Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GIMBIYA HAKIMA CHAPTER B

GIMBIYA HAKIMA CHAPTER B

- - Post a Comment

 GIMBIYA HAKIMA CHAPTER B


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

         *GIMBIYA HAKIMA*

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻


*🌎MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️


     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

________________________________


  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''


+

37&38"Gimbiya Hakima Uwargijiyarmu barka da dawowa wanann masarauta mai albarka."

"Uhmmm! Ladi ina fatan kuna aiki yanda ya kamata."?

"Eh Uwargijiyarmu muna yi, muna farin cikin dawowarki uwar marayu."

"Zaki iya tafiya, ki gayama yan'uwanki da su tabarta da suna aiki akan lokaci."


"Angama ƴar'sarki jikar sarki, na barki lafiya, "Uhmm."

"Larai! Mu godema Allah wanan karatun yasa Gimbiya Hakima ta chanza baki ɗayanta."

"Aiko dai Larai, karki so kiga kallar farin cikin da nike, domin koni jiya da naje yi mata barka da dawowa fuskar sake ba kamar da ba."


"Alhmdulh! Hakan ma mungode, indai babu wanann zagin dake yi mana ai ba komai."

"Zaman lafiyarku da Gimbiya Hakima shine ku ringa yin aiki kan lokaci, dan ita Gimbiya Hakima batasan taga mutun bai san abunda yake ba."


"Hakane kuma Inna Lantana insha Allah zamu kiyaye duk abunda Gimbiya Hakima bata so, insha Allah zamu kiyaye."


"Allah yasa, ni na wuce wajen Gimbiya tana jirana, "a fito lafiya."

"Hutawarki lafiya ƴar'sarki matar sarki."

"Lantana na fahimci bakisan ki dunga ganina cikin gidan nan ko."?

"Allah ya huci zuciyarki, ai idan baki gidan nan muma ai barinshi zamuyi, dan kice gidan baki ɗaya zaman ki muke Allah ya taimakeki."


"To maiyasa kike ceman matar sarki."?

"Allah ya taimakeki, ai aure dole ne Gimbiya Hakima uwar marayu, muna fatan muga jininki a hannunmu."


"Hmmmm Naji yanzun dauko wannan tsarabar da mukayi ma bayin shashena ku raba kuba kowa kosan shi, sannnan ace ma su Ab'u yau su haɗa Liyafa mai kyau anjima zani ci abincin dare da kowace ma'aikaciyar shashen na ni Hakima a babban parlour na."


"Angama Gimbiya Hakima, Allah ya ƙara lafiya ya rabaki da murmushin mahassada."

"Yanzun kinji matsalarki, kedai baki gajiya da fadanci tashi ku fara aikin da na saku, ke kuma Azima shiga toilet ki haɗa man ruwan wanka."


"To Uwargijiyarmu, Allah ya ƙara girma."

Nan Azima ta shiga toilet ta fara haɗama Gimbiya Hakima ruwan wanka, su kuma su Bilkisu suka fara rabon tsarabar da Gimbiya Hakima tayi masu..

STORY CONTINUES BELOW

"Allah ya taimakeki, nagama haɗa ruwan yana jiranki a bayi."

"Ok! Nasan kinfisu sanin kaya masu kyau, dan su sun tsufa basu san zamani ba dan haka ki fiddo man kaya wanda ina gani zan yaba, inkin fiddo ku wucewarku kuma ku fara shiryawa kafin lokacin Liyafa."


"Ranki yadaɗ'e angama, a fito lafiya uwar marayu, ", Allah yasa."

Nan Azima ta fiddo ma Hakima kaya sannan suka kwashe tsarabar su suka wucewarsu..


"Sannunku mutanan madafa, "yauwa Aa ya mukaga iyayyen kaya a hannunku haka."?

"Ga naku tsarabar Gimbiya Hakima ce tace a kawo maku, sannan kuyi abinci mai rai da lafiya tare da ita yau za'ayi Liyafa a babban parlour dinta anjima da dare dan haka sai kuyi sauri ku gama kuje ku shirya muma shiryawa zamuyi."


"Alhmdulh! Alhmdulh!! Alhmdulh!!!."

"Allah mun godema ka da  ka anshi addu'armu da ka shiryar da wanann baiwa taka Gimbiya Hakima."


"Jama'a wai da gaske ne yau ɗin nan Gimbiya Hakima zatayi Liyafa damu? Bayan mu bayi ne wanda ta tsana take ƙama mune abun wulakantawarta a kullun."?


"Ai Allah kenan, kinga Gimbiya Hakima zatayi abunda ba'a taɓe yi ba a masarautar kano, dan shekarata asherin (twenty) a masarautar nan ba wani ɗan Sarautar da ya taɓe cin abinci cikin bayin shi sai Gimbiya Hakima da zata fara a yau ɗin nan."

"Gaskiya hakane Inna Lantana Allah yasa ta ɗaure a haka, "Amin mu mun wuce mukai ma sauran tsarabar su, kuma kuyi sauri ku gama dan Allah kafin lokaci yayi."

"Insha Allah Ba'ba Bilkisu, daman mun kusa gamawa da yardar Allah."


Nan su Bilkisu suka cigaba da rabama bayi tsaraba suna gaya masu su shirya zuwa anjima zasuyi Liyafa da Gimbiya Hakima cikin babban parlourn ta..


Nan take maganar ta gauraye masarautar baki ɗayanta kowa yana mamakin wai Gimbiya Hakima itace da ba bayinta tsaraba harda Liyafa zasuyi anjima..

"Ranki yadaɗ'e Gimbiya Fulani, yau nazo maki da labari mai daɗin saurare."

"Ina saurarenki Zainabu Allah yasa naji daɗin da kike faɗi."

"Zama kiji Uwargijiyata! Daman yau Gimbiya Hakima ta raba ma bayin ta tsarabar dawowa, sannan tace anjima su shirya zasuyi Liyafa tare a bangarenta da daren nan na yau."


"Alhmdulh! Gaskiya ko Zainabu kin kowaman da labari mafi dadi cikin labarin da kike kawoman, dan haka kije na baki kyautar gold da murjani."

"Godiya nike, uwar masu adalci Allah yasa Gimbiya Hakima ƴar'sarki ta ƙara koyi da ƙyaukwan hali irin naki."


"Uhmmm! Abunda Gimbiya Fulani tace ma Zainabu sannan ta bata kyautar da tayi mata..


Rasa inda zata sa kanta tayi dan murna, dan ba ƙaramin dadi taji ba Hakima ta fara janyo bayinta a jiki ba, bata san sanda ta tashi ta dauki hanyar shashen Maimartaba dan tasan Gimbiya Yakumbo tana can shiyasa batasan abunda daughter dinta tayi ba...


"Ranki yadaɗ'e Gimbiya Yakumbo! Gimbiya Fulani tana neman ki bata iso tana san kuyi magana."


"Maza kije kice mata ya shigo, "angama Allah ya ja da tsawancin kwana, Allah ya taimakeki Gimbiya Fulani! Gimbiya Yakumbo tace ki shigo, a fito lafiya."

"Assalama Alaikum."

"Amin wa'alaikumus Sallam."

"Fulani naji kince kina san magana dani?, "eh Yaya! Ina Maimartaba yake."?


STORY CONTINUES BELOW

"Yana ciki yanzun zai fito, ga dunkan alamu yau kina cikin farin ciki Fulani, dan ga shi nan fuskarki ta nuna."


"Sosai ma Yaya, sannu da fitowa Maimartaba, "yauwa Amaryata Fulanita, fatan lafiya dai ko? Ko kuma Yayartaki kika biyo."?


"Aiko dai, kasan ban iya kwana banga Yaya ba, daman zuwa nayi nagaya maku yau Hakima tayi abunda ba'a taɓe yinshi ba amasarautarnan."


"A'aa mai tayi kuma Hakimar?, "yau taba bayinta tsaraba sannan tace anjima su shiryasa tare zasuci abincin dare."

"Alhmdulh! Kunga abunda nike nuna maku ko? Da kun kun nace a dole sai na fidda Hakima kasar waje karatu, ba kamar ke Yakumbota."

"Hakane gaskiya mijinmu! Munga amfanin karatu cikin talkawa ko, dan tuni na fahimci Hakima ta chanza hali tun dawowarta ta farko."


"Ai daman nace maku zaman da zatayi cikin talkawa tana ganin yanda suke rayuwa dole itama watarana ta chanza, balle nasan duk mulkin Hakima sai tayi ƙawa, shiyasa ban ajiyeta a nan BUK ba na kaita kasar zaria."

"Gaskiya ko! Godiya muke sarki mai adalci, "Allah ya ƙara shige mana gaba, "Amin ya Allah ni na barku lafiya."

"Fulanita gobe ki turoman Hakima dole nayi mata kyauta da wannnan halin da nuna mai kyau cikin masarautar nan."


"Insha Allah, mu kwana lafiya, "Allah yasa."

Nan Fulani ta koma shashenta tana jin daɗin yanda suke zaman lafiya itada Yakumbo kamar ba gidan sarauta ba.


"Zainabu kije kice ma Hakima gobe inasan ganinta, "angama ranki yadaɗ'e yanzun ancika umirninki."

Nan Zainabu ta tafi shashen Gimbiya Hakima ta gaya mata sakon Fulani sanann ta koma, ta gayama Fulani tace to..


Masha Allah laƙuwata ilabillah! Tafiya take cikin isa da mulki ga kuma uwa uba aji da kyau dasu ƙara sata jin tafi kowa a kano state baki ɗaya gata kuma ƴar'sarki kuma matar sarki..

'''Amman bani Jameey nace matar sarki ba, Inna Lantana ce babu ruwana ba'ajin mutuwar sarki bakina🤭'''


Wani Arnan black material ne jikinta, dinki doguwar riga akayi mata, dinki yabi jikinta yayi bala'in ya mata kyau, ga wata alkyaiba da ɗaura a bisa rigar sai ta ƙare fitowa *GIMBIYA HAKIMA* dan ko tafiya dakyal take yinta kamar tana tausayin taka kasa kawai mulki ne yake sa Gimbiya Hakima wanann tafiyar..


"Sannunki da fitowa Uwargijiyarmu."

Bata kyalesu ba balle su sa ran ansawa, sai da ta zauna ta huta sannan ta kyalesu ɗaya bayan ɗaya sai tace, "yauwa sannunku kuma."


"Fatan duk kuna lafiya ba mai bukatar wani abu kuma."?

"Eh Alhmdulh Gimbiya bamu bukatar komai sai farincikinki uwar marayu."

Kallon su Bilkisu kawai tayi suka tashi suka fara saving ɗinta, sanann sukayi na sauran baki ɗaya bayan sungama suma sukayi nasu suka zauna...

Gimbiya Hakima ta tashi tayi masu addu'ar cin abinci sannan kowa yayi bissimilla suka fara cin abinci..

Wajen shiru baka jin motsin komai sai na cokali, duk da Gimbiya Hakima ba cin abincin take sosai ba dan bata jin yunwa, amman taci yanda ya kamata suma bayin sunci dan harda masu ƙarawa sai da kowa ya koshi sannan suka kama gabansu, bayan sun gyara wajen..

Koda Gimbiya Hakima ta koma ɗaki wanka tayi sanann ta kwanata ta fara waya da Maryam bayan sun gama waya ta kwanata bacci dan zata tashi sallahr dare...


Washe gari bayan Gimbiya Hakima ta gama duk abunda take ta wuce shashen Gimbiya Fulani, bayan anyi mata iso ta shiga..

"Fulani ina kwana?, "lafiya lau Hakima ya kika tashi?, "Alhmdulh."

"Daman kiran da nayi maki shine kyauta zan baki dan naji dadin abunda kika yi ma bayinki jiya, dan haka na baki kyautar zinari da azurfa sai kudi million ɗaya."


"Fulani basuyi yawa ba?, "basuyi ba Hakima dan jiya ƙin farantaman sosai, "nagode Fulani."

Sanann kije shashen Baffahn ki shima yana neman ki, anjima zakiji kuɗin sun shigo a asusunki, ga zinarin da azufarnan wuce dasu Allah yayi maki albarka."

"Amin ya Allah Fulani, na barki lafiya."

Nan Gimbiya Hakima ta wuce Shashen maimartaba bayan anyi mata iso ta shiga..

"Momy ina kwana?, "lafiya lau Daughter, ya kika tashi?, "Lafia lau, Baffah ina kwana?, "lafiya lau Mamana."

"Naji dadin abunda kikayi jiya Allah yasa ki ɗaure haka, sanann anshi wannan makulin motane ki dauka na baki."

"Baffah! TOYATA  A M G MERCEDES 2020 ka bani fa?, "eh Hakima na sani, "wow! Nagode sosai Baffah Allah yaƙara girma, "Amin Hakima."

"Ni Hakima zan turo maki million ɗaya ta account ɗinki anjima, "nagode Momy, ina sonku sosai iyayena, na barku lafiya."

Nan Hakima ta tafi tana farin cikin kyautar da iyayenta suka yi mata, tana zuwa shashenta ta kira Maryam waya ta gaya mata..
_By Jameelah Jameey ✍🏻_Share

Comment

Vote

Like

pls👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

         *GIMBIYA HAKIMA*

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻


*🌎MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️


     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

________________________________


  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''39&40"Kilishi ya kamata ki tashi mu tafi wajen Bokan nan tunda ƙafafu sun ɗaga."

"To Gimbiya yanzun daman nike shirin aiko maki Mariya naji ko kin shirya."?

"Amman kifara fita sanann na biyo bayanki duk da munyi ɓata kama amman mu kiyaye."

"To mu hadu ta baya, dan yau sai naji abunda yasa Hakim bai mutu ba har wata hudun yayi."

'''Niko nace da alamu Gimbiya Zulaha ta manta da Allah, dan naga kominta a boka ta miƙa shi ba ga Allah ba ☹️😡'''

"To shikenan! Nima yanzun zan biyo bayanki, "kidai yi sauri dan nasanki da nawa sosai."

Bayan fitar Gimbiya Zulaha, Gimbiya Kilishi ta fara magana kamar haka.

"Sakara ai ko bakice ba dole na biki wajen bokan nan naga idan yake nima na ringa zuwa dan da alamu aikinshi yana aiki."


"Dole naga bayan Hamad, ke kuma Zulaha zan barki kiga bakin ciki, kina kallo Humad zai mulka masarautar Zaria, kina ji kina gani zan zama uwar sarki, shashasha kawai marar wayau kin ɗauki yarda kin ɗauraman."


Haka Gimbiya Kilishi ta kama surutunta har ta gama shiryawa suka ɗauki hanyar zuwa wajen boka..


Wani ƙauyene cikin Zaria tafiya ce mai nisa amman ba sosai ba, dan wani dajin Allah suka kama ketawa suna shiga cikinshi ko tsoro basuji..

Dan a bakin tati aka ajiyesu saboda mota bata shiga cikin dajin, amman su Gimbiya Zulaha suka fidda tsoron komai suka kama zurma kai cikin wannnan gurmin dajin da bakajin kukan komai sai na tsubtsaye..


"Wai Gimbiya har yanzun bamu ida isowa ba?, "ai da nisa ƙadan ma mun kusa isowa, karki damu Kilishi wanann bokan aikinshi na kyau shiyasa bani aiko kowa nike zuwa da ƙafaffuna."


"Wai hakane kuma, kinsan ance zuwa da kai yafi aike, "yauwa kinga ga bukarshi can mun iso."

"A shigo da baya-baya bamu bukatar Sallama wajen nan, karku cire takalminmu."

Haka suka shiga da baya baya basu tsoran komai sudai burinsu bukatarsu ta biya shikenan..

"Gafara dai ubanmu, mai taimakonmu mai share hawayenmu."

Kallon su yake da jaijayen idanuwanshi wanda basuda banbanci da manja nan take ya kalli Kilishi take yaji yana sha'awar kusantarta, dan tunda yake bai taɓe ganin macen da dayi mashi ba kamar Kilishi..

STORY CONTINUES BELOW

'''To fa Jama'a kunga fa Gimbiya Kilishi takai kanta da kafaffunta🤣'''


"Ku zauna."ya faɗi yana zara masu idanuwa kamar na aljanu..

Nan suka zauna suka fara miƙe gaisuwa wajen boka.


"Gimbiya Zulaha yau kece da sabon jini."?


"boko mai share hawayenmu wannan kishiyatace Gimbiya Kilishi itama bada burin taga gawar Hakim."

"Amman ka bamu wata hudu kace zanga gawar Hakim boka shiru nikeji har anyi wata biyar, shine nazo naji ko lafiya."?


Hahahhahha! "Ai daman Gimbiya nasan zaki dawo, angayaman zaki dawo keda Kilishi daman tambayarki nayi naji ko zaki yi man karya.""Ai aljanu sunce ba za'a kashe Hakim ba sai nan da Shekara biyar."

"Shekara biyar boka."?

"Haka kika ji nace Zulaha, nima sako aka bani na gaya maki dan sun fara aikin ma kawai dai zai kaisu shekara biyar shiyasa."


"Boka amman ba za'a tambayesu su rike ba, domin shekara biyar tayi yawa, har fa Sallah baki ɗaya boka sun hanani kuma har Shekara biyara ban sake sallah. "


"Dakata! Wata kallar tsawa boka ya bugama Zulaha sai da Gimbiya Kilishi tashi zata ruga Gimbiya Zulaha ta riko ta🤣..


"Turmurturs baya magana ya chanza, ko kin manta Zulaha."?

"Ina neman afuwa boka hankalina ne ya tashi naji yace shekara biyar, Amman aneman afuwarshi na barmai wuƙa da nama baki ɗaya a hannunshi."


"Yayi hakuri yace zaku iya tafiya, ki dawo nan da shekara biyar godia zakizo yi mashi dan gawar Hakim kawai zaku gani."


"Godiya muke boka, ga wanann anba Turmurturs ina godiya."

"A fita da gefe gefe a fidda takalmi."

Nan su Gimbiya Zulaha suka fita ta gefe da takalminsu a hannu suka shiga mota sai gida ba wanda yayi ma wani magana a cikinsu har suka isa gida kowace tayi shashenta..

Washe gari bayan Gimbiya Kilishi ta gama abunda take ta wuce shashen Gimbiya Zulaha ta shiga bayan an mata iso..


"Gimbiya sannun da hutu."

"Yauwa Kilishi! Ina nan abun duniya ya ishe ni Turmurturs yace sai nan da shekara biyar zai kashe Hakim, kuma baka da ikon neman raki sai kayi laifi."


"Hmmm! Niko banga wani abuba ga shekara biyar, shekara nawa mukayi muna kashe kuɗin mu a banza amman bamu ganin cigaba."?


"Hakane gaskiya, dan ni tun kafin a haifin Hakim a duniya nike san na kasheshi."

"Kinga dan Turmurturs yace nan da shekara biyar ai sai mu zuba ido, mu koma muga taya zamu kashe ubanshi kafin shekara biyar."

"Shikenan! Kema kin kawo shawara mai kyau Kilishi, zamu san yanda zamuyi da ubanshi kafin shekara biyar ɗin."

Nan dai suka gama tautaunawa yanda zasu kashe sarki sanann Kilishi ta koma shashenta ta kosa dare yayi ko taje wajen Turmurturs itama ya kashe mata Hamad kafin nan da shekara biyar yana kashe mata Hamad daman ya kashe Hakim maimartaba ya mutu sai kawai aba Humad sarauta ita wannan abu yayi mata dadi zata jefi tsuntsubiyu da tarko ɗaya...


'''Niko nace ayya Kilishi tana san gaskiya kuwa, ace mutun burin yaga wani ya mutu wai harda mijinka saboda da duniya☹️'''


Dare na fara yi Kilishi ta shirya ta kama gabanta, dan bata yarda dare yayi sosai ba dan ita ɗaya ce tayi tafiyarta cikin motarta...

Bayan tayi parking bakin tati inda ko anwuce ba'agane motartace ta dauki hanyar zuwa wajen Turmurturs, hankalinta kwance ita fatanta ma karda tadda layi, aiko tazo a sa'a mace ɗaya ta tadda wajen Turmurturs bayan ta gama da ita ta ida isa..Hahahahahaha! "Gimbiya Kilishi daman nasan zaki dawo wajen mai sharemaku hawayenku."

"Mai share hawayenmu! Nima nazo ka shareman hawayena ba tare da kowa yasan zuwana ba, inasan zuwa ya dunga zama shiri tsakanina da Turmurturs."


"Ke."


Wata tsawa ya dakama Kilishi yana zare mata ido tare da lashe baki, dan gani ɗaya yayi mata yasama ranshi saduwa da ita..

"Waya gaya maki Turmurturs yana tuno shirin wasu?  bayan shi mai share hawayenku ne."?

"Ina neman afuwan Turmurturs, "mai ke tafe dake."?


"Daman so nike Turmurturs ya kashe man Yarima Hamad cikin shekara biyar ɗin da yace zai kashe Yarima Hakim, dan inasan ɗana Yarima Humad ya gaji wannan sarautar."


Hahahahaha! "Inasan haka, inasan naga ba'ariƙe Amana, dan haka  Turmurturs yayi maki alkwarin kashe Hamad cikin shekara biyar amman Turmurturs yana da sharaɗi."


"Wani sharaɗane Turmurturs yake dashi? Inajiran ya gayaman ko wani irine ni Kilishi zan yishi mudin Humad zai ma sarki nikuma akirani da uwar sarki."

Sai da ya ƙara kalleta tsab sosai yana lashe baki gami da zare mata idanuwan nan nashi mararsa kyaun gani sanann yace!..

"Zaki ringa zuwa Turmurturs yana yi maki wanka duk sati har shekara biyar ta cika randa za'a naɗe Humad sarki sai kinzo Turmurturs yayi maki wanka na karshe, inkin shirya zamu fara yanzun."


"Indai Humad zai zama sarki nayi ma Turmurturs alkwari zan dunga zuwa yana yi man wanka duk sati har sai randa aka ba Humad mulki zan daina zuwa."


"Shigo daga ciki a fara yi maki wanka Kilishi, "to Turmurturs."


Subuhanalillah😰


Haka Gimbiya Kilishi tayi zirgir gaban ƙaton Allah yayi mata wanka bayan ya gama ya sadu da ita ta gaba da ta baya, sai da suka gama abunda suke sanann tasa kayanta..


"Gaskiya Turmurturs yanada dadi sosai dan har yafi sarki dadi.$

"Duk ki ringa zuwa Turmurturs yana baki dadi kinga ke riba biyu ga dadi ga kashe Hamad da zai yi."


Nan Gimbiya Kilishi ta tafiyarta cikin farinciki dan ita wannan bashi bane farkon wankan ta ba, bokaye nawa sukayi mata wanka suka kusanceta ta baya da gaba, balle Turmurturs da take ganin zatayi nasara a aikinshi.

😭😭😭😭😭  Wallahi mata muji tsoran Allah saboda da neman duniya ka kama sabon Allah, yanzun abunda ke faruwa kenan ga mata masu bin boka,sai su kama zina da bokaye wai su a dole suna son bukatarsu ta biya..


Damai zakuji da zinibin zina ko da na zuwa wajen bokaye😰wallahi muji tsoran Allah baki ɗayan mu, Allah yasa mufi karfin zuciyarmu..


Haka ta koma gida tayi wanka ta cigaba da baccinta ba sallah balle salati dan ta manta yaushe rabonta da tayi su ☹️.._By Jameelah Jameey✍🏻_

Share

Comments

Vote

Like

pls👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

         *GIMBIYA HAKIMA*

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻


*🌎MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️


     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

________________________________


  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''


41&42Bayan Gimbiya Kilishi ta tashi daga bacci, babu sallah balle salati ga ankwaso uban laifika amman hankalinta kwance bata da damuwar komai yanzun a ranta..

Dan ita yanzun tana jiran shekara biyar tayi, lokacin har rawa sai tayi dan mutuwa uku lokaci guda, Hakim da Hamad sannan Maimartaba, lokacin  za'a naɗa Humad Sarkin zaria...

"Hmmm! Ni Kilishi nakusa zama uwar sarki, hahahhaha! Waya gayamasu ni ta wasace ya zama dole nazama uwar sarki saboda ubana sarkine kakana suduka biyu sarakunane mijina sarkine dan haka ya zama dole Humad ya zama sarkin zaria, Humad ko kana so ko baka so wallahi sai kazama Sarkin zaria."

Haka Kilishi ta kama cewa tana girgiza jiki cikin taƙama da gadara tana ganin babu wanda ya isa ya hanata bin bokaye..

"Mariya."


"Allah ya taimaki Gimbiya Kilishi, "Mariya ya kukayi da wannan sakaran Bokan naki wanda baisan kan aikinshi ba."?

"Uwarjiyata boka yace shidai bai iya yawa da Hakim dan Hakim tsaye yake wajen ibada yace shi karma nasake dawo mashi."

Mtssssss"aikin banza aikin wofi yo sai mai dan yace karda mu sake dawowa Mariya? Shine kika shiga cikin damuwa dan ya gaza? Ai wanann gazawa ce inba gazawa maizaisa yace Hakim yafi karfinshi."?


"Ranki yadaɗ'e nima abunda nagani kenan, wallahi boka Dasheshe ya bani mamaki, wai ace Dasheshe yake faɗi da bakinshi bai iya aikin Hakim, yanzun Gimbiya uwarjiyata ya zamuyi ina zamu samu wani Bokan."?

"Mariya nasamu boka wanda yafi Dasheshe aiki wanda yasan kyaun aikinshi."

"Yanzun naji magana uwarjiyata wanann wani kalar Bokane wanda yafi Dasheshe iya aiki."? 

"Tabbs Mariya yafi Dasheshe iya aiki da komai ma."

Gimbiya Kilishi ta faɗi tana zagaya ɗakinta cikin taƙama da mulki sannan ta cigaba da faɗin.

"Mariya Turmurturs yafi Dasheshe iya aiki nisa ba kusa ba, Turmurturs yace zaiyi man aiki nan da shekara biyar aiki zaiyi amfani, amman duk sati zandunga zuwa yana yiman wanka."


"Wanka Uwarjiyata."?

"Eh Wanka Mariya kina mamaki ne."?

"Aa baniyi mamaki ba Uwarjiyata, dan ba wanann bane na farko ba, amman ina tsoron karda yayi maki wanka yazo aiki baiyi ba, kinga shi yaci riba mu kuma muka faɗi."


STORY CONTINUES BELOW

"Yi man shiru mutuniyar banza mutuniyar wofi, dan bakisan waye Turmurturs ba shiyasa kike wanann zancen naki na banza."

"Wallahi zan iya yin komai dan naga Humad yayi mulkin zaria, ke ko mutun zan iya kashewa mudun Humad zai zama magajin masarautarnan, balle dan Turmurturs yayi man wanka, ni naso yace duk bayan kwana biyu nazo yayi man wanka dan Turmurturs ni kawai nasan abunda naji gamai dashi shiyasa kike cewa haka ni tashi ki ban waje."

"Allah ya baki hakuri uwarjiyata na barki lafiya."

Nan Mariya ta tafi tana mamakin halin Kilishi, dan ta lura Kilishi bata dauki zina a bakin komai ba..

Bayan tafiyar Mariya Gimbiya Kilishi ta shirya ta dauki hanyar shashen Gimbiya Zulaha...

"Uwarjiyata Gimbiya Kilishi tana neman iso, "ji ki shigo da ita."

"Kilishi tun shekaran jiya ban sake ganin ki ba ko lafiya."?

"Lafiya lau Gimbiya kai nane keman ciwo shiyasa baki ganni kwana biyu ba."

"Ayyya sannu  Kilishi ya jikin naki."?

"Da sauki Gimbiya, ya kin hakura sai nan da shekara biyar din."?

"Eh mana Kilishi na hakura yanzun banida matsalar komai sai ta Hamad, baki daya Hamad ya kasa daina wannnan halin nashi baki daya Kilishi."


"Karki damu Gimbiya, zai daina da zaran ya ganshi bisa kujerar Mulki zai daina komai yake."

"Hakane kuma ban kowa wannan a zuciyata ba, shiyasa nike sonki Kilishi kinada ilimi sosai."

"Godiya mai kyau Gimbiya, ni zan wuce na shirya kafin lokaci yayi na wuce wajen Maimartaba."

"Mu kwana lafiya."


____________________________


"Hakima gida ya ansheki sosai, "ba dole ba Maryam wanann karan Fulani da Maimartaba kamar su goyani dan kawai naci abincin dare da bayina."

"Allah sarki, gaskiya nima naji dadi sosai  dan Allah Hakima ki ƙara jan bayin nan naki a jiki please ƙawata."


"Ai ina iyakar bakin ƙokarina naga ina bin shawarki sosai, "nagode Hakima, yanzun tashi mu shiga class Yaya Hakim ya shigo school tun eight kuma munada shi."Mtsssss"wai har level 2 ɗin ma sai Hakim ya koya mana ina dalili ina murnar na rabu da Hakim ashe mayen yana nan ya biyonu har 200 level sai da ya biyomu ina anfani."

"Yanzun Hakima Yaya Hakim kike cema maye? Kuma a gabana bayan na gaya maki Yayana ne."

"Naji mai Yaya, kedai wallahi kin bani da janye janyen wallahi ni taso mu shiga karda ya wulakantamu cikin mutane dan ba ƙaramin aikinshi bane."

Nan suka shiga cikin class suka zauna, suna labari amman ita Hakima ranta ke ɓace dan ba karamin haushi take ji ba suna zaune Hakim ya shigo..

Ido cikin ido suka yi da Gimbiya Hakima, sai da gaban shi ya faɗi dan ba karamin kyau tayi ba, "yarinya har yarinya amman batada tarbiya bata san darajar na gaba da ita ba."

Hakim yace haka cikin zuciyarshi dan yau ba karamin kyau Hakima tayi mashi ba, haka dai ya kama kanshi ya fara abunda ya kawo shi..

Class din shiru baka jin komai sai muryar Hakim, dan Hakim koyawa yake cikin kwanciyar hankali da natsuwa dan Hakim bai cika san hayaniya ba, shiyasa idan ya shigo class duk wani mai waya sai ya maidata swichoff ko kuma silent amman baya daukar yana cikin, lecture yaji wayar student dinshi tana ringing ko kuma yaga student yana wasa ko wani abu daban...


Dan shi Hakim yana san yaga student ɗinshi ya zama serious baya san yaga student un-serious ko koɗan a rayuwarshi kuma bai san marar kunya shi idan yaga mutun baida kunya to basu zama inuwa ɗaya dashi tsanar mutun yake shiyasa Hakim yayi hating din Gimbiya Hakima dan tunda ya lura bata da kunya ko ɗaya..

Suna cikin lecture, domin lecture ɗin ba ƙaramin dadi tayi masu ba baki ɗayansu more especially ma Hakima da baki ɗaya hankalinta yana wajen Hakim dan ba ƙaramin dadi lecture ɗin tayi mata ba..

Tana mamakin yanda Hakim ya iya koyarwa dan dun rashin ganewarka indai Hakim ya koya maka sai ka gane shiyasa take san lecture ɗin shi, sai dai bata iya daukar cin fuskar da Hakim ke yi mata cikin mutane..

Wayar Hakima ce ta dauki ringing baki ɗaya attendance ɗin class ya koma wajen Hakima dan kowa yasan roles ɗin Hakim baya san yaji ringing ɗin waya a class amman ga wayar Hakima nan tana ta neman agaji a dauketa..

Baki ɗaya jikin Hakima ƙarma yake, dan batasan ya akayi ba haka ta kasance ba ita dai tasan ta maida wayarta silent amman gashi taga akashin haka, duk bata ji dadi ba dan tasan conform sai Hakim ya wulakantata cikin class tana cikin tunani taji Hakim yana cewa..

"Tashi ki fita kibarman class kiyi wayarki,  baki ɗaya baki ganewa balle rabawa inba kina donkey ba taya zaki shigo lecture hall da wayarki normal baki sata silent ba."?

"Oya! Get out useless girl wanda batasan komai ba sai rashin wayau da rashin kunya monkey."

Haka Hakima ta fita class tana bakin cikin yanda Hakim yake ce mata donkey and monkey, dan ita bata damu da yace mata useless ba dan bashi bane farko ba, amman wallahi bazata kyale Hakim ba tunda har ya ce mata donkey and monkey cikin mutane bayan ita tasan tasa wayarta silent...


Bayan fitowar Hakima, Hakim ya gama yi masu lecture ya kama gabanshi dan baki ɗaya baiji daɗin abunda Hakima take yi mashi , dan tana rainashi cikin student dinshi, dan haka dole ya dauki mataki mai girma gaskiya...


"Hakima dan Allah kiyi hakuri, wallahi nice na fidda maki waya a silent ɗazun kafin Prof Hakim ya shigo please forgive me Hakima."


"Maryam bakomai ya wuce a wajena har abada, amman wallahi Hakim sai yasan yace ma GIMBIYA HAKIMA donkey and monkey cikin mutane dan wallahi zan hakura da komai amman banda wulakancin Hakim."


"Ibeg you! Please Hakima kiyi hakuri wallahi bansan that habit, bai da kyau ko ɗaya ba'asan ramuwa dan Allah kiyi hakuri kinga rashi ne ya ɓaci shiyasa yayi maki haka amman wallahi Yaya Hakim ba haka yake ba mutun ne mai sauki hali ga sanin darajar mutane."


"Dakata haka! Taya zaki yiman kallar wanann maganar? Bakiga abunda yayi man ba na fahimci baki sona to as from today bani bake wallahi Maryam karki sake nuna kinyi friendship dani idiot."


"Wallahi baki isa kicemab idiot ba, kece dai idiot wanda batasan mutunci mutane ba, sai mai Hakima dan kince baki ƙara abotaka dani ban damu ba kuma nagode."


"Uhmmmm."

A bunda Hakima tacema Maryam kenan ta wucewarta gida dan tana mamaki yanda Maryam kullun take goyan bayan Hakim dan takamar yana Yayan ƙawayenta, haka har ta isa gida..


Ta kuma Maryam direct gidan su Hakim ta wuce, dan baki ɗaya bataji dadin abunda ya hadasu da Hakima ba, dan tasan Hakima tanada kyaun hali da mutunci, kuma taga itace bata da gaskiya,"why! Why!! Why!!!  Why Hakima zaki ceman idiot duk da ranki na ɓace bai dace kiceman idiot ba kuma wallahi ban daukar wanann mulkin naki Hakima gaskiya."

Haka maryam tatai maganar har ta isa gidansu Maryama...

_By Jameelah Jameey ✍🏻_


Share

Comment

Vote

Like

pls👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

         *GIMBIYA HAKIMA*

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻


*🌎MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️


     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

________________________________


  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''


43&44


Tafiya take tana tunanin wannan halin na Hakima, bata san yanda zatayi taga ta koyama Hakima Son Hakim ba..

Dan itadai tana san Hakima ta aure Hakim amman gashi su duka basu da maƙiya kamar junansu, haka dai Maryam ta kama wanann tunanin har ta isa gidan su Hakim..

Bayan tayi parking ta fito nan suka hadu da Aliyu shima shigowarshi kenan gidan wajen aiki yaje..

"Aaaa! Maryam kice a gidan namu."?

"Yaya Aliyu ina wuni? "Lafiya lau Maryam daman kamar kinsan inasan ganinki."


"Sai kuma gani Yaya Aliyu ina jinka."

"Aiko naji dadin ganinki Maryam, ko zamu zagaya lambu muyi maganar dan tanada tsawo gaskiya ba laifi."

"Alright then, let go Yaya Aliyu bakomai,"ok Maryam,  thank you sister."

Haka Maryam da Aliyu suka dauki hanyar Lambu, Maryam tana mamakin wata kalar magana Aliyu zaiyi mata haka wanda bata yuyuwa a bakin mota har sai anje Lambu...

"Have a sit Maryam, "ok thank Yaya Aliyu."

Bayan Maryam ta zauna nan shima Aliyu ya zauna ya fara magana kamar haka..

"Maryam nasan kina mamakin maganar da zanyi dake ko."?

"Gaskiya hakane Yaya Aliyu ina mamaki sosai dan haka bata taɓe kasancewa ba shiyasa nake jin tsoro."

"Ok kwantar da hankalinki Maryam, ba wata magana bace bayan ta ƙawarki Hakima."

"Hakima kuma Yaya Aliyu."? 

"Yes of course Maryam ,Hakima, inasan Hakima ta auri Hakim amman abun yafi ƙarfina na kasa shawo kan Hakim shine na biyo ta wajenki ko zaki shawo mana kan Hakima."?

Sai da Maryam ta numfasa sanann tace, "Yaya Aliyu abunda ke zuciyata shike cikin zuciyarka, amman am late tooo."

"Bangane kin makara ba Maryam wani abu? Dan kinsani a duhu."

"Eh wani abu Yaya Aliyu, saboda da wani abun shiyasa nace am late, nafi kowa farincikin su zama masoya kuma ma'aurata amman su sun tsani junansu."

"Tabbas Maryam sun tsani junansu amman kuma akwai soyayyar junasu cikin idanunsu, kawai dai kiyayar tayi tasari a kansu shiyasa suka kasa gane soyayyar dake tsakaninsu tunin daɗewa."

"As how? Yaya Aliyu taya haka zata kasance kace suna son junansu bayan kasan basu da wanda suka tsana kamar Junansu."


"Eh hakane Maryam amman suna son junansu sosai, dan haka kema kinsan yanda zakiyi fitting wajen ganin sun mallaki junansu ta hanyar aure, nima zanyi iyakar yina."


STORY CONTINUES BELOW

"Yau munyi faɗa da Hakima saboda na goyi bayan Yaya Hakim har tace ba ita ba ni kaga wannan aikin bani a cikin shi sai dai new friend ɗinta."

"Karki damu wannan fushine kawai yasa tace maki haka, amman zata sauko zata nemaiki da kanta ma."

"Allah yasa Yaya Aliyu dan na damu sosai, ni kuma zanyi iyakar yina naga sun fara soyayya by the grades of God. "

"Thank Maryam Allah ya bamu sa'a baki ɗayanmu Maryam, "Amin Yaya Aliyu ni na wuce cikin gida."


"Ok ki gaidaman da Gimbiya ta nima, "Hahaha! Yaya Aliyu kenan kaima har ka kama Gimbiyarka kenan , to wacece a cikinsu."? 


"Ko wace a cikinsu Maryam, duk inaso, "ok shikenan ni na wuce, "ok byeee."

Nan Maryam ta wuce cikin gida bayan sun gaisa da Fulani Kubrah ta wuce cikin room din su Sadiya..

"Sai yanzun kika zuwa?  ai nasa kin fasa."


"Aa munyi magana da Yaya Aliyu ne shiyasa, "ok Lafiya kika kira waya cikin tashin hankali? Ko wani abu ya samu Hakima."?


"Ba abunda ya samu Hakima sai dai Hakima tace mun rabu."

"What! Because of what Maryam."?

"Dan sunyi faɗa da Yaya Hakim na shigarma Yaya Hakim na bata rashin gaskiya, sai daga baya nasan shine baida gaskiya."

"Haba Maryam ta haka zamu shawo kanta taji interested akan Yaya Hakim, ai ya zama dole a gabanta ki nuna itace mai gaskiya gashi yanzun kin ɓata komai Maryam."

"Maryama wallahi ran nane yayi mugun ɓaci, dan bakiga yanda Hakima take gayaman magana ba ban iya dauka gaskiya shiyasa nima na maida mata."


"Yanzun dai duk ba wannan zamuyi ba, Maryam idan aka kwana biyu kije ku sasanta tsakaninku keda Hakima lokaci dukanku kun huce daga fushin da kuke da juna amman ya kukagani."?


"Haka ma yayi Sadiya, Maryam dan Allah kiyi hakuri karki biyema zuciya please ku shirya zamu ji dadi dan wallahi nidai Hakima tayi man inayi ma Yaya Hakim shi'awar aurenta please Maryam."

"Ok shikenan naji zanyi abunda ya dace ni zan wuce gida ko gida banje ba nayo nan."

"Ko byee thank you, ki gaida Mami sai munzo, "ok byeee."

Nan Maryam ta wucewarta gida..

_______________


"Mariya ki barshi ba sai ki rakani ba ni zan wuce  ki kula sosai Mariya karki gayama kowa."

"Adawo lafiya uwargiyata, zanzamo mai riƙe amana a gareki uwargiyata."

Nana Gimbiya Kilishi ta wucewarta wajen Turmusturs tana rawar jiki dan tasan shine gatanta yanzun😰..

Bayan tayi parking din mota bakin daji inda ba wanda zai ganta ta wucewarta wajen Turmurturs hankalinta kwance..


"Gafara dai sarkin masu aiki gaka da iya wankan dadi Turmurturs."


Hahhahhahha! "Inasan haka."Ya faɗi yana zare ido gamai da lashe baki kamar wani tsohun maye..


Haka Gimbiya Kilishi ta sake tuɓewa gaban Turmurturs ba komai a jikinta nan ya fara yi mata wanka da wani bakin magani bayan ya gama yi mata wanka ya kusance ta ta baya da gabanta sai dai ya moreta sosai san ranshi dan sai da ta kusa yi mashi kuka sannan ya kyaleta ba dan ya gaji ba..


'''Allah ya tsaremu daga sharin aikin zuciya🙏🏻😰'''

Bayan sungama aika-aikan su sanann ta maida kayanta ta wuto gida, bayan ta dawo gida wanka tayi, ikon Allah🤔😟 Gimbiya Kilishi bata wankan tsarki sai dai wanka soso da sabulu bayan duk najasar dake jikinta😧.. .


'''Ni ko nace wani wanka Kilishi zatayi matar da ko sallah batayi balle salati kunga ai ba amfanin yin wankan tsarkin ko? 🤨'''

______________________________

Tafiya take cikin kwanciyar hankali duk da ta kusa tayi latting amman haka bai hana Hakima tayi tafiya cikin natsuwa ba kuma ita ganin take a hakan ma sauri take ta shiga classs..


Bayan ta shiga ta samu sit ta zauna ta cigaba da game dinta kafin Dr Moha ya shigo dan shi ke garesu yau..


Haka itama Maryam ta shigo ta samu sit ta zauna bata kalli inda Hakima take ba, duk ita Hakima bama tasan da shigiwarta ba cikin class din...


Bayan zamansu da kamar 5min Dr Moha ya shigo yayi masu abunda ya kawosu kowa yakama gabanshi ...


Hakima direct gida ta wuce, bayan tayi wanka ta cigaba da karatun ta dan har sun fara tests shiyasa bata damu da wani abu ba sai karatunta, ba ruwanta da su Azima dan ta sa karatunta gaba shiyasa suma suke abunda suke so cikin gidan dan yanzun suna jin dadin zama da Gimbiya Hakima...


Bayan ta gama karatu ta sake yin wanka tayi sallah tayi diner sanann ta kwanta bacci..

Washe gari bayan ta tashi tayi breakfast ta wuce school, bayan ta shiga Hakim ya shigo ba ƙaramin kyau Hakim yayi ma Hakima ba amman sai tayi tsaki tace ita ina ruwanta da kyaun da yayi bayan baida mutunci..


Haka Hakim ya gama yi masu lecture ya kama gabanshi dan ba ƙaramin kyau Hakima tayi mashi ba ko dan yau tasa hijab shiyasa yaga tafi kullun kyau haka ya kama tunaninshi har yana mamakin kanshi..Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wasa-wasa Hakima da Maryam sunyi kunsan wata ɗaya suna gaba, ba tare da sun fargaba dan yanzun sun shiga shirin fara exams hankalinsu baki daya ya koma wajen karatunsu...


*Wattpad JameelarhSadiq


*share

*Comment

*Vote

*please👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

         *GIMBIYA HAKIMA*

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻


*🌎MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️


     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

________________________________


  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''+

45&46

"Hakima ban iya gaba ba, maiyayi zafi Hakima."?

"Mai kikagani? Nima ai bani gaba."


"Naji Hakima yi hakuri please komai ya wuce mu koma yanda muke da please nidai nagaji da wannan abun da muke."


Hmmmm! "Maryam kenan taya zan cigaba da abotaka dake baki sona."?

"Hakima nice bani sonki."?

"Ehmana Maryam komai akayi sai kice nice banda gaskiya inada gaskiya banida da gaskiya haba Maryam nifa ƙawarkice amman kike yi man haka."


"Shikenna Hakima na daina insha Allah, "Allah yasa Maryam."


Nan Hakima da Maryam suka koma kamar yanda suke da shakuwa mai karfi ta ƙara shiga tsakaninsu sosai...

Yau zasu fara exams din Second semester 200 level dan haka yau tun saven Hakima ta shigo school ta take karatu lokacin shiga nayi suka shiga exams hall sukayi exam dinsu suka fito...

"Hakima ya exam din? "Alhmdulh Maryam Allah ya bamu sa'a,"Amin yauwa Hakima dan Allah ki rakani join zani anshi wani abu wajen friends din na."


"Ok ammn dan Allah karda ki daɗe kinsan munada karatu gabanmu sosai."


"Insha Allah nuna ansa zamu wuce ba daɗewa zamuyi ba let go."


Nan suka shiga motar Maryam suka tafi join suna zuwa suka wuce wajen su Maryama da Sadiya da suke zaune suna jiransu tuni daman...

"Oyoyo! Sannunku da zuwa, "yauwa kuyi hakuri mun barku zaune kunsan yau damu aka fara exam."


"Hakane Maryam Allah dai ya bamu sa'a baki ɗayanmu."


"Amin ya Allah, gafa ƙawata Hakima, Hakima ga friends ɗina Maryama da Sadiya."


Cikin class Gimbiya Hakima ta ɗago face dinta tana yi masu smile dan tunda ta gansu taji sunyi ma sun shiga zuciyarta shiyasa ta miƙe masu hannu tana cewa, "Nice too meet you my Friend, "nice too me you too Hakima."

Haka suka kama gaisawa sai da sukayi labari ba laifi Gimbiya Hakima ta bada concerntration wajen labarin amman bai wuce Uhmmm ba...

Bayan sun gama gaisawa Maryam tayi droping din Hakima gida itama ta wuce gida..

_____________________________


"Kai Hamad baka da hankali zaka shigo gida cikin wannan yanayin salon maimartaba ya ganka haka ya zamu yi kenan."?

"Haba Gimbiya Laifine dan nashigo gidan ubana."?

Hamad yake yima Gimbiya Zulaha wannan question din cikin maye dan baki ɗaya bai cikin hankalinshi...

"Ubanka nace Hamad na zaka tona ma asiri, yanzun da ubanka ya ganka shikenan ka ɓataman aikin da nike jira nan da shekara biyar kaji man yaro."


"Ni zan wuce tunda baki murna da gani na ba, daman zuwa nayi na gaidaki tunda baki so ni zankoma daman Baby nacan tana jirana."


"Na shiga ukuna ni Zulaha, Hamad yaushe zaka chanza hali ka dawo mutun, kasan masarautarnan ba'a ba mai-shaye-shaye mulki a haka zamuyi mulkin."?

"Karki damu Gimbiya i'll be change insha Allah ni zan wuce sai kin sake gani na."

Haka Hamad ya tafi ya bar Gimbiya Zulaha cikin bakin ciki tana bakin cikin ganin Hamad cikin wannan yanayin gashi shi kawai yake shaye-shaye cikin iyalen maimartaba..

Haka ta gama tunaninta ta kwanta bacci da yake dare yayi daman...

________________________


Haka Hakima ta maida hankalinta wajen exams din da take , dan karatu take ba kama hannun yaro..

Yau suke Second to the last papper dan haka da wuri taje school bayan sun fito daga exam ta wuce kasuwa tayi abunda take bukata dan gobe tana fitowa exam gida zata wuce dan tayi missing din su Fulani sosai...

Washe gari bayan ta fito last papper ba ƙaramin murna tayi ba zata shiga 300 level  da sun dawo zasu shiga, bayan ta dawo daga school suka dauki hanyar kano..

*Wattpad JameelarhSadiq*


*share*

*Comment*

*Vote*

*please*


*Kuyi magane pls yau banjin dadi shys*👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

         *GIMBIYA HAKIMA*

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻


*🌎MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️


     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

________________________________


  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

47&48


"Hakima sannu kinsha karatu kinga yanda kika koma."? 

"Momy ba dole ba wallahi karatun naija ba sauki shiyasa naso Baffah ya fidda ni turkey amman yaki yarda."

"Daughter ai zuwanki Zaria kin chanza sosai ba kamar da ba, tunda gashi yanzun bayinki suna samun sausauci."


"Uhmmm! Ni daman ko da Momy ba abunda nike yi masu kawai dai kuke ganin Ina matsa masu."


"To Daughter ki kara sabo dasu kinj."?

"Eh naji Momy, "Daughter yanzun har zaki shiga 300 level amman banji kin fara kula samari ba, komai yasa."?

"Haba Momy ai ni yarinya ce fa duka duka yanzun  nike da shekara sha tara fa, ni gaskiya ban isa aure ba."


"Aiko kice kika isa aure, ki fara kula samari in ba haka ba Maimartaba ya fidda maki da kanshi kinsan dai kina gama karatun nan aure zaiyi maki."


"Momy jibaini fa yarinya dani Baffah yayi man aure tun yanzun ina laifin na gama masters din sannan."

"Daughter waya gaya maki gidan sarauta ana karatu."?

"Momy amman.. "Da kata Hakima."


Yakumbo ta tsada Hakima cikin fushi dan ta lura Hakima batada ra'ayin kula samari kuma tana tsoran karda maimartaba yayi mata auren dole...

"Daughter gidan sarauta ba'a karatu sai dai mulki yanzun ne da zamani ya shigo mu masu sarauta muka dauki boko muka sama kanmu Amman mu da mulki aka sanmu."


"Kuma Ina laifin da ya barki kikayi degree, ki fidda master a zuciyarki kisa aure, Daughter ki fara kula samari kafin dare yayi maki shawarata kenan a matsayina na Wanda ta daukeki diya."


"To insha Allah Momy zan duba, ni zan wuce Momy na barki lafiya."


"To Daughter, kin gaida Fulani KO? "Aa yanzun zan wuce wajenta daman daga wajen Baffah na biyo wajenki sanann wajenta, "OK Daughter."


Haka Hakima ta dauke shashen Fulani tana tunani maganar da Yakumbo tayi mata ba kamar wannan maganar, "Daughter ki fara kula samari kafin dare yayi maki."


Haka Hakima ta Kama maimata wanann maganar har ta iso shashen Fulani, nan akayi mata iso ta shiga..

"Fulani ina wuni, "Lafiya Hakima ya karatun."?

"Lafiyalau Alhmdulh, "to Allah ya bada sa'a, "Amin ya Allah..."


"Na sa maiki Lafiya."?

"Lafiya lau, in kina bukata ki shirya gobe zamu adamawa bikin Yarima Bishir."?

STORY CONTINUES BELOW

"Ok daman Yaya Bishir aure zaiyi kenan? Shine babu ko gaiyata."


"Hakima taya Bishir zai gaiyaceki bikinshi bayan kin gujeshi? Wani irin sone Bishir baiyi maki ba."?

"Ai Fulani ni yarinyace ban isa aure ba shiyasa ban yarda da soyayyarshi ba."


"Ai sai ki ta zama Hakima har sai randa kika isa auren sai kiyi, shidai Bishir jibine aurenshi yar'sarkin Yobe zai aure Gimbiya Zaituna."


"Allah ya basu zaman Lafiya, "Amin ya Allah."


"Ni zan wuce nasa a fara shiryaman kayana kafin goben."


"To mu kwana lafiya, "Allah yasa Fulani."


Haka Hakima ta dawo shashenta tasa Azima ta shirya masu kayansu ita da su Inna Lantana..

_____________________________


"Kilishi kinga wannan maganin shi za'a sama Maimartaba cikin abinci yana ci ya gama aiki."


"Ar'riri nanaye, Gimbiya wannan abun yayi man dadi sosai bani shi nan naje na sama shi tunda yau nike dashi."


"Daga ganin Sarkin Fawa sai Miya tayi zaki."?

"Ai Gimbiya zafi-zafi a kan buga karfe ko."?

Hmmm! "Ai duk saurin unguwar zoma dan ubanta ta bari a haihu sanann tazo ta yanke cibi."


"To Gimbiya gayaman ya za'ayi."?

"Ajiye maganin zamuyi sai nan da shekara biyar sanann."


"Maiyasa kikace haka Gimbiya."?

"Eh Kilishi yanzun muka bashi magani yasha ya mutun kafin shekara biyar kinga dole aba Hakim mulki."


"Kin kawo shawara kuma mai kyau."


"Wallahi na tsani naga Hakim yayi mulki kona kwana daya ne, dan uwarshi za'a kirata da uwar'sarki, na tsani naji ana kiranta da wanna sunan."


Haka suka kama tautaunawa sannan kowa ya kama gabanshi..

______________________________

"Ranki ya daɗ'e angama shirya komai."


"Azima kin tabbata komai da komai kika shirya."?

"Eh duk abunda nasan zaki bukata na shirya shi kawai umirnin ki nike jira uwar marayu."


''Ok zaki iya tafiya ki fiddo naku kayan sai mu wuce shashen Gimbiya Fulani."?

"Godiya muke uwar marayu, yar'sarki jikar'sarki uwar sar... "Dakata haka mana Azima kinsan bansan wannan surutun naku na banza tashi kije Kiyi abunda na saki kafin ranki ya ɓaci yanzun."


Hakima ta faɗi cikin ɓacin rai dan ba abunda ta tsana duniya bai wuci kace mata uwar'sarki ba dan ita bata shirya aure ba dan yanzun balle har ta zama wata uwar'sarki..

Haka Azima ta tashi tana mamakin Hakima ta lura duk yanda kake da Gimbiya Hakima mudun kace mata uwar'sarki sai ta nemi wulakanta mutum ko waye shi nan Azima ta cigaba da fiddo kayan su amman tunanin na cikin zuciyarta bata tace, "oni Azima ko maiyasa Gimbiya Hakima batasan ace mata uwar'sarki."?

Batasan maganar ta fito fili ba sai ji tayi Ba'ba Bilkisu nacewa, "ai abunda yasa Gimbiya Hakima bata san kiranta da uwar'sarki saboda bata shirya yin aure ba yanzun."


"Sannan bata gaji da mulkamu ba san ranta yanda take bukata duk da yanzun Alhmdulh komai yayi sauki ba kamar da ba."


Hmmmm! "Aiko idai hakane gaskiya muna da aiki nida nike murna ta kusa gama karatunta sai aure amman ace mutun bai san aure."


"Azima kisa a ranki ki ko gidan aure tare zaki da Gimbiya Hakima sai dai kawai mu samu muna shiga jikinta sosai yanda zata ji kunyar wulakanta mu cikin mutune."


"To shikenan kawai ku taso mu tafi kunsan bata san jira, "aiko dai."


Nan suka tafi suka ida shirya ma Gimbiya Hakima

Sannan suka wuce shashen Gimbiya Fulani...

Bayan Gimbiya Fulani ta gama shiryawa suka dauki hanyar Adamawa...

Bayan sun isa Adamawa aka tarbaisu tarba ta girmamawa aka saukesu shashen Gimbiya Fulani dake cikin gidansu nan tayi yan-matancinta..

Bayan sun huta Suka dunguma sai shashen tsohon sarki  Maimartaba Sarki Kabir mahaifin Fulani Aisha..

Nan suka gaisheshi sannnan suka wuce shashen Maimartaba Sarki Al-Khamis shine sarki mai mulki yanzun yayan Fulani Aisha ne uwa ɗaya uba ɗaya ɗanshi ake yima biki Yarima Bishir..

Bayan sun gama gaisawa ta wuce shashen Gimbiya Mabaruka wato mahaifiyarta sai da suka gama gaisawa sannan ta wuce shashen kowa suka gaisa ta dawo shashenta..

Washe gari aka fara hidimar biki ba karamin kudin ake zubda wa ba haka aka kama al-adu kala-kala sune basu je suka kwanta ba sai dare..

Haka ma wan shekare aka ɗaura daga inda aka tsaya bayan angama kowa yaje ya kwanta..

Washe gari aka daura Auren Yarima Bishir da Gimbiya Balaraba yar'Sarkin Yobe..

Nan Gimbiya Hakima taje yi ma Yarima Bishir Allah yasa alkhari..

Tafiya take cikin natsuwa da kwanciyar sai kace wanda take jin tausayin kasa bata san takata, wani irin lafoyaiyen lace ne black a jikinta ba ƙaramin kyau yayi ma Hakima ba abun ka da farar fata sai kace itace amaryarma..

Tunda ta doso wajen Yarima Bishir ya kafeta da ido yana ainama kanshi duk rintsi sai ya mallaki Hakima da sunan matar aurenshi dan ba ƙaramin so yake yi ma ƙanwartashi ba..

Sai da ta iso wajenshi ta fara magana sannan ya dawo cikin haiyacinshi, dan ƙaramin bakinta yake kallo tana motsashi kamar anayi mata dole..

"Ina tayaka murna Yaya Bishir Allah ya baku zaman lafiya"..

"Hakima maiye aibuna a wajenki?  Maiyasa baki sona? Nifa ɗan'uwanki ne Hakima kuma ina masifar sonki da kaunarki"...

"Haba Yarima Bishir taya zakayi wannan maganar bayan abun ya wuce tuni gashi yau aka daura maka aure"..

"Dakata haka Hakima nayi alwari komai nawa zai ƙare sai dai ya ƙare wajen neman auren ki dole ki aureni Hakima ko kina so ko baki so"..

Ya faɗa cikin fushi da ɓacin rai ya barta tsaye da mamaki..

*Tota Team Hakim gafa Yarima Bishir nan ya sake dawowa anya wannan abun zai yuyu kuwa?*


'''Nidai question nayi maku ina jiran answers🤷🏻‍♀️'''

Yan wattpad ku kawai zan ringa yi ma. Update dan inajin dadin comment idan kuma kuka daina kuma zan daina yi maku update sai na daina writing baki ɗaya.

_By jameelah Jameey ✍🏻_


*Share*

*Comment*

*Vote*

*Like*

*please*

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________
+
  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

49&50

Tunda Yarima Bishir ya tafi Hakima batayi motsi ba tana mamakin yanda Bishir yake yi mata gadara har haka, "sai mu gani Bishir ni kuma bani sonka, baka isa ka sani dole ba."
Haka Hakima ta ce sanann ta wuto warta shashen su ta cigaba da hidimarta hankali kwance dan tasa a ranta ko kasheta za'ayi baza ta iya auren Yarima Bishir ba...
Haka suka gama shagalin bikinsu sanann suka dawo gida..
"Lantana anjima ki shirya zani wankin kai da gyaran jiki dan haka  a gaya ma masu shirya fita cikin gari."

"Angama uwar marayu, Allah ya kaimu anjimar lafiya."

"Amin sanann kice ma su A'bu kar suyi abincin dare dan yau shashen Fulani zanci abincin dare."

"To Allah ya taimaki Gimbiya Hakima komai kika ce haka za'ayi zan isar da saƙonki yanzun nan na barki lafiya."

"Ki turoman da Azima tazo yanzun ba sai anjima ba ina san ganinta."
"Angama uwargijiyata, na barki lafiya."

Nan Lantana ta tafi kai saƙon Gimbiya Hakima, ita kuma Gimbiya bayan ta fiyar Lantana kwanciya tayi tana waya da Maryam dan Maryam ta gaya mata gobe ake resuming school...
"Haba Maryam! Am tire wallahi ko,  wanann karatun ya fara fita raina sai mutun yana cikin hutu yana jindaɗinshi sai a wani koma school."
"Gaskiya ne Hakima dole kice haka tunda kina gida kina mulki, kuma mai ya rage tunda mun shiga 300 level saura one year fa."
"Haka mutane ke cewa saura one year, bakusan wata kalar kura ke cikin one year ɗin ba."

"Kuma kinsan karatun ba dadi sai dai hakuri kawai Hakima, "wallahi Maryam abun ba dadi sai addu'a nima this week zan dawo insha Allah."
"Allah ya kaimu lafiya, "Amin ya Allah byeee zana shirya zan tafi gyran kai da jiki."

"Ehyeeh! Gyaran kai da jiki kamar wata amarya, "wannan al'adata ne Maryam na saba gyaran jiki  duk mouth koda ina ƙauyenku."

"Kindai faɗi dan kiji dadi amman kinsan Zaria tafi ƙarfin a kirata da sunan ƙauye."

"Naji masu kishi, kowa kanshi ya sani byee."

Bayan ta gama waya da Maryam Azima ta shigo ta haɗa ma Gimbiya ruwan wanka..
"Ranki yadaɗ'e ga ruwan can yana jiran ki."

"Ok kisamu kaya mararsa nauyi ki fiddo man, dan naji ana zafi ba laifi."

"Angama uwargijiyata."

Nan Gimbiya ta shiga wanka Azima ta fiddo mata kaya, bayan ta fito Gimbiya ta shirya tayi kyau sosai sannan suka tafi gyaran jiki...
____________________________
"Kilishi nifa Ina lissafi saura shekara uku Hakim ya mutu."
Hahahhahhaha! "Haba Gimbiya ai nafiki lissafi dan har rubutawa nayi a litaffi, dan na gaji da ganin Hakim yana yawo bisa doran kasa."

"Na tsani Hakim, ban ƙaunar na bude ido naga Hakim yana numfashi baki yanda nike ji ba Kilishi."
"To ai hankalinki ya kwanta Gimbiya tunda Turmurturs yace shekara biyar nasan aikinshi ba wasa daga ganinshi."
"Tabbas ni zan cemaki aikin Turmurturs bana wasa bane, kawai musa ido muga ranar wasa-wasa ta kusa zuwa tunda har munyi shekara biyu da zuwa."
"Aiko kinga bayan ya mutu da kamar sati sai mu sama ubanshi maganin nan yasha kinga sai muce baƙin cikin matuwar Hakim yasa jininshi ya hau ya bishi tunda yana sonshi."
"Haka mana kinga ba mai sama mana alamar tambaya, hahahhaha! Wallahi Kilishi inacikin farin ciki na kusa zama uwar'sarki."
☺️☺️☺️☺️☺️ Niko nace GIMBIYA ZULAHA ko sakara tana ta dariya gaban makasarta bata sani ba, amman ita taba GIMBIYA KILISHI Amana, Allah ka tsaremu daga sharin zuciya😭😭😭..

Wani kallar kallo Gimbiya Kilishi tayi ma Gimbiya Zulaha da taji tace ta kusa zama uwar'sarki ji tayi kamar ta sheƙeta ta huta dan ita duniya ba wanda ta tsana kamar Gimbiya Zulaha itada ɗanta Yarima Hamad..
"Aiko dai munkusa zaman uwar'sarki nan da shekara uku masu zuwa."
"Daman Kilishi ni kaɗai nasan abunda zanyi ma Fulani Kubrah idan Hamad ya hau milki dan sai na wulakanta ta nasa Hamad yayi ma wanann yan-iskan yaran nata faɗe sanann mu koresu subar garin baki ɗaya nasan bata nisa zata mutu saboda bakin ciki."
"Kin kyauta ko Gimbiya ni zan wuce kinga dare yayi, "to mu kwana lafiya."
Bayan Gimbiya Kilishi ta fito shashen Gimbiya Zulaha ba inda ta wuce sai wajen Turmurturs..
Sai da suka gama sheƙe ayarsu sanann ta wuto gida, wanka kawai tayi ta kwanta bacci..
_________________________

Bayan Hakima sun dawo daga salon ta wuce shashen Fulani taci abincin dare sannan ta dawo ta kwanta...

Haka rayuwa  ta cigaba da tafiya dan yau Gimbiya Hakima take komawa school bayan ta gama shiryawa sukayi sallama dasu Gimbiya Yakumbo sannnan suka wuce school...
Bayan sun isa su Lantana suka gyara gida tas sannan suka haɗama Gimbiya ruwanka...
"Allah ya taimakeki ga ruwan wanka can yana jiranki."
"Bilkisu  Ki haɗoman Tea."

"Angama uwar marayu, amman asa sugar ko kar'asa."?
Wani kallar kallo Gimbiya Hakima tayi ma Bilkisu sannan ta wucewarta toilet, dan gani take raini ya fara shiga tsakaninta da Bilkisu...
Bilkisu take jikinta ya fara rawa tana mamakin yanda baki ɗaya Gimbiya Hakima ta chanza daga tambayar asa sugar, "oh ni Bilkisu mai hali dai baya chanza halinshi."
Abunda Bilkisu tace kenan sannan ta tashi taje ta haɗo ma Gimbiya Hakima Tea amman bata sa sugar ba sai dai ta ɗebo sugar ta shigo dashi baki ɗaya...
Bayan Gimbiya Hakima ta fito wanka Azima ta shafa mata mai ta tayata shiryawa sanann ta kalli Bilkisu tace, "idan kin tashi kijuyo buhun sugar kinji ni ko."?
"Ina neman sausaucin uwar marayu tuba nike bazan sake kallar wannan laifin ba."

Uhmmmm! Abunda tace kenan sannan ta anshi Tea ɗin tasa aka zuba mata sugar ta fara sha..
Kash! Itadai Gimbiya Hakima badai Mulki ba yanzun common imaging sugar ma baki sawa da hannunki sai anzuba maki🙄..

Tana shan Tea su Bilkisu nayi mata tausa ita kuma Azima tana karanta mata novel bayan ta gama shan Tea ta kwanta bacci sannan suma suka wuce suka kwanta..

_By Jameelah Jameey✍🏻_
*Share*
*Comment*
*Vote*
*Like*
*Please*

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________
  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

51&52


Washe gari bayan Gimbiya ta tashi daga bacci shiryawa tayi sannan ta fito yin breakfast..
Tafiya take kamar bata san taka kasa dan yau zata kaima bayin masarautar ziyara sannan ta wuce shashen wazari zata gano shi da jiki dan baiji daɗin jikinshi ba kwana biyu..
+
"Allah ya taimaki Gimbiya Hakima takawarki Lafiya yar'sarki jikar sarki gaba dai gaba dai Uwar Marayun kano baki ɗayanta."
"Lantana maza kije ki kiranta shugaban gidan horo inasan ganinshi yanzun kafin mu tafi ziyarar nan."
"Angama Uwargijiyata, muna neman sausaucin Uwar Marayu, na barki Lafiya."
"Bilkisu yi maza ki ɗauko kan wayata wanda nike waya da ita dan naga alamu baku fito da ita ba ko ni kuka bari na ɗauko maku wayar."?
"Allah ya ja da tsawancin kwana ina neman afuwar Gimbiya Hakima Uwar Marayu wallahi safa'a nayi nasa duka na ɗauko su."
"Ya isa haka Bilkisu ba abunda zanyi maki tashi kije ki ɗauko karki ɓatamana lokaci da wannna shurutun naki, kudai baki ɗayanku kun cika shurutun masifa wallahi haba."
Nan Bilkisu ta tashi ta ɗauko waya tana godema Allah da Gimbiya Hakima tace batayi mata komai dan ba ƙaramin tashi hankalinta yayi ba, dan taji ta aika a kira mata shugaban gidan horo baki ɗaya bama sarkin Bulala ba..

"Allah ya taimakeka, Gimbiya Hakima tace tana san ganinka yanzun -yanzun nan inma da hali mu taho tare ƙafata ƙafarka."
"Lantana Allah yasa ba wani abu kuka yi mata ba."?
"Ba abunda mukayi kawai dai tana san ganinka , amman ba abunda akayi mata."
"To shikenan, mu tafi daman bansan naji ance wata baiwa tayi laifi a shashen Gimbiya Hakima dan bansan naga a na hukunta mata dama maza lafiya lau."
"Aiko dai Allah ya ƙara mana hakurin zama da ita, "Amin ya Allah Lantana."

Nan suka tare da Lantana su tautaunawa yanda lokaci guda Gimbiya Hakima ta chanza halinta baki ɗaya bayan sun isa Lantana tayi mashi iso wajen Gimbiya Hakima sannan suka shigo tare..
"Allah ya taimakeki Allah ya ƙarama Gimbiya Hakima tsawon rai, gani na ansa kiranki cikin gaugawa ina jiran umirninki."

"Mudi kana jina."?
"Eh Uwar Marayu ina sauraranki."

"Duk wanda yake cikin gidan horo a sallameshi ya koma bakin aikinshi, na yafema kowa koda bani yayi ma laifi ba balle nasan duk wanda yake cikin gidan nace sillar Shigarshi ciki."

"Godiya suke Uwar Marayu yanzun nan zai zartar da umirninki, na barki Lafiya."
Nan Mudi ya tafi fiddo bayin dake kulle gidan horo, ita kuma Gimbiya Hakima ta tafi ziyara gidan bayi ba ƙaramin kyauta tayi ma bayi ba daga nan ta wuce gidan waziri ta duba jikinshi sannan ta wuto shashen ta..

Masauratar kano a ranar ba ƙaramin murna sukayi ba dan har sai da bayi suka haɗama Gimbiya Hakima walima gobe za'ayi ta..
"Uwar Marayu gobe insha Allah baki ɗaya bayin gidan nan suna gaiyatarki walima bakin ruwa, zamu nuna maki godiya da jindaɗin abunda kikayi a jiya."
"Bilkisu Allah ya kaimu goben, yanzun bacci zanyi sannan kuma ku fara shiryawa jibi zamu koma makaranta."
Washe gari bayan Gimbiya Hakima ta gama shiryawa direct shashen Gimbiya Yakumbo ta wuce kafin dare yayi taje walimar da bayi suka shirya mata..
"Momy kin tashi lafiya."?
"Lafiya lau Hakima ya koƙari?, "Alhmdulillah Momy, Momy gobe zan koma school fa."
"Ai ya dace a koma tunda ankusa gamawa insha Allah."

"Aiko dai Momy sauran Shekara ɗaya insha Allah, "Allah ya kaimu Hakima, "Amin Momy Yaya Annas shima da mukayi yawa yace next year ɗin nan zai dawo ya gama shima baki ɗaya."
"Eh kinga tare zaku gama keda shi, "Aa Momy shi harda masters yayi fa nikuma degree kinga ai da banbanci sosai."

"To Allah ya baku Nasara baki ɗayanku, "Amin ya Allah ni barki lafiya Momy zan biya na gaise da Fulani."

"To Daugter Allah yayi maki al'barka, "Amin Momy."

Bayan ta wuce shashen Gimbiya Fulani suka gaisa sosai, "Fulani zanyi missing ɗinki gobe ne zan koma school."

"Nima zanyi missing ɗinki Hakima, dan Allah ki kula da mutuncin kanki kiyi abunda ya kaiki wannan gari."
"Insha Allah zan kiyaya, "idan mu iyayenki bamu ganinki to Allahn da ya halliceki yana kallonki kuma duniya duk abunda ka suka shi zaka girba dan haka kiji tsoran Allah sannan ki guji abunda zai ɓatama iyayenki rai har ya sasu hawaye."
"Insha Allah Fulani, bayan Fulani ta gama yi ma Hakima wa'azi sanann ta fito ta wuce shashen ta, shiryawa tayu sannan suka wuce walima.
Ba ƙaramin dadi Gimbiya Hakima tayi dan bayi sunyi koƙari sosai wajen ganin sun faranta ma Gimbiya Hakima rai, kuma Alhmdulillah suma sunji dadi dan a fuskar kawai zasu gane Gimbiya Hakima taji dadin abunda suka yi mata dan sai murmurshi take, bayan anci ansha sanann kowa ya tafi makwancinshi..

Wanka kawai Gimbiya Hakima tayi sannan ta kwanta bacci, washe gari karfe biyun rana suka ɗauki hanyar Zaria..

*Oooooooo🥺wallahi nagaji sosai typing is no essay guy kuyi manage da wanannna pls inayinku ovver and over💃🏼❤️🖤💯*

*ANJIMA ZANYI MAKU WANI UPDATE INSHA ALLAH*

_By Jameelah Jameey✍🏻_

*Share*
*COMMENT*
*Vote*
*Like*
*Please*

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

53&54


"Boka Turmurturs na kawo kukana wajenka ina san ka shareman hawayena."

"Ina san haka, Gimbiya Kilishi ai ke ta daban ce wata matsala ce kuma ta kunno kai kuma."?
"Turmurturs kwana biyu maimartaba baya kulani ba kamar da ba shine nace anya ba shiga tsakaninmu akayi dashi ba."?
"Tabbas Gimbiya Kubrah ta shiga tsakanin ki da mai gidanki, dan haka idan muka cigaba da yin wanka lafiya lau kin fi karfin duk wani makirci."?

"Ni Kubrah zata haɗa da maimartaba shikenan Turmurturs kabarta tayi lokacine nan da shekara biyu sai Kubrah ta zama baiwata."

"Au to dan aiki yana nan yanda ya kamata dan Turmurturs yace ankusa gamawa da Hakim harda Hamad ɗin da kikace a kashe maki."

"Yauwa ina godiya Turmurturs."

Nan Turmurturs yayi mata wanka da abunda suka saba duk sati sanann ta wuce gida hankalinta kwance..
Bayan ta dawo gida wanka kawai tayi ta kwanta cikin farin ciki, dan gani take Humad ya gama Mulkin zaria, dan bata ɗauki shekara biyu wani abu ba tunda har tayi hakurin shekaru tana bin bokaye amman ba biyan bukata sai yanzun ta Zulaha ta haɗata da Turmurturs tasan bukatar ta tabiya, haka dai har bacci ya kwasheta..
_____________________________
Bayan Gimbiya Hakima sun iso gida, gyara gidan akayi sannan ta shirya ta wuce school dan suna da lecture three dan haka hutawa kawai tayi sannan ta wuce school..
"Hakima kinga yanda kika koma kamar wata sarauniya matar Sarki."
"Kinji ki wallahi Maryam kin cika surutu har wani abu na ƙara kenan? Ke bance kin ƙara wani abu ba sai ke."?
"Ai ni ba abunda na ƙara, amman ke baki ganki ba masha Allah kamar yar India, anya Hakima bakida dangi a Indiyawa ko kuma larabawa."?

"Ke dai akeji Maryam, wani lecturer ne zan ɗaukemu 300lvel wai."?
"Prof Hakim da Dr Moha sai wasu ni ban riƙe sunansu ba dan vistors lecturers ne."
"Ok Allah ya bamu sa'a, "Amin ya Allah result ya fito naga kece over'roll ma, gaskiya Hakima kinyi koƙari sosai Allah yasa ki gama da First class ɗinki."

"Kedai Allah ya bamu sa'a baki ɗayanmu ,"Amin ya Allah ga Dr Moha nan, "na ganshi daga shi sai gida kenan."?
"Eh ai last week Prof Hakim yayi  attendance wai mune serious students tunda mun dawo kan lokaci, shine muka ce ai duk ku ba garin kuke ba shiyasa  amman ya nuna I don't care a kan reason din da aka bashi."

Mtsssss"matsalarshi nasan saboda dani yayi attendance dan yaga ban dawo ba kuma bani da damuwa da wannan."

"Aa Hakima kije ki bashi hakuri, dan naji yace shine a matsayin first C. A din shi kinga dole kije office ki bashi hakuri dan mutane sai zuwa suke kuma yana yi masu favor kinga ai kema sai kije daman kamar kece karshen dawowa."

"Ba zuwan ba, wallahi wulakancin shine bani ɗauka kin sani kawai na hakura mun haɗa a second c.a da exams kawai."

"To shikenan tunda kince haka kinga Dr ba shigowa yayi ba captain ya kira Allah ya sa ba fixing zai yi mana ba, "Amin."

Haka suka gama zamansu babu abunda suka yi suka koma gida, washe gari suka dawo suka yi lecture din Hakim..

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, dan tsakanin Hakima da Hakim abun nasu sai Allah dan ba kaunar junansu suke ba..
Karatu yayi nisa sosai dan 300lvel ba abun wasa bace shiyasa Hakima take karatu ba kama hannun yaro, duk da Hakim yace ya zama dole sai ta zo office dinshi dan ta bashi hakuri, kamar yanda duk wanda baiyi ma attendance suka zo har office  bashi hakuri, ita kuma tace bata zuwa sai wannan abun ya zama sillar caryover dinta..

Yau da wuri ta shirya ta wuce school saboda Dr Moha zai yi masu test shiyasa ta fito tun eight duk da sai ten zaiyi masu test din, tunda taje karatu take dan ta lura course din Dr shima ba laifi yana da wahala shiyasa ta dage mashi, sai wajen nine thirty Maryam ta shigo itama..
"Hakima tun yaushe kika zo?, "tun eight mana, sannu da zuwa late comer, "Yauwa dan Allah Hakima idan kika fito test din nan kije ki ba Yaya Hakim hakuri ai malaminki ne karki biye ma zuciya."

"Maryam ban daukar wulakancin Hakim shiyasa,  na gaji da abunda Hakim yake yi man na gaji am tired wallahi."

"To mai yayi saura keda kin kusa gama baki daya baki sake ganin shi tunda ba garinku daya ba, "to naji zan je kinga ga Dr nan yazo Allah ya bamu sa'a baki daya, "Amin."

Bayan Dr Moha ya shigo yayi masu test ba laifi dan sunyi mamaki saboda ba haka suka ran test din zata yi masu ba amman tayi dadi sosai , dan question yayi masu masu sauki sosai, bayan sun fito Maryam ta raka Hakima Office din Hakim amman bata shiga ba sai ta tsaya bakin office din..

Nocking tayi sannan ta shiga, bata damu da yace ta zauna ba ta samu wani sit ta zauna ta jiran ya gama waya dan ta lura waya yake mai mahinmanci shiyasa..

Bayan Hakim ya gama waya ya juyo ya kyaleta sanann yace, "what Wrong with you? Kin zo ki sani gaba sai kallo kike kamar tsohuwar maiya."

"Lafiyarce ta kawo haka, dakata Hakim komai kake karka kuma ceman Maiya, kuma inni maiyace nafi karfin na cinyeka kuma kasan office dinka kallo bai isheni balle har na cinyeka."

"Shut up, stupid girl, wai Hakima sai yaushe zakiyi hankali dan Allah dan Annabi?  ace mutun kamar ciwon ciki, ki kiyayeni Hakima, to wata tsiyar ta shigo dake."?

"Ni ba tsiya ta shigo dani office din ka ba, daman zuwa nayi akan attendance din da kayi first week din dawowa, nazo ka sa suna kamar yanda kasa na su tunda mu ba garinku muke ba shiyasa bamu shigo week din farko ba."

Tunda Hakima ta fara magana Hakim ke kallon dan karamin bakinta dan ba karamin burgeshi tayi sai yaji ina kartayi shiru ta cigaba da maganar, shidai bai san reason ba amman yana san yaga Hakima na magana ba tun yau ba, amman shi dai baya daukar raini duba da yanda take magana kamar tana bashi comment..

"Ta shi ki barman Office Hakima ba wani sanyaki da zanyi tunda na fahimci baki iya magani ba."

"Bangane ban iya magani Malam duk maganar nayi ita maicece?shikenan zan tafi Allah yana sane da Hakima."

Nan Hakima ta fita office din Hakim cikin fushi wai ita Hakim zaice ma bata Iya magana ba ga kuma yace mata maiya._By Jameelah Jameey ✍🏻_

#JameelarhSadiq
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

+
55&56

"Hakima ya naga kin fito cikin fushi ba dai bai yi maki ba."?
"Kyaleshi Maryam shiyasa nace maki bani zuwa dan nasan ko naje wallahi sai Hakim ya bata man rai, wai ni Hakim yake cema Maiya."

"Maiya kuma Hakima.''?
"Haka kika ji nace, wallahi na tsani Hakim ban san Hakim dan haka in dan ya gadama ya bani C. O, nidai nasan Allah yana tare dani."

"Aiko bai kyauta ba, bari na dawo, "ina zakije Maryam."?

"Kedai ki jirani kawai am coming."
Nan Maryam ta shiga office din Hakim, dan bata ji dadin abunda yayi ma Hakima, dan ji take kamar ita yace ma Maiya ba Hakima ba..

"Yaya Hakim sannu da aiki, "Yauwa Maryam, lafiya mai ya samaiki naganki haka."?
*🥶🥶Hakim na kusa fa to Team Hakima kunji Hakim mai kanwa ko? Duk ya shiga damuwa amman yanzun ya gama wulakanta Hakima cikin office din shi bai damuba🙄.*

"Yaya Hakim why? Maiyasa kace ma Hakima Maiya."?
"Ke tashi ki barman office tun kafin na taitaikaki, ke har ni zaki sa gaba kina yi ma silly questions kamar wani abokinki."?

Cikin kuka Maryam ta fara magana dan baki daya ta fara gajiya da abunda suke kamar kananun yara..
"Haba Yaya Hakim wai sai yaushe zaku fara rage tsanar da kuke yi ma junanku kai da Hakima."?
"Yaya Hakim bai kamata ba wallahi totally is round ace kaine kake kallar wannan abun ka biye ma Hakima, koda Hakima bata gaya man ba nasan ni kaina na girme Hakima Yaya Hakim maiyasa."?

"Dan Allah Yaya Hakim mai Hakima tayi maka har haka da wannan bakar tsanar ta shiga tsakanin ku."?

"Ya isa Maryam is enough."
Hakim yace ma Maryam cikin fushi dan yaga Maryam nason raina mashi wayau..
"Get out of my office useless girl, kin biye ma wancan  useless girl din ta bata maki rayuwa kin fara rashin Kunya wawiya kawai zaki fita ko sai nayi ball dake."?

Haka Maryam ta fita duk ba dadi dan ita gaskiya ta gaji da wannan abun, dan ta gaji iyakar gaskiya..

"Maryam yi hakuri wuce mu tafi, kibar Hakim da halinshi."

STORY CONTINUES BELOW

"Dan Allah Hakima ki kara hakuri da halin Yaya Hakim nasan kina hakuri ki kara yin wani insha Allah komai ya kusa zuwa karshe."

"Naji ni zan wuce gida thank you, "ok bye."

Tunda Maryam ta fita office din Hakim, Hakim yake tunanin maganganun da Maryam tayi mashi, "wai daman Hakima ta tsaneshin kenan."?

Abunda Hakim yake maimaitawa kenan, "oooo! Ni Hakim maiye abun damuwa dan Hakima ta tsane, nima da man na tsaneta to mai aciki dan Hakima ta tsanani."
Tambayar da Hakim yayi ma kanshi kenan sannan ya cigaba da aikin gabanshi..

Tun bayan wannan cases din da Hakim yayi da Hakima, Hakima bata sake yarda wani abu ya hada ta da Hakima ba dan ta gaji da halin Hakim shiyasa ta kama mutuncinta ta cigaba da karatunta dan har ta fidda rai da course din Hakim..
_____________________________

Rayuwa na tafiya komai faruwa yake cikin gidan su Hakim dan Gimbiya Kilishi  ta zage wajen bin bokaye dan yanzun ba wajen Turmurturs kawai take zuwa ba.
ita kuma Gimbiya Zulaha bata damu da zuwa wajen ko wani boka ba, dan tasa ma ranta shekara biyar nayi zataga gawar Hakim, amman daga baya tana yi ma Kilishi zagon kasa wajen Maimartaba dan so take kafin shekara biyar Maimartaba ya saki Kilishi, saboda bata shirya zama da Kilishi ba.
(Kuma kai su Gimbiya Zulaha ba Amana tsakanin ki da Gimbiya Kilishi ko wananku yi ma dan uwanshi yake daga boye😝.)

Ita ko Gimbiya Fulani Kubrah bata damu da abunda suke ba duk da tana sane da dun wani tungu da kulle-kullen da suke cikin gidan amman bata damu ba ta barma Allah lamarinta baki daya..
_________________________ 
Rayuwa ma tafiya dan Hakima yanzun an shiga 400lvl yanzun haka second semester take final year, Allah yaso Hakima ba Hakim ke mata project supervisor ba, shiyasa hankalin ya kwanta ta cigaba da hidimar gabanta dan yanzun bata da damuwar komai sai ta karatunta..

yau Hakima suke fara exams shiyasa ta cika zaman gida, ba dan so take ta gama fresh ba tare da spell over ba shiyasa bata tsayawa baye ma kowa duk da Samari sunyi ma Hakima ca, amman basu gabanta.

Exams sai dai ace Alhmdulh yau Hakima ke gama Exam kuma take gama *AHAMADU BELLO UNIVERDITY ZARIA* bayan sun fito final exmas ba karamin murna suka yi ba nan sukayi exchagings numbers da kawayenta sannan ta wuce gida tana zuwa gida suka dauki hanyar Kano daman already su Azima sun shirya masu kayan su jiran fitowarta suke su kama gabansu dan suma murna suke zasu zauna waje daya, amman da basu kano basu zaria karatun ne kawai basu yi ba amman suma sun sha wuya..

Tafiya suke dan sosai Bala yake ba mota wuta cikin ikon Allah suka iso gida lafiya..
Direct shashen Gimbiya Yakumbo a ka wuto da ita dan yau shima Yarima Annas ya dawo gida shima dan shi da safe ya dawo da shi yayi niyar zuwa ɗauko ƙanwar tashi Maimartaba ya hanashi yace itama zuwa anjima zata iso sai gashi ta shigo itama..

"Momy Momy Momy! Alhmdulillahi Momy yau nayi degree."

"Oyoyo!  Daughter am so happy today, Daughter kinga komi yayi farko yana karshe ko."?

"Hakane Momy, ina Yaya Annas?, "yana shashen Fulani kin sani."
"Na tafi naga Yayana, "to nima da man yanzun zan tafi shashen ta Baffanku nacan shima, "to Momy mu tafi."
Nan suka tafi tare shashen Gimbiya Fulani ko wacansu fuskarta dauke da murmushin farinciki..

Suna shiga Hakima ta ruga da gudu ta fada jikin Annas tana cewa, "Yaya Annas am so happy to see you yau, congrats Yaya angama phd lafiya Allah yasa angama a sa'a."

"Congrats tooo,, ƙanwa kema ina taya ki murnar gama degree ɗinki, "thank you Yaya."

Bayan sun gama murnarsu Maimartaba yake shida masu gobe za'a yi masu walima a bakin kogin masarautar haka suka gama sanann kowa ya wuce shashen shi cikin farinciki..

Tana zuwa shashenta bayi suka fara yi mata Allah yasa alkhari, yasa ta gama karatun nan nata a sa'a..

Amin kawai take ce mashi bayan ta shiga wanka ta fito ta shirya hutawa tayi sannan ta kira Maryam waya nan take gaya mata Annas ya dawo gida shima ya gama karatun shi bayan sun gama waya ta kwanta bacci..

Shima Annas bayan ya gama gaisawa da bayin shi yayi wanka ya kira Hakim waya yake gaya mashi ya dawo gida shima bayan sun gama waya shima ya kwanta dan yana san ya tashi da wuri gobe insha Allah..._By Jameelah Jameey✍🏻_#JameelarhSadiq
#Share
#Comment
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

57&58
"Allah ya taimakeki angama haɗa ruwan wankan yana jiran ki."
"Azima ki fiddo man kaya masu sauki dan kwaliya kawai zamu tafi sai gyaran jiki cikin gari kafin lokacin walimar yayi."

"Angama uwar marayu a fito lafiya, "Uhmmm."
Bayan Gimbiya Hakima ta shiga wanka Azima ta fido mata wani material wanda ya ansa sunan shi material, dan Azima ba daga baya ba wajen iya zaɓen kaya shiyasa Gimbiya Hakima take san duk inda zata ta tafi da Azima dan tana da kallar waye wa..

Sai da tayi kusan awa biyu sanann ta fito daga wanka, nan su duka ukku suka haɗu wajen shirya ta, bayan sun gama shirya ta ita da Azima suka ɗauki hanya sai salon dan Gimbiya Hakima ba daga baya ba wajen tsata ba..

Shiri akeyi naga ni na faɗa dan sai mutun yayi tunanin biki ake ko suna amman ba ko ɗaya kawai walimar gama karatun su Hakima Sarki Abdulhadi ya shirya dan ba ƙaramin san yaran nashi biyu yake ba dan su kawai Allah ya bashi kuma gashi Allah yasa yana da rabon ganin kammala karatunsu lafiya dole ya haɗa liyafar da ba'a taɓa yin kamarta ba a masarautar kano.

Niko nace ina da zaiyi masu aure ai abun mai faɗuwa sai dai.. Ba ruwa 🤭.

Shima Yarima Annas ba'a barshi a baya ba wajen shiri duk da ba wani aboki ga gareshi ba a cikin masarautar hakan bai hanashi yayi abunda ya ga ya dace ba, shida Hakim abokaine a makaranta suka haɗu lokacin shi yarima Hakim yana Phd ɗinshi shi kuma Yarima Annas yazo yin masters degree  nansu haɗu sai tasu tazo ɗaya duk da Hakim ya dan girmi Annas amman ba wani girma yayi mashi sosai ba kuma halin su yazo ɗaya shiyasa freindship ɗinsu yazo dai-dai.

Sai da Yarima Annas ya gaiyyaci Hakim yazo walimarsu amman Hakim yace yayi hakuri bai da lokaci comitement sunyi mashi yawa amman insha Allah ya samu time zai zo yayi mashi congrats ya gama karatu lafiya..

Bangaren sarki kuwa ya gaiyaci ko wani sarki da yake Nigeria suzo su taya shi murnar kammala karatunsu Hakima, su ma su Gimbiya Yakumbo ta gaiyyaci ko wace matar sarki da matan yan siyasa dan tayata murnar gama karatun su Hakima.

______________________________
*× ZARIA×*
"Hakim cikinku ku ukun nan ɗaya ya shirya insha Allah zamu masarautar kano , domin taya Sarki Abdulhadi murnar kanmalawar karatun yaronshi da ya dawo daga dubai."

"Ba sai na gaya maku ba waye Sarki Abdulhadi ba a wajena ba, don Sarki Abdulhadi Aminane na hannun dama tare mukayi karatu da shi masarautar su na zauna da nayi karatu B. U. K Kano, dan haka hallatar walimar ta zamai mana dole koda muna da uziri mu ajiyeshi gefe muje."

"Allah ya taimaki adalin Sarki Abdulmatalak, ai ba wanda ya dace da ya baka zaria inba Hamad ba tunda shine babba."

"Zulaha wa ya baki izinin magana ?, "Ina neman afuwa, "ni ban damu da babba ba kuma in ta girma zan bi ai da Hakim zan tafi kenan tunda kinsan ya girmi Hamad kowa ma ya sani cikin masarautar nan ban san tashin hankali Zulaha dan haka akiyaye."

"Cikin ku wa kuka fidda mu tafi tare."?
'Allah ya taimakeka, nidai na hakura cikinsu sai ka tafi da ɗaya."
"Ina ai ba zai yuyuba idan har za'a tafi da Hamad sai dai a tafi da Humad dan shima Humad ɗin ba wani girmanshi a kayi sosai ba da za'a ringa nuna mana banbanci."

"Kilishi kema ko? To tunda abun ya zama haka ku tashi ku ban waje ban zuwa da kowa baki ɗayansu daga ni sai waziri zamu tafi."
"Allah ya huci. "Ya isa haka ku tashi ku ban waje."
Haka suka fita ana hararar juna tsakanin Gimbiya Kilishi da Gimbiya Zulaha, ita dai Gimbiya Fulani Kubrah bata tanka ba nata ido duk abunda akace shi zatayi..

Bayan ta fiyarsu Sarki ya shirya ya sa aka kira mashi Hamad suka tafi tare ba dan yaso ba, amman ba yanda zaiyi dan shi da Hakim yaso zuwa amman haka Allah ya so.

Haka suka ɗauki hanyar kano, shi ko Hakim direct shashen shi ya wuce dan ya lura kwana biyu bai da aiki sai tunanin Hakima gashi ta tafi shi ko garinta bai sani ba, "maiye amfanin tunaninta!?? Wai mai ke damuna ni Hakim, ina no gaskiya ba haka bane ni Hakim zan so wannnan useless girl ɗin Allah ya tsari kakana da asara, kawai dai dan mun saba faɗa da ita shiyasa banjin daɗin gamawar da suka yi."
Haka Hakim ya kama yan surutanshi har ya samu ya ɗauro alwallar wal'ha ya fara sallolinshi yana neman tsarin ubangiji Allah dan ya lura maƙiyanshi ba kyaleshi suke ba, shiyasa ya miƙama Allah lamarinshi shida ƙannanshi da kuma mahaifiyarshi.

Bayan ya gama sallahrshi ya tafiyarshi school ya fara marking ɗin papers din su Hakima..

Ko da yazo wajen paper ɗin Hakima yayi mamaki sosai dan yanda yaga waje ɗaya ta faɗi shima wajen final answer ne ta rubuta ba dai -dai ba.
"Uhmmm! Gaskiya yarinyar nan tana da koƙari shiyasa wani time ɗin take bugerni."

Hakim ya faɗa yana ajiye paper ɗin Hakima wajen da yayi marking sai da yayi da yawa ba laifi sannan ya ɗauki hanyar Join domin yana bukatar refresh ɗin brain ɗin shi, saboda hayaniyar da su Gimbiya Zulaha su kayi ɗazun ba ƙaramin ciwon kai take sa shi ba.

Anya Hakim hayaniyar su Gimbiya Kilishi ta saka ciwon kai🤔, nidai babu ruwa na 🤭, Team Hakima ina jiran ansarku.


_A gaskiya masoyana bani da bakin da zani yi maku godiya sai dai nace Allah ya bar kauna masoyana❤️💃🏼_

'''Tabbas naga masoya, da wanda nasani da wanda ma ban sani ba, ina ganin ruwan comments da ma fatan alkhari da masoyana suke yi man duk suna isowa gareni dan haka ba abunda zance sai Allah ya barman ku my Fans much love❤️💯'''

*Yan wattapad kuma ba'a barku a baya ba, kuna nuna man iyakar kaunarku kuma inayin ku over and over kudia ku cigaba da comments and vote ni kuma na cigaba da surbudu mako da zafafan litaitafai da litafin na suna hanya very soon kudai cigaba da biyoni 💃🏼💃🏼💃🏼*
_Yan facebook ban san mai Zance ba aiku sai dai kwando godiya da miko zuwa ga duk wani masoyana da suke facebook inajin dadin ganin comments ɗin ku kuma😍_

_By Jameelah Jameey_✍🏻

#JameelarhSadiq
#Share
#Comments
#Vote
#Like
#please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

59&60

"Ranki ya daɗ'e, asa maki eyeshadow ne."?
"Azima kyalenni sosai kinga ya nayi idan ya dace a saman eyeshadow ɗin sai ta saman."
"To Allah ya taimakeki."

Masha Allah ba ƙaramin kyau Gimbiya Hakima tayi ba abunka da farar fata sai abun ya wuce masali, dan tsayawa na gaya maku irin kyaun da Hakima tayi ɓata lokacine dan haka Team Hakima wanan aikin naku ne sai ku gaya man kalar kyaun da Hakima tayi 😍.

"Allah ya taimakeki gskiya ko ba'asa eyeshadow ba kinyi kyau a haka, amman a sanya maki dan ƙara ma kwaliyar armashi."
"Uhmmm."
Abunda Gimbiya Hakima tace kenan, sannan mai make-up ta cigaba da aikin ta bayan ta gama yi mata kwaliya wata arniyar atamface black and red a Hakima tasa sanann aka murza mata ɗaurin dankwali mai kyau da aji bayan angama ɗaura dan-kwalin ta ɗaura alkaibarta bisa kayan sanann tasa takalimin viccin half-shop tasa sai ta sake fitowa Hakimarta yar'shekara 22,bayan sun gama shirya ta dubu ɗari hudu ta ba masu gyaran sannan suka wuto gida.
Bayan sun koma gida direct shashen Fulani ta wuce nan ta sake gyara idan ta ga ya dace ta gyara sannan ta wuce shashen Yarima Annas su Lantana na take mata baya.
Bayan ta isa bakin shashen shi aka yi mata iso ta shiga su kuma su Lantana suka tsaya bakin shashen suna gaisawa da sauran bayi yan uwansu.
"Yaya sannu da hutawa."

"Yauwa Hakima, masha Allah gaskiya ƙanwar nan tawa tayi kyau sai kace wanda zataje kasar kyau."
"Haba Yaya Annas karka fasa man kai fa, "Hakima ai gaskiya na faɗi amamn sirikin nawa zai hallaci wannan walimar ko."?
"Rufan asiri Yayana ina Hakima ina kula saurayi? Kaganni nan bani da wani saurayi kawai dai kwaliya akayi man saboda wannan walimar."
"Hakima kina aikin mai baki tsada miji ba? Bayan kin san Baffah aure zai yi maki tunda kin gama karatu."

"Yaya Annas am still young fa, duka duka yanzun nike da 22yrs ban isa na fara kula samari ba."

"Shut up Hakima, ke ɗince baki isa kula samari ba dan sakarci irin naki na banza."?
"Yaya Annas, haba maiyasa ni ba'a sona cikin gidan nan inba ba'a sona ba taya za'a yiman aure inada wannan shekaru."?

"Hakima kisa ranki anyi maki auren dole angama, dan wallahi nasan Baffah aure zai yi maki kuma laifin kine, kinga ni da man nasan Baffah zai fidda man mata shiyasa ban kula ko wace yarinyaba, amman ke dai Baffah ya baki chain ke kika yi wasa damarki tashi mu tafi naga am fara taruwa."
STORY CONTINUES BELOW

"To shikenan, nasan insha Allah Baffah ba zai yi man haka ba, "kina da wanda ki fidda a matsayin miji."?

"Aa babu, "kinga baki da magana ƙanwata tashi mu tafi naji ance Sarki Abdulmatalak da Sarki Abubakar Sadiq sun fara isowa."

"Saraukunan ina ne su?, "da Sarkin Zaria da Sarkin Katsina, "ok shikenan mu tafi."

suna fitowa waje kunyangen suka take masu baya suna kirari suna cewa, "takawarku lafiya ya'yan sarki jikokin sarki, Allah ya taimakeka Yarima Annas sarki mai jiran gado, Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima, Gimbiya uwar'sarki da yarda Allah, kunyi gaba maƙiyanku suna bayan ku ba mai ganin bayan ba dai maƙiyi ba".

Haka suka kama kirari har suka isa wajen da aka tanadarnasu domin zamansu, tunda suka taho Yarima Hamad yake kyallon Gimbiya Hakima take ya ji shi duniya ba wanda yake sha'awar aure inba ita ba dan bai san da yace Masha Allah ba saboda da kyaun da tayi mashi son Gimbiya Hakima ya shiga cikin zuciyar Yarima Hamad ba tare da ya fargaba.

Tunda ake yi masu wanna kirari har suka zauna sannan suka tashi suka fara miƙa gaisuwa wajen sarakunar da su ka hallaci taron da ma wanda basu samu damar zuwa ba suka aiko da Waziransu, tafiya suke cikin natsuwa da man Gimbiya Hakima ba daga baya ba wajen iya tafiya shima Yarima Annas ba'a barshi a baya ba.

Sunje gun ko wani sarki sun kai gaisuwa, ki wani sarki da kyautar da yake basu har suka zo wajen Sarki Abdulmatalak shine ya ba Gimbiya Hakima kyautar Mota shi kuma Yarima Annas ya bashi kyautar mota da gida.

Tunda Sarki Abdulmatalak ya ga Gimbiya Hakima ya ji yana san ya haɗata aure da Yarima Hakim, dan ya yaba da tarbiyarta da hankalinta yana yi ma Hakim sha'awar auren ta, dan haka ya gudurinma kanshi zai nema ma Hakim auren Hakima bayan an gama taro.

Bayan sun gama gaida manyan da ke wajen suka koma suka zauna, nan Sarki Abdulhadi ya tashi yayi bayanin ya kuma miƙa godiya ga manya baƙin da su hallaci taron.

Anci ansha an koshi sanann ko wani sarki ya kama gabanshi yana yi masu fatan alkhari, bayan ko ya watsa Sarki Abdulmatalak ya bukaci san yin magana da sarki Abdulhadi.

Bayan sun ƙara gaisawa nan Sarki Abdulmatalak ya fara magana kamar haka, "Abokina gaskiya ina mai ƙara taya ka murnan sosai, Allah yasa karatun da sukayi ya anfani al'ummar musulmai baki ɗaya."

"Amin ya Allah, nagode sosai Abokina dan kunyi man kara kuma naji dadi sosai, "haba ai yi ma kaine, ai wannan abun na taya murna ne, in tambayeka mana Abokina."?

"Sosai ma ina saurarenka yi man ko wace tambaya ce Allah yasa inada answer ɗinta."

"Da man ina san naji ko ka fidda ma Gimbiya Hakima miji, idan baka fidda mata ba muna bisa ga so dan zanso mu haɗa jini da kai, ina nemama ɗ'ana *YARIMA HAKIM* auren *GIMBIYA HAKIMA*  amman idan ba'a rigamu ba."

Wani kallar farin cikine ya mamaye Sarki Abdulhadi dan daman yana da niyar yi ma Sarki Abdulmatalak maganar Hakima ya haɗa ta cikin yaranshi, dan zumincin su ya ƙara ƙarko.

"Alhmdulillahi Wannan magana tayi daɗin ji sosai, ai Abokina ba sai ya nemi aure ba ni Abdulhadi Abdulsalam na ba ɗ'ana Hakim auren Hakima kawai yazo suga junansu sanann a ɗaura  tunda daman ta gama karatunta."

"Aiko naji daɗin wannan kyautar da kayi mana ina godiya Abokina."
Nan suka gama maganarsu sannan suka fito, shi kuma Hamad yana can yana san magana da Gimbiya Hakima amman bai ga fuska ba, yana cikin haka sarki Abdulmatalak yace su wuto su wuce gida, haka suka ɗauki hanyar Zaria ba dan ya so ba.
*Wata sabuwa inji an ca_ca Sarki Abdulmatalak ya nema ma Hakim auren Hakima ba tare da sanin Hakim ba😱*

*Sarki Abdulhadi ya Amince da magana har ya bada ba tare da sanin Hakima ba😱*

*Yarima Hamad ya faɗa kogin son Gimbiya Hakima ba tare da shirya ba😱*

_Wai Allah wannna shine ɗaurin goron😝, kudai ku cigaba da biyoni_
*Shin  Gimbiya Hakim zata amince da auren Yarima Hakim kuwa?*
*Yarima Hakim zai Amince da Auren Gimbiya Hakima shima?*

*Yarima Hamad zaiyi hakuri da soyayyar da yake yi ma Gimbiya Hakima ya barma Yarima Hakim tunda shi ance na bashi?*

*su Gimbiya Zulaha zasu yarda Hakim yayi aure nan, kuma zasu hakura da shekara biyar ta ida cika suka aikin boka Turmurturs yana yi?*

_Turkashi wanann ansoshin duk suna nan gaba cikin wannan labari mai albarka na Gimbiya Hakima ku cigaba da biyo kawai_

*#JameelarhSadiq*

#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

61&62

Bayan tafiyar Sarki Abdulmatalak, Sarki Abdulhadi ya haɗa Gimbiya Fulani da Gimbiya Yakumbo cikin daren nan yace yana san yayi magana da su.
Bayan sun zauna suna jiran jin maganar da Maigidan nasu zai yi su cikin daren nan, bayan bai taɓa yi masu kallar wannan neman na gaugawa ba.

"Yakumbo! Fulani."

"Allah ya taimakeka, Allah ya sa lafiya dai? Dan tunda nike dakai baka taɓa taramu cikin dare ba, koda zaka auri Fulani ba cikin dare kayi man maganar auren ta ba."

"Yakumbo lafiya lau, wanann abun a faɗi ne da zafin-zafinshi ba sai ya huce ba shiyasa na tare ku."

"To Alhmdulh yanzun hankalina ya kwanta, muna sauraranka Mijinmu."

"Da man maganar Hakima ce."
"Hakima kuma Maimartaba sarki Abdulhadi."?
"Eh Yakumbo Hakima Allah yayi na fidda ma Gimbiya Hakima miji."?

"Miji? Hakima ka fidda ma Miji."?
"Eh miji, ya naga kamar hankalinki ya tashi wani abu? Ko tana da wanda take so."?

"Aa ko ɗaya, kawai ina mamakin Hakima da miji, naga duka duka yaushe ta gama karatun har kuma an fara maganar aure."

"Karki damu, daman ai nasha tambayarki nace Daughter ɗinki tanada wanda takw so kice babu, to ni Abdulhadi Abdulsalam na baka Yarima Hakim Abdulmatalak auren Gimbiya Hakima ko bayan raina ban yarda a ɗaura ma Hakima ko wa ba inba Hakim ba."

"Ai ba matsala naji dadi da Hakim ka ba auren Hakima, dan nasan Gimbiya Kubrah zata kula da Hakima sosai."

"To kunji abunda zan gaya maku, in Allah ya kaimu gobe ina san sake ganinku baki ɗaya harda su yaran, dan inasan gaya ma Hakima wannan albishir ɗin."

"To Allah ya kaimu goben lafiya."
Nan Gimbiya Fulani ta fito tana murna dan taji dadin haɗin da mijin nata zaiyi ma ɗiyar tata, nan ta bar Gimbiya Yakumbo dan ita take da kwana a turakar mai Maimartaba.
____________________________
*×ZARIA×*

Bayan Sarki Abdulmatalak ya huta yake tara duka iyalanshi taron gaugawa a babban parlournshi.

STORY CONTINUES BELOW

Sai da kowa ya zauna sannan ya fara magana, "dalilin da yasa na tara ku ba komai bane ila maganar auren Hakim."

Ba su Gimbiya Zulaha ba, harda shi kanshi Hakim ɗin sai da hantar cikinshi ta motsa dan baiyi tunanin wanann ranar tana gan da zuwa ba, kawai kallon Maimartaba yake shi ba a mutun kuma ba mataitace ba.

''Aure kuma? Auren ma na Hakim ba na Hamad ba."?
"Haka kikaji nace Zulaha auren Hakim,na nema ma Hakim auren yar'sarkin Kano dan haka kai Hakim Umirni na baka ba shawara ba kaje ku gana da junanku."
Zubewa Hakim yayi yana kwasher godiya wajen mahaifin nashi, "godiya nike Abba Allah ya ƙara tsawancin kwana bani da zaɓi da ya wuce zaɓin iyayena, nasan kun fini sani abunda ya dace dani."

"Allah yayi maka albarka, daman abunda yasa na taraku kenan sai Ku tashi Allah ya yi maku albarka baki ɗayanku."

Haka suka fito ko wane da abunda yake cikin ranshi kallon kallon kawai ake yi ma juna.
Bayan su Yarima Hamad sun shiga shashen Gimbiya Zulaha ya fara magana, "Gimbiya wallahi mudun Abba ya ɗaura ma Hakim Gimbiya Hakima wallahi sai na kashe Hakim dan dani Hakima ta dace ba Hakim, dan akan Hakima ina iya kashe ko waye koda shi Abban ne wallahi."

"Wacece Hakima kuma?, "Gimbiya Hakima itace yarinyar da mukaje walimar gama karatun su ita da Yayanta Yarima Annas, Gimbiya inason Hakima ina kaunar Hakima akan Son Hakima zan iya kashe waye wallahi."

"Baka da hankali Hamad? Bani san kana faɗin wannan kalmar ta kashe mutun kai tsaye haba Hamad ka bari nayi tunani mana."

"Har sai yaushe zakiyi Tunani? bayan kin san  Abba yace Hakim ya shirya yaje su ga juna, kuma Abba magana ɗaya yake baya chanzawa."

"Ba dai kana san Gimbiya Hakima ba."?
"Eh inasan Hakima, Gimbiya ki taimakeni wallahi Hakima ce rayuwata mudun ban samu hakima ba zan iya kashe kai na ko kuma a waye gari ki tadda gawata ciwon son Hakima yayi ajalina."

"Yau ɗin nan zani wajen Turmurturs ba sai gobe ba Hamad, dole ka auri Gimbiya Hakima ko ta wani hali ne nayi maka wanan alkwarin."

"Nagode Gimbiya, shiyasa nike sanki mahaifiya mai share hawayen ɗanta."
"Tafiyarka Hamad Gobe zani nemaika kaji yanda mukayi da Turmurturs , "na barki lafiya Gimbiya."
Haka Hamad ya tafi ya bar Gimbiya da tunani dan bata shirya rashin Hamad ba dan haka sai dai inda karfinta ya ƙare.

"Mariya ba zan bari ayi wannan aika-aikar ba, taya zan bari Hakim yayi aure muda muke san kasheshi."

"Uwargiyata, Gimbiya Kilishi mai zai hana mu koma ma boka Dashshe nasan ba'a rasa yanda za'ayi ba."

"Aa Mariya, bari kiga ba tafi wajen Gimbiya Zulaha mun san yanda za'ayi, "To adawo lafiya ranki ya daɗ'e."

Nan Gimbiya Kilishi ta tafi shashen Gimbiya Zulaha hankali tashe dan batada wata mafita hankalinta ya fita jikinta bayan ta shiga dan yau ko iso bata aika nema ba wajen Gimbiya Zulaha ba sai dai kawai Gimbiya Zulaha taga Gimbiya Kilishi tsaye gabanta.

"Kilishi kenan daman nasan zaki zo shiyasa ban zo ba ni."
"Ba dole ba Gimbiya, kinji abunda wannan sakaran mijin namu yace wai aure zai yi ma Hakim mu da muke jiran ganin gawa nan da shekara biyu, salan ya ƙara aza mana wani aikin a kanmu."

''Hmmmm! Ni bansan ya zanyi ba, kuma yarinyar Hamad yace yana sonta amman san zuciya yasa akace Hakim zai aure ta."
Sai da Gimbiya Kilishi taji kamar fitsari zai kunce mata a wando dan batayi tunanin Hamad zaiyi yana san yarinyar ba , amman ita tasan yanda zatayi.

"Tashi mu tafi wajen Turmurturs ko ya share mana hawayenmu, dan nima abunda naso nace kenan ai Hamad shi ya dace ayi ma aure ba Hakim."

"Aiko dai amman ai mu ba'asan mu sai su an so ko?, "rabu dasu mudai mu tafi."

Haka suka ɗauki hanyar zuwa wajen Turmurturs dan ya share masu hawaye a cewarsu ba😰.

Bayan sun je wajen Turmurturs nan Gimbiya Zulaha ta fara bayani.
"Turmurturs ina san ka share mana hawayenmu, kamar yanda ka saba, wata sabuwa wai Abdulmatalak zaiyi ma Hakim auren da yar'sarkin kano."
"Hahhhha! Daman inasane da zuwan ku, ku dakata kuji aure ba fashi sai anyi shi sai dai ansa wata mafita bayan auren nasu, kuma Hamad hakuri zai yi ta aure Hakim har bayan mutuwar Hakim sai ya maida auren Hakima kanshi."

"Turmurturs. "Da kata Gimbiya Zulaha haka abun yake kuma haka zakuyi aure ya zama dole sai dai bayan bikin Turmurturs ya san yanda zaiyi ya hana Hakima ɗaukar cikin Hakim, amman duk wanda ta matsa tace sai ta hana bikin nan to nidai ba ruwana."

Haka suka ajiye mashi kudi suka taho biki sake, bayan sun koma gida Gimbiya Kilishi ta fara magana, "Gimbiya shawarar Turmurturs kawai za mu bi, indai zai hana Hakima haihuwa da Hakim lafiya lau suyi aurensu nan da shekara biyu sai shi Hamad ɗin ya auri Hakima kinga sai ta cigaba da haihuwarta."

"To nima abunda na gani kenan, dan haka zanyi ma Hamad bayani yanda hankalinshi zai kwanta, "yauwa ni na barki lafiya."

Bayan Gimbiya Kilishi ta koma shashen ta ta buga ma boka Turmurturs waya take ce mashi ya san yanda ya hanaa Hakima ɗaukar ciki yanda koda Hakim da Hamad sun mutu sai a ɗaura ma Humad Hakima.

Kunji wata sabuwa kuma my Fans, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyarmu Amin🤝🏻

*#JameelarhSadiq*
#Share
#Comment
#Like
#Vote
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''
63&64

*×KANO×*
Washe gari Gimbiya Hakima ta ɗauki hanyar shashen Maimartaba itada su Lantana suna take mata baya suna labari dan yanzun Gimbiya Hakima ta yarda da maganar Fulani da tace mata inma bata fiddo Lantana ba matsalarta, ta yarda da wanann maganar dan yanzun bata san abunda zai ɓatama su Lantana rai saboda suma basu san suga ɓacin ranta.
A bakin shashen Maimartaba suka haɗo da Yarima Annas na suka shiga tare su kuma Lantana suka tsaya suna gaisawa da dogarawan Annas.
"Yaya Annas wai neman mai Baffah yake yi mana."?

"Hakima nima ban sani ba, amman may be maganar Aure zai yi mana da man wannan ranar tana nan zuwa tunda mun gama karatu."
"Maganar Auren kuma Yaya Annas."?
"Eh, amman ai ce maki nayi may be ko."?
"Wai har naji hankalina ya kwanta, insha Allah ba maganar auren zai yi mana ba dan miko ban shirya aure yanzun ba."

"Allah ko Hakima."?
"Sosai ma Yaya Annas, "Ok Hakima Allah ya bamu sa'a dai, "Amin ya Allah Yayana."

Haka suka shiga parlourn Maimartaba amman Annas yana mamakin yanda Hakima take furta bata shirya aure yanzun ba bayan tasan Maimartaba ba ƙyaleta zaiyi ba, ko shi Maimartaba ya ƙyaleta to shi ba zai ƙyaleta ba haka suka shiga suka samu waje a kasa suka zauna shi kuma Maimartaba shida su Yakumbo suna bisa three siter suna kallon yaran nasu yanda suka haɗa kansu hakan yana yi masu dadi, bayan sun gama gaidasu sannan Maimartaba ya fara magana.
"Mamana."

Sai da gaban Gimbiya Hakima ya tashi da taji da sunan ta Baffah ya fara kira bana Yarima Annas ba, kasa magana tayi sai dai ɗago kanta da tayi tana kallon Baffah jira take kawai taji abunda zai gaya mata, koda Maimartaba ya fahimci sarautar har ta hau kanta ba ansawa zatayi ba amman hankalinta baki ɗaya yana wajen shi sai ya cigaba da maganar shi.
"Hakima na fidda maki mijin aure nan da kwana biyu zai zo kuga juna sai ayi biki ɗan sarkin Zaria ne."

"Nagode Baffah, Allah ya saka da Alkhari, nasan ba zaka zaɓe man abunda zai cutar dani kuma ya zama dole na bi Umirninka dan kaine mahaifina kafi kowa iko da ni, ina godiya Baffah Allah ya ƙara girma da ɗaukaka."

"Allah yayi maki albarka Mamana,nasan bazakiyi kuka ba akan zaɓin da nayi maki Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a ɗaiyaba wanda zasu taimaki al'umma baki ɗaya."

STORY CONTINUES BELOW

"Amin."
Baki ɗaya parlourn suka ansa banda Hakima ta da duƙe kanta kasa tana wasa da zoben zinarin dake maƙale a hannunta bata damu ba dan Baffah ya fidda mata miji ba ita dai fatanta Allah ya basu zaman lafiya.

"Allah yayi maki albarka Daughter, nasan Baffahnki ba zai zaɓa maki abunda zakiyi kuka ba."

Ita dai Gimbiya Hakima ba tace komai ba, amman tana mamakin wai ita za'ayi ma aure yarinya da ita.
*{hahahha! Team Hakim kunji wai Hakima bata isa aure ba😉}*

"Sai kuma kai Annas kaima ka zama cikin shiri dan aurer da kai zanyi ina nema maka mata dai-dai dakai, dan haka ka zama cikin shiri."

"To Baffah godiya muke, Allah yaja da tsawancin kwana, "Amin zaku iya tafiya Mamana ki fara shirin zuwan baƙon naki, "To Baffah insha Allah mun barka lafiya."
Bayan sun fito suka wuce shashen Gimbiya Yakumbo baki ɗayansu, bayan sun zauna Yakumbo ta fara magana."

"Daughter Allah yayi maki albarka, gaskiya kin burgeni Daughter kuma nasan Hakim yaron ƙirkine bazai cuceki ba, sannan mahaifiyarshi mutuniyar ƙirkice sai dai kun kula dan masarautar zaria ana tungu da surkule dan haka sai kin kula da hannunki."

"Momy da man Yarima Hakim Baffah zai ba auren Hakima."?
"Ehmana Yarima Hakim ne, da man kasanshi? Dan nasan rabonsu da nan masarautar tun haihuwar Hakima dasuzo sunan Hakima."
"Eh nasanshi sosai muna mutunci sosai da shi muyi zama dashi a dubai."

Ita dai Gimbiya Hakima batace komai ba, kuma bata kowa komai a ranta ba duk taji sunce Hakim amman bata kowa prof Hakim ba dan ta manta dashi ma.
*{gaskiya Hakima bata kaunar Hakim tunda ta iya mantawa dashi, salan naji Team Hakim kunce ba haka bane😎}*

Bayan sun gama maganarsu dan Gimbiya Yakumbo taba Hakima shawara sosai yanda zata zauna masarautar su Hakim ta gaya mata shirin masarautar sosai har suna mamakin yanda Yakumbo ta san masarautar har haka.
"Momy ni wallahi har na fara tsorata taya zan iya da halin su Gimbiya Zulaha? Bayan ni ban taso naga gidan mu ana haka ba."?
"Zaki iya Hakima sosai ma, abunda zakiyi shine karki yarda kice wani abu da ya fito daga hannu baiwar gida ko kuma hannun su Zulaha da Kilishi, karki yarda da ko wace baiwa sai wanda zaki tafi dasu daga nan masarautar suma da mutun uku zaki Lantana da Bilkisu sai Azima suma dan na yarda dasu amintaitun bayine nasan basu yarda a haɗa baki dasu a cuceki ba."

"Sannan karki shiga sabgar kowa, kuma nace maki Gimbiya Kubrah bata da matsala dan matace mai kawaici da mutunta mutane dan haka sai ki yaye Hakima, nasan ki baki ɗaukar rainin bayi to karki yarda wata baiwa daga cikin masarautar ta ringa shigarmaki shashen har zuwa cikin ɗakuna dan haka su azima su zasu gyara ɗaki da girki kinjini ko."?
"Eh Momy, naji kuma insha Allah zanyi abunda kikace man, dan ba zan yarda ba su Gimbiya Kilishi su raina ni nafi karfinsu da ayar Allah, amman Momy taya kikasan sirin masarautarsu har haka."?
"Nasan sirinsu wajen Gimbiya Zulaha, da aminatace sosai saboda amintakar da ke tsakanin mijina da mijinta, lokacin daga ni har ita bamu samu haihuwa ba taso taja ra'ayina wajen bin bokaye da malamai nice ban bata fuska ba muna cikin haka sai Sarki Abdulmatalak ya bujuro da auren Gimbiya Fulani Kubrah, hankalin Gimbiya Zulaha ba ƙaramin tashi yayi ba dan ba wajen bokon da bataje ba amman bakinsu ɗaya aure sai anyi ba, bayan anyi aure Allah mai iko yaba Fulani Kubrah ciki daga zuwanta nan ma Gimbiya Zulaha ta fita ta shiga taga cikin zube amman babu nasara har aka haifi Yarima Hakim, bayan haihuwar Yarima Hakim Gimbiya Zulaha itama ashe tana ɗauke da ciki, Hakim yana da wata biyar a duniya Gimbiya Zulaha ta haifi yaronta namiji shine akazo dashi wajen walimarku Sunanshi Hamad, Hamad yana da wata biyu na haifi Annas tunda Gimbiya Zulaha taga Hakim shine magajin sarki Abdulmatalak ta tada hankalinta shine take bin bakoye dan har yanzun tana kan bakarta na Hamad sai yayi mulkin Zaria ba sirihin da bata yi ma Hakim amman Allah ya kareshi daga sharinta, Gimbiya Kilishi kuma su Hakim nada shekara biyu a duniya sarki Abdulmatalak ya aureta da basu yar ga maciji tsakaninta da Zulaha daga baya da suka fahimci halin su ɗaya suka zama Aminan juna dan tare suke komai nasu ita kuma Kilishi ita ta haifi Yarima Humad kinji taƙaitacen labarin gidan surukanki Hakima zaki shiga gidan sarauta mai rikici dan haka sai kin iya takunki karki kuskura ki nemi bokaye dan haka ki riƙe Allah da ibadodi sune gatanki dan ita addu'a takobin mumunice."

"To Momy insha Allah, amman Momy taya kuka bar Abokantaka keda Gimbiya Zulaha."?
"Lokacin da Baffahnki zai auri mahaifiyarki, dana gaya mata shine ta nunaman naje wajen boka a hana bikin, ni kuma nace ban ƙaucema Allah saboda ɗ'a Namiji naje nayi saɓon Allah dan haka ban hana Abdulhadi aure koda mata uku zai aure nidai fatana muyi zaman lafiya, shine tace ba ita bani tunda ba halinmu ɗaya ba,daga ranar bata ƙara zuwa wajena ba sanan ku za'azo wannan masarautar bata zuwa ko sunanki ba ita tazo ba Gimbiya Fulani Kubrah tazo sunanki ita da Yarima Hakim kawai sukazo suna kinji abunda ya rabamu."
"Mutane saboda san duniya da san zuciya sai suyi abunda zasuyi da nasi nan gaba, Allah yasa mu dace, "Amin Hakima."
Nan dai suka gama maganganunsu sannna kowa ya wuce shashen shi.
_______________________________

*×ZARIA×*

💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
*YAR UWA KADA KI WUCE BAKI KARANTA BA DOMIN KUWA AKWAI ƘARUWA A CIKI*

      *_🗣️ALBISHIRIN KU🗣️_*

*JAMA'A KO KUSAN MATASHIYAR MARUBUCIYAR  NAN WATO JAMEELAH JAMEEY WANDA AKA FI SANI DA YAR'MUTAN KANKIA TAYI SHIRI TSAF DOMIN FITO MAKU DA SABBABIN LITTATAFANTA GUDA BIYU.*

*SANADIN LINK*

*_HAHAHA YAR UWA DAGA JIN SUNAN WANI BOOK BASAI NA FAƊA BA KINSAN ZA'A SHA SOYAYYA. _*

*IZZA KO MULKI*

*WAI WANNAN KO BANSAN MAI ZANCE BA KUNSAN DAI YANDA LABARIN GIMBIYA HAKIMA YA KASANCE TO GA WANI NAN KUMA DAN SHI DABAN YAKE  DA SAURAN☺️*

*TAKU CE JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA MARUBUCIYAR👇*

*NANA JAWAHEER*
*GIMBIYA HAKIMA*
*A HAKA NIKE SONTA*
*YAN MATAN ZAMANI*
         _SAI KUMA_

*SANADIN LINK*
         _DA_
*IZZA KO MULKI*

*MASOYANA KUDAI KU CIGABA DA BIYONI DOMIN SUNA KAN HANYA, 🤫KARKI BARI A BARKI A BAYA😁*

#JameelarhSadiq@wattpad
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________
  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

65&66

*×ZARIA×*
Tunda su Gimbiya Zulaha suka dawo daga wajen Turmurturs, Gimbiya Zulaha ta kasa zaune ta kasa tsaye dan gani take kamar boka yana yi mata yawo da hankali amman da ta tuna Turmurturs ne sai taji hankalinta ya kwanta dan boka Turmurturs ta amince yana share hawaye waya ta ɗauka ta kira Hamad akan komai yake ya ajiyeshi yazo tana san ganinshi.

+
"Hakim ya na ganka cikin damuwa Allah yasa lafiya."?
"Aliyu ina fa lafiya Abba zaiyi man aure."
"Aure kuma Hakim.''?
"Wallahi aure zaiyi man wai yar'sarkin kano, maganar da nike yi maka Fulani tace gobe zani je wajen yarinyar.''

"Innalillahi wa'inna'alaihirajiun, Hakim abunda nayi maka gudu kenan shiyasa naso kanemi yarinyar nan Hakima dan wallahi ba ƙaramin marching kukayi ba, amman girman kai yana hanaka wai kai cewa ma kake ka tsaneta bayan ga sonta nan cikin idanunka ina gani."
"Allah ya tsareni Aliyu, ai gwara da Abba ya fidda man mata, ni natsi Hakima bansan Hakima ban ƙaunar Hakima kai mai ma irin sunan Hakima bani santa da wall... "Da kata haka Hakim, wallahi karya kake ni Aliyu nace karya kake kana san Hakima kuma nan gaba zakace na gaya maka."
Aliyu ya ƙarashe maganar cikin fushi dan bala'in haushi yake ji idan Hakim yace baya san Hakima bayan ga sonta yake ta ɗawainiya dashi wannan abun na bashi haushi gashi har za'ayi mashi auren dole.
'''🤣 niko nace Aliyu kwanatar da hankalinka burinka ya kusa cika'''

"Ya isa haka Aliyu enough, taya zaka zo kasani gaba kana gaya man maganganu saboda wata useless girl zaka sani gaba kana yi man tsawa, ka wuce ka ban waje kabarni da abunda ke damuna please."
"Ba inda zani kuma dole nayi maka tsawa Hakim dan wallahi banji dadin auren da Abba yake niyar yayi maka ba, gashi bamu san garin da Hakima take ba da nabita na nemo maka aurenta."

"What are you said?Aliyu kana cikin hankalinka kuwa? To bari kaji zanyi biyaiya na auri wanda Abba ya bani kuma zan koya ma kaina sonta after that kasan bani da budurwa to tada hankali name? Karka kuskura ka sake haɗani da wannna idiot gril ɗin take note".
"Hakim wallahi kana yaudarar zuciyarka, kayi kokari ko bayan aurenka ne kaje ka nemo garin da Hakima take ka aure ta dan nasan tuni kadaɗe da kamuwa da soyayyar Hakima itama haka Hakimar dan haka is ur on choice ni kaga tafiya ta office kayi tunani."
STORY CONTINUES BELOW

Haka Aliyu ya tafi yabar Hakim dan tunani, "Tabbas Aliyu bai ƙarya ba idanuwana sun kamu da soyayyar Hakima amman zuciyata ba abunda ta tsana kamar haka, how comes taya haka zata kasance? No impossible i hate you Hakima."
Abunda Hakim yace kenan ya tashi ya wuce shashen Fulani ko yaji saukin abunda yake ji a cikin zuciyarshi.
Tunda Gimbiya Zulaha ta kira Hamad waya ya ɗauko hanyar zuwa dan ji yanda zasuyi Hakima ta zama tashi dan abun bata samu mafita ba yana aikata komai mudun Hakima zata zamo tashi, dan ya ɗaukarma kanshi zai iya kashe koda Sarki Abdulmalak ne mudun ya hanashi auren Hakima.
*(Wai Allah na wata sabuwa anya Hamad yana da hankali kuwa🤔, taya zai kashe ubanda ya haifeka saboda mace, macen da bata san da zamanshi ba, Allah yasa mudace ya bamu zuri'a ɗaiyaba🙏🏻).*

Bayan ya shigo royal house ɗinsu direct shashen Gimbiya Zulaha ya wuce dan yaji abunda zata ce mashi, bayan anyi mashi iso ya shiga ya samu waje ya zauna yana saurarenta dan baki ɗaya hankalinshi wajen mahaifiyar tashi ya maida shi.
"Hamad kanaji na ko."?
"Eh ina saurarenki Gimbiya, "yauwa munje wajen Turmurturs amman yace aure dole ya ɗauru ba yanda zaiyi ya hana auren."

"To naji kinga tunda shi Turmurturs ya kasa, ni bari yanzun naje na sarema Hakim kai da man naga yana gida tunda naga motarshi"yana tashi tsaye yake maganganun dan da gaske yake zuwa zaiyi ya sarema Hakim kai tunda shi Turmurturs ya kasa.
"Na  shiga ukuna ni Zulaha, Hamad baka da hankali? Ko dai kayi shaye-shaye ne kafin ka shigo gidan nan".?
"Ba abunda na sha da hankali na wallahi kashe Hakim zaiyi ba zan bari ba ya auri Gimbiya Hakima ba, wallahi zan iya kashe koda ubantane balle Hakim da daman na tsaneshi komai za'ayi cikin gidanan shi Abba yake sawa saboda shine ɗan so, to idan na kasheshi uban kowa sai ya huta."
Tas! Tas! Tas!, Gimbiya Zulaha ta wanke Hamad da zafafan marika har guda uku dan gani tayi sai ta mareshi zai dawo cikin haiyacinshi.
"Gimbiya ni.. "Yi man shiru ko na ƙara wankeka da  mari wallahi sakaran banza sakaran wofi, zaka zauna ko sai raina ya ɓaci."?
Haka Hamad ya zauna yana dafe da kuncinshi da ya sha mari, wata sabuwar tsana yaji yana yi ma Hakim dan saboda shi Gimbiya Zulaha ta mareshi abunda Gimbiya ba ta taɓa koda dungurinshi ba amman yau shine tasa hannu ta mara becouse of Hakim.

"Hamad yaushe ka zamo wawa wanda baya aiki da tunani."?
"Amman Gimbiya, "Amman mai Hamad kasan bala'in da zaka ballo mana idan ka kashe Hakim".?

"To tsaya kaji ni, mudun ka kashe Hakim, to kaima kasa a ranka sai ankashe ka, kaga mulkin da muke jira ya koma hannu Kilishi kenan munyi wahalar banza."
"Amman idan kabi a hankali ba wanda yaji ba wanda ya gani zamu kashe Hakim cikin ruwan sanyi, ba wanda zaice kashe shi akayi, "taya haka zata kasance Gimbiya? Sannan sai yaushe zaku kashe Hakim."?

"Yanzun Hakim zai aure Hakima, amman boka Turmurturs yace zasu hana Hakima haihuwa da Hakim, suna kashe Hakim kuma sai a maida aurenka da Hakima kaga shikenan mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya."

"Amman ina kishin Hakim ya rigani sanin Hakima a matsayin mace, zanyi hakuri da shawararku Gimbiya ni zan koma aiki."
"To shikenan, karka kuskura na sake jin kalma sai ka kashe Hakim , kajini ko".? "Eh naji na barki lafiya.
Tunda Hakim ya tafi shashen Fulani ya kasa komai dan ko abinci kasa ci yayi shidai kagashi nan kamar ba shi ba haka yake jin kanshi.
"Hakim ko baka san zaɓin da Abbanku yayi maka."?
"Aa Fulani wallahi inaso, in ban bi umirnin iyayena ba umirnin wa zan bi, kawai ji nike kamar bani ba yau ɗina."
"Ka yawaita addu'a Allah yana tare dakai kaji yaron kirki."?
"Eh naji Fulani, ni gobe zan tafi kano ni ɗaya zani ko na tafi da Aliyu."?
"Aa ka tafi kai ɗaya ganin juna zakuyi kuma bikin saura wata ɗaya haka naji Abbanka yace.''
"To Allah ya kaimu, ni zan wuce massallaci na barki lafiya."

Bayan Hakim ya dawo daga sallah Tea ya sha sannan yayi addu'oi sannan ya kwanta dan ya gaji sosai ga washe gari zashi kano.
_______________________________
Tunda Hakima taji gobe Hakim zaizo bata zauna ba dan shiri take duk da tanajin ba dadi a zuciyata amman haka take ɗaurewa dan taba mutanan gidansu mamaki.
Bayan sun gama wani shirin dan Hakima ƙara komawa tayi wajen gyaran jiki aka sake yi mata su dilka sannan ta dawo gida, har yanzun bata samu lokacin waya da Maryam ba balle ta gaya mata ba, amman tana ranta tana san gaya mata, bayan ta dawo wanka kawai tayi sai bacci.

Washe gari tunda safe su Lantana suka tashi suka fara aikin tarar bako dan suke kamar mai abinci ake kala-kala dan har abun ya fara ba Gimbiya Hakima tsoro dan gani take kamar yau ce ranar bikin dan hidimar da bayin gidan keyi duk dan tarbar bakon da zatayi a yau kawai.

_Too My Fans wani kallar drama za'ayi idan Hakima da Hakim suka ga ashe junansu zasu aura? Am watting urs Answers🤣😎_
_BY Jameelah Jameey✍🏻_

#JameelarhSadiq
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
+
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''


67&68

Bayan anfito daga sallar asuba, Hakim yaje wajen Maimartaba yake gaya mashi tunda safe zai ɗauki hanyar kano dan baisan yayi tafiyar dare, nan Maimartaba yasa mashi albarka da fatan zuwa lafiya da dawowa lafiya.

Daga wajen Maimartaba wajen Gimbiya Fulani Kubrah ya wuce nan itama tayi mashi fatan zuwa lafiya da dawowa lafiya, sannan ta bashi wata super aura da wani laces dan two million tace ya ba Hakima idan yaje haka ya ansa yana godiya ya fita.

Shashen shi ya wuce ya ajiye kayan, sannan ya shiga wanka bayan ya fito daga wanka  ya fara shiryawa cikin wani black bowel da kaga wanan bowel ɗin kasan kudi sunyi kuka a wajen sayanshi balle Allah kaɗai yasan nawa ya bada wajen ɗinkinshi, takalminshi dan campany oriflame shida watch ɗin da ya manna a hannunshi ita kanta watch din abun kalloce balle azo ga hular da yasa ita black and red Infact Hakim ba karamin kyau yayi ba.

Bayan ya gama shiryawa ya dauki hanyar Kano, yana mamakin yau shine zashi wajen mace da sunan zance, macen ma da yanzun sauran one mouth bikinshi da ita.
"Dole ni Hakim na koya ma kaina san wanan baiwar Allah da Abba ya hada ni da ita, sannan  dole na cire tunanin wanna stupid girl din cikin zuciyata dan ba anfani na kama tunaninki Hakima, I hate you too Hakima ki fita daga rayuwata."
Abunda yace kenan ya cigaba da driving dinshi da yaga abun ba mai ƙarewa bane sai ya kunna ƙira'ar Ahmed Sulaiman yana sauraron, sanan ya fara dawowa dai-dai.
____________________________
*×KANO×*

Bayi aiki suke tukuru dan tun Hakima tana lisafa kalar abunda ake haɗama bakon nata har ta daina dan gani take abun ya wuce misali sai kace wanda za'ayi ma biki.

Ruwan wanka mai rai da lafiya Lantana ta haɗa mata dan har sun fara yi ma uwargijiyar tasu shiri na musaman saboda kowa yasan bikin saura wata ɗaya shiyasa suka tashi tsaye wajen ganin su shirya ta yanda dace.
Bayan ta gama haɗa mata ruwan wankan sannan Hakima ta shiga, ita kuma Azima ta fiddo mata kaya nagani na faɗa, dan already Azima taje ta ɗauko mai make-up Hakima kawai suke jira ta fito wanka su fara aikinsu.

Sai da  Gimbiya Hakima tayi kusan minti talatin a toilet sanann ta fito ta zauna aka fara tsara mata kwaliya mai rai da lafiya, bayan angama tasa kaya aka ɗaura mata dan-kwali ɗaurin Zara Buhari  akayi mata amman ya fidda shapes sosai.

Bayan Hakim ya iso Yarima Annas yayi mashi jagora shashen Maimartaba ya fara gaidashi sannan ya wuce shashen Gimbiya Yakumbo itama ya gaidata sanann shashen Fulani itama ya gaidata, tun anan Yarima Hakim yasan yazo gidan sarauta kuma gidan sarauta masu mutunta mutane suka jarajar dan adam nan take yaji dadi dan da alamu masarautar kano ba'a tungun da akeyi a masarautar su, bayan sun fito daga shashen Gimbiya Fulani bayi suka kama gaidashi suna yi mashi barka da zuwa masarauta mai albarka, kuma yaga alama, shashen Yarima Annas suka koma sannan Yarima Annas ya kira Gimbiya Hakima yace tazo shashen shi bakonta yana jiranta.

Abinci aka fara jerama Hakim gabanshi kala-kala dan har Hakim sai da yayi mamakin karanci irin na wanan masarauta gaskiya suna da karanci da sanin mutuncin mutane, dan yaga yanda bayinsu suke walwala kamar ba bayi ba bayan sun gama ajiye mashi abinci suka fita.

Yarima Annas ya matsama abokin nashi yaci abinci sosai dan sai da yaga yaci sosai sanann ya kyaleshi nan suka ƙara gaisawa ya tafiyarshi ya bar Hakim yana zaman jiran isowar Gimbiya Hakima.
Wooow! Masha Allah tafiya take cikin natsuwa da ɗaukar hankalin duk wani ɗ'a Namiji mai lafiya, lace ne purple a jikinta ɗinkin riga da siket ba karamin kyau kayan sukayi mata ba alkalbarta black ce sanan takalminta ma black ne agogonta yar company Gucci  itama black  ce, ba wata kwaliyar hauka akayi mata ba dab sai ka rantse kace ba a shafama Hakima poder a fuska ba dan pure skin Hakima ke gareta, take mata baya bayinta ke take mata baya sun ɗagemata alkalbarta dan karta share kasa, sai ka rantse kace yau ake ɗaura ma Hakima aure zabar kyaun da tayi.

Har cikin parlourn Yarima Annas bayinta suka rakota sune ɗage da alkalbarta daga ita har Hakim ɗin basu gane juna ba dan shi Hakim ba ita yake kyalo ba yana mamakin kalar mulki na amaryar tashi ne dan tafiyar ta kawai zai shedda maka da tanada mulki,  bayan su Lantana sun gama gaisheshi hannu kawai ta ɗaga masu sannan suka tashi suka fita baki ɗayansu.
Ɗagowar da Hakima zatayi suka haɗa ido da Hakim, su duka suka miƙe lokaci guda suna nuna junansu da hannu nan Hakima ta fara magana tana nuna nashi da yatsa tana cewa...

"Waya ka woka gidanmu, ubanme kazo yi mana.. "Hakima enough ya isa haka."... Yana dakatar da ita ranshi ɓace.
Hakim ya faɗa kamar zai ɗauke Hakima da mari, ita kanta Hakima sai da ta tsorata dan tunda take da Hakim bata taɓa ganin ɓacin ranshi ba irin wanann.

"Lock at you, ni nafi karfin nazo nace inasanki dan kawai biyaiya zanyi ga mahaifina da ba abunda zanyi dake sann... "Hakim karya kake wallahi baka isa kace man haka ba, kayi yanda kayi ka iko mahaifinka wajen Baffah dan a ɗaura maka aurena ko? To tsaya kaji kayi maza-maza kace ma Babanka ka fasa aure na dan wallahi Hakim da ka aureni gwara karkayi aure a rayuwarka har ka mutu dan ni *GIMBIYA HAKIMA* na tsaneka bani kaunar dan haka  bala'i da masifa zaka auro ma kanka gwara tun wuri kaje kace ka fasa Auren nan tun kafin dare yayi maka."

"Ke ɗin banza, ke har kin isa kice naje nace ma Abba na fasa aurenki to bari kije na gaya maki ni *YARIMA HAKIM* yanzun nayi niyar aurenki Hakima, zan aureki ba dan inasanki ba, zan aureki dan na koya maki hankali da tarbiya dan yanzun muka fara wasan nida ke Hakima useless girl."

"Aiko zaka ɗauro ma kanka wutar dafa kanka Hakim, "as we wish kina iya gaya ma mahaifinki bazaki aureni ba tunda daman ke ba kunya gareki ba, amman ni Hakim ba zan iya yin jayaiya da mahinfina ba dan nasan darajar iyaye, amm.." Dallah shut up ur darting mouse, har kai kake cema wani baiyin bayaiya ga iyayenshi, kamar yanda kayi biyaiya nima ita zanyi amman kasani bakai ba zaman lafiya a gidanka dan ni dai Hakima ba kaunar ka nike ba idiot wanda baisan mutuncin matune ba, ka godema Hakim haduwarmu tayi kyau amman haduwarmu ta gaba sorry to said."

Nan Hakima ta tafi tabar Hakim tsaye da mamaki baiyi mamakin rashin kunyar da tayi mashi ba dan ya san da man ba Kunya ke gareta ba, mamakinshi ɗayane daman ashe yar'sarkice? Shine yake mamaki ba rashin kunyar ba, bayan ya fito sukayi Sallama da Yarima Annas sannan ya wuto gida dan sakon Gimbiya Fulani daman already yaba Gimbiya Yakumbo ta ba Hakima.

_By Jameelah Jameey✍🏻_

#JameelarhSadiq@wattpad
#Share
#Comments
#Vote
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________
  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''
69&70+

Hakima direct shashenta  ta wuce ta ɗauki waya ta kira Maryam, "Hello Maryam kina jina."?
"Eh ina jinki Hakima, lafiya maike mafaruwa naji kamar baki cikin hankalinki."?
"Na shiga ukuna Maryam, bansan ya zanyi ba Baffah zaiyi man aure cikin watan nan."

"Aure kuma Hakima."?
"Eh aure kinsan ma da wa zai haɗani Maryam."?
"Aa ina saurarenki dai Hakima, da wa Baffah zai haɗa ki."?
"Wai prof Hakim, "Alhmdulh Allah na gode maka wallahi bakiji yanda hankali na ya tashi ba amman yanzun Alhmdulh komai namu wanan shine tuwo.. "  shut up, haba Maryam ya ina gaya maki problem ɗin na amman kina wata maganar daban."?
"Cool down mana ƙawata, wallahi kasa boye farincikina nayi domin maganar gaskiya Hakima Allah ne ya cika mana burinmu nida su Maryama to taya zaƙi yin farinciki."?
"Ok thank you ni zan kashe waya ta da man na kiraki ne ki kagayaman yanda zanyi amman kin ƙara ɓataman rai kin kyaunta Maryam."

"Wait Hakima karki kashe wayar zan gaya maki iyakar gaskiya a matsayina na aminiyarki Hakima, "Uhmmm! Am watting ina jinki."

"Maganar farko Hakima yin biyaiya ga iyaye yanada mahinmanci ga rayuwa dan Baffah yasan waye Yaya Hakim shiyasa ya bashi aurenki."

"Amman Maryam tsakani da Allah kin san bansan Hakim shima baya sona dan bakiji kallar maganganun da ya gayaman ba yau da sai na baki tausayi, NO Maryam Impossible ba banzan iya zama da Hakim ba please help me."
"Keko zaki iya zama da Hakim, Hakima sai kace ba mace ba? Ke fa mace ce kinsan yanda zakiyi ki shawo kan Namiji ko waye shi wallahi, dan ba abunda Allah ya rageki dashi duk da ance mutun tara yake bai cika goma ba amman ke daban ce cikin mata."
"Allah yayi maki kyau ga Ilimi, ke ɓata lokacine tsawa baiyana maki kallar baiwar da Allah yayi maki, kuma wallahi daga ke har Yaya Hakim ɗin kuna san junanku kawai san zuciya ya hanaku ku fahimci haka, amman very soon nan gaba zaku gane."
"Gashi ance masarautar su bata da daɗin zama saboda maƙirci yayi yawa a cikinta Maryam."

"Hakima ina wasu wanda muka taɓa gaisawa dasu su biyu lokacin da muna 300lvl."?
"Wasu yan-biyu ko."?
"Yauwa su, Maryama da Sadiya ko."?
"Hakane na tunasu, maiya samaisu."?
STORY CONTINUES BELOW

"Ai ƙannan Yaya Hakim ne, ta dalilinsu muke zuminci da Fulani Kubrah itace mamansu ni kuma makaranta ɗaya mukayi dasu tun nusery har university shiyasa nike cewa Yaya Hakim gunsu na sanshi, Yaya Hakim mutune mai mutunci da sauƙin hali ba zan tsaya gaya maki ba amman nasan nan gaba da ƙanki zaki gayaman halayen Yaya Hakim masu kyau ne shima da ƙanshi zai gane Gimbiya Hakima tana da hali mai kyau."

"Kena nufin yan-matan nan ƙannan shi ne wanda mukaita labari randa n a rakaki wajensu."?
"Kwarai kuwa uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, labarin faɗanki dashi nike basu shiyasa suka ce suna san watarana su ganki shiyasa na janyo ki suka ganki."
"Har naji sanyi wallahi Maryam ko ba komai na samu ƙawaye nadan ji sauki watarana."

"Aiko kedai kiyi biyaiya Hakima watarana zaki san iyayenki sun maki zaɓin kwarai, "nagode Maryam wallahi ba ƙaramin kyautarman da hankali kikayi ba, ni zani shashen Gimbiya Yakumbo sai mun haɗu a Jameey Novel Fans anjima."
"Ok shikenan, kin san ko yau akwai  chapter sosai, "aikuwa sai mu haɗu dai dan yau ban kunna data ba nasan tayi posting ɗin *A HAKA NIKE SONTA* da *YAN MATAN ZAMANI* nasan yau za'a sha comment."

"Idan kin dawo daga shashen Gimbiya Yakumbo kin karanta dan yau Fatima ba ƙaramin tausayi ta banta hmm gaskiya  *A HAKA NIKE SONTA* ba ƙaramin dadi yayi ba Fatima tana ban tausayi."
"Gaskiya nima Fatima tana bani tausayi, sanan Hafsat tana burgeni sosai dan tafi  Zainab da Sadiya hankali wallahi, "nima Hafsat tafi burgeni a *YAN MATAN ZAMANI* dan ita tafisu sanin abunda take, amman su kawai sunce burinsu sai ya cika ta kowace hanya, "aiko kinsan ko haka yan matan zamanin nan suke, Allah yasa mu dace dai ni zan tafi sai mun haɗa a Jameey Novel fans ɗin."

Sister idan baki karanta wannan litaitafin ki nemaisu dan karda a barki a baya *A HAKA NIKE SONTA* & *YAN MATAN ZAMANI* Hmmm ni ba zan ce komai ba sai dai indan kin karanta ke/kai zakuce komai😎.
Bayan Hakima ta gama waya da Maryam ta tafi shashen Gimbiya Yakumbo.
_*YAN MATAN ZAMANI YANA HANYA MASOYAN MU, MUNAJIN KORAFE KORAFENKU NA HAR YANZUN MUNBAR YI MAKU POSTING TO ALBISHIRINKU YAN MATAN ZAMANI YANA HANYA DAN BAMU MANCE DA KU BA MASOYAN MU💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼*_
_*A HAKA NIKE SONTA KUMA MUNA SANE DAKU ZAMU CIGABA DA YI MAKU POSTING AMMAN SAI KUN GYARA KUNA YI MANA COMMENTS YANDA YA DACE WANANN ALBISHIRNE NA BAKU MASOYAN BUK ƊIN A HAKA NIKE SONTA KARKU MANTA DR MUBARAK YANA SO DEEN MA YANA SO TO CIKIN WA FATIMA ZATA SO🤔🤪*_
______________________________

*×ZARIA×*
Tunda Hakim ya koma gida yake mamakin yanda Hakima take furta bata Sonshi bata kaunar shi wannan kalma tana yi mashi ciwo bayan shi yasan idanuwanshi da kunnuwanshi ba abunda suke san ji da gani inba Hakima ba, amman zuciyarshi bata san Hakima, amman ita Hakima baiga haka tartare da itaba inba tsanarshi da yagani zallah a cikin kwayar idanunta taya zai zauna da Hakima bayan bata sanshi ta tsaneshi? *{wannan answer team Hakima ku zaku ba Hakim ita ba dai ni ba😉}*

Da yaga abun bamai ƙarewa bane sai ya kira Aliyu yazo ya dawo amman su haɗu a shashen Gimbiya Fulani Kubrah sai su wuce Lambu."
Bayan yaje wajen Gimbiya Fulani Kubrah nan yake gaya mata yaje yaga Hakima kuma tayi mashi ɗari bisa ɗari, Gimbiya Fulani Kubrah tayi farin ciki sosai dan daman bata da gurin da ya wuce da taga auren Hakim kuma gashi cikin ikon Allah lokaci ya kusa.
Bayan sun gama magana da Gimbiya Fulani, ya tafi Lambu shida Aliyu su kuma su Gimbiya Maryama da Sadiya suka hau Murna dasukaji yace tayi mashi dan daman sun san Gimbiya Hakima ce Abba ya nema mashi aure tunda sun santa kuma gidansu su biyune ita da Yayanta Yarima Annas.
Bayan sunje Lambu Hakim ya fara magana yana cewa, "Aliyu Hakima ce."

"Bangane Hakima ce ba? Kodai kafara sub'batu Hakim."?
Hmmm! "Ba sub'batun da nake Aliyu,Hakima ashe y'ar Sarki ce Aliyu."

"Kana nufi Hakima itace wanda Abba ya nema maka auren ta."?
"Tabbas Aliyu,  Hakima itace wanda za'ayi mana aure wannan watan amman matsalar ɗaya Hakima ta tsaneni bata sona ko kaɗan, ni kuma zuciyata bata san Hakima amman kunuwana idanuwana suna san ganin Hakima da jin amon muryar Hakima."
"Kaima karya kake wallahi zuciyar ka tana san Hakima yaudarar kanka kake Hakim, itama Hakimar tana sanka duk kuna yaudarar kanku nan gaba zakace na gaya maka amman shashen za'abudema Hakima sabo ko kuma shashenka zata zauna."?
"Mun ma gama wannan maganar da Abba, shashena zata zauna tunda babba ne part ukune a cikin shashena to ba idan zata tana shashena ina lura da duk wani motsin ta, kuma banda matsala wajen mutanan gidanan dan Hakima bata kyale ta kwana nasan bazata shirya dasu Gimbiya Zulaha ba."
"Nima harda haka na matsa ka auri Gimbiya Hakima dan nasan su Gimbiya Zulaha ba zasu samu fuskar da suce zasuyi wani aminci da ita dan ita Hakima kallo ɗaya zakayi mata sai kaji shaskarta ta shigeka haka Allah yayi ta."
"Hakane Allah dai yasa mu dace, amman idan Hakima tace muyi zaman lafiya zamuyi mudun tace zaman rashin mutunci zamuyi wallahi zan biye mata daga baya mun sasanta, "Aa ban goyi bayanka ba Hakim, "saboda mai."?
"Saboda nasan ka baka iya hakuri, "ko? Da da babu Hakima na mutu."?
"Ai lokacin baka sama ranka ba, sanan ba ka ganin mace sai ka fita waje amman yanzun shashenka fa zaku zauna tare ai kai ba Sahabi bane da zakace bazakaji kana san ta baka haƙinka ba."
Uhmmm! "Zanko baka mamaki, "Allah yasa tashi mu tafi sallah lokaci yayi, "ok."

Bayan sum dawo daga sallah tea kawai Hakim yasha ya kwanta bayan ya tofe jikin da ayatul-kurshiyu da dai-dai addu'oi kala-kala sannan ya kwanta, kafin uku tayi ya tashi ya fara sallahr dare kuma sai asuba.

_By Jameelah Jameey✍🏻_

#JameelarhSadiq@wattpad
#Share
#Comments
#Vote
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

71&72

Tunda Hakima ta tafi shashen Gimbiya Yakumbo nan suka zauna suka fara magana.
"Daughter kinga Hakim ko."?
"Eh naganshi Momy kuma yayi Allah dai ya albarkaci Aurenmu."

"Amin ya Allah, daman nasan kuna ganin juna zaka amince da juna saboda ba ƙaramin dacewa kukayi da juna ba."
"Gaskiya ne Momy, yana da hankali ga dukan alamu dan jiya kawai muka fara ganin juna amman naga hankali a taitare da shi."
*{kunji Hakima da wata sharaton wai jiya suka fara ganin juna 🤣🤣}*

"Ai haka yake kuma gado yayi waje biyu daga uban har uwar, nidai Daughter dan Allah karki bamu kunya ku zauna lafiya keda wannan baiwan Allahn, Allah yayi maku albarka."
"Amin Momy, insha Allah ba zan baku kunya ba, "haka nike san ji ai ga wannan ya kawo da kudi dubu ɗari biyar."
"Wooow! Momy gaskiya nagode, amman ban ansar kudin nan sunyi man yawa ina da kudi sosai."
"Kinga a haka akayi ma kowace mace indai gidan sarauta ta fito sai uwar miji ta bada tukuncinta na fara zuwa neman aure kuma kw zakiyi amfani da komai da aka kawo wanan ne zaki nuna kin gode."
"To Momy nagode, na zan wuce na fara jin bacci, "to Daughter Allah ya kaimu, "Amin ya Allah."
Azima ta anshi kayan hannun Gimbiya Hakima sanann ta wuce dasu su kuma su Bilkisu suka take mata baya zuwa shashen ta, tunda Azima ta anshi kaya sai da ta kaisu kowane shashen dake cikin masarautar baki ɗaya sanann ta dawo wajen Gimbiya Hakima.
"Allah ya taimakeki, gaskiya Yarima Hakim yayi koƙari dan tunda nike ban taɓa ganin irin wanan kyautar ta ganin farko ba sai gunku."
"Uhmmm! Azima ku riba kuɗin ga duk wani bawa dake shashena sai kuyi hakuri ba yawa, sai ku fara shirin bikin kafin na baku abunda zaku bukata su kuma wanann super aura da wanann laces ɗin akai ma ɗikin fatan kinjini."?
"Allah ya taimakeki yanzun zani cika Umirninki, muna godiya Gimbiya Hakima Allah ya ƙara tsawancin kwana ya raba ki daga shirin maƙiya."
"Amin, ku wuce ku ban waje ina bukatar na huta, "to mun barki lafiya."
Haka suka tafi suna murna, ranar bayin shashen Gimbiya Hakima sunyi murna daman basu wuce su bakwai ba aiko sunsha kudi, Gimbiya Hakima ko tasha addu'oi kala-kala.
Bayan tafiyar su Lantana,  Hakima online ta hau direct *JAMEEY NOVEL FAN* ta shiga nan suka fara comment da shirhi na novels ɗin Jameey dan suna gani koƙarinta wajen yanda take baje basira take Nishad'antar da masoyan ta, bayan sun gama sannan ta sauka online ta kwanta bacci.
        *SOME DAYS LATTER*

Tunda Hakim yazo bai ƙara waiwayar Hakima ba itama bata damuba dan daman ita ba jiran wayarshi take ba balle zuwanshi, hidimar gabanta take balle biki yanzun saura sati ɗaya dilkar da halawar da ake yi mata sun ma isheta dan jike kamar ta kurma ihu da gyaran jikin da ake yi mata.

Gimbiya Yakumbo yanzun bata da lokacin zama dan gyara Hakima take ciki da waje, dan tace idan kana da kyau to ka ƙara da wanka shiyasa ta ko ina gyara Hakima take dan yanzun Hakima ta dawo shashenta da zama baki ɗaya.
Daga can bangaren kuma Gimbiya Yakumbo tsaye take tana ba Hakima maganin kariya daga shirin shidanu sannan kuma tana ƙara janjamata ta riƙe Allah dan shine gatan ko wani bawa.

Shiri suke ba kama hannun yaro, cikin lokaci ƙalilan Hakima ta koma kamar balarabiya dan baka gane ta sai tayi magana, maganar ma idan tayi sai ka kyaleta sosai zaka gane Gimbiya Hakima ce  saboda ta chanza baki ɗayan ta.
_____________________________
*×ZARIA×*

Itama Gimbiya Fulani Kubrah ba abarta a baya ba dan ta zage tayi ma Gimbiya Hakima lefe nagani da buɗe, duk da Maimartaba Sarki Abdulmatalak ya bada kuɗi amman itama ta ƙara da kuɗinta banda kuɗin da Hakim shima ya bada, dubai taje itadasu Maryama suka haɗo ma Gimbiya Hakima Lefa set 42 akayi mata banda gana most go guda shidda ba abunda ke cikinta sai bags da dai sauransu.
Bata damu da fidda hannu da su Gimbiya Zulaha suka yi ba, daman tasan haka zai faru shiyasa taita hidimar gabanta badamu da abunda suke ba, ta ba banzaye ajiyarsu.
Su kuma su Gimbiya Kilishi bakin ciki kamar ya kashesu, ba kamar yanda sukaga iyayen lafe su duk a tunaninsu Maimartaba Sarki Abdulmatalak shi ya bada kuɗin duka akayi wanann lafe ga kuma sunga dubai akaje aka haɗo su hakan ya ƙara tun zuramasu zuciya.

Gimbiya Kilishi abun ya isheta kasa zaune tayi hakan yasa ta ɗauki hanyar shashen Gimbiya Zulaha hankali tashe dan batada wata kwanciyar hankali gani take dukiyar Maimartaba ce duka Gimbiya Fulani ta ansa taje tayi ma Hakim wanann ƙarya injisu ba.
"Gimbiya wai kina ganin abunda ke faruwa cikin masarautar nan."?
Hmmm! "Ina gani Kilishi, daman tuni nasan Abdulmatalak yana nuna mana banbanci tsakaninmu da Kubrah, yafi sonta a kanmu kuma asirine kawai tayi mashi shiyasa baya saurarar kowa sai ita."

"Ina wallahi bazai saɓuba budunga a ruwa, ya zama dole muma idan su Hamad suka tashi aure ayi masu fin abunda akayi ma wance gawar, suna wahalar banza basu san saura shekara ɗaya ya mutu ba."

"Ai ni harda haka yasa na kwantar da hankali na su gama wahalar banza saura shekara ɗaya ya mutu kinga komai suka saya Hamad za'aba shi duka harda ita matar dasuke rawar ƙafa a kanta."
"Aiko dai hakane kawai mu samasu ido suka gama haukansu wawaye kawai dasu, ai gobe ne zamu kai lefe ko."?
"Eh gobe ne, "ok muna jiran goben tayi zamu kai lefe yanda take bukata mudai musan karshen lefen namu ne."
"Ehmana, kedai bari Kilishi ni kawai sama Kubrah ido nayi tagama bikinta da dariyarta nan da shekara ɗaya kuka zatayi sannan tanaji tana gani za'a ɗaura Hamad mulki na maida ta baiwa ta bikin ciki zaiyi ajalinta."
Uhmmmm! Abunsa Kilishi tace kenan ta tafiyarta dan ita kaɗai tasan abunda zatayi ma Gimbiya Zulaha, nan da shekara ɗaya itama zatayi kuka karshe bikin ciki zaiyi ajalinta itama, dan gaban idonta za'a ɗaura Humad mulki, haka tai ta tunaninta daga karshe ta kama dariya dan gani take komai ya kusa zuwan mata karshe tana haka bacci ya kwasheta ba tare da tayi addu'a ba, to ina ma zatayi addu'a matar da ko sallah batayi.

*{yan uwa muslmai wallahi muji tsoran Allah ita wannan duniyar ba matabbata bace, duka nawa duniyar take da zakiyi ma Yar'uwarki hassada da bakin ciki bayan kunsan cewa hassada ga mai rabo takice🤔😰, to maiye abun yi ma mutun hassada bayan Allahn da baya mutun shi zai baki idan kina da rabo wanda kike ma hassada karki manta bashi ya ba kanshi ba, Allah ya bashi dan haka nidai shawarace tawa sisters murage yi ma junanmu hassada kaima kayi addu'a Allah yabaka abunda zai zamaka Alkhari ka nema Alkharin Allah, Allah yasa mudace Amin}*_By Jameelah Jameey✍🏻_


#JameelarhSadiq@wattpad
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

+
73&74

Washe gari bayan su Gimbiya Zulaha sun gama shiryawa suka ɗauki hanyar Kano dan zuwa kai lefen Gimbiya Hakima da Yarima Hakim.
"Kilishi yau dai zamuga wannan Hakimar da Hakim ke yi ma rawar kai".
"Aiko dai yayi ya gama  dan shekara ɗaya zaiyi ita, ta zama ta Hamad baki ɗaya har abada kuma ta haifamana sarki".
"Hhhhhh! Kilishi kina sani farinciki wallahi shiyasa nike sonki, insha Allah zuri'ata ta dunga zama sarki kenan har abada Kilishi ".
Wani kallon banza Kilishi tayi tana aiyanawa cikin zuciyar ta itace zata kama ganin sarki a cikin zuri'atar , dan wannan komai da komai da Humad ya dace basu Hamad ba.
*Niko nace bawan Allah Humad shi baima san Gimbiya Kilishi na wanan wahalar ba dan bai damu da mulki ba🤣*
Haka dai suka kama yan maganganun su har suka iso masarautar Kano.
Baki sake su Gimbiya Kilishi dan sunga tarba ta girma, sunga idan akeyin abun girma da nuna arziki duk da Gimbiya Zulaha tasan masarautar Kano amman rabonta da masarautar Kano tunda da Sarki Abdulhadi zai auri Fulani  bata sake zuwa ba ita acewarta ba halinta ɗaya da Gimbiya Yakumbo ba shiyasa suka rabu.
Bayan angama ansar lefe suka wuce shashen Gimbiya Yakumbo, da yake a shashen Maimartaba Sarki Abdulhadi aka anshi lefen, zasuje suci abinci sannan su wuce gida.
"Sannunku da zuwa Gimbiya Zulaha, ashe rai kanga rai".?

"Gimbiya Yakumbo gashi kuwa, ya na samaiki keda ɗana Yarima Annas ".?
"Lafiya lau kika samaimu, harda ma ɗiyarku Hakima ita da mahaifiyarta duk muna lafiya".
"Haka nike san ji, yau dai saura yan kwanaki akawo mana Amaryar mu, "eh daga gobe zamu fara aladar bikukuwan sarauta insha Allah ".
"Da kyau, ina ita Amaryar take bata zuwa ta gaidamu".?
''Aa fa Zulaha kin taɓa ganin ida Amarya ta fito ranar da ake kawo lefenta".?
"Ai nasa zaki kirata tazo mu gaisa ba wanda yaji ba wanda ya gani".
"Aa ni ba haka nike ba, kuma Hakima bata gidan ma baki ɗaya kuyi hakuri ta kusa dawowa masarautarku baki ɗaya ma".
"Shikenan muna maraba lale da zuwan ta Amarya Gimbiya Hakima ".
"Yauwa haka nike san ji daga gareku, kuci abincin mana, "to yanzun ko zamuci".
STORY CONTINUES BELOW

Bayan sun gama cin abinci suka ɗauki hanyar komawa gida, bayan sun koma gida basu ce ma kowa komai ba ita dai Fulani Kubrah bata damu da rashin gaya mata yanda komai ya kasance ba daman bata ran za'a gayamata ba.
Yau ake fara hidimar biki dan yau ake sa Amarya laile hidima ake kamar kama hannun yaro tun safe aka tafi da Hakima shashen Gimbiya Yakumbo aka fara shafama amarya laile, wanann yana farkon al'adar masarautar Kano kafin a fara biki za'a fara sama amarya laile sannan zasu cigaba da yin sauran al'adun.
Tunda aka fara shafama Hakima laile take bakin ciki dan ba haka ta so ba, ita da ba san Hakim take ba amman sai wani gyara ake yi mata sai kace gidan wanda take so da kauna za'a kaita.
"Momy dan Allah ki barni haka ko ina fa naga kun shafaman".

"Gidanku Daughter, idan bamu gyaraki ba mai kike san ayi maki".?
"Amman Momy tunda akayi baiko kuke duraman abubuwa cikin cikina,sannan kuma kuke man shafe-shafe Momy".
"Wannan shine gatan, nidai Daughter dan Allah karki bamu kunya ku zauna lafiya keda wannan baiwan Allahn, kinga dai yanda Hakim yake da hakuri kema banjinki Daughter fatana ku zauna lafiya kuba mariƙa kunya".
"Insha Allah Momy ba zan baki kunya ba zani kasance mai yi maku biyaiya har tsawan rayuwa nayi maki wanan alkwarin".
"Allah yayi maki albarka Daughter, sannna ban yarda ki sake da kowa ba inba uwarmijinkina ba da ƙannansa, amman ban yarda ki yarda dasu Gimbiya Zulaha ba".
"To Momy, wai jiya su suka kawo lefe ko".?
"Eh sune sunso su ganki ni na hanasu, so suka yi su ganki abun ya zama gori nan gaba suna cewa baki da kunya dake aka anshi lefenki, shiyasa na hanasu basu san ƙar nake kallonsu ba, kuma halin Gimbiya Zulaha ba wanda ban sani ba tana iya aikata komai saboda kishi da hassada".
"Allah ya kiyaye dai Momy, "Amin ya Allah Daughter.
Ana sama ta laile Gimbiya Yakumbo tana bata shawara dani shirin zama da miji, kuma Hakima tana ɗauka duk da ba wani san Hakim take ba amman duk abunda Yakumbo ta gaya mata suna cikin kanta dan ta rigeshi sosai.
Bayan ta wanke lailen kuma ta fara zuwa shashe tana kai gaisuwa duk inda taje sai anbata tukunci haka ta gama yi har dare yayi sannan ta wuce shashen ta duk ta gaji sosai.
Wanka kawai ta shiga, shi kanshi ruwan wanka ba ƙaramin kayan haɗi ya sha ba ruwan sai kamshi yake kamar anyi ɓarin turere cikin ruwan, saboda da kanshi da ruwan yake ga kuma zafin da yake dashi shi yaba Gimbiya Hakima dama daɗewa sosai tana gasa jikinta sai da taji ta dawo dai dai sannan ta fito.
Mai kawai ta shafa ta kwanta, da Azima ta lura da uwargijiyar tasu ta gaji sai suka kama yi mata tausa suna bata labarin mai dadi har bacci ya kwasheta ba tare da ta sani ba, sai da suka tabbatar da tayi nisa cikin baccin sannan suka tashi suka tafi shashen su dan gobe za'ayi hawan daba.
_____________________________

"Hakim ya maganar biki damai damai ya zamuyi naga har yanzun baka gaiyaci friends ɗinmu ba".?
"Aliyu ni ba wanda zan gaiyata kuma ba abunda zaiyi ai hidimar biki tana wajen Hakima tunda itace Amarya".
"Duk da haka Hakim, ya kukayi da Hakima mai take bukata kudi ko wani abu".?
"Kash ni ko number ɗinta bani da ita, amman nasan bata bukatar komai".
"What".?
"Eh Aliyu bani da number ɗinta, ko laifi nayi naga ka tsareni da idanu sai kace wanda yayi laifi".?
"Baka kyauta ba gaskiya Hakim, ai at list ko wayace kun ringa yi haka zai kawo maku shakuwa kafin bikin".
"Ni ban damu da na shaku da Hakima ba Infact nasan ba sonta nike ba itama ba sona take ba zaman biyaiya kawai zamuyi kaga ba amfani kenan".?
"Kace ba Hakim ina gaya maka gaskiya amman bakaji ko".?
"Wata gaskiya kake gayaman wanda ban ji ba Aliyu ".?
"Ehmana gashinan Hakim, wai har sai yaushe zaka gane ka yaudarar kanka, Hakim ka fidda girman kai ka rungumi matarka hannu biyu ka nunamata kallar soyayyar dakake yi mata hakan zaisa itama taji tana sonka tana nuna maka irin nata son da take yi maka".
"Naji Aliyu zanyi yanda kake bukatar ni zan shiga wanka, "ok shikenan Hakim nima bacci nike ji na wuce mu kwana lafiya angon gata".
"To goron gata, kaima ka yi fushi ka shigo layinmu a daina ce maka goro".
"Gaskiya ne Hakim tun kafin akawo Hakimar har ka fara kirana da goro ina da ka shiga daga ciki".?
Hmmmm! Abunda Hakim yace ma Aliyu kenan ya shigewarshi wanka yana murmushi, shi dai baisan dalilin dayasa yake san Aliyu yana yi mashi maganar Hakima sai yaji wani dadi wanda bai iya musulta irinshi.
Bayan ya fito wanka sallah yayi sannan yayi addu'oin bacci ya kwanta yana nishaɗa dan yana son a anbaci sunan Hakima gabanshi hakan na yi mashi dadi.
_By Jameelah Jameey✍🏻_

#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

75&76

_______________
Tunda Hakim ya tashi ya ansa kiran da Maimartaba Abdulmalak yake yi mashi, duk da yaji dadin yanda ya bashi umirnin ya shirya yaje Kano ayi duk wata al'ada da akeyi dashi amman kuma sai yaji ba dadi tunda Hakima ba sonshi take ba kuma bata ɗaukin zuwan nashi tunda ya dawo daga gidansu Hakima bata kirashi waya ba duk da yasan bata da numbers ɗinshi, amman ai ba zasu yi mata wahalar samuba tunda Maryam ƙawartace kuma Maryam tanada numbers ɗinshi kamar yanda su Maryama suke da duka numbers dinshi.
Bayan ya koma shashen shi ya ɗauki waya ya kira Aliyu yake gaya mashi ya shirya zasu biki, dan basu dawowa sai da Amarya, bai damu da duk saigantakar da Aliyu yake yi mashi ba ya tsinke wayarshi ya kira Maryam yace ta turo mashi number ɗin Hakima, Maryam taji dadi sosai da Hakim ya tambaye ta number ɗin Hakima,tasan cewa ko sunyi aure Hakim ba zai biye ma Hakima ba suyi ƙarantar da sukayi ba a school.
Tura mashi number din tayi sannan yace ta shirya zasu kano biki itada su Maryama amman kar ta kuskura tace dasu Maryama zatazo balle shi, haka ko akayi Maryam tace mata zasuzo biki amman itada wasu course mate ɗinsu zasuzo, tunda maryam ta gaya ma Hakima take murna dan itaji dadi sosai ta samu kawar shawara da ita ɗaya da Azima kawai take shirinta tunda babu age mate ɗinta a masarautar baki ɗaya.
Haka suka gama shiri suka ɗauko hanyar kano shida su Maryam.
___________
Yau tun safe bayi ke aiki tukuru saboda yau ake hawan daba, shiyasa kowa da yake masarautar ba zaune yake ba yana aikin da shuwagabannin bayi suka bashi.
Harta Hakima bata gida tana wajen make_up, kwaliya ake yi mata tana gani ta faɗa dan da ka ganka sai kasan kudi sunyi kuka bisa fuskar nan tata, yau su Maryam da wasu friends ɗinsu zasujo bikin, shiyasa tun safe bakin Hakima yake bude ta kasa kulleshi dan batayi tunanin Maryam zatazo mata biki ba, amman abun yayi mata dadi sosai.
bayan angama shiryata ta fito Amaryarta sak,marron material aka sa mata sai alkalbarta itama marron takalminta marron color ne dan kyai ko Hakima tayi shi dan ɓata lokacine wajen tsayawa na gaya maku kallar kyaun da Hakima tayi sai dai kuyi imaging  da kanku 😛.
Angama haɗa komai yanda ya dace dan su Hakim su iso har abinci sunci a shashen Yarima Annas Hakim da Aliyu suka sauka dan nan zasu zauna har agama hidimar bikin baki ɗaya sanann, Yarima Annas da kanshi ya kai su Maryam Shashen Hakima sunce abinci sanan sukayi wanka suka hau kwaliya suna cikin yin kwaliya Hakima ta shigo hauka ne kawai batayi ba san murnar ganinsu da tayi, bayan sun gama kwaliya suka jera suka fito da amarya dan kowa ya hallara banda Amarya.
STORY CONTINUES BELOW

Tun daga nisa Hakim yake kallon Hakima yana gaya ma Allah, dan tunda yake a duniya bai taɓa ganin mace mai kyau ba kamar Hakima, dan komai nata daban yake dana sauran, haka dai har suka iso wajen da zasu hau dokuna ita da Hakim suyi yar rere.
Hakima keda farin doki Hakim yanada bakin doki, kasa hawan dokin Hakima tayi, tayi kokarin taga ta hau amman ta kasa, Koda Hakim yaga ta kasa hawa sai ya sauko daga bisan nashi dokin ya je wajen Hakima dai dai setin kunnanta yace mata, "Idan kinsan baki iya hawa ba ai sai kice a taimakamaki yan mata, ba sai kinyi nukunuku ba."yace yana kashe mata ido ɗaya.
Bata ankara ba taji mutun ya ɗagata sama ya ɗaurata bisa dokin yana ɗage mata gira ɗaya yana mata nuni da shine boss, wata kunya da takaici ya turnike Hakima wai ita Hakim zai ɗauka, sai kace wata ƙawarshi da zai ɗauketa kuma gaban su Yarima Annas da Maryam dan ya kama rainata, ita bama ɗaukarma dariyar da suke yi tafi bata haushi dan suka ƙara koɗa mashi kai, bayan ya ɗaurata shima ya sake hawan nashi sannan akayi masu counting one-three sannan suka ba dawakansu wuta.
Hakim abun mamaki ya bashi yanda Hakima ta zage tana san ta wuce ita a dole ta yo na ɗaya ba Hakim ba, shikuma Hakim daya ga haka sai ya ƙara ma dokinshi wuta in munite ya taddo Hakima kallon-kallon suke ma junanshi na Hakim yace mata, "Yarinya ke nemi alfarma a ɗaga maki ki wuce dan wannan wasan na jarumaine ba na ƙanannan kiyashi ba."gwallo yayi mata sannan ya rage gudun nan Hakima ta wuce tayi na ɗaya, nan fa ƙawayen Hakima suka hau murna sunyi na ɗaya, bayan sun gama hawan dawakan akaci abinci kowa ya wuce masaukinshi.

Bayan Hakim ya huta ya ɗauko wayarshi ya lalubo number ɗin Hakima, ya daɗe yana kallon number sanann daga baya ya fara tura mata textmassege kamar haka👇.
_"Yarinya ki fara shirya zama da maƙiyinki, dan kinsan Yarima Hakim ba sonki nike ba kuma kinsan ke ba zaɓi na bace, nan gaba zaɓi na zata shigo ku zauna da ita dan haka take note."_

Tunda shigowar massege ɗin a wayar Hakima ta ɗauka ta karanta bada damu da abunda Hakim yace mata ba dan daman tasan ba son juna suke ba, dan haka itama ta mayar mashi da answer ɗinshi dan bata iya ɗaukar gaya magana marar dadi.
_"mtssssss, daman wa ya gaya maka ana sonka, kaima ka shirya zama da maƙiyarka wanda bata sonka bata kaunarka kawai biyaiya zatayi ta aurenka, kuma in katashi ba ɗaya ba ka kawo uku bayan ni duk matsalar ko baka san sai ana son mutun akeyin kishinshi ba to ni bani sonka balle nayi kishinka take note, sannan kuma kayi gaugawar goge number ta cikin wayarka."_
Shigiwar massege ɗin Hakim ya karanta take yaji baiji dadi ba ,da man shi yasan Hakima bata taba sonshi, daman yayi message ne yaga ko zata damu amman ga abinda ta mayarmai da answer, shi dai Hakim gashi nan dai dan baiji dadin jikinshi tunda Hakima ta turo mashi answer, kwaciya yayi yana juye juye dan da ya kulle idonshi sai ya hango daukar da yayi ma Hakima ya daura ta kan doki, ko kuma da ya kulle idonshi sai ya tuno fadan da sukeyi a school, murmushi kawai yake dan abun yana yi mashi dadi sosai haka dai bacci ya daukeshi.

Itama Hakima bayan ta turama Hakim da answer suka cigaba da labarin duniya ita dasu Maryama dan daman can sun san juna shiyasa, sune basu kwanta ba sai wajen biyun dare sanan ko wancansu ta kwanta bacci.

Yau za'ayi wanki, wani program ne da ake gidan sarauta mai suna *WANKI*, wanki dai suna nufin wankin lailen da akayi ma Amarya, dan haka da wuri suka tashi suka shirya ba ƙaramin kyau Hakima da ƙawayenta sukayi ba, karfe hudun rana aka fara gudanar da wanki, gaskia ko Hakima taga gata wajen wanki dan ba ƙaramin kudi a zubda mata ba sai mangrid sannan a ka tashi.
Wanka kawai Hakima tayi ta kwanciyarta bacci, duk da ba baccin take ba tunanin zaman da zasuyi da Hakim Yanzun yake neman hanata bacci gashi gobe ne ɗaurin aurensu, tuna message ɗin da Hakim yayi mata ya tada ma hankali batasan sanda hawaye suka fara zuba a idonta ba, dan tasan zata sha wuya wajen Hakim dan ma saukinta gasu Maryama nan da Sadiya tana da abokan ɗebe kewa, gashi yan jere sunjr sunce a shashe ɗaya zasu zauna da Hakim, harda haka yake ƙara tada ma Hakima hankali, parlour ɗaya ne babba sai bedrooms da suka zagaye da parlourn kitchen kuma ɗayane toilet ne kawai basu haduwa da Hakim sai bedroom dan suma ance suna da yawa a shashen nasu, haka dai ta kama juyi tanajin su Maryam suna lissafa kudin da suka samu yau wajen Wanki, har suka gama laissafi suka kwanta bacci amman ita idonta biyu tana tunanin rayuwar da zata shiga daga gobe.
STORY CONTINUES BELOW

Shima haka takasance Hakim, tunda suka dawo kasa cin abinci yayi yana mamakin yanda Hakima ta tsaneshi da yawa har haka, yana san kasancewa da Hakima inuwa ɗaya koda ko zasuyi faɗan dasuka saba, duk da yasan cewa ba sonta yake ba amman yana san yaganta kusa dashi, sai yanzun ya ƙara amincewa da kunnunwanshi da idanuwanshi suna son Hakima, amman zuciyarshi bata son Hakima, yana taƙaicin yanda ita Hakimar batajin haka a taitare dashi, da tana jin haka da tayi kishi jiya da ya tura mata message zai mata kishiya amman a banza ko a jikinta, daɗinshi ɗaya ma shashe ɗaya zasu zauna ma dole ne zasu ringa ganin juna ko wani lokaci bacci kawai zai rabasu ko wane zaitafi ɗakin baccinshi, a haka dai ya kama tunaninshi yana hangon kyaun da Hakima tayi wajen al'adar bikin nasu, duk da yasan cewa Hakima kyaukyawace amman tayi mashi kyau sosoi haka har bacci ɓarawo ya kwasheshi.
Yau masarautar kano ta fara sanin zatayi hidimar biki, dan sarakuna da yan siyasa yan kasuwa da duk wani mai faɗa a ji a nigeria sai da ya hallaci kano dan kawai ɗaurin auren Gimbiya Hakima da Yarima Hakim, da yake ɗaurin auren 1pm za'ayi shiyasa jama'a suke samun damar zuwa ayi dasu tunda ɗaya ne za'a ɗaura auren.
"Haba Hakima dan Allah ki tashi ayi maki make-up ɗin nan kinsan one za'a ɗaura wannan auren naku kuma gashi yanzun 12 tayi amman kinƙi tashi ayi maki make-up haba please."
Itadai Hakima bata ce ma Maryam komai ba, sai dai ido ta tabita dashi, kuma bata tashi ba, ji tayi an bugar mata cinya sannan tayi ajiyar zuciya tana cewa, "Maryam wallahi banson auren nan, banson Hakim kinfi kowa sani bansan ya zanyi ba."
Ta sowa Maryam tayi ta zauna kusa da Hakima, tana zama su Maryama na shigowa suma direct wajen suka zauna dan sun san komai suma, dafa ƙafarta sukayi su duka ukkun sannan Sadiya ta fara magana, "Hakima munsan cewa baki san Yaya Hakim, amman kisani Yaya Hakim yana sonki yana kaunarki, Yaya Hakim yana yi maki so wanda har yanzun baisan adadinshi ba a cikin birnin zuciyarshi ba."
"Ta..., "dakata Hakima mu gama gaya maki waye Hakim, da mai-da mai Hakim yake so da wanda bai so, koda baison ki idan kina yi mashi abubuwan da muka gaya maki wallahi zaki juya Yaya Hakim kamar ranwa, Hakim zai zama mijintane daki juyashi yanda kike bukata, domin zai soki kamar ranshi, amman idan kinbi shawarar da muka baki."
"Yaya Hakim mutun ne maison a girmamashi, yana son kwaliya more expecially yaga kinsa jan baki, yana son yaga mace yar'kwaliya da kisisina da shagwaɓa, baya cin abincin bayi dan haka ki shiga da niyar ke zaki ringa yi ma mijinki sauwa , ki tabbbatar da ke gwanace wajen iya girki da kwaliya, Hakima tsafta tana gaba wajen sace zuciyar ɗ'a namiji yanga da jan aji ko yayake ko, dan kitson nan da kunshi zu zama abokanarki Hakima suma suna ƙarama mace martaba a wajen mijinta, ki rige Ibada da neman tsarin wajen ubangijinmu Allah, wallahi Hakima idan kika rige abubuwan da muka gaya maki sai kinzama zara a wajen Yaya Hakim, sannan naji watarana a lambu yana gaya ma Yaya Aliyu idan mace na cin chingum tana taso mashi da shi'awarshi dan haka sai ki tafi da kwalin chigum, wannan zaman da zakuyi ki kasance mai yawan cin chigum amman a gabanshi kina sa ƙananan kaya masu masifar ɗaukar hankalin ɗ'a namiji zaki sha mamakin yanda Yaya Hakim zai nemi ku sasanta kanku ku zauna lafiya mudai muna maraba dake muna kaunarki a matsayinmu na ƙannan Hakim."
"Nagode sosai Sadiya, kuma insha Allah zanyi duk abunda kuka gaya man, amman mai Hakim yafi so wajen abinci."?
"Yafi son tuwon shinkafa miyar kuka, sannan kuma yanason dambu sosai, "nagode Allah ya bar zuminci, "Amin ya Allah Hakima, ku taho ayi make-up ɗin sha-biyu da rabi har tayi fa."

Nan aka yi ma Hakima kwaliya, wata atamfa tasa mai ratsin ja da baƙi atamfar tayi mata kyau sosai, sannan ta ɗaura alkarba sama ana ɗaura aure za'a tafi da amarya gidan mijinta, shiyasa ta shirya.
Kutsawa nike cikin mutune dan na kwaso maku rahota wata kallar kwaliya ango Hakim yayi, wai na samu na ganoshi shida friends ɗinshi, farar shidda yasa tasha aiki masha Allah ga babbar riga duk ya ɗaura a bisa rigar aikin ɓakin zare aka yima atamfar abundai masha Allah kawai zamuce.
Da kaga Hakim kaga ango dan bakinshi yaƙe kullewa dan murna, dan koshi kanshi yana mamakin yanda yake farin ciki har haka sai kace wanda zaiyi auren soyayya, amman shi yasan yau babbar ranace a wajenshi, ya rasa yanda zaisa kanshi dan murna duk da tsokanarshi da Aliyu yake amman bai damu ba shidai ya kosa ma a ɗaura auren bak ɗaya, dan ji yake inama ya matso da time ɗin.

Hausawa sunce rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya, to haka ta kasance dan yau aka ɗaura auren *YARIMA HAKIM ABDULMALAK DA AMARYARSHI GIMBIYA HAKIMA ABDULHADI*  a kan sadaki naira dubu ɗari biyar, mutane da dama suka shida wannan ɗaurin aure, bayan angama ɗaura auren aka fara taya Hakim murna shidai kawai kallon mutane yake dan abun mamaki yake bashi wai shi yau aka ɗaurama auren da kuma Hakima, abunda yana bashi tsoro da mamaki, haka dai haka gama komai aka fara shirya ma amarya dan kanta gidan mijinta.
Wa'azi tasheshi wajen iyayenta guda uku, tasha kuka kamar ba gobe da Lantana da Bilkisu da Azima kawai ta tafi gidan miji, haka suka ɗauki hanyar Zaria domin kai amarya gidan mijinta.

_By Jameelah Jameey✍🏻_
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_
    *(Yar mutan kankia👸🏻)*
 

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''
77&78
Tun daga farkon masarautar Zaria ake yin busa anayi ma Hakima lalai da zuwa masarauta mai albarka, itadai Hakima kanta yana cikin alkarba bata ganinsu sai dai jinsu, shashenta aka kaita da addu'oi ta shigo gidan masarautar haka ma da addu'oi ta shiga shashenta da addu'oi ta shiga room din da aka saka ta, bayan tayi addu'oi ta zauna bisa gadon da yake mallakinta, ita dai Hakima abun mamaki yake ba wai yau itace a gidan miji, mijinma ba wani bane face Hakim makiyinta.
+
Bayan sun huta aka kawo masu abincin saukar Amarya sannan fa aka shiryama Gimbiya Hakima dan zataje gaida mutanan gida, kwaliya akayi mata mai kyau sannan aka fito da ita shima Hakim ya shirya ya fito tuni ita suke jira dan haka su kuma al'adarsu take idan aka kawo amarya zata je gaida iyaye ita da ango bisa doki, Hakim da kanshi ya ɗauketa ya ɗaura ta bisa doki sannan shima ya hau, direct shashen Gimbiya Zulaha suka dosa daga ita sai shi sai dogarawa masu lura da dokin da suke sama, suna isa ya sauko ya sauko da ita da, sanan yaje saitin kunnanta yace mata sai ta kula sosai kuma komai Gimbiya Zulaha zata ce mata karta ce mata komai iyaka kawai ta gaisheta sai da Hakima taji tsoro dan batasan lokacin da tayi addu'oi ba, hakan da tayi ya burge Hakim sosai riƙe mata hannu yayi sannan yace "kwantar da hankalinki ba abunda zai faru, kedai kawai kiyi abunda nace maki."
Ɗaga mashi kai kawai tayi sanna suka shiga cikin parlourn daman ayi ma iso tuni, sallama sukayi baki ɗayansu tunda suka shigo Hamad yake kallon hannun Hakim da ya riƙe Hakima dashi ji yake kamar ya tashi yaje ya sare ma Hakim kai dan wani bakin kishine ya turniƙe shi zuciyarshi tafasa kawai yake daga zaune, duk abunda yake Hakim yana sane dashi dan yasan yana son Hakima da kunnanshi yaje na gayama Gimbiya Zulaha, bayan sun samu waje sun zauna nan Hakim ya fara gaida Gimbiya, "Gimbiya ina wuni mun samaiku lafiya."?
Kallon sama da ƙasa tayi mashi sannan tace, "da ban wuni ba da kangan ni, ko kuma da ba lafiya ai da asibiti zaka samaini kwance a gadon asibi ɗ'anso."
Hanjin cikin Hakima suka fara kaɗawa daga zuwanta har ta fara ganin masifa, hannunta Hakim ya riƙe gam dan ya lura Hakima ta kusa zundumawa da gudu daga zaunan dasuke.
"Ina wuni."

Hakima tace cikin ɗari-ɗari dan ta tsorata da lamarin gidan su Hakim amman ta ɗaukarma kanta bata shiga harkar kowa zata dage da neman tsarin Allah kamar yanda kowa ke cemata.
"Lafiya, amarya bata laifi ko kin kashe dan masu gida, ai kin bude mana fuskar mu gani ko."?
Hakim da kanshi ya bude ma Gimbiya Zulaha fuskar Hakima ta gani, ba Gimbiya Zulaha ba harda Hamad dake kwance yana kallonsu sai da ya zauna yana kallon sahibarshi Hakima dan wata wutar sonta ke ƙara ruruwa cikin ƙahon zuciyarshi, shi dai Hakim dariya yake a zuciyarshi dan bakin ciki ƙarara yake gani kwance a bisa fuskar Gimbiya Zulaha, itama Hakima duk da kanta na duge sai da ta ɗago kanta ta kallesu dan ji tayi shirun yayi yawa, dakal Gimbiya Zulaha ta bude baki tace, "ba laifi, ashe tsohon naka ya iya zaɓi."?
"Uhmmm, gashi nan dai kin gani, Abba ya zaɓin ma son kowa son wanda ya rasa.", yace yana miƙewa tsaye zasu tafi, zinari da lu'unlu'un ta ba Gimbiya Hakima na barka da zuwa masarautar zaria tayi godiya suka fito suka wuce shashen Gimbiya Kilishi.
Tunda su Hakim suka fita Gimbiya Zulaha ta fara magana tana cewa, "Hamad banga laifinka ba dan kace kana son Hakima ba, ashe haka take da kyau."?
"Hmmm, Gimbiya kiyi wani abu tun kafin ni nayi da kaina dan wallahi ina iya sace Hakima mu bar ƙasar baki ɗaya muje muyi soyayyarmu baki sake ganina har abada."
"Rufaman asiri Hamad saura shekara ɗaya Hakim ya mutu Hakima ta zama taka halak malak karka damu."
"To shikenan, nidai ina nan ina jiran lokacin yayi."

_🙄Kai su Hamad sai kace ku ke da lokacin🤔, naga alama kuna mantawa da Allah fa😰_
______________

Bayan sun iso shashen Gimbiya Kilishi aka yi masu iso suka shiga, Humad yana zaune yana kallo kusa da Kilishi ya tashi ya gaidasu Hakim yayi mashi Allah yasa alkhari sannan ya tashi yace ma Kilishi shi ya barta lafiya zaima tafi massallaci, bayan Humad ya tafi, Gimbiya Kilishi ta tashi ta rungumi Hakima tana yi mata lale da zuwa  masarautar kano, hakan yayi ma Hakima dadi Hakim ya lura da haka yana mamakin yanda Kilishi ta iya duniyanci kala-kala sai kace wata tsohuwar karuwa.
Bayan sun zauna suka gaisheta ta taya su murna sosai sannan itama taba Gimbiya Hakima zinari da lu'ulu'u kamar yanda Gimbiya Zulaha ta basu sanna suka fito suna fitowa suka wuce shashen maimartaba shima sun gaidashi ya ba Hakima kyauta, sanann suka wuce shashen Gimbiya Fulano Kubrah Hakima taga gata wajen Fulani Kubrah dan har abun ya fara bata kunya ma, sosai Fulani Kubrah taja Hakima jiki dan kafin su koma shashen su sai da shekuwa ta shiga tsakaninsu kuma ta ƙara gaya mata yanda masarautar take dakuma waye Hakim, Hakima taji dadi sosai sai dare sanan suka koma shashen su bayan kyautukan da Gimbiya Fulani Kubrah ta cika ta dasu, koda suka koma shashen su abun mamaki bata kowa ba dan duk wanda suka rakota sun koma gida an barta ita ɗaya kamar maiya, suna shiga parlourn ta fisge hannunta daga rikon da Hakim yayi mata ta samu kujera ta zauna ta fara aikin kuka dan taji haushi da suka tafi suka barta, su Lantana ma bata gansu ba sun tafi shashen bayi, Hakim bai nuna ya damu da kukan da take ba duk da kukan yana jinshi har cikin zuciyarshi amman sai ya shigewarshi bedroom ɗinshi ya faɗa wanka, da Hakima taga kukan yana ma sanata ciwon kai ita ma ta tashiga ta shiga wanka a bedroom ɗinta, bayan ta fito daga wanka ita dai tasan room ɗin ita ɗaya ke dashi tunda taga Hakim ba shi ya shiga ba kuma kofar a kulleta take wannan dalilin yasa tana fitowa daga wankan ta saɓile towel ɗin baki ɗaya daga jikinta ta tsaya babu komai a jikinta sai da ta goge jikinta sosai sanann ta wuto wajen mirror domin shiryawa tayi bacci,  dump light taje ta kunna sannan ta zauna bisa dreesing mirror ta fara shafa mai, ɗaga kanta da zata yi taga mutun tsaya bisa bayanta yana zara ido kamar mai tsorata tayi tayi wata uwar ƙara ta duge ƙasa tana ƙare ƙirjinta da hannuwanta, tana kuka, tsaki Hakim yayi sanann yace "idan kin gama kukan isakancin naki ga abinci nan sai kice, mai zangani da kike boyewa mtsss."ya wucewarshi yana balbalin bala'i.
*Niko nace da ba abunda zaka kalla mai zaisa ka tsaya kallonta tun fitowarta wanka malam Hakim😛*
Tunda ta duke take kuka, bata tashi ba sai ta taji ta fita sannan ta tashi ta fara cewa, "Allah ya isa ban yafe ba, kawai ka kalli banza kawai."
Haka Hakima ta kama guguni tana shiryawa har ta samu ta gama abunda take saboda da fushin da tayi ko abincin ma bata ci ba kawai addu'a tayi ta kunna suratul baƙara ta kwanta baccinta.
Tunda Hakim ya samu ya baro ɗakin Hakim direct room ɗinshi ya dawo duk da wanka da yayi amman sai yaji yana da bukatar sake wani sabon wanka bayan ya fito daga wanka sallahr nafila yayi sannan yayi addu'a shima ya kwanta, tunda ya kwanta bai samu bacci ba dan daya kulle ido sai ya ga Hakima tana tuɓe towel ɗin da ta fito wanka tun yana ɗaukar abun wasa har yazo da ya girmi tunaninshi da wata kalllar shi'awace ta adabi Hakim ya rasa ya zaiyi da rayuwarshi dan tunda yake bai taɓa jin kallar wannan station ɗin ba sai yau, bai da damar kulle idonshi sai yaga Hakima tana yi mashi gizo ba kaya a jikinta da yaga abun ba sauki ya tashi ya nufi ɗakin Hakima cikin bukatuwar kasancewa da ita dan yayi ma kanshi alkwarin zan sar hakinshi ko ta wani hali ne.

_By Jameelah Jameey✍🏻_

#Share
#Comment
#Like
#Vote
#Please

Post a Comment for "GIMBIYA HAKIMA CHAPTER B"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...