sonkifa Da Kalmominda Yajanyo Bakin Zarenta Kenan Ni
Mahaka Tare Da Tsura Masa Ido Ban Yarda Ta Zarce Da
Dariya BaBu Kyau
Rainuwa Fa Babu Kyau Nazifi Ya Kauda Kai Tasha Jinin
Jikinta Tajuyo Da Kafadarsa Meyai Zafi Ido Zaici
Wuta?
Fadamin Laifi Nayiko?
Nasani Baka Cancanci Laifiba,ina Neman Afuwa tun Kafin
Katuna Min Laifin Yai Murmushi Ainazaci Ninai Laifin Ake
Hukuntani Da Boyemin Abinda Yakamata Nasani
Tashi Ga Cikin Dimuwa Menake Boyemaka?
Ko Menene Banyi Da Gayya вa,a,
"Da Gaske?"
Aiko Da Mamaki Ace Bakida Dalilin Sanar Dani Kina Da
Ciki Har Sai Likita Daga Waje Yafadamin Nandanan Tai
Fuska Oh!Wallahi
Nazaci Kasani
Nasani?
A Ina Zansani?

Ta Dubeshi Ido Cikin Ido Aina Kake Sanin Abubuwan
Danake Yi Lokacinda Bamatare?
Yadanyi Kasake Saikuma Yamike Cikin Kuzari Yana Kai
Komo A Falon
Itakuma Tai Tagumi Kawai Tana Kallonsa Da Sauri Ya
Nunata Da Yatsa Wannane Dalilinda Yasa Kika
Boyemin Kina Da Ciki?
Bare Har Na Rubanya Miki Tattalina Kukasance Cikin
Koshin Lfya Keda Bebin?
Cikin Dakewa Ta Kada Masa Kai Yajima Yana Kallanta
Fuskarsa Ba Yabo Ba Fallasa Yanufi Daki Yana Cewa Ina
Zuwa Ta Bishi Da Kallo Cikin Fargaba Tana Hasashen
Abinda Zaiyi
*** **** ***
Yana Dogare Da Kofar Dakin Yawatsa Wa Somoli Takarda
Yana Huci Idonsa Akan Mominta Ya Ce Ina Fata Zaku
Hada Kare Yanzu Kubarmin Gida A Tafi A Babbakamin
Gidan Wani Nidai Allah Ya Kubutar
Danawa Dan haka Kudin Da Kuka Dauka Saiku Yi Hidimar
Haihuwar Dasu Dama Abinda Zanyi Dasu
Kenan Ya Fice Abinsa Cikin razana Musamman Da Suka
Ga Saki Uku Momi Ta Dora Mayafi Aka Jikinta
Sai Karkarwa Yake Kinga Kwantar Da Hankalinki Kiyi
Zamanki Zanje In Sami Boka Tafice A Gaggauce Tabar
Sumoli Cikin Mawuyacin Hali Da Nadama Kaitsaye Yushau
Gidansu Ya Zarce Ya Kwashe Komai Yagayawa Hajiyarsa
Dukda Cewa Ta Razana Dajin Hakan Ta Ce Kaikuma Haka
Allah Ya Jarrabeka
Da Sakin Mata Kuma Da Ciki Musamman Ma Wadda Take
Gargarar Haihuwa ?
Cike Damamaki Yake Kallonta Kodayake Mai Daki
Shiyasan Inda Yakemasa Yoyo Amma Sumayya Ko Cikin
'yan Dari Take Dashi Ya Cancanta Yaimata Saki Uku
Karfe Sha Biyun Dare Yakoma Gidansa Idonsa Akan Dakin
Sumoli Yaga Alamar Tanan Cikin Tafasar Zuciya Yanufi
Dakin Yakwankwasa Babu Jimawa Ta Zo Ta Bude Kofar
Yajima Yanamata Kallon Mamaki Ke Kinsan Allah?
Ko Kwalam Ta Koki Ce Ta Kawoki Duniya Saikin Bar
Gidannan!Wallahi Sai Kinbar Shi Zama Dakena
Haramtawa Kai Har Abada Saboda
Haka Nayi Miki Alfarmar Safiya Ki Hada Tsiyarki Kifita
Daga Rayuwata Jafa'inki Yafi Karfina Sumoli Ta Daga Kafa
Da Kyar A Kokarinta Na Komawa Dakι Sakamakon Wani
Matsanancin Ciwon Ciki Dataji Ya Soketa Lokacinda
Yushau Ya Bar Gurin Wasa Wasa Ya Zarce Ciwon Mara
Batasan Sanda Ta Rarrafa Kofar Dakin Yushau Ba Tana
Bugawa Yushau Yadinga Tsaki Yana Juyi A Gado Yanajin
Nishin Sumoli Har Na Tsawon Fiye Da Minti Ashirin Yana
Kwance Sai Nasihar Mahaifinsa Ta Fado Masa Ka
Kyautatawa Kanka Ta Hanyar Bin Umarnin Ubangijinka
Bisa Kyautata Mu,amala Tsakaninka Da Matan Daka saki
Hakanyasa Ya Fito Kilama Haihuwa Ce Amma Me?

Yana Bude Kofar Yaci Karo Da Ita Kwance Cikin Jini Da
Alama Ta Mutu!
*** *****
Idon Ruma Nakan Hanya Nazifi Yafito Dakin Hannunsa
Dauke Da Wayoyi Biyu Yazauna Kusa Da
Ita Ta Fahimci Wayartace Da Tasa Wayar Cikin Dukan
Zuciya Daitake Binsa Da Kallo Tana Canki Cankar Meyake
Nufi Iyakar Zamanta Dashi Bata Taba Ganin Wayarta A
Hannunsa Ba Yadago Wayarta Yana Karemata Kallo A
Hankali Ya Ce BB PORSCHE Ya Dago Ya Dubeta A Ina Kika
Sai Wayar Nan?
A Rude Take Ta Ce Milkyway Mana Ai Tunda Kuka Tsafeni
Ko katin Waya In ba na Can ba Sai Inga Bashi Da Auki...
ᴬˢᴹᵞᴳᵞᴳᴳ
Dan Aunty
GORAN DUMA (P 66)
.
.
Nawa Kika Siya Ina Tsammanin Ko Dubu Tamanin Ne Ko
Saba'in Ne Mts Na Manta Dai Zaki Iya Tuna Ranar Dakika
Sai Wayar?
Ban Mance Ranar Dana Siya Ba Ranar Sha Biyar Ga Watan
Nuwambar Shekarar Dubu Biyu Da Sha Biyune Na Rike
Ranarne Lokacindana Shiga Tarkonka Na Bincika Kuma
Na Tarar Kaine Nazifin Dana Fara Haduwa Dakai Ranar
Danaje Siyen Wayar Kinsan Gaskiyar Kudin Wayarnan?
Ta Zuramasa Ido Tana Dawani Farashine Bayan Wanda
Na Siya? Kudin Wannan Wayar Yana Kamawa Daga Dubu
Dari Uku Zuwa Sama,ruma Ta Saki Baki Kawai Tana
Kallonsa Har Tsawon Dayagama Danne Dannensa A
Wayar Ya Dago Suka Hada Ido Yasakar Mata Murmushi
Itakuma Ta Basar Ta Kawar Dakai Amma Yasanya Ta
Dawo Dakan Ta Dubeshi Lokacinda Ya Cemata Inasonki
Rumasai Muryarta Na Sarkewa Ta Ce Game Din Bai Kare
Ba Kenan?
Yadan Kai Mata Dukan Wasa Cikin Raha Wato Game ne?
Kai Ka Kirashi Da Haka Ta Fada Yanisa Hakane Ubangiji
Mai Cewa Kasance Kuma Ya Kasance Shi Yajefamin
Kaunarki Farat Daya
A Ganin Farko Danayi Miki A Harabar Milkyway Ranar Sha
Biyar Ga Watan, Nasan Zaki Tuna Yadda Naso Nuna Kaina
A Wajenki Kika Ki Bani Hadinkai Inda Har Na Kai Ga Yimiki
Karya Na Karanta Jarida A
Jami'ar Bayero Na Kuma Dace Na Fada Daidai Alhalin Ban
Taba Karatu A Kanoba Ta Daga Masa
Hannu Alamar Jinjina Tana Murmushi Daga Nan Saime?
Yakama Hannunta Yahada Da Nasa Shirine Ni Da Masud
Wato Manajana A Karbi Wayarki Da Zummar Za A Sanya
Miki Credit Anan Muka Dauki Lambobin Wayarki Ta Zaro
Ido Cikin Mamaki Eye!Ai Tukunna Ya Fada Yana Dariya Ta
Sauke Ajiyar Zuciya Sannan Ta Zame Hannunta Daga Nasa
Ta Mayar Da Tagumi To Cigaba Yakarbi Wayarta Yana

Dubawa Wannan Wayartaki Ko Sati Daya Banyi Da
Mallakarta Ba Na Siye Ta A Japan Sannan Wani
Abokin Karatuna Kuma Kwararre A Fannin Kerekere Yayi
Aikin Sanya Mata Wata Software Mai Suna "droid Air Ya
Ajiye Wayar Tata Sannan Ya Dauko Tasa Ya Shiga Matso
Hotuna Kana Ya Ci Gaba Kinsan Ko Wacce BB Tana Da
Blackberry Id Wannan Ne Yake Bayar Da Damarko
Ansace Ta Ake Iya Ganota Ta Wannan Hanyar Kuma Ana
Iya Ganin Abinda Ke Gudana A Wayar Kamar Aikawa Da
Sakonni Kira Da Shiga Internet a Sannan Kuma Ana Iya
Gane Inda Take Ruma Tadinga Kallon Wayar
Cike Da Doki Bayan Haka Ita Wannan BB Porsche Din
Tana Iya Daukar Hoto Mai Ita Ta Tura Wani Guri Daban
Idan An Saita Ta Yamika Mata Daftarin Wasu Hotuna Daya
Budo A Wayar Sa Hannunta Na
Karkarwa Ta Karba Cikin Baza Ido Dantun Kafin Wayar
Tazo Hannunta Ta Gane Hotunanta Ne Cikin Rawar Ido Da
Jiki Tafara Duban Hotunan Daya Bayan Daya A Abujane A
Kano Ne A Motane A Rano Ne A Kan Dutsene Gasunandai
Dayawa Yamiko Hannu Ta Bashi Wayar Amma Takasa
Kawai Sai Ta Dago Ta Zuba Masa Ido Numfashinta Na
Bugawa Da Sauri Da Sauri Ya Boye Damuwar Rikitar Yaci
Gaba Dayimata Bayani Waccan Software Da Abokina
Yasanya Min Ana Samunta Ne A Irin Wannan Android Din
Yanuna Mata Wayar Sa Dake Hannunta Idan Aka Saita
Wayoyi Biyu Masu Wannan Software
Duk Nisan Dake Tsakaninmu Ko Da Inanan Nigeria Kina
China Zaniya Sarrafa Wayarki Yaddanaso,zaniy
a Gano Indakike Zaniya Daukar Hoto Zaniya Nado Sauti
Zan iya Shiga Mesgs Dinki Hakadai Ya Ci Gaba Da
Nunamata Ita Kuma Taita
Godiya Ga Allah Dayasanya Bawani Abin Asshan Take
Aikatawa Ba A Boye Lokacin da Kike Tsaye A Harabar
Milkyway Muna Tsaye Nida Masud Muna Kallonki Tare Da
Kulla Yadda Zamu Bullowa Lamarinki Har Lokacinda
Kawarki Ta Shigo Kuka
Shigo Tare Kawai Sai Ga Sani Ya Rugo Fadamana Ai Ipad
Kikazo Siya To Anan Ne Ba Tare Da Dogon
Nazari Ba Masud Ya Kawo Shawarar A Siyar Miki Da
Wannan Wayar Ruma Ta Rasa Bakin Magana Sai Kallonsa
Kawai Take Babu Kiftawa Cikin dariya Ya Hura Mata Iska
Ta Wadannan Hanyoyin Nai
Tracking Din Ayyukanki Ta Haka Nasan Ke 'yar Jarida Ce
Har Nagano Jaridardakike Da Wa Aiki Wanda Hakan Ya
Saukakamin Gano Muhallinki Ta Haka Nasanke Sikila Ce
Ta Haka Nasankin Taba Aure Har Nasanwa Kika Aura
Nasan Kintaba Son Wani Auwal Amma Ya Rasu Nasan
Ranar Birthday Dinki Saidai Nasan Ki Da Kyau Daga
Nanan Gidanku Abuja Har Mazauninki Na Kano Kafin Nan
Tunda Nasan Ke Sikila Ce Na Shiga Neman Sani Akan Sikle
Cell Naziyarci Kwararren Likitan Da Ya Shawarceni Tare
Da Gwaje Gwajen Har Na Dace Da

Cewa Zan Iya Aurenki 'ya'yanmu Su Tsira Saida Duk Na
Gama Danan Sannan Na Dauki Hanyar Kano Dan
Haduwa Dake Nana Kum Nayi Katarin Haduwa Da Sani A
Matsayinsa Na Abokin Abokina Shi Kenan Yaimin Tsanin
Haduwa Da Alhji Wadda Nan Ma Na Sake Katarin Ashe
Yasan Mahaifina Wannan Katarin Ma Yakara Saukaka Min
Samin Aurenki Musamman Ta Bangaren Mahaifiyata
Waddata Kyamaci In Auri Bazawara Amma Mahaifina Na
Jero Mata Lissafin Daga Gidan Dakika Fito Saita Saki Ya
Tayar Da Kallo Akanta Cikin Dage Gira Wannan A Takaice
Kenan Kin Gamsu?
Jiki A Sanyaye Da Kuzarin Karfin Hali Ta Girgiza Kai
Sannan Ta Shiga Cikin Wayarta Ranar Sha Daya Ga Watan
Sha Biyune Naje Abuja Dan Tsira Daga Basajarka Ta Kano
Nakuma Zarce Milkyway Da Zummar Tura Wasu Ayyuka
Ta Yanar Gizo Tunda Na Sauka Abuja Na Fahimci Mutane
Na Binada Kallo
Haka Ma A Milkyway Din Kowa Yasamin Ido Miyasa?
Mutanen Gari Dake Kallonki Tsarguwa Kawai Kikayi
Jama,ar Milkyway Kuwa Duk Sunsan Da Zamanki A
Zuciyata Harma Masud Ya Basu Umarni Duk Lokacinda
Suka Ganki Su Sanar Masa Ta Kada Kai Alamar Nuna
Gamsuwa Sannan Tajefo Wata Tambayar Yaya Akai Kasan
Zanyi Rubutu Akan 'yan
Maye Ko Zuwana Gidan Hafsa?
Na Nadi Sautinku Lokacinda Kuke Hira A Mota Da
Mubarak Tare Da
Abokinsa Haka Zalika Na Nadi Sautin Farkon Hirarku Da
Hafsat Ruma Tajima Cikin Kada Kai Da Tunani Sannan Ta
Furzar Anji Amma Tayaya Kake Gane Abubuwan Da Nake
Rayawa A Zuciyata?
Cikin Zaro Ido Ya Ce Kai Haba!Saika Ce Wani Maye?
Sukayi Dariya Su Duka Sannan Tazarce Da Magana Misali
Ranar 16th Ga Watan Biyu Dubu Biyu Da Sha Uku
16-2-2013 Ranar Naje Rogo Kuma Na Hau Dutse
Sakonka Na Daidai Lokacin Tamkar Kalubalanta Ne Ga
Radadin Da Zuciyata Take Dalilin Hasashen Da
Kaicon Daya cikata Tana Sauke Numfashi Ya Amsa Mata
Idan Ina Son Abu Ko Wane Irine Ina Da Juriyar Nunawa
Allah Shi Na Tsananta Addua Akanki Fiye Da Yadda Kike
Tsammani A Tsawon Dararena Dan Haka Karkiyi Mamaki
Idan Na Dinga Aikin Da Zai Dinga Dacewa Da Abinda Uwar
Dakin Zuciyarki Ke Kimsawa Abuna Gaba Kuma Daya
Kamata Kituna Digirina Na Farko Halayyar Dan Adam Na
Karanta Babu Laifi Ina Iya Karantar Mutane A Yayin
Furucinsu Ko Kallonsu Lokacinda Suke Wani Aiki Kamar
Dai Yadda Na Kalli Fuskarki Akan Dutse Sanin Kankine
Duk Wanda Zai Nufi Daji Ya Kurawa
Horizon Ido Cikin Aihini Tabbas Sai An Tarar Yana
Jinjinawa Makagin Sammai Da Kassai In Kuma Zai
Zurfafa Tunaninsa Sai Ya Dangana Da Mutuwa
Ruma Ta Sake Rafka Tagumi Tana Kallonsa Cikin

Murmushi Can Ta Sauke Wata Wawuyar Ajiyar Zuciya
Wato Abinda Kaimin Kenan,?
Kwarai Da Gaske Kyautatawa Nayi Ko Laifi?
.
Idan an samu isashshen commnts zamuyi post din
karshe anjima....
.
Dan Aunty
GORAN DUMA
KARSHE...
NA MAIMUNA BELI
TARE DA ABBAS ABDULKADIR HADA HADA
.
.
Eh To Uhum Ka Kyauta Din Kenan Kila Ba Dan Kayi Haka
Bada Yanzu Bansami Maijin Kaina Nida 'ya'yana Ba Cike
Dajin Dadi Yace Ko Banyi Haka Ba Dole Zamu Hadu Allah
Ya Hukunto Tuni Cewa Sai Mun Auri Juna Saboda Haka
Dole Mu Hadu In Baki Wannan Bebin Tare Da Kannensa
Masu Zuwa Ya Shafi Mararta Ko?
Tafada Cikin Kunya Da Dariya Toke Yaya Kika Gani?
Yatareta Cikin Dole Dan Karta Ci Gaba Da Sharewa Takada
Kai Hakane Yadanyi Shuru Zuwa Wani Lokaci Sannan Ya
Ce Idan Nasami Lokaci Mai Kyau Zan, Samu In Wargaza
Saitin. Ya ShiGa Duban Agogo Sannan Yasake Dubanta
Lokacinkine Yanzu Kin Kuma Cinye Shi Da TuhumeTuhume Karka Damu Duk A Ni Din Ne Yakura Mata
Ido Har Saidata Tsargu Tanemi Baasi Da Ido Ya Ce Wai Da
Gaske Zaki Haifo Min Ya'yan Dazasu Janyo Na Kara Sonki?
Kuma Nima Idan Na Haifo 'ya'yan Nasan Tawa Zuciyar
Zata Iya Tarar Da taka Zuciyar Wadda Ta Shahara A Sona
Ya Kame Kafadarta Da
Sauri Tokice In Kara Murna Haihuwarki
Nafada Ka Kara Murnar Suka Tuntsire Da Dariya Su Duka
********* ***
Duk Da Yushau Ya Yanke Kaunar Kawai Sumoli Ta Mutu
Bai Kasa Kwasarta Cikin Tashin Hankali Yanufi Asibiti Ba
Ananne Aka Tabbatar Masa Da Bukatar Jini Bayan Ta
Farko Daga Dogon Sumanta Lokacin Dake Gwada Jininsa
Dan Neman Dacewa Da Nata Saida Ya Kawar Dakai Cikin
Hawaye Ga Ruma Can Wadda Ta Cancanci A Bata Abinda
Yafijini Tana Can Tana Rayuwa Da Jininsa Amma Ba A
Matsayinsa Ba Wannan Asarar Da Kyar Zai Iya Mayar Da
Gurbinta Jinin Sumoline Ya Hau Abinda Ya Sabbaba Mata
Barin Jini Kenan Ta Galabaita sosai,
Aka Fara Yimata Karin Jini Da Jiran Cikar Waadi Da Idan
Bata Haihu Ba Sai Ayimata Aiki Cikin Ikon Allah Kafin Sfya
Ta Haifi Santalelen Danta Namiji Bayan Yai Waya Gidansu
Ya Sanar Da Hajiyar Su Haihuwar Saiya Mikawa Sumoli
Wayar Wadda Ke Kashangare Tana Kallansa Bakin Cikin
Sakin Dayai Mata Ya Hanata Farin Cikin Karuwar Data
Samu

Ungo Ki Kira Mutanen Gidanku Ki Sanar Dasu Kin Haihu
Kai Bazaka Sanar Dasuba?
Ta Tambaya Ya Kawar Dakai Yana Kara Bata Rai Idan Kina
So Su Sani Kawai Ki Sanar Dasu Kaitsaye Ta Amsa Cikin
Kuramasa Ido To Banaso Su Sani Dan Allah Ka Daukeni
Mu Koma Gida Na Rantse Zan Rayu Dakai Kai Kadai
Batare Da Kowa Ba Kuma Nai Alkawari Zanzame Maka
Zallar Farinciki Har Mutuwa Ya Gwasaleta Ya Ce Allah
Sarki Bakin Alkalami Aiya Bushe Sukai Shuru Har Tsawon
Wani Lokaci Saida Sumoli Ta Ga Babu Sarki Sai Allah
Sannan Taiwa
Mominta Waya Ta Sanarmata Yushau Na Harabar Asibitin
Mahaifan Sumoli Sukazo Tare Dawasu Yayyenta Yana
Sane Ya Boye Musu Suka Shige Har Saida Yagano Nasa
Mahaifin Sannan Yataro Su,
Tunkafin Su Shiga Dakin Suke Jiyo Bambamin Fadan
Mahaifin Sumayya Wanda Ya Saci Jin Hirar
Anyiwa Sumayya Saki Uku A Dalilin Satar Kudi Tsakanin
Momin Da Yayyenta Masifar Dayake Batawasa Ba Ce Yana
Nuna Tsananin Bakincikinsa Da Auren Momi Wadda Ta
Tarwatsa Masa Rayuwar 'ya'ya Yanzu Zawarawanta Hudu
A Gaba Allah Ya Kubutardani Abinda Yushau Ke
Maimaitawa Cikin Ransa Kenan Ganin Su Yasanya
Mahaifin Sumoli Yin Shuru Saida Aka Gaggaisa Tare
Dayiwa Juna Barka Sannan Mahaifin Sumoli Yanemi
Komawa Fadansa Alhjin Yushau Yatareshi Ai Alhji Duk
Hakuri Za Ai Kai Yushau Daure Ka Mayar Da Matarka Cike
Da
Karsashi Yushau Ya Ce Ai Saki Uku Ne Alhji Kayi Wauta
Yushau Alhji Yadinga Maimaita Cikin Alhini
Yushau Kuma Yai Sagare Yana Kallan Alhji Sannan Ya Dubi
Sumoli Wannan Kadai Yaisa Tabbatar Da
Nufinsa Na Sumoli Tafi Karfin Hakuri Duniya Mahada
Duniya Maraba Inji Wani Mawaki Anan Dangi Biyu Suka
Hakurkurtar Da Juna Tare Da Alkawarin Kin
Yasar Da Zumunci Daganan Kowa Ya Kwashi Nasa Iyalin
Akai Gida Dukda Yushau Yadinga yi yana Ta Satar Kallon
Dansa A Goye Bayan Sumoli Zuciyar Sa Cike Da Dokin Ya
Cika Shekaru Biyu Ya Dauko
Abinsa Ba Tare Daya Tashi Gidan Da Ake Rowar Tarbiya
Ba.
Wani Lokaci Ciwon Ruma Yatashi Yadda Take
Murkususun Ciwo Cikin Kuka Haka Nazifi Ke Murkususun
Ciwon Zuciyar Tausayinta Cikin Hawaye Sai Bayan Allura
Tafara Ratsa Ta Harta Sami Bacci Sannan Ya Kwashi
Sanyayyar Gwiwarsa Ya
Bar Dakin Da Aka Kwantar Da Ita Ya Cimma Likita A
Ofishinsa Likita Wane Aikine Ka Ce Ana Yiwa Sikila A
Rabasu Da Ciwon?
Likita Wane Aikine Kace Anayiwa Sikila A Rabasu Da
Ciwon?
Likita Yadan Dubeshi A Razane Baki Na Rawa Ya Amsa

"'Bone Marrow
Transplant""
Wato Dashen Bargo Kasancewar Ciwon A Ainihin
Jininsune Kuma Bargo Ke Samar Dajini Dan Haka Saidai A
Canja Shi Da Wanda Zai
Samar Dajini Mara Wannan Kantararrun Sel Din To Ina So
Ayi Wa Matata Likita Ya Dubi Nazifi Da Kyau Saiya gane
Sam Ba Cikin Hayyacinsa Ma Yakeba Saboda Haka Ya Bar
Kujerarsa Yadawo Kusa Dashi Yadinga Rarrashinsa
Tsawon Lokaci Har Ya Fahimta,
" Ka Manta Ne?"
Amma Tun Zaman Farko Damukayi Na Sanar Dakai Cewa
A Nigeria Ba A Taba Wannan Aikinba Sai A Kasashen Turai
Acandin Ma Saiwane Da Wane Akewa Saboda Yana Lasar
Miliyoyin Kudi Nazifi Ya Katsi Numfashinsa Nawane Kudin
Farashin Yana Canzawa Daga Wannan Kasa Zuwa Wannan
Amma Dai Yana Lasar Makudan Daloli Likita Ya Amsa
Nazifi Yamike Dafe Dakai Yana Ambatan Innalillahi Wa
Inna Ilaihirajiun Sannan Yanuna
Alamun Fadawa Tunani Mai Nuna Kwantar Da Hankali
Yadinga Safa Da Marwa A Ofishin Cikin Dukan Zuciya
Likita Na Kallansa Cike Da Tausayi Sai Can Yaga Nazifi Ya
Daga Hannaye Sama Cikin Hawaye Fuskar Sa A Sakeya Ce
Ya Ubangiji Ina Rokonka Da Iliminka Nashaida Kaine
Ubangiji BaBu Wani Bayan Kai Makadaici Wanda Bai Haifa
Ba
Kuma Ba A Haifeshi Ba Ubangiji Kaika Ce Duk Wanda
Yarokeka Zaka Amsa Masa Ina Rokonka Ka Hore Min
Halak Dinda Zan Biya Kudaden Daza Aiwa Matata Ruma
Da 'yarta Hamida Aiki Sannan Ka Saukaka Musu Su Da
Sauran Sikila Irinsu Tare Da Dukkan Marasa Lfya Allah Ka
Sanya Wannan Ciwon Yaimusu sauki, Kasa Yai Sanadin Shi
Ga Aljanna In Har Sun Bayar Da Gaskiya Dakai Kuma Ka
Bawa Jagororinsu Juriyar Kula Dasu
Amin Likitaketa Faman Amsa Masa Cike Da Jintausayi
Yana Kallan Nazifi Wanda Ya Goge Kwalla Sannan Ya Juyo
Yai Masa Murmushi Yana Daga Masa Hannu Har Yafice
Likita Yakoma Mazauninsa Jiki A Sanyaye Cike Dajin Wani
Irin Kaye A Zuci Dama Dai Duk Sikila Suna Samun Irin
Wannan Gatan Daga Mazaje Ko Iyayensu Dama Hakan
Takasance Rayuwa Yacigaba Da Wanzuwa
Cike Dajin Dadi Da Kulawar Nazifi Har Allah Ya Sauki
Ruma Lfya Tasamu Danta Kyakyawa Maikama Da Ubansa
Cike Da Koshin Lfya Batare Da Sikila Ajikinsaba Inda Suka
samasa Sunan Mahaifin Yushau Sunakiransa Da Irfan Dan
Ruma Tana Alfahari Da Alhji Yajajirce Kwarai Akanta Da
Lfyarta Wanda Tai Amanna Koda Mahaifantane Iyakar
Abinda Zasui Matakenan.
.
ALHAMDULILLAH
KARSHE
Marubucia MAIMUNA IDRIS SANI BELI.

.
Naso ace an iso wajen da Ruma zata samu lapia , ace
koda a cikin dangi ne an hada kudin da za a mata aiki da
erta Hamida,
ciwon bashi da dadi ko kadan, nasan ciwon, shine
sanadin tafiyar kanwata mai bina, yanzu haka karamin
kani na yana dauke da kwayan ciwon.
Likitoci sun tabbatar ba cuta bace, halittace abun kamar
yadda kuka ji a cikin littapin, mace da na miji su suke
haipar da irin kwayar cutar a jikin d'an da zasu haipa.
Shi yasa yanzu likitoci suke bada shawaran kowa yasan
Genotype din sa, tun kapin soyayyar ku tayi nisa kusan
makomar ku, ammana kuskure ne sai ana saura kwana 3
aure aje gwajin genotype, da dama basa barin auren su
koda an same su da duka A.S , suna duba soyayyar dake
tsakanin su alhali basu san illar ciwon ba,
a cikin littapin nan kadan aka ambata muku game da illar
ciwon , ga wanda suka sani sun sani,
ciwon kaman iska, yanzu-yanzu zaku zauna da mutun
lapia anjima kadan ya birkice babu lapia.
A binciken da akayi a dunia a Nigeria tapi yawan masu
dauke da ciwon sikila,
kuma arewacin Nigeria ne, saboda ba'a gwaji yayin aure
shi yasa muka pi kowa dauke da masu shi ciwon,
kwanaki nagani a jarida wasu en mata da aka musu
dashen bargo tun suna yara, a lokacin an musu dashen
bargon ne ko wacce kimanin 26m a Austrilia,
A yanzu kuma kudin ya kama kimanin 100m (Miliyon
dari,)
a kudancin Nigeria ma wai an para, anyiwa mutun 6 an
samu nasaran mutun biyu,
lititocin sunce idan ana son abun ya daure dole sai
gwamnati ta shiga ciki ta bada nata gudumowar da tura
likitoci kara ilimi da kayan aiki.
.
dan Allah ina kira ga samarin gidan nan da en mata da ku
ziyarci asibiti domin a muku gwajin wannan GENOTYPE
din saboda koma yasan makomar sa.
Ina ganin yadda mahaipiya ta take pama da ciwon, tayi
jinyar kanwata, ta rasu 2015, tun tana wata 8 ake pama
da jinyarta, san da takai shekara 15 ta rasu,
yanzu ma haka ga kanina ana pama da jinyar sa shima
tun aihuwar sa,
shi da zapin ciwo yana kuka mahaipiya da hawaye....
Kusan kullun haka suke shi da ita idan ciwon ya tashi
babu bacci a idon su, haka zasu ini haka zasu kwana.
Mahaipiyata kullun tana hanyar asibiti tare dashi....
Ciwon babu dadi ko kadan.
Ina mai Addu'ar Allah ya sawaka wa masu pama da cuta
komin kankantarta Ya basu lapia Ya yaye musu,
mu kuma da muke da lapia Allah Ya kara mana lapia mai
albarka.

Aamiin
.
Dan Aunty... Angon Hamida.. Ehem..


Post a Comment for "GORAN DUMA CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...