Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ARZIQI RABO CHAPTER C KARSHE

ARZIQI RABO CHAPTER C KARSHE

- - Post a Comment

 ARZIQI RABO CHAPTER C KARSHE


Lokacin da ya dawo gida su Umma na falo yana jiyo su ita da Zainab,d'akinsa ya shiga ya zauna yana ta tunano Nasreen.+


      Se yanzu ya sake gane rashin kyautawar da yayi na rashin bata kulawar da ta wajaba a kansa.


  °°°

Se wajen maghrib daya fito zeje masjid Zainab ta ganshi.


     "Laa dama ka dawo gida".

      " Eh ai ban jima da dawowar ba". Ya amsa.


      "Masallaci zaka?" Ta tambaya.


      "Uhm". Ya amsa.


      " Toh seka dawo". Ta fad'a.


          Zainab bayan fitarsa ta shiga kitchen had'a abincin dare.


                   ***

  Reyhana tana d'aki hankalinta ya d'aga Sameer yazo Nigeria d'azu ya kirata ya fad'a mata.Yanzu bata da 'karyar da zata fad'a masa,bama shi kad'ai ba har Abba.Nasreen tuni tayi bacci ita kad'ai se juyi take ta kasa bacci tunani ya isheta.


       Saudat ce abokiyar shawara yanzu kuma dare yayi sede gobe,abunda ya fad'o mata a rai kenan.Dakyar ta samu ta iya yin bacci.


                     ***

      Washegari da safe bayan ya gama shirinsa ya fito falo ,Zainab ya tarar tayi shirin school da alama ma shi take jira.Shi ya mance ma da kaita school se yanzu ya tina.


       "Ina kwana yaya". Ta gaisheshi.


        " Lafiya lau". Ya amsa.


     'Kokari yayi ya kauda idonsa daga kallonta dan kwalliyarta tana masa 'kwarjini,sosai tayi mugun kyau.Doguwar riga blue tasa se rolling datai golden d'in mayafi ta sa'kala jakarta golden fuskarta tasha kwalliya ga maroon lipstick daya haskata.


      "Ka shiryo kenan".Umma ta fad'a sanda ta shigo falon.


        " Eh d'azu na shigo mu gaisa kuma kin koma bacci,ina kwana". Ya gaisheta.


       "Lafiya lau,bazaka karya ba?" Ta tambaya.


        "Eh se anjima". Ya amsa.


         " Toh sekun dawo"Ta fad'a.


          Yana ficewa tabi bayansa,a cikin ranta tana jin dad'i musamman da taga sunyi ango shi yasa blue d'in shadda.


        Cikin 'kan'kanin lokaci ya kaita kafin ta fita daga motar ya 'kara mata kud'in makaranta dukda ana bata daga gidansu.


•••


Yauma daga aiki be koma gida ba seya je school d'insu Nasreen,4pm lokacin yana tsaya a gate d'in yana tunanin yadda ze ganta.


      Da'kyar mey gadi ya barshi ya shiga wani daga cikin malamanne ya kira Nasreen tazo.


      "Kinsan wannan?" Suka tambayeta.


      Seda ta tsaya na d'an lokaci tukun tace "Eh".


      Wata daga cikin malaman tace " Ai gashi ma kamar su d'aya".


     Dama sun fito sallah basu koma ba dan haka ya kamo hannunta suka zauna daga wani bench a compound d'in makarantar.Ita de Nasreen tana jin d'ar-d'ar musamman idan ta tuna abinda Ummienta tace.


        "Nide ummiena ta hanani kula mutanen waje".Ta fad'a.


        " Kinmanta ni Uncle ne? Na kawo maki wannan ".Ya ciro mata Twix guda biyu daga aljihunsa.


        Aiko da sauri ta mi'ka hannu ta kar'be" Amma karka fad'a wa Ummiena kaji".Ta fad'a harda zaro ido.


       "Toh". Ya amsa tare da kad'a kai.


STORY CONTINUES BELOW

        "Karatu zaka koyamini wai?" Ta tambaya tana 'bare ledar.


        "Eh amma yanzu zaku shiga aji se anjima idan kun tashi ina waje ina jira".


        " Kai zaka kaini gida?"Ta tambaya.


        "A'a".


        " Dan Allah ka kaini gida  ,kullum kullum semun dad'e ake zuwa d'aukan mu".


       "Ai zanyi hira daku kafin a zo d'aukanku".


        Kai ta kad'a tana cigaba da shan chocolate d'inta.Ba jimawa ta koma aji,kamar yadda ya fad'a seda ya jira aka tashesu.


       Tana fitowa ta ganshi a bakin gate da gudu ta 'karasa inda yake taji dad'i ganin ya jira an tashesun kamar yadda ya fad'a mata.


     Kan mota tasa ya d'orata suma sauran yaran ma'kotan nasu haka kafin driver yazo.


    Littafinta ta bud'o se nuna masa H/W d'inta take da C/W,kusan seda suka 'kara 15min driver yazo da sauri yaran suka je,Nasreen ce 'karshe sam drivern be kula bama ya jasu suka tafi ita kuwa se waving bye take wa Ahmad.


       Ya kasa dena murmushi har ya isa gida,ya ji dad'in yadda Nasreen ta sake jiki dashi dama hakan yake so.


       Yana shiga gida be jima ba ya fito waje ,Zainab ya gani tana tahowa se sauri-sauri take daga gefenta kuwa wani saurayine da alama magana yake mata amma ta'ki sauraronsa.


      Har 'kofar gida yana biye da ita ,se a lokacin Zainab ta kula da Ahmad dake tsaye .Shikuwa yiyai kamar be gansu ba dan kauda kansa yayi gefe kamar besan da mutum a gurin ba.


       "Assalamu Alaykum". Yaji anyi masa sallama.


     Se lokacin ya lura Zainab har ta shige gida.


      Hannu ya mi'ka masa suka gaisa,ita kuwa Zainab data shiga gida wuf ta shige d'aki ko Umma bata ji sallamarta ba.


       Tana cikin sa'ke-sa'kenta a d'aki taji shigowar Ahmad, kunya taji ta lullu'beta tana jiyo muryarsa yana magana da Umma gudun karya fad'awa Umma yasa tayi sauri ta fito.


       " Zainab dama kin dawo?"Umma ta tambaya.


       "Eh yanzu ban jima ba ". Ta amsa.


      Tana had'a ido da Ahmad taga yayi mata murmushi ko ba'a fad'a ba tasan ma'anar murmushin,a take ta sauke kanta katsa.


       Umma ce ta koma d'aki tabarsu a tsaye gun,Zainab ma da sauri zata juya ya tsaida ita da fad'in.


     " An bani sa'ko".


      "Yaya sa'ko kuma?" Ta tambaya.


       "Eh ba'konki na waje shi yace na fad'a miki".


        " Mey?" Ta tambaya tana had'e gira.


        "Wai yana sonki". Ya amsa.


         Bata sake cewa komai ba ta koma d'aki ,kafin ya sake wata maganar yaga ta bace masa dan haka ya koma d'akinsa.


     A d'aki tunani ta shiga yi shin wace amsa Ahmad ya bashi? Ko zeji haushi? wata zuciyarce tace mata" Be damu ba".


      Jitai ba dad'i dan batai tsammanin haka ba,a tunaninta ze nuna kishi a fuskarsa sede taga ba hakan ba harda ma yimata murmushi.


  •••


    Koyaushe Ahmad inde ya dawo daga aiki seya biya school d'insu Nasreen, ta saba dashi sosai har home work yake koya mata idan taje gida ta fad'a musu se sike tunanin ko Uncle na school ne.


     Ta 'bangaren Sageer kuwa abu kullum gaba yake ko abinci yanzu be fiya ci ba a d'aki yake zama ya'ki fitowa ga wani mugun rama da yayi Mommy tun abun baya damunta yanzu ya soma ,kuma tambayar duniya baze fad'a mata ba Reyhana ma ta'ki fad'ar abinda ke damunsa.

   

     Reyhana kuwa data yiwa Saudat magana akan Sameer shawara ta bata akan ta cigaba da addu'a.


      Yau wasu 'kannen Umma  banda mahaifiyar Zainab suka zo daga Zaria,sanda suka zo Ahmad baya nan se Zainab yau bata da lectures.


      Tunda take da Ahmad basi ta'ba maganar Reyhana ko Nasreen da ita ba,yau tana jinsu Sister's d'in Umma suna hirar zasi je gidansu Reyhana suga Nasreen.


     Tana daga d'aki amma kunnanta yana kwashewa,ita jitai tsoro ya shigeta kada ace fa Ahmad ya dawo da Reyhana.


       Umma tana kallo suka fita wajen 4pm,hadda yi mata siyayyar kayan biscuit.


     Sanda suka shiga Walida suka tarar a falo, ita taje ta fad'awa Mommy da tana d'akinta Anty Asma'u tazo.


       Da farko Mommy bata gane su ba seda sukai bayani.Anty Asma'u tasa Walida ta kira da tana d'akin Mommy.


                    °°°

        Ahmad daga aiki ya wuce wajen Nasreen ,yana zuwa aka tashesu.Kamar koyaushe tana ganinsa ta ruga da gudu ta d'ale shi.


      "Uncle ina chocolate d'ina?"


       "Gata".Ya d'akko a aljihunsa.


        Tana tsalle ta kar'be suma sauran abokan tafiyarta ya basu nasu.


°°°

  Reyhana datai waya da driver yake fad'a mata yana kwance baida lafiya dan haka daga gidan Saudat tayi makarantarsu Nasreen.


       Daga gefen gate tai parking ta fito ,'yan tsirarin student dake wajen ta kalla ko zata ga Nasreen.


       Daga can nesa ta hango Nasreen d'are-d'are a kan mota.Mutum taga tsaye a kusada Nasreen amma kuma ya juya baya.


     'Karasawa tayi har inda suke,seda ta 'karasa kusa tukun Nasreen ta ganta.


      " Ummie!!!"Ta kira sunanta da 'karfi.


      Ahmad daya ji ta 'kwala kira ta ambaci Ummie hakan ya tabbatar masa Reyhana ce.Cak ya tsaya ya kasa motsi balle juyowa.


     Da gudu ta 'karaso inda Reyhana take ta rungumeta.


     "Yau da kanki kika zo d'aukanmu?" Ta tambaya.


     "Eh". Reyhana ta amsa.


     " Ummie kinga Uncle".Nasreen ta fad'a tana nuna inda yake.


       Se lokacin Reyhana ta dawo da kallonta kansa.


      "Uncle kaga Ummiena". Nasreen ta fad'a.


      Ya rasa mey zeyi ,wata zuciyar tana cewa kar ya waigo ? "Toh idan ma be waigo ba ya zeyi baida choice dole ta ganshi".Ya fad'a.


     A sanyaye ya juyo idanunsa suka sauka kan Reyhana, wani irin blinking ido tayi tana so ta tantance gaske ko mafarki.


       Suman tsaye tayi ta kasa ko motsi ganin ba mafarki take ba,duk cikinsu kowa ya kasa magana kuma basu dena kallon juna ba...1

Duk cikinsu kowa ya kasa fad'ar koda 'a' ce ,daga cikin zuciyarsu kuwa tambayoyine iri-iri musamman Reyhana.

     Kamar 'kiftawar ido yaga taja hannun Nasreen sun shige mota,'ki'kam yayi be motsa ko ina ba kamar wani gunki.
   
       Nasreen cikin rashin nuna damuwa tayi ta waving bye ,cikin 'kan'kanin lokaci yaga wayam.Se a lokacin yayi 'kwa'kwarar 'kifta ido.

     "Meyasa ma na barta ta tafi?" Ya fad'a  a ransa.

      "Am stupid!" Ya daki saman motar.+

       Gwiwa  ba 'kwari ya shige mota sannan ya bar gurin

       Reyhana da ikon Allah ta iya tu'kin motar dan hankalinta baya wajen,Nasreen da take mata hira ko sauraronta bayi take ba.Suna shiga gida taga Anty Asma'u da Mommy se maganganu suke suna kumfar baki.
  
        "Banda rainin hankali kai tsaye su sunzo ganin 'yarsu  bako tunani". Cewar Anty Asma'u.

         "Nasreen jeki d'aki gani ina zuwa". Reyhana ta fad'a da'kyar dan bakinta yayi nauyi.

      Ba musu ta wuce sama,su Mommy kuma lokacin sun bar hayaniyar da suke." Mommy meya faru?" Reyhana ta tambaya.

     "Yanzunnan 'yan uwan Ahmad suka fita ,saboda tsabar rashin kunya irin tasu wai gurin Nasreen suka zo harda wani tarkacen ledarsu sunan sunyo mata abin arzi'ki ca akai musu bata ci kowa irinsu neh mitsiyaci!"
    "Kuyi shekara shida baku waiwayi yarinya ba shine seyau ku kwaso tarikican 'kafarku kuce kunzo ganin yarinya". Anty Asma'u ta fad'a.

      Reyhana ta kasa cewa komai illa zame jiki datai ta haye sama dan kanta yana shirin bugawa ta rasa da wanne zata ji,ganin Ahmad koh zuwan wa'acen?

       Da'kyar 'kafafuwanta suka kaita zuwa d'akinta,a sanyaye ta zauna kan gadon Nasreen da har ta 'kwa'be uniform d'inta ,'karasowa tayi inda Reyhana take.

    " Ummie ki d'akko min kayan da zan saka".

     Sam hankalinta bayan gurun ta tafi nisan tunanin seda taji tana jijjiga mata kafad'a ta dawo hankalinta.

      "Ina zuwa ".Ta fad'a tare da mi'kewa ta bud'e wardrobe ta ciro mata.Nasreen tana gama sa kayan ta fita.

     "Shine Uncle da take magana? Meyasa se yanzu? may be aure yayi ya haifi wasu 'ya'yan shine ya tuna da Nasreen koh matarsa tasa yazo wajen 'yarsa ? Naughty brain nashi be fad'a masa abinda ya kamata ba seda.. No it can't be..what if yayi auren ai it's possible but...Ohh " Abinda yake ta mata yawa a 'kwakwalwarta kenan ,se yanzu kuma abunda su Mommy suka fad'a mata ya dawo mata.

°°°

Ahmad yana zuwa gida ya shige d'akinsa ya rufo 'kofa ,se yanzu yake daya sani.Tunani ya shiga yi koh ya kira ta a waya wata zuciyar tace"Kana gani koh magana bata had'aku ba a fili ma kenan balle waya".

     "Reyhana am sorry!" Ya fad'a a fili cikeda nadama kamar tana kusa dashi.

      Yana wannan tunane-tunanen har maghrib tayi be samu zuwa masjid bama se a gida yayi sallahr,se bayan ya idar da sallah tukun ya fita zuwa parlor.

         Umma tana zaune kujera fuskarta ba walwala shi be kawo komai a ransa bama,opposite da kujerarta ya zauna.
       Tunda ta amsa sallamarsa bata sake magana ba se yanzu.

       "Ahmad meyasa kayi min 'karya?" Ta tambaya.

       A razane ya d'ago da kai ya kalli Umma se lokacin ya kula da yanayinta.

     "Abinda kayi ka kyauta kenan? Ashe duk zaman da akai iya tsahon lokacinnan kusan shekara biyu kenan ni gani ka maida ni bansan mey nake ba koh? Ka janyo wa iyayenka wula'kanci da cin mutunci yanzu wa gari ya waya?" Se lokacin ta tsaya da magana.

      Yanzunne ya gane mey ya faru,Aunty's nashi sunje gidansu ,finally Mommy ta fad'a musu 6yrs rabonsa daya taka 'kafa gidansu Reyhana.

       "Ya Allah ka taimakeni". Ya fad'a a zuciyarsa.

    Ya bud'e baki zeyi magana Umma ta katseshi.

      "Ina tunaninka da iliminka ? Ha'k'kin 'yarka dayake a kanka duk ka mance ba ruwanka haka kake kuma jin dad'in bacci ni gani ka d'auke ni shashasha ashe kallon wawiya wacce batasan abinda take ba kake min ban isa na fad'a maka abinda zakai ba kai, gaka ka girma ka zama banban mutum koh? mahaifiyarka za kaiwa 'karya".

       Umma a rayuwarta ba abinda ta tsana kamar ai mata 'karya,gata da mita kuma idan tayi fushi se ansha wuya ake shawo kanta.

     Duk wannan fad'an da tai masa Zainab tana daga d',aki tana jiyowa ,ji take kamar ita akai wa fad'an sosai tausayin Ahmad ya kamata.

      Yana so ya bata ha'kuri amma ga mamakinsa se gani yayi ta tashi ta bar masa parlorn.

     Jiyai duniyar tayi masa zafi ya rasa inda zesa kansa, tashi yayi ya fita daga d'akin yana jiyo sanda ta banko 'kofar d'akinta,d'akinsa ya koma ya rasa mafita yunwar dayake jima ya dena ,wayarsa ya d'auka ya kira Imran ya fad'a masa duk yanda ake ciki ,nan yake fad'a masa gobe zezo suyi magana.

                ***

     Mommy tana ganin Abba ya dawo ta fad'a masa abinda ya faru ,a gaban idonta seya nuna mata bega laifinsu ba amma a ransa ba haka bane.

     Yau dinner d'in boring dan daga Reyhana har  Sageer ba wanda ya hallara ba, Mommy ma haka d'aki ta shige. 
 
       12:44am sam ta kasa bacci ga wani zafi da idanuwanta keyi ,tunanin  d'azu ta shiga yi fuskar Ahmad ta fara yimata yawo a kai.Canji kad'an taga yayi mata ,saje dayake kwance a fuskarsa se d'an murjewa daya 'karayi ga haske daya 'karu a  fatarshi.

      Bata ankara ba taji danshi a fuskarta ,ita kanta batasan dalilin kukan ba ,da tayi tunanin zata iya mance da rayuwar da sukai da Ahmad amma a yanzun taga ba haka bane komai ya dawo sabo.

      Ganin kukan baze mata magani ba ta tashi ta d'auro alwala ta tada sallah.

•••

  Washegari Saturday Nasreen ba school da wuri ta farka ta hana Reyhana komawa bacci gashi idanuwanta sunyi mata nauyi.

      "Ummie mije kitchen muyi indomie tare". Nasreen ta fad'a.

         " Nasreen please mana ga Aunty Walida ". Cewar Reyhana a kasalance.

          " Ai ita duka na zata yi idan na taso ta". Ta fad'a.

      Haka dole ta ha 'kura da baccin suka shiga kitchen.Labarin Uncle ta fara bata,chocolates dayake suyo mata.

      "Nasreen tun yaushe yake zuwa makarantar ku?"

      "Kullum kullum ya dad'e ,ya d'orani a lilo ya siyamin chocolate". Nasreen ta fad'a tana nishad'i abinta.

      Reyhana tunani ta tsindima ta mance da frying pan da ta d'ora a cooker gas ,seda taji 'kauri ta tuna da sauri ta dan'ki handle d'in hannunta ya goje ta 'kona d'anyatsa.

      " Arghh!" Ta saki 'kara.

     Takaici biyu ya isheta batasan sanda ta tsuguna ta soma kuka ba.

  °°°

    Zainab tun da ta tashi ta kasa fitowa,daga Umma har Ahmad tsoron had'uwa dasu take, tana tsoro kar ya huce a kanta,Umma kuma batasan ko har yanzu bata dena fishi ba akan abinda akai wa 'kannenta ba.

       Tana wannan batun ne sega Umma ta shigo d'akinta.Tana ganin shigowar Umma tayi sauri ta mi'ke daga kwance,cikin rissinawa ta gaisheta.

     Umma fuskarta a sake ta amsa tare da fad'in."Yau ba makaranta kenan".

      "Eh".Ta amsa.

       " Dama naji ki shiru nace bari na duba ki".Umma ta fad'a.

       "Uhm yanzu dama nake son fitowa".Zainab ta fad'a fad'a tana sosa kai.

        Umma bata dad'e da fita daga d'akin ba Zainab ta fita itama,kamar koyaushe ta shiga kitchen taya ta had'a breakfast sede ta raba hankalinta biyu tana tunanin fitowar Ahmad.

•••

Mommy a tsugune ta tarar da Reyhana a kitchen d'in se sharar hawaye take,Nasreen tana daga gefe tana kallon Ummienta na kuka fuskarta itama kamar mey shirin yin kukan.

      " Reyhana meye haka? Menene?"Mommy ta tambaya.

      Shiru tayi bata ce komai ba sede yanzun tayi dena kuka,tashi tayi tsaye a daddafe tana share hawayen .

      "Kukan na meye? Mutum da giramansa yasa kuka ga yarinya babarta na kuka kince itama tayi kenan". Mommy ta fad'a.+

     Kai kawai ta girgiza ba tare da tace komai ba taja hannun Nasreen ta fita zuwa d'aki.Tana zuwa ta tarar da missed call d'in Sameer bata jin zata iya calling back dan a yanzu bata son magana da kowa.

     Nasreen d'in ma kayan wasanta ta d'akko mata ta bata,ita kuwa kwantawa tayi kawai tana 'ko'karin mancewa da damuwar dake ranta.

                   ***
     Umma suna zaune a parlor Ahmad ya shigo,rissinawa yayi ya gaisheda ita ba tare da yana tsammanin amsarta ba.

    " Lafiya lau". Ta amsa ba tare da tana kallonsa ba.

     Zainab ma 'karfin hali tayi ta gaisheshi,yana amsata ya koma d'aki koh takan abinci be biba.

       Wajajen 11:15am sega Imran yazo,yana gaisawa da Umma ya komo wajen Ahmad.

       "Ya ake ciki neh yanzu?" Imaran ya tamabaya.

       "Ya kwa ake ciki ganinan na rasa abinda zanyi". Ahmad ya fad'a.

       " Yanzu ka samu ka kira su Aunty's nakan ba basu ha'kuri atleast za'a samu relief and maganar 'boye-'boyennan bashi bane ka rife ido kawai kaje gidansu ayi magana frankly kuskure ne an riga da anyi ba abinda ze chanja, hakane?"

        Kai Ahmad ya gid'a alamar "Eh".

        " Yaushe toh zakan?" Ya tambaya.

       "Today". Ahmad ya amsa.

         " Good".

    Ahmad bayan tafiyar Imaran ya kira Aunties nashi d'aya bayan d'aya ya basu ha'kuri.

     Da kansa ya shiga kitchen ya zuba abinci yaci ya komo d'aki.

    °°°
Se 11:16am Reyhana ta farka daga baccin dan bata san lokacin data soma ba.Yanzu taji d'an ded ba kamar d'azu ba ,seda tayi wanka ta shirya tukun ta sakko 'kasa.Ba kowa a parlor, kitchen ta shiga ta zuba abinci tukun ta dawo parlor ta zauna.

      Mommy da ta sakko ta ganta seda ta sake tambayarta dalilin kukanta amma ta'ki fad'a dan haka ta rabu da ita.

      Yau Nasreen dama ta samu se wasanninta take dukda bame taya ta kowa yana harkarsa.Walida tana d'akinta Ikram kuwa ta fita Bassam ma yana d'aki,Sageer da yanzu yama dena fitowa parlor balle cin abinci a table.

STORY CONTINUES BELOW
      Se bayan ta koma d'aki ta duba wayarta taga message na Sameer,numbernsa tayi dialing ba jimawa yai picking.

        "Assalamu Alaykum". Yayi sallama.

          " Waalaikumussalam".Ta amsa murya a sha'ke.

      "Are you ok?" Ya tambaya.

      "Yes". Ta amsa a ta'kaice.

      " D'azu na kira koh kina bacci ne?"

       "Eh". Ta amsa.

       " Ok".Ya fad'a.

       "Reyhana". Ya kira sunanta.

     Daga yadda ya kira sunanta ta san maganar da zeyi.

      "Reyhana mun gama karatun ,ga school 'yarmu ta soma zuwa, what are we waiting for?"Ya tambaya cikin sassanyar murya.

    Shiru tayi bata ce komai ba har kusan 2min.

     " Uhm? say something ".Cewar Sameer.

      " Reyhana this is the right time,shekaru suna ja fa ko so kike na tsofe?"Ya 'kare maganar da dariya kad'an.

      "Kowa fa ke yake jira,family sun 'kagu suga in-law d'insu kullum se sin tambayake koh bakyason barin gida neh? don't worry Nasreen na tare dake and you know am always by your side".

      " Sameer please ina so a yanzun ka bani dama nayi shawara".Reyhana ta fad'a.

      "Karki damu inde shawara ce ni zanfi kowa jin dad'in hakan ,na baki dama kiyi shawara Reyhana duk abinda kike so shi nake so". Sameer ya fad'a ba tare da alamar ya damu ba.

      " Nagode".Ta fad'a.

       "Is OK"

       Hira kad'an suka ta'ba sannan sukai sallama, wayar ta dire gefe tana tunanin abin yi.

    •••

Ahmad seda ya bari yayi sallar Asr tukun yayi shirin zuwa gidan su Reyhana, ba tare da ya sanar da Umma ba ya fita dan yasan ba sauraransa zata yi ba.

     Yana hanya a zuciyarsa addu'a yake tayi Allah yasa komai yazo masa da sau'ki ,gashi yanzun baida buri irin Reyhana tayi masa magana ko yaji sa'ida.

     Bayan yayi parking seda yayi kusan 5min tukun ya fito daga motar,a sanyaye ya 'karasa gate d'in,yana shirin tura 'kofar gate d'in sega motar Abba nan ta kunno kai.

      Abba da farko be gane Ahmad ba seda ya fito daga motar ya kula.Cikin rissinawa kansa a sunkuye ya tsuguna ya gaida Abba.

      "Ahmad ne a gidannan" Cewar Abba bayan ya amsa.

      Shiru yayi Ahmad bece komai ba yana jiran Abba ya sake wani maganar."Mu shiga daga ciki koh".Abba ya fad'a.

      Cikin gidan suka 'karasa Ahmad yana biye a bayan Abba.Bassam ya kira ya shigo masa da motar.Parlorn ba'kinsa Abba ya wuce da Ahmad.

      Bassam bayan ya koma ciki yaje ya tsaiguntawa Mommy,tana daga kwance amma seda ta mi'ke zaune tana mamaki.

       "Yanzun yana ina?" Ta tambaya.

       "Abba ya shigar dashi parlonsa". Ya amsa.

       " Jeka kira min yayarku". Ta fad'a.

       A d'an 'kan'kanin lokaci sega Reyhana ta shigo d'akin Mommyn.

      "Reyhana kinji wani abun mamaki?" Cewar Mommy
   
        "Mey?" Ta tambaya.

STORY CONTINUES BELOW
        "Yanzunnan Bassam yake fad'a mini Ahmad wai yazo ,yanzu haka yana parlorn Abbanku".

      Reyhana bata wani yi mamaki sosai ba dan tasan za'ai haka.

       " Toh wajen Abban yazo ai"Ta fad'a.

        "Ehyyi yasan ba saurararshi zan ba". Mommy ta fad'a.

        " Ina Nasreen?"Reyhana ta tambaya.

        "Au kai masa ita zaki?"Cewar  Mommy.

         " A'a ya za'ai na kaita gurinsa ,ban ganta bane a d'akin". Reyhana ta fad'a.

       °°°
"Ahmad ya akai haka shekaru 6 baka waiwayi  yarinyarnan  ba?" Abba ya tambaya.

      Labari Ahmad ya shiga bashi duk yadda akai,daga 'karshe ya bashi ha'kuri.

     Abba ba d'an zafi bane dama saboda haka ya ha'kura da laifin da yayi na 'kin zuwa sanda ya kamata.

     Abba da kansa ya kira Mommy da Reyhana ya fad'a masu komai a gaban Ahmad, itan ma ha'kuri ya bata sosai dukda yasan hakan baze sa ta dena jin haushinsa ba amma shi a yanzu ba wannan ce damuwarsa ba ,bashi da abinda ya wuce Reyhana ta kula shi.

     Tun sanda ta shigo naki ta'ki bari su had'a ido dashi tana jin idanunsa a kanta.

   Abba da aka kirashi a waya ya tashi ya bar parlorn Mommy ma tashi tayi ta fice ta bar Reyhana.

      "Reyhana". Ya kira sunanta a sanyaye.

      Banza tayi dashi batace komai ba.

     " Please talk to me,baki yarda da abinda Abba ya fad'a bane ? nasan ban kyauta ba shiyasa nake so na baki ha'kuri please ki saurareni".
       "Toh waya ce ba ha'kuri kazo bayarwa ba ? Ai nasani you don't have to tell me again,anji ka bada ha'kuri shikenan komai ya wuce then se kowa ya shiga harkarsa koh akwai wani abu daya rage baka fad'a ba a labarin naka?"
     Duk wannan maganar da take masa tana daga zaune.

     "We are not done mana atleast idan baza mi wani maganar ba ai semi ta Nasreen". Ahmad ya fad'a.

      " Really?"Ta fad'a cikeda rainin wayo.

      "Reyhana please". Ya fad'a.

       "Meyasa baza ka cigaba da plan naka ba na wasan 'buya scretely kake ganinta kamar yadda ka saba yi ,I think haka zefi maka at the end kuma sega sace ta". Reyhana tana gama fad'ar haka ta tashi da sauri ta fice.
 
      Baki wangalau ya bita da kallo " A yaushe yace ze sace ta? Yaushe Reyhana ta zama haka? " Abinda zuciyarsa ke tambaya kenan.

      Abba daya dawo d'akin ya tarar da Ahmad shi kad'ai,Ahmad ba tare da ya nuna damuwarsa ba yayi sallama da Abba ya fito.

     A harabar gidan ya tarar da Nasreen ta fito,tana ganinsa ta ruga a guje ta rungumeshi.

     "Yeyy! Uncle yazo gidan mu".
      " Uncle yaushe kazo?" Ta tambaya bayan ta d'ago kanta.

      "D'azu ban ganki bane". Ya fad'a.

      " Zaka zauna miyi wasa?" Ta tambaya.

    D'an murmushi Ahmad yayi kafin ya sunkuyo kad'an yace"Wani lokacin se miyi wasa ,fad'amin mey kike so na kawo miki ?"
     "Kayan wasa da chocolate se 'yatstsana irin na MBC 3". Ta fad'a.

      " Ok don't worry zan saya maki".

      Tsalle ta shigayi tana murna,bye bye tayi mishi tukun ta koma ciki shima ya tafi.Reyhana tana hangosu ta window tun d'azu har ya fita tukun ta dawo ta zauna.

         Waya ta d'auka ta kira Saudat ta fad'a mata abinda ke faruwa.

     "Toh ya zakiyi idan baki ha'kura ba?" Saudat ta tambaya.

      "Hanashi zuwa inda take zanyi ,yana sonta ya tafi ya barta". Cewar Reyhana.

     " Bakida gaskiya anan,kede taki dashi ku tsaya anan amma banda Nasreen babu yadda zaki 'yarsa ce yau ya nemi ya kar'beta ba yadda zaki". Saudat ta fad'a.

     "Cabb! Ya isa ya d'auken ita? Ya kaita ina d'in?" Ta tambaya.

    "Wajen matarsa". Ta amsa ta.

    " Ya dad'e beyi haka ba". Reyhana ta fad'a.

     "Kishi koh,kema kiyi naki auren ga Sameer bawan Allah har ya gaji da jira". Saudat ta fad'a.

     " Toh ke wayace maki ma yayi aure?"
      "Kefa kikace kina tunanin hakan". Saudat ta amsata.
    
      " Oho de". Reyhana ta fad'a.

      "Ke wai ya Sameer d'in har yanzu bani ce masa komai ba?"
       "Eh". Ta amssa.

       " Reyhana baki san alkairin dake tare dashi ba nide ina ganin kawai ki ha'kura ki aureshi mutmunninan yana sonki dayawa fah".

     "Naji ni karki isheni kuma am hanging". Reyhana ta fad'a.

     " Toh kide yi tunani ta Sameer ta Ah.." Bata bari ta 'kare ba ta katse wayar.
Abba zaunar da Mommy yayi a d'aki yana tuna mata abubuwan da tayi wa Ahmad a baya.
 
      "Kinga de yadda ikon Allah yake koh?"Cewar Abba.+

         Mommy shiru tayi bata ce komai ba tasan dama se ya dawo mata da zancen.

       "Shiyasa koyaushe nake fad'a maki ba wanda yasan gobe,yarannan ba irin abinda baki a kansa ba kika d'ora masa karan tsana ke seya saki 'yarki kuma bayan kindena ganin shi a gidanki nan ma ba'a tsira ba toh gashi ya dawo wajen 'yarsa".

     " Kai kuma dawo da zance baya duk abinda ya riga ya faru ai ya faru kuma meye amfanin tada zancen,maganar ya dawo ni be shafeni ba".Mommy ta fad'a cikeda borin kunya.

    "Tunatar dake nayi". Abba ya fad'a.

      "Wannan yaran fah baka ta'ba magana a kan halin dayake ciki ba". Mommy ta fad'a tana son chanja topic d'in.

    " Wa fah?" Abba ya tambaya yana neman 'karin bayani.

    "Sageer mana".Ta amsa.

     " Shi d'in kuma mey yake damunsa?"
      "Gashinan baya shiga cikin mutane abinci ma baka ganinsa ya ci aikin ma ni bansani ba koh baya zuwa".

     "Amma de ai shi ba yaro bane da za'a dinga jawo shi ana tambayarsa meke damunsa". Abba ya fad'a.

     " Toh zira masa ido zamu zauna miyi kenan koh me ze faru ya faru kenan". Cewar Mommy.

     "Ni kin ta'ba fad'a min idan ba yanzu ba?"
     "Toh yanzu ai na fad'a maka".
      " Toh Allah ya sawwa'ke".Ya fad'a.

      "Ameen". Ta amsa
 
                ***
  Ahmad daya koma gida zuciyarsa fyas ,Umma da Reyhana ne damuwarsa yanzu.

     8:13pm bayan ya dawo daga masjid ya d'auki wayarsa yai dialing numbern Reyhana.

•••

   Tana parlor a zaune ita da su Ikram da Mommy sega kira ya shigo wayarta.Sam bata kawo Ahmad bane dan ba layin data sanshi dashi bane.

     " Assalamu Alaykum".Tayi sallama bayan tayi picking.

     Seda yayi gyaran murya tukun ya amsa. "Waalaikumussalam".

      Da tana jingine da jikin sofa amma jin muryar yasa ta gyara zama." Kamar Ahmad ". Ta fad'a a zuciyarta.

   " Reyhana ".Ya kira sunanta.

     Tashi tayi tsam daga parlorn ta haye sama, su Ikram idansu 'kir akan ta bama su kad'ai ba hatta Mommy seda tabi bayan ta da kallo.

     " Waye?" Ta tambaya duk da kuwa ta gane mey magana.

     "Yanzu kin manta da muryar tawa ma?"
      "Da zaka fad'a min da wanda nake magana da yafi dan ina da abun yi". Ta fad'a.

     " Toh ranki ya dad'e ,Ahmad ne". Ya amsa.

      "Wane Ahmad d'in?" Ta tambaya.

      Dariya tambayarta ta bashi dan yanzun ya gano tasan mey magana sarai.

    "Reyhana please mana nasan kin gane mey magana,ina so miyi magana". Ya fad'a.

     " And nace a'a".Ta fad'a.

     "Please ,am very sorry". Ya fad'a.

     "Mey kayi min da zaka bani ha'kuri ?"

     "Laifi mana ,lokacin da ya kamata ace nazo ban..." Be 'karasa magana ba ta katse wayar
STORY CONTINUES BELOW
       "Reyhana". Ya kira amma shiru yake ji

     Koda ya sake kira bata d'aga ba,daga baya ma kashe wayar tayi ta barta a d'aki ta dawo parlor tana so tayi pretending komai is normal.

     Haka dolensa ya ha'kura ya ajje wayar gefe ,tunane-tunane ya shiga yi ta yadda ze sake 'bullowa ta saurare shi.

    Washegari da safe yana tashi yaje ya gaisheda Umma itama kamar koyaushe ba fuska balle ya zauna yayi mata wani surutai ,Zainab tana d'akinta bata fito ba.

      Wajen 'karfe uku ya fita yayi wa Nasreen siya-siyen kayayyakin data lissafo,suma su Umma yayi musu wasu 'yan siyayyar.

      Zainab ce ta 'kar'bi kayan daya siyo ta kaiwa Umma,ba tare da ta duba ba tace takai store ta ajje.

     Seda yamma tayi tukun ya tafi gidansu Reyhana,lokacin da ya isa 'kofar gidan ya kira Reyhana a waya amma ta'ki picking dan haka yayi mata text ya fad'a mata yana  waje.

      Reyhana bayan ta karanta text d'in ta ta'be baki." Toh ina ruwana"Ta fad'a a fili.

      Yana waje shiru-shiru beji reply ba ,ya jingina da mota yana tunanin wani way d'in ya hangi Nasreen tana fitowa daga ma'kotansu.

      Dad'i yaji sosai ganinta ,tana ganinsa ta 'karaso da gudu ta ma'kaleshi."Uncle yanzu kazo baka ganni ba koh?"

    "Ehyyi". Ya amsa.

     " Ummiena bata san na fita ba ,tana d'aki na gudo waje".Ta fad'a tana dariya.

    "Laa kina so Ummienki ta damu sosai?"

     "A'a". Ta fad'a tana girgiza kai.

      " Toh ki dena fitowa bata sani ba kinji".
      "Toh". Ta amsa.

      " Uncle ka kawo mini kayan wasan?" Ta tambaya.

      "Ehyi na kawo miki suna mota". Ya amsa yana murmushi.

      " Yeyy! "Tasa tsalle tana le'ka motar.

      'Karasowa yayi ya bud'e mata ya d'akko ya mi'ka mata" Yeyy! Uncle thank you".Ta fad'a tana bud'e jakar ledar.

      "Uncle ka taho mije na nunawa Ummiena".

       " Zan dawo yanzu zanje unguwa".Ya fad'a.

       Ma'kale kafad'a tayi tana buga 'kasa."Kace idan kazo zamiyi wasa".

     "Eh mana ba'kyaso naje unguwa na sake siyo miki chocolate?"

      "Ina so". Ta amsa da sauri".

      " Yawwa good girl,toh maza jeki gida".Ya fad'a.

      "Bye bye". Ta fad'a tare da shigewa gida.

       Shima bye d'in yayi mata waving tukun ya shige motarsa ya bar layin.

       Tana shiga parlor ta shiga nuna musu.

       " Ummie kinga 'yatstsanata.


      Reyhana ko ba'a fad'a ba ta san Ahmad ne ya siyo.

      "Toh wanne za'a bamu acikin chocolate d'in?" Walida ta tsokane ta.

     "A'a bazan baku ba".Ta fad'a tana ma'kale kafad'a.

      " Kinga nima bake ba game a waya ta". Walida ta fad'a.

      "A'a".
      Seda ta game kalle chocolates d'in sannan da'kyar ta za'kulo 'kwaya hud'u ta ajje mata.

STORY CONTINUES BELOW
      " Sauran nawa neh ni kad'ai".Ta fad'a.

       Mommy da lokacin ta fita daga kitchen ta ta'be baki ta haye sama.

      Reyhana ko zama batai ba sanda ta shiga d'akinta sega wani kiran na Ahmad yanzu harta gane numbern ma duk da batai saving ba.Bata dad'e da katsewa ba sega kiran Sameer ya shigo seda ya kusa tsinkewa tayi picking.

     Ahmad daya sake kira yaji  tana waya ,katsewa yayi ya ajje wayar a gefe amma sam hankalinsa ya kasa kwanciya.

     Bayan kamar 10 min ya sake kira, ga mamakinsa seya ji har lokacin waya take,ganin ya isheta tayi rejecting kiran nashi.

     Nan fa ya sake Shiga damuwa a zuciyarsa yana fad'in."Wannan wane irin waya take har ta kaita more than 10 min?"

     Tunani ya shiga yi iri- iri wayarma wulli yai da ita gefe ya kasa samun sukuni.

       Ita kuwa tana gama wayar ta kashe wayar gaba d'aya.

               °°°

Washegari da safe tana bud'e wayarta da text d'in Ahmad ta fara cin karo.

      I am sorry for all i have done,i know i have hurt you badly. I don't know what got over me to behave that bad.Please i am sorry forgive me.

Tana gama karancewa tayi deleting ta ajje wayar gefe.

      Tuna yau Monday yasa ta tashi Nasreen da wuri tayi mata wanka ta shiryata ,sanda suka sakko 'kasa kowa ya hallara a dinning table.

      Yau da kanta ta kaita school driver har yanzu ba lafiya.Nasreen ta cika aljihun jaka da chocolates badan Reyhana ta duba ba da dasu zata shiga class.'kwaya biyu ta rage mata ta kwashe sauran  ta ajje a mota. "Sekace hauka chocolate abinci ne". Reyhana ta fad'a.

     Nasreen kuwa kuka tasa da'kyar ta fita ta shiga makarantar.

°°°

Ahmad da wuri ya fita ,Zainab bata da lecture da wuri shiyasa basi tafi tare ba.

      Yau daga wajen aiki be dawo gida ba ya wuce school d'in Nasreen,lokacin sun fito sallar zuhr.A cikin mota suka ci abincin daya tsaya ya siya a restaurant.

      Ko takan abincin school bata biba ,tana gama ci ta d'akko ragowar chocolate d'in ta ta 'bare.

     " Uncle kaga yau Ummie ta 'kwace min chocolates d'ina ,guda biyu kawai ta bani nayi kuka amma bata bani ba". Nasreen ta fad'a.

     "Toh kiyi ha'kuri Ummie bata so kiyi ciwon ha'kori". Ahmad ya fad'a.

      " Ha'kori na zeyi ciwo ina sha dayawa?"
      "Eh". Ya amsa.

       Seda aka koma class tukun ta koma ciki Ahmad ya tafi, a hanya ya kira Reyhana a waya duk da kuwa yasan baza ta d'aga ba,kusan sau uku ya kira bata d'aga ba ya ha'kura.
     
      Wajajen 7:30pm bayan ya koma gida ya iske Umma a parlor, tafiya da zeyi gobe zuwa Lagos ya sanar mata.

    "Allah ya kaimu" Ta fad'a.  
     "Ameen". Ya amsa .

     Ya zaci zata tambayi kwana nawa zeyi amma yaji ba haka ba,a sanyaye ya mi'ke ze fita ta kirashi.

     " Ahmad ".

   Da sauri ya waiwayi " Na'am".Ya amsa.

     "Kwana nawa zakai a can?" Ta tambaya.

      "Kwana biyu". Ya amsa.

      "Toh bayan ka dawo zami wata magana da kai". Ta fad'a.

     " Toh Umma".Ya fad'a.

     Se bayan ya koma d'aki tukun ya shiga tunanin maganar da zatai masa."Ko mey zata ce? Ko akan Reyhana ne?" Ya tambaya a ransa.

     Da daddare ya had'a kayansa a suit case ,wayarsa ya d'auka ya kira Reyhana, kamar yadda yayi tsammani batai picking ba.

        Pick my call please, i want to talk to my daughter.

Text d'in dariya ma ita ya bata."Watoh gadara ma zeyi,lalle wuyansa ya isa yanka let see".Ta fad'a.

     Sake kiranta yayi karo na biyu,bakinta fal da magana ta shirya rashin mutunci ,ba jimawa tayi picking.1
Teddy bear image above.

Ahmad yana sane ya fad'i haka dama so yake ta kulashi.+

Shiru tayi lokacin da tayi picking ,yana jira yaji tayi magana amma shiru dan haka shi ya fara.

"Bata wayar koh". Ya fad'a.

" Seriously? master right?" Ta fad'a.

"Reyhana waya zaki bata yarinya tana son jin muryar babanta"

"Force me,gara ma kadena wannan mafarkin dan bata san da kaiba kadena wani shishshige mata atoh dan kwanannan seka dena ganinta".

" Ko kuma ke ki dena ganinta ba". Ahmad ya fad'a.

"Au haka ma zaka ce? Yaushe kasanta ma gabad'aya ? Sanda take bu'katarka ina kake?"

"Reyhana kidena fad'in haka ,yaushe zaki yarda dani ne? Believe me ba'a son rai na na d'au tsahon wannan lokutan banzo gareta ba,please i am sorry forgive me".

" You better stop apologizing".Ta fad'a cikin jin haushi.

"Ok then wazan tambaya Nasreen?"
"Don't ever try it,tana yarinyarta bazaka jagula mata lissafi ba"

"Ok toh naji,yanzu tana ina?" Ya tambaya.

"Mey zakai mata?"

"Gaisawa mana". Ya amsa.

" Tayi bacci ".Tayi 'karya.

"'Karya".Ya fad'a.

" Ni nake maka 'karya?"

"Au sorry".Ahmad ya fad'a kamar mey shirin yin dariya.

" Don't sorry me ".Ta fad'a.

Kafin ya sake wata maganar har ta katse wayar.Conversation d'in da sukai ba 'karamin dad'i yayi masa ba ,text ya tura mata kamar haka.

Am sorry Ummien Nasreen,goodnight 😘😘 to my Angel.I mean Nasreen

Check your whatapp pls..

Tana gama karancewa tayi tsaki abin nasa ya soma isarta dan taga alamar ya 'karo wula'kanci.

Da ta ajje wayar se kuma ta d'akko ta kunna data ta hau whatapp.Number d'inshi taga ya turo message tana bud'ewa taga image na teddy bear pink an rubuta
"for someone special❤

Reyhana:"Mey zanyi dashi?"


Ahmad: "Waya ce naki neh? na Baby na neh".

Reyhana: Toh meye na turo mini se ka bari idan ka had'u da ,'yar taka ka nuna mata"

Ahmad:"Bafa baby Nasreen ba,ki gane mana".

Reyhana:" Wai kai 'kalau kake? Wace babyn taka tukunna ma"

Ahmad:"Bafa ke nace ba,ina nufin...."

STORY CONTINUES BELOW
Reyhana:"Kai ya rage ma".

Daga haka ta sauka ta ajje wayar gefe ,shima ganin bata kai ya ajje wayar.

***
Tunda ya tafi Lagos be samu sunyi waya da ita ba sede yana turo mata apology text,kwanansa biyu ya dawo kano se bayan maghrib ya diro kano a ranar be samu yaje gidansu Reyhana ba.

Umma ta sakko yanzu ta dena fishin da koda ya tafi tana kiransa taji lafiyarsa.

Yau wajajen 10:30am ya biya makarantarsu Nasreen be jima ba ya komo gida ,daya gwada kiran Reyhana yaji switchoff.

Yana zaune Umma ta shigo d'akin,dama yana jira yaji tayi masa maganar da tace zasi bayan ya dawo kuma yaga bata yi ba.

Gefe guda ta samu ta zauna kan wani wani kujera.Gyaran murya tayi kafin ta soma magana.

"Kaga yanzu de baka da wata matsala da take a gabanka da zaka ce ta hanaka yin aure,da farko nayi tsammani na fara jin maganar daga gareka amma shiru shiyasa da kaina zan tambayeka akwai wacce kake da burin aura koh babu a yanzu?"

Tambayar Umma ba 'karamin razana shi tayi ba ,ba dan komai ba se dan baida amsar da zai bata.

"Baka ce komai ba". Cewar Umma.

" Uh..babu".Ya amsa yana sosa 'keya.

"Babu". Ta mamimaita a fili.

Dama haka take son ji dan ta dad'e da 'kudura wani abun daban ,da ace zece da akwai wata bata da hujja amma yanzu tunda babu komai zezo yadda take so.

" Toh mu muna da ta gida". Ta fad'a.

A rikice yace "Uhm?" Yana so ya tantace ko kunnensa neh beji dede ba.

"Nace akwai a gida,abune ya riga daya faru tun farko kuma dama Allah yayi da rabon 'ya shiyasa ba yadda za'ayi amma dama shiyasa so dayawa iyaye da kakanni suka fi gane auren gida gudun irin faruwar hakan ,d'an uwanka yafi sanin darajar ka da mutuncin ka ba kamar bare ba,kuma nasan wannan yarinyar bazata ta'ba wula'kanta ka ba yarinyace me hankali ".

Duk wannan maganganun da take shi ba sune damuwarsa ba kawai soyake yaji ta fad'i yarinya da take nufi.

" Kai kanka kasan halin yarinyarnan Zainab a zamaninnan masu hali irin nata tsirari ne".

"Zainab? Ni nace mata ina son Zainab?
"Toh dole seka ce?" Wata zuciyar ta fad'a masa.

"Amma Umma.." Be 'karasa ba ta katse shi.

"Wani uzurin zaka zake bayarwa? Zan baka gurguwar shawara ne kake tunani ? Kai shikenan kafi so ka cigaba da zama haka ,ka gama karatun,ka samu aiki mey kyau kuma mey kake bu'kata?" Ko wata 'karyar zaka sake yi min?" Ta 'kare fuskarta tana nuna alamar fushi.

Tuna yadda Umma bata iya fushi ba kuma baya so ya sake 'bata mata rai laifi goma da ashirin shiyasa yai shiru yana tunanin amsar da zata fito daga bakinsa.

"Umma duk yadda kika ce ,hakan ba damuwa bane Umma kuma nasan baza ki za'bamin wacce ba ta gari ba".

Umma taji dad'in amsarsa sosai ,tasan yin hakan ba 'karamin farantawa iyayen Zainab ze ba ,kuma zasu ga sun saka musu da tallafawa Ahmad samun aiki da mahaifinta yayi.

STORY CONTINUES BELOW
"Barka haka nake son ji ,zan kira kawunka miyi magana dashi anjima".

" Umma amma ita ai bata gama makaranta ba".Ahmad ya fad'a du dan ya samo mafita.

"Makaranta ai ba matsala bace abinda ta kusa gamawa ma ,koh Lagos d'in za'a tafi da 'Yar tawa ban sani ba". Cewar Umma cikeda zolayi.

Murmushin ya'ke kawai yayi dan hankalinsa ya d'aga.

Yana ji tana masa maganar ya soma gina wani plot dayake dashi kawai uhm yake amsata tunaninsa sam baya gun har ta fita.

Ya rasa wanne daga cikin abokanansa ze kira yaji sa'ida ,yasan sadiq dariya ma zeyi masa gwara Imran.

Koda ya kira imran ba wani support hakan ba'karamin sake bashi haushi yayi ba,yau yaga abu da girmansa za'ai masa auren dole sekace a 'kauye .Abinda yayi tunani a zuciyarsa kenan.

Ko abincin rana kasa ci yayi be fito daga d'aki ba se lokacin da taji Umma ta kirashi yaje ya d'akko Zainab daga makaranta.

A hankali yake tu'kin har ya isa makarantar ,yana parking ya kirata ya fad'a mata yana jiranta.

Ba'a wuce 5min ba ya hangota tana tahowa.Kallanta yayi tayi tana tahowa shi tunda yake be ta'ba kawota a ransa a matsayin matar da ze aura ba.

Yana wannan tunanin ta 'karaso har motar.Ita kallonta da yake yasa ta sunkuiyar dakai a tunaninta ko du cikin love ne.Se da ta bud'e 'kofar motar tukun ya dawo daga tunanin dayake.

"Yaya barka da rana". Ta fad'a sanda ta shigo.

" Yawwa ya school d'in?"Ya tambaya.

"Alhamdulillah". Ta amsa.

Daga haka be sake cewa komai ba har suka isa gida.

Yana shiga d'akinsa ya sake kiran Reyhana yayi sa'a akai picking.

" Hello".Yaji an fad'a cikin 'yar 'karamar murya.

"Nasreen?" Ya tambaya dan yaji kamar ita.

"Na'am". Ta amsa.

" Uncle neh".Ya fad'a.

"Laa! Uncle ,d'azu Auntynmu ta kawo ni gida kaina yana tayi mini ciwo nayi kuka". Nasreen ta fad'a.

" Ciwon kai kuma,ayya! Sorry kinji ,kinsha magani?" Ya tambaya.

"Eh Ummiena ta bani". Ta fad'a.

" Yanzu ya dena?" Ya tambaya.

"Eh".Ta amsa.

" Ina Ummienki?"Ya tambaya.

"Tana kitchen na kai mata?"

"A'a anjima". Ya fad'a dan yasan kashewa ma zatai.

Labarin school tayi ta bashi kafin daga bisani sukai sallama.

Nasreen da kanta taje har kitchen ta fad'a ma Reyhana tayi waya da Uncle

" Ban hanaki d'aga min kira ba?"

"Ummie Uncle ne fa". Ta fad'a.

" Karki sake kinji koh".Tayi warning d'inta danma tayi ciwon kai da se taja mata kunne.

°°°

Umma ba 'bata lokaci ta kira kawun Ahmad tayi masa bayanin komai bayan ta gama ta kira wata sister tata itama ta sanar mata da abinda ake ciki.

***
Ko sati d'aya ba'ai ba aka je neman auren Zainab,dududu wata uku aka sa Ahmad gani yake kamar mafarki kawai kallon su yake suna abinsu,Zainab murna a gurinta ba'a misaltawa.

Reyhana yau da kanta ta kai Nasreen makaranta ,daga nan zata biya school fees na Nasreen seji tayi an fad'a mata Ahmad ya biya.

"Watoh ta nan kuma yanzu ze 'bullo". Reyhana ta fad'a.

Tana wannan batun sega kiran Ikram,tana d'agawa taji suna asibiti Sageer ba lafiya,da sauri-sauri ta shiga. mota se asibiti.

Mommy, Abba se Ikram sinyi cirko-cirko a bakin 'kofar d'akin da aka shigar dashi.

" Mommy meya sameshi?" Ta tambaya.

"Bassam ne ya shiga d'akinsa ze Kira shi ya tarar dashi a sume".Cewar Mommy.

" Subhanallahi".Reyhana ta furta.

Bata sake wata maganar ba sega doctor ya fito daga d'akin.

Da Abba da Mommy ya kira ya zaunar dasu yake tambayarsu tsahon lokacin da Sageer shafe baida lafiya

.Nan Mommy ta zayyane masa irin halin da suka tsince shi.

"Hajiya wannan yaron depression yana nema ya kamashi,ga dukkan alamu damuwa ta mishi yawa".

" Subhanallahi".Suka furta a tare kowannensu fuskarsa da damuwa.

"Amma yanzu ya samu sa'uki InshaAllahu zamu cigaba da bashi kulawa kafin a sallame ku". Doc ya fad'a.

" Toh muna godiya likita".Cewar Abba kafin daga bisani suka fita.
Sageer bayan kamar 30min ya farka,lokacinda suka shiga be bari ya had'a ido dasu ba ya kawar da kansa.+

         Dukkansu suna tunanin wannan wata damuwa ce ke damun Sageer data saka shi ya shiga cikin wannan halin banda Reyhana da ita tasan komai.

                    ***
      Around 3pm bayan ya dawo gida ya tarar da Sadiq,yana parlor suna hira da Umma.Ahmad suna gaisawa ya koma d'akinsa seda ya watsa ruwa tukun ya fito zuwa parlor lokacin Umma bata ciki.

     "Abokina yane?" Cewar Sadiq.

     Daga yadda yayi magana ya gano d'aya daga cikin rashin mutunci ne irin na Sadiq yasan Umma ta zayyane masa komai.

       Banza yayi masa bece komai ba sema wayarsa daya d'akko yana tapping.

      "Yanzu sede naji magana a wajen Umma instead ka same ni ka fad'a mini da kanka?" Sadiq ya fad'a.

       "Ni nasan ma mey kake nufi". Ahmad ya fad'a yana cigaba da danna wayarsa.

      " Zaka gane neh  na Zainab ".Sadiq ya fad'a yana 'kare maganar da dariya.

       " Kai! zan zageka".Cewar Ahmad wannan karan ba waya  yake kalla ba.
   
      "Seda kar a kuma, bani labari mana mey kake shirya mana neh?"

       "Bansani ba".Ahmad ya fad'a.

       " Munafiki kana so kana kaiwa kasuwa ,kayi ka gama".Sadiq ya fad'a.

       "Base ka ganni ba zakai". Ahmad ya fad'a yana mi'kewa yabar d'akin.

       " Ina kuma zaka ,koh ka manta zaka d'akko Zainab".Ya jiyo Umma ta fad'a.

        "Nima ze ragen hanya" Sadiq ya fad'a yana daga parlor.

       "Toh kaji". Umma ta fad'a.

      Ahmad a cukule ya fita banda Sadiq daya biyo shi yana sake 'kular dashi.Dama ba wani rage hanya dan har school dashi aka je d'akko Zainab se bayan suna hanyar dawowa ya sauka.

        Ko shiga gida Ahmad beyi ba ya tafi makarantar su Nasreen ,seda ya tsaya yayi mata siya-siye.

       •••

    Sageer kwanansu biyu a asibiti aka sallamesu har yanzu be fad'a musu abinda ke damunsa ba.Se bayan sun dawo gida Mommy ta titsiye Reyhana dan taga alamar akwai abinda take 'boyewa.

        "Mommy wata yarinya fa yake so shine iyayenta suka 'ki ,su cousin d'inta suke son su bata". Reyhana ta fad'a.

       " Yanzu dama akan haka ya shiga wannan halin !?"Cewar Mommy.

       "Tun yaushe akai hakan baku fad'a ba?" Ta tambaya.

        "An d'an dad'e". Ta amsa.

        " Yayi kyau da 'boye-'boye ga result nan ai kungani ze kashe kansa akan wata yarinya ".

        Mommy d'akin Abba taje ta zayyane masa komai, shi fad'a yayi tayi." Akan wata soyayya yana nema ya samu shiga cikin wani yanayi sakarai kawai".
       Har d'akinsa Abba yaje, Mommy tana tsayar dashi amma ko sauraronta beyi ba.

        "Kai yanzu dama wannan abun ne yake damunka kabi ka wahalar da mutane!?"
        Sageer daya sunkuyar dakai ko 'kala ya'ki fad'a yana jin Abba yana fad'a.

       "Karka fasa damuwar tunda a kanka aka fara soyayya baban soyayya kaji".Abba ya fad'a tare da ficewa.

STORY CONTINUES BELOW
        Gidan tsit kowa ya shige d'akinsa Mommy an barta da tunani,a zuciyarta tana fad'in." Kamar d'anta za'a guje shi,meya rasa yaranta ba talaka ba da iliminsa kuma shi ba muni ba kuma baya shaye-shaye ko wani abu makamancin haka wane dalilin ne zesa a 'kishi ?" Abinda yake ta mata yawo aka.

                °°°
        8:34pm Ahmad bayan ya dawo daga masjid yai dialing numbern Reyhana kusan sau uku ya kira amma batai picking ba.Da farko ajje wayar yayi amma wata zuciyarta sake zigashi ,haka ya sake kiranta still batai picking ba be gaji ba ya cigaba da kira ,yafi sau 15 .

     Reyhana jin ya takura mata banda silent da tasa ba dama tayi anfani da wayar ko yaya ta soma tapping seta ga kiransa.

       "Lafiya?" Cewar Reyhana bayan ta d'aga wayar.

       "Ina fa lafiya". Ahmad ya fad'a.

       " Toh se aka yi yaya?" Ta tambaya.

       "Ina Nasreen?" Ya tambaya.

        "Tayi bacci". Ta amsa.

         " Toh ki shafa min kanta".

         "Bata bu'katar hakan tunda kullum babarta tana mata addu'a".

          " Toh mungode da hakan".Ya fad'a.

      Shiru ba wanda ya sake cewa komai kuma ba wanda ya katse.

      "Reyhana". Ya kira sunanta cikin sanyayyar murya.

      "Meye yanzu kuma?" Ta tambaya.

       "Just want to say sorry". Ya fad'a.

       " For what?" Ta tambaya kamar bata gane inda ya dosa ba.
    
       "For everything".Ya amsa.

         " Is that all?"Ta tambaya .

          "No". Ya fad'a.

           "Meya rage?"

           "Goodnight". Ya fad'a.

         Hanging tayi ba tare da ta sake magana ba kuma bata jira shima ya sake yi ba.

         Wayar kawai yabi da kallo yana murmushi sannan ya ajje ta a gefe.

         Reyhana bayan data katse wayar bata ajje ba seda ta 'karewa numbern kallo tukun ta maido da kallonta kan Nasreen da take ta bacci.

                  ***
      Mommy da ta kwana da damuwar d'anta a rai da safe bata iya ha'kuri ba dan haka taje tana ro'kon Abba daya yi wani abun akai.

       " Ni kike so na kwashi 'kafa kenan naje nace a bawa d'ana yarinyar!?"
        "Ba haka nake nufi ba amma de idan aka tura manya ai zasu ga da gaske ake koh" Mommy ta fad'a.

       "Ke baki ji bayanin bane since cousin d'inta zasu bata ,toh kuma se 'ka'ka zaki iya hanasu ne?"

       "Ya kake magana haka  kasani ko su chanja ra'ayinsu".

        " Saboda d'anki shine autan maza koh?"Cewar Abba.

       "Dan Allah na ro'ke ka ,ka taimaka kayiwa 'yan uwanka magana".

       " Naji shikenan amma inde basu amince ba bazan sake sa 'yan uwana a wannan mganar ba".

        "Na yarda".Mommy ta fad'a da sauri.

          Aiko hakan akai ,Sageer ya basu address d'in gidansu yarinyar suka je sukai magana da mahaifin yarinyar.

       Mommy tun basu dawo ba ta sakko 'kasa tana jiran su dawo taji ya aka kaya.Shima Sageer yana d'aki duk abinda ake hankalinsa nakai amma ya kasa fitowa dan kunya.

STORY CONTINUES BELOW
      Seda aka shafe kusan 30 min sega su sun dawo Mommy ziba ido tayi tana jira taga sun zauna taji bayani.

  °°°

Ahmad daga aiki ya biya d'akko Zainab daga makaranta,a da yana so idan ya maida ita gida yaje makarantar su Nasreen amma kuma lokaci baze bari ba dan lokacin tashin su ya kusa,hakan nan ya tafi da Zainab makarantarsu Nasreen.

     Ita de taga an baud'e hanya amma bata tambaya ba,shima kuma beyi bayani ba har suka isa school d'in.

     Lokacin har an tashe su sun fara fitowa,chan sega Nasreen ta fito.Yana ganin fitowarta ya fita shima.

      Da gudu ta 'karaso inda yake tana tsalle." Uncle !"

     Zainab da take daga mota tana hangensu ,tana ganin Nasreen ta kawo ita ce 'yar tashi a ranta.

      "Uncle dawa yau kazo?" Ta tambaya tana hangen Zainab dake mota.

       Waigowa yayi ya kalli Zainab tukun ya juyo da kallonsa kan Nasreen.

       "Anty ce". Ya amsa.

       " Anty sunanta?" Ta tambaya.

        "Eh". Ya amsa.

     Da sauri ta 'karaso motar harda 'ko'karin bud'ewa,Zainab ganin haka yasa itama ta bud'e mata 'kofar.

      " Ina kwana".Ta gaisheta.

      Zainab tana murmushi ta amsa "Lafiya lau har yanzu safiya ce kenan" Ta fad'a tana murmushi.

       "Sunanki Anty koh?" Nasreen ta fad'a.

        "Eh sunana Anty Zainab". Ta fad'a.

       " Anty Zainab".Nasreen ta  maimaita.

        "Eh,an tashi daga makaranta koh".

        " Eh yanzu driver zezo ya d'auke mu".Ta fad'a.

         Hira sosai tayi tayi da Zainab kamar dama ta santa,seda driver yazo tukun ta tafi suma suka komo gida a hanya Zainab take maganar Nasreen,kad'an-kad'an yana amsata.

   °°°

     Abba ne ya soma tambayarsu ya ta kaya,mommy tayi 'kuri tana ji.

     "Ba yadda bami da mahaifinta amma ya'ki, mahaifinta ya riga ya tsaida magana yace mu baku ha'kuri da shima yaron". Wani daga cikin 'kanin Abba ya fad'a.

      Wani takaici ne ya ziyarci Mommy tana mamakin irin wannan mutanen daga baya ma tashi tayi daga parlon ba tare da ta gama sauraran su ba dan ba wata kalma da zata sa taji sanyi.

       Nasreen kuwa tana dawowa gida koh uniform bata cire ba ta soma bawa Reyhana labarin Uncle da Anty Zainab.

       " Nasreen kika ce Anty Zainab tare suka zo?" Ta tambaya.

        "Eh da uncle suka zo ,na nuna mata classwork d'in da Anty ta bamu a aji". Ta fad'a.

     Reyhana ko 'karanshe labarin ma bata ji ba tuni ta tafi tunani.Tunanin last ganinta da Zainab d'in ma ta Shiva lokacin da suka je Zaria suka taho da ita ta zauna gidan Umma.

     " Dududu bata fi 13yrs ba lokacin ".Ta fad'a a zuciyarta.

     " Toh haka kuma zatai ta zama after all shekaru shida da suka wuce!?" Wani 'bangeren taji zuciyarta ta fad'a.

      "Atleast fa tayi 19 koh 20 yanzu,toh koh...anya..kai no..ko ya aureta ma? "
       Lokaci guda taji kanta ya fara d'aukan zafi,haushin sa ne ya sake kamata ma watoh ya raina mata hankali shine harda matar daya aura Zeke zuwa wajen 'yarta.

       Tana wannan batun sega kiran Ahmad, a 'kule ta d'auki wayar tare da switching off."Zaka ga wacce zata d'aga ,watoh ga sakarya".Ta fad'a a fili.
Ahmad beyi mamakin
'kin picking call d'insa da Reyhana ta'ki yi ba kusan daman an saba shiyasa be kawo komai a ransa ba.+

Ita kuwa Reyhana ta kasa samin sukuni se tunane-tunane takeyi ,ranar batai cikakken bacci ba.
***

An d'auki kwana biyu Reyhana bata picking call d'insa text kuwa baya gajiya haka zeta tura mata tana ignoring.

Yau da safe tana shirya Nasreen se ro'konta take barta taje gidansu Anty Zainab.

"Ko zaki d'ige bazaki ba gara ma kidena tunanin zuwa". Reyhana ta fad'a.

Chono baki tayi tana buntsire-bintsire baki." Tashi mije kiyi breakfast ki tafi makaranta".Reyhana ta fad'a

"Toh". Ta amsa.

Reyhana ce ta fara fita a tunaninta ko Nasreen tana biye da ita.Ganin Ummienta tayi gaba tayi sauri ta bud'e wardrobe ta ciro kayanta kala d'aya ta cusa a cikin jakarta ta fito se muzurai take.

Mommy kafin ta 'karaso dinning d'in ta nufi d'akin Sageer.

" Yau ma bazaka aikin ba?"Ta tambaya.

"Zanje se anjima". Ya amsa.

" Toh ka fito kayi breakfast mana kai shikenan kuma se kaita 'buya a d'aki".

Da 'kyar ya taso,sake cin magani yayi dan ya lura da su Ikram kallon munafinci sike masa,daga ya had'a ido da Abba seya kauda kai.

"Nasreen ya naga jakarnan ta 'kara wani tudu mey kika sa aciki?" Walida ta tambaya.

Reyhana se lokacin ta lura da tudun jakar,hannu tasa tana shafawa ko zataji wani abun da sauri Nasreen taja baya.

"Ba komai fa". Ta fad'a kamar mey shirin yin kuka.

" Toh kiyi sauri ki gama ci kafin driver yazo".Reyhana ta fad'a.

Mommy da hankalinta baya gunsu ko tanka musu ma batai ba.

°°°

Mommy bayan ta komo d'aki ta kira Anty Asma'u ta sanar mata halin da ake ciki daga baya Anty Asma'u tace zata zo Sageer d'in ya kaita gidan itama ta gwada tata sa'ar.

Ahmad se bayan ya dawo gida ya tafi school d'in su Nasreen, lokacin daya je ba'a tashe su ba seda ya jira.

Tana ganinsu ta kyalla da gudu hadda tuntu'be.

"Uncle !" Ta kira sunansa.

"Uncle ita Anty Zainab bata zo ba yau?" Ta tambaya.

"Ehyyi". Ya amsa.

" Uncle ka kaini wajenta". Ta fad'a.

"Driver zezo ya d'auke ki ,ki bari se kin fad'awa Ummienki".

" Ai na fad'a mata ,kaga ta bani wasu kayan ma". Ta fad'a tana zuge zip d'in jakar.

Shide yasan Reyhana baza ta bari ya kaita gida ba.

"Ummienki bata san kin d'akko ba koh?". Ahmad ya fad'a.

" Toh dan Allah ka kaini ai bazan dad'e ba seka fad'a mata".

"Ince mata mey?"

"Kace mata ka kaini wajen Anty Zainab".

" Yanzu yamma tayi ki bari se gobe kinga ba school ma".Ya fad'a.

"Uncle dan Allah ka kaini". Ta fad'a tana bubbuga kafa kamar zatai kuka.

Seda ya d'an nisa tukun yace " Toh zan kaiki".

Tsalle ta shiga yi tana murna ,da sauri ta shige motar.Ahmad seda driver yazo d'aukansu ya fad'a masa Nasreen baza ta biyo su ba.

STORY CONTINUES BELOW
Ya kira Reyhana a waya dan ya fad'a mata amma ta'ki d'aga wa ,daga baya kawai ya tura mata text  sannan suka tafi.

     Sanda suka isa gidan Nasreen ta 'ki sakewa.

    "Taho ki gaishe da Umma". Ahmad ya fad'a tare da kamo hannunta.

       A hankali ta 'karasa wajen Umma kanta a sunkuye ta gaisheta.

      " An dawo daga makaranta koh?" Umma ta fad'a.

      "Eh". Ta amsa tare da gid'a kai.

      Ganin Zainab ta shigo yasa ta yin murmushi tare da 'karasawa inda take.
 
      "'Yan mata yau kece a gidan?"
 
        Nan ma kai ta gid'a bata ce komai ba.

     "A cire jakar koh?"Zainab ta fad'a.

      " Eh,kayana ma suna cikin jaka".Ta fad'a.

       "Iyee kwana nawa za'ai mana?" Umma ta tambaya.

        "Zaki kwana?" Zainab ta tambaya.

     Kai ta gid'a tana murmushi ,Zainab ce ta jata d'akinta ta sauya mata kayanta, cikin 'kan'kanin lokaci ta fara sakin jiki tana ta labarin school.

     Reyhana yanzu ne ta lura da text d'in daya tura mata a take ta kira Ahmad.Yana parlor kiranta ya shigo dan haka ya d'an fita tukun yayi picking.

     "Ina ka kaimin yarinya?" Ta tambaya bayan ya d'aga.

     "Kinsan de bazan sace taba koh" Ahmad ya fad'a cikin sanyin murya.

     "Taya zan shede ka nasan mey ka zama". Cewar Reyhana.

      " Don't worry ba dad'ewa zatai ba".Ya fad'a.

       "Yanzu nake so ta dawo ni bana son gantali".Ta fad'a.

        " Ita fa tace a kaita wajen Zainab ".Ya fad'a.
  
         " Ni be shafen ba a dawo min da yarinya yamma tayi".Ta fad'a.

       "Toh an gama". Ya fad'a kamar mey shirin yin dariya.

      Bata jira ya sake wata maganar ba ta katse.

        Jealous?  Ya tambayi kansa.

      Yana komawa yace Nasreen ta taso ya maida ita ta'ki ita se anjima,Umma ma hakan tace haka ya 'kyaleta.

     Ba zato ba tsammani hadari ya murtike garin kafin ace mey ruwa ya sauka.Reyhana ta gama 'kulewa takaici ya isheta ita a tunaninta ma yana sane ya'ki dawo da ita.

     Ahmad kuwa ba haka bane a gunsa ya 'kagu ruwan ya tsagaita ya kaita amma shiru 'karfin ruwan ma 'karuwa yake.Nasreen kuwa ko a jikinta se game take a wayar Zainab a haka lokaci yai ta ja, gashi idan ya kira Reyhana baya samunta saboda 'karancin network.

       Har bayan maghrib ana ruwa,Ahmad du yabi ya damu dan yasan Reyhana tana nan ta cika tayi fam.

       Zainab wayar ta amsa daga hannun Nasreen tace zatai mata photo, ba musu ta bata.Tsayawa tayi ta nutsu ta bada attention tana jira a  'kyasta mata.

    Ana d'auka  ta kar'ba taje ta nuna wa Ahmad.

Nasreen

   " Iyye! Toh jeki nuna wa Umma". Ahmad ya fad'a.

      Da sauri taje ta nuna mata itama ,bayan nan Umma ta zuba mata abinci taci ,ba jimawa tayi bacci.

        "Bakai waya da mamanta ba ka fad'a mata?" Umma ta tambaya.

        "Na kira ban sameta ba ba network me kyau". Ya fad'a.

        " Toh ga wayar Zainab ka kira koh zaka semeta kaga shirin ba dad'i".Cewar Umma.

      Wayar Zainab yayi amfani da ita ya kira Reyhana kiran farko ta d'aga.

      "Assalamu Alaykum". Tayi sallama.

      " Waalaikumussalam".Ya amsa.

       "Reyhana it's me". Ya fad'a.

       "Mey zaka fad'a mini kuma?" Ta tambaya cikeda takaici.

       "Na dad'e ina kiranki bana saminki ,kinga yanayin garin baze yiwu mu fito ba". Ahmad ya fad'a.

      " Kana sane kayi hakan ,daga nan ta ri'keta karta baro ta ta dawo". Ta fad'a daga nan tayi hanging.

       Daman yasan za'ai haka bata tsaya ma ta saurare shi ba balle yayi mata maganar tayi Nasreen tayi bacci.

       Reyhana tunda take bata ta'ba kaiwa irin wannan lokacin bata tare da Nasreen ba dan ba inda take iya zuwa ta kwana.

     Su kansu 'yan gidan kowa kewarta yake,tunda Reyhana taga 9pm yayi ta fidda ran dawowarta yau.

      Kowa ya shige d'akinsa itama haka ,ta 'kurawa side da Nasreen take yin bacci se tunanota take,bata jin zata iya yarda Ahmad ya raba ta da Nasreen.

        Wata zuciyarce tace mata ta kira shi,dan haka ta d'auki waya ta kira.Tana tsammanin taji muryar Ahmad amma seta ji muryar mace.

       "Assalamu Alaykum". Aka fad'a.

       Da'kyar ta iya cewa "waalaikumussalm".

      " Uh..ya mance wayar ne a gida".Taji an fad'a.

        Bata ce komai ba ta katse wayar, a zuciyarta tana sa'ke-sa'ke.

         "Zainab?" Ta tambayi kanta.

         Tashi tayi daga zaunen tana ta tunani iri-iri  da ta kalli window ta hangi kamar hasken mota daga gate.'Karasawa wajen tagar tayi ta le'ka ,gani tayi da gaske mota ce ta tsaya lokaci guda zuciyarta ta fad'a mata Ahmad ne.

      Mayafinta tai sauri ta yafa ta fita a sand'a dan garin yayi tsit ga sanyi -sanyi daya ke busawa.

°•°
      Ahmad yana gani ruwan ya tsaya around 9:09pm ya d'auka key ,Nasreen da tayi nisa da bacci haka ya d'auketa ya fita.Zainab se bayan ya fita ta lura da phone d'insa daya manta,bayan mintina da fitarsa taji ringing d'in wayar da batai niyyar d'agawa ba seda Umma tace ta d'aga tukun.

        "Azizaty❤" sunan da tagani a screen d'in,dan haka a sanyaye ta d'aga ,da'kyar ta iya tayi bayanin baya nan  and lastly abinda tayi noticing shine an katse wayar.

          Koda ta komo d'aki ba abinda yake mata yawo aka kamar sunan da taga ni a jiki.

       "Har yanzu yana yin waya da ita kenan? hakan yana nufin ze dawo da ita?"

        "Toh ko wata budurwar tashi ce ?" Abinda tayi ta tambaya kenan wanda bata da amsarsu.

      Ahmad koda ya isa gidansu Reyhana wayarsa ya shiga laluba dan ya kira ta amma yaga babu.

         Yana shawarar fitowa daga motar sega Reyhana ta bud'e'kofar gate d'in.
 
     Tana daga bakin 'kofar ta'ki 'karasowa gashi fitilar motar ta hasketa.+

Fitowa yayi daga motar ya 'karasa har inda take a ransa yana tunanin mey ze fara ce mata.

"Reyhana am sorry ban kawo ta da wuri ba". Ya fad'a .

" Yanzun tana ina?" Ta tambaya.

"Tana cikin mota ,tayi bacci ne".Ya amsa.

Takawa tayi ta 'karasa inda motar take, ta bud'e 'kofar zata d'akko ta ya maida 'kofar ya rufe.

" Ka d'auke hannunka a 'kofar nan".Ta fad'a.

"We need to talk". Ya fad'a.

" Bani da wannan lokacin".Cewar Reyhana tare da watsa masa harara.

"Se yaushe ? Gobe? jibi? Yaushene zaki yarda dani ? Reyhana how many times do I have to tell you,kema kinsan ina nan bazan ta'ba d'aukan wannan tsahon lokacin ban zo ba ,ko bayan da na dawo kece kika hana ni zuwa you know why?" Cikin d'aga murya yake wannan maganar.

"Saboda na rasa abinda zance maki ki yarda dani a wannan lokacin,Umma tayi iya 'ko'karinta tazo amma mey ya faru ? Can you explain that?"
Reyhana shiru tayi ta kasa sake cewa komai ta kau da kanta gefe.

"Why are you punishing me like that ? am begging you please forgive me ,am very sorry!"

Bata ce masa komai ba , kasancewar ya d'auke hannunsa daga 'kofar motar hakan ya bata dama ta bud'e ,Nasreen dake kwance ta kinkimeta ta d'ora a kafad'a.

Bece mata komai ba ya bud'e 'kofar gidan gaba ya ciro jakar Nasreen ya mi'ka mata.

Hannu tasa ta kar'ba ta wuce,seda yaga shigewarta gida ya komo mota ya tafi.

Tana shiga gida ta kwantar da ita ,se lokacin taji sa'ida ba 'karamin dad'i taji ba daya dawo mata da ita.Se lokacin ta samu itama ta kwanta amma kuma se tuna muryar Zainab da taji d'azu take a wayar Ahmad,da wannan tunanin tayi bacci.

***
Washegari da safe bayan Nasreen ta tashi ta soma bawa Reyhana labari.

"Anty Zainab ce ta chanja min kayana". Nasreen ta fad'a.

" Jiya dama kaya ne a jakar ki koh ,shine kika hana a gani".

"Kuma ta d'aukeni a wayar ta". Nasreen ta fad'a.

"Kinci abinci jiyan?" Reyhana ta tambaya.

"Eh Umma ce ta bani ma". Ta amsa.

" Umma?".Reyhana ta tambaya.

"Eh Umman su Uncle ce ".

" Gidan Umma suka je kenan? Toh ko beyi aure ba daman?" Ta fad'a a zuciyarta.

Daga baya Nasreen ta shiga yin wasanta ta bar Reyhana da tunani.

°°°

Su Anty Asma'u yau Sageer ya kaisu gidansu Fatiman sa ,Mommy tana gida tana jiran su dawo taji bayani Abba sam besan da wannan batu ba.

Suna dawowa Mommy ta shiga tambayarsu ya aka 'karke.

"Matsalar daga kece Maryam". Anty Asma'u ta fad'a.

" Kamar ya ?" Ta tambaya tana neman 'karin bayani.

"Mahaifiyar yarinya tayi mana bayanin komai,tace dalilin daya sa suka guji Sageer shine sun samu labari ke bakya yarda 'ya'yanki si auri talakawa ,shiyasa suka ji tsoron abinda ze biyo baya kada daga baya azo ana da an sani".

STORY CONTINUES BELOW
Shiru Mommy tayi ta kasa cewa komai." Zancen duniya baya 'buya ,shedar da aka yi mata kenan ashe tin sanda tasa Ahmad ya saki Reyhana ". Ta fad'a a zuciyarta.

" Dama wannan dalilin ne yasa suka guji Sageer?"
"Ehyyi haka ta fad'a mana mahaifiyar yarinyar ,kinga kece sila ashe". Wata daga cikin yayyin Mommy ta fad'a.

Mommy kai ta dafe ta kasa cewa komai, tana mey jin haushin kanta ,gashinan halinta yasa d'anta ya shiga cikin wannan halin".

Har sisters d'inta suka tafi ta kasa sakewa,d'aki ta shiga ta zauna tana tuna irin takurawa Ahmad datai a baya ,ta d'ora masa karan tsana har seda tasa ya saki Reyhana,shi Sageer da bema yi auren ba amma ga irin halin da ya shiga shikam Ahmad harda 'ya a gaskiya bata kyauta ba ,batai musu adalci ba.

"Ashe irin halin da mahaifiyarsa ta shiga kenan sanda ya rabu da matarsa ,ya Allah na tuba Allah ka yafemin".

Mommy nadamar abinda tayi ta shiga yi tana dana sani.

Da kanta taje gidansu yarinyar ta fahimtar da ita ,ta fad'a musu bazata 'ki d'iyarsu ba.Se bayan Abba ya dawo da daddare take fad'a masa ,dama shi baida buri kamar Mommy ta gyara halinta kuma yanzu yaji dad'i tunda ta gane kuskurenta na abinda tayi a baya ,dan haka yace mata taje gidansu Ahmad ta bawa Umma ha'kuri.

•••

Kwana biyu Reyhana bata ganin kiran Ahmad haka text d'insa daya saba turo mata shima shiru.Tunani ta fara yi ko lafiya ,wata zuciyar kuma tace koh fushi yake?

" Toh ni nayi masa laifi neh da zeyi fishi ,oho masa".Ta fad'a.

Tashi tayi ta sauka 'kasa ,Walida ce kad'ai a parlorn.

"Walida ina Mommy?" Ta tambaya.

"D'azu ta fita tace bazata dad'e ba". Ta amsa.

" Ina taje?"Ta sake tambaya.

"Nima ban saniba". Ta amsa.

Kai kawai ta gid'a sannan ta shiga kitchen.

°°°

Umma tana parlor taji sallamar Mommy, abinda bata ta'ba tsammani ba kenan.

Iso tayi mata ta shigo parlor Mommy a sanyaye tana mey jin kunyar abubuwan da tayi a baya.

"Ina wuni". Mommy ta gaisheta.

" Lafiya lau ,ya yara?" Umma ta tambaya.

"Yara lafiya lau". Ta amsa.

Shiru ne ya ziyarci parlorn kafin daga bisani Mommy ta fara magana.

" Umman Ahmad, abubuwa da dama sun faru a baya wanda kowa beji dad'insu ba ,ni na zamo silar komai dan Allah ina neman yafiyar ku kiyi ha'kuri da abinda nayi miki inshaAllahu hakan baze sake faruwa ba nasan nayi kuskure ,kiyi ha'kuri".Mommy ta fad'a cikeda nadama.

"Mommyn Reyhana Allah ma ana masa laifi ya yafe ,kuma mu d'an Adam neh muna kuskure fatan mu dama idan minyi laifi mu gano kuskuren mu kuma tunda Allah yasa aka gano hakan an gode Allah ,komai ya wuce dama rayuwa ta gaji haka Allah ya yafe mana baki d'aya".Umma ta fad'a.

" Ameen ,nagode sosai".Ta fad'a.

Zainab da lokacin ta dawo daga school ta shigo parlorn.

"Ina wuni".Ta gaida Mommy cikin rissinawa.

" lafiya lau".Mommy ta amsa.

"Kun dawo kenan". Umma ta fad'a.

" Eh".Ta amsa.

STORY CONTINUES BELOW
Daga haka ta fita daga parlorn, Umma kuwa bata 'boyewa Mommy ba ta fad'a mata Zainab itace wacce Ahmad ze aura.

Mommy fatan alkairi tayi taja bakinta tayi shiru,seda Ahmad ya shigo shima suka gaisa cikin mitintawa,shima seda ta bashi ha'kuri yace mata ba komai shi dama be ri'ke ta ba.

A yanzu ne Mommy taji sakat da ta nemi yafiyarsu,ranta fyas ta koma gida ta tarar da yaran duka sun dawo kowa yana gida ,hatta Sageer shima yau yana parlor damuwa ta tafi komai ya dedeta.

Sannu da zuwa sukai mata duka yaran bayan ta amsa ta wuce d'aki.Bayan maghrib ta kira Reyhana ta fad'a mata taje gidansu Ahmad.

"Reyhana kema nasan kina..." Bata 'kare ba ta katseta.

"Mommy komai ya wuce dama Allah ya riga daya tsara ba yadda zami ,ki dena tunanin wani abu".Reyhana ta fad'a.

" Toh Nasreen fa zaki fad'a mata yanzu? "Mommy ta tambaya.

" Mommy ni ina ganin a bari nan gaba da kanta zata fahimci hakan".

"Idan yayi aure kina ganin baze kar'bi 'yarshi ba?"
"Mommy ya za'ai ya d'auke ta ,ni bazan yarda ba gaskiya".

" Toh ya zakiyi za'a cigaba da zama a haka ne?,kema wataran ai auren zaki ko wane namiji ne ze ri'ke 'yar da ba ta shi ba?"

Shiru tayi batace komai ba ta tur'bune fuska dan bata so taji ana maganar rabata da Nasreen d'inta.

"Baki ce komai ba?" Mommy ta fad'a.

"Toh Mommy ai bece ze kar'beta ba".
" Lokaci na zuwa,Ummansa ta nuna min wacce ze aura". Mommy ta fad'a.

Wani iri taji jin abinda Mommy ta fad'a, abu de yana shirin tabbata, gaske ne abinda take tsammani Ahmad Zainab ze aura?"
"Kema ya kamata ki kira Umman tashi ki bata ha'kuri ". Mommy ta fad'a.

Se lokacin ta bar tunanin da take ta amsa da " Toh".

Har bayan ta koma d'akinta bata dena tunanin abinda Mommy ta fad'a mata ba.

°°°

Bayan fitar Mommy daga gidan Umma take tambaya Ahmad shirye-shiryen biki ,shi sam baya so take tuna masa.

Duk abinda ta tambayeshi "uhm" kawai yake ce mata, ganin Mommy yasa ya sake karkata wajen Reyhana yana ganin yanzu baida wata matsala gameda dawo da Reyhana tunda Mommy ta ha'kura.

8pm yana d'aki lokacin, number Reyhana yayi dialing ba kamar koyaushe ba yau a kiran farko tayi picking.

"Assalamu Alaykum". Tayi sallama.

" Waalaikumussalam". Ya amsa.

"Nasreen d'in tana kusa?" Ya tambaya.

"A'a". Ta amsa.

" Ok toh shikenan". Ya amsa sannan ya kashe.

Wayar tabi da kallo ta rasa ma mey zata yi,ba abind a ya bata haushi kamar yadda ya kashe maimakon ita ta zama ita ce ta katse.

Washegari kamar yadda Mommy ta fad'a haka tayi, ta kira Umma ta bata ha'kuri.

Tana ajje wayar sega Walida ta shigo d'akin.

"Yaya ga ya Sameer yazo shida sisters d'inshi".

" Yanzun?" Ta tambaya.

"Ehyi suna parlor". Ta amsa.

"Toh kice musu ganinan".Ta amsa.

•••

Yau Ahmad da kanshi ya d'akko Nasreen ze kawo ta gida ,tun daga nesa Nasreen ta hangi motar Sameer.

" Kalli motar Uncle Sameer yazo gidanmu".Ta fad'a tana nuna motar.

"Uncle Sameer?" Ya tambaya.

"Eh Uncle Sameer". Ta fad'a.

Seda suka 'karasa ya lura da Reyhana da take tsaye a 'kofar gidan gefe kuwa Sameer ne suna magana amma besan mey suke cewa ba.

Ita kuwa Reyhana rakiya ta fito koda sisters d'in nashi suka shiga mota Sameer ya tsayar da ita suna magana sega Ahmad.

Yana parking Nasreen tayi sauri ta fito " Ummie yau Uncle ne ya kawo ni!" Ta fad'a tana 'karasawa inda sike.

Sameer se lokacin ya dubi motar ya hangi Ahmad sannan ya dawo da kallonsa kan Reyhana.

"Ahmad, shine mahaifin Nasreen". Reyhana ta fad'a.

Kai ya d'an gid'a sannan ya mayar da kallonsa kan Ahmad.Da Ahmad beyi niyyar fitowa ba amma ganin Sameer yasa ya fito ,a hankali ya tako har inda sike.
Yana 'karasawa wajensu ya mi'ka wa Sameer hannu su gaisa,beyi musu ba ya mi'ka masa shima.

       Sede kowa a zuciyarsa da abinda yake tunani.Ita de Reyhana ido ne nata.

         "Sannu koh". Ahmad ya fad'a yana kallon Reyhana
    
          " Yawwa".Ta fad'a ciki-ciki.

       Daga haka ya wuce ya shiga gidan,yana gaisawa da Mommy ya fito dede lokacin Reyhana tana shigowa.

       Kallo d'aya tayi masa ta d'auke idonta ta wuce ta barshi a tsaye ta shige,shima ba tare da yayi magana ba ya fita ,har ya koma gida be dena tunanin Sameer daya gani ba.

        Lokacin daya shiga parlor Umma bata nan se Zainab.

      "Sannu da dawowa ya Ahmad". Ta fad'a.

        " Yawwa".Ya amsa.

         Shiru ne ya ziyarci parlorn kafin daga bisani Zainab ta sake wata maganar.

        "Yaya naga sa'ko na gode". Ta fad'a.

       " Uhm?" Ya tamabaya cikeda neman 'karin bayani.

       "Na agogo da ka bada a bani". Ta fad'a.

        "Uh..ok". Cewar Ahmad yana tunane-tunane.

       " Sadiq?" Ya fad'a a ransa.

       "So ,shine ya bata agogo yace ni na bashi ya bata.." Ya fad'a a ransa.

       "Ka dawo kenan" Umma ta fad'a sanda ta shigo.

        "Eh na dawo". Ya amsa.

         Tashi yayi ya fita ya koma d'akinsa ya d'auki way a ya dannawa Sadiq kira.

       " Na zee".Sadiq ya fad'a yana dariya.

        "Sadiq zan maka wula'kanci". Ahmad ya fad'a.

        " Daga nayi maka abin arzi'ki,dan'kon soyayya na 'kara maku fah".

        "Bana son irin wannan ". Cewar Ahmad kamar yana ganinsa.

        " Kode kishi kake? Gaya mini in baka so nake mata magana sena dena".
        "Ni na saka ka saya mata agogo har kace nina ce ka bata?"
        "Beyi kyau bane agogon?" Sadiq ya tambaya cikeda rainin hankali.

     Ahmad dan tsabar takaici kashe kiran yayi ,ya ajje wayar gefe.Tunani Sameer da Reyhana ne ya sake dawo masa a take ya d'auki wayarsa ya kira ta.

     Seda ya kira sau uku tukun tayi picking.

    "Assalamu Alaykum". Tayi sallama.

     " Waalaikumussalam,nayi sa'a an d'aga min  kira". Ya fad'a bayan ya amsa.

      "Eh ai saboda ban gane number d'in ba shiyasa banyi picking da wuri ba". Ta fad'a.

     " Au dama har yanzu number ta bata chanchanta ayi saving ba?"

       "Eh". Ta amsa a ta'kaice.

         " Toh yanzu ina fatan kingane mey magana?" Ahmad ya tambaya.

           "Ina fatan bazaka sake yimin irin wannan tambayar ba?"
       "Ni na isa". Ahmad ya fad'a.

        "Reyhana wannan dana ganku tare waye?" Ahmad ya tambaya dan sam hankalinsa ya kasa kwanciya.

     "Ina ruwanka dashi?". Reyhana ta fad'a.

STORY CONTINUES BELOW
      " Kawai inaso na sani neh". Ya fad'a.

      "Toh ,shine wanda zan aura". Ta fad'a cikin rashin nuna damuwa.

       Shiru yayi na d'an lokaci kafin yace." Toh Allah ya tabbatar da alkairi".

      Ita kuwa ta amsa da "Ameen".

     " Nasreen fa?" Ya tambaya.

      "Tana wasa". Ta amsa.

     " Ok,kinji Mommy tace za'a kawo ta wajen Umma tayi kwana biyu koh?"
      "Uhm". Ta amsa duk da kuwa bata san anyi hakan ba.

     " Kinga daganan semi ri'keta kawai idan tanaso". Ahmad ya fad'a.

     "Da fitowa kai fili ka fad'a kana yin aure zaka kar'beta daya fi  kwane-kwanen da kake".Ita kanta batasan zata fad'i haka ba,se da ta fad'a taji haushin kanta kar yace koh kishi take.

       " Ni nace maki zan kar'beta? A ina kika ji ma zanyi aure".Ya tambaya dan besan ta sani ba.

       "Base ka 'boyen ba naji ,wannan be shafen ba kawai de inaso ka sani tunanin ka kar'bi Nasreen ma ka dena dan bazan ta'ba yarda wata tayi mini ri'kon 'yata ba I can do it my self". Ta fad'a.

      "Karki damu tare zakui". Ya fad'a.

       " Mean?"
        "Ga Ummienta ga Auntynta se wadda ta za'ba ai ana tare".
     Yanzun ta gano inda ya nufa aiko da saurinta tace" Allah ya kiyaye".
      "Zamu zama happy family  fa".

       " Bade dani ba chan ka samo wata,ka dena wannan tunanin".
      "For Nasreen". Ahmad ya fad'a.

       " Na fad'a maka ina tare da ita,abinda kake fad'a ma is not possible ".

        " Reyhana kina so kice kin mance da rayuwar mu ta da,bakyaso mu komo...."Be 'kare maganar ba ta katse shi.

      "Maganar baya ta wuce, am hanging". Ta fad'a.

      " Reyhana.. ". Ta katse wayar.

       Wani saban tashin hankali ne ya tunkareta,batajin zata iya zama da kishiya haka bazata yarda a d'auke mata Nasreen d'inta ba koda wuni d'aya ne ,imagine ta shiga yi wai gata ga Zainab a matsayin kishiyarta Ahmad mijinsu.

     " This is not going to happen ". Ta fad'a tare da dafe kai.

       Ko fita parlor ta kasa yi tunani ya addabe ta ji take kamar ta tsala ihu.

°°°
     Ita kuwa Zainab koda ta koma d'akinta agogon ta d'akko se kalleshi take tana jin dad'i a ranta." Watoh nauyi yake ji shine ya kasa bani da kansa, my Ahmad kwai miskilanci". Ta fad'a a ranta.
          
       Ciro shi tayi daga box d'inshi ta saka a hannunta se kalla take tana yaba kyan agogon.

              
STORY CONTINUES BELOW
                      ***
   Kullum abu gaba yake ranakun aure suna matsowa , wata weekend da akai Mommy tasa Sageer ya kai Nasreen gidan Umma tayi kwana biyu lokacin ma Ahmad yayi tafiya.Reyhana a kwana biyunnan kamar tayi musu ihu dan koyaushe tazo kwanciya Nasreen d'inta seta fad'o mata a rai.

      Ahmad kam ta 'bangarensa abu sake 'karfafa yake dan a rana idan beyi mata text sau biyar ba toh yayi sau uku shi da gaske yake so yake ta komo,bama ya tuna cewa ga abinda ke gabatowa.

         Yau wani weekend d'in ya sake zagayowa ,a cikin yaran Anty Ummi ake bikin d'aya daga ciki su Ikram se shirye-shirye sike banda Reyhana da tana zaune koh kayan fita bikin bata sa ba.

       Mommy kuwa tin safe tana gidan uwar biki ,su se yanzu 4pm sike nasu shirin ,Nasreen ma anyi mata kwalliyarta dan yau da ita za'a coz ba dinner bane.

        "Ummie ki shirya dan Allah mu tafi". Nasreen ta fad'a.

        " Ke ki rabi dani ".Reyhana ta fad'a.

         Tana nu'ku-nu'kunta da ta saba a haka ta gama shirin wajen 5pm lokacin, kowa ya gama shiryawa.

        Wannan karan da Walida da Ikram ne sukai anko ,ita Reyhana nata tasa daban.Maroon lace tasa wanda ya amsheta sosai tasa golden gyale.

      Tana shirin fita daga d'akin ta jiyo muryar Sameer a parlor yazo.Shi besan ma da fita bikin ba seda Nasreen take fad'a masa.

      Sam bata so zuwansa ba haka ta sauka suka gaisa.

     " Dukanku zaku fita?" Ya tambayeta.

       "Eh"Ta amsa.

        " Ok idan ba damuwa ai sena kaiku".Ya fad'a.

        "Da ka bari ma". Ta fad'a.

         " Yaya Bassam seya kaimu kawai a motarki ku kuma..."Bata bari Ikram ta 'kare  maganar ba ta galla mata harara.

       "Yes shikenan ma haka za'ai". Sameer ya fad'a.

       Zata sake magana sega kiran Ahmad yana shigowa a,da farko 'kin d'agwa tayi se'a na biyu.

        " Assalamu Alaykum".Tayi sallama
   
     "Waalaikumussalam". Ya amsa.

       " Gani a waje".Ya fad'a.

        "Toh se akai yaya?" Ta tambaya a hankali yadda bazasi jiyo ba dan ta d'an matsa nesa dasu.

      "Nifa ba gunki nazo ba Mommy nazo gaisarwa". Ya fad'a wanda a ransa ba haka bane kuwa itan de ta kawo shi.

       " Mommy kuwa bata nan ba".Ta fad'a.

       "Nasreen fa?" Ya tambaya.

        "Fita zami muma ka bari gobe".Ta fad'a.

         " Aiko shigowa zanyi idan bazaki bari tazo ba".Ya fad'a.

          "A'a gatanan zata zo". Tayi saurin fad'a dan bata so su had'u da Sameer.

        " Am waiting ".Ya fad'a yana dariya dan yadda tayi saurin maganar yasa shi yin dariya.

       " Nasreen".Ta kira ta.

       "Jeki ga Uncle chan yazo kiyi sauri ki dawo". Ta fad'a.

        Da sauri kuwa ta fita tana zumud'i." Uncle kaga nayi kwalliya".Ta fad'a sanda ta 'karasa.

    "Inye! Kinyi kyau sosai ina za'a ?" Ya tambaya.

      "Biki zamu Uncle Sameer yace ze kaimu da Ummiena". Ta fad'a.

        Wani irin haushin Sameer ne ya kamashi " Shine ma ze kaita watoh ,shiyasa bata so ya shiga gidan yanzu Sameer ya fishi a gunta?" Ya tambaya a zuciyarsa.

       "Uncle Ummiena tace nayi sauri na koma ". Nasreen ta fad'a.

      D'an murmushi yayi mata ya gid'a kansa ,da sauri ta koma tana bye-bye ta shige gida.

     Ahmad tunani ya shiga yi ta yadda ze 'bullo da al'amarin,baya jin ze iya jurar ganin Reyhana da wani a mota d'aya ma da sunan za'a kaita biki " Nasan tayi kwalliya ma ,oh shikenan yaga kwalliyanta".Wata zuciyar tasa ta fad'a.

    Tunani yayi ko ya tafi kawai ya huta ganin takaici,a sanyaye har ya bud'e 'kofar motarsa ze tafi wani idea ya zo masa.A take ya saki wani makirin murmushi  da ban ta'ba ganin yayi ba.

      Kalle -kalle ya shiga yi a wajen kamar mey neman wani abu ,can daga  gefe ya gano wata 'kusa doguwa me tsini,da sauuri ya dur'kusa ya d'auka be tsaya a ko ina ba se jikin motar Sameer.Tayar baya ya zage ya chaka mata 'kusar har seda ta sace haka d'ayar ma yabi ya sace na gaba kawai ya bari.Allah yaso ba mutane a layin, ba wanda ya ganshi(😂😂 believe me da'kyar na iya typing d'innan saboda dariya ,bansan Ahmad da irin wannan muguntar ba😂😂😂).

   Komawa yayi jikin motarsa ya jingina harda crossing arms ya basar.
Su Bassam ne suka fara fitowa Ahmad yana tsaye suka wuce a mota,su kuma su Reyhana lokacin suke fitowa da Sameer,Nasreen tana tsakiyarsu.+

     Wani irin takaici yaji a ransa ji yake kamar ya sha'ke Sameer.Haka ya daure har suka 'karaso jikin motar Sameer.

      "Shikuma mey yake be tafi ba?" Reyhana ta tambaya a zuciyarta sanda ta lura da Ahmad.

     Kau da kanta tayi tana tsaye jikin motar.Sameer ya sakankance ze bud'e gidan gaba yaga d'anyan aiki.

     Taya tayi da'bas kamar ta shekara da sacewa,se yanzu daya waiwayo ya lura da Ahmad da idonsa akan wayarsa yana tapping kamar besan suna wajen ba.

      Dubawa yayi bayan mortar ya d'auki spare taya ,nan ya sake ganin tayar d'ayan side d'in a sace gashi spare d'in d'aya ne koya sauya ma seya gyara d'ayan.

      Indan Reyhana take ya 'karaso yake fad'a mata abinda ya faru.

     "Toh bari ma sami ko Napep ne". Reyhana ta fad'a.

      " Ummie mun fasa zuwa unguwar?"Nasreen ta tambaya.

        "A'a zamu..." Bata 'karasa ba sega Ahmad tsaye ya 'karaso wajen.

         "Da matsala ne?" Ya tambaya yana kallon Sameer.

      Shiru yayi masa be amsa shi ba se Reyhana ce tace "A'a".

     " Uncle ka kaimu kaga wai motar Uncle ta lalace".Nasreen ta fad'a.

      "Ayya! Do you need help?" Cewar Ahmad yana wa Sameer wani kallon tara saura.

       "No need". Sameer ya fad'a.

         " Ummie mu tafi".Nasreen ta fad'a cikeda 'kosawa.

        Sameer ganin yanda Nasreen ta 'kagu a tafi yasa ya shawarce ta Ahmad ya kaisu dan yasan gyarannan bana yanzu bane.

     "I think it will be better Ahmad ya kaiku kinga lokaci yana 'kurewa and kinga Nasreen ma ta damu". Sameer ya fad'a.

      " Don't worry zami iya jira ma". Reyhana ta fad'a dan ta tura wa Ahmad.

       "Don't mind ,it's ok like that kuje kawai". Sameer ya fad'a.

       " Ummie mije". Nasreen ta fad'a tana jan hannunta.

       "Mije koh". Cewar Ahmad fuskarsa d'auke da murmushi mey nuna fassarori.

      Rolling eyes tayi badan tanaso ba ta tafi zuwa motar shi.Ahmad harda bud'e mata gidan gaba aiko ta'ki shiga ta shige baya,Nasreen kuma ta shiga gaban.
       Ahmad basarwa kawai yayi ya zagaya ya shiga mota,harda wani gyara morror na ciki yana kallo Reyhana da ta kau da kai tana kallon waje.

     Sameer yana tsaye suka bar layin haushi ya isheshi ya daki tayar motar da 'kafa gumm! Ya bige 'kafa." Ahhg!" yai  'yar 'kara.

    Tunda ta fad'i sunan gun da zasu bata sake magana ba, tafiya ake shiru bame cewa komai sai Nasreen jefi-jefi tana wa Ahmad hira.

      Radio yayi turning on channel d'in da sike saurara akai playing wa'kar india "Zaalima"

Jo tere khatir tadpe pehli se hi,kya usse tadpana🎶

O Zaalima o zaalima🎶

(The one who is already longing for you,
Why torment him even more?
he one who is already misled for you,
Why mislead him even more)?

STORY CONTINUES BELOW
Jo tere ishq mein behka pehle se hi,kya usse behkana🎶

O Zaalima o zaalima🎶

(The one who is already longing for you,
Why torment him even more?
he one who is already misled for you,
Why mislead him even more?)

Ankhein marhaba 🎶

Baatein marhaba🎶

Main sa martaba 🎶

Deewana hua

(Your eyes are great,

Your talks are great
I am crazy for you a hundred times over)

Mera na raha🎶

Jabse dil mera🎶

Tere hudn ka🎶

Nishana hua🎶

(My heart ceased to be mine,
Since it became a target of your beauty)

Jisku har dhadkan tu ho aise🎶

Dil ko kya dhadkana🎶

O Zaalima o zaalima🎶

(The one whose every heartbeat are you,
Why quicken his heartbeat?
O cruel one!)

Saasson mein🎶

Teri naz deekiyon ka🎶

Ittar tu ghol de-ghol de🎶

(Mix the perfume of your closeness In my breath)

Main hi kyun 🎶

Ishq Zaahir Karin 🎶

Tu bhi kabhi bol de..bol de🎶

(Why I alone should express my love,
You too express your

Le ke jaan hi🎶

Jayega meri🎶

qaatil har tera🎶

Bahana hua🎶

(Your every excuse is a killer,
It will definitely kill me)

STORY CONTINUES BELOW
Tujhse hi shuru🎶

Tujhpe hi khatam🎶

Mere pyar ka🎶

Fasan hua🎶

(The story of my love Commenced
and culminated at you)

Tu shamma hai to yaad rakhna🎶

Main bhi hoon parwana 🎶

O Zaalima o zaalima🎶

(If you are a candle, remember that
I am a moth (Moth is attracted to the flame)
O cruel one!)

Deedar tera milne me baadhi🎶

Chhote meri angdaayi🎶

Tu hi bata de kyun Zaalima🎶

Main kehlaayi🎶

(I pandiculate only after I see you
Now you tell me,
why I am called cruel?)

          Wa'kar har ya gama playing Reyhana bata kalle shi ba ,ta sani yana sane ya 'karo volume d'in.

      Zaalima (lol)

       Yana parking Nasreen ta fara fita se itama Reyhana tayi saurin yun'kurin bud'e 'kofar Ahmad yai saurin kullewa.

        "Ka bud'e min na fita".Ta fad'a ba tare da ta kalleshi ba.

        " Why are you punishing me like this Reyhana?"Cewar Ahmad bayan ya waigo.

       "Kaide kake punishing kanka".Ta fad'a.

       " How?"Ya tambaya.

        "Please ka bud'en na fice". Ta fad'a.

        " Naji zan bud'e miki amma sekin amsan tambayar da zanyi miki".
       Banza tayi dashi bata ce komai ba ta kauda kai.

      "Do you really love him?" Ya tambayeta.

       D'an murmushi tayi ta kallo shi"Yes i do meyasa zaka damu kanka?"

     "Saboda nasan 'karya ne, ba kya sonshi I can see it in your eyes"

     "Really?"

     "Yes,Reyhana ki dena pretending nasan you still love me ,don't worry bazaki zauna da kishiya ba". Ahmad ya fad'a.

  " Tunda na amsa maka ai yanzu seka bud'e min koh".Ta fad'a.

     "Fine ". Ya fad'a sannan ya bud'e 'kofar ta fita,ko waiwayowa batai ba ta shiga wajen taron.

         Se bayan ta shige tukun ya tafi.

                    ***

   2days later°•°

         Nasreen a kwana biyunnan tana fama da rashin lafiya ,an kaita asibiti amma zazza'bi ya dawo.

      " Reyhana ki kira Ahmad ki fad'a masa yarinyar nan bata da lafiya". Mommy ta fad'a.

STORY CONTINUES BELOW
      "Mommy ki bari kawai zan maida ita da kaina base an fad'a masa ba".

      " Koh kin kaita da kanki ai ya kamata de ki fad'a masa koh". Cewar Mommy.

      "Toh". Reyhana ta fad'a.

      Tare da Walida suka tafi asibitin Nasreen se kuka take tana shagwa'ba,doctor na duba ta aka ce se an mata 'Karin ruwa zama ya kamasu.

      Hakannan bayan an d'aura mata drip ta kira Ahmad ta fad'a masa.Aikoba jimawa yazo wajen 12pm lokacin.

       " Uncle". Nasreen ta kira sunanshi murya a sanyaye.

      "Sorry kinji  zaki sami sau'ki". Ya fad'a yana dafa goshinta da zazza'bin ya soma sauka.

       "Meyasa baki fad'a mini da wuri ba?" Ya tambaya yana kallon Reyhana.

       Shiru tayi bata amsa shi ba sema phone d'inta data d'auko a jaka ta fara tapping.

         Ahmad ganin tayi masa banza bata yi masa magana ba ya tura mata da text.

    Ana yi miki magana kin'ki amsawa why?

Se lokacin ta d'ago ta kalleshi sannan ta kauda kanta.

         Gefe ya samu ya zauna ya kira Umma yake fad'a mata.Tashi yayi ya fita bata san ina zaije ba shima be fad'a mata ba.

      Fruit ya siya masu da gasashshen chicken se takeaway da juice ya dawo ,fuskar daya gani a room d'in yasa ya had'e rai lokaci guda.

         "" Wannan banzan meya ke yi anan?"Ahmad ya fad'a a zuciyarsa.

        'Karasowa yayi ciki ya samu waje ya ajje ledar kayan sanna yaja gefe ya tsaya,kallon -kallon suka shiga yi da Sameer da take opposite dashi ,Reyhana kuma ta zaune gefen Nasreen da ta ri'ke mata hannu karta barta .

      Ahmad wata uwar harara ya watsa masa  shima Sameer ya mayar masa,yau ko gaisawar basi ba.

     Takawa Ahmad ya yi har kusa da Nasreen ya shafa mata kai yana mata sannu,ta gefen ido kuwa yana kallon Sameer yana so ya nuna  shine fa mey 'ya.Itama Reyhana ta gano haka amma setai kamar bata gansu ba.

         Bayan kamar 20min sega su Mommy da Abba kusan dukansu banda Sageer da Ikram.Suma shagwa'bar tayi ta musu tana nuna musu hannunta da aka saka mata carnular.

       Sameer ne ya fara tafiya kafin Ahmad dan se wajen 3pm hakan ma bawai ya tafi duka bane su Umma ya tafi d'aukowa.Mommy ce ta bud'e ledar taga siyayyar daya yo musu ta bawa Nasreen,Reyhana kuwa 'kinci tayi ,abincin da su mommy suka kawo shi ta ci.

         Reyhana da batai tsammanin ganin Zainab a asibitin ba tasha mamaki ganin su tare da Umma ,a zuciyarta tana fad'in."Haka ta girma yarinyarnan?"

      Kamar bazata amsa gaisuwa ba Reyhana tace "Lafiya".Bayan Zainab ta gaisheta.

         Ahmad yana kallonta ya gano sauyin fuskarta suna had'a ido ta watsa  masa
harara ,shi dariya ma ta bashi kai de basarwa yayi.

      " Anty Zainab anan zaki sauna?" Nasreen ta tambaya.

       Murmushi tayi mata ba tare da ta amsa ba.

     "Ai ba kwana zami anan ba anjima zamu tafi".Reyhanana ta fad'a tana kallon Zainab.

       " Kijimin mata kallonnan na miye kuma?"Zainab ta fad'a a ranta.

       Da Umma suka tashi zasi tafi Nasreen tace ita  a lalle se Zainab ta zauna,haushi du ya ishi Reyhana .Mommy tace toh su sesi ragewa Umma hanya anjima Zainab sesu tafi da Ahmad.

      Haka kuwa aka yi Umma tabi su Mommy ,aka bari daga Zainab ,Reyhana se Ahmad.Shuru ne ya ziyarci d'akin bame magana itama Nasreen d'in ta gaji.

     Zainab a gefenta na dama Reyhana a hagu Ahmad yana daga gefe.

        Lokacin maghrib ya yi Ahmad ya fita  sallah ,bashi ya dawo ba se bayan isha'i.Yana shigowa yaga doctor yazo ,lokacin za'a sallamesu.Duk wani charges Ahmad ne ya biya ,sannan suka fito tafiya.

      Ya d'auki Nasreen da ta langa'be a kafad'a."Ni ba a gaba zan zauna ba ,a baya nakeson kwantawa ".Nasreen ta fad'a lokacin da suka 'karaso jikin motar.

        Bayan ya bud'e ya kwantar da ita tukun ya bud'e nashi gidan gaban.A tsaye ya gansu kowacce bata Shiga ba  ,suna daga bayan,kowacce a ranta tana tunanin mey shiga gidan gaba.

     " Ko a zuwanma a gidan gaba ta zauna ?da alama yanzun ma so take ta zauna ,Chab! aiko sede ta zauna a baya".Cewar Zainab.

     "Rawar jiki kike ki Shiga gaba? aiko sorrynki gaba nake dake yarinya duk da ba son shiga nake ba yau sena zauna let me see tsakanin nida ke waya fi damuwa da ita ,naga duk wannan kurarin da ake a iya ina ya tsaya son". Reyhana ta fad'a tana matsawa gaba.

      " What is she trying to do ? Matar nan itace mey 'kin shiga gaba amma yanzu ,she is looking for trouble ,wait itama Zainab shigar take so tayi?"Ya tambayi kansa lokacin da yaga itama Zainab tana matsowa.
Ahmad ya kasa cewa komai yana kallonsu,Reyhana wani kallon tara saura tayi mata tun daga sama har 'kasa sannan ta 'karasa bakin 'kofar ta bud'e ta shige cikeda ta'kama.+

     Zainab baki ta saki taga 'karfa-'karfa,chak ta tsaya batada alamar shiga motar.

     Ahmad ne yai mata alama ta shiga baya lokacin da suka had'a ido ,seda taci 1min tukun ta shiga baya ta ra'be gefe haushi ya isheta.

    Shiru kowa yayi a ransu kowa da sa'ke-sa'ken da yake. A haka har aka 'karasa gidansu Reyhana ,yana parking ta fito daga motar ko takan Nasreen bata bi ba tasan dole ze d'akkota kuma da biyu tayi hakan dan ta sake ba'kanta wa Zainab.

       Bayan ya fito ya bud'e gidan baya ya d'akko ta ,tayi nisa ma da bacci.

      Zainab lokacin da taga yana fitowa daga gidan ta kauda kanta ta sake had'e rai,tunda ya shigo motar ya fiskanci hakan.

      "Ki dawo nan gaba". Ya fad'a.

       Yitai kamar bata ji ba seda ya sake maimaitawa tace.

        " A'a nan ma yayi".Ta fad'a muryarta ciki-ciki.

        "Zainab ki dawo nace".Ya fad'a wannan karan ya waiwayo.

        Bata sake cewa komai ba ta fita ta koma gaba tare da rufo 'kofar da 'karfi.

       " Fishi kike da Antyn taki?" Ahmad ya fad'a bayan ta shigo.

       "Anty ta". Ta maimaita tare da ta'be baki.

       "Ehmana ko kin mata ita Antynki ce?"

        Shiru tayi bata sake wata maganar ba tana kallon waje har suka  isa gida.

     Tunda suka shiga gida ta shige d'akinta takaici ya isheta.

                  ***

      Reyhana bayan tafiyarsa ta kai Nasreen d'aki ta kwantar da ita,tunani ta shiga yi na abinda ya faru,murmushi ta tsinci kanta tana yi ."Ko zata koma gaban oho mata".Ta fad'a a zuciyarta.

       Tana wannan batun sega kiran Ahmad ya shigo wayarta,yau a karan farko tayi picking.

      "Assalamu Alaykum". Tayi sallama.

       " Waalaikumussalam"Ya fad'a.

        "Ya jikin nata?" Ya tambaya.

         "Da sau'ki har yanzu bacci take". Ta fad'a.

          "Ok,toh idan ta tashi karki manta ki bata magani".Ya fad'a.

          " You don't have to mention dan bazan manta ba".Reyhana ta fad'a cikin sanyin murya.

      "Kina so kice kin fini damuwa da ita kenan" Ahmad ya fad'a.

       "Toh wa zai had'a ma". Cewar Reyhana.

        " Haka de kika ce ,itama ai ta sani".Ya fad'a.

        "Cabb! Waya fad'a ma nide kullum kodayaushe muna tare ko bacci baya raba mu".

      "Kwana nawa ne zan d'auke ta". Ahmad ya fad'a.

      " Ba inda zata".Reyhana ta fad'a.

       "In kina so ki zauna tare da ita seki biyo ta". Ya fad'a.

       "Hmm".
       " Hmm meh?"Ya tambaya.

        "Babu ,am hanging now". Ta fad'a.

STORY CONTINUES BELOW
       "So kike ki wayance de ,shikenan toh goodnight". Ya fad'a.

        " Ok ,ka gaida Umma". Ta fad'a.

         "Kinyi mantuwa". Ya fad'a.

          " Name fa?" Ta tambaya tana neman bayani.

          "Baki ce kina gaida Zainab ba". Ya fad'a.

           " Goodnight ". Ta fad'a tare da katse wayar.

      Hakan yasa shin yin dariya ,text ya tura mata tukun ya ajje wayar gefe.

       Ta ajje wayarta taji sa'kon text tana dubawa taga Ahmad ne ya turo.

        
"Your eyes are great, your talks are great I am crazy for you hundred times over
I love you very much,goodnight Azizaty❤"

      A take ta soma blushing ta kasa dena maimaita karanta text d'in,har ta kwanta text d'in yana mata yawa a kai.

   °°°

    Washegari Nasreen ta samu 'kwarin jiki  sosai ,bayan tasha magani ta takura Reyhana ta kira mata Uncle dan ya kira da safe lokacin tana bacci.

     Numbern sa tayi dialing shiru har ta katse beyi picking ba,na biyu ma haka be d'aga ba.

     Ahmad kuwa lokacin suna hanya ze kai Zainab makaranta sannan ya wuce aiki ,ya tsaya a gidan mai be jima da fita daga motar ba sega kiran Reyhana.

     Zainab tana le'kawa ganin "Azizaty❤" ta share kiran koda Ahmad ya dawo bata fad'a masa an kira ba shi kuma be samu ya duba wayar ba suka tafi.

       Reyhana jitai ba dad'i ganin lokaci ya sake ja be ko kira ba,tayi tsammanin kiransa amma taji shiru dan haka itama bata sake kira ba.

      Se wajen 12pm ya lura da missed call d'in,ba 'bata lokaci yayi calling back,se a karo na biyu tayi picking.

       "Assalamu Alaykum".
        " Waalaikumussalam"Ya amsa.

         "Sorry kin kira bana kusa seyanzu naga kiran" Ya fad'a.

        "Tun fa d'azu kusan 3hr baka gani ba?"
         "I am sorry Ummien Nasreen kinji ai min afuwa". Ya fad'a.

        " Ga Nasreen zaku gaisa". Ta fad'a.

        "Toh ai baki ce kin ha'kura ba".
        "Naji toh shikenan". Ta fad'a.

        " Thank you".
        Nasreen tasa wa wayar a kunne"Ga Uncle ". Reyhana ta fad'a.

         " Uncle". Ta kira sunanshi.

           "Nasreen ya jikinki ?" Ya tambaya.

            "Da sau'ki Uncle yaushe zaka zo?" Ta tambaya.

          "Anjima zanzo ,kinsha magani?"
          "Eh". Ta amsa.

            " Yawwa toh mey kike so na kawo maki?"

        "Chocolate". Ta fad'a.

         " Good girl,zan kawo miki kinji ,ina Ummie?"
        "Gata nan". Ta fad'a.

STORY CONTINUES BELOW
        " Yawwa toh bata wayar".

       Mi'ka mata wayar tayi ,Reyhana ta amsa.Ahmad ya cigaba da janta da surutu.

     •••

   Waya se abinda ya 'karu dan yanzu Reyhana bata 'kin d'aga wayarsa gashi ta dena jin haushin 'kwata-'kwata hira suke yi sosai,da kanta ma kira take ta bawa Nasreen su gaisa bayan nan kuma sesu 'bige da waya.

                   ***
 
3 weeks later biki yana ta matsowa a yanzun Ahmad ya damu sosai dan ko zama be fiya yi a parlour ba balle Umma tayi masa zancen bikin a yanzu ana maganar lefe ,tun jiya Umma take masa maganar amma ya'ki tsayawa ma suyi maganar.

        Yau da ta gaji ta tare shi har d'aki ta soma yi masa maganar.

        "Kai shikenan kuma dan ance yarinyarnan 'yar uwakka ce kuma seka ke haka? Cha a kai ma auren bazawara ne?"
       "Umma zan fa bada ni kud'i kawai zan bada ba ruwana da wani lefe".Ahmad ya fad'a.

      " Toh har sai yaushe? Kud'in base a bayar da wuri ba".Umma ta fad'a.

      "Kaga yarinyarnan taje gida mey kake so tace da iyayenta? Ko kuwa so kake a d'aga bikin?"

      "Dama ai yakamata a d'aga". Ahmad ya fad'a.

      " Aiko baza'a d'aga ba ,mey make jira ? Gida ne ka gama kuma mey ya rage bazan zama mey baki biyu ba".

     "Amma Umm.." Be 'kare maganar ba ta katse shi.

      "Idan ma abinda kake tunanin gaske neh toh kama dena tuananin haka". Umma ta fad'a.

      " Mey fa?" Ya tambaya.

       "Reyhana, idan tunani kake ka dawo da ita ni bazan hana ka ba amma ba a wannan lokacin ba kaima kasani da farko kenan kuma abu na biyu shine inde Zainab bata son zama gida d'aya da ita ba bazaka had'asu ba".

       Shiru Ahmad yayi yana jin abinda Umma take fad'a shi sam ba haka yake so ba ,baida wacce tafi Reyhana a gunsa ita da Nasreen kawai yake burin yaga sun komo gareshi.

         "Kaji de mey nace maka". Umma ta fad'a.

         Daga haka ta tashi ta barshi yana ta tunane-tunane.

     
                    ***

  Reyhana a yanzu tana son komawa gidan Ahmad d'inta ,abu biyu ke bata tsoro shine aurensa da Zainab ga Sameer batasan ya zatai dashi ba.

      Yanzun ma tana d'aki tana tsammanin kiransa taji ya Umma zata d'auki abun dan cayai mata ze fad'a wa Umma amma ya kasa.

      A sanyaye ya d'auka waya ya kirata.

      " Assalamu Alaykum".Ta fad'a bayan ta d'aga.

       "Waalaikumussalam". Ya amsa.

       " Kayi magana da Umma".Ta tambaya.

     Shiru yayi bece komai ba tana tunanin ta ze soma bayani.

        "Reyhana..". Be 'karasa ba yayi shiru.

         " Ahmad i understand everything, na fad'a maka wannan ba abune mey sau'ki ba dole nasan Umma bazata ji dad'in haka ba kuma bazan so mu 'bata mata rai ba ,ina ganin kawai mu ha'kura".Ta fad'a.

       "No kidena fad'ar haka ". Cewar Ahmad.

       "Haka ne mana ,idan nayi haka banyi wa Zainab adalci ba d.."

      "Stop talking like this na fad'a maki,baza a kai wannan tsahon lokacin ba tare da kun kasance dani ba".

      " Mey kike tunanin yi?" Ta tambaya.

       "Kafin.."

       "Kafin ka auri Zainab na komo gidanka ? No bazan iya yin haka ba mey kake so Umma ta d'aukeni ? "

        Shiru yayi bece komai ba a zuciyarsa yana ta sa'ke-sa'ke,kowa da abinda yake tunani.Har suka 'kare wayar ba wani solution.

        Tunani ta shiga yi ko kawai ta ha'kura ta auri Sameer a huta.
Bayan kwana biyu Zainab ta dawo,jikinta a yanzu ya fara sanyi da auren wannan karan ko fad'a masu batai ba zata dawo kawai ganinta Umma tayi.

Shi Ahmad yana aiki daga nan d'in ma seya biya gidansu Reyhana tukun ze komo gida.Tunda tayi tafiya Zaria befi sau uku sukai waya ba satinta d'aya a can.

°°°
Reyhana tana jin sanda ya shigo parlour amma bata sauka 'kasa ba se Nasreen ce taje.Koda ya kirata 'kin picking tayi har ya tafi bata sakko ba.

Tana zaune Nasreen ta shigo tana murna hannunta ri'ke da leda "Uncle ya bani". Ta fad'a tana nuna mata.

" Toh naji ". Reyhana ta fad'a.

Kayan ciye-ciye ne kala-kala ya siyo mata.

•••

Koda ya koma gida d'akinsa ya shige besan ma Zainab ta dawo ba.

Yana zaune sega kiran Imran." Aboki yane?" Cewar Imran.

"Ya kua". Ahmad ya fad'a.

" Da matsala ne?" Ya tambaya.

"Kaima ka sani ai"Ahmad ya fad'a.

" Reyhanan de?"
"Ehyi ita".Ya amsa.

" Kaima ka bari se bayan wannan auren tukun ".

" For how long?"

"Duk yanda ya kai mana, kai da ka ha'kura da Zainab d'inka ma". Imran ya fad'a.

" Kai baza ka gane ba,tunda mike dake na ta'ba ce maka ina son Zainab? Imran nifa bana son yarinyarnan kawai de saboda Umma shiyasa zan ha'kura". Ahmad ya fad'a.

Zainab duk wannan zancen dayake yi a kunnenta ,tana tsaye jikin 'kofar d'akin sa.Umma ce ta sata kira mata shi ,zuwan da tayi ta riskeshi yana waya kunnenta ya jiyo mata wannan maganar.

Gwiwoyinta sinyi mata li'kis da 'kyar ta iya komawa d'akinta.Kuka mara sauti ta zauna ta shiga yi ba 'ka'k'kautawa.

"For all this long dama Ahmad be ta'ba sonta ba ,so Umma ce tasa ze aureta ashe ? Shiyasa baya nuna damuwa dani ". Abinda take fad'a a ranta kenan.

Umma jin shiru yasa ta biyo sawu ,Zainab na hango tahowar Umma tayi saurin goge hawayen ta.

" Zainab, naji shiru koh baya nan?" Ta tambaya.

"Yana.. yana zuwa". Ta fad'a.

Gid'a kai tayi tukun Umma ta fita ta koma d'akinta. Zainab sake goge fuskarta tayi sannan ta fita taje ta kira shi ,sam bata nuna alamar wani abu ba kuma shima be gano hakan ba.

D'akinta ta koma ta shiga wani sabon kukan ,tana son Ahmad sosai ba 'karamin ciwo abin yai mata ba duk wannan abun da take ashe shirmenta take,bata ga amfanin auren wanda bata so ba.Ta fad'a a ranta.

***
Sameer yau da yamma yazo gidansu Reyhana, da kanta ta kira shi tace tana so siyi magana a ranta ta gama yanke shawarar fad'a masa zata aureshi.

Bayan yazo sun gaisa da Mommy ta tashi ta bar musu parlourn Nasreen dama bata dawo daga school ba.

Bayan sun gaisa Reyhana tayi gyaran murya kafin ta soma magana.

"Ahma..uh..Sameer". Ta kira sunansa shaf ta mance ta kira shi da Ahmad.

" Dama ina so na fad'a maka shawarar da na yanke,uhn..Sameer na..."Be bari ta 'karasa ba ya katse ta.

"Reyhana base kinyi bayani ba na gano abinda kike so kice,na dad'e da fahimtar hakan ni kaina tun sanda naga Ahmad.."

STORY CONTINUES BELOW
"Sameer ba haka nake nufi ba n.."

"Karki damu kanki ,kada ki manta na fad'a miki duk abinda kike so shi nake so ,Ahmad shi yafi kowa dacewa dake ,ya kamata ku kasance tare".

Shiru tayi ta zama speechless dan bata zaci haka ba daga wajen sa.

"Amma Sameer.."

"Is ok don't worry,Ahmad is the best husband for you I know you still love each other ,you have second chance to be together Reyhana,don't worry about me am really happy for you".
Tausayinsa ne ya kamata sosai Sameer is a very kind person duk wani abu da zatai baya ganin laifinta kuma tasan yana sonta sosai and duk wani abunda take so shi yake so.

" I am so sorry Sameer ". Ta fad'a.

" Don't worry".Ya fad'a.

"Thank you".

" Don't mention". Ya fad'a fuskarsa d'auke da murmushi.

Itama murmushin ta mayar masa tana jin tausayinsa.

***

•°• 4 month later•°•
Reyhana ce zaune a parlour tana ri'ke da wayarta tana chatting da Ikram.

Reyhana: "Ke wannan status d'in fa ? 'boye fuskar mijin naki kike kar wasu siyi miki snatching"

Ikram: " Hhh ,shima haka yake min bara kiga"

Reyhana: "Iyye ,Amaryar Sameer.

Ikram: "Kinji yaya ,kema Amaryar Ahmad"

Reyhana: "Au ramawa zaki"

Ikram:"Toh ku ina naku pic d'in,a turon na gani".

Reyhana: " Kizo har gida tukun"

Ikram: "Nafi kowa son hakan"

Reyhana: "Sorrynki yarinya se nan da 3yrs😝"

Ikram:"Chabb! Nan da wani watan zan duro 9ja"

Reyhana:"Kiyu biyayya se a kawo ki"

Ikram: "Ha ,ina Nasreen 'yan mata?"

Reyhana: "Tana school"

Ikram: "Se ke kad'ai,gaskia ya kamata ayi mata 'kani da wuri"

Reyhana: "Kede mike jira yarinya 😝 da twins zaki duro 9ja"

Ikram:"Hhhh lokacin kinada 4 koh😋"

Reyhana: "Kin manta 7😎"

Ikram: "Lol"

Ikram: "Am waiting"

STORY CONTINUES BELOW
Reyhana: "What?"

Ikram:"Naku pic d'in"

Reyhana: "Ok"
1
Ikram: "😱 kinganki kuwa"

Reyhana: "Mey?"

Ikram: "Kinyi kumatu anya😂😝"

Reyhana:"Zan bige ki"

Ikram:"Ummien boy zan ke kiranki yanzu"

Reyhana"Ke kuma Maman girl"

Ikram:"Hehe wayaga"

Reyhana: "Hahaha kallo ze koma kanki yarinya"

Ikram: "Jeki girki kar habeebinki ya dawo💕"

Reyhana: "Ke kai"

Ikram: "Ai tare mike girkin"

Reyhana: "Iyye lovayya😻"

Ikram:"Ha"

Reyhana:"Toh ki gaisheshi inya dawo"

Ikram:"Ok bye "

Daga haka Reyhana ta sauka daga chat d'in ta shiga kitchen domin yi musu girkin rana.

A wata hud'unnan abubuwa da dama sun faru,Zainab da kanta ta fad'a wa Ahmad ta janye aurensa da Umma ta sani ba yadda batai da ita ba suma yayyin Umma da mahaifiyarta suka sata a gama kowa yana mamakin 'kinta na auren Ahmad da suka isheta ma kuka take sa musu haka ba yadda suka iya dole aka rabu da ita suka ha'kura ,Ahmad dama haka yake so. Ta koma Zaria ma dan ta kammala karatunta.

Shi kuwa Sameer ya koma wajen Ikram a kai sa'a ta amince,lokaci d'aya aka yi aurensu,Sameer da Ikram,Ahmad da Reyhana. Sameer ana yin biki suka tafi America,yau wata uku kenan da yin bikin su duka.

Nasreen 'yar Ummienta da Papa(sunan da take kiran Ahmad kenan).

Sadiq abokin Ahmad shima sati biyu kenan da yin aurensa ,se Imran shima yana shiri.

2:30pm,Reyhana ta gama girkinta ta sake gyara fuskarta se turare da ta fesa mey taushin 'kamshi tayi kyau sosai dark blue d'in doguwar riga mey dogon hannu tasa se veil 'karami Pink purple data yafa.

Not more than 10min sega Ahmad ya dawo,kafin ya dannan door bell ta bud'e 'kofar,tsaya wa yayi fuskarsa d'auke da murmushi yana kallonta.

"Come in". Ta fad'a cikin sanyayyar muryarta.

STORY CONTINUES BELOW
Yana shigowa ta kar'bi briefcase daya ri'ko.

" Welcome back ".Ta fad'a tare da hugging d'insa,shima yayi hugging back.

" My pretty cute Azizaty ".Ya fad'a.

" Kinganki kua". Ya fad'a bayan sunyi breaking hug d'in.

"Kamar karna dena kallonki". Ya fad'a.

" Toh yanzu mije kayi shower,kaci abinci".

"As you said". Ya fad'a.

Bayan kamar 20min ya fito sanye da T shirt fara se jeans blue,tana dinning table ta gama jere abincin.

Kujera taja baya ya zauna tukun ta zuba abincin a plate d'aya." Kinci abincin ?"
"A'a". Ta amsa.

"Har 3 fah ,Allah sarki my Azizaty nasan ni kike jira"
"Bana so kike zama da yunwa fa". Ya fad'a.

" Don't worry ai bana jin yunwa tunda ba da wuri nayi breakfast ba". Ta fad'a.

"Iyye wannan baccin irin na da ne ya dawo koh".

" A'a"Ta amsa tana dariya.

"Zama de mu gano ki gama 'boye-'boyen". Ya fad'a.

" Toh yanzu de muci abinci ". Ta fad'a tare da saka musu spoon biyu a plate d'in.

Basu dad'e da gama cin abincin ba suka ji knock ,Ahmad ne yaje bud'e 'kofar ,ga mamakinsa yaga Nasreen tsaye ita da Nanny d'in makarantarsu.

" Nasreen 'karfe nawa har kin dawo meya faru ?"Ya tambaya.

Tsaye tayi tana kallonsa bata ce komai ba tayi wani kalar tausayi.

"Bata da lafiya tana ta kuka shine aka ce na kawo ta gida". Nanny d'in ta fad'a

" Toh mungode".Ya fad'a tare da ri'ko hannun Nasreen suka shigo ciki.

Reyhana se yanzu ta 'karaso taga Nasreen.

"Mey zan gani ,ita wannan mey take yi a gida 'karfe 3?"

"Wai bata da lafiya".Ya amsa.

" Zonan".Reyhana ta fad'a.

'Karasawa tayi India Reyhana take ,Reyhana ta d'ora hannunta a wuyanta taji ba zafi .

"Anya ba 'karya kike ba".Ta fad'a.

Girgiza kai tayi ta sunkuya ta'ki d'agowa su had'a ido dan dariya ce ma'kale a fuskarta bataso su gano ta.

" D'ago kanki mey kike 'boyewa?".Reyhana ta tambaya tare da d,'ago ha'barta.

Aiko tana d'ago ta ta saki dariya tana ja da baya."Dama wayo nayi wa Anty nace banida lafiya cikina yana ciwo tace a kawo ni gida".Nasreen ta fad'a tana dariya.

Ahmad ya ri'ke baki tsaye yana kallonta ,ya rasa wannan iron wayo na Nasreen 'karama da ita ta iya tsara babba.

"Aiko sekin koma yanzunnan". Reyhana ta fad'a.

" A'a".Ta ma'kale kafad'a kamar zatai kuka.

"Zonan". Ta fad'a.

" A'a rabu da ita ,abinda ta riga da ta tafi".Ahmad ya fad'a.

"Ni da kaina zan maida ta". Cewar Reyhana.

" Dan Allah ki barni bana so na koma".Ta fad'a.

"Ki barta kawai tunda ta riga da ta dawo,karki sake kinji". Ya fad'a.

Kai Nasreen ta girgiza tare da fad'in." Toh Papa".

Gefe ta ma'kale tana yiwa Reyhana gwalo."Sekije ki cire uniform d'in".Reyhana ta fad'a ta bar wajen.

Ba musu ta tafi d'akinta taje ta kwa'be kayan ta zira skirt da shirt ta fito da kayan wasanta dama abinda take so kenan.

"Ai kya samu kici abinci tukun ko".Reyhana ta fad'a.

" Bana jin yunwa".Ta fad'a.

°°°
Bayan maghrib Ahmad ya dawo daga masjid,Nasreen tana ri'ke da wayarsa se game take tun sanda ya fita.

"Ki tashi kiyi Sallah na fad'a miki". Reyhana ta fad'a sanda ta fito parlour.

" Tashi kinji idan kin iddar seki cigaba da game d'in".Ahmad ya fad'a.

"Se a d'auken photo ko?" Nasreen ta fad'a.

"Eh". Ya amsa.

Da sauri-sauri tai alwala ta zira hijab tayi sallar sannan ta dawo ta zauna.

" Papa ayi mini".Ta fad'a.

"Toh zo ai miki". Ya fad'a

Matsawa tayi aka kyasta mata ,sukai tare daga baya Reyhana ma tazo.

" Banda me kuma". Reyhana ta fad'a.

"Ummie dani za'ai"

"No ke ba mey gudun makaranta ba,matsa min". Reyhana ta matsar da it's gefe.

" Rabu da Ummie zatai sake kinji". Cesar Ahmad.

Reyhana ce ta kyasta musu iya su biyu kowannensu fuskarsa d murmushi.
Alhamdulillah,a nan na kawo 'karshen littafinnan AR💖 ,ina mi'ka godiya ta zuwa gareku masu voting, readers 'boyayyu thank you very much.Ina godewa Allah daya bani ikon kammalawa,ina fatan an amfana da abinda ke ciki.

Post a Comment for "ARZIQI RABO CHAPTER C KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...