Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GANI GA WANE CHAPTER B

GANI GA WANE CHAPTER B

- - Post a Comment

 GANI GA WANE CHAPTER B


® *INTELLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

     *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*


    _*GANI GA WANE....*_🌷


_*STORY & WRITING ~ BY*_

     _*AUFANA*_✍

_Whattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee) my granny's*_

   _*PAGE 27~28*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Ahankali Ruk'ayya takai hannunta akan cikin nata tana shafashi cikin rashin fahimtar abunda RAIHAN d'in tafad'a, shuru tai can kuma tace "K'awa cikin naki sosai ne yake maki ciwo" anan kam kasa magana tai jin hakan yasa Ruk'ayya tamik'e a tsaye tafita,,,,,..+

Kai tsaye office d'in vice principal d'insu tawuce wacca Abdallah yabada amanar RAIHAN a hannunta, tana isa nantake tafad'a mata halinda RAIHAN take ciki, cikin sauri tariko hannun Ruk'ayya suka fito. Koda suka iso kuwa RAIHAN sai faman juyi take tana zubda kwallah hannunta d'aya dafe da cikinta, cikin sauri taduk'a tad'agota tad'ora kan cinyarta tana shafe mata kwallanda suke zuba daga idanunta sannan tace "Sunhanallah RAIHAN 'yata meke damunki n..." kasa k'arasa zancentai saboda ganin jini a wandanta na uniform haryafara b'ata kayan,,,,, wani murmushi tai sannan tamik'e a tsaye tareda mikarda'ita, kai tsaye clinic d'indake cikin School d'in tawuce da'ita suna zuwa kuwa suka karb'eta nan Mama vice tamasu bayanin abindake damunta, haka su RAIHAN ke kiranta ( Mama vice),,,,..

Ganin yanda takeshan wuya sosai yasa sukai mata injection na bacci sannan suka gyaramata jikinta tareda koyarda'ita yanda zata dinga gyaran jikinta, batafi 5mnts dayimata injection d'inba bacci yad'auketa,,,,,..


Saida takusan 2hrs tana bacci sannan tafarka nan Mama vice tahad'a mata tea mai kaurin gaske tasha sannan akabata abinci taci, bayan tacine mama vice tazauna tana fuskantarta sannan takira sunanta "RAIHAN" ta amsa ahankali cikin sassanyar muryarnan tata mai dad'in saurare nan tacigaba "inaso nafad'amaki wani abune kokuma nace natina maki saboda nasan dik kinsansu domin nasan anafadamaku a islamiyya" shuru tai tabada attention nata dika ga mama vice saboda jin menene zata fad'amata wanda har takecewa tasanshi,, ganin tabada hankalinta yasa tacigaba dafad'in "RAIHAN yau kinshiga cikin jerin matanda suka nallaki hankalin kansu kinfita jerin k'ananun yara kinshiga sahun manyan mata ma'ana kingirma kinshiga sahun matanda ke fitarda jinin cuta wato haidha wanda ke bayyanarda girman 'ya mace danhaka yanzu dole ki k'ara mayarda hankalinki akan addininki domin sanin yanda zaki bautawa ubangijinki dakuma yanda zaki tsalkake kanki, RAIHAN nasan kinsan me'ake kira da haidha kuma kinsan kashe kashensa dakuma abunda ke kawoshi dakuma abunda ke nuna alamar wucewarsa dakuma abundake nuna samuwar tsarkin mace danhaka dik abunda kikasani yanzune lokacinda zaki fara amfani dashi kuma k'ara mayarda hankali domin sanin abunda baki saniba saboda kisan yanda zaki dinga tsalkake kanki daga najasa,, Sannan kuma inaso najamaki hankali akan kiguji mu'amala da maza karki kuskura namiji yamakai wayo ko yamatso kusa dake kokuma yace zai tab'i jikinki koda kuwa hanunki ne, RAIHAN kada kiyadda wani namiji yatab'a jikinki koda hanunkine saboda nantake zaki d'auki ciki idan har kika 'yarda wani namiji yatab'a hanunki",,,,..

Jin abunda tafad'a yasa tad'ago da kanta dasauri kaman tana ganinta tasake maimaita kalmar "CIKI" murmushi mama vice tai mara sauti saboda kartaji sannan tace "kwarai kuwa dik kika yarda namiji yatab'a hanunki tosai kinyi ciki" shagwab'e fuskarta tai kaman zatai kuka tace "Mama vice harda Yaya Abdallah da ya Ammar d'ina" dikda maganarta tabata dariya sosai saboda yanda tai maganar kaman wata sabuwar marainiya amma haka tadake tace "kwarai kuwa koda sune kuwa danhaka yanzu ki kiyaye sosai dan wallahi wallahi nidai baruwana dik abunda yasameki tinda dai nafad'a maki" tsoro ne maiyawa yad'arsu acikin zuciyarta jin yanda mama vice kemaganar kaman zata daketa,,,,..

Shuru tai batasake cewa komaiba nan itakuma tacigaba da tsoratarda'ita tareda razanata domin tagujewa sharrin samarin zamani daga karshe kuma tadinga bata shawarwari dakuma yimata y'an nasihohi,bayan tagama ta tabbatar bawata natsala sannan ta tashi tafita tana tausayin RAIHAN ganin yanda tamatuk'ar shak'uwa da Abdallah adik lokacinda yazo School d'in to dakyar yake tafiya saboda zata mak'alk'alemashi ne taita kuka kaman ranta zai fita saiyaje da'ita can OSUN shikuwa sam bayasan kukanta haka zaita b'ata lokaci yana rarrashinta harsaita daina kukan sannan yatafi tareda mata alk'awarin zaije da'ita idan sunyi hutu, hakama Ammar wanda kullum shike kawota kuma shike zowa d'aukanta idan suntashi tana ganin yanda suke tsakaninsu kullum shike rik'o hannunta idan yakawota harsaita shiga class sannan yabata sandarta yawuce acewarsa sam bayasan asan k'anwarsa makauniyace shiyasa a dik lokacinda suke a tare baya barin tarik'a sanda saidai yarika hanunta har suje inda zasuje sudawo,, wannan abun yasa take tausaya mata saboda sunriga sun sangartata amma gwanda tamata haka kuma tasan ahankali zata saba,,,,..

Lokacinda Ammar yazo d'aukanta haka yaganta so so silent bakaman yanda yasaba ganinta ba kuma daya tambayeta saitace bakomai saboda yanzu wata'iriyar kunya takeji sam bazata iya fad'amasa ba, haka yakyaleta dole harsuka isa gida bawanda ke magana acikinsu,, bayan tadawone fatima tace taje tai sallah tace toh amma bata tashiba tasake dawowa tace ta tashi tai sallah tafita tasake tadawowa dik bata tashiba, ganin tana d'an nike nike yasa taganota dariya tai sannan tace "kai Alhmdllh 'yar uwa shine baza'afad'amana ba mui murna muma mungirma, dariya tai tarufe fuskanta nan fatima tafita itama tana dariya,,,,..

Acikin kwanakin fatima tazage dantse tana koyawa RAIHAN yanda zatadinga tsarkake jikinta kar wani yaji wari ko kazni ajikinta takuma bata tirarukanda zata dinga amfani dasu ciki harda Miski kuwa,, dika dika kwananta biyu dashi tasamu tsarki nan tai wankanta na tsarki kaman yanda malaminsu ke koyardasu sannan tafara sallah,,,,..

Haka rayuwa tacigaba da tafiya dai dai gwargwado yayinda Ammar ke kuka da'ita sosai hakama fatima na k'ok'arinta sosai Salma kuwa har yanzu baruwanta da'ita, yanzu Salma da fatima suna a 200level inda Salma ke karanta Low fatima kuma degree in Norse inda RAIHAN kuma ke ss2 second term Alhmdllh komai natafiya dai dai,,,,..


Mami ce kwance a d'akinta tana waya da Abdallah sun kammala aikinsu amma har yanzu ba'abasu izinin tafiya ba, RAIHAN ce tashigo taji tana waya danhaka tajuya tawuce islamiyya,,,,..

Yau takasance thursday basushiga islamiyya nan fatima tajata suka fita yawo, harkusan 4:00am basu dawowaba ashe wani kyakkawan saurayine yatare RAIHAN akan hanya wai yanasanta itakuwa dikta damu tadawo gida gakuma wani tsoro da fargaba datakeji narashin sabo da tsayawa da namiji dasunan wai tad'i, itakuwa fatima da'dine fall a zuciyarta saboda yaron kyakkawane kuma maiji da naira gashi kuma d'an gaye wayayye,,,,..

RAIHAN tamatsu sosai dik abunda yace Eh ko aa kawai take bashi amsa dataga bashida alamar kyaleta danhaka tasaka sandarta tafara tafiya nanshikuma yashiga yimata magiyar tashiga mota yakaisu gida, k'inshiga tai saida fatima tasaka bakinta dakyar ta'amince tashiga shikuwa dad'i kamar yakasheshi alokaci d'aya yaji sonta yashigesa,,,,..

Bayan sun iso gida ma k'inbarinta yai tawuce nan yadinga janta dafira fatima nagefe d'aya tana jiransu kuma hankalinta baya gunsu,, Sallama sukaji a day'an gefensu, ahankali tad'agoda fuskarta jin daddad'an k'amshin tirarenda ko acikin bacci bazata tab'a mantawa dashiba, cikin jin da'di da murmushi tawashe fararen hak'oranta tai dariya sannan tace "ya Abdallah na oyoyo oyoyo sannu da zuwa barka da dawowa" jin yamata shuru baice komaiba yasa tasha jinin jikinta tai shuru, wanda suke tarene yamik'a masa hanu tareda yimasa musabaha nan shima yamik'amasa fuskarsa ba walwala sukai musabaha sannan yajuya yashiga cikin gida,,,,..

Baifi 5mnts dashigaba suma sukashigo suka taddashi tsaye acikin falour sai kai kawo yake yarungume hannayensa acikin k'irjinsa, yana ganin sun iso yak'ara tamke fuskarsa tamau kaman baitaba dariya ba sannan yazo dab dasu cikin d'agawar murya yafara magana "uban waye naganki taredashi a waje" shuru tai takasa cewa komai jikinta kuwa sai b'ari yake saboda tinda take bata tab'a jin Abdallah yamata irin wannan tambayarba, sake tambayarta yai "nace ubanwaye naganki dashi a waje ok wato kin rainanine koh toh wallahi bara kiji idan nak'ara ganinki dawane a waje wallahi saina mugun sab'amaki wato ke kingirma koh yai kyau nima zan nuna maki har yanzu ke yarinyace nasake ganin wani yazo dasunan tad'i gunki zakiga abunda zan maki" yakarasa tareda nunata da yatsa sannan yajuya yawuce d'akinsu,,,,..

*manage*👏


#/Vote

#/Share

#/Comment

'''AUFANA for life '''

  *I.W.A*🖊® *INTELLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

     *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ)*


    _*GANI GA WANE....*_🌷

_*STORY & WRITING ~BY*_

      _*AUFANA*_✍

_Whattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) my granny's*_


   _*PAGE 29~30*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Wani nannauyan numfashi tasauke azuciyarta kuma tana godiya ga ubangiji dabai daketaba dan harta gama yanke dukanta zaiyi, zuyawa tai tawuce izuwa cikin gida fatima ita tini tabar wajen saboda tsabar tsoronda taji,,,,..

Tinda takoma d'akinsu takasa samun sukuni ganitake sam bata kyautaba gashi har yayanta yai fushi da'ita nantake tayanke shawarar zuwa tabashi hak'uri,, Sallama tai cikin ladabi sannan tabud'e k'ofar tashiga tana dogara y'ar sandarta tana neman wajen zama, jin d'akin shuru yasa tafara kiran sunansa cikin zazzak'ar muryarnan tata tamkar kanari mai zakin sauti, "yayana.. Yayana ya Abdallah kana inane" dik abunda take yana kallonta yana gefenta akan kujera,Cikin shan murr yakarb'amata sannan yace "lafiya meya kawoki nan" shagwab'e fuska tai kaman zatayi kuka tace "dan Allah ya Abdallah kayi hak'uri wallahi narantse bazan sakeba wannanma takurani yai wai saimun nunamasa gidanmu sona yake" wannan kalmar data fad'a ta k'arshe jinta yai tamkar saukan aradu cikin zafin nama da zafin zuciya yamik'e tsaye tareda fizgota tafad'o jikinsa tudun bobbs d'inta yamanne a k'irjinsa nantake sukaji wani shook unexpected yazo masu hakan yasa yai saurin saketa sannan yace "banasan sakejin wannan zancen kifitarman acikin d'akin kuma wallahi dik nasake ganinki dawani saina mugun b'ata maki rai stupid girl kawai" dikda ranta yab'aci amma haka tahak'ura tinda tasan itace batada gaskiya nan tadogara sandarta tafita tana zubda kwallah,,,,...+

Bayan tafitane yazauna zuciyarsa namasa zafi wanda yarasa miye dalilin hakan, awani b'angare kuma mamakin girman RAIHAN yake yanzu dayaganta ba hijab dan d'azu dahijab take tak'ara girma sosai gak'irjinta yak'ara cika da dukiyar fulani sab'anin da dayabarta matasan zamanta suma sunyi manya sosai,, lokacinda yahad'ata da k'irjinsa saida yaji wani yaarr ajikinsa gakuma shook d'inda yaji wanda yasa yai saurin sakinta daga rik'onda yamata, kai shidai yakasa ganewa me hakan ke nufi wannan shine abunda yaketa tambayar kansa wanda kuma yakasa samun amsarsa,,,,,..

Tanafita tawuce d'akinsu tafad'a kan gadonsu tafara rera kuka kaman wata k'aramar yarinya, haka tawuni kuka kuma tak'icin komai fatima tai tai taci abinci amma tak'i bayan sallah ba abunda ketadata daga kan gado,, haka tawuni kuma takwana kuka shine abincinta kuma abun shanta,,,,..

Around 3:00pm ranar Saturday fatima sundawo daga School tazo tashiga d'aki, koda taje saitaga RAIHAN a kwance kuma sam bata motsi, k'arasawa tai kusa da'ita tareda bugata taji shuu tasake kai hanunta tad'ago da hanunta tasake saitaga yafad'i k'asa, a tsorace cikin firgici tafita dagudu, tana fitowa kuwa saiga Abbu da Abdallah sunshigo ganinta cikin wani yanayi yasa sukai tsaye suna tambayanta ko lafiya, cikin sheshekar gudunda tai tafad'a masu abunda ke faruwa aikwa batako k'arasaba Abdallah yawuce dagudu sukuma sukabi bayanshi,,,,,...

Yana isa cikin tashin hankali yahau kan gadon sannan yad'agota yana bubbugata tareda kiran sunanta, kiran sunanta yake dikyarikice yarasa mezaiyi Abbu ne yad'akko wasu sauran ruwa dake gefen gadon yafara zubamata yana shafamatasu a fuska tareda zubamatasu a ka, can saikwa numfashinta yadawo tai ajiyan zuciya ahankali sannan tabud'e idanunta,ahankali tafara magana cikin muryar kuka "yayana dan Allah kayi hak'uri wallahi bazan sakeba dan Allah kayi hak'uri" shuru yai yakasa mema zaice dakyar yace "haba RAIHAN yanzu akan d'an wannan abunne kike nema kikashe kanki bayan kuma kinsan hukuncin wanda yakashe kanshi da kanshi, shikenan nayi hak'uri amma saikinci abinci" toh zanci. Tafad'a kai tsaye, Abbu kuwa abun mamaki yabashi batareda yace komaiba yai murmushi yace d'akinsa yana jiran uwar gidansa tadawo tafita unguwa ne,,,,..

STORY CONTINUES BELOW

Bayan fatima takawo abincin nan yazauna dakansa yadinga bata tanaci kuma tana saka hannunta tana kakkare jikinta saboda sleeping gown ce ajikinta tanada kauri amma k'aramace batada girma sosai kuma hannun bre gareta, hmm aikuwa naki yakasa d'auke idonsa akanta sai satan kallonta yake,, haka yadinga bata abincin abaki hartak'oshi sannan yabata ruwa tasha nan yamata fad'a akan kartasake aikata irin wannan koma makamancinsa, nan itama tanasa alk'awarin bazatasakeba yai murmushi sannan yatashi yafita Salma haushi datakaici kaman yakasheta taita zabgamasu uwar harara ammafa a b'oye,,,..

Yau kimanin wata biyu da dawowarsu Abdallah antantancesu anmasu dikwani abu daza'ai yanzu and'aukesu ankaisu kowa annuna masa gun aikinsa dakuma office d'insa, Abdallah wata babbar boda ce aka kaishi wacca ke tsakanin Nigeria da Ghana kuma tananne ake shigo da manyan kayan fasa kwauri ganin jajircewarsu k'ok'arinsu dakuma kwazonsu yasa aka kaisu acan su shidane aka kai can sannan kowanne anbashi naira dubu dari takwas da tamanin saboda suji dad'in gudanarda aiki yanda yadace,, su fatima ansamu hutu satinsu d'aya dayin hutu Salma tashirya tawuce KEBBI wai zataje gaida iyayenta kasancewar dama sukanje idan anyi hutu saidai ba itakad'ai kaman yanda taje yanzu subiyu kezuwa ita da fatima amma yanzu itakad'ai taje wannan kuma baidami fatima ba saboda bayanzu tasan Salma ba tasan halinta fiyeda kowa saboda itake tareda ita any time,,,,...

Watan Abdallah uku a ghana sannan yadawo, kwana biyu da dawowarsa Abbu yakirasa a d'akinsa,, zaune yake agaban mahaifinsa kansa a k'asa yana sauraron abunda zaifito daga bakin mahaifin nasa, gyaran murya Abbu yai tareda gyara zamansa sannan yakalli Abdallah yakira sunanshi "Abdullahi" nan yad'ago ahanakali ya'amsa sannan Abbu yacigaba "to Alhmdllh dikkan yabo da godiya sutabbata ga Allah Abdullahi nasauke nauyinda ubangiji yad'ora man akaina natarbiyyantar dakai nabaka ilimi kagirma kuma ka mallaki hankalin kanka gashi kuma yanzu kasamu aikinyi danhaka yanzu abu d'aya yarage shine namaka aure idan kanada wacca kakeso toh kafad'a mana saboda naje nagana da iyayenta muyi magana" jin zancen yai kaman zuwan bazata saima yarasa mezaice dakyar cikin in in na yace "to aini Abbu banida wacca nakeso kuma koma inada ita ai banida inda zansakata dika dika aikin yaushenema muka farasa bare harnai maganar aure" murmushi Abbu yai itadai mami kallonsu kawai take tana sauraransu, "hmm Abdullahi kenan indai zancen wajen zamane bakada matsala matar kawai nakeson naji idan kanada ita, najima dasiyan gida a tudun wada kuma har angama gininsa cikin kwanan nan zamu tare part uku ne d'ayan daban yake dasauran wanda shine namu sai biyun kuma d'aya naka d'aya na Ammar ne, saikuma mata dama munjima dayin magana da Alhaji Zayyan mahaifin Salma akan zamu hadaku aure kuma Alhmdllh ita Salma d'in ta'amince harma sunfara shirye shirye acan gidansu shinema silar tafiyarta can gida saidai ni nadakartada nawa shirin har naji daga bakinka kuma Alhmdllh naji da'di tinda kace bakada wacca kakeso saboda haka kaje kasan yanda zaku sasanta kanku kai da ita kufahimci juna insha Allah nanda karshen wannan watan za'a d'aura aurenku mukuma jibi zamu tare a sabon gida acan nakeso muyi shagalin biki koba komai yafi wannan girma sosai za'afi sakewa sosai",,,,..

Dik abunda Abbu kefada sauraronsa kawai yake wani zufa ne ke ketomasa tako'ina najikinsa yayinda zuciyarsa kuma ketafaman yimasa zafi da rad'ad'i, jin yai shuru baice komaiba yasa Abbu yace "Abdullahi kayi shuru bakace komaiba" k'ak'aro murmushi yai sannan yace "to Abbu nagode sosai da zab'inda kaman ka cancanci kamana dik zab'inda kaga dama nasan tabbas bazaka tab'a yiman mummunan zab'iba Allah yasaka da Alkhairi nagode sosai" wani murmushin jin da'di Abbu yai sannan yace "Allah yamaka albarka Allah yasanyawa rayuwar aurenku albarka" baice komaiba yatashi yafita yana murmushi,,,,

Kai tsaye d'akinsu yawuce yanashiga yarufo k'ofar dak'arfi tareda buga k'afarsa ak'asa cikin tsananin b'acin rai yana magana shikad'ai "haba haba wannan wane irin san zuciya ne me zanyi da wannan k'azamar sha sha mara hankali da tarbiyya arasa wacca za'ahad'ani da'ita sai Salma wacca ko gaidani ma dakyar takeyi itace kuma za'ahad'ani da'ita kai ina sam bazai tab'a yuwaba wallahi dan sam Salma bata cikin tsarin kalan matanda nakeso bare kuma har nai tinanin aurenta" hakadai yaita maganarsa shikad'ai daga bisani yaga ba sarki sai Allah nan yashirya aranar yawuce gun aikinsa saboda sam bazai iya zama ananba,,,,..

Acikin kwanakin kuwa suka tare a sabon gida wow masha Allah yahad'u kuwa bakad'an ba, a part d'in mami 4bedrooms ne da falour biyu Central falour da falon bak'i sai kitchen da store, gidan kuma gate biyu ne nagaba dana baya na baya gefensu Ammar ne nagaban kuma gefen Abbu da yara, gidan yatsaru sosai kuma yahadu su fatima da RAIHAN sai murna ake andawo sabon gida,,,,..

Kimanin satinsu uku da dawowa sabon gida Aunty zinatu ta'iso da lefe yaranta biyu kyawawa mace da namiji ASLAM DA ISLAM ISLAM itace takwarar mami wato ( AMEENA ) sai ASLAM kuma sunan mahaifin mijinta ne wanda yarasu ( MUSA ), murna agun RAIHAN ba'amagana hakama Zinat d'in murna take sosai daganin 'yan uwanta,,,,, kimanin kwananta uku dazuwa akafara shagalin biki nan take gidan yafara cika da bak'i na nesa dana kusa saidai har yanzu angon bai dawoba, aranar Saturday ne za'ayi kamu ranar ne masu lalle sukazo sukayiwa su RAIHAN da Aunty zinat harda mami saidai ita ja akamata sukuma bak'i da ja aikwa zo kuga tauraruwar tamu abunka da farin mutum saiyamata tamkar ahaka yake ba zanashi akayiba, damisalin 4:15pm sukaje saloon sai 8:00pm sannan sukadawo ISLAM namanne ajikin RAIHAN y'an kwanakinda sukai har sunsaba da juna, angyarawa RAIHAN sumarta tai kyau sosai tak'ara bak'i da tsayi sai santsi take,,,,..


Cikin sauri suka shirya sannan suka wuce gunda za'ayi kamun acikin motar mijin Aunty zinatu, 8:30pm dot akafara gudanarda kamun....#/Vote

#/Share

#/Comment

'''AUFANA for life '''

    *I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

      *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*


   _*GANI GA WANE....*_🌷

_*STORY & WRITING ~BY*_

     _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) my granny's*_


   _*PAGE 31~32*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Anjima sosai ana gudanarda shagali taro yai taro komai yak'ayatar, 11:00pm akagama shagalin nan mutane suka watsewa yarage saura y'an gida kawai, RAIHAN ce da fatima tsaye agaban motar mijin Aunty zinat suna jiranta tafito suwuce gida Islam na'akan shoulder d'in RAIHAN tana wasa, sallama sukaji daga day'an gefensu nan Fatima tajuya domin ganin mai sallamar sannan tareda amsa sallamar, wani kyakkyawan saurayine d'an gayu sanye take da shaddah milk colour wando da riga mai dogon hanu kansa kuma sanye da hula milk, brown and white colour sai zuba k'amshi yake kaman anyi b'arin tirare ajikinsa,,,,,bayan sungaisa sannan yaceda fatima "dan Allah idan badamuwa inaso ataimaka man abani aron some mnts domin na'isarda sak'onda nake tafe dashi" yai maganarne cikin murmushi, nan itama tai murmushin saboda tini tagano inda zancensa yadosa sai tace "OK no problem zaka iya fad'ar abunda kake tafe dashi" tafad'a cikin yanga da yauk'i "ok nagode da wannan karamcin dikda ba'asan koni wayeba" wani murmushi tai mai d'aukeda ma'anoni kala kala sannan tace "karka damu wannan d'abi'atace karrama bak'o koda bansanshiba" two nagode sosai dafarko dai sunana TAJUDEEN ILYAS ni curse mate d'in Salma ne, y'ar uwa wallahi tinda kukashigo wajennan nahangoki naji kinman inasan nayi ratuwar aure dake wato kizameman abokiyar rayuwa at har abada kuma inafatar wani bai rigani maye wannan gurbinba. Yakarasa yana mai zubamata dikkanin idanunsa dakuma hankalinsa domin jin abunda zai fito daga bakinta,,,,,...+

Murmushi tai sannan tace "uhmm toh bazan baka wannan amsarba harsaika shigo daga ciki kaganewa kanka danhaka bismillah" dariya yai yace "toshikenan amma ataimaka man da contact dakuma suna saboda nasamu sauk'in yin dik wani abunda zanyi domin sanin hakan" ok badamuwa sunana FATIMA UMAR IBRAHIM. Bayan tafad'a masa sunanta sannan tabashi number nata tareda address d'inta sannan yamata sallama yawuce,, dik abunda suke RAIHAN najinsu amma tai banza dasu saboda tasan hauka kawai take dan bazata tab'a yarda yaje gidaba dan Ya Abdallah ko dukansa zaiyi wallahi tamanta yanda yamata kenan ranar dawani yabiyota gida, bayan angama komai zinat tadawo sannan suka shiga mota suka wuce gida,,,,...

Kimanin kwana uku akai anagudanarda shagalin kuma har yanzu Abdallah yak'i dawowa anyita bugamasa waya amma ba'asamu yakashe aikwa ran Abbu yab'aci sosai saida mami taita tausansa tana bashi hak'uri,, zaune take akan kujera agaban mirror d'aure da towel ajikinta Aunty Zinat na taje mata sumarta fitowarta kenan daga wanka, k'aramin towel ne iya cinyoyinta yarufe, sallama sukaji tareda bud'o k'ofar aka shigo wazasu gani Abdallah ne tsaye Zinatu tab'ata rai tafara masa magana "hmm wallahi d'anuwa kabani mamaki ashe koda auren dole akamaka tinda har iyayenka suka maka yakamata ka karb'eshi da hannu biyu kodon samun rahamar ubangiji dakuma gujewa fushinsu da b'acin ransu, yanzu dan Allah abunda kai ka kyauta kenan ace afara bikinka amma har gobe za'ad'aura aure amma bakai ba labarinka mutane sai tambayarka suke mukuma munamasu k'arya kasakamu sai sabawa ubangiji muke dan kawai mukare martaba da kimar gidanmu" shuru yai yaitsaye yana sauraronta saboda yasan halin auntyn tasa idan ranta yab'aci, ahankali yatako yak'araso yazauna sannan yakalleta yace "big aunt wallahi ke kanki kinsani sam yarinyarnan banasanta biyayyace kawai nai na'amince koda Abbu yafad'aman sunriga sungama magana bayanda zanyi danhaka dolefa kuyi hak'uri dani dan ba zab'ina za'a auramanba" kallonsa kawai tai tajuya tacigaba da abunda take,, shikuwa matsowa yai kusada RAIHAN yai murmushi yace "k'anwata ba gaisuwa" itama murmushin tai sannan tasaka hannayenta tarufe fuskarta tace "kayi hak'uri yayana sannu da zuwa barka da dawowa" hmm saida narok'a toh banaso. "aa yi hak'uri dama inada niyyar gaidaka" the naji yakike. Tace "lafiya k'alau" dik zancenda suke sam hankalinsa baya garesa yanaga sunarta da zinatu ke tajewa can kuma saiyad'an saci kallon surarta kyakkawa, ganin idan yacigaba da zama a d'akin akwai matsala yasa yatashi yafita abunsa itadai zinat binsa kawai take da ido,,,,,...

STORY CONTINUES BELOW

Hakama Abbu fad'a yamasa sosai kaman zai dakesa saida yaita bashi hak'uri sannan yakyaesa yashige d'akinsa, hakama mami tajamasa kunne sosai akan yarik'e matarsa yau biyayya insha Allah zaici ribar yin biyayyar haka yatashi jikinsa ba kwari yafita,,,, ranar Monday around 10:00am aka d'aura auren Abdallah d'a Salma akan sadaki naira dubu hamsin, bayan angama d'aura aure mahaifin Salma yashirya masu walima saikusan 2:00pm sannan aka watse Abdallah bawani abokinsa daya gayyato sai wani abokinsa wanda suke aiki atare Captain AHMAD MUSTAPHA shikad'ai ne shima ba gayyatarsa yaiba  kan hanyarsa yake tazuwa gida shine daya tadda daurin auren sai yatsaya har agama gobe yawuce,,,,..

Bayan angama sai suka dawo gida saboda sungaji sosai suna buk'atar su huta,,,, Zaune suke acikin lambu RAIHAN da Islam sai ASLAM dake rarrafe yanzu Zinatu ta tashi tabarshi tashiga cikin gida ta d'akko abu tadawo,, wani daddad'ar sautin busa taji mai kama da kanari mai zakin sauti, shuu tai tana sauraron busar da sautin ke kawomata wasu zafafan kwallah suka fara bin kuncenta kaman tana tino wani abu, tashi tai tadinga tafiya tanabin gunda takejin sautin nafito bata ankaraba saitaji tai karo da mutum tai suluu zata fad'i shikuma yakai hannunsa yai saurin rik'o k'ugunta yadawo da'ita dasauri tafad'o k'irjinsa,,,,,..

Saida sukai kusan 15mnts tana manne a k'irjinsa can kuma saikawai tai saurin janye jikinta daga nashi, shikuwa dik daburcewa yai saboda tsintar kansa acikin wani situation dayakejin kansa aciki dik lokacinda gangar jikinsa ta had'u da tata,, k'arfin hali yai yace "RAIHAN inazije haka kike nema kijiwa kanki ciwo" shuru tai kan tad'aga kafad'arta alamun nima bansaniba. Yalura da yanayinda take ciki dan haka yarik'a sandarta suka kama hanyar cikin gida,, sunzo dabda zasushiga cikin gida saiga zinatu tafito nan yamik'amata ita sannan shikuma yawuce abunsa,,,, around 10:00pm dot aka kawo amarya Salma agidanta saida akafara kawota gunsu mami sukaimata huduba mai ratsa zuciya sannan akawuce da'ita sashenta,,,,,..

Bayan sati d'aya da gama biki su RAIHAN suka koma School hakama su Salma da fatima aunty zinat ma mijinta yad'auketa sun wuce k'asar Italy kasancewar yanzu acan yake gudanarda business  d'insa,,, rayuwa tacigaba da tafiya yayinda RAIHAN ahankali memory nata ke dawowa dan yanzu harma tafara kiran wasu sunaye waenda idan aka tambaita nawaye saitace itama batasaniba,, ahalin yanzu kuma suna gabda fara jarabawan zango na biyu wato second term danhaka yanzu kusan kowanne lokaci indai ba islamiyya sukeba toh tana gida tana karatu saboda sam RAIHAN bata wasa da karatu tana bashi muhimmanci sosai,,,,,..

Zaune take acikin falour ita da Ammar yana koyamata wani abu saiga Abbu yashigo nan suka gaidashi sannan suka masa sannu da dawowa,, kallon Ammar yau yace "Ammar jeki ka kirawoman Abdallah inasan magana dashi yasameni aciki" toh. Yace sannan yatashi yawuce shikuma yashiga ciki, bayan yadawo sannan yazo suka cigaba da inda suka tsaya,, nifa inda RAIHAN ke birgeni ko acikin gidane zaka ganta da hijab tarufe jikinta dama sauran y'ammatan wannan zamanin zaku kwaikwayi halayyar RAIHAN wallahi dakunhuta da samarin banza da bawani shege ko d'an iskanda zai tinkareki da maganar banza saboda baiga fuskaba bare hanya Allah yak'ara tsaremu ameen,,,,..

Abdallah ne zaune a gaban Abbu bayan yazauna sannan yagaidashi cikin tsintsar ladabi, cikin murmushi Abbu yace "Abdullahi dama bakomai nake kirankaba sai nafad'a maka fa mutane sai zowa suke sunasan RAIHAN kwanan baya wani yazo jiya kuma saiga malaminsu na islamiyya Alk'asim yazo yana nema amashi izinin ganinta sannan ga Ammar shima santa yake aa abun yai yawa danhaka abata dama tazabi wanda takeso daga cikinsu dan ahuta kaga idan aka tsyarmata da d'aya dole sauran sujanye jikinsu" wani nannauyan ajiyan zuciya yasauke sannan yace "Abbu dik ka kasharesu kawai ni banasan tafara soyayya yanzu karatu nakeso tayi saboda haka dik ka kyalesu Ammar kuma zanjamasa kunne idan har bazai d'auketa amatsayin kanwarsaba to yafita sabgarta ya kyaleta dik wani dake gidannan matsayin 'yar uwa yadace yadauki RAIHAN danhaka ba wannan zancen nawai yanasanta" yana gama fad'ar haka yatashi yawuce abunsa fuskarsa tamke ba walwala ko kad'an,,,,..

Yana fitowa kuwa yasami Ammar a falour tareda ita nan yai cikinsa yadinga balbala masa masifa kaman yadakesa kuma yace karya kuskura yasakejin wannan zancen idan kuma yak'i to wallahi zai yanke dik wata alak'a dake tsakaninsa da'ita kuma saiya b'ata masa rai,, shidai kallonsa kawai yake har yagama masifarsa yawuce baice dashi k'ala ba dikda ransa yab'aci sosai amma yakwantane saboda shi yayansa ne gaba yake dashi,,, tindaga wannan ranar yajanye jikinshi gareta tin abun baya damunta har yafara damunta data tambayeshi KO laifi tamashi sai yace aa yanayin rayuwane kawai haka takura ta kyaleshi amma badan tanajin dad'i ba saboda idan fatima batanan shine abokinta shike tayata fira yana d'ebemata kewa saikwa idan taje d'akin mami,,,,...

Hakadai rayuwa tacigaba da gudana tana karatunta sosai, wata rana ne suna zaune su duka a falour harda Salma kasancewar yau bataje School ba su RAIHAN kuma yai weekend ne sunje islamiyyar safe sundawo, Abdallah ne yashigo fuskarsa d'auke da fara'ah yazauna sannan yakalli Abbu da mami yace "Abbu anhadani da likitanda zaiyiwa RAIHAN aiki kuma ance kwararre ne sosai insha Allah idan yamata ganinta zai dawo matuk'ar dai ba'ahaka aka haifetaba" wani irin dad'i sukaji dajin wannan maganar Abbu yai saurin cewa "kai Alhmdllh masha Allah naji da'di sosai wlh ubangiji yabada sa'ah kuma yasa adace yasa anyi a sa'ah" nan yace ameeen hakama mami tanuna jin da'dinta sosai, fatima kuwa rungume RAIHAN tai cikin murna "wayyo Allah da'di karka kasheni 'yar uwata zata warke ganinta zai dawo kamar kowa kamar yanda kowa ke gani" itama rungemantan tai tana dariyar farinciki,, salma kuwa d'an murmushin yak'e take azuciyarta kuwa cewa take "Allah ma yasa karsu gyaru wallahi Allah yasa ahaka tazo duniya wannan yar barikin shikuma sai wani nan nan yake da'ita yana wane biyemata k'anwata k'anwata kaman wata jaririya ko gold",,,, haka suka wuni aranar cikin farinciki da jin dad'i musamman fatima da'ita kanta RAIHAN d'in,,,,..

Zaune take a gefen gado tana sauraran karatun Qur'an daga bakin sheikh mahir almuakhir, binsa take da'alamu tanasan kira'ar tashi dakuma yanayin yanda yake karatun, sanye take da hijab blue colour yamata kyau sosai fatima ce a gefenta tana tsefa saiga Abdallah yashigo....
#/Vote

#/Share

#/Comment


'''AUFANA for life '''

   *I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

    *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*


    _*GANI GA WANE....*_🌷

_*STORY & WRITING ~BY*_

     _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) my granny's*_


   _*PAGE 33~34*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Fatima ce tagaidashi sannan itama tagaidashi, zama yai yana fuskantarta sannan yamik'a mata wani file yace ta karb'a, karb'a tai tabi file d'in tana shafa da hanunta sannan tace "ya Abdallah menene...?" murmushi yai sannan yace mata "takardune dazamu cike na shaidar mun amince ayimaki aikin idanu" itama murmushin tai wanda har saida fararan hak'oranta suka bayyana sannan tace "OK toh Allah yasa adace" yace "ameeen" nan yamatso kusa da'ita kaman zaimata rada a kunne yace "kawo hanunki kiyi signing" can ak'asan mok'ogoronshi yai maganar hakan yasa dakyar taji abunda yafad'a sannan tad'ago hanunta shikuma yasaka nashi yarik'a nata tareda ink yakai ga file d'in yai signing d'in,,,,..+

Bayan yai signing sannan yad'auki takardun yafita yabarta tai shuu tana tinanin wani abu, adik lokacinda Abdallah yahad'a gangar jikinsa da nata saitadinga jin wani shauk'i da feeling taita hard'e hannayenta kaman maijin sanyi tana murmushi sab'anin Ammar toko meyasa hakan oho,,,..

         ******  ****  ******  ******


Dik wani cike cike da za'ayi anrigada anyi kuma har Abdallah yabiya kud'in aikin dama komai da za'abukata inda Doctor d'in kawai sukejiran dawowarsa daga k'asashen waje kadancewar babban likitane da ake jidashi afadin k'asarnan harmada wajen ta,,, RAIHAN tacigaba da zuwa School sunfara exam harma sunkusa gamawa wannan nema yasa Abdallah yad'an dakatarda tafiyarsu SUDAN gyaran idanunta saboda yanaso sukammala exam sannan sutafi,,,,,...

Salma ansami ciki aikwa sai zuba iskanci take cikin yanabata wahala shiyasa Abdallah kedan tausayamata yana kula da'ita idan tace wannan yanzu anjima kuma wani zatace dikdai yana biyemata gakuma karatinta dataki hak'ura dashi gashi kuma yanayin karatun low akwai wahala sosai amma dikda haka ko lecture d'aya bata yarda tai missing haka take daurewa taje,,,,...

Maganar d'an samrayin Fatima kuwa ta kankama wato TAJUDEEN yazo gida yanemi izinin magana da'ita kuma anbashi cikin kwanaki kad'an har soyayyarsu tafara wanzuwa yayinda kuma k'aunar junansu keta wanzuwa acikin zukatansu, wata rana dayazo yakawomata tsaraban waya POP1 kiran techno red colour mai kyan gaske hmm aikwa murna da tsalle kam ba'amagana agunta dan ranar bacci tai tana mafarkin wayar,, hhh Lol,,,,..

RAIHAN sunkammala exam yau saura kwana biyar kacal suwuce SUDAN domin nemamata lafiya dan doctor d'inda suke jira yadawo,, ranar wata Saturday Abdallah yad'auketa  sukaje sukayo shopping dik wani abu dazata buk'ata yasaimata shi hadda pad kuwa ( always ), hakama fatima da za'ai tafiyar da'ita itama yasiyamata nata amma bakamar na RAIHAN ba,,,,,..

Abbu ne zaune da mami suna fira a falon bak'i saiga Abdallah yashigo yadurk'usa yagaidasu sannan yazauna, tinda yashigo Abbu yaga fuskarsa yasan akwai damuwa gareshi, kallansa Abbu yai cikin hikima irinta mai yawan shekaru yace masa "aa Abdullahi waya tab'aman kai dandai tinda naga fuskarka nasan akwai damuwa gareka menene meke faruwa....?" yamasa tambayar cikin murmushi,, ahankali yad'ago fuskarsa ba walwala yace "wallahi Abbu yarannan ne 'yan biyu kokad'an banso dawowarsu nanba dama kunbarsu acan wallahi dik iskancinda zasuyi bamuganiba can a hukuntasu amma nan kaga dole ranmu yab'aci yanzu duba kaga last month fa nakwace jirginsu na ruwa da'ake kawomasu kayan fasakwauri aciki again yanzu kuma gayanan sunsake ciko trailer's da miyagun kwayoyi to gwandama Hassan shi baya sha amma hussain fa yanasha kuma yana siyarwa yana hallaka yaran mutane yabasu kud'i kuma yabasu kwayoyin maye, gaskiya gaskiya ni Abbu nagaji wallahi kullum cikin yin k'arya nake na karesu daga shiga gidan yari ansakamasu mari yafi a k'irga amma kaman baayi a banza kosunce sundaina kwana biyu dasun dawo kuma sai sutada haba abun is too much wallahi nagaji" dik bayaninda yake Abbu da mami sunyi shuu suna saurarensa can dai Abbu yanisa sannan yace "Abdallah ba abunda zan iya cemaka sai kak'ara hak'uri wallahi nikaina abun ya'isheni badai yanda naiya ne tinda jininmune dole muyi hak'uri tinda kaga shi kanshi mahaifin nasu basu barshiba shekaranjiya ma a asibiti yakwana hawan jininshi yatashi kuma dik akansune su d'ibo kud'inshi batareda yasaniba suje suita shashancinsu suna banzatawa ga 'yammata dakuma siyen kayan fasakwauri, abun haushin kuma shine koda sunsiyo a banzace suke siyarwa mutane,, Abdullahi ba abunda zance maka illa ka k'ara hak'uri kacigaba dayi dikda nasan kanayi wallahi Allah yashiryardasu yamaidasu hanya madaidaiciya" nan suka amsa da ameen daga nan kuma suka kauda zancen da maganar tafiya SUDAN neman lafiyar RAIHAN saida aka kira sallar azahar sannan suka wuce masallaci mami kuma tashige ciki,,,,...

Yau takasance Monday saura kwana biyu kacal tafiyarsu SUDAN, RAIHAN da fatima ne a d'aki suna shirya kayansu, zama tai akan gado tareda yin ajiyan zuciya tace "wash wallahi nagaji kishima nakeji" dariya fatima tai tace "raguwa kawai taci kije kisha ruwan toh karkiman kuka" itama dariyan tai sannan tace "kai k'awata kullum dai baby kike k'ara maidani kawai dan inajin kishi sainai kuka aini ba Aunty Salma bace mai kuka dan ba'asiyomata agwaluma ba" tana fad'a suka kyalkyale da dariya sannan tafita domin tashawo ruwan tadawo,,,,,...

Tana fita kuwa tanacikin tafiya saitaji k'afarta ta take wani abu mai laushi kuma mai sanyi kan ta ankara kawai taji sentsi yajata yatafi da'ita tai suluu sai k'asa kaji abun diipp tafad'i k'asa wanwar, wasu taurari tafara gani namata yawo a idanu can kuma shikenan bata sake sanin inda takeba,, ashe b'awan aiba ne  aka yada akan tiles bata saniba ta taka yaja santsi shine yakaita k'asa,,,,..

Jinta shuru har kusan 30mnts bata dawoba yasa Fatima tafito domin dubata kawai saita ganta a k'asa kwance kaman gawa,, sauri tai taje gareta tareda bubbugata wai ta tashi tareda kiran sunanta....


*Kuyi manage da wannan kuma kuyi hak'uri da tyaiping error ba editing*#/Vote

#/Share

#/Comment


'''AUFANA for life '''

    *I.W.A*🖊® *INTELLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

    *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

    _*GANI GA WANE....*_🌷

_*STORY & WRITING ~BY*_

    _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) my granny's*_

  _*PAGE 35~36*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Bubbugata take cikin tsananin tashin hankali amma ina RAIHAN ko motsi batayi, ganin haka yasa ta tashi dagudu tawuce d'akin Mami ahargitse tafad'a ciki muryanta na sarkewa take tafad'awa mami abunda ke faruwa, cikin sauri mami tariko hannunta suka fito atare,, koda suka iso saisukaga Abdallah da Abbu akanta Abdallah na bubbugata yana murza hannayenta da k'afafunta waiko jinintane ya dazk'are amma ina shuru ko alamun motsi batayi,, hankalin Abbu yatashi matuk'a hakama mami ita fatima kuwa kuka take sosai,,,,..

Ganindai har yanzu bawani alamun tashinta yasa Abdallah yad'auketa zuwa asibiti Abbu da fatima sukabi bayansa akabar mami da salma saboda itama salma d'in batada lafiya,,, suna isa kuwa cikin gaggawa aka karb'eta aka wuce daita ICU room, oxygen suka sakamata domin ya taimakamasu wajen janyo numfashinta sannan sukamata wasu injections,,,".+

Harkusan 12:00pm numfashinta bai dawoba kusan likita uku akanta kowanne na nashi k'ok'ari dansusamu numfashinta yadawo,, dakyar dakyar da bone akasamu jiyojinta sukafara aiki daganan suka sake yimata wasu injection waenda zasucigaba da taimakamata ta janyo numfashinta,, sannu ahankali numfashinta yadawo gareta aikwa doctor's dinnan saida sukai wani nannauyan ajiyan zuciya tareda godiya ga ubangiji nan suka d'ora mata drip sannan sukamata injection na bacci don tana buk'atar hutu,,,,".

Bayan komai ya dai daita sannan suka fito suka fad'awa su Abdallah cewa numfashinta yadawo hmm aikwa farinciki agun Abdallah baya misaltuwa dan saida yai murmushi har fararan hak'oransa suka bayyana nan akamasu izini dasushiga suganta amma banda hayaniya saboda tanabukatar hutu,, haka kuwa akayi bayan sunganta Abbu da Abdallah sukawuce masallaci saboda lokacin sallah yayi sukabar fatima agunta,,,,,..

Around 3:00pm na a zaune tana karanta wani littafi a wayanta *MUHIBBAT* na marubuciyar zamani wati *SAINAH UMMUN MEENAL* saitaga RAIHAN tafarka tana motsi sannan tasaka hannunta tacire oxygen d'inda aka sakamata, tayunk'ura zata tashi sai fatima tai saurin rik'eta ta maidata kwance,, ahankali tafara bud'e idanunta tana fad'in "ya Amadi... Ya Amadi... Hindu ina kike ne" tana fad'ar haka harta bud'e idanunta tawaresu tana kallon sama,, fatima ce tace "k'awata RAIHAN sannu ya jikinki...?" ahankali tajuyo fuskarta inda taji anyi maganar RAIHAN tamaimaita sunan sannan tace "Hindu inane nan d'in nake" shuru fatima tai takasa cewa komai dan abun yabata tsoro wacece hindu kuma wanene Amadi,, d'aukan wayarta tai zata fita kenan saigasu Abbu sunshigo Abdallah yace "ina zaki kuma keda ke jinya" shuru fatima tai sannan tace "ya Abdallah RAIHAN tafarka amma wasu sunayi naji tana fad'a nikam na tsorata wallahi shine nafito nakiraku kuji" wasu sunaye kuma. Fatima tace "Eh" to mushiga ciki mana. Cewar Abbu, nan suka wuce ciki,,,".

Suna shiga kuwa suka tadda ita a zaune tana kuka wanwar hawaye sai zuba suke kaman anbude famfo jin motsi alamun shigowar mutane yasa tai saurin cewa "ya Amadi na Ya Amadi kaine ina hindu ina mami na" dikkanninsu shuru sukai suka kasa magana dakyar Abbu yak'arasa kusa da'ita yazauna tareda rik'o hanunta sannan yace "'yata basu bane" to suwaye ku dan Allah karku illatani kukaini gidanmu gun mami na da ya Amadi na dan Allah. tai maganar cikin muryar kuka, aran Abbu cewa yake "Alhmdllh wahala tazo k'arshe" a fili kuma cewa yai "kwantarda hankalinki fadaman inane gidanku kuma ya sunanki zan kaiki har gun mamin naki kinji" share hawayenta tai da hannunta sanna tace "ni sunana KHADIJA amma kowa nagidanmu dana kauyenmu yana kirana da KUBRAH sunan kauyenmu ZAGA" jin ta ambaci sunan ZAGA yasa Abbu yin mamaki sannan kuma yai wani murmushi yajuyo ya kalli Abdallah daya dazk'are a tsaye,, "shikenan 'yata KUBRAH ki kwantarda hankalinki zan maidake gida kinji amma kibari harki warke" ni lafiyata k'alau wallahi dan Allah ka maidani gida. Taimaganar cikin magiya, hmm...!!! Abbu yanisa sannan yace "to shikenan naji",,,,..

Abdallah kam fita yai yakasa cewa komai fatima kuma ta zauna gefe d'aya, bayan yafita sannan yasake dawowa tareda doctor, y'an gwaje gwaje yamata ya tabbatar ba matsala sanna yafita, bayan yafita ne Abbu yazuba mata abinci yazuna dakansa yana bata tanaci yanakuma yimata 'yan tambayoyi wasu tabashi amsa wasu kuma tai shuru alamun tamanta ko bata saniba shikuwa dayaji tai shuru sai yakyaleta ko ya kauda wannan zancen dawani daban saboda yafahimci bakomai nata yadawoba,, taci abincin sosai bayan tagama fatima ta rakata toilet tayo alwala sannan suka fito taranka sallolinda ake binta,,,,"..

        ******  ******


Kimanin kwanansu biyu a asibiti sannan aka sallameta acikin kwanakin kuwa har tasaba da fatima takuma san abubuwa da dama acikin rayuwarta datai ta baya kaman sunanta RAIHAN yayanninta guda uku Abdallah da Ammar dakuma Aunty zinatu musamman ma Abdallah irin yanda suka shaku komai zatai ya Abdallah dai dakuma irin taimakonda zinat ta bata alokacinda take tsananin taimakon wanda zai maye mata gurbin uwa dakuma 'yar uwa hakama Ammar yanda yake sakata farinciki da nishad'i alokacinda take cikin damuwa, to bare kuma uwa da ubanta wato Abbu da mami, adik lokacinda fatima ke bata labarin rayuwarsu ta baya takanji dama ace tinaninta bai dawoba musamman idan tana bata labarin rigimarta da Abdallah idan tanason abu yak'i siyamata dakuma irin shakuwarsu wacca takai har Salma take kishinta,,,,...

Bayan kwana biyu da dawowarsu tamatsa sai anmaidata garinsu tin tanayi ba'akulata har akafara kulata saboda ganin yanda tad'aga hankalinta dan harda kuka ma takeyi hawaye kaman anbude famfo, ganin haka yasa Abbu yakira  Abdallah yace sushirya yanaso sumaidata hannun iyayenta sannan sumasu dikkanin bayanin komai abunda yafaru Abdallah kuwa cewa yai bayanzu zai maidata ba yanaso yacika alk'awarin da yad'auka sannan yamaidata, ganin zancensa abun dubawa ne yasa Abbu yakyalesa bai takurasa ba,,,,"..

       *****  ****  ****


Bayan kwana uku da dawowarta daga asibiti suka wuce k'asar SUDAN KUBRAH hadda kukanta ita bazatajeba yamaidata garinsu dakyar mami da Abbu suka lallabata sannan akai tafiyar wannan karon kam hadda Salma cikin tafiyar zinat kuma takira tace itama sunanan SUDAN d'in idan sunzo sumata waya sai tazo tad'aukesu,,,,.

Haka kuwa akayi 1:00pm dot jirginsu yasauka k'asar jajayen fata wato SUDAN suna saukowa sukaga zinat da mijinta har sun iso suna jiransu nan suka kwashi kayansu aka saka mota sannan suka wuce,,,,..

Wani katafaren gidane yagina anan kawai saboda idan sunzo suzauna basai sunkama hotel ba,, d'aki d'aya aka bama Abdallah da Salma fatima kuma da KUBRAH, tinda sukazo Islam tamak'alewa KUBRAH alamun tashaidata haka itama tad'auketa tana wasa ajikinta, zinatu sam batasan tinanin KUBRAH yadawo ba dan da sunan RAIHAN takirata itakuma saita karb'a saida fatima tamata bayani aikwa nan sukaita dariya sannan Zinat taita jin da'di tana murna da tinanin KUBRAH yadawo yanzu zasusan ko ita wacece,,,,"..

K'asaitaccen lonch Zinatu tahad'a masu sukaci sukasha sukai hani'am sannan akawuce masallaci mata kuma suka wuce cikin gida,,,,..

Kwanansu daya da zuwa akafara shirye shiryen wucewa asibitin da za'ayimata aikin,, ranar Thursday bayan sundawo daga wajen photo wanda akayi mata na idanun suna zaune acikin falour sai Abdallah yakira likitanda zaimata aikin, bayan sungama magana sai taji yace "ok thanks doctor FARUK M GARSO nagode sosai" dikda hankalinta bayagun maganarda yake amma lokacinda taji sunanda yafad'a nantake tamayarda dikkanin tinaninta da hankalinta agareshi,,,,".

Doctor Faruk m Garso tasake mai maita sunan...
#/Vote

#/Share

#/Comment


'''AUFANA for life '''

  *I.W.A*🖊® *INTELLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

    *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*


   _*GANI GA WANE....*_🌷

_*STORY & WRITING ~ BY*_

     _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) my granny's*_

   _*PAGE 37~38*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Doctor Faruk m Garso tasake maimaita sunan batareda tace komaiba, tanajin zancenda suke har suka gama yakashe wayar yajuyo yakalleta yace "gobe  insha Allah zamu wuce hospital d'in doctorn ya'iso jiya dan haka gobe zamu tare acan saboda akwai abubuwanda dole sai kina acan za'ayi" to kawai tacemasa sukacigaba da firarsu,, har kusan 11:00pm basu kwanta sunata fira Salma ce tafara hamma tamik'e tacemasu saida safe Fatima ma ta tashi tace bacci takeji, ganin haka yasa dole suka tashi har k'ofa zinat taraka KUBRAH saida tashige ciki sannan tajuyo tawuce gun mijinta,,,..

Washe gari bayan sunyi sallah suka shiga kitchen sukahada breakfast atare amma banda salma wai batasan k'amshin kitchen hhh Lol shikwa wannan cikin danashi salo yazo,,, bayan sungama sannan suka d'akko suka fito dashi kowa yafito suka baje akaci sai zuba santi ake,, bayan sungama ne sukashiga shirin wacewa asibiti, 10:00am dot suka isa asibitin,,,,"..+

Bayan sun isa ne likitin yabukaci ganinta nan fatima tarik'a hanunta tana gefe d'aya Abdallah kuma yana gefenta d'aya ma'ana sun saka KUBRAH a tsakiya hmm nan taku taharde gabas da yamma ta tsuke baki tasha kunu ji take kaman takashe KUBRAH dan haushinta datakeji,,,.

Sallama suka sannan Abdallah yai norking d'in k'ofar daga ciki akamasu umarnin su shigo nan yabud'e k'ofar suka shiga, yana isa cikin sauri yamik'a masa hanunsa cikin murmushi yace "Nice to meet u Doctor Faruk Muhammad Garso young Doctor" Nice to meet u too my frien.....bai k'arasaba tai saurin fad'in "Faruk m Garso" idanunta suka fara zubda kwallah doctor d'in yace "yes" Abdallah yai saurin cewa "ke lafiyarki kuwa wannan wane irin shashancine kokinsanshine" shuru tai batace komaiba amma kuma idanunta basu daina zubda kwallah ba,,,,..

Can saikuma tace "bansan wannan ba saboda bansan kamanninsaba amma dai nasan wani mai irin sunansa kuma shi nasan kamanninsa" mtssssss.... Abdallah yai wani mugun tsaki yace "dallah malama kizauna ga kujera nan a bayanki karki b'atamana lokaci" likitan kuma cewa yai "haba d'an uwa kabari tafad'a muji wata kilma nasan wanda takenufi d'in" sai yajuyo gareta cikin murshi yace "k'anwata fad'i kamanninsa naji k'ilama nasanshi dan akwai wani wanda mukai karatu mai irin sunana" hmm...!!! tanisa sannan tafara magana "shima sunanshi FARUK kuma sunan Abban shi muhm'd inkiyarsa kuma Garso bafulatanine d'an k'auyen ZAGA kuma shi k'ane ne agun mami na,, shi fari ne mai d'an tsayi yanada cikar suma yatsunsa dogaye ne hancinsa mai tsayi ne a gefen idonsa d'aya na hagu kusa da sumarsa ta kai akwai wata tsaguwa wacca yai alokacin yana k'arami" tana kawowa nan tatsaya tai shuru,, Abdallah ne yajuyo ga kallonsa gun likitan saiyaga kwallah nazuba daga idanunsa shimadin kallonsa yai yana d'aga masa kai kuma yana juyasa yace "tabbas nine FARUK d'inda kike nufi nine nine wallahi" kaine kawuna dagaske kaine dama kawuna shine likitanda akace zaimun aiki a idanuna ganina yadawo.. "nine y'ata"

Nan takwance hanunta daga na fatima tafara tafiya tana laluben inda yake shima takowa yai yarik'o hanunta yace "ganinan 'yata" dika hannayenta tasaka tana shafa fuskarsa da jikinsa tana juya dara daran idanuwanta kwallah nazuba daga idanunta, janyota yai ajikinsa yarungume yanafadin "kidaina kuka yarinyata",,,.

Tsawon 5mnts suka d'auka ahaka yana rarrashinta saida Abdallah yasaka bakinsa sannanfa tadaina kukan suka zauna,, wasu takardu yad'akko yaciccike sannan yakira wayar telephone tanan asibitin saiga wata norse tashigo tana shigowa yamik'a mata takardun tafita, juyowa yai yakalleta yace "'yata yasunanki" tai murmushi tace "khadija" sai fatima tace "kokuma KUBRAH" sukai dariya, wasu abubuwa naga yad'akko yazo yad'aga kanta sannan yabud'e idanun yasaka fitila yana kallon cikin idanun,, saida yakusa 30mnts yanamata wasu gwaje gwaje sannan yajasu suka fita,, wani d'akin yawuce da'ita gun wasu manyan likitocin suka d'orata akan wani gado sannan suka kunna wasu na'urori suna duba idanun nata, har kusan 30mnts sannan suka sauketa daga kan gadon bayan sungama bincike bincikensu,,,,..

Bayan sungama sannan yarik'o hanunta suna tafiya suna fira har suka fito suka wuce gunda aka kwantar da'ita kan lokacin aikin yayi,,,,..

Bayan sun isa ne yake tambayanta 'yar uwarsa wato mahaifiyarta asma'u dakuma sauri mutanen gida sannan yatambayeta waennan dasuke atare suwaye su,,dariya tai sannan tabashi labarin iya abunda tasani mahaifiyarta kuma yau kimanin shekara 8-9 kenan rabonta da'ita dakuma k'auyensu gaba d'aya,, yatausayamasu sosai irin rayuwarda sukai a gidan mahaifinta sannan yai Allah wadai da hali irin nasa dadikma wani mai hali irinnasa sannan yaji da'di sosai da irin rik'onda Abdallah da iyayensa suka mata,, haka suka wuni sunashan fira dan ranar gabad'aya yace tatace,,,,..

        *****  ****  *****


Kwananta d'aya a asibitin dik wani abu daya dace ayi anyi gwaje gwaje kowanne anyi kuma sun tabbatarda za'ayi aikin kuma insha Allah zatawarke ganinta zai dawo saboda glass d'in idanunta lafiya k'alau yake aikwa murna da farinciki agunta baya misaltuwa,,,.

Gobe itace ranarda za'ashiga theater da'ita 10:00am dot insha Allah, adaren ranar kasa bacci FARUK yai nan yai alwala yawuce masallaci yafara nafiloli yana rok'on ubangiji nasara a aikin, hakama Abdallah sallar yake yana rok'on Allah itama gogar nafilar take tana istigfari tana rok'on ubangiji yasa ayi a nasara,,,"..

Dasafe bayan tai sallah Aunty zinat tazubamata abinci taci kasancewar dik sunzo, tanacikin ci saiga norses sunshigo, kayan sakawa suka kawo mata waenda ake sakawa idan za'aimaka theater, zinatu ce takarb'a tace saita gama cin abinci sannan tasaka haka kuwa akayi bayan tagama ci tasaka,, batafi 5mnts dasakawa ba akazo wucewa da'ita nan suduka sukafita yimata rakiya, har k'ofar shiga theater room d'in suka rakata saida suka shiga aka rufe sannan sukadawo suka zauna suna jira,,,,"..

Basufi 5mnts da zamaba saiga doctor FARUK zaishiga d'akin nan yatsaya suka gaisa sukamasa fatan samun nasara yai godiya sannan yashige,,, Yana shiga kuwa akamata injection nasaka bacci sannan suka kwantar da'ita ahanakali ahankali bacci yad'auketa sannan suka fara aikin,, kusan 2hrs suka d'auka suna aikin cikin ikon Allah suka kammala komai sannan aka dakkota  akawuce d'akin hutu da'ita idanunta narufe da bandegii....
#/Vote

#/Share

#/Comment


'''AUFANA for life '''

    *I.W.A*🖊® *INTELLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

     *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

     _*GANI GA WANE....*_🌷

_*STORY & WRITING ~BY*_

     _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) My granny's*_

   _*PAGE 39~40*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Bayan ankaita d'akin hutu sannan doctor faruk yafito yafad'a masu cewar tana d'akin hutu nan suka rankaya suduka suka wuce izuwa d'akin,, kimanin 30mnts takwashe bata farkaba saikusan 1:00pm sannan tafarka saidai har yanzu injection d'in bata sakeba, ahankali ahankali tafara sakinta dan har tafara magana da mutane hakan kuwa bak'aramin dad'i yayiwa doctor faruk ba yanzu abu d'aya suke jira shine lokaci yayi abude idanun agani idan ancinasara,,,,,"..+

Bayan tafarka Aunty zinat ta taimaka mata tashiga da'ita toilet tai tsarki tai alwala sannan suk fito,, sallah tafara yi bayan tagama sannan taci abinci amma mai ruwa ruwa saboda likitocin sun hanata cin mai k'arfi kaman tuwo,, bayan tagamaci sannan takwanta, haka zinat tadinga hidima da'ita dik abunda tace tanaso angama Abdallah kuwa d'an kallo yazama danko sako zancensa batayi idan yashigo tagaidashi shikenan, ankira su Abbu yafadamasu cewar anyi aikin angama yanzu jira suke ranarda za'abude idanun agani idan aikin yayi,,,,,..

Kimanin sati d'aya da kwana uku kenan dayin aikin yau kuma takasance monday kuma itace ranarda za'abude idanun KUBRAH,, 10:00am kowa yahallara a asibitin hadda Usman mijin Zinatu da yaransu Islam da Aslam,, a zazzaune suke suna fira itakuma tana a gefe d'aya zaune kan gado kusa da Zinatu kanta na'akan cikinta, Faruk ne yashigo tareda wasu manyan likitoci y'an uwansa guda uku sai norse's guda biyu waenda ke d'auke da faranti masu kaya akansu,,,,"..

Cikin dariya yashigo suka gaisa sannan suka gaida sauran doctor's d'in tareda masu barka da zuwa,, KUBRAH tanajin alamun Faruk ne yashigo sai taisaurin tashi a zaune tana murmushi tace "Auncle Faruk barka da safiya" cikin murmushi yace "barka dai 'yata ya jikin...?" tace "Alhmdllh" good yace tareda shafa fuskarta sannan yace "insha Allah yanzu zamu kwance wannan bandage d'in domin ganin wace nasara muka samu a wannan aikin" dikda kowa na zumud'in hakan amma daya fad'i wannan maganar diksai sukaji wani iri kaman wani abu zai faru,,,, Abdallah ne yai k'arfin halin cewa "ok toh bismillah Allah yasa muga alkhairi" nan suduka suka amsa da ameeen jiki a sanyaye,,,,"..

Almakashindake akan farantin d'aya daga cikin norse's d'in yad'auka yanatso kusa da'ita sannan yasakashi ya yanka bandage d'in, bayan ya yanka sannan yamaidashi ya ajiye,, basmalah yai da ta'awwizi taredayin wasu addu'oi sannan ahankali yafara warware bandage d'in,, dik wani wandake acikin d'akin yatattaro hankalinsa yamaida akan KUBRAH domin ganin mezata haifar,,,,..

Ahankali yacigaba da warware bandage d'in har yakai k'arshensa dazai cire na k'arshen saiya ritse idanunsa sanna yasakeyin wata basmala d'in sannan yabud'e idanunsa yacire gaba d'aya, shuu tai idanun na'arufe cikin sassanyar murya yace "bud'e idanunki" ahankali tabud'e su tafara waresu tana kallon cikin d'akin, dafarko wani duhu tafara gani ahankali saikuma duhun yagushe taga haske,, kallon d'akin take batareda tace komaiba kawai saisukaga kwallah nakwaranya daga idanunta wannan yabasu tabbacin abunda suke tsammani, zinatu da fatima kasa hak'uri sukai bakinsu yahad'u wajen fad'in "KUBRAH kina ganinmu...?" wani murmushi tai tareda zubar kwallah sannan tad'aga masu kai alamar Eh aikwa basusan lokacinda suka rungumetaba Abdallah kuwa wani nannauyan ajiyan zuciya yasauke tareda fad'in Alhmdllh acikin zuciyarsa sannan yadurk'usa yai sujudul shukru Faruk kuwa wani irin murmushi yai tareda yin hamdala ga ubangiji,, Zinat da fatima kukan farinciki suke, kallonsu tai tace "ashe akwai ranarda zatazo indinga ganin kowa da komai kamar kowa ashe haka duniya take ashe haka kalolin mutane suke wani fari wani bak'i ashe ko bangon gini anamasa kala ashe akwai ranarda zatazo inaganin komai da komai tabbas Allah shine mabuwayi kuma abun godiya" jiyowa tai kwallah nazuba daga idanunta takallesu tace "yau nima ina ganin komai saitadaga kanta sama da hannayenta tace "Alhmdllh bini'imatika ya rabbi" tasake juyowa takallesu cikin murmushi tace  "wacece Aunty Zinat d'ina acikinku" itama murmushi tai kwallah nabin fuskarta tace "nice KUBRAH" tai murmushi tarungumeta sannan tajuyo ga fatima tace "fatima na k'awata" itama dariya tai tana kada mata kai suka rungume juna,,,,"..

D'agota tai tanuna Abdallah da yatsa tace "ga yayanki can Abdallah" murmushi tai ta tashi ta'isa gunsa tatsuguna agabansa tace "nagode sosai ya Abdallah da taimakon rayuwata dakai tabbas bazan tab'a mantawa dakaiba arayuwata kanacikin tarihin rayuwata kabani gudumawa wacca wani mutum yakasa bani a rayuwata tabbas bazan taba mantawa dakaiba nagode nagode nagode sosai Allah yasaka maka da mafificin alkhairi" cikin sauri yakai hannayensa yad'agota cikin murmushi yace "kidainaman godiya k'anwata bani yadace kiyiwa godiya ba Allah ne" tai murmushi sannan tace masa "ina Kawuna yake" yanuna matashi da yatsa yace "gayacan" cikin murmushi taje tarungumesa sannan tad'ago tadurkusa tashafa fuskar Islam da Aslma tareda sumbatarsu a goshi,,,,"..

Bayan komai yanutsu sai likitocin suka sake dubata ko akwai wata matsalar cikin ikon Allah kuwa saisukaga bawata matsala nan suka kafamata dokoki da sharuda domin cigaba da kula da lafiyarta,, aranar aka sallameta suka wuce izuwa gidan Zinat kowa zuciyarsa na cike da farinciki musamman ma Abdallah wanda yake gani yasauke wani babban nauyi daya rataya a wuyansa,,,,..

Kwanansu d'aya Faruk yazo yad'aukesu yakaisu gidansa gun iyalinsa matarsa Saudat da d'ansa Muhsin, tin aganin katafaren gidan Faruk Salma tafara raina kanta saboda shi kanshi ginin zaka rantse da Allah ba mutum bane yayishi saboda had'uwarsa dan tinda uwarta ta haifeta bata tab'a ganin gida wanda ya amshi sunanshi gidaba kaman wannan tsabar tamanin kud'inda aka zube wajen narkashi sunfi k'arfin kwakwalwa ko k'aramar calculater su k'irgasu,, ranar acan suka wuni sai dare sannan sukadawo gida, Saudat kuwa tabama KUBRAH kayan make-up masu tsadar gaske da tiraruka masu da'din gaske da tsada had'e da sarkoki da awarwaraye masu tsada da kyau ,,,kwana uku kacal suka k'ara suka tattaro suka dawo harda su zinat da yaranta amma banda mijinta saboda kasuwancinsa bazai barshi yazoba,,,".

Ammar da Abbu ne sukazo daukansu a airport tin daga kan matattakalar jirgin tafara gudu harta sakko tana gudun tana dariya had'e da kwallan farinciki tana isowa tarungume Abbu tana dariya shima d'in dariyan yake zuciyarsa cike da farinciki, hakama Ammar dake a gefensu murmushi yake shima ji yake kamar tarungumeshi shima, kai ammar Lol,"..#/Vote

#/Share

#/Comment


'''AUFANA for life '''

   *I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

     *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

    _*GANI GA WANE.....*_🌷

_*STORY & WRITING ~BY*_

    _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) My granny's*_

  _*PAGE 41~42*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Kwallah take tana fad'in "Abbu na yanzu ni ba makauniya bace nima ina ganin komai Abbu ashe haka marasa gani keji ashe haka gani yake da dad'i ashe haka duniya take tabbas dik wanda Allah yayiwa baiwar ji da gani yagode masa idan kuwa bai gode ba to tabbas yacika cikakken butulu" tabbas hakane 'yata ina tayaki farinciki. Juyowa tai gun Ammar tai murmushi tace "ya Ammar koh" ya d'aga mata kai alamar eh tasakeyin murmushi su Abdallah ne suka k'araso suka gaida Abbu yamasu barka da dawowa sannan suka shiga mota suka wuce,,,,,"..+

Suna isowa gate man yazo yabud'e masu gate Ammar yadanno motar cikin gidan wajen ajiyeta sannan suka fito, suna fitowa kuwa saiga mami tafito tareda autanta tana fad'in "lale marhaba da y'ata oyoyo oyoyo RAIHAN tawa" cikin sauri KUBRAH taje tarungume mami tana dariya mami ma tarungumeta tareda sumbatarta a goshi sannan tad'ago fuskarta tana murmushi tace "RAIHAN ina tayaki murnar dawowar ganinki 'yata yau kema kinfita daga jerin makafi kindawo sahun masu gani ubangiji yasa kinemi aljannarki dashi" tace "ameen mami na" juyowa tai tayiwasu Abdallah sannu da dawowa sannan suka wuce cikin gidan,,,,..

Bayan sun shiga kowa yawuce d'akinsa sukai wanka suka canja kaya izuwa nashan iska sannan suka fito falour,, wasu riga da wando ne KUBRAH tasaka Indian design rigar red ce wandon kuma black color sai mayafinsu shima black, kayan sunmata kyau sosai kuma sunkarbeta dikda bawata kwalliya taiba amma hakan baihana kyanta ya bayyana a filiba,, koda duka fito kuwa suka tarar mami tahad'amasu had'adden girki namusamman aikwa nan suka baje suka faraci Abdallah sai santi yake yana fad'in "kai mami na shiyasa kullum nake k'ara k'aunarki mami na dik irin girkinda naci sainaji da bambamci naji dik ba dad'i saboda kin shagwab'ani da girkinki mai d'an karen da'di" kallonsa tai da witsiyar ido tace "kai gaskiya girkinnan na mami yanada sihiri wato hadda salma idan tamaka girki cinshi kawai kake" cewar Aunty zinat nan suka kwashe da dariya aikwa nan Salma tahad'e rai tasha kunu shikwa yai shuu yana hararan KUBRAH dake kyalkyala dariya tanamasa gwalo tana fad'in "Allah yanzu mami bataka bace tamuce ni da Junior da fatima" hannunsa yakai yamata rankwashi tashagwab'e fuska zatai kuka mami tace "toh babban banza karka k'ara dakarman yara kaje matarka tamaka girkin mana" aikwa KUBRAH taji dad'i tak'ara masa gwalo,,,,"..

Haka suka kammala cin abincin suna raha da barkwanci abun gwanin birgewa,bayan sungama ne suka koma falour suna fira, suna acikin firarne wayar Abdallah tai k'ara yasaka hanu yaciro sannan yafita, kusan 5mnts da fitarsa yadawo fuskarsa d'auke da fara'ah yak'araso kusa da Abbu yakallaesa yace "Abbu Captain Ahmad ne yakirani yanzu yace agaidakai yana kan hanya anan zai kwana gobe sai yawuce" Ah kai haba Allah sarki Ahmad yaron kirki toh Allah yakawosu lafiya. yace Ameen, Abbu yasake cewa "to kai yaushe zaka wuce ne yakamata kaima ka koma gaskiya kada kajawa kanka matsala agun aiki" murmushi yai yace "karka damu Abbu bawata matsala insha Allah inaso agama case d'in yarannan ne su Hassan kaga lokacin dik mundawo daga k'auyensu KUBRAH namaidata hannun iyayenta hankalina yakwanta sai inwuce" hakane kuma toh Allah yataimaka. yace ameen,,,, dik zancenda suke KUBRAH najinsu wani irin dad'i taji dataji ance zaamaidata k'auyensu,,,,"..


Around 5:15pm yashirya yaje d'akko abokinsa Captain Ahmad yana isa kuwa yai dai dai da isowarsu kenan nan suka rungume juna cikin farinciki sannan yad'akko kayansa yasaka a mota suka shiga suka kama hanyar gida,, bayan sun iso ne yashiga toilet domin yayi wanka shikuma Abdallah yafita domin kawomasa abinci, koda yafito daga wanka saiyaga ba Abdallah bai damuba nan yashirya yacanja kaya sannan yai safara sallah, yana cikin sallah Abdallah yashigo ya'ajiye masa abincin yazauna yana jiran gamawarsa,,,,"..

Bayan yagama ne sannan yaci abincin yanaci suna fira har yagama, bayan yagama sannan suka fita atare yaje yagaida su Abbu sannan suka fita domin su zaga gari,,,..

      ******


Kwance take akan gado kanta na'akan cinyar fatima suna fira zinat na'agefen kan gado salma kuma na'akan tiles tanacin d'an malele da mai da yaji,, suna cikin firarne take fad'amasu Abbu yace jibi zasuje k'auyensu nan suka tayata murna tanatajin dad'i tana dariya, kiran sallar magrib ne yatadasu suka wuce zuwa sallah,,,,"..

Saikusan 6:15pm sannan suka dawo bayan sundawo suna zaune suna fira kawai saiya tashi yabud'e jakarsa yafito da wani abu mai kama da sarewa wacca ake busawa, Abdallah yakallesa yace "kaidai Captain kanasan wannan abun na 'yan yara" murmushi yai yace "yana d'ebeman kewar wani abu nawa danarasa shekaru masu yawa da suka shud'e kuma adik lokacinda nad'akko sa yana tinaman wannan abun dana rasa shiyasa koda yaushe bana bari yai nisa dani" murmushi Abdallah yai batareda yasake cewa komaiba haka shima baisake cewa komaiba yagyara abar busar tasa ahankali yafara busata cikin wani'irin salo mai dad'in gaske danko Abdallah saida yafara kad'a kansa saboda yaji da'din busar sosai,,,,..

Fitowarta kenan daga toilet tad'auro alwala saitaji daddad'ar wannan busar tadoki kunnenta dasauri tayaye labulen window tabud'e ta tana dube duben inda zataga mai busar amma bataganshiba kuma batadaina jin sautin busar ba, wani irin farinciki taji yana ratsa zuciyarta kai tsaye nan tadinga dariya tana rungume hannayenta acikin k'irjinta, dikda y'ar mitsitsiyar rigardake jikinta batahanata fita da guduba, ganin tafita da gudu yasa fatima tabi bayanta domin ganin abundake faruwa,,,,..

Yanacikin busa sarewar sai sukaji kiran sallah danhaka ya'ajiyeta yatashi suka wuce izuwa masallaci,,, suna wucewa itakuma tana isowa ta tsayawa tana shesheka tana dube dube fatima ma tana isowa dube duben tafara kaman yadda taga tanayi amma itakam hartagama dube duben bataga komaiba, juyowa tai gareta saitaga kwallah nazuba daga idanunta janyo hanunta tai tace "KUBRAH menene meke faruwa ne..." shuru tamata batace komaiba amma kuma kwallah basu daina zuba daga idanuntaba, jan hanunta tai suka wuce izuwa d'akinsu,,,,"..


Bayan sun iso cikin d'aki ta zaundar da'ita itama ta zauna tana fuskantarta tace "KUBRAH lokaci dayawa alokacinda tinaninki bai dawoba dik kikaji irin wannan sautin busar saikindinga zubda kwallah shin meke faruwa ne marokeki kifad'aman gaskiyar lamarin" ahankali tad'ago da fuskarta takalleta sannan tafara magana "Fatima wannan labarine mai tsayi amma adik lokacinda naji wannan busar tana tinaman da yayana Amadi mai sona mai k'aunata mai share man hawayena adik lokacinda ya kwaranya ya Abdallah shine mutum nabiyu wanda zuciyata bazata taba mantawa dashiba bayan ya Amadi" murmushi fatima tai tace "tabbas wannan abune na sirrin zuciya kuma ina tabbatarmaki da saikin had'u da ya Amadin ki tinda har kikejin alamunsa akusa dake wannan wani abune wanda yake nuna miki cewar yana atare dake kuma insha Allah zan tayaki addu'ah Allah yahad'a fuskokinku" wata iriyar dariya tai mai had'e da kwallah tace ameen y'ar uwata tareda rungumeta,,,,"..

Tashi sukai sukayi sallah sannan suka fita falour,,, around 6:00am Abdallah yaraka abokinsa Captain Ahmad airport yahau jirgi yawuce sannan yadawo gida,,,,..

Ranar Sunday damisalin karfe 8:00am dai dai suka kama hanyar k'asar KEBBI izuwa k'auyen ZAGA zuciyar KUBRAH cike da tsintsar farinciki mara misaltuwa....
#/Vote

#/Share

#/Comment


'''AUFANA for life '''

   *I.W.A*🖊® *INTELLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

    *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

   

   _*GANI GA WANE....*_🌷

_*STORY & WRITING ~BY*_

    _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) my granny's*_

  _*PAGE 43~44*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


11:00am suka iso k'asar KEBBI sannan suka hau hanyar k'auyen ZAGA, tinda suka kama hanyar k'auyen KUBRAH kejin wani irin nishad'i da farinciki na ratsata yayinda wani daddad'an iska ke ratsata sai faman murmushi take tana waige waige tana kallon waje,,,,"..

Tafiyar kilometers 103 sukai sannan suka iso k'auyen, wani mamakine yakama KUBRAH ganin k'auyen ZAGA yadawo birni anyi sababbnin gine gine kuma na zamani sab'anin da dasuke na k'asa, batagama tsinkewa ba saida taga sun iso a bakin gidansu dan dikda itake masu kwatance har suka iso amma hakan baihana mamakinta ya bayyana a fili ba, cewa take anya kuwa nanne gidan,,, tanacikin tinaninne taji fatima ta dafata tace "madam kinbar mutane a tsaye kodai kinyi batan kai ne kika kawomu nan" murmushi tai tace "aa ina kallon k'auyen namune yanda komai yacanja" Allah sarki to muje koh gasu Abbu nan sunfito. Nan tarik'a hanunta suka shiga tana sauri harda gudunta tashiga gidan, inna tabawa ce duk'e tana shara jin sallamar su yasa tamik'e a tsaye tareda amsa sallamar sannan tai tsaye tana kallonsu saboda bata shaidasuba, k'arasawa tai tana tafiya slowly kwallah nazuba daga idanunta tace "inna ta baki shaidaniba koh" shuru tai abun kaman tad'auremata kai tace "Eh 'yar nan" Inna ta KUBRAH ce y'ar bakwainiyark..." tin batako k'arasaba inna tayada tsintsayardake hannunta ta fasa kuka mai sauti tareda yin salati KUBRAH kuma taje tarungumeta tana kuka itama innar kukan take tana fad'in "KUBRAH ashe idanuna zasu sake ganinki KUBRAH ashe zan ganki da rayuwata kuma da taki ainikam nad'auka sai a lahira zamusake ganin juna" inna gani gani kinganni ina raya kema kuma kina a raye kuma insha Allah zamucigaba da rayuwa a tare,,,,,"..+

Malam tanimu dake a d'akinsa kwance jin k'ararda inna tai yasa yafito ba shiri danko takalma baisakaba yafito domin ganin abunda ke faruwa, inna naganinsa tace "malam zo kaga ikon Allah KUBRAH y'ar gidan asma'u" KUBRAH fa kikace. Malam yafad'a kai tsaye, "Eh ita malam" k'arasowa yai yana kallonta fuskarsa d'auke da tsintsar mamaki a fili, KUBRAH yasake kiran sunanta tace "na am malam" tafad'a muryarta na rawa alamar tana kukan, hannunta yarik'o danya k'ara tabbatarda abunda yake gani nan taje ta rungumeshi tana kuka shima d'in kwallan yakezubarwa,,, sun d'auki tsawon mintina ahaka sannan tace "malam banikadai bace tareda wasu nake kaje kugaisa kamasu iso" malam d'in yace "toh" sannan yashiga dakinsa yasako takalmansa da babbar rigarsa sannan yafita,,,,..

Kallon inna tai tace "inna ina mami na ina ya Amadi dik bangansuba" murmushi tai tace "Allah sarki KUBRAH bayan b'atanki abubuwa da dama sunfaru bayan b'atanki wanda mu muka d'auka akan kin mutu ne saboda adik fad'in kauyennan dama wasu k'auyuka dake makwabtaka da wannan k'auyen ba'inda bamuje nemanki amma shuru bamu ganki munyi kuka munyi kuka munyi bak'in ciki ba kad'an ba KUBRAH, shekaru natafiya kuma bamu daina nemanki amma shuru wannan dalilin yasa muka d'auka watak'il kin mutune amma itakam mahaifiyarki tak'i ta amince dahakan, bayan b'atanki da shekara d'aya mahaifiyarki tacigaba da sak'ardatakeyi tana zuwa kasuwa tana kaiwa tasiyar sannan tadawo to acan ne wannan bawan Allahn yaganta yace yanasanta, dafarko tak'i ta amince saida malam yasaka bakinsa sannan ta'amince akayi auren yanzi haka tana k'asar SUDAN tareda mijinta dakuma yaranta uku biyu tagwaye ne sai kuma day'an wanda ta yaye yanzu kuma tana d'aukeda ciki na hud'u, khalees da khaleesat sai Kursum",,,..

Tana kawonan tatsaya tareda yin murmushi, itama murmushin tai sabodajin daddad'an labarin mahaifiyarta tasake cewa "inna ya Amadi fa" tasakeyin murmushi tace "Amadi kuma Gomnatin wannan k'asar ne suka bama malam gurbin yara shiga na karatu kyauta inda zasuyi karatu su sami ilimi a kyauta wato ilimin BOKO daga matakin primary har izuwa secondry a wata makaranta mai suna TSANGAYA, bayan yayita yagama ne yanemi aikin soja kuma cikin ikon Allah yasamu yanzu haka yanacan k'asar inyamurai anturasu tsaron boda dake k'asar OSUN saidai har yanzu Amadi yak'i yai aure yace wai ke yake jira" wata iriyar kunya taji takamata taduk'arda kanta k'asa taredayin murmushi "kuma kinga gidannan dikshi yagyara mana shi kaman yanda yagyara nasu na kauyensu wato gidan iyayensa,,,,..

Sallamar shigowarsu malam ce takatse masu labarinsu nan suka amsa sallamar sannan suka gaisa da inna tamasu sannu da zuwa sannan suka rankaya izuwa  falon malam tanimu,, bayan kowa ya zauna ne akasake gaisawa sai Abbu yace "malam nasan baka shaidaniba koh" malam yai murmushi yace "wallahi kuwa inata kallon fuskar kaman nasan mai ita amma kuma nakasa ganewa" Abbu yai dariya yace "Umaru ne d'angidan mai gari" Ah kai haba ikon Allah ai wallahi tin d'azu naketa kallon fuskar kaman wacca nasani toh kasan abunne dayawa shekaru dayawa ba'aganin juna shiyasa. Abbu yace "hakane kam, toh dama yaronane Abdallah" yanuna Abdallah sannan yacigaba "shine yabige KUBRAH da motar mai gidansa akan titi a hanyarsa takomawa gida YOLA, toh bayan yabigeta mukaje asibiti tai jinya acan bayan ta warke kuma sai akasami matsalar tarasa tinaninta dakomai nata" nandai yacigaba da bashi labari tin bigeta da Abdallah yai har izuwa dawowar tinaninta dakuma dawowar ganinta dakuma gano kawunta datai faruk" hmm....!!! Malam yanisa sannan yace "tabbas ikon Allah dagirma yake wannan abun al'ajabi haka saidai kuma wani abu dabaka saniba shine KUBRAH fa 'yarkace" dik wandake a cikin falon saida yakalli malam tanimu tareda neman k'arin bayani, yafahimci hakan nan yai murmushi sannan yacigaba "ina nufin y'ar d'an uwanka habu" cikin mamaki Abbu yace "kana nufin kaceman KUBRAH 'yar habubakar ce" tabbas kuwa amma a da saboda yanzu y'ata ce dakansa kuma da bakinsa a gaban mutane kuma a bainar jama'ah yace bayasonta yabani ninaduka,,,,"..

Kallonsa Abbu yai cikin rashin fahimta harzaiyi magana sai mami tace "dama nasan za'arina dan wallahi tinda naga KUBRAH naji ajikina ita jininmu ce kuma adik lokacinda nakalleta sainaga tanaman kama da wani wanda nasani saidai kuma nakasa gane waneneshi wanda takeman kama dashi ashe kuwa tinanina da hasashena yazama gaskiya habubakar ne" cikin sauri KUBRAH tamik'e a atsaya kwallah nazuba daga idanuwanta tace "kudaina dangantani da wannan mugun mutumin azzalimi mara tausayi niba 'yar sa bace wallah.." batak'arasaba taji Abdallah yawanketa da mari tass tass kakeji cikin kakkausar murya tareda nunata da yatsa yace "karki kuskura nasake jin waennan kalaman sunsake fitowa daga bakinki bakida hankali ne to bari kiji komai lalacewar masa tafi k'arfin kashin shanu kuma dikyanda kikai mahaifinki ne komai lalacewarsa kuwa dole ace shine mahaifink..." shima bai k'arasaba ta katseshi da fad'in "niba mahaifina bane ban had'a komai dashiba kaman yafad'a ni ba y'arsa bace haka nima zancigaba da fad'in shi ba mahaifina bane ban had'a komai dashib..." bata k'arasaba yasake wanketa da mari zai sake marinta Abbu yadaka masa tsawa mai k'arfi tareda fad'in "are u mad Abdallah u are very stupid kanada hankali kuwa idan hankali fa yabata hankali akesakawa ya nemoshi angayamaka haka akeyin hukunci" fita tai dagudu tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu ganin haka yasa fatima tabi bayanta domin ta rarrasheta,,,,"..

Shuru yaratsa falon nawasu y'an dak'ik'u can Abbu yace "malam mekefaruwa ne wai naga dik y'a ta kirki tanayiwa mahaifinta addu'ah ta kwarai kuma tana farinciki da alfaharin ace ita 'yarsa ce kuma KUBRAH yarinyace mai kirki mai cikakkiyar tarbiyya natabbata tanada cikakkiyar hujjar yin hakan" hmm...!!! Malam yanisa sannan yafara magana "tabbas itakuwa keda hujja amma saidai labarine mai tsayi, natabbata kasan auren asma'u y'ar malam GARSO wannan makwabcina da d'an uwanka habu" Abbu yace "Eh nasani" to KUBRAH y'a ce ga asma'u wacca ta haifa tareda habu...." nan yacigaba da bashi labarin dik abunda yafaru bai boyemasa komai ba har izuwa sakin wulak'ancinda yayiwa asma'u dakuma dalilinsa nayin hakan, idan ran Abbu yayi dubu to ya b'aci Abdallah kuwa motsin kirki kasawa yai nantake tausayi da b'acin ran abunda habu yai  yacika zuciyarsa,,,,...

Abbu ne yafara magana yace "tirr da masu wannan halayyar irinta habubakar rabon danaji irin wannan labarin tin a zamaninnikan baya y'ay'a mata ai rahama ne da matan da mazan bakasan wanda zakaci amfaninsaba watakil ma kaci na matan fiye dana mazan, hmm...!!! Allah yak'ara shiryardamu"  nan suka amsa da ameeen,,,,,"..

Bayan komai ya lafane malam tanimu yakira Amadi a waya yashaidamasa ga KUBRAH ta dawo hakama asma'u mahaifiyarta itama ankirata saidai itakam tace yanzu zata biyo jirgin k'arfe 2:00pm dan sam bazata iya hak'ura har gobeba,,,  abinci inna tadafa masu mai kyau wanda KUBRAH da fatima suka tayata girkasa,, bayan sunci sun sha Abbu yanemi alfarmar yabashi KUBRAH suje gidan maigari domin suganta itama taga kakanninta, malam ya'amince dahakan amma KUBRAH sam tak'i amincewa acewarta lokacinda ita da mahaifiyarta ake wulak'antasu ake gana masu azaba basusan ita jikarsuceba sai yanzu data girma tazama abun kwarai sannan sukasan ita jikarsuce,, dasuka matsamata akan taje sai kawai tafashe masu da kuka tashige d'aki tarufe kanta dole tasa suka wuce badan sunso hakan ba,,,,"..

Around 3:15pm dot asma'u da iyalanta harda mijinta suka iso k'auyen ZAGA..
#/Vote

#/Share

#/Comment


'''AUFANA for life '''

   *I.W.A*🖊® *INTELLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

    *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*


   _*GANI GA WANE....*_🌷


_*STORY & WRITING ~BY*_

    _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_


_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) My granny's*_

   _*PAGE 45~46*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Around 3:15pm dot asma'u da iyalanta harda mijinta suka iso k'auyen ZAGA,, dikda k'aramin cikinda take d'auke dashi amma hakan baihanata yin sauri harda d'an had'awa da gudu wajen ganin fuskar y'arta datajima tana k'ishirwar gani, koda tashigo cikin gida kuwa ta tadda inna a waje fitowarta kenan, k'arasowa tai inna namata sannu da zuwa amma ko kallonta batayi burinta kawai taga y'arta inna data fahimci hakan saitai murmushi tace "Allah sarki d'a da mahaifi sai Allah" rik'o hanunta tai tana murmushi tace "kwantarda hankalinki batafiya zataiba tana nan" nan tarik'a hanunta suka shiga ciki,, haryanzu KUBRAH bata bud'e k'ofarba azatonta za'atilastamata saitaje gidan kakanninta ne,,,,,"..+

A hankali inna tafara buga k'ofar tareda fad'in "y'ar bakwainiya ta bud'e k'ofar ga mahaifiyarki ta'iso" k'in bud'e k'ofar tai saida asma'u tai magana "KUBRAH bud'e k'ofar nice" aikwa tanajin muryar mahaifiyarta dagudu tazo tabud'e k'ofar suka rungume juna suna zubda kwallan farinciki, cewa take "yarinyata nayi matuk'ar kewarki nasani wallahi baki mutuba saboda inaji ajikina baki mutuba kuma komai dad'ewa komai nisa zansake ganinki koda suke fad'ar wai kin mutu nikam sam ban amince dahakan ba" tad'ago fuskarta tana tarik'eta da dika hannayenta sannan ta sumbaceta a goshi tasaka day'an hanunta tashare mata kwallan dake zuba daga idanuwanta tace kibani labarin yanda akayi kika b'ata kuma ina kikacigaba da rayuwa bayan kinsan kinbarmu acikin tashin hankali" ahankali tad'ago da fuskarta dara daran idanuwanta diksunyi ja tafara magana "mami labarine mai tsaye bazaiyiwu a tsayeba" ok toh muje muzauna koh. Taja hanunta danufin suwuce ita a zatonta har yanzu KUBRAH bata gani inna da KUBRAH diksun kula da hakan sukai murmushi tacigaba dabinta ahaka inna ce tace "asma'u nasan bakisan KUBRAH tana ganiba" mamakine yakamata jin abunda inna tafad'a, cikin mamaki tajuyo takalli KUBRAH itakuma saitaki d'ago fuskarta, murmushi asma'u tai tace "Alhmdllh godiya, jinjina da yabo sukara tabbata ga ubangiji wanda yake juya bak'in ciki izuwa farin ciki" sukai murmushi atare sannan suka k'arasa falour,,,,,"..

Bayan sun isa ne KUBRAH tabata dikkanin labarin bata b'oyemata komaiba kuma ta fad'a mata mahaifinta Abdallah yayane ga habubakar mahaifinta,, acikin zuciyarta farinciki ne fall da Allah yasa KUBRAH tagirma agidan yayan mahaifinta koba komai tasan tanada y'an uwa kuma suma sunsan itadin y'ar uwarsuce bawai su hassan ne kad'ai y'ay'an habubakar ba, amma a fili tanuna rashin jin da'dinta a fili kuma tace idan zata wuce da'ita zatawuce bazata bari suwuce da'ita ba,, hakan kuwa da mahaifiyarta tace sam bataji dad'insa ba amma kuma bata nuna a filiba,,,,..

Malam ne yashigo tareda mijin asma'u da yaranta kyawawa farare tass kowannensu na sanye da wando da riga matan an tufke masu sumarsu da ribom mai kyau sai 'yan takalmansu da Teddy's d'insu a hanunsu namijin kuma irin shigar mahaifinshi akamasa kasancewar shine babba shine kuma hassan,, cikin murmushi asma'u ta gaida malam sannan tanuna wa maigidanta KUBRAH, cikin ladabi KUBRAH ta gaidashi sannan tajanyo k'anenta a jikinta ta rungumesu tanajin wani dad'i da farinciki na ratsata, Alhaji Usman Baffa Canji shine sunan mijin asma'u shugaban masu canji na SUDAN,, Shima yanuna tsananin farincikinsa a fili saboda yanzu yasan farincikin matarsa abar k'aunarsa yadawo dan tinda ya aureta tana fadamasa bafata da farinciki matuk'ar bataga fuskar y'arta ba, yayima abubuwa da dama waenda zasusaka tamanta da wannan abun kaman ginamata shahararren Company mai d'aukeda sunan KUBRAH, amma dikda hakan baihanata cigaba da zama acikin damuwa ba,,,,,"..

Suna zaune acikin falon suna fira saiga su Abbu sunshigo asma'u na ganinsa tashaidashi saikuma rayuwarda tai a baya tadawomata sabuwa acikin zuciya yayinda fuskar habu keta faman zarya acikin idanuwanta, shima dai Abbu yana ganinta yashaidata ranarda zasu wuce makaranta shi da habu dakuma turawanda sukazo daukansu har k'ofar gida tarakosu,, bayan sunzauna sannan suka gaisa nan asma'u tamasu godiya da irin kyakkawan rik'onda sukayiwa KUBRAH dikda basusan itadin jininsu ceba,, Abbu ne yaimagana yace ai bakomai yiwa kaine tai murmushi tace "ina Abdallah ne" yad'ago kansa cikin jin kunya yace "gani nan" tai dariya tace "dazuwana akafara bani labarinka anshashi harnafara k'oshi" wata iriyar kunya takama KUBRAH tanoke kanta a k'asa,  Salma dake gefe d'aya kusa da mami tab'ata fuska aranta tace "shegiya mayya saidai kinbarsa wallahi tinda ba kanen ubanki bane" tai maganar azuciyarta tana hararan KUBRAH,,,,"..

STORY CONTINUES BELOW

Haka suka wuni ranar sunashan fira zuciyoyinsu cike da tsintsar farinciki inna ji take kaman ta goye KUBRAH sai nan nan take da'ita mamin KUBRAH kuwa dikta kalleta saitai murmushin farinciki tana mamakin girman KUBRAH dan da'ake cewa jikin KUBRAH dik natane ta biyo itakuma sai take ganima kaman KUBRAH saitafita cika musamman ita da yanzu ne take cikar budurcinta saidai fuskarta kam daka ganta kasan 'yar habubakar ce dan sak shi tabiyo,,,,..

Da dare kuwa bayan sunci abinci su Abbu sukace zasu wuce gidansu su kwana sunso KUBRAH tazo suje acan takwana amma tak'i itafa bataso ne ko k'ofar gidan mahaifinta tagani hakama ta kakanta haka suka hak'ura sukatafi suka kyaleta,, a daren kuwa haka KUBRAH da mami suka raba dare suna shan fira KUBRAH nata bata labarin rayuwarta ta baya da irin yanda Abdallah yaita hidima da'ita dakuma iyayensa,, dik acikin labarin kusan rabinsa dik na Abdallah ne mami kuwa sai dariya take mata amma ita sarkin wauta sam bata fahimci abunda mami ke nufiba, saikusan 12:00am sannan tamata saida safe tawuce d'aki takwanta,,,,...

Dasafe bayan sun k'arya tad'auki wayar asma'u tasaka nmbr d'in Abdallah ringing d'aya a nabiyu ya d'auka, cikin wata iriyar murya wacca ita kanta batasan tanada itaba tagaidashi ya amsa tareda tambayar wacece dikda kuma yagane muryarta danko acikin bacci yaji sautin muryarta zai gane bare kuma a farke,, in in na tafara dakyar tace "KUBRAH ce" ok KUBRAH antashi lafiya. tace "lafiya k'alau dama fatima ce nakeso nayi magana da'ita" ok toh bara naje gida dan yanzu ba gida nakeba. "kana ina ne ya Abdallah" tajefo masa tambayar kai tsaye, murmushi yai sannan yace "ina gun kakannina muna fira" tanajin yafad'i haka sai takashe wayar yai murmushi dan yasan hakance zata faru,,,,"...

Around 12:00pm Amadi ya'iso k'auyen ZAGA sai zuba sauri yake ya'iso gida, cikin sa'a kuwa yana shigowa yatadda asma'u da maigidanta k'ofar gida suna magana, cikin girmamawa yagaidasu asma'u tace "aa soja maganin wani soja ankaraso kenan" yace eh yana shafa kansa tareda sunne kan nasan k'asa alamar kunya tai murmushi shikuma yawuce cikin gida, kai tsaye falour yawuce yana kiran sunan KUBRAH fatima dake falon ce tace masa tanacikin d'aki baiko tsaya yagamajin abunda take fad'aba yawuce d'akin, yana isa itakuma tana fitowa sukai kicib'is itace tai saurin ja da baya tareda fad'in Bismillahi shikwa cikin zumud'i yace "ina KUBRAH take ne" jin tambayarda yaima yasa ta tabbatar Amadi ne, murmushi tai tace "tanaciki gun inna" nan yawuce ciki itakuma tai tsaye tana kallonsa tana dariya nan take rayuwarsu ta baya tadawo mata sabuwa acikin zuciyarta ta tinada yanda yake goyata yana yawo da'ita dakuma yanda yake shagwabata fiyeda kowa, wani irin murmushi tai mai wahalar fassara sannan tabi bayansa,,,,"..

Tana isa saitai tsaye k'ofar d'akin tana kallansa yanda yake masifar inna ina KUBRAH ina KUBRAH kaman yai kuka haka yake maganar inna kuwa sai dariyanshi take kuma tak'i tacemashi komai,, murmushi tai sannan tace "ga KUBRAH nan" juyowa yai ahankali saiyaga ai itace wacca yagani yanzu tacemasa KUBRAH nagun inna,, inna ce takatseshi da fad'in "lallai Amadi ashe idan KUBRAH shekara ashirin tai bata gidannan idan tazo bazaka shaidata ba" murmushi yai yace "to ai inna naga KUBRAH makauniya ce itakuma wannan tana gani amma kuma saikice itace KUBRAH" Eh tabbas itace saboda yanzu ita ba makauniya bace. K'arasowa tai ciki tana murmushi sai kawai tarungumeshi kwallah suka fara zuba daga idanunta "nice ya Amadi nice"  inna kuwa kasa tsayawa kallon wannan rashin kunyar tai tafita tabar d'akin, sunyi kusan 5mnts ahaka can saiya rik'o hannayenta sannan yad'ago fuskarta tareda sharemata kwallanda suka zubo mata yace "KUBRAH kibani labari ina kikaje muka kasa samunki a dik fad'in k'asarnan ta KEBBI" ya Amadi labarine mai tsayi amma bara nataikata maka. Nan tabashi labarin dik abunda yafaru tindaga bigeta da Abdallah yai har izuwa yanzu dasuka maidata gida,,,,,"..

Murmushi yai tareda fad'in "kai Alhmdllh tabbas ubangiji shine abun godiya Allah mungode maka" itama tai murmushi tace "ya Amadi bakai aureba har yanzu nad'auka koda zamuzo har yara kanada gaskiya yakamata kai aure hakanan" dariya yai sosai yace "toh ai tinda kinzo kinga saiki nemaman matar na'aura" aikwa zan nemamaka wallahi musha biki. Hannunta yarik'a suka fita waje, suna isowa k'ofar fita sai sukai kicib'is da Abdallah zai shigo cikin mamaki Abdallah yace "Captain Ahmad" shima yace "A U Ibrahim" dama kaine Abdallahn da KUBRAH tabani labarinka yanzu. Murmushi Abdallah yai yace "Eh nine kaima naji labarinka agunta ashe kaine ya Amadi" yace "Eh nine" nan yabashi hannu sukai musabaha sannan suka shigo atare,,,,...

Zan iya cewa yanzu tsintsar farinciki kawai ke gudana acikin waennan ahali biyu, kimanin kwanaki uku suka kwashe suna gudanarda zumunci a tsakaninsu acikin kwanakinne Abdallah yasamu damar yin nasarar rok'on asma'u akan tabar KUBRAH taje kakanninta suganta saboda mahaifiyar habu har kuka take sosai saboda tasan sun cutarda asma'u da KUBRAH tanasan tanemesu gafara,, dafarko bata aminceba sai daga baya dasukafi karfinta da nasihohi masu ratsa zuciya sannan tahak'ura tabarta sukaje,,,...

Gidanma asauyamasa fasali a da ginin k'asa ne kuma baifi d'aki uku ba sai fadar mai gari amma yanzu komai ansauya ko fadarma anyita mai kyau kamar ta sarkin musulmi suma matansa anmasu tasu ginin kowacce da nata part gakuma part biyu da'akayi extra d'aya na habubakar da iyalansa idan sunzo d'aya kuma na Umaru wato Abbu da nasa iyalan idan sunzo abundai gwanin birgewa,,, part din nenne suka fara zuwa wato mahaifiyar Abbu kaman yanda su fatima ke kiranta, nenne taji da'din ganin KUBRAH sosai dan dik abunda ke faruwa sunaji suma sundauka ta mutu ne amma yanzu labarinda sukaji yamatuk'ar yimasu da'di, daga sashenta suka wuce sashen Inde wato mahaifiyar habu kaman yanda jikokin su fatima ke kiranta,, itakam hadda kuka saidatai tadinga rok'on KUBRAH gafara itama KUBRAH kukan take tana fad'in tayafe mata kuma itama mahaifiyarta tayafe mata bakomai Allah i yafemana baki d'ai suka amsa da ameen,,,"..

Daganan aka kaita fadar maigari wato mahaifinsu habu da Abbu shikam wani irin farinciki yaji ashe ba gaskiya bane da'akace ta mutu nan yarik'o hanunta yazaunardaita kusa dashi yadinga yimata wasan jika da kaka tintana nok'ewa harta fara biyemasa tana ramawa abun gwanin birgewa sukaita kyalkyala dariya ita da shi hakan kuwa bak'aramin dad'i yayiwa Abbu ba Abdallah kuwa tsabar farinciki kasa  zama yai yafita yawuce yana murmushi,, aranar dai anan KUBRAH tawuni sai nan nan ake da'ita sai da dare sannan suka koma gida ita da fatima,,,,...

Kwanansu biyar da zuwa suka fara shirin tafiya asma'u tashirya da yaranta da maigidanta dakuma KUBRAH dan tace da'ita zataje haka kuwa akayi tin 8:00am jirginsu yad'aga zuwa k'asar SUDAN, KUBRAH sai kuka take na rabuwa dasu fatima,, suma 10:00am dot suka kama hanyar garin YOLA ADAMAWA sukayiwa garin KEBBI bye bye sunrabu suna matuk'ar kewar juna saidai Abdallah yatafi dawani buri aransa wanda yayiwa kansa alk'awarin cikashi,,,,"..

       ***** ***** ****


Around 10:30am jirginsu yasauka k'asar SUDAN koda suka sauka kuwa driver's nasu harsun iso suna jiran saukansu, wasu dalla dallan motoci ne KUBRAH tagani bak'ak'e wulik sai shining suke suna dauke da sunan Highlander, suna saukowa kuwa suka kwashi kayansu suka saka a mota sannan suka shigo suka wuce,, tinaninta bai gama tsinkewa ba saida suka iso wani katafaren gida tsarin ginin London, da'isowar su gate yawangare suka danna motocin sai ciki sannan suka tsaya dasauri wani yazo yabud'e mata murfin motar tasakko k'afarta a hankali tafito tana ware dara daran idanuwanta domin basu hak'k'insu...


#/Vote

#/Share

#/Comment


'''AUFANA for life '''

   *I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

    *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

   _*GANI GA WANE....*_🌷

_*STORY & WRITING ~BY*_

    _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) my granny's*_

   _*PAGE 47~48*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Filin gidan kad'ai abun kallo ne bare kuma abubuwandake cikinsa, shuke shuke ne na flower's kala kala masu kyan gaske k'asan gidan dik greens carpet ne yabaje abun gwanin ban sha'awa gakuma masu kula dasu sunata aikinsu,, suna ganin sun fito cikin sauri sukazo suka zube suna kwasan gaisuwa sukuma suna amsa masu cikin fara'ah,, hanunta asma'u tarik'o suka kama hanyar shiga cikin gidan,,,,"..

Acikin wani katafaren falour suka fara isa wanda shine zaki fara gani kan kishiga cikin gidan, numfashinta ne yakusa d'aukewa saboda ganin tsabar tamanin kud'inda aka kashe wajen had'a falon komai nasa yahad'u daka gansa kasan bak'ak'anan kud'i aka kashemasa ba, zama sukai acikin falour Abban khalees wato mijin asma'u yakalli KUBRAH cikin murmushi yace "y'ata Khadija kinga gidanmu inaso kisaki jikinki kiyi yanda kikeso acikinsa kema gidanku ne kuma kema y'ata ce jinin jikina kamar su khalees kinji koh kuma dik abunda kike buk'ata kifad'aman insha Allah zanmaki shi matuk'ar baifi k'arfina ba kinji koh" murmushi tai sannan tace "toh Abba nagode sosai Allah yak'ara arziki mai albarka" yace ameen sannan yasake cewa "kishirya anjima idan maleek yazo kuje shopping kisiyo sauran abunda bakidashi gobe kuma insha Allah mai lesson naki zai fara zuwa saboda haka kishirya saboda inaso kicigaba da karatu saboda Company naki yadawo hanunki nanda 1year insha Allah" wani irin farinciki taji yaratsata saboda dama tanasan takoma School, godiya tadinga masa hadda kwallan farinciki takalli asma'u cikin dariya kwallah nazubarmata tace "mami na kitayani godiya" itama murmushi tai tace "aa miye nawa aciki tsakanin uba da y'arsa kiyimasa da kanki" tana gamafadar haka ta tashi tawuce itakuwa dariya tai haka shima dariyar yai yace "kyaleta kinji y'ata bakomai ai yiwa kaine Allah dai yataimaka yakuma baki sa'a" tace ameen,,, "..+

Fita yai yawuce part dinsa tareda khalees ganin haka yasa itama tad'auki Kursum tarika hanun khaleesat suka shiga ciki,,,,"..

Dakinda tagani a bud'e shi tashiga dan da'alama dai shine na asma'u,  tana shiga kuwa taganta nan tazauna tasauke kursum akan gado, bayan asma'u tagama abunda take sai tajata suka fita tanuna mata d'akinta, hmm shima d'akin wata aljannar duniya ne yahad'u karshen had'uwa komai yaji nan tanunnuna mata komai da bata saniba sannan tafita,, bayan tafita ne tai tsaye tana k'arewa d'akin kallo mamaki take wai yau sune acikin wannan daular wacca ko a mafarki bata tab'a tinanin zata shigotaba, wardrobe tabud'e nantaga kayanta na sakawa kala kala hijabs da mayafai komi wajensa daban an tsarasa rufeta tai tasake bud'e wata drower k'arama datagani itakuma takalma ne acikinta Hill's da plat kala kala a gefe d'aya kuma jakukunane kala kala, bayan tagama gani tarufe tazo kan mirror inda taga creams kala kala set d'in NIVEA dakuma lotions kala kala masu gyara fata,,,,...

Bayan tagama ganin komai sannan tashiga toilet, wanka tai tamurje jikinta da mayukan wanka da tiraruka kala kala da sabulai na wanka masu sulb'une fata su gyarata tsab,, bayan tagama sannan tafito tashafa mai tabud'e wardrobe tadakko kayanda zata saka,,,,"..

Wata atamfa ce Super wax k'irar England green and white color d'inkin mutan kebbi riga da sket, dikda batai make up ba amma tai masifar kyau kuma kayan sunmata kyau sosai d'inkin ya karb'i jikinta dukiyar fulaninta sun fito a sama saboda rigar tad'an matseta hakama sket d'in matasan zamanta sun fito gakuma hips d'inta kaman zasu tsaga sket d'in sufito,, bayan tagama shiryasa sannan tafeshe jikinta da tiraruka masu dadin k'amshi sannan ta fece sumarta tashafamata mayuka masu sakashi sentsi da baki, bayan tagama feceshi tasaka ribom ta tufkeshi sannan tadakko mayafinta ta yafa tareda takalmanta plat kalan mayafinta white mai ratsin green kadan aciki,, bayan tagama tai tsaye akan mirror tana kallon kanta, ita kanta tasan tai kyau sosai murmushi kawai tai sannan tawuce tafita,,,,,"..

STORY CONTINUES BELOW

Koda tafita ta taddasu dinning area sunacin abinci nan taje tazauna itama tafara ci,,, suna cikin ci saiga Maleek d'in yak'araso yana isowa yadurk'usa yagaida asma'u sannan yagaida Abban khalees sannan yazauna yana kallon KUBRAH,, murmushi tai tacemasa "barka da wuni ya maleek" shima cikin murmushi ya amsa mata da "barka dai k'anwas anzo lafiya ya hanya" tace Alhmdllh. kallonsa Abban khalees yai yace "shagon Ibn mahiir zaka kaita dik abunda takeso tad'auka kaji koh" murmushi yai yace "yes dad dagirman kujerarka" dariya sukai suduka saboda maleek d'an ban dariya ne akwaishi da barkwanci "maleek ka rainani koh yamaka kyau zakasa nace batun auren nan afasa har nex yea.." baiko K'arasa ba yai saurin cewa "afuwan afuwan ya Abi" tareda hard'e hannayensa duka biyu ya marairaice ya shagwabe fuska kaman wani k'aramin yaro tareda saurin mik'ewa tsaye yad'auki Key's dinsa yafita yana fad'in "k'anwas kifito muje" aikwa mezasuyi inba dariya ba nan ta tashi tabi bayansa tana fad'in "muntafi Abba mami saimun dawo" Allah ya kiyaye hanya asma'u tace Abban khalees kuma yace "adawo lafiya y'ata,,,"..


Sunjima acan wajen shopping d'in kayane masu kyau tasiyo hadda kayan bacci dakuma creams kala kala da sark'a da awarwaro kala kala masu tsadan gaske saikuma abayoyi kala kala,, sunjima sosai suna zab'ar kaya, saikusan 2:00pm sannan suka dawo gida,,,..

Kula tamusamman ake bama KUBRAH acikin gidan, washe gari around 10:00am dot mai lesson d'in yazo suka wuni sunatayi yanajin dad'in koyarda'ita sosai acewarsa bai tab'a yaranda yake koyardasu yanajin dad'i ba kaman KUBRAH bcoz KUBRAH she's very Intelligent and very brilliant tanada basira sosai daka fad'amata abu nantake take fahimtarsa kuma tana mayarda hankali sosai bata wasa,,,,"..

Haka malam yazage dantse wajen koyamata muhimman abubuwanda yadace tasani amatsayita na wacca zata shiga jami'ah kuma Alhmdllh komai natafiya dai dai,,,Satinta biyu kacal dazuwa aka samamata admission awata katafariyar University dake babban birnin k'asar SUDAN cikin kwana d'aya aka kammala mata komai nafara karatu tafara zuwa School tana d'aukan lecture,, d'aya daga cikin driver's d'in Abban khalees yabata domin yadinga kaita kuma yad'akkota idan zata dawo, cikin k'ank'anen lokaci KUBRAH ta goge tazama big girl idan kaganta taci gayu zata School zaka d'auka wata gogaggiyar yar BOKO ce musamman datasami k'awa yar gayu mai suna NAJWA itama d'aya daga cikin d'aliban School d'in ne, Najwa wayayyiya ce sosai mahaifinta mai kud'i ne suma y'an Nigeria ne aikine yakawo mahaifinsu har suka zama y'an k'asar, a d'an zamanda KUBRAH tai da'ita tasan abubuwa dayawa takoyar da'ita rayuwa sosai,, ahalin yanzu idan kaga KUBRAH sam bazaka ganetaba tasauya gaba d'aya fatarta ta sauya jindadi da gayu sunzauna mata ajiki sai shek'i take yayinda tasaka karatu agaba ba wasa,,,"..

Yauma kamar kullum bayan tadawo daga School tai wanka tai sallah ta kwanta kasancewar sunci abinci a restaurant shiyasa batajin yinwa, littafenta tadakko tabud'e tanadan dubawa saboda ahalin yanzu exam suke fuskanta shiyasa any time tana mak'ale da littafe,, khaleesat ce tashigo dagudu tana fad'o kanta tana dariya tana fad'in "Aunty khady Ummi tace infad'amaki wai yanzu yaya Abdallah yakira yace afad'amaki Aunty Salma tahaihu ta haifi baby girl mai kyau kuma ga wani abu nan ya'aiko maki arufe ummi tak'i bari mubud'e" tak'arasa maganar tana shagwabe fuska,, dasauri KUBRAH tamik'e tsaye tai tsalle tacire hijab d'inta taredayin wata iriyar k'ara tana dariya sannan tad'auki khaleesat suka fita,,,"..

D'akin asma'u tawuce koda taje tana kwance tana fama da tsohon cikinta, zama tai kusa da'ita tana murmushi sannan tace "mami dagaske Aunty Salma ta haihu wai" wani kallo tamata sannan tace "toh k'arya zan maki ne" tafad'a tareda mik'o mata wani abu dayake a rufe sannan tace "gashinan inji yayan naki yace akawo maki kishirya jibi kuwuce dasu khaleesat Abban ku zaiyi tafiya shima saikuwuce atare a saukeki a kebbi sannan kuwuce can yola kuma sati d'aya kawai wallahi yace kuyi danma kisani da'angama biki ki tattarosu kudawo" wani irin dad'i taji tace "toh mami na" tana fadar haka ta tashi tafita,,,,"..

D'akinta tawuce cikin zumud'i tafara bud'e abunda ya aikomata dashi, first abunda tafara gani letter saikuma dalleliyar waya Ipon8 sabuwa dall, wani irin farinciki taji yakamata tarungume wayar tafad'i kan gado tana wani'irin murmushi wanda ita kanta batasan namiye ba Yayinda wani irin nishadi da iska mai sanyi tafara ratsa jikinta takara k'ank'ame wayar tana murmushi tareda lumshe dara daran Idanuwanta,, ahankali tabud'e letter d'in domin ganin abunda take k'unshe dashi, wani irin rubutune akayi acikinta nan tafara karantashi ahankali kamar haka,,..

_Assalamu Alaikum Khadijatul Kubrah inafatar kina cikin k'oshin lafiya_

_KUBRAH inaso kiyiwa zantukana kyakkawar fahimta tayanda zaki fahimci cikakken sak'ona agareki_

_KUBRAH najima da wani ciwo acikin zuciyata wanda nakasa samun maganinsa ina rok'onki daki taimaka kibani maganin wannan ciwon nawa saboda nasan tabbas bawanda yakeda maganinsa sai ke_

_KUBRAH inaso kisani tinda nahad'u dake nafad'a a TARKON k'aunarki inaso kisani bawai inasonki da wani abu dakika mallaka bane wallahi aa K'aunarki nake k'auna wacca baruwanta da kyau ko nasaba k'aunarki nake tsakani da Allah_

_Inaso kifahimci zancena kitaimakaman ki amince da tayin soyayyata KUBRAH dan Allah dan Allah badan niba wallahi KUBRAH inasanki so mara misaltuwa zan iya rasa raina gaba d'aya idan har kika k'i amincewa da tayin soyayya ta, I really love u with all my hert KUBRAH pleace and please karki gujeni_

_I love u I love u KUBRAH, u are such important part of my life, I love u forever, u my 1 true love, nothing could ever change my love to u, I love u with every fiver of my being, i thank God every day for bringing u in to my life, my heart race whenever I see u, when i see ur face and hear ur voice my worries fade away, I would do anything to put a smile on ur face all i want to do is to make u happy u make my dreams come true, u make my feel so special, when I close my eyes all see is u......_

_I LOVE U KUBRAH WITH ALL MY HERT_.


Wani irin daddad'an farinciki taji yaziyarci zuciyarta pillow tajanyo tarungumeshi tanajin nishadi acikin zuciyarta,, tajima tana nazarin wannan letter hmm wai itace ya Abdallah ke so harda rubutomata wannan zunkud'ed'iyar Wasik'a,, wayar tad'akko tafara had'awa wani abun mamaki data gani shine komai yasiyomata hadda simcard har biyu nan tasaka su sannan takasheta taje ta jonata kan chaji kaman yanda taga anrubuta a kwalin wayar kar afara amfani da'ita harsai tayi chaji,,,"..

Kimanin kwana biyu suka d'auka suna shirin tafiya aranarda yarage saura kwana uku suna a ranar Suka sauka Nigeria a katafaren filin jirginnan na AHMADU BELLO INTERNATIONAL AIRPORT dake cikin garin KEBBI suna sauka driver's sukazo suka daukesu suka wuce k'auyen ZAGA....#/Vote

#/Share

#/Comment


'''AUFANA for life '''

   *I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

    *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

   _*GANI GA WANE....*_🌷

_*STORY & WRITING ~BY*_

    _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_

_*Devoted to - Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) my granny's*_

   _*PAGE 49~50*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Koda suka isa kuwa saisuka tadda Amadi shima yazo yana shirin tafiya can yola bikin, yaji dad'in zuwan KUBRAH sosai saboda dama yabasan yasami lokaci yaje can Sudan d'in yacimmata domin ya bayyana mata sak'on zuciyarshi,,,"..

Taso suwuce ranar Yola amma inna tak'i bari suwuce saboda maraice tagabato sosai itakuma batasan tafiyar dare da mota, badan taso hakan ba tahak'ura har gobe sannan suwuce,,, zaune take acikin d'aki tanayiwa su khaleesat shirin bacci saiga Amadi yashigo cikin sallama, cikin murmushi ta amsa tareda gaidashi ya amsa su khaleesat ma suka gaidashi ya amsa tareda d'aukan kursum yad'ora kan cinyarsa,,,,..+

Yar fira suka farayi har tagama shiryamasu sannan ta tashi takaisu d'akin inna tadawo tasameshi har yanzu yana nan baifitaba, zama tai gefen gadon tareda fad'in "wai ya Amadi ina k'awata Hindu tinda nadawo bangantaba" murmushi yai sannan yace "ai tin lokacinda kika b'ata mahaifiyarta tad'auketa suka koma k'auyensu kinsan dama zamane yakawo mahaifinta nan" Allah sarki k'awata ina missing nata wlh. Murmushi kawai yai bai sake cewa komaiba sai satan kallonta yake time by time,,,, Can dai yadago fuskarsa ahankali yakira sunanta cikin wata'iriyar murya "KUBRAH" a yanayinda yakira sunan ne yabata mamaki tad'ago tareda amsawa tana kallonsa, shuru yai kuma yakasa magana saida yad'auki tsawon 5mnts sannan yacigaba da fad'in,,,"..

KUBRAH nadad'e ina dakon son ki acikin zuciyata tsawon shekarunda nai bana tareda ke har izuwa yanzu da Allah yasake had'amu, KUBRAH nadad'e ina k'aunarki acikin zuciyata saidai narasa yanda zanyi in furta maki ne, Inaso kisani KUBRAH zuciyata cike take da tsintsar k'aunarki dakuma begenki nadad'e ina rainon son ki acikin zuciyata yanzu ne yagirma yanzune kuma lokacin da yadace na bayyana maki shi,, KUBRAH i really Love u, I love u forever and ever........ever, I don't want to miss u in my life KUBRAH please and please KUBRAH karki gujeni ki taimakawa zuciyarda ta dad'e tana k'aunarki ki taimakawa zuciyarda take cike da begenki KUBRAH kitaimaka man ki amince da tayin Soyayyata dan Allah Please..... Kubran Amadi,,,,"..

Shuru tai taduk'arda kanta kasa takasa cewa komai yayinda dik wata gab'a tajikinta tadaina motsi komai nata yatsaya cakk,, jin shurunda tai yasa yasauke kursum dake ajikinsa tana bacci kan gado yadurk'usa k'asa yasauke guiwowinsa k'asa fuskarsa tana fuskantar tata yace "my KUBRAH will u marry me....??" jin maganar tasa tai a bazata tamkar saukan aradu nan tai saurin mik'ewa a tsaye kwallah nazuba daga idanunta tazuba masa dara daran idanuwanta batareda tace dashi komaiba saikuma tajuya tafita dagudu,,,,....

Jikinsa yai sanyi sosai saikuma yatsinci kansa dayin dana sanin abunda yai yanzu danhaka yamik'e tsaye yafita domin ya rarrasheta yabata yahak'uri yakuma k'aryata kansa da kansa akan abunda yafad'amata yanzu,,, koda yafita saiya taddata d'akin inna a kwance kan gado tarufe idanuwanta kaman tai bacci saidai yasan sam ba bacci takeba, haka yak'ura yayiwa inna saida safe yawuce,,,,"..

Washe gari tindawuri ta tashi bayan tahad'amasu breakfast sunci takaiwa malam nashi da inna yarage saura na Amadi kad'ai, harta ce bazata iya kaimasa ba saikuma ta d'auka tawuce izuwa d'akinsa,,,..

Cikin sallama tashiga d'akin koda tashiga yana kwance a kan kujera yana danne dannen system, d'agowa yai yakalleta sannan ya'amsa sallamar sai kuma yak'ura mata mayun idanuwansa,  tak'aramasa kyau sosai kayanda tasaka sun karb'eta sosai, gaidashi tai tareda duk'awa ta ajiye farantin abincin batareda tasakecewa komai ba tajuya tafita abunta,,,,"...

STORY CONTINUES BELOW

Around 10:00am dot sukabar k'auyen ZAGA suka kama hanyar yola Adamawa, saikusan 1:30pm sannan suka isa cikin garin kai tsaye gidan suka dosa,, suna isakuwa gate man yazo yabud'e masu gate driver d'in yashiga dasu, saida yakai gunda aka tanadar domin ajiye motoci sannan yatsaya sukuma suka fito,, tana fitowa bata tsayawa yin komaiba tawuce izuwa cikin gidan dasauri harda d'an gudu gudunta tana kiran sunan fatima,,,"...2

Fatima....! Fatima....!! Fatima....!!! tadinga kwalla mata kira, fatiman dake d'akin mai jego tana rik'e da baby jin muryar KUBRAH yasa tai saurin ajiye babyn tafito da gudu tana fad'in "oyoyo oyoyo da yar uwata kai maraba lale marhaba da mutan SUDAN" nan suka rungume juna cikin kewar junansu, d'agowa tai cikin dariya tace "ina mami na da Abbu na inakuma ya Ammar d'ina" dik suna nan k'alau mami tana d'akinta Abbu kuma yana office ya Ammar shima yana gun aiki. Kallonta tai cikin tsokana tace "toh baki tambayin yayankiba" dariya tai takaimata dukan wasa suka wuce izuwa cikin gidan,,,,"..

D'akin mami tafara zuwa ta gaidata sannan suka wuce gun maijego, cikin sallama tashiga d'akin tana murmushi tace "Aunty Salma mai jego barka da wuni ya baby" wani watsattsen kallo tamata ta yatsine baki tajuya fuskarta sannan tace "gatanan agabanki" tai maganar tanacigaba da aikinda takeyi, sam KUBRAH bata damuba saboda idan da sabo tasaba da halayyar da salma ke mata, d'aukan babyn tai tarunguma sannan ta zauna tana kallonta, babyn kyakkawa ce sosai kamarsu d'aya da mahaifiyarta, fita fatima tai tabarta acikin d'akin saboda KUBRAH indai taga baby ji take kamar tatace kamar ta d'auke tatafi da'ita,,,,..

Tana a zaune saiga k'awayen salma sunshigo cos mate d'inta daka gansu kasan yan duniya ne nagaske sai taunar cwingom suke kowacce tad'age d'an kwali gefe d'aya kaman karuwai, gaidasu KUBRAH tai cikin fara'ah sai d'aya daga cikinsu take "ke yar duniya waye sa'anki acikinmu wallahi shiga taitayinki yar bariki kawai kije ki nemi naki miji bazakiyiba saidai kizo kina mak'alewa mazan wasu karya kawai mara zuciya wato shine anzo suna koh daganan abarbad'amasa acikin abinci yaci akuma zubamasa acikin ruwan wanka amallakeshi koh toh wallahi karyanki tasha karya kigayawa bokanki k'awata tafi karfinki wallahi ta Allah batakiba" shuru tai tana sauraronsu dafarko bata fahimci abunda take nufiba sai daga baya, wasu kwallan bak'inciki ne suka zubomata saboda takasa cemasa komai,,,..

Wani kallo salma tamata sannan tafashe da kuka cikin kukan take magana "ai wallahi da'ace a gidannan kuke dakun tausaya mani yanda yake wulak'antani akan wannan yarinyar harda ceman wai ban iya girkiba ban iya kwalliya ba KUBRAH tafini iya komai" ai wallahi daina kuka k'awata dolene mu d'aukarmaki fansa dole ne mu ramamaki abunda aka maki wallahi. Itadai shuru tai tana sauraronsu can data kasa sai kawai ta tashi ta'ajiye babyn tafita dasauri,,,..

Tana fita tawuce d'akinsu cikin sa'akuwa bakowa acikin d'akin nantafada kan gado tana zubda kwallan bak'inciki, fatima ce tashigo ta taddata ahaka dasauri taje tad'agota cikin damuwa tana tambayarta abunda ke faruwa, sauri tai tashare kwallan sannan ta d'ago tareda k'ak'aro murmushi dik dan kartafahimci abunda ke faruwa saidai batasan dik abunda akai tajiba, kallonta tai tace "KUBRAH karki b'oyeman komai dan naji komai, KUBRAH inaso kisani Salma da k'awayenta sam basuda halayya takwarai kuma ya Abdallah yasanda haka biyayya ce kawai yayi ya Aureta amma badan yanasanta ba, KUBRAH inaso kisan kece zabin yaya Abdallah yadade yana sonki saidai yakasa furtamaki, nafahimci hakan ne lokacinda yake nuna tsintsar kishinsa agareki yahana kowa yazo gunki dasunan SO yahanaki tsayuwa da kowa tad'i ciki kuwa hadda d'an uwansa Ammar saboda haka karkiji tsoron Salma da shashaShun k'awayenta ki amince da tayin soyayyar yayan ki masoyinki mai k'aunarki tsakani da Allah kuma d'an uwanki, idan kikai haka natabbata zakisaka wannan ahalin namu acikin farinciki kuma zaki k'ara d'ankon zumunci a tsakaninmu please aminiyata ki amince dan Allah" shuru tai batace komaiba sai kwallah kawai datake zubarwa, can saita d'ago da fuskarta ahankali sannan tafara magana "Fatima inaso kisani salma bata bata damuna saboda idan da sabo nasaba da halayyarta Saidai matsalar itace shekaranjiya bayan ya Abdallah yaturaman letter dakuma sabuwar waya ya Amadi shima yafurtaman kalmar so shima yace yanasona fatima narasa yanda zanyi shin wazan amsawa tayin soyayya acikinsu kuma kema dakanki kinsan dikansu sun cancanci nasosu saboda kowannensu yataka rawar gani ga rayuwata abun yad'auren kai" murmushi fatima tai tareda rik'o hannayenta sanna tace "gaskiya hakane dikansu sun cancanci ki sosu amma shawararda zan baki shine kiyi ISTIHARA insha Allah dik wanda aurensa yake alkhairi agareki zaki gani acikin baccinki" numfashi ta sauke sannan tace "toh insha Allah zanyi nagode sosai y'ar uwata" Ah karki damu bakomai idan banmakiba wazanma, kinga tashi muje mami tabamu kud'in lalle da gyare gyare. "aa basai munje guntaba Abban mu yabani kud'i dazamuzo nayi dik abunda nakeso saboda haka shirya kawai muje bara nad'akko su kursum kamin ki shirya" ok toh badamuwa.. Nan tafita tabarta tana shiri,,,"..

Wani katafaren shagon gyaran jiki sukaje akamasu lalle da saloon yaran kuma akamasu lalle da kitso masha Allah sunyi matuk'ar yin kyau sosai musamman tauraruwar KUBRAH jan lalle akamata sumarta tasha gyara sai shining take, bayan sungama sai fatima takira saurayinta wanda akamasu baiko dashi wato Tajudeen yazo yad'aukesu yamaidasu gida,,,..

Around 4:00pm dot Aunty zinatu ta'iso yola nan suka hade anatafirar yaushe rabo su Islam angirma tasake haifar baby boy wanda yaci sunan Abbu wato UWAR amma suna kiransa da Affan,,,,"...

Da dare bayan sunci abinci sai suka had'e a falour sunashan fira kasancewar Abbu yadawo kowa na gida dik suna cikin falon amma banda Abdallah sai raba idanu take amma batagansaba gakuma Amadi da Ammar zaune amma bandashi,, tashi tai tafita tai cikin gida, tazo dai dai k'ofar d'akinsu zata wuce izuwa kitchen sai kawai taji anjanyota dak'arfi cikin d'akin,,,"..

Baki tabud'e zatai k'ara sai taji anrufemata baki sannan andatseta ga bangon ginin d'akin kusa da k'ofar, rintse idanuwanta tai zuciyarta na dukan tara tara, k'ura mata idanu yai yanamata wani irin shu'umin kallo yana murmushi ahankali yaduk'o da bakinsa dai dai kunnenta cikin wata iriyar murya mai taushi yamata magana cikin rad'a "sarkin tsoro bud'e idon nine" jin muryarda ko amafarki tajita tasan kota waye yasa tafara bud'e idanuwanta ahankali tana murmushi, tana bud'e idanuwanta saitai kicib'is da nasa aikwa dasauri tai saurin d'auke nata cikin jin wata'iriyar kunya, murmushi yai sannan yamatsa baya tareda rik'o hanunta sukazo kan gado yazaunardaita sannan yazauna,,,,..

Zama yai dab da'ita tareda k'ura mata mayun idanunsa yana murmushi yace "nasan kinga sak'ona koh" k'ara sinne kanta tai k'asa sannan tace "Eh naganiba" toh baki bani amsa ba kuma kinsan acike nake da zumud'in jin amsarki. Shuru tai can sannan tad'ago ahankali tace "Ya Abdallah inaso kabani d'an lokaci dan Allah insha Allah nanbada jimawaba zakaji amsa amma dai bayanzuba" shuru yai yana kare mata kallo tareda rungume hannayensa yana murmushi,, kallonda yake mata wata iriyar kunyarsa takejin nak'ara shigarta nan tak'ara sinne kanta k'asa tana murmushi, shima murmushin yai sannan yace "ok badamuwa nabaki nan zuwa jibi saboda banasan bikinmu yawuce nanda 1 month" jin abunda yafad'a yasa taisaurin d'ago da kanta ta kallesa cike da mamaki sai ya d'aga mata kai tareda fad'in "yea of course saboda haka ina sauraran amsarki nanda jibi" yana gama fadar haka yatashi yafita abunsa yabarta nan tana tinanin zancensa,,,"..

****Tinda sukazo har yanzu Amadi baisamu yayimagana da KUBRAH ba ganin irin ho inkula datake masa yasashi k'arayin dana sanin abunda yai saidai har yanzu yakasa k'aryata kansa garesa akan abunda yafad'a mata saboda shi har ga Allah kaunarta yake k'auna ta gaskiya,,,,...

Kwanansu biyu da zuwa akayi suna yarinya taci sunan UMMUL KHAIR suna mai dad'i wani abunda salma batasaniba shine KUBRAH ce tasaka wannan sunan, anci ansha wajen bikin su KUBRAH k'irjin biki can kake hangosu ita da fatima da k'awayensu sunyi kyau sosai suna rik'e da Ummul khair sunashan pic's,, saikusan 5:00pm sannan mutane suka watse yarage yan gida ne kawai suka rage,, da dare bayan tayiwa su khaleesat shirin bacci sai itama tai nata, wata y'ar rigar bacci ce tasaka iya guiwa pink color sai sumarta da tufke gu d'aya,,,"..

Bayan tagama sun kwanta sai itama ta kwanta, karar wayarta taji alamar message yashigo danhaka ta daukota tabud'e domin taganin abunda yashigo.....#/Vote

#/Share

#/Comment

'''AUFANA for life '''

  *I.W.A*🖊

Post a Comment for "GANI GA WANE CHAPTER B"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...