Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ANA ZATON WUTA A MAKERA CHAPTER B KARSHE

ANA ZATON WUTA A MAKERA CHAPTER B KARSHE

- - Post a Comment

 ANA ZATON WUTA A MAKERA CHAPTER B KARSHE


***Misalin k’arfe tara na same ta isa gidan, gidan shuru da alamun yaran gidan suntafi makaran ta haka ma mazan gidan suntafi kasuwan cinsu. Batare da shakka ko d’arba tanufi d’qkin Baba Wanda k’ofar taga a kare.

Da sallama tashiga d’akin ta sauke idon sa akan Baba da Fauza wayan da bacci ya kwashe sakamakon rashin baccin dabasu samu ba a daren jiya.

Gefen gadon Baba tasamu ta kishingida bayan ta ajye ledar dake hannun ta, cikin muntina k’alilan bacci mai nauyi ya d’auke ta,kwata kwata batajin dad’in jikin ta jinta take kamar wata sabuwar halitta ga zuciyar ta a cunkushe tarasa dukkan tunanin ta,ita dai gatanan ne a toshe takejin kwanyar ta.

A firgice Fauza ta farka tareda kiran sunan Allah a dalilin wani irin mummanan mafarki datai a game da ‘yar uwar ta,addua tayi ta tofa dama da hagun ta, d’agowar dazatai tayi tozali da Saudat wacce ke bacci a gefen gadon Baba,

Saroro tayi tana bin Saudat da kallo cike da mad’aukakin mamaki,nan da nan jikin ta yayi laasar hawaye ya zubo kan kuncin ta,tasa hannu ta goge. b’angaren da Baba take bacci taduba tasa hannu tana tayar da ita tareda kiran ta. Baba,Baba. Dake ba nauyin bacci ne gareta ba ta amsa da cewa”naam Fauza har kin tashi ne? Eh Baba kema tashi, da kyar ta yunk’ura ta tashi zaune tana fad’in” kedai wannan ‘yar kinfiya hayyatar jaraba ace munkwana a zaune jiya bazaki barmu mu rintsa da safe ba? D’azu da asuba har canaiwa larai kar a kuskura ata damu baccin safe zamuyi hatta baban ku canai karya tadani amma dake ked’in. Cikin sik’ewa da mitar ta tace” Baba bafa haka kurum natada ke ba bud’e idon ki garau kiga Sauda tadawo,

Ai Baba da hanzari tak’arasa tashi zaune ta dubi inda Fauza ke nuna mata tak’ara murje idon ta kan tace” ikon Allah yaushe ta shigo? Nima farka wa nayi naganta harta soma bacci.

Nandai suka zubawa sarautar Allah ido can dai Baba tace” kinga jeki gurin larai ki amso mana abin karin mu mu karya wannan bacci na Sauda bana k’are bane.

….. …… ……

Wani irin gware sukai a yayin da take shirin futa daga gidan shukuma ya sawo kai zai shigo,zuwan sa kenan ko babur d’insa bai shigo dashi ba yadai barshi a wajen zuwa anjima.

Da sauri taja da baya tareda dafe goshin ta daya hadu da nasa suka k’ume, ta bugu da yawa kamar yanda shima yaji a jikin sa. D’agowa tai da niyyar bashi hak’uri amma me?

Wata iriyar fad’uwar gaba taji a sanda idan ta ya sauka a cikin nasa, take taji tsigar jikin ta natashi tafad’a cikin wani irin yanayi. Kasa d’auke idon ta tayi daga kansa har saida yakira sunan ta da cewa” Fauza lafiya?

Aida sanyayyar maganar sa ta ‘yan gayu da hutu taratsa kunnenta saida takusa suman tsaye dakyar ta iya kwato kalma d’aya dakyar tace” mefa?

Wani mugun tsaki yaje cikin jin haushin ta yace” kedai naga sanda zakiyi hankali ya ina tambayar ki kema kina tambaya ta? Wuce ni kibani guri wawiya naga sanda zaki waye.

A cikin soron gidan ta tsaya maimakon ta tafi aiken da akai mata, wani irin yanayi ta tsinci kanta cikin sa wanda takasa sanin me hakan ke nufi, tananan tsaye tana tunani idon ta lumshe fuskar ta d’auke da murmushi tana maimaita sunan sa cikin ranta tamkar mai hadda,(YAYABBA:))batayi aune ba ta cinkayi muryar Baba ta kwad’a salati ta dire,

Yanzu Fauza tunda kikafuto kinanan a rab’e baki tafi kinje kin amsomin sak’on ba? Nanfa ta dawo duniyar mu ba shiri ta gyara gyalenta tayi waje tareda ‘yar dariyar mitar da Baba tasomaj mata.

Misalin k’arfe takwas na dare suna zaune a gefen gadon su Saudat na gyara farcen ta daya soma taruwa, Fauza dake zaune akasan leda ta dubeta tareda cewa” Saudat,tace” naam, tacigaba,

Saudat baki fad’an inda kukaje dasu Islam ba har kika kwana gashi kindawo da kaya kin ajye ko tab’asu baki tab’a yiba yau kwana hud’u kenan, hmm ta sauke numfashi,cikin sakin fuska tace” biki na rakasu dare yayimana shine nakwana a gidan su aina fad’awa Baba Ashe bata fad’amiki ba? Hmm tace” kanta cigaba, Dan Allah Saudat karki kuma irin wannan bakiga yanda hankalinmu yatashiba har yaufa Baba baisan kinje wani guri kin kwana ba,ke ba wanda yasanima kinga da wasu sunji zasu zatama wani yawon kika tafi.

Cikin murmushi tace” nagode ‘yar uwata bazan kuma ba kinji bara naje nayi guga a d’akin Baba kanna dawo ki d’auko kayan cikin jakar ki futon dasu saimu gani duk islam ce tabani,(taboye).

Allah sarki Fauza rashin sani yafi dare duhu.

Jakar ta d’auko tazuge tashiga futo da kayan dake ciki,kayane kala goma dinkakku masu tsada tareda kayan shafa masu kyau da k’amshi da turaru, a tsorace tai saurin ja da baya don ganin k’udi a k’asan jakar ‘yan rafar dubu d’ai-dai har guda biyu ga kuma waya a gefen kud’in,in bata manta ba a hannun su islam ta tab’a ganin irin wannan wayar saikuma sau d’aya taga yaya Abba da irin ta.

Hannunta yana karkarwa ta d’auko wayar tareda mik’ewa tsaye cike da fargaba take kallon wayar, motsin dataji a bakin k’ofar ne yasata saurin b’oye wayar a bayan ta, tadube shi yakwa zuba mata mayun idanun sa. Cikin in ina tace” am yaya abba wata uwar tsawa ya daka mata aibatasan sanda tai wulli da wayar ba tai tsalle ta dira saman gado sabida tsabar firgici,

Salati ya saki yana jijjiga kai cike da mamaki, sunkuya wa yayi ya d’auko wayar yashiga juyata kan ya jawo jakar yayi tozali da wangkudi:oops:.

Cikin takun isa yake takowa inda take,Allah sarki tamkar zaki haka take ganinsa idon sa yai jajir tuni jikin ta ya d’au bari, a gaban ta ya tsaya tamkar zakara a yayin da takure bango,

Ganin babu alamun wasa cikin idonsa yasa itama tadake tama kauda kanta daga kallon sa. Cikin tsawa yace” wannan wayar wace? Batare da shakka ko tsoro ba tace” tawace,(wayyo bakidai shiyake yanka wuya)

Cikin mmki yace”tareda kankance idanunsa, takice ke kinsan kuwa kudin wannan wayar? Uban waye yabaki wannan wayar da wannan uban kud’in?

Allah tabashi amsa kai tsaye, ganin tana neman raina hankalunsa yasa ya dauke ta da bahagon mari, nanfa tarike kunci idonta yy jajir alamin marin yashige ta,

Baibi ta kantsba yashiga bude wayar,Abin mamaki da layinta da komai da alamuma ana amfani da wayar, don haka yashiga contact yasoma duba numbers din dake ciki duka numbers ne babu suna,yadawo cikin galary, Anan ibtila in yake, ai pics ne na mata kala kala iri-iri tunda yake baitab’a ganin tsiraici ba amma yau hashi Fauza ta janyo masa,wani irin jiri jiri yasoma ji sabida kad’uwar da yayi,

Dakwa yashiga vidios aisai tsayuwar ma ta gagare shi yadin jiri yana neman fad’uwa, dab’ar ya zube a k’asa tareda dafe kansa yana ambaton sunan Allah donkar kwanyar sa ta fashe.

Halin dataga yashiga yayi masifar tsoratar da ita, har tasoma tunanin me yaya Abba yagani cikin wayar? Dan haka ta tako a hankali danta leka taga meyagani?.

Momhaneep+

***da sauri taja dabaya ta dafe k’irji tareda cewa”na shiga uku! Idon ta tamkar yafad’o k’asa don tsoro tunj jikin ta yad’au b’ari, cikin zuciyar ta kuwa tana fad’in INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJUUNA,
Cikin sanyin jika ya yunk’ura yatashi, binta yake da kallo yana kara tabbatar da abinda yake zargi a tareda ita, cikin tsantsar damuwa ya kira sunan ta.
Fauza! Kincuci kanki, kincuci rayuwar ki da dukkan masoyin ki,shjn Fauza mekika rasa a rayuwar ki? Dame mahaifinki ya rageki? Dama kinanan da halin ki baki daina ba? wai yaushe kika lalace haka Fauza? Ace wannan rayuwar kika tsabarwa rayuwar ki? toni bazan toni asirin kiba amma zan d’auki mummunan mataki akanki don wallahi bazan zuba ido ki bata sunan zuri’armu ba, a haka dai gakinan mutum sak amma zuciyar ki babu tsoron Allah a cikin ta, yanzu ke rayuwar ‘yar uwar ki bata baki sha’awa bata birgeki? Bakyajin dama kece da irin halin ta a cikin ranki? Ok ai bak’ar zuciyar ki bazata barki kiyiwa rayuwar ki abin alkairi ba, inai miki adduar shiriya Fauza.
Baisan fuskar sa tajik’e da hawaye ba,sai bayan yakai aya yafarga da hawayen dasuka had’e da gumi suka jik’ashi sharkaf. Bai tsaya gogewa ba,illa ya tarkata kud’in da wayar ya zurasu a babban aljihun rigar dake jikin sa yafuta.
A hankale ta silale tazame ta zauna tana wani irin kuka mai tsuma zuciya tareda sheshsheka, zuciyar ta tana raya mata”meyasa kikai haka Fauza? Meyasa baki futo fili kin fad’i gskyar maganar ba? Shikenan kinzama ‘yar mad’igo a idon yaya Abba? Bayan dama akwai tsohon tabo da yaimiki tun zamanin k’uruciyar ki?.
Shihowar Saudat ita takatse tatayi firgigit ta d’ago da jajayen idon ta,ta kuma rushewa da kuka har tabawa Saudat tsoro.
Rike ta tayi tana tambayar ta meyafaru? Duk tasata cikin damuwa fad’i take” wai menene Fauza? Meyasame ki? Lafiya fa nabar ki, ko keda yaya Abba ne? Dama naga futar sa yanzu ransa a b’ace, d’ago fuskar ta tayi kan tace” in wani abin yayi miki ki fad’amin naje narama miki donni ba tsoron sa nakeji ba.
Ganin Saudat ta harzuk’a cikin idon ta babu alamun tsoro tasan zata aikata abinda ta furta. Jijiga kai tashiga yi da kyar ta furta cewa” babu abinda yayimin Saudat,
Nina jawa kaina,nina kashe rayuwa ta da kaina Saudat,nina bad’awa kaina bak’ar toka wacce babu Wanda ya isa ya wankeni sai Allah.
Da hannu ta dakatar da ita, dakata Fauza nariga nagano abinda yafaru tsakanin ku, ki kwantar da hankalin ki kidena cewa” kin cuci rayuwar ki waye waye,akan yaya Abba yaki k’arbar soyaiyar ki aiba ca akai shikadai ne autan maza ba, munanan dake Allah zai baki Wanda yafishi,
Saroro tabi Saudat da kallo kukan ma ya tsaya cak don mamaki, yamutse fuska tayi kan tace” soyaiya? tacigaba,
Kwarai kuwa ai ina lure da irin k’aunar da kikewa Yaya Abba tunda yazo gidan nan, zatai magana ta katse ta da cewa” kingafa niba k’aramar yarinya bace karma ki soma b’oyemin tun ranar dayazo nagano sonsa kike,
Shine kuma yasamu damar yimiki wulak’anci ko? To aishikenan shiganinsa yake yafi kowa sabida yayi karatu.
Nandai taita mita yayinda Fauza tayi shuru tana binta da ido
Yo ido mana ana wata ga wata.Kubiyomu
Momhaneep&haneefa usman
[4/8, 9:29 PM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK’ERA…40&42
©NWA
Mamanhaneef&Haneefa Usman
***Tsantsar damuwa batabar Fauza ta rintsa ba, illa juyi da taitayi tareda sak’a da warwara, matakin da yaya Abba yace xai d’auka akan ta shiyafi da munta dashi ta kwana cikin ranta.
Baccin bai tashi d’aukar ta sai daf da assalatu harta so ta makara sallah da kyar dai Saudat tayi nasarar tashin ta k’arfe shida na safe. Duk da tanajin bacci haka ta daure tatashi idon ta cike da bacci bayan kunburin dayayi.
d’akin Baban su tanufa kamar yanda tasaba,duk safiyar Allah zataje gaidashi bayan ta shiga sun gaisa da Baba da Anty larai kan kuma tashiga madafa don taimakawa Anty larai.
Turus ta tsaya a k’ofar d’akin Baban ta don jiyo muryar yaya Abba datayi daga cikin d’akin. Dafe k’irji tayi tareda karanto dik adduar datazo bakin ta, a tunanin ta ko yazo yafad’awa Baba wata maganar data dangan ci abinda yafaru jiya ne.
Don tafi jiyo abinda yake fad’ane yasata nemi guri ta zauna a zuwan jira take yaya Abba yafuto tashiga. Nankwa ta tsinkayo muryar sa yana cewa” insha Allahu zaa dace Baba, inada tabbacin idon Fauza zai dawo dai-dai tunda ba ahaka aka haifeta ba.
Cikin jimanta lamarin tsjiyo Baba yana fad’in” nidai daza abi ta tawa Abba da kun kyale ta,tsawon shekaru kusan sha uku idon Fauza yana a haka sai yau rana tsaka kazo da maganar ai mata magani maganinma na bature? Haba Abba kayiwa Allah da manzan sa kabar wannan batu, to a duniyar nanma akwai wanda ya isa ya juya halitta inba Allah ba?
Hmm ya sauke ajiyar zuciya kan yace” Ka fahimce ni Baba, bawai zaa juyo da idon Fauza ta k’arfin tsiya bane @@ akwai dai wasu dabaru da su likito cin suka kirkira dasuke wa masu irin idon Fauza harara garke,kuma cikin ikon Allah saikaga idon yana gyaruwa ya juyo ya dai daita, kasan yanzu anjigaba Baba akwai abubuwa da dama naban mamaki da inkajisu ma saika k’aryata inhar ba ganikai da idanu wanka ba.
Uhm inajinka Abba aibanki ta takaba ni gani nake da zaabar mata abinta haka to zaifi ko?
Adai gwada agani tukun Baba, sabida shi wannan Dr danai maka bayani d’azu Dr hashim kwararren likitan ido ne, yayi karatu mai zurfi awannan fanni,abokina ne Baba ni naga wanda idon sa yafi na Fauza amma cikin yardar Allah yanzu yaran yana gani balle ita Fauziyya juyewa ne kawai.
Duk maganganun dasuke tattaunawa a kunnen Fauza, ganin maganar tayi tsayi yasata barin gurin takoma d’aki cike da fargaba.
Tsoron ta d’aya kar yaya Abba yayi amfani da wannan damar yafake da kaita asibitin ido ya gudu da ita yaje ya gana mata azaba donba imani gareshi ba, kuma takwana da sanin tuntuni yaya Abba bamai kaunar ta bane sam jinin su bai had’uba, kuma tun ada baitaba zuwa da maganar akaita asibiti ai mata magani ba sai yanzu?
Nanfa cikin ta yad’uru ruwa, tak’ara tabbatar wa da kanta akwai abinda yaya Abba ya b’oye don tanajin sa yana tsara Baba kamar yanda yatsara babanta.
Yinin ranar Fauza tayi tane babu walwala ga kuma d’inbin damuwa da ta cika ranta ko sallamar Abba taji gaban ta saiya fad’i. A b’angaren Baba kuwa tafi kowa murna dajin wannan labari, don tunda Abba yafad’a mata bata minti biyar batare da ta shiwa Abba albarka ba,duk ta fadawa jamaar gidan, itakuwa Fauza maganar dukta gundireta yak’e kawai take. Saudat ma zata dameta da maganar ta gwaleta da cewa” to naji.shikenan tasamu lafiya.
A b’angaren su hajiya Lubna, duniya taimata dadi tasamu yanda takeso tana juya islam sai yanda tayi da ita ko kara tasa bata iya ketara shi batare da izinin taba su Kansu abokan huldar su suna mamakin wannan canjin.
Kwanan Saudat biyar da barin gidansu Islam hajiya lubna taso kiran Saudat don a yau tashirya keb’ewa da ita, ba karamin shiri tayiba don acewar ta wannan ranar ranace mai daraja a gurin ta ranar da zatayi muamala da Saudat ai dole ma tayi shiri.
Tagama shirinta tsaf ta d’auko gunki da boka yabata don kiran Saudat wayar ta tayi k’ara, saida taja mugun tsaki don ganin number baban su Islam Wanda tayi save din number sa da suna,hotiho.
Nandai yake shaida mata dawowar sa a
ranar.don haka dole tashiga taitayinta takori shaidanun kawayen ta Alhaji yabata mata shiri, haushi kuwa da bacin rai kamar ta cinye kanta, hakanan tanaji tsna gani ta maida gunkin tareda mayar da kwadayin Saudat daya hanata sukuni a kwana biyu.
…..
Tunda sukabaro garin kura take kuka don gani take shikenan yaya Abba yaraba ta da dangin ta ya yaudaresu da cewar asibiti zai kaita,
Inta tuno yanda suka rabu dasu Baba dasu Saudat cike da fatan alkairi don sunata adduar Allah yasa adace, Baba harda kukan dadi don har catai zatayi azumi guda uku in Allah yadawo dasu,duk dan asamu narasa.
Wani sabon kuka tasaki don tausayin Baba ba asan ransa yaya Abba yataho da itaba don dai ya kafene kuma Baba ta goya masa baya.
Abba dake gaban motar abokinsa ilyasu, ya juyo ya dubeta tareda cewa bayan yadoka uban tsaki mtsssw” munafuka algunguma in bakimin shuru ba a dokar dajin can zan saukeki kura ta cinye ki marage iri, dubeki shegiya mai siffar salahai.
Ilyasu ne yai magana da cewa”haba Abba kabar ta da abinda ke damunta barin gida fa akwai ciwo dole tayi kewa.
Ai dole tundani dokar daji zan kaita,cewar Abba, cikin tsiwa tace” wayasa ni Abu a duhu? Juyowa yayi yace” tome kike nufi mara kunya? Kikiyaye ni Fauza karkisa nacasa ki a cikin motar nan wallahi,
Cikin kunkuni tace” Allah sarki sannu ubana, baiji abinda tace ba don haka bai kulata ba.
Karfe biyun rana suka iso cikin garin kano tadabo ci gari. Kollon unguwoyin take cikin shaawa itadai yanayin cikin garin yana birgeta rabon ta da cikin garin tun randa tagama karatu sac sch a makarantar kwana ta dala.
Tana tsaka da tunanin rayuwar datai cikin makaranta kwatsam taga annufi unguwar nassarawa GRA daita nanfa gaban ta yafad’i ko shakka babu gidan kakannin ta yakawota,(gidansu mahaifiyarta)
Nanfa tsoro yacika ranta tareda fargabar kardai yaya Abba xuwa yai yafad’a mahaifiyar ta abinda yafaru? Kai amma da ya cuceni ni Fauza da wanne ido zankalleta nace k’aryane bani bace Saudat ce? Dafe kanta tayi dayaji yana sarawa.
A k’ofar tangamemen get din gidan ilyasu yayi parking baishiga ciki ba wuce wa zaiyi. Nandai suka futo ya dubeta a yayin da tayi tsaye a gefe tana jiran umarni, cikin hantara yace”
Towaye zai d’aukar miki kayan ki? Kina nufin dako zanmiki? Nanfa ya wurgo mata jakar data zuba kayanta kala biyu, sunkuyawa tai cike da jin haushin sa tace” banza mutum sai bakar masifa yaushe kwa zakai kumari kasa masifa a ranka?duda a ciki tai maganar yad’anji kalbar B data fara ambata don haka ya juyo yace”what?
Saida ta basar kan tace” aa canai Banana ayaba gatanan kasiyamin,
Juyawa yayi yadube teburin mai ayaba da lemo yadawo da dubansa kanta yayi tsaki yayi gaba abinsa, shikam ilyasu mai zaiyi inba dariya ba? Don tabbas yaji abinda tace….Kubiyomu
Momhaneef+***Gidan Alh Bashir, gidane babba mai d’auke da b’angarori da dama, kallo d’aya xakaiwa gidan kasan gida ne namasu hannu da shuni, tsarin gidan tsarine irinna zamani wanda yake samun kulawa akai-akai kusan ko wacce shekara Alh bashir zaisa agyare gidan asake sabon fenti tare da duk wani abu dake bukatar gyara ko yatsufa zai canja shi, don haka inba fad’a akai ba zakayi tunanin mutan gidan basu jima da tarewa ba sbd tsabar kulawar da gidan ke samu.

Alh Bashir yana tareda matar sa hajiya Bilkisu wacce Allah y albar kace su da tarin ‘yaya har guda goma mata biyar maza Biyar,

Cikin su harda mahaifiyar Fauza da Saudat(Saadatu)Allah yaiwa Alh bashir arziki wanda ba yayansa da yan uwan sa kadai ba hatta makotan sa suna alfahari dashi, mutum he mai tausayi da jinkai ga uwa uba kyauta.

Duk inda yayansa suka shiga inhar ansan sune  andinga girmama su kenan anasan hulda dasu don akwai su dason jamaa kai bakace ‘ya’yan wani bane, Halin ubansu yajawo musu farin jini.

Bayan rabuwar Sa’datu da malam sama ila tayi wani auren har sau biyu amma dake ba gidajen zamaba ne kuma masu iya magana since Aure rai gareshi, in zaman yakare ko anaso ko baaso saifa anrabu.

Tunda suka rabu da mijin ta na uku bata k’ara tunanin karayin wani auren ba, karshe ma makaran ta takoma taci gaba da karatun ta,

Cikin iyayen ta ba wanda yata kurama ta asalima mahaifin ta yanajin tausayin ta ganin dauriyar datai na rabuwa da yaran ta wanda a zahiri sunsan tana k’aunar yayan ta amma sabida kawaici irinnata ko dawai basu tabajin ta ambaci zataje ganin suba, hakama mahaifinsu baitab’a kawosu su ganta ba,

Sai shine dakansa Alh bashir din yaitattaki yaje da kansa ya gano jikokinnasa. Tundaga wannan lokacin yake musu aike kuma yana zuwa ya gansu.

Sau daya ne wani zuwa dayayi yanemi alfarmar tahowa dasu,don suga mahaifiyar su itama tagansu, tundaga wannan lokacin kuma sukanzo hutu gidan kakan nasu.

Fauza kwa datai karatu cikin garin kano tafi sanin y’an gidan har visiting sukan jemata haka in anyi hutu drever gidanne yake d’aukota kan Yaya Abba yazo ya d’auketa ya maidata gida.

TAKAITACCEN LABARIN SAADATU KENAN.

…… ……. …….

Jikokin gidan ne suka rugo da gudun su sunai mata oyoyo kasancewar Yaya Abba daya shiga ya shaida musu tare da Fauza suke.

Duk sinbi sun daneta tarasa yanda zatai ma,haushin yaya Abba taji dabai tsaya taiwa su Muneep tsaraba ba gashi yanzu tarasa me zata basu su kyaleta? da dabara ta kwace rikon dasukai mata takoma kantin dake gefen gidan tasai musu sweet nanfa suka hau murna suka nufi ainihin cikin gidan.

Har k’asa ta zube tana gaida kakarta wacce suke kira da amme ga kuma yayan mahaifiyarta A gefe shima ta gaidashi wanda shine babban d’a a gurin Alh bashir.

Cikin mamaki Alh sagiru yake duban ta yana fad’in”yanzu Fauziyya ce ta girma haka? Ikon Allah yadubi gefensa inda Saadatu wacce suke kira da mamy take a zaune hannun ta rikeda waya yace” lailai ashedai mun tsufa saadatu kice yarannamu sun zama y’an mata haka bamu saniba? Gaskiya inawa Abdallah ruk’o.

Itadai murmushi tayi cike da kunya tace” yaya babba aisu Fauza basa sonku yunda basa zuwa inda kuke sunfi son dangin mahaifin su yanzu ma bakaga Abba ne ya dauko taba dasu juwairiyya suka dameshi dayazo last week,

Itadai Fauza shuru tai a zuciyar ta kuwa cewa tai” ai k’aunar ce tasakika zabi y’an uwanki akanmu yayanki, to muma basai mu zauna inada Allah ya ajyemuba?

Yaya Abba yace”ba haka bane mamy suma sunasan zuwa makaran ta ke hanamusu komai. Bawani kaidai zaka kare ‘yar uwarka inji amme, yaya babba yace”yanzu Saudatu? Kanta sunkuye tace” tana gida. A takaice,

Nandai suka danyi hira kan Alh sagiru yayi musu sallama tareda bawa Fauza kudi yakuma shaida mata zaituro a dauke ta taimusu kwana biyu.

Mikewa tayi ta hau sama bayan tace Abba yasa meta a falon sama. Binta tayi da kallo harta kule a ranta tana aiyana” wai mamy ce mahaifiya su? Sabida inba fad’a maka akaiba saika rantse yayar suce barema Saudat data debo kamanninta har farin saika zaci yane da kanwa.

Mamy(Saadatu)tanada karamin jiki yanzu nema datai kiba kyawunta yakuma bayyana gata da nutsuwa komai nata cikin nutsuwa tamkar dai Saudat ada don batada yawan magana ga kuma tsare gida shiyasa dayawa ake shakkar ta,

Rashin sakin fuskar ta yasa Fauza takasa sakin jiki da ita ko dakin ta bata zuwa indai ba dole ba dakin amme da tsohuwa(mahaifiyar Alh Bashir)sun isheta,tamafi son zama acan tsohuwa taitai musu tatsuniya.

Tunda Mamy tace yaya Abba yasameta a falon sama jikinta yayi mugun sanyi, hira suke da amme kakar ta amma hankalin ta baya gurin gaban ta fad’uwa yake tana tsoron karfa yaya Abba ya shaidawa mamy maganar wayar daya kamata da ita.

Amme ce ta dubeta ganin duk tayi wani sak da ita tace”Fauziyya tundazu inata magana kinyi shuru ga abinci nan ankawo miki ga furanan tsohuwa tadamo miki duk ba wanda kika kalla,

Yake tayi tace” uhn bari nakai wa yaya Abba nasa nadawo sai naci nawan.

Tayi hakane don taji abinda yaya Abba yake fadawa mamy ko bataji duba zata fahimci wani abin,don haka ta zuba nasan ta nufi saman dashi.

Tundaga steep din karshe take jiyo salatin mamy tata harta ida k’arasa wa falon, gaban tane ya yanke yafadi data hango wayar dake hannun mamy ga kuma kudin a gefen ta, jitai kamar tasaki fitsari don tsoro da tasamu dama data juya da gudu don wani mugun kallo dataga mamy tana wurgo mata.

Ta wutsiyar ido ta gallawa yaya Abba harara a zuciyar ta taraya cewa”munafiki andai ji body"

Ajye tiren tayi tamik’e cikin Sauri nufi hanyar futa jikin ta har karkarwa yake, Fauza!!! Mamy ta ambaci sunan ta cikin wata iriyar murya….

Kubiymu+Z [4/23, 11:04 AM] mamanhaneef: [4/23, 10:14 AM] mamanhaneef: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...58&60.          *                                        *Mamanhaneep&Haneefa Usman.                       *                                       *numfashin tane ke futa da kyar,hannunta dake dafe da kirjin ta tasa takamo hannun Fauza dakyar take iya furta magana da cewa" zo Fauza zonan kimin shaida, Allah yagani banida wata masaniya akan abinda Saudat ke aikatawa, Allah ne shaidata nabawa 'ya'yanki kulawa da tarbiyya fin wacce nabawa 'ya'yana nacikina, kiyi hkr Saadatu duk abinda yafaru da bawa mukaddari ne, inbaki mantaba ada Saudatu mutuniyar kirkice mai tsoron Allah mai hani da aikata b'arna, kodan dana haifa a cikina baimin irin biyaiyar da Saudatu taimin ba, zamanine ya lalata min Saudat, dan Allah karku kujeta karku kya maceta kumata uziri rudin duniya ya rudeta, anan tari ya sark'eta,cikin tausayi mamy tace" Sannu Baba nayaba da irin tarbiyyar dakikai musu, kuma su nakine har abada BAba rayuwar su malakin kina, shiriya a hannun Allah take, naimiki alkawarin bazan kyamaci Saudatu ba amma zan zage dantse narabata da mutanen da take tareda su.                       Saudat dake gefe tana numfarfashi tajawo jiki ta rike hannun Baba, cikin muryar kuka tace" kiyi hkr Baba, wlh ban watsar da tarbiyyar da kika baniba, na rantse miki da Allah nadena bazan karaba, kitashi Baba karki mutu kibarmu zangyara rayuwa tamkar yanda take ada, Fauza ce ta rungumota har zuwa yanzu kuka take".           Abba dake rik'eda Baba yace" Mamy bari naje nakira Dr akwai wani likita a bayan layin nan, harya mik'e Baba taruk'o shi tareda cewa" karka wahalar da kanka da samaila kakirawomin da sauran 'yan uwansa dayafi don inaji a jikina bazan tashiba, ya durk'usa tareda cewa" zaki tashi Baba kidena fadar hakan bari na kirawo Dr yaduba ki saina wuce nakirawo su Baba.                              Hannunsa tajawo tahad'a dana Saudat, tace" Abba ga Saudatu nan karike min ita Amana, a hargitse ya juyo ya dubi Fauza itama shidin tajuyo tana duba, kallo mai cike da manufofi, Saudat ce tazame nata hannun daga nasa,tace" Haba Baba yazakiyi haka bafa mutuwa zakiyi ba zaki tashi kiyi farin cikin ganin nagyara rayuwa ta ke zaki kaini dakina da hannun ki, dan Allah karki mutu Baba, Murmushjn yak'e Fauza ta kakalo tace" ki kwantar da hankalin ki Baba Saudat batada miji sai yaya Abba ko bayan ranki maganarki bazata rushe ba, rikota tayi tareda cewa" Allah yaimiki albarka Fauza Allah yabaki miji nagari Allah yakare munku da kariyar sa,                       Abba da har yanzu duban Fauza yake zuciyarsa nabuga da sauri da sauri, mik'ewa yayi cikin sanyin jiki yanufi hanyar futa, mamy binsa tayi da kallo cike da mamaki a ranta taraya" meke faruwa ne tana kallon sa yana share hawaye da babban yatsansa.

[4/23, 10:48 AM] mamanhaneef: Tarine yakuma Sarke Baba take jikinta yashiga karkarwa, salati mamy tashiga furta mata itama tanabin bakin mamy, tana idawa taja dogon numfashi ta kalli sama take jikinta yasaki wuyanta ya karye, Abba dake shirin futa daga dakin yadawo a tsorace a yayinda mamy tarufe idon ta tareda jero kabbara, nanfa suka rude suka kankameta tareda matsanancin kuka, Jijigata Saudat take" cikin kuka take kiran sunanta" kitashi Baba Dan Allah nashiga uku Baba ninayi sanadiyyar mutuwarki wayyo Baba  kin mutu da bakin ciki na, sunbatu tashiga yi har saida Fauza ta rik'eta, kuka sukashigayi abin tausayi.  Tuni Abba yafuta don kirawo su Baba.                                *                                        *cikin kankanin lokaci gidan yacika da jamaa yan karbar gaisuwa, yan uwa nakusa dana nesa duk sun hallara, nandai aka had'ata aka suturtata aka kaita gidan ta na gaskiya.        Fadar rudanin da zuriar wannan gidan suka shiga bamai yuwuwa bane saidai muce Allah ya jikan ta tareda dukkan nin musilmi baki d'aya AMEEN.          *                                       *                                       Kwana uku ana karbar gaisuwa har zuwa wannan lokacin suna cikin alhini don ba k'aramin gib'i mutuwar Baba tayi musu ba,karma Saudat taji labari itada tadauki laifi tadowarawa kanta gani take itace silar mutuwar Baba, tun randa tarasu har zuwa yau ruwa ke shiga cikin sai shayi shima sai anmatsa musu duk sanfige sun rame, a ranar amme sukazo gaisuwa a karo na biyu yayinda suka rankaya suka tafi har mamy fazasu koma,                   tabar su Fauza cikeda kewar Baba tareda alkawarin zata dawo ran sadakar bakwai.         *                                        *                                        * A kwance take akan makeken gadon ta sanye da wasu irin futunannun kayan bacci, Islam dake gefen ta itama sanye takeda kayan baccin, tadube ta da jajayen idon ta tace" Islam bankad'a k'asan gadona ki d'aukon wani kwali kiyi a hankali fa karki cuceni, batare da tace komai ba tad'auko kwalin tamiko mata, bude kwalin tashigayi cike da mamaki Islam take duban gumakan dake cikin kwalin kowanne da suna ajikin sa, tace' Anty wannan gunki nanfa? Murmushi tayi kan tace" wayan nan dasu nake kiran yarana aduk sanda na bukace su, yanzu ba baby Saudat zan kira yau ita neke shaawa,(waiyazubilla) karaf Islam taruke hannunta tareda cewa" haba Anty kirasa lokacin dazaki kira Saudat sai yau yaufa ake sadakar ukun kakarta data rasu, ina laifi kobari sai anyi sadakar bakwai? Kinsan yanzu tana cikin alhinin mutuwa kuma tana cikin yan uwanta,

[4/23, 11:04 AM] mamanhaneef: Tsaki taja mtsssw,ta watsa mata harara kan tace" don anyiwa Saudat rasuwa nikuma saina zauna kwadayinta ya kasheni? Tonikam a yanzu zankirata mutuwa ita tashafa, Anty kiji tausayin Saudatu ki kyaleta ni gani na fansheta amma ki kyale Saudat Dan girman Allah, mtssw inkedin nake bukata aiba saikin kawo kankiba zan kiraki da kaina don haka baabin da zan fasa.                                  *                                       * washe gari da asuba Fauza tafuto daga bandaki hannun ta rikeda buta tayi alwala, sai ganin Saudat tayi tashigo daga waje tamkar wacce aka jeho, saroro tabita da kallo cike da tsoro da fargaba batasan sanda tasaki butar dake hannun taba, a ranta kuwa nazari tashigayi yaushe Saudat yafuta? Tasan dai basu kwana a daki daya ba kardai ace Saudat ba a gidan ma takwana ba? Gaban ta yafad'i waige waige tashigayi don takara battatarwa da itakai dai taga shigowar Saudat? Tayi ajiyar zuciya dataga duk yan zaman makokin hankalinsu yanacan sunbi masallaci Sallah,  bayan Saudat tabi, a sheme taganta akan gado har bacci ya soma daukar ta, duka ta dana mata cikin masifa tace" muryarta kasa kasa, daga ina kk? Wani mugun kallo ta watso mata da jajayen idanu wanta, tuni Fauza taja dabaya don ganin kamarma ba acikin hayyacin ta takeba hannu tadora aka tarushe da kuka tareda cewa" nashiga uku, Allahumma ajirni fi masibati wa akfilni kairan minha.๐Ÿ‘

[4/23, 5:45 PM] mamanhaneef: 60&62.                             *                                       *wani mugun tsaki Saudat taja mtsssw tareda juyawa d'ayan b'arin takoma baccin ta, cike da damuwa takoma ta daura alwala tayi sallar ta har karatun alk'ur ani tayi, tajuma tanaiwa Baba addua kan tatashi daga kan sallayar ta.         *                                        *tundaga wannan ranar Fauza tasaka ido akan Saudat ko zataga wata alama dazata nuna ta rashin gaskiya ko futa yawo amma shuru har ana igobe sadakar bakwai Saudat bata k'ara futaba,hakan yayi mata dad'i don tana tsoron kar mutane su farga da halin da Saudat take ciki. Tana wannan tunanin ne mamman yashigo yakira ta yace" Fauziyya kizo kinyi baki daga kano, saida tayi Jim tana nazari kan tace" ina zuwa, tadubi Saudat tace" kinji baki sunzo dg kano ko 'yan uwan mamy ne? Tabe bakitai kan tace" komasu waye aike suka sani kuma kesuka tambaya saikije ai, wannan wacce iriyar magana kike Saudat? Kinsan dai gaisuwa sukazo yimana ko? Zakice waini kadai suka sani mtsw tayi tsaki tai ficewar ta.         *                                         *a jingine jikin mota ta tardasu, da faraar ta tak'ara garesu, cikin murmushi ta furta" Abdallah? Shima fuskar sa dauke da faraa ya amsa da cewa" naam Fauza 'yan mata, nandai tai musu iso har d'akin Yaya Abba anan ta saukesu, suka gaisa tareda yimata taaziyya ta mike don kawo musu ruwa,  inda Saudat take tanufa tace" Saudat kije Ku gaisa su Abdallah ne d'angidan dady sagir yayansu mamy. Banza tai mata, ganin hakan yasa tadauki ruwan takoma takai musu, harta fiddaran zuwan Saudat sai can saigata a takaice ta gaisa dasu takoma sam Fauza bataji ddn yanda tai musuba,  nan dai sukayi yar hira kansuyi sallama sutafi har bakin mota tarakasu kan tajuyo.                       *A soro tayi turus don ganin yaya Abba tsaye a soro fuskar nan tasa a hade tamkar baitaba dariya ba, tace" yaya Abba lafiya? Cikin dacin rai yace"uban waye yace" kikawomin wasu k'atti daki? Angaya miki dakina na shigar kowanne kare da doki ne? Sororo take dubansa kan tace" kai yaya Abba, Abdallah ne fa kuma ganinai ba bako bane shiyasa nakaisu dakin ka,  to daga yau karki sake ni dinnan dakika gani banason shashanci inbanda shashanci ko kunya bakiji ba kisaki baki kidinga yashe hakora kinai musu dariya harda daga musu hannu ko kina tunanin bangan kibane? Yanzu yaya Abba meye laifina danna sauki bakina da fara'a shine fa sirikin naka, ai Abba baisan sanda ya kwashe Fauza da mari ba,cikin fushi yace" inna kumajin Kalmar saurayi a bakinki saina cusawa iyayen Ku zagi bayan nafasa bakin dake musu dariya, munafuka uwar shishigi uwar kalen dangi, Allah yasa nakumaji kin ambaci A bama Abdalla ba kiga hakoran ki a hannun ki, ita dai cikeda mamaki take duban sa tarasa bakin magana a ranta kuwa. Fadi take" oh ni Fauza dama in masifa taiwa mutum yawa saiya rasa kalar wacce zaiyi wannan fadan banga dalilin saba. A fili kuma catai" yanzu munafinci menayi maka kuma ai ab,sai tayi shuru, ainagama dan uwanane tunda d'ane a gurin mamy๐Ÿ˜, hakakikace ko? Ganin ya durfafota yasata shigewa da sauri tana kunkuni.๐Ÿ‘         *+

[4/25, 5:17 PM] mamanhaneef: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...62&64.               *                                         *                                       ***Ayau ne Baba tacika kwana bakwai da rasuwa, 'yan uwa da abokan arziki sun taru anyima ta adduar bakwai kamar yanda akasa ba. A yaune mutuwar tadawo wa su Fauza d'anya don ganin 'yan uwanta dasukazo sunfara hada yanasu yanasu wasuma tun safe suka tafi kan la'asar gidan ya d'ad'e sai iyasu sai kuma su Baba dake waje sumad'in iyasu dinne.                              *                                       *tana zaune ne kawai cikin ranta fal yake da damuwa jitake tamkar tabi mamy wacce take jiran driver yazo d'aukar ta, yayinda Saudat ke gefe ta harde kafa daya kan daya tana danne danne a cikin tafkekiyar wayar dake hannun ta, kaida kaganta kasan chtt take wanda yatafi da hankalin ta gaba d'aya,  sunanan zaune driver mamy yazo don haka tashiga cikin gidan tai sallama da sauran mutanen gidan Fauza tana biye da ita lakaci zuwa lokaci takan share hawayen dake kwaranya cikin idonta, nandai sukadawo dakin tadubi Fauza wacce keta sheshekar kuka tai murmushi kan tace" kukan ya isa Fauziyya kiyi hkr Dan Allah Baba fa ba dawowa xataiba k'aunar dazaki nuna mata kimata addua, cikin muryar kuka tace"kuka na bazai kare ba mamy inhar zancigaba da rayuwa cikin gidan nan babu Baba,ki duba irin rayuwar da ake a cikin gidan nan mamy, kowa nasa yasani Baba ce a kullum mai lura da lamuranmu to yanzu haka zamuyi rayuwa yanda muka tsara abar mu? Baba yafuta tun safe sai dare,yaya Abba dake saka mana ido shima sai karshen wata yake zuwa kinga kenan babu mai tsawatar mana tunda babu ran Baba!!, cikin tausayawa mamy tace" ki kwantar da hankalinki Fauza, ki mika lamuranki ga Allah shizai iya miki, a shekarunki zaki iya lura da kanki harma ki tarbiyyantar da wasu don haka kizama jaruma kisa a ranki Allah ne xaikareki ba mutum ba,'yan uwan mahaifinku dabasa zumnci daku to inaso daga yau kudinga zuwa gurinsu kuna gaishe su, ku dinga girmamasu zakuga canji nina fad'a miki wannan inada tabbacin bakwa huldasu shiyasa suma basayi daku, cikin sigar lalashi tace" ki share hawayenki kinji, yanzu tafiya xaki kibarmu mamy? Murmushin yake tayi tajawota ta rungime dukta karya mata zuciya, nandai taciro kudi a jakarta tabata tareda cewa" ki ajye wannan a hannunki inkuna bukatar abu kusaya duk abinda kkso kikarani a waya zan bawa Abba waya yakawo miki inya koma aikin sa, jikin ta tajanye a hankali tace" Allah ya kiyaye hanya mamy a gaishemin da amme, ganin Saudat dake zaune taki magana yasa ta zungureta da kafa tace" Sauda mamy zata tafi, budar bakinta sai catai"ku sauka lafiya Allah ya bada lada, mamy dako saurarar ta bataiba tajawo hannun Fauza suka fita don yimata rakiya.                               *a kwar gida sukai sallama da Baban Fauza tareda kumai masa taaziyya kan sud'au hanya.                  *                                         *
[4/25, 6:21 PM] mamanhaneef: ***Cike da takaici tadubi Saudat, tace" wai Saudat meyake damunki ne? Kina kallon mamy ko sallamar arziki baki mataba? Ina lure dake tunda kika gaisheta mgnr kirki bakiyi mata ba, mtssw tasaki tsaki cikin masifa tace" to saiki zo ki dakeni tunda naimiki ba dai dai ba, nifa banga uban dazai takurawa rayuwa taba,kinsamun ido komai nayi idonki nakai na? To kishiga hankalinki indai akan mamy kk fad'amin magana kije nabar miki ita, aiduk kaunar dazata nuna miki daga baya ne tunda da hak'oranki ta ganki, kokuwa kinason kinunamin mamy tafini kusan ce dake? Toni bata gabana bansan taba ban rayu da ita ba Baba kadai nasani, tunda ranta bata hanani shakatawa ba sai bayan ranta ace zaa takura mini.               *                                            * wani wawan mari Abba ya d'auketa dashi Wanda shigowarsa kenan yajiyo muryar Saudat na zazzagawa Fauza rashin mutumci, a zuciye yakuma dauketa da mari yasa k'afa yayi ball da ita, Fauza ce tasha gaban sa tareda cewa" kayi hakuri yaya karka jimata ciwo, nandai yashiga yimata fad'a saida yaimata tatas sannan yafuta. Maimakon jikin ta yayi sanyi? Saita tashi ta sulla wanka tai ficewarta kiran duniya Fauza nakiranta ko waiwayota batai ba.   Wannan kenan                                  *
[4/25, 7:11 PM] mamanhaneef: ****Cikin nutsuwa take sauraran nasihar da mahaifin su ke masu,yayin da Saudat ta had'erai tai kicin Kicin alamun itafa wannan batu bai dadarata da k'asa ba, cikin muryarsa mai sanyi dattijo mai hak'uri da tawakkali da tsoron Allah.yaci gaba" ba asan raina zakuyi nisa dani ba,sai adole, kunsan Alh bashir yanada k'ima a idanuwana tunda ya ka rya billansa yanemi alfarmar rukonku yakoma hannun sa bazan iya hanashi ba, don haka ina baku hkr, kuyi hkr da yanayin rayuwa duk a yanda tazo muku, yadan jima yanai musu nasiha a k'arshe ya rufe da cewa" yanzu kuje ku had'a kayanku anjima zaituro a d'aukeku, kushiga ko ina kuyi sallama da iyayen ku, cike da farin ciki Fauza tashiga shirya kayan ta, Saudat kuwa kamar anmata bushara da mutuwar ta, nandai suka shiga sukai sallama da yan gidan Wanda suka fara shiri dasu tun bayan rasuwar Baba duk abinda suka dafa saisun bayar ankawo musu wani zubinma Fauza a gurinsu take yini kwanciyar bacci. Ke dawo daita bangaren su, harta soma zargin damacan rashin fahimtar junane yasa suke tunanin zuminci ne basayi dasu. Inna kuwa mahaifiyar Abba jitayj tamkar karsu tafi don sunsaba mutuka damacan itamai k'aunar suce ganin basa rabar su yasa itama bata zafafa ba,amma ko dinki taiwa yarta dije saita hada da Fauza da kuma yar Anty larai,  cikin wannan alhini suka hada kayansu suka rabu tamkar karsu tafi. Suna k'okarin shiga mota wani yaro ya dakatar dasu yace" wacece Fauza? ganinan tafada tana duban yaron, letter ya mik'o mata yace" gashi ance nabaki, ta amsa tace" injiwa? Yaron yace" wacce tabani catai inkika gani zaki ganeta, jin ance macece shiyasa tayi zatan ko acikin k'awayen tane bata dubaba saida tashiga motar ta zauna ta bud'e ninkin farko, tayi tozali da sunan wacce tayo sak'on. ISLAM! GABANTA YA FADI TAYA MUTSE FUSKA TAREDA CEWA"WACCE ISLAM?+

[4/26, 9:17 PM] mamanhaneef: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...64&66            *                                        *Mamanhaneep&Haneefa Usman                      *                                        *                                        ****tsaki taja mtssw kan tace"ba matsala ta bace bazan ma dubaba balle naga takaici donnasan mistake yaron yayi Squdat akace yabai wa, nandai ta ninketa tacusa cikin jakar ratayen dake hannun ta.                                     *                                        *** Cike da murna amme ta saukesu kasancewar duk yaran gidan suna makaranta 'yan matan gidan ma suna makaranta wanda suke cigaba da karatu a B.U.K Amal ce kad'ai a NORTH WEST.amme ce itada tsohuwa a gidan sai masu aiki don mamy ma tatafi Makaranta Wanda take a matsayin Principal a makarantar  'yan mata ta BALARABE HALADU ISLAMIC ACADEMIC.        *Cikin murna da d'auki Fauza ta rungume amme wacce bakin ta yak'i rufuwa tana cike da farin cikin ganin jikokin nata, Saudat kuwa a d'arare tashiga gaidasu sakamakon rashin sabon dabatai dasu ba, ganin hakan yasa amme taruk'o cikeda faraa tana zolayar ta da cewa" su kifin rijiya yau anfito anga gari incedai kokin ware ido kin kalli duniya da kyau? Dariya sukai gaba d'aya dake itama Saudat kwai baki tace" mezan kalla cikin gidan tsofaffi? Ai bani guri zakiyi yau Abba abin kifin rijiyar zaici, dariya suka kumayi tsohuwa tace"sannu rasa kunya kinmanta da tsohuwar Zuma ake magani? Nandai sukaita zolayarta harta saki jiki hira ta sarke, anan falon amme suka zauna sunacin abinci da aka saukesu dashi.      *                                         *ranar sunjima suna hira da yaran gidan kunsan in yan mata suka had'u dole ayita tad'i, sunyi farin cikin ganin Saudat da Fauza hakanan sunason zama tareda su, hakama da Abba yadawo a nan falon yayi zaman akai hirar dashi  kan daga bisani yayi nasa b'angaren. K'_arfe 10 na dare mamy dake gefe hannun ta rik'eda wayar data siyawa Fauza tana kuma check din wayar don takuma tabbataewa da kanta duniya bata gaban Fauza, aikuwa babu abinda ta tarar a wayar sai wak'ar hausa guda d'aya ta mamman shata,sai kuma hotunan dasukai a dazu bayan zuwan su, batare da tadube suba,tace" kowa yatafi ya kwanta dare yayi, nankwa sukaiwa juna sallama kowacce tanufi nata d'akin ciki harda Fauza, tsayawa tayi donjin mamy takira sunan Saudat. Cikin muryarta ba wasa, tace" ki tattaro kayanki ki maidosu bedroom d'ina, saroro Saudat tabita da kallo, Fauxa batasan sanda tace" meyasa mamy? Ga dakican amme tasa angyara mana, bazanji dadin zama nikad'ai ba.  Wani mugun kallo ta Watson mata kan tace" da kan Squdat tazo kedawa kike kwana a d'akin? Cikin in ina tasoma magana, nanfa ta daka mata tsawa,ba Fauza ba Saudat ma saida ta tsorata, bashiri tanufi hanyar d'akin zuciyar ta fal tausayin Saudat don tasan karsnsu da mamy ba kyau.
[4/26, 10:12 PM] mamanhaneef: Cikin sanyin jiki tace" Dan Allah mamy kibarni tareda Fauza nibazanji dadin zama a d'akin kiba,sabida rashin sabo, bata kuma kallon koda inda Saudat take a tsaye ba ta mik'e tayi tafiyar ta tabarta agun,tow dama ance shuruma mgn ce, warkima guri yagani.                                          Batada zab'i adole takoma d'akin da amme tabasu a matsayin nasu takwaso manyan jakunkunan dake shak'e da kayan ta,takaisu d'akin mamy kamar yanda ta umarce ta, jikinta fa yasoma yin laasar don duk yanda take tunanin mamy tawuce nan, bata tab'a tunanin mamy tanada zafi haka ba,ga kwarjini da tunda suka hada ido a sanda tadawo dg makaranta bata kara marmarin sukara hada idoba, sai taji giggiwarta da rawar kanta anzaresu tas batada sauran lakka, bata tsinke da lamarinba saida taga yanda yaran gidan ke masifar shakkarta tareda 'yan aikin gidan, a ranta kuwa catai" wato dataje mana gaisuwar Baba kenan zubamin ido kawai tayi nake abinda naga dama? Tana cikin wannan tunanin ne taji ankirata sunan ta, tadan tsorata don bataji shigowar mamy dakin ba, batasan sanda tasaki wani irin kuka ba wanda itakanta batasan dalilin zuwan saba, tasan dai a tsorace take don tasan ita mai laifice, mamy ma binta tayi da kallo cikeda mamakin kukan datake jitai tamkar ta nada mata duka dan haushi, cikin bacin rai tace" ke cikin wannan daren zakimin kuka a d'aki? Salon amme tazata wani abin nake miki? Nizakiwa makirci? Tunkan na dosheki da abinda kinsan wajibine na tambaye ki akansa?  Nanfa takuma tsorata tashiga hankalin ta, a zuciyar ta tana raya" nashiga uku ni yanzu yazanyi? Mezancewa da mamy? Bayan ido da ido taganni? Balle nace karya ne? Cikin sanyaiyar murya tasomai mata magana, ita kanta tayi mamakin yanda mamy ta sauke muryarta tashiga yimata magana cikin sanyi.  Na farko inasan nasan, ke wacece? Duk da Nagani da idona to inaso kibude baki kibani amsar tambayata, karkimin k'arya inkuma kikaimin karya wlh wlh rankine kawai bazan iya futar miki dashi ba amma inai miki albishir da cewa" hannuwanki da kafafunki xancire miki tayanda babu damar dazaki iya futa balle kije kiyi mad'igo. Nanfa Saudat ta tsure ta rikice tuni tarasa nutsuwarta duk kuwa da tasan a salama mamy take mata tambayar,  cikin muryar kuka tace" wallahi ba halina bane wasune suka koyamin, zan fada miki gsky mamy amma dan Allah karki yanken hannu na da kafafuna wlh ada ban iya komai ba su Islam ne kawaye na suka kaini, nanta tsaya tana cigaba da kukan, mamy dik jikinta ya saki tarasa dalilin dayasa takejin tausayin saudat, rayuwarta ta baya ta tuna da yanda mutane ke yabon kyawun halinta, kawai saita fashe da kuka,wai 'yar data haifa a cikinta itace a wannan halin? Fauza dake lab'e jikin kofar tana share hawaye duk abinda suke tanajin su, ganin mamy da kanta tana zubar da hawaye yasata shigowa d'akin, a gaban mamy ta dire guiwowinta...๐Ÿ‘+[4/27, 9:02 PM] mamanhaneef: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...66&68.            *                                     ©NWA๐Ÿ“–.                       *                                               * Cikeda sheshek'ar kuka tace"ki dena zubar da hawayenki mamy,kinmanta zubar hawayenki musiba ce ga rayuwar mu? Saudat ba kukanki take buk'ata ba mamy, adduarki itace garkuwa a gareta, nikad'ai nafi kowa sanin halin Saudat, wlh mamy kaddara ce tafad'a wa Saudat amma sam ba halinta bane. Saudat dake gefe kanta cikin guiwowin ta,tarasa da wanne idon zata kalle su bata tab'a nadamar abinda take aikatawa ba saiyau da mamy ta tsirata, hawayen ta tashare kan tace"najima inaran ganin ta inda Allah zai jarrabe ni, a rayuwa ta bantab'a samun matsala ba, bantaba cin karo da wata kaddara illah ta rabuwa da mahaifin ku, ashe kece kaddarata Saudat  dake Allah ya jarrabe ni ? Shiyasa Allah yad'oran K'aunar ki da tausayinki Ashe kece silar bak'in ciki na a rayuwa ta? Tir da halinki Saudat Albasa batai halin ruwa, nayi nadamar haihuwar ki,wallahi da haihuwar irinki gwara b'arinki, Allah ne kadai yasan yawan yaran dakika b'ata,Allah ne kadai yasan irin zunuban dakika d'aukar wa kanki, danasan zaki sance a cikin mutane masu sab'awa Allah dana zubar da cikinki na hutashe ki, danasan zan haifi irinki a tsatsona dana shakeki kinmutu tun kina zanin goyo, da nasan rayuwar ki bazata amfani Al Umma ba saidai ta batasu wallahi dabazan bari kizo duniya. Da rarrafe tayo kanta tareda rike kafafun ta tanafadin" ki yafeni mamy bazan sakeba natuba, inhar nasake na yarda kimin duk abinda kikaga dama wlh nadena,wayyo nashiga uku kiyi hkr karkimin baki nabi duniya Dan Allah ki yafeni, juyowa tayi kan Fauza, ki taimakeni kibata hkr Fauza ki fadamata nadena zancenja halaye na daga yau bazan kara biyewa su Islam ba, nadena Fauza bazan karaba, cike da tsananin tausayin Saudat ta rungomata tsam a kirjinta kukan ma yaki futowa tamkar zasu had'iyi zuciya su mutu,    a cikin ranta takejin ciwon abinda Saudat tayi jitake kmr jininta ne ya hau,don haka tadafe kirjin ta tace" kuimin shuru, koki dena ko karki dena ruwanki, rayuwar kice batawani ba, nidinnan ba abinda zan iyayi miki don duk abinda naimiki kinriga kin cuceni, nagode Allah dabake kadai na haifa, amma kisani  inkika mutu cikin wannan kazantar wallahi wutar Allah saitaci naman jikinki tsakanina dake saidai nace" Allah ya shiryeki inkinada rabon shiriya,  cikin gigicewa take fadin" nadena mamy Allah zai shiryar dani bazan mutu ina aikata saboba kimin addua mamy, damacan ni ba halina bane, su Islam ne suka kaini. Cikin d'acin rai da kufula tace" ubanwa yasa kibiye musu? Da anyi magana kice su Islam kama hannunki sukai da karfi suka kaiki? Inbaki kai kankiba ubanwa ne yakaiki? Eyi nace ubanwa ya jaiki

[4/27, 9:13 PM] mamanhaneef: Ya kaiki? Cikin tsawa take maganar duk ta tsoratasu, itadai Fauza dataga ba haza saitaja gefe, aikuwa tana shirin yin magana mamy ta damkota ta buga ta da bango tahau kanta tashiga duka,ganin ta shaketa yasa Fauza ta taso jikinta sai rawa yake don tsoro ta rike mamy tana kuka tareda cewa" karki kasheta mamy, kiyi hkr kibarta, kituna abinda Baba tafad'a miki kanta rasu, kituna mamy har alkawari kikai mata, jikin tane yayi sanyi, ta saketa, ita kanta batasan sanda zuciya ta debeta tayikan Saudat ba don tsananin bakin ciki,          *nandai ta zauna taita lallamin mamy tareda yimata nasiha ta yarda da kaddara ta cinye jaraftar ubangiji hardai tasamu fushinta ya sauka sai a lokacin ta dubi Saudat wacce ke kwance ko motsi batayi ita kanta tasan ba k'aramin duka tai mata ba, Fauza ce tatab'a takuma jijigata taji shuru, nanfa tsoro ya d'arsu cikin ranta a tsorace cike da fargaba tajuyo tadubi mamy tace" mamy? Saudat bata motsi fa, nashiga uku shikenan kin kashemin 'yar uwa mamy nanma takuma jijigata wata k'ara tasaki itama tafad'i a gurin cikin fargaba tayo kanta tana fad'in Fauza!Fauza!Fauza!+

ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...71

©NWA ๐Ÿ“–

Mamanhaneep&haneefa Usman.

***glass din dake sanye cikin idon sa yazare, yadubi Fauza tareda mik'a mata takardar dake hannun sa wacce Fauza tabashi ya karanta,amsa tayi tareda cewa" yanzu yaya meye abinyi? Saida yanisa hmm kan yace" kin tabbatar abinda tarubuta cikin takardar nan gsky ne? Cikin rashin tabbas tace" banida wani tabbaci amma zancen Islam da k'amshin gsky a cikin sa, wlh yaya ca akai har tsaface mutum suke, nidai zuciyata ta gasgata mgnr Islam.

Tamshikenan yanzu ke zaki iya shiga gidan su Islam din nasanki da tsoro Fauza kar asamu matsala fa? Zan iya yaya Abba tunda bakai tsaye zamu Shiga ba da taimakon Islam.ko insake karanto maka ne? Eh sake biyowa naji daga bakin ki, nifa ina tsoron kar aje ko wata shiryayiya suka shirya aje ayi biyu kuma, cikin sigar wasa ta harare shi da wurkilallun  idanu wanta, baisan sanda yasa dariya ba kan yace" kinsan me natuna?  tace"a'a, mganar idonki danaiwa Baba natuna Allah sarki Baba ashedai babu rabon taga Fauza wurk'il takoma Fauza rarass, saida ta dara kan tace" ai dama nasan tsara Baba kawai kayi don ya amince kataho dani gurin mamy ta lallasani, aa mganar tananan ko kwanaki mamy tayi mgnar idonki amme da tsohuwa ne suka soma korafi wai abarki kar aje a tsokalo miki wani abin amma zanyi bincike sosai akan matsalar tunda ba a haka aka haife kiba,+

Ok to shikenan muyi abinda ya zaunar damu ko? Eh inajinki karanto don nasan Batool tazuba๐Ÿ‘‚taji meke cikin wannatakardar๐Ÿ˜‰@jika.

Cikin lumshe ido yake saurarar dad'ar muryarta wacce yakejinta tamkar busa take masa.Ta fara karanto masa takardar kamar haka.

Assalamu Alaikum.ina fatan zaki nutsu ki bani hankalinki donkifi fahimtar abinda zan fada miki, ni sunana Islam kamar yanda kika sanni a baya, kuma kinsan matsayina a gurin 'yar uwarki Saudat.to da farko dai ina neman gafararki don duk wani hali da Saudat ta tsinci kanta nice sila don nasan kinsan Saudat tana d'aya daga cikin members namu basaina fada miki ba kinsan mudin ko suwane, dalilin yimin wannan doguwar takardar shine, inason shaida miki da kudena wahalar da Saudat don Sam Saudat bata cikin hayyacinta, sunjawo ta cikin Mu da karfin sihiri wanda ko karshen duniya kuka kaita don Ku tserar da ita inhar suka kirata saitazo. Karkiyi mmki ba Saudat kadai ke cikin wannan had'arin ba akwai mata dayawa yara da manya Wanda aka janyosu ta hanyar asiri.karki karya tani don duk yanda kike tunanin kungiyarmu sunzarce haka, nidai ina mai baku shawara daku dage da addua donku taimaki rayuwar Saudat, ina matukar tausaya mata shiyasa nakasa hakuri na rubuto miki don kusan yanda zakuyi wajen karya asirin dake jikin Saudat, wannan asiri kuwa yana karkashin gadon hajiya lubna wacce itace shugabar kungiyarmu dazan iya datuni na dauko na karya to amma babu dama, inma bazaku iyaba to kudage dayi mata addua shine solution bawai kuita wahal da itaba, inkina Neman karin bayani ki kirani a wannan no din(    ) nizan taimaka miki ki shigo har cikin gidanmu ki ciro gunkin 'yar uwarki ammafa inkin yarda dani, karkiji tsoro kisa Allah a ranki kisawa zuciyarki kece silar kawo k'arshen mad'igo a cikin gidan mu,inkika daure kika jajirce zaki iya donna sanki da jarimta, ladanki yana gurin Allah, tukwuicinki gareni ki kwaso dukkan gunkinan bayin Allah da'aka asirce, kiyi wannan jihadin kokisa ayi, saina jiki, from lez Islam to Fauziyya.

Cikin sanyin jiki tarufe takardar tareda cewa" yaya Abba inaji a cikin raina, kozan rasa rayuwa ta zanje nagwada dauko wannan asirin don nayarda a wannan zamanin zasuyi abinda yafi haka ma. Kan Abba yayi magana suka jiyo muryarsa daga gefe tareda takowa har inda suke yana furta" na jinjina miki kuma nabaki goyan baya kuma zan taimakeki wannan tafiyar dani zakiyi ta,bazanso kije kekadai wani abu yasame kiba uwar 'ya'yana dolena na baki kariya har Allah ya cikan burina na mallakar ki,

Kai dallacan,Abba ya katseshi rai bace,tuni annurin fuskarsa y canja cikin dacin rai yace" waya gayyatoka? Ansa baki dai? To babu inda zaka bita Allah ne zai kareta, yo a d'auri kashi ko ab'ata igiya?.

Sam abinda yaya Abba yayi bai mata dad'i ba cikin rashin kuzari tamik'e kan tace" nagode yaya Abdallah duk randa zanyi tafiyar zannemeka amma inason mganar tazama sirri Dan Allah, da kuma girman son dakake kirarin kanaimini, cikin murmushi yace" yauwa tawan nagode kwarai ina tabbatar miki wannan sirrine daganj saike sai Allah karki manta Squdat nima 'yar uwata ce, cikin jin dd taimasa godiya yajuta yai tafiyarsa dama futowarsa kenan  zai tafi gida ya hangota a zaune, Ashe itada wannan masifaffenne,cewar Abdallah.

Ina Wuta Abba ya jefa Fauza don bala'i,wato ma d'an iska kika maidani,g abinda nace kema ga abinda kikace ko? Yaushe aka d'aura muku aure har kk zama uwar y'ayansa? Duk ya balbaleta da fad'a tarasa ma wacce amsa zata bashi, can dai ta marairaice tace" haba yaya Abba waiya kakeso nayine? Me Abdallah yai maka? Son dayakemunne laifi ko akwai abinda ya tsare maka? Kanada matar da zaka aura nima kabarni narike Wanda Allah yabani! Cikeda mahaukacin mamaki ya juyo a slow yana dubanta, da sauri ta toshe bakin ta, don batasan sanda ta furta wannan kalma ba, tuni tajada baya yanda jikinsa yad'au bari gani take tamkar zai maketa ne.

[5/8, 4:23 PM] Mamanhaneep: [5/7, 4:50 PM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...72

©NWA๐Ÿ“–

Mamanhaneep&Haneefa Usman.

***cikin kakkausar murya yace" maimaita abinda kk fad'a! Kayi hkr bafa wani Abu nace ba, ki maimaita nace" canai fa kabarni da Abdallah, tunda shi dakatar da ita Yy tunkan ta k'arasa, fuskar sa d'auke da murmushin takaici yace" nabarki da Abdallah ko? To nabarki dashi d'in har duniya ta nad'e, cikin fushi ya figi motar sa yabar gidan hatta kwa maigadin gidan saida yayi mmk, a ransa kuwa ya aiyana"me akaiwa Abba? Don Abba mutumin sane sunsaba da juna mutuka duk sanda Abba yazo yakan zauna suyi hira kanma yashiga ko inya futo.

Tun daga wannan ranar Fauza tashiga damuwa abubuwa sukai mata yawa, tunanin yaya Abba yafi nukurkusar zuciyar ta don tun ranar dasukai fad'a bai k'ara tako kafarsa zuwa gidan ba tsawon sati biyu kenan, ga matsalar Saudat kullum da ita take kwana kuma take tashi, shikansa Abdallah tundaga ranar baidawo gidan ba, tarasa ma yanda zatayi dama yaya Abba kadai take iya tunkara da damuwarta shikuma Yy fushi, nandai ta yanke shawarar kiran sa a waya,+
Cikin dar-dar takira wayarsa bugu biyu ya d'aga muryarsa ta doki dodon kunnen ta, dakyar ta furzo sallama daga bakinta, abinda yabata mamaki cikin sqkin fuska ya amsa muryar sa wasai tamkar babu abinda yafaru. Nanfa tasamu karsashin cewa" yaya Abba ina kashiga kwana biyu kmr baka gari munata kewar ka?hmm inanan kwana biyu ne bana samun lokaci kinsan kwanakin baya anyi wuyar mai, hakane Allah y taimaka, Ameen ngd, yaya Abba sai mgnr damukai akan Saudat zuwan fa yananan Kai nake jira, kmr ya kenan? ba kungama mgn da d'an uwanki ba? Cikin marairai cewa"haba yayana kasan dai kafishi kusanci dani katuna banda tamkarka shida nasanshi dg baya?nidai nafi aminta da kai yaya, wani sanyi yaji cikin ransa don yaji ddn kalaman ta ko bkomai ta wanke laifin ta, murmushi Yy kan yacigaba" kin tsayar da ranar tafiyar ne? Aa inason nayi mata mgn ita Islam din amma inajin tsoro yaya, ki daure kimata wayar kinsan dai dole saida taimakon ta kanki shiga gidan, to shikenan zankirata duk yanda mukai daita zan kiraka, OK bye. Suka ajye wayar tare.
[5/7, 5:55 PM] Mamanhaneep: Duk wani shiri sunyishi da Islam akwai wasu dabaru data shiryawa Fauza Wanda zata shiga cikin gidan su batare da ansamu matsala ba, don haka suka shirya yanda zasuyi tafiyar ranar Asabar ranar da babu aiki kenan, duk wannan shiri dasuke Sam mamy batada labari bare Saudat da akeyin shirin don ita.

Tun sassafiyar asabar Abba ya dira a gidan ko ciki bai shigaba yakira wayar Fauza, hakanan ta shirya cikin riga da wando na Pakistan tayi rolling mayafin akanta, duda a tsorace take haka ta daurewa zuciyar ta, a dakin mamy tasoma shiga ta shaida mata yaya Abba yazo, cikin mmk tashiga tuhumarta me yazoyi da safe haka? Nanfa tarasa abin fad'a karshe ma ta rungume mamy ta baya tareda sakin kuka, don tana ganin kmr ta siyar da rayuwar ta ne, mamy dai tacika da mmk, dakyar ta b'anb'are Fauza a jikinta tad'ago da habarta kan tace" Fauziyya? Meyake faruwa ne? Ina zaku da safe haka? Shuru tayi ga kukan bata fasa shiba, muje tanuna mata k'ofa,

Nandai ta tasata a gaba har inda Abba yayi fakin motar sa a kwar gidan, baitaba tsammanin zai gansu tareda mamy ba, nandai suka gaisa tana tambayar Abba ko ina zasu? Duk yanda tayi akan su fad'i inda zasu amma sunk'i, illa Fauza dake sharar hawaye kai kace duniyar zata bari, ganin mamy duk ta damu Yasa Abba yace" bawani guri zamu mai nisa ba, ki kwantar da hankalin ki zamuje garin kura ne, ba jimawa zamuyi ba mudai fatan Mu kimana adduar Allah ya kaimu lpy yadawo damu lpy,
Banfa ganeba Abba, waime kk b'oyemin? Ismail ya mutu ne? Inji mamy, Yanzu Ace Baba y mutu ki ganmu a haka mamy? Jikin tane yayi sanyi tace" shikenan tunda bazaku fad'an ba kuje Allah y kiiyaye hanya, kukula Dan Allah, inada tabbaci akanka Abba bana shakkar komai inhar a kankane sabida rikon amanarka, duk cikin yan uwan ismail kaida mahaifiyar kane Baku yadani ba, har nan kake biyoni ka gaisheni, Allah ne yahad'a k'auna tsakaninmu dakai da mahaifiyar ka, ga Fauza da Saudat nan ko bayan raina Amana suke a hannunka. Tana zuwa nan tajuya takoma cikin gida.

STORY CONTINUES BELOW

Nandai suka d'au hanya jikin su duk a mace, tasha mamaki dataga yad'auki hanyar gidan su Abdallah, batace k'alaba har suka isa, a k'ofar gida suka taddashi don haka tafuto dg gaban motar takoma baya, shikuma ya zauna a gaban motar,
Hakan ya k'ona ran Abba har yakasa hak'uri yayi d'an tsaki bayan ya shekawa Fauza harara.

Tofa, kubiyo mu๐Ÿ‘
[5/8, 9:36 PM] Mamanhaneep: [5/8, 8:24 PM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...73

©NWA๐Ÿ“–

Mamanhaneep&Hanefa Usman

***tafiya suke amma fa irin ta kurame, don Abba ya had'erai yayi kicin-kicin yana muzurai, ba damar ta d'ago kai saiya wurga mata harara, ga Abdalla daya tsareta da idanuwa duk d'agowar dazatai idonsa na kanta fuskar sa d'auke da murmushi, ba damar ta mayar masa yaya Abba ya watso mata harara,

Data ga babu dama saitayi kwanciyar ta takamo karatun Alk'ur ani cikin wayarta tanabi, tuni ta manta dasu har bacci ya d'auke ta.

A gefen tangamemen get d'in gidan Abba Yy faking, cike da tsoro da mamaki Fauxa take duban girman gidan, tunda take bata tab'a tunanin akwai gida kmr wannan ba cikin garin su, gida tamkar a maraya? nanfa tsoro y d'arsu cikin ranta tadubi Yy Abba tace" nidai ina tsoro Yy karnaje ko gidan yankan Kaine jifa girman gidan ko ina a kulle, bawani yankai ki kira wayar ta kice mata munzo aiba ke kadai zaki shiga ba,
Sunan zaune cikin motar sukaga an bud'e k'ofar dake jikin get d'in anfuto, Islam ce sanye cikin kayan bacci da alama wayar da Fauxa tayi mata ne yatashe ta, gaban Fauza yafad'i  don ganin Islam nanfa taji wani sabon tsoro Yakama ta sam taki yarda da Islam gani take tamkar wani shiri ne na Islam,

Ganin Yy Abba yafuta sun shiga gaisawa har yana d'an tsolayar ta da cewa" 'yan gayu basu tashi da wuri mukuma mun doko sammako, tace" laa babu komai wlh ina Fauziyyan? Ai jitai kmr ta zura da gudu inta futo, nandai tafuto a d'arare Abdallah ma yafuto suka gaisa, gabanta yana dukan uku uku, Islam tace" yanzu abinda xa'ayi mutum d'aya yatsaya anan yajira futowar Ku sabida tsaro, inta kama akira police na wajen saiya kira in munje gaba d'aya in matsala tafaru bana fata kunga munshiga hannu donnima nashiga matsala, Abdalla yace" muje tare ina ganin zanfi kula dake ko Fauza na? Yak'arasa cikin kashe mt ido fuskarsa d'auke da murmushi, nanfa ya kular da Abba, cikin dacin rai yace" to na mata na mata kai zaka jiramu anan a wannan rawar kannaka da giggiwar zaka iya kula daita? Kabari inmun koma gida kayi batun soyaiya ba ita takawo muba romiyo,๐Ÿ˜‚.

Islam batasan sanda ta tuntsire da dariya ba kan tace" kuyi hkr duka, kuzo muje kaika xauna anan d'in Allah dai yabamu saa, abdalla yace". Amenn don ko kad'an bai nuna yaji haushin abonda Abba yayi masa ba, illa Fauxa datayi kicin-kicin alamun bataji ddba,

Nandai tai musu jagaba suka shiga cikin tangamemen gidan, ganin su tareda Islam yasa masu tsaron gidan kobi takansu basuyi ba, nandai sukaita kutsawa cikin gidan kowani lungu da sak'o saida Islam takaisu suka shiga sabida tsaro, kan suzo wani katon corido ananne tace" Abba ya tsaya anan zasu shiga sashen hajiya lubna, jin ance Abba y tsaya ya tsorata Fauza nan tahau kuka takasa bin islam tarik'e hannun Abba kamkam, sun bata lokaci gurin lallaminta har tasa zuciyar islam ta harzuka tace" kinga inbazaki iyaba kiyi bayani mukpma karkije kibamu matsala ki cuceni, sanin kankine dazan cutar dake hanyar danabi najawo Saudat nan zanbi nasamo ki,

Cikin lallami Yy Abba yace" haba Fauza karkiban kunya mana kefa kika d'au Alk'awarin zaki iya bada ranki ki ceto rayuwar Saudat, kinfi kowa jin dajin halin da Saudat take ciki, inkika kasa tofa kamar kin yarda kin aminta da hajiya lubna taci gaba da sarrafa rayuwar Saudat ne, da hannu ta dakatar dashi, tadubi Islam tareda cewa" muje, a hankali tazame hannunta cikin nasa, shikansa jiyai tamkar karya cika hannunta, suna duban juna ahaka har suka shige cikin b'angaren hajiya lubna.tofa kubiyomu
[5/8, 9:35 PM] Mamanhaneep: A k'ofar d'akin hajiya lubna sukaja tunga, Islam ta dafa kafadar Saudat kan tace" nan shine d'akin lubna yanzuma tana cikin sa, ki lura kibi a hankali, ke mace ce kinsan yanda zakiyi ki yaudare ta don macace ita mai saurin yarda da mutane, tunjiya tasan da zuwan ki batare da tasan abinda yakawo kiba, ina kara tuna miki duk abinda tabaki karki ci ko kisha ammafa ki amsa kisan yanda kikai ki boye kartaga baki ciba, ni yanzu zanje dakina nasaman bene, duk abinda yake faruwa zan dinga ganin Ku, akwai na'urar datake d'aukar duk abinda ake a cikin d'akin ninayi hakan, sabida in mahaifin yaji halin matar sa inya karya ta na kunnamasa yagani, kidaure Fauza inai miki fatan Alkairi Allah yaga zuciyar ki shizai kare ki, ki saki jikin ki, bakowa cikin gidan dagamu sai ita, abokan shaid'ancinta sai yamma zasuzo,

Cikin dakewa ta k'ak'alo murmushin yake tace" nagode saina jiki inkinga da Matsala fa ki sauko ki taimakeni, insha Allahu kuwa Fauza.

74

***kwankwasa k'ofar tayi, ba tareda b'ata lokaci ba, hajiya lubna ta bud'e k'ofar, nanfa ta hau murna don ganin Saudat tareda yarinyar datai mata alk'awari, cikin wani irin salo na duniyan ci tashiga yiwa Fauza sannu da zuwa,  itakam cike da mamaki take duban matar, nan take tadena jin shakkarta don ganin ta matashiya daita itada take tunanin zataga hamshak'iyar mace k'atuwa? A ranta taraya" wannan ai dake bazata daken ba,

Nandai tai musu iso cikin katon falon ta, a gurguce sukai y'ar hira har tana korar islam a wasance, wai itanan y'ar duniya"inji Fauza,
Nanfa tashiga nan nan da Fauza, da alamu matar nan tafiya iyayi d rawar kai takasa zaune takasa tsaye, ta raya a ranta, cikin wani irin salo take mgn tareda jijjiga sassan jikinta bata yardaba sotake ta birge Fauza,

Cikin tik'ewa da haushi mai d'auke da kyama Fauza tace" kaini d'akin baccin ki a gajiye nake, saroro tabi Fauza da kallo, don ganin kwata kwata batai kama da irin yaran d islam take kawo mataba asalima ta lura da irin kallon da Fauza ke mata, gashi babu alamun tana buk'atar kasancewa daita, itada ko kallon mace tai saita rissinar da idonta don kwarjini? Kuma ko hannun mace ta kama saitaga canji cikin idon ta haka nan jikinsu yaita b'ari tunkan tazo garesu meyasa bataga alamu a gurin wannan ba?

Nanfa tasha jinin jikinta tadubi Fauza duba na tsanake kan tace" ya sunanki? A dake tace" Fauziyya, malama fauzy anyakwa kintab'a muamala da Irina? Tambayar ta fad'ar mata da gaba, nandai ta daure tace" aa, tace" islam fa? Kintab'a luv da ita? Nanfa tarasa amsar bata don batasan me Islam tace" daita ba. Cikin ikon Allah kiran islam yashigo wayar ta, nanfa taji sanyi cikin ranta tad'aga wayar, tunkai tayi magana islam tace" kice mata eh kuma kirage dakewar dakike don zata xargi wani Abu, bani ita muyi mgn, nanfa tamik'a Haj lubna wayar, kome sikace oho tagadai Haj lubna na dariya,1

Duk abinda takawo mata bata Ciba k'arshema ta wayance dacewa" nifa bana bukatar komai a yanzu sai kwanciya xuwa anjima mayi break din tare ko?

Nandai ta kwasheta sukai tafkeken d'akin baccin ta, d'akine na had'uwa bazan iya kwatanta haduwar saba,

Nandai tashiga nunawa Fauza wani irin salo salo nasu nayan duniya, tundaga sama tasoma sunbatar ta tareda shafata hartazo kan lab'anta, tanaji tana gani takama labbanta tanayi a zuciyarta kuwa wani irin amai ne ke taso mata don tsabar kyankyami ga wani k'arni dataji Haj lubna nayi tamkar wacce kecin d'anyen nama,
Tinda tasoma idonta na rufe, istigfari tashiga nanata cikin ranta, ganin tana neman zura hannu cikin rigar ta yasata k'akalo tari na k'arya harda durk'u fawa tana tarin hardai ta janye jikinta,
Nanfa Haj lubna tashigai mata sannu, cikin nuna gajiya Fauxa tace" inane band'aki nad'an watsa ruwa narage kayan jikina? tace' oh ninama manta yi hkr hankalinane Yy gaba Fauzy duk kin rikitani muje na rakaki wankan ma saimuyi shi tare, jin hakan yasa tayi turus tadanyi yak'e kan tace" a haba daj kibari a kwana biyu mana ai indai nice nazama taki halak malak, gudun kartayi wata mgnr yasata kwasa a guje tai bandakin sabida aman dayake taso mata,

Hakan datai bakaramin birge hajiya lubna tayiba hartana binta da dariya cike da shaawa,
Amanta tagama kwarawa sannan ta wanke fuska da wuyanta da hannuwa d kafa tamkar dai tayi wanka, tafuto ta tardata kwance akan makeken gadonta idon nan Yy jajir don masifa,

Cikin sakin fuska tace" haj ta bani kaya Mara nauyi ko nad'an rage na jikina kan kema kiyi wankan ki rage naki kayan, tace" gsky kina burgeni inason muamala da mace maj tsafta,

Shigarta wanka keda wuya, kiran islam yashigo wayarta tace" yimaza ki d'aga gadon ki d'auko kifuto inkin futo ki kullota tawaje yi sauri,

Nanfa ta dage k'arfinta ta ture katifar a gurguje ta d'age katakon yayi baya yafad'a kan katifar, idonta ya sauka kan kwalin tayi kansa ta bud'e idonta ya sauka kan wani gunki an rubuta Saudat ajikinsa cike da karsashi tasa hannu ta d'auko ta idonta ya sauka kan wata kwalba bata b'ata lokaci ba ta d'auko ta tabude ta tatsiyaye ruwan ciki a k'asa ta suri wayarta tayi waje,
Dagudu tabar sashen tanajin wayarta na kara tasan kiran Islam ne bata tsaya a ko inaba sai a gaban yaya Abba Wanda keta safa da marwa, cikin murna ya tareta tashiga nuna masa gunkin ya k'arba yana tambayar ta ina sauran kona Saudat kawai ta d'akko?
Turus taja tatsaya, yace" zomu tafi tunda kinsamo nata. Saroro tabishi da kallo kan yajuya da gudu, rikota Yy tareda cewa" bakida hankali ina zaki? Komawa zanyi, ke kina haukane? Aikan Abba y rufe baki Fauza tajuya takoma cikin sashen. TOFA๐Ÿ‘[5/9, 7:55 PM] Haneepa: [12:15PM, 5/9/2016] M Haneef: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...75


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneep&Haneefa Usman


***a guje tafad'o dakin tamkar an jefota, turus ta tsaya don ganin Haj lubna a tsaye rik'eda kugu fuskar ta da alamun mamaki, cikin masifa tadaka wa Fauza tsawa kan tace" dama abinda yakawo ki kenan? Ni zaku munafun ta? Wayar ta tad'auko tasoma Neman wata number, cikin zafin nama tasa hannu ta fizge wayar ta dokata a k'asa, nanfa tayo kanta da duka kokawa ta hard'e kasancewar ba karfin su d'aya ba ta kayar da Fauza ta shaketa,

A can kuma Abba yashigo yn neman Fauza yarasa inda ta bulla cikin ikon Allah saiga islam ta Sakko dg sama, zomuje tace dashi, suka rankaya suka nufi d'akin,

Ganin dayaiwa Haj lubna akan ruwan cikin Fauza yasa baiyi wata wata ba ya d'auki center table dake gefe ya saukewa Haj lubna shi a kanta, k'ara tasaki ta sulale agun hannun ta dafe da kanta Wanda yasoma zubda jini,+


Nanfa yad'ago da Fauza ita kuma Islam ta d'auko kwalin suka futo sukabar Haj lubna yashe a gurin,


Cikin hanzari sika baro sashenta, Islam tamik'a wa Abba kwalin dake hannun ta wandake dauke da gunkinan mutane da dama tace" ungo wannan kufuta dashi Ku tabbatar kun faffasa su ni zanje nak'ara sa aikina,

Fauza tace" wanne aiki ne Islam? tace" akwai wani d'aki a cikin gidan nan Wanda Haj lubna take b'oye yaran mutane a cikin sa" duk yarinyar da aka kawo mata taimata gaddama asiri kuma yaki cinta to wannan dakin ake kaisu a boye har saisun aminta da ita insun gamai mata amfani akaisu titi a watsar wata ma saidai a futar da gawar ta wasu kuma a rufe bakin su ko juyar da tunanin su, to d'akin zanje ko zanyi nasarar futar dasu,


Cikeda Al ajabi Abba yace" Dan kari ashedai abinnaku aximinne? Yanzu abinda zaayi ke Fauza kije girin Abdallah kutafi gida nizanbi Islam na taimaka mata, aa niba inda zantafi muje tare,

Agurin sika faffasa gumakan suka duresu cikin kwalin take wani hayak'i yashiga futa daga jikin kwalin, Islam tace" kinga kuzo mutafi,


Cikin gidan suka kutsa ta kaisu har lungun d d'akin yake, nanfa sukayi tsarko tsarko don basusan ta inda zasu bud'e d'akin ba, Abba yace" yanzu ke bakida safayar mukullan d'akunan amma kk kwasomu zuwa bud'ewa? Tace babu gsky amma ina ganin in mukayi kokarin b'alle handle din shikenan ko? To dame zamu b'lle? tace ina zuwa,

A gurguje takoma ta d'auko wuk'a a kicin tadawo ta mikawa Abba tareda cewa" wannan kosushin zamu kwance muna kwancewa saimu jijjige shi,


Hakan kuwa sukai, cikin kankanin lokaci suka jijige handle din, naciki kuma jin ana Neman jijige k'ofar yasasu tsorata duk sukayi gefe suka tsure guri d'aya suna ihu,

Ihun da yaran suka farane ya ankarar da 'yan aikin gidan wayanda dakunan su ke bayan gidan nan, nanfa babbar cikin su ta sheko da gudunta donta shaidawa Haj lubna, dakin tagani a hangame, cikin mamaki tashiga kai tsaye tayi arba daita a kwance a sume,


Nandai tayaiyafa mata ruwa ta farfad'o a razane kanta yanaimata wani irin ciwo nanfa tayi hankoran tashi takasa kafarta tai mata nauyi, tace" maza kije kicewa mai gadi injini karyabar kowa yafuta daga gidannan su kulle ko ina har Islam kar abarta tafuta,


Acan kuma sunyi nasarar bud'e d'akin suka Shiga, Abba kuwa yanasa kai yajuyo don bazai iya shigaba don kafatanin su tsirara suke, abin takaicin harda yara k'ananu wanda ko kirgar dangima basu faraba,

Don tausayi Fauza kuka tasa musu, nanfa islam tabude sif din dake dakin tashiga watso musu kayan dake cikin sif din, nanfa suka shiga saka kayan abin tausayi,


Sai lakacin Abba yashiga d'akin yace" yanzu ta wacce hanya kike ganin zamu futar dasu daga cikin gidan nan?


Wlh nima bansaniba

[12:15PM, 5/9/2016] M Haneef: Bangane baki saniba kina tunanin masu tsaron gidanku zasu barmu Mu fita da wayan nan mutanen? Fauza tace" tabdijam aikwadai bazasu barmu ba saidai in Mu haura ta baya,


STORY CONTINUES BELOW

Abba yace" akwai k'ofa tabaya ne? Akwai ammafa akwai mutane a bayan gidan suna iya zuwa su fadawa Haj lubna kuma mukullin kofar yana hannun ta, bkomai muje zamusan yanda zamuyi Allah zai taimake mu, nandai suka tasasu agaba sukusan goma suka futar dasu bayan,

Jamaar dake hidimar girki agun da masu wanke wanke sai binsu da kallo suke gefe d'aya kuma wasu wanki suke, har suka Isa bakin k'ofar ananne suka rasa abinyi,


Wata daga cikin su tace" hajiya Islam ina zaku haka? Tace" babu ruwanku kuma duk wacce tayi yunkurin futa daga gurin nan saina fadawa dady na, jin hakan yasa ko wacce tashiga harkar ta,


Abbane yashiga kicin din kozai samu abin takawa duk binciken sa maiga komai ba, ya dubi uwar tuwon yace" kunada tsani dazamu taka Mu haura? Tace aa bamu dashi saidai ko wannan k'atuwar tukunyar zaku kifa kutaka inaga tsayinka zai kai,


Aikwa bashiri sika gangara ta gurin tareda taimakon ma'aikatan, Abba ne yahau saman tukunyar  da taimakon mutum uku a cikin maaikatan suka dinga d'aga yaran shikuma saiya rikosu ya Dora akan katangar saisu dira,


Fauza ce taiwa Abdallah waya yazago bayan gidan da motar duk wacce tadiro ya dauketa yasata a motar. Cikin ikon Allah babu wacce taji ciwo. A haka har suka gama dirowa, ana cikin hakanne wata tashigo cikin sashen tasaki baki cikeda mamaki tace" kai au nan kuka taho? Tosaina koma nagaya wa hajiya, tana kokarin juyawa islam tad'au farantin tangaram ta rotsa mata aka,


Abba yace" barta kizo mutafi, nandai suka haura da Islam, cikin rashin saa Fauza ta dirga tafad'a akan hannunta na dama, aikuwa tasaki kara duk sukayo kanta har Abba daya diro yanzu,


D'agowar dazasuyi sukaga anzagaye su da bindigogi nanfa kowa Yy saranda banda Islam datai musu tsawa tace" ku meye haka? Dayan cikin sune yace" hajiya ce tabada umarnin akamo Ku kuma harke tace akama,


Kutsowar wata mota cikin layinne ya danja hankalin su, cikin tsananin farin ciki Islam ta furta"dady, nanfa suka sauke bundogogin su bayan Yy fakin a gefe,  islma ta ruga gurinsa tasaka kuka yace" lafiya? Ku meye haka? Zakwakurin yace" hajiya ce tace" mukamo su haurowa sukai ta Katanga zasu gudu, yace" bangane ba firsina ce acikin gidan daza ace sun hauro zasu gudu?


Cikin nutsuwa yaya Abba Wanda Yy futu futu yace" Alh wannan mgnr mgn CE mai tsayi dole sai an xauna an nutsu kan ayita, a takaice dai wayan nan yaran dakagani daga cikin gidanka muka kwatosu a hannun matar ka wacce take tsare dasu wata da watanni a dalilin cika wata manufa tata tadaban,


Cikin Al ajabi yake dubansu, wayan nan duk a cikin gidan a tsare? Nandai ya umarci masu tsaron gidan suja dasu akoma cikin gidan gaba d'aya ba,


Jin hakan yasasu rushewa da ihu Abba yace" ku kwantar da hankalin ku aikuma komai yazo k'arshe asirin lubna yariga yatonu,


A farfajiyar gidan sukai kacib'us da Haj lubna wacce dakyar da taimakon wannan munafikar ta iya Jan k'afarta tafuto, anannema tabasu damar su kamosu, ganin datai musu tareda Mahaifin su Islam ya tsorata ta don haka ta kwasa da gudu zatai cikin gidan k'afar tace batasan wannan,


Nandai yabada umarnin a tsareta tukun, duk wani lungu da sako Wanda Haj lubna take aikata shashancin ta saida Islam takai babanta yagani da idon sa, innalillahi kawai yake ambata cike da mamakin wai a cikin gidan sa ake aikata wannan bad'alar bai saniba?

[5/12, 8:55 PM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...76


©NWA๐Ÿ“–

Mamanhaneep & Haneefa Usman


***nandai mahaifin Islam yakira likitan su a waya tare da tura masa yaran don ya duba lafiyar su kan ya mik'asu ga mahaifen su, Fauza kuwa tuni yaya Abba yayi gida da ita sakamakon hannun ta daya kumbura kasancewar fad'owar datayi akan hannun,Baban Islam ba yanda baiyi dasu ba akan su bari akai ta asibiti tare da sauran yaran Abba yak'i, don haka yakai ta gida ai mata gyaran gida.


STORY CONTINUES BELOW

Ba k'aramar wuya Fauza tasha ba, a yyinda ake gyaran hannun ta Wanda tayi gocewar k'ashi, nan dai aka gyara hannun ta zauna a nan gida gurin mahaifiyar Abba tana jinyar hannun ta.


A can kuma mamy ta zuba ido don ganin ta ina Fauza da Abba zasu b'ullo? Shuru-shuru sai misalin takwas na dare Abba yazo gidan anan ya kwashe abinda yafaru yafa d'awa mamy,


Ta cika da mamaki tareda jinjina musu sakamakon namijin k'ok'arin da sukai na kub'utar da bayin Allah,tareda tausaya wa Fauza itadai tanajin k'aunar Fauza har cikin ranta,  tana shaawar kyawun halin ta da d'abi unta da kuma soyaiyar da ta kewa Saudat zallar k'auna wacce tayi k'aranci cikin wannan zamani, abinda yafi birge ta sadaukar da farin cikin ta tare da rayuwar ta gaba d'aya don rayuwar 'yar uwarta ta inganta. Nandai tayi alawa dai da hali irinna haj lubna tare da dukkan masu hali irinna ta,

Nandai suka rabu akan zataje ta duba Fauza, haka nan taji tana muradin ganin ta,


A b'angaren Saudat kuwa? Tashi d'aya taji wani irin canji yazo mata tashiga wani irin yanayi tamkar anzare wani nannauyan Abu cikin zuciyar ta, nanfa tasoma tunanin ya akai lokaci d'aya rayuwar ta ta canja batare da niyya ko sanin yanda abubuwan sukai ta kasance ba? Nan take tasoma tunanin abubuwan dasuka faru cikin kwanakin baya dasuka shud'e tana ganin su cikin idon ta tamkar a majigi,


Nandai nadama ta tsiyarci zuciyar ta tsoron Allah ya d'arsu cikin ranta, zunbur tamik'e tayi band'aki tayo tsarki ta tsarkake jikin ta tana mai zubda hawayen ta, tana jimamin yanzu dawane ido zata dubi gabas? Da wanne hannu zata nemi gafarar ubangijin ta? Hannun daya aikata sab'o? Sutturar tama kasa sanya wa tayi, ta d'auko kayan Fauza tazura a jikin ta, ta tunkari sallaya zuciyarta fal rauni tare da kunyar abinda ta aika bayan tasan Allah yana ganin ta kuma yabata wadataccen ilimin addini tasan halak tasan haram amma ta take tasab'i Allah da sab'o mai girma? Cikin wannan yanayi mamy tashigo tasame ta,


A gefe ta zauna don tajira ta ta idar da sallah, cike da tausayi take dubanta don ganin yanda take jero Salloli Wanda ita kanta batasan raka'a nawa tayi ba, idon nan yayi jajir don tsananin kukan datake, bayan ta sallame ne tashiga kwararo addua da istigfari Wanda har saida mamy taje ta rik'eta ta rungume ta don tausayin ta,

Cikin kuka tarik'e mamy tareda cewa" me zanyi Allah ya k'arbi tubana mamy? Waini nice nasab'i ubangiji ta wannan hanyar? Mamy nasab'i Allah da wannan hannun mai karatun Alk'ur ani? Nasabi Allah da wannan k'afar mai takun lada kanta juya ga taka alhaki? Nasabi Allah da wannan ni'imtacciyar fuskar da Allah yayimin? Nasab'i Allah da bakina Wanda nake kiran Allah da karanta littafinsa dashi? Nasab'i Allah da goyan bayan zuciya ta wacce ada take cike da tsarki da kusanci da ubangiji na mamy? Wai shin meyasa nayi hakan?


Inada ke mamy inada Baba inada Fauziyya a doran k'asa amma kuka bari rayuwa ta talala ce? Me naiwa Fauza ta sakarmin ragamar rayuwa ta haka? Duk k'aunar danake wa Fauza tabari rayuwa ta tab'aci haka? Ina Fauza? Bacci take ko idonta biyu ko bata cikin hayyacin ta dazata barni nasab'i Allah haka? Shikenan narasa gata cikin rayuwa ta, tunda babu Wanda ya tsallakar dani daga rudun duniyar dana jefa rayuwa ta,


Mamy ce ta katseta don ganin sunbatun yayi yawa tamkar wacce bata cikin hayyacin ta,da cewa" bawa baya tsallake kaddarar sa Saudatu, Allah ne ya jefaki cikin rayuwar da kika tsinci kanki,don ya jarraba imanin mu, kisani Allah ne mai shiryawa kuma ya b'atar da bayin sa kuma babu yanda zamuyi dole ne Mu amshi k'addara duk a yanayin data zomana,


Ada sanda Fauza tayi rashin jinta akwai wanda ya shiryata? Koke ada kekika kimtsa kanki? To Allah ne mai shiryawa duk ahalin dakika ga bawa ki bishi da addua, Allah dayayi shi shiyasan yanda zaiyi dashi,


Fauza da kike gani babu abinda bata bakiba cikin rayuwar ta, farin cikin ta, lafiyar ta ranta, duk ta sadaukar miki dasu, yanzu haka Fauza tanacan gidanku tana jinyar hannun ta, a dalilin ki,


Duk jikinta yayi sanyi kukan ne bai tsaya ba har yanzu, nandai mamy tashiga zaiyane mata abubuwan dasukai ta faruwa tundaga ranar da Abba yazo mata da maganar  kud'aden da wayar daya kwace a hannun Fauza" har tayi kuskuren gasawa Fauxa gyada a hannu ba cikin hakkin ta ba,ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA SAI GATA A MASAK'A),


nan da nan hankalin ta yatashi, hawayenta yak'aru, tacika da tausayin Fauza, duk labarin sam bai mata dad'i illa Abu d'aya(mgnr Auren ta da Abba) wacce Baba Allah yajikar rai ta k'ullah,


Jitake tamkar tayi tsintsiwa ta tafi garin su a yau, don Fauza kawai take muradin ganin cikin wannan lokacin, suna cikin wannan yanayinne amme tashigo d'akin, duk cikin su babu wacce tasan shigowarta tun farkon fara maganar tashigo, tunda taga mamy tashiga dakin su tabiyo bayan ta, don tajima tana zargin akwai abinda suke boye mata,


Ganjn idon amme fal hawaye ya tabbatar musu da taji duk abinda yafaru, nandai suka had'u su ukun suka kuma tattauna mgnar sukai aman su suka lashe.


Acan kuma b'angaren haj lubna, tananan a tsare a wanni d'aki dake farfajiyar gidan, tayi kukan tayi magayar amma ko kadan babu Wanda ya saurareta, da misalin k'arfe biyar kuwa, bak'inta ne suka soma hallara cikin gidan, manyan hajiyoyi da 'yan mata wanda a shekaru bazasu wuce ashirin da uku zuwa da biyar ba, duk wacce tashigo ta faka motar ta take masu tsaron gidan zasu kwace jakarta da wayar ta su turata d'akin da haj lubna ke tsare, hakanan suka dinga kamesu da d'ai da dai duk wacce tazo gidan nan a ranar tashiga hannu. Washe gari da safe ne, Mahaifin Islam yakira kwamishinan 'yan sanda ya shaida masa halin da ake ciki, batare da b'ata lokaci ba saiga yan sanda mota hud'u nanfa suka duresu cikin mota sukai gaba dasu,


Cikin ikon Allah dukkan yaran babu wacce aka samu wata gagarumar matsala dg gareta, likitocin sunyi kokarin ganin sunbawa yaran kulawa a cikin kwana uku kacal sundawo hayyacin su, nanfa kowacce tabada kwatancen gidan su mahaifin Islam da kansa yaraka ko waccen su gida tareda d'inbin ban baki tareda abin arziki,


Sanin da akai masa kasancewar sa mutumin kirki yasa iyayen yaran basu wani d'aukaka maganar ba, illah farin cikin ganin yarannasu tareda godiya ga Allah, don sunbarwa Allah komai, inma akwai me korafi a cikin su to sunbarwa cikin su, sanin da sukai a wannan marrar ta yanzu baa sharia da masu arziki gwara kabarwa Allah yafi maka( fad'an dayafi k'arfin ka...)


A b'angaren Fauxa kuwa tanajin saukin hannun ta sabida kulawar da inna ke bata sam batada wata matsala ga Anty larai itama tana bakin kokarin ta ganin ta kyautata mata, Baban kuwa duk abinda yagani naci yakan siyo yakawo mata,


Sau buyi su mamy nazuwa dubata, batajin ddn yanda basa zuwa da Saudat a cewar mamy inhar tazo tafa kamar ta fallasa sirrin dasuke kokarin rufewa ne, don inhar sun had'u to dole maganar zata tashi bayan sun boye gskyr maganar don har yanzu basusan dalilin gocewar kashin da Fauza tasa muba,


Duk karshen mako Abba yake zuwa don ganin cigaban da akasamu na warkewar hannun Fauzan, a yau ma zaune suke suna hira da mahaifiyar sa gefe kuma Fauza ce ta idar da sallar isha, shigiwar mahaifin Abba, Wanda suke kira da kawu, ne yasa Fauza tabasu guri bayan tai masa sannu da zuwa b'angaren Anty larai tashiga don tanasan yiwa Baba mgnr tafiyar ta tunda tasamu Sauki kuma ta kagu taje taga Saudat,dama tagaji da zaman a duk sanda ta futo taga dakin Baba duk saitaji kewarta taka mata,

A wannan zamanne kawu ya bijirowa da Abba maganar aure, budar bakin innan sa kuwa sai catai" wanne irin ya futar da matar aure bayan ga k'anwar sa nan a gida? Gida bata koshiba aiba a kaiwa dawa ba,


Cikin jin ddn furucinta kawu yace" To Allah ya zaba mafi alkairi, Abba yace" aini dama inna tuntuni Baba taimin mata lokaci kawai nake jira.ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...77


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneep&Haneefa Usman


*****Bayan sati biyu***


Umar faruk(Abba)kyakyawan matashi ne Wanda ke burin auren kyakyawar mace tamkar shi, Abba fari ne k'al k'al dogo mai d'an kauri daga sama, wanda yake cikin shekararsa ta 32 a halin yanzu, Abba mutum ne mai kirki ga son zumunci tare da girmama na gaba dashi.


A halin yanzu, wata iriyar nutsuwa ce tak'ara shigar Saudat,yayin da kyawunta yak'ara bayyana ga wani irin annuri dake futa daga kyakyawar fuskar ta, duk Wanda yaganta yasan tasamu nutsuwa saika rantse canja Saudat akai ba waccen Mara kunyar bace, kafatanin sutturun ta tadaina amfani dasu haka ma kud'aden dake cikin asusun ta na banki duk ta futar dasu da taimakon Abba ta sadakar da kud'in, mutan gidan suna mamakin canja war Saudat, ta nutsu tadawo mai kunya har wata 'yar kiba tayi a cikin 'yan satittikan,

Biyaiya da girmama Abba datake tareda kyawun surar da Allah yai mata sun taka rawar gani wajen jawo hankalin Abba gareta, Saudat mutum ce mai saurin shiga ran jamaa ta iya muamala da mutane, tuni ta kankane ko ina na zuciyar Abba, yazamana baida tunani sai nata tun abin baya damunsa har ya tsinci kansa d inbaije yaga Saudat ba bayajin dad'i, ada yakanje gidan k'arshen mako, to a yanzu duk kwana biyu yakanje ga kuma wayar dasuke kusan raba dare sunayi.+


Ranar da mamy ta farga da soyaiyar da ke Neman k'ulluwa tsakanin Abba da Saudat,Sam saitaji hakan bai mata dad'i ba, har saida ta furtawa amme mahaifiyar ta, nan dai ta ce" to yanzu ke mai kike nufi da bakyason zaryar da Abba yakewa Saudat? Kina nufin byakason had'a zuria da Abba ne? tace" zuri a kuma aita riga tahad'u amme, abinda Yy Saudat aishi yai Abba, to nima dai abinda nagani kenan, ko sabida isma'il zaki hana kulluwar wanj Abu tsakanin su ne? Cikin rashin fahimta tace" nifa bandoshi nan ba amme, kawai dai naji ina tausayawa Fauziyya ne kuma Sam Abba bai dace da Saudat ba,


Salati tasaka tareda tafa hannu kan tace" au banban ci zaki nuna cikin yaran ki Sa'adatu? Ita Fauziyya catai miki tana son Abba dazaki shiga tausaya mata don kinga Abba na zuwa gurin Saudatu? To wallahi kikasan ce mai adalci Sa'adatu, kizuba wa sarautar Allah ido, waima na tambayeki, kin tabbatar da Abba son Saudat yake? Kodai kokwanto kike? Amme jinai ance inkaga kare yana shinshina takalmi..., hmm to naji amma kizuba musu ido kigani ko wacce cikin su Abba yake so duk d'ayane kuma watan kusan tafi wata.


Duk budirin da akeyi Fauza baiwar Allah tana garinsu a yau ne take dawowa gidan, driver mamy ne yaje ya d'aukota, hannun ta ya warke sumul tamkar bataji rauni ba,

Cike da zumid'in ganin Saudat take, har Allah Allah ta dingayi su isa gidan saitaga tafiyar ma tayi tsayi sabida zumid'i har suka isa bata daina mamakin abinda yahana yaya Abba zuwa d'aukan taba, akwai canje canje data soma fuskan ta a gurin sa don yanzu sai yafi sati bai kirata ba sai dai ita takira shi har tagaji ta watsar ita ma,


Cikin murna da tsantsar kewa tashiga gidan, nanfa gida yad'au sowa sunata murnar ganin ta, bayan hayaniyar ta lafane tace" mamy ina Saudat bangan ta cikin masu tarbata ba,


Tab'e baki tai kan tace" baki ganta a set room ba?da fuskar mamaki tace" bangan taba, bari naje gurin ta, cikin sauri tamik'e don Saudat kawai takeson gani,


A can b'angaren Saudat kuma, suna tare da Abba a set room sunashan hira, a halin yanzu ma, Abba yariga yayi nisa don Saudat tagama narkar masa da zuciya burinsa kawai ya mallake ta a matsayin matar auren sa, yanzu ma kyakyawar fuskar ta yake kallo da shanyayun idanuwan sa, fuskar nan tasha make up don Saudat ta waye idon ta yariga yabud'e, cikin salon kauna ya ce"'kina nufin baki fahimci abinda nake nufi ba? Cikin yanga da salon jan hankali tayi far da ido kan tace" ya zanyi nasani niba Allan musuru ba, kafuto ka fahimtar dani yaya Abba kasa a ranka duk abinda kakeso zaka samu inhar a gurina nane, kina nufin duk abinda na nema zansamu? Ta gyada masa kai, yaci gaba, kinga wannan hankicin na hannun ki? Yoshi nakeso kibani donnasan yana d'auke da kamshin ki, inna rikeshi zanji tamkar ina tare dake, cikin murmushi da salon wasa ta miko masa, ya rik'e amma bata cika ba, nan dai suka bi juna da wani irin kallo wanda susukan maanar sa, hannun su rik'eda hankicin, a daidai nan Fauza tashigo cike da zumud'in ganin Saudat, tayi arba dasu cikin wannan salo na mayen soyaiya,


Cak tatsaya takasa gaba balle baya,nanfa bugun zuciyar ta yak'aru take taji wani irin haki ya zomata, hawayen daya sauka kan kuncin ta yasata dawo hankalin ta, dakyar ta iya furta sallama, amma shuru, ta daure ta k'akalo yak'e tace" Saudat! Nan ma shuru, sai taji tamkar ta hadiyi zuciya don haushi,


Batasan sanda tsaki ya kubce daga bakin taba" Mtssssw tamkar xata tsinke harshen ta,sunji tsakin ya doki kunnan su har suka jiyo a tare don ganin waye mai tsakin, da sauri Saudat ta isa gareta ta rungume ta saita saki kuka, don tana jinjina wahalar da Fauza tasha a kanta,


D'agota tayi tashiga share hawayen ta, yayin da ta watsa wa yaya Abba wurk'ilallun idanun ta, tajuya tai fucewar ta, Fauza! Yakira sunan ta, amma ina ko waigowa batai ba, nanfa jikin Saudat yayi sanyi ta dubi Abba tace" meyake faruwa ne?oho yabata amsa, a hanzar ce tabi bayan Fauza.[5/21, 6:59 AM] Mamanhaneep: [5/17, 10:08 AM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...78


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneep & Haneefa Usman


***Kallo d'aya mamy taiwa Fauza wacce tashigo yanzu ta haye sama, a ranta ta raya" nasan arina, Saudat ce tashigo tabi bayan ta da alamun damuwa cikin fuskar ta. Uhm mamy tace" a ranta kuwa tana kissima abubuwa da dama dangane da lamarin Saudat da Abba, tabbas babu tantama akwai soyaiya tsakanin Abba da Saudat, ga kuma uwa uba amanar da Baba Allah yajikan rai tabashi,


A zuciyar ta taca" yazama dole kiyi hkr Fauza ki dau dangana, kalar taki kaddarar kenan, son maso wani,


A d'akin su ta tadda Fauza zaune gaban madubin su, ba kuka take ba amma da kaganta kasan akwai nannauyan abinda ta b'oye, ta cikin madubin ta dube ta tadafa kafad'ar ta kan tace" ban tsammani haka daga gareki ba Fauza na zaci zangan ki cikin farin ciki kuma ina tunanjn zakifi kowa farin cikin shiriyar da ya nufeni da ita.


Mik'ewa tayi takamo hannun Saudat kan tace" ina tayaki murnar sabuwar rayuwar da tazo miki a yanzu, Allah y shiga tsakanin da duk wani abin haramci ya had'aki da Alkairi har karshen rayuwar ki, gurin kayan ta tanufa bayan tasaki hannun Saudat, kayan ta tashiga cirowa dg akwati tana jerawa cikin sif, saroro Saudat tabi Fauza da kallo, cikin yamutsa fuska tace" waime yake damunki Fauza? Naga baki da walwala Sam, kuma ba haka kk min ba in anbata rankine don Allah ki fad'amin,+


Murmushin yak'e tayi kan tace"walwala kuma Saudat? Aini nariga nayi bankwana da ita, tuntuni nariga na sadaukar da farin ciki na a gareki inhar zakiyi farin ciki toni banida bukatar sa, a yau nakuma tabbatar da hakan nayi bankwana da farin ciki, cikin rashin fahimta tace" meye farin cikin ki Fauza? Naki mana, ai farin cikin ki shine nawa,

Bata gamsu da amsar Fauza ba, tadai kawar da zancen da cewa" yasu Baba da inna? Mamman yakoma sch? Eh yakoma kuma duk suna lpy, amma Baba yayi fad'a sabida rashin zuwan ki, naso nazo kodon naga hannun ki mamy ta hana zuwan, bkomai hkn yafi ai, saiki samu lokaci kije Islam tazo gurina har sau biyu dad dinta ma yazo yadu bani, kuma yace" inkinje garin a fada masa yanason ganin ki, ni kuma mezai min? Bazai wuce aka case din haj lubna bane don har yanzu suna tsare, Allah sarki Fauza kin wahala sosai Allah yasaka miki da alkairi, Ameen niwai kin manta da yaya Abba a waje ne? Au namanta wlh bari naje amma yanzu zandawo, da ido tabita har tafuta daga d'akin ta runtse idon ta wata zazzafar hawaye yazubo mata a bakin gadon ta zauna tashiga rero kuka don tsananin tausayin kanta.

[5/17, 1:13 PM] Mamanhaneep: ***Tun daga wannan lokaci Fauza tadena sake wa da Saudat, tara sa dalilin dayasa batasan koda doguwar hira ta had'asu ta gwammace tatafi gurin su amal sukan d'ebe mata kewa, tsakanin ta da yaya Abba kuwa sai gaisuwa sai yazo sau nawa gidan bata yarda sun had'uba, tun abin baya damunsa har saida yakai karar ta gurin mamy wai tadena kulashi, mamy kwa hkr tabashi tareda cewa"yanayin rayuwa ne,,


Saudat kuwa, hakan da Fauza take mata kusan ince yai mata dad'i don wani abinma da gayya takeyin sa don ta lura da yanayin da Fauza take Shiga a duk sanda take tare da yaya Abba, tasha kama Fauza tana kuka cikin dare Wanda take zargin duk akan yaya Abba take yinsa, to inba akansa take kk ba maizai sa Fauza kuka? Bayan tuntuni nariga nasan Fauza tajima tare da kaunar yaya Abba?

A b'angaren Fauza kuwa? Duk yanda taso tayaki ce Abba daga cikin ranta takasa, batasan yaya Abba yariga ya mamaye ko ina na rayuwar taba saj a yanzu data ke neman yaki ceshi cikin ranta, ta kauracewa ganin sa tayi adduar tayi kukan duk don yafuta cikin ranta amma tamkar turi, sunyi shakuwar da rabuwar su zai matukar wahalar da junan su, shikan sa Abba inhar yazo gidan sabida Fauza yake shiga ciki don kawai ya ganta amma saiyake ganin kmr gudun sa take yadamu mutuka da rashin ganin ta, a yau ma tare suke da Saudat a kofar gidan jingine jikin motar sa,


Fauza ce itada rukayya suka shigo layin hannun ta rik'e da leda sun amso d'inki a bayan layin su, tunda tadosu gaban ta yashiga fad'uwa don wani irin kallo Abba ya kafeta dasu har saida Saudat ta fahimci hankalinsa   baya kanta, juyawar dazatai taga Fauza ce da rukayya, take kishi yataso mata har tad'anja k'aramin tsaki a dai-dai lokacin da suka k'araso kofar gidan, sama-sama rukayya  suka gaisa da Abba Fauza kuwa ko kallon inda suke batai ba kanta tsaye tanufi cikin gidan,


STORY CONTINUES BELOW

Muryar sa ce ta katse ta, Fauziyya yakira sunan ta, cak tatsaya batare da tajuyo ba tace" na'am, zonan inasan ganin ki, ba asan ranta ba haka tadawo tatsaya dg gefe  fuskar ta hade tamkar bata tab'a dariya ba, Saudat datai kicin-kicin taduba tareda cewa" bamu guri Saudat zanyi mgn da Fauza, wata uwar harara tabi Fauza da ita kanta juya tashige cikin gida, bai kula da abinda tayiba yajuyo kan Fauza dake tsaye rungume da hannun ta a k'irji, saida yak'are mata kallon kan yace" Fauza ba fad'a meya kawo gaba? eyi menai miki kk yadani haka? Inban manta ba rabon danasa ki a idona anfi sati biyu, ko wayar ki nakira bakya d'auka kina tunanin zan barki nazuba miki ido kita gaba dani? Abin da kikai min kin kyauta kenan? In laifi naimiki saiki kirani ko a waya ne kifad'a bawai kimin irin wannan hukuncin ba,


Kina sane Fauziyya munyi shak'uwar da bazan iya jure rashin kiba, rashin ganin ki kwana biyu yasani cikin damuwa, Dan Allah karki sakemin haka,

Tunda yasoma magana kanta nak'asa illah hawayen dake zuba cikin idon ta, juyin duniya yayi don tayi magana amma taki sai kukan ta dayakara karuwa kallon sa kawai take tareda sharar hawaye, sai can tace" kayi hak'uri...๐Ÿ‘

[5/21, 6:59 AM] Mamanhaneep: [5/20, 9:28 AM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...79


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneep&Haneefa Usman


***Cikin yanayi na mamaki yace"bangane inyi hak'uri ba ki na nufin kin dak'ile zumincin dake tsakanina dake? girgiza kai tayi tareda cewa" ni bance nadena zuminci da kaiba, akwai abubuwan dake damuna babu wanda yasani sai Allah kuma shi zaimin magani, don haka kadena damuwa da canjin yanayi na kowama na canja masa kaidai kataya ni da adduar Allah ya shigemin gaba,


Hmmm ya sauke numfashi kan yace" tamshikenan indai addua ce zanmiki amma ki fad'amin damuwar ki, kokin manta ni abokin shawarar kine? Nine fa Abban ki abokin fad'an ki kosai na tuno miki da diramar mu tada Fauza wurk'il ko 'yar bak'a sari daddawa? Batasan sanda dariya ta kufce mata ba, kallon ta yake dauke da murmushi cikin fuskar sa, shidai yanason yaga Fauza cikin farin ciki, tace" baka da mantuwa Yy Abba, wai har yanzu ni 'yar baka ce? Aina danyi haske ko? Bawani haske har yanzu kinanan a bakar ki,  murmushi tayi tareda goge ragowar kwallar ta kan tace" ko shiyasa maza ke guduna? Cikin mmki ya dube ta tareda cewa" bangane maza na gudun kiba wani abin gareki daxaisa ayi gudun ki? Cikin yake tace" kodaya kasan Allah yakawo Mu zamani Wanda bak'ar mace bata da farin jini, mazan yanzu idon su da dukkan burin su yanaga farar mace, balle ni nida nake cikin jerin masu nakasa, kasan dole a gujeni ga bak'i ga muni ga nakasa a ido, Amma ina godewa Allah dayabani kyawun hali don shine jari na,

tana kaiwa nan tashige gida tana sharar hawaye, tabar A tsaye cike da tausayin ta jikin sa duk yasaki yarasa kuzarin sa, Allah yagani yana kaunar Fauza bazai taba zuba ido yabarta cikin kunci ba, sai lokacin yashiga zano surar Fauza cikin ransa, doguwa ce mai d'an kauri daga k'asa, mai 'yar fafadar fuska mai dauke da fararen idanuwa mai matsakai cin hanci da karamin

[5/20, 11:18 AM] Mamanhaneep: Baki mai d'auke labba masu tudu, yanda idonta yake fari kal haka hakoranta suke karkar, sai bakin gashin daya sauka kan kafadunta irinnamu na hausa fulani, Fauza bakace irin bakin nan mai kyau wanda keda matukar tsada wanda a cikin bakakema da wuya kasamu goma cikin dari masu irin sa, zamu iya kiran ta mai kananun kyau, mai tareda wani boyeyen sirri wanda Allah ne kadai yai mata baiwar sa,


Hmmm ya sauke a jiyar zuciya dakyar ya iya jan kafafun sa yashiga mota yabar harabar gidan,


Kacib'us sukai da Saudat a matakalar benen sama, cikin sakin fuska tace" Saudat nabaro Yy Abba a waje, dakatar da ita tayi, cikin fushi tashiga gaya mata mgn kishi yarufe idon ta, Fauza kirasa wacce zaki munafunta saini? Aidama nariga na fahimci irin son dakike wa Yy Abba tuntuni, to zan gargadeki da kifuta shirgin sa karki kuskura nakuma ganin ki tareda shi, wato tunda baice yana sonki ba shine zaki cusa kanki gareshi? to bari kiji nariga nai miki nisa bazaki taba nufar inda na dosa ba wlh don haka tun wuri kisan inda dare Yy miki Abba ba saanki bane, sonsa dakika dauka kika dora cikin ranki saikije ki cireshi tunkan ya kashe ki,


STORY CONTINUES BELOW

Tunda tasomai mata masifa kanta nak'asa idon ta kuwa yayi jajir don bacin rai, cikin sanyin murya tace" Baki karyaba ina kaunar yaya Abba amma kisani tunda kaunar ki bata kasheni ba haka ma kaunarsa bazata kasheni ba, tsayawa da yaya Abba yanzu nafara sabida bake kk hadamuba kuma bake zaki rabamu ba, cikin fushi ta shak'ota ta had'ata da bango ta mak'ure, Allah sarki Fauza ko kwakwaran motsi bataiba cewa tai" wlh ko zaki kasheni bazan yi fad"a dake ba saidai na zauna ki dake ni iya sanran ki, don innai fad'a dake akan namiji wlh bazan tab'a yafewa kaina ba,


Cika ta, muryar ta tadoki kunnen ta, dawowarta kenan daga gurin aiki, tahawo saman Ashe rabon tazo ta kwaci Fauza ne, ba shiri Saudat ta cikata sumi sumi tayi hanyar da kinsu,


Hannu tasa tajanyo Fauza ta rungumeta cike da tausayin ta, tashiga lallashin ta don wani irin kuka dake taso mata tamkar ta had'iyi zuciya nandai tajata har cikin d'akin ta zaunar da ita a gefen gadon ta, saida tayi wanka ta kimtsa tukun ta dawo kusa da Fauza ta zauna ta fuskance ta tareda cewa" waime yake damun rayuwar ki Fauza?


Kukanta ne yadawo sabo, cikin gyada kai mamy tace" Abba ko? Tsintar kanta tayi da gyada mata kai  takuma barkewa da kuka tace" mamy Allah y jarrabeni da sonsa narasa yanda zanyi nacire sa, mamy yaya Abba baimin adalci ba yasan ina sonsa shine yafara soyaiya da Saudat kawai don ya bakan ta raina, dakatar da ita tayi da hannu kan tace" kin fadawa Abba kina sonsa? Tsaro ido tayi tareda cewa" bantaba fada masa ba sabida gudun barar da kimata a idon sa, da kyau mamy tace, to karki kuskura kikuma nuna wata alama dazaisa Saudat taci mutuncin ki akan sa shima karki kuma nuna damuwarki akansa, kisaki jikin ki kidawo da walwalar ki, kisani aure nufin Allah ne, wani baya aurar matar wani karki bata lokacin ki akan soyaiya kisawa ranki rabonki zaizo yasame ki har inda kike, in Abba mijin kine ko baki sonsa saikin aure shi hakama duk sonda kk masa inba mijin ki bqne saidai kiyi hkr,

Kuma ninasan Abba yana k'aunar ki, kisani Fauza 'yar uwarki shu'uma ce, karkiga laifin sa, cikin sanyin jiki tace" mamy tayaya Abba zqi soni? Abba kyakyawar mace yakeso kuma fara ni kuma ki dubeni mamy badana abin da Abba yake buri ga matar auren sa, ni baka ce  kuma mummuna ga nakasa cikin halittata mazan yanzu gaba daya farar mace sukeso mamy basason mummuna bak'a Abdallah ma don bayanda zaiyi ne dady ne ya hadani dashi,


Subhanallahi haba Fauza ki godewa Allah baiwar dayai miki babu wanda yafi wani gurin Allah sai wanda yafi jin tsoron sa, kuma kowa akwai baiwar da Allah yayi masa, Fauziyya Ki gode Allah, Allah yaimiki baiwa wacce ido bazai ganeta ba haka ma baki bazaj iya furtata ba wannan baiwa Allah ne yaiwa mijin auren ki shiyasa a koyaushe nake miki adduar samun miji nagari tamkar yanda kike mai nagarta koma fiye dake, Fauza tunda Allah yayoki mai nutsuwa mai amana da son zumunci ga kuma kusanci da mahaliccin ki toki gode masa kuma inasa ran ubangiji zai miki kyakyawan sakamako,


Koba komai taji sanyi cikin ranta mgnr mamy tasan yayar da gabobin ta cikin kunya tace"naji dadin kalaman ki mamy amma naso sufito daga bakin da innajisu zasu zauna cikin raina tareda dawamammen farin ciki, fuskar ta d'aukeda murmushi tace" zaki samu fiye da haka dg masoyin ki kedai Allah yazab'a miki miji na gari, fuska ta rufe duk kunya ta rufrta wai yau itada mamy ke tad'in soyaiya abin kmr a mafarki, dafa kafadar ta tayi tace" karki kuma saka wata damuwa cikin ranki Allah yana sane dake, haka ma Saudat ki cireta aranki kisani a fuskane take Saudat taki a zuci kuma wata ce daban kisa aranki waccen Saudat din taki tajuma da mutuwa wannan kuma kibita da addua,yanzu kije ki kimtsa ki huta kiyi ramuwar bacci don bance tunanin Abba yana barin ki kiyi bacci ba, cikin kunya tace" kai mamy inayi fa, dariya sukai gaba d'aya tabita da kallo harta futa daga dakin๐Ÿ‘

[5/21, 6:59 AM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...80


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneep& Haneefa Usman


***Cikin wannan kwanakin Saudat tashirya taje gida kwanan ta biyu ranar dazqta komo ne ta ziyarci gidan su Islam don an shaida mata baban Islam nason ganin ta,a darare tashiga cikin gidan yynda islam da kannanta wanda sukadawo hutu suka amsheta da hannu biyu cikin sakin fuska, nandai suka zauna tareda bawa juna hkr akan abjnda yafaru, mahaifinna suma hak'urin yabata tareda kara tabbatar mata da cewa" lubna na tsare kuma baza abarta ba face anyanke mata hukunci dai dai da laifin data aikata, don a halin yanzu tuhumarta ake da satar yaran mutane tareda laifin tirsasawa, nan dai suka rabu bayan sun yafi juna, Dad din islam da kansa yadawo da Saudat gida cikin ikon Allah ya tarda Babanta a gida, nan dai suka gaisa cikin mutunci da girmama juna, sun dan juma suna tattauna wa daga bisani kuma yai musu sallam yatafi, Saudat ma ร  ranar takoma gida.


STORY CONTINUES BELOW

A tsaye suke cikin farfajiyar gida suna hira, da alamu hirar tanaiwa Abba dadi hakoran sa kawai kk gani daga ganinsa yana cikin nishad'i, Fauza dake gefen sa itama cikin nishadi a yau takejin kanta, suna tsaka da hira ne irinta zuminci Saudat ta shigo cikin gidan hannun ta rikeda jakar kayan ta, yanda gaban ta yafad'i haka ma gaban Fauza yafad'i, tunkan tak'araso tadubi yy Abba tace" nizan shiga ciki sai anjima,


Dakata yace" ya muna hira zaki wani ce sai anjima mezakiyi a ciki inkin koma?bkomai kawai dai zanshiga ciki ne nasan yanzu mamy tana kicin zan tayata aiki yau tana azumi, wani d'an gajern murmushi yy kan yace" kidai tsaya ban sallame kiba, ba yanda zatai hakanan ta tsaya tana jiran umar ninsa,


Saudat kuwa wacce tazo iya don gani take da gayya suka tsiri sabuwar hira don sunga tadawo, kenan ma tunda tatafi yy Abba sai yazo gurin Fauza kenan kome?wani mugun tsaki taja mtsssw tafigj jakar kayan ta ranta b'ace tayi cikin gidan duk suka bita da kallo, tawuce su fuuu, ko sannun da Fauza take mata bata amsa ba,


Abba kuwa saiya sake sabuwar hira, zuwan Abdallah ne yakatse hirar su, nandai sukai sallama yatafi bayan sun gaisa da Abdallah, nanfa suka shiga hirar dunya ammafa duk rabin hankalin ta yana can kan Saudat, duk saitaji tadamu sam batasan ganin b'acjn ran Saudat, a gefe kuma ga abdallah daya kafa mata mitar taki amincewa ya tura magabatansa sune momasa auren ta domin shifa da gsky yake, yau ma ansar data saba bashin itan tabashi, ka kara hakuri abdallah in lokaci yy dakaina zan maka mgnr karka damu kanka, haka nan yake hkr batare da ransa yaso ba.


A hanzar ce tanufi dakin su don tanason jin yaya Saudat tazo gida? Ko bkomai taji lbrin su Baba, yanda taga yanayin Saudat ya sanyayar mata da jiki, nandai ta basar tace" Saudat kin dawo lpy ya kika baro su Baba da kawu da innah? Bayan tanemi kusa daita ta zauna,


Tamkar jira take taida mgnr ta mike cike da zafin rai tashiga fad'in, bansani ba tunda ba aikena kikai ba, shin Fauza kin manta naimiki tsakani da Abba ne ko kinSane? Ina sane, tabata amsa kai tsaye, to mekike nufi danine nifa bangane ba? Kinanufin cin amana ta kuke keda yaya Abba? Yanzu Fauza ni zaki munafunta? Haba wa shiyasa naga abba yana neman wulakantani ya gannj harda dauke kai bayan harara duk a dalilin ki Fauza? Kknmin adalci kenan? To bari kiji ingaya miki tun wuri kije ki nemi mijinki, don bazantab'a barmiki yy Abba ba, niyagani yace inaso don haka nizai aura don hk kisan mekike ciki, banza wacce batasan ciwon kantaba wacce takasa banbance aya da tsakuwa, me yy Abba zaiyi dake? To yaya Abba ba tsaranki bane kidai yi hkr tsaranki yanann tafe wurkilili irin ki, badai Abba tassss! Taji and'auketa da mari batare da tak'ara sa ba,

Cike da mamaki tadubi Fauza kan tace" nikika mara Fauza? An mare ki Saudat kiyi abinda zakiyi, kina tunanin tsoron ki nakeji ne dazaki dinga cin karanki babu ko babbaka akai na? tobari kiji duda nakasar datake tare dani niba banza bace don nasan me nakeyi, kuma bazan bari akan namiji ki dinga neman yagan rigar mutunci ba, kuma nagode Allah dabake kk halicci kanki ba abinda yayini kema shiyayi ki, baiyoki kyakyawa don yafi sonki dani ba, hakaza baiyini mummuna don baya sona ba, aa saidan ya jarraba imanin mu, kuma naimiki alkawarin saina nuna miki ba farar mace kyakyawace kad'ai keda farin jini a duniya ba, maza sai farar mace, ko a cikin kawaye ne farar mace tafi farin jini haka ma a littafai na soyaiya farar mace itace tauraruwa?kowa farar mace kyakyawa tomu bakaken rami za a haka a binne mu? Kokuwa haka zamu kare rayuwar mu cikin bakin jini?

To kisani Saudat, abjncin wani gubar wani, kuma inwani yakika da wuni wani da kwana zai soka, hakaza tsjnken daka raina shiyake tsole idanun ka, wlh wlh wlh dabanyj k'auren bakiba bakida gurin tsugunne a zuciyar yy Abba balle har ki zauna, Amma kowa inya samu guri dole ya shanya,


Amma karki manta Saudat bakida abjnda zanyi kyashi akansa harna munafinceki ko naci amanar ki, don har ila yau ina tausayjnki Saudat ke abar tausayi ce, memakon ki kama kanki kikoma ga Allah kiyi kokarin wanke zunuban ki amma shine kkzauna kina barnatar da lokatan ki a banza a wofi, rayuwar da batada tabbas ina amfanin cin Alwashi cikin ta?


barta haka Fauza, ta tsinkayi muryar mamy daga bayan ta, dakyau kinmin dai-dai Fauziyya  jeki abinki kibarta da halin ta,Allah yaimiki Albarka, Saudat wacce ke rikeda kunci tunda Fauxa tasoma mgn takasa furta kalma daya balle ta dakatar da ita, da mamy tashigo sai guiwarta takuma sagewa a ranta tana aiyana, wai meyasa duk sanda muke fada da Fauza sai Allah yakawo mamy ta kwaceta? Wannan yana bakanta ranta mutuka gaya, gaban tane yafad'i a yayinda maganganun mamy suka shiga dokar dodon kunnen ta.


Kinci Amana Saudat kina daya daga cikin mutane masu son Kansu da son zuciya, kin kasance butulu mai rama kairi da sharri, kinzama ciki mai manta naci yau bari na hkr gobe,kinzama mai manta alkairi kiyi yankan k'auna ga 'yar uwarki zanso ace bana raye abubuwan dasuke faruwa a yanzu suka kasance, wlh ko rantsuwa nayi bazan kaffara ba, keba Saudat dina bace, gangar jikin kice Saudat amma zuciyarki bataki bace, bazan tab'a yafewa wanda Yy silar lalata minke ba Saudat, duk halaiyar ki ta canja kinzama wata iriya bakyajin kunya, bakida kara balle kawai ci bakida tunani balle hangen nesa, bakida mutunci balle karamci, duk wata k'auna dake cikin ranki an zareta, anbarki data futuna? Meyasa haka Saudat? Laifin wa?


Ada kinkasance kamilalliya mai tsoron Allah, amma tashi daya kk juye kika koma fandararriya, bayan ita wacce akewa duban fadararriyar ta taka sawunki, ta amsa sunanki bayan kuma a zahiri fuskarki itace tata, a badini kuma fuskarta itace taki, wlh ki kiyayi duniya Saudat, Ki godewa Allah daya baki 'yar uwa irin Fauza, mai miki k'auna ta gsky guda d'aya jal,wacce duk duniya bamai miki ita, mai sadaukar wa a gareki Wanda duk duniya babu Wanda zai sadaukar miki da rayuwarsa guda daya jal bayan ta,

Wacce irin wuya ce Fauza bata shaba? Duk adalilin ki, ranar da Fauza ta tashi a jinyar hannun datasa Mu rauni domin ki ranar kika soma dasa mata bakin ciki wanda bb Wanda yatabai mata makamancin sa saike? Ke y'ar uwarta kawarta aminiyarta wacce take dubanki a kinfi kowa kusanci da ita yauke Saudat sabida ke butulu ce macuciya Mara tausayi Mara imani kekike jifan ta da muggan kalamai har kike mata gori akan abinda bake kika bawa kanki ba kyma babu abinda zai amfanar dake a gobe kiyama shi kyawun dakike takama dashi, illah halunki Wanda kika jefar shikadai zai amfanar dake, inkin ga dams kikoma ki tsinto inkina da rabo,


Haka za kuma da yardar ubangiji Fauziyya saita shayar dake mamaki, badaj kina murna kinyi mata yankan kauna kin rabata da farin cikin ta bayan kin san k'auna ce wacce ba wani mahaluki ne ke kullata ba sai Allah har kike tunanin kinyi nasarar rabata? Toki farka inma bacci kike, soyaiya itace kyalkyal banza don tana yankewa, amma k'auna kuwa karyarki badai mutum ba saidai Allah,

Kuma tun a duniya Allah saiya sakawa Fauza, kinci amanarta Saudat ta amince miki kin cutar da ita ta wahalta miki kin tankwabar da tagomashin ta, ta sadaukar da abubuwa da dama a gareki kinmata sakayyar sharri wlh inbaki nemi gafarar Fauza ba hakkin ta bazai barki ba, tunatar wace naimiki da kuma shawara nayi gangancin baki, kinsan bakada tabbas akan Wanda yakejin kansa daya yake da kowa cikin duniya, inkinga kuwa tsakaninka da danda baka Isa dashiba Wanda baya ganin kimarka aisaidai shawara babu umarni bare tursasawa,๐Ÿ‘[5/22, 10:10 PM] Mamanhaneep: [5/22, 9:37 PM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...82


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneep&Haneefa Usman


***Tunda yaya Abba yabar gidan a wannan ranar bai kuma dawowa ba har yau don ya tsinki kansa cikin wani irin yanayi na tausayin Fauza a gefe daya kuma soyaiyar Saudat na azalzalar sa, a satin har wata 'yar rama yayi don bayason yakuma duban fuskar Fauza batare da ya share hawayen dake kwaranya akan taba.


A b'angaren Abdallah kuwa? Yacika da dinbin farin ciki don samun cikar burin sa, amma b'angare daya cikin zuciyar sa yaki dena tunatar dashi,fuskar yayanta Abba a lokutan daya dinga nuna kwanjinsa akan Fauza, yarasa dalilin dayasa zuciyar sa take zargin kishine Abba yake nunawa akan Fauza karara ya fahjmcj ita kanta Fauzan tagano irin kishin dayake nunawa inhar ya gansu tare, tunanin hakanne ya sagar masa da guiwa har murnarsa take kokarin komawa ciki, dafe goshjn sa yayi tateda da cewa" ya Salam! Inhar ka auri Fauza to gangar jikin ta ka aura, take zuciyar ta ta rangado masa wannan batu don haka yakoma ya kwanta yasoma tunanin  yanayin dayake riskar Fauza ciki duk sanda yaje gurinta, tabbas Fauza bata farin ciki da zuwan sa, anyama kwa ba mamy takewa kara ba? Tofa Abdallah kana cikin rikici.


A zaune ak'asan kafet ta taddasu mamy na lallamin Fauza taci abinci don jiya kwana tayi da zazzabi da ciwon kai mai zafi, takasa cin komai shine dalilin dayasa mamy tasata agaba don taci tasha magani kotasa Mu salama duk da tasan maganin asibiti bashine maganin dazai warkar da Fauxa ba,


Cikin girmama ta tsugunna har k'asa tana gaida mamy, sanye take da doguwar rigar a tamfa yar Holland kalar ganye tayi matukar yi mata kyau, abjnka da farar mace, dik da babu kwalliya cikin fuskar ta amma tayi kyau fuskar tayi wasai, rataye take da jaka alamun unguwa zata, bayan sun gaisa ne tace" mamy dama zuwa nai na shaida miki zanje gida da yamma zandawo ba kwana zanyi ba, cikin mmki suka bita da kallo tareda cewa" gida kuma mexakiyi a gida Saudat? yaushe kika dawo har zaki koma? akwai mgnar da zanyiwa Baba ne shiyasa nake sauri don nasameshi a gida nafad'awa Abba yace driver ki yakai ni,

Cikin dasashiyar murya Fauza tace" bari na shirya muje tare hankalina bai kwanta da tafiyar kiba Saudat, Aa Fauza keda bakida lpy ki kwantar da hankalin ki ba abinda xai sameni insha Allahu, nandai sukai sallama tafuto tayi sallama dasu Amme tafuta suka d'au hanya itada drever mamy.


Cikin farin ciki ta isa gidan don taga Babur d'in Baban su a kwar gida da Alamun bai futaba, saida tagama zagaye b'angarorin dake cikin gidan ta gaidasu kan ta isa d'akin Anty larai Wanda anan tajiyo muryar Baban yana magana da sauran k'annanta,


Anan d'akin ta zauna suka kuma sake gaisawa, ganin akwai mgn a bakin Saudat yasa Anty larai ta janye yaran ta suka basu guri bayan an zubewa Saudat kayan Karin kumallo, tareda Baban suka karya suna d'an hira kadan kadan kan daga bisani tagyara zama tareda jan gyalen ta tace" Baba nadawo ne akan mgnr da mukai kwanaki har nace maka zanyi shawara,

[5/22, 10:10 PM] Mamanhaneep: yace"auto naji maganar Alhaji ko? tace eh Baba inya kuma aikowa ace masa na Amince, cikin gajeran mamaki yace" kin tabbata kin amince Saudatu? Karfa nangaba azo asamu matsala babban mutum kmr Alhaji babu mgnr wasa cikin lamuran sa, ko jiya damu ka sauko dg masallacin jumaa ya tari kawun Ku da mgnr cewa" yaji shuru har kawun naku yabashi hkr yace zamu kara tuntub'ar ki muji kokin gama shawarar?

Cikin Dan gajeran murmushi tace" wlh Baba da gsky nake na amince harga Allah, dama Fauziyya ce abokiyar shawara ta sjiyasa bamu dau wani lokaci ba, yace" tamshike nan Allah ya tabbatar da Alkairi Allah yaimiki Albarka, dama bakiji yanda nakejin nauyin mutumin nanba, ace babban mutum kamar sa yanai maka zarya ai babu dad'i, yanzu bari naje nasamu kawun Ku kan yafuta muyi maganar ko?

Eh Baba nima daman tafiya zanyi ba kwana zanyiba, nandai yaje gurin 'yan uwansa sukai mgnr da zasuyi, karfe uku Saudat tabar cikin grain,yayjn da a wannan lokacinne Baban ta yaturawa Alhaji cewa ya turo magaba tansa Saudatu ta amince da auran sa,


STORY CONTINUES BELOW

Sabida tsabar farin ciki Dan Aiken da kyautar kujerar makka yadawo gida in lokaci yayi,


Tuntuni yakamu da son Saudatu, nauyin matar sa da kunyar yayan sa yasashi kasa furta wannan nauyaiyan son daya jima yanai mata tun kallon farko dayai mata, don haka da wannan badakalar tafaru yaga wannan damace daya samu wajen baiyanar da abindake ransa gareta, a farko yacire tsammani amma a yau da wannan Al bishir yazo masa, saiya kara tabbatar da 'yar gidan mutumci ce yarinyar abinda yafi birgeshi kuma tunda yake zuwa gurin mahaifan ta kwandalar sa basu taba amsaba a Hanzarin sa nayi musu alkairi,

Sudai fatan su? Saudatu tafitar dasu kunyar wannan bawan Allah dabaiyi laakari da girman sa da isarsa da arzikin saba, yafuto fili yanemi iri dg garesu kasancewar su bayin Allah masu rufin asiri ba๐Ÿ‘


Gareku makaranta ko zaku canki wanene wannan Alhajin? ina jiran comments dinku, taku har kullum, momhaneep LOVE YOU ALL๐Ÿ˜˜

[5/23, 1:51 PM] Mamanhaneep: [5/23, 10:48 AM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...83


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneef&Haneefa Usman


***Tunda tadawo gida takama bakin ta tayi shuru ko Fauza bataiwa mgnr dady Islam ba, iyaka dai tana yawan ganin ta tana waya a nutse hakanne y tabbatar mata da bada yaya Abba take wayar ba, hardai a yau takasa hkr ta tambaye ta da cewa" wai dawa kike waya Saudat? Na fahjmci kmr ba yaya Abba bane ba, to don kiji kishi nake taya yaya na, takara sa da sigar tsokana,


Murmushi tayi kan tace" ba yaya Abba bane inyazo yau kya ganshi, hmm tasauke ajiyar zuciya kan tace" tome hakan ke nufi kinsan dai babu kyau yaudara ko? ga yaya Abba gakuma wani kinjajubo kinsan dai dole kirabu da wannan, toki sallame shi tunkan yace kin yaudare shi, cikin zolaya tace" to in yaya Abba na ajye fa? Kai tsaye tabata amsa, shima kin yaudareshi, ke mubar wannan mgnr tukun Albishirin ki? tace" goro, anjima kawu da Baba zasuzo nan gidan nasan baki saniba ko? Cikin dan mamaki tace" mezai kawo su kuma? To nimadai bansani ba, jiya Baba ke Fadamin kuma mamy tasani,


Tom Allah yasa muji Alkairi, kodai mamy xaibawa hkr takoma auren sa? Saudat batasan sanda takwashe da dariya ba,  tace" maybe hakanne. Uhm kyaji dashi ina zargin akwai abinda kika boyemin, inyazo kyaji koma mene,


Washe gari,


Cikin fushi tashiga dakin har kofar tabada sautin bom. A tsorace ta kai duban ta kan Fauza wacce tashigo yanzu tareda cewa" lfy? Cikin b'acin rai tashiga magana da cewa" meyasa zaki haka Saudat? Meyasa zaki cutar da kanki cin amana kuma kika koma? Baban Islam zaki aura Saudat? Kin yaudari yaya Abba zakici amanar Islam kin manta taimakon datai miki? Zakimata sakayya da wannan? A tunanin ki wannan dai dai ne? Saudat mezakiyi da Baban Islam kinsan dai yaimiki tsufa da kuruciyar ki kikare da auren Baban kawar ki? Gsky kisake tunani Sam baki dace dashi ba, ni abinda nake jiye miki karkije 'yayan sa su hanaki zama dashi su futune ki, dazaki bi shawarata dakin hkr Saudat gaggawar mekike? Saudat komai fa nufin Allah ne,


Kai Fauza nihar kinbani tsoro wlh, zonan zauna kiji yanda abin yafaru karkiga laifina, ta janyo Fauza wacce tahade rai tai kicin kicin tazaunar daita a kusa da ita, takamo tattausan hannun ta tareda cewa" kinaji na?banida wata mufuta wacce tawuce ta auren sa, ke kanki shaida ce Baban Islam mutumin kirki ne duk Wanda ya kwana cikin garin Mu yasan da hakan, bai dubi illar danaiwa kaina ba yafuto yace yaji yagani zai aure ni baiduba raunin Mu ba a matsayin sa mai arziki yafuto yanuna mana kauna Baba har kunyar sa ya dingaji mutum kmr sa yanai masa zarya akan abinda yafi karfin yasamu mafiyin saba,  to Fauza inbai kini ba nima bai kamata nakishi ba, kodon nafutar da Baba kunya zan iyayin hakan balle ma nima naji ina sonsa zan iya rayuwa dashi kodasu Islam zasu yanki naman jikina, yaya Abba kuma ki ajye mgnr sa a gefe, kyawuna yaja hankalin yaya Abba bawai asalin so guda daya Wanda Allah ke dasawa bayin saba, wannan damar Fauza kekadai kk sameta a gurin sa, kuma inban da abinki Fauza Auren baban Islam shine rufin asiri na, bazai min gori ba tunda 'yayan sa susuka batani, nima kuma bazan masa ba, batun tsufa kuma nibaimin tsufa ba tamkar yaro Dan shekaru 30 nake duban sa, dariya Fauza tayi tace" tamshikenan Allah y tabbatar da alkairi, yauwa ki kwantar da hankalin ki Fauza na more miji, cikin dariya takai mata dukan wasa tareda cewa" kai Saudat bakida kunya ko? Dariyar suka kumayi, mamy dake tsaye gefen window itama murmushin tayi tacika da farin ciki tana hamdala cikin ranta da Allah ya daidaita tsakanin yan biyun ta,

[5/23, 11:15 AM] Mamanhaneep: ***           ****          ***


Yanda suka tsinci maganar auren Saudat a bakin kawu haka ma yaya Abba ya tsinci mgnr a cikin gidan, karshen mako ya ziyar ci garin don ya gaida iyayennasu saiya tarda mgnr auren wai a ranar ma ake shirin kawo sadakin ta tareda sauran kayan aure na Al ada,


Mgnr auren tayi masa nauyi a lokacin da kawu kemasa bayani, dg bisani kuma saiyaci wani irin sanyi yana ratsa sassan zuciyar sa har munar takasa boyuwa tafuto fili, aikuwa yazage aka amsha kayan taredashi kasancewar mazane suka kawo ba mata ba, sun tsayar da daurin aure wata mai kamawa a yanzu kwana ashirin da bakwai yarage,


Kwanan Abba daya agarin yadawo bakin aikin sa, haka nan yaji yanason zuwa gidan gefe daya kuma yanajin kunyar mamy sakamakon k'aurar dayayi musu don rabon sa da gidan ya kwana biyu, in ancire mamy har Amme saida takira wayar sa tajiko lfy kwana biyu suka jishi shuru?, nandai y kare kansa da cewa aikine yayi masa yawa amma insha Allahu yananan tafe cikin satin zaishigo ya gaida su,


A yayinda ya isa gidan, Saudat ya hango a set room tareda angon nata suna hira cikin kwanciyar hankali, don haka dayayi farkin ya isa ciki suka gaisa da Baban Islam kasancewar sunsan juna a sanda suka shiga gidan shida Fauza, nandai yabaro su yashiga gidan ya tarar da tarin mita wajen mutanen gidan kan ya zauna yakare kansa da karyar rashjn lfy, Amme hartana tausayin sa da cewa" Allah sarki har kuwa kad'an rame,


Anan falon Saudat tashigo ta taddasu ta zauna suna hirar da ita wacce rabin hirar ta bikin ce, zuwa can, Abba yai musu sallama tareda yimusu alkawarin zaidawo don basuso yatafi ba don Abba akwai iya hira daban dariya, Saudat ce tayo masa rakiya har bakin motar sa, cikin jimami tace" kayi hakuri yaya Abba kaga yanda ubangiji ya juya lamuran ko? Cikin zolaya ya harare ta kan yace" kanwa ta kenan bkomai ai komai sai Allah yanufa, nidai kitaya ni ban baki naga Fauziyya fushi take dani ko gaisuwa a ciki ta gaidani, murmushi tayi kan tace" karka damu indai Fauza ce batada wuyar sauka kasani.๐Ÿ‘

[5/23, 1:50 PM] Mamanhaneep: ASSALAMU ALAIKUM

MAKARANTA NA NAGA COMMENTS DINKU KUMA NAGODE, INAI MUKU FATAN ALKAIRI,ALLAH YASA MUDACE BAKI D'AYA AMEEN.ANA ZATAN WUTA A MAKERA...81


©NWA


Mamanhaneep&Haneefa Usman


***Fauza dake gefe ta zubawa mamy ido don ganin yanda tai kokarin nunawa Saudat kuskuraen ta, tace" Saudat Allah yagani duk wani taimako daya rataya a wuya na nayimiki shi banida sauran abinda zanyi miki a yanzu illah na tunatar dake kuma inason kema ki tunatar da wasu donnaga har yanzu kanki narawa baki tsaya kin tantance girman laifin dakika aikata ba balle kiyi adduar Neman tsari da makaman cinsa, to kisani inhar baki tuba kin nemi gafarar Allah ba to kin kashe mijine baki sare kansa ba kuma ako wani lokaci shaidan zai iyayin nasara akanki don kina tare dashi, to bari kiji kibede kunnuwanki kibani hankalin ki.


Luwadi da Madigo yanzu awannan zamanin sun zama kamar ruwan dare atsakanin Matasa maza da mata. Sun biye ma sha'awa irin ta shaitanci wacce ta mamaye zukatansu, Sun afka cikin mafi Qazantar laifin da aka taba aikatawa adoron Qasa.

Hakika aduk cikin nau'o'in zina da danginta, Luwadi shine mafi Muni, kuma mafi Qazanta. Kamar yadda Allah yake gaya mana acikin Alqur'ani:


"KA TUNA ANNABI LUUT LOKACIN DA YACE MA MUTANENSA "ME YASA KUKE YIN IRIN WANNAN ALFASHAR? BABU WANI WANDA YA RIGAKU AIKATAWA DAGA CIKIN TALIKAI (HALITTU BAKI DAYA)".+


"KU KUNA ZUWA MA MAZAJE TA FANNIN SHA'AWARKU MAIMAKON MATAYE, BARI DAI KU MUTANE NE MASU MUTUKAR 'BARNA".


(A'araf ayah ta 80).


Kuma saboda munin laifinsu shi yasa Allah yayi musu azabar da bai taba yima kowa kafinsu ba. Allah ya aiko da Mala'iku suka ciccibe garin zuwa sama, suka watsa narkon azaba sannan suka Kifar dasu.

Acikin Suratu Huud (as) Allah yace:


"YAYIN DA AL'AMARINMU YAZO, SAI MUKA SANYA SAMAN BIRNIN YA ZAMA KASANTA, (WATO MUKA KIFAR DA BIRNIN) SANNAN MUKAYI MUSU RUWAN DUWATSUN WUTA NA SIJJEEL".


Kamar yadda Allah (SWT) yake cewa :


"SAI MUKAYI RUWAN (DUWATSUN AZABA) AKANSU, LALLAI RUWAN DUWATSUN AZABAR NAN TA WADANDA AKAYI MUSU GARGADI YAYI MUNI KWARAI"


(suratun Namli ayah ta 58).


Saboda tsananin bala'in da yake cikin wannan aika-aikar, Manzon Allah (S.A.W) yace:


"MAFI GIRMAN ABINDA NAKE TSORACE MA AL'UMMAH-TA, SHINE IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUUT".


(Tirmizy ya ruwaitoshi acikin Sunanu, hadisi na 1,457. Ibnu Maajah hadisi na 2,563).


Awani Hadisin kuma, Manzon Allah (S.A.W) yana cewa :

"TSINANNE NE DUK WANDA YAYI JIMA'I DA DABBA, KUMA TSINANNE NE DUK WANDA YA AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUUT".


(Imam Ahmad ne ya ruwaitoshi acikin Musnad, Hadisi na 1878).


Acikin wani hadisin kuma, Manzon Allah (S.A.W) ya fadi irin hukuncin da Shari'ar Musulunci ta tanadar ma masu Luwadi. yana cewa:


"DUK WANDA KUKA TARAR DASHI YANA AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUUT, TO KU KASHE MAI AIKATAWAR DA KUMA WANDA AKE AIKATA MASA"


(aduba Sunanut Tirmizy hadisi na 1,456. da kuma Sunanu Abee Dawud, hadisi na 4,462. Da kuma Sunanu Ibn Maajah, hadisi na 2,561).


LUWADI da Madigo Mummunar Annoba ce wacce ta kauce ma hanyar da Allah ya halicci dukkan halittunsa akai. Don koda dabbobi ba zaka tarar suna yin irin wannan abun ba.

Shi yasa Annabi Luut (as) yace ma mutanensa


"KUNZO DA ALFASHA WACCE BABU WANI DAGA CIKIN HALITTU (MUTANE KO ALJANU KO DABBOBI) WANDA YA RIGAKU AIKATAWA".


Imam Ibnul Qayyim Aljawziyyah yana cewa : "Dukkansu guda biyun (wato Zina da luwadi ko Madigo) suna kunshe da mummunar ALFASHAR da ta kauce ma Fitrar Allah.

Kuma Luwadi yana Qunshe da bala'o'in da ba zasu Qidayu ba. Kuma Duk wanda akayi Luwadi dashi, zai gwammaci gara ya mutu da ace an aikata wannan fasadi  dashi. Domin idan ya riga akayi dashi, to zuciyarsa zata riga tayi lalacewar da babu sauran tsammanin daidaituwarsa ko kuma dawowarsa kan hanya.

Kuma ba zai sake jin wata sauran kunya ba, ko awajen Allah, ko awajen halittunsa.

Kuma ruwan Maniyyin da Mai Luwadin ya zuba masa yana zama a Cikin wanda aka zubawa baya narkewa har ya zama tsutsotsi saboda bashi da Mahaifa, aduk lokacin da suka bukaci Abinci inbabu wannan Maniyyi sai suna cin naman jikin Dan Adam, ya zama kamar guba ne ajikinsa da kuma ruhinsa. (Shi yasa yana da wuya su iya yin cikakkiyar tuba wacce Allah yake so. Kuma duk lokacin da abun ya motsa musu sai sunje sunyi, Ko kuma anyi dasu).


Ibnul Qayyim Aljawziyyah yaci gaba da cewa : "Malamai sunyi sabani akan cewa:


SHIN 'YAN LUWADI ZASU SHIGA ALJANNAH, KO KUMA HAR ABADA BA ZASU SHIGA BA?"


Na taba jin Shaikhul Islami Ibnu Taimiyyah yana bayanin ra'ayin Malamai akan haka"


(Aduba Aljawabul Kaafiy, Shafi na 115).


Shi yasa Shari'ar Musulunci tace kashewar ita ce mafi alkhairi gareshi fiye da rayuwa cikin Qaskanci da Wulakanci da kuma rashin Imani.

Ka tuba zuwa ga Allah, ka sani cewa rahamar Allah tana da yalwa, kuma ALLAH yana son bayinsa masu tuba.

"KACE MUSU YA KU BAYINA WADANDA SUKA YIMA KANSU 'BARNA!! KAR KU FIDDA TSAMMANI DAGA RAHAMAR ALLAH. HAKIKA ALLAH YANA GAFARTA DUKKAN ZUNUBAI BAKI DAYA, SHI SHINE MAI GAFARA KUMA MAI JIN-QAI"


(Suratuz Zumar ayah ta 53).


Ka nisanci Miyagun abokai. Manzon Allah (S.A.W) yana cewa :


"MUTUM YANA BIN ADDININ ABOKINSA NE. DON HAKA KOWANENKU YA KULA DA WANDA ZAI YI ABOTA"


(Sunanut Tirmizy, Hadisi nan 2,378).


Ka rika zama cikin mutanen Kirki, kuma ka kula da Sallolinka na farillah da nafilfili. ka yawaita zikirin Allah ako yaushe.

Ka nisanci kalle kallen haramun azahiri ko acikin Wayar salularka. Ka sani cewa Allah ya baka amanar dukkan gabobin jikinka ne. Kuma akwai ranar da zai tambayeka wannanr Amana.


Inai miki fatan Alkairi don kofar tuba abud'e take kituba ki tsarkake zuciyarki don gudun komawar ki cikin ruwa, kisani bantab'a mai miki bakin ciki ko hassada ba nakasan ce cikin tausaya miki don koda wannan nabar ki ya isheki, inai miki murnar samun gwarzon namiji kamar Abba, shiya dace da rayuwar ki don zai kula da Al amarinki bazai bari ki kasance cikin tab'abbu ba,


Bazan iya musalta iya rudanin da Saudat take ciki ba, illah kukan data rushe tareda dora hannun ta aka tazabga ihu tace" nashiga uku meyasa na manta da wannan tarin musibar dake taredani? Mamy na rokeki ki gurfanar dani a yanken hukuncin da Allah y zartar wa masu hali irinnawa, bana bukatar cigaba da rayuwa don Alk'awarin Allah baya karyewa, kisa akasheni nahuta mamy,


Fauza kiyi hakuri duk abinda na akaita a gareki banyishi asanda ina Saudat ba, nayishi ne ina cikin tsiniwar Allah karki manta rayuwa ta bazata tabayin kunya ba bazatai albarka ba kuma bazata dai dai ta yanda kikeso ba, bakin alkalami yariga yabushe,


Abba kuwa sam baidace dani ba, kamilin mutum nutsatse Allah bazai aura masa tanbadaddiya kamar niba, kaunar dazaku nunamin a yanzu kukai ni a yankan hukuncin kisa shine mafuta a gareni, kutuna Allah da kansa yafada rayuwar irinmu batada amfani gwara mutuwar Mu,


Cikin kuka Fauza ta toshe bakin ta, tace" Aa Saudat baa shiga tsakanin Ubangiji da bawan sa, inkika koma gareshi zaiyafe miki don shi bai karbar tubane,


Yaya Abba kuma shiyafi dacewa dake don irin ki suna bukatar gwarzon namiji, da sauri tazare jikin ta tabar dakin, tana isa nasu dakin tadau wayar ta takira Abdallah yana dagawa tace" Abdallah na Amince da mgnr auren ka katura gidan Mu neman aure na, batare da tajira cewar saba ta katse kiran ta ajye wayar, a hankali ta furta" shikenan shikenan nakasance mai zalintar kaina donna faranta ran 'yar uwata,

tabaya taji an rugumota, juyawa tayi takuma shiga cikin jikin ta batada mai rarrashjn ta sai mamyn ta Mai tausayin ta.๐Ÿ‘[5/24, 6:04 PM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...84


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneef&Haneefa Usman


***shirin bikin Saudat ya kankama, don komai saidai in baa samasa rana ba, A b'angaren su Islam kuwa Sam basuyi farin ciki da auren Saudat da Baban su zaiyi ba, haka nan kuma basuyi bakin ciki ba, gasunan nedai kawai don gani suke inhar dad dinsu ya auri Saudat to shikenan kashin su yabushe don Islam tayiwa Saudat farin sani kuma tasan ba kanwar lasa bace, tunda asirin su yatonu dad dinsu yadena sakar musu kamar da, babu inda suke zuwa ga 'yan uwan sa dayaje ya d'auko ya ajye a gidan yaware musu b'angare daban a cikin gidan, su kuma yabar su dawata k'anwar mahaifin sa mafada ciya ta saka ido a Kansu komai suke idon ta na kansu, waya da sauran na urorin zamani duk ya kwace su, wannan dalilinne yasa jikin su yayi sanyi tundaga yanzu don suna ganin kmr dady yadena sonsu ne.


A b'angaren Amarya Saudat kuwa, shirin ta take hankalin ta kwance, a ranta kywa catake gwarama nayi auren nahuta, shiri suke bana wasa ba don angonna ta yasakar mata kud'i abinda takeso shi zaayi, a b'angaren mamy kuwa babu wani shiri dataiwa Saudat don 'yan uwanta sunmata kara, su sukaiwa Saudat duk wani gyara da shiri da amarya take bukata, a gsky sunyi zuminci.


A bangaren Fauza kuwa?duk wani shiri da ita akeyinsa don sune kawayen amaryar bayan itada su amal batada wasu k'awaye a nan kano sai kuwa a garin su, a gefe daya kuma, tunanin Abdallah yakan hanata sukuni don tunda sukai mgnr zai tura magabatan sa gidan su har yau bai k'ara tada mgnr ba, gidan ma yadai na zuwan sa tanajin amme na cigiyar sa,+


A b'angaren yaya Abba kuwa? Akwqnakin sanm baisamu zama ba, amma yana waya d amaryar don jin meke akwai, acan gidan suma yayi namijin kokari don duk wani Abu da uba yakewa 'yarsa yaya Abba yadauke wa su Baba shi harta abincin daza a bukata na bikin duk yadau nauyin sa,

A gefe guda kuma Baban Islam yasa akasoma gyaran gidan surukan nasa, sudai kawai sai ganin ma'aikata sukai suka cika da mamaki bayanda suka iya haka nan suka bada gurin aka gyare musu gidan Wanda baidau wani lokaci mai tsayi ba a sati biyu aka gyare duka bangarorin dake gidan, shima Abba saj zuwa yayi ya tarda gyaran,


Aikuwa Baban Islam yayi rawar gani, hakan yakara masa daraja da kima cikin idon surukannasa, yayi hakanne donya faranta ransu donya rasa ta wacce hanya zai saka musu don sunki yarda kwandalarsa tashiga hannun su, 'yadai don Allah suka bashi badon isarsa ko arxikin saba.


Tsakanin Abba da Fauza kuwa babu wani shiri illah kallon kallo dasuke wa juna, daga karshe ma yasakar mata dariyar mugunta, itadai tanajin haushin dariyar dayake mata don takasa fassara wacce iriyar dariya ce haka? Harta soma tsargin kodai Yy Abba ne ya korar mata Abdallah oho!.


Biki bidiri bired'e, Alhamdilillahi ayaune akayi kamun amarya Saudat wacce tafuto cikin shiga ta alfarma da kaganta kaga matar manya, tayi matuk'ar yin wani shu'umin kyau Wanda bazan iya musalta kyawun datai ba,


Haka ma k'awayen amarya sunyi matuk'ar kyau cikin ankon su Wanda yayi macin dasu abindai sai Wanda yagani, hakanan aka kama amarya akatashi dg taron lfy,


Washegari haka aka tashi cikin hidima da yamma sukai walima wacce suka kira manyan malamai mata sukai nasiha ga amarya a daren ranar ne sukai mothers day mata zallah wanda mamy ta shirya tareda goyan bayan 'yan uwanta, sunyi matukar kyau mamy ma cikin 'yan uwanta da kawayenta saika rantse bikin kanwarta ake bawai na 'yarta ta cikin taba,Fauza kuwa sainace muku tafi kowa na gurin yin kyau don wani irin sirrin kyaune yafuto dg jikin ta wanda ita kanta amaryar saida tafurta mata cewa" Fauza ke kyakyawace pls daga yau ki dinga make up,


Ayau ma ran dinner Fauza tayi wani irin futunannen kyau duk inda tayi walwali take idon mazan gurun akanta Yaya Abba kuwa daya hango tauraruwar tasa, baisan sanda yashiga hamdala cikin ransa ba, shikadai yasan abinda yagano a tareda ita, dg karshema hakanan yakamo hannun ta yazura a mota ya kaita gida don tsananin kishi don ya lura kafatanin mazan gurin kallon ta suke. Abdallah kuwa tuni ya watsar da fushin yashiga shige mata, shinefa Abba ya yanke wannan hukuncin, tun amotar tashiga rera kuka don haushi duk ta bata kwalliyar ta, a kofar gidan yayi farking bai shiga ciki ba yajuyo ya dubeta yace" ga kayan kinan a baya kibude ki dauka kisasu gobe inzaku tafi gida, karna ganki da wasu kayan inba suba, cikin fushi tace" inkuma bansasun bafa? Zan shayar dake mamaki, cikin kuka tace" to bazan saba d'in kuma wlh Allah saiya sakamin duk Wanda ya zalinceni, aidama Allah mai sakayya ne kuma zai sakawa Wanda aka zalin ta, hakan danayi shine dai-dai don Allah ne kadai yasan iya mazan dakika zalinta q gurin dinner nan ciki kuwa har dani,ni ban zalinci kowa ba saini da aka zalinta, waye ya zalince ki yanzu? Shuru tai tareda kauda kanta gefe. Ganin batada niyyar d'aukan kayan yasa shi zira hannu ya dauko mata yabata, nandai ta dauka tafuta cikeda fushi ta bugo masa murfin kofar jikake gam, tai cikin gidan taje tadasawa mamy kuka, kasancewar basuje dinner ba ta ango da amarya ne,

[5/24, 6:23 PM] Mamanhaneep: Nandai mamy tashiga bata hkr, cikin murmushi mamy tace"kiyi hkr Abba yafiya kishi abinda daga yau shikenan basake wani fartin zaayi ba? A hankali tadago tadubi mamy tareda cewa" kishi mamy? Jijiga kai tayi tareda daga mata gira tace" kwarai kuwa, kidube kifa Fauza, inbaiyi kishin kiba tome zaiyi? Lailai Abba ya hango baiwar dake tare dake Fauza sainan gaba zaki tabbatar da hakan, mikewa tayi tsaye tashiga karewa kanta kallo takuma nanata Kalmar kishi kishi!, da suka hada ido da mamy kuma saj kunya takama ta, nandai ta tattaro kasan doguwar rigar material din dake jikin ta Wanda dinkin yayi mata das das, takwasa da gudu tai waje ko takalminta bata dauka ba,


A washegari anata shirin tafiya garin su Saudat Wanda zaa daura auren acan ayi yinin biki akai amarya gidan ta. Banda Fauza wacce tunda tafuto dg wanka tazauna ta zuba tagumi hakanan taji gabanta na faduwa duk jikin ta yayi sanyi tanaji a jikin ta akwai abinda zai faru da ita, nandai kowa yashirya wasu motocin ma har sunyi gaba abinsu, dakyar ta iya shiryawa cikin shaddarta ta daurin aure nanfa mamy tasata a dole tacire tasaka wacce Yy Abba yabata a daren jiya, wata dakakkiyar shaddace mai kyau da tsada surfanin jikinta shikansa abin kallo ne, dinkine yaja raayinta taji tanason saka kayan don shaddar tayi mata kyau, nandai tasaka tadauko takalmi da jaka kalar farare tas tas, duk a hade suke a kayan da Abba yabata, ga wanj  hadaddan turare mai sanyaiyan kamshi duk aciki, nandai ta shirya a gurguje tafuto wani karin takaici kuma zatabi ayarin amare Yy Abba ya kafe tasa motar yakira ta, tanaji tana kallo yatura ta gaban motar ya rufe, tana kallon su Amal naimata dariya, ta kumbura tamkar ta fashe[5/25, 8:43 AM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...85


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneef&Haneefa Usman


***Tunda suka d'au hanya babu wanda yayi magana sai saukar numfashin su dake tashi, Fuskar ta rufe take cikin farin mayafin dake sanye a jikin ta, tamkar dai amaryar gsky, sautin kukan tane yafara dukon dodon kunnan sa yajuyo ya dubeta tareda cewa" hmmm kuka nagaba yarinya gwarama kiyi shuru inmai dalilin yazo kyayi,  waima menaimiki dazaki sani agaba kinaimin kuka Fauza? Cikin bacin rai tace" katakura min yaya, bansan me natsare maka ba, ina zargin ma kaika korarmin Abdallah yadena zuwa gurina, jiya dakaga zamu shirya a gurin dinner shine karaboni d gurin gaba d'aya, kuma  hakan dakai bai ishekaba yanzuma kahanani bin ayarin amarya kasakoni motarka harda riken hannu kawai donka kuntatamin,

Ajiyar zuciya ya sauke hmmm kan yace" indai wannan ce kuntatawa tonai miki d'in kuma kina iya ramawa, batun Abdallah kuma nibanda lokacin wannan saunan sanin dayai bakin rijiya bagurin wason yaro bane shiyasa ya janye jikin sa, hannunki kuma ko yanzu nagadamar rikewa saina rike saidai in ki mutu,

Nanfa yakuma tunzuro ta taciga ba da rera kukan ta, saida suka shiga cikin garin yayi farkin a gefen hanya yajuyo ya dubeta yace" kukan nan yaisa haka kigoge fuskarki kiwa mutane shuru don bazaki shiga cikin gida a haka ba, banza tai dashi kuma bata fasa kukan ba, cikin dakakkiyar muryarsa yace" ko bakiji bane? Nidai karabu dani ai abin kukan akaimin shiyasa nayi, inban yi shurun ba dukana zakayi? bazan dakeki ba amma abinda zanmiki saikin gwammace na dake kinma, tadan tsorata da furucin sa don haka tagoge hawayen ta dauko powder cikin Jakarta tashafa tareda lipstick,+

Nandai yaja motar suka k'arasa gidan, duk sauran motocin sun rigasu zuwa sabida tsabar shininikin days ldingayi a hanya, Amal ce tafara tareta da cewa" su Fauza sai yanzu? Tace eh wlh, tome ya dadar daku haka? Bansani ba, kunbiya wani gurinne? eh, tabata amsa tayi ciki, nanfa takwashe mata da dariya.


Nandai akaita shirin d'aurin auren, karfe 10 am k'ofar gidan damk'am yake da jama'a anata hidima da mutane, wanda bakine na b'angarori uku, bakin ango, dakuma bakin Alh nasir  sai kuma na amaryar, nandai aka shiga d'aurin auren Saudat da Alh Ibrahim mahaifin Islam,


A can cikin gidan kuma sumadai hidimar suke, Fauza da tafuto dg kicin yanzu hannun ta d'auke da jug cike da kunun gyad'a wanda ta damawa mamy zata kaimata, karaf tajiyo sanarwa dg bakin marok'a, ALHAMDILILLAHI ANKAMMALA D'AURIN AUREN UMARUL FARUKU DA FAUZIYYA AKAN SADAKI NAIRA DUBU HAMSIN LAKADAN DA AJALAN BA,


Cak tatsaya hannun ta rikeda jug din tayi sararo tabi jamaar dake tsakar gidan da kallo suma itan suke kallo, nanfa tasaki jug d'in takwasa da gudu tayi d'akin Baba wanda su mamy ke ciki, nanfa jamaar suka d'au sowa da gud'a don a zahiri Fauziyya tabasu dariya,

Jikin Mamy tafad'a tasaki wani kuka mamy dai bayan ta tadafa batare da habata ba, don tasan in Fauza batai kukan farin ciki ba to bazai na bakin ciki ba, bata k'ara tabbatar da abinda tajiba saida aka shigo da Saudat tareda damk'a musu sadakin su a tafin hannun su, itakam jitake tamkar mafarkin data sabayine b gsky bane,


Nandai jamaar suka soma watsewa suka nufi gurin walimar d'aurin auren da Alh bashir ya shirya, angoma yaja tasa tawagar suka nufi tasu walimar,

Yinin ranar anata hidimar yinin biki banda Fauza wacce take kwance wani a zababban zazzab'i yarufe ta hakoran ta har kad'uwa suke,

[5/25, 10:25 AM] Mamanhaneep: Amarya suna can b'angaren inna suna nasu budirin itakam tana d'akin Anty larai a kwance, k'arfe biyar na yamma 'yan d'aukar amarya sukazo da motocin su na alfarma nandai aka had'a amarya aka damk'ata amana a hannun yan uwan mijin ta, tayi sallama da kowa ciki harda Fauza wacce taji tamkar karsu rabu su zauna sucigaba da rayuwarsu tada mai dad'i, haka nan ta lallab'a taiwa Saudat rakiya har cikin gidan ta tareda alhinin rabuwa da ita,

Misalin k'arfe takwas nadare suka baro gidan amaryar kasancewar angon dai ba yaro bane balle su Amal iyayen rawar kai su zauna zaman jiran siyan baki, komadai menene yasayi abinsa,


Washegari litinin suka tarkato yanasu yanasu sukadawo gida, bayan y'anmatan ciki sunkaiwa Saudat ziyara tareda yimata wasu gyare gyaren, Fauza taso tabusu gidan Saudat yaya Abba yahana zuwan harta shirya yayo mata waya karta kuskura tabisu hakann ta hkr tana kallo suka tafi abinsu, kanwar mamy Anty halima ita taita bata hkr dake a gaban ta akai komai, dasu mamy zasu tafima waya yayo mata karta bisu ai ita tazo gida kenan, hakann taci kukan ta takoshi tana kallo suka tafi sukabarta duk iskanci da Amal take mata saida tabata tausayi.


Shima Yy Abba a ranar da daddare yai musu sallama yakoma kanon sabida aikin sa, amma sabida tsabar mugun ta irin tasa saida ta kwana uku cir sannan yazo d'aukar ta, dukda  gidan sune mahaifarta tushenta taji ddn zuwansa don dama dukta takura tagaji da zaman.


Nandai sukai sallama dasu inna jitake tamkar ta maidata ciki don kauna, nandai sukabaro su cikin kewa, wani dadine ya ziyarci zuciyar Fauza dataga yanufi gidan Saudat daita, a sanda suka isa mai gidan yanann don haka suka zauna a settrom tareda Abba, itakuma Fauza suka k'ule a d'aka itada 'yar uwarta tuni hira ta barke tsakaninsu cikeda murnar ganin juna, Fauza saitaga Saudat harta soma canjawa tak'ara d'ashewa cikin kwana uku kacal gawani annuri dake futa daga cikin fuskar ta, tuni 'yar uwarta ta birgeta har taji tana muradin tarewar ta anata gidan tareda gwarzon mijin nata, suna tsaka da hira ne k'anwar Islam tashigo takira ta wai zasu tafi, anan take tambayarta Islam, nandai suka futa tarakata har gurin su Islam din dayan uwan mijin ta suka gaisa cikin mutunta juna,


Tare sukadawo da Islam wacce tai mata rakiya, sunata hirar su dake Islam akwai iya hira, Saudat kuwa tacika da murna tarasa mema zata baiwa Fauza, ta rakito mata wannan ta dauko wannan har saida ta dakatar da ita hakanan, har bakin mota Islam ta rakota tariko mata kayan da Saudat tahad'o mata, nandai suka gaisa da Yy Abba sukai sallama da angon Saudat har yana zolayarta itadai duk kunya ta isheta hakanan sukabar gidan  cikeda kewar 'yar uwar ta.


A maimakon yakaita gida da suka shigo cikin gari saitaga ya karkata motar sa yanufi wata unguwa daban, bai zame ko inaba sai unguwar rijiyar zaki tafiya kawai suke batareda tace k'alaba, nandai taga sundoshi wani gida mai get kalarsa ruwan toka, nandai yafuto yasa key yabud'e get din yashiga da motar sa, matsakaicin gidan ya birgeta, don gida matsakaici wanda yahadu matuka kai daga ganin ginin gidan kasan maginan sa masu fasaha ne, falone biyu kowanne da dakin bacci biyu da kicin da bandaki, gidan shirye yake tsafar sai k'amshi dake tashi,

Kayan dake cikin gidan irinna Saudat ne sak kalace ta banbance hatta kayan dake kicin d'in iri dayane dana Saudat kayan su set biyu da Wanda Abba Yy masu dana gurin Alh bashir kakan su,


A gsky gidan Fauza Yy matukar kyau ankawata gidan da kayan more rayuwa yanda gidan yake dai dai amarya HK kayan ciki suke babu wani tarukece ko ina tsaf tsaf yake,


Akan hadaddun kujurun dasukai wa falon kawanya ta zauna tadubeshi tace" yaya nifa nagaji muje kakaini gida nahuta,


Gida kuma wanne? Aibaki da gida sai wannan, eh nasani ai ba kawoni kayi Nagani ba? Tonagani gida Yy kyau amarya kawai gida yake jira yanzu abinda yafi sauki kazo ka kaini gida, furucin ta yabashj dariya don haka yace" koh? Zakiyi bayani da manyan baki yarinya, tashiyai ya shige dayan falon Wanda shine mallakin sa, binsa tayi da kallo zuciyarta fal tsiro tace" kut sabon salo.


๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚sabon salonn gsky,


Kubiyomu muna k'ara baku hkr book din gab yake da k'arewa๐Ÿ‘[5/26, 9:50 AM] Mamanhaneep: [5/26, 6:49 AM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ARA...86


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneef&Haneefa Usman


***Shuru shuru tana zaune tana jiran gawan shanu,can dai tamik'e tanufi falon dataga ya shiga, abin mamaki baccin sa yaketa shara har yayi nisa cikin baccin sa hankali kwance, tadubi agogon dake bango k'arfe d'aya na rana don haka tanufi band'akin dake falon ta d'auro alwala tazo tayi sallah,


Tanann zaune kan sallayar baccin ya sureta itama karfe biyu Abba ya farka Yy alwala yanufi masallacin dake kusa dasu, harya dawo bata tashi daga baccin ba, don haka yasake futa yayo musu take away a wani gidan abici dake bakin titi,


Saida yayi sallar laasar sannan yatada ta don ganin baccin nata yayi nisa, sunan ta kawai yakira tamik'e zaune tareda gyara mayafinta mayafin ta d'ankwalin ta ma saida ta nemoshi, nandai tayi alwala tayi sallah yabata abincin daya siyo taci kad'an  don jitai duk ya isheta hankalin ta duk Yy gida,

[5/26, 9:49 AM] Mamanhaneep: Juyowa ta dubeshi tareda cewa" Yy Abba laasar tana neman wuce wa yakama ta mutafi haka, in duk hankali na Yy gida sonake naga mamy, zakije gida amma ba yanzu ba kuma karki takuramin tunda ba cinyeki zanyiba,  to sai yaushe kenan? Banza Yy daita yashiga danna wayar sa,


Hankalin ta bai tashiba saida taji kiran sallar mgriba take tsoro ya tsirga mata gaban ta yashiga fad'uwa, bayan yadawo dg masallaci ne yatar data tana kursheken kuka tahad'a kai da guiwa tana fama,+


Nan gefenta ya zauna ya kunna tauraron d'an Adam, cikin muryar kuka tace" Dan Allah Dan Annabi Yy Abba kazo kakaini gida wannan ai abin kunya ne ace baakawoni gidan kaba kai kadaukoni kazo ka ajye kasan duk wanda yaji rashjn kunyata zaa gani,


Abu kamar wasa har karfe goma Abba baiyi yinkurin maidata gida ba, dayagaji da sauraran kukan ta saiya tashi yashige ciki yabarta a gun, binsa tayi da kallo ta sauke idon ta akan muk'ullin motar sa gefe kuma ga wasu mukullan nan, nanfa tamike tazari mukullin batareda tunanin komai ba tadau jakarta da takalmin ta tanufi kofa tabude kofar tayi waje, unguwar tsit sai haushin karnuka haka nan tasoma tafiya a tsorace burin ta tafuto titi,  shikuma Abba yana kwance  yajuyo kamar antaba kofar waje can kuma saiyaji kamar iska na buga kofar aa, candai yataso gaban sa yafadi dayaga kofar a bude take ya hango mukulli a kasa anyar, ya salam yafurta ya dauki mukullin yafuto ya kwa hangota har takusan futa daga layin, ya ware murya ya kwala mata kira, Fauza! Tanajin yakira ta takwasa da gudu shima da gudun ya kwasa suka zuba tsere,

Baitab'a tunanin Fauza taiya gudu haka ba, kiranta yake amma ina gudu take bil hakki, cikin ikon Allah wata motar police takawo kai cikin unguwar sunga mace na gudu a daran nan suka dakatar daita, suna ke lfy meyafaru? Ruku u tayi tanacin uban haki hakinma ya hanata mgn, ganin wani na dososu yasa suka dakata da tambayarta harya karaso inda suke tsaye, yn zuwa tashige bayan d'an sanda hkn Yy balain kona ransa take kishi yataso masa ganiyai kmr ma kirjinta saida yagogi bayan sa,

Dan sandanne yace" kai lfy meyafaru kakebin yar mutane saceta zakayi ne?cike da haushi yace musu, ba saceta zanyiba matata cefa, cikin mmki dayan yace" matar ka? Amma take gudunka haka ke zonan wai mijin kine?

Cikin tsoro tace"ni kawai gidanmu zantafi ban sanshiba ma, cikin mmki ya dubeta yace" lallaima yarinyar nan nizakiwa wannan rashin mutumcin to shikenan kije duk inda zaki kije ni kinga tafiya ta, da sauri y rukoshi yace" tsaya malam kai mana bayani mana, mgnr gsky wannan matata ce sunanta Fauza yau dinnan naje na daukota a gidan mahaifinta gobe kuma zankaita gurin mahaifiyar ta sakamakon basanan yau d'in shiyasa nakawota nan insun dawo goben zan kaita gida, mutuwa akai musu shekaran jiya duk mutanen gidan basanan, shine wai tafuto cikin darannan zata gudu saikace wacce zan cinye ko baki sanniba ai bakyayimin haka ba balle ubanki da nawa ciki daya suka futo gakuma alakar aure dake tsakanin mu,


STORY CONTINUES BELOW

Jikinta duk Yy sanyi, shikuma juyawa Yy yayi tafiyar sa don ransa Yy mugun b'aci, nandai suka sata a motar sikabi bayan Abba, Abba kuwa yana zuwa yashige ya garkame kofar, dakyar da magiya yabude suka shigo cikin gidan daita, anan suka tabbatar da matar sace ga gidan nan na amare sabon aure,

Nandai Abba Yy musu godiya hardai musu alkairi sukuma suka kara bashi hkr, Yy kwafa yadubeta da harara yace" kuma wlh zakisan nikike gudarwa abinda kike gudarwar saina yishi, nanfa ta rushe da ihu tana shirin komawa bayan d'an sandan ya funciko ta aikuwa takuma saka kukan duk ta tsorata, sukace kayi hkr yarjnta ce ke damunta, yace" zakiga yarinta kuwa, nandai sukatafi shikuma ya rufo kofar yatasa keyarta gaba tanai masa kuka tana bashi hkr, yace" wlh wlh kinji na rantse? Saina baki mamaki badaini kika gudarwa ba? Nida kin kwantar da hankalin ki babu abinda zanyi miki sabida ni komai nafoson nayishi hankali kwance da isashen lokacin dazan samu hutu, amma tunda kika gudu wlh sainayi, nanfa takuma rushewa da kukan tana bashi hkr,


Ya shige dakin baccin sa yabarta anan, duk tsoro yacika ranta ga abubuwa sunai mata gizo can kuma sai d'if NEPA suka d'auke wuta, nanfa takuma tsorata g kukan gyare, yanada ka dakin yana jiyo b'urun tunta tarasa kofar dakin dayake, candai tasoma kiran sunan sa tana kuka, yn jinta yymata shuru, saidaji karar kumewa kum tabige da bango takwayi kara tana mulmula gurin sannan yataso yasha dariya ya gode Allah sannan yafuta yace" to meye zaki wani dameni da kira? Da sauri tanufoshi ta rikeshi, tana fadin, nidai yau nashiga uku naga takaina daman dan ka wahaldani yasa kakawoni gidan nan dakabarni nayi tafiya ta aida shikenan, yace" yanzuma jeki kofa abude take ammafa kanki tafi yaseen sainaga kwakwaf, tace" kayi hkr yaya, ai wlh baki isaba sainayi, cikin ikon Allah NEPA suka dawo da wutar,nanfa takwasa zata gudu ya damko hannun ta, baisake a koina ba sai adan daryar d'akinsa tana turjiya tana bashi hkr saida yakaita,


Abinda take zatan zaiyin bashi yayiba don haka tasaki jiki ta Shari baccin ta, da garin Allah ya waye kuwa, tashitai jikinta yana ciwo don Yaya Abba bai mata tawasa duk ya gajiyar da gabobin jikin ta lebbanta kuwa har zugi suke don zabar bakon lamarin daya riskesu, a ranta kuwa tana hamdala da Allah yabata gwaezo kmr Abba Wanda yabata mmki a daren jiya ya tabbata masoyi a gareta ya isar da sakkwaninsa wasu bangarori na jikinta kuma sunyi naam, a fili taraya, wannan kenan ranar daya ida cikashe burinsa koyaya zanji? Oho, motsin shigowarsa taji ta hade ranta ta shiga kunkuni kasa kasa nankwa cikin ranta fal yake da begen sa tareda kunyarsa.


Hakanan sukayini tare yahana ta sakat, data zauna zaizo yakamo tashar jiya yadora inda ya tsaya datayi mgn yace" yace" saifa nayi, saida yaga yakureta harta farai masa kukan tukewa yace" jeki aidai na d'ana. A ranar yamaidata gidan ta tarar kanwar tsohuwace ta rasu nandai tai mata taaziyya. Tundaga wannan ranar mamy tashiga gyarata da kanta duk wani Abu datasan zai gyare yar tata tasiyeshi komai tsadarsa don tasan Fauza ba karamin dace tayi da miji ba,


Tundaga wannan rnr bata kuma barin Abba yatab'a koda dan yatsan taba, don mamy tazauna taja kunnenta da takula da hakan, batasan tuni Abba yaraga yarage  zafi ba,


Abba kam tunda yariga yalashi Zuma a bakinsa yarasa sukuni ya kagu ayi ayi akawo masa matarsa gani yake tamkar satitikan daka sanya na bikin bazasu zoba,ita kanta tana muradin mijin tanason sakancewar su tare, amma babu yanda zatai tundama kwana nawa yarage?inta zauna takantsinci kanta cikin nishad'i a yayinda take tuna dramar su ta rijiyar zaki,


Nandai shirin bikin yakankama Saudat tun ana saura kwana biyu tazo takara kyau tayi k'iba abinta kana ganjnta kaga matar manya, a daren ranarne Yy Abba yazo gidan sunjima suna hira a seetroom harda Saudat dg bayane tabasu guri, kmr jira yake Saudat tafuta ya damketa don dama ya gaji hkr nasa yakare, itama sanin halinsa yasa batai masa wata gaddama ba tabashi yarage damuwar sa dakyar ya iya rabuwa daita yatafi cikeda kewarta, wannan yana daya dagacikin abinda Abba keso atare da Fauza Sam batada gaddama abinda ya umarceta shizatayi wannan yakara mata kima da karin soyaiya a gurunsa, ga uwa uba daukin dayake nata burinsa ya ida mallakarta ko hankalin sa zaidawo jikinsa.


STORY CONTINUES BELOW

Hakadai aka shiga hidimar bikin kulawa da tattalin daya dinga nunawa matarsa ya isa ya tabbatar da irin kaunar da soyaiyar data ginu cikin zukatan su, hakann ayi komai cikin tsari aka kai amarya gidan ta, yan biki kowa yanufi muhallinsa dauke da abin arziki don a zahiri bikin yakayatu basuyi bidioi ba.

[5/26, 6:25 PM] Mamanhaneep: [5/26, 6:17 PM] Mamanhaneep: [5/26, 4:24 PM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...87


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneef&Haneefa Usman


***Cikin nutsuwa suka kammala gabatar da nafila da adduoin da manzon Allah S.A.W ya umarci kowanne maaurata suyi a daren su na farko, daga bisani kuma suka ciyar da junan su cikeda bawa kowannen su kulawa, a gurguje sukai shirin bacci don Abba jiyake tamkar ya maidata ciki don k'auna, nandai yashiga raya Daren sa tareda burin cikar burin sa, ko kad'an batai masa gaddama ba don ta fahimci halin da angon nata ke ciki,  cikin kwarewa da tattali da tausayawa yashiga sarrafa gonar sa, amma me? tunda taji lamarin yasoma sauya salo daga nishad'i ya riked'e yakoma radad'i tafara turjiya sam takasa dauriya har tayi nasarar kwatar kanta batare da cikar burin yayan nata ba, duk tafita hayyacin ta don ita kam ba hakan ta zataba ita a nata tunanin yanda yai mata kwanakin baya hakan ce zata sake kasancewa shiyasa a farko tasaki jiki,


Ransa inyai dubu Yy matuk'ar b'aci don bai zaci hk daga gareta ba, tunda dai ita ba k'aramar yarinya bace dazai ce batasan komai ba balle yayi mata bayani, Nandai ya rarrashi zuciyarsa don haryayi fushi saiya sake tunani don baison tabata masa wannan farin daren daya juma yanacin buri akan sa, dubanta yayi wacce ta matsa can gefe dashi tana sauke numfashi duk a tsorace take dashi yace" meye haka Fauziyya mekike shirinyi haka? Kmr jiratake Yy mgn tasaka masa kuka shuru Yy yana sauraran kukan yarasa ta inda zaifara lallashin ta, nandai yahad'o tarin banbaki da rarrashi da lallami da musalai harda guntun waazin sa amma Fauza tayi fur taki aminta da hakan saitake ganinma kmr wayo yake shirin yimata, hakann ya had'iyi takaicinsa ya maida kwadayjnsa ya kyaleta, don anasa ganin inhar yace zai tilas tamata to babu wanj farin ciki dazai d'orar,


Ammafa tasha b'akar mita dadan karan tsawa donko kwakwaran motsi tayi zai juyo yace" ke saurara, a ranta kuwa catake eh naji, a cikin su bb Wanda Yy baccin kirki sai barawo, da asubar farima bayan yadawo dg masallaci yakuma jarraba nanma fir taki yarda itadai tsoro yake bata da karshema kukan dai takuma saka masa,kukanta yana bakanta ransa don haka ma data isheshi koro ta Yy daga dakin tareda kashedin in yakuma ganin kafarta to saiya karyata,duk haushi ya isheshi gani yake tana sane duk abinda tai masa,


Tanayin bak'i yafuta yabar mata gidan don haushi a gsky ta gwanyawa YAbba๐Ÿ˜œ, ko gaisuwar kirki basuyi dashiba hakanan yayi fucewar sa a gurguje

[5/26, 5:47 PM] Mamanhaneep: Tunda yasa kafa yafuta duk kuma saitaji tadamu takasa sukuni zuciyarta tana rayo mata ina yatafi? Sam takasa nutsuwa saikaita mata mgn tanacan tana tunani tasan dai bata kyauta masa ba,


Dik halin datake ciki Saudat tana lure daita, don tunda sukazo gidan taga Yy Abba fuska daure sama sama suka gaisa yabar gidan ko annuri bb cikin fuskarsa bare ransa tasan akwai matsala, Fauza kuwa kallo daya taimata tasan bata cikin nutsuwar ta a darare take zuba mata ido kawai tayi amma a ranta bataji dadin yanda ta tarda masoyan ba,


Wajejen azahar ne bayan sun kammala girki akasarin wayanda sukazo tare suntafi sai su Amal suka rage, tashiga dakin don tayi sallah ita kuma tafuto dg wanka, tunda tafuto dg wankan ta zauna bakin gado tazuba uban tagumi har Saudat ta idar da sallar tananan zaune,

Fauza takira sunanta, tayi firgigit tajuyo tayi yak'e tace" naam harkin idar? Eh kishirya kifuto muci abinci duk kinyi zuru zuru anyama kwa kinyi break Fauza? Nayi mana mekika gani, tam muna jiranki dai ko saikin jirashi yadawo? Uhm tamike batare da ta amsa ba, harta kusan futa ta kirata, Saudat tajuyo sai kuma tace shikenan jeki, bangane injeba kinkirani sai kuma kice inje waini Fauza meyake damunki ne? Naga Yy Abba ma cikin k'unci yafuta kinmasa laifi ne?

STORY CONTINUES BELOW

Hawayen daya shiga zarya a fuskartane y kuma tabbatar da zargin ta, tadawo ta zauna tareda cewa" tokuma meye na kukan ke komai kuka Fauza yaushe zaki girma da kuka?

ba dole nai kuka ba Saudat ni danasan hakane Allah bazanyi auren ba nayi zamana gurin mamy, tofa meyasa kkce haka Fauza jiyafa aka kawoki gidannan mema kika sani a bacin ran d'a namiji? tunjiya yaketai min masifa kinsai dai halin yy Abba da masifa dg zuwana jiya harya gundireni wlh, nasan da barene bazaimin wannan masifar ba, jinjina kai tayi kan tace" aishi Yy Abba baya fada babu dalili saidaj ko akwai abinda kikai masa a jiyan, kuma kinsan inkikai masa laifi ba kyaleki zaiyi ba waima mekikai masa dg zuwanki jiya jiyan nan? Ba kunyar Saudat takeji ba amma a yanzu saita tsinci kanta dajin kunyar ta, tadai kauda kanta kan tace" waifa dannace masa Yy hkr yabari saiyau shinefa yabi yadagan hankali ko baccin kirki baibari nayi ba,  ke banfa fahimceki ba meye wani yabari sai yau? Kau dakanta tayi tace" tunda baki ganeba shikenan, dariya ce taciyo Saudat tace" Fauza ta Yy Abba, ganin tanaimata dariya yasata cigaba da kukan datasoma dazu cikin kukan tace" ni wlh tsoron sa nakeji Saudat nidai gsky bazan iyaba binku zanyi mutafi gida,


Cikin mmki ta dubeta kan tace" tab dijam karki soma wlh, nidai naga sanda zaki waye Fauza yanzu wayake wannan shirmen inbandake? yanzu duk kaunar da Yy Abba yanuna miki sakayyar dazakima sa kenan? Duk wani masoyi cikar burinsa kenan fa toke kince bazaki iyaba agaba kikeso yasaki yaita kallon ki? Nifa akwai abinda nakejin tsoro Saudat, kome kkjin tsoro haka zaki daure inhar kinason zama da mijinki lfy duk wacce kikaga tazauna lfy gidan mijinta to biyaiya take masa, balle ma abinda kkwa tsoron na lokaci d'ayane dakin daure kin bashi a jiyan datuni shikenan yawuce, yanzu kinsan damuwar dakika jefashi a jiyan? Yakwana yn fushi dake Allah da malaikunsa suna fushi dake, yanzu meye ribarki kuma abinda kk boyewa dole dai saikin badashi bayan kinriga kuma kin zubda kimarki da darajarki cikin idonsa don tun ana lallabi akoma hattararki a karshema ace miki dole kikawo kanki, to ina amfanin b'adi ba rai? Dama tunda naganki nasan akwai damuwa a tare dake, yanzu ki kwantar da hankalin ki inyadawo ki marairaice kibashi hkr kuma kiyi alkawarin bazaki sake masa gaddama ba, saiki daure ki jajirce kibashi abinda yakeso shikenan kin huta kema da fargaba,


Yanzu da tunkan Ku tare yanemeki saiki ki? A gsky bakida wayo Fauza, mace fa ita take  sayawa kanta daraja agun mijin ta, duk iya son da namiji ke miki inhar zakiyi masa musu ko gaddama ko ki dinga jayaiya dashi kina kinbin umarnin sa to a sannu zaki sire masa duk wannan soyaiyar ta rikide takoma raini da wulakanci, duk macen data bari mijinta y rainata to wlh tashiga uku, don haka tun wuri kiwa kanki fad'a kibi mijinki sau da kafa duk abinda y umarce ki kiyimasa saikiga kun zauna lfy kuma kullum tauraruwa kike a gurinsa komai tsufanki zakiga zai cigaba da darajaki y mutuntaki sabida tun farko kin mutunta kanki kin daraja shi, kuma ga ribar dazaki samu ranar gobe kiyama kinsan dai aljannarki tana k'asan kafarsa ko? To yanzu misali kinbata ransa kema nan kin yini cikin damuwa duk Wanda yaganki zaigane kina cikin matsala kuma gashidai dik laifin nakine to ina riba anan? Inkwa kk faranta ransa yafuta cikin farin ciki yabarki cikin sa kuma zaidawo miki cikin farin ciki hakan baifi dadi ba? To wlh kikula nidai shawarar dazan baki kenan duk Wanda kikiagani cikin farin ciki to shiyaso, kinsan dai halin Yy Abba bakai masaba ma ya kuka karke balle kuma kinmasa?

Duk jikinta Yy sanyi duban Saudat kawai take a hankali ta furta, kema haka kikai wannan hkr Saudat? tace" eh kowama haka Yy kuma kema hakan zakiyi hkr kibada,


Nandai taita bata shawarwari yanda zata kula da mijinta tareda kara kwantar da hankalinta donta fahimci ta tsorata dayawa, karfe hud'u sukabar gidan don Saudat tana son takoma gidan ta a ranar don gobe take saka ran dawowar me gidan ta,


Shawarwarin Saudat sunatai mata yawo cikin ranta, don haka tadake ta kudiri aniyar jurewar, a b'angaren Abba kuwa ya shiryawa yanda zaiyi mata don a ganinsa inya biye mata a hakan rainine zai shiga tsakaninsu, don haka ya hadiye fushinsa da maitarsa ya tattara yazuba mata ido don ganin idon ruwan ta,

Ta shirya bashi hkr a ranar ganin ya basar da mgnr yasa itama ta basar suka kwana suna juyi a gado daya, a ran kwana na biyar ne, tayi wanj azabebben ciwon ciki tamkar batayi rai ba, hankalin sa dik yabi yatashi yakwasheta zuwa asibiti akabata magunguna suka dawo gida, cikin ikon Allah tanashan maganin bacci mai nauyi ya dauketa na wuya, sai bayan ta farka ne tashiga kicin ta shirya masa girke girke naban mmki don tanason faranta masa don a dazu yabata tausayi don ganin hawaye yana zuba akan fuskarsa a dalilinta har ya zubar mata da hawaye don tausayin halin data shiga a dazu to itakuwa mezaisa bazata agajeshoba duk da yanuna taci kanta shi ya k'oshi?

Asanda yashigo gidan k'arfe takwas tundaga waje yasoma ganin canji, hakama daya shiga cikin gidan ya taddata cikin wani futunanne shiri Wanda yatada hankalin sa duk kokarinsa na yakame karya zubda girman sa said a ta hango jirginsa, nandai tashiga taraira yarsa cikin salon d'aukar hankali tayi nasarar narkar da zuciyar sa,

[5/26, 6:15 PM] Mamanhaneep: ***A lokacin kuma sai tsananin kunya ta kamata har ya fahimci hakan a ransa kuwa yace" kedai kika sani, ganin yakuma basar daita yasa tashiga tayi shirin bacci don a zahiri shikawai take bege, anan falonsa ta tardashi hannunsa rike da rumot a gefen sa ta zauna takai hannu zata amshi rumot d'in ya rik'e kam kam taja taja yaki saki kawai saita d'ora hannunta a saman nasa hannun tashiga shafa hannunsa batare da tajiyo ta dubeshj ba, hakan datai yy matukar tasiri cikin ransa har yaji yana muradjn maida mata da martani, nandai ya yakice yamike da nufin barin gurin yaji ta riko hannun sa, cak ya tsaya ya juyo da kansa ya dubeta tasowa tai tazo gab dashi muryarta k'asa kasa tace" kayi hkr yayana, ka gafarceni, bazan sakeba kasan dai bana cikin masu saba umarnin ubangiji ranar ma tsautsayine yasani bijire maka amma Dan Allah kayi hkr zan kasance mai maka biyaiya, cikin tattausar murya yace" tun a ranar nayi miki uzuri na yafe miki donni mai alfarma ne a gareki, na kyalekine ki gama gulmar ki don nasan zaki dawo hanya gashi kuwa tunkan aje koina kin ajye zaran kin kamo katangar k'arfe don haka ki ajye wannan gulmar kibada kai bori ya hau, cikin kunya da taboye Kanta cikin rigarsa tana dariya k'asa kasa yasamu damar rungumeta tsam cikin jikin sa, nanfa yasoma aika sakonsa gareta nandanan ya birkita lissafin ta yaimata masauki akan gadon sa, dg nan narufo musu kofar donnaga sun manta dani tareda su,


Fuskar ta dauke da murmushi take shafa inda d'igon jini ya bushe akan zanin gadon ta a wannan halin yazo ya tardata shima nasa hannun yadora saman nata yace" in alfahari da wannan Allah yasaka miki da alkairi Fauziyya yabamu zuria dayyiba, nandai yadau lokaci mai tsawo yana yabonta tareda jinjina mata yanajin kaunarta nakuma ratsa sassan jikinsa,


Bayan wata biyu,

[5/26, 6:24 PM] Mamanhaneep: Akwance take saman kujera tayi matashi da cinyar sa, yayinda yake murza gashin kanta wani bacci bacci ke zuwar mata, suna d'an hira sama sama tana gyangaydi wayarta tayi ringing nan yamika hannu ya d'auko mata Saudat tafad'a kanta d'aga, cikin hanzari tace" kunna TV Fauza kiga ana yankewa haj lubna hukunci, tuni baccin dake idonta ya watsake tamike ta kunna TV.[5/27, 8:26 PM] Mamanhaneep: ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA...88


©NWA๐Ÿ“–


Mamanhaneef&Haneefa Usman


***Gidan TV na NTA takamo kasancewar a had'e take, komawa tayi ta zauna tazubawa TV ido don ganin yanda ake yanke hukunci rataya,

Duk wani shaidu da kotu take bukata tasamu an tabbatar da tuhumar da akewa haj lubna tareda sauran k'awayen ta susu takwas, cikin su akwai wayanda aka yankewa hukuncin rataya, yayin da aka yankewa haj lubna tareda aminan ta hukuncin jefewa, tunkan azo zartar da hukuncin haj lubna tasoma rashin lfy, wani irin ruwa ke futa ta jikinta mai d'ankaren d'oyi da zarar taje kama ruwa sai kuma tsutsotsi dasuke futa dg k'asanta duk tabi ta ishi sauran mutanen dake gurin da wari da doyi, cikin wayannan kwanakinne Alh Ibrahim Baban Islam yazo gurin ta tareda bata takardar sakinta, tanata kuka da ban hkr ko kad'an baiji tausayin taba illah Allah wadai daya k'arayi da halin ta a ransa kuwa cayake mutuwar irinku tafi rayuwar su Alkairi, Allah ne kadai yasan iya yawan yaran data lalata da wayanda ta salwantar da rayukansu a dalilin cikar burinta,


Nandai aka yankewa kowannensu hukunci, haj lubna kuwa daaka haskota jikinta tamkar ya rube don fatarta tayi jajir tamkar d'anyan nama hakanan aka jefeta a gaban dubban jamaa, gani ga wane aiya ishi wane tsoron Allah.+


A can b'angaren Saudat duk abinda yafaru akan idon sune itada Alh a gefen su kuma gasu Islam nan dik ilahirin jikinsu yayi sanyi, Saudat kuwa batasan sanda kuka ya kwace mata ba cikin kukan tashiga istigfari tareda Hamdala sumadin kukan suke cike da nadamar kuskuren dasuka tafka cikin rayuwar su, nandai Baban Islam ya hadasu ya rarrashesu tareda kara tsoratar dasu da azabobin da Allah ya tanadarwa duk mai hali irinna haj lubna, a karshe ya umarce suda kowaccen su tayiwa Saurayin ta mgn yaturo magabanta sa duk hadasu zaiyi ya aurar dasu ya huta.


A b'angaren Fauza ma tana rungume a jikin Abba yana rarrashinta, kuka take sosai don tsananin tausayin halin dasu haj lubna sika jifa kansu babu gaira babu dalili kazo duniya Abanza ka komata a wofi tana tausayin duk wani Wanda ya tsinci kansa a halaka don Allahne mai shiryawa kuma shine mai b'atarwa wanda yabatar bazai taba ganewa inhar ba shine ya ganar dashi ba, nantake wani imani ya k'ara shigarta dakyar Abba Yy nassarar lallashinta.


MU FARKA MU IYAYE MATA!,


A matsayinki na uwa yazama dole kisaka idanu akan 'yayanki wajibi ne kijajirce wajen kula da tarbiyyar yaranki, karki sakankance wai kice kinbawa yaranki tarbiyya kinsan bazasu iya aikata kazaba, to lala a wannan zamanin bakida tabbas akan komai na duniya kedai kidage da addua,dolenmu musaka ido akan yaranmu musan mutanen dasuke mu'amala tareda su walau a gida ko a makaranta, in a makaranta ne ki lura da yanayin d 'yarki take ciki ki dinga bugar cikinta donjin yanda yake muamala da mutane kidage wajen sanin dawacce kawa 'yarki take tare a makaranta, haka ma a cikin gida karkiga waidan 'yarki tayi bakuwa kibasu guri su kule cikin d'aki aa Sam bai kamata ba kidinga kaikawao a tsakar gida don sanin me sukeyi cikin dakin, dakinga kawar da bata kwanta miki ba tokiyi gaggawar takamata birki tafuta hanyar 'yarki, inkun zauna ki dinga tambayar yaranki ko akwai wani Abu dasike boye miki ma duk cikin siyasa zakijishi, kija yaranki cikin jikin ki kizama maj share hawayen su aduk sanda kika lura suna cikin damuwa, mudage wajen kula da guraren da kike aiken yaranki in yaro yanuna baisan zuwa shagon wane ko gurin wance tokarki takura masa ki lallabashi har kiji dalili, hakann inkinzo yimasu wanka kidinga gargadin su karsu yarda wani ko wata yace zaitab'a koda hannun su bare wandon su, ki tsoratar dasu wlh kikabar yaranki kara zube a wannan zamanin inba Allahne yakareba saikinyi kuka da idanunki, hakann karki bar yarki taita yawace yawace ki xaunar daita cikin gida inbabu makaranta ko kicin zaki Ku shiga tare ikana sata daukomin waccen mikomin wannan to a haka zata saba wataran tabaki mmki, hakann in gyaran gidane kauda wannan dauko wannan wataran kina xaune zataimiki inkoka koya mata, bawai sai lallai mace ba inma namijinne hakan zakisaka ido akansa tunda masifar babu Wanda ya tsira, in macence kina cikin takatsantdan hakama namijin dole ki jajirce akansa, don billahil azim wannan musibar tawuce duk inda muke tunaninta, Addua itace makaminmu tareda jajircewar mu, don saiki tarbiyyantar da yarki tsawon she karu tashi daya inkikai sake sai a tarwatsata, kmr dai yanda tafaru da Saudat, don haka Mu iyaye mata Mu farka mudage da addua bamuda wayo ko dabara Allah ne xai karemu shikuma yace Ku rok'eni zan amsa muku, SHAWARATA KENAN GAREMU MU IYAYE MATA.


Bayan shekara daya, zuwa wannan lokacin babn Islam tuni ya aurar dasu, yayinda mamy tayi aure da wani maaikacin banki Wanda uwargidansa ta rasu tabar masa yara biyar,  a wannan lokacin Saudat tasoma laulayi abin kmr hadin baki itama Fauza tasoma laulayin shekarar data zagayo suka haifo yaransu kyawawa tsiran kwana dayane tsakanin su, karkaso kaga farin ciki gurin mazajen nasu Yy Abba kuwa badai acewa komai sai godiya ga Ubangiji.

[5/27, 8:56 PM] Mamanhaneep: ***sun cigaba da rayuwarsu tareda dorewar farin ciki da tattalin iyalan tareda mazajen su abin alfaharin su, ga dankon zumincin da kullum kara yaduwa yake cikin zuriar su.


TAMMAT BI HAMDULLAH


Anan nakawo karshen wannan littafi ANA ZATAN WUTA A MAK'ERA.


Godiya ta tabbata ga ubangijin sammai da kassai, tsarki ya tabbata ga ubangiji mai rahma da jinkan bayinsa, Ya Allah kagafarta mana kurakurenmu kasa muna cikin yan tattun bayi cikin wannan watan mai tarin niima da daukaka Ramadan Mubarak,wandake gabato wa, Allah kabamu ikon yin ibadunmu tareda samun tsira a cikin sa,


Sadaukarwa

    gareku mahaifina marigayi Alh Ismail Ahmad tareda d'an uwana marigayi Kamal Ismail Ahmad, Allah yajikan ku da rahma ya kyautata makwancinku yasa kunatare da masoyinmu manzon rahma SAW, tareda dukkan musilimi baki daya.


JINJINARKI DABANCE ABOKIYAR RUBUTUNA,

HANEFA USMAN ALLAH SAKA MIKI DA ALKAIRI AMEEN.

Post a Comment for "ANA ZATON WUTA A MAKERA CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...