ALJANAR FATIMA CHAPTER B KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ALJANAR FATIMA CHAPTER B KARSHE

ALJANAR FATIMA CHAPTER B KARSHE

- - Post a Comment

 ALJANAR FATIMA CHAPTER B KARSHE


~"Ke dan iskanci da rainin wayo ni kika biyo har nan kika zubarwa da Abinci?".   "Eh an zubar din mugu macuci kawai". Ta bashi amsa a hatsale   Hannu ya daga ya kai mata mari cikin hanzari ta Duke. tana dagowa kuwa ta wanka mishi mari Tass!!!...~

_»»Dafe kunci yayi. "Ni kika mara?, Ni kika mara?".   Ya maimata sau uku, "Eh an mare ka azzalumi kawai ai irinku bama mari ya kamace su ba, Duka da bulala ne ya kamace ku..." juyawa tayi ta kalli mutane dake wajen masu shan shayi da masu cin indomie wanda duk sun zura mata ido, Tace "Munafukan banza dubeku dallah, ba kunya ba tsoran ido da yawa daga cikin ku magidan ta ne, Sai ku baro matan ku da tuwan masara miyan kuka. Ku kuma kuzo nan a fashe muku kwai shayi hadin kauri. Wai abinci mai kyau to ku da mata waye ne yafin bukatar abinci mai kyau mai gina jiki da kara lafiya?. Su fa haihuwa suke. Kai Tirr! Da irin halin ku".  Ta juya ta kalli Umar "To  kai malam zaka wuce mu tafi gida ne ko kuwa?".  Abun ne yayi mugun kona mishi rai yaga idan ya kalle ta mutanan wajen daga yau zasu raina shi in ba sa'a bama su ringa ce mishi mijinta ce.  Wawurar ta yayi da kokowa ai kuwa suka tayi tututur-tututur.  Sun dade suna yi amma Umar ko raba ta da kasa ya kasa yi.  Haushi ma abun ya bata ai kuwa tq daga umar ta nuna wa Allah tukun ta maka shi da kasa. Jin jama'a sun kwashi ihu! Yasa shi yayi sauri ya mike._

_Yana kallanta cikin fushi yana huci "Ke dani zaki Wallahi karki kuskura kice zaki ja dani yanzu sai in ka karya ki, Yanzun ma sa'a kika ci nayi tuntube kika shammace ni bar ganin mutane na ihu! Wallahi zasu kai ki su baro ne kuma bari ki gani".  Da karfi yake maganar ita kam Rafy a tsaye take cik! Tana kallansa ko hijab dinta bata cire ba. 'Yar wayar sa da 'yan canjin sa ya kai wa mai shayi ya ajiye masa tukun  ya dawo fili. Ya tsaya yana mata surutai sai da ta sakankance tukun ya durfafe ta cikin shammace. Kamar dazun haka ta kara yin hajijiya da shi ta maka da kasa. Mutane da tune sun cika gurin suka bushe da dariya ana ihu! Tashi yayi ya ka kabe Wandan sa. A zuciyarsa cewa yake, "Anya kuwa wannan Rafi't dina ce kuwa, Haba ai karfin yayi yawa  yaseen wannan ko kona za'ayi a nan bazan iya kayar da ita ba. Abunda yafi kawai shine in fece".  Jama'ar wajen ne suka fara ihu! Suna fadin "Raggk mace ta kada shi".  Umarvya kalli wasu daga ciki yace, "Aikin banza abunda ma ban shirya ba". Kamar dazun a hankali ya ringa matsawa kusa da ita yana shirin kama kafafun ta ya kadata.   Ita kuwa tsaye take ba abunda take in ba kallansa ba. Wawura ya kai mata cikin rashin sa'a kuwa ta sake Damke wuyansa kamar ta kama kaza haka ta fara wulwulawa da shi. Umar ihu! Ya farayi yana neman taimako jama'ar wajen kuwa ba abunda suke in banda dariya. Wasu na cewa mai kashi daya ce, Basu san *ALJANAR FATIMA* Bace.  Sai da tayi juyi kusan hudu da shi tukun ta sake shi ya fada kasa sharaf!._

_Nan ma mutane suka fara kyalkyala dariya. Umar ya dan jima a zaune domin hajijiyar da tayi da shi kansa ya dan fara juyawa. Mike wa yayi cikin fushi ya nanade kafar wandansa. Yana mikewa ya kwasa a guje mutane kuwa suka ta mishi ihu!  Yaji tsoran mace.  Sai da ya danyi nisa tukun ya tsaya ya juyo da karfi ya fara magana. "Ke ba dai ni kika wa haka a cikin jama'a ba, Wallahi yau sai nayi maganin ki yau bazaki kwanar min a gida ba kuma Wallahi idan kika shiga hannuna sai na dandana miki azabar da baki taba tunani ba. Yana fadar haka ya juya ya nufi gida a guje bai ko tsaya karbar wayar sa da 'yan canjin sa ba na wajen mai shayi.  Da shigar sa gida ya saka kwado a kofar gidan ya kulle yana cewa. 'Yar iskan banza yau sai muga a inda zaki kwana nasan dai gidan ku ko kinje koro ki zasuyi.   Tun daga tsakar gida yaga hasken fitila a daki a zuciyarsa yace, "Ashe ma a kunne ta bar fitilar ta fita masifa".  Yana shiga dakin yaga mace kwance sai dai ta juya baya. Baya iya ganin fuskarta, da alama barci take yi.  Tsaye yayi kofar dakin ya tsare ta da kallo kamar matar shi kamar kuma ba itaba. A hankali ya fara matsawa  sai da yaje gaf da ita yaga ashe ta dan lulube fuska da Wani gyale. A hankali yasa hannu da niyar ya Cire yaga ko wace ce. Shi dai yasa a baya ya baro matar shi.  Yana taba gyalan Firgigit!  Rafi'at ta tashi. "Mai gida ka dawo sannu da zuwa". Ta fada tana mamakale wa dan tsoran shi kamar yanda ya saba.  Da ya tsora ta kuma sai wani tunanin ya zo mishi yace, "Haba kaga mata ta nan ga tsoro nan a fuskarta waccan Aljanar ce ba ko shakka".   Tsawa ya daka mata, "Dan ubanki bana hanaki kwantawa a kan gadan nan ba?".  Da sauri ta sauka tana bashi hakuri.   Tsaye ya mike yana kallanta yana dariyar mugunta farin ciki yake ji. Na ganinta domin yanzu zan rama duk abunda Aljana tayi min, Haka ya ayyana a Ranshi.   Mari ya galla mata dan tabbatar wa. Ai kuwa ta saki kara ta fara kuka tana bashi hakuri.  Wani murmushi yayi na mugunta domin yanzu a ganin sa ya tabbatar da matarsa ce ba aljanar._

_Murtuke fuska yayi ya kalle ta, "Wato in ma yi hakuri kike cewa ko, Da nayi niyar yi miki babban hukunci amma tunda kin bani hakuri bulala 20 ce ba yawa".  Ya juya ya nufi kofar fita a dakin domin ya dauko bulala.  Rafi'at abun tausayi har kafar shi take kamawa wajen bashi hakurin amma sai dai ya fusge.  Nan ya barta zaune a tsorace sai kuka take tana bashi hakuri.  Umar ya fita ya dauko bulalar katuwar Dorina ce mai baki  biyu.  Ya shigo da ita dakin, Ba abunda ya daure mishi kai sai ganin Rafy a tsaye ta tsare shi da kallo fuskar nan tata babu annuri. Shi da ya barta tana kuka yanzu kuwa ko hawaye babu a fuskanta. Da ganin haka ya yarda bulalar domin ya kyaro Aljana ce. "Mai gida me zakayi da bulalar nan?".  Rafy  ta tambaya cikin bacin rai!.  A  tsorace yace "Wallahi dama can din ne inda nake ajiye ta naga rana an dakar ta shine na daukko zan canza mata wajen ajiya".  Ok ta fada lokacin da ta nufe shi ta durkusa ta dauki dorinar Umar karkarwa ya farayi dan a tunanin sa zane sa zatayi. Kamar yayi waje da gudu kuma sai ya tuna gida a kulle yake da kwado.   Sanda ta wulwula bulalar tukun ta dorq mishi daya. Ihu! Ya kwada "wayyyo!!..".   Da sauri tace "Haba sweetheart karka bada maza mana. ni fa dama tambayar ka zanyi akwai zafi?".    "Ehh   A'aaa".  Ya bada amsa biyu a jere, yana sosa inda ta dake shi domin taji bulalar. Daga wa tayi da niyar kara mishi.  Da sauri  yace "Akwai akwai zafin". Sannan ta wullar da bulalar gefe.  Sweetheart to muje mu kwanta mana.   To ya fada da sauri yaje ya haye gado. Itama taje ta hau ta wani shishige mishi. shi kuwa duk a tsorace yake a haka har barci ya kwashe shi.  Tana ganin haka ta bace cikin abunda baiyi Minti daya ba taje ta dauko Real Rafy ta hada su hade da cewa karta kuskura taji tsoran shi....._
__________________

_Fatima tunda tajw gida ta shiga daki ba abunda take sai kuka sai da tayi mai isar ta tukun barci yayi gaba da ita.  Kamar yanda ta saba kullum idan ta tashi zata fitsari da babyn ta take zuwa dake a gado daya suke kwana. Yau kuwa tana farkawa taga ba yar baby ta tuna abunda ya faru jiya sai kuwa ta hau kuka. Ameera ce ta farka a lokacin, Sai da taci uban Fatima tukun Fatima tayi shiru.  Washe gari tun da asuba Mama Asiya ta fito daga dakinta tafiyar kamar marar lafiya domin yunwa taci-taci. A falo ta zube a kasa  ita kam tama rasa abunyi har jiri take gani.  Tashi tayi ta nufi kitchen kamar ance ta bude store ta bude. Komai nasu ya dawo abun ne taga kamar gizo yake mata, hakan yasa ta murjw idanu.  Haba gaba daya yunwar da wani rashin karsashi tafiya sukayi a lokacin. Kira ta fara kwallawa su Zuwaira.  Ko wacce na dakinta suma ba barcin suke ba yunwa ce taci ubansu.   Shiru suka mata Alhalin kuma suna jinta. "Hauwa Zuwaira ku fito kuga ikon Allah abincin mu ya dawo".  Haba kafin ta rufe baki tagan su kowa ta fito a sukwane. Kitchen din suka koma suna gani kuwa suka fara murna Zuwaira kam duk da tana jin yunwa har da rawa.  Indomie suka zuba a tukunya wajen guda 10. Tun kafin ta Dahu mama Asiya taci Indomie danya leda biyu.    Cin hauka sukayi wa indomie din domin ko bari ta huce basuyi ba. Sai da kowa ya cika cikin sa mama asiya kam tayi zari da yawa dan har sai da tayi amai._

_Da safe bayan kowa ya karya akayi shirin islamiyya domin ba boko an bada hutu,  Fatima tace bata da lafiya kanta ke ciwo mama Asiya tace "Munafuka wato makarantar ce bakya san zuwa shiyasa kika azawa kanki ciwan karya ko?. To Alqur'an sai kinje maza wuce ki sako Uniform dinki". Fatima kuka ta fashe da shi ta nufi daki tana cicila kafa.  Mama asiya ta juya ta kalle ta. Ta kama baki alamaun mamaki. "Iyeeee! Fatima ni kika wa wannan rashin kunyar dan na taimake ki nace ki tafi makaranta ko, oya zo nan dan ubanki dawo". Fatima ta dawo tana kuka ta durkusa a gaban mama asiya, "jiya dama naji kin shigo kina kuka ana ta lalashin ki miye kike wa kuka?". Zuwaira ta tambaya.   Cikin kuka Fatima tace "Ba malamin mu na islamiyya bane ya kwace min Babyn na ya yanka min ba". Da jin haka mama Asiya ta bushe da dariya "Shegiya Allah ya kara, dama ni wannan Aljanar ba santa nake ba, ni gaba daya ma na tsane ta".  Zuwaira tace "Au!  Dama a kanta ne kike kuka ake ta rarashin ki amma kika ki ji, Ai ni dana sani wallahi da duk da ina jin yunwa da sai na taso na fafala miki mari, mu wannan ai rahama ne ma rabuwar mu da ita".  Korar ta sukayi ta tafi daki tana kuka, Su Asmart suna canza kaya suna sa na islamiyya ta shigo tana kuka. Nasmat na ganin ta ta nufo ta tana zazaginta. Wai ta musu shiru, Fatima duk da ta so ta rike kukan amma yaki rukuwa.  Nasmat dunkule hannu tayi ta Dankwashi Fatima a kai, haba ai kuwa sai ta kara fashe wa da kuka, Fiddausi na ban daki jin kukan Fatima yasa tayi sauri ta fito.  "Keee! Keee!  Wallahi in kika sake dukan ta sai naci uwarki". Fiddausi tace lokaci  da ta nufi inda suke.  Maganar ce ta dakatar da Nasmat da tayi niyar yiwa Fatima dundu.  Nasmat tana gunguni ta koma gun Asmart dariya asmart tayi tace "Nasmat mugunta ko wato dake Kinga *ALJANAR FATIMA* Bata nan".     Nasmat tace "ai sai na rama duk abunda tayi min"._

_"Asmart tace bari a dawo daga Islamiyya zata daku ai a waje na".  Fiddausi ta tambayi Fatima me take wa kuka Fatima ta fada mata mama asiya ce yace sai taje makaranta kuma kanta ke ciwo. Fiddausi hannu  ta dora a jikin Fatima taji da zafi, hakan yasa taje ta dauko mata magani ta bata tashi tukun tace ta kwanta. Sunzo tafiya mama Asiya tace ala dole sai Fatima taje makaranta, Sai da Fiddausi tayi yaki sosai tukun mama asiya ta barta.  Ai kuwa suna fita mama asiya ta koro Fatima waje. Wai ta koma cikin rana Mai zazabi baya san sanyi dan salan mugunta. Aljanar Safuratu ce tafe cikin iska tun daga nesa ta hangi mama asiya sai jaraba take wa Fatima tana dankwashin ta ita kuwa tana kuka hakan  yasa ta kara sauri....................................._

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 61-62

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

πŸ‘πŸΌ *NASAN NAYI MUKU LAIFI KUYI HAKURI DAN ALLAH MASOYA.*

πŸ™ƒ _JIYA KAM NAGA MASOYAN ALJANAR FATIMA. HAR KARFE GOMA MASSAGES BASU DAI NA SHIGOWA WAYA TA BA. DUK MASU JIRAN POST NE._

πŸ‘πŸΌ _NA GODE MUKU MASOYAN WANNAN LITTAFIN NAWA, SANNAN IN BAKU HAKURI BISA RASHIN POST DINA. WALLAHI INA CIKIN TYPING TUN KARFE 5 BIYAR BACCI YA DAUKE NI BAN FARKA BA SAI WAJEN 9. TO BAKU KADAI NAWA LAIFI BA HAR DA UBANGIJINA_ 😭

😍😘 I LUV OLL MY FANS.  ANA MUGUN TARE πŸ™ƒ

   *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Aljanar Safuratu ce tafe cikin iska tun daga nesa ta hangi mama asiya sai jaraba take wa Fatima tana dankwashin ta ita kuwa tana kuka hakan  yasa ta kara sauri.~

_*K*afin Safuratu ta karaso wajen mama Asiya ta shige ciki,  Tana ganin haka ta bace ta dawo sufar Ameera,  ta kofar gidan ta shigo taje gurin Fatima. "Ke wai miye tun jiya kike tayi wa mutane kuka?".  Fatima ta dago cikin kuka tace "Malam ne ya kwace min Babyna jiya ya yayanka".    Sai a lokacin Safuratu ta lura yar babyn a hannun Fatimar,  Da sauri ta juya tana fita daga gidan ta bace bata zame ko ina ba sai kofar mai shagon, inda aka sayo 'Yar babyn  shagon ta gani a kulle_
________________

_A gidan Umar kuwa Safuratu na ganin Asuba ta kusa to sai tayi sauri ta dauke Rafy ta mayar da ita gida ba tare da tama sani ba tana barci, Ita kuwa ta juye zuwa rafy din ta zo ta kwanta. Da asuba Umar ya farka zaune yayi ya zuba wa Rafy da ke barci ido, Tunani yake a ranshi  wannan Rafy din ce ko kuwa, Da dabar ta yayi Rafy! Rafy! Tashi asuba tayi_

_Firgigit! Ta tashi a dan tsorace shi kanshi ma sai da ta tsorata shi.  "Sannu mai gida lokacin sallah yayi ko?".  Ta fad murya a sanyaye daga jin haka a zuciyarsa yace "Wannan Rafy ce ba Aljanar ba".  Kai ya daga mata alamun eh, Ita kuwa ta saukko taje tayo alwala shima alwalar yaje yayi yazo ya tada musu sallah.  Bayan sun gama salar ma ya juyo y kalle ta yaga dai alamar Rafy din ce. domin kamar yanda ta saba ko Ido bata iya hadawa da shi haka ma yanzu Safuratu alamun tsoro take nuna mishi. Bayan ta gama adduo'i da sauri ta rissina cikin Ladabi ta gaishe shi ya amsa. Ta shi tayi ta cire hijab din jikin ta koma kan gadan ta kwanta.  Umar da ganin haka ya murtuke fuska ya shiga zancen zuci. "Amma fa yarinyar nan in ita ce ta raina min wayyo._

_Harda wani hayewa kan gado, Amma bari in gwada ta inga Aljanar ce ko kuwa".  Da karfi ya fara maganar "Rafy! Rafy!  Saukko kasa malama kin wani je kin daare gado kamar na ubanki".  Da sauri ta tashi ta sauko a tsorace. Murmushi yayi yace Yauwa wannan Rafy dita ce.  "Yauwa ke abunda nake so kiyi min a yau zan zana miki yanzu kuma Wallahi in bakiyi daya daga ciki ba har kika 'yar da na dawo,..Kema kin  san sauran".   "To mai gida ina jinka".    Ya wulla mata harara tukun ya fara lissafi da yatsun sa yana kirga mata aikin. "Na farko yanzu ki tashi kije ki dafa min ruwan wanka, Kafin in fito ki dafa min abun break.  Na uku kinga kayana can sun taru sun kusan kala ashirin  ki wanke min su ki goge,  Na hudu kiyi min Taliya da farfesun kaza kinji ni da kyau".   Kuka ta fashe da shi, cikin kuka tace "Haba mai gida so kake yi ka kashe ni wannan aikin ai sunyi yawa Wallahi bazan iya ba duk ni kadai a rana. Kum..." Tass! Taji saukan mari a fuskan ta, "Kaji 'yar isakar 'yarinya to idan baki min ba wa zaiyi min wato a nufin ki in baki ci da sha in barki gida mimike a kan gado kamar  gasasar kaza ko?. To Wallahi ban lamunta ba, oya maza tashi".  Ball yake shirin yi da ita hakan yasa ta tashi ta fita a guje shi kuwa ya zauna a bakin gado. Dariyar mugunta ya fara yi. Juyowar da zaiyi yaga Rafy tsaye tana kallansa.  Tsayawa yayi da dariya  tukun yace "Ke me kika yi a nan maza wuce kije kiyi abunda nasa ki". "Kai tashi maza je ka dafa min ruwan zafi ka kai min bayi, Kuma mintuna 15 kadai na baka".   Kamar daga sama yaji magana, juyawa yayi yaga lalai Rafy ce ke maganar, "Kanbuhun uba!.   Wato ina baki Umarni kema kina bani da Alamar dukan safe kike bukatar ki karya da shi yau".  Ta sowa yayi da hanzari zai dake ta ai kuwa ta rike hannun ta murda shi. Ihu ya kwalla Tukun ta sake shi. "Oya wuce kayi abunda na saka ka kafin raina ya baci"."Rai nin wayo ma, ina mijin ki ne zaki sa in miki wani ruwan zafi To Qur'an bazan yi ba. To ni in gaya miki a tarihin rayuwa ta ban taba tsugunna wa gindin ba".  "Au bazaka yi ba kenan!".  "Eh bazan yi ba"  ya fada a dan tsorace domin  ya gano ba Rafy bace._

_Juyawa tayi ta dauki Bulalar jiya ta nufe shi, Tun kafin ta karasa wajen shi ya farq ihu! Yana bata hakuri. Batayi wata-wata bata fara zura mai bulala,  shi kuwa ba abunda yake sai ihu! Dake a daki ne ba'a ji sosai waje. Sai da ta mishi wajen  bulala ashirin tukun tace "Yanzu zakayi ko kuwa?"  Da sauri yace "Eh Wallahi zanyi Allah zanyi ko ma abincin kike so zanyi miki, Amma dan Allah ke wace ce"   kaji dan rainin wayo Nice matar ka au! Dama duk abun da kake min baka san kyale ka ne nake yi ba saboda san da nake yi ma?, To yanzu kuma naga ba wata soyayya a tsakanin mu kullum sai dai ka dake ni, Hakan nema yasa nima sanka ya fita fit!  A raina yanzu in kaga ka dake ni to kyale ka nayi, Maza tashi kaje kayi min abunda na saka ka".    Cikin  hanzari ya tashi ya fita yaje ya dora ruwan sai da yasha wuya tukun wutar ta huru.  Ruwan har yayi zafi ya kusan tafasa Rafy ta fito.  "Yauwa uwar gida ruwan ya kusan tafasa ya fada yana kallanta yana dan murmushi yak'e".  Da sauri ta zo wajen sa ta kama hannun sa. "Mai gida tashi mana miye kake haka, ina ce ni kasa in dafa maka ruwa, Ashanafa kawai naje daukkowa shine kuma zaka zo ka fara dafa wa. Haba sahibina ai sai kaja min tsinuwar Allah haba mai gidana koma daki abunka kar sanyi ya illata min kai".  Tunda ta fara maganar ya saki baki Galalah yana kallanta, Tunanuka iri-iri suke ziyartar kwalwar sa. Mike wa kawai yayi ya fara tafiya ya nufi daki, Ya saka kafa daya cikin dakin kenan yaji ta shako rigar sa ta baya. "Munafuki ina zaka ka wani nufi daki, Au! Wato ko dukan ne bai ishe ka ba kari kake so?. Maza malam kaje ka karashe dafa min ruwan zafi na". Umar ji yayi kamar ya fashe da kuka dan bakin ciki, Abu biyu yake tunani ko dai Aljana ce ko kuwa Aljanar ce ta shiga jikin matar sa. Sai da ya tafasa ruwan duk tana tsaye kansa tana zafga mishi masifa, yaje ya surka ya kai mata ban daki. Ta saka shi ya dafa musu tea kafin ta gama wanka. Ba yanda ya iya domin zuwa yanzu yayi sanyi sosai mugun tsoran ta yake.  Bayan ya dora tea din ne ya lura ba sugar sai da ya jira ta fito ya sanar mata. Tace yaje sayo kamar jira yake dama ai kuwa ya tafi da sauri har ya kusan zuwa kofar yaji ta ambaci sunansa. "Wallahi in ka wuce minti 15 sai na bika har inda kaje na babalaka, ba daka tafi da sauri a nufin ka ka gudu ba".    Kamar kuwa tasan niyar guduwa yake.  Maganar da tayi kuwa ta tuna mishi jiya hakan yasa jikin sa yayi sanyi.  Fita yayi daga gidan yana tafe a hankali ji yake duk duniyar tayi masa kunci baya jin wani dadi balle farin ciki._

_Abokin sa Muhajeed ya tuna, "Yes". ya ambata direct ya nufi gidan Muhajeed din. Bayan yayi sallama Muhajeed ya fito nan suka zauna ya kwashe labarin duk abunda yake faruwa a gidan sa daga jiya zuwa yau ya fada wa Muhajeed.  Dariya sosai Muhajeed yayi tukun yace "Kai amma Wallahi ban taba sanin kai so ko ne ba sai yau, Haba dai nawan karka bada maza mana Uhmm!  Ace mace ta ringa buga ma irin wannan game din haba ai yanzu an wuce wannan yayin".    Dan bata rai Umar yayi yace "Abokina baka fahimta bane irin karfin da naji a jikinta ya nuna ba ita kadai  bace da aljanu a tare da ita".      Mtseeeew   "Aljanaun banza ni fa ban wani 'yar da da akwai wasu aljanu ba, Malam kawai jamfin mutane ne, Ni da mata ta ce ta tsuro  min da wannan iskancin Wallahi da tuni  nayi maganin ta".    Umar ya kada kai yace "Shin yanzu idan na baka dama zaka iya zuwa ka Ladaftar min da ita?".   Muhajeed yaji zancen mugunta da sauri yace, "Kwarai kuwa abokina. idan ban mayar ma ita kamar mata ta ba daga yau mu raba abotar nan".  Umar yace "ok to
shikenan yi sauri tashi muje mintuna 15 dam ta bani".  Muhajeed dariya ya tashi tana wa umar wai ya zama mijin hajiya har tym.ake bashi.   A zuciyar sa kuwa tunanin irin bugon da zaiwa Rafy yake,  Yana murmushi mugunta yana kara ganin wawancin abokin nasa._

_______________________

_Wajen karfe 11 tukun mai shagon ya bude. Safuratu a sufar alhaji salim taje ta tambayi irin 'yar babyn ai kuwa taci sa'a saura daya irin ta Ta kuwa sayo.  Fatima na zaune har wani gyangyadi take daga zaune. Domin kanta sosai ciwo yake. Karar bude gida taji abunda yasa ta bude idan ta ta zurawa kofar ido kenan dan ganin  mai shigowa.  Bisa mamaki taga 'yar tsanar ta ce ta taho. Dungwai-dungwai Hannun ta rike da jakar kayanta.  Wani ihun! Jin dadi Fatima tayi hade da tashi da gudu ta tarye ta tana mata oyoyo. Daukar ta tayi tun dag nan take kwalla kira "Mama Asiya! Mama Asiya! Babyn ta dawo".  Haka take fada har ta karasa falo a iske su mama Asiya suna kallo. Kan mama Asiya Fatima ta fada tana murna,  da karfi mama Asiya ta tura ta kasa suka yi daya-daya da babyn da dan akwatin. "Ji 'yar iskan yarinya karya ni zakiyi?".  Fatima dan bata rai tayi dan taji zafi daukko babyn tayi tace "Mama Asiya babyna ce ta dawo".  Sai yanzu ma suka lura da babyn "waya kawo miki ita malam din?,"  Kusan a tare suka yi tambayar "Aa da kanta fazo". Inji Fatima Asiya tace "Zo Fatima". Tana zuwa kuwa ta zafga mata mari, "Dan ubanki bana hanaki karya ba?".   Kuka Fatima ta fara cikin kuka tace "Wallahi mama ba karya nake ba".  Gashin kan Fatima ta kama taja da karfi kamar zata cira shi. "Dan ubanki Bana ce karki kara ce min Mama ba?".  Hakuri Fatima ta shiga bata bata. Ita kuwa kamar kara tunzurata take. Lafiyayun marika har biyu mama asiya ta wa Fatima. Hade da yin ball da ita ba tausayi da ganin karamtar ta.  Daukar 'yar babyn da Jakar tayi ta fita waje ta tulla su can saman kwano. Ta dawo tace "Inga ubanda zai daukko miki".  Ran Safuratu ya baci sosai, Bat ta bace ta dawo falan ba tare da suna ganin ta ba.  Muguwar harara kawai take bin Mama Asiya da shi Allah-Allah take mama Asiya ta bar cikin falon.................................._

πŸ™†πŸ»‍♂😰  *YAU WASU ZASU DAKU, MAMA ASIYA, MUJAHEED*

πŸ˜” *KAICO FATIMA*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 63-64

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

*KIN CANCAN Ce SHI. NA BAKI PAGEN DUK DADIN SA. KE KADAI. (ROUKIE BABY)*

🌺🌺🌺 *LABARI NA*🌺🌺🌺

✍🏼 *Writing by*
ROOKIE BABY

πŸ‘― JINJINAR BAN GIRMA GARE KI RUKKAYA.  DAYA KIKE TAMKAR DA DUBU. INA GWANIN WANI GA  TAWA GWANAR BA GWANAR A GUN FADA BA KO ZAGI. JINI NA MIJIN FAMA. HADARI SA GABANKA INDA KAKE SO.GIWA KIKA BAKI WAI WAYE IN KUN NAUSA. GWANKI MAI RANGWANGWAN.  ZAKI SA MAZA GUDU. KABEWAR KAN KABARI BAKIN CIKKN MAI TAUSHE.  MURUCIN KAN DUTSE. MAHASSADAN KI A YAU SUNE FADAWAN KI. LA'ILAHA ILLALAHU".πŸ‘»πŸ™Š.

πŸ€™πŸ½ _Hakika kinyi rawar gani kin kawo abunda ake so labari ne mai dadi cike da ma'ana labarin da zai sa matasan mu su hankalta musamman ma mata.  Labarin da akayi amfani da salo mai burgewa wajen jan hankalin mai karatu. Idan na fara karanta page ya kare  kamar in daka wayar da kasa nake ji._ 😘 *Godiya muke yi yar uwa Allah ya kara basira zakin hannu. Allah ya kara hada kawunan mu.  All Zamani Writers.  Wuta kawai kuke ina biye da ku ina barbada Fetur*

🀀 Autan ku ne. *King boy*

  *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ta dawo tace "Inga ubanda zai daukko miki".  Ran Safuratu ya baci sosai, Bat ta bace ta dawo falan ba tare da suna ganin ta ba.  Muguwar harara kawai take bin Mama Asiya da shi Allah-Allah take mama Asiya ta bar cikin falon.~

_»» *S*u Umar hanya suka biyo sai sauri suke Muhajeed har ya matsu aje gidan dan hannun shi kaikayi yake, Abun da basu sani ba duk abunda suke yi Aljana Safuratu na gurin tana jinsu. Mujaheed yayi mugun bata haushi, A ranta tace yanzu fa da Rafy ce da sai y same ta ya Zane baiwar Allah.  Lokacin su Umar suka karasa gidan, dake ba bulala kusa Umar da kanshi ya dauki wani itace dan dogo ya mikawa Mujaheed. Shi kanshi Mujaheed yaga Girman iccen, Amma dan mugunta sai bai ce yayi girma ba. Umar ya bashi Izinin shiga. Kamar wani uban ta haka ya fada dakin. Dake dakin da dan duhu Rafy ta kunna fitila yana shiga ya iske ta  a bakin gado cikin shiga ta bakar doguwar riga. "Munafuka algunguma, Tazo yayi wani mukus kamar wata salaha to yau dai Allah ya toni Asirin ki kashin ki ya bushe. Umar ne ke fadar haka lokacin yana kokarin saka kwado ya garka me dakin kwadan ne yaki rufuwa dan haka ya saka kubobi kawai ya barshi.  Haka tagar ma. (Window) ya rufe ta. Juyowa yayi ya nufi Rafy da har yanzu tana kan gado duk abun da yake yi ido kawo take binsa da shi, Duk wanda yasan  Rafy in yaga ta yanzu yasan idanunta sun kara girma.  Bai yi wata-wata va ya fara zura mata bulala. Yana dukan nata da karfi yana fada._

_Yayi mata kusan bulala goma amma yaga shiru ne domin ko motsawa batayi ba In  banda manyan idanun ta da take binshi da su ga ta wani daurw fuska. abun ya daure mishi kai sai ganin iri  dukan da yake mata ko icce ne sai haka.  Umar na waje jira yake kawai ya fara jin ihu!  Rafy amma shiru.  Mujaheed ya daka iccen dake a matsayin bulala zai narka mata kenan, cikin hanzari ta mike saurin su irin na Aljanu ta kwace icen ta bace da shi. Mujaheed waige-waige ya kamayi a cikin dakin yana neman ta.  Hihihihihihhi-hihihihi. Wata siririyar dariya ce ta fara cika dakin. "Waye? Waye waye mai dariyar nan?  In ba tsoro ba fito mana. Ni fa nan da kike gani na a shirye nake ba raggon namiji bane".  Aljihu Umar ya laluba ya dauko wata laya ya rike a hannu yaci gaba da cewa ta fito mana. Ta baya yaji an turo da karfi ya nufi bangon dakin kafin   ya isa bangon yaji  an tare shi da hannu ba tar da yaga wanda ya tare shi din ba. Mari fasss! Fasss! A duk kumatun  nashi biyu,  Rike kumatun yayi kamar yayi ihu kuma sai ya yi tsoran kar abokin sa yaji ya kunyata.  Ji yayi an dan dadabe shi.  "Kaaaa!" Yana juyawa baiga kowa ba sai saukar wasu tagwayen marukan.  Wayyo! Mujaheed ya fada a hankali ba da karfi ba ya dafe kumatun sa. "Muguwa kawai wannan tsoro ne ma. Ku fito fili mana mana ayi ga da ga, in ba tsoro ba".  Mujaheed ke maganar ya dunkule hannu kamar dan dambe sai juye-juye yake so yake kawai yaga ta bullo._

_Dariya yaji da karfi a bayan sa.  Hahhahhhhhhhh!  Yana juyawa kuwa abunda ya gani ya tsorata shi sosai.  Wai katan dodo ne mai bakin gashi buzu-buzu ko'ina jikinsa gashi ne. Hannunsa kuwa wasu mugayen farcina ne masu kaifi, Girman abun ya kai A hade Mujaheed biyu ko uku. Babban abun tsoran shine kan Rafy ne, Idanun ta sun juye sunyi baki. A haka take nufo inda Mujaheed yake tana dariya, Duk lokacin da ta wangale bakin ba abunda zaka hango ciki sai wasu rubabbun hakora.  Duk jikin Mujaheed ya fara rawa mugun tsoro ya kama shi, faduwa yayi kasa yana ja da baya yana bata hakuri cikin kuka kuka."Dan Allah kiyi hakuri, Wallahi bazan kara ba, kuuuummaaaa maaa..." Ya fara magana karkarwa ganin abun ya kusan iskoshi.  Daga waje yace Umar yace "Abokina wai ya dai naji shiru ne har yanzu bata fara ihu ba, Nafa gaya maka karka raga mata kaci ubanta sosai ni na saka ka". Cike da takaici Mujaheed yace "Ka yanzu zakaji ihu na ni...".  Kafin ya rufe baki yaji an shaki wuyansa kamar wani zakara an daga shi sama Ihu! Ya fara "Wayyo! Allah na Wayyo! Wayyo!". Da karfi yake ihun! Fitsari ne ya fara zuba shaaa! Wulli tayi da shi ya maku jikin bango. Sa'ar shi Daya ba kan shi ya budu ba._

_Tashi yayi a guje ya nufi wajen kofa, ai kuwa wutar dakin ta dauke duf!  Baka iya ganin komai ko'ina duhu ne.  Inda ya nufa ya azo kofa zai ji, Kawai sai yaji yaci karo da mutum haka kuma aka dalla mishi mari, Wani bangaren ya sake nufa nan ma yaji saukar mari. Ba abunda yake in banda kuka da ihu! Yana neman agaji domin yanzu abun yayi yawa mari da duka ta ko'ina kawo mishi ake. Umar daga waje ihun yake ji kamar na matar shi haka yasa ba abunda yake yi sai murna yana fadin "'yar banza gobe ma ki kara".  Mujaheed ya daku sosai dan fuskar sa har sai da ta fara kunbura.  Yana nan duke ya rufe kanshi da hannnuwa dan dukan shi da ake. Ba abunda yake sai ihu da neman agaji. Tsik! Yaji an dakata da dukan nashi,  a hankali ya fara bude ido yaga ashe haske ya dawo. Yana bude idan ya ga ashe tsugunne yake gaban gado Can kuma kan gadan rafy ce ke kallan sa tana murmushi.  A tsorace yaja da baya. "Dan Allah, Dan annabi kiyi minn Rai ki barni in tafi gida ki yafe min Wallahi ko can dam ni wa'azi nazo in miki kibi mijinki...".    Tsawa ta daka mishi wanda sai da yayi muguwar zabura. "Wa'azi kazo ko dai kara rikita al'amura?, Ashe dai dama kai ne muna fuki wanda ka raba su da farin ciki da shawarwarin ka na mugun ta da ke ta. Umar  Ya dauke ka tamkar dan uwa ne komai zaiyi sai ya sanar da kai amma kai gurinka ka na ya za'ayi ka saka su cikin damuwa ne shida matar sa ko?"._

_Duk hawaye ne da majina da a fuskan sa. Da sauri yace "Aa Wallahi ba haka ban...".  "Rufe min baki ko in kara maka dukan da ya fi na dazun".  Hannu yasa ya kame bakin sa. Aljanar taci gaba da cewa "Tunda kai ne wanda ya jefa su cikin wannan halin to Wallahi kasan yanda zakayi ka dawo musu da farin cikin su. Daga yau zuwa gobe na baka.  Sannan kuma ina so in gaya ma karka yarda ka fadawa Umar cewa na dake ka".  Wani zane ta wurgo mishi tace "Oya goge hawayen da majinar. Ka fita a hankali kana murmushi".  Da sauri ya dauka ya gogo ge.  Tashi yayi zai fita alamun tsoro ta gani a fuskan sa gashi har yanzu yana 'yar karkarwa. "Kai dawo ka fita kana Murmushi nace ba karkarwa  ba". Wani mugun yake yayi tukun ya juya ya fara cire kubobin.  Yana ganin daki ya bude haba wa sai ya kwasa a guje kamar bai ji duk abunda ta fada mishi ba. Safuratu ta girgiza kai tace "Hmm yaro bai san wuta ba aka ce sai ya taka". Umar na tsaye yaga mutum ya wuce a guje kamar wanda aka harbo. Ai kuwa ya rufa mishi baya. Sai da sukayi gudu mai nisa. Duk wanda ya  tambaya lafiya Sai  Mujaheed yace "Aljana! Aljana!  Haka ya ta tsorata wasu suna rugawa suma. Sai da ya gaji da gudu tukun ya tsaya ya zauna a wata inuwa duk jikinshi yayi sharkaf da fitsari ga Gumi ga hawaye. lokacin bai ko san Umar na biye da shi ba. Da karasowar umar da zai tashi da gudu sai kuma ya tsaya da yaga Umar ne._

_Umar na zuwa ya fara tambayar sa "abokina wai ya haka naga ka fito a guje bayan dazun naji tana ihu".    "Dallah can ni rufe min baki ta gama ihu ko na gama ihu!.  Ashe kasan haka matar ka take da kartin Aljanu shine ka hadani da ita".  Umar yace "Abokina sai fa dana fada maka wannan matar Aljanu ne da ita kaki yarda. To yanzu miye abun yi danni gaskiya tsoran komawa ma nake yi".   Mujaheed yace "In dai kana da kudi wannan ba matsala bane akwai wasu 'yan bori da na sani aikin su kenan fidda aljanu nake gaya ma fit! Daya zasu fidda wannan Aljanar karamar kwaro ce ai.  Dan ko ni nan abunda yasa taci galaba a kai na ban shiryo bane........_
: _________________

_Mama Asiya zaune take suna hira ta fara jin wata murya na kiran ta.  "Aaaaasssssiyyyyaa!"   Da sauri ta waiga baya wayam ba kowa.  "Aaassiyya".   Ta kara juyawa ba kowa.  "Wai dan Allah bakwa jin ana kiran sunana?".  Ta tambaya gaba daya suka ce su basuji ba.  Tashi tayi ta nufi dakin ta wanda daga nan guraren ne take jin kiran.  Da bude kofar da wartar ta ciki duk daya.  Duk kibar ta kiiii!! Taji an jata bata ganin mai jan nata. kasa kofar kuwa ta koma ta rufe gam! Jikin bango aka makata.  Wash!  Ta fada. Wutar dakin ta fara rawa zuwa can kuma wata iriyar dariya marar dadin ji ta kaurade dakin.  Ahhhhhhhhhh!  Mama Asiya ta saki ihu!  Mai karfi hade da rufe kunnuwan ta.  An dan dau lokaci a haka ta rufe idan ta gam ta kuma toshe kunnuwa da hannaye. Zuwa can taji an tsaya da dariya wani abu taji na jika ta. Kamar ruwa.  Da sauri ta bude ido.  Ahhhhjh!  Ta kara sakin Ihu!  Jini ne gaba daya ya malaye dakin  tashi tayi tsabal!-tsabal tana taka kafa cikin jinin ta nufi kofa da nufin ta gudu.  Har ta kusan zuwa taji kamar an jawo kafafun ta shuuuu!  Sulbi ya kwashe ta ta koma. Hahahahaha! Taji dariya hade da wani irin gwalan gwalantu na fitowa daga Cikin wardrobe.  Karkarwa take duk ta rude kayan jikin ta sun koma jawur kamar wacce ta fito daga kwata. Tashi tayi ta nufi wardrobe din hannun na karkarwa ta bude. Ihu! Ta saki mai shegen kara Ahhhhhhjjhhhhjhhhhhhhhhh!.  Su mammiya ta zube a gurin..........................._

😰 *MUJAHEED* 😰
Karfin hali sata a jikin gawa.   Wato baka ma daku ba kenan.  Ai kuwa in dai Safuratu ce zata yi maganin ka...

πŸ‘» *MAMA ASIYA* πŸ‘»
Allah yasa yau ki daku ki kusan zaucewa ma

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 65-66

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

*GODIYA NAKE MASOYA*

JINJINA GA ALL MEMBERS NA
πŸ“š *ANSHOLLY NOVELS* πŸ“š
✍🏼 *KING BOY ISAH NOVELS* πŸ“š
_Na yaba da kaunar ku gare mu_

🌺 *HADIZA TUNAU(.* 🌺
Na ga sakoki Allah ya saka.

*IDDAH*

*MEERAH DANFODIO*

*MISS PRETTY*

*ZAYYNERB*

*SUWAIBA*

_Allah bazan iya lisSafo ku ba._

πŸ™‹πŸ»‍♂ *king dai Nata dago hannu masoyan Aljana wanda na sani dama wanda ban sani ba.* πŸ˜‰ Ana mugun tare

🀦🏻‍♂ _KUYI HAKURI DA DAN WANNAN PAGEN NIMA KAI NA NASAN YAYI KADAN.  WAYAR TAWA CE YAU KAMAR TA SHA GIYA SAI YANGA TAKE_

     *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Karkarwa take duk ta rude kayan jikin ta sun koma jawur kamar wacce ta fito daga kwata. Tashi tayi ta nufi wardrobe din hannun na karkarwa ta bude. Ihu! Ta saki mai shegen kara Ahhhhhhjjhhhhjhhhhhhhhhh!.  Su mammiya ta zube a gurin.~

_Ta dan dade a suman zuwa can ta farfado. A kwance kan gado ta tsinci kanta idanta a rufe sai kanta da take jin yana mata zogi.  Har zuwa yanzu bata bude ido ba kan ta dan dafa wash! Wash.Tana  Bude ido ta saki wani kara Ahhhhh!  Da sauri ta mike ta sauka kasa. Wata tsohuwa ce ta gani kwance a gefan ta tana mata murmushi fuska duk a yamutse.  "Wace ce ke?".  Mma Asiya ta tambaya.  Tsohuwar ta tashi zaune ta kalli Mama asiya ta wangale baki tayi mata dariya sai yanzu munin ta ya kara bayyana domin hakoran gaba duk babu su sun zube. Ga bakin jajur da shi kamar wacce taci danyan nama. Duk zaman da nayi gidan nan  baki sanni ba?.  Amma anyi yarinyar banza makaryaciya  nasha dazun kika wullani saman soro, To ni Aljana ce sunana Safuratu".

  _Karkarwa Mama Asiya ta farayi  baki na rawa "Daddadda dan Alllllah ki yyiiii  hakkkkuurrrri karkiiiii ki kashe ni".  Kwashe wa da dariya Aljana tayi tace "oh! Baki so in kashe ki ko?".  Da sauri Mama asiya da haryanzu ko'ina jikin ta karkarwa yake ta daga kai alamun eh.  "To shikenan kinyi alkawari duk abunda nasaki zakiyi a wunin yau?. Wannan shine zai kubutar dake kar in kashe ki". Mama Asiya ta zube kasa "Eh Wallahi na yarda duk abunda kika ce komai wuyar shi zanyi in dai bazaki taba min lafiyan jikina ba".     HHHHHHHHH Aljanar tayi dariya "To yanzu tashin farko maza tashi kije ki hau kan Soro ki daukko wa fatima 'yar babyn ta. Dama kince kiga uban da zai daukko ta to ba ubanda zai daukko ta sai ke maza tashi". Aljanar ta karashe maganar cikin tsawa ta kuma murtuke fuska. A razane mama Asiya ta tashi da sauri tubur-tubur da ita tazo ta wuce Su Hauwa dake falo. Zuwaira na ganin Mama Asiya a haka tace "Aunty Asiya lafiya kuwa?".  Juyowa tayi tace "Ina fa lafiya, ku dai da kuke lafiyan kuna da amm...".  Aljanar taga ta bayyana a Kan sofa kusa da Juwaira. Haba ai kuwa bata karashe maganar ba tayi waje a guje. Da fitar ta ta fara kira maigadi yana daki ya fito da sauri. "Yauwa aiken ka zanyi dan Allah jeka gidan Alhaji mudi ka karbo min aran kuranga. (Tsani)".  "To"  ya fada da sauri ya juya ya fita nan ya barta sai bari take ta kasa zama gu daya. Kai ta daga ta kalli gurin taga da dan nisa. "Kai amma fa hawa can gun zai min wuya anya kuwa zan hau".   A fili take yin maganar Wannan tsohuwar taga ta bullo "Bazaki hau ba kenan".    "A'a ni nama isa dama kawai fada nayi". Ta danyi murmushi mai wuyar gane ma'ana._

_Mai gadi ne ya shigo ba kuranga.  Mama Asiya na ganin sa bata ma tsaya jin  ta bakin sa ba kawai ta hau shi da masifa. "Kai dai musa mugun mashiririci ne. Ban ma taba ganin mai gadi irin ka ba, To ina abunda aka aike ka ka kawo din?. Ka wani dawo wa mutane hannun bibiyu baka san abun Emergency bane".  Shiru yayi har sai da ta kai aya tukun yace "Hajiya wai cewa sukayi An amsa aro ne sai dai wai muje gidan Naseer mu daukko".  "Ah!  To me kake jira kuma da bazaka je ka daukko din ba".   "Hajiya gaskiya ni kam bazan iya daukko wannan kurangar ni kadai ba. Tayi min nauyi".  Aljanar ta bayyana bayan Mai gadi tana hararta da sauri tace "Maza muje in  kamo ma mu daukko".    Mai gadi  yayi mamaki sosai shi tunani ma yake, ko mi za'ayi da kuranga bayan yasan ba wani gyara za'ayi ba yana san tambaya kuma yana tsoran masifa. Ko gyale Mama Asiya bata sako ba a haka suka je har can suka daukko kurangar sai wani sauri take saka shi, Bayan sunje aka aza kurangar a saitin gurin da zata hau din. Mai gadi ganin tana shirin hawa yace "Hajiya me za'a daukko miki bari in daukko miki".  Ta juyo kenan suka hada ido da Aljanar "A'a bari".  Ta fada lokacin ta fara hawa kurangar a hankali take tafiya gata lutuyi  ba dan kurangar karfe bace da ta ballata dan can kake hango ta tuli guda. Har tayi dan nisa ta waiwayo kasa. Tsoro ne ya kama ta ta fara karkarwa ji kakae ratsatsam!  Suka zubo kasa tare da kurangar.  Mama da jin haka sai gaba dayan mutanan dake  cikin gidan suka fito. "Lafiya! Lafiya" ake ta tambaya "Lafiya lumi".   Ta fada lokacin da ta mike ta fara kokarin mayar da kurangar. Mai gadi dake tsaye Dariya taci karfin sa tun yana matsewa har ya fara saka ta fara fitowa fili.  Yana 'yar dariyar ya nufo ta lokacin  tana kokarin hawa. "Hajiya na gaya miki kinyi nauyi bazaki iya hawa ba bari in hau in dauko miki.  Kama jaki haka Mama asiya ta harb mishi kafa ta kuwa ci sa'a ta same shi a baki ba wanda baiyi dariya ba a gun. Mama asiya a hankali ta hau  har can ta ta daukko 'yar tsanar har da jakara._

_Bayan ta sauko tace wa Mai gadi ya mayar ma da masu kuranga abunsu. Aljanar ce ta bullo "Kinyi kokari sosai, yanzu abunda  nake so dake shine ki Je kiyi wa diyar nan wanka ki mata kwalliya mai kyau irin ta amare in bakiyi ba kuma sai naci abunki". "To". Kawai su Zuwaira suka ji mama Asiya tace ta nufi daki da sauri rike da 'yar baby su dai basu ga wanda take magana da shi ba._
_____________________

_Umar ya kalli Mukhtar   yace Abokina yanzu dai bani da kudi a jikina amma idan kana da su ka ara min muje a daukko yan borin nan gwara a fidda Aljanar nan ko na sama zaman lafiya". Mukhtar yace "Ai kai ba a baka Rancen kudi ba ka ki biya da wuri amma ga kudi nan wurina kudin uwar gida ne dubu 20 Zan sayo mata fulawa da mai, kasan sana'ar ta kenan".  Umar yace "Haba abokina ai ka sani bama 'yar haka da kai Wallahi ina da kudi a gida yanzu haka ba dai ina tsoran Aljanar nan ba da munje na daukko. Amma tunda kai jarumi ne ko muje in kwatanta maka inda kudin suke ka daukko".  Da sauri Mukhtar yace "Kaiii! Amma kama raina min wayo waye zai yarda ya koma hannun Aljanar can.  Kaga tashi muje in ara maka kudin kawai".  Tashi sukayi suka hau mota basu zame ko ina ba sai wani kauye gida daya-daya. Tun daga farkon gari su Umar suka fara jiyo garaya kidan 'yan bori na tashi. Gidan suka nufa suna shiga suka iske masu kids daban masu rawar bori mata da maza daba. Sarkin borin wani dan gajeren mutun ne baki_

_Wani dan baki dashi sanye yake da wasu jajayen kaya jikin sa duk layoyi da guruka.  Ga wata hular gashi da ya da ya saka a kai sai ta kara mishi muni. Duna kenan sarkin 'yan bori na wannan yanki. da ganin su ya daga wa masu kidan Hannu duk sai suka dakata. "Mai ke tafe da ku?". Ya tambaya yana zazare musu idanu.  Mukhtar ne ya dan Risina ya dan kirara shi tukun yace "Mun kawo karar wata shedaniyar Aljana ce da ta takurawa wannan bawan Allah. Nine na bashi shawarar mu zo gurin ka nasan kai ne kadai zaka iya maganin ta. Aljana ce ta shiga jikin matarsa sai azbtar da shi take yi".    HHHHHHHHH Sarkin borin ya kece da mahaukaciyar dariya sai kawai suma fadawan sa suka fara yi sai da yayi mai isarsa su dai su Umar tsaye kawai suke suna kallan ikon Allah. "Shegiya 'yar mintsila tayi kamu".inji sarkin bori. Ya hade gira yace "'yar mintsila ce wannan aikin ku mai sauki ne bama sai naje da kai na ba yara na zan hada ku da su suje su fatatake ta. Ko jiya mun fitar da ita daga gida uku da take kokarin raba aure. Fatan a shirye kuke?".   Mukhtar yana dan murmushi yace "kwarai kuwa a shirye muke Sarkin bori".   Kudin aljihunsa ya fiddo ya ciri dubu biyar yaje ya ajiye agaban sarkin bori. HHHHHHHHHH Duna yayi dariya tukun yace Lalai wannan ashirye kuke.  Da mutane Biyar ya hadasu masu kida guda biyu 'yan bori uku.  Nan suka hayo mota suka nufo gidan Umar.   Tun daga zaure masu kidan suka fara kidan Su kuwa Masu borin kamar da gaske suka farayi sai hauka suke wai su gasu sunzo gida mai aljanu.  Shugaban yan borin da aka hado su da shi ne yace wasu umar su kulle gidan. Ai kuwa suka fita daga gidan daga waje suka garkame gidan da padlock. Safuratu abun mugun dariya ma ya bata ganin wannan  mutanan masu hauka wai sun zo wai su ita suka zo  fitarwa.  Fitowa tayi daga cikin dakin da sufar Rafy Sai dai idanunta Tsanwar shar._

_Ta kuma murtuke fuska ba abunda take bisu da shi sai harara. Da ganin haka masu ku kidan suka kara kaimi haka masu borin ma kara haukata sukayi har kusa da ita suke zuwa. Sun dade suna yi amma shiru basu ga wani sauye ba domin tsaye take cik! Sai zuba musu idanuwan ta masu abun tsoro.  Ganin rainin wayan su yana yawa yasa ta nuna daya daga cikin matan 'yan bori.  Wani iska ne ya fito daga hannun nata ya kwashi matar yayi sama da ita......................_

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*SU MUKHTAR ABUN HARDA MUGUNTA A KULLE 'YAN BORI DA ALJANA A GIDA*

πŸ˜πŸ˜‚
*MAMA ASIYA YAU AN ZAMA SOJAN SAMA*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boyπŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 67-68

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

~Ganin rainin wayan su yana yawa yasa ta nuna daya daga cikin matan 'yan bori.  Wani iska ne ya fito daga hannun nata ya kwashi matar yayi sama da ita...~

_*D*a ita ya dawo da ita kasa tum!.   Sannan ta mika hannunta ya zama wani zakalele  ta daukko abun da ake kidan duk ta farfasa su. Da ganin haka duk suka rude.  Rafy bacewa tayi ta koma daki taje ta daukko dorina. Suna tsatsaye kowa yasha jinin  jikin sa sai gani suka yi bulala ta fito daga daki ta nufo su ba tare da sunga mai rike da ita ba. Nan fa bulalar nan ta fara binsu daya bayan daya tana zane wa nan da nan gidan yacika da ihu! Ba abunda kake ji sai ihun su da kuma karar bulalar. Da gudu wani ya nufi kofa ya hau bubugawa yana cewa. "Ku bude, Ku bude zata kashe mu".  Saukar bulala yaji abunda yasa ya zabura kenan ya koma suka hau zagaye-zagaye Gaba daya sun rasa maboya. Su Umar najin Mutanen na ihu!  Amma suka ki bude haka makwabta duk lokacin wani ya fito ya tmbaya lafiya sai suce mishi "Babu komai ana dan wani aiki ne".  Umar kalli Mukhtar yace "Abokina ni fa ina tunanin Aljanar ce take dukan 'yan  borin nan. Kamar ihun bana mutum daya nake ji ba".  Mukhtar ya kalli Umar yace "Haba dai kamar dai wasu garori. Yo ai nake gaya maka wannan su aikin su kenan suna cire manyan aljanu ko sunkai dubu ne ma balle wannan kwara dayar kuma ma mace".  Umar dai baice komai ba.  Cikin gidan kuwa tuni tayi musu rudu-rudu wata mata ce daga cikin masu borin ta sake komawa wajen  kyauren da karfi take girgiza wa tana cewa "Dan Allah dan Annabi ku bude karta kashe mu wannan Aljanar ko kadan bata da imani".  Umar yace "kaji ko, To Wallahi gwara mu bude kar muyi kisan kai". Mukhtar ya kalle sa yace "Kai dai Wallahi ka cika naci to bari dai na bude ka ganwa idan ka, Ni dai nasan Aljanar ce ake suburbuda. Shine take neman agaji". Mukhtar  y fara bude kofa da cire kwado matar nan  ta fito a guje kamar an harbo ta. Ai kuwa duk da suna maza sai da ta bangaje su suka fadi har kasa. 'yan borin nan daya bayan daya suka ringa bi ta kansu daga karshe dai da kyar suka samu suka tashi suka rufawa 'yan borin baya. Wanda har yanzu dorinar bata dai na binsu tana  Shadar su haka yansa basu daina gudu ba.  A kasa suka je har kauyen. Sai da Safuratu taga an  kusan shiga kauyen tukun ta shafa musu lafiya ta koma gida._

_Da gudu suka ringa fadawa gidan sarkin bori haba wa wasu daga cikin masu kidan da masu borin duk wartsakewa sukayi  suka fara zabgawa a guje ganin mutane na shigowa a jere.  Shi kanshi sarkin borin kadan ya hana ya tashi ya gudu kawai dan dai kar  yaji kunya ne kuma yaga iya mutanen sa ne.  Har dubawa bayansu yake ko zaiga abunda ke biye da su shima yayi ta kansa amma bai gani ba.  Zubewa sukayi a gabansa sai huci sukeyi kowa yasha gudu hatta su Umar sun galabaita. "lafiya-lafiya!".  Sarkin bori ya fara tambaya ciki  su ba wanda ya iya daga baki yayi magana domin duk a wahalce suke. Sai zuwa can Mukhtar yace wa sarkin borin "Wallahi Aljanar ce duk taci ubansu ta farfasa kayan su. Bama wannan ba har nan ta biyo mu tun daga can  a kasa muka zo tana basu kashi.  Sai da suka zo bakin garin nan tukun ta koma".  HHHHHHHHHHHHH  Duna Sarkin bori ne ya ke ta kyalkyala dariya. Zuwa can kuma kamar dauke war nepa dif!  Ya dakata da dariyar ya murtuke fuska. Mikewa tsaye yayi ya fara magana.  "Shegiya 'yar mintsila, Ashe tasan wasa ma guri gare shi. Tasan da ta karaso nan. Kai da ta ma karaso garin nan da kwanan ta ya kare kenan  bama wahalta ta zanyi ba, Yaseen da kashe ta zanyi, Yo me ake da masu irin halinki 'yar mintsila". Gatsine-gatsine ya fara yi kamar wani mahaukaci. Mukhtar ya kalle shi yace "sarki yanzu miye abunyi?. kaga dai wannan bawan Allah 'yar mintsila ta hana su sakat! Ta hana su wali shi da matar sa...".  "Dakata malam".  Cikin daga murya sarkin bori ya fadi hakan. Shi kadai ya yata magana "To, Naji, Aa, Baza a kara ba, Sunyi kadan ko, hihihihihi, Zanja musu kunne".  Duk maganganun da yake shi kadai ne idanunsa kuma rufe._

_Bude idanu yayi fuskarsa a murtuke ya gallawa Mukhtar harara yace "Aikin banza, ai duk abunda yafu kune kuka ja domin kudi kadan ka bayar, Wannan dalilin ne ma yasa sarkin aljanun da muke aiki tare da shi yayi fushi lokacin da na aika yara na yaki  ya bisu, Dan haka sai kun karo kudi yanzu ni da kaina ma  zanje in furtume ta, Mintuna 5sunyi yawa tabar gidan".  Mukhtar ne ya kalli Umar da alamun yana so ya tambaye shine ya kara ko kuwa?. Umar da ya fahimci haka tun kafin Mukhtar yayi magana yace, "Sarkin bokaye in dai kudi me ba matsala. Mu dai gurin mu ta bar gidan".  Naira dubu biyar Umar ya karba a gun Mukhtar ya kara musu. Amma sarkin bori yace Sai dai Goma.  Ba yanda suka iya dubu goma suka kara mishi kudin wajen sa suka zama 15K.  Shiri sosai sarkin bori yayi layoyi da turaren magani. Ha tayar da mutum Kusan goma daga cikin yaran shi Masu Kida da masu borin.  Duk da yasan wajen akwai nisa amma da isa da takama da nuna shi sarkin borin ne a kasa ya taho.  Mutum biyu rike da kasko hayaki na tashi daya bayanshi daya a gabanshi.  A haka suka nufi gidan umar........._

___________________
_Mama asiya da sauri ta karasa ban dakin ta. Ta farawa 'yar baby wanka. Tana cikin gurza mata soso kawai sai kan ya kille. Mama Asiya juyawa tayi gabas da yama kudu da arewa bata ga Aljanar ba ga kuma kan 'yar babyn a hannunta.   Tsoro ne duk ya kamata tama rasa abunyi nan ta fara kokarin mayar dashi amma daga ta lika sai ya fado.  Suuuuuuuuuu!  Taji wani kara hade da iska a bayanta  a tsorace ta juya. Tsohuwar nan ta gani tsaye cikin wata doguwar jan riga yanzu tama fi muni ga abun tsoro idan nata sunyi wani kwala-kwala gasu jajaye farin ba yawa.  Fuskar duk a jagule take abun tsoro da kyama. Mama Asiya karkarwa take domin ta tsorata sosai.  "Kiiii kii yi haaakuuurii Da dada dama".  Matar ce ta daka mata tsawa "Munafuka ba abunda zaki gaya min harda wani karkarwa. Ashe dama haushin Babyn nan kike ji ko? Gashi kin dai cire mata kai da gangan".   Da sauri Mama Asiya tace,  "A',a Wallahi ina mata wanka ne ya fita. Kiyi hakuri please".   "Kina so in hakura?!.  "Eh". Mama asiya ta fada da sauri. "In kina so in hakura to ajiye 'yar babyn ki jiyo". Da sauri ta ajiye 'yar babyn a saman Bath din, ta juya suka fuskanci juna da Aljanar. "Ba wani abu mai wuya bane kawai kuka da dariya nake so ki min a lokaci daya. In bakiyi ba kuma yaseen sai na maida ki kuli-kuli"._

_Dajin haka mama Asiya ta fara. Hahahahaha wiiiiiii wiiiiiii hahahaha yiiii yiiiii Hahahahaha Uhmmm uhmmm hahahaha.  Ta dade tana yi Aljanar ce ta Wanke ta da mari Tats!! "Dan ubanki haka ake kuka dama a garin ku ba hawaye?".   Zafin marin da mugun takaici sune suka saka Mama Asiya kukan gaske hawaye suka fara kwaranya.  "Yauwa haba ko ke fa. Yanzu naga kina kukan gaskiya sauran kuma Dariya".   Mama Asiya da tuni kuka yaci karfin ta rasa ya zatayi dariyar tayi. Hakan yasa ta kama Bude hakori tana yak'e.  Da gani haka Aljanar tace "Wannan ai ba Dariya bace maza yiwa kanki chakulkuli. Kiyi Dariya".  Chakulkulo tahau yi wa kanta Ta karfi da yaji sai da dariyar ta zo mata ta hada da kukan tana yi. Aljanar kanta abun ya bata Dariya Hakan yasa tace wa mama Asiya "Oya yanzu na yafe miki kuma na gyara kan  babyn juya kici gaba da mata wankan".  Da fadar haka ta bace, Ita kuwa mama Asiya ta juya taci gaba da wa 'yar baby wanka.   Safuratu a wani  *KURMIN DAJI* ta bullo ba abunda take sai Dariya.   Mama Asiya bayan ta gama mawa 'yar tsanar wanka ta tsane ta tas!. Taje da ita gaban mirror ta fara mata kwalliya.  Irin kwalliyar da Asiya ta tsaya ta tsara wa 'yar babyn ko ita kanta bata taba  yin ta ba._

_Ji tayi kawai 'yar babyn tace "Daukko zani ki goyani". Da sauri Mama Asiya ta bude wardrobe ta daukko zani tazo zata goya ta kenan taji tace, "Yaseen kin ma mugun Rainani, Da wannan tsohon zanin zaki goyi gimbiya guda?. Maza ki daukko sabo". Komawa tayi ta daukko sabo a cikin kayanta wanda bata ko taba sawa bama, Tazo ta goya 'yar habyn da goya ta kawai sai ji tayi ta kama kuka.  Mama Asiya tsuru tayi jira kawai taji me yasaka ta kukan. Wani mugun tsunkuli taji an mata wanda har sai da tayi 'yar kara. "Shegiya muguwa wato kina ji ina kuka shine baza ki ringa jijiga ni irin "yanda ake wa jariri ba ko?.  Maza fita dani ki ringa jijiga ni ko nayi shiru".  Da fadar haka 'yar babun taci gaba da kuka. Ai kuwa mama Asiya ta hau jijiga da lalashi kamar ta sama jaririn gaske.  Su Zuwaira na falo suna hira. Kawai sai ganin Mama Asiya sukaye ta fito daga dakin ta goye da 'yar baby Sai faman jijigata take tana fadar "Yi shiru- Yi shiru. su basa ko jin.........................._

😰 *Yaseen na gaji

πŸ˜‚ MAMA ASIYA πŸ˜‚ *RENAN DOLE YA SAMU...*

😧 *SARKIN BORI DUNA* 😰

An nufo gidan Umar.  Allah yass kai ma a raka ka har gida kamar yanda akawa yaranka πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 69-70

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

πŸŽ€πŸŽ€
*BADDEEYERH*
               πŸŽ€πŸŽ€

Written; *BEAUTY QUEEN*
πŸ€™πŸ½ _JA MUJE GWANA TA. ALLAH YA KARA BASIRA DA FASAHA. KINYI ABUN A YABA. TABBAS MUTANE ZASU KARU DAKE SOSAI. KICI GABA KUMA KI MAIDA HANKALI WAJEN ZAKULO IRI-IREN MATSALOLIN NAN DAKE ADDABAR MU A WANNAN ZAMANI. HAKIKA DA YAWA ZASU HANKALU TA DALILIN LITTAFIN_

πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
*ZUBAR HAWAYE*

Written by. *ZEETTY*

Cogrt Sis kinyi rawar gani, Kinyi abun azo a gani.  ZUBAR HAWAYE.

BABBAN DARASIN DA KE CIKI.
_GARE KU SAMARI MAYAUDARA. FATAN IN KUKA KARANTA LABARIN NAN ZAKU HANKALU KU GUJE YAUDARA. SHIN KUNSAN YAYA TA KWASHE DA AHMED AMARYARSA DA FEEDO?_

_MASU SOYAYYAR_ SHAN MINTI.πŸ€” _KU BAKU TUNANIN NAKU YAN UWA MATA IDAN KAGA ANAYI DA KANWAR KA ZAKAJI DADI?.  KUMA MATA AI DA LAIFIN KU SHIN IDAN KIKA KI AMINCEWA ZAI MIKI DOLE NE? IDAN KUMA YA DAI NA ZUWA GURIN KI RASA MIJIN AURE ZAKIYI NE?. UHMMM ZEETTY TAYI KARIN HASKE A LITTAFIN NAN NATA ZUBAR HAWAYE_

πŸ€— ZAMANI NA ALFAHARI DA KU. MUNA JIRAN SABABBIN LITTAFAN KU

πŸ’ƒπŸΌ KU BANI KIDAN BIRTHDAY A SAMAπŸ’ƒπŸΌ
πŸ—£MASU GUDU SU GUDU

πŸ’ƒπŸΌ YAU BIRTHDAY QUEEN NE MUKE KU SANI πŸ’ƒπŸΌ
πŸ—£MASU GUDU SU GUDU

πŸ’ƒπŸΌ BIRTHDAY HAUSY FA DAN KU SANI πŸ’ƒπŸΌ
πŸ—£MASU GUDU SU GUDU

πŸ’ƒπŸΌ DUK ZAMANI MUNA MURNAπŸ’ƒπŸΌ
πŸ—£MASU GUDU SU GUDU

πŸ’ƒπŸΌ NI NE RARA NAZO IN FADIπŸ’ƒπŸΌ
πŸ—£MASU GUDU SU GUDU

πŸ’ƒπŸΌ ALJANA TA ZO BIRTHDAY, KUJI YA πŸ’ƒπŸΌ
πŸ—£MASU GUDU SU GUDU
πŸŽ‚πŸŽ‚πŸ°πŸ°
πŸ€— *HAPPY BIRTHDAY TO YOU MY QUEEN HAUWA HAUSY* 😘

*Ina Wishing u More Albarka Years Ahead Dear.* 😘

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Kawai sai ganin Mama Asiya sukaye ta fito daga dakin ta goye da 'yar baby Sai faman jijigata take tana fadar "Yi shiru- Yi shiru. su basa ko jin.~

_Tafe yake jama'ar na binshi baya har da su Umar sune masu gwada mishi hanya.   Har kofar gidan, Kaskon Hayakin  ya karba ya fara shiga gidan  sannan yaranshi suka rufa mishi baya, Su Umar kam a tsorace suke sai da suka bari kowa ya shiga tukun da labe-labe suka shigo a hakan ma suka tsaya a bakin kofa.  Sarkin bori tsaye yayi a tsakar gidan yana wani zazarr ido yana waige-waige cikin tarwatu Da gagautawa ya fara cewa yaransa "Kuyi sauri ku kukuna hayakin nan ga shegiyar nan tana fama ta gudu, Kuyi sauri, Kuyi sauri". Da sauri yaran nashi suka daukko wani kullin magani suka zuba a kaskwayan  kusan guda shida aka kunnawa wuta. Ai kuwa hayaki ya cika gidan ba abunda kake ji sai tarin su, Gaba daya har sarkin borin. Su Umar kuwa dajin haka sukayi waje nan makwabta 'yan gaf! Da gidan su suka fara fitowa suna mishi masifa. Shima dake ya iya Mukhtar ya kama mishi suka ta  Bala'i da 'yan anguwa. Sarkin bori da yaji ba haza hayaki na neman illata su da sauri yake cewa "Ku kashe-Ku kashe, Ai ga Aljanar nan ma har mun sumar da ita, Yanzu karasa ta kawai zamuyi_

_Ruwa aka debo aka kwarayawa kaskunan suka mutu. Safuratu na dakin tana jinsu duk abunda Suke ta kyale su. Sarkin bori yasa aka fara kida. Nan da nan Suka fara bori Har shi din sai wani girgiza kai yake, Bori suka cika gidan sunayi. Aljanar ce ta fito yanda taga gaba dayan su sun haukace kowa da irin haukan da yake, Wasu har tsalle suke su fado kasa.  Kawai sai abun ya bata dariya, ji tayi kawai tana so ta gwada taga shin borin gaskiya ne ko kuwa iskanci ne.  Wasu mata ta kalle su uku sai bori suke A cikin su har da mai kwantawa kasa tana malolowa.Safuratu ta saura zuwa wani make ken Kadangare irin jankwatakwalan nan.  Da gudun tsiya kadangaren ya nufi matar nan mai birgima a kasa tana bori.  Tana kyalla ido ta ganshi haba wa sai ta saki ihu! Ta tashi a guje Taje tana kokarin Kama katanga ta haura. kamar ba ita ke bori ba Haka sauran matan ma da ganin kadangaren suka wartsake suka tashi zasu tsere.  Sama ko kasa su kuwa su Sarkin bori basu ko ga kadangaren ba. "Mine ne?-mine ne?".  Sarkin Bori ya ke tambayar Ruzaina wacce ta nufi katanga tana kokarin haurawa. Juyowa tayi tana dube-duben ba ko alamar Bori a  tare da ita. "Kadangare na gani ya nufo ni".  Cikin masifa sarkin bori yace "Kadangaren banza kadangaren Wohi!. Ai yanzu gashi kin bata mana aiki. Ga Aljanar har ta fara kuka, tana Bani hakuri tana cewa in kyale ta in mata Rai. Aiki yayi nisa Amma kin dawo damu baya".  "Ayi hakuri sarkin sarakunan 'yan bori, Kadangaren ne ya tsorata ni".   Dakuwa ya mata "Kinci ubanki ke da kadangaren. Yo ni ba kadangare ba ko zaki na gani ina bori ai bazan ma kula da shi ba". Yana fadar haka yayi tsaki ya juya yace aci gaba da kidi. Nan fa suka dora daga inda suka tsaya._

_Aljanar ta ji maganar da Sarkin bori yayi, Ai kuwa tace bari mu gani sarkin bori yana tsakar haukansa ta bori yayi tsalle ya fado kasa dabar! kenan yaji maciji a wuyansa kamar an cillo shi. Ihu! Ya fara yi yana kokarin kankare macijin a wuyansa. Da sauri macijin ya nanade sa cikin hanzari. Yaransa masu bori tsayawa sukayi yana kallansa kawai domin su basa ganin macijin. Haka Su Umar sun kwalalo mishi idanu.  Macijin Ta gabanshi ya zagayo ya fasa kai dai-dai fuskar Sarkin borin. Shaaaaaa! Kake ji Sarkin bori ya saki fitsari. "Dan Allah kayi hakuri karka sare ni Wallahi na daina". Waaaaa! waaaaaa!  Ihu! Sarkin bori yaci gaba da yi. Sulalewa macijin yayi ya sauka ya nufi wani waje. Sarkin bori yayi ajiyar zuciya Hade da cewa "Wash!!" Sai yanzu ma ya lurada idanuwan da aka zubo mishi kowa bakin sa da Alama dauke yake da tambaya. Wani ne daga cikin masu kidan ya nufi gurin sarkin bori yana tambaya lafiya?. Sarkin bori da jin haka sai abun ya bashi mamaki wannan ya tabbatar mishi da cewa basu ma ga Macijin ba. Hakan tasa ya tashi ya takarkare ya bushe da Dariya.tukun yace "Yau naga sakarkari Wai dama duk borin da kuke baku taba ganin nayi kalar wannan ba?". Kamar hadin baki sukace "Ina fa muka taba gani sarki".  Dan murmushi yayi tukun yace "Karku damu zan koya muku. Yanzu aci gaba da gashi, Aljanar nan karshen ta ya zo, Yanzun nan ta tashi ta gudu daki. Dan haka yanzu zan bita inci ubanta"  Su Umar ya kalla tukun yace, "Kashe ta kuke so ayi ko korar ta?"._

_Da sauri Umar yace, "Haba a kashe 'yar banza kawai, Me ake da wannan shedaniyar Aljana".  Sarkin bori yace, "Ok ku saka kubobin ku rufe gidan dan ma kar ta sama wajen guduwa in na furtumo ta daga daki".  Shiri ya shiga yi ya dauki karin layoyi ya nufi dakin.  A hankali ya dan daga labulen ya leka. Da lekawa kuwa akayi charaf! Da kan aka rike. Nan fa ya fara kokarin kwato kanshi, Da ake faman janshi cikin dakin. Hannu yasa a kufar dakin yana cicije wa amma ina. Sai da aka ja shi cikin dakin da karfi._

_Kii! Ake janshi kasa ana zagaye tsakar dakin da shi. Tun yana shiru har ya fara Ihu! Domin da gudu ake janshi bayanshi na gurzuwa a kasa.  Har yanzu baiga mai jan nashi ba. Ji yayi an kama kafarshi daya anyi sama da ita kamar wani dan akuyan da ake Fida. Kanshi na kasa yana reto,Wata irin Dariya ce marar dadin ji ta kaurade dakin, Magana akayi wacce bazaka ce gata bangaren da ta fito ba a dakin, Cikin wata Siririyar murya "Wai kai  sarkin bori ko".  "Kwarai ni ne sarkin bori".  Ya fada yana cicira ido duk a tsorace yake.  Saukar Tagwayen marika yaje a fuskar Tas! Tas!. Maganar sake ji "Kai ne sarkin bori ko".  Da sauri yace, "A'a Wallahi bani bane, Ni sunana Duna".  Wani Saukar marin yaje, Abunda ya sashi saurin cewa. "Wallahi sunana na gaskiya mamuda". Cikin Tsoro da tashin hankali yake maganar.  Hhhhhhhhhh! "Makaryacin banza makaryacin Woofi! Wai kai sarkin bori kazo ka fidda Aljana ko kama kashe ta kace ko?".  "Aa Yaseen kawai ina fadar haka ne amma a zuciya ta nufina in na ganki in miki Nasiha  ince ki fita ki bar musu gidan su".   Cikin Tsawa yaji Ance Rufe min baki, Dan iskan Karya kawai, Ai naga duk abunda kake da idanuna. wai ni in tambaye kama Me yasa ka farq bori har kazo ka zama sarki".  "Wallahi tallahi Sharrin shedan ne".  Kayau! Aka sake wanke shi da mari. "Munafuki, Ai kai ne shedan yanzu kuma tunada ka tara yaran mutane maza da mata, Kana koya musu wani haukan banza wai bori.Yanzu abunda nake sanka da shi, Shine ka biya su Umar kudin su sannan kuma daga yau ka ajiye bori haka suma yaranka, In kuwa bakayi haka ba to fa ba kai bs zaman lafiya"._

_"Zanyi kamar yanda kika ce kuma nayi miki alkawari na dai na bori sai dai ma in ringa wa masu bori Wa'azi su bar bori".  Dim! Aka saki kafarsa ya fado kasa, Da ganin haka ya tashi ya fita a guje. Har yanzu yaranshi kidan bori kawai suke ba abunda yasha musu kai. Dakatar da su yayi yaje ya bawa su Umar kudin su yace musu Ai yama kashe Aljanar amma kyauta yayi baya san kudin. Lafiyayun mari aka mar har biyu. "Kan uba! Wannan shine SAKAMAKON ALHERIN? naga dai ni kyauta nayi muku Amma shine zaku mare ni?"  Sukam tsayawa kawai sukayi suna kallansa.  A bayan Umar wata mumunar Aljanar marar kyan fasali mai shegen abun tsoro ta bayyana, Sarkin bori take harara da wasu manya-manyan idanunta, Karkarwa ya hau yi Jiki na bari ya juya. "Daga yau ina so in gaya muku cewa na daina bori Ba ruwana da maiyin bori. Sannan kuma kudin ma ina so in kara tunatar muka da cewa wannan ba hanya mai bullewa bace, Ku tuba ku dai na bori kuma daga yau kamar yanda nayi".  Nan sarkin bori ya fara cire kayan borin layoyi da guruka.  "Shirman banza shirman wofi! Wannan ai maganar banza ce, To in mun bar bori wacce uwar zamuyi. Kaga in bazaka iya ba kawai ka sanfe ni fa dama na dade ina mafarkin hawa karagar nan taka ta sarkin bori Sai yau ga... Marin da aka dauke shi da shine ya dakatar da shi. Juye-juye y fara yi "Cikin ku uban waye ya mare ni?". Gaba daya suka ce basu bane.  "Au! Dan nace bazan dai na bori ba shine k turo Aljana ya mare ni. To bazan dai naba din kuma bori yanzu ma na fara". Ya juya ga sauran Yan uwansa yace "duk wanda yake tare dani ya daga hannu", Kafin kace me gaba daya suka dadaga hannunwa. Da faruwar haka sai ji kake Fass! Fass! Dum! Dum! Mari da kulli ta ko'ina kai musu ake ba tare da sunga mai dukan nasu ba..............._

🀧πŸ˜ͺ MURA
*KWANA BIYUN NAN SAI KUYI SORRY. ABUBUWA BIYUN SUN HADE GA DAUREN AURE GOBE. GA WATA MURA SABON KAMU. IN GAYA MUKU WANNAN PAGEN TUN JIYA NAKE RUBUTA SHI. WANI ABUN MAMAKI DAGA NA FARA RUBUTU SAI BARCI YA KWASHE NI.HHH YASEEN KUSAN SAU UKU ANA HAKA. TO DAI IN KUNJI NI SHIRU KU MIN UZURI. DAN YANZU HAKA MURA TAUNANA TAKE.'YAN ZUWA DUBIYA KAR A MANTA DAI DA KAN RAGO. LOLZ*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boyπŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 71-72

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

😭😭😭  KING BOY NAYI KUKAN RABUWAR MU  DAKE NI FA BAN SO BA.  RAI NA YANA RADADI NI DAKE GASHI ZAMUYI BANKWANA SAI WATA RAN! 😭😭😭
🚢🏻

DEDICATED TO YOU 😘 AMΓ†L  NA GODE DA ADDUO'IN KI GARE NI ZAN IYA CEWA KINFI KOWA KAGUWA AKAN LITTAFIN NAN.πŸ™Š AU! ASHE FA NAKIN NA SANI BANSAN NA WASU BA. πŸ™‹πŸ»‍♂ JAMA'A NA GODE DA ADDUO'I  BAZAKU LISSAFU BA DANA LISSAFA. 😘 ANA MUGUN TARE 🀝

πŸ‘― NA GODE AL'UMA NA GODE. NA KARA MUKU GODIYA MATAN KU DA MAZAN KU. KING BOY ISAH, GANI INAI MAKU BAITIN GODE WA, KU FADA NA GODE. πŸ‘―

πŸ‘¦πŸ» 🎼🎀 BAN RAINA ADDU'A DA KUKAI TA YI MINI BA

πŸ‘§πŸ» 🎼🎀 MUN GODE 'YAN UWA

πŸ‘¦πŸ»πŸŽΌπŸŽ€ NAI KUKA HAR NA ZUBDA 'YAR KWALLA.

πŸ‘§πŸ»πŸŽΌπŸŽ€ MUN GODEEE

πŸ‘¦πŸ»πŸŽΌπŸŽ€ NAGA YANDA MASOYA SUN KA MIN JAJE

πŸ‘§πŸ» 🎼🎀 MUN GODE 'YAN UWA

πŸ‘¦πŸ»πŸŽΌπŸŽ€ CUTA BA MUTUWA BA HAKAN NA FADA

πŸ‘§πŸ» 🎼🎀 MUN GODEE

πŸ‘¦πŸ»πŸŽΌπŸŽ€ DUBI YANDA NA KOMA DUK NA RARAME πŸ™Š...

πŸ‘¦πŸ»πŸŽΌπŸŽ€ NA GODE KU FADA.

πŸ‘§πŸ» 🎼🎀 MUN GODE 'YAN UWAπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ

ALHMDULILAHI ALAH KULLI HALIN. πŸ™πŸ»‍♂

*HAUSAWA CUNCE CIWO BA MUTUWA BA.  NA DAWO YAU DAGA JINYAR 'YAN KWANAKI WACCE NAYI. ALLAH YA BANI LAFIYA, SAI DAN ABUNDA BARA A RASA BA. NA GODE DA ADDUO'IN KU A GARE NI. ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI. NASAN KUNYI MISSING NAWA KAMAR YANDA NIMA NAYI NAKU.* 😘 NA DAWO GARE KU ABOKAI. ACI GABA DA GASHI, πŸ™„ AMMA FA BA *ALJANAR FATIMA* CE BA TA SHAKE NI. 😘 INA KAUNAR KU MASOYA NA. 🀑

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Kafin kace me gaba daya suka dadaga hannunwa. Da faruwar haka sai ji kake Fass! Fass! Dum! Dum! Mari da kulli ta ko'ina kai musu ake ba tare da sunga mai dukan nasu ba.~

_*N* an fa kowa ya fara neman wajen tsira, Wasu suka nufi kofa wasu kuma katangu suke kamawa da nufin su tsallaka gidan makwabta. Sai dai duk wanda ya nufi kofa kafin ya karasa gurin sai yaji an turo shi da karfi sosai.  Wanda kuma suke kokarin hawa katanga sai sun kama kawai suji an jawo kafar mutum yayo kasa. Umar Muktar da sarkin bori su kadai ne ba'a maka.  Suma kuwa sun sama wajen sunyi tsugunnin biri Najin sanyi.  "Kaiiii!  Kowa ya dakata a inda yake ya kuma saurare ni" Cikin wata muguwar tsawa mai kamada maganar basamude suka ji anyi maganar. Tsi! Kowa ya tsaya inda yake suka hau waige-waige matan kuwa tuni har sun fara kuka suna dora hannun a ka!.  "Nasan zuwa yanzu kunnuwan ku ba abunda suke bukata sai sanin waye mai magana sannan gangunan jikin ku ya zuwq yanzu sun mika wuya neman ceto kawai suke daga duka da mari.  Ba wani bane mai dukan ku kuma ba wani bane mai magana. Sai Aljanar da kuka zo gidan nan domin ku kore ta ko ku kashe ta. To in kun shirya bari in bayyana ku kashe ni". Haba wa da fadar haka suka fara zubewa kasa ba abunda kake ji sai bada hakuri magiya da Neman afuwa. "Munahikan banza wato kunsan bazaku iya ba kuma kuka tarka?, Ai ni a zato na_

_Gaskiya dokin karfe ce Ko ku dubu kuka hau bazai karye ba. Ba’kon munafuki ba na mutum ‘daya ba ne". Dan haka daga yau ina umartar ku gaba daya da ku daina bori in kuwa Bah...".    Da sauri suka fara "Wallahi mun  daina daga yau, Dama  duk abun karya ne".  Hahahhahahaha ta saki wata uwar dariya.  Kofar gidan suka ta bude da kanta. "Na bude muku gidan, Kuzo ku wuce kuma daga nan idan kuka fara gudu bana so ku tsaya a ko'ina sai a garin ku. Ko hutawa ban yarda kuyi ba. Sannan zan dinga bin didigen ku. Duk wanda ya yarda ya koma borin karyar nan to fa kwanan sa ya kare". Hhhhhahaha Tayi dariya, A guje suka ringa fita gaba daya har su umar din.  Sarkin bori a gaba sai tika uban gudu yake, Bayan shi kuma jama'ar sa ne. Su Umar kama tuni sun sabe.  Matai makin sarkin borin ne ya tsaya. "Kai ku dakata Ni fa yaseen bazan iya tafiyar nan a guje ba. Haba kawai asaka mutane gudu kamar wanda 'yan BH  suka tasi gaba. Kunga kawai mu tafi a hankali abun mu, Kai idan muka sama mota ni da kai ma ma zan biya mana kudi mu hau".  Da gama fadar haka suka hau shewa suna fadin "Sai oga".  Alamun dai maganar tashi tayi musu dadi.  A hankali suka tafi suna hira abunsu. Shi kuwa sarkin bori tuni yayi nisa sai gudu yake. Kamar ance wa daya daga cikin su ya waiga baya.  Haba yana juwa kuwa ya hangi wasu bak'ak'en karnuka wanda yawan su sunkai ashirin.  Ko wanne sai fiddo harshe yake gasu da masifar gudu.  Ai bai ko tsaya gaya ma su oga ba, A million ya zabga a guje ya wuce su.  Da ganin  haka sai sauran suka juyo.  Lokacin kuwa karnukan sun kusa karasowa. Duk wanda ya juya yaga karnukan nan sai ya ari ya kare. Kafin dan wani lokacin sai gasu sun isko sarkin bori a hanya. Karnuka na biye da su baya. Ko da sarkin bori ya juya shima yaga mugun abun da ke biye da Jama'ar tasa. Haba shima sai giya ta tsinke. Gudu kamar wanda yaci kafar  barewa._

_____________________

_Mama Asiya sarfa da marwa take kawai a falo tana jijiga diyar roba tana fadin, "Yi shiru-Yi shiru".  Su Zuwaira suka bushe da Dariya harda dage kafa.  Hauwa bayan ta dan tsagaita da dariyar tace "Aunty Ladiya kuwa ?".  Harara ta watso mata ba tare da Tayi musu magana ba.  Zuwaira tace "Allah ina tunanin ba lafiya, Baki ga wai 'yar babyn Fatima bace a bayan nata".  "Humm Na gani mana yau kam, Ina ga wata sabuwar kauna ce ta kullu tsakanin Fatima da Aunty Asiya".  Nan ma harare ta wullo musu. Daga bayan ta taji 'yar tsanar tace "Yunwa nake ji zansha madara".   "To, To".  Mama Asiya ta fada lokacin ta nufi dakinta da sauri.  Wata sauran madara da tasha jiya ta daukko ta sauke 'yar babyn kafin ta dungura mata kofin a saitin bakinta.  Kafin kiftawar ido taga ba komai cikin kofin, Mamaki ne da tsoro suka ziyarce ta a lokaci daya domin har kara daga kofin take tana leka kasar kamar wata sokuwa.  Shaaaaa 'yar babyn tayi aman duk madarar. Mama Asiya bata san hauwa ba bata san sauka ba sai ji tayi an dauke ta da mari mai karfe. Da sauri ta dafe kumatun ta. Da wata siririyar murya babyn ta fara magana.  "Muguwa azzaluma kinsan madarar ba sanyi shine zaki bani?.  Wato ke gaki 'yar bak'in ciki in sha in mutu, To ta Allah b taki ba".   Mama Asiya cikin kuka-kuka "Dan Allah kiyi hakuri, Naga sanyi sanyi ake shiyasa ma bansa ta...". Rufe min baki yanzu tashi ki goye ni mu fita waje tsakar gida. Dan iska nake so insha". Mama Asiya jiki na rawa ta dauki 'Yar babyn ta goya ta nufi waje. Su Hauwa na ganin ta wuce suka kara kwashe wa da Dariya. Juyowa tayi a fusace "Zanci kaniyar mutum Wallahi, Kaji 'yan iskan karya".  Lokacin ta juyo ta dawo gaban su. "In da wacce ta isa ta sake yi min Dariyar".  Shiru sukayi kowa ta matse Dariyar.  Mama Asiya na tsaye gaban su sai surfa masifa take. Bayan ta taji wani mugun tsunkuli  kamar za'a ciro fatar jikin ta.  Ihuu tayib"Wayyo bayana". Ba shiri ta juya sauri-sauri gudu-gudu ta bar falon._

_Da isa tsakar gida Sai ganin matar nan tayi tsaye sai harare  ta take, Yanzu kuwa tama fi abun tsoro. Idanunta sun wani kara girma. Girman da ya haura ka'ida. Da wata iriyar murya, marar dadin ji matar ta nuna wani bango wanda wajen yayi dukun-dukun da datti. Fetin Yellow ne amma an mayar da gun ja. "Waya mayar da wajen can ja haka?".  Jiki na karkarwa Mama Asiya tace "Wannan shegiyar fatim...". Da sauri ta rike bakin ta. Kafin sunan ya idasa fitowa. Dum!  Taji dundu a bayanta mai karfi. "Munahika ke wato kamai na gidan nan 'yar marainiyar nan kike likawa ko. To naji ita ta bata gun ni kuwa nace kije ki sa soso da sabulu ki wanke bango ya fita tas!". "Aummm! Ummmm Naaaan Ceee baaaaaa". Inina ta fara yi cike da tsoro domin jin uban aikin da aka tsiro mata da shi, wanda ita kuwa bata saba da wahala ba. Nan dai take tsaye, Ita kuwa matar ta bace. Mama Asiya ta kalli bangon wajen da dan tsayi ji tayi kamar ta fashe da kuka.  Cikin gunguni take cewa. "Shikenana yanzu rayuwa ta zama abunda ta zama. Duk wanda yaga ya fika karfi sai yata zaluntar ka. Wallahi ni dai Allah,..".  Cikin wata tsawa wacce sai da cikinta ya kada. "Keeee wai ba aiki na saka ki ba".  Haba da jin hka mama Asiya ta rude. Da sauri ta nufi wajen tanki ta dauko boki ta cika da ruwa Dubi-tubi ta kai wajen bangon ta ajiye.  Mai gadi na daga can kan dan benchin sa kallanta kawai yake, sai tunani yake ya gaza gano me hajiya take shirin yi. Mama Asiya taje ta daukko wani dan karamin bokitin tasa soso ta kada kumfa duk abunda take 'yar babyn Fatima na goye a bayanta. Sosan ta dora jikin bango ta fara gogawa. Da ganin haka mai gadi ya taso da gudu yana fadin  "Dakata Dakata hajiya".  Tsaye ta mike tana aika mishi wani mugun kallo ranta a bace.  Yana kara sowa gurin ta ya fara cewa "Hajiya me kike shirin yi ne haka. Naga dai alhaji yana iyakar kokarin shi kusan ko wacce shekara sai ya canza fenti yanzu haka ma nasan yana gaf! Da canza wa..."  Hannu ta daga mishi hade da dan juya mai fuska "Ya isa haka dan Allah.  Ko na kira ka ne da zaka zo ka fara jawo min wannan doguwar aya da tun kafin ka shigo gidan nan na harda ce ta harar yafi a kirga?. Malam koma kayi aikin dake ganka ka barni inyi nawa aikin"._

_Da gama fadar haka ta tsoma soso cikin kunfa ta juya taci gaba da dirzar bango. "Haba Hajiya ko dai aikin nan ya zama dole ne ai bake ya kamata kiyi  shi ba tunda gamu a gida". Bata ko kula shi ba sai kara da dagewa tayi ta kara kaimi wajen dirzar bangon ta.  Mai gadi  ya kara matsawa domin ya karba yaci gaba. Wani wawan duka ta kawo mishi, Takuwa ci sa'a ta same shi a wuya gata dama abu ga mai jiki. Mai gadi ihu ya kwada ya nufi cikin falo yana fadar "Jama'a gida ku fito Hajiya ta haukace". Juyawa tayi ta harare shi tace, "Shege dan sa ido kadan nayi ma. Allah yasa ka kuma dawowa".  Hauwa Zuwaira da sauran 'yan kananan  yara duk akayo waje. Su hauwa abun Dariya ya basu amma sai suka basar. "Haba Aunty Asiya miye kike haka kamar wacce ta sama tabuwa, Bango ne fa kike wanke wa".  Zuwaira ce ta fadi haka lokacin da ta dan matsa kusa da Asiya din.  Mama Asiya ko kallanta batayi ba kawai aikin ta take tukuru. Hauwa'u ta kalli  Zuwaira tace "Gaske fa aunty wannan ba abun kyale wa bane kina ganin fa abun yaci gaba, Mama Asiya hauka kawai take a yi gagawar nemo malami y duba ta...". Sakin aikin da take tayi ta nufo Hauwa tana nun mata yatsa.  "Inji uban yace na haukace, Gaya min ko kuma ke ma yanzu inyi kasa- kasa dake a nan wajen".  Da sauri Hauwa ta boye bayan Zuwaira tana bada hakuri.  "To kiji in gaya miki  lafiya ta garas ki  ganni nan  nama fiki lafiya". Ta fadi hakan ne cikin daga murya a fada ce. Harda dakar kirji ya bada sauti Dum! Dum! Ta wani gir-gir za. Zata kwaso wani zancen ta hangi wannan Aljanar a bayan mai gadi ta nufo su.  Haba ai kuwa da sauri ta koma bakin aiki ta.  Wayar Zuwaira ce tayi ringing da sauri ta daga. Abba ne dan Mama Asiya. Wato yayan Ameera. "Hello Mama Zuwaira wai lafiya na kira wayan maman mu shiru, Dama ina so in sheda mata ne gani nan a hanya".  Zuwaira tace, "Eh to da sauki dai, Dan Allah kayi sauri ka karaso".  Da fadar haka ta tsinke wayar suka ci gaba da bawa Asiya baki wai tayi hakuri ta daina Wankin bango. Amma ko sauraren su taki tayi._

^^^^^^^↓

_Ameera, Nasmat, da Asmart ne suke tafe jere an taso daga islamiyya.  Asmart tace,  "Yau bari muje gida nayi target din duk abunda Fatima zatayi mu. Domin wallahi ba sasauci". Nasmat tace,"Ke dai bari, Ni ai nafiki tsara mugunta a kanta. Kinga yau sai nasa ta share duk gidan nan. Sai nasa tayi mopping din duk dakunan gida. Kaya na ma wajen sat 5 sunyi shegen datti amma sai nasaka ta wanke su, Ke in gaya miki da ace ni nake girki da ita zansa tayi duk  wani abu da nasan zai ban wuya".  Dariya asmart ta kwasa, Kafin tace "Gaskiya ke babbar muguwa ce".  Ameera da jinsu kawai take sai yanzu tayi magana cikin murya kasa-kasa.  "Kai Wallahi ku kiyayi kanku da wannan yarinyar in kuwa ba haka ba zaku ci uban ku".  Cikin hadin baki suka ce "Saboda me".  Ameera kamar munafuka ta kalli gabas ta kalli yamma, Cikin rada tace "To in gaya muku wannan 'yar babyn ta Fatima Aljana ce". Da jin haka suka bushe da Dariya. "Ashe ke sai yanzu kika sani?, ai mu in gaya miki ni da Asmart tuni mun san da wanna. Kawai mugunta ne ya hana mu fada muku".  Suka kara sakin wata Dariyar. Asmart tace, "Yanzu ma kuma abunda yasa muke tsara wannan muguntar saboda mun san an yanka 'yar babyn ne jiya a Islamiyya".  Ameera tace "Aiho! Kuma fa haka ne, ai kuwq nima sai na dauki fansar abunda Aljanar tayi min ranar nan".  Lokacin suka karaso kofar gida.  Da sallamar su suka hangi su Zuwaira sai fama da Mama Asiya suke suna so su hanata wankin bang amma taki hanuwa.  Suna karasawa wajen  Zuwaira tace wa nasmat tayi sauri taje gidan ASP ta kirawo shi tace Aljanu sun kama Mama asia.  Da sauri Nasmat ta juya data falla a guje bata tsaya ko'ina ba sai gidan ASP. Da shigar ta kuwa batayi birki ba har cikin falo. Ta shiga Ko sallama babu, A falo ta iske su shida matar sa. Cikin shigar kayan aiki da alama ma tafiya zaiyi. Nasmat daga ka ganta kaga wacce take a rude. "ASP, ASP kayo taimako gida mu ba lafiya".  Asp cik da san yaji me ke faruwa yace, "Ke miye akayi". Cikin rudu Nasmat kamar uwar da danta zai mutu take fadar "Dan Allah ka taimaka ASP kataho mu tafi, Banda bata lokaci karsu kashe ta". Lokacin da Nasmat ta kama hannunsa tana kokarin jawo shi.  Shi kuwa sai kara tatogewa yake. Da sauri cikin hadin baki shida matar sa suka ce "Suwa?"._

_A zabure tace, "Aljanune suka cika gidan mu gasu can kuma sun kama mama Asiya sai azabtar da ita suke". Da fadar haka ASP yasha jinin jikinsa. Domin shi in dai harka ta aljanu ce akwai shi da tsoro ta bangare.  "Aljanu?".  Ya kuma maimata maganar. Nasmat tace "Eh".Zainab matarsa tace, "Mai gida ya naga kamar ka tsorata ne daga yin maganar Aljanu".  Wani shegen yak'e  yayi,  "Haba ke kuwa Zainab kamar baki sanni ba. Kamar ni jarumin jarumai A duk cikin 'yan sanda kice wani  ina tsoro?. Haba dai".  Ya kalli Nasmat yace, "Ke yi gaba gani na  tahowa bari inje in daukko bindiga ta. Kunsan ko Aljanu tsoran bindiga suke yi".  Asp ne ya fadi haka yayin da ya juya ya nufi dakin sa. Zuciyar sa sai sake-sake yake yanda zai tsere. Domin Allah ya gani bazai iya zuwa gidan ba. "To ni in naje ma uban me zan musu?".  Ya tambayi kansa.  "Kai alquran bazan je ba".   Ya fada cikin dan daga murya............................._

☺ ```Wayyo mama Asiya nayi miss dinki 🀣 yau kam kina gasuwa. Ai gwara ki dinga irin wannan aiki ko jikin ki ya sabe. πŸ˜† yau duk wanda yaje kusa da mama Asiya zaici ubansa. Dan na lura neman wanda zata huce haushi a kansa take. πŸ˜‚ Haba asp karka ba maza kunyi mana.
😘 I love All my fans. I'm  back``` 🀑

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy

08144420347

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 73-74

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

😍😍😍
     *ZAMANI WRITERS*  _*SUNAYEN KU A RUBUCE SUKE DAYA-BAYAN-DAYA A ZUCIYATA.  BANSAN YA ZAN BAYYANA IRIN KEWAR KU DANAYI BA.*_  _*KULLUM TUNANIN KU NAKE. NAKAN CE "Ah Duniya kenan, kamar jiya ne nake tare daku yau gashi rashin ta ya nisanta ni daku".   SAI DAI INA MAIYI MUKU ADDU'AR DAUKAKA KUYI KWARI KU ZAMA GANJI, DUK BAKIN CIKIN MASASAKI SAI DAI YA SASSAKA YA BARKU.*_ _*ZAMANI WRITERS ALLAH YA SAKA HASKE A RAYUWAR MU ALLAH KASA MU RINGA RUBUTA ABUNDA ZAI AMFANI JAMA'A.*_

🀠Dan autan ku ya dawo.  A dora daga inda aka tsaya

✍🏻
_MARUBUCIN KWARE BABBAN BURINSA SHINE YA RUBUTA ABUNDA ZAI AMFANI AL'UMARSA, KO BAYAN RAISHI.  SHI BA GORIN SHI YA TARA MAGOYA BAYA DA DUMBIN MASOYA BA._

😭😭😭😭😭
MATSALAR DA TA AFKU KUKAJI NI SHIRU
*Makon da ya gabata lafiyan ta lau ina tsaye sai gani nayi ta fadi kasa kanta ya bugu da kasa. Tayi tsalle ta kara mirginawa a galabaice. Nan take ni da wasu jama'ar wajen muka nufe ta dan ceto rayuwar ta.  Kafin mu karasa wajen har ta sume. Nan fa na shiga rudu da kidima.  Wani bawan Allah ya kawo pure water aka yayyafa mata amma shiru bata ko motsi balle ta bude ido. Da ganin haka na kara tsurewa. Nan take na fara kuka ina rairawa baitotin kauna. Domin duk wanda ya sanni ya sanni da ita. Duk wanda ya taba ta batawa nake yi da shi. Duk inda muke tare ko barci baya raba mu. Itace abokiyar hira ta. Ba komai ne ke kara burgeni a game da ita ba. Sai ilimin ta zakuyi mamaki idan nace muku duk yaren duniya tana jin shi. Takan koya min karatu takan tunatar dani ta min nasiha.  Ko kadan bata bari raina ya baci. Duk lokacin  da muke tare kuwa har mantawa nake da na kusa dani. Uhmm abun dai da yawa. Sungumar ta nayi da gudu na nufi asbiti mafi kusa.  Nan take akayi emergency da ita. Likitoshi gaba daya sukayi kanta. Da kyar suka samu ta fara bude ido. In takaice muku labarin dai Sai jiya Dr. Tasi ya samu nasarar ceto Rayuwar wayar tawa bayan jinya mai tsanani da tayi.*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜†πŸ˜† Nayi missing dinta sosai

_ALHAMDULILLAH.  ​YANZU DAI JIKIN NATA DA SAUKI. SAI DAI DUK TA RARAME. MUNA KYAUTATA ZATAN ALJANA KURSIYYA CE TA SHAKE TA DAN HAKA MUKE CIGIYAR SARKIN BORI EMERGENCY. WANDA YA GANSHI KO YAJI LABARIN SA_

      *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Asp ne ya fadi haka yayin da ya juya ya nufi dakin sa. Zuciyar sa sai sake-sake yake yanda zai tsere. Domin Allah ya gani bazai iya zuwa gidan ba. "To ni in naje ma uban me zan musu?".  Ya tambayi kansa.  "Kai alquran bazan je ba".   Ya fada cikin dan daga murya.~

_*"M*ai gida tana jira fa" Zainab ce ta kwalo kira. Asp Abdul naji yace "gani nan  bindigar ce ban gani ba".    Cikin dan daga murya.   Ganin bashi da wani zabi ne yasa ya dauki bindigar ya fita. Yana fita falon yaga Nasmat tsaye. "Au! Ke ba cewa nayi kiyi gaba gani nan zuwa ba?". Nasmat tace "Dama kai nake jira ai mu tafi". "Kaji yarinya da rashin kunya wato ke dole sai mun jera kugu, Tukun mun tafi tare?. Ai kuwa abunda bazai yuyu ba kenan, idan kina so inje to fa sai kin fara yin gaba".  Asp Abdul ne ya fadi haka lokacin da yake kokarin zama a kan armchair.  Nasmat da dai taga mutumin da gaske yake idan bata tafi ba bazai je ba sai ta juya tace, "Na tafi to dan Allah brox kayi sauri karsu kashe ta Aljanun basa da imani".  Da fadar haka ta juya ta fita shi kuwa da ganin haka sai ranshi yayi fari ya tashi yace wa Zainab "Yau zan baki mamaki zaki ji jarumtar mijin ki. In gaya miki aljanun  ko irin na ranar nan ne sai na fatataki aniyar su. Sai ni asp na Xainab ba gaba da gaba ba yiiiihuhu". Yayi dan ihu irin na kauraye. Zainab ba abunda take bishi da shi sai "Allah mai gida".  Daga karshe kuma ta bushe da dariya jin  yayi ta kauraye. Sallama yayi mata ya fita hade da cewa "Daga can bazan ko dawo gida ba wajen aiki zan wuce".  "Ok Allah ya kiyaye min kai ya dawo min da kai lafiya jarumina"  shine abunda Zainab ta fada. "Ameen godiya nake gimbiyar mata".  Ya fada kafin ya fita har a zuciyar sa yaji dadin addu'ar.  Yana fita daga gidan ya kalli gabasa wato saitin da gidan su Nasmat yake. Wata hayaniyar mutane yaji da dan karfi-karfi. Ji yayi kamar an cewa. "Kuyi sauri ku kira ASP din". Ai kuwa dajin haka a zuciyar sa yace ai kuwa ko kurata bazaku samu ba.  Yamma yayi a guje. Kafin asmart da aka sake aiko wa ta fito tuni har ya sha kwana. Asmart ta koma gidan Asp tace wa Zainab  "Ance ASP din yayi sauri".  Zainab tace ai ya fita yanzu-yanzu bai je gidan naku bane?".   "Eh kawai Asmart tace ta juya da sauri ta koma tacewa su Zuwaira ance ya taho nan._

_Tsuru su Zuwaira sukayi domin su kam sun rasa abun yi. Mama Asiya sai faman wankin bango take, Duk wanda ya matsa kusa kuwa domin ya amshe sosan sai ta nufo shi da duka.  Su Nasmat kam abun tsokala ma suka samu. Domin da gangan suke zuwa suce ta bashi su tayata dan ta biyo su ko ta xage su suta Dariya.  Ana cikin haka sai ga Abba ya shigo jaye da akwatin sa. Da ganin sa su Nasmat suka kwashi hayaniya "ga yaya Abba! ga Yaya abba!"   Ihun da suke ne ya tayar da Fatima da take  can daki sai barci take. Da sauri Asmart ta karbi akwatin ta tafi kai mishi daki.  Shi kuwa mama Asiya ya nufa sai tambayoyi yake. "Momy lafiya-lafiya".  Bata ko kalle shi ba. "Mama Zuwaira me ya same ta ne haka take abu kamar na yara?" Abba ya tambaya. Zuwaira tace "Kadai gani Wallahi tun dazun muke fama da ita ta bari amma taki, Watakil dai iskokai ne".  Dake Abba ya biyo jikin Asiya shima irin babbar jikin nan gare shi in ka kalle shi a fuska ne zaka gane yaro ne.  Baiyi shakka ko tsoran tunkarar Mama Asiya ba, Hannuwanta ya rike yana mata magana cikin sanyi. "Haba momy miye kike yi haka?. Dan Allah ki bari". Hararen shi tayi "Kai sakar min hannu ko inci mutuncin ka. Miye ruwan ka da abunda nake yi".  Abba yace "Momy bango ne fa kike wanke wa. Bayan kuma an kusa sake fentin ma baki daya".  "Ok wato kaima a mahaukaciya ka dauke ni ko? Kana nufin bansan me nake ba. Ai nasan bangon ne"._

_Abba ya dan marairaice cikin shagwaba. "Please momy ki bani ni zan wanke gun. Ke muje ki huta". Nan ma kin yarda tayi magiya kala-kala yayi mata taki yarda ta bari hakan yasa ya fara janta da karfi.  Ba yanda ta iya ganin zai kadata tace. "Abba nema kake ka balla ni ka cike naci. To naji muje in huta amma fa sai na dawo na karasa aiki na".  Abba.yace "Eh naji muje dai".   Haka suka runkuta Cikin falo su zuwaira, Hauwa, Nasmat, Da dai sauran su suka rufa musu baya. Mama asiya duk ta gaji ji take kamar an bubuge ta. Domin aikin da tayi yau bata taba yin kalar sa ba tunda aka haife ta.   Fatima ce ta fito daga daki  gaban tane ya fadi ganin Abba. Shima kuwa yana ganin ta ya fara hararen ta domin ko kadan jinin su bai hadu ba.  Cikin hanzari Fatima ta dan rissina tace,  "Yaya abba ina wuni?. Kazo lafiya".    Maimakon ya amsa sai ya murtuke fuska rai a bace yace, "Zo nan". Jiki na rawa ta fara matsowa gurin sa tafiyar kamar wacce aka sawa Dabai-bayi.   Tsawa ya daka mata. Hakan yasa ta karasa wajen nashi da sauri. Tana isa bai ko dubi kankantar ta ba ya kwashe ta da mari da karfi.  Dan karfin marin sai da Fatima ta fadi. Ai kuwa ta fasa ihu!.  Da faruwar haka mama Asiya ta Juya wanka wa Abba mari hade da cewa. "Baka da hankali ko so kake yanzu ka jawo mana masifa, Me tayi maka ne da zaka daki yar mutane daga zuwan ka".   Abba cikin bacin rai kamar ya fashe da kuka yace, "Mum yanzu a kan wannan Yar banzar Yarinyar ne kika daga hannu kika mare ni? Abunda baki taba yi min ba. To Wallahi ta shiga uku tunda tasa aka mare ni ni kuwa a kullum kuma duk haduwar da zamuyi sai na mare ta".  Yana fadar haka ya tashi yana gunguni ya nufi bangaren sa.  Mama Asiya na kiranshi amma yake ko waigowa.  Da sauri ta kama Fatima ta dorata a kan kujerar da take kai. Da zanen jikin ta ta share mata hawayen fuskar ta ta shiga lalashi. Ita kanta Fatima abun yayi mugun daure mata kai, Ta rasa dalilin yin hakan.  Haka suma su Zuwaira abun ya basu mamaki yanda Mama Asiya ta tsani Fatima yau kuma ita ce harda lalashin ta._

_Ita kuwa ko kula da su batayi ba sai  wani rawar jiki take gani Fatima sai kuka take tsoro take Aljanar taci ubanta duk da dai ba ita ta mari fatin ba. Fatima kuka take tayi domin fuskar ta sai zogi take. Da sauri Mama asiya ta kunto yar babyn Fatima ta mika mata "Yi shiru Fatima na, Ga babyn ki ma na daukko miki kuma nayi mata wanka da kwaliyya kalli tayi kyau kuwa?".  Fatima sai a yanzu taga babyn nata. Dakatawa tayi da kukan ta wani wangale baki cike da farin ciki ta karbi yar babyn nata tana jujawa. "Mama Asiya ke kika mata wannan kwaliyyar?. Amma tayi kyau sosai".  Itama mama Asiya cike da farin cikin ta rabu da alkakai tace, "Eh ni nayi mata tashi ki kaita daki barci take ji".  Fatima tace to Mama Asiya Ina akwatin kayan ta?".  "Jeki kawai yana dakina anjima zan kai miki". "To Fatima ta fada ta juya ta wuce dakin su cike da farin ciki.  Tana shiga dakin Mama Asiya tayi ajiyar zuciya. " Ita kuwa ko kula da su batayi ba sai  wani rawar jiki take gani Fatima sai kuka take tsoro take Aljanar taci ubanta duk da dai ba ita ta mari fatin ba. Fatima kuka take tayi domin fuskar ta sai zogi take._

_Da sauri Mama asiya ta kunto yar babyn Fatima ta mika mata "Yi shiru Fatima na, Ga babyn ki ma na daukko miki kuma nayi mata wanka da kwaliyya kalli tayi kyau kuwa?".  Fatima sai a yanzu taga babyn nata. Dakatawa tayi da kukan ta wani wangale baki cike da farin ciki ta karbi yar babyn nata tana jujawa. "Mama Asiya ke kika mata wannan kwaliyyar?. Amma tayi kyau sosai".  Itama mama Asiya cike da farin cikin ta rabu da alkakai tace, "Eh ni nayi mata tashi ki kaita daki barci take ji".  Fatima tace to Mama Asiya Ina akwatin kayan ta?".  "Jeki kawai yana dakina anjima zan kai miki". "To Fatima ta fada ta juya ta wuce dakin su cike da farin ciki.  Tana shiga dakin Mama Asiya tayi ajiyar zuciya, Hade da wata doguwar mika tace, "In Allah yaso falke sai kayan sa su tsunke a gindin kaba. Komai kayi hakuri kaga karshen sa".   Da fadar haka sai ganin wannan tsohuwar ta bayyana a gefan ta "Wannan maganar dawa kike?".  Aljanar ta tambaya. Mama Asiya na ganin ta ta wani wuntsila ta saman kujera ta fada kasa. Tana faduwa ta tashi tayi daki a guje._

πŸ‘ΊπŸ‘ΊπŸ‘ΊπŸ‘ΊπŸ‘ΊπŸ‘ΊπŸ‘ΊπŸ‘ΊπŸ‘ΊπŸ‘Ί

_Umar tun ranar da wannan abun ya faru ya dai na bin layin gidan sa. Kullum sai dai yaje gidan iyayen sa ya kwana. Yau kusan kwana biyu kenan sun tambaye har sun gaji amma yaki gaya musu me ya ke hana shi kwana gida. Haka yauma sai da Inna ta tambaye shi Rafy Yace mata lafiyan ta lau yaja mashin dinsa ya fita aiki.  Misalin karfe daya na rana Safuratu Cikin sufar Rafi'at Taje gidan su Umar Inna na ganin ta ta tarye ta cikin fara'a Rafy kuwa tun daga bakin kofa tq fara kuka.  Nan kuma Inna ta shiga jero tambayoyi "Aa Rafy lafiya zaki shigo lafiya kuma ki kama kuka. Me  yake damun ki?".  Inna ta kama hannun ta tajata suka sama waje suka zauna. Rafy tayi ajiyar zuciya bayan dan shiru da tayi Inna na tambaya. "Inna Umar ne gaba daya ya fita lamarina tun Shekaran jiya waccan Umar baije gidan ba. Haka kuma bai fada min inda zashi ba.... .......................  ............._

😰 Al qura'an na gaji

☺I'm back My Fans aci gaba da gashi

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 75-76

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

😍😘 DEDICATED TO ZAMANI. ABAR ALFAHARINA  KUN ZAMA YAN UWANA. πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» BANA GAJIYA DA JIN ZANCEN KU KARKU BARI. KO BACIN RAI NAYI IN NA TUNO KU SAI INJI FARIN CIKI ALLAH YA KARA MANA SAN JUNA DA HAKURI DA JUNA. ALLAH YA KARA DAUKAKA YAN UWA NA πŸ€”

πŸ‘·πŸ»πŸ‘·πŸ»πŸ‘·πŸ»πŸ‘·πŸ»πŸ‘·πŸ»πŸ‘·πŸ»πŸ‘·πŸ»πŸ‘·πŸ» *KAMAR YANDA AKE YIWA AMARYA KAYAN DAKI. MUMA MAZA TA KAMATA A RINGA WA ANGO WADANNAN ABUBUWAN SABO DA TSARO.*

KNIFE PROOF

TABARYA PROOF

MUCIYA PROOF

BULLET PROOF

HAKORI PROOF

MAGANIN TAURI

ACID PROOF

MAGANIN RUWAN ZAFI

KAI ALQURAN HAR ALLURA PROOF A HADA πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

*IRIN WANNAN KISA NA RASHIN IMANI.  TO MAZA SAI A KULA A RINGA GOGE CHAT KO TEXT IN ANYI DA BUDURWA.* πŸ˜†πŸ˜‚ *KUMA MAZAN AURE A BAR SAKACI DA WAYA HAR UWAR GIDA TA DAUKA. KAI SAN SAMU MA KULLUM KA RINGA CHANGE SECURITY* πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜‚πŸ’ƒπŸ»

        *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Rafy tayi ajiyar zuciya bayan dan shiru da tayi Inna na tambaya. "Inna Umar ne gaba daya ya fita lamarina tun Shekaran jiya waccan Umar baije gidan ba. Haka kuma bai fada min inda zashi ba.~

_*R*af'iat taci gaba da magana. "Lokacin da zai tafi inna bai bar min kudin abinci ba. A kwana biyun nan ni nake sayan abinci yan kudin hannuna duk sun kare. Da na dauka Umar garin ya bari. Sai dazun wata makwabciyar mu take cewa ta ganshi a nan"._

_Inna ta rike baki hade da jijiga kai. "Ahhh! Ni RashidahYanzu Dama duk tambayar ki da nake a gun Umar yana cewa lafiyan ki lau ashe karya yake yi".  "Eh Wallahi Umma rabo na da shi tun jiya".  Inna ta bata rai sosai tace "Shikenan barni dashi zauna har ya dawo".    Rafi'at tace "To"  na ta shiga taya Inna aiki har yamma tayi amma Umar bai ko leko ba.  Umar yana yawon acabar shi suka hadu da Mukhtar shima yana jan yar kurkurar shi.  Nan suka tsaya suna gaisawa Mukhtar yace "Abokina ya kwana biyu bana jin motsin ka ko dai Aljanar kace ke boye ka a gida?".   Umar ya hade gira yace "Kaga bana san wulakanci ya zaka ringa sako mana maganar Aljana ana maganar kirki".  Mukhtar yayi dariya yace "Ai kuwa dole in tambaye ka kai da matar ka dan me bazan tambaye ka lafiyan ta ba?".    Mtseeww  Umar yaja tsaki kafin yace "Ni fa wallahi in kana yi min maganar wannan Aljanar yanzu sai inja mashin dina inyi gaba".    Mukhtar yayi murmushi yace "Aa abun har yayi zafi haka?".   Umar yacr "Ya ma wuce haka domin in gaya ma Tun fitowar da mukayi da Yan borin nan ban sake lekawa gidan ba"._

_Mukhtar ya kece da dariya harda buka kafa. "Kaji matsalar ka fa. Sai mutum yazo ya gaya maka matsalar shi amma ka ringa mishi dariya mtswww".  Umar  ya bata rai. Lokacin Mukhtar ya dan tsagaita da dariya yace "Haba abokina karka ce haka mana. Abun ne   ya bani dariya, Amma kasan me Na samo mafita in dai zaka amince". Umar yace "Rike abunka bana so nasan yanzu zakace ka samo wasu yan borin". Hhhhh Wata yar dariyar Mukhtar yayi tukun yace "Haba ai koni yanzu ba ruwana da wasu yan bori.  Wato naji labarin wani shahararren boka ne wanda ya kware yayi matukar iya aiki.
Domin shi din aiki yake da Aljanu kuma walllahi na yarda da wanda ya fada min sosai, Sannan kuma shi wannan bokan ba zuwa zamuyi mu daukko shi ba, Shi wannan daga munje mun fada mishi shi da kanshi zai kirawo Aljanar ya daure ta yaci ubanta a gaban mu".  Umar yaja dogwan lunfashi da jin wannan dogon jawabi na abokinsa. Kasar zuciyar sa kuwa ta rabu biyu. Wani barin na gaskata zancen wani na karyatawa.  Zuwa can yace wa Mukhtar. "ka tabbata baza'a sake samun matsala ba kuwa?. Gudu nake a je  a kara yin irin na sarkin bori  Duna".  Muktar yayi kasa da murya yace "Abokina ka yarda dani ni sam bani da gurin cutar da kai a rayuwa. Duk Shawarar da kaji ta fito daga bakina to mai amfani ce".  Umar yace "Na fahimta na gode sosai abokina yanzu dai kaga Yamma tayi dan haka ka bari gobe mu shirya muje".  Mukhtar yace "To Allah ya kai mu amma ka tanadi yan karraffa".   Dariya Umar yayi yace "Karka damu abokina ai ni in dai za'a rabani da waccan Aljanar a dawo min da mata ta to ko nawane zan iya kashe wa".  "Su Umar an zama MIJIN ALJANA". Sukayi dariya gaba daya tukun sukayi ban kwana Umar  yaja mashin dinsa shima Mukhtar yaja Adai daitar sa kowa ya kama gaban shi.    Safuratu na gidan su Umar tana jira ya dawo har dare yayi tara ta kusa.  Da har tace zata tafi gida Inna ta hana tace dole sai ta jira Umar din ya dawo sun tafi tare._

_Wajejen karfe Tara Umar ya nufo gida domin yau aikin kawai yake ko abinci yakin saya yayi  wai tara kudin zuwa wajen boka yake. Tafe yake a kan mashin din yana yan wake-wake yana jijiga kai. Da zuwa kofar gida yaje gaban shi yayi wani Dum! Ya fadi bai kula ba ya kutsa kai da mashin dinsa ya shiga har yayi parking  bai kula da mutanen dake zazaune suna kallan shi ba.  Da juyowar sa sukayi ido hudu da Ummansa da kuma Rafi'at. "Innahumin sulemanu wa'innahu bissmillahi rahmanurrahim". ×3  Da sauri yake ambatar ayar zuwa can kuma ya durkushe a gun ya fara cewa "Dan Allah dan annabi ki taimaki rayuwa ta, ki fita daga jikin mata ta. Kin hanani zama a gidan mata ta. Na taho gidan mu nan ma kin biyo ni, Wai ya kike so inyi da raina ne?.  Me nayi miki".  Da jin haka Rafi'at ta  fashe da kuka tace Umma kinji fa ni yake cewa Aljana".  Cikin fushi Inna tace "Au!  Umar wato duk abunda take fada ashe gaskiya ne?.  Kai wanne irin marar imani ne da zaka baro matar ka a gida kazo ka ringa kwana a nan?. Ba dan jaruma bace ai da tun ranar zata biyo ka".  Shi kam Umar gaba daya
Kanshi ya kulle yama rasa abun da zai ce._

_Inna taci gaba da cewa. "kalli yar baiwar Allah duk ta rarrame  Ka baro ta da yunwa ashe duk cewa da kake yi lafiyar ta lau karya kake ko gidan baka lekawa?".  Umar dai baice komai ba tunani yake shin wai Rafy din shi ce wannan ko kuwa Aljanar ce. Ita kuwa Rafy sai faman kuka take. Inna ta dafa kafadar Rafy tace "yi shiru kinji share hawaye. Kai kuma maza ka tashi ka koma gida da matar ka. Kuma in na sake ji ko na sake gani ranka sai yayi mugun baci".  Umar kamar yayi kuka ya fara magana "Inna dan Allah kiyi hakuri amma ni gaskiya bazan koma ba Wallahi munafuka ce Aljana ce wannan ba Rafy ba". Rafy na jin haka ta kara Karfin kuka. Tana cewa "Inna kina ji fa ni yake cewa aljana". Da sauri Inna ta rungume ta tana lalashi. Cikin fada da masifa tace "Kai Umar tashi  maza na gaya maka ku kama hanya ku tafi gida kai da matar ka tun kafin rai ya baci bana san jin komai daga bakin ka. Dan iskanci Matar taka kake cewa Aljana?".  Har Umar zaiyi magana Inna ta taso ta nufo shi zata daka da gudu ya nufi waje. Rafy tayi wa Inna sallama ta bishi.  A jere suke tafe har gida ba wanda yace wa wani uffan daga cikin su.  Umar shi kam jikin shi sai rawa yake duk a tsorace yake.  Suna shiga yaga gidan a gyare tsaf! Ko ina ba wani datti. Sai da ma suka shiga dakin abun ya kara burge shi. Dakin sai uban kamshi yake. Komai kuma gyare tsaf babu ko kyalle a yadda a kasa. Cikin wata irin murya mai Dadi da sanyaya  Zuciyar masoyi, Rafy tace "Sannu babyn na da gani kasha rana ka wahalar min da kanka. Dan haka bari in hada ma ruwa kayi wanka tukun kazo in baka abinci kaci". Rafy na fadar haka ta fita tsakar gida dan ta kai mishi ruwa ban daki. Umar suman tsaye yayi gaba daya ji yake kamar ba shi ba.  Har Rafy ta dawo bai ko motsa daga inda yake ba_

_Tana shiga ta kama hannun shi taja shi har bakin kofar ban dakin ta kara kashe murya tace. "Sahibina ni fa ji nake kamar bazan iyayin hakuri in jure har ka fito ba domin idanuwa na Basa iya jure rashin ka na dan lokaci kalilan. Badan wani boyayyen dalili ba dani zan shiga in ma wankan babyna. Luuuu! Umar yaji kamar zai fadi dan dadin kalaman matar tashi.  Wani murmushin jin dadi ne ya kubuce mishi ba tare da yayi niyar yi ba. Bai san lokacin da yace "Karki damu My onlyone yanzu zan fito nazo gare ki".  Yana fadar haka ya shige ban dakin wanka yake yana bangala dariya kama bashi ne mai tsoran Aljana ba. Farin ciki yama mantar da shi cewa akwai Aljana a gidan.  Allah-Allah yake ta fito daga wankan.  Bai dau lokaci ba ya fito sai zumudi yake ya nufi dakin. Yana daga labulan yaga Rafy tayi maza ta kauce kanta hade da Rufe idanu da hannuwa.  Abun ne ya kara burge shi nan take ya fara tuna rayuwar su ta baya irin ta masoya da sukayi shi da Rafy.  A hankali ya dinga takawa har yaje daf! Da ita tana jun nunfashin  shi  a wuyan ta ta baya. "Haba Rafy tawa. Ya zaki nemi mayar dani kahon karfi da yaji?. Idan kika hanani kallan fuskar ki idanu zusu makance. Juyo ki kalle ni Mana baby na".   "Dan Allah kai baka jin kunya na ne?".  Rafy da ta juya baya ido rufe ta fadi haka.  Umar yace "Kunya kuma my ai tsakanin miji da mata ba kunya".  Rafy tace "Kwarai haka ne annurin zuciyata. Amma ai ya kama ta ko gajeran wando ne ka...". Ai kafin ta kai aya tuni Umar yayi waje da gudu sakamakon Zumudin da yake na ya fito ashe ya ma manta ko Gajeran wando bai sa ba Tsirara yake. Sai yanzu da ta fada ma ya lura hakan yasa yayi waje a guje................................._


~Ai kafin ta kai aya tuni Umar yayi waje da gudu sakamakon Zumudin da yake na ya fito ashe ya ma manta ko Gajeran wando bai sa ba Tsirara yake. Sai yanzu da ta fada ma ya lura hakan yasa yayi waje a guje.~

_*B*an daki ya koma ya sako kayan shi tukun ya dawo duk kunya ta cika shi. Lokacin da ya dawo tun daga bakin kofa yake jin kamshin abinci. Yana shiga dakin ya iske Rafy zaune tana zuba mishi abinci a plat "Babyna zo zauna in baka a baki".  Yana murmushi ya karasa wajen ya zauna. Kallan ta kawai yake yana kara jin santa a ranshi yana tuna rayuwar su ta baya.  A baki ta fara bashi abincin kamar yaro. Tana mishi hiraraki masu dadi. Har ya koshi,  Tukun ta janye abincin gefe. Shiru  ta biyo baya Kafin Umar yace "My wife ban tambaye ki mana?".   "Ina jinka Uban 'ya'yana".  Umar yace "Dan Allah ina kika samo wannan shinkafar gashi naga miyar harda nama?". Dan murmushi tayi tace "Hmm mai gida kenan. Da kudina na saya kawai dan in faranta maka. Domin nayi miss din dukan ka da zagi".  A kunya ce ya sunkuyar da kai. (Kamar wanda yaje kwartanci gidan surikan shi)  Rafy tace "Dama ina so in maka wata tambaya in ba damuwa babyna".  "Ba damuwa inajinki"  ya fada ba tare da ya dago kai ba. "In zaka tuna lokacin da mukayi aure Mu masoya ne na azo a gani. Ko kadan bana san abunda zai bata maka rai. Kullum cikin hidimar ka nake. A kanka har matsala muka samu da iyaye na. Amma Umar wata biyu baya sai ka mayar da gidan nan kamar gidan kaso a guna. Zuciya ta da take cike da farin ciki lokaci guda kasa kafa kayi facali da shi. Fuskar ka da ta zame min abar bege wanda nake kallo ina jin dadi. Sai ka mayar da ita Abar tsoro, abun gudu. Jikina da ya kamata ya sama kyakyawan kulawa daga gare ka. Amma sai ya zama abun duka. Umar mamaki na shine lokaci daya canjin yazo. Meyasa?_

_Umar yaja dogon lumfashi yayi kasa da murya yace "Ba wani abu yasa ba sai ganin lokacin idan na yarda mukaci gaba da zama a haka zaki rainani ki daina jin maganata. Hakan yasa..."  "Karya kake Umar ba wannan bane fada min gaskiya in ba haka ba yanz in wuji-jiga ka a anan domin Ni ba Rafy dinka ta gaskiya bace".  Cikin wata iriyar murya mai tsoratar wa Sufuratu tayi mishi maganar  cikin tsawa.  Wani iska kamar doguwar guguwa ya zagaye inda take Sai gani yayi ta canza hallitta zuwa wata dodanuwa mai ban tsoro. Mugun tsoro ne ya ziyarci Umar lokaci guda domin har fitsari ya fara kubce masa.  Da baya aya fara ja yana Mata magiya yana cewa "Dan Allah kiyi hakuri Wallahi zan fada miki gaskiya. Zan fada zan fada".   Aljanar cikin murya ba dadi tace "Ka sani cewa in ka yarda kayi min karya na kuma bincika na gano haka Wallahi sai ka gane kuren ka".   Umar ya fara mata magana wanda bata fahimtar ma abunda yake cewa domin rawar darin da yake saboda tsoro. Tace mishi ya kwantar da hankalin shi ba abunda zata mishi muddun bai yi mata karya ba.  Nan ya fara kora mata bayani._

_"Mukhatar dai babban abokina ne tun kafin in auri Rafy muke tare duk wasu abubuwana shi yake ban shawara. To bayan auren mu da wata biyu muna zaman lafiya da matata sosai idan na shigo wasa da dariya irin na masoya abun gwanin sha'awa. To wataran muna hira da Mukhtar sai nake gaya mishi irin zaman mu ni da matata. Ina gama bashi labarin sai ya bushe da dariya yace ashe ni banza ne marar wayo. Na tambaye shi dalili yace min ai wasan nan da muke yi da Rafy shi zai jaho raini a tsakanin mu raini na har abada.  Da na musa mishi amma ya cika ni da zance har dai na yarda yace in gwada Murtuke wa.  nuna mata wasa ya kare amfanin abun da yake gaya min.  Ni kuwa na amince a zuciya nace zan gwada in naga abun baiyi min ba sai in dakata.  To washe gari haka na tashi abu kadan idan tayi min sai in kyare ta idan ta nuna wasa take min nan ma in hantare ta.  A ranar dai na canza mata sosai kuma tun a ranar ta fara jin tsoro na. Hakan yamin dadi nan na koma na fadawa Mukhtar sai yayi dariya yace Sai ma na ringa hada mata da duka zata na min ladabi kamar babanta. To ni kuwa dake na yarda da shi sosai dan ya fada min cewa shima haka yake wa matar shi.
Da yaga na nuna rashin amincewa washe gari yaja ni gidan nashi. Nan fa naga idan ya mata magana har rawar jiki take. Haka duk abunda za'ayi bata ko iya daga kai ta kalle shi  dan tsoro. A gabana ya bata naira Dari yace ta sayo masara da kayan miya da nama tayi musu tuwo da dare. Ko.gardama batayi ba ta amsa tana godiya kamar wacce ya bawa dubu. Nan na tambaye shi nace ya dari zata isa a sayo masara nama da kayan miya. Nace ai ko kayan miya kadai wanda za'a saya sunfi na dari. Yayi dariya yace ai ita zata cika a cikin kudinta. Dake naga tana sana'a shiyasa ban ko musa ba. Kuma abun ya burge ni  Kwadayin hakan yasa nima na hau hanya. Wannan shine gaskiyar zance._

_Dajin haka Safuratu ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya. Ta dade tanayi tukun ta da kalle shi cikin dariya tace, "Amma Wallahi ka bani mamaki wannan ai shirme ne da rashin hankali. Daga baka wannan banzar shawarar dan karta rai naka shikenan sai ka maisheta jaka kata duka Wai ni kuwa kana santa kuwa?".  "Da sauri Umar yace sosai ma ina santa Wallahi".  Safuratu ta watso mishi wata irin harara da idanuwan ta irin na dodannin wanda in ka kalle su baka shirya ba sai ka sume tsabar tsoro. Da sauri Umar ya kauce kanshi.  "Karya kake baka santa Umar. Domin masoyin gaskiya haka kawai bazai ringa azabtar da masoyiyar sa ba. Masoyi kullum burin sa shine yaga masoyin sa cikin farin ciki. Shin kai kuma kayi hakan?.  Ai ko kadan ba wanda zai yarda cewa kana san Rafy dan haka ni yanzu zanje in sama iyayen ta in basu hakuri kai kuma maza rubuta mata takardar saki".  Durum!  Gaban Umar yayi mummunan fada ji yayi kamar jiri na debar shi. Bai san ma yana san Rafy har haka ba. Tunanin irin wulakanci da cin zarafin da yayi mata amma ta jure take zaune da shi haka yayi. Nan ya zube gaban Safuratu magiya da roko ko wanne kala yazo bakin shi fada yake. Yana hadata da Allah ta rufa mishi asiri karta rabashi da matar shi.  Safuratu tace "wato ma da ita kaci gaba da jibgarta  kana cin zalin ta ko?. To bazai yuyu ba". Kuka Umar ya kama tun karfin shi yana magiya Ita kanta ta tausaya mishi batayi zatan yana san matar tashi har haka ba. Abunda ta lura dashi shine duk abunda yayi bayin kansa bane laifin Mukhtar ne._


_Cewa tayi "Umar bazan rabaka da matar kaba amma in kamin alkawarin bazaka sake mata irin abubuwan da kake mata na wulakanci duka da sauran su a baya". Da sauri Muktar yace ya amince. Safuratu taci gaba da cewa  "Sannan kamin alkawarin zaka rabu da Mukhtar domin Mukhtar munafuki ne duk abunda yake gaya ma ba gaskiya bane domin kamar mijin hajiya take tsoran matar shi yake. Duk lokacin da kaje ka iske shi a waje to laifi ya mata ta koro shi wajen".   Umar zugun yayi zuciyar shi sam.bata amince da maganar da Safuratu tayi a kan Mukhtar na tsoran matar shi ba.  Safuratu tayi wata yar guntuwar dariya tace "Nasan bazaka yarda da zancen da na fada maka ba. Domin ganin yanda matar tashi ke nuna maka idan kuka shiga gidan nunawa take tsoran Mukhtar. take wanda kuma hakan wani plant ne shi Mukhtar din ya hada. Duk wannan zabure-zaburen da yake mata da zarar ka fito a gidan sai ya biya ta kudi dake kasan mayyar kudi ce.  Amma abunda nake so dakai yanzu Bari inje in dawo ma da matar ka gobe zan nuna ma a zahirin waye abokin ka". Kafin Umar ya daga baki Safuratu ta bace nan ta barshi sai cicira ido yake. Ita kuwa can taje gidan kawun Rafy a sufar Umar ta dakko Rafy.  Da kawun nata yace ta bari sai da safe ta shirya amma taki yarda dake ita kant ta gaji da zaman gidan duk da ba takura amma tafi san gidan mijin ta. Kuma tun da taga Umar tasan Safuratu ce kuma tasan akwai wani abun.    Tun a hanya Safuratu ta kwashe labarin duk yanda sukayi har da labarin su sarkin bori ta bawa Rafy.  Rafy tayi dariya sosai a zuciyar ta kuwa addu'a take tana fargaba game da Umar.  Tare suka shiga har cikin daki Umar ba karamin tsorata yayi ba ganin Safuratu da sufar shi sak! Har kayan jikin sa ba banbanci. Da har ya tashi zai ruga ya boyi Safuratu ta tsayar da shi. Rafy kuwa dariya ma abun ya bata.  Domin ita yanzu bata ma tsoran Safuratu ko kadan dan ta gane ba macuciya bace.  Safuratu tace kaga malam ga matar ka nan na dawo ma da ita ni na tafi sai da safe gobe ka shirya zamuje gidan Mukhtar ka gane wa idan ka.  Da fadar haka ta bace Battt!..............................._

Ganin Safuratu ta bace nima nace bari in gwada bacewar.  Batt!! .Lolz

*NA GAIDA SAFURATU. KIN KUSA SAITA NAN GIDAN SAURAN SU MAMA ASIYA*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boyπŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 79-80

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

😍😘 DEDICATED TO ZAMANI WRITERS. JINKU NAKE KAMAR YAN UWA NA NA JINI. ROKON ALLAH NAKE YA KARA DAUKAKA DA BASIRA. ALLAH YA TSARE MU SHARRIN MAHASSADA. ALLAH YASA ALBARKA A WANNAN KUNGIYA TAMU.

πŸ’ƒπŸ»  Yanzu halin wasu bakin hanga.. »Baki na hanga...

πŸ’ƒπŸ» Basu ganin wani yanada burga...
»Yanada burga...

πŸ’ƒπŸ»Sai su bi daya biyu su zaga..
» biyar su zaga..

πŸ•ΊπŸ» Munsan arzikin mune.. Zaya bimu...

πŸ•ΊπŸ» Inadai lokacin mune za a jimu...

πŸ•ΊπŸ»Kalmomi adansune Tubalin mu...

πŸ•ΊπŸ»Harshe zamu tsarkake har ya kaimu.... πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ•ΊπŸ»πŸ•ΊπŸ»πŸ•ΊπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ•ΊπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ•ΊπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ•ΊπŸ»

πŸ•ΊπŸ»Kyan lafazinka kwaliyar ka...

πŸ•ΊπŸ»Inka biyata sai a dauka...

πŸ•ΊπŸ»Sai makiyin ka ma yabika...

πŸ•ΊπŸ»Ayita fada dashi a kanka...

πŸ’ƒπŸ» Kada harshe ya kai ya barka...
» Yakai ya barka..

πŸ’ƒπŸ»Yi tunanin amo ka saka...
»Amo ka saka...

πŸ’ƒπŸ» Adabi shi ka gyara littafi πŸ˜†
» ya gyara littaf...

πŸ•ΊπŸ»Nazarin duniya misali....

          *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Domin ita yanzu bata ma tsoran Safuratu ko kadan dan ta gane ba macuciya bace.  Safuratu tace kaga malam ga matar ka nan na dawo ma da ita ni na tafi sai da safe gobe ka shirya zamuje gidan Mukhtar ka gane wa idan ka.  Da fadar haka ta bace Battt!.~

_Washe gari da safe bayan su Umar sunyi wanka ya sayo musu abun kari sun karya ya  sun zauna suna hira sai gani sukayi Wata yar farar Yarinya ta bayyana a gaban su tana kallan su tana murmushi. Tsorata sukayi dan Umar har zai tashi ya ruga. Yarinyar tace "Nice fa Safuratu *ALJANAR FATIMA".* sai ta yaji haka tukun ya dawo ya zauna suna wa junan su dariya shi da Rafy na tsorata da sukayi.  Rafy tace "Kai dai Wallahi raggo ne kamar ba namiji ba. Ace mace ma ta fika rashin tsoro".  Umar yayi dariya yace "Ah! Ke kuwa ai da gaskiya ta wa zai tsaya kallan ruwa kwado ya mai kafa". Hhhhh Rafy tayi dariya tace "Ai duk Safurat ta bani labarin ka har da kokowa wajen mai shayi nayi dariya sosai.  Ga kuma Sarkin bori mai cire Aljanu".   Gaba daya  suka kwashe da dariya.  Nan dai suka gaisa da Safuratu da take a sufar Yarinya. Tace "To dan Allah Umar ko kai fa. Yanzu zaman a haka ba yafi dadi ba?.  Kuna hirq da matar ka kuna dariya.  Amma da in ka shigo sai ka wani bata fuska kamar wanda aka kai gaban sarki bai karya ba aka mai bulala dari".   Dan murmushi Umar yayi hade da sosai keya yace "In sha Allah hakan bazai sake faruwa ba. Wancan karon ma sharrin Mukhtar ne".  Safuratu tace "Yauwa haka ake so. Amma fa akwai mazan da suke haka wanda a waje_

_Zakaga suna ta bude baki suna  wangale hakora kamar wanda aka wa alkawarin Hajji bana.  Haka in suna hira suta zuba sai kace Anyiwa waziri aku gorin labari. Amma da zarar sun zo gida shikenan sai kaga sun daure fuska maganar ma sai kaga dakyar suke wa matan kamar wanda aka makure akace suyi dole.  Kai wani fa hirar arziki ma bata hada shi da matar shi, balle wasa da Dariya. Wani abu kadan da matar shi tayi masa sai hantara in bata ci sa'a ba harda duka. Kamar dogari a fadar sarki haka suke wa matan  da kinyi kuskure kadan.  Haba wai su me yasa basa fahimta ne aure fa ana yinshi ne dan cika Umar nin ma'aiki sannan ba'a ce ka auri wacce baka so ba. Wai wasu kamar dai kai yanda ka zaunu a shawarar Mukhtar.  Wai suna yin duk hakan ne dan kar matan su raina su.  Haba muma matan muna da hankali fa shikenan dan ina wasa da mijina sai in raina shi a kan me?. Raf'iat ko kina ganin zaki iya raina Umar dan wasan da kuke yi".  Safuratu ta mayar da kallan ta zuwa ga Rafy shima Umar haka.  Rafy tace "Haba-haba  ko da wasa Wallahi bazan rainashi ba. Duk abunda kuwa zan mishi cikin wasa ne irin na masoya domin ni tun a waje lokacin ina budurwa na tsara zamana a gidan miji kamar yanda ko wacce mace take tsara nata. Tsarina zan Girmamashi zan kuma maida shi abokin wasa na duk da kuwa nasan cewa shugaba na ne. Amma a nawa tunanin wasa tsakanin ma'aurata na kara dankon soyayya a tsakani. Amma fa ba mugun wasa ba wasa dai irin na masoya. Kamar yanda Addini ya Halarta mana._

_Sannan wasan yana taka muhimmiyar rawa ta bangaren Fushi. Wani abun idan nayi mishi daga naga alamun yayi fushi sai in mayar da abun wasa. Haka wani lokacin ko mun fara cacar baki mun fara fada sanadin wasa da muka sabayi sai kiga abun ya juye ya koma wasa. To ni dai gaskiya bana tunanin zan wasan da muke zaisa in raina shi ko da yaushe zan bawa mijina girmanshi in lokacin wasa ne ayi. In kuwa ba lokacinshi bane a bari".  Raf!  Raf! Raf!  Safuratu ta fara tabi tana kallan Rafy tana murmushi. Shima Umar tafa mata yake.  Safuratu tace "gaskiya kin burge ni kuma ni banga kuskure a maganar ki ba.  Umar bari muje gidan Mukhtar yau zaka sha mamaki. Karbi wannan abun ka hadiye".  Hani farin abu kamar magani ne ta mika masa ba gardama ya karba ya afa baki. Yana hadiyewa ya bace wa Rafy bata ganin shi.  A rude ta mike "Innalillahi, Ina Umar din".  Umar yana zaune agun yana kallanta amma ita bata ganin shi. Umar da baima san ya bace ba'a ganin shi ba ya kalli Rafy da duk ta rude tana cewa Safuratu ina yake. "Rafy miye haka gani nan a gaban ki ki ringa cewa wai ina nake".   Rafy kam bata ji maganar shi ba._

_Dariya Safuratu tayi Ta kalli Umar tace "Ai yanzu ba wanda zai ganka kuma ba wanda zaiji maganar ka daga Allah sai ni. Yanzu haka ka bace Rafy bata ganin ka. Maganar da kayi yanzu ma bata ji ba". Mamaki ne ya kama Umar. Safuratu tace wa Rafy "Ke ma kwantar da hankalin ki ga Umar dinki nan ba sace shi nayi ba. Yanzu zamu tafi gidan Mukhtar ne da shi to har ciki zamu shiga dan haka bazasu gan mu ba. Mun tafi sai mun dawo".  Da fadar haka sai suka bace ita da Umar din sai gasu sun bayyana a gidan Mukhtar.  Da bullowar su suka ji Murja a daki sai masifa take surfawa Umar hakan yasa Rafy tace su karasa cikin daki.  Umar kam duk a tsorace yake dan gani yake kamar Mukhtar zai ganshi.  Sai da suka suka shiga dakin ya tabbatar da cewa ba'a ganin shi Nan sukayi tsatsaye suna kallan su Mukhtar din.  Mukhtar ne zaune gefan gado Murja matar shi a gefan shi ta rike kugu cikin daga murya da kakatu tace "Kai malam tun dazun magana nake maka amma kayi shiru kamar ina magana da dutse. Kasan dai cewa gidan nan ko kwayar hatsi bama da shi balle kace ayi dan banzan kokon nan da ka saba cewa ayi a karya da shi._

_Dan Wallahi yau bazan karya da koko ba. Duk kayana na saide-saide mun cinye su baka  bani kudina ba. Gashi yanzu ina so inje kasuwa inyo sari amma ba kudi a hannuna duk suna gunka.  Dan haka tattaro min gaba daya kudina rankatakaf! Ka bani in yaso karka bada kudin Abin karyawa din ma".   Duk masifar da take yi Mukhtar yayi shiru bai ce kala ba. Sai yanzu ne ya dago cikin sanyin murya yace "Haba Murja ni fa mijin ki ne ko kin manta ni shugaba ne a gare ki kike daga mun murya haka. Wallahi kiji tsoran Allah Murja".   Ya nuna ta da yatsa.  Makr yatsar tayi da hannu ta rike baki "Iyeeeh daga bani kudina sai wa'azi?.  To Allahu akbar amma fa in kana so wa'azin da kake ya dinga shiga kunnena to a bani kudina".  Mukhtar tsabar jin haushi kamar wanda zaiyi kuka yace "Murja ni kike bigewa hannu?".  A hatsale tace "Au! Tambaya kake kenan, Baka ma yarda da hakan ya faru ba kenan".   Bai bata amsa ba ya tashi da niyar ya fita waje. Ya fara tafiya kenan ta shaki wuyanshi ta baya ta wani jayoshi. "Malam ba inda zaka, Wallahi sai ka biyani kudina".  Nan fa Umar ya saki baki yana kallan Muktar a zuciya yana jin haushi abunda ya sashi yayi wa Rafy.  Mukhtar da aka shake ma wuya ta baya. Dakyar ya samu ya markayi hannunsa baya ya kwace cikin fushi yace "Cewa nayi bazan baki kudin ki bane?. Inace dai sai naje na samo tukun zan baki?"._

_Murja tace "Kaga malam ni yanzu nake san kudina domin kaji wani yaro can ma yana a bashi mai. Amma babu duk ka cinye min kudi a bashi. Yanzu fa dubu biyar nake binka".  Muktar yace "Naji yanzu sakar min riga Yau yau zan biya ki kudin ki in dai huta da jaraba da masifa".  Zazaro ido tayi Cikin daga murya tace "Ni kaks cewa masifafiya?.  Ni kake cewa jarababiya ko Mukhtar?".  "Ni fa ba dake nake ba".   Sakar mishi riga tayi hade da cewa. "Jeka ga hanya nan. Kuma Wallahi tallahi yau in baka kawo min kudina ba zaka ga jaraba da masifa da kake fa. Badai ni kake cewa masifafiya ba. Hmm".   Mukhtar bai sake magana ba waje kawo yayo. Zuciyar sa sai kuna take._

_Yana fitowa su Safuratu suma suka biyo shi baya.  Umar ya girgiza kai yace "Kai amma gaskiya ba karamin rashin hankali nayi ba. Wai ashe haka matar Mukhtar take mishi amma shine har da bani shawara wai kar matata ta rainani. To dan Allah wane raini yafi wannan?.  Kai gaskiyar masu iy magana da sukace (RASHIN SANI *YAFI DARE DUHU*).  Wallahi zanso inga ya zasu karata in bai biya ta kudinta ba".   Safuratu tace "ka dai gani da idanka. Idan kana so kuma ni zan iya hana shi kawo kudin".  Uamr yace "Tayaya zaki hanashi".   Gaba ta shiga ta fara tafiya. "Muje kaga ta yanda zan hanashi ya kawo kudin".  Baya suka bi Umar har wajen ogan su inda yake karbo napepk din.  Nan fa Safuratu ta juya zuwa wata jabebiyar mata. Ta shiga yar kurkurar ta zauna gaba daya ta cika kurkurar in aka cire inda umar zai zauna baza'a samu wajen zaman wani ba. tace wa Umar ya shigo.   Baiyi gardama ba ya shiga.   "To kaga yau  a nan zamu ta yawo ba wanda zaima tsayar da shi in yaga mutane a ciki".  Umar ya girgiza kai shi dan a tsorace yake. Dan girman matar yayi over. Mukhtar zuwa yayi ya dan kakabe kurar yar kurkurar ya hau ba tare da yasan Su Umar na ciki ba.  Haka yata zuba gudu yana bi lungu da sako ko mace daya bata tsayar da shi ba. Tun abun bai damunsa har ya fara damunshi. Domin yaga abun ba kamar yanda ya saba ba._


_Haka ya ringa wuce mutane wanda kuma ya tabbata Napepk suke jira amma da sun ganshin suka hangi Safuratu sai suki tsaida shi.  Abun har ta fara bashi haushi ya fara zage-zage. Wasu yan mata ya hanga su biyu sun ci kwaliyya abun su sai kallan hagun da dama na titi suke. Alamu sun nuna cewa abun hawa suke jira. Muktar ya kalle su yace. "Matsala ta da mutane kenan wasu yan rainin wayo ne Wallahi.  Yanzu wadancan fa da gani Napepk suke jira amma ina zuwa sai kaga sun ki tsayar dani. Amma bari mu gani".  Ta gaban su yaje ya wuce ganin wannan katuwar mata yasa basu tsayar da shi ba.  Muktar har yayi gaba kuma cike da takaici yayo baya. Diiiiiit!  Ya musu hon hade da cewa "Tafiya ne?".  Dayar tace "Eh tafiya ne ya akayi?".   Yace ok to ku shiga mujr mana ina za'a kai ku?".   Yar siririyar cike da masifa tace "Malam bamasan rainin wayo ya Napepk dinka  cike kuma zaka zo kana cewa wai mu hau.  To nan ina xamu hau?.  Ko kan wanna tikekiyar matar mai kama da giwa zamu hau?".  Tana fadar haka suka kwashe da dariya ita da kawqr ta. Safuratu kuwa dajin abunda suka fada sai ya bata mata rai. Kanta ya juye ya koma na giwa. Yan matan nan na ganin kan mata ya koma giwa. Yar karamar ta banke Mai dan jikin ta fadi itana ta wuntsila tsukakun kayan jikin su Bai hana su zabgawa a guje ba.  Dan ko tsayawa tata re sket ba wucce tayi.  Takalman su kuwa tuni kowacce a ciki ta yi wulli da nata dan tafiya da su bata lokaci ne. Wani gida suka shige a million suka fada daki. Matar gidan na gani  haka ta bisu daki itama a guje ta turo kyaure._

_Mukhtar sakin baki yayi yana kallansu. "To su kuma wannan me suke nufi?.  Ko dai maciji suka gani a ciki".  Juyawa yayi baya ya leka har karkashin kujerar baiga ko kiyashi ba.  Bai aminta ba. Ya fito sai da ya zagaye Napepk din ya duduba baiga ko mai ba. Yaja tsaki ya hau Napepk dinshi yayi gaba............................. ...   .........._

😰😰😰
     TASHIN HANKALI
                 😰😰😰

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 81-82

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»

            ​GIDAN MARAYU​
πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»πŸ™ŽπŸ»

          _Story&written by✍🏻
          ​​Beauty Queen​​πŸ’‹πŸ’‹

​ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

*INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIN RAJUN*

KULLUNAFSIN ZA'IKATUL MAUT.
*UMMU RUMMA,* WACCE KUKA FI SANI DA *BEAUTY QUEEN* ALLAH YAYI WA YAYANTA MAI SUNA *ABDURRAHMAN* RASUWA.  MUNA ROKON ADDU'A DAGA GARE KU ALLAH YA JIKAN SHI YA MAI RAHAMA. ALLAH YASA ALJANNA CE MAKOMARSA AMIN.  SU KUMA ALLAH YA BASU HAKURI DA JURIYAR RASHIN SHI.

       *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Juyawa yayi baya ya leka har karkashin kujerar baiga ko kiyashi ba.  Bai aminta ba. Ya fito sai da ya zagaye Napepk din ya duduba baiga ko mai ba. Yaja tsaki ya hau Napepk dinshi yayi gaba.~

_*H*aka yaci gaba da zaga gari amma shiru.  Wata mata ce ta tsayar da shi har ya tsaya kuma sai taga su Safuratu tace, "Sannu ko baiwar Allah ai ban ganku ba".  Safuratu tace "yauwa sannun ki dai". Mukhtar yace "Yauwa hajiya shiga muje ina za'a kaiki?".   Matar a fadace tace "Kan cinyar ka kake so na hau ko ina?.  Amma kai dan rainin wayo ne ma wallahi kasan napepk dinka ta cika shine ma har ka tsaya".   Muktar  juyawa yayi set din baya shi dai ko kwaro bai gani ba. "Kinga malama ba rainin hankali nace kiyi min ba. Kinga mutum ne a ciki da zakice wai a ciki take. Kinga dallah malama ware kama gabanki tunda ba hawa zakiyi ba".  Jan Napepk dinshi yayi cike da haushi.  Can wani tunanin ya fado mai. Wanda yasa ya juya kan napepk din ya nufi gida.  Da isar sa ya sauka ya shiga ciki. Su Umar suka saukko suka bishi.  Murja na ganin shi ta haushi da masifa wai ya cika lalaci tun yanzu har ya dawo. Nan yace ta saurare shi dakyar ya samu ta dakata da masifar.  Nan ya fada mata cewa tunda ya fita gashi har larfe sha biyu ta kusa amma ko mutum daya baiyi ba. Nan  fa ta sake rikicewa wai wannan karyar banza ce yake fada. Ai ba yanda za'ayi yace wai har yanzu bai kama ko biyar ba. Tace "Wannan ai salon munafirci ne. Wato so dai kake ka hanani kudina to wallahi baka isa ba. Tashi ka koma"._

_Mukhtar yayi ajiyar zuciya yace, "Ni fa kinji matsala ta dake kenan. Ke gaba daya baki sasauta mun, Ji yanda kike masifa dan Allah kamar ba da mijin ki kike magana ba. To ni dama ba wani abu ya kawo ni ba. Kamar yanda naji ance idan mutum basuyi rabuwar arziki da matar shi ba idan ya fita kasuwa bata mishi dadi. Shiyasa na dawo domin mu fahimci juna amma kin wani hau masifa".   Murja na jijiga kamar wacce aka kunna tace."To wace irin fahimta kuma?. Ai ni in ba kudina ka kawo min ba ba wani zancen fahimta dan ma kaji. Ni in ba Dumus! Naji ba da matsala".  Takaici ne ya cika Mukhtar yayi waje ba tare da yace mata uffan! Ba.  napepk ya dawo ya shiga  yana surutai. "Wai matan yanzu me yasa basu da lura ne. Haba mutum yaje yata fama wani idan yaje neman abincin ma har duka yake shi, Amma daga karshe in ka dawo gidan baza'a kwantar ma da hankali ba. Ji wannan matar wai na dawo mata da laluma amma ta wani dau zafi. Da ace zan samu mata kamar Rafy matar Umar ai Wallahi da yau-yau zan bata takarda".  Baki Umar ya rike jin abunda Mukhtar din ya fada. Nan take tsanar sa ta karu a zuciyar sa dan ji yake kamar ya buge sa._

_Mukhtar ya koma ya hau napepk din ya sake dannawa cikin garin.  Har wajen karfe daya yana yawo amma  ko an tsayar da shi ma sai ace taje abun duniya ya isheshi nan ya sama wata inuwa ya faka hade da cewa "Yin barci na ma yafi mini da inta kone maina a banza. Nan ya fiddo abun sallah ya shimfida ya dan ringesa.  Yana ta masifa shi kadai. Bai dade da kwantawar ba barci yayi gaba da shi. Su Safuratu kuwa suna cikin. Wasu gayu ne guda biyu dagani kasan yan shaye-shaye ne. Gudaya ya kalle guda yace "Baabah yau fa nake gaya ma dawa tayi nama. Kalli can".  Ya nuna mishi Mukhtar dake kwance yana barci.  Dayan yace "Kambuh!  Laili yau Allah ya kai damo ga harawa.  Kaga zagaya ta can ka dubo mana key nasan yana jikin shi".  Wanda ake kira da Muhsan yaje jikin Mukhtar ya fara dube-dube ko zaiga makulle.  Can ya hange shi a Karkashin kan Mukhtar a hankali ya zare shi.  Ba tare da Mukhtar ya farka ba. Safuratu tace Umar ya sauka ya jire Mukhtar ita zata bi barayin. Da sauri ya sauka.  Su kam barayin basa ganin su Umar. Yana ciro makullin ya mikawq abokin nasa wanda shi tuni har ya dare napepk din. Ai kuwa ya tayar yaja ta a guje.
Duk abun da ake Mukhtar ko motsawa baiyi ba. Barci yayi dadi. Da gudun yake jan yar kur-kurar sai da yayi tafiya mai nisa dan har ya fara fit daga garin tukun ya ratse ya sauka daga titi yabi wani jan birji nan ma sai da yayi nisa sosai ya kara kutsa ta cikin daji. Sai da ya shiga cikin wasu bishiyoyi tukun ya tsaya.  Kallan juna sukayi kamar hadin baki kuma suka kwashe da dariya. "Kai baabah lalai yau dawa tayi nama yanzu ya kake gani zamuyi?".  Dan siririn ya tambaya wanda ya jawo kurkurar. "Ai nake gaya ma abun duk bige ne bari zamuyi kawai dare yayi sai muyi wuf! Mu shiga da ita gari mu shigar da ita". Dan siririn mai suna Rafson yace kai mutumina nake gaya maka in dai muka shigar da wannan. Kaga na daya Zan sayi kwalin sigari giya wiwi Kai Wallahi har koken sai na saya".   Muhisan yace "kaji banza gara Kai duk a yan bushe-bushe kawai zaka kare.  Ai ni nake gaya ma zuwa zanyi gidan magajiya wuuuuyyif!  (Yayi fito)  ta dorani a hanya ka dai gane".  Ya daga mishi gira. Safuratu kallansu kawai take suna hirar rashin hankali. A zuciya tace yanzu su wannan shikenan fa sun bata rayuwar su da shaye-shaye ga abun har ya kai ga sata. Yanzu haka kuma in ka bincika rashin aikin yi ne ya jefa su".
Sai wajen karfe uku Mukhtar ya farka.  A gigice ya tashi ganin ba kekenapepk dinsa............................._

*Ayi Hakuri dan tsito ne*

πŸ˜³πŸ˜‚πŸ˜‚
Su malam Rafson fa an dauko babban kaya lalai yau dawa tayi nama. Dan kura da kallabin kitseπŸ˜†

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 83-84

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

😍 DEDICATED TO YOU πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ˜

✍🏻 SALMA QUEEN ✍🏻

✍🏻 ZUWAIRA MADARA ✍🏻

✍🏻 ACTION BABY ✍🏻

✍🏻 BEAUTY QUEEN ✍🏻

✍🏻 FATIMA(UMMU BASHIR) ✍🏻

✍🏻 AUNTY MAIMUNA ✍🏻

✍🏻 RABI'AT SHU'AIBU ✍🏻

✍🏻MMN NAJWA✍🏻

☺ NA ROKI ALLAH YA KARA MUKU BASIRA ALLAH YA TSARE MIN KU. ALLAH YA KARA FIKIRA DA FASAHA☺

        *KARSHEN PAGEN BAYA*
~A zuciya tace yanzu su wannan shikenan fa sun bata rayuwar su da shaye-shaye ga abun har ya kai ga sata. Yanzu haka kuma in ka bincika rashin aikin yi ne ya jefa su". Sai wajen karfe uku Mukhtar ya farka.  A gigice ya tashi ganin ba kekenapepk dinsa.~

_*G*aba daya a gigice ya tashi nan fa ya dora hannu kamar ya fasa ihu!  Waige-waige kawai yake yana rasa abun yi. "Anan fa. A nan nayi parking".  Juyawa yayi wajen  wani mutum dake taho wa. A rikice ya taryi gabansa "Malam dan Allah baka ga wanda ya daukar min  napep ba?".  "Ban gani ba wallahi".    Cewar mutumin da Mukhtar din ya tambaya. Durkushewa Muktar yayi ya kama kafar mutumin."Dan Allah dan annabi in kaga wanda ya dauka ka taimaka ka gaya min please wallahi ba tawa bace sojan haya na daukko".   Mamaki ne ya kama shi. "Kai bawan Allah wai napepk waya ce ko wani karamin abu da za'a sata ba tare da ka gani ba?. Abun naka rainin wayo ne ma". Yana fadar haka ya fizge kafarsa yayi gaba.  Mukhtar haka ya ci gaba da taryar mutane yana tambaya amma kowa cewa yake bai gani ba. Duk abunda yake Umar na kallan shi. Amma shi baya ganin Umar din. Mukhtar kamar yayi hauka duk mutumin da ya gani yaro ko babba mace ko namiji sai ya tambaya. Da dai yaga abun bayayi sai kawai ya sama waje  ya dora hannuwa a kai ya fashe da kuka. Cikin kuka yake cewa."Yanzu ya zance wa Bash da wanne idanu zan kalle shi ince an satace Napep dinshi tama za'ayi ya yarda". Kara fashewa yayi da kuka. Umar  ya tausaya mishi sosai a nan gurin duk da yasa Napep din bazata salwanta ba.  Mukhtar nan ya zauna sai kuka yake yana tunani ya saka wannan ya kunce ya saka wannan. Har yamma tayi magariba ta kawo kai suna wajen. Can dai Mukhtar ya mike ya nufi gidan yana tafe yana yan surutai yana zubda hawaye kamar wanda akawa mutuwa.  A haka har ya karasa gida sallama ciki-ciki ba'a ko ji yayi. Murja na daki batama ji sallamar sa ba. Waje ya samu ya zauna yayi tagumi. Shi kam tunanin ya zaicewa Bash. (Mai napepk) din yake. Nan fa ya fara zance har yana fitowa. "Yanzu Inje incewa bash duk yau ban yi ko sisi ba kuma ina barci an sace Napep din.  Kash! Sam! Bazai yarda ba wallahi"._


_Murja ce ta fito daga daki tana yan wake-wake, Tana ganin Mukhtar tace. "Au! Malam dan karka bani kudina shine kazo ka wani zauna a waje?".  Karasawa tayi gaban shi tana zuwa ta wani gyara dan kwali daurin (Ture kaga tsiya) ta rike kugu da hannu daya.  Dayan kuwa ta mika wa Mukhtar hade da kauce kanta ga barin kallansa. Alamar ba mutunci. "Malam bani kudina bana san wani waye ya mutu waye ya tashi. Dan Wallahi duk wani plant dinka na gama gane shi". Cike da takaici Mukhtar ya kalle ta a zuciya yace " Wai wannan mata ta ce. Bata ma lura da irin halin da nake ciki ba".  Hawaye ne suka gangaro mai a fuska.  Murja ganin taji shiru yasa ta kalle tana ganin hawaye a fuskar shi cikin kwaratsi tace. "Dole ka zubda hawaye. Wai ance Saurayin budurwarka ya mutu. Kukan munafurci kenan ma to wallahi baka isa ba malam. Yau naga sadodo wai harda kirkirar hawaye, Eh lalai Malam Mukhtar zaka iya film daga bani kudina sai  hawaye to a nufin ka. In durkusa gabanka ina share ma hawayen ina baka hakuri ince kabar kudin ko yaya?. To Wallahi bari kaji yau in baka bani kudina ba bar ganin dare yayi wallahi sai na dauki wani abu naka wanda yayi kudina na sayar na dauki kudina".  Mukhtar magana kasa-kasa yace "Haba murja me yasa kike haka ne. Baki san damuwar mutum ba kizo ki kara mai wata damuwa. Ko so kikr hawan jini ya kamani ne in fadi in mutu".   "Wannan kuma kai ta shafa. Ni kudina kawai nake bukata in baka bani ba kuma kaga tashin hankali harda rufu'a Wallahi".  Muktar yace "Murja An sace napep din da na daukko sojan haya".   Murja ta dan sasauta murya kamar abun kirki. "Kaico!  Napepk din aka sace ashe ai ni baka gaya min ba tun da wuri in maka jaje.  Allah yasa a ganta ya tsare gaba. In ba'a ganta ba Allah yasa mai ita ya maka afuwa".  Mukhtar yace "Amin yanzu abun..".  Kafin ya karasa ta taryi nunfashin sa. "To an sace napep nayi maka Jaje kumaa gode wa Allah da ba kudina ne a ka sace ba.  Da danaji kana zancen sacewa har gabana ya fara dukan uku-uku na dauka  kudina aka sace.  Tunda basu ne ba Alhmdulilah. bani kudina in adana kar suma garin sakaci irin naka kaje a sace. Atoh! Wanda ya bari aka sace napep ai kudi bazasuyi wahalar sata a gunsa ba. Bani kudina malam"._


_Maganar tayi mugun bata wa Mukhtar rai ji yake kamar ya tashi ya hauta da duka. Matsalar daya yasan ba abunda zai dauka a jikinta. In ma fadan ne bata kashi za'ayi. (Ragas).A zuciyarsa yake tunani cike da tsanar murja "Wannan wai wace irin mata ce. Anya kuwa Murja ba shedaniya ce ba. Kai ai ko shedan ne ke bina kudi na gaya mishi abunda ya faru ya daga min kafa...".   Shirun da taji yayi yana tunani ta wani daka mishi tsawa. "Kai malam ka bani kudina wallahi tun muna sheda juna".  Nan ma shiru yayi dan yama rasa abunda zaice mata. Kukan kura tayi ta chakumi wuyan rigar sa. Ta fara magana dan masifar kamar mai shirin yin kuka gashi da karfi take maganar. "Mukhtar yau fa ba mutun ci Wallahi sai ka biyani kudina. A take a nan ko kuwa yanzu in maka lahani Wallahi".   Mukhtar kokarin kwacewa yake daga shakar da tayi mishi amma ya gaza. Murya a makure yace. "Sakarni ni yanzu ba ko kwandala a jikina in na saaamu zaaan baaki".   Maimakon ta sake shi sai ma ta kara shakar shi. Nan shima ya fara kokarin shake nata wuyan jin tana kokarin ta kar shi. Amma ina ya shaketan amma a banza.  Ihu! Ya fara kugawa.  Wani makwabcin su ne ya shigo sa gudu yazo yaga abunda ke faruwa dakyar ya kankare mukhar a hannun Murja. Nan ya tambayi murja me ke faruwa ta gaya mishi.  Tambayarta yayi nawa ne kudin tace dubu biyar. Da sauri Mukhtar yace karya take hudu da dari biyar ne. Ibrahim ya zaro Dubu biyar ya mika mata. Yana bata Mukhar yace "An biya ki kudin ki to na sake ki saki daya. Zama dake ai bala'i ne".   Murja cikin nuna rashin damuwa ta wani jujuya kudin dake hannunta tayi guda yiiiriiyirri. "To dan ka sake ni sai me. Kai ne a kasa wallahi domin nice rufin asirin ka kuma  dan kaji in gaya ma saki daya ba inda zani. In ka cika dan halak ka karashe biyun".  Mukhtar har ya daga baki da sauri Ibrahim ya rufe mishi baki da hannun yaja shi waje.  Nan suka bar Murja nata masifa.  Duk abunda ya faru Umar na gani sai dai bashi da ikon rabawa ko magana domin yana cikin plan din Aljana._

********************
_Lokacu misalin karfe takwas na dare ne amma shiru kake jin dajin in ba kukan tsuntsaye ba shima ba sosai ba.  Kasancewar ba farin wata rudum! Wajen yake duhu in kana tsaye bazaka ga abunda ke kasa ba. Muhisan da rafson ne jingine da yar kurkurar ba abunda suke sai busa sugari. Can kuma Rafson ya kalli Muhisan yace "mu tafi yanzu mana".  Muhisan yac "Kai mahaukaci ne naga alama. Yanzu fa dare baiyi ba bar ganin duhun nan sauyin yanayi ne yanzu haka ko tara batayi ba".  Shiru Rafson bayi magana ba. Daga cikin Napep din Aka zuro hannu aka dan ja kunnen Muhisan. A fusace ya juya ga Rafson yana mishi jaraba wai ya daina kama mishi  kunne. Shi kuwa yace baima san anyi ba. Kafar  Rafson yaji anja daga kasar napepk din da sauri ya janye kafar hade da cewa "Baabah akwai matsala fa. Kafata naji ana ja daga karkashin nan". Muhisan yace "Kai dallah can rufe muna baki to me kake nu..".  Kafin ya rufe bakin yaji anja tashi kafa"Kuturun uba! Bari inga uban miye ke ja min kafa".  Durkusawa yayi da nufin lekawa Wani abun kulli aka mai a duron baya wanda ya bada sauti Dum!. "Kai! Kai! Yau banga mai hanani inci kut... Ubanka ba a jejin nan. Me nayi ma da zaka min dundu"?. Muhisan ne ke fadar haka yana dagowa ya wanka wa Rafson mari shima kuwa ya rama nan fa suka hau kunce. Shuuuuuuuuuu! Sukaji wata irin kara mai karfi ta nufo gunsu. Tsayawa sukayi da kuncen suka fara waige-waige_

_Ji sukayi an watso musu wani abu kamar ruwa. "Kai waye ke watso mana ruwa?".  Suka fada cikin hadin baki.  Muhisan yaji abun da dan danko hakan yasa ya fiddo leta ya danna. "Jinine yaseen".  Abunda ya furta kenan. Da sauri Rafson ya matso kusa. Yana ganin jinin sai suka hau dube-dube  wata kururuwa sukaji marar dadin ji a bayan su da sauri suka waiga gefan. Wani katan abune ga dukan alamu baki ne. Idanunsa kawai suke hangowa masu kamar singnonin mashin abun ya durfafo su yana wani irin gunji. Da gudu suka fada napepk  nan fa sukayi sukayi ta tashi amma taki.  Ga abun na kara kusantowa karar shinna cika musu kunne.  Da dai sukaga bazata tashi ba sai gaba daya suka fita suka runtuma a guje._

_Gudu suke sosai a birjin hasken da suka ga ya nufo su a baya yasa su juyawa. Napep din ce ta nufo su ba kowa a ciki. Da ganin haka suka kara kaimi wajen gudu. Basu ankara ba sai gani wannan Bakin Aljanin ya duro a gaban su kamar an cillo shi yana musu wata iriyar dariya mai karfi ga rashin dadin ji a kunne. Wata uwar turjiya suka ja gaba dayan su sai da suka fadi domin tsayuwa ce bata san rai ba.  Sunyi yunkurin tashi kenan sai ganin wanna aljani sukayi a gaban su. Abunda ya kara tsoratu su kenan. Cikin murya marar dadin ji yace. "Kuje ku shiga mu tafi".  Tashi sukayi suka shiga napepk din jiki na karkarwa.  Ba tare da sunga mai tukin ba sukaji anja napep din a guje.  Ihu! Suka fara yayin da wata murya ta mace tace "Kuyi mun shiru barayin banza".  Shiru sukayi haka napep tata shara gudu har suka kusan isowa gari inda suka tarar da  wani gate na yan sanda masu binciken motoci a hanya. Haka suka bi layi ana ta bincike ana zuwa kansu dan sandan yaji ance. "Barayi ne na kawo muku ku hukunta su".  Dan sanda ya bata rai hade da cewa su Rafson kai ku fito dan ubanki.  Fitowa sukayi ya ja su har wajen ogansu dake can zaune kan benci.  "Yallabai ga wasu yan iska nan. Wai mu suke cewa su barayi ne. Wasa suke da hankalin police sir!".  Ogan harara ya gallawa su Rafson yace "yan iska dama daga ganin ku yam shaye-shaye ne dan...".  "Nice nan na kawo chu bachu chuka kawo kanchu  ba". Wata yar Yarinya ce wacce bazata wuce shekara 4 ba ta bayyana a gaban su sanye da bakaken kaya idadun ta manya sun wuce kima. Gata baka.  Ai kafin ta rufe baki tuni Ogan yan sanda ya wuntsila daga kan bencin yayi kundunbala ya tashi ya zabga a guje haka suma duk sauran yaran shi da su Rafson kowa ya kama gabansa........................................._

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 85-86

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

😍 DEDICATED TO YOU πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ˜

My Dear πŸ’¦πŸ’§  *Queen Hauwa Haucy* πŸ’§πŸ’¦

πŸ’ƒπŸ» Na yabba da kaunarki gare ni. Bansan da wanne irin kalamai zanyi amfani wajen yaba miki da godiya a gare ki. 🚢🏻

Sai dai ince Allah ya barmu tare Allah kara basira da daukaka na gode matuka da irin Kaunar da kika nuna min. ☺

        *A PAGEN DA YA GABATA CIKIN LITTAFIN ALJANAR FATIMA. LOLZ* 😜
~Wata yar Yarinya ce wacce bazata wuce shekara 4 ba ta bayyana a gaban su sanye da bakaken kaya idadun ta manya sun wuce kima. Gata baka.  Ai kafin ta rufe baki tuni Ogan yan sanda ya wuntsila daga kan bencin yayi kundunbala ya tashi ya zabga a guje haka suma duk sauran yaran shi da su Rafson kowa ya kama gabansa.~

_*M*ukhtar da Ibrahim suna fitowa Ibrahim ya bada shawarar suje police. Haka suka dunguma suka nufi police din suna cikin tafiya kawai Mukhtar ya hange napepk dinshi anyi parking dinta a gefan tati. Da ganin haka ya ruga da gudu cike da zubudi yaje yana lalekawa yana fadar "Wallahi itace"2×. Umar Safuratu ya ga ta leko daga cikin napep din tace ya shiga. Dajin  haka yaje ya shige napepk din. Mukhtar sai murna yake ya shiga gidan baya yana duduba wani abu sai ji yayi anja adai-daitar a guje. Nan ya fara kwalla ihu yana neman agaji. Ba abunda ya kara tsorata shi sai ganin ba driver  napep din ita kadai kejan kanta.  Ibrahim yayi kokarin ya sama abun  hawa ya bisu amma ina. Lokacin da ya samu ya tsayar da wani mashin su tuni har sun bace mai baima san inda sukayi ba. Safuratu bata tsaya da napep din ba sai a kofar gidan Umar da isar su ta sauya zuwa yarinya. Ta kuma bawa Umar wata koya tsanwa yana sha sai gashi ya bayyana. Mukhtar tsoro ne ya kamashi dan ya gane Aljanar gidan Umar ce.  Safuratu tace mishi ya fito su shiga daga ciki nan fa ya fara kakafe wa. Umar yayi iya bakin kokarin shi amma Mukhtar yaki  yarda ya shiga gida. Abun ne ya bawa Safuratu haushi. Da hannu ta nunashi sai ji yayi an daga shi sama ana nufar kofar gida da shi. Nan fa ya fara ihu yana bada hakuri. Safuratu tace ba komai zasuyi mishi ba amma yaki yin shiru.  Daga dayan hannun ta wata wulfefiyar wuka ta fito taje ta tsaya saitin makogwaran Mukhtar Safuratu tace "kayi min shiru ko in umarci wakar nan ta cire ma kai". Shiru yayi ko uffan bai kara cewa ba har suka shiga gidan. Ba nefa gida duk duhu ne Safuratu ta kalle kwan nepar sai wani haske ya fito daga idanun ta ya shige shi nan take gidan yayi hask fayau!._

_Nan suka zaunar da Mukhtar Rafy kam tuni ta gaji da jira har tayi barci. Safuratu tace "Zanyi ma wasu tambayoyi. Amma kasan da sani in ka min karya zan gano ka dan haka gwara ka taimaki kanka a fadan gaskiya".   Mukhtar bakin shi na rawa yace "To, To zan fada miki gaskiya".  Safuratu ta kalle shi ta  nuna Umar "Miyasa ka bawa Umar abokinka shawarwari na banza. Wanda kasan kai ba haka kake wa matar ka ba?".  Mukhtar yayi jim! Kadan tukun ya nunfasa yace. "Hakikanin gaskiya na bawa Umar shawarwari na banza ne domin tun muna yara mu abokai ne kuma na riga shi yin aure sai kuma naga ya fini jin dadin auren wannan yasa na kirkiri hanyar da zata dakushe jin dadin nashi shima ya dawo kamar ni. Amma daga karshe nayi nadama".   "Karya kake mugu azzalumi macuci'. Umar ya taso mai da fada da niyar ya shake shi. Safuratu ta miko hannunta ya zama xankalele ya shiga tsakanin su. Can Umar ya koma yana hararen Mukhtar yana huci._

_Safuratu ta kalle Umar "Haba kai da nake ganin ka mai hankali shin bakaji abunda Mukhtar din yace bane?. Kai yanzu bazaka tausaya mishi ba. Kalle fuskar shi ka kalle cikin idanunshi kaga cike yake da nadama da tarin dana sani. Umar na kawo shi nan ne dan in muku sasanci  ba fada ba dan haka ka saurare mu kawai in bance kayi magana ba karka kara saka baki".  Umar jikin shi yayi sanyi da jin haka.  Safuratu ta kalli Mukhtar taci gaba da magana, "Mukhtar amma kai miyasa ka auri mata kallar wannan?.  Shin auren soyayya ne ko hadi ne".  Mukhtar yace "Auren soyayya mukayi da murja sai dai tun tana budurwa ake fada min irin mugayen halayanta. Amma nake kauda kai wasu abokan nawa har rikici muke in suka aibata ta a gabana. Ni a ganina duk rashin kyan halinta ai ni bazata min ba tunda ni mijinta ne. Sai da na aure ta tukun na karyata kai na. Domin kuwa abubuwan da murja take sam basuyi kama da na mai neman gidan aljanna ba ita fa duniya kawai ta saka gaba. Kullum zancen ta kudi-kudi lokacin da mukayi aure idan na bata kudin cefane sai ta murkushe rabi. Idan na auno shinkafa ko Masara sai ta kwashi san ranta taje ta sayar daga nayi magana sai tayi fushi tace wai zarginta nake yi.  Da dai naga abun yayi yawa lokacin inada dan arziki na sai na hada yan kudade kusan dubu dari da goma ne. Na bata nace taja jari ni a gani na ai rufin asirin ta nawa ne kuma rufin asirina nata ne._


_Taja jari kuma sana'ar ta karbe ta tana sayar da fulawa. Man kwanti. Shinkafa. Da dai sauran kayan miya.  Kwanakin baya sai aka kore ni daga wajen aiki na dawo zaman gida. Duk da ni na bata jari amma kullum bata da abun yi min sai gori wai na zama mijin hajiya ita take cida ni. Da abun ya bani haushi sai naje nace ta bani kudina dubu dari dana bata jari. Nan fa tace ta cinye kai tsaye. Abun yayi kamari har ta kai mu ga dambe. Nayi mamakin karfin murja dan dagani tayi ta ringa nunawa mahalicci tana bugawa da kasa.  Da dai naga tana neman jinyata ni sai nace na hakura. Bayan kwana biyu sai na sama wani mashin din ina achaba. Mun dade a haka ina ciyar da ita duk da ta fini samun kudi. To ranar sai mai mashin din ya sayar da shi. Nan na sake komawa gidan jiya kekenapap din nan itace ake bani duk sati to kinga kuwa ko ni kadai ne baxata iya rike ni ba balle ma harda mata ta. Wannan yasa na fara cin bashi a gurin domin ita bazata bada ba sai bashi a haka har na tara kudade da yawa. In kinga irin rashin mutuncin da take min a kansu bazaki taba cewa ni mijin ta bane".  Safuratu taja dogon nunfashi tace, "Tabdijam kaga irin abunda ake gaya muku. In kun tashi aure ku nemi mace mai hankali tausayi da sanin ya kamata. Amma sai ku bige da neman mace Fara kyakyawa doguwa. Baku ma damu da kalar tarbiyar ta da halayyarta ba. Hmm in kuwa kuka cigaba da haka lalai zaku ta tsintar kanku cikin irin wannan matsala Mukhtar. Umar abunda nake so daku shine ku yafi juna nasan duk hassadar da yake maka sharrin shedan ne".  Umar ya sauke ajiyar zuciya ya kalle Muktar yace "Ba komai abokina na yafe maka Allah ya rabamu da sharrin shedan kuma".    "Na gode abokina ameen Allah ya saka da alkhairi".  Umar yace mu duka Safuratu ce ya kamata muyi wa godiya. Muna matukar godiya Safuratu. Hakika da za'a samu irin ku a cikin al'umar aljanu da wasu abubuwan sun saitu a cikin mu mutane".   Murmushi tayi kafin tace. "A komai ai ana samun na gari ta yuyu bani kadai bace ma.  Yanzu Mukhtar ya zakayi da matar ka?". Mukhtar ya bata rai yace "Ni fa na sake ta saki daya. Amma kuma tace bazata bar gidan ba". Dariya Umar da Safuratu sukayi.
Safuratu tace "Ji shegiya kamar gidan ubanta. Bari inje in korar maka ita". Mukhtar yace "Jira bari in karashe sauran saki biyun su zama uku domin na tsani murja gaba ki daya bazan iya zama da ita ba". Takarda aka samo mishi ya idasa sakin Safuratu ta amsa ta bace.  A kofar gidan Mukhtar ta bayyana cikin sufar Mukhtar din.  Ta shiga gidan bata iske murja a tsakar gida ba hakan yasa ta wuce daki. A zaune fake Mukhtar din ya iske Murja a bakin gado da gani ranta a bace yake. Yana shigowa ta fara binshi da harara. Shima martani yake mayarwa. Takardar ya fiddo daga aljihun shi  ya mika mata. "Sauran saki biyun ne wannan ki hada da na farko na sake ki saki da uku".  Karbar takardar tayi ta lunkuma a baki ta tataune tukun ta bushe da dariya daga bisani ta bata rai ta tashi cikin tsiwa da bala'i. "Kai Mukhtar To bari kaji karyarka tasha karya wallahi.baka isa ba wannan sakin bai saku ba.  Ni da kai mutu  ka raba ba inda zanje".   Mukhtar yace "Ki tatara ya naki-ya naki kiyi gagawar barin gidan nan tun kafin jikin ki yayi tsami".   Yar dariya tayi irn ta raini wayyo hade da cewa, "Ayyiriri iyye nanaye.  Kai baka ma ji kunya ba da ka fadi haka?.  Waye zai karya ni kai ko kuwa wani?. Na ma ga alamun dukan kake so dan haka bari kaga". Juyawa tayi da sauri waje taje ta daukko tabarya ta nufi Mukhtar tasha mamaki ganin ko motsi baiyi ba duk da kuwa a haukace ta taho da niyar buga mishi. Tana kawo tabaryar yayi charf! Ya rike hade da wanka mata wani wawan mari wanda sai da ta gigice bata ma  san lokacin da ta saki tabaryar ba ta fadi kasa. Belt Mukhtar din ya daukko ya fara bulalata tana ihu! Bai sasauta mata ba duk sai da ya farfasa mata jiki tana ihu! Da jan jiki ta fito daga dakin kafin ta tashi ta fita a guje bata ko sake wai-wayo baya ba. Safuratu tace "Yar nema gobe ma ki kara"................................................_

πŸ˜‚ Murja yar masifa yau anji jiki 😜

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 87-88

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

_*THIS PAGE DEDICATED TO ELOQUENCE ASSOCIATION*_

🌟 ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION 🌟

πŸ’ƒπŸ»πŸ˜ *MUSA MELODY, AUTA* πŸ’ƒπŸ»πŸ˜
_(Autan Eloquence)_

πŸ’ƒπŸ»πŸ˜ *MUHIEVERT INDIA* πŸ’ƒπŸ»πŸ˜
_ єя ΞΉΠΈ∂ΞΉΞ± Er love)_

πŸ’ƒπŸ»πŸ˜ *SHAMSIYYA SALIS* πŸ’ƒπŸ»πŸ˜
_(Autar Eloquence)_

πŸ’ƒπŸ»πŸ˜ *BASIRA N. DABO* πŸ’ƒπŸ»πŸ˜
_(Basira)_

πŸ€— Kai dama duk members wanda ban sani ba. Ina muku Fatan alkhairi. Allah ya kara daukaka. Allah ya kara muku basira da Hazaka.

*ZAMANAWA*
Nayi muku fatan alkhairi πŸ’‹❤❤

    *A PAGEN DA YA GABATA CIKIN LITTAFIN ALJANAR FATIMMA*
~Belt Mukhtar din ya daukko ya fara bulalata tana ihu! Bai sasauta mata ba duk sai da ya farfasa mata jiki tana ihu! Da jan jiki ta fito daga dakin kafin ta tashi ta fita a guje bata ko sake wai-wayo baya ba. Safuratu tace "Yar nema gobe ma ki kara".~

_*S*afuratu ta bayyana gaban su Mukhtar dake zazaune a tsakar gida hannun ta rike da wasu daurinan kudi. "Mukhtar na kori Murja kuma ina kyautata zatan bazata sake ma irin rashin kunyar da take ma da ba".  Daurin kudi ta mika wa Umar da Mukhtar kowa daya-daya hannun har karkarwa yake wajen amsa. "Wannan kudin da kuke gani kar kuyi tunanin a banki na sato ko kuma kudin wani. Aa kudina ne mallaki na inada dukiya mai yawa a boye a inda mun biye su ne a wani waje wanda mu biyu kadai muka  sani daga ni sai Ummana. Wacce yanzu ita bata raye.  Dubu dari-dari ne ku samu koja jari da shi domin neman na kanku. Sallama nake muku sai kuma wani jikon. Umar karka yarda inji ko inga kawa matar ka wani abu makamancin wanda kake mata a baya. Dan in na kama ka da hakan bazaka ji dadi ba. Idan ta tashe kuce mata ni na tafi sai Allah ya sake hada mu". Tana kaiwa nan ta bace bat!. Godiya suka kamayi mata kala-kala suna murna.  Mukhtar tunowa yayi bata bashi makulin napep ba. Har ya fara rudewa da tunanin ina zai ganta kuma sai ya hangi keys din a kan tabarma.  Da safe da suka gayawa Rafy bata ji dadi ba sosai. Har hawaye tayi tana fadar Safuratu bata kyauta mata ba. Ya zata tafi basuyi bankwana ba. Umar kuwa lalashin ta yake yana cewa ai zata dawo tace......_
______________________

_Gidan shiru kake ji ba hayaniya hakan ya nuna cewa yara sun tafi makaranta kenan. Zaune suke sun tattara hankulan su gaba li daya sun mikawa TV dake makale a bango.  Mama Asiya ce ta shigo itama ta sama waje ta zaune hade da cewa "Sannun ku".  "Yauwa suka amsa gabaki daya".   Kafin Zuwaira tace "Aunty Asiya tun washe garin ranar da abun nan ya faru nake tambayar ki me yasa kika yi duk wannan abubuwan harda goya babyn Fatima amma kinki bamu labari". Asiya ta waiga hagun da dama  tace "Yanzu zan fada muku amma abun sirrine dan haka ku dawo nan".  Tashi sukayi gaba daya suka koma kan sofa chair din suka hada kai da ganin kasan abun munahinci ne. Mama asiya tayi kasa da murya ciki-ciki tace "Wato ni kaina ina so in sanar daku abunda ke faruwa to sai dai duk lokacin da zan fada muku sai inga wannan shegiyar Fatima. Sai inyi shiru.  Shin ko kunsan wannan yar babyn ta hannunta Aljana ce?".  Kallan juna Zuwaira da Hauwa sukayi cikin rashin fahimta "Bamu gane ba aljana kamar yaya?".  Mama Asiya ta lumfasa tace "Kwarai Aljana nima ban zata ba sai ranar. Duk abubuan nan da kukaga inayi to ita take saka ni. Har bullo min take a cikin wata irin suffa abun tsoro".  Kwashewa sukayi da dariya gaba dayan su harda ma rike ciki. Hauwa tana fadin "Wai Aljana sai mu zauna ki mayar damu aljanu ai". Zuwaira tace "Heheheheh!, Kinji fa dama na gaya miki ai motsa jini ne take ba komai ba. Shine zaki bige da ce mana wai Aljana ce..."._

_Asiya ce ta mike a fusace. "Dariyar ta iska haka kuma in kuma mutum bai bari ba Wallahi yanzu zan narki kayan banza. Aa kaji mun yan rainin wayo. Ni dai na gaya muku kuyi hankali da Fatima. Dan yanzu ba ita kadai bace ba kamar da bane da muke mata duk abunda muke so. To yanzu in mutum ya zalunce ta akwai ma rama mata. Dan haka kuyi hankali. In kunne yaji to jiki ya tsira".  Tana fadar haka tayi gaba ta nufi dakin ta. "Ni dai cikin abubuwan da nake wa Fatima ba abunda zan fasa sai ma karawa da zanyi Wallahi.  Bari ma ta dawo inci ubanta sai muga Aljana.  Hhh kawata wai kinji mu za'a mayar Aljana". Zuwaira ce mai wannan maganar. Asiya kam bata ko juyo ta kalle su ba ta shige abunta._

_Safuratu na dawowa gidan taga Fatima bata nan wannan ya tabbatar mata tana makaranta ne. Jikin yar Babyn taje ta shiga. Lokacin tasowa Fatima Nasmat, Da Asmart tare suka shigo gidan sai wasa suke a tsakanin haka ya tabbatar wa da Safuratu cewa Fatima bata cikin wani damuwa.__Kwana biyu nan Zuwaira da hauwa suna so su taba Fatima su gani kuma suna tsoro. Dan kar suje abunda Asiya ta gaya musu gaskiya ne. Haka shima bangaren abba kullum cikin target yake na yanda zai yiwa Fatima mugunta wacce zai huce haushin marin da mama Asiya tayi mishi a kanta.  Safuratu kuwa da taga kwana biyu hankalin Fatima kwance  ranar nan tana zaune sai ta tuno da su Kamal da matar sa  Khadija hakan yasa tace bari ta nufi can taga irin halin da ake ciki ga Muktar ma._
**************
_Zaune yake a tsakar gidan yana goge takalmin sa da alama fita zaiyi.  Yarinyar ce cikin uniform dinta na makaranta tazo ta durkusa ta gaishe shi ciki-ciki ya amsa mata rai a bace. Kamar dai ta bari kuma sai tace "Baba bani naira hamsi".  Cike da masifa da hargowa yace "Kinci ubanki ke da hamsin din kaji marar kunya marar tunani yanzu duk halin babu da ake ciki ke baki gani da zaki ce wani wai in baki Hamsun to ko kwandala bazan bayar da.  Bace min da gani ko in make ki". Hannu ya daga kamar zai bige ta. Da ganin haka ta tashi ta ruga a guje tana kuka. Ummiey ce ta fito Cikin nuna bacin rai tace "Baban Hawwer gaskiya abun da kake baka kyautawa ko kadan. ko dan kaga Aljanar nan bata dawo shiyasa ka fara wa yarinyar nan rashin mutunci?".  Muktar ya dago cikin fushi "Ummiey bana san haka fa. Miye ruwan ki in ma Aljanar ta dawo nasha dai ba wajen ki zata zo ba ko?. Kin anta irin gatan da na nuna wa wannan  yarinyar ne?.  Ai ko hawwer ban mata abunda na mata ba. Na mata ada lokacin da nake tunanin Aljanar nan zata dawo. Yanzu kuwa tunda naga bazata dawo ba, Ai sai in sakata in wala".  Ummiey Tace "To ai ita wannan dukiyar ta ce. Sannan kuma kaga tunda Allah ya karbi Hawwer bai sake bamu wata yar ba. Ya kamata mu rike maryam kamar Yar mu hawwer Domin ni jinta nake sosai a raina kamar yar dana haifa".  Mtsww.. Muktar yaja tsaki tare da sa takalman sa yace "Naga alamar maganar kike so to ai ga bango nan sai kiyi da shi. Nasan bazai taba gajiya ba. Ni dai na tafi". "A dawo lafiya". Shine abunda Ummiey ta fada bai ko amsa ba yayi gaba.  Safuratu da duk abunda ya faru a gabanta ya faru kai ta girgiza "Lalai wannan ashe bakayi hankali ba. Zamu hadu da kai"._


_Gaba dayan unguwar an taru sai kallan masu jigilar watso kaya waje. Ba mai bada hakuri balle a hana. Wani mutum mai sanye da Jacket ranshi a bace sai cewa yake "Yauwa ku fito da su bana so inga ko cokalin su a gidan nan. Yau yau nake so su tashi su bar gidan nan".   Can gefe kamalu ne zaune yayi tagumi yayi wani tsamo-tsamo kamar bera ya fada ruwa an fiddo shi. Gefan shi kuwa Khadija ce ba abunda take sai kuka tana  zubar hawaye. Tana tunanin irin wannan bakar rana wai yau sune ake watso musu kaya a kan titi. Kaddara kenan.  Safuratu na ganin haka ranta yayi mugun baci. Nan take ta Juye suffarta zuwa wani saurayi mai kwarjini.  Tsakiyar mutane ta ratsa ta fara bin masu fiddo kayan tana Fasfaska musu mari tana fadin "Ku mayar da kayan nan kafin Rai ya baci". Ai kuwa basuyi gardama ba suka fara dibar kaya suna  mayarwa.  Daga baya wannan mai sanye da jacket ya fara bala'i ya nufo Safuratu. Yana zuwa ya duma mata kulli. Da juyowar ta ta shaki kwalarsa da hannu daya ta dage shi sama. Kafafun shi na reto...................................................._

πŸ€” *NAN FA AKE YINTA*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 88-90

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

πŸ€— *WANNAN PAGEN NAKU NE MASOYAN LITTAFIN ALJANAR FATIMA A DUK INDA KUKE*

πŸ’ƒπŸ» _A KULLUM FARIN CIKINA DA JIN DADI BAYA MISALTUWA IN NA TUNO DA KU MASOYA NA. INA JIN DADIN _COMMENTS NAKU KUNA A RAINA._  COMMENTS NAKU NADA MATUKAR MAHIMMAN CI A GARE NI. KO BA KOMAI ZAN KARA SAMUN KWARIN GWIWA._

😰 _*DAN HAKA YAU DUK WANDA YA KARANTA BAITI COMMENT BA SAI NASA SAFURATU TA SAKO MAI DUTSE A KAI*_ πŸ™ŠπŸ˜œ

Luv u oll supporting ❤😍😍😍
πŸ€— Har  Unsupported din ma πŸ˜‰

        *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ai kuwa basuyi gardama ba suka fara dibar kaya suna  mayarwa.  Daga baya wannan mai sanye da jacket ya fara bala'i ya nufo Safuratu. Yana zuwa ya duma mata kulli. Da juyowar ta ta shaki kwalarsa da hannu daya ta dage shi sama. Kafafun shi na reto.~

_*H*arbe-harbe ya kamayi yana neman kubucewa amma ina rikon da tayi mai ba na wasa bane. Wulla shi tayi ya fadi kasa. Da ganin haka wasu yan kallon suka fara sabe wa suna guduwa. Masu fito da kaya kuwa suka kara azama wajen mayar da kayan cikin gida. Mutumin da Safuratu ta koma shi ya nufi Mai jacket din nan a jiki. ya fara da cewa. "Lalai kai ka cika marar imani da tausayi da har zaka sa a watso wa da mutane kayansu tsakiyar titi. Wannan wane irin cin mutunci ne?. A kan kawai basu biya ka kudin hayaba ko mai?. Shin kai baka tunanin in kai ne ake wa hakan baza kaji dadi ba". Mai jacket din ya mike yana kaka be jiki, kafin  mutumin ya karaso gare shi ya nuna shi da yatsa. Yace "ba dai ni kawa haka ba a bainar jama'a. to ina tabbatar maka da cewa sai kayi nadamar abunda ka aika ta min. Domin alhaji dayyabu sam! Bazai rabu da kai ba dole ya dau kwakwaran mataki a kanka". Da fadar haka ya juya ya tafi. Safuratu kuwa tace, "Ina nan ba inda zani ina jiran alhji Dayyabun. Ko uban waye yazo inaji dashi. Banza wanda bai san mutuncin dan adam ba".  Mai jacket din wanda ake kira da Dan ladi na alhaji Dayyabu. Ya juyo ya kalle Safuratu. "Alhaji kake zagi?. Lalai yau mai kwatar ka a hannun alhaji sai Allah". Juwaya yayi ya hau mashij dinsa ya buga ya tafi a guje._

_Kamalu ne ya taso yana mishi godiya. Safuratu tace "Ba komai ai yi wa kai ne". Kamal fuskar shi cike da damuwa yace "Mun gode da abunda kayi mana, Kuma naga abunda ya faru dan haka nake rokon ka da ka bar gurin nan domin alh. Dayyabun nan da kaji ana fada hatsabibin mutum ne. Yana da kudi sosai shi yasa yake takada duk wanda yaga dama. Yanzu nasan in yazo ya tarar da kai a nan sai ta Allah. Dan Allah ka taimaka ka bar nan".   Safuratu dake suffar namiji tace "To wai wannan gidan nashi ne. Haya kuke a ciki ne?".  Kamal ya kama hannun mutumin suka shiga daga ciki dan ganin mutane na kallan su. Khadija ma tashi tayi ta bisu. Bayan sun zauna kamal yace, " Wannan da kake gani. Gidana ne kwanakin baya wata kaddara ta fado mana matata ta kamu da wata cuta. Asibiti suka nemi kudi million daya da rabi. Na hada jarina gaba daya Dubu dari hudu ne.Na nemi taimako wajen masu kudi da dangi amma ban samu ba. Gidan nan shi kadai ya rage min. Kuma Allah ya gani a kan matata ba abunda bazan iya yi ba. Da har nayi tunanin sayar wa sai wani abokina ya bani shawara inje wajen Alh. dayyanu yana bada aro amma ya shaida min cewa, Baya ba mutum aran kudi sai ya tabbatar da mutum nada wata kaddarar da tafi abunda ya ara. Yace mutumin baya da mutunci idan kuka sa lokaci baka kai mishi kudin sa ba. To zai zo ya sayi gidan ka ko mota ko wani abun yanda yaga dama ya cika ma kudin ya kuma kore ka. Da naji haka da har nace ban amince ba. Koma sai na canza shawara na amince. Naje na aro million daya da dubu dari na cika da kudin gurina na kai asibiti akayi wa matata aiki. Bayan ta sama lafiya da wata daya alh. Ya fara aiko min dan ladi shine wannan mai jacket din da ka gani.__Hakan tasa ni  dole na saiyar da gidan kuma shi Alh. Dayyabun shi na sayar wa.
Da sukaga watan ya shude ban kai musu kudin su ba shine Alh. Ya turo wasu matasa yan daba suka dauke ni, Suka kai ni wajen sa. Nan yake gaya min tunda naki bayan kudin sa to ya saya gidana. 1.5 million.  Yanzu zai cika min dubu dari hudu. Da na nuna rashin amincewa sai yace wa da yan daban nan suta duka na har sai na amince. Nan fa suka fara jifga ta da dai naga suna neman hallakani sai nace na amince. Nan yayi dariya ya kawo dubu dari hudu ya bani. Wannan abun da nake gaya ma ya faru shekaran jiya ne. Yace in tattara kayana in tashi daga gidan in ba haka ba ya min korar kare. Nace to, jiya nayi neman duniya in sama gida ko na hayane in biya shekara amma abun ya gagara.  Shine fa yau tun safe ya turo dan ladi da wannan matasan suka zo suka fara watso mana kaya waje.  Mutumin ya ja dogon nunfashi yace "Lalai wannan mutumi ya cik...". Hayaniyar da sukaji a kofar gida ce ta tsayar da mutumin bai karashe magana ba.  Kamal jiki na rawa yake cewa. "Wallahi Alh. Ne kaga sai da nace ma ka gudu-ka-gudu amma kaki, to yanzu gashi nan ya debo yan daba".  Mutumin hankalin shi kwance yace "Abunda nake so da ku yanzu shine kuyi sauri ku shige daki kai da matar ka".  Ba gardama kuwa suka shiga suka kulle dakin._

_Alh. Dayyabu Ne a gaba Gefan shi Dan ladi sai kuma wasu garada su hudu Katti ne majiya karfe ko wanne ka kalla fuskar shi zata gaya ma ba imani. Kursiyya tsakar gida ta zo ta yi tsaye ta dan bubuda kafafu ta mayar da hannuwa baya. Irin tsayuwar guards. Alhji ba abunda yake in banda zage-zage. Yana ganin mutumin da tsayuwar sa sai ya tsaya cik!  Suma gaba ki daya suka tsaya. Alhj._

_Ya kalle mutumin sama da kasa tukun ya bushe da dariya yace "Kai Amma Dan ladi ban taba sanin kai mashiririci ne ba sai yau. Yanzu dan Allah a kan wannan dan Yarinyar ne ka taso mu ni nama dauka wani jibeben gardi zan gani har na kwaso karti hudu. Hakan ma cewa kake wai na kara wasu. Yo wannan karamin alhakin ko ni ai sai in tumurmusa shi".  Dan ladi ya kara matsawa kusa da alhji yayi ya mai rada a kunne. "Alhj bar ganin shi haka kashi daya ne da shi. Da hannu daya fa ya dagani sama".  Cikin fada da bacin rai alhaji yace. "Kai rufe min baki matsoraci   kawai bari kaga insa ayi min guduwa-guduwa da shi. Tiger Da Musa lion ku kamo min yaran nan yau sai ya gaya min gidan na ubanshi ne da har zan sa a fitar da mutane ya ce a mayar".  Rufe bakinsa ke da  wuya, Sai kuwa karti biyu suka nufi Safuratu ko wannen su a murmurde yake fuskokin ba annuri. Safuratu  Da  ganin sun nufo ta sai ta ruga a guje ta shige bandaki.  Su tiger suka bita a guje suma. Da zuwa suka tarar da ba kowa a ban dakin sai wata yarinya dake kallan su tana murmushi. Musa Lion ya chakumi rigar ta ta baya ya dage ta sama da hannu daya. A haka suka fito sa ita. Alhaji tun kafin su karasa gurin sa yake cewa. "Kai bana san iskancin banza fa. Ya nace ku kamo min wancan dan Yarinyar zaku kamo min wannan karamar tsakuwar".   Tiger ya bude baki maganar shi ita kadai ta isa ta tsorata mutum. "Alhaji ai shine ya koma haka dq alamu yana da layar zana"._

_Alhaji yayi dariya. Hehehehehehe, "Au! Wato shine ya koma wannan Yarinyar nufinshi zamu kyale shi ne".  Alhaji ya matsa gaf da Safuratu dake rike a hannun tiger sosai alhaji ya matsa kusa da ita yana mata wani irin kallan raini. har hancin shi na gogar nata. "Wato kana nufin da ka koma wannan Yarinyar muyi hakuri mu kyale ka ko. To kuwa kayi kuskure domin da ka tarye ni fada gwara ka taryi RUNDUNAR SADAUKAI. Domin ni nan da kake gani na nafi kububuwa hadari. Sannan bani da imani ko miskala zarratun, Saboda rashin imanina cinnaka ake cemin baka san na gida ba ciji Jariri in uwar ta motsa in galla ma..." Ai kafin ya rufe baki Safuratu ta cije shi a hanci harda jini. Kafa tasa ta harbi tiger a ciki. Dan zafin da yaji baima san lokacin da ya sake ta ba.  Da gudu ta nufi wani bangare na gidan. Alhaji rike da hanci yace "Ku kamomin wannan dan iskan ku cinye shi danye". Da fadar haka su duk hudun suka bi Safuratu da gudu. Kamar biri haka ta kama gini makal-makal ta haye kan soro. Su tiger na zuwa sukayi tsaye suna kallanta. Irin dutsen da ake dorawa a saman kwano gudun kar iska ya dauke ya yace kwano. Shi Safuratu ta dauka ta daga sama alamun jefowa zatayi. Da ganin haka suka tsaya cik suna kallanta. Dariya Safuratu kafin tace "In da mai so ya bakunci lahira a cikin ku ya karaso"._

_Cik! Suka tsaya suna kallan ta domin kuwa sun san cewa duk wanda aka bugawa wannan dutsen ba a kai ba ko a  wani bangare na jiki ne ya banu. Ganin sunyi tsaye ba mai niyar zuwa alhji yace, "Tiger dama abunda na daukko ku kuyi kenan?. Bana san iskancin banza fa". Cikin maganar su irin ta yan daba yace "Wannan maganar rai ce fa ake, ahhee Bar gani na a haka daga ta kwada min shi zaka ga na fara ah yane a nan gurin. Allah. Alhaji".  Ran alhaji ne ya baci nan ya fara tattare babbar riga "Bari ni inje tunda ku bazaku iya ba". Da sauri dan ladi ya rike shi. "Aa alhaji karkaje wallahi Waccen daga gani ba imani zatayi ba". Safuratu ajiye dutsen tayi ta kalli tiger suna hada ido sai kuwa idanun shi suka koma bakake wul! Ba ko alamar baki a ciki. Da faruwar haka ta diro daga saman Soran.  Musa lion da sauran biyun suka nufe ta a guje kafin su karasa sai ganin Tiger sukayi ya shige gaban ta. Da ganin idanuwan shi suka gane ba lafiya ba. "Ku tsaya". Tiger ya fada da karfe muryar kamar wanda yayi magana a Loudspeaker. Cik suka tsaya. Abun mamaki duk wanda suka hada  ido da tiger sai shima idanun su koma baki kirin gaba dayan su haka.Alhaji da Dan ladi suna tsaye kallan ikon Allah kawai suke. Da faruwar haka Safuratu tace "Kuje ku daukko min alhaji da yaran sa dan ladi ku kawo min shi gaba na".  Gaba daya su hudun suka juya suka nufi alhaji. Da gudu dan ladi ya juya da niyar ya tsere ai kafin ya isa kofa tuni wani yasha gaban shi. A kafada aka sabo su alhaji aka dire a gaban Safuratu. Alhaji na karkarwa yace...........,......................_

πŸ€” *KAIKAYI YA KOMA KAN MASHEKIYA* 😳

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 91-92

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

😘😘 DEDICATED YOU MY SON *MUBASHSHIR*​

     ​HAPPY BIRTHDAY *MUBASHSHIR*​

πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚?
πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Allah ya karo shekaru masu albarka

Happy  2+ 😘😘😘

?πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚

πŸ’ƒπŸ» *I'M HAPPY* πŸ’ƒπŸ»

*HAPPY MAULIDIN NABIYYU SALLALAHU ALAIHI WASALLAM*  ☺πŸ’ƒπŸ»

*Bazamu taba mantawa dake ba ya masoyin Allah.*

*Bamu da kamar ka ya shugaban mu..*

*Mun san cewa duk irin so da kaunar da muke maka bazamu yi rabin san da kake mana ba ya Habibullah*

*Mun gode wa Allah muna kara gode masa a kullum.da ya bamu kai ya Rasulillah.*

*Bamu da komai bamu da kowa sai kai manzan Allah. Ka cece mu ranar da ba mai ceto sai kai. Ba dan matsayin mu ba dan girman Allah ya Rasullillah* πŸ‘πŸ»πŸ’ƒπŸ»

Makiyan ka sun tabe. Masoyan ka baza su taba tabe wa ba. Saka mu cikin masoyan kaπŸ‘πŸ».

Dole muyi murna da zuwan ka ya shugaba. 😟 Wanda basa murn bakin ciki ya kahe su 🀷🏻‍♂

*YA ALLAH KA KARAWA ANNABI DARAJA. AMIN*

       *KARSHEN PAGEN BAYA*

_*"D*an Allah dan annabi kiyi min afuwa ki ceci rayuwa ta wallahi bansan ke din Aljana bace".  Safuratu ta harare shi. "To ai yanzu kasan ni Aljanar ce. Naga kamar ka kwaso wadan nan kartin banzan ne domin suzo su tumurmusa ni dan na hana a  watsar wa da nayin Allah kayan su ko". Da sauri alh. Yace Aa wallahi sam ba da niyar haka na zo ba. Ni nazo ne ma in c na bar musu gidan su rike. Amma dan Allah karki yi min komai".  Kamal da kadija da sukaji shirun yayi yawa basu ji ihun mutumin nan ba. Sai kamal ya taso ya leko. Yana ganin Yarinyar nan kuwa kwalwarsa ta shiga aikin bincike yana kokarin tuna inda ya santa amma hakan ya gagara. Khadija ya kari itama ta leka kamar dai shi. Itama taso ta san Yarinyar amma ta manta a ina._

_Safuratu tace "Aa  ka rike gidan ka ai yanzu idan ka basu kyauta. Watakil wata mai tsayuwa zaka zo kace su tashi ka fasa. Dan haka bari a biya ka kudin gidan ka". Bat! Safuratu ta bace. Sai bayan kamar mintuna biyar ta bayyana rike da jaka. Ta mikawa alhj. Dayyabu hannu na karkarwa ya karba. Tace ya daga ya gani. Ya daga kudi ne bandir-bandir na dubu-dubu. Safuratu ta dauki biyu daga ciki tace. "Kudin nan Million daya da dubu dari ne. Ina ce dai sune kudin da ka arawa kamala".  Kai ya jijiga alamun eh. "Wannan dubu dari biyu da kaga na dauka kuwa Khadijah zan bawa matar kamala domin ta sasayi duk abunda yaranka suka lalata mata wajen fiddo kaya. Daga yau karka kuma kallan gidan nan balle ma kayi mafarkin zai zama naka".   Alhj. Duk a tsorace yake kamar kace arrr! Ya zurq aguje. Yaran shi kuwa sunyi tsaye kem! Kamar wanda aka sasaka. "Kamala! 2×". Safuratu ta kwala mai kira. Da sauri ya amsa suka fito tare da matarshi suma duk tsoro ya kamasu domin idanun su sun gane musu abunda duk ya faru._

_Safuratu tace "Na biya wanna mutumin kudin shi da ya ara maka. Yanzu wannan 400k din dake wajen ka kaja jari ke kuma ga wannan ki saya duk abunda suka lalata miki wajen fito da kaya".  Kamal da matar shi mamki suka cika da shi sai godiya suke. Kana kallan fuskokin su kuwa zaka gane akwai alamar tambaya.  Tsaya Safuratu ta dakawa alhji. Da yaran shi, tashi  yayi ya runtuma a guje haka suma yaran firgigit! Ko wannen su kamar wanda aka tayar daga barci sukayi waje a guje. Safuratu ta mike tace "To ni zan tafi kuma sai wani lokacin. Cikin su ba wanda yace uffan!. Har ta fara tafiya Kamal yace "Dan Allah ke din wace ce?". Jiyowa tayi fuskar ta dauke da murmushi wanda shi ya kara fito da kamanin Yarinyar kwanaki nan take suka gane ta. Safuratu tace "Ni ce Yarinyar da kuka taimaka kwanakin baya. Wannan sakamakon alkhairi ne. Kunsan Allah ma yace . "Shin kyautatawa nada wata sakamako?,Face Kyautatawa".RAHMAN 60 AYA:._

_"Kuyi hakuri wancan karon da na tafi ba tare da nayi muku sallama ba. Ni kaina naji dadin zama daku. kuma zan so ci gaba da zama daku duk da ni ba mutum bace sai dai kuma ayyukan gaba na baza su barni in zauna tare da ku ba shiyasa ma kawai na tafi a lokacin".  Hawaye ne ya fara zubowa Khadija. "Shin dan Allah yanzu ma tafiya zaki ki barmu?. Kinsan irin Son da ake miki kuwa. Tun ranar da Kamal ya kawo ki gidan nan ya fada min cewa baki da kowa kuma gaki kurma. Hakan yasa na kamu da tsantsar sanki da kaunar ki dan a lokacin sai naji kamar an yaye min bakin cikin da nake ciki na rashin haihuwa. Kwatsam kuma a daren ranar sai kika gudu kika barni. A ranar ga kamal nan wuni nayi ina kuka domin ji nayi kamar Na haihu 'yar ta mutu ne".  Tana zuwq nan ta fashe da kuka Kamal ya kwanto ta jikin shi yana lalashi. Sosai ta bawa Safuratu tausayi domin itama sai da hawayen suka zubo mata. "Khadija kiyi hakuri ki sani cewa aikin da na daukko babban aiki ne bazan iya tsayawa a nan gidan na wasu kwqnaki ba domin in nayi hakan wasu da dama zasu shiga matsala. Zan dai riga zagayo ku in na sama dama in sha Allah. Kuma zan na taya ku addu'a Allah ya baku haihuwa". Da karashe fadar haka Safuratu ta bace._

_Bata bayyana a ko ina ba sai kofar shagon Muktar. Ta bayyana ne a cikin shigar wata tsohuwa almajira fuskar ta duk a yaya mutse, Duk wanda yaga tsohuwar nan sai ya tausaya mata. Faced din shagon matar ta nemi waje ta zauna.  Ba abunda take sai kallan Muktar. Duk juyowqr da zaiyi sai yaga sun hada ido da matar a zuciya yace "Waccen fa ina ga yunwa take ji. Kuma yaseen ko mutuwa zakiyi bazan baki komai ba".  An kwashi mintuna ya kara juyawa yaga dai again shi take kallo abun ne ya bashi haushi a fusace ya fito daga shagon dan bala'i ko rufe wa baiyi ba kanta yaje ya tsaya yana ta surfa masifa sai kace ya sama sa'ar shi. Ita dai ba abunda tace sai idanu da ta kwalalo mishi ko kiftwa batayi. Daga karshe yace "Kinga malam in ma ke mayya ce wallahi kurwata tafi karfen ki. Haba wannan kallo kamar naci ban biya ba". Ganin taki tankawa ya juya ya koma shago. Abun haushi da takaici har yanzu bata daina kalla shi ba. A zuciya tunanin abunda zai mata yake domin iya bacin rai ranshi ya gama baci. Wai tama rasa wanda zata je ta tsare da kallo duk shagunan makwabtan shi sai shi. A fusace ya kara fita ya koma wajen ta masifa har kamar ya dake ta yake. Mutane na ganin haka suka je suka bashi hakuri hade da tada tsohuwar daga wajen.  Can da yamma kuma sai gata hannun ta rike da kwanan bara.  "A bamu saraka a bamu ta annabi. Alllah ya baku mu samu. Ka bada Qalilan rabbana ya maiyar da Kasirran"._

_Shiru Mukhtar yayi ba tare ya dago kai ya kalle ta ba. Kamar dazun sake maimaitawa tayi "A bamu saraka a bamu ta annabi. Alllah ya baku mu samu. Ka bada Qalilan rabbana ya maiyar da Kasirran". Dogan tsaki yaja.  Tsohuwa bata tafi ba kara fada tayi "A bamu saraka a bamu ta annabi. Alllah ya baku mu samu. Ka bada Qalilan rabbana ya maiyar da Kasirran". A fusace Muktar ya dako "Anki a bada malam dallah ki ware ki  ishi mutane". Kara murtuke fuska yayi "Ke wai me zan miki ne tun dazun kin takura min haba malama ni kadai ne mutum a nan ne. Ko kuma sadakar dole sai ni ne zan bayar..."   Fada yake surfa mata kamar wanda ya sama diyar shi.  Kyalkyale wa tayi da dariyar mugunta. Hannu tasa ta kwaye rabin fatar fuskar ta. Abun da yayi mutukar girgiza Muktar kenan nan take ya kama karkarwa ya zube a wajen yana bata hakuri domin ya gane wace ce._

_Muryar ta ba dadi Tace "Wato dama abunda duk na gaya maka bai shiga kunnen ka ba ko. Naga ma yanzu saura kadan ta rage ma ka fara dukan maryam yarinyar da na baka amana. Da kudin ta fa kake ci kake sha. Amma naira hamsin ka kasa bata".   Muktar yama rasa ya zayi yasan dai yanzu bashi da wani abunda zai kare shi.  Magiya hadata da Allah da annabi yake. Safuratu ta daka mishi tsawa hade da cewa yanzu zan yi ma hukunci kuma irin shi zanci gaba da yi ma muddun baka dai na abunda kake ba. Zan raba ka da duniyar mutane can zan kaika in da bazaka ga kowa ba sai Dabbobi su kuwa sun fika rashin mutunci, kaga sai ku hadu kutayi in baka ci sa'a bama Kora ko zaki wani ya cinye ka".  Tana rufe baki bat! Suka bace yare muktar sai ganin shi yayi a wani kurkurmin daji ba abunda kake ji sai kukan tsuntsaye ga kuma kukan namun jeji. Wata murya da Muktar ya rasa daga ina take fitowa "Muktar wannan shine hukun cin da ya dace da kai zan barka a nan kayi yan kwanaki nasan zaka kara daukan darasin zaman duniya ka gane cewa rayuwa ba komai bace". Hannu muktar ya dora a kai ya fashe da kuka "Dan Allah dan annabi kiyi hakuri wallahi na tuba bazan karaba karki min wannan hukunncin". Shiru yaji ko uffan ba'a ce masa ba. Nan ya durkushe yana ta kuka........................................_

πŸ™†πŸ»‍♂😧 *MUKTAR DAGA YAU SAI ASAN MUTUNCIN DAN ADAM. KO YA YAKE BA ABUN A WULAKANTA BANE. BAKA SAN KALAN BAIWAR DA ALLAH YA MASA BA*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi  like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  king boy

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 93-94

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

😘😘 *DEDICATED MY ASSOCIATION ZAMANI*

πŸ‘πŸ»πŸ˜° ```FATAN ZAKUYI MIN AFUWA. MUNYI BIKI NE BANA SAMUN TYM DIN TYPE. AMMA YANZU IN SHA ALLAH IDAN NA FARA SAI NAJE KARSHE``` 😟

INA ALFAHARI DAKU MASOYA NA πŸ’ƒπŸ» ANA TARE 😘

_Bayan ya gama kukan ya tashi ya hau zagaye dajin, Yayi yawo sosai amma ko alamar gida balle mutum bai gani ba. Safuratu kuwa gida ta koma ta juye zuwa Muktar din. Haka taci gaba da kula da harkokin sa har na tsawon sati guda. Muktar kuwa na can dajin wani lokacin ma abincin da zaici wuya yake masa,_

_Loaci daya rayuwa ta juye mai barci sai dai ya sama wani dan kogun dutse ya shiga ya kudundune. Haka kuma ruwa sai dai yaje wani dan gulbi da yaga ruwa na taruwa yasha. Yayi kuka sosai kuma yayi nadamar abunda ya aikata. A zuciyarsa ya kudurci niyar cewa bazai sake aikatawa Maryam makamancin wannan ba. Yayi kudirin zai rike ta da gaskiya kamar yarsa. Haka kuma kwanakin nan  da yayi duk lokacin da yunwa ta takura mishi sai ya dinga tunowa da almajirai masu zuwa wajen shi, Abunda yake zuwa mai a rai shine suma fa haka suke ji yayin da suke jin yunwa. Mukhtar a zuciya yake kudurtar niyar bazai kara hakan ba. Yau aka cike kwanaki bakwai cik! Da kawo Muktar daji. Tun da safe Safuratu ta bayyana mishi nan ta zaunar da shi yana ta tuba yana neman afuwa. Tace "Muktar ya zuciyar taka tayi sanyi ne ko har yanzu cike take da rashin imani da gurin cutar yar da take a matsayin sana'ar ka. Rufin asirin ka".  Muktar da yake durkushe gwiwowin sa a kasa. Harda hawaye, Cikin kuka yace, "Dan Allah dan annabi kiyi hakuri dan Allah ki ceci rayuwa ta ki fitar dani daga wannan wahalar._

_Nayi miki alkawarin cewa bama Maryam ba in sha Allah duk wani wanda yake neman taimako zan taimaka masa gwargwadan iyawata".  Safuratu tayi mai wani irin kallo na tuguma, Kafin tace "Na saba dajin rantse-rantse daga bakin ire-iren ku na karya. To ka sani cewa in har baka daina cutar da maryam Allah, Allah kaji na rantse ko. To gaba daya sai  na amshe duk dukiyar ka ka dawo kamar dai da yanda kake a lokacin da ka karbe musu kudi. Zanje kuma in nemi mutumin kirki in bashi amanar Maryam. Da wannan karon ma abuna nayi niyar yi kenan. Kuma in kana ji wasa to ka sake kwatanta Rashin imanin da kake"._

_Muktar ya sauke ajiyar zuciya yace, "Na rantse miki har da Allah na canzu zaki same ni ba kamar da ba. Domin wannan horan da kika min ya ankarar dani abubuwa da dama. Dan haka ki taimaka ki mayar dani gida. Nayi kudirin ko da kuwa kin kwace Maryam da dukiyar ta daga hannuna bazan fasa wannan kudirin ba. In sha Allah zan taimaka wa duk wanda ke da bukatar in taimaka wa". Wasu kaya Safuratu ta mika mishi tace yaje ya saka su.  Ba dade ba sai gashi ya sanyo su. Makulin shagon ta bashi kafin kiftawar ido sai ganin shi yayi a kofar daki. Dake ya saba da shiru na cikin daji yanzu duk sai yaji hayaniyar nan ba dadi. Bankwana Safuratu tayi mai hade da kara nanata mishi cewa ya kula ya canza hali.  Safuratu yau din nan ta tashi ne da tunanin Fatima kuma zuciyar ta na raya mata ba lafiya ba.  Hakan yasa ta tashi da niyar komawa bauchi yau._

_____________________

_A bangaren Fatima kuwa bayan kwana biyu da tafiyar Safuratu Zuwaira da Hauwa suka  taso ta gaba wai su sai sunga abunda mama Asiya ta gaya musu ko gaskiya ne. Ai kuwa suka fara takura wa Fatima tun suna zaginta har suka fara dankwashi. Ganin ba abunda ya faru ne yasa suka kara kaimi wajen cin zalin ta. Daga karshe ma a gaban jama'a har da kuwa Mama Asiya  hauwa da Zuwaira suka karbe yar babyn Fatima sukayi gutsun-gutsun da ita. Nasmat, Asmart, Ameera, da Mama Asiya duk sai suka fara tausaya wa su Zuwaira a kan abunda suka wa yar babyn dan a tunanin su Aljanar in bata kashe su ba sai ta kusa. Su kuwa su Hauwa hankalin su ko tashi baiba._

_Daga karshe ma tatara yar babyn sukayi suka kone ta rumus a tsakar gida. Fatima ta fara kuka   ai kuwa suka same ta suka ta narka taci duka har sai da ta gode wa Allah.  Bayan kwana daya-biyu su Mama Asiya sunyi mamkin ganin ba abunda ya faru da su Zuwaira gashi kuwa kullum cikin duka da zagin Fatima suke. Hakan yasa suma gaba daya gidan suka koma ruwa. Wato kowa ya koma kamar da zalluncin da ake wa Fatima har ya kusan linka na da ma. Haka abba yanzu kusan kullum sai ya daki fatima ko ya aike ta gu mai nisa. Fatima na shan wuya sosai. Dan ko yau haka ta tafi makaranta ko guntun biredi bata ci ba. Safuratu na isa gidan tace ta duba dakin su Fatima bata ganta ba. Shiyasa tayi tunanin ko tana makaranta ne. Sai dai  kuma ta duba inda Fatima ke ajiye babyn ta amma bata ga komai ba. Hanyar makarantar ta nufa. Dan daga nan har sai da ta shiga gidan Umar. Kallo daya tawa Rafy ta gane cewa tana cikin farin ciki. Domin sai aikin gida take hankalin ta kwance tana wake-wake._

_Nan dai ta bayyana suka gaisa take tambayar Rafy ya zama gidan. Rafy tayi mata godiya tace ai yanzu suna zaman lafiya sosai da mijin ta. Hamdalla Safuratu tayi nan dai suka hau hira. Safuratu kam hankalin ta duk yana wajen Fatima. Lokacin ta so su Fatima nayi tayi sallama da Rafy ta fito ta taryi Fatima.  Tafe take tana wani rangaji kamar zata fadi, sai zubar hawaye take. Ba komai akayi mata ba yunwar ce kawai ke cinta domin bata saba kai war haka bata ci komai ba.  Daga nesa Safuratu ta hange ta. Karasa wa kusa da ita tayi tana kare mata kallo. Irin  ramar da Fatima tayi ne abun ya tsorata Safuratu. Domin in ba kayi wa Fatima kwakwaran sani ba. Bazaka iya gane ta ba a yanzu. Dan duk kashin wuyanta ya fito ta rame sosai. Tangal-Tangal din da Fatima keyi har idanta na rufewa hakan ya shedawa Safuratu Fatima najin matsanan ciyar yunwa._


  _Sharf!  Fatima ta fadi kasa Safuratu na ganin haka tayi sauri ta shiga jikinta. Mutane har sunyo kanta da niyar agaji kuma sai sukaga Yarinya ta mike.  Karasowa sukayi wasu na kakabe mata jiki suna mata sannu. Idanun Fatima suka kara zarowa daga ka ganta zaka ga ba kamar da ba. Yar ledar littatafan Fatima ta dauka ta nufi gida. Kwan! Kwan! Kwan! Kwan! Da karfi Fatimar ke buga gida. Mai gadi najin haka ya taso a rikice yana fada yana fadin "Waye wannan yake mana irin wannan buga gida kamar tashin duniya".  Buga gidan bana wasa bane domin da karfi Fatima ke bugawa.  Har mai gadi yazo yana kokarin budewa amma bata dai na bugawa ba. Yana budewa yaga itace. Ya tsaya tsabar haushi har karkarwa yake. Dan ji yayi kamar ya mare ta duk da tana yar gidan. Fatima ganin mai gadi baya da niyar matsawa. Fuuu! Ta bangaje shi ta wuce can ya fadi kasa a gigice. Domin irin bangajewar da Fatima tayi mishi ba karamin kato bane zai yi masa ita har ya fadi. Yayi mamaki sosai. Tashi ya kakabe jiki ya juya yana kallan Fatimar domin ya kara tabbatar da ita din ce ko wata.


_"Tabbas Fatima ce, to amma ina ta sama wannan karfi haka".  Shi kadai yake kallan ta yana magana shi daya. Kofar falo Fatima ta ja da karfi kamar zata ballata. Yanayin yace labulan kadai kai in ka gani kasan bana arziki ba.  Hauwa ce kadai a dan ringeshe kan sofa tana tauna Cingum tana daddana waya. Tana jin shigowar Fatima ta tashi zaune. Ita Fatimar ta nufo. Ita kuwa wani matsiyacin kallo take bin Fatima da shi mai dauke da harara._

_"To shegiya har an taso daga makaranta wato za'a zo a ishi mutane da kuka. To kafin ki fara komai ajiye kayan makarantar ki shiga dakina kiyi mopping dinshi ki gyara komai kafin kizo in fada miki next work naki". Fatima kam tsaye take ta kafe Hauwa da ido bata ko giftawa. Hauwa ganin Fatima taki wuce wa tayi abunda tasaka ta tace. "Ke dan uwarki ba kiji abunda nace kije kiyi ba. Yar buhun uba kin wani tsare ni da wannan shegun idanun naki. Ko dai na jaki kike so yan...".   "Ina abincina?".  Shine abunda Fatima ta fada hakan yasa Hauwa bata karashe maganar da ta fara ba.  "Iyee Fatima ni zaki wa rashin kunya?.  To bari kiji dan ubanki ko langen taliya bazaki ciba yau a gidan nan. Oh! Baki ji abunda aunty zuwaira tace ba ken...".  Cikin tsawa da kagara Fatima ta kara fadar, "Ina abincina na ce?".  Abun ne ya fusata  Hauwa hakan yasa ta daga hannu da zafin ta da niyar wanka wa Fatima lafiyayan mari. Charf! Fatima ta rike hannun hade da Wanka wa Hauwa mari da dayan hannun ta................................._

~Cikin tsawa da kagara Fatima ta kara fadar, "Ina abincina na ce?".  Abun ne ya fusata  Hauwa hakan yasa ta daga hannu da zafin ta da niyar wanka wa Fatima lafiyayan mari. Charf! Fatima ta rike hannun hade da Wanka wa Hauwa mari da dayan hannun ta.~

_*G*alala Hauwa ta saki baki tana kallan Fatima cingum din da take ci ma bata san lokacin da ya fado ba. Rike kunci tayi tana jin radadi a zuciyar ta tana fadar "Anya wannan Fatima ce?".  Hannu Fatima ta sake dagawa da nufi mari "Ina abincina nace?".  Da sauri Hauwa tace "Bari in daukko bari in daukko miki". A tsorace ta mike ta nufi kitchen din Fatima na binta da wani malalacin kallo._

  _Hauwa taje ta zubo mata abincin ta kawo. "Yauwa Fatima ga abincin".  Ta mika hannun ta na dan karkarwa.  Fatima na amsa ta zauna a nan ta fara cin abincin hannun baka-hannu kwarya. Juyawa Hauwa tayi da nufin haurawa upstair dakin ta. "Ina kuma zaki je dawo ki zauna". Fatima ta fada ba tare da ta dago kai ta kalle Hauwa ba.  "Umm umm da... Da.. Ma zanje ina... Jin fitsari nee".  Hauwa tayi maganar murya na karkarwa. Dan duk ta tsorata da Fatima tasan ba ita kadai bace, Akwai lauje cikin nadi. "To ba yanzu ba dawo ki zauna". Fatima tace ba tare da ta kalle ta ba. Hauwa har zatayi magana. Fatimar ta daka mata tsawa hakan yasa ta gimtse bakin ta. Sumi-sumi ta zo ta zauna. Sai kallan Fatimar take wanda sai cin abincin take kamar wacce tayi shekara bata ci ba. "Innalilahiwa'inailaihirraji'un 2×, Me zan gani haka".  Zuwaira ce ka fadar haka lokacin da take saukko daga kan matakalar tayo kasa._

_Da sauri ta karaso gurin ta tsaya kan Fatima tana zazaga masifa. "Hauwa haka mukayi dake wato in kafa doka har kin isa kisa kafa ki shure ko?. Wato wuyanki yayi kwari, Ni dake waya fara shigowa gidan nan ko da baki min biyayya a matsayin ki na kanwata wacce nafi shekaru ba. Ai ya kamata kiyi min biyayya a matsayina na wacce ta riga ki shigowa gidan nan". Hauwa kallan Zuwaira kawai take tana kallan Fatima dake faman dibar Shinkafa fara da miya. batace ko kala ba. Zuwaira taci gaba da cewa "Sanin kanki ne nace yau yarinyar nan bazata ci ko kwayar shinkafa ba a gidan nan amma gashi nan kin dauka kin bata. Wato ke uwar tausayi. Zanyi maganin ki kuwa". Hauwa kallan Zuwaira kawai take tana mata wani kalan uku goma hudu shabiyar. Kasan ranta kuwa  addu'a take Allah ya kai damo ga harawa._

_Fatima ce ta mike rike da filet din abincin. Kamar jira take Zuwaira na juyawa kuwa ta yaba mata shi a fuska. Bata jira komai ba ta juya ta nufi dakin su.  Hauwa na ganin abunda ya faru ta kwashe da dariya harda rike ciki. Zuwaira kuwa cik ta tsaya kamar wacce suka gasar tsayu ita da gunki. Haushi ya kule ta can kasar ranta tunanin abunda zatayi wa Fatima take. Dan kakabe jikin ta tayi miya duk ya bata mata kaya. In ka ganta sai ka rantse wasa da miya tayi.  "Ni ni ni Fatima tayi wa haka,_

_Lalai Yarinyar daga ni kuwa bazaki kara ba. Yau ko makiyin ki sai ta tausaya miki Fatima".  A fusace tayi waje, Nan take zuciyoyi suka shiga aikin bata shawarwari na mugunta wanda zatayi wa Fatima. Dakin mai gadi ta zarce. "Fito-fito mai gadi, Ina wannan dorinar taka mai baki biyu?".  "Tana daki Hajiya". Har dan jijiga take yi dan kaguwa "Bani aranta yi sauri dan Allah".  Kallan ta ya tsaya yana yi "Hajiya wa kuma za'a daka da ita. Naga yaran duk suna makaranta?". Tsawa ta daka mai, Nan da nan ya zabura ya shiga daki ya daukko mata. Yana bata ta nufi wajen tankin ruwa ta debi ruwa a irin yan kananun bokitin nan. Ta nufi falo da shi. Fridge ta nufa da sauri ta daukko kankara ta zuba a ciki tukun ta shiga tsiyayya ruwan sanyi. Ita kadai take magana. "Dan ubanki ai yau kin shiga uku sai na jikaki da ruwan sanyin nan tukun in miki dukan kawo wuka. Badai ni kika wa wannan wulakancin ba".  Tana gana matse pure water mai sanyi ta dauki dorinar da bokitin ruwan wanda zuwa yanzu tuni ruwan yayi mugun sanyi. Ta nufi dakin su Fatima. Hauwa dai na zaune a falo ido kawai take binta da shi._

_"Ayi dai mu gani in tusa tana hura wuta".  Inji Hauwa ta fada da dan karfi. Zuwaira taji ta amma bata kula ta ba. Dashigar ta dakin ta fara kwallawa Fatima kira. "Fatima! Fatima! Fito dan kut...uban ki. Yau ai sai kin raina kanki". Shiru bata ji ko motsi ba. A tunanin ta  Fatimar na ban daki. "Ki fito na gaya miki dan Wallahi in na iskeki a bandakin nan bazamu kwasheta da kyau ba. Sai nayi miki jini da majina Wallahi". Nan ma shiru bata ji an tanka ba. Bulala da bokitin ruwa ta dauka buzun-buzun ta nufi ban dakin da zuwa tasa kafa ta haura kofar da karfi. Kofa na budewa taga wayam. "Shegiya asbe ta gudu daga dakin". Falo ta fito "Hauwa ina wannan shegiyar Yarinyar ta nufa da ta fito?". Hauwa ta kalli Zuwaira Mamaki karara a fuskanta. "Au! Fatiman fitowa tayi ne?". "Kina nufin baki ma ga wucewar ta ba?. Fatima zaki gama guje-gujen ki kidawo ki iske ni har gida". Zuwaira ta fadi haka ta ajiye bokitin da bulalar a gurin, ta nufi Upstair da niyar taje dakin ta canja kaya._

_Da bude daki ta tsaya cik! Tana karewa tsakar dakin kallo Fatima ce gaba daya ta bince ke wardrobe din da su kabbet duk ta wurwatsa kaya a  tsakar daki. Yanzu ma sai bincike take tana bubude lokoki. "Aunty Zuwaira jan baki nake ta nema tun dazun a ina kika ajiye shi". Wani kululun bakin ciki ne yazo wa Zuwaira makogoro. Nan take ta kai dubanta Mirror ta hangi duk kayan kwaliyar ta har da jan bakin ma a wajen, "Wai amma dan rainin wayo wannan yarinyar tace wai jan baki take nema. Kai kawo dai wani tashen iskanci da rainin wayo ne. Amma bari inyi maganin ki yanzu". Jawo dakin tayi da sauri ta koma falo da gudu ta daukko bokitin ruwa da bulala.  Tana dawowo  ta bude daki kuma sai gani tayi wayam! Ba kowai sai tilin barnar da Fatima tayi mata. Domin shirya kayan da Fatima ta warwatsa kadai jarabar duniya ne. Gashi wasu kayan a goge ma suka amma Fatima ta kara tattake su. Hauwa na zaune a falo taga Fatima ta fito daga saman beni bayan ita kuma bata ga fitowar ta daga dakin su bama. Abun ne ya kulle mata kai. Fatimar tafe take hannun ta rike da dan karamin mirror na kallan fuska dayan hannun kuma jan bakine da take ta faman Gogawa a lips inta.  Tsaye taje tayi a kusa da Hauwa tana shafa jan bakin. Zuwaira tun daga sama kake iya jiyo jarabar ta. "Yarinyar kamar Aljana,yanzu nan fa na baro ta a dakin nan wai amma bata nan. Hmm dani kike zancen Fatima._

_Ai Wallahi in dai kere na yawo zabo na yawo wataran a hadu. Wai ni ta...".  Bata karashe fadin abunda tayi niya ba hango Fatima da tayi a falo. Nan take ta fara sauri tana kokarin sakkowa. Fatima hanyar dakin su ta nufa. Zuwaira dake rike da bokiti da bulala a hannu da gudy taje tasha gaban Fatima. "Ina zaki munafuka Allah ya kama ki. Yanzu zan chaskwala ki".  "Bani waje in wuce". Fatima ta fada cikin kagara. "Iyeee! Lalai Fatima arzikin rashin kunya yaci uban na da.Har ni zaki iya kallan kwayar idona kice wai in matsa ki wuce. Bari ki karbi hukunci tukun sai ki wuce ko da jan gindi ne". Kokarin ajiye ruwan take. Ai kafin ta ajiye wata irin bangaza da Fatima tayi wa Zuwaira can ta fadi kasa bokitin  ruwan yayi sama ya fado duk ya jijika Zuwaira da Carpet din falon. Wata mahaukaciyar  dariya hauwa ta kwashe da ita. Har da rike ciki hade da hawayen dariya._

_Zuwaira tace "Hauwa wai Giwa ce ta bangaje ni ko Saniya ko Rakumi?".  Hauqa kara kwashewa tayi da Dariya. Cikin matsanan ciyar dariya tace, "Duk ba ko daya a ciki".  "To dan Allah jirgin kasa ne ko mota._

_Domin kuguna ji nake kamar ya karye bani iya tashi yanzu".  Hhhhhhhhhhhhhhh Dariya kamar zata kashe ta. Karar dariyar ta ne ya tashi Mama Asiya dake can sama tana barci. Da sauri tayo Downstairs tana "Lafiya-lafita mi yake faruwa ne?".  Falan taga kaca-kaca Can an watsar da shinkafa da miya. Nan an kwarayar da ruwa. Hauwa ta kalla dake ta faman Dariya. "Ke kuma wanne irin iskanci ne zaki bata mana falo haka. Nan fa ba falon ki bane ke kadai balle kiyi mana kazanta".  Hauwa ta dan rage dariyar kadan tace "Aunty Asiya Wallahi bani bace aikin Fatima ne".  "Kuturun kareee!  Wace Fatimar?".  "Fatima tamu ta nan gidan mana". Cikin fusata Mama Asiya ta nufi dakin su Fatima tana fadar. "Ina take dan ubanta Wallahi sai ta gyara dakin nan tsaf!"................................................_

πŸ€£πŸ˜‚ *Wayyo cikina* _HAUWA DOLE IN TAYA KI DARIYA. SU ZUWAIRA MADARA ANJI JIKI, SAI KUMA A TASHI AJE AYI JINYA_ 🀧

_*KU BIYO NI ZAI-ZAI DAN WANNAN KARAN WANDA AKAYI BABU SHI BAI MORI LITTAFIN BA*_ 🀝

DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  King Boy Isah

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 97-98

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

DAN KADAN NE DAI. KUNSAN ANCE *"DA BABU GWAMMA BA DADI".*

*DEDICATED TO* πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ

😍😍
      *BIGBOY ISAH FANS*
        😍😍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
               😍😍
*GIDAN MARAYU FANS CLUB*
                       😍😍
*3STAR HAUSA NOVELS* πŸ’ƒπŸ»
😘 GODIYA TA MUSAMMAN GARE KU TARE DA FATAN ALKHAIRI. BANI DA KALAMAI KO AZANCI DA ZAN IYA MUKU GODIYA DA SHI. SAI DAI KAWAI ALLAH YA BAR MU TARE.

      *KARSHEN PAGEN BAYA*
~MUN TSAYA A INDA HAUWA TACE, "Aunty Asiya Wallahi bani bace aikin Fatima ne".  "Kuturun kareee!  Wace Fatimar?".  "Fatima tamu ta nan gidan mana". Cikin fusata Mama Asiya ta nufi dakin su Fatima tana fadar. "Ina take dan ubanta Wallahi sai ta gyara dakin nan tsaf!".~

_Mama Asiya na shiga ta iske Fatima zaune a gefan gado ta juya mata baya. "Fatima! Fatima!2×".  Shiru fatima ko waigowa batayi ba. Kara matsawa wajen ta tayi "Ke dan iskanci da rainin wayo kinaji ina kwala miki kira amma kikayi banza dani. Zonan dan ubanki". Gashin kan Fatima ta kama ta jawo ta kiiii! Har cikin falo, "Maza jeki daukko kayan mopping kizo ki tattara shinkafar nan da kika zubar ki wanke wajen miyar nan da kika zubda. Sannan in kin gama ki daukko tsumma kizo ki matse wannan carpet din da kika zubda ruwa a kai". Harara kawai Fatima ke binta da shi. Hauwa da Zuwaira dake zaune kan armchair tana wash-wash ba abunda suke sai kallan Mama Asiya da fatima. Zuwaira fatan da take shins Allah yasa Mama Asiya tayi ganganci wa Fatima._

_Duk maganar da Mama Asiya take Fatima ba abunda take mata sai mugun kallo. Mama Asiya da ta gama jawabin nata ta juyo taga Fatima na hararen cikin fada tace "Ke Fatima ba magana nake miki ba. Wallahi tallahi in raina ya baci bazaki ji dadi ba. Dan ba wanda ya isa ya kwace ki a gidan nan...". Duka ta kaiwa Fatima dim!  "Ni kike wa gatsine da uban ki. Bari ki gani".  Juyawa tayi ta dakko dorinar wajen Zuwaira. Fatima na ganin haka ta kyalkyale da dariya lokci daya kuma sai ta hade girar kasa da ta sama. "Zaki iya duka na da bulala. Na baki offer nan. Amma ki sani cewa duk bulala daya idan kika min ni goma zan miki". Mama asiya bata dakata ba ta nufo Fatima tana zuwa ta lafta mata balula. "Wuce kiyi abunda na saki". Wani malalacin kallo Fatima tsare mama Asiya da shi. Dan bulalar da aka mata sai ka rantse ba jiki aka daka ba domin kuwa ko motsi batayi ba. Mama Asiya ta kara buga mata bulalar tana nuna mata hanya da hannu._

_}"Ki wuce kiyi abunda na saki nace ko?".  Zata kara mata ne Fatima ta rike bulalar.  "Bulala ashirin ya ishe ki dan wannan jikin naki ba lalai ya dauki talatin ba". Tunanii mama Asiya ta shiga yi nazari take akan maganar da Fatima ta fada. Domin ita bata gane nufin ta ba. Tana tsakar tunani sai ji tayi Fatima ta fisge bulalar daga hannun ta ta Zura mata._

_"Wai-wai wai.. Fatima ni kika dak..". Ai kafin ta rufe baki ta kara jin saukar wata bulalar. Hakan yasa ta nufi Fatima da nufin ta kwace bulalar. Da gudu ta shige ta. Hakan yasa Fatima tayi saurin gocewa kuma tasawa Asiya kafa. Rigijimmm!  Kake ji ta Fatima. Su Zuwaira in banda dariyau ba abunda suke yi. Sai dai kuma daga Fatima ta harare su sai kowacce ta matse bakin ta. Fatima kan Mama Asiya taje tana Maka mata bulala tana kirge. "3..4..5..6..". Mama Asiya na tashi ta kara nufar Fatima a fusace. Tana Zuwa kusan ta Fatima ta kara sa kafa ta hangiza ta baya._

_Tagal-tagal ta tafi zata fada kan Coffee tabal din dake tsakar falo. Ganin in ta fada kanshi ya gama aiki dake na Glass ne  da sauri Fatima ta rike hannun ta. Ta mike tsaya. Ko da taga ta mike sai taci gaba da dukan ta. Wannan karan Asiya da gudu ta hau zagaye falon tana neman dauki. Fatima na binta tana zana. Duk wacce mama Asiya ta nufa. Hauwa ko Zuwaira sai su arce a guje. Sai da Fatima tayi mata bulala ashirin cik!. Tukun ta zauna kan kujera tasa Mama Asiya tayi Kneltdown a gabanta. Dage kai tayi gefe ta fara wa mama Asiya magana kamar yanda tayi mata dazun._

_Cikin gadara fatima tace, "Maza jeki daukko kayan mopping kizo ki tattara shinkafar nan da na zubar, ki wanke wajen miyar nan da kika zubda. Sannan in kin gama ki daukko tsumma kizo ki matse wannan carpet din da kika zubda ruwa a kai".  Jikin Asiya har yana rawa tace "To to an gama ranki shi dade". Zuwaira da Hauwa sun jin haka suka nufi Hanya zasu tsere._

_Kan Fatima a kasa ba tare da ta dago ba tace, "Ku muna fukai na baku damar tafiya ne?". Tsaye cik! Sukayi suna kallan juna. "Ku dawo nan ku tayata wannan aiki.  Bari inje in siyo halawa. Kuma saura inzo inga wata bata abun da na sata. Uhmmm Wallahi da jaki ma sai ya tausaya mata".  Fatima na fadar haka ta mike har ta nufi kofa kuma ta juyo. "Au!  Ashe ba kudi a guna". Kallan su tayi daya-bayan-daya Suma ita suka kwalalowa ido kamar wasu mujiyoyi. "Mai nera dari ta bani kun wani kwalalo min idanu. To tubarkallah kuci kanku".  Dajin haka suka shiga raba idanu, Suna kallan junan su. "Kaaaaaaaaaaaaaa! Daku fa nake". Wannan muguwar kuwwar ta daka musu wanda yasa duk sao da suka rufe kunnuwa. Dajin haka har rige-rige suke wajen daukko kudin._

_Zuwaira ce ta fara kawo mata. Hannu na karkarwa kamar wacce ke rawar sanyi ta mika mata  hade da cewa "Gashi dari biyar ne ba canji".  Wata muguwar harara Fatima ta bita da shi tukun ta karbi kudin fuuuuuu! Ta wuce. Dai-dai lokacin Mama Asiya da Hauwa suka fito da sauri ko wanne rike da kudi.  Zuwaira ta juyo "kudin ku sun huta. ta ai ta tafi". Mama Asiya tayi ajiyar zuciya hade da kallan su gaba daya "Shin mai kuka fahimta game da lamarin nan".  Kamar hadin baki su hauwa sukace. "Aljanar ce ta shige ta ba wani abu ba". Mama Asiya tace. "Haba nima nayi tunanin haka. Ji yanda Yarinyar ta juye lokaci guda ta zama abar tsoro. Ai kuwa sai munyi taka tsantsan domin Wallahi wannan zata iya sabauta mutum".  "Ahh! Ni Zuwaira yau naga tashin hankali. Gaskiya dole mu dauki matakin gagawa". Hauwa ce tace "Kunga Wallahi gwara muyi abunda tace kafin tazo ta fatatake mu". Mama Asiya ce ta koma kan kujera ta zauna._


_Da ganin haka itama Zuwaira ta je ta zauna.  Hauwa tayi musu wani irin kallo a gantsare tace "Shin me hakan ke nufi?. Ko kuna nufin bazakuyi aikin bane?". Su Mama Asiya kallo kawai suke binta da shi.  "Chabb! In kuwa haka ne Wallahi nima bazan yi ba. Gwara in Aljanar ta dawo tayi mana koma miye a tare".  Hauwa na fadar haka ta nufi wajen su ta nemi waje itama tayi zamant...................................................._

πŸ˜°πŸ‘πŸ» Kuyi hakuri da wannan kuyi min afuwa. Wallahi sai da karume-karume nayi type din nan. πŸ˜† Sai na fara sai kawai wani uzurin ya zo. Yanzu haka wani abokina ne  ya kawo min ziyara. I'm busy 😰

DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  King Boy Isah
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 99-100

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼  *®Z.W.A*

_*WANNAN PAGEN NAKA NE AUTAN ELOQUENCE. ALEWAR KANKANA MELODY*_

_Ku bani kidan birthday a sama._

πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Autan- Eloquence,  Kuce min Auta Eloquence Today is u birthday πŸ’ƒπŸ» Today is you birthday πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ».

πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚
*HAPPY BIRTHDAY MUSA MELODY AUTAN ELOQUENCE*

🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰

_Happy birthday Melody wish you many more Albarkakun years  head_ 😍😘

πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚

Allah ya yafe maka zunubanka na shekarun da suka wuce. Kuma allah ya baka wasu shekarun Masu albarka πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»​

     *KARSHEN PAGEN BAYA*
~"Chabb! In kuwa haka ne Wallahi nima bazan yi ba. Gwara in Aljanar ta dawo tayi mana koma miye a tare".  Hauwa na fadar haka ta nufi wajen su ta nemi waje itama tayi zamant.~

_*M*ama Asiya na ganin hauwa ta zauna sai tace, "Haba hauwa wai ke a zatan ki bazamuyi aikin bane?. Haba mu mun isa. waya isa yaki yi aljana ta zo ta karyashi. Kinga dama ni jira nake ki daukko kayan ne fa".  "Yauwa nima abunda na gani kenan". Cewar Zuwaira. Hauwa tace "To ai da na dauka  nufin ku bazakuyi ba ne". Fita tayi ta kwaso kayan mopping Har su tsintsiya da abun kwashe shara.  "To ku tashi gashi na daukko".  Mika mama Asiya tayi "Wayyy! Wallahi ni kam duk na gaji please dan fara. Kafin in taso". Zuwaira tace, "Ashe bani kadai ba gajiyar nan. Kinji kuwa yanda kuguna yake kamar zai balle"._

_Cikin hantara "Dallah yi min shiru muguwa kawai. Ai ban taba sanin ku mugaye bane azzalumai yan bakin ciki sai yau". Kallo suka tsare ta da shi, Yayin da ita kuma taci gaba da magana. "In ba zalinci ba kunsan cewa Yarinyar nan Fatima ba lafiya lau take ba, Kuna ganin zan mata ba dai-dai ba amma kuka ki dakatar dani...".  Tun kafin ta krasa maganar Zuwaira ta karbe ta da cewa "Wannan kuma Hauwa zaki cewa muguwa. Domin tun farko ita tasan cewa Aljanu sun shiga jikin Fatima amma taki wa mutane magana".Yar dariya Hauwa tayi hade da cewa, "Daga baya kenan. Ku tashi muyi aikin nan tun wuri Wallahi". Ganin basu da alamar tashi ita ma hauwan ta zauna hade da cewa "Wallahi bazanyi sharar nan ni kadai ba. Gwara in ta zo ko kashe wa zatayi ta kashe mu tare"._

_"Kanki ake ji".  Cewar Zuwaira.  Zaune suke kowa da tsoro a zuciyar shi, amma cikin su ba mai so a gane yana jin tsoran. Karar bude kofa sukaji.  Ai kafin kace kwabo, Tuni ko wacce daga cikin su ta tashi da sauri ta dauki abun ta fara aiki.  Su Asmart ne suka shigo gidan. Su mama Asiya na ganin su. Kowacce ta yarda abun hannun ta ta koma ta zauna. Mtsweeee!  Mtsewwww! Mtsewww Sautin tsaki kawai kake ji yana tashi. Su Nasmat kuwa mamaki ne ya cika su. Daga shigowar su sunji an tarye su da tsaki.  Har sun nufi dakin su Zuwaira ta kira su. "Kuyi sauri ku cire uniform din islamiyar nan kuzo ku share gurin nan".  To suka ce ciki-ciki suka wuce suna gun-guni. Bayan sun fito ne suka kama aiki, Fuskar su ba mai annuri kamar ta shanu sai gunguni suke. "Wai daga dawowar mutum daga makaranta ko hutawa baiba a saka shi wani shar...".   Shigowar Fatima ya hana Asmart karashe maganar zucin da take._

_Lollipop ne a bakin ta yana tsotsa ga wani biscuit a hannunta. Su mama Asiya gaba daya sun tsorace dan Zuwaira har yar karkarwa take. Nasmat tace "Wannan Yarinyar kuma uwar wa ta bata kudi har ta sayi wannan katan biscuit din?". "Uwarki ce ta bata".  Zuwaira ta bata amsa.  Shiru tayi tana kallan uwar tata da duk ta lura da yanayin ta a tsorace take. Asmart tace "Ke Fatima zo nan dan ubanki ki share wajen nan kal!, ki goge". Da sauri Mama Asiya tace "Sai dai ni uwar ki in share". Da fadar haka su Asmart suka fara tunanin akwai lauje cikin nadi. Fati dake bin su Zuwaira daya bayan daya da harara sai yanzu tayi magana tace wa su Asiya "Ku ku tashi ku tafi abun ku". Har rige-rige suke wajen tashi. Zuwaira har ta kusan zuwa Stairs ta juyo. "Uhmmm! Fatima chanji na fa". Cikin gadara Fatima tace, "Na bawa almajirai sadaka. Ko da magana?". "Aa"._

_Zuwaira tace ta wuce sama da sauri Fatima rufe ido tayi kamar me gyangyadi. Cikin tsawa Asmart tayi magana "Ke Fatima in kika yarda na  karaso wajen ki wallahi sai kin raina kanki". Shiru bata bude ido ba balle tayi magana. Nasmat dake kallan tace, "Ke wai ba magana ake yi miki ba?. Kin wani rufe ido kamar kazar dake gwaida".  A fusace Asmart tayo kanta da nufin ta dake ta._

_Fatima na bude ido tayi turus! Asmart taja birki tayi baya a guje. Haka itama Nasmt bata san lokacin da ta tsallake kojera ba ta wuce.  Kofar dakin su sukaje zasu shiga kenan sukaji an turo kofar da karfe.  Ba komai ne ya tsorata su ba. Idanun Fatima ne suka koma baki kirin gashin kanta ya wani mimike tsaye. "Ku dawo ku share gun nan. Ina zaku?". Suna karkarwa hade da kankame juna suka juyo. "ba inda zamu".  Cikin tsawa tace suzo su share gun. Da sauri suka taho suka hau aiki. Rufe ido Fatima tayi ta sake bude wa nan take kuma idanun ta suka dawo Normal. Su Asmart sai shara suke suna goge carpet ita kuwa Fatima ta mike kan Sofa Sweet take sha abunta tana wasa da Biscuit dinta.  Abba ne ya shigo yana jin waka._

_Ganin su Asmart na aiki Fatima a kwance ya daka mata tsawa wai ta tashi ta taya su aikin.  Fatima ko kallon shi batayi ba. Su Asmart ne suka ce yaje ba komai zasu karasa aikin. Washe gari da safe. An zuba wa kowa abun kari Indomie da biredi sai tea.  Asmart da Fatima gefan su guda. Fiddausi da amira ma. Haka suma yan kanana yaran. Sai abba da ya dawo falo ya zauna a nan yake break din.  Fatima ce ta fito daga dakin su ta nufi Dinner. Bata wani tambayi ina abincin ta ba taje ta dauke Tea da indomie na gaban Mama Asiya. Da ganin haka Abba ya daka mata tsawa. "Ke dan ubanki sa'ar kice da zaki daukar mata abinci".  Wata muguwar harara ta watsa mishi. Hade da murguda baki "Nata nake so kuma shi zanci in ka isa ka hana. Kuma ko da naka naga damar ci shi zanci".  Fatima ke kallan shi tana maganar. Tashi yayi ya nufi dinner din a fusace._

_Mama Asiya kamar ta dakatar da shi kuma wata zuciyar sai ta bata shawarar cewq ta barshi watakil Aljanun Fatima mata kawai suka raina.  Abba yana zuwa ya daga hannu ya kai mata mari, cikin hanzari ta goce.  Duka ya kara kai mata da kafa. Nan ma ta goce tana binshi da wani shu'umin kallo tana murmushi.  Mama Asiya da ta lura d Fatima da sauri ta zo ta janye danta dan kar a sabauta mata shi. Shi kuwa tuni ya hau daukin zuciya sai huci yake. Yana hararen Fatima da ita kuwa ko kula da shi batayi ba taje kusa da Fiddausi ta zauna tana shan tea.  Tana gamawa ta tashi  zata fita waje. "Ke dan uwar ki dawo kije kiyi shirin makaranta". Cewar Abba.  Ficewa tayi ba tare da tace mushi komai ba.  Abba yace_

_"Fatima ina tausaya miki. Dan Wallahi in na kamaki daga ni sai ke sai nayi miki fata-fata, Dan yau naga kin tashi da wani sabon salon iskancin". "Ko?". Fatima ma juyo tace mishi. Kofin shayin dake hannun shi ya wulla mata.  Ba abunda ya bashi mamaki sai ganin da yayi kofin yayi Kwana ya nufi wani wajen. Bayan ya gama shan shayin ya tashi ya nufi dakin shi domin yaje ya huta.  Yana shiga kafin ma ya bude kofa yaje kofar ta rufe kanta da karfki. Tsuru Abba ya tsaya yana kallan Kan bad dinshi wani abu ne cikin Blanket dinshi Yana gurnani marar dadi yana kuma mamotsawa._

_A hankali Abba ya nufi wajen hannun shi har karkarwa yake. Duk ya gama tsoracewa domin shi bai bar kowa a dakin ba. Kuma baima taba jin gurnani kalar wannan ba. Zuciyoyin suka shiga bashi shawara wata zuciyar na cewa ya bude yaga miyr wata zuciyar kuma na cewa ya fita ya gayawa su Mama Asiya. Ta wani fannin kuma ceqa yake "inje in sanar da su kamar dai ni din va namiji bane. Bari kawai in bude inga miye.  Hannun na karkarwa sai ya kusa kama bargon kawai sai yaja baya a tsorace. Kusan sau biyar yana yin haka. A na shida ne ya daure ya kama bargon yaja da karfi. Ahhhhhhhhhhhhhh! Ya sakk ihu!............................?.....?......._

DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  King Boy Isah
πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 101-102

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

.               πŸ‘©πŸ»‍πŸ’»πŸ‘¨πŸ»‍πŸ’»       .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​
.         ✍🏼  *®Z.W.A*     .

.              πŸ“         .
_*WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ Κ€Ι›Ι‘Ι—Ι›Κ€ΰΈ£*_

        *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ta wani fannin kuma ceqa yake "inje in sanar da su kamar dai ni din va namiji bane. Bari kawai in bude inga miye.  Hannun na karkarwa sai ya kusa kama bargon kawai sai yaja baya a tsorace. Kusan sau biyar yana yin haka. A na shida ne ya daure ya kama bargon yaja da karfi. Ahhhhhhhhhhhhhh! Ya sakk ihu!.~

_*I*tama ihun ta kwada. Yana ganin Fatima ce sai ya bata rai hade da watsa mata harara. "Ke uban me kike a nan dakin?. Wa yace ki shigo min daki?". Shiru tayi tana kallan shi ba tare da ta bashi amsa ba. Dube-dube ya shiga yi yana neman abun da zai dake ta. Ganin ba bulala ko wani mabugi a wajen ne yasa shi tsawa yana mata mugun kallo. "Oya tashi ki bar dakin nan ko inyi kasa-kasa dake a nan wajen".  "Bazan tafi ba din yau a nan xan wuni".  "Ke ni kike gaya wa wannan maganar?".  Ya nufo wajen ta ya daga hannu zai mare ta yaji hannun ya tsaya cik! a lankwashe. Hahahaha ta kwashe da dariya. Abba kuwa fama yake ya mike hannun shi amma ina abun ya gagara.  Ga Fatima sai Dariya take mai.  Abun ya kara fusata shi nan take ya kara daga dayan hannu da nufin ya wanka mata mari.  nan ma hannun ya tsaya cik! Duk hannuwan nashi biyu suka makale suka tsaya a lank'washe.  Fatima da ganin hakan ta tashi ta fita daga dakin a guje tana Dariya. Su mama Asiya lokacin sun gama cin abinci yara kuma duk sun tafi makaranta. Sai su uku zaune a falo suna tadi._

_Fatima suka gani ta zo ta wuce a guje tana dariya. Zuwaira da Hauwa har yun kura zasu tsere suma a tsorace sukaji Abba a daki sai kwalla kira yake. "Mama! Mama!". Da sauri suka nufi  dakin nashi a hanya sukayi kicibus. Hannuwan shi biyun duk a lankwashe. Ya rasa yanda zaiyi har ya fara zubar hawaye. Su duk  ukun tambayar shi suke me ya faru. Cikin kuka ya  fada musu duk abunda ya faru. Da jin haka mama Asiya tana jin haka tac "Kaico!  Wai kai Abba me yasa baka gane wa ne.  Yarinyar nan tunda kaga ina raga mata ai ya kamata kasan cewa akwai lauje cikin nadi. Aljanu ne suka shiga jikin Fatima. sau tari ina nuna maka ba ruwanka da ita amma kaki yanzu gashi ka jawo mana bala'i. Dama yanzu nake so in zo in gaya maka cewa ka fita harkar ta kar ta sabauta min kai. Ban sani ba ashe har ta faru ta kare". Ta kalli su Zuwaira tukun taci gaba da magana. "Dan Allah yanzu miye abun yi?. Kunga ta mayar min da da Masaki"._

_Jugum! Su Zuwaira sukayi suna nazari can Zuwaira tace, "Wannan abun ba wani abu ne ya jawo shi ba sai rashin sani wanda kuwa kowa yasan cewa *YAFI DARE DUHU*. To amma yanzu abun da ya dace shine muje mu roki Fatima ta taimaka ta mikar mishi da hannun shi. Tunda durkusa wa wada ba gajiya wa bane in dai za'a sama biyan bukata". Gaba daya suka aminta da shawarar Zuwaira. Kofar dakin su Fatima suka nufo tun daga nesa suka jin sautin dariyar ta. Mama Asiya tace "A gaskiya gidan nan ba lafiya. Aljanun jikin fatima rikakkun gardawa ne. In bamuyi a hankali ba duk sai sun babala mu. Kuma ya kama ta mu sanar da alhaji ya tafi wannan shegen aikin nashi ga gida yana so ya fi karfin mu".  Hauwa tace, "Gaskiya ne amma ai naji yace ya ran Friday zai dawo". Zuwaira tura kofar tayi taji a rufe gam! kwankwasa kofar ta shiga yi tana fadar "Fatima! Fatima!. Dan Allah ki bude mana. Ba dan halin mu ba dan Allah".  Shiru fatima taki bude wa. Sun dade a wajen kowa na tofa albarkacin bakin sa na magiya. Abba ma cikin kuka yake rokon ta ta bude ta mikar mai da hannun shi. Domin yaga wanki hulana neman kai shi dare.  Fatima ta bude kofar cikin uniform dinta na islamiya rai a bace tace,_

_"Ku gafa in wuce ko in hangiza ku gaba daya kuma ko mutum ya karyw ba abun da yasha ruwana".  Ta make kafada alamun ko Oho. Mama Asiya da Abba lokaci daya suka zube kan gwiwoyin su suna magiya. Fatima ta kwashe da yar banzan Dariya. Wai yau su Mama Asiya ce da durkusawa gaban Fati ana  bada hakuri. Sai da Fatima tayi dariya mai isar ta cikin isa da iko ta kalli asiya tace, "In kina so in mikar mai da hannu sai kinyi tsallan kwado".  Tsuru!  Suka zazaro ido gaba dayan su. Hauwa da Zuwaira kamar su kwashe da dariya.  Zuwaira da san gulma ta wa Hauwa rada a kunne. "Yau zamu ga tsallan kwado a gun Asiya. Tubur-tuburtu kenan".  Wata muguwar dariya ce ta zo wa hauwa. Da kyar ta iya samu ta matse bakinta.  Asiya tayi misisi da ido ta marairaice, "Haba Fatima kiyi hakuri mana ni yanzu ina zan iya tsallan kwado?".  Fatima tayi hanyar wajen "Bakya so hannun danki ya mike ashe?"._

_Da sauri Asiya ta mike ta shiga gaban Fatima, "Yi hakuri dan Allah karki tafi ki bar Abba na a cikin wannan yanayin".  "To maza ina jiranki fara". Mama Asiya ta tsuguna. Juyawa tayi ta kalli Su Zuwaira dariya suke mata sosai amma ciki-ciki ba yanda Fatima zata ji ba. tsalle mama Asiya taso tayi amma ko rabuwa da kasa kafafunbatayi ba saboda nauyi da jikin ta yayi. Hahhahhahah Fatima ta kwashe da dariya, "Malama kiyi sauri kiyi ina jira kinga dai na makara makaranta". "To....To. Bari in kokarta".  Tsalle mama Asiya tayi niyar yi a karo ma biyu. Akayi rashin sa'a kuwa kafarta bata zo a dai-dai ba. Sai ji kake rigijif! Ta fadi._

_Fatima ta tuntsite da dariya. Haka ma su Zuwaira. Sai da Fatima tayi dariya har tana rike ciki. Tace, Kin fadi jarabawa amma tun da dai kin sani dariya Abba mike hannun ka na dama". Tana fadar haka ta juya ta wuce, Kamar wasa Abba ya mike hannun shi na dama yaka ya mike lafiya lau kamar bai taba lankwashe wa ba. Yayi murna sosai sai dai kuma hannun hagun har yanzu  a lankwashe yake.  Tun daga tsakar gida Fatima ke kwalawa Mai gadi kira yazo ya bude mata.  Da sauri ya fito yana ganin Fatimar ce yayi tsaki. "Wai ke wannan yarinyar yaushe kika koma haka ne?.  Ina tarbiyar ki take. Wato naga kwana biyun nan tashen rashin kunya kikeyi".  Gatsine da harara kawai take binshi da shi.  Haushi abun ya bashi ya nufo ta zai daga. "Wallahi kana dukana kayi ta aikin ka. Sanin kanka ne Alhaji baya san abunda zai taba ni kuma ran Friday zai dawo".  Yanq ji ta fadi haka sai jikin shi yayi sanyi.  Tsaki yaja yaje ya bude mata kofar._

_"Zo ki wuce jarababa kawai. Ke ma dai su Asmart sun koya miki wannan masifar ashe".  Bata tanka mishi ba dungwai-dungwai ta wuce har makaranta.  Makaranta ta cika makil! Sai karatu ake Fatima ba tare da wani fargaba ba ta shiga ajinsu. Malamin su na ganin ta ya fara binta da harara. Ita kuwa ko a kwalarta. Domin yunkurin wucewa ta zauna ma take yi. Malam yace, "Ke gidan ku, Ina zaki ko baki san kin makara bane?".  "Ayi hakuri malam, na tsaya yin wani abu ne".  "Kaniyar ki. Zo nan". ba gardaa taje. Tana zuwa kuwa ya fara zafga mata bulala. Sai da yayi mata uku. Yace "Oya maza wuce ki nema waje ki zauna".  Tsaye tayi ta kafe shi da ido tana hararen shi. Tsawa ya kara daka mata amma taki tafiya.  Hakan yasa ya kara juyowa yaci gaba da dukan ta abun yayi matukar tsorata malam yanda yasan Fatima da shegen kuka bulala daya ko biyu yake mata ta fashe da kuka yau kuwa gata sai duka yake amma ta kafe shi da ido tana harara ko kwalla babu. Sai da ya gaji da dukan dan kanshi ya barta yaje yaci gaba da darasi yace, "In kinga dama ki kwana a nan tunda bazaki je ki zauna ba.  Da fadar haka Fatima ta wuce ta zauna. Abun ya daure wa Malam kai a zuciya yake saka "Anya kuwa wannan Fatima ce?"._

_Basarwa yayi yaci gaba da darasi. "Yara yau zamu ga mai tsantsar hazaka daga cikin ku. Idan baku manta ba kwanaki munyi bayanin taimama a cikin littafin ahdari. Sanan kuma mun kwana biyu munayi wanda sai da na tabbatar kun hardace tukun na daina biya muku. Dan haka yanzu ina bukatar Dalibin da zai tashi ya mai-maita mana. Kuma zan bawa duk wanda ya karanta min dai-dai kyauta. Yara biyu ne suka tashi daya mace daya namiji sai duk sai sun fara sai su kakare. Fatima ce ta mike. "Ni zan karanta kuma bana bukatar kyautar". Malam kallo kawai ya bita da shi. Nan take ta fara_

_*"Tafiyar da bata sabon Allah ba. Da marar lafiya, (Wanda yaji ciwo ko kuma dai yaa jin matsanan cin sanyi, Yana iya Taimama). Sallar farillah ko ta nafila. Mazaunin gida lafiyayye. yana iya Taimama dan Gudun fital lokacin sallah. FARILLAN TAIMAMA: Niya da bigiri (waje) mai tsarki. Shafar fuska, da shafar hannuwa zuwa dantse. Da bugun kasa na farko da gagautawa. Shigar lokaci da sadar da ita zuwa sallah.  BIGIRE: (WAJE) Wajen da ya hallata ayi taimama a shi. Turbaya tubali. Da dutse da kankara da waje mai danshi da makamantan su. Taimama bata halatta da suminti ko abun dafawa. Ko kan tabarma. Da itace da ciyayyi.*_

  _*Anyi rangwami ga marar lafiya ya shafi bango in dai bai sama wanda zai samo mishi kasa ba. SUNNONIN TA: Sabun ta bugun bigiri wajen shafar hannuwansa da shafar abunda ke tsakani  Ku'i biyu da dantsen sa. Da jerantawa. MUSATAHBBANTA: Yin bisimillah,  Gabatar da Zhirin Zura'i (Tsuntsuyar hannu). A bisa badinin sa. Farkon sa a bisa majinkircinsa. MASU WARWARE TAIMAMA: Masu warware ta daya suke da masu warware alwala. Ba'a yin sallar nafila biyu da taimam daya. Wanda yayi taimama domin yin Sallar farillah ya halatta a gare shin yin farillah bayan ya gama. Ya halatta ka taba Alqurani dawafi, da Tilawa. Da sadar da ita kafin fitar lokaci. Ya halatta ayi duk abunda aka ambata da taimama. Wanda yayi taimama yayi sallar isha'i yayi sha'i da wuturi, ba tare da ya jinkirta ba. Wanda yayi taimama yana da janaba. Babu makawa sai yayi niyar ta".*_

_Tana kaiwa nan ta koma ta zauna abunta. Malam kuwa tun da ta fara kallan ta kawai yake yana kada kai da alamun mamaki. Bai san lokacin da bakin sa ya furta. "Attakabir" Ba. Yara suka kwasa. ",Allahu akbar". Har aka tashi daga islamiyya malam na mamakin Fatima yau gaba daya ta canza.  Fatima tunda aka tashi daga makaranta ta tafi gidan Rafy. Rafy kuwa dake tasan halin Safuratu sai tayi tunanin ko itace tayo sufar fatin. Nan sukata hira Fatima na taya ta wasu aikin gida.  Bayan la'asar Fatima ta koma gida. Yau ma kamar yanda ta sabawa mai gadi haka tata buga get din da karfi. Wannan karan yana budewa ta bangaje shi ya fadi can gefe ta wuc fuuuu! Abunta. Asmart Nasmat Ameerah da Fiddausi dake gefe tana karanta novel a Facebook. Sune a falon. Suna kallon Mtv. Fatima na shigowa ta nemo remote ta rasa. Kawai sai zare Socket din tayi. Asmart na ganin haka tayo kanta da masifa........................................._

DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  King Boy Isah


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 103-104

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

.               πŸ‘©πŸ»‍πŸ’»πŸ‘¨πŸ»‍πŸ’»       .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​
.         ✍🏼  *®Z.W.A*     .

.              πŸ“         .
_*WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ Κ€Ι›Ι‘Ι—Ι›Κ€ΰΈ£*_

​πŸ“š _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

πŸ“© _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com

πŸ‘πŸ» *MASOYA AYI HAKURI DANI. WALLAHI KWANA BIYU INA BUSY NE BANA SAMUN TIME DIN TYPE* πŸ˜’πŸ˜ *MASU CEWA JAN AJI NE. DUK SAI NA HADAKU DA ALJANU* 🀧

       *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Asmart Nasmat Ameerah da Fiddausi dake gefe tana karanta novel a Facebook. Sune a falon. Suna kallon Mtv. Fatima na shigowa ta nemo remote ta rasa. Kawai sai zare Socket din tayi. Asmart na ganin haka tayo kanta da masifa.~
_"Ke Fatima bana san iskanci da tambada mayar mana da socket ko in lakada ki yanzun nan Wallahi". "Baza'a mayar ba".  Asmart da taga Fatimar bata da alamun mayar da socket din dai ta nufo ta a fusace, Kafin ta karasa wajen ta. "Kai! kai! kai!._

_Rufa mana asiri in ba sokikr mu shiga uku ba yanzu". Hauwa ce ta fadi haka lokacin da ta fito daga kitchen. Asmart dakata wa tayi tana kallan Hauwa'u. Fatima tace, "Duk wanda ya kunna tv din nan yau ni da shi ne a cikin gidan nan". Da fadar haka ta juya ta wuce daki. Asmart tace,  "Me ke faru Aunty Hauwa?".  Hauwa tace. "Wato ku duk baku san me ke faruwa a gidan nan ba kenan?.  Ai tun jiya Aljanu sun shiga jikin Fatima su suke sakata duk wani iskanci da take. Kuma gasu da shegen karfi. Kai dazun ma Abba da yaje dukan ta Wallahi hannun shi tsayawa yayi a lankwashe, Da kyar muka samu ta mikar mai da hannun daya, Dayan kuma taki mikar mishi wai sai Aunty Asiya tayi tsallan kwadi". Hhhhhhhhhh Nasmat tayi dariya, "Lalai Aunty Hauwa kin iya tatsuniya.  Wai yanzu kina nufin daga naje dukan Fatima kawai dai hannuna ya makale".  Hauwa tace, "Kwarai in kuwa baki yarda ba gaki gata. Inda ba kasa nan ake gardamar kokowa".  Asmart tace, "Kai nima dai ban yarda da wannan jawabin ba. Haba dai yo ai ni ko a Tv ban taba gani ba. Kuma wallahi yanzu zan kuna TV din tayi abunda zatayi". Hauwa tace, "To marar kunya wato duk da ina auren baban ku matsayina bai haura karyatawa kai tsaye ba.  To shikenan ni na barku lafiya. Ba dani ba raban fadan Zakuna. Wanda baiji bari ba yaji hoho, Ni kunga tafiya ta".  Hauwa na fadar haka ta haura sama abunda. Asmart tsaye tayi abun nayi mata yawo a kwakwalwa.  Tunani take ta Mayar da socket din ko ta fasa. Nasmat ganin asmart ta kasa kunna tv yasa ta tashi ta nufi wajen "Dallah matsoraciya matsa ni in jona in ke tsoro kike. Abunda dama wannan 'yar tsanar ce Aljanar kuma an toyata"._

_Asmart na jin haka tace "Kuma fa haka ne". Nan suka fara rige-rigen mayar da socket din. Fiddausi na jinsu duk abunda suke ko uffan bata ce musu ba. Ta dukufa wajen karatun novel da take a waya. Ameera kuwa game take a waya sai ihu! Take kamar zautacciya. Nasmat da Asmart daga wannan taje saka  socket din sai dayar ta ture ta. Wai kowa na fadin shi zai mayar. Da suka dade suna haka sai kuma suka tsaya suka sasanta a kan a kama a saka a tare.  Da mayar da socket din da dauke war wutar dakin duk daya. Juye-juye suka shigayi. Fiddausi da ameera su kansu sai da suka dakata da abun da suke.  Gam! Gam! Gam! Windows din falon ne suke rufe kansu da karfi. Duk da rana ce a lokacin amma sai falon ya zama duhu rudum, kamar tsakar daren da ba farin wata. "Nasmat!, Fiddausi!, Ameera!. Kuna ina?"._

_Suma din gabaki daya a rikice suke sai kiraye-kirayen juna suke. Domin duhun yayi yawa ko tafin hannun ka baka iya gani. Fiddausi ji tayi kawai anyi sama da ita ana ja kamar wacce iska ke tafe da ita. Ihu! Take tun karfen ta hakan yasa su Nasmat suka kara rikicewa suma. Kofar falo ta bude Fiddausi sai ji tayi an watso ta waje.  Mai gadi ne yayo kanta yana tambaya "Lafiya-lafiya me ke faruwa".  "Aljanu ne". ta fada tana nuna mishi falo yayin da take kokarin tashi. Tana tashi ta zangara  a guje. Mai gadi ma da gudu ya koma daki ya garkame kanshi. Su Asmart da sukaji ihun! Fiddausi ya lafa sai suka shiga kiranta. A hankali Asmart ke fadar "Aunty Fiddausi! Aunty Fiddausi!". Shiru bata ji an amsa ba. A tafiyar da take tana lalube irin na makafi sai taji hannuwanta sunci karo da mutum. Nan take ta fara lalubata tana kiran sunayen su. "Nasmat ce?, Ko aunty Ameerah ce?.  Fiddausi ce?. Yi magana mana".  Shiru bata ji yarinyar tayi magana ba.  "Wai Fatima ce?". Ta kuma tambaya tana shafa fuskar.  Tana zuwa saitin bakin sai ji tayi an gallara mata cizo.  Ahhhhhhhhh!.  Ta saki ihu! Abunda ya kara dugunzuma su Nasmat kenan suma suka rikice. Gudu suka ringa yi ba tare da sun san ina suka nufa ba. Bango birki. Nasmat na tafe a cikin duhu taji tayi karo da mutum. Tunani  ta Asmart ce. Cewa tayi "Asmart wai duhun miye wannan?".  Shiru  bataji tayi magana ba._

_Lalube ta kamayi kuma sai taji ai yarinya ce taci karo da ita din. "Fatima! Fatima!". Wata irin walkiya suka gani kamar an kawo nepa an dauke. Nan take suka kara dimaucewa.  Hahahahhaha gaba dayan dakin ya kwashi dariya, Zuwa can kuma sai wani ja  haske ya cika dakin  gaba daya. Nan take suka ga junan su bayan sun hadu waje daya ne suka kuma jin wata irin dariya kamar ta yara a bayansu. Ahhhhh!  Suka fasa ihu a tare. Ba komai bane suka gani sai kan Fatima na tafe q kan iska wuyan wani irin jini ne mai kauri ga danko yake zuba kasa. A bakin ta kuwa wani danyan nama ne take ci duk jini na zuba. Ga kuma gashin kanta da ya koma wasu murda-murda ba kyan gani sai motsin yake da kanshi kamar macizai. al'amarin duk wanda yaga abun dole ya tsere in ba'aci sa'q bama mutum sai ya suma. Wannan kan na Fatima mai shegen abun tsoro n ya nufi su Asmart su kuwa kamar wanda aka rike wa kafafu sun kasa guduwa. Suna nan tsaye sai tsala ihu! Suke. Kan na zuwq saitin Ya wangare baki ya wani kara fadi. Kamar zai hade su baki daya. Luuuw! Suka ringa zubewa sumammu.  Kafin kiftawar ido falo ya dawo yanda yake. Su Mama Asiya duk ihun da ake baya zuwa wajen su hakan ne ma yasa basuji ba. Zuwaira ce ta sakko daukan wani abu. Tana ganin su Nasmat a shimfide ta rude nan-da-nan ta fara kwallawa su Mama asiya kira. Suma da gudu suka sakko downstairs din suna tambayar me akayi.Zuwaira ta nuna musu Asmart da yatsa. Ai da sauri hauwa ta dakko ruwa mai sanyi aka fara yayafa musu._

_Duk wacce ta farfado sai ta kankame ta kusa da ita a firgice suna sambatu da ambatan sunan Fatima. Mama Asiya da duk ta rude take tamabay me akayi. Hauwa tace, "Ni dai dazun na barsu nan lokacin Asmart zata daki Fatima shine na dakatar da ita na fada musu cewa Fatima nada aljanu. Shine har suke karyata ni. Sannan kuma Fatima ta zare socket tace duk wanda ya mayar zatayi maganin sa". Hauwa ta kalle gurin socket din taga an mayar, "Af!  Socket din suka mayar ai yanzu gashi sun jawa kansu". Mama Asiya cikin masifa ta fara magana. "To Wallahi bazai yuyu ba. Dole a dauki mataki Wallahi ko in bar gidan nan yau. Haba ya zan tsaya ina kallo aljanun Fatima su kashe min yara. Bari in kira alhajin shima da yaje yayi zaman shi a kasar mutane kamar can aka yanke mai cibi". Da sauri ta koma daki ta daukko wayar ta kira Alhaji. Ko gaisawa basuyi ba ta fara binshi da masifa take gaya mishi duk abunda ke faru. Alhaji kuwa wufantar da zancen yayi. Yake cewa. "Wato Asiya kuma ta nan zaki bullo wa Yarinyar nan ashe har yanxu wannan zaluncin da kike wa Fatima baki daina ba. In banda karya da sharri ya zaki ce wai Fatima ta addabi gida kaza-da-kaza?".  Mama Asiya cikin masifa ta kara kai'mi. "Au! Abun da zaka ce kenan. To Wallahi in haka ne zan tatara yarana in tafi da su gidan mu. Haba ina dalili yaseen bazan yarda Aljanu su kashe min yara ba. Yanzu haka ga su Asmart nan rai hannu Allah Aljanu sun dadake su duk sun ji musu ciwo".  Daga can alhaji yayi magana da alamun shima ya fusata. "To naji zaki iya tafiyar ki amma karki sake ki fitar min da yaro ko daya. Ke in ban isa inyi iko dake ba ai na isa inyi da yara na. Kuma in sha Allah wannan juma'ar zan dawo sauran inga kuma ba dai-dai ba. Ko inji Fatima tace min zalumtar ta kuke. Wallahi da sai na dau kwakwaran mataki wanda bazai miki dadi ba".  Yana fadar haka ya kashe wayar._

_Tsaki mama Asiya taja, "Wato kai kana can ka bar mu da Aljana na neman sabautamu". Haka dai gidan ya wuni cikin dar-dar, Fatima kam ta zama abar tsoro dan in tazo waje gaba daya sai suyi tsit. Da dare da kyar suka yarda da su kwanta a dakinsu. Wajen karfe 11 na dare Fatima ta tashi ta tafi sama mama Asiya na barci taji ana tashin ta. Tana farkawa kuwa taga Fatima. "Fatima me akayi kike tayar dani tsakar daren nan?".  Mama Asiya take maganar cike da tsoro.  "Murya na fitowa biyu-biyu Fatima tace, "A nan zan kwana dan haka ki tashi ki koma falo ki kwanta".  Mama Asiya na karkarwa ta tashi ta yayimi bargo ta fita a dakin.  Tun kafin ta sakko daga kan matakalar ta hangi mutum a zaune a falo mace ce kin bakaken kaya. Ta juya mata baya........................................._

πŸƒπŸ»πŸƒπŸ»πŸƒπŸ»πŸƒπŸ»πŸƒπŸ» A dakace ni yaseen na gajiπŸ™Š

DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  King Boy Isah


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 105-106

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

.               πŸ‘©πŸ»‍πŸ’»πŸ‘¨πŸ»‍πŸ’»       .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​
.         ✍🏼  *®Z.W.A*     .

.              πŸ“         .
_*WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ Κ€Ι›Ι‘Ι—Ι›Κ€ΰΈ£*_

​πŸ“š _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

πŸ“© _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com

*DEDICATED TO YOU* 😁

QUEEN HAUCY

MINEERT

AMÆL

SALMAH

MINEERT

QUEEN MEIMIE

PHATEEMA

MARYAMU πŸ™Š

MUHIEVER INDIA

❤  KUNA A RAINA KU DIN NA DABAN NE A HEAR DIN KIN. πŸ’ƒπŸ» INA SANKU MASOYANA. ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MUKU A  DUK INDA KUKE.

        *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Mama Asiya na karkarwa ta tashi ta yayimi bargo ta fita a dakin.  Tun kafin ta sakko daga kan matakalar ta hangi mutum a zaune a falo mace ce kin bakaken kaya. Ta juya mata baya.~

_Cikin muryar tsoro mama Asiya ke magana. "Wacece?. Waye a nan?". Shiru bata amsa ba. Kara matsawa tayi tsoran ta na dada karuwa. Sai tambya take amma anyi mata shiru. Nan ta tsaya tana sake-saken ta juya ko kuwa ta karasa. Zuciyar ta ce ta bata shawarar cewa taje ta gane wa idan ta waye a zaune. Gwara nan da can din wajen Fatima.  Cikin Kwarin gwiwa ta nufi wajen matar ta dan kauda tsoran ranta. "Waye-waye". Ta kara tambaya firgigit matar ta juyo Hauwa ce, da alamu gyan-gyadi take. Mama Asiya na ganin Hauwa ce tace, "Hauwa wannan wane irin kaniya ce. Kina ji ina miki magana kika share ni, Wallahi har kin bani tsoro". Hauwq na murza ido tace, "Ni wallahi cikin barci ne ma naji kiran ki".  Mama asiya tac, "To ke kuma wace uwar ta dawo dake falo ga dakin ki can kin baro?". Hauwa ta waiga baya alamun marar gaskiya. Murya kasa-kasa tace "Wallahi Fatima ce ta bini daki ta koro ni wai in dawo falo ita zata kwanta a dakin". Zagayawa mama Asiya tayi ta zauna._

_Cikin rada mama Asiya tace, "Taf! Di jam, Kika ce Fatima ce ta koro ki".  "Eh Wallahi ita ce, Yanzu haka tana can saman gado na tayi kwanciyar ta".  "To Fatima aljanun nata ko har sun fara raba ta gida biyu ne?. Domin yanzu ta koro ni fa daga daki na wai...". Sautin saukkowar da suka ji daga stairs ne ysa mama Asiya bata karashe maganar da ta fara ba. Suka juya su biyun suka zura wa wajen ido dan ganin wanda zai sakko. Ba kowa bane Zuwaira ce itama rike da bargon ta a hannu kamar almajirin da ya fito rani. Mamaki ne ya kama ta ganin su Asiya a falo. "Aunty Asiya, Me kuma kuke yi a falo". Zuwaira ke tambay. Asiya tace, "Ai ke ya kamata mu tambayi me ya fito dake daga dakin ki da tsakar daran nan harda kwaso blanket".  Zuwaira ta juya baya tukun tayi kasa da murya tace, "Aljanun Fatima ne suka koro ni. Wai fa dan daukar alhaki ina kwance abuna sai ji nayi ana tayar dani, Bayan na bude ido naga Fatima ce, Kar kuso kuji cikin irin muryar da take magana. Da shi abar tsoro shine ta koro ni falo".  Su mama asiya suka ce ai sai kizo ki hau layi domin muma nan da kike gani ita ta koro mu".  Zuwaira tace, "A gaskiya ya kamata mu dauki mataki haba Aljanu ma ai suna da maganin".  Asiya tace, "Rage murya kar su jiki, Dan Wallahi yanzu zakiji ana gaura miki mari". Da sauri Zuwaira ta matse bakin ta da hannaye.  Bayan sun baje a falo.  mama asiya tace, "Nasan matakin da zan dauka. Ku bari gobe zan gaya muku"._


_Washe gari tun da asuba kafin su mama Asiya su tashi daga barci, Fatima taje ta debo ruwa a waje mai shegen sanyi. Nan tazo ta fara kwara musu. Gaba daya a gigice suka ringa tashi. Suna tashi suka ganta zaune kan 3Stars tana musu dariyar mugunta. Daga bisani ta bata rai tace, "Maza ku tashi aje ayi sallah sannan a zo a shiga kitchen".  Suna rawar dari suka tashi ko wacce ta nufi dakin ta dan yin sallah.  Fatima ta tashi ta shiga dakin su, Nasmat, Ameera da sauran yaran sai barci suke abun su. Fiddausi ce kadai ta tarar kan sallaya tana karatu.  Da sauri Fatima ta koma ta kara debo ruwa ta zo ta dingi watsa musu tana tashin su suje suyi sallah. Ameera watsa mata ruwan da akayi, abun yayi matukar bata mata rai. A fusace ta nufi Fatima, Batayi wata-wata ba ta kwasa mata mari. Sannan ta dora da fada, Yayin da ita kuma Fatima ta sadda kai kasa. "Ke Fatima bar ganin ana cewa wani kina da Aljanu. Wallahi ni ba raga miki zan ba. Aljanun banza, Shikenan dan kina da Aljanu sai kita takura wa mutane. Miye zaki wani watsa wa mutane ruwan sanyi da safiyar nan. Anki ayi sallahr".  Firgigita Fatima ta dago kai. Dagowar da tayi idanun ta sun koma kamar garwashi har wani tartsatsin wuta ke fita a idan.  Gabaki daya mutanan dakin sai da suka tsorata. Su Asmart kam kankame juna sukayi hade da runtse idanu. Fiddausi kanta da take karatu abun ya firgitata. Nan take ta fara karatun da karfi tana tofawa saitin  Fatima.  Fatima bata kula ba. Hannu ta mika saitin Ameera dake baya-baya a tsorace kamar tayi kuka. Ameera sai ji tayi an shake mata wuya. An dage ta sama ba tare da subga wanda ya daga tan ba. Sai da aka wul-wulata kafin aka mako ta kasa._

_Sa'arta daya kan katifa ta fado. Fatima cikin wata murya mai zaburar wa tace, "Maza kafin in kirga goma kowa yaje yayi alwala,.....1....2..".  Ai da gudu aka ringa rige-rigen shiga ban daki dan yo alwala. Bayan sun yo alwalar sun fito kuma sai sukaga fatiman bata nan. Daki-daki.Fatima tabi ta tattaro su mama Asiya aka shiga kitchen domin hada abun kari.  Tukun taje dakin Abba ta tayar da shi shima yayi sallah. Har ya fara mata magiya a kan ta mikar mai da dayan hannun shi, Ta daka mai tsawa hakan yasa ya kyale ta. Su mama Asiya sunji jiki sosai yau a Kitchen, Domin kamar yanda suke wa Fatima. "Dake wannan kul-kula wancan kwashe can gyara nan", A da. Haka itama Fatima yau ta ringa  juyasu, kamar ta sama bayin ta.  Haka wajen cin abinci ta ringa bada doka. Domin ko katuwar loka taga mutum yayi sai ta kwala mishi Cokali. Gaba dayan gidan kuwa tsoranta karuwa yake a gare su. Ana gama cin abinci Fatima tace to masu zuwa islamiyya a tashi ayi shiru, Ku kuma matan gida a gyara gida shara wanke-wanke da goge-goge. Tana fadar haka ta wuce daki. Yayin da suma masu zuwa islamiyyar tuni sun fece sun bar wajen. Mama Asiya ta rike baki alamun mamaki "Oh! Duniya kowa ya sama waje sai kiga ya baje kolin shi. Yanzu dai ga Fatima aljanu sun sata tana mana iskancin yanda taga dama kamar mu yaranta ne"._

_"Ke dai bari wannan abun takaici. Ya muka iya haka zamuyi hakuri mu jure har Alh. Ya dawo muga irin matakin da zai dauka". Cewar Zuwaira. Asiya ce ta katse mata hanzari ta hanyar cewa. "Kai aradu bazamu jira har sai ya dawo ba. Yau fa laraba kuma shi yace sai ya kai juma'a tukun zai zo, Dan haka yau zamuyi maganin abun ku dai bari wannan aljanar ta tafi makaranta  tukun".  Nan suka fara share-share suna kakauda kayan da suka ci abincin. Ba'a jima ba sai ga fiddausi da Fatima sun fito cikin uniform din islamiyya. Wani dan iskan kallo fatima ta jefa wa su mama Asiya kafin tace, "Ai na dauka da bazakuyi abun da na saka ku ba"._

_Tana fadar haka bata ko jira sun tanka ba ta kama hannun Fiddausi suka fita. Ita dai Fiddausi duk a tsorace take da Fatima gudu take cutar da ita.  Bayan yara duk sun tafi makaranta su mama asiya suka shirya mama asiya tace musu malami zasu je su samo yayi masu Ruqiya ya fitar da aljanun.  Gaba daya suka amince da haka. Ga motar alhaji amma suka fita a kasa. Kasancewar a cikin su ba wacce ta iya mota. Suna tafe har sun kusan barin layin sukayi kicibus da wata mata da alamu yar anguwar su ce, Tafe take tana rausaya kamar wata budurawa, Ba hijab bane a jikin ta gyale ne ta dan yafa a kafada. Fuskar tasha hudar wacce zan iya ce muku har taso tayi yawa. Cingum ne a bakin ta tana tauna lips din yasha jan baki. Da gani kasan yar duniya ce. "Asiya Anguwa za'a fita, Da safiyar nan?".  Washe baki su Asiya sukayi "Eh wllh Nafisa daga ina haka".  Asiya ta fada.  Matar tace Wallahi naje sayo abu ne. Ina zaku je haka". Asiya ta kwashe duk  abunda ke faruwa ta fada mata.  Rike baki nafisar tayi hade da cewa "Aljana fa kika ce?. Tabb! To yanzu ina zaku sama malami".  Mama asiya tace "Aa gamu dai mun fito da wajen limamin masallacin jama'a zamuje watakil a dace".  Nafisa ta roke baki "ah!  Liman to bari kuji in  gaya  liman ba abunda zai muku. Sai dai yace kuje kuci gaba da addu'a. Amma akwai wani malami da na sani ya kware wajen fitar da aljanu, In kun amince na hutar daku ni zanje in kawo muku shi har gida"................................._

DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  King Boy Isah

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 107-108

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

.               πŸ‘©πŸ»‍πŸ’»πŸ‘¨πŸ»‍πŸ’»       .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​
.         ✍🏼  *®Z.W.A*     .

.              πŸ“         .
_*WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ Κ€Ι›Ι‘Ι—Ι›Κ€ΰΈ£*_

​πŸ“š _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

πŸ“© _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com

πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•

​SAI NA AURE TA​

πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•

   ωяιттєи Π²Ρƒ:
​shamsia salis​

​Eloquence Writers Association
____________________________________
Na tayaki murnar Autar Eloquence. Allah ya kara basira. Allah yasa mu amfana da darrusan cikin littafin amin
____________________________________

      *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Amma akwai wani malami da na sani ya kware wajen fitar da aljanu, In kun amince na hutar daku ni zanje in kawo muku shi har gida".~
_Su Zuwaira sukace "ba dai boka ne ba ko?". Nafisat tace "Aa ko daya wannan shahararren malami ne. In kun amince yanzu ma daga nan bazan karasa gida ba sai in juya in daukko muku shi".  Mama Asiya tace "To shikenan je sanar wa mai gidan ki to sai kizo ki karba kudin mota, ko kusa ne?".   "Aa Wallahi can wani kauye ne kudin motar mutum biyu Dubu daya ne. Dubu biyu zuwa da dawowo. Batun mai gida kuma da kike. Dallah rabu dashi miye na sai naje na gaya mishi".  Hauwa da Zuwaira tabe baki sukayi suna kallan Nafisa din.  Asiya bata ce komai ba ta fiddo dubu uku a handbag dinta ta bawa Nafisa "Gashi kije ki daukko shi muna jiranshi. Mu in dai zai cire mana wannan Aljanar to ko nawa ne zamu iya bashi". Ta juya ta kalle su Zuwaira "Ko ya kukace yan uwa".  Da sauri suka ce "Kwarai kuwa ko nawa ne zamu iya badawa mu dai gurin mu ta bar gidan".  Nafisa tace "Karku damu aikin wannan malamin sha yanzu magani yanzu ne".  Su Asiya suka juyo suka koma gida inda ita kuma Nafisa ta tsayar da napep ta hau tace a kai ta Sabon layi, Daga anguwar su nan naira saba'in ne.  Tana sauka ta nufi wata kofar gida wanda kofar gidan wasu samari ne ke zaune ba abunda suke sai busa sigari da gulmar masu wucewa kan hanya.  "Sannun ku dai dan Allah Aliyu ko ta bare yana gida". Gudan ya kalle ta yace "wani abu yayi mike ne?.  Ko dai yayi tsiyar ne". Nafisat tace "Ba abunda ya min ni dai kawai ina neman shi ne in yana nan".  Dayan yace mata "Yaje can sama wajen wata cuwa-cuwar sa amma yanzu zakigan shi ya dawo".  "To na gode". Nafisat tace ta koma gife tana jiran  Ko ta bare. (Sunan da ake kiran aliyu kenan). Bata jima a wajen ba ta hange shi ya taho, Duk da kasancewar shi dattijo hakan  bazai hana ka gane cewa dan duniya bane. Yana hango nafisat ya fara wasa ta yana mata kirari.
"Kaga shegiyar uwa mai saka 'ya'ya biyayyar dole, Kaga kaska rabi mai jini wanda ke da dan kadan ma abishi a tsotse. Ke ba maciji ba kinfi macijin dafi.  Da ganin nasan bakin ki a kwai batu. Dan banza bata kai zomo kasuwa._

_Kuma Wallahi da kaga kura ta ba nama ka tabbata ba dan Allah ta barshi ba. Yanzu dai miye labari ne".  Nafisa kam kallo kawai take binshi da shi tana murmushi domin ita da shi kar ta san kar ne. Daya baya neman daya sai za'a aikata wani mugun abun wanda za'a dan fizgi wani abu a ciki. Tana yar dariya tace "Shege Ko ta bare, Wato ka san dai in ka ganni gidan ka  ba banza ba". Yace "Eh mana ai nasan bazaki taba wanke kafafun ki takasan ki kawo min ziyara ba. Da gani nasan akwai wata harkar ne".  "Tabbas kuwa akwai babbar harkar.  Wacce in dai ka yarda zakayi nake gaya ma zamu sma kudi sosai".  Aliyun yace "Gaya min mana kinsan fa ni dan kasada ne bakiji suna na bama. Ai kawai ko miye na zanyi in dai za'a sama yan karafa".  Nafisat tace "Yauwa mutumina. To dama can wasu makwabtan mu ne suka neman za'a fitar musu da aljanu, kuma gidan masu kudi ne. Watakil ma ba wani Aljani kawai firgitane suke. Shine wai na hadi da su a hanya zasu je neman malami mai fidda Aljanu to kawqi ganin za'a sama wani abu shiyasa ma wannan shawarar ta zo mun".   Tsuru ya tsare ta da ido yana mata kallan yan iska. Lura da hakan yasa tace "Kai malam bana san wulakanci ya zaka wani zura mun na mujiya. Ko naci ban biya bane".
A fusace yace,"Ina fa kika biya, ai bansan dan banza kika dauke ni ba sai yau".  Cikin rashin fahimat da neman karin haske tace, "Ban gane na dauke ka dan iska ba?".  "Kwarai kin dauke ni dan iska tunda. Har wai ni zaki ce naje na cire Aljanu. Yo na cire Aljani ko kuma Aljani ya cire ni".  Kwashewa da dariya Nafisa tayi, Zuwa can kuma ta dan tsakaita hade da cewa,"Ko ta bare, wallahi ban taba sanin kai mugun matsoraci ne ba sai yau". "Aa ba tsoro bane, ai gaskiya ne. Duk iskancina ai bazanyi wa Aljani ba.kinsan ance aikin guguwa ta dau kara da karmami, bata shiga rumbu ta dauko dammunan hatsi".  Nafisat tace, "To kwantar da hankalin ka. Wannan kar ya dame ka, dan bana tunanin aljanun gaske ne. Ni ina tunanin ma kag'e ne sukeyi mata". Aliyu ko ta bare yace,"Au! Kina tunanin ba aljanun bane". Nafisa tace,"Kwarai ba Aljanu bane iskancin sune kawo irin na masu kudi".  Ko ta bare yace, "To in dai haka ne na amince". "Yauwa ko kai fa. To yanzu abunda za ayi shine, ka shiga gida ka sako fararen kaya sababbi, masu babbar riga da katan charbi sannan ka fito muga ko kayi kama da malami. Dan in bakayi kama da malami ba wallahi wani zan nema in sashi wannan aikin".  Gemun shi yaja hade da cewa,"Haba ai ni din nan da kike gani in  nasha manyan kaya bazaki iya banbanta mu da limamin anguwar ku ba. Yanzu bari in sako kayan sallah na". Ciki ya shiga ya sako shadda ce fara kal har dauka ido take, yasha malum-malum ga hula zannah.  Matsalar daya baya da charbi. Nafisat na ganin shi tace komai yayi. Nan yake gaya mata cewa bashi da charbi. Nafisat tace ba komai suje kasuwA._„

_Nan take suka nufi kasuwa ta sayo mai katan charbi hade da wasu turaruka. Ya fashe jikin sa sai kanshi yake kamar sabon ango. Sun taho a hanya Nafisa ke tsara mishi yanda zaiyi take fada mai sunce Yarinya ce karama mai aljanun dan haka abunda zaiyi shine yace a saka su daki daya su kwana idan yaga asuba ta kusa kawai sai ya shake yarinyar ta suma. In yaso da asuba sai yace ya gama fitar da aljanun a sallame shi sai ya gudu.  Fashewa yayi da dariya yace ya fahimta. Bayan sun kamalla duk shirin su suka nufi gidan. Nafisa ta fara shiga ta sanar musu gashi ta zo da malamin, Su mama Asiya suka ce ta shigo da shi ciki.  Makeken carbi ne a hannun shi yana ja bakin shi na motsi ka rantse da Allah kace tasbihi yake, Alhalin shi kanshi bai san abunda yake fada ba kawai motsa bakin ne.  Da shigowar shi falon ya kwashi kamshi. Su Asiya na ganin shi suka zube kasa cikin ladabi da girmamawa.  Nafisa a ladabce ta nuna mishi 1star tace ya zauna. Da bismillah ya zauna nan take su Mama Asiya suka fara kwasar gaisuwa. bayan ya gama gaisawa yayi hamdala tukun ya fara daga kai yana kare wa falon kallo sama da kasa yana jijiga kai alamun a kwai magana. Cikin ladabi Nafisat tace "Malam me ke faruwa?. ko aljanun ne".  Gyaran murya yayi tukun ya kalli mama Asiya yake cewa sunyi sakaci da har suka bari Aljanu suka cika musu gida haka. Cikin hanzari ya nuna wani bangare a falo, kunga ga fatalwa can ma ta fito daga dakin can zata gudu. Kunsan fa aljanu ko fatalwu basa yarda su hada wajen zama dani in dai ba masu shegen taurin kai ba. Su Mama Asiya kallan wajen da ya nuna sukayi wayam ba kowa, Zuwaira tace,"Allah shi gafarta malam fatalwar da ta gudu yanzu mace ce ko namiji?". "Mace ce gata can fara ce kuma siririya".  Sallalami suka fara gabaki dayan su. Nafisat ta tambaya me suke wa sallalami, mama Asiya tace, "Kin manta kishiyar mu uwar Fatima wacce ta mutu". Nafisat tace "Na tuna ta, ko kuna tunanin itac fatalwar?".  Zuwaira tace, "Kwarai ita muke zargi domin aljanun ma duk a kan yarta Fatima suka tare".  Aliyu yace, "Ba mamaki itace, Domin kuwa nayi mamakin ganin gadajen Aljanu ba adadi a tsakar gidan nan. Wannan ke tabbatar min da cewa Aljanu da yawa ne ke rayuwa a gidan nan". Asiya ta kalle shi hade da cewa, "To yanzu malam miye abun yi"._

_"Karku daga hankulan ku tunda dai gani nan na zo yau-yau sai na kore duk aljanun gidan nan. Dan haka yanzu ku kawo min yarinyar mai suna Fatima da kuke zargin ko yar fatalwar can ce". "Ai suna makaranta. Amma sun kusan dawowa". Inji  Hauwa da sai yanzu tayi magana.  Aliyu tace, "To ai shikenan bari mu jira ta ta dawo. Dan in san ta inda zan faro".  Mama asiya tace, "Yauwa Allah shi gafarta malam, Akwai wani dana mai suna Abba da Fatima ta lankwasar mishi da hannu. Munyi-munyi taki ta mikar mishi da hannun".  Aliyu yace,"Ina yake ku kawo shi inga". Hauwa ta tashi da sauri ta nufi dakin Abba ta kirawo shi. Yana zuwq ya zube gaban malam yayi gaisuwa. Bayan Aliyu ya amsa, yace Abba ya miko mai makalallen hannu. Ba gardama Abba ya mika mishi. Malam Aliyu ya ware karfin shi yasa hannaye biyu yaja hannun da niyar ya mikar da shi ta karfi. Ihu! Abba ya kwada hade da cewa. "Wayyo zai karya min hannu". Malam na jin haka yayi saurin sakin shi. Ana cikin haka sai ga Fatima da Fiddausi sun dawo daga islamiyya. Da shigowar su falon, Fatima ta fara hararen malam aliyu ko ta bare.......…………………………………………………………_

πŸ€” Lalai Malam Aliyu cire Aljanu da kyau πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  King Boy Isah


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

Page 109-110

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

.               πŸ‘©πŸ»‍πŸ’»πŸ‘¨πŸ»‍πŸ’»       .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​
.         ✍🏼  *®Z.W.A*     .

.              πŸ“         .
_*WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ Κ€Ι›Ι‘Ι—Ι›Κ€ΰΈ£*_

​πŸ“š _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

πŸ“© _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com

          *KARSHEN PAGEN BAYA*
"Wayyo zai karya min hannu". Malam na jin haka yayi saurin sakin shi. Ana cikin haka sai ga Fatima da Fiddausi sun dawo daga islamiyya. Da shigowar su falon, Fatima ta fara hararen malam aliyu ko ta bare.~

_Tunda yaga tana zare mai ido ya gane cewa itace Fatima hakan yasa yayi saurin mikewa tsaye yana kallanta yana tofe-tofe.  Su  Zuwaira sukayi saurin mikewa suma. suna cewa, "Yauwa malam itace wannan din".  Malam yace ai ba sai kun gaya min ba. Domin tana shigowa naga Aljanu da ifiritai kusan million a tare da ita. Amma ni naga ma kokarin ku da har kuke iya kwana a gidan nan. Shin wai basa baku tsoro ne".  Zuwaira tayi sauri tace,"Ai ba tsoro kadai bama har da duka. Mu dai malam ka taimaka".   Aliyu yace,"Karku damu, Yau bazan bar Aljani ko daya ba a gidan nan.  Amma aikin ku fa nada wahala sosai gaskiya domin ma yau ta kama dole ma sai na kwana a gidan nan".  Gaba saya suka ce ba damuwa su dai gurin su a fitar da aljanu. Nafisat kallo kawai take bin Aliyu da shi.Yanda ya takarkare yana zuga karya wa su mama Asiya. Kamar wani malamin kwarai._

_Fatima da Fiddausi basu wani tsaya sauraren su ba. Kai tsaye dakin su suka wuce. Malam na kiran Fatima! Fatima! Ko wai-wayen shi batayi ba. Balle ya sa ran zata juyo.  Zaunawa yayi yace da su mama asiya yana bukatar kayan aiki. Domin yanzu zai fara. Su mama Asiya suka tambaye shi dame-dame yake bukata. Nan yake gaya musu cewa Yanzu dai yana bukatar daki guda. Sannan a sayo soyayyun kaji amma a tabbatar da farare ne.yaci gaba sa ce musu a samo abinci kamar fillet biyar pure water leda daya. Domin ina so zan kafawa Aljanun gidan nan tarko ne dan akwai masu shegen gudu. Wanda zan kama ta dalilin abincin nan. Sai da ya gama lissafin shi su mama asiya suka tura mai gadi yaje ya hado duk abuda malam ya bukata. Dakin da aka ware mai yace a kai kayayyakin.  Sannan ya tashi ya shiga dakin hade da ce musu yana zuwa.  Wani mugun kallo Nafisa tabi shi da shi. Wato sai yanzu ta idasa gano tantirancin Ko ta bare. Asiya tace "Mu ko nawa ne zamu iya kashewa, in dai za'a fitar da Aljanun nan"._

_Nafisa tace,"Karku damu ai in dai wannan malamin ne bani da shakka a kanshi. Aikin shi kenan kama Aljanu". Su mama asiya sukace Allah yasa su fita domin kuwa yan taurin kai ne.  Aliyu na shiga dakin ya fara debar girki sanda yaci abinci sosai yaci ya koshi yaci nama san ranshi tukun ya sha ruwa ya goge bakin shi. Filet biyu ko wanne da kaza a kai ya fito da su yana tofe a ciki. Kamar mai addu'a da gaske. Yace wa su mama asiya su sa a daukko sauran abincin da naman a kai bayan dakunan amma a rufe. Yake cewa yasan aljanu da shegen kwadayi suna zuwa dauka zasu makale. Dan karfin addu'ar da yayi a ciki. Su mama asiya da kansu suka shiga suka dakko sauran abincin sunyi mamakin ganin anci abincin har hauwa ta kasa daure wa da ta tambaye shi. Sai yace Aljana ce taci lokacin da mai gadi ya kai su. Wai kafin ya karasa Aljanar taci  kuma ma wai ya kashe ta._

_Haka dai suka raraba abin cin nan harda ruwan. Duk abunda suke mai gadi na kallan su ga muguwar yunwa da yake ji. Nafisa kuwa banda harara ba abunda take aikawa Aliyu.  Waje ya samu ya zauna a falo aka kunna fanka aka kawo gaban shi aka kuma kawo abinci da lemu. Malam yace ai shi ya koshi domin Aljanu ke kawo mishi abinci duk lokacin da ya bukata.  Baici ba sai Nafisa aka bawa ta cinye. Yana nan gidan  har dare yayi ita kuwa Nafisa sallama tayi musu a kan cewa gobe zata dawo.Aliyu Da yaga ish'i tayi sai ya faki idanun mutane ya zagaya bayan daki wajen abincin nan yana zuwa yaga duk an cicinye naman nan haka abincin ma duk an babata gun. Daga can yaga wani flat din wanda ba'a taba ba. Sai da yaci ya koshi tukun ya goge bakin shi yaje yace wa su mama asiya suzo su gani. Suna zuwa sukaga duk anci abincin nan an rage wani wajen an fara cin cinya an yar. Ruwan ma duk an fafasa anyi wasa da shi. Tambayar shi sukayi a kan waya ci abincin.  Nan ya karkace hula ya fara zabga musu karya wai ai Aljanu ne sukaci addu'ar da yayi ne ya manta baiyi bismillah ba shiyasa wai Aljanun da suma zo ci basu makale ba. Su Asmart najin haka suka kyal-kyale da Dariya. Su mama Asiya suka tambaya me suke wa Dariya. Basu bada amsa ba suka ci gaba da dariyar hakan yasa Zuwaira taji haushi ta kora su da gudu suka koma falo suna daria. Nasmat taks cewa Asmart ita gaskiya bata yarda da mutumin nan ba.wai tana zargin ko ba malamin gaske bane. Asmart kam cewa tayi, "Au ke ashe zargi ma kike?. Kina gani fa gashi kiri-kiri ya maka karya. Wai yace Aljanu sukaci abincin bayan kuma mu muka ci".  Nasmat ta kyalkyale da Dariya Dariya tace,"Watakil mune aljanun".  Asamrt tace,"Yanzu mu rufa mishi asiri ne ko kuwa?". "Kyale shi muga iya gudun ruwanshi tukun. Ba dai yace zai cire Aljanun Fatima ba yau". Dariya Asmart tayi hade da cewa."Ai kuwa dai mu rufa mai asiri zuwa goben mu gani"._

_Acan kuwa su amam asiya suka cewa malam ya yake ganin za'ayi. Ce musu yayi shi yasan yanda zaiyi wai in ya kama aljanun Fatima zasu kawo mai sauran. Falo suka dawo aka kawo mishi abinci nan ma yace ya koshi wai Aljana ta kawo mishi yaci.  Fatima yasa aka kawo mai gaban shi nan yata tofe ta da miyau kallan shi kawai take yi tana hararen shi ba tare da tayi magana ba. Da abun ya bashi haushi sai ya fara kashe ta da mari yan cewa tayi magana. Su mama asiya suke cewa mai yasa yake dukan ta. Sai yace musu ba ita yake duka ba Aljanun ne wai dama yasan sai sun mishi garda.  Nan yata jifgar Fatima amma taki cewa ko uffan!. Wajejan karfe goma na dare Aliyu yace a kai Fatima daki domin a can zaiyi aikin kuma yace a daren duk tauri  kan aljanun sai ya cire su.  Daki aka kai ta ya shiga ya kulle bayan yace wa kowa ya shiga daki ya rufe. Bayan Ya musu gargadin kar wanda ya fito ko da fitsari ne.  Gado ya dale abu  shi ya kalle Fatima dake tsaye tana zare mai  idanu yake ce mata in kinga dama ki  zauna ko ki kwana a tsaye ma ni ba ruwa na.  Barci yake abun shi har da munshari.  Can cikin barci yayi mafarkin wasu mugayen halitu masu ban tsoro gasu da girma sukata tsorata shi suna firgiya shi daga karshe suka kai shi wajen wata yarinya da ba kai a jikinta sai iya gangar jikin. Hannun ta rike da wuka._

_Ko da yaga haka sai tsoro ya kara kama shi. Wannan halittun suka kai shi gaban ta bata jira komai ba ta daga takobin ta jaka mai a ciki. Da cakawa ya farka firgigita.  Ya tashi da ihu mai makon yayi addu'a.  Fatima ya gani tsaye yanda ya barta lokacin da ya kwanta har yanzu haka take bata ko motsa ba. Kasancewar dakin da hasken dake akwai nepa. Ya kalli agogon dake makale a bangon dakin yaga karfe biyu.  Ya juya gax. Fatima da niyar yi mata magana. Wayam yaga wajen ba kowa. Dube-dube ya kamayi. Ya sakko kasa  yan kiran sunanta dake yaji an fada mai. Ya duduba duk inda yake tunani  bai ganta ba. Sai karkashin gado. Yana lekawa da nufin yaga ko ta na nan yaji an rike mishi kai. Ihu! Ya farayi yana neman agaji. Jan kan nashi ake shima yana iya kokarin shi yana neman ya kwace amma ya gaza. Sai da yasha wuya sosai tukun aka sake shi.  Da sauri ya yashi ya koma kan gado ya lulube da bargo yana lumfashi day-day.  Dif!  Yaga wutar dakin ta dauke. Nan take kuma yaji dakin ya gauraye da wata ibilishiyar dariya wacce kunnuwanka bazasu iya sanar da kai inda take fitowa ba. Domin in kaji Dariyar sai kace gaba daya ma dakin ne da kanshi yake dariyar.  Ga dariyar ba dadin saurare. Aliyu yasa hannuwa ya toshe kunnuwa hade da kara dukun-kunewa.  Kiii!  Yaji an kama kafar shi an jawo shi kasa cikin duhu ya mike tsaye yana lalube-lalube.   Can yaji ya dafo wani abu kamar mutum mari aka dauke shi da shi wanda karfin marin yasa har sai da ya wuntsila.  Ihu! Ya kwalla mai uban kara ya fara bada hakuri. Wata dariyar ta kara kaurade dakin. Ba tare da hasken dakin ya dawo ba ya kara mike wa tsaye.  Kamar iska ya kwashe shi yaji an maka shi da bango. Kafin ya yunkura ya dawo yaji an kara fisgar shi an maka da kasa. Ji yayi kamar bayanshi ya karye. Ihu ya fara kwallawa va kaf!-kaftawa su Zuwaira na dakunan su sai da karar ihun ya tashe su. Su kuwa basu kawo a ransu cewa malam ne ke ihu ba. Su wai zatan su aljanu ne. Hakan yasa suke kara dukunkunewa.........................................................._

DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  King Boy Isah

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

*Before last Page 112-113*

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

.               πŸ‘©πŸ»‍πŸ’»πŸ‘¨πŸ»‍πŸ’»       .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​
.         ✍🏼  *®Z.W.A*     .

.              πŸ“         .
_*WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ Κ€Ι›Ι‘Ι—Ι›Κ€ΰΈ£*_

​πŸ“š _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

πŸ“© _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com

❤ DEDICATED TO MASOYAN LABARIN *ALJANAR FATIMA* ❤

πŸ€— Kun taka rawar  gani a yaba ba kadan ba. Masu bibiyar labarin nan. Dole nayi jinjina na kuma yi muki fatan alkhairi masoya na.  Hakika in baku bazan iya ba. Allah shi bar kauna. Safuratu na bankwana *HAUSAWA NA CEWA A JURI ZUWA RAFI. WATARAN TULU YA FASHE.* 🌝

          *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ihu ya fara kwallawa va kaf!-kaftawa su Zuwaira na dakunan su sai da karar ihun ya tashe su. Su kuwa basu kawo a ransu cewa malam ne ke ihu ba. Su wai zatan su aljanu ne. Hakan yasa suke kara dukunkunewa.~

_Haka Fatima taci gaba da tsorata malam Aliyu tana bashi wahala. Kafin safe sai da ta sumar da shi.Har Waje-jen karfe bakwai su mama Asiya basuga malam ya fito ba balle suji ya akayi. Nan wasu ke cewa aje a bude a gani. wasu kuwa cewa suke abar shi watakil aikin ne bai gama ba.  Suna zazane a falo bayan sun karya sai ganin Fatima sukayi ta fito daga dakin ranta a bace. Fuskar ba wal-wala.  Batayi wa kowa magana ba. haka kuma ba wanda yayi mata magana, Taje ta shiga dakin su jimawa kadan sai ta fito. Tana zuwa ta makore wuyan mama Asiya da karfe. Ba tare da tace mata komai ba. Mama Asiya tayi iya kar kokarin ta ta kasa kwabcewa. Sai da ta nemi agaji tukun da kyar sauran jama'ar suka kwace ta. Ana kankare ta daga nan ta sake shake wuyan Hauwa nan ma da kyar aka kwace ta. Nan fa ta shiga layi daga an rabata da wannan sai ta malale wa wannan. Kuma shakar da take bana wasa ba._

_Dan ji zakayi kamar wani Rikakken gardi ne ya shake ka. Kuma kafin a kwace kaji jiki. Da gudu su nasmat suka fita waje aka nemo mutane. Aka daure Fatima da kyar. Domin su kansu masu daure tan sunji jiki. Wasu duk tajiji musu ciwo.  A nan falo aka hadata da karfen jikin Matatakala (Stairs)  aka daure ta. "Duk sai na kashe ku ranar da na kunci". Abunda ke fita daga bakin Fatima kenan. Bayan hankalin yan gidan ya dan kwanta ne. Su mama Asiya suka tuna da aliyu. Da sauri suka nufi dakin kwance suka tarar da shi har lokacin a sume. Aka kawo ruwa aka yayafa mishi a firgice ya tashi yana raraba ido. Yana mikewa ya zabga a guje Kamar wani sabon mahaukaci. Ana kiran shi ko waigowa baiba. Da ya isa falo yaga Fatima a daure na hararen shi sai ya kara kaimi wajen guduwa. Asmart da Nasmat dariya kawai suke su. Zuwaira ta daka musu tsawa take tambayar su miye na dariya. Nan suke gaya wa mutane cewa Da gani Aliyu malamin karya ne. Nan suke fadar cewa su suka ci abincin da Aliyu yace Aljanu ne suka ci. Sallalami su Asiya suka kwasa. Zuwaira ke cewa in kuwa haka ne sai sunyi maganin Nafisa. Asiya tace "Ai ba wani ba wata zuwa zamuyi ta biya mu duk kudin da muka kashe kawai"._

_Zuwa sukayi suka same ta da masifa. Da kyar suka kankaro dubu uku a gunta. Haka Fatima ta kasance a gun a daure abinci ma hanata suka ringa yi sai dai fiddausi ta bata a sace. Abba kuwa har yanzu hannnun shi daya a makale. Sunyi-sunyi Fatima taki gyara mai hannu. Su Asiya duk a tsorace suke kullum fargabar kar Fatima ta kunce suke. Dan suna shan barazana da kashe di a gunta. Domin cewa take in dai aka kunce ta sai ta kashe mama Asiya Zuwaira da Hauwa. Hakan yasa ma suka gagauta kiran alhaji. Cewa yayi sharri suke mata. Hankalin shi bai tashi ba yaji ya matso ya dawo gida sai da yaji sunce sun daure Fatima. A lokacin ne yaje ba abunda yake so sai gida. Yau take juma'a ranar da Alhaji zai dawo. Tun da safe akata shirye-shirye aka gyara gidan tsaf!. Safiyanu da matar shi da yaran su uku sunzo. Haka ma Yusuf shida matar shi. Kowa yaci kwalliya in banda Fatima dake daure. Su Safiyanu da basu san me ke faruwa ba sai a lokacin suka tambaya mama asiya ta zauna ta shirya musu karya da gaskiya._

_Abba murna yake sosai domin yasan in dadyn su yazo dole Fatima ta mikar mai da hannu. Tun wajen sha biyu su Safiyanu suka yafi airport domin tarbo Alhaji.  Sai wajen karfe uku jirgin su ya karaso. Suka runkuto a mota suka taho gida.  Ba abunda yake tambaya sai Fatima. Haka da suka shigo gida duk iyalai sun fito kofar gida cik da farin ciki. Shi kanshi yaji dadin irin taryar da aka mai a tafiyar yan watanni kamar yaje yayi wani shekaru. Abunda ya rage mai farinciki shine kawai da baiga Fatima ba.  Aliyu da Abdul suka shiga jidar kayan da Alhaji ya kawo suna shiga da ita. Alhaji na shiga falo sukayi ido hudu da Fatima dake daure jikin karfe. Ta fashe da kuka hade da fadin "Dady kaga yanda suka daure ni ko?". Hankalin shi a tashe ya nufe ta tausayi ya kama shi kamar ya fashe da kuka. Nan take yaji wani irin haushin su Mama Asiya.  Kunce ta yaje ya farayi. Mama Asiya Zuwaira da Hauwa. Hankalin su yayi matukar tashi ganin abunda Alhajin ke shirin yi. Asiya da sauri tanufo shi tana hada shi da Allah karya kunce Fatima. Tsawa ya daka musu hade da cewa "mutanan banza marar tausayi. Wato abun naku har ya kai ku daure ta dan kunga uwar ta ta mutu ko?". Zuwaira da hauwa suma magiya suke binshi da shi akan ya hakura karya kunce Fatima ya saurare su amma. Yaki. Yana kunce Fatima ya warware mata igiyar dake jikin ta. Nan take suka rungume juna. Alhaji Salim tsabar tausayi sai da ya zubar da hawaye. Safuratu na ganin an kunce Fatimar sai ta koma jikinta. lokaci daya Alhaji yaji Fatima ta zabura ta kwace jikinta daga jikin shi kamar wacce aka tsinkula. Nan take idanunta sukayi jajur kamar wacce ta kwana tana kuka. Da gudu ta nufi kitchen kamar wata mahaukaciya. Bata jima ba akaga ta fito hannunta rike da wukA._

_Da gudu ta nufi su mama Asiya. Sa ganin haka sukayi waje da gudu. Fatima ta bisu. Alhaji Safiyanu da yusuf da sauran matasan da gudu aka bi su. Sai da kyar aka samu aka rike Fatima su mama Asiya kam har sun kusa fita daga layin sai da sukaga lala-lalai an rike ta an kwace wukar tukun suka juyo.  Kusan karti biyar ne ke rike da Fatima amma sai juyasu take kamar wanda  suka rike giwa. Hankalin Alhaji a tashe yasa aka nemo masu Ruq'yah. Bai wani bata lokaci ba malamin mai suna Bashir Halilu Tabiyyah. Ya karaso.  Yana shiga ya tarar sai fama ake da Fatima ana rirrike ta. Kai tsaye ya nufi gunta ya tofa mata wasu addu'o'i. Yace su sake ta. Ba tare da gardama ba suka sake ta.  Sunyi mamakin ganin ta tsaya cik ta natsu. lokacin su mama Asiya suka shigo. Kukan kura tayi ta warci wuka ta nufe............................................,..................._

🌝 Komai yayi farko zaiyi karshe 🀹🏻‍♂🀹🏽‍♂

DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee  King Boy Isah


πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

   *^^^^^^^______^^^^^*
    *ALJANAR FATIMA*
   *^^^^^^_______^^^^^*

πŸ‘ΊπŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘Ί

*THE END*

©πŸ€΄πŸ» *KING BOY ISAH* ✍🏼
πŸ‘‘

.               πŸ‘©πŸ»‍πŸ’»πŸ‘¨πŸ»‍πŸ’»       .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​
.         ✍🏼  *®Z.W.A*     .

.              πŸ“         .
_*WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ Κ€Ι›Ι‘Ι—Ι›Κ€ΰΈ£*_

​πŸ“š _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

πŸ“© _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com

*JIJINAR BAN GIRMA GA MAKARANTA LABARIN NAN. KAMAR YAU NE NA FARA DA ONE PAGE YAU DAI GANI A END*

       *KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ba tare da gardama ba suka sake ta.  Sunyi mamakin ganin ta tsaya cik ta natsu. lokacin su mama Asiya suka shigo. Kukan kura tayi ta warci wuka ta nufe.~

_Su Mama Asiya. Da gudu suka koma. Malam yayi caraf! Da Fatima. Nan take ya fara tofa mata wasu addu'o'i shiru tayi tana kallan mutane. Malam ya mata karatu cikin kunnenta na hagun. Tukun ya dafa kirjinta yaci gaba da karanta ayoyin ruk'yah.   Ji sukayi ance "Dakata malam ni ba azzaluma bace".  Cikin bacin rai malam yace, "Ke kuwa ce azzaluma tunda gashi kin shiga jikin yar karamar yarinya kina kuma yunkurin kashe wasu". Aljanar tace, "Kwarai na shiga jikin Yarinya kuma hakan kariya ne daga wadancan azzaluman matan ubanta. Domin in ban kashe su ba su zasu iya kashe ta ita".  Tsuru aka zurawa Fatima ido da bakinta ne kawai ke motsi amma ba ita ke maganar ba. Alhaji har rawar jiki yake domin sosai yake san Fatima. Nan malam yasa aka kirawo su Asiya a tsoarace suka zo suna baya-baya da Fatima wacce sai hararen su take kamar idanun zasu fado kasa.  Malam yace wa Safuratu me su Asiya sukayi wa Fatimar na zallunci.  Bata boye komai ba duk ta kwashe abubuwan da su Asiya da 'yav'yan sukayi wa Fatima ta fada. Malam ya juya gare su ya tambaya haka ne. Jiki a sanyaye ta amsa cewa eh duk abunda ta fada gaskiya ne. Alhaji a zuciye ya nufi Asiya da niyar ya dake ta yana fadin "Amma Asiya kin cika macuciya maciya amana. Amanar ma ta marainiya kuma yarinya". Ba dan malam ya dakatar da shi ba kuma ta gudu da sai ya ji mata ciwo. Nan malam ya kwantar mishi da hankali ya kuma ga Safuratu yake tambayar ta ta yaya akayi ta zo gidan har take taimakawa Fatimar. Bata boye musu komai ba ta sheda musu cewa wannan aikinta ne. Ta dade tana irin taimakon nan da sasanta matsalolin ma'aurata.  Gaba dayan falon sunyi mamaki malam yake tambaya. Shin a kwai irinta ne dama a cikin Aljanu. Tace ita dai bata sani ba amma tasan cewa. Ba duka aka zama daya ba._

_Malam ya tambaye ta a kan me yasa take irin wannan taimakon. Tace "Dogon labari ne amma dai bari in baku shi a gajarce yanda kuma zaku fahimata. Uwata da ubana mutanen kirki ne a cikin mu aljanu tun kafin a haife ni a kasarsu wani babba daga cikin aljanun shi ne abun bautar su. Wata rana sai sani Aljani wanda shi ya kasance musilmi ne. Yaje garin bisa batan hanya. Da yaje kasar kuma mahaifina ne mutum na farko da suka fara haduwa da shi. Kuma shi ya sauke shi a agidan shi. Ko da lokacin sallah yayi. Ya tashi yayi su sai suna kallanshi ba tare da sun ma san ko me yake ba. Bayan ya gama sallar yaga sun tsura mai ido basu tashi sukayi sallah ba. Da ya tambaye su sai suka nuna basu ma san me yayi ba. Nan suke fada mai su ai shugaban su suke bautawa. Natsuwa yayi ya musu bayanin Islam sosai kuma suka fahimata suka gane. A kwana a tashi iyayena da wannan bakoj aljanin suka ta zagaye gari suna shedawa mutane addinin da suke ba na gaskiya bane. Muslinci shine addini  gaskiya suna amfani da hujjoji kwarara wanna yasa aljanu da dama suke aminta su karbi muslinci. Ana haka har magana ta kai ga wannan shugaba nashi. Nan take ya bada umarnin duk wanda aka kama a kashe shi daga iyayen nawa har wanda suka karbi muslinci.  An kama wasu an kashe wasu kuma sun tsira. Cikin wanda aka kashe harda mahaifina. Mahaifiyata da wannan bakon aljanin da kyar suka sha. A ranar suka bar kasar. Suna fitowa daga kasar mu aka ci sa a ya gano hanyar kasar su. Suka nifi can shi da uwata. In takaice muku labari a can garin mahaifiyata ta haife ni. Ta haife ni da kwana daya tace ga garin ku nan. A hannun matar wannan aljanin na taso labarin irin wuyar da nasha a gunta da 'ya'yan ta nada tsayi. Da naga dai abun yayi yawa suna neman sabautani saboda sunga ni marainiya ce bani da kowa. Sai na gudu. Garin yawo na har na iso kasashen mutane. Lokacin ban taba ganin dan adam ba.  Wacce na fara gani kuma yarinya ce yar karama. A wani daji_

_Ta jifgo itace da yawa a kanta. Da kyar take tafiya. Al'ajabi da mamakin ya cika ni. Hakan yasa na bita a baya ba mukata tafiya domin lokacin na lura da bata gani na. Sai da muka kusan zuwa gari na ringa hangen mutane kalar yarinyar. Da muka shiga nata ganin su kala-kala fari da baki. Ban  daina bin Yarinyar ba dai da mukaje har gidan su. Nasha mamaki ganin yanda mater wacce da farko nayi zatan uwarta ce. Tata dukan Yarinyar wai ta debo itace kadan. Sannan ta sake sata wani aiki. Haka dai naci gaba da bibiyar ta har dare. Abun ya bani mamaki sosai ganin ni irin abunda matar wancan Aljanin da yaranta suke min. Haka itama wannan Yarinyar matar nan da Yaranta suke azabtar da ita. Da na tsananta bincike sai na gano cewa ashe ita din marainiyace bata da uwa. Ubanta kuwa baya cewa komai ko a gabanshi aka mata abu. Hakan yasa ni kuwa nayi amfani da damata nata taimakon Yarinyar nan ina rama mata duk abunda aka mata. Dan dole suka shafa mata lafiya. Daga karshe na bayyana a gabansu na tsoratasu a karsu kara cutar da ita.  Kuma nayi musu kwakwarar kashe di.  Sai da na tabbatar sun daina mata duk abunda suke mata sannan na rabu da su.  Da nayo gaba a garin da na iske still na sake iske wata marainiyar haka dai naci gaba dayi zuwa yanzu bansan yarinya nawa da mata nawa na gyara wa rayuwa ba. Bana barin azzalumi. Kuma ni bana kisa. sai dai in wahalar. Ko su Asiya ma kawai ina musu barazana ne. Wannan shine takaitaccen labarina".  Ko da Safuratu. ta zo nan a zancen ta kusan mutum biyar sukayi ajiyar zuciya a lokaci daya. Nan malam da sauran mutane suka jinjinawa Safuratu hade da karfafa mata gwiwa. Su mama Asiya nadama ce  karara shimfide a fuskokin su. Malam yayi musu nasiha mai ratsa jiki. Ya kuma fadi musu illolin cutar da maraya da zaluntar sa. Da kuma irin ladar da mai kyautatawa maraya yake sama a gurin Allah. Sosai sun ji wa'azin dan wasu daga cikin su harda hawaye. Nan suka dauki alkawari cewa bazasu sake musgunawa Fatima ba. Suka kuma nemi gafara gun Safuratu. Tace ita ba ita sukawa laifi ba Fatima ce. Ta kara da cewa kyautata mata da yi mata alkhairi shine zai tabbatar mana da kun daina abunda kuke kun tuba. Sannan ku sani zan dawo ko ba yau ba. Da fadsr haka sukaji Fatima na attishawa. Daga bisani wani farin  hayaki ya fito daga bakin ta. Nan da nan gumi ya jike ta sharaf! Ba'q jima ba sai barci. Su mama Asiya har rige-rigen daukar ta akata daki ake. Alhaji shi kam baic komai ba. A zuciya yake addu'ar Allah yasa su Asiya su cika alkawari._

_Alhmdulilah kwana biyu gidan ya canza kowa san Fatima yake. Dan a cikin su Asiya har rasa wanda yafi san Fatima Alhaji yake. Haka bangaren yara ma. Su Nasmat duk inda zasu sai suja Fatima. Godiya Alhaji yayi wa Allah. Domin Allah shine mai saita komai. Gashi a lokaci daya Allah ya shirye matanshi sun gane gaskiya._

A nan nima nake cewa.

TAMMAT BIHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN πŸ“ΏπŸ•‹

```A nan na kawo karshe labarin Aljanar Fatima. A yanda na tsara littafin yafi haka. Saboda wasu dalilai yasa na yanke shi. Ina rokon Allah ka kurakuran dake cikin littafin nan wanda nayi da sani da wanda nayi ba da sani na ba. Ya Allah ubangiji ka yafe min. Allah kasan kudurina a kan littafin nan nayi shi ne dan fadakarwa Allah ka shiryar da masu irin halin  nan ta Dalilin littafi na. Domin kai ne mai shiryarwa.```


Post a Comment for "ALJANAR FATIMA CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...