BAKUWAR FUSKA CHAPTER B - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BAKUWAR FUSKA CHAPTER B

BAKUWAR FUSKA CHAPTER B

- - Post a Comment

 BAKUWAR FUSKA CHAPTER B


A cikin mayafin lapayarta ta dukar da kanta. Misalin karfe takwas da rabi ke nan na dare, Haneefa da Saleemah suka taimaka mata ta shirya cikin riga da zani na atampa purple, sannan ta nada lapaya fara mai digo-digon purple. Ta yi matukar kyau sai wani irin ni'imtaccen kamshi ke fita daga jikinta.


"Taba kirjina ki ji bugun zuciyata Sally. Am afraid...wallahi ina jin tsoro." Ta fada jikin Saleemah hade da fashewa da kuka, cike take da rauni. Tsoro da fargaba sun taru sun cunkushe a duniyarta. Yanayin da take cikinsa, ita kanta ba ta san a wane mizani za ta ajje shi ba. Ba ta san a wane hali take ciki ba. Na farin cikin mallakar burin zuciyarta? Ko kuwa na bakin cikin kurkukun da ta kawo kanta da kanta? Fargaba take, tana kara hasko yanda duniya za ta murde mata, ta juye mata tamkar yanda ake juya waina. Duk farin cikinta take ji yana dunkulewa a wuri guda, yana neman barin zuciya da ruhinta, yana rikida izuwa kunci da bakin ciki.


"Haba MB! Muradin zuciyarki ne fa kika aura. Kukan na mene ne to? Yanzu lokacin farin cikinki ne. Sam kuka bai cancanci amaryar da ta auri burin zuciyarta ba."


Jin maganganun Saleemah take tamkar tana qara rura darma, wuta na fartsatsi a tsakanin kirjinta. Kirjin nata ya mata nauyi, ya za ta yi da shi? Ya za ta yi ta sauke wannan nauyin da take ji tun daga gefen haggu har zuwa gefen dama na zuciyarta?+


"An miki kwalliya amma kukan farin ciki ya sa kina neman bata ta ko?" Haneefa ta fada a daidai shigowar ta dakin, ta gama turara turaren wuta a duk gidan.


"Hanee kin san fa abun is not easy. Rabuwa da gida ba wasa ba ne. Fadawa sabuwar rayuwar kanshi abun kuka ne. Idan ba za ki iya rarrasarta ba ki mana shiru ni zan iya."


Tabe baki Haneefa ta yi bayan ta ajje burner ta hau gyaggyara kan dressing mirror. "To Allah ya bada ikon rarrashi kin ji. MB zan kawo bucket a cika mun shi da hawaye kafin wayewar gari."


Duk da cikin kuncin da take hakan bai hana ta yin dariya ta kai ma Haneefa dukan wasa ba. Haka suka hau gyaran gidan har ya zam tas, sai kamshi yake bad'ad'awa.


Karfe tara suka ce za su tafi. Cikin kuka ta jawo hab'ar rigar Saleemah "Me ya sa za ku tafi ku bar ni ni kadai?"


"Saboda ba za mu iya zaman jiran dawowar mijinki ba. Waye ya san sai yaushe zai zo? Gwara mu koma gida mu adana tsufanmu. Akwai gajiya ke ma kin sani." Haneefa ta fada cike da tausayin yanda kawarta ke kuka bilhakki.


"Ki yi hakuri Boobah. Dare ke yi ga shi gidajenmu ba kusa ba. Na tabbata ba da jimawa ba angon zai zo..." kafin Saleemah ta rufe baki ta jiyo sallamar su Khaleed. "Yauwa Alhamdulillah! Kin ga ga 'yan halak din nan ma. Hanee mu wuce ko?"


Kuka sosai Mahboobah ke yi, tana kallon su suka fita, ta qara qarfin kukan nata tamkar karamar yarinya.


Fitar su parlor sukaci karo da Khaleed zaune Ishraq a tsaye suna magana.


"Kawayen amarya ya na ga har kun fito tun ba a sa ango daki ba?"


Kallon junansu suka yi, kafin Haneefa ta dan murmusa. "Dare ke yi ne abokin ango. Ga mu duk mata ban san wa zai taimaki wani ba idan muka hadu da abun tsoro a hanya. Gwara ma ni a kan wanna farar kurar." Ta kalli Saleemah tana dariya.


Dariya Khaleed ya yi sosai har da dafe ciki. "Kin gan ki da tsokana. To yanzu dai jira za ku yi mu fita tare. Duk da na ga da motarku a waje sai in zama dan jagora ina gaba kuna biye da ni."


STORY CONTINUES BELOW

Ba su da wani zabin da ya wuce su koma wurin Boobah. Tana ganin su ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Ba ta gaji da ganin su ba, shi ya sa ta ji dadi sosai da ta jiyo yanda suka yi da Khaleed Zannah.


*

"Wannan wane irin wulakanci ne da cin fuska Khaleed? A gaban wadannan yaran kake wani cewa a saka ango daki. Waye za a sa a dakin? Ko na fada maka ban san hanyar shiga ba ne?"


Banza Khaleed ya yi da shi. Ya dauki babbar ledar da suka shigo da ita. Kayan tea ne, ya jera su a kan dining table sannan ya dawo ya zauna.


"Bari in raba muku kazar kai guda ita guda. Lemon ma ga nata nan bari in kira kawayenta su kai mata. Don na san in kai ne sai dai ledar nan ta kwana a haka. Ko kuma ka cika cikinka ita kuma ka bar ta da yunwa." Shi ke kidanshi yake rawarshi. Ishraq dai bai ce komai ba sai latsar wayarshi da yake yi ya kishingida bisa 2 seater.


Khaleed ya kwala kiran Haneefa, ta fito ya mika mata ledar Mahboobah sannan ya ce su fito su wuce dare na yi. Wani sabon kukan Mahboobah ta fasa, tana jin wani irin takaici a kasan ruhinta.


Bayan sun fita Ishraq ya je ya rufe gate, sannan ya dawo ya rufe kofa. Kai tsaye kitchen ya nufa ya dauko plate, kazarshi ya juye a ciki ya kwance foil din da aka nade yaji ya barbada a kai. Da ma yunwa yake ji ko wurin reception bai iya cin komai ba. Sai da ya ji shi ya yi nat sannan ya mike ya je ya wanke hannunshi ya dawo. "In kwashe plate da kayan nan ma ko in bar su?" Ya fada cikin tunani. "Mtsww! Ba ma zan kwashe ba. Tun da ga baiwata an kawo mun har gida, ita za ta kwashe idan ta matsu." Cikin halin ko'inkula ya wuce dakinta. Babu ko sallama a bakinshi ya kalli yanda ta lumar da fuskarta a cikin cinyoyinta, tana sakin wani irin kuka mai ban tausayi.


"Ehem ehem!" Ya yi gyaran murya don har a lokacin ba ta san da wanzuwarshi a dakin ba. Ta dago ta kalle shi, tana jin tsananin bugun zuciyarta na hauhawa. Ta kafe shi da ido ko kyaftawa ba ta yi. Kukan ma ta neme shi ta rasa sai saukar ruwan hawaye kawai take ji.


"Idan ke mayya ce sai dai ki ci kanki KK. Kurwata ta fi karfin karamin alhaki irinki. Ban shigo don ki tsare ni da kallo da wannan mayin idanuwan naki masu kama da na mujiya ba. Shigowa na yi in miki albishir da kalar rayuwar da kika jefo kanki da kanki a karkashin inuwar Ishraq Sulaiman." Ya tabe baki yana mai matsowa kusa da gadon da take zaune a kai. Ya saki dariyar gefen lebo wadda ke kara fitar da ainahin kyawun fuskarshi.


"KK!" Ya murza yatsunshi biyu. "Ki sani cewa ba rayuwar aure kika shigo yi a gidana ba. Ki dauka a ranki cewa kin zo yi wa Ishraq Sulaiman bauta ne. Kin zo wurin da zai qarisa tumurmusa jalli-jogar zuciyarki ne. Gidana ya fi kurkuku, domin kuwa duk tsananin kurkuku akwai rayuwar nishadi a ciki koda a tsakanin fursunoni ne. A nan gidan babu ke babu nishadi KK. Ke da nishadi kun yi hannun riga tun daga lokacin da aka shaida daurin aurenmu. KK, ke ce macen da ta shiga tsakanina da farin cikina, Ameerah Muhammad. Ba zan taba yafe miki ba a kan haka. Kin zame mini karfen kafa, shi ya sa na mayar da sunanki KK. Na aure ki ba don na kasance da ke a matsayin matar aurena ba. Na aure ki ne don auren naki ne kadai rufin asiri da farin cikina a daidai lokacin da mahaifiyata ta fara fushi da ni. Sannan a karshe, ki sani gidana babu mai gadi, babu 'yar aiki, sannan babu almajiri mai hidima. Ke ce mai gadin, ke ce 'yar aikin, hakazalika ke ce almajirar gidan Ishraq Sulaiman." Daga fadar haka ya fara takawa domin barin dakin. Har ya isa bakin kofa kuma ya juyo ya kalle ta, "Ba zan fasa neman Ameerah ba har sai ranar da numfashina ya tsaya, zuciyata ta daina bugawa. Duk kuwa ranar da na gano ta, ki daga hannu ki gode ma Allah, domin wannan ranar ce za ki fita daga ka-fi kurkukun da kike ciki." Bai kara fadin komai ba ya fice ya bar dakin cike da tsanar ganin Mahboobah.


Duk maganganun da yake kanta a duke yake tun daga sadda ya kira idanuwanta masu kama da na mujiya. Sannu-sannu take yin kuka sai yanzu da ya fita ta fasa mai kara, tana mai rasa abin da za ta yi a daidai wannan lokacin. Ji take tamkar ta hadiyi zuciya ta mutu. Tabbas da a ce an halalta idan kunci ya ma mutum yawa ya kashe kanshi, to da babu abin da zai hana Mahboobah Bukar kashe kanta. Don kuwa ta gwammaci mutuwa a kan halin da take ciki. A duk cikin maganganun Ishraq babu wadda ta fi jin zafinta sama da sabon sunan da ya yi mata. Da farko da yana kiran ta KK ta fada kogin tunanin maanar sunan, sai dai ko a sannan ta san ba sunan arziki ba ne ba face na zallar wulakanci. Sai kuwa ga shi ta tabbata din. Karfen kafa shi ne sunan da mijinta na aure ke kiran ta da shi.


Ta ja majina hade da mikewa. Kayan jikinta ta cire, akwatinta ta bude ta ciro rigar bacci ta saka. Ta shiga toilet ta wanke kwalliyar da kuka ya gama dame ta. Yunwa take tsananin ji. Ta kalli ledoji guda biyu da plate da cup din da su Haneefa suka ajje mata. Tana son ci, sai dai damuwa ta taso ta a gaba, tana jin nauyin kirjinta kamar ba zai iya barin ta hadiyar abinci ba.


Wutar dakin ta kashe hade da jawo wayarta. Tana bude whatsapp ta ci karo da hotuna masu yawa Khaleed ya turo mata. Bayan ta bude su ta gaggauta kashe data gudun surutun mutane, ta san dole za a magantu don ba yanda za a yi amarya daren farkonta a gan ta a online.


Kallon hotunan take, tana ganin yanda suka yi wani irin kyau mara misaltuwa. Babu wanda zai gan su ya ce ba auren soyayya ba ne ba daga duka bangarorin. Kowanne Ishraq ya yi murmushi, a wani kuma ya yi dariya har hakoranshi sun bayyana. Wanda suka fi burge ta su ne wadanda suka kalli juna ita da shi. Duk da a cikin kallon junan da suka yi babu abin da ta hanga a tsakiyar idanuwanshi face zallar tsana da kiyayyarta.


Ta share hawayenta. Kallon hotunansu da ta yi ya mantar da ita bakaken maganganunshi, a lokaci guda kuma suka sake dawo mata, ta gyada kai hade da kashe wayar ta kwanta bacci.


End of chapter


Duk ya kuke ya iyalai? Unexpected post, right?💃🏻


Afwan yau dai ba ku samu da yawa ba. A yi maleji da wannan a tari next post in shaa Allah.


Allah sarki! Mahboobah kina ruwa tsundum. I pity you😤1


Princess Amrah

RAZ 2Kunci, bakin ciki, fargaba da bacin rai su ne cunkushe a zuciyar Mahboobah Bukar tun da aka daura musu aure watanni hudu da suka gabata. Tsakaninta da Ishraq ta yi mishi girki ya kwasa, saboda Mahboobah gwana ce a girki, yayin da Ishraq kuma ya kasance gwani a bai wa ciki hakkinshi. Da sassafe yake fita, ba ta ma ganin shi. Kuma ba zai dawo ba har sai sadda ta yi bacci. Iyaka ya je dining table ya zuba abinci ya ci. Kwanonin ma a nan zai bar su har safe ta sake kwashewa. Idan wani cefane ko nama ya siyo zai ajje mata a fridge, washe gari ta gyara ta mayar a fridge din. Cika irin wadda amare ke yi sam babu ita ga Mahboobah. Ta rame sai zallar kashi, kamar wacce ta shekara rabon da ta ci abinci.


Hawayen fuskarta ta share. Yau sati biyu ke nan rabon da ta sanya shi a idanuwanta tun ranar da suka yi zuwan karshe gidan Mami.

Ta tashi da matsanancin zazzabi mai zafi hade da ciwon kai, ga shi ko kwayar pain reliever ba ta da ita hakan ya sa zazzabin ya kwantar da ita sosai ko sallah da kyar ta iya tashi ta yi a zaune. So take ta tashi ta girka mishi abinci kamar yanda ya umurce ta da ba ya son fashin girki. Sai dai ba za ta iya bah. Ba ta da karfin ko mikewa a saman kafafuwanta balle na shiga kitchen ta girka abinci. Sai dai kuma me, tana tsananin tsoron tashin hankalin da zai iya doso ta a lokacin da Ishraq ya zo bai samu abinci ba.

Yunkurin mikewa ta yi amma jiri ya mayar da ita. Jikinta tauna yake yi sosai ruwan hawaye sai kwarara yake yi mai tsananin gumi. A haka ta samu wahaltaccen bacci ya dauke ta.+


*

Kamar yadda ya saba koyaushe, ya paka motarshi ya bude kofa ya shigo. Yunwa yake ji sosai don shi a ka'idarshi ba ya cin abincin waje, sai dolen doliya. Da farko ya tsiri komawa wurin Maminsa ya ci, zuwan shi biyu ta taka mishi burki. Ta ce ya koma ya rinka cin na matarshi tun da dai ba ta da naqasu wurin iya girki. Ta kawo mata ta ci ta ji ta iya ba sau daya ba ba sau biyu ba. Wannan dalilin ne ya sa ya tilasta wa Mahboobah yi mishi girki.


Briefcase dinshi ya kai daki, ko kayan jikinshi bai rage ba ya fito parlor tare da zarcewa dining area. Wayam ya gani in banda canister set da ke girke a tsakiyar table din na su sugar da sauran kayan tea. Da mamaki ya kariso isowa, da gaske babu komai a kai. Ya nufi kitchen a tunaninshi ko ta yi ne ta manta ba ta kawo mishi ba. A can din ma babu. Ya tsaya tunanin matakin da zai daukar mata, yana hasko yanda zai shaki wuyanta ta fada mishi me ta taka da yau ba ta mishi girki ba duk yunwar da ya kwaso?


A cikin wahaltaccen baccin da take yi ta jiyo hargaginshi. Bai cika daga murya ba ko masifarshi zai mata cikin sassauta murya yake yi. Sai dai wannan ya sha bamban. Daga muryarshi yake yana fadin "Ke! KK! Baccin uban me kike? Waye ya ba ki damar yin bacci ba tare da kin girka mun abinci ba? Ko kuwa kayan miyar da aka saba kawowa daga gidanku ne suka kare? Ehh, daga gidanku mana. Don in da ni na siyo na kawo ai ba za ki qi yi mun girki ba."


Yanda zazzabi ya ci jikinta ba ta jin ko magana za ta iya yi mishi. Ta dago fuskarta ta kalle shi, idanuwanta sun kada sun yi jajur saboda azabar ciwo da ta kuka.


"Ki tashi KK! Ki tashi ki dora mun abinci ko kuma in fitar da ke daga gidan nan ki kwana a kofar gida shi ne hukuncinki! Idan kika bari na sake magana sai dai ki ji saukar yatsu a fuskarki."


A cikin dukkan tashin hankalin da ya mamaye Mahboobah, ta rasa wane ne ya fi dan uwanshi ciwo. Zafin ciwon da yake addabarta? Ko kuwa zafin bakaken maganganun da suke fita a tsakanin labban Ishraq Sulaiman? Kanta a kasa, zuciyarta na dokawa da dukkan karfinta a kowacce gaba ta jikinta. Muryarta a raunane, ta dago ta kalle shi a karo na biyu,


"Ba zan iya ba Likita." Ta share sabon hawayen da ya fito mata.


"Yanzu ke har kanki ya yi kwarin da za ki kalle ni cikin ido ki fada mun wai ba za ki iya ba? Tukunna ma, wai waye ya ba ki damar kwanciya ba tare da kin gama aiwatar da aikinki ba? Kitchen dinki kanshi ba ki gyara shi ba. Daki babu inda kika share amma kin zo kina bacci. Wa ya ba ki wannan damar KK?"


STORY CONTINUES BELOW

Tsoro da shakkunshi sun taru sun cunkushe a zuciyarta, a haka ta daure ta tashi zaune. Me za ta ce da shi ne? Ta hau tunani. Tun da har tsananin tsana da kiyayyarta ya sanya shi kasa fahimtar ba ta lafiya, to kuwa ba ta da sauran hanyar bayyana mishi larurinta. Sai kuma wani tunani ya zo mata. Ta daure ta mike ta tafi luuuu kamar za ta fadi, ta dafe gado a hankali ta isa gabanshi.

Kallon ta yake yana son sanin abin da take nufi, bai yi aune ba ya ji ta kamo hannunshi ta kanga a goshinta. Tamkar zafin wuta haka ya ji. Lamarin ya ba shi tsoro matuka, domin kuwa sosai temperature dinta ta hau. Ga yanda ya ji alamun jijiyoyin kanta duk sun tashi, wanda ke tabbatar da cewa tana fama da matsanancin ciwon kai.


Ba ta sake cewa uffan ba daga nan, ta tattaka a hankali ta koma ta kwanta hade da jawo bargonta ta rufa, jikinta sai rawa yake, hawaye na ci gaba da sauka a saman kumcinta.


Bai ce komai ba ya fice daga dakin zuciyarshi cike da rauni. Duk tsananin kiyayyar da yake mata ya tausaya ma yanda ya ji jikinta. Shi mutum ne mai matukar tausayin mara lafiya, shi ya sa ko a asibiti yake tausaya wa patients dinsa.

Ya jera tsaki ya fi goma. Yunwa yake ji bai ma san me zai yi ba. Ya je ya dauko medium bowl ya hada madara da sugar da ruwa sannan ya zauna yana shan cornflakes. Tun da ya siyo shi kimanin watanni hudu da bikinsu, ba a taba sha ba sai yanzu da ya fasa. Bayan ya gama ya mike jiki ba kwari ya wuce dakinshi.


Washegari ya shirya kamar yanda ya saba fita da sassafe, ya hau motarshi sai dai kai tsaye bai nufi asibiti ba sai ya je wata Pharmacy da ba ta da nisa sosai tsakaninta da gidansu. Ya sayi magunguna, ya mata mix na typhoid da na malaria sannan ya hada da panadol. Ya dawo gida. Ji yake kamar yada kai ne ya bude dakin ya ba ta maganin. Ya ja tsoki sannan ya bude. A zaune ya same ta bakin gado sai yunkurin amai take yi, sai dai babu komai a cikinta da za ta iya hararwa. Hawaye sai jerangwama suke a bisa kumcinta. Jikinta sai rawa yake yi. Fita ya yi daga dakin sai ga shi da bottle water, ya ballo magungunan sannan ya ajje su a gabanta hade da ruwan.

"Ba a shansu idan ba a ci komai ba." Maganar da ya samu ya ci karfin zuciyarsa ya iya fadi ke nan sannan ya mike a saman kafafuwanshi ya doshi waje inda ya baro motarshi.


Yanda ya ajje magungunan a haka ta bar su. Ko kadan ba ta da karfin da za ta iya tashi ta nemi abinci. A zaunen ma jiri take gani. Sai dai kuma, yanda ciwon yake nukurkusarta ya sa ta ga gwara ta sha maganin ko da babu abinci a cikinta. Wannan shawarar ta dauka, ta watsa magungunan a bakinta ta bi da ruwa ta shanye.


Kusan awa uku da shan maganin Mahboobah ta fara jin wani irin ciwon ciki mai tsanani. Ta hau juye-juye tana ambatar sunan Allah, tana neman agaji. Kuka take sosai, tana jin tsananin ciwon cikin tamkar ya zarce na zafin zazzabin da take yi.


A cikin wannan halin Fareedah da ta iso ta yi ta knocking ta ji shiru, tana tura kofar ta ga ashe a bude take. Dakin kaca-kaca babu gyara. Ga abubuwan da Ishraq ya yi amfani da su duk a kan dining table bai kwashe ba. Ta hau mamaki, domin kuwa ta san halin yayarta da tsafta, ba dai a ga kazanta ba a komai nata. Cike da mamaki ta hau kwada sallama, amma ta ji shiru. Ta nufi kitchen nan ma duk a hargitse. Kai tsaye ta zarce dakin Mahboobah. Tun kafin ta isa ciki take jiyo nishin Mahboobah sama-sama, sunan Allah bai yanke daga tsakanin labbanta ba.


"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un!" Da gudunta ta iso gaban 'yar uwarta. "Yah Boobah me ya faru da ke? Lafiya? Me yake damun ki? Ya Salaam!"


Gyada kai kawai Mahboobah ke yi, ta kasa fadin komai rikon cikinta take yi tana juye-juye.


"Yah Boobah mu je asibiti. Don Allah ki mike in kai ki da motan Mommy na zo da ma." A rikice take wannan maganar, ta jawo hijabin Mahboobah ta fara kokarin saka mata. Daga nan ta kama ta tana son ta mikar amma ta kasa, ta dora hannunta a kai cike da tashin hankali tana neman mafita. Ba za ta iya daga Mahboobah ba da sai ta dauke ta. Ga shi babu mai taimako unguwarsu tsit take. Ga ciwon na dad'a ta'azzara.


Kamar da wasa ta jiyo muryoyin mutum biyu, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tabbatarwar da ta yi cewa gidan ne suka shigo. Da sauri ta fita parlor ta same su. Mami ce da aminiyarta Hajiya Saratu. Ba ta ko gaishe su ba take nuna musu hanyar dakin Mahboobah da hannu, tana yi tana kuka.


"Subhanallahi! Reedah lafiya? Me ya faru?"


"Mami...Yah Boobah ba lafiya. Na zo na same ta unconscious na ce ta tashi mu je in kai ta asibiti ta kasa. Ni kuma ba zan iya daukarta ba kar in kayar da ita."


Tun kafin ta rufe baki Mami da Hajiya Saratu suka nufi dakin. Wannan shi ne zuwan Mami na farko gidan. Tun bayan biki Ishraq ke ta bin kanta ta zo ta ga gida amma kara da kawaici suka hana ta. Ita ma kanta Mahboobah ba yanda ba ta yi ba da ita a kan ta zo amma ta ki. Karshe dai Hajiya Saratu ta taso ta a gaba ta ce ya kamata ta zo. Shi ne suka yanke shawarar yi musu zuwan ba zata don kar ta fada musu za ta zo su hau yi mata wani shiri. Alhali ita ganin gida kawai ta zo.


Cike da tashin hankali suke su duka ukun. Hajiya Saratu ce ta wawuri Mahboobah kamar yanda ake daukar jarirai. Da gudu Fareedah ta je ta bude musu bayan motarta, aka kwantar a ciki. A tsawon wannan lokacin ma kukan da Mahboobah ke yi ya kafe. Ta yi shi ta yi shi har ta nemi hawayen ma ta rasa. Sai dai yanda fuskarta take a kumbure, dukkan wanda zai kalle ta zai gane cewa ta yi kwanan da ya wuce biyu tana yin kuka.


Ko tsayawa rufe gidan ba su yi ba a haka suka fice, bayan sun fita ne Reedah ta karbi makullin motar Hajiya Saratu ta saka motar a cikin gida sannan ta rufe gate din ta dawo suka tafi.


Tun da suka shiga motar Mami ke kiran Ishraq a waya bai dauka ba yana theatre. Ranta ya yi kololuwar baci. Ta yaya zai tafi ya bar diyar mutane a wannan halin? Da gani an san ta jima tana fama da ciwon, sai dai ta tabbatar da babu kula. Don da da kula ba zai bar ta ita kadai ba ko da kuwa a ce a gida ne yake mata treatment.


Dialogue hospital suka nufa, inda Hajiya Saratu suke da family card don komai ya zo musu a saukake, kai tsaye aka karbi Mahboobah emergency.


Cikin sa'a Mami na gwada sake kiran Ishraq ya dauka. Cike take da haushinshi ya sa ko gaisuwarshi ba ta amsa ba.

"Kana ina?"

"Ki yi hakuri Mami kina ta kira na, na shiga theatre ne fitowa ta ke nan yanzu haka ko kaya ban canja ba."


"Ka zo yanzun nan ka same ni a Dialogue Hospital!" Daga haka ta tsinke wayar tana tunanin hujjar karyar da zai zo mata da ita.


End of chapter


Assalamu alaikum warahmatullah! Ya kuke ya kwana biyu ya iyali? Fine in shaa Allah. It's Princess Amrah with chapter 20 of BKF. Happy?


Wannan zama na Ma'ish anya kuwa? Rayuwa za ta dore miji ba ya kaunar matarshi? Wai me maza suka dauki domestic violence ne?😓mace ta wuce wannan, domin kuwa ita ce jin dadin namiji. Ita ce silar zuwan shi duniyar ma baki daya. Cin zarafin mata na daya daga cikin manyan abubuwan da suke lalata ma mata rayuwa. Yake addabarsu, yake kashe future dinsu. Kuma an fi samun irin wannan matsalar daga wurin mazan Hausawa? Why? This is not right😞


Ko ya Ishraq zai kare da Maminsa da ta dauki soyayyar duk duniya ta dora ga Mahboobah?


Princess Amrah

RAZ 2Gudu yake sosai, yana yi yana tunanin dalilin daure mishi fuskan da Mami ta yi, da kuma neman gaggawar da take mishi. Ko kadan bai kawo komai a ranshi ba, saboda bai yi tunanin za ta je gidanshi ba a daidai lokacin.


A parking space ya paka motarshi, tun a nan ya tsorata yin tozali da motar Mommy da ya yi. Bai gama tabbatar da hasashenshi ba sai da ya hango Fareedah wurin pharmacy din cikin asibitin. Ya dafe kanshi cike da tunanin abin da Maminshi za ta tarbe shi da shi.


A reception ya same su zaune su duka biyun hankali ba a kwance ba. Kadan ya hana idanuwan Mami su kawo ruwa. Tunanin halin da Mahboobah ke ciki kawai take yi.


"Sannunku Mami." Ya fada sukuku jiki babu kwari. Banza da shi Mami ta yi, sai Hajiya Saratu ce ta amsa mishi tare da tambayarshi ya aiki.


"Alhamdulillahi Umma. Waye ba lafiya ne?"


Sai a sannan Mami ta dago ido ta kalle shi cike da jin haushi ta yi kwafa tana dauke kallon ta daga gare shi.


"Ishraq kana nufin ba ka san halin da matarka take ciki ba?"

"Umma...uhm na san dai na fita na bar ta tana zazzabi. Bayan shi ban san tana fama da wani ciwo ba."


"Haba Ishraq! Kana likita za ka yi sakaci har ciwon matarka ya yi ta'azzarar da za ta fita hayyacinta? Me yake damun ka? Aikinka ya fi ta muhimmanci da daraja? Ni ban san ka da wannan halin ba. Ishraq din da na sani yaro ne mai tausayi da kular mara lafiya."+


Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya zauna a kusa da Hajiya Saratu. Ya saci kallon Mami ya ga ba ma ta shi take ba. Ya ce, "Wallahi Umma zazzabi na san tana yi, kuma kafin in fita da safe na siyo mata magunguna."


"Da ka ba ta magungunan ka tsaya ka ga ta sha a gabanka?" Ta jeho mishi tambaya. Saboda da a ce ta sha maganin da ciwon bai tsananta haka ba.


"Ina sauri ne na makara, sai na balli maganin na ba ta da ruwa na ce mata ta ci abinci kafin ta sha, ni kuma na tafi Office ina da aikin gaggawa."


"Shi ke nan Ishraq. Allah ya kyauta gaba. Matarka na can yanzu haka likita na kanta. Kanwarta Fareedah ta je gidan ta same ta tana ta nurkususun ciwon ciki. A cikin wannan halin mu ma muka je. Shi ne muka gaggauta kawo ta nan asibitin."


Kasake ya yi, hannunshi rike da habarshi yana tunanin rashin kyautawarshi, ga shi har Maminsa tana fushi da shi. Sosai ya kara jin haushin abin da ya aikata. Sai dai kuma ya zai yi? Mai faruwa dai ta riga da ta faru.


After 4 hours (Bayan Awa Hudu)


Da sunan Allah ta bude bakinta, ta daga kai ta ga drip din da ke makale ana kara mata. Sai a yanzu ta tuna da halin da ta shiga ciki wanda har ya gusar mata da tunaninta.

Fareedah ta yi sauri ta iso gare ta, fuskarta kunshe da murmushi ta furta "Alhamdulillah! Muna ta jiran farkawar ki Yah Boobah. Bari in je in fada ma su Mommy." Da gudunta ta fice daga dakin, a lokacin har dare ya yi. Babu yanda Mommy ba ta yi da su Mami ba a kan su tafi gida su huta amma Mami ta ce sam ba ta san da wannan ba. Ba za su tafi su bar Mahboobah a wannan halin ba har sai sun ga farkawar ta.


Ganin yanayin da Fareedah ke ciki ya sa tun ba ta furta abun da ya kawo ta ba suka fahimta. Dukkansu suka kara yin godiya ga Allah tare da bin bayanta.


Murmushin karfin hali Mahboobah ta rinka sakar musu, babban burinta shi ne su samu kwanciyar hankali, saboda a yanayin da ta gan su ta tabbatar ba su a kwanciyar hankalin.


STORY CONTINUES BELOW

"Na ji sauki sosai Alhamdulillah!" Ta fada murya kasa-kasa, da murmushin da iyakarsa bisa labbanta.


"To Alhamdulillah ai haka ake so. Allah ya kara miki lafiya kin ji. Ki yi hakuri da kalar halin mijin naki. Ki yi hakuri da ko'inkula dinshi Mahboobah. Na san halinshi sarai na san waye Ishraq. Na san kina hakuri amma ki kara a kan wanda kike yi kin ji, wata rana sai labari." Mami ce ta yi wannan maganar, cike da tausayin Mahboobah.


"Ba fa laifinshi ba ne Mami. Kafin ya fita sai da ya ba ni magunguna, kuma ya tabbatar mun da kar in sha su sai na ci abinci, ni kuma ban ci abincin ba na sha. Shi ne tun bayan nan ciwon ciki ya turnike ni. Ko kadan ba shi da laifi Mami, laifin nawa ne."


A daidai shigowar shi dakin ya ji maganganun da ke fita daga bakin Mahboobah. Ya daga kafada alamun ko a jikinshi, sannan ya karisa shigowa cikin dakin.


"Sannu Mahboobah. Ya karfin jiki?" Ba za ta iya rike yaushe rabon da Ishraq ya kira sunanta ba. Karfen kafar nan dai da ya saka mata da shi yake kiran ta. Amma saboda ganin idon mutane yau da sunanta na yanka ma yake kiran ta.

Ta yi kokarin share guntuwar kwallar da ta sauko mata, "Na ji sauki sosai." Ta ba shi amsa cikin jarumta, ba ta so mutanen da ke zagaye da ita su fahimci akwai wata b'araka mai girma a tsakaninsu.


"Sannu Allah ya kara lafiya. Kin ci abinci? Me kike so a siyo miki? Yanzu me yake miki ciwo?" Duka a jere Ishraq ya zubo mata wadannan tambayoyin, yana yi yana satar kallon Mami, don ita yake yi da ma, yana so ya wanke kanshi ne gare ta, kuma ya tabbata Mahboobah ba za ta watsa mishi kasa a idanuwa ba.


Tsabar al'ajabi ma kasa amsa mishi ta yi, ta kalle shi tare da kawar da kallon ta, ta gaza furta komai sai al'ajabin duniyanci irin na Ishraq Sulaiman take yi.


"Okay ba ma sai kin fada ba, na san me kika fi so. Ina ga, Ummah ko za mu je in sauke ku gida? Na ga dare ya yi, kuma tun da ta ji sauki gobe idan Allah ya kai mu sai ku dawo. Idan na sauke ku zan siyo mata abinci."


Hajiya Saratu ta jinjina kai. "Haka ne to bari mu tashi. Hajiya, sai mu ce Allah ya kara lafiya. Mahboobah sannu kin ji. Sai gobe da yardar Allah za mu sake dawowa mu duba ki. Fareedah..." ta mayar da kallon ta gare ta, "Ki tabbatar da ta ci abinci kin ji, sannan ki kira nurse ta bata magunguna ta sha. Ki kula da ita sosai."


Mommy ta tashi ta raka su har bakin mota tana yi musu godiya, a ranta tana jinjina halin karamcin mutanen biyu, tare da yin allawadai da halin Ishraq, Fareedah ta fada mata komai game da halin da ta samu Mahboobah a ciki. Ta tabbata maganar da Mahboobah din ta fada ta yi ne kawai don ta kare shi, ba ta son laifinshi ba ta so kowa ya ga laifinshi.


Hajiya Saratu ce zaune a gaban mota Mami na baya, kai tsaye ita ya fara kaiwa gida, ya ce zuwa safe zai kai mata motarta bayan ta ba shi makullin, sannan kai tsaye ya wuce gidan Mami. Ko uffan bai shiga tsakaninsu ba har suka iso gida. Bayan ta fita ya bi bayanta har parlor. Ta wuce dakinta, ta yi wanka ta saka kayan bacci sannan ta dawo parlor. Ta same shi zaune inda ta bar shi.


"Dare ya yi ba za ka tafi ba?" Ta fada ba tare da ta kalli ko inda yake ba.


"Mami ba zan iya tafiya ba bayan har yanzu ba ki mun magana mai dadi ba, kina fushi da ni. Hankalina ba a kwance yake ba, ba zan taba samun nutsuwar zuwa gida ba."


Ta sauke ajiyar zuciya tana fuskantarshi. "Ishraq, duk wani fushi ko bacin rai da zan nuna maka, ba wai yana nufin ina tsana da tsangwamarka ba. Ka auna sosai ka kuma dora lamarin a kan mizani. Idan a kan kanwarka wannan abun ya faru ya za ka ji? Ranka zai yi fari ko kuwa zai yi baki? Sannan wace irin dauka za ka yi wa mijin kanwar taka? Kana tunanin duk wani uzurinshi zai karbu a wurinka?"


STORY CONTINUES BELOW

Shiru ya yi bai ce komai ba, ya sunkuyar da kanshi kasa, yana maraba da duk wani fada nata, in dai fadan zai sa ta yafe laifukanshi.


"Mahboobah yarinya ce mai karamci da mutunci, wacce ta samu ingantacciyar tarbiyya. Za ka kara tabbatar da hakan idan ka tuna cewa ta rufa maka asiri a asibiti, wanda ta cikin kwayar idonta na hango rashin gaskiyar maganarta. Ta kara shiga raina, domin kuwa duk macen da ke kokarin rufe asirin mijinta, rufe sirrin aurenta to mace ce ta gari abar alfahari." Ta gyara zamanta tana mai saita gannanta gare shi. "Ishraq, ka ji tsoron Allah! Idan har ka san akwai wani nau'i na zalunci ko daukar alhaki da kake ma yarinyar nan ka sani fa Allah ba zai bar ka ba. Yarinyar nan marainiya ce, amana take gare ka, gare mu baki daya. Idan ka so ka ci amana, ruwanka! Ni dai nawa hakkin shi ne in tunasar da kai, ka dauka ko ka watsar aiki ya rage naka." Ta kai karshe tana kokarin mikewa.


"Mami...don Allah ki dawo ki zauna ki ji. Ni fa babu abin da nake yi mata, hasali ma zaune muke cikin kwanciyar hankali babu wata matsala a tsakaninmu. Wannan din ma duk abin da na fada muku haka aka yi. Kuma kun ji daga bakinta ma."


Gyada kai Mami ta yi. Ta rasa yanda aka yi ta kasa gamsuwa da batun Ishraq. Sai dai ta nuna mishi ta yarda. A karshe ta saka mishi albarka sannan ya mike ya mata sallama hade da barin gidan.


A hanya sai sake-sake yake yi. Yana jin tsanar Mahboobah na dad'a ninkuwa a zuciyarshi. Tunani yake ta yanda karamar yarinya kamar ta take neman shiga tsakaninshi da mahaifiyarshi. Shi kuwa komai kusancinshi da mutum ya nemi shiga tsakaninshi da Mami, to tabbas zai rufe ido ne su yi batala.


Da tunani kala-kala ya isa gida. Yana jin sassauci a cikin zuciyarshi. Ko ba komai Mami ta yafe mishi ta daina fushi da shi.


Washe gari da safe likita ya shigo ward round, biye da shi nurse ce wadda ke rike da files din mutane.


"Mahboobah Bukar?" Ya fada yana kallon ta. Ta daga mishi kai.


"Okay! Ya karfin jiki?"


"Alhamdulillah!" Ta ba shi amsa tana kokarin tashi zaune.


"No kwanta abunki. Yanzu me kike ji? Me yake miki ciwo?"


"Zazzabi da ciwon kai ne har yanzu."


"Shi fa cikin ya daina ciwo?"


"Eh ya daina. Zazzabin dai ne ko cikin dare sai da na yi. Kaina ma yanzu haka ciwo yake yi."


"Kar ki damu duk za su warke in shaa Allahu. Su kadai ne kike ji ko da saura?"


Ta dan yi jim, kafin ta ce "Komai na ci sai na yi amai, babu abin da yake zama a cikin. Ga ciwon mara da na tashi da shi mai tsanani, kuma ba lokacin period dina ba ne."


"Eyyah sorry kin ji. Are you married? (Kina da aure?)"  Ta sunkuyar da kanta hade da jinjina kai.


"Okay za a yi miki PT. It's too late yanzu a yi na fitsari saboda da early morning urine (fitsarin farko) ake amfani. So za a yi miki na jini may be you're pregnant. Idan hasashena ya tabbata akwai possibilities guda biyu da za su iya kawo miki ciwon marar. Number 1 is common ga pregnant woman, because mahaifa idan tana daidaita kanta ana iya samun ciwon marar. Number 2 shi ne damuwar, idan ya kasance magungunan da kika sha jiya ne suke neman illata abin da yake cikin cikin naki. Kin san ba kowanne irin magani ba ne mai juna biyu take amfani da su. Ba wuya su yi leading to miscarriage musamman idan cikin karami ne. Sha let me confirm first." Ya dan tauni lebenshi. "When last kika ga period naki?"


Cikin jin nauyi Mahboobah ta ce "Ko last month ma na yi. 3 weeks ago."


Ya juya ga nurse ya ce " ki je nurses station ki fada musu a zo a dibi jini a mata pregnancy test. Sai ki dawo mu ci gaba da rounding wards."


"But...Sir...!" Nurse din ta fara kokarin yin magana.


"Yes...go on!"


"Sir ka san ba lallai a ga positive ba tunda bai yi 1 month ba. Ko akwai zai iya boye shi."


"Don't worry, a yi din dai. Tunda ta fara jin symptoms na pregnant gwara a yi domin a tabbatar. Kar a je a yi ta ba ta magungunan da za su iya illata mata unborn baby." Ya kalli Mahboobah yana mata murmushi.


Tun da ya fara ambatar gwajin ciki gabanta ya fadi. Ba ta so hakan ta tabbata, domin kuwa matukar ciki ne da ita, ta tabbata tana cikin matsala. Sau daya kadai ta taba sanin namiji a rayuwarta. Daga nan ne ciki zai samu matsuguni ya zauna? Har suka bar dakin ma ba ta san sun fita ba.


Ba a bata lokaci ba aka dibi jininta, saukar hawaye take ji wanda ta gaza dakatar da su. Babu yanda Fareedah ba ta yi ba da ita don ta fada mata dalilin kukan amma sai cewa ta yi zafin zazzabi ne. Ta ce da ita ko ta kira nurse amma ta hana, ta ce ai an ce idan ta karya za a zo a yi mata allura a kuma ba ta maganin safe. Though likitan ya ce a dakata daga duk wani treatment har sai an tabbatar bata da juna biyu.


End of chapter


Hello cupcakes! Ya kuke ya kwana biyu? Fatan na same ku lafiya. A yi ta hakuri da ni dai, yanzu ba kamar da ba. Masu korafin rashin samun posting kodayaushe ku yi hakuri. In shaa Allahu zan rinka kokarta komai lalacewa dai a sati ku samu sau daya, in dama ta bayar ma har sau biyu kuna iya samu. Ya danganta da lokacin da na samu.


To fa! Idan ta tabbata Mahboobah na dauke da juna biyu ya lamarin zai kaya? Sau daya tak ta taba sanin namiji, waye wannan?


Princess Amrah

RAZ 2Kuka take da iya karfinta, jikinta na karkarwa, zuciyarta na bugawa, kanta na sarawa, zazzabi na dad'a mamaye halittar jikinta. Tsana da haushin kanta take ji, ta yadda ta yi sake har ciki ya shiga jikinta. Sai dai kuma ya za ta yi? Ba a ja da ikon Allah. Ta shafi mararta, tana ambatar 'Astaghfirullah!' Soyayyar halittar da ke kwance a kasan mararta na shigar ta. Ta share hawaye, tana tuno abinda ya faru kwanaki ashirin da suka gabata...

***

Tana kwance a dakinta, har kayan bacci ta saka ta tuna da akwai kayan miyar da ba ta gyara ta saka a fridge ba. Da hanzari ta mike, guntuwar riga ce a jikinta, irin mai kwanciya sosai a jiki din nan mai hannun vest, pink colour. Ta doshi kitchen, ta fara gyara kayan miyar tana tsaye a gaban sink, ta jiyo karar bude kofa. Tsananin tsoronshi da take yi ya sa ba ta so ya tarar da ita a kitchen din ba. Ta gaggauta wanke hannunta da hand wash, ta doshi barin kitchen din. Kicibus suka yi ita da shi, tun daga kwabrin kafarta yake kallon ta har sai da ya dire a saman fuskarta. Bai taba jin shaawarta ba daidai da rana daya, sai yau. Gabanta ya fadi na ganin irin kallon da yake bin ta da shi. Ko kadan ba ta kawo ma ranta kallon shaawa ba ne. Ta hasasho wani balbalin masifar ne zai bi ta da shi. Nan take jikinta ya hau karkarwa, ta hau fadin,


"Don Allah ka yi hakuri ka yafe mun, ban san yanzu za ka dawo ba da ban fito ba."


Maganar da ta yi kanta burge shi ta yi, ya ci gaba da kallon ta yana jin tamkar ya hadiye ta, tamkar ba wannan karfen kafar tashi da ya yi ma muguwar tsana ba.+


Cike da salon soyayya ya rungumo ta a jikinshi. A zuciyarta ji take ko dai dan shaye-shaye ne ta aura? Da ma halin Ishraq kenan? Sai kuma ta tuno yanayinshi, yanda yake da aji da girma.


Daga lokacin da Ishraq ya fara kissing din Mahboobah ta fita hayyacinta. Tun tana dojewa har ta sakar mishi ragamarta. Ishraq ya samu gamsuwa da ita, sai famar sauke ajiyar zuciya take yi.


Sai da ya gama samun nutsuwa sannan ya kalle ta ya kalle shi, ya hau tariyar abinda ya faru yana yi yana kallon ginin kitchen din da ya kasa hakuri su koma daki. Wani irin takaicin kanshi ya ji, ya ci gaba da binta da kallon tsana da tsangwama.


"Tirrr da wannan dare! Allah Ya isa tsakanina da Khaleed Zannah! Da na san abin da ya saka a shayin nan ke nan da ban sha ba. Yau ga shi na kasa controlling din kaina, ni Ishraq Sulaiman na kusanci halittar da na fi tsana a duk duniyar nan."


Borin kunya ya sa daga wannan maganar bai kuma fadin komai ba, ya yayi kayanshi ya wuce dakinshi, ya bar ta sai faman kuka take yi.

***


Ta share hawayenta, tana tunanin a halin da Ishraq zai karbi cikin jikinta duk da tarin tsanarta da ya yi.


Kwananta biyar a asibiti aka ba ta sallama, tare da kayyade mata lokutan da ya kamata ta rinka zuwa domin kula da cikin jikinta.


A tsawon zaman ta asibiti, kullum sai Mami da Hajiya Saratu sun zo duba ta, tare suke wuni da su Mommy. Haneefa da Saleema ma ba a bar su a baya ba, sosai suke kula da ita.


Ishraq bai san tana da juna biyu ba sai bayan an ba ta sallama, likita na fada musu abubuwan da suka dace a nan ne ya gane cewa Mahboobah na dauke da juna biyu. Ranshi ya yi kololuwa wurin baci, ko kadan bai ji kaunar abin da yake cikinta ba, sai ma kara allawadai yake yi ga Khaleed Zannah da ya yi silar afkuwar komai.


Da dare bayan duk an watse an bar su daga shi sai ita a gida, ya same ta dakinta fuskarshi babu ko alamun annuri.


"Karfen kafa!" Ya kira sunanta. Dagowa ta yi ta kalle shi jiki babu kwari.


STORY CONTINUES BELOW

"Daga ke har abun cikin cikinki na tsane ku, ba zan taba kaunarku ba har duniya ta nade! Wannnan cikin da yake jikinki babu abinda ya kara a tsakaninmu face kiyayya. Allah Ya yi ni da son yara, ina son haihuwa sosai, sai dai ba da ke ba KK! Ban shirya ba, ban shirya tara zuria ba, har sai sadda na mallaki Ameerah Muhammad a matsayin matata. Don haka gobe da safe ki shirya mu je asibiti, zan zubar da cikin nan."


Dum! Ta ji gabanta ya yi mummunar faduwa. Ta dago kanta ta kalle shi, ta shafi kasan mararta. Ta ina? Ta yaya za a zubar mata da cikinta na sunnah? Yo ko na shege ne ai ba za ta taba yarda a mata abortion ba balle wannan da aka yi shi na sunnah.


"Ba zan yarda ka zubar mun da ciki ba Ishraq. Ba ka isa ba!"


Ya dago kanshi cike da takaici ya kalle ta, "Ba na magana biyu, ke ma kin sani. Kar ki bari raina ya baci, ki shirya da sassafe tare za mu je asibiti." Daga haka bai sake fadar komai ba ya fice ya bar ta sake da baki.


Ta ayyana a ranta, ko da Ishraq zai kashe ta ba za ta taba bari a zubar mata da ciki ba. Duk tarin wulakancin da yake mata har yanzu tana son shi, tana son abinda ya shiga tsakaninta da shi. Tana kaunar unborn child dinta.


Wayarshi ya dauka ya latsa kiran Khaleed, bugu biyu ya dauka. Bai ko tsaya sauraron sallamar da Khaleed din ke mishi ba ya hau balbale shi da masifa,


"Burinka ya cika Khaleed, abinda kake so ya afku, ciki ya shigi Mahboobah a daren nan da ka yi mun mugunta."


Khaleed bai bi ta kan masifar da Ishraq ke mishi ba ya tulle da dariya har yana dafe ciki.


"Me kenan? Ka ganar da ni likita."


Cikin zafin rai ya ce, "Ba zan ganar da kai ba din, wannan dariyar da kake yi ita ta tabbatar mun da ka gane manufata. To wallahi ba zan iya hada zuria da karfen kafa ba. Gobe-goben nan zan je in zubar da cikin nan. Ban tashi haihuwa da halittar da na fi tsana ba a duk duniyar nan, ba zan iya ba Khaleed, I just can't!"


Tuni Khaleed ya kawar da wasa daga muryarshi, ya yi bayyanannen tsaki, "Ba ka da hankali Ishraq na ga alama."


"Ba ni da shi Khaleed, in dai a wannan batun ne."


"Kar ka aikata."


"Sai na aikata."


"To shi kenan. Ka aikata din. Ni kuwa ina mai tabbatar maka da cewa yanzu a cikin daren nan zan kira Mami in shaida mata abinda yake faruwa. Sai ka tanadi amsoshin ba ta." Daga nan ya kashe wayar cike da takaicin halin Ishraq.


Maman Junior ta kalle shi ta ce, "Tun ranar da ka ce sai ka zuba mishi maganin nan a cikin shayi sai da na ce da kai kar ka ba shi Abban Junior, ni ba shi nake ji ba; Mahboobah nake ji. Burin kowacce mace shi ne mijin aurenta ya kusance ta a cikin shauki, amma shi sai aka samu akasin haka, kawai ya kusance ta ne domin biyan bukatar kanshi, ko in ce don aikin da magani ya yi mishi. Ni ban ga amfanin wannan auren nasu ba. Tsananin kiyayya ta sa miji ya tsani hada zuria da matarshi. Gaskiya wannan gidadanci ne."


Bai ce da ita komai ba ya ci gaba da latsar laptop dinshi. Ya san gaskiya ta fada mishi. Ba ma gidadanci ba ne wannan, jahilci ne mai lasisi.


Ya dora hannunshi a kai, ya ma rasa abinda zai yi ya ji dadi. Ji yake tamkar ya kurma ihu ko zai samu sassauci. What if Khaleed Zannah ya kira Mami ya sanar da ita? Wace amsa zai ba ta? Ta yaya zai iya kare kanshi? Ya yi tsaki ya fi goma. A karshe dai ya yanke shawarar sake kiran Khaleed din.


STORY CONTINUES BELOW

Kamar kar ya dauka sai kuma ya daure, bai ce komai ba bayan ya kanga a kunnenshi, yana jin numfashin Ishraq, dukkansu sun ma junansu shiru.


"Ina jin ka fa. Idan ba ka da abun fada dare na yi zan je wurin iyalina."


"Khaleed! Wai me ya sa a kodayaushe kake yin wasu abubuwa kamar ba aminina ba? Me ya sa kake fifita wata a kaina? Ni Ishraq Sulaiman da muka yi yarinta tare muka girma a tare?"


Ajiyar zuciya Khaleed ya sauke,


"Kokari nake in ga na daidaita tsakaninka da iyalinka Ishraq. So nake in ga ka zama adalin miji. Ina son ganin ka amsa tambayar yanda ka kiwaci Mahboobah ranar gobe kiyama."


"Ba ta wannan hanyar za ka bi ba Khaleed. Ni sai nake ganin kamar ka daina so na ne, kamar soyayyar da kake mun tana neman komawa ga karfen kafa."


Murmushi Khaleed ya yi, "Ka daina fadar haka abokina. Girman amincinmu ne nake dubawa ya sa ka ga duk ina haka."


"To na ji. Don Allah kar ka fada ma Mami wannan maganar."


"Ba zan fada mata ba Ishraq matukar ka janye batun zubar da cikin nan. Idan kuwa kana kan bakarka sai ka zubar da shi to tabbas ba ma a waya ba, zan kwashi kafa ne in je gidan Mami in sanar da ita komai, har kalar zaman da kake yi da Mahboobah."


Bayyanannen tsaki Ishraq ya yi, "Na ji, na janye. Amma ka sani, ba zan taba son Karfen kafa da abinda yake cikinta ba. Na tsane ta na tsani duk wani abu nata. Zan rubuta a takarda kai ma ka zama shaida, na yafe mata koma miye ta haifa, ita ce da hakkin mallakarsa ba ni ba."


"Kar ka tafka wannan babban kuskuren Ishraq. Ina guje maka regretting."


"Babu babban regretting sama da auren Karfen kafa."


"To shi ke nan. Allah Ya ba ka sa'a."


Suka yanke wayar daga nan.


***

Tun bayan sallar asubah ta kasa komawa bacci. Hankalinta a tashe yake, tana tunanin yanda za ta yi da Ishraq da safe. Ita dai ta yi alwashin duk rintsi ba za ta bari ya zubar mata da ciki ba. Domin kuwa ta dauki dukkan soyayya ta dora a kan abinda yake cikin cikinta.


Tana jiyo motsinshi ta nade cikin bargo. A tunaninta zai shigo dakin ne sai ta ga akasin haka. Tana jin sadda ya bude gate ya tada motarshi ya fita. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, tana al'ajabin rashin zuwanshi. Sai kuma ta kawo a ranta ko ya makara ne watakila sai gobe za su je.


Tashi ta yi ta hau gyare-gyaren gidan. Ya yi datti sosai ga tarin wanke-wanke a kitchen. Ganda da kyuya ba su bar Ishraq ya rinka wanke ko da kofin da yake shan tea ba.


Tana gamawa kusan goman safe Fareedah suka zo, ita da Haneefa da Saleema. Tun daga kofa suke tsokananta wai mai ciki. Sai dai murmushi kawai ta sakar musu saboda har a lokacin ba ta gama murmurewa ba, ga kuma gajiyar aikin da ta sha na gyaran gida.


Wayarta ta yi ringing, ta duba Mami ce. Cikin girmamawa ta gaishe ta, ta amsa mata da sakin fuska.


"Yanzu nake jin farin labari a bakin Khaleed abokin Likita. Ashe dai wannan ciwo mai albarka ne. Allah Ya raba lafiya."


Shiru Mahboobah ta yi cike da kunya. A zuciyarta kuwa farin ciki take; kenan Ishraq na maraba da cikinta tunda har ya fada ma abokinshiKhaleed Zannah? Ba ta gama tunani ba ta jiyo muryan Mami ta kuma fadin, "Na ji matukar dadi da haka Mahboobah. Don haka na yanke shawarar turo miki wata ta rinka taya ki yan ayyuka, don ki samu sassauci."


"Na gode Mami." Kadai ta iya furtawa, kunya mamaye da ita.


"Ki daina yi mun godiya Mahboobah. Idan na faranta miki tamkar na faranta ma kaina ne. In shaa Allahu za a samo dattijuwa, idan cikin ya cika wata bakwai sai ki koma gida ki karisa rainonshi a can."


Ta yi shiru ba ta ce komai ba.


"Idan Ishraq din ya dawo ki ce ina nemanshi. Kodayake, bari ma zan kira shi da kaina. Ki huta lafiya."


Suka yi sallama.


End of chapter


Princess Amrah

RAZ 2"Goggo! Goggo!!" Ta kwala kiran dattijuwar matar da ke mata aiki. Cikin girmamawa matar ta iso ta sunkuya a gaban Mahboobah,


"Yi hakuri kina ta kira na Boobah, ina dan tsantsame kayana ne."


"Goggo..." ta dafe kai. "Goggo don Allah har sau nawa ne zan ce da ke ki daina rusunawa a gabana? Wallahi ni dai nauyi nake ji sosai. Ina jin kunya tana lullube ni. Don Allah ki daina."


Murmushi ta yi dattijuwar, ta kalli Mahboobah, a zuciyarta tana kara yabawa da kyawawan halayen da da gani an san a nono ta shawo su. "To ki yi hakuri, zan daina in shaa Allahu."+


"Yauwa Goggona na gode. Dama...Albishir zan yi miki, Mami ta biya mana za mu je umrah ni da ita. Ban san da wa zan raba farin cikin nan ba a daidai wannan lokacin sai ke." Murna take yi, da ta kasa latsa kiran Mommy ta sanar da ita. Goggon dai, ita da suke zaune a gida daya tukunna.

"Alhamdulillahi!" Goggo ta furta cike da taya Mahboobah farin ciki. "Gaskiya wannan lamari ya yi mini dadi. Na yi murna kwarai da gaske. Sai dai kuma zan yi kewarki sosai Boobah."


"Babu komai Goggo ai duka sati biyu ne za mu yi. Umra ce za mu yi ba hajji ba. Ba za mu jima ba za mu dawo. Kin ga ke ma sai ki je gida ki yi zumunci."


"Haka ne. To Allah Ya sa a je lafiya a dawo lafiya. A bi a hankali da jikana kar a wahaltar min da shi."


Mahboobah ta ji kunya ta sunkuyar da kanta.


*


"Ni wallahi tunda nake ban taba ganin mutum irin Mami ba." Ya furta a bayyane a lokacin da yake sanya safa a kafarshi, kasantuwar yana sauraron duk maganar da Mahboobah ke yi ita da Goggo.


Ya daura agogon rado a hannunshi sannan ya feshe jikinshi da turaren oud wood. Bai ko tsaya sharce sumar kanshi da ta cukurkude ba ya fito. Goggo ta gaishe shi ya amsa mata da sakin fuska. Mahboobah kam ba ta ko kalli inda yake ba, a yanzu ta fara kokarin yakar zuciyarta a kanshi, duk da cewa akwai soyayyarshi fal a zuciyar tata.


Bayan ya tada mota wayarshi ta dauki kara. Ya duba ya ga bakuwar lamba ce ya dauka. Muryar namiji ya ji, bayan sun gaisa ya ce da shi sunanshi Noor, ya kawo yaronshi ne ya duba shi sai aka ce bai kai da isowa ba, shi ne ya samu lambar wayarshi ya kira.


"Am so sorry but I have a lot of workouts. Akwai doctors da yawa ka kai shi su duba shi. Yanzu haka ina da emergency aiki ne."


Zai kashe kenan Noor ya dakatar da shi. "Sorry for the disturbance Doctor Ish. But kai kadai ne aka ba ni assurance cewa za ka duba yaron nan yadda ya kamata a duk asibitinku, saboda bangarenka ne. Zan iya jiran ka ko ma karfe nawa ne. Idan ka gama sai ka kira ni."


Bai san yadda aka yi ba muryar Noor din ya yi mishi kwarjini. Sai ya samu kanshi da kasa musa mishi, duk kuwa da yawan ayyukan da suke gabanshi.


"To babu damuwa Mallam Noor. Idan na gama wannan aikin, zan yi squeezing time in kira ka. Kuna iya tafiya gida idan na kira din sai ku taho."


"I can't thank you enough Doctor Ish. Allah ne kadai Zai biya ka. Allah Ya sa a gama lafiya."


Daga haka suka yi sallama yana kashe wayarshi.


*


Da farin ciki take shaida wa Mommy biya musu umrah da Mami ta yi.


STORY CONTINUES BELOW

"Gaskiya matar nan tana da kirki sosai, kin yi sa'ar uwar miji Mahboobah. Allah Ya dauwamar da ku haka. Shi kuma Ishraq Allah Ya sa ya gane gaskiya ya daina kuntata miki."


Jin Mommy na neman kaucewa ya sa Mahboobah yanayinta ya canja. Mommy ta yi murmushi. "Na tabo wanda ba kya son laifinshi ko. To yi hakuri. Yaushe ne tafiyar taku?"


"Ta ce ba za mu wuce sati daya ba mu tafi ba." Ta ba Mommy amsa cikin sauyin yanayi.


"To Allah Ya kai mu. Allah Ya sa a yi karbabbiyar ibada."


"Ameen Mommy. Ina Reedah? Ba ta da cikon alkawari sam Mommy."


Daidai shigowar Fareeda dakin Mommy ta ce,

"Fareeda ungo 'yar uwarki. Ki mata murna ma umrah za su tafi."


Da hanzari Fareedah ta karbi wayar ta gaishe da Mahboobah.

"Su Yah Boobah ashe sai keta hazo."


"Ban sani ba mara kirki kawai."


"Na san matsalarki Yah Boobah, ba ya wuce cewar da nake yi zan zo gidanki kuma in ki zuwa. Wallahi ba da gangan ba ne, ni na tsani in zo gidanki mijin nan naki ya rinka yin biris da mutane, yana kallon mutum yana bata rai kamar ya ga kashi."


Mahboobah ta daure fuska. "Ba ki so zuwa ba ne. A yaushe ma yake samunki a gidan? Mutumin da duk sadda za ki zo yana asibiti amma tsabar sharri da rashin hujja kina neman fakewa ta nan." Ta cikin muryarta za ka karanci tsantsar haushin da ta ji na maganar Fareedah.


"Allah kuwa da gaske nake. Duk rasa sukuni nake yi idan ya zo ina nan. Amma dai zan yi squeezing ranan Monday in zo da safe kafin yamma in tafi."


Bayyanannen tsaki Mahboobah ta yi, "Kanki kuma ake ji."


"Allah kuwa zan zo in shaa Allahu."


"To Allah Ya yarda. Ki gaishe mun da Yah Aliyu."


"Zai ji."


Suka tsinke wayar.


Cikin watanni biyar ne a jikinta, amma sai a rantse da Allah cewa ya kai wata takwas, saboda ba laifi Mahboobah tana da girman ciki. Da kyar take tattakawa tana dan zagaye dakinta bayan ta gama cin abinci. Karar bude kofarshi ta ji, ta yi biris tamkar ba ta ma san da shi a wurin ba. Bayan ya shigo babu ko sallama ya iso inda take. Sama da kasa yake kallon ta, yana ganin muninta, cikin jikinta sosai ya  munana fuskarta a ganin shi.


"Mami ta fada mun za ku tafi Saudia."


"Eh." Kawai ta ce da shi tana ci gaba da tafiyarta.


"Ok. Kar dai zuciyarki ta riya miki cewa ni ne na biya. Ko sisina ba su koka ba, ba kuma za su taba kokawa ba a kanki." Ya dage kafada, ba tare da ya kalli gefen da take ba.


Murmushi ta saki tana tabe bakinta. Ko kallo bai ishe ta ba ita ma, ta karisa cikin dakinta.


Kitchen ya shiga neman abinci amma ya tarar babu komai. Bayyanannen tsaki ya yi, ya fara kokarin dama madara ya sha cornflakes. A zuciyarshi kara mamakin rainin da Maminsa ta siyo masa a wurin Mahboobah kawai yake yi. Tsoron shi da take ji a baya yanzu babu shi ko alama. Ta muryarta kadai yake fahimtar akwai raini. Ya yi kwafa bayan ya nufi dakinshi.


Wayarshi ce ta dauki ruri, ya duba ya ga Noor ne, ya sauke ajiyar zuciya hade da daukar kiran.


"Barka da dare Mallam Noor. A yi mini afu..."


STORY CONTINUES BELOW

"Babu komai Doctor Ish. Na tabbata akwai dalilin da ya hana ka sake waiwayata. Ni ma kiran gaggawa aka yi mini dole na hakura har zuwa gobe idan ka ba ni dama. Idan kuma babu sai in kai yaron Private Hospital."


Sekeke ya yi yana kallon wuri guda. Ya ma raina mishi wayo wannan mutumin. Amma ai ya san da private hospital din kuma ya roki ya duba mishi yaronshi ko?


"Okay no problem. Ka kai shi din kawai."


"Take it easy Doctor Ishraq. Na san irinku da commitments ne, kuma ga yarona jikinshi is getting worst. Ina nufin goben ma idan babu time I can take him to private hospital."


"Ok." Kawai Ishraq ya fada hade da tsinke kiran.


Noor!

Ruwa mai gumi yake jika towel da shi yana shafewa a fuska da jikin yaron. Cikin sanyin jiki ya ce,


"Sannu Ameer. Sannu ka ji! In shaa Allahu sauki ya kusa zuwa."


Yaron da bai san abin da Noor ke fadi ba ya yi shiru, ana ganin shi an san a galabaice yake.


Suna cikin haka wata mace ta fito, ba wata babba ba ce ba don ba za ta haura ma shekara ashirin da biyar ba. Ta daura zanin atampa da riga t-shirt kanta babu dankwali.


"Sameera." Noor ya fada ba tare da ya kalle ta ba.


"Na'am. Ashe kun dawo." Ta fada cikin halin ko'inkula.


"Ai ba za ki san mun dawo ba tunda ciwon ba a jikinki yake ba, ba kuma ki san darajar d'anki na cikinki ba."


Kallon sama da kasa ta bi shi da shi, kafin ta ce, "Ka ga Mallam, kar ka rainan hankali mana. Ta yaya zan tsuguna in haifi da da cikina kuma ka nuna ka fi ni son shi?"


Gyada kanshi ya yi Noor, yana kara jin takaicin kalaman da suke fita a tsakanin labban matarshi. "Da gaske ba ki damu da damuwar Ameer ba Sameera. Ciwon Ameer bai kai darajar chatting dinki ba, bai kai darajar aikinki ba."


"An zo wajen! Da ma na san nan ka dosa Nura! Ko za ka shekara kana goranta mun ba zan taba daina aikina in koma d'a kwance uwa kwance ba. Wa yake dogara da miji? Waya kuma da kake gani ba wai iya chatting nake yi da ita ba, akwai ayyuka na Office da nake da ita. Don haka ni ba zan daina ba. Da ni da kai duk daya muke a rayuwar Ameer. Tunda kai ka zabi ajje zuwa wurin aikinka ka tsaya jinya ai shi kenan. Za ka samu lada sosai. Hakan yana da kyau."


"Okay then. Aiki dai kika zaba ko? Fine. Ki ci gaba da zuwa aikinki Meerah. Sai dai duk abin da zai taso a gaba kada ki yi kuka da kowa face kanki! Ni dai ba zan iya barin yarona ga 'yar raino ba alhali yana da bukatar kulawarmu. Kuma kin fi kowa sanin abin da ya faru lokacin da kika kawo waccan 'yar rainon. Don haka na zabi zama in yi jinyarshi na dan wani lokaci. Idan ta kama kuma zan mayar da shi can gida wurin iyayena..."


Tun bai kai karshe ba ta dalla mishi wata irin muguwar harara. "D'an nawa za ka kai kauye Noor?! Wallahi ba ka isa ba! You're not serious."


"Zan nemi mafita mai girma fa."


Ya dauki Ameer dan shekara hudu ya nufi dakinshi da shi.


Kafadarta ta daga hadi da komawa dakinta, ita ba ta ga dalilin da zai sa ta bar aikinta ba, aikinta da ya kasance babban rufin asiri a duniyarta.


*


Tsaki ya sake yi wanda shi kanshi ba zai iya lissafa adadin wanda ya yi ba a 'yar tsayuwarshi yana jiran fitowar Mahboobah. Goggo ce ta fara fitowa janye da akwatin Mahboobah na trolly, Mahboobar biye da ita suka karisa isowa gaban motar Ishraq. Girar sama ya hade da ta kasa yana jin takaicin jerawar da zai yi da Mahboobah a cikin mota. Sau daya ta taba tunanin zama a bayan motar, girman kai ya hana shi yi mata magana ta dawo gaba, da suka isa gidan Mami sun same ta a harabar gida ta fito rakiyar Hajiya Saratu, sosai ta yi mishi fada, don a ganin ta ba ta ga dalilin da zai sa ya bar Mahboobah da zaman bayan mota ba, kamar dai ba matarshi ba.


"Goggo za ta koma gida kafin mu dawo." Ta samu matsowa da kyar, tana jin zafin maganar da ta kasance dole sai ta yi mishi.


Kudi ya zaro ya kirgi dubu goma ya ba ta. Ba ta bin su kudin aiki saboda ana yin albashi Ishraq yake biyanta. Wannan dubu gomar ya ba ta ne saboda ta yi kudin mota, ta kuma samu na yin tsaraba.


Har kasa ta sunkuya tana musu godiya, kafin ta juya ga Mahboobah, cikin muryar da ke nuna cewa za ta yi kewarta ta ce, "Allah Ya tsare hanya Boobah, Allah Ya sa a yi karbabbiyar ibada. A saka mu a addua, Allah Ya biya mana dukkanin bukatunmu na alkhairi."


Murmushi ta yi Mahboobah, tana sanya hannun Goggo a cikin nata da fadin, "In shaa Allahu zan miki Goggo. Zan yi kewar ki sosai."


Ya gaji da tsayuwar, so yake ya ba ta umurnin ta shiga mota su tafi, amma yana jin ba zai iya yi mata magana ba, ta san daidai, ta kuma san ba ya son jira.


Ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska ya sa Mahboobah bude gaban motar, tana zama da rungume handbag dinta, Goggo ce ta rufe mata motar, bayan ta bude gidan baya ta sanya akwatin Mahboobah.


A kofar gidan Mami ya yi parking, za ta bude kofa ta fita ya kalle ta, ba ya son yi mata magana amma ya zama dole ya yi mata a yanzu. "Za ta fito ne mu tafi." Ya samu ya fada a kasan makoshinshi, kasa-kasa.


Ajiyar zuciya ta sauke. Sauraron muryarshi kadai kan jefa ta a duniyar nishadi. Tana son Ishraq, so mara iyaka. Maganarshi, tafiyarshi, shiru-shirunshi, tana son komai nashi. Tana son Ishraq Sulaiman a karan kanshi.

Jin karar bude bayan mota ya sanya ta dawowa a duniyarta. Ishraq ne ya bude ya ciro akwatinta yana mayarwa a cikin booth bayan ya saka na Mami. Ashe ba ta sani ba har ya shiga gida ya dauko akwatin.


Da Mami ta fito sai da ta bude kofa ta fita ta gaishe ta, kafin duk suka shiga cikin motar, Mami na jin dadin yadda ta ga Mahboobah ta kara kyau, cikin jikinta ya yi mata kyau, an ce idan ciki ya fara tsufa mace muni take yi, amma ita Mami kyan Mahboobah take gani. Komai nata abun burgewa.


Tuki yake yi, yana jin yadda Mami ke kokarin jan su da hira amma bai ce ko uffan ba. Mahboobah ce ke amsa ta. Har suka isa Airport bai ce da su komai ba. Ya bude motar ya fita, yana zagayawa ya bude wa Mami gefenta.


"Da ka bar ni ma na bude da kaina. Ka bude ma Mahboobah ita ce ta yi nauyi."


Haushin maganar ya ji. Cikin ikon Allah ma kafin ya bude ita ta bude da kanta ta fito.


End of chapter


Assalamu alaikum.

Ni kam kunyarku ma nake ji wallahi.

Na bar ku da jira ko?

Ku yi hakuri domin Allah.

Ni ban ma san me zan ce da ku ba

Ban san da wanne baki zan ba ku hakuri ba

Ban san uzurin da zan ba ku wanda zai zama gamsasshe ba.

Am so sorry for keeping you waiting.

In shaa Allahu hakan ba za ya sake faruwa ba.

Zan ci gaba da kawo muku BKF a kai a kai duk sadda na samu dama.

Na gode sosai masu bibiyata.

Pricess Amrah

RAZ 2Kamar yadda suka sanya kwanakin tafiya Saudia, haka kwanakin dawowar su kasar Nigeria ya juyo. Jin ta take tamkar a bisa gajimare, wani irin nishadi na lullube ta, yana daukar ta daf, yana ajiye ta a cikin duniyar nishadaddu. Sosai ta ji dadin zaman kasar Saudia, sun yi kwanaki hudu a birnin Madina, daga nan suka wuce Makka, inda suka sauke umrarsu. Sai dai dadin da take ji a yanzu da take zira kafarta daga cikin kofar jirgi, ji take tun da take a duniyarta sau daya ta taba jin irinshi. Kanta ta daga sama, ta kalli sararin samaniya, tana mai jinjina girma da buwayar Allahu gagara-misali, ta yadda Ya zana baiwa a cikin kwakwalwar mutumin da ya fara kirkirar jirgin sama. Kafin ta dawo da kallon ta ga mutanen da ke zagaye da jirgin, kowa yana jiran saukar dan'uwanshi.


Fuskarta ta shafa da tafin hannunta, tana bude idanuwanta da ke sauka ga mutumin da ta fi kauna a duk duniyarta bayan mahaifiya da siblings dinta. Gabanta take jin yana tsananta bugawa, tuna cewa ita kadai ce ke haukarta, kewarshi ta yi, sai dai ta tabbata shi bai yi ba. Matsawa ta yi kusa da shi, tana jin yadda zuciyarta ke ruruwa da wutar kaunarshi. Rashin ganin shi da ta yi na sati biyu, ji take tamkar an zarce watanni uku ne ba ta dora shi a idanuwanta ba.+


Tun da suka tafi, ko sau daya Ishraq bai taba kiran Mahboobah da wayarta ba. Sai dai idan sun gaisa da Mami, yana cewa ta ba ma Boobah wayar, don ya san halin Maminsa, tana iya gane yanayin alakarsu, duk da a hakan ma ta sanya ma abun alamar tambaya. Sau daya da Mamin ta tambaye shi me ya sa ba zai kira Mahboobah ba a wayarta sai dai da tata, ce mata ya yi


'Duk daya ne Mami.'

Tun da yake waya da Mahboobah ko sau daya bai taba tambayar ta lafiyarta ba, ballantana ta abin da yake cikin cikinta. Abun yana mata ciwo matuka. Domin kuwa, ba ita ta dasa ma kanta cikin ba. Halittar Allah ce, Ishraq sanadinshi. Ita duk zaton ta yadda take ganin miji na ririta matarshi yayin da take da juna biyu a cikin fina-finai ko kuma littattafai, ta dauka ko rabinsa za ta samu a wurin Ishraq, duk da ta san yadda yake tsanarta. A wasu lokutan takan zubar da hawayen da ita kanta ba za ta ce ga dalilin zubar su ba. Sai dai ta san ba su rasa nasaba da rayuwar da ta tsinci kanta a cikinta, rayuwar da take da tabbacin a cikinta za ta dauwama, tun da ta zabi zaman aure da Ishraq Sulaiman.


Ranar farko da Ishraq ya ce da Mami ta ba ta wayar, bayan ta karba ce mata ya yi,


'Ki rinka kirkira maganar fadi idan a gaban Mami kike. Ko kuma ki rinka tashi ki bar wurin, ki yi shiru har sai lokacin da na ga dama na kashe wayar. Ba ni da shaawar jin muryarki KK. Ko kadan ba ki kasance a sahun mutanen da nake jin ko da motsin fitar numfashinsu zai shige ni ba.'


A ranar ta yi kukan da ta jima ba ta yi irinshi ba. Ko da Mami ta tambaye ta dalilin kukan, sai ce mata ta yi mahaifinta ta tuna. Mami ta yi ta mata nasiha, a karshe ta ce da ita ta dage da yi mishi addua.


"Sannunku da isowa Mamina. Na yi kewar ki sosai."


Maganar Ishraq ce ta dawo da ita a duniyarta. Tana matse idanuwanta guntun hawaye na sauka daga cikinsu. Hannunta ta sa ta goge, tana kirkiro murmushin da ko kadan bai da alaka da nishadi.

"Yauwa likita. Mun same ku lafiya?"


"Lafiya nake Mami. Mu karisa wajen parking, motar tana can." Har ya yi tunanin wucewa, sai kuma ya tuna tare suke da Mami kuma tana lura da yadda ko kadan bai mayar da hankalinshi kan Mahboobah ba, hakan ya saka shi kirkiro murmushin dole, yana kallon Mahboobah da ta tsare shi da idanuwanta, tana ganin yadda ya kara yi mata kyau.


"Sannunku da hanya Boobah." Kadai ya iya samun fadi. Duk yadda ya so ya matso wata maganar a gaba kasawa ya yi. Cikinta ya kara girma a kan yadda ya gan ta kafin su tafi. Fuskarta ta kara yin munin da shi kadai ke ganin shi.


STORY CONTINUES BELOW

"Alhamdulillah! Ya muka same ku?"


Bai amsa ta ba duk da ya ji ta. A wannan karon sai dai idan Mami za ta gane ta gane. Ba ya jin zai iya dora wata maganar bayan wadda ya yi mata a farko. Jakar Mami ya karba, ta Mahboobah kuma ya kira irin helpers din nan da suke cikin Airport ya dauka, yana bin shi a baya, Mami da Mahboobah biye da su.


*


Kayan jikinta ta rage, tana son shiga ta yi wanka, sai dai ba za ta iya ba har sai ta kira Mommy ta sanar da ita zancen dawowar tasu, saboda ba ta sani ba, duk a zaman sai washe gari za su dawo ake, sai kuma aka yi sa'a suka dawo a yau.


Bugu biyu Mommy ta dauka, da farin cikin muryarta take fita, ta yi kewar diyarta, tana son ganin ta, tana son dora ta a idanuwanta.


"Ina ganin lambar Nigeria na san an dawo. Sannunku da hanya Boobana."


Ajiyar zuciya ta sauke Mahboobah, tana jin wani irin sanyi yana ratsa zuciya da ruhinta. Iyaye rahma ne. Ta fada a kasan zuciyarta.


"Muna zaune kawai sako ya riske mu wai mu yi dawafin bankwana jiya da tsakar dare, yau da asubah muka tafi Jiddah. Saukar mu Nigeria ke nan, ko wanka ma ban samu na yi ba."


Da dalla-dallar maganarta da ke burge duk na kewaye da ita ban da Ishraq take labarta wa Mommy yadda abun ya kasance.


Kai ta daga Mommy,

"Alhamdulillah! Allah Ya sa an yi karbabbiyar ibada Mahboobah. Ya Mamin taku take?"


"Tana lafiya." Mahboobah ta ba ta amsa, cike da kaunar halittar da Mommy ta ambaci sunanta.


Ba ta kara gasgata mutunci da karamcin Mami ba sai da suka yi tafiyar nan. Mace ce da ta san darajar halittar Allah. Mace ce da sam abun duniya bai rufe mata ido ba. Tun da suka sauka Madina, har suka dawo kasar Nigeria Mahboobah ba ta taba cire sisi da sunan za ta siyi abinci ba. 'Yar tsarabar da ta yo ma 'yan gidansu da kawayenta ma Mamin ce ta ba ta kudin da ta yi.

"Mami na da kirki sosai Mommy." Ta samu kanta da fadi, tana tuna yadda suka yi rayuwa a kasa mai tsarki, tamkar ba suruka da sarakuwa ba, tamkar mahaifiya da diyar cikinta ne.


"Ni ma shaida ce a kan haka Boobah. Kin yi dace, zan kira in mata sannu da zuwa da godiya, kafin ta gama hutawa in je har gida in mata sannu da zuwa."


"Allah Ya bada iko Mommy." Ta furta, tana jin karar shigowar Ishraq parlor.


"Ki yi wanka ki huta kin ji. In shaa Allahu yanzu Fareedah da Aliyu za su zo."


"Mommy ke fa?" Ta fada a shagwabe.


"Kin san ba zan zo gidanki ba Mahboobah. Su Reedah dai za su zo. Idan kin gama hutawa sai ki zo nan gida mu gaisa."


Ta san kawaici irin na Mommyn tata. Ta sani da ma ba za ta zo ba, ta dai fada ne kawai dan neman magana.


Sallama suka yi, ta kashe wayar tana neman towel a cikin wardrobe, ta daura ta shiga wanka.


***


Satinsu biyu da dawowa daga Saudiya Mami ta ce da Mahboobah ta shirya ta koma gida rainon ciki. Duk da ta ji dadin hukuncin na Mami, sai dai kewar Ishraq da za ta yi ta mata katutu a tsakanin kirjinta. Ta tabbata dai Ishraq ba zai je gidansu da sunan duba ta ba. Gida daya ma suke tare suna kwana, bai taba tambayarta yadda ta tashi ba, duk da ciwukan yau da gobe da aka san mai juna biyu da su.


STORY CONTINUES BELOW

Akwatinanta ta tasa gaba, tana jin dumin hawaye na wanke kumatunta. Idan ta ce ba ta son komawa gidansu ta yi karya. Idan kuma ta ce ba za ta yi kewar kamshin turaren Ishraq ba shi ma din karya take. Tana cikin haka ta jiyo motsinshi. Da ma Mami ta fada mata shi zai mayar da ita. Sai sun fara biyawa gidan Mamin sannan su wuce gidan iyayenta.


Sallama Goggo ta yi mata, "Sannu da hutawa Boobah." Tana dorawa da "Alhaji ya ce ki fito mu tafi." Ta boye sauran maganar da ya yi mata.


A lokacin da ya ba Goggon umurni ta kira Mahboobah, cewa ya yi


'Ki ce mata ta fito yanzu yanzu. Idan kuma ta kara ko minti daya sai dai ta hau a daidaita sahu.'


Ajiyar zuciya ta sauke Mahboobah. Tana ma Goggo nuni da shirgin akwatunanta. Ko yanzu haka akwai sauran wata biyu akalla kafin ta haihu. Sannan bayan ta haihun ma, akwai kwanaki arba'in lafiyayyu da za ta yi, kafin ta yi tunanin dawowa. Shi ya sa ta lodi kaya.


Ta gaban shi suka wuce, duk da ya san cewa ba wannan akwatin ne kadai ba, hakan bai sa ya yi tunanin shiga ya taya Goggo kwaso kayan ba.


Bayan ta gama ciro su duka, ta tsaya a bakin booth din tana jira ya bude mata ta saka a ciki. Guntun tsaki ya yi wanda ya tsaya a bisa labbanshi kawai, yana danna remote din motar, booth din ya bude da kanshi. Akwatin farko ta saka, mara nauyin kenan. Ta jinjina wani, ta ji ba za ta iya daga shi ba. Da murmushinta ta roki Ishraq da ya taimaka ya saka, kayan sun fi karfinta.


'Ban san haukan da ya sanya ta shirgo wannan tulin kayan ba kamar wadda za ta dauwama a gida.'


Ya fada a zuci, a zahiri kuma "To." Ya ce, yana isa gaban Goggo, yana jera akwatunan, yana tunanin yadda booth din ma ba zai kwashe kayan ba.


"KK!" Ya furta kasa-kasa, yana jiran ta mishi banza ya samu damar ci mata mutunci.


"Na'am." Ta jinjina, tana mai takowa gabanshi.

"Ba zan iya jibga wa motata wannan tulin akwatunan ba. Sai dai ki zabi daya, ko rage akwatuna mu tafi tare, ko kuma ki tsayar da keke napep, ki jera kayanki a guda, ki hau guda."


Ta runtse idonta, tana jin ciwon maganganun nashi. "Ka yi hakuri, zan rage." Ta furta, idanuwanta na son kawo ruwa tana yakarsu, ba ta son zubar su a gaban Goggo, ko alama ba ta son Goggon ta gane mata, duk da cewa ta san kashi sittin cikin dari na matsalolin da Mahboobar take fuskanta a gidan aurenta.


Babba daga cikin akwatunan ta ja gefe, duk da akwai muhimman abubuwa a cikinshi, duk siyayyar da ta yo ta baby a Saudia cikinshi ta jera. Tun daga kan kaya uni sex, takalma, safa, baby towels, da sauransu. Ta zabi fitar da shi ne saboda ta san haihuwar da dan sauran lokaci. Idan abun ya matso, sai ta turo Fareedah ta daukar mata.


"Na cire wannan." Ta fada, tana goge maikon hawayen da ya manne a kwarmin idonta.


Rufe booth din ya yi, yana komawa gaban motar, ya bude ya shiga, ya zauna yana latsar wayarshi. Ganin haka ya sa Goggo jan akwatin ta nufi komawa ciki da shi. Bayan ta fito, suka shiga cikin motar, shi kuma ya fita ya rufe gidan.


Gidan Mami suka fara biyawa. Duk yadda Mahboobah ta so ta boye damuwar da ke lullube da zuciyarta kasawa ta yi. Fuskarta ta nuna, ta nuna kuncin da ke dabaibaye da ita.


"Me yake damun ki Mahboobah?"


Dabarbadcewa ta yi, tana son boye damuwar da ta riga da ta fallasa kanta. "Babu komai Mami. Lafiya lau nake." Ta kirkiro murmushi.


"To Allah Ya sa haka." Mamin ta fada, ba ta son zurfafawa, amma tabbas ta hango damuwa shimfide a fuskar Mahboobah. Sai kuma zuciyarta ta karkata, ta kitsa mata ko kewar Ishraq da za ta yi ne ya janyo haka.


"In shaa Allahu zan rinka zuwa a kai a kai ina duba lafiyarku. Allah Ya raba lafiya. A gaishe da su Maman Reedah."


"Za su ji." Kawai ta iya cewa, tana jin kunyar amsa adduar da Mamin ta yi mata.


"Hafsatu, da na yi tunanin ki zauna a nan tare da ni, kafin Allah Ya budi idon Mahboobah lafiya. Sai kuma muka yi magana da Hajiya Rukayya mahaifiyarta, ta ce kawai ku tafi tare, zuwan naki zai yi amfani sosai."


Murmushi Goggo ta yi, "Babu komai Hajiya. Fatanmu dai, Allah Ya raba su lafiya."


"Ameen ya Allah." Tana mayar da kallon ta ga Ishraq, "Ku je ko."


Gaba ya yi su Mahboobah na bin bayanshi. Sai da Mami ta ga sun tafi sannan ta dawo gida, zuciyarta cike da kaunar Mahboobah din.


End of chapter

Na fada muku in shaa Allahu na dawo kenan😻ko ba kullum ba dai, in shaa Allahu za kuna samu bakin gwargwado.

Princess Amrah

RAZ 2Ba za ta iya cewa kai tsaye ga inda yake mata ciwo ba, domin kuwa kowacce gaba ta jikinta ciwo take mata. Hakan ya sa ko kadan ba ta kawo a ranta cewa haihuwa za ta yi ba. Littafin hisnul muslim din da ke hannunta tuni ta ajje shi, tana cizon labbanta, idanuwanta a runtse, hannunta dafe da kugunta.


"Ya Rahmaan." Ta furta da kyar tana jan numfashinta, tana gyada kanta, zafafan hawaye na sauka bisa kumcinta, wanda ko alama ba za ta ita kiran shi da kuka ba, hawaye ne da ita kanta ba ta san saadda suke fita ba ballantana saukarsu. Hawaye ne masu cike da zafi da radadin wahalar da take jin tana taso mata, tun daga duga-dugan kafarta, har zuwa tsakiyar kanta.


So take ta kwala kiran Mommy ko Goggo, amma hakan yana mata wahala. Sunan Allah ma alamar fitar shi bisa lebo kadai ce, wanda yake zaune ga shi ga ta ma ba zai iya jin abin da ta fada ba.


"Ya Allah!" Ta furta, a daidai lokacin da mararta ke katsawa, hakan ya tabbatar mata da cewa haihuwa ce. Cikin ikon Allah, sai kuma abun ya dan lafa mata. Cikin dauriya ta mike a saman tafin kafarta, hannunta tallabe da cikin da ya yi zundum a gabanta. Da kyar ta isa falo, ta samu Mommy da Goggo suna kallon shirin Sapne Suhane a tashar Arewa 24. Ganin ta ya yi saurin gigita su duka biyun. Har rige-rigen tambayarta lafiya suke yi. Kai kawai take jinjina musu, kafin ta samu da kyar ta ita fadin,+


"Mommy ko haihuwar ce."


"Me kike ji? Da ma ba ki da lafiya ne? Me yake miki ciwo?" Duka a jere Mommy ke rattabo mata wadannan tambayoyin, tana dafa kafadarta cike da tausayi.


Babu amsa ko daya da Mahboobah ta iya ba ta. Sai dukewa da ta yi a wurin, kasantuwar wani azababben ciwon da ya sake taso mata.


Wayarta ta dauko Mommy, ta latso kiran Aliyu tana sauke nunfarfashin da ke cike da tashin hankali da damuwa. Yadda Mahboobah ke dukewa tana hawayen wahala, haka ta rinka yi ita ma a duka haihuwarta uku. Wahala take sha sosai wurin nakuda, kuma tana yi tana komawa baya. Haihuwar Fareeda har an ce sai an mata aiki an ciro yarinyar, cikin ikon Allah sai kuma ta samu ta haihu da kanta. Wannan wahalar da take tunawa ce ke kara mata tausayin diyar tata. Tana jin Aliyu na fadin 'Mommy' ta kara sauke ajiyar zuciya.


"Idan ba ka yi nisa ba Aliyu ka zo ka kai mu asibiti, Mahboobah na labour."


"Ban yi nisa ba Mommy. Bari in juyo yanzu. Ku kama ta ta fito kafin in kariso."


A waje suka same shi, shi ya taimaka musu suka saka ta a mota, cikin lokaci kankani Mahboobah ta galabaita, idanuwanta sun yi zuru-zuru, tana jin azabar da tun da uwarta ta haife ta ba ta taba jin ko mai kama da ita ba. Ta wahala sosai a lokacin da take fama da ciwon zuciyarta, sai dai ba za ta taba alakanta wahalar nakuda da waccan ba. Ba ta sani ba ko don waccan akwai kuruciya a tattare da ita wannan kuma ta mallaki hankalinta.


Asibitin Almadina suka isa, babu bata lokaci nurses suka yo kan Mahboobah janye da kujera, suka dora ta, Mommy na jin yadda wata dattijuwa a cikin ke fadan sai da suka bari ta galabaita sannan suka nufo asibiti da ita. Tashin hankali bai bar ta tsayawa yi wa matar bayanin su ma sai a yanzu suka sani ba.

Abun mamaki, wai duk wannan wahalar da Mahboobah ta sha a 2CM ta tsaya. Dattijuwar matar ta gyada kai, tana jin tausayin Mahboobah da alamu suka nuna haihuwar farko ce.

Sai a wannan lokacin Mommy ta tuna da kiran Mami. Ta latso kiran ta, bugu biyu ta dauka da sallama a bakinta.


"Barka da rana Hajiya Mariya." Mommy ta furta, tana dorawa da "Ga mu nan a asibiti, Mahboobah na labour."


STORY CONTINUES BELOW

"A wace asibitin kuke Maman Reedah?" Mami ta bukata, tana mikewa da yafa hijabin da ta gama sallah da ita.


"Ba nisa muka yi ba, muna Almadinat Hospital ne."


"Ok to ga ni nan zuwa yanzu in shaa Allahu. Allah Ya raba lafiya ya sauke ta lafiya." Ta yanke wayar tana lalubo lambar Ishraq.


"Ka je asibitin ne likita?" Ta tambaye shi, don a tunanin ta ko ya san halin da ake ciki.


"E, ina asibiti yanzu haka Mami. Mun yi meeting ne, amma mun gama yanzu zan kama hanyar gida. Lafiya dai ko Mami?"


"Ba wannan asibitin ba nake nufi Ishraq. Matarka, Mahboobah na can sun tafi Almadina haihuwa ta zo. Ka wuce can mu hadu da kai, mu ne ya kamata mu biya duk wani abu da ya dace, amma da alama sun gama komai. Mu dai hadu can din."


Bai san yadda aka yi ba, yau sau daya a rayuwarshi ya ji tausayin Mahboobah ya dan tsirga zuciyarshi. Yana tsananin tausayin mace a lokacin da take nakuda. Duk da cewa ba bangaren da ya karanta ba ke nan, amma yana gani ko a wurin abokan aikinshi, yana ganin yadda mata ke wahala, yana ganin yadda wahalar haihuwa ke daukarsu daf, ta kai su can wata duniyar, da su kadai ne suka san ta.


"Allah Ya raba lafiya." Ya furta, yana son kawar da tausayinta daga zuciyarshi, ba ya so, ko alama ba ya son wani abun alkhairi ya gitta ta tsakaninsu. Babban burinshi a rayuwa bai wuce ya gano inda Ameerah Muhammad take ba, ya aure ta, ya mallaka mata dukkanin soyayyarshi, tare da sauwake ma karfen kafa.


Gaban motarshi ya isa, yana murza murfin kofar, ya shiga ya rufe, sannan ya tada yana nufar Almadinat Hospital kamar yadda Mami ta fada mishi.


*

Sun dauki kimanin awa daya da mintuna hamsin ba tare da sun ji wani batu ba a kan Mahboobah, hakan ya sa Mommy yanke hukuncin bin su har cikin labour room din. Ba a barin kowa shiga ciki, daga masu haihuwa sai ma'aikatan wurin, hakan ya sa ta ja burki, tana kwankwasa kofar da aka rufe ta.


Wata nurse ce ta bude kofar, Mommy ta tambaye ta halin da Mahboobah Bukar take ciki, nurse din ta ce "Muna kan bakin kokarinmu, in shaa Allahu za ta sauka lafiya."


Kyakkyawar magana ma sadaka ce, injin Manzon Allah SAW. Sai kawai Mommy ta samu kanta da samun nutsuwa daga maganar Sister Maryam Alkali. Hakan ya sa ta kama hanyar komawa inda su Mami da Goggo suke, sai Fareedah da Mommyn ta kira daga makaranta, ta gaggauta zuwa gida ta dauko dan riyo din da suka hada ita da Mahboobah tun da cikin ya cika wata tara.


"Yaya ake ciki Maman Reedah?" Mami ta furta cike da tashin hankalin da take jin yana linkuwa, rashin sanin halin da Mahboobah take ciki.


"Sun ce suna bakin kokarinsu. Ana sa ran samun nasara da yardar Allah."


"To Alhamdulillah!" Goggo da Mami suka hada bakinsu suna fadi.

Bayan kimanin awa biyu Sister Maryam Alkali ta fito sai hada zufa take, inda su Mommy suke ta iso, da azama Mommy ta mike tana tambayar ta halin da Mahboobah take ciki.


"Mahboobah ta galabaita sosai, hakan ya sa ta kasa yunkurin kirki, ga babyn da alama shi ma kanshi yana wahala. Mun kira Doctor ya ce sai dai a yi mata CS in dai ana son ceton uwa da babyn. Muna neman wani cikinku ya yi signing za a shiga aiki da ita yanzu."


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'in!" Shi ne abin da dukakkansu suke maimaitawa, har da Saleema da Haneefa da suka iso yanzu, suna tsintar kalaman da Sistern take fadi.


STORY CONTINUES BELOW

"In shaa Allahu ba wani matsala ba ne. Haihuwar ma ta fi shi wahala Hajiya. Yanzu za a yi aiki a ciro muku bouncing babynku cikin koshin lafiya, da yardar Allah."


Sister Maryam Alkali ta iya kalami masu sanyaya zukata. Da a ce irinsu ne ake samu a kowacce asibiti, hakika da an tsinci kai a duniyar nishadi yayin da ciwo yake nukurkusar marassa lafiya. Babbar matsalar da ake samu a wannan zamanin, su kansu ma'aikatan lafiyar wasunsu ba su iya magana ba. Ma'aikacin lafiya da ake so ya zama mai hakuri da juriya, ya zama nutsattse mai kwanatar da kai, ya zama mutum mafi soyuwa ga marassa lafiyansu. Amma a yanzu, su ne ginshikin tayar da cutukan majinyata. Ba su kula da su ba ma yadda ya kamata balle a yi maganar kalami mai dadi. Sai wulakancin da suka matar tamkar abincin cinsu.


Waya Mami ta dauka ta latsa kiran Ishraq, ya dauka yana amsa sallamarta.


"Ka zo ka cike form likita, aiki za a yi wa Mahboobah. Ta galabaita sosai ta kasa haihuwa da kanta."


Gabanshi ne ya fadi, bugawa daya kafin ya amsa da ga shi nan zuwa. Tare suka iso shi da Khalid Zannah, suka bi bayan Sister Maryam bayan an tabbatar mata da cewa su ne za su cike form din.


Bayan sun isa gaban dakin, ta juyo gare su tana tambayar mijin Mahboobah.


"Khalid zai cike." Kawai Ishraq ya fada. Yana zama a kan kujera daya cikin wadanda suke jere a bakin wurin.


Gyada kanshi ya yi Khalid Zannah, yana bin ta suka shiga ciki, ya karbi form din ya cike sannan ya fito, suka koma wurin su Mami.


Dakin tiyatar masu haihuwa ba daya ba ne ba da sauran theatre room, shi a jikin maternity yake, ta yadda ana gama aikin za a wuce kai tsaye da su maternity din. Babu wani nisa daga inda su Mommy suke.


Cikin mintuna ashirin da biyar aka ciro kyakkyawar baby girl daga cikin Mahboobah Bukar. Yarinyar bul-bul take, jajur da ita, kanta cike da kwantacciyar sumar da ke jere har bisa goshinta.


Da farin cikinta Sister Maryam Alkali ta sanar da su Mommy halin da ake ciki. Hamdala suka yi dukkansu, ban da Ishraq da ko kadan bai ji wani abu ba. Ajiyar zuciyar dai da ya sauke na lafiyar da aka tabbatar musu da Mahboobah da babynta suna cikinta.


*


Kwananta bakwai a asibiti aka ba ta sallama. Bayan sun koma gida Mahboobah ta kwanta kan gado, idonta kyan a kan jaririyarta da ta ci sunan Mami, amma har a lokacin ba ta tantance sunan da za a rinka kiran ta da shi ba. Fareedah ta rinka jero mata sunaye sai dai dukkansu babu wani mai ma'anar da take ji  za ta iya kiran diyarta da shi. Ranar da aka yi ma yarinyar huduba ma ba Ishraq ba ne ya yi, Aliyu ne, kasantuwar Ishraq din ya ki ya yi, kallon yarinyar ma bai tsaya ya yi ba, duk da Mami ta tilasta mishi daukar ta, sai ya fake da kunya yake ji.


Hawaye ne ta ji suna sauka a bisa kumcinta, baki daya fuskar yarinyar tamkar an tsaga kara, haka ta kwaso kamannin Ishraq. Babu ta inda za a kalle ta a ce diyar Mahboobah ce, sai dai ko a gaba, kasantuwar kamannin jariri a kowanne lokaci sauyawa suke yi.

Kaunar yarinyar take ji ta kowacce kusurwa a cikin zuciyarta. Baccinta take yi yarinyar cike da kwanciyar hankali. Ajiyar zuciya Mahboobah ta sauke, tana sumbatarta, tana fadin

"Allah Ya raya mana ke Ameerah..." tana jin nauyin maganar, tana jin kishin da ita kanta ba ta san daga inda yake fitowa ba.


Ta zabi kiran yarinyar da Ameerah ne, a zatonta ko hakan zai sa Ishraq ya so ta, ta tabbata zai yi farin ciki idan ya ji haka, kaunar da yake yi wa Ameerah Muhammad za ta sa ya kaunaci gudan jininshi da har yanzu bai san kalarta ba.


Ta share hawayenta, tana jin dumin wasu na saukowa, a daidai lokacin da yarinyar ke motsi hadi da kwanyara kukan tashi daga bacci, da alama yunwa take ji.


Daukarta ta yi ta dora a saman cinyarta, tana shayar da ita, wasu hawayen na ci gaba da kwarara, wanda ta rasa dalilin fitar su.


Bayan ta gama shayar da ita ta mayar da ita kan katifarta, tana dauko wayarta da ke jikin chaji.


Text message ta rubuta ma Ishraq cewa,


'Allah Ya raya mana Mariya (Ameerah).'


Ta tura mishi tana lumshe idanuwanta. Ta sani ba zai waiwaye ta ba, ba zai ba ta amsa ba, sai dai hakkinshi ne ya san komai game da yarinyar, hakkinshi ne ya san alkunyar diyar cikinshi.


Bai yi responding din ba kamar yadda ta yi tsammani. Sallamar su Haneefa ta ji hakan ya sanya ta murmusawa, tana tabe baki da fadin "Da ba ku zo yau ba da ni kadai na san hukuncin da zan yi muku."


Dariya suka yi su duka biyun. Suna rige-rigen daukar Ameerah.


"Wai wanne suna za a rinka ce mata ne?" Haneefa ta tambaye ta, tana manna ma yarinyar kiss a goshi.


"Ameerah..." ta furta, tana jin nauyin maganar.


"Ameerah?" Suka hada baki wajen tambayar ta. "Kina da hankali kuwa Boobah? Ameerah dai Ameerah da mijinki yake wulakanta ki saboda ita kuma kika saka wa diyar da kika haifa?"


Kanta ta jinjina, tana kallon Haneefa da ke magana cike da takaicin abin da Mahboobar ta aikata.


"Ban taba ce muku Ishraq yana wulakanta ni ba tun da muka yi aure. Me ya sa kuke tunanin yana min wulakanci? Ni lafiya lau nake da mijina." Ta fada, k'arara fuskarta na nuna karya take yi.


Murmushin takaici Saleemah ta yi. Ba ta ce komai ba saboda ba ta son ratsa sirrin da Mahboobah ke kokarin ginawa, duk da cewa a rushe yake wurinsu, babu wanda zai kalli Mahboobah ya ce tana da cikakken kwanciyar hankali.


"Babu komai. Allah Ya raya ta." Shi ne kawai Saleemah ta fada, Haneefa kuwa takaici bai bar ta sake fadin komai ba sai ma tashi da ta yi ta fice daga dakin.


"Ban ga dalilin da zai sanya ni yin kishi da halittar da shi kanshi Ishraq din bai san inda take ba. Bai sani ba ta yi aure ko ba ta yi ba. Bai sani ba tana raye ko ba ta raye. Ina son faranta mishi, ina jin dadi sosai idan na gan shi yana jin dadi."


Da ido kawai Saleemah ta bi ta, tana mata kallon 'Ba ki da hankali' Mahboobah kuma tana mata kallon 'Ki yarda da ni'.


"Allah Ya raya mana Ameerah Ishraq Sulaiman." Saleemah ta furta, tana kokarin goya yarinyar da ta sake komawa bacci.

"Ko ki yi ma Goggo magana sai ta goya ta."


Hararar ta Saleemah ta yi, "Ina cikin gidan ne zan bari Goggo ta goya min 'ya? Ni ban iya wannan shirmen ba." Ta saki guntun murmushi.


End of chapter


Ina ta ganin karancin comments da likes. Ban san miye aibu ba don mutum ya dangwana 'yar karamar tauraruwar can da ko a ido take da kyawun duba ballantana kuma idan an taba ta. Kar ku gajiya mutanena😍kamar yadda ni ma ban gajiya ba da typing.


Princess Amrah

RAZ 2Yana zaune a cikin Office ya ji karar shigowar message dinta. Dubawa ya yi ya ga abin da ta rubuta, ya yi bayyanannen tsaki yana al'ajabin mutum irin Mahboobah, yana mamakin zuciya irin tata, wadda sam ba ta san wani abu wai shi fushi ba. Tun da yake da ita sau daya ya taba ganin ta bata ranta, a lokacin da ya ce zai zubar da cikinta.+


"Ameerah?" Ya fadi a bayyane, ya ji dadi, sai dai a take ya karyata kanshi, ya karyata jin dadin da yake tunanin ya yi. Halittar da bai taba jin soyuwarta ba ce za ta haifa mishi diya har ya so ta? Ba ya tunanin akwai ranar, ko kadan ba zai taba son yarinyar ba.


Wayar tashi ya ajje, ya jawo wasu takardu yana dubawa, sai dai duk layi daya da zai karanta, text message din Mahboobah ne ke dawo mishi, yana zaga duk wani noti da ke cikin kwakwalwarshi. Sai kawai ya ji yana son ganin hoton yarinyar, yana son ganin ta, sai dai ta yaya? Ba ya son duk waya alama da za ta nuna yana son yarinyar. Idan ya tambayi Khalid, Khalid din zai yi tunanin ko son yarinyar yake tun da har ya nemi ganin hotonta. Mahboobah? Ya gyada kai, yana jin dacin tunanin da ya ambatar mishi sunanta. Bai ma da lambarta a babbar wayarshi da yake chatting da ita. Ba ya jin zai iya cewa ta turo mishi don ma kar ta ji dadi.


*

Ba wani taron suna aka yi ba, saboda Mahboobah ta ce ba ta son taron, ita din da ma can ba ma'abociyar son taron mutane ba ce, ko na bikinta ma don an matsa ne, wannan kuwa dole suka bar ta, saboda ta kafe a kan ba ta so din.


Har a wannan lokacin Ishraq bai san kalar gudan jinshi ba. Amma duk da haka sun yi kaya na gani na fada, duk da cewa ba shi ya siya ba, Mami ya tura ma kudin ta siyi komai aka kai. Ita kanta uwar jegon kaya kala goma sha biyu aka mata, Ameerah kuwa, ba a magana. Tsadaddun kaya irin na kasashen ketare aka gwangwaje ta da su.


Ranar da suka cika wata biyu, ranar ne Mommy ta sanya musu lokacin komawa. A wannan lokacin sosai Ameerah ta shiga zukatansu, saboda irin yaran nan ne masu tsananin shiga rai, ga ta farar fata, jikinta gubul-gubul,  tun kafin a yi arba'in dinta take dariya sosai. An mata aski, amma kanta har ya sake cika.


Fareedah, Saleemah da Haneefa ne 'yan rakiyar, sai Goggo, suka yi sallama da Mommy suna isa motar Yah Aliyu wanda zai kai su.


Ko da suka isa gidan, gate din a rufe yake, karamar kofar jikin gate din ma a datse. Mamaki ne ya kama su, kasantuwar sun san Ishraq ya san da batun dawowar, har lokaci sai da aka fada wa Mami, minti biyar kadai suka kara a kan yadda suka fada din.


Takaici ne ya kama su su duka banda Mahboobah da zuciyarta ke riya mata akwai dai yadda aka yi.


"Ki kira shi mana." Aliyun ya fada, yana tsananin jin haushin wannan rainin wayon na mijin da kanwarshi take aure.


Tana tsoron kiran wayar tashi, sai dai ba ta da zabin da ya wuce hakan. Wayar ta danna tana latsa kiranshi, tana jin gabanta na tsananta bugawa, idan ma ya dauka din, ba ta san abin da za ta fada mishi ba, ko kadan ba ta da kwarin guiwar da za ta iya daga labbanta ta yi mishi magana.

Dukkansu suna lura da yanayinta, suna lura da yadda duk ta daburce daga cewa ta kira shi a waya. Mamaki suke hade da tausayin kangin rayuwar da take cikinsa.


Sau uku tana kiran shi amma bai dauka ba. Kamar za ta yi kuka ta ce da Aliyu "Bai dauki kiran ba Yah Aliyu. Watakila yana wani aikin ne." Tana kokarin kare Ishraq din.


"Ko wanne irin aiki yake amma ai ya san da zuwan mu ko? Ke dai ba kya son laifinshi MB, kuma dole a fada."


Kallon ta ta mayar ga Haneefa, tana rasa kalmar da za ta yi amfani da ita wurin kare laifin da ita kanta ta san ya yi shi.


STORY CONTINUES BELOW

"To ko ki kira Mami." Fareedah ta fada cike da tausayin Yayar tata. Wannan kalar rayuwar ai jarrabta ce mai matukar girma. Rayuwar da mace za ta jefa kanta a cikinta tana ji tana gani, saboda soyayyar da ita kadai ke yin ta, son maso wani.


Kanta ta gyada Mahboobah, a wannan karon tana jin saukar hawayen da ta gaza tantance dalilin saukar su. "Idan fa ya ga kamar mun masa gami da mahaifiyarsa?"


"Ya Raheem!" Saleemah ta fada tana dafe kanta. "Kin ki taunuwa kin ki haduwa MB. Yanzu ya kike so a yi? Mu koma gida ko mu bar ki a nan zaman jiran masoyinki?"


Lambar Mamin ta latsa, bugu biyu ta dauka da sallama a bakinta. "Ya kuke?" Ta furta bayan ta tsinkayi gaisuwar da Mahboobah ke mata. "Yanzu za ku koma ne ko har kun tafi?"


"Mun tafi Mami, har ma mun isa gidan." Tana son dorawa da 'Gidan a rufe kuma mun kasa samun Ishraq' amma tana jin tsoro, ba ta ma san ta inda za ta fara fada mata ba, ba ta jin za ta iya kai karar Ishraq.


Ganin ba ta da niyyar aikata dalilin kiran ya sa Haneefa ta kwace wayar tana dora ta a saitin kunnenta, ta gaishe da Mami da sakin fuskarta ta amsa.


"Mami mun kusa minti ashirin tsaye a waje, gidan a rufe, babu Ishraq din, kuma ta kira lambarsa bai dauka ba."


Kallon ta Mahboobah ke yi, tana gyada mata kai, tana jin saukar wadansu hawayen.


"Kuma fa ya dan jima da barin nan, har da abincinku ya taho da shi, na ce da shi kai tsaye ya wuto ashe wani wurin ya nufa. Ina zuwa." Ta fada cikin jin haushi.


Kiran shi ta yi, bugu daya ya dauka yana fadin "Mamina..." ta dakatar da shi.


"Wannan wace irin dabi'a ce likita? Don me ya sa za ka shanya mutane a kofar gida tun dazu suke jiran ka, bayan kuma ka san da zuwan su? Kuma abun haushi sun kira ka ka ki dauka? Wulakanci ne ko mene ne?"


Cikin tsananin takaici take wannan maganar, tana jin kamar ta sanya bulala ta zane shi yadda ake ma kananan yara idan suka yi laifi.


"Mami...aiki fa nake yi..."


Ta dakatar da shi da fadin "Wane irin aiki ne wanda ya fi iyalinka muhimmanci Ishraq? Kowanne namiji ana tsintar shi cikin walwala da nishadi a lokacin da irin haka ta faru da shi amma ban da kai. Idan wani ne ma, yana kofar gida zaman jiran iyalinshi. Sai kai ne za ka bayyana wa duniya ba ka son Mahboobah ba ka son diyar da ta haifa, gudan jininka Ishraq?"


Wani irin dokawa gabanshi ke yi, wanda ya jima bai yi irinsa ba. Ya kasa gane madosar zantukan Mami, fadan da take mishi kadai ya kasa kunne yana sauraro, sai dai tsantsar mamaki ya sa ba ya fahimtar komai, har sai da ta zo gabar da ta sanya shi tsananin al'ajabi.


"Na san komai Ishraq. Na san duk wani hali da kake ciki tsakaninka da Mahboobah. Kamar yadda ba ka taba fada min duk wani abu da ya danganci rayuwar aurenku ba, haka Mahboobah ma. Babu komai da take fadi game da kai face alkhairinka. Na saka muku ido Ishraq, tun farkon aurenku na fara ganewa, sai dai rashin hujjar dogara ya sanya ni zura idanuwa, har sai ranar da kwan zai fashe. To ina so ka sani, kwai ya fashe a yanzu, na sani, na san ba ka kaunar Mahboobah, ba ka kaunar takwarata Ameerah!"


Ta karisa da furzar da wani irin iska, tana tuna sadda Khalid Zannah ya zo har gida ya same ta bayan haihuwar Ameerah. Bayan ya gaishe ta ya ce 'Mami magana na zo da ita mai muhimmanci.' Yana sauke idonshi kanta. Duk da bai so fadin zancen ba, sai dai ya zame mishi dole ya sanar da Mami, ko hakan zai sa Mahboobah ta samu 'yanci a gidan Doctor Ishraq. Tun da aka haifi Ameerah yake bin kan Ishraq din a kan ya je su kara duba yarinyar amma ya ki. Kai tsaye ma ce mishi ya yi 'Na tsani Karfen kafa, na tsani abin da ta haifa.' Wannan maganar ce ta ingiza Khalid Zannah, ya ga cancantar fada wa Mami, idan abun ya fi karfinta, dole Mahboobah ta hakura ko ba ta so a raba aurenta da Ishraq din.


'Ina sauraron ka Khalid.' Mamin ta fada, tana mayar da dukkanin hankalinta gare shi.


Sai da ya dan ja numfashi, yana jin nauyin maganar, kafin ya ce,


'Mami a kan zamantakewar Ishraq ne da Mahboobah...' a takaice ya labarta wa Mamin duk abubuwan da suka faru, tun daga yadda auren ya samo asali, jiran Ameerah Muhammad da yake yi, har zuwa kalolin azabar da ya rinka gana wa Mahboobah bayan ya aure ta, sai dai ya boye wa Mamin batun zubar da cikin da Ishraq din ya ce za a yi daga farko.


Kai Mami ta gyada, tana jin hawaye na niyyar zubo mata, sai dai ta yake su, ta komar da su ta karfi da yaji, ba ta so ta zubar da hawaye ta silar bacin ran tilon dan nata, ko kadan ba ta so. Ta san illar zubar hawayen mahaifiya ga danta.


'Ban zo da nufin shiga tsakaninki da Ishraq ba Mami. Tun da jimawa Allah Shi ne shaida a gare ni, na yi bakin kokarina don ganin na daidaita tsakaninsu sai dai abun ya gagara. Ishraq ba ya son Mahboobah ko kadan, ya tsane ta. Daidaita tsakaninsu ba abu ba ne mai sauki. Ki gwada taku ta dattawa Mami, watakila za a dace.'


Godiya Mamin ta hau yi wa Khalid, tana mishi alkawarin da yardar Ubangijin sammai da kassai komai zai daidaita, za ta kokarta don ganin ta daidaita tsakanin ma'auratan biyu.


"Ka yi maza-maza ka koma gida ka bude musu kofa su shiga likita, sannan ka zo ina neman ka."


Ta fada tana jaddada mishi. "To" kawai ya iya furtawa, yana jin tsanantar faduwar gaba a tattare da shi. Ta tsinke wayar ba ta ko tsaya sauraren to din tashi ba. Tana jin zuciyarta na mata radadi, tausayin yarinyar marainiya na kama ta, a wani bangaren kuma, kaunarta take ji da dukkanin ruhi da zuciyarta. A wannan zamanin, samun yarinya irin Mahboobah ba abu ne mai sauki ba. Samun mutumin da ke maka kauna ta tsakani da Allah kamar yadda Mahboobah take ma Ishraq ba abu ne mai sauki ba. Hakuri, juriya da rikon sirrinta ko wata matar da ta yi shekaru sittin a duniya ba za ta iya yin su ba. Idan wata ce da tuni duniya ta gama sanin rayuwar aurenta. Tafin hannunta ta sa tana share guntuwar kwallar da ta yi nasarar sauko mata.


*

Ba a fi minti sha biyar ba sai ga Ishraq din ya zo, da wani irin gudun masifa kamar zai tashi wurin. Sai da ya zo gaban gate inda suka faka tasu motar, ya yi fakin yana fitowa daga ciki. Bai ko kalle su ba ya bude musu gate din, ya kwaso kulolin abinciccikan da Mami ta hada musu, sannan ya koma motarsa yana juya akalarta, gidan Mami yake son wucewa, yana so ta kalli kwayar idonshi ta fada mishi abin da yake faruwa da har ya sa take mishi kalar fadan da ta kusan shekara biyu rabon da ta mishi ko makamancinshi.


Dukkansu mamaki ne ya kama su. Idan har ba su cancanci ya gaishe su ba, ai sai ya musu sallamar da ta zama wajibi. Da zuciya irin ta Aliyu, tuni ya kawo wuya. Kallon Mahboobah yake yi da ke murmushin yake, tana kokarin kare bacin ran da ya gama bayyana kanshi a fuskarta.


Kallon tsana Aliyu ya bi Ishraq da shi, yana kallon yadda ya danna ma motar wuta kamar zai tashi sama. Ya dawo da kallon shi ga Mahboobah, yana jin nauyin maganar da zai yi, sai dai kuma ta zame mishi dole, matukar yana son kanwar tashi da gaskiya. Mahboobah ba za ta taba yin zaman 'yanci a gidan mijinta ba, matukar ba an nuna ma Ishraq cewa ita din diyar so ba ce ba kamar kowa.


"Ku shiga mota mu koma gida." Ya fada cikin bada umurni, fuskarshi babu alamun wasa, babu ta inda za ka iya musa wa maganar tashi.


"Yah Aliyu..." Mahboobah ta fada, tana son dorawa da 'Kar ka yi min haka.' Ta kasa, sai saukar hawaye da ta ji yana bin ta tamkar an kunna famfo.


"I don't want to hear anything from you Boobah. Just keep quiet Mahboobah. Yarinya duk kin bi kin sukukuta kanki a kan wancan mutumin da bai san darajarki ba, bai san darajar danginki ba, bai san darajar dukkan mutane ba ma."


End of chapter


Take it easy Aliyu Zakin fama🤣sarakan fushi da saurin sauka.


Princess Amrah

RAZ 2Jerangwama take yi Mommy, daga bakin tv zuwa 3 seater, hannuwanta duka biyun dafe da bayanta, fuskarta shimfide da bayyananniyar damuwa.


"Mommy, dole ne a san abun yi. Ba zai yiwu ba mu zira ido muna kallo soyayya ta nemi nakasta zuciyar Boobah. Wallahi sam mutumin can ba mutumin kirki ba ne. Na yi da na sanin biye wa Mahboobah tun tashin farko har aka daura aurensu."


Gyada kanta ta yi Mommy, "Rubutaccen al'amari ne Aliyu. Da ma can Allah Ya zana alkalamin kaddarar auren Ishraq a rayuwar Mahboobah. Ko mun so ko mun ki dole sai an samu rabon Ameerah a tsakaninsu. Amma ni ina ganin, abin da ya aikata muku yau bai yi girman daukar masa hukuncin da kake da niyyar yi ba. Hakuri..."


"Mommy..." Ya fada yana takowa kusa da ita. "Har sai yaushe ne kalmar 'hakuri' za ta fice daga bakin iyaye yayin da aka cuzguna wa ya'yayensu a gidan aure? Mommy har sai yaushe ne za a rinka bin hakkin mataye? Me ya sa kalmar 'hakuri' ta zama tamkar abar ado ga iyaye?"


Ajiyar zuciya ta sauke Mommy. Yaro yaro ne, ta fada a zuciyarta. "Hakuri abu ne mafi girman daraja a duniyarmu Aliyu. Hakuri shi ne jigon zaman aure, hakuri yana sama da dukkan komai, hakuri na sama da soyayyar da ake ganin dominta ake gina aure." Ta dafa kafadarshi. "Ko ka taba ganin a nasihar aure an ce a je a yi ta zaman soyayya? Ba a fadin haka Aliyu. Sai dai a ce a je a ci gaba da zaman hakuri, saboda an san shi ne ginshikin rayuwar auren dukkanta, shi ne jigon zaman aure. Matukar aka ce za a zabi zaman aure babu hakuri, to ina mai tabbatar maka da cewa ba zai yi karko ba. Laifi kadan za a rinka daukar zafafan hukunci ga juna. Amma idan aka yi hakuri, sai ka ga an zauna lafiya."+


"Amma Mommy wani hakurin da shi gara babu shi. Mommy kina ina ake yin hakurin da ake kuntata wa zukata? Sai ki ga an maka abu ka shanye, ka yi hakuri, amma yana nan a cikin zuciyarka zaune daram. Irin wannan hakurin ne ke illata zuciya. Irinshi ne sai dai a wayi gari ki ga mace da cutar hawan jini, ciwon zuciya, ko kuna kawai ta girde ta fadi. Irinshi ne depression ke kama mata."


"Haka ne. Na yarda da duk kalamanka. Sai dai kuma yawaitar hadisan da suke magana a kan muhimmancin hakuri ya take wannan maganganun naka Aliyu. Ka yi hakuri kawai Mahboobah ta koma gidan mijinta. Tun farko ita ta ji za ta iya ta zabi zaman aure da shi duk da ta san ba ya son ta. Da zurfin ciki irin nata kuma duk abubuwan da suke faruwa a gidan aurenta daidai da rana daya ba ta taba samun wani da su ba. Don haka tashi za ka yi ka mayar da ita. Ta je ta ci gaba da zaman hakuri tun da haka ta ga ya fiye mata."


Runtse idanuwanta ta yi Mahboobah. A duk kalamansu babu wanda ta tsinta sai maganar Mommy ta karshe cewa ya tashi ya mayar da ita. Wani irin dadi ta ji ya sauka a kasan zuciyarta, wanda ta kasa boye shi har sai da ya bayyana a saman fuskarta. Ta saki murmushi tana dan cije harshenta.


"Ka gani ko. Kalli fuskarta ka ga dadin da ta ji don na ce ka mayar da ita. Alamun duk kukan nan da take yi don ka ce ba za ta koma ba har sai an tattauna da dangin Ishraq ne. Sai ki tashi ku tafi ai." Mommy ta fada tana mayar da dubanta ga Mahboobah.


Sai kuma ta ji wata irin kunya ta tsarga ta, ta lullube ta. Ba ta san yadda aka yi ta yi murmushin ba. Da ta san sadda zai fito da ta yake shi ya tsaya a cikin zuciyarta. Kasa motsawa ta yi saboda kunya.


"Ki tashi mu tafi." Fareeda ta fada cikin sanyin murya tana mika Ameerah ga Goggo da ke zaune ake komai a gabanta. Babu musu ta mike, ta rayata baby bag din Ameerah, sannan ta je dakinta ta kira su Haneefa suka fice.


*

"Ka ji tsoron Allah Ishraq. Ka sani cewa hakkin Mahboobah ba zai taba barinka ba. Duk yadda kake ganin ka ci bulus don ka zalunci marainiyar Allah to wallahi ba ka ci ba. Matukar ba ka nemi gafararta ba kuma ka gyara kuskurenka to wallahi sai Allah Ya bi mata hakkinta."


STORY CONTINUES BELOW

Kanshi ya sunkuyar a kasa yana sauraron kalaman Mami. Yana jin zafinsu, yana kara jin tsanar Mahboobah da ta kasance a tsakanin duk wani farin ciki nashi da na Maminshi a yanzu.


"Idan ka ci gaba da cuzguna wa Mahboobah, ban yafe maka ba Ishraq. Idan ba ka kyautata wa Ameerah diyar cikinka ba ko lahira kada Allah Ya hada ni da kai." Ta fada tana mikewa, tana tsananin jin dacin maganganun da suke shiga tsakaninta da tilon danta, mafi soyuwa a gare ta, kuma gudan jininta. Sai dai ba ta da zabin da ya wuce ta yi hakan, matukar tana son kawo gyara a tsakanin ma'auratan guda biyu. Hakkinta ne a matsayinta na uwa mai son ganin danta ya samu rabauta a wurin Allah madaukakin Sarki. Shi ya sa take son shimfida kyakkyawar alaka a tsakanin Ishraq din da Mahboobah.


Tashi ya yi a bisa kafafuwanshi, sai dai kanshi ya dauki zafi, jijiyoyin jiki duk sun mike, idanuwanshi sun kada sun yi jajur, jiri na neman dibarshi ya yi gaggawar komawa ya zauna. Ya fi karfin minti talatin a wurin yana tufka da warwara. Sai da ya ji kan nashi ya dan saki, sannan ya dauki waya da makullin motarshi ya fice.


A mota ya yanke shawarar ba zai sake kula Mahboobah ba bare har ya cuzguna mata Allah Ya isar Mami ta bi shi. Zai sauke duk wani nauyi nata, tun daga kan ci, sha, da kuma sutura. Sai dai maganar sauke nauyin aure ne ba zai yi ba. Wancan karon ma kaddara da tsautsayi ne suka gitta, kuma ya mayar da hakan rabon samun Ameerah a tsakaninsu.


Sidi and Sons Supermarket ya biya, ya siyo kayan tea da duk wasu abubuwa na bukatar gida. Sannan ya kwaso diaper mai guda dari, ya siyo carton din faro water, bayan ya biya kudin ya kwasa ya kai mota. Daga nan ya wuce Taraba suya, kaji guda uku ya siya sannan ya kwaso fruits kala-kala ya kama hanyar gida.


A falonta ya jibge kayan. Ya isa dakinshi ya dan watsa ruwa, ya gabatar da sallar maghrib sannan ya dawo falon ya kunna kallo. Guntun tsaki ya saki sannan ya mike ya nufi dakinta. Ya gan ta kwance ga Ameerah gefenta sai wasa take tana tsilla kafafuwa. Ya yi sallama hadi da isa gabanta. Bai ce mata komai ba sai daukar Ameerah da ya yi ya nufi fita. Har ya kai bakin kofa kuma ya juyo ya ce mata "Ga kaya can na zo da su ki kwashe daga falo." Ya karisa maganar yana fita daga dakin.


Bin bayanshi ta yi da kallo, tana mamakin ganin canji a tattare da shi. Tun daga kan sallamar da ya yi mata har zuwa daukar Ameerah da ya yi. Ta dan runtse idanuwanta tana bude su, tana jin wani ni'imtaccen dadi na ratsa bargo da jijiyarta, yana zarcewa a cikin jinin jikinta, yana kaiwa har cikin zuciyarta.


Cikin nutsuwarta ta taka ta isa falon. Ta samu kayan da ya jibge, ta fara kwashewa a hankali cike da al'ajabin abin da yake faruwa. Diaper da ruwan faro da ta tabbatar na Ameerah ne ta kai dakinta, kajin kuma ta dibi kadan ta zuba a plates kashi uku, sauran ta cire cabbage da albasan da suke ciki sannan ta saka a cikin fridge.

Ishraq ta kai ma guda, ta kai ma Goggo guda sai ta tafi dakinta da gudan, zuciyarta na dokawa da sauri da sauri ganin canjin da ta samu daga wurin abar kaunanta Ishraq Sulaiman.


Kazar take ci amma sam ba ta jin dandanonta. Tsantsar farin cikin da take cikinsa ya zarce dandanon kazar da ta kasance mafi soyuwa a gare ta.


Idonshi kyam yake kan Ameerah. Tsantsar kamanninta da suke bayyane da nashi ne ke ba shi mamaki. Babu ta inda yarinyar ta baro shi. Da zarar ta hada ido da shi sai ta wangale mishi baki tana dariya. Haka kawai ya tsinci kanshi da kaunarta, duk yadda ya so ya karyata hakan abun ya gagara. Kaunarta ce ke ratsa duk wani bagire da yake cikin zuciyarshi. Ya dauke ta ya manna a kirjinshi, yana jin bugun zuciyarta, yana jin wata irin ni'ima na sauka a duniyarshi. Ashe haka iyaye suke ji yayin da suka rungume ya'yan da suka haifa? Bai taba zaton zai so Ameerah ba, daidai da rana daya bai taba tunanin akwai ranar da zai so abin da Karfen kafa ta haifa masa ba. Sai ga shi ya tsinci kanshi a yanayin da bai taba jin irinshi ba. Soyayyar Gudan jininshi na yawo ta ko'ina a cikin jikinshi.


Wayarshi ya jiyo tana ringing daga dakinshi. Ya tallabi yarinyar a kafada yana nufar dakin nashi. Ya duba, ya ga sunan Khalid Zannah. Bayyanannen tsaki ya yi, yana jin ba zai iya daukar wayar Khalid ba. Duk da Mami ba ta fito kai tsaye ta fada mishi daga inda ta ji labarin rayuwarshi da Mahboobah ba, jikinshi ya ba shi aikin Khalid ne. Ya gane Khalid ba masoyinshi ba ne na gaskiya. Babban burinshi shi ne shiga tsakaninshi da Mami.


Sai da ya sake kira a karo na biyu sannan ya dauka, yana dafe wayar tsakanin kafada da kunnenshi, don yana gudun kar ya saki Ameerah ta fadi, bai iya daukar jarirai ba.


Bai ce komai ba har sai da Khalid din ya yi magana. "Ina ka shige ba ka dauki waya ba."


Bayyanannen tsaki ya yi, Khalid bai yi mamaki ba don ya san tsaki karamin aikin Ishraq din ne. Ya sake maimaita "Ina ka shiga?"


"Khalid..." ya fada yana kwantar da Ameerah a kan gado. Ya dora da "Na taba tunanin shiga tsakaninka da Ummi? Tunda kake a rayuwarka ka taba aikata wani abu na same ta na fada mata?"


Mamaki ne ya kama Khalid. Ko a wasa bai kamata ba Ishraq ya soko mahaifiyarshi a maganar da yake yi. Sai dai yana fadin haka ya gane inda ya dosa. Ya gane cewa Mami ta yi mishi magana ne.


"Ta rasu." Ya fada da sanyin murya.


"Allah Ya gafarta mata. Amma kafin ta rasu nake magana. Na taba kwasar issue dinka na gidan aure na fada mata? Ba ma issue na family dinka ba, akwai wata rayuwa taka da na taba zuwa na samu Ummi na gulmata mata?"


Gyada kanshi ya yi Khalid, yana jin ciwo da dacin maganganun da Ishraq ke jifar shi da su. "Ba ka taba ba, ban kuma ga ta hanyar da za ka taba ba din, saboda ba ka da hujjar dogara, lafiya nake da iyalina, ban taba cuzguna mata ba tun da muka yi aure, sai dai sabani na yau da gobe."


Dacin kalaman da Khalid ke sakar mishi cikin sanyin murya ya sanya shi jin wani irin tukuki da da na sanin yi ma Khalid din maganar. Lallai ya kai Khalid kwano, mai hakuri bai iya fushi da bacin rai ba. Tun da yake da Khalid din wannan shi ne karo na farko da ya taba sakar mishi magana mai zafi kwatankwacin wannan. Tare suka tashi tun yarinta. Iyayen Khalid 'yan Maiduguri ne, yaren Kanuri. Kasuwancin kayan kamshi ne silar dawowar su garin Kaduna, sai kuma suka samu wurin zama a nan. Har lokacin da Allah Ya dauki rayuwar mahaifinshi Alhaji Zannah Abdullah, a lokacin duka Khalid din bai wuce shekara ashirin ba a duniya. Dangi da iyayen mahaifiyarshi Ummi Yakura sun so ta koma cikin dangi, amma ta turje ita ta ga wurin zama. Ta riga ta saba da Kaduna don haka ba za ta iya tafiya ba. A haka suka bar ta ta ci gaba da zama tare da ya'yanta biyar, Khalid ne babba sai mai bi mishi Khalil, sauran kuma mata ne Halimatu, Zarah da Rabiatu. Akwai shakuwa mai tsananin karfi tsakanin gidan su Khalid da na su Ishraq. Wanda wannan zumunci ya samo asali ne ta makwaftakarsu, tare yaran biyu suka tashi da kaunar junansu, har zuwa lokacin da mahaifin Khalid ya yi ginin kanshi a Hayin Rigasa, suka bar Unguwar Rimi.


"Ishraq, ban je na samu Mami da maganarku da nufin shiga tsakaninku ba. Ka fi kowa sanin ni ba magulmaci ba ne, kuma ko zan yi gulma ba zan yi taka ba Ishraq, idan ma zan yi din, ba zan yi ta ba da mahaifiyarka. Ba na nufinka da komai face alkhairi. Amma na ga alamun hakan ya maka zafi har kake kokarin goranta min. Babu komai, ka yi hakuri idan abin da na yi da niyyar gyara ya bata ranka. Sai an jima." Kit ya kashe wayar, yana tsananin jin dacin maganganun da Ishraq din ya yi mishi.


Yana kallon yadda Ishraq ke sake kiran shi amma ya ki dauka. Dole sai ya nunar mishi da ya ji ciwon maganganun shi ko zai samu salama a cikin zuciyarshi.


Runtse ido Ishraq ya yi, yana tuno aminci da yardar da take tsakaninshi da Khalid Zannah. Me ya sa bai yi tunani ba kafin ya aikata? Me ya sa ya bi rudin zuciyarshi, yake kokarin yakice alakar da suka gina tun yarinyarsu, a kan wata banza can Karfen kafa? Ya gyada kanshi, yana jin yadda haushin kanshi ke mamaye zuciyarshi. Shi ya sa ba a son yanke hukunci cikin fushi. Yau ga abin da hakan ya aikata mishi. Babban aboki kuma amininshi ya dauki zafi da shi.


Ajiyar zuciya ya sauke, yana jin kukan Ameerah da ta gaji da kwanciya. Ya sabe ta a kafada yana dosar dakin Mahboobah.


End if chapter


Princess Amrah

RAZ 2Ranar da Ameerah ta cika wata shida, Fareedah, Saleemah da Haneefa suka shirya mata saukakkiyar walima wadda ba wani gayyatar mutane da yawa suka yi ba, 'yan uwa ne da abokan arziki. Ba su fada wa Mahboobah ba sai yau din kawai suka ce mata ta je gida akwai suprise. Ta fito parlor a daidai sadda Ishraq zai fita ta gaishe shi ya amsa ba tare da ko kallon ta ya yi ba.


"Ina so zan ne gida ne." Ta fada cikin tsoro-tsoro tana sinne kai.


"Ok." Ya fada yana zaro kudi daga aljihunshi ya ajje a gabanta.


"Sai da dare zan dawo."


"Ok." Ya kara cewa yana kama gabanshi. Har ya fice daga dakin tana bin bayanshi da kallo tana jin wutar kaunarshi na kara ruruwa a cikin zuciyarta. Ko a wancan lokacin sadda yake guma mata takaici, ba ta taba jin daidai da rana guda soyayyarshi ta ragu a zuciyarta ba. Balle kuma yanzu da suke zaune ba yabo ba fallasa. Ta mike jin wayarta na kara ta isa dakinta. Reedah ta gani rubuce a jiki, ta dauka da fadin,


"Ga ni nan zuwa yanzu in shaa Allahu Fareedah. Wanka kawai zan yi, na shirya Ameerah tun dazu."


"Kamar kin san dalilin kiran ke nan, na san ki da sanyi ne Yah Boobah komai naki slowly. Kina ma iya cewa sai kin yi girkin rana kafin ki taho."


Dariya suka yi su duka biyun, Mahboobah na fadin, "A'a wallahi da ma ina da niyyar cikin satin nan in zo in wuni, to kuma sai ga wannan kiran naku na ba zata da kuka ki fada min dalilin yin sa."+


"Ba kuma za mu fada ba har sai kin zo ki gane wa idonki." Ta jiyo muryar Saleemah tana fadi.


"Allah Ya shirya ku ni dai. I don't know ko baikon wata daga cikinku aka yi kuke boye min. Sha anyway, sai na zo din."


Ta tsinke wayar tana matsawa kusa da Ameerah da ke kokarin saukowa daga kan gado.


"Oh yarinyar nan akwai ki da karfin hali. Rarrafen ma da kike yi ba wani kwarin kirki ya yi ba amma wai saukowa za ki yi daga kan gado. Kar in sake gani."


Dariya kawai ta bala wa Ammin tata. Sai da ta shayar da ita sannan ta ajje mata teddies dinta da kayan wasa ita kuma ta shiga wanka.


*

Tuki yake yi amma baki daya hankalinshi na ga Ameerah da bai saka a idanuwanshi ba yau. Duk ranar da ya fita bai dauke ta ta mishi wannan dariyar tata ba jin shi yake incomplete.


Tun bayan da ya fara son yarinyar yake kokarin ganin ya kyautata wa Mahboobah a matsayin tukuicin haifa mishi Ameerah da ta yi. Har yau bai taba jin yana son ta ba, sai dai kuma yana jin ta a kasan zuciyarshi. Kyautatawarta a gare shi na girmama matsayinta gare shi. Sau da dama yakan tuno rayuwarsu ta baya, yadda karara ya rinka bayyana mata karan tsana, yake cin mutuncinta, amma hakan bai taba sanyawa ba daidai da rana daya ta canja daga kyautata mishi. A baya can kafin ya aure ta ya yi sabo da abincin Mami, sai dai kuma yanzu da nata ya yi sabo. Komai daren da zai yo a waje ba zai ci abinci ba har sai ya dawo gida ya ci girkinta. Ko za ta mishi magana ya mata banza ba ta taba fasa gaishe shi ba a kowacce safiya. Ba ta taba barin dakinshi da datti ba. Toilet dinshi kullum a wanke yake cike da ni'imtaccen kamshi. Wardrobe dinshi da yake yamutsewa ita ce ke aikin gyaranta. Komai nashi tsaf-tsaf ba ta taba fasa gyarawa ba. Ko a films ko a littattafai bai taba jin mace mai makamancin halin Mahboobah Bukar ba, sai kuwa Amrah, Amran Annur ta cikin Amrah Nake So. Kwatankwacin tarbiyya da ilmin addininsu na mishi kamanceceniya.


Gyada kanshi ya yi, yana son gusar da tunanin da yake yi daga zuciyarshi, kafin kuma Khalid Zannah ya fado mishi a rai. Rabonsu da juna tun ranar da Khalid ya kashe mishi waya. Babu wanda ya sake waiwayar wani a cikinsu, duk da Ishraq din cike yake da kewar amininshi, cike yake da da na sani da nadamar abin da ya aikata gare shi.


STORY CONTINUES BELOW

A haka ya isa Office zuciyarshi a rabe, wani bangare na cikinta na fada mishi ya samu Khalid Zannah har gida su sasanta kansu. Ba girmansu ba ne wannan.


*

Tun daga shigowarta tsakiyar gidan take kallon yadda aka yi kyakkyawan decoration, ko ina manne da hoton Ameerah, sai kuma daga can inda babban filin yake an yi wata yar karamar kofa da aka zagaye ta da balloons pink colour, daga ciki kuma kujera ce irin ta yara ita ma zagaye da ado, sai daga can sama an lika wata takarda an rubuta 'Princess @ 6 months.' Komai na wurin abun shaawa ne. Sai ma mamaki ya kama ta, ta yadda dukkansu ba su mance da yau Ameerah ke cika watanni shida ba amma ita abun ma bai fado mata a rai ba. Da saurinta ta shiga cikin gida tana kwala kiransu.


"Wannan irin suprise haka." Ta fada tana ma rasa ta inda za ta fara yi musu magana.


"To uwar shisshigi ina ruwanki don mun yi wa diyarmu abu?"


"Babu." Ta fada tana tabe ma Haneefa baki da ta yi maganar.


Dakin Mommy ta wuce ta gaishe ta, bakinta ya gagara rufuwa.


"Ina Goggon taku ne?"


"Ba ta nan Mommy, jikarta ce babu lafiya ta je ta duba ta, tun jiya ta tafi amma ina ji gobe za ta dawo, don kwana biyu ta ce za ta yi."


"Allah Sarki. Allah Ya ba ta lafiya."


"Ameen Mommy. Ina shigowa gida na gan shi cike da ado wadancan yaran sun yi. Ni wallahi da ma ni suka kashe ma kudin." Ta fada tana dariya.


Harararta Mommy ta yi. "Sannu uwar son banza. Ai diyarsu suka mawa ba ke ba. Wancan decoration din tun gari bai gama wayewa ba suka zo da mai yi aka yi shi. Yanzu kuma aikin yin snacks suke yi a cikin kitchen."


"Iyye." Ta fada tana kwalalo ido. "Lallai ma yaran nan. Bari in je in gani."


"Ina Ameeran ne?"


"Tana wurin Saleema Mommy. Ni kam bari in je kitchen din ko samosa in ci."


Ta gaggauta fita tana jin Mommy na mata dariya.


Da yamma wuraren karfe biyar suka fara shagali, hatta rigar da aka saka ma Ameerah Haneefa ce ta siye ta, princess crown, takalmi, socks masu tsada kuma Saleema ta siya. Fareeda kuma ita ce da daukar nauyin snacks din da suka yi. Elhassan Photography suka gayyato tun daga Katsina ya zo ya dauki hotuna. An ci an sha, an gyagije. A ranar sun kara tabbatar ma Ameerah ita din yar gatansu ce. Har sai da yarinyar ta gaji da dauka duk hakurinta ta yi kuka Saleema ta goya ta, ashe ma bacci ne take ji.


Karfe bakwai suka fara haramar tafiya. Da ma a cikin motar Haneefa suka zo, Mahboobah ma ta ce za ta bi su su wuce da ita su ajje ta.


Sallama suka ma Mommy tana ta shi musu albarka suka tafi. A mota sai hirarsu suke yi cike da kaunar juna. Mahboobah suka fara saukewa, sai da suka ga ta bude gidan ta shiga sannan suka tafi.


Babu wuta a gidan da ta shiga, ga wata irin gajiya da ta yi, ita ma kanta da alamu gajiyar ta yi sai kuka take yi wanda ba dabi'arta ba ne.

"Na san wanka kike so Ameerah. Ga gajiya ni ma kaina na yi. Bari in miki wanka sannan ni ma din in yi." Ta fada tana kokarin kunna fitilar wayarta. "Wancan generator mai wahalar tayarwa dai ba zan iya da shi ba. A haka za mu zauna a duhu har su gaji su kawo wuta ko kuma Daddynki idan ya dawo ya tayar mana. Na san yana hanya yanzu."


STORY CONTINUES BELOW

Toilet ta shiga ta hado ruwan wanka a robar Ameerah, cikin lokaci kalilan ta gama shirya ta ta kwantar da ita, tana shayar da ita ma sai ta yi bacci. Hamdala ta yi tana mikewa ta shiga wanka. Bayan ta fito ta saka rigar barci tana nufar kitchen domin tanadar ma Ishraq abinci. Tana da yankakkin vegetables a freezer, ziplock din ta ciro ta dibi kadan a ciki,  ta ciro blended kayan miya ta soya a mai, bayan sun soyu ta tsaida ruwa ta zuba seasonings, curry da black pepper kawai ta zuba a spices, saboda taliya ce za ta yi, taliya kuwa ba ta son a cika mata spices da yawa. Bayan sun tafaso ta sauke. Ta dora wani pan mai fadi a kai, ta zuba mai kadan ta soya taliyar bayan ta datsa ta kanana. Sai da ta yi brown sannan ta kwashe. Ta zuba albasa da attarugu ta soya, ta kawo vegetables dinta a ciki sai da suka soyu sannan ta kwashe. Ta sake mayar da wancan tafasasshen ruwan a wuta, ta zuba soyayyar taliya da vegetables din. Minti kadan suka dahu ta sauke ta zuba a food flask. Ta duba tana da sauran pepper chicken a cikin fridge, a microwave ta yi warming dinshi sannan ta saka a bowl mai murfi duka ta jera a kan dining table.


Agogo ta duba, ta bata kusan awa daya da rabi tana aikin, tara har ta gota. Turaren wuta ta saka mai kamshi sosai ta turara ko'ina cikin gidan har dakin Ishraq. Dakin Goggo ne ba ta kai ba, shi ma din kuma har ta yi niyyar kaiwa ta yi guntun tsaki tuna cewa babu kowa a dakin kuma jiya ta saka. Zama ta yi ta zuba abincinta ta ci, ta dauki plate din ta kai shi kitchen.


Bayan ta koma dakinta ta ji motsin Ishraq. Ajiyar zuciya ta sauke tana sakar ma kanta murmushi. Jin motsinshi kadai kan saka ta a walwala mai girma.


Generator ya tayar ya dawo cikin falon. Yunwar da yake ji ta sa ya ji ba zai iya yin wanka ba har sai ya ci abincin da tun daga bakin gate yake jin kamshinsa. Duk da kamshin turaren wutar da ta sa hakan bai hana bayyanuwar kamshin girkin da ta yi a kurarren lokaci ba. Kamar an ce ya waiga, wa zai gani?


Gardi ne ya fito daga cikin dakin Goggo, suf-suf hannunshi rike da dogon wandon jeans, da riga t-shirt. Sai farar singlet da gajeren wando lemon green a jikinsa.


Cikin sakwannin da ba su wuce ma biyar ba launin idanuwan Ishraq suka canja. Gabanshi ke bugawa da sauri da sauri yana gaggauta mikewa. Gaban mutumin ya shiga, yana bin shi da wani irin mugun kallo mai cike da tarin ma'anoni.


"Don Allah don Annabi ka rufa min asiri, ka yi mini rai. Wallahi ba da son raina ba ne."


Ci gaba da bin shi da kallo Ishraq ya yi. Yana son kar zarginshi ya tabbata. Hayaniyar mutumin ce ta fiddo Mahboobah.


Kamar yana jira kuwa ya mayar da dubanshi ga Mahboobah yana fadin "Boobah don Allah ki fada mishi ba da son raina ba ne. Sai da na ce miki ba zan zo ba amma kika nace sai na zo. Ba a nan muka saba haduwa ba amma tsautsayi da rabon sai an kama ni ya sanya ni zuwa. Ka yi hakuri yallabai."


Kyakkyawan mari Ishraq ya wanke shi da shi. Mahboobah kuwa mutuwar tsaye ta yi. Ba ta taba gasgata irin haka na faruwa da gaske ba sai yau. Kana ji kana gani a bi ka da mummunan kazafin da za ka kasa fitar da kanka daga kanginsa.


Kanta take gyadawa tana kallon Ishraq. Runtse idonshi ya yi, "Kar ki ce min koma Karfen Kafa." Duk tsanarta da ya yi ko da wasa bai taba tunanin za ta aikata haka ba. Daidai da rana daya bai taba kawowa Mahboobah mazinaciya ba ce ba.


Sanin ko ya fada wa Mami ba lallai ba ne ta gasgata ya sanya shi fuskantar mutumin, "Zan rufa maka asiri, zan kuma bar ka ka tafi. Amma da sharadi."


"Wallahi zan yi. Zan yi ko ma mene ne in dai za ka rufa min asiri. Wallahi tsautsayi ne ya kawo ni gidanka."


Idonshi jajur yake Ishraq, ya latso video din wayarshi yana saita ta a fuskar mutumin. "Ina so da bakinka ka fada mini yadda aka yi. Idan ka yi mini karya ina da hanyar hukunta ka."


Sai kuma wani irin tsoro ya kama shi, yana gudun kar wani mummunan tarko ne Ishraq yake son d'ana mishi ta hanyar daukar shi video a wayarshi. "Don Allah kar ka yad'a ni a duniya..."


"Ba rufin asiri kake so ba? Zan rufa maka. Ka fada mini abin da ya faru yanzu-yanzu!" Ya karashe maganar da daga murya sosai.


"Uhm dama...dama ni saurayin Mahboobah ne. Muna biya wa junanmu bukata, wani lokaci tana zuwa dakina, wani lokacin kuma ta kama mana hotel. Sai dai ba koyaushe ba, sai lokuttan da ta tabbatar ta nemi izinin fita a wurinka, ko kuma ka yi tafiya. To yau ba ta nan, mun yi da ita karfe bakwai za mu hadu, sai kuma ba mu samu damar haduwar ba, dawo da ita aka yi. Shi ne ta ce in same ta a gida. Babu yadda ban yi ba da ita a kan mu hakura da haduwar yau, ta ce ita dai a matse take tana da bukatata. Ta kuma tabbatar min da cewa ba za ka dawo ba har sai mun yi mun gama..."


Tas! Tas! Tas! Mahboobah ta wanke mutumin da mari, tana ji wata irin zuciya na taso mata, ta wawuro side stool ta jefa mishi, tana neman sake wawuro wani abun Ishraq ya daka mata tsawa da karfi dole ta koma hayyacinta. Kuka take mai cin rai, kuka take da iya gaskiyarta. Ba ta san me za ta yi ba ta ji sanyi a zuciyarta.

End of chapter


Wallahi I hate sharri! I hate kazafi😭ko a film ko a littafi aka yi wa mutum shi ina jin hawaye cike da idona.


Wannan kangin da aka jefa Mahboobah fitarshi ba abu ne mai sauki ba. Ba lallai ba ne ba ta iya cire kanta daga cikinshi, har sai ranar da gaskiya ta yi halinta.


Abun kuma sai ya hade ga Ishraq da da ma ba kaunarta yake yi ba.


Tambaya;

Shin waye ya shirya wa Mahboobah wannan kullin? Kaidin wanene?


Princess Amrah

RAZ 2Kafar wandon Ishraq ta kama, tana kuka mai cin rai, tana son gusar mishi da karairayin da azzalumi kamar yadda ta saka mishi suna ya shirya wa Ishraq din.


Fizge kafar wandonshi ya yi yana hada mata da mari mai zafi.


"Babu ta inda za ki iya karyatawa. Kin saba tambaya na za ki fita ki je gidanku ko wani wuri, amma kin taba ce min sai dare za ki dawo? Ba ki taba ba!

Wannan ma kadai wata hujja ce mai karfi.


Ban taba sanin mazinaciya ce igiyar aurenta ke rataye a wuyana ba sai yau. Na yi da na sanin aurenki, na yi da na sanin hada zuri'a da ke Karfen Kafa!"


Jin maganganunshi take yi tamkar ya watsa mata tafasasshen ruwa. Tamkar an barbada gishiri a rubabben rauni ko kuma gyambo.


Fincikarta ya yi, yana jefar da ita can gefen kujera, fuskarta ta daki katakon hannun kujerar da yake royal ne masu cike da adon katako. Jin d'umi na bin fuskarta ya sanya ta sanya hannunta ta shafo, jininta ta gani kwance a hannun, tana kuma jin yadda yake barazanar shiga cikin idanuwanta.


Numfashi take saukewa da sannu da sannu. Idan da sabo ya ci a ce ta saba da bakaken maganganun Ishraq tun farkon aurensu har zuwa lokacin da ya daina yi mata su. A kullu yaumin ya yi mata wata bakar magana jin ta take sassanya a cikin zuciyarta. Komai zafin maganar da zai mata da sanyi take tarbarta. Sai dai a yau, a yau sabanin haka ne. Tukuki take jin zuciyarta na mata. Runtse idanuwanta ta yi tana mikewa, ta matsa a kusa da shi, ido cikin ido take fadin,+

"Anya kuwa akwai zuciya a kirjinka Ishraq? Ka tuna da cewa kai namiji ne da ya kamata a ce ka tsaya ka binciki komai kafin ka zartar da hukunci. Ishraq, kafin ka kira ni da mazinaciya yana da kyau ka fara binciken gaskiyar lamarin. Da wuya idan kana tsoron Ubangijin al'arshi mai girma, wanda Ya shimfida adalci a tsakanin ma'aurata."


Da matsanancin tashin hankali da bala'i ya yo kanta. Wani marin ya sake dauke ta da shi.

Sai dai ba zafin marin ya shige ta ba sama da zafin kiranta da kalmar 'mazinaciya' da ya yi.


"Na sake ki saki daya, Mahboobah!" Uku ya so yi mata, da kyar ya iya kwabar zuciyarsa ya tsaya a dayan.


Kanta take gyada mishi. Tana son yin magana amma tana rasa ta inda za ta fara. Hawayen da take yi din kanshi ya kafe.

"Za ka yi da na sani Ishraq, a lokacin da da na saninka ba za ta amfane ka da komai ba. Sannu a hankali gaskiya za ta yi halinta. Na sani ba zan iya fitar da kaina ba, amma Allah'n da Ya halicce ni Shi zai fitar da ni. Ba zan ce ina nadamar aurenka ba Ishraq, domin kuwa ko a yanzu zan daga hannu a sama in gode wa Ubangijin da Ya halicce ni, saboda Ya cika mini burina na aurenka Ishraq. Da na sani da nadama guda daya zan yi, shi ne na butulce wa maganar iyaye da dangina, na zabe ka a kan farin cikinsu, na zabi zama da kai duk da cewa ba su so."


Ta saki murmushin takaici, tana dorawa da "Alhamdulillahi da Allah Ya halicci Ameerah a tsakaninmu. Na gode miShi da Ya shimfida ta a tsakaninmu, rayuwar shekaru biyu da muka yi ba ta tashi a iska ba. Ko gobe zan yi alfahari tare da nuna ta a matsayin gudan jinina, gudan jininka, wadda muka haifa ta hanyar auratayya ni da kai.


Na sani Ishraq, na sani wannan video din da ka dauka don ka tallata ma duniya ni ne. Shi ya sa ka rinka yi kana daukar fuskata a daidai lokacin da nake rasa abun cewa. To ka sani, in dai mahaliccina Ya san gaskiyar abin da ya faru, bai zama dole sai duniya ta shaidi hakan ba. Karkarinta dai a ce zan rasa mijin aure ko? To ban damu ba. Aure ya shayar da ni giyar mamaki. Rayuwar aure ta karantar da ni darussa masu tarin yawa. Ko gobe ba na marmarin sake auren kowa har ranar da mutuwata za ta zo ta dauke ni."


STORY CONTINUES BELOW

Tabe bakinshi ya yi, yana barin wurin. Da na sani hade da takaicin auren Mahboobah na dad'a taso mishi. Da kuma ta yadda kaddara ta jefa shi hada jikinshi da nata har tsautsayin samuwar Ameerah ya gitta a tsakaninsu. Har ya tafi kuma ya juyo ya kalle ta cike da tsana.


"Idan kin so kina iya bari har gobe ki tafi. Don kar ki tafi min da 'ya a cikin daren nan."


Ta kwashi fin minti talatin duke a wurin tana kuka. Zuciyarta take ji tana mata tsattsauran radadi, har tana ji tamkar ta bude tsakiyar kirjinta ta zaro ta waje ko za ta samu sassauci. Goshinta ta dafe, tana jin wani radadin wanda ta ma manta da ta ji ciwon.


A daddafe ta mike zuwa daki, kayanta ta hau hadawa a babban akwati guda, sai ta zuba na Ameerah a karamin akwati. Ta dauki duk wani abun bukata sannan ta shayar da Ameerah, ta goya ta a saman bayanta.


Ta fito waje, tana sake waiwayar gaban gidan, tana tunanin duniya, tunanin kalaman mutumin da ta so fiye da numfashinta take yi. Ba ta ma san da wanne ido ba ne za ta kalli wani da matsalarta. Domin idan akwai wani mai laifi bayan ita yake. Ita da ta jefa kanta a rayuwar aurensa.


Da kyar ta samu keke napep, ta kwatanta mishi gidansu ya ce ta bada dari biyar. Babu musu ta shiga bayan ya dora akwatunanta biyu a ciki. Ta kwance Ameerah daga goyon tana rirrigarta a kafada.


Bayan sun isa gidan ta sauko, shi da kanshi ya ciro akwatunan ya ajje a gaban gate. Ta zari dari biyar dinshi daga cikin jaka ta mika mishi.


Idonta ta runtse, tana jin wani sabon hawaye biye da ita. Ta ina za ta fara? Ta gyada kanta tana karisa isa cikin gidan.


A falo babu kowa, wutar ma a kashe take alamun kowa ya kwanta. Kai tsaye ta zarce dakinta da babu kowa a ciki, ta kwantar da Ameerah sannan ta koma waje ta jawo akwatunanta, tana mamakin yadda aka yi gidan a bude, falo ma a bude.


Wutar dakin nata ta kashe tana kwanciya. Tunani kala-kala na zo mata. Baccin da ba ta yi ba ke nan har aka fara kiraye-kirayen sallar asubah.


*

Bayan ta gama sallar asubah ta yi adhkaar, tana kokarin mikewa ta ji kukan Ameerah. Da sauri ta dauke ta tana dan rirriga ta a hankali. Mommy da ke dakinta ce ta jiyo kukan yarinya a rude ta fito har suna cin karo ita da Fareedah suna tambayar juna.


Dakin Mahboobah suka nufa su duka biyun suka same ta sanye da hijabi tana shayar da Ameerah. Babu wadda ta iya cewa komai a cikinsu. Mommy ta kariso gaban Mahboobah tana son gasgata shin ita ce ko ba ita ba?

"Mommy..." Ta fada tana fasa kuka mai daci, ta fada jikin Mommyn jikinta har karkarwa yake yi. Ganin tana neman yar da Ameerah ya sa Fareedah gaggauta daukar yarinyar da ke sauke ajiyar zuciya tana kuka.


"Mahboobah me ya faru?"


Sauke idonta ta yi daga kan na Mommy, tana tsananin jin kunyar fada mata Ishraq ya sake ta. Ba ta ma san ta inda za ta fara fada musu abin da ya faru ba. Zuciyarta take jin tana mata tsananin zafi, tuna munanan kalaman da Ishraq ya jefe ta da su. Ta sake fasa wani kulan tana narkewa a jikin Mommy.


Bubbuga bayanta Mommy ke yi a hankali ba tare da ta ce komai ba. Sun fi minti goma a haka, Mahboobah ta dan samu salama, hada jikin iyaye da yaransu ba karamar nutsuwa yake saukarwa a tsakaninsu ba.


Dagowa ta yi, tana kauce ma haduwar idanuwanta da na Mommy. "Ya sake ni saki daya." Kawai ta fada, tana runtse idanuwanta, hawaye masu dumi na jerangwama a kai.


STORY CONTINUES BELOW

Cikin mamaki Mommy ke bin ta da kallo, tana ayyana girman laifin da zai sa Ishraq ya saki Mahboobah kuma a cikin dare.


"Me kika yi masa?"


"Wallahi sharri ne...kazafi aka yi min Mommy."


"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un! Allah Ya sa hakan shi ne mafi alkhairi to."


Fareedah ta sauke ajiyar zuciya tana fadin "In shaa Allahu ma shi ne alkhairin." Hade da barin dakin, ta samu nasarar rarrashin Ameerah ta yi shiru tana neman komawa barci.


"Ban san me na yi musu ba, ban san su waye ba Mommy. Kwarto ya fito daga daki ba tare da na san yana ciki ba, kuma a daidai shigowar Ishraq din gida." Kuka take mai kara, kuka mai tsuma zukata, kukan da duk wani mai digon imani a zuci idan ya ji shi sai ya tausaya mata. Ta dora da "Ya fada mishi ni na kai shi, wai har ma mun saba haduwa da shi a dakinshi, ko kuma in kama mana hotel..." a wannan gabar Mommyn kanta kuka take yi. Ba don Mahboobah na tata ba, amma za ta iya rantsuwa da Allah sharri ne daga masharranta. Ita ta haifi Mahboobah, ta kuma san abin da ta haifa. Hausawa suna cewa ba a shaidar d'an yanzu, amma tsaf Mommy za ta iya shaidar Mahboobah a gaba ko a bayan idonta.

"Mommy...kalamai masu daci Ishraq ya rinka jifa ta da su." Ta ja numfashi, tana dorawa da "Mazinaciya ya kira ni." Ta karisa maganar tana dukewa kasa, tana jin kanta na sara mata ta ko'ina, tana jin zuciyarta na mata zafin da ba ta taba jin irinshi ba ko a can baya da ta yi ciwon zuciya.


"Ina son shi Mommy, ina son Ishraq amma ya rabu da ni. Ya zan yi Mommy? Zuciyata zafi take yi min."


Cike da tausayi Mommy ke kallon Mahboobah, tana rasa ma ta inda za ta fara rarrasarta. A zuciyarta tsine ma ko wane azzalumi ne ya ma Mahboobah wannan kazafin.


"Sai dai Mommy...na muku alkawari daga yau na cire Ishraq daga zuciyata. Na cire shi daga babin rayuwata. Zan yi yaki da soyayyarshi har in samu nasarar zubar da ita kasa. Zan dawo asalin Mahboobah, Mahboobarku mai yawan nishadi da walwala."


Aliyu da ke bakin kofa tun dazu ya karisa shigowa. A gefen Mommy ya zauna zuciyarshi cike da tausayin kanwarshi. A wani bare na zuciyar tashi kuma ya ji dadin rabuwarta da Ishraq, ko ba komai za ta huta da kaddararren auren Ishraq Sulaiman.


"Mahboobah..." ya fada yana dorawa da "Ki fada mana tsakaninki da Allah. Idan kin boye mana gaskiya ba za ki boye wa mahaliccinki ba, domin kuwa Yana biye da komai, Yana kallon duk wani abu da bayinSa suke aikatawa." Ya ja numfashi, yana jin nauyin maganar da yake son fitarwa daga tsakanin labbanshi. "Mahboobah ba ke kika kai mutumin ba?"


Gyada kanta take yi, tana mikewa a saman kafafuwanta, tana rasa kwarin guiwar da za ta yi wa yayan nata bayani, tana son warware mishi iya gaskiyarta, ba ta san komai a kai ba. Kamar yadda Ishraq ya ga katon, haka ita ma ta gan shi. Hasali ma, Ishraq din ya riga ta ganin shi.


"Yah Aliyu wallahi..." Sai kuka, idanuwanta sun kada sun yi jajur, tun jiya take kuka, har wayewar garin yau. Ji take tamkar ita kadai ce tashin hankali yake addabar duniyarta. "Ban san shi ba ban taba ganin shi ba sai jiya. Wallahi ban san komai a kai ba." Ta duke hade da fadawa jikin Mommy.


Rayuwar Mahboobah abar tausayi ce. Tun da ta tashi da yarintarta take fama da larurin ciwon zuciya. Rayuwarta raba-da-rabi a asibiti ta yi ta saboda yawaitar tashin ciwon zuciyarta. Sun jima suna mata fatan samun kwanciyar hankali a rayuwarta ta gaba, amma abu ya gagara.

"Ya isa to ki yi shiru. Idan duk duniyar nan kowa bai yarda da ke ba ni na yarda da ke Boobah, na sani ba za ki taba aikatawa ba. Ban haifi mazinaciya ba a cikin ya'yana ba, ba na fatan ko a gaba halinku ya juye. Allah Ya sa rabuwar taku ita ce mafi alkhairi. Allah Ya saka miki ko ma waye ya kulla miki wannan sarkakiyar mai wuyar kwancewa."


"Ameen Mommy. In shaa Allahu ma alkhairi ne. Amma dai yana da karamar zuciya tun da ya iya zartar da hukuncin saki ba tare da yi kwakkwaran bincike ba." Aliyu ya fada yana kara jin tsanar Ishraq din.


"Yah Aliyu har da video ya yi wa mutumin, kuma yana yi yana daukar fuskata. Ina gudun kar ya yi blackmailing dina..." ta karisa maganar da kuka sosai.


"Ya Allah." Mommy ta fada tana jinjina bakin hali irin na Ishraq.


"Chai! Ni fa na ma fara zargin ko shi ya kawo kwarton da kanshi don kawai yana neman hanyar rabuwa da ke."


Dagowa suka yi su duka biyun suna kallon Aliyu. Ya jinjina musu kai, "Haka kawai ban yarda da gaskiyarshi ba Mommy."


End of chapter


Assalamu alaikum. Barkanmu ya gida ya iyali? Fatan komai lafiya. Ina so in mana wata guntuwar masiha ne.


Hakika aure ibada ce mai girma. Sannan kuma Allah da kanShi Ya halatta saki kuma Yake kinsa. Don haka saki abun ki ne.


Sai dai kuma, akwai ta bangaren da saki yake zama alkhairi ga mutane. Wani zaman auren da shi gwara babu.


Mu daina kuntata wa zukatanmu yayin da saki ya gitta tsakaninmu ko ga danginmu. Hangen rayuwar baya za mu yi kafin komai.


Kamar misalin rayuwar auren Mahboobah da kowa ke allawade da ita, sai kuma ga saki. Idan da gaske hakan ta fado ga yayarki ya za ki yi? Ni dai wallahi murna zan yi, zan taya ta jin dadin rabuwa da alakakai da ta yi. Yo ai gaskiya ce😬kila ku ga sakin ya zama alkhairi a tsakanin su duka biyun. Kila kuma ya zama silar gyaruwar wata b'araka.2


Sai kuma abin da Aliyu ya yi, shi ma ya kyauta sosai. Bai kamata ba don tana tashi kai tsaye ya goyi bayanta, yana da kyau ya tabbatar idan da gaske ne maganarta kafin ya yi kane-kane a tsakani.5


Princess Amrah

RAZ 2Kamar yadda Mahboobah ta yi kwanan kunci, haka Ishraq ma ya yi shi. Kai tsaye ma ba zai ce ga dalilin kuncin nashi ba. Sai dai idan ya yi wani nazarin, yana ganin kamar yardar da ya yi da Mahboobah ta ci amanarshi ne silar shigar shi damuwa.


Ya yi juyi mara adadi kafin ya mike ya hau sintiri daga bangon toilet zuwa bangon da gado yake. Ya kasa zama, kamar yadda barci ya yi kaura daga idanuwanshi.


Ya fi karfin minti talatin yana sintiri, kafin ya zauna, yana manna tafukan hannunsa da kumatunshi. "Allah Ya isa tsakanina da kai..." ya fada a bayyane, yana kuma son gyara maganar tashi 'Da ke' ya kamata ya ce a ganin shi, saboda ita ce ta ci amanar tashi ai. Da a ce ba ta ba gardin dama ba, da komai bai faru ba.


"Ai shi ne katon dan iskan, mai bin matan mutane."


Bayyanannen tsaki ya saki. Miye kuma nashi a ciki. Me ya sa zai damu don wani kato ya so karfen kafa da ba kaunarta yake yi ba dama can. "To ai kuma matata ce." Ya sake fadi yana kwanciya hade da yin ruf da ciki.


Kamar wasa ya fara jiyo assalatu. Ashe har lokaci ya kai haka. Mikewa ya yi ya shiga toilet, alwalla ya dauro ya yi nafila sannan ya yi karatun Al'Qur'ani da ya mance yaushe rabon da ya yi shi idan ba a cikin sallah ba. Sai da ya ji kira sannan ya tashi ya nufi masallaci.+


Washe gari bai samu zuwa asibiti ba saboda kanshi da yake jin yana sara mishi. Gidan Mami ma yake son zuwa amma ba ya jin zai iya yin tuki. Babur ya tsayar ya kwatanta mishi gidan Mamin tashi.


Yana zuwa ya same ta a falo zaune da wani mutumi da ya ba shi baya keyarshi kawai yake iya gani. Duk da ya so ya shaida ko wanene amma a hakan ya tako ya shigo cikin dakin. Sallama ya yi, yana kallon Khalid Zannah da ke sanye da farar shadda da light brown din hula. Kamar ba shi ba. Rabon da ya saka shi a ido an fi wata hudu. Ganin shi da Khalid din ya yi ya sa ya mika mishi hannu suka gaisa. Duk da bai yi niyyar tafiya ba a daidai lokacin amma ba ya jin zai iya ci gaba da zama saboda zuwan Ishraq.


"Mami ni zan koma in shaa Allah. Sai kuma wani lokacin idan na zagayo."


"Na gode sosai Khalid, Allah Ya yi maka albarka. Ka gaida iyalin. A ce da Junior tunda dai ba ya kawo toshi tabbas zan canja sheka. Wani mijin zan nemo."


Dariya Khalid ya yi, zai fita ke nan ya ji muryar Ishraq yana kiran sunanshi.


"Ka dawo mu yi magana."


Ba tare da ya juyo ba kawai ya gyada kanshi yana fita daga kofar. Da saurin Ishraq ya sha gabanshi. Da tsiya ya janyo shi ya dirar a tsakiyar falon da ke shimfide da babban carpet.


"Lafiya kake likita? Ya kake jan shi haka kamar wani karamin yaro?"


"Ba lafiya ba Mami. Matar da duk ku biyun nan kuke fushi da ni ta silarta nake son tabbatar muku da mummunan halinta gara ko'inkular da nake yi da ita. Mami..." ya fada yana jin kanshi na tsananta sara mishi. "Mami ashe mazinaciya na aura..."


"Ya ishe ka haka Ishraq! Ahir dinka da kulla wa diyar mutane sharri. Wato kiyayyar har ta kai ga dora mata mummunan kazafi haka ko? Kar in kara jin magana ko mai kama da wannan."


Idonshi ya matse, yana jin kamar kar ya gwada musu videon, kamar gwadawar wata fallasa ce ga Mahboobah. Sai kuma ya tuna, akwai abu mafi muni sama da matar aure ta rinka bin maza a waje? Ya bude security din wayarshi. Videos ya shiga, ya kunna, yana saita wayar ga Mami da Khalid da har yanzu ya kasa cewa komai.

STORY CONTINUES BELOW

Kallon videon suke su dukka biyu, Mami na salati, yayin da Khalid Zannah ke gyada kanshi. Psychologically yake kallon fuskar kwarton, yana kuma kallon yadda Mahboobah ke bin shi da ido tana rasa abin da za ta ce. Har ya kai karshen videon. Inda yasallami kwarton, ya tafi yana mishi godiya.


Kuka Mami ta fasa, kukan yardar da ta yi da Mahboobah amma ta zamanto da wannan mummunan halin. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah Ya shirya ki Mahboobah. Allah Ya sa wannan ya zama silar shiryuwarki."


"Na sake ta Mami." Ya fada, yana jin dacin kalmar. Ko ga kowa ma takaici yake ji ya ga an yi saki, balle kuma shi da ya yi shi da kanshi.

"Me ya sa ka sake ta ba tare da kwakkwaran bincike ba?" Khalid ya fada, yana karbar wayar daga hannun Ishraq, yana son sake mayar da videon baya.


"Wane bincike kuma ya yi saura bayan abin da zahiri ta nunar?"


Kai ya gyada Khalid Zannah, yana kara jin haushin karamar zuciya irin ta abokinshi. "Mene ne zahirin? Ka kama su kwance ne a tare?"


Ya gyada masa kai. "Amma ko ban kama su ba ai ka ji ta bakin kwarton nata ko? Me kuma ya yi saura?"


"Abubuwa da yawa sun yi saura Ishraq. Ko kai ka so kana iya aikata abin da mutumin ya yi. Bakyam kawai za ka yi a daki, daga zarar ka ji isowar mai gidan sai ka fito, ka fara neman hanyar guduwa, amma ba za ka yarda ka fita ba tare da ka bari an gan ka ba. Saboda da ma abin da ya kawo ka ke nan."


Daga haka Khalid ya ajje mishi wayarshi, yana takawa hade da barin dakin, ya isa motarshi ya tayar, zuciyarshi na tabbatar mishi da cewa ba gaskiya ba ne maganar mutumin. Ko kadan fuskarshi ba ta yi kama da mai gaskiya ba.

A fuskar Mahboobah ya hango tsantsar gaskiya. Da shirunta ya gane cewa ta rasa abun cewa ne kamar yadda take kasancewa ga duk wanda aka yi wa kazafi.


"Amma dai ka yi gaggawar sakinta likita. Da ba ka yi ba har sai ka tsananta bincike."


Hawayen da ke bin idonshi ya share. "Mami...ban san me zan aikata ba ne a lokacin. Zuciyata ta zafafa, dole ne koma waye ya ji zafi, a ce matar da kake aure ce ta kawo maka gardi a cikin gida. Hobbasa guda daya na yi Mami, da abun ya tsaya a saki guda. Shi ma din kadan ya hana in cikashe sauran."


Ta sauke ajiyar zuciya, tana jin tausayin rayuwar da Ishraq ya jefa Mahboobah a cikinta. "Rashin ba ta hakkinta na aure ne ya jawo haka Ishraq. Ba kowacce mace ba ce ba za ta iya daurewa. Wannan abun shi ne jigon aure, shi ne musabbabin aure, amma ka wofintar, ka yi watsi da shi. Irin siradin nan yana da wahalar tsallakewa."


Shiru ya yi, yana gasgata maganar Maminshi. Tabbas, ko shi kanshi daurewa yake yi, a matsayinshi ma na namiji. To ina ga Mahboobah mace, mace mai rauni, a yi fatali da sauke wannan gagarumin nauyin nata, dole za ta iya fada ma harkar banza. Shi ya sa da dama daga cikin matayen auren da ke bin mazan banza a waje za ku same su mazajensu ba masu yawan zama ba ne, masu fifita can wata harkar ta daban ce a kan rayuwar iyalinsu. Don haka su kuma matan sai su fada harkar banza. Su nemi masu biya musu bukatarsu ko ta halin kaka.


"Ba ka kyauta ba...ko kadan ba ka kyauta ba likita." Ta share maikon kwallar da ke makale a kwarmin idonta. Tana dorawa da "Da ka sani ka sauwake mata tun farko, da ba ka bari ta fada ma harkar banzan nan ba. Watakila da tuni ta yi aure ta manta da duniyarka. Ga shi nan, ibtila'i mafi muni ya afka mata. Kai ne sila, kai ne silar koma Ishraq." Kuka mai karfi ya kwace mata. Sosai take tausayin Mahboobah. Tana tuna tarbiyya da girmamawar da yarinyar take da su.


STORY CONTINUES BELOW

Mikewa ya yi ba tare da ya sake fadin komai ba. Yana neman hanyar fita ya ji Mamin ta kira shi. Tsayawa ya yi cak hade da juyowa, kanshi sunkuye yana guje ma haduwar idanuwansu.


"Ka ci abinci?" Ta tambaye shi, tana karantar yadda yunwa ke cin shi. Ko kadan Ishraq bai da juriyar yunwa. Daga zarar ya ji yunwa to sai kowa ya gane mishi.


Kai ya gyada yana jin wani sabon hawayen na saukar mishi. Ta hannu ta ba shi alama a kan ya zo. Bai musa mata ba, ya kariso yana zama a kusa da ita.


"Ka cire damuwa ka fauwala ma Allah lamurranka. Duk abin da kake ganin ya faru da bawa to da ma can kaddararshi ce ta zo da haka. Ba a kanka farau aka fara kama kwarto a gidanka ba, ba kuma za ka zama karau ba. Ka kwantar da hankalinka, ka manta da komai, ka dauka cewa komai bai faru ba."


A ranshi yake tunanin wai mene ne ma dalilin da ya sa damuwar nan ta yi mishi yawa? Me ya sa ba zai daga hannu ba ya gode ma Allah da asirin Mahboobah ya tonu? Me ya sa ba zai yi farin cikin rabuwa da karfen kafa da ya fi tsana ba duk duniya a kan kowa? Wannan wata dama ce gare shi, da zai fita neman Ameerah Muhammad da gaske, ya auri muradin zuciyarshi.


Murmushi ya saki a daidai wannan gabar, tuno Ameerah kadai kan haifar da walwala a kasan ruhinshi.

Ganin ya yi murmushi ya sa ita ma Mamin ta murmusa, a tunaninta nasiharta ce ga shige shi.


"Yauwa mu je in zuba maka abinci ka ci. Pancake ne na yi, ban iya abun dorawa a saman ba ka san girkin na yan zamani. Nutella kadai nake da ita."


Ya saki murmushi har hakoranshi suka bayyana, bayan ya mike tsaye ya ce "To Mami a ina kika koya?"


Harararshi ta yi da fadin "Yo ce maka aka yi dole sai 'yan matan zamani ne za su yi kayan makulashen? YouTube nake shiga in nemo duk recipe din da nake so. Barin ma yanzu da na yi subscribing a channel din Amrah's Kitchen. Videos dinta kana kallo tamkar a gaban idonka ake yin komai. Babu ha'incin ingredients, bayani dalla dalla."


Dariya ya yi sosai a wannan gabar. "Lallai a jinjina wa Amrah's Kitchen. Wannan yabo da kike mata Mami ko dai ta biya ki kudin advert ne?"


Dariyar ta yi ita ma Mami, suna karisa isa gaban dining table. "Babu abin da ta ba ni likita. Kawai dai ka san idan mutum ya yi abu mai kyau a fadi, abun yabo a yabe shi. Da gaske ina son ta, ina son bibiyar duk girke-girkenta. Shi ya sa na danna subscribe saboda da zarar ta dora sabuwar video in gani."


(Ku taimaka ku min subscribing a YouTube chanell dina. Kawai wurin searching za ku je ku rubuta Amrah's Kitchen, sunana zai fito sai ku shiga. Ku danna  subscribe sannan ku kalli duk video din da kuke so, na tabbata za ku karu sosai. Thank you as you do.)


Da nutella da strawberry yake cin pancakes din, sai zuba santi yake yi. "Mami Allah dai Ya sa akwai saura, ina son tafiya da shi, asibiti zan je."


Ta gyada kanta tana murmushi. "Babu sai guda daya ne ka gan shi, ci zan yi." Ta fada tana zuba guda dayan a plate din da ya gama.


Mikewa ya yi, yana jin nutsuwa na saukar mishi. Ya dauki wayarshi ya yi wa Mami sallama sannan ya tsaida babur ya tafi asibiti.


Bayan ya zauna, ya jawo wani file yana duba takardar ciki. Yana cikin karantawa ya ji wayarshi ta yi ringing. Bai mayar da kanshi ba har sai da ya kai karshe, yana jin wayar tashi tana kara dokawa.


Guntun tsaki ya yi bayan ya ga bakuwar lamba ce ke kiran nashi. Ya dauka ba tare da ya ce komai ba. Yana jin saukar nishi wanda hakan ya tabbatar mishi da ko ma waye yana jin shi. Ba zai yi magana ba har sai ya ga iyakar mai kiran nashi.


Cikin susucewa ta ce "Hello Yah Ishraq."


Kamar ya so daukar muryar, kamar ya taba jin ta ko ma a ina ne, sai dai ba zai ce ga wurin ba. Ba zai ce ga inda ya san muryar ba.


"Yah Ishraq ina wuni. Ya aiki, Ya Mami, Ya kwana biyu?" Dukka a jere ta zano mishi tambayoyin, tana jin wani irin yanayi mai wahalar misaltawa.


"Lafiya." Kawai ya ce, yana son dorawa da 'Wace ce' amma yana jin wahalar hakan. Idan ta matsu ita da kanta za ta fada mishi ko wace ce ita.


"Na san ba ka gane wace ce ba, sunana Bilkisu, Bilkisu Imran." Ta furta cikin zakuwa da son jin maganarshi.


"Uhm...lafiya dai ko?"


"Lafiya kalau Yah Ishraq. Na kira ne kawai na gaishe ka. And...uhmm...uhm Yah Ishraq."


"Go straight to the point. Idan ba ki da abun fade ni ina da aikin yi."


Kamar za ta yi kuka ta ce "No Please, kar ka kashe..." Ba ta kai kashe ba ta ji kit ya kashe.


End of chapter


Hello everyone, barkanmu da saduwa da ku a wannan rana mai tarin falala da albarka. Ina yi mana barka da jumu'a tare da fatan alkhairi.


Bilkisu Imran na neman gindin zama wurin Ishraq.


Ishraq dai ya ce sai Ameerah Muhammad.


Ameerah Muhammad kuma tuni ta sheke.


Tsoka mafi daraja, mafi mafi soyuwa da aka halitta a jikin Ameerah Muhammad ita ce shimfide a tsakanin kirjin Mahboobah Bukar.


Cakwakiya.


Princess Amrah

RAZ 2"Mommy, ina neman wata shawara ne a wurinki. Ban san me ya sa ba tun daga sadda na gama idda zuciyata ke ta dokawa a kan in koma makaranta, tun da dai wancan din na yi asararshi. Amma Mommy ya kike gani?"


Bayyanannen murmushi a saman Mommy ta ce "Gaskiya wannan tunani ne mai kyau Boobahna. Da ma zaman ba shi da dadi a haka. Na gode ma Allah da har kika yi wannan tunanin, kuma ina miki fatan alkhairi, addu'ata tana tare da ke a kullu yaumin. Ba dare ba rana, ba zan fasa ba da izinin Ubangijinmu Azza wa Jallah."


Dadi sosai Mahboobah ta ji, tana tuno hirarta da Khalid Zannah, kwanaki can da ya je gidan duba Ameerah ta yi fama da rashin lafiya, shi ma Mami ce ke fada mishi har ma ta je duba ta. 'Ki yi hakuri ki fauwala wa Allah komai Mahboobah. Ki cire kunci da duk wata damuwar abokina Ishraq. Ki dauka cewa ba a kanki aka fara saki ba, ba kuma za a kare shi ba a kanki. Kowane bawa da yadda kadararshi take zuwa, wani tana zo mishi da cikar duk wani abu da zai sanya a gaba, wani kuwa akasi tare da dangarda sukan gitta a komai nashi, kuma hakan ba wai Allah na nufin ba ya son shi ba ne, akwai wani tanadi dai da Ya yi mishi a can gaba. Don haka nake so ki dauka tamkar komai bai faru ba ne. Ba ganin idonki ba, daidai da rana guda ban taba jin zuciyata ta aminta da cewa ke ce kika kai mutumin a gidanki ba. Dukka wanda zai tsayar da hankalinshi dole zai tabbatar da hakan. Wasu abubuwa da ya kamata a ce Ishraq ya bincike su kafin ya yanke hukunci, me ya sa kwarton ya riga ki fitowa bayan kuma dukkanku motsin shigowar Ishraq din kuka ji shi ya sa ya nemi guduwa? Karkarinta dai ya ce ba daki daya kuke ba, watakila kin shiga naki dakin ne yin wani uzuri. To dakinki bai fi kusa ba da hanyar shigowa a kan inda wancan din yake?

Sannan me ya sa ba tare da an tambayi mutumin ba zai rinka tona muku asiri ke da shi har yana fadin ya yi hakuri tsautsayi ne ya kawo shi gidan ba a nan kuka saba haduwa ba? Idan har da gaske ke ce kika kawo shi, to kokarin rufe baya zai yi, sai dai kawai ya ce tsautsayi ne ya kawo shi. Ba zai dora da wata magana ba kuma.

Tunani na karshe da ya kamata a ce Ishraq ya yi, idan har kwarton gaske ne mutumin, dole zai nemi hanyar guduwa. Ba tsayuwa zai yi ba yana mayar da kanun labarai, tun da ba 'yansanda ba ke akwai gidan, ba kuma wani makami ba ne Ishraq din gare shi. Don haka guduwa ba abu ba ne mai wahala ko don gudun tonuwar asirinshi.+


Da wadannan nake so Mahboobah, ki zira ma sarautar Allah ido. Ki ci gaba da rayuwarki tamkar babu wani abu da ya faru, tamkar ba ki taba sanin wani mahaluki wai shi Ishraq Sulaiman ba. Ki rufe babinsa, ki rufe babin duniyarshi ma baki daya. Ki ci gaba da kula da diyarki, ko ya mata wani abu ko kar ya yi, kada ki yi wasa wani abu ya fi karfinta a rayuwa. Ki gina kanki, ki gina ta diyarki, ki ajje dogara ga kowa, ki mike da kafafuwanki, tare da dogara da kanki.'


Tun daga sadda Khalid Zannah ya mata wadannan maganganun ta hau tunanin me ya kamata ta yi. Kasuwanci? Ko kuwa ta koma makaranta? Makarantar dai ta yanke shawarar komawa. Shi ne ta samu Mommy da zancen, idan har ta goyi baya, daga nan sai ta fara cuku-cukun samun admission.


Cikin sa'a kuma sai ga shi Mommyn ta goyi baya, tana maraba da tunanin da Mahboobanta ta yi. Alamun babu sauran wata damuwa a kasan ruhinta ke nan, duk da dai da ma tana kokarin ganin babu ko alamar damuwa a saman fuskarta, sai dai su sun sani akwai, akwai damuwar fal, kamar yadda akwai sauran soyayyar Ishraq Sulaiman a zuciyarta da ba ta san ranar da za ta gushe ba.


Wayarta ta dauka ta kira Aliyu, jin shi busy ya sa Mahboobah yin murmushi, gayen nan fa ya gane yawan waya yanzu, da alama wata sabon kamun ya samo. Mun kusa shan biki."


Murmushi Mommy ta yi hade da tabe baki. "In dai yan matan Aliyu ne ma kya gaji da kirga. Ni dai wadanda muka gaisa da su a waya ba su da adadi. Wata da ta nace wa kira na ma tausayi ta rinka ba ni. Wani lokacin tana kuka tana rokona wai in taimaka in ba shi hakuri saboda yana fushi da ita. Kuma idan kin bibiyi ba'asi za ki ga karamin laifi ne ta yi mishi. Kawai ba son ta yake yi ba."


STORY CONTINUES BELOW

Dariya sosai Mahboobah ta yi tana tafa hannu.  "Iyyee wai duk a yaushe aka yi haka ban sani ba? Lallai ma Yah Aliyu ashe muna mishi kallon wani salihi ba haka yake ba."


Mommy ta zaro ido, "Ban fa ba ki labari ba kuma don ki je ki dame shi da zolaya."


Cikin muryar dariya Mahboobah ta ce "Ai kuma shi ke nan Mommy. Har Ameerah sai na ba ta wannan labarin."


"Hmm Allah Ya shirya ki. Yarinyar da ko shekara daya ba ta cika ba amma ki zauna ki yi ta zuba mata labari ita kuma tana miki yare irin da gaske tana fahimtar hirar taki."


Su dukkansu dariya suke yi. Suna cikin haka Fareeda ta shigo hannunta sab'e da Ameerah. Bayan ta ajje ta ta ce "Wash Allahna! Wallahi na gaji."


Mahboobah ta mata gwalo, "Maganin mai shegen yawo ke nan kuma kin san Ameerah da son yawon ita ma dole ta ce za ta bi ki. Ga daukar wannan yarinyar sai mutum ya shirya. Nauyi kamar buhun masara."


Turo baki gaba Fareeda ta yi, "Mutum dai yake hadawa da tubarkalla. Kuma ma ai irinsu sun fi dadin dauka. Waye yake son sakai-sakai din yaro ka dauke shi kamar zai bi iska."


"Kanki kuma ake ji."


"Kanki dai Yah Boobah."


Tashi ta yi za ta bi ta ai kuwa sauran kadan ta sha kaye. Dariya sosai Fareedah da Mommy suka dauka, har da ma Aliyu da ke daidai shigowa falon.


"Yauwa Yah Aliyu da ma nemanka nake. Na kira ka kuma kana ta waya da Antinmu da ba mu san ta ba." Ta fada tare da komawa ta zauna kusa da Mommy.


"Ku babu dama ku ji mutum busy sai ku ce da budurwa yake waya?"


Turo bakinta ta yi Mahboobah, "Uhm uhm fa Yah Aliyu. Ai idan ba budurwa ba ce da tun dazu ka gama wayar."


"Zan mauje ki Mahboobah." Ya fada yana neman mabugi ai kuwa ta gaggauta barin kusa da shi tana dariya.


"Idan ta yi tsami ma ji." Ta sake fadi tana dariya.


"Yah Aliyu in kamo maka ita?" Fareeda uwar neman suna ta fada tana yin gefen da Mahboobah take tana son kama ta.


Dire-dire Mahboobah ta hau yi tamkar karamar yarinya. "Wayyo Allah Mommyna kin ga sun hade min kai ko?" Tana matso kwallar karya.


Mommy ta gyada kai tana ma Ameerah da ke zuba mata yarensu na yara dariya.


"Yauwa Yaya, joke aside don Allah. Yanzu muka gama magana da Mommy, a kan ina son komawa makaranta." Ta fada tana karisowa kusa da shi ta zauna.


"Ma shaa Allah." Ya furta yana murmushin da ke fitowa tun daga kadan zuciyarshi, saboda tsananin dadin da ya ji na maganar tata.


"Yauwa, to Mommy ma ta yi na'am da shawarar. Shi ne nake son ka bincika min komai a kan karatuna. Amma ba na son KASU, in dai da hali ABU Zaria nake so, kuma fannin asibiti, medicine ko pharmacy."


"Kai yarinyar nan ba ki taba burge ni ba irin yau. Allah Ya mana jagora Ya sa a dace. An fara registration din JAMB, sai  dai kuma samun medicine na wahala ta JAMB gaskiya. Kamar gara ki yi IJMB. Za ki samu admission a saukake in dai kin ci jarabawa."


Wani irin farin ciki Mommy ke jin yana saukar mata, wanda ta jima rabon da ta ji irinshi. "Ina rokon Allah Ya sa wannan karatu da za ki koma ya amfane ki ya amfani al'ummar musulmi. Allah Ya sa ki fara a sa'a Boobahna."


STORY CONTINUES BELOW

"Ameen Ya rabbi." Dukkansu suka amsa. A karshe dai suka tashi da zancen Aliyu zai binciko mata ya ji sadda ake fara registration na IJMB din. Daga nan sai su san mataki na gaba.


*

Yau ta kasance asabar, ranar da dukkanin wani ma'aikacin gwamnati yake samun hutawa, masu iyali su kasance tare da iyalansu, wanda suke zaune da iyayensu ma haka su zauna a cikinsu.


Tsadaddar farar shadda ce ya saka mara aikin komai, sai links ya saka a hannun rigar, ya dauko bakar hula ya sanya, ya  fesa turaren oud al'abiyad  sannan ya fara kokarin daura agogo ya ji wayarshi na ringing. Ganin sunan Khalid Zannah ya sanya shi gaggauta dauka yana matse wayar a tsakanin kunne da kafadarshi. Yana ci gaba da daura agogonshi.


"Khalid ya..." Ya furta yana dorawa da "Ya iyali?"


"Lafiya kalau suke Doctor. Da ma tambayarka zan yi. Akwai kanwar matata da ke son yin medicine a ABU Zaria, suke neman follow up wurin samun admission. Ban san ko akwai wani taimako da za ka iya yi ba. Ka san karatun kasar tamu yanzu an fi saukin samunshi idan an san wani babba."


Shiru jim Ishraq ya yi, kafin ya ce, "Akwai wani malamina Prof Salman, dan India ne. Babba ne sosai a medical department din. Bari zan kira shi in ji ko akwai wani taimako. Amma dai ai ka san duk wani taimako da za a iya yi na yanzu ne ko? Daga zarar sun fara karatun shi ke nan sai aikin kwakwalwarsu."


"Yes ba matsala in don wannan. Ka kira shi din I will be waiting for you."


"Okay." Ya tsinke wayar yana sanya ta a cikin aljihu. Falo ya koma, ya kalli yadda ya yi kututu da datti kamar babu rayayyen halitta a cikin gidan. Ya waiga ya kalli dining area, komai a watse ga tarin cups da spoons babu wanda yake mayarwa a muhallinshi. Saukin ma duk kayan sun ragu, saboda babu abin da aka bari na Mahboobah, an kwashe komai tun gama iddarta. Jinjina kanshi ya yi yana dad'a tuna muhimmancin mace a cikin gida.

Bayan ya rufe gidan ya fita. Sai da ya zauna a kujerar tuki kafin ya tada motar sannan ya kira Mami. Bayan sun gaisa yake fada mata ba zai samu shigowa da safe ba kamar yadda ya saba kowanne weekend can yake sammakon zuwa sai bayan la'asar yake tafiya. Ta mishi fatan alkhairi sannan ya tsinke wayar ya lalubi Prof Salman. Bayan sun gaisa da shi yake fada mishi dalilin kiran. Prof din ya ce ba matsala yarinyar ta yi IJMB sai a tura mishi sunanta zai yi kokarinshi don ganin ta samu admission din medicine. Godiya Ishraq ya mishi yana sake kiran Khalid.


"Na kira shi Khalid. Ya ce ta yi IJMB sannan a tura mishi sunanta. Idan dai an tashi zan turo maka lambarshi. Yana da kirki sosai bai da matsala."


"Ok to ba damuwa likita. Kana gidan Mami ne?"


Murmushi Ishraq ya saki yana kallon gefen fuskarshi ta mirror. "Neman aure zan je."


Murmushi shi ma Khalid din ya yi, "Ka gano Ameeran ne?"


"Nemanta dai zan fita, shi ne babban neman auren ai." Ya kwashe da dariya. Khalid ma ya yi dariyar, yana fadin,


"To abokina Allah Ya sa a dace." Da ameen suka yanke wayar. Ishraq na jinjina halayen kirki irin na amininshi. Ya tuna ranar da ya iske shi har gidanshi ya nemi gafararshi a kan abin da ya yi mishi. Murmushi kawai Khalid din ya yi ya ce 'Babu komai tunda dai ka gane ka yi kuskure. Allah Ya nisantar da mu daga dukkan sharrin shaidan.'


Tada motar ya yi Ishraq, yana tunanin rabon da ya fita neman Ameerah har ya manta. An tinkari shekara uku yanzu. Bai ma san ta inda zai fara ba, kawai ya tashi da son fita ne ko zai dace.


Kai tsaye shagon Mujaheed ya dosa. Ya samu shagon ya canja kamar ba shi ba. An fadada gininshi sannan ya cika makil da kaya, wata supermarket ce kawai a takaice.


Da sallamarshi ya shiga ciki. Ya samu wani mutumin daban zaune wurin biyan kudi. Bayan sun gaisa ya tambaye shi Mujaheed,


"Mujaheed kuwa yanzun nan ya je gida ya dawo. Amma da yake ba nesa ba ne gidan nashi. Zan iya kwatanta maka sai ka same shi a can."


Murmushi Ishraq ya yi, "Mallam Mujaheed ashe an yi aure."


Mutumin mai fara'a da sakin fuska ya ce, "Ashe ba ka sani ba. Ai har da Ahmad ma an samu watanninshi kusan biyar kenan da haihuwa."


Ya fadada murmushinshi Ishraq. "Ma shaa Allahu ai ban sani ba. Da yake rabo na da nan din na jima gaskiya. Shi ya sa ma na ga shagon duk ya canja min, har zan wuce a zatona ma Mujaheed din ya canja wani wuri ne."


"Ai kuwa nan ne mutumina. Yauwa bari in kwatanta maka gidan. Ko kuma in ba ka lambar wayarshi sai ka kira ku hadu."


"Ba ni lambar tashi, da ma kuwa na jima da yin missing dinta wallahi, da alama shi ma ya yi missing din tawan ne shi ya sa bai neme ni ya sanar da ni daurin aurenshi ba."


Lambar Mujaheed din ya karanto mishi, sannan ya kwatanta mishi gidan ya tafi da godiya a bakinshi.


End of chapter.


Shi fa Ishraq nan da gaske neman Ameerah Muhammad yake🥵kana ruwa Mallam.


Princess Amrah

RAZ 2A kofar gidan Mujaheed ya dakata, yana latsa kiran shi tare da sanar da shi isowarshi kofar gidan. Bayan Mujaheed din ya fito ya ba shi hannu suka gaisa, fuskarshi shimfide da murmushin da ya bayyana jin dadin ganin Ishraq a gabanshi.


"Kwana da yawa Doctor Ishraq." Ya fada yana rike da hannunshi gam, suka shiga cikin gidan tare.


Drinks aka ajje a gaban Ishraq, ya dan kurbi ruwa kadan kafin ya kalli Mujaheed da har yanzu yake murnar ganin shi.


"Na jima da yin losing lambarka Mujaheed." Ya dora da "Ban san ko ka tsinci wani sabon labari ba a kan Ameerah Muhammad."


Fuskarshi Mujaheed ta sauya daga annuri zuwa damuwa. Ya sauke ajiyar zuciya yana kallon shi, kallo mai cike da tausayi. Jikin Ishraq ne ya yi sanyi. Ya kawo a ranshi babu wani labari har yanzu. Gabanshi ke dokawa da sauri da sauri tamkar shaka da fitar numfashi.


"Ameerah Muhammad ta jima da rasuwa Doctor Ishraq, idan har ba ta yi shekara shida ba to tabbas ta haura ma biyar..." ya runtse idonshi yana bude su a kan Ishraq da ya kasa ko da kyafta idonshi, labbanshi na motsi, yana son yin magana, yana son neman karin bayani, amma tashin hankali bai bari ba. Wasu irin hawaye masu gumi ya ji suna ketowa a tsakanin idanuwanshi. Bai san da fitar su ba, sai dai hannu da Mujaheed ya sa yana share mishi su sannan ya gane me yake yi.


"Da gaske Ameerah ta rasu Ishraq." Ya furta, yana jin dacin maganar, yana tausayin Ishraq, yana jinjina ma rikon amana da soyayyarshi, cikin nutsuwa da son sanyaya mishi zuciya ya hau labarta mishi yadda ya san zancen mutuwar Ameerah.


Shekaru uku da suka gabata


Ranar wata Laraba, da yammaci, yana zaune a cikin shagonshi sai ga wasu 'yanmata su biyu sun shigo, dukkansu masu sakin rai da fara'a, suka gaishe shi ya amsa musu shi ma da sakin fuska, sannan gudar ta ce mishi indomie noodle suke so guda hudu manya.


"Babu manya wallahi sai dai a ba ku kanana guda takwas." Ya ba su amsa, yana kallon babbar da ita ma shi take kallo.


"Eh don Allah ka ba mu kananan ma muna so, ka taimaka ka hanzarta, ka ga hadari ya taso ga iska."


Ya juyo wurin kwalin noodles din, ya dauko guda takwas ya zuba a leda, kafin ya kai ba mika musu ruwan sama ya balle, mai tsananin karfi.


"Kin gani ko Yah Maryam, sai da na ce miki kar mu fito akwai hadari kika ce sai mun fito, ga shi nan ai ruwa ya sauko sai ki san yadda za ki yi da mu."


Kamar za ta yi kuka wadda ta kira da Maryam din, ta ce "Kar ki nemi dora laifi a kaina Hafsa. Ke fa kika fara cewa indomie din za ki ci, kuma Yah Nafeesa ta fada miki tasu ta kare sai dai mu fita mu siya. Na rako ki din kuma shi ne za ki juyar da abun a kaina?"


"To ai dai da muka fito waje na ga hadarin sai da na ce mu koma mu fasa siyan noodle din kika ce sai mun zo."


Guntun tsaki Maryam din ta yi, "Sai kuma ki yi ta yi ai."


Dariya suka bai wa Mujaheed, a wani bangaren kuma zuciyarshi sosai ta kamu da son Maryam, tun shigowarta cikin shagon ya ji ta kwanta mishi a rai. Yana son mace mai sanyin hali, yana son mace mai fara'a da girmama mutane, kuma duk ya tsince su a wurin wannan baiwar Allah da ke tsaye a gabanshi.+


"Ku zauna a nan ga benci nan, kafin ruwan ya yi sauki sai ku tafi." Ya kalli Maryam da ta bata fuska, "Ba ku da wani zabin da ya wuce zaman a nan."


STORY CONTINUES BELOW

"Muna da shi." Hafsa ta fada da gatsine baki.


"Sai ki fada mana ai mu ji idan mai billewa ne." Maryam ta furta hade da bin Hafsan da harara.


"Kawai mu tafi cikin ruwan nan..."


Ba ta kai aya ba Maryam ta zaro ido da fadin "A cikin wannan ruwan mai karfi ne za mu tafi? Ba da ni ba wallahi ke idan za ki tafi ne ki tafi. Kin san ni duk yadda ruwan sama ya buge ni zazzabi nake mai wahala."


"Ku yi hakuri ku zauna a nan din, in shaa Allahu ba da jimawa ba ruwan sai saukaka, ai maghrib ta kunno kai."


Ba su da wani zabin da ga wuce zama bisa bencin, ga shi su dukka biyun ba su fito da waya ba. Kamar wasa dai ruwa ya ki tafiya, har maghrib ta yi. Cikin marairaicewa Maryam ta ce,


"Don Allah Mallam ko za ka ara min wayarka in kira Yayata. Na san mijinta ya isa dawowa gida yanzu, sai ya zo nan ya dauke mu."


Sai da fa fada kuma ta tuna da ba ta haddace lambar Yah Nafeesa ba a kanta. Ta tambayi Hafsa ta ce ita ma din haka. Tunawa ta yi da a falo ta baro tata wayar, don haka ta ce "Bari in kira layina, Allah Ya sa Yah Nafeesan ta dauka."


Lambarta ta saka. Sau hudu tana kira amma Nafeesa ta ki dauka, sai ma tsaki da ta yi tana cewa samarin zamani ba dai kwazaba ba.


Can dai ta ji kiran ya yi yawa, ta dauka da fadin "Ba ta kusa mai wayar..." Tana neman kashewa ta jiyo muryar Maryam.


"Yah Nafeesa ni ce fa. Muna nan wani shop bakin titi tun dazu muna jira ruwa ya yi sauki mu dawo amma ya ki. Idan Babban Yaya ya dawo ki ce ya taimaka ya zo ya dauke mu. Ga shi Daddy ya ce da ma kar mu kai maghrib ba mu koma gida ba."


"Tun dazu kuke a zuciyata Maryam. Wallahi Saleem bai dawo ba ai da tun dazu ya fito nemanku. Ku zauna kar ku fito cikin ruwan nan, in shaa Allahu yana isowa zai zo ya dauke ku." Nafeesan ta fada cike da damuwa a fuska da muryarta.


Daga haka Maryam ta kashe wayar, tana jin saukar hawaye a saman kumcinta.


Sai bayan maghrib sannan ruwan ya tsaya. Da wayarta Nafeesa ta kira Mujaheed ya kwatanta musu shop din nashi, nan da nan sai ga su sun zo. Godiya sosai suka ma Mujaheed sannan suka tafi.


Kai tsaye gida suka wuce su mayar da su, saboda dare ya yi sosai.


Tun da suka koma haka kawai Maryam ta samu kanta da murmushi a duk sadda ta tuna da Mujaheed. Abinci ma tana ci tana sakin murmushin da ita kanta take mamakinsa.


Wuraren goma na dare ya kira ta. Bayan sun gaisa yake fada mata shi ne, ba tare da bata lokaci ba ya gabatar mata da kudurinshi na aurenta in dai ta amince. Lokaci ta ce ya ba ta, bai musa ba. Bai sake kiran ta ba sai da sati ya cika sannan. Bayan ta dauka ta fada masa ta amince da aurenshi, ta tura mishi lambar iyayenta, sannan ta ba shi address dinsu.


Ba a wani dauki dogon lokaci ba maganar aurensu ta kankama. Soyayyar da ba su jima da fara ta ba amma ta rikide izuwa rayuwar aure. Wani irin so suke ma junansu wanda su kansu mamakin kansu suke.


Wata rana bayan biki suke hirar ta yadda soyayyarsu ta fara, Mujaheed na jinjina iko irin na Ubangijinmu.


"Wani lokacin har zama nake ina mamakin yadda daga haduwa sau daya muka kamu da soyayyar junanmu." Ta fada dana sanya tuffa a cikin bakinta.


STORY CONTINUES BELOW

"Ai ba abun mamaki ba ne. Namu ma mai sauki ne ai a kan wani bawan Allah Doctor Ishraq. Ban taba ganin soyayya irin wannan ba. Daga haduwa da yarinyar sau daya ya kamu da soyayyarta. Kuma abun haushi fitsara da rashin kunya fa ta yi mishi."


Dariya sosai Maryam ke yi, Mujaheed ya hau ba ta labarin duk yadda abun ya kasance. A karshe ya dora da "Ameerah Muhammad ta tafi da zuciyar Ishraq. Mun rasa gidan da ta je har yanzu ba mu gano ba balle mu san ainahin garinsu. Tun muna nema har ma mun jingine, kodayake ban dai san a nashi bangaren ba ko har yanzu yana kan bakarshi na neman ta. Ga shi yanzu har ma na rasa lambarshi."


Yana bayanin farko Maryam ta gane Ameeransu ce yake magana a kai. Idonta ta ji ya cika taf fa kwalla, tana hasko lokacin da Ameeran ta fito siyan detergent, da kuma komawarta tana dariya tana ba su labarin gamonta da Ishraq da mai shago.


Mamakin ganin tana kuka ya yi, duk ya bi ya rikice, da kyar ya iya hada "Ba fa ni ba ne mai son ta, Doctor Ishraq ne."


Gyada kanta ta yi Maryam, tana share hawaye wasu na saukowa.


"Ameerah Muhammad ta rasu, kusan shekara biyu da rabi kenan."


Ido ya kwalalo waje, yana jin wani irin yanayi a tattare da shi. Yana tuno yarinyar, yana tuno kaunar da Ishraq yake mata.


"Da gaske Ameerah ta rasu?" Ya jinjina kai yana jin baki daya jikinshi ya yi sanyi.


"Ta rasu. Da Babanta da Babana uwa daya uba daya suke. Kuma zuwa shagonka da ta yi a wancan lokacin, sadda aka kawo Yah Nafeesa ne. Bayan ta koma sai da ta ba mu labarinku da duk yadda kuka yi." Ta sauke ajiyar zuciya, tana dorawa da "A gidanmu take zaune tun bayan rabuwarta da Nurah saurayinta na can garinsu Hunkuyi. Ta fara karatu. Sai wata rana da ta samu hutu ta shirya tafiya gida. A kan hanyarsu kafin su isa Zaria suka tafka mummunan hatsarin motar da babu wanda ya fita da rai a cikinsu. Sanarwar da aka bayar da kuma rashin isar Ameerah Hunkuyi har dare ya yi ya sa aka gaggauta zuwa asibitin da muka ji sanarwar. A can aka sami gawar Ameerah." Ta share hawayenta. Tana tuna yadda suka ji radadi da zugin rashin Ameerah. Babu wanda zai zauna da ita bai ji dadi ba. Mutum ce da ta san abin da take yi, wadda ko kadan ba ta yarda ba ta bar mutum a cikin damuwa idan ta tsince shi a yanayin.


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah Ya ji kanta Ya gafarta mata." Mujaheed ya fada, yana tunanin ta inda zai gano Ishraq din ya sanar da shi.


*

Kuka Ishraq yake yi, kuka yake da zuciya da idanuwanshi gaba daya. Wannan mummunan labari ne Mujaheed ya sanar da shi. Hannuwanshi ya dora a saman fuskarshi, yana share hawaye, amma wasu ne ke kara fitowa.


"Ka yi hakuri Ishraq, dukkan mai rai mamaci ne. Da ma can Allah Ya rubuta sau daya tak za ka ga Ameerah. Ka yi fatan Allah Ya ba ka madadinta."


"Ameen." Kawai Ishraq din ya ce, yana mikewa hade da kirkiro murmushi, ya mika ma Mujaheed hannu yana mishi sallama zai wuce.


"Na gode sosai da ziyara likita. Idan kana da shaawar zuwa gidansu ina iya kwatanta maka, ko kuma in ba ka lambar mahaifinta sai ka mishi gaisuwar rashinta."


Jinjina kai ya yi Ishraq, yana mika wayarshi ga Mujaheed, tare da ba shi izinin saka mishi lambar Mallam Muhammad.


A kan hanyarshi ta komawa gida wayarshi ta fara ringing. Yana dubawa ya ga sunan Noor ne. Ya dauka bayan ya sanya wayar a hands free yana ci gaba da tukinshi.


Gaisawa suka yi, Ishraq din ya mishi ya mai jiki.


"Ameer ya ji sauki sosai Doctor Ish. Typhoid ce ta mishi mummunan kamu ashe, shi ya sa yake ta wahala. Amma dai Alhamdulillahi yanzu, yana ta shan magani. Ka san ta ita ba ta iya kama mutum ba. Fin shekara biyu ke nan yana fama da ita."


Cikin tausayi Ishraq ya ce "To Allah Ya kara mishi lafiya Ya yaye mishi baki daya."


"Ameen ya Allah. Da ma na kira ne kawai mu gaisa, kwana biyu."


"Wallahi yanayin ayyuka ne. Zan yi kokari in shaa Allahu in zo har gida in duba Ameer din da jiki. Zan je in dauko mishi 'yar uwarshi ma Ameerah in kawo ta su gaisa."


Cike da farin ciki Noor ya ce "Au wai da ma kana da baby? Ameerah? Wow! Ma shaa Allah. Sunan da na fi so kenan a duk duniyata. Halittar da na so kuma nake kan son ta, wadda zan so har nan gaba da abada."


Murmushi Ishraq din ya kirkiro, duk da zancen mutuwar Ameerah na nan ya mishi tsaye a makoshi. "To Allah Ya bar ku tare har karshen numfashinku." A tunaninshi ko matar Noor din ce Ameerah.


Ajiyar zuciya Noor din ya sauke. "Ameerah ta rasu, ta jima da rasuwa ta hanyar hatsarin mota, more than 6 years ke nan da mutuwarta Doctor Ish."


Ido Ishraq din ya kwalalo, yana kallon yadda yake neman kai ma motar gabanshi karo tsabar rikicewa. Da kyar ya iya saita kanshi, tambaya yake so ya ma Noor din amma bai ma san ta inda zai fara ba.


"Ina driving Mr. Noor, will call you later." Kawai ya iya matsowa ya fada. Yana jin zuciyarshi na ba shi tabbacin Ameerah Muhammad ce Noor din yake magana a kanta. Ameerarshi da yake mutuwar so, wadda ya ci buri da aurenta. Da gaske yarinyar tana da zama zuciya sosai, tana da halayen da duk wanda zai zauna da ita dole ya ji ta shiga ranshi.

"Ameerah mallakin Yah Nurah." Ya fada a bayyane, yana hasko sadda Ameerah ke fada ma Mujaheed wannan maganar cike da tsiwa.


End of chapter


Princess Amrah

RAZ 2Da kyar Ishraq ya iya kai kanshi gidan Mami. Bai same ta a falo ba ya san tana dakinta. Can ya bi ta yana zama a bakin gado jin motsinta a toilet. Tana fitowa ta saki murmushi. "Likita ai sai ka tsorata ni. Ban ji shigowar ka ba."


Damuwa bayyane a saman fuskarshi ya ce "Mami...Mami Ameerah ta rasu."


Da karfi ta ji dirar maganar tashi a zuciyarta. Sauri-sauri take jin zuciyarta na bugawa. Hawaye na neman cika idanuwanta.


"Ba ta da lafiya ne ko tun wancan..."


"Hatsarin mota ne Mami." Ya tarbe ta da shi.


"Innalillahi wa Inna ilahi raji'un! To ina ita Mahboobar? Ba ta dai ji ciwo ba ko?"


Sai a yanzu ya gano inda Mamin tashi ta dosa.  "Mami ba Ameerah nan ba. Ameerah Muhammad dai wadda kika san ina kauna, ina son aurenta."


Nannauyar ajiyar zuciya Mamin ta sauke. Tana jin wani irin sassauci ya sauka a zuciyarta. Amma dai duk da haka ta shiga jimamin mutuwar Ameerah Muhammad din ma. Ko ba komai yadda Ishraq ya kuntata wa rayuwarshi dominta, dole za ta taya shi jimamin rashinta.


"Allah Ya gafarta mata da dukkan musulmai."


Bai ko iya amsawa da ameen ba kasantuwar dukewa da ya yi yana jin wani irin radadi a zuciyarshi. Hawayen ma yake nema sun ki zuwa. Watakila da zai samu ya fiddo su da radadin zuciyar tashi ya saukaka.+


"Mami zuciyata zafi take yi min." Cike da tausayi ta kama shi ta tasar zaune. Cikin rarrashi take fadin "Ka yi hakuri likita ka rungumi wannan kaddarar ka ji. Mutane da yawa suna rasa makusantansu kuma suke hakuri da rashinsu, ciki kuwa har da ni nan kaina. Ba ni da uwa ba ni da uba. Mijin da nake aure ya kwanta ya mutu. Duk duniya kai kadai ne makusancins Ishraq, sai kuwa kanne da yan uwana. Kuma a haka na daure, na ci gaba da nishadi duk da kewar su da nake yi.


Ishraq ka rasa mahaifi, gatanka, masoyinka. Ka kuma hakura ka ci gaba da rayuwar ba tare da ciwon zuciya ba.


Me ya sa Ameerah da ka taba ganin ta sau daya tal mutuwarta za ta sanya maka ciwon zuciya?


Da Allah nake hada ka, ka dubi girmanShi, ka saukaka ma kanka, ka gusar da dukkanin kuncin da kake ciki, in dai kana son ganina a walwala."


Sosai nasihar tata ta shige shi. Yana son Ameerah, son da bai taba tunanin akwai macen da za ta samu ko kwatankwacinshi ba a duniyarshi. Amma a hakan zai daure, zai rungumi wannan kaddarar tashi.


"In shaa Allahu Mami...da izinin Ubangijin da Ya halicci Ameerah kuma Ya dauke ta a lokacin da Ya so, komai ya wuce, zan kokarta zare damuwar rashinta daga zuciyata."


"Alhamdulillah!" Mamin ta fada, tana jinjina ma taushi da sanyin zuciya irin na Ishraq.


*

An dauki kimanin makwanni biyu da jin labarin mutuwar Ameerah, Ishraq ya tuna da alkawarin da ya yi ma Noor. Tun bayan da ya saki Mahboobah bai taba zuwa gidansu ba ko da sunan ya je duba Ameerah. Sau daya dai ya ga yarinyar, an kai ma Mami ita. Tun daga nan kuma bai sake sanya ta a idonshi ba. Sai dai duk da haka yana dauke da nauyin yarinyar, duk wata sai ya yi siyayya tun daga kan diaper da kayan shayi, zuwa ruwan da yarinyar take sha, da duk wani abun bukata na yau da gobe yana aikawa, har da dorin kudi ma. Sannan idan an dauki kamar wata biyu, zai sayi kaya yan kanti masu kyau da tsada, na yayi ya aika mata da su.


STORY CONTINUES BELOW

Yana tsananin son ganin diyarshi, yana son dora ta a idanuwanshi. Hakan ya sa ya dauki wayarshi karama, lambar Mahboobah da ya yi saving da KK ya gano, yana sakan ma kanshi murmushi, tuna ma'anar sunan da ya yi.

Ya latso kiran ta amma ba ta dauka ba. Ita kuwa tsantsar mamaki ne ya hana ta dagawa, ta jima da goge lambarshi daga wayarta, sai dai kuma tana nan zane a cikin kwakwalwarta. Sai da ya kira a karo na biyu sannan ta dauka, tana rasa abin da za ta fada mishi.


A nashi bangaren ma rasa abin da zai ce mata ya yi. Da kyar ya iya tattaro gaisuwa ya yi, ta amsa da murya ciki-ciki.


"Ameerah nake so a shirya gobe, zan zo in dauke ta akwai gidan abokina da za mu je."


"Allah Ya kai mu." Kawai ta ce, tana yanke kiran.


Bai san yadda aka yi ba ya ji babu dadi. Canjawar da Mahboobah ta yi ce babban abin da ya daure mishi kai. Daidai da kadan bai tsinci soyayyarshi ba a muryarta kamar baya. In da da ne, ko ba ta ce komai ba ba za ta katse mishi kira ba.


Ita kuwa ta kasa daina mamaki. Mommy da ke gefenta ta tambaye ta abin da ya faru. "Ishraq ne. Wai gobe zai zo ya dauki Ameerah zai kai ta gidan abokinshi."


Ta fada idonta na kawo ruwa. "Mommy kar ya ki dawo min da ita."


Murmushi Mommy ta yi, cikin kwantar mata da hankali ta ce "Yarinyar da ke shan nono ya zai yi da ita? Dan boko ne mai ilmi, ya san darajar nonon uwa. Na tabbata zai dawo da ita ba za ta kwana ba."


Marairaicewa ta yi tana jin haushin Ishraq. Kawai gani take yi ba zai dawo mata da Ameerah ba duk dubara ce ya yi.


Washe gari da safe ta ga text dinshi ya ce wuraren sha daya na safe zai zo ya dauki Ameerar. Hakan ya sa ta mike da wuri ta nufi falo. Ta samu Mommy da Ameerar zaune tana ta zuba wa Mommy yare. Fareeda kuma ta tafi makaranta.


Bayan ta gaishe da Mommy cikin hamma ta ce "Mommy wai 11am zai zo ya dauke ta."


Ita Mommyn ta ma manta da zancen sai yanzu ta tuna. "Fareedah ta mata wanka kafin ta fita sai dai ko za ki canja mata kaya. Sai kuma ki hada mata da extra kaya da diaper. Ki kuma hada mata tea a bottle dinta."


To ta ce tana barin wurin. Baby suites biyu ta hada da yar kanti guda a cikin baby bag dinta. Sai ta sanya diaper guda biyu ta feshe kayan da turare ta zuge.


Sai da ta ga sha dayan ta yi sannan ta hada tea din a feeder. Ta ba ta nono ta sha sosai sannan suka ji sallamarshi.

Kasa ya tsugunna ya gaishe da Mommy ta amsa da sakin fuska tana ba shi izinin zama bisa kujera.


A da, jin kamshin turarenshi kadai kan rikita Mahboobah. Sai dai a yanzu sabanin haka ne. Kallon shi take cike da tsana, irin kallon da ba ta taba tunani ba ko a mafarki za ta jefi Ishraq din da shi.


Kallon ta ya yi ta basar kawai tana sauke Ameerah daga jikinta. Ba ta ce mishi komai ta bar falon ya bi inuwarta da kallo.


Mommy da kanta ta mika mishi Ameerah. Ya ga yadda yarinyar ta kara wayo sosai a kan sadda ya mata ganin karshe. Ga gashi yalwatacce a kanta. Kamanninta da shi sun kara bayyana sosai.


Kasantuwar Ameerah ba ta da kyuya ya sa ba ta ki Ishraq ba. Ba a jima ba sai ga Mahboobah ta fito rike da baby bag din Ameerah ta girke a kusa da shi. Komawa ta yi daki tana jin wani irin tukukin haushin tafiyar da zai yi da diyarta da take ganin ya wofintar a baya.


STORY CONTINUES BELOW

Bai fi minti biyar ba ya mike yana tallabar Ameerah a kafadarshi, ya ma Mommy sallama bayan ya dauki jakar yana shaida mata zuwa la'asar za su dawo tunda ba a yaye yarinyar ba. Cikin karamci suka yi sallama ya fita.


Da yake Ameerah akwai son yawo sai farin ciki take yi. Kuma Fareedah ta koya mata wasa sosai tana son wasa. Shi ya sa ta ji dadin yadda Ishraq din yake jan ta wasa.


Ya kira Noor ya kwatanta mishi gidanshi. Bai wani sha wahala ba suka isa gidan. Sauka ya yi daga motar tallabe da Ameerah, ya zagaya ya bude gaba ya dauki jakarta sannan ya yi knocking.


Bayan an bude ya ga Noor, wannan ita ce haduwar su ta farko a zahiri bayan tsawon lokacin da suka dauka suna zumunci a waya, duk da a farko Ishraq din ya yi ta nokewa. Ganin mutumin kirki ne ga dukkan alamu ya sanya shi aminta da shi din.


Karbar Ameerah ya yi yana mata wasa suka isa cikin gidan. Da gudu Ameer ya zo wurinsu saboda ganin Ameerah. Yana son kananan yara sosai amma mahaifiyarshi ta zabi dakatar da haihuwa a cewar ta babu amfanin kara haihuwa tunda ba ta da lokacin zama ta kula da yaran.


"Ameer ba ka iya gaisuwa ba ne ba za ka gaida Uncle ba" Noor ya fada yana kallon Ameer din da ya kadaddabe Ameera kamar zai hade ta.

Kusa da Ishraq ya matsa tana gaishe shi. Ishraq ya dafa kafadarshi "Sannu Ameer ya jikinka?"


"Da sauki." Ya fadi yana komawa wurin Ameerah.


"Ai fa babu sauran nutsuwa tunda ya ga kawar wasa." Ita ma Ameerar sai zullo take ta sauko kusa da shi. Kayan wasanshi ya je ya tattaro mata suka ci gaba da wasa.


Shi dai Ishraq babban burinshi daya su yi maganar Ameerah Muhammad. Sai dai mamakin da yake yi, ya ji motsin mutum a cikin dakin da ke bayanshi, da alama matar Noor din tana nan, amma ya gagara ta fito ta gaishe shi. Drinks ma sai Noor din ne da kanshi ya kawo mishi.


"Mr Noor, rannan a waya ka fara ba ni labarin Ameerah sai tsautsayin hatsari ya kusa afko mini na kashe wayar."


Murmushi mai ciwo, wanda iyakar shi bisa lebo  Noor din ya yi. Yana runtse idonshi, yana sauke su a kan Ishraq da ya zuba mishi nashi idanuwan, yana neman karin bayani.


"Ban taba jin son wata halitta koma-bayan Ameerah ba. Na so kasancewa da ita a karkashin inuwa guda, na so mallakar Ameerah a matsayin matar aure na, sai dai kaddara, da rabon auren Sameerah ya sa mahaifina ya farraqa mu, ya raba soyayyarmu ta karfi da yaji a ranar da aka yi baikonmu."


Saurin shafe kwallar da ta fara disa bisa kwarmin idonshi ya yi, yana kallon Ameer da Ameerah, yana gwada musu hanyar dakin Ameer din. "Ameer kama ta ku tafi dakinka ku yi wasan, can ya fi muku."


Da ma surutun da Abbanshi ke yi da Baban Ameerah ya dame shi, sai ya ji dadi, ya kama Ameerah ya kai ta dakin, ya sake dawowa ya kwashi kayan wasansu.


"Tun bayan rabuwata da Ameerah ban sake nishadi ba, zuciyata ba ta daina dokawa da soyayyarta ba, idanuwana ba su daina mararin ganin ta ba, kunnuwana a kullum mararin jin muryarta suke." Ya dakata a nan, yana tsananin jin soyayyarta na taso mishi. Ya dora da "Baki daya rayuwar Ameerah ta koma a garin Kaduna, gidan yayan mahaifinta. Tafiyar Ameerah daga Hunkuyi ya kara sukukuta ni, kullum cikin kuka nake ba dare ba rana, na rasa sukuni, na rasa Ameerah rabin rayuwata."


Ya gyada kanshi a kan wannan gabar, yana sakin murmushi da ya tuno wasu daga cikin halayen Ameerah. "Ameerah mutum ce mai raha, mutum mai walwala mai kokarin saka na zagaye da ita walwala. Ba ta bakin ciki a rayuwarta, haka kuma ba ta bakin ciki da rayuwar kowa. Yarinya ce mai tsokana, sannan mai burin saka kowa a nishadi. Ameerah na da fara'a, a kodayaushe ba ka rasa fuskarta da annuri." Ya dafe kanshi yana jin yadda yake sara mishi. "Idan za mu kwana a nan ba zan iya kai maka karshen kyawawan halayenta ba. Ameerah mutum ce har da rabin mutum."


Gyada kanshi ya yi Ishraq, yana jin yadda hawaye ke cika idanuwanshi. Ashe shi aikin banza yake yi, ga wanda ke son Ameerah da gaskiya, wanda suka so auren juna aka farraka su.


"Har bayan Ameerah ta shekara da barin Hunkuyi ban koma asalin rayuwata ba. A wata ranar lahadi mahaifina ya zo ya same ni da zancen komawa birni gidan Alhaji Ahmad Danja, abokinshi da na zauna gidanshi lokacin da na yi bautar kasa ta.


'Ka shirya maza-maza da safiyar gobe Monday ka tafi Kaduna. Ya ce an sama maka aikin yi, ban dai san ko a ina ba ne sai ka je za ka ji.'


Duk da na ji dadin zancen samun aikin, sai dai jin dadin ya koma ciki a lokacin da na tuno dalilin samun aikin. Diyarshi Sameerah ce take so na tun zama na gidan sadda nake NYSC. Ganin ba ni da aikin yi ya sa aka jinkirta zancen auren.


Ban fi sati guda ba da komawa Kaduna offer ta ta fito na samu aiki a Kaduna State Government. Abin da suke jira ke nan da ma, sai aka fara zancen aurena ni da Meerah.


Daidai da rana daya ban taba jin son ta ba, sai dai na aure ta ne domin nuna godiya ga mahaifinta a matsayinshi na jigon rayuwata a lokacin, ba na son zama butulu, ko kadan.


Na auri Sameerah da ke aiki a Access Bank. Sai dai tun da na aure ta na gane auren mai aikin Banki bai da amfani. Da safe za ta riga ni fita daga gida, kuma ba za ta dawo ba sai kusan maghrib a lokacin na jima da dawowa ni. Ban san wani abu wai shi dadin aure ba Ishraq. A weekend ma da ya kamata mu samu lokacin juna, to ita ba ta da nawa lokacin, sai ta ce hutawa take yi, kwanaki biyar babu hutu shi ne ba zan bar ta ba ta huta na kwana biyu. Ta kwanta ta wuni tana sharar barci, abinci ma sai dai ko in fita in siya ko kuma in sha tea ko cornflakes.


A cikin wannan rayuwar ta samu cikin Ameer. Sai abun ma ya kara lalace mana. Tun cikin na da wata hudu ta koma gidansu wai goyon ciki, ba ta sake dawowa ba sai bayan ta haihu. Rayuwar Ameer baki daya ta koma a hannun yar aiki. Daidai da homework dinshi bayan ya shiga makaranta ni nake masa. Karatun islamiyya ma ni ne mai yi."


Ya sauke ajiyar zuciya yana sauke kanshi a kasa saboda kunyar fidda sirrin rayuwar auren shi da ya ji. Bai taba ba wani labari ba sai a yau. Duk sai ya ji wani iri.


"Na so a ce Ameer mace ce in saka mishi sunan Ameerah, sai ya zo a namiji. Wannan shi ne dalilin saka mishi sunan, saboda marigayiya Ameerah Muhammad..."


Wani irin wawan ashar ya ji an banka daga bayanshi. Sameerah ce ta fito sai huci take yi tamkar bakin kumurci.


"Wato ma ashe sunan tsohuwar budurwarka ne ka saka ma yarona ko! To wallahi ba ka isa ba." Ta juya ga Ishraq,


"Kai kuma tsohon munafuki ka kasa kunne kana jin sirrin mata da miji. Bari in bar muku gidan ku ji dadin yin gulmar."


Ta fice da wani dan siririn mayafi, ga riga da skirt din atamfa da ta saka sun matse ta, ta daura dankwali gashin dokin da ta kara duk ya bayyana.


End of chapter


Yau Ishraq ya ganu da gamonshi😂5


Princess Amrah

RAZ 2Cikin takaici Noor ya kalli Ishraq da ya kasa daina mamaki ya ce, "A haka nake rayuwa da Meerah fin shekara biyar. Ko kadan ba ta san darajata ba, ba ta san darajar aure ba. Idan ta cika ni na mata fada, sai ta hau goranta mini, saboda hatta gidan da na kaita da farkon auren ma na mahaifinta ne, sai daga baya na kama hayar wannan. Ko kadan ba ta san darajar iyayena ba, ba ta taba girmama su ba. Akwai sadda na tirsasa mata zuwa Hunkuyi bikin kanwata, tun da ta je ba ta ma kowa magana. Ruwan gidan ma ba ta sha sai dai ta siyo na roba. Ko Ameer ba ta ma wanka da ruwan gidan, pure water na leda take fasawa ta mishi tsabar ta raina komai namu.


Ban taba jin karin takaicin auren Meerah ba sai fara ciwon nan na Ameer. Ta fifita aikinta a kan kula da shi, yar rainon ma tashi muka gane zaluntarshi take yi muka sallame ta. Ishraq ni na dauki hutu a wurin aiki na koma zaman gida ina kula da shi. Kuma na ce zan mayar da shi Hunkuyi a gaban iyayena don ya samu kyakkyawar kula ta ce ba ta amince in kai mata yaro kauye ba. Wai a cewar ta ma a can ya samu typhoid."


Gyada kai kawai Ishraq ke yi yana mamakin al'amarin. Bai taba gasgata akwai mata irin wadannan ba sai yau.


"Ba ni da katabus a gidana Ishraq. Ban isa in hana ba, ban kuma isa in bada umurni ba. Ka ji salon tawa rayuwar."


Ya rufe maganar da dariyar da ta bayyana hakoranshi a waje.


"Lallai kana ganin rayuwa Mr. Noor. Allah Ya daidaita lamarin idan mai daidaituwa ne." Ya fada yana tuno tashi rayuwar da Mahboobah, yadda ta rinka kyautata mishi amma daidai da rana daya bai taba appreciating mata ba, bai taba nuna mata ya ma san tana kyautata mishi ba. Abu daya da ba zai taba mantawa ba game da ita shi ne soyayyarta gare shi. Tun da yake a rayuwarshi bai taba ganin soyayya irin wannan ba, bai taba ganin inda mace ta fito karara ta bayyana soyayyar da take ma namiji ta tsakaninta da Allah ba irin yadda Mahboobah ta rinka gwada mishi. Sai ji ya yi tamkar wani abu ya soki zuciyarshi, yana tsargowa har cikin kwayar idanuwanshi, yana ratsa su yana fitowa hade da wasu irin hawaye masu gumi.+


Da kyar Ishraq ya iya daidaita kanshi, cikin sanyin murya ya ce "Sunan Ameerah Muhammad shi ne aka saka ma Ameerah Ishraq."


Cike da mamaki Noor din ke bin shi da kallo. Kai Ishraq ya jinjina mishi tare da labarta mishi komai game da Ameerah. Murmushi Noor ya yi, "Ai na fada maka, babu wanda zai zauna da ita ba ta shiga ranshi ba."


"Wallahi Mr. Noor ban taba jin son wata mace ba koma-bayan Ameerah Muhammad."


Cikin mamaki Noor ya zaro idanuwa. "Har matarka?"


Murmushi ya yi Ishraq, "Har ita." Ya ba shi amsa yana zuba lemu a glass cup.


Noor ya kasa daina mamakin Ishraq, "Amma garin yaya haka ta faru?"


Murmushin takaici Ishraq ya yi, yana jin ba zai iya fallasa tsakaninshi da Mahboobah ba, tsantsar soyayyar da ta gwada mishi kadai ya isa ya sanya shi rufe sirrinta, sirrin silar aurenta da ya yi, da kuma silar rabuwar shi da ita.


"Auren hadi ne..." Ya fada, yana dorawa da "Mami ce ta hada mu. Zahirin soyayyata na ga Ameerah Muhammad."


Wani irin tukukin kishi Noor ya ji ya soke shi, don me ya sa Ishraq zai ci gaba da ambata mishi soyayyar da yake yi ma Ameerah? Bai san sadda fuskarshi ta juye daga sakin fuska zuwa damuwa ba. Kishi yake ji ta ko'ina yana ratsa shi. Ishraq din ya fahimci haka, ya saki murmushin da ya bayyana fararen hakoranshi.


"Sai dai, ya zama dole in zare soyayyar Ameerah da karfin tsiya daga zuciyata. Ko da a ce tana raye, ba ni ba ne ya cancanta in so ta kwatankwacin yadda nake son ta ba a yanzu. Kai ne...kai ne Mr. Noor."


STORY CONTINUES BELOW

Nannauyar ajiyar zuciya Noor din ya sauke. Yana dafa kafadar Ishraq da hannunshi na dama. "Ita soyayya duk sunanta soyayya. Na fahimci yadda ka so Ameerah Dr Ish. Ina fatan wannan soyayya mai tarin girma da tarihi za ka dunkule ta tsaf, ka jefa ta a saitin zuciyar Maman Ameerah."


Hannunshi ya sanya Ishraq, ya shafi idanuwanshi, sannan kamar mai rada ya ce "Aurenmu ya jima da yankewa, ba mu tare da ita."


Ido ya zaro Noor, wani irin tukuki ya ji zuciyar shi ta dauka. "Amma me ya sa? Ita ma ba ta son ka ne?"


"Tana so na, sosai ma."


"To me ya jawo rabuwar? Me ya sa ka kasa kwakkwafar zuciyarka Ishraq, me ya sa ka kasa koya ma zuciyarka son ta?"


Gyada kanshi Ishraq din ke yi yana jin duniyarshi babu dadi. "Kaddara da rabon karshen zaman mu ke nan shi ya jawo haka. Kusan wata bakwai ke nan da na sake ta."


Sosai wannan labarin bai yi ma Noor dadi ba. Ko shi da yake cikin kangin rayuwa, ba ya jin dadin zama da Meerah sam amma yana daurewa da halinta, bai taba tunanin rabuwa da ita ba. Sai Ishraq?


"Na tabbata ko da a ce Ameerah ke raye idan ta ji labarin ka saki matarka ta silarta ba za ta ji dadi ba, ba za ta taba yafe maka ba Dr. Ishraq."


"Ba silar soyayyar Ameerah na rabu da Mahboobah ba. Ba na son ta ne, ban taba jin son ta ba daidai da rana daya. Ina amfanin zaman da sam ba ta jin dadina?"

Ishraq din ya ba shi amsa yana kallon shi.


"Sannu a hankali lamurra suke daidaituwa. Kamar yadda na fada maka a baya, ban taba jin son Meerah ba, ba na son ta ko kadan. A haka muke rayuwa ko kyautatawar da za ta iya sanya ni son ta ma ba na samu a wurinta. Kuma a haka nake zaune da ita da tsiya ina koyon zaman, sannu a hankali har na saba da iya shiga kitchen in girka abinci, na iya share gida, na iya mopping, na iya shirya Ameer. Soyayyar Sameerah ce har yanzu ban koya ba, kuma ita ma din ina fatan sannu a hankali zan koya."


Duk sai ya ji jikinshi ya yi sanyi Ishraq. Ya ma rasa abin da zai sake cewa, sai wani irin tausayin Mahboobah da ke taso mishi.


Da lokacin sallar azahar ya yi suka mike domin nufar masallaci. Tare da Ameer Noor din ya saba tafiya, sai dai yau ya ce bari ya bar shi a nan saboda Ameerah.


Daga masallaci suka wuce wata restaurant da ke kusa da gidan, suka yo takeaway na abinci sannan suka dawo gida.


Sai bayan sallar la'asar sannan Ishraq ya mike don tafiya. Ameer har da kukanshi sai ya bi su, Noor ya ce ya yi hakuri zai kai shi da kanshi, amma fir-fir yaron ya ki yin shiru. A karshe dai Ishraq ya roki Noor din a kan ya dauko ma Ameer kaya su tafi da shi.


Ba shi kanshi yake ji ba, mahaifiyar yaron yake ji. Yana gudun masifar da zai jangwano ma kanshi idan ta dawo ta tarar Ameer din ba ya nan. Murmushin dole ya kirkiro hade da fadin, "Ai Ameer idan yana son abu fa yana so. Bari in kawo mishi kayan yanzu ina zuwa."


Har da tsallen murna Ameer din ke yi, ya ji dadi sosai, saboda a dan wunin nan da ya yi da Ameerah sosai suka saba, yarinyar ta shiga ranshi.


Ba a jima ba Noor ya fito da jikar goyo ya bude bayan motar Ishraq ya saka. Bayan duk sun shiga motar ya ba Ishraq hannu suka sake gaisawa.


"Mr. Noor." Ishraq din ya fada yana sakar mishi murmushi. "Wai ma abin da na manta in tambaye ka, garin yaya Nurah ya koma Noor?"


STORY CONTINUES BELOW

Dariya sosai Noor din ke yi har yana dafe cikinshi. "A wasa-wasa ka iya zolaya Doctor Ish." Ya dan tsagaita da dariyar, yana dorawa da "Meerah ce. Ita ta ce ta kashe Nurah sai dai Noor, wai shi ne a wayance."


"Sai kai kuma ka biye mata..."


"To ya zan yi da ita? Tun rud'in amarci na fizgar mu ne dai gaskiya na gaza musa mata. Tun ban saba ba ma har na saba da sunan. Ya ma fi Nuran dadi ai."


Dariya shi ma Ishraq din yake yi, yana jinjina halayyar kirki irin ta Noor. "To bari mu wuce, in shaa Allahu nan da kwana biyu ko uku zan dawo da shi."


"To Allah Ya kai mu." Ya jawo jakar Ameerah ya tura kudi a ciki wanda ko shi kanshi Ishraq din bai san ko nawa ba ne. Gyada kanshi kawai ya yi da murmushi ya mishi godiya sannan ya tada motar.


*

"Momy har yanzu fa su Ameerah shiru." Mahboobah ta fada tana jin zuciyarta babu dadi, yini gudan da ta yi ba tare da yarinyar ba duk sai ta ji wani iri.


"In shaa Allahu zai dawo da ita Boobah ki kwantar da hankalinki."


Kai kawai ta jinjina takaici na kama ta.


"Ai gara ma ki saba da rashinta Mahboobah, ke da za ki fara karatu nan ba da jimawa ba."


Ba ta ce komai ba Mahboobah ta wuce Kitchen tana dora tuwon semo.


Ishraq kuwa kai tsaye ba gida ya wuce da su ba sai da ya kai su havilla suka sha ice cream sannan ya wuce gidan Mami da su. Mamin ta ji dadin ganin su, ya mata bayanin Ameer da kuma mahaifinshi.


Sai wuraren karfe biyar sannan ya mayar da su. A falo ya tarar Mahboobah ce kawai zaune tana kallon Zee World. Bayan ya yi sallama ta daga kanta ta kalle shi hade da watsa mishi harara sannan ta amsa sallamar.


Da gudu Ameerah ta isa inda take tana ambatar Ammi. "Oyoyo Ameeran Ammi na yi kewar ki sosai."


Raba jikinsu ta yi tana zuwa wurin Ameer ta jawo shi. Duk su biyun Mahboobah ta hada ta rungume.


"A ina kika samu aboki?" Ta fada tana kama hannun Ameer ta saka a cikin nata suka gaisa.


"Ina yini." Ameer din ya fada da fara'a a fuskarshi don ya ji dadi kwarai yadda Mahboobah ta saki jiki da shi fiye da yadda Mamanshi ke mishi.


"Lafiya lau yaron kirki. Ya sunanka?"


"Ameer." Ya ba ta amsa yana wasa da yatsunta.


"Ka ce dai sunanku daya da Ameerah. Ina Mommy?"


"Ba ta nan. Ai na biyo Ameerah ne a nan zan yi ta kwana ga kayana nan ma na zo da su."


Sosai Mahboobah ta ji yaron ya shiga ranta. Tana son yaro irin haka wayayye mai son mutane.


Ishraq kuwa ganin Mahboobah ba ta da lokacinshi ya sa ya mike tsaye zai tafi. "Ki ce da Mommy na wuce ina sauri."


Banza da shi ta yi tana ci gaba da jan Ameer da Ameerah hira. A daidai nan Mommy ta fito tana ma Ishraq din murmushi. "Ashe an dawo."


Gaishe ta ya yi ta amsa sannan ya mata sallama tare da cewa zai dawo ya dauki Ameer bayan kwana uku.


Yana fita wayarshi ta dauki ringing. Bai dauka ba har sai bayan ya shiga motar ya zauna ya rufe.


"Yah Ishraq don Allah ka saurare ni."


Kanshi ya dafe yana jin tsanar jin muryarta na dad'a taso mishi.


"Don Allah Bilkeesu ki kyale ni, ki rabu da ni na ce ba na son ki. Shin wai ana soyayya dole ne?"


"Ina son ka Yah Ishraq ka taimaka ka aure ni. Ka ga haka nan ka ki aure na a farko ka auri wannan banzar...ga shi a karshe ka gane ashe ma 'yar iska ce kuma fasika. Ka gani gida bai koshi ba bai kamata a kai dawa ba. Ka ji Yah Ishraq."


A yadda ya ji zafin kalamanta tabbas da kusa yake da ita sai ya mare ta. "Kar ki sake kiran matata banza, kuma ki daina ambatar mata fasikanci. Shin wai a ina ma kika ji wannan zancen?"


Dariya ta yi sosai tana fasa kwan cingam. "Labarin duniya yana boyuwa ne Yah Ishraq? Tun a sadda abun ya faru ai na ji zancen. Kuma ma, matarka ta ina bayan kun jima da rabuwa?


Tunani ya hau yi ta inda labarin ya fita. Shi dai ya san tsakaninshi da Allah duk duniya daga Mami sai Khalid Zannah kadai ya fada ma zancen. Kuma ya tabbata Mami dai ba za ta fitar ba, uwa uba kuma Khalid asusun ajiyar sirrikanshi.


"Ka daina mamaki Yah Ishraq. Na sani, duk duniya ma ta san cewa mazinaciya ce Mah..."


Kit ya kashe wayar, yana jin dacin maganganunta, yana jin da a ce a kusa da shi take sakinsu da tabbas sai ya raunata ta.

Duk da ya san cewa Mahboobah ta aikata, amma sai yake jin ciwon aibanta ta din da Bilkeesu ke yi. Ya ji zuciyarshi na mishi wata irin tafarfasa.

Tuka motar ya yi ya tafi. Yana rasa gane dalilin da ya sa baki daya a yanzu yake jin sauyin yanayi game da Mahboobah.


End of chapter


Doctor Ish ya dai?😂ko dai ko dai?

Meh wannan kiyayyar ke shirin komawa ne?

Uhm...babu ruwana ni ma dai ban sani ba😂Mu zira ido a gaba mu sha kallo kawai.


I love Ameer and Ameerah😍


Princess Amrah

RAZ 2Bayan shekara biyu.


Janye take da madaidaicin trolly, da sallamarta ta shiga falon tana ganin sauyin da ya samu, kasantuwar ta jima rabon da ta zo hutu.


"Wai ba kowa ne a gidan?" Ta fada da karfi bayan ta zauna kasa bisa kafet.


Da gudu Ameerah ta fito tana rungumeta. "Ammi yaushe kika zo?"


"Just now Ameerah. Ke kadai ce a gidan?"


"Mommy tana toilet." Ta ba ta amsa tana tsananin farin cikin ganin mahaifiyarta.


"I've missed you Ammi."

"Missed you to my baby. Ya school? Ina Mamama?"


"She's fine. Jiya ta zo nan." Ta fada tana waigen Mommy da ke shigowa falon tana ma Mahboobah sannu da zuwa.


"Ke ce da wannan sammakon kamar korarriya?"


"Wallahi Mommy kin san halina idan na so gida. Kuma hutun ba wani na kirki ba ne gara in saving dinshi a gida tare da ku."


Murmushi Mommyn ta fadada bayan ta zauna. "To ya karatun? Na san dai yanzu dole kina jin bambancinshi da na baya."+


"Mommy ina ma za a hada karatun IJMB da na yanzu. Wahala muke sha sosai wallahi. Don ma dai Hausawa suka ce sa rai wanda ya fi bauta ciwo. Gaskiya dai ina jinjina ma likitoci."


"To da ma mana ai ba a samu daga kwance dole sai an dage. Ke dai abin da nake so da ke ki mayar da hankalinki ki yi karatu sosai, nasara tana tare da ke da izinin Allah."


Mikewa ta yi Mahboobah tana jan akwatinta. "In shaa Allahu Mommy." Bayan ta kai akwatin nata daki ta dawo falo tana zama bisa kujera kusa da Mommy. "Mommy ya wurin su Fareeda? Kwana biyu ba mu yi waya ba tun shekaranjiya, na fada mata zan yi exam mai zafi jiya shi ya sa ba ta kira ni ba."


"Fareeda na lafiya Boobah. Jiya ai ta zo nan, ta so tafiya da Ameerah na hana. Ita ma Ameerar har fushi ta yi da ni na ce ta yi ta gama ta dawo min don duwawu nake mai dadin zama."


Dariya suka yi su duka, Aliyu ya shigo yana mata sannu da zuwa.


"Yauwa angon Hanee." Ta fada cikin dariya. "Wai Yah Aliyu mu za a boye mawa to ai gaskiya ta yi halinta." Ta kare fuskarta da filon kujera tana dariya.


"Mommy wallahi yarinyar nan ta raina ni. Ki ba ni izini in zane ta a cikin gidan nan." Ya fada yana gyada kai cikin murmushi.


"Yah Aliyu ai dai ba karya na yi ba. Sally ce ke gulmata min ni ma ashe duk tsawon shekarun nan kuna tare kuna ta sheka soyayyarku an bar mu a duhu."


"Wallahi ba zan hana shi zanarki ba Boobah tunda dai ke ba za ki girma da tsokana ba."


Tabe baki ta yi Mahboobah. "Mommy ni fa dadi abun ya yi min wallahi za mu yi tuwona maina."


"Allah Ya shirya ki Booban Daddy." Mommy ta fada tana kai mata bugun wasa.


"Uncle Aliyu muna fada ne?" Ya ji muryar Ameerah ta fada cikin fushi.


"Ameerana are we fighting?" Ya maimaita mata kalar tambayar da ta yi mishi.


"We are not." Ta fada kan jikinshi hade da kankame shi.


STORY CONTINUES BELOW

"Ba ke kin ga Amminki ba shi ne za ki share ni?" Ya fada yana harararta.


"No Uncle ba ina ta kallon ka ba amma ka ki kallo na shi ne na yi fushi."


"Common my baby ban gan ki ba ne sorry kin ji."

"Uhm...kanku dai ake ji. Mu dai a yi sauri a yi magana mu sha biki." Mahboobah ta fada bayan ta bar dakin ta nufi nata.


Kayan jikinta ta cire ta daura towel ta shiga wanka. Bayan ta fito mai kawai ta shafa ta nemi doguwar riga mai gajeren hannu ta saka.

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani irin dadi yana ratsa zuciyarta. Idan har auren Haneefa da Yah Aliyu ya tabbata za ta fi kowa farin ciki. Soyayyar da take ma Haneefa da Saleema ya sa take jin ina ma a ce tana da wani dan uwan ma ta ba Saleema shi duk su tare a gida guda.

Murmushi ta saki tana tuno sadda Saleema ke mata gulmar.


'Wai kina da labarin soyayyar Hanee da Yah Aliyu dai ko?'


Cikin mamaki ta zaro ido duk da a waya ne tana neman karin bayani.


'Wallahi duk zaman nan ashe soyayya suke a boye duk ba mu sani ba. Sai yanzu ne Haneen ta fara ba ni alama amma duk da haka ba ta fito kai tsaye ta fada min ba. Na dai gane tabbas suna tare da alama ma gidansu an san da shi don na ji rannan Ruky ta so ta fara min maganar Hanee ta kore ta daga dakin.'


Wata irin shewa Mahboobah ta saka tana jin dadin wannan gulmar. 'Kai amma dai mutanen nan sun cakar da mu da yawa.'


'Cakarwa sosai ma MB. Ai so nake ki yi ki zo hutu mu iske Hanee har gida mu zuba mata rashin mutuncin boye mana da ta yi.'


"Ammi wayanki na ringing." Ameerah ta katse mata tunanin da take yi.


Bayan ta dauka da sallama a bakinta ta ji muryar namiji ya amsa. "Afwan ban gane mai magana ba."


Ajiyar zuciya ya sauke, "Na san ba za ki gane ba da ma tunda ba ki san ni ba gaskiya. Sunana Muhammad Saddam. Ni haifaffen garin Zaria ne dan sarautar Zazzau. Na samu lambarki ne a wurin wani abokin karatunki Haidar. Tun kina IJMB nake son yi miki magana amma ina jin nauyi don na ga ba da kowa kike magana ba sai Haidar kadai. Ina so ki ba ni dama mu zama friends saboda kina burge ni sosai."


"Ikon Allah." Ta furta hade da sauke ajiyar zuciya tana dorawa da "Ba na friendship da maza am sorry."


Cikin marairaicewa ya ce "Shi fa Haidar waye idan ba friend dinki ba? Ni za ki ma wayo ko Mahboobah. Shi kenan ma bari in yi ta kuka tunda kora na kike." Ya yi muryar kuka.


Dariya ya ba ta har ta kasa boyewa. "Ka ji ka kamar wani dan yaro."


"Eh mana to ai ni dan yaro ne. Kuma kuka nake yi duk sadda ban samu abin da nake so ba." Ya fada yana jin dadin dariyar da ya saka ta.


"A ina kake dan yaron bayan kana neman friendship din budurwa."


Ya yi dariya. "To na ji ni ba dan yaro ba ne. Ni jinjiri ne." Ya fada yana kara yin wata dariyar.


"Ko Ameerah ba jinjira ba ce balle kai gotai-gotai aure bana haihuwa badi." Ta fada tana dariya.


"Wace ce Ameerah?"

STORY CONTINUES BELOW

"My one and only daughter."


Gabanshi ne ya ji ya bada ras. A cikin yan seconds idanuwanshi suka canja launi. Ya yi tsit daga nan bai kara fadar komai ba sai saukar numfashinshi kawai da take ji.


"Hello...are you with me?" Ta tambaya jin shi shiru.


"Yeah am with you. Ina ta mamaki ne na ji kin ce kina da daughter."


"And kai kuma ba ka kawance da wadda take da baby ko?"


Murmushi ya kirkiro. "No it's not like that. Kawai dai na yi mamaki ne ba ki yi kama da matar aure ba."


"Idan ina da aure zan yi ko seconds goma ina magana da kai ne? I have a 3 years old daughter amma ba na tare da mahaifinta." Ta ba shi amsa ba wai don tana son bude mishi sirrinta ba sai don janye zargin da ka iya darsuwa a zuciyarshi.


"Eyyah sorry. Allah Ya sa hakan ne mafi alkhairi Ya kawo nagari. Allah Ya raya mana Ameerah."


"Ameen ya Allah."


"Now bari in bar ki ki huta anjima zan sake kiran ki. Daga nan ma sai ki hada ni da Babyn tamu mu gaisa."


"Okay no problem. Thank you so Much Muhammad."


"Welcome darling." Ya fada yana tsinke wayar.


Falo ta nufa ta tarar babu kowa hakan ya ba ta damar shiga kitchen domin girka abincin rana.


*

Yana zaune a cikin Office ya ji knocking din Kamal. "Yes, come in." Ya ba shi izinin shigowa. Bayan ya shigo Kamal din ya shaida mishi yana da bako a waje. Ishraq din ya tambaye shi ko ya san shi ya ce bai taba ganin shi ba. "Ka ce da shi ya shigo." Ya umurce shi.


Babu jimawa sai ga mutumin ya shigo, sanye yake da light blue din shadda wadda ta gama jin duniya. Fuskarshi duk gashi irin na kazantar nan wanda ya gagara ya aske.

Hannu ya ba Ishraq din suka gaisa sannan ya ba shi izinin zama.


"Ba ka gane ni ba ko?"


Sai a sannan Ishraq din ya kalle shi ya kara kallon shi. Ta ina ma zai manta da shi? Ta yaya zai manta da mutumin da ya shiga tsakanin zamanshi da Mahboobah Bukar, ya kawo karshen zamanshi a karkashin inuwa guda da gudan jininshi Ameerah?


Mikewa ya yi Ishraq din, yana shakar wuyan mutumin, a take idonshi suka canja launi. Bugun zuciyarshi ya sauya. "Uban me ya kawo ka Office dina? Na ce me ka zo yi min a office? Ko so kake in shigar da kai kara?" Kamar mahaukaci haka Ishraq ke jero mishi wadannan maganganun yana bin shi da mugun kallo mai cike da tsana.


"Ba na nufinka da komai sai alkhairi..." Ya fada yana son ci gaba amma wawan kallon da Ishraq din ke bin shi da shi, da kuma zafin shakar da ya yi mishi ne suka sanya shi yin shiru.


"Mazinaci mai bin matan aure ne ke nufina da alkhairi? Wanda ke bibiye da matata ta sunna?" Ishraq ya furta yana ci gaba da watsa mishi harara.


Wani irin kwarjini Ishraq din ke yi mishi wanda ya sanya shi kasa fadin abin da ya yi niyya, sai wani irin huttai yake yi saboda zafin matsa.


"Ka fada min me ya kawo ka inda nake? Me ya sa kake bibiye da ni har ka gano Office dina bayan tsayin shekarun rabuwarmu?"


Cikin firgici ya ce "Ka sassauta mun riko zan fada maka komai. Wallahi tallahi ba Mahboobah ce ta kai ni gidanka ba, hasali ma ba ta taba gani na ba ban taba ganin ta ba sai ranar."


Sakin shi Ishraq ya yi yana firfito da idanuwanshi waje cike da mamaki, kallon shi yake, kallo mai kunshe da ma'anoni kala-kala. Bai san sadda ya fada kan kujerarshi ba dab'as ya zauna. Kanshi yake ji yana sara mishi. Da duk tashin hankalin da ya mamaye duniyarshi yake jin komai yana birkice mishi tamkar a mafarki.


"Ban san ta ba ba ta san ni ba. Duk abubuwan da na fada maka lokacin sanya ni aka yi. Wallahi kazafi ne muka yi wa Mahboobah." Ya fada yana matse idanuwanshi da ke niyyar kawo ruwa.


"Ban taba kwartanci ba, ban taba sha'awar bibiyar matan banza ba. Gidan matan aure ma idan ba na muharramaina ba ne ba na shiga. Rashin madafa ne ya sanya ni aikatawa, wallahi ba da son zuciyata ba ne ba." A wannan gabar ya kasa dakatar da hawayenshi, kuka yake yi, kuka mai zafi da ciwo, kukan da ke fita tun daga cikin zuciyarshi, yake ratsa kwayar idanuwanshi.


Ishraq ya kasa ko kwakkwaran motsi, in banda kallon mutumin babu abin da yake yi, wani irin yanayi yake jin shi a cikinshi, wanda ba zai iya misalta shi ba.


Suna cikin haka Khalid ya shigo, ganin duk sun yi cirko-cirko ya sanya shi tambayar ko lafiya. Babu wanda ya kula shi a cikinsu. Hakan ya sanya shi neman wuri shi ma ya zauna yana zira ma sarautar Allah ido.


A zuciye Ishraq ya sake cin kwalar mutumin. "Idan ka kuskura ka yi min karya wallahi ka ji na rantse sai na nakasa ka. Ka fada min gaskiya."


Kuka sosai yake yi matashin, "Zan fada maka komai tun daga farko har karshe, sannan zan fada maka ko wa ya saka ni amma kafin nan, ina so ka saurare ni, kar ka katse ni har sai na kai aya."


Khalid dai bin su kawai yake yi da kallo, sai dai yana tunanin kamar ya san fuskar mutumin ko ma a ina ne.


"Sunana Ibrahim, ni dan asalin garin Katsina ne a wata karamar hukuma Dutsi. Mun tashi cikin rashin gata ni da kanwata daya mai suna Zainab. Mahaifinmu ya rasu sai mahaifiyarmu da ke fama da ciwon suga..."


Da hannu Ishraq ya dakatar da shi. Sannan ya ce "Duk waye ya tambaye ka wadannan? Ka fada min wa ya turo ka gidana? Kuma wa ya ce ka yi wa Mahboobah wancan sharrin?"


Sai a sannan Khalid ya fara fahimtar inda zancen nasu ya dosa, da kuma inda ya san fuskar mutumin wato a cikin wayar Ishraq sadda ya gwada mishi video. Ya sauke ajiyar zuciya yana fuskantar Ishraq, "Likita ba a haka. Kamar yadda ya roke ka kar ka dakatar da shi to kamata ya yi ka bar shi ya fara tun daga farko har karshe."


A kufule Ishraq din yake kallon Khalid da ke jinjina mishi kai, bai ce komai ba sai kallon mutumin ya yi alamun ya ci gaba da maganar.


End if chapter


Hausawa suka ce komai nisan jifa kasa zai fado. Kamar yadda komai tsawon dare gari zai waye. Ita karya fure take ba ta ya'ya, haka kuma raminta kurarre ne.


Kamar yadda mutumin ya lailaya karairayi ya shirga ma Ishraq, haka kuma ya zo da dukkanin zuciyarshi domin warware mishi gaskiyar lamarin.


Ko yaya za a kare?

Daga ina wannan kasurgumin kazafin yake?

Wa ya sanya shi aikatawa?


Dukkan amsoshin suna cikin shafin gaba in shaa Allahu.


#BKF

#NWA

#MA'ISH

#ANATARE


Princess Amrah

RAZ 2"Mun dawo garin Kaduna da zama ne saboda a nan kaninta yake zaune da iyalinshi, kuma ba mu da wani makusanci sai shi, gararin rayuwar da muke cikinsa ya sanya shi cewa mu dawo inda yake, duk da shi din ma ba wani karfi gare shi ba sai dai rufin asiri, yana sana'ar faci a Unguwan Mu'azu. A nan muka ci gaba da rayuwa cikin rufin asiri tare da iyalinshi. Kwatsam wata rana a wurin sana'arshi wata tirela ta yi kanshi, ta murje shi, a take ya mutu ko minti guda bai kara ba. Mutuwar Kawu Dahiru ba karamin jijjiga mu ta yi ba. Kafin ma a kai ga jinginar da bayanmu da muka yi a jikinshi, shi din mutumin kirki ne mai kyautatawa ga dukkan kowa. Mun yi kuka sosai inda a karshe dole muka hakura, tun da dai ba mu isa mu ja da ikon Allah ba.


Rayuwa ta ci mana gaba cikin wahala. Abincin da za mu ci ma da kyar muke samu. Wannan dalilin ne ya sa na tashi tsaye domin nema mana madafa, sai dai abun ya faskara domin kuwa na rasa yadda zan yi, duk inda na je neman aiki ba na samu, sai a karshe da kyar ba samu a wani gareji. Ban iya komai ba amma daga zuwa Allah Ya taimake ni na iya, Oganmu ya dauki soyayya ya dora a kaina saboda yadda nake da rikon gaskiya. Ashe wadanda muke tare da su duk suna jin ciwon yadda suka jima a wurin amma Oga Bash bai yarda da su ba kamar yadda ni ya yarda da ni. Ban san abin da suke aikatawa ba, sai dai Rabe ya yi alkawarin neman mafita a ranar da Oga Bash ya ba ni kyautar wasu kudi.+


'Wallahi ba ka isa ba daga zuwa ka fi mu daukaka. Dole ma in nemo mafita.'


Ban zaci cewa har cikin zuciyar Rabe ya yi maganar ba. Kwana biyu bayan haka Oga Bash ya yi mini kaca-kaca bayan ya sallame ni cewa a cikin kayana ya samu kwayoyi da kayan maye, sannan an sace mishi kudi a ranar kuma ya gan su a cikin kayan nawa.


Hankalina ya tashi, saboda ba ni da wani sauran galihu kuma. Cikin damuwa na koma gida, sai dai ina zuwa na tarar jikin Mama ya yi tsanani sosai. Da dan sauran canjina na ce Zainab ta kama ta mu tafi asibiti. Bayan ta dauko katinta na asibitin muka fito, a daidaita sahu muka tsayar ya kai mu asibiti.


Sosai likita ya yi ta mana fada, saboda duk wasu abinciccika da aka hana masu ciwon suga su ci ita Mama cin su take yi. Suganta ya yi wani irin hawa na ban mamaki. Aka rubuta mata magunguna likitan ya ce in gaggauta in siyo su idan ba haka ba kuma komai zai iya faruwa, za mu iya rasa ta ma.


Hankalina ya tashi na fita da takardar maganin ina neman mafita. Pharmacy din cikin asibitin na je, ko da aka yi total naira dubu goma sha bakwai ne kudin maganin. Ga kuma kudin daki dubu uku da dari biyar.


Hannuna na dora a kai, kamar zan zaunce, kamar in kurma ihu ko zan samu sassauci. Takardar na karba na bar wurin, na fita daga asibitin ma duka ina neman mafita.


Wata mota na gani daga gefen titin, saurayi da budurwa tsaye sun bude gaban motar da alama lalace musu ta yi. Ganin suna da bukatar taimako ya sanya na musu sallama muka gaisa. Na tambaya ko motar ta lalace mutumin ya fada min eh, amma ya kira mai gyara zai zo.


'Ko za ka bari in gwada sa'ata, ni ma aikina kenan. Ina son hada kudi ne mahaifiyata ce kwance a asibiti kuma kudin maganin da yawa. Ga shi jikin nata ya tsananta.'


Babu gardama mutumin ya ba ni makullin motar. Cikin minti kadan na gano matsalarta sai dai ba ni da kayan gyara.


Abin da ya mutu a motar na fada mishi ya ce bari ya je ya dawo. Ya bar mu tsaye a wurin ni da budurwar.


Kamar daga sama na ji tana min magana, wai tana neman taimakona idan zan iya yi mata aiki za ta siya min magungunan ko nawa ne.


Daga nan ta nemi in aikata abin da na yi a gidanka. Ta ce kafin nan za ta yi bincike a kan yanayin al'amurran gidanka. Daga farko na ji ba zan iya ba, sai dai na amince ne saboda rashin tudun dafawa. Idan har ban yi ba babu inda zan samu wadannan makudan kudaden.


STORY CONTINUES BELOW

Sai da ta bincika ta tabbatar da mai aikinku ba ta nan, ta shirya min komai da yadda zan yi abun, ta kuma gargade ni kan cewa komai rintsi kar in bari asirina ya tonu. Idan kuma har ya tonu kar in bari sunanta ya fito, matukar ya fito to a kurkuku zan karisa rayuwata saboda ita tana da mai fitar da ita.


Wannan shi ne gaskiyar abin da ya faru. Wallahi babu abin da Mahboobah ta sani. Ba ta san hawa ba ba ta san sauka ba muka kirkira mata."


Innalillahi wa inna ilaihi raji'un suka maimaitawa su duka biyun. Wannan labarin sosai ya yi kama da kirkirarrun labaran da ake rubutawa a littafi ko kuma film.

"Wace ce wannan ta sanya ka...kuma me ya sa yanzu ka zo yin confessing?" Khalid ya fada cikin karfin hali yana kallon shi.


"Sunanta Bilkeesu Imran..."


"What?" Ishraq ya gaggauta tambaya yana mikewa tsaye.


"Tabbas sunanta ke nan. Abin da ya sa na zo na tona ma kaina asiri, tun bayan da abun nan ya faru ban kara samun kwanciyar hankali ba. Dalilin da ya sanya ni aikata abun ciwon mahaifiyata ne...mahaifiyar tawa ta rasu. An yi ma kanwata Zainab fyade. Gidan Kawu Dahiru da muke ciki sun tashe mu wai gyaran gidansu za su yi saboda hakkin magadanshi ne. Bala'iku kala-kala suka rinka hawa kaina. Tun daga nan na gane cewa sharrin da na aikata ne yake bibiyata. Na je na samu malamin islamiyyar wani masallaci da nake sallah a ciki. Na labarta mishi dukkan abubuwan da na aikata. Shi ne ya ba ni shawarar neman ka duk inda kake in ba ka hakuri, in wanke Mahboobah, sannan in nemi gafararta. Matukar ban aikata wannan ba to yanzu na fara ganin tashin hankali. Ya ce Allah ma Ya so ni da rahma ne tunda hakan take ta kasancewa. Don haka in yi amfani da wannan damar in fadi gaskiyar abin da ya faru."


Kai Khalid ya dafe, yana jinjina kaidi da sharri irin na wadansu matan. A wani bare na zuciyarshi kuma tausayin Mahboobah ne ya kama shi, Yana tsananin jin dadin bayyanuwar gaskiyar lamarin.


"Ka yafe min kuma don Allah ka fada min inda zan gano Mahboobah ita ma in roki gafararta ko zan samu salama a cikin rayuwata."


Duk sanyin ACn da ke ratsa dakin amma bai hana Ishraq keta gumi ba. Zuciyarshi sai tafarfasa take yi, yana rasa abin da zai aikata.


"Ka tafka babban kuskure Ibrahim. Kodayake dai ka gane ka yi kuskuren, babu alamun maimaitawa. Sai fatan Allah Ya kara tsarkake mana zukatanmu." Khalid ne ya yi wannan maganar yana tsananin jin tausayinshi.


"Mahboobah tana makaranta, sai dai ko in kira maka ita a waya ka ba ta hakurin."


Ya share hawayenshi mutumin. "Na fi son haduwa da ita a zahiri in yi mata bayanin komai, don wannan ba zance ba ne na waya. Ka kwatanta min gidansu zan je, idan ma ba ta nan zan iya zuwa har makarantar tasu."


Ishraq dai tamkar gunki haka yake zaune, kwakkwaran motsi ma ya kasa yin shi in banda sharce gumin goshinshi babu abin da yake yi.


Biro Khalid din ya jawo da jotter a kan table din Ishraq, ya rubuta mishi address din gidan su Mahboobah. Har ya mika mishi sai kuma ya canja shawara. Kallon Ishraq din ya yi, ya ce "Tashi za ka yi mu je gidan nasu tare, idan ma ba ta nan mu warware wa mahaifiyarta komai."


Cikin mamaki Ishraq ya kalli Khalid "Mu je ina? Ba zan iya ba wallahi. How can I face Mahboobah? Ta ina zan fara? Ba zan iya ba Khalid ku je kawai on my behalf."


Kafadarshi Khalid din ya dafa. Cikin kwantar mishi da hankali ya ce "Mahboobah na da hankali, kuma a wurin iyayenta ta gado shi. Daga ita har mahaifiyarta za su fahimce ka Ishraq. Ba zai yiwu ba ne mu je mu kadai, dole sai tare da kai."


STORY CONTINUES BELOW

Bai da yadda zai yi, duk da ranshi ba ya so amma a haka ya mike jiki babu kwari, suka fita tare daga Office din ya ba Kamal umurnin rufewa.


A kan hanya suka tsaya yin sallar la'asar. Daga nan suka wuce gidan su Mahboobah.


Zaune suke ita da Ameerah, tana ma Ameerar yankan akaifa sai surutu take zuba mata.


"Ammi Ameer ya zo sadda ba kya nan amma bai kwana ba."


"To ya kyauta sosai."


"Ammi bai fa kwana ba na ce miki."


"To ai duk da hakan dai ya kyauta sosai Ameerah ya yi zumunci."


"To Ammi ni ma ai ina son zuwa gidansu."


"Na hana ki ne?"


"Daddyna ne bai kai ni ba."


"To ai sai ki kira shi ya kai ki."


"Ki kira min shi to."


"Ba zan kira ba."


"Please Ammi..."


Dago kai Mahboobah ta yi ta mata kallon da dolenta ta shiga taitayinta. Sallamar su Khalid ce ta sanya Mahboobah sake dago kanta tana amsa sallamar da murmushi a saman fuskarta. Sai dai tana ganin biye da shi Ishraq ne ta sauya zuwa daure fuska. Ba ta ko sake kallon su ba balle ta ga mutumin da ke biye da su a baya.


Da gudu Ameerah ta mike tana fadawa bisa jikin Ishraq. "Kar ki karya ni Ameerah." Ya fada yana cilla ta sama.

"Ai ba ni da nauyi Daddyna."


Khalid ya kamo hannunta yana cewa "Wato Daddynki kadai kika sani ko Ameerah?"


Kan jikinshi ta koma tana karbar wayarshi. Da ma ta saba daga sun hadu da Khalid wayarshi yake ba ta, akwai game din da Junior ke yi ita ma tana son shi sosai.


"Sannunku da zuwa." Kadai Mahboobah ta fada tana mikewa za ta bar falon. "Ameerah je ki kira musu Mommy ki ce ta yi baki. Kar kuma ki shigo min daki kaina na ciwo."


Tana neman tafiya Khalid ya dakatar da ita. "Ba wurin Mommy kadai muka zo ba Boobah. Wurin ku dukka muka zo."


Wani irin takaici ne ya kamata, ba tare da ta ce komai ba ta koma ta zauna tana ci gaba da latsar wayarta.


Babu jimawa Mommy ta fito sanye da hijabi tunda ta gama la'asar tana zaune a kafet tana adhkaar din yamma sai da Ameerah ta kira ta.


Zama ta yi tana yi musu sannu da zuwa fuskarta a sake. Suka gaishe ta ta amsa. "Boobah ya ba ki kawo musu ko ruwa ba?"


Mikewa ta yi tana nufar kitchen. Ruwa da lemu ta jero a bisa tray sannan ta dora cups guda uku ta dawo falon. A kan center table ta ajje haushi duk ya kama ta. So take ta bar musu dakin amma babu hali, Khalid ya tsayar da ita.


"Mommy na san za ki yi mamakin zuwan mu mu uku. Wani boyayyen al'amari ne Allah Ya yi naShi ikon a yau. Gaskiyar da ke nannade ce ta warware. Allah Ya kawo karshen kazafin da aka kulla wa Mahboobah."


Kallon shi suka yi da Mommy da Mahboobah suna so ya warware musu zancen. Ya ci gaba da cewa


"Wannan bawan Allah'n na zaune, da shi ne aka kulla wa Mahboobah sharri, kuma shi da kanshi ya zo ya warware mana..." ya kwashe komai da ya faru ya fada musu, sannan a karshe Ibrahim da kanshi ya maimaita musu, yana neman gafarar Mahboobah.


"Idan har ba ki yafe min ba na sani ba zan taba samun rabauta ba saboda ba karamin abu na aikata miki ba. Don Allah ba don ni ba ki yafe min, na gane kuskurena ba zan maimaita ba da izinin Allah."


Kuka take sosai, kuka take da zuciya da fuskarta. Wani tsohon tabo ne wanda ya jima da warkewa aka tayar mata. Mommy kanta hawaye take yi, hawaye masu zafi. Wannan son zuciya har ina. Lamarin mutane akwai ban mamaki a cikinsa. Ba ta san mai baiwar Allah Mahboobah ta tsare ma wadda suka ji an ambata da Bilkeesu ba.


"Ku yi hakuri duk ku duka Mommy. Idan Allah Ya riga da Ya rubuta abu to babu makawa dole sai ya faru. Ku dauki wannan a matsayin kaddarar Mahboobah."


"Haka ne Khalid." Mommy ta fada tana share kwallarta. "Amma dai an zalunci Boobah. An dankara mata bakin fenti mai wahalar wankuwa."


Wannan maganar ce ta Mommy ta kara ingiza Mahboobah, komai da ya faru a wancan lokacin ne ke dawo mata. Ta hau tariyar bakaken kalaman da Ishraq ya rinka jifarta da su. Ya kira ta da kalma mafi muni wadda tunda take a rayuwarta ba a taba jifarta da ko mai kama da ita ba. Ta runtse idonta, hawaye na kara saukowa. Ta bude su a fuskar Ishraq, a cikin ido take kallon shi, a cikin ido take aika mishi da sakon tsana da kiyayyarshi. Kafin ta mike a saman kafafuwanta, ta isa gare shi, cikin dakiya ta fara magana,


"Na gode ma Allah da Ya sa soyayyarka ba ta zama ajalina ba, zananniyar kaddarar aurenka ba za ta taba goguwa ba da tuni na share ta daga cikin babin rayuwata. Na yi da na sani, sosai na yi nadamar kasa fin karfin zuciyata har na aure ka Ishraq." Kuka ke son sake zo mata, sai dai yaki take yi da shi, ko kadan ba ta son sake zubar da kwalla a gabanshi, musamman yanzu da take son amayar mishi da dad'add'un maganganun da suka jima suna ci mata rai.


"Godiya ta tabbata ga Ubangijin da Ya shimfida soyayya a zukatan 'yan-adam. Sannan Ya shimfida kiyayya a tsakaninsu. Kamar yadda na nemi haukata kaina ta silar soyayyarka Ishraq, ina son tabbatar maka da cewa na tsane ka a yanzu, ba na kaunarka. Ina kara godiya ga Allah da Ya bayyana gaskiya, kazafin da aka yi min, da kuma munanan kalamanka ba su yi silar mutuwata ba har sai da wannan ranar ta bayyana a gaban idanuwana. Ko a yanzu mutuwata ta zo ina maraba da ita, ina maraba da mutuwa Ishraq...!"


Tana neman ci gaba da magana, dole ta dakata sanadiyyar muguwar tsawar da Mommy ta daka mata.


End of chapter


Mai hakuri bai iya fushi ba. An kai Mahboobah kwano a yau dai ta samu damar amayar da damuwarta.


Su Mallam Ishraq tsit kake ji😂


Princess Amrah

RAZ 2

Post a Comment for "BAKUWAR FUSKA CHAPTER B"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...