Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ARZIQI RABO CHAPTER B

ARZIQI RABO CHAPTER B

- - Post a Comment

 ARZIQI RABO CHAPTER B


Ahmad jin amsar ta yasa ya kasa sake cewa komai ,shiru dukansu sukai credit na tafiya.

       Mommy data ke tsaye a jikin 'kofar d'akin 'karasowa tayi kusa da Reyhanan.Wayar ta kar'ba daga hannun Reyhana ma'kale a kunnenta.

       "Ahmad yanzu abinda kayi ka kyauta kenan? Reyhana ta cancanci kayi mata haka?" Mommy ta fad'a.


       Ahmad jin muryar Mommy kamar daga sama yasa ya gyara tsaiwarsa da yana jingine a garu amma jin muryarta yasa ya mi'ke tsam.

       "Eyyi? Activities naka sunfi lafiyarta,ace tun shekaran jiya rabon da kayi waya da ita rashin damuwa da ita ne komey?" Mommy ta d'ora akai.
      
         "Mommy wlh wayata ce ta samu matsala se d'azu na kar'bo daga gyara jiya na kira a wayar umma bana samun ta". Ahmad ya fad'a.

      " Mommy dan Allah kiyi ha'kuri".Ahmad ya fad'a.
       
       "Kiyi ha'kuri". Ya sake bata ha'kuri.

      Mommy bata sake cewa komai ba wayar ta katse sakamakon credit daya 'kare.

      " Matalauci". Mommy ta fad'a.

         Reyhana taji abinda Mommy tace amma tayi kamar ba sauraro take ba.

     Ahmad kuwa ba tare da ya 'bata lokaci ba ya taho izuwa gidansu Reyhana.
     Seda yayi kusan 5min ya iya shiga gidan dan nauyin had'a ido da Mommy yaji balle Abba.

         Yana shiga tun a harabar gidan ya had'u da Sageer.Bayan sun gaisa ya 'karasa dashi ciki.

     A parlour suka tarar ba kowo dan haka Sageer ya hau sama ya sanarwa da Mommy.

        Babyn na hannu Mommy lokacin Sageer ya isketa.

      "Mommy gafa ya Ahmad yazo". Sageer ya fad'a.

      "Shine yazo?" Cewar Mommy.

      "Eh yana parlour". Ya amsa.

        " Toh ungo ta kai masa ". Mommy ta fad'a tare da mi'ka masa babyn.

         Hannu yasa ya amsa sannan ya fice.

          Itade Reyhana ko " a" batace ba kuma bata tashi ba .

       A parlour Ahmad yana tsammanin ganin Mommy amma yaga Sageer tafe da baby,bawai be damu da yaga babyn ba amma a yanzu Reyhanansa yake son gani.

      A sanyaye ya kar'beta daga hannun Sageer daya mi'ko masa.

       Yana mi'ka masa ya fita daga parlourn dan school ze koma, Ahmad daga shi se baby a hannunsa.Ji yake kamar ba 'yarsa ba saboda mamaki.Daya kalli fuskarta da idanuwanta suke a rufe a ziciyarsa yana me godewa Allah.

       Sunan da za'a saka wa babyn ne ya fad'o masa dan,tuna Reyhana data ce zata fad'a masa sunan da take so a saka wa babynsu ya shiga yi.

      A zuciyarsa kuwa yana fad'in ina ma yana nan ta haihu.

      Addu'oi yayi ma babyn ya 'kura mata ido yana sake ganin kammaninsa a fuskarta.

      Sakkowar Mommy ce tasa yayi saurin d'ago da kansa.So yake ya sakko 'kasa daga kan kujerar amma kuma ga baby a hannunsa,hakannan ya 'kwantar da ita a kan kujerar daga gefe ya sakko 'kasa.

      "Ina kwana ". Ya gaisheta.

      " Lafiya". Ta amsa.

       "Mun samu 'karuwa kuma ,Allah ya raya ". Mommy ta fad'a.

       " Ameen".Ya amsa a hankali.

       Yana so ya tamabayeta jikin Reyhana amma ya kasa, Mommy ta gano hakan kuma dama haka  take so shiyasa bata cewa Reyhana ta sakko ba.

STORY CONTINUES BELOW

       "Kaci gidanku bazaka ganta ba"Mommy ta fad'a a zuciyarta.

       Inno tasa ta kawo masa abin sha har lokacin Reyhana bata fito ba Mommy kuma ta bar parlourn.

      Wayarsa ya d'auka yayi dialing numbern Reyhana yaji ba kud'i dan haka yayi rance ya kirata.

      Tana jin wayarta tana ringing tasan shine,ya kira kusan 3× amma bata d'aga ba.

      Please pick my call am sorry.

      Ya tura mata,tana karantawa taji tausayinsa ya kamata ta sani haka kawai baze kashe wayarsa ba dole sede da dalili.

     Tana cikin wannan tunaninne tajiyo kukan baby da alama ta tashi.Sosai take tsala ihu Mommy kuma tana d'akinta ta shiga toilet inno ma tana sashen d'akinta bata jiyo ba.

      Reyhana jin shiru Mommy bata shigo da baby ba yasa ta sauka dan ta kasa jure kukan da babynta take๐Ÿ˜œ

    Wani sanyi Ahmad yaji a ransa ganin Reyhana kukan babyn ma be damesa ba.

     'Karfin hali tayi bata ce komai ba se tsayawa datai tana jira ya mi'ka mata.

       Mi'ka mata yayi idanuwansa yana kanta,ita kuwa bata bari sun had'a ido ba ta kar'ba.

      Ya kula da yanayin kumburin fuskarta da idanuwanta take yaji tausayinta.

     "Reyhana please kiyi ha'kuri kiyi min magana dan Allah". Ya fad'a a raunane.

     "Reyhana baki yarda da abinda na fad'a maki bane ? kinsan bazan barki ba ina sani koh please ki amsa min i am sorry".

        " Please ka barni yanzu de kaga kuka take".Ta fad'a.

       "Toh ki zauna mana anan ki..."

      Be 'kare ba sega wasu ba'kin suna shigowa parlourn,dan haka dole ya basu guri ya fita haraba ya zauna a kujera dake wajen.

      Umma ya kira yake fad'a mata tayi masa fad'a ,tace laifinsa ne.

     Reyhana zama tayi ta bata mama tasha tukun ta mi'ka musu.Mommy ta fito suka gaisa da ba'kin.
    
       Ahmad kuwa yana waje har lokaci ya sake ja ,kiran wayarta ya sake yi again shiru kuma tana d'aki ta lura da kiran ta'ki picking.

         "Am very sorry please forgive me" Ya sake tura mata text.

       Tana karance text d'in ya sake kira seda ta kusa tsinkewa tayi picking.

     "Azizaty kina son kasheni ne?"

     "Mey kuma nayi?" Cewar Reyhana.

     "Baki sani bama? Please ki saurareni dan Allah kiyi ha'kuri". Ya fad'a.

      " Kin ha'kura?"Ya tamabaya.

       Shiru tayi bata ce komai ba.

       "Please badan ni ba". Ahmad ya fad'a.

       " Toh naji".Reyhana ta fad'a.

       "Thank you so much Azizaty ,toh ya jikinki?". Ya tamabaya.

       " Da sau'ki".Ta amsa.

       "Are you sure?"

       "Sure". Ta amsa.

       " Sannu my Azizaty nasan babynmu ta baki wahala".

       "Maman baby wane sunan aka sama mana?" Ya tambaya.

      "Uh...sunan Umma". Ta amsa.

      " Are you serious? "Ya tambaya yana me mamaki dan sam be kawo hakan ba.

     " Yes".Ta amsa.

      "Nagode sosai,zan kira Umma yanzu na fad'a mata".Ahmad ya fad'a.

      " Kaga ma tana kirana".Reyhana ta fad'a.

      "Ok toh bara na katse ki amsa i will call u back". Ya fad'a.

       Bayan tayi picking call na umma tayi mata barka sannan ta sake bata ha'kuri.

       Suna gama waya da umma Ahmad ya sake kira.

       " Azizaty ban gaji da ganinki ba fa keda baby ya za'ayi ne?"

        "Ga baki basu tafi ba".Ta fad'a.

        " Azizaty kinsan ya za'ai?"

        "A'a". Ta fad'a.

         " Anjima da maghrib zan dawo tare da umma ma zamu zo kinga lokacin Abba ma ya dawo koh?"

          "Eh". Ta amsa.

          " Toh yanzu de kiyi wa Mommy magana zan tafi se miyi sallama".Ahmad ya fad'a.

       "Toh". Ta amsa.

        Tana gama wayar ne ma sega Mommy ta shigo.

      " Mommy ga Ahmad ze tafi yace zakuyi sallama"Reyhana ta fad'a.

     "Uhm waya kukayi kenan". Mommy ta fad'a tare da ta'be baki.

      " Yaran yanzu baku da zuciya".Mommy ta fad'a.

      "Mommy kuka fa take shine naje kar'barta".Cewar Reyhana.

      "Rabu dani ". Mommy ta fad'a.

      Daga haka ta fita sukai sallama dashi.Wajen aiki ya wuce se wajen 4pm ya tashi kafin yaje gidan umma ya tsaya a store yayi wa Reyhana 'yan siyayyan mey jego dede halin sa.

               ***
   Around 6:40pm suka je gidan su Reyhana,har da'ki Mommy tayi mata iso shima Ahmad d'in tare da ita ya shigo.

        Bayan sun gaggaisa Mommy ta fita ,Reyhana ce ta rage a d'akin sesu Umma.

       "Umma Reyhana ta miki ta'kwara fah". Ahmad ya fad'a.

      " Toh!  mashaAllah an gode Allah, Allah ya raya mana AISHA".
 
       "Ameen ". Suka amsa.

      Suna zaune Abba ya dawo shima ya shigo suka gaisa dasu,lokacin da zasu tafi ya ajje kayan da ya siyo.

        A waje Ahmad ya ke'be da Abba ya bashi ha'kuri akan abinda ya faru Abba yace komai ya wuce.

        Mommy bayan sun tafi da ta shigo taga kayan kawai ta'be baki tayi bata ce komai ba.

        Se lokacin Reyhana ta samu tayi wanka akaiwa baby ma ,nan su Ikram sukai ta rangad'a mata pic iri-iri.

          Kusan kullum Ahmad seya zo ya dubasu idan ya tashi daga aiki,a haka kwanaki suka ja har ranar suna tazo.

        Anyi shirye-shirye sosai komai Mommy sun tanada Ahmad ya aiko da ragon suna aka yanka yarinya taci suna AISHA Mommy taji ba dad'i sede bata nuna ba.

      Nasreen za'a ke kiranta dashi,tasha ado daga ita har mey jego Reyhana  swiss lace purple me white torches tasa se necklace silver Ikram ta rangad'a mata d'auri sekace amarya.

      Ansha hotuna 'yan uwa da abokan arz'iki sun hallara,Ahmad da yamma shida abokansa uku suka zo se Umma da wasu sisters daga zaria.

       Reyhana dama ta tanadar musu abinci da sauran lemuna ta ajje dan haka da suka zo ta basu,sukai hotuna suma.

       Bayan an watse daga Nasreen har Reyhana sun gaji sosai ana wa Nasreen wanka tayi bacci Reyhana ma wannan tayi tasha tea ta kwanta.

       Nima pen d'ina na ajje na kwanta๐Ÿ˜€

AR²๐Ÿ’–

 Washegari gajiyar da dama-dama sede Nasreen tasha bacci dan har lokacin bata farka ba.


      Har tayi wanka tayi breakfast Nasreen bata tashi ba,koda ta duba wayarta taga missed call na Ahmad ya kira tana bacci dan haka tayi calling ba.


      Kira d'aya tayi masa yayi picking.


       "Ummu Nasreen". Ahmad ya kira.


       "Abu Nasreen". Reyhana ta fad'a itama.


       " Ina kwana ".Ta gaisheshi.


       " Lafiya lao Azizaty,ya gajiyarku?"Ahmad ya amsa.


      "Gajiya ansha ta,har yanzu bacci take". Ta fad'a.


      "Allah sarki babyna du mutane sun wahalar min da ita".Ahmad ya fad'a.


      " Sannu mey baby".Reyhana ta fad'a cikin zolaya.


      "Ha! Toh ai gaskiya na fad'a". Cewar Ahmad yana dariya.


      " Toh nikuma fa banfita gajiya ba?" Reyhana ta fad'a.


     "Iyye! Kishi" Ahmad ya fad'a.


      "Haba kinsan da ina kusa da nayi maki tausa".Ahmad ya fad'a.


      " Nayi missing Azizaty ta ,your cooking pretty face everything yours Ummu Nasreen ".+


      " Me too".Reyhana ta fad'a.


      "Toh yanzu kayi breakfast?" Ta tambaya.


      "Tea kawai nasha,yanzu zan fita ma". Ahmad ya fad'a.


      " Please ka samu kaci wani abun ko a wajen aikin ne".Cewar Reyhana tana mey nuna damuwa.


      "Ok Azizaty i will". Ya fad'a.


      " Toh bari na barka ka shirya".Ta fad'a.


      "Ok ki shafamin kan babyna i love you all". Ya fad'a.


     " Love you too,Allah ya kare mana kai".


     "Ameen". Ya amsa.


     Daga haka sukai sallama kowannensu fuskarsa d'auke da murmushi cikin ransu suna 'kara jin son junansu".


      Ba jimawa Nasreen ta tashi ,da kuka ta farka dan yunwa da take ji.Ta ded'e tana shan nono tukun aka yi mata wanka.


        Komai ya cigaba da gudana, Nasreen har bayan suna ana zuwa barka ga kayan gudumawa da ake bawa Reyhana yarinyar tayi goshi sosai banda kayan da Abba ya 'karo mata akan wanda su Umma suka kawo na barka.


        Ikram idan suna gida itace me d'aukan Nasreen Reyhana hutawarta take ,yarinyar ana ji da ita a gidannan Ahmad ma yana yawan zuwa baya kwana uku beje ba.


        Umma ma tana yawan kiransu su gaisa taji ya ta'kwararta.


      3weeks later,Ahmad yana ta irga musu kwanakinsu bashida buri su cika kwana 40 su dawo baya jin dad'in gidan kusan koyaushe yana unguwarsu wajen abokansa.


                  ***

      Mommy yau tai shirinta na zuwa gidan Anty Asma'u dan tunda Reyhana ta haihu bata samu ta fita ba.


         " Mommy dan Allah ku dawo da wuri saboda wankan Nasreen".Reyhana ta fad'a.


      "Yau ke zaki mata da kanki ai gara ki koya". Mommy ta fad'a.


       " Cabb! Kina so nasa mata sabulu a hanci". Reyhana ta fad'a.


      "Gaki gata kika samata kyasan yadda kikai". Mommy ta fad'a.


      Walida da tun tuni ta gama shiryawa Mommy take jira kawai su tafi.


STORY CONTINUES BELOW

        " lala Yaya baby Nasreen tayi pupu".Walida ta fad'a tana toshe hanci.


       "Ga babarta ta wanke mata danni na gama nawa". Mommy ta fad'a.


       " Kai Mommy nifa ban iya ba".Reyhana ta fad'a.


      "Zaki iya ne, ga inno can kice ta cire mata danni nayi nan,Walida taho mi tafi". Mommy ta fad'a tana sa'kala Jakarta.


      " Se kun dawo".Ta fad'a.


       "Muhmm! Me d'oyin kashi". Reyhana ta fad'a lokacinda  Nasreen ta kalleta.


       Haka nan ta tashi ta cire mata tana yi tana toshe hanci.


                  ***


      Mommy a d'an 'kan'kanin lokaci ta isa gidan Anty Asma'un.


        Suna parlour ita da yaranta." Oyoyo Walida".Anty ta fad'a tare da nufo inda suke.


       Walida tana gaisheta ta nufi inda Ameera take,kusan itace sa'arta sukuwa Mommy suka tafi d'aki.


        "Ya masu jego ?"Anty ta tambaya.


        " Mey jego tana nan qalau ita da baby".Mommy ta amsa.


        "Saura 'yan satittika su koma koh?" Cewar Anty.


        "Hmm!" Mommy ta furta .


         "Ya hmm! da wani abune?" Anty ta tambaya tana neman 'karin bayani.


        "Kusan de". Cewar Mommy.


        " Mey fah?" Anty ta tambaya.


        "Nifa ba maganar komawa da yarinyar nan zatai". Mommy ta fad'a.


        " Toh! dalili?" Ta tambaya.


         "Nifa bazan yarda da irin wannan rayuwar ba ta gidan Ahmad Reyhana ba class d'insa bace ki duba kiga nauyi ya 'karu a kansa idan da yana kula da mace d'aya toh yanzu ga nauyin babynnan abin is not easy". Mommy ta fad'a.


       " Amma fa kin matsa dayawa kina tunanin Abbanta ze bar faruwar hakan?"Cewar Anty Asma'u.


       "Barni dashi nasan ta inda zan 'bullo masa". Mommy ta fad'a.


       "Su kuma ya zaki dasu?" Anty ta tambaya.


        "Wannan bame wuya bane Reyhana ba kamar Ikram take ba,taimakon rayuwarta zanyi ita bata san kanta ba ita so ya rufe mata ido bazan zuba ido ta sake samun cikin na biyu ba gara tun wuri na dakatar dama rabon 'yace ya had'asu".Mommy ta fad'a.


      "Maryam kenan ,toh Allah ya saww'ake deh". Anty ta fad'a.


       " Yanzu Toh yaushe zaki fad'a ma Reyhana d'in?" Ta tambaya.


     "Nan bada jimawa ba". Mommy ta fad'a.


       Daga nan suka tsindima wata hirar ta daban.


        Reyhana kuwa a gida tana ta fama da Nasreen dan ta'ki komawa bacci gashi ta barta a d'aki ita d'ai tasa ihu Ikram bata dawo ba balle ta taya ta ,inno kuma ta fita.


        Ahmad daga wajen aiki ya tashi da wuri,wajen 4pm yazo gidansu Reyhana. Har lokacin Mommy bata dawo ba ,kiranta yayi a waya ya fad'a mata yana haraba tace ya shigo.


       A parlour ya zauna chan ba dad'ewa ta fito Nasreen a hannunta.


       Murmushi ya sakar mata me 'kayatarwa itama ta mayar masa,be jira ta zauna ba ya mi'ke domin kar'bar Nasreen.


            " Ummu Nasreen irin wannan kyau haka".Ahmad ya fad'a.


       Kuma powder ne da lipstick kawai ko kwalli bata sa ba,tayi kyau sosai cikin green d'in atamfar.


       "Babyna ta gane ni kinga tana mini murmushi". Ahmad ya fad'a yana 'ko'karin zama.


      Itama Reyhana zama tayi a kujerar dayake three seater ce.


       " Watoh har ta fara gane ka?"Cewar Reyhana.


      "Ehmana baki gani ba taga mey kama da ita". Ya fad'a.


      " Sonkai koh".Ta fad'a.


      "Mommy bata nan?" Ya tamabaya.


      "Ta fita d'azu". Ta amsa.


      " Yau ke aka bari da babyn tamu,karfa kice zaki mata wanka karki sa mata ruwa a hanci".Ahmad ya fad'a.


      "Aiko na iya". Reyhana ta fad'a.

      " No sekun dawo zaki dinga yi mata".Ya fad'a.


      "Kin fara had'a muku kayan ku de koh?"


      "Wane kaya ana zaune lau,sekace gobe zamu komo". Reyhana ta fad'a.


     " Lalle just kwanaki ne fah,gara ma ki fara shiri dan kun kusa komo wa keda baby Nasreen ".


       Tashi tayi ta tafi kitchen ta had'o masa abunsha da snacks ta kawo masa.Hira sosai sukai tayi har Ikram ta dawo Nasreen tayi bacci ta kaita d'aki,se kusan maghrib ya tafi har lokacin Mommy bata dawo ba.


      Se to 8pm tukun ,ba dad'ewa Abba ya dawo.Mommy se lokacin akai wa Nasreen wanka,Reyhana kuwa bayan tafiyar Ahmad.


        Mommy maganar tana cinta amma ta kasa fad'a wa Abba,a kwana a tashi Reyhana sunyi kwana 37 Mommy bata yi wa Reyhana maganar komawa ba.


     Shikuwa Ahmad kullum cikin lissafi dan yanzu a tunaninsa baza suyi 5days basu dawo ba,dan har siyayyar 'yan kayan stuffs yayi musu jiran dawowarsu kawai yake.


     Mommy yau de ta d'au alwashin fad'a wa Abba duk abinda ke ranta,around 8:32pm bayan sun gama dinner ta shiga d'akinsa lokacin yana 'yan danne-danne a phone d'insa.


       " Abban Reyhana ina so zami magana ne".Mommy ta fad'a tana tsaye.


     "Toh shigo ina jinki". Ya fad'a tare da ajje wayar gefe.


    Mommy waje ta samu ta zauna a kan gadon tana tunanin ta inda zata fara.


        " Dama akan Reyhana ne,ina nufin komawarta".Mommy ta fad'a.


       "Toh ina sauraro". Ya fad'a yana 'kara tattaro hankalinsa gareta.


      " A gaskiya nifa bazan yadda yarinyar nan ta koma gidanta ba".Mommy ta fad'a.


       Kuma yadda take maganar zaka gane da gaske take.Abba zama ya gyara yana kallon ikon Allah.


       "Toh bazata koma ba a gidanki zata cigaba da zaman auren kokuwa mey kike nufi?" Abba ya tambaya.


      "Ina nufin Ahmad ya sawwa'ke mata". Ta amsa ba tare da ta nuna alamar damuwa ba.


      " What!" Abba yayi exclaiming cikeda nuna damuwa.

Sis feezoh tnx for ur concern, Allah ya bar zumunci we are always together๐Ÿ˜˜

  Mommy da ganin yanayin reaction na Abba yasa ta sake zage dantse.+

      "Eh sakinta zeyi".Ta fad'a babu alamar damuwa tare da ita.
 
      " Kina da hankali kuwa Maryam? Ina tunaninki? Ina iliminkii ? Kina abu kamar wata 'karamar yarinya wannan ai shirmene!"Abba ya 'kare maganar  cikin d'aga murya dan ransa ya 'baci.

      "Ba zancen rashin hankali,nide da raina bazan bari 'yata tashiga wani hali na rayuwa ba,wannan yaran baze iya ciyar da Reyhana ba balle bata sittira kana gani wani nauyin ya sake hawa kansa".

       " Maryam arz'ikinnan kece mey bayarwa neh? Kada ki manta bada arzi'kina kika aureni ba".Abba ya fad'a.

      "Da daban yanzu daban,shikenan kafiso kadinga ciyar da ita tana gidan auren nata ? Haka ake rayuwa?"

       "Maryam bana son sakarci fah,ke yanzu  ba abun kunya bane a gareki ace d'iyarki daga zuwa wanka gida aure ya mutu yaran da koh shekara biyu da aure basi ba".Cewar Abba.

      " Du kai ka janyo mah yarinyarnan ta aureshi tun farko seda nace maka kada ayi ka'ki jina, yanzu kaga irin halin 'yarka data shiga kuma wai a haka kake so ta cigaba da rayuwa,kafiso sede kullum ka dinga yafita mata kud'i tana cida kanta da mijin koh? "

     "Maryam ke meyasa bakya jin magana neh a rayuwarki?" Abba y fad'a tare da mi'kewa tsaye.

    Itama Mommy tashi tayi daga zaunen."Kasan Allah bazan ziba ido Reyhana ta shiga cikin rayuwar 'kunci ba ,yarinyar da bata taso a wahala ba kawai rana d'aya ta shiga 'kuncin rayuwar da bata san ranar barinta ba".Mommy ta fad'a.

      "Baza a raba masu aure ba na fad'a maki ,wannan haukar baza ayi dani ba". Abba ya fad'a.

      " Shikenan idan kai bazaka d'au mataki ba ni zan d'auka".Mommy ta fad'a.

     Ba tare da ta jira Abba ya sake magana ba ta fita daga d'akin fuuuu.Yana kiranta amma tayi banza dashi ta koma d'akinta.

       Daga yara har Reyhana ba wanda yasan meyake faruwa sede sunji ba Mommy a parlor ba Abba dan ko alamar su babu ,dukansu kowa d'akinsa ya koma Reyhana itama haka.

     Tunanin komawarta gidanta ta shiga yi ,sede kuma abin da yake bata mamaki shine haryanzu Mommy bata yi mata maganar hakan ba.

    Tana cikin wannan batunne kiran Ahmad ya shigo.

     "Ummu Nasreen". Ya kira sunanta.

      Bayan sun gaisa yake tamabayarta ya batin dawowarsu.

       " Azizaty ana ta shiri?"Ya tamabaya.

       "Uhmm".Ta amsa.

       " Kin jiki ,gara ma ki bud'e baki ki magana kin shagwa'be da zaman gida koh toh aiko ki shirya ina nan ina jiranku".Ahmad ya fad'a.

       "Se mun 'kara sati biyu".Ta fad'a cikin zolaya.

       " No shekara".Yayi gatse.

      Haka suka sha hirarsu lokaci har yaja ta fara jin bacci dan haka sukai sallama ta kwanta.

             ***
     Washegari da safe koda Reyhana ta tashi taga Mommy bata ma shigo ba,Nasreen  ta lura taga itama ta tashi dan haka ta d'auketa.

       Tana bata mama sega Walida ta shigo d'akin dama  yau Saturday.

       "Mommyn Nasreen ina kwana". Walida ta gaisheta.

       " Au yau kuma sunan da aka samun kenan".Reyhana ta fad'a bayan ta amsa.

       "Mommy bata fito ba?" Reyhana ta tamabaya.

       "Eh nima ban ganta ba". Ta amsa tare da zama kusa da Reyhana tana shafa gashin Nasreen.

          Abba around 8:30am ya sakko 'kasa, Walida ya tarar da Ikram a 'kasa yake tambayarsu Mommy suka ce bata sakko ba.

       Abba kai kawai ya kad'a ya koma sama dan yasan dalilinta na 'kin fitowa.Koda yaje a bakin d'akinta ya tsaya yana knocking tare da kiran sunanta amma tayi burus.

        " Maryam ki fito na fad'a maki".

        "Na fito na muku mey?" Mommy ta fad'a.

          "A'a kamarya ? Da haka kike yi ga yara nan suna jiranki a 'kasa,ki fito kiyi breakfast".Abba ya fad'a cikin sanyin murya.

       Haka ya rabi da ita ya sakko daga shi se yaran sukai breakfast ,Reyhana ma se daga baya tayi nata breakfast d'in.

       Abin ya fara damun yaran dan Mommy bata saba haka ba.Suna cikin  wannan batun ta sakko.
   
      " Mommy ina kwana ".A tare suka gaidata.

      Sun lura mood d'in Mommy hakan yasa suka d'an yi shiru.

       " Lafiya".Ta amsa muryarta a ciki-ciki.

        Kitchen ta nufa ba tare da ta sake cewa komai ba.

       Abba kuwa yana d'akinsa,Reyhana tana d'aki itama basu jima da yin waya da Ahmad ba.

       Mommy a kitchen tayi breakfast d'inta ta shiga d'akin Reyhana.

        "Mommy ina kwana". Ta gaidata
    
        " Lafiya".Ta amsa.

        "Reyhana".Mommy ta kira sunanta cikin wata murya lokacinda ta zauna.

         "Na'am". Reyhana ta amsa gwiwarta ba 'kwari.

           "Kinsan ni mahaifiyarki ce kuma bazan yi wani abu dan cutar dake ba koh?" Mommy ta tambayeta.

         Kai kawai Reyhana ta kad'a alamar "eh" ba tare da tace komai ba.

          "A gaskiya ni ban amince da komawarki gidan Ahmad ba,bazan amince ki cigaba da zama a irin wannan rayuwar ba". Mommy ta fad'a.

          Wani irin fad'uwar gaba taji ,a take zuciyarta saurin bugunta ya 'karu.

        "Reyhana a kullum ina fad'a maki ke ba tsarar Ahmad ba ce,ki duba kiga aikin dayake baze iya ri'keku ba kuma yanzu nauyi ya 'karu idan yau Abbanki ya baki kud'i gobe wa ze baki idan matsala ta faru? Wannan abubuwan nake guje maki shiyasa tun farko na'ki amincewa da aurenki dashi,dan haka tun ba'ai nisa ba gara a yanke ala'kar aurenku ,gatanan dama Allah yayi itace rabon auren". Mommy ta fad'a tare da kallon Nasreen.

        Reyhana jinta take kamar wata kurma ,kwalla ta cika taf a idanuwanta a take ma'koshinta ya bushe.

            " Mommy? " Reyhana ta fad'a lokaci guda kuma hawaye ya gangaro a idanuwanta.

          "Reyhana nasan hakan baze zo maki da sau'ki ba amma ki sani dan farincikinki nake komeh da kika gani".

      Bata sake wata maganar ba Abba ya shigo d'akin dan already ya jiyo su da Mommy.

        Mommy tana ganin ya shigo ta tashi ta bar d'akin ,hakan yasa Reyhana ta gano sun sami sa'bani da Abba kuma tasan baze wuce akan maganar aurenta ba.

        " Ta fad'a maki koh?" Abba ya tambaya.

       Kuka Reyhana ta fashe dan bata da wani sauran dauriya a tare da ita.Bece sake cewa  komai ba yabi bayan Mommy.

        Ita kuwa Reyhana gefe guda ta ajje Nasreen ta shiga rera kuka,a lokacin kuma taji wayarta na ringing koda ta duba taga Dear❤

       Seda ta katse ya sake kira tukun ta iya  picking, d'an share hawayen tayi tare da sassaita muryarta tai magana.Duk da haka seda yaji yanayin muryar tata ya tamabayeta.

        "My Amarya meya faru?"
Yaya ba komai ,kawai de kaina ke ciwo". Tayi 'karya.+

       " Toh! Allah ya sawwa'ke kin sha paracetamol? " Ya tamabaya.

       "A'a amma zansha". Ta fad'a.

       " Toh ki samu ki sha,ya Nasreen?"

        "Tayi bacci". Ta amsa.

         " Toh ki shafan min kanta".Ahmad ya fad'a.

          "Kema ki samu ki baccin  kan ze dena,nima yanzu zan fita".

            "Ok,toh seka dawo". Ta fad'a.

        Daga haka sukai sallama ta ajje wayar wani sabon hawaye ya sake gangarowa a fuskarta.

       Mommy kuwa kafin Abba ya 'karasa d'akinta ta rufo 'kofarta,tana ji yana kiran sunanta amma tayi burus.

     Ba 'karamin 'baci ransa yayi ba haka ya koma wajen Reyhana ya tarar da ita tana kuka mey cin rai,rarrahinta yayi yana bata ha'kuri.

              ***

     Sageer ya lura da irin change da aka samu kwana biyu a gidan ,Mommy,Abba,Reyhana ba kamar yadda ya saba ganinsu ba ,kawai de be tanbayi Reyhana bane,abinci ma Mommy ta dena ci tare dasu  dinning haka Reyhana ma ko da daddare idan ya dawo d'akinsa yake shigewa dan yason ko meze ce wa Mommy ba sauraransa zatai ba.  
      
     Reyhana sun cikake 40 harda kwana biyu akai ,Ahmad har ya soma gajiya dan haka yau yazo gidansu Reyhana.

       Sanda ya shiga ya tarar da Sageer dake parlour nan suka gaisa ya hau sama yake fad'a ma Reyhana.
     
         Jiki a sanyaye ta tashi ko Nasreen bata d'auka ba dan bacci take.

         Reyhana tana taka step dan ta sau'ka bata 'karasa zuwa parlour ba ta hangi Mommy a palourn.

     Ba shiri ta tsaya cak,da alama Mommy bata dad'e da zuwa parlourn ba,lokaci guda bugun zuciyarta ya 'karu.

      "Shikenan Mommy zata fad'a masa komai". Ta fad'a a ranta tana ja da baya,da sauri ta koma d'aki ta fad'a gado ta shiga aikin kuka.

       A parlour kuwa Mommy bayan sun gama gaisawa da Ahmad ta soma gyaran murya.

       " Uh..Ahmad nasan dole wannan maganar da zan fad'a maka zaka ji nauyinta,amma banyi haka dan na ba'kanta muku ba nayi haka ne dan nema muku sau'kin rayuwa".Mommy ta d'iga aya amma bawai ta gama ba.

      Jin irin kalaman Mommy yasa Ahmad ya tsinci kansa a irin wani yanayi na daban.

      "Ri'kon mace ba abune mey sau'ki ba,kuma musamman ga Reyhana da bata saba da rayuwa irin ta gidanka ba,yanzu kuma idan ka duba zaka ga nauyi ya sake 'karuwa fiye da da wanda ba abune mey sau'ki gareka ba,sana'arka ba mey 'karfi bace da zaka iya ri'ke su dan haka ina neman alafarma daka sawwa'ke wa 'yata Reyhana".
       Ahmad maganar Mommy yadda ta doki kunnensa ze iya cewa be ta'ba shiga tashin hankali kamar na ranar ba,dan jiyake kamar mafarki.Reyhana matar tasa?Ummu Nasreen Azizatynsa?Tir'kashi!

      " Mommy dan girman Allah ki taimaka mini ki dena fad'ar wannan maganar ".Ahmad ya fad'a kamar mey shirin yin kuka.

       " Gaskiya ce dole na fad'a Ahmad,kuma babu uwa da zata so 'yarta ta shiga cikin wani yanayin wahala,inde har soyayyar da kake mata ta gaskiya ce toh baza ka bari ta sha wahala a rayuwarta ba".Mommy ta fad'a.

       "Mommy kiyi ha'kuri amma rabuwa de Reyhana ba abu ne mey sau'ki ba". Ya fad'a already 'kwalla ta cika idanuwansa.

       " Ai nasan da hakan shiyasa nace maka alfarma,kuma nima ba abune mey sau'ki ba na bari 'yata ta shiga wahala".Mommy ta fad'a a lokacin ta fara 'kosawa.
  
      "Mommy ki duba ki tausaya wa rayuwata da halin da zamu shiga nida Reyhana na sani itama bazata so hakan ba". Ya fad'a muryarsa na rawa.

STORY CONTINUES BELOW
       " Ahmad na gama maganar nan bazan chanja ra'ayina ba,kaje ka sake tunani".Mommy ta fad'a tare da barin parlorn.

        Ahmad ai zama yayi dirshan hawaye na ziba a fuskarsa ya rasa inda ze saka kansa.Wayarsa ya lalubo a aljihu yai dialing number ta Reyhana.

       Ya kirata yafi a 'kirga amma bata d'aga ba,koba a fad'a ba yasan tana cikin wani hali yanzune ya gano dalilin dayasa bata maganar komowarsu sede kullum shi yayi mata.

       Mommy kuwa tana hayewa sama d'akinta ta shige ita kanta ta tausaya masu amma ba ta jin zata iya 'kyalesu haka.

      Reyhana kuwa tana ganin wayarsa amma ta kasa picking dan tuni tasan aikin gama ya gama,batasan mey zata ce dashi ba.

       Ya shafe yafi 30min kafin ya fita daga gidansu Reyhana jiyake kamar yaje d'akin da Reyhana take,haka da'kyar ya iya tafiya direct gidan Umma ya wuce.

     Umma ta tsorata ganin yanayinsa ,kuka yasa mata a tsakar parlour kamar d'an yaro ,ta 'kosa taji abinda ya faru ita ta zaci ko wani abunne ya sami Reyhana ko Nasreen.

       "Ahmad kukan ya isa nace, ka fad'a mini mey yake faruwa se kayita kuka". Umma ta fad'a.

      " UMMA Reyhana,bazan iya rabuwa da ita ba".Ya fad'a cikin kuka.

      "Reyhana? Wa yace zaka rabu da ita?" Ta tamabaya a  kid'ime.

        "Mommy ce  Umma ,bazan iya ba Umma dan Allah kije ki bata ha'kuri". Ahmad ya fad'a.

      Umma ita kanta batasan sanda hawaye ya zubo a fuskarta ba,take tausayin d'anta ya 'karu a zuciyarta.

       "Innalillahi wa inna ilaihi raji'u". Abinda ta furta kenan.

      " Ita Mommy da kanta tace ka rabu da 'yarta?" Ta tamabaya.

      "Mommy wai na saki Reyhana taya zan iya rabuwa dasu Umma ?"

     Umma dafe kanta tayi ta rasa mey yake mata dad'i.An d'an tsahon lokaci a haka ,Ahmad ya bar sheshe'kar kukan sede hawaye gashi idanuwansa yayi ja jijiyoyinsa ma sun tashi fuskarsa tayi jazir.

        "Kayi ha'kuri in Allah ya yarda baza ka rabu da ita ba ,addu'a zakai". Umma ta fad'a.

     Duba da lokacin yasa bata tafi gidan ba ,8pm tayi.

           Gidansu Reyhana kuwa shiru kukeji kowa yana d'aki dan koda Abba ya dawo Sageer ya zayyane wa Abba komai dan yana jiyo Mommy da Ahmad.

      Abba ransa a 'bace ya shiga d'akinsa jira yake gobe tayi ya shawo kan matsalar(Hmm๐Ÿ˜ถ).

            Reyhana da dare yayi ko bacci ta kasa gashi Nasser tana ta mata kuka koh cikinta yake ciwo ,ita kad'ai take ta lallashinta amma ta'ki shiru hakan yasa itama Reyhana ta taya ta sukaita kuka bame rarrashin kowa.

       Ahmad ko gidansa be koma ba yana parlourn Umma sallah yayi koh abinci ya'ki ci tunanin Reyhana da Nasreen kawai yake.

               ***
Washegari da safe Umma tun asubah bata koma ba ,shiko Ahmad dama jiya beyi wani bacci ba sallah yayi yaita adduo',ise around 4:30am bacci yai gaba dashi.

        Tun bayan sallahr Asubah be koma ba dukda kuwa baccine a idanuwansa.

       Umma around 8am ta tafi gidansu Reyhana dan hankalinta ya kasa kwanciya,inno ce tayi mata iso.Nan inno taje ta sanarwa da Mommy ,ba dad'ewa ta sakko 'kasa.

        Sama-sama ta gaisa da Umma dama tasan meke tafe da ita.

         "Mommyn Reyhana meyai zafi haka...". Ko 'kare maganar batayi ba Mommy ta katseta.

        " Duk wani abu da zan fad'a na riga na fad'a wa Ahmad saboda haka banga amfanin dawo da zance baya ba".Cewar Mommy ba ko damuwa a tare da ita.

        "Ehyi nasan da haka amma dan Allah ki tausayawa yaranannan ki bashi dama ,Ahmad rabuwa da Reyhana matsala ne a gunsa abune me wuya". Umma ta fad'a cikeda tausayawa.

      " Itama Reyhana zama dashi abune mey wuya  a gunta damu kanmu baza muso ta shiga 'kuncin rayuwa ba".Mommy ta fad'a.

       "Dan Allah kiyi ha'kuri ki bar maganar nan". Umma ta fad'a.

       Mommy ta 'kosa sosai dan ta fara kad'a 'kafa komai ze iya fitowa daga bakinta.

       " Nifa yanzu takardarta nake jira bana san sake jin komai".Mommy ta fad'a.

        "Baze sake tan ba".Abba ya fad'a.

       Dama ya gano sanda Umma ta shigo gidan a d'akinsa.

       " Kiyi ha'kuri Umman Ahmad inshAllahu ma yau zan maido da ita gidanta da kaina.Abba ya fad'a.

       "Ba inda zata je, ta gama zaman gidan Ahmad". Mommy ta fad'a.

       Umma da take zaune ta mi'ke tsaye taga abun ba na zama bane.

      Itako already Mommy tun sakkowar Abba ta mi'ke tsaye.

        Ikram datake shirin sakkowa ta hangi abinda ke faruwa dan haka ta shiga d'akin Reyhana da sauri ta fad'a mata.

       " Yaya Umman Ahmad tazo ,kinga Abba ma ya fito suna magana Mommy kuma...".Bata 'karasa ba tayi shiru.
         
     Reyhana ko bata fad'a ba ta gano inda ta nufa,da sauri ta tashi zuwa parlour.

       Daga can gefen bene suka tsaya itada Ikram suna kallon ikon Allah.

      "Ni na fad'a a yau seta koma gidanta". Abba ya fad'a cikin d'aga murya.

      " Ba inda zata je".Cewar Mommy.

       "Dan Allah ayi ha'kuri". Umma ta fad'a.

     Da ace tasan hakan abin ze kaya da bata zo ba,dan haka tayi ta basu ha'kuri.Suna kallo ta fita daga gidan,su kuwa basu fasa ba.

      " Ke kike da iko da ita koh ni?"Abba ya fad'a.

      "Bani bace,kayi yanda kake so kaji". Mommy ta fad'a cikin fushi.

       " Kece kuwa ? ".Abba ya tamabaya .

      Yana mamakin yadda ta sauya ,yasanta da zafi amma ba irin haka ba ace yau har a gaban sirika yana fad'a tana fad'a.

       Yana cikin wannan batun Mommy tayi wucewarta ta haye sama yaran suna kallo.Sageer da se lokacin ya fito daga d'akin ,wajen Abba Reyhana ta 'karasa tana basa ha'kuri ,ba abinda yake illa jinjina kai.

       " Mommy ina zaki je?" Suka jiyo muryar Walida da ta biyo bayan Mommy.Wani irin shock gabaki d'ayansu suka ji ganin Mommy tana sakkowa da trolley.

        Ta yafa gyale ga takalmi data saka hannunta key na motarta,hakan ya bayyana tafiya zatai.

        "Mommy?" Reyhana ta furta cikeda mamaki.

        Har gabansa ta 'karaso ba tare da ta kalli yaran ba tace."Sanda kaga bana nan seka tabbata nice,ga yaranka kaine kake da iko dasu".Mommy ta fad'a fuuu ta wuce.Gabaki d'aya yaran da sauri suka 'karasa wajen Mommy da ta kusa kaiwa 'kofar fita.+

       "Mommy dan Allah karki tafi ki barmu". Walida ta fad'a tana ta'be baki zatai kuka.

      " Mommy please kar kiyi haka".Reyhana ta fad'a ta ri'ko hannun Mommy.

     Se lokacin ta kalleta ,Sageer ma 'karasowa yayi.

     Mommy dan Allah ".Ya fad'a muryarsa a raunane.

       " Sakeni".Mommy ta fad'a tana mata wani kallo.

       Reyhana a hankali ta sauke hannunta dan tasan duk dalilinta hakan ta fara.

       Suna ji suna kallo ta fita ,Walida take ta buga 'kafa tana ta kuka tana kiran Mommy.

       Abba da tun d'azu be kalli inda take ba duk da kuwa abun ya damesa sosai ,seda yaga ta fita ga Walida tana kuka.Fita yayi ,yaran zasu biyosa yace su tsaya.

      "Maryam". Abba ya kira sunanta.

      Yana 'karasawa inda take ya fisge trolley d'in daga hannunta.

      " Mey kike tunanin yi? Idan kin tafi ina zaki je"?" Ya tamabaya.

    "Gidan kawu na". Ta amsa.

     " Ki shiga ciki nace".Abba ya fad'a yana nuni da 'kofa.

     "Kusha zaman ku kaida yaranka muddin baze saketa ba ni kuma bazan dawo gidannan ba". Ta fad'a.

       " Adalci kenan ,ki raba auren yarannan?"

       Shiru tayi bata ce komai ba tana tsaye ita bata shiga motar ba kuma bata koma ba.

       "Ki duba kiga yarannan,haka zaki tafi ki barsu wani hali zasi shiga? Abba ya fad'a a sanyaye.

      " Nide na fad'a maka muddin na koma toh seya saketa".Mommy ta fad'a.

      "Muje ki shiga ciki". Abba ya fad'a.

      Tana huci tabi bayansa yaran suna kallo ta shigo da sauri suka je wajenta.

     Reyhana kuwa komawa tayi d'aki jiki a sanyaye. A zuciyarta tana tunanin mafita " Yanzu a kaina yau Mommy take 'ko'karin barin gidannan!" Reyhana ta fad'a a zuciyarta hawaye na gangarowa a idanuwanta.

               ***

   Umma tana komawa gida Ahmad ya 'karaso inda take.

      "Umma ta ha'kura Mommyn" .Ya tambaya muryarsa a raunane.

      Kallonsa kawai tayi amma ta kasa cewa komai.

      "Umma ki fad'a min". Ya fad'a.

      " Ahmad sede mu cigaba da addu'a ,Mommyn ta ta'ki amincewa mahaifinta ne de ya goyi bayanta ba". Umma ta fad'a.

     Labarin duk abunda ya faru ta zayyane masa,hannu yasa ya dafe goshi kansa yana sarawa.

     "Ha'kuri zakai Ahmad duk abinda kaga ya faru Allah ne ya tsara". Umma ta fad'a.

      Seda tayi da gaske yaci abinci kad'an koh fita ya 'kiyi,wayarsa ya d'auka bayan yayi sallahr zuhr yayi dialing number na Reyhana.

     Seda ta kusa katsewa tayi picking.

       " Reyhana ".Ya kira sunanta.

      " Uhmm".Ta amsa dan idan tayi 'kwakkwarar magana kuka zatai.

      "Reyhana dan Allah karki rabu dani ,bazan iya zama bake ba ina 'kaunarki Reyhana". Ya fad'a muryarsa na rawa.

      Jin haka yasa ta shiga kukan da take dannewa." Ahmad taya zanso na barka kaima kasan bazan so na rabu da kai ba".Ta fad'a.
    
       "I know Reyhana". Ya fad'a.

STORY CONTINUES BELOW
       " Yaya ina tsoro".Ta fad'a.

       "Reyhana inshaAllah muna tare". Ya fad'a duk da kuwa zuciyarsa ta karaya.

      Labarin abunda ya faru bayan tafiyar Umma ta basa, hakan ba 'karamin tsorata sa yayi ba.

       " Yaya bazan iya bari Mommy ta bar Abba a dalilina ba".Ta fad'a.

      Kai kawai ya kad'a kamar yana kusa da ita,sun d'au lokaci kafin Ahmad ya sake magana.

       "I love you so much that I can't afford lose you Azizaty".Ya fad'a.

       " Idan na rabu dake ya zami da Nasreen ? Reyhana I can't do this".Ya fad'a zuciyarsa na sake karaya.

        Kud'in wayar ne da suka 'kare yasa basu cigaba da magana ba ,Reyhana wani sabon kukan ta soma yi Allah yasa Nasreen bacci take.

       Kowa rayuwar ta'ki masa dad'i ,dukansu sun shiga damuwa gashi idan yaje gidan baya samun ganinta yanzu Mommy ma wayar ma so take ta hana su kuma.Reyhana jikinta yayi sanyi dan bata jin zata iya bari a dalilinta Mommy tabar gidan dan haka yanzu tana ganin zatace wa Ahmad ya bata takardarta muddin hakan ze dawo da faruncikin Mommy.Dan yanzu Mommy bata wani sakkowa 'kasa idan kuwa Abba yana parlour bata zama.

      Ahmad koya kira Mommy ya sake ro'konta bata picking call d'insa sede yayi ta tura mata text amma kamar bayi yake ba.

        Reyhana tana d'aki tana shirya Nasreen Ahmad ya kira ,wani tausayinsa taji dan yau kusan kwana biyu Mommy ta hanata picking call d'insa.

      "Reyhana". Ya kira sunanta bayan ta d'aga.

     " Yaya".Ta kira sunansa itama.

      "Are you OK?" Ya tambayeta.

      "No am not". Ta amsasa idanuwanta na tsiyayar hawaye.

      " Reyhana ki dena kuka please ".Ya fad'a

       Bata 'kara magana ba sega Mommy ta shigo.Wata uwar harara Mommy ta watsa mata dan haka ta katse wayar.

     Mommy 'karasowa inda wayar take ta d'auka tayi switching off ba tare da tayi magana ba ta fita.

       An d'au kusan month da arba'in ,ba abunda ya chanza Mommy haryanzu tana kan bakarta dan yanzu ta gaji da zama a haka da ake so take Ahmad ya rubutowa Reyhana takardarta.

     Da kanta yau ta d'au 'kafa taje gidansu Ahmad,Umma kad'ai ta samu a gidan.

      Bayan sun gaisa Mommy take fad'a mata abinda ya kawota.

       " Mommyn Reyhana ba wanda yasan gobe gabaki d'ayanmu,shiyasa nake ro'konki da ki sake bashi dama ko ze samu wani aikin".Umma ta fad'a.

      "Umman Ahmad banzo nan ba dan mu sake tattaunawa akan maganarnan ba ,takardarta nazo kar'ba".Mommy ta fad'a.

      Hakan ba 'karamin 'konawa Umma rai yayi ba ,tasan ta d'areta nesa ba kusa ba danma bata haifi Ahmad da wuri ba amma shine take mata irin wannan maganar cikin kakkausan harshe sekace 'yarta ko si'arta.

       " Amma yanzu de ai kinga yaron baya nan koh?" Cewar Umma.

       "Toh ai shiyasa na zo sanar wa da mahaifiyarsa wata'kila koya rubuta". Mommy ta fad'a.

      " Shikenan inde takardarta ce ze kawo mata da kansa".Umma ta fad'a ranta a 'bace.

       Tashi tayi Mommy ta fita disappointed dan taso ace Ahmad yana nan.

     Umma kawai bin bayan ta da kallo tayi ta girgiza kai.

       Ahmad yana wajen aikinsa amma hankalinsa yana gun Reyhana baida tunani sai nata.

       Wajajen 4pm Ahmad ya shigo gidan dan yanzu kusan koyaushe yana gidan kwana ne yake maidashi gidansa.
    
      Umma seda taga ya kammala cin abincin sannan tayi masa maganar zuwan Mommy.

      "Ahmad yaushe zaka bata takardarta?"Umma ta tambaya.

       "Umma ya kike fad'an haka?" Cewar Ahmad.

      "Kai baka gaji da wannan abun ba ,lokaci yayi da zaka ha'kura Ahmad babu yanda zami da 'kaddara". Umma ta fad'a.

      " Umma saki fa ba abune mey sau'ki ba".Ahmad ya fad'a.

      "Ka fiso a cigaba da zuwa ana cimin mutunci ko,har yanzu baka gaji da wula'kanci ba? Kokuwa so kake se an kai maganar kotu?" Cewar Mommy, daga yadda take maganar ya gano tana cikin 'bacin rai.

     "Umma mey tace miki?" Ya tambaya lokaci guda zuciyarta ta fara tafasa dan zaey iya jure komai amma banda wulan'kanta mahaifiyarsa
    
      "Jin mey tace mini ba shine ba kawai kayi ha'kuri ka sawwa'ke mata kowa ya huta". Umma ta fad'a.

    Kai kawai ya kad'a ba tare da yace komai ba ya fita.

     Gidansa ya nufa,d'akinsu ya shiga ya bud'e wardrobe d'in wasu kayan Reyhana da bata tafi dashi ba ya d'auka yana sha'kar 'kamshin turarenta ,take hawaye ya gangaro fuskarsa.Tun farkon had'uwarsu da ita ya tuna da auren su,sanda tana laulayi,da tafiyarta gida.

      " Shine 'karshen zamanta a gidana kenan?"Ya tamabayi kansa.

      Tuna maganar Umma da yayi yasa ya janyo drawer ta gadon ,takarda da biro ya d'akko ,se 'karewa takardar kallo yake a zuciyarsa yana jin nauyin rubuta mata saki.

      Ya shafe kusan 20min kafin ya d'ora biro a kai.

       Ni Ahmad Yusuf, yau laraba ././... Ya rubuta date.Na saki mata ta Reyhana saki d'aya.

       Yana gama rubutawa yai folding d'inta.

        Seda yasha kukansa tukun ya fito daga gidan,be tsaya a ko ina ba se gidansu Reyhana. A 'kofar gida ya tarar da Sageer ,cikin mutuntawa suka gaisa ya mi'ka masa takardar dan bayajin zai iya bata hannu da hannu.

     Yana bashi ya tafi,shikanshi Sageer jiyake kamar yai kuka.Ko ba'a fad'a ba yasan mene,a d'aki ya isketa tana ta lalla'ba Nasreen tayi bacci.

     Ganin Sageer 'ki'kam a tsaye ya kasa magana amma fuskarsa da damuwa.

        "Sageer meya faru?" Ta tambaya.

      Takardar ya mi'ka mata ba tare da yace komai ba ya fita.

    A sanyaye ta bud'e takardar gwiwarta tayi sanyi...
Safar  da take hannunta ta Nasreen ta saki a 'kasa,kukan ma ta kasa.

     "Ahmad ya sakeni?" Abinda take ta nanatawa kamar zautacciya.

     Kuka mara sauti ta soma,ita kuwa Nasreen se wuri wuri da ido take tana d'aga 'kafafuwa sama.

       Ahmad kuwa daga gidansu Reyhana gidansa ya koma yai zaman dirshan ,hotunan bikinsu ya d'auko yana ta kalla harda murmushin yake.

      Umma tayi tsammanin dawowarsa amma taji shiru,da ta kira wayarsa a kashe taji dan kuwa baya son jin kowa komai kawai yafison ya zauna shi kad'ai.

      Mommy da maghrib bayan tayi sallah ta shiga d'akin Reyhana lokacin tana toilet.Har zata fita ta hangi takardar a kan gado.

    A hankali ta 'karasa ta d'auka,koda ta karanta wani sanyi taji ya ratsa ta a zuciyarta tace"Alhamdulillah,an rabu da 'kaya".

      Hannunta ri'ke da takardar Reyhana ta fito fuskarta ba annuri da ka ganta za kasan tana cikin damuwa.

      Mommy ita kanta rasa abinda zata ce mata tayi dan tasan a wannan lokacin tana tare da 'bacin rai saboda haka Mommy ta ajje takardar ta fice.

         Abba kuwa da ya dawo Mommy ko kunya haka ta shiga d'akinsa ta sanar masa.

      "Toh yanzu hankalinki ya kwanta koh?" Abba ya fad'a
  
       Mommy shiru tayi bata ce komai ba se turo baki datai a zuciyarta kuwa tana mey jin dad'i.

           Ahmad se wajen 10:30am tukun ya koma gidan Umma da hankalinta ya tashi.

          "Kai kuwa ina ka shiga ina kiranka a kashe wayar?" Umma ta tambaya.

          "Naje gida neh". Ya amsa ciki ciki.

          " Du ka tayar min da hankali". Umma ta fad'a.

         "Kiyi ha'kuri". Ahmad ya fad'a.

           " Abinci fa?" Ta tambaya.

           "Na 'koshi ". Ya amsa ya shige d'aki.

        Kai kawai ta girgiza ta koma d'aki.

       Daren ranar daga Reyhana har Ahmad ba wanda ya iya bacci,daga ya fara gyangyad'i seyai mafarkin Reyhana tana kuka a firgice yake tashi.

                   ***

2weeks later

       Mommy itada Anty Asma'u sukaje gidan Ahmad suka sa aka kwaso kayanta ,dama kud'in hayar ya kusan 'karewa dan haka suna kwashe kayansu Ahmad ya dan'kawa mey gida gidansa.Shi kuwa ya komo gidan Umma.

        9:46pm yana rigingine ya 'kurawa ceiling ido yana tuna last maganar da sukai da Reyhana a waya.

  ** Waiwaye**

     
       " Reyhana am so sorry, I have no choice ".

        " Yaya na fahimta,stop apologizing ".Reyhana ta fad'a.

        "Wannan itace 'kaddararmu". Ahmad ya fad'a.

            Da'kyar ya iya rintse idonsa ba isashshen bacci yake ba yanzu.

            Mommy kuwa abin Reyhana ya fara isarta tun sanda Ahmad ya bata takardar ta ta dena sakin fuska ,fitowa parlour ma wataran se a wuni bata fito ba.

       Tana gyara gado dan shirin kwanciya Mommy ta shiga d'akin.

       Waje ta samu ta zauna,bayan data d'auki Nasreen da har lokacin idonta biyu.

STORY CONTINUES BELOW
      " Reyhana ".Ta kira sunanta.

      " Uhm".Ta amsa tana cigaba da abinda take.

       "Reyhana saboda nasa Ahmad ya rabu dake shine bakya son yi mini magana?" Cewar Mommy.

      "Mommy ba haka bane".Ta fad'a tabar abinda take.

         " Toh yayane?"Mommy ta tambaya.

        'Karasowa tayi kusa da Mommy ta zauna gefen gado ta zauna opposite da Mommy.

       "Mommy taya za'ai na'ki yi miki magana akan haka". Reyhana ta fad'a.

      "Toh ya akai kin chanja bakya shiga cikin 'kannanki ko abinci ma bakya ci damu kinga dole nayi tunani ko kina gab..". Mommy bata 'karasa ba Reyhana ta katse ta.

       " Mommy kidena fad'in haka,dan Allah kiyi ha'kuri amma banyi hakan dan na 'batamiki ba ,na bari ".Reyhana ta fad'a tare da tasowa ta zauna gefen Mommy tasa hannunta ta ri'ko yatsinta tana murzawa.

       " Kiyi ha'kuri Mommy ".Reyhana ta fad'a hawaye na sakkowa daga idanunta.

      Mommy kafad'arta ta d'ora kan Reyhana tana tapping bayanta" Ya isa kukan".Ta fad'a.

      Kai kawai take kad'awa ba tare da tace komai ba.

       Daga wannan lokacin Reyhana ta cigaba da sakewa dasu,sun dawo kamar da tana sakkowa parlourn suyi kallo duk wata damuwarta ta danne a ranta.

       Ta 'bangaren Ahmad a 'yan kwanakinnan yakan fita majalissa wajen abokansa,ko be fito ba Sadiq abokinsa da kansa yana shigowa ya tayashi hira kuma yana kwantar masa da hankali.

      Yau d'inma ganin be fito ba yasa sadiq ya zo gidan.A d'aki ya tarar dashi ,wayarsa ce a hannunsa amma bawai tapping yake ba kawai wasa da ita yake a hannunsa amma hankalinsa baya gun.

      "Maza! Yane ka zauna a d'aki kai d'aya baka fito ba?" Sadiq ya tambaya.

        A kasalance ya d'ago da kansa ya kalli sadiq.

      "Sadiq". Ya kira sunansa.

        Zama yayi kusa da shi kan katifarsa.

       " Ahmad kai baka gajiya neh? Koyaushe cikin tunani haba mana ya kamata ka dena damun kanka haka".Sadiq ya fad'a.

      "Sadiq baza ka gane bane,bakasan yanda nake ji bane". Ahmad ya fad'a.

       " Ai gashi se rama kake,lafiyarka nake jiye ma se kace ba namiji ba duk wani abu daya sami mutum qaddararsa ce haka ba yadda zami,yin haka ba abinda ze 'karama illa kashe maka zuciya".Sadiq ya fad'a.

      "Toh naji".Cewar Ahmad yana gyara kwanciyarsa.

       " Ni da zaka bi shawara ta ma da ka mance da wannan damuwar".Sadiq ya fad'a.

      "Na mance" Ahmad ya maimaita cikeda rainin hankali.

      "Yes,akwai wani scholarship da naji ana cikewa na cyprus ,abinda yasa banyi ba    saboda waec d'ina banda English ,kai kuwa naga kana da result mey kyau why not kai applying?"

       "Mtchww! Ina cikin wannan yanayin zakai min maganar scholarship". Ahmad ya fad'a.

      " Cigaba ne fa ,wai kai shikenan ka kashe rayuwarka ko meh,rabuwa da Reyhana baya nufin yin destroying life d'inka koh ita ance ma haka zata zauna tayi ta damuwa kamar yadda kake ?" Sadiq ya fad'a cikin fushi.

      "Ni kaga rabu dani". Ya fad'a.

       "Karka saurareni d'in rago kawai ". Sadiq ya fad'a tare da talle masa tafin 'kafarsa ya fita.

      Ahmad ya d'au pillow da niyyar cilla masa yaga ya fice.

          Washegari da safe koda ya gaisheda Umma yaji tayi masa maganar da Sadiq yayi mishi jiya.

          " So zuwa yayi ya fad'a mata".Ahmad ya fad'a a ransa.

       "Umma ki rabu dashi shirmensa ne". Cewar Ahmad.

      " Kaide kake shirme,ca akai ma kowa irinka neh da be iya ri'ke 'kaddara ba".Umma ta fad'a.

      Shiru yayi bece komai ba ,ita kuma ta tafi kitchen had'a karin kumallo.

                   ***

    Ahmad kalaman Umma da Sadiq ne suka fara tasiri a zuciyarsa,dan yana ganin inde ya cigaba da zama haka zuciyarsa ce zata mutu gara ya mi'ke ya zama cikakken namiji.Zuciyarsa ta fad'a.

      Sede fa yana tunanin kuma barin Umma ita d'aya haka bayanan waze dinga kula da ita?

        Haka yayi ta tunaninsa gashi koyaushe cikin addu'a yake Umma ma bata dena ba.Cikin ikon Allah yaji 'kuncin da yake zuciyarsa yana raguwa kuma scholarship d'in ya soma kwanta masa a rai.

      5days later ,da kansa yace wajen Sadiq ya fad'a masa ya amince ,sosai Sadiq yaji dad'i .Ba 'bata lokaci yayi applying cikin ikon Allah yaci jarabawar,sauran month ya rage su tafi.

       A cikin 'yan kud'ad'en aikinsa yayi wa Nasreen siyayyar 'yan kayan pampers da sabulun wanka.Umma da kanta ta kai wa Reyhana ,cikin girmamawa suka gaisa da Umma ranar Mommy ma bata gida.

       Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa da dad'i babu ,tafiyar Ahmad ya rage week shida Umma sunje Zaria yayi sallama da wasu 'yan uwan ,wani yayan Umma ya bashi 30k ,shima wasu 'yan kud'ad'en nasa ya had'a dasu kad'an daga ciki yayi wa Umma 'yan siye-siyen kayan abinci.

       Ana saura kwana biyu tafiyarsa ya kira Reyhana suka gaisa yake tambayarta Nasreen, sede beyi mata maganar tafiyarsa ba,da ba zeje gidan ba seda Umma tayi da gaske yaje,Nasreen ta sake wayo kamanninta dashi sun sake bayyana yayi mata pics a sabon wayarsa da ya siya.

    Umma harda kukanta amma bata nuna a gabansa ba ,ranar da ze tafi shi kansa ya kasa cin abinci har airport Umma da Sadiq suka rakasa ✈(Nima nayi 'kwalla๐Ÿ˜ง).

Thank you so much for your warm support Ummeeytr,sisi kema ban manta dake ba ina godiya ,masoyan littafinnan na whatapp godiya mara adadi Allah ya barmu tare ๐Ÿ˜˜ Ameen.

         Umma da suka dawo tare da Sadiq jikinta a sanyaye ,tana tunanin yadda ze gudanar da rayuwarsa har tsahon lokacin da ze gama karatunsa,dan d'an nata be ta'ba yin nisa da ita ba kamar wannan karan.+

       Around 8pm Umma taji ringing d'in wayarta ,koda ta duba international number ta gani,dama a cikin ranta tayi tunanin Ahmad d'inta neh.

         "Umma". Ya kira sunanta.

         " Ahmad kaine".Umma ta fad'a da saurinta.

         "Eh". Ya amsa.

          " Kun isa lafiya?" Ta tambaya.

          "Lafiya lau Umma". Ya asa.

           "Toh kuna makaranta ne ko kuwa?" Ta tambaya.

           "A'a mun samu Apartment ne tare da  wasu 'yan kano da muka tafi dasu". Ahmad ya fad'a.

          " Toh abinci fah ?" Ta tambayesa.

           "Zanci". Ya amsa.

            " Toh ka samu de kaci karka zauna da yunwa kaji".Cewar Umma cikeda damuwa.

        "Toh inshaAllahu". Ya fad'a.

         " Yawwa ka kula sosai".Ta fad'a.
     
         "InshaAllah". Ya amsa.

     Daga haka sukai sallama,bayan nan ya kira Sadiq ma ya sanar masa ya isa.

        Ahmad ya samu yaci abinci kad'an duk da kuwa yana jin yunwa ,kawai kewa ce da ba'kunta suka sa ya kasa ci dayawa.

       Sauran da suke apartment d'aya dashi suna falo su uku se surutu suke kamar ba wanda yau neh zuwansu na farko ba,Ahmad kuwa rufo 'kofar d'akin da yaye ya kwanta dukda ba shi kad'ai ne a d'akin ba.
 
        Da'kyar ya samu bacci ya kwashe shi dan daya rufe idanuwansa Reyhana yake gani.

Washegari,6:08am ya tashi,hayaniyarsu ce ta tashe shi.
    
         Da sauri ya mi'ke yayo alwala yayi sallah.D'ayan room mate nashi yaga ya baje se narkar bacci yake da alama beyi sallah bama.

      'Karasawa yayi gadon da yake ya tasheshi,daga nan ya komo ya zauna.

       Ba jimawa sauran guda biyun sukai knock a d'akin.
        " Shigo". Ahmad ya fad'a.

         "Assalamu Alaykum". Sukai sallama.

      Ahmad ya amsa musu ,'karasowa sukai  wajensa sukai handshake.

        Nan suka sake introducing kansu.Da Ibrahim da  Idris se room mate na Ahmad, Imran sunansa.

        Kusan shine  sa'an Ahmad sauran kuwa baza sufu 22 zuwa 23 ba.

        Tare dukansu suka fita cin abinci a restaurant bayan sun shirya.

        Shawara sukai a junansu suka siyi kayan abinci ,inyaso sa dinga girkinsu a gida.

STORY CONTINUES BELOW
        Hrs later Ahmad ya kira Umma suka gaisa ,basiyi wani hira mey tsaho ba credit ya 'kare.

        Shi gashi ba mey hira ba sosai,yana hangosu a falo suna ta hirarsu kowa yana bada labarinsa banda shi da ya ma'kale a d'aki.

                    ***

       Duba da sun fara shiga class Ahmad ya bada attention akan karatunsa,inda yaci sa'a shima Imran yana son karatu,kuma a kwana biyu ya fara sakin jiki dashi sede har yanzu duk cikinsu ba wanda yasan Ahmad ya ta'ba yin aure.Suna waya da Umma amma ba koyaushe ba ,Sadiq ma.

     Tunanin Reyhana da Nasreen kuwa kullum dashi yake kwana yake tashi gashi har yanzu be sake yin waya da ita ba.

                    ***

Nigeria ***

        Umma ganin an d'an kwan biyu bata jin labarin 'yar jikallenta Nasreen dan ba waya take da Reyhana ba haka yasa ta shirya zuwa gidan.

        Lokacin da inno tayi mata iso falo sisters d'in Mommy suna nan sun baje se hira sike irin ta mata sun cika falon da hayani.

     Umma kan kujera ta zauna ,Anty Ummi ce ta lura da shigowarta ta gaisheta.Suma sauran suka gaisa da ita ba nuna alamar sun ganeta,Mommy tare da Anty Asma'u suka sakko daga bene.

       "Kamar babar Ahmad nake gani". Cewar Anty Asma'u 'kasa-'kasa.

       " Ehyi itace".Mommy ta amsa.

       "Toh ita kuma mey tazo yi?"Cewar Anty asma'u.

        "Kema kya fad'a". Mommy ta fad'a.

        Shiru sukayi basu sake magana ba lokacin da suka 'karaso inda Umma take.

        Umma bayan ta gaisa dasu take tambayar su Reyhana.

        "D'azu yara sun fita da ita za'ai mata photo,Reyhana kuma tana bacci". Mommy tai 'karya dan kuwa tana d'aki tare da Reyhana.

        " Ayya!"Umma ta fad'a a ranta bata ji dad'i ba.

         Daga haka shiru ya ziyarci d'akin,su kansu masu hirar shiru sukai suna 'kus-'kus Anty Ummi se alamu take musu da siyi shiru suka 'ki.

      Hakan yasa Umma ta tsargu,tana jiyo wata daga cikinsu tana cewa Anty Ummi "An rabu kuma meye na bibiya".
         Umma in ranta yayi dubu ya 'baci,a ranta tana fad'in "Zuwa ka duba 'yar d'anka ma ya zama laifi".

       Mi'kewa tayi taiwa Mommy sallama ta fita, bata kai bakin gate ba tajiyo kukan Nasreen kasancewar window na d'akin Reyhana a bud'e yake.

         Umma jin kukan Nasreen yasa ta gano 'karya Mommy tayi mata,ba yadda ta iya haka ta fita.

       Se bayan tafiyar Umma Reyhana taji Ikram da Sageer suna maganar,ji tayi dama ta sakko falo lokacin." Sema ta d'auka ko ina sane na'ki fitowa".Ta fad'a a ranta.

                  ***
      Umma tana isa gida taga Sadiq a 'kofar gida.

         "Umma unguwa kika jene?" Ya tambayeta.

        "Naje gidansu Reyhana duba Nasreen ne". Ta amsa .

      Daga yadda ya kula da fuskarta ya gano wani abu,seda suka shiga ciki ya sake tambayarta.

        "Ta 'kara wayo koh?"
         "Ai dayake ban samu na ganta ba". Umma ta fad'a tare da shimfid'a tabarmar dake jingine a tsakar falon.

STORY CONTINUES BELOW
      "Toh ya akai haka?" Cewar Sadiq yana son sake jin 'karin bayani.

      "Cha sukai wai an tafi kaita photo". Umma ta fad'a.

      " Cha sukai? Kuma Umma kin yarda? Toh ina ita Reyhanan?" Sadiq ya tambaya.

        "Nide ban ganta ba tana bacci suka ce".Umma ta fad'a.

       "Rainin hankali". Ya furta.

        Umma kaf ta bashi labarin abinda ya faru ,Sadiq   dama akwai saurin fushi lokaci guda ya hau masife -masife shi har Reyhana d'inma yayi blaming.

        Umma seda tayi ta bashi ha'kuri wai seyaje gidan yayi musu rashin mutunci.

  Cyprus 10:07pm ,Ahmad yana zaune kan kujera yasa litattafi a gaba yana karatu wayarsa tayi ringing.

     Koda ya duba yaga Sadiq,fuskarsa d'auke da murmushi yai picking.

       "Saddiqu". Ahmad ya kira sunansa.

       " Ya ,ya karatu?" Ya tambaya.

      "Alhamdullilah gashi muna tayi". Ahmad ya fad'a.

       " MashaAllah,toh bari na barka".Sadiq ya fad'a.

       "No !wait". Cewar Ahmad.

       " Wani abune?" Sadiq ya tambaya yasan Ahmad idan yana so ya fad'i abu haka yake.

       "Umma tana zuwa ganin Nasreen kuwa?" Ahmad ya tambaya.

       "Danme zata ke zuwa ana wula'kantata". Cewar Sadiq ba tare da yasan ze fad'i hakan ba.

        "Bangane ba Sadiq? Zuwa tayi suka wula'kantata!?" Ahmad ya tambaya ,pen d'in dake hannunsa ma ya ajje.

       Shiru yayi kafin ya fad'a masa duk yadda akai.Bayan sunyi sallama dashi ya ajje wayar gefe yana mey jin zafin abinda sukaiwa Umma.
        Da tunanin abin ya kwana ko karatun ma 'kin cigaba dayi yai ya rife littafin.

           °°3 years later°°
        
     Abubuwa da dama sun sauya ,Reyhana har yanzu bata sake wani auren ba duk wanda yazo yana sonta korarsa take tace ita bata shirya ba,tun Mommy tana magana har ta gaji ,ta koma Masters ma ta'ki aikin ma a nemo mata bazatai ba.Abba kuwa duk abinda tace bataso baya takurata ,Mommy ma sanin dalilinta Reyhana ke zawarci yasa bata takura mata.

       Nasreen ta 'kara girma ,3yrs da 'yan kai kamanninta da Ahmad ba abinda ya sauya sede 'karuwa ma.

       Ikram ce ta fito daga d'akinta taci kwalliya,yanzu ake jin 'yanmatanci tana 21yrs, biki ake a dangin Abba shine zasi dinner.

      D'akin Reyhana ta shiga inda ta tarar da ita ko d'auri batai ba se fama take da Nasreen ita a lalle setayi kwalliya ,kuma kawai salon 'bata fuska ne da kayan kwalliyar kansu.

       "Kai! Yaya ko d'auri baki ba haba dan Allah wannan ai har a gama dinner d'in". Ikram ta fad'a.

       " Inyee irin wannan d'auri haka pls nima d'auran irinsa".Reyhana ta fad'a.

       "Anty nima ki d'aura min". Nasreen ta fad'a cikin muryarta da bata gama fita ba.

        " Kinga fuskarki kuwa!" Cewar Ikram sanda ta kalli Nasreen.

         "Barni da ita nide gama d'aurin". Reyhana ta fad'a tana mi'ka mata d'ankwalin matiriyal  d'in.

       Sky blue ne ,d'inkin ya hau jikinta sosai doguwar gown ce ta shawu,itama Ikram irin kayan ne a jikinta.

STORY CONTINUES BELOW
       D'auri Ikram ta tsantsarawa Reyhana ga kwalliya data 'kara mata sosai ta fito kamar ba itace mey 3yrs daughter ba.

        Farin gyale d'an siriri ta yafa se purse silver ta zira takalminta me tsini silver.

         " Ummie zan biki". Nasreen ta fad'a tana miko hannunta.

         "Allura akewa yara a wajen,ki zauna da anty Walida". Reyhana ta fad'a tana spraying turare a jikinta.

       Dede lokacin Mommy ta shigo,baki wangalau ta saki ganin irin yafen da Reyhana tayi.

       " Reyhana mayafinne zaki sa'kala haka  a kafad'a?" Mommy ta fad'a.

       "Dinner fa akace". Ta fad'a tana kallon mudubi.

        " Toh ita wannan fa?" Mommy ta tambaya tana kallon Reyhana.

         "Tana tare daku mana Mommy". Cewar Reyhana.

           "Ikram mije,bye baby girl". Cewar Reyhana tare da shafa kumatunta ta d'auka key d'in motarta.

            Ko jira abinda Mommy zata ce basi ba suka fice,take Nasreen ta rusa ihu,Mommy kanta ta dawo tana rarrashinta" Atoh babarki ta ya dake".Mommy ta fad'a.

        Galleliyar farar Accord Abba ya siya mata bata fi shekara d'aya ba.

        Da sauri ta zugesu suka bar gidan gudun kar Abba ya dawo yace dare yayi tunda 9pm ya shige.

         Ba jimawa suka isa wajen bikin, sakin baki sukai dukansu ganin Sageer a wajen shida wata beb suna zaune.

          "Ikram kinga yarannan koh?" Reyhana ta fad'a disbelievingly.

          "Yes,na ganshi". Ikram ta amsa tana kad'a kai still bata d'auke idonta a kansu ba.

        " Ina cayai mana baze samu zuwa ba kansa ciwo yake,amma kin ganshi".Reyhana ta fad'a harda nuni da hannu.

       "Ai bama wannan ba kalli jibgegiyar da yake kulawa wannan ai seta zaune shi". Ikram ta fad'a.1

      Dariya suka hau yi ganin de abin bana 'kare bane suka 'karasa ciki ba tare daya kula dasu ba,dan yayi nisa se tsarata yake, ita kuwa madam d'in ta hakince se blushing take.

       Sageer bade 'yan mata ba,number 1 ne wajen kula bebs,ga tsaurin ido as age d'insa 24 da 'yan kai se a gansa da 'yan 25 zuwa 26 ma,duk wannan abin da ake Mommy bata da labari dan ita a ganinta Sageer har yanzu yaro neh.

       Reyhana tunda tayi pic da Bride ta samu seat ta hakimce,Ikii ta bari can itada sauran sa'anninta suna ta shoshalewa.

        Kamar daga sama taji muryar namiji.

        " Assalamu Alaikum".

    Tana d'ago kanta taga Sameer(D'an yayan Mommy).
            "Sarkin naci". Ta fad'a a ranta.

             A ciki -ciki ta amsa sallamar,take ta d'aure fuska.

            " Toh waye ya fad'a masa ina nan?" Ta tambayi kanta,wata zuciyarce tace"Ikram".

       "Munafuka!" Ta furta.

       "Na'am?" Cewar Sameer.

        "No bance komai ba".Ta wayance ,batai tunanin yajita ba.

         " Surprise, right?"Ya tambaya yana d'age gira .

     Hakan yana d'aya daga cikin abinda yasa take jin haushinsa,iyayin tsiya.

        "Surprise d'in mey kuma?" Ta fad'a cikeda 'kosawa.

         "Ehman,I know zaki mamakin ganina anan tunda baki sanar mini ba". Ya fad'a.

          " May i sit?"Ya tambaya.

          "Uhmm". Ta fad'a.

      Ji take kamar ta kurma ihu,hirarsa tamkar kukan sauro haka take ji.

      " Thanks". Ya fad'a.

     Thanks d'in ma cikin wani murya da bata so ya fad'a.

       Dinner d'in ma seda tayi regretting zuwa saboda Sameer,ya cika ta da surutu iya kaci tace "Eh ko a'a.

       10:39pm na bugawa ta kira Ikram suga tafi,kafin su tafi a wajen ma seda ya isheta.

     A hanya tayi ta balbale Ikram da masifa har suka is a gida ,Nasreen tuni tayi bacci da sand'a suka shiga d'akunansu kar Abba ya jiyo su.

       Sameer tun kafin tayi aure yake son Reyhana ,amma fafur ta'ki shi.Bata dad'e da aure ba ya tafi America ,befi shekara  d'aya da dawowa ba yaji labarin mutuwar auren Reyhana shine ya sake komowa har yanzu beyi aure ba ,yana da shekara 32 a yanzu.Ba fari bane chan yana da kyau shima kuma dogo ne,ba 'karamin son Reyhana yake ba gashi duk yadda takai ga shunning d'insa baya ha'kura.

    Cyprus***

         Zaune kan kujera a falo,su Imran sun d'an fita.Ahmad yanzu sun zama 'yan gari sun saba da abubuwa ,Imran dashi sun zama abokai sosai shi kad'ai yasan ya ta'ba yin aure,hakan ma wani lokaci ne daya ga pics na Nasreen a wayarsa kuma yana yawan ji yana maganarta a waya idan sunyi waya da Umma.

        Babu wani chanji sosai gameda shi na shekaru sede fatarsa data 'kara yin haske, ga gashin kansa ma da yanzu ba sosai ya fiya askeshi duka ba ,yananan luf-luf hakan yana daga cikin amsarsa da weather d'in 'kasar tayi.

       Kiran daya shigo wayarsa ne yasa ya ajje cup d'in tea dake hannunsa.

    Number ne daga Nigeria ya gani amma besan mey shiba.

            "Assalamu Alaykum". Ya fad'a bayan yayi picking.

            " Waalaikumussalm". Yaji muryar mace ta amsa.
Ya Ahmad ina kwana".Aka fad'a daga d'ayan 'bangaren.+

         " Lafiya lau".Ya amsa yana so yayi recognizing muryar me magana.

            "Zainab ce". Ta fad'a.

             " Oh! Zainab, ban d'auki muryar ba ya gida?" Ya tamabaya.

              "Lafiya lau,ya karatu?" Ta tamabaya.

              "Alhamdulillah". Ya amsa.

              " Ina gidan Umma fah".Ta sanar masa.

             "Ok ,kuna hutu ne??" Ya tambaya.

              "Uhh ai mun kammala ma". Ta amsasa.

        " Good,Allah yasa albarka". Ya fad'a.

           "Ameen,ga Umma zakui magana". Ta fad'a.

         " Ok bani ita".

        Umma da take kusa da ita ta mi'ka mata.

        "Ahmad kaji wayata shiru koh?" Cewar Umma bayan ta ma'kala a kunnenta.

        "Eh na kira bana saminki". Ya amsa.

         " Wayar ce ta samu matsala shine nasa Zainab ta kira ka ,tazo nan gida dayake ta samu admission a B.U.K  zata fara zuwa".Umma ta fad'a.

     "Ok,yanzu take fad'a mini sunyi graduation ashe har ta samu admission". Cewar Ahmad.

      " Ehh,na sami mey taya ni zama".Umma ta fad'a.

        "Gaskiya kam,zan kira sadiq seya kai maki gyaran wayar taki".

        Hira kad'an suka ta'ba sannan sukai sallama.

                ***
     Ta 'bangaren su Reyhana kuwa Inno ta tafi garinsu anyi rasuwa,yau kowa daya tashi seya nufo dining yaga wayam.

        " Mommy kuwa ta fito?" Reyhana ta tambayi bassam da yake falo shida Walida suna kallo.

       Bassam a shekaru ukunnan ya 'kara girma sosai dan ya kere Reyhana a tsaho yana 18yrs a yanzu,Walida ma ta 'kara tsaho se siranta kamar a 'balla ta๐Ÿ˜‚

       "A'a". Suka amsata.

       " Tohh! 9am fah,kace yau za'a sha yunwa kuwa".Reyhana ta fad'a tare da shiga kitchen d'in.

      Ruwan tea ta d'ora a tea pot ta komo falo tai joining d'insu.

     Ba jimawa Mommy ta sakko."Ina kwana ".Suka gaisheta a tare.

      " Lafiya".Ta amsa had'e da yin hamma.

     "Bade baku d'ora wani abu ba?" Mommy ta tambaya.

      "Ina fa,yanzu kowa yake tashi". Reyhana ta amsa.

      " Aiko yau kowa ya d'and'ana inno kunsan bata nan nima yau hutawa zanyi kwasan yadda kukai".Mommy ta fad'a.

    "Nide na d'ora tea,Ikram da Walida kuyi saura". Reyhana ta fad'a.

      Ikram tana bacci Walida ta taso ta se turo baki take ita batason aiki.

       Sageer yana fitowa daga d'akinsa yaji kiran Reyhana, sasu tayi a gaba har bassam suka shiga kitchen Mommy tai zamanta a falo.

      " Oya jeki d'ebo dankali keda Walida zaku fere"Reyhana ta fad'a.

      Sageer shi dariya ma abin ya bashi saurayi dashi wai za'a had'a da girki.Gefe guda ya tsaya ya nad'e hannunsa  yana kallan ikon Allah ,jira yake yaga shi kuma nashi aikin.

STORY CONTINUES BELOW
      "Toh su Sageeru se'ai blending pepper da onion". Reyhana ta fad'a tare da dire kayan miyan data d'ebo a bowl.

      Wani dariya ya fashe da ita harda ri'ke ciki." Haba kema da wasa kike ki dubi kamar ni kice nayi wani blending sekace cooku".

     "Kana mamaki koh,karkayi yaro in kasan wata bakasan wata ba".Ta fad'a tare da d'an matsowa kusa dashi ta rad'a masa yadda  su Walida baza suji ba.

       "Koh kayi ko kuma na fad'a wa Abba da Mommy d'ansu ya girma har Beb yana da ita".

         Sageer da sauri ya zaro ido yana mamakin yadda akai ta sani,what if da gaske zata fad'a ? Ya tambayi kansa.

     " Naji".Ya fad'a.

    Murmushin da yake ma ya koma ciki,turn d'in Reyhana ne se murmushin mugunta take.Su Ikram da suke jira suga zeyi ko baze ba take suka hau 'kunshe dariyarsu.

     Bassam kuma aka had'ashi da 'bare spices da za a had'a sauce d'in.

      Kowa aikinsa yayi facing Ikram se masifa take wa Walida wai tana fallatsa mata ruwa idan zata saka dankalin a ruwa.

     Sageer wai dan yayi sauri se wani cakumar attarugu yake yana cire 'ya'yan attarugun da hannu yana cillawa a blender d'in.

     Bassam mey spices har ya gama yana shirin fita ta tsayar dashi."D'an albarka  a soya wa 'yata indomie da 'kwai mana".Ta fad'a tana masa winking eye.

     Buga 'kafa yayi ya dawo se 'kun'kuni yake.

       Sageer bayan ya gama blending har ze fita yaji saman idonsa na 'kai'kayi, yatsansa ya d'ora ya sosa wheui!

    Lokaci guda ya fara dancing a tsakar kitchen d'in, Reyhana da ta d'ora kaskon suya taji 'kara.

     Kallone ya dawo kansa,Mommy da take falo ma seda ta jiyo ta shigo kitchen d'in.

      "Lafiya?" Ta tambaya.
   
      "Mommy idona!" Abinda yake fad'a kenan.

       "Kai mey ta kaika sa yaji a ido sekace yaro". Mommy ta fad'a tana dafa ha'ba.

        " Zoka tara idon a fanfo ka wanke".Reyhana ta fad'a kamar mey shirin yin dariya.

        "A daddafe ya 'karasa sink d'in yaje ya tara fuska ,duk da ya wanke idon be fasa dafe idon ba.

       " Ka tsaya mana a hure ma".Reyhana ta fad'a tana d'age ta dafe kansa sekace 'kan'kanin yaro.

      Ba su Ikram ba har Mommy seda tayi dariya,'kwace kansa yayi ya tsaya yana gogewa da hannun rigarsa.

     Ficewa yayi daga kitchen d'in ya barsu suna dariya."Maganinka kenan".Reyhana ta fad'a.  
     Kafin su gama girkin seda suka 'bata kitchen d'in, se 10:30am suka chi abincin.

     Nasreen da ta dad'e da tashi amma bata fito ba tana toilet ta saki fanfo se wasan ruwa take.

        Seda Reyhana ta koma d'aki ta jiyota,fito da ita tayi ta 'kwa'k'kwad'eta tayi ta kuka seda Abba ya rarrasheta.

       Har Reyhana tayi wanka ta shirya Nasreen bata sake hawowa saman ba,a falo ta iskesu ita da su Mommy.

      "Zo muje nayi miki wanka".Ta mi'ka mata hannu.

      Kafad'a ta ma'kale ita bazata yi ba,Reyhana ta mance ma fushi take.

      " Ki zauna hakan ina ruwa na,ki fara zuwa makaranta kowa ma ya huta".Cewar Reyhana tare da zama daga gefen Walida.

STORY CONTINUES BELOW
     Ba jimawa wayarta tayi ringing, tana dubawa taga Sameer.

        "Mtchww!". Tayi tsaki ta ajje wayar.

         Mommy data kula da ita tace " 'Kalau?"

       "Sameer ne". Ta amsa.

        "Toh kuma seki 'ki picking? Ni bana son wula'kanci".

         " Mommy damuna zeyi kawai".Reyhana ta fad'a.

      Se a kira na biyu neh tayi picking,bayan sun gaisa take ce mata yana bakin gate.

      "Toh ka shigo mana". Ta fad'a.

        Bata jira amsarsa ba ta katse wayar,wani haushinsa take ji.Yana shigo bayan sun gaisa ta koma d'aki taja hannun Nasreen da se surutu take masa.

               ***
   Har Sameer ya tafi bata fito ba tana d'aki.Da yamma Aunty Asma'u tazo gidan Mommy.

        " Ya kuwa wannan mutanen har yanzu shiru?" Anty ta tambaya.

       "Hmm har yanzu, duk tsahon shekarunnan da aka shafe shiru koh waya basu sake yi ba". Mommy ta fad'a.

      " Amma wannan basu da mutunci,ace ko kira suji lafiyar 'yarsu bazasi ba balle akai ga ha'k'ko'kinta kuma,wannan akwai mutanan banza,ita Reyhana idan ta kirashi baya amsawa neh?" Anty Asma'u ta tambaya.

      "Toh wayar ta samu tashiga ma tukun,kuma idan ma an sameshi tace masa meh?" Mommy ta 'kare da tambaya.

     "Tuna masa zatai ba dutse bace 'yarsa ,su wannan da wane idon ma zasi kalli yarinyarnan? 'yarda a yanzu idan ance babanta bata sani ba".

     " Ita ajinta kakanta ne Abbanta ai,barsu su cigaba da yanda suke so lokaci zezo zai nemi 'yarsa aikoh".Cewar Mommy tana jinjina kai.

               ***
     2 days later

       Zainab around 9:30pm lokacin tana d'aki Umma ma ta kwanta,wayarta ce a hannunta tana chat a Whatapp.Contact take dubawa idanta ya tsaya kan sunan "Ya Ahmad" kamar yadda tayi saving.

     Tana gwada bud'ewa taganshi online,haka kawai ta tsinci kanta tana son yi masa magana,typing tayi ta tura masa sa'ko kamar haka;
"Assalamu Alaykum,ina yini".

   Seda aka shafe kusan 10min yayi reply dan har ta fita daga profile d'insa.

        Ahmad be kula da message d'in ba da wuri,ganin  "Xynab" kamar yadda yayi saving yayi reply da;   
      
                   "Wa'alaikumussalam,lafiya lau".

      " Ya kke? Ya school ?"Ta tura.      

    "Alhamdulillah,ya kuke ?" Shima ya tambaya.

"Lafiya lau".Tayi replying.

" Ina Umma koh tayi bacci?" Ya tambaya.

    "Eh". Ta amsa.

      " Ok". Ya amsa.

Yatsa ta sa a baki tana tunanin mey zata kuma cewa ,kusan 2min basu sake magana ba.
    "Kin fara zuwa school d'in?" Ya tambayeta.
     
 
M

urmushi ta fara yi ganin ya sake mata magana wanda bata zata ba.
     
   
   "Se Monday". Ta amsa.

" Ok,wani course?"Ya tambaya.

"Industrial chemistry". Tayi replying.

" Good๐Ÿ‘ Allah ya bada sa'a".Yayi sending.

"Ameen, tnx". Tayi replying fuskarta d'auke da murmushi.

  " It's 10pm right? You should have sleep.

"Yaya by 11:00 dae koh". Tayi sending.

" ๐Ÿ˜ฑ it's late ,what will you do?"

"Ha! Chatting with you mana". Ta tura.

     " Are you sure? "Yayi sending.

    " Yes mana don't you believe me?"

"I do believe, ok am quitting now".Ya tura.

" Ok,nima yanzu zan kwanta".

"Gudnight ,recite du'a before sleeping".

" Tam night,bye".Ta tura.

Kamar yadda yace tayi addu'a tukun ta kwanta,shima ajje wayar yayi ya dauro alwala ya tada sallah.
     
Alhamdulillah we reach page 20,happy page twenty๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ   Umeeyr tace "Zainab want to snatch our ya Ahmad " ๐Ÿ˜‚
Juma'at Kareem.

     Reyhana kwance a kan gado ,Nasreen na manne da jikinta ta zagaye hannunta a bayanta da hannin damanta na hagunta kuma tana shafa mata gashin kanta,Nasreen da tayi nisa da bacci hankalinta kwance.+

       Babu rana da zata wuce Reyhana batayi tunanin Ahmad ba,idan ta tuna shekarun da aka shafe basu sake had'uwa ba kuma ba waya seta ji haushinsa wani 'bangaren zuciyarta kuwa har yanzu da gurbin sa a ciki."Meyasa ze guji 'yarsa? Mey Nasreen tayi masa a duniyannan daya watsar da ita?" Abinda kullum take tambayar kanta wanda amsar hakan ta gagara.

       Bata yi aune ba taji danshi a fuskarta,hannun ta sa da goge hawayen ,the more tana gogewa the more yana sake fitowa dan haka ta dena mah,gam ta sake ri'ke Nasreen a jikinta tare da d'ora ha'barta lightly a goshinta ,idonta ta rufe gam ba jimawa bacci yai gaba da ita.

                 ***

    Zainab 8am ta tashi dan bata fiya bacci dayawa ba bayan subh,kamar kullum a nitse tayi shara ba tare da Umma ta tashi ba,haka toilet ma ta wanke sannan ta koma d'aki.

       8:20am,wayarta dake jone a charge ta zare.Chat da sukai da Ahmad jiya ta shiga dubawa a hankali step by step tana sake karantawa tana murmushin.

       Data tayi switching on ko zata ganshi online,koda ta duba taga be hau ba tun jiyan.

       Tana jiyo fitowar Umma daga d'aki ta ajje wayar ta fita,cikin rissinawa ta gaisheta.

      "Zainab da sassafennan kika tashi harda shara".Cewar Umma.

      Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba." To sannunki da 'k'o'kari".Umma ta fad'a.

       Har abincin breakfast tare sukai da ita,ko wanke-wanken ma bata bari Umma tayi ba ,haka Umma tayi ta shima ta albarka halin Zainab yana birgeta.

            ***
    Kiran Sameer ne yau ya tashi Reyhana 8:47am taji 'karar wayarta.

      "Hello". Ta fad'a bayan ta d'aga muryarta a cushe.

       " Morning ". Ya fad'a.

       " Morning ". Ta amsa rai a 'bace.

      " Tun d'azu nake jiran 9 yayi sena kira ki amma  I can't even wait,just want to know how you're doing ". Ya fad'a.

      " Am ok". Ta amsa kamar ta sha'ke shi.

     "Nasreen fah is she awake?" Ya tambaya.

      "Ya Allah". Ta furta a ranta dan ta gaji da amsasa ,magana da safe aiki yake mata haka kurum ma balle da Sameer.

       " Bata tashi ba nima bacci nake". Ta fad'a.

      "Oh am sorry na tashe ki,I just can't wait to hear your voice"

        "Uhmm". Ta fad'a.

        " Ok mayi waya anjima,yanzu ki koma bacci kinji bye". Ya fad'a.

         Ko amsasa batai ba tayi hanging taja tsuka.Baccin ma se ha'kura tayi.

      Tun kafin ta 'karasa sakkowa take jin hayaniyar su  Sageer.
  
        "Ku kuma kun cikawa mutane kunne daga tashi". Ta fad'a bayan ta sakko.

         "Hira muke me dad'i". Cewar Ikram.

         " Ni rufen baki". Ta fad'a tare da nufa kitchen.

STORY CONTINUES BELOW
     Mommy ta tarar tana had'a breakfast, tama kusa gamawa nan ta taya ta suka gama.

   °Cyprus°
 
       Yau Ahmad ba class saboda haka shida Imran suk a fita zagayawa bayan sunyi breakfast.

        Imran ya takura Ahmad seyayi pic,kusan seyace be ta'ba gani ya tsaya yin pic ba a hanya.

        "Kawai d'aya zakai,haba ko Umma ai ka turawa taga d'an handsome d'inta". Imran ya fad'a yana dariya.

       " Malam rabi dani". Ahmad ya fad'a yana cigaba da da tafiya.

        Imran daya tsaya daga can baya ya 'kwala masa kira.Shi ya zaci ko wani abune ,yana juyawa yaga flashing camera.

        "Wow! Kaganka kuwa". Cewar Imran yana 'karasowa inda yake.

         Ahmad a jikin pic d'in ya zira  hannunsa d'aya a aljihu hakan ya bada style sosai gashi fuskarsa da d'an murmushi (If u want to see the pic comment with yesss let me see who fall for Ahmad๐Ÿ˜‚).

      "Let me know idan kana son pic d'in kai magana na turo ma,if not senai posting a insta kaga baza a rasa masu so ba". Ya fad'a.

      Ahmad jin ya ambaci insta yasa ya ciro wayarsa ya mi'ka masa.

           " Ha! Better ". Imran ya fad'a.

           Sun d'an zazzaga gari tukun suka komo gida.

       Su Ibrahim kuwa dama jiran dawowarsu suke coz suke da kitchen๐Ÿ˜‚

         " Alhamdulillah gashi ya dawo".Ibrahim ya fad'a.

       Shi Ahmad ma ya manta shaf inba yanzu da sukai magana ba.

       "Maza yau mey za'a dafa mana neh?" Idris ya tambaya.

        "Se abinda kuka gani". Ya amsa.

         "Nikam yau d'an wake nake son ci". Cewar Ibrahim.

          " Nikuma sakwara".Idris ya fad'a shima.

         "Nikam dambu". Imran ya fad'a.

         " Kun dad'e baku ci ba".Cewar Ahmad ya watsa musu harara.

        Dukansu dariya sukai daman salan sashi magana ne.

         D'aki ya shiga ya rage jacket d'in daya d'ora kan kayanshi sannan ya fito zuwa kitchen.Seda yai kusan 5min yana tunanin abinda ze girka, idea ya d'auke yau da gobe ta'ki wasa sun gaji da abinda suke dafawa.
      
      Fridge ya bud'e yana kalle items d'in ciki,idea neh ya fad'o masa ya d'akko wayarsa yai searching nan ya gano stew na cous cous
       
       "Butter nut squash and White bean"
        
     Daya duba yaga suna da items da ake bu'kata,ba tare da 'bata lokaci ba ya fara had'awa.

         Kitchen yayi kaca-kaca everything scattered Maza! anyi girki๐Ÿ˜‚

       1hr later table is complete lunch is ready,Imran shi ya fara serving su Idris da 'kamshi ya bigi hancinsu suma suka d'ibi nasu.Ahmad kallonsu ya tsaya yi yana jira yaga ya taste d'in abincin nasa ze kaya.

       Imran spoon d'aya yakai baki yana tattaunawa still bece komai ba,alama Ahmad yayi masa da gira "yaya?"

        "That's yummy! bro"Imran ya furta yana sake d'iban wani loman.

        " Kai dama kasan da wannan kake barinmu da jollof?" Cewar Idris.

       "Wannan anyi mugun mutum". Ibrahim ya fad'a bakinsa cike da abincin.

STORY CONTINUES BELOW
       Bece komai ba se murmushi kawai dayake shima yaja plate ya ziba.

       Bayan sun gama ya koma d'aki,in less than 2min sega kiran Xynab.

          " Assalamu Alaykum".Tayi sallama.

         "Waalaykumussalam". Ya amsa.

         " Ina yini".Ta gaishesa.

          "Lafiya".ya amsa.

           " Ga Umma zaku gaisa".Ta fad'a.
           
           "Bari na kira". Ya fad'a tare da hanging.

       Baya so yai exhausting credit nata tunda alhamdullillah ana basu allowances.

         Umma ce tayi picking bayan ya sake kira,nan suka gaisa sun jima suna hira da ita kafin daga bisani sukai sallama.

                 ***

 Zainab  tun chat da sukai rannan basu sake yiba har ta fara zuwa school kuma yanzun an gyara wayar Mommy dan haka bata sake kiransa ba,shima test da yake dashi kwana biyu yasa baya hawa chat.

       Kusan about 2weeks kenan ,Zainab an 'kwame gaban mirror ana tsara d'auri farar fusakarta tasha make up as always bata fiya zama ba janbaki ba se kwalli shima bata fashin sawa ko ba fita zatai ba.

       Zainab itama tana da nata irin kyan most her exciting lips O shape matsakaicin tsaho gareta and ba siririya bace a murje take but not fat whoo! (Don't ask me about her hair fah,idan nace muku Fulani ce you know kawai!
๐Ÿ˜)

       Ko breakfast bata tsaya tayi bama,12:30 sun fito daga class a cafeteria suka tsaya it a da friend tata koda taci abinci wayarta ta d'auko ta bud'e whatapp luckily taga Ahmad online wani farinciki ne ya ziyarceta.

Xynab: "Hello"

" Hi".Yayi replying bayan  1min.

Xynab:"Ya school?"

Ahmad:"Alhamdulillah".

Xynab:  " Ni baka tambayi nawa school en ba". Ta tura bayan kamar 3min.

Ahmad:"Ohh ya school? ".

Xynab:" Seda na ro'ka

Ahmad:"Sorry". .

Xynab:" Is OK".

Xynab:"Toh kai wani course make studying?"

Ahmad:"Computer science".

Xynab:" Nyc".
Ahmad:"Where are you now?"

Xynab:"School".

Ahmad:" At school and you are chatting? "

STORY CONTINUES BELOW
Xynab:"Ai bana class".

Ahmad:" where? "

Xynab:"Guess!"

Ahmad:"Hmm masjid"

Xynab:"No"

Ahmad:"Ok,school compound"

Xynab:"Hhh No"

Ahmad:"Then where?"

Xynab:"So you gave up"

Ahmad:"Uhmm"

Xynab:"Cafeteria".

Ahmad:" Acici"

Xynab:"Am not๐Ÿ˜ž"

Ahmad:"Are you really not?"

Xynab:"Yes"

Ahmad:"I take back my word,Ok for you?"

5min silent batai reply ba,kuma bawai ta fita bane tana so taga ze damu.

Ahmad:"Hello are u there?"

Xynab:"Uhmm"

Ahmad:"I said am sorry "

Xynab:"๐Ÿ˜"

Ahmad:"Hmm Xynab"

Xynab:"What??"

Ahmad:"Nothing"

Xynab:"Please say it"

Ahmad"U are acting childish
๐Ÿ˜"

     Xynab:  "Am not"

Ahmad:"OK let see,how old are you?"

Xynab:"๐Ÿ˜ฏ"

Ahmad:"Look at you girl,you think I don't know?"

Xynab:"Yes๐Ÿ˜•"

Ahmad:"Look at you ,I even..."

Xynab:"Yaya what?"

Ahmad:"Forget about it ๐Ÿ™Š"

Xynab:"๐Ÿ˜ฑ"

Ahmad:"Time up,prayer time"

Xynab:"OK"

Ahmad:"Bye"

Xynab:"✋"

Gaahide ya sauka amma ya kasa dena murmushi,Zainab had seda 'kawarta Siyama tayi tapping d'inta ta dawo daga tunanin data tafi wata duniyar.

       She can't stop blushing yau tayi chat da Yaya conversation d'in ya mata dad'i ."Ashe yana magana haka" Ta fad'a a ranta.1

                    ***
    Reyhana koyaushe Sameer seya kira baya damuwa zata d'aga ko bazata d'aga ba.

      Sageer daba school yanzu take zuwa ba tinda ya gama  Ikram da ya rage mata 1yr kullum fama take da Sageer wajen kaita school ,Reyhana idan 'yan mutuncinta sun tashi wasu lokutan tana kaita.Yau ma ta shirya Sageer take jira jin shiru yasa Reyhana ta tashi taso shi dan idan Ikram da kanta zata rashin mutunci yake mata.

        Koda ta Shiga ta tatar yana bathroom ,har zata fito ta hangi wani rose flower akan mirror, dan san gulma da sauri ta 'karasa wajen ,rose d'in ta d'auka taga  greeting card daya sha ado cover d'in da heart kala-kala a ajje.

       "Lover boy". Ta furta a fili.

     " Yaya!" Ya kira ta da 'karfi tare da 'karasowa ya wafce rose d'in da card.

     "Iyee wata za'a kaiwa wannan Sageer?" Ta tambaya tana murmushi.

   "Babu". Ya amsa yana turasu a drawer.

" Idan baka fad'a min ba a bakin Abba Yaro".

   "Kai dan Allah waike.."

    "Yanzu de fara fita ka kaita school idan ka dawo mayi maganar lover yaro". Reyhana ta katseshi tare da fita tana dariya.
Zainab yanzu har ta saba ma kanta inde batai chatting da Ahmad ba bata jin dad'i,duk ranar friday kuwa seta kirashi sun gaisa.Umma har ta soma gano wani abun gameda Zainab dan ta tana lura da ita bata da zance sena Yaya Ahmad.

      Har pic d'insa ta saka ya turo mata wai duk sunan Umma ce zata gani dukda kuwa ba haka bane.Tun bata gasgata abinda zuciyarta ta fad'a yanzu ta yarda she fall for him.

                ***
Reyhana ce tsaye  hannunta ri'ke da yarinya ,a hankali ya 'karasa inda suke a tsayen.Koda ya isa wajensu ya tarar sun juya masa baya.

        "Reyhana". Ya kira sunanta cikin sanyin murya.

         A hankali ta juya fuskarta cikeda hawaye da nuna alamar damuwa.Kallonsa ya mayar kan yarinya ,a hankali ta waigo sede fuskarta ba komai(Hollow)
   A razane Ahmad ya farka,lokaci guda ya had'a zufa .Agogo ya kalla yaga 2:30am ,jikinsa a sanyaye ya shige bayi ya d'auro alwala ya tada sallah.

        Ko bayan ya idda sallar ya kasa komawa bacci,mafarkin da yayi ne yake ta masa yawo a kansa.

      " Koh wani abun ne ya faru?" Ya tambaya a zuciyarsa.

       "I have to call Reyhana  tomorrow morning".
        Wayarsa ya d'akko ya shiga gallery,photo na Nasreen tana baby ya bud'o yana kalla,hannu ya d'ora kan fuskarta yana shafawa a ransa yana ta sa'ke-sa'ke.Wayar na hannunsa bacci ya saceshi ,kan 'kirjinsa ya kifata ya soma bacci.

         Washegari da safe bayan yayi breakfast ya shige d'aki.Wayarsa ya d'auko ,number d'in Reyhana ya sa a wayar dan numbern ta baze goge a memoryn kansa ba.Da 'kyar ya samu yai dialing sede bata fara shiga ba ya katse.

      Kusan seda ya maimaita haka yafi sau hud'u amma sam baida courage yana tunanin ta ina zai soma magana kuma mey ze fad'a mata? Ya fad'a a ransa.

      Haka ya ha'kura da kiran ya ajje wayar gefe yana mey jin haushin kansa, da ace be d'au tsahon wannan lokacin ba da ba abinda ze hana ya kirata.

      Umma ya kira suka gaisa se sadiq shima dan sun kwana biyu basi waya ba.

               ***
Reyhana 'kawarta saudat ta haihu yau ake suna last two years tayi aure.

       Nasreen se tsalle take yau za'a unguwa da ita ta ishi kowa da maganar duk wanda ta gani seta fad'a masa Ummienta zata unguwa da ita dan Reyhana bata fiya fita unguwa da ita ba gara ma Mommy.
     
     
    3:30pm ta shirya ,itama Nasreen an shiryata tayi kyau sosai kamar a d'auka a gudu.

       Sallama sukai da Mommy suka fita.Ko barin layinsu batai ba mota ta tsaya yin duniya ta'ki tashi.

       Gashi Sageer baya gida balle ta kirashi ya kaita Mommy kuwa ta dena basu motarta.

      Tana cikin tunanin yadda zatai sega motar Sameer ta doso layin.

       "Shikenan kuma anace yazo". Ta fad'a tare da dukan steering motar.

        Aiko yana ganin motarta ya tsaya,yasan ko ya sauke glass d'in motarsa ba sauke nata zatai ba dan haka ya fito.

      Se da taga yazo daf ta zuge glass d'in.

       "Fita zaki ?" Ya tambayeta.

         Kai ta girgiza masa alamar "Eh".
        " Ok,but amma kamar motarki ya samu matsala koh?"
       "Eh amman zan samu napep". Ta fad'a dan karma yai mata tayi.

       " You don't need that,am here Reyhana senai dropping d'inki wajen da zaki". Ya 'kare maganar da murmushi.

STORY CONTINUES BELOW
       "No Sameer thanks don't worry zan tafi da kaina". Ta fad'a.

       " Reyhana come on ni nace fah'.Ya fad'a.

        "Sameer..."

          " Please".Ya katseta.

           "Ok". Ta furta.

     Dande ba yacca zatai neh kuma batason missing zuwa shiyasa dole ta ha'kura ze kaita.Baba mey gadi tasa ya kira mata mey gyara kafin ta dawo.

       Se janta da hira yake amma bata wani responding sosai " Eh" ko "A'a" shine abinda take amsasa. Ya rasa gane wace irin mace ita,har yanzu bata chanja ba tana nan da halinta ,sekace yau ta fara ganinsa.

    Rabin hirar ma da Nasreen sukai ,yana kaisu tace ya tafi zata kira Sageer yazo d'aukansu.

      ***

  Zainab yauma taci sa'a Ahmad na online, waje na musamman ta samu ta 'kule 'kuryar d'aki an d'auki pillow an d'ora a cinya ta aza hannunta akai se tapping phone take.

        Xynab: "Yaya an bamu wani assignment naso ace kana nan da ka koya min".

    Ahmad:" Hmm".

    Xynab: .Yaya wai me hmm d'innan take nufi da anyi magana sekace hmm".

    Ahmad: "Sarkin tambaya ".

Xynab: " Eyi ina so na sani".

Ahmad: Haka kike a school? "

Xynab:"Yes ๐Ÿ˜€"

Ahmad: "Ok, kina nufin kice duk wannan samarin class d'in naku haka kike musu koh"

Xynab: "Laa! ๐Ÿ˜ฑ Yaya ni bana kula mazan class d'in mu fa ,ni idan bakai bama ba wanda nake kulawa".

Ahmad:"Hmm".

Xynab: "Ka ganka koh๐Ÿ˜’"

Ahmad:"Stubborn ".

Xynab:" Naji,yaya saura wata nawa ka dawo?"

Ahmad: "Mey kika tanadar mini?"

Xynab: "I just ask".

Ahmad :"not more than 9"

Xynab: "๐Ÿ˜ฑhar 9"

Ahmad: "Yayi nisa?"

Xynab: "Sosai,kai bama ka damuwa".

STORY CONTINUES BELOW
Ahmad:Toh ya zanyi inma na damun?"

Xynab:Umma kam tana kewarka"

Ahmad: Umma kad'ai?"

Xynab:"Uhm.."

   Ahmad :Wannan sister tawa batai missing d'ina ba".

A ranta seda taji ba dad'i ,ita bataso yake ce mata sister gara ya kira ta da sunanta.

Xynab: "I do mana๐Ÿ™ˆ"

Ahmad: "Uhm harda rife ido".

Xynab:"...."

Ahmad: "Mey hakan yake nifi?"

Xynab: "๐Ÿ˜๐Ÿ˜"

Ahmad: "Kin ganki koh,shiyasa nace maki.."

Xynab: "Kace ni yarinyace koh? Yaya university fa nake kuma wanda yake 17yrs shine za'a kirashi yaro ? nide ba yarinya bace๐Ÿ˜ "

Ahmad :"Hhh just 17 ,sannu aunty Zainab"

Xynab: "๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ฌ kuma an dena chat d'in".

  Kusan 5min bata sake typing ba shima haka,ganin da gaske take dan yaga alamar ta sau'ka seya kira.

      " Hello".Ta fad'a ciki-ciki.

      "Ayya sister sorry am just joking". Ya fad'a.

      Boom! Taji zuciyarta tayi alert ,wani tsantsar sonshi ne ya sake shiga zuciyarta,yanayin yadda yai magana ne yayi mata dad'i  dan bata ta'ba ji yayi irinta ba(Ahmad fa ya manta bada Reyhana yake magana ba๐Ÿ˜‚)

        " Na'ki d'in". Zainab ta fad'a cikeda shagwa'ba.

        "Please". Ya fad'a.

         " Toh a koma chat tukun".Cewar Zainab.

         "No,sekin ha'kura.Ya fad'a.

           "Toh idan na ha'kura baza ka sake cemin yarinya ba?"

         "Bazan 'kara ba". Ya amsa.

           "Toh na ha'kura". Ta fad'a.

           " That's my zee". Ya fad'a shi kanshi besan lokacin ba.

      "Wannan wata irin su'butar baki ce ta sameshi?" Ya fad'a  a ransa.

      Zainab ta kasa sake cewa komai dan ruwan kanta ya 'kone what if shima yanda take ji haka yake ji? Kai amma da tafi kowa jin dad'i.Du ita kad'ai take zancenta a zuciyarta.

       "Zainab are you there?" Ya tambaya.

       "Eh". Ta amsa a hankali.

        " Bacci koh?" Ya tambaya.

          "Uhm". Ta amsa duk da ba baccin take ji ba kawai de over happy yasa wayar ma ba zata iya ba a yanzu.

            " Ok,toh kiyi addu'a ki kwanta". Ahmad ya fad'a.

         "Toh ,seda safe". Ta fad'a.
   
       Shima seda safen yace tukun yayi hanging.Da 'kyar ta iya saita kanta ta kwanta wayarta a gefen kanta tayi bacci dan pic nasa da imran yai masa ta 'kura ma ido tayi ta kalla.

      Yana ajje wayar gefe ya lura da Imran da yai tsaya yana wani murmushin na tarfo ka.

        " Mey kake kai kuma bakai bacci ba?" Ahmad ya tambaya yana wayancewa.

          "Mallam ba abinda zaka 'boyen,na jiyo ka". Imran ya fad'a.

          " Kaji mey? "Ahmad ya tambaya yana nuna be san komai ba.

         " Karka rainan hankali ka gane mey nake nifi,kullum ace sister toh yau 'karyarka ta 'kare".

      "Idan ba sister ta bace taya zance maka haka".

      " Ai shiyasa naji kana kwantar da murya ,ashe kaima ka iya, ko dayake dama ance irin ku.. "

    Be 'kare ba Ahmad ya cilla masa pillow a fuska.Dariya yai tayi sannan yace.

      "Gara ka lalla'bani ka bani labari idan ba haka ba na fallasa magana gun wa'ancen kasan su baza su raga ma ba".

        "Allah Imran ba wasa nake ba ni ba wani abu tsakanina da Zainab kawai na d'auketa a matsayin sister ne". Ahmad ya fad'a fuskarsa ba alamar wasa.

       " Hmm ai daga sister d'in ake zarcewa,kuma ni ai hakan ma dad'i yayi mini kaga du sauran damuwarka na past zaka manta dashi".Imran ya fad'a.

       "Na fad'a maka ni aure ma baya gaba na,koda ace na gama karatu ba aure zan bafa". Ahmad ya fad'a.

      " Kasan kaima hakan baze yiwu ba mahaifiyarka bazata bar hakan ba,akan wata bazaka kashe life d'inka ba".


       "Who knows ma koh ita tayi nata auren,saboda haka kawai ka bawa Zainab dama bakasan irin alkairi dake tattare da ita ba kuma koh a yanzu kasan she is a kind person".

        " Imran please let not talk about this now,bacci nake ji".Ahmad ya fad'a.

      "Ok ,amma kayi tunani". Imran ya fad'a tare da nufar nashi gadon.

      Ahmad sam bawai baccin yake ba kawai de ya kwanta ne ,kalaman Imran sun basa tsoro mussaman maganar " Who knows ma ko tayi nata auren".Abinda ya tsaya masa a rai kenan.

       "What if abinda ya fad'a gaske ne,3yrs zeyi wuya ace bata sake aure ba,but Zainab? toh ita Zainab damage tana da feelings a kaina ne? taya zata so ni? taya zan aureta ma yarinya ce fah? No this is not possible". Da wannan tunanin yayi bacci.
Ahmad tun sanda sukai chat da Zainab be sake hawa online ba yau sati d'aya.Yana so yayi avoiding d'inta yana mey tsoron kar maganar Imran ta tabbata,d'azunma yana ganin kiranta amma ya'ki picking.

       Littafinsa ya d'auko ya soma karatu su Imran sun fita shi kad'ai ne a gidan.Kiran Umma ne ya shigo wayarsa,da farko yayi tunanin koh Zainab ce seya share,se a kira na biyu ya duba yaga Umma.
  
        "Umma ina kwana". Ya gaisheta.

        " Lafiya lau,ya karatu?"Umma ta tambaya.

        "Alhamdulillah". Ya amsa.

         " D'azu muka dawo daga asibiti Zainab bata da lafiya". Umma ta fad'a.

         " Toh! Meya sameta?"Ya tambaya.

         "Malaria neh". Ta amsa.

          " Allah ya sawwa'ke".Ya fad'a.

          "Ameen". Ta amsa sannan sukai sallama.

      " Shiyasa ta kirani ashe,Allah sarki".Ya fad'a a ransa.

     Dialing number d'inta yayi amma batai picking ba kusan 3× dole ya ha'kura a ransa ya ayyana ko fushi tayi tunda taga ya amsa kiran Umma.

      Karatunsa ya cigaba dayi se bayan 1hr tukun ya sake kiranta ,se a karo na biyu ta d'aga.

      "Assalamu Alaykum"
       "Waalaikumussalam". Ta amsa a hankali.

        " Zainab ".Ya kira sunanta.

         " Uhm".Ta amsa a ciki.

          "Ya jiki?" Ya tambaya.

           "Naji sau'ki". Ta amsa.

   Sunfi 2min ba wanda ya sake cewa komai.

       " Am sorry d'azu bana kusa da wayar lokacin da kika kira".Ahmad ya daure ya fad'a.

       "Uhm na gane".Ta fad'a.

        " Kinsha magani?" Ya tambaya yana so ya chanja topic.

      "Eh nasha". Ta amsa.

      " Toh ki daure ki dinga cin abinci kinji".

       "Tahm". Ta fad'a.

       Daga haka sukai sallama,ta ajje wayarta befi 1min ba message ya shigo.

    " Get well soon Sis"

     Lokaci guda ta saki murmushi ,har cikin ranta taji dad'i ya damu da ita.

                 ***
     Reyhana ce a d'aki ta ciga tayi fam haushin ya isheta saboda Abba yayi mata zancen Sameer.

      Mahaifiyar Sameer da kanta tazo wajen Mommy sukai maganar Reyhana Mommy kuma ta fad'a wa Abba abinda yake faruwa.

     Tana cikin wannan yanayin Walida ta shigo take fad'a mata Sameer yazo.

      "Kije kice ganinan".Reyhana ta fad'a.
   
      Mayafi ta d'auka ta yafa sannan ta fita.

      A falo ta tarar dashi shi kad'ai ko Nasreen bata nan,zama tayi opposite dashi.

       Bayan sun gaisa Sameer ya fara magana"Uh..Reyhana bakya ganin it's the right time?".

      " Right time for what?" Ta tambaya.

        "To give me chance, Reyhana baza kice bakisan abinda ke raina ba   duk iya tsahon shekarunnan ,at first nayi losing and now ga second chance na sake samu i don't want to miss it you know ,I so much care about your life,  everything yours you are always in my mind ,my love for you  will never vanish from my heart you are the only one i ever loved,  you are my first love and no woman can ever take your place in my heart, yet I never find someone like you  ,Reyhana you are different from others, you are unique, if am to stay here for years I can't stop describing how i valued you and the love that I have for you,Reyhana please consider".

STORY CONTINUES BELOW
       Reyhana sam kalamansa beyi tasiri a zuciyarta ba dan be hanata fad'a masa;" Sameer,a yanzu inaso na koma karatu and i need to wait for Nasreen to start schooling".

       "Kina nufin kice se ta fara makaranta and se kin kammala masters right?"

      "Yes". Ta amsa.

        Jira take taga mey zece ,zuciyarta tana fad'a mata " Shikenan kin kawo 'karshen abin,Sameer baze iya jira har wannan lokacin ba".

       D'an guntun murmushi yayi kafin yace"Reyhana how many times do i have to tell you i am always your supporter I promise to be by your side always and forever, wannan ba wani matsala bace I promise to wait for you no matter how long it wiil take us".

         "Sameer taya zaka jirani har wannan lokacin b..." Bata 'kare ba ya  katseta.

      "I promised Reyhana".

       Shiru tayi bata sake cewa komai ba ,shigowar Nasreen  tasa basu cigaba da magana ba.'Karasowa tayi wajen ummienta tana mata hira,daga baya ta koma gun Sameer.

            °•° >3 years Later <°•°

   " Nasreen!" Reyhana ta kwala mata kira tana daga d'aki.

         Seda ta kwashi minti kusan 5 ta shigo d'akin,tana manne daga jikin 'kofa ta 'ki 'karasowa se zazzare ido take cikeda tsoro.

       "Zonan!" Ta kira ta tsawace.

          "Ummie dan Allah karki dakeni". Ta fad'a cikin rawar murya.

           " Ayyo! Watoh kinsan mey kikai? Zonan nace".Reyhana ta fad'a tana mata nuni da yatsa.

     A hankali ta 'karaso gurin kanta a sunkuye.

      Rigar uniform d'inta ta makaranta ta d'auko ta nuna mata.

       "Waya yanka wannan?" Ta tambayeta.

        Shiru tayi bata amsa ba yanzun ta d'ago kanta.

       "Ba magana nake ba?"

        "Ummie kiyi ha'kuri na dena". Ta fad'a kamar zatai kuka.

        Reyhana da hanzari ta tashi tana shirin fizgota sega Abba ya shigo d'akin.

     Da gudu taje ta ma'kale a jikin Abba.

      " Toh meya faru kuma?" Ya tamabaya yana d'ago kanta.

     "Dukana ummie zatai".Ta amsa.

     " Ya da haka?" Cewar Abba yana kallon Reyhana.
  
      "Abba rigar makarantarta ta yaga saboda karta je gobe".Ta amsa tana nuna masa.

       "Ayi mata afuwa yanzu bazata 'karaba ,uniform d'in ba biyu bane?" Abba ya tambaya.

    Se lokacin ta tuna biyu ne da idonta ya rife,Nasreen jin ance biyu ta tur'bina fuska dan bata son zuwa makaranta.

STORY CONTINUES BELOW
      "Ungo chocolates d'inki". Abba ya fad'a tare da mi'ka mata nylon dake hannunsa.

     Tsalle ta shiga yi tazo wajen Reyhana tana nuna mata.

     " Toh nagani seki ce kin gode".Ta fad'a.

      "Abba thank you". Ta fad'a.

       " Yawwa 'yar baturiya".Abba ya fad'a.

      Tare suka sauka 'kasa da Abba ta ruga a guje  wajen su Walida tana nuna musu.

         Walida da anzama 'yan mata da ace dane da seta ce ta bata, yanzu kuwa kau da kanta tayi ta cigaba da abinda take.

       A shekaru ukunnan abubuwa da dama sun gudana.Reyhana ta kammala masters d'inta,Nasreen kuwa an sata makaranta 2yrs da suka wuce yanzu tana nursery 2 koyaushe fama ake da ita wajen shiryawa school.

      Sageer tuntuni ya fara aiki a asibiti as medical laboratory technician ya zama busy ba kasafai suke ganinshi a gida ba se dare.

       Ikram ma ta zama cikakkiyar journalist tana zuwa aikinta itama,se Bassam da saura shekara d'aya ya rage ya kammala degree d'insa,Walida wannan shekarar tayi graduating yanzu admission take jira.

       Sameer kuwa ya koma America amma yana zuwa jefi-jefi kuma wani sa'in suna waya da Reyhana.

       Mommy se kallo dan wani lokacin idan ta gansu full house setaga kamar ba ita ta haifesu ba ,kowa ya girma.

                   ***
Ahmad°•°

        Shigowarshi gida kenan daga gidansu Sadiq yake bayan ya dawo daga aiki ya biya se yanzu ya shigo gida,6:02pm.

        D'akinsa ya shiga ya watsa ruwa tukun ya fito cikin 'kananan kaya blue jean da ba'kin T-shirt.

    A falo ya iske Umma,cikin girmamawa ya gaisheta.

      "Yaushe ka shigo banjiba?" Ta tambaya.

       "Ba jimawa". Ya amsa.

        " Toh abinci fah".Ta tambaya.

       "A'a na 'koshi". Ya amsa.

        " Nikam gajiya akai da abincin nawa yau kusan kwana uku ba a ci".Umma ta fad'a.

        "No kawai bana jin yunwa neh fa anjima zanci". Ya fad'a da murmushi kad'an a fuskarsa.

     "Toh ai shikenan". Ta fad'a.

       Remote  dake kan center carpet ya d'auka ya chanja channel daga Arewa24 zuwa MBC Action.

         " Aikin kenan ,wannan masu damben koh me za'a kalla anan oho". Umma ta fad'a.

       Ahmad kuwa murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba ya cigaba da kallonsa.

       1 year kenan da fara aikinsa ,mahaifin Zainab shi ya taimaka masa ya samu aiki a NGOs(Non-governmental organizations).

     Komai ya sauya tun sanda ya samu aiki,Ya gyara musu gidansu ya koma kamar sabo ba abinda Umma ta rasa a yanzu inde na bu'katar alatu da sauran wani jin dad'i although rayuwa ba koyaushe ake cikin jin dad'i ba no matter how billionaire you are.

       A yanzu haka yana da farmland na noman shinkafa kuma cikin ikon Allah yana samun profit kuma wannan shawarar Umma ce ta sashi yin noman shinkafar.

      Zainab tana zaria, ta kwashe 2weeks a can amma nan da kwana biyu zata dawo tunda wannan week d'in aka koma school.

      Zainab ba abinda ya chanja a cikin ranta gameda son da take wa Ahmad sede har yanzu bata fito tace tana sonsa ba.

     Tun sanda ya dawo gida Nigeria Umma tayi ta tirsasashi yaje gidansu Reyhana amma kullum seya ce mata ba yanzu ba,daya gaji da tunatar dashi da take seyai 'karya yace yaje,idan ta tambayeshi ya sake zuwa seyace mata "Eh" akan haka ya barta.

     Daga yayi attempting zuwa seya fasa, baida kalaman daze fad'a mata(A tunaninsa) from bad to worse da ana maganar 4yrs yanzu 6yrs be saka 'yarsa a ido ba,shikanshi idan ya tuna yana jin haushin kansa.

                    ***

     Reyhana kuwa a zuciyarta tana 'ko'karin mantawa da Ahmad amma kamannin da Nasreen ta d'auko na Ahmad yasa bazata mance da fuskarsa ba,ita tama fidda ran sake ganinsa a rayuwarta.

      9pm lokacin baccin Nasreen,seda tayi addu'a kamar koyaushe Reyhana tana karanta mata ita kuma tana repeating.

     Seda ta tabbata tayi nisa da bacci tukun ta komo falo,duk yaran gidan suna falon amma banda Sageer.Kusan kwana biyu haka yake seya 'ki fito ba kamar da ba dayake fito a d'an yi hira kafin su kwanta.

     "Walida Sageer be dawo bane?" Reyhana ta tambaya.

    "Ya dawo yana d'aki". Ta amsa.

     " Yaci abinci?" Ta sake tambaya.

     "Beci ba ,Yaya Ikram ma tana masa magana yayi banza da ita ya wuce d'akinta".Cewar Walida murya 'kasa-'kasa.

        Kai kawai ta kad'a ta zauna kan kujera.
Did you see the pic above??๐Ÿ‘†

Washegari da safe around 8:15am kowa ya hallara a dining seat d'in Walida ne kad'ai empty se Nasreen da tun d'azu driver ya kaita makaranta.+

   
"Walida bata tashi bane?" Abba ya tambaya.

"Ta tashi". Ikram ta amsa.

" Toh mey take baza ta fito ba?" Mommy ta fad'a.

"Ikram kije ki kirata". Cewar Mommy.

" Mommy nafa makara is almost 8:30am".Ikram ta fad'a.

"Bari na kirata". Reyhana ta fad'a tare da mi'kewa.

Murya taji 'kasa-'kasa lokacin da ta shiga d'akin,blanket taga alaman Walida ta rufe kanta dashi.

" My Prince ka daure kasha magani idan ba haka ba kanka ze cigaba da ciwone kaji".

Baki Reyhana ta saki jin muryar Walida tana waya.'Karasawa gadon tayi ta cukuikui blanket d'in ta yaye ta.

       Cikin razana Walida ta mi'ke zaune ,wayar ma tayi cilli gefe da ita,a zatonta Mommy ce.Ganin Reyhana ce yasa ta d'an ji relief tasan komai zezo da sau'ki
    
       "Iyye abinda kikeyi kenan?" Reyhana ta fad'a.

     Walida a sukwane ta d'auki wayar tayi hanging sannan ta dawo da kallonta wajen Reyhana.

       "Da 'kawata fa nake waya". Walida ta fad'a.

        " Shiyasa naji kina cewa My Prince ko? Ke bazaki nutsu ba koh ? Shikenan zan fad'a wa Abba kinga se ya aurar dake kowa ya huta naga alamar aure kike so".
       "Yaya dan Allah kiyi ha'kuri bazan 'kara ba". Walida ta fad'a.

       "Waye wannan d'in?" Reyhana ta tambaya.

        "Waseem". Ta amsa tana sosa kai.

         " A ina yake?"
        
          "Uhm..uhh d'an school d'inmu". Ta amsa a kunyace.

          " Class mate d'inki?,'karya yake miki wannan iyayensa ba aure zasi masa yanzu ba har nawa yake,just wannan year d'in fa kukai graduating kuma shine kike kulashi sakarya ,duk sanda na sake gani kina waya dashi sena fad'a wa Abba ya miki auren dole".

       Shiru tayi kanta a sunkuye ta'ki cewa 'kus.

     "Tashi ki wuce ki breakfast". Ta fad'a tare da ficewa.

      Bayanta tabi suka sauka 'kasa lokacin har Ikram ta tafi aiki.Muzurai tayi tayi kar Reyhana ta fad'a wa Mommy.

            ***

     Ahmad yau ko breakfast beyi ba ya fice a motarsa marcedes mey black color, yana hanya sega kiran Zainab.

        " Yaya ina kwana". Ta gaisheshi.

         "Lafiya lau". Ya amsa.

          " Umma tace gobe zaki dawo koh?"
           "Eh".Ta amsa.

            " Ok toh Allah ya kaimu".Ya fad'a ta amsa da Ameen ,daga haka sukai sallama ba tare da sunyi doguwar hira ba.

°°°

   3pm Reyhana da Mommy suna zaune a falo kamar daga sama suka ji an turo 'kofa da 'karfi.

     Sageer suka gani da sauri ya wuce d'akinsa ko ta kansu bebi ba.

STORY CONTINUES BELOW
      "Mommy wai Sageer lafiyarsa lau kwana biyu?"Cewar Reyhana.

       " Atoh gashinan de kullum cikin 'kunci da fushi".Mommy ta fad'a.

       "Bari naje".Reyhana ta fad'a tare da mi'kewa ta nufi d'akinsa.

         A bud'e ta tarar da 'kofa saboda haka sallama tayi ta shiga.

       A kwance ta iskeci yayi rigingine hannunsa akan goshinsa ya 'kura wa ceiling ido ko takalmin dake 'kafarsa be cire ba.

       " Sageer meyake faruwane wai?"Reyhana ta tambaya.

        Se lokacin ya kula ma tana d'akin.

       "Babu". Ya fad'a ciki-ciki.

        " Amma na ganka haka".

        "Kawai na gaji ne". Ya fad'a.

        " Nifa ba wacce zaka 'boyewa abu bace, meye amfanin 'yan uwa idan bazasu san matsalar ka ba su taimaka maka kayi solving ba?"

      Mi'kewa yayi zaune fuskarsa damuwa 'karara ta banyana.

      "Wannan abun ba abune wanda zaku iya taimaka min ba kuma ina ganin ma na makara". Ya fad'a.

       " Koda addu'a ai mu masu taimaka maka ne,tell me meyake faruwa".Reyhana ta fad'a tare da 'karasowa inda yake.

        Wayarsa kawai ya d'auko ya bud'o wani pic na mace 'yar budurwace kyakkyawa a kai.

      "Fatima". Ya fad'a.

      " Fatima? Itace damuwarka koh?"

      "Ummien Nasreen Allah bazan iya rayuwa ba ita ba,I can't bear to loss her,suna nema su rabani da ita".

       " Suwaye?" Ta tambaya cikin nuna damuwa.

       "Iyayenta ,sune zasu aura mata cousin d'inta".Ya 'kare maganar kamar zeyi kuka.

       Reyhana tausayin 'kanin nata ne ya kamata lokaci guda kuma ta tuno rabuwarsu da Ahmad.

      " Komai zezo da sau'ki Sageer,zan taya ka da addu'a  kaima ka dinga yi".Ta fad'a.

       Kai ya gid'a almar "Toh" tare da fad'in "Amma karki fad'awa Mommy".

      " Don't worry bazata sani ba".

             "Thank you". Ya fad'a.

     Murmushi ta 'kalo tace " Is okay".

             ***

    Ahmad yana komawa gida ya tarar da Imran yazo,Umma tana fita daga falon Imran ya tinti'beshi.

       "Ya ake ciki har yanzu baka Jeba?"

      "Uhm". Ya amsa.

      " Ina baka shawara ka gaggauta zuwa kar kazo kayi da kasani,this is too much 6yrs ba wasa bane Ahmad ya kamata ka gane".

      "Ni kaina nasani Imran tunanin yadda Reyhana zata yarda da abunda zance mata nake"Ahmad ya fad'a.

      " Malam ka cire wannan abun  a ranka,ta yarda karta yarda Nasreen is your daughter ba yadda zasi ,dan haka gara ma ka mi'ke ba wajensu zaka ba 'yarka kaje gani".

      Sosai maganar Imran ta shigeshi,yaji 'karfin gwiwa a yanzu ya shirya zuwa gidansu Reyhana.

    
     Da daddare Umma take fad'a masa gobe ze d'akko Zainab daga tasha.

      Beso kasancewar hakan ba saboda lissafinsa ze ruguje na zuwa gidansu Reyhana.

°°°
      2days later
       Daga aiki koh gida be komo ba Ahmad direct ya wuce gidansu Reyhana around 5pm lokacin.

     Daga can nesa yai parking a zuciyarsa yana sa'ke-sa'ke iri -iri ,ya shafe kusan 30hrs be fito ba se shawarwari yake,gashi bega ko mutum d'aya na gidan ba a waje.

        Ya dafa hannunsa a steering ya maida kallonsa gate d'in gidan ,mota ya gani ta sauke yara guda uku ta juya.

       Biyu daga cikinsu mace da namiji d'ayar kuwa Nasreen ce suna sanye da uniform na Tahfiz.

      Guda biyun gidan dake gefensu Reyhana suka shiga ita kuwa Nasreen bye tayi musu da hannu tsayawa tai gate ta hau kan wani tudu se cisgo flowers da suka shingid'o ta bango take.

     Sam ya kasa bawa kansa amsar abinda zuciyarsa ke tambaya."Is she Nasreen? My daughter ?"

      Baro 'kofar gidan tayi tana nufowa inda motarsa take,daya kalli direction da takeyi ya kula ashe ita mage ta biyo takeson d'auka.

     A sanyaye ya fito daga motar ya bita da kallo magen ta gudan mata ,komowa tayi zata shige inda yake ya tsayar da ita.

       "'Yar yarinya". Ya kira ta.

       Waiwayowa tayi ta kalleshi" Ni gida zan tafi ummiena ta hanani magana da wasu a waje".Ta fad'a.

      "Eh yanzu ai zan tafi,amma ya sunanki?" Ya tambayeta.

      "Nasreen, Aisha Ahmad Yusuf". Ta amsa.

      Amsar data bashi ya isheshi tabbatar da abinda yake tunani.

     Ma'kwat! Ya had'iyi yawun daya tokare a ma'kgoronshi.

       " Kaji kunya 'yarka bata sanka ba".Zuciyarsa ta fad'a.

      Daurewa yayi yace" Ni sunana Uncle".

     "Uncle ? Koya min karatu zaka yi?" Ta tambaya.

     Fuskarsa d'auke da murmushi yace "Eh".

      " A nan?" Ta sake tambaya.

       "A'a ,ya sunan school d'inku?"

       Amsa masa tayi sannan tace"Ummiena zata jamin kunne idan ban koma ba".

      "Eh kije gida yanzu". Ya fad'a.

      Da sauri ta wuce ta shiga gidan yana tsaye har ta shige tukun ya koma mota ya tafi.

      Nasreen kuwa tana shiga gida ta soma bada labari taga wani sunansa Uncle.

      " Ban hanaki yiwa mutanen waje magana ba?" Cewar Reyhana.

     "Shine ya fara yimin magana wai ze koyan karatu".

     " Toh karki sake kinji koh".Reyhana ta fad'a.

      "Toh ummie". Nasreen ta fad'a tana cire hijabi.

     Reyhana tunani ta shigayi wannan waye?

Post a Comment for "ARZIQI RABO CHAPTER B"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...